﻿[04/01, 11:59 am] OumƊahirah نفيسة: 🌱🌱🌱🌱🌱

      *SHAREEF*
             _SexyBoy_
🌱🌱🌱🌱🌱


_Writer: Nafisat Isma'il Lawal_
_Wattpad: UmmuDahirah_

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝*



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

       *P.W.A✍️*










__________
*BOOK1*
_______________*FREE PAGE1to2*
             Malam Sama'ila Abashe; Mutum ne mazaunin Zaria cikin anguwan Ƙofan kibo, sana'ar sa shi ne jan babban mota, yana bin babban Motan ɗan gote. Shi yasa kodayaushe ba wai ya cika zama bane, idan ya tafi wurin sana'ar sa ya kan yi fiye da watanni uku before ya dawo. Ya jima Allah bai sa yayi aure ba; don sai da yakai aƙalla shekaru arba'in sannan Allah ya ba shi Matarsa wacce ya aure ta a gida, bazawara ce kuma yar uwansa ne, tunda tayi aure bata taɓa haihuwa ba har Mijin ya rasu, bayan fitowan ta shi kuma yace, "yana sonta zai aure ta."

Kowa a dangi yayi murna tunda bai taɓa zancen aure ba sai a wannan karon, ko an kawo mishi Mace ba ya auren ta sai ya gudu zuwa Legos idan aka matsa mishi, a haka dai yake shashantar da zancen har ga shi da lokacin yin sa yayi, dama aka ce aure lokaci ne, baza ka taɓa yi ba idan har ba lokacin ka ne ya zo ba. Ga shi sai a wannan karon Malam Sama'ila ya samu Samira ya aura

Sun yi aure cikin rufin asiri tunda Allah yana buɗa mishi sosai, baya ga jan Motan yana sana'o'i na siye da siyarwa a can inda suke zaune. Yanzu haka ya gina sabon gidan sa a nan Ƙofan Kibo sun tare da Matarsa. Suna zaune lafiya babu wani CeCe-kuce a tsakanin su, suna mutunta junansu matuƙa tare da taimakon juna, domin tunda aka yi auren Samira take ɗan saye da sayarwa na kayan miya. Shima tun lokacin da yayi auren ya rage daɗewa a can garin, ya kan yi wata ɗaya ko fiye sannan ya dawo, zaman su son Barka kowa yana sha'awar su

Abun da suka soma fuskanta shi ne rashin haihuwa, tunda tun sanda aka yi auren yau kimanin shekaru biyu kenan Samira bata haihu ba, ga shi Allah ya zuba mishi son ya'ya tunda yayi auren nan. ya kan ce, "yana son ganin ƴaƴansa tunda yanzu lokacin sa ya soma tafiya, ya fara manyanta ga shi bai yi aure ba sai Yanzu."

Yanda yake damuwa shiyasa itama Samiran ta soma damuwa, tunda ta san cewa daga ita ne matsalar kasancewar tayi wani auren bata haihu ba. Malam Sama'ila bai fito fili ya gaya mata wata magana mara daɗi da zai tayar mata da hankali ba, amma a yanda take ganin shi da kuma yanda yake ƙaunar yara, bai da zance sai maganar haihuwa, ga yawan damuwa a kan fuskarsa shiyasa ta gane halin da yake ciki, kuma ta san tabbas ya damu da ya ga ƴaƴan sa. Shi yasa a wata rana ta zaunar da shi tayi masa maganar ƙarin aure, tace, "ita a ganin ta tunda ba ta haihuwa bai kamata ya zauna haka nan ba, ya ƙara aure domin ya ga ƴaƴansa, ita ta yarda ta amince ya auro ko wace ce."

Da farko bai amince da maganar nata ba, har an shafe kusan rabin shekara da tayi mishi maganar. Ganin ta matsa da zancen dole ya amince yace mata, "shikenan zai nemo."

Su ma iyayensa sun ba shi goyan baya tunda hakan shi ne maslaha, bazai zauna babu ya'ya ba dole ya nemi wata, duk da wannan ƴar uwansa ne amma ba an yi don a wulaƙanta ta bane, bare suna matuƙar ƙaunarta kasancewar ta mai hankali da natsuwa, akwai son jama'a da  faram-faram.



               Da yin maganar bai fi wata uku ba ya samu Mata a nan A.B.U Samaru, sai dai ita budurwa ce kuma yarinya ce sosai, Allah ya haɗa su a can Kano lokacin ta je hutun makaranta wajen ƴan uwan Babanta. Dayake kuma tana son shi shiyasa nan da nan ta ba shi dama suka soma soyayya, basu jima ba ya tura gidan su tunda shi ya ƙosa ya ƙara auren

Sai dai iyayenta sun ce, "sai dai ya jira har ta ƙarisa karatun ta tunda bai fi wata biyar ba."

Kuma ya amince, shiyasa ya nemi a saka ranan auren zuwa lokacin. Aka saka ranan auren ya ci gaba da neman ta

A hankali - a hankali biki ya zo tunda komai aka saka mishi lokaci zuwa yake yi. Aka sha biki Amarya Bilkisu ta tare

Allah da ikon sa kuma sai suka fara zaman lafiya da Samira sosai, tamkar Ƙanwa da Yaya tunda Samiran tana da hankali matuƙa, bata ɗauki Bilkisu a matsayin kishiya ba sai Ƙanwarta kasancewar ta girme mata, ta riƙe ta da amana sun zauna lafiya. Haka itama Bilkisun tana girmama ta kamar mahaifiyarta, komai ita take mata ba ta barin ta tayi komai, idan ka shigo gidan za ka yi tunanin uwa da ƴa ce tsaban biyayya da girmama juna

Kowa yana cewa, "Sama'ila yayi dacen Mata." Tunda kowa sha'awar su yake yi. Duk yanda Mutane suka so su shiga tsakanin su abun ya faskara tunda soyayyar junansu a jinin su yake

Allah da ikonsa da shigan Bilkisu ta samu ciki, sai dai kasancewar ba mai laulayi bane shiyasa basu gane ba sai da yayi kusan watanni biyar. Sun yi murna matuƙa tunda har sun cire rai a tunanin su shima Sama'ila yana da matsalar ne. Nan aka je asibiti da ita aka duba ta komai Lafiya, daga nan ta ci gaba da zuwa asibitin tana awo

Daga lokacin kuma Samira ta amshi komai na gidan ita take yi, ta hana ta komai tace, "baza ta sake yin aiki ba sai ta haihu."

Amma Bilkisu ta ƙi yarda tace, "tunda cikin ba mai wahalar wa bane Ita dai ta barta ta riƙa yi, shima ƙarin lafiya ne ga cikinta tunda motsa jiki zata yi."

Shi yasa Samira ta ƙyale ta tana yin wasu abubuwan, amma ba masu wahala ba

Cikin ikon Allah lokacin haihuwa ta haifi ɗanta namiji sak irin Babansa kamar an tsaka kara. Zo ku ga murna a wurin familyn nan, domin kowa yayi murnar zuwan Yaron nan duniya, tamkar ba a taɓa haihuwa ba a dangin su saboda ƙauna

Sai dai kuma Allah yayi nufin Malam Sama'ila bazai ga girman Yaron sa ba, yanda yayi murnan zuwan Yaron nan ko abinci ba ya iya ci tsaban bai da lokacin kansa sai na yaron, wuni yana hannunsa tunda aka haife shi. Ana gobe suna aka kira shi a kan an yi mishi lodi. Farko yace, "bazai je ba saboda gobe ne sunan ɗansa." Amma Matansa suka dage sai ya je tunda idan bai je ba zai iya samun matsala, ƙarshe ya rasa Motan ma, shi kansa ya san da haka, but tsaban ƙaunar ɗan shi ne yasa ba ya son ya jirga ko nan da can. Shi yasa da suka matsa mishi sai yace, "to shikenan tunda kun matsa zan je, amma bazan wuce sati ɗaya ba in sha Allahu zan dawo. Ga Yarona nan kafin in tafi zan bada kuɗin rago, zamu yi magana da Yaya Shehu komai na sunan zan ba shi, Yaro na raɗa mishi Ahmad Allah ya raya shi."

"Amin Amin." Suka amsa mishi cikin farin ciki. daga nan suka sake sallama dashi sannan ya bar gidan bayan ya haɗa ƴar Jakar shi

To tafiyar kenan wanda basu kai can inda zasu je ba; Allah yayi mishi cika wa sakamakon mummunan hatsarin da suka yi, ko gawan su ba a samu ba sai toka

A sanda labari ya riski Matan sa sai suka yanke jiki suka faɗi a nan take. Aka yi da su asibitin Ƙauran Wali domin basu taimakon gaggawa. A can jini ya ɓalle wa Samira ashe itama cikin take dashi, wanda babu wanda ya sani sai Allan da ya ɓoye kayan sa, ko ita bata san cewa tana da juna biyu ba ashe har ya kai wata Bakwai. A take a nan ta soma naƙuda cikin wahala ta haifi ɗiyarta Mace

Lallai Allah gagara misali ne, mai raya wa kuma mai kashe wa, ga shi ya ɗauke Uba ita kuma ƴa ta zo. A sanda ya amsa sannan yayi musu kyauta

Hakika babu wanda bai ji mutuwar Malam Sama'ila ba, su kansu Matan shi an rasa kansu domin ba kaɗan ba mutuwar tayi muguwar ratsa su, musamman ma Samira; tunda ita sai da tayi kusan kwana goma a asibitin tana fama da kanta, haihuwar ta zo mata da matsala sosai, ga kuma rashin Mijinta wanda yasa ta damu ta kasa kwantar da hankalinta, tayi jinya sosai tunda hawan jini ne ya kama ta. Daga baya aka sallame ta

Already an sanya wa yarinyar suna Hafsah duk da babu wanda aka yi suna. Daga Ahmad har Hafsan, mutuwar Mahaifin su yasa aka jingine sunan, sai dai an yi kokari an yanka musu rago. A haka har aka yi arba'in na mutuwar sannan suka yi takaban su

Bayan sun gama. Bilkisu ta ƙi komawa gida kamar yanda iyayenta suka so ta tafi. A cewar ta, "zata zauna da Yaya Samira ba ta son rabuwar su." Amma yanda iyayenta suka hura mata wuta a kan dole sai ta komo gida; shiyasa ba don ta so ba tabar gidan. Sai dai sun sha kuka kamar baza su rabu ba, shaƙuwar su yasa sun ji ciwon rabuwa ba kaɗan ba

Koda Bilkisu ta tafi hakan bai sa sun watsar da zumuncin su ba, akai-akai suna ziyartan juna har lokacin da iyayen Bilkisu suka sama mata gurbin karatu a can Kano, zata koma wurin yan uwan Babanta sai ta ci gaba da karatun a can, sun so su amshi Ahmad ita ta tafi ita kaɗai, amma furr ta ƙi yarda, haka ta tafi dashi bayan ta je ta yi wa su Samira sallama

To sanadiyar tafiyanta kenan, tunda a can ta samu Miji tayi auren ta, ko rufa shekara bata yi ba Allah ya kawo mata Miji. Haka nan ta yaye yaron ta koma gidan Mijinta, kuma dashi ta tafi tunda sai da suka yi yarjejeniya da Mijin; da ɗanta zata tafi

Su ma ƴan uwan Malam Sama'ila basu taɓa yunƙurin karɓan Yaron ba, sun bar mata shi duk sanda ta tashi kawo shi don kanta sai ta kawo shi

Ita kuma Samira bata sake aure ba illa ci gaba da tayi da kula da ƴarta, ta koma yin sana'a kala-kala domin taimakon kanta da ƴarta. Duk da ta samu waɗanda suka ce zasu aure ta but ta ƙi, domin kwata-kwata a yanzu ba ta buƙatar wani auren, gani take yi kamar idan ta kuma yi Mijin zai sake tafiya ya barta, aure biyu kenan tana rasa su, baza ta iya ba a wannan lokacin. Haka nan ta ci gaba da rayuwarta duk da ba wai zumuncin su ya taɓarɓare bane da Bilkisu. Duk sanda ta zo Zaria wurin iyayenta tana ƙoƙarin ziyartan ta

Samira ta ci gaba da kula da Hafsah tunda kasancewar yarinyar bakwanyi ne tana matuƙar tausaya mata. Ga soyayyarta da Allah ya dasa mata, tana sonta sosai duk abun da take so shi take mata. A haka har tayi karatun ta ta gama ta shiga makarantar nursing. Allah da ikon sa tana da shekaru goma sha tara a wannan lokacin ta samu Miji

Sai dai fa Mijin asalin sa ɗan ƙauye ne mazaunin garin Kugu. Amma yana aiki a nan cikin Zaria. Allah ya haɗa soyayyarsu shiyasa ta manne mishi kamar chewing gum 

Duk yadda Samira ta so ta raba su tare da nuna mata illar auren sa, tunda a ganin ta tana yar birni kuma tana karatun ta mai zai sa ta koma ƙauye? Ta taso a cikin gata zata ƙare a wahala

Amma sai Hafsah ta dire a kan dole sai shi. Kuma tace, "ai yayi mata alkawarin a nan zasu zauna, bazai kaita can ba."

Shi yasa sai Samira ta barta tunda ita ta zaɓa haka, amma ta so ta hana kasancewar hankalinta bai kwanta ba, ba ta son ƴarta tilo ɗaya wacce take matuƙar kauna ta ƙare a wahala

An saka ranan auren nan da wata shidda, yayin da Hafsan ta ci gaba da karatun ta tunda a lokacin saura shekaru biyu ta ƙare

Tun ana saura kwana biyu Bilkisu ta zo tare da Ahmad da Ƙannin sa biyu Mata da ta haifa, shima Ahmad ɗin ya girma ya zama ɗan Saurayi, yanzu yana karatu ne a can BUK yana aji na biyu, dayake duk sa'annin juna ne da Hafsan tunda kwana shidda ya bata, shiyasa suke wasa sosai da ita, ta ɗauke shi tamkar Abokin ta domin wani lokacin har rigima suke yi idan tace, "baza ta kira shi da Yaya ba, wai ai shekarun su ɗaya bai girme ta ba."

Ƙanninsa su yi ta musu dariya suna kallon draman su, idan ka zauna da su dole su ba ka sha'awa, kallum cikin rigima suke yi suna musu ga junan su, wata rana har sai Inna Samira ta tsawatar musu tana yi wa Hafsan faɗa a kan, "koda awa ɗaya ya riga ta zuwa duniya ya girme ta, dole ta girmama shi."

Ita kuma tayi ta kumbura baki tana fushe-fushe a kan bata yarda ba, dayake akwai ta da rigima kasancewar yanda Inna Samira ta raine ta cikin gata da sangarta

To an sha biki har Hafsah ta tare a gidanta a nan ɗan Magaji; inda Mijinta Haruna ya kama haya. Gida yayi kyau Masha Allah duk da ba ita kaɗai bane a gidan, su uku ne kuma dukka Amare ne, ɗaya tana da ɗanta ɗaya, ɗayan kuma bata haihu ba, ga shi Hafsan ta samu kaya ba kaɗan ba, komai an yi mata na ƴar gata ne

Bayan bikin; su Ahmad suka koma Samaru gidan Kakannin shi, daga can ne suka wuce Kano

Rayuwa ta miƙa, ga shi har Hafsah ta gama karatun ta amma Allah bai bata haihuwa ba, duk da dama an ce ana gadon uwa na rashin haihuwa, idan Mahaifiya itama tayi jinkirin haihuwa ƴaƴanta ma suna gado. To ga shi Hafsah a yanzu tana neman shekaru na uku da aure Allah bai sa ta haihu ba

Kuma a wannan lokacin ne ta soma fuskantar matsala tunda iyayen Haruna sun matsa mishi sai ya ƙara aure, sannan kuma sai ya dawo da Hafsan ƙauye itama ya haɗa su da Matar. Dayake ya siyi fili a can har ya soma gini, shiyasa suka ce mishi, "dole sai ya dawo da ita nan, idan bata dawo kusa da su ba taya zata san ƴan uwa?"

Duk yanda ya so ya fahimtar da su a kan Hafsah ƴar birni ce bata saba da irin rayuwar can ba, amma sun kasa fahimta, sun matsa mishi sosai dole yayi abun da suke so

Dayake itama Hafsan ba baƙuwar zafi bace kuma tana son Mijinta, shiyasa ta amince ta bi shi, yana gama ginin ta koma, a lokacin kuma har an saka mishi rana da wata ƴar uwan shi 

Gidan sa yayi matuƙar kyau domin duk ƙauyen babu mai kalan gidan sa, dogon gini irin na ƴan birni yayi kuma da bulon sumunti, sannan ko'ina ya sha filasta ga pentin zamani, kana doso ƙauyen da gidan za ka soma cin karo tunda ya fita daban ne, ya haska ƙauyen sosai, kowacce da sasanta yayi musu ciki bibbiyu, sai shima nashi da kuma safayan daki, sai kuma wani ɗakin na kaji tunda yana kiwon kaji

Gab da bikin kuma Hafsan ta soma laulayin ciki, cikin mai wahala ne ga tsurfa; amma haka nan ta jure tana kula da kanta kasancewar ta Malamar jinya, tana kiyaye duk abubuwan da zai sa ta samu matsala

Shima Haruna yana taimaka mata sosai, duk abun da take so yana siyan mata, ko birni zai je sai ya nemo mata duk abun da tace tana so

Cikin ya kai watanni Bakwai aka yi auren sa da Jummai. Jummai ta tare a gidan Haruna tare da ƙudurin fitar da Hafsah saboda zugin ƴan uwa, tunda ba son Hafsan suke yi ba, suna baƙin ciki da ita kaf dangin nasu musamman da suka san ta fi su komai, ga ta wayayyiya a cikin su

Sai dai kuma Jummai bata samu Sa'a ba tunda Haruna yana matuƙar ƙaunar Hafsah, itama kuma Hafsah akwai iya zama da mutane, bata taɓa biye wa Jummai a kan shirmen ta ba, ta toshe kunnen ta da idanuwanta bata taɓa tanka mata a kan duk wasu rigingimu da take taƙalanta dashi ba, bare dama Haruna yana goyan bayanta shiyasa ta bar wa banza ajiyan ta, idan tana haushin karen ta tamkar bata san da ita take yi ba

A haka har Hafsan ta haihu, ta haifi ɗiya Mace aka sanya mata sunan mahaifiyarta, wato Samira suna kiranta da Ummita; kasancewar sunan da Hafsah take kiranta dashi ne shiyasa ya bi ta.




             A wannan lokacin ne kuma aka yi bikin Ahmad; har Hafsah ta je bikin can Kano, tare da su Inna Samira suka tafi, kwanan su biyu suka dawo

Dayake itama yanzu Jummai tana da ciki shiyasa duk wasu abubuwan ta dena yi tunda tana shan wahala, Hafsan ne ma take kula da ita batare da ta duba irin zaman da suke yi da ita ba, sosai take bata taimako tunda kamar cikin ya zo da matsala ne, da rabon za a haife shi amma ta sha bak'ar wahala, kuma Hafsah ta amsar mata haihuwar

Shi yasa daga ranan ya zamana duk wacce zata haihu a ƙauyen ake kiran Hafsah, ko ciwo Mutum yake yi wurin ta yake zuwa tunda tana siyar da magunguna

Hakan ne yasa Haruna ya buɗe mata shago a kofar gidan su, duk da ba zama take yi ba amma idan an zo siyayya zata je ta ɗauko musu, kuma duk idan an kira ta zuwa gida zata je ta duba mutum. Da haka ne Mutanen karkaran suka rage tsanarta har ana zaman mutunci

Itama Jummai ta rage kishi da ita suna zaune lafiya sai dai idan tsiyan ya taso, wanda ba a raba kishiyoyi da shi. Yarinyar Jummai itama ta soma wayau sai suka taso kansu ɗaya da Ummita, itama sunan mahaifiyarta aka saka Aisha suna kiranta Indo

Kusan shekaru biyu da haihuwar su basu sake haihuwa ba

Fannin Ahmad kuma matarsa har ta haihu ɗa namiji, Yaron aka sanya mishi suna *SHAREEF*

Watan shi uku Hafsah ta sake haihuwar namiji, yaron ya ci suna Naziru. Daga nan ne bata sake haihuwa ba sai Jummai da ta sake haihuwar yara biyu Maza. A haihuwa ta biyun ne suka haihu tare da Jumman dukka Maza, daga nan kuma Hafsah ta ƙara Mace shikenan kuma haihuwar ta tsaya, yanzu yaranta huɗu, Ummita da Naziru, sai Bashir da Maryamu

Ita kuma Jummai; daga Indo sai Faisal da Ashiru, Halliru, Bintu sai Shatima

Yanzu Yaran Malam Haruna da suke kiransa da suna Baba; yaransa goma kenan. Ya aurar da Indo da Ummita duk a cikin garin, sai Yaya Faisal shima yayi aure, gidansa yana kusa da su babu nisa

Yanzu haka an saka wa Yaya Naziru rana shi da Yaya Ashiru, kuma su ne sukai karatu har matakin B8, yanzu ma suna ajin ƙarshe ne, bayan sun gama za a tsayar da lokacin a yi auren. Yaya Ashiru matarsa ƴar gaban ƙauyen su ne, shi kuma Yaya Naziru Matarsa ƴar cikin gari ne a Maɗachi. Wani lokacin Yaya Naziru shi yake zaman ma Innarsu a shagonta na Chemist, idan ba shi da lectures yana shagon tunda shima fannin likitanci yake karanta.





              Fannin Alhaji Ahmed wanda a yanzu yayi kuɗi sosai. Allah ya buɗa masa tunda yayi karatu mai zurfi, yanzu haka ya kai matakin professor. Yaransa uku dukka Maza, SHAREEF sai Hanif mai sunan Baba Sama'ila, wato mahaifin Alh. Ahmad. Sai Auta Sadiq

SHAREEF ya gama karatun sa yana aiki a companin Dadyn su, shi yake jagorantar companin gaba ɗaya

While Hanif kuma ya gama degree ɗin sa yanzu haka yana karatu a England inda SHAREEF ɗin yayi karatu

Haka Dadyn su ya tsara musu duk wanda zai yi masters can yake tafiya

Allah yayi ma Hajiya Bilkisu rasuwa wato Kakan su SHAREEF, bayan tayi dogon jinya Allah ya karɓi abun sa kusan watanni biyar kenan

Yaranta biyu da ta haifa da Mijinta, su ma sun yi aure dukkan su tunda Mata ne, kowacce tana garin da tayi auren.





        To yanzu labarin zai fara, sai a gyara zama domin jin wane ne SHAREEF?


       SHAREEF kyakkyawar matashi wanda kowacce Mace take fatan ya so ta, idan na tsaya faɗa muku yanda ya haɗu to kamar na rage mishi matsayi ne, Mutum ne mai matuƙar aji da tsantsan wayewa, ɗan boko ne zalla domin komai nasa da rayuwarsa gaba ɗaya irin na wayayyun ƴan boko yake yi, yana da son girma shiyasa ba kasafai yake da fara'a ba, idan baka fahimce shi ba za ka kira shi mai wulaƙanci da rashin son jama'a sabida ƙyanƙyamin sa da nuna shi ɗan masu kuɗi ne, ya tsani rayuwar talauci shiyasa ba kasafai yake ziyartan ƴan uwansu na ƙauye ba, zan iya cewa tunda yayi wayau bai taɓa zuwa ƙauye da sunan gaishe da ƴan uwan Dadyn shi ba, iyakansa cikin Zaria shima sai a shafe shekaru da dama bai leƙa su ba, sai idan Dadyn su yayi mishi faɗa sosai sannan yake zuwa, rayuwarsa yana yin abun sa shi kaɗai ne domin ba shi da wani Aboki sai iyayensa da ɗan uwansa Hanif, tunda sun taso tare basu da tazaran shekaru shiyasa suka zama kamar Abokai. Baya ga su babu wanda ya yarda da su a duniyar nan face Mace ɗaya, Macen da ya ƙwallafa rai a kanta yake sonta tamkar rayuwarsa, ba shi da buri sama da ya mallake ta a faɗin duniyar nan, bazan iya misalta muku irin ƙaunar da yake mata ba; amma zai iya bada ransa a kanta, komai zai iya mata saboda ƙaunar da yake mata, idan nace komai ina nufin komai.


Shin wace ce wannan yarinyar?.

        
[05/01, 8:52 am] OumƊahirah نفيسة: 🌱🌱🌱🌱🌱

      *SHAREEF*
          _SexyBoy_
🌱🌱🌱🌱🌱


_Writer: Nafisat Isma'il Lawal_
_Wattpad: UmmuDahirah_

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝*




*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

       *P.W.A✍️*










__________
*BOOK1*
_______________ *FREE PAGE3*
              Yana zaune a saman kujeran sa na office, inda ya ɗaura earphone a kunnensa yana faman latsa computern da ke gabansa a saman table, cikin ƙwarewa da zafin nama haka yake danna computern wanda da alamun aikin da yake yi mai muhimmanci ne a ciki. Sanye yake da farin suit daga na ciki har na wajen dukka fari ne, komai nasa fari ne in banda suman gashin sa da ya sha gyara yayi aski ya bar na gaban

Nocking ake yi a door ɗin; but bai san ma ana yi ba tunda already ya toshe kunnuwansa yana sauraron music, wani lokacin ma har kaɗa kansa yake yi

Sai da wanda yake nocking ɗin ya gaji before ya buɗe ƙofan ya shigo, PA ɗin sa ne riƙe da wasu files a hannunsa. Koda ya shigo ɗin ma bai san ya shigo ba tunda kacokan hankalinsa ba ya wurin, kuma bai ji ƙaran ƙofan ba, shi kuma PA ya san dama yana ciki bai wuce earphone ya saka a kunnensa ba since ba ya rabo dashi. Nufan wurin sa yayi tare da ɗan buga teburin

Hakan ne yasa ya ɗago ƴan madaidaitan idanunsa da suke fari tarr kamar madara; ya zuba masa su ba tare da yayi magana ba

Shi kuma PA ɗin sai yayi murmushi cikin girmama wa yace mishi, "Weldon sir."

A hankali ya zare hannunsa daga saman computern yana ɗaura wa a kunnensa tare da cire earphone ɗin ya sauke a wuyan sa, still ya bi PA ɗin da kallo yana jiran jin mai zai ce

Shi kuma sai yace, "sir ga files ɗin na gama dasu, and kuma akwai meeting mutane har sun taru amma na ji ka shiru ba ka fito ba."

Maimakon yayi magana sai ya ɗauke kansa yana azawa a saman wrist watch ɗin sa, nan take ya lumshe idonsa tare da buɗe wa yana jingina jikinsa sosai a saman kujeran, cikin yanayin gajiya da maganarsa mai fita da sanyi kasancewar sa mara hayaniya, yace dashi, "wlh i forgot." Sai kuma ya ɗan ja huci yana narai-narai da idanu kamar wanda yake jin barci, miƙewa yayi da zummar shiga toilet yake cewa, "za ka iya tafiya, ina zuwa."

"Ok." PA ya furta sannan ya ajiye files ɗin ya fice

Bai ɗauki lokaci ba ya fito yana nufan table ɗin sa tare da ɗaukar handkerchief da ke saman, ya share hannunsa sannan ya ajiye yana ƙoƙarin juya wa, wayansa ya ji ta soma tsiwa alamun kira ake yi, sai ya ɗan leƙa kansa; ɗan yatsan sa ɗaya na kan gemunsa yana faman sosawa. Lokaci ɗaya ya zuba murmushin da dukka dimples ɗin sa na gefe da gefen kumatun sa suka lotsa, ya zagaya ya ɗauki wayan a saman table tare da nufan bakin window yana mai amsa Call ɗin. Lokaci ɗaya ya lumshe idanu saboda jin sassanyan muryanta ya duki kunnensa. "Sweetheart." Ya furta a hankali wanda idan ba itan ba babu wanda zai iya ji, sai dai laɓɓansa da ya motsa alamun yayi magana... Shiru ya ɗan yi na daƙiƙu before ya sake magana, "I'm sorry, aiki ne yayi min yawa shiyasa ban kira ba." Sai ya sa hannu ya zage Curtain ɗin yana leƙa waje... "Ok meye labari?"... Taɓe baki yayi ba tare da ya sake cewa komai ba, ya ɗauki tsawon lokaci da alamu yana sauraron ta ne, sai kuma ya katse wayan bai sake furta wani kalma ba. Daga haka ya juya zai fice a office ɗin, kafin ma ya kai bakin ƙofan har wayan ta sake yin ƙaran kira, bai ɗauka ba sai ya sanya ta a silent tare da tusa wa a aljihu ya fice, yayin da fuskarsa babu walwala ko kaɗan, duk da dama shi ɗin ba wai mai fara'a bane; domin ba kowa yake ganin fara'an sa ba sai idan a gida, amma kuma na yanzu ya fi kowanne tunda kyakkyawar fuskar nan a haɗe take murtik, sai kuma yayi kyau ainun tunda yana da kwarjini matuƙa, Mutum ne mai cika ido da kamala, duk yanda ka kalle shi sai kwarjinin sa ya cika maka ido


Kai tsaye hole ɗin da suke yin taro ya nufa. A ƙalla ya kwashi fiye da mintuna talatin kafin ya dawo office, sai dai yana shigo wa ya sauke ido a kanta

Tana zaune a kujeran sa sanye da rigan suit ɗin sa da ya ajiye a jikin kujerar, jikinta kuma ta saka baƙin straight skirt da farar riga mai santsi, an yi shokin gefe da gefe yana da dogayen hannu, sai ta yafa farin Vail wanda ya yi wa kyakykyawar fuskarta kyau. 


             HASEENA kenan. Yarinya ɗaya da duk duniya idan aka cire iyayen SHAREEF yake matuƙar ƙaunarta. Budurwa ce da aƙalla baza ta fi 22years ba, tabbas Haseena kyakykyawa ce kuma ta cika Macen da kowanne namiji ya ganta sai ya ƙyasa, tana da hasken skin but tana ƙara wa da mai kaɗan; wanda hakan ne yasa ta koma fara, tana da gata a wajen iyayenta duk da kasancewar su biyu suka haifa tare da ƙanwarta, amma sun ɗauki son duniya sun ɗaura mata shiyasa ta taso cikin gata da sangarta, abun da take so shi take yi. Sai ga shi kuma Allah ya haɗa ta da SHAREEF da ya shigo cikin rayuwarta suna matuƙar ƙaunar juna, iyayenta sun sani sai dai nashi iyayen basu sani ba, but yana da ninyar faɗa musu a nan kusa tunda yana bukatar aure


Tun shigowar sa ta washe baki tana miƙewa tare da cewa, "welcome my dear. I have been here waiting for you." Sai ta nufe sa tare da manne wa a jikinsa, a hankali tayi masa kissing a laɓɓansa

Bata kai ga janye bakin ba, sai ya matso da nasa ya haɗe bakunan nasu wuri ɗaya, take a nan ta lumshe idanu; while shi kuma ya sanya  hannayensa ya kama ƙugunta tare da sake manne ta a jikinsa. Tsawon mintoci suna a haka before ya janye bakinsa yana bin ta da kallo; kallon soyayya

Daga ɓangaren ta itama hakan ne, sai dai tuni ta sake maida jikinta ta rungume sa sosai tana sauke ajiyan zuciya

A yanzu ɗaya hannunsa yana bayanta yana shafa mata tamkar ƙaramar yarinya, sai kuma ya janye jikinsa before ya kama hannunta ya nufi couch ya zaunar da ita, shima ya zauna a gefen ta yana facing ɗin ta, ƙura mata ido yayi bai iya cewa komai ba illa bin ta da kallo da yake ta faman yi

Ita kuma sai ta shagwaɓe fuska tare da cewa, "meyasa ka kashe min waya muna magana?"

Sai da ya saka hannunsa cikin nata ya haɗe yatsun yana kallo, yake furta, "I told you I don't want you to leave, meyasa baza ki bari ba sabida farin cikina?" Ya ƙare maganar yana sake tsira mata ido

Tura baki tayi tace, "don Allah ka bar ni Nidai, just two years ne fa zan yi karatun nan in gama, kuma na fi son can wlh bazan iya karatu a ƙasar nan ba, when I come back everything will come to an end; sai mu yi auren mu ko?"

Numfashi ya ja before yace, "Ni ba haka nake so ba, kin fi kowa sanin cewa ina matuƙar buƙatarki a halin yanzu, bazan iya jira har nan da two years bamu yi aure ba, ki canza wannan shawaran Please sweetheart?"


"But I don't have any advice kuma, Abbana yake son in je in yi karatu na a can bazan iya bijire masa ba, tun farko na baka kaina amma ka ƙi amince wa, to me kake so in yi maka? Tunda muna son juna why not baza ka amince mu ji daɗin rayuwar mu kafin auren mu ba? Please dear nima ina buƙatar ka a rayuwa domin ji nake yi kamar idan na tafi bazan dawo ba, don Allah ka fahimce Ni." Ta ƙare maganar kamar zata yi kuka tana sake shige masa 

"Haseena." Ya furta sunanta ƴan madaidaitan idanunsa suna a kanta

Kasa amsa wa tayi sabida bata saba jin yana kiran sunanta ba, but sai dai tuni ƙwalla sun tarun mata a idanu tana shirin kuka

Girgiza mata kai yayi tare da cewa, "I don't want you to cry please sweetheart, Ni mai ƙaunarki ne ba maƙiyin ki ba, ba na son wani abu ya shiga tsakanin mu ba tare da aure ba, ko kin fi son mu aikata Zina ne?"

Kanta itama ta girgiza hawayen cikin idonta suna sauka, sai tace, "but amma ai muna ƙaunar juna, kai ne fa za ka aure Ni, meyasa baza ka fahimce Ni ba?"

"Shiiiii!" Ya furta yana ɗaura hannayensa biyu a saman face ɗin ta tare da share mata hawayen, sai ya sauya maganar tare da cewa, "yaushe ne tafiyar naki?"

"Later than ten o'clock at night."

Murmushi yayi mata mai yalwa wanda kyawawan dimples ɗin sa suka fito

Sai ita kuma ta sanya hannunta a cikin guda ɗaya; while itama tana murmushin cike da tsantsan ƙaunarsa

"I love you sweetheart." Ya furta tare da kama hannunta zuwa bakinsa yayi kissing ɗin ta, sai ya zuba mata idanunsa a cikin nata tare da ƙara faɗin, "zan yi kewarki matuƙa a cikin raina, zuciyata zata azabtu da rashin ki, but I will wait until you come back, two years is like two days, zamu kasance a tare a kodayaushe. Zuwa anjima zan zo gidan in raka ki zuwa airport."

Da sauri ta ɗago ta faɗa kansa tare da furta, "i love you so much dear, ina sonka sosai a raina, don Allah kar ka ci amanata bazan taɓa iya jurewa ba."

Bayanta yake shafa wa a hankali a yanzu ɗin cikin rarrashi, tare da ɗaura bakinsa setting kunnenta yana raɗa mata maganganu masu kwantar da hankali da zauta ta. Sai dariya take yi cikin fari ciki tana ƙara manne mishi. Hakan ne yasa a hankali ya soma romance ɗin ta cikin ƙwarewa da tsantsan soyayya, sun shiga wani irin yanayin da baki ma bazai iya furta wa ba

Daƙyar SHAREEF ya janye ta a jikinsa lokacin duk jikinsu yayi laƙwas, sai jaraba da tsantsan feelings da ke gudana a idanuwansu, yanda take manne mishi tana shirin mishi kuka shiyasa ya soma lallaɓa ta cikin ƙaunarta yace, "ta je gida idan ya gama aiki zai zo ya same ta."

Ba ya son irin hakan na faruwa dasu saboda matuƙa yana cutuwa, yana buƙatar Mace a rayuwarsa but bazai iya kusantar kowace ce ba idan har ba ta hanyar aure bane, yana tsoron Allansa a kan Zina. Ita kaɗai ce Macen da ya san ya iya haɗa jiki da ita, kuma ƙaunar da yake mata ne shiyasa bazai iya jurewa ya kasa taɓa ta ba, komai yana yi da Haseena sai dai kusantar ta ne bai taɓa yi ba, Allah yana kare sa a wannan wurin duk da ita ta sha faɗa masa, "ta gama mallaka masa komai nata, yayi abun da yake so da ita tunda aure zasu yi." Sai dai ya ƙi amincewa ya bar wannan ranan a matsayin Babban ranansu da zata kasance bayan auren su, wanda fatansa kenan ranan ta zo, sai ga shi kuma zata tafi karatu bayan ba haka ya so ba, ya so nan da ɗan lokaci kaɗan ya sanar da iyayensa don su je nema mishi auren ta, amma kuma yanzu haka nan zai jira har ta dawo tunda yana son abun da take so, ko mene ne zai iya haƙura dashi a kan ƙaunar da yake mata, ciki kuwa har da jiran dawowarta daga karatun ta.








🔆🔆🔆🔆🔆🔆🔆


            Wani kallon sama da ƙasa tayi masa, sai kuma ta kwashe da dariya tana nuna sa da yatsa

Hakan ne yasa shima ya bi jikin nasa da kallo yana mamakin abun da yasa take mishi dariya. Ganin ta ƙi dena dariyan ne sai ƙara kwashe wa take yi da dariya har da tafa hannaye kamar wata mai kwantaccen kai. Sai yace, "wai lafiya Maryamu? Meyasa kike min dariya?"


Lokaci ɗaya ta ɗauke dariyan tana tamke fuska cikin yanayin ta na rashin mutunci tace, "wlh kana bani mamaki Jamilu, kai har kakai matsayin da zan iya sonka? Ji be ka fa..." Ta ƙara nuna sa da hannu kallon sama da ƙasa, sai tace, "wai tsaya, me ya ba ka ƙwarin gwiwar zuwa wurina?"

Cike da rashin jin daɗin abun da tayi masa yace, "amma ai na san kin san waye Ni a ƙauyen nan Maryamu, sannan na san ke ce Macen da ta fi kowa kyawu shiyasa nima na zo wurin ki saboda dani kaɗai kika dace, ina da yaƙinin za ki so Ni tunda kin san ina fita Birni aiki."

Kama ƙugu tayi da hannu biyu cikin tsiwa tace, "Allah ya kyauta, don kana fita Birni aka ce maka irin Mazan da nake so kenan? To wai ina ruwana da matsayin ubanka a garin nan? Bari ka ji Ni na fi ƙarfin ku wlh, babu Mijina a wannan ƙauyen, ka dube Ni sama da ƙasa." Sai ta juya jikinta a gabansa tana mirza jiki kasancewar Allah ya bata ƙirar jiki, sam babu rama a tare da ita wanda hakan ke ƙara jawo hankalin samari a kanta, kuma duk ƙauyen gani suke yi ta fi ƴan matan kyawu. Sai tace, "to Ni ba sa'an wasan ka bane, kar in sake ganin ka tako ƙofar gidan nan da sunan ka zo wuri na, wlh tallahi ka san hali na bani da mutunci zan shuka maka babban rashin mutuncin da sai ka yi dana-sanin sani na a rayuwa." Sai ta ja dogon tsaki tana juya wa zata shige gida

But sai ya dinga kiran sunanta har yana bin bayanta da sauri

Da sauri itama ta juyo a fusace tana kwaɗa mishi mari, "baka ji mai nace maka ba ko? To wlh ko Ubanka da yake mai anguwa na fi ƙarfin shi bare kai ƙaramin alhaki."

Zallan mamakin abun da tayi masa ne yasa ya kasa motsa wa yana riƙe da kuncin sa, sai da ta shige gidan ya dena ganin bayanta sannan ya soma ƙifta idanu ya dawo cikin tunanin sa, tsaban yanda ransa ya ɓaci ya rasa ma wanne mataki zai ɗauka, ba marin da tayi masa bane; yanda ta ci masa mutunci kuma ta haɗa da ubansa ne ya yi matuƙar ɓata mishi rai tare da mamakin yanda har rashin mutuncin nata ya kai haka ashe, duk zancen Mutane gani yake yi kamar shi ya fi ƙarfin tayi mishi haka har ya iya biye wa zuciyarsa, ashe akwai ranan da zata wulaƙanta sa duk matsayin mahaifinsa a garin, tabbas sai ya ɗauki mummunan mataki a kan yarinyar nan, domin bazai taɓa yafe mata wannan cin zarafin ba, zai nuna mata shi yana da bambanci da sauran Mutanen karkaran, sannan Babansa shi ne shugaba. Juya kai yayi da sauri ya wuce yana gode Allah da babu wanda ya ganshi. 



           Ita kuma Maryamu tana shiga gidan sai masifa take yi har da kumfar baki

Umma Jummai ita ta soma tambyarta, "ita da waye zata shigo tana surutu?"

Sai da ta ja tsaki tana tsittar da yawu, sannan tace, "wlh Umma na kusa tayar da bambamin bala'i ga duk ɗan iskan da bai bar zuwa kofar gida kirana ba, don sun raina Ni sai kowanne kare da doki ya zo yace yana sona tunda sun gama raina min wayau? wlh daga yanzu duk wanda ya zo sai nayi mishi abun da ko Uban shi sai yayi dana-sanin haifo sa...."

Bata ƙarisa zancen ba Innarta ta bugo salati tana fitowa daga bayi, "innalillahi wa'inna ilaihi raji'un... Wai Maryamu kanki ɗaya kuwa? Wato ba ki da mutunci ba ki san Annabi ya faku ba ko? Tam shikenan ki ci gaba da abun da kike yi na rantse da Allah sai na saka Naziru yayi miki mugun duka a gidan nan tunda ba ki da mutunci; banzan yarinya kawai."

Umma Jummai ta karɓe da faɗin, "Ni na rasa kan wannan yarinyar Hafsatu, anya abubuwan da take yi baza a je a duba ƙwaƙwalwan ta ba? Kullum ace ba ta jituwa da Samari sai faɗa da zage-zage wannan abun zai yiwu kuwa? Gwara dai a nema mata magani wlh."

"Ni wlh lafiyata ƙalau Umma. Ya za a yi a mayar da Ni mara hankali bayan baku taɓa ganin na hau iska ba? Ras nake wlh." Tayi maganar tana tura baki tare da wuce wa ɗakin su tana ci gaba da ƙunƙunai

Inda Inna ita kuma tayi ƙwafa tana cewa, "kin gani ko? Iskanci ne ba wai wani abun ke damun Maryamu ba, ta ɗauki burin banza ta ɗaura wa kanta, to a yi mu gani idan wannan hanyar da kika ɗaukar wa kanki zai fishshe ki, kuma dan ubanki ki fito ki wuce Islamiyya tunda kin dawo gantalin naki, kar ki bari in sake miki magana."

"Gani nan." Tayi maganar da ƙarfi daga ɗaki

Su kuma suka ci gaba da tattauna halin Maryamun ita da Umma Jummai, a kan yanda take wulaƙanta Samari, suna faɗa mata, "idan ta ɗauki wannan hanyar wata rana zata yi dana-sani tunda baza su zuba ido su barta babu aure ba, tana ƙauye a tunanin ta wane mutum ne zai zo ya aure ta ɗan birni? Ta ɗauko abun da ya fi ƙarfin ta."

Zurum sai ga ta ta fito tana tura baki da cewa, "Ni fa yanzu ba shine damuwata ba, tunda babu wanda ya isa yayi min aure yanzu dai ina ƙarama ta, na rantse baza a tauye min haƙƙina haka kawai a yi min aure a wannan time ɗin ba, karatu nake so domin sai na cika burina, sai nayi ilmi har na fara aiki in samu daidai ra'ayi na, ku kanku zaku ji daɗi ace yau ga Mijin Maryamu a Mota ɗan gidan masu kuɗi, amma haka kawai na ƙare a ƙauye? Na taso a ƙauye babu ci gaba sai kuma na ƙare a nan? A'a gaskiya bazai yiwu ba."

Inna ta kasa magana don takaici. Yayinda Umma Jummai ta riƙe baki tace, "lallai abun naki ya shahara Maryamu, to ai sai ki jira mai motan ya zo ya aure ki tunda iskancin naki gaba yake yi."

Yaro ne ya shigo a lokacin ya zo siyan panadol

Inna tace, "idan kin gama rashin kunyar ki zo ki amshi mukulli ki ɗauko mishi, kuma kar ki bari in sake miki magana ba ki wuce makarantar nan ba, Allah Maryamu zan mummunar ɓata miki rai."

"Kai Inna! Ni wlh ban san mai nayi miki ba yanzu komai sai faɗa, Ni nace miki bazan je bane? Gaskiya Ni na fi so ma a mayar da Ni wurin Iya kawai in ci gaba da karatu na a can, wlh bari Baba ya zo sai na faɗa mishi Ni dai na fi son karatu."

"Ai gwara ki faɗa ma Baban naki tunda shi ne dai-dai ke kuwa." In ji Umma Jummai tana tashi ta shige ɗakin ta riƙe da kwanon garin tuwo

Ita kuma Inna ta miƙa mata mukullin batare da ta sake ce mata komai ba; ta soma ɗaura alwala

Maryamu fita tayi da yaron; ta buɗe shagon ta ba shi sannan ta mayar mata da mukullin, Hijabin ta ta zura ta fito bayan ta saka takalmi mai tsini tana tafiya daƙyar kamar baza ta taka ƙasa ba

MARYAMU kenan. Yarinya mai tashe a cikin ƙauyen nasu, haƙiƙa tana da farin jini sosai duk da dama ita kyakkyawa ce, ga ƙira mai kyau komai ya ji a jikinta, yarinya ce da bata gaza shekaru goma sha biyar ba, baƙa ce irin Black beauty ɗin nan, Allah yayi mata kyawu ga manyan idanu farare sol, tana da dimples waɗanda suke ƙara mata kyau musamman idan tayi murmushi ko dariya. Ba wata mai tsawo bace ƴar matsakaiciya ce kuma bata da jiki; amma kuma bata da rama ko kaɗan, zubin ta irin waɗanda Maza suke so ne shiyasa suke rushing ɗin ta, sai dai ita ta ɗauki buri ta ɗaura wa kanta, bata da buri sai auren mai kuɗi kyakkyawar saurayi ɗan birni, shiyasa fatan ta a yanzu tayi karatu mai zurfi wanda ta san cewa shine kaɗai zai sa ta samu cikan burin ta, idan tayi ilmi to ta san kowanne namiji zata iya samu

Sai dai tunda suka gama junior secondary ita da Bintu har yanzu basu ci gaba ba, tunda burin Babansu yayi musu aure kasancewar sun kai minzalin aure, kuma a garin yarinya ba ta wuce shekara sha uku bata yi aure ba, kuma yawancin su ba sa karatu, amma dayake shi Babansu ya san daɗin karatun kuma yana barin yaran shi shiyasa su ma ya bar su, Matan ba sa kai wa secondary yake aurar dasu, su Maryamu ne kawai suka gama junior

Kuma a yanzu ita tana burin ta ci gaba duk da zata sha wahala; kasancewar babu senior secondary a cikin garin, dole sai an fita birni. Ita kuma ta matsa a barta ta koma wajen Kakarta Iya Samira tayi karatun ta a can, har yanzu dai Babansu bai yarda ba, tunda tayi masa magana sau ɗaya ma bata sake mishi ba kasancewar yayi mata faɗa sosai a lokacin.
[08/01, 8:25 am] OumƊahirah نفيسة: 🌱🌱🌱🌱🌱

      *SHAREEF*
          _SexyBoy_
🌱🌱🌱🌱🌱


_Writer: Nafisat Isma'il Lawal_
_Wattpad: UmmuDahirah_

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝*



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

       *P.W.A✍️*


*Don Allah ina baran addu'a daga bakunan ku masu albarka, ina cikin matsananciyar damuwa, ina neman addu'a gare ku ya Allah ya yaye min abun da ke damuna; da duk wanda ke cikin irin hali na, 😭 innalillahi wa'inna ilaihi raji'un.*









 
__________
*BOOK1*
_______________*FREE PAGE4*
             Bai tashi daga aiki ba, sai kusan ƙarfe shida da rabi, duk da ya saba jima wa but ba ya kaiwa haka, ya kan yi ƙoƙarin tashi by 5 o'clock. Shi yasa gaba ɗaya a gajiye yake jin sa, tafiyan ma daƙyar yake yi fuskarsa a turɓune kamar zai saka kuka, yanayin sa kuma sai ya koma tamkar ƙaramin Yaro abun burgewa ga duk wanda ya kalle shi, shiyasa a koyaushe Mata suke matuƙar ƙaunarsa; domin ta ko'ina SHAREEF ya kai namijin da Mace zata mutu a soyayyarsa. Sai dai kuma babu fuskar da kowacce Mace zata iya tunkurar sa gudun wulaƙanci

Majority Matan da suke aiki a companin babu wacce ba ta yin sa, wasu har ba sa iya ɓoye ainihin abun da ke ransu dole sai sun tunkare shi duk da wulaƙancin da zai yi musu. Shi yasa yawanci suke rasa aikin su, domin ba abun mamaki bane daga kallo ma kaɗai idan bai gamshe shi ba ya kore ka. Companin kowa ya san ba ya wasa bare ɗaukar raini, kuskure kaɗan zai kore ka domin ba ya ma Mutum uzuri. That's why kowa yanzu ya kama kansa yana taka-tsan-tsan kar ya shiga gonan SHAREEF. Domin idan ya yanke hukunci ko Dady ba ya cewa uffan

Yanzu ma Dady ya dena zuwa companin ya danƙa mishi komai shi yake yi, sai jefi-jefi ne yake zuwa ko duba wurin, amma komai SHAREEF ke yi, sai wani lokacin idan Hanif yana gida ya kan zo su yi aikin tare

Sadiq kuwa dama babu ruwansa da companin tunda yace, "babu abun da ya haɗa sa da Kasuwanci." Dayake karatun lauya yake yi. Yanzu haka yana BUK shima ya kusa gama wa ya wuce England

Hanif kuwa, ɗan watanni ne ya rage mishi ya ƙare. So yanzu ma yana gida bai koma ba.



    **** **** ****



             Tunda ya hau motan sa ya soma tuƙawa a hankali; yana yi yana duba wayansa fuskarsa yalwace da murmushi. Wanda hakan ba kasafai yake yin sa ba sai da ƙwaƙƙwaran dalili, yanzun ma chart suke yi da Haseena shiyasa kacokan hankalinsa ya bada gare ta. Sai jefi-jefi yake ɗago kai ya duba hanya a haka har ya ƙarisa gida. Horn ɗaya yayi aka buɗe masa ƙofan ya shige da Motan. A wajen parking space ma sai da ya ɓata time ya ƙi fitowa yana ci gaba da chatting ɗin. Daga ƙarshe kuma ya fito hannunsa ɗaya riƙe da waya, ɗayan kuma ya riƙo Jakar office ɗin sa; inda ya ɗaura suit ɗin sa a saman kafaɗa yana tafe yana duba wayan

Dama already masu aikin gidan sun san halin sa ko gaisuwar su ba ya amsa wa; bare su kawo mishi ɗauki wajen taimaka masa da amsar Jakar, tunda ya hana su yace, "kar ya ƙara ganin wani ya zo inda yake."

Ire-iren halayyar nan na ƙyama da yake nuna musu shiyasa kowa yake jin tsoron sa, a kuma taka-tsan-tsan suke yin komai nasu musamman in yana gida, domin yanzu zai hau su da faɗa yana zagin su. Shi kaɗai ne ya fita zakka a gidan tunda kowa suna jin daɗin zama dasu ban da shi

Falon ya shiga ko sallama babu tunda hankalinsa yana a kan waya. Har ya nufi kan steps zai hau sama sai ya ji kiran Mahaifiyarsa. Yana ɗago kai suka haɗa ido da ita tana zaune a saman kujera tana kallon tashan Arewa24 da ake haska maimacin shirin gari ya waye

"Mom." Ya furta yana ɗan yaƙe haƙora cike da kunyar ganin ta a wurin

Ita kuma sai ta dalla mishi harara tana sake kafe shi da ido ko ƙyafta su ba ta yi

Domin ba abun da yake shakka sama da idon mahaifiyarsa, kasancewarta mai manyan ido shiyasa take yawan hukunta shi da su, domin shi ya sha sanar mata, "yana matuƙar tsoron idanun nan nata." Shi yasa da zaran ta kafo mishi su ya san laifi yayi. Sai ya sunkuyar da kai yana sussune kai, ko kuma ya soma bata haƙuri

Yanzun ma hakan ne, tunda ya yaƙe haƙora ya soma sosa ƙeya kansa a ƙasa

"Zo nan."

Dole ya tako a hankali ya isa inda take. Ya san me take nufi, shiyasa ya duƙa a gefen ta still kansa a ƙasa

Maimakon ta ja masa kunne kamar yanda ta saba, sai ta ranƙwashe shi da ƙarfi yanda zai shige shi, tana kuma ƙara wa da murɗe mishi kunnen 

"Oushh! Momy. Da zaafi..."

"Ai zafin nake so ka ji, ba ka jin magana ko SHAREEF? Wai sau nawa zan riƙa maimaita maka magana?"

"Allah Momyna na manta ne, amma da kika kira Ni nayi a zuciyata."

Kunnen ta sake murɗe mishi tana cewa, "au ka yi a zuciya? Haka aka koya maka don ƙaniyar ka? Kana ɗan musulmi zaka shigo mana gida babu sallama bare ma ka ɗaga kai ka kalli Mutanen ciki ko?"

Fuskarsa ya kwaɓe kamar zai yi kuka sai dai ya kasa cewa komai

Sai ta tamke fuska tana cewa, "to kar ka sake bari na kara maka magana."

"To." Yayi maganar a hankali

"Ba to zaka ce ba, ka aiwatar ne, don na gaji da jin to ɗin nan naka amma kullum sai ka ƙara aikata wa, zamu hau sama da kai SHAREEF wlh."

"Ke da Yaron naki ne? Me kuma yayi?" Cewar Dady da ya sauko daga saman benen, yana nufo su da murmushi a kan fuskarsa

"Wlh kuwa, halin nasa ya sake, sai ka yi wa SHAREEF faɗan halinsa sam ba ya jin magana, ban san meyasa yake wasa da addinin sa da yawa ba, kwata-kwata ba ya damuwa da abin da ya kamace shi, yanzu kamar SHAREEF zai shigo mana gida babu sallama?"

"Kullum maganar kenan ai, kai kuma ka ƙi gyara wa har na haddace faɗan nan. Ka yi wa kanka faɗa ka dena saka Mahaifiyar ka magana, ko Sadiq bazai yi abun da kake yi ba." Cewar Dady yana ɗan murmushin sa wanda ba ya rabo da yin sa, domin yawancin sa yana komai nasa ne cikin raha da barkwanci, ba shi da faɗa ko kaɗan, ko faɗan ma zai yi maka baza ka iya ganewa ba tunda yana yi yana saka wasa ne, ko kuma ka ga fuskarsa a sake wanda ba ka iya tantance faɗan ma yake yi, ko kaɗan ba shi da zafi Mutum ne mai sauƙin kai. Shi yasa kowa yake son shi domin ba shi da girman kai irin na masu kuɗi, ga taimakon jama'a kowa nashi ne. "Yanzu tashi ka je ka yi alwala ka ga an kira sallah kar lokaci ya ƙure. Ke kuma Momyn Yara a dena mishi faɗan haka, har yanzu shi Yaro ne wata rana zai dena."

"Hmm kullum haka kake cewa ai."

Murmushi yayi yace, "to ai hakan ne, yanzu SHAREEF ai kai yaro ne ko?"

Dariya yayi yana sosa kansa tare da gyaɗa mishi kai

While Dadyn yace, "yauwa ɗan albarka, to yi maza ka je ka yi alwala kar lokaci ya ƙure. Hanif ma yana ɗaki ka sake koro sa."

"To Dady." Yayi maganar yana wuce wa upstairs

Inda shima Dadyn yace ma Momy, "bari in je Masallaci."

"To sai ka dawo." Ta amsa mishi tana tashi itama ta wuce nata ɗakin domin ɗaura alwala

SHAREEF kuma yana shiga ɗakin, ya tarar da Hanif yana kwance barci ya ɗauke shi a saman kujera, da alamun aiki yake yi tunda ga computer nan a gaban shi tana buɗe

Sai da ya isa bakin gadon su ya ajiye Jakar hannun sa da wayan, ya zare suit ɗin shima ya ajiye sannan ya nufe sa yana kai masa duka a saman kumatu

Lokaci ɗaya kuwa ya farka yana zuba masa idanu

Sai ya harare sa yana cewa, "ka zama mushe ne? Barcin meye kake yi haka?"

Ɗan kwaɓe fuska yayi yana miƙa tare da salati, kana a hankali cikin mayen barci yake cewa, "wlh maganin mura na sha, ban san barcin ya ɗauke Ni ba." Sai ya ɗan ja tsaki sabida jin ana kwaɗa kiran sallah. "yanzu wai har nayi barci da yawa haka?"

"Tun yaushe kake barcin?" SHAREEF ya tambaye sa yana ƙoƙarin zare necktie ɗin wuyansa, tare da koma wa gefen gado ya zauna, sannan ya soma cire Cumbas ɗin sa da socks

Hanif kuma yana basa amsa shima ya miƙe yana ƙara miƙa tare da jujjuya jikin sa, "tun four nake nan barci ya kwashe Ni."

"Da alamu bai ishe ka ba ma, ka koma kawai."

"Sallan kuma fa?"

Taɓe baki SHAREEF yayi tare da cewan, "sai ka yi anjima."

Numfashi kawai Hanif ya ja yana nufan hanyar toilet bai ce komai ba, sai da ya buɗe ƙofan ya zura takalmi sannan ya shige

Kafin ya fito shima SHAREEF har ya zare kayan sa, ya zauna daga shi sai guntun wando yana latsa waya, sai murmusawa yake yi

"Brother sallah fa?"

Ɗago kai SHAREEF yayi yana kallon sa, sai kuma ya ɗauke kan ya ci gaba da latsa wayan, kafin kuma ya ajiye ya wuce toilet ɗin shima

While Hanif tuni ya saka doguwar jallabiya ya fice

Sai da SHAREEF yayi wanka sannan shima ya fito ya zura jallabiya irin na Hanif, before ya fita da sauri duk da har an idar da Sallan ma. Shi yasa ya bi ta ƙofan baya don kar Momy ta gansa ma

Sai da aka yi sallan isha'i sannan ya dawo. Yayi saurin shirin sa ya saka riga da wando ƙanana sai tashin ƙamshi yake yi, Allah ya zuba mishi tsafta shiyasa koyaushe ƙal-ƙal zaka ganshi tamkar bazai taka ƙasa ba, ga iya ɗaukar wanka da kowacce Mace ta gansa sai ta juya ta sake kallonsa, musamman yanda yake da kwarjinin nan da ɗaukar ido sabida farar fatarsa mai kyau da burgewa

Hanif tunda ya ga ya ci wannan gayun, ya san wurin Haseena zai je, sai ya taɓe baki yana cewa, "lallai soyayya ta motsa kenan! Kodaye kullum a cikin ta kake."

SHAREEF tamkar bai san dashi yake yi ba, sai da ya gama komai yana miƙewa tare da sake feshe jikinsa da turare; yake cewa. "kai yaushe zaka koma makarantar ne wai?"

"Ba yanzu ba."

"Sai yaushe kuma?" Ya ƙara tambayarsa a yanzu yana tsare sa da ido

"For a week."

Jinjina kansa yayi ya nufi ƙofa zai fice, sai kuma ya juya yana kallonsa tare da cewa, "sweetheart zata tafi karatu ne Abroad, shi ne zan je in raka ta."

Da mamaki Hanif yace, "kamar ya kenan?"

"Kamar yanda ka ji." Yafaɗa yana yatsina kyakkyawar fuskarsa

"To auren naku fa? Wanne karatu kuma zata je?"

"Nima haka tace min."

"Kana nufin zaka jira har ta dawo?"

"Eh." Ya furta a taƙaice

Shiru Hanif ɗin yayi, har sai da ya ga SHAREEF zai fice before ya sake cewa, "Bro anya yarinyar nan tana sonka?"

"Kamar ya?" Yace dashi yana juyowa da sakar masa wani kallo

"To na ga kace zata je karatu, ina ga hakan bai kamata ba, yanzu abun da ya dace shine ta tsaya ta fuskanci auren ku, but ba haka ba, I think akwai wani abun a zuciyarta."

Wani banzan kallo ya sake masa. Sai bai ce komai ba ya juya ya fice

Shima sai Hanif ɗin ya ɗage kafaɗa alamun bai damu ba, ya miƙe ya fita zuwa Falo
   

Kasancewar SHAREEF ta Kofar baya ya fita shiyasa su Momy basu ganshi ba, tunda duk suna zaune a Falon

Kai tsaye mota ya yau ya nufi gidan su Haseena. Lokacin da ya isa kiranta yayi a waya yace mata, "yana waje."

Katse kiran yayi sannan ya fito ya nufi cikin gidan. Nocking yayi sai ga mai gadi ya zo ya buɗe mishi

Da sauri ya duƙa har ƙasa yana gaishe shi cikin girmamawa

Amma sai SHAREEF bai ce mishi komai ba ya wuce ciki hankalinsa a kan waya. Kai tsaye gidan ya tasar wa tunda tace mishi ya shigo ne. Tura ƙofan yayi ya shiga but babu kowa a cikin Falon sai tv da ke faman aiki. Kai tsaye saman kujera ya nufa ya zauna yana harɗe ƙafa tare da ajiye wayan sa a hannun kujera. Shiru ya ɗan yi na lokaci idanunsa a saman TV

Sai ga Umman Haseena ta fito ta hange shi, da fara'anta ta nufe sa tana cewa, "ah ah! SHAREEF ne ashe?"

Kallonta yayi, sai yayi murmushi yana ɗan shafa kansa tare da cewa, "eh Umma. Ina yini?"

"Lafiya lau, ya kake? Ya su Momyn naka?"

"Suna nan lafiya."

"Masha Allah. Bata fito bane Haseenan?" Ta tambaye sa tana zama itama a kan kujerar

Sai yace, "eh. But ta san da zuwa na ai."

"Ok to, bari a kawo maka ruwa kafin ta fito."

"A'a Umma a bar shi kawai."

Murmushi tayi sai tace, "sai ka ji kuma Haseena zata tafi karatu?"

"Wlh kuwa Umma."

"Haka ne, mahaifinta ya yanke hukuncin, duk da Nima gaskiya ban so ba, domin na fi so ku yi auren ku ku huta hakan zai fi."

Murmushi yayi yace, "ai Umma kamar yau ne zata gama ta dawo."

"To Allah yasa. Ni dama kar a shiga haƙƙin ka ne, but tunda ka amince zaka iya jiran ta babu damuwa ai." Ta furta da fara'a

Wanda a lokacin ne Haseenan ta fito tare da ƙanwarta Haajara. Har ta gama shirya wa lokacin tafiyan kawai take jira, sai kuma Abban su da ya fita sai ya dawo zasu raka ta airport

"Dear." Haseena tafaɗa tana nufan inda yake fuskarta yalwace da fara'a. Tana zuwa ta zauna a kusa dashi tare da kamo hannunsa babu kunya tayi masa kiss

To dama suna da wayewa hakan ba komai bane a wurin mutanen gidan. Inda ita Umma ma murmushi take yi tana tsokanar su da cewa, "ko dai za a ɗaura muku auren nan ne kawai ku tafi tare?"

Dariya suka yi, har Haajara da itama ta zo ta zauna a ɗaya side din shi, tana cewa, "Yaya SHAREEF ina wuni?"

Murmushi yayi yace, "lafiya lau ƙanwata. Kin ɓoye da yawa?"

Sai ta langaɓe kai tare da cewa, "wlh school ne Yaya ya ɓoye Ni."

Haseena kuma da ke magana da Umma kasancewar maganar da tayi, sai ta juya tana kallon SHAREEF tare da cewa, "wai haka Dear? Ko zamu yi auren mu before in tafi?"

"Ai lokaci ya ƙure Haseena, da tun farko muka yi wannan tunanin."

Tura baki tayi tana ɗaura kanta a kafaɗan sa

While Umma tace, "ka ji ka ƙyale rigimammiyar nan, Nima wasa nake muku."

Hajara kuwa dariya tayi tace, "Umma kar ki sata kuka fa, yanzu sai ki ga ta soma hawaye tunda ta ga Yaya SHAREEF a kusa."

Hararan ta Haseena tayi tace, "ina wasa da ke ne?"

Dariya take mata tana ɗan matsa wa

SHAREEF ya raɗa wa Haseenan magana a kunne sai murmusawa suke yi suna sake manne wa wuri ɗaya

Suna nan a wurin gaba ɗaya suna ɗan taɓa hira, sai ga Abba ya dawo. Tunda kasancewar lokaci ya soma tafiya shiyasa aka fito wa da Haseena kayan ta, masu aiki suka kai mata wajen mota aka saka mata

Gaba ɗaya suka ɗinguma zuwa airport ɗin. Sauran suna cikin mota while SHAREEF da Haseena suna a Mota ɗaya driver na tuƙa su. Hakan ne ya basu damar manne wa da juna suka soma romance kamar zasu cinye junan su, daga sallama abun ya juye sun kasa jure wa. Kacokan ma saman SHAREEF ɗin Haseena ta koma sai cakuɗa juna suke yi, while hannun sa na a cikin riganta yana matsa mata breasts har ya zare mata gyalen da ta sanya. Bakinsa cikin nata suna socking juna. Ga nishi da suke fitar wa a hankali alamun sun yi nisa a wannan yanayin

Driver na jin su sai dai babu halin juya wa ya kalla tunda ya san sauran, ba SHAREEF ɗin ba; ba kuma Haseenan ba. Yanzu zai ja wa kansa ya iya rasa aikin sa, don haka tsoro ma ya hana sa kallon mirror 

A hankali SHAREEF ɗin ya zame bakinsa a cikin nata yana ɗaura fuskarsa a kan nata, tare da sauke mata numfashin sa idanunsa a lumshe

Itama hakan ne, domin a yanda take ji tamkar tayi hauka sabida tsananin sha'awar da yake taso mata. Kawai sai ta buɗe idon tana kamo hannunsa tare da kaiwa saman ƙirjinta, tana ƙara shige masa cike da shagwaɓa tace, "Please ka ci gaba bazan iya jure wa ba."

Yanda take mishi ne gaba ɗaya ta gama rikice wa, dole ya sake biye mata suka canza salo. Shi kansa ya kasa riƙe kansa saboda wutar sha'awar da ke taso masa

Har aka kai airport basu san ma an kai ba. Domin time ɗin sun yi nisa. Sai da suka ji tsayuwar mota sannan suka ankare

"Sweetheart an kawo." Ya furta daƙyar yana manne da ita yana shinshina mata wuya zuwa fuska

Sai tayi kamar zata yi kuka tace, "ba na son in rabu da kai, don Allah ka biyo NI."

Murmushi yayi yace, "in bar aikin nawa kenan?"

Sai kawai ta saka mishi kuka

"Oh! Sorry mana sweetheart, ke kin cika rigima, shikenan zan zo, but sai kin tafi zamu yi magana, yanzu mu fita kar a ji mu shiru."

"To yi min kiss."

Shafa fuskarta yayi yana kai bakin sa ya lashe mata saman lips, tare da cewa, "hakan ya isa ko?"

"No. Ni ba haka ba." Sai ta shigar da bakin ta cikin nasa tayi masa zuƙa kamar zata cinye sa, a hankali ta raɗa masa, "duk ka saka Ni na jiƙe da yawa."

Dariya yayi yace, "me too sweetie, but ke kika ja mana."

"No. Ni dai ba Ni bane." Tayi maganar da shagwaɓa

Sai da suka ji an ƙwanƙwasa ƙofan sannan suka fita. Already dama driver ya fice tun sanda aka kawo. Sai su ma suka fita suka nufi wajen su Abba hannayen su saƙale da juna

Ba a jima ba jirgin su Haseena ya ɗaga zuwa Australia

Tun a nan SHAREEF yayi musu sallama ya shiga nashi motan. Shi kuma dreiver ya koma wancan motan ya tuƙa su suka tafi

A yanda SHAREEF yake jin wutar sha'awa daƙyar yake iya tuƙin ma, gaba ɗaya hankalinsa a tashe yake dauriya kawai yake yi. Kafin ya kai kansa gida sai cikin nasa ya murɗe, a daddafe ya isa ciki ya fito riƙe da gefen cikin sa

But sai dai fa abun yayi tsamari nan da nan ya riƙe cikinsa da yayi wani irin murɗawan da ya kasa tafiya ya zube a wurin, yana faɗin, "wayyo Allah." 

Masu aiki suka ankare dashi shiyasa suka rugo a guje wurin sa. Kafin zuwa lokacin SHAREEF ya gama galabaita sai kawai ya sume nan take. Hankalin su yayi matuƙar tashi, a guje ɗaya ya nufi ciki don sanar da su Dady.
[09/01, 12:26 pm] OumƊahirah نفيسة: 🌱🌱🌱🌱🌱

      *SHAREEF*
          _SexyBoy_
🌱🌱🌱🌱🌱


_Writer: Nafisat Isma'il Lawal_
_Wattpad: UmmuDahirah_

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝*



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

       *P.W.A✍️*



*DATA SHARE*

Call, message or whatsap  07065334256

*MTN*
500MB 150
1gb  280
2gb.  560 
3gb.   840
4gb.    1120
5gb      1400
6gb.     1700
Verlid for 30 days












__________
*BOOK1*
_______________*FREE PAGE5*
            Hankalin su Dady yayi matuƙar tashi da suka ga halin da SHAREEF yake ciki, dole aka ɗauke shi aka nufi dashi asibiti a mawuyacin halin da bai san inda kansa yake ba

Daga Momy har Sadiq hawaye suke yi domin sun kasa jure wa. In ban da Dady da yake karfin hali a cikin su but ko Hanif hawayen ne kawai bai zuba ba, amma tashin hankalin sa ya fi na kowa. Abun da bai taɓa faruwa da SHAREEF bane tunda yake basu taɓa ganin ya shiga irin wannan halin ba, asali ma shi ba Mutum bane mai yawan ciwo sosai ba, but yanzu kuma ji be yanda aka ɗauke shi bai san ma inda kansa yake ba

Sun kai shi asibiti kuma an amshe shi cikin gaggawa. Suna ta jiran sakamako tsawon lokaci kafin a gama duba sa babban Likita ya nemi ganin su. Dukkan su suka nufe shi zuwa cikin office ɗin sa har a yanzu Momy tana kwararar da hawaye, babu wanda a cikin su ba ya hasashen abun da za a ce ya same shi, shiyasa zuciyoyin su ke ta tsinke wa

But bayanin Likitan ya matuƙar hautsina musu gaba ɗaya tunanin su da sake saka su a cikin matsanancin tashin hankali. Sakamakon bayyana musu da yayi, "SHAREEF yana fama da ciwon ƙoda wanda a halin yanzu gaskiya sai du'a,i, domin abun yayi worse da yawa don ya kusa lalacewa gaba ɗaya, yakamata ace tun yaushe sun san da ciwon sun ɗauki mataki, amma a yanzu basu da abun da zasu yi mishi sai dai su taya shi da addu'a da kuma ɗaura shi a magani, wataƙil za a dace ba sai an sauya mishi wani ba, idan kuma abu ya ƙi dole sai an canza mishi tunda dukka sun kamu da ciwo, sai dai ɗaya ya fi lalacewa don haka ko dayan ne za a iya canza mishi." Duk da haka dai ya buƙaci, "za a ɗaura shi a magani kafin su ga abun da hali zai yi, in da yiwuwar a canza to." Daga baya ne yace ma su Hanif, "su fita zai yi magana da iyayen su." Bayan sun fita sai Likitan ya ƙara kallon su tare da jan numfashi yana cewa, "a gaskiya Alhaji Ahmed, ba wannan ciwon bane kaɗai ke damun ɗanka ba, a halin yanzu yana bukatar aure domin abun da muka gani a tare dashi kenan, don haka yakamata dai a duba halin da yake ciki a masa aure saboda gaskiya yana fama da ciwon ciki, kuma abun ya tsananta ne sakamakon ciwon ƙodan da ke jikinsa shiyasa har ya shiga wannan halin, shawarata sai a nema masa Mata sauran kuma a bar wa Allah insha Allahu komai zai wuce."

Dady ya jinjina kansa cikin tsananin damuwa tare da cewa, "to Doctor, na ji mai ka ce, insha Allahu zamu yi ƙoƙarin ganin yayi auren, amma yanzu ta ina zamu fara?"

"Babu damuwa ai, zamu ɗaura sa a magani mu ga abun da hali zai yi, yanzu na fara ba shi taimakon gaggawa kafin ya tashi, akwai magungunan da za a soma siya mishi, ina ga... Bari in rubuta su sai a nemo."
Daga nan Likitan ya rubuta maganin, yace ma Dady, "za a je a kawo ba sai ya je ba ma." Dama already shine Likitan su, shi yake kula da Dady tunda yana ɗan fama da ciwon sigar duk da bai kama shi can-can ba

Haka suka fito suka shiga ɗakin da aka kwantar da SHAREEF ɗin, tunda Likitan yace, "zasu iya duba sa."

Gaskiya sun ga tashin hankali a ranan, duk da dai baza su ce ga yanda jikin SHAREEF yake ba a wannan lokacin. Amma sun kasa kwantar da hankalin su, domin har zuwa ƙarfe sha ɗayan dare suna asibitin gaba ɗaya. Daga ƙarshe aka bar Hanif ya zauna dashi suka koma gida

Wayan SHAREEF ɗin yana hannun Hanif, shiyasa tunda ya ga Haseena tana ta faman kira sai kawai ya kashe wayan yana mayar da hankalin sa a kan ɗan uwansa, tare da tunanin halin da ya shiga a wannan lokacin, kamar ba yanzu suka rabu babu jimawa ba, Allah kenan, shi ne mai rayawa kuma shi ne mai kashe wa. Sai ya ja numfashi yana buga tagumi ya bi fuskar nasa mai kama da nashi sak yana kallo

Domin dukkansu suna tsananin kama da juna, idan ma suka zauna wuri ɗaya su ukun zaka yi tunanin ƴan uku ne saboda kamannin su, sai dai idan ka kula da kyau shine zaka iya bambance su. A ciki dai SHAREEF duk ya fi su haske kuma shine halayyar sa ya fita daban gaskiya. Sauran kuwa suna da kirki da sanin yakamata, basu da shiru-shiru da wulaƙanta mutane kamar shi, duk da Sadiq shi ya biyo idanun Momyn su ne shima yana da manyan ido masu kyau, shiyasa duk ya fi su kyau, ga shi da fara'a sosai irin na Mahaifinsa

Familyn suna son junan su matuƙa tunda a haka suka taso aka koya musu, suna da girmama juna gaskiya, kuma idan suna raha baza ka ce ɗaya ya girmi ɗaya ba dukkan su suke haɗuwa a yi hira kamar Abokan juna. Har SHAREEF da yake da halin miskilanci, wannan kuma a waje yake yin sa domin idan a gida ne baza ka taɓa cewa shi ne ba, ya ma fi zama Yaro a cikin su tunda kullum shine ake wa bari-bari da magana.

      


             Zuwa washe gari sai ga su sun dawo gaba ɗayan su da sassafe, a tunanin su ma zasu zo su ga ya farka ne, amma har yanzu yana nan a yanda yake

Likita yace musu, "babu komai zai iya farkawa a koyaushe insha Allahu."

Babu jimawa kuwa ya farka ɗin. Sai Sadiq ya je ya kira Likitan ya zo ya duba sa, kasancewar yana ɗan jin jiki bayan ya gama duba sa sai ya saka mishi ruwa, sannan yace, "a ba shi abinci ya ci sai ya sha magani."

Momy da kanta ta haɗa mishi tea ta ba shi ya sha. Sannan aka ba shi maganin ya sha tukun ya koma ya kwanta

Har hankalin su ya ɗan kwanta saboda ganin jikin da ɗan sauƙi. Duk da shi ba ya iya magana sabida matsa mishi cikin da ya ɗan yi, amma idanunsa a buɗe yana kallon su, har ya ɗan musu murmushi

Daga baya ne Momy ta kira gidan su ta shaida musu halin da ɗanta yake ciki, duk da Mahaifi kaɗai take dashi sai kishiyoyin Uwa, sannan sai ƴan uwanta da take dasu wadanda suka haɗa Uwa da kuma ƴan Uba. A taƙaice dai babban family ne dasu kuma suna zaune a nan Kano ne. Shi yasa tunda aka faɗa musu suke ta tururuwan zuwa gaishe shi

Zuwa yamma ma jikin nasa ya ɗan yi ƙwari sakamakon maganin da ya fara sha. Ganin haka ne ma Likitan yace, "da yiwuwar maganin zai amshe shi sosai, don haka ba sai an yi gaggawar mishi aiki ba, zai iya samun sauƙi a hakan ma, kawai ya riƙa shan magani insha Allahu komai zai zama normal."

Shi yasa su Dady suka ji sanyi sosai har hankalin su ya kwanta. Shi Dady ma bai sanar da ƴan uwansa ba tunda suna nesa ne, kuma hakan bai kamata ace ya ɗaga musu hankali ba.





🔆🔆🔆🔆🔆🔆🔆🔆


            Tafe suke su biyu suna hira a tsakanin su. Maryamu da ke sanye da dogayen takalma sai turguɗe wa take yi kasancewar har yanzu bata iya saka su ba, amma sai aukin son gayu da iyayi, bata da takalma sai kalan su, shiyasa da wuya ka ga flat shoes a ƙafafuwan ta in har ba a gida bane, ko a gidan ne ma sai ta ga dama

Bintu da ke afa gyaɗa, sai ta kalle ta a lokacin da ta sake turguɗe wa tana ta faman jan tsaki tana zagin takalmin, sai Bintun ta taɓe baki da cewa, "ke kam wahala bai ishe ki ba Alkur'an, ai sai ki yi tayi, kuma wlh ki ɗago ƙafa na gaji fitsari nake ji."

Maryamu da ke ƙara tafiya a hankali don kar ta ƙara turguɗe wa, sai tace, "don Allah mu je gidan Yaya Faisal ki yi fitsarin a can, yau nayi alƙawarin sai na sha mangwaron Haliru Taurin can, sai dai duk abun da zai yi yayi."

"Ƙutt... Wlh babu ruwana ga hanya nan, Ni kinga tafiyana zan yi."

Jawo mata hijabi Maryamu tayi tana marairaice wa tare da faɗin, "haba mana Bintu, wlh bazan jima ba, kuma bazan bari ya ganmu ba ta gidan Yaya Faisal zan tsinka, idan kika koma gida ke kaɗai kin san halin Baba kuma kin san ya dawo, mu je ki raka Ni Ko a waje ne ki jira Ni Please help i." Ta ƙare maganar da shegen turancin ta da bata rabo dashi tunda bata iya ba, amma ta dage sai tayi kamar wata mangofan

Babu yanda Bintu ta iya dole ta yarda zata bi ta, domin ta san Maryamu akwai shegen naci baza ta ƙyale ta ba, sai tayi ƙwafa tace, "Allah yasa ma Yaya Faisal ɗin yana nan inga ƙaryan tsiya."

"Bakin ki ya bi ki, ai Insha Allahu ma bai dawo ba, kin san Allah jiya da mafarkin mangwaron nan na kwana kamar wata mai ciki, dama na sha alwashin in dai muka biyo hanyar nan sai na tsinko."

Suna ƙarisa wa gidan suka buga sallama suka shige

Matar Yayan su Asabe ta amsa musu tana cewa, "ah ah Ƙannina, daga ina haka?"

"Daga school Aunty, me and she just came back and followed here."

"Manyan tura wa, Ni fa ba gane miki nake yi ba, da kin min Hausa da na fi fahimtar ki."

Dariya Maryamu tayi tace, "gwara Yaya Faisal ya mayar da ke makaranta tun kafin ki ba shi kunya wata rana Alkur'anin Allah, amma ace kamar shi ɗan gaye yana zaune da ke, to sanda ya zo da Abokansa na birni ya zai yi?"

Tsaki Asabe ta ja tare da cewa, "ai kuwa kin san ba daga nan yake ba, domin kin san na fi ƙarfin raini tunda shima Faisal ɗin Kyawu na ya ruɗe shi ya aure Ni, meyasa bai je ya auro mai ilmin bokon ba? Ƙaryan banza ƙaryan hofi."

Bintu da fitowar ta daga bayi, tana ajiye buta tace, "kin ji Aunty ki ƙyale ta, in kika biye ta Maryamu Allah kin dinga jin haushi kenan, ki barta kawai."

Ita kuwa Maryamu sai dariya take yi domin har ta yaye hijabin ta tana nannaɗe skirt ɗin ta zuwa sama, sai tace, "ina wai Yaran nan ne ban ji motsin su ba?"

"Su ma basu dawo daga makaranta ba amma yanzu za ki gansu."

"Wai don Allah ki yi sauri mana, wlh idan Yaya ya dawo ya ganmu babu ruwana."

"Me zata yi ne?" Asabe ta tambaya tana kallon Maryamun

Kaɗa kai Bintu tayi tare da cewa, "wai mangwaro zata tsinko."

"Huhh! Ki rufa wa kanki asiri, wlh Haliru tauri na nan a gida, idan kuma kika ce za ki tsinko ke dashi ne domin kin san halin shi, yanzu na gama jin shi da yaran maƙota."

"Sai fa na tsinko, bari ma ki gani, yo Ni da zan tsinka ta gidan ki ina zai ganni?" Sai ta nufi katangan da ya raba gidan dana Haliru tauri, ta kama garu daƙyar tana ƙoƙarin hawa. Sai ta rage murya tana cewa, "Bintu zo ki cinciɗo Ni."

"Sai dai kar ki hau, bazan zo ba."

"Wlh kar ki saka rai kuwa."

Jin hakan yasa Bintu ta je wurin ta taimaka mata, tunda ta san idan ma bata yi ba baza ta bata ba, sai mita take yi sabida nauyin Maryamun, komawa gefe tayi bayan ta gama cinciɗa ta, daga ita har Asabe suka zura mata ido suna kallon ikon Allah

Ita kuwa kamar wata ƙadangaruwa da jan gindi take tafiya a saman katangan, sai da ta isa dai-dai wajen bishiyan sai ta kama ta ɗare ta shige can saman bishiyan ko ganin ta ba a yi

Dai-dai nan Haliru ya fito daga ɗaki yana kakkaɓe takalma, sai ya zauna yana gyara wa yana ɗaure wa da igiya, tare da raira waƙar sa na Mamman shata, batare da ya kula da Maryamu da ke saman kansa tayi ɗare-ɗare ba

Sai da ta cika bujen ta da mangwaron, kuma tayi toking ta tusa su a cikin rigan ta ta cika fam. Sannan ta soma ƙoƙarin sauka, har ta kusa kama bangon, ɗaya ya faɗo ya ƙwandalo wa Haliru a kai. Ya saka salati yana sallallami tare da ɗaga kansa suka yi arba da Maryamu

Ai tuni ya miƙe tsaye yana cewa, "wacce matsiyaciyar ce wannan? Ke.. ke.. ke."

Amma inaa. Tuni Maryamu ta dira ƙasa, kan kace me ta yayimi hijabin ta sun fice a guje ita da Bintu da jikinta sai rawa yake yi, akwai shegen tsoro ne da ita. Suna fita suka hango sa shima ya fito daga gidan riƙe da icce, ai sai suka ɗibi gudu ana artabu daga su har shi ɗin, ya bi bayan su yana ƙunduma musu zagi

Yayinda Maryamu kuwa ta riƙe riganta ƙam don kar mangwaron su zubo, duk da wasu duk sun yi ƙasa amma haka ta ƙwaƙume su ko takalma babu a ƙafanta; tunda bata tsaya ta ɗauka ba suka fece

Haliru tauri na take musu baya a gujen shima da icce a hannu kamar mahaukaci.
[11/01, 9:05 am] OumƊahirah نفيسة: 🌱🌱🌱🌱🌱

            *SHAREEF*
                _SexyBoy_
🌱🌱🌱🌱🌱


_Writer: Nafisat Isma'il Lawal_
_Wattpad: UmmuDahirah_

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝*



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

       *P.W.A✍️*





*DATA SHARE*

Call, message or whatsap  07065334256

*MTN*
500MB 150
1gb  280
2gb.  560 
3gb.   840
4gb.    1120
5gb      1400
6gb.     1700
Verlid for 30 days










__________
*BOOK1*
_______________*FREE PAGE6*
                Su Umma Jummai suna tsakar gidan suna aiki, sai suka ji didima su Maryamu sun shigo a sukwane kowacce tayi wurin ɓuya

Ɗakin Umma Jumman suka shige gaba ɗayan su, har cikin uwar ɗakar ta kowacce ta shige cikin shirgin kaya suna mayar da numfashi

"Ta.. da alamu sun nemo rigima." Cewar Shatima da yake dariya ƙasa-ƙasa

Kafin ma su yi magana, sai ga sallaman Haliru tauri a waje kamar zai tsaga gidan

"Wa'alaikumus Salam. Shatima je ka duba wane ne?" In ji Inna da ke yafa mayafi a kanta tana shirin fita itama

Da gudu Shatima ya fita, sai ga shi ya dawo yana cewa, "wlh Haliru tauri ne, ya ce a fito mishi da shegun Yaran nan."

Umma Jummai tace, "ai wlh tunda na ga sun shigo da wannan gudun sun nemi wurin ɓuya, to tabbas sun nemo rigima ne, dan kutmar uban ku baza ku fito min a ɗaki ba? Ku fito nace?"

"Ki ƙyale su, bari ki ga in yi maganin su, baza ku jawo mana rigima muna zaune ƙalau ba wlh, wannan mutumin da bai da imani yanzu ma sai ki ga ya shigo gidan, gwara da Allah yasa ku ka yi Baban naku ya dawo, kai Shatima maza ka kira shi a bakin masallaci yanzu ya fita."

"To Inna."

Ita kuma ta wuce kitchen ta ɗauko icce ta fito. Ta nufi ɗakin Umman tana cewa, "wlh idan na shigo baku fito ba kowacce sai ta ji a jikinta tunda ku baku da mutunci."

Tsit suka yi dukkan su suna sake lafewa a maɓoyan su. Maryamu na bayan kabot ɗin Umma Jummai ta maƙale cikin kayan wanki da aka jibge a wurin. While Bintu kuma tana ƙarƙashin gado daƙyar ma ta shiga saboda kaya da aka tula a ƙasa, ƙafafunta a waje. Shi yasa Inna tana shigo wa ta soma hango ƙafafun Bintu, ai sai ta nufi wurin ta rafka mata iccen tana cewa, "fito dan uban ki."

Kuka Bintu ta saka jikinta na rawa, saboda ba kaɗan ba ta ji shigan iccen a ƙafafun ta. Sai ta fara ihu tana cewa, "don Allah Inna kar ki ƙara min wlh zan fito."

"To fito tunda ba na wasa da ke." Tayi maganar fuskarta babu wasa. "Ina ita ɗayan dan uban ta?" Sai ta koma dube-duben ɗakin. Kai tsaye wurin shirgin kayan ta nufa domin ta san baza ta wuce wajen ba tunda ba wani sauran wurin ɓuya a ɗakin. Ilai kuwa ta hange ta tana zazzare idanu

Tun kafin ma ta ɗaga iccen, Maryamu ta fito tana ihun faɗin, "don Allah Inna ki bari, gani nan na fito."

Hannu tasa ta mangare mata kai tana cewa, "tunda ku baku isa a gaya muku magana ba ko? To mu je wajen tun kafin in zane muku jiki yanzu." Ta tasa ƙeyan su suka fito

Tuni Maryamu ta zubar da mangwaron a cikin ɗakin Umman suka fito jiki na rawa

Lokacin Bashir ya shigo gidan yana cewa, "wa ya taɓo Haliru tauri ne?"

"Yauwa. taho ka tasa min ƙeyan su mu je can wajen a yi a gaban shi, tunda sun tono shi can ya ƙare musu."

Sai dariya yake yi yana cewa, "yau akwai kallo kenan, wlh zaku ci uban ku ga Baba da su Yaya Naziru nan a waje."

Bilhaƙƙi da gaske kuka Bintu take yi saboda duk ta gama ruɗe wa, sai rantse-rantse take yi a kan babu ruwan ta

Ita kuma Maryamu ihun kawai take yi amma babu hawaye, itama sai tsalle-tsalle take yi tana cewa, "don Allah Inna ki yi hakuri, wlh bamu yi mishi komai ba. Umma ki saka baki wlh bamu yi mishi komai ba."

"Baku yi mishi komai bane zai biyo ku a gujen nan? Ku dai ba kwa jin magana ko?" In ji Umman tana miƙe wa tsaye daga gaban kwashe tuwon da take yi

Inna kuma tace, "sai sun fita wlh ko tayi musu dukan tsiya."

Bashir sai tara-tara yake musu yana ƙara ruɗa musu ciki da cewa, "yau zaku ci uban ku Alkur'an, ba ku marasu jin magana ba? Yau kashin ku ya bushe." Shi ya riƙe su gam saboda ƙoƙarin guduwa da Maryamu take yi

Ana haka su Baba suka shigo cikin gidan

Dayake Yaya Ashiru yana da saurin fushi, shi ya nufe su da sauri ya amshi iccen hannun Inna yana cewa, "ku dan uban ku uban wa ya kai ku gidan mahaukacin can da har ku ka haye mishi gida?"

"Wlh wlh babu ruwana, Maryamu ce ban dani." In ji Bintu tana kuka sosai

Sai kawai ya haɗa su dukka ya soma rafka musu iccen yana cewa, "wato ku ba kwa jin magana ko? Duk yanda aka yi daku sai kun nemo mana magana? To gobe ku sake zuwa in kun samu ƙafan yawon yau."

Baba ne yayi saurin dakatar da shi yace, "ya ƙyale su." Ganin yanda suka cika gidan da kuka suna ihu. Tsawa ya daka musu yace, "su yi shiru."

Tsit suka yi suna zaune a ƙasa kowacce sai rawan jiki take yi

"Ban san meyasa ba kwa jin magana ba Yaran nan? Amma kuna Mata meye ya kaiku hawa bishiya?"

"Wlh Baba bani bane, Maryamu ce tace in raka ta, amma Ni ban hau ba."

Baba yace, "dama na san sai ita. To gobe sai ku sake kun ji ko tunda dukan kuke so, har yanzu baku san kun girma ba, tunda yanzu mun ba shi haƙuri gobe sai ku ƙara koma wa. Maza ku tashi ku yi alwala ku yi sallah. Kar in ƙara jin kuma kun ƙara wannan sakarcin."

"Ai Baba da ka bari na ci uban su tunda sun ga ana ƙyale su ne, Yara mara su jin magana ba a isa a hana su ba? Daga wannan fitinan sai wannan." In ji Yaya Ashiru ransa a ɓace kamar zai sake kai musu wani dukan

Inna tace, "ai laifin duk na Maryamu ne, ita ce mai kunnen ƙashi, gani take yi ta fi kowa tashin balaga, rashin kunya fal cikin ta."

Yaya Naziru yace, "wlh kuwa Inna, domin yanzu muka haɗu da Jamilu ɗan gidan mai gari yake faɗa min wulaƙancin da tayi mishi ɗazu, wai kawai don ya zo wurin ta zance shine har da kwaɗa mishi Mari, ta ci mishi mutunci har da saka mahaifin shi a ciki, ba ma shi kaɗai ba, majority Mazan ƙauyen nan suna kawo min ƙaran ta."

"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un..! Mari kuma? Abun naki har ya kai ki mari namiji Maryamu?" In ji Inna cikin al'ajabin maganar har tana dafe ƙirji

Baba shima ransa a ɓace yace, "wato tarbiyyar da muka yi miki kenan Maryamu? Kanki ɗaya kuwa?"

"Wlh Baba ban mare shi ba, ƙarya yake min." Tayi maganar tana yarfe hannu cikin gunjin kuka

"Ni nake miki ƙaryan ko shi?" In ji Yaya Naziru yana amsar iccen hannun Yaya Ashiru zai maka mata

Sai tayi saurin tashi ta je ta ɓoye a bayan Umma Jummai tana kuka wi-wi tana rantse-rantse, "Alkur'anin Allah ƙarya yake min, wlh Yaya karya ya faɗa maka..."

Tsawa ya daka mata yace, "za ki yi mana shiru ko sai na canza miki kamanni a nan? Shegiyar yarinya mara jin magana, dama tara ki nake yi ba na sanar wa Baba, amma yanzu abun naki ya wuce hankali kullum maganar ta ake yi a garin nan."

Baba yace, "ai kuwa zan ɗauki mataki a kanki Maryamu tunda ba ki da kunya, ku ƙyale su mu wuce mu je masallaci tunda an kira sallan."

Haka suka fita a gidan har su Shatima

"Ai kinga gobe ma ki ƙara, dalla sake Ni tunda ana faɗa muku gaskiya amma kuna ganin mu Abokan wasan ku, gwara da suka ci uban ku yanzu."

"Ai laifin duk na wannan yarinyar ne, kuma wlh muddin kika ce za ki ci gaba da wannan ɗabi'ar naki za ki sha wahala, Allah na gode maka ma tunda akwai masu maganin ku, baza ku fi ƙarfin mu ba, ke kuma baza ki tashi ba kin wani langaɓe a wurin?" Ta ƙare maganar tana kallon Bintu da ke zaune dirshan sai ɓarzan kuka take yi

Miƙe wa tayi tana share hawayenta ta nufi hanyar ɗakin su

Itama Maryamu tuni ta wuce ɗakin tana zumɓura baki tare da ƙunƙunai tana zagin Haliru tauri, sai jan Allah ya isa take yi

Babu wanda ya kula ta. Su ma alwalan suka yi suka shige ɗaki yin Sallan

Bintu itama ta fito tayi nata alwalan ta shiga nasu ɗakin. Kallon Maryamu da ke zaune a bakin katifar ta tana duba jikinta inda take jin kamar an karya ta tsaban yanda dukan ya shige ta. "Wlh Allah ya isa na, muguwa azzaluma duk ke kika ja min, tun farko nace bazan je ba amma kika saka Ni na bi ki, ga shi nan ban ci nanin ba nanin ta ci Ni."

Sai kawai Maryamun ta fashe da dariya, duk da a yanzu ɗin hawaye ne kwance a saman kuncin ta, waɗanda basu fito ba sai a yanzu a karan banza, dariya Bintun ta bata shiyasa ta fashe mata da dariya tana cewa, "ai ba Ni za ki yi wa Allah ya isan ba."

"To uwar ki zan yi ma wa?" Tafaɗa a fusace tana hararanta

"Sai dai Uwar ki, son banzan ki ne yasa kika bi Ni, kuma wlh bazan ba ki ko alili ba."

"Shegiya banziya, kar Allah yasa ki bani, kuma wlh bazan taɓa yafe miki ba."

Don ta bata haushi shiyasa ta dinga mata dariya tana cewa, "ai bani za ki yi wa Allah ya isan ba, Yaya Ashiru za ki yi ma wa tunda shi ya dake ki, shegiya da ƙoton kai kamar na Biri."

"Uban ki ne da Ƙaton kan..." 

"Wai baza ku dena wannan iskancin naku ku zo ku yi sallah ba? Bari Baban naku ya shigo to." Inji Umma Jummai da ta leƙo ɗakin nasu tana furta hakan

Shi yasa Bintu ta tayar da Sallan bata ce komai ba

"Au ashe ke ce ma ba ki fito kin yi alwalan ba? To zaman me kike yi?"

Baki ta tura tana kwanciya a saman katifar tace, "ba na sallan to."

"Yayi miki kyau ai." Ta furta tayi gaba

Ita kuma Maryamu sai jan tsaki take yi tana ci gaba da ƙunƙunai, tare da alwashin, "wlh sai ta rama, tunda Haliru tauri ya saka aka bige ta sai ta ƙara koma wa, matsiyaci kawai, fatararre, in ban da tsiya ma a kan mangwaron banza sai ya nuna shi matsiyaci ne."
Ta ƙi yin shiru da bakin ta sai zagin shi take yi tana tsine mishi daga shi har mangwaron nasa

Bashir ne ya shigo dakin yana dariya yace, "ah ah, ƴan mata an sha duka kenan? Ya jikin to? Ashe kin san mangwaron na matsiyaci ne kika je tsinkar mishi? Da kin bar mishi kayan shi mana."

Wata uwar harara ta jefa mishi tana miƙe wa a fusace tace, "wlh ka bari, idan ba haka ba Allah zan haɗa ka da Baba."

Zai yi magana, sai ya jiyo muryan Inna tana cewa, "wai Bashir uban me ya kaika ɗakin nan? Neman magana ko?"

Sai da ya taho ya ranƙwashi kan Maryamun, sannan ya fita a guje yana cewa, "wlh a'a Inna, kawai na je duba jikin su ne."

"To ka mayar da hankali tunda ka fi son su raina ka. Ka zo ka ɗauki abincin ka. Ina shi Hallirun ne?"

"Wlh bai dawo ba Inna, ina tunanin yana kan hanya yau yayi dare." Ya bata amsa yana nufan hanyar ɗakin Umma Jummai da aka jera abincin kowa an zuba mishi nashi

Umma Jummai da ta fito itama daga ɗakin nata, ta ɗauko miyan tuwon, sai ta ajiye tana cewa, "nima abun da nake ta zicci-ziccin tambayar ka kenan, na ga yau ka dawo ban dashi?"

"Eh Umma. Yana da sauran gyara ne a garejin shiyasa ya zauna, yace gobe bazai leƙa ba gwara ya ƙarisa yau."

"Tom shikenan. Ɗauki naka ga yi nan ka zuba miyan."

Burum Maryamu ta fito tana cewa, "ina nawa nima?"

Harara ta samu a wurin Inna

Shi kuwa Bashir sai yace, "kin dafa ne kin ajiye?"

"Kai dai ba ka jin magana wlh, ka cika neman tsiwa." In ji Umma

Inna kuma sai tace, "ki bar shi kawai, dama raini yake so."

Dariya shi kuwa yake yi tunda ya saba, akwai shi da neman tsokana, bare dama saƙo da saƙo suke da Maryamun, kullum sai an ji su da ita, su yi ta cacan baki tunda baza ta iya shiru ba. Shi kuma ya samu damar ranƙwashin ta kenan yana faɗin, "ai ta raina shi ne tunda yana faɗa tana faɗa." Haka suka saba koyaushe.






            *********

          Bayan an yi sallan isha'i. Duk sun zauna suna hira a tsakar gidan, har da su Baba tunda haka suke yi

Maryamu da Bintu har sun manta da abun da ya faru tunda dama sabon su ne haka, lokaci ɗaya zasu yi faɗa kuma su shirya, sun matsa gefe sai hira suke yi suna ƙus-ƙus

Baba yace, "ku taso ku dawo nan mu yi magana."

Hakan ne yasa suka taso suka zauna a kan tabarman wanda su Baba suke kai

Ya Kalle su yace, "ke Maryamu da ke zan fara, kina da wanda kike so ne?"

"Baba..." Ta furta tana ɗan zare ido

"Ina jinki faɗa min mana? Domin aure zan muku tunda na gaji da shirun ku, ku ba karatu ba sannan ba aure ba, don haka lokaci yayi da zaku fito da Mazajen da kuke so a yi auren ku a huta, inyaso ma sai a haɗa dana su Naziru kawai, Allah zai hore mana domin hakan zai fi sauki."

Umma Jummai tace, "gaskiya ne Malam, hakan ma yayi wlh, nima abun da nayi tunani kenan, tunda zaman kawai suke yi, duk sa'annin su sun yi aure ban da su, karatun nan dai sun yi iya yin su, auren shi ya kamace su."

Tura baki Maryamu tayi tace, "wlh Baba Ni ba na son aure yanzu, karatu nake so, nima ina son in yi karatu mai zurfi."

"Idan ma za a bar wani yayi karatu ai baza a bar ki ba, a wannan halin naki." In ji Yaya Ashiru yana ban ka mata harara

Sai tace, "to Yaya Ashiru me nayi ne Ni? Wlh ba abun da nayi, kuma ban da saurayin ma ai."

"To ai Ni ina dashi tunda ke ba ki dashi." In ji Baba yana kallonta, tare da cewa, "na faɗa miki babu wani karatu da za ki yi, gwara tun wuri ki nemo saurayi tun kafin in nemo miki. Ke ma haka Fatima gaba ɗayan ku ku fito da Mazajen Aure, in Allah ya yarda Allah ya hore za a haɗa auren ku a huta."

Inna da Umma suka haɗa baki wajen furta, "Allah ya tabbatar da alkhairi."

Ita kuwa Maryamu sai faman zumɓura baki take yi kamar yanda ta saba tana ƙunƙunai, amma ta kasa furta abun da ke ranta

Bashir yace, "ya dai Meramu? Akwai magana a bakin ki fa, ko auren ne ba kya so?"

"Ai ko ba ta so sai an yi shi, don nima na gaji wlh, wata rana sai ta jawo mana abun da ya fi ƙarfin mu in dai wannan yarinyar ce, auren za a yi mata tunda haka ta zaɓa." Innar su tafaɗa hakan cike da jin haushin halin Maryamun da ta fita Zakka a gidan nasu

Itama sai ta tashi tana wuce wa ɗaki tare da cewa, "wlh Ni dai har ga Allah ba na son aure, babu wanda zai min aure sai nayi karatu mai zurfi na zama Shugabar ƙasar ma gaba ɗaya."

Sai maganar nata ma ya basu dariya

Baba yace, "ina ruwan mashirmaciya, kya yi a gidan Mijinki amma ba a nan ba Meramu, nima in ɗana irin na Bashir."

Sai dariya suke yi. Haka suka zauna cikin raha suna ta hira. Daga ƙarshe Samarin ne suka soma zame wa suka shiga ɗaki

Itama Bintu tuni ta wuce ɗakin su, lokacin har Maryamu tayi barci, tunda kasa ce, ba ta tsawon hira sai dai ka ji ta tana jan rago. Rufe musu ƙofan tayi itama ta haye nata katifar ta kwanta.


        Washe gari bayan su Baba sun tafi wurin aiki. Maryamu ta zauna a tsakar gidan tana ta ma su Inna rashin kunyar, "Alkur'an ba a isa a yi mata aure ba, sai dai ta gudu kowa ma ya rasa."

Inna tace, "to in kin fasa dan ubanki, ko akwai wanda zai neme ki ne? Ki tafi mana yanzu tunda ba a ɗaure miki ƙafa ba."

"Na rantse Inna baza a yi min aure ba, kuma kuna ganin wasa ne sai na aikata abun da nace." Ta miƙe tana ɓata rai tare da cewa, "haka kawai, wlh bazan yarda ba, babu wanda zan kawo bare ma a yi min auren."

Umma Jummai tace, "to wai mu ina ruwan mu da kika zo kika tasa mu gaba kina mana rashin kunya iyee?"

"Ki bar ta don Allah, na kusa karyata a gidan nan, kuma billahil lazi in ba ki yi wasa ba sai na saɓa miki kar ki bari mu saka ƙafan wando ɗaya da ke."

Shiru tayi bata ce komai ba sabida ganin yanda Innar take kallonta, ta san tsab zata ci uban ta. Sai ta wuce ɗakin su bata ma bi ta kan Bintu da ke zaune tana tsintan shinkafa ba, Hijabin ta ta ɗauka zata fice

Amma sai Inna tace, "kar ki fita gidan nan Maryam, wlh ƙafan ki ta fita gidan nan za ki ji a jikin ki."

"To Inna Ni fa ba wani wuri zan je ba, gidan Aunty Ummita zan je, dama tace in zo in taya ta gyaran ɗakin ta."

"Baza ki je ba. Tunda yawon kike so ki zo ki wuce ki ɗauki key ki zauna min a shago."

Babu yanda ta iya haka ta wuce ta ɗauko key ɗin. Tana fita kuwa ta zarce gidan Aunty Ummitan batare da ta shiga shagon ba

Tana cikin tafiya tana rera waƙa. Sai turguɗe wa take yi amma hakan bai sa ta cire takalmin ba. Har ta kusa isa gidan Aunty Ummitan sai ganin Jamilu tayi a gaban ta yana kiran ta. Ja tayi ta tsaya tana cewa, "lafiya? Wannan wanne irin halin karnukanci ne da zaka zo kana shan min gaba? Kana da mind?"
 

"Halin karnukancin na zo in nuna miki yanzu kuwa, tunda ke ba ki da mutunci yanzu zan nuna miki kin taɓa wanda ya fi ƙarfin ki, zan yi maganin rashin kunyar ki yanzu".
[12/01, 10:08 am] OumƊahirah نفيسة: 🌱🌱🌱🌱🌱

      *SHAREEF*
          _SexyBoy_
🌱🌱🌱🌱🌱


_Writer: Nafisat Isma'il Lawal_
_Wattpad: UmmuDahirah_

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝*



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

       *P.W.A✍️*





*DATA SHARE*

Call, message or whatsap  07065334256

*MTN*
500MB 150
1gb  280
2gb.  560 
3gb.   840
4gb.    1120
5gb      1400
6gb.     1700
Verlid for 30 days










__________
*BOOK1*
_______________*FREE PAGE7*
          "Hehehe! Uban kutru yayi kaɗan, wlh mai magani na a ƙauyen nan sai ya shirya, Jamilu na fi ƙarfin Ubanka ma bare kai banzan bazara wawa jaki." Tafaɗa cikin tsiwa da rashin kunyar ta

Ai kuwa hakan ne ya harzuƙa Jamilu, ya watsa mata mari tare da ƙoƙarin fincike mata gyalen yana cewa, "daga yau baza ki sake marmarin zagin wani ƙauyen nan ba, abun da kike taƙama dashi da tashen rashin kunyar ki yau zan raba ki dashi."

Sosai Maryamu ta tsandara ihu sabida yanda marin ya shige ta. Lokaci ɗaya suka soma kokawa dashi saboda ganin yanda yake ƙoƙarin fincike mata gyale. Ihu ta dinga zuba wa ta zame ƙasa a wurin tana zagin shi

Ihun nata ne ya fito da Aunty Ummita da Mijinta, tunda babu nisa da wurin, suna jin ihun da ya karaɗe gidan su, da sauri suka fito suka ga abun da ke faruwa. Sai Mijin Aunty Ummitan ya nufe shi da sauri yana kiran sunan sa

Hakan ne yasa Jamilu ya dakata daga abun da yake shirin yi, sai huci yake yi yana haki

"Kai kana da hankali me ya faru da ka kama yarinyar mutane kana jibga haka?"


Tuni Aunty Ummita ta zo ta kama Maryamun da ke ta kuka har da su majinu, cikin tashin hankali take duba ta saboda ganin yanda gyalen ta yayi gefe har ya yaga mata gefen riga

Kafin ka ce me mutane sun taru a Wurin. Saboda yanda Maryamun ta ƙi yin shiru sai ƙara volume ɗin kukan ta take yi, tana yi tana zagin shi tare da bayyana musu cewan, "fyaɗe zai yi mata."

Shi kuma Jamilu yace, "ƙarya ne, rashin kunya tayi masa, har zagin Mahaifinsa take yi, shi kuma bazai iya jure wa ba ya duke ta."

A fusace Ummita tace, "don ta zage ka shine zaka yaga mata riga har ka cire mata gyale? Me hakan ke nufi iyee?"

Ganin abun na son zama rigima babba, shiyasa Lado Mijin Ummita yace, "a wuce kawai wurin mai gari sai a yi sulhu a can."

Tunda sosai Maryamu take kuka tana cewa, "wlh baza ta yarda ba sai an bi mata haƙƙin ta." Sai birgima take yi a wurin

Daƙyar Ummita ta rarrashe ta ta ɗaga ta aka wuce wajen mai gari

Mutanen anguwa sun taru har labari ya je wa su Inna gida

Inna tace, "baza ta je ba, tsuntsun da ya ja ruwa shi ruwa kan duka, tunda ba ta jin magana ta je tayi duk abun da zata yi."

Sai Umma Jummai ne suka fito da su Halliru zuwa ƙofar gidan mai garin

Lokacin har an kira Baba a bakin kasuwa, tunda a can yake kasuwancin sa yana da shagon provision, yanzu ya dena zuwa birni ya buɗe nasa a cikin kauyen su, dama tun farko riƙon shago yake yi a kasuwar tudun Wada, yanzu alhamdulillah Allah ya buɗa mishi ya buɗe katafaren shago, babu abun da ba ya siyar wa a ciki

An taru sosai, aka ce Maryamu ta faɗa abin da ya haɗa su

Tana kuka ta sanar musu cewan, "kawai tana tafiya ya sha gaban ta a kan wai tunda ta ƙi amsar soyayyarsa, sai yayi mata fyaɗe kowa ya guje ta ƙauyen, wai sai yayi maganin rashin kunyanta." Sai ta ƙare maganar tana ɓarke wa da sabon kuka har yanzu babu ko ɗigon hawaye a idanunta

Salati mutanen wurin suka ɗauka har da mai Garin

Jamilu kuma tuni ya soma rantse-rantsen ƙarya ne ba haka bane

Ummita tace, "wlh ranka ya daɗe! Gaskiya ce, saboda tare da Mijina muka fito muka ga yana kokawa da ita, har ta faɗi ƙasa amma bai ƙyale ta ba, ga rigan ta nan ma sheda inda ya yaga mata." Tafaɗa tana buɗe wurin da ya yage

"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un...! Yanzu abun kunyar da ka ɗauko mana kenan Jamilu? Wannan wanne irin baɗala ne? Abun da muke yaƙi dashi a ƙauyen shine a gidana za a samu mai yi?"

"Na rantse da Allah Baba ban aikata ba, wlh ban yi mata komai ba." Jamilun ya furta yana hawaye

"Yi min shiru mutumin banza kawai, ai dole doka ta hau kanka, kuma daga yau babu kai babu yarinyar nan, duk sanda aka ce ko magana ce ta haɗa ku zaka ga yanda zan yi maka, hukunci kuma dole zaka amshi sakamakon ka tunda baka fi kowa zane ba." Sai ya dubi Maryamun yace, "ki yi shiru kinji? Insha Allahu zamu ɗauki mataki a kansa hakan bazai sake faruwa ba. Malam Haruna muna roƙon afuwar ka a kan abun da ɗana ya yi wa ƴarka, a yi haƙuri don Allah."

"Babu komai ranka ya daɗe! Dama Yara ka haife su ne baka haifi halin su ba, idan da laifin Jamilu har da laifin Maryamun." Sai ya ɗan ja numfashi tare da cewa, "amma Allah ya ƙara tsare gaba."

"Amin ya Allah." Dattawan wurin suka amsa baki ɗaya

Kana aka sallami kowa aka watse. Inda Mai gari ya sanya a shiga da Jamilu ɗakin horo a hukunta shi

Ummita tuni ta kama hannun Maryamu; sun wuce da su Umma Jummai zuwa gidan su. Baba na biye da su a baya yana kaɗa kansa

Da shigan su, tsumagiya Baban ya ɗauka ya soma dukan Maryamun

Nan da nan ta kure gidan da ihu da kururuwa tana neman agaji

Ransa a ɓace yace, "wlh Ni baza ki ja min abun kunya a garin nan ba, uban me ya kaiki inda yake da wani abun zai haɗa ku? Maryamu ke ba kya jin magana ko? Kina son ki fi ƙarfin mu tunda kinga ina ƙyale ki ba na ɗaukar mataki a kanki." Haka yake dukan ta ya riƙe ta gam ya ƙi sakin ta, sai da ta bugu lilis sannan ya ƙyale ta

Su Umma suna tsaye cirko-cirko babu wanda yayi ƙoƙarin ƙwatan ta

Shi kuma yana gama wa ya fita gidan ransa a ɓace

Inna itama sandan ta ɗauka ta nufo ta tana cewa, "shegiyar yarinya mara jin magana, gwara da yayi miki dukan tunda ke ba a isa a saka ki a hana ki ba, kin fi so ki gagare mu a gidan, ba a taɓa yin yarinya kamar ki mara jin magana ba, ko ke kaɗai ce yarinya a gidan da kullum sai kin ɗauko mana magana iyee?" Tafaɗa tana maƙure ta sosai tana jan mata gashi

Duk da kuka da ihun da Maryamu take yi but ta ƙi sakin ta

Su Ummita suka zo ƙwatan ta amma Inna ta ƙi sakin ta, sabida ta kaita maƙura, fushi sosai Inna tayi sai jibgar ta take yi kamar an aiko mata da jaka. Daƙyar su Umma suka ƙwace ta

Da gudu Maryamun ta miƙe ta shige ɗakin su ta saka saƙata tana ta gunjin kuka

"Ai wlh sai na karya ki a gidan nan tunda kin ce abun da kika tsirfo wa kanki kenan, har in hana ki zuwa inda kika yi ninya amma ki nuna min ban isa ba, zamu zuba kuwa." Innar take faɗa cikin ɓacin rai saboda ba kaɗan ba ranta yakai ƙololuwa da ɓaci. Musamman da ta ji abun da ya faru, "yanzu da ace ƙaddara ta afka yayi miki wani abun ya zamu yi? Shikenan kin gama zubar mana da mutunci bamu da sauran ƙima a garin."

Daga Ummita har Umma Jummai haƙuri suke ba wa Inna, saboda basu taɓa ganin ta ɗauki zafi a kan Maryamun ba duk da rashin ji irin nata, kullum da akwai abun da take janyo musu, yau kuwa da alamun ta kaita maƙura tunda ta shaƙa sosai

Ƙarshe dai Ummita tafiya tayi ta bar Innar a haka tana ta masifa, sun kasa bata haƙuri tunda a tunzure take

Ita kuwa Maryamu tana ɗaki tana ta kuka tunda ba kaɗan ba ta bugu a hannun su, daga ƙarshe ma barci ne ya kwashe ta a wurin kasancewar ta mara wahalar Barci, sai lokacin ne ma ɗis-ɗis na hawaye yake zuban mata a kunci, duk wannan kukan da ta sha basu fita ba sai yanzu a karan banza da hofi.




🔆🔆🔆🔆🔆🔆🔆🔆

              Jikin SHAREEF da sauƙi sosai kamar ba shi ba, har ma ana shirin sallaman sa, Likitan ne yace, "ya ɗan zauna na kwana biyu su ga yanayin jikin." To Alhamdulillah musamman ma yau ya tashi da kuzarin sa sosai

Yanzu ma suna zaune dashi da Hanif, suna ɗan taɓa hira. Yake ce masa, "ina wayansa?"

Hanif yace, "ai tun jiya na kashe na ajiye ta, yau ma har na fito na koma na ɗauko maka, maybe you need it."

"Yeah. Miƙo min." Ya furta a hankali yana ɗan gyara zamansa ya zauna sosai

Ciro wayan Hanif yayi daga aljihun wandon sa ya miƙa masa. Sannan ya miƙe ƙafafun sa sosai yana saka earphone a kunnen sa ya mayar da hankalin sa a kan wayan sa

Shi kuma SHAREEF tuni ya kunna wayan yana jiran ta gama daidaita. Kafin wani lokaci saƙonni sun soma shigowa cikin wayan sa. Na Haseena ya soma duba wa yana kallo yana murmusawa, duk ƙorafin ta a kan rashin ɗaukar wayanta da bai yi bane, and kuma daga baya da ta kira sai ta ji wayan a kashe. Cije leɓen sa yayi yana ɗan lumshe kyawawan idanunsa, tare da buɗe su ya zuba wa Hanif su yana cewa, "meyasa ka kashe min waya?"

Ɗan ɗago kai Hanif yayi shima yana kallonsa, sai ya ware idon yace, "to me yasa zan bar shi a kunne tunda za a neme ka?"

Numfashi ya ja yana kawar da kan nasa. Kana ya soma ƙoƙarin danna wa Haseenan kira

"Oh! I forgot, na ga sweetheart ta kira, so ban san me zan ce mata ba that's why na kashe wayan, maybe sabida ita kake min ƙorafi?" Ya ƙare maganar idanunsa ƙir a kansa

Shi kuwa SHAREEF taɓe baki yayi batare da yace mishi komai ba, saboda ganin ta ɗauki wayan, sai ya kara a kunne yana sauke ƙafafun sa a ƙasa tare da zama sosai a kan gadon, That's why he turned Hanif

Daga can ɓangaren Haseena ita ta soma magana cikin tsantsan shagwaɓa; wadda alamun kuka take yi tana faɗin, "Why did he turn off the phone all this time when she was looking for him and did not see him?"

"I'm sorry sweetheart. Wayan bata hannu na."

Kuka ta fashe dashi tana cewa, "No. Kana son juya min baya ne dai, and tun kafin in yi nisa ka soma canza min, meyasa zaka kasa nema na after ka san cewa kiran ka kaɗai nake jira? Kowa ya kira Ni but ban da kai, and I called you but you hung up on me?"

Shiru yayi ya kasa magana sabida yanda yake jin kukan nata yana ratsa shi, sosai yake jin ciwo sabida ganin tana kuka, ko kaɗan ba ya jin daɗi ya ga tana cikin damuwa, yana shiga matsanancin tashin hankali. And kuma a yanzu ɗin ya kasa magana bare ya rarrashe ta

Hakan ne yasa ta ci gaba da kukan nata tana kiran sunan sa but ta kasa cewa komai

"I'm sorry sweetheart. Bani da lafiya ne... That's.. why." Ya ƙare maganar cikin ɗaiɗai tare da jan numfashi

Lokaci ɗaya sai ta rikice ta tsayar da kukan tana cewa, "shi ne baka sanar min ba? Me ke damun ka don Allah ka faɗa min kar zuciyata ta buga?"

"Realise sweetheart. Na ji sauƙi, babu komai ciwon ciki ne kawai, amma na fi son ki yafe min don ba na son ranki yana ɓaci haka."

Cikin shagwaɓa tace, "ai tun farko idan na san baka da lafiya bazan yi maka ƙorafi ba, at least ko text sai kayi min ba wai ka bar Ni a haka ba, dole hankalina ya tashi."

Murmushi yayi cike da ƙaunarta yace, "to shikenan, nayi kuskure amma bazan sake ba, ya school ɗin?"

"Alhamdulillah. Amma ka ji sauƙi ko? Ba na son komai ya same ka hankali na ya tashi."

"No. Ba abun da zai same Ni Sweetheart, na ji sauƙi sosai, and ko dambe zamu iya yi da ke tunda na fi ki lafiya a yanzu."

Dariya take yi sosai yana taya ta

Sai ta soma mishi shagwaɓa tana cewa, "ita wlh tana jin garin babu daɗi, fuskarsa kaɗai take son ta gani ko hankalinta zai kwanta, tunda ta sauka ta kasa samun natsuwa ko fita ta kasa yi, Please dear mu yi video call in ganka, I missed you." Ta ƙare maganar tana bubbuga ƙafa tana kukan shagwaɓa

"Oh! Sweetheart za ki kashe Ni."

A rikice tace, "mene ne? Me ya faru?"

Murmushi yayi yana koma wa ya kwanta tare da lumshe idanunsa yana faman cije baki, sai dai ya kasa magana a wannan lokacin saboda yanda yake ji a jikinsa

Wanda Hanif kuwa kallonsa kawai yake yi yana mamakin ɗan uwan nasa, idan yana waya da Haseena ya kan manta kansa da wanda ke wurin ne, sosai yake jinjina tsantsan soyayyar da SHAREEF yake yi wa Haseena, wanda har ba ya iya control ɗin kansa da tsananin soyayyar nata. Numfashi kawai ya ja yana kawar da kansa domin a lokacin ma ya dena jin mai suke cewa saboda tunanin da ya faɗa. Har sai da ya gansa ya gama wayan yana ƙoƙarin shige wa toilet. Bai ce mishi komai ba sai da ya shiga ya fito sannan ya bi shi da kallo yana murmusawa

Harara ya samu daga wurin SHAREEF ɗin yana cewa, "lafiya Malam?"

"Babu komai."

Sai ya ja tsaki yana cewa, "ka ji da gulman ka, ban san saka ido wlh."

Murmushi Hanif yayi yace, "babu wani saka ido, but Ni dai shawaran da zan baka a rage wannan soyayyar tunda aure ba yanzu ba, ta yiwu ma in riga ka auren tunda na ga Sarauniyar ta gudu ta bar ka, nan kusa zaka ji nayi yi wa su Dady maganar aure."

Baki ya taɓe bayan ya zauna a saman gadon, sai ya ɗauki wayansa yana hawa WhatsApp, tare da furta, "ina ruwana to? Ka haifi Yara da yawa ma bai shafe Ni ba."

Dariya sosai Hanif yake yi. Yana cewa, "Ni dai ba ruwana, kar ka ga nayi kace zaka ɗaga hankalin ka, ina tunanin ma su Dady baza su amince in yi aure in bar ka ba, gwara ka samu solution wlh."


Shiru SHAREEF yayi masa bai ce komai ba. Ya ci gaba da latsa wayan kamar ruwa ya cinye sa

Hakan ne yasa Hanif ya canza topic ɗin. Duk da ba kasafai SHAREEF ɗin yake amsa mishi ba, jefi-jefi suke hira

Daga baya ne su Sadiq suka zo shi da Abokan sa. Shi yasa Hanif ya bar asibitin ma gaba ɗaya.




              Zuwa washe gari aka sallami SHAREEF tunda komai normal. Jikin nasa ya warware shi yasa the following day ya koma bakin aikin sa. Yayinda gefe ɗaya soyayya da shaƙuwa take ƙara gudana tsakanin SHAREEF da Haseena, tamkar zasu cinye junan su

Su Dady ko kaɗan basu yi wa SHAREEF maganar aure ba, duk da suna son su yi mishi domin ya fito da Mata kasancewar abun da Likitan yace

Ga shi yanzu kusan sati ɗaya da kwanciyar sa a asibiti. Lokacin ne kuma Hanif zai koma karatun sa. Shiyasa SHAREEF yace, "zai bi shi har can ya raka sa." Sabida so yake yi daga can ya wuce wurin Haseena

Babu wanda ya hana sa kasancewar an san shaƙuwar su da Hanif. Tamkar Abokan juna suka ɗauki kansu, babu mai kallon su yace Yaya da Kani ne saboda yanda suke gudanar da al'amuran su gunun sha'awa.
[13/01, 12:00 pm] OumƊahirah نفيسة: 🌱🌱🌱🌱🌱

      *SHAREEF*
          _SexyBoy_
🌱🌱🌱🌱🌱


_Writer: Nafisat Isma'il Lawal_
_Wattpad: UmmuDahirah_

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝*



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

       *P.W.A✍️*





*DATA SHARE*

Call, message or whatsap  07065334256

*MTN*
500MB 150
1gb  280
2gb.  560 
3gb.   840
4gb.    1120
5gb      1400
6gb.     1700
Verlid for 30 days











__________
*BOOK1*
_______________*FREE PAGE8*
               Tunda aka yi wa Maryamu dukan nan, zazzaɓi ya kwantar da ita tunda bata taɓa shan duka irin wannan ba, musamman ma Baba duk rashin jinta bai taɓa dukan ta ba, iyakan yayi musu faɗa ko ya tsawatar musu, dama Yaya Ashiru ne mai ɗan dukan nasu shima ba sosai ba, domin tunda suka ɗan soma tasawa Baba ya hana ana taɓa su. To kasancewar ta ba mai son a taɓa lafiyar jikinta ba, abu kaɗan sai ka ga ciwo ya rafkar da ita, amma sai rashin jin tsiya, domin Maryamu ba ta jin magana, ita kaɗai ta fita Zakka a gidan su, akwai ta da rashin tsoro ne; uwa uba rashin kunya da fitsara, bare tana tashen balaga jinta take yi kanta ɗaya da kowanne shege

Duk wani abu tare suke yi da Bintu duk da ita bata kaita rashin ji ba, sabida ita akwai shegen tsoro, ba kasafai take biye mata ba, sai dai idan Maryamun ta tilasta ta su yi wani abun, to a nan ne bata da yanda zata yi zata biye mata tunda komai tare suke yi, basu da ƙawaye su kaɗai ne ƙawayen juna. Tunda babu mai iyawa da halin Maryamu, kullum sai an ji ta da sa'annin su suna cacan baki ko dambe, bare yanzu duk sun yi aure sai ɗaiɗaiku


Shi yasa Baba tunda abun nan ya faru ya ƙara matsa musu sai sun fito da Miji

Amma Maryamu fir tace mishi, "ba ta son aure baza ta yi ba." Sai kuka take yi tana rigimar nata tamkar wata ƙaramar yarinya, don wani abun ma ko ƙaramin Yaro bazai yi abin da take yi ba, ko don tana ganin ita ce Auta a wurin Innar ta oho? Shiyasa a kwanakin ba ta iya fita ko ina saboda yanda jikinta ya rikice. Ta saka rigima a ranta a kan auren da Baba yace zai yi musu

Domin a lokacin har manemin Bintu ya turo tunda dama tana da tsayayye. Ɗan uwansu ne ma kuma a ƙauyen yake

Yanzu haka har an tsayar da lokaci idan Maryamu ta kawo wanda take so sai a saka rana

An yi haka da kusan sati biyu, amma Maryamu ta ƙi bin umarnin Baban ta, sai ma ci gaba da rayuwarta da take yi ba ta kula kowa in yazo, Sai cin mutunci da zage-zage da take musu, shiyasa kowa ya ɗauke ƙafa da zuwa wurin ta

Shi yasa Baba ya dinga mata faɗa yace, "tunda ta ƙi kawo wanda take so shi yana da inda zai bada ita." Nan ya yi wa Abokinsa magana saboda yana da Yaro Sule wanda yake sonta dama, kuma Baba ya san da haka saboda ba sau ɗaya ba, ba sau biyu ba; ya sha ganin sa yana zuwa ƙofar gidan wurin Maryamu. Dalilin da yasa yace, "kawai su turo sai a haɗa auren gaba ɗaya." Tunda ya yarda da tarbiyyar sa

Dama yanzu bikin su Yaya Ashiru ya rage saura wata uku ne. Suna gama jarabawar ƙarshe na B8 da suke yi, za a yi auren

Wannan maganar ba ƙaramar rikita Maryamu yayi ba. Kuka sosai ta dinga yi tana cewa, "wlh tallahi babu wanda ya isa yayi mata auren dole, ba ta son Sule baza ta taɓa auren sa ba, sai dai duk abun da za a yi a yi." A gaban Baba take furta waɗannan kalaman nata tana ta birgima da ihu, "wlh ba a isa ba baza ta aure shi ba."

Baba samun sanda yayi, yayi mata dukan tsiya yace, "shikenan zai gani idan ita ta haife shi."

Amma duk dukan nan da ta sha Maryamu ta ƙi haƙura baza ta yi auren ba. Tun abun yana ba wa su Umma haushi, har ta soma basu tausayi saboda yanda ta fige a lokaci ɗaya, bata da aiki sai kuka da nacin, "ita baza tayi aure ba, ba ta son wanda aka kawo mata."

Ranan ma da ya soma zuwa taɗi wurin ta. Dutse ta samu ta ƙwandala masa a kai tana cewa, "wlh in dai bai fasa auren ta ba sai ta fasa masa kwanya ya mutu a banza a hofi, idan kuma ya isa ya aure ta ya gani."


Haka fa Maryamu ta dawo tamkar mahaukaciya. Domin gaba ɗaya ƙauyen sai da suka taru a kanta ana ganin ikon Allah. Sun ga abun tamkar wasa sai kuma abu ya zo ya zama babba. Saboda yanda Maryamun take yi ashe wai aljanun ta ne suka tashi

Har ga Allah ƴan gidan basu taɓa tunanin tana da aljanu ba sai ranan. Kowa ya sha mamaki, amma kuma idan aka ga yanda take yi tun farko dole a saka ayar tambaya a kanta

Yaya Faisal aka kira yayi mata ruƙiya tunda yana da sani sosai a kan addini. Har koyarwa yana yi a Islamiyyar su duk da ba kullum ba, sai sati da Lahadi kasancewar aiki da yake yi a Birni, so ba ya zama sosai, lokacin an ci Sa'a yana gida shi ya zo yayi mata ruƙiya. Daƙyar aka samu ta dawo hayyacin ta

Gaba ɗaya gidan sun yi cirko-cirko har da su Aunty Indo da Aunty Ummita duk suna gidan, saboda tunda labarin abun ya faru kowa ta bazamo gida. Gaskiya hankalin su ya tashi sosai sabida basu taɓa zaton Maryamu tana da wannan laluran ba

Ga shi jikinta ya ƙi daɗi, tunda suka tashi take kwance magashiyan tana faman rawan jiki, sai zazzaɓi ya rufe ta. Dole Inna ta saka mata drip aka bata magunguna don dai aga yanda hali zai yi

Ba a samu kanta ba sai washe gari, sai dai ta tashi tana ta fushe-fushe, kowa ta ƙi kula wa a gidan, kana mata magana ma zata hau gaya maka maganganu tana zumɓure-zumɓuren baki kamar wanda zai taɓo sama

Shi yasa kowa ya shafa wa kansa lafiya tunda basu san yanda Aljanun nata suke ba, kowa ya fita harkan ta

Ƙarshe ɗaki ta shige ta kwanta ta ƙi kula kowa

Dayake suna da islamiyya. Sai Bintu ta zo tana ce mata, "ta tashi ta shirya su tafi ƙarfe huɗu saura."

Banza tayi mata ta juya kai tana kallon sillif idanunta a buɗe. Manyan idanun nan yanda ka san gauta gaba ɗaya sun rikice sun yi jazur

Bintu bata sake kula ta ba, tana gama abun da zata yi ta shirya ta fito

Umma Jummai tace mata, "ya haka kin fito ke kaɗai? Ita Maryamun baza ta je bane?"

"Ni nayi mata magana ta ƙi kula Ni shiyasa na ƙyale ta."

"To shikenan je ki, sai ki gaya wa Malamin naku bata da lafiya ne."

"To." Ta furta tana yin musu sallama sannan ta tafi

Maryamu da ake maganar a kunnen ta duk tana jin komai, miƙe wa tayi fuska a turɓune ta ɗauki Hijabin ta ta saka, cikin kayanta ta duba ta ɗauko dubu ɗaya a ciki wanda dama shikenan ya rage mata a cikin jakar. Wata shegiyar takalmi mai tsini ta ɗauka ta zura a ƙafafuwan nata sannan ta fita. Ko kallon su Inna bata yi ba tabi hanyar waje zata fice

"Ke kuma haka za ki tafi babu sallah?"

Banza ta yi wa Innar da take mata magana ta yi ficewar ta. Ta sha alwashin baza ta taɓa zama a yi mata auren dole ba, gwara ta gudu kawai ta huta da ace ta zauna a yi mata aure. Kai tsaye hanyar barin garin tayi tana ta tafiya ita kaɗai sai faman turguɗe wa take yi, a zuciyarta kuwa lissafin inda yakamata ta nufa take yi; da tunanin matakin da ta ɗauka shi ne dai-dai a wurin ta.





🔆🔆🔆🔆🔆🔆🔆🔆


         Har England SHAREEF ya raka Hanif, a lokacin da suka sauka dare yayi shiyasa ya kwana a can. Da sassafe ya soma shiri zai wuce wajen Haseena

Hanif sai tsokanar sa yake yi yana cewa, "shi gani yake yi kamar ya fi sonta a kansa, sabida ya fi bata kula wa duk yanda suke da shi, amma ace daga zuwan shi sauri-sauri yake ya tafi ya bar shi, maimakon ya ƙara ko kwana biyu ne su ɗan zagaya garin, sai ya je ya ga friends ɗin sa zasu yi farin ciki."

But SHAREEF ko kula sa bai yi ba, sai da ya gama shirya wa sannan ya jefe shi da harara yace, "common tashi ka kai Ni airport, ba na son wannan surutun."

Dole Hanif ya miƙe yana ɗaukar key, tare suka fita zuwa haraban gidan

Ganin yanda Motan tayi ƙura sosai, sai SHAREEF ɗin ya yamutsa fuska yana cewa, "kai bazan hau wannan motan ba, mu je in hau Texsi."

"Ok to." Shima Hanif ya amsa mishi suna yin waje suka fita

Har airport ya raka sa, sai da ya ga ya hau jirgin Australia sannan ya dawo.
**********


              Fannin Haseena, tunda ta san yana zuwa, ta sanya mai aikinta tayi mishi girki kala-kala, ita kuma ta ɗauki wankan ƙananan kaya, ta tsuke a cikin wandon jeans, sai shaining take yi fuskar nan ta sha kwalliya tayi ɗau, dama abun da SHAREEF ya fi ƙauna a gare ta kenan, ya ga tayi irin wannan kwalliyan, sau tari yana yawan gaya mata, "tana tafiya da imanin sa muddin ya ga fuskarta haka." Shi yasa yawanci take yawan yi idan zasu haɗu since bata cika ƙaunar kwalliya ba

Tana zaune ta ji ƙaran buɗe ƙofa, tunda gida guda Abban ta ya kama mata haya, since da ta ji buɗe ƙofan ta san bazai wuce SHAREEF bane, da sauri ta miƙe ta fita wajen, ai kuwa shi tayi tozali da shi

Shima tunda ya hango ta ya tsaya a wurin yana zuba mata murmushin sa mai kyau da ƙara masa kwarjini

Da gudu ta nufo sa cikin tsantsan farin ciki ta rungume shi

Sai ya sa hannu ya manne ta sosai a jikinsa yana raɗa mata magana a kunne, "i miss You sweetheart!"

Ɗagowa tayi tana kallonsa tana murmushin itama, sai tayi masa kiss a laɓɓa tare da furta, "more than you dear."

Kumatun ta ya ja tare da cewa, "Ok let's get into it, I need a break I'm so tired." Yayi maganar yana ɗan yatsina fuska, alamun da gasken ya gaji da yawa

Shige masa jiki tayi sosai, tare da zagayo da hannunta a ƙugunsa, a haka suka shige ciki suka yi wa kansu masauki a saman kujera, kana ta tashi ta ɗauko mishi drinks tana cewa, "Are you going to take a shower first? You will feel better about your body."

"No. I don't need a bath, I will drink." Sai ya sa hannu ya zuba drinks ɗin a cup, tare da kaiwa bakin sa yana sha kaɗan

Murmusawa tayi tace, "ka san me Dear?"

"No. Sai kin faɗa sweetheart." Ya furta yana ajiye cup ɗin tare da kanne mata ido daya

Sai ta shige jikinsa tana cewa, "Today I am happy because you came, we will go out together. Nayi tunanin baza ka zo ba."

"Me zai hana sweetheart? ai duk abun da kike so nima shi nake so, I'd rather see the happiness on your face."

Dariya tayi tace, "I know you love me a lot dear, I also love you very much, let's go eat and I will prepare interesting things for you; domin in burge ka." Sai ta miƙe tana janyo hannunsa ta ɗaga sa

Direct kan dinning suka nufa, ta ja mishi kujera ya zauna sannan ta zauna a side din sa. A one plate tayi musu save, ita ta soma ba shi abincin a baki tana cewa, "haaa bakin."


Dariya yayi yace, "kina son ki mayar da Ni Yaro ko?"

Fari tayi masa da ido tace, "ai ka fi Yaro a wuri na, ganin ka nake yi tamkar Jariri, dole sai da tarairaya kar Matan banza su ƙwace min kai, ka san yanda nake ji da kai." Sai ta ja numfashi tana ƙara wa da faɗin, "ina jin soyayyarka kamar zan yi hauka SHAREEF, ba na fatan ace wani abu ya zo ya raba mu, duk sanda ka bar Ni mutuwa zan yi, don Allah kar ka taɓa rabuwa da Ni, ina matuƙar ƙaunar ka!" Ta ƙare maganar tana shirin zubar da hawaye

Ɓata fuska yayi yace, "kuma za ki fara ko?" Sai ya amshi cokalin tare da ɗibo kaɗan ya kai bakin ta, "ki dena faɗin haka sweetheart, babu wanda ya isa ya raba mu da juna, domin ke ce wacce har zuciya nake ƙauna, ke kaɗai nake so, don haka ki dena wannan maganar; I don't want to see you in trouble. Oya buɗe bakin ki ci sosai mu je mu zagaya gari."

Cike da soyayya yake ci da ita, don shi ya ƙi ci tun wanda ta ba shi, koda tayi masa complain sai ya nuna mata, "ba ya jin yunwa ne." Shi yasa ta ƙyale sa

After ya gama suka fita a tare zuwa yawon buɗe ido, a duk inda suka je suna manne da juna suna shan soyayyar su tamkar zasu haɗiye juna. Sosai SHAREEF ɗin ya saki jikinsa suka sha soyayya, domin ya kasa control ɗin kansa musamman da suka dawo gida, biye mata yayi suka sha romance tunda abun da take so kenan, kusantan ta ne kawai bai yi ba a wannan lokacin, amma sai da suka gama yamutsa juna suka yi wanka a tare sannan suka kwanta, tana jikinsa ta lafe sai matsa ta yake yi kowannen su babu kaya

Har ga Allah ya ji dad'i matuƙa a yau domin duk wata sha'awar sa sai da ya watsar da ita, sosai ta gamsar da shi da wasan da suka sha, tunda ya bata haɗin kai shiyasa har ya fitar da abun da ke jikinsa. Don ma ya ƙi biye mata ya kusance ta amma sun kasance cikin farin ciki a wannan lokacin tamkar zasu haɗiye juna

Saboda haka ne ma, SHAREEF ya kasa dawowa cuz kulawar da Haseena take ba shi ya kasa koma wa. Koyaushe suna manne da juna babu wanda zai kalle su yace ba Mata da Miji bane

Kwanan sa biyu ba shi da alamar dawowa. Sai da Dady ya kira sa yana masa fadan, "kuma sai ya je ya zauna a can haka ake yi?" Tunda a tunanin sa yana wurin Hanif ne, basu san cewa yana wurin Haseena ta riƙe sa ba

Sai da yayi ta lallaɓa ta ma; sannan ta yarda zai tafi, bayan yayi mata alƙawarin, "zai dawo Very soon."

Har airport ta raka sa, sannan suka yi sallama daga can ya dawo Nigeria cike da kewarta da ƙaunarta a rai, tare da burin a ce ya mallake ta a matsayin Mata a nan kusa ko don ya samu abun da yake so, domin a yanzu ba shi da wata buƙata sama da ta zama Matarsa, kasancewar sa mai buƙatar aure a yanzu, amma soyayyarta yasa ya biye mata batare da ya nuna damuwarsa a kan tafiya karatun nata ba, domin ko kaɗan ba ya son ɓacin ranta, dole ya danne abun da yake ji haka nan zai haƙura har sanda zata gama su yi aure.




_Juma'at Mubarakh FAN'S, Allah ya bamu albarkatun ranan nan mai albarka._
[15/01, 10:45 am] OumƊahirah نفيسة: 🌱🌱🌱🌱🌱

      *SHAREEF*
          _SexyBoy_
🌱🌱🌱🌱🌱


_Writer: Nafisat Isma'il Lawal_
_Wattpad: UmmuDahirah_

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝*



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

       *P.W.A✍️*





*DATA SHARE*

Call, message or whatsap  07065334256

*MTN*
500MB 150
1gb  280
2gb.  560 
3gb.   840
4gb.    1120
5gb      1400
6gb.     1700
Verlid for 30 days













__________
*BOOK1*
_______________*FREE PAGE9*
                Kai tsaye cikin Zaria Maryamu ta nufa, tana hawa mota aka sauke ta a Maɗachi, shi ne daga nan ta hau machine ya kawo ta Ƙofan Kibo gidan Iya Samira

Lokacin tana tsaka da ƙulle-ƙullen kayan siyarwan ta, tana zaune a tsakar ɗaki ta ƙure rediyo, sai ganin Maryamun tayi ta faɗo mata daki ko sallama. "Maryamu, ke ce haka? Daga ina?" Tayi mata tambayoyin, bayan ta ɗaga kai ta ganta cike da mamakin zuwan nata

Ita kuma sai ta zauna a gabanta tana mai tanƙwashe ƙafa, fuskarta a kumbure tace, "daga gida mana."

Kashe rediyon Iya Samira tayi, kafin tace, "in ce dai lafiya ba wani abun ne ya faru ba? Ke kaɗai kika zo?"

Kai ta gyaɗa mata tana tura baki ta ƙi cewa komai

"Buɗe baki mana ki yi min bayani, ko wani abun ne ya faru a ƙauyen? Kin ɗaga min hankali."

Sai ga hawaye shaaa a fuskarta, cikin muryan kuka take cewa, "ba Baba bane zai yi min auren dole, shi ne na gudo nan."

"La haula bisha'atil lah! Auren dole kuma Maryamu? Shi Harunan yace zai miki auren dole?"

"Eh mana Iya, Ni kuma wlh tallahi bazan zauna ba, Ni karatu nake so ba aure ba; ana yin abu dole ne?"

"Yo ai laifin nasu ne ba naki ba Mero, in ba don ƙauyen ba taya zai yi miki auren dole tunda kin nuna ba kya so? Maza share hawayen ki babu mai miki aure in har bada yardan ki ba, ita Hafsatun haka aka yi mata? Ina ce nan nayi-nayi da ita baza ta auri Mahaifin naku ba tunda ba kalar ta bane, Mutum ya fito daga ƙauye amma ta nace sai ta aure shi, babu abun da na iya haka na yarda, amma kuma don tsine wa su ba a tilasta musu auren dole ba zasu yi miki? to in ga wanda zai yi miki kina nan baza ki koma ba, karatu kuma ko su baza su saka ki ba Ni zan saka ki, ba dai karatu kike so ba?"

Cikin washe baki Maryamu tace, "eh Iya, na fi so in yi karatu mai zurfi ko don in taimake ku."

"Ai Insha Allah za ki yi sa kuwa, duka-duka nawa kike da za a yi miki auren? tunda zamani ya canza idan an yi wa Yayyinki ai yanzu ba da bane, tunda ke kina buƙata babu mai tauye miki haƙƙin ki, kina nan babu inda za ki koma inyaso Ni zan kira su in faɗa musu na amshe ki, dama ai na fi so ki zauna a nan kusa da Ni. Maza tashi ki ɗibo abinci yana nan a kichen ki ci sannan ki yi wanka ki huta."

Cikin farin ciki Maryamu ta tashi zuciyarta fari tass, domin tunda ta zo nan babu wanda ya isa yayi mata auren dole tunda Iya Samira baza ta yarda ba, musamman yanda take matuƙar ƙaunarta, tun ba yau ba take jelan a bata Maryamun ta riƙe ta amma Iyayen sun ƙi

Matsalar dama daga wurin Mahaifiyar Baba ne, tunda ita tace, "babu inda Yaran sa zasu je domin baza a raba mata kan Jikoki ba, duk rintsi kar ya bar Yaransa su je wani wurin."
Duk da a yanzu ma ba ta raye, kusan watanni goma kenan da rasuwar ta.
*****



       A can kuwa gida, duk a tunanin su Inna, makaranta Maryamu ta tafi, shiyasa babu wanda ya damu; har sai da Bintu ta dawo ita kaɗai

Sannan ne Inna take tambayarta, "ina wannan rigimammiyar yarinyar ta tsaya? In ce dai ba nemo mana wata faɗan zata yi ba tunda mai hali ba ya fasa halin sa?"

Bintu ta tsaya tana kallonta, tace, "Wai Maryamu kike nufi Inna?"

"Eh ita mana, tunda kika fita ta saka ƙafa ta bar gidan itama."

"To ai kuwa bata je makaranta ba wlh, har Yaya Faisal ma yana tambayana a kan meyasa bata zo ba? Nace mishi bata ji sauƙi bane, shine ya ce to zai shigo gidan, amma wlh bata zo ba."

"Bata zo ba kuma? To ina ta je?" Inna tafaɗa tana al'ajabin maganar Bintun

Umma Jummai wacce ta shigo gidan da sallama, tana yaye mayafin kanta take cewa, "ya naga kun yi cirko-cirko, lafiya?"

Cikin takaici Inna tace, "yanzu nake tambayar Bintu ina Maryamun? Ashe wai bata je ba, duk a tunanin mu fitan da tayi can ta nufa, ashe yawonta ta wuce, ita ta sani ai zata zo ta same Ni kuwa zan ci mata mutunci; tunda yawon ya fiye mata makaranta."

"To Allah ya kyauta, rashin jin magana ce irin na ƴan yau, ke Bintu ki cire Hijabin sai ki je ki leƙa gidan Indo ko tana can, sabida yanzu ma haka daga gidan Ummita nake bata je can ba gaskiya, ko ki zaga inda kika san za ki ganta ki kira ta." Umma ta furta tana yin gaba abun ta

Itama tuni Inna ta ci gaba da aikin ta bata sake bin zancen ba

Koda Bintu ta cire Hijabin, bayi ta shiga sannan ta fito ta rataya gyale a gefen kafaɗanta ta fice. Amma duk inda ta san zata ga Maryamu ta je ba a ganta ba. Bata dawo gidan ba har sai da aka kira sallan magriba, ta dawo ta sanar musu, "duk inda ta je an ce bata zo ba."

"To ina ta je?" Umma ta furta tana kama haɓa

Inna dai bata tanka ba, a lokacin tana tsaka da alwala ne, sai da ta gama ta dubi Bintu da ke zaune tana ci gaba da faɗa wa Umman gidajen da ta je, sai tace, "zo ga buta ki ɗauka ki yi sallah, ita kuma zata gamu da Baban nata bari ya dawo, tunda abun da zata tsiro wa kanta kenan, ki fita tun ɗazu ba a san inda kika je ba?" Sai ta ja ƙwafa tana miƙe wa ta wuce ɗaki.

         A haka fa shiru -shiru har su Baba suka dawo Maryamu bata dawo ba. Aka sanar musu shiyasa Baba yake ta faɗa, ya saka su Ashiru su je su duba ta, amma duk inda suka je babu labarin Maryamu. Hankalin su ya soma tashi matuƙa, shiyasa suka jira a fito sallan isha'i su gani ko zata dawo

A gida kuwa Umma ce kawai ta nuna damuwar ta, shiyasa har fita tayi tana duba maƙota ko ta je

Inna kuwa sam ta ƙi zuwa, duk da a cikin ranta sosai ta damu, amma bata nuna a kan fuskarta ba sai harkokin ta take yi.
***

       A lokacin Maryamu tana can ta ma manta da wani mutanen gida, ta tasa Iya Samira tana ta faman yin mata tatsuniya, tunda itama shaf ta manta cewan zata kira iyayen Maryamun ta sanar musu kar hankalin su ya tashi basu ganta ba 

Sai a lokacin ma ta tuna ta buga salati tana cewa, "Maryamu miƙo min wayata a ɗaki in kira Hafsatu in faɗa mata kina nan, in ba haka ba ai sai hankalin su ya tashi ke kina nan, su suna faman neman ki."

Dariya Maryamun take yi, ta je ta ɗauko tana cewa, "barin ma Baba, don na san sai ya fi tashin hankali, yanzu ki ga yana zagaye bayi."

"Gidan ku, kira min numban shi ko ta Innar taku, ban san shirmen nan naki."

Kiran numban Baba tayi, sai dai bai shiga ba sabida babu kuɗi

"An shige su! ashe babu kuɗi kuma?" Sai ta ja tsaki tana ƙoƙarin miƙe wa tare da cewa, "ina zuwa bari in dubo kamar ina da gudan ɗari a bankaɗen kayana, na san idan ke na aika baza ki gani ba sabida shegen ɓuya da nayi masa."
Babu jima wa kuwa sai ga shi ta dawo da ɗarin, ta miƙa mata tana cewa, "amshi nan, ki fita ƙofar gida ki siyo a shago, tunda an fito masallacin, maza ki siyo wurin Laminu ko Isah a nan bakin gida, ki ce in ji Ni ne zasu ba ki tunda ɗari da goma ne."

Maryamu da ta amsa kuɗin, sai faman juya shi take yi, sai ta soma warware wa tana cewa, "kai Iya wannan kuɗi ta sha ɓoyo da yawa, ji be yanda ta koma."

"Ba dai zata biya mana buƙata ba? Da Allah maza ki je ki dawo kar su ji shiru."

Hijabin Iya Samira ta ɗauka ta zura, sannan ta fice

Bata jima ba ta dawo da katin ta saka a wayan. Sai ta kira numban Baba

Lokacin suna tsakar gida sun yi cirko-cirko ana jimami, sun rasa ma me ya kamata su yi. Sai ga kiran wayan Iya Samira

Haka nan Baba ya amsa wayan muryansa cikin damuwa, bayan ya amsa wayan yake gaishe ta cike da girmamawa

Ta amsa tana cewa, "ya mutan gidan? Ina fatan kowa lafiya?"

Ɗan jim yayi, sai kuma yace, "to Iya kowa lafiya zamu ce..." Sai kuma yayi shiru ya kasa faɗa mata abun da ke faruwa

Ita kuma sai tace, "halan Maryamu kuke ta faman nema?"

"Wlh kuwa Iya, ashe an faɗa miki?"

"A'a babu wanda ya faɗa min, tana nan gidana ta zo tun ɗazu, kuma Ni na manta ban kira na sanar muku ba."

"Iya tana nan wurin ki?"

"Eh ƙwarai kuwa, ga ta nan ma zaune a wuri na, tace ta gudo nan baza ta zauna ba tunda auren dole zaku yi mata, shiyasa ta taho."

"Ikon Allah!." Abun da ya iya furta wa kenan ya kasa ma magana saboda mamaki

"To don haka Jikata dai baza a yi mata auren dole ba, ta dawo wurina da zama don haka baza ta dawo nan ba, Ni zan riƙe ta tunda ku kun gaji da riƙe ta, kuma zan saka ta a makarantar har lokacin da Allah zai fito mata da Mijin aure."

"Amma Iya ban ƙi ta taki ba, kin san yanda mu nan muke aurar da yarinya, kuma mu ba auren dole muka so mu yi mata ba, ita Maryamun ce ba ta jin magana, kawai daga an yi mata maganar ta fito da Miji a yi musu aure tunda ƴar uwanta ta fito dashi, kuma kinga ba karatu suke yi ba tunda sun gama ƙaramar secondary, duk sa'annin su sun yi aure shiyasa Nima zan yi musu, amma Iya ai babu wata maganar auren dole a ciki."

"Eh to babu wata maganar auren dole a ciki, amma ai ita ta nuna bata so; karatu take so, tunda ku baku da kuɗin saka ta ai Ni ban rasa ba, ka barta a hannuna ta ci gaba da karatun ta, zuwa nan da ta gama Sakandiren sai ka ga ta kawo wanda take so, shikenan ma sai a yi auren, kuma ka ga bata ma zauna a ƙauyen ba balle a riƙa gutsiri tsoma, ko ya kace?"

Cike da kunyar ta tunda bazai iya mata gardama ba, yace, "shikenan Iya, yadda kika ce haka za a yi, Allah yasa hakan shi ya fi alkhairi."

"Amin ya Allah, ai karatu da dad'i, ko baka ga yanda Hafsatu ta zama bane a ƙauyen? To itama sai ka barta ta yagi rabon ta tunda haka zamanin namu ya zo, ai an ci gaba har karkaran ba a saurin Aure, Allah ya rufa mana asiri ya bamu dacewa kawai."

"Amin Amin Iya, to mun gode Allah ya saka da alkhairi, bari in sanar da mutanen gida tunda gaba ɗaya hankalin mu a tashe yake dama."

"Gaskiya kam, ai Ni ce ma da mantuwa, da na kira tun ɗazu da baku shiga ɗimuwa ba, ka gaishe da su sai da safen."

"To Iya, mu kwana lafiya." Ya ƙare maganar yana sauke wayan a kunnen sa tunda tuni ta kashe ma

Sai ya kalli Iyalan nasa, waɗanda suke zaune gaba ɗaya a tsakar gidan, in banda su Yaya Faisal da har yanzu suna can suna neman Maryamu, amma har su Ummita suna cikin gidan, duk da basu ji me Iya take faɗi ba amma kunnen su yana ga Baba suna sauraron shi

A nan ne yayi musu bayanin halin da ake ciki, Maryamu tana can wurin Iya Samira

Sai kawai suka soma murna kowa na furta alhamdulillah, har Inna da tayi nata a zuciya, wacce tana ɗaki a saman darduma, tunda tayi sallah bata tashi a wurin ba cikin tsananin damuwa da tunanin inda ƴarta ta shiga. Amma jin wannan bayanin hankalin su gaba ɗaya ya kwanta

Nan Baba ya aiki Halliru ya je ya kira su Nazirun tunda an san inda take

Sai ga su, su ma sun shigo gidan kowa hankalin sa ya kwanta

Su Ummita, sai suka tashi suka yi musu sallama suka koma gida

  

Shima Yaya Faisal bai jima ba, yayi musu sallama ya tafi, tare da ɗansa wanda suke tare tun idar da Sallah basu koma gida ba, sai ya ajiye shi a gidan, shi kuma ya tafi ana neman Maryamun tare da shi.
*****

          Da safe Iya Samira ta fita ta je gidan su, tunda har sun yanke hukunci ita da Maryamun a kan za a nema mata makarantar nan na Ƙofan Kibo, wato Jama'atu. Shi yasa tace, "da sassafe zata je tayi magana da ɗan wurin Kawunta Shehu tunda Malami ne a can, sai su ji yanda za a yi a samo mata Form."

Maryamu sai murna take yi, domin barci ma ya gagare ta a ranan, sai lissafi take yi tana dariya tare da yi wa Iya Samiran alƙawarukan, "duk sanda ta gama karatu ta zama babba a cikin gomnati, ita zata soma jin dadin ta, albashin ta na farko tayi mata alƙawari ita zata ba."

Itama Iya Samiran sai dariyan shirmen ta take yi, shiyasa ganin yadda ta damu da karatun, safe nayi ta fita ta je ta yi wa Malam Aminu magana. Ɗan Kawunta Shehu da yake koyarwa a school ɗin. Da inda suke da makarantar babu nisa shiyasa Iya Samira ta fi son Maryamu tayi makarantar, ko don sauƙaƙawan wahala

Sai dai an yi rashin Sa'a, Malam Aminu ya sanar mata, "ai kuwa Form ya ƙare, sun rufe ma karɓan ɗalibai."

"To Aminu yanzu kana ganin baza a samu ba? Ko ɗan ciwa-ciwan nan mana kayi mana tunda kaima Malami ne a makarantar, na san baza ka rasa hanya ba."

Dariya yayi da cewan, "ai Iya da ne ake wannan ɗabi'ar, tunda gwamnatin Nasiru El Rufa'i ya hau aka dena, wlh ko ƴar Masu kuɗi ce yanzu sai ta bi ƙa'ida a ƙasar nan take samun gurbin karatu, ai yanzu an ci gaba sosai a kan harkan Ilmi. Ki bari kawai zan yi wa Abokina magana na san baza a rasa a makarantar su ba, sai a nema mata a can tunda da nan da can ɗin duk ɗaya ne, su ma can makarantar Arabia ce tana da kyau matuƙa."

"To ai matsalan, ba na son tayi nesa da gida ne, ka san yanda harkan biyan abun hawan nan yake, shima ƙarin jidali ne."

"A'a kar ki damu Iya, tunda aka sanya ta school ai transport bazai gagara ba, nan Sheikh Ibrahim Arab ne fa, Karau-Karau na hanyar Gaskiya, ashirin ma zai kaita zuwa makarantar. Kinga Hamsin ma ya isa ya kaita ya dawo da ita har da na shan ruwa." Ya ƙare maganar yana dariya

Itama tayi dariyan tana cewa, "to Masha Allah, ai shikenan kuwa, na ji dad'i wlh, Allah yasa a samu, Ni sai in riƙa bata saba'in ma tayi break da sauran, don Allah ka ƙoƙarta min."

"Babu komai Iya, yanzu zan kira sa ma in faɗa masa, duk yanda muka yi dashi za ki ga na zo gidan."

"To Shikenan na gode, bari in je." Ta miƙe da ninyar fita daga ɗakin

Sai ga Matar Malam Aminun, Shafa'atu, ta shigo da Kofin koko da Ƙosai tana cewa, "wai Iya har za ki tafi? Ki bari in kawo miki abun kari mana ga shi."

"A'a wlh Shafa, sai da na karya kafin na fito, ki bar shi kawai, ina Yaran ko har sun tafi makarantar ne?"

"A'a, ai dayake da Babansu suke fita yana sauke su a tasu makarantar, sun shiga cikin gida ne, yanzu za ki gansu."

"To Ni na tafi, sai anjiman ku." Ta fita ta saka takalman ta ta fice daga gidan, batare da ta shiga can cikin gidan ba, tunda dama sashin Malam Aminun a bakin hanya yake, ba sai an zurfafa ciki ba.
***

           Kamar yanda Malam Aminu ya faɗa ma Iya Samira ne, sai ga shi ya zo gidan da yamma har da Form ɗin Maryamun an samu, yanzu kawai kuɗi ya rage in an cike Form ɗin sai a maida musu tunda an samu. Shi yasa duk ya faɗa musu abubuwan da ya kamata su yi ko nan da sati ɗaya ne a yi a gama komai, tunda har an fara karatu time ɗin ya ƙure, shima Form Allah ne yasa za a samu don ya ƙare gaba ɗaya sai guda ɗaya

Shiyasa Iyan ta cire kuɗi ta bayar, tace, "ya siyo mata har da kayan makaranta da littafai, abun da bai samu ba ko a hankali sai a siya in har ta fara zuwa."

Maryamu sai murna, tunda ta samu cikan burin ta, karatun shine abu na farko da take buri a rayuwarta, tana son ilmi matuƙa, tana son ta zama ƴar boko wayayyiyar yarinya, wacce ake dama wa da ita a gwamnati. Ta san wata rana sai ta zama ɗaya daga cikin ma'aikaciyar gwamnati tunda shi ne abun da ta fi ƙauna a duk ayyuka, ta ganta cikin office ɗin ta mai sanyi, tana da dogon buri gaskiya a rayuwa, kuma da sannu zata cika sa.
    


_Ko burin zai cika?_
[17/01, 9:40 am] OumƊahirah نفيسة: 🌱🌱🌱🌱🌱

      *SHAREEF*
          _SexyBoy_
🌱🌱🌱🌱🌱


_Writer: Nafisat Isma'il Lawal_
_Wattpad: UmmuDahirah_

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝*



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

       *P.W.A✍️*





*DATA SHARE*

Call, message or whatsap  07065334256

*MTN*
500MB 150
1gb  280
2gb.  560 
3gb.   840
4gb.    1120
5gb      1400
6gb.     1700
Verlid for 30 days












__________
*BOOK1*
_______________*FREE PAGE10*
             "Sadiq."

"Na'am Dady." Ya amsa yana ƙoƙarin dawowa

"Kuma baka cinye abincin ba zaka tafi, sauri kake ko me?"

"Eh Dady, ina da text da zan yi by 10 o'clock, shiyasa nake son in shiga in duba littafina."

"Ok, kira min SHAREEF, sai ku taho tare, akwai maganar da nake so mu yi daku."

"To Dady." Ya amsa yana wuce wa upstairs

Inda shima Dadyn bai jima ba ya tashi daga saman dinning ɗin, ya koma cikin falon yana gyara malin-malin ɗin sa

Momy da ta shiga kichen domin haɗo masa coffee kamar yanda ya buƙata, sai ta kawo masa tana miƙa masa tare da cewa, "har ka gama Alhaji?"

Numfashi ya ɗan ja kaɗan yana cewa, "wlh kuwa, kin san sauri nake yi, kuma na fi son shan wannan ma."

"Dad ga shi nan fitowa, yanzu ya tashi."

"Ok zauna." Ya furta yana kallonsa, kafin ya dubi Momy yace, "zuwa gobe idan zan je Kadunan nan, ina son in wuce Zaria sabida mun kwana biyu bamu je ba, ya kamata in je in gaishe da Uwata in ga halin da take ciki, don haka zamu wuce da Yaran nan."

Momy tace, "ai ba su kaɗai ba, har Ni ya kamata mu je kuwa, tunda mun jima ɗin gaba ɗaya bamu je ba."

"Eh, abun da na so yi kenan, amma kinga ba kai tsaye can zamu wuce ba, shiyasa naga dacewar tafiya da su since Maza ne, sannan sun jima basu je ba musamman ma SHAREEF da naga alamun ba ya son zumunci."

Sadiq yana dariya yace, "Dady kamar ka san ina son zuwa, domin Ni kaina har na manta hanyar garin ma, tun lokacin bikin Aunty Ummita ban sake zuwa ba."

"Oh! Ashe zaka iya tuna wa ma? Ai kayi ƙanƙanta lokacin, domin ina ganin ko Ummitan ka gani yanzu a gabanka baza ka santa ba." Cewar Momy tana dariyan itama

Shi kuma sai ya shagwaɓe fuska yana faman faɗin, "wlh yana da wayon sa a lokacin, tsab zai gane ta, har da ma sauran ƴan uwanta, sai dai in bai gan su ba."

A lokacin SHAREEF ya sauko daga saman, cikin kayan barcin sa masu taushi farare, three quartern wando robber da ya matse sa, ita kuma rigan mai dogon hannu da V neck. Ƙafafuwan sa kuma babu takalami a haka ya iso sululu babu ƙwari jikinsa; ya zauna a gefen Sadiq yana gaishe su

Suka amsa, Momy tana cewa, "sai yanzu kenan SHAREEF? Lafiyar ka dai ko? Na ga duk yanayin ka ya sauya?"

Fuskarsa a yatsine yake cewa, "Mom, ba na jin dad'i ne, cikina ke min ciwo."

"Ka sha maganin ka kuma? Ba na son fa kana wasa da lafiyar ka SHAREEF?" Cewar Dady yana bin sa da kallo

"Eh na sha Dady, but da sauƙi fa." Ya furta da shagwaɓa

"Dama haka zaka ce, ina rasa irin ka wlh." In ji Momy tana miƙewa tare da nufan wurin dinning din. Breakfast ta haɗo masa ta kawo masa har wurin tana cewa, "yi maza ka karya ban son kana zama da wannan yunwan."

Dady na dariya yace, "wa ya ga ɗan gatan Momy, don haka ka mayar da hankali ka samu lafiya don nima ba na son ganin ka a haka, kuma ga shi gobe ina son mu tafi tare, zamu wuce Zaria gaba ɗaya don sada zumunci, musamman kai SHAREEF da har yanzu baka san ƴan uwanka sosai ba, irin hakan ne ba na so wlh tunda wata rana akwai mutuwa, zumunci yana da dad'i sosai, gwara mu tafi tare, in har ka samu lafiya gaba ɗaya tare zamu wuce."

Shiru SHAREEF ɗin yayi batare da ya furta komai ba, illa juya tea cup ɗin da ke gabansa yake yi a ransa yana tunanin hanyar da zai bi domin daƙile zuwan sa wannan garin, don shi ba Mutum bane mai son takura, kuma ba ya son wani biye-biyen dangi musamman ma na Dady ƴan ƙauyen can, don ya san dole sai sun je cikin ƙauye in har suka je Zarian, since ya san a nan Ƙanwar Dadyn take aure. Shima rabon sa da zuwa tun bikin su Ummita, lokacin da ya je har aka samu matsala ƴan ƙauyen suka kusa rotsa mishi kai sabida ya mari wani, shi harkan talauci da mu'amala da ƙasƙantattun mutane kwata-kwata bazai iya jure wa ba, dole yayi wani abun. Shi yasa gaba ɗaya ya ƙi sake wa a lokacin duk da ba ya jin wani ciwo a jikinsa, lafiyar sa lau, amma ya nuna kamar bai ji sauƙi ba, shiyasa ya ƙi fita aiki ya langaɓe ma Momy a wurin

Har Dady yace, "gwara su je asibiti a duba sa, maybe ciwon sa ne yake kokarin tashi."

Amma ya ƙi yarda, yace, "idan ya sha maganin zai sauka, kuma zazzaɓi ne ba wani abu ba".

Har washe gari SHAREEF ya ƙi fita aiki duk ya langaɓe a zuwan bai samu lafiya ba, shiyasa dole Dady suka shirya shi da Sadiq suka kamo hanyar Kaduna. A can zasu kwana daga can sai su wuce Zaria

Suna tafiya kuwa ya ware ya tafi aikin sa

Momy tace, "ka ga min ɗan ƙwal uba. Anya SHAREEF ba rashin son zuwa garin nan bane yasa ka langaɓe?"

Tura baki yayi yana shafa kansa tare da cewa, "a'a Momy, Ni fa jikina ne ya matsa min, kuma yanzu na ji sauƙi shiyasa zan leƙa kar aiki ya taru min."

"To shikenan, Allah ya taimaka ya baka Lafiya, ka kula da kanka kaji ko? Kar kuma ka yi wasa da maganin ka kamar yanda ka ji Likita ya faɗa."

"To Momy, ga shi nan ma a jaka. Sai na dawo." Yayi kissing ɗin hannunta before ya tashi ya fice; waya a hannu yana ƙoƙarin kiran Haseena.









🔆🔆🔆🔆🔆🔆🔆🔆


       "Maryamu. Fito ga tuwon-tuwon ya sauka."

"Kai Iya! Ki bari mana in ɗan yi barcin nan, kinga fa har ya soma kwashe Ni."

Tsaki Iya Samira ta ja tana cewa, "yanzu fa kika dawo kina min rangajin yunwa kike ji? Sai da na gama kuma za ki ce barci kike ji?"

Tura baki Maryamu tayi tana zuwa gaban kichen ɗin

"Ɗauka ki je ki zauna ki ci kinji ƴar albarka, kin dawo da yunwa ina kika ga barci? Idan kin ci sai ki kwanta ki huta, tunda har yanzu ba a fara zuwa islamiyyan ba ai kina da lokacin hutu."

Ɗaukar abincin tayi, wanda Iya ta sake mata a cikin robber mai faɗi sai tururi yake yi, ta koma saman tabarman bakin ƙofan Iya Samiran, tana cewa, "yauwa Iya, Ni wlh makarantar nan kwata-kwata bai yi min ba, da da hali a sauya min wata kawai, gaba ɗaya fa na ƴan Arabia ce."

Kama haɓa Iya Samira tayi tare da cewa, "au iyee! Daɗin yayi miki yawa ne har haka? To mene ne illar hakan kenan? Ina ce dai duk makaranta ce?"

Yamutsa fuska tayi tana haɗiye wanda ta zuba a bakin ta, tace, "ke ba ki ga bambancin su bane Iya? Wannan fa makarantar Larabci ne, kusan rabin ta Arabia ne, Ni kuma da nake son zama ƴar Boko zalla ina Ni ina wannan makarantar? gaskiya a canza min ba na son ta wlh, sam bata dace dani Ni ba, I can not da zama a can."

"Ai kuwa sai dai ki tattara komatsanki ki koma gidan ku tunda ba ki san abun arziki ba, eh.. gwara ki koma can a yi miki auren ƴar Jakar Uba, yanzu duk wahalar da na sha na kashe ɗan jari na amma kike cewa bai yi miki ba? Ke ba riban ki bane ace kin iya ajamin kuma kin iya Bokokon?"

Ture kwanon abincin tayi tana shura ƙafa tare da cewan, "Ni wlh Iya makarantar nan bai yi ba, shikenan kuma don ke kika sani bazan faɗi ra'ayina ba? To taya kuma zan zama ma'aikaciyar gwamnati? Wannan ai sai dai in ƙare a makarantar islamiyya ina koyar da yara, daga zuwa makaranta ban ƙaru da Yes da No ba amma sun cika Ni da na'am.. hakaza.. duk inda ka bi larabci ake yi, to ta ina zan iya turancin? Ɗan guntun da na iya ma wlh neman sa zan yi in rasa, Allah Iya don ba ki je kin ga makarantar bane."

Ƙwafa Iya Samira tayi tana cewa, "to sai dai kar ki yi makarantar nace, in har baza ki yi hakuri da inda Allah ya ajiye ki ba, miƙo min abincin tunda baza ki ci ba."

"Ni nace miki bazan ci ba? Fushi nayi wlh, amma zan ci." Sai ta jawo robbern ta ci gaba da ci, but tana cewa, "I can't believe wannan, I should be removed and put me another wani school ɗin, ya fi min wlh."

"Ƴar Jakar Uba, ke kika sani, tunda ba ki san abun arziki ba, Ni dai bazan yi wahalar kuɗina ba, in kinga baza ki iya ba ki tattara ki koma inda kika fi wayau."

"Daga an yi magana sai ki fara min gori Iya, to albashina na farko ma na fasa ba ki dukka, rabi zan ba ki tunda baza ki canza min beautiful school ba."

Iya Samira tace, "kinga Maryamu, wannan makarantar da kike gani ya fi waɗanda kike so, na san dai bazai wuce irin na arnakun nan kike so wanda za a yi ƙaryan turanci ba, amma kinga wannan riba biyu ke gare ki, duk inda kika je baza a raina ki ba, yanzu ɗan guntun turancin nan da kika yi ko za a kashe ki baza ki yi shi da larabci ba, ga harshen Annabin mu amma kike gudun shi?"

"Wlh Iya me I can, lá' ba'asu, na'am, sa'as'habu ilal baiti. Kin gani Iya, na iya sosai wlh." Tafada tana washe haƙora

Itama Iya Samiran tana taya ta da faɗin, "ah! Ashe Jikar tawa ƙwaƙwalwa ce da ita? Za a je da ke kuwa, nan gaba ma baza a gane ki ba in kika karya murya wlh."

Farin ciki kamar ya kashe Maryamu, sai washe baki take yi tana jin dad'i, sai ta koma kuma ta ci gaba da larabcin tana gwamutsawa da shegen turancin ta, har da su kill U, da Sa'amutu a cikin maganar, don ita wani abun faɗa kawai take yi don ta nuna wa Iya Samira ta ƙware sosai

Ana haka suka ji sallaman wasu Matasa su biyu sun ɗauko buhunan shinkafa suna shigowa da shi

Iya Samira ta amsa musu tana cewa, "ah ah! Isah daga ina kuma waɗannan kayan?"

"Wlh baƙin ki ne Iya, suna nan a waje, Alhajin ne yace mu shigo da su."

"To to.. wa kuma muka samu ye? Ku zuba a nan ne." Ta nuna musu bakin ƙofa ganin zasu wuce mata dashi ɗaki

Suna ajiye wa suka koma suka kwaso sauran, har da su galan ɗin mangyaɗa, da su katan taliya, kaya dai kala-kala na masarufi

Tuni Maryamu ta tsame hannu a cikin bushashshen tuwon da take ci, tana faman lanɗe hannu tare da bin su da kallo, sai kuma ta kalli Iya Samira wacce ta gama ma Matasan magana, tana cewa, "Wai Iya kayan waye wannan? Zamu ci dad'i ashe?"

Bata kai ga bata amsa ba, sai ga Alhaji Ahmed tare da Sadiq sun shigo gidan da sallama

Iya ta amsa tana faɗin, "maraba lale, haba! Ni dai a raina sai da na kawo ko mutan Kano ne? Ashe kuwa su ne. Maza ɗauki robbern nan Maryamu ki kai kichen." Sai ta matsa itama tana ja musu tabarman da cewa, "ku zauna mana."

Takalma suka cire suka zauna

Iya da ke duban su baki a washe tace, "har da Mijina Sama'ila aka zo yau? Gaskiya yau farar rana ce mai yaye duhu."

Dady da ke murmushi yace, "a'a Inna, Sadiq ne, Hanif yana makaranta bamu zo dashi ba."

"Ikon Allah! Wannan Abubakar ne ya zama haka? Girman ɗan Mutum babu wahala, tun yana ƙarami rabon sa da nan shiyasa na kasa gane shi, ga shi yayi tsawo kuwa, don dai na san ƙila ya kamo yayyin nashi a tsawo."

Suna dariya gaba dayansu, while Dady yace, "kamar kin sani kuwa Inna, tsawon su ɗaya."

"Masha Allah! Sannun ku da zuwa. Maryamu zo ki siyo musu ruwa a shago su sha su ji sanyi."

"Inna a bari kawai, bari mu gaisa." Ina wuni? Mun same ku Lafiya?"

"Lafiya ƙalau alhamdulillah, ya jama'ar gida? Ya su Khadijah da Yara? Ina Babban ɗan naka bai zo ba?"

"Alhamdulillah Inna, wlh bai da lafiya ne shiyasa bai zo ba, amma dashi muka so zuwa."

Cike da fuskar tausayi tace, "Allah Sarki! Allah ya ba shi lafiya, shima dai anya idan na ganshi zan gane shi? SHAREEFU ya guje mu ba ya zuwa, shi da yake babban su ma."

"Ina wuni Inna?" Cewar Sadiq yana risinar da kansa da girmamawa

Ta amsa cike da yalwan murmushi a kan fuskarta tana tsokanar sa da cewan, "ai kuwa da kai zan yi Miji Abubakar, don da alamun ka fi min su sauran, Allah yasa zaka riƙa zuwa gaishe Ni tunda su sun manta dani?"

Dariya yayi yace, "eh Inna insha Allahu, dama don makaranta ne ya ɓoye Ni, amma yanzu za ki riƙa gani na."

Sai a lokacin Maryamu da ke zuƙune kamar wacce take neman gafara, tana bin su da ido sai faman washe baki take yi, sai ta soma gaishe da Dady bakin nan a washe kamar gonan auduga

Ya amsa ta yana kallonta, sai kuma yace, "wace ce wannan mai kama da Ƙanwata?"

"Autan ta ne ai, ashe zaka gane ta?"

"Ikon Allah! Wai Maryam? Ai dayake kamar su na gani, kamar an tsaga kara, wai ita ce ta girma haka Inna?"

"Ai kuwa ita ce, ka san dayake girman ƙauye babu wahala, ga ta nan ta zama Uwar Mata."

Rufe fuska Maryamu tayi tana dariya

"To ba ki gaishe da Yayan naki ba? Ga Abubakar nan Yayanki ne, don na san ba ki sansu ba ko a fuska, shi ne Autan ɗana."

Tana dariya tace, "Iya na san Kawu mana, amma wannan ne ban sani ba."

Sai shi Sadiq ɗin yace, "ai Ni na sanki." Sai kuma ya kalli Iya Samira yace, "itama ƴar Gwaggon mu ce, ƙanwar Aunty Ummita da muka taɓa zuwa biki?"

"Eh, ita ce kuwa Abubakar."

"Ai na santa lokacin. She was young at that time, I think tana rurrufe a lokacin ne ma." Yafaɗa yana dariya

Su ma suna taya sa har ita Maryamun da dad'i ya kusa kashe ta, ta ga ƴan gayu, koda ganin su ta san ba ƙananun mutane bane, ita dai sau daya ta taɓa ganin Kawu ya zo kauyen su, aka ce Kawunta ne, to bata manta fuskarsa ba gaskiya

Dady ne yace, "ta zo miki hira ne kenan Inna?"

"A'a, wai makaranta take yi a nan, kwanan ta biyar kenan da fara zuwa, dayake Mahaifinta zai yi mata aure ne tunda ka san halin ƴan ƙauye, shine ta gudo nan wai karatu take so, Ni kuma na goya mata baya har na saka ta ma; yanzu ga shi tana zuwa."

Cikin murmusawa Dady yace, "Masha Allah! Abu yayi kyau, ki ce ƴar tawa tana son Ilmi haka? To ai shi ne rayuwar dama, ai kuwa dole in taimaka don cikan burin ta, ko can Kano sai na tafi da ita tayi karatun ta har sanda ta ji ya ishe ta, ko ƴata? Ko ba kya son mu tafi tare?"

Da sauri har tana sarƙe wa da yawu wajen amsa wa, sai ta soma tari sosai

"Ashsha! Maza ki je ki sha ruwa, sannu ko." Cewar Dady yana ɗan saka hannu ya dafa ta

Sai ta miƙe ta nufi wurin randan ruwan ta buɗe tana sha. Tana jin lokacin da Dadyn yake cewa Iya Samiran

"In har ta yarda zai tafi da ita gidan shi, sai tayi karatun a can, Khadijah ma zata ji dad'i tunda tana burin ta ga ta riƙe Mace a hannunta, zasu yi farin ciki matuƙa idan an basu Maryam sun tafi tare."

Sadiq shima yayi saurin tsulma baki yana cewa, "wlh kuwa Inna, don Allah ki bamu ita mu tafi tare, nima na samu ƙanwa."

"To ai ban ƙi ta taku ba Ahmadi, sai dai ka san tunda Mahaifinta yana raye sai da yardan sa, in ya amince ai babu komai sai ku tafi da ita."

"Dama ai Inna dole sai da amincewar sa, har ƙauyen nasu zan je in ga Ƙanwata tunda dama ina da burin zuwa can, amma sai gobe kasancewar a nan zamu kwana."

"To Shikenan ai, Allah ya rufa asiri dai, ya ƙara arziki da buɗi, muna godiya da irin ɗawainiyar da kake mana."

"Haba dai Inna, ai babu maganar godiya a tsakanin mu, ke tamkar mahaifiyata ce, babu bambanci a tsakanin ku, Umma har ta mutu tana mini wasiyyar riƙe ƙi da gaskiya, bani da kowa face ke, ke ce tushe na tunda duk inda na je na dawo da nan zan yi tutiya, kawai ki yi mana fatan gama wa da ku lafiya amma duk abun da nayi muku babu godiya."

Shi yasa Iya tayi ta masa addu'a da fatan gama wa da duniya lafiya

Sai daga baya ne Maryamu ta je ta siyo musu ruwa da lemu har da su tsire, don Iya Samira tace, "sai sun ci dole."

Bayan sun ci ne suka fita ta raka su babban gidan su don ya gaishe da jama'a

Yace mata, "bai je can Samaru gidan su Umman sa ba, zasu wuce ko zuwa dare sai su dawo tunda a nan yake da ninyar kwana."

Dayake akwai ɗakin Mahaifiyarsa wanda in har suka zo dama a nan suke kwana, komai akwai a ciki tunda ya gyara musu gidan, kuma har kayan ɗaki shi ya canza wa Iya Samira

Tare suka tafi da Maryamu tunda ta nuna sai ta bi su, sai jin dadi take yi tana maƙale musu, musamman yanda Sadiq yake jan ta a jiki kamar ƙanwar sa da suka fito ciki ɗaya, sai farin ciki take yi.
***


              Washe gari su Dady suka wuce ƙauyen su Maryamu, Kugu. Dayake Sadiq ke tuƙin; shi kuma Dady yana nuna masa hanya, suna kaiwa bakin ƙofar gidan ya dakatar da Motan. Suka fito a tare suna ɗan kallon yanayin garin, duk da babu mutane amma sai da suka jira suka samu wasu Yara

Dady yace, "don Allah su taimaka musu, su shigar da kayan nan." Dayake su ma yayi musu tsaraba suna cikin Boot

Lokacin babu su Baba suna wurin sana'a. Sai Inna da aka kira ta fito wajen, tana ganin Yayan nata murna ya cika ta, cikin farin ciki take cewa, "Yaya, kai ne a garin mu yau?"

Yana dariya yace, "wlh kuwa Hafsah, kin ganmu cikin bazata babu sanarwa."

Dariyan farin ciki tayi, sai tace, "haba dai Yaya, ai babu komai ku shigo." Sai ta kalli Sadiq kuma, bata ce komai ba sabida farin ciki tayi musu iso ciki

Umma Jummai tana ɗaki ta ji shigowar su, shiyasa itama ta fito tayi musu lale marhaban. Tare suka tarbe su aka shimfiɗa musu tabarman kaba, suka zauna sannan aka gaisa

Inna tace, "ga shi kuma Malam ba ya nan, amma yanzu zan sa a kira shi."

Umma tace, "bari Ni in kira sa, zauna Innan Ummi." Ta ƙare maganar tana mike wa da sauri tayi ɗaki

While su kuma suka sake gaisawa, Inna tana tambayar mutanen gida, sai kallon Sadiq dai take yi, sai a lokacin ma ta tambaya tana cewa, "wai wannan SHAREEF ne ko Babanmu? Ni ban gane shi ba."

Dady cikin barkwancin shi yana shafa kan Sadiq ɗin tare da cewa, "ka ganka, ka yi tsawon ƙafa duk sun kasa gane ka, to nema kake ka fi yayyin naka ma Sadiqu."

Baki a washe Inna tace, "wai yanzu Sadiq ne haka? Ikon Allah! Wlh yayi saurin girma, kamar ba sa'an su Bashir ba, Ni wlh in ka bar Ni zan iya cewa a cikin su Baba ko SHAREEF ne."

Dariya suke yi dukkan su. Inda Innan take sake cewa, "Sadiq ka yi girma da yawa, anya baza mu nema maka Mata a nan ba? Kawai ka dawo wurin mu da zama."

Sai dariya yake yi yana sussunne kai, su kuma suna taya sa Inna tana ci gaba da tsokanar sa

A haka Umma ta dawo ta sanar musu, "yana nan tafe."

"Ai da baku kira shi ba, zaku katse mishi hanzari."

"To Yaya ai dole a kira shi tunda yanzu sai magriba shi da ya dawo gidan nan, kuma ai ba nan da nisa bane, gwara ya zo ku gaisa kafin ku tafi."

Abinci suka so kawo musu, amma Dady ya hana, yace, "baza su ci komai ba su bar shi kawai."

Daƙyar ta samu suka sha ruwa, shima Sadiq ne ya sha amma Dady bai sha ba

Babu jima wa kuwa sai ga Baba ya iso.  Ya shigo suka gaisa faram-faram cikin girmamawa 

A lokacin ma har Umma ta kusa gama abincin rana, shiyasa Baban yace, "a zuba musu su ci gaba ɗaya."

Bayan sun ci sun natsa ne, sai Dady ya kawo nashi bukatun, na son tafiya da Maryamu can Kano ta zauna a wurin sa

Baba dai ya kasa ƙin amince masa, amma yace mishi, "ya fi son Maryamu tayi aure ne gaskiya, saboda har ga Allah ba ya son tayi zurfi a karatu, musamman yanda ita Maryamun halin ta ya fita daban a gidan nan, kuma ka ga akwai ƴar uwanta da suka taso tare za a yi musu auren gaba ɗaya, shiyasa hankali na zai fi kwanciya Maryamu tayi aure, amma ban ƙi ta taka ba Alhaji."

Murmushi Dady yayi tare da cewan, "ai Ni nayi ninyar tafiya da Maryam, tunda naga da alamu tana da buƙatar bin mu, musamman dana kwaɗaita mata komai zurfin karatu zata yi shi, Ni zan ɗauki nauyi, don haka wannan ba wata matsala bace in har zaka bani ita sai in nema wa ɗana auren ta, kafin mu tafi sai a ɗaura mata aure da SHAREEF; hakan zai fi ko?"
[18/01, 9:58 am] OumƊahirah نفيسة: 🌱🌱🌱🌱🌱

      *SHAREEF*
          _SexyBoy_
🌱🌱🌱🌱🌱


_Writer: Nafisat Isma'il Lawal_
_Wattpad: UmmuDahirah_

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝*



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

       *P.W.A✍️*





*DATA SHARE*

Call, message or whatsap  07065334256

*MTN*
500MB 150
1gb  280
2gb.  560 
3gb.   840
4gb.    1120
5gb      1400
6gb.     1700
Verlid for 30 days.












__________
*BOOK1*
_______________*FREE PAGE11*
           Baba ya kasa yin magana sabida jin maganar da Dady ya zo mishi dashi

Sai Dadyn ne yake cewa, "kar ka damu Malam Haruna, ai yanzu mun zama ɗaya, dama ina buƙatar SHAREEF yayi aure a wannan gaɓar, kuma haƙiƙa zan ji dad'i idan har Maryam ta auri ɗaya daga cikin ƴaƴana; sabida hakan zai ƙara ƙarfafa mana zumunci, to na yaba da hankalin Maryam na san zasu dace da ɗana SHAREEF, idan ma kana wasi-wasi ne a kan haɗin, za ka iya faɗan ra'ayin ka ko kuma in turo SHAREEF ɗin ku gana sabida ku san wanda ƴarku zata aura."

"Haba dai? Wlh kar kayi wani tunani a ranka, shirun da ka ga nayi farin ciki ne ya yi min yawa wlh, na san Hafsah zata fi ni farin ciki tunda haɗin zumunci ne babba, Ubangiji Allah ya sanya albarka da alkhairi a cikin wannan auren da zamu ƙulla, gaskiya nayi farin ciki matuƙa." Cewar Baba da rawan murya, yayinda fuskarsa a washe matuƙa da murna

Shima Dady yana murmushin yake cewa, "sai dai alfarman da zan nema shi ne, zuwa gobe zamu tafi Insha Allahu, ko yau ko gobe sai a ɗaura auren su mu wuce da ita."

"To to, ai babu damuwa Alhaji, duk yanda ka ce, Maryamu dai ɗiyarka ce duk yanda kake so haka za a yi, fatana dai a ce mun ƙulla alkhairi wanda zai jawo farin ciki a zukatan mu gaba ɗaya."

Daga haka Dady yace, "a bari zuwa gobe sai a ɗaura auren su wuce, yanzu dai duk a sanar da jama'a tunda ƙurarren lokaci suke dashi".
***


         Koda Baba ya sanar da su Umma Jummai zancen auren, haƙiƙa sun yi farin ciki sun nuna murnan su, barin ma Inna domin tamkar ta zuba ruwa a ƙasa ta sha, yau ga shi ƴarta zata auri ɗan ɗan uwanta, dama a koyaushe tunanin ta da damuwar ta bai wuce inda Maryamun zata yi aure ba, sabida halayyarta na rashin haƙuri, ga rashin kunya da tsiwa, wannan idan bata yi dace da mai ƙaunarta ba a lokaci guda zata cika sa ya sake ta, Maryamu tana da ƙarancin hankali da wauta; girman ne kawai a jiki amma sai rashin jin magana, ta san idan ta je gidan ɗan uwanta zasu riƙe ta amana, musamman ma da ta san Momy Mace ce mai matuƙar kirki da kawaici, tabbas Maryamu ta samu gidan dattako, sai dai kawai halin Mijin ne da bata sani ba har yanzu, tunda ba wai zuwa suke yi ba Yaran shiyasa baza ta iya gane halin kowannen su ba, but tana kyautata zaton samun farin ciki mai ɗaure wa ga Maryamun.




            Dangi sun yi murna, wasu kuma suna ta mamakin yanda auren ya zo a bakatatan, musamman yanda suke ganin Alhaji Ahmed shiyasa suke cewa, "dama kuɗi ai babu abun da ba ya sa wa, Malam Haruna ya siyar da ƴarsa kawai, idan ba haka ba; aure a rana ɗaya kacal? Ai wannan maganar abun duba wa ne."

Babu dai wanda ya saurare su. Don a ranan ma Sadiq da shi da Bashir da Halliru, tunda sa'annin juna ne, tare suka tafi cikin Zaria suka ɗauko Maryamu

Tun a waya Baba ya kira Iya Samira, ya shaida mata halin da ake ciki, farin cikin Iya ba ya misaltuwa, don har guɗa take ta faman yi tsaban murna

Ita kanta Maryamun har da rawa da Iya Samira ta shaida mata batun. Oh! Yau ga shi ita ce zata auri ɗan masu kuɗi? Tun kafin a je ko'ina burinta zai cika. Ko kaɗan bata damu da sanin wane ne shi ba, amma ta san tabbas shima kyakkyawa ne kamar su Sadiq, ta san ta more tunda gidan masu hannu da shuni ne, shikenan yanzu ta koma ƴar gayu, karatu kuma sai ta ture kenan?

Sai baza ɗuwawu take yi a tsakar gidan tana rawa tana gantsare wa da faɗin, "ah ha! Eh.. eh.. eh... Yau burina zai cika, na zama Amarya, gobe za a ɗaura eh... Eh... Eh.., Shikenan na zama Matar santalelen saurayi, wohh! Ni Maryamu Matar manya, kai dad'i kashe Ni, farin ciki zai kar Ni."

Iya Samira ta taka mata birki tana cewa, "amma ke kam an yi sakaryan yarinya, tsaban rashin kunya a gabana kike rawa kina wannan gantsare-gantsaren? Maimakon ki shiga damuwa sabida rabuwa da zamu yi amma kike murna?"

Dariya ta kwashe dashi tana tafa hannu da faɗin, "Ahayye Iyalle na. Wanne damuwa bayan kina ji aure zan yi gobe? Kuma ɗan guyu fa zan aura ɗan Kawuna, haba dai, ai damuwa ta kau na rantse da Allah, kar ki damu ai ba mutuwa zan yi ba, duk inda na je zanna riƙa dawowa muna gaisa wa, kai Iya ba abun farin cikin ki bane ma ki ganni Nima na zama ƴar masu kuɗi?" Sai kuma ta nufo wurin Iyan tana cewa, "amma Iya gidan su akwai bene ko? Akwai kuma teyes ko?"

"Da Allah ja can, ina ce ba zuwa gidan za ki yi ba? Ki bari idan kin je za ki gani, sakaryan yarinya kawai, ki tashi ki haɗa kayan ki ga su Sadiq nan zasu zo ɗaukar ki."

Tura baki Maryamu tayi tana taɓe shi, ta miƙe tana maganganun ta ƙasa-ƙasa, "ai sai kiyi tayi, Ni dai nayi gaba babu mai hana Ni nuna farin cikina, yo Ni ina ruwana." Ta shige ɗaki tana ci gaba da raira ma kanta waƙa, tana ta rawa da ɗuwawu tana tuttura su

Iya Samira tana jin ta amma bata ce komai ba, sai ta ci gaba da ayyukan ta, tana gama wa ta ɗauki gyale ta wuce gidan su don ta shaida musu auren

Maryamu ma bata san ta fita ba, sai da ta fito tana ta ƙwalla mata kira amma ta ji shiru, sai itama ta saka kai ta fice a gidan

Har su Sadiq suka iso bata dawo ba. Itama Iya Samira har ta haɗa kayanta tace, "zata bi su, su tafi tare, itama ta kwana a can." Duk da ta so sai gobe ne ta taho da sauran dangi da zasu je, amma kuma sai ta canza shawara gwara ta bi su kawai

Ana ta neman Maryamu sai daga baya ta dawo, nan Iya Samira ta rufe ta da masifa tana tambayarta, "ina ta je bayan ta san jiranta ake yi?"

Bashir yace, "ai Iya wannan yarinyar shegen yawo ne da ita, Allah yasa dai baza ta yi halin nata a can ba, don yanzu ba da bane, za ki tafi da auren ki ne, idan kika yi yawo a can babu wuyan an sace ki dan ubanki, sai dai ki ganki a gidan yankan kai kina ƙwalala idon nan kamar robber."

Dariya suka kwashe dashi, daga Sadiq har Halliru

Ita kuma ta zumɓuro baki tana cewa, "ka manta ne kwano ne, haushin rashi dai, kai mu ga naka robbern, da ƙwaƙulallen idonka kamar mazubin ruwa."

Ai kuwa ya biyo ta a guje, ta kwasa bayan Iya Samira tana ihu kamar zata fasa gidan tun kafin ya taɓa ta

"Don Ubanki Ni kike faɗa wa haka? Dama kwana biyu hannuna ƙaiƙayi yake yi ban bugi banza ba, amma yanzu zan fara har ki tafi zan bugi rabo na."

Iya Samira ta ture sa tana cewa, "an yi babban banza wlh Bashari, ƙaton kawai, ka rasa da wa zaka yi faɗa sai da ƙanwar ka? ai kai kake ja take raina ka ma, dalla ja can, idan ka kuma dukan ta zan saɓa maka, baza ka bari ba?"

Sai da ya ƙara ranƙwashin ta a kai, sannan ya haƙura yana ƙwafa tare da cewa, "wlh Iya ba ki san yanda yarinyar nan ta raina Ni bane, Allah yasa ma idan ta je can Yaya SHAREEF ya riƙa jibgar ta kamar Jaka."

Kafin kowa yayi magana, Maryamun ta cafe tana kuka da haki tace, "wlh ba Amin ba, ƙarya kake mugu azzalumi, kuma bakin ka ya sari ɗanyen kashi, mugu azzalumi, luluup!  Wowhowho! Yana jin haushi ne dai zan koma gidan masu kuɗi."

Yanda take maganar ne duk sai ya basu dariya

Itama kuma sai kuka take yi babu hawaye, tana ci gaba da tsiwan nata, har da yin ma Bashir ɗin gori, "wai ko ya zo can baza ta bari ya shigan mata gida ba, sai dai ya koma, kuma wlh idan ma ta zo nan itama baza ta nuna ta san shi ba, kashi ma mai ɗoyi sai ya fi shi daraja."

"Haba ƴar ƙanwar mu, ki yi shiru mana haka, mu je kinji ki ɗauki kayan ki mu wuce, kinga dare ya soma yi, ki bar wannan Yayan naki, yanzu Ni ne Yayanki ba shi ba." A cewar Sadiq da ya riƙo mata hannu yana rarrashin ta

Ita kuma sai dage wa take yi tana ƙara ƙwaƙulo kukan nata, sai a lokacin ne ma ɗan ɗiss na hawaye ya fita a idanunta

Bashir sai mata dariya yake yi, yana cewa, "zai kama ta ne, su koma gida ta ga yanda zai yi da ita, banzar yarinya mai kuka babu hawaye."

Iya Samira tace, "ga ka nan ƙaton banza, ka dena tsokanar ta ka zo ka ɗaukar mana kaya mu tafi."

Tare da Bashir da Halliru suka ɗauki jakan kayan nasu. Shi kuma Sadiq tuni ya ja Maryamu sun fita tare zuwa wajen mota. Ya shiga gaba itama ta zauna a gefen sa, su Iya Samira kuma suka zauna a baya sannan suka wuce ƙauyen.
*****


        Washe gari kamar yanda aka sanar wa da jama'a, da ƙarfe 07:00am. kowa ya shaida auren Muhammad SHAREEF Ahmad da Amaryan sa Maryamu Haruna, a cikin sadaki ƙalilan domin samun albarkan auren

Zuwa ƙarfe biyu suka yi musu sallama suka ɗauko hanyar Kano

A lokacin da suka isa, Momy ta gama shirya musu abinci tunda ta san da zuwan nasu, har labarin auren, shiyasa take ta murna, tunda ta ji diran Motan su ta fita ta tarbe su a can, hannun Maryamu ta kama tana murmusawa da cewa, "ƴata sannu da zuwa."

Maryamu na faman washe baki da sunne kai ta kasa amsa wa

Sai Momyn ta kalli Dady tace, "kuma ƴar tawa tubarakalla Masha Allah, I didn't expect to see her like this. so beautiful."

"Allah ko?" Cewar Dady yana dariya

Shi kuma Sadiq cikin farin ciki yace, "Momy sai ma kin zauna da ita, tana da shiga rai, na samu ƙanwa. In fact, I am more than happy that she is with us, I am very happy."

"To ku mu je ciki, mu dena tsayuwa a nan, kai Sadiq shigo da kayan namu kawai." Dady ya furta yana yin gaba

Momy ta bi bayansa hannunta saƙale a cikin na Maryamu 

While Sadiq ya tsaya daukar Jakar su. Har ɗaya daga cikin masu aikin gidan ya zo da nufin ɗauka, but sai ya tsayar dashi yana murmushi tare da cewan, "a'a, bar shi kawai zan ɗauka." Ciro Jakar yayi, da nasu dana Maryamu da ta ɗibo kayanta kaɗan a ciki, ya nufi ciki da su

A falo ya tarar da su zaune, Maryamu na kusa da Momy ta manna ta a jikinta tana ce ma Dady, "gaskiya ya kyauta da ya yanke wannan hukuncin, don farin cikin da take ciki baki ma bazai iya misalta shi ba, musamman da ta ga Maryamun zata yi dai-dai da ra'ayin ɗanta; domin sun dace matuƙa, ita farin cikin ta ma yanda aka kawo mata ƴa, don yanzu ta samu ɗiya Mace, ko ba haka ba Maryam?" Ta ƙare maganar tana kallon Maryamu fuskarta cike da fara'a

Kai Maryamu ta ɗaga mata tana ƴar dariya sai wurga ido take yi tana kallon tsarin gidan

"Yauwa, kinga daga yau sai ki riƙe Ni a matsayin Mahaifiyar ki, kamar ƴaƴana ke ma kina kira na Momy ko?"

Sadiq da ya zauna yana cewa, "Ni kuma Momy yanzu na tashi a sahun Auta, ga Auta nan kin samu, don nima yanzu na girma, har Innanta tace zata bani Mata a can."

Baki Momy ta buɗe tana dariyan maganar sa

While Dady yayi masa daƙuwa da cewa, "ka ganka? Ashe baka da kunya kaima? A gaban mu kake furta wannan maganar?"

"I'm sorry Dady, ALLAh wasa nake yi fa."

"Shikenan, amma maganar da zan yi yanzu, ga dai Maryam ta zo gida a matsayin Matar SHAREEF, duk da ban so ta tare a wannan lokacin ba saboda karatu da nayi mata alƙawarin zata yi, but zamu jingirta tarewan ta zuwa nan da kamar 1year in ta saba damu, zata ci gaba da zama a nan batare da kowa ya san Matar SHAREEF bane, don haka kai Sadiq na san halin ka kar ka sanar da ƴan uwanka komai a kai, ka bari idan lokaci yayi sai mu sanar musu har shi SHAREEF ɗin."

"To Dady, bazan faɗa ba Insha Allahu."

Momy kuma ta so tayi magana a kan maganar, sai kuma ta fasa tana cewa, "bari in kai ƴata ɗakin ta idan tayi wanka sai mu ci abincin gaba ɗaya, tashi daughter in nuna miki dakin da za ki zauna ko."

Miƙewa Maryamu tayi bayan ta amsa da to, suka nufi ƙaramin corridor da ke nan downstairs, ɗakin da Momy ta kaita a nan ƙasa yake tunda saman babu wani ɗakin kuma. Sadiq ya biyo su da kayanta ya ajiye ya fita. Ita kuma Momy ta nuna mata komai tana cewa, "duk abun da bata gane ba sai ta tambaye ta, yanzu ta shiga tayi wanka sai ta canza kayanta ta fito suna jiranta."

Su ma su Dady sallah suka je suka yi, tunda a hanya la'asar tayi musu, sannan suka dawo suka zauna a Falon

Jin shiru Maryamu bata fito ba, sai Momy ta leƙa ta ta ganta tana ƙoƙarin saka riga

Da sauri Maryamu ta duƙa tana ɓoye jikinta sabida kunyar shigowar Momyn ta ganta a haka

Murmushi Momy tayi, bata ce komai ba sai tace mata, "har yanzu ba ki shirya ba ashe? To yi sauri ki gama, ki yi sallah sai ki fito ko?"

"To Momy." Ta furta tana zazzare ido still tana duƙe a ƙasa

Murmushi Momy tayi tana fice wa a dakin, ita kanta mamakin yarinyar take yi, ga ta ƙarama da ƙira mai kyau, mamakin saurin girman ta take yi tunda bata manta sanda suka je sunan yarinyar ba, farin ciki ne ya ƙara cika zuciyar Momyn, tana ganin kamar ɗanta ya gama dacen Mata, ƴar kyakkyawa da ita, ko ita Mace ta bata sha'awa bare namiji, wannan idan ta samu gyara ba ƙaramin ƙara direwa da kyawu zata yi ba, "hmm Allah yasa SHAREEF ya so ta." Ta furta a fili tana ci gaba da murmusawa. Wurin su Dady ta koma tana zama tare da cewa, "ga ta nan fitowa."

"Bari in je in ɗan huta a ɗaki, sabida akwai aikin da nake so in yi."

"Amma Alhaji baka ci abincin ba zaka tafi?"

"Deeja ba na jin yunwa yanzu, sai dai zuwa dare, but ki haɗa min coffee sai ki kawo min in sha."

"To Shikenan." 

Shi kuma Dadyn ya wuce zuwa sama

While Momy ta kalli Sadiq tace, "Sadiq zuba abincin mana ka ci, ka dena danna wayan nan haka."

"Ok Mom." Yayi maganar yana miƙewa tare da nufan dinning ɗin, chart yake yi yana sanar da Hanif auren SHAREEF ɗin da aka ɗaura yau, yana faɗa masa, "but kar ya sanar da SHAREEF tunda Dady sai da ya gargaɗe shi."

Fitowar Maryamu daga ɗakin, shiyasa Momyn bata tafi ba, ta bi ta da kallo tana cewa, "kin yi sallan daughter?"

"Eh nayi."

"To je ki wurin Sadiq ki zauna ki ci abincin ki, ki cika cikin ki fa ba na son ganin ki da yunwa, ina zuwa."

Murmushi Maryamu tayi tace, "to Momy." Sai ta nufi wurin Sadiq ɗin da saurin ta

Ita kuma Momy ta wuce kichen

Sadiq yana ganinta ya ajiye wayan yana dariya da cewa, "ƴar ƙanwata, wannan ɗigon a goshi fa?"

Itama dariyan tayi tace, "kwalliya mana, but i forgot ban shafa hoda bane, i like ɗigon goshin."

"Wow! Kin iya turanci ashe?"

Fari tayi da ido tana tallabo kumatun ta da hannayenta dukka, sai tace, "ƙwarai kuwa, I'm sure I learn."

Dariya ne ya suɓuce masa, sai yayi kamar ta burge sa ne, yace, "wow! Wow! My dear, I'm happy fa, gaskiya kin burge Ni, to me za ki ci in zuba miki?"

Kallon plate ɗin gaban sa tayi, sai ta wani yatsina fuska tana wurga ido da cewa, "anything ma zan ci. Amma ka zuba min irin naka."

"An gama ranki ya daɗe! Matar Yaya SHAREEF." Ya furta yana ƴar dariya tare da ƙoƙarin save nata

Sai ta ɗan rage murya tana matso da fuskarta, cikin murmusawa tace, "wai Yaya Sadiq, ina Mijin nawa yake? Na ga har yanzu ban ganshi bane, zan so in ganshi wlh."

"Oh! Kar ki damu, yanzu za ki ga ya dawo ma, time ɗin tashin sa a wurin aiki yayi, za ki ga ya shigo." Sai ya nuna mata hotunan da suke can bangon falon yace, "kin ganshi can Yaya SHAREEF ɗin."

A kan pictures ɗin su, su uku idanunta suka sauka, sai kuma ta kalle shi tace, "wanne daga ciki? Na ga duk kuna kama?"

"Wancan mana, wanda yayi murmushi kaɗan na hannun dama."

Baki ta washe tsaban murna, sai kuma tace, "wlh ya haɗu shima, kenan wannan shi ne Mijina Yaya Sadiq?" Tayi maganar tana dawo da idanunta a kansa

Murmushi yayi yace, "eh mana Maryam, Yaya SHAREEF kenan, shi ne babban Yayanmu, sai Yaya Hanif, but yanzu yana school a ƙasar waje, in ya dawo zaku haɗu ai."

Farin ciki ya cika Maryamu sai kallon fuskar SHAREEF take yi

"To ki ci abincin mana kar yayi sanyi."

"Wlh mamaki nake yi Yaya Sadiq, wai a ce wannan Baturen ne Mijin dana aura. Ashe gaskiya Nima mai Sa'a ce, yana da kyau sosai, ban taɓa ganin mai kyau irin sa ba wlh, har ya shiga raina nima ina son sa sosai."

Ganin yanda take maganar cikin gaskiyar ta, sai yace, "ai ke ma mai kyau ce Maryam, ko ba ki taɓa jin an ce miki kina da kyau bane? Musamman in kika yi murmushi dimples ɗin nan naki suka fito irin na Yaya SHAREEF, suna ƙara miki kyau, ga manyan idanu kamar irin na Momy."

Dariya tayi tace, "ai haka ƴan ƙauyen mu suke cewa, shiyasa nake tsula tsiyata wlh, na ƙi kowa sai ɗan birni mai waye wa."

"Sai ga shi kin samu kuwa." Ya faɗa yana dariya. Itama tana taya sa

Lokacin Momy ta fito daga kichen ɗin, tana cewa, "wai abincin kuke ci kuwa ko surutu? Ka zuba mata abincin Sadiq?"

"Eh Momy, ga shi nan zata ci."

"Ok to, bari in kai ma Dadyn ku coffee, Maryam ga Yayanki nan sai ku zauna tare ina zuwa."

"To Momy."

Tana tafiya sai Sadiq yace, "ki ci abincin mana ki dena surutu."

Dariya tayi, sai kuma ta saka cokalin ta soma cin abincin cike da farin ciki, tana yi tana kallon fuskar SHAREEF cike da wani irin tsagwaron annashuwa. Zuciyarta fari ƙal sabida ganin wane ne Mijin nata, ai ta more kuwa in dai wannan ne Mijinta, lokaci ɗaya ta ji ta kamu da sonsa har a cikin zuciyarta, irin Mijin da take mafarkin samu sai ga shi Allah ya bata, haƙiƙa Allah na sonta, to amma shi zai so ta? Allah yasa ya so ta shima kamar yanda take jin ƙaunar sa ya ɗarsu a cikin ƙalbin ta, babu mai raba su wlh.
[20/01, 8:16 am] OumƊahirah نفيسة: 🌱🌱🌱🌱🌱

      *SHAREEF*
          _SexyBoy_
🌱🌱🌱🌱🌱


_Writer: Nafisat Isma'il Lawal_
_Wattpad: UmmuDahirah_

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝*



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

       *P.W.A✍️*





*DATA SHARE*

Call, message or whatsap  07065334256

*MTN*
500MB 150
1gb  280
2gb.  560 
3gb.   840
4gb.    1120
5gb      1400
6gb.     1700
Verlid for 30 days.












__________
*BOOK1*
_______________*FREE PAGE12*
             Daga hall da suka yi taro suka fito, kai tsaye hanyar office ya nufa cikin takunsa na ƙasaita a kuma natse. PA ɗin sa na biye da shi a baya har zuwa cikin office din sa 

Shigan sa office din, sai ya kai duban sa kan agogon hannunsa yana jan tsaki, ganin har 7 ta kusa, kallon PA ɗin yayi, wanda yake ajiye masa documents a saman table. Guntun tsakin ya sake ja, cike da sanyin muryan sa yace, "What time will we have the meeting tomorrow?"

"Sir, by ten ne."

"Shikenan ku yi magana da Shuraihu a kan kayan nan, and ka sanar da Mr. Pitter by tomorrow zamu shiga meeting din."

"Ok sir, I will let him know."

Bai ce mishi komai ba ya matso bakin table ɗin, yana ɗaukar bairo ya buɗe da nufin yin sing

Shi yasa nan da nan PA ya buɗe mishi ɗaya daga cikin document din yayi sing a ciki. Yana gama wa sai ya rufe yayi masa sallama ya fice

Shi kuma SHAREEF ya tattara kayansa tare da ɗaukar ƙaramar jakarsa ya fito

Da sauri PA ya zo zai amshi jakar hannun nasa

"No leave it." Ya furta a yatsine yana yin gaba da saurin sa after ya jefa masa keys na office din sa. Kai tsaye bakin motan sa ya nufa ya buɗe ya jefa jakar, ya shiga ya ja cikin sauri sabida gaba ɗaya ya gama gajiya, yau bai tashi da wuri ba ga shi har 7 ya kusa, tun karfe 4 suke meeting a kan haɗakar kwangilar da zasu amsa da wasu Companonin, a kwanakin nan duk meeting suke yi sabida yanda zasu tafiyar da tsarin, gobe ma haka duk zasu haɗu da sauran Companyn da zasu yi haɗaka su tsayar da magana ɗaya. So yau kansa yayi zafi sosai shiyasa ko wani abu bai nema ya saka a cikin sa ba illa ruwa, shiyasa ransa duk a jagule yake

Yana isa bakin gate ɗin su, ya danna horn da ƙarfi kamar zai tashi gidan, akai-akai yake danna wa cikin sauri

In a hurry Mai gadi ya zuge mishi gate, sai ya ja motan a guje zuwa packing space. Bai ɓata lokaci ba ya fito daga motan riƙe da jakarsa yayi hanyar gidan. Kamar yanda ya saba yau ma bai yi sallama ba, tunda ba sabon shi bane sai ya ga dama, ko kuma yayi a ciki-ciki, yau kuma yanda yake jin sa a tsananin gajiye ya ƙosa ya huta. Yana shiga idanunsa suka sauka a kan su Maryamu da ke zaune a falon; ita da Sadiq suna ta hira suna dariya. Ɗan tsaya wa yayi yana kallon fuskar Maryamun cike da mamakin ganin baƙuwar fuska a gidan, ganin yanda take bin sa da kallon itama ko ƙyafta ido ba ta yi, sai ya turɓune fuska yana takowa zuwa ciki

Sadiq yace, "sannu da zuwa Yaya."

Kallon Sadiq ɗin yayi, kamar zai yi magana kuma sai ya dauke kansa ya sake mayar wa kan Maryamu. Da mamakin sa sai kuma ya ga ta washe mishi haƙora

"Sannu da zuwa Yaya SHAREEF." Ta furta cikin murna tana ɓashe baki, sai dimples ɗin ta dukka suka bayyana fili suka kara wa Black beauty face ɗin ta kyawu

"Wannan kuma daga ina?" Ya furta yana yatsina fuska

"Yaya, Maryam ce, tare muka taho da ita ƴar kanwar Dady ne."

"Oh God! what kind of frustrating is this? What will she do for us at home; and you bring her?" Sai ya ja tsaki yana yin gaba cikin sauri, har yana haɗa wa da gudu a kan matattaƙalan benen 

Da kallo Maryamu ta bi bayansa dashi cikin farin ciki, har ya ƙule ta kasa ɗauke ido a kansa sabida yanda take jin tamkar ta bi bayansa, ya mugun tafiya da ruhin ta musamman yanda ta ga yana magana cikin aji da tsantsan wayewa, muryansa mai matuƙar sanyi da daɗin sauraro

Taɓo ta Sadiq yayi yace, "ai ya tafi ko?"

Kallon Sadiq ɗin tayi, sai kuma ta rufe idonta cikin kunya tace, "har ka bani kunya wlh, ban san ina kallonsa ba fa."

Dariya Sadiq yayi yace, "ikon Allah!"

"Amma fa ya haɗu Yaya Sadiq, ya fi kyau ma a fili, kuma ka ga ban san me yace ba ma da turancin."

Jin hakan sai Sadiq ya sake murmusa wa tare da cewa, "ba da ke yake yi ba ai."

Shiru ta ɗan yi, sai kuma ta ɗan ɓata fuska da cewa, "yanzu shikenan bazan faɗa masa Ni Matarsa bace? Yanzu bai san Ni Matarsa bace ba ko?"

"Eh, kin san me Dady yace ai, kar ki sanar mishi kinji ko? But da alamu kina sonsa Because I see that in your eyes?"

Kanta ta ɗaga tana yin fuskar tausayi

"Yauwa sai ki dage ke ma ki saka sonki a zuciyarsa, hakan ne zai sa kawai Yaya SHAREEF ya riƙa kallonki yana kula ki, domin shi ba irin halin ƴan gidan nan ne dashi ba, yana da wuyan sha'ani, da sannu za ki fahimci ko wane ne shi kinga sai ki riƙa kiyaye abun da ba ya so kin ji?"

Dariya tayi tace, "to Yaya Sadiq, ai nima ka ce ina da kyau, kuma Nima na san haka, baka ga daga shigowar sa ba yana ta kallona ba? Shima ya ga na burge sa ne, ya ga ina da irin wannan lotsawar na kumatun sa, bare in na zama ƴar birni ina saka kaya masu kyau da tsada." Sai ta kaɗa harshen ta da cewa, "ka bari ka ga yanda zan nuna mishi kalan tawa soyayyar, shima sai ya riƙa bi na kamar sauran Samarina na ƙauye."

Kumatu Sadiq ya tallabo yana bin ta da kallo yana dariya, da alamu ya lura yarinyar tana da wauta da ƙauyanci irin na ƴan ƙauye. sai kuma yace, "I know za ki iya ai, Mijinki ne dama ya kamata ki yi ko mene ne, Ni nan zan ba ki satar amsa a kan abubuwan da yake so da wanda bai so, amma yanzu kinga time na sallan magriba ta gabato, Let me tell you some other time."

Kaɗa masa kai tayi duk da bata fahimci mai yace a karshen ba

Sai ya miƙe yace mata, "bari ya je dakinsa zai yi alwala ne, idan Momy ta fito yana ɗaki." Sai ya kunna mata kallo yace, "ki yi kallo ya ɗebe miki kewa before a kira sallan ke ma sai ki je ki yi ko?"

"To Yaya Sadiq." Ta amsa mishi tana kallon TVn

While shi kuma ya wuce saman benen.
***

          Momy kuma da takai ma Dady coffee din, lokacin har ya gama waya da su Baban Maryamu, har Iya Samira ya kira sun gaisa ya sanar mata, "sun sauka lafiya." Ya sauke wayan kenan Momy ta shigo. Shine yake sanar mata, "ya kira Zaria ne ya faɗa musu sun sauka lafiya, sun ce a gaishe ta."

Sai da ta zauna sannan ta amsa, tana cewa, "ai da ya bari ta zo sun gaisa tunda bata samu damar zuwa ba."

Dady yace, "kuma kinga shaf na manta, dayake ƙanwata Hafsah ita ta soma kira shiyasa, amma zuwa gobe sai ki kira su ku gaisa ki bama Maryam itama."

Momy tace, "to Allah ya kaimu.",
A nan kuma ta sauya alaƙar maganar nata da tambayar sa, "meyasa bazai bari Maryamu ta tare tun yanzu ba tunda yarinyar ba wata ƙarama bace sosai? Ta ishi SHAREEF su zauna lafiya a haka, saboda maganar ma Doctor da ya faɗa musu hakan zai fi, kar kuma a zo abun ya ci gaba daga baya ya fi ƙarfin sa ya faɗa halaka."

Numfashi Dady ya ja bayan da ya ajiye coffee din da ya kurɓa, tare da cewa, "nima nayi tunanin hakan, but kinga duk da haka Maryam ƙaramar yarinya ce, just she's 15years, kuma tana da son karatu sosai na kula da hakan, abun da yasa ma ta yarda ta biyo mu kenan, shi kuma auren da aka yi mata don Mahaifinta ya fi ƙaunar ta tafi da auren ta ne that's the reason da na yanke wannan hukuncin, duba da yanda doctor ya faɗa mana matsalar da ke damun SHAREEF, ba hakan kuma zai sa mu tauye wa yarinyar haƙƙin ta bane, Ni ina ga ta zauna a wurin mu ta soma fahimtar rayuwa da abun da ya kamata da ita before a kaita ɗakin Miji, yana da kyau ta samu ilmi since kinga yanda SHAREEF yake, zai iya bamu matsala musamman idan ya ganta ƴar ƙauye ce, kin san halin sa tunda mu muke zaune da shi, don haka gwara ta soma zama da mu for some time, ke ma ki riƙa koya mata wasu abubuwan da kuma abun da SHAREEF yake so, and kina kula da shi shima yanda ya ɗauki yarinyar, in kinga akwai kyakkyawar fahimta a tsakanin su fine, zamu iya ba shi Matarsa su zauna a gidan nan, before zuwa wani lokacin sai ya zaɓa gida daga cikin gidajena su koma."

Murmushi Momy tayi da cewa, "shawara mai kyau Dadyn mu."

Hakan ne yasa shima Dadyn yin murmushi yace, "yana da kyau ke ma ki bada taki gudummawar fa."

"Insha Allah, kar ka damu, Maryam ai ƴata ce, kuma a yanda nake neman ɗiya Mace Allah bai bani ba, sai ga ta a yanzu na same ta cikin sauƙi, dole zan riƙe ta kamar Ni na haife ta, don haka zuwa gobe ma zamu shiga kasuwa sai nayi mata siyayya, fatan mu dai Allah ya haɗa soyayyar su abun farin cikin kenan."

"To ai jini ba wasa ba, ko babu komai Maryam jinin sa ne bazai taɓa ƙin ta ba, nima ina ga zuwa jibi zan sa SHAREEF ɗin ya kaita school ɗin Doctor a yi mata komai a can, inyaso zuwa Monday ta fara karatu, zan kira Doctor ɗin ma muyi magana cuz makarantar ya fi min, ana koyarwa sosai, kuma kinga har da islamiyya a can."

"Lallai ƴata ƴar gata ce, I enjoyed this topic, Allah yasa hakan shi ya fi alkhairi."

Dady ya amsa mata cikin fara'a yana ƙoƙarin rufe jaridan hannunsa, sabida jin ana kiran sallah

Ita kuma sai ta dauki farantin da ta daura masa coffee a sama, duk da bai shanye ba kurɓa biyu kacal yayi, sai ta fice dashi a ɗakin ganin yace mata, "bari ya shiga toilet yayi alwala, ta wuce dashi kawai ya gama."

Tana sauka ƙasa ta ga Maryamu kwance a kan kujerar tana ta kallo, "ah ah daughter, ke kaɗai ce? Ina Sadiq ɗin ya tafi?"

Da sauri Maryamun ta tashi zaune, tana kallon Momyn da cewa, "Momy ya shiga ɗaki zai je yin alwala."

"To shikenan, ke ma taso ki je kiyi sallan tunda an kira, ki je ɗakin naki da na nuna miki ki yi sallan a can."

Tashi Maryamun tayi after ta amsa mata, sai ta nufi ɗakin da saurin ta

While Momy ta bi ta da kallo tana murmusawa, sai kuma ta juya ta nufi kitchen zuciyarta tana bijiro mata wasu tunanin na daban.
*** ***


          Tunda ya shiga ɗaki, kwanciya yayi a saman gadon ko cumbas ɗin ƙafafunsa ya kasa cire wa, idanunsa a lumshe sai sauke ajiyar zuciya yake. Ya ɗauki good 10mint a haka before ya ɗago yana faman yatsina fuska da taɓe baki, alamun gajiya ce tsantsa da yunwa da ya ci ya cinye sa, shiyasa har yana jin gefen cikin sa ya soma ƙulle wa yana mishi ciwo kaɗan-kaɗan. Hakan ne yasa yayi ƙarfin halin soma yunkurin zare cumbas ɗin daga ƙafafun sa, sai da ya cire su gaba ɗaya sannan ya zuge necktie na wuyan sa ya zazzago da shi, sai da ya kwance agogon hannunsa sannan ya cire suit ɗin yana mike wa ya nufi toilet, takalman da ke bakin ƙofan ya zura a Zara-zaran ƙafafuwan sa farare ƙal kamar zasu tsillo jini don haske da tsafta, ya shiga cikin toilet ɗin ya soma kwarara ruwa daga saman sa har ƙasa batare da ya cire sauran rigunan jikinsa ba, sai da ya jiƙa kansa da ruwan sanyi ya ji sanyi ya ratsa mishi ƙwaƙwalwa da jikinsa, wanda har tsigan jikinsa tashi suke yi tsaban sanyin ruwan, yayinda shi kuma sai faman cije laɓɓa yake yi idanunsa a lumshe. Ya ɗauki like 5mint a haka before ya tuɓe ya silla wanka kamar zai canza halitta, ko kaɗan bai damu da lokacin Sallah da ta shiga ba. Sai da ya gama tsab sannan ya yi alwala ya fito ɗaure da towel, ɗaya kuma a kansa yana goge suman kansa. A bakin mirror ya dakata yana kallon kansa yana goge jikinsa, sai da ya tabbatar ya tsane jikinsa sannan ya ɗibi lotion a hannunsa ya soma shafa wa, after ya gama ya feshe lungu da saƙo na jikinsa da turaren jiki masu sanyin ƙamshi. Ya ɓata lokaci yana abu ɗaya wajen gyara suman kansa tare da ƙalƙale jikinsa kamar bazai taka ƙasa ba, don ma wai cikin sauri yake yin komai kasancewar ya ji har an fito sallah, shiyasa ya dakata ya koma ya ciro farar jallabiya ya saka a jikinsa, itama ya feshe ta da turaren sa me shegen ƙamshi, wanda ta game ɗakin gaba ɗaya, komai nasa irin ƙamshin ne already ya bi jikinsa da komai nasa, sai da ya gama sannan ya fice, ta ƙofan baya ya bi ya sauka ƙasa ta corridorn da ɗakin Maryamu yake, ya bi ta wurin ya fice ta wata ƙofan ya nufi Masjid.
***

       Su kuma suna falo dukkan su. Dawowar su Dady kenan yake tambayar Momy, "wai ina SHAREEF ɗin ne? Ya ga motansa a waje ya dawo but bai je masallaci ba?"

"To ai Ni ban ma san ya dawo ba, tunda bai fito ba." Sai ta kalli Sadiq tace, "Sadiq duba sa a ɗaki ko wani abun yake yi."

"Ok Mom." Ya furta yana miƙe wa ya nufi upstairs ɗin

Bai jima ba ya dawo yace musu, "ina ga ya fita fa, don ba shi a cikin ɗakin."

Sai Momy ta kalli Maryamu tace, "da kika fito falo kinga Wani ya fita ne?"

Girgiza kanta tayi tace, "a'a Momy, ban ga kowa ba."


"Ok, maybe, ya fita ta ƙofan baya ne, ba shi da gaskiya ne." Cewar Momy tana kaɗa kai, don ta san halin sa sau da dama hakan yake yi musamman in ba ya son su ganshi suna zaune a falo, ko zai fita batare da sanin su ba ko kuma an yi sallah har an idar bai je ba.
[22/01, 1:31 pm] OumƊahirah نفيسة: 🌱🌱🌱🌱🌱

          *SHAREEF*
              _SexyBoy_
🌱🌱🌱🌱🌱


_Writer: Nafisat Isma'il Lawal_
_Wattpad: UmmuDahirah_

   *SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝*



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

       *P.W.A✍️*





*DATA SHARE*

Call, message or whatsap  07065334256

*MTN*
500MB 150
1gb  280
2gb.  560 
3gb.   840
4gb.    1120
5gb      1400
6gb.     1700
Verlid for 30 days.












__________
*BOOK1*
_______________*FREE PAGE13*
                  SHAREEF bai dawo ba sai da aka yi sallan isha'i sannan suka shigo da su Dady

Lokacin su Momy su ma suna falo ita da Maryamu, sai labari Maryamun take bata don tuni ta saki jikinta kasancewar ta mai saurin sabo, sai zuba wa Momy labarin ƴan gidan su take yi itama kuma tana shan dariya

Shigowar su ne yasa suka dakata, bayan Momy ta amsa musu sallaman sai ta bi SHAREEF da kallo; da ke ƙoƙarin wuce wa kansa tsaye wajen dining, daƙyar ma yake tafiya tsaban yanda yake jin jikinsa babu ƙarfi, ga zafi da cikinsa ke masa hakan ne yasa shi kama gefen cikin nasa. Momy da ke kallon sa ganin yanayin nasa sai tace, "SHAREEF lafiyan ka kuwa?"

Juyawa yayi ya kalle ta, sai suka haɗa ido da Maryamu da ta kafa masa na mujiya kamar zata cinye sa ɗanye, hakan ne yasa ya haɗe rai yana duban ta sosai, kafin a hankali ya furta, "Mom lafiya."

"Anya? Kuma kake riƙe ciki?"

"Wai wannan yarinyar aina ku ka samo ta ne take bin mutane da kallo kamar wata mayya?" Yayi maganar cikin ƙunan rai ganin yanda Maryamun ta ƙi ɗauke ido a kansa tamkar ma ta manta da kallonsa take yi, ta tafi wata duniyar tunanin

Dady ne yace, "mayya kuma SHAREEF? Ƴar uwanka ce fa."

Itama Momy sai tace, "to laifi ne don ta Kalle ka? Kai da wanne idon ka ga tana kallon ka?"

Ɓata fuska yayi yana dauke kai, sai ya nufo wurin su kuma ya zauna ya fasa zuwa kan Dinnig ɗin, idanunsa a kan Dady yace, "Dady, welcome back from the trvl, ina tsaraba na?"

Dady na murmushi ya Kalle shi yace, "bayan ka ƙi bin mu kuma zamu baka tsaraba? To ga tsaraban nan na kawo maka Ƙanwarka zata zauna da mu a nan, zata yi karatun ta nan, sunan ta Maryam."

Maimakon SHAREEF ya furta wata magana a kan abun da Dady yace, sai ya kawar da kai yana ciccije laɓɓa, kamar zai yi kuka kuma ya kalli Momy yace, "Mom yunwa nake ji."

"Subhanallah... Kenan baka ci abinci a wurin aikin ba ko? Don na san halin ka dama?"

Tura baki yayi yana narai-narai da ido

Momy ta kalli Maryamu da har yanzu take bin SHAREEF da ido kamar zata zalalar da yawu, ya mugun tafiya da imanin ta don ji take yi tamkar ta haɗiye sa, Allah bata taɓa ganin wanda ya taɓa mata kyau da burge ta a cikin rayuwarta irin SHAREEF ba, ji be yanda yake shagwaɓa like a small boy, har tunani take yi a ranta, "dama manya na shagwaɓa ne? Ko kuma shi wannan ne daban da saura?"


Momy ne ta taɓo ta tana cewa, "Maryam, tashi ki je ki ɗibo ma Yayanki abinci a saman Dinnig ki kawo mishi."

"No Momy, ita ce zata ɗibo min abincin?" Ya furta maganar yana ware madaidaitan idanun nasa a waje; cike da sanyin muryansa da ta ƙara low daƙyar yake iya furta zancen ma

"To mene ne a ciki don ta ɗibo maka abinci SHAREEF? Ban son fa iyayi a nan; ƙanwarka ce." Momy tayi maganar tana hararansa

Shi kuma sai ya ɓata rai yana miƙe wa da sauri ya nufi wurin dining ɗin batare da ya sake magana ba, don a yanda yake ji ba ya jin zai iya magana mai ƙarfi, kuma ga haushin yarinyar nan da ya cika sa, kallon fuskarta ma tayar masa da zuciya yake yi bare ya ga sun haɗa ido, gaskiya akwai matsala in wannan bak'ar yarinyar mai fuskar Mage a gidan su zata zauna. He hates useless things in his life, ko meye na kwashe-kwashen abar nan oho? Sai ya ja guntun tsaki yana ƙara haɗe rai tare da zama a saman dining ɗin. Batare da ya sake kallon inda suke ba ya ɗaga murya a hankali yana kiran Sadiq

Hakan ne yasa Sadiq ya miƙe ya nufi wurin da saurin sa yana amsa mishi

While su Momy kuwa, basu yi mamakin abun da SHAREEF yayi ba, tunda akwai shi da tsantseni dama. Ko masu aiki shi ya hana a kawo su gidan sabida ya dinga hantarar su kenan kamar ya ga kashi, ba ya ƙaunar ya ga wasu sun raɓe su koda ƴan uwansu ne ba ya son baƙi a gidan

Ganin akwai Maryamun a wurin shiyasa basu yi wata magana ba, sai ma Momy da ta koma tambayar ta tana cewa, "ta ci gaba da bata labarin kauyen nasu."

Kamar jira take yi kuwa, ta buɗe baki ta ci gaba da bata labari

Dady cikin barkwancin sa yace, "shikenan ma kin samu ƴar taya hira babu ruwan ki da rediyo."

Dariya suka yi gaba ɗayan su. Har Maryamu tana ɓoye fuskarta wai ta ji kunya ta liƙe idanu

Dady yace, "to a fara kawo min abinci nan mu ci da ƴata before a ci gaba da bamu labarin, ai yau bamu ba kunna TV."

"Kamar ka sani kuwa Dadyn Yara, ai Ni yanzu sharr abu na; na samu ƴar taya hira, kallon ma mun dena yanzu, tana nan tana bani labarin ƴan ƙauyen su."

"Ai nima sai a yi dani ko Maryamu na?"

Ta washe baki tana cewa, "eh Dady."

"To bari Momy ta kawo abinci idan mun gama sai a dasa sabon labarin."

Momy ta tashi ta nufi wurin dining ɗin. Lokacin har Sadiq ya gama zuba wa SHAREEF nashi abincin, sai ya soma zuba nasa. Momy da ta iso wurin sai ta ja kunnen SHAREEF ɗin tana cewa, "SHAREEF ban san lokacin da zaka girma ba wlh, dayake ba ka jin magana ɗazu ana kiran sallah but ka ƙi zuwa sai da aka idar ko?"

"Momy wa ya faɗa miki?" Yayi maganar yana narai-narai da ido

"Ƙaniyar ka ta faɗa min, ai na san halinka tunda ka bi ta baya baka fito ka tafi sallah a kan lokaci ba, kuma wlh zamu sa kafar wando ɗaya da kai tunda sallan ne ka mayar abun wasan ka."

"Momy wlh ban dawo da wuri bane, kuma na tsaya yin wanka that's why ban je nayi sallan da wuri ba."

Ranta a ɓace tace, "to dole ne kayi wankan After you see it's prayer time?"

Shiru SHAREEF yayi yana duƙar da kai

"Ka kiyaye Ni fa, ba na son wannan shirmen, idan ka je ka haɗu da Allah mai zaka ce mishi? Sallan ne zata zama abar wasan ka? Kar ka kuma aikata hakan, in ba haka ba zaka ga ɓacin raina." Ta janye hannunta a kan kunnen nasa tana ɗaukar plate ta soma zuba abincin

Dady yana jin su amma bai ce komai ba

Ita kuma Maryamu idanunta a kansu tana mamakin yanda Momyn take masa faɗa, babba kamar sa ana yin masa faɗa shiyasa ta ji mamaki tunda bata saba gani ba, har zuciyarta kuma sai ta ji tausayin sa ganin yanda yayi ya sunkuyar da kansa, "da alamu ƙila ya ji zafin kama masa kunne da tayi ne?" Take hasashe a ranta har da riƙe nata kunnen

Momy ne ta iso wurin da abincin, tace mata, "ta sauko su ci."

Shine dalilin da yasa ta dena saƙa da warwaran da take yi a ranta tana sauko wa. Abincin take ci but gaba ɗaya hankalin ta da tunanin ta suna a kan SHAREEF, jefi-jefi tana ɗago kai ta duba inda yake

Shi kam bai ma san tana yi ba tunda ba ya facing wurin da take, tuni ma ya manta da abun da ya faru since ba sabon abu bane a wurin sa in dai faɗan Momy ne, da yana jin magana ma baza a kai har wannan lokacin ana maimaita masa magana ɗaya ba, kullum sai an ji su da Momyn tana masa faɗa sai ka ce shine ƙaramin Yaro a gidan, kullum da laifin da yake yi, shi har ya manta hankalin sa yana a kan wayansa yana chart da rabin ransa. Sai zuba murmushi yake yi

Sadiq tuni ya gama ya koma Falon wurin su Momy

Yanda chart ɗin sa yayi daɗi bai san adadin lokacin da ya dauka a wurin ba, sai da ya ji muryar Dady yana cewa, "wai SHAREEF baka san dare yayi bane kake zaune? And you know you have work tomorrow?"

Ɗago kai yayi, sai kuma ya miƙe yana zura wayan a aljihu tare da yin miƙa ya nufi wurin su. Tunda ya ɗaura idanunsa a kan Maryamu da ke barci a saman Cerfet, sai ya ɗauke kai yana yatsina fuska. "Dad. We will talk about the Company. Gobe zamu yi zama a kan gwangilar da nace maka zamu amsa."

"Ok. Did you stop talking? Kun samu daidaituwa da su ne?"

"No Dady, amma gobe za a ƙarƙare since zasu zo Company, maganar ta ƙi ƙarshe but da yiwuwar gobe in sun zo everything will finish. Amma ina tunanin mu zasu siyar wa da gaba ɗaya hannun jarin."

Dady yace, "Masha Allah, haka nake son ji ai, Allah ya kaimu goben lafiya, na so in zo amma kuma gobe nima akwai inda zan je, i know zaka iya ne shiyasa na baka Companin nan ka tafiyar da shi yanda ya kamata SHAREEF, don haka ka jajirce, wannan ba kwangila bane na wasa. Allah ya bada Sa'a."

Daga Momy har shi suka amsa a tare

"Since ka ga ɗan uwanka kaɗan ya rage ya kammala, sai ya zo ya dafa maka ku ci gaba da yi, tunda Yaran nawa Jarumai ne izuwa yanzu ma ya kamata in sakar muku komai in dena fita." Ya ƙare yana dariya

Shi kuma SHAREEF murmushin gefen baki yayi yana ɗan motsa ƙafafu tunda yana tsaye ne, sai kuma yace,"Dad, Mom, zan kwanta sai da safe."

Momy tace, "af! Zo ka ɗauki Maryam ka kaita ɗakin ta tunda tayi barci, dama neman mai ɗaukar min ita nake yi."

"What! But you are kidding, Mommy?in rasa wacce zan ɗauka sai wannan ƙazamar?"

Baki suka saki gaba dayansu suna kallon ikon Allah

Yayinda Momy ta nuna ta da yatsa da cewan, "ƴar uwanka ce ƙazama? Ko don ka ga daga ƙauye ta fito?"

Buga ƙafafu ya soma yi yana faɗin, "Mom I can't gaskiya. I feel sleepy, I went to the room." Ya wuce abun sa har da wani sakin guntun tsaki cikin ƙasa da murya yake furta, "This useless girl, he will take her to the room? Never. And I hate her!" Da gudun sa ya taka steps ya wuce dakin sa

Yayinda Dady yace, "da alamu wannan Yaron naki akwai taurin kai, sai kin yi da gaske fa."

Momy cikin rashin jin daɗi tace, "Allah ba abun wasa bane wannan, zan taka mishi burki tunda nema yake yi ya zama bauɗaɗɗen Mutum, bazan ɗauki wannan sakarcin na SHAREEF ba, ko baka ga abun da yake nuna wa a kan Maryam bane?"

Dady yace, "na gani Deeja, amma ki yi masa uzuri since yau ta zo gidan, a hankali zasu saba, duk wani abu da ya shafe ta yanzu shi zamu ɗaura a kai, a hankali zai saba da ita, kin san halin ɗan naki, yanzu ɗauke ta ki kaita ɗaki mu je mu kwanta dare nayi."

Tashi Momy tayi ta soma ƙoƙarin ɗaga Maryamu. Ai kuwa sai ta tashi nan take tun kafin ma ta ɗaga ta, sai dai cikin magagin barci take, Momy ta riƙe ta tana ce mata, "su je ɗaki ta kwanta."
Bin Momyn tayi wacce ta riƙe ta tunda bata gama warware wa daga barcin ba. Suna shiga dakin sai ta kwantar da ita a saman gadon, ta rufe ta da bargo sannan ta fita after ta ja mata ƙofan

Ganin babu Dady a falon shiyasa itama ta haura sama.
***
       

          While SHAREEF yana shiga nasa ɗakin, maganin sa ya soma sha sannan ya sauya kayansa zuwa na barci, ya haye kan gado yana lumshe idanu, duk barci ne sosai a idanunsa but bazai iya ba dole sai yayi chart da Haseena. Ba ya jin ƙarfi sosai a jikinsa That's why he couldn't call her, he went online, and they continued to chat.


          The following day after ya tashi around 09:00am. Kasancewar ya makara sosai since bai samu barci ba a daren jiya, shiyasa bai ɓata lokaci ba wajen shirya wa cikin kayan sa na suit wanda koyaushe da su yake zuwa wurin aiki, shigansa kenan in har aiki zai je, yau kuma sai ya saka jan suit riga da wando, tare da farar riga mai dogon hannu a ciki, kayan sun amshe sa ƙwarai tunda farin Mutum ne, ga haiba da kamala gami da kwarjini da Allah ya zuba mishi, tsab ya feshe jikinsa da performers masu tsananin ƙamshi da ratsa zuciyan wanda ya ji, sai yayi using da white cover shoes and wrist watch. Ya gyara suman sa duk da ba gashi ne dashi ba yana aske wa, iyakan na gaban tare da siririn saje yake iya bari, zama yayi a saman gadon ya buɗe wayan sa. Nan kuwa messages suka soma shigowa cikin wayan, bai duba kowanne ba sai na Haseena wacce ta tura masa na good morning, yana smile nasa mai burge wa yake mayar mata da reply. Abun da ya rubuta kawai.

"If you wake up in good health, keep in mind that I am also in good health. idan kina lafiya tamkar ina lafiya ne, damuwar ki shi ne damuwata, Take good care of yourself, I will call you later."

Sai ya saka emoji na tsananin kewarta da ƙaunarta, yayi mata send yana cije leɓen ƙasan bakin sa, kana ya lumshe idanu tare da shafe gefen sajen sa zuwa gemun sa, ɗan sosa wa yake slowly still idanunsa a rufe ruf, shi kaɗai ya san me yake ji a wannan lokacin, bai san meyasa yanzu yake matuƙar bukatar auren su da Haseena ba fiye da baya, sai dai kuma ba ya son ɓata mata rai bare ya furta mata abun da bata so, but yana ganin kamar bazai iya jure har tsawon 2yrs yana faman jiranta sannan suyi aure ba, no bazai iya ba, dole ya san me zai yi, dole zai yanke hukunci koda aure ne su yi ta koma can ta ci gaba da karatun ta, inyaso duk sanda yake buƙatar ta sai ya je can ya same ta

Kawo nan a tunanin sa, sai ya buɗe fararen idanunsa masu madaidaitan girma da kyawu, ya zuba su a jikin bangon ɗakin yana faman murmushin sa mai kyau wanda ba kasafai ya cika yin sa ba, haka kawai yake jin farin ciki a ransa, ya tabbata in three months zasu iya samun hutu, idan ta dawo zasu zauna suyi magana ta fahimta a tsakanin su, shi karatu ba matsalar sa bane in har zata yarda suyi aure a yanzu, gwara ta tafi da auren sa zai yarda tunda dai dole ta zama mallakin sa, ita kanta abun da take buƙata kenan ya san baza ta ƙi ba, karatu kuma ta je tayi ta yin sa har sai ta ga ƙarshen Biro ma, ba shi da case da wannan

Miƙe wa yayi bayan ya duba wayansa ya ga nine fifty har tayi, da sauri ya miƙe yana ɗaukar wayansa

Kamar ana jiransa ya ɗauka sai ga kiran PA. Bai ɗauki wayan ba sai da ya je cikin wardrobe ya ɗauki maganin sa da zai sha yanzu, da wanda zai sha anjima before ya yi answering Call ɗin, time ɗin ma har ta katse ya sake kira, "I'm on my way."  Abun da ya furta kenan batare da ya tsaya jin me zai ce ba, ya katse kiran yana zuge jakarsa da ke saman gado, ya zuba maganin sannan ya ɗauka ya fito

Tafiya yake yi yana duba wayansa, ya san dole sai yayi late tunda by ten zasu yi meeting din, tsaki ya ja yana tura ƙofan ɗakin Momy, batare da ya shiga ba kuma; ya soma yin sallama a hankali cike da sanyin muryansa da a kodayaushe a haka take

Momy ta amsa mishi wacce take zaune a gaban mirror itama tana gyara fuskarta; since fita zasu yi da Maryamu su je kasuwa tayi mata siyayya. Ta ba shi iznin shigowa ciki

Ƙarisa tura ƙofan yayi yana shiga tare da nufan inda take, "Mom good morning."

"Morning ɗan albarka, ashe zaka je aikin baka fito da wuri ba?"

Tura baki yayi yace, "Mom late nayi, and kuma ina da meeting yanzu fa. Time will run out before I get there."

Murmushi tayi sabida yanda ta ga yana ta tura bakin sa, dama in yana jin tsiya haka yake yi, shiyasa sai tace, "but breakfast fa? Ka san bazan bar ka katafi haka nan batare da ka zura komai a cikin ka ba, don na ga wasa kake yi da lafiyar ka kuma ka san ba ƙoshin lafiya ka ci ka ba."

"Mom Allah zan ci, amma bani da lokaci yanzu, gwara in je can, in na gama meeting zan ci i promise you."

"Did you promise me? I don't want you to disagree with me."

"Allah Mom." Yayi maganar yana marairaice fuska

"Shikenan, but baka manta da maganin ka ba ko?"

Gyaɗa mata kai yayi yana kallonta

"Ok go, sai ka dawo, amma kar ka manta baka ci komai ba SHAREEF na gaya maka, ba a shan magani babu abinci wata matsalar ne kuma. Allah ya bada Sa'a, ya kare ka da dukkan maƙiya masu bin ka da sharri."

Sai a lokacin yayi murmushin sa da ya fito da jerin haƙoransa; kuma ya bayyana dimples ɗin sa masu ƙara matsa tsantsan kyawu, ya kama hannunta yayi kissing, tare da amsa wa da, "Amin Mom, bye." Ya sakar mata hannun yana fice wa da sauri. Da ɗan gudun sa ya taka steps ya sauka ya nufa hanyar fita

Dai-dai lokacin Maryamu ta fito daga nata ɗakin, ta hange sa yana ta zuba sauri, sai ta ɗaga murya cikin zaƙin muryanta da son burge sa tace, "Yaya SHAREEF good moni."

SHAREEF da har ya taɓa ƙofan zai buɗe, sai ya tsinkayi muryanta a cikin kunnen sa, wanda hakan ne yasa shi juya wa don ganin wace ce; since ya manta da akwai baƙuwa a gidan nasu fa

Ɓashe masa baki tayi suna haɗa ido, sai ta ɗaga mishi hannu tana sake cewa, "ina kwana Yaya."

Wani kallo ya sakar mata mai nuni da ƙyamar da yake mata, sama da ƙasa ya kalle ta, sai kuma ya ja tsaki ya juya ya wuce ransa na son ɓaci da ganin wannan baƙar fuskar nata, meye haɗin shi da yarinyar nan da take son raina shi? Har shi zata kira ta gaishe? Lallai kam.. kaɗa kai yake yi yana tunanin ranan da zata shigo hannunsa, yana tunanin sai ya fito mata da ƙwala-ƙwalan idanun nan nata waje, ya taye mata fuskar Magen nan, but yanzu ba shi da ishashshen lokacin ma da zai tsaya jan mata worning.
Motansa ya shiga ya ja ya fice a gidan da gudu kamar zai tashi sama

While Maryamu tana tsaye a wurin sai faman sosa kai take yi tana tura baki gaba, ita ta lura kamar ba ya ƙaunarta ne ma, shiyasa gaba ɗaya ta ji zuciyarta ta soma mata zafi, yayinda take jin tsananin ƙaunarsa na sake huda mata magudanan jininta, kamar ana sake masa halitta ne saboda gani take yi ya fi jiya kyawu da haiba, a ranta take cewa, "Yaya SHAREEF ina sonka, komai naka mai kyau ne." A hankali cike da sanyin jiki ta juya ta koma cikin falon tana zama, yayinda tunanin ta ya bar jikinta ya tafi ga SHAREEF, "Allah ina sonka babu mai raba Ni da kai."

"Ke da wa haka kike magana?" Cewar Momy da ta sauko daga sama, Maryamu bata ji tahowar ta ba

Da sauri ta ɗaga manyan idanunta tana ware su a kanta, sai kuma ta soma soshe-soshe da cewan, "babu kowa Momy, Ni da kaina ne."

Momy da tayi gajeriyar dariya, sai tace, "kin taɓa ganin inda mutum ke magana da kansa Maryam?"

Dariya kawai tayi batare da tace uffan ba, sai kallon Momyn take yi wacce tayi kyau sosai cikin shiganta na farar less mai kama da kamfala, an yi adon shi da sky green color, tayi matuƙar kyau kasancewar ta jawur ce usulin bafulatana

Duk cikin ƴaƴansu ita suka biyo tunda ita ce jawur, so sun biyo hasken ta sosai, musamman ma SHAREEF don shi ya fi ta haske mai kyau tunda shi fari ne tarr, ya bambanta da irin hasken ta. Momy bafulatanan Yola ce, mahaifiyarta da mahaifinta duk ƴan can ne, amma zama ya dawo da su nan tunda suna kasuwanci ne, Allah da ikonsa aka haifi su Momy duk a nan, sai ya zamana gaba ɗayan su a nan suka yi aure, illa Autan su da take aure a Abuja

Mahaifiyar Alhaji Ahmed, wato Hajiya Bilkisu, gidan da tayi aure kusa da na su Momy ne, sanadin da yasa Alhaji Ahmed ya ga Momy har ya aure ta kenan, duk da a lokacin ba ita ya so ya aura ba, ƴar uwanta ce, amma ita tana da wanda take so, sai ta faɗa mishi gaskiya tare da haɗa sa da ƙanwarta, to Alhaji Ahmed bai ja zancen ba tunda a lokacin bai taɓa ganin Momy ba, bayan ya ganta sai ya ga ta fi su kyau ma sosai, tunda a zahiri ita ta biyo iyayenta sak bafulatanan Usul. Sun yi soyayya sosai kafin su yi aure, tunda a lokacin Alhaji Ahmed yana tsaka da karatun sa ne, daga baya kuma ya aure ta bayan ya gama degree ɗin sa, daga nan ya ci gaba da karatu itama tana yi. A yanzu Momy ta gama masters ɗin ta amma ba ta sha'awar aiki, tunda tace, "zaman gidan Mijinta ya fi mata komai." Ita take yin komai na gidanta babu ƴan aiki sai dai masu kula da haraban gidan Maza, duk da daga baya-bayan nan ta so samun masu aiki, amma SHAREEF ya hana su zama, ko an kawo su sai ya kore su, mugun halin da yake nuna musu ma ba ya barin su zama, dole Momy ta haƙura da masu aikin ta ci gaba da ayyukan ta, tunda dama ba ya mata wahala, kawai ta ga yanzu girma ya soma zuwa ne tana buƙatar hutu, ta samu mai yin mata shara da wanke-wanke, shiyasa take yin abun ta da kanta yanzu.
***


      Dayake Momy tace ma Maryamu, "ta je ta shirya zasu fita kasuwa."

Shi yasa ta tashi ta je ta ɗauko gyalen ta tunda har tayi wanka ta saka riga da skirt sababbi, ɗaya daga cikin ɗinkunan da ta zo dasu ne waɗanda suna ɗaya daga cikin wanda Baba yayi musu da Sallan nan, dama duk sababbi ta kwaso kayanta since Birni zasu je. Hoda ta shafa tare da yin ɗigo a goshin ta kamar yanda ta saba yi koyaushe, ya zama ɗabi'ar ta ma, sabida ko bata yi kwalliya ba sai ta ɗiga shi, sai ta ɗauki gyale ta yafa a gefen kafaɗanta tare da zura shegun takalman ta da ba ta rabo da su, masu shegen tsini

Momy sai dariya take mata, sabida ganin yanda take turguɗe wa, tace, "wai baza ki haƙura da takalman nan ba sai sun ka dake ƙasa?"

"Momy ai na saba saka wa, baza suyi min komai ba."

"Yanzu ba ga shi kina ƙoƙarin faɗi ba? Kaii! Anya baza ki je ki canza su ba?" Ta ƙara maganar ganin Maryamun ta kusa zube wa ƙasa, sai ta dafa Momyn tana dariya

"Momy bani da wani fa, kuma wlh na fi jin daɗin su, ko a ƙauyen mu da su nake tafiya duk inda zan je."

Murmushi Momy tayi tace, "to mu je, amma in mun je dole zan siya miki flat shoes ki haɗa, waɗannan sun yi miki tsawo, sai a siya miki ƴan madaidaita."

"To Momy." Maryamu ta amsa mata cikin farin ciki da zumuɗin ta


Haka suka fita driver ya tafi da su Market.
[24/01, 8:09 am] OumƊahirah نفيسة: 🌱🌱🌱🌱🌱

      *SHAREEF*
          _SexyBoy_
🌱🌱🌱🌱🌱


_Writer: Nafisat Isma'il Lawal_
_Wattpad: UmmuDahirah_

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝*



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

       *P.W.A✍️*




             *NASIHA*
Idan kana fama da damuwa mai tsanani ko wata rashin lafiya da aka kasa gane kanta ko wata bukata da kake so Allah ya amsa maka ita cikin gaggawa, toh ka yawaita abu ukun nan:
1. Sallar dare (ko da raka'a biyu ce)
2. Sadaka
3. Kyautatawa iyaye.










__________
*BOOK1*
_______________*FREE PAGE14*
          Lokacin da SHAREEF ya isa Company, har an taru shi kaɗai ake jira

PA din sa yana bakin hall ɗin yana ta faman duba agogon sa, ga shi SHAREEF ɗin ya ƙi ɗaukar waya bare ya san me ke faruwa har yanzu bai iso ba?
Sai ganin Motan sa yayi ya faka, da sauri ya isa wurin sa yana buɗe masa ƙofan Motan, tare da amsar Jakar hannunsa yana gaishe shi lokaci guda

Bai amsa mishi ba sai da ya fito a natse, tare da kallonsa a fizge ya amsa mishi a takaice cikin isa da taƙama irin nasa, wanda in har ka sanshi a waje baza ka taɓa cewa wancan SHAREEF ɗin bane na gida, kwata-kwata ba shi da fara'a a waje, kuma ba shi da mutunci bare ganin ƙimar mutane

"Sir, kowa ya hallara kai kaɗai ake jira."

Bai yi magana ba, ya soma taka wa zuwa bakin hall ɗin cikin natsuwarsa tamkar ba jiransa ake yi ba, don yanda yake takawan kamar bazai tafi ba

PA na biye dashi a baya sai duba agogo yake yi,
Da sauri yayi gaba yana buɗe masa ƙofan hall ɗin

Shi kuma ya shige ciki yana ƙara gyara daidaituwar rigan sa

Hall ɗin cike yake da manyan mutane a ƙalla zasu kai su ashirin a ciki, gaba ɗaya in ka kalle su manyan mutane ne masu ji da kansu da kuma kuɗin su, duk babu sa'an SHAREEF don gaba ɗaya sun girme shi,
Har da wasu tura wa su uku waɗanda su ne suka bada kwangilar aikin da za a yi musu, na gina katafaren Company a Abuja, tare da haɗakar da zasu samu da companonin su SHAREEF domin samun biyan buƙatar su, shiyasa dole sai an sanya hannun jari da companoni manya-manya don a samu yiwuwar aikin,
Yanzu haka Companin SHAREEF yana ɗaya daga cikin manyan company a nan Kano, shiyasa suke buƙatar amincewar sa domin ya shiga cikin aikin gadan-gadan, tunda zasu samu abun da suke so ba kaɗan ba,
Sai kuma aka samu rashin Sa'a wanda Abokan hamayya suka shiga cikin zancen a kan dole sai an saka Companin su,
Wato Alhaji Inuwa da kuma Honourable Ja'e Ali,
Su ne suka kawo tsaiko a kan harkan, har aka yi kwana biyu ana yin meeting don tsayar da shiyan kowanne a cikin companin

SHAREEF ya ƙi yarda da tayin da suke so a basu, shiyasa yau Turawan suka buƙaci zama a yi taron da su don ganin an samu matsaya,
Tunda idan maganar ta ci gaba da tsawo zasu yi asara babba

Yanzu shigowar SHAREEF shiyasa hall ɗin ta dena hayaniya, wanda duk faman hayaniyar nan ana yi ne a kan SHAREEF ɗin da ya shanya su bai zo ba, har ya ƙara musu mintina 15 a kan lokacin da suka ɗiba,
Suna ganin kamar har da wulaƙanci shiyasa ya ajiye su ya ƙi zuwa a yi magana a gama

"I'm sorry. I was late and did not arrive early." Yayi maganar yana ɗaga musu yatsa ɗaya batare da ya kalli kowa daga cikin su ba, ya samu wuri a inda aka tanadar mishi ya zauna

"Ok, tunda kowa ya hallara kamar yanda ake buƙata, ya kamata a fara gudanar da abun da ya tara mu." Cewar Sharaihu Managern SHAREEF ɗin

Mr. Pitter shi ya soma magana da cewan, "now we should stop at one point, we are listening today and you should make your decision, if the work is possible then tell us because time is running out for us, the reason why we gave you this work is because we know that we will not get it wrong. but you still failed to give us a single solid answer." Ya ƙare maganar yana bin su da kallo

Honourable Ja'e ya yi gyaran murya tare da cewan, "mu bamu da matsala fa, hukunci yana ga SHAREEF idan har ya amince, kowannen mu zai ɗauki kaso ɗaya bisa uku, shi ne tsarin mu. For this work is not his alone."

"Gaskiya ne. Domin shi yake ja mana lokaci, wannan aikin ba companin ka kaɗai suka iya ba, and mu ma dole zamu ɗauki kaso ɗaya bisa uku kowa ya ƙaru, abun da yasa ake ta jayayya domin ku saka naku hannun jarin, don su suna ganin kamar idan sun saka Companin ka a ciki zasu fi ɗaukaka ne, wanda kowa ya san ba haka bane a nan, amma sun dage, kai kuma ka mayar da mu ƙananan mutane kana so ka nuna mana kamar ka fi mu wayon, don haka raba-dai-dai za a yi don shi ne kawai adalci." Cewar Alhaji Inuwa da ya fi kowa jin haushin SHAREEF; kasancewar sa ƙaramin su amma yana taka su son rai

Da yawan mutanen wurin suke ta faɗan, "gaskiya ne wannan, babu shakka."

SHAREEF da ke mirza yatsun sa cikin yanayin ko-in-kula da su, tamkar ma maganar bai dame shi ba tunda babu wanda yake kallo a cikin su, but a cikin ransa maganar nasu ya sosa shi matuƙa har ransa ya ɓaci, amma ya ƙi yayi magana bare su ji ra'ayin sa

Sharaihu yace, "Ni ina ga, ku bi abun nan a hankali komai zai zo ƙarshe, tunda ga su Mr. Pitter a wurin, su zasu yanke hukunci kai tsaye, su zasu san wa zasu ba wa babban shiya."

Mr. Pitter yace, "We have finished speaking, right from the beginning we needed SHAREEF Company, so what he said we will do, we have no choice."

Wani killer smile SHAREEF ya saki, yayinda ya ɗago kyawawan idanunsa ya zuba a kansu, a natse cikin sanyin muryansa tamkar babu abun da ke damun sa yace, "idan na yanke hukunci ba na canza wa, ba wai na dage dole sai an bama Companin mu aikin nan bane, and ban ce dole sai mun saka hannun jari ba, amma su da kansu suka zaɓi namu Companin, don haka a cikin ku babu wanda zai zo yayi mana iko a nan a kan alfarma da kuke biɗa." Ya ƙare maganar yana nuna su Alhaji Inuwa da yatsa, idanunsa har sun soma sauya kala alamun ya soma ƙule wa. "idan baza ku yi aikin bisa tsarin da nake so ba, so sai dai mu cire hannun mu a cikin tsarin nan. I'm done talking, we will take two out of three, anyone who doesn't do it for him, it's not said that he has to do it." Sai ya mayar da idanunsa a kan su Mr. Pitter yace, "If you don't agree, as long as we leave this work, I don't care."

"No, mun yarda, dama aikin ka muke bukata ai." Cewar Mr. Pitter, before kuma ya juya ga ƴan uwan nasa ya soma musu ƙus-ƙus kasancewar su ba sa jin Hausa sosai, kuma tun maganar ma basu furta komai ba

Yayinda su Alhaji Inuwa ransu yayi baƙi sabida baƙin cikin abun da SHAREEF yake son yin musu, su ma sai ƙus-ƙus suke yi suna musayar yawu a tsakanin su

Sai ɗaya Baturen ya ɗago yayi magana a kan, "sun amince, zasu yi aiki da Companin SHAREEF, duk wanda bai amince ba basu gayyace shi ba, amma su ɗaukakar Companin su suke buƙata tunda kasuwanci suke yi, don haka duk wanda zai bi bayan shi suyi aiki tare basu da case da wannan, amma hannun jari gaba ɗaya sun sayar mishi ne, inyaso ya basu wani kaso daga ciki basu da damuwa. Sun tsayar da magana in a three weeks za a fara aiki."

Jin hakan sai SHAREEF ya cije laɓɓansa yana murmushi. Bai ƙara furta komai ba har aka rufe taron kowa ya soma tashi zai wuce

While su Alhaji Inuwa suna zaune sun ƙi tafiya. Suna ganin SHAREEF zai mike sai suka buƙaci magana da shi

Bai ce komai ba ya koma ya zauna a inda ya tashi

Mutane na fice wa, Alhaji Inuwa cikin zafi yace, "Kai SHAREEF yanzu har rashin mutuncin naka ya kai ka wulaƙanta mu a kan wannan kasuwancin da ka san komai ga yanda ake yi? Ko Mahaifin ka ne ya zo nan da kanshi bazai yi mana haka ya kasa amsar tayin mu ba bare kai, and mai kake taƙama dashi kuma nawa kake bukata a wurin mu; mu baka domin ka bamu hannun jarin mu ma? Ba aiki kaɗai muke bukata ba mu ma muna son saka hannun jarin mu a ciki."

"Exactly, don haka ka faɗa mana ko me kake so zamu baka, wannan aikin bazai yiwu a ce muna kallo ka ci kai kaɗai ba, tamkar ɗaukakar ka ne kai kaɗai idan har mun yi aikin nan babu hannun jarin mu, don haka dole mu ma ka bamu kason mu."

Miƙe wa SHAREEF yayi yana bin su da kallon ƙasƙanci, ransa a ɓace yace, "bazan bayar ba, ba Dadyna bane a nan a gaban ku; Ni ne SHAREEF. SHAREEF Ahmad, idan aikin bai yi muku ba kuna da damar ajiye wa tunda mu zamu iya, and babu wanda ya isa yace zai nuna min fin ƙarfi a nan since nima ina da wayon ɗina." Sai ya buga table ɗin cikin huci ya ƙara da cewa, "waye bai son ci gaba? Kuna ɗauka na ban san me nake yi ba? Ku canza tunani."
Ya wuce ba tare da ya sake bi ta kansu ba ya fita daga wurin

Su kuma suka bi bayansa da kallo ransu a ɓace. Alhaji Inuwa da ya fi daukar zafi ya soma faɗin, "wlh sai na koya ma wannan Yaron hankali, bai isa ya ci bulus haka ya tafi ba, aikin da muke jira tsawon lokaci amma a ce shi za a danƙa ma wa? Wlh karya ne sai inda ƙarfi na ya ƙare."

Honourable Ja'e da shima yake cike da ɓacin ran, sai yace, "ka ga mu je, mu bar nan don ba a nan ya kamata mu yi magana ba, ko ma me ke akwai zamu san ya zamu yi, ai ƙwace goruba a hannun kuturu ba abu bane mai wahala, mu je kawai zai san da wa yake yi, mu ne garin fa."
Ya ja hannunsa suka nufi ƙofa suka fice suna baza riguna.
***


              Kai tsaye shi kuma SHAREEF office ɗin sa ya wuce, da Shuraihu da PA suna ciki suna jiran sa,
Shigowar sa sai ya nufi kan kujerar sa kai tsaye yana zama; fuskarsa a matuƙar haɗe babu ko ɗigon walwala a tare da shi

PA ya kasa yin magana don ya san halin sa tunda ya ga ya shiga wannan yanayin, da alamun ran ɗan Maza ya ɓaci, ya lafiyar Kura ma bare tayi hauka?

Shuraihu ne ya soma magana yana cewa, "SHAREEF bai kamata a ce kana nuna ɓacin ranka a kan waɗannan ƙananan alhakin ba, already aikin nan dai mu zamu yi, don haka mu fuskanci abun da ke gaban mu zai fi mana." Sai ya ɗago computern sa da ke hannunsa yana cewa, "Ni yanzu na riga da na fitar da sumfurin building na komai, sai a duba a gani in akwai wata shawara."
Sai ya ajiye computern a gaban SHAREEF yana matso mishi dashi yanda zai gani

Kallo ɗaya SHAREEF ya yi wa fuskar computern yana ɗauke idanunsa; da suka rage haske saboda halin da yake ciki, har yanzu a hassale yake da ɓacin ran su Honourable Ja'e, shiyasa cike da taƙama irin nasa, and kuma cikin sanyin muryansa wacce ko a ɓacin rai yake ba ta sauya wa, sai ma dai ta ƙara sanyi sabida isa da izza ta yanda yake sarrafa ta kamar bazai yi ba, a yatsine yace, "ba na buƙatar wannan zanen, already mun yi magana da Hanif shi zai fitar, abun da nake so da ku." Sai ya ɗago kai ya tsira wa Sharaihun ido yana ƙara wa da faɗin, "kai da Mahmud da PA zaku fara zuwa ku ɗauko mana hotunan wurin gobe, da komai na tsarin wurin." Sai ya janye idanunsa tare da matsar da computern Sharaihun yana ɗaura nasa a wurin, tare da soma daddanna wa ba tare da ya sake ce musu komai ba

While Shuraihu duk yanda ya so ya ɓoye abun da ke ransa ya kasa, ransa suya yake yi da jin hukuncin da SHAREEF ya yanke, wanda har hakan ya bayyana a kan fuskarsa batare da ya sani ba, sai ya kasa haƙura yace, "but sir, na ga Ni nake yin zane idan irin hakan ta kasance, and kuma already na rigada na fitar da zanen tunda sun bamu jadawalin wurin, wannan babban aiki ne fa, idan muka ce zamu fara amfani da sabon zane a hannun wanda bai taɓa yi ba akwai matsala..."

"To and so what? Hanif zai yi wannan zanen ba na son gardama." Yayi maganar bai ɗago da kansa ba yana ci gaba da danne-dannen shi

Shi kuma Sharaihu sai ya haɗiye yawun takaici yana ƙoƙarin danne baƙin cikin sa daga fuskarsa, musamman yanda ya ga PA yana kallonsa

Wanda shi PA ya san dama za a rina, don ba a yi wa SHAREEF gwanin ta, shi dama haushin Sharaihu yake ji yanda yake kane-kane a companin don an ba shi dama, amma ga shi lokaci guda abun mamaki SHAREEF yana son daƙile shi a kan wasu harkokin

"Wannan shi ne sumfurin zanen da Hanif ya tura min, zan tura maka ta e-mail sai ku je dashi ku duba, and ga wanda Mr. Pitter ya tura min." Sai ya ɗan yi shiru yana jan numfashi kaɗan, tare da furta, "make sure today you all check and send me again."

Dukkan su suka amsa mishi, while Shuraihu yana dauke nasa computern tare da duba zanen da SHAREEF ya tura mishi, sai ya miƙe tsaye yana mishi sallama ya fice

"Ka je ka tattaro min files ɗin nan na sabbin ma'aikata, ka kai ma Mahmud ya duba a tantance waɗanda za a ɗauka, kar su gaza mutane biyar."

"Ok sir." Cewar PA cike da girmamawa yana tashi, sannan ya fice daga office din

Shi kuma SHAREEF sai ya ci gaba da latsa computern sa bai sake ɗago kai ba. Like a ten minutes ya ɗauki wayansa yana latsa wa, jima wa kaɗan ya kara a kunnen sa tare da manna wayan da wuyan sa still yana duba computern

Daga can Hanif ya amsa call ɗin yana cewa, "Bro how fer?"

"Fine. And you?"

"Alhamdulillah komai normal."

"Ok, mun gama magana a kan aikin nan nasu Mr. Pitter, zan tura maka iya girman wajen, but zuwa gobe za a sake zuwa a ɗauka gaba ɗaya zan tura maka, sai ka duba Please Do everything for us in one week, everything will be ready."

"Wow! Masha Allah. Did you say that everything is finished? They agreed to give you the shares?"

"Yeah, sai dai waɗannan ƙananun mutanen suna son kawo min cikas, and babu wanda zan raga mishi ciki wlh muddin suka ce zasu taɓa Ni."

Murmushi Hanif yayi tare da cewa, "wooh! Na Haseena, ba da kanka a sare ka je gida ka ce ya faɗi, calm down mana, me zai sa ranka ya ɓaci a kan su?"

Murmushi SHAREEF yayi yana cije laɓɓansa, sai ya ɗan ja numfashi tare da rufe computern, at the time yana ba shi amsa da cewan, "har ka sa zuciyata tayi sanyi, but raina a sama yake tunda muka fito meeting ɗin nan." Sai ya ɗan ja guntun tsaki tare da cewa, "bari in wuce gida, zamu yi waya idan na koma, ina jin yunwa sosai." Ya ƙare maganar yana langaɓe kai kamar zai yi kuka

Hanif da ke murmusawan shima yace, "Ok bro, bari in bar ka nima ina son shiga school now. And stop worrying about these people, since everything is in our hands. Congratulations, fatan nasaran aiki."

SHAREEF smiled and said, "Thank you my brother."

Daga nan suka yi sallama ya katse wayan yana tashi tsaye. Jakarsa ya ɗauka bayan ya mayar da wasu files a ciki, sannan ya nufi ƙofa ya fice yana zura wayansa a cikin aljihun wandon sa. Babu PA a office nasa, shiyasa ya fice kawai yana nufan lifter ya shiga ya saukar dashi ƙasa

Duk inda ya wuce ma'aikata ke gaishe shi, amma ko ci kanku bai ce musu ba. Idan ma da sabo sun saba, ba ya amsa gaisuwar su sai ya ga dama, ko zai amsa sai dai ya ɗaga musu hannu, sosai girman kanshi ya yi yawa da ganin mutane a ƙasƙance, ba ya damuwa da damuwar mutane sai nashi, ba ruwan shi da shiga harkan mutane bare ya san matsalar su, in dai sun yi mishi ba dai-dai bane ko kuma sun shiga gonan shi, yanzu za ka ji ruwan bala'i da masifa, kuma daga ƙarshe ya yi maka koran wulaƙanci; don ba ya iya ba wa mutum dama ta biyu

Motansa ya hau ya figa zuwa gida, a ɗan ƙanƙanin lokaci ya isa gida ya dinga danna horn kamar zai tashi sama

Da sauri mai gadi ya wangale mishi gate ɗin jikinsa yana rawa. Shi kuma ya kutsa motan ciki ya nufi packing space. Tsayar da Motan yayi ya fito hannunsa rike da Jakar sa, tare da nufan cikin gidan yana zura hannunsa ɗaya a aljihu, tare da taka wa a hankali tamkar ƙwai ya fashe mishi kansa a ƙasa

Lokacin su Momy dawowarsu kenan daga Market. Shi yasa ta tasa Maryamu suka shiga kichen domin su haɗa lunch

Maryamu sai farin ciki take yi tana wani rawan kai, yau ga ta a kichen ɗin ƴan gayu zata yi girki, kamar ba ita ce wacce ko tsinke aka saka ta ta kawar a gida; ta dinga ƙunƙunai kenan kamar zata bigi Mutum. Amma yanzu daga Momy ta ce, "ta taso su je kichen." Da gudunta da rawan jiki ta bi ta tana taya ta sai hira take mata. Ita kuma tana mata murmushi da sauraron ta

Jin an buɗe ƙofan shigowa, shiyasa Momy ta kalli Maryamu tace, "duba ki gani wane ne? Na ji shigowar Mota maybe Sadiq ne ya dawo."

"To Momy." Maryamu ta amsa mata da sauri tana share hannunta a kayanta, tare da nufan ƙofan ta fice kamar ana ingiza ta.
[25/01, 8:45 am] OumƊahirah نفيسة: 🌱🌱🌱🌱🌱

          *SHAREEF*
              _SexyBoy_
🌱🌱🌱🌱🌱


_Writer: Nafisat Isma'il Lawal_
_Wattpad: UmmuDahirah_

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝*



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

       *P.W.A✍️*





*HIRA MAI DADI TSAKANIN NANA A’ISHA (RA) DA MANZON ALLAH (SAW).*
Wata rana Nana A’isha {r.a} suna zaune da Manzon Allah {s.a.w} ta kura masa ido tana kallonsa, can sai tace, "ya Rasulillahi wai don Allah ya ya wannan yusif din yake? aka ce Mata saboda tsaban kyansa idan sun ganshi har yanka hannayensu suke??"

Sai Manzon Allah {s.a.w} ya bude tafin hannunsa mai albarka, ya nuna mata fuskar Annabi Yusif yace mata, "ga Yusif din," sai Nana A’isha tayi murmushi tace, "wani abu sai Mata. Inama baku yanka hannayenku ba kuzo kuga shugaban kyawawa," ta ƙara da cewa, "ya Rasulillahi {s.a.w} tafin hannunnan naka yafi fuskar Annabi Yusif din kyau".

Ya Allah ka sada fuskokinmu da ta shugaban kyawawa Annabi Muhammad Sallallaahu'alaihi Wasallama. Amin.












__________
*BOOK1*
_______________*FREE PAGE15*
               Lokacin da Maryamu ta fita Falo, har SHAREEF ya soma hawa matattaƙalan benen, shiyasa ta koma da sauri tana ce ma Momy, "Yaya SHAREEF ne ya dawo."

"SHAREEF kuma? A wannan lokacin?" Sai kuma ta zazzage maggin da ta gama ɓare wa a cikin miyan, tana ɗan juya wa kaɗan tare da cewa, "taho nan ki juya min miyan ina zuwa, ki yi a hankali fa kar ya tsillan miki a idanu."

"To Momy."

Ta sakar mata ludayin tana fice wa. Kai tsaye saman itama ta haura sabida ganin babu SHAREEF. A hanya suka ci karo ya fito daga ɗakin ta shima

Sai yace, "Momy."

Tana kallonsa tace, "ya aka yi ka dawo kuma yanzu?"

"Mom na gama abun da nake yi ne, na dawo na karya ne sai na koma zuwa anjima."

"Ai ba ka jin magana ne SHAREEF, yanzu da ka karya ai baza ka sake wahalar dawowa ba kuma. We have now entered the house, da baka ganmu ba ai." Sai ta juya tana cewa, "bari in haɗa maka ko kunun gyaɗa ne ka sha since muna da ƙullun."
Sai ta sauka ƙasa ta koma kichen

Shi kuma sai ya shiga ɗakin sa ya rage kayan jikinsa, ƙaramar t.shirt ya saka sai wando three quarter, dukka kalan ruwan zuma, da suka yi masa kyau matuƙa suka sake fitar mishi da haibar sa da kamalan sa. Wayansa ya zura a aljihu sai ya ɗauki maganin sa ya fice. Direct falo ya nufa ya wuce bakin fridge, ya buɗe ya ɗauki ruwa tare da kora wa da maganin, sai da ya haɗiye sannan ya ɗan lumshe ido yana buɗe wa, ya nufi hanyar kichen ɗin a natse tare da zaro wayansa a aljihu yana duba wa; jin ƙaran messages na shigo wa

Ƙamshin turaren sa ne ya soma sauka a hancin Maryamu, da sauri ta juya kai suka haɗa idanu lokaci guda. Ware idanunta tayi a kansa yayinda zuciyarta ta shiga wani irin zillo gami da sanyin da ke ratsa ta lokaci guda; ga wani farin ciki da ya mamaye mata zuciya sabida arba da tayi da kyakkyawar fuskarsa

Shi kuma yatsina fuska yayi, lokaci guda ya ɗauke idanunsa a kanta sabida ko kusa ba ya ƙaunar suna haɗa ido, ganin yanda idanunta suke da girma tamkar na mahaifiyarsa, yanda take kifa masa idon shiyasa lokaci guda yake jin tsanarta na mamaye mishi zuciya, gami da haushin ta a cikin rai, amma girman kai da izza irin nasa bazai bari yayi mata magana a kan yanda take bin sa da kallo kamar ta samu TV ba. "Mom. Ba a gama ba?" Yayi furucin yana mayar da idanunsa a kan Momy da ke ta faman haɗa masa kunun

"Eh ban gama ba SHAREEF, ka jira kaɗan yanzu zan gama, sai in soya maka ko ƙwai biyu ne ka ci dashi, and ga arish ma."

"No, kunun ya wadatar Mom, zan sha haka nan."

"Ok. Go and I will send Maryam to bring you to the living room."

"Kin san ba na son masu aiki suna taɓa abun da zan ci Mom. I hate dirty girls."

Sai lokacin Momy ta juya tana kallonsa. She said in surprise, "Is this your sister? Ita ba ƴar aiki bace."

"What is their difference? Dukkan su ƙazamai ne, and bazan iya cin abun hannunta ba, idan kin gama zan zo in amsa." Yayi maganar cikin ko'in kula da rashin damuwa, ya juya yana fice wa tare da kara wayansa a kunnen sa

While Momy ta bi shi da kallo kamar an datse mata baki, sai kuma ta dubi Maryamu da tayi tsimi a wurin tana kallon SHAREEF ɗin kamar zata haɗiye shi, ita kawai bakin sa take kallo da yanda kumatun sa suke lotsa wa irin nata gaba ɗaya ta gama shagala da kallon sa. Momy ta taɓa ta tana cewa, "Maryam. Tunanin me kike yi haka? Ai ya tafi ko?"

Kunya ne ya kama ta, tayi saurin rufe idon ta da hannayenta biyu, tare da cewa, "Momy wlh ba shi nake kallo ba."

Dariya Momy tayi, sai ta girgiza kanta tana cewa, "bari in gama ki kai mishi kunun nan, and ki dena zuba mishi ido irin haka don ba ya son kallo kinji Ni?

Kai Maryamu ta gyaɗa mata itama tana kallonta, yayinda ta mayar da hankalin ta a kan yanda Momyn take haɗa kunun, bata ce komai ba har ta gama ta zuba mata a cup, tare da ɗaura mata a plate ta miƙa mata. Sai ta amsa ta nufi ƙofa da sauri kamar zata kifa

Mom ta kira ta tana cewa, "ya ki Maryam."

Dawowa tayi tana kallonta

"Ki dena tafiya irin haka, kiyi a hankali kar ki je ki zubar."

"To Momy." Sai ta juya ta fita tana sanja takun tafiyan nata

Momy ta bi ta da murmushi har ta fice, "lallai akwai aiki a gabana, SHAREEF yana da matsala fa." Sai ta ja numfashi tana ci gaba da aikin ta

While Maryamu ganin babu SHAREEF a falo, sai ta dawo tace ma Momyn, "babu shi."

Momy tace, "to ya koma daki kenan, ki hau sama za ki ga ƙofofi uku a jere, idan kin wuce su akwai lungu da bene a wurin, to ƙofan da ke wurin nan za ki buɗe ki shiga, yi sauri kar ya gaji da jira."

Fita Maryamun tayi ta nufi upstairs kamar yanda Momy tayi mata kwatance. Ɗakin ta tura ko sallama ta shige ciki

SHAREEF na kwance a kan gado yana waya da Haseena, sai kashe murya yake yi idanunsa a lumshe, ya ji kamar motsi shiyasa ya buɗe idanun yana zuba su a kan Maryamu da ta shigo masa ɗaki. Da sauri ya miƙe zaune cikin tsawa yace, "Who brought you to this room, who gave you permission to enter my room da waɗannan kazantattun kafafun naki? Kee!.

Rawa jikin Maryamu ya soma yi sabida tsawan da ya daka mata, kasancewar bata saba da jin irin wannan tsawan ba nan da nan ta rikice tana sakin plate ɗin hannun ta

"What...!" Ya furta cikin zaro idanu waje sabida ganin aika-aikan da tayi mishi

Daga cikin wayan Haseena da take jin maganar SHAREEF ɗin, sai ta soma tambayarsa tana cewa, "dear lafiya wai?"

Da sauri ya katse wayan yana miƙe wa kamar ƙiftawar ido ya isa inda Maryamu ke ƙoƙarin guduwa. Sai ji tayi ya cafko ta ta dawo baya ta faɗi dirshan a ƙasa. "Dan ubanki uban wa ya ba ki damar shigo min ɗaki har kika zubar min da wannan abun a ɗaki? Ke Jakar ina ce wa ya ba ki permission shigo min ɗaki?"

"Momy ce... Momy." Tayi maganar cikin rawan baki sabida gaba ɗaya ta gama ruɗewa ganin yanda ya hayayyaƙo mata da alamun a fusace yake, lokaci ɗaya tsoron sa ya ɗarsu a ranta musamman da ta ganshi a gabanta

Cikin baƙin ciki da takaicin yanda take kallonsa, ya saka hannu ya jawo ta yana kifa mata kyakkyawar mari a face ɗin ta

Lokaci ɗaya ta yanka uban ihu tana kururuwa kamar zata tsaga mishi kunne

A take ya sake ta shima sabida yanda ƙaran ya doɗe mishi kunne. Ganin yanda take ihu sai ya daka mata tsawa yace, "ki yi min shiru ko in kakkarya ki a nan wurin, I said to shut up or I will kill you."
Yayi maganar yana ɗaga hannayensa kamar zai shaƙe ta don Jaraba

Lokaci guda ta shanye kukan nata tana kama bakinta cikin rawan jiki, tare da matso hawayen da suka kasa fitowa daga cikin idon nata, sai dai sun cika idanun har sun soma sauya kala alamun ta ji shigan marin

Huci kawai yake yi tsaban takaici da tsananin tsanar ta, ya kasa ma ce mata komai sabida yanda ya ga ta ƙi kawar da idanunta a kansa kamar wacce zata haɗiye shi duk da tsoratan da tayi dashi. Cije laɓɓan sa yayi yana jan numfashi cike da ɓacin ran da ke ƙara kunno mishi, sai ya dubi inda ta zubar mishi da kunun ransa sai ƙara suya yake yi. Nuna wurin yayi da yatsa yace, "Get up quickly and clear the place for me; ko in kashe ki a nan wajen, maza tashi."

Da sauri ta rarrafa wurin tana rawan jiki, ta soma ƙoƙarin ɗauke cup ɗin, hannayenta biyu ta saka tana kwalɓe kunun tana mayar wa a cup ɗin

Yayinda shi kuma yake bin ta da kallon ƙasƙanci yana sake jin ransa na ƙara baƙi, ji yake yi tamkar ya je ya mangare ta, amma sai ya ɗauke kansa yana nufan wurin wayansa da ke ta faman ruri, zama yayi yana mayar da ajiyan zuciya tare da sassauta yanayin sa. Ya ɗauki wayan yana kara wa a kunne

"Dear me ke faruwa ne? Kai da wace ce haka?"

Ɗan jan numfashi yayi yana lumshe idanunsa tare da shafa gefen kumatun sa, a hankali cike da sanyin muryansa yace, "Ni da wata Jaka ce ƴar ƙauye, ta zo tayi min ɓarna a daki."

"What...! A ɗaki kuma dear? Meye haɗin ka da ita da zata zo maka ɗaki?"

Ido ya buɗe yana kallon wurin da Maryamu take, tana ta faman kwalɓe kunun da hannu cikin rawan jiki. Ƙin magana yayi sai da ta sake tambayarsa, sai yace, "sweetheart ki share maganar nan raina ɓaci yake yi."

A fusace Haseena tace, "taya zan share maganar after telling me you are in the same room with another woman? I can't."

"Calm down mana sweetheart, wata ƴar aiki ce Mom ta aiko ta kawo min kunu, and shi ne ta zubar min a ɗaki."

Haseena cike da kishi tace, "You know I'm jealous, I don't want you to be in the same place as any other woman dear, ba na son ka ci amanata."

"Oh! Sweetheart meyasa kin cika rigima ne? Akwai wata Mace da nake so bayan ke ce? Ba a haife ta ba har yanzu, idan kina duniya babu wata wacce ta isa in kalle ta, put in your heart I am yours forever. I love you so much!" Sai ya sakar mata kissing yana lumshe idanunsa

Yayinda a wannan lokacin Maryamu kamar zuciyarta zata fashe don baƙin ciki, tsaya wa tayi ta kasa ƙarisa abun da take yi tana jin zuciyarta ta soma zafi, idanu ta ɗago ta zuba mishi lokacin ne hawaye ke tseren gudu a kan kuncin ta

Lokacin SHAREEF ya buɗe ido sai suka faɗa cikin nata, yanda ta zuba mishi manyan idanun nata da suka ƙara buɗe wa suka yi luhu-luhu da ja, sai da gabansa ya faɗi, janye idanunsa yayi da sauri yana dafe kansa, sai ya rage murya yana cewa, "sweetheart bari in zo, Give me a little time to call you." Wayan ya kashe ba tare da ya jira cewar ta ba, sai ya mayar da idanunsa a kan Maryamu wacce har yanzu ta kafa masa ido ko ƙyafta su ba ta yi. Ƙarfin hali yayi ya daka mata tsawa

Sai ta motsa idanun tana lumshe su tare da buɗe su nan take, mike wa tayi ta fice a ɗakin bata saurare shi ba duk da kiran da yake mata

SHAREEF da mamakin yanda tayi banza dashi ya bi bayanta da kallo, "lallai wannan yarinyar, zai koya mata hankali, har shi yake kiranta tana banza da shi?" Sai ya miƙe yana nufan ƙofa ya fice. In quickly ya sauka ƙasa ya isa kichen yana kwaɗa kiran Momy

Mom tace, "lafiya wannan kiran SHAREEF? Mene ne?"

"Mom. Ina wannan shegiyar yarinyar? Sai na ci ubanta in na kama ta, babu mai ƙwatan ta a gidan nan." Yayi maganar a fusace cikin ɗaga murya 

Momy tace, "kanka ɗaya kuwa SHAREEF? Me tayi maka da kake neman ta? And I said, what did she do to you?"

Huci yake yi ya kasa ma magana don takaici

Sai ta ɗaure fuska tace, "ko me zaka yi zan iya jure wa amma ban da cin zalun SHAREEF, yarinyar ƙanwarka ne You better ka kiyaye abun da zaka riƙa faɗa, ba na son haka fa."

"Mom zubar min da kunu tayi a ɗaki fa, kuma kike cewa bazan taɓa ta ba? Why did you send her after I told you I don't want? Ba na son ganin ta." Yayi maganar cikin ɗaga murya da nuna faɗan sa. Sai kuma ya juya ba tare da ya jira cewar ta ba ya bar kichen ɗin a fusace

Sai Momyn ta biyo bayansa tunda ta san halin SHAREEF, tsab zai iya zane yarinyar kamar yanda ya faɗa tunda ta ga ransa ya ɓaci. Fitowa tayi but bata ga Maryamun ba, shiyasa ta shiga har ɗakin ta amma babu ita. Dole ta koma kichen don ta duba abincin ta kar ya ƙone.
***

             Maryamu kuma tana can ta bi ɗayan benen ta fita ta ƙofan baya. A faranda ta samu wuri ta zauna tana ta zubar da hawaye, wani irin zafi take ji a cikin zuciyarta, haka kawai take jin tsananin kishi mai zafi sabida jin wayan da SHAREEF ɗin yake yi da wata, hannu ta sa ta sharce hawayen ta tana ɗaura kanta a saman gwiwowin ta, yayinda ta dinga shashsheƙan kuka a hankali tana ƙara dulmiya kanta a tsakankanin cinyoyin ta

Sadiq shi ya hango ta lokacin da ya shigo gidan yana shirin wuce wa, har ya gota kuma sai ya dawo baya sabida hango ta da yayi, ya taka ya isa wurin ta yana kiran sunanta da mamakin kasancewar ta a wurin kuma a wannan yanayin. "Maryam, wa ya buge ki?"

Ɗago kai tayi da sauri sabida bata yi zaton ganin sa ba, shiyasa ta tsorata ta ɗaga kai a firgice, ganin shi ne sai ta soma sharce hawayen tana ƙoƙarin share su daga fuskarta, amma wasu ke fito wa kamar ana ɓulɓulo su

Zama yayi gefen ta yana kama mata hannun tare da cewa, "wa ya taɓa ki Maryam? Faɗa min mana inji me aka yi miki?"

Cikin shashsheƙan kukan take cewa, "Yaya SHAREEF ne..."

"Me yayi miki Yaya SHAREEF ɗin? Oya tell me, let's share the problem together."

Kasa magana tayi sabida kukan da ya ci ƙarfin ta a lokacin. Sai ya sake kama hannunta yana faɗin, "haba ƴar ƙanwata, kina so ciwo ya kama ki ne kike wannan kukan? Ki yi shiru kar ki sa wa kanki ciwon kai, Ni ne fa Yayan ki Sadiq faɗa min me Yaya SHAREEF ɗin yayi miki?"

"Kawai daga Momy tace in kai mishi Kunu ɗaki, shi ne ya mare Ni."

"Mari kuma Maryam? Shi Yaya SHAREEF ya mare ki?"

Kai ta ɗaga mishi tana ƙara tsiyayar da hawayen har tana jan numfashi

Hannu yasa cike da tausayin ta yana share mata hawayen tare da cewa, "to ki yi haƙuri don Allah. I don't like what he did to you, but I apologize, kinji ƴar ƙanwata share hawayen naki haka nan."

Sai ta ɗago ido tana kallonsa, yayinda ta ja majina a hankali tace, "amma meyasa Yaya SHAREEF ba ya sona? Har ce min yake yi Jaka ƴar aiki ƙazamiya, kuma na ji yana ce ma wata a waya yana sonta, kenan Ni ba ya so na?"

Yanda tayi da fuska ne, sai yayi mata murmushi yace, "in ji wa? Shi Yaya SHAREEF ɗin ya ce ba ya sonki ne?"

"Ko ba ya sona amma ya tsane Ni, shi ba irin ka bane ko kallo na ba ya yi, shikenan Ni bazai so Ni ba tunda yana da wata wacce yake so?"

"No, ai ke Matarsa ce, kuma idan kika zama yanda yake so ai zai so ki ke ma kamar kowacce Mace, kuma wancan da kika ji yana waya da ita maybe friend ɗin sa ce, don haka ki share zancen ta, yanzu ke Matarsa ce, duk abun da Yaya SHAREEF yake so shi za ki riƙa yi, nan gaba ai bazai na kiran ki ƴar ƙauye ba since yanzu kin zo cikin birni za ki canza ko? Common mana my little sister ki dena kuka a kan wannan ƙaramin abun haka, i know ke Jaruma ce, Yaya SHAREEF haka yake, duk abun da zai ce miki kar ranki ya ɓaci, just ki ba shi mamaki ne, ki zama abun da bai yi zato ba, sai ya zo da kanshi yana kukan ki so shi."

Baki ta washe lokaci guda, kamar ba ita ce take kukan yanzu ba, sai tace, "Allah Yaya Sadiq?"

Hancin ta ya lakuce yana murmusawa tare da cewa, "i swear my little sister. Ai ke kyakkyawa ce, kuma Yaya SHAREEF zai so ki in har kin zama yanda yake so."

Fuskar tausayi tayi tace, "to taya zan yi abun da yake so?"

"To kinga yanzu na dawo school a gajiye, idan na huta na ci abinci sai mu zauna in lissafa miki duk abubuwan da yake so da wanda ba ya so, za ki ga a hankali kina jawo hankalin shi gare ki lokaci ɗaya shima zai faɗa kogin soyayyarki kamar yanda kika faɗa nashi, don na ga ƴar ƙanwar tawa alamun soyayya ya yi mata diran mikiyan da babu sauƙi cikin ta, dole sai da taimako na."

Dariya tayi tana rufe ido

While shima yana taya ta tare da furta, "daga baya kenan za ki ji kunyata? Amma da kin manta da kunyar ai, uhm ƴar ƙanwata akwai drama fa."

"Yaya Allah ka bari, Ni fa ba wai sonsa nake yi haka kawai ba, don kawai Mijina ne shiyasa zan so shi, kuma ba na son wata ta ƙwace min shi haka kawai bayan ya zama nawa."

Waro ido yayi yana cewa, "really ƙanwata?"

Fari tayi da ido tace, "to ai haka Matan suke yi wlh, kuma Ni ba irin Matan nan ne da ake ƙwace musu Miji bane, komai zan iya yi sabida Mijina, Allah zaka sha mamaki na duk ranan da na ga Wata ɗiya Mace da Mijina." Sai ta cije leɓe tana ƙwafa da margaya kai

Dariya Sadiq yayi da mamakin maganganun Maryamun, yace, "Ni fa na ga alama za a yi fama da ke Maryam, to ai ki fara ajiye wannan batun bari mu fara kama Yaya SHAREEF ɗin a hannu." Sai ya haɗa hannayensa biyu wuri ɗaya yana cewa, "dama Nima gwanin soyayya ne. I will help you a lot, don haka bani hannun ki mu tafa."


Hannun ta ba shi cikin murna tana dariya, suka tafa. Sannan suka tashi suka shiga ciki suna dariya kamar ba su ba.




[27/01, 8:13 am] OumƊahirah نفيسة: 🌱🌱🌱🌱🌱

      *SHAREEF*
          _SexyBoy_
🌱🌱🌱🌱🌱


_Writer: Nafisat Isma'il Lawal_
_Wattpad: UmmuDahirah_

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝*



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

       *P.W.A✍️*





          *NASIHA*
A suratul Noor aya ta 26, tana nuna mana cewa lallai mata nagari na Maza nagari ne.
Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace; "Idan wanda ku ka yarda da addininsa da dabi'unsa yazo neman aure wajenku ku aura masa. Idan baku yi hakan ba, to ɓarna mai yawa zata kasance a bayan kasa. Tirmizi ya ruwaito shi.











__________
*BOOK1*
_______________*FREE PAGE16to17*
              Da Momy suka ci karo itama ta fito daga kichen riƙe da plate a hannu, ta sake zuba wa SHAREEF abincin tunda ta gama. Sai tace, "Sadiq ina ka samo min daughtern kuma?"

Yana dariya yace, "can na ganta a faranda zaune tana huta wa." Ya ƙare maganar yana kallon Maryamun; tare da kashe mata ido ɗaya

Momy ta dube ta tace, "Allah yasa ba wani abun SHAREEF yayi miki ba? Ko ya taɓa ki ne?"

Kamar zata faɗa mata, kuma sai ta girgiza kanta tana cewa, "a'a Momy."

"Yauwa to, har na ji dad'i, kai Sadiq amsa ka kai mishi dakin shi, and sai ka share wurin da Maryam ta zubar da kunu yana nan a ɗakin."

"Ok Mom." He took the plate and went upstairs

Ita kuma ta tasa Maryamu suka wuce kichen domin ƙarisa sauran aikin. Da wayon da dabara Momyn take faɗa mata, "ta riƙa saka natsuwa tana yin abu a hankali idan an saka ta, ta dena rawan jiki, musamman ma idan aikin na SHAREEF ne, kar ta je tayi abun da zai doke ta tunda ta ga yayi fushi a kan zubar mishi da kunun da tayi, bai da haƙuri ko kaɗan zai iya zane ta."

Maryamu dai tana sauraron ta bata ce komai ba. Har suka gama suka mayar da komai a saman dining table

Sadiq na zaune a Falon. Shi yasa Maryamu ta je ta zauna a wurin sa

Ita kuma Momy ta tambayi Sadiq ɗin, "ko SHAREEF ya wuce ne?"

"Eh Momy, yanzu ya fita, bai ma bar gidan ba."

Wuce wa tayi ta haye sama, ta bar su a nan.




🔆🔆🔆🔆🔆🔆🔆🔆


                       Suna zaune su biyun a office din Honourable Ja'e. Inda shi Alhaji Inuwa yake kurɓan juice da aka kawo mishi a farantin silver, yayinda suke tattaunawa a kan hanyoyin da zasu bi domin daƙile SHAREEF a kan aikin nan da zai yi, domin sun ɗauki alwashi sai sun ga bayan shi in har a kan aikin nan ne, muddin bazai bi abun da suke so ba, kuma already ma sun rigada sun gama tsara hanyar da zasu bi domin ganin sun kai ga ci

Inda a lokacin ne Secretary na Honourable Ja'e yayi nocking a bakin ƙofan. Bayan an ba shi izni sai ya shigo yana sanar musu da cewan, "baƙon da suke jira ya iso."

Honourable Ja'e yace, "ok. Shigo da shi mana."

Fita Secretaryn yayi, sai ga shi sun shigo tare da Shuraihu yana biye da shi a baya, sai da suka shigo sannan Secretaryn yace, "ranka ya daɗe! Ga shi nan." Daga haka ya fita ya rufo musu ƙofan

Su kuma suka yi mishi iso ya zo ya zauna a ɗaya daga cikin kujerun na huta wa, da aka zuba su set ɗaya a office ɗin. Bayan ya zauna suka gaisa sannan Honourable Ja'e ya soma yin magana da cewa

"Bismillah MD, ga drinks nan sai ka taɓa ko?"

Murmushi Shuraihu yayi tare da cewa, "No, na gode."

Su ma murmushin suka yi gaba ɗaya. Inda Honourable ya sake cewa, "to Alhaji ko zaka fara mishi bayanin abun da yasa muka nemi ya zo mu tattauna ne?"

Gyara zama Alhaji Inuwa yayi tare da duban Shuraihu yana cewa, "na san tunda ka ji wannan kiran a gare mu, dole zuciyarka zata kawo maka zargin abun da yasa muke neman ka? Duk da mun so mu bari muyi maganar ne a waya, amma kuma gani muke yi maganar baza ta yiwu a wayar ba, dole muna buƙatar keɓe wa fuska da fuska." Sai ya ɗan ja tsaiko tare da ci gaba da faɗin, "a kan maganar wannan kwangilar ne da muka kasa samun karɓuwa hannun uban gidanka, shiyasa muka ga ya dace mu nemi taimako a wurin ka tunda kai ne MD a companin, na tabbata idan muka haɗa hannu da kai zamu samu sauƙin aikin mu, shiyasa muka neme ka."

Shuraihu da ya kafa mishi ido yana sauraren shi, sai yace, "idan na fahimce ka Alhaji, in taimaka muku wajen shawo kan SHAREEF domin ya amince da taku buƙatar da ku ka zo da shi?"

Jinjina kai suka yi ba tare da sun furta komai ba

Shi kuma sai ya gyara zaman sa sosai yana haɗe hannayensa wuri ɗaya; tare da cewa, "ba na tunanin gaskiya akwai taimakon da zan iya muku tunda har ku ka kasa cin galabar shawo kansa tun a wurin meeting, wannan abun a bayyane yake ku kanku kun gama fahimtar wane ne SHAREEF, so ina ga sai dai ku haƙura ku ɗauki iya aikin da ku ka samu a wannan kwangilar, domin tunda ya dage bazai baku ba, ba na tunanin Ni zan iya shawo kansa ya amince." Sai ya girgiza kansa tare da cewan, "SHAREEF ba irin mutanen nan bane da suke da sauƙin fahimta ko bin ra'ayin wasu ba, No. Since he said the same thing, I don't think he will change his words."

"Ƙwarai mun san da haka, Yaron yana da taurin kan da zai bamu matsala matuƙa, mun so mu fara tuntuɓar Mahaifinsa a kan wannan zancen, so sai kuma muka ga mene ne bambancin dambe da faɗan? A haƙiƙanin gaskiya; ƙudirin mu babban ƙudiri ne da sai da na jikinsa zamu kai ga ci, shiyasa muka zaɓe ka don mu yi aikin nan tare. Muna fatan a ce mun bi hanyar da zamu ga mun kawar da SHAREEF'S Company daga kwangilar nan gaba ɗaya, dukkan mu burin mu ne a ce mun samu hannun jari a wannan aikin da muka daɗe muna tsimayen shi, jiran mu ba na yanzu bane, kai kanka ka san companonin mu suna ɗaya daga cikin manya-manyan companonin da suka fi kowanne a nan garin Kano har da sauran garuruwa, kuma an sanmu ana dama wa damu sosai, amma lokaci guda SHAREEF'S Company ya zo yayi mana zarra wanda har hakan yana son shafan durƙushewan ma'aikatan mu, mun jima da sanin Turawan nan zasu zo ƙasar mu Nigeria domin su bunƙasa wannan aikin nasu, sai ga shi abun da muke jira tsawon shekaru ya zo, amma muna son mu rasa komai, wanda kuma gagarumar koma-baya ne zamu samu in har bamu da kamasho a wannan katafaren Companin da zasu kafa a Abuja, baza mu taɓa bari wannan damar ta suɓuce mana ba. Ko nawa ne MD zamu baka domin mu ga mun lalata aikin SHAREEF'S Company a tafiyar nan, we want to remove the approval that the Turawa gave him, and take everything from him. Don haka muna neman taimakon ka MD."

Shiru Shuraihu yayi ya kasa magana bayan gama jin zantukan Alhaji Inuwa

Sai Honourable Ja'e yace, "ka ga Shuraihu, wannan taimakekeniya ce, kuma abun da zaka samu damu ko kwatan shi baza ka samu a  SHAREEF'S Company ba, in har ka taimaka mana haƙan mu ta kai ga ci, to, muna da babban kwamasho da zamu baka, burin mu kawai mu lalata aikin nan nashi, mu jawo musu asara sannan kuma komai ya dawo gare mu, sai da taimakon ka zamu samu damar cin galaba a kansa, yanzu idan ka amince ka haɗa hannu da mu, zamu tura maka 20 millions dollars. Wannan somin taɓi ne idan burin mu ya cika komai ya dawo hannun mu."

Jin wannan kuɗaɗen sai da murmushi mai sanyi ya bayyana a kan fuskar Shuraihu. Tabbas dama ce da zai yi amfani da shi domin nuna wa SHAREEF kuskuren sa na sauya sa da yayi wurin zana wannan sumfurin aikin. Shi yasa cike da nuna farin cikin sa a fili yace, "If so, I trust you, I will help you in this matter."

Murmushi dukkan su suka yi jin sun yi nasara a wannan fannin, tunda ko kusa basu taɓa tunanin amincewar sa cikin sauƙi ba, kawai sun yi masa tayin ne domin su gwada sa'ar su, amma abun mamaki lokaci guda sun yi nasara

Yayinda Alhaji Inuwa yace, "matuƙa mun ji daɗin amincewar ka, don haka kar ka samu damuwa in har kana tare da mu, to tamkar ka gama samun farin ciki ne, zamu yi tafiyar nan da kai kuma muna so ka nemo mana hanyoyin da zamu bi domin ganin mun ga bayan wannan companin, tare da sauran mutanen da zaka jawo mana hankalin su; su shiga cikin mu su ma, musamman ma PA na SHAREEF, don shima zai yi mana amfani a tafiyar nan, domin dana jikinka ake iya cin ka yaƙi."

Shuraihu yace, "well. you don't have any problem with that, I will help you a lot. Sai dai ina ga a nawa shawaran bai kamata a ce mun saka PA na SHAREEF a wannan zancen ba."

"Saboda me ka ce haka MD?" In ji Honourable Ja'e da ya riga furta hakan

Yayinda shi kuma Alhaji Inuwa yake ci gaba da kurɓan juice ɗin sa, while yana kafa wa Shuraihun ido da sauraron abun da zai ce musu

Shi kuma yace, "Ni ina ga kamar baza mu samu haɗin kansa ba, so kar kuma mu zo mu ɓata aikin mu, and kuma duk abubuwan da PA zai taimaka a kan tafiyan nan, babu wanda bazan iya taimakawa a kai ba, because a kaso ɗari cikin sirrukan companin, 30% shi ne wanda zamu iya sani daga Ni har shi, domin SHAREEF Mutum ne mai wayon da basira fiye da zaton ku, daga shi sai ɗan uwansa su suka san komai na sirrukan companin su, ba ya fitar da komai nashi sai idan ya san cewa Ni da PA mun sani, so kun ga babu amfanin kawo shi cikin tsarin."

Honourable Ja'e yace, "duk da haka MD, Ni ina ga PA zai yi mana amfani matuƙa, ka san shi ne yake tare da shi a koyaushe, wataƙil zai iya sanin abun da baka sani ba, duk da bamu ƙi ta taka ba, ai hanya komin ƙanƙantar sa muna buƙatar sa a tafiyar nan, dole muna bukatar PA na SHAREEF a wannan tafiyar, sauran kuma sai ka ji mana da su su ma. Ka fara tuntuɓar mana PA ɗin tare da nasa kason da muka yanke mishi 15 millions dollars in har zai ƙarba."

Jinjina kai Shuraihu yayi tare da cewa, "I will do what you want, from now on listen to Me you can always hear me."

Murmushi suka yi su dukka, suka ce, "You Are welcome MD."
Sai suka miƙa mishi hannu suka sake yin musabaha kowannen su cike da walwala da farin ciki a kan fuskarsa,
Inda suka yi sallama daga nan ya miƙe ya fita. Su kuma suka ci gaba da tattaunawa a kan matsalar tasu; suna jin daɗin yanda komai zai zo musu cikin sauƙi.






🔆🔆🔆🔆🔆🔆🔆🔆


                   Da dare lokacin suna zaune suna cin abinci a kan dinning. Dady yace ma SHAREEF, "zuwa gobe zai kai Maryamu school ɗin Abokinsa, already ya faɗa masa zai je da ita a yi mata komai, inyaso zuwa Monday sai ta fara zuwa school."

Da sauri SHAREEF ɗin ya ɗago kai yana kallon Dadyn, nan da nan ya haɗe rai yana cewa, "Ni kuma Dady? Meyasa sai Ni?"

"Sabida kai na zaɓa, kuma na ga gobe ba ka zuwa wurin aiki sai after juma'at that's the reason."

Ɓata fuska yayi yace, "Ni gaskiya bazan iya zuwa ba, Sadiq ya kaita. I don't have time to go anywhere, and tomorrow I will join the company early because we have work to do."

Murmushi Dady yayi yace, "kai nake so ka kaita, na gama magana fa."

"Dad..."

"SHAREEF, shut up, I don't want to hear from you again, kai duk yanda aka yi da kai sai ka saka gardama?"

Kallon Momyn yayi yana sake narke fuska, kana kuma ya mayar da kansa a ƙasa yana ci gaba da juya spoon ɗin hannunsa, tare da jin baƙin ciki na shigan sa nan take, meyasa Iyayensa suke son dole sai sun riƙa haɗa shi da wannan yarinyar ne? Shi fa ya tsane ta. He hates her so much, and he doesn't want to see her face, har cikin zuciyarsa yake jin haushin yarinyar haka nan. Ɗago kai yayi ya kalli inda take, sai ya ganta kuwa ta kafa mishi ido kamar mayya, zuciyarsa ne ta sake yin baƙi, ransa ya ƙara ɓaci, sai ya kafa mata nashi idanun shima kamar ya kai mata hannu ya kifa mata duka haka yake ji, amma ya san mai zai biyo baya muddin ya taɓa ta a gaban iyayen shi, musamman yanda ya ga alamun suna ji da ita. dayake tana kusan setting shi ne, shiyasa ya daidaici wurin ƙafanta ya hamɓare ta da ƙarfi

Wanda yasa Maryamu janye ƙafan nata da sauri tana sakin ihu

Dukkan su suka kalle ta, a tare kuma suka hau tambayarta cike da kula wa

Kallon da SHAREEF yake mata shiyasa tayi saurin haɗiye yawu tana ɗauke kanta, sai ta shagwaɓe fuska tace, "taune harshe nayi."

Dariya suka yi mata. Momy tace, "taune harshe kuma Maryam? Sai ki saki ihu kuma?"

Mike wa SHAREEF yayi sabida takaicin yarinyar, musamman yanda ya ga duk sun raja'a a kanta suna mata dariya. Falo ya koma ya zauna yana mayar da hankalin sa a kan wayansa, a hankali ya soma latsa wa yana hawa online tare da ƙoƙarin duba messages da suke shigo masa, yayinda ƙasan zuciyarsa kuma yana jin ɓacin rai har yanzu, maganar Dadyn ya tsaya mishi a rai matuƙa, a rasa wanda za a saka yakai kucakar yarinyar nan makaranta sai shi? Ga driver amma shi Dady zai zaɓa. Shi yasa ya kasa jure wa ya miƙe ya haura sama domin kiran Haseena a waya, don idan ya ci gaba da zama a haka ransa ƙara ɓaci yake yi, muddin yana son jin farin ciki da kwanciyar hankali, Haseena ce kaɗai zata iya sanya mishi wannan farin cikin, muryanta zai saka ya huce ya manta komai da ke ransa, shiyasa ya shige ya rufe kofar, yana faɗa wa kan gado tare da lalubo numban ta ya danna mata kira.
***

         Su Momy bayan sun gama cin abincin, su ma Falo suka koma suka yi zaman su a can. To kasancewar gobe za a kai Maryamu makaranta shiyasa tace mata, "ta je ta kwanta da wuri don ta tashi da wuri, sabida gobe kar ta makara."

Shi yasa dole Maryamun ta wuce ɗaki, tunda dama bata dogon hira sosai, yanzu suna fara hira zata ɓingire. Tana shiga ɗakin ta haye kan gado, yayinda ƙafafuwan ta suna a ƙasa tana kallon rufin ɗakin, sai kuma ta miƙe zaune tana shafo inda SHAREEF ya mare ta a ɗazu, yayinda lokaci guda ta tuna Jamilu wanda ta wanka mishi mari kawai don ya nuna yana sonta, sai ta ga tamkar ramuwa ce abun ya kasance, ga shi tana ji tana gani wani ya wanka mata mari bata da yanda zata yi bare ta rama, ya wuce da ajin ta; ya fi ƙarfin ta nesa ba kusa ba, lallai kuwa da ace wani ne ba shi ba, bata san me zai faru ba a wannan ranan, sai dai kuma har cikin zuciyarta tana jin shakka da ganin girmansa a idanunta, uwa uba kwarjinin sa da yake cika mata ido, tana ganin sam baza ta iya mishi rashin kunya ba, tunda ta ƙilla ido ta ganshi har yanzu bata samu sukuni a ranta ba, wani abu mai rauni ne yake mamaye mata zuciya domin ji take yi kamar tayi ta kurma kuka ko zata ji sanyi a ranta, tabbas ƙaunar SHAREEF ne yayi mata mugun kamun da ita kanta bata gama tantance mene ne ke damunta ba, kawai ta yarda tana sonshi amma ba wai azahiri ta san SO bane, kuma tana ganin babu mai raba ta da shi muddin tana numfashi sai ta zama Matar SHAREEF, ko me zai nuna mata zata iya jure wa har sai lokacin da ya ƙaunace ta. Miƙe wa tayi ta koma bakin mirror, sai ta saka hannu ta tuɓe doguwar rigan da ke jikinta, tana tsira wa halittar jikinta ido yayinda murmushi mai sanyi yake kwance a kyakykyawar bak'ar fuskarta, wani farin ciki ke fitowa daga ƙasar ranta sabida ganin yanda komai na cikakkiyar halittar Mace ya gama bayyana a jikinta, tabbas bata da makusa ko kaɗan, kuma ta kai Macen da zata iya zama a ɗakin Miji ba tare da tsoro ko fargaba ba, a yanda take da girman jikinta a zahiri wanda ya ganta zai yi tunanin ta haura shekaru 18, amma yanzu ne ma take shirin shiga shekara ta 16

Ƙugunta ta kama tana juya wa a hankali, daga bisani kuma ta soma magana da kanta a fili tana wani yatsina fuska cike da yanga, "Yaya SHAREEF babu mai raba Ni da kai, na zama chewing gum a cikin rayuwarka, wlh duk wanda ya sake yace zai raba mu sai na ga bayan shi nima, raba mu tamkar rasa numfashi na ne na har abada, domin babu wanda zan iya rayuwa da shi a cikin duniyar nan face kai, kai kaɗai ka dace da rayuwata, sai ka zauna da Ni ko ba ka so, zan jure komai a kanka."
Dariya ta kwashe dashi kamar wata somun hauka, sai ta ci gaba da juya wa tana ta kallon tsarin zubin halittar ta, har ta gaji don kanta sannan ta saka rigan ta koma ta kwanta. Wanda a ranan daƙyar ta samu barci ya ɗauke ta tsaban tunanin SHAREEF, gaba ɗaya ta hana kanta sukuni ta kasa barin zuciyarta ta huta a kan tunanin sa, wanda ya jawo har mafarki tayi da shi sun kasance a tare yana nuna mata madaran ƙauna tamkar zai cinye ta don so

Wannan dalilin ne yasa ta farka da safe cikin farin ciki da walwala. Ga ɗokin zasu fita tare shiyasa gaba ɗaya ta kasa sukuni, jikinta yana ta rawa, ga kuma heartbeat ɗin ta da ke ta faman buga wa tamkar zata faso ƙirjinta ta fito. Daƙyar ta iya shiryawa ta fito, shima don Momy tace mata, "tayi sauri ne ya fita waje yana jiran ta."
Tana sanye da doguwar rigan Abaya, rigan tana ɗaya daga cikin kayan da Momy ta siyo mata a jiya ne, duk da bak'a ce rigan amma bai hana yin mata kyau ba, kasancewar itama kyakkyawa ce ga manyan ido da Allah ya bata su tubarakalla, masu haske da ɗaukar hankali. Ta saka hoda a fuskarta sai ɗigon da tayi a saman goshin ta, sai ta shafa jan-baki raɗau a laɓɓanta. Gyalen kayan ta yafa wai ita zata yi irin na ƴan gayu, sai zame wa yake yi curin gashin ta da ya narke wuri ɗaya tsaban rashin gyara da samun kitso akai-akai, haka yake ta bayyana kan nata tana faman riƙe bakin wuyan ta, sai ƙafafun ta da ta sanya dogayen takalma masu igiya, since Momy ta fahimci tana son dogayen takalma shiyasa ta siyo mata masu igiya wadanda baza su kayar da ita ba, ai kuwa ɗagwas-gwas haka take tafiya da su

Su Dady sai dariya suke mata musamman yanda suka ga ta fito tana tafiyar nan, ga ɗankwalin kayan da ta yafa yana zame wa

Shi yasa Momy ta amsa tayi mata rolling ɗin sa, nan da nan baby face ɗin ta ta ƙara fitowa tayi ɗas, bakin nan sai walƙiyan jan-baki yake yi

Dady ya miƙa mata kwalin takardun ta yace, "daughter ga wannan ki tafi dashi tunda bai ɗauka ba, idan kun je can sai ki ba shi, takardun ki ne a ciki."

Sadiq ne ya amsa ya riƙe mata, suka fita a tare zai raka ta wajen, don shima mota zai hau ya wuce school

Ganin babu Motan SHAREEF a cikin gidan, sai Sadiq ya tsaya yana dube-dube da tunanin ko SHAREEF ɗin ya tafi ne. Kiran mai gadi yayi yace mishi, "ina Yaya SHAREEF?"

Mai gadi yace, "ya fita waje, yana nan yayi packing motan nasa a waje."

Kallon Maryamu yayi yace, "to yi sauri ki je ki same shi a waje kar ya gaji da jiran ki, bye sai kin dawo ƴar ƙanwata, ki kula min da kanki fa, and kin san me nace miki ko? Ki kama kanki ki ja aji ban da neman magana."

"To Yaya sai na dawo." Ta ɗaga mishi hannu tana farin ciki, ta nufi bakin gate ɗin a ƙafa

While Sadiq shima ya wuce wurin Motan sa yana shiga tare da tayar wa

Dalilin da yasa mai gadin ya ruga a guje ya buɗe mishi gate ɗin

Itama Maryamu sai ta fice ta babban ƙofan tunda already kafin takai Mai gadin ya buɗe, can gaba ta hango Motan SHAREEF a fake, alamun ita yake jira don motan ma a kunne take. Zuciyarta ne ta buga lokaci ɗaya; ɗan natsuwar da ke tattare da ita ta nema ta rasa. While she continued to have a strong heartbeat wanda yasa daƙyar take iya jan numfashi, haka ta nufi wurin Motan tana tafiya daƙyar kamar zata kife a ƙasa, sai faman zare ido take yi tana kallon Motan duk da ba ta hangen kowa a ciki.
[29/01, 8:47 am] OumƊahirah نفيسة: 🌱🌱🌱🌱🌱

      *SHAREEF*
          _SexyBoy_
🌱🌱🌱🌱🌱


_Writer: Nafisat Isma'il Lawal_
_Wattpad: UmmuDahirah_

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝*



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

       *P.W.A✍️*





*DATA SHARE*

Call, message or whatsap  07065334256

*MTN*
500MB 150
1gb  280
2gb.  560 
3gb.   840
4gb.    1120
5gb      1400
6gb.     1700
Verlid for 30 days.












__________
*BOOK1*
_______________*FREE PAGE18*
              Tsaya wa Maryamu tayi a wurin Motan; ta rasa yanda zata yi ta shiga tana ta zare ido

SHAREEF wanda ke cikin Motan, fuskarsa a matuƙar haɗe yana bin ta da kallo tun sanda ta fito, yayinda ransa ke ƙara ɓaci sabida kawai kallon fuskarta da yake yi, sai ƙare mata kallo yake yi yana ayyana wai wannan kucakar yarinyar bagidajiyar ƴar ƙauyen; ita zata shigar masa Mota? Bai san meyasa har cikin ransa yake jin mugun tsanar yarinyar ba, kwata-kwata ba ya jin ɗigon ƙaunarta a matsayin ƴar uwansa. Horn ya danna mata da ƙarfi yana kallon inda take, sai ya ga nan da nan ta firgita ta soma ƙoƙarin buɗe ƙofan gaban. A tsawace ya daka mata tsawa yana cewa, "You fool, don Ubanki ɓalla min motan za ki yi? Ko uban ki ya siya min iyee?"

Yanda yayi maganar dole yasa ta ja da baya, tana bin shi da kallo kamar zata haɗiye shi

Shi kuma wani tsawan ya daka mata yana cewa, "shegiya Jakar ƙauye, uban wa ya faɗa miki kin kai matsayin da za ki shigar min gaban mota? Common rufe min ƙofa ko in tattaka ki a nan wurin, ki ci gaba da kallo na wata rana sai na ƙwaƙule idanun." Ya ƙare maganar yana narka mata hararan da shi kansa bai san ya iya ba, don baƙin cikin da yake ji ma a lokacin, ji yake yi tamkar ya kifa mata mari

Maryamu kuwa nan da nan hawaye suka cika mata ido har sun soma ɗiga a kan dandamalin fuskarta, yayinda ta saki ƙofan da sauri tana kai hannunta saman kuncin ta tare da ƙoƙarin share su da sauri, domin ita kanta tayi mamakin zuban hawayen nata lokaci guda haka, kasancewar ta ba mai saurin kuka ba, zai yi wuya ka ga hawayen Maryamu koda kuka take yi baza su fito ba, amma kuma yanzu bata san meyasa raunin ta yake son bayyana a kan wulaƙancin da SHAREEF yake ƙoƙarin yin mata ba, zuciyarta ta kasa ɗauka, maganganun sa sun mata zafi, ta kasa jirga wa a wurin because does not know what to do next

Hakan ne ya ƙara fusata SHAREEF, sai ya fito da sauri yana kallonta, ya kasa ma magana don takaicin ganin yanda ta rufe ido tana faman hana bayyanuwar hawayen ta ƙasa. "Kee. Do you want to spend time with me? Muddin kika bari na taho inda kike wlh sai na kifa miki mari."

Har ga Allah bata san me zata yi ba tunda gani take yi ya hana ta shiga Motan, kuma bata san me yake nufi ba, shiyasa duk ta ruɗe ta kasa motsi a wurin, cikin raunin murya irin wacce ƙiris take jira ta saka kuka tace, "don Allah ka yi haƙuri, ban san me ka ce ba."

Gani yake yi kamar tana son mayar da shi mahaukaci, shi Mutum ne da zai yi wuya ka ji muryansa a sama koda faɗa yake yi, amma lokaci guda ɗan tsawan nan da yake daka mata sai da kanshi ya soma sara mishi, har idanunsa sun soma sanja kala tsaban ɓacin rai, sai ya taho kawai ya buɗe bayan motan, ya shaƙo wuyanta ya tura ta cikin Motan. And he said in a raised voice, "If you sit in my chair with this your dirty body sai na ci ubanki."

Tsaban ruɗe wa ma, bata fahimci mai yake nufi ba, shiyasa tuni ta tsoma ɗuwawun ta a kan kujerar

Ya kifa mata mari yana cewa, "sauka min a kujera, Jakar banza kawai Bagidajiya."

Kuka sosai Maryamu ta fashe dashi saboda zafin marin da ya ratsa ta, tuni ta sauka ƙasa jikinta na faman rawa ta haɗe kai da gwiwa tana sakin kuka mai tsuma rai

He had already closed the door, got back into the car, and quickly pulled forward, yanda kukanta ke ratsa mishi kunnuwa, shiyasa ya ja wawan burki, ya juya yana kallonta tare da cewa, "Shut up, or I'll throw you out."

Dole tayi shiru tana ƙara ƙudundune kanta daga tsakankanin cinyoyin ta, yayinda take ajiyan zuciya a hankali tana sake runtse ido While hawaye masu zafi suna sake zubo mata. A hankali take sauke numfashin kamar ranta zai fita a jikinta sabida yanda ta matse kanta sosai idanunta a rufe ruf, still hawaye masu zafi suna gudun tsere a kuncin ta, nan da nan kanta ya soma sara mata saboda yanda marin ya shige ta sosai, wadda bata saba ji ba, shiyasa nan da nan ta ruɗe jikinta sai rawa yake yi, tsawan da yayi mata har da shi ya ƙara ruɗa ta, lokaci ɗaya ta soma fita a hayyacin ta tunda ta hana kanta shaƙar iska sai faman kokawa da numfashinta take yi, yayinda kalaman SHAREEF ɗin suke ƙara sanya mata zafi da baƙin ciki a zuciyarta, musamman zagi da kiranta Jaka da yake yi, sai kawai wasu hawayen masu zafi suke ƙara ziraro mata tana sakin shashsheƙa a hankali

Tuni SHAREEF ya saka earphone a kunnensa, sabida ko kaɗan ba ya ƙaunar sake jin kukan nata daga cikin kunnensa, sai faman doka tsaki yake yi ransa yana ƙara ɓaci tare da jin ƙyamar ta kamar zuciyarsa zata fashe. Tsayar da Motan yayi a gefen titi ya saka face mask a fuskarsa, sannan ya feshe cikin motan da airfreshna yana yatsina fuskarsa

Just when Maryam raised her head and saw what he was doing. A hankali wasu hawayen suka ci gaba da ɗiga daga kan fuskarta, tana jin zuciyarta babu dad'i tare da jinta a muzance, sai ta mayar da kanta ta sake maida wa a kan cinyarta tana mai lumshe ido; tare da sakin nimfarfashi a hankali, a ranta tana tunanin abun da SHAREEF ɗin yayi mata a yanzu, amma duk da haka har a cikin zuciyarta wani sabon ƙaunarsa ne yake ƙara ruruwa a cikin ranta, duk da tana jin ciwon abun da yayi mata amma hakan bai sa ta sauya daga yanayin matsayin da ta ajiye sa ba, tana jin zata iya jure ko mene ne in har a kan ƙaunarsa ne, even in her heart she feels as if she will not spend time without getting his love, zata iya jure ko mene ne, soyayyarsa ita ce raunin ta, domin ji take yi kamar idan babu shi tamkar baza ta iya rayuwa ba kuma. Ɗago kai tayi ta tsira mishi ido yanda bazai fahimci tana kallonsa ba, yayinda wani sanyi da farin ciki ke ƙara huda mata zuciya a nan take, ta kasa ɗauke ido a kansa tsaban yanda ta shagaltu da kallon ƙira da baiwar halittar da Allah ya yi mishi

Komai nashi fes-fes ne kamar ka latsa shi jini ya zuba, ko daga kallonsa ka san yana ji da tsabta da gayu, fararen shadda ne a jikinsa bugaggiya da alamun ma sabo ne fil, don har wani ɗaukar ido take yi tsaban sabunta da yanda take shining, uwa uba da kallo ɗaya ka san kuɗin ta ya wuce a tsaya ana lissafi, sai shigan ta ƙara fito mishi da tsantsan kwarjinin sa gami da kamalan sa, kansa ɗauke da baƙin hula da ya mirza ta ta zauna mishi daram, yayinda sajen sa sai ɗaukar ido yake yi ya kwanta luf-luf har zuwa ɗan tsut ɗin gemun sa mai ban sha'awa. Sosai Maryamu ta gama shagaltuwa da kallonsa, har ta manta ma a inda take sabida yanda ta shige tunani tana ayyana abubuwa da dama a cikin ranta

Sai ji tayi ya dakatar da Motan, wanda hakan ne ya dawo da ita cikin hayyacin ta nan take, sai ta sake ware manyan idanunta a kansa tana jin zuciyarta na buga wa da sauri tare da fargaban kuma abun da zai biyo baya, musamman yanda ta ga ya fice daga cikin Motan, shiyasa itama sai tayi tunanin fice wa kar tayi wani laifin kuma. Tana jan ƙofan ta ga ta buɗe; shiyasa ta fice da sauri tana manne da kwalin takardun ta

Kallo ɗaya yayi mata ya wuce ba tare da ya sake bi ta kanta ba, har yanzu kuma akwai face mask a kan fuskarsa, sai ma ƙara gyara mishi zama yayi saboda ba ya son a ga fuskarsa tare da wannan kucakar yarinyar; It is his greatness that will spill

Da sauri Maryamu ta bi bayansa ba tare da tunanin komai ba, can daga nesa take biye da shi a hankali sabida ganin shima tafiyar da yake yi, kamar bazai taka ƙasa ba don taƙama da izza, "komai nasa shi dai mai kyau ne, ji be yanda yake tafiya?" Har shagaltuwa tayi da kallon tafiyar nasa zuciyarta na fari; ta kasa ko kallon tsarin makarantar ma bare ta san inda take jefa ƙafafun ta

Kasancewar school ɗin kowa na aji, tsit makarantar babu hayaniyar students kowa yana class yana ɗaukar darasi

Dayake SHAREEF bai taɓa zuwa school ɗin ba, shiyasa sai da ya tambaya wani Malami da ya gani a hanya, ya tambaye sa office ɗin principle, shi ne yayi mishi kwatance har ya dangana ga can

The principal is sitting on his chair, wanda alamun fitowar sa kenan daga ban-ɗaki yana share hannunsa da handkerchief. After he heard knocking, he gave permission to enter and looked at the door

SHAREEF ya shiga ciki, Maryamu na biye dashi a baya kamar wata jela sai zare manyan idanunta take yi

Cikin mutunta wa principal din yayi masa iso, tare da nuna masa wurin zama. Bayan ya zauna sai suka yi musabaha daga bisani kuma SHAREEF yace

"My dad told me to come and meet you, because you know about my arrival." Yayi maganar daƙyar fuskarsa babu walwala

Sai principal din ya ɗan sake kallon sa da kyau, sai kuma yace, "ok ko kai ne ɗan wurin Alhaji Ahmed da zaka kawo yarinya?"

Kai ya jinjina mishi Without saying anything

Sai ya ɗan faɗaɗa fara'an sa tare da cewa, "well. Doctor ya faɗa min ai, ita ce wannan yarinyar?" Ya ƙare maganar yana duban Maryamu

A yatsine dai SHAREEF ɗin ya amsa mishi, idanunsa a kan wayansa yana duba wa

Sai principal din ya kira Maryamu ta matso inda suke, ya dube ta da kyau yace, "ƴan mata mene sunan ki?"

Kai tsaye tace mishi, "Maryamu Haruna."

"Good. What school did you come from?"

Ɗan jim tayi, sai kuma tace, "Shaikh Ibrahim Arab Zaria."

"Masha Allah, kawo takardun mu gani, duk da dama already Doctor yayi min bayanin ajin da zamu saka ki.." sai ya tsayar da maganar nasa yana duba takardun. Bayan ya gama ya ɗauki waya yayi kira

It was not long before a teacher entered the office

Sai ya dube sa yace, "ku je da yarinyar nan sai a yi mata interview, SIS 1 za a bata, A. ko B. duk wanda ka ga ya dace da ita, sai ku je a ɗaukar mata har da uniform, a bata komai na school please ka hanzarta ko?"

"Ok sir." Ya amsa mishi cikin girmamawa, tare da duban Maryamun yana ce mata, "su je."

Haka Maryamu ta bi bayansa suka tafi

Kamar yanda principal din yace, hakan aka yi mata, tunda dama private school ne, komai su suke bayar wa har kayan makaranta da littafai, shiyasa duk aka bata ta dawo dashi office ɗin, after Malamin ya kaita har ajin da zata zauna ya nuna mata, SIS 1B

Daga nan SHAREEF ya miƙe suka yi sallama da principal ya fice abun sa. Kai tsaye motansa ya shiga ya kunna yana jiran ta shiga, yana jin sanda ta buɗe Motan ta shiga shiyasa ya ja da ƙarfi ya nufi bakin gate

Inda ta zauna ɗazu, yanzu ma nan ta zauna, don bata yi gigin sake zama mishi a kan kujera ba, yanzu sai farin ciki take yi sabida ganin an gama mata komai, sai zuwa school kenan? Ga Makarantar mai kyau kuwa, sosai ya bata sha'awa, musamman yanda students ɗin suka soma fitowa a lokacin da zasu fito daga school ɗin, alamun an tashe su break ne. Numfashi ta ja tana bin kayan hannunta da kallo; amma bata iya motsa su ba bare ta buɗe ta gani, tana tsoron tayi motsin da zata ɓata wa SHAREEF rai, shiyasa ta haƙura ta lafe kai a jikin kujerar tana ta satan kallon sa

A lokacin ma waya yake yi, da alamu ransa a ɓace yake, sai tsitsiya faɗa yake yi duk da muryansa ba a sama take ba, kuma da turanci yake maganar bata fahimci mai yake cewa ba, amma alamu ya nuna tsiya yake yi. Sai can kuma ta ga ya ja tsaki yana tsayar da Motan a dai-dai kan layin gidan su

Ba tare da ya juya inda take ba ya bata umarnin fita. "Get out."

Yanda muryan nasa ta ratsa mata kunne, nan da nan sai jikinta ya soma rawa, da sauri ta saka hannu ta buɗe motan ta fice. Kafin ma ta ƙarisa rufe murfin motan; ya figa motan a guje ya bar wurin da reverse. Da kallo Maryamu ta bi shi har ya ƙule ma ganinta, kana ta sauke ajiyan zuciya tana ɗan lumshe idanunta, meyasa take samun sauyin yanayi idan tana tare da shi? Bata san meyasa take firgita ta rasa ƙarfi da kuzarin ta ba, uwa uba tsoron shi da take ji wanda ba sabon ta bane hakan, sosai take jin shakkar sa da ganin girmansa a idonta, shi ne mutum na farko a rayuwarta da take tsoron ɓata mishi rai

Kayan ta kwashe a wurin, sabida tun lokacin da ta fito daga motan jiki na rawa ta sake su sabida ƙoƙarin ta na ganin ta rufe mishi ƙofan motan. Kwashe wa tayi ta miƙa hanyar da ta ga sun biyo ɗazu, Allah yasa an shigo anguwan kuma daga nan babu nisa, shiyasa ta gane gidan. Tana zuwa ta buga gate ɗin; Mai gadi ya buɗe mata ta saka kai ciki.
***



            While SHAREEF kuma, kai tsaye hanyar Company ya nufa, mirza Motan yake yi a hankali, yayinda yake duban wayansa yana laluban numban PA, The phone was ringing in his ear, while his eyes were looking at the street. A natse ya soma magana cike da izza yace, "Are you gone or kuna nan?"

"Sir bamu tafi ba, muna jiran MD ne yanzu zai ƙariso."

"Ok, ka bar su su tafi kawai, you stop and wait me, ka kira Mahmud su wuce tare."

PA bai tambayi meyasa ba, don haka ya amsa mishi cikin girmamawa

Shi kuma sai ya kashe wayan yana ƙoƙarin ajiye wa. Amma sai kiran Hanif ya shigo wayan, hakan ne yasa ya rage speed na Motan sosai yana ɗauka, in a slow voice yace, "Hey Guy, ina ka shiga na kira ban ji ka ba?"

"Bro I went to school, I was there taking a lecture, kai ya ɗauki zafi. I didn't see your call sai yanzu."

"Oh! Kuna shan gwale-gwale kenan?" Sai ya ɗan yatsina fuskarsa tare da furta, "na ɗan tausaya maka kaɗan."

Dariya Hanif yayi yace, "I didn't say I needed tausayin ka, nima na kusa huta wa since aski ya zo gaban goshi, mun kusa zuwa ɗaya ai."

"Ba wannan ba, ka duba message da na tura maka ta e-mail?"

"No, ban duba ba, yaushe ka tura?"

"Yau da safe ne, ka duba zamu yi waya later. I am driving now."

"Ok Bro, ya su Momy? Ban samu na kira su ba."

"Fine."

"Ya kanwarmu? Is that why you didn't tell me about her coming to the house? Kuma at least kai ya kamata in fara jin maganar a wurin ka."

Cikin rashin fahimta SHAREEF yace, "I don't understand you, who are you talking about?"

"Maryam mana, yarinyar da Dady ya kawo ta ƴar wurin sister ɗin sa. I am very happy, you see we got a sister, a little sister." Ya ƙare maganar da farin ciki

While SHAREEF sai ya ja tsaki tare da furta, "You are not serious wlh, I thought it was an important statement, to ina ruwana da ita?"

Da mamaki Hanif yace, "it is our sister ai, at least zamu yi farin ciki da zuwan ta, ko ba haka ba? Kuma don naga zata zauna tare da mu ne."

"I am also saddened by her arrival, kai baka ganta bane that's why kake furta hakan, wata mumu da ita, baƙa sai ƙaton ido a tsakar ka, ga kallon tsiya; alamu tsohuwar mayya ce yarinyar nan, duk yanda aka yi a ƙauyen su sun saba cin mutane." Sai ya ja guntun tsaki sabida takaicin tuno fuskarta da yayi

Yayinda Hanif kuma dariya ya kwashe da shi sabida jin abun da SHAREEF ɗin ya furta, "oh! Akwai aiki kenan Bro?"

Da rashin fahimta yace, "na me fa?"

"Har ina tunanin ko zamu haɗa ƴar gida ne, We just give her to you to marry, ashe kana mata kallon mayya ce...?"

"What...! Am I kidding you Hanif? Have you ever seen us play this game with you, or you want to annoy me?" Ya faɗa cikin tsawa da ƙoƙarin jan burki a bakin tanƙamemen gate na Companin su

Jin hakan da Hanif yayi ya san ya taɓo ƴan Maza, don ya san halin ɗan uwan nasa, shiyasa sai yace, "Sorry Bro, wasa nake maka Allah, Let's leave the conversation since you don't want to."

Cikin ƙunai rai yace, "dole ka faɗa haka mana, sabida baka kusa da Ni wlh da sai ka ga mai zan maka, shashasha kawai." Ya ja tsaki yana katse wayan,
Sai ya ajiye yana danna horn da ƙarfi ransa na suya,
Ana buɗe masa gate ɗin ya harba Motan ciki kamar zai banke mutanen da suke zirga-zirga a haraban Ma'aikatan, since ransa ya gama ɓaci da maganar Hanif ɗin.
[30/01, 9:06 am] OumƊahirah نفيسة: 🌱🌱🌱🌱🌱

      *SHAREEF*
          _SexyBoy_
🌱🌱🌱🌱🌱


_Writer: Nafisat Isma'il Lawal_
_Wattpad: UmmuDahirah_

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝*



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

       *P.W.A✍️*





*DATA SHARE*

Call, message or whatsap  07065334256

*MTN*
500MB 150
1gb  280
2gb.  560 
3gb.   840
4gb.    1120
5gb      1400
6gb.     1700
Verlid for 30 days.













__________
*BOOK1*
_______________*FREE PAGE19to20*
           Maryamu Sarkin zumuɗi, ta ƙosa Monday yayi ta soma zuwa school, kullum maganar ta kenan, har su Momy sun gaji da ji suyi ta mata dariya. Dole Momy ta saka Sadiq ya ɗauki Maryamun ranan Sunday suka je kasuwa aka sake mata siyayyar abubuwan da zata buƙata na makarantar, shoes and socks da kuma bag da littafai duk sai da aka sake siyo mata, dama dayake makarantar text books suka bata wanda dole a school zaka siye su tare da uniform. Komai an kammala mata; fara zuwa kaɗai ya rage

Ranan Monday kuwa da duku-duku Maryamu ta tashi, yau tana zumuɗi shiyasa ta tashi da wuri. Kafin ƙarfe shida da rabi har ta gama shirya wa ta saka uniform ɗin, ai kuwa ba ƙaramin kyau suka yi mata ba, duk da kasancewar ta Black beauty sai kayan suka haska ta, rigan fari ne da Hijabin, sai coffee color na wando irin mai zane-zane da aka yi shi da kalan farin, babu ɗankwali tunda Hijabin mai hula ne da aka yi da kalan wandon, ba ƙaramin mugun fito da kyawunta kayan suka yi ba, kamar don ita aka yi, sai tayi ƴar ƙarama a kayan yarintan ta ya fito ainun, ta sha Powder tare da ɗigon goshin ta, sai ta saka lipstick a laɓɓanta sai shining suke yi,
Ƙafafunta kuma sanye da cover shoes baƙi da farin socks dogo, sai ta goya Jakarta mai ruwan zuma babba wanda daƙyar take iya ɗaukar ta ma don girma,
A haka ta fito Falo ta tarar da su Dady zaune

Dady na riƙe da jarida tunda babu inda zai je yau, kayan jikinsa ma Jallabiya ne, suna ɗan taɓa hira da Momy, wacce take zaune gefen sa tana fifita mishi tea. Sai ganin Maryamun suka yi ta fito tana washe baki

"Inye.. inye.. wow daughter, ke ce kuwa?" Cewar Dady kenan cikin barkwancin sa yana dariya da kallonta

Ƙarisowa wurin tayi still tana washe baki; baki har kunne alamun farin ciki ya cika ta ne

Momy ma tace, "kin ganki kuwa ƴar Dady? Kin yi kyau Masha Allah, so beautiful."

Dariya tayi tana kama hannayenta wuri ɗaya, kanta a ƙasa ta kasa furta komai tsaban murna

Momy tace, "taho nan ki zauna, kuma haka ake yi har da ɗigo bayan kin san makaranta za ki je? Zo in goge miki."

Ƙarisa wa kusa da ita tayi, ta zauna Momyn ta kama mata hannu tana saka daya hannun nata tare da ƙoƙarin goge mata

While Dady kuma yana kallonsu da murmushi a face ɗin sa, sai yace, "to daughter yanzu sai fara zuwa makaranta, kinga sai ki mayar da hankali kiyi abun da ya kaiki, ban da wasa da shiririta kin ji ko?"

"To Dady."

"Masha Allah, ƴar Dady Allah yayi miki albarka."

Daga Momy har Maryamun suka amsa da Amin

Momy tace, "yanzu sai ki je ki karya kafin Sadiq ya fito ya kaiki, tashi maza ki je kar lokaci ya ƙure."

Miƙe wa Maryamun tayi ta wuce wurin dinning ɗin

Ajiyan zuciya Dady ya sauke tare da furta, "na so SHAREEF ne zai riƙa kaita tunda kinga muna bukatar shaƙuwar su sosai, amma taurin kai ne da Yaron nan wlh, duk da haka zan matsa mishi dole ya riƙa kaita wata rana, duk ranan da Sadiq bai da lecturen safe sai shi ya kaita in zai wuce wurin aiki."

"Nima haka na gani Alhaji, bari in duba Sadiq ɗin ko ya gama shirya wa tunda time ya kusa." Sai ta miƙa masa tea ɗin tana tashi ta wuce sama,
Ɗakin Sadiq ta shiga ta ganshi har ya gama shirya wa yana saka takalma a ƙafan sa,
Murmushi tayi tace, "Autana kayi kyau!"

Kwaɓe fuska yayi yana kallonta da cewa, "Oh! Momy, Ni yanzu fa na tashi a Auta, Maryam ne Auta ba Ni ba."

Shafa kansa tayi tace, "ban da abun ka, ai akwai Autan Maza, don haka har yanzu kai Autana ne, sai kayi aure sannan zaka girma a wuri na."

Dariya yayi yace, "kai Momy."

"To tashi mu je kar ka sa Maryam tayi late, har ta shirya ga ta can tana jiran ka."

"Ok mom I'm coming."

Fita tayi ta bar sa a nan yana gama ida shirin nasa, bayan ya gama ya ɗauki car key ya fito rataye da ƴar ƙaramar Jaka na Maza. Falon ya sauka ya ƙarisa wurin su Dady yana sake ma Dadyn Barka da safiya

Ya amsa shi cike da fara'a yana ƴar tsokanar sa kamar yanda ya saba wani lokacin, "ina ka shiga ka shuka min daughter tana faman jiran ka? Ka sa zumuɗi ya hana ta zama sai sunturi take yi."
Ya ƙare maganar yana kallon Maryamun da ta taso da sauri sabida ganin Sadiq ɗin ya fito

Dariya suka yi, har ita wacce ta iso wurin

Momy tace, "kin gama karyawan ne da kika taso?"

"A'a Momy, na ga Yaya Sadiq ya fito ne zamu tafi."

"To ban da abun ki, ai shima bai karya ba, ku je tare ku gama sai ku wuce kar lokaci ya ƙure."

"Mu je Little sister." Ya furta yana yin gaba,
Sai da suka ƙarisa wurin sannan ya kalle ta yace, "kin yi kyau my dear, dole na miki hoto in mun fita, I will save the history to remember another day."

Murmushi tayi duk da bata san me yace daga ƙarshe ba, sai tace, "amma Yaya SHAREEF bai ga kyawun da nayi ba? Ba na son nayi asarar kwalliyan nan nawa tunda nima nayi kyau."

Yanda tayi maganar cikin alfahari shiyasa shi yin dariya, yace, "kai Maryam kina da abun dariya wlh, and he will not wake up now,  amma idan nayi miki hoton zan tura mishi ko?"

Kai ta ɗaga mishi, sai kuma ta ɗan yatsina fuska da cewan, "ba haka na so ba fa amma. Anyway..." Sai kuma tayi shiru saboda bata san taya zata furta maganar da take son yi da turanci ba

Murmushi Sadiq yayi yana mamakin kakkamban yarinyar, tamkar ba a ƙauye ta fito ba, sai yace mata, "Oya mu ci abincin mu tafi."

Ita ta haɗa mishi tea, shi kuma ya zuba arish da ƙwai a plate, suka ci a tare tana korawa da ruwan tea ɗin ta wanda ta haɗa shi tun ɗazu, har ta cinye nata arish ɗin, but ganin ya zuba nashi ta saka hannu suna ci tare

Bayan sun gama suka dawo Falo, Sadiq yace, "zasu wuce."

Tare suka yi musu addu'a da fatan Nasara, sannan suka fita suka wuce inda Motan Sadiq ɗin yake, gaba ta shiga ya ja suka bar gidan

Sai surutu Maryamun take mishi a cikin Motan, tana faɗa masa yanda take jin zuciyarta na harba wa da fargaban makarantar

Shi kuma sai dariya yake mata yana cewa, "oh! Ashe kina da tsoro haka?"

Murmushi tayi tace, "kar in manta Yaya, kayi min hoton ka ji."

"Ok, let's go to the school, I'll do it for you. Da alamu ba kya son kyawun nan ya wuce Yayana?" Ya ƙare maganar cikin smile

Ita kuma sai ta rufe fuska tana ɗan jan numfashi tare da murmusawa. She feels happiness coming from the bottom of her heart, halin da take ji a game da SHAREEF ɗin bazai iya misaltuwa ba, amma ta san cewa shi ne farin cikin ta a yanzu, komai zata iya yi domin shi. Yatsunta ta haɗa wuri ɗaya tana murɗa wa bata sake cewa komai ba, yayinda ta faɗa duniyar tunanin sa wadda lokaci guda murmushin fuskarta ya gushe, cus bata san ta ya zata iya saka soyayyarta a cikin zuciyarsa ba, tana cikin matsananciyar fargaba duk ranan da ya ƙi amince wa da ita, tana ga kamar baza ta iya rayuwa ba a lokacin, kuma a ɗan wannan kwanakin da tayi a gidan; ta ga alamun tsanarta ƙarara a fuskarsa, da yanda yake nuna mata ko kusa babu ɓurɓushin soyayyarta a zuciyarsa, illa ma ƙyama da ƙiyayya da yake nuna mata ƙarara babu ko shakkar su Momy, abun na mata ciwo, ga shi kuma kamar tana ganin raunin ta a tare da shi, tana jin kamar baza ta iya jure ƙiyayyarsa ba

Hannunta Sadiq ya rike. Hakan ne yasa ta ɗago manyan idanunta da suka ɗan canza kala, ta zuba masa su tana bin sa da kallo kamar tana neman wani abun a fuskarsa

"Mene ne Maryam? Ya na ga kamar kin canza?"

"Yaya Sadiq, gani nake yi kamar Yaya SHAREEF bazai so Ni ba, ya tsane Ni sosai fa, ban san me nayi masa ba, kuma ka ga ina yin duk abun da kace in yi, amma ba ya so na."

"Haba ke kuwa, meyasa za ki ɗaga hankalin ki a kan ƴar wannan matsalar? Halin Yaya SHAREEF ne haka, idan kika ce za ki ci gaba da damuwa za ki ja ma kanki wata matsalar ne, Yaya SHAREEF halin sa kenan, ki bi sa a sannu wata rana zai riƙa nuna miki kulawa kamar sauran ƴan gida, kar ki damu ƴar kyakykyawar ƙanwata, Clear this word and focus on studying, you will be a big girl. Har durƙusa miki zai yi wata rana."

Dariya tayi tace, "haba dai, ba dai Yaya SHAREEF ba, ai ya wuce hakan wlh."

"Ok wasa kike gani ko?"

Murmushi tayi bata iya cewa komai ba tsaban farin cikin maganar nasa

A lokacin ya karya kwana ya shiga layin makarantar nasu, sai da ya isa bakin gate ɗin ya dakatar da Motan, sannan ya dube ta yace, "yauwa Masha Allah! Mun iso, bamu yi latti ba." Ya ƙare maganar yana duban haraban wurin da ɗalibai suke ta taho wa suna shiga cikin makarantar

Itama kallon wajen tayi, sai kuma ta dube shi tana langaɓe kai da cewa, "to saura hoton."

"Kai little sister ba kya mantuwa? Oya to, gyara in yi miki." Yayi maganar yana ciro wayansa

Gyara wa tayi da sauri tana kallonsa ta tsaya ƙyam ko ƙyafta ido ba tayi

Dariya ta ba shi, sai dai bai ce komai ba ya soma ɗaukar ta hoton, guda biyu yayi mata, tayi kyau kuwa, bakin ta a washe kamar gonan adduga, shiyasa dimples ɗin ta suka bayyana suka sake ƙawata Black beauty face ɗin ta. "Wow! My dear kin yi kyau sosai, kin gani." Sai ya nuna mata pictures ɗin

Sai murna take yi da farin ciki. Then they said goodbye and she left in the car, ya ja motan ya tafi tana ɗaga mishi hannu, sai daga bisani ta shiga ciki ta bi ayarin dalibai da ta ga suna ta faman gudu zasu wuce wurin assembly,
Itama can ta nufa kasancewar ta ga ɗaliban sun taru a wurin, ta shiga wurin ta shige cikin su ba tare da ta tantance layin wanne aji bane

Basu ɗauki lokaci ba aka gama duk abin da za a gabatar musu, sannan suka basu damar wuce wa class

Since already an nuna mata ajin da zata je, don haka can ta nufa kanta tsaye,
A lokacin ma duk ƴan ajin sun gama shige wa kowa ya zauna a wurin sa suna ta hayaniya,
Raba idanu ta soma yi tana neman inda zata zauna,
Sai wata wacce ke layin farko ta hannun dama ita kaɗai, ta ɗago ido suka haɗa ido da Maryamun, murmushi tayi mata tace, "Are you new here? zo ki zauna mana."

Babu musu kuwa Maryamu ta nufe ta ta zauna a gefen ta, basu kai ga magana ba sai Auntyn su ta shigo class din,
Don haka suka yi shiru kowa ya tashi don gaishe ta

Ta amsa su tana basu umarnin zama. After kowa ya zauna sannan ta soma gabatar da abun da ya kawo ta

Ita dai Maryamu nata ido ne don ba komai take fahimta ba, dayake zallan turanci ake musu kuma kasancewar ƙwararriya ce Malamar ga shi Physics take yi, so ba ta fahimtar komai sai dalala mata waɗannan manyan idanun nata da take yi, sam ba ta gajiya da kallon Mutum in ta zuba masa ido, haka zata tsatstsare ka dasu there was no sign of fear with her,
Har Auntyn ta gama ta fice wani malamin ma ya shigo

Kwata-kwata basu samu hutu ba sai da aka kaɗa break, sannan ne fa suka samu damar magana, wacce ta bata wurin zama ta miƙa mata hannu tana murmusawa tace, "Suna na Amina Khabaeer, na ji daɗin haduwa da ke."

Hannunta ta saka a nata sannan tace, "Ni kuma Maryamu Haruna."

"Wow! Nice name, kin shiga raina, I hope we will be friends?"

Kai ta ɗaga mata bata ce komai ba

Sai Aminan tace, "ki tashi mu je break mu ɗan sha iska."

Babu musu Maryamu ta tashi tana goya Jakarta a baya, kasancewar yanda ta ga Aminan tayi itama ta ɗauki nata Jakar, kuma yawanci ƴan ajin duk ficewa suke yi da Jakar su

Hannunta ta riƙe suka fita suka nufi wurin wasa inda aka tanadar a makarantar, wurin manya daban na yara daban. Wani ɗan corridor suka samu suka zauna, Aminan ta ciro musu food flaks a jaka, ta saka musu spoon tace, "su ci."

Sai Maryamun ta girgiza kanta tana furta, "a'a, nima na zo da nawa."
Itama ta ciro Jakarta tana fito da manya-manyan biscuits da ta zo da su

"To ai naki daban nawa daban, mu ci tare please sabida bazan ji dadin ci Ni kadai ba, na saba ci da Feena amma yau bata zo ba." Ta ƙare maganar tana ɗan langaɓe kanta

Maryamu da ke duban ta tace, "wace ce Feena?"

Murmushi tayi mata tace, "Feena wacce muke zaune sit ɗaya da ita ne, ita yarinyar mai makarantar nan ne, tun last Friday ba ta zuwa cus bata da lafiya, I think ma yau zata zo sai na ji shiru, shiyasa nace ki zauna a kusa da Ni."

Shiru Maryamun tayi bata ce komai ba

Sai da Aminan ta matsa mata sai ta ci abincin, dole ta saka spoon suka ci tare, in wannan ta ci sai ta ba wannan, daga ƙarshe bayan ta gama sai itama ta bata biscuits ɗaya. Daƙyar Aminan ta amsa tayi mata godiya.
Sai da suka ji an kaɗa class sannan suka koma aji

Dayake ajin basu da wani yawa, kuma dukka Yaran masu kuɗi ne kowa ba ya shiga harkan kowa, sannan ma da rashin sabo tunda duk yawanci new students ne, shiyasa babu ruwan kowa, wasu ma basu gama sanin sunan ƴan ajin ba, Maza da Mata ne a haɗe. Layin Maza daban na Mata daban

Ita dai Maryamu har aka gama karatun bata fahimci me ake yi ba, har suka tafi break na biyu wanda suka gabatar da sallan azahar. Daga nan ne suka soma gabatar da karatun Arabia da litattafan Islamiyya, tunda makarantar tsarin su kenan, sai ƙarfe biyar ake tashi kullum ban da ranan Friday 

Before a tashi ma har sun yi sabo da Amina tamkar sun san juna, tunda duk kusan Sa'anni ne haka suka saki jiki suna ta hira da dariya, ko'ina tare suke zuwa, Amina sai nuna mata wurare da dama take yi inda ya kamata ta sani,
Shi yasa Maryamu ta ɗan samu walwala a makarantar, karatu kuwa dama ba a magana tunda bata fahimta ba, ga shi ba a Hausa sai turanci da larabci, tsarin makarantar yayi mata matuƙa musamman yanda ta ganta cikin ƴaƴan masu kuɗi tsundum, dama Maryamu da rawan kai da nuna iyayi, shiyasa nan da nan ta saje da su tana nuna itama kamar ƴar masu kudin ne, domin babu wanda zai ganta yace ba daga ƙauye ta fito ba, sai ficchi da iyayi take yi, yau rana ɗaya daga zuwan ta sai da suka kusa dambe da wata yarinya

Bairo ne ya faɗi a ƙasa, sai yarinyar ta ɗauka tana ƙoƙarin saka wa a jaka. Maryamu kuma tana ƙilla ido ta ga lokacin da ta ɗauki bairon, bata tantance nata bane kawai ta ƙwace bairon tana hararan yarinyar

Ita kuma ta bi ta da kallon mamaki tana cewa, "ke lafiya za ki ƙwace min bairo?"

Wani hararan Maryamu ta maka mata tana cewa, "to ɓarausu, daga ganin bairo ya faɗi sai ki kama ki ɗauka za ki wani ƙaƙaba a Jaka? To Allah yasa na ganki balle ki ce naki ne."

"Nawa ne mana, yanzu fa na yar sai ya gangaro wurin nan na zo dauka."

"Karya kike yi wannan bairona ne, ki je wata ƙaryan ba wannan ba."

"Yau na ji ikon Allah! Ni da bairona ki ce ba nawa ba? Wlh sai kin bani."

"To zamu gani tunda uwar ki ta siyan min, daga zuwa da bairo yau har zai zama naki? A gidan uban wa ya zama naki?"

Jin zagin da Maryamun take liliyo wa, sai ƴan ajin suka saki baki suna kallonta

While Amina ta shiga tsakani tana kallon yarinyar tace, "Hafsah kin tabbatar naki ne?"

    

"Wlh nawa ne, yanzun nan ya faɗi shi ne na zo ɗauka kuma ta ƙwace."

"Kan Uba.. sannu sara mai baƙar ta kashi, na rantse da Allah ko kin fi uban wa maita a nan bazan ba ki Bairon nan ba, kaji min yarinya da shegen tsurfa a gidan uban wa Bairon zai zama naki? Bayan yanzu kika ɗauka a gefen ƙafa na? As for i, me hate lies and me hate those who make them." Tayi maganar tana tsuke ƴar ƙaramar fuskarta

Duk wurin sai suka yi shiru suna zuba mata ido da ganin ikon Allah, musamman yanda ta saka wannan shegen turancin nata. Nan fa wasu suka soma ƙumshe baki suna son yin dariya, amma kuma tsoro ya hana su saboda gani suke yi tsab Maryamun zata iya komawa kansu ganin yanda take da tsiwa sai wur-wurga idanu take yi tana fiƙi-fiƙi dasu alamun babu tsoro a tare da ita

Yayinda ita Hafsah tsaban takaici ne ya hana ta magana, ƙiris take jira tayi kuka musamman zagin da ta ji Maryamun na liliya mata

Amina ce ta kalli Maryamun, itama jikinta a sanyaye tace, "but sister ki duba Jakar ki mana, idan ba ki ga naki ba sai mu san abun yi ko?"

Maryamu duban ta tayi, sai tace, "to ai na san a nan na ciro nawa, in ba fiffike ne dashi ba taya zai koma cikin Jakana? A nan na ajiye shi tun lokacin da Teacher ɗin nan ya fita."

Shiru suka yi suna zuba mata ido babu mai magana

One of the class members, da alamun shi ne Monitor ma, sai ya dubi Maryamu yace, "ke meyasa baza ki duba Jakar naki a gani ba? Ki duba mu gani in kin saka naki."

Yatsina fuska tayi tana ɗauke kanta a kansa, sai ta sake tsuke fuskarta ta ɗage kai alamun baza tayi abun da yace ba

Cikin rarrashi Amina ta ƙara matsowa kusa da ita tana cewa, "Please Maryamu miƙa mata Bairon, ina da wani sai in ba ki."

"Allah bazan bayar ba, tunda ba ita ta siya min ba, bazan taɓa bata bairon nan ba, haka kawai daga zuwa da abu yau sai ta sace min? Tunda ɓarauniya ce ita."

Kuka Hafsah ta saka saboda jin sunan da Maryamu ta kira ta dashi

Yayinda ƴan class din su kuma suka soma hayaniya, wata da friend ɗin Hafsan ne tace, "sai ta je ta faɗa ma Uncle tunda Maryamu ta kira Hafsah da ɓarauniya."

Ana haka sai aka kaɗa bell alamun an tashi,
Miƙe wa Maryamu tayi ta tusa Bairon a Jaka tana rufe wa, sai ga wani ya faɗo daga jikinta alamun ya maƙale ne a rigan ta

Da sauri Amina ta ɗauka tana cewa, "yauwa Maryamu ga naki nan fa, kin gani ko, ga shi ya faɗo a jikin ki."

Shiru Maryamun tayi tana kallon Bairon

Ƙawar Hafsah mai suna Luwaisa tace, "ashe ke ce ma big Thief bamu sani ba? Amma kin zo kina ma mutane rashin kunya daga zuwan ki yau kin soma fitsara da rashin kunya, wlh kamar a kunnen Uncle Allah ya kaimu gobe sai mun kai ƙaran ki."

Ko kaɗan Maryamu bata nuna tsoron ta a fili ba, duk da jikinta yayi sanyi sabida yanda ta haƙiƙance tana surfa tijara, sai ga shi ita ce da laifin. Shiyasa ta jefa wa Hafsan Bairon tana cewa, "kin daɗe ba ki kai ƙaran nawa ba, inyaso kar a bar Ni da rai kin ji ko?" Ta ja tsaki tana ƙwace Baironta daga hannun Amina tare da zura wa a Jaka, ta goya Jakar a baya tana jan jiki ta wuce ba tare da ta kula kowa ba,
Duk da hayaniyar da class din suka ɗauka suna surutu a kan abun da Maryamun tayi,
Wasu kuma suna bama Hafsah haƙuri a kan abun da tayi mata, ciki kuwa har da Amina wacce take cike da mamakin Maryamun, daga zuwa yau ta soma neman rigima, ko tsoro ba ta ji a ɗauki mataki a kanta

Ita kuwa Maryamu kai tsaye hanyar fita makarantar ta nufa kamar yanda ɗaliban school ɗin suke ta tururuwan fice wa zuwa haraban wajen gate, since ba a barin Motoci su shigo ciki in har ba na teachers bane, kowa a bakin gate yake faka wa tunda akwai fili mai yalwa, sai su ɗauki yaran su daga nan,
Maryamu na fita ta hangi Motan SHAREEF a waje a fake, duk da a ranta tayi mamakin ganin Motan sak irin nasa, kuma ta tabbata shi din ne, shiyasa har ranta ta ji wani irin sanyi ya mamaye mata zuciya, lokaci ɗaya ta manta da komai da ya wakana nan farin ciki ya bayyana a kan fuskarta, da sauri ta nufi wurin a zuciyarta tana fatan a ce shi ɗin ne ba wani mai kama da Motansa ba, since ba a ganin na cikin Motan.
[01/02, 9:57 am] OumƊahirah نفيسة: 🌱🌱🌱🌱🌱

      *SHAREEF*
          _SexyBoy_
🌱🌱🌱🌱🌱


_Writer: Nafisat Isma'il Lawal_
_Wattpad: UmmuDahirah_

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝*



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

       *P.W.A✍️*





*DATA SHARE*

Call, message or whatsap  07065334256

*MTN*
500MB 150
1gb  280
2gb.  560 
3gb.   840
4gb.    1120
5gb      1400
6gb.     1700
Verlid for 30 days.











__________
*BOOK1*
_______________*FREE PAGE21*
               "Are you still here, baka tafi ba?". Shuraihu said that when he entered the office, he saw Mahmud working

Kallonsa Mahmud yayi yana faɗin, "eh har yanzu ina nan, ina son in kammala wannan lissafin ne, cus chief accountant yana jiran in tura mishi, that's why na zauna ina son in ƙarisa."

Samun wuri Shuraihu yayi ya zauna yana duban sa, tare da cewa, "There is something I want to talk about, that's why I'm following you here."

Ɗago kai Mahmud yayi yana dakata wa daga latsan computern da yake yi, tare da kallon Shuraihun yace, "ok Ina jin ka, Allah yasa lafiya?"

Smile Shuraihu yayi yace, "lafiya lau sai Alheri." Sai ya gyara zaman sa sosai a kan chair ɗin da ya zauna, tare da faɗin, "ina son ka fahimci maganata Mahmud, na san zaka ji maganar tawa ta zo maka wata iriya, amma kuma Ni a ganina ƙaruwar mu ne sosai, abun da zamu samu a Companin nan kaɗan ne da wannan aikin da zamu yi." Sai ya ɗan ja numfashi yana ƙoƙarin kamo bakin zaren ta inda zai fara sanar da Mahmud ya fahimce sa

Yayinda shima ya natsu sosai ya zuba masa ido yana jiran me zai ce

"Na san abubuwan da ke faruwa a game da wannan kwangilar da muka amsa na su Mr. Pitter, kuma ka san a halin da su Alhaji Inuwa suke ciki a game da son dole sai sun samu hannun jari a cikin companin nan, to shi ne muke so mu haɗu mu taimaka musu kamar yanda suke buƙata, they promised us more money than we will get in this job, ka san cewa dai idan mun yi aiki a wannan Companin ba wani abun kirki zamu samu ba, kawai zamu haɓaka Companin ne amma ba wai don mu ƙaru ba, shiyasa suka yi mana tayin nan mu samu mu taimaka musu aikin nan ya lalace ko kuma su samu wata shiyya a ciki, don muma mu ƙaru."

Mahmud wanda yayi kasaƙe yana kallon Sharaihu da ke koro bayani, mamaki sosai ne ya cika sa wanda yasa ya kasa magana sai buɗe baki da hanci da yayi yana bin sa da kallo kamar ya samu TV, a yanda ya fahimci maganar Sharaihun abun ya ɗaure masa kai matuƙa, bai taɓa tunanin Shuraihu yana ɗaya daga cikin waɗanda zasu ga sun durƙusar da wannan Companin don kawai son abun duniya ba, duba da yanda ya ga SHAREEF ya taimaka masa a rayuwa, abun mamakin lokaci guda Shuraihu ya zo ya samu aiki a wannan Companin aka ba shi muƙamin Manager, kuma amma wai yau da shi ake son haɗa baki domin a durƙusar da companin; after all ya san cewa muddin suka yi wannan aikin ba ƙaramin ci gaba Companin zata samu ba, kuma ba ƙaramin maƙudan kuɗi za a samu ba, zata yi suna fiye da nan ƙasa Nigeria ma, tunda aikin da zasu yi haɗaka ne da sauran ƙasashe na ƙetare. Har a cikin ransa ya ji babu dad'i da jin zancen Shuraihun, wanda yana jin cewa bazai taɓa cin amanar wannan Companin domin ya haɗa hannu da wasu don ganin bayan su ba, ko me zai samu kuwa ba ya jin zai iya taimaka wa wannan zaluncin, shiyasa ya buɗe baki yace, "MD ban taɓa tunanin waɗannan maganganun zasu fito daga bakin ka ba wlh, haba kai kuwa, ko ma me zaka samu ai ina ganin bai kai ya wannan Companin ba, kar ka manta a ƙarƙashin ta kake aiki, idan kuma ka ƙi ci gaban su mene ne amfanin zaman ka a ciki? Ai idan kana so kayi alfahari shi ne ka taimaki wurin da ka san kana samun gumin ka, a ce sun fi kowa ci gaba; ba wai ka bada goyan bayan durƙushe su ba."

Shuraihu dariya ya ɗan yi kaɗan yana cewa, "to ban da abun ka Mahmud ina ci gaba a nan? Ina maka zancen miliyoyin kuɗi ne fa wanda zamu samu a wannan aikin in mun taimaka musu su ma sun samu, kana ganin a nan zamu samu ne? Iyakan fa a biya mu albashin mu ne shikenan fa, ka ga idan zaka yi aikin nan kawai ka faɗa min mu san abun yi, tunda sai da taimakon ka zamu samu biyan buƙata cikin sauƙi, 15 millions dollars suka yi maka alƙawari in har zaka bamu haɗin kai."

Girgiza kansa ya soma yi tare da furta, "never, baza a yi wannan cin amanar da Ni ba, bazan iya taimaka wa ba MD."

"Baza ka iya taimaka wa ba?" Shuraihu ya maimaita zancen nasa cike da tsantsan mamakin jin furucin sa, tunda a tunanin sa da ya ji kuɗin da zai samu zai iya bayar da haɗin kai

Shi kuma sai ya ba shi tabbaci da cewa, "ƙwarai kuwa, bazan iya ba, a inda Allah ya ajiye Ni a nan zan zauna, tamkar cin amana ne wannan, bayan ka san cewa wannan Companin su suke da alhakin gudanar da ayyukan nan, amma kuma don son zuciya a ce mun ɓata komai domin wasu su samu? Ai nima ina son ci gaban wurin aiki na, bazai yiwu ba tunda ba dasu nake aiki ba, a nan nake aiki, don haka bazan so ganin durƙushewan ma'aikatan nan ba."

Shiru Shuraihu yayi yana mai mamakin maganganun Mahmud ɗin, ya san cewa shi ne Supervisor na companin gaba ɗaya, wanda sai da sahalewar sa ake shigowa da kaya kuma a fita da su, shi ne ja-gaba da in har suka saka shi a tafiyar nan, komai zai zo musu da sauƙi, zasu iya ɓata shirin ma'aikatan; su gurɓata ayyukan, amma kuma ga shi ya nuna bai amince musu ba

Mahmud wanda ya mayar da kansa ya ci gaba da latsa computern nasa, ba tare da ya sake bi ta kan Shuraihu ba, sai dai a ransa yana tunanin zancen Shuraihun da ya tsaya mishi a rai

Mike wa yayi yace, "Let me pass, but think again Mahmud, you still have a chance if you agree."

Ɗago kai yayi ya ɗan tsira masa ido, but bai ce mishi komai ba har ya fice yana faman bin sa da kallo, sai da ya rufe ƙofan before ya ja numfashi yana girgiza kansa, dole yayi wani abu a kai, tabbas bazai taɓa yarda su ci galaba a kan Companin nan ba, dole ne ya sanar da SHAREEF halin da ake ciki, amma kuma ba wai sanarwar bane, ta yanda SHAREEF zai amince da maganar yake tunani, tunda ya san yanda SHAREEF ya ɗauki Shuraihu a wannan ma'aikatan, suna ɗasawa sosai, kuma ya yarda da shi matuƙa, shi kansa yana mamakin meyasa Shuraihu yake son cin amanar SHAREEF ne, amma ko mene ne dole ya san abun yi, dole su canza taku a kan wannan aikin nasu, ya kamata ya san ta ina zai ɓullo.
***



              Shi kansa Shuraihu ya shiga zullumi da tunanin abun da zai biyo baya kasancewar Mahmud bai basu goyon baya ba, tunda bai taɓa tunanin hakan ba, ga shi yanzu ya bayyana mishi ƙudurin su kuma ya ƙi basu go ahead, fargaban sa idan kuma ya sanar da SHAREEF ɗin fa? Wannan fa babban ganganci ne, idan ya sanar mishi tamkar ya gama rusa mishi mafarkin sa ne, shikenan zai rasa aikin sa, SHAREEF dole zai kore sa, ya ga samu ya ga rashi kenan, shi bai samu kuɗin su Alhaji Inuwa ba, sannan kuma ya rasa babban aikin sa, me zai yi? Hankalin sa ya tashi fa, don haka ya koma office ɗin sa ya kira numban Alhaji Inuwa ya zayyane mishi halin da ake ciki

Shi kansa ya ruɗe kuma ya shiga damuwa, "yanzu ya kake ganin zamu yi?"

"Gaskiya akwai matsala Alhaji, tunda har ya ƙi amince wa kuma ga shi ya san sirrin mu, duk abun da ya biyo baya dole mu zai zarga, kuma na tabbata Mahmud ba lallai ya bar zancen a iya cikin sa ba, dole zai fesar wa SHAREEF ya san halin da ake ciki."

"To in haka ne zamu ƙara mishi kuɗin ko zai amince mana, kayi masa tayin 20 millions domin samun amincewar sa."

Shiru Shuraihu yayi yana tunanin anya Mahmud zai amince? Amma sai yace, "shikenan Alhaji, ko me ke akwai zan sake tuntuɓar ku."

"And if he doesn't agree, then we know what to do."

"Ok Sir."
Daga nan yayi sallama da shi ya kashe wayan, tare da soma sintiri a cikin office ɗin nasa yana yi yana cizan yatsa.







🔆🔆🔆🔆🔆🔆🔆🔆


              Direct wurin Motan Maryamu ta nufa zuciyarta na ɗan bugawa da ƙarfi, duk da farin ciki da zumudin saka ran ganin SHAREEF ne ba wani ba. Ita dai a sanin ta wannan ne Motan da yake hawa, shiyasa da ta isa bakin motan sai ta saka hannu ta buɗe back door, nan idanunta suka sauka a kansa yana zaune ya ɗaura earphone a kunnen sa, babu hula a kansa sai wannan askin nasa mai tarin gashi a gaban ya sha gyara yayi baƙi siɗik, jikinsa sanye da white suite, komai na jikinsa whit color ne, inda ya ɗaura kansa a jikin kujerar ya lafe sosai kansa a sama idanu a lumshe

Jin an buɗe Motan; shi ne dalilin da yasa ya buɗe ɗan madaidaitan idanunsa da suke fari tarr gunun sha'awa. Ko kaɗan bai juyo ya kalli inda Maryamu take tsaye ba saboda ya san cewa bazai wuce ita ɗin bace, ba ya buƙatar kallon bak'ar fuskarta shiyasa ya tayar da Motan

Hakan ne yasa Maryamu tayi saurin shige wa ciki jikinta yana rawa, bata yi gigin zama mishi a kujera ba since he warned her from the beginning. A ƙasa ta zauna ta manne fuskarta a jikin kujerar gaban tana faman leƙan fuskarsa, zuciyarta na mata wani irin sanyi wanda take ji har can cikin ƙasan zuciyarta, a hankali duk wani kasala da damuwa ya soma gushe mata, ba ta ganin komai sai fuskar SHAREEF wanda take mata ƙawa da saka ta a nishaɗi da manta inda take a duniya, tunda ta kafa mishi ido bata ɗauke su a kansa ba sai faman haɗiyar yawu take yi tana lumshe ido kamar mai jin barci

Wanda shi SHAREEF bai san a halin da take ciki ba, domin tunda ya taka motan ya soma tafiya sai ya ƙure ƙaran waƙar da ya sa; yana kaɗa kansa a hankali, tare da son gusar da ɓacin ransa da ke cikin zuciyarsa, har a ransa haushi da takaicin dauko yarinyar yake yi, wanda daƙyar Dady ya tilasta mishi a kan dole sai ya dauko ta, shiyasa yake jin ɓacin rai a zuciyarsa, dalilin da yasa ya ɗaura earphone a kunnensa kenan yana sauraron waƙar da zai kwantar masa da hankali don manta halin da yake ciki. A cikin ƙanƙanin lokaci ya iso gida sabida gudun da ya sharara a kan kwalta. Ana buɗe masa gate ya harba motan ciki zuwa packing space. Dakatar da Motan yayi yana faman ajiyan zuciya a hankali, tare da lumshe idanunsa yana cije leɓe yana jiran yarinyar ta fita sannan shima ya fita

A sa'ilin itama Maryamu ta dawo hayyacin ta, bata san cewa an kawo ba sai da ta kalli haraban gidan; ta ga a inda suke. Sannan ne fa ta saka hannu tana buɗe motan da sauri ta fice, har tana sake waigen sa sannan ta rufe ƙofan, ta wuce cikin gidan tana harɗe ƙafafu kamar zata kifa don gajiya da nauyin Jakar da ke bayanta,
Tana shiga Falon babu kowa shiyasa kai tsaye ta wuce ɗakin ta, tare da zare Jakar daga bayanta tun kafin ta kai, sabida ba ƙaramin azaba kafaɗun ta suke mata ba tunda bata saba da wannan jibgegiyar Jakar da aka cika mata da Littafai ba


Tun fitan ta shi kuma SHAREEF ya ƙi fitowa a Motan bare ya buɗe idanunsa, sai da ya tabbatar ta daɗe da fice wa sannan ya buɗe ido ya zare earphone ɗin daga kunnen sa, wayansa ya cire yana buɗe Motan ya saka ƙafafuwan sa a waje, before ya zaro jikinsa ya fito gaba ɗaya yana riƙe da Jakar aikin sa, wayansa kuma a hannu ya nufi cikin gidan kansa tsaye, inda fuskarsa kaɗai zata nuna iya tsananin gajiyan da ya kwaso

Shigansa cikin Falon yayi dai-dai da fitowar Momy daga ɗakin ta; ta biyo steps tana sauko wa. Doguwar riga ce a jikinta mai sauƙin nauyi fara ƙal da ɗige-ɗigen kore, ƙafafunta sanye da slippers; kanta kuma ta ɗaura baƙin ɗankwali. Idanunta ta sauke a kan SHAREEF ɗin tana kallonsa ba tare da ta furta komai ba

Shima idanunsa a kanta yana ɗan narke ido tare da nufan inda take. "Mom barka." Ya furta sa'ilin da ya iso kusa da ita yana ɗan kawar da kansa daga kallon da take mishi

Ita kuma kallon tuhuma take mishi tare da cewa, "ban ji sallaman ka ba?"

"Mom nayi da na shigo."

Hararansa tayi tace, "kai ɗin? Dama ban san hali bane, ai da kayi tun daga nan zan ji."

"Mommy." Ya furta yana narke fuska ya kasa kallon cikin idonta

"Ka dena kira na tunda ba ka jin magana, baza ka dena wannan ɗabi'ar ba, sallama ya gagari ɗan musulmi bayan sarai ba ciwon baki kake yi ba, muryan da zaka ɗaga kawai ka buga sallama kowa ya ji amma kana ganin asara?" Sai ta ja tsaki cike da ɓacin rai

Sanyi jikin SHAREEF yayi, but ya gaza ɗago kai ya kalle ta sabida ba ya son su haɗa ido da ita

Wuce wa tayi zata nufi kichen, har ta gota sa sannan tace, "ina fatan ka ɗauko Maryam daga school?"

"Eh na ɗauko ta." Ya amsa yana bin bayanta da kallo

Bata ce mishi komai ba ta wuce kichen kai tsaye

Shi kuma sai ya kasa tafiya sabida yanda Momyn ta nuna masa, ya san ranta ya ɓaci, sai da ya ɗan ja lokaci a tsaye a wurin sannan ya wuce ɗakin sa since ya gaji sosai, wanka yake so yayi ya samu relief. Shiyasa yana shiga ya soma kwaɓe kayan sa ya faɗa wanka.
***

          Maryamu kuwa tunda ta shiga ɗakin ta sai ta jefa Jakar a kan gadon ta, tare da hawa kai ta zauna tana sauke numfashin wahala, sai a yanzu ta ji wata muguwar yunwa tana ƙwaƙulan ta, miƙe wa tayi ta cire kayan jikinta dukka ta zuba a saman gadon, sannan ta duba closet ɗinta ta ciro Riga da wando ƴan kanti ta saka a jikinta bayan ta saka under dress. Kayan masu taushi ne kalan peach, sai rigan da aka yi mishi kwalliyan saƙar farar zare, kamar aiki a gaba ɗaya gaban rigan, kayan suna da kyau da tsada shiyasa suka yi mata kyau itama,
Hula ta ɗaura a cinkus ɗin gashin ta da bai samun gyara bare kitso, sai ta fita da sauri ko takalma babu a ƙafanta ta nufi Falo,
Har ta kalli dining kuma sai ta wuce kichen sabida jin ɓuruntu a ciki

Kamar yanda tayi tsammani kuwa Momy ne a ciki tana aikace-aikace zata ɗaura abincin dare,
Tana shigowa itama Momyn ta ɗago tana kallonta, fuskarta da yalwan murmushi tace, "ah ƴan makarantar Bokoko, har kin dawo ashe?"


Murmushi itama Maryamun tayi cike da farin ciki tace, "eh Momy, sannu da aiki."

"Yauwa, ya karatun? Ina fata an mayar da hankali sosai?"

Ɗaga kanta tayi tana murmusawa

"Masha Allah, yanzu ki je kan dining ki zuba abincin yana can."

"To." Ta amsa tana ƙoƙarin juya wa ta fice

Momy tace, "ina takalman ki kika fito haka nan?"


Tsaya wa tayi tana juya wa ga Momyn, sai kuma ta kalli ƙafanta tare da bata amsa da faɗin, "Momy na bar su a ɗaki."

"Kar in ƙara ganin kin fito babu takalma kin ji ko? Ko sanyin teyes ma ai zai dame ki, ki fara zuwa ki saka takalman first before ki dawo."

Cikin girmamawa ta amsa wa Momyn tana juya wa da sauri ta fice. Kai tsaye dakin ta koma ta ɗauki slippers ta zura a ƙafafunta, kana ta wuce saman dining ta zauna tana buɗe babban coolern da ke wurin, shinkafa mai man gyaɗa ne da wake a ciki, kaɗan ne ma a ciki don ya kusa ƙare wa. Sai ta ɗauki plate ta shaƙe shi da abincin, sannan ta zuba salad a sama ta saka spoon ta soma haɗiya cikin sauri; sabida yunwar da ke addabar ta, ga daɗin abincin da yake motsa mata har kunne tsaban yanda testing ɗin yake kai mata,
Kamar daga sama ta hango SHAREEF yana sauko wa daga matattaƙalan benen, lokacin dai-dai ta saka wani ƙaton loma suka haɗa ido dashi,
Lokaci ɗaya ta shaƙe sabida wata uwar harara da ya jefa mata idanunta na shiga cikin nasa,
Lokaci ɗaya ta kasa riƙe kanta, nan da nan ta ƙware da abincin kamar zata shiƙa, har hawaye sun taru mata a idanun sun kaɗa sun yi ja, daƙyar ta haɗiye tana ɗaukar ruwa ta soma kwankwaɗa

SHAREEF tun wannan kallon da yayi mata ya ɗauke ido a kanta, yayinda haushi da tsanar yarinyar ya sake diran masa a rai musamman yanda ya ga tana zuba wannan uban loman. Lokaci ɗaya ya saki wani siririn tsaki yana wuce wa kichen cike da takunsa na isa kamar bazai yi ba. Sanye yake da three quartern wando pencil maroon color, sai farar t.shirt mai gajeren hannu da ta matse shi gam ta fito masa da surar jikinsa, ƙafansa kuma sanye da wasu slippers masu shegen taushi baƙaƙe,
Ya zura kai cikin kichen ɗin yana kallon Momy. A hankali ya furta, "sannu da aiki Momy."


Itama tuni ta san da zuwan shi tunda turaren sa mai shegen ƙamshi da shiga ƙwaƙwalwa ya gama baibaye ilahirin kichen ɗin. Amsa mishi tayi ba tare da ta ɗago ta kalle shi ba

Ganin haka yasa ya gane har yanzu tana fushi dashi ne, a hankali cikin sanyin muryan sa yace, "Mom I'm sorry."

"For what?"

Shiru yayi ya kasa magana sai kallonta yake yi

"Ka je ka zuba abinci ka ci, kayi min rumfa a nan ba na samun iska."

"Mom..."

"Mene ne?" Ta faɗa tana tsare shi da waɗannan manya-manyan idanunta da suke shiga jikinsa sosai

A hankali ya sauke ƙwayar idanunsa a ƙasa yana cewa, "Dady fa?"

Sai da ta ɗan ja seconni tuni ta mayar da hankalin ta a kan yankan albasan da take yi, ta ba shi amsa da faɗin, "ka duba sa ɗakin sa."

"Momy wlh nayi sallama dazu, nayi a zuciya ne kiyi haƙuri."

"Tunda ka ce baza ka ji maganata ba ba shikenan ba? Ka tafi Please kana ɓata min lokaci a nan."

Juya wa yayi ya fice cike da sanyin jiki. Yana fita ya sake haɗa ido da Maryamu wacce har yanzu tura abincin a baki take yi, sai dai a yanzu ta rage cin abincin da sauri; tana ci ne a natse gudun kar ya sake kama ta tana wannan uban loman, don ita kanta ta ji kunyar kama ta da yayi,
Yawu ya haɗiye yana ɗauke kansa, tare da ɗaure fuskarsa tamau ya nufi wurin fridge kai tsaye. Kwalin Holandia ya zura hannu ya ɗauka sannan ya juya ya haye saman

Maryamu ta bi sa da kallo kamar zata haɗiye shi, sai da ya ƙule sannan ta samu damar sauke ajiyan zuciya tana ƙarisa cin abincin, kafin ta tashi ta koma kichen

Momy tace, "har kin gama?"

"Eh Momy."

"SHAREEF yana wurin ne ko ya tafi?"

"Ai bai zauna ba, ya dauki kwalin Holandia a fridge sai ya hau sama."

"Ok, je ki tattaro min kayan wurin; ki zo ki wanke su."

"To Momy." Ta furta tana bin umarnin ta ta fice, kai tsaye kayan ta kwaso ta dawo kichen ɗin ta soma wanke-wanke,
Bayan ta gama suka ƙarisa girkin da Momy sannan suka kai saman dining suka jera

Lokacin ma an kira Magriba shiyasa Momy tayi mata umarnin, "ta je tayi sallah."

Tana tafiya Sadiq ya fito daga daki, shima yayi alwalan ne yana ƙoƙarin warware hannun rigan sa da ya nannaɗe

Duban sa Momy tayi tace, "sai yanzu ka tashi barcin kenan?"

Langaɓe kai yayi yace, "No Momy, na jima da tashi fa."

"Eh na ga alama, tunda ga idanunka nan sun yi ja."

Dariya yayi yace, "Allah Momy da gaske ba yanzu na tashi ba, nayi kusan minti talatin ma ina zaune ne ban fito ba."

"Ok, ka kira SHAREEF yana ɗaki don na san bazai fito ba sai an kira shi." Tayi maganar tana wuce wa ta haye steps din zuwa ɗakin ta

Hakan yasa Sadiq ya bi bayanta shima yana wuce wa ɗakin SHAREEF ɗin.
[02/02, 9:30 am] OumƊahirah نفيسة: 🌱🌱🌱🌱🌱

      *SHAREEF*
          _SexyBoy_
🌱🌱🌱🌱🌱


_Writer: Nafisat Isma'il Lawal_
_Wattpad: UmmuDahirah_

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝*



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

       *P.W.A✍️*





*DATA SHARE*

Call, message or whatsap  07065334256

*MTN*
500MB 150
1gb  280
2gb.  560 
3gb.   840
4gb.    1120
5gb      1400
6gb.     1700
Verlid for 30 days.












__________
*BOOK1*
_______________*FREE PAGE22*
               Sadiq ya fara dawowa daga masallaci sallan magriba da suka fita. A nan Falo ya tarar da Maryamu ita kaɗai ta tasa TV a gaba tana kallo, shigowar sa yasa ta gyara zama tana kallonsa da murmushi a face ɗin ta

Shima zama yayi gefen ta yana cewa, "har kin yi sallan ne My Ƙanwa?"

"Eh Yaya, ban ganka ba da na dawo makaranta?"

"Ina ɗaki My Ƙanwa, yau na dawo a gajiye shiyasa na shiga na kwanta after nayi sallan asar, to ya school ɗin ina fata kin yi enjoy?"

Ɗan tura baki tayi gaba, cike da sakarci tace, "wlh ba dad'i Yaya, kwata-kwata ban fahimci komai ba yau."

"Haba dai? Sabida me to?"

Ɗan yatsina fuskarta tayi tace, "to Ni dai karatun ne ba sa yi yanda zan gane, turancin ma babu dad'i."

Smile yayi yace, "kar ki damu na san rashin sabo ne My Ƙanwa, but zan riƙa koya miki in muka samu interval a hankali za ki riƙa fahimta."

Momy wacce ta sauko daga matattaƙalan benen, jin abun da Sadiq yake cewa, sai tayi murmushi tana cewa, "ai kuwa gwara dai ka riƙa mata lesson a gida hakan zai fi, ko zuwa gobe sai ku fara."
Zama tayi tana ƙara faɗin, "ina Dadyn naku basu dawo bane?"

"Eh Momy, basu shigo ba."

Miƙe wa tayi ta wuce kichen

"Yaya ka bani wayanka in kira numban Innar mu, Allah nayi kewar su."

Ciro wayan yayi a aljihu yana furta, "oushh! Na manta ma zan saka caji, tashi ki jona min a can, idan yayi sai kiyi wayan."

Amsar wayan tayi ta miƙe ta nufi wurin TV plasman ta jona

A time ɗin ne Dady and SHAREEF came in. Directly SHAREEF next to Sadiq sat with his eyes on his phone

While Dady kuma yana kallon Maryamun da ta taso daga wurin TVn, yana ƙoƙarin zama yake cewa, "ah ah.. my daughter, ya makaranta? Fatan kin yi karatun cikin kwanciyar hankali?"

Tana murmusawa tace, "eh Dady."

"Yauwa Masha Allah haka nake son ji, taho ki zauna a nan kusa da Ni, ki bani labarin makarantar ma sabida in ji yanda tayi miki daɗin."

Isowa tayi ta zauna a gefen sa cike da farin ciki, dayake yana a kan two seater ne, while su SHAREEF suna a kan three seater, kuma suna fuskantar juna. Hakan yasa Maryamun take kallon SHAREEF zuciyarta na mata sanyi

Kamar ya san tana kallon sa kuwa, sai ya ɗago suka haɗa ido da ita, ya rasa meyasa yarinyar take kafa mishi ido kamar mayya, tabbas dole ya ci uban ta ko zata shiga hankalin ta, shi a rayuwa kallo ne ba ya so, bare wannan idon yarinyar da kwata-kwata ba ya son suna haɗuwa da nashi tsaban yanda idanun suke da girma kamar na Momyn su, suna saka mishi faɗuwar gaba idan nasa idon suka shiga nata, kamar dai yanda yake jin tsoron na Momyn nasa. Abun haushin ma yanda ya kama ta tana kallonsa amma hakan bai sa ta cire idanun a kansa ba sai ma ware su da tayi sosai tana zuba mishi murmushi kamar ba ta hayyacin ta. As he opened his mouth to speak, his phone started ringing, hakan ne yasa ya miƙe tsam ya bi hanyar fita falon ma gaba ɗaya

While Maryamu ta raka shi da kallo har tana waigen sa. Sai da Dady ya taɓo ta sannan ta juya firgigit tana kallonsa

Smile Dady yayi yace, "Oh! Yayan naki ya dauke miki hankali ko sanin me nake cewa ba ki yi ba? Anya wannan kallon daughter baza a bani tukuici ba? Since haɗin da nayi ashe ba banza ba, ƴar tawa tana so."

Dariya ne ya ƙwace mata ta rufe fuskarta da sauri sabida kunya

Sadiq ma yana taya ta da cewan, "wai Dady sai yanzu ka kula da ita? Ai ta jima da faɗa wa wannan tarkon, ina tunanin sai an haɗa da addu'a nan gaba don Maryam ba ta ji ba ta gani in har a kan Yaya SHAREEF ne, nan gaba bamu san ya zata kasance ba."

Dady cike da farin cikin jin abun da Sadiq yace, sai ya murmusa yana kallonta yace, "I'm glad to hear that, ai haka ake so, dama fatana ace wannan haɗin da muka yi ya tabbata har ƙarshen rayuwar mu, bazan so a ce an tauye mata haƙƙin ta ba, abun ya zo gidan sauƙi kenan tunda itama tana da interested a kai, don har na fara tunanin yanda nan gaba komai zai kasance, to tunda haka ne daughter dole ki fara kamun ƙafa da Ni, don ɗan nawa zazzafa ne samun sa akwai wahala." Dadyn ya ƙare maganar nasa cikin barkwancin sa still da sihirtaccen murmushin sa mai kyau a kan face ɗin sa

Momy da komai tana iya juyowa daga kichen tunda ta nufo hanyar fitowa, sai tace, "ai kuwa nima ƴar tawa tubarakalla Masha Allah ne, ba cikin sauƙi za a same ta ba sai da tsayuwar dare da hailala, don haka a faɗa mana farashin sa mu ma sai mu faɗa namu farashin, muna gama biya sai a ɗaura da nata biyan."
Ta ƙare maganar tana isowa tare da zama inda SHAREEF ya tashi

Dukka dariya suka yi, while Dady yana cewa, "ban da abun ki, ai daughtern ne ta gani tana so ba ɗana ba, kinga kuwa dole sai ta wuri na zata kama ƙafa domin ta samu the handsome young guy din nan, zazzafan saurayi son kowa ƙin wanda ya rasa, kin san ɗan nawa ai?" Ya ƙare yana ɗan ɗage mata gira yana dariya

They were all laughing cike da nishaɗi, musamman yanda Dadyn yake ƙara kwarzanta SHAREEF yana nuna musu darajan shi ko a kasuwar gold.
***


              Shi SHAREEF bai san ma suna yi ba, don yana fita a gefen faranda ya samu wuri ya zauna. Lokacin da kiran har ya katse ma, shiyasa ya latsa wayan ya danna numban Haseena wacce yayi mata save da sweetheart, sai ya kai wayan saman kunnen sa yana ɗan jan numfashi a hankali tare da sauraron jin muryanta. Ai kuwa cikin shagwaɓa ya ji saukar muryanta a cikin kunnensa, hakan ne yasa ya lumshe idanunsa yana ɗan danne ƙasan laɓɓansa da ƙarfi. Ya kasa yin magana sabida yanda ya ji matuƙar kasala ta saukar masa sabida saukar sassanyan muryanta da ke matukar saka shi farin ciki da shiga wani hali, musamman in tana mishi wannan shagwaɓar mai fizgar hankali

Jin yayi shiru bai ce komai ba, sai ta ƙara shagwaɓe muryan tana cewa, "shi ne kuma kayi min shiru After I know you hear me? wai me nayi maka ne?"

Daƙyar ya iya buɗe idanunsa yana sake jan tagwayen numfashi, tare da furta, "na me fa sweetheart?"

Kukan shagwaɓa ta saka mishi lokaci guda har yana iya jin bugun ƙafafunta. Sai yayi saurin furta, "sweetheart I'm sorry, Ni ne ko? Ki yi shiru ya isa haka."

Kasa yin shiru tayi, sai ta ci gaba da kukan a hankali tana ƙara ɗan ɗaga muryanta alamun kukan da gaske take yi

"I'm sorry nace, ki yi shiru haka nan in ba so kike yi zuciyata ta buga ba. Ki faɗa min mene ne Pleaseeee?" Ya ƙare maganar yana ɗan jan ƙarshen cike da tsananin kasalar da ta saukar mishi

"Ni ban san me nayi maka ba today at all you did not call Me, and ina tambayar ka kana tambaya na bayan ka san bazan iya jure rashin ka ba, I called you twice today but you haven't peaked until now, alamu ya nuna ba na ranka ko? Or kana fushi dani?" Ta ƙare maganar da jiran amsar abun da zai ce


"Fushin me zan yi da ke sweetheart? Kuma wa ya faɗa miki ba kya raina? You are in my heart, ko second ɗaya ba ya wuce wa batare da nayi tunanin ki a cikin raina ba, you are still playing with the love I have for you, I don't know why you can't understand the love da nake miki." Sai yayi shiru yana jan numfashi. "Ina sonki Haseena, ina matuƙar ƙaunar ki, ƙiftawar ido ba ya wuce wa ba tare da kin faɗo a raina ba, duk laifin da za ki yi min Ni a wuri na na yafe miki har abada, ki ƙaddara cewa soyayyarki ƙaddarata ce, babu mai fitar da ita daga zuciyata face numfashi na ya rabu da gangar jikina ba."

Wani irin dad'i da sanyi ke ratsa zuciyar Haseena, kalaman SHAREEF sun ƙara narkan mata da zuciya har bata san wanne irin yanayi ta shiga ba, jin ta take yi tamkar wata Sarauniya wacce babu irinta a duniyar masoya. Ta kasa magana sai shiru da tayi tana sauraron yanda yake zubo mata kalamai masu dad'i tamkar don bakin sa a kayi su, ita kanta tana mamakin yanda ake yi SHAREEF yake iya irin waɗannan kalaman; after all ta san ita kaɗai ya taɓa so, a kanta ya san mene ne soyayya, amma tana mamakin yanda idan ya rikiɗe cikin magagin soyayyarta yake kwararo mata kalamai masu kwantar da hankali, da jin farin ciki da nishaɗi wanda ba ya gushe wa,
Lumshe idanu tayi ta buɗe sabida jin sassanyar muryasa yana furta

"Sweetheart kina jina kuwa?"

"Ina jinka My dear, daɗin kalaman da muryanka ne suka hana Ni yin motsin kirki bare in katse ka daga furta min su."

Murmushi yayi mai ƙara wa fuskarsa kyawu, yana ɗan shafa sajen sa yake cewa, "kiyi haƙuri a kan rashin kiran ki da ban yi ba, aiki ne yayi min yawa, kuma na so na hau WhatsApp muyi chart but ban samu dama ba, I'm very sorry."

Dariya ta ɗan yi, dariyan farin ciki, tace, "kar ka damu dear, I think maganar da nayi maka ne shi ne kake fushi da Ni shiyasa baka kira ba, kishin ka ne yasa na kasa control kaina a daren jiya, that's why na faɗa maka haka, amma bazan sake ba, kuma ba na so ka sake min irin wannan zancen."

"Ba kya laifi a wuri na ai, ko me kike so shi nake so, farin cikin ki shi ne nawa."

Murmushi tayi cike da farin ciki, sai ta matse pillown da ke ƙirjinta tana narkar da murya da kiran sunan sa, "dear."

"Um." Ya amsa ta cikin wani irin yanayi sabida jin yanda muryan nata ya ratsa shi

"I love you, ina matukar ƙaunarka, ina kuma kishin ka matuƙa, zan iya yin komai sabida kai, idan na ce komai to ina nufin komai, don ko da rana ɗaya kar ka taɓa juya min baya, ka tuna wannan zuciyar tawa a cike take da wata iriyar mahaukaciyar guguwar ƙaunarka, wadda idan ta rasa ka tamkar ta gama moruwa ce a cikin gangar jikin da ke gudana da jini da tsoka, jinin zai kwaranya sannan tsokar zata zagwanye tamkar ba a taɓa yin halitta mai kama da ita ba, idan har ka rabu da Ni to ka ƙaddara cewa mutuwa zan yi, bani da sauran wata rayuwa a cikin duniyar nan, Please dear kar ka taɓa rabuwa da Ni, don Allah ko me nayi maka a rayuwa ka yafe min, da kai kaɗai nake son na ƙarisa rayuwata..."

"SHAREEF."

Kiran da Dady yayi masa ne yasa shi yin firgigit ya ɗago kansa yana kallon su, sun fito shi da Sadiq zasu wuce masallaci

Shi yasa Dady da mamaki yace, "me kake yi a nan ne ka zauna haka?"

"Dad, waya nake yi." Yayi maganar yana zare wayan daga kunnen sa

"Ok, ka tashi ana ƙoƙarin shiga sallah."

"Ok Dad."

Wuce wa suka yi suka bi hanyar gate.
While shi kuma sai ya mayar da wayan a kunnensa yana cewa, "sweetheart bari in je in yi sallah, zan kira ki in na shiga ɗaki."

Cike da shagwaɓa tace, "Please don't leave me for a while ina faman jiran ka."

Smile yayi yace, "ok, I love you, ki kula min da kanki." Ya sakar mata kissing mai zafi

Itama sai ta mayar masa da martanin kissing tare da furta, "i love You too, bye."

Kashe wayan yayi yana miƙe wa tsaye. Kai tsaye sai ya koma cikin gidan domin sake alwala, sabida ya san dole alwalan sa ta ɓaci. Ganin babu kowa a falon sabida yayi ninyar shiga toilet ɗin falon ne, hakan ne yasa ya fasa ya haura sama da gudun sa ya shige nasa ɗakin. Sai da ya canza alwala sannan ya bi ta ƙofan bayan ya fice,
Time ɗin ma an kusa idar da sallan, domin raka'a biyu ya samu a jam'i. After an idar sai ya tashi ya ƙarisa ciko sauran, bai tsaya yayi wani addu'a ba ya fice daga Masallacin. Daga gidan su da masjid ɗin; ta zaran tafiyan mintina 5 to 6 ne. Haka ya taho ya buɗe gate ɗin ya shige gidan ko sauraron Mai gadi da ke mishi sannu bai yi ba, sai ma tsuke fuska da yayi yana kicin-kicin da ita tare da nufan cikin gidan hannayen sa zube a aljihun wandon sa

Da ya shiga ya tarar da su a saman dining suna dinner. Sabida sanin halin Momy shiyasa yayi sallama da ɗan ƙarfi yana nufan inda suke a natse

Amsa mishi suka yi su dukka, ban da Maryamu da ke ƙoƙarin cusa shinkafa a baki, wanda har ta kai cikin bakin nata ta cusa shi a ciki, ta ɗago ido tana kallonsa

Karaf kuwa idanunsa suka shige cikin nata, ransa ne ya ji yayi mugun ɓaci, wani irin kallo ya sauke mata yana jan dogon tsaki

Sai da dukka suka ɗago suna duban sa da mamakin jin wannan dogon tsakin da ya saki

Momy tace, "lafiya SHAREEF?"

Bai bata amsa ba sai da ya samu wuri ya zauna idanunsa a kan Maryamu; wacce ta ɗauke kai da sauri tana duƙar da kanta cike da tsoron da ya sakar mata. Ransa a ɓace ya nuna ta da yatsa yana cewa, "wannan yarinyar ne mana, na rasa meyasa take min wannan shegen kallon da ba ya ƙare wa, wlh na kusa nayi mata dukan tsiya a gidan nan in har bata fasa zura min ido ba, da wasu ƙwayayan idanunta kamar na mayu, wawuya mara hankali..."

"SHAREEF." Momy ta kira sunan sa da ƙarfi tana bin sa da kallo, itama ranta a ɓace

Kallon Momyn yayi yana ɗan jan numfashin fitar da hucin ɓacin ransa, don yanda yake ji ma bai san yana furta waɗannan kalaman a gaban su ba, ɗauke kansa yayi ya soma ƙoƙarin yin save da kansa

"Na ga alamun baka san inda ke maka ciwo ba SHAREEF, wannan yarinyar ƙanwarka ce amma nema kake yi ka shigo da wasu ɗabi'u na banza da hofi a cikin gidan nan, kai da wanne ido ka san tana kallonka iyee?" Tayi maganar tana jiran amsar sa. But ko ɗago kai bai yi ba bare ta sa ran zai amsa mata, sai ta ja ƙwafa tana cewa, "ka ci gaba da abun da kake yi ka ji ko? Yarinya tana baƙuwa a matsayin kanwar ku amma baza ka iya janta a jiki ba; sai ƙoƙarin nuna mata baƙin halin ka, duka-duka Maryam nawa take da kullum baka da aiki sai ƙoƙarin ka na muzanta ta? Wannan tarbiyyar muka baka?"

Dady ne ya kalle ta shima cikin rashin jin daɗin abun da ya faru, yace, "kiyi shiru haka nan Deeja, ba na son kina zafafa wa da yawa haka."
Sai ya dubi SHAREEF ɗin yana cewa, "ya maganar kuɗin da kace kana bukata? Bamu ƙarisa magana ba."

SHAREEF da kansa ke ƙasa zuciyarsa na tafarfasa sabida bakin cikin faɗan da Momy take masa a kan wannan yarinyar, ransa yayi mugun ɓaci amma ya kasa ɗago kai bare ya kalle su, har idanunsa sun soma canza kala sabida yanda yake jin ɗaci da ɓacin rai daga ƙasan zuciyarsa. Koda Dady yayi masa magana bai iya ɗago kai ba bare ya tanka sa, sai da ya sake maimaita mishi tambayar sannan a hankali muryansa na fita daƙyar yace, "30 millions muke buƙata yanzu."
Sai yayi shiru yana ɗan sauke ajiyar zuciya a hankali a hankali 

"Kana ganin sun isa? Kuma yaushe ne kayan zasu iso? More explain please?"

"Gobe ne kayan zasu iso Dad, i think ma baza mu ɗauki lokacin da suka ɗiba mana ba zamu fara aikin, da zaran waɗannan kayan sun iso, kuma Dad muna buƙatar 30 millions sabida already kayan 50 millions yanzu zasu shigo, and muna da 20 a Company, shiyasa zamu fara aikin kawai, zuwa gobe zasu iso, sai a wuce da na companin can."

Jinjina kai Dady yayi tare da furta, "Masha Allah, bari mu gama cin abinci sai mu san me za a yi."

Daga nan babu wanda ya ƙara magana daga cikin su, har suka gama cin abincin wanda SHAREEF ya fara tashi, don bai ci komai ba a wurin, daƙyar ma yayi loma biyar ya miƙe sabida ƙagara da yayi ya tashi

Dady yace, "har ka gama?"

"Eh Dad." Ya furta yana jan kujerar ya wuce, kai tsaye bai tsaya ba ya nufi ɗakin sa

Sai a lokacin Maryamu ta saki ɓoyayyiyar ajiyar zuciya tana jin ranta babu daɗi; da irin faɗan da Momy ta yi wa SHAREEF, har cikin zuciyarta ta fi damuwa da ganin halin da SHAREEF yake ciki fiye da abun da yayi mata, bata so Momy tayi masa faɗa ba, amma ta kula Momyn tana da saurin zafi da faɗa, don haka dole ne ta rage kallonsa bare ta ɓata mishi rai irin haka, ga shi yanzu ya tafi yana jin haushin ta, sai ta ji duk ranta babu daɗi sabida ta san Sadiq ya faɗa mata ta riƙa yin duk abun da zai ji sanyi a ransa ya so ta, amma yanzu ga shi ta ɓata mishi rai, sabida ita an mishi faɗa, yanzu zai ƙara tsanarta kenan?...

Momy ce ta katse mata tunanin nata, tana cewa, "ki tashi in kin gama ne, ki dena wanann tunanin da bai da amfani."

Ɗago kai tayi tana kallonta, sai lokacin ma ta kula har kowa ya tashi sai ita kadai, dole ta tashi jiki a sanyaye ta nufi cikin Falon

Momy ta bi ta da kallo a ranta tana kitsima abubuwa da dama, sosai yarinyar take bata tausayi, musamman yanzu da suka kula tana matuƙar ƙaunar SHAREEF ɗin, amma shi bai san tana yi ba, illa ma nuna ƙiyayyarsa gare ta, taya ya zata iya taimaka mata wajen ganin SHAREEF ya so ta? Yarinyar abar tausayi ce, ga ta ƙarama amma wannan wahalar yana son riskar ta, ga shi already an yi musu aure,
Tashi tayi ta haɗa kan plates ɗin tare da kaiwa kitchen,
Tana dawowa tace ma Maryamun, "ta wuce ta je ta kwanta sabida kar tayi late na makaranta."

Hakan ne yasa Maryamu tayi musu sai da safe sannan ta wuce, dama barcin take ji, amma tunanin SHAREEF ya hana idanunta su runtsa, koda ta je ɗakin ta kasa barcin, tunda ta kwanta take faman juyi da tunanin sa, sai daga ƙarshe barcin ya sure ta tare da mafarkin sa da ya soma zame mata jiki,
Shi yasa ta tashi cike da farin ciki a ranan. Wanka ta soma shiga tayi, har ta gama sai kuma ta tuna maganganun Sadiq da ya faɗa mata,  "SHAREEF yana son tsafta a rayuwarsa, ba ya son ƙazanta, don haka ta dage shima mataki ne na jawo hankalin sa a gare ta."
Dalilin da yasa ta koma ciki ta sake silla wani wankan, wanka sau uku tayi sannan ta gurje bakin ta ta dinga brush har sai da ta ga bakin yana jini sannan ta haƙura, gashin kanta ta shafa ta ji yanda ya cinkushe ya danƙare a wuri ɗaya, don rabon ta da kitso gaskiya baza ta iya tuna wa ba, bare wanke shi kwata-kwata ba ta son abun da zai taɓa mata kan nan nata, sabida muddin aka taɓa mata sai tayi ciwon kai, shiyasa ta tsani kitso bare ta so abun da zai taɓa mata, rigimar su da Inna koyaushe a kan kanta ne, har sun gaji sun ƙyale ta ma

Jikinta a sanyaye ta sake koma wa toilet ɗin, zuba ruwa tayi ta soma ƙoƙarin wanke gashin, daƙyar take cuɗa wa saboda tsananin cinkushe wa da dattin da ya danƙarar da shi. Ba ƙaramin datti ta fitar ba don ita kanta ta sha mamakin yanda datti ke zuba kamar bazai dena ba, sai da ta ga zata ɓata lokaci sannan ta bar shi haka ta fito,
Tun a wannan lokacin ta soma jin yanayin ta ya sauya, wani ciwo -ciwo ne yake ratsa mata can cikin ƙwaƙwalwa da tsakiyar kanta, dama ta san dole hakan zai faru, amma tana son ta canza ko don SHAREEF, tana matuƙar sonshi zata jure ko mene ne don ganin ya so ta,
Daure wa kawai take yi har ta gama shirya wa, amma wani irin ciwo ne ke ratsa ta kamar za a ɗaɗɗake mata kan, har manyan idanuwan nan nata masu shegen haske sun soma canza kala,
Daƙyar ta iya daukar ƙaton Jakarta ta fice daga ɗakin tana ɗan sakin numfashin azaba.
[04/02, 9:05 am] OumƊahirah نفيسة: 🌱🌱🌱🌱🌱

      *SHAREEF*
          _SexyBoy_
🌱🌱🌱🌱🌱


_Writer: Nafisat Isma'il Lawal_
_Wattpad: UmmuDahirah_

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝*



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

       *P.W.A✍️*





*DATA SHARE*

Call, message or whatsap  07065334256

*MTN*
500MB 150
1gb  280
2gb.  560 
3gb.   840
4gb.    1120
5gb      1400
6gb.     1700
Verlid for 30 days.












__________
*BOOK1*
_______________*FREE PAGE23*
            Shigowar sa kenan, ya nufi Office ɗin sa kai tsaye, har ya shiga ya zauna ya ji nocking a bakin ƙofan, shiyasa ya bada iznin shigo wa yana ƙoƙarin kunna computern sa

Shuraihu ne ya shigo ciki yana masa murmushi

Ya ɗan yi mamakin sake ganin sa da sassafe haka, sai dai bai nuna halin da ya shiga ciki da ganin nasa ba, sai miƙa masa hannu yayi suka yi musabaha sannan ya janye hannun sa

Shiru Shuraihu yayi yana ɗan tunanin ta inda zai faro maganar har Mahmud ya fahimce shi, don dole ne ya san hanyar da zai bi ya amince dashi kafin ya tona masa asiri a wurin SHAREEF, duk da yana fargaban cewa dole Mahmud ɗin ya yi wa SHAREEF maganar, shiyasa hankalin sa ya kasa kwanciya yana ganin ya shigo ya biyo shi office, bai da tabbacin cewa bai sanar mishi ba. Janye shirun yayi da furta, "Mahmud a kan maganar da muka tattauna jiya ne, na san dole zaka sanar da SHAREEF komai abun da ya faru tunda ka ƙi amsar tayin da aka yi maka, duk da su Alhaji Inuwa sun ƙara maka kuɗin yanzu ya zama 20 millions sabida suna buƙatar taimakon ka matuƙa, ya ka ce?"

Murmushi Mahmud yayi tare da furta, "MD bazan taɓa yin abun da kuke so ba already na faɗa maka, bazan yi cin amanar nan ba, Companin da nake aiki da shi na fi buƙatar su haɓaka a kan na wasu, ba na bukatar waɗannan kudaden halal ɗina ya ishe Ni."

"Amma wa yace maka wannan haram ne da kake fadar haka?"

"Ka ga MD ba na son jan zance, I told you ba Ni cikin wannan tafiyar taku."

Jinjina kansa yayi yace, "haka ne, nima sai da muka yi maganar daga baya abubuwan ke damu na a cikin rai, musamman da na san zaka iya sanar da SHAREEF asiri na ya tonu na rasa aiki na, kar ka manta da wannan aikin na dogara, kuma taimakon su Alhaji Inuwa da nayi ninyar yi don ba yanda zan yi ne sun tilasta min ne, shiyasa na sake dawowa domin in roƙe ka a kan tona mini asiri da zaka yi, na san dole zaka fada mishi Mahmud, kuma muddin ka fada mishi tamkar ka ruguza rayuwata ce."

Tsare sa da ido Mahmud yayi tare da faɗin, "meyasa kake tunanin zan iya barin wannan maganar bazan fada masa ya ɗauki mataki ba? Kana ganin hakan ya dace?"

"Na san baza ka bari ba shiyasa na zo na roƙe ka, muddin ka bayyana suna na a cikin wannan maganar tamkar ka ruguza min rayuwata ce, ina baka haƙuri Please help me, don't let my name go bad in SHAREEF, Ni na janye hannu a kan wannan tsarin don na rigada na canza shawara nima."

Jin hakan yasa Mahmud yayi murmushi tare da cewa, "ba komai MD, Ni dama ban yi ninyar ɓata maka suna ba tunda kai Abokina ne kuma Abokin aiki na, kuma ka kwantar da hankalin ka babu yanda za a yi in faɗo sunan ka a cikin wannan maganar."

Shima murmushin ne ya suɓuce mishi jin ya samu kuɓuta, sai yace, "na gode Mahmud, bazan manta da wannan alfarman da kayi min ba, thank you so much."

"Kar ka damu, yi wa kai ne, sai dai dole mu san yanda za a yi mu tsayar da su daga abun da suke son shirya wa, duk da na san SHAREEF ba lallai ya yarda da abun da zamu fada mishi ba, amma muna bukatar mu sanar mishi, sannan mu kare kanmu wajen rufe duk ƙofan da zai sa su ci nasara a kanmu, har su ɓata mana ayyukan mu, wannan kwangilar tana da matukar muhimmanci a wurin mu."

"Haka ne, nima nayi tunanin wannan, duk da basu faɗa min hanyar da zasu bi ba, amma dole mu tashi tsaye domin sosai suke hassada da wannan Companin, zasu iya yin komai don ganin sun cin ma nasaran su."

Gama maganar nasa sai suka yi shiru dukkan su,
Yayinda a dai-dai lokacin ne wayan Mahmud tayi ring, ɗago wayan yayi ya ga sunan SHAREEF ɓaro-ɓaro yana yawo, hakan ne yasa ya ɗaga kiran da sauri, "good morning Sir."
Shiru ya ɗan yi kaɗan, before daga baya ya furta, "ok I'm coming."
Ajiye wayan yayi yana kallon Shuraihu tare da cewa, "SHAREEF na kira na, bari in je muyi magana, inyaso sai mu ƙarisa tattauna maganar daga baya, after mun samo solution sai mu san yanda zamu yi mishi bayani."

Kansa ya ɗaga tare da furta, "eh hakan ma yayi, ok ba matsala, nima bari in je don akwai abun da ya kamata in yi kafin in zo office din."

Mike wa suka yi su dukka, sannan suka fita a tare kowa yayi hanyar da zai bi

While Shuraihu office din sa ya nufa yana mai jin farin cikin cire kansa daga zargin da Mahmud zai fara mishi, tabbas bazai sake gangancin sanar da PA wannan maganar ba don ya san shima ba lallai ya amince ba, tunda ya zare hannunsa ya ci nasara har Mahmud ya yarda dashi, to yanzu ya kamata su canza tsarin plan since basu samu goyan bayan Mahmud ba, kuma hakan yasa dole sai sun canza shiri, ya kamata ya sanar da su Honourable Ja'e abun da ke wakana.








🔆🔆🔆🔆🔆🔆🔆🔆


             Tunda suka fito Sadiq ya kula da yanayin Maryamun, alamun kamar tana cikin tsananin damuwa, don ko magana ta kasa yi sai faman cije laɓɓa take yi, yanda ya san ta da surutu amma ko uffan ta kasa cewa har sun kusa isa school ɗin, shiyasa ya kasa yin shiru bayan ya kalle ta ya ɗauke kai tare da mayar wa a kan hanya, kiran sunan ta yayi, amma ya ji shiru bata amsa ba, shiyasa ya sake kiran sunan nata yana kallonta


Firgigit ta ɗan yi itama ta zuba mishi idon, idanun nata sun ɗan yi ja da su

Hakan ne yasa Sadiq yace, "lafiya ƙanwata? Me ya same ki haka na ganki so cool? Anya lafiyar ki lau?"

Daure wa tayi tana ƙoƙarin ɓoye yanayin da take ji daga jikinta, musamman kanta da ke sara mata tamkar zai rabe gida biyu, ko motsa shi ba ta son yi sabida zafin ciwon da take ji, a hankali cike da sanyin murya tace, "Yaya Sadiq babu abun da ke damu na, kawai ina tunani ne." Sai kuma cikin son ta mantar da shi tambayar da yake mata sai ta sake duban sa da faɗin, "ina kewar su Inna, jiya i forgot ban ɗauki wayanka na kira su ba."

Sadiq yace, "ko don sabida su ne kika shiga wannan halin? Anya Ƙanwar tawa tana da juriyar da zata iya bari ta zauna a nan babu su Inna? Ko dai zamu mayar da ke ne?"
Ya kare maganar yana ƴar dariya tare da kallonta

Murmushi ne ya suɓuce a kan fuskarta, har ta buɗe baki da ninyar yin mishi magana sai idanunta suka sauka a kan titi inda suke ƙoƙarin buge wani tsoho,
Da sauri ta kwatsa ihu tana ware idanunta

Wanda hakan ne yasa Sadiq ya ankare yana duban titin shima, da sauri ya ja burki ba tare da yayi ciki da tsohon ba,
Ba ƙaramin buga wa zuciyarsu tayi ba saboda sun matuƙar tsorata a tunanin su dole ne su buge sa

Tsayar da motan yayi dai-dai da ɗago idanun tsohon daga kallon ƙasa ya zuba wa motan, tsoho ne tukuf don ko alamun baƙin gashi babu a kansa, har zuwa gemunsa da sajen sa, a duƙe yake tafiya tare da sandan dogara wa, tsohon Mutumin koda ganin sa ya ji jiki matuƙa, ya fita a hayyacin sa har kamannin sa, kayan jikinsa duk sun yayyage, farar jallabiya ce amma ta dafe ta canza kamanni ta gama fita a hayyacin ta gaba daya, doguwa ce har ƙasa ko ƙafafun sa ba a gani. Tunda ya kalli motan sai ya fara ƙoƙarin dogara sandan ya nufi wurin su

Har yanzu Sadiq yana riƙe da sitiyarin Motan hannayensa sai rawa suke yi, domin ya sadakar ya buge shi. Ganin tsohon ya nufo wurin Motan shiyasa ya bi shi da kallo har ya ƙariso

Haka itama Maryamu kallon tsohon take yi cike da wani irin yanayi, musamman yanda ta ga idanunsa sun yi jazur manya da su yana ware wa a kansu, yanayin ƙazantar jikinsa ne yasa ta ɗauke kai tana yatsina fuska

Kafin Sadiq yayi magana, wanda har ya buɗe baki da ninyar ba shi haƙuri. But sai tsohon ya soma magana a ɗan fusace cikin faɗa

"Kai Yaro baka da hankali ne, ko ba ka gani ne da zaka biyo hanya ba ka duba wa? Don iskanci da wulaƙanci salon ka buge mutane sannan ka gudu ka bar Ni da jinya wato? Tunda ba a koya muku tarbiyya ba baku san na gaba da ku ba, ina Tsoho ma baza ku raga min ba, dama ƴaƴan masu kuɗin nan haka kuke da babu tarbiyya a wurin ku sai raina mutane, da ko kayi gangancin buge Ni da nayi maka bugun da zaka kasa tashi a nan wurin, don bani da haƙuri nan da kake gani na."

Daga Maryamu har Sadiq sakin baki suka yi suna mai tsananin mamakin furucin Tsohon, wanda yasa har Sadiq ya kasa furta komai sai ma bin sa da ido da yayi ko motsin kirki ya gaza

Ita kuma Maryamu abun ma haushi ya bata har ta kasa yin shiru, wani irin tsaki ta ja tana narka wa Tsohon harara da faɗin, "haba tsoho, har a hakan naka ne zaka yi mishi bugun da zai kasa tashi? Lallai ma wannan tsohon ka ci uwar rainin wayon, ka zo ka tsaya mana a hanya sannan ka biyo mu kana cin mana mutunci? ka ga fa, duk tsufan nan naka bazai hana mu bar ka kake gaya mana magana son ranka ba, yanda ba ka da haƙuri mu ma haka bamu da haƙurin, kuma idan baka tashi mana a nan ba wlh ka ji na rantse sai mun buge ka mu ga ta tsiya, in ka isa sai ka dauki matakin, yau na ga tsohon najadu mutum ya gama taƙwarƙwashe wa amma neman rigima yake yi."

Maimakon tsohon ya ji haushi da jin kalaman Maryamu, sai kawai suka ga yana murmusawa tare da kafa mata ido har yana lashe bakin sa

Hakan ne yasa Sadiq ya soma tsorata da yanayin tsohon, nan take zuciyarsa ta soma rawa ya soma ƙoƙarin kunna motan tare da barin wurin

Itama kuma Maryamu sai ta sake fusata da abun da yake mata, tace, "banza tsohon najadu kawai, idan maula kake nema ai ba sai ka biyo ta wannan hanyar ba, ko kai maye ne sai dai ka ci kanka, dama daga ganin ka ba mutumin arziki bane."
Ta ja dogon tsaki tana hararan sa, har suka bar wurin bata dena zagin sa ba tana juya wa da kallon inda yake, take ta ga tsohon ya ɓace ɓat a wurin, lokaci guda ta datse bakin ta tana zare idanu tare da kallon wurin, alamun dai babu tsoho babu alamar sa ya ɓace ɓat

Tsayar da motan Sadiq yayi a dai-dai bakin gate ɗin, don dama sun yo kwanan makarantar ne ya kusa kaɗe tsohon can

Baki ta buɗe da ninyar sanar da Sadiq abun da ta gani da idanunta, amma ta kasa furta komai sai rawa bakin ta yake yi, duk yanda taso ta sanar mishi abun da ta gani zahiri bakin ta ya ƙi magana

Sadiq kuwa da ke cike da tsoro, sai ya dube ta yana cewa, "Maryam meyasa kika yi mishi rashin kunya haka?"

Shiru tayi tana zare idanu ta kasa yin magana, yayinda take jin yanda kanta ke sara mata kamar zai ɗaɗɗake, hakan ne yasa ta kai hannunta tana riƙe wa da sauri tare da runtse ido

"Maryam lafiya? Mene ne?" Sadiq yayi maganar yana kallonta cike da damuwa

Hannunta ta cire tana kallonsa, girgiza masa kai tayi daƙyar ta furta, "babu.. komai."

Shiru yayi yana kallonta, "ko dai wani abun ke damun ki? Ki sanar da Ni kar in tafi?"

"Yaya Sadiq babu komai nace maka, kaina ne kawai yake ɗan min ciwo kaɗan-kaɗan."

"Eyya sorry, da tun farko kin faɗa a gida ai da kin sha magani, amma yanzu ki fita ki shiga school kinga lokaci na ƙure wa."

Bata ce mishi komai ba ta buɗe ƙofan ta fice, Jakarta ta janyo ta fitar da ita sannan ta rufe mishi ƙofan, kasancewar baza ta iya magana a halin da take ciki ba, shiyasa ta ɗaga mishi hannu kawai ta bar wurin

Lokacin ana assembly shiyasa can ta nufa kai tsaye. Tana zuwa ta tsaya a baya-baya ba tare da tayi tunanin ta nemi layin ƴan ajin nasu ba yau ma, kawai tsaya wa tayi kanta a ƙasa tana riƙe da Jakarta da ta kasa goya wa, jikinta sai rawa yake yi domin ba ƙaramin daure wa take yi daga azaban ciwon kan da ke nuƙurƙusan ta ba, sosai yanzu idanuwanta suka canza kala zuwa ja fiye da koyaushe, tsayuwar ma ya soma gagaranta ga wani irin jiri da ke barazanar ka da ita, lokaci guda ta tafi tayi ƙasa zata zube.
[07/02, 8:24 am] OumƊahirah نفيسة: 🌱🌱🌱🌱🌱

          *SHAREEF*
              _SexyBoy_
🌱🌱🌱🌱🌱


_Writer: Nafisat Isma'il Lawal_
_Wattpad: UmmuDahirah_

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝*



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

       *P.W.A✍️*




*DATA SHARE*

Call, message or whatsap  07065334256

*MTN*
500MB 150
1gb  280
2gb.  560 
3gb.   840
4gb.    1120
5gb      1400
6gb.     1700
Verlid for 30 days.














__________
*BOOK1*
_______________*FREE PAGE24*
_____ *AUSTRALIA*
               *SYDNEY*
       Tun tashin ta yau take jin alamun tahowar period ɗin ta, dama ta san cewa tunda kwanan wata yakai 8, baza ta rasa zuwan shi ba, sabida ba ƙaramin wahala take sha ba in ya zo. Zuciyarta ne ke mata ɗaci cuz ta tsani wannan yanayin, idan da ace tana da halin yanda za a yi ta dena wannan jinin na al'ada; wlh babu abun da zai sa bata tsayar ba, amma kuma duk dabara da shaye-shayen magungunan ta har yau bata dace ba, ta sha jin ana cewa akwai abubuwan da ke tsayar da shi in har Mace ba ta son yi, amma ita ko ta sha ba ya tsaya wa dole sai ya zo, babban takaicin ta ma yanda yake zuwa mata da mugun ciwo na fitan hayyaci, sai tayi kwana goma cif sannan yake dakata wa jinin, kuma ba wai zuwan wasa yake yi ba, bata da wani sukuni har sai idan ta gama, ga tsananin ciwo ga rashin samun kwanciyar hankali da natsuwa

Yanzu ma ga shi tana buƙatar tashi ta shirya ta je school, amma hakan ya faskara, ta san babu damar ta haƙura da zuwa yau ɗin, since karatun da suke dashi mai muhimmanci ne, and ga program da za a gabatar wanda dole ne mutum ya hallara, tunda maks yake dashi. Ba ma wannan ba, school ɗin suna da matuƙar tsauri da ƙa'ida, ba haka kawai ake fashi ba dole sai da ƙwaƙƙwaran dalili, kuma sai ka rubuta letter

Tana nan kwance tana juye-juye a saman gadon nata, wanda duk ta mutsutstsuke shimfiɗan sabida azaban ciwon da ya taso mata. Almost ten minutes tana a wannan yanayin tana ta sakin huci tare da cije laɓɓa, idanunta a lumshe ko kaɗan ta kasa buɗe su, sai da ta ji ciwon ya lafa mata kaɗan, sannan ta samu ta ware idanunta tana kaiwa saman agogon bangon da ke maƙale can sama,
Ganin tana da sauran lokacin da zata iya shirya wa ta tafi, shiyasa dole ta daure ta daddafa ta miƙe zaune, numfashi ta ja tana miƙa hannu tare da buɗe drowan gadon, maganinta ta ɗauka duk da ta san ba wani amfani zai yi mata ba, idan wannan ciwon ya fara mata ko ta sha maganin bazai bari ba sai ya jera kwana uku yana abu ɗaya, sai dai ya riƙa lafa mata lokaci zuwa lokaci, tabbas ba ƙaramin azaba take sha ba a wannan yanayin, ta san babu abun da zai kawar mata dashi in har ba aure tayi ba, auren kuma da ba ta tunanin faruwar sa tunda Abbanta ya turo ta nan karatu, shi kuma wanda take tunanin zai taimaka mata ta san bazai taɓa aikata zina ba, since duk rarrashin da tayi masa a baya bata ci galaba ba bare yanzu, yana da kyau tayi wani abu a kai, tana buƙatar kasancewa da SHAREEF ta kowanne hali, in ba haka ba mutuwa zata yi, baza ta iya kaiwa iya adadin waɗannan shekarun ba tare da ɗa namiji ba, namijin kuma ba kowa ba face SHAREEF ɗin ta, shi kaɗai ne zata iya ba shi kanta, shi kaɗai take so kuma shi ne mallakin jikinta, tun farko da zata iya aikata zina da ta jima da aikata wa, amma kuma ta rigada ta rufe wannan babin, SHAREEF kaɗai take iya kallo a matsayin namiji ɗaya tilo a faɗin duniyar nan

Ziro ƙafafuwan ta tayi daga saman gadon, ta zuba su a saman lumsassen Cerfet ɗin da ke mamaye da bedroom ɗin. Kana a hankali ta jawo room slippers dinta ta zura a ƙafafun, mike wa tayi tana tallabe da cikin ta da hannu daya, ɗayan hannun kuma maganin da ta ɗauka suna zube a cikin shi, daga ita sai riga da wando sleeping dress da ke jikinta, kanta babu ɗankwali sai gashin ta da ya gama mitsitstsike wa sabida halin ciwo. Kai tsaye falo ta nufa ta ɗauki ruwa a fridge ta sha maganin, bayan ta gama ta dawo cikin bedroom ɗin, komai a hankali take yi sabida yanda cikin nata ke faman murɗa mata a hankali. Cire kayanta tayi ta shiga toilet ta watsa ruwa, after ta fito sai ta natse jikinta sannan ta shafa lotion sama-sama, kasancewar ba ta jin daɗi kwata-kwata bata tsaya yin kwalliya ba, bak'ar doguwar riga kawai ta zura a jikinta after ta saka pad da pant, sannan sai ta saka baƙin dogon wando a ciki,
Sai da ta bi jikinta ko'ina ta shafa turare yanda ko'ina nata zai riƙa tashin ƙamshi, sai tayi rolling da farin gyale sannan ta dauki Jakarta ta zuba pads da abubuwan da zata buƙata. Fita tayi ta rufe ƙofan sannan ta hau motan ta ta fice a gidan

A hankali take driving ɗin, cuz ba ƙaramin ciwon ne ya taso mata ba, daure wa kawai take yi amma daƙyar ta iya kai kanta cikin school ɗin. Packing tayi tana ɗaura kanta a saman sitiyarin, shiru tayi tana matse cikin nata tana faɗin wayyo Allan ta,
Ta jima tana murƙususu before ya lafa mata, hakan ne yasa ta daure ta fito riƙe da Jakarta ta rufe motan tana jefa key ɗin a cikin Jakar, sannan ta taka a hankali ta soma ratsa cikin makarantar har ta isa class ɗin su

Time ɗin ma lecturer ya shiga, don har ya soma musu karatu. Shiyasa ta lallaɓa ta bi ta baya ba tare da ya kula da ita ba,
Sai da ta zauna sannan ta ajiye numfashi tana ƙara kai hannunta saman cikinta ta matse shi sosai,
A haka suka ci gaba da karatun duk da ba wata fahimta take yi ba, sabida zafin ciwo da ke huro mata time to time

Yana gama wa wani lecturern ya shigo, shiyasa duk a galabaice Haseena ta gama karatun, bata tsinci komai ba a ciki, kawai ta san cewa zuwan nata yana da muhimmanci ne, if not kuma ta samu matsala,
Lecturern yana fita ta ɗaura kanta a saman desk ɗin tana sauke numfashi, duk idanunta sun kaɗa sun yi ja har da ruwan hawaye, musamman yanzu da ta ji gadan-gadan ciwon ya taho mata, salati ta soma yi tana juya kai, ta kama cikin gam ta matse shi sosai

Kasancewar class ɗin sun rage yawa, since basu da wani karatun sai zuwa anjima,
Shiyasa wata matashiyar budurwa wacce ke zaune a gaba, ta samu damar hangar Haseenan lokacin da ta juya bayanta saboda jin sautin kamar ana salati,
Ba ita kaɗai ba, hatta tsirarun da ke ajin sai da hankalin su ya kai kanta tunda sosai take juye-juye da salati,
Hakan ne yasa wannan budurwan ta taso da sauri sabida ta fahimci wacce ke wurin, quickly ta nufi wurin Haseenan tana kiran sunanta tare da dafa ta

"What's wrong with you? Why did you get into this situation?"

Daƙyar Haseenan ta ɗago kanta tana shashsheƙa, tare da sauke idanunta a saman fuskar budurwan batare da ta iya furta komai ba

Hankalinta ya tashi sabida yanda Haseenan ta koma, shiyasa ta zauna a gefen ta tare da tallabo jikinta tana ƙara tambayarta? Hannunta ɗaya a saman fuskar Haseena tana shafa mata cike da tausaya wa

Dakyar Haseena ta iya mata bayanin, "cikin ta ne ke ciwo."

"Eyya sorry, ki tashi mu je room ɗina sai ki kwanta ki huta, then sai in samo miki magani ki sha."

Gyaɗa kanta tayi ba tare da musu ba, shiyasa budurwan ta ɗaga ta tare da mannata a jikinta suka nufi waje. A hankali suke tafiya har suka fita haraban wurin suka tasar wa inda jerin ɗakunan makarantar suke. Kai tsaye ɗakinta ta kaita tana shimfiɗe ta a saman bed ɗin ta, sannan ta nufi fridge ta ɗauko mata ruwa tana kawo mata, taimaka mata tayi ta mike zaune ta bata ruwan ta sha, sai da ta sha kaɗan sannan ta sake tambayarta, "period take yi ko kuma ciwon ciki ne?"

Idanunta da suka canza kala ta sauke a kanta tana ɗan jan numfashi a hankali, a takaice ta bata amsa da, "period ne."

Murmushi tayi ita kuma tana ɗan cije laɓɓanta, sai ta miƙe ta fita, babu jima wa ta dawo mata da magani ta ƙara tashin ta zaune tace, "ta sha zata samu relief."

Babu musu ta amshi maganin ta sha sannan ta sake koma wa ta kwanta. Idanunta a lumshe tana sauraron yanda cikin nata yake sake murɗa wa a hankali, sai sauke numfarfashi take yi slowly. Kusan mintina goma sannan ta soma jin raɗaɗin yana rage wa, hakan ne yasa ta ware idanunta a saman fuskar Nana wacce ta zura mata ido tana duƙe a gabanta, gwiwowin ta a ƙasa

Murmushi Nanan tayi mata tana cewa, "kin soma jin sauƙi ko?"

Kai ta gyaɗa mata tana ci gaba da sauke ajiyar zuciya

"Yauwa to, sai ki tashi ki shiga toilet ki kimtsa jikinki, a hankali za ki ji ciwon ya rage ma, kar ki damu maganin yana da kyau." Cewar Nana tana ci gaba da murmusawa idanunta suna a kan Haseena ko ƙyafta su ba tayi

Ita kuma sai ta kawar da kanta domin tun ba yau ba ta tsani irin wannan kallon ƙurillan da Nana take mata, in fact ma ba ta bata fuska bare magana ya haɗa su, sabida yanayin ta wanda sam bai yi wa Haseenan ba, kallon ƴar iska take mata, amma kuma yanzu bata da yanda zata yi tunda ita ta taimaka mata, don haka ta miƙe tsaye da taimakon Nanan suka je toilet

Sai da ta tabbatar ta shiga sannan ta fito ta zauna a gefen gadon tana cije bakin ta, dai-dai inda aka huda mata aka zura mata ɗinkunne, bama nan kaɗai ba, hatta hancin ta akwai ɗinkunne har biyu a wurin, hannayenta suna ajiye a saman cinyarta, dukka yatsun sun sha zobuna farare sol da ratsin ja a jikin su, haka ma babban yatsar kafanta ta hagu, sai kuma sarƙan ƙafa da kowanne ƙafan ke dashi,
Tana sanye cikin riga da wando ne waɗanda suka yi matuƙar matse ta suka fitar mata da surar jikinta, boobs ɗin ta har leƙo wa suke yi waje, baza ka taɓa cewa ƴar musulma bace a kallo ɗaya da kayi mata, ga ƙarin gashi da tayi kalan ja da fari a kanta, kwata-kwata bata da zubi da mutanen kirki, duk wanda ya san kansa bazai iya mu'amala da ita ba, sabida komai a zahiri yake duk wanda ya kalle ta ya san babu alamun tarbiyya a wurin, musamman yanda idanunta suke a tsaitsaye ga su manya Masha Allah, sun buɗe da harkan duniya

Yatsar ta ɗaya ta ɗaura a bakin ta tana tsotson shi, yayinda fuskarta yake dauke da shu'umin murmushin ta da bai rabo a fuskarta. Yau tana jin damar ta ne ta samu, abun da ta jima tana hari wato Haseena, yau ga shi ta zo hannu har cikin dakin ta, abun farin cikin ma samun ta da tayi tana period, a hankali ta saki yalwataccen murmushi tana magana a fili tare da furta, "Haseena kin shigo hannu, dama na jima ina burin yanda zan samu wannan damar, sai ga shi cikin sauƙi na samu big chance..."
Shiru tayi sabida ganin Haseenan na ƙoƙarin fitowa, sai ta waiga tana kallonta tare da mike wa tsaye ta nufi inda take, kama mata hannu tayi ta kawo ta bakin gadon ta zauna, sannan tace mata, "ina zuwa." Bata jira cewar ta ba jiki na rawa ta koma cikin toilet ɗin, nan kuwa idanunta suka sauka a kan pad ɗin da tayi amfani dashi ta cire ta ajiye, da sauri ta ƙarisa wurin; ta buɗe ta ga jini kwance a ciki, sai ta saki ajiyar zuciya mai ƙarfi tana sakin murmushin farin ciki, kana kuma ta juya ta koma bedroom ɗin tana mata sannu, zama tayi gefen ta tana tambayarta jikin nata?

Cike da sanyin jiki tace, "da sauƙi."

"Good, yanzu me kike buƙata in dafa miki? Sai ki ci ki kwanta before lokacin lecture, i know zuwa lokacin ma kin koma normal."
Ta ƙare maganar cikin Hausar ta da bai fita sosai tana murmusa mata

Hakan ne yasa itama Haseena ta saki jikinta har tana mayar mata da martanin murmushin, duk da tana ɗar-ɗar da ita kasancewar da rashin sabo, kuma duk wanda ya ga Nana dole ya ji tsoro da shakkar shiga jikinta. Cewa tayi, "ba ta buƙatar komai."

Amma sai Nana tace mata, "dole ne ta ci wani abu, since a yanayin da take ba a buƙatar zaman ta da yunwa."

To kasancewar itama Haseena da yunwar a tare da ita, tunda bata yi breakfast ba ta fito, shiyasa ta gyaɗa mata kai tare da furta, "Whatever she cooks for her, she will eat it."

Murmushi Nana tayi, tana shirin tashi a wurin sai wayanta tayi ƙara, sanya hannu tayi ta ɗauka daga cikin aljihun wandon ta, tare da latsa ta da Zara-zaran ƙumbunan ta waɗanda suka ji fenti mai ƙyalƙyali, kunnen ta ta kai tana furta, "Hello."

Haseena kuwa idanu ta zuba mata tana mai mamakin yanda Nanan ta koma wai kuma ƴar musulma ce, musamman da ta taɓa jinta tace mata, "itama asalin ƴar Nigeria ce."
Tabbas ta yarda tunda ga Hausa nan a bakin ta duk da ba raɗau take fita ba, "Amma to me ya mayar da ita haka ta koma kamar mara addini ta kile ta zama ƴar duniya?" Wannan tambayar ta jima tana yawo a zuciyar Haseena tun sanda ta fara ganin ta. in fact ma babu mai kallonta yace ta haɗa jiɓi da baƙin fata sabida yanda take rayuwarta cikin waye wa, kuma kaf friends ɗin ta da take yawo da su mazauna nan ne. Har a ranta tana son ta san wace ce Nana? Duk da tana tunanin ba karatu kaɗai ya kawo ta nan ba, maybe a nan tayi rayuwarta, kallon da Nanan tayi mata a yanzu ne yasa ta ɗauke kanta daga gare ta

Murmushi ita kuma Nanan tayi tare da furta, "I am with her now in the room."
Shiru ta ɗan yi, sai kuma ta sake furta, "I will come soon, give me some time."
Sai ta zare wayan ta ajiye a bed side drower, kallon Haseenan tayi; smile tayi mata ta miƙe ta fita falo

Hakan ne yasa Haseena ta sauke ajiyan zuciya tana lumshe idanunta, babu abun da take buƙata a yanzu face jin sassanyar muryan SHAREEF, wanda take jin hakan zai ƙara kwantar mata da hankali muddin ta ji muryansa, shiyasa itama ta laluba Jakarta ta ciro wayanta tana latsa wayan a hankali, bayan ta danna dealing contact nasa sannan ta kwanta tana mayar da idanunta ta rufe su ruf,
Ring daya biyu ya amsa call ɗin. Hakan ne yasa ta marairaice murya tana kiran sunan sa

Yayinda daga can ɓangaren SHAREEF, wanda yana cikin katafaren office din sa, zaune a kan chair ɗin sa yana juya wa a hankali

Gefe kuma Mahmud ne ke zaune shima, ya kasa kunne yana sauraron Ogan nasa tamkar ba shi yake saurare ba, sabida tunda ya ɗauki wayan shima sai ya zaro nasa wayan yana latsa wa kamar hankalinsa ba ya wurin

Yanayin yanda ya ji muryar Haseenan na fita, ya san cewa tana cikin damuwa, shiyasa tambayar da ya soma jeho mata a kan abun da ke damun ta ne?

Sai ta sake narke wa kamar zata yi kuka tace, "dear bani da lafiya, kamar zan mutu yau."

Cikin yanayi na tashin hankali da ya nuna a muryansa yake faɗin, "Ya Salam! me ke damun ki Sweetheart? Ina fata kin sha magani dai?"

Yanda ya jeho mata tambayoyin cike da nuna ruɗu da damuwar sa, hakan ne yasa ta ɗan saki yalwataccen murmushi tana cewa, "kar ka damu yanzu ina jin sauƙi kaɗan -kaɗan, kuma na sha magani ba da jima wa ba, ciwon da na saba yi ne ya taso min."

Ɗan numfashi ya ja cike da tausayin ta yace, "I'm sorry sweetheart."

Buɗe idanunta tayi tana murmusawa a hankali, sai kuma tace, "but yaushe zaka zo? I'm really miss you, ba na jin zan iya one week ban sake saka ka a idona ba, na soma gajiya da halin kaɗaicin da nake ciki."

Ɗago ido SHAREEF yayi yana duban Mahmud, sai kuma ya ɗauke kansa yana ƙara rage murya a slowly ya furta, "Sweetheart ina cikin aiki yanzu haka, zuwana wurin ki zai yi wuya, but let me promise you that I will come wani lokacin."

Kukan shagwaɓa ta sakar mishi lokaci guda, yayinda nan da nan yayi tasiri a wurin sa ya ruɗe yana tambayarta dalilin kukan nata. "Ni dai ka zo nan kusa dear, bazan iya ci gaba da jure rashin ka ba, Please ka zo."

Shiru ya ɗan yi, sai kuma yace, "ok, zan duba in gani, amma yanzu tunda ba ki da lafiya ki kwanta ki huta, later zan kira ki kinji ko?"
Ya ƙare maganar da lallami,
Daƙyar ya samu ta haƙura har suka yi sallama, ajiyan zuciya ya sauke yana ɗan jan huci tare da fesar wa, sai ya ajiye wayan yana saka hannu ya soma mirza idanunsa, tunanin yanda zai yi ya samu damar zuwa wurin Haseena yake yi, domin shi kansa yayi matuƙar kewarta since tunda suka fara soyayya, basu taɓa rabuwa haka ba, kullum sai sun ga juna, amma yanzu har ana iya shafe tsawon kwanaki ba tare da sun ji ɗumin junan su ba, sai dai video call wanda yake matuƙar taimaka musu wurin jin sauƙin raɗaɗin rashin ganin ɗayan su...

"Sir."
Mahmud ya kira sunan sa lokacin da ya ji shiru bai ce komai ba, kuma ya gama wayan

Hakan ne yasa SHAREEF ya cire hannunsa daga idanunsa yana kallon Mahmud ɗin

Mahmud yace, "Sir, lokaci yana running, yanzu haka time na shiga meeting ya kusa, kuma ana buƙatar wuce wa da kayan yanzu, ya kamata mu je ka gani. Sannan akwai maganar da nake so in yi maka."

Tsira masa ido SHAREEF yayi ba tare da yace uffan ba, alamun yana jiran ya ji mai zai ce

Shi yasa Mahmud ya ƙara da faɗin, "ba na tunanin zamu samu shigowar kayan nan yau, sai dai gobe, jiya da dare na tura maka saƙo a WhatsApp after na ji wayan ka a kashe, i think baka duba ba?"

"Eh ban duba ba, amma meyasa baka faɗa min da wuri ba?" Sai ya ja guntun tsaki yana miƙe wa tsaye, tare da furta, "mu je kawai, Allah ya kaimu goben lafiya."

Shima miƙe wa Mahmud yayi, yana amsa wa da Amin, sai ya bi bayan sa suka fice a Office ɗin, cuz tuni shi SHAREEF yayi gaba abun sa.
[07/02, 8:24 am] OumƊahirah نفيسة: 🌱🌱🌱🌱🌱

      *SHAREEF*
          _SexyBoy_
🌱🌱🌱🌱🌱


_Writer: Nafisat Isma'il Lawal_
_Wattpad: UmmuDahirah_

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝*



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

       *P.W.A✍️*





*DATA SHARE*

Call, message or whatsap  07065334256

*MTN*
500MB 150
1gb  280
2gb.  560 
3gb.   840
4gb.    1120
5gb      1400
6gb.     1700
Verlid for 30 days.











__________
*BOOK1*
_______________*FREE PAGE25*
_____Saurin dafa na kusa da ita tayi, shi ya hana ta faɗi ƙasa daga tsananin jirin da ya kusa yasar da ita. Ita kanta yarinyar da ta fahimci halin da Maryamu ke ciki, shiyasa bata ce mata komai ba illa kallonta da take yi, har ta ƙare dai ta buɗi baki tana tambayarta, "ko lafiya?"
Amma sai Maryamu ta girgiza mata kanta alamun babu komai,
Daƙyar ta iya tsayar da kanta a wurin har aka gama assembly; kana ta doshi inda class ɗin su yake kamar yanda ɗaliban suke ta tafiya, Jakarta na hannu sabida baza ta iya goya wa ba, tana shiga class ɗin; ta nufi sit ɗin su ta zauna, sai ta manne da bango ta ɗaura kanta a deks

Ƴan class ɗin sai shigowa suke yi kowa yana samun wurin zaman sa ya zauna. Amina tare da Feena ne suka shigo a ƙarshe suna hira a tsakanin su suna dariya

Ganin Maryamu zaune a layin nasu, sai Amina tace, "yauwa, kin ganta ma, ashe ta zo, Maryamu." Ta ƙare maganar da kiran sunanta after ta zauna a kusa da ita tana dafa bayanta

While ita kuma Feena har ta samu wuri a saman deks ta zauna idanunta a kan Maryamun

Ɗago kai tayi tana kallonsu cikin yanayin ciwo

Hakan ne yasa Amina tace, "lafiya me ke damun ki? Ko ba ki da lafiya ne?"

Gyaɗa mata kai tayi alamun eh amma bata da alamun buɗe baki tayi magana

"Eyya sorry, amma meyasa kika zo makaranta kin san ba ki da lafiya?"

Shiru tayi don ko kusa ba ta son yin magana a halin da take ciki, tamkar kanta zai rabe gida biyu haka take ji in har ta motsa bakin ta

Dukkan su kallonta suke yi cike da tausaya wa, har Feena wacce bata santa ba sai yau ɗin da Amina ta bata labarin ta

Hannayenta Amina ta riƙe tana sake mata sannu cike da tausaya wa, sai tace, "ko kuma ki kwanta in za ki fi jin dadi, before Teacher ya shigo ko?"

Mayar da kanta Maryamu tayi ta kwantar a saman deks ɗin tana lumshe idanunta

"Ke kuma ki zauna a sit tun kafin uncle ya shigo ya ganki a saman nan, kin san halin sa ya hana, kuma na ga ya zo yau ma."

Zamo wa Feena tayi tana zama a gefen Amina, sai suka saka ta a tsakiya, har ta buɗe baki da ninyar yin magana, sai kuma ga class teacher din su nan ya shigo, hakan ne yasa tayi gum bata furta komai ba

All class ɗin suka miƙe a tare suna gaishe shi,
Ya amsa musu cikin fara'a yana basu umarnin zama, haka shima ya nufi wurin sit ɗin shi ya zauna ba tare da ya kula da Maryamu da ke kwance ita bata tashi ba

Luwaisa wacce ke ƙus-ƙus ita da Hafsah, a kan abun da Maryamu tayi mata, tunda ita Luwaisan ta rantse sai ta sanar da Uncle din su in ya zo, shiyasa ta miƙe zumbur tana cewa, "Uncle jiya an yi dambe a ajin nan fa."

"Dambe kuma? A class ɗin nawa?" Yayi maganar da mamaki

"Yes Uncle, wata new student aka kawo, shi ne ta dinga zagin Hafsah har da zagin mata uwa, kawai don ta yar da bairo zata dauka, shi ne ta dinga zagin ta wai nata ne ba na Hafsah ba, har da kiranta ɓarauniya."

Cikin mamaki yace, "wace ce?"

Da sauri ƴan class ɗin suka nuna inda Maryamu ke zaune

Ya bi wurin da kallo, sai dai ganin Maryamu kwance sai yace, "ya aka yi ta kwanta min a class? Amina, Nafisa, ba ku faɗa mata dokokin class ɗina bane?"

"Uncle bata da lafiya ne."
Cewar Aminan tana kallonsa a ɗar-ɗar

"Mene sunanta?"

"Maryamu Haruna." Ta ba shi amsa da sauri

Kiran sunan Maryamu ya soma yi cikin ɗaga murya, hakan ne yasa dole ta ɗago da kanta ta zuba mishi manyan idanunta da suka soma kumbura sun yi jazur lokaci guda

Tsare ta yayi da kallo na tsawon daƙiƙu, sai yace, "me ke damun ki daga zuwa aji za ki soma kwanciyar min a deks?"

Shiru tayi masa ta kasa ba shi amsa, sai ma duƙar da kanta da tayi jikinta ya soma rawa

"I'm talking to you and you keep quiet? I don't like asking questions and getting no answers."
Shirun da ta sake yi ne, shiyasa shi ya ɗan fusata ya daka mata tsawa ya bata umarnin mike wa tsaye

Sai Maryamun ta ƙi miƙe wa, ta koma ta kwanta lokaci ɗaya ta fashe da kuka mai ƙara, nan da nan ta soma rawan jiki ko'ina na jikinta kakkarwa yake yi

Amina da Feena sarakan tsoro tuni sun tashi sun tsatstsaya suna kallonta,
Duk ƴan ajin ma kallon yanda Maryamun take yi da jiki suka zuba ido suna yi,
Sai kanannaɗe wa take yi tana cure wa wuri ɗaya tana kuka sosai

Hakan ne yasa Uncle din nasu ya tabbatar da cewa bata da lafiya ne, shiyasa ya miƙe yace ma su Amina, "su taimaka su riƙo ta zuwa clinic." Wurin da ake duba ɗaliban in basu da lafiya

Duk da suna cike da tsoro, amma babu damar yin mishi gardama, shiyasa suka saka hannu suka ɗago ta daƙyar tana langaɓe wa tana ci gaba da kukan nata, har sun fito da ita cikin sit ɗin nasu suna ƙoƙarin fita da ita waje, amma sai ta rinjaye su ta faɗi tim a ƙasa, daga nan bata sake motsi ba

Babu yanda Uncle din nasu ya iya, dole ya fita ya je ya kira wata Auntyn su ta zo ta ɗauki Maryamu kamar wata jaririya aka fita da ita

Duk ƴan aji sun yi tsumu suna kallon ikon Allah, kowa jikinsa yayi sanyi tunda basu san me ke damun yarinyar da basu gama sanin ta ba ma, daga jiya zuwa yau da zuwanta har ta shiga wannan halin,
Dawowar Uncle din su class ɗin shiyasa suka mayar da hankali a kan karatun su,
Har ya  gama musu ya fita ba a dawo da Maryamu ba,
Tana can ana duba ta amma an kasa gano me ke damun ta, in fact ma tunda ta dena numfashi bata sake farfaɗo wa ba, duk taimako an bata but bata farfaɗo ba

Dole principle yace, "a mayar da ita gida, wataƙil yarinyar tana da wani ciwon da su basu san dashi ba sai iyayenta, don haka gwara a mayar musu ita gida su yi mata magani da gaggawa."
Shi principle ya bada address ɗin gidan su Maryamu, tare da key din Motan sa, Uncle Teejay da Aunt Fatima wacce ta taimaka mata, su aka bama damar su kaita gidan,
Shi yasa Uncle Teejay da kansa ya je har class ya ɗauko mata Jakarta sannan aka saka ta a Mota suka wuce.

    




🔆🔆🔆🔆🔆🔆🔆🔆

               *AUSTRALIA*
                  *SYDNEY*
       She cooked Indomie and eggs for her, cikin sauri ta gama mata, domin ba ta son ta ɗauki lokaci tana jiranta. After ta gama sai ta zuba mata a plate ta kawo mata har cikin bedroom ɗin,
Ajiye mata tayi a saman bed ɗin tana mata wannan murmushin nata da bai rabo a kan fuskarta, sai tace, "I'm done, ki daure ki cinye; then go to bed and rest."

"Thanks." Haseena itama ta furta cikin murmushin cike da jin dadin kulawar da take bata

"Your welcome dear."
Taka wa tayi tabar cikin bedroom ɗin domin ta barta ta saki jikinta sosai

Hakan ne yasa Haseena ta saki ciki ta ci indomien tayi nak, after ta gama sai ta sha juice ɗin da ta kawo mata, ita kanta bata san wanne irin juice bane, amma abun ciki ja ne sosai kuma mai kauri, sai shegen dad'i a baki, tana son ta tambayi Nana wanne irin juice ne haka? Amma kuma ganin bata dawo ba shi yasa ta gyara kwanciyarta tana ɗaukar wayanta; tare da tura wa SHAREEF text mai daɗi, daga nan sai ta saka wayan a silent ta gyara sai barci

Almost 20 minutes Nana tana zaune a falo tana latsa wayanta, daga baya ne ta leƙo ta ga Haseena na shara barcin ta hankali kwance, alamun jiki yayi sauƙi bata da wata matsala. Dariya tayi kaɗan tana nufan inda take, ta sanya zara-zaran ƙumbunan ta a saman face ɗin ta tana shafa wa a hankali cikin salo, a fili ta furta, "I love you so much! I can't let you go, I've been waiting for this chance, tun sanda na fara ganin ki naji kin kwanta min a raina, ina matuƙar sha'awar ki, daga yanzu kin zama tawa Ni kaɗai." Ta ƙare maganar cikin Hausar ta da ba ta fita sosai; tana lashe bakin ta cikin wani irin yanayi da kallon da take yi wa Haseena, mai nuni da tsantsan sha'awa da ƙaunarta da ke fito wa a ƙwayar idanuwanta,
Janye hannunta tayi sabida ganin tana motsa wa, sai ta bi ta da kallo har ta dena motsin, tukunna a hankali ta miƙe ta shiga toilet, kuma babu jima wa ta fito ta nufi dressing mirror ta ɗauki wani ƙaramin kwalba sannan ta koma toilet ɗin. Jinin Al'adan Haseena ta zuba a ciki sannan ta rufe kwalban ta fito, kai tsaye wayanta ta ɗauka wadda ta ajiye a saman bed side drower, ta fice a ɗakin.
***



         Ba ƙaramin barci Haseena ta sha ba, almost 4 hours tana barci before ta farka, ita kanta da ta duba agogo tayi mamakin barcin da ta sha, shiyasa ta tashi zaune tana bin bedroom ɗin da kallo, ta jima zaune kafin ta tashi ta fita falon tana duba wa ko zata ga Nana; but babu ita, har kichen ta duba babu Nana a ciki, shiyasa ta koma toilet ta kimtsa kanta ta sake canza pad, sannan ta dauki waɗanda ta cire ta ƙudundune ta zura su a jaka,
Tana nan zaune a bakin gado sannan ta ji motsin shigowa,
Ƙofan take kallo sai ga Nana ta shigo don ita tayi tsammanin gani

Cikin wannan shu'umin murmushin nata ta ƙariso kusa da ita tana cewa, "Baby har kin tashi barcin?"

Smile Haseena tayi tace, "yeah."

"Ok, nima na fita ne sai yanzu na dawo, I see it's time to go to class now, that's why I hurried back to wake you up, ashe kin tashi? Ya kamata mu hanzara mu tafi, time yayi."
Ta ƙare maganar tana duban agogon hannunta,
"You have finished everything?" She spoke again and her eyes were looking at her

Haseena tace, "yes, thank you for your help."

"No kar ki damu, tashi mu je."

Mike wa Haseena tayi tana ɗaukar jakarta ta rataya, suka fita a tare while Nana ta datse ƙofan da key,
Basu sake wata magana ba har suka isa class ɗin,
Time ɗin ma Teacher ya shiga ajin,
Shi yasa suka samu wuri kusa da Herin and Jenifer; friends ɗin Nanan, a kusa dasu suka zauna

From this lesson they have no one else, that's why after they finished, Haseena waved goodbye to them and left

Herin wacce ta bi bayan Haseena da kallo har ta fice, sai ta mayar da kallonta kan Nana cike da kishi tace, "As for me, I don't like this girl, I really don't like what you did, now are you going to stop loving me? I don't want to see her in us."

Kamo hannunta Nana tayi tace, "Ha, common babe, I won't stop loving you, she is different and you are different outside of me, all your positions are different, so don't worry too much, we are here together, there is no one to separate us. She will join us because I need her, I love her very much, she won't give you any problems, don't worry ok? Oya smile now."
Ta ƙare maganar tana shafa mata kumatu cike da so da ƙauna

Murmushin tayi but duk da haka tana yatsina fuskarta, duk da ba haka taso ba

Jenifer tace, "now do you think it won't be a problem for us?
Don't let her come inside us and destroy our plans, After she learned our secret. From the beginning, she did not say that she was interested in joining us, the situation we are in requires privacy."

"Don't worry babies, There is no problem, I just need her from us, and I will not tell her about anything about us, I can only pay for my needs with her. Finished." Nana ta furta hakan tana ɗage hannayenta

Dukkan su taɓe baki suka yi

"Ok let's go."

Tashi suka yi suka bar class ɗin, wanda tuni an gama watse wa an bar su su kaɗai a ciki, kai tsaye room ɗin su na cikin school ɗin suka wuce suna ci gaba da sake tattauna wa a kan Haseena wacce suke son ta shigo cikin su, duk da su biyun basu so hakan ba, amma Nana ta dage da buƙatar ta a cikin su, cuz ita take matuƙar sha'awar ta da ƙaunarta

Tun farkon zuwan Haseena makarantar Nana ta so ta jawo ra'ayin ta ta shiga cikin su, but sai dai hakan bai samu ba, sabida tun lokacin da ta ɗaura ido a kanta ta ji matsananciyar ƙaunarta ya kama ta, duk wani hanya ta bi domin Haseena ta riƙa mata magana su zama friends, bata samu dama daga wurin ta ba, tunda sosai Haseena take ƙyamatar yanayin Nanan da ko fasali bata dashi, shigan da take yi da kuma yanayin rayuwarta da su Herin sam bai kamaci ƴar musulma ta haɗa hanya da su ba, duk da Haseena tana son rayuwar waye wa amma ba irin wannan ba, to taya ya ma zata yi ƙawance da irin waɗannan mutanen? Sai ka ce bata da mafaɗi?

Nana tayi ƙoƙarin ta nuna mata irin ƙaunarta da take mata, amma sam babu fuska, shiyasa ta ƙyale ta sai dai kallo daga nesa, sai ga shi kwatsam Haseena ta shigo hannunta cikin ruwan sanyi, wanda hakan ne yasa Nana tayi amfani da damar ta wajen ganin ta mallaki zuciyar Haseena da ƙarfin tsafin su. Ƙwarai tsafi suke yi. They are in a secret society and lesbianism,
Shi yasa Nana take son saka Haseena a ciki, duk da iya lesbianism take buƙatar ta, since ba kowa suke buƙatar ya san wannan sirrin nasu na secret society ba, amma a hankali idan suka yi nisa da friendship din su zata yi kokarin jawo ta ciki don itama ta san mene ne duniyar,
Yanzu haka tana son yin amfani da jinin Al'adan Haseena wajen mallakar ta ta zama nata ita kaɗai, ta sanya mata sha'awar ta da tsananin bukatar ta, da ko ta tunkare ta da abun da take muradi a tare da ita, baza tayi mata musu ba, domin ba ta jin zata iya hakura da ita, Allah ya ɗaura mata matsananciyar sha'awarta ne, kuma tana so ko ta halin ƙa-ƙa sai tayi amfani da ita, she knows she won't get it easily, that's why she has to use her chance now that she got it.



_Ina jin masu ƙorafin ba na more update, abun da yasa sabida ba na ganin comments ɗin da ke faranta min bare har in ji ƙwarin gwiwa, duk yanda ku ka gani kawai._
[08/02, 11:37 am] OumƊahirah نفيسة: 🌱🌱🌱🌱🌱

      *SHAREEF*
          _SexyBoy_
🌱🌱🌱🌱🌱


_Writer: Nafisat Isma'il Lawal_
_Wattpad: UmmuDahirah_

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝*



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

       *P.W.A✍️*





*DATA SHARE*

Call, message or whatsap  07065334256

*MTN*
500MB 150
1gb  280
2gb.  560 
3gb.   840
4gb.    1120
5gb      1400
6gb.     1700
Verlid for 30 days.














__________
*BOOK1*
_______________*FREE PAGE26*
_____*NIGERIA......*
*KANO STATE*
Wani irin dokan daji ne da babu gida gaba bare baya, dokan dajin da babu mahalukin halittan da zai iya kawo kansa; sabida tsaban duhu da dogayen bishiyu masu naɗi kamar macizai, babu abin da bai tara ba ciki kuwa har da muggan namomin daji masu ban tsoro da mugun kallo a ido,
A wannan dajin da babu kyan gani Maryamu ta tsinci kanta; a saman wata murɗaɗɗiyar bishiya mai kama da zubin ƙattin Macijiya, kawai buɗe idanunta tayi ta hange ta a saman bishiyan nan wadda lokaci guda zuciyarta tayi wani irin buga wa da ƙarfi, a hankali ta soma bin dokan dajin da kallo yayinda zuciyarta take wani irin hautsine wa gami da zallan tsoron da nan take ya kawo mata mamaya, wani irin jiri ne ya soma kawo mata cafka nan take ta soma gani dishi-dishi manyan idanunta suna ƙoƙarin rufe wa, duk sabida firgici da tashin hankalin da ya riske ta nan take, har wani irin sanyi-sanyi take jin yana huda mata can cikin ɓargon ta, gami da sanya mata wani irin zafi wanda lokaci ɗaya gumin tsoro ya soma tsiyaya daga cikin gashin kanta yana gangaro wa zuwa gefe da gefen kumatun ta, tamkar a mafarki haka take ganin abun, anya ba mafarki take yi ba? Ko kuma ta mutu ne ta buɗe ido ta tsinci kanta a irin wannan wurin mai ban tsoro da ban al'ajabi?
Ina ne nan? Wane ne ya kawo ta?
Tsaban ruɗe wa da shiga halin firgici, nan take ta sulale babu numfashi a jikinta, wanda hakan ne yasa ta faɗo tim daga saman bishiyan; ta sauka a saman ganyayyakin da suka bushe suka zuba a ƙasa

A hankali bishiyar nan da ta faɗo daga kanta, nan da nan ta rikiɗe lokaci guda ta zama tsohon nan da suka kusa kaɓe wa a hanya, lokaci ɗaya ya saki wani ƙayataccen murmushi yana nufan inda Maryamu take kwance tamkar babu rai, a gabanta ya duƙa yana kallon fuskarta da idanunsa jawur babu kyan gani, girgiza yayi nan take ya koma sak SHAREEF yana ɓaɓɓaka dariyan da dukka baƙin dajin nan sai da ya amsa da sautin dariyan, hannu ya sanya ya shafa fuskar Maryamu

Nan take sai ta farfaɗo ta soma yunkurin buɗe idanunta, a hankali ta gama motsa idanun har ta ware su cikin nasa, tsira mishi ido tayi na ɗan wasu daƙiƙu; kafin daga bisani tayi wani irin zillo nan take sai ga ta zaune a kan ƙafafunta; zaro idanu waje taji tana kallon SHAREEF da tsananin mamakin bayyanar sa a gabanta, nan da nan jikinta ya soma rawa musamman yanda ta ga fuskarsa ɗauke da sihirtaccen murmushin sa mai ƙara mishi tsantsan kyau da kamala, ta kasa yin magana domin halin ruɗe wa yasa fargici da zullumi kawai ke ɗawainiya da ita

Tsawon lokaci suna wannan yanayin babu mai cewa uffan a cikin su. Ita Maryamu tsoro da tashin hankali gami da mamakin ganin SHAREEF a wurin ta, yasa ta manta da abun da yakamata tayi bare tayi tunanin tantance inda take da kuma abun da ya kawo ta

Shi kuma SHAREEF tsaya wa kawai yayi yana kallonta har yanzu da murmushin nan a kan fuskarsa bai gushe ba. A hankali ya sanya hannu ya kamo nata yana ƙoƙarin tayar da ita

Wanda hakan ne yasa jiki na rawa ta miƙe kamar yanda ya so miƙar da itan, kamar wata sokuwa haka ta bi bayansa har zuwa wani saman bishiya mai kama da kujera ya kaita wurin, sai a lokacin ta samu damar ƙare wa dokan dajin kallo, nan da nan tsoron ta ya ƙaru fiye da baya, jikinta ya ci gaba da kakkarwa wanda lokaci guda bakin ta ya buɗe, cikin tashin hankali ta kira sunan SHAREEF tana cewa, "Yaya SHAREEF don Allah ina ne nan? Wane ne ya kawo Ni? Wayyo Allah!."
Sai kawai ta fashe da kuka ta ƙi zama a inda yake ƙoƙarin zaunar da ita

Hannu yasa ya rufe mata bakin yana zare mata ido tare da furta, "shiiii!"

Lokaci guda ta shanye kukan nata tayi shiru kamar ruwa ya cinye ta

"Babu abun da zai same ki, ba gani a kusa da ke ba?"

Wannan maganar nasa tamkar an sanya mata wani irin natsuwa ne, a hankali jikinta ya rage rawan da yake yi, nan take tayi shiru tana bin sa da ido kamar ta samu TV har ya zauna a gefen ta ya zuba mata ido shima

Murmushi yayi mata ba tare da ya furta komai ba, wadda ita kanta ta matsu ta ji mai zai ce mata, kuma mene ne dalilin zuwan su nan? Taya ya ma hakan ta kasance har suka zo? Kuma ba da kowa ba sai da SHAREEF...

"Na san a yanzu kina nan kina tunani a zuciyar ki; a kan yanda aka yi kika zo nan ko?"

Da sauri ta gyaɗa mishi kai tana haɗiyar yawu in quickly, domin ita kanta ta matsu ta ji daga gare sa, tana ga kamar mafarki ne har yanzu take yi abun da ke faruwa ba gaskiya bane. Zuba masa ido tayi tana kallonsa

Hakan ne yasa ya ɗaura hannunsa a saman fuskarta yana latsa wa a hankali, baki ta saki tana bin sa da kallo, yayinda take jin jikinta tamkar ana tsotse mata ruwan jiki, wani irin sanyi ne ke ƙara huda mata can cikin jiki yana saukar mata da kasala, yayinda laɓɓanta suke kakkarwa alamun tana son buɗe baki tayi magana, amma ta gaza, kamar an saka glue an nane mata, tana kallonsa yana shafa mata fuska har zuwa wuyanta zuwa saman ƙirjin ta, yayinda ya gangaro hannunsa zuwa saman cikin ta, yanayin da ta shiga yasa ta kasa jure wa, nan ta rufe idanunta ruf tana fatan a ce idan ta buɗe su ta ga mafarki ne, "anya SHAREEF ne a gabanta ko mafarkin da ta saba yi ne? Ya soma sonta ne?"

"Eh na soma sonki ne."

Amsar da ya bata yasa ta buɗe ido da sauri tana mamakin yanda aka yi ya san mene ne a zuciyarta

"Kina mamaki ko? Yanda na san abun da ke zuciyar ki? Ba iya nan ba, komai na sani a kanki, shiyasa na ɗauko ki na kawo ki nan domin in faɗa miki wani sirrin da ba ki sani ba..."
Take a nan yayi shiru da maganar, lokaci ɗaya ya soma girgiza ya saki wani uban ihun da sai da ya firgita Maryamu ta faɗo ƙasa, kafin ta tantance me ke faruwa sai gani tayi ya soma zama wuta yana ci bal-bal

Kurma ihu tayi wanda yasa lokaci guda ta farka daga suman da tayi, tana buɗe idanunta sai ganin Momy tayi a gefen ta tana tofa mata addu'o'i, ta riƙe ta sosai, ashe fizge-fizge take yi still tana ci gaba da kwarara ihun tamkar zata tsaka falon,
Hakan ne yasa Momy ta ƙara ƙaimi wajen karanto mata addu'o'i musamman yanda ta ga ta buɗe idanunta tana motsi, hakan ne yasa hasashen ta ya soma zama gaskiya, tabbas Maryamu aljanu ne da ita, domin tun sanda Malaman makarantan suka kawo ta suka shimfiɗe ta a wurin, jikinta na rawa tayi tunanin kiran Dady since ba ya gidan, ganin wayan ta ƙi shiga babu service shiyasa ta dawo kusa da Maryamu; wacce aka shimfiɗa ta a saman dogon kujera, sai jinta tayi tana sambatu, abun mamakin har da kiran sunan SHAREEF, dalilin da yasa ta zauna ta soma karanta mata addu'o'i kenan,
Sai ga shi kuma ta farfaɗo, a hankali kuma ta dena fizge-fizgen nata, hakan ne yasa Momy ta furta alhamdulillah tana shafa fuskarta tare da kiran sunan ta

Dishi-dishi Maryamu take kallon Momyn, ga kanta da ke wani irin sara mata kamar zai ɗaɗɗake, hannu ta kai saman kan nata tana runtse idanu gam, a hankali kuma ta sake buɗe su ta zuba wa Momy, nan ƙwaƙwalwanta ta soma dawowa har ta fara tuna abun da ke faruwa, "Momy." Ta furta sunan Momyn tana ƙoƙarin tashi zaune

Saurin kama ta Momy tayi ta tayar da ita tana mata sannu

Shiru tayi tana ɗan jan numfashi a hankali, "Momy wane ne ya kawo Ni nan? Ko dai duk mafarki nake yi?"

"Ba mafarki kike yi ba Maryam, daga school aka dawo da ke gida, yanzu kika farfaɗo daga suman da kika yi."

Shiru tayi tana sake tuna wa, amma tayi mafarkin ganin ta a dokan daji, ita da SHAREEF, kenan duk mafarki ne?
A ranta take wannan saƙe-saƙen tana ci gaba da runtse ido, domin ba ƙaramin azaban ciwon kai ke damunta ba

"Sannu Maryam, yanzu me ke miki ciwo?"

Hannunta ta nuna a kanta daƙyar ta iya furta, "kaina Momy."

"Sannu, bari in kawo miki magani sai ki sha ki kwanta ki huta." Cikin tausaya wa Momyn take mata sannu, kana ta cire hannunta a jikinta tana mike wa ta nufi ɗakin ta

Runtse idanu Maryamu tayi tana sake tariyo abun da ya faru ita da SHAREEF, kenan duk mafarki ne? tabbas ta san cewa dole sai mafarki; tunda ba yau ta saba ba, amma wannan ya fita daban, meyasa take jin kamar gaske ne? Sannan mene ne dalilin kaita dokar daji ba yanda suka saba haɗuwa ba, tuna yanda ya soma cin wuta tayi, abun kamar a idanunta yanzu yake faruwa, shiyasa tayi saurin buɗe ido tana jan nimfarfashi kamar ranta zai fice, ko kusa ba ta jin iskar da ke shiga ƙofofin hancin ta tana wadatar da ita, shiyasa ta dinga fitar da nishi mai karfi kamar mai cutan asthma, cikin wani irin ƙara da ke fitowa daga kunnen ta taji ana furta mata, "zan dawo gareee ki, zan dawooo. Dole zamu kasance tare na har abada."
Zamo wa ƙasa tayi tana zare idanu sabida mamakin yanda ake mata magana a cikin kunne, duk ta firgice lokaci guda ta saka hannu a kunnuwan ta domin ta doɗe jin sautin, amma kamar ana ƙara wa sai kururuwa ake mata da dariya,
"Wayyo Allah na! Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un! Na shiga uku na!"

Ɗif ta ji an dena mata kururuwan,
Sai kuma ta soma jin ƙaran takalman Momy tana sauko wa daga kan steps, da sauri ta ɗaga kanta tana kallon Momyn wacce take nufo wurin ta

Da mamaki Momy take bin ta da kallo ganin ta sauka ƙasa ta zauna dirshan, kuma ta takure wuri ɗaya,
Da sauri ta iso wurin ta tana kiran sunan ta, "Maryam, meyasa kika zauna a ƙasa kuma?"

Girgiza kanta ta soma yi alamun babu komai

"To tashi ki sha magani sai ki kwanta ki huta, sannu, idan jikin bai yi sauƙi ba sai mu san abun yi." Momy ta furta tana kama hannunta tare da zuba mata maganin, sai ta ɗauki ruwan Faro da ke wurin ta buɗe ta miƙa mata, yanda ta ga jikin Maryamun na rawa shiyasa duk tausayin ta ya kama ta, tana da tabbacin akwai mutanen ɓoye a kanta sabida yanda take yi duk ta wani firgice ta fita a hayyacin ta, dole hakan ya baka al'ajabi, amma kuma kasancewar Momyn tana da addu'o'i a bakin ta sosai, shiyasa ta zuba ruwa a cup ta sake yin mata wasu addu'ar, sannan ta bata ta sha, sai ta miƙar da ita tace mata, "su je ɗaki ta kwanta."
Har ɗakinta ta kaita ta kwantar da ita, sannan ta fito ta koma kichen ta soma haɗa lunch, duk da a zuciyarta halin da Maryamun ke ciki ya tsaya mata a rai

Har ta gama aikin nata ta koma ɗakin ta duba ta, still tana barci, shiyasa ta wuce ta soma gyaran falon sabida nan ne kaɗai bata gama gyara wa ba, sai da ta gama sannan ta kwaso abincin ta jera a saman dinning,
Time ɗin ƙarfe 01:20pm.
Ɗakin Maryamu ta nufa domin ta tayar da ita tayi sallah

Tana shiga ta ganta zaune a saman gadon ta tashi, yanayin da ta ganta ma kaɗai zai tabbatar mata da samun lafiyar ta, shiyasa ta washe baki tana cewa, "Maryam har kin tashi?"

Kallonta Maryamu tayi, tace, "eh Momy, amma Momy ya aka yi na dawo daga school time bai yi ba?"

Murmushi tayi ta shafa mata kai da cewan, "dawowa da ke aka yi ba ki da lafiya. Ashe duk ba ki san me ke faruwa ba? To ya jikin naki yanzu?"

"Babu abun da ke min ciwo." Tayi maganar a hankali

"Yauwa Masha Allah, yanzu tashi ki shiga bayi ki ɗaura alwala ki yi sallah, idan kin gama ki fito falo in zuba miki abinci ki ci."

"To Momy."

Bata fita ba sai da ta ga ta shiga toilet ɗin tana ɗaura alwala, shiyasa ta fita ta koma nata dakin itama don tayi sallan.
***

_____A sanda Maryamu ta fita Falo, ta tarar da Momy da Dady ne zaune suna magana, kuma duk a kan abun da ya faru da Maryamun ne take sanar mishi, tunda bai jima da dawowa ba

Ganin ta fito, shiyasa ya kira sunan ta yana kallonta, tare da bata umarnin zuwa ta zauna kusa da shi, bayan ta zauna ya kama hannunta tare da cewa, "Momyn ku tace min ba ki da lafiya? Yanzu ya jikin naki?"

"Dady alhamdulillah na ji sauki."

"Masha Allah, ina fata kina addu'a da azkar ba kya wasa da su?"

Kanta ta gyaɗa mishi

Sai yace, "to ki dage, ba na son kina wasa da addu'a, kin san miyagu sun yi yawa yanzu, kin ji my daughter ki dena wasa da addu'oi ki dage da azkar kina jina?"

"To Dady, Insha Allah zan riƙa yi."

Momy da ke sauraron su, sai ta tashi ta je ta ɗibo mata abincin a plate ta miƙa mata, tare da ajiye mata magani a saman Centre table tace mata, "in ta ci sai ta sha maganin."
Addu'a tayi a cup ta ajiye mata tace, "ta sha dashi."

Haka Maryamu ta dauki abincin ta soma ci a hankali idanunta na a kan kallo

Yayinda su kuma su Momy suke ci gaba da ɗan taɓa hira a tsakanin su, daga baya ma Dady ya tashi ya koma dakin shi,
Ya bar Momy da Maryamu a wurin; since yace, "bazai ci abincin yanzu ba sai anjima, zai je ya kwanta ya huta."

    
Babu jima wa shima Sadiq ya dawo gidan, yayi mamakin ganin Maryamun shima, shiyasa yake tambayar dalilin dawowan ta

Momy ta ba shi amsa, "bata da lafiya ne shiyasa aka dawo da ita."

"Eyya sannu my Ƙanwa, Allah ya ƙara lafiya."

"Amin yaya Sadiq, ai na ji sauƙi ma, ka bani Aron wayanka in kira su Inna."

"Dama kina neman wayan ne ba ki tambaye Ni ba? Tashi ki dauko nawa yana nan a ɗaki na na manta da ita a can, ki dauko ki yi wayan."

      
"To Momy." Ta amsa mata cikin zumuɗi tana mike wa

Tare da Sadiq suka nufi upstairs ɗin, shi ya wuce dakin sa ita kuma ta shiga dakin Momy ta dauko wayan ta dawo, kasancewar ta riƙe numban Innar su since most of the time ita take amfani da wayan ma, shiyasa layin ta kaɗai ta iya riƙe wa a kanta, da sauri ta saka ta danna mata kira, babu jima wa kuwa ta ji sallaman Innar a cikin kunnen ta, cikin farin ciki ta amsa mata tana kiran sunan ta

Daga can Inna, wacce ta tabbatar da muryan Maryamun, sai tace, "Auta ke ce?"

Kamar zata yi kuka tace, "eh Inna Ni ce, kin manta da Ni, ko kiran Dady ba kya yi bare ki ce ya bani?"

Innar Dariya ta ɗan yi, sai tace, "ashe har yanzu kina nan da shirmen ki? Ban da abun ki wacce uwa ce zata manta ƴarta? Kina nan a raina."

Hakan ne yasa Maryamu farin ciki, tace, "to Inna ya su Bintu da Umma?"

"Suna nan lafiya, yanzu Bintu ta fita zuwa gidan Indo, ita kuma Umma tana waje, bari in kira miki ita."
Mike wa Inna tayi ta fita ta kai mata wayan

Hakan ne yasa Maryamu ta jiyo muryan Umman tana kiran sunanta da faɗin, "mutanen Kano Meramun Inna."

"Ina wuni Umma?"

"Lafiya lau Maryamu, ya mutanen gidan ya kuma Kanon?"

"Kowa lafiya Umma, ina su Baba?"

"Ai duk sun tafi wajen aiki, dama yau nake ta zicci-zicci muyi maganar da Innar ki, ta kira mu ji lafiyar ki, domin mun yi kewar ki ba kaɗan ba wlh, Allah yasa an dena rashin jin a can?"

Dariya Maryamu tayi tana tura baki tace, "Kai! Umma, ina ni ina rashin ji kuma? Bayan kin manta yanzu na girma? Ai na bar ma ƴan baya su Shatima."
Tana jiyo sautin dariyan su har Inna, tunda a handsfree wayan take dukka suna jin muryanta

Itama Momy da ke zaune tana sauraron Maryamun sai murmushi take yi, duk da ba ta jin me suke cewa su can,
Sai da ta ɗan jima tana wayan sannan tace mata, "itama ta bata su gaisa."
Hakan ne yasa ta miƙa mata wayan, Momy ta gaisa da su cike da mutunta juna,
Daga karshe sai ta mayar mata wayan suka ci gaba da yi

Da zata kashe wayan tace, "zata sake kira in Bintu ta dawo sai a bata su gaisa."
After ta tsinke wayan sai ta miƙa wa Momy

Momy tace, "ki bar ta a hannun ki zuwa anjiman sai ki kira ta."

Hakan ba ƙaramin dad'i ya yi wa Maryamu ba, tana ta jin dad'i.
***

         Lokacin sallan asar nayi, suka wuce yin Sallah, toilet ɗin ɗakinta Maryamu ta shiga domin yin alwala, har ta soma sai kuma ta ji motsi kamar an shigo ɗakin, shiyasa ta dakatar da alwalan ta fice, nan idanunta suka sauka kan SHAREEF yana bakin ƙofan ɗakin yana mata murmushi, gabanta ne ya faɗi da tunanin ko dai ya soma mata fatalwa ne? Hakan ne yasa ta mitstsike idanunta ta sake kallon wurin, still tana ganin sa a wurin, zuciyarta wani irin buga wa take yi musamman yanda ta ga ya nufo wurin ta a yanzu babu wannan murmushin a kan fuskarsa, sai ma ɗaure ta da yayi murtik kamar yanda ya saba mata; ya tafi kai tsaye wurin ta.
[09/02, 8:21 am] OumƊahirah نفيسة: 🌱🌱🌱🌱🌱

      *SHAREEF*
          _SexyBoy_
🌱🌱🌱🌱🌱


_Writer: Nafisat Isma'il Lawal_
_Wattpad: UmmuDahirah_

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝*



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

       *P.W.A✍️*





*DATA SHARE*

Call, message or whatsap  07065334256

*MTN*
500MB 150
1gb  280
2gb.  560 
3gb.   840
4gb.    1120
5gb      1400
6gb.     1700
Verlid for 30 days.












__________
*BOOK1*
_______________*FREE PAGE27*
_____Tsaya wa yayi a gabanta yana faman kallonta, yanda ya zuba mata kyawawan idanun nan nasa, shiyasa duk ta diririce zuciyarta sai buga wa take yi kamar zata fito a ƙirjinta, yayinda take jin wani irin sanyi na mamaye ta tun daga can ƙarƙashin ƙafafuwan ta har zuwa cikin jikinta, take tsigan jikinta ya soma tashi sai wani irin kasala da rashin ƙwarin jiki ya mamaye ta, ƙwaƙwalwanta ta gaza ɗaukar tunanin shin SHAREEF ne a gabanta ya zuba mata ido? Ko kuma wani ne daban?
Bata gama tantance abun da zuciyarta ke saƙa mata ba, sai gani tayi ya saka hannayensa biyu ya saƙalo da su ta bayanta, yayinda ya janyo ta jikinsa yana haɗa ta sosai da body ɗin sa, sai ya hura mata iska mai sanyi a kan idanunta,
Lokaci guda ta ƙifta su tana ware idon sosai a kansa

Murmushi yayi mata mai kashe jiki, sai ya matso da fuskarsa kusa da nata ya furta mata, "kina mamakin ganina ne?"
Bai bari tayi wani motsi ba sai ɗaukar ta yayi zuwa saman gadon tare da ɗaura ta a kai ya kwantar da ita flat, tamkar sokuwa haka kuwa ta biye mishi still idanunta a ƙafe a kansa ta dena motsi sai dai shi ya motsa ta, amma tana jin yanda bugun zuciyarta ke buga wa da ƙarfi da ƙarfi alamun tsoro da firgicin abun da ke faruwa yasa ta shiga wani irin yanayin da ta kasa kataɓus, kamar an hana ta motsa kowacce gaɓa na jikinta haka take ji, yayinda wani irin barci-barci ya soma ƙoƙarin lulluɓe mata ido, take a nan ta soma ganin ɗakin ya canza launi zuwa ja, sai kuma a hankali ya soma yin duhu ko'ina na ɗakin ya yi baƙi, fuskar SHAREEF kawai take iya hango wa yana mata wannan murmushin nasa mai ƙara masa kyawu da kamala,
Daga lokacin idanunta suka rufe komai na jikinta suka dena motsa wa, amma kuma tana jin sautin muryansa a kunnen ta yana faɗa mata

"Ke Matata ce, kina ganin ban san sirrin da ake ɓoye min bane? Daga yau zan riƙa zuwa ina amsar haƙƙi na a duk sanda na so, don haka ki shirya tarbar Angon ki a kowanne hali, ina farin cikin sanar miki da cewa daga yanzu zan mayar da ke cikakkiyar Mata ta, babu mahalukin da ya isa ya mallake ki face Ni kaɗai, Ni kaɗai ne mallakin ki."

Sai ta ji wani irin sautin dariya da ke fita bibbiyu a hankali daga cikin kunnen ta, duk yanda ta so ta motsa amma abun ya faskara, abun kamar a mafarki, kamar kuma a farke take jin komai, domin tana jin lokacin da yake zame mata kayanta amma ta kasa motsa wa, duk wani motsi nasa tana jin yanda yake shafa ta babu halin magana, idanunta ma sun ƙi buɗe wa,
Abun ya faru ne kamar ƙiftawar ido, daga nan bata sake sanin inda kanta yake ba domin ta kasa jure abun da ke gudana a cikin rayuwarta, wanda bata taɓa shirya wa zuwan sa ba, abun ya zo ne a cikin wani irin rikitaccen yanayi

Momy ce ta shigo ɗakin, abun mamakin sai ta ga Maryamu kwance a saman gado tana ta shirga barci, abun ya bata mamaki, daga ta je tayi sallah sai kuma ta koma barci? Anya yarinyar nan lafiyarta?
Sanin cewa barcin yamma bai da Amfani, shiyasa Momy ta soma tayar da ita, daƙyar ta samu ta soma buɗe idanunta, amma kuma wani irin sambatu take yi mara sa kan gado, hakan ne yasa Momy ta soma karanta mata addu'o'i tana tofa mata

A hankali kuma sai ta soma natsuwa ta dena motsawan da take yi, sai kuma can ta buɗe idanunta tana sauke su a kan Momy, zumɓur ta miƙe tana kallon jikinta cikin tsananin mamakin ganin ta ba kaya sai bargo da aka rufa mata

Ita kanta Momy sai yanzu ta kula da rashin kayan a jikinta, tunda bargon ya zame, da mamaki take kallonta tace, "Maryam, daga ki je ki yi sallah sai ki hau barci? Kuma barcin ma babu kaya?"

Shiru Maryamu tayi tana zazzare ido, sai kuma ta soma ƙoƙarin kama kanta sabida wani irin sara mata da yayi, ko kusa ba ta jin ƙarfi a jikinta tamkar an yi mata dukan tsiya haka take ji, zuciyarta wani irin ƙunci da zafi take jin kamar ana rura mata, ta kasa tuno abun da ke faruwa da ita, bata iya fahimtar komai ba, sai ma wani irin firgici da ya riske ta tamkar ba ta cikin hayyacin ta, lokaci ɗaya idanunta suka soma canza kala zuwa ja, har sun soma tara ruwan hawaye, sai wani irin juye-juye take yi kamar ba ta cikin tunanin ta

Hakan ne yasa Momy ta riƙe ta tana kiran sunan ta, amma yanda ta ga tana yi tamkar ba ta jinta, sai juya kai take yi tana sauke ajiyan zuciya kamar wacce tayi tseren gudu, duk yanayin ta ya gama canza wa gaba ɗaya, kamar ba ita ba,
Kiran sunan ta Momy take yi amma ta ƙi amsa mata, da ta fahimci ba ta cikin hayyacin ta, shiyasa ta kamo hannunta ta soma mata addu'o'i cikin matuƙar tausayin ta da al'ajabin abun da ke faruwa da ita yau ɗin 

Can sai ta ga tayi shiru ta dena motsa wa, kanta a saman pillow ta rufe idanunta, a hankali kuma ta buɗe su tana kallon Momyn tare da furta sunan ta

"Na'am, kin yi sallah kuwa?" Momyn ta amsa ta tana mata wannan tambayar, sabida ta kula cewa yarinyar ba ta cikin tunanin ta gaba daya, da alamun ko jikin nata ne ya sake motsa wa

Ita kuma Maryamu wacce ta tuna komai a yanzu, sai ta girgiza mata kai alamun a'a

"To tashi ki saka kayan ki kiyi sallah yanzu, ina jiran ki a falo ki zo yanzu akwai maganar da zamu yi."

Amsa mata tayi da to cike da sanyin jiki, don har yanzu ba ta jin ƙarfin jikinta. Da kallo ta bi bayan Momyn har ta fice, kana ta bi jikinta da ido tana tunanin abun da ke faruwa da ita? Anya ba mafarki take yi ba? SHAREEF ya shigo dakin nan kuma shi ya cire mata kayan ta. Shiru tayi tana tuna maganganun da yayi mata, lokaci ɗaya kuma sai ta saki murmushin farin ciki, idan da gaske ne kenan SHAREEF ya san cewa ita Matarsa ce? Yanzu yana sonta kenan? Shi ne ya zo amsar haƙƙin sa? Shi ya cire mata kayanta yayi wani abu da ita?
Wani ɓangare na zuciyarta ta kasa yarda cewa da gaske ne, mafarki ne kawai take yi, amma ba gaskiya bane, taya ya SHAREEF zai zo ɗakin ta ya faɗa mata waɗannan kalaman? Bayan ta san cewa Dady ya hana a sanar mishi da auren su? And sannan SHAREEF ya tsane ta, lokaci guda sai ya zo wurin ta har ya nemi haƙƙin sa?
Da sauri ta tashi tana duba jikinta, bata ga komai da zai nuna an yi mata wani abun ba, kaya kawai aka cire mata, kanta ya ɗaure ta rikice ta rasa wanne magana zata kama, idan SHAREEF bai zo ɗakin ta ba ya aka yi kayanta suka fita daga jikinta?

Ganin zata rikita kanta shiyasa tayi saurin cire tunanin tana mayar da kayanta, tare da shiga toilet ta ɗaura alwala shaf-shaf tayi sallan ta fita Falo,
Abun mamakin tana doso falon, da SHAREEF ta soma tozali, kuma exactly kayan jikinsa da shi ya zo mata cikin daki, amma kuma suna haɗa ido dashi sai ta ga ya ɗauke kai a kanta, ya ci gaba da latsa wayansa da ke hannunsa, ɗaya hannun kuma yana riƙe da juice cup

Momy na zaune itama a gefen sa tana duban TV, hannunta riƙe da remote da alamun tana canza channels ne,
Ganin Maryamun ta fito, shiyasa ta ajiye remote ɗin tana mayar da hankalin ta sosai a kanta,
"Zo nan."
Ta kira ta tare da nuna mata kusa da ita alamun ta zo ta zauna

Ɗago kai SHAREEF yayi yana duban Momyn, sai kuma ya kalli Maryamu da ke ƙoƙarin zuwa inda suke, tsaya wa yayi domin ya ga ikon Allah ina Momy take tunanin yarinyar zata zauna?
Kasancewar suna a kan two seater ne, kuma babu wani space sabida yanayin zaman da SHAREEF yayi duk ya cike wurin

Momy matsa wa tayi kaɗan ta nuna mata tsakiyar su tare da furta, "zauna a nan."

Kallon SHAREEF Maryamu tayi, shima ita yake kallo ya haɗe fuska babu ɗigon walwala a tare da shi, yanda yake bin ta da wani irin kallo shi ne dalilin da yasa ta kasa zama

"Zauna mana daughter, me kike jira?" Momy ta faɗa tana kallonta

"Mom, wai ina zata zauna? Ba dai a nan ba?"

"A nan zata zauna, wani abun ne?" Momyn ta ambaci hakan tana tsare sa da ido

Fuska ya turɓune cike da ƙulewa yace, "no ba dai kusa da Ni ba, taya wannan abar zata haɗa jiki dani? That will never happen."
Sai ya ja dogon tsaki yana miƙe wa tare da ajiye cup ɗin ya koma saman one seater

Daga Momy har Maryamu baki suka saki suna kallonsa, sai dai shi ko kallon inda suke bai yi ba, tuni ya mayar da hankalin sa a wayansa duk da har yanzu bai saki fuskarsa ba

Hannunta Maryamu; Momy ta kama tana zaunar da ita a gefen ta,
Sai kuma ta mayar da hankalin ta a kan SHAREEF ta kira sunan sa

Ɗago kai yayi ya zuba mata ido, sai dai bai amsa ba, ganin yanda ta kifa mishi waɗannan gulu-gulun eyes ɗin nan nata, hakan ne yasa ya ɗauke nasa idon yana tura baki

"SHAREEF meyasa ba a maka magana ɗaya ka bi; sai an ta nanata maka kamar ƙaramin Yaro?"

"Mom me nayi?"

"Uwaka kayi, wlh ka fita idona ka shiga taitayin ka tun kafin in ci maka mutunci, kuma ko ka ƙi ko ka so Maryamu ƙanwarka ce, duk kyaran da zaka nuna mata baka da yanda zaka yi da ita a gidan nan, kuma daga yau zan gargaɗe ka a kan kar ka ƙara wulaƙanta ta, tunda itama ƴar Adam ce kamar kowa, ba na son kana hantarar ta a gidan nan, muddin kuma ka ci gaba da yi, ranka zai yi mummunar ɓaci, this is the first and last worning da zan sake maimata maka magana a kanta; kana ji na?"

Shiru yayi ya kasa yin magana sabida wani irin haushi da ya turniƙe sa, bai iya cewa komai ba, sai ma ɗago kai da yayi ya yi musu duba ɗaya, sannan ya miƙe da zafin nama ya bar wurin ransa a ɓace

Har ya ƙule Maryamu ta kasa janye ido a kansa, sai yanzu ta tabbatar da cewa mafarki take yi abun da ya faru yau ba gaske ne ba, SHAREEF bazai taɓa sonta ba bare har ya tako ƙafafunsa zuwa ɗakin ta, amma meyasa take wannan tunanin haukan?...

"Maryam, kuka kike yi kuma?"

Ita kanta sai a lokacin ta san cewa hawaye na gudana a saman kuncin ta, tamkar Momy ta kunno ta ne, kawai ta fashe da kuka zuciyarta na mata zafi sosai da wani irin kunci da ya mamaye mata ilahirin maƙogwaron ta, har wani ɗaci take ji a saman harshen ta; haka yawun ta lokaci ɗaya ya ƙafe daga bakin ta. Duk yanda Momy ta rarrashe ta tayi shiru ta kasa, ƙarshe ma sai kwantar da kanta tayi a saman jikin Momyn tana ta shashsheƙa kamar ranta zai fita

"Wai Maryam ban son shashanci baza ki yi shiru ba? Kawai kin zauna kina kuka kamar wata ƙaramar yarinya, ki yi shiru ki faɗa min abun da ke damun ki."

Shiru tayi tana jan nimfarfashi, har yanzu hawayen idanunta sun kasa tsaya wa duk da haka, ita kanta ta kasa sanin dalilin kukan nata, amma yanda zuciyarta take mata ƙunci da baƙin ciki tana jin kukan shi ne salaman da zata ji

"To tunda baza ki faɗa min abun da ya saka ki kuka ba, tashi muyi magana."

Tashi zaune tayi sai dai kanta a ƙasa tana ci gaba da shashsheƙan kukan

Tsira mata idanu tayi na ɗan lokaci, sai tace, "Maryam kin taɓa yin aljanu ne a garin ku?"

Ɗago kai tayi tana kallon Momyn, sabida jin tambayar da ya zo mata a bazata, bata fahimci mai Momyn take nufi ba shi yasa tace, "aljanu kuma Momy?"

"Eh, abun da nake tambaya kenan."

"A'a Momy, Ni bani da komai wlh." Tayi maganar cike da shagwaɓa tana tura baki

Murmushi Momy tayi tace, "to ki dai dage da addu'a don ba na son kina wasa da azkar musamman in za ki kwanta, kin san yanzu miyagu sun yi yawa musanman yanzu da sanyi ya soma kaɗa wa."

Shiru tayi tana tunanin meyasa Momy tayi mata wannan tambayar?

"Kina jina ba ki ce komai ba?"

"To Momy."

"Yauwa, idan muna tare zamu riƙa karatu tare na littatafan addini, sannan kuma na san kina kuka ne a kan SHAREEF a game da abun da yake miki, kar in sake ganin kin zubar da hawayen ki a kan shi, yaushe ma kika san soyayya Maryam da za ki riƙa kuka a kan namiji? Ko kin fi son ya raina ki ne?"

Yanda Momyn tayi magana shiyasa Maryamu tayi dariya

"Au dariya kike min ko? To ki dena ɗaukar maganata da wasa, kar in sake ganin kin yi wa SHAREEF kuka a duk abun da yake miki, ki zama Jarumar Mace mai aji, Mace mara aji ita take yi wa namiji kuka, sannan SHAREEF naki ne babu wata Macen da zata iya ƙwace miki shi, lokaci kawai muke jira da zamu danƙa ki a hannunsa, amma tukunna, sai kin dena shiririta kin mayar da hankalin ki a kan karatun ki, ke ƙaramar yarinya ce, ki mayar da hankalin ki a kan karatun ki domin shi ne zai gyara miki goben ki, idan kika zama Mace mai ilmi da wayewa; gami da sanin addinin Islama tare da zamantakewar rayuwa, to kin gama samun komai a duniyar nan, bar ganin SHAREEF yana kallon ki a ƙasƙance, wata rana da kanshi zai so ki, da kanshi zai rika duƙa miki yana miki biyayya. namiji kamar raƙumi ne, duk ta inda kika ja sa nan zai bi, ki kasance mai juriya Maryam, idan har kina son Yayan ki SHAREEF; to, yaƙi za ki yi a kan abun da kike so, duk hanyar da kika san za ki bi domin ki mayar da kanki kalan Macen da yake so, ya dena kallon ki a ƴar ƙauye Bagidajiya, shi za ki bi, ina mai tabbatar miki da cewa SHAREEF zai dawo tafin hannun ki, domin babu mai raba ki dashi sai Allah, SHAREEF yana cikin zanen ƙaddaran ki ne, dole zai zauna da ke ko yana so ko ba ya so."

Sosai Maryamu ta natsu wuri ɗaya tana sauraron zantukan da Momy take mata, wasu tana fahimta; wasu kuma bata san me take nufi akai ba, amma haka tayi shiru tana jin ta har sanda ta gama mata maganganun, sai ta bata umarnin tashi su je kichen su ɗaura abinci

Tare suke yin komai, sabida Momy ba ta son ta barta ba ta aiki, dole ne ta koya duk wani abu na zaman rayuwar aure, kuma daga wannan lokacin ta dauki alwashin sai ta mayar da Maryamu Macen da SHAREEF zai so ta, sai ya dena mata kallon ƴar ƙauye ballagaza a idanunsa, domin ta rigada ta gama karantar SHAREEF tas, kuma ta san me yake nufi da Maryamu, amma zata koya mishi hankali ko don wulaƙancin da yake mata, sabida ta kula SHAREEF yana da hali na wulaƙanta na ƙasa dashi, musamman yanda yake ƙyamatar masu aikin gidan, tun farko SHAREEF ya tsani baƙauyen mutum da kuma rayuwar talauci; bare ya san cewa Maryamu daga can ƙauye ta fito, shiyasa tsanar nata ya ƙara tasiri a ransa, ko kusa ba ya son ya buɗe idanu ya ga yarinyar sabida ko bak'ar fuskarta ya kalla ƙara jin tsanarta yake yi a ransa, bare yanda Momy ta soma mishi faɗa sosai a kanta, a ganin sa tana son shiga tsakanin sa da iyayensa.







🔆🔆🔆🔆🔆🔆🔆🔆


_____ *AUSTRALIA*
         *SYDNEY*
Kasancewar yau basu da lectures na safe, shiyasa Haseena ta sha barcin ta ba tare da ta tashi ta nemi abin da zata saka a cikinta ba, musamman yanda ta ji daɗin jikinta kwata-kwata babu ciwon cikin da ke addabar ta tun maganin da Nana ta bata, in fact ma jinin gaba ɗaya neman sa tayi ta rasa

Ta sha barci har karfe sha biyu before ta tashi, wanka ta soma yi ta saka riga da wando masu taushi sannan ta fita kichen domin neman abin da zata saka a cikin ta, cuz sosai take jin yunwa,
Tana cikin dafa indomie sai ta ji ƙaran door bell daga waje, tayi mamakin jin ƙaran since ta san babu wanda take expecting gani, in fact ma har yanzu bata saba da kowa ba a ƙasar ita kaɗai take rayuwarta a ciki, sauke indomien tayi sabida ganin ya gama dafuwa, sai ta kashe wutan; ta nemi plate ta zuba indomien a ciki, har yanzu ana buga ƙofan shiyasa dole ta fita ta je ta buɗe

She was surprised to see Nana standing there smiling at her

"You didn't think to see me in your house, na zo duba jikin ki ne." Nanan ta furta still tana mata shu'umin murmushin nan nata

Dole Haseena ta ɗaura murmushin itama a kan fuskarta, sannan ta bata damar shigo wa ciki

Kai tsaye cikin gidan suka wuce zuwa Falo; kujera Nana ta nufa ta zauna, tana ƙare wa falon kallo tana faman hura iska a bakin ta

Ita kuma Haseena wurin fridge ta nufa ta dauko mata kwalin juice tare da cup, ta kawo mata ta ajiye a saman Centre table; tare da mata bismillah

Murmushi tayi mata tace, "no kar ki damu, bazan sha komai ba, I just came to check on your body since we don't have lectures until the evening, that's why I asked to come and check on you, ina fatan jikin da sauƙi?" Ta ƙare maganar tana kallon ta daga sama har ƙasa kamar zata cinye ta

While Haseena murmusawa tayi tace, "jiki alhamdulillah, I really enjoyed the help you gave me, I will thank you even more. Thank you so much."

"No.. No don't worry, I didn't do it for you to thank me, since we are together."

"However, I have to show you my happiness, and even you came home to see me, I didn't expect that from you." Haseena ta furta cikin jin dad'i, sai kuma ta mike tace mata, "tana zuwa."
Kai tsaye kichen ta nufa ta dauko plate ɗin indomien, ta zo ta ajiye a saman Centre table ɗin tana zama tare da kallon Nanan tace, "Please eat this food, it will make me happy, kar kuma kin zo gidana ba ki ci komai ba."

Ɗage kafaɗa tayi ta furta, "why not? I will eat, but let's eat together since I know don ke kika yi, I hope we are friends now?"
Ta miƙa mata hannu tana smile

Hannun itama Haseena ta saka a nata tace, "yeah."
Kafin ma ta cire hannun sai da ta ji wani irin yanayi mai kama da kamar an soka mata wani mashi a zuciya, kanta kuma ya sara mata, nan take ta zame hannunta tana riƙe kan

Ita kuma Nana sai murmushi take mata irin na farin cikin nan, tana kallon yanayin da Haseenan ta shiga a lokaci ɗaya, amma bata ce mata komai ba sai kallonta da take yi har ta soma dawowa hayyacin ta, "are you Okey?"

"Yeah I'm okay." Tayi maganar tana ɗan ƙanƙame jikinta kamar wata mai jin sanyi, har idanunta sun soma canza kala

"Ok eat."
Nana tayi maganar tana ɗaukan spoon ta soma cakalan indomien tana kaiwa bakin ta

Hakan ne yasa itama Haseena ta soma cin nata tana tura wa a baki, sai dai duk yanayin ta ya sauya nan take, idanunta sun sake kaɗa wa sun yi jazur, abincin take ci amma kwata-kwata ba ta jin daɗin sabon yanayin da ke shiganta, daure wa kawai take yi tana tusa wa a cikin ta

Kasancewar Nana ta san halin da take ciki, shiyasa bata yi mata magana ba amma tana kula da all movement din ta, har suka gama cin abincin sannan ta kalle ta kamar bata kula da halin da take ciki ba, sai tace, "sister what happens?"

Ɗago kai Haseena tayi ta zuba mata ido, nan take sai wani abu tamkar walƙiya ya fito daga cikin idon Nana ya shige na Haseena, take a nan ta lumshe ido tana sake buɗe su a kanta, wani irin yanayi ta soma ji a game da Nanan, matsananciyar sha'awa ce ya taso mata tare da wani irin kasala, kallon Nanan take yi ta kasa ɗauke ido a kanta, because she doesn't feel anyone's need, except Nana's, musamman yanda take hango laps ɗin ta dukka a waje, haka ma her boobs that she can see from the small shirt she wears. Tana lumshe idanun tana buɗe su a kanta

Miƙe wa Nana tayi ta dauki plate ɗin, ta juya tana kaɗa mazaunai ta nufi cikin kichen domin ta ajiye plate ɗin

Haseena kuwa riƙe cikinta tayi tana dafe dai-dai maranta sabida wani irin murɗa mata da yayi, ɗaura kanta tayi a saman cinyarta ta ƙanƙame jikinta tana jin tamkar ta mutu don wutar sha'awar da ke taso mata, baƙin cikin ta ma yanda take jin a ranta Nana kawai take son ta ji ta a jikinta, daure wa kawai take yi amma hakan ya cutura, daƙyar ta miƙe ta nufi bedroom ɗin ta, a haukace ta faɗa ciki ta soma neman wayanta, a kan gado ta hange ta shiyasa ta nufa da sauri ta zauna tana ɗaukar wayan, hannunta ɗaya kuma dafe da maranta, ta rasa wanda zata kira ya taimake ta, sai kuma da sauri jikinta na rawa ta soma neman layin SHAREEF, sai dai kuma wani irin murɗa wa da cikin ta yayi; take ta jefar da wayan tana murƙususu, ta zamo ƙasa tana faman fitar da nishin azaba, kasa jure wa tayi sai kuma ta tashi tana rarrafa wa ta nufi falon, ai kuwa tana hango Nana zaune a saman kujerar, a haukace ta nufe ta ta faɗa kanta cikin fitan hayyaci ba tare da ta san me take ƙoƙarin aikata wa ba, burin ta kawai ta samu sauƙi daga azaban wutan sha'awar da ya turniƙe ta, ji take yi idan bata biya wa kanta bukata ba komai zai iya faruwa, tana jin mutuwa zata yi,
Ƙoƙarin cire mata riga take yi amma sai ta fashe da kuka saboda gani take yi kamar ba ta sauri, domin yanda hannunta ke rawa ta kasa taɓuka komai

Nana kuwa ganin yanda ta samu wannan babbar daman, haƙan ta ya cimma ruwa, take a nan ta ƙanƙame Haseenan a jikinta tana zira harshen ta cikin bakin ta,
Nan ta cafke kuwa suka soma tsotson juna a haukace musamman Haseena tamkar zata cinye ta, don yanda take rawan jiki burin ta kawai ta samu biyan buƙatar ta

Ganin haka yasa Nana ta janye bakinta tana kallon fuskarta da murmushi, riƙe hannunta tayi tana cewa, "Babe are you Okey?"

Wani kukan Haseena ta saka mata tana cewa, "help me please, zan mutu ki taimaka min."

Dariya Nana tayi tana miƙe wa zaune tare da janye Haseenan tace, "ok, wait, I don't know what you need from me? Can you tell me?"

Bata san ya zata iya mata bayani ba, amma gani take yi kamar zata ɓata mata lokaci, idanun Haseena sun rufe kawai kokari take yi ta afka mata ko ta halin ƙa-ƙa, burin ta ta samu biyan buƙata, sai dai ba ƙarfin su ɗaya ba, cak Nana ta ɗauki Haseena suka wuce cikin bedroom, domin gani take yi idan bata taimaka mata ba zata iya mutuwa tunda ta kai maƙura a halin da take ciki, ita kuma ba haka take so ba.
[11/02, 7:36 pm] OumƊahirah نفيسة: 🌱🌱🌱🌱🌱

      *SHAREEF*
          _SexyBoy_
🌱🌱🌱🌱🌱


_Writer: Nafisat Isma'il Lawal_
_Wattpad: UmmuDahirah_

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝*



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

       *P.W.A✍️*





*DATA SHARE*

Call, message or whatsap  07065334256

*MTN*
500MB 150
1gb  280
2gb.  560 
3gb.   840
4gb.    1120
5gb      1400
6gb.     1700
Verlid for 30 days.










__________
*BOOK1*
_______________*FREE PAGE28*
_____ *NIGERIA*
            *KANO STATE*
Bell ɗin da aka buga, shiyasa ɗaliban makarantar suka dinga fitowa kowa yana nufan hanyar gate cike da farin ciki

Amina, Feena da Maryamu suka fito a jere suka nufi bakin gate ɗin,
Bayan sun fita bakin gate babu wanda aka zo ɗauka a cikin su, shiyasa suka ja gefe suka tsaya suna ɗan taɓa hira, duk da hiran daga Amina sai Feena suke yin ta, Maryamu kuma na sauraron su tana baza idanu a kan hanya don ta ga ta'inda Motan SHAREEF zai zo ɗaukar ta, domin ta fi saka ran ganin sa since shi ya zo ya ɗauke ta ranan farko

Feena ce ta taɓo ta tana ce mata, "wai Ni kam Maryamu in tambaye ki?"

Dawo da idanunta tayi a kanta, sai ta gyaɗa mata kai alamun tana sauraren ta

"Ɗazu na ga kamar Sadiq ne ya kawo ki school ɗin nan, right?"

"Eh, kin sanshi ne?"

Dariya tayi tace, "haba, wlh na ga kamar ta ɓaci, Ni dai kamar shi na hango a cikin Motan. Na san shi mana, anguwan mu ɗaya dashi fa, and kuma Dad ɗin sa Abokin Abbana ne."

Ɗan washe baki Maryamu tayi jin abun da Feena take faɗa; sai tace, "ashe ke ma a anguwar mu kike?"

"Eh a nan nake, tazaran gidan mu da gidan su ba wani mai nisa bane, mu muna layin farko ne, su kuma na biyu, amma ban taɓa sanin ki a gidan ba; because a baya ina zuwa kafin karatu yayi zafi na dena samun time. But Momy tana yawan zuwa mana."

Maryamu tace, "nima ba a gidan nake ba, ban jima da zuwa ba, Ni ƴar Zaria ce, da Dadyn su Yaya Sadiq da Innata brother and sister ne."

Dariya suka yi, sai Feena tace, "wow! Amma duk da haka kuna yanayi da Sadiq wlh, yanda kike da manyan idanu haka shima, wani in ya ganku zai ce ƙanwarsa ce ta jini, duk da dai dama akwai jinin ƴan uwantaka."

Murmushi kawai Maryamu tayi bata ce komai ba, duk da a ranta ta ji dadin ce mata da aka yi suna kama da Sadiq ɗin 

Amina tace, "Friends bari in wuce, ga driver na nan ya zo, but I am glad to hear that you are the same the village, wata rana idan na kawo miki ziyara sai ki raka Ni gidan su Maryamu ko?"

"Kar ki damu ƙawalli, ai har sai kin gaji da zuwa ma, duk sanda za ki zo tare zamu kai mata ziyara in har tana so?"
Feena ta ƙare maganar tana ƴar murmusawa da kallon Maryamu

Ita kuma tace, "mai zai hana? Zan yi farin ciki da hakan."

"Ok na tafi, kar ya gaji da jira na, sai tomorrow."
Ta ɗaga musu hannu ta wuce wurin Motan

Yayinda su kuma suka ci gaba da tsayuwa a wurin har an watse amma ba a zo ɗaukar su ba

Feena tace, "anya baza mu samu abun hawa mu wuce ba since duk wuri ɗaya zamu tafi, hakan zai fi ko?"

Maryamu da ba ta son tafiyan, sai ta girgiza kai tace, "a'a mu ƙara jira, Ni dai na san za a zo ɗaukana, kuma idan ya ga babu Ni ransa zai ɓaci."

Dariya ta ɗan yi, tace, "Sadiq kike nufi?"

"No, Yaya SHAREEF."

In surprise Feena tace, "haba, shi yake zuwa daukar ki?"

Jinjina mata kai tayi tana bin Motan da ta zo ta faka a gefen su

Hakan ne yasa Feena bata ce komai ba sai ta kalli Motan tana cewa, "yauwa ga Yayana nima ya zo, ki zo mu je sai ya sauke ki a gida tunda duk anguwa ɗaya muke, kar mu tafi mu bar ki a nan."

"A'a, ki tafi kawai, zan jira."

"To Shikenan, tunda ba kya son taimakon nawa, bye sai gobe." Ta furta tana mata murmushi

Itama murmushin tayi mata tare da ɗaga mata hannu, sai ta sake gyara tsayuwa a wurin tana kallon hanya

Wurin Motan Feena ta nufa, ta buɗe ɗaya side din ta shige, fuskarta yalwace da murmushi tace, "Yaya Hunaip, I didn't think you would come and take me, ashe da gaske kake yi?"

Murmushi yayi mata, yana ɗan duba agogon sa tare da furta, "dole na ne ai, duk da ina da wurin zuwa but ɗauko ki ya fi min komai muhimmanci."
Sai ya ɗan ɗaga kansa yana duban wurin da Maryamu ke tsaye sai baza manyan idanunta take yi tana kalle-kalle, a natse ya furta, "wancan fa?"

Wurin da yake kallo ta bi da kallo, sai tace, "oh! Maryamu, tana jiran Yayanta ne itama ya zo ya dauke ta."

Tsira mata ido ya ɗan yi, sai kuma ya dubi Feena yace, "but time ya wuce sosai, baza mu iya ɗaukar ta bane; in bata da nisa?"

Jin hakan ne yasa Feena shiga farin ciki, don ta san halin Yayan nata zai yi wuya ya kula ta ma, amma abun mamakin da kansa ya nemi rage mata hanya, shiyasa cikin farin cikin jin hakan tace, "Yaya Hunaip, ai gidan su Dadyn SHAREEF take, sister ɗin su ne ita."

Ɗan waro ido yayi tare da furta, "serious Auta?"

"Allah kuwa Yaya."

"Ok, ki kira ta tazo mu wuce."

Fita Feena tayi tana ajiye Jakarta, sai ta nufi wurin Maryamu tace, "friend, ki zo mu je, Yayana ya ce ki zo mu ajiye ki a gida, kinga time ya ƙure har six ta kusa, dare zai yi miki a nan in har kika zauna, maybe wani abun ya tsayar dashi bai samu damar zuwa ba, but tunda duk wuri ɗaya zamu je why not ki biyo mu."

Ita kanta Maryamun tana tunanin bazai zo ɗaukar ta ba, maganar Feenan akwai ƙamshin gaskiya, shiyasa ta gyaɗa kanta ta bi bayanta zuwa wurin motan

Da kanta Feena ta buɗe mota back sit ta shiga, sannan ta rufe itama ta shiga gaba

Maryamu na daidaita zamanta a kan kujerar, ɗago kan da zata yi suka haɗa ido da Hunaip da ke faman kallonta ta cikin mirror, kallon kallo suka yi wa juna, before ita ta dauke kanta tana mayar da hankalin ta a kallon hanya

Shi kuma mamakin yanda suka haɗa ido da ita har ta kalle shi, sannan ta ɗauke kai a kansa yake yi, at least ko gaisuwa ya kamata tayi masa since taimakon ta suka yi ai.






🔆🔆🔆🔆🔆🔆🔆🔆


_____Slowly ya cusa hancin Motan cikin gidan har zuwa packing space, dakatar wa yayi tare da kashe Motan yana ɗan jan huci kaɗan, kallon kansa yayi a mirror yana ganin yanda tulin gashin gaban kansa ya cukurkuɗe tamkar babu gyara, shi kansa ya manta rabon da ya je ya gyara gashin bare har yayi aski ya rage tsawon sa, sabida aiki da yayi masa yawa a ɗan kwanakin, ga rashin jin dad'in jikinsa da yau yake jin cikin sa yana ɗan takura masa da ciwo, musamman gefen cikin sa, duk wani abu da yake yi duk na karfin hali ne, amma har ga Allah a ɗan kwana biyun nan ba daɗin jikinsa yake ji ba, kuma ba ya son zuwa asibiti bare ya nuna alamar da ƴan gidan su zasu gane, ya san dole Dady zai matsa mishi zuwa ganin Likita. Ɗan yatsina fuskarsa yayi yana hura hanci kaɗan, sai ya saka hannu ya gyara gashin sa yana ɗan kwantar wa tare da shafa saman sajen sa har zuwa gemun sa da ya ƙara tsawo sosai a yanzu. Numfashi ya ja ya buɗe ƙofan yana ɗaukar jakarsa tare da fito wa, rufe ƙofan yayi ya nufi hanyar shiga ƙofan gidan cike da takun ƙasaita; yana yi yana kwaɓe fuska kamar ya ga kashi, tura ƙofan yayi da sallama a bakin sa

Dady da ke zaune a saman one seater, Yana sanye cikin shuɗiyar Jallabiya ƴar Dubai, ya ɗaura ƙafafunsa a saman Centre table yana karatun Jarida, idanunsa sanye da medical glasses. Ɗago kai yayi yana duban SHAREEF wanda ya shigo ciki a yanƙwane kamar zai zube tsaban yanda yake tafiyan, amsa masa sallaman yayi yana masa murmushi, sai da ya ga ya iso daidai wurin sa yake cewa, "oh! Ka ga ragwon my Son, duk wannan tafiyar don ka nuna mana ka gaji ne?"

Yatsina fuska yayi yana zama a saman two seater wanda yake facing Dady, sai yace, "Dady baka san ya nake ji bane, but ina shan gwale-gwale everything is too much for me, things are starting to be too much for me, wlh na ƙosa Hanif ya dawo."

Dariyan da Dady yake yi, shi ya fito da Momy daga kichen riƙe da bowl ta zuba fruits a ciki, sai tace, "dariyan me kake yi ne haka Alhaji?"

"Ni da my Son ne, ya zama ragwo yanzu, I see his efforts but now he is showing me his failure, ki ce ko aure ma yayi zai riƙa nuna wa Matar tasa ragwancin nasa."
Ya ƙare maganar yana ci gaba da dariyan sa

While Momy na taya sa, sai tace, "ban da abun ka, ai aiki daban riƙe Mata daban, i know ko Mata biyu aka hada wa SHAREEF zai iya riƙe su kuma a ga sauyi cikin one month ma, don haka Yarona ba daga nan ba, dole abun yayi masa yawa aikin Company guda ba wasa ba."

Ɗan janyo eyeglasses ɗin sa yayi zuwa saman hancin sa yana dalalo wa Momy idanunsa da fadin, "Oh! Yau kuma? Ke ce da kare SHAREEF?"

"To ai na ga kana nema ka mayar min da shi weak man ne, bayan na san Jarumin namiji ne ɗana. Amma tsaya muna magana ban ga Maryam ba? Ko baku dawo tare bane?"
Ta ƙare maganar tana kallon SHAREEF wanda ya rufe idanunsa yana faman cije laɓɓansa

Maganar Momyn ne yasa ya buɗe idanun, sanin da yayi da shi take yi

"Basu shigo tare ba, maybe bai ɗauko ta ba kenan?" Dady ya furta shima yana mayar da hankalin sa ga SHAREEF domin jin mai zai ce


"Wai SHAREEF ana magana, ina yarinyar nan? Kar dai a ce baka dauko ta daga school ba?" Momy ta ɗan yi maganar a zafafe sabida ganin yayi musu shiru yana tsilla ido

Shi wlh shaf ya manta da yarinyar, kuma ya ga jiya ba shi ya ɗauko ta ba shi yasa yau bai yi tunanin zuwa ba, in fact ma bai tuna da ita ba bare yayi tunanin zuwa school har ya dauko ta, since Dady yayi masa gargaɗin he will always come and pick her up.
"Mom wlh na manta."

Salati Momy ta saka tana tafa hannunta, "to hurry up and go get her tun kafin in saɓa maka wlh."

"Mom don Allah ki yi hakuri, wlh ba na jin daɗi, call Sadiq to pick her up since it was too late before I went."

Harara ta watsa mishi tace, "miƙo min wayar ka."

Miƙa mata yayi yana tura baki

Dady yace, "wato baka ji maganar da nayi maka ba? Na ce kullum kai zaka na zuwa ka dauko ta but ashe ta bayan kunnen ka ya bi ko?"

"Dad, the problem in my head is why I forgot, and today I passed five thirty before leaving the office, I forgot."

Girgiza kansa kawai Dady yayi yana mai ɗaukar jaridar shi da ya ajiye, sai kuma ya sake duban sa yace, "ya maganar wurin aikin? Ina fata komai normal?"

"No Dad, har yanzu dai kayan nan basu iso ba, i think akwai wata matsalar ne."

"Meyasa baka faɗa min ba? Ba yau ka ce za a kawo ba?"

"Eh Dady, but I don't know the problem, har yanzu kayan bai wuce Singapore ba."

Guntun tsaki Dady ya ja yana ajiye jaridar tare da furta, "But you should inform me of this important matter, amma ba wai ka bar maganar ba."
Wayansa ya ɗauka yana latsa wa

At that time, Momy finished talking to Sadiq, sai ta miƙa masa wayan tana cewa, "riƙe wayarka, and from today if you come back to this house without her; zaka ga mai zan maka."
Ta ja ƙwafa tare da ɗaukar wuƙa ta soma yanka fruits ɗin

Shi kuma SHAREEF miƙe wa yayi bai ce komai ba, ya nufi upstairs, yanayin da yake ciki ma bai sa ya damu da faɗan Momyn ba, tunda sosai yake jin ciwon na ƙara taso masa a yanzu, dauriya kawai yake yi

Tsayar dashi Dady yayi sabida ya gama wayan da yake yi, yana kallonsa yace, "kayan nan baza su samu ba sai zuwa three to four days, ina tunanin akwai matsala gaskiya." Yayi maganar cike da damuwa

Tsaya wa SHAREEF yayi a saman benen yana kallon Dady, sai kuma bai ce komai ba ya juya ya wuce zuwa dakin sa, since bazai iya jure tsayuwa ba, gwara ya je ya sha magani idan ya dawo sai su yi maganar.
  




🔆🔆🔆🔆🔆🔆🔆🔆


_____"Wai ƙawar taki ba ta magana ne? Since we started walking, she didn't say a word."

Dariya Feena tayi tace, "she talks a lot Yaya." Sai kuma ta ɗan juya tana kallon Maryamu tace, "friend, ga Yayana Hunaip, ba ku gaisa ba?"

Sai time ɗin itama ta tuna basu yi gaisuwa ba, sai tace, "ina yini?"

"Lafiya lau Friend, ai nayi tunanin laifi nayi baza a yi min sannu ba?"

Dukka murmushi suka yi sabida jin me yace,
Ita kuma sai ta ɗauke kanta daga kallon inda yake ganin suna haɗa ido dashi ta cikin mirror, ita abun da ke ranta ma ya fi damun ta, har ranta bata ji daɗin rashin zuwa ɗaukan ta ba, ta saka ran ganin SHAREEF amma kuma babu shi, maybe don an tilasta mishi ne shekaran jiya shiyasa ya zo, maybe kuma ba shi zai riƙa zuwa ya ɗauke ta ba.
Tunanin da ke ta faman yawo a cikin kwakwalwar ta kenan, har ma ba ta jin hiran da suke yi, sai da aka kawo ƙofar gidan su sannan ta jiyo sauti kamar na muryan Feena tana kiran sunan ta, firgigit tayi ta zuba musu ido

While su ma haka kallonta suke yi cike da mamakin ana ta magana amma ba ta ji

Feena tace, "friend ina ta magana ba ki ji ba? Kin faɗa dogon tunani. I hope kina lafiya?"

Gyaɗa kanta tayi, sai tayi duba ga inda suke, ganin ƙofar gate ɗin su ne yasa ta ajiye ɓoyayyen numfashi tana kallon su, "na gode."

Hunaip yace, "ba godiya tsakani, ki gaishe da mutanen gidan."

Kai ta gyaɗa mishi tana tura ƙofan ta buɗe, sai da ta fita sannan suka yi sallama da Feena ta rufe musu ƙofan, ta wuce bakin gate ɗin ta shige

Shi kuma ya ja Motan a hankali bayan ya ga shigewar ta, sai da ya juya kambun motan sannan yace, "na ga ƙawar taki kamar wani abun na damun ta? Ko haka take ba ta son magana?"

"I don't know Yaya, since nima jiya na fara sanin ta, ranan Monday ta fara zuwa but ban zo ba, amma ina tunanin rashin lafiyar da tayi ne har yanzu bata wartsake ba."

"Rashin lafiya? Kina nufin bata da lafiya?" Yayi maganar yana ɗan kallon fuskarta

"Eh, jiya mayar da ita gida aka yi ba ta jin dad'i, i think shi ne dalili."

Jinjina kansa yayi ba tare da yace uffan ba, yayinda yake ƙara tuna zanen fuskarta daga idanunsa, numfashi ya ja a ransa yace, "she's very beautiful, ta shiga raina".
[12/02, 9:13 am] OumƊahirah نفيسة: 🌱🌱🌱🌱🌱

      *SHAREEF*
          _SexyBoy_
🌱🌱🌱🌱🌱


_Writer: Nafisat Isma'il Lawal_
_Wattpad: UmmuDahirah_

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝*



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

       *P.W.A✍️*
*DATA SHARE*

Call, message or whatsap  07065334256

*MTN*
500MB 150
1gb  280
2gb.  560 
3gb.   840
4gb.    1120
5gb      1400
6gb.     1700
Verlid for 30 days.












__________
*BOOK1*
_______________*FREE PAGE29*
_____Suna nan zaune sai ga Maryamun ta shigo cikin falon da sallaman ta,
Amsa mata suka yi suna bin ta da kallo, 
Momy tace, "ina Sadiq ɗin? Ashe har ya ɗauko ki?"

Kwaɓe fuska tayi tana takowa wurin su tare da zame Jakar; take cewa, "a'a Momy, bai zo ba, na jira na jira but ban ga kowa ba."

"Bai zo ba? To wane ne ya ɗauko ki? Kar dai a ce da kanki kika dawo?"

"A'a Momy, wani ya ɗauko Ni, Yayan wata class mate dina, sun ce a nan suke shiyasa suka rage min hanya."

"Kawai ba ki san Mutum ba sai ki hau Motan sa Maryam? Duka-duka yaushe kika fara zuwa school ɗin da za ki yarda da wani?"

"Tunda ta dawo lafiya dai, a dena maganar Deeja, ki bar yarinya ta huta, maza tashi daughter ki je ɗaki ki cire kayan, time na sallah ma yayi, sai ki yi sallah kafin ki fito."
Dady ya furta yana mata murmushi

"To Dady."
Ta miƙe da Jakar nata a hannu ta wuce hanyar ɗakin ta

Ita kuma Momy sai tace, "bari in kira Sadiq sabida na san yanzu haka ya tafi ɗauko ta, since yace min yana kan hanya ne dama."

"Ok, gwara haka dai, ki kira sa, nima bari na je nayi alwala na wuce masjid."

A tare suka miƙe suka wuce upstairs ɗin,
Momy ɗakin ta ta tafi, ta kira Sadiq ta faɗa masa, "ya dawo kawai tunda Maryam tana gida."
Daga nan bayan ta ajiye wayan itama alwala tayi ta zo ta tayar da sallah.
***

_____Wasa-wasa SHAREEF tunda ya shige ɗaki basu ƙara jin ɗuriyar sa ba, ashe har masallaci bai je ba tunda cikin sa ya matsa mishi, kwanciya yayi tunda ya afa maganin ya kasa kataɓus, jikinsa sai rawan sanyi yake yi dole ya rufe kansa yana murƙususun ciwo

Dady ne da ya kula bai je sallah ba, after sun dawo yace, "Sadiq ya je ya duba sa a ɗaki."

Zuwan Sadiq sai ya ga halin da yake ciki, hankalin sa ya tashi ya nufi wurin sa yana faman kiran sunan sa

"Sadiq, I'm not feeling better, go and tell Daddy."

"Ok Yaya."
Ya amsa mishi cike da tausayin shi yana juya wa ya fita da sauri,
Kai tsaye Falo ya je ya sanar musu halin da ya ga SHAREEF

Sosai suka tashi hankalin su, da sauri suka taso a tare suka nufo dakin nasa

Maryamu na zaune bata tashi ba sabida tsoron ya hana ta shiga dakin sa, amma har ranta ta damu da jin cewa ba shi da lafiya ne, dama a ranta tana jin tamkar wani abun ne ya same sa, yanda zuciyarta ke beating kamar zai faso ƙirjin ta; ta kasa natsuwa ta ci abincin da ke gabanta

Tana nan zaune sai gani tayi an fito da SHAREEF ɗin, Dady da Sadiq sun riƙo sa

Take hawaye suka silmiyo mata a kan kuncin ta, da sauri ta tashi tana bin su da kallo ta kasa motsa wa, sai rawa da jikinta yake yi,
Ganin sun fita waje itama sai ta take musu baya da saurin ta, a gabanta aka saka shi a Mota tana tsaye kusa da Momy wacce take maganar zata bi su

But Dady ya hana ta, yace, "su zasu je asibitin, ta zauna a gida."

Dole ba don ta so ba ta haƙura, suna gani Motan ta fita before su koma ciki

Maryamu kasa cin abincin tayi tana zaune tana kallon Momy da ke ta faman zirga-zirga fuskarta ɗauke da matsananciyar damuwa

Sai daga baya ne itama ta kula da halin da take ciki, ta kalle ta cike da tausayin ta, sai ta nemi wuri ta zauna tana ce mata, "ci abincin ki Maryam, kar yayi sanyi."

"Momy bazan iya ci ba." Tayi maganar tana ƙoƙarin fashe wa da kuka

"Kar ki yi min kuka a nan, ki ɗauki abincin nan ki ci, SHAREEF babu abin da zai same shi zai warke insha Allahu."
Sai ta soma rarrashinta tana bata baki, daƙyar ta samu ta ƙara yin loma a cikin abincin, sannan tace, "su je suyi sallah, sai su yi masa addu'a Allah ya basa lafiya."

Jiki babu ƙwari Maryamu ta koma ɗakin ta, sai a lokacin wasu hawayen masu ɗumi suka soma sintiri a kan fuskarta, hannu ta sanya tana share wa before ta shiga toilet ta daura alwala, sallah tayi sannan ta yi wa SHAREEF ɗin addu'a, tana gama wa ta tashi ta koma Falo ta zauna

Lokacin ma Momy bata fito ba sai daga baya. haka suka zauna zugum duk da Momy tana gwada kiran numban Dady, but wayan tana ring bai ɗauka ba, zuwan sa ɗaki yin alwala a can ya bar wayan, sai daga baya ne dabaran kiran Sadiq ya faɗo mata, ta danna masa kira tana fatan a ce ya dauki wayan.
Ai kuwa bata daɗe tana ring ba ya ɗauka, hankali a tashe take tambayar sa jikin SHAREEF ɗin?

"Mom har yanzu dai duba sa ake yi, basu fito ba Likitocin."

"Ina Dadyn naku?"

"Ya shiga office din doctor ya kira sa."

"Ok, idan ya fito sai ka sake kira na."
Sai ta kashe wayan tana ajiye wa tare da kallon Maryamu, "Maryam ki je ki sake zuba abincin nan ki ci, sai ki je ki kwanta ki huta, kinga kin wuni a makaranta."

"A'a Momy, na ƙoshi, kuma ba na jin barci."

Shiru tayi bata sake ce mata komai ba, sai ta kunna musu TV ta kamo Sunna TV ana haska wa'azin Bin Usman. Kallon suke yi amma ba wai fahimtar me ake yi suke yi ba, daga ita Momyn har Maryamu

Kusan ƙarfe goma suna wurin amma har yanzu su Dady basu dawo ba, duk da Momy ta sake kira sun yi magana da Dady ya faɗa mata, "ba gado za a basu ba zasu dawo yanzu."

Lokacin Maryamu har ta soma gyangyaɗi sabida mugun barci take ji, amma ta hana kanta yi, da ta fara zata tashi ta mayar da idanunta a kan kallo

Cike da tausayin ta Momy take kallonta, don ta san ta damu sosai da SHAREEF ne, tana tausaya wa yarinyar, ƙarama da ita amma ta mace a soyayyar namiji, tayar da ita tayi tace, "ta je ta kwanta, sabida ya samu lafiya yanzu ma suna kan hanyar dawowa."

Jin wannan bayanin yasa hankalin Maryamu ya ɗan kwanta, har ta samu ƙwarin gwiwan zuwa ɗaki ta kwanta, tana shiga ta faɗa kan gadon sai barci babu ko addu'a, tunda barcin ne kaɗai a idanunta, burin ta kawai ta samu ta kwanta.
***



_____SHAREEF kuma an basa taimakon gaggawa ne, bayan Likitan ya gama duba sa sai ya fita ya bar Male Nurse a wurin sa after ya ba shi umarnin yin masa wasu allurai da aka kawo masa,
Sannan ya fita zuwa office din sa shi da Dady. A nan yayi masa bayanin, "kar ya damu, ciwon da yake fama dashi ne na ƙoda ya tashi masa, kuma gaskiya abun yana ɗan yin gaba ne ba kamar baya da suke tunanin idan yana shan maganin za a dace ba, don haka da yiwuwar kowanne lokaci za a iya buƙatar yin mishi aiki domin a canza mishi guda ɗaya, tunda ɗayan ya fi lalace wa da yawa, hakan ne yasa ciwon zai riƙa tashi masa at any time."

Dady yace, "ai babu zancen kwantar da hankali kenan, tunda ba ci gaba aka samu ba."

Murmushi Doctor yayi yace, "to ya zamu yi Alhaji, dole ku kwantar da hankalin ku tunda idan ku ka tayar da hankali, shi kansa mara lafiyar zai damu kuma hakan ya zo yayi effected din sa, don haka a yanzu dai baza mu rike ku a asibitin ba, zaku iya tafiya gida sai ya ci gaba da shan magungunan da muka rubuta mishi, one week sai ku dawo daga nan sai a yi maganar aikin, don shi zai fi gaskiya."

"Shikenan, na gode Doctor, ba damuwa, duk abun da ka ce haka zamu yi."
Ya miƙa masa hannu suka gaisa, sannan suka miƙe a tare suka fita suka wuce room ɗin da SHAREEF yake ciki

After an kawo maganin, sai suka riƙe shi suka fito da shi zuwa bakin Mota, duk da jikin nasa da ɗan sauki ba kamar yanda suka kawo shi ba, amma hakan bai sa Dady ya ƙyale shi ba sai da suka riƙe shi har ya shiga Mota,
Sadiq ya ja motar suka wuce gida

Lokacin da suka isa Momy tana nan zaune tana tsimayen su, tana jin ƙaran Mota ta fito da sauri ta nufi wurin su,
Time ɗin har sun fito cikin Motan, da sauri ta ƙarisa tana kallon SHAREEF ɗin har zuciyarta tayi sanyi ganin alamun da sauƙi jikin nasa,
Sai ta amshi maganin da ke hannun Sadiq tana masa sannu,
A haka suka ƙarisa ciki suka zauna a saman sofa

Dady yace, "ta samo masa abinci ya soma ci, sai ya sha waɗanda aka ce ya sha yanzu."

Mike wa tayi ta nufi kitchen ta ɗibo abinci, since ta kwashe komai na saman dining ɗin ta mayar can, a plate ta ɗibo mishi ta kawo, sannan ta ɗauko warm water ta ajiye masa

Dady da ke duban Sadiq, yace mishi, "Sadiq je ka ɗaki ka kwanta tunda dare yayi, ka ga gobe kana da school."

"Nima abun da na gani kenan, gaba ɗaya yau a school ya wuni, tashi Auta ka je ka kwanta."

Tunda shima yana jin barci bai yi gardama ba, sai da safe yayi musu tare da ƙara yin ma SHAREEF sannu da jiki, sannan ya wuce

Momy tace, "ka ci abincin mana ka zauna ka tasa a gaba, ya kamata ka ci kaima ka je ka kwanta ko?"

A hankali ya sanya hannu ya dauki spoon ɗin yana ɗibo abincin, daure wa kawai yake yi sabida yanda ya ga sun damu dashi suna ta lallaɓa shi, haka ya ci abincin kaɗan sannan ya sha maganin,
Har ɗaki suka raka sa; sai da ya kwanta sannan suma suka je suka kwanta.
***

_____Can cikin dare Maryamu na cikin barci ta ji kamar Mutum a jikinta, duk yanda ta so tayi barcinta ta manta da yanda take jin motsin, but ta gaza, saboda yanda ake taɓa mata wasu sassa na jikinta ana mata wani irin wasa da ta kasa jure wa, dole ta buɗe lumsassun idanuwanta masu cike da barci, a hankali take buɗe su har ta ware su a saman fuskar SHAREEF da hasken wata ya haska mata shi, mamaki ne ya kama ta duk da wani irin barci ne ke fizgar ta a lokacin, amma hakan bai sa ta ƙi wartsake idanunta ba; nan take ta sake ƙura masa ido zahiri dai take gani, wani irin doka wa zuciyarta tayi sabida jin ya kai kansa saman ƙirjinta ya manna a wurin, take ta buɗe baki da nufin yin ihu, amma sai ta ji gum ya rufe mata bakin yana ɗago kansa tare da zuba mata jajayen idanunsa da suka ƙara girma suka yi wani irin kala da su,
Mutsu-mutsu ta soma yi tana ƙoƙarin kwace jikinta, domin sai a lokacin ta gama fahimtar babu kaya a jikinta, haka shima, suna cikin blanket ya rufe su,
Duk yanda ta so ta motsa ta ƙwace jikinta ta kasa,
Sai kawai tayi shiru tana jan numfashi yayinda zuciyarta take beating kamar zata faso ƙirjin ta

"Kar ki hana Ni abun da zuciyata take so, na san kina so na da yawa baza ki so na mutu a irin wannan halin da nake ciki ba, Ni Mijinki ne ba ki da hurumin hana Ni kanki, ki bar Ni in yi yanda nake so da ke, idan kina hana Ni kanki mutuwa zan yi, ko kina so in mutu?"

Gum tayi masa sai zuciyarta da ke ci gaba da buga wa, ita har yanzu ganin abun take yi kamar a mafarki, tabbas mafarki take yi SHAREEF bazai zo wurin ta da wannan buƙatar ba

Kamar ya san me take magana a zuciya, sai ya haɗa bakinsa da kunnen ta, tare da furta mata, "na san me kike tunani, ba mafarki bane, zahiri ne, don haka in har kina son in so ki; sai kin taimake ni, ba na son kina min musu, ke Matata ce."
Yana gama furta wa ya haɗe bakin su wuri ɗaya

Abu kamar wasa Maryamu ta kasa gane kanta, ta kasa hana sa abun da yake mata, in fact ma daga lokacin tamkar bata san me ke faruwa ba, idanunta a rufe suke tana jin duk abun da yake yi da ita amma ta kasa motsa wa bare ta hana shi, kuma ta kasa yin kuka, komai yana wakana ne kamar a mafarki, daga baya ma ta dena gane komai bata sake sanin inda take ba sai da gari yayi haske sosai, bata farka ba sai da Momy ta zo ta tashe ta, sannan ta tashi ta ganta babu kaya a jikinta, take komai abun da ya wakana jiya ya dawo mata fil, zahiri ta yarda cewan ba mafarki bane, SHAREEF ne yake bibiyan ta, a fili ta furta, "kenan ya san cewa ita Matarsa ce har yana bibiyan haƙƙin sa?" Maimakon ta ji haushin abun, sai ma farin ciki da ya kama ta, tabbas tana ganin cewa wata rana dole SHAREEF ya ƙaunace ta, tunda har yana iya biyo ta ɗakin ta domin amsar wani abu daga wurin ta, ta tashi da fargaba amma sai ta ji wasai a zuciyarta, tare da jin farin ciki har cikin ƙasan zuciyarta

Da sauri tayi wanka ta shirya sabida tunanin cewa SHAREEF ya ji sauƙi an dawo dashi gida jiya, ta ƙosa tayi tozali dashi,
Koda ta fita falo babu shi, har suka gama breakfast ita da Sadiq zasu tafi amma bata ga SHAREEF ba, shiyasa ta tambayi Momy tace, "Momy ko in je in duba Yaya SHAREEF ne?"

Murmushi Momy tayi tace, "har kin san cewa ya dawo ne ashe? Kin damu da wannan Mijin naki, maza tashi ki je ki gaishe shi sai ku wuce, kin ga time ya kusa ƙure wa za ku yi late."

Farin ciki ne ya cika ta, jiki na rawa ta nufi benen zata haye

Momy ta ɗaga murya tana cewa, "ki yi a hankali don Allah, ba na son wannan rawan jikin naki."

Tana jin Sadiq yana mata dariya, amma bata juya ba sai da ta ganta a bakin ƙofan ɗakin nasa, sannan ta saki ajiyar zuciya tana tunanin wanne abun zata tarar? Har a ranta tana jin tsoron shiga, amma kuma tuna abun da ya faru daren jiya, sai hakan ya bata ƙwarin gwiwa tana murmusawa tare da buɗe ƙofan ta shige ciki

SHAREEF na zaune a saman gadon sa yana tsane jikinsa, cuz fitowar sa kenan daga wanka, yayi domin ya samu ƙwarin jikinsa, duk da Momy ta takura masa ya fito yayi breakfast sai ya sha maganin sa. Yana jin motsi kamar an shigo masa part ɗin, amma ya ji shiru ba a yi magana ba, hakan ne yasa a hankali ya lallaɓa ya miƙe yana nufan ƙaramin falon nasa

Lokacin Maryamu tana tsaye ta kasa shigowa ciki sosai saboda ganin babu kowa, kuma ta ƙi magana sai kallon tsarin falon take yi tana buɗe ƙofofin hancin ta tare da shaƙar ƙamshin SHAREEF da ke ratsa mata har cikin ƙwanya, wani irin daɗi na ratsa ta, har wani lumshe idanu take yi tsaban farin ciki

"Kee."

Muryan SHAREEF ɗin ne ya dawo da ita hayyacinta, firgigit ta dawo da kallonta gare shi, yanda ya tsare ta da kallo babu kaya a jikinsa, da sauri ta kawar da kanta sabida wani irin yanayi da ya riske ta, wani yawu ne mai ƙauri ta haɗiye yayinda ta kasa furta ko kalma ɗaya

"Me ya kawo ki nan? Kin tsaya kamar wata munafuka; ban miki gargaɗin shigo min ɗaki ba? I don't like to see this black face. get out."
Ya daka mata tsawa muryansa alamun a ɓace 

Hakan ne yasa ta ɗago manyan idanunta ta zuba mishi, maimakon ta fita kamar yanda yace, sai kawai ta saki wani murmushi wanda sai da dimples ɗin ta suka fito sosai, ya ƙayata kyakkyawar fuskarta, ba komai ne yasa ta yin murmushin ba, sai tuna kamar ba shi ne jiya ya zo wurin ta da buƙatar sa ba, amma yanzu kuma yana ɗaure mata fuska, hakan ne ya bata dariya har ta murmusa tana sake bin jikinsa da kallo kamar zata haɗiye shi

Hakan ne ya fusata SHAREEF, tare da mamakin ganin yanda ta kifa masa manyan idanun nan nata kamar wata mayya kuma tana masa dariya, takowa yayi ya nufo inda take,
Kafin ya ƙariso har ta ruga zata fice cikin ɗakin, amma sai yayi caraf ya cafke ta yana mayar da ƙofan ya rufe, "ke kina da hankali da za ki shigo har ɗaki na kina min dariya? Mene kika gani a jikina da ya ba ki dariyan? Oya tell me ko in kakkarya ki."

"Wlh babu komai Yaya SHAREEF, ba da kai nake yi ba, wani abu na tuna."
Ta furta tana runtse idanunta ganin tayi kusa dashi wadda yasa ta kasa kallonsa

Tura ta yayi yana yatsina fuska, tare da furta, "shashshan banza, fitan min a daki ko in ci ubanki, idan kika sake gigin shigo min ɗaki a karo na uku, sai na canza wa mumun fuskar nan taki kamanni, Oya tashi ki fita mana."

Tashi tayi tana fice wa da sauri kamar ana hankaɗa ta, sai da ta fita sannan ta sauke ajiyar zuciyar tsoro, dantsen hannunta ta kama tana shafa wa, dai-dai wurin da ya kama mata, yayinda take jin wani sanyi da farin ciki a zuciyarta, komai nasa abun kyau ne, kwata-kwata ba ta jin haushin abun da yake mata, a fili ta furta, "ina sonka wlh, koda yanka Ni kake yi haka nan zan jure, domin in rayu da kai, kai kaɗai ne farin cikina a yanzu, Allah zan iya bada raina sabida kai."
Sai ga tagwayen hawaye sun fito daga idanunta sun sauka a saman kuncin ta,
Jin motsi kamar ana taho wa, shiyasa tayi saurin share hawayen; ta nufi hanyar downstairs da saurin ta; tana kaɗa kanta.
[13/02, 10:12 am] OumƊahirah نفيسة: 🌱🌱🌱🌱🌱

      *SHAREEF*
          _SexyBoy_
🌱🌱🌱🌱🌱


_Writer: Nafisat Isma'il Lawal_
_Wattpad: UmmuDahirah_

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝*



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

       *P.W.A✍️*





*DATA SHARE*

Call, message or whatsap  07065334256

*MTN*
500MB 150
1gb  280
2gb.  560 
3gb.   840
4gb.    1120
5gb      1400
6gb.     1700
Verlid for 30 days.












__________
*BOOK1*
_______________*FREE PAGE30*
_____Yau ma bayan an tashi daga school, Feena tace ma Maryamu, "ta zo su ajiye ta a hanya."

Sai tace, "a'a baza ta bi su ba, ta san za a zo ɗaukar ta."

Duk yanda Feena ta so ta biyo su but ta ƙi, sai da ta wuce ta shiga Motan, Hunaip ya tambaye ta; take sanar mishi yanda suka yi

Shi da kansa ya sauka ya ƙarisa wurin ta, ya tsaya yana kallonta fuskarsa ɗauke da murmushi yace, "haba friend, ya za a yi mu tafi mu bar ki a nan bayan ba a zo ɗaukar ki ba? Ki zo mu sauke ki tunda mu ba baƙi bane a wurin ki."

Ɗago kai tayi ta ɗan kalle sa kaɗan tana dauke idanunta a kansa, sai ta haɗe fuska da cewa, "gaskiya bazan bi ku ba tunda jiya an min faɗa, ku tafi kawai za a zo ɗauka ta, Momy sai da tayi min gargaɗi za a aiko driver."

Murmushi yayi jin zancen nata, yana ɗan shafa gemun sa a yanzu yake kallonta cike da burge wa, komai nata mai kyau ne har yanda take maganar tana yatsina fuska alamun tsiwa a tattare da ita, tsab ya ƙare wa halittar ta kallo yana jin a ransa gaskiya ya samu Mata, yarinyar tayi masa duk da ƙarama ce sosai, amma har a ransa ta kwanta masa, shiyasa ya ɗan ƙara kwantar da murya tare da furta, "don Allah kar ki yi min katanga ga hana Ni taimakon tsaleliyar budurwa kamar ki, haba taya ma zan bar ki a nan wurin in tafi? Please ki taimaka ki biyo mu tunda har yanzu drivern bai ƙariso ba, Ni zan shiga da kaina in yi wa Momyn bayani tunda na san bata fahimci motan da kika hau bane."

Yanda yake mata maganar raɗa-raɗa cikin kwantar da murya, da kuma jin abun da yace, shiyasa ta sake kallonsa kaɗan tana dauke idonta, ba wai don ta yarda da maganar nasa bane, sai don ganin girmansa da tayi, kuma ga shi sai wani lallaɓa ta yake yi da wasu kalaman da ta kasa gane musu, baza ta iya masa musu ba tunda babban Mutum ne, shiyasa ta gyaɗa kanta alamun ta amince

"Yauwa ko ke fa, har na ji sanyi a raina, mu je in bude miki ƙofan."
Ya nuna mata hanya alamun ta wuce

Babu musu tayi gaba duk da har ranta tana mamakin yanda yake nuna mata a yanzun ɗin, musamman yanda ya saki jikinsa har yana mata murmushi, bata dai kawo komai a ranta ba ta shiga Motan bayan ya buɗe mata

Ita kuwa Feena daɗi ne sosai ya ratsa ta ganin yanda Babban Yayan nasu yake yi wa Maryamu, da alamu ta soma gane Hunaip yana son Maryamun ne, kuma hakan yayi mata dad'i, don tayi mamakin ma yau da yace mata, "ta jira sa zai zo daukar ta." Ashe da biyu ne, ta riga da ta harbo jirgin, sai ta ji farin ciki da wannan haɗin, duk da basu daɗe da Maryamu ba amma ta shiga ranta since tana da kyawun da kowace zata so ƙulla alaƙa da ita

Tunda suka shiga Motan Maryamu bata ce uffan ba, yau ma tana zaune a gidan baya tana jin shi yana yi wa Feena magana tana basa amsa, daga ƙarshe ne ya sanyo ta a cikin zancen nasu yana cewa, "meyasa ba ta son yin magana kamar kurma?"
Murmushi kawai tayi bata ce uffan ba still, a ranta tana jinjina yanda yake faɗin, "wai daga ganin ta shiru-shiru ce babu ruwan ta, kuma alamu ya nuna bata da hayaniya, don haka zai ja kunnen Feena kar ta riƙa jan ta da surutu a class don ya san halin ta."
Taɓe baki kawai tayi tana mayar da hankalin ta a kan hanya, ita tunanin SHAREEF ma ya fiye mata jin hiran nasu, tana can ta faɗa duniyar soyayya da tunanin farin cikin nata, har ba ta sanin sanda take zuba murmushi ita kaɗai abun ta; tsaban tunanin yana jefa ta cikin nishaɗi

Kamar yanda Hunaip yace zasu shigo ciki ne, shiyasa yana yin packing ɗin motan, yace wa Feena, "ta fito su shiga ciki su gaisa da su Momy."

Tare suka shiga, suna gaba yana bin su a baya sai kallon Maryamu yake yi ko ɗauke ido ba ya yi a kanta, fuskarsa ɗauke da murmushi, har ransa yana jin yanzu ya samu Matar aure, duk da kusan shekaru biyar kenan da mutuwar Matarsa bai taɓa saka wata Mace a rai da sunan yana sonta ba, sai Maryamu, lokaci guda ta shiga ransa kuma tayi dai-dai da zaɓin zuciyarsa, don haka ba ya tunanin zai yi sanya a wannan karon, kafin ya koma bakin aikin sa zai sanar da Abbansa a zo a nema masa iznin neman ta, a jiya bai samu ya runtsa ba saboda tunanin Maryamu, duk da yana ganin yarinyar ƙarama ce sa'ar Autar su Feena, amma zai iya jira koyaushe ne in har za a ba shi...
Ɗan numfashi ya ja yana fitar da hucin bakin sa, tare da bin bayansu zuwa cikin Falon kasancewar har sun shige su

Momy suka samu a falon, don itama zaman ta kenan; ta shiga kaiwa SHAREEF kunun gyaɗa da ta gama dama mishi,
Ganin fuskokin su Hunaip ya sanya ta faɗaɗa fara'an ta tare da furta, "kai! Yanzu su wa nake gani haka kamar Hunaip da Nafisa? A gida na?"

Dukkan su dariya suka yi

"Ku ƙariso ku zauna, lale marhabun, ah! Lallai yau muna da manyan baƙi, barkan ku da zuwa."

Bayan sun zauna ne Hunaip ya soma gaishe ta yana murmushi

Ta amsa cikin kula wa tana cewa, "Hunaip ashe kana gari? Saukar yaushe?"

"Shekaran jiya Momy."

"Ikon Allah! to ya aikin fatan komai lafiya?"

"Alhamdulillah Momy, komai lafiya wlh."

"Momy ina wuni?" Feena itama ta gaishe ta

Sai ta harare ta tana cewa, "No, ke bazan amsa gaisuwar ki ba, tunda ga baki ga hanci amma ba ki san ki zo gidana ba, i know ma yanzu haka Hunaip yace zai zo kika biyo sa."

Duk dariya suka yi, har Maryamu da ke zaune gefen Feena itama tana jin su

While Feenan tace, "Laa wlh Momy a'a, ina son zuwa school ne ya ɓoye Ni, amma yanzu zan riƙa zuwa."

"Wai ko dama motan ku Maryam ta hau jiya take faɗa min Yayan class mate din ta ne?"

Hunaip da ke murmusawa yace, "gaskiya ne, yanzu ma tace baza ta hau bane shiyasa nace zan shigo in yi miki bayani, that's the reason da ta hau."

"Allah Sarki! To tashi mana ki dauko musu drinks su sha Maryam, ki shiga Kitchen ki duba freezer za ki ga cakes a ciki ki zubo musu."

"Momy Allah da kin bar shi, zamu wuce ne yanzu, but Dady ba ya nan ne?" Cewar Hunaip yana ɗan kallonta

Tace, "eh ba ya nan, tun safe ya fita a kan wasu kaya na Company da suka samu matsala, ina tunanin ma maybe sai gobe zai dawo, amma duk da haka baza ku wuce ba sai kun taɓa wani abu. Bari ta kawo muku."

"Ina SHAREEF yana nan kuwa?" Ya sauya maganar da furta hakan, tunda ya san ko yace zasu tafi, baza ta bar su ba sai sun sha drinks din

A nan ta faɗa mishi, "yana ciki a kwance ba lafiya ai, but jikin da sauƙi dai."

"Subhanallah.. amma bamu ji labari ba? Ko Abba bai da labari ina tunanin?"

"Eh, ai dayake jiya ne jikin nasa ya tashi, kuma da sauki gaskiya."

"To Allah ya ƙara lafiya, bari mu duba sa Momy kafin nan."

"To." Tace tana tashi tare da sake furta, "mu je sai in raka ku."

Wuce wa suka yi saman har Feena

Time ɗin Maryamu ta gama ajiye musu komai a saman Centre table, shiyasa ta wuce dakin ta don ta sauya kaya tunda ta san ɗakin SHAREEF suka tafi

Su kuma bayan sun shiga, Momy ta shiga har bedroom ta taso shi, har tana mishi faɗan, "ta ajiye masa Kunun ashe bai taso ya sha ba? Da bata sake shigowa ba haka zai bar shi ya ƙandare."

Sai murmushi su Hunaip suke musu,
Bayan Feena ta gaishe shi da jiki, sai suka fita da Momy suka bar su

Hunaip ya sake mishi ya jiki yana cewa, "ashe an taɓa file ne Kanina?"

Smile SHAREEF yayi yana cewa, "wlh kuwa Yaya Hunaip, amma jiki Alhamdulillah baka ga yanda na koma ba? har ƴar ƙiba nayi."

"Exactly na ga alama ai, haka ake so shiyasa na ga har tara ƙwanji kayi."

Tare suka yi dariya gaba ɗaya

"Ina Hanif da Sadiq ban gansu ba?"

"Hanif yana England, shi kuma Sadiq i think bai dawo school ba shima."

"Oh! Har yanzu Hanif bai gama karatun nan ba ashe?"

"Wlh kuwa, ya bar min aiki Ni kaɗai ina ta fama, amma ya kusa gama wa just few months ai."

"Ok Allah ya taimaka, Ni bari in zo in wuce. Sai mun yi waya duk da ba son zumuncin kake yi ba, ɗan gwara Hanif da kai; kwanakin baya ina ganin kiran sa, amma kai kuwa."
Sai ya ɗan girgiza kansa yana miƙe wa

Shi kuma SHAREEF murmushi yayi yace, "sorry Babban Yaya, na san nayi laifi amma zan gyara."

Ɗan ɗage kafaɗa yayi yana cewa, "da dai ban san hali bane, get well soon Ƙanina, sai kuma na sake kewayo wa before na tafi."

"Ok thanks."

Hannu ya basa sannan ya fice ya koma Falon,
Suna zaune gaba dayansu har Feena ta soma taɓa abun da aka kawo musu,
Sai yace, "Mom zamu wuce mun gaishe ku."

"A'a, ba fa zaka tafi ba sai ka taɓa wani abun, tunda na sa aka kawo sai kun ci."

"Mom Allah ina sauri akwai inda zan je, amma bari in sha ruwa."

"Hmm shikenan tunda baka yi ninya ba, ku gaishe da Maman taku, insha Allahu nima zan leƙo kwanan nan tunda na jima ban zo ba, yaushe zaka koma Abujan? Ko an ɗiba mana hutun da yawa za a riƙa leƙo mu?" Ta furta tana ƴar dariya

"Uhm Momy wannan ma hutun da ya ya na samu? One week ne kawai sannan zan wuce, amma zan sake zuwa insha Allah tunda bamu haɗu da Dady ba."

Daga nan dai sallama suka yi suka fita, Maryamu har bakin farandan gidan ta raka su suka sake sallama da Feena

Shi kuma Hunaip tuni ya wuce wurin Motan yana waya, duk da sai da ya juya ya sake kallon Maryamun har ta shige, sannan shima ya shiga Motan yana jiran Feena

Motan su na fita gidan wata motan ta shigo, Babbar Mace ce a cikin Motan, Yayar Momy ce duk da ba Uwa ɗaya suke da ita ba, Uba suka haɗa, Hajiya Salma kenan

Maryamu ce kadai a falon tana cin abinci, while Momy kuma ta wuce ɗakin ta,
Shi yasa da Hajiya Salman ta shigo tana doka sallama, Maryamu ta amsa mata tana kallonta

Haka itama Hajiya Salma kallonta take yi tana ɗan yatsina fuskarta, sai tace, "ba ki iya gaisuwa bane kin kafe Ni da ido? Haka ake yi?"

Kawar da kai Maryamun tayi ta ƙi cewa komai, sai ma ci gaba da cin abincinta tayi

Hakan ya fusata ta tace, "Kee, ba da ke nake yi ba?"

"Ai ban san dani kike yi ba." Maryamu tayi maganar tana tura baki, sai da ta yatsina fuska kafin tace, "ina wuni?"

"Au iyee? Lallai ne ma, wato Khadija fitsararriya ta ajiye a gidan ta?" Ƙwafa tayi tana sake kallonta tace, "ina Matar gidan take?"

"Tana ciki." Ta bata amsa batare da ta sake ɗago kanta ba

"Lallai yarinya, tabbas kafin in bar gidan nan ina tunanin zan yi maganin rashin kunyar ki, don daga gani fitsararriya ce ke ko a ƙauyen naku, ai wannan masifa aka ajiye wa Khadija a gida, amma ki kuka da kanki."
Ta buga mata yatsun ta alamun warning tana wuce wa saman benen

Yayinda Maryamu ta raka ta da kallo tana ƙunƙunai har da jan guntun tsakin ta, "wai zata yi magani na, mai magani na sai ya shirya, don kin zo a lokacin da nayi sanyi ne amma ba na ɗaukar raini wlh, ga ki nan fitsararriya mai ruwan ƴan duniya, tana yi tana wani baza ɗuwawu kamar faranti wai ga ta ƴar fi'ili, to Ni digree ne dani a fi'ilin, tun daga Nahawu na farko har na ƙarshe sai da na sauke ."
Ta sake jan dogon tsakin cike da haushin Matar saboda kallo ɗaya har ranta ta ji Matar bata yi mata ba, ko meye ruwanta da ita da zata ce dole sai ta gaishe ta?

Ita kuma Hajiya Salma ɗakin Momy ta shiga, ta same ta ta fito daga toilet

Da fara'a Momy ta tarbe ta sabida bata yi expecting ganin ta ba, ta bata wuri suka zauna ta fara gaishe ta tana cewa, "ina son zuwa gidan ma tunda na ji wayanki ta mutu kwana biyu ba na samu, ashe ke ma kina hanya?"

Taɓe baki tayi tace, "eh ina hanya, nan maƙotan ku na zo shiyasa na ce bari in ƙariso nan mu gaisa, Hajiya ma ta faɗa min SHAREEF ba lafiya dalilin shigowa ta kenan."

"Wai har sun sani? Sai da na cewa Aunty Najwa kar ta sanar musu, don na san zasu ce zasu gaishe shi, jikin da sauki wlh."

"To ai sai in faɗa musu, don nima daga nan gidan zan yi, ba zama ya kawo Ni ba, gobe za a kawo kaya shiyasa nace bari in zo mu ƙarisa maganar tunda ban san da me- da me za ki siya ba? Wayata ta samu matsala ce shiyasa ma ba ki ji Ni ba."

Momy tace, "kayan ai ba nawa bane, na Maryam ne, dama nayi mata siyayya ne kuma kinga yakamata a zaɓa mata har da su atamfofi, shiyasa nace bari in miki magana, ki zaɓa mata kala biyar masu kyau ƴan 10k, sai materials da less su ma guda biyar biyar ɗin, waɗanda dai zasu yi wa bak'ar Mace kyau, ko kuma bari in kira miki yarinyar sai ki ganta don ba na son a samu matsala, ki haɗa kuɗin da lissafin mayafan da na ɗauka kwanakin baya."

"Wai kina nufin waɗannan kayan duk yarinyar nan za ki siyan ma wa? Ai na ganta ba sai kin kira ta ba, yarinyar da ta nemi min rashin kunya idanu a tsatstsaye ko gaisuwa babu?"

Da mamaki Momy tace, "rashin kunya kuma Aunty Salma? Ita Maryam ɗin?"

"Eh ita fa, ai wlh ina mamakin ki Khadijah, a ce har dangin Miji sun fi miki mu ƴan uwanki, nan nace miki Mubeena zata dawo wurin ki da zama tunda ba ki da ƴa Mace, ko ƴan aikace-aikace ta riƙa taya ki dashi, zaman ma zai fi miki daɗi tunda Yaran nan Maza ne ba zama suke yi ba, amma kika watsa min ƙasa a ido kika ƙeƙashe kika ce ba kya so, dama aka ce in baka yi Sharan masallaci ba zaka yi na coci wlh, ga shi nan an jajibo miki ƴar ƙauye an kawo miki, wannan yarinyar kuma sai kin yi aiki da ita daga ganin ta, don wlh idanunta suna gama buɗe wa da jin daɗi da sanyin AC, ke kanki sai ta gagare ki."

Baki sake Momy take kallon Hajiya Salman yadda take ta rattafo zance, duk da ta san cewa hali ne, mai hali ba ya fasa wa, amma ita kanta baza ta iya jajibo Mubeena ƴarta ta kawo ta gidan nan ba tunda ta san yarinyar bata da kunya ko kaɗan, ita kuma tana da ƙattin Maza baza ta iya haɗa su gida da wannan yarinyar ba, dama laifi tudu ne; ka taka naka ka hango na wani, ita bata ga halin yarinyar ta ba sai na Maryam wacce tana jin cewa haka kawai Maryam baza ta yi wa Hajiya Salma rashin kunya ba, sai dai in faɗa tayi, kuma yanzu Maryam ai daban take tunda tana auren ɗanta, duk da ba wai sun sanar da kowa bane zancen sun bar shi a tsakanin su ne, sai lokacin da Maryam zata tare a ɗakin ta sannan Momy take tunanin sanar da kowa a dangin su, duk da ta so ko Aunty Najwa Yayarta ta sanar mata,
Ɗan numfashi ta ja tare da kallon Aunty Salman da har yanzu take tsiyan ƙin amincewar zuwan ƴarta Mubeena gidan, don ta ji haushi ba kaɗan ba, shiyasa Momy tace, "to ki yi haƙuri Aunty Salma, Ni wannan yarinyar fa babu yanda za a yi in kore ta ko in hana ta zuwa, tunda gidan Ubanta ne, Alhaji ya fi Ni iko da gidansa zai kawo duk wanda yake so ya kawo gidan sa, amma Ni sai da amincewar sa, bani da hurumin koranta tunda shi ya je ya dauko ta."

"Ai dama haka za ki ce, dole dai sai kin nuna wata kusar ta fi wata, wlh na tabbata da ace Aunty Najwa ce ko Zainab; su suka ce zasu kawo nasu gidan nan, baza ki ƙi amince wa ba, tunda sun fi mu a wurin ki."

Cikin rashin jin daɗin maganar Momy tace, "a'a Aunty Salma kar ki ɗaura min Jakar tsaba Kaji su bi ni, mene ne abun magana a cikin nan? Ni a wuri na baku da bambanci da su tunda ɗaya na ɗauke ku, shikenan tunda kin faɗi haka idan Alhajin ya dawo zan yi mishi magana; kinga in ya amince ki dawo da ita Ni babu abun da ya shafe Ni, wurin zama ai akwai su birjik tunda ba a kaina zata zauna ba sai ki kawo ta."

Sanin cewa ta gaya mata magana ne, tunda ta san halin Momy ba a faɗa mata tayi shiru in har tana da yanda za tayi sai ta rama, shiyasa sai Aunty Salman ta miƙe tsaye tana cewa, "ina kuwa ƴata zata zo tunda tun farko ba a yi ninyar zuwan ta ba? Ko ta zo yanzu ma babu amfani, Ni kinga tafiyana, kuma na manta ban faɗa miki ba; jibi za a wuce Katsina ba ki kawo gudummawar ki ba, in kuma da ke za a je to?"

"A'a ba dani za a je ba, na kira ta a waya nayi mata Barka, sai ki ɗauki atamfa ɗaya da kayan jarirai guda biyu na sanyi ki bata nawa gudummawar, Allah ya raya."

"Amin." Hajiya Salma ta furta cikin jin zafin abun da Momyn ta bayar, wai duk wannan tulin dukiyar da take ciki, ga ƙaton gida amma ta rasa me zata ba wa ƴar ƙanwarta sai wannan tsiyar, amma ta san da ƴar wacce suka fito ciki daya ne baza ta basu wannan kaɗai ba, tun ba yau ba ta gama kula da Momy maƙon tsiya ne da ita, ƴan ɗakin su kaɗai ta sani in dai a alheri ne, dole sai ta nuna su ɗin ƴan Uba ne. Ƙwafa tayi a ranta take cewa, "matsiyaciya, da kin bar tsiyar ki ma, ai mun fi ƙarfin wannan."

Momy kuwa wacce ta taso domin ta raka ta, bata san ma tana yi ba, sai cewa tayi, "mu je Aunty na taka miki zuwa wajen, ki gaishe da su Hajiya in kin je gidan."

"Zasu ji."
Ta amsa mata tana yatsina fuska tare da yin gaba, sabida ba kaɗan ba a yanzu ta sake ƙule wa da halin Momyn, musamman yanda ta barta hannu rabbana sai gaisuwa da ta aike ta dashi ta kaiwa su Hajiyar su, kuma gani take yi don kawai babu Uwarta a ciki ne, amma da tana a raye baza ta ƙi bata wani abun takai musu ba,
Dama wanda yasa rai a abun wani dole zai sha wahala, wanda take yi don ita bata san ma tana yi ba

Koda suka sauka Falo ma babu Maryamu a wurin, ta shiga ɗaki ɗauko littafin ta domin Sadiq ya duba mata assignment ɗin da aka basu

Sadiq kaɗai suka tarar, shima sauri yake yi yana afa abinci sabida yunwar da ya dawo dashi sosai, ga shi har an soma kiran sallah yana son cinye wa ya wuce masallaci,
Bama su kula dashi ba tunda yana kan Dinnig ne, sai shi ne ya ɗaga murya yana gaishe da Hajiya Salman

"Ah... ah! Sadiq, ashe kana nan? Na shigo ban ganka ba?"

"Ina nan Aunty, yanzu na dawo school, ina wuni?"
Ya sake gaishe ta kasancewar bata amsa wancan gaisuwar ba

Ta amsa da fara'a tana tambayar sa school ɗin?

Yace, "Alhamdulillah."

Bayan sun gama gaisa wa ne suka fita da Momy, ta raka ta har bakin Mota sannan ta juya cikin gida.


[14/02, 9:30 am] OumƊahirah نفيسة: 🌱🌱🌱🌱🌱

      *SHAREEF*
          _SexyBoy_
🌱🌱🌱🌱🌱


_Writer: Nafisat Isma'il Lawal_
_Wattpad: UmmuDahirah_

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝*



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

       *P.W.A✍️*





*DATA SHARE*

Call, message or whatsap  07065334256

*MTN*
500MB 150
1gb  280
2gb.  560 
3gb.   840
4gb.    1120
5gb      1400
6gb.     1700
Verlid for 30 days.












__________
*BOOK1*
_______________*FREE PAGE31to32*
_____Kwana biyun da suka wuce, duk SHAREEF yana gida babu inda yake zuwa sabida rashin lafiya da yake fama dashi, duk da dasauki but Dady ya hana sa zuwa wurin aikin, sai dai ya duba ayyukan a cikin computern sa

Gefe guda kuma suna ci gaba da waya da Haseena koyaushe, duk da a yanda yake jin matuƙar kewarta a wannan lokacin, shi kansa yana son zuwa ya duba ta since an kwana biyu bai je ba, duk wayan da suke yi da bidiyo call hakan ba ya gamsar dashi, shi kansa yayi mamakin ma yanda bata sake nuna mishi buƙatar son zuwan nashi ba, tunda ya santa in ta fara rigima a kan abu; baza ta bari ba sai ta samu, amma har ita take ce mishi ma, "ya zauna kawai tunda ba shi da lafiya ya huta, ta yafe zuwan nasa."
Shi kuma ya nuna mata ba haka ba, tunda har ga Allah yana matuƙar kewarta, yana buƙatar zuwa su ji ɗumin juna tunda ba ya jin zai iya jure wa, already ya saba da ita, hakan ne kawai yake samun salama daga buƙatar da ke taso masa,
Amma ya san babu yanda za a yi ya bar ƙasar ba tare da sanin iyayensa ba, dole ya soma fitowa waje yana daure wa kamar ya samu lafiya

A ranan da kayan su ya iso ma, har shirya wa yayi ya wuce wurin aiki, tunda so yake yi ya samu damar da zai je wurin Haseena, already ya yanke shawarar da zaran an wuce da kayan gobe, since jibi za a soma aikin, sai ya fada wa Dady, "zasu je Abujan ko two days su yi a can; a fara komai a gaban su."
Shi kuma sai ya samu damar da zai wuce kansa tsaye Australia ba tare da ya je Abujan ba, tunda akwai su PA a wurin ba dole sai ya je ba, zasu faɗa mishi komai abun da ke faruwa,
Wannan tunanin nasa shi ya saka shi shiga farin ciki da walwala, tunda ya samu solution na matsalar sa.
***

_____Yayinda Maryamu tana can tana haukan soyayyarsa bai san ma tana yi ba, tunda ko kallo bata ishe shi ba, in fact ma ko fuska ba ya bata bare ya san Allah ya yi ruwan tsakin ta idan yana wuri,
Amma hakan bai damu Maryamu ba, kullum sake jin matsananciyar ƙaunarsa take ji a ranta, bata damu da halin da yake nuna mata ba tunda ta san yana zuwa wurin ta neman buƙata a cikin dare, kuma bata taɓa hana sa ba duk da sau huɗu kenan abun yana faruwa, tana shiga ɗaki zai zo ya lallaɓa ta yana mata magiyan ta taimaka mishi zai mutu, ita kuma sonshi ya rufe mata ido, burin ta kawai ta faranta mishi kamar yanda yake bukata, tunda tana jin komai nata zata iya ba shi in har SHAREEF zai yi farin ciki, tana mamakin yanda yake nuna mata halin ko'in kula a gidan, amma bata damu ba tunda yana sanya ta farin ciki idan ya kasance tare da ita, tana ganin ko banza dai ta taimake shi a yanda ya raina ta yana ganin ta ba kowa ba

Yanzu kuma abun ya soma damun ta tunda sabida rashin ganin sa da ba tayi a jiya da yau, ko ta kwanta barci ba ta yin mafarkin sa kamar yanda ta saba,
Hakan ya soma damun ta amma babu halin ta nuna,
Tunda da zaran ta canza Momy zata hau tambayarta abun da ke damun ta?

Kullum Sadiq shi ke kaita school ya dauko ta; tunda yana gida a wannan time ɗin,
Kasancewar ya ɗan samu hutu ba ya zuwa school shiyasa yake mata lesson a gida

Ita kuma Momy tana koya mata wasu littafai na addini, tare da hisnul Muslim tana nuna mata muhimmancin yin azkar kodayaushe, kasancewar sun zauna da Dady ta sake mishi bayanin halin da Maryamun take ciki, don ita tana ganin Maryamu tana da aljanu dole sai an taimaka mata, duk da bata ƙara ganin wani alama da zai nuna akwai su a jikinta ba, amma tace wa Dady, "gwara a riƙa amso mata rubutu ana bata tana sha."

Shima Dady ya amince da maganar Momy, tunda akwai malamai a anguwan nasu shiyasa ya yi wa wani malami magana aka soma amso mata rubutun, Sadiq yake zuwa da safe bayan ya kaita school sai ya amso mata, kuma ikon Allah tun daga ranan ne Maryamu bata sake mafarke-mafarken da take yi ba, wanda tana ganin ita a gaske ne, komai da ke faruwa saduwar da ake yi da ita SHAREEF ne yake zuwa wurin ta ba mafarki bane, amma kuma tsaban wauta irin nata bata taɓa ganin alama a jikinta ko na wani abu ba, sai dai ta ga babu kaya a jikinta, hakan yasa ta gasgata SHAREEF ne da gaske yake zuwa wurin ta, kuma dena mafarkin ya jefa ta jin haushin kanta, don bata so hakan ya dena faruwa da ita ba, har tana jin a ranta ko dai zata je ɗakin sa ta ba shi haƙuri ne; wataƙil laifi tayi masa ya dena zuwa, baza ta so ta rasa wannan damar da ta samu ba,
Amma kunya da tsoron abun da zai biyo baya yasa ta haƙura bata je ba


Bata san ma yayi tafiya ba sai yau asabar da Sadiq yake faɗa mata, "SHAREEF yana Abuja, zai yi kwana biyu before ya dawo."

Haka kawai ta ji zafin tafiyan nasa duk da bata da yanda zata yi, shiyasa kwata-kwata ranan bata yi walwala ba

Momy da ta fahimci halin da take ciki, sai ta zaunar da ita tana tambayarta dalilin ɓacin ran yau, sai faman fushi take yi tana kumbura fuska

Maryamu tace, "babu komai, ba ta jin dadi ne."

Momy murmushi tayi tace, "ko dai duk sabida SHAREEF kike wannan fushe-fushen? Ba ki so yayi tafiyar bane?"

Kallon Momyn tayi, sai ga hawaye sun cika mata ido, sai tayi saurin dauke idanun sabida ba ta son Momy ta fahimci halin da take ciki, ta girgiza kanta alamun a'a ta kasa magana, domin in ta buɗe baki tana jin kamar zata fashe da kuka ne


Momy wacce ta gama fahimtar ta gaba ɗaya, har ga Allah tana tausayin yarinyar, ƙanƙanuwa da ita da shiga matsalar soyayya, tana jinjina wanne irin so Maryamu take yi wa SHAREEF da har take kasa ɓoye shi, sai tace mata, "ki je ki kwanta to, in kin tashi sai mu ɗaura karatun."

Da sauri kuwa ta miƙe ta nufi hanyar ɗakinta ta shige

Momy ta raka ta da kallo sannan ta miƙe ta koma ɗakin Dady, a can ta same sa zaune, shiyasa ta faɗa masa shawaran da ta yanke a kan barin Maryamu ba tare da an yi bikin auren su an huta ba, gwara a ba wa SHAREEF Matarsa tunda shi kansa yana bukatar Mata kusa dashi, bata ga amfanin zaman Maryamu a haka da auren ba, tunda itama tana son SHAREEF ɗin, idan ba a kusanta shi da ita ba SHAREEF bazai taɓa sonta ba, ko don yanda suke zaune a gidan babu wani ci gaba gwara a ba shi Matarsa ya san cewa Matarsa ce wataƙil zai haƙura ya ƙaunace ta

Dady da ya gama jin zantukan Momyn, sai yace, "a yanzu dai ba shi da wata matsala gaskiya, yanda ta ga ya dace hakan za a yi, idan SHAREEF ɗin ya dawo sai su faɗa mishi, inyaso a sanya ranan tarewa su zauna a nan."

Ita kanta Momy bata yi tunanin zai canza shawaran nasa ba, shiyasa ta ji daɗi tace, "wlh ban yi tunanin zaka amince ba."

Yana murmusawa yace, "haba sabida me? Ai na san yanda ƴata take son shi nima bazan so in ci gaba da ƙuntata mata haka ba, idan aka yi auren; mu ma sai mu huta tunda na ga alamar ɗan naki shegen taurin kai ne dashi, yana buƙatar auren amma babu Mata a gaban shi, alamu ya nuna ko budurwa tsayayya ba shi da ita, gwara kawai mu faɗa mishi ga Mata a gida mun yi mishi, Allah ya dawo dashi gida lafiya mu ji mai zai ce."

"To Amin, sai mu fara shirye-shirye kenan? Domin za a yi biki sosai ne gaskiya."

Haka dai suka ci gaba da hiran bikin dukkan su suna farin ciki,
Bayan sun gama maganar ne Momy ta fita, sai kuma wayan Dady ta soma ring, yana duba wa ya ga Abokinsa ne Doctor Umar, Mahaifin su Hunaip. Shi ne ya kira sa a kan zancen Hunaip ɗin dayake ya sanar mishi, duk da a waya suka yi maganar kasancewar Hunaip tuni ya koma wurin aiki sabida kiran gaggawa da aka yi mishi, bai ma gama hutun da aka ba shi ba haka nan ya tafi ba da son ransa ba, ya wuce da Maryamu maƙale a ransa, duk da ya so ya bar maganar sai ya sake samun hutu idan ya dawo sai ya sanar da iyayensa, amma zuciyarsa ta azalzala mishi haka nan ya kira Abbansu ya sanar mishi, shi kuma ya kasa hakura sabida farin cikin maganar; shi ne yanzu ya kira Dady yana shaida mishi, "Hunaip ya ga iri a gidan sa yana so."

Dady yayi mamakin maganar, shiyasa ya gyara zamansa sosai yana cewa, "wai kana nufin Hunaip ya ga Maryam ƴar ƙanwata ne?"

"Wlh kuwa, yace min ya ga yarinyar yana so, tunda kwanaki kafin ya tafi shi yake dauko Nafisa daga makaranta, to a can suka haɗu, yanzu yake faɗa min."

"Ikon Allah! Ai kuwa ban san da maganar ba, tunda Momyn su bata sanar min ba, sai dai kuma akwai matsala gaskiya."

Doctor Umar yace, "wacce irin matsala kenan? Ka faɗa min kawai; ai yanzu ba maganar ɓoye-ɓoye muke yi ba."

Nan Dady ya sanar mishi cewan, "tun a can da ya je ɗaukar yarinyar; aka ɗaura auren ta da SHAREEF, yanzu haka da auren SHAREEF a kanta."

"Ikon Allah! To amma shi ne Alhaji Ahmed baka taɓa faɗa min ba? Abun farin ciki haka amma ka ɓoye min?"

"Kayi haƙuri Docta, mu kanmu ka ga maganar ba wai mun sanar da kowa bane, tunda ban so yarinyar ta tare tun yanzu ba, amma yanzu muka gama maganar da mahaifiyar SHAREEF ɗin; muke cewa gwara a miƙa masa Matarsa zai fi, amma kayi haƙuri."

"Babu komai wlh, ai da Hunaip da SHAREEF duk ɗaya ne a wurin mu, abun farin ciki ne wannan, Allah ya sanya alkhairi, shi kuma Hunaip ɗin Allah ya basa wata, zan kira sa sai in faɗa masa yanda muka yi."

Nan Dady ya amsa da Amin, daga nan suka ɗan yi hira nasu na Abokai, before suka kashe wayan.

🔆🔆🔆🔆🔆🔆🔆🔆 






_____ *AUSTRALIA*
      *SYDNEY*
Sabuwar rayuwa, sabuwar duniya, ta shigo wa Haseena a lokacin da bata taɓa zato ko tunanin cewa wata rana zata iya faɗa wa irin wannan rayuwar ba, duk da ita ƴar gata ce, ta taso gidan su babu kwaɓa bare takura da hantara, abun da suke so shi suke yi iyayen su basu wani basu tarbiyya mai kyau kamar yanda addini ya shar'anta ba, amma dai-dai gwargwado tana da kamun kai tunda bata taɓa ba wa wani namiji kanta ba, in fact ma bata taɓa yin saurayi ba sai da SHAREEF ya shigo cikin rayuwarta, wadda daɗi soyayya da tsananin ƙaunar da suke nuna wa juna yasa suke tafiyar da soyayyar su bisa tsarin wayewa da ƙetare iyakan addini, rayuwar da suke yi sam bai kamaci ɗan musulmi ya tafiyar da soyayyarsa a haka ba, amma su sun ɗauki hakan shi ne rayuwa a yanzu, ita Haseena tarbiyya da ilimin addini bai ishe ta ba, yayinda take ganin komai dai-dai ne a wurin ta; in har zata ji daɗin rayuwarta,
While SHAREEF dama shi Boko ya rufe mishi ido, ya ɗauki aƙidar yahudawa ya ara ya yafa, zamansa a England lokacin da yayi karatu; sosai halayyarsa ta canza, ya ɗauki ɗabi'un turawa yayi tasiri a zuciyarsa, musamman kasancewar sa Mutum mara son takura da hayaniya, yana rayuwarsa silent ne ba tare da ya shiga shirgin kowa ba; bare shi ya takura wa kansa, hakan ne yasa daga cikin ɗabi'un sa na al'adan bahaushe; ko in ce ɗabi'un da aka san ɗan musulmi da su, ya ajiye su gefe ya ɗauki zamani da wayewar rayuwa ya saka a kansa, abun har ya shafi addinin sa, sallah ma wani lokacin sai lokaci ya gifta yake yin ta

A taƙaice dai; ruɗin duniya yasa Haseena ta faɗa babban bala'in da muke fama da shi cikin rayuwarmu ta yanzu, wato lesbian. Kuma kaso mafi rinjayen laifin Mahaifinta ne, tunda yana ganin shi ɗan boko ne, wayewa ne kuma abun alfahari ne a ce yau ƴaƴansu sun tafi abroad karatu, wanda bai san cewa hakan na taimaka wa da yawan Yaran mu na Arewa su ajiye ɗibi'un su da aka sansu da shi na ƴaƴan Bahaushe; su ɗauki halayen turawa su ɗaura a kansu ba, wasu daga nan tarbiyyar su ta gama gurɓacewa kenan, a can zasu iya haɗuwa da mutane kala-kala masu aƙidu daban-daban, kuma kowanne da zai yi tarayya da ƴaƴan ka akwai gudummawar da zai bada, komin tarbiyyar Mutum da addinin sa, dole ne zai sauya wasu ɗabi'u, idan ma Allah ya tsare sa kenan, amma ana haɗuwa da ɓata gari da dama masu canza wa Mutum alƙibla, ya afka bala'in da bai taɓa tunanin zai riski kansa a ciki ba

Kwatsam Nana ta shigo rayuwar Haseena, kuma tayi tasiri wajen cin galaba tare da sauya mata tunani, ada Haseena SHAREEF shi ne kaɗai namijin da take ganin zata iya ba wa kanta, shi kaɗai take sha'awa wanda take fatan ranan da zasu kasance tare a koyaushe, bata taɓa sha'awar wani namiji ba bayan shi, sai dai kuma tunda Nana tayi amfani da damar ta wajen shayar da ita zuman daɗi da gusar mata da dukkan damuwarta da buƙatarta, sai tayi dana-sanin cewan da tun farko ta san wannan harkan yana da daɗi, babu abun da zai sa bata afka mishi ba, domin tana ganin tamkar hanya ce mai sauƙi ta samu wacce zata biya wa kanta buƙata ba tare da wani namiji ya shigo rayuwarta ba, tunda baza ta taɓa iya kallon wani namiji bare har ta ba shi damar taɓa jikinta ba; Mutum ɗaya ne SHAREEF, matuƙa ta ji daɗin shigowar Nana cikin rayuwarta, kuma ta bata goyan baya ɗari bisa ɗari musamman da ta san cewa tamkar taimakon ta tayi; wajen gusar mata da ƙishin ruwan da ke damun ta,
Wani irin daɗi da farin ciki ne ke gudana a cikin rayuwarta wanda a ɗan kwanakin nan ba ƙaramin sauya wa Haseena tayi ba, lokaci ɗaya ta faɗa ruwa tsundum gaba ɗaya ta makance da tsananin bukatar Nana, burin ta kawai su rika kasancewa tare suna jiyar da junan su daɗi, idanunta sun rufe ita kaɗai take iya hango wa, sun ƙulle sun zama Abokan juna koyaushe Nana tana zuwa gidan ta domin su jiyar da kansu daɗi, har ba sa gajiya duk da Haseena sabon shiga ce amma abun sai ya zo mata a wani irin yanayi, ba ta sukuni in har bata ganta tare da Nana ba, tsawon kwana biyu Nana tana gidan ko koma wa nasu gidan bata yi, gaba ɗaya ta ba wa Haseena lokacin ta tana nuna mata soyayya mai tsaya wa a rai, ko school ba sa zuwa duk da a da Haseena tana gudun fashi, amma yanzu tuni ta biye wa Nana ko labarin makarantar ba ta yi, kasancewar Nanan ta faɗa mata, "basu da matsala da school ɗin, komai zasu iya samu in har tana tare da ita, so ta kwantar da hankalinta."

Shi yasa Haseena itama ta shashantar da labarin school ɗin. Hatta da maganar zuwan SHAREEF da ya sanar mata zai zo shaf ta manta, tana can tare da Nana sun fita tare zata kaita room school ɗin su, daga can zasu wuce wani party ne da aka shirya isu-isu ƴan Lesbian, su Jenifer suna can suna jiran su

Suna kan hanya ne Haseena ta samu kiran SHAREEF, bayan ta amsa call ɗin yake sanar mata da saukar sa, har ya je gidan but ya ga doors a rufe. Ita kanta ta manta ya sanar mata zuwan nasa, shiyasa gaba ɗaya tadaburce tayi saurin katse wayan after ta faɗa masa, "ga ta nan zuwa yanzu."
Sai ta dubi Nana tace, "Please ki sauke Ni a nan, bazan samu zuwa ba, ina son koma wa gida yanzu akwai wanda yake jira na."

Da mamaki Nana take kallonta tace, "I don't understand? Is there someone waiting for you? Who is he?"

Sai da ta ɗan ja numfashi kaɗan tana rufe idonta, ta buɗe su da sauri tana sake duban Nanan tare da furta, "My boyfriend."

"Boyfriend?" Ta maimaita sunan da mamaki, sai kuma tayi shiru tana mayar da idanunta a kan titin tare da ci gaba da mirza sitiyarin cikin ƙware wa

Hakan yasa itama Haseena tayi shiru bata ce komai ba tana jiran ganin Nanan ta faka motan

"Da alamu it is important in your life? The situation you went through showed me that?" Ta furta tana kallonta cike da tsantsan kishi

Smile tayi kaɗan tana gyaɗa mata kai, before ta furta, "It is impossible for me to leave him alone, since he came from Nigeria for me."

"Are you about to get married?"

Ɗan kallonta tayi saboda yanda ta ji tayi maganar, da sauri ta ɗauke kanta tana haɗiye yawun tsoron ta, "No, sai na gama school. But..." Sai tayi shiru kuma

Dakatar da Motan tayi a gefen titi, kafin ta juyo tana kallonta tace, "I will let you go because I don't want your anger, amma bazan iya jure kina sharing ɗina da wani ba, ina da zafin kishi, ba na buƙatar alaƙar ki da kowa, ban damu ba ko me za ki yi; ki bi hanyar da za ki bi domin rabuwa da shi..."

Tun kafin ta ƙarisa zancen ta soma girgiza kanta nan da nan hawaye suka cika mata ido, da sauri ta furta, "No, Bazan iya ba, shi rayuwata ne, idan kika raba Ni dashi kamar kin raba numfashi na da gangar jikina ne. I can't live without him, he's different."

Wani killer smile Nana ta saki, still fuskarta yalwace da murmushin tace, "must be very important in your life, Wow! Har na ji ya burge Ni since ke ma kina sonsa, no problem babe, now go and we'll talk later."

Jin hakan yasa Haseena ta ji sanyi a ranta, sai da Nanan ta gajula ta ta bata good bye kissing before suka yi sallama ta fita. Ta tari Taxi ta hau ya mayar da ita gida.
***

_____Shi kansa SHAREEF ya ga sauyi da yawa a tattare da Haseena, duk da ba ƙaramin farin ciki ya ji ba lokacin da ya ga kyakkyawar fuskarta mai sanya shi farin ciki da natsuwa a zuciya, musamman idan akwai kwalliya a kan face ɗin ta, shi kansa yana manta kowanne irin tunani ne a ransa ya shagaltu da kallonta, ba ƙaramin kyau tayi masa ba musamman kasancewar makeup ɗin da tayi Nana tayi mata, sosai kwalliyar ta ƙara tsatso kyawunta, haka kayan da ta sanya ya fito da ainihin dirin jikinta wanda yasa har SHAREEF ya gaza haƙuri sabida kishi, yayi mata complaint ɗin fitan ta a haka babu ko mayafi kuma ba da Motan ta ba

Murmushi tayi ta manne mishi a jiki tace, "haba dear, daga zuwan ka sai ƙorafi kuma? Maimakon mu fara shiga ciki ka huta sannan ko me zai biyo baya sai ya biyo, ka san dai babu yanda za a yi in yi tarayya da wani bayan kai, You are the only man I see in my eyes, so duk wanda zai kalle Ni sai dai ya ba idanunsa abinci amma na fi ƙarfin sa, balle nan ba irin local ƙasar mu ba ce da zasu damu da shigan da nayi, ko bai yi maka kyau bane? Domin ka nayi fa."

Ba ƙaramin tasiri kalaman ta suka yi a cikin zuciyarsa ba, wanda lokaci ɗaya ya lumshe idanunsa yana ware su a kanta cike da wani irin soyayyarta da yake ƙara tsaga mishi magudanan jini yana shige wa, hannu ya sanya ya kamo nata yana duban yatsun ta da ta maƙala zobe guda biyu kalan ja, wanda Nana ta bata su a daren jiya, ita kanta bata san zoben mene ne bane, kawai ta amsa a matsayin gift ne, kuma ba ƙaramin kyau suka yi mata ba, wanda kyawun da suka yi wa SHAREEF a ido ne; yasa ya kasa yin shiru yana tambayarta, "Aina ta siya?"

Shiru tayi tana tunanin ƙaryan da zata yi masa, sai kuma tace masa, "a super market ta siye su, cuz sun yi mata kyau ne."

Kissing hannun yayi before ya furta, "nima sun yi min kyau sosai, sun ƙara ƙawata hannun ki."
Rungumo ta yayi sosai a jikinsa sannan suka nufi cikin gidan,
Gaba ɗaya SHAREEF ya maƙale mata ya hana ta ko kwaƙƙwaran motsi tayi, wani irin kewa da buƙatar ta ne ke ɗawainiya da shi, haka ya dinga matsa ta yana romance ɗin ta cikin ƙware wa da nuna soyayya

Babu yanda Haseena ta iya dole ta biye mishi, sabida itama har ga Allah tayi kewarsa sosai, sai dai kuma ko kusa ba ta jin sha'awar sa a tattare da ita, ba kamar baya ba, yanzu kamar an cire mata ƙaya sam-sam ba ta jin wata buƙatar sa, kuma kwata-kwata ba ta jin daɗin abun da yake mata, amma ya zama dole ta biye mishi kar ya zargi wani abun; kasancewar ya santa kullum ita ce da ƙorafin ya kusance ta, har kuka take yi in suna tare tsaban yanda take matuwar son su ji daɗi tare, ita kanta tayi mamakin yanda ta ji gaba ɗaya ta sauya sam-sam ba ta farin ciki sosai da zuwan SHAREEF, sabida ta san tamkar takura ce a tare da ita, duk da soyayyarsa bai ragu ko kaɗan a zuciyarta ba, amma kuma ba ta jin sha'awar sa kwata-kwata; daure wa kawai take yi tana biye masa suna shan soyayya, ga shi a wannan lokacin tamkar wani maye yanda ka san chewing gum haka ya maƙale mata, wani sabon salo ma ya tsiro mata dashi ko gajiya ba ya yi da maƙale mata, wuni a ranan suna manne da juna sai da dare ne ta huta time ɗin yayi barci, har ta samu suka yi waya da Nana don ita lokacin ne ta haukace da nata buƙatar, sai da suka yi video call sannan ta samu ta runtsa,
Yayinda ta kwana da tunanin hanyar da zata bi domin samun fita gobe ita kaɗai su haɗu da Nana, don baza ta iya jure halin da take ciki ba, kuma bata san ranan tafiyan SHAREEF ba since bai faɗa mata ba, zuwan sa gaskiya ya zame mata takura wanda daga baya gaba ɗaya farin cikin ta yayi ƙaura, da saƙe-saƙen abun da zata yi ta samu ta fita batare da shi ba; ta kwana a ranta

Sai dai kuma a washe garin ne SHAREEF ya samu waya daga PA ɗin sa, mummunar labari kayan da suka kai Abuja gaba ɗaya sun ƙone ƙurmus. Kayan da ya kai kusan 100 millions wanda ba a san daga ina gobaran ta tashi ba, komai da komai ya ƙone. Tashin hankalin da SHAREEF ya shiga baki ma bazai iya misalta shi ba, lokaci ɗaya ya rikice sabida wannan babban asara ne suka samu, dole ya ruɗe tunda ya san cewa hakan na nufin rasa komai nasu

Ita kanta Haseena hankalin ta ya tashi sosai da ya sanar mata, kuma ta tausaya mishi sabida ganin yanda ya koma duk ya rasa sukunin sa

Nan da nan ya nemi jirgin Nigeria, duk da bai samu ba sai can yamma, ya rasa inda zai saka kansa sai amsa calls yake yi daga ma'aikatan sa suna faɗa masa halin da ake ciki

PA ma har ya sanar masa, "yanzu haka Dady ma yana can wurin, kuma ya tambaye shi amma yace mishi ya koma company sabida kiran gaggawa da ya samu, don haka ya kamata ya san yanda zai yi yayi saurin dawowa tun kafin Dady ya fahimci ba ya ƙasar ma baki ɗaya."

Wani irin sabon rikice wa SHAREEF yayi, har wani zazzaɓi-zazzaɓi yake ji a jikinsa, gaba ɗaya ya rasa ƙwarin jikinsa, kawai tunanin halin da zasu shiga yake yi musamman Dadyn sa, tunda wannan dai ba ƙaramin asara suka samu ba, dole zasu kasance cikin tashin hankali. Ƙarshe airport ɗin ya je ya zauna tare da Haseena, sai da lokacin tashin su yayi sannan ya tafi

Basu kai Nigeria ba sai a washe gari kusan ƙarfe goma na safe, suka sauka a airport na Aminu Kano. Ya rasa ma inda ya kamata ya wuce, don ya san idan yace zai je gida yanzu akwai matsala, dole can Abujan zai wuce, tsaya wa yayi gefe ya nemi layin PA ya danna masa kira, a nan ya soma tambayarsa halin da ake ciki

PA ya faɗa masa, "har yanzu suna can har Dady suna wurin, dukkan su a can suka kwana, an samu damar kashe wutan tun jiya amma wurin yana nan cike da hayaƙi, su Mr. Pitter ma sun samu zuwa yau, kuma suna ta tambayar ina yake?"

Runtse idanu SHAREEF yayi yana tare mai Texi, ba tare da ya jira ƙarisan abun da PA zai ce mishi ba, sai yace, "ga shi nan zuwa yanzu."
Katse wayan yayi yana shiga Motan yace mishi, "ya wuce dashi Abuja drop zai yi, zai biya sa ko nawa ne."

Jin haka babu musu mai Texi ya kunna mota ya figa hanya, a murnan sa tunda kallo ɗaya ma da ya yi wa SHAREEF ya san cewa akwai maiƙo a wurin

SHAREEF wanda yake duban hanya yana ganin tamkar ba ta sauri Motan, sai yace mishi, "ya tuƙa da gudu sosai, ba ya son delay."

Ai kuwa sosai mai Texi ya ƙara wa mota gudu, kawai figan Motan yake yi kamar zai tashi sama

Amma shi SHAREEF gani yake yi kamar ba a sauri, gajen haƙuri irin nasa ya kasa yin shiru haka ya ƙara damun sa, "ya ƙara gudu fiye da wannan, don yana buƙatar su isa Abuja cikin ƙanƙanin lokaci."

Mai Texi yace, "gaskiya Oga sai dai kayi haƙuri, wannan gudun ma da nake yi ya isa haka nan in ba so kake yi mu tashi sama ba, ai komin saurin ka dole kayi haƙuri mu isa a hankali kar mu samu matsala."

Kasancewar wayan SHAREEF ɗin ta soma Ring, shiyasa bai saurari mai Texi ɗin ba, sai ma jan dogon tsaki da yayi yana ƙoƙarin amsa call ɗin wanda ya ga sunan Hanif ya fito ɓaro-ɓaro

A dai-dai nan kuma mai motan ya shige wa tirela da nufin wuce ta tunda ta kare musu hanya, amma sai aka yi rashin Sa'a ya gogi tirelan; ƙuuuuuu! Wani ƙara mai sauti ya biyo baya nan da nan murfin Motan da ke side ɗin drivern ta fice fit tare da na baya. Hakan ya ɗaga wa mai Texi hankali, wanda yayi ƙoƙarin ya kawar da motan tare da matsa wa daga jikin tirelan, amma halin ruɗe wa da ya shiga ya kasa, take motan ta haɗe da tirelan har ta kusa shige wa ƙasan ta, lokaci ɗaya suka yi mummunar hatsari a wurin.
[16/02, 9:47 am] OumƊahirah نفيسة: 🌱🌱🌱🌱🌱

      *SHAREEF*
          _SexyBoy_
🌱🌱🌱🌱🌱

_Writer: Nafisat Isma'il Lawal_
_Wattpad: UmmuDahirah_

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝*



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

       *P.W.A✍️*





*DATA SHARE*

Call, message or whatsap  07065334256

*MTN*
500MB 150
1gb  280
2gb.  560 
3gb.   840
4gb.    1120
5gb      1400
6gb.     1700
Verlid for 30 days.












__________
*BOOK1*
_______________*FREE PAGE33*
_____Tashin hankali! Bazan iya misalta muku irin tashin hankalin da iyayen SHAREEF suka shiga ba, sakamakon riskar su da labarin hatsarin sa ya je kunnen su. Dole Dady a ranan ya dawo Kano ya bar su PA a can da su Shuraihu, ya dawo wurin ɗansa hankali a tashe, duk da har lokacin ba a basu wani result na sakamakon abun da ya same su ba, amma an tabbatar drivern take ya mutu ko shura wa bai yi ba

Momy da Sadiq suna asibitin cikin tsananin tashin hankali, kallo ɗaya kayi musu ma ka san cewa sun yi kuka har sun gaji, kowanne a cikin su idanunsa jawur,
Har wasu daga cikin ƴan uwan Momy Maza sun zo wurin ana ta jira a ji me Likitan zai ce tunda har yanzu basu fito ba

Shi kansa Dady da ya iso wurin ya kasa natsuwa sabida ganin halin da iyalansa suke ciki, kallo ɗaya da yayi musu sai da zuciyarsa ta karye domin yana ji a jikinsa tamkar ya rasa ɗansa ne, tunda ya gama jin labarin irin mummunar hatsarin da suka yi, har an rasa drivern ma

Hankali fa ya tashi, sai dai kuma zuwan Doctor da bayanin da suka samu shi ya kwantar musu da hankali har suka iya jin sanyi a ransu, sakamakon bayyana musu da yayi, "SHAREEF yana raye har yanzu, sannan ba wani ciwo sosai ya ji ba Allah ya tsare shi gaskiya, kansa ne kawai ya bugu sai targaɗe da ya samu a hannu, sai kuma ƙananun ciwuka da ya ji a ƙafafunsa, amma jikinsa da sauƙi ko zuwa anjima zai farfaɗo."
Sai ya keɓe da Dady kuma ya sanar masa, "gaskiya da yiwuwar a sauya wa SHAREEF ƙodan nan da gaggawa tun kafin a samu matsala, because of this accident that caused the place to be slightly damaged, inda hali kafin a sallame shi a jinyar nan kawai a yi aikin a huta hakan zai fi."

Dady da ke cikin wani yanayi da jin abun da Likita yace, sai ya ja numfashi yace, "shikenan Doctor, yanzu ya kake tunanin zamu yi? Ko za a duba namu kidney ɗin ne sai a cire wanda zai yi?"

"No Alhaji, ai kai kana fama da kanka zai fi kyau dai a samo wani sai a cire nasa, kana fama da ciwon sigar and your wife also has high blood pressure, it would be better to find someone else and get tested, idan kuma za a samo na siya ka san akwai matsaloli irin wannan, sannan sai an kashe kuɗi sosai."

"Duk da muna cikin wani hali, kuɗi ba damuwa bane Doctor, a jaraba samo wa in zamu dace, ko nawa ne zan bayar, then I will go and see if we can find it at our place and you will hear Me."

"Ok no problems." Daga haka ya basa hannu sannan suka rabu.
***

_____Ƴan uwa da Abokan arziki suna ta zuwa duba SHAREEF duk da har yanzu bai farfaɗo ba, amma ana shiga duba sa, su Momy ma suna tare da shi ita da Aunty Najwa da ta zo tun da abun ya faru bata tafi ba

Sai da hayaniyar ya ɗan yi yawa ne sannan aka dena barin mutane suna shiga, sai suka dawo haraban ɗakin aka shimfiɗa tabarma su Momy suka zauna a wurin, a nan suka wuni har yamma suna wajen

Maryamu kuwa tana can makaranta bata san me ke faruwa ba, kuma lokacin tashin su yana yi Sadiq ya tafi ɗauko ta since Momy ta tuna masa, "in time yayi ya je ya dauko ta, ya wuce da ita gida."
Hakan kuwa yayi, kuma bai sanar mata da komai ba sai da suka koma gida ganin babu kowa yasa ta dame shi da tambayar inda Momy ta tafi?
Ce mata yayi, "ta je ta canza kayan ta ta ci abinci sai ya faɗa mata inda Momyn ta tafi, zai kaita can ne."

Cikin sauri kuwa ta gama kimtsa wa suka ci abincin tare tunda shima tun safe bai saka komai a cikin sa ba, sai yanzu ne da ya ɗan samu natsuwa shiyasa ya ci. Bayan sun gama yace mata, "Momy tana asibiti, Yaya SHAREEF ba ya jin dad'i, shi ne aka je duba sa."

Duk da bai faɗa mata ainihin mai ke faruwa ba gudun tashin hankalin ta, since ya san yanda SHAREEF yake a wurin ta, amma hakan bai hana ta rikice masa ba, sai ga hawaye sun soma gudu a kan fuskarta cike da rawan murya take cewa, "Yaya Sadiq, dama bai da lafiya ne? Don Allah me ke damun sa ka sanar min?"

"Calm down mana Maryam, ba fa na faɗa miki bane don ki tashi hankalin ki ba, SHAREEF yana cikin ƙoshin lafiya kin san dai ciwon da yake fama da shi; shi ne ya ƙara taso mishi aka kai shi asibiti a duba sa."

Shiru tayi tana hawaye, sai kuma ta sake duban sa tace, "to amma an ce ciwon ƙoda ba a warke wa, kenan zai mutu ya bar Ni? Wlh bazan iya rayuwa babu shi ba ina sonsa."

Ƴar dariya Sadiq yayi yace, "da can da kike rayuwa babu shi fa ya kika yi? Ki dena wannan sakarcin Maryam komai da kika ga yana faruwa muƙaddari ne daga Allah, har yanzu ke yarinya ce ba ki san so ba bare ki ce baza ki iya rayuwa babu shi ba, don haka babu wanda ya san gawan fari mu dashi gaba ɗaya, kuma ciwon da yake yi ana warke wa da zaran an yi masa aiki an canza mishi ƙoda zai samu lafiya bazai sake ciwo ba."

Jin abun da yace yasa tayi shiru ta kasa magana, yayinda jikinta yayi sanyi, sai ta kifa kanta a saman kujerar tana shashsheƙa zuciyarta na zafi tare da wani irin harbawa kamar zata faso ƙirjinta, gaba ɗaya jikinta ba ya mata dad'i har wani irin rawa yake yi

Shi kansa Sadiq yana mamakin yanda Maryamun take nuna soyayyarta a wurin Yayansa, gani yake yi kamar har da ƙuruciya har yanzu Maryamu yarinya ce bare ta san irin wannan soyayyar, amma kuma ganin halin da take ciki sai ya koma yana rarrashinta yana faɗa mata kalamai masu dad'i tare da bata tabbacin, "SHAREEF bazai taɓa mutuwa ba."

"Don Allah ka kaini in gansa, ina son ganin sa."
Ta furta tana fashe wa da wani irin kuka da ya kufce mata, "don Allah ka kaini wurin sa."

"Ki yi shiru mana, I told you jikinsa da sauƙi, su Momy ma suna can, ki zauna a gida idan ya dawo sai ki gansa zai fi."

Kuka ta ci gaba da yi ta kasa yin shiru, duk yanda ya so ya rarrashe ta amma ta ƙi amince masa ita tana son ganin sa

Shi yasa yace, "to ta je tayi sallan magriba tunda an kira, shima zai yi sai ya dawo su tafi, maybe ma kafin lokacin su Momy sun dawo."
Da haka ya samu tayi shiru har ya fice ya barta

Ita kuma ta shiga ɗaki da sauri don yin Sallan kafin ya dawo, har yanzu jikinta sai rawa yake yi kamar mazari, wani irin sara wa kanta yake yi ga wani irin yanayi da ke riskan ta duk a kan SHAREEF ɗin, har a ranta tana matuƙar tausayin SHAREEF, baza ta taɓa samun sukuni ba har sai ta gansa sannan hankalin ta zai kwanta, domin yanda zuciyarta take buga wa tana jin kamar akwai abun da ya same sa.
Alwala tayi ta fito, a time ɗin ta ji kamar an shigo da mota tun tana toilet, shiyasa tayi saurin fita don a tunanin ta su ne suka dawo,
Amma tana fita sai ta hangi Dady ne ya shigo falon ya nufi wurin steps ya tsaya yana amsa call,
Wurin sa ta nufa ba tare da shi ya ganta ba

Yayinda shi kuma ya ci gaba da wayan yana sanar da Doctor Umar yanda suka yi da Doctor kan ciwon SHAREEF

Tsab ta gama jin komai, hankalinta ya ƙara tashi, sai a lokacin ta fahimci cewan ashe hatsari yayi, kuka ta saka sosai a lokacin

Yayinda Dady ya juyo a rikice yana kallonta, don bai yi tsammanin ta a wurin ba, "daughter."
Ya kira sunan ta yana kamo ta hankali a tashe, "what's wrong with you? Wa ya taɓa ki yi shiru haka nan, ki yi shiru nace ki sanar min me ke damun ki kike kuka?"

Shiru tayi tana shashsheƙa but ta gaza yin magana, sai rawa da jikinta ke faman yi

Ganin yanayin da take ciki, sai ya kamo ta zuwa cikin falon ya zaunar da ita, tare da furta, "ina Sadiq ɗin? Ya aka yi ya bar ki ke kaɗai?"

"Dady ya je yin Sallah." Ta furta tana ci gaba da shashsheƙan kukan

Yace, "to ya isa, fada min me aka yi miki kike kuka? Ko tsoro kike ji?"

Girgiza kanta tayi tana sake matso wasu hawayen, a hankali ta furta, "Dady Yaya SHAREEF."

Sai a nan Dady ya gane musabbabin kukan nata, shiyasa cikin kula wa da tausayin ta yace, "SHAREEF yana nan lafiya zai samu sauƙi daughter, ba abun da zai same sa, yanzu haka jikinsa very easy har ya farka ma, kinji ki kwantar da hankalin ki ko zuwa gobe za ki je ki duba sa."

Kallonsa tayi idanunta jawur tace, "Dady amma ka ce sai an yi mishi aiki? Na ji kana faɗa a waya za a sauya mishi Ƙoda, don Allah Dady a saka mishi nawa ba na son Yaya SHAREEF ya mutu ya bar Ni."

Da mamaki Dady yake kallonta, sai yace, "Maryam ba yanda za a yi a cire miki ƙoda a saka mishi, ke yarinya ce ƙarama ki dena tayar da hankalin ki a kan wannan matsalar, ba wai an rasa ƙodan bane za a samu kuma za a saka mishi zai warke kamar kowa ya tashi kina jina? Kin yi sallah ma?"

Kanta ta girgiza mishi, sai kuma cike da sanyin murya tace, "don Allah Dady a saka mishi nawa wlh na amince zan ba shi nawa ƙodan, ai shi Mijina ne ina da damar da zan iya taimaka masa a rayuwa."

"Maryam ba ki da hurumin da za ki iya bada ƙodan ki ba tare da sanin iyayen ki ba, in fact ma ke amana ce a wuri na bazai yiwu haka kawai a cire miki ƙoda a saka wa SHAREEF ba. Ko kina da damar taimaka masa sai da sanin iyayenki. Ki bari zamu ga abun da hali zai yi, in ba a samu ba sai a cire naki a saka mishi, hakan yayi miki?"

Da sauri ta ɗaga mishi kai cikin farin ciki

Sai yayi mata murmushi yace, "yauwa to, je kiyi sallan ki dawo sai mu wuce asibitin ma ki duba sa."

Kafin ma ya rufe bakin; har ta amsa mishi ta tashi ta wuce da sauri

Yayinda ya raka ta da kallo yana mai ci gaba da mamakin yarinyar; da kuma wani irin tausayinta da ya kama shi don ya san cewa yanda take ƙaunar SHAREEF har zuciyarta; shi ba ya mata haka, dole zata sha wahala yarinyar, bai san meyasa SHAREEF ya tsane ta ba, kuma shi ba wata budurwa ce da shi ba bare yayi tunanin hankalin sa yana a kanta ne, amma koma dai mene ne bazai taɓa barin SHAREEF ya wulakanta ta ba, ko yana so ko ba ya so sai ya zauna da ita, auren su mutu ka raba ne babu saki a tsakani, Maryamu ita ya zaɓa wa ɗansa SHAREEF

Mike wa yayi ya wuce saman da sauri yayi alwala, sannan ya fito ya wuce masallaci

A tare suka dawo da Sadiq suka tarar da Maryamu tana faman jiran su, shiyasa Dady yace, "su wuce gaba ɗaya zuwa asibitin."

Bayan sun je lokacin Momy ne kaɗai a wurin sa, itama idar da sallanta kenan tana zaune tana lazimi,
Shi kuma SHAREEF ɗin yana kwance a saman gado, sai dai idanunsa biyu amma ya rufe su, jin shigowar su Dadyn ne ya buɗe idon yana kallon su

"My son, ya jikin naka?"
A cewar Dady yana bin sa da kallo tare da shafa masa kai

Murmushi yayi yace, "alhamdulillah Dady."

Sadiq shima ya jikin yayi masa yana ƙara matsowa kusa dashi

Ya amsa cikin kula wa yana kallonsa, har yanzu da ɗan guntun murmushin sa

"Taho nan daughter ki yi masa sannu da jikin, Sadiq janye jikinka tunda ka gaishe shi." Cewar Momy tana kamo hannun Maryamu da ke bayansu

Tunda SHAREEF ya ɗaura ido a kanta sau ɗaya bai sake kallonta ba

Yayinda ita kuma ta matso sosai wurin sa, duk idanunta sun kaɗa sun yi jazur kowa ya kalle ta ya san tayi kuka, muryanta ma a raunane take yi wa SHAREEF ɗin sannu

Amma bai amsa ba sai da Momy tayi masa magana sannan ne ya amsa ta a daƙile. Dukkan su sun fahimci yanayin da ya amsa mata tamkar ba ya so, sai dai ba wanda yayi magana a cikin su, sai Momy ne da ta koma tambayar Maryamun dalilin yin kukan nata sabida ganin yanda idanunta suka yi

Sadiq yace, "ai Momy tunda na sanar mata ta tayar da hankalin ta tana ta kuka wai sai na kawo ta." Ya ƙare maganar yana ƴar dariya
       

Ita kuma ta harare sa tana cewa, "to wa yace ka faɗa mata don ƙaniyar ka? Cewa nayi fa ka ɗauko ta a school ba wai ka sanar mata halin da yake ciki ba, yanzu ga shi nan ka saka min ita kuka." Sai ta ƙara kallon Maryamun da a yanzu take shirin yin wani kukan, don har idanunta sun cika da hawaye ta kasa jure wa, "kar dai a ce wani kukan za ki sake yi? Ya isa haka Maryam ba ki ga ya samu sauƙi bane?"

Gyaɗa kanta tayi tana saurin saka hannunta; tare da share hawayen da har sun sauka a kan fuskarta

While SHAREEF kamar ya maƙure yarinyar haka yake ji; sabida yanda ya ga iyayen nasa sun raja'a a kanta suna bata baki, nufin ta kenan don shi take kukan? Tsaki ya ja a ransa yana lumshe idanunsa tare da sake jin haushin ta sosai,
Allah ya gani ya tsani yarinyar wlh, bai san meyasa ba duk idan ya kalle ta haushi da ɓacin rai; gami da zallan tsanar ta yake ƙara tasiri a zuciyarsa, in so samu ne ya dena ganin ta gaba ɗaya a cikin rayuwarsa, don shi ba ya son abun da zai takura sa bare ya saka mishi damuwa a tare da shi, har yaushe ma wannan ƙanƙanuwar yarinyar da yake ganin ta ƙaramar alhaki; har yaushe ta san soyayya?

Bayan sun gama rarrashinta ne Momy take sanar da Dady zuwan Hanif da ya dage sai ya dawo, "don haka gwara ya kira sa yayi mishi magana don ita ta hana shi amma yace sai ya dawo."

Dady yace, "ok zan kira shi, ai bai kamata ya dawo ba since jikin SHAREEF ɗin da sauki, zan kira sa muyi magana, bari in je wurin Doctor in dawo."

Daga haka ya fita ya bar su a ɗakin. Sadiq ya zauna a gefen ƙafafun SHAREEF

Ita kuma Maryamu tana saman kujera wacce Momy tace ta zauna a kai. Sai kallon SHAREEF ɗin take yi zuciyarta cike da tsananin tausayin sa, musamman yanda ta ga bandage na kansa da aka sanya mishi duk ya jiƙe da jini, wani yawu ta haɗiye mai kauri tana lumshe idanunta, jin wasu hawayen suna shirin fito mata shiyasa tayi saurin buɗe idon don ba ta buƙatar Momy ta sake fahimtar tana kuka. Karaf idanunta suka shige cikin nasa da shima ya buɗe ya aza a kanta,
Wani irin kallo ya watsa mata wanda yasa lokaci ɗaya ta ɗauke nata idon a kansa, sosai take jin bugun zuciya kamar ana zare mata laka daga jikinta, bata sake ɗago kai ta kalle sa ba bare tayi magana, wani irin kuka ne yake son kufce mata, bata san meyasa Yaya SHAREEF ba ya ƙaunarta ba, amma me tayi masa a rayuwa? Hakan na saka ta ta ji zuciyarta tana mata zafi sosai, tana son tayi abun da zai so ta sosai, tana son tayi rayuwa dashi, baza ta iya jure wannan yanayin ba, ba ta son yana nuna mata tsana, tana son ya kasance kusa da ita domin samun farin ciki a zuciyarta, ko kallonsa yanzu ya hana ta yi, tsoron kallonsa take yi don kar ta ɓata mishi rai, amma ya zata yi?

Har suka tashi tafiya ta kasa sakin jikinta a wurin, sabida da zaran ta ɗago kanta sai sun haɗa ido dashi yana sakar mata mummunar kallon nan nasa da ke faɗar mata da gaba, har tsoron kar ya furta wani abu a kanta take yi don ta san tsab zai iya zagin ta ko yace tana kallonsa, shiyasa duk ta kasa sakin jikinta,
Har suka tashi tafiya aka bar Sadiq a wurin sa tunda shi zai kwana dashi,
Daga nan suka wuce gida

Basu tsaya wani hira ba Momy tace, "ta je ta kwanta."
Haka nan babu yanda ta iya dole ta tafi ɗaki ta kwanta, duk da tana jin barci bazai taba zuwan mata ba saboda halin damuwar da take ciki, da kuma tunanin SHAREEF da ya gallabe ta

Dady kuma bai ɓoye wa Momy komai ba halin da ake ciki, a kan zancen Doctor tunda bata san da maganar ba, yanzu dole sai dai su tashi tsaye da yin masa addu'a don ganin an dace an yi aikin nan lafiya, sannan ya faɗa mata abun da Maryamu tace duk da bai ɗauki maganar nata da wani muhimmanci ba

Haka zalika itama Momy, don ta san bazai yiwu a ce Maryamu ce zata bada ƙodan ta bA, ko ma dai mene ne zasu san yanda za a yi a samu kafin kwana biyu da doctor ya ɗiba musu

Amma kuma me? yanda Maryamu ta ga rana haka ta ga dare a ranan, gani take yi kamar in tayi wasa bata taimaki SHAREEF ba zata iya rasa shi a duniya, gani take yi tana da hanyar taimaka masa, wataƙil ma idan aka cire wani abu a cikin jikinta aka sanya mishi zai ƙaunace ta, domin ta sha jin labarin irin hakan, idan aka cire wani abu daga cikin mutum aka sanya wa wani, to jinin su zai haɗu su ji suna ƙaunar juna matuƙa, hakan ya bata ƙwarin gwiwa da tunanin dole sai dai a cire nata ƙodan a saka mishi, baza ta taɓa bari a saka mishi na wani ba tunda ita take sonshi, kuma ta tabbata in har aka sanya mishi zai ji a ransa yana sonta sosai, ko bai san ita ta ba shi ba zai iya ƙaunarta. Don haka da safe ƙin shirya wa tayi ta tafi makarantar, ta sami Dady har da kukan ta a kan, "a cire nata don Allah a saka mishi, wataƙil zai so ta in wani abu nata yana yawo a jikinsa."

Su kansu mamaki ne ya kusa kashe su da zancen Maryamu, don gani suke yi tamkar bata da hankali akwai wauta a tare da ita, don an cire ƙoda an saka wa SHAREEF ba hakan ke nufin zai so ta ba, duk yanda suka so su fahimtar da ita amma ta ƙi gane wa; kuka sosai take musu sun rasa yanda zasu yi da ita

Wannan wanne irin soyayya ce Maryamu take yi wa SHAREEF? Dady yace, "Maryam ko ba ki ba shi ƙodan ki ba ke Matar SHAREEF ne, babu mai raba ku sai mutuwa, don haka ki kwantar da hankalin ki za a yi mishi aiki ba sai an taɓa lafiyar ki ba."

Kuka ta fashe da shi tare da furta, "don Allah ku taimaka min ku saka mishi nawa, wlh zan fi samun farin ciki muddin ƙoda na ta shiga jikinsa, ina matuƙar sonsa, bazan bari a saka mishi na wani ba, Ni ce Matarsa zan iya taimaka masa Ni dai na amince a saka mishi ƙoda na, Ni ba sai kun sanar da iyayena ba wannan sirri ne daga Ni sai shi, ba na son kowa ya sani ku taimaka min kar ya mutu, idan ya mutu nima mutuwa zan yi."

Yanda ta fita hayyacin ta tana musu kuka kamar ranta zai fita, dole suka amince a kan sun yarda da maganar ta, sannan fa suka samu kanta, sun rasa ma yanda zasu yi da ita, duk da basu so hakan ba amma gani suke yi soyayyar da Maryamu take yi wa SHAREEF yayi yawa, sannan ma kasancewar ta Matarsa basu da yanda zasu yi tunda ta matsa sosai, ga halin da take ciki duk ta haukace musu

Bayan Dady ya je wurin Doctor ya sanar mishi da samun kidney ɗin, amma yayi masa bayanin, "ƙaramar yarinya ce in da wata matsalar da za a samu ya faɗa masa, yarinyar ce ta nace dole sai nata za a saka tunda Mijinta ne, baza ta yarda a saka mishi na wani ba."


Shi kansa Doctorn yayi mamakin yarinyar musamman da ya ganta, duk da babu wata matsala don har ya sanya musu ranan da za a yi aikin nan da gobe insha Allahu, tunda an samu baza a tsaya wani jira ba.
  
[18/02, 7:18 am] OumƊahirah نفيسة: 🌱🌱🌱🌱🌱

          *SHAREEF*
            _SexyBoy_
🌱🌱🌱🌱🌱


_Writer: Nafisat Isma'il Lawal_
_Wattpad: UmmuDahirah_

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝*



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

       *P.W.A✍️*





*DATA SHARE*

Call, message or whatsap  07065334256

*MTN*
500MB 150
1gb  280
2gb.  560 
3gb.   840
4gb.    1120
5gb      1400
6gb.     1700
Verlid for 30 days.













__________
*BOOK1*
_______________*FREE PAGE34*
_____A washe gari kamar yanda Doctor ya saka ranan da za a yi aikin, 
the operation was done successfully, and everything is fine, there are no problems, inda kowannen su an ajiye sa a ɗaki daban kuma ana basu kula wa

Duk da an yi aikin amma su Dady basu sanar ga wanda ya bada ƙodan ba, domin suna gudun surutun mutane musamman dangin Momy da ba sa iya gani su ƙyale, sun cika gutsiri tsoma, kawai an fada musu an siya ne daga wurin wani Mutumin da yake buƙatar kuɗi, duk da haka dai ana ta ƙananun maganganu

Ita dai Momy bata ce komai ba, domin ko yan uwanta da suke ciki ɗaya bata faɗa musu gaskiyar zancen ba

Sadiq shi ke zama a wurin Maryamu in Momy tana ɗakin SHAREEF tare da mutane, shiyasa babu wanda zai fahimci wani abu

Bare jikin Maryamun ma da ɗan sauƙi, don ita kwana ɗaya tayi ta farka, sai dai ba ta iya yin komai sai an yi mata, in fact ma ba ta gane wasu mutane

Shi Dady ba ya zama saboda wannan kwangilar da suka ɗauka, da kuma asarar da suka samu na ƙonewar kaya, yayinda Turawan sun matsa a kan aikin su, don su basu damu da wata asara ba, ba sa son lokaci ya ƙure ba a fara musu aiki ba, shiyasa Dady yake zuwa Company, inda har ya yanke hukunci dole ya sako su Alhaji Inuwa suka yi raba dai-dai a kan hannun jarin, tunda ba su da yanda zasu yi, an rigada an ja musu asara sun rasa dukiyar su, sannan ko yace zai siyar da ƙadarorin sa za a ɗan ja lokaci, shiyasa da su Alhaji Inuwa suka kawo mishi ƙoƙon baran su na cewan, "a basu hannun jari zasu biya nan take, don a ci gaba da aikin gadan-gadan." Bai ja wata gardama ba ya amince da bukatar su, tunda duk taimakekeniya ce, sannan shi Dady ba kamar SHAREEF yake ba, yana da sauƙin kai, in dai wani zai samu a harkan ba ya ma Mutum baƙin ciki, gwara kowa ya ƙaru, tun farko shi bai ma san da zancen ba; tunda a tunanin sa Companin sa kaɗai aka siyar wa da hannun jarin gaba ɗaya, babu masu bukata, abun da SHAREEF ya faɗa masa kenan, kuma yayi murna tunda ba ƙaramin ci gaba zasu samu ba, amma kuma sai ga shi yanda Allah ya kasance komai muƙaddari ne.
***

_____Inda su Alhaji Inuwa suka yi farin ciki matuƙa da samun nasarar nan, tunda already su saka yi kurɗa-kurɗan da suka yi suka ƙona kayan; tare da taimakon Shuraihu

Babu wanda ya kawo zargin cewa da sa hannun magauta a wannan gobarar, Mahmud shi kansa da farko ya so ɗaura zargi tunda ga abun da ya faru, yana ji a ransa dole da saka hannun su Honourable Ja'e a gobarar nan, amma kuma kasancewar bai sanar da SHAREEF tun farko ba, sannan bai da wata hujjar da zai iya cewa su ne, shiyasa ya bar abun a cikin sa, duk da ya samu Shuraihu da zancen yana faɗa masa, "yana tunanin ko su ne suka aikata hakan domin su samu cikan burin su, tunda ga shi nan sai da hakan ta kasance, daga karshe sun samu hannun jari a ciki, shi dai yana zargin su, kuma dole su tsaurara bincike domin samun hujja mai ƙarfi, daga nan su gabatar wa da SHAREEF."

Shuraihu yace, "a'a; gaskiya ba na tunanin da saka hannun su, taya kake tunanin zasu iya ƙona miliyoyin kaya irin haka; ba tare da asirin su ya tonu ba? Ni dai ina kyautata zaton gobara ne kawai daga Allah, kuma ƙarshe baka ga yanda komai ya zama toka bA? Abun mamakin ya za a yi kaya irin waɗannan su zama toka har da abubuwan da wuta ba ta cin su? Mahmoud kar mu saka kanmu inda zamu kasa fitar da kanmu, Alhaji Inuwa da Honourable Ja'e ba ƙananun mutane bane, muddin muka ce zamu shiga gonan su daga ƙarshe mu zamu kwana a ciki, mu bar maganar nan."

Mahmud yace, "shikenan, dama nima ba wai nace wani abu bane, kawai hasashe na ne ya kawo hakan, tunda ga yanda suka sha alwashi sannan komai ya kasance yanda suke so."

"Mu bar maganar nan don Allah, Ni bari in wuce."

Mahmud kuma har zuciyarsa ya kasa barin zancen, kuma tabbas yana ji a jikinsa su suka aikata hakan, dole zai yi bincike sannan zai sanar da SHAREEF da zaran ya samu lafiya.






🔆🔆🔆🔆🔆🔆🔆🔆

_____Almost two weeks suka yi a asibitin before a sallame su, jikin da sauƙi but koda suka koma gida sun ci gaba da shan magungunan su ne

SHAREEF shi bai san cewa ƙodan Maryamu aka sanya mishi ba, in fact ma bai damu ya sani ba tunda a gaban shi a asibiti ya ji Momy tana yi wa wasu daga cikin dangin ta bayanin yanda aka yi aka samu, to a tunanin shi da gasken siya aka yi, shiyasa bai damu da maganar ba, bai san ma Maryamu bata da lafiya ba sai da suka dawo gida, kuma bai tambaya ya san me ke damunta ba since ba ta gabansa a yanzu,
A halin yanzu farin ciki yake yi kasancewar Haseena ta ce, "zata zo gaishe shi, zuwa gobe ko jibi zata dawo."
Hakan yasa yake farin ciki tare da tunanin gabatar da ita wurin iyayensa don su san wacce yake ƙauna, inyaso da zaran ta dawo hutu sai a yi musu aure, tunda abun yana ransa ba ƙaramin bukatar aure yake yi ba a wannan gaɓar

Itama Maryamu tunda jikin da sauƙi a washe gari Sadiq ya kaita school

Kawayenta su Feena ba ƙaramin tausaya mata suka yi ba, don kallo ɗaya da suka yi mata sun ga ta rame sosai, har haske tayi ta ƙara fresh sai hucewar mura a gefen bakin ta, koda gani ka san tayi jinya sosai

Amina ta kalle ta tace, "I'm sorry friend, wlh mun so zuwa gida mu duba ki amma Allah bai yi ba, ga shi har kin ƙare rashin lafiyar ki bamu zo ba, bamu kyauta miki ba."

Feena itama tace, "kiyi haƙuri don Allah, Nima tun ranan da muka zo asibiti duba SHAREEF Ni da Mamana; sai na tambayi Momy ina kike? take fada min ba ki jin daɗi kina gida, kuma wlh mun so zuwa Ni da Amina har gida, bamu samu mun zo ba, I'm sorry bamu san cewa ciwon yayi miki tsanani haka ba." Ta ƙare maganar kamar zata yi kuka ta kamo hannun Maryamu

While Maryamu sai tayi murmushi tace, "don't worry, na samu lafiya, nima ba wai sabida ciwona na ƙi zuwa school ɗin ba, kun san rashin lafiyar Yaya SHAREEF ne yasa ko na zo bazan fahimci komai ba, shiyasa nayi zama na."

Amina wacce ta ɗan harare ta na wasa tace, "ok kuma don shi sai ki ƙi zuwa school? Ba na tunanin haka ke ma daga gani kin ji jiki sabida duk kin sauya, Allah dai ya baku lafiya."

"Amin ya Allah. tnx U."

Sai suka ɗan yi shiru dukkan su

Sai kuma Feena tace, "karatu fa ya wuce ki da yawa, kuma Ofer week zamu fara tests, ya kamata ki yi copyn note."

Ɗan yatsina fuska tayi tace, "Allah me can't, leave Me alone da abun da yake worries me."

Dariya suka yi saboda jin turancin nata

Sai Amina tace, "to me ke damun ki? Na kula fa ba kya son karatu Maryamu? Ba tun yau ba na kula da ke."

Hmm kawai tace batare da ta furta komai ba

While Feena tace, "ai kuwa ya kamata ki dage so that mu zama masu hazaƙa more than anyone else in this class, don wlh Yaya Hunaip sai da ya gargaɗe Ni in har ban ci na ɗaya ba zai haɗa Ni da Abba a kaini boarding school."
Ta ƙare maganar tana ɗan kwaɓe fuska

Maryamu kuma dariya ta fashe mata dashi, tace, "lallai! Ki ce za ki je ki sha gwale-gwale kenan? Kina shan garin kwaki kullum; da yin ma ƙattin banza aiki, ai Ni wlh in da za a kai Ni makarantar kwana sai na gudo, ina zan iya da wahala? Ai kalata ma ba na wahala bane, haka kawai in je in lalace in ƙara baƙi, tab! Bazan iya ba." Sai ta taɓe baki tana ɗan kallon monitorn ajin da ya tashi yana musu announcement

Daga Feena har Amina kuwa murmusawa suka yi jin zancen Maryamun; da mamakin iyayin ta, sai kuma suka mayar da hankalin su kan monitorn batare da sun furta komai ba suna sauraron sa

Inda yake sanar musu bayanin Malamin Maths da zai shigo musu aji yanzu, wai zai yi musu text a yau, don haka su shirya da kyau

"Wayyo! Akwai matsala fa, gaskiya dole mu duba littafi idan ba haka ba ban san me zan rubuta ba."
Cewar Amina tana saurin ɗauko Jakarta tare da zuge wa

Haka itama Feena tana cewa, "ba ke kaɗai ba, na rantse ban iya komai a maths ɗin nan ba, in fact ma ba na gane karatun sa kwana biyu, ya zamu yi?"

Yanda suka ruɗe but Maryamu ko a jikinta, don ita bata damu ba, su kenan da suke zuwa makarantar bare ita da ba ta zuwa, ita har yanzu a cikin darussan bata tsinta komai ba a ciki; duk da kuwa Sadiq yana koya mata wasu abubuwan, amma ba kasafai take gane wa ba ta fi gane na littafan islamiyya, kuma kawai rashin mayar da hankali ne tunda SHAREEF ne a ranta ba komai ba, ita a yanzu ji take yi karatun ma ya fita a ranta, Ada tana burin tayi karatu mai zurfi ta zama wata aba a ƙasar ma, amma yanzu ba ta sha'awar karatun, burin ta kawai ta ganta a gidan SHAREEF, ya ƙaunace ta shi kaɗai ta fi buƙata

Ganin suna duba littafi all class ɗin, but ban da Maryamu, shiyasa su Feena suka yi mata magana. Hakan yasa ta ciro littafin ta tana duba wa tare da sauraron nasu karatun in suna solving maths ɗin, kawai jin su take yi amma bata wani gane wa

Har Malamin ya shigo class ɗin tare da solver musu na yau, bayan ya gama ya goge ya rubuta musu text ɗin a wanda yayi musu a yau

Shi yasa ƴan ajin suka ji daɗi sosai tunda sun mayar da hankali sun fahimta, sai suka ga abun da sauƙi kuma tunda a na yau kaɗai yayi musu questions

Maryamu dai sai dai ta kwafa na su Feena, tunda su suka yi kokari suka solver kayan su, ita kuma ta kwafe ta bayar

After sun fita break ne; Amina take mata faɗan, "ta mayar da hankali a kan karatu, don gaskiya ta kula kamar ba ta son karatun."

Ita kuma tace, "ai kamar kin sani, don Ni ba shi ne a gabana ba yanzu."

Har haɗa baki suke yi wajen tambayar ta, "mene ne a gaban nata in ba karatun ba?"

"Ba sai kun ji ba, kawai ku share."

Feena tace, "ba abun in ce Yayana bane a gaban ki; since na san bai faɗa miki yana son ki ba, da sai in ce shi kike tunani."

"Wanne Yayan naki?" Maryamu ta tambaye ta da ɗan mamakin ta

"Yaya Hunaip mana, ko ba ki fahimci yana sonki bane? Ai Ni tuni na gano, kuma don an kira sa a wurin aiki ne na tabbata da tuni ya sanar miki."

Cike da farin ciki Amina tace, "haba dai Feena? Da gaske kike yi don Allah?"

"Wlh kuwa, na kula, shiyasa nima nayi farin ciki matuƙa, zan so a ce Yaya Hunaip ya auri Maryamu wannan zai ƙara mana zumunci, haka nan Allah ya haɗa jinin mu, wlh I'm so excited."

"Tab! Ina zan saka babban Mutum kamar wannan Feena? Allah ba na sonsa, in kai shi ina to?" Ta ƙare maganar tana ƴar dariya

Sai duk suka tsaya suna kallonta, gaba ɗaya basu ji dadin maganar nata ba; musamman ma Feena

Ita kuwa Maryamu ko a jikinta, don a ganinta bata yi wani abun da bai dace ba, sai ma ci gaba da kwatanta Hunaip ɗin da take yi, tana cewa, "ai yayi mata ƙato, wannan in ma auren kauye ne yayi ƴa kamar ta, in fact ma tana tunanin ya girmi Babbar Yayarsu Ummita, don dai ita Mace ce amma ta tabbata da namiji ne itama zata kai kamar shi. Har da furfura fa ya soma."

Amina tace, "kai Maryamu, wasa-wasa fa ba ki da mutunci, a fakaice dai kin zauna kina ci wa Feena mutunci ne, ko ma meye a zuciyarki bai kamata ki faɗa a gabanta ba, Yayanta ne kuma dole zata ji haushi."

Ita kanta Maryamu sai a lokacin ta gane suɓul da bakan da tayi, sai jikinta yayi sanyi saboda ganin yanda Feenan tayi, "I'm sorry, don Allah ki yi hakuri, ban yi hakan don ɓata miki ba, ki yi hakuri in kin ji zafi."

Murmushi Feena tayi tace, "don zafi na ji zafi, but ba yanda zan yi ai, Allah yasa hakan shi ya fi alkhairi tunda alamu ya nuna ba kya son Yayana." Sai ta sauya maganar da faɗin, "mu je mu zauna mu ci abincin mu before a kaɗa class."

Babu wanda ya sake magana, haka suka wuce inda suka saba zama suka zauna.
***

_____Tun karfe biyu Haseena ta kira wayan SHAREEF ta sanar mishi da saukarta a jirgi, wani irin farin ciki ne ya cika sa, jiki na rawa ya miƙe yayi wanka ya shirya cikin farin yadi wanda aka yi masa design da brown colour a gaban, haka nan yayi using hula and wrist watch din sa kalan design ɗin, wani irin kyau yayi fiye da koyaushe, don ba ƙaramin ɓata lokacin sa yayi wurin ƙalƙale jikinsa ba kamar zai je gasar kyau, don yanda ya fito tsab-tsab gunun sha'awa, duk wacce ta kalle sa baza ta so ta ɗauke ido a kansa ba tsaban haɗuwar da yayi, SHAREEF ba baya ba wajen daukar gayu, uwa uba kyawun da Allah ya basa, sai wani sihirtaccen ƙamshi mai daɗi yake fitar wa daga jikinsa, ga wani annurin farin ciki a tare dashi, tsab ya gama shirya wa ya sauka ƙasa ya samu Momy ita da Sadiq a falon

Su kansu sai da suka saki baki suna kallonsa don kyawun da yayi musu

Mom tace, "SHAREEF wannan kwalliya haka? Ina kake ƙoƙarin zuwa kai da baka gama jin sauki ba?"

Murmushi yayi yana zuwa ya zauna a gefenta tare da furta, "Mom akwai baƙuwar da zata zo duba Ni ne, shiyasa kika ga nayi wannan kwalliyan."

Ɗan waro ido tayi da mamaki tace, "ban gane baƙuwa ba? Wace ce?"

"Oh! Mom in ta zo za ki ganta, but a yi mata wani abun don ta kusa zuwa Please."

Sakin baki tayi tana kallonsa, sai tace, "SHAREEF wai wace ce wannan? Baka taɓa irin wannan zumudin don zaka yi baƙi ba, in fact ma baka taɓa kawo Mace nan ba and kuma kana zancen Mace? Wace ce ita a wurin ka?"

"Mom in ta zo za ki ganta, but sai ta zo zan faɗa miki wace ce ita. I will give you a big surprise."

Sadiq da ke dariya ƙasa-ƙasa, sai yace, "Yaya anya ba Auntyn mu ba ce? Wannan kwalliyan da kayi mata dole Auntyn mu ce zata zo i know na ji a raina."

Hararansa ya ɗan yi yace, "kai ban son wasa fa, Please tashi ka je ka gyara min ɗaki na; na hargitsa, ka fito da farantin abincin nan."

"Ok Yaya."
Ya amsa masa yana tashi da ɗan tsallen sa ya wuce

While Momy ita kuma ta kalli SHAREEF fuskarta babu wasa tace, "SHAREEF faɗa min gaskiya, wace ce yarinyar? Meye haɗin ka da ita?"

"Mom, she's my girlfriend, and I have been with her for a while, zata zo duba Ni ne that's why today I will introduce her to you, kuma Momy gaskiya ita nake burin aura, that's why nake son yau ta zo ku ganta cuz I need to marry her soon."

Kasa magana Momy tayi da jin bayanan sa, sai tayi shiru kawai tana kallonsa kamar zata haɗiye shi da manyan idanuwan nan nata masu firgita shi

Shima sai ya kasa ƙwaƙƙwaran motsi sabida kallon da ya ga tana masa, take ya soma jin jikinsa ya fara sanyi tare da fargaba a zuciyarsa, don ya san irin wannan kallon na Momy ba kasafai take masa ba sai da dalili.
[19/02, 9:35 am] OumƊahirah نفيسة: 🌱🌱🌱🌱🌱

          *SHAREEF*
               _SexyBoy_
🌱🌱🌱🌱🌱


_Writer: Nafisat Isma'il Lawal_
_Wattpad: UmmuDahirah_

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝*



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

       *P.W.A✍️*





*DATA SHARE*

Call, message or whatsap  07065334256

*MTN*
500MB 150
1gb  280
2gb.  560 
3gb.   840
4gb.    1120
5gb      1400
6gb.     1700
Verlid for 30 days.












__________
*BOOK1*
_______________*FREE PAGE35to36*
_____Riga da skirt ne a jikinta waɗanda suka kama ta sosai, tare da bayyana mata tsarin halittar jikinta a sarari, tayi makeup a kan fuskarta wanda ya tafi da zubi da kyawun fuskar, sai ta sanya hill shoes masu kala da hangbag ɗin ta da ta ɗauka, komawa gaban mirrorn tayi tana sake feshe ko'ina na jikinta da turare; before ta fita a ɗakin, ta sauka downstairs, ganin babu kowa a falon shiyasa ta koma saman; ta shiga ɗakin Umman su tana kwaɗa mata kira

Umma da ke shirin fitowa itama, sai tace, "wai har kin shirya Haseena?"

"Yes Umma, yanzu zan tafi."

"Haba! Ba dai a haka za ki tafi da wannan figegen gyalen ba, ko kin manta gidan surukai za ki je?"

Kwaɓe fuska tayi tana faɗin, "Umma, what is the crime of my entering?"

Hararanta tayi tace, "ke yanzu ba ki ga yanayin shigan da kika yi ba? Ban so kika saka waɗannan kayan ba, kamata yayi ki saka kayan ki na Hausawa zai fi ƙaro miki ƙima da daraja a wurin su, kuma dole ku tafi da Haajara since ba ke kaɗai za ki je ba."

A yangance tace, "kai Umma Ni fa bazan sauya shiga na ba, a haka zan tafi, and kuma baza ta bi Ni ba, ki bari in tafi Ni kaɗai."

"No baza ki je ke kaɗai ba, meyasa ba kya jin magana ne Haseena? Gidan surakai ne ba gidan wasu ba, ki jira Ni in kira Haajaran ta shirya ku tafi tare, na gama magana."
Ta ƙare maganar tana wuce ta ta fita

Itama Haseenan sai ta bi bayanta tana cewa, "gaskiya Umma kina da matsala, yanzu ga shi za ki ɓata min lokaci; har sai na jira ta ta shirya kenan?"

"Ai ba jima wa zata yi ba, ki je falo bari in yi mata magana."

"No Umma, mu je tare ta ga tsawo na zata fi saurin shirya wa."

Haajara na ɗakin ta ta saka disko tana cashe wa, duk ta haɗa gumi sai girgiza jiki take yi, ganin sun shigo mata ɗaki sai ta tsayar da rawan tana kallon su

Before tayi magana Umma tace, "ana ta sana'ar? ba ki da aiki sai rawa, ke kenan ba kya gajiya ko?"

Dariya tayi tana ɗan juya mazaunan ta, tare da nufan wurin EMP ta kashe tana juyo wa wurin su da faɗin, "wai Aunty Haseena ba ki tafi ba?"

"Tare zaku tafi ki raka ta, tunda kin san gidan surukai ne baza ta tafi ita kaɗai ba, ki shirya ku tafi."

Washe baki tayi tace, "Ok! Dama wlh na gaji da zama wuri ɗaya sai ka ce tsautsayi, bari in shirya yanzu."

"Don't waste my time tunda Umma ta nace sai kin bi ni, hurry up and get ready or I will leave you." Tayi maganar fuska a ɗaure tana nufan wurin gadonta zata zauna

Tsalle Haajara tayi tace, "yanzu kuwa Aunty, faka-faka zan yi in shirya."
Sai ta ruga a guje ta nufi hanyar toilet tana zura takalman ta

While Umma kuma da ke duban Haseena tace, "amma za ku yi mishi siyayya ko? Ya kamata ku shiga shop ku siya wani abun ku riƙe zai fi."

"Ok Umma, I will do."

Juya wa Umma tayi ta fice a ɗakin.

    

🔆🔆🔆🔆🔆🔆🔆🔆

_____"Mom, you keep quiet and not say anything?" Ya furta a sanyin murya da tsinkewar zuciya

"SHAREEF dama kana soyayya ne? Kuma tun yaushe kuke tare da yarinyar?"

murmushi ya ɗan saki irin na kunyan nan, sai ya shafa ƙeya yana furta, "mun jima Mom, i think zamu kai two to three years."

"Shi ne baka taɓa sanar mana ba? Kuma ka san kana soyayya amma ka kasa fito da Mata kayi aure? Wannan wanne irin shirme ne?"

Kamar zai yi kuka a yanzu yake kallonta, sai yace, "to Mom mene ne laifi na?"

Shiru tayi saboda itama bata san meyasa ta ɗauki zafi haka ba, amma tana jin cewa hakan yana da nasaba da tuna auren Maryamu da ke kansa, ɗan gyaɗa kanta tayi before tace, "shikenan Allah ya kawo ta lafiya."

Wani irin farin ciki ne ya cika sa jin Mom ta karɓi zancen, ya san ba shi da wata matsala, kuma ya san zasu amshi zaɓin nashi

Yayinda Mom kuma tunani ne a cikin ranta, jikinta yayi sanyi, bata san cewa ɗanta yana soyayya ba, kuma ga dukkan alamu a yanda ta fahimci yana wannan zumuɗin dole hakan zai nuna akwai soyayya mai ƙarfi a tsakanin su, amma dole ne suyi wani abu, bari dai yarinyar ta zo su ganta, sannan sai suyi tunanin yanke hukunci, ko ma dai mene ne yanzu dole ya san cewa akwai auren Maryamu a kansa, ba bukatar kuma kawo wata a cikin rayuwarsa


Tashi Momy tayi ta je ta haɗa musu drinks, tunda babu abinci a gidan sai ta ɗaura musu taliya

Har ta kusa gama komai before suka iso gidan, da kansa SHAREEF ya fita ya tarbo su fuskarsa yalwace da farin ciki saboda tozali da yayi da Haseena. Har cikin falo ya kawo su suka zauna, babu kowa sai sanyin ac da ƙamshi da ke tashi a cikin falon, komai neet gunun sha'awa,
Su kansu gidan ya burge su tunda Haseena bata taɓa zuwa ba, yau ga ta a gidan su SHAREEF

Zuwa yayi ya kira Momy da kansa tunda bata fito ba tana kichen, ita kanta ta jinjina irin zumuɗi da farin cikin da ya cika sa a time ɗin, shi da kansa ya ɗauki tray na abincin ya fita musu da shi ko kunya babu a tare dashi

Ta bi bayansa tana mamakin sa. A kan ƴan Mata biyu ta sauke ido wadda bata tantance wace ce budurwan ɗan nata ba, cuz dukkan su kansu ɗaya ne baza ka iya bambance babba a ciki ba, amma tayi mamakin ganin irin shigan nasu duk da ɗaya atamfa ta saka, amma yanayin ɗinkin da kuma gyalen da tayi amfani dashi sam-sam babu tsarin tarbiyya a wurin, bare a kai ga wacce tayi shigan English wear, kallo daya Momy tayi musu but sai da ta ji gabanta ya faɗi, tare da tunanin abun da SHAREEF ya gani a wurin su har ya iya kwaso irin waɗannan Yaran, babu tarbiyya bare kunya a tare da su. Babu yabo babu fallasa ta amsa gaisuwar nasu bayan ta zauna tana sake duban su

While SHAREEF da ke tsaye sai ya nemi wuri a hannun kujeran; kusa da Haseena ya zauna

Mom har yanzu bata bambance wace ce surukar nata ba, amma ganin SHAREEF ya zauna gefen Haseena sai hasashen ta ya soma kawo wa a kanta

"Mom ga Haseena, ita ce wacce zan aura."

Karaf sai a kunnen Maryamu da ke shigowa riƙe da Jakarta, Sadiq na take mata baya, wanda dalilin jin furucin SHAREEF yasa ta kasa yin sallaman da ta buɗe baki tana shirin yi, sai ta tsaya cak a wurin tana zuba musu ido lokaci ɗaya yanayin ta ya sauya

Sadiq da ke bayanta ya ɗan zungure ta da faɗin, "mu je mana, ya kika tsaya?"

Ɗan motsa wa tayi tana waiga wa inda yake, sai kuma ta mayar da idanunta cikin falon tana kallon su

Yayinda su ma dukkan su hankalin su ya dawo kansu har Momy, sabida jin maganar Sadiq ɗin

"Tsayuwar me kike yi Maryam? Shigo mana."
Momy tayi maganar tana kallonta

Dukka zura mata ido suka yi har SHAREEF, wanda shi tunda yake bai taɓa mata kallon minti ɗaya ba sai yau

Takowa tayi a hankali ta nufo ciki

Sadiq tuni ya wuce ya shiga tunda ya ga akwai baƙi ne, yana zuwa ya zauna yana ɗan kallon su Haseena, a ransa yana mamakin yanda ya gansu but sai ya buɗe baki yana gaishe su

Suka amsa a tare dukkan su suna murmusawa

SHAREEF yace, "Sweetheart, Ƙanina Sadiq kenan da nake ba ki labari."

Wannan kiran da ya yi wa Haseena; ba ƙaramin dukan zuciyar Maryamu tayi ba, kai ba ita kaɗai ba, har su Momy sai da suka bi SHAREEF ɗin da kallo kamar wani TV. While Maryamu kamar an saka mata glue an nane ta a inda ta tsaya, zuciyarta wani irin buga wa take yi yayinda nan da nan jikinta ya soma tsuma sabida wani irin abu da ya dunƙule mata a ƙirji, tuni zuciyarta ta hasaso mata abun da ke faruwa a wurin sabida maganganun su da suke yi a yanzu, wanda ta kasa jure wa har ƙafafun ta rawa suke yi, take wani karfi ya zo mata bata san sanda ta bar wurin ba da sauri tana shigewa dakin ta, da gudu ta ƙarisa gefen gadon ta sulale a ƙasa ta zauna, duk da ta fahimci me ke faruwa amma ta ƙi yarda da cewan ƴan Matan SHAREEF ne a wurin, bata yarda cewa da gaske abun da ta fahimta budurwan sa ne ya kawo ba, "wlh bazai yiwu ba, Ni kaɗai ce Matarsa, su wane ne wadannan?" Ta furta da rawan murya, sai kuma ta matse kanta a cinyoyinta ta fashe da kuka gunun tausayi, yanda jikinta ke rawa da kuma abun da take ji a zuciyarta ita kanta ta kasa jure wa, baza ta iya ba, wani irin kishi ne ya tabaibaye ta, sosai take kukan tana ci gaba da matse kanta

Momy ne ta shigo dakin; ta ganta a haka, da sauri ta isa wurin ta tana kiran sunan ta

Itama sai ta ɗago kanta a firgice tana kallonta, nan da nan ta saka hannu ta soma share hawayen still jikinta na faman rawa sosai

"Maryam, mene ne kike kuka? Wa ya taɓa ki?"

Girgiza kanta ta soma yi duk da wasu hawayen ne ke zubo wa, sai dai ta kasa magana sabida ɓarin baki da take yi

"Faɗa min mana mene ne kike kuka? Ko wurin ciwon naki ne ke miki zafi?"

Wani kukan ne ya taho mata domin ta kasa jure wa, sai ta kifa kanta a kafafun ta ta fashe da sabon kuka

Hannu Momy ta sa tana ɗago mata kanta, sosai Mom hankalinta ya tashi sabida ganin halin da Maryamu take ciki, cike da kula wa da damuwa a face ɗin ta take kara rarrashinta tare da ci gaba da tambayarta

Daƙyar ta iya furta mata, "Momy Yaya SHAREEF, wata ya kawo gidan nan zai aura?"

Shiru tayi tana kallonta, "wai dama duk don shi kike wannan kukan? Wa yace miki auren ta zai yi? Ba na son sakarci ki share hawayen nan naki tun kafin in ɓata miki rai, tashi ki cire kayan bari in kawo miki abincin ki da maganinki ki sha, kar kuma in ƙara ganin kin zubar da hawaye."

"Amma Momy..."

"Shiiii! Ba na son ji, lafiyar ki ta fi komai a yanzu, ki share hawayen nace ba na son ganin su." Tayi maganar babu wasa a tare da ita

Dole Maryamu tayi abun da tace, amma kuma wasu hawayen ne suke gudun tsere a kan face ɗin ta don ta kasa tsayar da su, yayinda zuciyarta take mata zafi sosai; ga wani irin buga wa da take yi kamar zata faso ƙirjin ta

Momy bata sake cewa komai ba ta fice a ɗakin

Ganin haka sai ta sake fashe wa da wani sabon kukan tana dafe gefen zuciyarta, "don Allah Yaya SHAREEF kar ka auri wata bayan Ni, Ni ina sonka... Na.. na fi koowa sonnka wlh.." ta ƙare maganar a ɗai-ɗai sabida yanda numfashinta yake sama-sama kamar zai ɗauke,
Duk yanda ta so ta jure amma ina, kuka sosai take yi har da su majinu, shikenan gani take yi ta rasa SHAREEF tunda yana da wata budurwan, ga shi har ya kawo ta gidan su

A haka Momy ta zo ta tarar da ita a wannan mawuyacin halin, numfashi ma daƙyar take yi tsaban jaraban kishi ya ci ranta, lokaci ɗaya har ta fita a hayyacinta

"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un...! Maryam, me kike son ki ja wa kanki ne? Kina so mu ɓata ne? Ba kya jin magana ko? Baza ki share hawayen ba?"

Yadda ta daka mata tsawa babu wasa a tare da ita, shiyasa dole Maryamu tayi abun da tace, da sauri ta share hawayen nata tana shashsheƙa gunun tausayi jikinta sai faman rawa yake yi

"Ɗauki abincin ki ci, Allah zan saɓa miki idan kina kuka a kan SHAREEF, Mutum bai damu da ke ba amma duk kin gama ƙwallafa rai a kansa, har yaushe kika san soyayya haka Maryam? Abun naki ma gaba yake yi ko? To bismillah ki ci gaba, common ci abinci ki sha maganin ina jiran ki."

Babu musu tayi yanda tace, haka take tusa abincin daƙyar kamar zata yi amai

Ita kanta Momy tausayi ta bata, musamman yanda ta ga sai faman rawa jikinta yake yi, hakan ne yasa ta buɗe baki tace mata, "kinga Maryam, ba na son kina tayar da hankalin ki a kan SHAREEF. SHAREEF Mijin ki ne already kin rigada kin zama Matarsa, kuma waɗannan Matan da kika gani koda ya kawo su ba hakan yana nufin zai auri yarinyar da yake so bane, yanzu haka ma mun yanke hukuncin za ki tare a ɗakin Mijinki, don haka duk wani tunani ki ajiye shi a gefe ke ce Matar SHAREEF ba wata ba, Dadyn ku na dawowa zamu zauna mu faɗa masa gaskiya sabida mu danƙa ki wurin Mijin ki."

Da sauri Maryamu ta ɗago kanta tana kallon Momy, yayinda wani sanyi da farin ciki nan da nan ya tabaibaye ta

Murmushi Momy tayi mata tace, "Oh! Maryam ko kunya ba kya ji ko? Ba kya jin nuna soyayyar ki a wurin mu?"

Saurin rufe fuskarta tayi da tafin hannunta tana dariyan farin ciki, wani irin dad'i ne ke ratsa ta saboda jin abun da Momy tace

Ita kuma sai ta ja numfashi tana miƙe wa tare da furta, "bari in je in sallame su, ki gama cin abincin sannan ki cire kayan makarantar."

"To Momy." Ta amsa da sanyin murya har yanzu tana jin farin ciki a ranta

Momy kuma ta fita zuwa falo, a can ta tarar da su har sun taɓa abincin; SHAREEF ya saka su dole sai da suka ci, duk da basu so ci ba, har sun tashi ma zasu tafi SHAREEF zai kira Momy, sai ga ta ta fito. Shi yasa ta ɗan saki fuska suka yi sallama, sai tace, "su jira ta tana zuwa."
Ɗakinta ta shiga ta ɗauko musu turare guda uku ta saka musu a leda sannan ta kawo musu, tace, "su gaishe da iyayen su."

Tare suka fita da SHAREEF har mota ya kaisu, Haajara ta shiga Motan ta bar su a nan a tsaye

While SHAREEF cike da farin ciki yake cewa, "yanzu ba ki ji wani irin farin ciki da nake ji ba, Finally yau dai Iyayena sun san da ke, sai kuma maganar auren mu." Sai ya kira sunan ta kuma cikin kwantar da murya yana tsare ta da ido

Yayinda itama ta kafa mishi idanun tana sauraron mai zai ce mata tunda ta ji ya ambaci sunan ta

Hannunta ya kamo ya haɗa da nashi yana ɗan matsa mata cikin wani irin salo, yayinda ya zuba mata narkakkun idanunsa masu ƙara mata tsananin ƙaunarsa a ranta. "you know I love you, a wannan lokacin nake so mu kawo ƙarshen matsalar mu Haseena, ina tsananin bukatar aure ke ma kin sani; kuma ke ma na san haka ne, i know baza ki watsa min kasa a ido ba sabida akwai shawaran da na yanke." Sai ya ɗan ja fasali tare da ƙara wa da faɗin, "since you will have holiday in two months na yanke shawarar zamu yi aure a wannan lokacin, idan na faɗa ma iyayena sun yarda zasu nema min auren ki, inyaso sai ki ci gaba da karatun ki ban damu ba, Ni dai burina a ɗaura mana aure a wannan lokacin, sai na riƙa zuwa har can ina duba ki hakan zai kawo mana sauƙi a lamurran mu."

Bata taɓa tunanin zata ji wannan maganar daga bakin sa a yanzu ba, shiyasa tayi shiru ta kasa furta komai sai kallonsa da take yi, while fuskarta ta sauya alamun kamar bata amince da zancen nasa ba

Hakan ne yasa ya ƙara riƙe hannunta tare da sake rarrashinta cikin kwantar da murya da nuna fuskar tausayi, yana ƙara bata baki da nuna mata muhimmancin auren nasu a yanzu, shi ya yarda kowanne irin karatu tayi in har za a ɗaura musu auren, daga baya sai ta tare after ta gama karatun, auren kawai za a ɗaura

Duk da haka ta ƙi amince wa, sai ta langaɓe mishi itama ta nuna masa, "zata yi shawara, kuma zata sanar da Abbanta in ya amince, ko mene ne sai ta faɗa masa."

"Please try sweetheart, I need to marry you now, hankalina zai fi kwanciya."
Ya furta yana ƙara mannewa a jikinta kamar zai rungume ta

Ɗan waro ido tayi kaɗan tace, "nan gidan ku ne fa, we will pass and sai mun yi waya dear, don't worry I will try to talk to Abba."

Dad'i ya ji sosai, sai da ya ɗan sakar mata kissing a hannu before suka sake yin sallama ta tafi, yana sanar mata, "zuwa goben in zata tafi zai zo su je airport tare."

Sai da suka tafi sannan ya shiga gida.
***



_____Ko kusa Momy bata yi wa SHAREEF maganar Haseena ba. After Dady ya dawo ta zayyane mishi komai

Shi kansa yayi mamaki saboda dukkan su basu yi zaton yana soyayya ba,
Shi yasa bayan sun gama cin abinci sai Dadyn yace, "su zauna gaba ɗaya yana da magana."

A tunanin SHAREEF maganar Haseena za a yi tunda yana tunanin Momy ta sanar da Dady, sai faman murmusawa yake yi. Saɓanin haka sai ya ji abun da ya girgiza shi har ya tashi tsaye a kan ƙafafunsa yana zaro ido, take ya soma jin wani irin gumi yana tsatstsafo mishi lokaci guda

Su kuma suka tsaya suna kallon yanda ya nuna firgicin sa kamar wanda aka faɗa masa mummunar abu

Da mamaki Momy tace, "ya haka da firgici sai ka ce abu mummuna ake sanar maka? Ka zauna mana."

Hannu ya ɗaga yana nuna Maryamu da yatsa, cikin sarƙewan murya kamar zai yi hauka yace, "wai kuna nufin wannan abar ce zata zama Mata ta? Noo! Impossible wlh, ba na sonta! Ba na ƙaunarta! Bazan taɓa zama da ita ba, i hate her so much! Wlh ku canza tunani Momy bazan taɓa zama da ita a matsayin Matata ba, never."

Tsawa Momy ta daka masa, "kana da hankali kuwa SHAREEF? Kanka ɗaya?"

Da idanunsa jawur yake kallonta cikin ƙunan rai yace, "Momy da hankali na, taya ya zaku yanke wannan hukuncin ba tare da sanina ba? Me zan yi da wannan yarinyar? Wlh bazan taɓa zama da ita ba, ina da wacce nake so."

Miƙe wa Momy tayi ta kifa masa mari tare da daka masa tsawa, "shut up! SHAREEF ko in baka mamaki a nan wlh, har kai ka isa ka riƙa faɗa mana magana irin wannan? Ashe baka da kunya? Mu kake fada wa magana haka?"

"Bar shi ya ci gaba Deejah, ai zai nuna mana shi ya haife mu bamu muka haife shi ba."

Kallon Dady yayi, sai hawaye ya soma zubo mishi shaaa, da sauri ya bi hanyar steps da gudunsa ko sauraron su bai yi ba, duk da yana jin kiran da Momy take mishi

While Maryamu tuni ta soma kuka sabida ganin yanda SHAREEF yake yi, musamman da ya nuna ba ya sonta bazai zauna da ita ba, yanda take ganin tsantsan tsanarta a wurin sa bazai taɓa ƙaunarta ba. Sai kuka kamar ranta zai fita, lokaci ɗaya numfashinta ya sarƙe ta zube a wurin sabida kasa jure halin da take ciki

Su kansu su Momy basu ankare ba sai da Sadiq ya kwaɗa kiran Maryamu ganin bata numfashi, dayake yana kusa da ita ya taɓa ta ya ji ba ta motsi, shiyasa ya dinga kiran sunan ta hankali a tashe

matuƙa hankalin su ya gama tashi, musamman yanda suka zuba mata ruwa amma ina ta ƙi farka wa

Dole Dady yace wa Sadiq, "ya dauko key su kaita asibiti."

Da gudu ya wuce ɗaki domin dauko key din Motan,
While Dady shi ya saɓa ta a kafaɗa ya fita da ita

Dukka suka tafi asibitin gaba ɗaya hankali a tashe. After sun isa ba ɓata lokaci aka amshi Maryamu; since yawancin doctors ɗin asibitin sun san waye Alhaji Ahmed

Kafin ma a yi mata wani taimakon har ta farka, sai dai kuma yanda take ta kela amai kamar zata zubar da ƴan hanjin cikin ta; gaba ɗaya ta gama fita hayyacin ta, Likitan da ke duba ta shi ya saka wata Nurse yace, "ta gyara ta, sai ta ɗibi sumfurin jininta ta je ta gwada; ta kawo mishi result ɗin office."
Sannan ya fita zuwa office suka wuce tare da su Dady a can suka zauna, yayi musu bayanin, "yanzu za a kawo result, ta farka ma but amai take yi, dole sai an gwada ta sun tabbatar da me ke damun ta."

Hakan ne ya ɗan sa hankalin su ya kwanta tunda sun ji ta farka. Suna nan suna jira; Likitan ma tuni ya bar su a cikin office ɗin ya koma wurin ta

After an yi gwaje-gwaje sakamako ya nuna ciki a jikin Maryamu, shi kansa Likitan ya ɗan yi confused kasancewar cikin bai fi two to three weeks ba, duk da ciki yana iya bayyana a wannan ƙanƙanin lokacin, to bai sanar musu ba sai da ya ƙara saka wa aka yi mata duk wasu gwaje-gwaje da zai ƙara tabbatar musu, har fitsarin ta sai da aka ɗiba, daga nan aka saka mata drip tunda duk ta galabaita a ɗan ƙanƙanin lokaci tamkar ba ita ba, sai nimfarfashi take yi idanunta sun kaɗa sun yi jazur sun fita a hayyacin su tana ta sambatun magana, that's why har alluran barci sai da aka yi mata, amma kuma hakan bai sa ta ɓingire da barcin ba, sai surutai take yi kamar na zafin ciwo, kamar kuma ba ta cikin hankalin ta

Almost ten minutes before su ga ta dena motsi, alamun barci ya ɗauke ta,
Sai Doctorn ya bar Nurse a wurin ta, yace, "ta kula da ita yana zuwa."
Office din ya koma ya zauna before ya sanar musu da result ɗin abun da suka samu, ɗan cikin da suka samu a jikinta

Kalman cikin suka maimaita a tare suna kallon junan su cike da tsananin mamaki da al'ajabi

Sadiq da ke tsaye a gefe, shima sai da ya ɗan zare idanu yana maimaita cikin a ransa a rikice 

"Ƙwarai ciki ne a jikinta, binciken mu abun da ya nuna mana kenan, kuma bai fi sati Uku ba, abun da yasa ma muka daɗe sai da muka ƙara mata duk wasu gwaje-gwaje da zai sake tabbatar mana da hakan, kuma tabbas ciki ne."

"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un...!" Abun da ke fitowa daga bakin Momy kenan tana ɗan shafa fuskarta

To wane ne ya yi mata ciki? Sun fa rikice sosai tunda basu san ya zasu ɗauki maganar ba

Dady ne ma yayi ƙarfin halin faɗin, "zamu iya ganin ta Doctor?"

"Eh zaku iya ganin ta, amma mun yi mata allura tana barci, mun ƙara mata ruwa ma, Insha Allahu komai normal ne zata samu lafiya da yardan Allah, Allah ya bata lafiya."

"Amin." Suka amsa da sanyin jiki zuciyoyin su na tsinkewa 

Sannan ya tashi yace, "su je ya kaisu ɗakin."

Duk yanda suka so su cire damuwar abun da ke ransu but sun gaza, abun da ɗaure kai, to ta ya ya Maryamu ta samu ciki after all SHAREEF bai taɓa sanin ita Matarsa bace? Sannan ma taya ya zasu zarge sa bayan sun san zaman da ke tsakanin su; SHAREEF ba ya ƙaunarta.
Dole akwai rikitar wa, amma ko ma dai mene ne ita Maryamu zata iya faɗa musu wanda yayi mata cikin

Ganin yanda Momy ta nuna damuwarta fiye da nasu har da ɗan guntun hawayen ta, shiyasa Dady ya sake kwantar mata da hankali sosai

Amma ita gani take yi kamar har da laifin ta, yarinya tana wurin ta tayi ciki ba tare da sanin ta ba? To wanne sakaci suka yi da har hakan ta kasance? In fact ma har Sadiq sai da ta kawo zargin ta a kansa, sai dai furta wa ne bata yi ba amma kaifafan idanunta suna kansa, but babu wani abun zargi a wurin sa

Dole ita Momyn ta zauna da ita; su kuma suka tafi gida since dare yayi sosai,
Ƙarshe kasa runtsa wa tayi ta zauna ta buga uban tagumi tana ta kallon Maryamun da ke kwance tamkar matacciya, babu inda ke motsi a jikinta,
Har garin Allah ya waye Momy tana zaune digir-gir bata runtsa ba, kuma har wannan lokacin itama Maryamun bata motsa daga yanda ta kwanta ba,
Sai kusan ƙarfe biyar da rabi time ɗin Momy tana zaune ta gama nafila zata gabatar da sallan subhi da ake ƙoƙarin shiga,
Bata san Maryamu ta farka ba har ta tayar da Sallan,
Sai ta soma jin sambatun ta tana kiran sunan SHAREEF, hakan ne yasa ta ɗan taƙaita sallan before ta idar; ta miƙe ta nufi wurin tana kama ta tare da kiran sunan ta

Ashe ma idanunta a rufe suke, sambatun kawai take yi bata gama farfaɗo wa ba

"Sannu Maryam, kin tashi?" Tayi maganar tana riƙe da dantsen hannunta

Buɗe ido Maryamu tayi tana kallonta, sai kuma ta soma tunanin abun da ke faruwa da ita since bata gama dawowa cikin hayyacinta ba, sai kallon ɗakin take yi kamar wacce take neman wani abu

Ruwa Momy ta ɗauka ta buɗe goran tana kaiwa bakin ta after ta tallabo ta

Kamar dama ta san tana jin matsanancin ƙishi, sosai bakin ta ya bushe wanda har saman laɓɓanta sun yi ƙamas sun fitar da fata

Sai da ta bata ruwan sannan ta sake tambayarta jikin nata?

Maryamu da ke dubanta tace, "Momy me ya kawo Ni nan?"

"Kwantar da hankalin ki, yanzu babu abun da ke damun ki ko kina jin wani ciwon a jikin ki?"

"A'a Momy."

"To bari in kira Likita ya sake duba ki. Ina zuwa."
Sai ta sake ta tana ajiye ruwan before ta fita da sauri


Lumshe idanu tayi tana ɗan kama kanta da ke faman sara mata kamar zai ɗaɗɗake, kwata-kwata bata tuna abun da ke faruwa da ita ba har ta zo nan, in fact ma bata fahimci a asibiti take ba duk da ta ga hannunta an saƙale shi da kanula, but ruwan tuni ya ƙare tun cikin dare Nurse ta cire mata, yanayin da take ji a jikinta da kuma yanda kanta ke juya wa ba ta fahimtar komai, har sanda Momy ta dawo da Likita kallon su kawai take yi bata san me suke cewa ba, sai dai kawai tana bin umarnin abun da Likita yace mata ne

Sai da ya duba ta ya gama sannan ya fita a ɗakin,
Momy ta zauna a gefen ta tana kallon ta tare da ƙara mata sannu

Murmushi Maryamu tayi bata ce komai ba, sai ma mayar da kanta da tayi tana rufe idanunta sabida yanda take jin kamar ana juya ta, kafin lokaci ƙanƙani wani barcin ya ɗauke ta

Fahimtar hakan ne yasa Momy ta dauki waya ta kira Sadiq, tace masa, "ya zo ya tsaya a wurin Maryam yanzu."

Bayan ya zo sai ita ta koma gida ta haɗa musu breakfast

Tun jiya da SHAREEF ya shiga ɗaki ya rufe kansa har yanzu ya ƙi fitowa, duk kiran da Dady yayi masa yayi burus dashi ya ƙi fitowa, ran Dady ya ɓaci matuƙa amma haka nan ya haƙura ya ƙyale sa. Ita kanta Momy da ta koma sai da ta neme shi amma ya ƙi buɗe musu kofa, dole suka fita harkansa bayan ta gama breakfast ɗin ta zuba suka tafi dashi; ita da Dady suka dawo time ɗin ma bata farka ba

Sai kusan ƙarfe goma sannan ta farka, jikin nata da sauki tana iya tuna komai sosai. Shi yasa ta soma kiran sunan SHAREEF tana hawaye

Momy tace, "ki yi shiru mana kinga ba ki da lafiya Maryam, zai zo yanzu ya duba ki ki dena kuka."
Daƙyar ta samu ta rarrashe ta har tayi breakfast ɗin,
Bayan sun ga hankalin ta ya ɗan dawo jikinta shine Momy tayi mata tambayar, sabida gaba ɗayan su da zullumin abun suka kwana,
Musamman ma Dady da hankalin sa ya fi kowa tashi, don dai kawai yana ɓoye abun a ransa ne amma ya fi su shiga matsananciyar damuwa

Ta sigan da Momy ta tambaye ta shiyasa cikin sauƙi ta sanar musu da cewan, "SHAREEF ne yayi mata cikin".
[21/02, 8:37 am] OumƊahirah نفيسة: 🌱🌱🌱🌱🌱

          *SHAREEF*
               _SexyBoy_
🌱🌱🌱🌱🌱


_Writer: Nafisat Isma'il Lawal_
_Wattpad: UmmuDahirah_

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝*



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

       *P.W.A✍️*





*DATA SHARE*

Call, message or whatsap  07065334256

*MTN*
500MB 150
1gb  280
2gb.  560 
3gb.   840
4gb.    1120
5gb      1400
6gb.     1700
Verlid for 30 days.












__________
*BOOK1*
_______________*FREE PAGE37*
_____Tunda SHAREEF ya rufe kansa a daren jiya ko fitowa ya ƙi yi, kwana yayi a cikin wani irin yanayin da bazai taɓa iya misalta shi ba, jin mummunar labarin nan ya ruguza masa dukkan farin cikin sa, wani irin ɓacin rai tare da tsanar Maryamu ya ƙara tasiri a cikin ransa, musamman in ya tuna sabida ita a karon farko Momyn sa ta ɗaga hannu ta mare sa, duk in ya tuna sai ya saka hannunsa a saman kuncin sa ya riƙe wurin yana jin zuciyarsa tamkar zata fashe don baƙin ciki, tsananin tafarfasa take mishi kamar ya haukace don mugun baƙin ciki da zafin zuciyar da ke tare da shi, idanunsa sun kaɗa sun yi jazur har da hawayen sa saboda ya kasa jure ƙunci da takaicin da yake ji, taya ya za a ce wannan ƙasƙantacciyar da yake ganin ta tamkar ƴar aikin gidan su; ita ce zata zama Matarsa? Shikenan ta rusa farin cikin sa da jin daɗin sa? Ta zo ta wargaza masa duk wani buri nasa da rayuwarsa, tabbas bazai taɓa yafe mata ba, kuma ko me za a yi bazai taɓa amince wa da ita a matsayin Matarsa ba, bazai taɓa yarda ba. Ƙarshe kwanciya yayi a ƙasan cerfet ɗin sa yana jin duk bugun ƙofan da Dadyn sa yake yi but ya ƙi buɗe wa, duk idan ya tuna maganar ma hawaye ne ke malale a kuncin sa yana jin zuciyarsa na ƙara tafarfasa kamar ya fito ya kama yarinyar yayi mata shegen duka, meyasa ta shigo rayuwarsa? Ba ya buƙatar ta kwata-kwata, kuma duk yanda za a yi sai ya fitar da ita, babu wanda zai mishi iyaka da abar ƙaunarsa

A haka ya kwana a wannan halin da ya sanya mishi matsanancin ciwon kai, har wani zazzaɓi yake ji a jikinsa ko runtsa wa ya kasa yi tsaban tunani da zullumin abun da zai biyo baya, yana ganin ko ta halin ƙa-ƙa bazai taɓa iya yin ma iyayensa biyayya ba in har sai ya zauna da yarinyar da bata isa ta kai matsayin Matarsa ba, tabbas bata kai matsayin ba, kuma idan har aka dage ya zauna da ita to haƙiƙa sai ya gasa mata Aya a hannu, sai ta gummace ba a haife ta har ta san shi ba, lallai zai nuna mata wane ne SHAREEF? Da kalan abun da zai iya aikata wa.



         Kafin safe duk ya gama fice wa a hayyacin sa, idanun nan nasa sun kumbura suntum sun yi ja, babu ko ɗigon walwala a tare da shi, yanda ka san an yi mishi bushara da mummunan abu, a haka ya tashi yayi sallah a ɗakin ya sake zama yana ta saƙe-saƙe da abun da zai aiwatar wajen yakice yarinyar, Haseena ce farin cikin sa, ita kaɗai yake da burin aure, ita ce Macen da yake jin zai iya auren ta ya samu farin ciki a zuciya, duk wanda ya shiga tsakanin su kuma sai inda ƙarfin sa ya ƙare wajen ganin bayansa, don haka dole ne ya nuna wa yarinyar iyakan ta

Koda ya ji muryan Momy daga baya itama ta zo tana dukan ƙofan nasa da kiran sunan sa, but ya ƙi buɗe wa, sai ma kwanciya da yayi ya rufe idanunsa yana jin tamkar zai mutu don ƙunci da ɓacin ran da ke tare dashi,
Sai daga baya ne ya kunna wayansa sabida ya san dole Haseena zata neme shi, ilai kuwa sai ga shigowar message ɗin ta tana faɗa mishi, "by ten zata tafi airport, in ya kunna wayan ya kira ta."
Bai tsaya kiran ta ba; sai ya tashi yayi wanka ya shirya cikin ƙananan kaya da suka yi masa kyau ainun, duk da babu fara'a a tare da shi, ya haɗe fuska sosai har yanzu idanunsa da kumburin da suka yi, kuma basu washe sosai ba, kana kallonsa ka san akwai abun da ke damun sa,
Fita yayi ta ƙofan baya ya shiga Motan sa zuwa gidan su Haseena,
Koda ya je bai shiga ba sai ya tsaya a waje,
Sai dai ya kira ta ya sanar mata, "yana waje."

Bayan kamar mintina goma sai ga ta ta fito ita kaɗai da Bag ɗin ta, ta cakare cikin ƙananun kaya riga da wando, sai ta yafa mayafi a kanta, sosai tayi kyau sai taunan chewing gum take yi yanda ka san karuwa, fuskar nan ta sha MakeUp kamar zata je gasar kyau

Kallon fuskarta kaɗai da SHAREEF yayi sai da ya ji sanyi a ransa, a hankali kuma ɓacin ran da ke tare dashi ya soma raguwa, haba; taya ya zai iya barin Mace kamar Haseena ya auri Bagidajiyar yarinya rainon ƙauye? Impossible! Hakan bazai taɓa faruwa ba, ko ta halin ya ya sai ya yakice yarinyar a jikinsa, Haseena ita ce zaɓin sa, zaɓin zuciyarsa, ita ce farin cikin sa, ita yake ƙauna, ita yake fatan ya aura, ita ce komai nasa, rasa ta kamar ya rasa farin cikin sa ne na har abada, kuma zai yi yaƙi a kan haka domin ƙwato farin cikin sa

Ita kanta Haseena tayi mamakin ganin yanda mood ɗin sa ya sauya, sabida tunda take dashi bai taɓa zuwar mata a haka ba, ta san wane ne SHAREEF, ta san yanda yake matuƙar kaunarta, dole akwai wani abun da ke damun sa, duk da ya ƙi faɗa mata duk iya tambayoyin da take mishi, sai ma jeho mata nashi tambayar da yayi a kan sanar da Abbanta auren su,
Tabbas ta yi wa Abbanta maganar auren

Amma shi yace, "ba buƙatar haka gaskiya, ta lallaɓa sa ya bar zancen domin ba yanzu zai yi mata aure ba sai ta dawo daga school, idan ta gama sai a yi auren, ko kuma in ya yarda ya turo Iyayensa a yi maganar auren a saka rana; after ta gama karatun ta sai a yi auren."

Wannan bayanin da ta sanar mishi; shi ya ƙara dagula zuciyar SHAREEF, babu wasa a cikin lamarin sa ya kira sunan ta yace, "Haseena, ba bukatar ki ci gaba da ɓata min lokaci raina yana ɓaci, kinga sabida ke wata gagarumar matsala tana shirin kunno min kai, idan ban samu tabbacin auren mu a yanzu ba komai zai iya faruwa, Haseena wannan lokacin babu wasa a cikin lamari na, ki shawo kan Mahaifinki a yi mana aure kamar yanda na ce miki; ko kuma zan rabu da ke na har abada."

Yanda ya tsare ta da ido yana faɗa mata maganar, tabbas ta hango tsantsan gaskiyarsa, kuma hakan ba ƙaramin ɗaga mata hankali yayi ba har ta kasa magana ta bi sa da ido tana ɓarin baki

Shi kuma fuska a ɗaure yake kallonta duk da ba wai har zuciyarsa haka zancen yake ba, bazai taɓa iya rabuwa da ita ba, amma dole zai nuna mata da gasken yake yi domin ta dauki maganar sa da muhimmanci

Kuma tabbas ta ɗauka, ta ruɗe matuƙa da jin kalaman sa wanda bata taɓa tunanin hakan ba, ba ta jin ita kanta zata iya rayuwa babu shi a tare da ita, already ya zame mata jinin jikinta, rasa sa kamar ta rasa rayuwarta ne, tana matuƙar ƙaunar SHAREEF har cikin zuciyarta, kuma baza ta so a ce ta rasa shi ba; bare har ta ga wata Macen a tare dashi ba ita ba, never. Sai inda ƙarfin ta ya ƙare.
Kuka ta saka mishi lokacin da ya tayar da motan yana ƙoƙarin tafiya

Duk da yana jin kukan nata har ransa, amma bai tsaya ba, bai kuma kalle ta ba, sai dai ya sassauta murya sabida bazai iya ci gaba da juran jin kukan ta batare da ya rarrashe ta ba, hakan ne yasa ya kira sunan ta yana furta, "Haseena ki yi shiru haka nan bazan iya jure kukan ki ba, yana taɓa min zuciya."

"Taya ya zan yi shiru bayan ka soma furta min zaka iya rabuwa da Ni?" Tayi masa maganar tana kallonsa hawaye na ci gaba da ɗigan mata, "yanzu ashe har ka soma tunanin haka a ranka? Me nayi maka da zafi haka?"

Ɗan kallonta yayi ya kawar da kai, sai ya ci gaba da tuƙin nasa murya a sanyaye yace, "abun da yasa na furta miki haka sabida ki san halin da nake ciki ne sweetheart, na ga kamar kina wasa ne ba ki ɗauki maganar da serious ba, ina cikin tashin hankalin da zan iya rasa ki gaba ɗaya a cikin rayuwata sweetheart, idan ba ki taimake ni ba komai zai iya faruwa, kin fi son mu rasa juna ko?"
Ya ƙare maganar yana tsare ta da ido

Girgiza masa kai tayi tare da furta, "but why can't you tell me the problem? Wannan ba hujja bace, tunda har zaka iya furta min zamu rabu; kenan ba ka sona a yanzu? A nan gaba ma zaka iya rabuwa da Ni bayan ka san ba laifi na bane."

Ganin yanda ta ɗauki maganar da zafi tana ci gaba da kukan nata, sai ya tsayar da Motan ya soma rarrashinta yana jawo ta a jikinsa, daga ƙarshe sai ya zura bakin sa cikin nata yana mata wani irin zuƙa cikin salo kamar zai cinye ta, dama abun da yake buƙata kenan, nan da nan ya soma romance ɗin ta cike da wani irin shauƙi da tsananin sha'awar ta, ya kasa control din kansa haka yake sarrafa ta tuni ya ɗaura ta a jikinsa sai matsa mata boobs yake yi yana mata salon sa mai fitar da mutum a yanayi

Haseena kwata-kwata ba ta jin daɗin abun da yake mata, kawai biye masa tayi idanunta a rufe tana jan numfashin wahala; ranta babu daɗi. Sai da ta ga yana son wuce gona da iri kuma zata iya missing Flight dinta sannan ta dakatar dashi daƙyar

Idanunsa sun sake yin ja sai fitar da numfashi yake yi yana jin kamar ya haɗiye ta don so da sha'awar ta, ya kasa ma magana sai tayar da motan da yayi ya ja suka tafi, babu mai magana a cikin su sai da suka yi nisa

Daga baya Haseenan take ƙara ba shi haƙuri tare da furta masa, "zata shawo kan Abbanta ya amince."

Sai lokacin ya ji sanyi a ransa, sai ya kama hannunta ya tamke sosai yana sakar mata kallon soyayya, "i love You Sweetheart, ina son ki matuƙa, ki san da sani ke ce farin cikina, already na rigada na ba ki kaina ki kula min da zuciyata amana, Ni taki ce har abada ki saka a ranki, duk wata Mace bayan ki take. Ina sonki!"
Haka ya dinga zuba mata sambatu har suka isa can, sai da ya sake lugui-luguita ta yayi mata kissing kamar zai haɗiye ta, before ya ƙyale ta suka yi sallama, har sai da ya ga shigan ta jirgi sannan ya shiga Mota ya tafi, gaba ɗaya ɓacin ransa da ƙuncin sa ya nema ya rasa, zuciyarsa tayi sanyi sai wani irin kewa da ke shigan sa, ji yake yi kamar ya bi ta haka yake ji; don ba ya son ya koma gida ya haɗu da matsalar nan kuma daga ƙarshe a ɓata masa ɗan farin cikin sa. Sai ya juya kan Motan zuwa Company duk da bai koma ba tun bayan yin masa operation, dama gobe yake saka ran koma wa.
🔆🔆🔆

    
_____Amsar da Maryamu ta bayar; ya saka su Momy cikin tsantsan mamaki da al'ajabi, SHAREEF. SHAREEF shi ne yayi mata cikin amma yake nuna irin wannan tukuburcin; har yana iya fiffiga yana musu tsaurin ido a kan ba ya sonta? Lallai wannan Yaron, rashin kunyan nasa ya wuce tunanin su, har ya iya zagayawa ya lallaɓa yarinya ƙarama; amma a gaban idanunsu yana musu pretending don shi mara kunya ne?
Lallai sun shaƙa da yawa, barin ma Momy ba ta ɗaukar abu da wasa, tana da zafi sosai fiye da Dady, kuma ta sha alwashin sai ta ci mutuncin SHAREEF in har suka koma gida, da ita yake zancen, ƙwafa kawai tayi bata sake yi wa Maryamu maganar ba, sai ma bayan Dady ya fita ta saka ta tayi wanka ta kimtsa jikinta,
Likita bai daɗe ba ma ya zo ya basu sallama tunda jikin nata da sauƙi,
Sai suka haɗa kayan su suka wuce gida tare da Dady da ya dawo daukar su; since Sadiq yana school tun safe da ya zo duba Maryamu ya wuce

Koda suka koma gida magani Momy ta bata ta sha bayan ta ci abinci, tace mata, "ta je ɗaki ta kwanta ta huta."

Bayan ta tafi suka zauna a Falon suna tunanin matakin da zasu ɗauka

"Yanzu Alhaji ya kake ganin za a yi da SHAREEF?"

"Bari in kira sa a waya."
Ya sa hannu ya ciro wayan daga aljihun sa yana lalubo numban SHAREEF, ring take yi but bai ɗaga ba har ta tsinke

Momy kuma sai kaɗa ƙafa take yi kamar zata ƙwace wayan don takaici, sosai tayi fushi da SHAREEF ɗin don wlh sai ta nuna mishi kuskuren sa, bai taɓa ganin ɓacin ranta ba a wannan karon zai gani in har bazai bi abun da suke so ba, ba a haifi Yaron da zai gagare su ba, SHAREEF har nawa yake da zai riƙa juya su?
Miƙewa tayi ta bar wurin ta shiga kichen domin nema musu abun da zasu ci, tana ɗan kaye-kayen ta can ta ji kamar Dadyn ya gama wayan, sai ta koma ta tambaye sa, "ya ɗauki wayan?"

"Ya ɗauka, na ba shi umarnin zuwa yanzu zai zo."

"Gwara haka dai, domin gani nake yi SHAREEF yana son ya gagare mu, don Allah Alhaji kar kayi mishi da sauƙi, Ni fa bazan taɓa bari SHAREEF ya auri wannan yarinyar da ko da ganinta ka san bata da tarbiyya ba, har yaushe yayi wayon da zamu nuna masa abun da ya dace dashi; amma ya ƙetare mana? Ruɗin duniya ya soma rufe masa ido, irin waɗannan Matan kawai yake iya hango wa yana ganin su ne dai-dai da shi; sabida ya raina Maryam tunda ita ta taso a ƙauye, ya san me zata zama a nan gaba ne? Amma don shi munafiki ne har da zagaya wa ya neme ta. Wannan abun da me yayi kama? To da ace ba matarsa bace ya kenan Alhaji? Wlh raina ya ɓaci matuƙa, kuma zai zo ya same Ni sai na ci masa mutunci, ko kunya bai dashi."

"Duk da haka Deeja, mu bi komai a sannu don Allah, har yanzu SHAREEF Yaro ne, kin san Yaran zamani kuma ka haife su ne baka haifi halin su ba, tunda har SHAREEF yana da wacce yake so zai yi wuya ya ɗauki Maryam a matsayin Matarsa har yayi mana biyayya, tun farko bamu yi wannan tunanin ba; da Hanif zamu aura wa tunda shi ya fi shi sauƙin kai."

Rai a ɓace Momy tace, "dole mana ya fi shi sauƙin kai tunda ya fi shi tunani da hankali, kuma in har wannan yarinyar ce ai gwara babu da ita, don wlh bazai aure ta ba ko me zai yi, mu muka haifi SHAREEF ba shi ya haife mu ba, Maryam dole ya zauna da ita tunda har ya iya ɗirka mata ciki dan Uban shi, Ni bari in je kichen na bar abu a wuta, ina jiransa zai dawo ya same mu."
Ta juya ta wuce cikin kichen bata saurari Dady ba

Shi kuma girgiza kansa yayi yana mamakin zafi irin na Momy, ɗaukar remote yayi ya kunna TV yana neman tashan da zai kalla

Almost 20 minutes before suka ji shigowar Motan SHAREEF, daga baya sai ga shi ya shigo cikin falon fuskarsa a haɗe har yanzu da ɗan kumburin a saman fuskarsa, shigowa yayi yana ɗan motsa bakin sa alamun yayi sallama

While Dady tunda yayi masa kallo ɗaya ya ɗauke kansa, har sai da ya ƙariso wurin sa before ya kalle sa yace, "ka tsaya min ƙerere ka zauna mana zamu yi magana."

Zama yayi a saman kujerar kansa a ƙasa bai ɗago ba

Shi kuma Dady yayi banza dashi yana ci gaba da kallonsa

Sai daga baya Momy ta fito itama tunda ta ga SHAREEF ɗin zaune ta haɗe fuska, ta taho tana zama tare da ninyar yin magana

Sai Dady ya katse ta da furta, "Momyn Yara ina fruits ɗin da nace ki yanka min?"

Ta sha'afa sabida Allah - Allah take yi ta fito ta samu SHAREEF, shiyasa ta manta dasu bata ɗauka ba, "wlh na manta Alhaji, ɓacin ran da Yaron nan ya saka min na manta ban taho da shi ba."
Sai ta mike ta shiga kichen ɗauko wa

While Dady ya dubi SHAREEF yace, "ashe SHAREEF akwai ranan da zamu nemi alfarma a wurin ka ka kasa mana? Mu aura maka yarinya amma ka nuna mana bamu isa ba dole sai kayi yaƙi damu? Ko wasu suka yi maka wannan kyautar ba Iyayenka ba zaka iya watsa musu ƙasa a ido? Mu mu Iyayenka?" Ya ƙare maganar yana nuna kansa da yatsa, sai ya jinjina kansa yana jan numfashi

SHAREEF kuma yana sauraron sa but kansa a ƙasa ya kasa cewa komai

A sa'ilin Momy ta dawo ɗauke da tray ta ajiye a saman Centre table tana matso mishi dashi

"To abun da kayi yayi maka kyau, amma ka san da sani Maryam ƴar uwanka ce kuma Matarka, wlh summa tallahi babu mai raba auren nan naku dole ne ka zauna da ita ko kana so; ko ba ka so, kayi kaɗan mu zaɓa maka abu ka ƙetare mana, muna ganin abun da ya dace da kai tunda kai Yaro ne, amma nema kake yi ka nuna mana ka fi mu wayon ko? Bamu san me ya kamata da kai ba ko?"

"Alhaji ai wlh kai ka zauna kana masa magana cikin sanyin rai, kuma don kai fitsarrare ne yarinyar da ka nuna ba ƙaunarta kake yi ba; ba ka sonta amma don kinibibi ka zagaya kana neman ta har kayi mata ciki, kuma kake tunanin zaka iya tsere wa auren ta? Ai baka isa ba SHAREEF, kayi kaɗan don Ubanka, Maryam dole sai ka zauna da ita tunda ka nuna tana da amfani a wurinka har ka iya zuwa ka biya bukatar ka a wurin ta."

Cikin tashin hankali SHAREEF ya ɗago yana duban Momyn wacce take tsitsiya mishi tsiya cikin fushi da ɗaga murya, kwata-kwata bai gama fahimtar maganar nata ba don ya kasa gane cikin da take cewa yayi mata, bakin sa na rawa yake cewa, "Momy ciki kuma?"

"Ciki fa, ko zaka ce ba kai kayi bane? Ko kuma don ka ɗauki Maryam ɗin ƴar ƙauye bata da wayon da zata nuna ka tace kai kayi mata cikin ne? Ai Allah ya kama ka tunda ga shi har da result ka samu, sai ka shirya zama da ita har ƙarshen rayuwarka, ba kai ba yarinyar nan mara tarbiyya wacce basu san darajar kansu ba, ita wannan ɗin da ka tsana ita ce dole ka zauna da ita."

Da sauri ya miƙe kan ƙafafunsa duk da wani irin jirin da ke mamayan sa, cikin tsananin damuwa da tashin hankalin da ya bayyana a kan fuskarsa da still yana ɓarin laɓɓa yake cewa, "wai Momy taya ya zaku ce nayi mata ciki? Ni... Ni ne zan yi wa yarinyar nan ciki? Ta ina nayi mata cikin? Wlh ƙarya take min sharri ne bazan taɓa iya haɗa shimfiɗa da ƙasƙantacciyar yarinyar nan ba, never..."

Mari Momy ta kwaɗa masa don tsananin fushi da takaicin maganar nasa, "dan Ubanka ƙarya zata yi maka? Ko kuma Cikin da Likita ya faɗa mana karya ne ba gaske ne ba? SHAREEF kana cikin hayyacin ka kuwa mu kake son ka wulaƙanta?"

"Momy wlh ban yi mata ciki ba, Ni ban yi mata ciki ba." Ya furta hawaye na tsiyayan mishi riƙe da kuncin sa

Takaicin sa yasa Momy ta kasa magana sai kallonsa take yi kamar zata shaƙe sa, tana masa kallon mara hankali da tunani

Shi kansa Dady mamakin SHAREEF ɗin ne ya cika sa, "to idan ba kai kayi mata cikin ba waye yayi mata? Zata yi maka ƙarya ne?" Dady ya furta a ɗan hassale yana bin sa da idanu

Sai kawai SHAREEF ya fashe da kuka sabida ya kasa jure abun da ke faruwa, taya ya zai yi mata ciki yarinyar da ya tsana? Ta ina yayi mata cikin? Kawai gani yake yi suna son ɗaura masa wannan sharrin don kawai ya zauna da ita, wlh bazai taɓa zama da ita ba, ko me zai faru sai dai ya faru ba ya sonta bazai zauna da ita ba, wace ce ita da ta isa tayi mishi wannan sharrin? Sai ya karya ta ya kashe shegiya muddin ta shigo hannunsa.
[22/02, 8:57 am] OumƊahirah نفيسة: 🌱🌱🌱🌱🌱

          *SHAREEF*
               _SexyBoy_
🌱🌱🌱🌱🌱


_Writer: Nafisat Isma'il Lawal_
_Wattpad: UmmuDahirah_

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝*



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

       *P.W.A✍️*





*DATA SHARE*

Call, message or whatsap  07065334256

*MTN*
500MB 150
1gb  280
2gb.  560 
3gb.   840
4gb.    1120
5gb      1400
6gb.     1700
Verlid for 30 days.












__________
*BOOK1*
_______________*FREE PAGE38*
_____"Wlh ko kukan jini zaka yi SHAREEF sai ka amshi cikin nan a matsayin naka, kana son ka nuna mana bamu san me muke yi ba ne? Kuma yarinyar zata yi maka ƙarya ne? ko kuwa Maryam tana da wayon da har wani zai yi mata ciki sannan ta laƙaba maka ne? To ka canza tunani da dabara, babu yanda za a yi Maryam tayi maka wannan mummunar sharrin, ai dama Likita ya faɗa kana buƙatar Mace a tare da kai, sai ga shi kayi amfani da damar ka ka shiga ka titsiye yarinya ka biya baƙatun ka; sai ya zamana Allah ba azzalumin Bawan sa bane ya nuna maka Iyakan ka, sannan ita ɗin Matarka ce, kai ko ba Matarka bace tunda har ka iya keta mata mutunci dole kai zaka aure ta, tarbiyyar da muka baka kenan ko SHAREEF?" Sai ta girgiza kanta tana jin zuciyarta na zafi musamman yanda ta ga yana kukan bilhaƙƙi da gaskiyar sa, sai ta daka masa tsawa tana furta, "zaka rufe mana baki ko kuwa? Uban wa kake yi wa kuka a nan?"

"Momy wlh bani nayi mata ciki ba, yarinyar nan sharri take min, yarinyar da na tsana..." Sai kuma yayi shiru yana haɗiye yawu tare da duƙar da kansa ya ci gaba da zubar da hawaye zuciyarsa kamar zata fashe

Momy koma wa tayi ta zauna tana kaɗa kafafu cike da tsananin takaici da haushin sa, ta rasa ma me zata ce don baƙin ciki, wai ga shi ƙiri-ƙiri abu ya bayyana yana ƙaryata su, ji take yi tamkar ta fashe da kuka; idanunta tuni sun kaɗa sun yi jazur

Fahimtar hakan yasa Dady ya dube ta yace, "Kinga Deeja, ki dena irin wannan fushin kina bari ranki yana ɓaci a kan abu ƙalilan, kin san dai kina da hawan jini bai kamata kina yin abun da zai tayar miki dashi ba."

Kamar jira take yi sai ga hawaye sun soma zubo mata, sai ta rufe fuskarta da tafukan hannunta tana jan shashsheƙa, kana kuma ta buɗe lokaci guda tana kallon wurin da SHAREEF yake, tare da nuna sa da yatsa tace, "Alhaji SHAREEF yake so ya nuna mana zai gagare mu, a kan abun da bai fi ƙarfin shi yayi mana ba, ashe akwai ranan da SHAREEF zai iya bijire mana? Ashe yana mana kallon da bamu kai ba bamu isa dashi ba?..."

"Khadijah na ce ki yi shiru ko, yanzu wannan hawayen da kike zubar masa ba ki san tamkar baki bane a gare sa, ba na so ki share hawayen ki nace." Yayi maganar cikin ɗaure fuska babu wasa a tare da shi,
"Kaima ka dena kukan nan na gaji da jin sa, kayi min shiru yanzun nan." Ya daka masa tsawa

Sanin halin Dadyn nasu bai iya fushi ba, shiyasa dukka suka bi umarnin sa,
Yayinda Falon ya ɗauki shiru kamar babu kowa

SHAREEF ya kasa tashi bare ya bar wurin sabida yanda jikinsa ke faman rawa tamkar zai haɗiye zuciya ya mutu don baƙin ciki da ƙuncin da ya cinkushe masa maƙogwaro. A kanta; a kanta komai yake faruwa, ita ce sila na son ruguza masa farin cikin sa, a kanta Iyayensa suna jifan sa da muggan kalamai, a kanta Mahaifiyarsa take zubar mishi da hawaye; wanda bai taɓa ganin hakan ta kasance ba, taya ya zai ƙaunace ta? Ba ya jin zai iya yafe mata har abada

Hango Maryamu da Dady yayi shiyasa yayi shiru bai yi maganar da yake son furta wa ba; yayinda yake kallonta cike da tsantsan mamaki gami da al'ajabi, har datse baki yayi wurin ƙoƙarin sa na furta sunan ta

Hakan ne yasa da sauri Momy ta juya itama tana kallon inda yake kallo, itama mamakin ne ya kusa kashe ta tayi saurin tashi a kan ƙafafunta

Sakamakon ganin Maryamun da suka yi cikin ta ya kumbura; tamkar na mai cikin wata bakwai, ita kanta hankalinta a tashe yake shiyasa ta fito a sukwane tana ƙoƙarin kiran sunan su; but harshenta ya karye ta kasa sarrafa shi, idanunta sun kaɗa sun yi jazur; sai kawai ta zube a wurin babu ko numfashi a tare da ita

"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un..! Maryam." Momy ta kira sunan ta hankali a tashe ta nufi wurin ta

Haka shima Dady jiki na ɓari ya take mata baya suka nufi inda ta zube 

Shi SHAREEF tunda yayi musu duba ɗaya, ya ɗauke kansa ya miƙe yana jin jiri na barazanar ka dashi, haka ya riƙe kansa da ke tsananin sara mishi kamar zai cire, hanyar ɗakin sa ya nufa batare da ya bi ta kansu ko ya damu da ganin halin da yarinyar take ciki ba; cuz Allah -Allah yake yi ya bar wurin ma sabida tsananin baƙin ciki da tsanarta da ke taso masa, burin sa kawai ya gansa a ɗakin sa ko zai samu salama daga azabar da yake ciki

Su Momy tashin hankali bai sa sun kula da SHAREEF ba, halin da Maryamun take ciki ya ɗimauta su tare da saka musu wasi-wasin ganin yanda cikin nata ya kumbura yayi ƙato

Dady ne yayi ƙarfin halin furta, "matsa in ɗauke ta mu kaita saman kujera, da alamu akwai matsala; kina ganin cikin da nake gani a jikinta?"

Momy tace, "nima abun da nake gani kenan, tabbas akwai abun da ke faruwa Alhaji, yakamata mu kira Malam ya duba ta, sabida ka san ina zargin dama tun farko tana da mutanen ɓoye."

Ɗaukar ta yayi ya kaita saman dogon kujera ya shimfiɗa ta, har yanzu ba ta motsi tamkar gawa. Sai ya dauko wayansa yayi dealing Malamin da ke bata rubutu tana sha

A sa'ilin Sadiq ya shigo gidan ya tarar da su a wannan halin, hankalin sa shima a tashe yake kallon yanda cikin Maryamun ya kumbura, a rikice ya dubi Momy yana tambayarta, "what's going on?"

Kasa ba shi amsa tayi; sai neman wuri tayi ta zauna tana kallonsa idanunta jawur but ta ƙi ce masa komai

While Dady kuma da ke wayan; bayan ya gama ya kalli Sadiq da sauri yace masa, "Sadiq maza ajiye Jakar; ka tafi gidan Malam Abdu ka ɗauko sa yanzu yana jiran ka."

"To Dady." Ya amsa mishi yana ajiye Jakar kamar yanda ya ba shi umarni, ya fita da hanzari

Su kuma suka zauna zugum-zugum kowannen su yana cike da al'ajabin wannan al'amari, sun kasa ma ƙwaƙƙwaran motsi bare su suyi wata magana a tsakanin su, sai kallon Maryamun suke yi sun zuba mata ido sun yi jigum da tunanin abun da zai biyo baya.
***

         
_____After Malam Abdu ya zo, bayan ya zauna yake kallon Maryamu, kallo ɗaya da yayi mata ya gane tabbas tana fama da mutanen ɓoye ne, amma bai ce komai ba sai da ya tambayi Dady duk abun da ke faruwa

Nan ya sanar masa tun daga result da Likitan ya basu, har kawo yanzu daga fitowar ta suka ga cikin ta a haka, da kuma zargin da suke yi a kan ɗansu ne yayi mata cikin tunda haka tace Maryamun

Sai da ya saki ɓoyayyiyar ajiyar zuciya ya sake kallon inda Maryamun ke kwance tamkar gawa, sai yace, "alal haƙiƙa abun da nake gani a nan Jinnul Ashiq ne suka shafi yarinyar nan, muddin suka kasance suna saduwa da ita dole zasu riƙa zuwa mata da siffofin mutanen da ta sani ne, wasu yana faruwar musu a mafarki ne, wasu kuma yana faruwar musu kamar zahiri, to idan har ba a dauki mataki ba abun zai ci gaba da tafiya, daga ƙarshe zasu hana kowacce Mace jin daɗin Mijinta muddin tana da aure, zasu cire mata sha'awar Miji sai wannan mafarkin da take yi shi kaɗai ne zai riƙa mata dad'i, wasu ma kafin su yi aure; daga zaran manemi ya zo wurin yarinyar, zasu yi ƙoƙarin koransa, daga nan ne fa zaka ga wasu Matan sun kasa auruwa sabida suna tare da wannan matsalar, babbar cuta kenan, ina ganin wannan ba wata matsala bace, duk da ban taɓa ganin irin nata zahiri ba. Sau da dama suna haihuwa da bil'adama amma a zahiri ba a ganin Yaran; su kaɗai suke ganin cikin sannan Yaran ma su kaɗai suka san dasu, amma kuma abun mamakin ita a zahiri abun ke faruwa, tunda ga ciki nan a fili."

Sosai bayanin Malam Abdu ya sake ɗaga musu hankali, gaba ɗaya sun yi shiru damuwa ce fal a kan fuskokinsu; yayinda zuciyoyin su ke cikin tashin hankali mara misaltuwa

Bayan ya gama musu bayanin ne; sai Dady yace, "don Allah Malam a san yanda za a yi a taimaki yarinyar nan, muna cikin tashin hankali matuƙa."

"Babu komai wlh, komai ka ga mafarin sa akwai ƙarshen sa, bare aljanu ne dole ayar Allah zai yi tasiri a kansu, don haka ku kwantar da hankalin ku, insha Allahu bi'iznillah yarinyar zata samu waraka, zan yi duk yanda zan yi wajen raba ta da su."
Nan ya saka aka kawo mishi ruwa a cup, ya soma addu'o'i tsawon lokaci bai dena ba, ya jima yana yi wanda ya ɗauke shi tsawon awanni kafin ya basu ruwan yace, "a zuba a gora a ajiye, kullum a riƙa shafa mata a cikin da saman kanta sau biyu a rana, insha Allahu ko me ke akwai da yardan Allah zamu ga sauƙin lamarin, idan ma akwai wata matsalar zan sake dawowa in Allah ya yarda, Allah ya bata lafiya."

"Amin ya Allah." Dukkan su suka amsa

Sai kuma ya sake cewa, "su samo littafi ya faɗa musu wasu addu'o'in da zata riƙa yi kullum da dare, idan baza ta iya ba ana karanta mata kowanne dare."

_Aya ta ɗaya zuwa goma cikin suratul Kahf.. sai kuma ƙarshen Suratul mu'uminun... Aya 54 zuwa ta 56 cikin suratul A'araf, sannan ta karanta wannan addu'ar kamar haka; Allahumma inni a'uzu bika min sú'i ahlami, wa'astajiruka min talaubish shaiɗan fil yaqzati wal'manàmi..._

Daga bisani Dady yayi masa godiya sosai, sai ya tashi ya raka sa bayan ya kira Sadiq yace, "ya zo ya mayar da shi gida."

Suna fita Momy ta ɗibi ruwan ta soma shafa mata a cikin nata, sannan ta cire ɗankwalin kanta shima nan ta shafa mata, but ko gezau Maryamu bata yi ba, a tunanin ta zata ga ta farka,
Shi yasa ta zauna shiru tana kallonta yayinda take ƙara jin tausayin ta,
Bayan Dady ya shigo take kallonsa da faɗin, "Alhaji hankalina ya kasa kwanciya, har yanzu bata motsa ba kuma na shafa mata ruwan."

"Deeja mu jira mu ga abun da hali zai yi, tunda Malam ya faɗa mana abun da ke damun ta; kuma kika ga ga abun da ya bayar, muyi mata abun da yace kawai, ciwo faraɗ ɗaya yake shiga; sauƙi sai a hankali, Allah zai bata lafiya."

Ta amsa mishi da Amin hankalinta na a kan Maryamun

"Yanzu abun da ya dace, sai ta koma ɗakin ki da zama don bazai yiwu mu bar ta a ɗaki ita kaɗai ba, sai ki riƙa taimaka mata addu'o'in ke ma kina mata, insha Allahu komai zai wuce."

"Allah yasa." Tayi maganar tana jan numfashi

A taƙaice dai haka suka kwana a wannan ranan cikin damuwa da zullumi, Maryamu bata farfaɗo ba tana nan a yanda take, abun duniya ya dame su matuƙa, amma sun tsaya su ga ikon Allah zuwa safiya

A washe garin ma da ta farka; jikin babu sauƙi gaskiya a yanda suka gani, tunda ko um bare um um ba ta cewa, tana kwance sai yanda aka yi da ita, shiyasa Momy ta dage da yin mata addu'o'i sosai tana shafa mata, wasu kuma ta bata, har yanzu dai jikin babu dad'i, ga zafin jiki kamar garwashin wuta, ƙarshe ma in ta rufe ido ta dinga barci ba ta farkawa sai ta jima tana barcin

Sai da Malam ya sake dawowa ya duba ta; yace, "su ci gaba babu wata matsala, a hankali zata samu sauƙi, da alamu Aljannun ba ƙananu bane; bayyanar su zai yi wuya, sun rigada sun jima a jikinta."
Ya daɗe yana mata karatu don ma ya tabbatar ya gani ko zasu bayyana; but sun ƙi bayyana, sai kuka da take yi tana ihu kamar ana yanka ta,
Har ya gaji ya dena karatun ya basu wasu addu'o'in yace, "a ci gaba da mata."

Duk wannan bidirin SHAREEF yana ganin abun da ke faruwa amma bai taɓa magana ba bare ta ba shi tausayi, don har yanzu ganin baƙin ta yake yi; tunda har ta iya masa sharri to kaɗan ma ta gani, bai taɓa jin ɓurɓushin tausayin ta ba, tuni ya koma aikin sa don ma kar ya ci gaba da zama a gidan yana ganin abun takaici, tunda yanzu Momyn ma fushi take yi dashi har yanzu ta ƙi saukowa, ko gaisuwar sa sai ta ga damar amsa mishi, Dady ne kawai bai canza mishi ba. Abun yana damun SHAREEF, shiyasa the more yana ƙara jin tsanar Maryamu a ransa ne, sanadiyyar ta mahaifiyarsa ta ɗauki tsawon wannan lokacin tana fushi dashi; babu magana mai daɗi a tsakanin su, har yanzu kuma yana nan a kan bakan shi don ya rigada ya saka a ransa bazai taɓa zama da mahaukaciya kamar ta ba, domin a yanzu kallon mara hankali yake mata, musamman ranan da ya dawo aiki ya ga Momyn ta danne ta tana mata karatu; alamun kamar aljanun nata sun tashi ne sai kuka take yi da kururuwa, tunda ya shigo ya sulale ɗaki ya garƙame ƙofa, bai fito ba sai da aka kira sallan magriba

Bayan ya dawo ne Momy ta same shi ta dinga mishi faɗa kamar zata ari baki, tace, "sabida shi ba a isa a saka shi abu yayi ba; duk halin da yarinyar nan take ciki bai taɓa kallonta yace mata sannu ba, tunda ciwon ba a jikinsa yake ba, sannan ba shi da tausayi ko kaɗan yana ganin yarinya tana a cikin lalura bazai iya ce mata ya jiki ba, wlh idan bai kuka da kansa ba wata rana sai ta ci masa mutunci tunda bai san inda ke masa ciwo ba."

Masifa sosai ta dinga mishi SHAREEF ya kasa ce mata komai, haka ta gaji tayi shiru don kanta

Shi kansa Dady abun ba ya masa dad'i, bai san wanne iri ne SHAREEF ba, me yarinyar nan ta tare mishi da ya tsane ta haka? Ba ya son ganin ta ne a rayuwa ko a gidan ne ba ya son ganin ta sun kasa gane masa?
Duk faɗan nan kuma da Momy tayi masa ya ƙi cewa komai, ƙarshe sai ya wuce ɗaki ya rufe kansa ya ƙi fitowa, ko abinci bai ci ba, su ma babu wanda ya kira sa bare ya damu dashi, ai cikin sa ne, idan ya ji yunwa zai fito.
***

             
_____Kwanaki sun soma ja kafin Maryamu ta soma samun lafiya har tana iya gane mutane, cikin nata ya koma ya ɓace ɓat, sun ga sauyi sosai, sai dai kuma rashin samun ishashshen lafiya da har yanzu babu a tare da ita, sai ya zamana ko tafiya yanzu ba ta iya yi saboda ciwon ƙafa da ya sako ta gaba, duk wanda ya kalli Maryamu a ɗan wannan lokacin zata baka tausayi saboda yanda ta koma tsaban ciwo, duk ta yanƙwane ta fita a hayyacinta gaba ɗaya, kullum bata da sana'a sai kuka saboda zafin ciwo, ga idanunta kullum a kumbure suke sun yi wani irin ja; abun ka da mai manyan ido baza ka so ka sake kallonta ba in kayi mata duba ɗaya. Tabbas ba ƙaramin jinya ta sha ba, don ma wai an tashi mata tsaye ne sosai da neman magani, ya zamana komai sai dai Momy ta yi mata ba ta iya yin komai tunda ba ta iya tafiya gaba ɗaya tana zaune wuri ɗaya, sai jikin kamar yayi dad'i sai kuma ya sake rikice mata

Su Feena da suka ji shiru ba ta zuwa school, musamman suka zo duba ta tunda a tunanin su jikinta ya tashi, ilai kuwa yanda suka yi hasashe ne; rashin lafiya ya ɓoye ta, sun yi mamaki matuƙa sanda suka zo suka iske ta cikin wannan laluran, dukkansu sai da suka zubar mata da hawaye domin duk wanda ya san Maryamu ada bazai ce ita ce yanzu ba, ta wani ƙanjame tamkar ba ta iya fahimtar wasu abubuwan ma

Su kansu su Momy sun rasa yanda zasu yi, dole suka ɓoye wa iyayenta halin da take ciki tunda baza su iya sanar musu ba, hankalin su zai tashi fiye da nasu, sai dai suna iya bakin ƙoƙarin su kasancewar akwai kuɗi duk inda suka ji mai magani suna kwatanta neman taimako wurin sa

Allah da ikonsa suka samu Malamin da ya soma basu taimako cikin ƙanƙanin lokaci sauƙi ya soma samuwar mata, shiyasa suka dage suna kaita wurin sa tunda an soma samun sauƙi. Shi kansa yayi mamakin irin baƙin aljanun da ke tare da ita, amma haka ya ci gaba da basu taimako har Allah da ikonsa ta soma samun waraka, a hankali ta soma takawa duk da ba sosai ba, jiki yayi sauki Masha Allah,
Hakan ya faranta ran su Momy, ba ƙaramin dad'i suka ji ba ganin yanzu Maryamu sosai sauƙi ke samuwa

Gefe ɗaya kuma SHAREEF tuni ya manta da wani shafin ta da ɓacin ranta a tare dashi, sabida yana tare da Haseena soyayyar su kullum daɗuwa take yi, Allah da ikonsa Abbanta har ya yarda cewan ya turo Iyayensa kamar yanda yace; idan an ɗaura auren sai bayan ta gama school sai ta tare, dama kwanaki ya rage yanzu suyi hutu, idan ta dawo sai a ɗaura auren,
SHAREEF ya rasa yanda zai yi ya sanar da Iyayensa, amma kuma yanda yake ji bazai iya jure ya bar abun a ransa ba, musamman yanzu da ba shi da buri sama da ya auri Haseena ko zai samu sassaucin abun da yake ji,
Don haka ya daure ya cije ya samu Dadyn nasu da zancen maganar auren; da kuma yanda yake so a nema masa auren ta daga baya sai ta tare after ta gama karatun ta.
[23/02, 8:43 am] OumƊahirah نفيسة: 🌱🌱🌱🌱🌱

          *SHAREEF*
               _SexyBoy_
🌱🌱🌱🌱🌱


_Writer: Nafisat Isma'il Lawal_
_Wattpad: UmmuDahirah_

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝*



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

       *P.W.A✍️*





*DATA SHARE*

Call, message or whatsap  07065334256

*MTN*
500MB 150
1gb  280
2gb.  560 
3gb.   840
4gb.    1120
5gb      1400
6gb.     1700
Verlid for 30 days.












__________
*BOOK1*
_______________*FREE PAGE39*
_____Dady da tsananin mamaki yake kallon SHAREEF ɗin ya kasa cewa komai

Shi kuma ya sunkuyar da kansa gabansa na faɗuwa yana tunanin hukuncin da zai biyo baya, musamman da ya ga akwai Momy a wurin

Amma wani abun mamakin ko uffan Momy bata ce ba, sai ma miƙe wa da tayi tabar wurin ta tafi yin aikin ta

Dady kuma da ke faman kallonsa sai yace, "yanzu SHAREEF ita yarinyar dama karatu take yi bata a ƙasan ma ashe?"

Ɗan ɗago kai yayi kaɗan yana margaya kai alamun eh ya gaza yin magana

"Lallai kam! Shikenan, tunda haka ka zaɓa, na ga alamun in bamu bar ka kayi auren nan ba komai zaka iya yi, ba komai abun da ka zaɓa shi zamu yi ma, amma ka sani auren ka da Maryam koyaushe yana nan, zan bar ka kayi wannan auren ne ba don komai ba sai don ita Maryam har yanzu ƙaramar yarinya ce; sannan ba da amincewar ka tabbas muka yi auren ba, dalilin da yasa zamu bar ka ka auri zaɓin ka gudun tauye maka haƙƙi sai ka haɗa su su biyu. Zan duba maganar naka mu gani, tashi ka tafi." Ya ƙare maganar yana harɗe ƙafafunsa tare da mayar da hankalin sa a kan kallonsa

Hakan ne yasa jiki a sanyaye SHAREEF ya mike ya haura sama ya wuce ɗakin sa ransa babu dad'i, kenan dai har yanzu auren yarinyar da ya tsana yana nan a kansa? Uhmm

Bayan tafiyar sa babu jima wa Momy ta dawo wurin ta zauna

Sai Dady yace, "kina jina da ɗanki ba ki ce komai ba kin tashi?"

"Me zan ce to Alhaji? Ni yanzu bani da abun cewa in dai a kan SHAREEF ne, ya fi ƙarfin mu, tunda haka ya zaɓa mu bar sa kawai yayi auren sa, domin Ni yanzu na rigada na yanke hukuncin Maryam baza ta taɓa shiga gidan sa a haka ba; don haka bamu da wani zaɓi face mu bar sa yayi auren ko don abun da Likita yace mana."

Gyara zama Dady yayi still yana kallonta da cewan, "ban gane inda maganar ki ta dosa ba Deejah, ki yi min bayani mana."

"Abun da nake nufi, idan har muka ba shi Maryam a yanzu mun san abun da zai biyo baya tunda muna ganin yanda SHAREEF yake nuna mata; babu ko ɓurɓushin tausayin ta a ransa, ka duba yanda take wannan ciwon amma bai taɓa buɗe baki yayi mata sannu ba, bai taɓa nuna damuwarsa a kanta ba, Maryam yarinya ce bazan so ta tare a ɗakin SHAREEF face ta mallaki hankalin kanta ba, don haka in har zaka bi ta shawarata; zan so a ce Maryam ta koma wurin Ƙanwata Surayya, ta zauna a can ta ci gaba da karatun ta, hakan ne zai sa hankalin ta ya kwanta ta manta dashi har ta mayar da hankali a kan karatun ta, idan ba haka ba a nan zata ci gaba da zama cikin ƙunci ne, shi kansa SHAREEF da ba ya son ganinta idan muka nesanta su ka ga tsanar da yake mata zai sassauta mata."

Shiru Dady yayi duk da ya gamsu da maganar ta, amma bai son Maryamu tayi nesa da su, don haka yace, "ban ƙi ta taki ba Deejah, amma taya ya samu nesanta ta da mu bayan amanarta aka bani? Sannan ma muna ta mata wasa da karatun ta; a can ma ta fara karatun ne na dawo da ita nan, yanzu kuma ga shi karatun nasu yayi nisa za a gama zangon karatu na farko; kuma ga shi zamu sake cire ta again."

"To ai Alhaji kuɗi ke aiki, haka nan zamu nema mata alfarma ta ci gaba daga inda ta tsaya, kuma abun da yasa na fi sha'awar ta zauna a wurin Surayya saboda tana da Yara sa'annin ta, zata fi jin daɗin zama a can fiye da nan, ka duba maganata don Allah, na fi son Maryam ta samu karatu ta zama Mace fiye da yanda SHAREEF yake tunani, ko don wulaƙancin da yake mata."

Murmushi Dady yayi yace, "Deejah kenan! Akwai ɗaukar zafi."

Fuskarta a ɗan turɓune tace, "ƙwarai kuwa, domin abun da na ga ɗanka yake tunani kenan, raini da wulaƙanci irin nasa yasa yake ganin Maryam bata kai ta zama Matarsa ba, sai wannan mai buɗaɗɗiyar idanun; idanunsa sun rufe a kanta ita kawai yake hange, to kwanyar sa ta faɗa tunda yanzu mun ba shi damar ya Aure ta, ga shi ga ta nan."

Ajiyar zuciya ya sauke tare da furta, "Allah dai yasa mu dace, amma ba yanzu zata tafi ba ko? Domin dole sai ta sake samun sauƙi, kuma kinga akwai bikin ƴan uwanta da zamu je, ya kamata mu tafi da ita don ta ga ƴan uwa."

"A'a Alhaji, bai kamata mu je da ita ba ko don halin da take ciki, kana ganin yanda ta rame ta zabge ɗin nan; baza su ji dad'i ba idan suka ga ƴar su a haka, mu bari dai wata rana sai ta je, duk ranan da ta dawo hutu daga Abuja sai ta je can tayi musu hutu, su kuma sai mu faɗa musu karatu yasa bamu zo da ita ba mun bar ta a gidan mu."

"To Shikenan, Allah yasa hakan shi ya fi alkhairi."

Da wannan hiran nasu suka rufe caftan

Yayinda Momy tuni ta kira Ƙanwarta Autar su da ke aure a Abuja; ta sanar mata da komai, sabida dama babu wanda ya san cewa an ɗaura auren Maryamu da SHAREEF; dukka Momy ta ɓoye musu har su da suke ɗakin su ɗaya, sai yanzu da take sanar da Surayya

Ita Surayya dama bata da wata matsala; Mace ce mai kirki da sanin yakamata, kuma ma'aikaciyar gwamnati ne, Mijinta kuma Babban Soja ne ba ya zama a gidan ma, yana ɗaukar watanni bai dawo gidan ba, Yaranta uku ne dukka Mata, Yusaira ita ce babbar ƴarta, sai Aakifah wacce ita ce Sa'ar Maryamu, sai kuma Auta Na'ilah yarinya ce da bata fi shekaru shidda ba.
***

     
_____Dayake a satin Hanif zai yi graduation; shiyasa Dady yace, "SHAREEF da Sadiq su shirya su je masa." Since shi bazai samu damar zuwa ba, in fact ma shi yake zuwa Abuja wurin aikin kwangilar da suke yi, duk da akwai ma'aikatan su a can

SHAREEF ya samu abun da yake so; tunda ya samu damar zuwa wurin Haseena, don haka da zasu tafi sai da ya gargaɗi Sadiq, "in ya sake ya sanar da su Dady inda ya wuce sai yayi mugun saɓa mishi."

Sadiq na tura baki yace, "I won't tell them."

Bai bi ta kansa ba, suna zuwa airport suka rabu, Sadiq ya soma wuce wa ya hau Flight da zai kaisa England,
While SHAREEF sai da ya jira zuwa 12 ya samu Flight na Australia ya wuce.
***

_____After Sadiq yayi landing, Hanif ya saka ran zai gansu su biyun, but sai ya ga Sadiq shi kaɗai, that's why da mamaki yake kallon Sadiq yace, "wai ina Brother ɗin? Aina ya tsaya?"

Faɗa wa kan kujera Sadiq yayi yana furta, "wash Allana! Wlh Yaya na gaji; rabo na da tafiya irin wannan na jima, duk gaɓoɓi na suna min ciwo."

"Ina tambayarka kana min wannan rakin naka? ina SHAREEF ɗin ko ba tare ku ka zo ba?"
Yayi maganar yana tsare sa da ido

Sai ya tsuke fuska cike da jin haushin yanda Hanif ya ƙi damuwa da damuwar sa, ciki- ciki yace, "ya wuce Australia wai, and Ni ban san me zai yi a can ba."

"Australia?" Hanif ya furta a matuƙar mamaki, wato yarinyar can ta fi sa? Har ya iya wuce wa wurin ta ya ƙi zuwa wurin sa, bai san wanne irin so SHAREEF yake yi wa wancan yarinyar ba; da har zai iya barin sa ya wuce wurin ta, ransa sosai ya sosu; don haka bai bar abun a cikin sa ba sai da ya samu ya kira sa, da farko bai samu layin sa ba, sai daga baya, lokacin SHAREEF ya sauka yana cikin texi zai wuce gidan Haseena. Yana amsa call ɗin yace, "abun da kayi min ka kyauta kenan ko? Meyasa sai a lokacin da nake buƙatar ka zaka wuce wurin wannan yarinyar? And you know this is my time, why would you do this to me?"

"Oh! Ko dai zaka bige Ni ne kake min shouting a kunne?"

"No bazan buge ka ba, but ban ji dad'i ba, kuma zan sanar da Dady tunda abun da kayi min kenan." Ya furta da ɓacin rai yana kashe wayan ba tare da ya jira cewar sa ba

Inda SHAREEF ya bi wayan da kallo, sai kuma ya ajiye ba tare da ya kira sa ba; tunda ya san bazai taɓa kiran Dadyn ba, kuma a ransa bai ji dad'i ba sabida ya san tunda Hanif ya nuna ɓacin ransa; yau da gasken ya ɓata mishi rai ne, kasancewar sa Mutum mara saurin ɗaukar zafi, bai yi ninyar zuwa ba; but dole ya sauya shawaran zuwa gobe zai bi jirgi ya je wurin sa; since a goben ne za a yi taron

Mai Taxi ɗin yana tsayar da Motan ya fito tare da ɗan ƙaramin trolly ɗin sa. Bayan ya sallame sa sai ya nufi bakin gate ɗin yana danna door bell, but shiru ba a buɗe masa ba, dama bazata yake son yin ma Haseena, tunda bai sanar mata ba. But da ya ji shiru bata buɗe ba tsawon lokaci, dole ya nemo contact ɗin ta ya soma ƙoƙarin kiran ta,
Sai ga wata bak'ar Mota ta zo ta faka a wurin, hakan ne yasa ya dakata daga duban wayan nasa yana bin Motan da kallo, ba ya kallon na ciki kasancewar glasses ɗin ɓaki ne

Daga ciki kuwa Nana ce tare da Haseena suka dawo,
Haseena wacce bata yi tunanin ganin SHAREEF ba; suna shanyo kwanan wurin; kyakkyawar fuskarsa ta soma hango wa, shiyasa cikin ruɗu da tashin hankali tace wa Nana, "ta tsayar da Motan a wurin."

Hakan yasa Nana ta dakatar tana kallonta da mamaki, before tace, "lafiya mene ne?"
Ganin inda take kallo sai itama ta bi wurin da kallo, sai a lokacin ma ta kula da SHAREEF da ke tsaye wanda tuni ya mayar da kansa yana latsa wayansa

Ƙaran wayanta ya zaburar da ita, ta duba wayan ta ga zahiri shi ne, sai tayi saurin duban Nana tace, "sorry Honey, go now because I have a guest, I will not be happy to see us together."

Wani kallo Nana ta sauke mata tace, "Is that the guy you're talking about? Meyasa zai zo a wannan lokacin and kuma ba ki sanar min ba?"

Marairaice fuska tayi tace, "nima ban san zai zo ba, yanzu nake ganin sa, I never thought it would come to this moment."

Ɗan taɓe baki tayi before tace, "ok zan tafi, but let's go and see him, I want to know him."

Hannunta tayi saurin riƙe wa tana girgiza kanta, before tace, "nop please, ba na son ya san da ke..."

"Because of what?" Ta katse ta da furta hakan

Shiru Haseena tayi tunda bata san yanda zata yi mata bayani ba, ta san halin SHAREEF kuma baza ta so ya san suna da connection da Nana ba, musamman a yanzu da tayi irin wannan shigan, bata da maraba da tsirara, ga wani shegen gashi da ta sanya red colour a kanta, yatsun hannunta zara-zara sun sha penti da zobuna, kallo ɗaya ma yayi mata zai fahimci wace ce ita, cuz a fuska ma ga hujin hanci ga na baki, kuma duk ta zuba dogayen ɗinkunne tayi ado na ban mamaki, sai wani shegen eyelashes da ta sanya ta danƙara MakeUp a face ɗin ta

"Is ok. Na fahimta." Nana ta furta tana cije baki cike da murmushin nan nata da bai rabo a kan face ɗin ta, sai ta sake cewa, "ok zan yi kewar ki, yakamata muyi goodbye romance, duk da ya katse min jin dad'ina da yawa, ba haka naso ba." Sai ta yatsina fuska tana zura hannunta a saman cinyan Haseena ta soma shafawa, yayinda ta matso sosai ta tallabo wuyanta tana zura bakin ta cikin nata

Duk da Haseena bata cikin kwanciyar hankali, amma haka nan ta cafke bakin Nana ta biye mata, kamar abun wasa sai da suka ɗauki tsawon lokaci suna manne da juna cikin wani irin yanayin da kowaccen su burinta ta nuna wa ƴar uwanta soyayya. Haseena har ta manta da wanzuwar SHAREEF a wurin sai da ta ji wayanta ta ƙara yin ring before ta ankare. A kasalance ta zame bakin ta daga tsotson da Nana take mata, sai dai bata sauka a jikinta ba ta manne mata idanunta a rufe tana mayar da numfashi, wani irin tsantsan sha'awarta take jin yana taso mata kamar ana ingiza ta, don bata yin awanni ba sa tare da juna tsaban yanda take jin wutar sha'awar ta kamar su dauwama a tare, amma babu yanda ta iya, dole ne yasa zasu rabu yanzu, ga SHAREEF yana jiranta ya ɗauki tsawon lokaci a wurin; bata san me zata ce mishi ba muddin ya ga ita ce ta fito a cikin motan

Nana da ke shafa mata face, sai takai mata kissing a kumatu tana lanɗe ta kamar mayya, a hankali take raɗa mata, "I will miss you so much, take care of yourself, ban yarda ki ba wani kanki ba, ke tawa ce Ni kaɗai, ba na son ki bama Boyfriend ɗin ki damar taɓa ki, ok?"

Murmushi Haseena tayi mata tana gyaɗa mata kanta

While ita kuma sai lashe ta take yi kamar wacce ta samu abinci, daƙyar ta haƙura tabar ta; sai da ta ƙara tsotse mata baki ta jagula ta son ranta sannan tace, "go, he is waiting for you, bye."

Jan jikinta Haseena tayi tana buɗe ƙofan motan; tare da ɗaukar wayanta ta fice ta rufo mata ƙofan

Da tsananin mamaki SHAREEF yake kallon inda Haseena take, while itama idanunta a kansa tana bin sa da kallo duk da fargaba da tashin hankali ne a tattare da ita; sakamakon yanda ta ga lokaci guda fuskarsa ta sauya daga irin kallon mamakin da yake mata, bata gane wanne irin kallo bane sai da ta bi jikinta tana kallo; nan take gabanta daram ya yanke ya faɗi, zuciyarta ta soma tsintsinke wa.
[25/02, 7:59 am] OumƊahirah نفيسة: 🌱🌱🌱🌱🌱

          *SHAREEF*
               _SexyBoy_
🌱🌱🌱🌱🌱


_Writer: Nafisat Isma'il Lawal_
_Wattpad: UmmuDahirah_

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝*



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

       *P.W.A✍️*





*DATA SHARE*

Call, message or whatsap  07065334256

*MTN*
500MB 150
1gb  280
2gb.  560 
3gb.   840
4gb.    1120
5gb      1400
6gb.     1700
Verlid for 30 days.












__________
*BOOK1*
_______________*FREE PAGE40*
______Saurin ɗauke kanta tayi tana haɗiyar miyau cike da tsantsan tsoron da ya bijiro mata a zuciya; inda a hankali ta sake bin kyakkyawar fuskarsa da kallo; wani irin sara wa gabanta ya ƙara yi, sabida ganin yanda yake bin Motan Nana da kallo,
Wacce tuni ta ja motan a slowly tayi reverse ta bar wurin, wlh shaf ta manta da kayan da ke jikinta sai yanzu da ta fito daga motan, riga da wando ta saka, wandon tsukakke da ya kama mata jiki ya lafe sosai sabida robber ne; ga shi kuma three quarter iyakan gwiwarta, dayake brown color ne babu wanda zai ce ta saka wando ma, sai wata shegiyar figaggiyar riga baƙa mai buɗaɗɗiyar gaba ana ganin boobs ɗin ta a waje, kanta kuma ta saka facing cap sai dogayen takalma masu kyau baƙi da su

Tuni idanun SHAREEF sun cika da zallan kishi gami da tsananin mamakin ta; lokaci ɗaya suka kaɗa suka soma zama ja

Ita kanta daga inda take tana iya hango ƙyallin su tamkar hawaye ne a ciki, shiyasa ta sake ruɗe wa ta kasa kataɓus a wurin, sai ɗan kame-kame da ta soma yi

For good five minutes ago suna tsaye a wurin; shi bai motsa ba kuma bai ɗauke ido daga kallonta ba, itama kuma bata ƙaraso inda yake ba sabida tashin hankali, duk alamun rashin gaskiya ya bayyana a tare da ita, gani tayi in ta ci gaba da tsayuwa a wurin komai zai iya faruwa, shiyasa tayi shahada ta nufi wurin kamar wacce ƙwai ya fashe mata a ciki,
Tana zuwa sai ta tsaya a gabansa yayinda ta kasa kallon ƙwayar idonsa, a hankali kuma cikin yanayin da muryanta ke shocking tace, "My dear, What kind of surprise is this? Nayi mamakin ganin ka a nan, Meyasa baka sanar min ba?"

Sai a lokacin ya ɗan lumshe idanunsa yana buɗe wa a lokaci guda, ya so ya iya danne abun da yake ji amma ina; hakan ya gagara, wani irin murya yayi amfani da ita wacce daƙyar haruffan nasa suke fita tsaban tuƙuƙi da baƙin kishin da ke taso masa, hannu na rawa yake nuna hanyar da Nana ta bi wacce ta ɓace ɓat ma, "wane.. ne shi; Haseena...?"

Danne tsantsan tsoron da ke tare da ita tayi tana ƙawata fuskarta da murmushi tace, "who? Kana tunanin naMiji ne? Mace ce fa, classmate ɗina ce ta kawo Ni gida, motata ta samu matsala that's why na fita haka nan."

Wani irin runtse ido yayi yana dunƙule hannunsa kamar zai kai naushi, ko bai sani ba ya san ƙarya take faɗa masa, shiyasa ransa ya ƙara ɓaci ya buɗe ido yana zuba mata rikitattun idanunsa, "Ni.. Ni za ki yi wa ƙarya Haseena? Kina nufin Ni SHAREEF za ki yi wa ƙarya?"

Murya na rawa kamar zata yi kuka tace, "wlh ba ƙarya nake maka ba, ƙawata ce, meyasa kake son zargi na ne?"

"Shut up! or I will deal with you." Yayi maganar cikin tsawa da ninyar kai mata mari,
Amma kuma sai bai same ta ba saboda ja baya da tayi

Da tsananin mamakinsa take kallonsa kamar zata yi kuka har hawaye sun soma subo mata, jikinta sai rawa yake yi sabida bata taɓa tunanin zai iya ɗaga hannu ya mare ta ba,
Sai kawai ta ga ya juya ya bar wurin da hanzari,
A guje ta bi shi tana rungumo sa ta baya, sai ta fashe da wani irin kuka mai sauti; don ta san cewa abun da ya fi tsana kenan ya ga kukan ta

Ai kuwa take ya rikice shima jikinsa ya soma rawa, amma ya gaza tsayawa a ƙoƙarin sa ya bar wurin, riƙon da tayi masa ba na wasa bane; ga kukan ta da ke shiga kunnen sa sosai yana ƙara masa ɓacin rai da hautsina masa zuciya, take ya tsaya yana sauke numfashi akai-akai idanunsa a rufe,
Itama ta ƙi sakinsa sai ƙara manne masa take yi, cikin kuka take ba shi haƙuri tare da ƙara gasgata mishi iya gaskiyar ta, sai da tayi ta mishi rantsuwa har tana duƙa wa ƙasa

Da sauri ya ɗago ta yana bin ta da kallo idanunsa sun yi ja, "is ok, na yarda, amma." Sai ya bi jikinta da kallo yana ƙara faɗin, "meyasa kika fito da irin wannan shigan har kika fita zuwa wani wuri? Kanki ɗaya kuwa Haseena? Meyasa za ki yi wannan shigan babu maraban ki da tsirara? Ashe dama abun da kike yi kenan?"

Har yanzu tears zuba suke yi a kan kuncin ta, tana girgiza mishi kai da ɓarin baki tace, "wlh ba haka bane dear, yau ne kawai na saka su amma ban taɓa fita a haka ba, da akwai Abaya na a cikin Motan cirewa nayi."

Wani kallon rainin wayon yayi mata, babu yarda a jin zancen nata yace, "taya ya kika cire rigan a Motan?"

Kame-kame ta soma yi, sai kuma tayi saurin cewa, "Juice... Juice na sha shine ya zube min, Ni kuma sai na cire rigan kuma yanzu da zan fito ban ɗauka ba, I'm sorry ka yarda dani."

"Haseena taya ya zan yarda da ke? Zuciyata ta kasa yarda da ke, har yanzu gani nake yi Motan namiji ne, meyasa kika ƙi fitowa a Motan after kina ganina a tsaye? Almost 20 minutes kina a cikin Motan fa?"

Jikinta sai kyarma yake yi sabida ta rasa me zata furta mishi, kawai sai ta fashe da kuka tana juya wa a guje ta ta nufi ƙofar gidan, da sauri ta zura key ta buɗe ta shige

Shiru yayi yana kallonta har ta shige, daga bisani kuma sai ya taka ya bi bayanta tunda bazai iya ganin ta a cikin wannan halin ba, dole ne ya tuhume ta amma kwata-kwata ba ya son ɓacin ranta, me zai faru idan namiji ne a cikin Motan? Zuciyarsa baza ta iya jure wannan baƙin cikin ba

Koda ya shiga ganin ta yayi a saman kujera ta kwanta tana ta kuka hawaye shaɓe-shaɓe a kan face ɗin ta. Jiki a sanyaye ya ƙarisa wurin ta yana ɗago ta, tare da ɗaura ta a saman jikinsa ya soma rarrashinta, don dole ya haɗiye nasa ɓacin ran sabida bazai jure ganin kukan ta ba, zuciyarsa tana masa zafi sosai, ya tsani ya ɓata mata rai bare ya ga damuwarta, tsananin son da yake mata ba ya jin zai jure ganin ta a haka.
Ganin ya kasa rarrashinta sai yayi ƙoƙarin canza salon nasa wajen zura hannunsa ɗaya a riganta, kafin ya soma lashe mata hawayen face ɗin ta

A take a nan tayi shiru tana mayar da numfashi idanunta a rufe ruf, bata iya motsa wa ba sabida ganin abun da yake mata

Shi kuma hakan ne ya ba shi damar zura bakinsa cikin nata ya soma socking cikin ƙwarewa da tsantsan bege gami da shauƙi,
Almost 3minutes yana abu ɗaya daga bisani ya buɗe idonsa yana kallonta, sai ya cire bakin nasa yana haɗa goshin su wuri ɗaya tare da sauke mata numfashinsa a hankali

Hakan ne yasa itama ta buɗe idanun nata tana bin sa da kallo, sai suka tsira wa juna ido tsawon lokaci

Slowly in cool voice yace, "sorry sweetheart, ni ne ko? Na ɓata miki rai? Bazan sake ba, ki yi haƙuri."

Margaya kanta tayi kafin itama ta buɗe baki tace, "Ni zan baka haƙuri, amma ka yarda da Ni bazan ci amanar ka ba, kaima ka san kai kaɗai nake so kuma kai kaɗai nake kallo a namiji, bai kamata a ce ka zarge Ni ba kuma bayan na faɗa maka gaskiya."

"Ki yi haƙuri bazan sake ba, mu bar maganar ta wuce kinji?"

Kai ta gyaɗa masa

Murmushin sa mai kyau ya sakar mata; wanda dimples ɗin sa suka bayyana fili

Sai ta saka hannun ta a guda ɗaya before tace, "i love You, ina matuƙar kaunarka dear!"

"Me too sweetheart, komi ina yi ne domin ki, i love You with all my heart!"

Kanta ta janye kafin tace, "but meyasa ka zo baka faɗa min ba? Kuma ga shi ban shirya maka komai ba."

Hannayenta ya riƙe yana haɗa su da tafukan hannunsa, kana ya sakar mata kissing a laɓɓa; idanunsa ƙyar a kanta yace, "bazata nake son miki, shiyasa ban sanar miki ba, amma sai dai..."
Sai yayi shiru yana tunanin abun da zai faɗa mata kar ya ɓata mata ranta

Ita kuma tsira masa ido tayi tace, "what?"

"Kar ki ɓata rai fa."

"No bazan ɓata ba, idan ina tare da kai babu sauran damuwa." Tayi maganar tana kwantar da kanta a ƙirjinsa

"Ok zuwa gobe zan wuce, dama na zo graduation na Hanif ne na wuto nan, and kuma goben zan je wurin sa."

Murmushi tayi a ranta tana mai farin cikin jin hakan, amma a fili sai ta furta, "kar ka damu my dear, nima ai ba daɗewa zan yi ba zan dawo, only two weeks ne, daga nan kuma zamu kasance tare, ko ka manta auren mu?"

Shima murmushin yayi with happiness in his heart, "yess bazan taɓa manta wannan lokacin ba ai, ba ki san irin farin cikin da nake ji bane, amma ina matuƙar jin farin ciki a zuciyata, wannan lokacin ya fi min koyaushe a rayuwata, zan mallake ki na har abada, bani da burin da ya wuce haka, daga nan kin zama tawa babu sauran damuwa, zamu yi rayuwar mu cikin farin ciki." Sai ya ƙara haɗe hannayen su wuri ɗaya yana saƙala yatsun su sosai tare da ci gaba da furta, "na tanadar mana rayuwa mai ban sha'awa da burge wa, zamu gudanar da rayuwar auren mu irin wanda wasu Masoyan basu taɓa yi ba, akwai abubuwan ban sha'awa masu rikitarwa da burge wa dana tanadar mana, duk ranan da aka kawo ki dakina a matsayin Matar SHAREEF; nayi alƙawarin zan ba ki mamakin da ba ki taɓa gani ba, ciki kuwa har da zama bawan ki da zan yi, tun a ranan zan soma ba ki wata iriyar madaran ƙauna mai cike da garɗi da dad'i gami da zaƙi fiye da zuma. Hmm!" Sai ya ja numfashi yana goga hancin sa saman nata while idanunsu dukka a rufe

Yayinda ita kuma murmushi ne kwance a kan face ɗin ta domin ba ƙaramin daɗin kalaman nasa take ji ba, musamman yanda ya ci gaba da zayyano mata abubuwan da zai riƙa mata domin ya mayar da kansa Bawanta, haƙiƙa tana jin daɗin kalaman sa, sai dai kuma idan ta tuna a halin yanzu ba ta jin sha'awarsa sai ƴar uwanta Mace; abun yana matuƙar damun ta, soyayyar da take masa ba ta jin zai ragu a ranta, tana matuƙar ƙaunar SHAREEF, domin irin soyayyar da yake nuna mata; ita kanta tana jin baza ta taɓa iya rayuwa babu shi ba; ko da babu sha'awarsa a tare da ita zata iya zama dashi a haka ta faranta masa ransa; tunda ita bata da wata matsala yanzu tana samun biyan buƙata wurin Nana, tana jin cewa ko sex bazai kai daɗin lesbianism ba, kuma Nana ta sha faɗa mata tunda ta fahimci tana soyayya da SHAREEF,
A cewar ta, "ta rabu da SHAREEF domin wannan rayuwar da suke yi ya fi komai dad'i, baza ta gane haka ba sai sanda SHAREEF ya kusance ta."
Ita kanta tana jin cewa hakan ne tunda bata taɓa jin kamanceceniyar sha'awar SHAREEF kamar yanda take jin azababbiyar sha'awa a game da Nana ba, daɗin da take samu da gamsuwa; ga wani irin kula wa da take bata, ba ta jin zata iya rabuwa da Ita, sabida tana samun farin ciki, uwa uba kuɗin da take zuba mata a account har yanzu ta kasa gane hanyar da suke bi ita da su Herin suna samun kuɗi maƙudai haka.
***

_____Zuwa washe gari SHAREEF ya wuce England. Dama bai sanar musu zai zo ba, tunda Hanif bai taɓa tunanin zai iya canza shawara ya zo wurin sa ba

Lokacin da ya shiga Falon; fitowar Sadiq kenan daga kichen ya dafa musu indomie zasu ci su shirya su tafi, daga shi sai short trouser tare da singlet a jikinsa, ya ɗibo nashi a plate. yana ganin SHAREEF ɗin sai ya washe baki yana welcoming dinsa

Shi kuma tahowa yayi ya zauna a saman sofa yana tambayarsa, "in Hanif?"

"Yana bedroom, now he will go in; and take a bath and get ready."

"Ok."

Zama Sadiq yayi gefen sa before yace, "in kawo maka drinks ne oh tea?"

Girgiza kansa yayi yana kallon indomien da ya zuba, sai yace, "waye ya koya maka dafa indomie haka? Sai tashin ƙamshi yake yi."

Murmushi Sadiq yayi cike da farin ciki yace, "babu kowa Yaya SHAREEF, ina ganin yanda Momy take yi that's why na iya."

Ɗan ɗage masa gira yayi yace, "oh! Really?"

"Yeah."

"Allah yasa kar cikin ka ya bumbure."

Dariya yayi yace, "Allah da dad'i, kuma ka ci ka ji."

"No need."

Sun ɗan jima suna hiran; inda Sadiq yake ci gaba da cin abincin sa,
Daga baya sai SHAREEF ɗin ya miƙe zai shiga bedroom ɗin

Before ya shiga sai ga Hanif ya fito sanye da dogon wando fari, sai singlet a jikinsa, yana faman gyara suman sa da ya shafa masa mai,
Ba ƙaramin mamakin ganin SHAREEF yayi ba don bai yi tunanin zuwan sa ba, amma sai ya haɗe fuska yana tsayawa kallonsa

While shi kuma ya taho ya rungume sa tare da murmushin sa mai kyau yace, "how fer?"

"No good, I thought baza ka zo ba ai, ban yi expecting ganin ka ba." Ya ƙare maganar yana ɗan dukan sa a ƙirji

"Oh! Kayi fushi kenan? I'm sorry."

Yatsina fuska yayi yace, "sosai nayi fushi, amma ganin ka yasa na sauke, da baka zo ba gaskiya bazan ji dad'i ba, kana nuna girlfriend ɗin ka ta fi Ni."

"Common mu bar maganar, mu je mu zauna."
Sai ya kama hannunsa suna isa wurin Sadiq suka zauna gaba ɗayan su a three seater

While Hanif yace, "Sadiq zubo min nawa in ci mu tafi, time na running."

Miƙe wa Sadiq yayi ya wuce kichen ɗin

SHAREEF said, "wai kana nufin kaima wannan indomien zaka ci?"

Murmushi Hanif yayi yace, "to ya na iya? Ban da time na girka wa shine nace yayi mana before in fito wanka. So ya Haseenan? Ka je kun sha soyayya Mr. Romeo."

SHAREEF bai kalle sa ba bare ya basa amsa, illa danna wayansa da yake yi yana smile

Hakan ne yasa Hanif ya leƙa wayan, sai ya janye kansa yana cije leɓen sa tare da girgiza kansa, ɗan uwan nasa yayi nisa ba ya jin kira, yana son yin masa maganar Maryamu amma ya san halin sa yanzu zai tono sa, shiyasa ya bar maganar ma later zai tambaye sa

Basu ɗauki lokaci ba suka gama shirya wa suka wuce makarantar su Hanif ɗin.
****

_Tofa masoya yau babban rana ce fa ko? Yau zaɓe Allah Ubangiji ya zaɓa mana shuwagabanni na gari waɗanda zasu ji tausayin mu, bamu da zaɓi Allah ka zaɓa mana zaɓin ka domin shi muka fi buƙata, Allah yasa a yi lafiya a gama lafiya Amin ya Allah._
[26/02, 9:04 am] OumƊahirah نفيسة: 🌱🌱🌱🌱🌱

       *SHAREEF*
           _SexyBoy_
🌱🌱🌱🌱🌱


_Writer: Nafisat Isma'il Lawal_
_Wattpad: UmmuDahirah_

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝*



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

       *P.W.A✍️*





*DATA SHARE*

Call, message or whatsap  07065334256

*MTN*
500MB 150
1gb  280
2gb.  560 
3gb.   840
4gb.    1120
5gb      1400
6gb.     1700
Verlid for 30 days.












__________
*BOOK1*
_______________*FREE PAGE41*
_____Yau su Feena suka sake dawowa gaishe da Maryamu, tare da Amina suka taho tunda Aminar ne ta je har gidan su Feena, shi ne sai suka taho tare kasancewar sun ji shiru har yanzu bata dawo school ba; sun san cewa har yanzu jikin babu sauƙi ne tunda bata zo ba

But lokacin da suka yi sallama suka shigo sun same ta a saman sofa ta kwanta tana kallon labarai a TV, tunda yanzu Momy ba ta yarda a saka Film ko don ciwon ta, iyakan a saka labarai ko wa'azi ko ƙira'a,
Sallaman su taji a sama shiyasa ta miƙe zaune tana kallon su cike da farin ciki, sai tace, "laà! Ashe ku ne?"
Sai ta miƙe tana nufan inda suke cike da murna

Su kansu ganinta a haka yasa sun ji dad'i, alamun sauƙi ya samu kenan, duk da ɗingishi take yi har yanzu, ga shi ta rame sosai tayi fayau da ita alamun ta sha jinya, rungume kowacce su tayi tana sake musu sannu da zuwa

Feena tace, "wow! Gaskiya mun ji daɗin ganin ki a haka, wlh hankalin mu har yanzu a tashe yake a tunanin mu jiki babu dad'i ne?"

Murmushi tayi musu tana riƙe hannunsu ta ja su zuwa kan sofa, bayan sun zauna sai itama ta zauna a gefen Amina; while Feena na kan one seater da ke facing nasu, tace, "alhamdulillah ai Ni yanzu garau nake ji na, kwanan nan zan dawo school."

"Ai kuwa yakamata, domin next week exams." In ji Amina tana ƴar murmusawa

Feena kuma tace, "ina Momy ne? Gidan shiru kamar ke kaɗai?"

"Momy tana sama yanzu ta haura, a kichen ma take shine ta shiga ɗaki yanzu, mu kenan mu biyu, su Yaya Sadiq ba sa nan tun shekaran jiya, sun je wurin Yaya Hanif."

"Wai ya gama karatun sa ne? Na ji Mamana tana maganar da Abba kamar ya gama, haka dai na ji suna tad'i." Feena ta furta tana kallonta

Ita kuma Maryamu ta bata tabbacin ya gama, sannan ta miƙe tana ɗauko musu ruwa da drinks a tray ta kawo musu, sai ta wuce kiran Momy a sama

Har Amina tana cewa, "da ta bari kawai sai ta sauko, sabida ƙafanta kar su wahalar da ita."

Bata ce musu komai ba ta wuce tana dariya

Su kuma suka bi ta da kallon tausayi, gaba ɗaya ta sauya musu duk ta zabge na ban mamaki, har sanyin hali ta koya, sai idanunta da suka fito waje kamar zasu faɗo, haka ma wuyan ta duk ƙashin wuya ya bayyana alamun ta rame ba kaɗan ba, tunda Maryamu Allah ya bata jikin Mata; bata da cika sosai amma babu rama a jikinta ko kaɗan, kuɓul-kuɓul take,
Koda ta tafi ma maganar ta suke yi har sai sanda suka ji motsin saukowan su

Tare suka dawo da Momy,
Momy da fara'a take cewa, "ah ah! Su Nafisa ne a gidan ashe?"

"Eh Momy, ina yini?"

"Lafiya lau. Ya su Maman naki?"

"Lafiya ƙalau Momy, suna gaishe ki."

Itama Aminan gaishe ta tayi cikin girmamawa tana ƙoƙarin ajiye ruwan da take sha

Ta amsa cike da fara'a tana tambayarta itama mutanen gida?

"Alhamdulillah Momy."

"Masha Allah! Haka ake so."
Sai ta miƙe tace, "tana zuwa."
Ta wuce kichen,
Babu jimawa ta ƙwala wa Maryamu kira,
Bayan ta je ta miƙa mata abincin da ta zuba musu tace, "takai musu."

Tana kaimusu ta ajiye tana cewa, "wai yanzu dole zan koma school ranan Monday kenan? Ni da bana zuwa ban san ma me aka yi ba?"

Feena tace, "haka ne kam, ga shi duk an yi Tests babu wanda kika samu sai na maths guda ɗaya, shi har three tests yayi mana, amma kar ki damu sai in yi wa Abbana magana tunda rashin lafiya ne, na san zai samu Principle da maganar komai zai wuce. Kodayake Dady ma ai zai yi wa Abban magana da kansa."

"Ai insha Allahu bata da matsala tunda komai hanya ne, bare kuma rashin lafiya ne kika yi, but ranan Mondayn za ki zo ko?" In ji Amina tana kallonta

Maryamu tace, "insha Allahu zan zo, ai na ji sauki sosai, tunda ina tafiyana ko'ina zan iya zuwa."

Daga nan hiran su suka ci gaba da yi duk na school ɗin, suna bata shawaran yanda zata yi karatu kafin ranan Litinin,
Feena tace, "zata kawo mata books ɗin ta sai tayi copying wasu abubuwan."

Momy kuma nata aikace-aikacen ta a kitchen tana jiyo hiran su but bata ce musu komai ba, har ta gama ta wuce ɗaki ta bar su a nan duk sun shantake kowacce ta cire hijabi sun zauna a ƙasa suna cin abincin har Maryamu; suna labarai da dararraku

A haka Dady ya dawo shima ya tarar da su, suka gaishe shi cikin girmamawa, ya amsa su da fara'a yana tambayar su iyayensu?
Har yana ɗan zolayan su suna ta dariya,
Daga baya sai ya wuce ɗakin sa; a can Momy takai masa abincin sa

After an kira sallan la'asar sai suka wuce ɗakin Maryamu suka yi sallan a can suka dawo,
Suna zama suka ji sallaman su Sadiq, domin har Driver ya je ya dauko su a airport,
Da drivern da Sadiq suka ɗauko wasu jakunkunan Hanif, suna gaba while Hanif da SHAREEF suna bayan su sun jero a tare kamar tagwaye domin basu da bambanci komai nasu iri ɗaya ne, har t.shirt ɗin jikinsu da suka saka fari, wando kuma na SHAREEF blue ne; na Hanif baƙi

Su Feena tuni sun gyara zaman su kowacce ta natsu suna ɗan bin su da kallo

Momy da ke sauko wa daga kan bene fuskarta dauke da farin ciki tana yi wa Hanif ɗin lale marhaban

Direct wurin ta ya nufa yana dariya tare da rungume ta yana cewa, "Momyna I'm back."

"Yr welcome Son, kun sha hanya."

"Wlh kuwa Momy, ina wuni na same ku lafiya?"

Tana shafa kansa ta amsa before ta riƙe masa hannu suka isa cikin falon tana kallon su SHAREEF da ke tsaye basu zauna ba,
While driver har ya fice ma tunda ya ajiye Jakunkunan hannunsa,
Shima Sadiq wurin Momyn ya nufa yana rungume ta

Sai lokacin su Feena suka buɗe baki suna gaishe su,
Hanif da ke kallonsu yana murmusawa, shi kaɗai ya amsa su yana nufo su tare da furta, "my sister, babu Oyoyo baza ki taso ki rungume Ni ba?"
Ya ƙare maganar yana kallon Maryamu da hankalin ta ke a kan SHAREEF duk ya tafi da wani natsuwar ta, zuciyarta sai buga wa take yi, ba ƙaramin sanyi da farin ciki taji a cikin zuciyarta ba saboda arba da tayi dashi

But shi gogan bai san ma tana yi ba, don tunda yayi musu kallo ɗaya ya mayar da kansa saman waya, dalilin da yasa bai zauna ba kenan yana duba abu a wayansa

Jin abun da Hanif yace, shi ne dalilin tasowar ta cikin farin cikinta ta nufe sa yayi hug nata, "sannu da zuwa Yaya."
Ta furta tana washe baki

"Yauwa our ƙanwa, ashe haka kike da kyau fiye da a waya? Sadiq bai ɗaukar min ke da kyau ba, Mom ƙanwar mu ashe Babbar Mace ce, ai a waya nayi tunanin ƴar ƙarama ce cuz ganin wannan cute baby face ɗin nata."

Dariya suka yi daga su Momy har su Amina da ke zaune a ƙasa basu tashi ba suna kallon su

Momy tace masa, "dama ai Autana Babbar Mace ce, don ma tayi ciwo ta zabge; amma tubarakallah Masha Allah ƙin kowa ƙin wanda ya rasa, yanzu ku zauna bari in kawo muku ruwa ku sha."

Sai lokacin SHAREEF ya ɗago kansa yana sauke wa a kan Momy tare da furta, "Mom Ni ba ki yi min komai ba, su kawai kika yi kewa kenan?"

Wani harara ta narka masa, bata kai ga yin magana ba Dady ya fito yana musu magana,
Hakan ne yasa bata ce komai ba ta wuce kitchen

Dukkan su suka nufe sa suka rungume sa,
Daga bisani ya kama hannun Hanif suka zo har kan sofa suka zauna a tare yana masa congratulations

Momy lokacin ta kawo musu ruwan, sai ta zuba wa Hanif kaɗai ta miƙa masa

Ganin haka ne yasa Sadiq ya dauka ya zuba yana sha tunda ishi yake ji

While SHAREEF kuma sai ya haɗe fuska har yanzu yana a tsayen ya ƙi zama, sai kawai ya juya ya nufi saman benen bai sake cewa komai ba

Maryamu ce kawai ta bi sa da kallo kamar zata zilalar da yawu, tana jin wani irin ƙaunarsa na ƙara mamaye mata zuciya, shi kaɗai take ganin kyawun sa a wurin, farar fuskarsa ta fi komai saka ta nishaɗi

Su Feena da suka kula da ita, suna ganin irin kallon da take yi wa SHAREEF ɗin, abun ya basu mamaki duk da su ma kallonsa ɗin suke yi, musamman ma Amina wacce bata sanshi ba, ita gani take yi kamar ƴan biyu ne da Hanif, baza ta tantance wanda ya fi kyau a cikin su ukun ba, sai dai SHAREEF ya fi kwarjini ne da ɗaukar ido sabida hasken sa mai kyau da dimples ɗin sa da ke bayyana in yayi magana, hakan ke jawo hankalin mutane gare shi; ba ƙaramin kyau yake ƙara masa da haiba ba, sai kuma sassanyar muryan sa ko magana yayi sai ka juya ka kalle sa,
But a zahiri Sadiq ya fi su kyau tunda shi yana da manyan idanuwa masu haske; kuma yana da ɗan fara'a a fuska,
Bata taɓa ganin waɗanda suka bata sha'awa irin waɗannan samarin ba, daga ita har Feena sun kasa sakin jikin su sabida ganin Samarin; kowacce tana jin kunya duk sun takure, ga shi Hanif sai jansu yake yi da hira kamar ya daɗe da sanin su, amma kunya ya hana su zama, dole suka yi musu sallama suka ce zasu tafi

Momy tace, "su je su yi wa Driver magana sai ya kaisu gida."

Tare da Maryamu suka fita har haraban gidan, sai da ta ga tafiyan su sannan ta ɗingisa ƙafa ta dawo ciki,
A wurin Hanif ta zauna suna hira a tare suna ta dariya gaba ɗaya,
Amma ban da SHAREEF don ya ƙi fitowa yana can ɗaki,
Sai da aka kira sallan magriba sannan ya fito suka haɗu da su Hanif suka wuce masallaci

Sai bayan sallan isha'i suka dawo gidan, dukkan su a saman Dinnig suka zauna a tare suka ci abinci yau,
Bayan an gama suka dawo suka ɗan taɓa hira kaɗan,
Shi Hanif tuni ya wuce daki tunda akwai gajiya a jikinsa, sai da ya ɗan jima da shigewa before SHAREEF ya bi bayansa

Dady yace, "kai Sadiq baza ka je ka kwanta bane; ka huce gajiyar?"

"No Dady ba na jin barci, ina nan tare da ku muyi hiran mu, ban jin gajiyar komai."

Murmushi Dady yayi

Ita kuma Momy tace, "mu ma ai ba jima wa zamu yi ba yanzu zamu kwanta, hiran ya isa haka."

"Ita dai daughter tuni tayi barcin ta ta huta, saura mu." Inji Dady yana ɗan muskuta zaman sa

Momy tace, "ai tun ɗazu nake kula da ita tana ta hamma, ban ma farga ba ashe har tayi barcin? Sadiq ko zaka kaita ɗaki?"

Ɗan waro ido yayi yace, "kai Momy wlh bazan iya ba, kina ganin ta nan wasa-wasa nauyi ne da ita."
Sai ya miƙe da ɗan kuzarin sa yana cewa, "nima dai na tafi, bari in je ɗaki in duba books ɗina, good night Mom, Dad."

Sai da ya tafi sannan Momy ta ɗauke ta takaita ɗaki, suka wuce su ma ɗakunan su suka kwanta

A washe gari sai ga su Aunty Najwa da Aunty Zainab sun zo yi wa Hanif murnan kammala karatu,
Dayake Aunty Najwa ita ta taɓa zuwa sau ɗaya time ɗin Maryamu bata da lafiya Momy ta faɗa mata, har ta zo musamman ta gaishe ta,
Aunty Zainab ce bata santa ba, bayan ta ganta take cewa, "kai yarinyar ga ta kyakkyawa kuwa Khadijah, Allah ta shiga raina, anya bazan yi wa Habeeb kamu ba kawai a yi dashi?"

A lokacin Maryamu tana wurin, dariya kawai tayi bata ce komai ba

Bayan tabar wurin ne; Aunty Najwa take cewa, "wannan tuzurun? Ai tayi mishi ƙanƙanta wlh, me ma zata yi dashi? Yarinya ƴar ƙarama da ita beauty a cuce ta."

Aunty Zainab ta ɓata fuska tace, "kai Aunty Najwa gaskiya ban son haka, ina laifin don na ce a haɗa su? Wlh na ga dacewar su Allah ba wasa nake yi ba."

Sai lokacin Momy take cewa, "ai kwanan nan ma zata wuce wurin Surayyya; a can zata ci gaba da karatun ta."

"Haba dai? To sabida me? Bayan ke ma kina buƙatar yarinyar; ke da kike son ƴaƴa mata sai ki bar ta ta koma can?"
Inji Aunty Najwa tana kallon ta

Sai Momy ta ja numfashi; tare da zayyane musu ainihin abun da ke faruwa na auren su da SHAREEF

"Ikon Allah! Wai kina nufin abun nan ya faru amma ba ki sanar mana ba Khadija?" Inji Aunty Zainab tana ɗan ware ido a kanta

"Kuyi haƙuri, na so faɗa muku amma ba yanzu ba, dalili kuwa ita kanta yarinyar bamu so ta tare a ɗakin ta ba tunda kunga yarinya ce, sannan ba ma son ma SHAREEF ya sani a time ɗin, amma yanzu komai ya fito fili har ya nuna ra'ayin ba ya ƙaunar ta sai wata yarinya da ya kawo, gaba ɗaya hankalin mu bai kwanta da ita ba; amma ganin take-taken shi nema yake yi ya bijire mana a kanta shiyasa kawai muka amince, Ni kuma ba na son Maryam ta tare a yanzu ba tare da ta mallaki hankalin kanta ba, tunda SHAREEF ba ya ƙaunar yarinyar sai fama muke yi dashi, idan ta tare akwai cutuwa a wurin ta, kun san halin sa shiyasa nake son tayi nesa da mu ta je tayi karatunta ta samu wayewa ta yanda zata mayar masa da martanin duk abun da yayi mata, ba na son ya cuce ta bare mu mu tauye mata haƙƙin ta."

Aunty Najwa tace, "dama wannan Yaron yana yi da wasu ƙananun idanu ai ba mutunci ne dashi ba, SHAREEF bai da kirki ga shegen jin kai da wulaƙanci, wlh dole zata sha wahala, gwara da kika ɗauki wannan matakin, ba don Ni a nan nake ba ai da na ɗauke ta ta dawo wuri na."

Aunty Zainab ta karɓe zancen tana cewa, "bare Ni da ta fi shiga raina, gudun kawai matsala ne tunda ta zama Matarsa shiyasa bazan ɗauke ta ba, amma da babu igiyar kowa a kanta wlh Yarona zan yi wa kamu tunda shi ba ya so; ai mu muna so ato."

Momy murmushi tayi tace, "shine mu ma abun da ke damun mu, kuma ba ma son raba auren amma da mun haɗa su da Hanif, shi ya fi shi sauƙin kai bazai taɓa bijire mana ba, amma yarinyar itama tana sonshi shine matsalar, shiyasa take bani tausayi wlh, hakan ne yasa muka yi magana da Surayya nace zan kaita can, da mun so sai an yi hutu sai mu kaita ta soma zuwa makarantar, amma tace mu kawo ta kawai yanzu tunda Jarabawa ya rage musu ranan Alhamis zasu fara; sai a kawo ta zata san yanda zata yi ko jarabawar sai tayi ai babu matsala, tunda Hanif ya dawo shi zai kaita ko zuwa jibi tare da driver sai su je."

"To Allah yasa hakan shi ya fi alkhairi." Aunty Zainab tace hakan

Suka amsa da Amin, daga nan suka koma hiran maganar auren SHAREEF ɗin da za a ɗaura da zaran yarinyar ta dawo hutu,
Duk da ransu bai so ba duk sun bada rashin goyon bayan su, a cewar su, "wanne aure ne za a yi yarinya ta tafi wata ƙasa da aurenta babu Miji? Wannan ba yi bane, ai tun farko gwara kar a ɗaura a bari sai ta dawo gaba ɗaya sai a yi bikin."

Momy dai bata da yanda zata yi tunda a so samun ta ne ma kar ya auri yarinyar, amma ba damuwa tunda haka Allah yaso, yanzu abun da ya rage mata kawai ta fahimtar da Maryamu; domin baza ta so ta tafi batare da ta san da maganar ba, ko don gudun wata matsalar.
[27/02, 9:04 am] OumƊahirah نفيسة: 🌱🌱🌱🌱🌱

          *SHAREEF*
               _SexyBoy_
🌱🌱🌱🌱🌱


_Writer: Nafisat Isma'il Lawal_
_Wattpad: UmmuDahirah_

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝*



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

       *P.W.A✍️*





*DATA SHARE*

Call, message or whatsap  07065334256

*MTN*
500MB 150
1gb  280
2gb.  560 
3gb.   840
4gb.    1120
5gb      1400
6gb.     1700
Verlid for 30 days.












__________
*BOOK1*
_______________*FREE PAGE42to43*
_____Momy ita da kanta ta zaunar da Maryamu tayi mata bayanin tafiyar nata; da suke shirin tura ta Abuja ta zauna a can tayi karatun ta

Maganar ya zo mata a mugun bazata, shiyasa bata yi ƙasa a gwiwa ba tace wa Momy, "don Allah Momy ba na son a kaini can, na fi son zama da ku Momy don Allah."
Sai ga hawaye sharr; domin abu ɗaya yasa ta ruɗe lokacin sabida ganin za a raba ta da SHAREEF, wadda ba ta jin zata iya jure wa, baza ta iya nesa dashi ba, baza ta iya ba

Momy kuma sai ta kama hannunta tana kallonta na ɗan wani lokaci bata ce mata komai ba, daga baya sai tace, "ki yi shiru haka nan ba na son wannan kukan naki, abun da yasa kika ji nace hakan sabida can za ki fi jin daɗin zama ne Maryam, kinga ita tana da Yara sa'annin ki za ki yi karatun ki cikin kwanciyar hankali, ai mu ma ba a son ranmu zamu bar ki ki koma can ba Maryam."

Sai tayi saurin girgiza mata kai tana hawaye sosai a wannan lokacin, yayinda cikin rawan murya take furta, "wlh Momy na fi son zama daku, ba na son na je wani wuri, nan ya fi min can."
Sai kawai wasu zafafan hawayen suka ƙara ɓulɓulowa, taya ya zata iya sanar da Momy baza ta iya zuwa can bane duk saboda SHAREEF? Taya ya zata iya yin nesa dashi? A'a bazai yiwu ba gaskiya. Yayinda take girgiza kanta ba tare da ta san tana yi ba

Inda ita kuma Momy ta bi ta da kallon tausayi, ta san meye a zuciyarta, lokaci guda ganin ta ruɗe shiyasa ta soma rarrashinta tana faɗa mata dalilin da yasa take son tayi nesa da nan, bayan ta gama ta ƙare maganar nata da cewan, "ki yi haƙuri kinji ko Maryam? Na san SHAREEF ne a ranki, amma idan kika yi nesa dashi hakan zai kawo soyayyarki a zuciyarsa, kuma zai rage ƙiyayyar da yake miki, ki je can ki yi karatun ki; ki sauya daga yanda yake kallon ki Bagidajiya ba ki kai ba, duk sanda kika dawo zai ƙaunace ki fiye da yanda kike tunani, kuma idan kika ci gaba da zama a nan baza ki yi karatu sosai yanda ya kamata ba; kinji Ni ko?"

Ita bata fahimci mai Momyn take nufi ba, taya ya tafiyar ta zai kawo canji a kan irin ƙiyayyar da SHAREEF yake mata? Taya ya hakan zai kawo sauyi? Zata tafi ta dena ganin sa ne, zai manta da ita gaba ɗaya bazai sake tuna ta ba, ita bata ga hanyar da zai sa ya so ta ba in har bata zauna a nan kusa dashi ba, sannan ma zuciyarta baza ta taɓa iya jure wa ba, wlh mutuwa zata yi, ko dai-dai da rana ɗaya ba ta son tayi missing ganin fuskarsa, hakan kaɗai yana saka ta farin ciki

Duk yanda Momy ta so ta fahimtar da Maryamu, amma ta kasa gane wa, ta tubure a kan, "babu inda zata je."
Dama Maryamu akwai gardama, don su Momy basu san halin ta bane, tunda ta zo wurin su bata nuna musu ainihin wace ce ita ba

Hakan ne yasa Momyn tayi mata tsiya-tsiya, ta turɓune fuska tace mata, "tana yin komai ne sabida ita, tana son ta mayar da ita Macen da SHAREEF zai kalle ta bai raina ta ba, sannan ma idan ta zauna a nan a banza tunda shi auren sa zai yi; ƙarshe ita za a mayar Bora baza ta taɓa tasiri a gidan sa ba, in ta fi son hakan ya faru sai ta ci gaba da zama tana ƙunsan bakin ciki."

Sai kawai Maryamu ta fashe da kuka jikin ta na wani irin rawa kamar mazari, lokaci ɗaya ta zamo ƙasa ta dunƙule wuri ɗaya tana ihu

Gaba ɗaya Momy ta rikice, domin bata taɓa zaton Maryamun zata tayar da hankalin ta haka ba

Hanif da ke ɗaki kwance yana huce gajiyar makaranta, shiyasa ba ya fita ko'ina tunda ya dawo, babu kowa a gidan sai su kaɗai, yana ɗakin su sama-sama ya jiyo kamar kuka, shiyasa ya tashi ya fito ya ga Momy tana ta rarrashin Maryamu amma ta ƙi yin shiru. Da mamaki ya iso wurin yana tambayar me ke faruwa? Hankalin sa shima ya ɗan tashi sabida ganin yanda Maryamun take kuka sosai ta ƙi yin shiru, lokaci guda ta fita a hayyacin ta

Momy ta kalle sa ta faɗa masa abun da ke faruwa

Haka kawai ya ji tausayin Maryamu ya kama sa sosai, duk da basu fahimci dalilin da yasa take kukan ba, a tunanin su rashin son zuwa Abuja ne, sai ya zauna ya ɗago ta ta koma saman kujera ya soma rarrashinta cikin kwantar da murya

Daƙyar suka samu tayi shiru, amma hawaye sun ƙi tsaya wa a kan face ɗin ta, faɗi take yi, "don Allah Momy kar a yi masa aure, ina sonsa wlh, zan iya zama dashi a haka, ku faɗa masa ina son sa kar ya auri Wata, ina sonsa."
Abun sai ya zame mata kamar taɓin hankali, bata cikin hayyacin ta abun da take ta furta wa kenan

Shi yasa Momy ta soma mata addu'o'i cikin tashin hankali, domin a tunanin su Maryamu ta samu sauƙi daga ciwon da take fama dashi, sai ga shi lokaci guda ta rikice kamar mai aljanu tana surutai mara su kan gado,
To make hankali ai bazai yi wannan abun ba. hakan ya tabbatar wa da Momy har yanzu Maryamu bata samu sauƙi dukka ba,
Addu'o'i ta dinga mata tana tofa mata cikin tsananin tausayin ta, yayinda take salati a cikin ranta

Inda shima Hanif yake bin su da kallo damuwa kwance a saman kyakkyawar fuskarsa, wani irin tausayin ta ne yake ƙara ratsa mishi zuciya, wai yarinya kamar wannan har ta san soyayya? Wannan wanne irin son maso wani ne? Bazai so a ce wani abu ya same ta ba domin yana jin ta tamkar ƙanwarsa da suka fito ciki ɗaya gudan jinin sa, ya san waye SHAREEF. Ya san kuma yanda yake matuƙar ƙaunar Haseena. Haseena ta zama komai nasa a yanzu, tabbas a yanda take gabansa bazai taɓa kallon Maryamu ba, kai ba ma ita kaɗai ba, kowacce ɗiya Mace SHAREEF bazai taɓa kallonta ba a yanzu, amma zai so SHAREEF ya tausaya mata ko don halin da take ciki, kamar ya zubar mata da hawaye haka yake ji. Sai ya buga tagumi yana kallon yanda Momy take ta mata tofi

daƙyar ta samu ta dawo hayyacinta, amma duk da haka bata dena kuka da magiyan, "Momy kar ta bari yayi aure, tana sonshi! Ita kaɗai take son shi baza ta iya rayuwa babu shi ba, su taimaka su roƙa mata shi."

Momy sai da ta zubar da hawayenta, ji take yi kamar ta kurma kuka sabida tsananin tausayin Maryamu, da tana da hali tabbas da ta cire soyayyar SHAREEF a zuciyar ƙaramar yarinyar nan; wadda bata gama sanin duniya ba amma wata mummunan ƙaddara tana shirin faruwa da ita, tabbas da tana da hali da ta canza Maryamu da Haseena a zuciyar SHAREEF; da ta saka shi ya so ta fiye da kowa a duniyar nan, yarinya ce bai kamata a ce ta san wannan soyayyar ba, babu yarinta ko wauta a irin yanda take ganin Maryamu tana ƙaunar SHAREEF, abun har mamaki yake bata,
Sai ta janyo ta jikinta tana sake rarrashinta tare da furta, "ki yi hakuri Maryam, ko so kike yi nima in yi kukan? Ai nayi miki alƙawari SHAREEF zai so ki wata rana; kuma SHAREEF naki ne har abada, auren shi ba shine zai sa bazai so ki ba amma ba na son ki shiga gidan sa ba ya ganin darajar ki kinji ko Maryamu na? Ki yi haƙuri ki dena damuwa da shi wata rana da ƙafafuwan sa zai zo gare ki, amma in kina wannan koke-koken zai raina ki ya ƙara wulaƙanta ki, ko ba haka ba Hanif?"

Kai ya ɗaga yana taso wa a inda yake zaune, ya zo ya kama hannun Maryamu yana cewa, "maza ki share hawayen ki ki dena wannan kukan, Momy ta rarrashe ki amma kin kasa yin shiru, share hawayen." Ya sakar mata hannun yana tsare ta da kallo

Ganin yanda yayi maganar babu wasa shiyasa ta share hawayen nan take, amma wasu ne suke ƙoƙarin fitowa, sai ta kalle sa da jajayen idanunta da suka kaɗa suka yi luhu-luhu, kamar zata fashe da kuka tace, "amma meyasa Yaya SHAREEF shi ba ya so na? Ku kuna so na amma ban dashi, me nayi masa da zafi haka? Kuma meyasa zai auri wata bayan gani Matarsa? Ka faɗa masa ina son sa, idan har bai so Ni ba mutuwa zan yi, zuciyata tana min zafi sosai, Momy don Allah ki taimaka min ki yi ceton rai."
Yanda take wani irin kuka shiyasa ta ƙarisa yin maganar tana kwantar da kanta a jikin Momy

Su kansu sun rasa yanda zasu yi da ita, abun ya soma basu tsoro, gani suke yi kamar Maryamu bata kai ta san wannan abun haka ba,
Dole sai dai Momy ta kira Dady ta sanar masa halin da ake ciki, domin wani irin zazzaɓi ne mai zafi ya kama Maryamun, sai da Momy ta nuna ɓacin ranta sannan ne suka samu tayi shiru, amma kuma sai jikinta ya rikice sun rasa gane kanta

Da sauri Hanif ya nufi ɗaki ya sauya kaya ya ɗauko key ya dawo, yace, "Momy mu je asibiti kawai a duba ta."

Momy ta girgiza kai tace, "ciwon Maryam ba na asibiti bane, ina ganin har da mutanen ɓoyen ta, babu yanda za a yi kamar Maryam ta riƙa wannan abun in har ba su bane, Ni ina kokwanto wlh, mu je kawai gidan Malamin da ke bata magani."

Hakan kuwa aka yi, shi ya ɗauke ta ya dire ta a cikin Mota,
Sanda suka tafi can sai ga kiran Dady,
Haka Momy ta ɗauka tace masa, "sun je gidan Malam ya biyo su can."

Da saurin sa ko zama bai yi ba ya fito suka wuce da drivern sa,
Lokacin da suka isa Malamin duk ya gama mata addu'o'i ya tofa mata, sai sannan suka samu natsuwarta ta dawo dai-dai duk da bata dena hawaye ba

Kiran sunan ta Malamin yayi, sai ta ɗago kai tana kallonsa, yace, "share hawayenki ki dena kuka kin ji Maryam?"

Babu musu ta share hawayen tana duƙar da kanta lokaci guda jikinta sai faman rawa yake yi

Sai ya kalli su Momy yace, "har yanzu mutanen nan suna nan kusa da ita basu rabu da ita ba, amma baza su taɓa cutar da ita ba, domin a bincike na na gane ƙaunar da ke tsakanin su da ita ne shiyasa har yanzu suke tare da ita, da suna son cutar da ita da tuni sun cutar da ita, amma kuyi haƙuri ku ci gaba da yin mata addu'o'i da magungunan da nake bata, itama kanta ku saka ta ta riƙa tsare jikinta da azkar, komai zai daidaita zata ga sauƙin abun, baza su taɓa cutar da ita ba, na tabbata su ne suke wannan haukan son ba ita ba, zaku iya tafiya yanzu ma babu wata matsala."

Godiya suka yi masa sosai, inda Dady ya basa abun sadaka sabida a yi wa Almajirai sadaka, sannan suka yi sallama suka tafi tare da maganar Malam da ya tsaya musu a rai

Har suka koma gida Maryamu bata sake magana ba, duk da jefi-jefi tana share hawaye a ɓoye,
Momy ta riƙo hannunta suka shiga ciki sannan suka zauna a saman kujera

Shima Hanif zuwa yayi ya zauna tare da Dady a kan two seater,
Dady da jikinsa yayi sanyi ya rasa me ke damunsa; sai ya kalli Momy yace, "Maryam ƴata ce da na ɗauko ta daga wani wuri domin ta zauna a tare da Ni, ba na son wani abu ya cutar da ita, sai dai ga shi Allah ya ɗaura mata wata lalura da nake ganin tamkar zai zama gazawata a nan gaba, bazan so a ce in sanar da Iyayenta halin da take ciki ba domin hankalin su zai tashi, yanzu me kika ce Khadija; ya zamu yi da ita?"

Shiru Momy tayi domin ta rasa me zata ce ma, illa kallon Maryamu da take faman yi har yanzu tana sharan hawaye jefi-jefi, sai can kuma bayan ta nisa tace, "duk da mu muka haifi SHAREEF amma bamu da ikon da zamu saka soyayyar Maryam a cikin zuciyarsa, amma mu Iyayensa ne muna da ikon da zamu zaɓa mishi abun da yake so, Maryam." Sai ta kira sunan Maryamun tana kallonta, bata bari ta amsa ba ta ci gaba da cewa, "idan kin fi son ki zauna da SHAREEF a haka ba ya ƙaunar ki kinga za ki iya; shikenan zamu tayar da bikin naku kwanan nan, sai a haɗa rana ɗaya da wacce zai aura, ko?" Ta ƙare tana ɗan shafa kanta

Shiru Maryamu tayi bata ce komai ba, sai dai kishi da baƙin cikin jin cewa zai haɗa su da wata shiyasa sam ba ta fahimtar me suke cewa, amma kuma idan zata zauna da SHAREEF shi ne cikan burin ta,
Shi yasa bayan Momy ta sake mata magana a kan, "ta amince zata tare a hakan?"
Sai ta ɗaga kanta tana faman share hawaye

"To shikenan, tashi ki je ki kwanta ki huta, saura kuma ki ci gaba da kukan naki kinji ko?"

Tashi tayi ta wuce ba tare da ta furta ko kalma ɗaya ba,
Suka bi ta da kallo; kallon tausayi har ta ɓace wa ganin su

Sai Dady ya ja numfashi yana kwantar da kansa jikin kujeran tare da zame hulan kansa

Hanif yace, "Momy gaskiya yarinyar ta bani tausayi, amma ina ganin kamar har da yarinta a lamarin ta, baku san yanda SHAREEF yake son Haseena bace, kuma kun fi kowa sanin wane ne SHAREEF da abun da zai aikata, wannan yarinyar ƙaramar yarinya ce, don Allah ku rarrashe ta kawai tayi karatun ta nan gaba sai ta tare, yanzu tayi ƙanƙanta sabida SHAREEF zai iya cutar da ita."

"Kai kenan da kake ɗan uwansa kake faɗin hakan." Momy ta furta ranta babu daɗi, kawai jinjina kanta take yi zuciyarta na mata zafi a kan SHAREEF ɗin, Yaro ɗaya yana son gagaransu,
"SHAREEF bai gagare mu ba, kuma bazai taɓa gagaran mu ba, Maryam dai mu muka zaɓa mishi haka nan zai yi haƙuri ya zauna da ita, abun da yasa na sauko da zaɓin shi domin kar mu shiga haƙƙin sa da yawa, amma duk ranan da ya muzguna wa Maryam, wlh zan ba shi mamaki, don haka yanzu zamu ci gaba da shirye-shiryen tariyan ta a ranar da za a ɗaura mishi aure, tun da wancan Uwar gantalin ba tarewa zata yi ba, sannan ma babu inda zamu kaita a part ɗin ku zata zauna, muna nan tare babu yanda za a yi ya cutar mana da ƴa."

Dady ya gyaɗa kai da furta, "tabbas hakan yayi, nima abun da nake tunani kenan."

Sun ci gaba da tattauna matsalar, while shi kuma Hanif sai ya miƙe yace musu, "zai je ya dawo."
Direct sai ya wuce ya nufi Companin su ya je ya samu SHAREEF a can

Time ɗin yana cikin office din sa ba ya aikin komai sai waya suke yi da Haseena,
A lokacin shi kansa ya ɗan yi mamakin ganin Hanif ɗin, bare yanda ya gansa fuskarsa babu walwala, sai ya yi wa Haseenan sallama yace, "zai kira ta later."
Sai ya dube sa yana cewa, "ya dai na ga fuskarka a haka? Ko wani abun ne ya faru?"

Bai basa amsa ba sai da ya zauna shima ya mayar da idanunsa a kansa before yace, "lafiya ƙalau, kawai ina cikin wani yanayi ne sabida abun da ya faru da Maryam."

"Wace ce Maryam kuma?" Ya tambaye sa da mamaki sabida har ga Allah yana manta wa da Maryamu a lokaci guda idan ba ya ganta ba, kuma bai yi tunanin maganar nata bane Hanif zai yi masa a nan

Shi kansa Hanif baki ya buɗe yana kallon SHAREEF ɗin, amma duba da ya san wane ne SHAREEF kuma ya san me zai aikata; tabbas zai iya yin fiye da hakan ma, that's why yace, "kana bani mamaki wlh Brother, ina maka maganar ƙanwar mu Maryam amma kake nuna kamar baka santa ba?"

Sai kawai ya haɗe rai yana mayar da kansa jikin kujeran, yayinda ya sakar masa wani kallo ba tare da yace uffan ba

"Baka tambaye Ni me ya faru ba?"

Dogon tsaki yaja yana cewa, "to me kake so in ce maka? Ni fa bani da lokacin jin maganar yarinyar nan sabida ba ta gabana, kai baka san yanda na tsani yarinyar ba ko? Yarinyar da ta ƙulla min sharri abun da tunda nake ba a taɓa min ba, wlh I hate this girl, even in my heart I tell you this, I don't like to see her face, kuma duk ranan da na samu dama sai na ɗanɗana mata kuɗan ta." Sai ya kaɗa kansa yana jin ransa na ɓaci sabida tuna ta

Shi kansa Hanif bai san mai ya faru ba tunda ba a sanar masa ba, amma yana mamakin yanda SHAREEF ya tsani yarinyar yake ciccije baki a kanta; har yana tada jijiyar wuya, sai yace, "don Allah Brother ka sassauta mata a kan wannan ƙiyayyar da kake mata, ban yi tunanin maganar Sadiq gaskiya bane sai yanzu nake ƙara gasgata wa, Maryam yarinya ce ƙarama wacce yakamata mu jawo ta a jiki but kai ba haka ba, ko don sabida Haseena kake wannan abun?"

Haɗe fuska yayi yana aika masa da wani banzan kallo yace, "me ya sako sunanta kuma a cikin wannan zancen?"

"Sabida a kanta kake ƙin Maryam mana, Dady ya aura maka ita but ba ka son zama da ita, kuma yarinyar tana matuƙar ƙaunar ka kai baka san me ya faru da ita bane yanzu, daga an ce zata koma Abuja wajen Ammee ta zauna a can duk ta tashi hankalin ta; har sai da muka kaita wurin Malamin da ke duba ta, duk saboda kai ne fa."

"And so what? Sabida Ni take wannan haukan? Kana ganin Ni ya dace in so yarinyar nan? Har abada! Wlh never Hanif, tun kafin raina ya ɓaci ma kabar min maganar ta." Yayi maganar da tsananin ɓacin rai yana buɗe idanunsa a kan Hanif ɗin

Sai shi kuma yayi murmushi, murmushin takaici sabida har ga Allah SHAREEF ya soma ba shi haushi, ya ƙara faɗin, "taya ya zan dena maka maganar ta bayan Matarka ce? Kuma a yanzu ma haka su Momy zasu baka Matarka ka zauna da ita, don Allah Brother Maryam yarinya ce duk da na san yarinta na ɗiban ta, amma bata rasa komai ba, yarinya ce kyakkyawa komai tana dashi; and ga ta karamar yarinya, da me Haseena ta fi ta?"

"Ya ishe ka dalla, ba na son jin zancen banzan ka." Ya daka masa tsawa da faɗin haka yana firfito masa da idanuwansa da suka soma kaɗa wa

Sai Hanif yayi dariya tare da furta, "oh! Ba ka son gaskiya ko? Soyayyar Haseena ta rufe maka ido, amma abun da ka kasa gane wa Maryam ta fita komai wlh, kuma nan gaba zaka ce na faɗa maka; but dole dai ko kana so ko ba ka so sai ka zauna da ita tunda already ta zama Matarka."

"Hanif." Ya kira sunan sa cikin tsananin takaici; yana buga teburin gaban sa

Sai shi kuma ya ja tsaki yana miƙe wa, "wlh ban san irin ka ba SHAREEF, ba ka son gaskiya, kana da wani irin zuciya da babu imani a cikin ta, babu tausayi."

Da sauri SHAREEF ya miƙe ya nufo sa, sai ya shaƙo wuyansa yana ƙara zare masa ido yace, "Ni kake faɗa ma haka Hanif? A kan wannan matsiyaciyar yarinyar?"

Zagin ya shige sa ba kaɗan ba, shima haka nan ransa ya ɓaci yace, "matsiyaciya SHAREEF?"

"Eh matsiyaciya nace, ko zaka rama mata ne? Nace ko zaka rama mata ne?" Yayi maganar cikin hargagi yana ƙara shaƙo sa kamar zai kashe sa

Sai shima Hanif ya sanya hannu ya shaƙo nasa wuyan ransa a mugun ɓace yake cewa, "don baka son a faɗa maka gaskiya? Na sha ce maka halin ka ba shi da kyau SHAREEF, ka sauya hali, ban taɓa biye maka ba sabida ba na son in nuna rashin kunya a matsayin ka na Yayana, amma baka da kirki ko kaɗan; baka da mutunci, ko babu komai yarinyar ƴar uwanka ce, idan wani abu ya faru da ita..."

Bai bari ya ƙarisa maganar ba ya kwashe sa da mari, ji kake fass ya kifa masa wani bahagon marin da sai da ya fitar masa da jini a hancinsa.
[28/02, 9:13 am] OumƊahirah نفيسة: 🌱🌱🌱🌱🌱

          *SHAREEF*
               _SexyBoy_
🌱🌱🌱🌱🌱


_Writer: Nafisat Isma'il Lawal_
_Wattpad: UmmuDahirah_

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝*



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

       *P.W.A✍️*





*DATA SHARE*

Call, message or whatsap  07065334256

*MTN*
500MB 150
1gb  280
2gb.  560 
3gb.   840
4gb.    1120
5gb      1400
6gb.     1700
Verlid for 30 days.












__________
*BOOK1*
_______________*FREE PAGE44to45*
_____Shi kansa Hanif bai taɓa tunanin SHAREEF zai saka hannunsa ya mare sa ba, sabida hakan bai taɓa faruwa da su bane, basu taɓa sa'insan da yakai har da cin kwala ba, ya san SHAREEF yana da zafi da saurin fushi, kuma jefi-jefi koda cacan baki ya haɗa su bai taɓa biye wa Hanif don yana faɗa masa gaskiya a kan halayyar sa ba, ko me zai ce masa kuwa, amma yau ya sha mamakin da ya ga ya ɗauki wannan fushin har yakai ga yana cin masa kwala kuma ya mare sa

Sai da ya mare sa kuma ya sake sa yana nuna masa hanya cikin ɓacin rai da ɗaga murya, tamkar ba shi ba, tamkar ba ɗan uwan nan nasa wanda suka taso tare suke komai tare ba, ya nuna masa hanya yace, "fita min a office ko in yi ƙasa-ƙasa da kai."

Hanif da ke riƙe da kuncin sa; dauriya sosai yayi ya hana bayyanuwar hawaye a fuskar sa, amma idanunsa sun kaɗa sun yi jazur, ya kasa magana sai ɓarin baki yake yi yana son magana but ya gaza, sai kawai ya juya ya fice da saurin sa

PA da ke tsaye ya kasa zama sabida jin hayaniyar su, yana tunanin shiga don bai san me ke faruwa ba, sai ganin Hanif yayi ya fito a fusace ya bar wurin, da kallo ya bi sa yana mamakin yanda ya fita da irin wannan ɓacin ran, tabbas akwai abun da ke faruwa tunda har ya ji hayaniyar su, amma ya san Ogan sa muddin ya shiga ƙarshe zai iya mayar da abun kansa

Shi kuma Hanif kai tsaye Motan sa ya nufa da saurin sa kamar zai tashi sama, yana shiga cikin Motan sai ya saki hawayen da ya maƙale su ya kasa fitar da su a gaban SHAREEF, wai yau SHAREEF ne ya mare sa a kan kawai ya faɗa masa gaskiya? Bai taɓa zaton hakan ba, ko me yayi masa kuwa yana ganin ya fi ƙarfin mari a wurin sa,
a yanda suka taso suka shaƙu ya zama shi ne kamar tagwayen sa, Amininsa; abokin shawarar sa da komai nasa, amma yau shi ya ɗaga hannu ya mare sa? Abun ya masa zafi shiyasa ya kasa tsayar da hawayen fuskarsa, ga haɓon da yayi masa har jini ya soma ɗiga,
Sai lokacin ya san da jinin, shiyasa ya ɗauki handkerchief da sauri ya share; ya ja Motan da gudu ya fice a ma'aikatan 



Yayinda SHAREEF da ke tsaye a bakin windown office din sa, yana hangen sa har yabar haraban Companin, sakin labulen yayi ya naushi bango zuciyarsa na tafarfasa da abun da ya yi wa ɗan uwansa, yau shi ya mari Hanif a karon farko a rayuwarsa? Duk sabida ita, ita ce Silan komai, tabbas ya ga ƙyallin hawaye a cikin idanuwansa; koda bai ga sun zuba ba ya tabbata Hanif yayi kuka,
Sai ya sake naushin bangon idanunsa sun kaɗa sun yi jazur tsaban ɓacin rai da tashin hankalin abun da ya yi wa Hanif, ba shi da sukuni ko kaɗan, ya gaza zama sai zagaye office din yake yi duk da yana jin wayansa tana ƙara but bai duba ba bare ya san wane ne

Ana haka sai ga Mahmud ya turo ƙofan ya shigo duk da PA ya faɗa masa, "kamar SHAREEF ba ya cikin mood mai kyau,"
ilai kuwa kallo ɗaya da yayi masa sai da ya tsorata, bai san sanda ya taho wurin sa cikin tsananin tashin hankali yana tambayar sa abun da ke faruwa dashi?

Amma ina SHAREEF kallo ɗaya yayi masa ya ɗauke kansa, fuskarsa a martuke idanunsa jawur ya wuce sa; ya je ya zauna a kan kujera cikin taƙama da nuna isa

Sai jikin Mahmud yayi sanyi sabida ganin yanda ya ƙi kula sa yayi masa banza, duk da ya san halin SHAREEF amma bai taɓa masa haka ba, shiyasa sai yayi masa uzuri yana kallon sa a inda yake a tsayen, yace, "I'm sorry, ban yi tunanin kana cikin wani hali a yanzu ba, but zan dawo sabida akwai maganar da nake so muyi da kai; kuma tana da muhimmanci."

"Zaka iya faɗa min." Yayi maganar muryansa a shaƙe yana ɗaura hannunsa saman computern sa ya soma latsa wa a hankali duk da yanayin da yake ciki na ɓacin rai

Zuwa yayi ya zauna yana kallonsa, sai kuma ya ɗan yi shiru duk da ya ƙi ɗago kai SHAREEF ɗin bare ya sake duban sa, "dama a kan maganar su Honourable Ja'e ne da Alhaji Inuwa, maganar ta jima tun sanda gobaran nan ta faru, na so in sanar maka sai dai halin da kake ciki yasa na jingirta; da kuma son samun hujja a kan su."

Jin haka yasa SHAREEF ya dakatar da abun da yake yi yana duban sa da har yanzu idanunsa a juye suke da ɓacin ran halin da yake ciki, bai yi magana ba amma ya basa hankalin sa kacokan yana jiran jin mai zai ce

Mahmud nan ya kwashe komai ya sanar masa a kan maganar da suka yi da Shuraihu, har dawowan da yayi ya sake samun sa da kuma zargin da yake musu, sannan da ɗan binciken da yayi ya samo hujjar cewa tabbas akwai hannunsu a ciki, duk da hujjar ba wata mai yawa bane, ɗaya daga cikin ma'aikatan su ne da ke tare da Mahmud ɗin, wanda suka haɗa baki tare da su Shuraihu, shi ya kama yana waya wanda hakan ne ya samu ƙwarin gwiwan tunkaran SHAREEF da maganar a yanzu yana sanar masa

Wani irin tashin hankali ne ya bayyana a kan fuskar SHAREEF, dama ga shi yana cikin tsananin ɓacin rai, sai hakan ya ƙara harzuƙa sa nan take fushin sa ya bayyana a fili, cikin wani irin yanayi yake duban Mahmud tare da furta, "meyasa tun farko baka sanar min ba sai yanzu Mahmud? Meyasa baka sanar min ba har suka ci galaba a kan mu? Meyasa?"

"Calm down! SHAREEF, ka san lokacin kana asibiti, sannan bazan so a ce na bayyana maka wannan maganar kana cikin halin rashin lafiya ba."

Wani irin buga teburin gabansa yayi yana miƙe wa yana sakin wani huci mai zafi, yayinda ya soma sintiri a tsakankanin kujeran nasa yana dukan hannunsa da ɗaya hannun, "tabbas bazan ƙyale mutanen nan ba, wlh yanda suka ja mana asara sai su ma sun yi asarar nan, inaa hakan bazai taɓa tafiya a banza ba." Sai ya juyo yana duban Mahmud tuni idanunsa sun sake rinewa sabida baƙin ciki da fushi, "kai kana ganin Shuraihu ya zame hannunsa a kan harƙallan da suka yi mishi tayi ne? Ƙarya yake yi, ya raina maka hankali ne, Ni .. Ni Shuraihu zai ci amana? Ni ko?" Yake nuna kansa yana huci

Shi kansa Mahmud hankalin sa a tashe ne sabida halin da yake ganin SHAREEF ɗin, sai yace, "Ni kaina ina kokwanto, amma duba da yanda ya roƙe Ni sai nayi tunanin da gaske yake yi, amma zai iya yiwuwa shi ya basu gudummawa, kuma duk yanda aka yi da saka hannun wasu daga cikin ma'aikatan da muka tura can wajen kula da kayan."

Tsira masa ido SHAREEF yayi yana kallonsa, tare da ƙoƙarin kokawa da ɓacin ran da ke ƙara taso masa, hannayensa biyu ya dafa a kan table ɗin yana furta, "Dady ya basu dama sun samu galaba a kaina, nayi baƙin ciki lokacin da ya sanar min abun da ke faruwa, bamu rasa kuɗin da Dady zai ƙara bada wa a shigo da wasu kayan ba amma kuma ya ƙi yin hakan, na ji baƙin ciki duk da su suka nemi alfarma a wurin sa, kuma Dady zai yi musu hakan, sun saka mu asara mutanen nan kuma daga ƙarshe sun samu abun da suke so, karon farko. A karon farko wani ya ci galaba a kaina, wlh sai na nuna musu basu isa ba kuma dole sai na ɗauki mataki a kansu, kotu zata raba mu. Mahmud." Ya kira sunan sa cikin tsananin kaushin murya, "ina son hujja, ina son hujja ko ta halin ya-ya domin gurfanar da mutanen nan gaban kotu, kuɗin mu baza su taɓa tafiya a banza ba sai sun biya mu, da duk wanda ke da hannu a cikin su, Ni ba na faɗuwa bazan taɓa yarda wani ya ci nasara a kaina ba. Shuraihu kuma daga yau ya dena aiki a Companin nan, zan nuna masa shi wulaƙantacce ne a wuri na."
Bai bama Mahmud zarafin magana ba yace, "ya je ya kira masa Shuraihu yanzu."
Har ya miƙe kuma ya zaunar da shi; ya koma ƙwala wa PA kira

Sai ga PA da sauri ya shigo cikin office ɗin yana amsa masa

"Kayi sauri ka je ka kira min Shuraihu."

Bai tsaya tambayar ba'asi ba sabida ganin yanayin Ogan nasa, sai juya wa yayi ya fita da sauri domin aikata umarnin sa

"SHAREEF don Allah ka kwantar da hankalin ka, ka san idan baka iya kama ɓarawo ba sai shi ya kama ka, a ganina koron Shuraihu a nan ba shine maslaha ba, kuma tamkar zamu basu damar da zasu hankalta da abun da muke shirin yi ne, zamu doɗe duk wata kafa na hujjar da zamu samu. Zaman Shuraihu a Companin nan shi zai kawo mana sauƙin samun hanyar da zamu gano ainihin yanda suka aikata wannan abun."

"No. Wannan karin maganar taka bata da muhalli a nan, ko Shuraihu yana nan ko ba ya nan dole zamu samo hujja, hujja kaɗai nake buƙata, kuma bazan ci gaba da bama maci amana muzuƙuni a muhalli na ba, bazai yiwu ba."

Ganin yanda yake huci da zagaye wurin yana furta kalaman; shiyasa Mahmud ya yi shiru da bakin sa don ya san a yanzu SHAREEF bazai taɓa sauraron sa ba, abun da ya ga dama shi zai yi

Bare dama a cike da ɓacin rai yake, shiyasa ko zama ya ƙi yi har sai da ya ga Shuraihu ya shigo office ɗin nasa, bai bari ya zauna masa ba ya kalle sa a wulaƙance yace, "abubuwa biyu na tsana a rayuwata, na tsani cin amana sannan na tsani faɗuwa, duk kaine ka bada damar da hakan ta kasance dani, a Matsayin ka na Managern Company na amma ka haɗa baki da wasu ku ka ci amanata? Tell me why?"

Shuraihu ya kasa yin magana illa rikice wa da yayi saboda tashin hankalin abun da ya ji SHAREEF ke tuhumar sa, ga kuma yanda ya ga ya koma masa tamkar wani Zaki idanunsa sun kaɗa sun yi jazur alamun ya kai ƙololuwar ɓacin rai, idanunsa da suka sauka a kan Mahmud ya sadakar da cewan dole shi ne ya tona masa asiri

"Will you talk to me or stand here looking at me? why did you do this to me?"

"I don't know what you are talking about, SHAREEF? What are you talking about?" Yayi maganar cikin ƙarfin hali da son ɓoye tashin hankalin da ke tattare dashi

Jin hakan yasa SHAREEF komawa mazaunin sa ya zauna, yana kallonsa a ƙasƙance cike da wulaƙanci, sai da ya ɗauki some seconds kamar bazai yi magana ba sai ɗan huci da yake fitar wa, while shanyayyun idanun nan nasa da suke buɗe da tsantsan fushi da tijaran sa ya zuba wa Shuraihu su, and he open mouth said, "I will not sit and repeat to you what you know about him, I know you know who I am and do you know what I will do? Bazan iya ci gaba da zama da maci amana irin ka ba, daga yau na kore ka daga aiki a Companin nan, ka je can ka ci gaba da yi wa karnukan farautan naka hidima, amma ka sani; ka kuma sanar musu cewan su jira abun da zan aikata musu."

"SHAREEF..."

"Shut up and leave me my office right now," he said loudly, banging on the table

Dole yasa Shuraihun yabar office ɗin cikin ɓacin rai shima, wanda sai da ya sauke wa Mahmud wani mugun kallo before ya fice a zuciye sabida irin wannan wulaƙancin da SHAREEF yayi masa, ko kusa bai taɓa tunanin hakan zata faru dashi ba, tabbas Mahmud ya shammace shi kuma zai ga abun da zai biyo baya

"Ina son daga yau; a binciko min duk mai hannu a cikin companin nan, domin suma bazan bar su su zauna min a company ba, tunda Companin ba na Uban su bane." Yayi maganar a gadarance yana ciccije wa; kai da gani ka san ran ɗan Maza yakai ƙololuwa da faɗi, dama ya lafiyar Giwa bare tayi hauka?
Hmm SHAREEF ne fa

Shi kansa Mahmud ya so ya rarrashe sa; but ya san bazai taɓa sauraron sa ba a yanda ya hau sama, shiyasa ya tashi yayi masa sallama yana fice wa

Shi kuma ya ci gaba da juya wa a kan chair ɗin sa zuciyar sa na masa zafi da baƙin cikin abun da su Alhaji Inuwa suka yi masa, tabbas bazai saurara musu ba, sannan bazai taɓa sukuni ba in har bai ɗauki mataki a kansu ba, su jirayi lokacin da zai wulaƙanta su,
Miƙewa yayi ya zuba komai nasa a Jaka ya nufi ƙofa ya fice, kallo ɗaya ya yi wa PA yana jefa masa keys ya wuce da hanzari,
Motansa ya shiga ya fice a Companin ya nufi hanyar gida, irin gudun da yake yi shiyasa nan da nan ya isa gidan 

Yayi fargaban cewa zai zo ya tarar da ɓacin ran Iyayansa sabida abun da ya faru tsakanin su da Hanif, a tunanin sa Hanif zai faɗa musu abun da ke faruwa, amma sai ya ga akasin haka, babu wanda yayi masa maganar ma,
Ita dama Momy ba ta kula shi sai ta ga dama yanzu,
Shi kuma Hanif ko kallo bai samu daga wurin sa ba, tunda ya ga haka ya san cewa fushi yake yi dashi, sai jikinsa kuma yayi sanyi domin bai saba ganin sa a haka ba, in dai Hanif ne bai da ruƙo ko kaɗan, basu taɓa yin faɗa makamanciyar wannan ba, ko SHAREEF ne ya dena kula Hanif; shi sai ya kula sa bazai taɓa ƙyale sa ba,
Shaƙuwar su na ban mamaki ne, sun kasance Abokan juna na ƙut da ƙut, suna sharing damuwar su ga junan su, farin cikin su da akasin haka duk tare suke komai nasu,
Tare suke kwana, komai nasu tare ne, ko kaya tare suke siya ba sa bambanta komai nasu, idan ka ga sun rabu to tabbas ɗayan su yana makaranta ne, shaƙuwar su ya wuce misali shiyasa suka mayar da junan su Abokan juna kuma Aminai masu ba wa juna Shawara, amma yau ga yanda ta kasance, shi kansa SHAREEF ya san bai kyauta mishi ba,
A yanda suka nuna babu wanda ya fahimci halin da suke ciki, don lokacin an kira sallan magriba, duk gaba ɗaya suka tafi har Dady da Sadiq, kuma basu dawo ba sai da aka kira sallan isha'i, since wani lokacin haka suke yi,
After sun dawo suka zauna cin abinci a dining table

Har Maryamu da ke gefen Sadiq zaune, ɗaya side din ta Momy ne zaune a wurin,
Babu mai magana a cikin su sai ƙaran cokula da plates, Maryamu duk ta kasa natsuwa abincin ma ta kasa ci sosai, tunda ta yi wa SHAREEF duba ɗaya; ya sakar mata wani shegen kallo da ya firgita ta, ita kanta ta kasa gane wanne irin kallo ne, amma sai da gabanta ya faɗi, tabbas a ranta tana jin akwai abun da tayi masa, domin bata taɓa ganin irin wannan kallon mai muni kamar wannan da SHAREEF yake mata ba, kuskuren ta da ta ƙara ɗagowa still irin kallon yayi mata wanda take hango tsantsan tsana da ƙyama a cikin ƙwayar idon sa, bata ƙara marmarin kallon sa ba har suka tashi a wurin, ita dai tana zaune duk da abincin tura sa kawai take yi ba ta jin daɗin sa, haka kawai take jin babu dad'i a cikin ranta, ranta a ɓace yake musamman in ta tuna dole SHAREEF yana wannan halin ne sabida ita, ko ba a faɗa mata ba ta soma karantar yanayin farin cikin sa da akasin sa, yanda ta ga fuskarsa yau ga tsananin ja da tayi; alamun babu annuri a tare shi kuma yana cikin ɓacin rai, itama sai ta ji komai ya fita ranta, tana roƙon Allah a zuciyarta, "Allah yasa ba ita bace sanadin shigan sa wannan halin."
Ko kusa ba ta son ɓata mishi rai, tamkar ta mutu haka take ji muddin ya nuna ba ya son abu ta aikata shi, tana jin haushin kanta, ba ta son ya shiga damuwa sabida ita, a yanzu ita kanta tana mamakin wanne irin abu take ji a kan SHAREEF? Tana ganin kamar ya wuce soyayya, ji take yi kamar ta haukace wlh ko kuma ta dinga kurma ihu sabida ƙunci da baƙin cikin da take ji a cikin zuciyarta a game dashi da rashin mata magana da yake yi,
Shi yasa tunda ta ga ya shige daki bai zauna a falo ba, itama sai ta yi musu sallama ta tafi daki tunda tana jin barci sosai

Sai da Momy ta ja kunnen ta tace, "ta yi addu'o'in da ta saba yi kafin ta kwanta."

Ta amsa mata da to, sannan tayi musu sai da safe ta wuce dakin ta

Hanif kaɗai ne ya zauna da su Momy suna ɗan taɓa hira, shima ya ƙi koma wa ɗaki ne duk saboda SHAREEF, ba ya son ya je su zauna tare bayan abun da ya faru ɗazu, shiyasa yayi zaman sa suna ta hira da Dady, domin daga ƙarshe Momy ta wuce ta bar su a wurin

Kusan ƙarfe sha ɗaya suka kai, sannan Dady yace masa, "ya je ya kwanta haka nan."

Tare suka tashi suka nufi saman after Hanif ɗin ya kashe komai na Falon, suka yi wa juna goodnight sannan kowanne ya shige dakin sa

Hanif a tunanin sa SHAREEF ya jima da barci, tunda ganin ya shiga tun ɗazu ɗaki, ashe idanunsa biyu, yana zaune a gefen gado daga shi sai short wando fari babu riga a jikinsa, hannunsa rike da waya, tunda ya ji motsin Hanif ɗin ya ɗago ido ya kalle sa, sai ya mayar da kansa ya ci gaba da yin abun da yake yi,
While shi kuma Hanif toilet ya shiga yayi uzurin sa sannan ya fito, ya sauya shigan sa zuwa doguwar rigan barcin sa, sannan ya haye kan gadon yana juya bayansa yayi shiru, idanunsa a rufe amma ya kasa barcin, ko kusa ba ya jin ma barcin a idanunsa,
Bai taɓa tunanin SHAREEF zai iya ba shi hakuri a kan abun da ya faru ba, shi kansa dauriya yake yi amma yana son yin masa magana, bai san ya zai amshe sa ba ganin yanda ko walwala ya ƙi yi bare ya sakar masa fuska, duk da shi SHAREEF ya mara amma ba shi da riƙo ko kaɗan, tuni ya manta abun da ya faru yanzu ransa ya saki sosai, fatan sa kawai komai ya wuce, wlh bai taɓa tunanin zai iya ba shi haƙuri ba a yanda ya san halin SHAREEF, amma sai ya tsinkayi muryansa yana ba shi haƙuri a kan marin da yayi masa,
Tuni Hanif ya miƙe zaune yana kallonsa, sai ya saki murmushi kawai yana furta, "Ni ne nayi maka laifi kuma Ni ya kamata in baka haƙuri Bro, wani lokacin ina manta kai Yayana ne har nake iya furta maka duk abun da ya fito daga baki na, amma bazan sake ba Insha Allahu."

"Kana da right ɗin da zaka sanar min ko ma mene ne, sabida kai ne ɗan uwana kuma Abokin shawarata, na ji dad'i da baka sanar da su Momy abun da ya faru tsakanin mu ba, na san da yanzu Momy ta sake ɗaukar fushi da Ni, ka fi komai a wurina Hanif, ka faɗa min duk abun da kake so bazan taɓa hana ka ba, Ni kaina ban san meyasa na ɗauki zafi har haka ba, amma kayi haƙuri komai ya wuce bazan sake marin ka ba."

Sai kawai Hanif ɗin ya rungume sa cike da farin ciki, yana sake cewa, "kayi haƙuri Yaya."

Janye jikinsa SHAREEF yayi yana ɗan hararansa da wasa, yace, "ba na son Yayan nan fa, wani sai yace na girme ka ne bayan a yanzu ka fi Ni tsawo sosai, let's just live as friends."

Dariya yayi shi kuma, ganin SHAREEF ya miƙe zai fita, sai yace, "ina kuma zaka je yanzu?"

Shiru ya ɗan yi, sai kuma yace masa, "ina zuwa zan sauka ƙasa ne in sha ruwa."
Bai jira cewar sa ba ya fice,
Kai tsaye downstairs ya sauka, ya tsaya yana tunanin inda zai bi ya nemi ɗakin Maryamu, shi kansa bai taɓa sanin ina ne dakin nata ba, amma yau yana buƙatar sani ko don ya dauki mataki a kanta, kai tsaye ɗakunan da suke wurin corridor ya nufa, kusan daki biyar ne a wurin, duk wanda ya taɓa a rufe suke, ɗaya ne kawai ya ji a buɗe, but koda ya shiga babu kowa, babu kaya ma a ciki sai bed, sai ya fito ya taɓa na ƙarshen, nan ma a buɗe yake, sai ya zurma kai ciki, a nan ya hango ta kwance a saman bed ta rufe jikinta da blanket, har da ɗan sauke ajiyar zuciyar sa; tukunna ya nufi wurin kansa tsaye da tunanin abun da yakamata yayi mata.









[02/03, 9:22 am] OumƊahirah نفيسة: 🌱🌱🌱🌱🌱

         *SHAREEF*
             _SexyBoy_
🌱🌱🌱🌱🌱


_Writer: Nafisat Isma'il Lawal_
_Wattpad: UmmuDahirah_

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝*



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

       *P.W.A✍️*





*DATA SHARE*

Call, message or whatsap  07065334256

*MTN*
500MB 150
1gb  280
2gb.  560 
3gb.   840
4gb.    1120
5gb      1400
6gb.     1700
Verlid for 30 days.












__________
*BOOK1*
_______________*FREE PAGE46to47*
_____Ƙarisa wa yayi gaban gadon, ya tsaya yana faman kallonta; duk da ba ya ganin face ɗin ta kasancewar ta juya baya, tunani yake yi ta yanda zai yi ya tashe ta, cike da mugunta kuma ya saka hannu ya ɗuma mata duka

Lokaci guda Maryamu ta ji wannan dukan har cikin barcin ta, ba shiri ta tashi a firgice tana neman wanda ya duke ta a cikin barci,
A tsaye ta ga Mutum ƙiƙam wanda bata gama tantance wane ne ba, kasancewar akwai duhu ɗakin baza ta iya bambance mutumin da ke tsaye ba, ga kuma barcin ta yayi nisa bata gama wartsake wa ba

Hannu ya sanya ya kifa mata marin da sai da ta hantsala ta dungura kanta a kan gadon sabida azaban zafi; da kuma yanda marin ya zo mata babu tsammani,
Wani irin kuka ta kurma sabida tsananin raɗaɗin da ya shige ta,
Take a nan jikinta ya soma kerma tana shirin ƙara kurma ihun, domin ta gama firgita ta gigice, ba wai don marin ba, sai don tsananin tsoron wanda yayi mata wannan aika-aikan cikin wannan daren,
Sai kuma ta ji saukar hannu mai tsananin taushi da aka ɓame mata baki; hakan yasa sautin kukan nata ya ƙi fita,
Saukar muryansa da ta fito a kausashe ya tabbatarwa da Maryamu wa ke tsaye a gabanta ya aikata mata wannan ɗanyen hukunci, lokaci guda ta sake tsure wa ga tsananin mamakin jin muryansa a kunnenta, a tunanin ta ko mafarki ne, shiyasa ta sake ware idanunta a kansa tana kallonsa da kyau ta cikin ɗan hasken da ya ƙillo a window na farin wata

Shi kuma saboda tsaban mugunta gam ya rufe mata bakin nata har yana haɗa wa da hancin ta, cikin wani irin yanayi da ɓacin ranta ya gama saka shi, yake cewa, "ke dan Ubanki aina kika taɓa ganin na taɓa wasa da ke?"
Ya zazzaro mata ido yana jiran ta ba shi amsa duk da ya ƙi sakin bakin nata

Jikinta sai faman rawa yake yi tana tunanin me tayi mishi, ga shi babu damar ta motsa saboda yanda ya ɓame mata baki da hanci numfashi ma daƙyar take yi, hakan ne yasa tayi saurin ɗaura nata hannayen a kan nasa tana ƙoƙarin cire mishi hannun

Amma sai ya buge mata hannayen tare da ƙara ɓame bakin, ya sanya hannunsa ɗaya ya buga mata a kan kunci, kauu ya kaure ta da wani marin; cikin kausasa murya irin wanda yake cike da tsananin tsana gami da jin haushin ta, yace, "dan Ubanki warning na zo in buga miki, daga yau idan har na sake jin suna na a bakin ki, ko kuma kika nuna Ni kike so a gidan nan, na rantse da Allah duk ranan da kika yi gangancin zuwa cikin gidana a matsayin Matata, sai na illata ki, sai na kashe ki kin mutu murus, banza wawiya ƴar ƙauye kawai, har ke kina da bakin da za ki ce kina so na? Ni sa'an wasan ki ne? Or did I ever play with you? Ƴar ƙarama da ke shegiya ba ki kai matsayin ƴar aiki na ba ma, ki saka a ranki Ni SHAREEF na fi ƙarfin ki har abada, bazan taɓa zama da ke a matsayin Matata ba, I hate you so much, I hate you more than anyone in this world, ba na ƙaunar ki! I don't like to see your ugly black face."
Sai ya sake kifa mata wani marin yana huci tare da buga mata tsawa sabida jin zata yi masa ihu, ya zazzare mata idanunsa da suka kaɗa suka yi ja yake cewa, "har ke za ki shiga tsakani na da Iyaye na; da ɗan uwana? Ba a haife ki ba wlh, duk ranan da kika bari kika kaini maƙura sai nayi miki dukan tsiya a gidan nan, kuma ki sanar da su Momy ba kya so na, kar ki yi gigin shigo min gida sabida bazan taɓa zama da Jaka ƙazamiya irin ki ba." Sai ya tofa mata yawu wanda yayi nasaran kwalɓa mata a fuska,
Ya juya ya fice ko sake waiwayo wa bai yi ba

Maryamu she couldn't move where she was, because she was in shock, almost 3 minutes before ta ja wani irin numfashi at the same time hawaye na ɗiga zuwa kan fuskarta, waɗanda sai a yanzu suka samu nasaran fitowa, wasu hawaye ne masu ɗumi suke gudun tsere,
Hannunta na rawa ta sanya a kan face ɗin ta inda ta ji saukar yawun sa a wurin, sharo wa tayi tana kallon hannun duk da ba ta ganin komai; sabida duhu da kuma ruwan hawayen da suka cika mata ido, kalaman sa suke mata yawo a zuciya wani abu ya zo ya tokare mata a maƙogwaro,
Sai kawai ta kifa kanta a saman gadon ta fashe da wani irin kuka mai ban tausayi, kuka take yi sosai tana jin zafi da tuƙuƙi na ƙaruwa daga zuciyarta, har wani riƙe maƙoshin ta take yi tsaban yanda ta ji wani ƙululun abu mai kama da yaji ya tokare ta,
Tunda take bata taɓa jin tayi matuƙar muzanta irin na yau ba, kalaman sa sun mata ciwo kuma yanda ya wulaƙanta ta ya tofa mata yawu a kan face; hakan ya ƙara saka ta cikin wani yanayi wanda tana jin dama a ce bata fara ba, dama ace bata fara sonsa ba, meyasa take son shi? Mene ne dalili? Wacce ƙaddara ce tasa har ta san shi a duniya? Yau tana dana-sanin sanin sa a rayuwarta, meyasa tun farko ta san shi? Meyasa zuciyarta take azalzalan ta a kansa? Meyasa baza ta iya jure wannan baƙin cikin ta cire sa a ranta ba?
Amma zata iya mutuwa, tabbas zata mutu duk ranan da aka ce ta rasa SHAREEF a rayuwarta, ji take yi kamar baza ta iya numfashi a inda ba ya nan ba, ya zata yi da ranta? Meyasa ba ya sonta? Me tayi masa da zafi haka?
Tuno kalaman sa da yake faɗa mata tace wa Momy ba ta son shi, hakan yasa ta ƙara fashe wa da wani sabon kukan tana ƙanƙame zanin gadon, sai kuka take yi ta kasa yin shiru bare ta saurara wa kanta,
Tun tana yi da iya ƙarfin ta har ta gaza sai hawaye ke fita a idanunta; yayinda wani irin tsananin ciwon kai ya saukar mata, inda jikinta sai faman rawa yake yi lokaci guda ta soma rawan ɗari,
A wannan daren bata runtsa ba sabida kuka ta dinga yi ta kasa koma wa barcin ta, kalaman SHAREEF kawai take tuna wa a ranta, meyasa ita bata zo a Sa'a ba? Don kawai ta kasance a ƙauye shi ne ya tsane ta?
Tana so ta faranta masa rai, bata son ta ci gaba da ganin tsanar ta a cikin idanunsa, tana son ya so ta, tana sonshi baza ta iya rabuwa dashi ba duk wulaƙancin da zai yi mata, tana ganin kamar son sa shi ne ajalin ta, ita nata ƙaddaran kenan son maso wani wanda yake ganin ta a ƙasƙance bata kai matsayin ya so ta ba,
Dole zata tafi tabar masa gidan ko don samun kwanciyar hankalin sa, ko kusa ba ta son ta ci gaba da ɓata masa rai bare ya ci gaba da ganin baƙin ta, ko iya haka tana ji a ranta tayi Nasara, nasaran da ta ceci abun ƙaunar ta a rayuwa, zata tafi tana mai farin ciki a ranta tunda har wani abu daga cikin jikinta yana yawo a jikinsa, wata rana idan ya tuna dole zai tuna da ita, zai san cewa ta taimake sa a rayuwa, ko bai so ta ba baza ta taɓa manta shi a rayuwa ba, ta gummaci ta zauna da auren sa a haka ta ci gaba da rayuwa domin baza ta taɓa son wani bayan shi ba, shi ne duniyar ta, shi take jin zata so har ƙarshen numfashinta

Kafin safe zazzaɓin ya rufe ta sosai, kuma ga tsananin ciwon da ko ɗaga idanunta ba ta iya yi, tana son ta nuna dauriya da juriya ta tashi but ta gaza,
Har garin Allah ya waye tana nan kwance sai rawan sanyi take yi

A haka Momy ta zo ta tarar da ita cikin wani mawuyacin hali, idanunta sun kumbura suntum sun rine alamun ta sha kuka da kuma rashin barci,
Momy ta kiɗime sosai da ganin Maryamu a haka,
Da sauri ta isa wurin ta tana yaye bargon jikin nata, sai ga wani huci mai zafi ya bugo ta, take ta furta kalman Subhanallah..! Tana jero mata tambayoyi hankali a tashe

Sai kawai ta fashe mata da kuka tsaban yanda take jin ciwo mai tsanani yana sukan ta a ƙirji, tamkar ta cire ƙirjin ta yasar saboda yanda yayi mata nauyi; ga wani abu da ya tokare mata wuya har yanzu ya ƙi wuce wa, muryanta kanta ba ta fita tsaban wahala da yanda ta kwana a cikin kuka

Take Momy ta juya ta fita ta kira Dady, sai ga su sun shigo gaba dayansu ban da SHAREEF da suka bari a Falo,
Dukkan su fuskokin su cikin damuwa da tashin hankali suke kallonta

Inda Dady ke tambayarta abun da ke damun ta?

Amma Maryamu ta kasa magana sai rawan ɗari da take yi

Momy ta ɗago ta cike da tsananin tausayinta tana sakin salati, "Allah ya yaye miki abun da ke damun ki Maryam.."
Sai kuma tayi shiru tana share hawayenta da suka fito sabida tsananin tausayin Maryamu, matuƙa tana tausaya mata duba da yanda take ƙaramar yarinya amma kullum tana cikin ciwo, basu san ya zasu yi da ita ba, daga wannan sai wancan

Hanif ne yace, "Momy ina ga fa, kawai mu kaita asibiti kar jikin yayi tsanani, kinga yanda take yi fa alamun zazzaɓi ne mai zafi a jikinta."

Dady yace, "eh abun da ya kamata kenan, sannu daughter Allah ya ba ki lafiya, bari mu tafi asibiti in sha Allahu za ki samu sauki."

Hanif da kansa ya dauko ta suka fito daga ɗakin,
A time ɗin babu SHAREEF ya koma ɗaki zai shirya ya tafi Company

Tare da Dady da Hanif suka wuce asibiti,
Momy ta zauna a gida; shi kuma Sadiq ya wuce nasa ɗakin don shirin school, duk ransu babu dad'i sabida tausayin halin da Maryamu ke ciki

Lokacin da SHAREEF ya gama shirya wa ya fito, bai ga kowa a Falon ba, kuma bai damu ya san me ke faruwa ba in dai a kan yarinyar can ne, sabida a yanda yake jin tsanar ta bai ƙi ta mutu ba, duk ita ta haddasa mishi baƙin ciki, tun zuwan ta gidan komai ya soma jagule masa, musamman da ya ji zancen auren su, yanzu bai san ya zai yi ba, bai san yanda zai yi ya sanar da Haseena yana da wata Matar ba, tabbas sai dai ta dauwama a haka amma bazai taɓa amince wa ta shigo gidan sa ba, bazai taɓa ɓata wa Haseenan sa rai ba, ita ce zaɓin sa ba wannan Bagidajiyar yarinyar ba, to ya kaita ina? Ai sai mutanen da suka sanshi suyi mishi dariya duk sanda aka kalle ta a matsayin Matarsa, duk yanda za a yi sai ya samo hanyar da zai rabu da ita, koda hakan zai ja masa ɓacin rai daga wurin Iyayensa, ya san dole zasu sauko wata rana, amma bazai zauna da ita ba.
***

_____Har suka ƙarisa asibitin; Maryamu kuka take yi kashirɓan sabida yanda jikinta ya rikice, ƙarshe Hanif ya ɗauke ta zuwa office ɗin Likitan

A can Likitan yace, "ya ajiye ta a saman gadon da ke cikin office ɗin."
After ya kwantar da ita sai ya soma duba ta; duk da yana ta bata baki tayi shiru but ta ƙi, azaba ya ishe ta musamman kanta kamar zai tsage, ga jikinta da ke faman kerma

Su Dady suna tsaye a office ɗin duk sun kasa zama, kukan ta na taɓa musu zuciya kamar su zubar mata da hawaye haka suke ji, ko da gani sun san tana jin jiki

Haka Likitan ya ƙoƙarta yana duba ta har lokacin bai dena bata baki ba,
Bayan ya gama sai ya haɗa allura ya zo ya tsira mata ba tare da ta san da zuwan sa ba, zafin ciwo ya hana ta sukuni idanunta a rufe sai jin allura tayi ya lume a hannunta, ko kafin ta buɗe ido tuni ya zare alluran,
Kuka ta sake fashe wa dashi tana murkususu
"Calm down mana Maryam, yanzu me ke miki ciwo?"

Kanta ta nuna masa da hannu alamun nan yake mata azaba, kuma ko buɗe ido sosai ba ta iya yi, duk sun kumbura idanun nata sun fita a hayyacinsu

Wani alluran ya sake haɗa wa, ya gane zazzaɓi ne sosai ya kama ta sakamakon rashin samun hutu da kuma kukan da ta sha, uwa uba fahimtar damuwar da ke tattare da ita, ya san in dai yayi mata wannan alluran zata samu sauƙi in har ta samu tayi barci zata samu relief, haka ya ƙara tsira mata wani alluran,
Kafin mintuna uku kukan nata ya ɗauke, sai kuma barci ya biyo baya

Sai lokacin su Dady suka sauke ajiyar zuciya suna ƙara matsowa inda take

While Dady yace, "ya jikin nata Doctor? Fatan dai babu wata matsala babu abun da ke damun ta?"
Yayi maganar a dame

Shi kuma don ya kwantar masa da hankali yace, "babu komai Alhaji, zazzaɓi ne kawai ke damun ta wanda yayi mata mugun kamu a lokaci guda, irin wannan zazzaɓin dama haka yake da rikitar da Mutum, balle ita akwai damuwa a tare da ita sannan da rashin barci, but komai normal zata wartsake da zaran alluran da nayi mata ya sake ta, sai in baku magungunan da ya kamata ta sha, kar ku damu tana nan ma idan ta tashi sai ku wuce da ita kawai, fatan mu dai ya kamata ta cire damuwa a cikin zuciyarta ta riƙa samun Hutu sosai."

Gaba ɗayan su numfashi suka ja suna sake sakin ajiyar zuciya na jin sanyi a ransu, duk da ba kaɗan ba sun damu da jin zancen Likitan na damuwar da ke damun ta,
Duk sun san cewa bai wuce a kan SHAREEF bane wannan abun,
Musamman ma Dady da ransa ya fi ɓaci da zullumin idan har bai yi wani abu a kai ba zasu iya rasa yarinyar, a wannan lokacin bazai saurara wa SHAREEF ba sai ya ci mutuncin sa wlh idan bai bi umarnin sa ba

Likitan rubuta maganin da zata sha yayi a pepper, sannan ya bama Hanif ya je amso wa,
While su kuma suka zauna suka ci gaba da tattaunawa duk a kan matsalar Maryamun, daga baya suka koma zancen ciwon Dady da yake sanar masa, "maganin sa sun ƙare, shima yana buƙatar a duba sa don kwana biyun nan ya soma jin sauye -sauye a jikin sa."

Hakan ne yasa Doctor ya duba sa,
Ko kafin Hanif ya dawo har ya gama kuma ya rubuta mishi nashi maganin yana ba shi wasu shawarwarin

Hanif ya sake komawa ya amso na Dadyn sannan suka ci gaba da zama suna jiran ta farka,
Tsawon lokaci har Likitan ya samu pation sannan suka tashi suka fita a tare

Dady yace ma Hanif, "ya koma gida shi zai zauna."

Bayan ya tafi babu jima wa Momy ta zo tare da driver, dayake Dady ya sanar mata, "ba gado aka basu ba yanzu zasu dawo da zaran ta farka."
Amma duk da haka sai da ta taho wa Maryamun da breakfast ɗin ta tunda bata ci komai ba

Suna zaune suna jiran ta farka,
Tsawon awanni huɗu tana barcin before ta farka,
Kuma jikin nata da sauƙi ba kamar yanda aka kawo ta ba, garau ta miƙe sai kanta da ke mata ciwon ne kaɗan-kaɗan,
Sun ji daɗin ganin ta a haka sai murmushi suke yi


Likita ya sake duba ta ya tabbatar musu da babu wata matsala, sannan yace, "a bata wani abu ta ci sai ta sha maganin, inyaso sai su wuce gida kawai."
Ganin yanayin jikin nata babu ƙarfi; ya san in aka bata abinci zata samu ƙwarin jikinta sosai, yace, "a hankali shima kan zai dena."
Sai ya fita ya basu wuri

Sai sannu suke mata kamar zasu mayar da ciwon jikinsu sabida yanda suka damu da ita, tamkar ƴar da suka haifa haka suke jin ta a ransu, suna matuƙar tausaya mata,
Momy ta haɗa mata tea a cup, ta soma bata da kanta tana yi mata sannu,
After ta gama sha sai ta ciro maganin; ta bata ta afa a baki, sannan ta ƙarisa da sauran tea,
Cus ta san halin ta a yanzu, ba ta cika son shan magani bane, sai dai a bata da wani abun ban da tsuran ruwa, ta dinga kwarara amai kenan, shiyasa tunda ta laƙanci halin ta sai take dama mata koko ko kunu; ko kuma tea sai ta sha dashi

Bayan sun ga ta samu natsuwa, sai Momyn take tambayar Dady me Likitan yace ke damunta?

Dady bai ɓoye mata komai ba ya sanar mata, da irin ɓacin ran da yake ji a cikin ransa

Ita kanta Momy baƙin cikin hakan take ji, shiyasa ta furta, "wlh Alhaji ina ji a raina idan har wani abu ya samu yarinyar nan; SHAREEF ne sila, komai da ke faruwa da ita shi ne silan komai, kuma duk sabida shi ta shiga wannan halin, kuma ke Maryam sai da na fada miki ki kwantar da hankalin ki in dai SHAREEF ne kin same shi kin gama, mun rigada mun miki alkawarin tarewan ki nan kusa a cikin wannan satin ma ba sai an je da nisa ba, to me yasa baza ki cire damuwa a cikin ranki ba? Kin fi son ki kassara kanki a kan wanda bai damu da ke ba? Kina nan kina haukan sonsa?"

Maryamu da idanunta ke rufe tana sauraron su, dayake ta jingina bayanta da matashin da aka saka mata a bayanta sabida ta ji dadin zama, Momy ta hana ta kwanciya kasancewar yanzu ta gama cin abinci,
Sai da suka gama maganar ta buɗe idanuwanta da suka yi mata nauyi sabida halin ciwo, daƙyar take iya furta maganar nata sabida muryanta ta rigada ta shaƙe ba ta fita sosai, a hankali tace, "Momy Ni yanzu na canza shawara ma, na fi son in yi karatuna tunda na samu dama, ba na son ci gaba da zama a nan ki kaini inda kika ce za ki kaini, ko kuma a mayar dani gida in je in yi karatu na a can, hakan zai fi min kwanciyar hankali."

Shiru suka yi dukkan su, duk da sun ji mamakin maganar nata amma tausayin ta ne ke tasiri a ransu

Ita kuma hawaye ne suke ƙoƙarin fito mata ta sanya hannu tana share wa, yayinda ta hana bayyanan su kan kuncin ta

Dady ya kamo hannunta yace, "Maryam ke ƴata ce halak malak, duk abun da kika nuna kina so ko aina yake in dai bai fi karfina ba zan miki, don haka maganar zancen soyayyar ki da SHAREEF da kuma tarewan ki a gidan sa tana nan daram a yanzu, wannan satin mai zuwa za ki tare a ɗakin shi, ba ki da wata damuwa ki cire komai a ranki kinji ko?"

Girgiza kanta tayi wanda idanunta sun kaɗa sun yi ja kuma ta ƙi yarda ta zubar da hawaye, sai dai ƙwalla da suka taru mata, cikin rauni tace, "Dady Ni dai ba na son in tare yanzu, na haƙura karatu nake so, dama shi ya kawo Ni garin nan shi nake son yi, don Allah Dady ku cika min burina ina son in yi karatu mai zurfi."

"Kin tabbatar hakan kike so? Baza ki saka wani damuwa a ranki ba? Babu wata matsala ko?"

Kanta ta ɗaga mishi alamun eh

Hakan ya yi wa Momy dad'i don wlh kwata-kwata ba ta son Maryamu ta tare tun wannan lokacin bata san ciwon kanta ba, akwai ƙuruciya a kan Maryamu, zata sha wahala a hannun SHAREEF, yanda ba ya sonta ɗin nan kuma ya tsane ta, komai zai iya mata; baza ta taɓa jin daɗin zama dashi ba, itama kuma ba ta son hakan, ta fi so ta zauna da soyayyar SHAREEF, yana sonta tana sonshi wannan shi ne burin ta, tana jin yarinyar kamar ita ta haife ta, musamman yanda take kamanceceniya da ɗanta Sadiq kamar tagwaye, ita kanta suna kama sabida idanunsu da suke kusan iri ɗaya, sai ka ɗauka sun haɗa jiɓi da Momy fiye da Dady ma, sai dai kawai baƙin fatar da take dashi ne amma suna kama sosai, shiyasa soyayyarta take ƙara shiga zuciyarta tana jinta a ranta kamar ƴar cikin ta.
***

          
_____A lokacin Doctor ya zo ya sallame su suka wuce gida, time ɗin jikin Maryamu yayi sauƙi sosai, ita kanta tayi ƙarfin hali wurin ɓoye damuwarta, ta saki jikinta kamar wacce bata yi ciwo ba

Hanif ya ji daɗin ganin ta sai tsokanarta yake yi, yana cewa, "kamar wacce ba ita bace ɗazu ta kusa mace musu, tafiya ma ta kasa sai shi ya ɗauke ta, amma yanzu ta dawo garau da ƙafafuwanta kamar ta fi shi lafiya ma yanzu."

Sai dariya take yi kuwa, ta saki jikinta sosai domin tana jin dad'in yanda Hanif yake wasa da ita, har sanyi take ji a ranta sabida ganin kaman su ɗaya da SHAREEF, tana jin kamar shi ne a gabanta suke magana tare, hakan na saka ta farin ciki

Su kansu sun ji daɗin yanda ta saki jiki tana dariya da raha, kamar ba ita ba, hakan yayi musu dad'i 

Koda Sadiq ma ya dawo ya ganta a haka ya ji dad'i sosai, sai murna yake yi domin hankalin sa a tashe yake, ya kasa zama yayi karatun sosai sai da ya kira ya ji ko lafiyarta, ana ce masa an sallamo ta sai ya dawo gida bai tsaya ya ƙarisa lectures din nasa ba

Haka suka taru suna ta sanya ta dariya da barkwancin su, suna zaune sun yi shame-shame a Falon sai hira suke yi har su Dady, shi ne ma gwanin tsokanar yana ta basu labarai lokacin da yake gwagwarmaya a baya yana saurayi,
Har yamma suna wurin Sallah kawai ke ɗaga su, sai kuma abinci da a wurin suka ci suka baje a falon, yau basu zauna a dinning ba 

Kamar yanda SHAREEF ya saba dawowa karfe biyar sai ga shi ya shigo gidan

Ganin sa yasa Maryamu ta lallaɓa ta shige ɗaki bata ko kalli inda yake ba, domin ba ta son ta ci gaba da kallonsa tana jin tsananin soyayyarsa a ranta, yanzu dole zata saba wa kanta rabuwa dashi, ada ji take yi zata mutu muddin wata rana aka ce za a raba su, amma yanzu tana jin zata iya jure wa gwara tayi nesa dashi, wataƙil abun da Momy ta sanar mata zai kasance Gaskiya, duk sanda aka ce ta sauya ta zama babbar Mace kuma ya dena ganin ta, ƙila zai ji soyayyarta a ransa,
Amma tana jin ƙunci da baƙin cikin kasancewar wata a ransa ba ita ba, wanda hakan yasa sai da ta kasa jurewa ta dinga kuka a cikin daki, kishi da baƙin ciki ya turniƙe mata zuciya, har yanzu tana jin wannan abun da ya tsaya mata a maƙogwaro ya ƙi tafiyar mata, wurin ya bushe koda ta jiƙa da yawu ba ta jin dai-dai, ta rasa yanda zata yi, tana tunawa dashi sai ta ji hawaye da wani irin zafi a zuciyarta, ga wani nauyi da yake mata kamar tana jin ciwo a wurin

Su kuma su Momy ko kusa basu yi wa SHAREEF maganar Maryamu ba, in fact ma basu nuna mishi komai ba kan face ɗin su ba, asali ma ita kanta Momy yau ya ga sakin fuskarta, shiyasa ya ji dad'i a ransa har ya saki jiki fiye da koyaushe,
Ita kuwa Maryamu bata a cikin ransa, ya san cewa warning ɗin da yayi mata ya shiga kunnen ta baza tayi gigin kuskure abun da ya furta mata ba.
***

   
_____Momy ta so a gobe Hanif ya kai Maryamu Abuja ne,
amma Dady yace, "a'a, a bari zuwa Monday time ɗin jikinta yayi sauƙi sosai."

Momy duk ta kira Surayya ta sanar mata da halin da ake ciki, da kuma irin taimakon da zata yi mata na gyara mata Maryamun; ta zama wayayyiyar yarinya fiye da tunanin mutane, duk abun da ta san zai amfane ta ta koya mata; ita kuma ko nawa ne zata kashe mata

Surayya na dariya tace, "ba ki da matsala Aunty, ko Ni zan bada tawa gudummawar ba dole sai kin biya wani abu ba, ai nima ƴata ce musamman ma da ɗanmu take aure, zan kula da ita fiye da tunanin ki, kuma Insha Allahu sai SHAREEF ya raina kansa wlh."

Momy sai jin dad'i take yi, haka suka ci gaba da wayan, sun jima before suka kammala.



           Ranan Monday aka shirya tafiyar nata, Hanif zai kaita tunda yana son zuwa ya gaishe da Ammeen nasu,
shima sai Sadiq yace, "zai je."
Shi yasa suka shirya gaba ɗaya zasu tafi

Har Dady sai da ya yi wa SHAREEF magana, "ko zai je?"

But yace, "a'a." Sabida ganin har da Maryamu a tafiyan shiyasa ya nuna sam bazai je ba, domin ba ya fata a ce doguwar tafiya ta haɗa shi da wannan bak'ar yarinyar da yake jin tsanarta a ransa, gwara su tafi su kaɗai

Maryamu sai kuka take yi kamar me, duk da kukan nata da biyu ne, na rashin SHAREEF da kuma kewar su Momy, haka suka yi ta rarrashinta kamar zasu goya ta,
Don ma wai tare da su Sadiq zata je shiyasa ta ɗan ji dama -dama

SHAREEF na gefe yana kallon abun mamaki, ji yake yi kamar ya tashi ya nakaɗa mata dukan tsiya, sai kallonta yake yi ransa na ƙara ɓaci saboda jin sautin kukan ta da ya cika masa kunne,
Tsaki ya ja ya miƙe yabar wurin ya koma ɗakin su, ta corridorn sama ya tsaya yana kallon haraban gidan; hannunsa riƙe da goran ruwa da ya ɓalle yana sha sabida jin maƙoshin sa ya bushe,
Yana tsaye a wurin ya hange su sun fito har da su Momy sun raka su bakin Mota,
Yana mamakin yanda suke lalace wa a kan wannan yarinyar, musamman yanda ya ga ta lafe a jikin Momy kamar zata mayar da ita ciki, har lokacin sai kuka take yi,
Daƙyar suka lallaɓa ta ta shiga motan,
Takaici yasa ya kawar da kansa yana kallon wani wurin zuciyarsa na masa zafi da tunanin wani abu a ransa,
To yanzu shi ya zai yi ma da auren ta bayan basu ce masa komai ba?
Ko banza zai ji sanyi a ransa kuma yana ji a jikinsa hakan na nufin sun haƙura da maganar kenan, wannan abun farin ciki ne, jira kawai yake yi suyi masa maganar takardan sakin ta,
Sai kawai ga murmushi a kan kyakkyawar fuskarsa wanda har dimples ɗin sa suna lotsa wa sosai, suka fito da ainihin tsantsan kyawun sa,
Dai-dai sanda ya ƙara kallon Motan still da murmushin kwance a kan face ɗin sa

Karaf suka haɗa ido da ita tana cikin mota itama ta ɗago jajayen idanunta da suka gama rinewa da kuka, bata yi tsammanin ganin sa a wurin ba amma sai ta gansa

Kallon-kallo suka yi wa junan su, inda tuni SHAREEF ya ɗauke murmushin da ke face ɗin sa, kowannen su da irin kallon da suke yi wa juna wanda ya sha bamban

Har Motan ta soma tafiya but Maryamu bata ɗauke ido a wurin ba, domin wani irin sanyi da farin ciki ne ya kawo mata mamaya lokaci guda musamman yanda ta ga kyakykyawar fuskar nan nasa mai cike da haiba da kamala tana fitar da sassanyar murmushi, lokaci guda ta ji wannan abun da ya tsaya mata a wuya ya wuce zuruf, yayinda kaso mafi yawan damuwarta kamar an yaye mata,
Bata damu da irin kallon da yake mata ba, amma har a ranta ta ji dad'i, sai kawai ta sakar masa murmushin da bata san lokacin da ya suɓuce mata ba

Hakan ne yasa SHAREEF yayi saurin ɗauke kansa a ransa yana tunanin wa take yi wa murmushi? Lallai wannan yarinyan bata da hankali, ko giyan wake ya sha zai iya soyayya da ita ne bare har ya ji sonta a ransa? Never, bata kai matsayin ba wlh, ya rasa ma wacce zai so sai ƴar tayin yarinyar nan, ko Haseena da ta girme mata yana ganin tayi masa ƙanƙanta bare wannan ƙaramar yarinyar wacce bata wuce ƴar cikin sa ba, amma ita Haseena ai daban take da wannan, tunda tana da abubuwan kallo fiye da wannan, kuma ta cika Macen da kowanne namiji zai so ta, tana da kwalitin da yake bukata ya samu a kan Mace, ta iya kwalliya, wayayyiya ce ajin farko, wacce ta fito daga gidan Hutu da jin dad'i, babu ƙauyanci a tare da ita, tana da class ta ko'ina zai ina nuna ta a Matsayin girlfriend ɗin sa,
Amma wannan kuma fa? Sai ya ja numfashi yana sakin guntun tsaki tare da jefa hannunsa ɗaya mara riƙe da goran ruwan; a cikin aljihun sa,
In ban da baƙar fata da dogon hanci, sai gwala-gwalan idanunta masu kama dana mujiya, bai san kuma abun da ta ajiye ba, a fili ya furta, "shegiya da wasu idanunta kamar zata yi zawo, in banda Jaka ce ita taya ya zata haɗa kai dani? Ta rasa wacce zata so sai Ni? Lallai ma yarinyar nan ta raina min wayon".
Sai ya juya yabar wurin yana jan guntun tsaki yana sake jin ransa na ƙara ɓaci.
[04/03, 9:00 am] OumƊahirah نفيسة: 🌱🌱🌱🌱🌱

      *SHAREEF*
          _SexyBoy_
🌱🌱🌱🌱🌱


_Writer: Nafisat Isma'il Lawal_
_Wattpad: UmmuDahirah_

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝*



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

       *P.W.A✍️*





*DATA SHARE*

Call, message or whatsap  07065334256

*MTN*
500MB 150
1gb  280
2gb.  560 
3gb.   840
4gb.    1120
5gb      1400
6gb.     1700
Verlid for 30 days.












__________
*BOOK1*
_______________*FREE PAGE48*
 _____Kusan la'asar su Maryamu suka isa Abuja,
A cikin barikin sojoji gidan da ƙanwar Momy take zaune yake, tunda Mijinta Soja ne kuma babba, gidan su yana farko-farkon layi, gida mai number 4,
Babban gida ne kwatas mai cike da flowers da aka ƙawata gidan 

Yanayin anguwar da gidan ba ƙaramin burge Maryamu yayi ba, sai baza idanu take yi har suka shiga gidan

Suna tsayar da Motan; Ammee da Yaranta suka fito tarbar su, yanda ka san Momy haka Maryamu ta ga kamannin su da Matar, suna tsananin kama sai dai Momy ta fi su haske, gaba ɗayan su ma ƴan dakin su in ka kalle su sai ka gane jini ɗaya suke, sai dai Ammee ta fi yanayi da Momy har jikin su da ɗan sirantan su, ga yanda kuma ta tarbe ta shiyasa lokaci guda ta ji Ammeen ta kwanta mata a rai,
Ga Yaranta su Yusaira da Aakifah yanda ka san ƴan biyu kansu ɗaya kamannin su ma ɗaya, sai ƴar Autar su Na'ilah wacce ita bata yi kama dasu ba ko kusa, ita yanda kasan Mahaifinsu yayi kaki ya tofar haka suke kama

Da gudu suka zo suka rungume su Hanif suna murnan farin cikin ganin su

While Ammee ita kuma Maryamu ta tarba bakin ta har kunne sabida ganin yanda Maryamun take, faraɗ ɗaya ta shiga ranta musamman yadda ta ganta ƴar kyakkyawa,
Tana riƙe da hannun Maryamun ne take kallon su Hanif tare da cewa, "Yarana yau an tuna dani ko? Sai yau da dalili ya kawo ku shiyasa zan ga ƙafafun ku?"

Dariya suka yi gaba dayansu

"Ok mu shiga ciki, ku kuma ku sake su kun wani maƙale musu daga zuwa."
Cewar Ammeen tana kallon su Aakifah wadanda sai faman murna suke yi

Cikin gidan tace musu, "su shiga."

Sai suka wuce a tare, while Sadiq ya ɗauki Na'ilah a kafaɗa suna dariya su biyun, musamman ita da sai farin ciki take yi sabida an ɗaga ta sama

Cikin Falon suka shiga a tare suka zazzauna a saman kujera, kana Ammee ta nufi wurin fridge tana kiran sunan Yusaira,
Ruwa ta fito da su tare da juice na kwali ta bata, tace, "takai ta ajiye musu."
Bayan ta gama kwaso wa sai ta ɗauko raguwar ta taho dashi, ajiye wa tayi a saman Centre table inda Yusaira ta jera sauran, ta sake ce mata, "ta je ta ɗauko cups ta kawo musu."
Sannan ta zauna tana kallon su da faɗin, "ina SHAREEF ya ƙi biyo ku ko?"

Hanif yace, "wlh kuwa, yace bazai zo ba."

"Hmm shi ya sani, na san dalili ai; cus Aunty ta sanar min komai before ku ƙariso."
Sai ta kalli Aakifah tace, "Aakifah je ki taho da samosan nan da na ajiye a tray ki kawo musu."

Aakifah amsa mata tayi tana miƙe wa tare da nufan kitchen ɗin

While Ammee ta mayar da hankali kan Maryamu da tayi shiru tana zazaare ido a falon, sai kallon hotunan Falon take yi, "Maryam Allah yasa dai baza ki yi min baƙunta ba? Tunda ga Yara nan sa'annin ki ki saki jikinki sosai kamar kina gaban Aunty Khadijah ne, don kulawar da zan ba ki sai ya fi nata ma."
Tayi maganar tana ƴar dariya

Su ma su Hanif dariyan suka yi, while Maryamu murmushi tayi kawai

Sadiq yace, "nima abun da nace mata kenan Ammee tun a Mota, kin san Momy ita ta cika faɗa wlh shiyasa nima nake son dawowa nan, musamman ma in Uncle yana nan na fi jin daɗin zuwa Abuja."

Hanif ya harare sa yace, "ai kuwa kamar a kunnen Momy."

Dariya Ammee ta fashe dashi Maryamu na taya ta; ganin yanda Sadiq ɗin ya kwaɓe fuska yana yi wa Hanif ɗin magiya

Da Yusaira da Aakifan tare suka dawo daga kitchen, ita Yusaira tana riƙe da cups; Ammee ta bata umarnin ta zuba musu ta basu, while Aakifah kuma ta ajiye samosan tana zama gefen Maryamu wadda suka haɗa ido suka yi wa junan su murmushi

Sai kuma Aakifan ta ɗauki ɗaya cup da kanta ta zuba wa Maryamu drinks tana miƙa mata, tace, "Ammee wlh kyakkyawa ce, muna sonta zamu ji dadin zama da ita."

"Haka nake son ji ai." Cewar Ammee tana murmusawa, "ki zuba mata samosan itama ta ci, bari ina zuwa."
Sai ta miƙe ta nufi kitchen tunda ta ɗaura ferfesun kayan ciki da take musu

Su kuma su Yusaira sun saka Maryamun a tsakiya suna ta hira da su Hanif,
While Maryamu tana kurɓan juice ɗin tana haɗa wa da samosan, ta saki jikinta sosai tunda bata da baƙunta, musamman da ta ga su Yusaira suna janta a jiki suna mata surutu, sai yaba kyawunta suke yi suna ce mata, "tana kama da Kajol Agriwal, don dai ita Black beauty ne amma kamar su ta ɓaci, kuma ita ta fi Kajol ido."

Ita dai Maryamu bata ce komai ba tunda bata san wace ce Kajol Agriwal ɗin ba, amma a yanda suke ta zuzuta kamannin ta har su Hanif suna taya su shirmen, shiyasa take ta jin dadi a ranta tunda akwai ta da son a yaba ta

Hira sosai ta ɓarke a tsakanin su, har sanda Ammee ta dawo ta kammala komai ta kwaso food flakes tana jera wa a dining, sannan tace, "su taso su ci abincin."

Gaba dayansu suka nufi wurin har su Yusaira since su ma basu ci komai ba

Bayan sun kammala cin abincin, sai suka ja Maryamu suka wuce ɗakin kwanan su,
Ammee kuma ta nuna wa su Hanif ɗakin da zasu zauna,
Sannan ta fita ta saka Mai gadin su ya kwaso musu kayan su a Boot, da akwatin Maryamu da aka ciko su da kayanta har biyu,
Bayan ya ajiye a Falo, ita da kanta Ammee ta ja na Maryamu takai ɗakin su Yusaira,
Time ɗin ma Maryamu har ta soma sallah, shiyasa ta cewa su Aakifah, "su haɗu su gyara mata kayanta a wardrobe."

Suka amsa mata da to, sannan suka tashi kowacce ta ja akwati ɗaya suka fara aikin

While ita kuma ta fita ta ɗauki ƙaramar Jakar su Hanif; su ma takai musu dakin su,
Na'ilah na tare da Sadiq sai didima take yi a jikinsa ta samu abun da take so, dama jinta take yi kamar ƙaramar yarinya bare an sangarta ta

Hanif ya shiga wanka; sai Sadiq ɗin da ke kwance a saman gado Na'ilah na jikinsa

Ammee ta harare ta tana cewa, "ke fa ba kya jin magana dama, daga zuwan su kin samu abun da kike so baza ki bar su su huta ba ko? Common zo ki wuce ki barsu su huta ki koma ɗakin su Aakifah."

Kwaɓe fuska tayi tana shirin kuka

Sadiq da ke dariya yace, "Ammee ki barta kawai, doki nake mata but in na gama zata fito."

"Kai baka san halin yarinyar nan bane, haka take yi wa Abee ɗin su sam bata girma, in ka biye nata baza kayi abun da ke gabanka ba, zo ki wuce idan kun kammala kimtsa wa sai ta dawo, ga sallah ma baku yi ba."
Sai da ta tasa Na'ilan sannan ta ƙyale shi, don har kuka ta soma yi, ta ja hannunta suka fice

Sadiq kuma yana faɗa mata, "tayi shiru ya kawo mata tsaraba, idan ta ci gaba da kukan bazai bata ba."

Hakan ne yasa tayi shirun har ta dena turjiya a kan bin Ammeen.
***

         
_____Kwana ɗaya su Hanif suka so suyi, but Ammee ta hana su tafiya sai da suka ƙara kwanan, tace, "tunda ba Abee gwara su zauna su yi mata kwana biyu."

Sai da suka zagaya garin gaba ɗaya har su Yusaira sai jin dadi suke yi, tunda ba a barin su fita, basu da lokacin ma kansu kullum suna makaranta,
Sun ji daɗi sosai da suka fita yawon zagaya wa, ga shi Hanif duk ya kashe musu kuɗi ya siya musu kaya da su chocolates kala-kala yayi musu siyayya sosai

Ranan da zasu tafi ko damuwa Maryamu bata yi ba tunda tuni ta saki jikinta, ko lokacin tunani ma bata dashi tunda su Aakifah sun ɗauke mata kewa kodayaushe suna tare da ita suna mata surutu, shiyasa kamar sun jima da sanin juna sun ƙulle sosai bare kansu ɗaya

Bayan su Hanif sun isa gida sannan Momy ta kira Ammee ta sanar mata, sun daɗe suna waya suna sake tattaunawa a kan matsalar Maryamun, daga baya suka yi sallama

To kasancewar Hutu ake yi a wannan lokacin shiyasa Maryamu bata fara zuwa makaranta ba, amma tuni Ammee ta gama cike mata Form an saka ta makarantar haddan su Aakifah da suke zuwa asabar da Lahadi, sai yamma suke dawowa,
Zuwan Maryamun ne yasa Ammee ta nema musu wurin koyan computer, a ɗan lokacin da suke dashi bayan sun dawo hadda da karfe huɗu, zasu riƙa zuwa sai su dawo ƙarfe shida, driver zai riƙa dauko su,
Amma yanzu da ake hutu shiyasa suke zuwa kullum

Lokaci guda rayuwa ta sauya wa Maryamu, kulawa da komai Ammee tana musu, ba ta barin su lalaci tunda Mace ce mai zafin nama itama kamar Momy, komai na gidan su suke yi, ita take raba musu kowa yayi aikin sa, dayake itama ba zama take yi ba tunda tana aikin ta, shiyasa kafin ta dawo sai dai ta zo ta tarar duk sun yi girki sun gyara gidan, idan ta dawo su kuma sai su tafi wurin koyon computern su, har da Na'ilah suke zuwa tunda itama tana Hutu, kuma idan suka barta a gidan ita kaɗai take zaune, sai su tafi da ita ta zauna a can tana wasa, wani lokacin ma har da ita ake koya mata, don dai tayi ƙanƙanta ne da yawa

Shekara ɗaya ne ake koyon computern sai su yaye mutane, shiyasa Ammee tace, "da zaran sun gama zasu koma wurin koyon kwalliya."

Su Aakifah sai daɗi suke ji domin sun fi son haka, domin yanda suke ƙaunar kwalliya in har suna gida zaka ga sun cakare sun yi makeup a kan face ɗin su, shiyasa tayi musu alkawarin, "da zaran sun gama zata mayar da su can su koya kwalliyar."

Ita kanta Maryamu suna burge ta matuƙa, duk da ba kasafai take son kwalliya ba amma idan sun ce zasu yi mata; haka zata basu fuskarta su zana mata suyi ta yabon ta suna cewa, "tayi kyau sosai."
To itama ganin tana yin kyau shiyasa abun ya soma tasiri a ranta, ta ji tana son itama ta iya, dole ta matsa musu su riƙa koya mata tunda ita dai bata iya ba sai nasu na ƙauye,
Tana yawan yin waya da su Innarta tunda yanzu sun san tana Abuja da zama, yanzu ga shi har bikin su Bintu ya zo saura kwanaki, ta so ta je bikin amma Allah bai yi ba, bata da yanda zata yi, tunda su Aakifah ba sa riƙe waya sai dai ta ari na Ammee ta kira gida suyi ta waya, yawanci sun fi daɗewa da Bintu suna wayan tunda yanzu Mijin da zai aure ta ya siyan mata waya, Maryamu ta samu abun yi; tayi ta zama tana bata labarin Abuja tana gaya mata irin daɗin da take sha da kuma abubuwan da suke koya

Sai Bintu ta ji kamar ita, har so take yi dama ace itama a kaita a fasa auren nan, amma babu hali

Izuwa yanzu Maryamu ta koya wa kanta rayuwa babu SHAREEF, duk da bata taɓa tunanin zata iya rayuwa a wani wuri inda babu shi ba, amma zamanta cikin su Aakifah ta soma saba wa da hakan, duk da yana maƙale a ranta, in dai zata zauna ita kaɗai sai ya faɗo mata a rai, har kuka tana yi a ɓoye sabida a kullum soyayyarsa azalzalan ta yake yi, tana shan wahala matuƙa jurewa kawai take yi domin ta saka a ranta baza ta ƙara ɓata mishi rai ba, kamar yanda ba ya ƙaunar ganin ta a tare dashi itama dole zata yi nesa dashi, a yanzu fata take yi Allah ya cire mata soyayyarshi a ranta tunda gani take yi kamar baza ta iya doguwar rayuwa a inda babu shi ba

Kullum Momy sai ta kira ta itama ta ji lafiyar ta, tana jin daɗi yanda ta ga Maryamun ta saki ranta a yanzu, kuma bata taɓa yin mata maganar SHAREEF ba haka itama bata tambaya ba, iyakan su Yaya Hanif take tambaya, in suna nan ma suna yin wayan tare

Dayake tunda bikin nan ya zo ana gobe Dady yace zasu tafi Zaria,
SHAREEF ya so ya botsare a cewar sa bazai je ba, sabida ganin a ranan asabar Haseena zata dawo ranan bikin kenan, bazai so ya tafi ta dawo ba ya garin ba, amma Dady yayi mishi jan ido yace, "dole sai ya je wlh, sabida ko don auren sa da Maryam iyayenta su sake sanin sa, don haka ya shirya dole su tafi tare."

Ran SHAREEF ya ɓaci jin abun da Dady yace, ashe har yanzu suna nan da maganar basu sauya Shawara ba? Shi a ganin sa lokaci kadan yake jira su ce ya sake ta, ashe har yanzu suna ganin ta a matsayin Matarsa basu canza ra'ayi ba, ai kuwa a haka zasu gaji har su raba auren kamar yanda suka ƙulla, don yanzu lokaci kaɗan ya rage masa ya mallaki Haseenan sa, sanyin idanuwansa; wanda yake jin a duniyar nan ita kaɗai ce farin cikin sa, ita ce jin daɗin sa, a ƙagare yake ta dawo amma ga shi an yi masa cikas, tunda ko ta dawo suna can Zaria, since a gobe zata dawo.
***

          
_____A ranan juma'a misalin ƙarfe biyar suka isa cikin Zaria, a gidan Iya Samira suka sauka, murna wurin ta ba a magana, musamman yanda ta gansu dukkan su suka taho, ta rasa ma inda zata sanya su don murna da daɗi, sai kallon su Hanif take yi domin bata iya gane su ba sai da ta tambaya, "wane ne Mijin nata a ciki?"

Momy ta bata amsa tana nuna mata SHAREEF da kuma Hanif ɗin shine Mijinta

"Lallai! Idan a hanya ne na gansu bazan taɓa gane su ba wlh, ba kwa son zumunci ko kaɗan Yaran nan."

"Wlh kuwa Inna, SHAREEF ma bai so zuwa ba sai da nayi masa jan ido sannan ya biyo mu." A cewar Dady

Iya Samira ta sake kallon SHAREEF ɗin tana washe baki, wanda tuni ya duƙar da kansa yana ta faman latsa waya fuskarsa a ɗaure, tace, "yo ai kai ne zaka zo mu ganka tunda yanzu ka zama Mijin Meramun mu, ai mun yi kewarta wlh ba kaɗan ba, ashe bada ita za a zo ba?"

Murmushi duk suka yi,
Momy tace, "tana can Abuja tana karatu shiyasa, kuma bata daɗe da tafiya ba shi yasa bamu zo da ita ba."

"Ai hakan ma babu komai wlh, wata rana zata zo ai, komai lokaci ne."

Haka suka dinga hira bayan sun yi Sallah sun natsa

SHAREEF tun zuwan su Sallan Asar da yayi musu a hanya, sai yanzu suka samu suka yi, sai ya wuce ɗakin zauren da aka gyara musu yayi zaman sa a can, sai yatsina fuska yake yi kamar ya shiga cikin masai tsaban yanda yake nuna ƙyamatar sa da gidan, jinsa yake yi a takure kamar ya kurma ihu ko ya gudu ya koma gida, wlh ba don ɓacin ran Iyayensa ba babu yanda za a yi ya ci gaba da zama a gidan nan, bare kuma wancan ƙauyen da ya fi tsana

Su Hanif kuwa babu ruwansu suna can sun saki jikinsu ana ta hira, ƴan uwa ma sai zuwa suke yi suna gaisa wa tunda Iya Samira ta je ta sanar musu

Shima Dady yace, "da bata je ba tunda zasu shiga har babban gidan."

Da suka je yin Sallan magriba ne shine suka shiga Babban gidan su Iya Samira aka gaigaisa,
Itama Momy daga baya suka je ita da Iya Samira,
A can suka zauna har bayan sallan isha'i before suka dawo gidan,
Kuma suka sake dasa hira tunda an daɗe ba a haɗu ba,
Dama tuwo Iya Samira tayi, haka nan suka ci don Momy tace, "ba sai an musu wani abincin ba, gwara a ɗumama tunda su ma sun jima basu ci irin wannan tuwon ba."

SHAREEF dai ya ƙi ci, koda aka zuba mishi yace, "a ɗauke mishi a gabansa."

Sadiq ya dauka ya mayar ya sanar musu yace, "bazai ci ba."

Iya tace, "to ko dai a dafa mishi ko fara da mai ne ya ci? Tunda shi bazai iya ci ba don na ga alamun ɗan gayu ne Mijin Meramun tamu, dama haka tafi so ƴar tselan uwa." Ta ƙare maganar tana ɓaɓɓaka dariya 

Momy tace, "a'a Iya kar ki wahalar da kanki, in dai a halin SHAREEF ne ko me aka ba shi in bai yi ninya ba bazai ci ba, don haka ki ƙyale sa cikin sa ne."

Shima Dady abun da yace kenan,
Shi yasa bata da yadda zatayi haka nan ta haƙura, amma bata ji dad'i ba duk da ta ga halin sa ya bambanta da sauran ƴan uwan nasa, da gani yana da ƙyanƙyami, amma ita hakan bai dame ta ba tunda sosai ta ji dadin ganin SHAREEF din a haka, a ganin ta Maryamu tayi dacen ɗan kyakkyawar saurayi kamar yanda take faɗa, wannan ai abun nuna wa ne da kwatance, ta san Iyayenta zasu ji daɗin ganin Surukin nasu na nuna wa Sa'a.

          Zuwa washe gari tunda ranan bikin ne, kuma karfe 10 za a ɗaura auren, safe nayi suka shirya suka wuce ƙauyen; har da Iya Samira ta bi su a motan su.
[05/03, 8:27 am] OumƊahirah نفيسة: 🌱🌱🌱🌱🌱

          *SHAREEF*
               _SexyBoy_
🌱🌱🌱🌱🌱


_Writer: Nafisat Isma'il Lawal_
_Wattpad: UmmuDahirah_

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝*



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

       *P.W.A✍️*





*DATA SHARE*

Call, message or whatsap  07065334256

*MTN*
500MB 150
1gb  280
2gb.  560 
3gb.   840
4gb.    1120
5gb      1400
6gb.     1700
Verlid for 30 days.










__________
*BOOK1*
_______________*FREE PAGE49*
 _____Sun isa ƙauyen; su Baba na ƙofar gida shi da wasu Abokansa suna ɗan tattaunawa,
Suka ga motan ta tsaya a ƙofar gidan, dayake Baba ya san da zuwan nasu shiyasa ya nufi wurin Motan tun kafin ma su fito

Dady ya soma fitowa shi da Hanif da suke baya, sai Momy da Iya Samira waɗanda su ma duk suna back sit; sabida Motan irin Jip ɗin nan ne ƙatuwa,
Sadiq ke tuƙa su; while SHAREEF na hakimce a front sit, ya ƙi ya fito bare ma ya ɗago kansa, wayansa na hannunsa yana chart da Haseena tana faɗa mishi, "yanzu haka ta hau jirgi zasu tashi."
Bai san ma mai ake yi ba sabida su Dady suna can ana gaigaisawa; har su Yaya Naziru sun fito daga gidan

Gidan suka nufa bayan sun gama gaisuwar, Baba da Dady suka fara yin gaba su Iya suka bi bayansu

Yaya Naziru da Yaya Ashiru suka ce ma su Hanif, "su shiga cikin gidan," tunda suna gefe ne sun gaisa tamkar sun saba da juna sabida yanda suka gaisa faram-faram, duk da dama an daɗe ba a haɗu bane, musamman ma Hanif dashi da SHAREEF 

Hanif ne ya kula kamar babu SHAREEF, shi ne ya juya yana duban wurin Motan before yace ma Sadiq, "ina Bro ne wai?"

Sadiq shima ya bi motan da ido yana cewa, "bai fito ba fa."

Hanif kallon su Yaya Ashiru yayi yana musu murmushi yace, "bari in kira bro sai mu shiga tare."

Su ma tsaya wa suka yi suna kallonsa ya nufi wurin Motan, duk da sun fahimci maybe SHAREEF ne Mijin Maryamun su, dukkan su sai suka zaƙu da su ganshi suna ta kallon wurin Motan

Hanif ƙwanƙwasa side din sa yayi yana jiran ya buɗe mishi

Sai lokacin ma ya dawo da hankalin sa jikinsa; ya ɗago yana duban inda Hanif yake tsaye, hannu ya sanya ya zuge glass din yana faman kallonsa fuskarsa babu wata walwala, da ido yayi masa alamun mene ne? yana tsare sa da idanun

"Ka zauna duk mun fita kai ka ƙi fitowa, ko baka san mun kawo bane?"

Yatsina face ɗin sa yayi yana ɗan juya wa ya bi inda suke da kallo, har ya sauke idanunsa kan su Yaya Ashiru da suke gefe sun kafo musu ido, kallon kallo suka yi wa junan su while tuni SHAREEF ya ɗauke idanunsa a kansu, ya wani yanƙwane fuska da furta, "and so what?"

"Ka fito mana, su Momy har sun shiga ciki, kuma ka san Dady zai tambaye ka."

Gajeren tsaki ya ja yana wani haɗe fuska

Shi kuma Hanif bai bi ta kansa ba ya sanya hannu ya buɗe masa ƙofan

Kamar bazai fita ba sai wani haɗe fuska yake yi yana sake bin garin da kallo ta cikin Motan, wai ji be ƙauyen da aka kawo su haka kawai an takura masa, to taya ya zai iya zama na mintoci a wannan bahagon garin? Wani dogon tsakin ya ja yana zuro ƙafafunsa a waje, kana ya fito cike da ƙyanƙyami yana wani hura hanci

Sadiq da ya dubi su Yaya Naziru ya ga sun zuba wa SHAREEF ido, sai ya ɗan yi murmushi yana ce musu, "ga Yayanmu nan ya fito Mijin Maryam."

Murmushi suka yi su dukkan su, duk da sun san shi amma an jima rabon su dashi, don haka ba ƙaramin sauya musu yayi ba, tabbas su kansu SHAREEF ya burge su sosai, gani suke yi kamar ya fi ƙarfin Maryamu sabida yanda suka ganshi ɗan Gaye, duk da basu da bambanci da Hanif amma SHAREEF ya fi shi wayewa da hasken fata, kuma bai da sakewar fuska koda gani yanda suka ga ya fito face ɗin sa a haɗe babu annuri yana wani hura hanci; daga gani zai yi jijji da kai ne, duk wanda ya kalle sa ma zai gane hakan

Hanif ne ma yace mishi, "ga su Nazir nan baku gaisa ba Bro."


Kallo ɗaya yayi musu ya wani ɗauke kansa yana saka hannaye a cikin aljihun wando

Naziru ne ya soma ba shi hannu yana cewa, "aslm alaikum ɗan uwa, fatan kun zo lafiya?"

Kamar bazai ba shi hannun ba don har wani jan lokaci yayi, sai kuma ya ciro hannun tare da miƙa masa suka gaisa

Ko kusa basu damu da abun da yayi musu ba tunda tun farko sun soma fahimtar halin sa, tun wani zuwa da yayi aka yi faɗa dashi, amma bai dame su ba, suna gaisa wa suka rankaya suka wuce cikin gidan,
SHAREEF na take musu baya kamar bazai taka ƙasan ba, ya haɗe fuskarsa babu ko ɗigon fara'a 

Can kuwa cikin gidan har an bama su Dady mazauni a ɗakin Inna, tunda gidan an cika da ƴan uwa ana ta hayaniya, suna ta kiciniyar ɗaura girki,
Labari har ya baza musu ana cewa, "mutanen Kano ne suka zo, iyayen Mijin Maryamu."
Shiyasa fa suka yi ta shiga ɗakin Inna suna gaisa wa da su Momy, kowa na son ya ga Mijin Maryamun, har wasu suna tambayar, "ko Maryamun bata zo bane?"

Iya Samira ce take basu amsa tace musu, "ba a zo da ita ba, amma Mazajen suna nan a waje zasu shigo, zasu ga Mijin Meramun da suka ƙosa su ganshi."

Ana haka sai ga su sun shigo, sai kallo ya koma kansu,
Su Hanif ne kaɗai suka samu damar gaishe da mutanen wurin cikin girmamawa,
Kowa ya ɓashe baki yana amsa musu suna baza idanu su gane wane ne Mijin Maryamun a ciki

Har dai wata Mata ta ƙare ta tambayi su Yaya Naziru da suke gaba; take cewa, "to wanne ne surukin namu?"

Yaya Ashiru ya nuna SHAREEF da ke baya ya turɓune fuska kamar zai saka kuka, ko kallon mutanen ya gaza yi sabida baƙin ciki da tsananin ƙyanƙyamin su,
Ya nuna sa yace, "ga shi nan."

Sai fa kallo ya koma kansa suna ta surutu wasu na yabon sa; wasu kuma suna mamakin ganin yanda ya haɗe fuska yayi kamar bai gansu ba

Kai tsaye dakin Innan; su Yaya Naziru suka wuce da su, suka shiga ciki gaba ɗaya

"Ina ku ka tsaya ne baku shigo ba sai yanzu?" Cewar Dady da ke kallonsu

Hanif yace, "mun tsaya gaisawa da su Nazir ne Dady."

Iya Samira da tayi tsulum tana ce ma su Inna, "ai ga ma Mijin Meramun nan sun shigo, kun ganshi ga SHAREEFUN nan, wannan kuma Mijina ne Sama'ila."
Ta nuna su tana dariya

Su Umma Jummai da Inna suka bi su da kallo fuskarsu a sake, suna amsa gaisuwar su Hanif ɗin, while idanunsu a kan SHAREEF da ke tsaye har yanzu shi bai duƙa ba, dukkan su sun zura mishi ido kamar zasu cinye sa ɗanye

Momy da ta kula da yanayin SHAREEF ɗin, sai ta dube shi tace, "ka zauna mana ka tsaya a tsaye? Kuma kana jin ana gaisuwa kai baka ce komai ba."

Sai lokacin ne fa ya samu wuri ya zauna, har yanzu rai a haɗe ya gaishe su a daƙile tamkar ba ya so

Jikin Inna yayi sanyi sosai tun sanda ta kalli SHAREEF ɗin ta fahimci wane ne shi, koda basu jima a ɗakin ba ta gane suna da bambanci sosai da su Hanif, ba halin su ɗaya ba koda gani, amma dai har a ranta tana fatan a ce ƴarta ta samu farin ciki da soyayya a wurin sa, tana mata wannan addu'ar a cikin ranta, don kallo ɗaya ta san cewa za a yi aiki da SHAREEF, ita bata damu da zancen mutane da suke ta yabon kyawun sa ba, amma ai hali ake so, yanda ta ga Hanif sai ta ji dama shine ya kasance surukin nasu

Shi kansa Baba da su Yaya Faisal haka suke kitsa wa a ransu, sabida yanda suka fahimci SHAREEF a ɗan ƙanƙanin lokaci,
Sai dai kowannen su ya bar abun a ransa suna fatan a ce Maryamu baza ta sha wahala a wurin sa ba, tunda bai dauke su da wata daraja ba, ƙyama ƙarara ya ware kansa a cikin su

Ana dawowa ɗaurin auren ma Mota ya shige yayi zaman sa,
Koda Hanif ya zo ya kira sa but ya ƙi fitowa, yace, "ya bar sa bazai iya da kayan takaici ba, duk an bi an takura masa."

Hanif shi kansa bai ji daɗin yanda SHAREEF yake yi ba, amma gudun fitina shiyasa bai yi mishi magana ba, sai ma lallaɓa shi da yake yi yace, "ya daure ya ci abincin tunda ya san bai ci komai ba, tun zuwan su Zaria bai ga ya saka komai a cikin sa ba."

Amma firr SHAREEF ya ƙi amince masa, kuma ba kaɗan ba tsananin yunwan yake ji tunda tun jiya bai ci komai ba, kallo ɗaya ma kayi masa zaka san ya jigata ba kaɗan ba, ya soma fita a hayyacinsa idanun nan sun yi zuru-zuru da su, ƙarfin hali kawai yake yi da kuma samun yanda hankalinsa ya ɗauke saboda waya da yake yi da Haseena, shiyasa ya ɗan samu ƙwarin gwiwa bai damu kansa sosai ba

Hanif kuma ya damu sosai da ɗan uwansa, ya san halin sa zai iya zama a haka in har suka ci gaba da zama a ƙauyen nan, tunda bai ci ba bazai ci bane don ya san shi da shegen tsentseni,
Hakan ne yasa ya samu Bashir yace masa, "aina zai samu shago? yana son ya siya biscuits ne da drinks in zai samu."

Bashir yace, "eh za a samu nan kusa, ko shagon Baba ma za a samu tunda ya bar Yaron shagon sa yana zaune, bari ya siyo masa a can."

Ai kuwa da sauri Hanif ya ba shi kuɗi dubu ɗaya yace mishi, "ya siyo mishi biscuits da fresh yo, ko kuma nutri milk in za a samu."

Yace masa, "to." Ya amsa ya tafi.
Jima wa kaɗan ya je ya dawo ya kawo masa dukka ya haɗo masa dashi kowanne guda bibbiyu, biscuits ɗin kuwa irin ƴan ɗari ne guda hudu ya kwaso, ya fi na kuɗin sa ma ya kwaso kayan ya ciko masa a leda

Hanif ya amsa yayi masa godiya sannan ya wuce wurin Motan ya buɗe ya shiga, kasancewar Motan ma an canza mata wurin packing can gaban gidan ne; sabida ɗaurin aure da aka yi, kuma Motan dayake baƙin glass ne da ita babu wanda yake damuwa akwai Mutum,
Yara ma sai dai su zo su shafa ta suna wasa a wurin, in su Halliru ko Bashir sun gansu su kora su

SHAREEF ganin abun da Hanif ya kawo masa; ba ƙaramin dad'i ya ji ba, don sai da ya nuna hakan a kan fuskarsa, yace, "thanks Bro."

Murmushi Hanif yayi yace, "i know na san kana jin yunwa ai, amma ƙyamƙyami ya hana ka kaci abinci ka ƙoshi, bari in shiga ciki don muna tattauanawa da su Nazir ne; tunda kai ka ƙi ƴan uwa."

Ko kallonsa bai yi ba bare ya ce uffan, sai faman cusa biscuits ɗin yake yi a bakin sa yana kora wa da fresh yo

Buɗe Motan Hanif yayi ya fita, yana ce masa, "idan Dady ya tambaye sa zai sanar mishi inda ya ɓoye."
Har ya tafi bai ce masa komai ba.
***

        
_____Sai yamma sannan suka koma cikin Zaria, tunda nan babu wurin kwana, kuma dama a gidan Iya Samira zasu koma su kwana a can, daga can ma baza su dawo ba zasu wuce shiyasa suka yi musu sallama

Momy da kanta ta nemo Bintu ta kira mata Maryamu ta bata wayan suka yi waya, tunda tayi mata alkawarin, "in dai suka je zata kira mata ita a wayanta ta haɗa su."

Bintu har da kukan ta wai, "ta ƙi zuwa mata biki, kuma ta saka rai sosai don bata fitar da ran zata zo ba."

Har da Iya Samira suka koma gidan ta tunda akwai baƙi baza ta bar su su kaɗai ba, shiyasa ta koma ta kwana gobe in sun tafi sai ta dawo

A washe gari sai karfe sha ɗaya suka bar gidan Iya Samira, daga can suka wuce Samaru gidan su Mahaifiyar Dady

Kusan ƙarfe uku suka wuce Kano,
Dama SHAREEF kamar a ƙaya yake tsaban ƙosawa da son ganin sa a gida, Allah - Allah yake yi su koma ya haɗu da Haseenan sa, sai lokacin walwalan sa ya dawo ya soma jin farin ciki a ransa

Sun isa kusan magriba, shiyasa basu wani huta sosai ba suka yi alwala suka wuce masallaci,
Dayake SHAREEF ya ƙosa ya je wurin Haseena, ji yake yi bazai iya jira ba; ana idar da sallan ya fito ya dawo gida ya bi ta ƙofan baya don kar Momy ta gansa, wanka yayi ya sauya shigansa ya saka ƙananun kaya riga da wando baƙaƙe masu kyau, sai da ya gyara jikinsa ya ƙalƙale sa kamar yanda ya saba, ya shafe ko'ina na jikinsa da turaren sa mai shegen ƙamshi, sai ya saka cover flat shoes ya ɗauki wayansa ya fita, motan sa ya shiga duk da ya ji ana ta sallah, amma bai tsaya yayi ba sai da yakai Kofar gidan su Haseena, dayake akwai ƙaramin masjid a bakin gidan su, a nan ya shiga yayi sallan isha'i before ya fito ya kira ta a waya

Tana ɗauka tace masa, "ya shigo ciki tana jiransa."

Dama in zasu yi taɗi ciki yake shiga, bai taɓa zama a waje ba sai dai idan sauri yake yi, Falon Abbanta take kaishi a can suke zuba soyayyarsu son ransu,
Yanzu ma koda ya shiga sai ya ga ƙofan Falon Abban a buɗe, alamun shi aka buɗe ma ƙofan, shiga ciki yayi yana mayar da wayansa a aljihu; ba tare da yayi sallama ba,
Babu kowa sai daddaɗan ƙamshi da ya game ko'ina na turare; da kuma ƙamshin abinci wanda aka gama jera wa a saman Centre table,
A hankali ya taka cikin takun isa ya nufi saman sofa ya hakimce yana ɗan duban Falon

Zaman sa da kamar two minutes sai ga takun sahun Haseena ta shigo

Yana ɗago kai suka haɗa ido da ita tana zuba murmushi, yayinda shi kuma ya bi ta da ido kamar zai haɗiye ta yana kallon irin wankan da ta ɗaukar masa

Sanye take cikin baƙin straight skirt mai tsagu ta baya; har zuwa kusan cinyanta, while ta sanya pink colour din shirt mai faɗin wuya, hakan ya ba saman breasts ɗin ta daman leƙowa da suka cika ƙirjin fam kamar zasu fashe tsaban yanda suka sha matsa da breziyan da ta sanya, tayi packing gashin ta da babu kitso wanda ta haɗa da attachment ya ƙara tsawo har saman kafaɗunta, sai ta ɗaure ba tare da ta sanya ɗankwali ba, ƙafafunta kuma ta sanya wani dogayen takalma baƙaƙe masu stones a sama an yi ado, fuskar nan tamkar zata je gasar kyawu sabida yadda ta ɗauki kwalliya ɗau bakin nan sai shining yake yi,
Wani irin rangwaɗa take yi tare da sauya takun tafiyarta sabida irin kallon da ta ga SHAREEF ke bin ta dashi, cikin yanga da kisisina irin na gogaggun ƴan duniyar nan da take gara musu a yanzu, ta taho zuwa inda yake; tare da samun wuri a gefen sa ta zauna face ɗin ta still da smile take kallonsa, "welcome my dear." Ta furta hakan tana narke idanunta tare da ɗan cije bakin ta cikin tsananin jan hankali

Wani irin yanayi SHAREEF ya faɗa, wanda tuni wannan kwarkwasan nata ya mugun tafiya da imanin sa, take ya ƙara jin tsananin ƙaunarta da sha'awar ta gami da tsananin kewarta ya mamaye sa, slowly ya lumshe idanunsa yana sake shaƙar ƙamshin turaren ta da ya game masa hanci, bai iya magana ba koda ya buɗe idanun ya narka mata su; illa sanya hannu da yayi ya kamo ta a hankali yana rungume ta much tare da soma shinshinar ta

Ita kuma dariya tayi kaɗan tana ƙara manne kanta a kafaɗunsa, ba ƙaramin kewarsa tayi ba, a hankali ta lumshe idanuwanta sabida maganar da ya soma mata a cikin kunne

"Wannan madaran kyau haka sweetheart; gani nake yi kamar ana sauya min ke a duk sanda zan ganki, mene ne sirrin?"
Yayi maganar slowly yana faman shinshina ta idanunsa a rufe cike da tsananin sha'awa gami da begen ta, ji yake yi tamkar ya mayar da ita a ciki, hannunsa ɗaya tuni ya ɗaura sa a jikinta ya soma sarrafa shi zuwa saman ƙirjinta yana matsa ta

Ita kuma cike da barikanci ta ɗan saki siririyar dariya tana ƙara langaɓe masa, cike da shagwaɓa tace, "ai ka fi Ni kyau dear, har ƙiba fa kayi sabida Hutu da jin daɗi."

"Ina wani ƙiba a nan sweetheart? Ke dai ki faɗa min gaskiya gaba ɗaya kin sauya, kullum ƙara miki kyau ake yi, kuma wannan gashin aina kika samo shi Ni ban sanki dashi ba? Mai kika sa gashin ki yayi tsawo haka?"
Yayi maganar yana ɗan ɗago kansa tare da taɓa gashin nata da ya sha gyara

Murmushi tayi tace, "nothing dear, kwalliya ne kawai nayi maka dashi, but ba nawa bane."

Shiru yayi yana ɗan duban kan nata, sai kuma bai ce komai ba ya sauya maganar da ci gaba da tambayarta school yana faman shafa ta kamar zai mayar da ita ciki

Sun shantake a haka a manne kamar zasu haɗiye juna sabida yanda suke faman jagula junan su,
Daga ƙarshe ya mayar da ita saman cinyansa suna facing juna, ya soma manna mata kissing a baki yana faɗa mata irin girman missing ɗin ta da yake yi, tare da bayyana mata yanda ya ƙosa ta zama tashi, a yanzu ji yake yi kamar ya haukace tsaban yanda yake tsananin bukatarta

Ita kanta ta san da haka, ta san yanda SHAREEF yake ƙaunarta, bai da buri sama da ya same ta cikin shimfiɗa, musamman yanda ta ga ya haukace mata a yanzu ya gama rikita ta, duk yanda take jin rashin sha'awarsa, yau sai da ya taso mata da ainihin feelings ɗin ta, take jin itama bata da wata buƙata sama da su mallaki juna,
Amma kuma maganganun Nana suna nan a ranta daram waɗanda tayi mata su kafin tahowar ta, sai da ta gargaɗe ta ko an yi auren kar ta sake ta bama SHAREEF kanta, domin bazai taɓa gamsar da ita kamar yanda ita take gamsar da ita ba, kuma a baƙin kishin ta zata iya yin komai a kanta, ta amince da barin ta tayi aure ne ba don komai ba don ba ta son damuwarta, amma ba wai hakan yana nufin zata bama SHAREEF kanta bane,
Itama Haseena ta amince mata, sabida babu abun da Nana zata nema a wurin ta ta rasa a yanda dai take jin ta a ranta, sun zama ɗaya duk abin da take so shi take yi, wannan ma don babu yanda za a yi ta rabu da SHAREEF ne, domin soyayyar da take mishi zai iya saka wa ta rasa ranta in har suka rabu, ta amince zata aure shi amma ba don su ji daɗin rayuwa ba, ta san auren shine maslaha tana ga kamar zata fi samun kwanciyar hankali musamman yanda SHAREEF ɗin yake matsa mata

Daƙyar ta samu ta lallaɓa shi ya ci abincin da ta kawo mishi, suka ɗan yi hira kaɗan sannan ya shiga ya gaishe da Iyayenta, har suka tattauna da Abbanta a kan zancen auren su,
Ya sake jaddada mishi a kan, "ya sanar da Dadynsa su zo a yi magana, since three weeks ne hutun Haseena, before nan da two weeks sai a ɗaura auren su."

Da farin ciki SHAREEF ya koma gida a ranan, tsaban zagwaɗi ya kasa barin maganar sai da ya samu Dady ya sanar mishi abun da Abban yace.
[06/03, 8:34 am] OumƊahirah نفيسة: 🌱🌱🌱🌱🌱

          *SHAREEF*
               _SexyBoy_
🌱🌱🌱🌱🌱


_Writer: Nafisat Isma'il Lawal_
_Wattpad: UmmuDahirah_

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝*



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

       *P.W.A✍️*





*DATA SHARE*

Call, message or whatsap  07065334256

*MTN*
500MB 150
1gb  280
2gb.  560 
3gb.   840
4gb.    1120
5gb      1400
6gb.     1700
Verlid for 30 days.













__________
*BOOK1*
_______________*FREE PAGE50*
_____Washe gari kasancewar ranan Hanif zai fara zuwa aiki, shiyasa shima ya tashi da wuri ya soma shirin sa, shi ya tashi SHAREEF ma daga baya tunda ya ƙi tashi ga time na ta wuce wa,
Sai da ya gama saka kayansa before ya isa wurin sa yana dukan pillown da ya ɗaura kansa yana kiran sunan sa, "Bro wake up mana, it's time to run, it's eight o'clock now."

Ɗan buɗe idanuwansa yayi masu cike da barci, daƙyar yake ware su yana kallon Hanif ɗin da ya koma gyara necktie ɗin sa. Ido ya tsira masa ganin yanda yayi mugun kyau a suit ɗin; cus bai taɓa saka wa ba shi yasa ya kasa ɗauke idanunsa a kansa saboda kyan da yayi masa

Hanif da ya ɗago eye balls din sa ya sauke a kan SHAREEF ɗin, sai ya murmusa yace, "ya dai Bro?"

"You look so cute."

Ɗan washe baki yayi yana murmusawa cike da farin ciki, sai yace, "Thanks, but kayi sauri zamu iya yin late, yanzu ƙarfe takwas ta wuce."
Ya ƙare maganar da ɗan duba agogon hannunsa

Miƙe wa zaune SHAREEF yayi yana jingina bayansa a kan allon gadon, tare da ɗan lumshe idanunsa yana faman hamma, a hankali ya furta, "barcin bai ishe Ni ba, ji nake yi kamar na hakura da zuwa office yau, tunda ga ka."

Dariya Hanif yayi yana zama a gefen gadon tare da ƙoƙarin zura cumbas ɗin sa, at the same time yace, "ina ga don ka ga zan fara aiki ne shiyasa zaka fara kasala, kamar ban san halin ka ba?"

Ɗan kwaɓe fuska SHAREEF yayi yace, "wlh kamar ka sani, abun da ke raina kenan, why not kai ka ci gaba da zuwa in zauna in huta na few weeks, ka ga abubuwa ma zasu yi min yawa since akwai hidimar aure a gaba na."

Ɗan kallonsa Hanif yayi, sai dai bai ce komai ba ya ɗauke kansa ya ci gaba da yin abun da ke gabansa, kuma bai tanka ba bai da alamun magana

SHAREEF yace, "ko ya ka gani? But ina son in je Abuja ma wlh, da zan iya da na bi Dady yau, su Mr. Pitter zasu shigo next time, da yiwuwar in je time ɗin."
Ya ƙare maganar da zuro ƙafafunsa ƙasa tare da miƙe wa tsaye,
Wayansa da ke gefen pillow ta soma ruri, yakai hannu ya ɗauka yana duba screen ɗin wayan; sunan Sweetheart ne ya fito ɓaro-ɓaro, take fuskarsa ta yalwata da murmushin sa mai kyau

Hanif da ke kallonsa yace, "please bro kayi sauri mana, Ni zan je in karya kar ka ɓata mana lokaci."

Hararansa yayi yana cewa, "kana ganin wasa nake maka ko? Ni fa hutu zan ɗauka wlh, yanzu lokacin ka ne."
Sai ya koma saman gadon yana zama tare da peaking wayan,
Bai saurari Hanif da ke masa magana ba ya mayar da hankalin sa a kan Haseena; da ta soma masa ƙorafin rashin kiranta da bai yi ba, har sai da ita ta neme sa

Fita Hanif yayi ya bar sa a wurin yana waya

Ya ɗauki time yana wayan tare da biye wa Haseena tana ta mishi Shagwaɓa. Ya jima zaune a wurin har sai da ya kalli agogon da ke bangon ɗakin, ya ga kusan tara saura, da sauri yayi mata sallama ya faɗa mata, "zai kira ta zuwa anjima in ya je office."
Miƙe wa yayi ya nufi bakin toilet ya zura takalman da ke wurin, ya shige ciki,
Sai da yayi brush sannan ya zare kayan barcin sa; riga da wando da ke jikinsa, sannan yayi wanka ya fito,
Bakin dressing mirror ya nufa yana faman tsane jikinsa da towel, sai da ya gama tsatstsafe jikinsa kaf ya ƙafe babu sauran ruwa, sannan ya soma shafa lotion, after ya gama ya koma bakin closet ɗin sa ya zaro suit sak irin na Hanif,
Fararen kaya ne riga da wando har na ciki, sai dai nashi necktie ɗin red colour ne; while na Hanif sky gree ne,
Sai da ya gama saka wa sai ya ɗauki cover shoes farare ya saka; ba tare da ya sanya socks ba,
Ya koma gaban mirror ya feshe jikinsa da performance ɗin sa sai tashin ƙamshi yake yi, iya ƙalƙaluwa ya ƙalƙalu gashin kan nan sai shining yake yi yana ɗaukar ido, duk da cikin sauri yake yin komai nasa but sai da ya ja time sosai

Amma a haka da ya fita Hanif na can yana jiransa a Falo. Tare da Momy kaɗai suke zaune since Dady ya fita shima yanzu,
Sadiq kuma na dakinsa yana shan barci tunda yanzu sun yi Hutu babu school

"Mom. Morning."

Kallonsa tayi, ba tare da ta amsa ba tace, "sai yanzu? Ka soma lalaci since kana ganin Hanif ya dawo kenan?"

Tura baki yayi

While Hanif da ke shan tea; cup din yana riƙe a hannunsa yake cewa, "haka yace Momy, abun da ke ransa kenan wlh, har ya soma ƙorafin hidima zai yi masa yawa tunda zai yi aure."

Harara Momy ta watsa mishi, tace, "auren da babu amfanin yin sa, har wani murna zaka yi? Ka je kayi breakfast ɗin ka time na wuce wa, in  ba dai fasa zuwa zaku yi ba gaba ɗaya, kaima nayi maka maganar ka tafi but ka zauna sai ka jira sa."

Tsuke fuska SHAREEF yayi yana wuce wa wurin Dinnig; ba tare da yace komai ba ya je ya zauna yana ajiye Jakarsa da phone din sa a other side,
Yana jin su suna hira but bai sake saka musu baki ba; duk a kan maganar auren sa ne duk da yana jin babu daɗi da yanda Momy take kushe auren, shi dai bai damu ba tunda ya samu zaɓin shi, kuma ya san cewa wata rana Momy zata so Haseena since bata da wata aibu a ganinsa, yarinya ce wayayyiya zata ji daɗin zama da ita, ya san duk sabida wancan mai bak'ar fuskar ne ba sa son Haseena, amma komai lokaci ne; da sannu komai zai wuce, shi dai bazai ɓata lokacin sa a kan wancan yarinyar da yake ganin ta tamkar mahaukaciya ba

Sai da Momy ta sake mishi magana sannan ya taso suka fita da Hanif ɗin, tsaban son jiki irin na SHAREEF tunda ya ga akwai Hanif, ya ƙi yin tuƙi sai dai Hanif ne ya tuƙa su

Bayan sun isa Companin; tare suka wuce kansu tsaye office din SHAREEF,
PA ya buɗe musu ƙofan sannan suka shiga, ya bi su riƙe da files suna gaisawa da Hanif cikin faram-faram since sun saba

Sai da suka zauna PA ya ajiye files ɗin a gaban SHAREEF, yana faɗa masa, "sabbin contract ɗin da aka amsa ne ana buƙatar ya duba sabida za a yi zama dasu, and sai kuma files na sabbin ma'aikata waɗanda yace za a ɗauke su."

Bai buɗe ba yace mishi, "ya miƙa ma Hanif shi zai duba, ya kai mishi office din sa ya ajiye, and ya kira masa Mahmud su zo tare."

After ya fita. Hanif yace, "nima zan tafi cuz na ga ka fara tuma min aiki, zan wuce in yi abun da ke gabana, amma kuma ana buƙatar masu aiki har guda nawa ne?"

SHAREEF da ke duba file ɗaya da ya ɗauka, sai ya dakata yana kallon Hanif ɗin tare da cewa, "kamar mutane goma muke son ɗauka, ka san yanzu mun kori wasu daga ciki, har Shuraihu yanzu haka ba ya aiki a Companin, we need a new manager."

In surprise Hanif ke kallonsa da cewan, "duk yaushe aka yi haka? Me ya faru ne Please tell me?"

Cikin rashin damuwa SHAREEF ya ba shi labarin komai, har waɗanda suke zargi da suka samu a Companin gaba ɗaya yayi musu koren kare, ya ƙare da furta, "idan waɗannan mutanen ban wulaƙanta su ba; ban cika Ni SHAREEF ba wlh, domin sai sun biya abun da suka aikata, gobe baza su sake wannan gangancin ba."

Cikin rashin jin dadi Hanif yace, "I never thought that from Shuraihu, he surprised me a lot, amma sai dai shawaran da Mahmud ya baka shi yakamata kayi amfani dashi tun farko, domin idan suna Companin nan shine zaka fi samun hujja daga gare su, yanzu ya ake ciki to? Tawanne hanya zamu iya cin galaba a kansu? Tabbas in ba a ɗauki mataki ba nan gaba zasu iya yin fiye da haka, nima raina ya ɓaci. What you have done is right, action must be taken against them."

"Let Mahmud come and see if there is anything at his place."

Suna nan zaune sai ga Mahmud sun shigo tare da PA, zama suka yi bayan Mahmud sun gaisa da su SHAREEF; yayinda Mahmud ɗin ya sake yi wa Hanif congratulations har suna ɗan zolayan juna since sun saba,
Hanif kowa nasa ne

After sun ɗauki lokaci SHAREEF ya katse su yana tambayar Mahmud ɗin a kan ci gaban da aka samu na hujjojin da suke nema?

Mahmud ya ɗan ja numfashi before ya sanar musu, "har yanzu babu wani ci gaba, don ya kasa samun ƙwaƙƙwaran hujja a kan su, sabida su Alhaji Inuwa ba ƙaramin wayon ne da su ba, yanzu ma already har su Shuraihu sun soma aiki a ƙarƙashin Companin su, sun basu office a can."

SHAREEF shiru yayi bai sake magana ba; yana sauraron zantukan su yayinda ya faɗa duniyar tunanin ta'inda zai samu damar ɗaukar fansa a kan waɗannan Mutanen, domin bazai taɓa ƙyale su ba muddin yana numfashi, bazai yarda yayi Failed ba

Sun jima suna tattaunawa sannan suka watse kowa ya tafi office din sa

Bayan Hanif ya koma nashi office din; sai da ya zauna ya natsa sannan ya kira secretary ɗin sa yace masa, "ina ma'aikatan suna ready ko?"

"Yes sir, suna nan a waje suna jira."

"Ok." Sai ya ɗauko files ɗin ya soma duba na farko, sunan da ya gani yace mishi, "ya je ya shigo da mai sunan."

Fita yayi, babu jima wa sai ga wata budurwa ta shigo cikin office ɗin, tana sanye da dogon Hijab baƙi har ƙasa ba a ganin komai nata, sai flat shoes ɗin ta da ta sanya masu ƙyalƙyali su ma baƙi, tana da ɗan tsawo da kaurin jiki, kuma ba fara bace can; za a iya kiranta da wankan tarwaɗa, tana da kyawun ta dai-dai gwargwado tare da dogon hanci kamar bairo mai ɗaukar hankali a kan face ɗin ta,
Bayan ta shigo sai ta tsaya a bakin ƙofan tana ƙwanƙwasa ƙofan

Hakan ne yasa Hanif ya ɗago yana duban ta suka haɗa ido, kallon kallo suka yi wa juna kowannen su bai iya ɗauke ido a kan ɗayan sa ba

While ita kamar da tsoro a tare da ita, amma ta dage tana faman haɗiyar yawu

Yana ganin yanda wuyanta ke motsi, shi mamaki ma yayi ganin ta tsaya ta kafe shi da ido kuma ta ƙi ƙarisowa, ga ta a cikin office din but tana mishi nocking,
Ɗan janye idanunsa yayi sabida yanda ta kafe sa da ido ta ƙi kawar da kanta, sai ya mayar kan computern sa yana cewa, "Yes come in."

Takowa tayi a hankali tana ɗan gyara wuyan Hijabin ta, tare da ƙara kame jikinta tukun ta samu wuri ta zauna; sabida har ya nuna mata wurin zama bai ce komai ba

"Ke ce Amra Abubakar?" Ya furta ba tare da ya kalle ta ba

Ita kuma sai tayi shiru tana kallonsa ganin ba ya kallonta, bata san ta yanda zata yi mishi bayanin ita ce ba,
Sai da ta ga ya ɗago kansa sannan tayi saurin murmusa mishi tana gyaɗa mishi kai

Har sai da gabansa ya faɗi sabida ganin wannan murmushin nata wanda ya ƙara bayyana kyawun ta,
Haka kawai ya ga yarinyar tayi masa kwarjini musamman yanda ta zuba mishi ido tana sakar mishi smile ɗin ta har yanzu bai gushe daga kan fuskarta ba,
Har ya ɗan shagala da kallonta sai kuma ya kama kansa yace, "kin taɓa aiki a wani wuri ne; ko kuma nan ne first inda kika soma?"

Kai ta ɗaga masa tana mishi nuni da hannunta; alamun tana masa bayani cikin kurmanci tunda baza ta iya magana ba

Shi kuma tuni ya waro ido sabida ganin abun da take yi, "kenan kurma ce?" Ya furta a fili ba tare da ya san ya ambata ba; mamaki kwance a kan face ɗin sa.
[07/03, 8:32 am] OumƊahirah نفيسة: 🌱🌱🌱🌱🌱

          *SHAREEF*
               _SexyBoy_
🌱🌱🌱🌱🌱


_Writer: Nafisat Isma'il Lawal_
_Wattpad: UmmuDahirah_

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝*



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

       *P.W.A✍️*





*DATA SHARE*

Call, message or whatsap  07065334256

*MTN*
500MB 150
1gb  280
2gb.  560 
3gb.   840
4gb.    1120
5gb      1400
6gb.     1700
Verlid for 30 days.












__________
*BOOK1*
_______________*FREE PAGE51to52*
_____Shiru yayi yana zuba mata ido; ganin yanda take ta bayani da hannu har ta gama tayi shiru itama tana kallonsa

Sai dai a yanzu babu ɗan murmushin a kan face ɗin ta; alamun kamar tana cikin damuwa ganin yanda Hanif ya tsare ta da ido ya ƙi cewa komai, idanunta har sun cika da hawaye domin tana ganin kamar a nan ma baza tayi nasara ba, duk sabida wannan laluran da Allah ya bata ana ganin kamar gazawan ta ne

A lokacin Hanif ya kasa yin magana ne don tsananin mamakin yarinyar, wai kurma kuma ta zo neman aiki a nan?
Shiru yayi yana ganin yanda idanunta suka soma ciko da ƙwalla, hakan ne yasa ya buɗe baki with surprise yace, "are you cry?"

Hawayen ne suka zubo a kan kuncin ta, sai ta sauko daga saman kujeran tayi kneel down tare da haɗe hannayen ta cikin roƙo take masa magiyan da bai san ma me take cewa ba; tunda bai iya maganar kurma ba, kawai dai ya fahimci tana roƙon sa ne tunda ga shi har da hawayen ta

Files ɗin ta ya soma kallo yana ganin duk bayanan ta, yayi mamakin hazaƙan ta amma kuma ga ta ta kasance kurma,
Lokaci guda a kuma yanayin da bai san wanne irin yanayi bane ya same shi, wani irin tausayin ta ne ya kama shi,
Mace kamar wannan amma a ce baza ta iya furta magana ba, Allah ya tauye ta ta wannan fannin, amma kuma ga shi bata zauna ba tana neman na kanta,
Har ga Allah ya ji tausayin ta tunda shi Mutum ne mai tausayi, yana ganin bazai iya bari ta tafi bai taimake ta ba, duk da babban matsala ce rashin maganar nata, ba kowa zai iya ɗaukar aiki kamar na Company ya ba Kurma wacce ba ta iya magana ba, sai dai ta ji magana but bata san ya za a yi ta mayar ba, duk da a yanayin aikin office zata iya yin aikinta normal babu matsala, idan za a duba maganar ta bazai kawo cikas a kan aikin ta ba,
Nuna mata yayi alamun ta miƙe ta zauna

Hakan ne yasa ta miƙe da sauri jiki na rawa ta zauna; tana faman share hawayenta, yayinda take bin shi da kallo tana jiran ta ji mai zai ce, a ranta kuma addu'a take yi Allah yasa ta dace, wannan aikin shi kaɗai ya rage mata a halin yanzu, sun rasa komai nasu,
Mahaifinsu gatan su ya mutu ya bar su a lokacin da basu yi tsammani ba, komai nasu ya ƙare ƴan uwansa sun danne musu haƙƙin su, lokaci guda rayuwa ta sauya musu, ga shi ita ce babba a wurin Iyayenta, sai Ƙanninta guda biyu Mata ƙanana waɗanda ko secondary school basu gama ba,
Ita kaɗai ce tayi karatu har ta kammala NCE ɗin ta; da jajircewar iyayenta duk da ba ta iya magana, amma sun dage sun bata ilmi, ashe akwai ranan da zai yi musu amfani, tunda ga shi a wannan gaɓar da suka rasa komai nasu abinci yana son gagaran su, dole ta ɗauki kwalin ta ta soma ƙoƙarin neman aiki kurɗa-kurɗa,
Amma duk inda ta je bata samun Sa'a; sabida tawayan da Allah yayi mata suna ganin kamar ta gaza, basu iya ɗaukar ta aiki a haka ba,
Amra bata sare ba tunda Yarinya ce mai ƙoƙari da nuna dagiyar ta a kan abu, haka ta ci gaba da nema ana wulaƙanta ta; har wasu suna buƙatar wani abu daga gare ta, amma bata taɓa watsi da tarbiyyar da aka basu ba, ta jajirce dole sai ta nemi nata ta taimaki ƴan uwanta da Mahaifiyarta, bata taɓa sare wa ba,
Tunda ta ji labarin wannan Companin suna neman sabbin ma'aikata a wurin ƙawarta, sai ta bazamo jiki sai da ta samu ta ga kwalin ta sun wuce sannan ta ɗan samu sanyi a ranta, sai ta zauna zaman jiran ranan da za a kira su a yi musu interview,
Kullum cikin zullumi da tunani take; tare da addu'a babu dare babu rana don ganin ta samu wannan aikin,
Baza ta so a ce wannan karon ma bata yi nasara ba, baza ta so hakan ta kasance da ita ba,
Amma ganin Hanif da kuma yanayin fuskarsa sai ta ga kamar yana da tausayin da zai iya taimaka mata, shiyasa har ta duƙa tana hawaye tana roƙon sa a kan ya taimaka mata tana mishi bayanin halin da take ciki,
Amma bai fahimta ba tunda ba sanin Yaren nata yake yi ba

Shi kansa yana son sanin wace ce ita, da kuma yanda ta dage take son sai tayi aiki,
Idanunsa ya kawar a kanta tare da janyo Memo ya miƙa mata, ya haɗa da bairo yana ce mata, "ki fada min dalilin son yin aikin ki bayan kin san kina fama da wannan laluran, kin san ba ko'ina za a iya daukar ki aiki ba, don haka ina son sanin reason din ki sabida in san yanda zan yi in taimaka miki."

Da sauri ta janye hannunta a saman face ɗin ta, bayan ta goge sauran hawayenta, sai ta saka hannu ta ɗauki Memon jiki na rawa ta soma rubuta masa irin halin da take ciki,
Sai da tagama sannan ta ba shi Memon

Ya amsa ya karanta yana yi yana kallon face ɗin ta,
Wanda itama tuni ta kafe sa da ido tana jiran mai zai ce mata,
Shiru yayi na ɗan lokaci yana ƙara nazartan abun da ta rubuta, har cikin zuciyarsa yana jin ya yarda da ita kuma yana jin tsananin tausayinta,
Murmushi yayi mata a karon farko yana duban ta, while ya furta, "zamu ɗauke ki aiki in our company, you don't have any problem now insha Allahu."

Wani irin farin ciki ne ya bayyana a kan face ɗin ta, har ta kasa rufe baki tsaban daɗi, sai ga wasu hawayen sun soma fito mata, har ƙasa ta duƙa tana masa godiya cikin yanayin maganar kurmanci

Shi kuma murmushi yayi sabida har a ransa shima ya ji daɗin yanda ta nuna murnan ta, sai yace mata, "ta miƙe ta zauna."
Nan ya ci gaba da duba file ɗin ta na ɗan wasu mintoci before ya bata iznin tafiya, ya faɗa mata, "gobe zata soma aiki, sai ta shigo da wuri."

Murmushi tayi tana kallonsa, sai ta miƙe cikin farin ciki ta haɗe hannayenta wuri ɗaya tana sake mishi godiya,
Before ta fice a Office ɗin har tana sake waiwayo shi

Shima dai ita yake kallo har ta fice, Allah Sarki! Ashe akwai irin waɗannan mutanen a duniya? Naƙasan su ba ya nuna kasawan su?
Ya faɗa duniyar tunani sai ga Secretaryn sa ya shigo office ɗin,
Hakan ne yasa ya daidaita kansa tare da ba shi wani sunan yace, "ya kira mai sunan".







🔆🔆🔆🔆🔆🔆🔆🔆


_____Farin cikin da Amra ta fito dashi daga office ɗin Hanif; ya gaza gushe wa a kan face ɗin ta,
Ko tsayawa bata yi ba ta nufi bakin gate da saurin ta cike da tsananin murna; da kuma Allah - Allah ta isa gida ta sanar da Mamanta,
Tana fita bakin titi sai ta tare adaidaita-sahu
Bata tsaya yin wata-wata ba ta tusa hannunta a cikin Jakarta da ta saƙale ta a hammata, sai ga shi ta fito da ƴar farar takarda mai ɗauke da address ɗin gidan su, ta miƙa masa fuskarta ɗauke da murmushi

Kallonta yayi, sai kuma ya amshi takardan da take ba shi yana duba wa,
Ya gane address ne shiyasa ya sake kallonta tare da furta, "can za ki je?"

Da sauri ta gyaɗa mishi kai alamun eh,
Domin sau tari hakan take yi idan zata je wuri, sai ta rubuta address ɗin sai ta miƙa musu su karanta,
Daga nan sai ta shiga a kaita in sun faɗa mata kuɗin da zata iya biya, in kuma baza ta iya ba sai tayi musu kwatance tare da ciro iya kuɗin da zata iya basu tana nuna musu,
A nan suke gane Kurma ce ita; har wasu su ji tausayinta su ce ta shiga ba tare da sun ja zancen ba

Yanzu ma wannan ya fahimci kamar Kurman ce, shiyasa yace, "ta shiga su tafi."
Haka ya ja napep ɗin har ƙofar gidan su ya dire ta,
Tare da amsan kuɗin da ta ba shi bai yi gardama ba ya wuce abun sa

Ita kuma da gudun ta; ta isa bakin gidan su tana tura ƙyauren gidan ta shige

Da Mamansu ta ci karo tana bakin famfo zata yi wanke-wanke, zaman ta kenan tana kwaɗa wa Ƙanwar Amra kira, wacce take bin ta mai suna Afra, tace mata, "ta kawo mata sauran Omon da ta ajiye a saman window."
Tana ɗago kai ta hangi Amra ta shigo gidan baki a washe ta nufo wurin ta,
Itama sai ta bi ta da kallo tana faɗin, "har kin dawo Amra?"

Kai tayi saurin ɗaga mata tana ƙarisowa wurin ta, cike da son fahimtar da ita samun nasaran ta; ta soma mata bayani da hannu bakin ta a washe kamar gonar adduga

Mama kuwa faɗi take yi, "Masha Allah! Alhamdulillah, an dace zasu dauke ki?"

Kai ta sake ɗaga mata tana ƙara bata tabbaci cikin farin ciki

Sai ga Afra da Salma sun fito daga ɗakin a tare tunda suka ji mai Mamansu take faɗa,
Afra na riƙe da Omon da ta ɗauko suka iso wurin, ita ta soma cewa, "wai Mama da gaske Aunty Amra ta samu aikin ne?"

"Eh, ta samu tace min, tace sun ɗauke ta, sai godiyar Allah, da alamu wahalar mu ta zo ƙarshe, alhamdulillah mun gode Allah."
Ta ƙare maganar tana ɗan share ƙwallan da suka fito mata da gefen zanin ta

Su kuma su Afra sai suka rungume Yayar tasu suna murna gaba ɗaya daya

Har ita Amran sai ɓashe baki take yi,
Sai da suka sake ta kuma ta samu wuri ta zauna a kan kujera ƴar zuƙuno da ke wurin

Mama ta dubi Salma tace, "ta je ta kawo mata abincin ta yanzu."

Wuce wa Salma tayi ta je ta dauko mata abincin; ta ajiye mata a gabanta,
Su ma duk suka samu wuri suka zauna a dakalin wurin suna sauraron Mamansu da take ƙara nuna farin cikin ta

Ta amshi Omon hannun Afra tana zazzagawa tare da cewa, "yanzu Amra to sai yaushe za ki fara zuwa? Yaushe suka ce za ki zo?"
Ta ƙare maganar tana duban ta don ganin amsar da zata bata

Ita kuma ta tsame hannunta tana musu bayanin komai yanda suka yi da Hanif,
Har tana faɗa musu, "da alamun yana da sauƙin kai ne shiyasa ya ɗauke ta aikin, amma ba don haka ba; ba ta tunanin zata samu."

Mama tace, "duk da haka har da roƙon Allah da muke yi, na tabbata ya fi kowa sanin halin da muke ciki domin kullum roƙon mu a gare sa ya kawo mana mafita. Insha Allahu da yardan Allah matsalar mu ta zo ƙarshe, komai zai tafi mana dai-dai ba tare da mun yi roƙo a wurin wasu ba bare a ga gazawar mu, da ikon Allah zan jajirce wurin ganin na taimaki rayuwarku har ranan da zan miƙa ku gidan Mazajen ku, ya Allah ka kawo mana sauyi da zai sa mu farin ciki gaba ɗaya, ya Allah ina roƙonka ka zaɓa wa Yaran nan Mazaje na gari waɗanda zasu ji tausayin ku su kula daku ko bayan raina."

Gaba ɗayansu sun yi shiru suna sauraron Mahaifiyar tasu, inda a ransu suke amsa mata da Amin zuciyoyinsu cike da damuwa, a kullum addu'ar Maman nasu kenan a kansu take ƙarewa, shiyasa wani lokacin sai su ga kamar itama zata tafi ta bar su ne, suna jin babu daɗi idan ta soma addu'ar nan tana nema musu zaɓin Allah tun kafin ƙasa ya rufe idanunta, sai su ga kamar itama zata tafi tabar su ne kamar yanda Babansu ya tafi; cikin faraɗ ɗaya ya gusa a duniyar ya bar su

Jikinsu yayi sanyi; wanda yasa Amra ta kasa cin abincin ma, sai ma tsame hannu da tayi tana nuna damuwarta kamar zata yi kuka

Mama ta fi tausaya wa Amra sabida ita ce a cikin lalura, tun farko soyayyarta ta fi tasiri a zuciyarsu sabida tun lokacin da aka haife ta ta soma wayau suka gano matsalar da take tattare da ita, daga wani ciwo da tayi tun tana ƙarama shine sanadi wanda har yanzu Amra ta kasa yin magana, suna matuƙar tausaya mata shiyasa suka nuna mata ƙauna mai ƙarfi, kuma suka jajirce wajen taimakon rayuwarta sabida gani suke yi idan sun bata ilmi tamkar shi ne Jigon da zai tafiyar da rayuwar ta, ko ina ta shiga muddin tana da ilimin ta baza ta taɓa gazawa ba, koda ta Allah ya kasance ita kaɗai ce ta rage babu su a duniyar; baza ta taɓa yin Bara ba kamar yanda masu lalura irin nata suke kasancewa,
Babansu sai da ya jajirce ya nemo mata makarantar Kurame tun tana ƙarama ta soma yi har zuwa girman ta, bayan ta gama secondary sai ya nema mata nan FCE ta ci gaba da karatun ta, da farko ya so ta karanci fannin su ne na Kurame special education

Amma sai Amra ta nuna mishi cewan, "ta fi son business; sabida nan ya fi burge ta, burin ta kawai ta karanci harkan kasuwanci."
Tabbas Amra ta fuskanci ƙalubale da dama a rayuwarta, musamman girman ta da fara karatun ta a Jami'a, amma tayi haƙuri ta jajirce tunda Mace ce mai hazaƙa, karatun kawai ta saka a gaba bata da buri a duniyar nan da ya wuce karatu, domin tana ganin kamar bata da sauran amfani a duniyar nan idan ba karatun ba, shine Abokin tafiyarta, bata da ƙawa ko saurayi; bata yarda tayi su ba tunda basu a gabanta, tana ganin kamar idan ta shigo da wasu a cikin rayuwarta zata samu matsaloli da dama wanda hakan zai kawo mata cikas a rayuwa, shiyasa ta zaɓi rayuwa ita kaɗai daga ita sai Ƙanninta da iyayenta da suke ɗebe mata kewa,
Sai kuma daga baya da tayi ƙawa A'isha wacce take anguwan su, sai da A'isha tayi naci sosai sannan Amra ta amshe ta a matsayin ƙawa har take kula ta, kuma dama abu ɗaya suke karanta a school shiyasa ƙawancen nasu har tayi tasiri suna taimaka wa juna

A wannan shekaran Amra ta gama karatun ta, kuma mahaifinsu kusan watanni uku kenan da rasuwar sa, inda ya bar su da tarin matsalolin ƴan uwansa da suka amshe musu komai wurin rabon gado, daƙyar suka tsira da wannan gidan da ya rage musu, kuma ba sa tallafa musu da komai sai dai cin zarafi da cin mutunci,
Karatun su ya tsaya cak har na islamiyya,
Gwara Amra ta gama school ɗin ta, yayinda take da burin ci gaba sai ga shi Allah ya dauke wanda suke dogaro dashi,
Afra tana SS 1 ne, inda Salma take JS 2, sai dai karatun nasu ya tsaya cak a yanzu tunda basu da kuɗin biya, wannan hutun da aka tafi basu da damar komawa yanzu ko an koma; sabida basu da kuɗin da zasu biya, tunda basu kai ga biyan schoolfees ba, a cewar Babansu, "zai biya musu idan sun shiga second time." tunda a wannan lokacin bai da kuɗi already ya biya kudin karatun Amra har da bashi ake bin sa, kuma yanzu bashin yake biya bazai samu damar biya musu ba since an matsa mishi. Ana haka ga shi har Allah ya dauke abun sa daga ciwon sati guda

Ganin yanda suka shiga damuwa dukkan su, sai Mama tayi ƙoƙarin kawar musu da halin da suke ciki, tace ma Amra, "ta ci abincin tayi sauri ta gama."

Dayake ɗumamen tuwo ne wanda suka ɗumama da safe, amma ita bata ci ba tsaban zumuɗi zata je wurin samun aiki, duk yanda Mama tayi nacin ta ci abincin kar ta tafi a haka, but ta ƙi tace mata, "sai ta je ta dawo."

Afra ta soma miƙe wa a wurin tunda dama sharan ɗaki zata yi, sai ta wuce ta nufi ɗakin ta soma share wa

Ita kuma Mama ta ci gaba da yin wanke-wanken. Bayan Amra ta gama da kwanon tuwon, sai ta amsa ta haɗa dashi tace musu, "su shiga ɗaki su zauna tana zuwa."

Ɗaki suka wuce, sai sa'ilin Amra ta cire hijabin da ke jikinta tana ninke wa, ta ɗaura a kan Ghana-most go na kayanta, sannan ta zauna tana kallon Ƙannin nata tare da musu albishir, "idan har ta samu albashin ta na farko; su zasu fara koma wa makaranta su ci gaba, don ta fi son su ƙarisa karatun su zai fi."

Sai murna kuwa suke yi, sun tasa ta a gaba tana ta basu labarin abubuwan da zata siya musu in ta fara ɗaukar albashi, har islamiyya zasu koma, daga ƙarshe ta soma basu labarin girman Companin da ta samu aikin a can

Har Mama ta gama ayyukan ta; ta zo ta zauna aka ci gaba da hiran da ita,
Suna nan zaune har rana tayi, sai suka dauko garin kwaki suka tsuma suka sha haka nan babu sigar; tunda basu dashi,
Bayan sun gama suka je suka yi sallah

Daga baya Amra ta shige ɗakin su, wanda suke kwana a ciki ta kwanta sabida huce gajiya, ga kuma barci da take ji wanda bata samu tayi ba a daren jiya tsaban zullumin zata je neman aiki,
Ita kanta bata san iya adadin lokutan da ta ɗauka a kwance a wurin ba, sai jin murya sama- sama tayi a kanta, wanda lokaci guda ta wartsake sabida gane mamallakin muryan

Ilai kuwa shi ta gani a tsaye a kanta tamkar zai faɗo mata, yana kiran sunan ta kamar zai tsaga ɗakin,
"Lallai ma ƴar shilan nan; kin samu duniya kina nan kina raɓashe wa amma aka ce min ba kya gidan? Don tsaban munafurci ko?"








🔆🔆🔆🔆🔆🔆🔆🔆

_____Around five o'clock suka tashi a aikin a tare,
Hanif shi ya soma zuwa office din SHAREEF ya jira sa har ya ƙarisa aikin nasa, sai suka fito a tare suka shiga Mota,
While wannan time ɗin ma Hanif ke tuƙa su,
Shi kuma Gogan yana hakimce a gefe ya ɗauki kiran Haseena wacce tayi masa a yanzu; suna shan soyayyarsu

Hanif tsam yayi yana sauraron ɗan uwan nasa cike da mamakin yanda ba ya jin kunyarsa muddin in yana waya da Haseena ne. Shiru yayi bai ce komai ba sai tuƙin da ya ci gaba da yi idanunsa a kan titi

Har sai da SHAREEF ya gama wayan before ya dubi Hanif ɗin; ganin yayi shiru kamar babu shi a motan, fahimtar da yayi kamar ma ba ya a cikin hayyacin sa ya faɗa tunani, sai ya taɓo sa yana cewa, "Mr. Man, lafiyar ka?"

Ɗago kai yayi ya zuba mishi ido, sai ya ɗan ɗage kafaɗa tare da furta, "mai ka gani?"

"Na ga ka tafi wata duniyar ne, me ke damun ka?"

"Nothing Bro."

Shiru SHAREEF yayi yana duban wayansa, sai kuma can ya sake cewa, "wai kai yaushe ne zaka kawo Budurwan ka kaima kayi aure ne?"

Kallonsa Hanif yayi, sai kuma ya taɓe baki da cewan, "aure kuma?"

"Yeah, aure. Ko maganar da ka taɓa faɗa min wasa ne?"

Murmushi Hanif yayi yace, "Nop, ba wasa bane, ai na so in riga ka yin aure fa, amma kuma yanzu tunda ka shawo kan Gimbiyyar taka i know zaka riga Ni, yanzu Ni ban ma da budurwan tunda Jamila ta yaudare Ni."

Tsaki SHAREEF ya ja yana cewa, "wannan banzan yarinyar Sha-sha-sha? dama wa zai bari ka aure ta?"

Sai Hanif ya kwashe da dariya har da dukan sitiyarin Motan, yace, "wlh ka san abin da na tuna? Kai lokacin fa mun yi rayuwa a BUK; tamkar baza mu rabu da Jamcy ba."

"Shege, ai kaima ka taɓa iskancin ka, lokacin ma Ni ban ma san da wata soyayya ba, ka riga Ni fitsare wa." SHAREEF yayi maganar shima yana dariyan,
Domin ya tuna lokacin da suka yi karatun su a BUK ne, inda wata mayyar yarinya ta liƙe wa Hanif har kuka take mishi tsaban yanda take mutuwar sonsa,
Ya gwara kanta ba kaɗan ba; daga ƙarshe kuma kamar wasa suka soma soyayya, ashe Hanif duk na ƙarya ne kawai ya biye mata ne tsaban iskanci, don lokacin shima kansa yana hayaƙi,
Lokaci ɗaya ya ɗauke mata bayan ya tafi Masters ɗin sa England, sanadin rabuwar su kenan,
Har wannan lokacin bai ƙara ganin Jamila ba tunda ya katse alaƙar su gaba ɗaya, ita kuma bata san gidan su ba; itama asalin ta ba ƴar nan bace, tana Jahar Bauchi take karatu a nan

"Hmm! Rayuwa kenan! Har yanzu gani nake yi kamar alhakin Jamila zai bi Ni, wlh yarinyar nan ta so Ni fiye da tunani, Ni kuma na cuce ta, a yanda na nuna mata soyayya ko Romeo albarka; ashe duk ƙarya ne."

"Ita kuma Jakar bata gane ba." SHAREEF ya furta yana dariyan mugunta; tare da duba wayansa jin ƙaran saƙo

Numfashi Hanif ya ja lokaci guda yana tuna fuskar Amra, sai ga murmushi a kan face ɗin sa, ya kalli SHAREEF yace, "ka san wani abu?"

Girgiza masa kai yayi ba tare da ya dube sa ba, hankalin sa na a kan wayansa

"Wani abun mamaki na gani yau, waɗanda nayi musu interview har da Kurma a cikin su."

"Kurma kuma?" SHAREEF ya maimaita yana kallonsa

Shi kuma sai ya jinjina masa kai da murmushi a kan face ɗin sa yace, "wlh kuwa, abun ya bani mamaki, yarinya ce wacce a tunanina baza ta fi 20years to 21 ba. Ita na fara ma interview, ta burge Ni wlh sabida ban taɓa ganin wata Mace kamar ta ba, Naƙasa bai sa ta dagushe rayuwarta ba, tayi ilmi har tana neman aiki."

Taɓe baki SHAREEF yayi domin maganar bai burge sa ba, sai yace, "to meye amfanin karatun nata da neman aikin tunda bazai mata amfani ba? Babu inda za a ɗauke ta kuwa in har a haka ne."

"Ni kuma sai na ga hakan ba wata matsala bace, since yarinyar tana jin me ake cewa, magana ce dai bata yi, kuma ka ga hakan babu wata matsala, already ma na ɗauke ta."

"What..! A hakan ka ɗauke ta aikin?"

Kai ya gyaɗa masa da faɗin, "Yes, don ta cancanta ne, ba wai don wani abu ba."

Tsaki ya ja yace, "baka da hankali wlh, bazai yiwu tayi aiki a Companin mu ba, gwara ma tun wuri ka sallame ta since bata da gurbi a wurin. Kurma fa?".
[09/03, 9:39 am] OumƊahirah نفيسة: 🌱🌱🌱🌱🌱

          *SHAREEF*
               _SexyBoy_
🌱🌱🌱🌱🌱


_Writer: Nafisat Isma'il Lawal_
_Wattpad: UmmuDahirah_

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝*



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

       *P.W.A✍️*





*DATA SHARE*

Call, message or whatsap  07065334256

*MTN*
500MB 150
1gb  280
2gb.  560 
3gb.   840
4gb.    1120
5gb      1400
6gb.     1700
Verlid for 30 days.












__________
*BOOK1*
_______________*FREE PAGE53*
_____"Itama ai Mutum ce kamar kowa Bro, bai kamata ace don tana Kurma mu ƙi ɗaukar ta aiki ba tunda ta cancanta..."

"Wanne cancanta kake faɗi a nan? A hakan ne zamu ɗauke ta bayan ba ta magana? Da me zata yi abun da ya dace? ko ka fi son ta jawo mana asara ne? Look Hanif, any thing that will bring us back in our company; mu yi asara a cikin Company, bazan yarda dashi ba."

"Please, let's give her opportunity, if we find her wrong, we will send her away, har zuciyata ina jin tausayin ta bazan ji daɗi a kore ta ba; bayan nace mata mun ɗauke ta aiki, already yanzu tana can cikin farin ciki tana saka rai, yanzu kuma mu kore ta, i promise you idan bata yi abun da ya dace ba sai mu sallame ta."

Wani kallo SHAREEF ya watsa mishi, sai yace, "every day we find her guilty, kai zaka amshi laifin, tunda ka matsa."

Murmushi yayi yace, "yeah, na amince."

Daga nan basu sake maganar ba, har suka isa gida; don SHAREEF ya mayar da hankalinsa kacokan a kan wayansa bai da lokacin hiran da Hanif yake masa.





🔆🔆🔆🔆🔆🔆🔆🔆

_____Da sauri Mama ta shigo cikin ɗakin, domin dama tana toilet ne ta jiyo muryan su Afra da Jabir suna faɗa mishi, "babu Amra a gidan," amma ya wuce su ya shige ciki yana faɗin, "idan ƙarya ne sai ya karya su."
Jin abinda yake faɗa ne shiyasa ta hanzarta ta fito don ta san ba mutunci ne dashi ba, ilai kuwa har ya shige ciki ya soma ƙunduma wa Amran zagi kamar yanda ya saba,
Tana shiga ta kira sunan sa tana cewa, "wai me kake yi ne haka Jabir? Kanka ɗaya kuwa?"

"Ke kai nawa kika gani a tare dani? In banda iskanci don na zo gun yarinyar nan ne har kuke min ƙarya ba ta ciki? To wannan wace ce?"
Ya nuna Amra da yatsa wacce take zaune duk ta tsorata da ganin sa

Tsaki Mama ta ja tace, "to wai meye haɗin ka da ita da kake son ka muzguna mata? Mu ji da wanne wai? Yarinyar nan lalura ce da ita amma tsaban rashin tausayi baza ka barta ta ji da abun da ke kanta ba, Ni fa wlh na gaji, idan baka ƙyale ta ba zan sanar da Mahaifinka don a yi mana tsakani."

Cikin rashin mutunci irin nasa ya karkace hanci da baki yana cewa, "to kin fasa mana. Tsoron sa nake ji ne? Yarinyar naki da take naƙasashshiya? Ba abun alfahari bace don na zo wurin ta na nuna ina son ta amma har wani jan aji kuke min, na rantse da Allah idan baku bi ni a sannu ba sai na farka yarinyar nan kowa ma ya huta, don wlh tunda na tashi da kwaɗayin ta sai na cika burina, ko ku bani ita in aura in yi maneji; ko kuma in karɓa ta ƙarfi, eh Allah wlh."
Ya ƙare maganar yana layi

Tuni hawaye sun soma sintiri a kan fuskar Amra, har jikinta ya soma rawa sabida jin abun da yake furta wa

While su Afra da gudu suka ƙarisa kusa da ita duk suka rungume ta; su ma cikin tsoro suka dunƙule wuri ɗaya 

Ita kanta Maman ta tsorata da jin furucin Jabir, don ta san halin sa ba hankali ya cika ba, already shaye-shaye ya gusar masa da hankali komai zai iya yi, shiyasa cikin faɗa da karfin hali irin nata, ta nuna masa hanya tace, "zo ka wuce ka bamu wuri tunda ba gidan ku bane."

"Amma ai gidan Ubana ne ko? Babu wanda ya isa ya kore Ni, kuma Yaran nan Ƙannina ne ba mai raba mu, Amra tawa ce a haka nake sonta sai na ɗanɗana ta wlh, gwara ma tun wuri ki yanke hukunci kafin in sake juyo wa kanku."
Sai yakai duban sa wurin su Amra yana fito tare da turo bakin nan nasa da yayi baƙi tsaban jaraban shaye-shaye, "ke yar shila, zan tafi, ke ma ki yi tunani da kyau kwanan nan zan faɗa ma Babana a zo a sha biki dan ƙwal uban ku."
Ya tsitta miyau ya fice yana faman layi kamar zai tuntsire

Yana fita Amra ta fashe da kuka

Mama kallonta tayi cike da damuwa a kan face ɗin ta, sai ta taho ta zauna a gefen Katifar su tana cewa, "don Allah ki yi haƙuri Amra, ba abun da zai iya miki, insha Allah zan ɗauki mataki a kansa Ni ko ƙaransa zan kai wurin Babansa, domin na gaji da wannan cin mutuncin nasa, ki dena kukan nan don bai da amfani yanzu, kar ki ja wa kanki ciwo."

Ɗago hannunta tayi tana mata bayani cikin kuka, tare da faɗa mata, "ita ta tsorata da Jabir, kar ya zo yayi mata wani abu, don Allah ta taimaka mata."

"Babu abun da zai miki wanda Allah bai miki ba Amra, bazai ci nasara a kanki ba ki kwantar da hankalin ki, yanzu ma zan je in sanar da Mahaifinsa komai, dole a yi mana iyaka dashi."
Sai ta mike ta fita ta koma ɗakin ta, mayafi ta ɗauka ta dawo ɗakin tana sake rarrashin Amra domin har yanzu kukan take yi

Su kansu su Afra hawaye suke yi sun gaza cewa komai jikinsu sai rawa yake yi

Sai da ta ja musu kunne a kan su yi shiru before ta fita, ta saka Salma ta biyo ta ta rufe gidan, idan ta buga sai ta buɗe mata

Amra kuma ta kasa yin shiru, domin ba abun da ta tsana sama da Jabir ɗan uwanta, gaba ɗaya ya takura mata a rayuwarta, nema yake yi ya haukata ta ya saka mata tsoron sa, ko kaɗan ba ta ƙaunar ta buɗe ido ta ga bawan Allan nan, wai a hakan sonta yake yi yayi ta muzguna mata,
Domin a baya ya sha zuwa gidan yana cin mata zarafi Allah kaɗai yake tsare ta, akwai kwanakin da ya zo lokacin Babansu bai jima da rasuwa ba, ya zo ya tarar da ita a gidan; ya kusa yin mata fyaɗe daƙyar ta tsira, sai ga su Afra sun dawo gidan, su suka je suka ƙanƙame ta Afra na dukan sa da kukan ya sakar musu ƴar uwa,
Dalilin da ya dawo hayyacinsa kenan ya haƙura ya tafi yana cizon yatsa, amma ba wai don ya haƙura da ƙudirin sa ba, don a yanda yake kwaɗayin Amra komai zai iya yi, bai da mutunci ko kaɗan, ga shaye-shaye ba ya ganin mutuncin kowa, tunda Babansu ya rasu ya soma addabar rayuwarsu, yayi ta zagin Amra yana kiranta da muggan sunaye a cewar sa, "tunda naƙasashshiya ce shi zai taimaka mata yayi maneji da ita ya aure ta."

Wannan dai lokacin har gida Mama ta je ta samu Mahaifinsa ta sanar mishi, kuma an ci Sa'a yana gida,
Bayan sun gaisa da Asabe mahaifiyar Jabir, sai ta nemi iso wurin Baba Jafaru mahaifinsa, kuma ƙani wurin Baban su Amra,
Asabe ta je har ɗaki ta sanar mishi; sannan yace, "ta shigo."

Zuwa tayi ta zayyane mishi abun da ke faruwa

Amma buɗan bakin Baba Jafaru, sai yace, "ƙazafi take yi wa ɗansa, ƙarya take yi, me zai yi da Kurma? Ya rasa wacce zai bibiya sai ita? Dama ya ga take-taken ta nema take yi ta ɗaura musu sharri tun ba yau ba, an gama na rabon gado, yanzu kuma abun da ta ɓullo dashi kenan, to wlh in ta saka wasa zai amshi Yaran gaba ɗaya tunda su yakamata su riƙe su ba ita ba, bazai bari ta ɓata tarbiyyar Yaran ɗan Uwansa ba, inyaso sai ta kama gabanta ta tafi."

Kuka Mama ta saka mishi, tana cewa, "yanzu duk halin da Jabir yake nuna mana; ban taɓa kawo ƙaransa ba sai a yau, amma nema kake yi ka mayar da laifin a kanmu, don kawai na zo na faɗa maka gaskiya amma maimakon ka tsawatar mishi gani kake yi kamar ƙage nayi mishi?"

"To ƙage ne mana Shafa, taya ya kike tunanin zan yarda da maganar ki? Ƙila ma ita yarinyar ce take bibiyan shi tunda itama ƴar taki yanzu yawon ta take yi, kina ce ban san me ke faruwa bane? Kurɗa-kurɗa yanda ƴarki take yawo a gari ina jin labari, to wlh bazan lamunta ba, mun kusa mu amshi Yaran sabida baza ki ɓata mana suna a gari ba, haka kawai don wulaƙanci ki zo kina son ɗaura wa ɗana laifi? Bayan naki yarinyar ne mai laifin, ai ta isa aure meyasa baza ki nema mata Miji ba? kun zaunar da ita a gida kuna haɗa kafaɗu da ita."

Kasa jure zantukan nasa tayi, shiyasa ta miƙe tana zubar da hawaye; ta dube shi da faɗin, "shikenan Allah na gani, kuma shi zai yi mana maganin dukkan matsalolin mu, wlh na rantse da Allah idan har baka ja kunnen ɗanka yabar zuwa mana gida ba; in har ya aikata muggan abu a kan ƴata, wlh tallahi sai inda ƙarfi na ya ƙare, bazan taɓa ƙyale wa ba, kuma Yarana babu inda zasu gusa daga kusa dani, sai dai duk abun da zaku yi ku yi."

Cikin tsananin mamaki yake kallonta, tare da furta, "haka kika ce Shafa?"

"Eh haka nace." Tayi maganar a zuciye ranta na ƙuna, idanunta jawur a kansa

Shima cikin ɓacin ran yace, "to zamu gani, tunda kin ce hanyar da za ki bi kenan, mu zuba mu ga wanda zai yi nasara."

Bata ce mishi komai ba ta juya tabar Falon nasa, ta fice tana sharan hawayen ta,
Ko kafin takai gida ta gyara fuskarta yanda Yaranta baza su gane halin da take ciki ba

Amma duk da haka sai da Amra ta fahimci akwai abun da ke faruwa, domin bata yarda da abun da Maman ta sanar musu ba a kan, "ta shawo matsalar komai."
Tana ji a jikinta dole akwai matsala, sai dai bata ce komai ba haka tabar abun a ranta ta kasa sakin jikinta, ko walwala ta kasa yi,
A haka ta kwana ranan cikin damuwa, domin har ga Allah tana tsananin tsoron Jabir da abun da zai aikata mata, ba ta son suna haɗuwa sabida yana cutar da ita

Kasancewar bata yi barci ishashshe ba sabida halin da take ciki, shiyasa bata koma barci ba tunda aka yi sallan asuba, tana zaune tana lazumi har gari ya soma haske,
Sai ta tashi ta je ɗakin Mama suka gaisa sannan ta fito ta soma aiki,
Tsintsiya ta ɗauka ta soma share tsakar gidan tunda akwai ta da gazar-gazar komai ita take musu, sai idan Mama ta sanya su Afra ne sannan take haƙura,
Amma yau bata da karsashi tunda barcin da bata yi ba ya saka mata weak a jikinta, tare da ciwon kai, kaɗan - kaɗan yake ratsa ta amma bata so Mama ta fahimta, kuma ga shi tana son fita wurin aiki da wuri gudun samun matsala

Mama kamar ta san halin da take ciki, sai tace, "tabar sharan kawai su zasu yi, gwara ta shirya da wuri kar tayi latti, daga fara wa kuma a samu matsala bata je da wuri ba."
Ce mata tayi, "ta hura wuta ta saka ruwan wanka, sai ta dama musu koko su sha."

Haka kuwa Amra tayi,
Ko kafin bakwai ta gama komai har wanka tayi ta shirya cikin riga da skirt na atamfa, sai ta ɗauki baƙin Hijab ta sanya har ƙasa ba a ganin komai nata, since yanayin shiganta kenan, a rayuwa tana bala'in son baƙin abu, shiyasa yawanci hijabanta bakake ne har ƙasa, zaka ga ta saka ta rufe komi na jikinta, illa fuskarta da ake gani ko kuma idan ta fito da hannayenta, sau tari wasu da suka santa suna tunanin ƴar Shi'a ce, sabida a koyaushe da baƙin Hijab zaka ganta kuma different designs; balle kace guda ɗaya take saka wa,
Yanzu ma bayan ta gama shan kokon sai ta saka socks a ƙafarta tare da baƙin cover shoes,
Ta ɗauki Ƙaramar Jakarta na hammata ta maƙale ta, ta yi wa Mama sallama zata wuce

Mama tayi mata addu'a sosai,
Haka su ma su Afra sai murna suke yi suna mata a dawo lafiya

Naira ɗari Mama ta dauko mata ta miƙa mata,
Tace mata, "ta kula da kanta sosai tayi abun da ya kaita, Allah ya bada Sa'a."

Sai lokacin ta ɗan saki fuskarta tana kallon Maman, idanunta sun ɗan kumbura sun tasa har face ɗin ta, sallama ta sake musu sannan ta fice ta nufi hanyar titi,
Daƙyar ta samu abun hawa har hankalin ta ya soma tashi, ga shi ta fito da wuri kuma tana neman yin latti

Bayan ta isa Companin an sauke ta, sai ta biya kudin ta wuce ciki da sauri cikin rawan jiki,
Lokacin Companin ya cika sai hada-hada ake yi,
Kai tsaye office ɗin Hanif ta wuce tunda ba a nuna musu aikin da zasu yi ba bare a basu wurin zama, sai yau ne za a nuna musu offices ɗin su,
Tana zuwa kuwa ta tarar da sauran sabbin da aka ɗauka, su ma sun zauna a wurin suna jira, tunda Secretary yace, "su jira."
Itama sai ta bi sahun su bayan ta ɗaga musu hannu alamun gaisuwa

Wasu da yawa sun kalle ta amma basu ce mata komai ba, wasu kuma hankalin su ba a wurin yake ba, kowa yana harkan gabansa, itama wurin tsayuwa ta samu tana faman ayyana abubuwa a ranta

Jimawa kaɗan sai ga Secretaryn ya shigo wurin da Files a hannunsa, sai ya wuce su ya shiga office ɗin Hanif, ba a jima ba ya fito yana kallonsu, yace, "yanzu zamu wuce daku zan nuna muku inda zaku zauna, zaku fara aiki Insha Allahu."

Dukkan su sai da fara'a ya yalwata a kan face ɗin su

Sai ya sake duban su da faɗin, "wace ce Amra Abubakar?"

Da sauri ta ɗaga hannunta har jikinta na rawa jin an kira sunan ta

"Ok, ki shiga, Oga na kiran ki, ku kuma sai ku biyo NI ko?"
Ya wuce yana yin gaba; suka take mishi baya

Aka bar Amra tsaye a wurin cike da zullumi da fargaba, wanda hakan ya jawo ta kasa yin gaba bare ta shiga office ɗin, gaba ɗaya fuskarta ta nuna tashin hankali da tunanin abun da zai biyo baya; ƙila koron ta za a yi an fasa ɗaukan ta.
[10/03, 8:51 am] OumƊahirah نفيسة: 🌱🌱🌱🌱🌱

       *SHAREEF*
           _SexyBoy_
🌱🌱🌱🌱🌱


_Writer: Nafisat Isma'il Lawal_
_Wattpad: UmmuDahirah_

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝*



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

       *P.W.A✍️*





*DATA SHARE*

Call, message or whatsap  07065334256

*MTN*
500MB 150
1gb  280
2gb.  560 
3gb.   840
4gb.    1120
5gb      1400
6gb.     1700
Verlid for 30 days.












__________
*BOOK1*
_______________*FREE PAGE54*
_____Tura ƙofan tayi ta shiga ciki; sannan ta mayar da ƙofan ta rufe,
Hanif na kallonta har ta zo ta zauna sannan ta gaishe shi

Dayake bai san gaisuwar nasu ba, shi dai bai amsa ba illa murmushi da yayi mata yace, "kina lafiya?"

Kai ta ɗaga mishi itama tana Murmushin

Sai shiru ya ɗan gibta kaɗan, idanunsa a kanta suna kallon juna, mamakin yanda face ɗinta ta tasa yake yi; da kuma yanda idanunta suka kumbura suka canza launi kamar tana cikin damuwa, ko kuma tayi kuka,
Tabbas ya fahimci akwai abun da ke damunta don ba haka ya ganta jiya ba,
Amma sai bai ce komai ba ya ɗauke idanunsa a kanta ganin itama ta duƙar da kanta, sai da ya ɗan ɓata time wurin duba computern nasa ba tare da yayi magana ba bare ya kula ta

Yayinda Amra tayi tsumu har ta gaji ta ɗago tana kallon yanda yake aikin, murmushin sa a gare ta ya cire mata fargaban da take ciki, har zuciyarta ta ji sanyi domin ta sadaƙar cewan an fasa ɗaukar ta ne

"Kina jina?" Yayi maganar yana ɗago kai ya dube ta

Kai ta gyaɗa mishi da sauri tana gyara zaman ta

"A nan office ɗin za ki soma aiki Insha Allahu, idan Secretary ya zo zai nuna miki inda za ki zauna cuz za ki zama mataimakiyar sa ne, let's wait for him to come back and show you where to sit."

Smile tayi mai yalwa tana ɗaga hannunta tare da mishi godiya

Bai ce mata komai ba ya ɗauke kansa ya ci gaba da aikin gabansa,
Har sai sanda secretary ɗin sa ya shigo, sannan ya umarce sa da, "ya kaita wurin zamanta a office ɗin sa, zata zama mataimakiyar sa, since ba ta iya yin magana sai ya amshi numban wayanta ta haka zasu riƙa communicating, ya bi ya koya mata duk abun da ya dace ta sani."
Sai ya kalli Amran yace, "ta tashi ta bi shi."

Miƙe wa tayi suka fita tare da Secretary

While Hanif ya bi bayanta da kallo har sai da ta fice, sai ya ɗan sauke numfashi yana lumshe idanunsa; tare da ɗaura hannayensa saman table ya tallabo gemunsa; har a ransa ya damu da sanin halin da take ciki domin yana da tabbacin akwai wani abun da ya faru da ita, shi kansa yayi mamakin yanda yarinyar ta tsaya mishi a rai daga jiya zuwa yau,
Murmushi kawai yayi ya janye hannunsa ya ci gaba da abun da yake yi.





🔆🔆🔆🔆🔆🔆🔆🔆


 _____Sabuwar rayuwar Maryamu da ta tsinci kanta; ta soma sanjawa fiye da yanda take a baya, to ta zo wurin wayayyun mutane, shiyasa duk abun da suke yi shi take yi, duk da babu takura a cikin zamansu, amma basu da lokacin kansu sai na karatu, sai kuma idan sun fita zuwa koyon computer, duk abun da suke so ana musu

Ga shi yanzu har an shafe wasu satikai da zuwanta can,
A lokacin take jin labarin auren SHAREEF da za a yi a gobe; a bakin Ammee, duk da Ammeen ba zuwa zata yi ba kasancewar babu tariya,
Amma ta ji suna magana da Momy a waya, kuma ta ji su Aakifah suna zancen, tunda su basu san tana da auren SHAREEF a kanta ba,
Da farko ta soma manta wa dashi since bata da lokacin tunani, amma jin wannan maganar ya fama mata gyambon da ta rufe tana ƙoƙarin binne shi a ƙasan zuciyarta,
Lokaci ɗaya jikinta ya mace ta kasa yin komai, sai wani irin ciwon kai da ya kawo mata cafka, take ta haye saman gado ta rufe kanta zuciyarta na wani irin zafi kamar zata faso ƙirjinta, ta kasa jurewa sai ta fashe da kuka, kuka mai cin rai,
Shikenan tana ganin ta rasa SHAREEF na har abada; tunda ga shi zai auri wacce yake so yake ƙauna, zai yi rayuwa da wata ba ita ba, meyasa ya kasa fahimtar zuciyarta? Ko tana da laifi ne don ta so shi? Meyasa ba ya da tausayi bazai iya tausaya mata ba?
Shikenan yanzu ya kuɓuce mata ya zama na wata? Ba ta jin zata iya jurewa, mutuwa zata yi sabida tsananin kishin da ke taso mata a can ƙasar zuciyarta,
Kuka sosai take yi tunda ta samu dama babu kowa a ɗakin, daga ƙarshe sai jikinta ya rikice sabida kukan da ta dinga yi; ga kuma ciwon kai, nan da nan zazzaɓi ya sauka a jikinta,
Amma duk da haka bata sarara wa kanta ba, tana kukan baƙin ciki da tsananin kishin rasa SHAREEF, tana son ta cire sa a rai amma hakan bazai taɓa yiwuwa ba, abu ne mai matuƙar wahala ta manta SHAREEF a rayuwarta, ya zama jinin jikinta, shi zuciyarta take so, kuma tana ji a ranta sai dai ta mutu da soyayyarsa

Yusaira ta shigo dakin ta tarar da ita a haka tana gunjin kuka, sai ta taho wurin ta cikin tsananin tashin hankali tana kiran sunan ta, hannu ta sa ta yaye bargon tana cewa, "Maryam, kukan me kike yi? Ba ki da lafiya ne?"

But ina Maryamu ta kasa amsa mata, ƙoƙari take yi ta tsayar da kukan nata amma ta gaza, wani irin sabon kuka ne ya taho mata ta sake shi lokaci guda tana sake ƙanƙame idanunta, domin a lokacin wani irin azababben ciwon kai da yake kawo mata cafka ko buɗe idon bata son tayi

Yusaira kuma sai ta tsorata da halin da take ciki, da gudu ta juya ta fita ta je ta sanar da Ammee dake zaune a falo su da su Aakifah

Hakan ne yasa itama ta taso hankalin ta a tashe jin abun da Yusaira take cewa,
Tare gaba dayansu suka yo cikin ɗakin suka shiga,
Sun tarar da ita a wannan yanayin tana ta kuka tana kiran kanta

"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un!" Kalman da Ammee ta furta kenan tana zama tare da tallabo ta jikinta, yanayin yanda ta ga jikin nata hankalin ta yayi ƙololuwar tashi, faɗi take yi, "Maryam me ke miki ciwo? Me ya faru da ke ne? Yanzu fa kika shiga ɗakin lafiyar ki lau."

Su ma su Aakifah sai ga hawaye, sun yi tsumu sun kasa kataɓus sai kallonta suke yi cikin tsananin tausaya mata, don ko da gani tana jin azaba yanda take ta juya kai

"Yusaira, maza je ki ɗakina ki ɗauko min first eid box."

Juya wa tayi da sauri bayan ta amsa mata, ta nufi dakin Ammee ta ɗauko ɗan akwatin magungunan su

"Buɗe min ki ɗaura a kan gadon, ke kuma Aakifah dauko ruwa."

Itama Aakifah da gudu ta juya ta fita Falo

While Na'ilah tuni ta haye saman gadon tana kukan itama, ganin yanda Maryamu take kuka duk hankalin ta ya tashi; abun ka da ƙaramar yarinya

"Yi shiru Maryam, ki dena wannan kukan shi zai ƙara miki ciwo, kan kaɗai ke miki ciwo ko har da wani abun?"
Ta tambaye ta tana sake tallabo ta jikinta

But Maryamu ta kasa magana sai gunjin kukan da ta kasa bari, tana faman jujjuya kai kamar wacce zata hau iska

Bayan an kawo ruwan; lallaɓa ta Ammee tayi ta bata maganin ta sha, daƙyar ta rarrashe ta ta dena kukan,
Sai tace, "ta koma ta kwanta Insha Allahu jikin nata zai yi sauƙi."
Tunda a ganin ta zazzaɓi ne kawai ya rufe ta

Ita kuma sai ta kwanta tayi lamo sai shashsheƙan kuka take yi, ta rufe jikinta gaba ɗaya idanunta a rufe tana sauke nimfarfashi,
Yayinda wasu siraran hawaye ke ɗiga mata suna bi ta gefe da gefen kunnuwan ta,
SHAREEF kawai take iya tuna wa a halin da take ciki, fuskarsa ne a idanunta yayinda take jin wani taƙuƙi gami da kishi na ƙara hudo mata ƙirji, shikenan ta rasa sa? Idan tayi tunanin wannan kalman ji take yi kamar zata mutu, sai kuma ta kama kuka wi-wi

Dayake Ammee ta kaɗa su sun koma Falo, basu san halin da take ciki ba, amma sun tausaya mata gaba dayansu, sun gaza yin aikin ma da ke gabansu,
Sai da Ammee tace, "su je su ci gaba da aikin su kar a kira Magriba."
Sannan suka tafi jiki a sanyaye, sun rasa me ke musu dad'i tunda suka ga Maryamu a haka,
Suna fatan a ce ta samu sauƙi da wuri, domin ba ƙaramin sabo suka yi ba yanzu, komai tare suke yi, shiyasa suka ji komai ya fitan musu a rai, daƙyar suka gama aikin nasu dama girki ne suka jera a saman dining

Ita kuma Ammee tana yi tana zuwa duba Maryamu,
Sabida tuni barci ya sure ta since ta haɗa mata da maganin barci, tana cikin kukan wani wahalallen barci yayi awon gaba da ita

Almost nine o'clock before ta farka, tunda Ammee ta hana a tashe ta har sai idan ta farka da kanta, ta san ciwon zai iya sauka a jikinta,
Ai kuwa ta tashi babu zazzaɓin, sai ciwon kan kaɗan-kaɗan

Time ɗin su Aakifah na tare da ita, suna ganin ta farka Aakifah ta je ta sanar da Ammee,
Shi ne suka dawo tare cikin ɗakin

"Ya jikin naki daughter?" Ammee ta furta hakan bayan ta isa gabanta ta riƙe ta

A hankali cikin muryanta da ba ta fita ta amsa mata

"Yauwa to alhamdulillah, yanzu bari ki yi wanka sai ki ci abinci; za ki sake samun ƙarfi a jikin ki,
Yusaira haɗa mata ruwan wankan, idan tayi ku fito mata da kayan da zata sa, in kun gama sai ku fito Falo tare."

"To Ammee." Suka amsa mata a tare

While Yusaira ta shiga toilet ta haɗa ruwan

Aakifah kuma ta taya ta har ta miƙe ta cire kayan jikinta tana ɗaura towel,
Har toilet ɗin ta riƙe mata hannu suka shiga sannan ta fito,
Ta ciro mata kayan da zata saka,
Yusaira kuma ta gyara gadon nasu,
Suna nan zaune har ta fito,
A tare suka fara mata sannu da jiki

Ta amsa a sanyaye sabida gaba ɗaya ba ta jin daɗin jikinta, ƙarfin hali ne kawai duk da babu wani ciwo a tare da ita, sai kanta da ke sara mata

Sai da ta gama shirya wa suka fita a tare zuwa Falo

Time ɗin Ammee ta zuba mata abincin a plate, ta ɗauko mata magani,
Sai tace, "ta zauna ta ci."

Zama tayi, su Yusaira suka zauna a gefen ta

Ammee tace, "Aakifah zo ki ɗauki Na'ilah ki kaita ɗaki tayi barci."

"To Ammee." Ta amsa mata tana tashi; ta ɗauke ta zuwa ɗakin Ammee

Su kuma suka zauna shiru idanunsu a kan TV. While Maryamu na cin abincin a hankali

Sai can Ammee ta dube ta tace, "ki ci abincin sosai mana Maryam, ki daure haka nan ki ci sai ki sha maganin, Allah zai ba ki lafiya."
Ta ƙare maganar cikin lallami

Duk basu san me ke faruwa da ita ba, Maryamu ta shiga wannan halin ne don kawai jin auren SHAREEF da za a ɗaura a gobe asabar, shiyasa hankalin ta ya ƙi kwanciya, komai ya fita a kanta, ƙarfin hali kawai take yi, amma ji take yi kamar ta ci gaba da kukan sabida in ta tuna da maganar hankalin ta tashi yake yi, gani take yi kamar ta rasa shi har a cikin zuciyarta 

Bayan ta gama sai Ammee ta bata maganin ta sha, tukun tace mata, "ta je tayi sallah sai ta kwanta."
Su ma su Yusaira ce musu tayi, "su bi bayanta daga nan su kwanta since dare yayi."

Miƙewa suka yi sukai mata sai da safe sannan suka wuce dakin su,
Kai tsaye Maryamu alwala tayi ta gabatar da Sallah before ta haye gadon kusa da su Yusaira ta kwanta,
Time ɗin suma har sun yi barci,
Amma ita sam ta kasa runtsawa, sai ma wani wahalallen kuka da ya bijiro mata, take ta toshe kanta ta dinga sharɓa kukan tana yi tana toshe bakin ta,
Ganin bata da mafita dole ta sauko daga kan gadon ta fita Falo, ko'ina duhu amma babu tsoro a tare da ita, zama tayi a kan sofa ta haɗa kai da gwiwa ta dinga rera kukan kamar zata mutu, sam barci ya ƙaurace mata, tunanin SHAREEF ne kawai a ranta, zuciyarta zafi take mata sosai kamar zata ɗaɗɗake, ta rasa me ke mata dad'i a rayuwa,
Daga ƙarshe ƙasa ta zamo ta kwanta ta rigingine; yayinda hawayenta ke zuba yana sauka a kan carfet, tsawon lokaci tana a wannan yanayin sam babu barci a tare da ita, kuma babu gajiya bare ta dena kukan da take yi,
Tuni sabon ciwon kai ya dawo mata, ɗakyar take iya buɗe idanunta tsaban azaba da raɗaɗi

Maryamu a haka ta kwana a wannan yanayin cikin wani irin halin da bata san inda kanta yake ba, illa sambatun kiran SHAREEF da take yi a bakin ta

Ammee ta fito da asuba da nufin ta tashe su, sai ta ji kamar maganganu a cikin Falon, take ta nufi wurin glop ta kunna sabida har ta ji tsoro tana tunanin ko waye ne?
Abun mamakin sai ta hangi Maryamu a tsakar ɗakin a kwance,
Da sauri ta nufi inda take tana kiran sunan ta,
Amma idanunta a rufe kuma tana ta maganganu mara sa kan gado,
Saurin duƙa wa tayi gabanta tana sake kiranta tare da kai hannu jikinta, zafi ta ji zauu kamar garwashi aka ɗoɗana mata, alamun dai zazzaɓin ne ya dawo,
Salati Ammee tayi tana sake kiran sunan ta tare da jijjiga ta

Sai a lokacin Maryamu ta buɗe jajayen idanuwanta da suka gama rinewa suka fita a hayyacinsu; sun ƙara girma sun yi luhu-luhu dasu,
Kallonta take yi amma bata fahimci wace ce ba cus zazzaɓin yayi mata yawa

Sosai Ammee ta ruɗe sabida ganin halin da take ciki,
"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un! Maryam."
Sai kuma ta sanya hannu tana tallabo ta jikinta cikin tsananin damuwa da tashin hankali,
Jin tana ambaton kamar sunan SHAREEF; shiyasa ta ɗan kasa kunnen ta tana jiyo me take furta wa,
Cike da tsananin tausayinta take kallonta sabida jin furucin nata,
Mayar da ita tayi ta kwantar da ita, sannan ta ruga aguje ta shiga ɗaki ta dauko mayafin ta da key,
Ɗakin su Aakifah ta shiga ta tayar da su tana faɗa musu, "su yi maza suyi sallah su kula da gidan, zata je kai Maryamu asibiti ne."

Ai sai suka ruɗe kowaccen su ta soma tambayar Ammeen

Bata kula su ba ta fita a ɗakin,
Su ma sai suka take mata baya,
A can suka tarar da Maryamun a halin da take ciki, kuka suka fashe dashi sabida tashin hankali, sabida  rashin sabo da ganin irin wannan ciwon nata, duk jikinsu rawa yake yi ganin yanda Maryamun take kwance a ƙasa tana juye-juye da sambatu kamar mara hankali, idanunta a buɗe sun kaɗa sun yi ja, shiyasa suka sake rikice wa da ganin halin da take ciki

Ammee ta cicciɓe ta ta fita da ita waje, suka bi ta can har wurin Motan ta,
Sai da Aakifah ta buɗe mata back sit ta saka ta, sannan ta shiga gaba tana jan musu kunne, "su yi aiki kar su zauna kafin ta dawo, kuma su shirya su tafi hadda."
Sai ta ja motan tabar haraban wurin; tare da nufan gate mai gadi ya buɗe mata, sai ta fice da gudu ta nufi asibiti.
[10/03, 7:38 pm] OumƊahirah نفيسة: 🌱🌱🌱🌱🌱

       *SHAREEF*
           _SexyBoy_
🌱🌱🌱🌱🌱


_Writer: Nafisat Isma'il Lawal_
_Wattpad: UmmuDahirah_

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝*



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

       *P.W.A✍️*





*DATA SHARE*

Call, message or whatsap  07065334256

*MTN*
500MB 150
1gb  280
2gb.  560 
3gb.   840
4gb.    1120
5gb      1400
6gb.     1700
Verlid for 30 days.












__________
*BOOK1*
_______________*FREE PAGE55*
_____Yau SHAREEF ya tashi a cikin farin ciki da zumuɗin zuwan ranan, kasancewar yau ita ce ranar da ta kasance rana mafi soyuwa a gare sa, a yau asabar zai mallaki zaɓin zuciyarsa; wanda ya daɗe yana zuwan wannan lokacin

Su kansu ƴan gidansu sun tabbatar da cewan SHAREEF yana cikin tsantsan farin ciki, kowa kallonsa yake yi da mamakin yanda ya ruɗe yana ta rawan kai

Momy dai bata ce komai ba,
Dady da Hanif ne suke tsokanarsa sabida ganin yanda ya kasa zaune ya kasa tsaye, har ya shirya tunda ƙarfe sha ɗaya na safe ne za a ɗaura auren

Wata iriyar shadda ya saka gezna mai tsananin tsada da ɗaukar ido, kalanta kalan sararin samaniya, ba ƙaramin mugun kyawu tayi masa ba, ya fito a Angon shi sak sai wani ƙyalli da kwarjini yake yi, a inda ya sha aski ya gyara sajen sa ya ƙara ƙawata face ɗin sa, ya fito fresh dashi idanun nan sun yi haske tarr, ga fara'a wanda ba kasafai ake gani a kan fuskarsa ba, shiyasa wani irin kwarjini ne da kamala ya sake fito masa,
Yayi using agogon sa da takalman sa cumbas Black color, kamar yanda aikin kayan aka yi mishi da baƙin zare, har da malin-malin ya saka, sai ya mirza baƙin hula wanda ya zauna masa ɗas, sai wani tashin ƙamshi yake yi kamar wanda ya shige cikin kwalban turaren sabida yanda yake wani sihirtaccen ƙamshi mai fizgar hankali

Dady da Hanif tare da Sadiq duk kala ɗaya suka sanya, suma wankan gezna ɗin suka yi, amma sky blue, komai nasu iri ɗaya ne; Dady ne kaɗai ya sanya malin-malin a sama,
A sanda SHAREEF ya fito sai suka tsaya kallonsa kawai suna mai mamakin irin tsantsan kyan da yayi, bakin su ya ƙi rufuwa duk yanda suka so da yin shiru

"Lallai Yaro na, wannan kyau haka? Anya na taɓa ganin kayi kyau kamar na yau?"
A cewar Dady da ya riƙe haɓa yana ƙare mishi kallo

A lokacin Momy ta fito daga kichen tana ɗan share hannunta a gefen zanin ta, ita ko kwalliyar bata yi ba, don dama tace baza ta yi ba, rigan barci ne a jikinta sai ta ɗaura zani a saman ta, fuskarta babu yabo babu fallasa duk da ta ga yanda SHAREEF ɗin yayi mugun kyau, ita kanta ta kasa ɗauke ido a kansa, tana sauraron yanda suke kwarzanta shi kamar zasu haɗiye shi suna fasa mishi kai

SHAREEF kuwa da ya hango Momy, langaɓe kai yayi yana zuba mata ido tare da cewa, "Momy ban yi kyau bane? Ke ba ki ce komai ba?"

Taɓe bakin ta tayi tare da furta, "me zan ce SHAREEF? Duk abun da zan ce sun riga Ni faɗa, cuz tun daga kichen nake jin irin yabon da suke maka, bani da abun furta wa."

Shiru ya ɗan yi, but idanunsa a kanta yana kallonta, sai dai yanda ta kawar da kai ta nuna halin ko'in kula dashi, ta koma tana yi wa su Dady magana, sai jikinsa duk yayi sanyi

Hanif ne ya matso kusa dashi yana mishi raɗa, "common Bro, kar ka ɓata fuskarka mana, ka fito da annuri kana ƙoƙarin turɓune fuska, kayi kyau sosai wlh, ban taɓa ganin kyawun ka irin wannan ba, ko don kayi shigan da baka taɓa yi bane?"

Murmushi SHAREEF yayi, shima yana bin jikinsa da kallo, cuz tunda yake bai taɓa sanya malin-malin ba, manyan kaya ma idan ba ya zama dole bane ba ya saka su, sai jifa-jifa ranan Friday

Ganin karfe sha ɗaya har tayi, shiyasa suka fita gaba ɗaya, a lokacin ma Mutane ƴan uwa duk sun hallara zuwan su kenan, dalilin da yasa Dady yace, "su fita waje su jira ko akwai saura waɗanda zasu zo, sai su wuce gaba ɗaya kawai."

Su Aunty Najwa a lokacin suma suka iso suka shigo cikin gidan,
Babu jimawa sai ga su Aunty Salma da wasu daga cikin dangin su,
Duk da Momy tace, "babu taro."
Amma hakan bai hana sun zo ba, ƴan nesa ne kawai baza su samu damar zuwa ba tunda ɗaura aure kawai za a yi, shiyasa sai dai a waya suka kira Momy suka yi mata fatan alkhairi.
***

          
_____Karfe sha ɗaya da rabi dai-dai dubban jama'a suka shaida daurin auren SHAREEF Ahmad da Amaryansa Haseena Tahir; a kan sadaki Naira na gugan Naira dubu ɗari biyar lakadan Ango ya biya

A wannan lokacin SHAREEF ya rasa inda zai saka kansa don murna, wani irin farin ciki ne a kan face ɗin sa, tamkar an yi mishi albishir da shiga aljanna, har ƙwalla ya tara a idanunsa sabida tsaban murna da daɗin mallakar abar ƙaunarsa, cus irin kaunar da yake mata baki ma bazai misalta ba, da dukkan zuciyarsa yake sonta, wannan rana tana a cikin ɗumbin ranakun da yayi a tarihin rayuwarsa mai muhimmanci, tabbas rana ce mai muhimmanci a gare sa, domin murnan sa yasa har hawaye sai da suka ɗiga mishi a kan face, handkerchief ya zaro a cikin aljihun sa ya ɗauke su nan take, yana mai ci gaba da amsar gaisuwa na daga Abokai da ƴan uwa da suke taya sa murna, bakin nan a washe ya kasa rufe shi

Hanif na gefen sa shima yana amsa gaisuwar, yanda ka san shine Angon don shima yana cikin farin cikin, cus yana taya ɗan uwansa mafi soyuwa a zuciyarsa murnan zuwan wannan rana

Direct SHAREEF da su Hanif; tare da su Mahmud, da wasu daga cikin ƴan uwan su Hanif ɗin Abokansa, can gidan su Haseena suka wuce, don dama an yi ɗaurin auren ne a ƙofar gidan Kakannin Haseena, iyayen Abbanta,
Daga nan sai suka wuce gidan su Haseena don su ɗauki hotuna kamar yanda ya zama al'ada a zamanin nan; domin barin tarihi,
Sannan akwai party da aka shirya zuwa ƙarfe huɗu, su Hanif suka shirya isu-isu Maza Abokansu, kawai za a je hotel ne a yi cima kala-kala

Koda suka isa ƙofar gidan su Haseena, SHAREEF ne ya kira ta a waya ya sanar mata da zuwan su

Hakan ne yasa tace mishi, "su shigo ciki zuwa Falon Abbansu."

Tare suka shiga gaba ɗaya zuwa cikin gidan, suma duk da babu taron biki amma gidan da yalwan mutane sosai, tunda ba baya ba suna da dangi da yawa, bare dama Ummanta irin mai shige da fice ne, tana da yawan ƙawaye, duk sun zo sun cika gidan,
Tunda suka ji an ce ga Ango nan sai duk suka fito waje ana gaisawa, wasu sun fito ne dama don su ga kalan Angon musamman ma tsirarun ƙawayen Haseena waɗanda suka yi karatu tare,
Sai fa kallo ya koma wurin ango sabida yanda yayi mugun tafiya da imanin su, babu shakka Haseena ta iya zaɓe a yanda suke furta wa kenan, iya haɗuwa ya haɗu sun ga kyakykyawar Gaye kowa sai faɗin albarkacin bakin shi yake yi

Dayake SHAREEF ba Mai son kallo ne da yawa ba, kuma ba ya son hayaniya ko kaɗan, shiyasa duk ya ji sa wani iri yanda aka zo aka yi masa caa, ɗakyar ya samu ya shige Falon Abba inda Haseena tace, "su shiga."
Sai daga baya su Hanif suka bi bayansa

Nan da nan aka cika musu gaban su da kayan motsa baki, su Hanif sun saki ciki sai kwasa suke yi

While SHAREEF kuwa ko ruwa bai sha ba, burinsa kawai ya ga Haseena ya ga irin wankan da tayi masa

Wasu daga cikin ƙawayenta tare da Haajara; su suka shigo cikin falon suka zauna ana hira da su, sai wani fi'ili suke yi suna yanga irin yanda dai ƴan mata suka saba idan sun ga Samari,
Haka suma Samarin a wajen su hakan take, sun saki baki sai hira suke yi dasu suna kashe musu murya

Da yawan Matan yanda SHAREEF ya tafi da imanin su, ji suke yi da su ne suka yi wannan Sa'an, amma ganin Hanif wanda ba shi da maraba da SHAREEF ɗin, kowa ya kalle su ya san ƴan uwa ne, tamkar twins haka suka kasance a idanunsu, sai wani shishshige mishi suke yi suna son ya tanka su, amma kuma shi dayake ya gane yanayin su, kuma babu wacce tayi masa shiyasa ya ƙi sakin musu fuska, sai suke ganin kamar dukkan su halin su ɗaya daga Hanif ɗin har SHAREEF, akwai tsare gida 

Itama Haajara tunda ta ga Hanif ɗin ta san wane ne shi a wurin SHAREEF, shiyasa take ta maƙale mishi sai rawan jiki take yi dashi, miƙe wa ma tayi tace mishi, "ya zo su ɗauki hoto."

Yana taso wa sai suma ƴan matan suka taso suka shige dole da su za a yi,
Daga nan ne fa aka fara hotuna

Jin Haseena shiru bata fito ba, SHAREEF ya ƙagara da ya ganta, sai ya ɗauki waya ya tura mata text message

Babu jimawa kuwa sai ga ta ta shigo cikin falon, cikin shiganta na Arabian gown mai ruwan zuma, rigan ya tafi tun daga sama har ƙasa ya bi jikinta ya lafe gunun ban sha'awa sabida shape ɗin jikinta ya bayyana, fuskar nan nata ta sha MakeUp mai ɗaukar hankali sai wani walwali take yi tamkar tauraruwa, hill shoes ne a ƙafafunta waɗanda suka sha jan lalli, haka ma hannayenta sun sha lalli mai ban sha'awa ga wasu zaro-zaron ƙumbuna da ta sanya, wani net ta ɗaura a kanta wanda ya tsaya mata iya kafaɗunta, an yi mata design da gashin ta dana attachment yayi tsiriri kamar tayi acuci

Shigowar ta sai da SHAREEF ya miƙe tsaye tsaban yanda ya ga tayi masa mugun kyau, ya kasa bari ta iso wurin sa sai taka wa yayi ya nufe ta, yana isa ya sanya hannu ya kamo nata tare da janyo ta jikinsa suka haɗe da juna, wani irin kallo suke wa junan su mai haɗe da zallan soyayya gami da farin cikin da suke ciki, sun manta ma a inda suke sabida irin shagaltuwa da suka yi wurin kallon junan su

Cousin ɗin sa Habib, shi ya matso inda suke yana tafa hannu tare da furta, "to lovers, kallon ya isa haka kar ku cinye juna."

Hakan ne yasa sauran ma suka ankare da su, sabida hankalin su ya ɗauke wurin yin hoto,
Ai take dukkan su suka nufo wurin su suna faɗin, "wow! Wow!" Sabida mugun dacewar da suka ga sun yi musu a ido, ba ƙaramin marching suka yi da juna ba,
Take a nan su Haajara suka soma ɗaukar su pictures a yanda suke tsaye rungume da juna, hannun SHAREEF a ƙugun ta ya riƙe ta ƙam kamar za a ƙwace mishi ita, yayinda face ɗin kowannen su da yalwan murmushi haƙoransu ya bayyana a fili

"Ku tsaya mu ɗauke ku hoton kawai a haka, sai ku sauya style."
A cewar Haajara tana ci gaba da kashe su da Camera

Haka fa suka dinga daukar su hotuna kala-kala cikin styles,
Bayan sun gama su Hanif suka shiga suma aka dinga ɗaukar su tare,
Shi dai SHAREEF yana manne da Haseena ya ƙi sakin ta bare su rabu, sun manne like a chewing gum,
Haka suka dinga daukar hotunan suka ɓata lokaci a wurin.
***

             
_____Duk da Momy bata so aka tarun mata a gida ba, amma bata da yanda zata yi, dole ta ɗaura girki tunda ƴan uwanta sun zo, wasu ma sai ƙara tururuwan zuwa suke yi duk da duk dangi ne a wurin,
Ana zaune ana ta hira, su Aunty Zainab kuma suna can suna haɗa abincin da za a ci

Ita kuma Momy jin Ammee bata kira ta yau ba, shiyasa ta dauki waya ta kira ta, amma jin yanayin muryanta cikin tashin hankali shiyasa ta miƙe tsam tabar cikin jama'a, ta haura sama ta shiga ɗakin ta, sai da ta zauna a kan gado take ƙara tambayarta tare da cewa, "wai lafiya Surayya duk kin ɗaga min hankali? Me ke faruwa ne?"

"Babu lafiya Aunty, tun asuba nakai Maryam asibiti, jikin babu dad'i."

"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un! Me ke damun ta; me likitocin suka ce?" Momy ta furta a ruɗe

"To zazzaɓi ne dai Aunty, amma yayi mata mugun kamu don tana jin jiki, sai yanzu ma na samu ganin ta wlh, amma tun ɗazu duba ta suke yi, yanzu ma gani a ɗakin da take tana Barci, sun sanya mata drip har biyu a dukka hannunta."

Momy kamar zata yi kuka ta dinga furta salati cikin tsananin damuwa

"Amma Insha Allahu sun ce da zaran ta tashi jikin zai yi sauƙi, da alamu yanayin jinin ta kenan da saurin ɗaukar ciwo mai zafi, haka suka faɗa, amma sun ce nan da nan zai sauka."

Ajiyar zuciya Momy ta sauke tare da faɗin, "to yanzu ya za a yi? Hankalina ya tashi wlh, bari Dadynsu ya dawo sai in faɗa mishi musan yanda za a yi."

"A'a kar ki tayar masa da hankali, mu bari mu ga yanda hali zai yi, Ni ina tunanin ko ta ji zancen da muka yi ne a yammacin jiya, domin tun jiya jikin nata ya rikice, da har ta samu sauƙi kuma yau da asuba jikin nata ya sake tashi, nan na tarar da ita tana ta sambatu tana kiran sunan SHAREEF, gani nake yi kamar ta san da auren da muka yi magana jiya da ke, sabida furucinta da ta dinga yi."

"Ba mamaki ƙila ta ji ne, mun ƙara tono mata da zancen, kai! innalillahi wa'inna ilaihi raji'un! Wannan wacce irin ƙaddara ce? Wlh na rasa ya zan yi? Taya ya zan sanya SHAREEF ya ƙaunce yarinyar nan? Tana azabtuwa wlh, Ni da da hali wlh sai na cire soyayyar shi a zuciyarta, ban taɓa ganin irin wannan soyayyar na Maryam ba, Allah ya ɗaura mata soyayyar maso wani, ba ki ga yanda SHAREEF yake farin ciki da wannan auren ba, na tabbata hankalinsa ba ya wurin Maryam, bazai taɓa sonta ba."

Cike da damuwa Ammee tace, "kar ki ɗebe tsammani Aunty, na tabbata wata rana zai so ta duk da irin soyayyar da yake yi wa wancan, mu dai taya ta da addu'a domin shi take buƙata a gare mu, Allah ya yaye mata domin ya zame mata masifa da cuta a tare da ita, tana cikin wani hali."

Shiru Momy tayi sabida ta kasa ma furta komai don tsananin damuwa da tunanin halin da Maryamu take ciki

Sai Ammee tace, "Aunty bari zan yi sallah yanzu, wlh tunda muka zo asibitin tun asuba ban samu nayi sukuni ba sai yanzu da na shiga na ga halin da take ciki, hankalina a tashe yake shiyasa ban kira ki ba sai yanzu da na samu sukuni; na ɗauki waya kuma sai ga naki kiran,
bari in yi sallah kar lokaci ya ci gaba da ƙure wa."

"To Shikenan, idan ta farka don Allah ki kira Ni."

Amsa mata tayi sannan suka yi sallama ta kashe wayan,
Miƙewa Ammee tayi ta shiga toilet ɗin ɗakin, alwala ta ɗaura sannan ta fito ta fita cikin ɗakin, ɗakin da ke kusa da su ta leƙa ganin da mutane sai ta shiga ta ari sallaya ta dawo, mayafin ta ta gyara tayi rolling ɗin sa sannan ta kabbara sallan,
After ta idar ta zauna doguwar azkar, ta jima tana zikiri daga baya ta soma addu'ar nema wa Maryamu sauƙi wurin Allah, domin har ga Allah yarinyar tana bata matuƙar tausayi,
Ta jima tana addu'a before ta miƙe ta mayar musu da sallayan, sannan ta zauna ta tasa Maryamun a gaba tana kallonta, ga shi babu halin barin wurin balle ta koma gida ta nema mata abun da zata ci, ita kanta yunwan take ji sosai, shiyasa ta ɗauki waya ta kira driver ta tambaye sa, "ko su Aakifah suna nan basu tafi makaranta ba?"

Ya sanar mata, "tun safe yakai su."

Haka nan ta sauke wayan cike da damuwa, sai kuma ta sauya shawara ta sake kiransa, "ka zo yanzu ka ɗauke Ni ka mayar dani gida."

"To ranki ya daɗe." Ya amsa mata cikin girmamawa

Tana ajiye wayan ta ci gaba da zama tana kallon Maryamu, a tunanin ta zata iya farkawa ma, amma har driver ya zo bata farka ba, shiyasa ta bi shi suka koma gida, cikin sauri-sauri ta haɗa breakfast ɗin a cikin basket; tunda su Aakifah sun yi komai, zuba wa tayi ta fito tace ma drivern, "ya koma da ita."
Allah yasa ma yau bata da aiki, da bata san ya zata yi ba,
Har ta koma Maryamu bata farka ba, shiyasa hankalin ta ya kwanta, zuba breakfast ɗin tayi ta ci nata sannan ta ajiye sauran; tabar ma Maryamu nata a food flakes.



_Finally an yi auren, sai mu jira mai zai faru kuma. Fatan alheri Masoya._
[11/03, 8:14 am] OumƊahirah نفيسة: 🌱🌱🌱🌱🌱

       *SHAREEF*
           _SexyBoy_
🌱🌱🌱🌱🌱


_Writer: Nafisat Isma'il Lawal_
_Wattpad: UmmuDahirah_

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝*



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

       *P.W.A✍️*





*DATA SHARE*

Call, message or whatsap  07065334256

*MTN*
500MB 150
1gb  280
2gb.  560 
3gb.   840
4gb.    1120
5gb      1400
6gb.     1700
Verlid for 30 days.












__________
*BOOK1*
_______________*FREE PAGE56*
_____Yau dai SHAREEF ya zama Ango already ya mallaki Haseena; kwanyansa ta faɗa. Allah -Allah yake yi ya samu damar da zai keɓe da Amaryansa, domin har ga Allah ba ya jin zai iya jira har wani lokaci, tunda ya mallake ta haka nan zai lallaɓa ta ya rika amsar haƙƙinsa since already ta zama nasa, amma kuma bai samu wannan damar ba a yau, sabida tunda suka tafi yin party ba su suka dawo ba sai gab da Magriba,
Koda suka dawo gida time ɗin duk an watse babu kowa a gidan,
Wanka suka soma yi dukkan su,
Hanif ya soma shirya wa ya fita zuwa masallaci tunda time yayi ana ƙoƙarin kabbara sallah,
Shi kuma SHAREEF sai da ya ɓata lokacin sa kamar yanda ya saba shiryawa, ya tsaya ƙalƙale jikin sa, domin so yake yi daga can ya wuce gidan su Haseena ya ganta, ko fita sai su yi inda zai samu ya huta, shiyasa sai farin ciki yake yi, wani farin yadi ya saka a jikinsa tamkar tissue, kayan sun halittu a jikinsa, bai saka hula ba sai yayi amfani da baƙin takalma sandal, agogon hannunsa kuma fari ne mai kyau da tsada, har wani daukar ido yake yi,
Bayan ya gama ya feshe ko'ina nasa da turarukan sa masu shegen ƙamshi da shiga rai,
Ya zura wayansa a aljihu ya fita ta ƙofan baya zuwa masjid, time ɗin ma an kusa idar wa, haka nan ya jona sallan ya gama sannan ya fito, direct cikin gida ya nufa ya dauki Motansa ya fice,
Wayansa ya ciro ya soma laluban numban Haseena, bayan ya kira ta babu jima wa tayi peaking, ɗaura wa yayi a kunne cike da nishaɗi ya kira sunan ta

Haseena na zaune a gefen gadon ta, fitowar ta kenan daga wanka tana tsane gashin ta da towel, sai ta ji kiran SHAREEF ɗin, hannu ta sanya ta ɗauka tayi peaking, jin ya kira sunan ta sai tayi murmushi tana cewa, "Ango ka sha ƙamshi."

Dariya ne ya kufce masa sabida jin abun da tace, "Wow! Sweetheart, by the way, ban ji daɗin kalman nan ba sai yanzu da naji shi a bakin ki, you didn't feel how happy I am, today I am very happy, kin fi kowa iya faɗa."

Murmushi tayi tana fari kamar yana gaban ta

"Ina kan hanya yanzu zan zo gidan ku, but ki shirya fa don fita zamu yi."

Ɗan waro ido tayi, tace, "ina zamu je?"

Dogon numfashi ya ja, kamar bazai yi magana ba sai ya rage murya kamar wani na jinsa, cikin wani irin shauƙi yace, "just zamu je hotel ne mu ɗan huta, kin san bazan iya jurewa ba dole yau in zama sabon Ango kamar yanda kike faɗa."

Gabanta ne ya faɗi, amma sai ta kanne cikin shagwaɓe murya tace, "dear, Ni yanzu ba na gida fa, mun tafi gidan Uncle ɗin mu, a can zamu kwana, sai dai ka bari idan mun dawo."

"Kina nufin bazan samu abun da nake so ba? And kuma ba ki sanar min ba?"

"I assume baza ka damu ba shi yasa, haba dear." Tayi maganar tana bubbuga ƙafa

"Shikenan, but ko in zo nan?" Yayi maganar kamar zai yi kuka, don wlh bai so hakan ba

"No, don ALLA Ni dai kar ka zo, already yanzu na zama naka, saurin me kake yi? Ka bari idan na dawo sai ka zo mu haɗu."

"Amma ban ji dadi ba sweetheart, any way zan iya jure wa since da yau da gobe duk ɗaya, amma ki faɗa min lokacin da za ki dawo please?"

Haseena tace, "sai yamma dear, cuz ka san tunda na dawo ban samu na je ba, shiyasa Abba yace mu bi su mu kwana."

"Ok, I'll go back home since I won't find what I'm looking for, we'll meet tomorrow and you should prepare, da zaran na dawo aiki by four zan zo in ɗauke ki mu fita, Please sweetheart ki tanadar min kanki da kyau yanda zan ji daɗin ki, You know I love you, tomorrow I want you to show me how much you love me."

Hmm kawai Haseena tace mishi, amma a ranta tana tunanin yanda za a yi ta kufce masa, amma ta san wayon da zata yi masa

Da haka suka ci gaba da wayan har sanda yace mata, "ya kawo gida, zai kira ta daga baya."

Daga nan ta ajiye wayan after ya kashe, shiryawa tayi cikin farar riga na barci har zuwa gwiwarta, mai kwalliyan less a gaban, rigan tana da kauri, hula ta sanya a kanta before ta ɗauki wayanta ta fita ko damuwa da yin Sallah bata yi ba, don yanzu gaba ɗaya ta dena sallah tunda ta hadu da su Nana, sosai rayuwar Haseena ta sauya fiye da baya.






🔆🔆🔆🔆🔆🔆🔆🔆

_____A ranan da daddare aka sallami Maryamu daga asibitin, since jikin ta da sauki sai dai haɗa mata magunguna suka yi kala-kala

Ammee ta ji dad'i sabida dama tunanin kwanan take yi a asibitin,
Kai tsaye gida suka wuce gaba ɗaya since su Aakifah suma duk suna asibitin a tare, tunda suka dawo makaranta driver ya kawo su,
Duk cikin su babu mai walwala sabida ganin yanayin jikin Maryamu, a hakan ma ta samu sauƙi babu abun da ke damun ta sai rashin ƙarfin jiki, da kuma damuwa da ta sanya wa ranta

Likitan da ya duba ta sai da ya sake gargaɗan ta, "ta kula da lafiyarta, ta dena sanya damuwa a ranta domin tana matsa wa kanta da tunani, kuma hakan zai iya haifar mata da babban matsala."
Faɗa sosai yayi mata tunda irin mutanen nan ne masu zafi da saurin faɗa in dai a kan lafiya ne, tunda ya faɗa mata, "in har ta ci gaba da saka damuwa ƙarshe ciwon zuciya zai same ta, since yanzu ma jinin ta ya soma hawa, akwai yiwuwar ta samu bugawar zuciya nan take a irin wannan tunanin da take sanya wa ranta."

Koda suka koma gida sai da Ammee ta zaunar da ita tayi mata nasiha da faɗa sosai, tace mata, "muddin ta naƙasa kanta a banza ne, tunda wanda take yi don shi bai san ma tana yi ba, in zata saki ranta ta koma rayuwarta normal; ta koya wa kanta rayuwa babu shi, ya fiye mata alkhairi, domin duk sanda ta samu ciwo shi babu ruwansa, bai ma san tana yi ba, sannan ma ita ta cuci kanta tunda hakan bazai ƙare ta da komai ba, shi yana can yana rayuwarsa cikin kwanciyar hankali, ita ta kwazzabi kanta ta hana kanta sukuni a kan ɗa namiji, haka zata ƙare rayuwarta cikin wahala tunda Maza haka suke babu tausayi a ransu, idan suka ƙilla ido a kan wata Macen; abu mai sauƙi ne su juya maka baya, bare ita da ba sonta yake yi ba, gwara ta yi wa kanta faɗa."

Kuka ta dinga yi tana sauraron faɗan Ammee ɗin

Daga karshe itama ta koma rarrashinta tana nuna mata muhimmancin lafiyarta, ko babu komai ta cire sa a ranta ko don lafiyarta, idan bata tsira da lafiyarta ba taya ya zata iya yaƙin ƙwato Mijinta? Sosai tayi mata nasiha ta bata shawarwari kala-kala yanda zata taimaki rayuwarta har ta samu sauƙi daga zuciyarta

Tabbas Maryamu ta ɗauki shawarwarin ta, kuma tayi ƙudirin amfani dasu koda hakan zai cutar da ita ne, daga yanzu dole ne ta haƙura da SHAREEF na har abada, domin wannan tana ganin shine ƙaddaran ta, ta sanya wa ranta haƙuri da juriya, dama tun farko ai bata sanshi ba, amma meyasa tayi rayuwarta normal? Sai yanzu da ta sanshi zata saka damuwa a ranta har take tunanin baza ta iya rayuwa ba?
A'a, ta dauki wannan ƙaddaranta ne, soyayyarsa ita ce babbar cuta a gare ta, kuma da sannu zata nemi maganin warakan

Don haka daga rana mai kama ta yau, ta sanya wa ranta baza ta sake zubar da hawayenta a kansa ba, ta yi wa kanta alƙawari, zata koma Jarumar ta wacce hawaye ke wuyan fita a idanunta, in har ta cika Mace tabbas sai ta nuna wa SHAREEF kuskuren sa, da sannu zata yi maganin matsalarta

Shi yasa tun daga ranan ta binne soyayyar SHAREEF a zuciyarta da iya ƙarfin ta, duk wani abun da zai kawo mata tunanin sa ta dena yi, ta fuskanci rayuwarta ɗoɗar babu wani gargada

Dawowa hutun makaranta, hakan ya taimake ta sosai, tunda ana dawowa Ammee ta je ta nema mata makarantar, dayake komai yanzu da kudi ake yi kamar yanda suka faɗa tun farko, shiyasa ba a sha wahala ba aka saka Maryamu ajin su Aakifah, tare da Yusaira da Maryamu SS 1C suke,
Ita kuma Aakifah tana SS 1A

Alhamdulillah makarantar ta yi wa Maryamu dad'i ba kaɗan ba, itama kamar makarantar da ta baro ne, tun safe sai ƙarfe biyar ake tashin su, har Islamiyya ake musu a can,
Tun dama Maryamu mai burin yin karatu ne, shiyasa bata sanya wasa ba a wannan lokacin, nan da nan ta soma gane wa ana tafiya da ita a class din, bare dukkan su aji ɗaya suke shiyasa suke zama suyi ta karatun idan sun dawo, wacce bata gane wani abu ba sai ɗaya ta tuna mata, da haka suke samun sauƙin karatun sosai,
Basu da lokacin kansu ma, da zaran asabar da Lahadi yayi zasu wuce makarantar haddan su, karfe daya in sun yi sallah a can suke dawowa, sai ya zamana yanzu ba sa samun lokacin zuwa koyon computer sai weekends ɗin idan sun dawo daga hadda

Haka rayuwa ta sauya ma Maryamu a ƙanƙanin lokaci, koma in ce ta sauya komai nata a ƙanƙanin lokaci,
Su Ammee sun ji dad'i ba kaɗan ba musamman yanda ta saki jikinta babu sauran wani abu kuma

Momy sai farin ciki, shiyasa jefi-jefi tana kiranta tayi ta bata shawaran abubuwan rayuwa

Kuma tana ɗauka gaskiya, tunda tana amfani da duk wasu shawara da zata bata, shiyasa yanzu take jin daɗin rayuwarta, SHAREEF kuwa da ƙarfi da yaji ta binne tunaninsa da soyayyarsa a cikin ƙasan zuciyarta, tamkar bata taɓa sanin halittar sa ba

Ana haka Abee ya dawo, sai dai bai jima ba ya koma, one week kawai yayi, don dama iyakan yawan hutun nasa kenan, in yayi wuta ne yayi wata ɗaya a gari, ba ya zama sosai

Ita kuma Ammee baza ta iya bin sa ba sabida aikin ta, sannan kuma da makarantar Yaranta ba ta son gantalin nan, ada tana bin shi sosai but tunda suka girma aka saka su a school ta aske wa kanta, ta zauna wuri ɗaya idan ya je ya dawo ya same ta a nan, dalilin da yasa ta nemi aiki kenan; sabida ragewa kai damuwa.






🔆🔆🔆🔆🔆🔆🔆🔆



_____Duk yanda SHAREEF ya so ya angwance da Haseena, abun ya faskara, domin ta ƙi ba shi haɗin kai, yayi nacin but ya hakura tunda ba ya son ɓacin ranta ko kusa, kullum sai sun fita tare sun je Hotel, a can yake hutawar sa, duk yanda ya so yayi mata wayon ya kasa, har fushi yayi da ita ya nuna, "ba ta ƙaunarsa, da tana sonshi baza ta ƙi abun da yake so ba, ta san tsawon lokaci abun da yake jira kenan, amma kuma yanzu gudun sa take yi."

Sai tace mishi, "ita bata shirya ba gaskiya, kuma tsoron ta kar ta samu ciki ne bayan tana tsaka da karatun ta."

Riƙo ta yayi ya ƙara manna ta da jikinsa, cikin sigan rarrashi yake ce mata, "haba Haseena, wanne ciki kuma don kawai za ki bani farin ciki? Kuma idan ma cikin ne ai abun farin ne, ko dai kin dena sona ne? Gaba daya kin sauya kamar ba Haseenan da na sani ba, Na san kin fi Ni bukatar wannan abun, amma yanzu guduna kike yi, kin fi son na mutu ne bayan kin san halin da nake ciki? Please sweetheart help me sau ɗaya fa kacal zan yi, bazan ba ki wahala ba i promise you."

Noƙewa tayi tace, "no Ni dai a'a, Please tashi mu koma gida ka ga dare yana yi, gaskiya bazan iya barin ka ba cus ba na son na samu ciki, after all nayi ma Abba alƙawari kuma daga baya ya zo ya ga ba haka ba, in fact ma yace min in dena fita gudun samun matsala."

Shiru SHAREEF yayi ya rasa ma abun yi, amma sai bai ce komai ba ya miƙe ya mayar da kayansa yace, "ta tashi su je."

Itama tashi tayi ta mayar da nata kayan tare da ɗaukar gyalen ta ta yafa, ta dauki jakarta ta bi bayansa sabida har ya fice, ko kusa bata damu da yanda ya nuna ba, amma don ta nuna mishi kamar ta damu, bayan sun shiga Mota sai ta soma ba shi hakuri har da ƙwallan ta

"Is ok, yanda kike so hakan zan yi, amma idan na mutu Haseena ke kika kashe Ni, ban san meyasa kike son canza min ba, akwai hanyoyi da dama da zamu bi wanda baza ki ɗauki ciki ba, duk hakurin nan da nayi ba kya gani ko?"
Ya kare maganar yana kallon fuskarta kamar zai yi kuka

Hannunta ta daura a saman cinyansa tana mai langaɓe kanta, "I'm sorry dear, Kayi hakuri ba a son raina bane, but kwana nawa ne ya rage zan gama karatun wai? Lokaci fa gudu yake yi please ka kwantar da hankalin ka don Allah."

Bai yi magana ba har ya kaita gida ya dire ta,
Sai dai dole ya saki face ɗin sa sabida yanda ta dame shi har da kukan ta wai, "ba ta son ganin sa a haka."

Shi dai ya rasa yanda zai yi haka nan ya biye mata ya wuce gida abun sa,
Tun daga ranan ya dena ma fitan da ita tunda ba ya samun biyan buƙata, ko sun fita karshe wahala yake sha, domin har ciwo sai da yayi a ɗan kwanakin nan, ya ƙwallafa rai a kan abu amma ya kasa samu, ba ya son ya ɗauki zafi a kanta since ba ya son ɓacin ranta,
Tun yana ɓoye wa Hanif dole ya sanar masa halin da yake ciki

Hanif yayi mamakin abun da Haseena take yi wa SHAREEF, amma gani yake yi son da yake nuna mata ne yasa yake biye mata take yin duk abun da take so, to meye amfanin soyayyar da kuma auren in har baza ta cire shi a wannan ƙangin da yake ciki ba?
Shi yasa ya sanar mishi, "shi fa yana ganin kamar Haseena hankalin ta ya soma barin wurin sa, yakamata su zauna su fuskanci juna idan ba haka ba zai iya halaka kansa."

SHAREEF ya kasa cewa komai don bai san me zai ce ba, domin shi kaɗai yasan iya azabtuwar da yake yi, ji yake yi kamar bazai kai gobe ba in har bai samu abun da yake so ba, amma ya zai yi? Har ga Allah yana sonta ba ya son ɓacin ranta, tun farko shi ya nace mata ya lallaɓa ta har ta amince suka yi auren, ya san idan ya matsa mata kamar ya cuce ta ne

"Ni ga shawara Bro in har baza ka bi wannan hanyar ba, mai zai hana tunda ba ita kaɗai bace Matarka; ka koma wurin Maryam domin biyan buƙatar ka, dama ai gida biyu maganin gobara ne, tunda dama ta ƙi sai ka koma hagu."

Sai da gaban SHAREEF ya buga sabida jin zantukan Hanif, shi har ga Allah ya manta da shafin yarinyar can, tab ɗijam! Tashin hankali kenan, mai zai faru idan Haseena ta gane yana da wata Matar? Tabbas akwai aiki a gabansa kenan

A tunanin Hanif yayi shiru ne yana sauraron sa, shiyasa sai ya ƙara gyara zama sabida son ya samu galaba a kansa, "Ni na san baka son yarinyar, amma mene ne amfanin ta? A irin wannan halin da kake ciki zaka iya samun solution Bro; ba tare da ka ɓata wa ƴar gaban goshin ka rai ba, Maryam zata iya ɗauke nauyin ka, zaka iya mu'amala da ita ba wai dole sai kana sonta ba, zaka iya biyan buƙatarka da ace ka cutar da kanka, kayi tunani Bro, itama Matarka ce halak malak".
[12/03, 9:19 am] OumƊahirah نفيسة: 🌱🌱🌱🌱🌱

       *SHAREEF*
           _SexyBoy_
🌱🌱🌱🌱🌱


_Writer: Nafisat Isma'il Lawal_
_Wattpad: UmmuDahirah_

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝*



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

       *P.W.A✍️*





*DATA SHARE*

Call, message or whatsap  07065334256

*MTN*
500MB 150
1gb  280
2gb.  560 
3gb.   840
4gb.    1120
5gb      1400
6gb.     1700
Verlid for 30 days.












__________
*BOOK1*
_______________*FREE PAGE57*
_____Wani kallo SHAREEF yake watsa mishi tun soma maganar nasa, tuni ya ɗaure fuskarsa zuciyarsa na tafarfasa da jin kalaman Hanif ɗin, "lallai baka da hankali Hanif, Ni kake nufi zan nemi wannan Jahilar yarinyar baƙauyiya sabida in kau da sha'awata? That will never be possible, because I was stronger than that girl forever, bazan taɓa neman alfarma a wurin wannan ƙasƙantacciyar yarinyar ba, don't do this to me again or you will see my anger again a second time, zan maka abun da baka taɓa tunani ba."
Ya ja tsaki ransa a ɓace yana miƙe wa yabar mishi ɗakin ma


Yayinda Hanif kuwa murmushi yayi yana shafa gemun sa, ko kusa maganar SHAREEF ɗin bai ba shi haushi ba, sai ma taɓe baki da yayi a ransa yana cewa, "akwai ranan ƙin dillaci."
Sai ya ɗage kafaɗa alamun bai damu ba yana mai miƙe wa tare da ajiye wayansa, ya nufi hanyar toilet ya shige.

          Wasa-wasa har hutun su Haseena ya ƙare ta koma school; SHAREEF bai samu abun da yake so ba, amma ya ya iya? Soyayyarta ta rinjayi duk wani abu,
But ya saka a ransa da sannu dole ne ya shawo kanta, ko bai yi nasara yanzu ba zai yi wani lokaci.
***

_____Yau da gobe rayuwa ta ɗaura ta ci gaba da tafiya kamar yadda ta saba, kwanaki na shuɗewa haka ma satikai, yayinda aka ɗaura watanni a kai

Kuma har wannan lokacin soyayyar SHAREEF da Haseena bai canza ba, tun tafiyarta bai samu ya je wurin ta ba, duk da yana ta mata mitan ta ba shi time but ta ƙi, ya lallaɓa ta har ya gaji, shiyasa ya yanke hukuncin zuwan mata a bazata,
Bai samu matsala wurin Iyayensa ba tunda yace musu, "zai je duba Haseena ne."
Ganin Matarsa ce babu wanda ya hana sa, iyakan jan masa kunne da Dady yayi a kan, "bazai riƙa zirya zuwa wurin ta a duk sanda ya so ba, don haka yasan da sani tun wuri dole ya riƙa sanin abun da yakamata, koda Matarsa ce bazai riƙa ziryan zuwa wurin ta a kai- a kai ba."

Shi dai tunda sun bar shi a murnan sa,
Shi yasa ya sanya rana, on Friday ya tafi, since zai dawo Sunday saboda aiki

While Hanif kuma ya ci gaba da kula da companin

Dady kuma shi yake zuwa Abuja idan hakan ta taso, ko shi ko su Mahmud tunda aikin yayi nisa yanzu sosai, gadan -gadan ake yi tunda akwai kuɗi, don ma companin yana da girma ne, ko kwata a yanzu dai ba a yi ba,
Alhamdulillah suna jin daɗin aikin har yanzu babu wata matsala,
Kuma har wannan lokacin suna nan suna neman hujjar da zasu kama su Alh Inuwa sabida ƙona musu kaya da suka yi,
Yayinda su Alh Inuwa sun ƙi barin kowanne kafa domin cin galaba a kansu, sosai suke takun-saƙa yanzu da su SHAREEF, ko magana ba sa yi idan sun haɗu a Abuja, dariya ma su Honourable Ja'e suke mishi don sun mayar dashi bai san ma abun da yake yi ba, tunda sun san sun toshe duk wata kafa da zai samu wata hujja bare ya ɗauki mataki a kansu

Amma SHAREEF ya ƙi haƙura, a ganin sa dole ya ci nasara a kansu, bazai taɓa yafe musu a kan abun da suka yi mishi ba, sai ya ɗauki fansa, SHAREEF akwai kafiya bare irin wannan babban laifi da aka yi mishi, ba zai ɗauki faɗuwa ba.




      🔆🔆🔆🔆🔆🔆🔆

_____Fannin Amra rayuwa ta soma sauya musu sosai, tun sanda ta soma amsar albashi ta mayar da ƙanninta makaranta na boko dana islamiyyar, a yanzu babu abun da ke gagaran su, sun fi ƙarfin komai, Alhamdulillah sai godiyar Allah suke yi, wurin aikin ta ma babu wata matsala tana gunadarwa cikin kwanciyar hankali; musamman yanda Hanif yake jin daɗin aikin ta, don har wani sabo suka yi a yanzu, duk da ita tana ja da baya sosai dashi, kasancewar ta Mace mai kamun kai, bata taɓa kai kanta inda Allah bai kaita ba, tana girmama Hanif matuƙa tamkar mahaifinta, domin gani take yi ya gama mata komai wlh, musamman a albashin ta na farko har ƙara mata kuɗi yayi kyauta,
Ya faɗa mata, "ta kawar da matsalolin gabanta since ta sanar mishi halin da suke ciki."

A lokacin ta ƙi amsa, amma sai da ya tilasta ta, har hawayen dad'i sai da tayi, tayi ta masa godiya har da duƙa masa

Sai ya nuna mata ɓacin ransa yana cewa, "kar ta ƙara duƙa mishi daga yanzu, duk abun da zai yi mata yayi mata ne don Allah."

Tabbas ta yarda, domin lokaci guda ta fahimci wane ne Hanif? Matuƙa yana da sauƙin kai da son mutane, Mutum ne mai kirki fiye da ɗan uwansa, tun bata jima da soma aiki ba ta kula da haka, tana mamakin yanda halin su ya bambanta da SHAREEF, sabida yanda shi yake mu'amalan sa alamun yana da girman kai da nuna isa, kowa ba kowa bane a wurin sa, bambancin halayya ne kawai a tsakanin su, a farko ma da ta fara ganin SHAREEF a zaton ta Hanif ne, sai daga baya ta bambance su since SHAREEF ya fi hasken fata, sannan a halin sa ko fara'a ma bai dashi bare yayi wasa da ma'aikatan

Ita a yanzu matsalar da yake damun ta bai wuce Jabir bane, ɗan uwanta da yake damun ta matuƙa, ya takurawa rayuwarta sosai, 
Duk yanda Mama ta so ta ɗauki mataki a kansa abun ya faskara, ga shi Mahaifinsa ba ya ganin laifin sa, ko takai ƙara cin mata mutunci yake yi yace mata, "tana son yin ma ɗanshi sharri."

Abun dai sai gaba-gaba yake yi ya takura wa Amra, shiyasa yanzu kwata-kwata bata da sukuni a ɗan kwanakin nan, sauƙin ta ɗaya ma bata zama a gida, dalilin da yasa kenan da duku-duku zaka ga tabar gidan ta wuce wurin aiki

Har Hanif yana mata ƙorafi yace, "wai kwana biyu tana riga su zuwa. Sai kace a companin take kwana?"

Ita dai dayake tasan matsalarta ba ta iya ce mishi komai sai murmushi,
Bai san cewa akwai dalili ba, hakan ne yasa ko sun tashi ta dena koma wa gidan, takan kai Magriba a ma'aikatan kafin ta tafi, lokacin kowa ya gama tafiya sannan itama take tafiya, su Hanif tun biyar zasu wuce amma ita baza ta tafi ba, saboda tasan tana komawa zata ga Jabir, amma in ta koma gida da duhun Magriba ba ta ganin sa

Mama tayi mata faɗa amma ta ƙi ji, don a ganin ta hakan shine maslaha gwara ta dawo da Magriba tunda baza ta haɗu dashi ba

Shi yasa yau ma tun ƙarfe biyar Hanif ya sallame ta,
Amma sai ta zagaya cikin ma'aikatan; ta ƙi tafiya har kusan shida da rabi, sannan ta fito ta samu abun hawa ya wuce da ita gida, suna zuwa lungun gidan su kamar yanda ta saba sauka, ta sauka ta miƙa mishi kuɗin sa sannan ta nufi gidan su, sai sauri take yi kamar zata tashi sama tunda har an soma kiraye-kirayen sallah,
Gab da zata shige gidan su; sai ta ji an cafko ta an dawo da ita baya kamar zata zube, amma sai jinta tayi cikin jikin Mutum babu zato,
Baki ta buɗe da nufin yin ihu sabida tsananin tsoratan da tayi,
But sai ta ji an rufe mata bakin ana faɗin

"Shiiii! Don uwarki Ni ne."

Take kuwa ta gane mai muryan, shiyasa nan da nan jikinta ya soma rawa kamar mazari, ta soma ƙoƙarin ƙwace kanta amma inaa; ya fi ƙarfin ta,
Kiciniya suka soma yi

Shi kuma sai ya bushe da dariya yana cewa, "shegiya ƴar shila, Ni za ki gwada wa ƙarfi ko? Wato saboda Ni kike ƙin dawowa gida sai kin kai dare? Ko kuma wani cikan kika samu a can yake danne ki kika guje Ni? Yo dama na san ai sai haka babu wani aiki da kike yi, yawon banzanki kike zuwa, amma Ni kin hana Ni na shana da wannan jikin naki mai yalwan albarka."
Ya ƙare yana tatse ta tare da ƙoƙarin ɗaura hannunsa a ƙirjinta

Kuka ta fashe dashi duk da muryanta ba ya fita, da sauri ta sanya hannunta tana riƙe nashi, jikinta sai faman rawa yake yi

Shi kuma sai ya soma yunkurin saɓa ta zai bar wurin da ita, inda har lokacin ya ƙi sakin bakinta

Amma ina Amra ta ƙi yarda, duk da ya fi ƙarfin ta but ta hana faruwar hakan, illa ma kiciniyar fincike jikinta da ta soma yi gaba ɗaya ta ruɗe sai fitar da ruwan hawaye take yi, ga ba bakin magana, tattakura tayi ta dinga yakushin shi a hannu ta kafe sosai ta ƙi bari ya ɗauke ta

Ganin haka sai ya gaura mata mari cikin zafin yakushin da tayi masa, "dan ubanki Ni za ki ji wa ciwo? Ai kuwa zan ga uban da zai ƙwace ki."
Hannu yasa dukka biyun ya kama ta da karfin tsiya ya saɓa ta a bayansa, sai ya nufi hanyar barin wurin yana huci

Nan ta sake rikice wa ta saka kuka tana yarfe ƙafafu da nufin sauka a jikinsa, Allah ya bata Sa'a ta zamo ƙasa but ya riƙe ta gam ya ƙi sakin ta sai ƙoƙarin shi na sake ɗaukar ta yake yi,
Ita kuma ta ƙi yarda kuka take yi sosai tana roƙon sa alamun ya sake ta

"Wlh sai na ci ubanki in ba ki min shiru ba, yau sai na kawar da kwaɗayi na a kan ki ko kina so ko ba kya so."
Take ya ja Hijabin ta ya cire sa da ƙarfin gaske, haka ya soma ƙoƙarin keta mata mutunci da karfi da yaji, duk ya yamutsa ta ya matse ta gam a jikinsa

Ita ko baiwar Allah kuka kawai take yi kamar ranta zai fita, takalmanta da Jakanta gaba ɗaya sun yi gefe, iya galabaita ta galabaita a hannunsa but duk da haka ta ƙi haƙura da kiciniyar ƙwacewa, a ranta addu'a take yi Allah ya kawo mata ɗauki, sai dukan sa take yi amma ina bai saurara mata ba, har rigan ta sai da ya yaga shi gida biyu gaba ɗaya albarkatun ƙirjin ta suka bayyana a idanunsa. Wani irin kuka ta saka mishi tana ƙoƙarin zame wa ƙasa

Amma sai ya tallabo ta jikinsa yana sambatu da ƙwaƙume ta, sai famar jagula ta yake yi kamar wani zautacce, faɗi yake yi, "ka ga ƴar tselan ƴa zata yi min tsakiyar da ba ruwa, wlh bazan taɓa barin ki ba, kaii! Ashe haka kike da kaya iya kaya amma kike min mugun fata?"
Haka ya dinga sambatu yana lashe ta kamar maye, tuni ya sake cafko boobs ɗin ta yakai musu damƙa cikin mugunta da fitan hayyaci, don a lokacin ma ya rigada ya manta a inda yake tsaban Jaraba da son kaiwa inda yake buqata

Yayinda Amra kuwa a time ɗin itama bata san inda kanta yake ba, tsananin tashin hankali da gigicewa yasa ta sume lokaci guda saboda ta kasa ɗaukar abun da ke shirin faruwa da ita.





🔆🔆🔆🔆🔆🔆🔆🔆


_____ *AUSTRALIA*
        *SYDNEY*
Da misalin ƙarfe goma na dare SHAREEF ya isa kofar gidan Haseena, a lokacin da ya isa ya so ya ɗauki waya ya kira ta, but yana taɓa ƙofan gate ɗin sai ya ga a buɗe yake, hakan ne yasa ya zura kansa ciki ba tare da tunanin komai ba, sai ya mayar da wayan cikin aljihu ya tunkari cikin gidan, zuciyarsa cike da farin cikin tozali da muradin ransa,
A bakin ƙofan shiga Falon ya tsaya, ya sanya zara-zaran hannunsa da nufin bude wa, but sai dai nan a rashin Sa'a kamar an sanya lock, hakan ne yasa ya ɗan yamutsa face ɗin sa, ya so har ya shiga ciki ba tare da ta san da zuwan sa ba sai dai ta sha mamaki,
Nocking ya soma yi a hankali while hannunsa ɗaya cikin aljihu, yayinda ya rataya Jakarsa a kafaɗa,
Shiru-shiru ba a buɗe masa ba sai ya ƙara gyara tsayuwar sa tare da kai hannu ya ci gaba da yin nocking ɗin, daga ƙarshe kuma ya koma buga door bell sabida jin shiru har ya soma gajiya,
Guntun tsaki ya ja tare da ciro wayansa,
Har ya soma lalubo numban ta sai ya ji kamar ana ƙoƙarin buɗe masa; at the same time ana faɗin,

"Who is there at the door?"

Jin wata murya daban bana Haseena ba, hakan ne yasa ya ƙi amsa wa sai yayi shiru yana tsira idanunsa a wurin,
Few seconds aka buɗe ƙofan; Nana ta bayyana a gabansa yayinda idanuwansa suka shige cikin nata,
Kallon kallo suka soma yi wa juna while shi SHAREEF tuni ya bi jikinta da kallo da wani irin yanayi da tuni mood ɗin sa ya sauya

Tana tsaye ne riƙe da ƙofan daga ita sai ɗaurin ƙirji, farin towel ne ƙal a jikinta ta ɗaura; wanda ya rufe mata saman ƙirjinta da cikinta, but gaba ɗaya santala-santalan cinyoyinta a waje suke, haka ma gashin kanta wanda ta baza shi har kafaɗun ta na attachment mai ruwan goro da style ɗin ja a ciki,
Kasancewar Nana ta taɓa ganin sa sau ɗaya duk da a ɗan nesa ne, ba sanin ƙurilla tayi masa ba, amma sai da gabanta ya faɗi haɗa idanun da suka yi, ko ba a faɗa mata ba ta tabbatar wannan kyakkyawar saurayin da ke gabanta shi ne Boyfriend ɗin Haseena

Yayinda a wannan lokacin SHAREEF shi kuma mamakin ta yake yi, musamman kallon da yake sauke mata a karon farko a kuma kallon farko zuciyarsa sai da ta hautsine sabida ganin ta, kallo ɗaya da yayi mata ya fahimci wace ce ita, idanunta da suke a tsaitsaye a buɗe sun fallasa mishi ba ƙaramar ƴar duniya bace, bare yanda ya ga bakin ta da hancin ta an zura ɗinkunne, idanun nan sun sha eyelashes duk da babu MakeUp a face ɗin ta, hannayenta ya bi da kallo waɗanda suka sha zobuna ga zaƙo-zaƙon ƙumbuna, sai ta fito sak a karuwarta irin tantiran ƴan barikin nan waɗanda idanuwansu a buɗe suke

Kamar yanda ya kasa yin magana yana bin ta da kallon ƙurilla, haka itama ta kasa furta kalma ko ɗaya illa bin beauty face ɗin sa da kallo da take yi, a ranta tana ayyana abubuwa da dama duk da ba ƙamarin kwarjini yayi mata ba



Muryan Haseena ne ya ratsa kunnuwan su ya katse musu kallon da suke aikawa juna, daga can ciki tana zaune a kan sofa itama babu kayan a jikinta, sai yaloluwar jan vest da bai rufe mata komai ba, jin shirun Nanan shiyasa take furta, "Baby, wai lafiya? Wane ne a wurin?".
       


Ubanki ne 🙊😳😂 in ji Ni fa.
[12/03, 6:49 pm] OumƊahirah نفيسة: 🌱🌱🌱🌱🌱

       *SHAREEF*
           _SexyBoy_
🌱🌱🌱🌱🌱


_Writer: Nafisat Isma'il Lawal_
_Wattpad: UmmuDahirah_

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝*



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

       *P.W.A✍️*





*DATA SHARE*

Call, message or whatsap  07065334256

*MTN*
500MB 150
1gb  280
2gb.  560 
3gb.   840
4gb.    1120
5gb      1400
6gb.     1700
Verlid for 30 days.












__________
*BOOK1*
_______________*FREE PAGE58*
_____Jin muryan Haseena yasa shi ɗan motsa wa yana ɗauke idanunsa da kallon cikin Falon; duk da ba ya hango ciki, yayinda ya soma yatsina face ɗin sa sabida tsananin ƙyama da ƙazanta da Nanan ta ba shi, ya ƙi yin magana har a lokacin bare yayi tunanin shiga ciki

While Nana kuma sai ta matsa mishi a hanya tana yalwata face ɗin ta a nan take da shu'umin murmushin ta, kasancewar ta ƴar duniya tuni ta washe face ɗin ta tana furta, "welcome, you can come inside." she finished talking looking at him, sai kuma ta saki ƙofan and went inside saying to Haseena, "Your guest has come."

In a surprise Haseena take kallonta, sai dai bata kai ga magana ba suka haɗa idanu da SHAREEF da ya shigo cikin Falon, wani irin zabura tayi nan take sai ga ta a miƙe ta waro ido a kansa,
In a short time, her body began to tremble because of the way he looked at her; mai kama da tuhuma gami da zallan mamakin ta

Ita kuma Nana ganin kallon da suke yi wa juna, ga kuma yadda Haseena ta ruɗe lokaci guda, shiyasa ta katse yanayin nasu da faɗin, "Come in and sit down, and stay here."
Tayi maganar da kallon SHAREEF again,
Sai kuma ta kalli Haseena, ta sakar mata wani irin kallo mai ma'anoni da dama, before ta sake faɗin, "Babe zan wuce, since kina da baƙo, zamu yi waya."
Daga haka ta wuce bata jira cewarta ba ta shige bedroom ɗin ta

Yayinda Haseena ta kasa kataɓus a wurin, har yanzu tana tsaye idanunta a kan SHAREEF da ya kafa mata nashi idanun shima ya ƙi motsa wa, sai dai eyes ɗin sa sun soma juye wa sabida ɓacin ran da ya kawo mishi cafka in a short time. Take ta sauke kai ƙasa ta kasa haɗa ido dashi; tana tsaye babu inda jikinta ba ya rawa, har wani zufa ne ya soma tsatstsafo mata a face ɗin ta,
Ganin good two minutes ya wuce bai motsa ba, shiyasa tayi ƙarfin halin sake ɗago kai tana kallonsa, sai ta sakar mishi murmushi cikin yanayin ruɗe wa tace, "SHAREEF..." Sai kuma tayi saurin gimtse bakin ta, cikin in-ina ta sake buɗe bakin a karo na biyu tace, "dear, ka zo.. ka zauna mana, meyasa baka faɗa min zaka zo ba?"

Idanunsa ya ɗaga yana sauke su a kan Nana da ta fito a yanzu ta saka kaya, ta sanya mini-skrit tare da guntun riga ko cibiyar ta bai rufe ba

Itama sai Haseenan; ta bi wurin da yake kallo da idanunta tana mai haɗiyar yawu sabida yanayin halin da ta shiga

Nana kuwa riƙe da wayanta a hannu ta nufi wurin Haseenan, tana murmusawa tare da rungumo ta jikinta, tayi mata kissing a gefe da gefen face ɗin ta before ta janye jikinta tace, "bye babe, sai mun yi waya, take care."

Ɗakyar Haseena ta iya amsa mata bayan ta ɗaura yaƙen murmushi a kan face ɗin ta,
Tana kallonta har ta fice sannan ta nufi wurin SHAREEF ɗin, cikin ƙarfin hali da ƙoƙarin ɓoye ruɗewan da ke tare da ita, tace, "dear wannan zuwan bazata haka?"

Sai lokacin ya buɗe baki yayi magana, cikin wani irin yanayi yana sauke mata wani kallo mai kama da tuhuma yace, "wannan wace ce? Aina kika samo ta?"

Murmushi tayi tace, "Ƙawata ce, Abokiyar karatuna ce."

"Abokiyar karatun ki? Wannan?"
Ya sake maganar yana nuna hanyar fita

Cikin dake wa tace, "Yeah of course, ko akwai wata matsalar ne?"

"Ni kike tambaya ko akwai wata matsalar ce? What is the reason why you are dating such a girl? kanki ɗaya kuwa Haseena?"

Hannunsa ta riƙe idanunta a kansa tace, "dear, mene ne aibun ta? Na ga dai ƙawata ce Abokiyar karatu na; babu wani abu kuma."

Janye hannunsa yayi yana ƙare mata kallo, tare da furta, "kina a haka cikin wannan shigan tare da wata, sannan itama tana zaune babu kaya a jikinta and kike ce min babu komai? Ko dama a gidan take kwana? Tare kuke kwana ne?"
Yayi maganar a ɗan zafafe

"To me kake nufi ne? Ina maganar ka ta dosa?"

shiru yayi ya kasa cewa komai, amma zuciyarsa tafarfasa take yi, sabida har ga Allah ransa zargin su ne ya kawo mishi mamaya, musamman yanda ya ga Nanan, exactly yanda ƴan maɗigo suke yi ne, har da sarƙan ƙafafu ya gani, daga ganin ta yar iska ce

"Ka zo ka zauna please, ka tsaya a tsaye kuma ka shawo hanya, ka zauna sai mu yi maganar." Tayi maganar cikin lallaɓa shi, don ba ta son ya ci gaba da zargin su bare ya san gaskiyar abin da ke wakana a tsakaninsu, in ba haka ba ta san ta kaɗe, sai buzun ta in asirin ta ya tonu

Ganin yanda take lallaɓa shi shiyasa ya nemi wuri ya zauna, but ya kasa hakura yace, "please sweetheart, Ni ban yarda da wannan yarinyar ba, ki rasa da wacce za ki yi mu'amala sai da ita? Ba kya ganin yanda take ne? Ina ɗan musulmi zai yi sha'awar haɗa hanya da irin wannan kafurar yarinyar da babu kyan gani?"

Wani iri Haseena ta ji a ranta sabida jin yanda yake muzanta Nana, shiyasa ta haɗe fuska tace, "Please SHAREEF, idan har baka san Mutum ba ka dena mishi mummunan zato, baka santa ba amma kake aibata ta haka, Nana bata da wani mugun hali, she's kind and helped me in my life, itama musulma ce da kake ganin ta haka, bata da wata aibu, please ka dena faɗan munanan maganganu a kanta bazan ji dad'i ba."

Shi kansa mamaki ne yasa shi bin ta da kallo saboda jin abun da take furta wa, "yanda kike kare ta kamar ta fi Ni matsayi nake tunani, and za ki raina min hankali ne; wannan ne zata zama musulma a hakan?"

"Yes of course, wlh musulma ce kuma asalin ta ƴar Nigeria ce, rayuwa ce kawai ta mayar da ita haka, sannan Ni ina tare da ita ne kawai don taimakona da take a kan karatu, ba wani abun ba."
Tafaɗa hakan tana ɗauke kanta

"But ba na son kuna tare gaskiya, in har kin ji maganata ki rabu da ita, bata yi min ba."
Yafaɗa cikin nuna isa da taƙamar sa

Kallonsa tayi, in few seconds kuma tace, "hakan kake so? Shikenan komai ya wuce, amma ban ji daɗin irin wannan zuwan da kake min ba, at least yakamata ka sanar min domin in tanadar maka wani abun ai."

Hannunsa ya sanya ya kamo nata yana tsare ta da ido, cikin sanyin murya yace, "sweetheart zuwan nawa ne ba kya so; ko kuma don ba ki shirya min wani abu bane?"

"No ba zuwan ka bane ba na so kaima ka sani, ba na son ka zo ban tarbe ka bane, kuma yanzu ba kasafai nake zama a nan ba ina kwana a hostel sabida karatu, yanzu idan ka zo baka same Ni ba ai bazan ji dad'i ba."

Murmushi yayi yana rungumo ta jikinsa, tare da furta, "kar ki damu bazan sake miki irin haka ba in har ba kya so, amma da laifin ki tunda na tambaye ki zan zo but kika ƙi yarda, Ni kuma kin san bazan iya jurewa tsawon lokaci ina da Mata a duniyar nan ba, sannan in zauna ina shan wahala, haba Haseena, ko tausayi na ba kya ji fa, gani nayi ke kin sauya gaba ɗaya komai bai dame ki ba, amma Ni kin bar Ni cikin wani hali cikin ciwo in rayu ko in mutu ko oho, wannan abun fa ba ƙare wa zai yi ba, sannan idan ma don Ciki kike tsoron mu kasance tare, zamu iya daukar mataki har sanda kike bukatar haihuwa."
Sai ya ja tsaiko tare da ƙara ƙanƙame hannunta idanunsa cikin nata, "alamu ya nuna kamar kin soma janye jikinki da Ni, ko in ce soyayyar da kike min ta soma raguwa, tunda har za ki iya hana Ni jin dad'in rayuwa, bayan kin san cewa a kullum da ƙishin abun nake kwana nake tashi cikin wani irin hali; but kin kasa tausaya min."
Sai ya sake marairaice fuska yana furta, "please help me sweetheart, don't let me die in this situation, I love you, I will do whatever you want, but for once let me enjoy my life."

Yanda ya rikice mata ta rasa yanda zata yi dashi, duk yanda ta so ta kufce masa ta hana shi abun da yake so, amma inaa; SHAREEF yayi nisa ba ya jin kira,
Tun a lokacin ya soma aika mata da zafafan kissing masu tsananin zautar da mutum, domin ya dauki ɗammaran dulmiyar da ita cikin tafkin ƙaunarsa da dole sai ta ba shi haɗin kai,
Ƙiri-ƙiri ya ƙi raga mata bare ya bata ƙofan da zata musa mishi,
Tun ba ta jin daɗin abun har ya kai ga tana amsar saƙonnin nasa masu tsaya wa a ran wanda ake mishi

Ganin wurin bazai mishi ba, nan take ya sure ta zuwa gado jikinsa sai faman rawa yake yi, yau SHAREEF ya samu abun da yake so, take nan ya afka mata da iya ƙarfin sa a zuwan zai buɗe sabuwar budurwa fitik,
Sai dai bai sha wahala ba wurin shige wa zuruf babu tsaiko, abun da ya ɗan so ya ruɗa shi kenan ya tsayar da abun da yake yi yana mai mamakin yanda ya shige tamkar inda aka saba shiga,
Wani ikon Allah, duk da SHAREEF bai taɓa sanin Mace ba, amma ya fahimci tabbas Haseena bai same ta da ainihin budurcin ta ba, to ina ya tafi?
Wannan tambayar ne ya ruɗa mishi ƙwaƙwalwa; lokaci guda ya soma ƙoƙarin janye jikinsa cikin tsananin tashin hankali da tunanin wani ya soma riga sa shiga gonan sa.
Tashin hankali! Haba, da sake kenan.



🔆🔆🔆🔆🔆🔆🔆🔆

_____Nana kuma da ta fita gidan a Motan ta, tana fita cikin gidan sai ta faka motan ta zauna tayi shiru tana tunani, yayinda take kaɗa hannayenta a jikin sitiyarin motan, face ɗin SHAREEF ne yake mata ƙawa a cikin idanunta, duk da ita ba ma'abociya sha'awar Maza bane, amma babu ƙarya ta ga kyawu da tsantsan haɗewa a wurin sa,
Wani murmushin gefen baki ta saki tana shafo kunnen ta, take ta soma jiyo maganganun su da suke furta wa, tsab ta gama jin komai har kushetan da SHAREEF ya gama yi,
Har a ranta ta ji babu dad'i amma kuma sabida jin Haseena na kare ta yasa ta bushe da dariya a fili ta furta, "This is your last chance, because it won't happen again."
Jin sun yi shiru sai nimfarfashin su da take ji, hakan ya tabbatar mata da abun da suke yi, wani irin kishi ne ya turniƙe ta, bata zata Haseena zata iya cin amanar ta ba har ta ƙetare maganar ta ba, tabbas ta yarda SHAREEF yana da wani babban matsayi a wurin Haseena ba tun yau ba, dole baza ta iya rabuwa da shi ba,
Amma ita tayi alƙawari dole sai ta raba tsakanin su, domin baza ta iya sharing Haseena da wanin ta ba, wanin ma namiji, baza ta yarda ba, wannan lokacin zata dauki mataki, time yayi da zata shigo da Haseena cikin ƙungiyar su, tabbas lokaci yayi,
Take ta tuƙa motanta tabar wurin a tsiyace kamar zata ƙona Motan sabida yadda ta bata wuta lokaci ɗaya wurin ya turniƙe da hayaƙi.

*Now the game has started, let's go into the story.*






..............................
_Free page ya zo ƙarshe da yardan Allah, ga mai buƙatar siya sai ya tura kuɗin sa. Nafisat Ismail 3194593808 First bank, shaidar biya a wannan numban 07065334256. Regular group 300, Complete document 400._

*Nagode Masoyana.*
A yi azumi lafiya.
12 March 2023.

