•… 💕 *CAPTAIN AYUSHERH*🥷 * 🍂🎀 (_The ShieldMaiden._) sʜᴇ ᴡᴀs ᴀ ɢɪʀʟ ᴡɪᴛʜ ᴀ ᴍᴏᴜɴᴛᴀɪɴ ᴛᴏ ᴄʟɪᴍʙ!!! https://whatsapp.com/channel/0029VaEZtE15a2429vfcpf20 BY - Nainarh KD.... 𝒩𝓀𝒹'𝓈❦♡ Don't Forget To Follow My Both Accounts; Nainarhkd3 @Wattpad. Nkds @Arewabooks. .. Copy is not allowed.¡! Ba kuma zan Lamunci a canzan labari kota wata siga ba.¡! _Na sadaukar da wannan Labarin kacokan ɗin sa gare ki ƴar uwa marubuciya kuma abokiyar shawara ƙawata kuma Takwarata Khadija M Abdulwahab A.k.a Queen Kainaat. Haƙiƙa keɗin ta musamman ce a wurina ba zan manta da Alkhairan ki a gareni ba, sai dai na ƙara da yi miki fatan Alkhairi a Rayuwa Allah kuma ya bar zumunci Tsakanin Mu💯... Daɗi da ƙari wannan labari ƙarin sadaukarwa ne ga duk wata ɗiya mace da ta sha gwagwarmaya a Rayuwa.💋_ .. .. Nainarh KD...✍️ MARUBUCIYAR: 1. SARAUNIYAR KYAU 2. TSANTSAR SO 3. ANEESERH ( The Innocent Girl.) 4. KIN CUCENI 5. RANAR BIYAN BUƘATA 6. BA TABBAS 7. CAPTAIN AYUSHERH!. +234 808 112 9487. Perfectly Pen's 🖊️ Lafazi Writer's Association... بسم الله الرحمن الرحيم Episode 1. BABUR TRIBE PEOPLE; Babur Har ila yau ana kiran sunan ƙabilar da Babar ko Baber. Wannan wata ƙabila ce ta wasu mutane da suka kasance asalin mazauna daji. Asalin da yawa na mutanen ƙabilar sun fito ne daga Yankin tafkin Chadi. YAWANSU; (POPULATION.) A ƙiyasi adadin mutanen ƙabilar zasu kai kimanin dubu ɗari biyu zuwa dubu ɗari uku. (200,000-300,000.) A faɗin Duniya. YANKI; (LOCATION.) Mutanen ƙabilar sun kasu kashi uku, mafiya rinjaye nasu suna a ƙasar Cameroon yayin da wasu suke a ƙasar Chadi. Har ila yau kuma wasu suna a ƙasar Nigeria. A Nigeria an fi samun su a yankin Arewacin ƙasar a wurare kamar irinsu; Borno da kuma Yobe State da sauransu. As well a ƙasar Cameroon kuma yawancin su, sun fi ne a Far North na Yankin ƙasar Cameroon. HARSHE; (LANGUAGE.) Ƙabilar Babur yawancinsu suna magana ne da harshen Bura. Da yake daga cikin reshe dake iyakan Nigeria Da Chadi da kuma Cameroon. (Biu-Mandara.) ADDINI; (RELIGION.) Mafi rinjaye na mutanen ƙabilar Babur sun kasance suna Bautar gumaka (Idolatry.) ne, yayin da wasunsu suka canja zuwa adddinin Musulunci (Islam.) kaɗan daga cikinsu kuma sun kasance Kiristoci ne (Christianity.) AL'ADA; (CULTURE.) Yawanci na Mutanen ƙabilar Babur sun kasance manoma ne, suna girban amfanin gona kamar irinsu; Gero. Dawa. Da kuma Gujjiya. Da sauransu. Sannan kuma akwai mafarauta a cikinsu sosai. Abubuwa da yawa nasu na al'ada yana Kamance da na Kanuri da kuma mutanen Shuwa Arab. WANNAN KE NAN!. ** *Mayo-Danay. Far North Region. Cameroon.* Mayo-Danay wani yanki ne ko nace sansani ko ƙauye da wasu daga cikin mutanen ƙabilar Babur dake a ƙasar Cameroon suke zaune a wurin shekara da shekaru. Mutanen ƙauyen Mayo-Danay sun kasance suna zaune lafiya ƙarƙashin jagorancin Arɗon garin komai yana tafiya dai dai. A wasu shekarun baya. Arɗo ya kasance mabiyin addini ne na al'ada dama sauran mutanen ƙauyen sun kasance akwai wuri da suka ware suna bautar gumaka kuma suna biki irin nasu na addini da kuma al'ada, lokaci bayan lokaci. Arɗo yana da Mata guda biyar rass, bisa adadin yadda addininsu ya umarta, yana kuma da yaran da bazasu ƙirgu ba. Babban yaron Arɗo a maza sunansa Babankaka ya kasance na daban cikin yaran Arɗo dama sauran mutanen ƙauyen gaba ɗaya domin ya taso ne da wata iriyar halayya da kuma ɗabi'a da ta yi daban da na mutanen ƙabilar. Sam bai yarda da bautan gumaka da Mutanen ƙauyen ke yi ba tun yana ƙaramin sa duk kuwa da yadda a ke so da shi amma yaƙi sam ko zuwa wurin bautansu bayayi. Ba irin azabtar war da Arɗo bai saka an yi ma sa ba wai duk dan ya koma ya zama kamarsu ya dinga bauta irin nasu amma sam yaƙi, haka dole suka saka masa ido, tare kuma da nazarin mummunar mataki da zasu ɗauka a kansa muddun bai canza aƙidar nasa ba. Domin ba kyalesa zasuyi ba. Akwai wani abin burgewa ga kowa da Babankaka yake da, domin shi ɗin ya kasance Gwarzo ne ta fannin farauta tun yana ƙaraminsa kuwa, domin lokaci da dama a daji yake ƙare Rana guda kuma a haka ya taso a daji yake gudanar da rabin Rayuwarsa shi ya sa ya kasance daban da saura yana da shekaru goma sha tara a ka naɗa sa a matsayin Sarkin Samari masu farauta na ƙauyen gaba ɗaya da hakan ya sa a ke kiransa da Jakadi. Rayuwa ta ci gaba bayan shuɗewar wasu ƴan shekaru wani gagarumin al'amari ya faru a tsakanin Jakadi (Babankaka.) da kuma mutanen ƙauyen su, lamarin dai shi ne a kan yaƙi ya yi bauta irin nasu kuma daga bisani suka sama labari a kan ya shiga wani addini daban ba tare da ya sanar dasu ba kuma hakan ya yi matuƙar fusatasu sosai da hakan kuma ya sa suka haɗa taro da gaba ɗaya mutanen ƙauyen a ka taru sannan suka bawa Jakadi zaɓi biyu a kan ko dai ya bar Addinin da ya shiga sannan ya shiga nasu ko kuma ya bar ƙauyen gaba ɗaya in kuma ba haka ba za su ɗauki mummunar mataki a kan sa. Kowa ya nutsu a lokacin a na jiran a ji amsar da Jakadi zai bada. Hatta shi kansa Arɗo sai da cikin shi ya ɗuri ruwa domin ba zai so Jakadi ya yi nesa da shi ba ko ya ya kuwa. Sai dai ga mamakinsu gaba ɗaya shi ne Jakadi ya zaɓa a kan ya bar ƙauyen da dai a ce ya bar Addinin da yake ciki a yanzu Addinin Rahma Addinin Musulunci. Wannan lamari ya matuƙar bawa kowa mamaki kuma ya fusata su kwarai, haka suna ji suna gani Jakadi ya bar ƙauyen ba kuma tare da ya ɗauki komai nasa ba kuma tun da ya bar ƙauyen bai dawo ba tsawon shekaru masu ɗan yawa domin an shafe sama da shekaru goma, kuma wannan shi ne ya zama dalilin da Arɗo ya kamu da mummunar ciwo a kan rashin Jakadi tun suna saka rai da dawowarsa har suka haƙura, sai dai zuwa lokacin Arɗo tsufa ya ƙaru sosai baya iya taɓuka komai haka dole Mulkin ƙauyen ya koma Hannun ƙaninsa domin yaronsa da ya kamata a bawa Mulkin bayanan. Al'amurra sun ci gaba da gudana mutanen ƙauyen suna gabatar da al'amurran su kamar yadda suka saba kwatsam a wani dare suka sama baƙon cin babban al'amari a tattare da su domin kuwa Jakadi wato Babankaka shi ne ya dawo musu garin a cikin wani irin yanayi jikinsa jina-jina da jini ga kuma sara da a ka yi masa ƙarin abin mamaki da ruɗani shi ne a tare yake da jaririya da ikon Allah ita kuma babu abin da ya sameta domin goya ta ya yi tam ta gaba kuma ya kakkareta daga duk wani farmaki, wannan dalilin ya sa babu abin da ya sameta. A wannan dare kowa da ka gani daga kan mutanen gari da suka yi cincirindo a ƙofar gidan Arɗo da su kansu iyalan Arɗon har ma da shi kansa Arɗon gaba ɗayansu mamaki ne a tare da su na ganin Jakadi a wannan dare cikin wannan hali a irin wannan lokaci ga kuma jaririya, mamaki, ruɗani, tashin hankali shi ne abin da ke tare da kowannen su kuma bakinsu ɗauke yake da tarin tambayoyi a garesa. Gaba ɗaya idanunsu suna a kan Jakadi ne dake zaune saman wani Marmara gaban wuta dake ci ranga-ranga kuma ta zama haske a wurin gaba ɗaya, zuwa yanzu ya kwance wannan Jaririyar daga goyan da ya yi ma ta, a halin yanzu tana riƙe ne a hannunsa ya zuba mata idanu yayin da ita ma Jaririyar take ɗan gif-gifta nata kyawawan Meadow Green Eyes ɗin tamkar tasan abin da ke faruwa. Arɗon yanzu, wato Sarkin da a ka naɗa a ƙauyen shi ne ya sake maimaita tambayar da ya yi ma Jakadi a karo na biyu da cewa cikin harshensu na Babur. “Tsawon lokaci kana ina, mene ya faru ka dawo mana a haka, wannan Jaririyar ta wacece, kuma daga ina ka samo ta?.” Sai dai a ka shafe kusan sakanni talatin da yi masa tambayar a karo na biyu. Kamar ba zai magana ba. Sai suka ji wannan murya tasa a yadda take wata kalar kakkaura mai daɗin saurare ya fara magana cikin harshen nasu da bada amsa kamar haka. “Nigeria ita ce ƙasar da na koma nake Rayuwa tsawon waɗan nan shekaru, wannan Jaririyar kuma Ɗiyata ce.” Abin da ya faɗa ke nan, ya yi shiru daga haka. Surutu ne sama sama ya fara tashi a wurin kowa yana faɗar albarkacin bakinsa ba abin da kake ji sai ƙus-ƙus dake tashi. Shi kuwa Jakadi har yanzu idanunsa a kan wannan kyakkyawar Jaririyar suke babu abin da yake tunawa sai maganganun Mahaifiyarta a garesa a sa'ilin da take dab da barin Duniyar. _Cikin Wata kalar wahalalliyar Muryar da ta gama galaɓaita da wahala ta ci gaba da faɗin. _“Jakadi! Na yarda da kai! Shi ya sa a wannan taƙin da nake tsakanin Rayuwa da Mutuwa, na bar maka Ɗiyata Halak, ina mai roƙonka a kan ka kulamin da ita sannan ka saka ma ta sunana wato AYUSHERH! sannan kayi min wata alfarma, kayi iya iyawarka wurin ganin Ayusherh ta zama Soja bayan ta girma domin ta hakan ne nake saka ran komai zai dai dai ta, duk wata ɓarna da a ka yi zata gyaru, azzalumai za su fuskanci mummunar sakamako daga zunubansu.”_ Daga haka kuma ta yi shiru ta ɗan rumtse ido sakamakon zugi da bayanta yake yi a dalilin wuƙar da mutanen da suka biyo ta, suna farautar Rayuwarta domin su halaka ɗaya daga cikinsu ya yi nasarar caka ma ta wuƙar ta baya!_ “Baka bamu amsar tambayar mu ba. Garin ya ya haka jikinka duk jini da kuma sara ta ko'ina sannan ina ita Mahaifiyar Jaririyar take?.” Arɗo ya ƙara yi masa wannan tambayar. “Ta mutu.” Cewar Jakadi a taƙaice. “Garin ya ya, kuma su waye suka kashe ta?.” Zuwa yanzu Jakadi ya fara gundura da waɗan nan tambayoyi. “Farmakin mu a ka yi a hanyar mu na zuwa nan kawo muku ziyara. Sanadin hakan ta mutu ni da wasu daga cikin mutanen ƙauyen da wannan al'amari ya faru da su mun yi ma ta sutura an rufe ta a can.” Jikinsu ne ya ɗan yi sanyi jin abin da ya ce, haƙiƙa wasu daga cikinsu sun tausaya masa, jin cewar ya rasa Matarsa duk a dalilin ya zo ya duba su. Wasu kam ko'a jikinsu sai ma cewa da suke tsinuwa ce take bibiyarsa a dalilin bijire musu da ya yi. “Har yanzu kana a wancan Addinin?.” Arɗo ya sake yi masa wata tambayar Again, domin kaf cikinsu shi ne mai zarrar da zai iya yi ma Jakadi waɗan nan tambayoyi ya zauna lafiya, don kuwa Jakadi ya amsa sunan nasa ta ko'ina. Wani irin ɗa go manyan idanunsa Jakadi ya yi tare da watsatsu a kan Arɗo ƙanin Mahaifinsa. Ba tare da ya yi magana ba ya miƙe tsaye riƙe da Yarinyar sannan ne ya basa amsa da faɗin. “Har gobe ina nan a cikin Addinina kuma babu abin da zai saka na canza har Abada. Ku ma ina yi muku fatan shiriya ku gane hanya madaidaiciya wata rana tun kafin lokaci ya ƙure muku.” Yana gama faɗar hakan ya juya tare da shiga cikin makeken gidan Arɗo ƙaton gaske da yake ginin yaɓe haɗe da bukka, kaf ƙauyen shi ne gida mai ginin yaɓe na jar ƙasar dake bakin tekun garin dake dab da wani ƙaton dutse. Bai ankara ba yaji yaci karo da Mutum daga yanayin kuma ya san Mace ce. Ya ɗa ga tsayayyun idanunsa yana dubanta. Kana ganin fuskarta tsoro ne zalla sai gif-gifta Manyan idanunta take yi yayin da take cukurkuɗa curkurkuɗaɗɗen gashin ta mai tsayi da hannunta guda, yayin da ɗayan ta kama bakinta dake rawa, idanunta a zare cike take da tsoron da ya fahimce na ganinsa ne. Raɓa ta ya yi ya wuce ciki, ta bisa da ido sai kuma ta daka tsalle tare da rugawa da gudu ta fita. Babaya ke nan sarkin shiririta da shirme kuma Ɗiya wurin Arɗon yanzu, Mahaifiyarta ta rasu tun tana tsumma, a Hannun kwarin Arɗo, ta taso kuma ta girma wato a hannun Mahaifiyar Jakadi ke nan. Wani ɗan ƙurmin ɗaki ya shiga tare da zama a saman gadon ƙasa dake ciki. Bayan ya rufe ƙofar ɗakin da take na kara. Ya tattara nutsuwarsa gaba ɗaya yana tuna abin da ya kasance ya afku a daren jiya. Shi kansa bai yi tsammanin zai tsira ba. Kuma yana da tabbacin Mahaifiyar wannan Jaririyar dake hannunsa a yanzu ta mutu. Domin kuwa a gaban idon sa komai ya faru. Ya sauke ajiyar zuciya a nutse. Yana tuna kalamanta a gare sa. Tabbas komai da ya faru cikin sauri ya kasance ya faru da haɗu wa da ita da ya yi a ƙurmin daji tana zabga gudu da tsohon ciki ga wasu muggan mutane dake bin ta. Da taimaka ma ta da ya yi har zuwa haihuwa da ta yi zuwa wayewar gari da kuma gano maɓoyarsu da waɗan nan mutane suka yi da wasiyyar da ta bar masa a kan Jaririyar da ta haifa, kafin nan domin ta san ita kam da wuya ta rayu. Sake gudun tsira da suka yi tare yana riƙe da Jaririyar tun farar safiya, gudu suke a dajin Allah ba hutu sai in idan ta ce ta gaji ne sannan su samu su tsaya hutu, kuma a wannan taƙin ne ta basa gaba ɗaya labarin ta da dalilin ta na son ɗiyarta da ta zaɓa ya saka ma ta suna Ayusherh da ta zama Soja, har ma da irin mummunar cin amana da a ka yi ma ta ita da mijinta da hakan ya zama sila na Rayuwarsa. Sai yammaci suka isa wani ƙauye, nan ne da kyar suka samu Mutanen ƙauyen suka taimaka musu har suka basu masauki. Da sharaɗin safiya nayi zasu ƙara gaba. Jaririyar da Mahaifiyarta suka sama kulawa da ta dace. A cikin dare kuma suka sama baƙon cin waɗan nan gawurtattun ƴan ta'adda da suka farma ƙauyen da mutanen cikinsa. Ƙauyen yana a dab da Iyakar Nigeria da kuma Cameroon ne. __ TOFA! Reader's kun dai ji ta yadda Labarin ya soma da salonsa. Wai shin wacece mahaifiyar wannan Jaririyar ce da ta zaɓi a sakama Ɗiyarta sunanta kuma take so bayan Ɗiyar nata ta girma da ta shiga aikin SOJA?. Mene ne ainihin labarin ta?. Shin ya ya Rayuwar Ayusherh zai kasance a wannan ƙauye cikin waɗan nan ƙabila da ba nata ba?. Wai ma mutanen gari za su bari Jakadi ya ci gaba da zama a cikinsu bayan ba addininsu yake yi ba?. Su waye muggan mutane da suka biyo Mahaifiyar Ayusherh domin su kasheta?, shin su ne waɗan da suka farmaki wannan ƙauye da har hakan ya yi sanadiyar mutuwar ta? Idan su ne, mene ne dalilin su, waye ne yake da alhakin duk waɗan nan????. Hummp muje zuwa domin yanzu a ka fara kafta wasar kuma da alama da zafi Zafinsa ya taho. Alƙamin Nainarh KD...✍️ 𝓐.𝓴.𝓐~𝒩𝓀𝒹'𝓈❦♡ •… 💕 *CAPTAIN AYUSHERH*🥷 * 🍂🎀 (_The ShieldMaiden._) https://whatsapp.com/channel/0029VaEZtE15a2429vfcpf20 BY - Nainarh KD.... 𝒩𝓀𝒹'𝓈❦♡ Don't Forget To Follow My Both Accounts; Nainarhkd3 @Wattpad. Nkds @Arewabooks. .. Episode 2. A cikin dare kuma suka sama baƙon cin waɗan nan gawurtattun ƴan ta'adda da suka farma ƙauyen da mutanen cikinsa. Ƙauyen yana a dab da Iyakr Nigeria da kuma Cameroon ne. .. Basu kyale kowa ba sun kashe mutane da dama yayin da suka raunata da yawa daga cikinsu. A lokacin Matar da ta faɗa masa ita ɗin General ce tana jinyar jikinta bayan an samu an cire wuƙar da a ka caka ma ta ne a yayin da a ka biyo ta. Duk iya kar ƙoƙarin Jakadi wurin ganin ya taimaka ma ta ta tsira daga hannun waɗan nan mugayen ƴan ta'adda abin ya cutura yanaji yana gani ta mutu shima ɗin da kyar ya tsira a hannunsu tare da wannan Jaririyar da ya ɓoye bai bari komai ya sameta ba, sai dai shi kam ya sha wahala ba kaɗan ba, domin sun sassareshi a baya wurare sun kai huɗu. Bayan guduwa daga gare su ne har Allah ya nufesa da ƙari sowa ƙauyen su har zuwa yanzu da yake tuna komai turyan turyan. Ƙasa da awa arba'in da takwas komai ya faru. A hankali ya sauke ajiyar zuciya yana duban Jaririyar da ta yi shiru kuma har yanzu idanunta a buɗe suke tamkar mai wayo. Yana sane da yadda tun da a ka haife ta bai ji ta yi koda irin wannan kuka da jarirai ke yi ba. Kuma abin ya ɗaure masa kai sai dai ya ƙudurta ba zai bar komai ya sameta ba zai tsaya da ƙarfinsa da jajircewarsa wurin ganin ya kula da ita har ta kai Matakin da Mahaifiyarta take so a Rayuwa zuwa nan kuma shi kansa bai san mai zai faru ba. Abin da ya sa ni, shi ne zai yi ƙoƙari matuƙa wurin koya ma ta duk wani abu da ya da ce ba kuma zai bari ta yi maraici ba, zai zama uwa kuma uba a gare ta, sannan kuma Gatanta. Yana da dalili na kawo ta cikin ƙauyen su domin anan ne yake da tabbacin Rayuwarta bata a cikin hatsari, zai ci gaba da zama anan tare da ita, har zuwa nan da ɗan wani lokaci kafin ya koma da ita Nigeria ya sakata a Makarantar sojoji. Wannan shi ne tsarin sa a yanzu. Duk ya gama ƙudurce hakan a ransa ba tare da ya san me ce ce abin da ƙaddara ta tanadar ba a gare su baki ɗaya. Haka ya kwana a zaune riƙe da Jaririyar nan da ya yi ma laƙabi da Ayusherh kamar yadda Mahaifiyarta ta so. Washe gari koda Mahaifiyarsa tsohuwar arziƙi ta yi masa magana a kan Jaririyar da neman yardar sa a kan ya bata ta kula da ita zuwa lokacin da zai ƙara Aure domin naimawa Ayusherh uwa don shi ɗaya ba zai iya rainonta ba. Jakadi bai ƙi ba domin ya san wacece Mahaifiyar tasa Mace ce da ta yi daban da saura. Sai dai tsoronsa ɗaya yana gudun kar Ayusherh ta taso da al'ada irin nasu da kuma addini duk da yanajin ba zai bar hakan ta kasance ba, koda kuwa hakan zai zama sila na Rayuwarsa. Ya ƙudurce abin da zai yi domin gina Rayuwar yarinyarsa Ayusherh ta taso cikin inganci da burgewa. Koda a ka tambaye sa mene ne sunan Jaririyar sai ce musu ya yi sunanta CAPTAIN! To da yake basu san mene ne ainihin ma'anar sunan ba, hakan ya sa suka yi ta yaba sunan kuma sunan ya kama bakin kowa kamar yadda Yarinyar ta shiga ran kowa. Sai dai fa duk kwakwazon mutum sai dai ya yi ya gama. Jakadi baya bari koda wasa Hannu ma ya kai ga Ayusherh da a ke kira da Captain, wai domin a taɓa ta, sai dai kallo, shima kuma daga nesa nesa. Ban da Mahaifiyarsa wato Mahtah baya taɓa bari wani daban ya ɗauke ta, to sai Arɗo shima da dai bawai don ya so ba, dan kuwa tsakani da Allah yana tsoron hali irin nasu, kar suyi ma ta wani abu dalilin bijire musu da ya yi a baya. Tun Ayusherh tana Jaririyar ta Jakadi ya kan goya ta, ya ɗauke ta, ya shiga daji farauta da ita a haka, tun Mahtah tana faɗar a kan hakan har ta haƙura ta zuba masa ido. Jakadi yana da watanni Biyar da dawowa ƙauyen, zuwa lokacin kuma Captain ta daɗe da fara zama har tafiya take ƙoƙarin farawa abin nata yana bawa kowa mamaki. A lokacin ne kuma a ka kawo masa wata magana a kan wai ya Aure Babaya ɗiyar Arɗon yanzu, wai ko dan Ayusherh ta sama uwa da ta rasa. Ba tare da ɓata lokaci ba ya ce musu shi kam baya da ra'ayin Aure a lokacin, kuma koda zai yi bayajin zai iya auren Babaya. Yarinyar da bata haure shekaru goma sha uku ba a lokacin, wai kuma a hakan ita ce ƙatuwar budurwa a ƙauyen. Badan ransu yaso ba suka haƙura da zancen sai dan basa so wani abu ya gifta da zai yi sanadiyar sake barinsa garin, wannan dalilin ya sa ko ibada basa iya hanasa. Haka Rayuwar take gudu yayin da Ayusherh take ƙara girma tana ƙara wayo kuma kyawun ta da kuma asalin kalan idanunta suna da ɗa bayyana, da kuma wata ɓoyayyiyar baiwa dake gare ta. Idanunta wasu kalar Meadow Green ne da basa tashi komawa Green color har sai dare ya yi, yayin da idan kuma rana ce sai dai su kasance su ba grey ba sannan kuma ba blue ba, su dai gasu nan ne tsaka tsaki gunin ban sha'awa. Har wa girman Ayusherh Mahaifin ta Jakadi bai dena zuwa da ita daji ba, idan zaije farauta kodai wani abun shi ya sa kuwa Ayusherh ta taso bata da wani wuri sai daji tun tana da shekaru goma sai ta ɗauki kwari da baka, ko wani abun na farauta, sai ta ce za ta tafi daji ta yi farauta kamar yadda Tata (It mean Father.) ɗin ta yake yi, kuma duk yadda a ka yi da ita, a kan kar ta je, to fa ƙi take yi, domin Ayusherh ta taso ne wata iriyar jarumar Mace da ba komai ne kasafai yake bata tsoro ba akwai ta da dakakkiyar zuciya. BAYAN WASU SHEKARU. Zuwa yanzu sai dai a ce Alhamdullilah, domin kuwa abubuwa da dama sun faru ciki kuwa har da Musulunta na da yawa na daga cikin mutanen ƙauyen su kayi, har shi kansa Arɗo tsoho da sabon ma da iyalansu, sai ya zamana ilimin addini ya yawaita a ƙauyen, a hankali, a hankali kuma mutanen ƙauyen dama makwabtan su suna ta tururuwar shiga addinin Rahma Addinin Musulunci. A lokacin da Ayusherh ta kai shekaru Biyar ne kuma a ka samu Jakadi ya Aura Babaya, bayan an sha fama da shi da kyar ya aminta, dama ita ta ce bata da miji sai shi, kuma sanadin hakan ne ma a lokacin Babaya ta karɓi addinin Musulunci. Ƙarin abin ya ja hankalinsa i zuwa auren ta shi ne tsananin so da kulawar da take yiwa Ayusherh, Shalelen sa. A halin yanzu Ayusherh tana da shekaru goma ta sha biyu a Duniya. Ta kasance ta taso ne wata kalar Mace da halayenta da ɗabi'unta suka sha banban da na sauran yaran ƙauyen, takan ware kanta taje saman wani ƙaton dutse dake kusa da katon tafki na garin, duk girman dutsen nan bata gani, haka take hawa ta zauna, wani lokacin kuma sai dai ta yi ta hura sarewa da Arɗo ya taɓa ma ta kyautarsa, yayin da wasu lokutan kuma sai dai ta zaune ta yita magana da Aku (Parrot.) nta da ta samu sanadin yawon farauta a daji. Jakadi ya yi matuƙar ƙoƙari sosai wurin ganin Ayusherh ta sama duk wata kulawa da tarbiyya da ya kamata dai dai gwargwado, ya yi ƙoƙari ta wannan fannin kuma Babaya da a halin yanzu yaranta biyu, Mace da Namiji, Namijin ne Babba sai mai bi masa mace mai suna Yayankaka. Sosai Babaya take kula da Ayusherh kuma kamar ƴa ta ɗauke ta ba cuta ba cutarwa. Kuma hakan ya samo asali ne bisa jajircewar na Jakadi. Domin shi da ka taɓa Ayusherh, Shalelen sa, gwara shi ka taɓa sa. A Rayuwar Ayusherh ba abin da tafi so sama da shiga daji yin farauta, kuma a yanzu bata da wani Babban buri da ya wuce ta shiga wani gasar takobi da a ke yi duk bayan shekara a ƙauyen, tsakanin Samarin ƙauyen majiya ƙarfi, da kuma Samarin ƙauyen dake makwabtaka da su. An saba a kan yi wannan Gasar ta takobi duk ƙarshen shekara kuma a kan fidda gwani wanda ya zama nasarar zuwa na ɗaya. To Ayusherh bata da wani buri da ya wuce shiga wannan Gasar idan lokaci ya yi duk da bata da tabbacin Tata zai barta, sai dai zata dage wurin roƙonsa domin ya aminta. Yau ma kamar kullum tana sanye ne da kayanta na saƙi irin na shiga farauta...FOLLOW NKDS @ AREWABOOKS APP. GET IT ON PLAY STORE. DOWNLOAD ON THE APP STORE. •… 💕 *CAPTAIN AYUSHERH*🥷 * 🍂🎀 (_The ShieldMaiden._) https://whatsapp.com/channel/0029VaEZtE15a2429vfcpf20 BY - Nainarh KD.... 𝒩𝓀𝒹'𝓈❦♡ Don't Forget To Follow My Both Accounts; Nainarhkd3 @Wattpad. Nkds @Arewabooks. .. Episode 3. Yau ma kamar kullum tana sanye ne da kayanta na saƙi irin na shiga farauta. .. Doguwar rigar mai dogon hannu mai launin ash mai duhu, ta ɗaura dogon mayafi ta rufe kanta, yayin da dogon baƙin gashinta da a ka yi masa kitso silli ɗaya. Da sauri ta sa hannu tare da dawo da gashin ta gaba, yadda zata ji daɗin ɗaukar ɗaya daga cikin baka nata da suke cikin ƴar jakar farauta dake saƙale a bayanta. Ƙasa ta yi da sauri dai dai ta ɗauki baka guda biyu, sannan ta haɗa da kwari dake hannunta. Ƙoƙari take sai ta harba barewa da take ma ta wasa da hankali, ɗan rage girman idanunta ta yi tare da sai ta dai dai bayan barewar sannan ta saki bakar, ai kuwa cikin sa'a ta sama barewar a inda take so. Sai a lokacin ta saki kyakkyawan murmushi tana miƙe wa tsaye tare da yaye mayafin dake kanta ta yi baya da shi, mayar da kwarin hannun hagunta ta yi, tana kuma nufar inda barewar take kwance, tsugunna wa ta yi gaban barewar, dai dai ta kai hannu zata taɓa ta ke nan, kaifafan kunnuwanta suka jiyo ma ta wani sauti da alama ita a ke tunkaro wa. A wani irin zafafe ta miƙe tsaye tare da ciwo takobin ta dake saƙale jikinta, ta yi saurin tare takobin da a ka kawo ma ta sara da nata takobin. Baya ta ɗan yi tare da ɗa go idanunta suka shige cikin na Samarin majiya ƙarfi da kowannensu yake riƙe da nasa takobin su huɗu sun zagaye ta. A karo na biyu ta ƙara murmusa wa tare da yin baya da takobin ta, da hannu ta yi ma matashin saurayin da fuskarsa yake lulluɓe da wani kyalle, ta yi masa alama da yatsunta biyu, alamar su fara. Karkace kai ya yi, dan ya fahimci abin da take nufi, ƙoƙarin shammatarta ya yi ta hanyar sake kawo ma ta wani harin da takobin dake hannunsa cikin sa'a a kuma zafafe ta tare da nata takobin, nan fa suka shiga wasa da takobin suna kai ma juna farmaki, sai dai kowannen su yana kare kansa da nasa takobin, ganin da sauran samarin suka yi a kan Ayusherh tana dab da ta yi nasara a kan ɗan uwansu ne ya sa suma su duka shiga sunayin faɗar tare sai dai fa duk yawansu da kuma horo da kwarewar da suke taƙamar suna da shi a ɓangaren wasan takobin, basu samu sun yi nasara a kan Ayusherh ba, sai ma ita da lokaci guda ta yi nasara a kan su gaba ɗaya ba kuma tare da gajiya wa ba, su kam zuwa yanzu sun gaji, dan sun fahimci Yarinyar ta fi su. Ƙasa suka yi gaba ɗaya alamar saranda dai dai ta kai takobinta da shirin kai farmaki gare su. Ganin haka ya sa ta sauke takobin, tana jijjiga kai. Ta mayar da takobin inda yake ta buɗe baki da niyyar magana suka jiyo tafi raf-raf a ta gefansu, da sauri su duka suka kai dubansu zuwa saitin da suka jiyo tafin. Wani farin mutum ne dogo da kai tsaye za'a kira da matashin dattijo, shi ne yake tafin yayin da yake ƙari sawa wurin da suke. Murmushi mai bayyana haƙora Ayusherh ta saki tana faɗin. “Tata!.” Yayin da take ƙoƙarin ƙari sawa gare sa. Miƙe wa samarin suka yi suma da ɗan murmushi, saurayin mai rufe da wani kyalle a fuskarsa ya cire kyallen, ta ke kyakkyawar fuskarsa mai cike da ƙuruciya ta bayyana, ɗauke da murmushi ya fara magana cikin harshensu da faɗin. “Lallai na yarda shekaru kawai lamba ne amma kwarewa yana ga jajircewa domin kuwa Captain ta bamu mamaki gaba ɗaya mun kasa nasara a kan ta. Ûná (Uncle) ya kamata a bar Captain ta shiga gasar takobi da za'a gabatar nan bada jimawa ba.” Ya ƙare maganar da kallon Ayusherh da ta kwaɓe fuska, domin bataso ya faɗa ba, taso a ce ita da kanta ta faɗa wa Tata ɗin nata, dan bata da tabbacin zai barta ta shiga, murmushi matashin ya yi ma ta, tare da ɗa ga ma ta gira, Ayusherh ta ƙara kwaɓe fuska tana ɗan hararar sa shi kuma ya yi murmushi kawai. “Ni kaina na yaba da kwarewarta domin na ɗan jima anan ina kallon ku, sai dai fa bani da labari a kan tanason shiga gasar takobi.” Mutumin wato Jakadi ya ƙare maganar tare da duban Ayusherh da ta ɗan yi ƙasa da kanta tana warware kitson silli ɗaya, da a ka ma gashin kanta, sannan cikin muryarta mai daɗin saurare yadda kasan ana raira busar sarewa ta ce. “Banaso ka hanani shiga Gasar ne, shi ya sa ban faɗa maka ba, amma ina ta neman hanyar faɗa ma ka ne.” Ayusherh ta faɗa hakan ta ɗan ɗa go manyan idanunta ta dubi Tata ɗin nata. Ga mamakinta murmushi ya yi ma ta. Ba kuma tare da ya ce Komai ba. “Laa! Tata ka amince na shiga?.” Ayusherh ta tambaya da sauri. Jinjina ma ta kai ya yi. Zai yi Magana suka jiyo sautin gudu ana tunkaro su, kafin wata yarinya da bata haure shekaru bakwai ba, da ita ce mai gudun, ta bayyana a gabansu tana sauke ajiyar zuciya da haki na gudun da ta sha. “Yayankaka! Wannan gudun na lafiya?.” Ayusherh ta tambaya da mamaki. Sam Yarinyar ta kasa magana sai ma dafe gwiwa da ta yi da hannu ɗaya bayan ga durƙusa, nuni take musu daga inda ta fito cikin rarrabewar murya ta ke faman faɗin. “Baána! Baána!!.” A ɗan ruɗe wannan matashin saurayin da yake yaron Ƙanwar Jakadi da ta rasu, ya duba Yarinyar da Ayusherh ta kira da Yayankaka ya ce. “Mene ne ya sama Baána ɗin kardai kice ciwon sa ne ya tashi?.” Ya tambaya Hankali a ɗan tashe domin kuwa Arɗo wato mahaifin Jakadi shi suke kira da Baána (Grandfather) to yana fama da ciwo ne matsananci, kwana biyu dai an samu abin ya lafa kaɗan. Girgiza kai Yayankaka ta yi sannan. Ta ce. “O máyi.” (He is Died) Maganar nata ya daki dodon kunnensu tamkar saukar aradu, domin basu tsammaci hakan ba duk da cewar yana jin jiki lokaci kawai a ke jira. Da wani irin gudu Ayusherh ta nufa hanyar da Yayankaka ta fito ba tare da ta iya furta komai ba, yayin da Yayankaka da Tata da ma wannan saurayi suka mara ma ta baya, hankalin su a tashe, ɗaya daga cikin sauran samarin ya tsaya ya ɗauki barewar da Ayusherh ta harba, sannan suma suka mara musu baya. Tabbas mutuwa gaskiya ce domin ta tabbata Arɗo ya riga mu gidan gaskiya, mutuwarsa ta daki mutane da yawa musamman ma iyalansa kowa ya yi kuka da rashin sa, Musamman Ayusherh da suka yi matuƙar shaƙuwa da shi, haka suka dangana suka bisa da addu'a, bayan wasu watanni kuma zuwa lokacin Ayusherh ta mayar da hankali wurin koyon wasan takobi tare da taimakon Tatan ta da kuma Mamman wato wannan saurayi da suka yi faɗan takobi, Ayusherh ta ƙara zama kwararriya ta ɓangaren, kuma bada jimawa ba, a ka gudanar da Gasar takobi na shekarar tsakanin Ayusherh da take jagorantar mutanen ƙauyen su da kuma Samari na ƙauyen da ke makwabtaka da nasu. An fafata, a filin gasa kuma Ayusherh ta bawa kowa mamaki ganin ta da ƙananan Shekaru sai kwarewa domin duk kwarewar waɗan nan Samari sun gaza yin nasara a kan ta daga ƙarshe dai an tashi gasar kuma Ayusherh ita ta yi nasarar lashe wannan Gasar. Abin mamaki ke nan da kuma farin ciki ga mutanen ƙauyen ai kuwa sanadin haka Ayusherh ta ƙara shiga ransu matuƙa, kuma har gwarya-gwaryar shagali suka haɗa domin murna a kan nasara da Aysherh ta yi. .. AYUSHERH Tsaye take tana kallon yadda ruwan ke ta zubowa daga wani dogon tsauni su na cika makeken wurin da take tsaye kusa shi da a ke kira Gulbi. Ɗabi'arta ce yin wanka a cikin wurin a wasu lokutan musamman idan ta kasance cikin yanayi mai daɗi, sai dai yau tsaye ta yi kawai ba tare da ta shiga ta yi wanka a cikin ba, kamar yadda ta saba. A kullum da koda yaushe Tata faɗa ma ta yake burinsa ɗaya shi ne ta sama Soja, lokuta da dama in ya faɗa hakan sai dai ta yi murmushi kawai ba tare ta ce komai ba. To yanzu kuma ya fara ma ta magana a kan zasu bar nan ƙauye za su koma can wata ƙasa wai Nigeria domin yanaso ya sakata a Makarantar sojoji dake ƙasar. Ita kuma har ga Allah batason barin wannan ƙauyen domin shi ne mahaifarta kuma marayarta, a yadda Tata ya faɗa ma ta Mahaifiyarta rasuwa ta yi, to ke nan hakan na nufin nan ɗin shi ne mahaifarsu gaba ɗaya. Bata san dalilin da ya sa Tata ya dage a kan sai sun bar marayarsu sun koma wata ƙasa da basu san kowa ba kuma basu da alaƙa da kowa a can. Wannan damuwar da tunani ya sa taji batajin yin wankan. Daga ƙarshe da ta gaji da tsayuwar sai ma ƙari sa kusa dab da Gulbin da ta yi, kana ta zauna tana zura ƙafafunta ciki, sanyin ruwan kuwa ya ratsa ta, ta sauke ajiyar zuciya tana lumshe Meadow Green Eyes ɗin ta. A haka ta kasance ta ɗan daɗe a wurin kasancewar yammaci ne duhu ya fara kunno kai ya sa ta miƙe tare da komawa inda ta fito cikin ƙauyen su. Duk da cewar ba wai tsoron duhun dare take ba, dan kuwa ita sam bata san wani abu wai shi tsoro ba a rayuwarta. .. Washe gari yau kuma zaune take a can saman makeken dutsen ta yi shiru tana kallon gefe guda, can kuma ta kai hannu tare da ɗaukar sarewar ta dake a je a gefe, ta ɗan saki murmushi domin sarewar tuna ma ta da Baána ta yi. Ta ke ta fara busa sarewar lokaci guda kuma ta kasance cikin nishaɗi sanadin hakan. Shi kuwa Mamman da kyar ya samu ya ƙari sa hawowa kan ƙaton Dutsen sannan ya ƙari sa gare ta, tare da zama gefanta. Ayusherh tana jinsa batace komai ba, kuma bata dena busa sarewar ba, domin tasan ba zai wuce shi ɗin ba. Ajiyar zuciya da yake saukewa a jejjere ne ya sa ta ɗan dakata tare da dubansa kaɗan, dariya ce ta ɗan kwace ma ta ganin yadda ya dage yana sauke ajiyar zuciya sai kace wanda ya sha tseren gudu. “Mman! Lafiya kuwa?.” Ta tambaye sa hakan bayan ta kirasa da sunan da take kiransa da shi tun tana ƙaramar ta har ta kawo i yanzu. Wata Nannauyar ajiyar zuciya ya ƙara saukewa tare da ɗan dubanta yana kwaɓe fuska yadda kasan yaro mai shekaru uku ba wai Babba kamarsa mai shekaru goma sha shida ba. “Captain Sannu da ƙoƙari kinji! A ce wannan ƙaton dutse baya yi miki wahalar hawa sam, ni kam da kyar na samu na hawo, domin ina hawa ina komawa na faɗi nayi hakan wurin sau uku amma ban dandara ba sai da na hawo nan.” Ya ƙare maganar yana yi ma ta alamar jinjina da Babbar yatsarsa. Ayusherh ta ɗan yi murmushi domin ita dariya ma ya bata, ita fa bata ga abin wahala ba a hawa dutsen nan, wata ƙila saboda ta saba ne, shi kuma bai saba ba, shi ne kawai. Dubanta ya ƙara yi jin batace komai ba. Ya ƙara kiran sunanta kamar yadda ya saba da faɗin...FOLLOW NKDS @ AREWABOOKS APP. •… 💕 *CAPTAIN AYUSHERH*🥷 * 🍂🎀 (_The ShieldMaiden._) https://chat.whatsapp.com/IV4urJf4kuL7656LTR8Zj5 BY - Nainarh KD.... 𝒩𝓀𝒹'𝓈❦♡ Don't Forget To Follow My Both Accounts; Nainarhkd3 @Wattpad. Nkds @Arewabooks. .. Episode 4. Dubanta ya ƙara yi jin batace komai ba. Ya ƙara kiran sunanta kamar yadda ya saba da faɗin. ... “Captain!.” Ya kira ta. Bata amsa ba, sai ma kauda kai da ta yi domin zuwa yanzu Tata ya sanar da ita ma'anar da kalmar CAPTAIN ke nufi, wani muƙami ne na sojoji. Wato ke nan tun kafin ta zama Sojar shi har ya zaɓa ma ta muƙamin. “Kamar fa kina cikin damuwa, ina lura dake tun kwanaki biyu baya, ki faɗa min mene ne yake damun ki, ni kuma nayi alƙawarin zan yi matuƙar ƙoƙari iya iyawata ganin cewar na yi maganin ko mene ne yake damun naki.” Ya ƙara faɗa cike da son sanin ainihin abin da yake damun nata har ya sakata a damuwa. Ba tare da Ayusherh ta kalle sa ba ta fara magana da faɗin. “Tata ne! Ya takura a kan zamu koma Nigeria wai zai sakani a makarantar sojoji na ƙasar, saboda soja yake so na zama wai ma ashe Captain da ya sa a ke kira na, sunan wani muƙami ne a cikin sojojin.” Ta ƙare maganar tare da dubansa da Meadow Green Eyes ɗin ta, bata bari ya ce komai ba ta ƙara da faɗin. “Ni kuma banason zama wata soja, nafi son ya bar ni cikin marayana na ci gaba da Rayuwa cikin ƙauyen nan da Mutanen cikinsa domin da hakan na saba.” Shiru ya yi yana sauraren ta, bai katse ta ba, har sai da ta kai a ya, sannan ta yi shiru dan kanta, sannan ne shima ya sauke ajiyar zuciya yana faɗin. “Matsalarmu da damuwarmu kusan ɗaya ne.” “Kamar ya ya?.” Ayusherh ta tambaya cikin rashin fahimta. Mamman ya ɗan taɓe baki tare da ci gaba faɗin. “Kin san dai kafin mahaifin ki, mahaifiyata ce mace ta farko a ƙauyen nan da ta fara taka al'ada ta bar ƙauyen a kan za'a aura ma ta wanda bata ra'ayi, har ta je ƙaddara ya kaita can wata ƙasar daban har ta yi Aure ta kuma haifeni, daga bisani kuma ta dawo nan dani ta nema gafarar kowa kuma take sanar da cewar mijin da ta aura ya sake ta shi ne ta dawo. Da hakan ya sa gulma da tsegumi ya yi yawa a kanta mutanen ƙauye suke cewa ba wani Aure da ta yi kawai taje a wayon duniya ne ta sameni, har wasu ma suke kirana da ba ɗan halak ba, a yawon duniya a ka sameni...” Mamman ya ɗan dakata a nan. Yayin da Ayusherh da ta yi zuru tana sauraren sa, tana kuma gyaɗa kai yadda kasan ƙadangaruwa, jin ya yi shiru ya sa ta faɗin. “Sai mai kuma ya faru da ka ce matsalar mu ya zo ɗaya?.” Mamman ya jijjiga kai tare da ci gaba da cewa. “Sanin kanki ne har Mahaifiyata ta rasu mutanen ƙauye basu daina yamuɗiɗi da ita ba a kan cewar yawon duniya ta tafi har hakan ya yi silar samuna. To ashe kafin rasuwar ta, ta bar wasiyya a kan inda za'a sama mahaifina ta kuma roƙi da a kaini wurinsa, to shi ne fa yanzu Ûná Arɗo ya matsa a kan zai ware mutane a dangi da zasu tafi tare dani domin neman mahaifina kuma su bar ni a wurinsa.” Mamman ya ƙara shiru da ya kai nan a zancen sa. Ayusherh da ta yi ma sa tsuru da idanu ta yi saurin faɗin. “To yanzu fa, ka yanke shawarar tafiya ne ka bar mu?.” Ta yi masa tambayar tana zuba masa Manyan idanunta. Mamman ya girgiza kai. “Banason hakan har zuciyata domin ba zan iya tafiya na bar ki ba, sai dai kuma idan na ci gaba da zama a nan haka zan ƙare rayuwata a na ɗauka na matsayin ba ɗan halak ba.” Wannan karon da tausaya wa Ayusherh ta dubesa da sauri ta ce. “To mene ne abin yi?.” “Nima ban sa ni ba.” Ya bata amsa. Ayusherh bata ƙara cewa komai ba, sai ma kanta da ta ɗaura bisa kafaɗarsa suka ci gaba da zaman shiru, zuwa can ya sauke kanta daga kafaɗarsa yana faɗin. “Babu kyau, ko kin manta mu ɗin ba muharraman juna ba ne?.” Turo baki Ayusherh ta yi ba tare da ta ce Komai ba, sai ma gunguni da ta fara. Mamman ya yi murmushi yana shirin magana ke nan suka ji wata ƙara da ta amsa a ko'ina na wurin da alama daga wuri mai nisa ƙarar ta taho. Gaba ɗaya suka zazzaro ido. Ayusherh na faɗin. “Wannan ƙarar kuma daga ina haka?.” Sai dai kafin ta rufe baki ne ta hango abin da ya tashi hankalinta matuƙa. Da sauri ta kai hannu tana yima Mamman nuni da cikin ƙauyen da suke hangowa wuta na tashi ta wasu wuraren yayin suke hango Mutane a warwatse da alama dai ba lafiya. Shima Mamman ya ga abin da ta gani, hankali tashe ya buɗe baki domin magana, sai dai tuni Ayusherh da ta tashi ta yi nisa yayin sauka daga saman dutsen, ganin haka ya sa shima ya yi saurin bin bayanta yana kiran sunanta domin ya fahimci ba lafiya da alama ƴan ta'adda ne suka kai ma ƙauyen nasu hari a wannan yammacin. Sai dai Ayusherh bata saurare sa ba har ta samu ta ƙari sa sauka gaba ɗaya daga saman Dutsen da mugun gudu ta nufa cikin ƙauyen nasu. Da kyar shi kam Mamman ya kusa saukowa daga saman dutsen yana dab da saukowa ne ƙafarsa ɗaya ta gurɗe gaba ɗayansa ya yo ƙasa. Ai kuwa ya yi mugun buguwa, amma haka ya daure yana ciccijewa ya miƙe tsaye tare da takawa shima ya nufa ƙauyen yana ci gaba da kiran sunan Ayusherh da tuni ta kai ƙauyen sai dai tashin hankali da ta tarar ne ya yi matuƙar gigita lissafin ta domin da gawarwaki na mutanen da a ka harbe ta fara cin karo, wasu a ma ce, wasu kuma iya rauni suka ji. Da gudun bala'i ta nufa hanyar gidansu tana kwala kiran sunan Tata da sauran mutanen gidan ganin haka shima Mamman yabi bayanta yana ci gaba da kwala kiran sunanta shima. Da gawar Matar mahaifin nata wato Babaya dake kwance a tsakiyar gidan cikin jini Ayusherh ta fara cin karo, ta saki wani lalataccen ihu tana Zubewa ƙasa tare da kiran sunanta sai dai shiru domin babu rai a tare da ita. “Ayusherh garin nan fa ba lafiya ki tashi kawai mu gudu muma a domin mu tseretar da Rayuwar mu.” Cewar Mamman yana ƙoƙarin kamo hannunta. Kallon sa Ayusherh ta yi kamar wata zararrariya tana girgiza masa kai. Ta share majina tare da miƙe wa tsaye da gudu ta fara dube duben ɗaku nan wai ko zata ga sauran mutanen gidan nasu. Kusan ɗaki biyu ta duba amma babu kowa, har ta fara cire rai ta shiga ɗaki na ƙarshe Mamman na biye da su. Har zata fi ce ganin babu kowa amma sai taji an riƙo ƙafarta ana kiran sunanta. Da sauri ta duba wurin, sai dai uban kaya ta gani, da mugun sauri ta fara yayyaye kayan ai kuwa ta ke Yayankaka ta bayyana, sai dai ba abin da ya sameta ita. Hankali a mugun tashe Ayusherh ta ce. “Yayankaka ina Tata yake ina kuma Ali shima yake?.” Kuka yarinyar ta saki tare da rungumo Ayusherh tana faɗin. “Nima ban sa ni ba, sai dai an kashe yah-yah (mama)” Da sauri Ayusherh ta miƙe tare da ɗaukar Yayankaka ta goyata katamau, yayin da shi kuma Mamman ya kamo hannunta da gudu suka baro gidan, hanyar gidan marigayi Arɗo Ayusherh ta nufa, sai dai ganin yadda gidan yake kamawa da wuta ga kuma ƙarar harbi dake ƙara tunkaro su ne yasa, Mamman jan hannunta suka ɗauki hanyar barin garin da gudun tsiya gudu suke kamar zasu tashi sama, zuwa yanzu sun gaji ga Ayusherh dake goye da ƴa ga kuma Mamman da yaji ciwo a ƙafa. Sun yi nisa sosai har sun kusa kai ƙarshe hanyar da suka ɗauka, suna dab da wani dogon tsauni wanda kogi ne shirgegen gaske a ƙasan sa. Kamar an ce Mamman ya juya ai kuwa ya hango ɗaya daga cikin ƴan ta'addan ya saitasu da bindigar sa katuƙar gaske, wani irin zaro ido ya yi tare da sakin hannun Ayusherh, ya matsa tare da ta re su Ayusherh dai dai ɗan ta'addan ya saki harbi. Ai kuwa alburushin bai sauka a ko'ina ba sai a saitin ƙirjinsa. Wani irin baya ya yi yadda kasan an ɗa ga shi sama, ya yi sama tare da faɗa wa ƙasan wannan tsaunin, da sanadin hakan ya sa Ayusherh sakin wani gigitaccen ihu tana duƙawa ƙasa ta ɗauki wani dutsen Marmara ƙarami dake wurin sannan ta ɗa go dai dai ɗan ta'addan ya kuma saitawa zai harbeta ta yi saurin jifarsa da dutsen cikin sa'a ta samesa a goshi ta ke wurin ya fara zubda jini ƙara jifarsa da wani dutsen ta yi wannan karon a hannu ta samesa da hakan ya sa Bindigar dake hannunsa ta faɗi. Ganin ya faɗi ƙasa ne ya sa Ayusherh saurin ƙari sawa tana leƙen ƙasan tsaunin, sai dai ganin ƙaton kogi da ta yi ne ya sa batasan lokacin da hawaye ya zubo ma ta ba, domin ta tabbata shikenan kuma Mamman ya mutu. Gudu ta ci gaba da yi cikin tsananin tashin hankali yayin da take ƙara nesa da ƙauyen nata kuma goye da Yayankaka wacce babu abin da take sai aikin kuka, ita ma Ayusherh tana zubar da hawaye na wannan farmaki da ƴan ta'adda suka kawo wa ƙauyen su. Gashi sanadiyar hakan ta rasa Mamman, mman ɗin ta mutum mai muhimmanci a rayuwarta idan a ka ce cire Tata ɗin ta, gashi yanzu bata da tabbaci a kan Tata yana raye ko shi ma waɗan nan ƴan ta'adda sun kashesa, sai dai jikinta yana bata cewar Tata ɗin ta yana raye. Gudu ta ci gaba da yi babu sassauta wa zuwa lokacin dare ya yi sosai bata dena gudu ba sai da ta tabbata tayi mugun nisa da ƙauyen, sannan ta fara tafiya a hankali zuwa lokacin ta sauke Yayankaka sakamakon gajiya da ta yi, suka ci gaba da tafiya a hankali ga mugun yunwa da ƙishin ruwa da suke ji, ita kam Yayankaka sai faman kuka take yi. Gaba Ayusherh ta gama galaɓaita, a Duniyarta gaba ɗaya batasan da wata wahala makamancin hakan ba duk da ba ta tashi cikin mugun jin daɗi ba, amma a wannan ɗan ƙaramin ƙauyen nasu ta taso a Babban gida, jikar shugaban ƙauyen. Ajiyar zuciya ta ci gaba da saukewa suna ci gaba da tafiyar da su kansu basu san inda suka dosa ba, tafiyar kawai suke yi. Kamar da wasa kaifafan kunnuwanta suka jiyo ma ta nishi da a hankali da yake fito wa, ta cikin wata gona da suka zo giftawa. Dakatawa da tafiyar ta yi tare da duban gonar, jin nishin da yafi kama da na wahala yana ƙaru ne ya sa ba tare da tsoro ko fargaba ba ta fara tunkarar cikin gonar yayin da kukan Yayankaka ya tsananta. Da mugun sauri Ayusherh ta sa hannu tare da ya ye tumin ɓawon masara da take jiyo ƙarar nishin ta ciki. Wani zaro ido ta yi a kiɗime cike kuma da tashin hankali na ganin waɗan da suke a wurin. Cikin Wata kalar raunanniyar murya a kato na farko da ta yi magana da kalar muryar ta ce. “Tata, Yâ tâ, Ali!!” Ta kira sunayen nasu cikin wata kalar murya tana fashewa da kuka. Jin sunayen da ta kira ne yasa Yayankaka saurin duban su ai kuwa ita ma ta fashe da kuka tana tattaɓo kakar tasu da suke kira Yâ tâ tana kuma kamo Hannun mahaifinta da ɗan uwanta da suma suke dubansu cikin wani irin yanayi. “Ayusherh dama baku mutu ba.” Ali ya tambaya yana kuka shaɓe-shaɓe tare da miƙe wa tsaye yana rungumo ta yana ci gaba da faɗin. “Sun kashe yah-yah waɗan nan azzaluman mutanan kuma mu ma da kyar muka samu muka gudo ni da Yâ tâ (kakarsu ta wurin Uba). Da kuma Tata gashi kuma sun harbi Tata a ƙafa shi ya sa baya iya tafiya.” Goge hawaye Ayusherh ta yi tana faɗin. “Na sani Ali sun kashe yah-yah.” Ta yi maganar tare da tsugunna wa gaban Tata tana hawaye ta kamo hannunsa, yayin da Ali ya taimaka wa Yâ tâ ƴar tsohuwar ta tashi zaune. “Kiyi haƙuri Ɗiyata ban iya na nemi inda kike ba.” Cewar Jakadi da kyar yana rumtse ido sakamakon zugi da gwiwar nasa da a ka harba take masa...FOLLOW NKDS @ AREWABOOKS APP. •… 💕 *CAPTAIN AYUSHERH*🥷 * 🍂🎀 (_The ShieldMaiden._) https://whatsapp.com/channel/0029VaEZtE15a2429vfcpf20 BY - Nainarh KD.... 𝒩𝓀𝒹'𝓈❦♡ Don't Forget To Follow My Both Accounts; Nainarhkd3 @Wattpad. Nkds @Arewabooks. .. Episode 5. _Note: Ku gane wani abu. Ba waɗan da suka kashe mahaifiyar Ayusherh ba ne suka dawo ƙauyen domin kashe Ayusherh. A'a. Su waɗan nan wasu ne daban ƴan ta'addan da suka kawo farmakin._ . Cikin dauriya Ayusherh ta ce. “Ba komai Tata, domin ka bani hoton da zan iya ceton Rayuwata da kaina. Duk da ƙananun shekaruna.” Ta kai maganar tana jijjiga kai. Ali ne ya dubeta a ɗan firgice domin baya ma a hayyacinsa sam, ya ce. “Mamman! Ina Mamman yake?.” Tambayar nasa da saida tasa zuciyar Ayusherh harbawa da sauri, ta kasa magana, har sai da ya maimaita tambayar, da kyar ta sama zarafin faɗin. “Sun kashesa, waɗan can azzaluman ƴan ta'addan sun kashe mana Mamman ɗin mu, ni a ka zo harba amma ya kareni harbin ya samesa a ƙirji, sanadin haka ya faɗa cikin teku ya mutu, ina ji ina gani na kasa ceton Rayuwarsa..” Ta ƙare maganar tana sakin wani kuka da bata sama damar yi ba sai yanzu. Da sauri Ali yaron da bai haure shekaru bakwai ba, domin ƴan biyu ne shi da Yayankaka, ya dafe kafaɗar Yayartasu Ayusherh shima hawaye yake yi yana tuna Mamman. “Shikenan rayuwarmu ta rushe sun kashe mana mutane da yawa yayin da wasu suka gudu domin ceton Rayuwarsu, a halin yanzu kam bamu da wani madogara ko kuma wurin zuwa dan nasan kafin gari ya waye sai sun lalubo inda muke, muma su kashe mu ko kuma su tafi da mu can wata ƙasar su siyar matsayin bayi.” Yâ tâ, kakarsu ita ce take wannan maganar yayin da ta ɗaura hannu a ka, abin ka da tsufa ga kuma tashin hankali da ta tsinci kanta ciki rana tsaka. Duk shiru suka yi suna sauraren ta ba tare da sun iya cewa komai ba, sai ma Tata ya ɗan nisa kana ya ce. “Zaman mu anan ba tsaro domin waɗan nan azzaluman zasu iya lalubomu ko su kashe mun ko kuma su siyar damu. Kamar yadda Yâ tâ ta faɗa.” Ya yi maganar yana tunanin abin yi, domin ba zai yiwu su ci gaba da zama a wurin na tsawon lokaci ba, dan ba tsaro. “Wannann ƙauyen shi ne garin mu anan muka taso bamu saba da kowa ba bayan mutanen ƙauyen, kuma a halin yanzu bamu da wani wurin zuwa.” Cewar Ayusherh. Girgiza kai Tata ya yi. Kana ya ce. “Tabbas akwai, ina nufin muna da wurin zuwa.” “Ina ne?.” Suka yi masa tambayar a tare. Tata ya jijjiga kai ba tare da ya ce komai ba, yana tabbatar da wurin da ya Kamata suje ɗin nan ne kawai mafita a gare su, kuma zai yi amfani da wannan lamarin da ya faru wurin cusa muradin zama nagartacciya jami'ar soja a zuciyar Ayusherh ko dan ta kare ƙasarta da al'ummar ta daga farmakin ƴan ta'adda. “A halin yanzu ba zamu iya wani tafiya ba, mu bari sai gobe sai mu kama hanya domin tafiya ce miƙaƙiya zamuyi.” Tata ya ƙara faɗa. “Ƙasar zamu bari.” Ali ya tambaya. Yayin da Yâ tâ ta ce. “Ina ne inda zamuje ɗin.” Ayusherh kuwa shiru kawai ta yi ba tare da ta iya furta komai ba. “Nigeria zamu tafi. Mu fara wata sabuwar Rayuwar a can?.” Tata ya basu amsa. Lumshe ido Ayusherh ta yi, haka kawai batasan dalilin ba, amma taji sauyin bugun zuciyarta ya canza lokacin da Tata ya ambaci ƙasar da za su koma. Ba wanda ya ƙara magana a cikin su, kowa dai da abin da yake saƙawa a ransa, shi kuwa Tata a nasa ɓangaren tunanin can baya yake yi, abin da ya faru bayan barinsa ƙauyen su. Ya sha matuƙar wahala sosai, yasha gwagwarmaya ya tsinci kansa a wuri wuri cikin mutane kala kala daban daban masu banbancin ɗabi'a, al'ada da kuma addini har Allah ya nufesa da sauka a ƙasar Nigeria ƙasar da rayuwarsa gaba ɗaya ta sauya a ciki domin sanadin zuwansa ƙasar ne ya fita daga duhun jahilci ya karɓa addini na Muslunci kuma cikin yardar Allah a lokaci ƙanƙani ya san abubuwa da dama da suka shafi addinin, kwarai sai a lokacin ya san cewar ya shiga addini na gaskiya, Jakadi ya matuƙar ƙoƙari a wancan lokaci wurin ganin ya sama ilmin addini dai dai gwargwado kuma lamarin kam sai godiya, ana a haka ne Jakadi yana ci gaba da gudanar da Rayuwa duk ta yadda tazo masa a ƙasar Nigeria, kuma bai taɓa tunanin ya yi aure ba domin a lokacin sam Aure baya gabansa yafi mayar da hankali ne wurin neman ilimi da kuma sana'a domin tsira da mutunci, ana a haka ne wata rana Ubangiji ya nufa ya sama aiki a gidan wani hamshaƙin mai kuɗi. Ba da ɓata lokaci ba kuma ya fara aikin a gidan, kuma ba laifi yana samu sosai kuma akwai fahimtar juna da girmama juna tsakaninsa da Matar gidan da ta kasance soja, za'a iya cewa yana zaune ƙalau da kowa a gidan amma ban da mace ɗaya wato Ƙanwar Matar gidan da ta kasance bata da abin wulaƙanta wa sai talaka wanda ba shi da komai, kuma yayar nata tana matuƙar ƙoƙari wurin ganin ta dena wannan ɗabi'ar amma abu ya cutura. BAYAN WANI LOKACI! A wata safiya ce kuma lokacin Jakadi ya gama yanke shawarar komawa gida can Asalinsa wurin Ahalinsa, domin bai manta da su ba. Ya je ya sama Matar gidan da suke kira da General dama haka muƙamin ta yake a soji, ya je ne domin ya yi ma ta magana a kan zai koma ƙasar sa domin duba Ahalinsa, sai dai da yaje ya tarar da saɓani ya shiga tsakanin yaya da Ƙanwar da har ta kai su ga cacar baki, kuma abin da ya gani da kuma maganganun da yaji Ƙanwar na faɗa ma yayartata abin ya matuƙar gigitasa. Sai dai da yake lamarin bai shafe sa ba, shi ya sa bai shiga zancen ba, iya ka dai ya nema izinin tafiya a wurin Madam kuma ta yarje masa har kuɗaɗe masu kauri ta basa a cewarta ya yi kuɗin mota, ai kuwa a ranar ya fara shiri, washe gari kuma ya musu sallama da niyyar tafiya, wuraren yammaci. A lokacin ba zai manta ba har General take zolayarsa da faɗin. _“Gashi kuma zai tafi ba tare da ta haihu ba. Balle yaga wani irin ƙani ɗan ta zai sama mace ko Namiji.”_ Domin a lokacin tana da ɗa ƙarami sannan ba shi da wata magana sai a kan kalar ƙani ko Ƙanwar da Mommynsa zata haifa masa. Shi kuma Jakadi a lokacin sai ya yi ta biyewa yaron. A lokacin da ta faɗa haka, murmushi kawai Jakadi ya yi sannan ya ce ma ta. Ai ba daɗe wa zai yi ba zai dawo. Maganar su ke nan ta ƙarshe, kafin ya musu sallama da niyyar komawa ƙasarsa Cameroon. A wancan lokaci da yammaci ya kama hanya kuma sai an yi tafiya mai nisa zai isa wurin da zai shiga mota. Hakan ya sa tafiyar tasa ya kai sa har dare ba tare da ya ƙari sa wurin shiga mota ba. Hakan ya sa shi yanke shawarar samun wuri ya kwana kawai in ya so da sassafiya ya ci gaba da tafiya. Ya ɗan shiga cikin daji a ta wurin da ya yanke shawarar kwana. Hakan ya sa shi ci gaba da tafiya a daren domin samun wurin kwana. To a wannan dare komai ya wakana. Tun daga kan haɗuwa da uwar ɗakinsa wato General da ya yi da mutane da ke bin ta domin su kasheta, har zuwa taimaka ma ta da ya yi da haihuwa da ta yi, washe gari kuma ya samu ya kai ta ƙauyen dake kusa da dajin, da biyo bayansu da waɗan nan mutane dake bin ta suka yi har buɗe wa ƙauyen wuta da suka yi da hakan ya yi silar rayuwarta yayin da shi kuma ya sha da kyar da kuma wahalhalu da ya sha kafin ya samu ya iya, isa ƙasarsu zuwa ƙauyensu dake dab da border dake tsakanin Nigeria da Cameroon. Komai ya faru ne cikin ƙanƙanin lokaci. Kuma ba tare da tsammani ba. WANNAN KE NAN. Dai dai nan kuma Tata ya farka a gigice daga baccin da ya ɗauke sa, har ya yi wani mummunar mafarki, Addu'o'i kawai yake jerowa. A lokacin ma gari ya ɗan waye haske ya karaɗe ko'ina. Ya kai dubansa ga Ahalin nasa da suka yi masa saura. Ali ne da Yayankaka ƙanƙame da Kakarsu Yâ tâ, suna kwasar baccin wahala. Ɗan kauda idanunsa ya yi domin ganin ta inda Ayusherh take sai dai sama ko ƙasa bai ga alamarta ba. Hakan kuma ba ƙaramin ɗa ga masa hankali ya yi ba, da sauri ya yi ƙoƙarin miƙe wa tsaye yana kwala kiran sunanta hankalin sa a ɗan tashe, sai dai ya kasa miƙe wan sakamakon ƙafarsa wurin da a ka harba ta yi tsami, dan ma a jiya da daren kafin su yi bacci Ayusherh ta matsa har sai da ya cire harsashin da kansa domin cewa ta yi ita zata cire masa, hakan ya sa cikin dabara ya cire amma ya sha matuƙar azaba ba kaɗan ba. Da sauri Ayusherh da take ɗan kewaye wurin domin ta ri ga kowa tashi, ƙari sowa wurin ta yi tana kiran sunansa da tambayar abin da ke faruwa a ɗan ruɗe. Zaro ido ta yi ganin gwiwar nasa yana fitar da jini, da sauƙi ta tsuguna a gabansa tare da kama rigar jikinta ta yaga, kana ta shiga ɗaure masa wurin da kyallen da ta yaga tana faɗin. “Sannu Tata.” Bai amsa ma ta ba, sai zuba ma ta ido da ya yi yana dubanta. Allah ya sa ni yana matuƙar son ta fiye da yaran da ya haifa a cikinsa kuma yana ma ta fatan nasara a Rayuwa, kuma zai dage da ƙarfinsa ya tsaya ma ta wurin ganin ta kai babban matsayi a rayuwa, domin ta wannan hanyar ne kawai zai biya iyayenta Alkhairai da suka yi masa a rayuwa. “Na hango alamun ƙauye anan kusa, sai dai kamar ruga ne, ku daure mu ƙari sa domin su taimaka mana muyi jinyar ciwon Tata a can, zuwa muga abin da hali ya yi.” Cewar Ayusherh a lokacin da ta gama ɗaure masa ciwon, ta yi maganar tana duban ƙannin nata da suka tashi. Washe baki Ali ya yi ya ce. “Da gaske.” Jinjina masa kai ta yi tana duban Tata kana ta ce. “Tata! Ai hakan ya yi ko?.” Murmushi ya ɗan ma ta ya ce. “E .” Gefe guda kuwa yana kallon fuskarta ne da ta ɗauko sak kamannin Mahaifiyarta babu abin da ta rage sai kalar fata da ta ɗauka irin na mahaifin ta da ya kasance ruwa biyu wato Hausa Fulani, yayin da mahaifiyarta ta kasance asalin cikakkiyar shuwa Arab ce. “Tata! Kanajina kuwa? an ya zaka iya tafiyar ma kuwa?.” ko dai na ɗauke ka?.” Ayusherh ta ƙara yi masa tambayar in serious tana dubansa. Ba Tata kaɗai ba hatta Yâ tâ da Ali har da Yayankaka maganar da Ayusherh ta yi ta matuƙar basu dariya. “Wai wa? Tata ɗin namu zaki ɗauka?.” Cewar Ali. Ayusherh ta ɗan dubesa cikin rashin fahimta ta ce. “E mana ko kana kokwanto ne?.” Gimtse dariya ya yi yana ɗa ga hannu ya ce. “A'a! Ni ban ce ba.” Ayusherh ta ja gwafa, dan ita bataga aibun abin da ta faɗa ba sam. Tata ya ɗan dara yana faɗin. “Na hutaceki da yardar Allah ma zan iya taka wa.” Ya faɗa yana ƙoƙarin miƙe wa tsaye. Ayusherh ta rungume hannu a ƙirji kana ta ce. “To gwada tafiyar mu gani. Amma ni...” Ta kasa ƙari sawa ganin Tata ya yi baya zai faɗi. Da sauri ta taro sa tana faɗin. “Ni dama na sa ni ba zaka iya ba, kawai Tata ka bari na goya ka ai zan iya.” Shi dai Tata bai ce komai ba. Ganin haka ya sa Ayusherh fara kici kici ita a dole goya sa zatayi, ta wani tsaya a gabansa tare da durƙusa wa tana faɗin. “Hau muje Tata.” Tata bai hau ba, dan ya san ba zata iya ba. “Tata ka taimaka ka hau, ko dan mu ƙure mai taurin kai da kafiya.” Yâ tâ ce ta yi maganar a yanzu. “E Tata ka hau mu gani.” Yanzu kuma Ali da Yayankaka ne suka haɗa baki wurin faɗa. Girgiza kai kurum Tata ya yi dan shi ya sani Ayusherh ba zata iya ba! Ina ai da sauran ta, ƙarfinta bai kai nan ba....FOLLOW MY ACCOUNT NKDS @ AREWABOOKS APP. •… 💕 *CAPTAIN AYUSHERH*🥷 * 🍂🎀 (_The ShieldMaiden._) BY - Nainarh KD.... 𝒩𝓀𝒹'𝓈❦♡ Don't Forget To Follow My Both Accounts; Nainarhkd3 @Wattpad. Nkds @Arewabooks. .. Episode 6. Yanzu kuma Ali da Yayankaka ne suka haɗa baki wurin faɗa. Girgiza kai kurum Tata ya yi dan shi ya sa ni Ayusherh ba zata iya ba! Ina ai da sauran ta, ƙarfinta bai kai nan ba. . “Yarinyata akwai ki da taurin kai.” Tata ya faɗa, yana ƙoƙarin hawa bayan nata. Ita ko Ayusherh har da cicciɗa shi lokacin da ya hau. Kamar da wasa ta taƙarƙare ta fara taku da Tata a bayanta an yi ɗaya, biyu, ana ukun ne gaba ɗayansu daga shi har ita suka yo ƙasa sakamakon ƙafarta da ta gurɗe. Ai kuwa Ali da Yayankaka mai zasuyi da ya wuce dariya. Ita dai Yâ tâ abin kunya ma ya bata, girgiza kai ta yi, ita tasan kaɗan ke nan daga aikin Ayusherh Yarinyar akwai kafiya, ita ta raineta saboda haka ta santa ciki da waje. “Wayyo! yi haƙuri Tata ƙafata ce ta gurɗe amma zan kiyaye Bara na taimaka maka ka tashi mu ci gaba da tafiya.” Cewar Ayusherh a lokacin da ta miƙe tsaye a ƙoƙarin ta na taimaka masa ya miƙe take wannan maganar. Cikin nutsuwa Tata ya ce. “Kin ga samomin sanɗa mai kyau da kuma kwari kawai da zata taimaka min wurin tafiyar.” Ya faɗa lokacin da ya samu ya tashi zaune. Amsa wa Ayusherh ta yi nan ta fara duba wurin da zata sama irin sandar da zata masa dai dai. Ta kuwa ci Sa'a ta samu, dawowa wurin ta yi tare da ba shi sannan ta taimaka masa ya miƙe tsaye da taimakon wannan sandar ya fara taka wa duk da haka Ayusherh tana taimaka masa. Yâ tâ da ɗan sauran gwarinta da kanta take taka wa haka suka fara tafiya, sai da suka yi doguwar tafiya sannan suka isa ƙauyen da Ayusherh ta hango. Ruga ne ma kuma ta Fulani. Kuma koda jin abin da ya samesu Fulanin da yake na kirki ne sun matuƙar tausaya musu sosai kuma sun basu wurin zama, sannan ne a ka sama wanda ya duba ƙafar Tata bayan sun basu abinci sun ci, da yake tun a hanya sun yi salla ta hanyar taimama. Kwanakin su Ayusherh biyar a wannan ruga zuwa lokacin ƙafar Tata ta warke sai dai ba ya iya tafiya har sai da sanda domin ba duka ya gama warware wa ba. A lokacin ne kuma suka fara shirya-shirye na ci gaba da tafiyar zuwa Nigeria. Sosai suka yi ma waɗan nan Fulani godiya da halaccin su a gare su kafin suka ɗauki hanya da su kansu basu san Ranar isa ba. *** Sun matuƙar shan wahala fiye da tunani ga yunwa da ƙishirwa domin guzurin da suka yi ma ta ƙare amma haka suka daure suke ci gaba da tafiya duk ƙauyen da suka gani za su ɗan tsaya su huta na ƴan kwanaki idan mutan ƙauyen sun tarbe su da ban girma matsayinsu na baƙi kuma matafiya. Daga ƙarshe dai a hanyar su na tafiya suka haɗu da wasu mutane suma masu tafiya amma saman raƙuma, su ne suka taimaka musu suka shiga dasu har ƙasar Nigeria a kan raƙumansu. To a ƙasar ma sun sha garari wuri wuri daji daji kafin Allah ya sa suka tsaya a wani ƙauye cikin jihar Taraba Mutanen ƙauyen sun haɗa da Fulani da kuma ƴan kabilarsu sai dai Fulani sun fi yawa, sun tarbe su cikin mutumci kuma Tata ya yanke zasu ɗaura da sabuwar rayuwa a ƙauyen har zuwa lokacin da zai sama wani abu mai gwabi su shiga cikin birni domin ya saka Ayusherh a makaranta, kuma su fara sabuwar rayuwa. A taƙaice dai yanzu suna a ƙauyen mai suna Mayo-Danay, kuma lokaci ƙanƙani suka saba da mutanen ƙauyen rayuwarsu ta fara komawa kamar baya. A halin yanzu Shekara guda ta wuce. Ayusherh ta kasance matashiyar jaruma wurin shiga daji domin farauta a kaf ƙauyen ba kamar ta a cikin ƙananun shekarunta da ba zasu haura Goma sha Uku ba. _Note: Mayo-Danay ya kasu kashi biyu ne, akwai a ƙasar Cameroon wato ƙauyen su Ayusherh. Akwai kuma a ƙasar Nigeria jihar Taraba wato nan inda su Ayusherh suka sauka._ .. AYUSHERH Baya ta yi, sannan ta yi ƙasa da gwiwarta ɗaya, ta rage girman idanunta tare da sakin kibiyar dake hannunta dai dai wurin da ta saita. Kibiyar ta ratsa ciyayun masu tsayi dake wurin ta nufe abin harin da Ayusherh ta saita da mugun sauri, wani irin zaro ido ya yi tare da yin ƙasa da sauri, hakan ya sa kibiyar bata samesa ba ta sauka a kan bishiyar dake wurin. Wata kibiyar Ayusherh ta ƙara cirowa zata saita wurin da ya tsugunna dai dai shi kuma ya sa hannu tare da ya ɗan yaye ciyawar dake basa kariya ke nan ya ga abin da take shirin yi da sauri ya miƙe tsaye cikin zaro ido yana faɗin. “No! Please don't...” Ya yi maganar yana ɗa ga hannu tamkar dai yadda ɓarayi ke yi in sun shiga hannu, to shima hakan ya yi, yana mai fara taka wa zai ƙari sa inda take. Ayusherh bata sauke kibiyar ba, kuma bata dena saita shi ba, har sai da ya gama fitowa daga maɓoyar nasa gaba ɗaya ya fara taka wa zuwa inda take a ɗan dake. Ita kuwa a karo na farko ta kai dubanta ga fuskarsa domin da fari da yake maganar ko dubansa batayi ba, lokaci ɗaya kuma tana ƙoƙarin magana cikin harshen fulatanci da zuwa yanzu ta gama kwarewa sai dai me?... Wani irin abu taji tun daga ƙwaƙwalwar kanta ya tsarga har ƙafafunta sakamakon ido huɗu da suka yi da shi, ba wai haɗa ido da suka yi ba ne ya jefata cikin wannan yanayi, a'a fuskarsa ce sanadi, fuskarsa da ta gani ne ta yi matuƙar rikita tunanin ta. Da wani irin sauri ta miƙe tsaye cikin rarrabewar murya take ƙoƙarin magana da kyar ta fisgo kalmomi ta tattara tare da kiran sunansa da faɗin. “Mamman!.” (..😳😳..) Ta yi maganar ne cikin wani irin yanayi tana kuma ƴar dariya jerarrun haƙoranta farare suka bayyana, da sauri ta fara taka wa domin ƙari sawa gare sa. Yayin da shi kuwa ya tsaya cak da tsananin mamaki ganin lokaci guda Mafarauciyar Yarinyar dajin dake ƙoƙarin farmakinsa ta dakata daga ganin fuskarsa har take kiransa da wani suna da bai taɓa sanin akwai sa ba sai yanzu. Fuskarsa da alamar mamaki ya saki baki yana dubanta. “Mman ɗina dama baka mutu ba?.” Ayusherh ta yi Maganar cikin wani irin yanayi na zallar zumuɗi, lokacin da ta ƙari sa garesa ta sa hannu tare da shafa fuskarsa tana ci gaba da faɗin. “Nayi kuka sosai a wancan lokacin saboda a tunanina shikenan Abokina Aminina sannan ɗan uwana Mman ɗina ya mutu! ashe ba haka ba ne kana raye..” A yanzu ta yi maganar ne gaba ɗaya fuskarta a washe tana zare manyan idanunta saman fuskarsa. “Ka sauya da yawa sosai fa!.” Ta faɗa tana duban yanayin fatarsa da ta kasance wata kalar ja jajur ɗin nan, gashi da ka gansa kasan hutu ya zauna ba ƙarya...FOLLOW MY ACCOUNT NKDS @ AREWABOOKS APP. •… 💕 *CAPTAIN AYUSHERH*🥷 * 🍂🎀 (_The ShieldMaiden._) https://whatsapp.com/channel/0029VaEZtE15a2429vfcpf20 BY - Nainarh KD.... 𝒩𝓀𝒹'𝓈❦♡ Wattpad @Nainarhkd3. .. Episode 7. “Am nace ba, wai wacece ke ɗin? Kuma mene ne kike faɗa ne, ni sam bana fahimta.” Ya faɗa yana dubanta cikin rashin gane inda ta dosa da kalamanta da kuma yanayinta, nuna wa take tamkar ta sansa a baya. Cikin harshen fulatanci ya yi maganar, saboda haka ta fahimta, lokaci guda murmushin dake ɗauke saman fuskarta ya gushe, da jin kalamansa. Ita ma cikin harshen fulatanci ta ce. “Mamman! Baka gane ni ba da gaske Ayusherh ce fa?.” Ta yi maganar cikin sanyin murya idanunta kafe a kan sa. Shi kuwa cikin rashin fahimta yake dubanta, ya ɗan yi shiru kamar mai tunani, a nufinsa wata ƙila ya tuno inda ya santa, sai dai ya kasa tunawa domin bai santa ɗin ba. “Abyaz! Shi ne sunana Am not a Mamman hasali ma ban shi ba.” Ya yi maganar yana jinjina ma ta kai alamar dai da gaske bai san wani Mamman ba kuma ba sunansa Mamman ba. Zuba masa ido Aysherh ta yi tana yi masa wani irin duba cikin rashin yarda da kalamansa duk da ba duka take ganewa ba dan yana haɗa wa da wani yaren da ba fulatanci ba. “Waye kai.” Ta faɗa tana ƙoƙarin saita kibiyarta a kansa. Abyaz ya ƙara zaro ido ganin abin da take shirin yi. “Na faɗa Miki Abyaz! Sunana.” Ya faɗa yana ɗa ga hannu sama. A dake ta ƙara tambayarsa da faɗin. “Mene ya kawo ka nan, kuma me ya sa kake bibiyata tun ɗazu ina lura da kai?.” Da sauri ya ce. “Motarmu ce ta sama matsala a hanyar mu na shigowa shi ne a ka tsaya gyara ni kuma na fara kewaye dajin shi ne na hango ki, na tsaya ganin yadda kike ke kaɗai kuma mace a irin dajin kinata training kamar...” “Mene ne training?.” Ta katsesa da faɗin hakan, bayan ta ɗan yi ƙasa da doguwar kibiyar nata mai yanayi da Bow, ɗabi'arta ce in zata fita daji ɗayan biyu ne kodai ka ganta da row and bow ko kuma wannan doguwar kibiya. “Ina nufin horo.” “Me ya sa kake kama da Mamman ɗina?.” Ya zaro ido jin tambayar da ta yi masa. “I don't know.” Ya faɗa yana taɓe baki tare da ɗage kafaɗa. A harzuƙe Ayusherh ta ƙara ɗa ga kibiyar zata saita shi. Da sauri ya ce. “Mi anda, Mi andani.” A yanzun ya maimaita abin da ya faɗa cikin harshen fulatancin kamar yadda ya fahimci harshen kaɗai takeji. Jinjina kai ta yi tare da mayar da kibiyar ta soke ta a ƙugunta jikin doguwar rigar jikinta. Sannan ta kai hannu ta damƙo kwalarsa ta juya tare da fara taku da shi a haka. Abyaz cikin mamaki yake faɗin. “Hey! Hey!! Ina ne zaki kaini haka, ki dakata mana.” Ya yi maganar yana biye da ita tamkar raƙumi da akala. Sai dai Ayusherh taƙi kulasa haka nan taƙi sakinsa. Shiru ya yi yana biye da ita, yana kuma jinjina ƙarfin hali irin na wannan Yarinyar daji, ko ina zata kaisa? Allahu Aalamu. Ba wai dan ba zai iya gwacewa ba ne ya barta ta ci gaba da tafiya dashi a haka. A'a kawai nishaɗi hakan ya saka shi. Ayusherh bata sakesa ba har sai da suka shiga cikin ƙauyen kowa da mamaki yake dubansu sai dai ko'a jikinta shi kuwa bata su yake ba, ta iya yake, yana cikin wannan shauƙi ne da ya ɗibesa yaji ta wancakalar da shi gefe, bayan ta saki kwalar nasa. Sai a lokacin ya lura da inda suka shigo wani gida ne na kara da ɗakunan suke na bukkoki. Zuba ma laɓɓanta ido ya yi yayin da ita kuma ta dage sai kiran sunayen mutanen gidan take yi, faɗi take. “Yâ tâ! Ali, Yayankaka, duk kuna ina ne Tata! Tata!!.” Harɗe hannu Abyaz ya yi a ƙirji tare da zuba ma ta ido dan shi ko'a jikinsa. Yâ tâ ce tare da Ali suka fito daga ɗaki yana ɗan taimaka ma ta domin bata iya tafiya sosai. “Mene ne ya faru kike mana wannan kira?.” Yâ tâ ce ta yi ma ta tambayar lokacin da suka ƙari sa fitowa daga ita har Ali basu lura da Abyaz dake tsaye ba. “Mamman!.” Ayusherh ta faɗa tana yi musu nuni da saitin da Abyaz yake. Cikin rashin fahimta suke dubanta jin sunan da ta kira, kafin su kai dubansu ga saitin da take nunawan, Yâ tâ faɗi take. “Ke ƴar nan me kika sha yau kuma da Mamman kika tuna Allah Sarki maragayi...” Sauran maganar nata ya maƙale a harshen ta sakamakon fuskar wannan saurayin da ta gani. Shi Ali ba wani wayo ne da shi ba, saboda haka bai wani tsorata ba amma jikinsa rawa yake saboda yasan dai wanda ya mutu baya dawowa, amma yau gashi ƙiri-ƙiri rana tsaka Mamman ya dawo kuma dariya ma yake yi musu. Yadda kasan mazari haka jikin Yâ tâ ya ɗauki rawa, bakinta ma kansa rawa yake yi na tsaban tashin hankali da tsoro, kawai sai ta saka kuka ta fara goge hawaye jikinta bai bar rawa ba ta kama salati kan ta kai wancan ta saki ta ɗauki wani faɗi take. “Allahumma Anta.. La'ilahaillah..” Sai kuma ta saki ƙara tana kiran Fatalwa. Dai dai lokacin ita na Yayankaka ta fito daga bayan gida, sakamakon sunanta da taji Yayartasu Ayusherh na kira. Sai a lokacin Ali ya sama damar motsa wa ai kuwa ɗaki ya nufa direct yayin da Yayankaka ta mara masa baya dan a ɗan taƙin ta fahimci abin da yake faruwa, haba sai ga Yâ tâ ta taka ƙafarta wurin gudu a ka shiga tsere na neman wurin ɓuya tsakanin ita da su Ali. Ɗaki suka faɗa tare da garƙamo ƙofar katakon garam. Sakin baki Ayusherh ta yi tana kallon ikon Allah. “To mene ne abin tsoron kuma?.” Ta tambayi kanta sai dai babu mai bata amsa. Shi kuwa Abyaz tsananin mamaki ne ya hana shi motsawa, sai kuma ganin reacted na mutanen gidan ya saka shi darawa, domin abin nasu ba ƙaramin dariya ya ba shi ba. Briefly dai ya fahimci kama yake yi da wani ɗan uwansu wanda ya mutu, shi ne ganinsa a yanzu da irin fuskar ɗan uwan nasu ya firgita su, sai dai yana mamakin yadda ita wannan Yarinyar dajin ko'a jikinta, ba wani tsoro a tare da ita. Dariyar da yake yi ne ya dawo da Ayusherh cikin hayyacinta. Ta dubesa a kufule, dama dab suke da juna, ai kuwa a harzuƙe ta kai masa kyakkyawan naushi a ciki. Ai kuwa ya yi ƙasa yana riƙe ciki dan ba ƙarya yaji zafi kuma shammatarsa ta yi. Ƙari sawa bakin ƙofar ɗakin da suka shiga Ayusherh ta yi, cikin kwantar da murya ta fara faɗin. “Yâ tâ, Ali, Yayankaka, Dan Allah ku fito mana, wannan fa ba Mamman ba ne wani ne fa dan shi daga birni ma ya zo yace ma sunansa Ab... Aby..” Ganin ta kasa ƙari sawa ne. Ya sa Abyaz ƙari sa ma ta da faɗin. “Abyaz.” “E Abyaz sunansa dan Allah ku bar jin tsoron nan ku fito.” Duk yadda Ayusherh taso ta lallaɓasu su fito abin ya cutura, sai ma ce ma ta Yâ tâ da ta yi. “Ƴar nan ki barmu kawai muddun ba ce mana kikayi ya tafi ba to fa ba inda zamu fito, kema ina mai baki shawara da ki yi gaggawan neman wurin ɓuya, ki a je wannan taurin zuciyar a gefe domin ba'a nunawa Fatalwa da aljanu wannan in ba haka ba labari ya sauya.” Ɗan tausayi tsohuwar ta bawa Abyaz jin yadda take maganar da alama har lokacin a firgice take. Ƙari sawa wurin ƙofar shiga ya yi, sannan ya fara magana da faɗin. “Grannny ki fito nayi miki bayani ba Fatalwa ba ne, ni mutum ne sunana Abyaz kuma ba zan cutar daku ba.” Ai kuwa a maimakon jin kalamansa ya saka tsoron dake tare da su ya ragu, ai sai ƙara firgicewa da suka yi musamman ma yaran. “Ƙaryar yaudara...” Yâ tâ ta faɗa tana shirin afkawa ƙarƙashin gadon ta mai rumfa. A fusace Ayusherh ta juya garesa, ta kamo kwalar nasa ta yi waje. Domin ta fahimci muddun ba gidan ya bari ba to fa babu wani irin lallashi da zai sa su Yâ tâ su fito. “Da alama ke jaruma ce sai dai kina da zafin kai...” Abyaz ya faɗa dai dai lokacin da ta yo waje da shi tare da sakin kwalar nasa ta juya zata koma gida. Sai dai maganarsa ta dakatar da ita. A hankali ta juya tare da yi masa duba ɗaya ta watsar tana shirin tafiya ne ta ji amon wata murya a gefensu tana faɗin. “Alhamdulillah My Son, ashe ba ɓata kayi ba, baka ga yadda hankulanmu ni da Daddynka ba yadda ya tashi ganin mun nemeka an rasa.” Matar da duba ɗaya zakayi ma ta kasan cewa cikakkiyar ƴar gayu ce kuma wayyayyiya da boko ya gama ratsa ta ga Naira, ita ke wannan maganar yayin da ta ƙari sa wurin Abyaz tare da rungumo sa tana goge kwalla dan ba ƙarya hankalinta ya matuƙar tashi da basu gansa ba, tana son yaronta da yake ɗaya tilo a gare su ita kanta batasan adadin son da take yi masa ba. “Ayusherh.” Ayusherh da ta saki baki tana kallon ikon Allah taji an kira sunanta juyawa ta yi cikin sakin murmushi dan Muryar ta zauna a kunnenta. “Na'am Tata..” Ayusherh ta amsa tana duban Tatan nata sai kuma idanunta ya sauka a kan Mutumin dake tare da shi, da yake sanye cikin suit Black da suka yi bala'in karɓarsa, kamanni sosai taga mutumin yake yi da Abyaz, kuma hakan ya matuƙar bata mamaki ta tabbata dai wannan ba shi ne Mamman ɗin ta ba. “Mom, Dad! Wannan ita ce Ayusherh kuma ita ce ta taimaka min domin makuwa nayi.” Cewar Abyaz da sauri Ayusherh ta dubesa shi kuwa ya sakar ma ta murmushi, sai taji ba daɗi na abin da ta yi masa. Alama ta yi masa da ya yi haƙuri, tana ɗan rau da ido. Dariya ma taso basa, amma sai ya girgiza ma ta kai alamar ba komai, Ayusherh ta yi murmushi. “Amma na gode miki sosai Yarinyata Ayusherh Allah ya yi miki Albarka.” Cewar Matar da Ayusherh taji Abyaz ya kira da Mom, kuma ta fahimci Mahaifiyarsa ce. Shima Mahaifin godiya ya yi ma ta, ita dai Ayusherh tana tsaye. Tata ne ya ce. “To Alhaji muje na nuna muku masaukin naku. Zuwa kafin a gama gyara motar taku Moddibo ya kawo muku.” Amsa wa suka yi sannan suka yi gaba, ganin haka ita ma Ayusherh tabi bayansu saboda Tata ɗin ta. Sun ɗan yi nisa da tafiyar Abyaz da ya lura tana bin su, ya ɗan yo baya suna jerawa tare da ita. “Ɗazu kin yi tambaya a kan me ya sa nake kama da Brother naki da ya mutu ba?.” Kallon sa Ayusherh ta yi ba kuma tare da ta dakata da tafiyar ba. Sai dai batace komai ba. Bai damu ba, ya ci gaba da faɗin. “Doppelganger! Ta yiwu shi ɗin Doppelganger na ne.” Ayusherh ta ce. “Mene ne shi wannan abun.” Ta tambaya dan ba za ta iya maimaita kalmar ba. “Idan ya kasance an sama wani mutum da yake Rayuwa a wani wurin kuma a ka ƙara samun wani mai tsananin kamanni da shi wanda shima Rayuwa yake yi a wani wurin daban, kuma basu haɗa duk wata alaƙa ta jini ba, hasali ma ba yarensu ɗaya ba, ba kuma ƙasa ɗaya suke ba, ya kasance kowannen su a mabanbantan sassa na duniya yake Rayuwa. Wannan shi a ke kira da Doppelganger.” Jinjina kai Ayusherh ta yi cikin fahimta da kalamansa, sai a lokacin ta yi masa kallon nutsuwa. Shi wannan Abyaz ɗin ya kasance kyakkyawa ne ajin farko ga fatarsa da take jajur, dogo ne, bashi da jikin mara, sannan ya yi shiga ne in casually, Graphic T-shirt da kuma Fitted Jean's ya ɗaura Hoodie na gayu saman T-shirt ɗin, yayin da ƙafafunsa ke rufe cikin wasu expensive sneakers, a kansa kuwa wata Baseball cap ce da ya saka a wani karkace, ga wani expensive wrist dake hannunsa kana ganinsa dai kaga Cikakken wayayye kuma ɗan gayu da yake bawa gayu haƙƙinsa. Wani irin ƙamshi mai daɗi yake fitarwa. Ayusherh ta ɗan lumshe ido bayan ta gama ƙare masa kallo a sace, bata san me ya hanata ganin wannan kyan nasa a ɗazu ba. “Ya ne Yarinyar daji?.” Maganar da ya yi ne ya sa ta dubesa, ta ɗan harare sa. A taƙaice dai wannan shi ne dalilin haɗuwar Abyaz da Ayusherh. Mahaifin Abyaz ya kasance Silviculturist ne wato dai Ma'aikacin gwamnati mai kula da Daji da mutanen cikinsa har ma da ci gaban dajin, to wannan karon aikinsa ne ya biyo ta ƙauyen Mayo-Danay sati guda zai yi shi ya sa ya taho familynsa domin su ne suka buƙaci hakan, domin Abyaz cewa ya yi ai suma sa buɗe ido a dajin. WANNAN KE NAN Kwanakin da suka biyo baya sun kasance Unforgettable ne a wurin Ayusherh, domin tun bata biye wa Abyaz amma nacinsa a gare ta ya sa ta saki jiki sosai da shi, har wasu ranakun take raka sa cikin ƙauyen ta zagaya da shi ko kuma su shiga daji ta yi ta nuna masa abubuwa iri iri, a wannan taƙin ne ya fahimce ta da kuma gaba ɗaya Rayuwarta a yadda ya fahimta mahaifinta wato Tata yana da wani kyakkyawan buri a kanta da yakeso ta cimma a Rayuwarta. Duba da yadda a duk ranakun duniya yake ware lokaci sau biyu a rana da safe da kuma yammaci yake bata horo na musamman. Abin yana matuƙar ɗaurewa Abyaz kai ganin yadda Tata ya iya bada horo tamkar a makarantar sojoji ko ƴan sanda, bai ƙara shan mamaki ba sai ganin kwarewar Yarinyar ƙwaƙwalwarta yana matuƙar ja, kuma gefe guda ta nace sai ya koya ma ta yaren da yake yawan yi wato Turanci, to a hakan yake koya ma ta ƙananan abubuwan da ba'a rasa ba, kuma dalilin hakan ya gano Burin Mahaifin nata a kan ta na zama Soja. A yadda ya fahimta kamar ita hakan bai kwanta ma ta ba, saboda tana ganin ba zata iya ba. Amma da dabara Abyaz yake cusa ma ta ƙaunar abin a ranta har yake faɗa ma ta cewar ta hanyar zama sojan ne kawai zata iya kawo ƙarshen irin azzaluman ƴan ta'addan da suka kai farmaki ƙauyensu, ya ƙara da faɗin gata kuma jaruma ta musamman zama soja ba zai ma ta wahala ba, da irin waɗan nan kalaman Abyaz ya yi amfani wurin taimakawa Tata a kan shawo kan Ayusherh ai kuwa nan da nan kwadayin zama Soja ya shiga ranta, ta ƙara mayar da hankali a kan koyon training iri iri da Tata yake koya ma ta, hatta shi Abyaz ba'a barsa a baya ba, sai dai Ayusherh bata tsayawa idan ma ya ce shi zai yi ma ta training ɗin a cewarta ba abin da ya sani dangane da harkar. Shi kam Abyaz sai dai ya yi dariya. Abin da Ayusherh bata sani ba shi ne Abyaz yana karatu ne a makarantar sojoji a ƙasar waje. Yanzun ma hutu ya dawo shi ne dalilin da ya sa shi da Mom ɗin sa suka biyo Dad ɗin sa wannan tafiyar na aiki. Cikin kwanaki bakwai kacal wata iriyar shaƙuwa ce mai tsafta da ban mamaki ta shiga tsakanin Ayusherh da Abyaz. Ta gefe guda kuwa tuni Abyaz ya gama magana da Dad ɗin sa a inda ya roƙe sa da a saka Ayusherh a makarantar sojoji domin ta hakan ne kawai Burin Mahaifinta zai cika. Ya roƙi hakan ne bayan ya basa labarin Ayusherh. To da yake Mahaifin nasa Mutumin Kirki ne ba ɓata lokaci ya sama Tata da maganar har yake sanar da shi ya nema wa Ayusherh gurbin shiga makarantar sojoji dake Abuja, zuwan da zai yi gaba tare zasu tafi gaba ɗaya saboda suga Makarantar ita kuma Ayusherh ta fara karatu. Tsaban farin ciki Tata har yana hawaye dama burinsa ke nan ganin ya saka Ayusherh a makarantar sojoji, ai kuwa ya yi ta zuba wa Mahaifin Abyaz godiya tamkar bakinsa zai kasu. A yau ne kuma sati ta cika da zuwansu Abyaz ƙauyen Mayo-Danay kuma a yau ɗin sun gama shirya wa tsaf domin komawa inda suka fito. An gama shigar da komai nasu a mota, hatta Mom da Dad sun shiga Abyaz kawai suke jira. A hankali suke takawa domin ƙari sawa motar kana ganin idon Ayusherh zaka fahimci ta zubar da hawaye karo na biyu ke nan tun da ta yi wayo da ta yi kuka, na farko dai a dalilin rasuwar Mamman ɗin ta na biyu kuma shi ne yanzu saboda Abyaz da suka yi mugun sabo zai koma. A hakan ma ya samu da kyar ya lallasheta ta haƙura ta dena kukan, shi ne ya samu zata rako sa wurin motar. Handkerchief ɗin mai kyau da yake fitar da ƙamshi mai sanyi ya ciro a trouser pocket ɗin sa, tare da miƙa ma ta yana faɗin. “Take it. Ki goge hawayen, kina ta damuwa tamkar an ce miki mutuwa zan yi, ko kin manta nayi miki alƙawari ne a kan kina shiga Military School nima zan tattaro karatuna na dawo Nigeria mu ci gaba tare ko kin manta hakan ne?.” Girgiza kai Ayusherh ta yi bata ce komai ba. Ya ɗan sosa ƙeya lokacin da suka ƙari sa dai dai wurin motar sannan ya dakata da tafiyar tare da dubanta ya ce. “In sha Allah, one day your dreams will come true...”💖 “Sankiyu.” (Thank you.) Shi ne abin da Ayusherh ta iya faɗa, ya yi ma ta kyakkyawar murmushi tare da shiga back seat na motar ya zauna. Wannan shi ne maganar su ta ƙarshe kafin suka yi sallama a ka tada motar suka fara tafiya. Ayusherh da Tata dama Ali sai kuma wani mutumi wato mai gari na ƙauyen da kuma wani matashi a tare da shi suna nan tsaye har motar ta ɓacewa ganin su. Gida su Tata suka koma Ayusherh tanajin gaba ɗaya kewa ya rufe ta yadda kasan sun yi Shekaru da sanin juna ita da Abyaz. UNEXPECTED HAPPENED!!!. A yammacin Ranar labari ya isa ga ɗaukakin mutanen ƙauyen na wani hatsari da ya afku da Ahalin da suka baro ƙauyen a safiyar Ranar. Lamarin shi ne sun yi wani mummunar hatsari kuma gaba ɗaya sun rasa ransu sakamakon ƙonewa ƙurmus da motar ta yi. “Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un...” Wannan shi ne kalmar da Ayusherh ta iya faɗa lokacin da taji labarin kafin ta zube ƙasa a sume. Sosai Ayusherh ta shiga cikin tsananin ruɗu da tashin hankali da kuma damuwa na faruwar wannan al'amari da hakan sai da ya kaita ga ciwo sosai, domin ta matuƙar saka damuwa a ranta. Sai da a ka shafe tsawon wata guda da faruwar hakan sannan a ka samu ta fara dawowa dai dai. A wannan taƙin ne kuma saƙo daga birni ya zo ma Tata daga hukumar Makarantar da Mahaifin Abyaz ya nema wa Ayusherh. Ashe tun kafin barinsu garin ya yi ma ta komai da komai ta fara zuwa kawai ya rage. Shi ne yanzu suka sama noticing daga hukumar Makarantar a kan lokacin fara zuwanta ya yi hakan kuma ya yi dai dai da aikin Driving da Tata ya samu a birnin cikin garin Abuja. A wani Company. Sun kuwa yi farin ciki sosai da wannan al'amarin, kuma sun ƙara yima iyayen Abyaz da shi kansa addu'a sosai a kan yadda suke yi dan basu manta da su ba, dama sauran ƴan uwansu da a ka kashe, nan da nan kuwa suka fara shirin komawa birni. Sai dai fa Ayusherh ta ce ita ba inda zata. Lallashin Duniyar nan Ayusherh taƙi. Sai da Tata a karo na farko da ya yi ma ta jan ido sannan suka samu lokacin da za su tafi ta bisu. A can Birnin ma sai da suka haɗa da tuna ma ta da burin shima Abyaz ɗin ke nan ta zama Sojan, idan ta ce ba zata je makarantar ba, batayi masa adalci ba. To fa da irin waɗan nan kalamai ne suka samu Ayusherh ta dawo musu dai dai kuma cikin ikon Allah ta fara zuwa tsadaddiyar makarantar ta Royal Military Academy, Abuja. BAYAN WASU SHEKARU! .......❤‍🔥 *_AYUSHERH! TA GIRMA 💃 TSAMMACI ABIN DA BA'AI TSAMMANI BA!!🔥_* .......🪄 •… 💕 *CAPTAIN AYUSHERH*🥷 * 🍂🎀 (_The ShieldMaiden._) BY - Nainarh KD.... 𝒩𝓀𝒹'𝓈❦♡ Episode 8. *_AYUSHERH! TA GIRMA 💃 TSAMMACI ABIN DA BA'AI TSAMMANI BA!!🔥_* .. BAYAN WASU SHEKARU! *Aguyi-Ironsi Barracks Cantonment ¹, Asokoro, Abuja.* Kyakkyawar budurwa ce doguwa da tsayinta yake dai dai misali. Tana da dara-daran idanu masu ɗaukar hankali launin meadow green, sai zuba shining suke daga cikin white eye glasses dake maƙale a idanunta da take ɗan lumshewa a hankali tare da buɗe wa. Hancinta dogo ɗan dai-dai da ya zauna kuma ya yi dai-dai da madaidaiciyar kyakkyawar fuskarta. A hankali laɓɓanta mai launi biyu, daga sama ɗan dark-dark yayin da daga ƙasa yake flash pink. Suke ɗan motsawa. Tsaye take kuma ta yi dress in Combat Uniform na female soldier. Shirt: Khaki-colored, short-sleeved shirt. Sai Jacket: Khaki-colored, lightweight jacket with epaulets. Sai kuma Trouser: Khaki-colored, combat-style trousers. Tana sanye da Black combat boots. A ƙafafunta. Tsaye take a tsakiyar Barrack ɗin cikin wannan shigar. Gyara Peak Cap dake a kanta ta yi sannan ta kai hannu cikin trouser pocket nata ta ciro wani farin Handkerchief mai kyau dake fitar da daddaɗan ƙamshi, riƙe Handkerchief ɗin ta yi tare da zuba masa ido tana tuna abubuwa da dama, a koda yaushe idan taga Handkerchief ɗin nan mutane biyu masu matuƙar muhimmanci a rayuwarta da ƙaddara ta yi sanadiyar rabuwar su na har abada take tunawa. Mman ɗin ta da kuma Abyaz. Murmushi ta yi kana ta fara magana cikin cool voice ɗin ta kuma idanunta a kan Handkerchief ɗin. “My Mman and Abyaz ɗina, Naso ace both of you kuna raye domin tayani murnar ganin wannan Ranar da zan fara aiki a matsayin Nigerian Army kuma ta musamman, bayan shafe shekaru cikin gwagwarmaya da karatu mai zafi tare da koyon training kala-kala da fuskantar ƙalubale ba adadi, kuma duka na jure har Allah ya nufa na kammala karatuna gaba ɗaya a Military School. Kun san mene ne ya faru daga nan?.” Ta yi tambayar sannan ta ɗan yi shiru kamar wacca take jiran amsa, sai kuma ta ci gaba da faɗin. “Potential path to consider na bi, wurin yin Apply for specialized training programs, na tsawon watanni, daga nan kuma bayan wasu watanni na gama cikewa tare da kai ga duk wasu sharuɗa na zama Soja. Briefly dai na zama cikakkiyar Soja da a tashin farko na sama muƙamin Captain bisa ga jajircewata.” Ta kai maganar in proud tana ɗa ga kai. Ɗan shuke bakinta ta yi, tana ci gaba da faɗin. “Gashi kuma yau gani tsaye a tsakiyar Barrack ɗin mu a matsayin cikakkiyar Captain kuma ta musamman, kamar yadda nayi rantsuwa a baya domin kare ƙasata da kuma aiki bisa gaskiya da jajircewa, to yanzu ma zan ƙara yi muku. Mamman Mman ɗina nayi maka Alƙawari a kan mayar da hankali wurin aiki da gaskiya domin kawo ƙarshen ira-iren ƴan ta'adda da suka kai farmaki ƙauyenmu har suka zama sila na rabuwar mu ta har abada!. Abyaz ɗin Ayusherh my friend, bestie, souvenir and everything nayi matuƙar kewarka irin sosai sosai ɗin nan har yanzu zuciyata ta kasa yarda a kan cewar ka mutu a wancan hatsarin sai dai yarda da hakan ya zama dole a gareni...” Ta ɗan ja ajiyar zuciya tare da yi ma Handkerchief ɗin kyakkyawar sumba tana ɗan lumshe ido. Haƙiƙa taso Mman tun batasan mene ne so ba, daga baya ta rasa shi, sai kuma ga Abyaz ya shigo Rayuwarta na ɗan lokaci bayan ta tabbatar ta rasa Mman ɗinta na har abada, shima Abyaz ɗin kuma tazo ta rasa shi by accident. Bayan rasa waɗan nan mutane masu daraja da Muhimmanci a Rayuwarta batajin zata sama wani wanda zai maye gurbinsu koma ya kai. Sannan bayan so da ta yi ma kowannensu kuma tazo ta rasa su bata tunanin akwai wani mahaluki kuma da zata iya ƙara so duk da batasan mene ne ƙaddara ta tanadar ba, sai dai koma mene ne batajin akwai sauran gurbi na son wani a zuciyarta. “Ke nan har abada a haka zaki ci gaba da kasancewa As a single?.” Wani ɓangare na zuciyarta ya jefo ma ta tambayar da ya saka ta buɗe ido da sauri cikin son lalubo amsar. Dai dai lokacin kuma wata soldier dake sanye cikin uniform ta ƙari so wurin da ɗan gudu-gudu tare da tsayawa tana kallon Ayusherh kamar yadda ita ma Ayusherh ta zuba ma ta ido ba tare da ta ce komai ba. “Jasmine Jasmir.” Ayusherh ta karanta sunan dake gaban rigar jikin Budurwar. Sai dai kafin ta ce wani abu ta jiyo sautin Muryar budurwar tana faɗin. “Hello! i am Jasmine Jasmir, Second Lieutenant (2LT) yau ce rana ta ta farko a aiki.” Ta yi maganar tana miƙa ma Ayusherh hannu kuma fuskarta ɗauke da ƙayataccen murmushi mai bayyana haƙora. Ita ma Ayusherh ta miƙa ma ta nata Hannun tana amsa ma ta da faɗin. “Hello! I am Ayusherh Tata, Captain (CAPT), ranar farko a aiki.” Murmushin Soldier ɗin mai suna Jasmine ya faɗaɗa, tana duban three star's dake jikin rigar Ayusherh ta shouldernta sannan ta ce. “Woww Babban muƙami haka tare da kyakkyawar soldier kamar ki, gaskiya hakan ya yi 100%.” Ta kai maganar tana haɗe yatsarta manuniya da kuma Babbar. Ɗan murmushi ta yi kana ta ce. “Thanks.” Jasmine ta ce. “Nevermind Dear, can we be friends?.” Ayusherh ta ɗan ƙara girman idanunta tana faɗin. “Why not.” Cikin murna kamar ba Soja ba Jasmine ta ce. “Many thanks Captain, daga yanzu mun zama abokai, nayi farin ciki da hakan, sannan naji daɗin haɗu wa dake dan nasan zan ƙaru sosai dan na fahimci kina da kirki.” Ayusherh tana ƴar dariya ta ce. “Ooo ke nan ke bashi da shi Kirkin?.” Jasmine ta ɗan zaro tana faɗin. “I have no word Captain Kawai ko ma ina da shi ko babu a ƙawancen mu zaki gane.” “Good.” cewar Ayusherh sannan ta ƙara da faɗin. “Ofishin General nake nema ko zaki iya nunamin?.” “Laaa ai nima ɗin can na nufa, muje kawai.” Jasmine ta amsa ma ta da faɗin hakan sannan suka nufa hanyar da Jasmine ta nuna suna fira Jasmine sai fira take zuba ma ta kamar dai ba Soja ba, sai ta zama kamar wata ƴar gidan radiyo a wurin Ayusherh a ɗan wannan taƙin. Fitowa suka yi daga elevator da suka hau dai dai Ayusherh ta sawo kai domin fita taci karo da soldier ɗin dake ƙoƙarin shiga elevator ɗin ita ma sanye cikin Uniform sai dai ya babanta da nasu. “Am so sorry...” Matar ta kasa ƙari sa maganar da ta ɗauko sakamakon ɗa gowa da Ayusherh ta yi tana dubanta, su kayi ido huɗu. “Sorry ban lura ba ne.” Ayusherh ta faɗa ganin yadda Matar ta zuba ma ta ido. “Kece Aysherh ko? Ahm ina nufin Captain da zata fara aiki a yau?.” Matar ta tambaya cikin murmushi. Da sauri Ayusherh da Jasmine suka kalla juna bayan kowannen su ya ga sunan dake jikin rigar soldier ɗin tare kuma da muƙamin ta. Cikin girmamawa Ayusherh ta ce. “Yes Sir! Dama office ɗin ki muka nufo tare da Jasmine.” (Kun dai san Sojoji mata ba'a kiransu da Ma ko kuma Madam a wurin aiki ba, sai dai Sir...😃) “Okay, Follow me.” General Lamrat Jabir Junaid ta yi maganar tana juyawa bayan taji abin da Ayusherh ta faɗa. Kallon juna Ayusherh da Jasmine suka yi sai kuma a tare suka saki dariya mara sauti kowaccensu tana toshe baki. Cikin raɗa-raɗa Jasmine ta ce. “Da alama ba mai zafin kai ba ce.” Murmushi Ayusherh ta yi, bata ce komai ba sakamakon office ɗin General ɗin da suka ƙari sa, ta nuna musu wuri suka zauna bayan ta zauna. Dama da jimawa file ɗin Ayusherh ya isa gareta matsayinta Na General kuma hasali ma sune suka buƙaci Ayusherh ta yi aiki a Barrack ɗin nasu sakamakon jarumtarta da suke samun labari akai. Kafin yau basu taɓa haɗuwa da Ayusherh ba. Iyakar saninta da General ta yi, shi ne a photo, to sai ashe ganinta a zahiri ya fi jin labarin ta. Sosai General ta ƙara yi musu bayani akan aikin yadda zasu fahimta duk da sun yi training na watanni sai dai ta ƙara musu da nata bayanin da kuma jan hankali. Bayan nan da kanta ta kai Ayusherh office ɗin dayake mallakin Ayusherhn matsayin ta na Captain yayin da Jasmine da take da muƙamin Second Lieutenant zata ke aiki a ƙarƙashin ta da kuma sauran Jami'an sojojin da General ta ce zuwa gobe kowa zai hallara gabanta domin ta sansu. Daga haka ta bar office ɗin Ayusherhn zuwa nata. Ai kuwa kamar jira suke ta fita Ayusherh da Jasmine suka rungume juna suna sakin ihun murna. Sai kuma Jasmine ta ja baya da sauri tana faɗin. “Sorry Captain.” Ta faɗa, tuna cewa Ayusherh a samanta take. A karo na farko Ayusherh ta yi Murmushi mai bayyana haƙora tana maimaita abin da Jasmine ta faɗa cikin magana da hanci da hakan ya sa Jasmine darawa tana faɗin. “Atoh gudu nake kar nayi wani laifi a rana ta ta farko a aiki, shi ya sa amma ai muna barin wurin aiki zamu ci gaba da kasancewa ƙawaye yayin da a ka dawo fagen aiki kuma ke ɗin ta gaba dani ce kuma ina girmama hakan.” Girgiza kai Ayusherh ta yi tana ɗan zura hannu a aljihu ta ƙari sa wurin da kujerar zamanta take, ɗan dafa kujerar ta yi da hannu guda tana fuskantar Jasmine ta ce. “Wai bakyajin wani proud haka dai kasancewar yau ce ranar ki ta farko a aiki?.” Ta yi ma ta tambayar tana kallon ta fuskarta da ɗan murmushi, sai dai ganin yadda lokaci guda fuskar Jasmine ya sauya daga murmushi zuwa yanayin Alhini ya sa ta ce. “Sorry in bakiji daɗin tambayar da nayi miki ba.” Ayusherh ta faɗa tana ƙari sawa wurin Jasmine ɗin tare da dafa kafaɗarta. Girgiza kai Jasmine ta yi tana faɗin. “A'a ba maganar ki ba ce ta sakani a wannan yanayin, kawai wani abu na tuno.” “Ayya. Sorry, kiyi haƙuri in sha Allah koma mene ke damunki zaki sama mafita da yardar Allah.” Thanks kawai Jasmine ta iya faɗa, tana tuna yadda iyayenta basu goya bayanta a kan burinta na son zama Soja ba. Hatta yau bayan ta shirya da ta zo yi musu sallama. Mom ɗin ta sai cewa ta yi. _“Jasmine kije kiyi aikin da kika zaɓarwa kanki, amma ki sa ni kar daga ƙarshe ki dawo gareni da kuka, na faɗa miki.”_ Ajiyar zuciya Jasmine ta sauke. Sai kuma ta yi murmushi tana faɗin. “Ya kamata mu a je photo na tarihi a ranar mu ta farko a aiki.” Ta faɗa tana ciro wayarta, ta shiga yi musu pictures ita da Ayusherh da ta biye ma ta suna ta yi cikin nishaɗi, har shi kansa office ɗin Jasmine bata kyale ba shima sai da ta ɗauke shi hotuna iri -iri Ayusherh sai dariya take ma ta tana faɗin. “Ni kam da ace bada Uniform na sojoji na ganki ba, to fa kai tsaye da ma'aikaciyar gidan rediyo zan kiraki.” Dariya kawai Jasmine ta yi tana faɗin. “Kamar kuwa kin sa ni. Burin Mom ɗina ke nan zama Hakan sai dai na wa burin ya sha banban da nata, ah to ya ta iya ta haɗu da ƴar zamani, bata sama cika burinta ba a kai na. Hummp a ƙarni na ashirin da huɗu fa muke normally, da hakan zamani ya zo dole muma bimu a jera da mu, but a cikin ƴaƴana zan yi ƙoƙari ɗaya ta cika ma ta Burin...”😅 Gaba suka yi dariya. A kusan haka kusa ƙarar da wannan taƙin. Kafin suka sama sanarwa na Meeting da General ta haɗa ga sabbin sojoji, sannan ne suka bar office ɗin domin halartar taron.....FOLLOW MY ACCOUNT NKDS @ AREWABOOKS APP. •… 💕 *CAPTAIN AYUSHERH*🥷 * 🍂🎀 (_The ShieldMaiden._) https://whatsapp.com/channel/0029VaEZtE15a2429vfcpf20 BY - Nainarh KD.... 𝒩𝓀𝒹'𝓈❦♡ Nainarhkd3 @Wattpad. Perfectly Pen's 🖊️ Episode 9. *National Muslim Orphanage, Plot 135, Cadastral Zone B02, Wuse II, Abuja.* Wata farar mota ce ƙirar Mercedes-AMG One, ta ƙari sa dai dai ƙofar Gate na Orphanage ɗin sannan budurwar dake driving ta paker motar a ɗan gefe kaɗan da Gate ɗin. Buɗe Handbag ɗin ta dake a je a gefe ta yi tare da ciro Wayarta ƙirar Huawei P40 Pro (Porsche Design) gyara zaman white medicated glass dake maƙale a idanunta ta yi, sannan ta lalubo wata lamba da a ka yi saving da emoji alamar. Protest, Power. (✊) Sannan ta danna kira, ringing ɗaya a na biyun ne kuma a ka katse kiran ta can ba tare da an ɗauka ba. Girgiza kai kurum ta yi domin inda sabo ya ci a ce ta saba da halinsa, wannan kaɗan ke nan daga ɗabi'arsa. A hankali laɓɓanta suka furta. “Arham! Sometimes you're protest but you're the G.o.a.t (The greatest of all the time!) for me and everyone.” Bata ƙara sakan biyar a hakan ba, a ka buɗe ƙaramar ƙofar Gate na Orphanage ɗin kafin wani dogo fari kyawawan Matashi ya bayyana, tafiya ya fara domin ƙari sawa wurin motar, yayin da Budurwar ta zuba masa idanu zuciyarta na ƙoƙarin kai ta ga wani tunani daban. Yes!! Arham kyakkyawa ne irin ajin farko ɗin nan babu Mace mai ji da kanta da zata gansa ba tare da ta kyasa ba, yana da tsayi wanda ya yi dai dai da yanayin jikinsa da ba rama ko kaɗan kuma ƙibarsa bai yi yawa ba, jikin nasa a murɗe kai da gani kasan ana bawa jikin kulawa da ta dace ta hanyar Gyming da sauran abubuwa na motsa jiki. Kwankwasa Glass na motar da ya yi bayan ya ƙari so, shi ne dalilin katsewar tunanin nata. Dubansa ta yi tare da buɗe gaban motar, ta gefanta, shiga ya yi ya zauna ba tare da ya kalle ta ba sai wani ciccin magani yake. Dariya ya bata, amma ta gimtse, ta ɗan saci kallon sa sannan ta kira sunanta tare da ci gaba da faɗin. “Arham Bro Me! Fushi kake dani ne wai?.” Ta yi masa tambayar tana kafesa da kyakkyawan idanunta dake cikin Glass. Huci ya furzar yana shafa sumar kansa mai ɗan yawa, ba tare da ya dubeta ba ya ce. “Haka na faɗa miki?.” Girgiza kai ta yi sannan ta ce. “Sam a'a, sai dai hakan na fahimta.” “Ba fushi nake ba.” “To tun da haka ne kayi dariya mai bayyana haƙora na gani.” Ta faɗa tana harɗe hannu a ƙirji tare da kafesa da ido, duk da tasan abin da ta faɗa ɗin bamai yiwuwa ba ne indai Arham ne. A karo na farko tun shigarsa motar ya dubeta ita ma shi ɗin take kallo. A hankali fuskarsa dake murtuke ta fara sauyawa yayin da simple murmushi ya bayyana. “Hakan ya miki?.” Ya tambaya tana mayar da fuskar yadda take a fari. Dariya take ta danne wa, ta daure ta ce. “Sam bai yi ba.” Wage ma ta baki ya yi dukkanin haƙoransa thirty two suka bayyana. A hakan ya ce da ita. “To haka ya yi.” Ya yi maganar muryarsa a sama kuma ta fito wata iri sakamakon bakinsa dake a buɗe. Gaba ɗaya suka saka dariya. Sai da ta nutsu sannan ta tada motar suka ɗau hanya, kana ya ce faɗin. “Kin iso lafiya?.” Idanunta na kallon titi ta amsa masa da faɗin. “Lafiya Qlau. Fatan na sameka lafiya?.” “Alhamdullilah..” A cewarsa. Shiru ya ɗan biyo baya. Sanin da ta riga ta yi muddun ta biye ta nashi sai dai su ci gaba da kasancewa zaman shiru a motar ne ya sa ta ce. “Allah ya sa ka fito da duka takardun da za'a nema?.” “Uhump.” Ya faɗa. Ita kuma ta jinjina kai, ta ƙara da faɗin. “Please Bro ka daure karka bani kunya a wannan karon ka nutsu ka amsa duka tambayoyin da za'ayi maka a yayin gudanar da interview ɗin kaji?.” Ta ƙarishe maganar tare da ɗan dubansa kaɗan. Murmushi ya saki yana amsa ma ta da faɗin. “To Mama, what next?.” Ɓata fuska ta yi. “I'm serious fa, kaga kusan companies biyar ke nan a ke nema maka aiki, amma zafin rai yake sa ka ka saka bada haɗin kai tun a wurin interview. Dan Allah ka daure kayi zuciya a wannan karon na shida ka basu haɗin kai wurin gudanar da interview ko dan na dena maka gori.” Ta kai maganar da ɗan murmushi. “Yusra!..” Ya ɗan ja sunan nata. “Na'amm!..” Ita ma taja wurin amsa wa, ba tare da ta dube inda yake ba, a ƙoƙarinta na kauce wa truck dake tunkaro su. “I Promise zan yi iya kar bakin ƙoƙari na wurin ganin wannan karon ba'a sama matsala ba, nayi miki alƙawari.” Tsaban farin ciki da mamakin kalamansa ya sa Yusra kusan sakin steering motar tana washe baki, da mugun sauri Arham ya kai hannu kan steering tare da kaucewa Truck ɗin da ta kusa yin ciki da su. “Yusra! Kina a hayyacinki kuwa? So kike kija mana mummunar accident ne?.” Ya tambaya murya a ɗa ge. Lokacin da ya yi gefen titi da su tare da tsaida motar idanunsa a kan ta. “Am so sorry Arham amma tsaban farin ciki ne ya sa na kusa sakin steering ba tare da na ankara ba.” “Farin ciki da me?.” “Da kalamanka mana.” Girgiza kai ya yi. “Dawo nan na lura ba zaki iya driving ba.” “Ah ka bar shi kawai ai yanzu ne zan matuƙar iya wa ma kuwa.” Ta yi maganar tana ƙoƙarin tada motar, shi dai bai ƙara cewa komai ba. Yusra ta ja motar suka ƙara hawa titi. Sanin da ta yi ne a kan da wuya ya ƙara magana kuma, hakan ya sa ta kunna. Karatun Alkur'ani mai girma, ta speaker na motar, daddaɗan ƙira'a na matashin Balaraben nan wato Saad Al-Qureshi na tashi cikin Suratul Maryam. *Precise Financial Systems Limited - Plot 1245, Cadastral Zone A05, Maitama, Abuja.* A nutse kowannensu ya fito daga ɓangaren sa bayan Yusra ta shiga da motar a cikin Company ɗin sannan ta yi parking a wurin da a ka tanadar. Ɗan gyaran murya Yusra ta yi, hakan ya sa Arham dubanta. “All the best.” Ta faɗa tana sakar masa murmushi. Jinjina kai ya yi ba tare da ya ce komai ba, ya yi ciki. Yayin da Yusra ta jingina a jikin motar tana kallon makeken ginin zamani skyscraper na companyn. Rurin da Wayarta ta fara alamar shigowar kira ne, ya sa ta ciro wayar tana duba sunan da ya bayyana saman screen na wayar. My Nusra, shi ne sunan da ya bayyana, hakan ya sa ta yi azamar ɗagawa ta kara a kunne tare da buɗe motar ta shiga, zama ta yi tana faɗin. “Ni kam nayi fushi domin an manta dani tun da a ka tafi Dubai.” Ta faɗa tana ɓata fuska tamkar wacca ta kiratan tana a gabanta. Daga ɗayan ɓangaren mai kiran, ta saki murmushi mai sauti sannan ta ce. “Kinji ki ke ma, ban da abin ki kwata kwata yaushe ne Bama tare, 2 days ne fa, kuma ai gashi yanzu na kira.” Yusra ta ɗan gyaɗa kai sannan ta ce. “Ni dai kam duk da haka nayi fushi.” “Kaina bisa wuya, Anty Yusra Tah ayi min afuwa tohm...domin kin san muddun baki dena fushin nan ba to fa ba zan iya ƙara kwana a Dubai ba, Nigeria zan yo direct.” Dariya maganar nata ya bawa Yusra ta dara tana faɗin. “Ah ah ba'ayi haka ba kuwa, tohm shikenan na haƙura, sai dai ina mamaki yau Nusra ɗita ce ta kirani da Anty da alama dai buri ya cika ko nace yana kan cika bani labari.” Ta faɗa tana gyara zama, ai kuwa nan Nusra ta fara bata labarin a kan abin da ya kaita Dubai da irin nasarar da ta samu a kwanaki biyu da ta yi a can. Sun ɗan jima suna wayar kafin daga bisani suka yi sallama. Yusra ta katse kiran tana ɗan murmushi, Allah ya gani tanason twins sister ɗin nata duk da cewar ta kasance wata kalar Mace da ba'a gane gabanta balle bayanta. Fitowa ta sake yi, ta jingina da motar ba tafi minti goma ba ta hango fitowar Arham yana nufota. Tun kafin ya ƙari so take faman washe baki duk da gefe guda na zuciyarta na ɗan harbawa domin batasan tsiyar da ya yi a ciki ba. Takardun dake hannunsa ya miƙa ma ta da sauri ta karɓa ba tare da ta duba ba, ta riƙe a hannun nata yayin da ta zuba masa ido tana jiran ji daga bakinsa. Fuskarsa ba yabo ba fallasa ya dubeta kamar yadda ita ma shi take duba. “S...Su...sun ɗauki Arham a aiki. Ina nufin na sama aiki.” Ya ƙari sawa maganar da ɗan ƙarfi yana sakar ma ta wani murmushi mai burgewa da ya sa ta kusan daskare wa a wurin. Idanunta a kan sa tana ƙoƙarin tariyo abin da taji ya faɗa dan ji take kamar ba dai dai taji ba. Ihu ta fasa tare ta rungumo sa tana faɗin. “Alhamdullilah Amma wallahi naji daɗi sosai...wato shi ne da fari ka rarraba maganar saboda kanason cikina ya ɗuri ruwa ko?.” Ta kai maganar tana sakinsa da ɗan hararar na wasa. Sai kuma a lokacin taji kunyar rungumar da ta yi masa ganin irin kallon da yake ma ta. “Sorry.” Ta faɗa cike da kunya tana buɗe motar ta shiga. Ya ɗan girgiza kai shima sannan ya shiga motar. “Ya kamata muyi kwarkwayar shagali na murnar aikin da ka samu ko?.” Ta tambaya tana kallon sa bayan ta tayar da motar. “A'a ba yanzu ba tukunna ki bani sati ɗaya muga yadda lamarin aikin zai kasance.” Ya faɗa ba tare da ya dubeta ba, idanunsa na kallon mirrorn waje na motar dai dai satin da yakeso dai dai lokacin kuma Baturen dake tsaye gaban wall Glass ɗin dafe da fuskarsa da ta ɗan kumbura ga kuma shatin yatsa alamar ya sha mari ya kai duba ga saitin da suke. Arham ya saki kyakkyawan murmushi yana girgiza kai tare da gyara zama. Yusra ta ja su suka bar Company ɗin. ...🪄💖 Ayusherh bata da ra'ayin zama a Barrack sam kuma Barrack ɗin akwai nisa sosai da Gidansu wannan dalilin ya sa a ka ware ma ta wani Flat home a ɗan gefe da Barrack ɗin kuma a zuba ma ta dukkanin abin buƙata zata zauna a ciki... Ta fara gudanar da aikinta cikin kwarewa da sanin makamar aiki, tun daga ranar ta ta farko. •… 💕 *CAPTAIN AYUSHERH*🥷 * 🍂🎀 (_The ShieldMaiden._) BY - Nainarh KD.... 𝒩𝓀𝒹'𝓈❦♡ Nainarhkd3 @Wattpad. *(🔥P.P✍️)* Episode 10. *No. 20, Kubuwa Road, Gwagwalada Abuja.* Buɗe ƙaramar ƙofar Gate na gidan ta yi bayan fitowarta daga Cab da ya kawo ta Anguwan. Madaidaicin Duplex ne mai kyan tsarin gini gashi ɗan dai dai mai hawa ɗaya, daga ta ciki three bedrooms ne a upstairs da kuma down, sai kuma kitchen da sauran wuraren da ba'a rasa ba, daga waje kuma bayan haɗaɗɗen garden da a ka qawata Duplex ɗin da shi daga gefansa kuma wani madaidaicin swimming pool ne, ga kuma waterfall gunin burgewa a tsakiyar compound na gidan, briefly dai Duplex ɗin duk da madaidaici ne amma fa ya haɗu obaaa. Gidan ya yi shiru tamkar babu kowa hakan kuma ba ƙaramin mamaki ya bata ba domin tasan kafin ta taho ta yi waya Tata har yana sanar ma ta da cewar dukkaninsu suna gida hatta Yayankaka dake makaranta ta dawo. Sannu a hankali take taka ƙafafunta dake rufe cikin Black combat boots. Har ta ƙari sa Entrance na palon, ta ɗan dakata da tafiyar tare da saka wani card ƙofar ta buɗe. Tura kanta ciki ta yi bakinta ɗauke da sallama tana kuma mamakin duhun da palon ya yi gashi shiru sai dai bata gama mamakin ba lokaci guda hasken sparkling mai kaloli blue da red sai yellow ya mamaye palon yayin da gaba ɗaya suka haɗa baki wurin faɗin. “Surprise.” Suna faɗa hakan ya yi dai dai da wasu irin ƙananun ƙyalƙyali suka fara zubawa daga sama suna sauka a dai dai saitin da take, can kuma daga gefe ilahirin mutanen gidan ne tsaytsaye kowannensu fuska ƙayace da kyawawan murmushi yayin da duk suka haɗa baki wurin faɗin. “Muna tayaki murna ta Ranar farko da fara aiki a matsayin soja.” Tsaban mamaki ya sa Ayusherh ta kasa magana ji take maganar ta yi kuka duk wani abu da zai sakata farin ciki Tata ya sanshi. Tahowa wurinta suka fara yi gaba ɗaya, ai bata bari sun ƙari so ba da sassarfa ta ƙari sa wurin Tata tare da shigewa jikinsa tana sakin kuka na farin ciki. Murmushin kowannensu ya faɗaɗa domin muddun a gidan mai cike da farin ciki kake to fa zakasan irin tsaftatacciyar ƙauna dake tsakanin ƴa da uban. Ɗan bubbuga bayanta Tata ya yi cikin dauriya ya ce. “To wannan kukan fa, yau fa Rana ce ta farin ciki a gareki damu Ahalin ki baki ɗaya ko kin manta?.” Ya faɗa bayan ya rabata da jikinsa yana goge ma ta hawayen. Murmushi ta yi yayin da kwalla ya taru a idon ta. “Dole nayi kuka Tata domin bani da bakin magana ko kuma godiya a gare ka haƙiƙa kai ɗin na musamman ne a cikin ubanni na duniya ina alfahari da kai.” Murmushi Tata ya yi kurum yana gyara tsayuwarsa tare da riƙe crutches dake taimaka masa wurin tafiya, yayin da ya sa hannu ya karɓa wani surprising box daga wurin Ali sannan ya miƙa ma ta yana faɗin. “Ga ƴar ƙaramar kyauta daga Tatan ki.” Hannu na rawa Ayusherh ta sa ta karɓa box ɗin bakinta a washe tsaban farin ciki ta rasa inda zata saka kanta. Hannu ta sa a hankali ta fara warware box ɗin sannan ta buɗe ta sa hannu tare da ciro wata Princess Gown dake zuba walwali, kallon Tata ta yi tana ɗan zaro ido kafin ta yi magana key dake jikin rigar ya faɗi ƙasa, da sauri ta tsugunna tare da ɗauka ga tsananin mamakinta key ɗin mota ne. Ayusherh ta tsuke baki kwalla na taruwan ma ta, ta kuma duban Tata jinjina ma ta kai ya yi tare da nuna ma ta box ɗin, ta ƙara kai dubanta ga box ɗin dake hannunta, ɗan ring box da kuma roba na sarƙa ta gani, ta ɗauka ring box ɗin tare da buɗe wa, hasken walwalin da ring ɗin ke yi ya daki idonta da yasaka ta lumshe ido jikinta na rawa. “Tata duk waɗan nan fa, duk dan ni ne?.” Ta faɗa cikin sanyin murya tana kallon sa. Jinjina ma ta kai ya yi tare da faɗin. “Muje daga waje kiga motar Allah ya sa ta yi dai dai da ra'ayinki.” Ya faɗa yana mai kamo hannunta suka nufa ƙofar fita, yayin da su Ali suka mara musu baya, Yayankaka tana riƙe da Yâ tâ da zuwa yanzu tsofa sosai ya kamata, sai kuma wani Matashi da bai wuce sa'an Ali ba sannan sai wata budurwa duk su kayi waje. Hannu Tata ya sa tare da ya ye yadin da aka rufe motar da shi ai kuwa take motar ƙirar Lamborghini Countach, mai launin ja ta bayyana. “A'a Tata abin ya yi min yawa please ka rage.” Cewar Ayusherh cikin rawar murya. Tata ya ce. “Kuɗin fansho na da na daɗe ina tarawa da su nayi amfani wurin siya miki duk waɗan nan domin tayaki murna na zama soja, tabbas zama Soja ba burinki ba ne ke kaɗai nima burina ne haka ma sauran Ahali saboda haka ki daure ki karɓa.” “Amma fa Tata wannan motar ta yi min girma price ɗin ta ya kai 2.5 million fa.” Girgiza kai Tata ya yi. “Har ta sama da haka ma muddun na saba dama ni ɗin mai siya mike ne.” Ayusherh dai ta gaza cewa komai ji take ƙaunar Mahaifin nata da darajarsa yana ƙara ƙaruwa a idanunta. “Yâ tâ please kice wani mana, abin ya yi min yawa.” Ayusherh ta faɗa tana duban Kakarnata. “Ki karɓa kawai muddun ba rainawa kika yi ba.” Cewar Yâ tâ fuskarta ɗauke da annashuwa. “E Captain ki karɓa kawai domin kin cancanta ne, ko kin manta saboda jajircewarki tashi guda kika sama muƙamin Captain ne” Gaba ɗaya ƙannin nata suka haɗa baki wurin faɗan hakan, har da su waɗan nan Mace da Namijin. Ma'az da Chanchal. Haɗa su gaba ɗaya Ayusherh ta yi ta runguma suka wani yi zobe gunin burgewa. “Ina son ku Ahalina irin sosai ɗin nan.”❤️ Cewar Ayusherh. Suma amsa ma ta suka yi da faɗin. “Muma muna son ki da yawa da yawa.”💖 “Yanzu ki shiga ki saka wannan rigar sai kizo mu fita da motar dan yau sai an zagaya damu ko'ina sai mun zagaye gaba ɗaya Abuja. Cewar Tata yana ƴar dariya gaba ɗaya dariya suka yi. Ba musu Ayusherh ta shiga ciki yayin suka mara ma ta baya, Up ta haye zuwa Bedroom ɗin da yake mallakinta, ta shiga wanka ta fara yi sannan cikin ƙanƙanin lokaci ta shirya tsaf cikin wannan Princess Gown ɗin tare yin light make-up, ta saka ring ɗin a ƙaramar yatsarta na ƙarshe, sannan ta saka sarƙar nan, tare da saka wani flat shoe mai kyau, daga ƙarshe ta rolling mayafi a kanta. Sannan ta nufa waje. Idan a ka ce kyau to fa ɗaya ke nan, Ayusherh tana da kyau irin cancan ɗin nan, dama gata kyawawa sai wannan shigar ya ƙara ma ta kyan, ta fito kamar wata Princess sai zuba shining take yi. “Wowww.” Ali ya furta lokacin da Ayusherh take taka matattakalan bene domin saukowa. “Aunty Ayush wannan mugun kyau haka kin ganki kuwa, kamar wata Princess gaskiya ya kamata nayi miki photo koda one card ne.” Ali ya yi maganar yana ciro wayarsa, nan take ya shiga Camera ya fara yi ma Ayusherh photo kala kala. “To ya isa haka na gaji da tsayuwar.” Ayusherh ta faɗa tana saukowa sannan ta ƙari sa wurin Tata kana ta ce. “Na shirya Tata amma a hakan zan iya driving kuwa.” Dariya Tata ya yi ya ce. “Mai zai hana.” “Amma ya kamata kafin mu tafi muyi photo a tare ko?.” Cewar Yayankaka.” “Shawara mai kyau, Bara nayi mana, ku marmatso.” Ali ya faɗa lokacin da ya ƙari sa inda Ayusherh take tsaye, ai kuwa gaba ɗaya suka marmatsa ya fara zuba musu selfie. Bayan sun gama suka yo waje a wurin motar ma sai da a ka tsaya a ka yi. Sannan ne duk suka shishshiga ya rage daga Yâ tâ sai Yayankaka ne basu shiga ba. “Haba Yâ tâ ki shiga motar mana mu tafi.” Cewar Yayankaka a gundure domin ta yi, ta yi Yâ tâ ta shiga motar amma taƙi, dama an saba haka da ita tun bayan lokacin da Tata ya sama hatsari na mota, Yâ tâ take tsoron shiga kowacce irin mota. Ali ne dake Posting ɗin hotunan da suka yi a Instagram ya duba Yâ tâ yana faɗin. “Wai yanzu Fisabilillah tsohuwar nan wai tsoron mutuwa kike ne?, keda kika kusa gangarawa?” Ya faɗa cike da shaƙiyanci yana riƙe haɓa. Ita dai Yâ tâ bata kulasa ba sai faman zazzare ido take kamar wacce ta yi ma Sarki ƙarya. “Ƙaniyarka nace Mahaifiyar tawa kake faɗa ma haka.” Cewar Tata yana fitowa daga motar da kansa ya ɗauki Yâ tâ ya saka a cikin motar. Shi dai Ali ya yi shiru yana gimtse dariya. Ayusherh da ta kasance zaune a mazaunin driver sai Yayankaka a kusa da ita sannan sai Tata, daga baya kuma Yâ tâ ce sai wannan Budurwar sannan sai Ali da wannan saurayin. A haka Ayusherh ta ja motar da suka isa wurin Gate Ali ne ya fita ya buɗe sai da ta fita da motar sannan ya rufe Gate ɗin sannan ya koma cikin motar suka ɗauki hanya. A shekarun da suka gabata ne Tata ya sama wani hatsari a yayin gudanar da aikinsa na tuƙi a Companyn da yake aiki, wannan dalilin ya sa baya iya tafiya da ƙafarsa ta dama, sakamakon a lokacin da ya yi hatsarin ƙafar ta sama karaya da kuma buguwa, a lokacin companyn sune suka ɗauki dukkanin ɗawainiya na jinyar da ya yi sannan suka bashi gida halak malak anan Gwagwalada tare kuma da ci gaba da biyansa albashi a kowanne wata duk da ba aikin yake yi ba sakamakon ƙafar tasa da baya iya tafiya da ita har sai ya haɗa da crutches. Haka kuma companyn suka ci gaba da biyansa kuɗin fansho a duk wata. A halin yanzu Ali da yake da shekaru goma sha takwas zuwa sha tara a duniya yana karatu ne a wata University of Sports dake nan Abuja, yayin da Yayankaka bayan ta gama secondary school ta shiga wata University na koyon gudu da kuma hawan doki, sai kuma Chanchal da Ma'az, Asalinsu ƴan ƙauyensu Ayusherh dake Taraba ne iyayensu sun kawo su wurin Tata da zama ne domin karatu yanzu haka ita Macen tana S.S 2. a Secondary, yayin da Namijin ya gama secondary yanzu yana a makarantar koyon tuƙin jirgin sama ne domin burinsa ke nan, iyayensu ke turo kuɗin karatun duk in lokaci ya yi, domin suma burin nasu ke nan ƴaƴan nasu suyi karatun. Duk da cewa Tsufa ya gama kama Yâ tâ sai dai hakan bai saka ta gaza gane mutane ba sai dai abin da ba'a rasa ba da kuma rikicin tsufa wasu lokutan, sai kuma ciwon ƙafa dake taso ma ta lokaci, lokaci shi ya sa lokaci da dama in ya taso ma ta sai dai ta dinga zama a wheelchair ko kuma ta riƙe sanda dan kuwa bata iya tafiya. WANNAN KE NAN. •… 💕 *CAPTAIN AYUSHERH*🥷 * 🍂🎀 (_The ShieldMaiden._) I'm on Instagram as @thenainarh. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/thenainarh?igsh=YzljYTk1ODg3Zg== BY - Nainarh KD.... 𝒩𝓀𝒹'𝓈❦♡ Nainarhkd3 @Wattpad. *🔥 Perfectly Pen's (P.P✍️* Episode 11. Sosai Ayusherh taji daɗin wannan bazata da Tata ya yi ma ta, kuma motar ta yi ma ta ɗari bisa ɗari, sun daɗe suna kewayen yayin ɗa na motar sannan daga bisani suka koma gida cike da nishaɗi. *- 100, Adeola Odeku Street, Victoria Island, Lagos, Lagos State, Nigeria* Daga yanayin yadda mutanen dake tsai-tsaye a compound na gidan suke, da kuma shigar da kowannensu ya yi, zai tabbatar maka da shirin film suke yi. Ƴan mata ne wurin su shida sanye cikin shiga kala guda wato doguwar Gown har ƙasa da taji ado ta yi kyau, kana ganinsu dai kaga waɗan da suka yi shiga irin na biki, yayin da gefe guda kuma maza ne suma sanye cikin suit Black sai dai banda mutum ɗaya, dake zaune saman wata tulip chair ya harɗe ƙafa yana karkaɗata a hankali, idanunsa a lumshe da alama shi ne jarumi a shirin. Can gefe kuma Amarya ce da angon a zaune sannan sai Iyaye daga gefe. Director ne ya tashi daga kujerarsa tare da ƙari sawa wurin Camera man yana gyara masa yadda zai saita Camera yayin ɗauka, sai da komai ya daidai ta sannan Director ya bada umarni ta hanyar faɗin. “In three two one, rolling Action.” Ya faɗa tare da alama da hannu. A yadda shirin yake shi ne Amarya da ango ne za su jefa flower idan Amarya ce ta jefa, to fa duk Macen da ta yi nasarar cafewa ita ce zata zama Amarya ta gaba a cikin shirin domin haka tsarin familyn yake, yayin da in ango ma ya jefa to fa duk namijin da ya yi nasarar cafewa shi ne zai zama ango na gaba a tsarin familyn ke nan tun fil-azal. Da sauri Amarya da angon suka tashi daga inda suke tare da ƙari sawa wurin, flower abokin ango ya basa. Juyawa angon ya yi tare da sai tawa sannan ya jefa flower ta bayansa, kowa ya zuba ido domin gani mai rabo da zai yi nasarar ca fe flower. Wani irin zaro ido ƴan matan suka yi gaba ɗaya ganin flower ta faɗa a jikinsa. A hankali ya buɗe idanunsa dake a lumshe ya zubawa flower da ta faɗo saman laps ɗin sa, sai kuma ya ɗauki flower tare da riƙe wa a hannu ya miƙe tsaye. Kamar yadda tsarin shirin yake, hakan ya sa ita ma Amarya ta karɓa nata flower tare da juyawa sannan ta jefa flower, haba ai nan dukkanin ƴan matan kowannensu ta daka tsalle tare da ƙoƙarin ganin wannan flower ya zo hannunta, ai kuwa cikin sa'a wacce ta kasance tafi sauran ƴan matan kyau kuma ita ce jarumar labarin ta sama nasarar ca fe flower ai nan da nan daɗi ya kusan karta, dama burinta ke nan ai tuni ta a je batun wani shirin film a gefe tana riƙe da flower ta ƙari sa wurin da yake tsaye a guje ba jira ta wani rungume sa tare da shigewa jikinsa. Gaba ɗaya mutanen wurin suka kwalalo ido domin su ba haka suka karanta a script ba, shi kuwa Director hannu ya ɗaura a kai kamar zai fasa ihu tsaban takaici, shikenan kuma ta ɓata komai, daɓas Director ya zauna saman kujerarsa yana goge gumi da hularsa. A hankali ya ɓanɓare ta daga jikinsa tare da zuba ma ta lafiyayyen mari, yana karkaɗa ma ta hannu alamar warning, ya tsittar da yawu cikin wani irin ɓacin rai, tare da cire farar rigar yadi dake jikinsa ya jefar cike da kyankyami, rai a ɓace ya bar wurin, shigewa ciki ya yi tare da ƙari sawa masaukin sa da a ka tanadar masa, da gudu shima Personal Assister nasa yabi bayansa haka ma Director yana fata ba fasa shirin gaba ɗaya ya yi ba domin ya san wane ne Haisam wannan kaɗan daga cikin rashin mutunci nasa ya ce ya fasa shirin gaba ɗaya. Ita kuwa wannan Budurwar duk da marin da ta kuma ya shige ta amma wallahi ko'a jikinta domin burinta ya cika ta haɗa jiki da Haisam Dawud Nasamu. Yaro Matashi haɗaɗɗe kuma ɗan kwalisa Burin kowace mace kuma gashi ɗa ɗaya tilo a wurin Alhaji Dawud Nasamu. Wato President mai ci a yanzu. Haisam sanannen jarumin film ne lamba ɗaya da ba a iya Nigeria ya tsaya da acting nasa ba, hatta ƙasashen ƙetare ɗaukar sa suke yi yana musu acting cikin fina-finan su, shi ya sa ko'ina ya shahara baga nan bama shi ɗin kyakkyawa ne ajin farko sai dai fa Haisam bai san wani abu wai shi mutunci da kara ba, ba ruwansa ko waye kai bai ƙi ya taka ka ya yi gaba ba, yana da matuƙar kyankyami shi ya sa a yanzu ma ransa ya yi masifar ɓaci da abin da wannan Budurwar ta yi masa haushin kansa ma yakeji da ya ɗaura hannu a jikinta. Haisam ke nan matashin billionaire sannan Actor, Kuma Dancer, and International Model. Yana shiga bai zame ko'ina ba sai bathroom ya sakarma kansa ruwa idanunsa a lumshe har yanzu ransa a ɓace yake kuma bai dena kyamar kansa ba na abin da Yarinyar ta yi masa. Ƙyazama ce ita a wurinsa kai bama ita ba hatta sauran matan kallon ƙazamai yake musu a to mai za'ayi da baƙar fata shi ya sa yafi ƙaunar rayuwa a waje ba takura. Sai da ya ɗauki aƙalla minti talatin a bathroom ɗin sannan ya fito yana ɗan jan tsaki, yayin da yake ɗaure da towel ga kuma ƙarami yana goge sumar kansa mai tsayi da a ka yi masa wani irin aski yayin da kaɗan ya zubo ya rufe masa fuska. Kar fa duk wannan abu ya sa kuyi tunanin Haisam babu ruwansa da mata!. Yana kula su sai dai ba irin baƙaƙe na nan da ya raina ba, cikakken ɗan soyayya ne sai dai duk da hakan bai taɓa wani abu da sunan haɗa shimfiɗa da wata mace ba iyaka sai dai a yi romance a tashi. Wannan kuma ra'ayinsa ne kuma ba mai take masa burki a matsayinsa na ɗan gata kuma Shalele a wurin iyayensa da basa ganin laifinsa a komai da zai yi sannan ba sa take masa burki a komai shi ya sa ya taso da wata iriyar halayya ta ganin kowa a ƙasa yake da shi. Haisam akwai ji da kai. Director da P.A suna tsai-tsaye curko curko a palon kowa da abin da yake saƙawa shi dai Director fatansa bai wuce kar Haisam ya ce ya fasa shirin ba, domin ya san hakan ba ƙaramin asara zai haifar masa ba, duba da irin manyan kuɗaɗe da ya kashe ma film ɗin. Yayin da P.A sai faman harara yake watsa ma Director ƙasa ƙasa domin shima an ja ma sa wani bala'in ne dama ya ya lafiyar kura. Daddaɗan ƙamshinsa ne ya fara isa gare su kafin ya bayyana yana taku ɗai-ɗai cikin shiga casually wata kalar Stylish riga a jikinsa mara dogon hannu da kuma buɗaɗɗen gaba, hakan ya sai ya bada damar bayyanar Thickchesk ɗin sa yayin da still yake sanye da wani Fitted Jean's, kai idan baka sani ba sai kayi tunanin yayyaga Jean's ɗin a ka yi, ta wurin gwiwa ganin yadda wurin yake a yayyage sai dai fa duk a cikin gayu ne a haka Jean's ɗin yake, zakuyi mamakin tsadarsa. Ƙafafunsa rufe cikin wani expensive comfortable sneakers yayin da fuskarsa dake a murtuke sanye cikin wani makeken Space da ya yi matuƙar dacewa da fuskar nasa mara hayaniya. Ganin dai kamar bai lura da su ba ya sa kai zai fi ce ne, ya sa da gudu suka bi bayansa Director sai faman basa haƙuri yake tare da alƙawarin zai ɗauki mummunar mataki a kan yarinyar Amma please kar ya ce masa ya fasa. Shi kuwa P.A faɗi yake. “Ya Yallaɓai Abuja zamu tafi ne?.” Bai kula su ba har sai da ya ƙari sa wurin jerin motocin sa dake a fake guda takwas cir. Ya shiga ta tsakiyar da tafi kyau da kuma tsada. Sai a lokacin ya dubesu sannan ya yi magana a taƙaice. “Director James ba zan iya wannan aikin ba, ka nemi wani, ina nufin na fasa.” Sannan ya dubi P.A ya ce a taƙaice. “Abuja.” P.A ya gane mai yake nufin cikin sauri da rawar baki ya ce. “Ya Yallaɓai na bincika babu Flight da zai tashi zuwa Abuja a dai dai wannan lokacin saboda yanayin weather na garin kuma yanzu yamma ta yi kuma...” Bai ƙari sa ba ya tsinkayi muryarsa yana faɗin. “Mu tafi a mota.” Yana faɗin hakan ya jingina bayansa jikin kujerar motar tare da lumshe ido bayajin zai iya ko ƙara awa guda ne a Lagos. Muƙut P.A ya haɗiye yawu yayin da Drivern ya rufe motar. Shi kuwa Director kasa koda motsi a wurin ya yi. A haka motocin a jere suka fita daga gidan harda baɗe shi da ƙura dan yaƙi ya matsa wa. Ƙasa ya yi zai zube Mataimakin sa ya yi saurin taro sa shima ransa ba daɗi haka ma sauran mutanen dake wurin tun daga masu ɗaukar shirin da sauran ƴan wasan. ** P.A sai kallon Agogo yake yi hankali a tashe tabbas akwai kasada tafiyar su a wannan daren, gashi daga Lagos zuwa Abuja ba nan kusa ba. Gashi Haisam yaƙi ya haƙura koda a hotel ne su kwana ko kuma su bari zuwa lokacin da za'a sama jirgin da zai tashi zuwa Abujan. A haka dai suka ci gaba da tafiyar. Gashi Yamma ta yi dan a lokacin wuraren biyar da rabi ne na yamma. * A hankali ya buɗe fararen idanunta sakamakon sautin shigowar kira da wayarsa ta yi, sunan Nusra ya bayyana saman screen na wayar. “Haisam!.” Nusra ta kira sunansa a lokacin da ya ɗa ga kiran, bata jira ya amsa ba ta ƙara faɗin. “Kana lafiya kuwa?.” “Yeah, what's up?.” Ya faɗa cikin taushin murya. “Tun da na tafi baka kirani ba shi ya sa nayi tunanin ko ba lafiya ba, sai dai kuma naji daɗi da ya kasance kana lafiya, ba ma wannan ba kasan wani abu kuwa?.” Ta yi masa tambayar cikin muryar da take nuna zallar zumuɗi da take ciki. “Nayi nasara Haisam ina nufin nayi nasarar zama ta ɗaya a fashion championship da a ka gabatar a Dubai, kaga hakan yana nufin nima na zama International Model.” Ta ƙare maganar cikin wata kalar murya mai cike da annashuwa tsaban farin ciki kamar ba Nusra da ya sa ni ba, koda yake Nusra Nusra ce sai dai Nusra daban take zama idan ta kasance tare da shi she was so caring and loving a kan sa, ya san hakan amma yake sharewa. “Nice to You, Congratulations and All the best.” Ya faɗa domin tayata murna. Nusra ta ɗan yi murmushi tana faɗin. “Thank you.” Sai kuma ta ɗan yi shiru shima hakan. “Zan katse kiran, ka kula da kanka, and I Love you.” Ta faɗa da kalar muryar da ta basa magana a garesa, bai amsa ma ta ba ya katse kiran, Nusra tabi wayar da kallo, tana sauke ajiyar zuciya. * Zuwa yanzu sun daɗe da fita daga Lagos kuma dare ya yi sosai sai dai shi Haisam ko'a jikinsa idanunsa ma a lumshe suke kamar mai bacci. Wani irin birki motocin suka ja a sakamakon abin da suka gani, kafin su yi wani yunƙuri lokaci guda ƙarar harba harbe ya cike wurin kafin ƴan fashin da kowannensu hannunsa ɗauke yake da Manyan bindigu masu hatsarin gaske, gaba ɗaya suka zagaye motocin ga kuma fuskokinsu dake a rufe baka iya gani komai sai jajayen idanun kowannensu. Wannan ke nan....✍️ *Prep-Room, Disclosed Location Abuja.* Dukkanin su zazzaune suke cikin Ɗakin da ya fi kama da na taro kowannensu zaune saman desk sun ɗaura hannu saman dogon table dake wurin, sanye suke cikin shiga kala ɗaya, baƙaƙen kaya haɗe da ja kaɗan fuskokinsu a rufe yake da hular rigar jikinsu, a haka suka fara taron, wanda ya kasance shi ne shugaba a cikinsu yana tsaye gaban farin allon wanda hasken kwan wutan projector ya haskesa, jiki kuma ɗauke da rubutu da Manyan baƙi. *SECRET OF US* Da alama sunan ƙungiyar ta su ke nan, magana ya yi kaɗan kafin ya bawa kowannensu damar faɗar damuwarsa. Ɗaya bayan ɗaya suke tashi kowa yana faɗar damuwarsa ko kuma wani buri nasa su kuma sai su tattauna a kan yadda za su ɓullo wa al'amarin a ka haka har a ka zo kansa. Alhaji Dawud Nasamu da shima ɗaya ne daga cikin manyan shugabanni na ƙungiyar ta su ta *Secret of Us* kuma mai faɗa a ji, magana ya fara kamar haka. “Wato Babban abin da ke damu na shi ne a kan zaɓe da ya gabato sam ban yi duk wasu ayyuka da na alƙawarta zan yi ba, gashi zaɓe ya gabato sannan bana da gwarin gwiwa a kan zancin zaɓen wannan karon sakamakon Abokin takarata da yake shiga min hanci da ƙudunduni, kuma na lura talakawa suna ƙaunarsa a yanzu shi ne matsala ta kafin a iso kan mutane ina nufin talakawa dan su wannan nasu mai sauƙi ne.” Ya ƙare maganar yana kaɗa kai yadda kasan mene ne. “Wannan ai ƙaramin abu ne Alhaji Dawud ko ka manta ƙarfin iko da wannan ƙungiyar tamu take da shi ne ga ka kuma President guda ai ka saka a ranka ka SAMU kawai kamar yadda inkiyarka take NASAMU.” Gaba ɗaya suka kece da dariya har da wanda ya yi maganar da shi kansa Alhaji Dawud Nasamu. Ci gaba da tattaunawa suka yi a tsakaninsu na yadda za su ɓullo wa al'amarin sun daɗe sosai kafin daga bisani suka watse. Alhaji Dawud Nasamu ya shiga cikin ɗaya daga cikin jerin motocin sa dake fake, alamar jinjina Matar dake zaune a motar ta yi masa tana ɗan murmushi, shima ya mayar mata da murmushin yana faɗin. “Nice to You Dear you're so amazing in all the time.” Ta ɗan yi murmushi gefe tana faɗin. “It all for you.” Ta yi maganar tare da ɗan kwantar da kanta a kafaɗarsa. A haka suka fara tafiya suka baro wurin Direct gidansa suka nufa da shi bayan shafe kusan minti talatin suna tafiyar sannan ne suka iso. Daga shiga unguwar zakasan ka shigo wuri na manyan mutane wurin da masu mulki ne kawai ke zaune da iyalansu sunan yanki shi ne The President Area a nan gidan Gwamnati take shi ya sa sunan yankin ya kasance haka. •… 💕 *CAPTAIN AYUSHERH*🥷 * 🍂🎀 (_The ShieldMaiden._) https://whatsapp.com/channel/0029VaEZtE15a2429vfcpf20 BY - Nainarh KD.... 𝒩𝓀𝒹'𝓈❦♡ Nainarhkd3 @Wattpad. +234 808 112 9487. *🔥 Perfectly Pen's (P.P✍️* Episode 12. A jere motocin suka shiga katafaren ƙeraren gidan, haɗaɗɗe iya ganin ka, basu kai ga ƙari sawa parking lot ba wasu motocin sojoji guda uku suka danno cikin gidan suma. A compound na gidan motocin sojojin suka faka. Da sauri sojan ya ƙari sa tare da buɗe motar dake tsakiya. Fitowa General Lamrat Jabir Junaid ta yi sanye cikin uniform na soji idanunta maƙale da Space yayin da take riƙe da Jacket a hannunta. Dai dai lokacin suma su Alhaji Dawud suka fito daga nasu motar shi da wannan Matar rungume da juna. Ɗauke kai General Lamrat ta yi tamkar bata gansu ba. Magana ta yi ma sojan da ya buɗe ma ta motar, sannan ta yi ciki. Matar nan ta ja tsaki ƙasa ƙasa tana bin General Lamrat da kallon banza. Yayin da shi kuwa Alhaji Dawud ya jinjina kai, rai a ɓace wato har shi ne Lamrat zata gani ta ɗauke kai. Lallai wannan aikin sojin ya saka kanta ƙara girma ringingin tun da har zata gansa ta ɗauke kai sai dai zai yi wa tufkar hanci. Kai ya kaɗa suma suka shiga ciki shi da ita, part ɗin sa suka wuce direct, ta taya sa ya yi wanka ya shirya sannan ta koma nata part ɗin. ... Shiga palon ya yi da sallama sai dai ba'a amsa ba, hakan ya sa shi ƙari sawa ciki sai dai ba kowa, direct bedroom ya nufa, tare da shiga ciki a masifance tsaban bala'i dake cin sa har wani kumfa kumfa yake fitarwa daga bakinsa.😅 “Wato ke Lamrat kin rainani ba, saboda kwana biyu nayi sanyi ko wato shi ne ɗazu kina gani na kika ɗauke kai sannan kikayi tafiyar ko saboda kin mayar dani shashashan namiji, to wallahi ba zata saɓu ba bindiga a ruwa, kuma waɗan nan gaddawan ɗirka ɗirkan mazan da kike zuwa dasu bana da ra'ayin sake ganinsu a gidana ina fata kinji?.” Ya ƙare maganar a wani kausashe yana nuna ta da ƴasa. A hankali cikin nutsuwa ta ɗa go tana dubansa, tun da ya fara maganar bata dubesa ba kuma bata tanka sa ba, har sai da ta ji ya yi shiru alamar ya gama. Ajiyar zuciya ta sauke tana girgiza kai still bata ce masa ƙala ba, ta dubi Ma'aikaciyarta dake tsugunne tana goge ma ta ƙafar da ta gama gasa ma ta da towel, a sakamakon ɗan rauni da taji a wurin aiki, ya sa taji ciwo a ƙafar yanzu haka ma daga hospital ne tayo gida. “Amira zaki iya tafiya na gode.” Ta faɗa bayan ta kauda kanta daga dubansa. Miƙe wa tsaye Amira ta yi kanta a ƙasa ba tare da ce komai ba ta fice sum-sum cike da tausayin uwar Ɗakin nata da wannan rashin mutunci da tijara da miji ke mata bai damu da su ƴan aiki suna wurin ba, wannan yana faruwa ne tun lokacin da ya aure ta gashi har yau bata canza zani ba shekara ɗai-ɗai har Ashirin da ɗauriya. Miƙe wa tsaye wa ta yi daga saman stool da take a ɗan kishingiɗe tare da ƙari sawa gaban dressing mirror ta zauna tana duban kanta a madubin dake a wurin. Shi kuwa sororo ya yi yana dubanta baki sake wato yau shi Lamrat take sharewa har haka lallai ne. “Kayi haƙuri ka dena yi min faɗa a gaban Ƴan aiki baka gudun su raina ka a matsayinka na President mai ci yanzu? Kuma Babban Mutum a idon kowa?.” Ta faɗa cikin sanyin murya. A kufule ya tunzura zai yi magana, sai dai ƙarar kira da ya shigo wayarsa ne ya sa ya dakata tare da duba wayar ganin mai kiran ba kowa ba ne fa ce P.A na Haisam ne ya sa ya yi hanzarin ɗa gawa tare da karawa a kunne sai dai bai kai ga magana ba ya zaro ido tashi guda hankalinsa ya ɗugunzuma wurin tashi, murya a ɗa ge ya ce. “Haisam ɗin ne a ka yi kidnapping nasa to garin ya ya?.” Sai kuma ya nufi ƙofa da sauri, tsaban sauri har yana kusan ƙumewa da ƙofar bai lura ba. Ita ma General jin sunan da ya ambata da kuma batun kidnapping ya sa hankalinta kai ƙololuwa wurin tashi kar dai a ce Haisam ɗin ta yake nufi an ce?. Zuciyarta ke yi ma ta wannan tambayar sai dai bata da mai bata amsarta. .. Da sauri ya ƙari sa shiga palon tare da ƙari sawa wurinta, tana durƙushe ne riƙe da wayar. Tallafota ya yi zuwa jikinsa yana faman lallashi. “Maimuna ki kwantar da hankali mana nayi miki alƙawarin ba abin da zai sama ɗan mu Haisam koma ina ne kidnapper's ɗin suka kaisa zai dawo wannan alƙawari na ne.” Kwace jikinta ta yi daga nasa tana yi masa wani kallo take faɗin. “Na kwantar da hankalina fa kace a sace yaron nawa guda kake maganar na kwantar da hankalina iye Dawud ka amsamin?.” Wani irin duba na tsanaki Mr President yake yi ma Maimuna wato mahaifiyar Haisam. Ƙasa ta yi da kanta tare da durƙusa wa, tana ƙara sautin kukan ta. “Mene ne yake faruwa?.” Gaba ɗaya suka jiyo dan ganin mai maganar. Wata kyakkyawar Mace ce da ba zata haure shekaru arba'in zuwa da sama ba, tana tsaye sanye cikin wata doguwar riga har ƙasa ta yi rolling da mayafi mai girma da kuma faɗi simple make-up ne a fuskarta ƙafafunta rufe cikin wasu flat shoe yayin da take riƙe da wasu littattafai a hannunta. Ta zuba musu ido tana jiran amsa. “Yaya Dawud magana fa nake wai meke faruwa ne naga Anty Muna tana kuka haka?.” Ta ƙara jefo masa tambayar. Ajiyar zuciya Alhaji Dawud ya sauke yana faɗin. “Dawha yaushe kika dawo? Dama Haisam ne masu garkuwa da mutane suka yi kidnapping nasa a hanyarsa na dawowa daga Lagos zuwa Abuja.” Wani irin banbara kwai maganar tasa ta yi ma ta. “Kidnapping!!!.” Ta maimaita a fili fuskarta ɗauke da zallar mamaki, sai dai duk abin da take yi cikin nutsuwa ne. Jinjina ma ta kai kurum Alhaj Dawud ya yi yana kara wayarsa a kunne sakamakon kira da ya shigo. Zuwa washe gari babu inda labari bai zagaya ba a kan sace Haisam da ƴan garkuwa da mutane suka yi, abin akwai matuƙar ɗaure kai a ce Mutum har Mr President Alhaji Dawud Nasamu ne a ka sace yaron sa guda, Lallai abin ya koma kan su ya bar kan ƙanana-ƙanana. *Aguyi-Ironsi Barracks Cantonment ¹, Asokoro, Abuja.* Shigowa cikin Ɗakin taron General Lamrat ta yi kana Ganinta kaga wacca ta kwana ba bacci ga idanunta sun ɗan kumbura yanayinta sam ba walwala ta shigo wurin tare da ƙari sawa matsayarta ta tsaya kusa da farin allon wanda hasken kwan wutan projector ya haskesa, tare da nuna hoton wani Matashi da allon ya bayyana. Sannan ta fara magana kamar haka; _You can continue reading this book on Arewabooks App, search @nkds._ It very short page sorry ahh!!!! _Oooo Mah people mu haɗu gobe huh domin sanin yadda za ta kaya in Allah ya kai mu, thank you for your support and love, Nainarh KD As you know na yi muku fatan Alkhairi bye...💋👋_ •… 💕 *CAPTAIN AYUSHERH*🥷 * 🍂🎀 (_The ShieldMaiden._) BY - Nainarh KD.... 𝒩𝓀𝒹'𝓈❦♡ Nainarhkd3 @Wattpad. *🔥Perfectly Pen's (P.P✍️* Episode 13. Bayan ta nuna hoton dake jikin allon majigin. “Wannan sunansa Haisam kuma ɗa ne a wurin Mr President Dawud Nasamu, a daren jiya masu garkuwa da mutane suka yi garkuwa da shi a hanyarsa na dawowa daga Lagos zuwa Abuja a mota.” Ta ɗan yi shiru bayan ta faɗa haka, yayin da duk suka nutsu suna sauraren ta, hankalinsu kacokan a kan bayanin da take yi. A hankali kuma ƙasa ƙasa Jasmine ta ce ma Ayusherh cikin raɗa. “Shi Mr President ɗin mijinta that's why she's so uncomfortable kuma ta damu sosai a kan lamarin.” Ci gaba da bayani General ta yi da faɗin. “A halin yanzu mun gano inda waɗan nan masu garkuwar suka kaisa, a halin yanzu suna a wani daji ne dake tsakanin Abuja da kuma wani ƙauye, ba tare da taɓa lokaci ba zamu shirya tawaga domin kai hari ga waɗan nan ƴan ta'adda, lastly kuyi iyakar ƙoƙarin ku wurin ganin an dawo da Haisam gida cikin ƙoshin lafiya ba tare da wani abu ya sameshi ba.” Ta faɗa tana ƙara jajjadawa a gare su, daga haka kuma a ka shiga shirya tawaga da za su kai sumamen ga ƴan ta'addan a domin kwato Haisam, Captain Ayusherh ita ce da tawagarta za su jagoranci kai harin, cikin ƙanƙanin lokaci sun gama duk wani abu da ya dace sun shirya tsaf sannan suka shishshiga attack helicopter suna bin map har suka ƙari sa dajin da ƴan ta'addan suke, nan kuma kowannensu ya shiga gyara bindigar dake hannunsa a sa'ilin da attack helicopter ɗin nasu ya shiga dajin, yayin da Captain take duba dajin tare da nazarinsa ta hanyar amfani da abin hangen nesa. Juyawa ta yi tare da duban sauran sojojin, da hannu ta yi musu alama dai dai wurin da take zargin ƴan ta'addan sun ɓuya, hakan ya sa suka sai ta makaman su, sannan biyar daga cikinsu suka sauka daga helicoptern dake zagaye dajin, cikinsu har da Ayusherh, cikin tafiyar sanɗa da bi ta cikin ciyayi, suka fara tafiya yayin da wasun su suke duba abin hangen nesa dake jikin bindigar hannunsu. Da Hannu ta yi musu alama da wani keɓantaccen wuri kamar gidan gona dake a dajin kuma da alama nanne ƴan ta'addan suka ɓuya, sannan ta yi musu alama da ita zata fara gaba sannan subi bayanta. Da sauri ta ɗan miƙe da ɗan gudu kuma ta ƙari sa wurin wani daga cikin ƴan ta'addan dake kewaye wurin hannunsa riƙe da wata jibgegiyar bindiga. Saitin wuyansa ta damƙa tare da murɗawa, take a wurin ya sume, bindigar hannunsa ta ɗauka tare da miƙa wa sojan dake biye da ita, sannan ta yi masa alama da ya bi wata hanyar, sannan ita ma tabi wata hanyar. “Boss an sama matsala, sojoji sun kawo farmaki.” Cewar wani daga cikin ƴan ta'addan da ya shiga cikin Ɗakin da shugabansu yake, ya yi maganar hankalinsa a ɗan tashe. “What!! amma garin ya ya sojoji suka gano maɓoyarmu.” Wanda yake tare da shugaban nasu ya faɗa yana miƙe wa tsaye daga zaunen da yake, tare da ƙari sawa wurin da ya a je bindigarsa sannan ya ɗauka. Dirowa ta yi daga ƙaramin katangar sannan cikin azama ta yi ƙasa tare da ci gaba da tafiya hannunta riƙe da bindigarta yayin da rabin fuskarta ke rufe da hular kanta, a ka sin sauran sojojin da wasun su da wani Green ɗin abu suka shafe fuskokinsu yayin da wasunsu kuma suka rufe fuskokinsu da mask mai haɗe da hular kansu irin mai kare harsashin nan. Da sauri ta ɓuya jikin wani ɗan corridor ganin ɗaya daga cikin ƴan ta'addan yana tunkaro wurin, har sai da ta dai dai ta ya kusan ƙari sowa inda take sannan ta fito tare da shammatarsa ta sakar masa harsashi a ƙirji, da sauri sojojin da suka biyo bayanta suka ƙari sa tare da janye sa daga wurin, sannan ita kuma ta yi gaba, Ɗakin da suke zargin nan ƴan ta'addan suke a tare da Haisam ta ƙari sa, sai dai ƙofar a garƙame take kuma irin ƙofar nan ne mai girman gaske da security na musamman muddun bata ciki a ka buɗe ba, to fa sai dai bomb ne kawai zai iya fasa ta. Hannu ta saka a cikin aljihun dake wandonta ta wurin gwiwarta ta ciro abin fasa ƙofar tare da manna shi jikin ƙofar, juyawa ta yi tana duban sojojin dake bayanta, sannan ta fara counting from one to three, sannan bayan ta danna wani madanni dake jikin abin fashewar, tana kai three a ƙirgar abin ya fashe tare da ƙofar, da sauri ta danna kanta cikin Ɗakin, dai dai shugaban nasu yana faɗin. “Kun manta ɗan waye muka sace ai dole sojoji su kawo farmaki sai dai sun ja zan yi abin da ban yi niyya ba...” Bai idda maganar ba suka ji ƙarar fashewar abu dai dai nan kuma ta shigo Ɗakin riƙe da bindigarta ta saitasu duk suka yi tsuru-tsuru domin duk basuyi tsammani ba kasancewar suna daga can cikin Ɗakin ne. Kuma at the same time da bomb ɗin ya fashe da ƙofar ita kuma ta shigo, so basu iya wani yunƙuri ba. Da sauri ɗaya daga cikinsu ya saita bindigarsa a kan Haisam dake zaune saman wata chair sun ɗaɗɗaure hannunsa da ƙafafunsa a ta bayan chair ɗin, fahimtar abin da yake shirin yi ne ya sa Captain ta yi wani tsalle tare da jifa da bindigar hannunta ta ƙari sa wurin da Haisam yake saman chair ɗin a ɗaɗɗeure tare da sa ƙafa ta ture chair ɗin ya yi ƙasa, sai dai duk da haka harsashin da wannan ɗin ya riga ya saki, fiu ya wuce bayan ya gogi gwiwar Haisam a sakamakon lokacin da Captain ta ture chair ɗin da yake kai ƙasa chair ta yi, wannan ya sa harsashin ya shafi gwiwarsa sannan harsashin ya bugi jikin bangon Ɗakin. Tim chair ɗin da Haisam yake kai ta yi ƙasa, da sauri Captain ta sa ƙafa tare da shure Bindigar dake a hannun wannan Kidnapper ɗin da yake ƙara ƙoƙarin sakin wani harsashin a saitin ta. Ca fe Bindigar nasa da ta yi sama Captain ta yi, tare da saitawa bata jira komai ba ta sakar masa lafiyayyen harbi a gwiwa, ganin haka ya sa kidnapper ɗin da ya shigo Ɗakin a ɗazu ya sanar dasu game da sojojin, ya nufa ƙofa zai gudu, sai dai kafin ya kai ƙofar Captain ta sakar ma sa nasa harsashin a kafaɗa. Shugaban Kidnapper's da babu bindiga a hannunsa da sauri ya fakaici idanunta tare da yin crawling ya ɗauki bindigarta da ta ƴar, sannan ya miƙe tsaye tare da saita Haisam da jikinsa gaba ɗaya ya mutu ya kasa koda kwakwaran motsi tun bayan lokacin da ya faɗi, a sakamakon gwiwarsa dake masa wata iriyar zugi na bala'i. “Ko ki a je bindigar hannunki ko kuma na fasa kansa da alburushi.” Cewar Shugaban kidnapper's ya faɗa haka yana ma ta nuni da Haisam dake kwance ido a lumshe, maganar da ya yi ne ya sa Haisam buɗe ido da sauri sai a lokacin ya lura da shugaban Kidnapper's da yake tsaye a kansa ya kuma nunasa da bindigar dake hannunsa. “No! Karka harbesa faɗa min mai kakeso nayi?.” Ta faɗa cikin sanyin muryar tanayin baya tare da yin alama da hannunta shi kuma hamagon ya ɗauka surrender ta yi. Hakan ha sa ya saki dariya yana faɗin. “Da fari ki a je Bindigar dake hannunki sannan sai ki ɗauki wancan wayar ki kira domin a kawo Miliyan hamsin da na buƙata ko kuma yanzu na fasa kanshi.” Ya ƙare maganar yana ma ta nuni da wata landline dake jikin side wall na Ɗakin. Sannan ya tayar da Haisam zaune, yana ƙara sai ta Bindigar a saitin kan Haisam. Yadda ya so ta yi ta hanyar a je bindigar sannan ta fara taka wa domin ƙari sawa wurin da landline ɗin yake, lankwasa yatsarta manuniya ta yi dai dai lokacin kuma suka ji wani ƙara ta waje, da sauri kidnapper's leader ɗin ya kai dubansa ga window'n Ɗakin yayin da Ayusherh ta yi amfani da hakan ta hanyar yin tsalle ɗaya ta ƙari sa inda yake tare da kwace Bindigar ta saitashi, nan fa ya hau zazzare ido, wani sauti ta fitar daga bakinta da hakan ke nuni da tana kiran sojojin, da sauri suka shigo tare da ƙari sawa wurin kidnapper's leader ɗin, ɗaya daga cikin sojojin ya saka ma sa handcuffs, yayin da Ayusherh ta ƙari sa wurin da Haisam yake tare da kwance sa, sannan ta duba ɗaya daga cikin sojojin kana ta ce, Lieutenant Hammad ka sanar a yi preparing abin da ya kamata domin ya sama rauni a gwiwarsa duk da alburushin bai shiga ba. Jinjina kai Lieutenant ya yi sannan ya yi amfani da Communicative device dake kunnensa ya sanar da sauran sojojin dake wurin helicoptern abin da Captain ta faɗa. Taimaka masa ta yi ya miƙe tsaye. “Zaka iya tafiya kuwa?.” Ta faɗa a karo na farko tana ɗa gowa ta dubi fuskarsa shi dama already itan yake duba duk da halin da yake cikin hakan bai hanasa furta. “Battle Angel ba.” a lokacin da idanunsu suka haɗu wuri guda, yadda kasan tafiyar masadar lantarki haka suka ji a tare wani abu ya fito daga idon kowannensu ya shiga na ɗan uwansa. “Oh Bara na taimaka maka.” Ta ƙara faɗa ganin ya buɗe baki sai dai bataji abin da ya faɗa ba. Hannunsa ta ɗaura a kan kafaɗarta sannan ta taimaka masa suka fara taka wa suka fito daga ƙaramin gidan gonar still idanunsa a kanta, ƙari sawa da shi wurin helicoptern nasu ta yi tare da taimaka masa ya shiga ciki sannan ya hau saman madaidaicin treatment Stretcher ɗin sannan ita ma ta shiga cikin helicoptern bayan sauran sojojin sun shiga ne helicoptern ta bar wurin yayin da ɗayan helicoptern da ya zo kuma wasu sojojin ne suka shiga tare da kidnapper's ɗin da suka ji rauni. Da waɗan da basu ji ba har ma da leader nasu. BAYAN AWA UKU. *Aguyi-Ironsi Barracks Cantonment ¹, Asokoro, Abuja.* “Good job, Captain aiki ya yi kyau, fatan nasara, and yanzu Haisam yana can asibiti yana samun kulawar da ta dace su kuma kidnapper's ɗin za su sama hukunci dai dai da abin da suka aikata dan wannan karon sun taɓo ɗan manya, yawwa Mr President ya ce na miƙa masa godiya zuwa gareki keda tawagarki na ceto ɗan sa da kukayi.” General ta ƙare maganar tana miƙe wa tsaye daga kan kujerar office ɗin ta sannan ta duba Captain Ayusherh dake tsaye ta ci gaba da faɗin. “Nima kuma a matsayina da nake tamkar mahaifiya a wurin Haisam na gode bisa ceton Rayuwarsa da kika yi.” Ta ƙari sa maganar tana dafa kafaɗar Ayusherh. “Ba komai Sir wannan ai shi ne aikin namu.” Cewar Ayusherh. “Good.” General ta faɗa. “Permission to leave sir.” Captain Ayusherh ta ƙara faɗa tana sara ma ta. “Okay, You can go.” General ta amsa ma ta fuskarta ɗauke da bayyanannen murmushi. Fitowa daga office ɗin Ayusherh ta yi sannan ta fara tafiya domin ƙari sawa office ɗin ta, ai kuwa da shigarta taga Jasmine zaune, tana waya. Ƙari sa shiga ciki ta yi tare da tsayawa gaban desk ɗin tana tattara wasu files. Bayan ta gama ta miƙa wa Jasmine key na office ɗin tana ma ta nuni da idan ta gama ta rufe office ɗin. Da sauri Jasmine ta katse kiran cikin murmushi ta miƙe tsaye tare da saita tsayuwarta ta wani yi saluting Ayusherhn tana faɗin. “Weldone Captain, you did the good job, gaba ɗaya media ta Hauka ce a kan zancen ki bisa ƙoƙari da kikayi keda tawagarki wurin ganin kun ce to ɗan president.” Ta ƙare maganar tana sakin murmushi. Girgiza kai Ayusherh ta yi tana dafa kafaɗarta ta ce. “Jinjinar ai har dake tun da kema kina cikin tawagar kuma kin bada naki gudunmawar da ta dace.” “Haka ne kam sai dai duka yabon naki ne, saboda badan ke ba da wata ƙila bamu sama nasara a kan ƴan ta'addan ba, by the way naga kina miƙo min key's ba dai gida zaki koma so early haka ba?.” Jasmine ta yi ma ta tambayar tana duban Ayusherh dake tsaye tana saurarenta. “Kwana biyu ban leƙa gida ba, to ina so na biya naga halin da suke ciki ne.” “Okay tohm muje na rakaki in ya so na dawo dan kin san ni a Barrack nake zaune.” Cewar Jasmine sannan ta ƙara da faɗin. “Wata ƙila ma a hanya na sama nishaɗi da zai fitar dani daga bad mood da wancan matar ta sakani.” “Ookay ba damuwa. Wacece haka?.” Ayusherh ta tambaya lokacin da suke ƙoƙarin fitowa daga office ɗin. “Mom ɗita mana, ta nace a kan sai nayi aure a kwanan nan, sam na rasa gane kan ta.” “Ayya, ai hakan ya kamata kiyi auren mana.” Ayusherh ta faɗa tana ƴar dariya. “Lallai ma Captain wato har dake ko?.” Cewar Jasmine tana ɗan kwaɓe fuska. “Ah to naga gaskiya ne.” “Hump kedai bar gaskiyar nan Indai haka take to fa bana buƙatar ta.” ....✨✨ *Nnamdi Azikiwe International Airport* Tsaye take jingine da motarta ƙirar Mercedes-AMG One, waya ce kare a kunnenta yayin da ta ci gaba da faɗin. “Okay ba damuwa, yawwa Arham please ka sanarwa ABAAN Kamasho ya sameni a gidanmu domin bazata nakeso nayi masa.” Ɗan shiru ta yi alamar tana sauraren abin da zai faɗa, sannan ta gyaɗa kai tare da katse kiran bayan sun yi sallama, dai dai kuma ta hango fitowarta, kyakkyawar budurwa ce irin First class ɗin nan tana da kyau irin sosai ɗin nan, sanye take cikin wata iriyar Fitted Gown mai launin ja da kuma adon stones, kafaɗarta kuwa tana rufe ne cikin wani knee high boots, yayin da idanunta ke maƙale da wani arnen round glass, make-up mara hayaniya ne a saman kyakkyawar fuskarta, kusan gaba ɗaya Long straight hair nata a waje yake, a domin yalolon Mayafin da ta yafa wanda da shi kwara babu, bai wani rufe kanta ba. A hankali take taka wa kamar bata taka kasa ba, yayin da take yanje da ɗan madaidaicin suitcase nata da shima launin ja ne, kusan gaba ɗaya shigar jikinta banda gashinta da kuma baƙin Glass ɗin da ta saka kusan komai launin ja ne da shi. Da sauri Yusra ta ƙari sa gare ta tare da yi ma ta side hug tana faɗin. “Oyoyo sister na I missed so much, ina fata kin dawo lafiya?.” Ta ƙare maganar bayan sun saki juna daga rungumar da ta yi ma ta. Ya mutsa fuska budurwar ta yi tana amsa ma ta da faɗin. “Missed You too dear, ki kaini Asibitin.” Ajiyar zuciya Yusra ta sauke jin abin da Nusra ta faɗa, karɓar akwatin nata ta yi, sannan ta a je a back seat na motar, yayin da Nusra ta shiga gaban motar, ita kuma Yusra ta zagaya ta shiga driver seat, sannan ta ja motar suka bar wurin. “Ki kwantar da hankalin ki, Haisam yana lafiya ba wani abu ba ne Babba ya sameshi.” Yusra ta faɗa a yayin da take tuƙin tana ɗan kallon Nusra. Shiru Nusra ta yi dan batajin zata iya furta komai ba tare da taga halin da Haisam yake ciki ba. Ganin haka ya sa ita ma Yusra taja bakinta ta yi gum, suka ci gaba da tafiya. *Nizamiye Hospital: Plot 113, Sector S. Cadastral Zone, Life Camp Abuja, Nigeria.* “Barka Malam Haisam kana iya ganina da kyau kuwa? Ya jikin naka kuma, daure ka tashi zaune.” Doctor ke maganar yayin da yake tsaye gaban gadon da Haisam ke kwance. A hankali yake buɗe idanunsa da suka ɗan yi nauyi sakamakon baccin da ya yi, har ya gama ware su tar a kan fuskar Doctor, ɗaya bayan ɗaya yake duban mutanen dake a room ɗin, yana ƙoƙarin tashi zaunen a ka turó ƙofar Nusra ta shigo tare da ƙari sawa wurin sa da hanzari, gaba ɗaya mutanen room ɗin kallon mamaki suke bin ta da shi domin ba wanda ya san ta dawo Nigeria. Yusra ce ita ma ta shigo da sallama. •… 💕 *CAPTAIN AYUSHERH*🥷 * 🍂🎀 (_The ShieldMaiden._) https://whatsapp.com/channel/0029VaEZtE15a2429vfcpf20 BY - Nainarh KD.... 𝒩𝓀𝒹'𝓈❦♡ Nainarhkd3 @Wattpad. *🔥 Perfectly Pen's (P.P✍️* Episode 14. “Yusra! ke nan dai kece kika ɗaukota? Domin bata faɗa wa kowa zata dawo ba. To amma me ya sa baki faɗa mana ba? Bakya tsoron abin da ya faru da Haisam ya faru ne a kan ku, tun da ba da Guard kika tafi ba, shima kanshi da yake da tarin masu tsaron ba uwar amfanin da suka yi masa ai.” Aunty Dawha wato mahaifiyar Nusra da Yusra ita ke wannan maganar tana duban Yusra da alama ranta ya ɗan ɓaci domin tana gudun abin da ya faru da Haisam su ya same tilon ƴaƴan nata biyu rak. Ita ko Nusra bata bi ta kanta ba, tana ji Yusra na bata haƙuri ita kam ko'a a gefen kyalenta, ƙari sawa ta yi wurin gadon da yake kwance sannan ta zauna a gefen gadon idanunta a kan sa ta fara magana cikin sanyin murya kamar ba ita ba, da alama dai abin da ya samesa ya masifar ɗa ga ma ta Hankali. “Haisam! Kana lafiya? Gaba ɗaya duk na shiga damuwa. Ya jikin naka?.” Ta jero masa tambayar a lokacin da Likitan ya taimaka masa ya tashi zaune, bayan ya buƙaci hakan. Bai yi magana ba sai kallon ta kawai da ya yi, sannan ya mayar da kallon sa ga Daddyn sa Mr President da kuma Mom ɗin sa. “Ina take?.” Abin da ya faɗa ke nan. “Ita wa ke nan?.” Suka haɗa baki wurin tambayarsa. “Battle Angel.” Ya faɗa yana ƙoƙarin tashi tsaye. Gaba ɗaya kansu ya kulle da sunan da ya kira. Wani irin bugawa ƙirjin Nusra ya yi, amma ta daure ta ce. “Wacece haka?.” Haisam bai bata amsa ba ya duba Daddy yana faɗin. “Daddy ba zan iya jira ba zan je na ganta.” “But... Son kana buƙatar hutu fa, ka koma ka kwanta zan kawo maka ita ɗin ko wacece.” Mom ɗin sa ta katsesa da faɗin hakan, duk da har zuwa yanzu bata fahimci wacca yake nufi ba. “No, Mom ba zan iya jira ba, kuma lafiya ta qlau babu abin da ya sameni saboda ita, ta ceci Rayuwata dole naje na ganta.” Ya yi maganar tare da zarar makullin mota dake hannun Daddy sannan ya yi waje. Gaba ɗaya suka bi bayansa har Doctor sai dai ban da Nusra da take jin nan Duniya ba'a taɓa cisgata irin haka ba, kuma wai Haisam ɗin ta ne ya yi ma ta haka, a kan wata ko wacece?. Kasancewar da sassarfa yake tafiyar domin da gaske ba wani sauran ciwo a tare da shi dama Mom ɗin sa ce ta matsa sai an kawo sa asibiti an dubasa a lokacin da Sojojin suka dawo da shi, kasancewar ya suma tun a cikin helicopter domin Haisam yana da wata cuta da baya iya jure hawa wuri mai tsawo ko kuma hawa bene take kansa zai fara juyawa kuma hakan ya samo asali ne tun yana yaro, shi ya sa ko Jirgi a kan dole yake shiga amma ba shi da nutsuwa har sai jirgin ya yi landing. Ƙari sawa wurin motar ya yi tare da buɗe wa ya bata key, bai saurari kiran da Mom ɗin sa ke masa ba, ya ja motar da gudu ya fi ce daga asibitin gaba ɗaya. “Ya Rabb! Ko me ke damun Haisam, wai kuma wacece wannan Battle Angel ɗin ne da yake ta faɗa ne?.” Mom ɗin sa ta yi maganar tana danne ɓacin ranta. “Kar ki damu soyayya ce ba komai ba, ke dai zo muje gida da kansa zai nememu bayan ya ganta.” Cewar Mr President yana dafa kafaɗarta, sai kawai Mom ta bisa da kallo cike da mamakin kalamansa, yayin da Aunty Dawha ta girgiza kai kurum, ita ko Yusra dama bata fito ba ta tsaya wurin Nusra ne. Gudu yake santalawa da motar kamar titin an yi ne domin sa, cikin mintina ƙilalan ya ƙari sa Barrack ɗin. Shigowar motarsa cikin Barrack ɗin bayan security's da suka daɗe da sanin kowane ne shi, sun buɗe masa Gate, hakan ya yi dai dai da fitar motar Ayusherh. Bai gama sai ta parking na motar yadda ya kamata ba, ya fito tare da ɗan yin tafiya kaɗan ya bi ta elevator ya ƙari sa office ɗin General. Ba tare da Kwankwasa wa ba ya shiga ciki yana faman faɗin. “Ammy, where is she?.” General Lamrat dake tsaye gaban shelf ta juya da mamakin jin murya kamar na Haisam, sakin baki ta yi tana dubansa da mamakin ganinsa a dai dai wannan lokacin, Mutumin dake asibiti. “Ah Haisam kai ne anan? Ƙari so ciki mana.” Ta faɗa ganin ya tsaya tsaye tun bayan shigowarsa da abin da ya faɗa. “No, Ammy wurin ta nazo, please kaini na ganta.” A matsayin ta na wacca tasan shi ciki da waje ta fahimci wacca yake nufi, amma ta sha re ta nuna kamar bata gane ba ta hanyar faɗin. “Wacece kuma haka, wai ma ba'a asibiti kake ba, garin ya ya kazo nan?.” Hannu ya zura a aljihu yana juya kai cike da ƙosawa ya ce. “Nifa ba abin da yake damuna, please Ammy ki kaini wurinta.” Tsakani da Allah yake maganar yana roƙonta yadda kasan Ɗa yana neman Mahaifiyarsa. Ajiyar zuciya General ta sauke tare da kiran sunansa ta ƙara da faɗin. “Haisam! Ƙari so ciki please.” Ƙari sawa cikin ya yi tare da zama a kujera yana fuskantar ta. Cikin nutsuwa ta fara magana da faɗin. “Wacece haka kakeson ganinta urgency faɗa min zan taimaka maka.” Ya mutsa fuska ya ɗan yi, domin duk wannan abin da yake ma bai san sunanta ba. “Hump Ammy na faɗa miki gaskiya? To ni ban san sunanta ba, amma ita dai wacce kuka tura ta taimake ni.” Gyaɗa kai Ammy ta yi, ta ƙara faɗin. “Yanzu idan na kira ta mai zaka ma ta ko kuma mai zaka bata?.” Ya saki kyakkyawan murmushi da ya bayyana two points nasa, sai kuma ya rasa abin faɗa hakan ya sa ya damƙe Hannuwansa duka biyun wuri guda. “Kana jina ba, ka fara tunanin abin da zaka bata ko kuma zaka faɗa ma ta sannan sai muga abin da zan iya a kan lamarin.” General ta faɗa tana ɗan sakin murmushi ganin yadda duk ya ruɗe. Shiru Haisam ya yi tare da nutsuwa yana tunanin abin faɗa da kuma dalilin da ya sa ma yake son ƙara Ganinta, wata zuciyar ke faɗa masa, Soyayya ce, ƙauna ce sila, sune maƙasudin da suka saka ya susuce lokaci guda a kan ta. To amma wannan abin nasa ya wuce iya soyayya kamar fa akwai wani abun daban, sai dai mene ne wannan abun?. Shi ne tambayar da ya kasa bawa kansa amsarta. Ya sauke ajiyar zuciya tare da miƙe wa tsaye ya zura hannu a aljihu yana faɗin. “Nothing...” “Ka tabbata?.” General ta tambaya. “Ooo Ammy!! Godiya kawai zan yi ma ta bisa ceton Rayuwata da ta yi.” General ta murmusa tare da faɗin. “Okay! Sai dai kuma an sama a ka si ta riga ta gama aikin ta na yau sai dai gobe.” Haisam ya ɗan cije laɓɓansa domin ba haka ya so ba, sai dai ba komai ai gobe ma rana ce. Juyawa ya yi zai fita. “Dakata mu tafi tare nima gidan na nufa.” Cewar General tana miƙe wa tsaye ta tattara abin da zata ɗauka sannan suka fito tare, motar da ya zo da ita suka shiga, ba tare da security guards ɗin ta suka tafi ba. A hanya ma ba maganar dake fitowa daga bakin Haisam sai a kan Captain da ya raɗa ma suna zuwa Battle Angel. Ita dai General sai mamaki take yi, koda yake wata ƙila lokacin shiriyar Haisam daga duk wasu abubuwan da basu kamata ba ne ya yi, ta silar soyayya, to amma ita Captain da batasan ma yana yi ba, ta ya zai shawo kanta ke nan. Fitowa suka yi daga motar a tare bayan Haisam ya dai dai ta parking motar a wurin adana motoci na gidan. Da gudu Mom ɗin sa dake zaune a main Palo ta miƙe lokacin da suka shigo palon, tare da ƙari sawa garesa cikin damuwa take faɗin. “Haisam! My son ka dawo, babu abin da ya sameka. Alhamdullilah na gode Allah.” Ta yi maganar tana ƙoƙarin rungumo sa. Ɗan baya ya yi yana ƴar dariya ya ce. “Mom! Am fine fa baki gani ba ne, kuma ni ba yaro ba ne ki dena damun kanki a kai na, banason wani abu ya saman min ke, by the way ni zan shiga ciki.” Ya ƙare maganar yana nufar Staircases cikin hanzari aka sin baya da a hankali yake bin stairs ɗin idan zai haura sama ko zai sauko ƙasa, amma yau da sassarfa yake taka stairs ɗin kuma da bibbiyu, ba komai ne sila ba sai ita, tunanin ta ne ya sa bai ma san yana hakan ba. Dawo da kallon ta a kan General da tabi Haisam da kallo tana ɗan murmushi Mom ta yi, tare da faɗin. “Lamrat ki fita harkar ɗa na na faɗa miki idan kuma ba haka ba.” Sai kawai taja gwada tare da kaɗa kanta ta koma ta zauna a inda suka su sameta. Ko ta kanta General bata bi ba, ta bi ta ɗayan staircases ɗin dake gefan wanda Haisam yabi ta wuce zuwa part ɗin ta. A palo ta zubar a tarkacen dake hannunta sannan ta ƙari Bedroom tare da zubewa saman gado tana lumshe ido. A hankali kalmar ta fito daga bakinta. “Wacece ni.” Ta faɗa ƙasa ƙasa cikin wata kalar murya mai cike da rauni da bata nunawa a gaban kowa. Tun shekaru sama da ashirin a kullum kwana nan duniya sai ta yi ma kanta wannan tambayar. Shekaru Ashirin da ɗauriya baya, farkawa ta yi a tsinci kanta a gadon asibiti, sai dai ta manta gaba ɗaya memory nata, ba zata iya tuna wacece ita ko kuma abin da ya faru har ta kasance a gadon asibiti ba, kawai abin da zata iya tunawa shi ne ita ɗin soja ce a wancan lokacin muƙamin ta shi ne; Major General daga haka bata iya tuna komai. Kasancewar koda mutum ya sama shafe war tunani ma'ana ya manta komai nasa, to fa fasaha ko kuma ilimin da yake da shi baya goge wa, a yadda bincike ya nuna ke nan. Likitoci ne a wancan lokacin suka sanar da ita cewar Alhaji Dawud shi ne mijinta sai dai bata taɓa haihuwa ba. Ajiyar zuciya ta sauke tana dafe da kanta da take ji kamar zai rabe gida biyu saboda ta kurawa kanta da ta yi da tunani.... *No. 20, Kubuwa Road, Gwagwalada Abuja.* “Tata!” Ayusherh ta faɗa lokacin da suka fito daga motarta bayan ta faka motar a tsakiyar compound na gidan kasancewar ba daɗewa zatayi ba. Da sauri ta ƙari sa wurin Tata dake tsaye yana bawa flowers ruwa. Murmushi ne ɗauke saman fuskar Tata a lokacin da Ayusherh ta ƙari so wurin da yake tsaye. “Tata nace ka dena wahalar da kanka wurin bawa flowers ruwa mene ne amfanin jibga-jibgan samarin da muke da su a gidan muddun za'a ce kaine zakake bawa flowers ruwa?, kuma ma wai ina security guard ɗin da na a je muku ne a gidan.” Ayusherh ta ƙare maganar tana ɗan ɓata fuska tare da karɓar abin bawa flowers ruwan dake a hannun Tatan tana faɗin. “Kawo na tayaka.” Ta faɗa tana karɓa tare da ci gaba da bawa flowers ɗin ruwa, yayin da Tata ya zuba ma ta ido yana ɗan murmushi. Komai nata sak na mahaifiyarta, sam Mahaifiyarta bata taɓa yarda taga ma'aikatan ta suna wahala. “Tata kana jina kuwa?.” Ayusherh ta ƙara faɗa ganin kamar hankalinsa baya a tare da ita. “Shalelen Tata ya aikin dan na san kuna fama, magana kike a kan sojan da kika a je domin yake tsaron gida ko, ai kuwa Ali da Ma'az sun ɗauke sa sun tafi kasuwa, saboda neman suna.” Dariya Ayusherh ta yi tana ɗan girgiza kai ta ce. “Lallai ma Ali na lura yaron nan zai yi kauɗi.” Tata ya yi dariya kurum. “Oh Tata ga Jasmine fa Abokiyar aikina a soji.” Ayusherh ta faɗa tana nuna Jasmine dake tsaye gefe ta ɗan basu tazara. Kallon Jasmine Tata ya yi yana ɗan murmushi ya ce. “Sannunki Soja fatan kina kular min da Captain ɗin yadda ya kamata.” Jasmine ta yi dariya tana amsa masa da faɗin. “Ai Yallaɓai Captain ɗin mu ta daban ce domin ita ke kula damu ba mu ke kula da ita ba.” Ɗan shiru Tata ya yi shi fa sai yanzu yake ɗan fargaba na abin da zai biyo baya da shigar Ayusherh Soja, gata sak mahaifiyarta a lokacin da take da shekarunta. “Ki kirani da Tata kamar Captain domin kema kin zama ƴar gida.” Cewar Tata yana duban Jasmine. “Woww Thank you Tata I really appreciate.” Jasmine ta faɗa cike da farin ciki tana ƙari sawa inda suke tsaye. “Naji gidan shiru da alama ba kowa ke nan?.” Ayusherh ta faɗa. “E to Kakarku ce kawai a ciki kinsan halin ta batason fitowa waje tana can duƙunƙune a ɗaki. Su kuma Yayankaka da Chanchal sun fita wai salon.” Tata ya bata amsa. Yana girgiza kai. Ayusherh ta ɗan yi murmushi yana mamakin kakartasu ta ce. “Lallai kam Bara to mu shiga ciki wurin mai tsoron mutuwa.” “Ao har dake ko?.” Tata ya faɗa yana ɗan ɓata fuska. “Oh sorry Tata amma Yâ tâ ɗin ce abin nata ba dama.” Ayusherh ta faɗa tana ɓoye dariya. Ita ko Jasmine cike da burgewa take duban ƴa da uban, ta lura akwai shaƙuwa da ƙauna mai tsanani, tsakanin su. Girgiza kai ta yi tana tunanin tana Mahaifin da bata san ma Kalarsa ba. Abin da ta sani shi ne ta taso tare da mahaifiyarta dake auren wani mutum daban wanda ba shi ne ya haife ta ba. *National Muslim Orphanage, Plot 135, Cadastral Zone B02, Wuse II, Abuja.* “Abaan!.” Arham ya kwala ma matashin da ba zai haure shekaru goma sha tara ba, dake tsaye yana duban yara maza na gidan marayun da suke gudanar da wasan ƙwallon ƙafan cike da kwarewa. Juyowa matashin ya yi yana duban Arham da ya ƙari so wurin. “Laa Babban yaya kai ne ta samu ne a ke nema na ko wani abun zan yi a bani Kamasho?.” Ya faɗa yana ƴar dariya. Arham ya ce. “Kai kam dole ma jama'a su saka maka suna Kamasho wannan son kuɗi haka kamar ɗan siyasa.” Arham ya ƙare maganar yana baza sumar kan Abaan dake barbaje mai kyau ga ɗan tsayi, dama ya saba masa haka duk in zasu haɗu sai ya yi ta baza masa gashi, acewar Abaan kuma ɓata masa gyaran gashi Arham ɗin yake. •… 💕 *CAPTAIN AYUSHERH*🥷 * 🍂🎀 (_The ShieldMaiden._) https://whatsapp.com/channel/0029VaEZtE15a2429vfcpf20 BY - Nainarh KD.... 𝒩𝓀𝒹'𝓈❦♡ Nainarhkd3 @Wattpad. _Masoya da masu bibiyar wannan littafi na CAPTAIN AYUSHERH ina ganin saƙonnin fatan Alkhairi daga gare ku kuma ina matuƙar godiya ga ƙaunar da kuke wa CAPTAIN AYUSHERH. THANKS ALOT Dearest..👍🪄✨💞_ *🔥 Perfectly Pen's (P.P✍️* Episode 15.. Abaan ya yi ƴar dariya at the same time yana ɓata fuska na abin da Arham ke masa da gashi. “Ai dole na nema kuɗi muddun ina so na ci gaba da zama ɗan Nigeria domin na lura gaba kaɗan za'a koma masu kuɗin su ne sarakai talakawa kuma bayi.” “Wato haka kake mana fata ke nan?.” “Ah no kawai hasashe nake.” “Okay, saƙo Yusra ta bani na faɗa maka.” Da sauri Abaan Kamasho ya ce. “Allah ya sa na samun kuɗi ne.” Ya yi maganar yana washe baki. Sai da ya sa Arham ya yi ɗan murmushi, wato dai shi Abaan bashi da wani zance sai a kan kuɗi kuma hakan ya samo asali ne tun yana ƙaramin sa ya taso yaro ne mai zafin nema, kuma baya taɓa bari a wulaƙanta shi zai dage ya nema na kansa, kuma shi ɗin Maraya ne gaba da baya, domin a gidan marayun ya girma har ya san kansa bayan ya gama secondary ma bai ƙara shiga wata makaranta ba, acewarsa ya fiye masa ya nema kuɗi kawai, shi ya sa mutane da dama da suka sansa suke kiransa da Abaan Kamasho. “Nima ban sa ni ba, amma ta ce ka sameta a gidansu koma mene ne kaji.” Cewar Arham. “To shikenan an gama babban yaya.” Kamasho ya faɗa yana janye kansa baya, tare da ci gaba faɗin. “woo Babban yaya shikenan kuma ka lalata min gyaran gashin yanzu dole gobe kafin naje wurin Yusra sai na biya na sake wani.” . Washe Gari Ayusherh ce tsaye ita da Lieutenant Hammad a office ɗin General Lamrat Jabir Junaid a dalilin neman gaggawa da ta yi musu sakamakon wani aiki na gaggawa da ya ta so. “Ku zauna mana.” Cewar General tana nuna musu kujerar dake jikin desk da na ta kujerar ke fuskanta, zaman suka yi suna sauraren ta yayin da ta ci gaba da faɗin. “Tun sati kan baya abin yake gudana to ƴan sanda sun yi iyakar bakin ƙoƙarin su wurin ganin sun magance matsalar sai dai abin ya cutura shi ne dalilin da ya sa a ka ɗamka lamarin a hannun mu. Lamarin shi ne an sama rabewar kai ta wurin wasu Matasa masu banbancin ƙabila da har hakan ya zama Babban faɗa kuma har ya jawo ɗayan matashin ɗan wata ƙabilar ya kashe ɗayan ɗan wata ƙabilar daban, to yanzu shi wannan matashin zakuje ku kawo, abin ba sauƙi ne da shi ba, domin shi matashin mugun Tantiri ne ya fasa kan jami'an ƴan sanda biyu a lokacin da suka je kamosa to kubi a hankali.” Ta ƙare maganar tana ɗan damƙe hannunta wuri guda ta ɗaura saman desk ɗin idanunta a kan su. Ajiyar zuciya suka sauke dukkanin su sannan Ayusherh ta ce. “To amma naji kince faɗar ya samo asali ne a kan banbancin ƙabila da suke da har hakan ya kawo rabuwar kai har ya zama silar da ɗan wata ƙabilar ya kashe Abokin rigimar nasa ɗan wata ƙabilar ba, haka ne?.” General ta yi Nodding kai tana faɗin. “Yeah, haka ne.” Jinjina kai Ayusherh ta yi tana ɗan ɗaura hannunta a ɗaya saman desk ɗin ta ce. “To amma a kan wata ƙabila ce duk suke hakan? Ina nufin shi wanda ya yi kisan a wata ƙabila yake sannan shima wanda a ka kashen ɗan wata ƙabila ce?.” General Lamrat ta ɗan yi shiru tana nazarin amsar da zata bawa Ayusherh, baya ta ɗan yi tare da jingina da kujerar da take kai, sannan ta ce. “Da fari ban so na sanar daku gaskiyar lamarin ba amma ya zama dole, a zahirin gaskiya faɗar nasu ba a kan ƙabilanci ba ne sai dai ya yi kama da hakan.” “Kamar ya ya? To amma kuma a kan mene ne?.” Lieutenant Hammad shi ne ya yi ma ta tambayar a yanzu. Ajiyar zuciya General ta sauke kana ta amsa masa da faɗin. “A wannan zamanin rashin ilimi musamman ma na addini ya yi ƙaranci ta ko'ina da hakan shi ne ya zama mussababi ko kuma sila na faruwar wasu abubuwan to kamar hakan take a yanzu shi wannan matashi mai suna Sa'idu ya kasance a yadda bincike ya nuna mana shi ne, ba shi da wani ilimi na addini na a zo a gani shi ne silar da ya sa ya dilmiya kogin ɓata da har ya shiga cikin jerin wasu mutane da suka ware kansu sam babu Allah a zuciyarsu kuma wai a hakan su Musulmai ne a yadda bincike ya nuna hatta salloli ma ware lokacin su suke daban kuma basu taɓa yarda a faɗa musu gaskiya idan ma a ka yi ƙoƙarin hakan sai su fusata, a koda yaushe basu da abin ambata misali bisa tsautsayi wani abu ya samesu a maimakon su kira sunan Allah a'a sai dai aji suna faɗin, 'Shehu, ko kuma Shehu ka taimake mu, a haka suka ɗaura turbar Rayuwarsu kuma suke janyo mutane musamman matasa a ciki an kai ƙorafi zuwa office na ƴan sanda a kan sai dai a na cikin bacci ko kuma an daɗe da yin salar isha'i wuraren tara sai a ji su sai lokacin suke nasu sallar babu ko tsoron Allah. In taƙaice muku wannan suna da suke kira sun ɗauke shi ne tamkar shi ne Allah'n... Astagfurullah...” General ta ƙare maganar tana jan kalmar Astagfurullah domin ita kanta abin wani banbara kwai yake ma ta. Sannan ta ci gaba da faɗin. “To a dalilin hakan ne an sama wani da ya yi musu magana a kan wannan ɓatacciyar hanya da suka ɗauko shi ɗin Malami ne shi ne dalilin da ya sa har abin ya zama faɗa kuma daga ƙarshe Sa'idu ya kashe shi Sannan yaƙi yarda a kama sa domin a yi masa hukunci.” General ta ƙare maganar tare da yin shiru. Yayin da Ayusherh da take jin wannan magana, wani irin yanayi ta tsinci kanta na zallar tashin hankali gaba ɗaya tsigar jininta ya miƙe ta ƙara damƙe hannunta ɗaya dake kan Desk ɗin, da kyar ta haɗiye wani kakkaurar yawu, tana da ilimi na addini dai dai gwargwado domin kafin su bar ƙauyen Mayo-Danay dake Taraba sai da ta yi saukar Alkur'ani mai girma kuma bayan haka tana ilimi dai dai gwargwado ɓangaren sauran littatafai na addini. Lieutenant Hammad ya ja wata doguwar ajiyar zuciya haɗe da faɗin. “To amma mene ne silar du wannan ne, mene ne mafari?.” General Lamrat ta ce. “Mafarin dai shi ne rashin ilimi musamman na addini domin inda akwai ba za'a yi duk wannan ba. Yanzu ga wannan file ɗin a kan lamarin ne ku ƙara nazartarsa kafin ku tafi zuwa kama shi Sa'idun address ɗin inda za'a samesa da komai yana ciki.” Ta yi maganar tana miƙa wa Ayusherh File ɗin kasancewar ita ce ta sama da Lieutenant, sannan ta sallame su. Fitowa Ayusherh ta yi daga office ɗin hannunta riƙe da file ɗin yayin da ta kara wayarta da kira ya shigo a kunne tana faɗin. “Hello 2LT kina ina ne haka?.” Daga ɗayan ɓangaren Jasmine dake driving hankali kwance cikin motar ta sojojin wato Jeep ta yi saurin faɗin. “Hanyar dawowa Barrack naje wani aiki ne.” Ta yi maganar da nutsuwa jin sunan da Ayusherh ta kira ta da shi tasan serious ne. “Okay! Zan turo miki wani address mu haɗu a can.” “Okay shikenan babu damuwa.” Jasmine ta amsa ma ta. Sannan Ayusherh ta katse kiran tare da tura ma ta address ɗin daga nan ta koma office ɗin ta a je file ɗin tare da ɗaukar abin da zata buƙata, da uniform ɗin aiki a jikinta ta fito daga office ɗin sai suka haɗu da Lieutenant Hammad da shima ya gama shirin duk wani abu da za su buƙata. Wannan ya sa suka fito tare da ɗaukar hanyar address ɗin wurin da Sa'idu yake, domin Ayusherh ta ce ba sai sun tafi da sojoji ba kawai dai sun tafi a motarsu mai jiniya ta sojoji. . .. *GA MASU TAMBAYA A KAN WANNAN LITTAFI NA CAPTAIN AYUSHERH, SHIN NA KUƊI NE KO KUMA KYAU NE?, CAPTAIN AYUSHERH DAI LABARIN DA TSAYI DAN BOOK 1 AND 2 NE, TO BOOK 1 SHI NE FREE YAYIN DA BOOK 2 ZAI KASANCE NA KUƊI SAI DAI BAN SAKA DA TSADA BA..👌💓* Sauri sauri yake saukowa daga stairs ɗin sanye cikin Uniform na soji da suka yi matuƙar karɓar sa sun yi masa kyau ba ƙarya, haka har ya ƙari sa saukowa Down ɗin sam shi kam bai ma lura da Mom and Dad ɗin sa dake zaune a Dining Room ba. Ya ƙari sa saukowa yana faman kiran sunansu. “Haisam! Me nake gani?.” Mom ɗin sa ta faɗa tana tashi tsaye daga zaunen da take a dining table tare ƙari sowa palon wurin da yake tsaye yana sakar ma ta murmushi. “Ah mene ne yake faruwa ne.” Maganar Nusra ya tsaya cak sakamakon ganin Hais ɗin ta da ta yi sanye cikin shigar kayan soji kasancewar ya juya ma ta baya ne ya sa ta yi saurin ƙari sawa tana fuskantarsa ta ce. “Hais kai ne kuma a haka?.” Ta faɗa tana nuna dress ɗin jikinsa, sannan ta ci gaba da faɗin. “Ba kaine da bakinka ba kace ba zaka taɓa saka kayan nan ba saboda bakason aikin sojan da Daddy ya nace sai da ka zama to yanzu me ya sa ka saka kayan?.” Ta ƙare maganar tana zuba masa Manyan idanunta. “Saboda ina ra'ayi a yanzu kuma naji ya kamata na fara aikin soja kamar yadda nake a matsayin sojan.” Haisam ya bata amsar kai tsaye tare da ƙari sawa wurin Mom ɗin sa ya ɗan rungumo ta tare da faɗin. “Mom bakice komai ba zan wuce.” Ya faɗa bayan ya raba jikinsu tare da ƙari sawa ya yi ma Dad ɗin sa Alhaji Dawud nasa rungumar. Mom Maimuna har ta buɗe baki zatayi magana sai kuma ta fasa sakamakon haɗa ido da suka yi da Mr President. Nusra ta ƙulu iya ƙuluwa batasan me ya sa Haisam yake shashshareta ba amma zatayi ma tufkar hanci. Tsaban takaici ya sa ta yi juyawarta tare da nufar Bedroom ɗin Yusra dake a nan Down ɗin domin ita ta zaɓa hakan kasancewar ta bata da zafi ba kamar Nusra ba. Tabbas su ɗin ƴan biyu ne amma masu banbanci halaye da Rayuwa. Zaune ta hango ta saman gado ta yi ɗai ɗai ga laptop a gabanta tana sarrafa ta da hakan ne ma ya sa bataji sallamar da Nusran ke yi ba har sai da Nusran ta sake yi, da sauri Yusra ta janye laptop ɗin daga gabanta tare da kashe wa ta a je gefe sannan ta duba Nusra da ta tsaya a tsaye tana yi ma ta wani irin duba. “Ah Nusra ƙari so mana.” Cewar Yusra tana saukowa daga saman Bed ɗin. Ko motsi Nusra batayi ba sai zuba wa Yusra ido da ta yi tana nazarin ta sannan ta ce. “Wani abu ke damunki ya naga idanunki sun yi ja?.” Yusra ta ɗan dakata daga abin da take shirin yi jin abin da Nusra ta faɗa sai kawai ta zuba wa Nusran ido cike da mamakin yau kuma ita ke damuwa da damuwar wani ganin haka ya sa Nusra ta basar. “Yau zan koma Shagona shi ya sa na biyo mu gaisa in zaki wuce office ne sai na rage miki hanya naga duk kusan hanya ɗaya ne.” Cewar Nusra. Yayin da Yusra ta ɗan sauke ajiyar zuciya tana faɗin. “Okay dama a shirye nake Bara sai mu wuce, sannan jiya da dare ban yi bacci ba shi ya sa idanuna suka yi ja.” “Okay.” Shi ne kawai abin da Nusra ta faɗa badan ta yarda ba. Sai dai a yanayinta ba zaka gane ta yardan ko bata yarda ba haka take. Sai a lokacin Yusra ta lura da irin shigar dake jikin Nusran, kamar dai yadda ta sabarwa kanta kuma ya zame ma ta al'ada tana sanye cikin shiga ja komai ja, riga da wando ne Designers a jikinta launin ja sai takalmi Chunky Heel mai launin ja da baƙi a ƙafarta. Yayin da baƙin gashinta da yake straight an yi masa wani gyara tare da launa sa zuwa baƙi da ja ja, ta tufke shi yayin da jelar ya zubo hular Bat ce a kan ta wannan ya sa gashin nata yake a bayyane, yayin fuskarta ta yi ɗau da Make-up ta yi kyau bakin nan ya sha jan baki. Kana Ganinta dai kamar wacca zata tafi Gasar kyau. Nusra ke nan ƴar kwalisa da ta san Sirrin gayu kuma take basa haƙƙinsa yadda ya kamata koma fiye. A yanzun International Model ce ita kuma Fashion Designer har makeken Shop na siyar da sarƙoƙi da gwala-gwalai gareta na ƙashin kanta kasancewar ta Mace da batasan ta jira a yi ma ta wani abu ba, tana daga cikin ƴan mata young millionaires dake nan garin Abuja. Bayan shagon gwala-gwalai dake gare ta har wani ƙaton Mall gareta na kayan Ado kama daga Takalma Jakun-kuna Riguna Designers da sauransu. Ɗabi'ar Nusra ce saka Jar kala, duk wata suturarta ja ce koma ba duka ne ja ba to fa zaka sama dole akwai launin ja a jiki in ma babu ja to akwai baƙi, ita ra'ayinta ke nan, Nusra ta kasance cikin mutanen da basu iya ƙarya ko kuma shakkar faɗan koma mene ne a gaban kowa ba kai tsaye abin da ke bakinta take furtawa ba ruwanta ko ya yi maka daɗi ko a ka sin hakan. Fitowa suka yi bayan sun yi ma Momyn su sallama dama already Mr President da kuma Mom Maimuna sun wuce kasancewar Mom Maimuna ita ɗin Political Social assistant ɗin Mr President ta musamman ce. Sai da Nusra ta a je Yusra a Bank ɗin da take aiki sannan ta wuce zuwa Shagon siyar da gwala-gwalan ta domin shi ta fi bawa muhimmanci. _Please ku faɗa wa wannan mai jar kayan gaskiya 😂 Hais bata ita yake ba 🤣_ _Ta ɓangaren su Captain Kuma ko ya zata ƙarke?? Mu haɗu a feji na gaba domin sanin yadda zata kaya.✨✨_ •… 💕 *CAPTAIN AYUSHERH*🥷 * 🍂🎀 (_The ShieldMaiden._) https://chat.whatsapp.com/IV4urJf4kuL7656LTR8Zj5 BY - Nainarh KD.... 𝒩𝓀𝒹'𝓈❦♡ Nainarhkd3 @Wattpad. *🔥 Perfectly Pen's (P.P✍️* Episode 16. GIDAN SARIN KAYA!!🔥🥳🤩 Hajiya shin kin gaji da siyan zannuwan gado suna koɗewa suna yin gashi? To ki garzayo wajen MAMAN AFRAH domin siyan masu inganci, babu kalar zannuwan gadon da babu a wajenmu. Idan kuma kin gaji da zama babu sana,a ne ki zo in baki sarin zannuwan gadon a farashi mai rahusa ki ɗora ribarki domin sana,ar ana samun alkairi sai kin gwada. Ina wacce ta gaji da siyan turarukan wuta masu ƙauri a garwashi, Ina da turaren wuta mai ƙamshi da daɗewa a ɗaki, idan kuma sana,ar turaren wutar kike ina bada farashin sari ina aikawa duk inda kike. Akwai humra mai musulmin ƙamshi da zaunawa a jiki, wacce nake wa laƙabi da sumar da mai gida don ƙamshi. Muna da Toilet cleaner in har toilet ɗinki ya dafe baya fita to ki gwada namu idan kika siya babu ruwan ki klin wajen wanki kumfa yake ya wanke bayi fesss ga ƙamshi da yake yi ɗaya za ki siya ko sari duk muna bayrwa. Akwai freshner mai ƙamshi, turaren wanka luquid soap, izal hypo, duk ina bayarwa sari a farashi mai rahusa. Ina wacce ta gaji da siyan shampoo da man kitso wanda bata ganin cigaba a gashin kanta da na ƴaƴanta? Gashin kamar gashin doki babu laushi sai tauri kina tajewa yana miki zafi, ki samawa gashinki da na yaranki mafita. Muna bayar da sari🥰 Akwai cotton material da lesuka da atamfofi siyan ɗaya ko sari. Tuntuɓe ni a wannn lambar 09013181851 -----------🙏______! Episode 16. AYUSHERH! Fitowa suka yi daga motar lokacin suka ƙari so Anguwan ta faka motar a saitin inda motar Jasmine ke fa ke, yayin da Jasmine ɗin take zaune saman motar tana latsa waya. Ƙari sowarsu Ayusherh shi ne ya sa ta sauko tare da ƙari sawa inda suke tsaye jikin Jeep ɗin da suka zo a ciki, tana murmushi ta ce. “Da alama aiki na musamman ne ya kawo Captain wannan area da kanta.” Ta faɗa a yayin da ta ƙari sa wurin tana fuskantarsu. Miƙa ma Lieutenant Hammad iPad ɗin dake hannunta Ayusherh ta yi tare da cire Farin Glass dake idanunta tana kallon Jasmine fuskarta ba walwala ta ce. “Ya a ka yi naga Anguwan ya lashe ne kamar ba masu rayuwa a ciki?.” Ta tambaya tana ɗan duban yanayin Anguwan da tafi kama da na masu ƙaramin ƙarfi. Ita ko Jasmine lura da yanayin da Ayusherh take ciki ne ya sa ta ce. “Nima dai haka nazo na tarar sai dai na sama wasu mutane da na tambaye su dangane da hakan sai cewa suka yi kowa yana gida ne a sakamakon abin da ya faru wai har shima Sa'idu wanda ya yi kisan yana gida Mahaifiyarsa ta ɓoye sa. So I was very confused saboda ban san mene ne yake faruwa ba.” Jasmine ta ƙare maganar tare da ɗa ga kafaɗa. Jinjina kai Ayusherh ta yi domin zuwa yanzu ta fahimci ainihin daga ina matsalar ta samo Asali. “Yanzu ya kake ganin za'ayi?.” Ta faɗa tana duban Lieutenant Hammad domin jin ra'ayinsa. “A gaskiya Captain bani da abin faɗa saboda lamarin yafi ƙarfin kaina na rasa ta yadda zan lissafi al'amarin.” “a, ah kai nifa kun ƙara sakani a ruɗani wai mene ne yake faruwa ne wanene shi Sa'idu yake ko wa?.” Cewar Jasmine tana kallonsu su duka. “Karki damu zan miki bayani.” Ayusherh ta faɗa tare da buɗe Jeep ɗin da suka zo a cikinta ta ciro wata madaidaiciyar loud speaker. “Ina ga wannan hanyar ce mafi sauƙi a garemu.” Ta faɗa tare da ɗan bubbuga hannunta a kan loud speaker ɗin sannan ta kai saitin bakinta ta ɗan yi gyaran murya tare da fara magana kamar haka. “Assalamu Alaikum Jama'a!. Ga waɗan da basu san ni ba, sunana AYUSHERH jami'ar soja muƙamin Captain. Nazo ne tare da abokan aikina Lieutenant Hammad da kuma Second Lieutenant Jasmine a domin tafiya da Sa'idu domin yanke masa hukunci dai dai da abin da ya aikata. Ku daure ku bamu haɗin kai ku fito a yi abin nan a gaban kowa, ku sani yanzu ba lokacin da jahiliyya ba ne da kuna da sani a kan komai amma kuke takewa kuma kuke ƙoƙarin kare masu laifi. Shi wannan matashi Sa'idu tun farkon fari abin da ya yi ya cancanci mummunar hukunci a kai ta fuskar addini da na hukuma amma ba'a yi komai ba, ban sani ba su Malaman Addinin bacci suke ne har haka ke faruwa ko ya ya ko kuwa su Jami'an hukumar basu sama horon da ya da ce ba ne har haka ke faruwa, abin takaici wai a ce har jami'an ƴan sanda ne za'a sama gama garin mutum ya fasa kansu da kwalba kawai dan sun zo tafiya da shi a kan laifi da ya yi. Hummp a ajiye duk waɗan nan a gefe kuyi wa Allah ku fito sannan ku bani amsar tambaya ɗaya tal da zan yi muku a kan wannan bawan Allah Sa'idu, daga nan ni da kuma ku sai a tattauna yadda ya kamata a yi masa.” Ayusherh ta yi shiru bayan ta kawo nan a zancen ta sannan ta a je loud speaker ɗin a saman Jeep ɗin. Tana mayar da Farin Glass ɗin da ya kasance a wasu lokutan yana taimaka ma ta wurin gani a dalilin wasu lokutan da take da matsalar gani hakan ya samo asali ne shekarun baya da suka gabata. “Hump bana tunanin mutanen nan za su bamu haɗin kai da ya kamata..” Cewar Lieutenant Hammad sai dai kafin ya rufe baki a hankali kuma cikin sanyin jiki mutane maza da mata yara da manya na Anguwan suka fara fitowa daga gidajensu kan ka ce kabo duk sun fifito tare da kafa layi a jere daga yanayin duban da suke ma su Ayusherh kamar a ce ƙyat su arce zaka fahimci a ɗan tsorace suke. Lura da haka ya sa Ayusherh ta yi wa Lieutenant Hammad alama da ya ɗauki loud speaker ɗin ya yi musu magana. Hakan kuwa ya yi, ya ɗauki loud speakern tare da fara magana kamar haka; “Ku saki jikinku domin mu ba mun zo nan ne domin cutar daku ba sai dan kare ku da kuma kama Mutum mai laifi daga cikinku amma sai da haɗin kanku.” Dai dai ya ƙare maganar idanunsa suka sauka a kan wata dattijuwa dake zaune gefe ta rafka uban tagumi ta yi jigum hankalinta ma ba'a kansu yake ba. Miƙa ma Ayusherh loud speaker ɗin ya yi sannan da ido ya yi ma ta alama da Matar. “Kafin nace wani abu zan so sanin wacece wancan Matar?.” Ayusherh ta faɗa muryarta raɗau ta loud speakern tanayi musu nuni da dattijuwar. Sai dai kaf cikin mutanen wurin an rasa mai zarrar da zai yi bayani har sai da ta maimaita amma shiru. Ganin haka ya sa ta sauke ajiyar zuciya sannan ta fara taka wa ta isa ga matar tare da ɗan tsugunna wa tana duban Matar ta ce. “Madam lafiya kuwa? Zamu iya sanin ko meke faruwa?.” Ta faɗa cike da kulawa. Sai dai shiru ba amsa daga matar. Ayusherh zata maimaita abin da ta faɗa taji murya daga bayanta ana faɗin. “Mama tsohuwa ce ita ce Kaka a Wurin Malam wanda Sa'idu Azzalumi ya kashe.” Ayusherh ta yi saurin juyawa tana duban yaron da bai haure shekaru goma ba ya yi maganar yayin da bai ƙari sa ba Mahaifiyarsa ta yi saurin toshe masa baki. “uhump ina sauraren ka mene ne ya faru ta kasance a haka?.” Cewar Ayusherh bayan ta ƙari sa wurin tanayiwa Mahaifiyar nasa wani irin duba, ganin uwar taƙi sakin ɗan ne ya sa Ayusherh ta ce. “Ci gaba ki ci gaba da hanasa faɗan gaskiya har har zuwa yadda ya yi miki, ina mai tabbatar miki daga samun uwa irin ku ne da ba za su ƙara ma yara kwarin gwiwa ba sai dai su hana su faɗar gaskiya to daga haka ne a ke samun al'umma a jirkice saboda tun farkon fari ba'a nuna musu faɗar gaskiya shi ne ba.” Girgiza kai Matar ta hau yi yadda kasan ƙadangare na neman manja, sai kuma ta yi saurin sakin bakin yaron da ta rufe da hannunta ai kuwa yaro kamar jira yake ya ci gaba da faɗin. “Ta ce ba zata ƙara magana ba muddun adalci bai samu ba daga kashe ma ta jika da Sa'idu Azzalumi ya yi.” “Wanene shi jikan nata kuma me ya sa a ke kiransa da malam sannan mene ne ya sa shi wannan bawan Allah Sa'idu ya kashesa?.” Ayusherh ta jero ma yaron tambaya. Ai kuwa ya wage baki tare da fara bata amsa dalla dalla. “Saboda Sa'idu ya kasance yana abin da ba dai dai ba kuma addini bai koyar ba shi ya sa Malam wato jikan Mama tsohuwa ya yi ƙoƙarin ganin ya ganar da shi gaskiya shi kuma Sa'idu ya fusata a cewarsa ya mayar da shi jahili shi ya sa ya zo masa da maganar, wannan abu ne ya kai su ga faɗa kuma laifin azzalumi Sa'idu ne kuma shi ne ya kashe mana Malamin mu na islamiyya a tsakiyar Anguwan a gaban mutane kuma ba wanda ya ɗauki mataki shi ne Mama tsohuwa ta shiga damuwa a kan haka Likita ma ya ce tana da hawan jini da ciwon zuciya.” Yaro ya ƙare maganar yana sheshsheƙa. Da sauri Ayusherh ta ciro Handkerchief ɗin daga aljihu ta ɗan goge ma hawaye sannan ta ce. “Yaro mene ne sunanka?.” “Sunana Muhammad Khabir.” Yaron ya bata amsa. “Ma sha Allah, zaka iya nuna min gidan su Sa'idun?.” Jinjina ma ta kai yaron ya yi alamar e. Ayusherh ta kamo hannunsa sannan ta duba mutanen tana ɗan girgiza kai ta ce. “Kuna da buƙatar canji a kankin kanku kafin na sama daku su gyara.” Ta faɗa tare da yin gaba abin ta tare da yaron suka nufa gidan, yayin da Jasmine da Lieutenant Hammad suka mara ma ta baya. Suma mutane masu son ganin kwakwaf da waɗan da jikinsu ya yi sanyi suka mara musu Baya. Ƙaton gida ne da alama irin gidan yawan nan ne?. Tsayawa suka yi a tsakiyar gidan Jasmine ta miƙa ma Ayusherh loud speakern sannan Ayusherh ta ɗan yi gyaran murya batace komai ba. Sai mutanen gidan kowa ya fara fitowa daga ɗaki suna yo waje. Daga ƙarshe wata ƴar duma-dumar mace ta fito hannunta janye da wani matashin saurayi da tana jansa yana boƙarewa shi ga ɗan banza. Tsayawa matar ta yi ƙerere gaban Ayusherh riƙe da ƙugu sannan ta nuna matashin saurayin ta ce. “Ga Sa'idun nan kuma naga mara kunya da kishin addinin da ya isa ya taɓa min ɗa, arnan banza kawai!.” Ta ƙare maganar da jan dogon tsuka, a fusace Lieutenant da Jasmine suka yi kanta, amma Ayusherh ta dakatar da su, sannan ta yi ma matar duban tsanaki kafin ya ɗan taka kaɗan ta isa ga matar ta ce. “Baiwar Allah ba hayaniya ne ya kawo mu ba, sannan ba mun zo ne mu tafi da Sa'idu ta ƙarfin tuwo ba, a tsanaki zamuyi komai. Baiwar Allah ki saurareni magana fa a ke ta addini shin wai ke da kunnen ki kika taɓa ji ko karantawa a Alkur'ani mai girma ko kuma a sauran littafai a inda a ka halasta musulmi na kwarai ya yi abin da ɗan ki ya aikata?. Laifukan nasa da yawa kuma masu tsauri ne duka na farko tsakaninsa da Ubangiji ne mahalicci da ya haɗa sa da wani bayanshi bayan kuma ya san hakan mummunar saɓo ne koda yake a wannan zamanin mutane da yawa basu ɗauki hakan a komai ba domin a zahiri Akwai masu yin irin abin da yake yi wai kuma da sunan su Musulmai ne, ni dai kam a'iya sanina babu wani littafi na addini ko kuma wata sura ko Annabi da a ka aiko a kan mutane irin ɗan ki suyi abin da suke aikatawa. Musulunci bai koyar damu haka ba, to amma son zuciya irin namu na ɗan Adam yana sakawa ana ganin gaskiya amma a take ta, sai kuma laifi na biyu da ɗan ki yayi shi ne kisan kai, a musulunci kisan kai Babban laifi ne da kai tsaye zai kai mutum zuwa wuta, gashi ɗan ki ya aikata ke kuma kin goya masa baya, har kike kiran mu da arna bayan kuma a addini kafirta musulmi shima Babban laifi ne, amma duk kin take wannan, to wai a hakan ne har kike gadara da kinason ɗan ki bayan sanin kanki ne a yanzu da zai mutum duk da bana da sani a kan gaibu amma da wuya ba wuta zai shiga ba, kiji tsoron Allah Baiwar Allah ki tuna ke musulma ce kuma uwa, yanzu abin da kika yi kinyiwa wannan Baiwar Allah mahaifiyar Malam adalci inda a ce baƙin cikin abin da ɗan ki ya yi, zai saka a mutu a yanzu to fa alhakin rayuka biyu a kan ɗan ki zasu kasance kuma har da ke kanki saboda ke kika mara masa baya.” Zuwa yanzu jikin Matar ya yi mugun sanyi da har maganganun Ayusherh suka saka taji bata kyauta wasu ma daga mutanen dake tsai-tsaye sai da suka zubar da hawaye. “Kuyi haƙuri Dan Allah nasan ban kyauta ba amma sharrin shaidan ne da kuma mahaukaciyar ƙaunar da nake ma ɗana da ya kasance shi ɗaya ne ɗana namiji kuma daɗi da ƙari da bakinsa ya ce min wai a mafarki yaga Ma'aiki Sallallahu Alaihi Wasallama, to nima kuma naga ai idan mutum yaga Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallama a mafarki ana masa kyakkyawan zato da samun aljanna shi ya sa naƙi yarda ɗana ya aikata abin da a ka ce ya yi kuma naƙi yarda a yanke masa hukunci na ƙeƙashe idanuna ina zuba rashin mutunci ga kowa amma Dan Allah kuyi haƙuri.” Matar ta ƙare maganar tana durƙusa gwiwowinta ƙasa cikin zubda hawaye. Girgiza kai Ayusherh ta yi, kana ta ce. “bamu ne zaki bawa haƙuri ba, da fari ki fara neman yafiyar Allah sannan ita ma mahaifiyar Malam ki nema yafiyarta. Shi kuma Malam Allah yaji ƙan sa da rahama.” Gaba ɗaya Jama'an wurin ne suka amsa da Ameen!!! Sannan Ayusherh ta dubi Matashi Sa'idu, da ya yi tsuru a wurin. “Ba zan ce maka komai ba, sai dai na tuna maka da kaji tsoron Allah.” Ta faɗa kana ta yi shiru. Sa'idu bai ce komai ba ya duƙƙar da kansa ƙasa haƙiƙa ya yi danasani na abubuwan da ya aikata sai dai danasanin ya kasance mara amfani saboda lokaci ya riga ya ƙure. Hannu biyu ya miƙa, alamar ya yi surrender. Ganin haka ya sa Lieutenant Hammad ya ciro handcuffs sannan ya saka masa. Darewa mutane suka yi suka basu hanyar fita. Waje suka fito Ayusherh ta ƙari sa gaban Matar da ta miƙe tsaye ganin an fito da Sa'idu. “My condolence about your Grandchild. In sha Allah za'a yanke ma Sa'idu hukunci dai dai da abin da ya aikata.” Ayusherh ta faɗa cikin sanyin murya bayan ta dafa kafaɗar Matar. Rasa abin faɗa ya sa Matar ta rungumo Ayusherh tana hawaye. Wani irin yanayi Ayusherh ta tsinci kanta domin tun da take a rayuwarta wannan shi ne karo na farko da wata mata uwa ta rungume ta har haka, kuma cike da ƙauna, sai ta tsinci kanta a yanayi mara misaltawa, soyayyar Mahaifiya tabbas daban yake da komai. Murmushi Ayusherh ta sakarwa Matar sannan ta ƙari sa wurin Yaro Muhammad Khabir ta dube sa ta ce. “Haƙiƙa kayi dacen mahaifiya da take ƙaunar ka kuma take gudun abin da zai sameka, ka riƙe da kyau kaji kuma ka bata kulawa ka nuna ma ta ƙauna fiye da yadda take maka saboda Mahaifiya daban take da kowa da kuma komai kaji?.” Jinjina kai yaron ya yi sannan ya ce. “To Anty Amma ina fata kema haka kike ma mahaifiyarki?.” Ayusherh ta ɗan yi jim da jin tambayar da ya yi mata, sai ta girgiza kai tana ɗan shuke baki ta ce. “Bani da mahaifiya, domin an faɗa min a lokacin da ta haifeni ta rasu, amma ina matuƙar ƙaunar ta kuma nayi kewarta sai dai a koda yaushe na tuna ta ina Kasancewa ne mai yi ma ta addu'a a koda yaushe.” Yaron ya yi shiru yayin da mutanen wurin jikinsu ya da ɗa sanyi. “To na bar miki Mahaifiyata daga yanzu ta zaman Mahaifiyarmu mu biyu dama ta ce tanason ƴa Mace sai dai bata ita daga yanzu kin ga ita ma mamana ta sama ƴa ko? Kuma muma mun sama soja a gidan mu.” Maganar yaron ta bawa Ayusherh dariya da kuma tausayi. Sai kawai ta ce. “Ai kuwa na gode kuma naji daɗi ina fata Maman zata karɓa sabuwar ƴar nata.” Ayusherh ta ƙare maganar tare da saita tsayuwarta. “E mana ko Mama ina ce zaki karɓe sabuwar ƴar ki soja?.” Jinjina mai Mahaifiyar yaron ta yi alamar e. Ayusherh ta ɗan yi murmushi zatayi magana Jasmine ta ce. “Woww kuma fa zakuyi kyau as a family, please Captain ɗan gyara nayi kuma hoto.” Ta faɗa da ɗan magiyarta. Murmushi kurum Ayusherh ta yi sannan ta gyara suka saitu, ita da Matar da kuma yaron ai kuwa Jasmine ta kafta musu photo. Daga haka ita ma Ayusherh ta yi musu selfie kala biyu ɗaya har da Jasmine, ɗaya kuma banda ita. Daga haka dai suka saka Sa'idu a motar da Ayusherh tazo ita da Lieutenant Hammad. Lieutenant ne ya ja motar yayin da Ayusherh ta shiga motar da Jasmine take daga nan suka bar Anguwan. _NOTE; Ba wai an ƙirƙira wannan ɓangare na Sa'idu ba ne ba wai domin cin mutumci ga wani ko wata. An yi ne duba da ganin irin makamacin abin da Sa'idu ke yi da wasu daga cikin mutane suka ɗauka suna yi ne bayan su da kansu sun san hakan ba dai dai ba ne. Muna fata za'a gane kuma a gyara, idan ma anga wasu sunayi sai a samesu domin sanar da su gaskiya idan ma hakan ba zai yiwu ba, a sama Malami na addini kuma na kirki a faɗa masa domin yaja masa kunne. Daga ƙarshe, Dan Allah Iyaye mata a dage a kan tarbiyyar yara domin su ne manyan gobe, makarantar nan idan sun je a ke kulawa da abin da suke yi dama yanayin hulɗar su da sauran yara Sa'anninsu, a wannan zamani da komai ya gurɓace bai kamata ake barin yara kara zube ba;;;; Allah ya sa mu gyara gaba ɗaya._ _Sannan mu haɗu a next page domin sanin yadda zata kasance. Kar fa a manta har yanzu Captain ɗin mu bata haɗu da Haisam namu na zamani ba 😂 Ni kaina na ƙosa su haɗun domin ganin yadda zata kasance 😆🔥_ Ga masu wani ƙorafi ko son magana dani zasu iya tuntuɓana ta lambar what'ssapp ɗina kamar haka; 08081129487 ko kuma 07067953066. Nainarh ce ƴar mutan KD na gode. 🥰🪄💝🌷🥀 •… 💕 *CAPTAIN AYUSHERH*🥷 * 🍂🎀 (_The ShieldMaiden._) https://chat.whatsapp.com/IV4urJf4kuL7656LTR8Zj5 BY - Nainarh KD.... 𝒩𝓀𝒹'𝓈❦♡ Nainarhkd3 @Wattpad. *🔥 Perfectly Pen's (P.P✍️* Episode 17. GIDAN SARIN KAYA!!🔥🥳🤩 Hajiya shin kin gaji da siyan zannuwan gado suna koɗewa suna yin gashi? To ki garzayo wajen MAMAN AFRAH domin siyan masu inganci, babu kalar zannuwan gadon da babu a wajenmu. Idan kuma kin gaji da zama babu sana,a ne ki zo in baki sarin zannuwan gadon a farashi mai rahusa ki ɗora ribarki domin sana,ar ana samun alkairi sai kin gwada. Ina wacce ta gaji da siyan turarukan wuta masu ƙauri a garwashi, Ina da turaren wuta mai ƙamshi da daɗewa a ɗaki, idan kuma sana,ar turaren wutar kike ina bada farashin sari ina aikawa duk inda kike. Akwai humra mai musulmin ƙamshi da zaunawa a jiki, wacce nake wa laƙabi da sumar da mai gida don ƙamshi. Muna da Toilet cleaner in har toilet ɗinki ya dafe baya fita to ki gwada namu idan kika siya babu ruwan ki klin wajen wanki kumfa yake ya wanke bayi fesss ga ƙamshi da yake yi ɗaya za ki siya ko sari duk muna bayrwa. Akwai freshner mai ƙamshi, turaren wanka luquid soap, izal hypo, duk ina bayarwa sari a farashi mai rahusa. Ina wacce ta gaji da siyan shampoo da man kitso wanda bata ganin cigaba a gashin kanta da na ƴaƴanta? Gashin kamar gashin doki babu laushi sai tauri kina tajewa yana miki zafi, ki samawa gashinki da na yaranki mafita. Muna bayar da sari🥰 Akwai cotton material da lesuka da atamfofi siyan ɗaya ko sari. Tuntuɓe ni a wannn lambar 09013181851 -----------🙏______! Episode 17. Da ƙari sawarsu Barrack ɗin fitowa suka yi bayan kowannen su ya yi parking a wurin da ya dace. Lieutenant Hammad ne ya tasa ƙeyar Sa'idu zuwa ciki. Yayin da Ayusherh ta juya baya tana amsa kiran waya da ya shigo ma ta, ita kuma Jasmine tana tsaye daga gefanta jira take ta amsa wayar su ƙari sa ciki. Kammala wayar Ayusherh keda wuya ta juya domin tayima Jasmine magana shi kuma a dai dai lokacin ya ƙari so wurin, tun shigowarsu cikin Barrack ɗin yake tsaye yana kallonsu har ta fara wayar da kuma zuwa yanzu da ta gama ta juya kai tsaye idanunta suka faɗa cikin nasa idanun ya yi tsaye yana kallon ta tare da sakar ma ta wani tattausan murmushi, ita ko Ayusherh da abin ya zo ma ta a bazata sai ta yi zuru ta kuma kasa cire idanunta cikin nasa sai ƙif-ƙifta idanun take, Lieutenant Hammad da ya dawo wurin ya buɗe baki yana shirin magana sai ya fasa ya tsaya ganin ikon Allah kamar yadda ita ma Jasmine ta maƙale cike da mamaki. Ayusherh ƙoƙari take ta tuna inda tasan wannan fuskar amma kafe ta da ido da ya yi yasa ta rasa ta inda zata fara tunanin. “I like you.” Ya faɗa ba tare da ya cire idanunsa a cikin nata ba. Sai idanunta suka ƙara girma jin kalmar da ta fito daga bakinsa, kafin ta yi wani yunƙuri ya ƙara faɗin. “Yes! Da gaske nake ina son ki.” Ya faɗa tare da ɗan ja baya, sai kawai Ayusherh ta tsinci kanta da galla masa harara sannan ta yi gaba, da sauri Jasmine ta bi bayanta dan tun kallon farko da ta yi masa ta gane Haisam ne, sai dai mamakinta bai wuce na ganinsa da uniform na soji ba. “Hararar ma kyau take ƙara ma ta, ya Ubangiji ina ƙaunar wannan Baiwar taka.” Ya faɗa yana ɗan shafa ƙeyarsa fuskarsa tab da annuri. Sun fito daga elevator Jasmine tana shirin yin magana suka ji wata murya a ta bayansu an yi magana. “Captain ko?.” Jin abin da a ka faɗa ne ya sa su duka suka juya da mamaki don ganin wanene, idanunsu ya sauka a kan wani ƙyamurarren Mutum sai dai kana ganinsa kaga ƙaƙarfa uniform ne na soji a jikinsa. “..shi ne fa Lieutenant General (LT GEN) mataimakin General Lamrat.” Jasmine ta faɗa ma Ayusherh ƙasa ƙasa. Jinjina kai Ayusherh ta yi tare da faɗin. “Hello Sir.” Bai yi magana ba sai ido da ya zuba musu na ƴan sakanni sannan ya jinjina kai tare da faɗin. “Hello Captain ya fama?” Ayusherh suka kalli juna sai ta amsa da faɗin. “Alhamdullilah.” Duk da cewar ta ga sunan shi ba musulmi ba ne. Ka ɗa kai ya yi sannan ya zagaye su ya wuce duk suka bi shi da kallo. “Lieutenant General Daniyal Adeola.” Suka faɗa sunan nasa kusan a tare. Sai kuma Ayusherh ta girgiza kai domin ita tun zuwanta Barrack ɗin bata taɓa haɗu wa da shi ba sai yau, office ɗin General Lamrat suka shiga bayan sun nema iznin shiga an basu. Tsaye suka hangota gaban wasu frames masu ɗauke da hotunan sojoji iri iri ta zuba musu ido, tana duban kowanne kamar tanason gano wani abu a tattare da pictures ɗin. Shigowarsu ne ya sa ta juya tare da komawa mazaunin ta ta zauna tattaunawa suka ɗan yi kaɗan game da aiki sannan General Lamrat ta ƙare maganar da faɗin. “Akwai Lieutenant General Daniyal Adeola yau ya dawo bakin aiki bayan shafe watanni bayan dakatar da shi da a ka yi bisa wani al'amari da ya faru, to in anjima idan za'ayi meeting zai gabatar da kansa a gareku.” “Okay tohm Allah ya kai mu.” Ayusherh ta faɗa suna miƙe wa, sannan suka nema izinin fita kana suka baro office ɗin suka koma na Ayusherh. Jasmine da kamar jira take su shiga office ɗin ta fara faɗin. “Woww Haɗaɗɗen Handsome haka amma nayi mamakin kasancewar sa soja.” Ta faɗa tana ɗaura hannu a fuskarta cike da zumuɗi. “Wanene kuma haka?.” Ayusherh ta faɗa a fizge tamkar bata gane wanda Jasmine take magana a kai ba. Jasmine ta juya tana fuskantar Ayusherh da ta zauna a kujerarta da mamaki. “Haisam mana.” Jasmine ta bata amsa sannan ta ƙara da faɗin.“Ai ina baki shawara kyauta Captain muddun da gaske yake yi to fa ki amince kawai dan kuwa samun mutum kamar Haisam data ko'ina ya yi 101% zai yi wahala, shi dai ga kyau ga ilmi kuma sananne gashi daga babban gida, Kai kai abin da yawa fa.” Jasmine ta kai maganar tare da zama bisa kujerar dake fuskantar Ayusherh har da wani lumshe ido. Bagarar da zancen Ayusherh ta yi ta hanyar ɗauko wani zancen daban, duk kuwa da yadda Jasmine taso a ci gaba da zancen Haisam. Ita ko Yusra ko bayan Nusra ta a je ta bank da take aiki, bata fi mintina talatin ba ta fito daga bank ɗin sannan ta hau cab ya kaita can wani restaurant sai kawai ta zauna a can ta ci gaba da aikin da take yi ta cikin Laptop ɗin ta, bata fi mintina goma da zama ba wanda take jira ya ƙari so kamar yadda suka tsara ya bata bayanan da suke a hannunsa, sun kai minti goma suna tattaunawa kafin daga bisani ya tafi... ita kuma sai da ta gama komai sannan ta bar restaurant ɗin kai tsaye gida ta wuce domin su haɗu da Kamasho kamar yadda ta ce ya sameta a gida sannan ta gefe guda wannan binciken da take yi gaba ɗaya ya sakar ma ta da jiki ita kanta bata san ya ya ƙarshen zai kaya ba sai dai jikinta ya yi sanyi da abin da ta fara ganowa dangane da Kawun nata Mr President. Ayusherh da yammaci lokacin ta fito domin tafiya gida dan ta gama aikinta na yau, ƙari sawarta wurin da ta yi parking motarta sai kawai ganinsa ta yi zaune a kan motar yana sakar ma ta wannan murmushin nasa. Ɗan dakatawa ta yi da tafiyar cike da mamaki take dubansa sai kuma ta sha re tare da ƙari sawa wurin motar kafin ta ce wani abu ya riga ta da faɗin. “Barka da ƙari sowa Battle Angel a taimaka a kula wannan ƙaramin masoyin da soyayya ta gama wujijjiga zuciyarsa da ruhinsa.” Ya yi maganar yana dai dai ta tsayuwarsa bayan ya sauka daga motar sai ya zamana a halin yanzu suna fuskantar juna shi da ita. “Zan iya wuce wa?.” Ayusherh ta faɗa tana ɗan kauda idonta daga gare shi ta lura kunya bai ishi wannan Guy ɗin ba, banda haka ai ba zai ke yin wannan abu har haka ba. “Ayi min alfarma na kai Battle Angel zuwa inda take da muradi.” Ya ƙara faɗar hakan a maimakon ya bata amsa. Dafe goshi ta yi tana ɗan shuke baki tare da girgiza kai ta lura da gaske bashi da aikin yi ita kam tana da abin yi. Raɓa wa ta yi ta gefansa ta wuce, ta kai hannu zata buɗe motar ya ƙara. “Please!! Domin ta hakan ne kawai zan nuna Godiyata a gareki bisa ceton Rayuwata da kika yi.” Ta sauke masa ajiyar zuciya ba tare da ta dubesa ba. Ta je key na motar a ta saman motar sannan ta je ta buɗe gidan baya na motar har zata zauna ya ce. “Woww ai kuwa zan so na zama drivern ki kuwa.” Fasawa ta yi, sai kawai ta buɗe gaban motar ta zauna. Haisam ya ɓoye dariya, daman haka yake so, ƙari sawa ya yi tare da shiga motar tare da bata wuta ya tayar, ba mai um bare um uhm suka fito daga Barrack ɗin ya ɗauki titi shantal. Ayusherh ta ɗan lumshe ido fuskarta na saitin window, yayin da shi kuwa Haisam sai murmushi yake zabgawa, yana masifar son ta Abin har mamaki yake bashi, domin wannan shi ne karo na farko da ya yi ma wata mace kalar wannan so haka, hasali ma bai taɓa wani abu wai shi dating da wata ba. Ayusherh ta kasa kunne tana jira ya tambaya address ɗin ta, sai dai taji shiru ga mamakinta kuwa Anguwan da gidan da take zaune ya kawo ta, bata ƙara shan mamaki ba har sai da taga ya yi parking dai dai ƙofar madaidaicin flat home ɗin. Fitowa ta yi daga motar Ba tare da ta bari ya shiga da motar ciki ba. “Na gode.” Ta faɗa a taƙaice tana shirin buɗe Gate ɗin ta shiga ciki taji ya ce. “Battle Angel ba za'a yimin koda tayin coffee ba.” Ɗan dakatawa ta yi tare da juyowa tana ɗan dubansa, sai ya langwaɓar da kai kamar maraya, hakan da ya yi kuma ba ƙaramin dariya ya so bata ba, amma ta kame tare da faɗin. “Okay ba damuwa shigo ciki kafin kayi min kuka.” Ta faɗa ko'a jikinta tare da shigewa ciki abin ta, Haisam ya yi murmushi mai sauti cike da nishaɗi yabi bayanta zuwa cikin gidan. Gidan ya tsaru kuma ya haɗu matuƙa duk da kasancewarsa flat kuma ɗan dai dai sai dai ya tsaru. Cikin madaidaicin palon suka shiga, Ayusherh ta a je Jacket da scarf ɗin ta a saman Hannun sofa tana faɗin. “Barka da zuwa fadar Captain Ayusherh.” Haisam ya yi murmushi yana jinjina kai, ai kuwa dai gashi nan kamar ƙaramin fada duk da ɗan dai dai ne kuma ba'a cika shi da tarkace ba amma ya haɗu, ya hakaito hakan a ransa domin shi kanshi palon ya tafi da shi. Hanyar kitchen ta nufa tana faɗin. “Bara na haɗo ma baƙo coffee.” Yayin da Haisam ya jinjina kai tare ɗan ƙari sawa yana duban makeken hotonta sanye da uniform na soji ita da wani mutumi da ya tabbatar Mahaifinta ne dukkansu suna murmushi a ka ɗauki hoton kuma sun yi kyau sosai, Haisam ya shagala da kallon frame ɗin yana sakin murmushi shi kaɗai sai jin muryarta ya yi tana faɗin. “Gashi ko?.” Ta faɗa tana miƙa masa madaidaicin cup na coffee dake fitar da daddaɗan ƙamshi da tiriri. “Thanks Battle Angel.” Ya faɗa tare da karɓar cup of coffee ɗin yana sakar ma ta murmushi. Mayar da dubanta ta yi kan frame ɗin da yake kalla, ta ɗan saki murmushi tana kai bottle water da ta buɗe a baki ta ɗan sha. “Ban ga naki coffee ɗin ba.” Haisam ya faɗa dan ya rasa abin faɗa kuma so yake suyi fira. Girgiza kai Ayusherh ta yi tana ɗan shuke baki, ta ce. “Banashan coffee da duk abin da ya danganci kayan chocolate zaƙi ma ba sosai ba.” Ai tun kafin ta dure maganar ya yi saurin dawo da cup na coffee dake hannunsa da yake yunƙurin kaiwa baki, sai ya fasa. Ayusherh ta dubesa da ɗan mamaki tana ɗan ƙara girman Manyan idanunta a kan sa ta ce. “Wani abun ne ya faru?.” Haisam ya bata amsa da faɗin. “Tun da bakyaso nima daga yau na dena sha, amma ai kina shan Black tea ba?.” Ayusherh ta ɗan saki murmushi a karo na farko tana juya ido sai ta girgiza masa kai alamar a'a. Haisam ya kwaɓe fuska. Hakan kuma ba ƙaramin dariya ya bata ba. Murmushin fuskarta bai gushe ba ta ce. “da wasa nake fa, karka damu ina shan Black tea.” Murmushi ya yi haɗe da sauke ajiyar zuciya sannan ya a je cup of coffee ɗin a kan desk dake wurin da suke tsaye da alama tana karatu ne ko wani aikin da shi tun da a ka a je a wurin. “By the way dai sunana Muhammad Haisam.” “Na sa ni ai.” Ayusherh ta faɗa tana bin hannunsa da ya miƙo ma ta da kallo. “Addinina bai bani damar gaisawa ko taɓa wanda ba hurrramina ba.” Ya ɗan yi murmushi yana janye hannunsa tare da ƙara faɗin. “Da gaske nake i really love you for the all my heart.” Ya faɗa in serious. “Na sa ni.” Ta faɗa a taƙaice. Ya yi saurin dubanta, ɗa ga masa gira ta yi. “Yeah! ba ka faɗa ba a ɗazu.” “Hump, Battle Angel ke ɗin ta dabance.” “Na gode.” Ta faɗa. Haisam ya ƙara sauke ajiyar zuciya cikin rashin abin faɗa. Ganin haka ya sa Ayusherh ta juya kamar zata koma kitchen shi kuma a dai dai lokacin ya juya zai juyo ke nan ita ma ta juyo sai suka buga karo. Baya ta yi tana ɗan shafe goshinta. “Am sorry.” Ya faɗa da sauri. Shiru ta yi masa sai ma zuba masa ido da ta yi. “Na gode da tarbata da kikayi zan tafi.” Ya faɗa. Ayusherh da ta ƙosa ya tafin, ta rakosa har bakin Gate sannan ta ce. “Na gode da rage hanya.” “Karki damu ai koma mai nayi kin cancanta ko kin manta kece silar ceton Rayuwata.” Girgiza kai ta yi. “Aikina ne shi ya sa.” “Haka ne amma ba zan dena godiya ba.” Jinjina kai ta yi. Har Haisam ya nufa motar da drivern sa ya ƙari so yana jiransa sai kuma ya yi saurin juyowa yana cewa. “Ooops! Kamar nayi mantuwa fa.” Jin abin da ya ce ne ya sa Ayusherh faɗin. “Okay Bara na duba.” Sai ya yi saurin faɗin. “Ai a tare dake nayi mantuwar.” Ta ɗan zaro ido tana bin sa da kallon mai kake nufi?. Haisam ya yi murmushi. “I love you.” Cewar sa yana zuba ma ta idanu. Ayusherh ta ɗan shuke baki. “Nima haka.” Ayusherh ta ƙara zaro ido jin abin da ya ƙara faɗa. Ya ɗan yi murmushi. “Nasan hakan zaki faɗa amma an tsaya sai an ga sani ko?.” Gimtse fuska ta yi tana ɗan ƙara shuke baki. “Okay take care.” “Oo kin amince kika ce?.” Ayusherh ta sauke ajiyar zuciya. “Karki damu bazan ƙosa ba kuma ba zan takuraki ba ki nutsu ki yi tunani da kyau.” Ya faɗa tare da shiga motar nasa driver yaja, yayin da Ayusherh ta bar nata motar anan waje domin tana so zuwa anjima zata ɗan fita. Ciki ta koma sai dai ta kasa kataɓus kalaman Haisam kawai take tunawa. “Woo wowo Ayusherh ki nutsu mana! Wai meke damun ki ne?.” “Wani abu ne mana.” Gefen zuciyarta ya bata amsa. Girgiza kai ta yi tana ɗan shuke baki. Da sauri ta ciro wayarta tare da dannawa Tata kira dan ta yi kewarsa kamar ba jiya suka rabu ba kuma ko ɗazu ma sai da suka yi waya. * Washe gari Ayusherh ce ta fito daga gidanta cikin uniform nata na zuwa aiki, motarta ta ɗan sama matsala ba zata iya zuwa aiki da ita ba, shi ya sa ta fito tana duban agogon hannunta tare da fatan karta makara zuwa wurin aikin domin akwai wani taro mai muhimmanci da za'a gabatar zuwa 9am. Sam bata lura da motar dake a fa ke ba, da shi kanshi da yake jingine da motar yana dubanta cikin sakin murmushi. “Battle Angel!.” Ayusherh ta ɗan tsaya cak jin sunan da aka kira da kuma muryar da taji. A hankali ta fara juyowa ta saitin wurin da ta jiyo muryar nasa. “Shin zan iya cin alfarma na rage ma Battle Angel hanya?.” Ya faɗa fuskarsa ɗauke da murmushi yana yi ma ta nuni da motarsa. Ajiyar zuciya ta sauke tare da gyaɗa kai, bata ce komai ba ta nufa motar tare da buɗe gidan gaba ta zauna. Haisam ya yi murmushi sannan ya zagaya ya shiga motar ya zauna. “Na gode.” Ayusherh ta faɗa lokacin da ya fara tafiya da motar. “Ba buƙatar kiyi godiya.” “Saboda me?.” “Saboda ni ne silar da motar ki taƙi tashi.” Ayusherh ji ta yi kamar ta bar motar nasa jin abin da ya faɗa domin ta fusata, sai tsintar muryarsa ta yi yana ci gaba da faɗin. “Wannan ce kaɗai hanya da zan iya sake rage miki hanya har mu sama ƴar shaƙuwar da zamu fahimci juna amma please kiyi haƙuri in kinji ba daɗi.” Ya ƙare maganar yana wani karyar da kai. “Ba komai, ya wuce.” Ayusherh ta faɗa. Haisam ya yi murmushi cike da jin daɗi. Haka ya yita ƙoƙarin janta da fira wani ta kulasa wani kuma ta yi shiru. Daga haka ma tun daga wannan rana sai dai Haisam yazo ya ɗauke ta zuwa Barrack ɗin, tun bata saba ba har ta fara sabawa da shi kanshi, har takai ta kawo wasu lokutan yana kaita zuwa can gida idan zata je wurin su Tata. Akwai Ranar ma da sai da ya takura ta haka nan ta amince ya shiga gidan suka gaisa da su Tata da yake ma lokacin duk mutanen gidan suna nan, ai kuwa Ali da Ma'az sai murmushi suke zabgawa acewarsu ai kuwa Anty Captain ta dace da saurayin nata 101% dan kuwa sun san wanene mahaifinsa da shi kansa haka ma Yayankaka da Chanchal sai murna suke. Shi kuwa a lokcin Tata da kallon tuhuma kawai yake bin Ayusherh. Ai kuwa suna keɓeta ya tuhumeta a kan alaƙar dake tsakaninta da Haisam. Sai kawai ta ce masa Abokin aikinta ne kuma Abokinta shikenan, Tata bai ƙara ma ta zancen ba. Sai ido da ya zuba musu, to daga nan kusan duk a sati da Haisam a ke cin abinci na dare a gidan. Kuma nacin da yake ma Ayusherh ne ya sa tun bata kulasa har dai ta bada kai bori ya hau. *** BAYAN WATA ƊAYA....✍️ _To! Reader's kun dai ji bayan wata ɗaya, ko mene ya guda na? Da alama fa an zo wurin domin Ayusherh za su fara soyayya da Haisam tun da an ce bayan wata ɗaya. Hummp turka-turka ke nan, me kuke tunanin zai faru? Wai ma mene abin da Yusra take bincike akai kuma ta ce ya shafi Mr President wato uncle ɗin ta bayan kuma ita ɗin ta kasance ma'aikaciyar banki ce?... Muje zuwa kawai._ Nainarh ce ƴar mutan KD na gode. 🥰🪄💝🌷 08081129487 . •… 💕 *CAPTAIN AYUSHERH*🥷 * 🍂🎀 (_The ShieldMaiden._) https://chat.whatsapp.com/IV4urJf4kuL7656LTR8Zj5 BY - Nainarh KD.... 𝒩𝓀𝒹'𝓈❦♡ Nainarhkd3 @Wattpad. *🔥 Perfectly Pen's (P.P✍️* Episode 18. GIDAN SARIN KAYA!!🔥🥳🤩 Hajiya shin kin gaji da siyan zannuwan gado suna koɗewa suna yin gashi? To ki garzayo wajen MAMAN AFRAH domin siyan masu inganci, babu kalar zannuwan gadon da babu a wajenmu. Idan kuma kin gaji da zama babu sana,a ne ki zo in baki sarin zannuwan gadon a farashi mai rahusa ki ɗora ribarki domin sana,ar ana samun alkairi sai kin gwada. Ina wacce ta gaji da siyan turarukan wuta masu ƙauri a garwashi, Ina da turaren wuta mai ƙamshi da daɗewa a ɗaki, idan kuma sana,ar turaren wutar kike ina bada farashin sari ina aikawa duk inda kike. Akwai humra mai musulmin ƙamshi da zaunawa a jiki, wacce nake wa laƙabi da sumar da mai gida don ƙamshi. Muna da Toilet cleaner in har toilet ɗinki ya dafe baya fita to ki gwada namu idan kika siya babu ruwan ki klin wajen wanki kumfa yake ya wanke bayi fesss ga ƙamshi da yake yi ɗaya za ki siya ko sari duk muna bayrwa. Akwai freshner mai ƙamshi, turaren wanka luquid soap, izal hypo, duk ina bayarwa sari a farashi mai rahusa. Ina wacce ta gaji da siyan shampoo da man kitso wanda bata ganin cigaba a gashin kanta da na ƴaƴanta? Gashin kamar gashin doki babu laushi sai tauri kina tajewa yana miki zafi, ki samawa gashinki da na yaranki mafita. Muna bayar da sari🥰 Akwai cotton material da lesuka da atamfofi siyan ɗaya ko sari. Tuntuɓe ni a wannn lambar 09013181851 -----------🙏______! Episode 18. # Captain Ayusherh # Battle Angel 🥰💋 # Haisam # Perfect lover🥳😍 # Arham # Tata # Nusra # Yusra # Alhaji Dawud Nasamu (Mr President) # Mom Maimuna # General Lamrat Jabir Junaid # Anty Dawha *** BAYAN WATA ƊAYA... Tata ya yi tsaye gefen titin cikin rashin mafita a sakamakon motarsa da ta ƙage taƙi ci gaba da tafiya, gashi Yamma ta ɗan yi kuma bazata yakeso ya yi ma Captain domin ya yi da ita a kan yau a gida zata kwana, shi ne zai je Barrack ɗin domin tafiya da ita ga kuma mota da ta yi masa tsiya. Titin ya yi shiru yayin da ababen hawa ɗai-ɗai ku ne ke wucewa suma cikin sauri gashi duk wanda Tata ya tsayar basu tsayawa. Yana nan a haka wata baƙar mota tazo wucewa ai ko da sauri ya kai hannu alamar ta tsaya sai dai motar bata tsaya ba, ta yi gaba sai dai kafin Tata ya yi wani yunƙuri motar ta dawo, ajiyar zuciya ya sauke tare da zuba ido a kan motar da mamallakinta ta fa ka a ɗan gefensa. Slowly Tinting Glass na motar ya zuge zuwa ƙasa, take fuskarta ya bayyana, Tata ya ɗan kauda kai yana jan istigfari, a can ƙasan ransa, wata ƙila ma Matar Aure ce, wani sashe na zuciyarsa ya raya hakan, sai dai kafin ya lalubo amsar da zai bawa kansa, ya ji muryarta tana faɗin. “Assalamu Alaikum! Yallaɓai akwai wani damuwa ne?.” Ta faɗa bayan ta baro motar ta iso dab da shi. “Wa'alaiki Salam, e akwai, mota ta ce mai matsalar.” “Ayya! Okay tohm idan ba damuwa ko zan iya duba motar?.” Sai Tata ya ɗan bita da kallo jin abin da ta faɗa, haka kawai ya tsinci kansa da gyaɗa ma ta kai, ita kuwa ta yi murmushi tare da ƙari sawa gaban motar dake a buɗe, takai kusan mintoci biyar a haka tana duba-dube a cikin gaban motar sannan ta ɗa go tana faɗin. “Matsalar Babba ce Yallaɓai shi ne ya sa motar taka ta maƙale taƙi tafiya, amma bari na kira wani bakanike ya gyara matsalar, amma kafin nan taimaka min da tsumma na goge hannuna.” Ta ƙare maganar bayan ta iso dab da shi, tana ɗan goge zufa da bayan hannunta da ya yi baƙi sakamakon taɓa motar da ta yi. Ba musu Tata ya buɗe murfin motar sannan ta ciro wani kyalle mai kyau ya miƙa ma ta. Karɓa ta yi sai da ta goge hannunta da kyau, sannan ta ƙari sa wurin motarta ta ciro bottle water tare da ɓalle murfin ta wanke hannunta fess! ta ƙara da goge wa da tsaftataccen Handkerchief da ta ciro a motar. Ƙari sowa wurin Tata ta yi kunnenta kare da waya tana kiran bakaniken. “Na gode sosai har ma ban san da wani kalma zan yi miki godiya ba, yanzu Bara na jira bakaniken yazo sannan muga ta yadda za'a ɓullo wa motar.” Tata ya ƙare maganar yana ɗan duban agogon hannunsa. “Ah ba komai Yallaɓai, sai dai bakaniken ya tabbatar min zai ɗan ja lokaci kafin ya iso, shin mai zai hana na ƙari she ladar nawa kawai ta hanyar ƙari sawa da Yallaɓai zuwa wurin da zashi?.” Tata ya ɗan dubeta yana ɗan gyaran murya ƙasa ƙasa dan ya rasa abin faɗa. “Karka damu fa babu komai dan naga alamar sauri kake yi da alama abu mai muhimmanci zakaje aiwatarwa, sannan in a kan motar ne karka damu har gida za'a mayar maka idan bakaniken ya gyara nayi maka Alƙawari.” Ta ƙara faɗa ganin kamar bai aminta da maganar da ta yi ba. Yayin da Tata ya ƙara riƙe sandar crutches ɗinsa da kyau yana mamakin kirki irin na wannan mata. Ba tare da musu ba ya kulle motar nasa sannan ya ce. “Ai kuwa ina matuƙar godiya Yallaɓiya Allah ya saka da Alkhairi.” Ya faɗa kansa tsaye yana nufar wurin motar nata. Yayin da ta bi bayansa, ya shiga ya zauna kusa da kujerar driver sannan ita ma ta shiga ta zauna kana ta bawa motar key, sai da ta hau titi shantal sannan ta ce. “Sunana Ummulkhair sai dai an fi kirana da Ummul.” Jinjina kai Tata ya yi yana faɗin. “Duba hanya da kyau a Barrack na sojoji dake ɗan gaba zan sauka.” Ummul ta ɗan dubesa kaɗan. “To kaifa mene sunanka Yallaɓai koda yake Yallaɓai ɗin ma sunane da ya yi matuƙar dacewa da kai.” “Haka kema Yallaɓiya ya yi masifar dacewa dake.” Ta yi dariya yayin da Tata ya ɗan murmusa. “Muhammad sunana sai dai yarana sunfi kirana da Tata.” “Woww mene ma'anar Tata?.” “A hausance yana nufin Baba.” “Tata..” Ta maimaita sunan. “Abin mamaki amma wannan wane yare haka naji alamar zai yi daɗi?.” “Yaren jama'ar Babur ke nan wato baburawa.” Tata ya faɗa a taƙaice yana ƙoƙarin kame kansa. “oops sorry ban sanar da kai ba, ai ka saki jiki Yallaɓai domin babu nauyin kowa a kaina.” Ta faɗa dai dai an buɗe ma ta Gate na Barrack ɗin tana ƙoƙarin cusa hancin motarta ciki. Shi dai Tata da dabara ya ɗan kalle ta jin abin da ta faɗa. Yana mamaki domin aƙalla zata kai shekaru Talatin da ɗauriya idan bai ɓata ba. “Ba abin mamaki ba ne dan na kasance a hakan ba tare da aure ba sai dai labarin da tsayi.” Ta faɗa tamkar taji abin da yake ayyana wa a ransa. Dai dai ta yi parking motar. *Aguyi-Ironsi Barracks Cantonment ¹, Asokoro, Abuja.* Tsaye suke a lokacin da suka fito daga elevator dai dai corridor da mutum zai bi domin fita ya isa parking lot na Barrack ɗin. Ayusherh tana sanye cikin uniform na soji ta yafa mayafi da ya rufe kafaɗunta ta yaba kuma ya sauka ƙasa sosai yayin da ta ɗaura hular ta soji launin khaki a saman a kanta wato a saman Mayafin. Wannan shigar ne shi ne shiganta a koda yaushe shi ya sa kowa yake bata girma domin lamarin aiki bai sa ta a je tsarin Addinin ta a gefe ba. Ta sake kallon Haisam da ya yi shiru kuma shi ne ya tsayar da ita lokacin da suka fito daga elevatorn sai dai shi ba uniform na soji ne a jikinsa ba, Red carpet shiga ya yi; Dinner Jacket sai Black trouser yayin da ƙafafunsa ke rufe cikin Patent leather shoes. Ya sauke ajiyar zuciya yana ɗan gyara Bow tie ɗin jacket ɗin ya duba Ayusherh da ita ma dubansa take yi tana ɗan sakin murmushi. Sai da ya yi gyaran murya sannan ya fara magana da faɗin. “Da alama dai haƙurin wannan crazy lover ɗin yana dab da ƙare wa, please Battle Angel yau dai a cire jan ran nan a bani amsar dana daɗe ina tsimayin ji.” Ya yi maganar cikin sanyin murya kamar zai fashe ma ta da kuka. Ayusherh ta ɗan zaro ido fuskarta wadace da kyakkyawan murmushi. “oo perfect lover kuka zakiyimin ne?.” “E ai haka kikeso tun da kin ƙi faɗin kina so na.” Sai maganar sa ya so bata dariya. Ta yi sannan ta ce. “Yi haƙuri karki kayi kuka kaji? In ba so kake General ta hukuntani ba.” Ayusherh ta faɗa domin a tunaninta General ita ce mahaifiyar Haisam duba da irin shaƙuwa da kuma ƙauna dake tsakaninsu, shi ya sa ta a je a haka ne, shi kuma bai sanar da ita gaskiya ba ya bar zancen a haka. Haisam ya ɗan kalla cufflink dake ɗaure a tsintsiyar hannunsa ya girgiza kai. Tare da sake dubanta sai ta ɗan ja baya shima ya bita ganin har ta jingina da bango, ta ɗan zaro ido zatayi magana suka ji magana ta gefensa. “Ayusherh!!.” Hankali tashe ta juya ai kuwa suka yi ido huɗu da Tata da ya tsaya fuskarsa ba walwala. Jikinta ya yi sanyi tana ɗan duba Haisam da ya saita nutsuwarsa yana ɗan ƙasa da kai sannan ta kuma duban Tata da ya ƙari so wurin. “Ta...ta!” Ɗa ga ma ta hannu Tata ya yi, yana ɗan danne ɓacin rai ya ce. “Mene ne a tsakaninku? Kada kiyimin ƙarya!.” Ayusherh ta sauke ajiyar zuciya ta ɗan duba Haisam da ya ɗa go yana dubanta sai ta kalla Tata, ta yi ƙasa da kai. “Saurayina ne, kayi haƙuri ban...” Tata ya sake ɗa ga ma ta hannu. “Naji!. fita waje ki jirani.” Simi-simi tamkar kazar da kwai ya fashe ma a ciki haka Ayusherh ta raɓa ta gefen Tata ta fita tana ɗan waigen Haisam da ya bita da kallo. Gyaran murya da Tata ya yi tare da faɗin. “Kallo ni ne.” Ya sa Haisam ɗin ya kuma ƙasa da kai tare da fara magana da zallar gaskiyarsa. “Kayi haƙuri ba abin da kake tunani a kaina ba ne, domin ina ƙaunar ‘yar ka Ayusherh da duk zuciyata kuma ita ma tanasona.” “Ɗa go kanka ka kallo ni.” Tata ya ƙara faɗa fuskarsa a tsume. Ɗa gowa Haisam ɗin ya yi ya kallesa. “Ka tabbata zaka kulamin da ita ba zaka bari komai ya sameta ba? Ayusherh Rayuwata ce ba zan jure ganin ta wulaƙanta ba.” Cike da gwarin gwiwa Haisam ya duba Tata sannan ya ce. “Nayi maka Alƙawari a kan zan kula da ita da duk zuciyata ba zan bari wani abu ya sameta ba sai dai ya fara samuna, wannan alƙawari na ne kuma nayi rantsuwa a kai...” Shiru ya ɗan ratsa. Ganin haka Haisam ya ƙara faɗin. “Ka taimaka Tata ina son Ayusherh fisabilillah kuma na tabbatar tana sona!.” Ayusherh tana tsaye daga waje abin Duniya ya ishe ta, batasan me suke tattaunawa a ciki ba, sai dai tanajin ba zata iya rabuwa da Haisam ba, ita kanta bata san ko yaushe ba ko a'ina ne ba, kawai abin da ta sani shi ne tana son Haisam matuƙa. “Captain?.” Taji Muryar Tata ya kira sunanta. Ai da sauri ta koma ciki, ta ɗan gefe nesa dasu tare da amsa wa. “Na'am Tata.” “kuyi sallama da Saurayinki ina jiranki a waje.” Tata ya faɗa sannan ya fita. Kusan a tare suka bi bayansa da kallo kowannensu yana sakin kyakkyawan murmushi na zallar farin ciki. Haisam ya ɗan zaro ido. “Kuma fa amincewa ya yi ba tare da mun sha wata wahala ba.” Ayusherh da ta riƙe baki tsaban farin ciki sai a lokacin ta sama zarafin faɗin. “Shi ya sa nake masifar ƙaunar mahaifina Tata domin yana sona da duk abin da nake so tun ban san kaina ba.” ____ To fa! Wacece kuma wannan Ummulkhair? 🤔 Kai da alama fa Tata ya kamu.🤭 Lallai kam Ayusherh da Haisam buri ya cika__Toh!! fatan Nasara 💃😃👊 Hummp da sauran rina a kaba fa! Wai kuwa kuna tunanin familyn Haisam za su amince da Ayusherh kuwa? Karfa ku manta ga dai Nusra a gefe ta kasa ta tsaree!!! Hump ku ci gaba da bibiya kawai CAPTAIN AYUSHERH 🥳 _____ Assalamu Alaikum Jama'a. Kwana biyu an jini shiru ba posting sakamakon banji daɗi ba, sai dai Alhamdullilah jiki ya warware ina godiya da kulawa Allah ya bar zumunci... Ameen!! ______ Toh;! Kamar dai yadda na sanar ne Book 2 na littafin CAPTAIN AYUSHERH zai kasance na kuɗi ne, kuma a halin yanzu saura page's kaɗan mu kammala Book 1. Sannan book 2 zai kasance a kan farashin Naira ɗari biyar ne (500₦) ne kacal. Amma akwai sassauci zuwa Naira ɗari uku.(300₦) Ga mutanen da za su fara biya daga yanzu har zuwa Ranar da zan kammala book 1. Abin nufi shi ne; zaku iya fara biyan kuɗin book 2 a kan farashin Naira ɗari uku, daga yau har zuwa Ranar da za'a kammala book 1. Sai ku fara biya ta wannan asusun. 8081129487, MoniePoint Mfb, Sabi'u Khadija. Sai ku turo shaidar biya ta wannan lamba. 07066953066. •… 💕 *CAPTAIN AYUSHERH*🥷 * 🍂🎀 (_The ShieldMaiden._) https://whatsapp.com/channel/0029VaEZtE15a2429vfcpf20 BY - Nainarh KD.... 𝒩𝓀𝒹'𝓈❦♡ Nainarhkd3 @Wattpad. *🔥 Perfectly Pen's (P.P✍️* Episode 19. GIDAN SARIN KAYA!!🔥🥳🤩 Hajiya shin kin gaji da siyan zannuwan gado suna koɗewa suna yin gashi? To ki garzayo wajen MAMAN AFRAH domin siyan masu inganci, babu kalar zannuwan gadon da babu a wajenmu. Idan kuma kin gaji da zama babu sana,a ne ki zo in baki sarin zannuwan gadon a farashi mai rahusa ki ɗora ribarki domin sana,ar ana samun alkairi sai kin gwada. Ina wacce ta gaji da siyan turarukan wuta masu ƙauri a garwashi, Ina da turaren wuta mai ƙamshi da daɗewa a ɗaki, idan kuma sana,ar turaren wutar kike ina bada farashin sari ina aikawa duk inda kike. Akwai humra mai musulmin ƙamshi da zaunawa a jiki, wacce nake wa laƙabi da sumar da mai gida don ƙamshi. Muna da Toilet cleaner in har toilet ɗinki ya dafe baya fita to ki gwada namu idan kika siya babu ruwan ki klin wajen wanki kumfa yake ya wanke bayi fesss ga ƙamshi da yake yi ɗaya za ki siya ko sari duk muna bayrwa. Akwai freshner mai ƙamshi, turaren wanka luquid soap, izal hypo, duk ina bayarwa sari a farashi mai rahusa. Ina wacce ta gaji da siyan shampoo da man kitso wanda bata ganin cigaba a gashin kanta da na ƴaƴanta? Gashin kamar gashin doki babu laushi sai tauri kina tajewa yana miki zafi, ki samawa gashinki da na yaranki mafita. Muna bayar da sari🥰 Akwai cotton material da lesuka da atamfofi siyan ɗaya ko sari. Tuntuɓe ni a wannn lambar 09013181851 -----------🙏______! Episode 19. “umhp tohm nifa bakya sona.” Haisam ya faɗa cikin zolaya. Sai kuma ya ƙara faɗin. “Saurayina ne kayi haƙuri Tata...” Haisam ya faɗa yana ƙasa da kai tamkar yadda Ayusherh ta yi ɗazu. Sai kawai ta kai masa naushi na wasa. Ai kuwa ya kauce cike da farin ciki yake faɗin. “Yau dai da taimakon Allah da kuma Tata na gano wata ta daɗe da narkewa a kogin so da ƙaunar Haisam.” “Hump.” Kawai Ayusherh ta ce tana murmushi domin abin nashi yafi ƙarfinta. “Maganar gaskiya nayi farin ciki kuma ina cikin farin ciki matuƙa da ganin wannan rana.” Cewar Haisam lokacin da ya ƙari so dab da ita. “Faɗa min mai kuka tattauna da Tata?.” “Sirri ne.” “Au ɓoye min zakayi?.” “Gashi kuma.” “Lallai ne zan rama.” “Za dai ki rame Yarinya.” “hump ina son ka.” “Nima haka kuma fiye da yadda kike tunani ko baki yarda ba?.” “Na yarda mana tun da naga kayi ƙasa da kai daga ganin Suruki.” Dariya ya yi suka fara tafiya. Har wurin motarsa ta rakasa lokacin da suka fito domin bataga Tata a wurin ba. Da yake Haisam ya faɗa ma ta wurin shooting zai tafi na wani sabon Film nasa da a ka fara ɗauka. Sai dai kafin nan zai fara tafiya wani wuri kuma zasu ƙari sa ɗaukar sabuwar waƙarsa. “Ni kam nace, kai ɗin mawaƙi ne ko kuma ɗan rawa?.” Ayusherh ta faɗa lokacin da ta zura kanta cikin motar da yake zaune gaban motar mazaunin driver domin duk yadda Mom taso ya fito da koda driver ne ƙi ya yi domin a cewarsa duk shirmen banza ne tun da har an iya kidnapping nasa babu abin da suka yi akai. “Wannne kika so na kasance a ciki?.” Shima ya jefo ma ta tambayar. Ayusherh ta ɗan zaro ido. “Ni! A'a ba ruwana ko wannne ne ma sai dai nayi ma ka fatan nasara duk da ba zan jura ganin wata ta saka idonta a kan ka ba.” “Au ashe ana kishi na har haka.” Murmushi ta yi bata basa amsa ba, ta gyara tsayuwarta tare da yi masa bye-bye shima ya yi ma ta sannan ya tada motar ya nufa Gate. Ayusherh ta sauke ajiyar zuciya dai dai lokacin kuma Tata ya ƙari so yana faɗin. “Mu tafi ko?.” “E Tata amma ina ka shiga ban ganka ba?.” “kina a cikin shaukin soyayya ta yaya zaki hango ni?.” Kunya ne ya ɗan kama Ayusherh. Suka fara tafiya suka nufa Gate na Barrack ɗin. “Laaa! Tata ina motar naka?.” “Ta ɗan sama matsala ne a hanyata na zuwa sai dai na haɗu da wani ya taimaka min ya ƙari so dani zuwa nan ita kuma motar an kira bakanike zai gyara ya kai min har gida.” Tata ya faɗa yana tuna yadda suka ƙare da Ummulkhair sai da ta amshi address ɗin sa acewarta bakaniken zata faɗa ma domin ya kai masa motar har gida sannan ya sake ma ta godiya ita kuma ta bar Barrack ɗin. “Ayya! Gashi ni kuma na bar tawa motar a gida domin na yanke hawa Cab ne kawai domin ƙari sawa gidan namu bayan na tashi daga aiki.” “Karki damu yanzu sai mu tara cab ɗin kawai mu koma a ciki.” Cewar Tata. Ayusherh ta ɗan yi shiru domin haka kawai taji yau kunyar Tata takeji. Tata yana lura da ita sai kawai ya yi murmushi yana girgiza kai, Ayusherh akwai kunya. Fitowa suka yi daga Barrack ɗin suka hau titi suna ɗan tafiya. Ganin shirun ya yi yawa ne ya sa Ayusherh ta ɗan yi gyaran murya sannan ta ce. “Wai kuwa Tata ka bani labari a kan Mahaifiyata mana!.” Ƙari sa maganar nata ya yi dai dai da bugun da ƙirjin Tata ya yi. Hakan ya sa ya ɗan dakata da tafiyar yana kiran sunan Allah a ƙasan ransa. “Tata wani abu ne ya faru?.” Ayusherh da ita ma ta dakata ta tambaya cike da kulawa. Da kuma damuwa dan har sai da ta yi data sanin tambayar da ta yi masa domin a tunaninta saboda ta tuna masa da Matarsa wato mahaifiyarta shi ya sa ya shiga wannan yanayin; tabbas kusan haka ne sai dai ba hakan ba ne domin wani abun ne daban ya faɗo ma Tata a rai, duk da yasan ba'a Barrack ɗin da Ayusherh take aiki ba ne Mahaifiyarta ta yi amma yana gudun kar maƙiyan mahaifiyarta su gano ta har su cutar masa da ita, shi ne abin da ya sa shi faɗuwar gaba. “Haƙiƙa tun da kike tambayata wani abu dangane da Mahaifiyarki ban kasance mai sanar dake komai ba, amma yau kuma yanzu san sanar dake kaɗan daga cikin kyawawan hali na Mahaifiyarki da yanayin mu'amalarta da kowa cikin sauƙin kai.” Tata ya faɗa a ƙoƙarin sa na ganin Ayusherh ta fita daga damuwa data shiga na ganin halin da ya shiga. Murmushi Ayusherh ta yi tana faɗin. “uhump u'um Tata nah kawai ka faɗa min yadda a kai kuka haɗu da Mahaifiyata.” Ayusherh ta faɗa fuska cike da annuri. “Babbar magana....” Tata ya faɗa ƙasa ƙasa. “Kace mene Tata ban jika ba?.” Da ɗan ƙarfi tamkar bata kusa da shi Tata ya ce. “Ban ce komai ba, zan dai sanar dake abin da kika tambaya ne.” “Yawwa Tata nah ina sauraren ka.” Tata ya yi gyaran murya har da ƙalƙala da ya yi masifar bawa Ayusherh dariya amma ta daure tanayi ƙasa ƙasa yayin da Tata ya fara faɗin. “Da fari dai kin san na sanar dake a lokacin da ina Matashi na bar ƙauyen mu da ƙasar mu bisa wasu dalilai na dawo nan Nigeria kuma a nan na haɗu da Matar da ta kasance da kallo guda ta sace zuciyata wato mahaifiyarki.” “Uhumph sai mai ya faru Tata ina saurare.” Ayusherh ta faɗa jin ya yi shiru. “Daga nan bayan na shawo kanta da kyar ina faɗa Miki muka fara soyayya har na samu na shawo kanta ta bini ƙasar mu bayan an ɗaura mana Aure dama na daɗe da karɓar Addinin gaskiya shikenan bayan fama da kyar su Arɗo iyayena suka amince muka ci gaba da zamanmu shikenan ƙurungus kan ƙusa...”😅 Dariya Ayusherh take yi sosai da jin kalaman Tata da yadda yake bata labarin tamkar yanayi ne sa'arsa dama ya saba musu haka lokuta da dama shi ya sa gaba ɗaya ita da su Yayankaka ba ƙaramin shaƙuwa ba ce tsakaninsu da mahaifin nasu. “Amma Tata har yau fa baka taɓa faɗa min ya ya sunan mahaifiyata ba, abin da na sani kawai shi ne ta rasu a yayin haihuwata ko?.” Ta ƙare maganar dai dai Cab ɗin da ta taro ya ƙari so wurin. Sai da suka shiga ciki tare da zama bayan Ayusherh ta yi masa kwatancen inda zai kaisu sannan Tata ya ce. “Sunanku ɗaya da mahaifiyarki kamar yadda a kamanni da komai naku yake iri ɗaya hatta wannan kunyar da kuma riƙo da gaskiya da son jama'a, kawai yanayin fatar ne ba ɗaya ba kuma ba Irin na mahaifin ki ba ne sannan hancinku ɗaya da Mahaifin ki kuma....” “Tata dama kai ba fari ba ne?.” Ayusherh ta jefo masa tambayar. Ai kuwa Tata ya zaro ido ganin sakin bakin da ya yi. Da sauri ya gyara maganar nasa da faɗin. “Ina nufin ke ɗin yanayin fatar ki ta kasance na daban kuma launin fata mai tsadar gaske domin irin ku ɗai ɗai ku ne a Duniya.” Ayusherh ta saki murmushi tana faɗin. “Irin na Queen ce ai.” “Wacece haka?.” “Queen of Beauty tamu mana.” “Kinji ki Captain ni kam ban san wata Queen of beauty ba.” A cewar Tata. Ayusherh ta ce. “Queen of beauty dai wata Baiwar Allah ce da ta gamu da iftila'in Rayuwa iri-iri daga ƙarshe komai ya zamo tarihi duk dai an sha gwagwarmaya.” “Ikon Allah ita bata da wani suna ne sai Queen of beauty?.” “Sunanta Afeefah Abubakar Mai Kyau, sai dai jama'a da dama musamman ma masoyanta an fi sani da kuma kiranta da Queen of beauty, domin ta kai a kirata da hakan.” Ayusherh ta ƙare maganar tana zabga murmushi. “Allah mai iko to idan kun haɗu ki miƙa min saƙon gaisuwa zuwa wurinta.” Tata ya faɗa. Ai kuwa Ayusherh ta amsa masa da faɗin. “Ba damuwa Tata duk da dai har yau Allah bai nufa mun haɗu ba abin da na sani shi ne na karanta Labarin ta mai matuƙar tsayawa a zuciya kuma ina fata mu haɗu da ita ko da zuwa nan gaba ne.” “Ma sha Allah, to Allah ya sa.” “Ameen!” Ayusherh ta amsa dai dai lokacin kuma suka ƙari sa anguwansu fitowa suka yi Ayusherh ta biya mai Cab ɗin kuɗinsa sannan suka shiga ciki suna taɓa fira. Kamasho. Wata guda ke nan da fara aikinsa a gidan Mr President ƙarƙashin jagorancin Yusra yana aiki ne a ɓangaren kula da flowers da kuma wasu abu da ba'a rasa ba. Kuma jiya ne Yusra take masa albishir da gobe zai haɗu da Uncle ɗin ta Mr President domin zai ɗauke sa aiki a ɗaya daga cikin companyn sa amma haɗu war a gida zai kasance. Shi ya sa yau ya tashi cikin zumuɗi ya shirya tsaf cikin shiga mai kyau sabon suit Black da ya siya. Shi dai Arham ido ya saka masa, to da yake akwai wuri mai muhimmanci da Arham ɗin zashi shi ya sa Kamasho ya nema da ya rage masa hanya, kuma ya yarda ____ Saura feji shida book 1 ya ƙare, saboda haka waɗan da suka shirya biyan kuɗin book 2 a kan farashin Naira ɗari uku, sai su biya ta lambar asusun da zan a je. 8081129487, MoniePoint Mfb, Sabi'u Khadija. •… 💕 *CAPTAIN AYUSHERH*🥷 * 🍂🎀 (_The ShieldMaiden._) https://whatsapp.com/channel/0029VaEZtE15a2429vfcpf20 BY - Nainarh KD.... 𝒩𝓀𝒹'𝓈❦♡ Nainarhkd3 @Wattpad. *🔥 Perfectly Pen's (P.P✍️* Episode 20. GIDAN SARIN KAYA!!🔥🥳🤩 Hajiya shin kin gaji da siyan zannuwan gado suna koɗewa suna yin gashi? To ki garzayo wajen MAMAN AFRAH domin siyan masu inganci, babu kalar zannuwan gadon da babu a wajenmu. Idan kuma kin gaji da zama babu sana,a ne ki zo in baki sarin zannuwan gadon a farashi mai rahusa ki ɗora ribarki domin sana,ar ana samun alkairi sai kin gwada. Ina wacce ta gaji da siyan turarukan wuta masu ƙauri a garwashi, Ina da turaren wuta mai ƙamshi da daɗewa a ɗaki, idan kuma sana,ar turaren wutar kike ina bada farashin sari ina aikawa duk inda kike. Akwai humra mai musulmin ƙamshi da zaunawa a jiki, wacce nake wa laƙabi da sumar da mai gida don ƙamshi. Muna da Toilet cleaner in har toilet ɗinki ya dafe baya fita to ki gwada namu idan kika siya babu ruwan ki klin wajen wanki kumfa yake ya wanke bayi fesss ga ƙamshi da yake yi ɗaya za ki siya ko sari duk muna bayrwa. Akwai freshner mai ƙamshi, turaren wanka luquid soap, izal hypo, duk ina bayarwa sari a farashi mai rahusa. Ina wacce ta gaji da siyan shampoo da man kitso wanda bata ganin cigaba a gashin kanta da na ƴaƴanta? Gashin kamar gashin doki babu laushi sai tauri kina tajewa yana miki zafi, ki samawa gashinki da na yaranki mafita. Muna bayar da sari🥰 Akwai cotton material da lesuka da atamfofi siyan ɗaya ko sari. Tuntuɓe ni a wannn lambar 09013181851 -----------🙏______! Episode;20 Tura ƙofar ta yi tare da shiga Ɗakin da sallama. Anty Dawha dake zaune gaban mirror ta ɗan dubeta tare da amsa sallamar. Ƙari sa shiga Ɗakin Yusra ta yi, ta ƙari sa wurin Mahaifiyartasu fuska tab da murmushi ta ce. “Aunty! Wai kuwa kin yi ma Uncle maganar ina fata dai bai fita ba?.” Ta ƙare maganar tana dafa dressing mirror idanunta ƙur a kan Mahaifiyar nata. “E nayi masa, amma da kyar ya yarda fa, ina fata kin faɗa ma shi yaron a kan yazo da wuri?, kafin haƙurin Uncle ɗin naki ya ƙare.” Da sauri Yusra ta gyaɗa kai tana kuma murmushi ta ce. “Amma kuwa na gode sosai Anty ke ɗin ta daban ce.” Anty Dawha ta ɗan yi murmushi tana girgiza kai. “to menene kuma na godiyar da alama bakyaso nan gaba na ci gaba da taimaka miki ta wasu fannin muddun zakike min godiya.” “Na tuba Aunty bani ƙara wa kawai dama tsaban farin ciki ne.” Yusra ta faɗa da sauri, kafin Aunty ta sama abin faɗa, Nusra ta shigo Ɗakin da sassarfa ta ƙari sa tare da faɗa wa saman Bed ta kwanta rigingine tana kallon ceiling. “Nusra lafiya kuwa?.” Yusra ta tambaya cikin kulawa. “Haisam ne! So yake na mutu a kan son shi, ya zama dole nasan abin yi na kuma san wacece wancan sojar da ya haukace a kan son ta.” Ta yi maganar tana dafe kanta da duka hannayenta, tare da rumtse ido, tana motsa red lip's ɗin a hankali. “Ki kula da kyau Nusra kar kije haukan kishi ya sa ki aika abin da zaki zo kina danasani daga baya.” “A halin yanzu bani da lokacin tsayawa nazari a kan abin da zan aikata domin ni kaina ban tantance mai zan yi ba.” Nusra ta bawa Yusra amsa tana tashi zaune, ta ɗauki wayar da ta cillar gefe lokacin da ta hau Bed ɗin, ta fara laluben lamba. “Nusra! Mai zaki aikata ne?.” Yusra ta faɗa da sauri domin tasan wacece ‘yar uwar nata. “Ki yarda dani mana Sisty ba abin da zan aikata, idan ma zan aikata wani abu zaku gani a aikata ce.” Cewar Nusra tana ɗan bubbuga wayar hannunta a saman laɓɓanta. “Idan kina da buƙatar taimaka wa ki sanar dani zan taimaka miki.” Anty Dawha ta yi maganar ba tare da ta duba inda Nusra take ba. “Bana buƙata kuma ba zan taɓa buƙata ba har abada.” “Why Nusra? Nifa Mahaifiyarki ce!.” Anty Dawha ta sake faɗa cikin ɗacin rai, da abin da Nusra take ma ta, ta gaji da halin ko'in kula da ‘yar nata ke ma ta. “E, na sa ni, shi ya sa bana buƙatar taimakon naki, muddun nima ba zaki sanar dani wanene ainihin mahaifinmu ba, kuma ki bani hotonsa mu gani.” Nusra ta faɗa tana miƙe wa tsaye. “Nusra ki gyara kalaman ki kin manta wacece a gabanki ne Mahaifiyarki ce fa.” Yusra da bata jin daɗin rashin fahimtar juna dake tsakanin ‘yar uwan nata da Mahaifiyar tasu ta faɗa. “Kin sanni kin san halina ban iya ƙarya ba, iyakar abin da ke raina nake faɗa, saboda haka ba zan taɓa neman taimakon ta ba muddun bata faɗa min wanenen Mahaifin ba kuma ta kai mu Wurin danginsa.” Nusra ta faɗa rai a ɓace tana nufar ƙofa. Sai kawai Anty Dawha ta saka kuka. Yusra ta yi saurin riƙe ta tana faman bata haƙuri. Ɗan jim Nusra ta yi bata juyo ba amma ta tsaya da tafiyar da take yi, sai kawai ta ƙari sa da sassarfa ta bar Ɗakin zuciyarta ba daɗi sai dai a duk wannan bata hango laifinta a ciki ba, duka laifin Mahaifiyar tasu ce da taƙi faɗa musu ainihinsu. Ai ko shege ma yana da Asali balle kuma su da ta tabbatar musu ba ‘yan gaba da fatiha ba ne, to mai zai saka taƙi kaisu wurin Dangin mahaifinsu?. “Mun iso.” Arham ya faɗa lokacin da ya fa ka motar a ɗan gefe kaɗan da katafaren gidan Mr President a katafariyar anguwan. “Tohm Babban Yaya Bara na shiga ciki a taya mu da fatan Khairan.” Cewar Kamasho yana ƙoƙarin fita daga motar. “Da yardar Allah koda yake ai nasan zaka iya fatan nasara Abaan.” Arham ya faɗa lokacin da Kamasho ya fito daga motar. “Godiya nake Babban Yaya.” “Yi sauri kaje kar lokaci ya ƙure.” Arham ya yi shiru zaune a motar ya ɗan zubawa katafaren gidan na Mr President ido yana nazari. Tun bayan da Kamasho ya shiga ciki bayan tarin security's sun gama bincike shi tsaf sannan suka barsa ya shiga ciki. Hakan ma dan sun san shi ne. Tada motar ya yi ya bar Anguwan da sauri domin shi kanshi bai san mene zai faru ba idan ya ci gaba da tsayawa a wurin. Gudu yake santalawa a titin tamkar zai tashi sama kuma hakan ya sa cikin ƙanƙanin lokaci ya iso inda zashi. *Kuje, Abuja, FCT, Nigeria.* Sai da ya fa ka motar a ɗan gefe kaɗan da Gate ɗin Prison ɗin, sannan ya fito daga motar, jingina ya yi da motar yana kallon rubutun dake saman wani allo dake daga sama kan ƙofar fitowa daga Prison ɗin. Inda a ka rubuta, Central Jail Abuja. Ya sauke ajiyar zuciya bai rufe minti goma ba a wurin, can a ka buɗe ƙofar Jail ɗin Dattijon mai cikar kamala ya fito daga ciki jami'an dake waje suka basa hanya, kai tsaye wurinsa Arham ya nufa fuskarsa ɗauke da walwala suka rungume juna kowannen su da abin da yake saƙawa a ransa. “Uncle nayi matuƙar farin ciki da ganin wannan rana sai dai ina tausaya wa Alhaj Dawud Nasamu domin a wannan taƙin karon namu da shi ba zai masa kyau ba.” Arham ya kai maganar yana furzar da zazzafan huci. Dafa kafaɗarsa Mutumin ya yi sannan ya ce. “Arham mu nutsu sannan kubi komai a hankali ta hanyar yin amfani da tunani domin Alhaji Dawud Nasamu ya wuce duk yadda muke tunani kuma a matsayinsa na President a yanzu zai iya aikata duk abin da yake so ba tare an tuhumesa ba. Kasan hakan saboda haka be patient kawai domin akwai lokaci.” Arham ya sake furzar da huci yana gyaɗa kai. “Tohm Uncle zan kiyaye, mu ƙari sa wurin mota.” Ba musu Uncle ya bisa suka shiga mota tare da barin wurin kai tsaye Gidan marayun suka nufa. *No. 20, Kubuwa Road, Gwagwalada Abuja.* “Barka da safiya fatan duk kun tashi lafiya?.” Ayusherh ta faɗa lokacin da ta ƙari sa Dining Room ɗin taja kujera ta zauna. Duk suka amsa ma ta. “Ina Tata yake?.” “Ya fita wannan sojan ne ya zo yake sanar da shi wai wata tazo a mota tana nemansa a waje.” Cewar Chanchal tana ɗan kallon Ayusherh da ta yi tambayar. “Mace kuma?....” “E Mace fa.” Wannan karon Ali ne ya faɗa tun kafin ta kai maganar. Sai dai kafin ta kai ga ƙara faɗin wani abu Tata ya shigo Palon tare da ƙari sowa Dining ɗin yaja kujerar da yake zaune tun farkon fari ya zauna. Duk suka yi shiru su na ɗan ɓoye dariya, yayin da Ayusherh ta ɗan yi gyaran murya bata ce komai ba ta fara kai loma. “Chanchal, Wato kema kin fara biyewa Ali ko? Wai ma dariyar me kuke ɓoye wa ne?.” Tata ya tambaya lura da ya yi suna dariya ƙasa-ƙasa. “Ai Tata ka rabu da yaran nan gulma ce kawai ta ciyosu.” Cewar Ayusherh. “Aunty Kiyi haƙuri da halin Nusra karki saka damuwarta a ranki in sha Allah zata gane kuma ta bari.” Cewar Yusra cike da kulawa ganin yadda duk Mahaifiyar tasu ta shiga damuwa. “Ba komai Yusra karki damu laifina ne.” Yusra zata sake magana suka ji bugun ƙofa, su duka suka bi ƙofar da kallo, kafin Yusra ta miƙe tare da nufar ƙofar, yayin da Aunty ta saka tafin hannunta ta rufe fuskarta ƙasa-ƙasa ta ce. “Nusra! Kina ƙoƙarin kai ni taƙin da bana da niyya zuwa a halin yanzu, ya zama dole na san abin yi.” “Ai kuwa na gani sai su bada hujja kam” Cewar Tata yana kai loma. Ita ma kanta Ayusherh ɓoye dariyar take yi ta ƙara faɗin. “Barka da safiya Tata, na fito na tarar baka nan shi ne suke faɗin wai ana sallama da kai a waje shi ne ka fita dubawa.” “E kam wallahi Bakaniken jiya ne sai yau ya kawo min motar tawa.” “Good, ta gyaru ke nan.” “E sosai ma kuma da alama ba wata matsala.” “To Allah ya sa.” “Ameen.” “Laaa! Tata dama Mace ce Bakaniken naji wannan sojan ya ce mace ce ke nemanka.” Chanchal ta faɗa tana duban Tatan kamar yadda sauran suma duk suka zuba masa ido. “Ah E haka... ne wai ke Chanchal yaushe kika koya Surutu ne?.” Dariya suka yi gaba ɗaya. Yayin da Tata ya maze. “Ali ne ya koyamin.” Chanchal ta faɗa tana nuna masa Ali. “Kaji sharri daga wurin bil'adama.” Ali ya faɗa yana wani zazzaro ma ta ido. Ai kuwa hakan da ya yi ba ƙaramin dariya ya basu ba. “Wai Chanchal na tambaye ki mana me ya sa baki kiran sunan corporal Aryan ne, sai dai ki kirasa da 'wannan sojan?.” Ayusherh ta faɗa tana duban Chanchal ɗin, ai kuwa duk suka zuba ma ta ido domin jin abin da zata faɗa. “Madam Yusra dama wannan Kamasho ya ce sunan ko, to dama shi ne ya zo wai yana neman ki.” Amira ‘yar Aiki ta faɗa lokacin da Yusra ta buɗe ƙofar. Yusra bata ce komai ba, ta juya tana kallon Aunty Dawha sannan ta ce. “Aunty ina ga gashin nan ya iso ma, Bara naje ina dawowa.” Gyaɗa ma ta kai Aunty Dawha ta yi, sannan Yusra tabi Amira suka fito daga Palon sannan suka yo ƙasa. Kasa ƙari sa saukowa Down Yusra ta yi tsaban mamaki tana duban Kamasho dake tsaye a Palon, sai kuma ta yi murmushi tana ƙari sa saukowa ta ce. “Wai kuwa ba gizo idona ke min ba, wai Abaan ne?.” Murmushi Kamasho ya yi yana amsa ma ta da faɗin. “Ai kuwa dai a zahiri ne ina fata shigan nawa ya yi?.” “Ɗari bisa ɗari ma kuwa.” Yusra ta amsa masa. Sannan ta ƙara da faɗin. “muje ko?.” Ta faɗa tanayi masa nuni da wata hanyar daban. Ta shiga gaba yabi bayanta suna ɗan magana kaɗan kaɗan. Ganin Chanchal ta yi shiru taƙi cewa komai ne ya sa Yayankaka faɗin. “Ai Aunty Captain labarin da yawa amma Bara na ɗan gutsira miki kaɗan, wai fa saboda sunan Aryan ɗin yanayi ma ta daɗi kuma tanaso wai ta sakama ɗan ta na fari shi ne take alkunya bata faɗa.” Tuntsirewa da dariya suka yi jin abin da Yayankaka ta faɗa. Yayin da Chanchal ta yi saurin fike kanta ƙasa tana ɓoye fuska. Kama baki Ayusherh ta yi tana ‘yar dariya ta ce. “Lallai kam waya ga manyan iyaye wannan ai shi ne tun kan a haifa an tanadi suna.” Ita dai Chanchal kunya ya hanata magana. “Ai wallahi Yasmin kinjama kanki sai na tona.” Chanchal ta faɗa cikin suɓu cewar baki. Ai kuwa Yayankaka ta zaro ido haka ma ita kanta Chanchal da ta yi maganar yayin da Ali da Ma'az suka fashe da dariya lokaci ɗaya. Sai kawai Tata da Ayusherh suka zuba musu ido cike da mamaki. “Wacece kuma Yasmin? Kuma mene ne zaki tona?.” Ayusherh ta tambaya tana mayar da hankalinta a kan Chanchal. Muƙut, Chanchal ta haɗiye yawu sannan ta ce. “Ba komai fa Aunty mantawa nayi nace Yasmin a maimakon Yayankaka.” Da sauri Ma'az ya ce. “Ƙarya take yi ainihin zance shi ne dukkanninsu waɗan nan da kike gani sun canza sunansu a school kuma ita Chanchal ɗin ce ta fara canzawa a cewarta sunan ya yi local da yawa kuma ‘yan class ɗin su suna yi ma ta dariya shi ne kawai ta lauya sunan ya koma Chandni a zamanance, kuma a ka yi katari sunan ya zo dai dai da kuma ma'ana wato The Moon's Light duk da dai haɗa sunan ta yi, Chan farkon sunanta d kuma farkon sunan Mahaifiyarta wato Dillaliya sai kuma ni inda ya kasance ƙarshen sunan Mahaifinsu wato Sani.” Ma'az ya ƙare maganar yana ƙara fashewa da dariya. Tata ma shi kanshi sai da ya murmusa. “Lallai kam to in banda abin ki ai kamar Chanchal ɗin ma yafi daɗi bisa wannan Chandni ko mene?.” Cewar Tata yana dubanta. Ita dai Chanchal bata ce komai ba. “Ita kuma Yayankaka ta koma Yasmin kuma da haka take amfani ma school.” Ma'az ya ƙara faɗa. “Ikon Allah to shi kuma Ali fa mai ya koma koda yake wata ƙila Haidar ko?.” “Yes! Ai kuwa kin cinka dai dai Anty Captain hakan kuwa ya koma.” “To kai kuma baka canza naka sunan ba ke nan?.” Tata ya tambaya. “Ni ba ruwana ai Ma'az sunane mai daɗi ban canza ba.” Duk suka yi dariya. “To har yanzu dai ba'a faɗa min ba mene ne Chanchal kike faɗin zaki tona.” Ayusherh ta sake maganar tana duban Chanchal. “Ah dama fa ba wani abu ba ne wai fa Yayankaka ne takeso ta shiga tseren doki da za'a gudanar kuma ta rasa ta inda zata faɗa muku ke da Tata.” “Ah to ai shikenan wannan ai ba wani abun damuwa ba ne a'ina ne za'ayi?.” “A Dreamworld ne.” Yayankaka ta yi saurin bawa Tata da ya yi tambayar amsa. “Karki damu zaki shiga kuma zakiyi nasara da iznin Allah, sai dai daga yanzu ban amince ku dinga ɓoye komai naku daga gare mu ba idan baku faɗa ma gida ma gida matsalar ku ba, a'ina zaku faɗa ke nan?.” “Babu.” Duk suka ba Ayusherh da ta yi maganar amsa. “Yawwa to ku kiyaye please duk ɗaya daga cikinku in yana da damuwa kukaga ba zaku iya solving matsalar ku kaɗai ba, ku faɗa ma Tata ko kuma ni ku sanar dani kunji ko?.” Duk suka amsa ma ta daga haka kuma suka ci gaba da karin kamallon yayin da Tata yake ƙara yabawa da Ɗiyar tasa Ayusherh. Sai da suka gama sannan Ayusherh ta shiga Ɗakin Kakarsu tana taya ta fira da yake yau ɗin asabar ce babu aiki. *Har yanzu ƙofa a buɗe take ga masu biyan kuɗin Captain Ayusherh book 2 , Naira ɗari uku ne. Bisa Discount, 8081129487, MoniePoint Mfb, Sabi'u Khadija.* •… 💕 *CAPTAIN AYUSHERH*🥷 * 🍂🎀 (_The ShieldMaiden._) https://whatsapp.com/channel/0029VaEZtE15a2429vfcpf20 BY - Nainarh KD.... 𝒩𝓀𝒹'𝓈❦♡ Nainarhkd3 @Wattpad. *🔥 Perfectly Pen's (P.P✍️* Episode 21. GIDAN SARIN KAYA!!🔥🥳🤩 Hajiya shin kin gaji da siyan zannuwan gado suna koɗewa suna yin gashi? To ki garzayo wajen MAMAN AFRAH domin siyan masu inganci, babu kalar zannuwan gadon da babu a wajenmu. Idan kuma kin gaji da zama babu sana,a ne ki zo in baki sarin zannuwan gadon a farashi mai rahusa ki ɗora ribarki domin sana,ar ana samun alkairi sai kin gwada. Ina wacce ta gaji da siyan turarukan wuta masu ƙauri a garwashi, Ina da turaren wuta mai ƙamshi da daɗewa a ɗaki, idan kuma sana,ar turaren wutar kike ina bada farashin sari ina aikawa duk inda kike. Akwai humra mai musulmin ƙamshi da zaunawa a jiki, wacce nake wa laƙabi da sumar da mai gida don ƙamshi. Muna da Toilet cleaner in har toilet ɗinki ya dafe baya fita to ki gwada namu idan kika siya babu ruwan ki klin wajen wanki kumfa yake ya wanke bayi fesss ga ƙamshi da yake yi ɗaya za ki siya ko sari duk muna bayrwa. Akwai freshner mai ƙamshi, turaren wanka luquid soap, izal hypo, duk ina bayarwa sari a farashi mai rahusa. Ina wacce ta gaji da siyan shampoo da man kitso wanda bata ganin cigaba a gashin kanta da na ƴaƴanta? Gashin kamar gashin doki babu laushi sai tauri kina tajewa yana miki zafi, ki samawa gashinki da na yaranki mafita. Muna bayar da sari🥰 Akwai cotton material da lesuka da atamfofi siyan ɗaya ko sari. Tuntuɓe ni a wannn lambar 09013181851 ----------🙏______! Episode;21 “Ba zai yiwu ba!.” Uncle ya faɗa a tsawa ce yana ci gaba da faɗin. “Ya zama dole Abaan ya bar aiki a ƙarƙashin Nasamu muddun ba so kake mu rasa shi ba.” Uncle ya ƙare maganar a zafafe yana juyowa tare da duban Arham da ya harɗe hannu a ƙirji tun bayan gama faɗa masa halin da ake ciki da ya yi. Arham ya ɗan waro ido ya ce. “To ta ya ya ke nan hakan zata yiwu bayan kuma already ya fara aiki a gidan nashi kuma yau ne yaje a domin ya yi masa interview domin ɗaukarsa aiki a ɗaya daga cikin company's ɗin sa.” “Ba zaka gane abin da nake hangowa ba Arham saboda Nasamu ya wuce duk tunanin mu tantirin Tantiri ne na san zai yi tsatstsauran bincike a kan Abaan kuma zai gano daga gidan marayun da ya fito, daga nan kuma ba zai tsaya haka ba dole bincikensa zai kai sa zuwa wurin da bamu buƙatar ya kai domin muddun ya kai wurin to fa tamkar asirin mu ne ya tonu.” Arham ya fesar da zazzafan huci yana ɗan gyaɗa kai ya ce. “To mene ne abin yi ?.” “Abin yi shi ne kawai kasan duk yadda za kayi ka hana Abaan komawa gidan Nasamu balle har ya kai ga fara aiki a Companyn sa.” “But..” Katse Arham dake yunƙurin magana Uncle ya yi sannan ya ce. “Nasan mai zaka ce kana tunanin Nasamu zai yi zargin wani abu ba?.” Jinjina masa kai Arham ya yi bai iya cewa komai ba. Uncle ya saki murmushin takaici ya ce. “Karka damu zamuji da lamarin.” Yana faɗin hakan ya taka ya isa wurin Bene dake a gefe cikin Ɗakin matattakalan benen ya taka ya yi sama sannan ya fito daga Ɗakin ƙasa da suke ciki. Arham ya sake furzar da iska sannan ya bi bayansa. Tun bayan baro Prison ɗin da suka yi da fari Arham ya nufa Gidan marayun amma Uncle ya hanasa tare da yi masa kwatancen nan inda suke sannan suka ƙari so anan ne Arham yake sanar da Uncle tsiraru daga abubuwan da suka faru bayan kasancewarsa a gidan kaso na tsawon shekaru goma sha Tara. Fitowa suka yi daga ƙaramin gidan da ya fi kama da gidan gona kai tsaye hanyar da zata sadasa da gidan marayun Arham ya miƙa lokacin da suka shiga motar. Cikin ƙanƙanin lokaci ya ƙari sa da su gidan marayun a nan tare da shugaban dake kula da gidan marayun Arham ya bar Uncle yayin da a gaggauce ya wuce zuwa Ɗakin sa da yake a ɓangaren maza samari kamarsa. Da sauri ya faɗa Ɗakin yana dafe kansa dake mugun sara masa, ƙam ya riƙe kan nasa ya tsaya a tsakiyar Ɗakin har yanzu juwa bata sakesa ba, kuma ba komai ne dalilin hakan ba sai tuno abin da ya faru da shi a shekarun baya da ya yi, da irin kisan wulaƙanci da Nasamu ya yi ma Mahaifansa a gaban idonsa take komai ya fara dawo masa a kai tirya-tiryan. _Flash Back._ _“Ki yarda dani Yarinyar nan ta zama ruhi da ɓargo na yaronmu bakiga yadda ya zama ba daga baro garin da muka yi ba?. Ya kamata ki fara shiri tun yanzu dan da alama yaron naki da gaske yake.” Dad ya yi maganar yana ɗan waigawa ya dubi Mom dake zaune a kusa da shi a gidan baya na motar. Mom ta saki murmushi cikin annashuwa ta ce. “Ai ko da zan fi kowa farin ciki idan hakan ta kasance domin na lura ita ma Yarinyar tana da feelings a kan sa.” Abyaz dake zaune gidan a gaba na motar kusa da driver ya ɗan juyo yana kallonsu fuska tab da walwala ya ce. “Dad and Mom to tun da kun lura da haka ai kawai mu juya kawai a ɗaura mana Aure sai mu taho tare da ita ko ya kukace kun ga daga nan kuma kun sama ɗiyar da baku da ita.” Ya yi maganar yana dariya. Mom ta yi masa daƙuwa tana faɗin. “Ungo naka wai Abyaz yaushe ka zama haka ne.” Dad yana dariya ya ce. “Ai da gaskiyarsa saboda haka ina ga abi shawarsa kawai mu juya.” Gaba ɗaya suka yi dariya shi da Abyaz yayin da Mom ta yi kicin-kicin tana faɗin. “Yaushe kuka taɓa jin an yi haka? Ai shi Aure ba'a masa haka, kuma ma ai Abyaz ɗina ba yanzu ba tukunna...” “Ai kuwa Mom da alama so kike in na koma Military School na kasa taɓuka komai.” Abyaz ya yi gaggawar faɗan hakan yana dariya. Maganar da Mom take yunƙurin yi ya katse a sakamakon mummunar karo da motarsu ta yi da wata Truck. Ko kafin ɗaya daga cikinsu ya sama zarafin wani yunƙuri motar ta yi sama da su sannan tayo ƙasa a karkace duk suka koma sama ta ƙasa. Kafin kowannensu ya kai ga tunanin abin da ke afkuwa a duniyarsa motar ta fara gungure da su bata tsaya ba sai da ta sadu da wata bishiya sannan motar ta tsaya. Tuni duk sun fi ce daga hayyacinsu yayin da tuni driver rai ya yi halinsa. Sakamakon mummunar buguwa da ya yi. Abyaz da bai wani bugu sosai ba sai kansa da ya bugu jini ya wanke masa fuska ya samu da kyar ta ƙuƙuta ya fito daga motar yana dafe kansa tare da isa ta saitin wurin da Iyayen nasa suke ya fara kiran sunansu cikin fitar hayyaci sai dai cikinsu ba mai amsa masa, sai can Dad ya ja wata doguwar ajiyar zuciya sai dai duk yadda ya so ya fito daga motar gagara ya yi a lokacin ne kuma hankalinsa ya kai kan Mom da bata numfashi cikin razana ya kai hannunsa dai dai saitin hancinta sai dai ba alamar numfashi a tattare da ita, bai fita daga wannan tashin hankali ba ya fara jin ƙarar taku yana isowa dab da su a razane ya kalla Abyaz dake durƙushe riƙe da kansa da har lokacin jini bai dena zuba ba. “Yarona tashi ka gudu!.” Abyaz ya ɗa go cikin razana da jin kalaman da Dad ya yi, sai dai kafin ya sama zarafin magana Dad ya ƙara da faɗin. “Mahaifiyarka ta riga da ta mutu nima kuma nasan ba za su barni a raye ba saboda haka rayuwarka tana da matuƙar muhimmanci shi ya sa nake cewa ka gudu Abyaz!!.” Dad ya ƙare maganar cikin azaba da kyar ya samu a hakan yadda yake sama a ƙasa ya lalubo briefcase ɗin sa da kyar ya samu ya jefa waje ya ce ka riƙe wannan zatayi maka amfani anan gaba kuma ita zata taimaka maka wurin sanin wanene wanda yake da alhaki a duk wannan.” Dad bai ƙare maganar ba yaji takun da yakeji yana ƙara isowa dab da su. A raunace ya kalla Abyaz dake rungume da briefcase ɗin da alama ya kasa yarda da abin da yake faruwa a ce cikin ƙanƙanin lokacin da bai haure minti biyu ba gaba ɗaya rayuwarsa ta karkace ta koma zuwa upsidedown. “Ka tafi Abyaz!!!.” Shi ne kawai abin da Dad ya iya furta wa sai dai kafin ya kai ga ƙare maganar wasu irin jibga-jibgan ƙosassun maza je masu ƙira da yanayi irin na samudawa suka bayyana su huɗu suka zagaye motar kuma a cikinsu drivern Truck ɗin da ya bige motarsu Abyaz yake. Ko kafin Abyaz ya yi wani yunƙuri domin ceton ransa wani irin hayaƙi ya turniƙe wurin kafin Mutumin ya bayyana yana busa sigarin kallo ɗaya zakayi masa kasan ba ƙaramin tsagera ba ne. “Nasamu!” Maganar Dad ya dawo da Abyaz hayyacinsa Mutumin ya saki wani lalataccen murmushi ya juya ido tare da duban Abyaz da ilahirin jikinsa ba inda baya rawa, ai take Abyaz ya fara ja da baya sai dai tuni biyu daga cikin waɗan nan garɗa-gaɗan mazan suka rirriƙeshi suna ƙoƙarin gwace briefcase ɗin hannunsa. “Nasamu, muddun wani abu ya sama yarona to fa ba zan taɓa kyaleka ba...” Fiuuu! Kakeji fitar harsashi daga jikin ƙaramar Bindigar dake hannun Mutumin da Dad ya kira da Nasamu, kwaf ɗaya harsashin ba tare da saɓa saiti ba ya fasa kan Dad ya shige. Ɗiff!! wutar Abyaz ya ɗauke yayin da gaba ɗaya duniyarsa ta tsaya cak, sakamakon abin da ya faru, da wani irin ƙarfi ya gwace kansa daga riƙon da waɗan nan mazan suka yi masa ya ƙari sa gaban motar yana jijjiga Dad da babu rai a tattare da shi, tsaban tashin hankali muryarsa ma bata fitowa. Cikin wani irin zafin nama ya miƙe tsaye tare da daka tsalle ya kai ma Nasamu wani naushi a ido a ka ci sa'a kuwa zoben hannunsa ya yi ma idon illa sosai, wafce briefcase ɗin dake hannun Nasamu ya yi tare da shammatar Mazan majiya ƙarfi ya fara gudu gaba ɗaya suka bi bayansa, yayin da Nasamu ya zube a wurin yana zuba ihun da ya amsa a gaba ɗaya dajin yana kuma dafe da saitin idon nasa da jini ke fita. Duk yadda waɗan nan maza majiya ƙarfi suka so su kama Abyaz abin ya ci tura domin yaron wani irin ƙarfi ne na ban mamaki ya zo masa domin har jima biyu daga cikinsu, mummunar rauni a fuska ya yi, suna tsaka da haka wata mota ta sha gaban Abyaz hakan ya sa ya tsaya cak, cikin sadaƙarwa dai dai lokacin kuma ɗaya daga cikin waɗan nan mazan ya ƙari so ta bayansa tare da buga masa bayan bindiga a kai, sai dai kafin ya sauke hannunsa, fiuuu!, kakeji harsashi ya ratsa ta goshinsa, mutumin da ya fito daga motar kuma ya yi harbin ya yi saurin tallafo Abyaz dake yunƙurin faɗuwa ƙasa a sume, nan da nan a ka shiga sakin wuta tsakaninsa da waɗan nan mutanen daga ƙarshe ya yi galaba a kansu ai kuwa da gudun bala'i ya tashi motar ya bar dajin tare da Abyaz da baya a hayyacinsa..._ Dai dai nan kuma Arham ya dawo hayyacinsa ya zube jigib saman Bed har yanzu bai saki kansa ba, can ya miƙe yana nanata sunan 'Nasamu a fili kana ya ci gaba da faɗin. “Ba zan Barka ba ka jira zuwa na gareka.” Sai kuma ya yi shiru, can ya faɗa cikin wata raunatacciyar murya. “Mene ne laifin da Iyayena suka aikata maka har ka zaɓi kayi musu wannan mummunar kisa? Shin laifi ne don Mahaifiyata ta tsaya takara kai ma kuma ka tsaya? Ko kuwa ceton Rayuwata daga hannun yaranka da Uncle ƙanin Mahaifiyata kuma Mataimakin ta ya yi shi ne ya zama laifi da har ka laƙaba masa sharrin kisan Iyayena da hakan ya zama sanadiyar da ya shafe tsawon shekaru a gidan kaso?.” Shiru ya yi yana wassafa abubuwa da dama a ransa game da wannan mutumin wato Nasamu. ** A wani madaidaicin Palo suka bayyana idanun Kamasho suka sauka a kan Alhaji Dawud Nasamu dake zaune ya harɗe ƙafa yana karanta jarida yayin da PA ɗin sa wato Matarsa Mommyn Haisam take zaune daga gefensa tana amsa waya, sai dai shigowarsu Yusra Palon ne ya sa ta katse kiran tana bin su da kallo daga ƙarshe ta sauke idanunta a kan Yusra tana yi ma ta wani irin duba na tsanaki. “Uncle, Mom M. na sameku lafiya?, Yawwa ga Abaan ɗin ya ƙari so.” Yusra ta ƙare maganar cike da ladabi tana duban Mr President. Murmushi ya sakar ma ta kana a nutse ya ce. “An gaisheki Yusra! And zaki iya bamu wuri domin mu gana da sabon ma'aikacin namu?.” Murmushi Yusra ta ƙaƙalo ta ɗaura a saman fuskarta sannan ta ce. “Ba damuwa Uncle, dama fita zan yi, sai anjima.” Ta ƙare maganar tana juyowa da sassarfa ta bar Palon gabanta na matsanancin bugu domin gani take tamkar Uncle ɗin nata Mr President ya san binciken da take yi a kan sa ne a kan baƙaƙƙen kuɗi da ta gano yana shirin fitarwa waje ba bisa ƙa'ida ba, kuma ta hanyar amfani da mabanbantan asusu, domin kada a gane, saboda baƙaƙen kuɗaɗen da ba za su ƙirgu ba sata ya yi...... “Malam Abaan shin zan iya sanin wani abu dangane da kai?.” Mr President ya faɗa yana maido da kallon sa kan Kamasho bayan ya sauke idonsa daga bin Yusra da kallo da ya yi. Kamasho ya ɗan haɗiye yawu sakamakon idanunsa da suka sauka a kan wani tabo dake fuskar Mr President kuma saitin idanunsa na hagu; wurin ya yi baƙi da alama baya gani da idon. “Ah..uhmp ni dai sunana Muhammad Abaan kuma ban wani yi karatu mai zurfi ba sai dai ina da gogewa ta fannin kasuwanci da sanin ta kan Rayuwa da hakan ne ma yaja hankalin Yusra, opss Madam Yusra ta yi tunanin taimaka min domin ganin na sama aiki a Companyn ka.” Mr President ya ɗan duba Mom M. Da ta yi kasaƙe tana sauraren Abaan, dai dai ita ma ta kallesa sai kawai ta girgiza masa kai, ya fahimci abin da take nufi sai kawai ya yi murmushi, yayin da Mom M ta miƙe tsaye ta ɗan fara taka wa har ta isa ta bayan Abaan da ya ɗofana a saman sofa, ta ɗan tsaya tana ƙara nazartarsa. “Okay! Amma zan iya sanin waye mahaifin ka?.” Kamasho ya ɗan yi jim yana tambayar kansa mai ya haɗa neman aiki da ya zo, da kuma tambaya a kan Iyayen sa. Haka kawai ya tsinci kansa da faɗin. “Bana da Iyaye sun rasu tun kan nasan kai na a hannun Kakata dake aiki a gidan marayu na taso shi ya sa na kasance bana da banbanci da yara marayun dake a gidan marayun.” Jinjina kai Mr President ya yi tare da rufe jaridar hannunsa. “Ka raya a ranka cewar kawai har an yi an gama domin ka sama aiki gobe ma zaka fara zuwa sannan idan akwai wani abun zan faɗa wa Yusra ta faɗa maka.” Mr President bai rufe baki ba Kamasho ya zube har ƙasa yana zuba godiya kamar ya ara baki, kallon juna Mom M da Mr President suka yi suka saki murmushi a tare. Nan dai Mr President ya sallami Kamasho ya tafi cike da farin ciki ai kuwa suna haɗu wa da Yusra a waje cike da farin ciki yake zuba ma ta godiya ita dai murmushi kawai ta yi, da yake ma ta shirya zata bar gidan domin akwai wuri mai muhimmanci da zata, shi ya sa ta rage ma Kamasho hanya suka fita tare, a hanya sai complain yake ma ta a kan ta rage zuwa gidan marayu. Ita dai murmushi kawai ta yi tare da bashi uzuri da aiki ne ya yi ma ta yawa, amma ya gaida ma ta da Arham. “Da alama yaron zai yi kaifin tunani shi ya sa na zaɓi na basa aikin domin ganin kamun kwaryarsa zuwa nan gaba na jefa sa cikin harkar siyasata ko domin zaɓe dake gabatowa dan da alama zai bada gudunmawa sosai.” Mr President ya ƙare maganar idanunsa a kan Mom M. Da take sakin murmushi, jinjina ta yi masa da Babbar yatsa, sannan ta ce. “Da alama tsautsayi da ƙarar kwana yana kiran wata ƴar ƙaramar mitsitsiyar kada, yanzu mai kake tunanin za'ayi ma ta domin ta tana dab da taɓo tsuliyar dodo ba tare da tunani a kan illar da hakan zai ma ta ba.” Ɗage kafaɗa ya yi yana ɗan taɓe baki ya ce. “Har yanzu ni kaina bansan mene ne ya dace da ita ba.” Mom M ta ɗan dakata da duba iPad dake hannunta sai kuma ta ɗan saki murmushi tana girgiza kai. Bata ce komai ba. Fira sosai Ayusherh suka yi da kakar nasu wato Yâ tâ kafin ta fito ta koma Ɗakin da yake a matsayin nata, sai kuma ta rasa abin yi hakan ya sa ta tsaya tsaye kewa yana cika zuciyarta, a hankali ta zura hannu a aljihu ta ciro Handkee ɗin da kamar koda yaushe yana ninke sai ƙamshi mai daɗi yake fitarwa, ta ɗan sumbaci hanki ɗin, tare da kallon ƙaramar sarewar dake a je cikin wani abu kamar dai an yi shi ne domin a je sarewar a ciki. Ayusherh ta ɗan saki murmushi at the same time tana sauke ajiyar zuciya, ƙasa-ƙasa ta furta. “Mamman da Abyaz ɗina, haƙiƙa nayi kewarku kuma zan ci gaba da kewarku har zuwa lokacin da rai na zai bar gangar jikina. Haƙiƙa nayi kewar ɗan uwa da bani da kamar ka wato Mamman ɗina sannan nayi rashi mai ciwo rashin ka Abyaz, na soka tun bansan mene ne so ba, har sai da na rasa ka, rashi kuma na har abada!.” Shiru ta yi domin tanaji idan ta ci gaba to fa kuka ne zai kwace ma ta. Hakan ya sa ta cikwikwiye Handkee n a tafin hannunta sai kawai ta fito daga Ɗakin ta ƙari sa ɗan gefe a cikin Palon dab da wani corridor, ta ɗan tsugunna tana duban Aku (Parrot) dake cikin madaidaicin ke jin wacce tana hango Ayusherh ta fara magana faɗi take. “Welcom Captain.” faɗi take tana ƙara wa. “Da alama kwana biyu da bana samun lokacin ki wani daga cikin iyayen ki dake gidan nan ya yi miki sabuwar hadda na magana.” Ayusherh ta faɗa tana ɗan kai hannu saitin kan Aku n dake cikin ke jin, dai dai lokacin kuma wayarta dake aljihun wandon Jean's dake jikinta ta soma ƙara alamar shigowa kira. Sai ta tsayuwarta Ayusherh ta yi tare da ciro wayar ta ɗan saki murmushi ganin Haisam ke kira. Ɗa ga kiran ta yi tare da karawa a kunne tana rangaɗa sallama cikin zazzaƙar muryarta. Daga ɓangaren Haisam ya lumshe ido yana gyara zaman da ya yi a bayan motar yayin da drivern ke driving nasa softly ya amsa sallamar tare da ci gaba da faɗin. “Nayi laifi fa, domin na shirya mana cin abinci tare da ƴan gidan mu a gobe ina fatan babu matsala?.” Ayusherh ta ɗan zaro ido tana shuke baki da hakan ya zame ma ta ɗabi'a sannan ta ce. “Amma dai wasa kake ko?.” “Allah da gaske nake.” “hump to ai shikenan Allah ya kai mu sai dai fa ina ɗan tsoro domin ban san wani irin tarfa zan samu daga wurin iyayen naka ba.” “Ki dena saka wata damuwa a ranki kinji domin ba abin da zai faru sai Alkhairi domin Momyna da Daddyna suna son duk wani abu da nakeso.” Dariya Ayusherh. “Ah lallai sannnu ɗan Mommy da Daddy.” Ta faɗa tana murmushi, shima ya yi murmushi ya ce. “Kuma Shalelen Battle Angel ɗin sa ba.” Girgiza kai ta yi ta nema damuwa da take ciki ta rasa, nan suka ci gaba da waya da Haisam yana ƙara kashe ta da kalamai, sun daɗe suna wayar kafin suka rabu kamar basa rabu ba, daga nan kuma Ayusherh ta wuce wurin Tata kasancewar ba wani fita yake ba in ba ta kama ba, saboda yanayin ƙafarsa, a can wurinsa ta sama Ma'az da Ali sai kawai ta jo ne suka ci gaba da fira da zalla tattaunawa suke yi a kan yanayin aikinta, Ali sai yaba ma ta yake dan shi acewarsa ko'a mafarki baya fatan ya yi aikin soja abu na sai da rai, shi ko yana matashin shi ɗayan jini, Ayusherh dai sai dariya suke masa domin Ali akwai tsoro kamar farar kura. *Saura ƙiris mu kammala Book 1, 👌 ga waɗan da suka shirya biyan kuɗin book 2 sai su biya ta wannan asusun. Naira ɗari uku. Kafin lokacin da zamu kammala book 1.* 8081129487, Sabi'u Khadija, MoniePoint Mfb. Sai ku turo shaidar biya ta nan. 07067953066 •… 💕 *CAPTAIN AYUSHERH*🥷 * 🍂🎀 (_The ShieldMaiden._) https://whatsapp.com/channel/0029VaEZtE15a2429vfcpf20 BY - Nainarh KD.... 𝒩𝓀𝒹'𝓈❦♡ Nainarhkd3 @Wattpad. *🔥 Perfectly Pen's (P.P✍️* Episode 22 GIDAN SARIN KAYA!!🔥🥳🤩 Hajiya shin kin gaji da siyan zannuwan gado suna koɗewa suna yin gashi? To ki garzayo wajen MAMAN AFRAH domin siyan masu inganci, babu kalar zannuwan gadon da babu a wajenmu. Idan kuma kin gaji da zama babu sana,a ne ki zo in baki sarin zannuwan gadon a farashi mai rahusa ki ɗora ribarki domin sana,ar ana samun alkairi sai kin gwada. Ina wacce ta gaji da siyan turarukan wuta masu ƙauri a garwashi, Ina da turaren wuta mai ƙamshi da daɗewa a ɗaki, idan kuma sana,ar turaren wutar kike ina bada farashin sari ina aikawa duk inda kike. Akwai humra mai musulmin ƙamshi da zaunawa a jiki, wacce nake wa laƙabi da sumar da mai gida don ƙamshi. Muna da Toilet cleaner in har toilet ɗinki ya dafe baya fita to ki gwada namu idan kika siya babu ruwan ki klin wajen wanki kumfa yake ya wanke bayi fesss ga ƙamshi da yake yi ɗaya za ki siya ko sari duk muna bayrwa. Akwai freshner mai ƙamshi, turaren wanka luquid soap, izal hypo, duk ina bayarwa sari a farashi mai rahusa. Ina wacce ta gaji da siyan shampoo da man kitso wanda bata ganin cigaba a gashin kanta da na ƴaƴanta? Gashin kamar gashin doki babu laushi sai tauri kina tajewa yana miki zafi, ki samawa gashinki da na yaranki mafita. Muna bayar da sari🥰 Akwai cotton material da lesuka da atamfofi siyan ɗaya ko sari. Tuntuɓe ni a wannn lambar 09013181851 ----------🙏______! Episode;22 Note: fejin jiya wato page 21 nayi mistake nace shekaru sha Tara Uncle ya yi a gidan kaso. To ba shekaru sha Tara ba ne, Shekaru Tara ne ya yi a gidan kaso. Tsaye yake ya juyama ƙofa baya, hannunsa a harɗe ya zuba ma wuri guda ido, a zahiri nazari yake a kan wani abu daban, yayin da a zahirin gaskiya kuma tunani ne fal ransa, tunanin da shi kan sa bai san Ranar denawa ba sannan bai san a kan mene ne ba, turo ƙofar da a ka yi tare da sallama ne ya sa shi juyawa suka haɗa ido da Kamasho da ya shigo Ɗakin fuska fal annashuwa. “Babban Yaya kana ta nan ke nan?, dama kai nake nema.” “Ai kuwa nima kai ɗin nake nema akwai maganar da nake so mu tattauna.” “Tohm yanzu ne ko kuwa sai na dawo kasan fa ba sauƙi tun da na sama wannan babban aikin.” Kamasho ya ƙare maganar yana ƴar dariya. “Opps! kace ka kusa tashi daga Kamasho ka koma Business Man na zahiri ke nan.” Arham ya faɗa tare da takawa ya isa wurin Kamasho ya riƙo hannunsa suka fito daga Ɗakin yana ci gaba da faɗin. “Gashi maganar da nake so muyi da kai a kan aikin naka da ka samu ne, ban san ya ya zaka karɓa maganar tawa ba sai dai ina so ka fahimce ni kada kayi min mummunar fahimta.” “to Babban Yaya kodai wani abu ne ya faru game da sabon aikin nawa?.” “E kusan haka, sai dai ba aikin naka ba ne mai matsalar, shi wanda kake aikin a ƙarƙashin sa ne.” “Ban gane ba.” Kamasho ya faɗa yana dakatawa da tafiyar tare da yi ma Arham kallon ina jiran ƙarin bayani dangane da kalaman ka. Arham yana shirin sake magana suka jiyo murya a ta bayansu duk suka juya suna kallon Uncle da ya ƙari so wurin idanunsa kafe a kan Kamasho dake bin sa da kallon rashin sani. “Ah Arham kuna ta nan ke nan dama kuwa kai nake nema.” Uncle ya yi maganar ga Arham sai dai still idanunsa suna kan Kamasho ne. “E Uncle nima wurin ka na nufa ai, tare da Abaan.” Shima Arham ya faɗa yana mai da dubansa kan Kamasho ganin irin kallon da yake yima Uncle ne ya sa Arham ci gaba da faɗin. “Abaan wannan shi ne Uncle jiya ya dawo daga ƙasar waje a baya yana ɗaya daga cikin masu kula da wannan gidan marayun.” “Oh Barka Uncle ya gajiya.” Kamasho ya faɗa cike da ladabi yana ɗan duƙawa da sauri Uncle ya ɗa gosa yana kamosa kasa jure wa ya yi sai kawai ya rungume shi ƙam yana lumshe ido cike da kewa. Arham ya yi tsam yana ka sa wani yunƙuri ya san za'ayi haka shi ya sa baiyi yunƙurin haɗa Uncle da Abaan ba tun a jiya. “Ah ah Malam wanene kai? Kuma me ya sa...?” Abaan ya faɗa yana gwace jikinsa daga na Uncle tare da bin sa da wani irin kallo zuciyarsa na buga wa da sauri sauri. “Babban Yaya kace min daga ƙasar waje ya dawo?.” Abaan ya ƙara faɗa yana duban Arham, shiru Arham ya yi masa ba tare da ya iya cewa komai ba. “Ba daga ƙasar waje na dawo ba daga gidan kaso na dawo bayan shafe tsawon shekaru Tara a bisa laifin da bani na Aikata ba, sharri ne kawai kuma ba kowa ne ya yi min sharri ba fa ce uban gidan da kake aiki a ƙarƙashin sa a halin yanzu wato Alhaji Dawud Nasamu ina nufin Mr President namu na yanzu, please ka sauraren mu, ka a je aikin da kake yi a ƙarƙashin sa ko domin....” Kasa ƙari sa maganar Uncle ya yi sakamakon ja da baya da Abaan ya fara yana bin sa da kallon tuhuma. “Abaan kada kayi masa mummunar fahimta gaskiya yake faɗa maka ko domin rayuwarka....” “Wanene shi da zai faɗa min gaskiya, domin ceton Rayuwata daga halaka? Mahaifina ne ko wa? To bana buƙatar duk wata kulawarsa a gareni, Mutumin wanda da bakinsa ya ce daga Prison ya dawo to mene ne ya sani dangane da dai dai ko rashin sa kuma...” Bai ƙari sa maganar ba, sakamakon wani gigitaccen tsawa da Arham ya buga masa yana kiran sunansa cikin fusata. Kallonsu duk su biyun Abaan ya yi da idanunsa da suka fara sauya kala, sannan ya watsar ya juya ya nufa barin wurin domin haka kawai yakejin haushin Mutumin na taso masa duk da shi kansa da za'a tambayesa dalili bai sani ba... “Idan kuma ya kasance ni ne Mahaifin naka fa, kuma shi ya sa nake faɗa maka hakan ko dan kiyaye ka daga shiga tarkon Nasamu?. ABAAN ka saurareni ni ne Mahaifin ka kuma bana faɗa maka haka ne domin rabaka da aikin da ka samu ba sai dai domin na kare Rayuwarka da nuna maka kulawar da ban samu nayi a baya ba.” Cak! Abaan ya dakata da tafiyar, yayin da kalaman Uncle suke ratsa majiyar sautinsa, cikin wani irin yanayi ya yi kamar zai juya ya kalla Uncle, sai kawai ya fasa, da sassarfa ya ci gaba da tafiyar ya bar wurin. Lumshe ido Uncle ya yi yana dafa dai dai saitin zuciyarsa tare da sauke nannauyar ajiyar zuciya, da sauri Arham ya ƙari sa wurin tare da tallafo sa yana faɗin..“Uncle kana lafiya kuwa?.” “Karka damu ina lafiya kai ni Gidan Sirri kawai mu je mu haɗu da waɗanda nayi maka Bayani a kan su.” Uncle ya faɗa cikin dauriya yana saita tsayuwarsa, ajiyar zuciya Arham ya yi sannan ya taimakawa Uncle suka ƙari sa wurin motar Arham ɗin suka shiga ciki sannan suka har gidan marayun. *** “Nifa tsoro nake ji kana tunanin Familyn ka zasuyi saurin aminta dani kuwa?.” Ayusherh ta tambaya yana duban Haisam dake driving a nutse. “Ya dai Battle Angel! da ya faɗuwar gaba haka, ko kin manta ke ɗin jaruma ce, kuma ta musamman a soji kin manta da duk wannan ne kikejin tsoro?.” “Hump kai dai ba zaka gane ba ne kawai domin ni kaɗai nasan yadda nakeji.” Ayusherh ta faɗa tana dafa dai dai saitin zuciyarta tare da lumshe ido tun da Haisam ya ɗaukota daga gida suka nufa gidansu domin haɗu wa da familynsa kamar yadda suka tsara, takejin wani irin mummunar faɗuwar gaba da ita kanta ta rasa Dalili, a zahirin gaskiya ba don zata haɗu da familyn Haisam ne kaɗai takejin wannnan yanayi ba, a'a wani abun daban sai dai ta rasa ko menene. Suna fira kaɗan kaɗan Haisam yana ƙara ƙarfafa ma ta gwiwa tare da kalamai masu taushi na soyayya, a haka har suka ƙari sa katafariyar anguwan sannan motar Haisam ta shiga cikin ƙararren gidan. Ayusherh ta sauke ajiyar zuciya lokacin da Haisam ya fa ka motar sannan ya bita da kansa ya zagaya tare da buɗe ma ta motar ta fito tana ƙara sauke ajiyar zuciya a nutse take bin gidan da kallo ba ƙarya ya burgeta. “Mu ƙari sa ciki ko?.” Haisam ya faɗa fuskarsa ɗauke da murmushi yana miƙa ma ta hannu alamar ta saka nata cikin nashi. Murmushi ta yi masa tare da girgiza kai kana ta ce. “Ka manta ne? Addini na bai bani damar yin hakan ba.” Murmushin shima ya yi yana yi ma ta nuni da hanya da su ƙari sa ciki. Taku ɗaya, biyu suka yi a na ukun gaba ɗaya mutanen gidan tun daga kan Mom M Daddy Nasamu da kuma General Lamrat sai kuma Yusra da Aunty Dawha duk suka fito tarbar Ayusherh, hakan ya sa suka dakata da tafiyar yayin da bugun zuciyar Ayusherh yaƙe ƙara ƙaruwa da duk taku ɗaya da familyn Haisam suke yi domin isa wurin ta. “Ya zama dole a daren nan mu samo wannan ma'ajiyar bayanai dake a cikin briefcase ɗin da Nasamu ya yi nasara gwara daga hannuna a shekarun baya lokacin da ya ƙalama Uncle sharri bayan Uncle ɗin ya taimake ni daga hannun yaran Nasamu a wancan daji.” Arham ya yi maganar a nutse yana kuma duban matashin saurayin da ba zai wuce sa'an sa ba dake tsaye a gefe yayin da Uncle yake zaune saman kujera ya ɗaura hannu a kan desk ɗin dake gabansa. Sannan Arham ɗin ya ci gaba da faɗin. “Sai dai fa ɗauko wannan ma'ajiyar bayanan zai yi matuƙar wahala duba da irin tsaron dake a gidan Mr President ɗin sannan kuma ta iya yiwuwa ma a halin yanzu ya daɗe da ƙona ma'ajiyar bayanan sannan kuma zata iya yiwuwa ma'ajiyar bayanan basu a gidan a halin yanzu.” Girgiza kai Matashin saurayin ya yi yana faɗin. “Nasamu ba zai taɓa gangancin ƙona waɗan nan ma'ajiyar bayanan ba domin akwai abubuwa masu tari yawa dangane da su kuma duk wasu laifukan da ya aikata ne yake sakawa a cikin ma'adanai na bayanan, a yadda bincike na ya nunamin ke nan kuma sannan wannan ma'ajiyar bayanan yana a cikin wani Ɗakine mafi Sirri dake cikin gidan Mr President.” “To mene ne abin yi?.” Arham ya faɗa. “Melikha fa me ya sa batazo ba bayan kuma an tsara da ita zamu haɗu yau.” Uncle ya faɗa yana ɗan buga desk ɗin gabansa. “Sorry Uncle wani aiki ne na gaggawa ya taso ma ta shi ya sa bata sama halarta ba.” Cewar Arham. Shiru Uncle ya yi sai kuma ya kalla matashin saurayin ya ce. _To dai duk da naso yafi haka, amma to dai mu haɗu gobe a next page domin jin yadda zata kaya._ A ci gaba da payment na book 2 fa. 8081129487, MoniePoint Mfb, Sabi'u Khadija. 07067953066 Nainarh KD...✍️ •… 💕 *CAPTAIN AYUSHERH*🥷 * 🍂🎀 (_The ShieldMaiden._) BY - Nainarh KD.... 𝒩𝓀𝒹'𝓈❦♡ Nainarhkd3 @Wattpad. *🔥 Perfectly Pen's (P.P✍️* Episode 23. “Amma Bilal...” Saurayin ya katse Uncle da faɗin. “Sorry Uncle karka yi yunƙurin dakatar damu daga ɗauko ma'ajiyar bayanan a yau dai...” ya ɗan shiru sai kuma ya ci gaba da faɗin. “Nasamu ya yi ma rayuwata illar da zan iya yin komai domin ganin na kaishi ƙasa saboda haka ka bimu da fatan nasara kawai.” Sauke ajiyar zuciya Uncle ya yi yana duban Arham. Gyaɗa masa kai Arham ya yi yana harɗe hannu a ƙirji, duk gaba ɗaya yau Arham bai san mene ne ya shiga kanshi ba, kawai dai ji yake muddun bai kai ga zuwa gidan Nasamu domin ɗauko wannan ma'ajiyar bayanan ba, to fa ba zai sama sukuni ba... “Maraba lale da zuwa sirikata.” Dam! Ƙirjin Ayusherh ya bada sautin bugu, a hankali ta ɗa go fararen idanunta suka sauka a kan familyn dake tsay-tsaye fuska tab da walwala yayin da ta sauke su a kan Matar da ta yi maganar, ƙaƙalo murmushi ta yi badan ƙirjin ta ya dena bugun lugude ba. Lokacin da suka ƙari sa dai dai inda Familyn suke tsaye sai Ayusherh ta ɗan tsuguna da girmamawa zata gaishe su. Da sauri Mom M ta kamo ta tana murmushi. “Barka da dare Aunty fatan na sameku lafiya?.” “Lafiya Qlau Ƴar nan mu shiga ciki ko.” Mom M ta faɗa tana riƙo hannun Ayusherh. “Laaa! Mom wato har an fara nuna min wariya dan an sama 'ya ke nan ko?.” Haisam ya faɗa kamar da gaske yana dakatawa da tafiyar. “Ai ba mai nuna maka wariya muddun ina kusa.” General ta faɗa tana kamo hannunsa. “That's you're special always, My second Mom.” Cewar Haisam yana murmushi, murmushin duk suka yi sannan suka shiga ciki, nan ne kuma Ayusherh ta gaisa da kowa cikin girmamawa bayan sun gama Aunty Dawha da kanta ta yi ma ta iso zuwa wurin da aka tana da domin Dinner. Duk suka ƙari sa wurin sai dai da mamaki suka ja tunga duk suka yi turus ganin Nusra zaune a Dining ɗin tana cin abinci hankali kwance. “Nusra dama kina gidan nan?, shi ne Yusra ta ce baki dawo ba?.” Aunty Dawha ta faɗa da alama ranta ya ɗan ɓaci da abin da suka tarar Nusra ke yi. Fuska ɗauke da ƙayataccen murmushi Nusra ta ɗa go tana dubansu tare da yin farrr! Da ido, sannan ta miƙe tsaye tana ƙari sawa inda suke tare da faɗin. “Oo sorry Dear Momma bacci na ɗan yi bayan na dawo, so Yusra ma batasan na dawo ba, yanzu kuma na tashi da yunwa obaa, shi ne nazo nema wa cikina haƙƙinsa.” Ta ƙare maganar dai dai idanunta sun sauka a kan Ayusherh dake tsaye gefen Haisam. “Woww ashe Auntyn tamu ce har ta ƙari so. Sorry Our Aunty ai Habibin naki bai sanar dani har da ke za'ayi dinner ba, I thought haɗu wa kawai za'ayi a san juna...” Bata ƙari sa ba Haisam da ransa ya kai ƙololuwa wurin ɓaci ya daka ma ta tsawa tare da faɗin. “Baki da hankali ne a garin wasu mahaukatan a ka faɗa miki haka a ke tarbar baƙo? Stupid kawai.” Rai a ɓace ya ƙare maganar tare da jan hannun Ayusherh duk da bataso ya taɓa ta ba ya ƙari sa da ita wurin Dining ɗin tare da ja ma ta kujera ta zauna. Jiki a sanyaye kowanne ya sama wuri ya zauna yayin da Haisam ya zauna gefen Ayusherh, Yusra tana shirin zama ta ɗayan gefen, Nusra ta yi saurin ƙari sawa tare da zama tana murmushi ta ce. “Sorry Sis barni na zauna kusa da Auntyn tamu ko ma yi fira.” Girgiza kai kurum Yusra ta yi sannan taja kujera kusa da Aunty Lamrat ta zauna. Cin abincin suka fara a nutse jefi jefi Aunty Dawha da Haisam suke yima Ayusherh fira wai ko dan ta saki jiki ganin kamar bata saki jiki ba, yayin da Mom M da tun tarban da ta yi ma Ayusherh a waje bata ƙara magana ba, shiru ta yi kuma komai kwakwan mutum ya kalla fuskarta bai isa ya ce ga ainihin yanayin da take ciki ba, lokaci lokaci suke haɗa ido da Alhaji Dawud, yayin da General Lamrat sai ta zama tamkar ita ce Mahaifiyar Haisam ɗin irin kulawar da take bawa Ayusherh, ita kanta Ayusherhn a yau ɗin take sanin ba General ce mahaifiyar Haisam ba. Yayin da Yusra da ta kasance dama Surutu bai dameta ba kuma ya yi dai dai da tana cikin wani yanayi shi ya sa tun gaisawa da suka yi da Ayusherh wata magana bata ƙara shiga tsakaninsu ba. Miƙe wa Nusra zatayi at the same time ta fakaici idon mutanen wurin ta hanyar kai hannu ta tura Glass cup mai ɗauke da juice a ciki, ai kuwa ya kwarara saman jikin Ayusherh duk ya ɓata farar doguwar rigar jikinta. Zaro ido Nusra ta yi a fili take nuna kiɗimarta ta yi saurin zarar tissue tana goge wurin da juice ɗin ya ɓata ma Ayusherh cikin faɗin. “Oo am so sorry dear ban lura ba ne. Bara na goge miki.” Miƙe wa tsaye Ayusherh ta yi a kufule take duban Nusra, tsaf ta gama fahimtar rainin wayo irin na Yarinyar amma ta sha re tare da faɗin. “Karki damu, nunamin hanyar da zan bi domin na wanke.” Ayusherh ta faɗa cikin taushin murya ba tare da ta kula Sannun da ɗaukakin mutanen wurin ke yi ma ta ba, shi kam Haisam ya fusata iya fusata sai dai haƙuri da General Lamrat take basa da ido shi ne abin da ya hana ya ɗauki mataki, sai dai duk da hakan uwar harara yake watsa ma Nusra tare da jan gwafa, ita kam ta yi kamar bata gani ba, sai ma kama Hannun Ayusherh da ta yi tana faɗin. “Zo muje na nuna miki kinji ina mai daɗa baki haƙuri.” Ta ƙare maganar dai dai sun isa wani ɗan corridor da zai sadasu da wurin da Ayusherh zata shiga ta gyara jikinta, Nusra ta dakata da tafiyar tare da juyowa murmushin fuskarta bai ɗauke ba ta ɗan kalla Ayusherh up to down tana juya ido ta ce. “Tohm Our Aunty gashi na kawoki wurin da zaki gyara jikintki ina mai da ɗa baki haƙuri kinji Please?!” Zagaye ta Ayusherh ta yi har zata wuce ba tare da ta ce ma ta komai ba, sai kuma taji Nusra n ta yi maganar ƙasa ƙasa duk da Ayusherh bata fahimci mai ta ce ba amma ta dakata tare da dubanta a tsanake ta ɗan yi taku ɗaya, biyu zuwa uku ta ƙari sa gaban Nusra sannan ta ce a taƙaice. “Nusra kike ko?, so i warn you to stop pretend like that, coz I hate it, just go straight to me, I will accept you as way I can.” Tana gama faɗar hakan ta juya tare da barin wurin ta shige ciki. Ɓacin rai da kuma mamaki ya sa Nusra ta bar wurin tana jan tsaki. Numfashi kawai Ayusherh take saukewa a bayin tana ƙoƙarin danne ɓacin ranta ba dan komai ba sai dan Haisam, sai da ta wanke tare da goge wurin da juice ɗin ya zuba sannan ta fito daga bathroom ɗin dai dai lokacin kuma wutar gidan ya ɗauke a karo na uku ke nan. domin a ɗazu da suna zazzaune wutar ta ɗauke sai dai basu wani damu ba, haka ma da ta shiga domin gyara jikinta wutan ta ƙara ɗauke wa a yanzu kuma da ta ɗauke a karo na uku sai Ayusherh taji bata gamsu da wannan ɗauke wa da kawowa da wutan ke yi ba. Din-ɗim! Haka kanta ya yi ma ta saboda duhun da gaba ɗaya ilahirin gidan ya ɗauka ita kuma a duniyar nan babu abin da ta tsana sama da duhu, wannan dalili ya sa ta tsaya cak wuri guda yayin da a hankali kaifafan kunnuwanta suka fara jiyo ma ta wani sauti kamar na tafiya da sassarfa, da sauri ta nufa ƙofa ta fita ta fara lalube cikin haka taji ta buga karo da Mutum sai dai duk tsayinta a'iya broadchest ɗin sa taji kanta ya bugu, ta yi saurin dafa saitin wurin da ta bugun tana faɗin. “Ouch!!” cikin jin zafin da goshin nata keyi ma ta. Shi kuwa Arham cak ya dakata da ƙoƙarin barin wurin da yake yi a gaggauce, jin wani irin yanayi dake fuzgarsa a dai dai lokacin da sautin faɗin 'ouch!' ɗin da Ayusherh ta yi ya isa zuwa majiyar sautinsa, take salon bugun zuciyar kowannensu ya sauya, Ayusherh ta buɗe idonta dake lumshe a dai dai lokacin da ya juyo suna fuskantar juna kuma a ka yi katari a taƙin ne hasken wutar lantarki ya dawo ya karaɗe gaba ɗaya gidan. Ayusherh ta ƙara girman manyan idanunta tana watsa su a saman fuskarsa dake rufe ruf da mask mai tambarin tiger, 5 secs suka ɗauka suna watsama junansu kallo ta tsakar ido kafin Ayusherh ta dawo hayyacinta dai dai lokacin kuma Bilal dake zaune a mota dake waje ya ce. “Arham! Wani shirme ka tsaya yi ba za kayi kazo mu gudu ba bayan kuma wutan ta dawo?.” Kalaman Bilal ta hanyar Communicative device dake maƙale a kunnen Arham su ne suka dawo dashi hayyacinsa, a dai dai lokacin kuma Ayusherh ta shammace shi tare da kai hannu zata wafce mask ɗin dake fuskarsa shi kuma ya yi baya, ita kuma Ayusherh da zafin nama ta yi yunƙurin wafce mask ɗin hakan ya sa ta yi taga taga zata faɗi a saitin waterfalls dake wurin a jere, hakan ya sa ta saki 'yar ƙara domin muddun ta faɗa a wurin ba ƙaramin rauni zataji ba, ganin haka ya sa Arham da har ya yi gaba ya yi maza ya dawo tare da janyo hannunta ta faɗa jikinsa, lokacin kuma sautin muryar Haisam ya karaɗe wurin yana kwala kiran sunan Ayusherh. Sakinta Arham ya yi ta miƙe tsaye yayin da ya yi wuf ya bi ta wata hanya tare da haure ƙaramar katangar mai cike da tsoro ya fice daga gidan, a dai dai lokacin Haisam ya ƙari so wurin tare da kiran sunan Ayusherh da ta yi zumu tana bin wurin da Arham ya bi da kallo. •… 💕 *CAPTAIN AYUSHERH*🥷 * 🍂🎀 (_The ShieldMaiden._) https://whatsapp.com/channel/0029VaEZtE15a2429vfcpf20 BY - Nainarh KD.... 𝒩𝓀𝒹'𝓈❦♡ Nainarhkd3 @Wattpad. *🔥 Perfectly Pen's....🖊️* Episode 24 “Thanks to Allah, Battle Angel kina lafiya?.” Haisam ya faɗa cikin sauke ajiyar zuciya lokacin da ya ƙari so wurin. Ajiyar zuciya ta sauke tare da gyaɗa masa kai ba tare da ta iya cewa komai ba. “Ah,ah to amma garin ya ya kika zo nan bayan kina ciki?.” Haisam ya jefo ma ta tambayar da ya sa gaban Ayusherh bugawa ji ta yi kamar ta faɗa masa gaskiyar abin da ta gani amma sai wata zuciyar ta gargaɗe ta domin bata da wani sheda daɗi da ƙari kuma abin da ya fi tsaya ma ta a rai shi ne taimakon Rayuwarta da Mutumin ya yi. “Ah.. dama.. dama kawai...” “Tsoro kikaji ko?.” Da sauri ta gyaɗa masa kai. Haisam ya kwashe da dariya sai kuma ya ce. “Au dama Battle Angel tana jin tsoro ban sani ba.” Shiru ta yi masa sai kawai ta nufa hanyar barin wurin. Ya yi saurin bin bayanta yana faɗin. “Sorry ai kam ki bar jin tsoro domin kina dani.” “Ka ganka ko?.” Ayusherh ta faɗa a shagwaɓe. “Mai kuma nayi?.” Cewar Haisam yana ɗa ge hannu. Ayusherh zata yi magana su Aunty Dawha suka ƙari so wurin suna tambayar meke faruwa?. Haisam ya ce. “Ba wani abu ba ne kawai dai taji tsoro ne lokacin da wutar ta ɗauke a sakamakon tana da lalura ta rashin son duhu shi ya sa.” “Tsoro kuma! Soja da tsoro? I thought ita ɗin soja ce mai muƙamin Captain ma, Hhh ai tsoro ba nata ba ne sai irin mu irin mu ai.” Nusra ke maganar sai kuma ta yi saurin kama baki ganin irin kallon da mutanen wurin ke yi ma ta. Haisam yaja gwafa. “Zamu wuce domin zan mayar da Ayusherh gida dare ya yi.” “A'a tun yanzu kuma” “E Aunty! Saboda Ayusherh ta gaji.” Haisam ya faɗa a taƙaice ba tare da ya duba Aunty Dawha da ta yi maganar ba, domin kowa ya sani, babu jituwa tsakaninsa da ita kuma hakan ya samo Asali ne tun yana ƙaraminsa da shi kuma bata sauya zani ba har wa yau, duk da irin kulawar da Aunty Dawha ke yi masa da kuma irin kyawawan ɗabi'unta da kowa ya shaida. Ayusherh ta yi musu sallama har zasu tafi General Lamrat ta je su jirata sannan ta shiga ciki, bata jima ba ta fito riƙe da ɗan ƙaramin kwali na turare ta bawa Ayusherh kyauta, da kyar ma a ka samu Ayusherh ɗin ta karɓa, ta yi ma ta godiya, sannan suka tafi. Bayan Haisam ya kaita can gidan ta da yake gobe Monday Ranar aiki sai da suka ƙara shan fira sannan suka yi sallama ya koma gida. Abin mamaki ko bayan ya koma a maimakon Daddy ya tarbe sa da tambayar ya dawo lafiya, sai kawai a daren ya kira shi Ɗakin shi tare da miƙa masa wasu takardu wai ya saka hannu. Kuma koda Haisam ya so jin menene takardun suka ƙunsa kafin ya saka hannun. Sai kawai ce masa Daddy ya yi. 'Ba masu wani muhimmanci bane kawai dai saka hannunka a ke buƙata.' Haka kawai Haisam yaji bai yarda ba domin ba wannan ne karo na farko ba da Mahaifin nasa yake basa Takardu at several times ya ce ya saka hannu ba, kuma ya saka, amma yau kawai sai yaji bai aminta ba kuma ya ƙudurta ba zai saka hannu ba har sai an faɗa masa abin da Takardun suka ƙunsa, shi kuma Daddy sai ƙumbiya-ƙumbiya yake yi yaƙi ya yi masa takamaiman bayani. A taƙaice dai a haka suka rabu baran-baran ba tare da Haisam ya saka hannun ba, domin alƙawari ya yi ba zai ƙara saka hannu a wata takarda ba muddun ba ayi masa bayani a kan abin da takardun suka ƙunsa ba, kuma ba komai ne yafi ɗaure masa kai ba sai Irin ƙin yarda da ya karanta takardar da Daddy ke yi, a ransa ya ƙudurta Tabbas wata rana sai ya lalubo inda Daddy yake a je takardun ya duba yaga wata uwa ce a jiki. Ran Daddy ba ƙaramin ɓaci ya yi ba, da Haisam yaƙi saka hannu hakan ya sa ya ɗau zafi har suka rabu a daren as baran-baran a haka suka kwana. Washe gari kuma Nusra ta matsama Haisam a kan yadda yake shareta bayan kuma ya san tana son shi tun batasan kanta ba amma shi ne tsaban cin fuska har ya iya kawo budurwarsa cikin gidan. A lokacin yana ɗakin sa fitowarsa daga wanka ke nan sanye da bathrobe ita kuma ta shigo Ɗakin cikin kayan Bacci take yi masa wannan maganganu. Ransa ya ɓaci amma ya danne ya samu ya lallasheta ta bar Ɗakin saboda shi da kansa ya san bai kyauta ba, yana sane tana son shi sosai da duk zuciyarta amma ya shareta ya yi watsi da ita. A dai dai Nusra zata bar Ɗakin shi kuma Daddy yake shigowa cike da mamaki ya bita da kallo ganin irin shigar dake jikinta ita kam ko'a jikinta ta kaɗa kai ta fice daga Ɗakin, sai kawai Daddy ya dawo da dubansa kan Haisam da har sai da ƙirjin Haisam ya buga dan ya gama sadaƙarwa wani kallon daban Daddy zai masa har ma ya tuhumesa, sai dai ga mamakinsa wani batun daban Daddy ya yi masa shi ne a kan saka hannu a takardu kuma ya ƙara da faɗin muddun bai saka hannu ba to fa dole ya fara zuwa aiki a ɗaya daga cikin company's. Zuwa wannan lokacin Haisam ya kai iya wuya. Cikin wani irin yanayi ya duba mahaifin nasa tsaban ɓacin rai can ƙasa maganar ma take fitowa ya ce. “Daddy! Sanin kanka ne bani da ra'ayin zama Soja ka saka na zama a dole ba yadda zan yi, nayi maka biyayya, buri na shi ne zama Cikakken Actor kuma Dancer, yeah tare da taimakon ka na zama hakan har kuma na kai ga kaiwa Babban matsayi na kasancewa International Model duk nayi farin ciki da hakan domin da taimakon ka na kai duk matakin da nake a yanzu, sai dai fa a wannan karon ba zan iya cika maka Burin ka da na fara aiki a Company ba, fisabilillah nawa kakeso na kasu ne? Kuma ma ni bani da goge wa a ɓangaren kasuwanci, a ma a je wannan batun a gefe, kace dole na saka hannu a waɗan nan Takardu kuma kaƙi kayi min bayani a kan abin da suka ƙunsa Ni kuma alƙawari nayi ma kaina muddun baka sanar dani abin da Takardun suka ƙunsa ba, to fa ba zan taɓa yi maka biyayya, ta hanyar saka hannu ba!.” Haisam yana gama faɗin hakan ya juya ya ci gaba da abin da yake yi. Rai a tsananin ɓace Daddy ya tashi ya bar masa ɗakin domin fitar nasa shi ne mafi a'ala, domin ji yake tamkar ya shaƙe Haisam ɗin, ya kashe har lahira. Sai dai yin hakan ba abu ne mai yiwuwa ba domin a wannan taƙin muddun ya kashe Haisam ai shima rayuwarsa ta tarwatse. BAYAN WATA UKU..! Haka Rayuwa ta ci gaba gangarawa yayin da soyayya ta yi ƙarfi sosai Tsakanin Ayusherh da Haisam kuma abin nasu sai sam barka sannan tana yawan zuwa gidansu Haisam ɗin domin musamman General Lamrat take shirya musu Dinner ko kuma lunch sai dai wani abin mamaki da yake faruwa da idon kowa bai kai, kai ba shi ne a duk ranar da Ayusherh zata je Gidansu Haisam, to fa sai an sama wani abu ya faru domin akwai wani zuwa da ta yi ma lokacin jami'ai ne suka je gidan wai da sunan bincike sai dai har suka yi suka gama basu sama Komai ba. Ayusherh taso ta dena zuwa gidan saboda hakan duk da dai ba wanda ya taɓa ma ta magana dangane da hakan, shi ya sa ma ta sha re ta barshi a katari kawai a ke yi, sai dai tun daga wancan Ranar bata ƙara haɗu wa da wannan mutumin ba duk da batasan fuskarsa ba sai dai har wa yau bata dena mamakin taimaka ma ta da ya yi a lokacin da bai barta ta faɗi ba. Ta ɓangaren ta da Nusra kam, sam Nusra bata gaban Ayusherh shi ya sa duk abin da take yi idan sun haɗu Ayusherh bata ko ɗa ga kai ta dubeta sai dai da alama Nusra ba haka taso ba. Ta ɓangaren Abaan Kamasho kuwa duk yadda Uncle ya so ya fahimce shi a kan ya a je aikinsa a ƙarƙarshin Nasamu Company, ƙi ya yi kuma baya taɓa yarda su zauna inuwa ɗaya Uncle ɗin duk da ya tabbata Uncle ɗin ne Mahaifinsa, sai dai gefe guda na zuciyarsa shi ɗaya ya san abin da yake shirya wa domin ya gano gaskiya a kan maganganun Uncle dangane da Alhaji Dawud Nasamu, Mr President. Yau ma kamar kullum tsaf ya kammala shirinsa cikin shiga na zuwa aiki sannan ya hau cab ya wuce zuwa ƙerarren companyn domin zuwa yanzu har Arham ya dena kulawa don laifin Uncle ne ya shafe shi. Bayan ya ƙari sa Companyn ya fito daga Cab ɗin tare da biyan mai Cab ɗin kuɗinsa sannan ya shiga ciki kai tsaye ta elevator yabi domin a jiya sun tattaunawa a kan yau idan yazo zai biya office ɗin Alhaji Dawud Nasamu domin ya karɓa wasu files hakan ya sa bayan ya fito daga elevator ɗin ya nufa office ɗin yana gyara maɓallin rigarsa, ya kai hannu zai bubbuuga ƙofar sai yaji ta a buɗe hakan ya sa shi kunna kai zai shiga ciki sai dai maganar da ya ji a na yi daga ciki ne ya ɗauki hankalinsa, hakan ya sa ya yi kasaƙe tare da kasa kunne yanajin abin da ake faɗa. A fusace Mr President ya watsar da takardun hannunsa saman teburin gabansa ya fara kai kawo yana fitar huci na zallar ɓacin rai yayin da Mom M dake sanye cikin coat da wando ta zuba masa ido tana kallon sa tare da nazarinsa kana ta ce. “Dawud wai a kan wannan ƙaramin abin kake duk wannan ɓacin ran?.” Juyowa ya yi yana dubanta, ya ɗaura hannu ya riƙe ƙugu sannan ya ce. “Wannan ba ƙaramin Abu ba ne domin duk yadda naso da wannan yaron ya saka hannu a Takardun ƙi yayi kuma hakan ya yi mugun fusatani ga kuma waɗan nan Takardun da suka ɓata a Ɗakin Sirri na rasa wa zan zarga a kan hakan.” Taka wa ta ɗan yi kaɗan ta isa gare shi tare da dafa kafaɗarsa. “Mu kashe shi kawai tun da ba zai yi mana biyayya ba.” Ta faɗa idanunta cikin na shi tana mai tabbatar masa da kalamanta. Furzar da iska ya yi. “Kashe Haisam ba shi ne mafita ba a halin yanzu domin kema kin san yana da tarin amfanoni gare mu kawai mu nema hanyar da zamu saka shi ya saka hannun ta ƙarfin tsiya.” “To ta ya ya ke nan?.” Ta faɗa cikin toshe War basira dangane da lamarin. “Ai kece zakiyi mana tunani ki nemo mana mafita kamar yadda a ka saba.” Shiru ta yi tare da ɗan fara taka wa kaɗan, lura ta yi da mutum tsaye a bakin ƙofa, da sauri ta kalla Alhaji Dawud da shima sai a lokacin ya lura da abin da ta gani. “Waye anan? Koma waye ya yi gaggawar nuna kansa tun kafin na nago shi.” Nasamu ya faɗa da ɗan ƙarfi. Da sauri Kamasho ya ɗan ja baya sai kuma ya dake, tare da tura ƙofar ya shiga da sallama. Da ɗumbin mamaki duk suke dubansa, babu wanda ya amsa sallamar da ya yi sai ma kafa masa ido da suka yi suna bin sa da kallon tuhuma Alhaji Dawud ya ce. “Mai kaji?.” “Kamar ya ya ban gane ba?.” Kamasho ya faɗa cikin dakiya. “Cewa nayi mai kaji muna tattaunawa a kai?.” Alhaji Dawud Nasamu ya kara faɗa da ɗan tsawa. Kamasho ya ɗan yi baya sai ya faɗi a kan sofa dake wurin. Hakan ya sa Alhaji Dawud ya janyo kujerar dake wurin ya zauna yana fuskantarsa yayin da Mom M take tsaye a bayansa ta harɗe hannu a ƙirji. “Salin'alin tun muna mu kaɗai ka faɗa mana mene ne kaji muna tattaunawa?.” Alhaji Dawud ya ƙara faɗa cikin ƙoƙarin danne ɓacin ransa. Sai dai fa kai da fata Kamasho ya dage a kan bai ji komai ba. “Ka tabbata?.” Cewar Alhaji Dawud yana zuba masa ido. Bayan ya yi tambayar duniya amma Kamasho ya ce bai ji komai ba har maimaita masa abin da suka tattauna ya yi amma ya ce bai ma san wannan maganar suke ba domin bai ji komai ba. “E na tabbata.” Kamasho ya faɗa da sauri. “Okay tashi ka tafi.” Tun kafin Alhaji Dawud ya rufe baki Kamasho ya miƙe da sauri ya bar office ɗin yana fita a maimakon ya wuce office ɗin sa sai kawai ya bar Companyn gaba ɗaya cikin tashin hankali ya tara Cab ya shiga tare da ciro wayarsa ya fara yunƙurin neman lambar Arham. “Dawud ma za ka saka abi yaron nan domin akwai na'ura a jikinsa.” Hankali tashe Alhaji Nasamu ya fara ƙoƙarin Dialing Lambar da ya yi saving da Crime Mentor. Yayin da kira kuma ya shigo wayar Mom M da sauri ta ɗa ga dai dai lokacin kuma Alhaji Nasamu ya gama sanar da Crime Mentor abin da zai yi. Zaro ido Mom M ta yi cikin ɓacin rai ta cillar da wayar tare da duban Alhaji Nasamu da ya yi kasaƙe yana jira yaji abin da a ka faɗa ma ta. “Lallai Yusra ta kira ruwa ta kuma taɓo wuliyar dodo ƙoƙari take ta tashi Mayunwacin Damisan dake bacci domin ta dage kai da fata sai ta tona mana asiri Dangane da waɗan nan baƙaƙƙen kuɗaɗen da wasun su a ka tanadar domin zaɓe, yanzu haka ɗan jaridan da ta kira zata bawa bayanan shi ne ya kirani yana faɗa min tare da cewa ko dai na bashi Miliyan ɗari ko kuma ya karɓa bayanan ya watsa a media.” Ragwajab Alhaji Nasamu ya zauna yana dafe kai sai kuma ya yi saurin dubanta cikin sauri ya ce. “Yusra ta kai ni inda ba zan jure ci gaba ganin tana ƙoƙarin tonamin asiri ba, faɗa min mene ne ya kamata muyi?.” Mom M ta furzar da iska daga bakinta sannan ta yi masa alama da hannu a kan a kashe ta kawai kana ta ƙara da faɗin. “Shi yaron ɗan jaridan na bashi address nace masa mu haɗu a can ka saka Crime Mentor ya aika yaransa su yagalgala ɗan jaridan sannan su a je shi a titin jirgin ƙasa. Ita kuma Yusra ka saka Crime Mentor ya kamota ya kaita inda ya kai Abaan Kamasho waɗan nan da kanmu zamuyi musu hukuncin da ya dace da su.” Jinjina ya yi ma ta da Babbar yatsa yana sakin murmushi tare da saurin ɗaukar wayarsa ya fara ƙoƙarin yin abin da ta ce. Yayin da ta mayar masa martani da yin murmushin gefen fuska zatayi magana ke nan iPad ɗin dake a je saman table ta fara ruri alamun dake nufin an taɓa wani abu dake cikin Ɗakin Sirri a can gida. Da sauri ta ɗauki iPad ɗin ai kuwa ta zaro ido cike da tsananin mamaki na ganin abin da yake faruwa a Ɗakin Sirri. Nunama Alhaji Dawud iPad ɗin ta yi a tare kuma a zabure suka nufa ƙofa tare da fita daga office ɗin cikin sassarfa suka sauka ƙasa tare da shiga motoci a gaggauce driver's ɗin suka ja motocin suka bar Companyn kai tsaye gida suka nufa cikin matsanancin gudu. _Baku da buƙatar sai nayi muku tuni a kan this page is second to the last Page of book 1, so hurry up and continue subscription... Book is in the corner, trust me kuma anan rikita-rikita da kuma tarin chakwakiya suke so kada ku bari a barku a baya._ Ɗari Uku. 8081129487, Sabi'u Khadija, MoniePoint Mfb. 07067953066. Nainarh KD. Haƙiƙa Bayan Sarauniyar kyau wannan shi ne littafi na biya da ya shiga raina nake ƙaunarsa da gaske...🥺🫶💔 •… 💕 *CAPTAIN AYUSHERH*🥷 * 🍂🎀 (_The ShieldMaiden._) Nainarh KD✍️ * Perfectly Pen's* Episode 25 End of Book 1....🥳 Cikin ƙanƙanin lokaci suka ƙari sa gida, ba tare da jiran driver ya dai dai ta faka motar da suke ciki ba, duk suka fito a tare da sassarfa suka ƙari sa Palon. Sai dai turus suka ja tunga, duk suka tsaya sunabin Haisam dake zaune ya harɗe ƙafa yana latsa waya, suka bishi da kallon mamaki, cikin rawar baki Mom M ta ce. “Son! Yaushe ka dawo?.” Ta faɗa a sakamakon Haisam ɗin baya nan kwana biyu ya tafi Lagos bisa aikin Film ɗin da yake a kai. A hankali ya ɗa go idanunsa, fuska tab da murmushi ya ce. “Surprised! Ban wuce mintina goma da zuwa ba, dama bazata na shirya yi muku, to ko dai bakuji daɗin bazatan ba ne na juya zuwa inda na fito?.” Ya ƙare maganar da kyar dariyar zolaya. Murmushi duk suka ƙaƙalo suka ɗaura bisa fuskarsu dake cike da ruɗani. Mom M ta ƙari sa tare da zama gefensa tana faɗin. “Mu a suwa zamu ce ka koma? Kawai dai bazatar naka ne ta bamu mamaki, sai dai nayi farin ciki My Son ya dawo kusa dani, kasan fa banaso kana nisa dani?.” Ta kai maganar tare da shafa fuskarsa cike da Tsantsar kulawa da kuma ƙauna. Murmushi ya yi yana sumbatar hannunta ya ce. “Mommy naji naki saura na Dad koda yake fushi yake dani na sani.” “Fushi kuma? Amma me ya sa?.” Mom M ta faɗa tana zaro ido tare da duban Alhaji Dawud tamkar batasan komai ba. Stairs Alhaji Dawud ya nufa yana faɗin. “Wato saboda kasan ba zan iya jure dogon fushi da kai ba shi ya sa kake faɗin hakan don ka haɗani da Mommynka ko?.” Dariya Haisam ya yi yana girgiza kai bai ce komai ba, sometimes yana mamakin Mahaifin nasa ta yadda yake canzawa, wani lokacin kasancewa yake tamkar wani maƙiyi a gare shi, yayin da wasu lokutan nuna wa yake yafi kowa ƙaunar sa. “Ka ci gaba da haƙuri da Daddynka kuma ka bashi lokaci zai canza yanzu Bara naje ba sameshi.” Mom M ta faɗa tana raurau da ido cike da nuna rashin jin daɗi na wasu abubuwan da mijin nata ke yiwa tilon ɗan nasu. “Karki damu a koda yaushe ni mai yi masa uzuri ne kuma ki cire damuwa a ranki kinji domin banaso wani abu ya saman min ke.” Shiru Mom M ta ɗan yi sai kuma ta miƙe da sauri tare da sumbatar goshinsa kana tabi Alhaji Dawud zuwa Upstairs. Yayin da Haisam ya bita da kallo yana sauke ajiyar zuciya, sai kuma ya yi saurin miƙe wa ya bi ya ɗayan stairs ɗin ya wuce zuwa part ɗin sa, da sassarfa. ** Wani wawan birki taja cikin sauri tana sauke ajiyar zuciya ta kifa kanta a kan steering sai kuma ta yi saurin ɗa gowa tare da buɗe motar ta fito ta ƙari sa wurin Mutumin dake durƙushe, gabanta na faɗuwa dan duk ta gama sadaƙarwa a kan ya sama rauni sakamakon bige shi da ta yi. “Bawan Allah! Bawan Allah! Kanajina kuwa?.” Ta faɗa bayan ta ɗan tsugunna a gabansa. Dam! Kirjinta ya buga a lokacin da ya ɗa go tare da zuba ma ta ido ya washe ma ta jajayen haƙoransa fuskar nan ta yi fututu. Saurayi ne da a ƙiyasi ba zai haure shekaru goma sha Tara ba, sai dai kana ganin yanayin shigarsa kasan talauci ya yi masa kamun kazar kuku, duba da wata iriyar fekakiyar yagalalliyar riga doguwa ta maza har ƙasa dake jikinsa, fatarsa ma ba zaka iya tantance wata iriyar launi gareta ba tsaban datti. “Ka...kana.. lafiya?!.” Ummul ta faɗa da ƴar rawar murya tana ƙoƙarin miƙe wa tsaye sai dai kafin ya bata amsa taji yo magana daga ta bayanta an ce. “Karki damu ba abin da ya sameshi. Kai kuma Siɗi taso mu yi gaba.” Ɗan zaro ido ta kuma yi ganin wanda ya yi maganar kammaninsa sak da na wanda ta buge. Hatta yanayin shigarsu ma iri ɗaya ne sai dai shi wannan da ya yi maganar idonsa ɗaya a liƙe yake da alama baya gani da shi duba da yadda idon ya yi matuƙar ƙanƙancewa ya zamana kamar a liƙe yake. “Kuyi haƙuri ban kula ba ne har na kusa bigeka sai dai kai ma ya kamata ka din ga duba hanya kafin ka yi ƙoƙarin tsallaka wa.” Ta faɗa lokacin da wanda a ka kira da Siɗi ya miƙe yana karkaɗe jikinsa. Basu bi ta kan haƙuri da take basu ba, suka haɗa baki wurin faɗin. “Daga gani kina tunani ne kuma ga dukkan alamu a kan wani ne shi ya sa ko?.” Su kai maganar suna ƴar dariya tare da nunata da hannu. “ah..e.. a'a, garin ya ya kuka sani?.” Dariya duk suka yi suna kallon juna. “karki damu da sanin garin ya ya muka sani, kedai kawai ki yarda damu mu kuma zamu saka soyayyarki ta yi nasara.” Zuwa yanzu Ummul ta fara tunanin da aljanu ta haɗu ba mutane ba. Da sauri ta kama murfin motar zata buɗe ta shiga sai kuma taji ɗaya daga cikinsu ya ce. “Saɗaɗa mu tafi kawai mu ci gaba da bararmu dan da alama wannan ba za'a sama komai a gare ta ba.” Da sauri ta dubesu jin maganar, ba ma maganar nasu ne ya bata haushi ko wani abun ba sai ma tausayi da suka bata, Samari kamar waɗan nan suke maganar Bara ita sai yanzu ma ta lura da robar Bara dake hannun kowannen su. “uhum nace ba.” Da sauri suka juyo. “Magana kike ne Aunty?.” Suka haɗa baki wurin faɗa. “Mene ne sunanku?.” Ta tsinci kanta da tambaya. “Siɗi da Saɗaɗa ke nan yara ƴan baiwa a cewar wasu mutanen mu biyu muke Rayuwarmu domin a hakan muka taso mu biyu shi ya sa komai namu iri ɗaya Bama iya nan muka tsaya ba, muna baki labari ba abin da bamu sani ba, mu da kike gani nan ba irin abin da bamu gani ba a rayuwa, Madam aiki zaki ɗauke mu? ko gadi kike so a dinga yi miki zamu yi.” Shiru Ummul ta yi cike da mamaki take kallonsu daga tambayar sunayensu sai wannan dogon bayani haka. Ita fa ba dan komai ta tambaya sunayensu ba sai tausayi da suka bata, taji tanaso ta taimaka musu. “Siɗi da Saɗaɗa kuma me hakan ke nufi? ban taɓa jin wannan sunan haka ba.” “Ai shi ya sa muka yi miki ƙarin bayani a kan mu domin karki tambaya ma'anar sunan.” “uhmp na fahimta wato ku ɗin nan ƴan komai da ruwan ku ne ke nan?.” “sosai ma kuwa shi ya sa muka ce miki ba abin da bamu iya ba.” “lallai kam to amma waye ya saka muku wannan sunan kuma garin ya ya kuke Bara a matsayinku na samari masu jini a jika ba zaku dage kuyi aikin da zaku nema na kanku ba sai dai ku fa ke da yin bara?.” Kallon juna suka yi sai kuma suka yi dariya suka ce. “Madam komai da kike gani a wannan Rayuwar akwai dalilin faruwarsa tabbas mu ɗin ba kowa ba ne sai dai bama Bara shigar da kika ga munyi akwai dalili.” “Ikon Allah! Amma fa kuna da abin mamaki. Ni dai Yanzu sauri nake ku riƙe wannan adireshi na ne.” Ta faɗa tana miƙa wa Siɗi card dake hannunta. ** “Me kake tunani ne Dawud tabbas Haisam ne ya shiga Ɗakin Sirri, to amma me ya kai shi ciki kuma garin ya ya, ya san da ɗakin?.” Mom M ta faɗa bayan ta shiga Ɗakin ta mayar da ƙofar ta rufe. Kallon ta Alhaji Dawud ya yi kafin ya yi magana ta ci gaba da faɗin. “Ina ga ka kyaleshi da maganar saka hannun nan har zuwa nan da wani ɗan lokaci.” Jinjina ma ta kai ya yi sannan ya ƙara faɗin. “Yaron nan fa ya shiga hannu ina nufin Abaan Kamasho, me kike ganin ya kamata a yi masa.” “Yanzu nima na sama saƙo shima ɗan jaridan ya shiga hannu sai dai na basu umarnin yi masa abin da muka tsara shi kuma Kamasho da kan mu zamuyi masa hukuncin.” “Ita kuma Yusra fa?.” Alhaji Dawud ya sake faɗa. Mom M ta ce. “Abin da ya dace da ita shi zamuyi ma ta.” Jinjina kai Alhaji Dawud ya yi yana zama a kan sofa. Shi kuwa Haisam koda ya shiga part ɗin sa zuciyarsa cike fal da tarin tunane tunanen musamman na rashin ganin abin da ya je nema a keɓantaccen Ɗakin Sirri na Mahaifin sa, da wannan tarin tunane tunanen ya yi wanka ya shirya tsaf cikin shigarsa na ƙananun kaya, sannan ya fito kai tsaye ya shiga mota ya wuce zuwa Barrack ɗin su. Kamar yadda suka yi da Ayusherh a kan zai biya ya ɗauke ta zuwa gida dan ta kwana biyu bata je sun gaisa da su Tata ba. Koda ya isa dama shi ɗin take jira sai da ya biya suka gaisa da General Lamrat sannan ya ɗauke Ayusherh suka wuce zuwa gidansu. *No. 20, Kubuwa Road, Gwagwalada Abuja.* “Dakata da motar.” Ayusherh ta faɗa lokacin da motar Haisam ta shiga anguwansu ya ƙari sa dai dai ƙofar Gate na Gidansu. Fitowa daga motar ta yi bayan Haisam ɗin ya fa ka motar a kusa da Gate ɗin, shima ya fito, idanunta a kan Tata dake tsaye ya juya baya suna magana da wata. Ayusherh so take ta yi surprising Tata dan ce masa ta yi ma bata garin sun tafi wani wuri bisa aiki, shi ya sa yanzun ta fara taku a hankali a hankali tana dab da ƙari sawa wurin da yake tsaye wayarta ta yi ƙara alamar shigowar kira da kuma hakan ne ya sa Tata ya juyo ɗan zaro ido ya yi da mamakin ganinta sai kuma ya yi murmushi yana jira ta gama wayar. “Jasmine kina ina ne nayita neman layin ki baya shiga?.” Ayusherh ta faɗa bayan ta ɗa ga kiran. Daga ɓangaren Jasmine ta ɗan dakata da tafiyar da take yi lokacin da ta isa ƙofar Room ɗin hotel ɗin da take ciki kana ta ce. “Kedai bari kawai Bestie Mom ce ta matsa wai sai nazo hotel na haɗu da Mutumin da takeso na aura.” “Ikon Allah kuma shi ne sai a hotel zaku haɗu?.” Cike da takaici Jasmine ta girgiza kai kana ta ce. “To ya zan yi, bana so na biye ma ta ne shi ya sa kawai na amince har nazo, yanzu ma gani a ƙofar Room ɗin Bara na shiga amma zan bar kiran karki katse kinji?.” Gyaɗa kai kurum Ayusherh ta yi dan ta rasa abin faɗa, sai a lokacin idanunta suka sauka a kan Ummul dake jingine da mota tana sakar ma ta murmushi, sannan ta sauke idon ta a kan Tata tana bin sa da kallon tuhuma zatayi magana ya riga ta da faɗin. “Shalelen Tata yaushe kuka dawo ne? Yanzu dai ga Ummulkhair ku gaisa dama baku taɓa haɗu wa ba su dai su Ali da Ma'az sun riga sun santa.” Ayusherh ta ɗan waro ido da mamaki, sai kuma ta yi murmushi tana mayar da kallon ta a kan Ummulkhair ta ce. “Barka.. lallai Tata ashe lamarin ya yi nisa bani da labari ai kuwa zan haɗu da su Ali za su gane ne shi ne wato basu bani Labari ba ko.” Ayusherh ta ƙare maganar da ƴar dariya. “Ah,ah dakata tsaya, tsaya me kike nufi ko nace mai kika fahimta ne? babu komai fa, kuma ba abin da kike tunani ba ne.” Tata ya faɗa da sauri. “Tata ke nan nifa bakaji nace komai ba, ko Aunty Ummu ina ce ba wani abu na ce ba?.” Ummul tana murmushi ta jinjina ma ta kai. “To kaji dai ni Bama wannnan ba Ummu Bara na sallama surukin naki sannan mu shiga ciki domin ƙara sanin juna.” Ayusherh ta faɗa, tana ɓoye dariya ganin yadda Tata ya yi shi a dole ba wani abu tsakanin shi da Ummul. Ayusherh dai ta juya tana duban Haisam dake jingine da mota gama waya da Yusra da ya yi ke nan yake tambayarta inda ta shiga kwana biyu baya samun wayarta, shi ne take faɗa masa kawai aiki ne ya yi ma ta yawa ba komai ba. Ayusherh ta buɗe baki zatayi magana ke nan ihun da taji Jasmine tana kwala wa ta cikin waya ya sa ta yi saurin duba wayar a firgice ita tama manta Jasmine ta ce karta katse kiran. Cikin kiɗima Ayusherh ta fara kiran sunan Jasmine tana tambayarta abin da ke faruwa sai dai Jasmine ta kasa magana sai faɗi take kawai tazo ta taimake ta. Hankali a matuƙar tashe Ayusherh ta duba Haisam da yake ita jiyo komai kasancewar wayar a speaker take. Sai kuma da sauri ta shiga motar tare da zama mazaunin driver sai da ta tayar da motar lokacin shima Haisam da ya tsaya faɗa ma Tata abin da ke faruwa ya shiga sannan Ayusherh taja motar da wani irin sauri suka bar Anguwan suka nufa hotel ɗin ta hanyar amfani da bididdigi na wayar Jasmine. A lokacin da Jasmine ta tura Ɗakin ta shiga bayan ta riƙe wayar a hannunta ba tare da ita ma ta katse kiran ba. Dam! Ƙirjinta ya buga a sakamakon ganin wani ƙaton gunsumin Mutum dake zaune a kan sofa dake Room ɗin, da kyar ta haɗiye yawu mai kauri tare da ƙari sawa ta zauna a kan sofa dake fuskantarsa tana ƙara mamakin dalili da kuma abin da mahaifiyarta ta hango har take son ganin ta haɗa ta aure da wannan baƙin Mutumin da fuskarsa bata da kyan kallo. Maganar da Mutum ya yi cikin wata kalar murya mai girma ita ta ƙara faɗarma da Jasmine gaba, ta dubesa a nutse a iya ƙiyasin ta ba zai haure shekaru arba'in zuwa da uku ba. “Ki sha Lemu mana Babe kin yi shiru kuma ko dai Uwar taki batayi miki bayani ba ne ba?.” “Bayani a kan me kuma?.” “Karki raina min wayo mana bayani a kan auren mu mana.” Jasmine ta sauke ajiyar zuciya tare da faɗin. “kayi haƙuri amma ni bana da ra'ayin Aure a yanzu...” “Saboda me? Ban yi miki bane ko kuwa kuɗaɗe nane suka yi miki low ko mene?.” Mutumin ya yi saurin katse ta da faɗin hakan tare da ci gaba da faɗin. “Bana tunanin ko sunana kin sani amma shi ne kike faɗa min baki da ra'ayin Aure yanzu.” Shiru Jasmine ta yi da mamakin. Ya daka ma ta uban tsawa yana faɗin. “Keee! Ki bar ganin ke ɗin Soja ce ina miki magana kin yimin Shiru kamar wani sa'an ki.” Tsam! Jasmine ta miƙe tsaye cikin ƙunar rai batasan Mahaifiyarta bata son ta ba har haka da zata yi tunanin haɗa ta Aure da wannan mai siffan dodoni ga baƙi kamar na zunubi ga ƙiba sai kace.... Tunaninta ya tsaya cak, a lokacin da ya tashi tsaye tare da shan gabanta yana suɗe baki tare da fito harshe kace tsohon maye. “Mene ne haka kuma dalla Malam ka bani hanya na wuce.” Jasmine ta faɗa a dake tana galla masa harara. Dariya ya yi ko'a jikinsa, ya fara ƙoƙarin cukumota da niyyar rungumarta yana faɗin. “laa laa ai Yarinya tun da har kika shigo gonata bisa kwaɗayin uwarki to fa ba zaki fita ba sai na lasa miki zuma ta mai garɗi.” Ƙirjin Jasmine ya yi mummunar bugawa jin kalamansa amma ta daure tare da saka iya kar ƙarfinta tana ƙoƙarin ganin ta gwace kanta daga garesa sai dai Abu ya cutura hakan ne ya sa ta kwala ƙarar da ya tashi hankalin Ayusherh tare da ci gaba da ihun neman taimako tana faɗa ma Ayusherh ta taimake ta. Domin ƙarfinta ya fara ƙarewa tana mamakin shegen ƙarfi irin na Mutumin. Ayusherh bata tsaya ta gama dai dai ta faka motar a harabar hotel ɗin ba ta fito daga motar a haukace tana kwala kiran sunan Jasmine tare da tambayarta lambar Ɗakin, zuwa lokacin Jasmine ta gama fita hayyacinta domin Mutumin ya sama nasarar ɗaurata a gado yana ƙoƙarin rabata da suturar jikinta domin shi tuni ya yi zigidir. Da kyar Jasmine ta sama zarafin faɗin lambar Ɗakin da ƙarfi yadda Ayusherhn zataji domin wayar ta daɗe ta faɗi a ƙasa sai dai kafin ta ƙari sa maganar Mutumin ya yi saurin ta ke screen ɗin wayar da ƙafarsa bai san tuni Ayusherh taji ba. Da wani irin sauri kamar zata tashi sama Ayusherh ta ke taka stairs tsaban ranta dake a mugun ɓace da uku uku take tsalle benen. Wani abin mahaukacin wawan bugu ta yi ma ƙofar sai dai an rufe ƙofar ta ciki. Hakan ya sa ta yi baya a zuciye tare da tafiya da gudu ta kuma bugun ƙofar da ƙafa ai ko ta ke ƙofar ta ɓalle Ayusherh ta shiga ciki da sauri, sai kuma ta yi saurin ja baya ganin yanayin da Mutumin ke ciki gashi kuma har ya raba Jasmine da rigar jikinta dama Wandon aiki ne a jikinta haka ma kanta hular soji ce riga ce kawai ta kasance irin Stylish top ɗin nan kuma Mutumin ya yi nasarar rabata da ita. A haukace Ayusherh ta ƙari sa tare da dukkan ƙarfinta ta janyo ƙafar Mutumin ya yo ƙasa ji kake. Ƙaram! Ya faɗi a kan tiles ai kuwa Ayusherh ta hau jibgansa tare da kai masa ruwan hamɓari da takalmin ƙafarta na sojoji mai shegen zafi. Sai kuma ta kyaleshi tare da ƙari sawa saman gadon ta cire mayafin kanta ta lulluɓama Jasmine dake kuka kamar ranta zai fita, ta rufe ma ta ƙirjinta tare da sauko da ita daga saman gadon. Zuwa lokacin ɗakin ya cika tab da mutane domin a yanayin yadda Ayusherh ta shigo hotel ɗin da kuma irin bugu da ta yi ma ƙofar har ta balla har ma da irin dukan mutuwar da ta yi ma mutumin shi ne ya ja hankalin jama'a, tuni ƴan jarida da ba'asan ma ta inda suka ɓullo ba sun cika Ɗakin, ɗaya daga cikin ma'aikatan hotel ɗin ne ya samu ya miƙa ma Mutumin Babban rigarsa dake a je a hannun kujera ai kuwa cike da kunya ya yi saurin karɓa ya zura. Tata da tun tafiyar su Ayusherh yaji hankalinsa bai kwanta ba hakan ne ya sa shi da Ummulkhair suka shiga motarta suka bi bayan Ayusherh ba tare da su Ayusherhn sun lura ba kasancewar bata a cikin hayyacinta shi kuma Haisam duk yabi ya ruɗe. Da tsananin mamaki Tata dake tsaye gefe ya ce. “Alhaji Manu!.” Tata ya faɗa da tsananin mamaki ya nuna Mutumin. “Au wai dama musulmi ne, amma Tata garin ya ya ka san shi?.” Ayusherh ta yi saurin tambaya sai dai kafin Tata ya kai ga bata amsa. Duk mutane suka marmatsa ma wata Mata mai tsananin kamanni da Jasmine da ta shigo kana ganinta kaga cikakkiyar ƴar gayu da boko ya ratsa ta ciki da waje taku take ɗaiɗai riƙe da jaka ta kuma ci uwar Glass wai kuma a hakan sauri take bugawa, ta ƙari sa wurin Jasmine ta shafa fuskarta tare da faɗin. “Dear ba abin da ya sameki?.” Wani irin tuƙuƙin baƙin ciki ya tokare zuciyar Jasmine ji take duk duniya ba wanda ya kaita rashin dacen uwa. Da kyar ta samu ta iya faɗin. “Mom why, why Mom kikayi tunanin haɗa ni da wannan fasiƙin Mutumin, kuma ma a hakan kin san cewa ba addinin mu ɗaya ba?.” Jasmine ta faɗa hawaye nayi ma ta kwarara dan ita Bama kasancewar mutumin, musulmi ba ne yafi bata haushi ba, ƙoƙarin rabata da martabarta da ya yi kuma ta ƙarfin tsiya. Shiru Mom ɗin Jasmine ta yi ta kasa magana cike da kunyar Ɗiyar nata. Nan dai jami'ai da suka ƙari so suka tasa ƙeyar Alhaji Manu yayin da yake bin Ayusherh da Jasmine da wani irin kallo mara ma'ana. “Aniyarka ta bika mugu azzalumi mara tsoron Allah wai kuma a hakan kai Musulmi ne ai ko an ji kunya kuma tun wuri ka nema tuba a wurin Allah dan ba'asan musulmi na kwarai da aikata irin wannan dabbanci ba.” Ayusherh ce ke maganar a fusace sai kuma ta mayar da kallon ta a kan Jasmine da har lokacin bata dena kuka ba cikin sanyin murya Ayusherh ta ce. “Ki kwantar da hankalinki in sha Allah ba abin da zai faru sai Alkhairi kinji ko? Tun da Mom ɗin ki ta zo Bara mu tafi sai mun yi waya.” Ayusherh ta kai maganar tare da dafa kafaɗarta. “Na gode sosai Captain.” Jasmine ta faɗa tana miƙa ma ta mayafinta domin tun ɗazu ta samu da taimakon Ayusherh ta mayar da rigarta. Ita ko Mom ɗin Jasmine duk da tasan Ayusherh ce ta taimaki Jasmine amma ba Sannu bare na gode hasali ma da wani irin kallo mara fassara tabi Ayusherh yayin da hakan ba ƙaramin zafi ya yi ma Jasmine ba. Hakan ya sa bata bi ta mahaifiyar nata ba ta fito daga hotel ɗin a fusace ta hau Cab ta wuce gida tare da rufe ƙofar ɗakin abin duniya duk ya ishe ta. Kuma koda Mom ɗin ta dawo bugun Duniya ta yi amma Jasmine taƙi ta buɗe ƙofar. Ta ɓangaren su Ayusherh kuwa kai tsaye gida suka koma cike da taraddadin wannan al'amari. Da isarsu gida Haisam bai wani jima ba suka yi sallama ya tafi yayin da Ummul suka sha fira da Ayusherh da ta saki jiki sosai da ita, kuma sai zolayar Tata take wai ashe ya kusa yi musu sabuwar Aunty amma basu sani ba, har su Ali da Ma'az suka dawo gidan, shi dai Tata shiru ne nasa dan abin a katari yake zuwa kawai dan wannan haɗu war shi ne haɗu wa na uku kacal da ya yi da Ummulkhair. BAYAN WATA ƊAYA.... A wannan lokaci ne kuma labarin ɓatan mutane biya da kuma gawar wani shahararren ɗan jarida da a ka samu a gadan jirgin ƙasa ya karaɗe ko'ina, su dai waɗan nan mutane biyu da suka ɓata ba kowa ba ne fa ce Abaan da a ka fi sani da Kamasho sai kuma ‘yar Ƙanwar Mr President wato Yusra Ma'aikaciyar Babban bankin ƙasa dake Abuja. Wannan labari a halin yanzu shi ne yake trading a ko'ina domin mutane biyun da a ka sace dukkaninsu suna da alaƙa da Mr President da har hakan ya sa wasu suke tunanin saboda zaɓe ya kusa shi ya sa abokan hamayya suka ɓullo ta hakan, yayin da wasu suke ƙaryatawa har ma da masu faɗin wai guduwa suka yi su biyun saboda suna son juna amma saboda Abaan maraya ne shi ne ya sa Ahalin Yusra suka ƙi amincewa da shi har hakan ya sa suka shirya suka gudu a matsayin sace su a ka yi, labarai dai makamantan waɗan nan da ba kai bare tushe suke faman yawo a media. Ba ƙaramin damuwa Nusra ta shiga ba da wannan al'amari shi ya sa ko fita bata iya yi batasan tana ƙaunar ƴar uwan nata ba har sai yanzu da a ka wayi gari bata nan haka shima Haisam ta ɓangaren sosai yake cikin damuwa na ɓatar Yusra musamman ma da ya kasance washe garin Ranar da suka yi waya ne ta taɓa gefe guda ma yana mamakin ɓatar da Kamasho ya yi duk da bai wani sanshi sosai ba. “Ka faɗa min mana wai ina ne zamuje?.” Ayusherh ta faɗa ganin yadda Haisam yake jan hannunta lokacin da suka shigo Gidansu suka tarar ba kowa hatta Aunty Dawha da Nusra sun fita, shi kuma Haisam ganin lokacin yammaci ne shi ya sa yakeso Ayusherh ta taimaka masa ya yi amfani da damar wurin duba Ɗakin Sirri na Mahaifinsa domin neman abin da ya daɗe yana nema domin a tunaninsa a nan ne kawai zai sama bayanai dangane da Second Momma ɗin sa da har kullum take cikin damuwa na rashin sanin su waye Asalin danginta. Haisam yana da tabbaci a kan Mahaifinsa yasan dangin Aunty Lamrat amma ya ɓoye saboda wani buri nashi shi ya sa a wannan lokacin Haisam yake so ya yi amfani da dama na biyu da ya samu domin bincika Ɗakin Sirrin ko da zai sama wani abu. Har sai da ya zagaya da ita ta can backyard na gidan ya tsaya dai dai ƙofar ɗakin sirrin, sannan ya dubeta kana ya ce. “Akwai abu mai matuƙar Muhimmanci da nakeso na duba a Ɗakin ne kuma Ɗakin ya kasance na Sirri ne da babu mai shiga ciki a gidan nan sai Daddy da Mommy shi ya sa ni nakeso na shiga yanzu saboda ina da tabbacin abin da nake nema yana ciki.” Ayusherh ta yi shiru tana dubansa har sai da taji ya yi shiru sannan ta ce. “Ikon Allah! Amma kuma baka tsoron wani abu ya faru?.” Haisam ya girgiza kai yana murmushi ya ce. “Ko ɗaya yanzu zo mu shiga ciki ki tayani dubawa.” Ya ƙare maganar dai dai lokacin da ya sama nasarar buɗe ƙofar bayan ya saka lambobin Sirri na Mahaifinsa da ya sani kuma ga ɗaukakin mamakinsa ƙofar ta buɗe. Ba musu Ayusherh tabi shi ciki duk da tanaji bata yarda da Ɗakin ba, kuma lokaci lokaci gabanta ke ɗan bugu na rashin dalili. Ƙari sawa gaban wani dogon abu wanda ya fi yanayi da Shelve na littafai suka yi sai da suka tsaya a wurin sannan Ayusherh ta lura ƙofa ne hakan ya sa ta kai hannu tare da zuge Shelve ɗin zuwa gefe ƙofa ta bayyana Again sai dai da alama ita ma sai an saka lambobi a ke buɗe wa, hakan ya Haisam ba tare da yabi ta kan ƙofar ba, ya bi ta wata ƙofa again dake ɗayan side na wall ɗin ya shiga yayin da Ayusherh ta ɗan kai hannu a kan tumin littafai da Takardu da ke jikin shelve ɗin tana dubawa a hankali ba tare da ta san me take yi ba. A hankali kuma ɗaya bayan ɗaya take duba Takardun dake wurin sannan ta a je ta ɗauki wani dandanan lokaci guda jikinta ya ɗauki rawa matsanancin tsoro da firgici ya cika ta lokacin da ta ɗauki wani takarda sai ƙaramar Camera ta faɗo daga wurin da ta ɗauki Takardun cikin sauri ta buɗe Camera ɗin da yake akwai caji hakan ya sa ta buɗe videon dake farko ta fara dubawa. Tsayuwarce take neman gagararta lokaci guda ta haɗa uban zufa jikinta ya ci gaba da rawa domin ganin komai take tamkar a mafarki. “Ayusherh lafiya kuwa? Mene ne ke faruwa? Zo muje ban sama komai ba kuma da alama Daddy da Mommy sun dawo ci gaba da zamanmu anan akwai matsala domin ban san me zan ce ma Daddy ba muddun ya ganmu a nan.” Ya kai maganar yana ƙoƙarin kamo hannunta domin su fita sai dai Ayusherh ta turje hakan ya sa da mamaki ya juyo yana kallon ta, sai kuma ya ɗan zaro ido domin sai yanzu ya lura da yanayinta da yadda idanunta suka ɗan yi ja kuma da alama a cikin firgici take. “Hai...Haisa... Haisam ma..Mahain...finka shi ne, shi ne ba mutumin kirki ba ne makashi ne kuma mara imani karka yarda da shi.” Ayusherh ta kai maganar cikin rawar murya domin rasa mai zata ce masa ta yi. “Ban gane ba mai kike nufi?.” Haisam ya tambaya da fatan Maganar da zata sake yi ya kasance a ka sin abin da kunnuwansa suka ji. Sai dai kash ƙara maimaita masa abin da ta faɗa ta yi. Haisam ya ɗan ja baya yana bin ta da wani irin kallo sai kuma ya girgiza kai jin ƙarar alamun ana tahowa ya sa shi ƙara yunƙurin riƙo hannunta yana faɗin. “Ba zai yiwu ba Ayusherh zo mu tafi tun kafin Daddy ya ƙari so wurin nan.” Still yanzun ma turjewa ta ƙara yi taja baya da sauri hakan ya sa Haisam ya tsaya dubanta da mamaki ransa kuma yana ƙoƙarin ɓaci. Cikin tsawa da ɗan ɗa ga murya Ayusherh da ta gama shiga ruɗani ta fara magana da faɗin. “Haisam! Ka yarda dani ba sharri nake masa ba. tabbas Mahaifinka ba Mutumin kirki ba ne kamar yadda kowa ke Zato!. Shi d'in ba kowa bane fa ce. Tantirin Criminal kuma mara Imani da zai iya aikata komai domin Nasararsa... Idan baka yarda ba ka buba wad'an nan Takardun. Idan suma basu gamsar da kai ba. Ina tunanin ka gane ABAAN wato wannan saurayi da a ka fi sa ni da Kamasho da ya ɓata a wasu watannin baya? To ka sa ni ba ɓata ya yi ba Mahaifinka shi ne ya kashe shi....” Duniyar ne ta fara juyawa ma Haisam ya shiga cikin tsananin ruɗani da tashin hankali da hakan ya sa ya gagara koda kwakwarar motsi. Mahaukacin bugu da ake ma ƙofar Room ɗin da suke ciki ne, ya sa Ayusherh ta yi saurin kallon Haisam da ke tsaye kamar Statue tun lokacin da ta fara Magana. Ganin da gaske ɓalla ƙofar za'ayi a shigo ya sa ta yi saurin kamo hannunsa shi kuwa ya bita kamar raƙumi da akala suka shiga Ɗakin da ya fara shiga, curko curko suka tsaya a ɗakin cikin tashin hankali yayin da Ayusherh ta fara neman wurin da zasubi domin su fita duk da tanada tabbacin Alhaji Dawud zai ga komai ta CCTV da ta gani a Ɗakin. Ajiyar zuciya ta sauke lokacin da ta hangi window ta ƙara kamo Hannun Haisam tana faɗin. “Bamu da lokaci kazo mubi ta nan mu gudu tun kafin su ɓalla ƙofar su shigo.” Sai dai Haisam yaƙi gaba bare baya ta dubesa da mamaki ta ce. “Kazo mu tafi mana.” Girgiza ma ta kai ya yi yana bin ta da wani irin kallo da har sai da ya sa gaban Ayusherh ya buga amma ta daure tana lallashin sa a kan ya zo su tafi amma yaƙi babu irin magiya da batayi masa ba amma Haisam yaƙi motsi, ganin da ta yi muddun ta ci gaba da zama a wurin to fa Rayuwarta yana a hatsari domin tasan tun da har tasan wannan sirri, to fa mahaifin Haisam ba kyaleta zai yi ba, kuma Takardun da Camera ɗin suna hannunta bata a je ba. Girgiza kai ta yi zuciyarta nayi ma ta ƙuna ta samu ta fasa Glass na window bata damu da jini da hannunta ke yi ba, ta haure ta window ta fice, tana durowa Security's ɗin da Alhaji Dawud ya kira suna buga ƙofar suka ganta. “Ku bita ku tabbata kun kamomin ita.” Alhaji Dawud ya faɗa cikin tsawa. Ganin yadda suka dunkaro ta ya sa Ayusherh ta miƙe da sauri ya kama katangar wurin tsalle ɗaya ta yi ta haure ta. Gudu sosai ta fara baji ba gani kuma sannan security's ɗin da suka biyo ta suma basu dena gudun ba. Tare mai Cab ɗin da ya zo zai wuce ta gefanta ta yi tare da shiga da sauri tana yi masa kwatancen inda zai kaita, cikin ikon Allah kuma ta saka mai Cab ɗin ya yi wasa da hankalin security's ɗin har su ɓace ma ganinsu. A ƙofar gida mai Cab ɗin ya a je ta ta yi saurin fitowa ba ta tsaya ma bashi kuɗin ba ta buɗe ƙaramar ƙofar Gate na gidan ta shiga, da yake uniform na soji ne a jikinta. Da Tata da ya fito ta fara cin karo ai kuwa ta ƙari sa wurinsa da sauri faɗi take. “Tata muje wurin ƴan sanda muje ofishin ƴan sanda mafi kusa.” Ganin kamar bata cikin hayyacinta ne ya sa Tata faɗin. “Nutsu ki faɗa min meke faruwa?.” Sai a lokacin ta ɗan nutsu tare da kallon sa kana ta fara yi masa bayani turyan turyan na abin da ke faruwa. “CRIME BAABAH! BAN SAN ME ZAKA YI KO IYA AIKATAWA A KAN WANNAN LAMARIN BA, SAI DAI INA TABBATAR MAKA MUDDUN BA'A KAMA WANNAN YARINYA AYUSHERH AN KASHETA BA TUN KAFIN DA TONA MANA ASIRI. TOFA K'ARSHEN DUK WANI TA'ADDANCIN MU NE YA ZO!.” Alhaji Dawud ya faɗa a fusace bai jira jin ta bakin mutumin da ya kira da Crime Baba ba ya katse kiran. A fusace tare da fitowa daga Ɗakin da ya shiga ya sauko ƙasa wurin Haisam yana lallashi. “Wannan lamarin bana zama ba ne kuyi maza maza ku haɗa kayanku garin zamu bari.” Tata ya faɗa lokacin da ya shiga palon ya tarkato kan yaran nashi Allah ya taimaka ma duk suna nan a gida. “Tata mene yake faruwa?.” Ma'az da Ali suka tambaya a tare kuma a ɗan ruɗe. Tata bai sama damar basu amsa ba a ka fara bugo ƙofar palon. Da sauri Ayusherh ta ƙari sa tare da buɗe wa Corporal Aryan ne tsaye cikin girmamawa ya ce. “dama mai Cab ne a waje yake jira.” Dafe kai Ayusherh ta yi tare da kallon Tata ta ce. “Tata mu fara zuwa ofishin ƴan sanda mu shigar da rahoto, kai kuma ku shirya komai shaf-shaf kafin mu dawo mu tafi can wani wuri mai nisa. Corporal Dan Allah ga ƙannina nan da Kakata ka kularmin dasu kafin mu dawo.” Ayusherh ta ƙare maganar da kallon corporal sai dai tun kafin ya ce komai Ali da kansa ya gama ɗaurewa da lamarin ya ce. “Wai ba zakiyimin bayani ba Aunty mu fa kin barmu a duhu.” Kallon sa ta yi ganin yadda duk ya damu ya sa a taƙaice ta faɗa musu abin da ke faruwa ba su kaɗai ba hatta Corporal Aryan sai da ya jinjina lamarin. Kuma ya yi ma ta alƙawarin kulawa da su Yâ tâ kafin suje su dawo. Cikin sauri Ayusherh da Tata suka fito daga gidan tare da shiga cab ɗin Ayusherh ta ce ma mai Cab ɗin ya kai su ofishin ƴan sanda mafi kusa. Ba tare da ɓata lokaci ba ya isa da su ai kuwa a ka yi katari lokacin da suka isa ofishin ƴan sandan har da wasu tsirarun ƴan jarida da alama wani abun ya kai su wurin. Ai kuwa Ayusherh ganin irin kallon da ƴan sandan ke yi ma ta tun lokacin da ta sanar dasu abin da ke faruwa ya sa ta juya ga ƴan jarida da suma maganarta ne ya sa suka dawo da hankulansu kanta. Ba tare da wani firgici ko tsoro ba Ayusherh ta fara yi musu bayani dalla dalla har da nuna musu Camera da kuma takardun hannunta ta kuma tabbatar musu da cewa Mr President criminal ne kuma shi ne ya sa a ka sace Abaan saboda ya san wani Sirrin sa ya yi masa kisa na wulaƙanci. Ai kuwa nan da nan hankalin kowa ya dawo kanta ƙananun maganganu suka shiga tashi a wurin yayin da tuni ƴan jaridan sun mayar da wannan zazzafan labari zuwa na kai tsaye wato live. Ayusherh zata ci gaba da magana ta hango wasu daga cikin security's ɗin Alhaji Dawud da suka biyo ta sun shiga ofishin ƴan sandan. Hakan ya sa jikinta ya yi sanyi nan da nan kuma jikinta ya fara rawa ta yi saurin duban Tata tana faɗin su bar wurin. Ai kuwa da lura da abin da ta gani ya sa Tata ya ja hannunta suka fito daga ofishin ƴan sandan kai tsaye suka shiga Cab ɗin suka koma zuwa gida sai dai wani abin tashin hankali da suka tarar shi ne na ganin yadda mutane suka taru a ƙofar gidan duk sun yi curko curko suna kallon yadda gaba ɗaya gidan yake ci da wuta ringi-ringi. Wani irin jiri ne ya ke ɗibar Ayusherh da hakan ya sa ta kasa tsayuwa da kyau cike da matsanancin tashin hankali take ƙoƙarin shiga gidan dake ci da wuta sosai amma Tata ya yi saurin kamo ta yana girgiza ma ta kai. Hawaye Ayusherh ke yi cikin tashin hankali duk yadda ta so Tata ya bar ta ita ma ta shiga wutan ƙi ya yi. Hakan ya sa taja baya tana sauke ajiyar zuciya ai kuwa cikin shammata mutumin da ya rufe fuskarsa da kyalle ya biyo ta bayanta tare da shaƙa ma ta wani abu a hanci nan da nan kuwa ta fice daga hayyacinta, lokacin da ya ɗauke ta cak ya nufa motarsa da ita ne kuma Tata ya juyo ai kuwa cikin matsanancin tashin hankali ya fara kiran sunan Ayusherh yana faɗin mutumin ya tsaya, sai dai ina tuni mutumin ya jefa Ayusherh a mota tare da shiga da gudun bala'i ya bar wurin. Hankali a matuƙar tashe Tata ta tari mai Cab tare da ce ma sa yabi bayan Motar, gudu sosai mai motar ke yi tun suna cikin gari har suka fara tsara daji kuma cikin rashin sa'a motar ta ɓace ma mai Cab ɗin, Ai kuwa cike da bala'i mai Cab ɗin ya tsaya ya ce shi dai daga nan ba inda zai ƙara shiga dan ba zai shiga daji ba ya je ya jefa rayuwarsa a cikin hatsari, ba yadda Tata ya iya haka ta fito daga motar tare da fara taka wa cikin wahala ya fara shiga dajin yana kwala kiran sunan Ayusherh ga ƙafarsa da baya iya gudu sosai tafiyar ma da kyar yake iya yi yin ta. ** Sassanyar ruwa da a ka kwara ma ta shi ne abin da ya sa ta farka a ɗimauce tana sauke ajiyar zuciya idanunta suka shiga cikin na Mutumin mara kyan gani dake tsaye gabanta, mutsu mutsu ta fara sai dai ta kasa tafiya, kasancewar ɗaure Hannuwanta a ka yi ta sama, sai kawai ta tsaya tana dubansa yayin da take ci gaba da lumshe ido a hankali tana buɗe wa saboda bata gama dawowa hayyacinta ba. Mari Mutumin ya ƙara kwaɗa ma ta a karo na ba adadi yana tambayarta inda ta a je Camera da kuma Takardun. Amma Ayusherh ta yi shiru tsaban taurin zuciya taƙi ta ce masa komai, kuma hakan ne yake ƙara fusata shi, a lokacin ne kira ya shigo wayarsa kuma daga yadda taji yana amsa kiran tana da tabbacin Alhaji Dawud ne batayi mamaki ba dan a halin yanzu ta gama sanin wanene Alhaji Dawud. “Crime Baabah!.” a hankali ta maimaita sunan da taji Alhaji Dawud ta wayan yana kiran Mutumin da shi. Dawowa wurin ta Crime Baabah ya yi bayan ya gama amsa wayar, yana ci gaba da faɗin ta faɗa masa inda ta kai waɗan nan Takardun da kuma Camera domin bata ba ƴan sanda ba. A hankali Tata ya saɗaɗo tare da buga ma Crime Baabah katakon da ya ɗauka lokacin da ya shigo wurin a kai, ai kuwa Crime Baabah ya zube yana dafe saitin wurin, cikin sauri Tata ta fara kwance Hannuwan Ayusherh yayin da ta fara hawaye faɗi take. “Tata mai ya sa kazo so kake kaima na rasa ka kamar yadda na rasa su....” Tau! Kakeji ƙarar fitar alburushi daga bindigar hannun Crime Baabah tare da shiga harsashin a gadon bayan Tata. Ayusherh taja da baya tana zare ido cikin tashin hankali. Duk da cewa Tata yana gargarar mutuwa ne amma hakan bai hanasa faɗin Ayusherh ta gudu ta ceci Rayuwarta ba. Crime Baabah ya miƙe da kyar ya saita Ayusherh da bindiga zai harba amma Tata ya tare harsashin ya ƙara samun sa a ƙirji zubewa ya yi yana fitar da numfashi sama sama. Wani irin ihu Ayusherh ta saka tare da tsugunna wa tana jijjiga Tata kuka take yi tamkar ranta zai fita. Harbi Crime Baabah ya sake yi amma Ayusherh ta yi saurin matsawa gefe bai sameta ba. A ɗimauce ta miƙe tsaye tare da juyawa da gudun bala'i ta bar wurin, ta fito daga kangon dake cikin ƙasurgumin dajin ta fara gudu yayin Crime Baabah ya biyo ta yana harba harbe. Tau! Kakeji, harsashin da Crime Baabah ya saki ya sama Ayusherh a baya, kafin ta ƙara wani yunƙuri ya ƙara sakar ma ta a kafaɗa, Ayusherh ta zube a wurin tana mai da numfashi cikin fitar hayyaci. Yayi da ciyayu na wurin Crime Baabah ya haɗe ya zagaye Ayusherh da shi tare da sa hannu yana lalubar leta domin ya saka ma ta wuta, sai dai bai ji ba, hakan ya sa ya tsugunna a gabanta tare da kai hannu saitin hancinta sai dai jin bata numfashi ya tabbatar masa da ta mutu hakan ya sa cikin sassarfa ya koma cikin kangon tare da janyo gawar Tata ya yi nisa can da shi kuma da yake a saman tsauni suke wurin hakan ya sa ya jefa gawar Tata ya faɗa ƙasa, sannan ya dawo wurin, sauri sauri ya ɗauki motarsa yaja tare da kiran Alhaji Dawud Nasamu ya sanar da shi aiki ya kammala Ayusherh ta mutu tare da duk hujjojin dake tare da ita. “Good job...Crime Baabah!.” Alhaji Dawud ya faɗa yana ƙyaƙyacewa da wata kalar mahaukaciyar dariya ta zallar rashin imani da tausayi..... ƘARSHEN BOOK 1 The Beginning, KE NAN, MU TARA A BOOK 2 The conclusion DOMIN JIN YADDA WANNAN AL'AMARI MAI CIKE DA SARƘAƘIYA ZAI KASANCE!!! 🥺😥 1. shin wai da gaske Ayusherh da Tata har ma da Abaan (Kamasho) sun mutu?. 2. Wai ina labarin Yusra ne 3. Ina Labarin Arham (Abyaz 4. Wane ne Uncle ɗin, garin ya ya Abaan ya kasance ɗan sa 5. Shin wane ne Alhaji Manu 6. Kuna ganin Ayusherh zata rayu? 7. Shin idan ta rayu ya ya makomar soyayyarta ita da Haisam ku tuna fa yanzu bata da wani maƙiyi sama da mahaifin Haisam 8. Ina labarin Jasmine 9. Shin kun yarda wutan da ta kama a gidansu Ayusherh ta ƙona kowa? 10. Wai shin wanene ma Asalin Alhaji Dawud Nasamu ne shi da Matarsa Mom M 11. Wacece General Lamrat Jabir Junaid gain ya ya ta manta tunaninta har ta kasance mata a wurin Alhaji Dawud kuma bai damu da ita ba 12. Ina labarin mahaifinsu Nusra kuma me ya sa mahaifiyarsu taƙi faɗa musu Asalinsu? 13. Mene ne kuke tunanin zai faru gaba???? Duk tarin amsoshin tambayoyin nan suna nan danƙare a cikin littafin CAPTAIN AYUSHERH Book 2 Mai Taken (An Yanka Ta Tashi....🔥🔥🔥🔥🔥 Kada ku bari a baku labari. 500₦ ne kuɗin littafin book 2, sai dai daga yau har zuwa Ranar 25/11/2024 akwai sassauci na kuɗin zuwa Naira ɗari uku kacal. Ku biya ta wannan asusun. 8081129487, MoniePoint Mfb, Sabi'u Khadija. Ku turo shaidar biya ta nan. 07067953066 Nainarh KD Sannan Ranar 25/11/2024 zan buɗe Paid group waɗan da suka biya zasu ci gaba da samun update.