Ummi Tandama: ________________ »SIRADIN RAYUWA✠*@Takori* Da Karfe Shidda Na Yamma Agogon Garin Miami Dr. Al’ameen Bello Makarfi, ke kwance cikin sofa mai juyawa dama zuwa hagu, idanun shi a rufe suke tamkar mai barci, amma a zahiri ba barcin yake ba, shi kadai ya san hakikanin abin da ke damunsa. Alal hakika rigimar matar shi IHSAN ne ya ishe shi a yau. Shi kam tun barin sa kasar haihuwar shi bai sake waiwayar ta ba balle ya tuna ta da sunan zama na din-din-din ba. America, ta bude wani shafin rayuwa mai dimbin tarihi da nasarori a tare da shi, ta maida shi wane, ta zamo silar dukkanin nasarorinsa a rayuwa ta warkar da bakin cikin kuruciyar da ya zo Miami da shi ta kuma shafe rayuwar shi ta baya, ta wanke tsanar kan shi da yake a da can, shin a kan me zai bar ta? Sai dai wani bangaren na zuciyarshi sam, ya ki amince mai da hakan. Idan ya yi hakan ya tabbata hakkin yarinyar kadai na iya wargaza masa farin cikin da yake takamar ya samu a Miami; Shekaru goma kenan cif da rabuwarta da iyayenta, shi kuma goma sha biyar cif in har lissafin da yake daidai ne bai rage ba, sun turo ta karatu sun sarke da soyayyar da har ta kai su ga aure ba tare da sanin iyayen ko dayan su ba. Ta jure rashin soyayyar nan ta iyaye a tare da ita tsayin shekarun nan wadda ta fi komai dadi da muhimmanci ga dan adam, idan shi namiji ya iya ya jure, ita Ihsan mace ce, ya kuma tabbatar ta yi hakuri kan hakuri ba don komai ba sai don masifaffen son da take masa. To shi don me ba zai nemo mata wannan soyayyar ba, ko don albarkacin wadda take masa? Shi kansa ya san a yanzun zuciyarsa ta yi sanyi da takaicin kuruciyarsa ta gida. Tunanin Daddy din shi ya addabe shi, ko an harbe shi? Ko har yanzu yana kulle a kurkuku (Prison)? Zuciyarsa ke bijiro masa da cewa, yanzu ne ya dace ya je ya tallafi mahaifiyarsa da ‘yan uwansa duk da ya san a kowanne hali mahaifiyarsu za ta iya kula da su, kasancewarta mace mai dumbin arziki. Yana ganin yanzu ne ya dace Hajiyarsu ta huta da guminsa, shi a yanzu ya san Allah ya yi masa ludufi da nasibi ta kowanne fanni a rayuwa; Bar ta kasancewarsa mamallakin shahararren asibitin kwakwalwa wato “MERITIMEâ€? da ke cikin birnin Miami, hakan nan shi ne babban likita a sashen kwakwalwa (consultant) a babban asibitin garin Miami (Jackson Memorial) da ke Florida. Har ila yau, Dr. M.A.B (Senior lecturer) ne da ke daukar daliban “Medical Psychologyâ€? a jami’ar da ya yi karatu (University of Miami), kuma masani a kan duk wata larura da ta shafi kwakwalwa. Don haka kasar America ke ji da shi, suna lailayar shi da ruwan arziki kasar su na amfana da dumbin baiwa da fasaharshi. Baya ko tuna kasar shi ta haihuwa (Nigeria) balle iyayen shi da ya tafi da niyyar barin su har bada, don yana ganin ba abin da zai masu, ‘ya’ya irinsa ba abin bukata ba ne, don haka bashi da amfani a gare su. Ga ingantacciyar kauna da kulawa daga matarshi abin kaunar shi Ihsan, yalwataccen gida a Miami, motocin hawan da ko a U.S. sai wane da wane. Kenan duk wani buri da dan adam zai iya ciwa rayuwar duniya, ya samu. To amma zai so ya mutu ba tare da sanin halin da iyayen shi ke ciki ba? Ba tare da ya kara sa wani jinin shi a idanun shi ba? Bai sake sanin halin da kanwarsa SARATU-INTISAR ke ciki ba, shakikiyarsa kuma kanwarsa da ya NAKASTA? Mafarke-mafarken da yake na Daddy a dan tsukin kadai na tayar masa da hankali, ya kasa nutsuwa kwata-kwata wanda hakan ya janyo masa yi wa wani mara lafiya (Patient) rubutun magungunan da ba su dace da lalurarsa ba, ba don Ihsan ta lura ba da an yi mamakin shi M.A.B ne da wannan danyen aikin. To haka ko rubutu yake yana daburcewa ya rasa me zai rubuta? Gaba daya hankalinsa ya yi gida ya kuma tabbatar kwanciyar hankalinsa kadai ya bude ido ya gan shi a gida. Baya jin zai sake samun nutsuwa bai baro Turai haka nan ba. Anya ma kuwa babu hakkin Dady din shi a kan shi? Mutumin da ya wanzar da ran shi da lafiyar shi cikin wahala, domin nema masu farin ciki, anya ya cancanci hukuncin da ya yanke masa? Bar ta so da gatan da yake nuna masa throughout sauran kannensa to haka Hajiyarsa, ya tuno yadda a kullum take gaya masa ba ta son ya yi nisa da ita, ya fiye mata duk sauran ‘ya’ya taran da ta haifa a duniya! Sai ya ji kansa ya yi wani irin gingiringim, idanuwansa sun yi mai nauyi, baya ko iya bude su. Ya lumshe ido cikin wani sabon yanayi a tare da shi. Allah kadai ya san halin da zuciyarsa ke ciki. Ihsan ta karaso rike da tambulan mai garai-garai cike da danyar madarar shanu mai sanyi (fresh) wadda shan ta ya zamewa likita Ameenu lazim a duk yammaci, a gida ne ko ofis. Sanye take cikin fararen kayan wanka (bikini), gashin kanta ke digar da ruwa tabbacin daga wanka ta fito. Ganin yanayin da Al’ameen ke ciki sai ta ja dan karamin tebur da ke gabansa ta ajiye kofin. Sannu a hankali ta kwanta jikin Al’amin sannan ta marairaice kamar za ta yi kuka ta ce, “Ameenu isn’t this enough? America is not our motherlandâ€?. Don Allah mu koma gida…â€? Sai kuka. Shiru ya yi cikin tunani, shi kam bai san ma abin da zai ce mata ba ma. Zuwa gida? Ai shi ne mai cewa a je ba ita ba yanzun. Bai ce komai ba, baya ga dora hannu cikin gashin kanta, don in ta soma yi mai wannan rigimar ta “a dawo gida…â€? da kyar yake iya samun kanta. Hakika tana ba shi tausayi, dole su baro MIAMI a wannan watan. ***** 1 GA WATAN SAFAR (HIJRIYYAH) Jirgin American Airways ya sauke su a birnin Ikko da karfe tara daidai na safe. Sai da kowa ya fita amma Al’ameen da Ihsan ba su ko motsa daga “seatâ€? dinsu ba. Gaba dayansu jikkunan su sun yi sanyi, domin a take zazzafan zazzabi ya rufe Ihsan, ba su san da fuskokin da za su aro su dubi iyayensu ba. Sai da wata ma’aikaciyar jirgin ta yi masu magana cewa za a rufe jirgin, sannan ne Al’ameen ya tuna cewa shi fa namiji ne, ya rungume matarsa da hannunshi na dama a yayin da na hagun ke rike da ‘yar kyakkyawar jakarta ‘Japaneseâ€? a haka suka soma tako matattakalar jirgin cikin nutsuwa har suka taka kasarmu mai dimbin albarka. Dole idan ka kalle su sai ka maimaita su kuma yi bala’in ba ka sha’awa. Kwarjini da cikar zati irin na Al’ameen da ke sanye cikin edpensive Italian suit, kalar baki da ratsin fari sol sun taimaka ainun wurin kara fiddo ilhama da cikar zatin shi, ya saya kwayar idon shi cikin bakin dark-spaces da ganinsa dai ka ga bakon Ba’amurke. To haka itama Ihsan din tamkar aljana take don kyau, baby face gareta mai dauke da kayatattun idanu tare da kyakkyawan dogon karan hanci da gassun gira mai tsari. Yarinya ce ‘yar gajeriya mai jiki kuvul-kuvul, kamar na tarwada saboda tsabar hutu tamkar ba bakar fata ba, domin tun fil’azal ita brown ce, sai kuma zaman kasar sanyi da jin dadin samun gwarzon miji irin Al’ameen Bello, da suka kara wanke ta tas. Dr. M.A.B zai yi wuya ka fassara daga kabilar da ya fito a lokaci daya, kamannin shi na da ruda tunani da sanya shakku, bi-ma’ana (by appearance) ba za ka kira shi Bahaushe ba sam-sam duk da cewa ya fi son yin magana da harshen Hausa a kodayaushe fiye da duk wani harshe da ake magana da shi a duniya. Hakan nan ba za ka ce shi din Balarabe ba ne, domin baya da tarin nannadaddiyar suma irin tasu kullum kansa cikin saisaye yake, amma ya bar siririn saje a gefen fuskarshi abin nan da ake kira Man’s pride. Mutum ne dogo siriri, don tsayi har ya rankwafa, wanda mutane da dama ke (kuskuren tsammanin) cewa yanayi ne don kwalisa, amma Al’ameen Bello komai nashi natural ne babu artificial. Idanun shi abin so ne, ba ga mata kadai ba har maza ‘yan uwansa will not keep wishing they were like him (Ba za su bar fatan ina ma a ce sune shi ba). Idanuwa ne manya kuma lumsassu, tamkar kuma an diga masu zaiba har wani maiko-maiko suke. Bai kama da Turawan ma sam-sam shi dai kawai Al’Ameen ne, haka Allah ya yi sa. Da wuya ka karanci zuciyar Al’ameen Bello, ko matar shi ba ta iya gane wasu al’amuran shi. Mutum ne murdadde mai yin komai straight forward (kansa tsaye) ba tare da tunanin illar da abin zai haifar ba, mai tsayawa a kan mgana daya, ba kankanin abu ke sa shi canza ra’ayi ba. Kuma mutum mai tausayi da masifaffar kyauta. Ya sha sauka daga mota in ya ga wani a gefen titi yana jiran bus a Miami, ya kira shi ya danka mai mukullin ya ce, “Tafi.â€? Shi kuma ya sayi wata. Tun Ihsan na masifa har ta gaji ta kyale shi don ta lura abin a cikin jinin shi ne. Ita kanta ba karamar barna yake wa kayan ta ba wurin baiwa masu karamin karfi dake tareda su. Sau tari, tana kwance a mike ya kan dafa mata abinci, ya dauko ya kawo mata yana sanya mata a baki, yana mai lallashinta ta ci sosai. Cewa yake wannan hakkinshi ne ya ciyar da matarshi, tunda a Alkur’ani mai tsarki babu inda aka ce mace ta ciyar da mijinta hakan nan bai son mata suke wahala, domin su ne uwayen al’umma duk wata wahala a wuyan su take. Idan suna nakuda ji yake kamar ya taya su. In yana fada mata irin wannan kallon shi kawai take ta yi dariyarta mai isar ta ta ce wata rana zai daina ne, don yana ganin ba su da kowa ne a nan inda suke sai junansu. Shi wani irin mutum ne da bai bambancewa cikin mu’amalarshi da kowa, abin nufi, mai kudi da mara kudi, mace ko namiji. Dr. Al’ameen Bello kowa nasa ne. Don haka ya sha fama da mata iri-iri a zamanin karatunsa, daga Turawan zuwa ‘yan sauran kasashen duniya da karatu ya hada su. Ihsan A.A kadai Allah ya bai wa sa’ar koda yake zan iya cewa, Al’ameen ya auri Ihsan ne domin ceton ta daga masifar son shi da ta sanya kanta, amma ba wai don wani mashahurin so na Allah ko na Annabi ba. Ihsan Abubakar Argungu, ‘ya daya tal ga mataimakin Governor na (Central Bank of Nigeria), Dr. Abubakar Argungu. Iyayenta mazaunan Abuja ne na din-din-din duk da cewa dukkansu aiki ne ya kawo su a garin, daman an ce wai birnin Tarayyah ne. Kasancewar Ihsan ‘ya daya jal ga iyayenta ya sanya duk wani buri na Dr. Argungu da mahaifiyarta Ann Hathaway wadda ta kasance Kirista ‘yar uslin Birnin Gwari, akan Ihsan yake. Mahaifiyarta Ann ce mamallakiyar bankunan Savannah da ECOBANK da ake damawa dasu a halin yanzu a kowacce jiha ta Najeriya, don haka gaba da baya Ihsan ‘yar gata ce ta karshe gun iyayenta baya ga watsi da ta yi da su kan son Al’Ameen Bello. Iyayenta sun turo ta karatun medicine ne a University of Miami, inda ta hadu da Al’ameen, wanda a lokacin ke ba da lacca cikin makarantar bangaren masu karantar lafiyar kwakwalwar dan-adam. Tun daga wannan lokacin Ihsan ba ta kara nutsuwa ba sai da ta zamo friend din Aminu. A hankali a hankali ta yi amfani da hilarta wajen jan ra’ayinsa gare ta tana bayyana masa yadda take son shi wani zubin har tana kuka take rokon shi ya aure ta gudun kar ta sanya kanta cikin gurbatacciyar rayuwa. Ga Al’ameen mutum mai tsananin tausayin mace, tun ba in tana fidda mai hawaye ba, sai dai sam a lokacin bai da ra’ayin aure, tunda kuwa zai sada shi ne da gidan da ya baro baya ko son tunawa. Yaya ma za ai ya yi aure, ba tare da sani da yardar mahaifansa ba da baya da kamar su? Don haka ya rungumi Ihsan suka tsunduma watsewarsu ba tare da tunanin illar da hakan zai haifar ba. Wannan ya fi komai dadi ga Ihsan domin dama ita ba auren ne a gabanta ba, illa tana tsoron idan ta bijiro mai da irin soyayyar da ta zaba musun ba zai amince ba, kasancewarsa mutum mai tsananin kamewa daga barin jin dadin rayuwar Turai a ko’ina kuma a cikin kowanne hali ya sami kansa, duk zalamar yarinya kuwa haka za ta ga Aminu Bello ta kyale domin abin da ya kai shi kadai yasa a gaba. To itama Ihsan din kowa da ke tare da su ya yi mamakin yadda ta samu Ameenun haka a hannu, ba mamaki, domin an ce kowacce ‘ya mace da kissarta ake haifarta, hakan nan Ihsan tun tana mitsitsiyarta take koyan kissa gun uwarta har girmanta iri-iri ba wadda ba ta iya ba, don haka duk saurayin da ta kimsawa kanta sha’awarsa ta same shi ta gama kuma da kyar ne yake kubuta daga tarkonta. To haka shi ma Al’ameen, ta tabbatar sha’awarshi ya fi son shi yawa a tare da ita kamin su yi aure, sai dai a dan zaman da ta yi da shi ta koyi kaunarsa saboda wasu kualities nasa da ke burge ta da ba duk maza Allah ya mallakawa ba. Don haka ne ma duk wulakancin da yake mata in ya bushi iska ko ya yi sabuwar girlfriend take hakuri tana shanyewa, don ta tabbatarwa kanta tana samu nutsuwa 100% and beyond a tare da Al’ameen fiye da duk wasu maza da ta taba mu’amala da su gida da wajen. Hakan nan tana ganin Al’ameen ko a cikin maza daban ne wurin nuna kauna. Samun maza irin su a matsayin MIJI sai mai sa’ar gaske. Ba ta taba haduwa da namijin da ke gamsar da ita ba har ya kure ta kamar Al’ameen ba. Ba ta taba haduwa da namijin da ya san darajar diya mace kamar Al’ameen ba. Don haka ta kara manne masa ta like masa tare da kara zage damtse wurin nuna masa ingantacciyar kauna da kulawar da ta sa shi dole ya so ta, ta kuma shiga yakar macen duk da ta gani tare da shi ba tare da shi din ya sani ba ma. Ta kuma alkawartawa ranta, ruwa ko iska baya raba su. Daga baya ne Al’ameen ya tuna cewa shi fa Musulmi ne, da kuma irin horon da Daddy dinsu ya yi masu, wanda da a ce yana tare da shi, hakan ba zai taba faruwa da shi ba. Ya roki Allah ya yafe masa ya kuma nemi Ihsan da ta yi Istibra’i su yi aure, ita kuma ganin lokacin Aminun na sonta kamar me ta ce ba ta san wannan ba, jin hakan shi kuma ya fita harkarta kwata-kwata, ko a tunaninta kuma ko a mafarkinta a lokacin ba ta kawo Al’ameen zai iya rayuwa ba tare da ita ba. Ta kuma tabbatar gab yake da ya shafe ta kwata-kwata a babin rayuwarsa in har bata amince su yi auren ba, ta amince ta saduda cewa shi din mai ra’ayin kansa ne, don haka ba ta isa ta sashi ko ta hana shi ba. Suka yi auren su mai tsafta ba tare da sanin iyayen ko dayansu ba. Daga baya ne ita Ihsan ta aikawa Ann cewa ta yi aure da wani likita Al’ameen. A lokacin hanyoyin sadarwa basu yi kamarin da suka yi yanzu ba. Ann din ta aiko mata da zagin cin mutunci ta waya da e-mail kan don me ta auri Musulmi ba ta auri dan Addininta ba, bayan ta yi mata alkawarin muddin ta tashi aure Kirista za ta aura, don wai sun fi rikon aure. Shi kuma mahaifinta ya ce kwata-kwata ba ta kyauta musu ba ta dauke su ba a bakin komai ba tunda kuwa har za ta iya ta yi aure ba tare da sani da amincewarsu ba, don haka ta je Al’ameen din ya maye mata gurbinsu. To Ihsan ranta ya baci sosai da iyayenta a ganinta gata ta yi wa rayuwarta ai, domin shi kansa auren ai mutunci ne ko bature yana daraja aure, da dai ta ci gaba da gurbatacciyar rayuwar turai da babu komai cikinta sai lalacewa, kuma ba su yi mata uzuri da soyayyar da ta rinjaye ta ba sun manta an ce luv is overall, wato soyayya tana gaba da komai. Wannan ya faru shekaru uku da suka gabata, tun daga lokacin Ihsan ba ta kara waiwayarsu ba, duk da cewa daga baya su din sun neme ta amma ta share su, don tana ganin son Ameenu ya fiye mata komai, ko in ta sauraresun me za su yi mata? Za su hana ta aurensa ne? To gara ita, shi din ko sanar da su bai yi ba, tunda kuwa a lokacin ya riga ya shafe gida kwata-kwata daga kundin tarihinsa illa sabuwar rayuwar da ya gina a gaba. Sai suka hade abinsu suka dunkule junansu wuri guda suka bude sabon shafin rayuwa cike da soyayya mai ban sha’awa. Daga Al’ameen har Ihsan kowa na son Da, musamman ita Ihsan da take ganin haihuwa da Ameenu ne kadai zai dorar da dangantakarsu. Tana ganin in ta haihu da shi zai mallaka mata dukkan so da kaunarsa da har yanzu kwakwalwarta take gaya mata bata mallaki komai a ciki ba duk da cewa da wuya a karance shi, amma hakika ta san bata da dukkan so da kauna a zuciyarsa. Hana rantsuwa za ta iya cewa ‘yana son taâ€? kadai. Wannan ita ce matsala ta farko da suka fara cin karo da ita a rayuwar auren su, kuma in har suna da matsala a auran to wannan ce. Lokacin da Al’ameen ya soma complain (korafi) wai abortion (zubar da ciki) da ta-yi ta-yi ya shafi lafiyar mahaifarta, cikin kwafa kuma sai ya ce ko ciki har nawa ta barar oho. Da haka suka fara fada, ta ce ya san tana bare-baren cikin ai ya neme ta da watsewa, don ita tun farko ai aure ta ce su yi. Yadda ta lurra Al’ameen mutum ne mai masifar son yara, ko tafiya suke bisa hanya ya ga yaro sai ya tsaya ya dauke shi ya yi kissing ya ba shi choculate da baya rabo da saye cikin kantuna. Ranar da Ihsan ta yi nadamar aurenta da M.A.B shi ne ranar da ya ce da ita wai shi dama tun ranar da ya soma saninta ya yi mamakin maza nawa ta sani? Shi ba irin matar da ya so aure ba kenan a rayuwarsa, amma ya zai yi da kaddara? A wannan ranar ne Ihsan ta yi kuka wanda rabonta da shi tun na sallamar ta da iyayenta shekaru goma a baya. Kewar iyayenta ya zo mata. Ta tuna masifaffen gatan da take da shi a wurin iyayenta da yadda suke sonta, suke kula da ita, suke gudun duk wani bacin ranta. Yau ga namiji kwaya daya na yi mata yawo da hankali. Sai take tambayar kanta ko me Al’ameen ke takama da shi da yake gara ta haka? Ba ya takama da komai illa jarababben son da take masa. Ta tabbatar duk wani cin mutunci ma in da a gaban iyayenta take zai zo da sauki fiye da nan din da yake ganin ba ta da kowa sai shi. Sai dai ta kudurce a ranta koma me zai mata ko duka ne ba za ta taba rabuwa da shi ba. Daga baya Al’ameen da Ihsan duk sun amince ba hayaniyarsu ko tashin hankulansu ne za ya ba su haihuwa ba, illa ma ya rugurguza masu kyakkyawar rayuwar da suke ciki, ta so da fahimtar juna, sai suka dangana. Shi Al’ameen yana addu’a ita ko Ihsan Addinin nata ma gashi nan ne, sallah sai in ya takura mata za ta yi in baya nan ko a hadu a gaba. Tun daga wannan rigimar da suka yi Ihsan ta soma yi wa Ameenu korafi da koken su koma gida ta ga iyayenta ta kuma roki gafararsu, tunda shi ba ya son nasa. Shekaru bakwai ta yi tana karatu, shekarun su uku da aure kuma a cikin shekarun tana aiki a asibitin (Baptis Health) da ke South Florida, cikin birnin Miami matsayin karamar likitar zuciya (cardiologist) kuma kwararriya a fannin heart-transplantation Da fari hankalin Al’ameen ya tashi da wanann sabon abu ko ko ya ce rigima da Ihsan ta kinkimo mishi har ya dinga ganin bekenta, to amma shi ma da ya yi tunani mai kyau sai ya ji shi din ma ba abin da yake so irin dawowar, ya kuma bude ido ya gan shi a gaban Daddy din shi ya ga SARATU-INTISSAR din da ta sa shi barin gida, ko a wanne hali take yanzun? Yaya take gudanar da rayuwarta a hakan? Uwa-uba tausayin Ihsan, yau shekaru goma kenan ba ta kara sa iyayenta a idanunta ba, shi kuma shekaru goma sha biyar kenan sai ko yau da jirgin da suka shigo ya sauke su a birnin Ikko. Ihsan Abubakar matashiya ce da jin dadi ke boye mata shekaru a kullum, amma a zahiri shekarunta ashirin da tara cif, don dai gajera ce kawai ba a fiya kimanta shekarunta ba, a yayin da Dr. Al’ameen Bello ke da talatin da biyar da wasu ‘yan watanni. Daga Ihsan har Ameenu kowa na ji da kyau, sai dai nesa ba kusa ba Al’ameen ya darawa Ihsan tsari. Kusan kyawun Ihsan ya fi yawa a fuska, amma ba ta da wannan fasalin na ‘ya mace sai ko ‘yar lafiyayyar fuskarta da Ameenu ke matukar so. Sanye take cikin English wears ruwan hanta riga da wando masu kauri, amma da yake ta baro Miami a yau ta dora bakar after dress kirar Oman a kai, bata da sumar kai mai yawa don haka sau da dama gashin kanta cikin tarin attachement yake. To yau ma hakan, sai dai ta yane kanta da gyalen abayar yayin da kyawawan tafin kafarta ke sanye cikin wani rantsatstsen ‘high hill shoeâ€? bakin takalmi (mai tsayin dunduniya) mahadin jakarta kirar Japan. In ka dauke zobban diamond kwaya uku da ta yi wa kyawawan yatsunta ado babu komai a hannunta don ‘yar jakarta na hannun Al’ameen ne har suka shiga jirgin da zai kai su Abuja. A Abuja Al’ameen ya riga Ihsan sauka don ta tsaya make-up dinta da baya karewa. Hannuwan shi duka biyu zube cikin aljihu ya doshi reception wato wajen karbar baki duk da dama shi bai yi tsammanin zuwan wani nashi ba. Nan ya hango wata mata sanye da malfa mai tsananin kama da matarsa, ko ba a gaya mai ba ya tabbatar Ann ce mahaifiyar Ihsan. Kallo daya ya yi mata ya dauke kai a ransa ya yi mamakin yadda mahaifiyar Ihsan ta kasance Kirista amma ba ta taba gaya mai ba, domin ya hango cross a sarkar da ke wuyanta. Har ya yi gaba sai kuma ya yi tunanin bai kyauta ba, ya juyo ya komo inda suke daidai lokacin da Ann ta rungume diyarta suna ta kukan dadi tamkar ba wani sabani da ya faru tsakanin su, sai ya yi fatan hakan ta kasance a gare shi shima. Ihsan ta saki mahaifiyarta ta yi mata nuni da Al’ameen da ya harde hannuwa bisa kirji yana kallon su kawai ta ce shi ne mijinta Al’ameen. Duk kin da Ann ke wa auren Ihsan da Al’ameen, amma kwarjini da kamala irin na Al’ameen Bello, ba ta san yaushe ne ta sami kanta a mai mika masa hannu ba, ya mika mata nasa a ransa ko cewa yake wai kakar ‘ya’yana ne wannan Inyamurar kuma suruka ta ke mika min hannu mu gaisa kamar a turai? DA YA SANIâ€? Wai me yasa har kullum yake gamuwa da DA NA SANI MARA AMFANI NE a rayuwarsa? To haka suka gaggaisa da sauran ‘yan uwanta ma gaisuwar hand shake fuskar shi ba annuri sam-sam sun nemi da ya bi su gidan su a Garki, domin ya gana da mahaifinta inda shi kuma ya nuna uzrinsa yana cike da dokin ganin nasa iyayen shima. Sai dai in ya huta ita ma Ihsan din ta huta zai zo su gaisa da shi din, ya kuma dauki Ihsan din zuwa gidan iyayen shi. How much do you like this story? 5/7/22, 13:10 - Ummi Tandama😇: ___________________________ *âœðŸ? SIRADIN RAYUWAâœðŸ?* Book one *@Takori* Page2ï¸âƒ£ Abuja Lahadi ce sassanya kuma ranar hutun ma’aikata, cikin wani katafaren gida a unguwar Atiku Abubakar Crescent. Tamkar sauran karshen satittika tsohon Brigadier Bello Makarfi, da uwar gidansa Haj. Nafi, ranar hutu ce a gare su. A irin wannan Lahadin ba sa zuwa ko’ina su kan kasance ne cikin ‘ya’yan su a yinin ranar baki daya tare da tattauna matsalolinsu na rayuwa musamman na karatu da hanyoyin warware su. To a yau ma suna gida, kananan ‘ya’yan su na baya-baya, wato Idris, Furkan da Khalil da ke karatu a jami’ar Gwagwalada duk suna tare da su a wannan satin suna hutu in ka dauke manyan ‘ya’yan da ke kudu. Daddy, kamar yadda dukkan al’aummar da wata alaka ta jinni ta hada su da shi ke kiransa, kwance yake a doguwar kujerar da ke main falon shi yana magana da dansa na biyar wato Yasir da ke Enugu yana aiki ta wayar landline da ke kife bisa ruwan cikinsa inda yake tambayarsa laifin da ya yi masu suka ki zuwa gida hutun karshen shekara, kamar yadda suka saba. Amsar da Yasir ya ba shi yasa jikinsa ya yi sanyi, to amma ya kasa tuno komai bai kuma damu da ya tuna din ba. Don Yasir ce wa ya yi “Daddy, ba za mu iya sake zuwa gida ba gaskiya, alhalin muna ganin irin rayuwar da Inteesar, ke yi ba tare da ta yi maku laifin komai ba, in ma laifin ta yi pls Daddy ba kwa afuwa? Cikin mu wa aka taba yi wa irin wannan horon ko don ita tana Mace? Bayan kuma an san cewa ita mace a komai mai rauni ce? Ko ko don Aunty Saratu ba ta gidan saboda Allah Daddy abin da Hajiyarmu ke yi ya yi daidai kenan? Ba mu da idon da za mu dubi Intisar alhalin tana irin wannan rayuwar a hannun mahaifiyarmu. Don haka Daddy, ba za mu iya zuwa gidan nan ba in har ba rayuwar gidan ce ta canza baâ€? za mu ci gaba da zama a nan inda muke har sai abin da Allah ya tsara…â€? Daddyn na iya jiyo kukan da Yasir ya saka masa a wayar da girmansa da mukaminsa na aiki da komai. Shi kansa baya ce ga hakikanin laifin da Saratu da Saratu su kai masa ba yake ganin su bakikkirin. Kafin ya yanke tunanin da ke addabar kwakwalwarsa ya jiyo tashin ihu da iface-ifacen jama’ar gidan daga waje, haka daga sassan Hajiya, idan har ba kuskure kunnuwansa suka jiyo masa ba ya ji tamkar muryar autansa Khalil na cewa, “Ya Aminu tun yaushe ku ka sauka? Me yasa ba ka gaya mana za ka dawo ba ai da mun zo airport taryon ka.â€? Sai kuma kukan Hajiya da karfi Ameenun na lallashin ta cikin tattausan harshensa. Sai kuma gaba daya lafiyayyar muryar Al’ameen din da har abada ke yi mai yawo a kwanya na tambayar. ‘‘Ina Daddy na?â€? Shidewa ya yi na wucin-gadi, kafin ya tabbatar lallai Al’ameen ne ya yi masu dirar mikiya yau a gidan. Lallai Allah Sami’ud du’a’e ne, mai amsawa bawa roko a sanda ya so. Bai kuma tabbatar da lallai Al’ameen din ne ba sai da ya ji shi kwance cikin jikinsa yana kira cikin muryar nadama. “Daddy, I know that I hurt youâ€? I hurt you, tunda na yi sanadiyyar zubar hawaye daga idanuwanka kada ka taba yafe mini…â€? Amma sai Daddy din ya sanya tafin hannunshi ya rufe masa baki, wato baya son jin abin da yake fadi. Al’ameen gaba daya ya rikice, ya rude ya kara tsanar kansa a karo na biyu da tunanin wace irin ukuba ya haifar wa iyayen shi? Daddyn ya hade hannun Al’ameen mai taushi cikin nasa yana kara damkewa ya ce, “Burina kadai ka dawo gare ni Al’ameen, ganin ka na rana daya ya shafe bakin cikin da rashin ka ya haifar shekaru goma sha biyar.â€? A kullum dama Bello Makarfi, mutum ne mai sanyi kamar ba tsohon soja ba, balle ga iyalinsa, kowanne irin laifi suka yi masa da sun ba shi hakuri shi kenan. Gani yake in bai tausasa masu ba, ya fadi ya mutu shi kenan fa ba za su kuma samun wannan kaunar ta uba ba. Sai ya sake cewa. “Al’ameen idan har ka dawo ne din-din-din, ni har kullum ai mai afuwa ne.â€? Al’ameen yasa gwiwoyinsa a kasa ya kama hannuwan mahaifinsa duk biyun ya ce, ‘Daddy zan kasance nan tare da ku muddin rayuwata. Ni kaina nadamar abinda na aikata ne can baya ga diyar ka Intisar, shin za ka roke ta ta yafe min tunda na san yanzu ta mallaki hankalin kanta? Ban ki dawowa ba sai don ji na yi na tsani kaina, ina ganin ba za ka taba iya yafe min ba, sai ko shaidan da ke kara ingiza zuciyata ga nisantar ku. A ganina ta hakan ne kurum na ke da amfani. Daga ni har Ihsan ba za mu kuma barin garin nan na tsahon lokaci ba.â€? Duk sai suka yi murmushi. To haka wannan family ya yi wunin farin ciki a ranar kamar yadda ya saba a baya. Sai Al’ameen ya ji ranar tamkar renaku irin na baya, masu cike da al’amuran da har abada ba zai manta ba. Bai zaci kuma irin wannan yafiyar da sauri haka daga Daddyn shi ba, don haka yana cike da matsanancin farin ciki a watan Safar. Wata mai dumbin tarihi a gare sa. Watan da ya bude wata sabuwar rayuwar da kuma wasu bakin al’amura masu ban mamaki (At his thirtieth) bayan wanda ya wuce cikin (twentieth) din shi. Ashe in da ranka za ka ga da yawa, ashe in ba ka mutu ba baka kare rayuwa ba, wai me yasa rayuwar take da ban mamaki ne? Al’ameen ya gaya wa iyayensa ya yi aure da Ihsan shekaru uku da suka wuce. Ba kamar yadda ya zaci za su karbi abin ba, matukar farin ciki suka yi, suka ce hakan ya yi kyau. Sun tabbatar har yanzu Al’ameen na bisa turbar Addinin shi, Islam. Wunin ranar zungur kowanne na ba da labarin abin da ya shafe shi bayan rabuwa, amma yawanci labarin juyin mulkin su Daddyn ne ya fi yawa. Hajiya ta rasa ina-taka-saka-ina-taka-aje da Ameenun ta. Da daddare ta same shi dakin Faisal da ke binsa wanda ke Birmingham a lokacin inda ya sauka, ta titsiye shi sai ya bata labarin surukarta Ihsan, fara ce ko baka, doguwa ce ko gajeriya? Sai ya ce, “In kin yi hakuri Hajiyana, da kafarta za ta shigo.â€? Ta ce, ‘Har yanzu bata haihu ba?â€? Ya ce, ‘Hajiya Ihsan fa kabila ce, Mamarta kirista ce, a bisa rashin sani na aure ta, ban san hakan ba sai yau din nan.â€? Da alama zancen bai ko dada ta da kasa ba sai ta ce, “To me ye? Ai ba haramun ba ne, gaya min inda Addini ya ce kada a hada zuri’a da ita tunda ma ba ita ce Kiristar ba, ko itan ce Addini ya amince.â€? Shi kam mamakin yadda Hajiya ta so Ihsan haka farat daya yake, tun ba ta gan ta ba. Ya ce, ‘Shin ina Aunty Saratu ne tun da na zo ban ji duriyar ta ba.â€? Ya kashe wancan zancen kenan. Hajiya ta yi wani dan jimmm, kafin ta ce “Tana gidansu?â€? Ya juyo ya dube ta ya ce, “Me ta ke yi?â€? Ta ce, “Ta haihu ne tana wankan biki.â€? Da far’arsa ya ce, ‘Allah Sarki Antynmu, sai yanzu Allah ya kara ba ta haihuwa again?â€? Hajiya ta kyale shi. Ya ce, “Gobe in Allah ya yarda a Makarfi zan yi sallar Azuhur, me aka samu ne?â€? Hajiya fa ta gaji da zancen su Saratu da yake ta yi mata, daurewa kawai take don kar ta bata wa Aminu rai daga zuwansa, amma da tuni ta zazzage shi, zagin da bai taba tsammanin wata uwa na yi wa dan da ta haifa da cikin ta ta shayar da mamanta ba. Amma lallai ya ce zai ci gaba da yi mata zancen su Saratu yanzun nan za su watse. Ya mike yana amsa call din Dr. Rehab babban likitan “meritimeâ€? cikin ‘yar masifaffar wayarshi da ba ta ma zo mana nan Nigeria ba, balle in san sunan ta, ya gama ya rufe ya dora bisa tebur ya wani irin juyo cikin slow motion hannuwansa duka biyu harde bisa kirjinsa ya yi facing din Mamarsa, muryarsa ta yi sanyi ainun kamar ya aro, a sanda yake cewa, “Hajiya na manta in tambaye ki Inteesar, ina Intissar diyar Aunty Saratu?â€? Hajiya ta hadiyi wani daddafan miyau da ya tokare mata makoshi, saboda zafin da kalamansa sukai mata a zuci, ta daure ta ce, ‘Tana makaranta a Riyadh.â€? Ya ce, ‘Har yanzu ba ta yi aure ba? Na yi zaton she may be a mother of one, two …or three kids? (Tana da É—a guda É—aya, biyu ko uku)?â€? Ta ce a dakile, ‘Har nawa Intisar din take ko sakandire bata gama ba.â€? Ya ce, ‘Yaya lalurar idon da na jawo mata, na tafi na bar ta da shi?â€? Ta girgiza kai da kafadu duka tare da yarfar da hannu alamar ko oho. ‘Ba ni da sani a kan wannan sam, kuma an ce da kai makancewa ta yi kwata-kwata?â€? Ta kwabe baki kamar ta rufe shi da duka. Ya juya mata baya ba tareda sanin halin da yanayin fuskarta da ma zuciyar ta baki daya ke ciki ba, ya kai hannu ya shafi tausassan labban sa ya yi murmushi shi kadai ya ce, “Na dade ina tunanin halin da na bar yarinyar nan, tunanin ta na daga cikin abubuwan da suka sa na ki kaina, na ki kasar haihuwa ta, da duk ‘ya’ya masu irin halina na taya iyayen su mata kishi. Ban sani ba kuruciya kan ingiza mutum ga abin da bai dace ba, idan ya mallaki hankalin kansa abin ya zo ya dame shi. Na sha gayawa Ihsan labarin yadda na nakasta ta, na sha gaya mata irin hazaka da kwazon ta, har Ihsan ke ganina as a wicked brother (mugun É—an uwa), haka na sha gaya mata irin kyawun Saratu tamkar ‘yar tsanar da ke motsi……â€? Hajiya ta mike, domin abin ya ishe ta ta ce, “Kai da Allah shashashan banza, ka cika min kunne da zancen hofi, Intasar din ta ci uwarta, uwar ta Saratu ta ci uwar ta, kakar ta Jummai ma ta ci uwarta, sai me?â€? Ya dube ta sakale! Duk ta hade rai kamar ta mutu don bakin ciki, ya ce, “Hajiya me ya yi zafi haka?â€? Ta ce, “Uban ka ne ya yi zafin, na gaya maka daga yau sunan yarinyar nan da na uwar ta ya fita a bakin ka, bana so!â€? Ya russuna ya riko kafafun ta ya ce, “Hajiya ki tuna, mu fa mu kai laifi, don na yi nadama na tambayi kanwata da muke uba daya laifi ne? Kin san dai dole na nemi yafiyar Intisar a cikin hankalin kan ta tunda ta nakasa a hannuna?â€? Ta ce, “Kalaman ka ne suka bata min Aminu, sai ka ce wani wanda ya yi kisan kai kuma ma dai ni bana son su a bakin ka kwata-kwata, don a duniya ba ni da makiya kamar wadannan mutanen amma ku kun kasa gane hakan, kun ki ku daina ambaton su. Yadda ake shafe matacce a doron kasa a mance da shi, haka nake so ku manta su, amma kun ki, kun fi son su da ni, ‘yan uwanka yau shekara guda ba su neme ni ba saboda tsinanniyar yarinyar nan Intisar nima na kyale su, ina murna ka dawo, don kai ne kadai mai sona da duk abin da nake so, amma za ka fara kai ma daga dawowarka. Ni Nafi na shiga uku! Saratu ta lashe min kurwar ‘ya’ya, ba mamaki, Intisar MAYYA ce, yo dama…â€? Sai ta fizgo dankwalinta ta toshe bakinta da karfi, aurentaâ€? za ta kashe da Bello Makarfi, wanda har yaumittakumi ba ta fata. Shi kadai take so, shi kadai take fatan su mutu tare, su rayu tare su tashi tare, sannan su fadi tare. Kishin sa ne yasa take duk abin da take domin ba ta son kowa ya rabe su ita da ‘ya’yanta, to amma ‘ya’yan kamar shegu shanyayyu, tana janye su, tana masu gataâ€? suna nesantar ta zuwa makiyanta? Sai ta sa kuka. Al’ameen ya juyo cikin karayar zuciya, ya russuna yana lallashin Mamarsa ya ce, “Hajiya ki daina fadar haka, ya ma za a yi mu so wasu fiye da ke? Kin kasa fahimtar mu ne, kar ki manta Intisar kanwarmu ce, jinin ta ke gauraye cikin gaurayen jikin mu, dole akwai wannan kaunar ta jini, don haka dole mu ji son ta ko yaya ne, amma kin sani, ko kowa na son Intisar BAN DA NI, har kullum ni Al’ameen ne dan Hajiyarsaâ€?., yafiyar ta kawai nake nema, na hakkinta da yake kaina.â€? Ta dago shi tsaye ta ce, ‘Na fahimce ka Aminu, amma ka yi min alkawarin ba za ka kara son Intisar ba har son zumuncin?â€? Da sauri ya ce, ‘NI dama ina son ta ne? Amma jini ya rigaya ya hada mu ko? Dole mu’amala ta hada mu. Alkawari daya zan iya yi miki Hajiyana, ba zan taba son ta irin son da Faisal ke mata ba!â€? Ta yi murmushi ta shafi kansa ta ce, “Aminu na, shi yasa na ke son ka fiye da kowa har kullum, me za ka ci gobe da safe in Allah ya kai mu in gayawa jikar Jummai tun yanzun?â€? Ya ce, “Ni bana cin girkin tsoffi, idan ba naki ba ne, da safen zan shiga kitchen da kaina in dafa koko in soya kosai.â€? Hausar shi ta ba ta dariya ta ce, “Ba a dafa koko damawa ake yi.â€? Ya dan fiddo ido ya ce, “Hajiya ta, ni fa ba abin da Amrica ba ta koya min ba, ni nake dafawa kaina abinci, tun kafin in yi aure har kuma na yi auren, ni nake dafa mana duk abin da za mu ci. Matata lazy gal ce in ta yi min nata bana iya ci.â€? Ta ce, “Wannan ‘yar aikin tawa in ta yi za ka iya ci, domin yarinya ce budurwa kuma ga ta da tsabta, hakan nan duk gidan nan girkin ta muke ci har baban ku, don tana da ilimin abun, don haka hutar da kan ka shiga kitchen.â€? To Al’ameen duk sai ya ji yarinyar ta burge shi tun da karamar ta da ita har take girkin da Hajiya da Daddy ke ci su yaba, ya san ba komai ke burge Hajiyarsa ba da wuya a yi mata abin da za ta ce an yi mata daidai kwata-kwata ba‘a iya mata, sai yau da ya ji daga bakin ta, uwa uba ta ce yarinyar tana da tsabta don a sanin da ya yi wa ‘yan aikin Hajiya a sanda yake nan duk mugayen kazamai ne barin Asbi da Ladi, kuma wai har ilimin girkin gare ta bayan ya sha jin Ihsan na cewa da ta tsaya ya koya mata girki gara ya sake ta a kan abincin. Kitchen bai fasa shiga gobe da safe in Allah ya yarda, in ya ga kwarai ta iya din ya kawo Ihsan ta koya mata, don yanzu ya amince shi kansa dole su canza tsarin rayuwarsu tunda kuwa rayuwar aure a Nigeria ba za ka taba hada shi da na Turai ba, inda culture (Al’adu) sun bambanta. Ko da yake in har bai manta ba ita da kanta Ihsan din wata rana ta taba gaya masa hakan, lokacin da yake sangar tata da yawa cewa, don yana ganin ba su da kowa ne a can din sai junansu. A lokacin bai yarda ba sai yanzu wai yake gayawa kansa dole Ihsan ta canza taku in har tana son rayuwar auren su ta tafi straight ba karkacewa. Ya manta icce tun yana danye ake tankwara shi. Washe gari autan su Khalil ne ya yi ta yi wa ‘yan uwan buge-bugen waya yana sanar da su dawowar ya Ameenun da matar shi Ihsan, hatta Faisal da ke Birmingham yana karatu a lokacin ya ji dawowar Ya Aminu. Yasir ya ce suna gaishe shi, amma suna masu tsananin fushi da shi su duka har sai sun ganshi a garuruwan da suke shi da Ihsan tukunna su huce. Al’ameen ya amsa zai je wa kowannensu shi da ba bakon zafi ba har ya isa ya ja masu rai? Ga dan zafi Najib kuwa ko sannu bai samu ba, don har yanzu yana kullace da Aminun, wannan ta wuce. Karfe bakwai na safiyar Litinin ya zuba koriyar shadda Edcellencior da aka yi wa dinkin Mohamed Abacha, kan shi ba hula, don bai da ita. Wannan shaddar ma ta jikin shi Furkan ya ba shi, don ba zai so Baffan su ya soma ganin sa cikin suit ba. Kasancewar ya dade rabonsa da irin wannan dressing sai ya fito a wata kala daban. Hakika kalar Maman shi ‘yar uslin garin Maiduguri, cikin kabilar nan Shuwa ne ya debo kamanni da zallar kyau, ta wani bangaren kuma sai ya fito a tsantsar Bahaushen sa sak mahaifin shi Bello Makarfi. Ya shirya ma fita karfe bakwai da rabi ne don yana da sabgogi da yawa da yake son gabatarwa a ranar in Allah ya ara mai rai da lafiya. Bayan zuwa wajen Baffansa da Aunty Saratu da ke garin Makarfi yana son neman filayen da zai yi ginunnuka ga takardun hijira da zai aika Miami ta komfuta da neman izininnikan medical branches da yake son assasawa anan kasar mu Nijeriya wanda zai kasance reshe daga meritime da ke karkashin kulawar Dr. Rehab da zai nema daga ‘Federal Ministry of Healthâ€?, wato hukumar lafiya ta kasa. Yana son assasa asibitoci anan Abuja, Kaduna da kuma kauyen su How much do you like this story? 5/7/22, 13:10 - Ummi Tandama😇: ___________________________ *âœðŸ? SIRADIN RAYUWAâœðŸ?* Book one *@Takori* Page3ï¸âƒ£ Makarfi Hakan nan yana son ya je ya gaida surukan shi a Garki, ya yi masu wata kyauta mai daraja ba don komai ba sai don neman albarka, duk da hararar gefen idon da ya ga ana yi masa duk da cewa he did not care, wai sai ya shiga yi wa kansa dariya, da ya ce zai kai wa iyayen Ihsan abu don neman albarka. To albarkar Kiristin zai nema? Ya yi saurin cewa a’a na uban da yake Musulmi, kuma mutumin kirki a bakin kowa. Akwai kuma muhimman kayayyakin su da suka taho da su musamman motocin su zai je port da airport ya fitar da su. Ya san idan ya fita yau sai Allah, don haka akwai bukatar ya yi kyakkyawan break-fast da abinci mai nauyi don shi ba ya jure yunwa sam. Kafarsa ko takalmi babu yana tafe yana magana da Ihsan din shi tana gaya masa yadda ta yi missing din shi ne a daren jiya, tana kuma tambayarsa ko how much did he missed her? Sai ya kada harshe ya ce, “Wai ke Ihsan kin yi murna da ganin Ann, da ki ka dame ni da mu zo ki gani? Ni ko sai na ga you are not happy as I am, don ni jiya har sha biyun dare ina tare da Hajiyana, muna hirar da for so long ba mu samu mun yi ba. Ina na tuna da wata soyayyar ki can?â€? Ta ce, “Ya yi kyau, ai ni dama kullum mantawa nake ni ke son Al’ameen, ni na damu da shi, ni kadai ke kaunar shi, amma duk kokarina bana burge shi, so ka yi hakuri.â€? Da haka ta katse layin, ko ba ta fada ba ya san ranta ya baci, shi ko sai ya yi murmushi ya ce, “Allah Sarki, nima ina son ki, damu ne ba na so, ko karyawa ban yi ba.â€? Sai ya bai wa kansa dariya a karo na biyu, lallai kam duk girman mutum a gaban iyayensa ashe yaro yake komawa, ko kuma don ya dade baya tare da su ne? Oho. Yadda kyawawan fararen kafafunsa ke mannewa bisa marbles ma kadai abin sha’awa ne, to haka his gait, his geniusness and his coolness ke da daukar hankali. Wata yarinya ce fara, irin farin nan da ke da jaja-jaja wanda Bahaushen tsantsa baya mallakarsa, doguwa sambaleliya tamkar kirar matan Seirraleone. Fuskar ta oval shape, mai wadace da kayataccen dogon karan hanci, tamkar ansa ruler, an ja shi an daidaita shi a tsakanin idanun ta. Idanuwan ta kadai sun isa su sa mutum ya so ta ko da ya ki Allah (Almond-Eyes). Girar idonta gazar-gazar kuma kakkaura siririya, bakinta dan surut jazur da shi mai matukar daukar hankali, yatsun ta na kafa da hannu zara-zara masu matukar taushi da kyan tsari, tamkar ba na ‘yar aiki ba. Sumar kanta yalwatacciya ta Fulanin usli nannade take kamar gammo duk ta wani irin mummurde alamun rabon da a taje ta har an manta, sanye take cikin wata zulumbuwar riga ja mara ado wadda a kullum suke cikin dattin kitchen, duk inda kyakkyawar mace mai fasali take to wannan yarinya ta isa har ta wuce. A ransa ya ce, ‘Kai Allah ya yi halitta tamkar Hurul’eeni???â€? Ya yi sallama har sau uku, amma yarinyar a zuci ta amsa ko dagowa ba ta yi ba balle ta ga waye mai sallamar, illa zuciyar ta cike da jin dadin yau an yi mata sallama sabanin da da duka ko zagi ke mata sallama. Hakan nan wannan wata murya ce da ake kira ‘huskyâ€? da ba duk maza Allah ya mallakawa ba sai ko wadanda suka amsa sunansu ba ‘muna-mazaâ€? ba. Murya ce mai shigen ta Ya Faisal, sai dai wannan akwai alamun sense of humour wato raha tamkar ta Daddy, ba ta raba daya biyun Yasir ko Nasir ne oho, ita yanzu ko a lahira ta ga ‘ya’yan Hajiya ba ta fatan Allah ya ba ta ikon kula su. To Al’ameen sai ya dauka ko ba ta ji ne kwata-kwata, ya kai hannu ya kwankwasa lockers din kichin din da karfi, ta dago a dan razane. Ta so ganin mamallakin wannan murya mai sanyawa mace kasala ba tare da ta ga mamallakinta ba, ta so ganin mamallakin wannan ni’imtaccen kamshi da ba ta taba ji ba a rayuwarta, sai suka yi ido biyu da mutumin da ba ta sani ba ba ta taba gani ba. Babu abinda ya firgita ta kamar kwarjini da cikar zati irin na Al’ameen wanda hakan ya janyo mata gigicewa tare da mance abinda take yi, wani matsanancin tsoronsa ne ya kama ta, tsammani take Hajiya ce ta turo shi ya sa mata shocking din da ta ce za ta sanya mata in ba ta kammalawa bakonta karin kumallo da wuri ba a safiyar yau. Tuni ta karasa rudewa ta rikirkice ta soma matso kwallah ta ci gaba da firar jibgin dankalin turawan da ke gabanta fiye da bokiti guda tana ferewa da dukkan karfinta da iyakacin saurin da za ta iya sai shap! Ta zaftare tsokar dan yatsan ta jini ya soma fita a guje, amma ba ta kula ba sam, aikin ta ta dage da yi. Aminu ya kama kai, ya karaso gabanta ya rusuna ya kama hannun ta mai rike da wukar ya ce, ‘Ke ba kya ganin kin yanke ne?â€? Maimakon ta bari, sai ma ta kara daukar dankalin da ya subuce a lokaci guda kuma tana kici-kicin kwace hannunta daga hannunsa ya ce, “Ki yi hakuri in tsayar miki da jinin?â€? Ta dago a hankali ta dube shi, to shi ma din kallon ta yake, suka yi wa juna kuri da ido; wani chemistry ya shiga aiki cikin ‘yan mintocin da ba su gaza uku ba, ita ta fara kawar da kai, ya mike ya fita da sauri yayin da ita kuma ta yi jigum ta na duban yatsanta da ke ta bulbular da jini ta ce a ranta wannan wane irin mutum ne he is so caring. Ya dawo rike da dan karamin First-aid bod cikin nutsuwa ya wanke mata yatsan da ruwan hydrogen tas babu ko kwayar jini, ya shafa iodine don azabar shi sai tasa kuka, yasa plasta karama ya nade yatsan, ya tsani ya ga mace tana kuka. Ya sarke yatsun su cikin na juna ya ce cikin tattausar muryar shi. ‘Ki yi hakuri, duk ni na jawo miki, don haka tafi daki, ni zan karasa miki.â€? Ta share hawayen ta da gefen rigar ta iodine na mata radadi da zugi, amma tausassan yatsun Al’ameen sun tsare komai. Da ya ga ta yi shiru da kukan da take sai ya zare hannunsa ya shiga aikin dankalin nan tukuru cikin dan lokaci ya gama ya zuba a katoton fraying fan da ke tafasar da mai ya soye shi tas, haka ya shiga hada kowanne kwai da dan uwansa ji ka ke kas! Sai ya juye cikin babbar silver nan da nan ya soye shi fes. Tuni ta kammala ragowar kananan aiyukan kamar su zuba ruwan zafi a filas da jera komai bisa faranti. Ya dauki plate mai tsabta, ya debi abinda zai yi masa ya dau cokali fork ya aza bisa ya juya ya fita, har ya kai bakin kofa sai ya dawo ya dube ta ya ce“Ke daga yau in kin gan ni kar ki sake firgita, don bana satar yara, hakan nan al’adana ne shiga kicin, don haka in ki ka sake yankewa ba ruwana.â€? Bai fita ba sai da ya bi Hajiya sassan ta suka gaisa, Daddyn bai fito ba don haka ya zauna zaman jiransa a falon gidan har ya gama. Shi ya sauke Daddyn a ofis yau kana ya wuce ya kama harkokin gabansa zuciyarsa cike fal da tausayin ‘yar aikin Hajiya, ya yi mamakin yadda kyakkyawar yarinya kamar ta da daga gani ta fito ne daga gidan hutu ke aikin wahala irin wannan. Idanuwanta kadai sun ishi kowanne irin namiji yanga da ita a matsayin mata. Ya alkawartawa ransa matsar ta ya ji dalilinta na wannan aikin wahalar duk da ya lura yarinyar ba ta son magana da kowa to shi dole ta yi masa. A Makarfi gidan Baffansu ya tadda kannensa su Najib sun zo suma, nan gidan Baffan ya kaure da murnar ganin Ya Aminu. Ya dade rike da kyakkyawar babyn ta Zarah, yana kallon ikon Allah don kamar su da Faisal har ya yi yawa (Zahara ce autarsu ‘yar amaryar babansu da ya saki). Ya ce, “Anty ko za ki ba Ihsan rikon Zarah don Allah.â€? Shi Al’ameen bai da masaniyar rabuwar Antin da Daddyn shi ya dauka wankan jegon dai take kamar yadda Hajiyar su ta gaya masa, sai ta murmusa ta ce, ‘Ban ga Ihsan ba, amma tunda na san a America aka aurota ba za ta so rikon dan da ba nata ba.â€? Ya yi murmushi ya ce, “Amma za ki ba Intisar?â€? Ta ce, ‘Idan mijin da ta aura na kirki ne ba?â€? Da haka ta kashe zancen, ta lura Al’ameen bako ne kawai daga Miami, bi ma’ana bai san komai ba cikin al’amuran da suka faru cikin rayuwarsu. Ba yadda Al’ameen bai yi da ‘yan uwansa sa ba kan su tafi Abuja tare, amma sun kiya wai a cewar su tafiyar dare za su yi wa Enugu. Abinda ya lura dukkanin su bakin su daya har Antin suna boye masa wani muhimmin abin da ke damun su ba sa so ya sani, ko ma meye. ai in ta yi wari zai ji ne tunda yana nan a kasar ba inda za shi. Ya kyale su da alkawarin har Enugu zai kai masu Ihsan. Wurin karfe goma na dare ya koma gida, a daidai lokacin Daddy na kokarin hawa sama shi kuma yana kokarin sauka, sai suka yi kacibus, dukkanin su suka yi wa juna murmushi mai cike da kauna irin ta da da mahaifi. Daddyn ya ce, “Ina ka yi ne Aminu tun safe ko gama hutawa ba ka yi ba?â€? Ya ce, “Masu cinikin fili man ke ta min yawo da hankali, amma yanzu mun daidaita da wani a Addis-Ababa Crescent.â€? Daddy ya ce, “Abin da nake gani ya fi kawai ku yi amfani da gidana da ke ‘Colorado Closeâ€?, don ba mutunci ba ne abar yarinya a gidan su har sai an gama ginin, gobe in Allah ya kai mu za ni mu gana da shi Dr. Argungu, don dama mun san juna sai dai ban taba tsammanin za ka hadu da ‘yarsa ba ma balle har mu zama daya.â€? Ya dan murmushi kadan, don ya lura su dai su Daddy suna son auren nan nasa ko don cikin samarin ‘ya’yansu kaf babu wanda ya yi auren fari ne? Bai sani ba. Daddyn ya kuma cewa, ‘Mun daidaita da kamfanin Julius Berger da za su yi ma ginin tun safe in ka samu filin?â€? Ya ce, ‘A’a a sallame su kawai don tuni na yi magana ta komfuta da kamfanin da ke yi min gini a Miami, ina son aikin su sosai, za su zo su cikin dan lokaci kankani za su zuba komai.â€? Ya ce, “Babu damuwa, duk yadda ka ke son haka za a yi.â€? Al’ameen har ya juya ya dawo yana sosa kai ya ce, “Af Daddy, na je fa Makarfi?â€? Ya dawo shi ma da dukkan attention dinsa gare sa cikin sanyin jiki ya ce, “Yaya ka baro su, suna lafiya ko?â€? Ya ce, “Kowa lafiya, Zahrah ta yi girma da wayo sosai, shin sai yaushe za su dawo ne?â€? Daddyn ya lura sam Al’amin bai san ya rabu da Aunty Saratu ba, ga shi shi kan sa a lokacin babu abin da ke damunsa kaman, shin wai ma ya a kai ya saki Saratu? Me ta yi masa? Iyaka tunaninsa ba ya ce ba, bai sani ba. Kuma wai har Intissar ta tafi, amma ya kasa wani abu a kai? Ya ce cikin jin nauyi. “Al’ameen na fa rabu da Saratu, amma gobe insha Allah ka raka ni biko, shi kenan? Allah ni kaina bana ce ga actual sabanin da ya faru ba, wanda kwata-kwata bai taba faruwa ba.â€? Al’ameen ya yi shiru ba don komai ba sai don tausayin mahaifin shi da ya lullube shi, ya san irin wannan nadamar, ai shi zai gayawa kowa nadama mara amfani, to amma me yasa Hajiya ta boye masa komai? Ba mamaki don ba ta son duk wani abu da ya shafi Saratu, ta kuma san a wannan lokacin ba zai goyi baya ba, to ko Intisar da ke Riyadh ta san wannan? Ya ce, ‘Ba komai Dady, haka Allah ya tsara, amma insha Allah komai zai daidaita, don ni Aunty Saratu ba ta min komai ba, heart and soul (Baka da zuci) kamar da, sannan in na sami lokaci zan je Riyadh in ga Saratu karama (Intisar).â€? Daddyn ya ce, “Au! Ta koma makarantar ne?â€? Ya ce, “Hakan dai aka ce da niâ€? “In za ka din, sai ka yi min magana mu tafi tare, rabon da in sa Saratu a idona tun ranar da Saratu babba ta bar gidan nan.â€? Da wannan Al’ameen ya kwanta, al’amura, ya rasa da wanne ma zai fara, tabbas ran Hajiya zai sosu in ta ji har da shi aka je mata bikon kishiya, bikon ma na mutanen da ta ki jini fiye da mutuwarta, to amma wannan ba zai hana shi gyara sunnah ba. Shi kawai hakan nan ya ke kaunar Anty Saratun saboda yakanar ta da abin da ya yi masu na rashin kyautawa can baya, amma ba ta damu ba, ba ta kullace shi ba, kai ko a fuska ba ta taba nuna masa ta san abin da yake ciki ba. Uwa-uba karin zuri’arsu daga gare ta. Hajiya wata irin halittar Allah ce, ba a iya mata. Dole ya raka Daddy. Sai ko tunanin murdaddiyar ‘yar aikin Hajiya, da son jin labarin ta da son sanin dalilinta na wannan aikatau din ya fi kowanne tunani mamayar 70% cikin kalbin shi. Amma dare ya yi nisa, yana kuma da muhimmin signing din takardu domin karbar licence daga hukumar lafiya ta kasa a goben haka ma zai raka Daddy Makarfi duka a goben in Allah ya yarda. Ya so kwarai ya ga yarinyar a yau, to amma da safe ma tana firgita in ta ga mutane bare da daddare? Haka ya kwana da sake-sake, shi kam zuciyarsa ta amince mai da ya taimaki kyakkyawar ‘yar aikin nan ta samu rayuwa mai kyau, don yana ganin idan ta ci gaba da irin wannan aikatau din mai matukar wahala (for her age), za ta yi asarar kuruciyar ta ne yarinyar ta da ita. Washe gari ta na goge-gogen kicin wurin karfe tara na safe, kasancewar a yau ta kammala komai da wuri ba kamar jiya ba, sauri take ta je ta huta sakamakon danyatsan ta da ke mata zugi, ga kuma menstrual pain (ciwon mara) da take fama da shi, don ma ta samu yanzun ya dan lafa, amma jiya kwana ta yi tana kuka, saboda azabar sa da radadin da danyatsan ke mata, ba wai don aikin ya kare ba, tunda kuwa nan da awa daya za ta soma aikin abincin rana. Al’ameen ya kwankwasa lockers din kicin din da yatsun sa biyu a hanzarce ta juyo sai ya sakar mata murmushi mai nuna sannu, ya ce, ‘Na ga ba kya amsa sallama, shi ne na ce bari in miki ta bature, watakila ke din Baturiya ce, ban sani ba?â€? Ba ta amsa ba, illa juyawa ta ci gaba da cleaning din ta tukuru, da gani ka san aiki ne da ya riga ya zame mata jiki, a ranta ko cewa take kai wannan mutum yana son matsanta wa rayuwata. Why? Ya tura hannuwan shi cikin aljihun wandon basachi da ke jikinsa yana kallon ta kurum, duk wani motsin ta a kan idonsa ne, nutsuwarta da yaukin ta a komai yana burge sa har bai san adadin mintocin da ya bata a hakan ba can ya ce, ‘Wai ke ba kya magana ne?â€? Nan ma ba amsa tamkar da dutse yake magana, ta koma ga juye snacks da ta kammala a cikin babbar roba a ranta ko cewa take wai wannan ina ruwansa da ni ne? A kan me ya damu da ita da zai ce lallai sai ta yi masa magana yana bin ta bashi ne? Ita fa duk wani da ya shafi Hajiya ba ta son gani, amma a zahiri ta rasa me yasa ba ta ko iya hada ido da wannan bako ko iya dubansa. Kwarjnin shi na da ban tsoro, shi kadai amma duk ya cika kicin din. Ta sha ganin maza masu kyau da cikar halitta a cikin duniya da nan cikin gidansu, amma ba ta taba ganin mai kyau tsararre da ilhama kamar wannan bakon ba, to amma an gaya masa ko mutuwa ta yi ta dawo za ta yi wa jinin Hajiyar gidan nan magana? Ba ta ankara ba hakan nan ko a tunanin ta ba ta kawo zai shigo cikin kicin din ba, ya doso ta cikin daure fuska tamkar bai taba dariya ba tunda uwarsa ta haife sa, ta yi kamar ba ta gan shi ba ta juya ta ci gaba da aikinta, sai ya fizge robobin ya kifar da duk abin da ke ciki a dandaryar kasa ya yi wurgi da robar, ya kuma bi su yana takewa daya bayan daya yana rugurguza su yadda ba za su moru ba. How much do you like this story? 5/7/22, 13:10 - Ummi Tandama😇: ____________________________ *âœðŸ? SIRADIN RAYUWAâœðŸ?* Book one *@Takori* Page4ï¸âƒ£ Ta bi cake samosa spring-rolls da doughnuts din da ta shafe awanni hudu cur tana aikinsu tun karfe shidda na safe da kallo rugurguje a kasa, tare da kiyasta irin azabobin da za a gana mata a kan wannan snacks, amma wannan ba karamin mugu ba ne, sai hawaye sharrr! To saime? Kafin ta gama tantance what will happen nedt (Me kuma zai faru?) Al’ameen ya kai mata wawura yana kokarin lalubar cikin ta tamkar mai shirin kwashe mata ‘ya’yan hanji da kayan ciki gaba daya cikin gigita, mamaki da tashin hankali ta ce. “Wayyo Dela, na shiga uku zai kashe ni.â€? Ya ce, “A’a ba kashe ki zan yi ba, cikin na ke so in duba in ji ko saurayin banza ne ya yi miki ciki, ki ka gudo daga gidan iyayenki, ki ka kama wannan aikin wahalar don cikin ya bare, ki ka kuma tsani duk maza ta kai ga ko sallamar su ba kya amsawa saboda shi wancan din? To ni na iya zubar da ciki ta hanya mai sauki ba ta wannan aikatau din da ki ke ba.â€? Ta zaro ido abin dariya abin tausayi ta ce, “Don girman Allah ka sake ni, wallahi ni ba ni da wani ciki ban ma taba yin wani saurayi ba a rayuwata.â€? Ya sake ta tare da maida hannuwansa baya ya sarke su cikin murmushinsa mai kyau ya ce, “Munafuka, ashe kina magana?â€? Ta sha kunu ta cika ta yi fam, kiris take jira ta fashe ta ce, “Shin don Allah ina ruwan ka da ni? Wane irin bako ne kai mai shishshigi ga rayuwar mutum da yawa? Ba ka san masifar da ka janyo min yanzun ba? Ba ka san in Hajiya ta san kana shigowa nan sai ta kusan kashe ni ba?â€? Sai ta sa kukan da ya karyar da zuciyar Al’ameen gaba daya. Ya ja kujera kwaya daya tal da ke cikin kicin din ya zauna dab da ita ya cure hannuwan shi wuri daya ya ce, “Ba abin da ya hada ni da Hajiya, ni dan uwan su mai gidan nan ne a Kaduna nake, halin rayuwa ya sa muka bacewa juna tun tuni sai yanzu suka gan ni muka gane juna. Hajiya ba abin da za ta yi miki tun da kuwa ni na kawo kaina ba ke ki ka janyo ni ba ko ke ki ka kirawo ni?â€? Shi kansa ya yi mamakin kansa kan karyar da ya samu kansa yana mai sharawa, a take ya soma Istigfari a zuci. Ta share hawayen ta da bayan hannu duk sai ta kara ba shi tausayi, ya ce, “Don Allah ki yi min wata alfarma guda daya, ni kuma zan taimake ki ki samu ‘yancin kan ki, in dai kudi ne daga naira daya zuwa million zan baki, ki koma gaban iyayen ki, ki je makaranta ko ki yi aure, ya fiye miki wannan wahalar wadda kwata-kwata ba ta dace da mace mai darajjah da kima kamar ki ba!.â€? Maganar shi ta karshe ta bata matukar haushi, ita nan har wata daraja gare ta? Shin ‘ya mace na da wata daraja ne ma? Ita da ubanta ke bal (bull) da ita? Yana cewa in aka tausasa mata bai yafe ma? To me ye amfanin rayuwarta tunda kuwa bata da wata daraja yanzun a wajen uban da bata da kamarsa? An yi wa uwar ta sakin wulakanci, an daidaita matsayinta da na ‘yar aikin gida mafi kaskanci, to me ye amfanin rayuwar ta in ba ta yi bauta ba? Wasu sababbin hawayen suka kwararo mata sharrr! Ta ce, ‘Ni ba ni da wata daraja ‘yar aikin Hajiya ce!â€? Ta tsugunna bisa gwiwoyinta a gaban sa ta ce, ‘Don Allah Yaya na kada ka kara zuwa nan, Hajiya har shocking take sa mini, ta sa kebur ta farfasa min jiki, ta sa kafa ta taka fuskata ta ce wai ni ba ni da amfani tunda ubana da kansa ya bata ni in yi mata bauta. Idan ta ji kana zuwa nan Allah shocking za ta sa min…â€? Ta kai hannu ta dan janye doguwar rigarta sama zuwa gwiwar kafarta, me zai gani? Jini ne kwance yarab-yarab lub-lub da shi abin ki da farar fata, zanen kebur birda-birda wani a kan wani, ya kau da kai da karfi ya juya mata baya. Ya ji idanunsa sun ciko da kwallah. Wai Hajiyarsa? Ita ce mai ganawa dan adam irin wannan rahsin imani, su ko ko mari wannan bai taba hada ta da su ba. Kenan ‘ya’yan ta kadai take so, ba ta yarda da na kowa ne ba? A yau kam ya yi nadamar kasancewarsa (Al’ameen dan Haj. Nafi). Ina ma shi dan Aunty Saratu ne? Yanzu ne ya godewa dabarar shi na boye mata ainahin ko shi wane ne, zai kuma ci gaba da boye matan. Ya tabbata da ba za ta kula shi ba, ko yanzu ma don ta ji ba abinda ya hada shi da Hajiyar ne, to ai ko shi ne, to wanda ke gana maka irin wannan azaba ina za ka daga ido ka dubi wani da ya shafe shi ma balle dansa na cikin sa? Ya zaro handkerchief din sa mai kamshi cikin aljihunsa ya mika mata ya ce, yana mai kawar da fuska daga gare ta, ‘Share hawayen nan maza-maza bana son in ga mace tana kuka, zan tafin yanzu, amma ki yi min alfarma daya ki gaya min me ki ka yi wa baban nan naki haka da zafi?â€? Ta sunkuyar da kai, ta rasa me yasa zuciyarta ta amince da Al’ameen haka farat daya, ba ta san me yasa ya shiga ran ta haka da sauri ba. Babu abin da take jin za ta iya boye masa a game da ita ban da abu daya, shi ne ba za ta taba tonawa wani cewa ita ‘yar daddy ba ce, kuma take cikin irin wannan kaskanci da rashin galihu a gidansa, wannan zai zubar mai da mutunci ne a idon dan uwansa da sauran jama’ar da ke ganin kima da mutuncinsa. Tunda shi Daddyn ya san da ita, amma bai gaya masa yana da ‘ya ba a gidan ita a kan me za ta fadi? Ita fa tana da zuciya, ba kuma ta tura kan ta inda ba a kai ta ba, bari kawai ta kara wulakanta kanta, tunda ita dama wulakantacciyar ce a gidan. Ta ce cikin wata irin sassanyar murya da ta kassara gabobin shi baki daya. “Ni ban san abinda na yi masa ba, kawai dai talauci ne ya ishe shi shi ne ya sayarwa da Hajiya ni.â€? Al’ameen ya sa hannu ya dafe kansa da ke sarawa tamkar ya rabe gida biyu, bai taba jin inda aka sayar da dan mutum ba a wannan zamanin dai da muke ciki kamar wani zamanin cinikin bayi? Da kyar ya samu kalma ta fito daga bakinsa ya ce, “Yanzu ina baban naki yake?â€? Ta ce, ‘Ai yana fita daga nan ranar da ya kawo ni mota ta kade shi ya mutu, uwata kuma tun muna kanana dama ya sake ta ban san inda take ba yanzun, dama kuma an ce ba ‘yar kasar nan ba ce.â€? Ta yi hakan ne don ma kada ya ce zai kai ta wani wuri, ita wannan rayuwar ta fiye mata duk wata rayuwar jin dadi da za ta yi a wani wuri, a gidan da ba na Daddy da ya nuna mata ingantaccen so da kauna a baya ba. Ba ta san hakan da ta yi kuskure ne babba ba, domin tausayi kan taimaka wurin kimsa ‘soâ€? na hakika. Ta ce, ‘Na rasa me yasa Hajiya ta tsane ni? Na dade ina yi wa kaina wannan tambayar, iyakacin biyayya ina kokarin in ga na yi mata tamkar Mama ta. Tunda nake a duniya babu wanda ya taba budar baki ko da wasa, ya gaya min ya tsane ni gaba da gaba tamkar mutuwar sa ba sai Hajiyar nan gidan, I don’t know why?â€? Al’ameen sai ya samu kansa a rashin yarda da abin da ta gaya masa na cewa wai talauci ne yasa ubanta sayarwa da Hajiya ita, to amma wacce hujja gare sa da zai karyata ta? Shi kam ko za a tsaida shi gaban alkali ko a ritsa shi da bindiga ba zai yarda ba ‘yar manya ba ce. Kai ba alamun ta taba kasancewa cikin talauci a rayuwarta. Muryar ta kadai ya ji ya san tana da ingantaccen ilimi, magana take a nutse, cikin sassanyar murya ta da ke sanya gabobin dan adam su yi sanyi, kai, unblievable.â€? Ya ce, “Kin san wani abu ne?â€? Haka kawai Allah kan halicci mutum ya kimsa kiyayyarsa a zuciyar wani, ba tare da wani dalili ba. Bai yiwuwa musamu soyayya daga kowa don ko Annabin Rahma Allah bai bar shi ba makiya ba. Idan har ba ki da makiyi, to ki binciki aikin ki. Dole wani ya so ka wani ya ki ka a duniya. Akwai wani shahararren (popular and famous American doctor) wai shi Dr. Fell da aka yi a kasar Amurka tun 19th Century (Karni na goma sha tara), wanda kasar ke ji da shi saboda fasahar shi, kowa na son shi saboda dumbin taimakon shi ga al’umma, ba shi da wani aiki sai na ceton rai, ba shi da wani buri sai na ya ceci rai a gaba dayan tsayin rayuwarsa, ba tareda ya karbi ko kwabo ba, amma sai wani mawaki makocinsa yake waka a cikin wani baiti da yake cewa: I don’t like thee, Dr. Fell I don’t like thee. I don’t like thee, Dr. Fell The reason why? I can not tell. A nan shi mai wannan wakar ya san dai ba ya son Dr. Fell duk da farin jininsa da da irin taimakon da yake wa al’ummarsa kuwa, amma bai san me ya hana shi son sh ba. To haka tsananin ki da Hajiya, ba wai sai da wani dalili ko wani abin ka wa mutum zai ji ya tsane ka ba. Don haka kar ki sa wannan a ranki har ya dame ki. Duk wani matsayi da ki ka ga dan adam a ciki to haka Allah ya rigaya ya tsara masa rayuwa sai ya rungume ta hakan nan ya kuma zamo mai godiya a gare si. Idan ya aiko mai da sauki, ana son ya yi farin ciki, ya rungumi wannan saukin, ya dauka cewa daga Allah ne. Don haka ni taimakon ki nake son in yi tsakani na da Mahalicci na, idan kin amince da ni.â€? Ya sunkuya ya dago habar ta, ya dubi yadda hawaye ke rolling one after the other (gudu bi-da-bi), a irin wannan fuska mai zati. Yasa hankici yana share mata sai ta runtse ido ta girgiza kai alamar ba ta so. Ya sakar mata fuska ya ce, ‘Ha-di-rah.â€? Idonta a rintsen ta ce, ‘Ni ba sunana Hadirah ba.â€? Ya ce, ‘To Halimah dube ni.â€? Ina! Al’ameen bai sani ba, muryarsa kamar wani maganadisu ne (magnet) mai jan zuciya tamkar jan wutar lantarki ta ce, ‘Ina ji.â€? Cikin wata raunanniyar murya, ta rasa me yasa idanun ta ke kasa dubar wannan mutum, wala Allah kwarjin shi ne? Ya tabbata ba za ta taba iya kallon shi ido cikin ido kamar yadda yake so ba, sai dai in su kwana a hakan sai ya ce, “Kin amince da taimakon da nake son yi mikin?â€? Ta yi shiru na ‘yan dakikai. In dai barin gidan Daddy ne ba za ta taba iyawa ba. Ta gwammace Allah ya dauki ranta a nan ta huta, to ma sace ta zai yi? Ko ko Hajiyar zai roka ta ba shi ita? To ya kai ta ina? Sam, ita ba ta son wani taimako, ba kuma ta son watsawa mutumin da ya taba nuna kulawa da rayuwar ta bayan Faisal kasa a ido. Ba shakka ta ji dadin maganganunsa, ta tabbatar shi mutum ne mai wadataccen ilmin kwakwalwar dan adam da aiki da shi, har take jin zuciyarta na yaudarar ta da gaya mata wai ta sami makwafin Faisal wurin kulawa da nuna kauna. Bai kuma zugata ta ki babanta da ta ce ya bada ta bauta ba, haka bai zuga ta da ta yi izgili ga Hajiyar da ta tagayyara masu rayuwa ba. Ya nuna mata yi wa kowanne dan adam uzuri komai abu ne mai matukar muhimmanci. Ga kuma hikimar kwantarwa da mai matsala hankali, cikin fasaha da ingantacciyar kulawa, she enjoyed meeting him hakika (ta ji dadin haduwa da shi). Da ya ga ba ta ce komai ba duk sai ya damu, ya karkatar da kai ya ce, “Halimah, ba ki amince ba ko? Na rantse da Allah ba ni da niyar cutar ki, hakan nan na samu kaina da son taimakon rayuwar ki da tausayin ki, amma ban sani ba ko ke har yanzun tsoro na ki ke ji ammaâ€?.â€? Ta katse shi, “By the way, in na amince ka taimake nin, ta wacce hanya ka ke ganin za ka taimake nin?â€? Ya yi shiru, shi kansa bai sani ba, amma can a karkashin zuciyarsa wani sako ne mai nauyi da ba zai iya fadi yanzun ba, in ya yi hakan ya yi garaje, akwai bukatar yin dogon nazari a kan al’amarin, ya binciki Addinin ta, usli, halayyar ta da iyayen ta don kar a kuma komawa ‘yar gidan jiya. Ya ce, “Nan da jibi ni da matata za mu koma gidan mu da ke nan garin, zan roki Hajiya ta ba ni ke a zuwan za ki ke taimakawa Ihsan a kicin, sai in maida ke makaranta, don zuciya ta na ba ni yakinin cewa kina da ingantaccen ilimin da ki ka fara ba ki kai karshensa ba, haka ne?â€? Ta yi murmushi kawai, sai dai tsarin sa kwata-kwatan bai yi mata ba. So take ta ce ya kai ta Makarfi, ta ga mahaifiyar ta ko da sau daya ne ya fiye mata duk wani taimamko da za a yi mata a duniya, ko da kuwa shugabancin kasar za a bata baki daya. Amma in ta fadi abin da ke zuciyarta ba mamaki ya dago ainahin ko ita wace ce? Wanda ita ba ta fatan hakan, ba don komai ba sai don mutuncin Daddy din ta. Za ta ci gaba da hakuri, har zuwa ranar da wannan ‘daukinâ€? na Ubangiji da aka kwadaitar da ita zai zo daga Allah, a lokacin da bata zata ba. Ta daga kai ta dubi angogon kicin din ta ga tsawon awoyin da suka share a zaune. A firgice ta mike ta soma hada kayan girki duk jikinta rawa yake ta ce, ‘Ka ga ka sa na yi lattin abincin rana, ka yi hakuri don Allah, na gode kwarai da kulawarka, amma bana bukatar kowanne taimako rather than in ga Mamana da ban san inda take ba.â€? Ta dauki bokiti ta fita. Dr. M.A.B ya dade yana kallon ta har ta kule cikin store yana kallon inda Ubangiji ke yin halittar mace har mace, wai a matsayin ‘yar aiki? Irin su sun fi dacewa da gidan auren so da kauna, inda za a so su a tarairaye su a kuma kula da su cikin tsantsar soyayya da jin dadi. Tafiya take illahirin jikin ta na rangaji tamkar reshen bishiyar da iska ke kadawa. Bai taba ganin macen da ta sa shi jan ido kamar wannan ba, bai taba katari da macen da ke burge shi ta kowacce siga, magana, tafiya, nutsuwa, murya da yauki na halitta kamar wannan ba. To ko dai idon shi ne shi kadai? Dole ya kara likewa matar har sai ay ginawa kansa matsayin da ita ma za ta ji shi har bargo da kasusuwan ta tamkr yadda yake ji game da ita a yanzun. Abin da ya lura da shi shi ne yarinyar wata irin murdaddiya ce hakan nan maza ba sa gabanta sam-sam, kai da alama ba ta san ma mene ne son ba; naive and innocent. Tabbas wannan wata kyauta ce daga Indallahi a dirowar shi Nijeriya kuma rabon soyayyar ta ya tunkudo ruhin shi gida. Bai taba tsintar kansa a irin wannan yanayin ba, wai son mace? Har cikin bargo da kasusuwan sa? Jin sa ya yi duk ya wani yamutse, wani sabon nishadi na bi shi (ya ma manta ya taba aure kuma yana da shi din). To bari mu bi su mu gani. A Makarfi ya yi sallar Azuhur shi da Daddy da Baffansu, kuma Al’ameen shi ya yi wa mahaifin shi bikon Antin shi. Kar ki so ki ga farin cikin da Baffan su Malam Sani ya yi, domin dama chairman din su na nan Makarfi ya matsa mai da maganar Saratun. Ba su baro Makarfi ba sai karfe hudu na yamma bayan komai ya daidaita. Ita kanta Antin ta amincewa ranta gidan su Zarah ne kadai za ta iya zaman aure. Babban farin cikin ta ma tarbiyyar Intisar din ta ya dawo hanunn ta kenan. Sai dai ta ce tana bukatar lokaci a kalla wata guda domin ta kimtsa a hankali, wannan ko odar Sharifi Mal. Sidi ne, domin ya ce sai ya shirya su sosai domin kishiyar ta hatsabibiya ce, kuma ya ce yana kokarin karya na Saratun ta da ya ce har ya fi nata tsauri da wahalar karyuwa, amma Alhamdulillah ya san ko a lokacin Daddyn na cike da tunanin, ko a wane hali take ne? Don haka Al’ameen sai karfe tara na dare ya shigo gida a gajiye lis don sai da ya gama da ministry tukunna, an amshe shi da dukkan yabo da izinin yin aiki tare da su ma idan yana so, gami da izinin gina asibitocin duba lafiyar kwakwalwa a ko’ina ya so a Nijeriya. Bai samu zuwa Garki wurin su Ihsan ba, wannan ya masifar kara fusata Ann, don yau kwana uku kenan suna zuba idonsa su kafa masa dokokin rikon Ihsan, amma ko wayar sa babu balle kafar sa. Ita Ihsan din ta neme shi ta tarar kwata-kwata ya rufe wayarsa ma. Baya jin gajiyar da ya yi da yunwar da ke tare da shi za su hana shi neman Halimah, (sunan da ya rada mata kenan bai kuma damu da sai ya ji sunan ta na hakika ba, tunda ba ta son fadi ai dole wata rana zai ji ne). Ba ya jin zai iya barci bai yi tozali da wannan fuskar mai zati ba, baya jin zai iya barci bai ji wannan muryar mai katse duk wasu jijiyoyi masu gudanar da jini a jikin sa ba. Shi kadai ya san me yake ji game da ita. Hakan nan ya wuni zungur da tunanin da baya da makama, ya tabbata son Halima ne ke spreading all over his body (Kurdawa cikin kowanne sako a jikinsa). How much do you like this story? 5/7/22, 13:10 - Ummi Tandama😇: ____________________________ *âœðŸ? SIRADIN RAYUWAâœðŸ?* Book one *@Takori* Page5ï¸âƒ£ Sannu-sannu yake takun shi mai karfi irin na mahaifin shi, bai san dakin da take kwana a gidan ba, amma zuciyarsa ke ba shi tana kicin din ta. Gidan Bello Makarfi na garin Abuja irin tafkeken gidan nan ne (family house) da wani sai ya yi wata bai ga dan uwansa ba, in har ba shi ya neme shi ba, don haka ba wanda ya san Al’ameen na zuwa kicin, in ma da wanda ya sani yake kuma kallonsa da duk wani takunsa to Dela ce, shugabar ma’aikatan gidan. Duk wani shige da ficen Al’ameen a kan idonta ne, tana kuma leken duk abin da ke faruwa cikin kicin din ta labulen dakinta sai dai ba ta iya jin abinda suke cewa. Ile kuwa tsammaninsa ya zama gaskiya, sai ya ganta kwance bisa tabarmarta, ta kifa wani littafi a fuskarta tamkar tana barci, sai in mutum ya lura ne sosai zai gane ba barcin take ba, ta dai yi karatun ta gaji ne ta afka kogon tunani; deep in thought. Ya tsaya bisan ta ya yi murmushi ya ce, “Halimah yau in na ce da ke Assalamu alaikum za ki amsa?â€? Ta zare littafin daga fuskarta, kana ta mike zaune cikin nutsuwa, muryarsa ta gane amma shi bata gane shi ba kasancewar ba kasafai take fuskantar mutane da daddare ba, ta zauna sosai kawai bata ce komai ba. Ya ja kujerar robarta kwaya daya tal da ke cikin kicin din da take zama don yin ‘yan yanke-yanke ya zauna idanun shi a kanta, ya lura idanunta sun yi jazur, tamkar an watsa masu barkono duk sai ta sake ba shi tausayi, ya sadda kai yana duban yatsan kafarsa, a tsammanin shi kukan tuna iyayenta ta yi shi ne har suka yi hakan. Bai sani ba, littafin take so ta karanta ba ta iya bambance rubutun da ke ciki, domin tana da lalura a ido, shine har suka yi hakan. A ransa ko ji yake kamar ya tsinewa wannan baban nata. Ya dago ya sake duban ta, ta yi shiru, ta dage kai sama tana kallon ceiling tamkar mai son irga adadin taurarin da ke can saman sa. Ya ce, “Kin san ko karfe nawa yanzun ki ke zaune still a kicin?â€? A nan ne ta yi masa magana ta ce, “Yanzu zan tashi dama.â€? Ya ce, ‘Halimah, idanun ki sun yi ja kwarai, what are you crying for? (Me ki ke wa kuka).â€? Ta ce, “Ni fa ba sunana Halima ba, haka kawai ka lika min wani Halima, kai na lika ma sunan wani duk da ban san sunan ka ba?â€? Ya murmusa kadan don ya lura son jin sunan nasa ke cin ran ta ya ce, “To ya sunan ki?â€? Ta yi shiru ta kyale shi sai da ya sake maimaita tambayarsa nan ma ta yi shiru, ya ce, ‘O.K, as long as you wish (zuwa san da ki ka ga dama), ki gaya min sunan naki, zan kira ki Halimahhhh, in ya so ran da ki ka yi niyyar gaya min sai na kira ki da sunan naki.â€? Ta ce, ‘Sunana mutum mana.â€? Ya ce, ‘Of course, we are all humans, (Dukkannin mu mutane ne), amma akwai wani suna kebantacce ga mai shi, wanda za a kira sa da shi ya amsa. Kin ga kenan tunda kowa mutum ne, in aka kira kowa da hakan ba za a bambance da wa ake ba. Kin ga kamar ni sunana Al’ameen amma mutum ne?â€? Yadda ya maida kansa wani yaro shi ma kamar ta ya bata dariya, haka maganar shi ta matukar bata dariya sai ka ce wani malamin Hausa, sai ta saki wani lallausar murmushi da ta dade rabon ta da yi tun kafin barin Faisal kasar Nigeria. Bai taba ganin ta yi murmsuhi ba, ashe kyawun ta ma na cikin murmushinta ne? Gaba daya jikinsa ya mace lis, wata irin kasala ta saukar masa wadda ta kai shi ga runtse ido da karfi kada ya yi abin da ba daidai ba. Babu wata gaba da bata amsa kaunar yarinyar a jikinsa ba. Bai taba jin irin wannan yanayin ba a duk matan da ya taba mu’amala da su cikin duniya hatta matarsa. Wannan shi ne ake kira natural love kenan da bai taba tsintar kansa a ciki ba? Ya sa hannu ya tallafi goshinsa ya sunkuyar da kai yana kallon kyawawan yatsun kafar ta tamkar na Balarabiya. Lokacin ne idon sa ya kai ga littafin da ta yasar a gefe guda, ya kai hannun shi ya dauka ya duba sai ya ga an rubuta Essential Biology, ya soma buda shafukan littafin anan ya ga ta yi alama a wani waje da wani dan karamin hoto daukar Saudiyyah mai dauke da fuskokin wasu kyawawan yara mata guda biyu suna kyalkyala dariya, ya jima yana kallon hoton ya ce, ‘Duk da ban sani ba, amma wannan kamar ta gaya min yaran nan kannen Halima ne?â€? Ta ce, “Ko daya, makaranta kawai ta hada mu, amma mutane da dama ba sa gane hakan har Mamar su ma kamar mu daya.â€? Ya aje hoton gefe daya ya ce, “Ya sunan su?â€? Ta ce, ‘Siririyar Hidayah kenan mai jikin kuma Hunainah, ni da su muna son juna sosai kuma mun shaku musamman Hunainah.â€? Ya ce, “Me ki ke karantawa cikin littafin nan?â€? Ya kashe wancan zancen kenan, don da alama in za a kwana ana yin sa ba za ta gaji ba, da gani ba karamar kauna take yi masu ba. Ta dubi littafin ta ce, “Duk gaba daya amma yanzun ba karatun nake ba.â€? Kamar da wasa ya ce, “Yanzu idan na tambaye ki abinda ba ki zata ba cikin Biology za ki iya amsa min?â€? Ta ce, ‘Na jima da barin makaranta, sai dai bana jin akwai abinda na manta, go on.â€? Ya yi murmushinsa (broad smile) kamar kullum, ya gyara zama har da gyara murya ya kuma sarke kyawawan yatsunsa cikin na juna, da gani ka ga malami mai fasahar koyarwa, ya canza harshe kwata-kwata ya ce, “Zan yi miki tambaya a cikin wannan darasin na Supporting Tissues in Plants.â€? Ta yi murmushi, hakan nan ta ji ya burge ta, bata taba jin mutumin da ke karya turanci ziryan with American accent hakan ba, ko don wannan lafiyayyen turanci ai ta amsa masa tambayoyin sa itama. Ta ce, “Kai na ke saurare.â€? Ya ce, ‘supporting tissuesâ€? nawa ne in plants?â€? Ta daga yatsun ta ‘sabbab, ibham da wusda da na karshen ta ce, “Hudu.â€? Ya ce, “Lissafo man su.â€? Ta ce, “Ka ga akwai turgid-parenchyma, akwai Sclerenchyma, Collenchyma da dylem.â€? Ya girgiza kai ya ce, “Wanne suna aka san dylem tissue da shi bayan dylem?â€? Ta ce, “Ana kiransa wood (Katako).â€? Ya ce, ‘Ta yaya dylem ke ba da support din shi ga plants?â€? Ta ce, “Dylem yana bada support din shi ta hanyar bai wa tsirrai suffa ne.â€? Ya ce, ‘Shi kuma parenchyma fa?â€? Ta daga kai sama ta ce, “Shi parenchyma sai a yayin da vocoules ke cike da sap ya ke bada karfi ga plants, ya kuma kare su daga barin karyewa da wuri.â€? Ya dube ta, thoroughly ya ce, “Fata, rubi nawa ce a jikin dan adam?â€? Ta ce, ‘Uku.â€? Ya ce, “Wannan dabbar kadangare a wane aji yake?â€? Ta ce, ‘Reptile ne.â€? Ya ce, “Kada fa?â€? Ta ce, ‘Ai shi ma haka.â€? Ya rike baki ya ce, “Gaya min sunayen cuttutukan hanta guda biyu.â€? Ta ce, ‘Akwai cirrhorses, akwai kuma dirrhorses.â€? Ya ce, ‘Tumatur, a cikin fruits din mu a wanne aji yake?â€? Ta yi murmushin raini ga tambayar ta ce, ‘Berry, of course?.â€? Ya ce, ‘To mango fa?â€? Ta ce, “Drupe.â€? Ya aje wadannan kananun tambayoyin a gefe, ya kara sarke hannun shi cikin yatsun shi ya ce, “Me yasa fatar tsoffi ke tattarewa?â€? Ta ce, ‘Saboda jini baya gudu a jikin su?â€? Ya ce, ‘Yes, ta wacce hanya kyankyaso ke numfashi?â€? Ta ce, “Tracheal system.â€? Ya dan kalmashe murya tabbacin zai kure ta anan ya ce, ‘Gaya min in zaki iya chemical formula na magnesium sulphate?â€? Ta daga kai sama, tamkar mai karantowa a ceiling, ba tare da ta sauke kannata ba ta ce, ‘Na sani, MgSO4.â€? Ya ce, ‘Na water fa?â€? Ta ce, ‘ana kiran sa H20.â€? Sai ya yi shiru yana duban ta. Allah kadai ya san me yake tunani, ba zai wuce yara irin su ake nema ruwa a jallo domin farfado da harkar lafiya a Nigeria ba, amma wai uban ta ya sai da ta? Kai ba zai taba yarda da wannan karyar ba, koma dai ya take ne ya amince da abinda zuciyar shi da gangar jikin shi ke so ba tun yau ba, a tun ranar da ya soma dora idanun shi a kanta, ya amince zai taimake ta da dukkan karfinsa, zuciyarsa, lafiyarsa da abin da ya mallaka in har suna taimakawa. Baya bukatar tambayarta makarantar da ta yi, ya tabbata koma ina ce to ba ta kananan mutane ba ce ba, ba kuma ta dakikan dalibai ba. Ya dago sannu a hankali ya dube ta, cikin wani sabon sauyi a tattare da shi da muryar shi gaba daya ya ce, “Kin ki gaya min gaskiyar labarin ki, kin ki gaya min ko ke wace ce? Amma Halimah ko ya ki ke, ko ke wace ce am sorry to sayâ€? I’m in love, shin za ki iya aure na?â€? Ko motsi ta kasa, babu wanda ya taba yi mata magana da irin wannan muryar mai kashe duk wata gaba mai motsi a jikin dan adam. Ba ta taba jin wani abu wai shi emotional disturbance ba sai yau. Bata taba jin ta takura a gaban namiji ba sai ko yau a gaban Al’ameen Bello. Tamkar an daure mata harshe da baki mai motsi ya fidda sauti ko kafafun ta ta kasa motsawa, son shi ke kara shiga kowanne lungu da kowanne sako na gangar jiki da tsokar zuciya kwaya daya da ta mallaka cikin tsakiyar kirjinta, ba tun yau ba, tun ranar da ta fara ganinsa. (A irin wannan yanayin ne ake cutar yara mata, musamman a shekaru irin nata (teenage). To amma Al’ameen ya amincewa kansa son Allah yake mata, babu wani tunani na banza ko kankani game da ita a tare da shi. He loves her because he loves her kawai. Ya tabbata itama ta ji son sa tun daga kokon rai har kwakwalwar ta ita ma, amma so yake yi ta fada masa da bakinta ta amince, don baya so ya takura ta, natural love yake nema don ya tsani love out of pity kamar irin nashi da Ihsan kenan, wanda yake jin dadin bangare guda takurar daya bangaren. So kawai yake ta ce ta amince, shi kuwa ko sama da kasa za ta hade sai ya aure ta ko da Hajiya za ta ki amincewa. Ya dago fuskarta, ta rintse idon ta da karfi, ya ce, ‘No, magana za ki min Halimah idanun ki widely opened (a bude tangararas) cewa kin amince ki aure ni?â€? Baki daya jikinta rawa yake, ta tabbata ba ta da mafita ban da ta ce ta amince din. Yadda numfashin su ke dukan na juna bata taba zama kusa da wani namiji so closed hakan ba, hakan kuma ba karamin sauyi ya kawo a gangar jikinta da ma bugun zuciyarta ba, don haka ta bude idanun ta da suka yi jawur tun tuni ta ce ta amince. Suka yi wa juna lallausan murmushi a tare. Sai da ya ga shigar ta dakin da suke kwana ya sake yin murmushin, ya juya. Yau kam ya yi barci mai kyau cikin kwanciyar hankali irin wanda bai samu yi ba a tun ranar da ya baro Miami. Baya ko tunanin gagarumar rigimar da yake shirin tayarwa. Washe gari da safe ya je gaida Hajiyarshi take nuna mai bacin ranta na kin zuwan shi Garki wurin su Ihsan ta ce, “Wannan ai rashin mutunci ne Aminu, jiya Daddy ya je ofishin Babanta sun gaisa ya ce abin da ka yi ya bata masu rai duka, yaya muna cikin gari daya amma a ce gaisuwa wannan ta gagara balle tahowa da itan bayan ba abin da ba a kammala a gidan ba, wannan ai wulakanci ne.â€? Ya shiga ba Hajiyar shi hakuri yana gaya mata matsalolin da ya kashe wadanda suka hana shi samun lokacin kansa, amma ta ki sauraron shi ya ce, ‘Ita ma Ihsan din ta sani saboda transfer din aiyukan su duka amma yanzu da ya karya kumallo (breakfast) can zai fara zuwa kafin ko’ina. Ina! Hajiya ta ki ta ce yanzu-yanzun ya tashi ya tafi ya ci abincin a waje, har tankado keyarsa ta yi daga kofar dakinta, sai ya yi murmushi ya lalubi ‘yan mukullayen motarshi ya tabbatar suna nan cikin aljihun shi sai ya fita. Zuciyarsa cike fal da jin haushin rashin ganin kyakkyawar fuskar Halimar shi a safiyar. Tafiya yake sannu-sannu bisa kyawawan titunan birnin Tarayya marasa tudu balle gargada. Dressing din da ya yi a yau ya burge kwarai, ga wani dan siririn farin gilashi da ya manna tamkar Ba’indiyen nan Bobby Doel, kira’ar (Khusairi) yake bi cike da nishadi, ya san yau zai gamu da fushin Ihsan din shi da ke ba shi dariya, don da an dan kissing din ta shi kenan ya kare, ko ko don tana son shi ne? Bai sani ba. Yana bin adireshin da ke jikin katin bai sha wuyar gane gidan ba, tun daga gate ya tabbatar su Ihsan kam ana ji da naira. Maigadi ya yi mai iso Ihsan ta ba shi izini ya kai shi can babban falon saukar bakin babanta. Ta samu Ann tana waya ta ce, ‘Kin ji Al’ameen ko sai yau ya waiwaye ni?â€? Ann din ta rufe wayar ta ta dauki malafarta ta kifa a ka, ta ce, “Fara bashi abinci tukunna, don daga ji sammako ya doko kada ya ce muna tsiya.â€? Ta yi dariya ta ce, “Kai Ann, ba ki da dama. Amma ai ko kofar gidan mu mutum ya kalla ya san ko jikokin-jikokinmu, su da tsiya sai da su ji ana labarinta.â€? To amma ita kanta Ihsan ta san wannan ba halin Al’ameen din ta ne ba, rainawa mutane kura, ta dai fada ne kawai don ta ga Ann da alama ran ta ya baci da Al’ameen sosai. Ta koma kicin ta bawa yaron su Ike umarnin abinda zai kai masa matsayin karin kumallo (American breakfast) kamar yadda ya fi so a kullum. Daga nan toilet ta yi ta fesa wanka na musamman ta zuba fararen undies kafin ta daura wani masifaffen tattausan lesi cotton fari sol, mai adon kala-kalar duwarwatsu. Wannan less da shi da babu duk daya don manyan hudojin da ke jikinsa sun wuce misali amma kudi na gugar wuri har naira dubu saba’in kudin mu na nan gida Nijeriya ta saye shi a London, ba don komai ba sai don Al’ameen mutum ne mai son farin abu, ya sha gaya mata in ba farar kwalliya ta yi ba, ba ta burge shi, kuma ya kan so ta don farin ta ba don kyan ta ba. To wannan ne dalilin da yasa ta sanya shi, haka ko ‘yanmatan Al’ameen jar fata sun fi yawa don dai Allah ya so ta da shi ne kawai duk da yake ita din ma fara ce, amma fari ne na jin dadi ba na halitta ba. To wannan na daga dalilin da yasa ta fiye farar kwalliya don ta lura Aminu fa sai da lallami ake samun shi. Tun can ba ta daura dankwali bare yau da kwalliyar ta musamman ce. Hakika ta azabtu da rashin ganinsa na ‘yan kwanakin nan, domin ba su taba kaiwa tsawon wannan lokacin ba sa tare ba, tun auren su, ko ofis tana like da kayan ta saboda nurses masu yi masa kallon da bai gamsar da ita ba. Ihsan kenan. Takalmi flat fari sol dan Thailand ta zura kafafun ta dan dagwas, turare mai suna turare ita kan ta ba ta san kala nawa ta fesa ba, musamman collection na Calvin Klein da Dior, ta yadda har ba za ka tantance kamshin wane turare take ba, wannan duk yana daga cikin koyarwar Al’ameen Bello, domin shi mutum ne mai masifar son kamshi, baya jin kyashin saya masu turare ko na nawa ne. Musamman zai je Paris don kurum ya sayo masu turare, wadannan na daga cikin dalilan da suka sa har kullum take son shi, take kuma kara kaunarsa a kowanne dakika, domin hakika shi din special ne, haka komai nasa na musamman din ne. Tun haduwar su bata kara duban wani da namiji a duniya da sunan so ba, shi kadai take so, shi kadai take sha’awa, shi kadai ke burge ta, hakan nan shi kadai ne namijin da zai iya yi mata kowanne irin wulakanci ta shanye. Dr. Ihsan kenan. Cikin takun kasaita ta wuce Ann ta ce, “Ba za ki je ku gaisa ba Ann?â€? Ann din ta dube ta sama zuwa kasa ta ga yadda ta wani hade kamr mai shirin zuwa dinar babbar aminiya, wani haushi ya kama ta don ita so take ta kashe auren kowa ya huta, don ba ta ga yaron da ya isa ya wulakanta gudan jinin ta ta kyale ba komai tashen nairarsa kuwa, kuma ko dan uban waye shi balle wani shirmen banza likitan kwakwalwa, amma ba ta son ta bata farin cikin Ihsan, don ta lura still tana son mijinta sai ta bi ta da siyasa. Ta juyar da kai kawai ta ce, “Ki je kawai ki ji wadda ya zo da ita, zan zo in raina ya yi sanyi, don har yanzu raina a bace yake. Kin kuma sanni ban iya boye bacin raina ba.â€? Ta kadai kai ta fita fuskar nan ba annuri sam, ta shiga taka matattakalar da za ta sada ta da falon, kasancewar ainahin ginin falon bakin Dr. Argungu a kasan gidan yake tamkar ka shiga rijiya ne ka tadda sabuwar duniya. Ta sa kai ba ko sallama. Aminun shima daman ya cika fam, da shanya shin da aka yi fiye da awa biyu kamar wani mai neman aiki a bankin su? How much do you like this story? 5/7/22, 13:10 - Ummi Tandama😇: ___________________________ *âœðŸ? SIRADIN RAYUWAâœðŸ?* Book one *@Takori* Page6ï¸âƒ£ Tsaye yake kikam, ya hade hannuwan shi a kirji yana kallon tangama-tangaman hotunan ta kamar ta fito ta yi magana da aka manna a kusurwa biyu na falon tabbacin ana ji da Ihsan kenan, kuma ita daya kenan a gidan tamfar rai ga iyayenta. Ko bude abubuwan da aka jera masa bai yi ba balle ya kai ga ci. Ta samu kujera can nesa da shi ta harde, ta dauki remote control ta karo karfin A.C ko sannu da zuwa ba ta ce masa ba balle ci kan ka. Shi ne ya gaji da shirun ya bara, ya dubi agogon hannun shi Jovial ya ce, “Saboda Allah Ihsan haka ake karbar baki ku a gidan ku?â€? Ta sake tunzura ta ce, ‘Da aka yi me?â€? Ya ce, “Kin san awanni biyu kenan kwarara, ina zaman jiran fitowar wani a cikin ku, amma shi ne sai yanzu ki ka ga damar fitowa?â€? Ta yamutsa fuska ta ce a zafafe, “Aminu, har kana da bakin gaya min haka? For God’s sake, yau kwanakin mu nawa a garin nan amma ka nuna wa iyayena ba ni da wata daraja a idon ka ba ka kuma damu da ni ba, shi ne kuma har za ka nemi gayan magana? Wai haka muke karbar baki, to ni ko iyayena da wa ka ke?â€? Ta tsatstsare shi da ido. Al’ameen ya san ba shi da gaskiya, kuma ko a wurin Allah ne ba shi da ita. Dole ya sauke nashi temper n ya samu masangalin kujera ya rage tsawo, ya sanya hannu cikin aljihu ya zaro wayar shi da ke ta tsuwwa a cikin aljihun kaftanin shi, ya dade yana magana da aminin shi Rehab wato babban likitan Meritime yana gaya masa irin muhimman ayyukan da suka gabatar ne a kwanakin, ya ce ya yi kyau ya kuma yaba komai, ya gaya masa akwai motocin sa har yanzu suna port bai san ba a auno su ba, sai jiya ya je da kansa ya auno masa ta jirgin ruwa, amma ta Nijar za su biyo don ba jirgin kaya tun bayan da suka taso, don haka ya je ya fiddo su a Yamai. Suka yi sallama ya maida wayar shi aljihu. Ya dubi Ihsan da sassanyan kallo ya ga ko kallon shi bata yi, ta maida fuskar ta can wani gefen daban bayan ta daure ta iya daurewa kamar bata san Allah ya yi ruwan tsirar shi ba ma, ransa ya sosu, amma sai ya yi murmushi ya ce, “Ihsan kenan, dadi na da ke ba kya tsayawa ki ji uzurin mutum sai kawai ki kama fushi, amma ai ke ma dai kin san I missed you very-very much…â€? Ya kira kalaman cikin tattausar muryar da ta kusa sa ta gyangyadi, amma da yake tana son ta nuna fushin nata sai ta cije ta kyabe baki a lokaci guda kuma tana girgiza kafa daya kan daya ita ala dole fushi take, duk sai ta ba shi dariya, ya mike har inda take ya mika mata hannuwan shi masu matukar taushi alamar ta tashi su yi sulhu, amman sai ta noke cikin jan aji irin nata, sai ya russuna ya kama hannayen ta duka biyun ya mikar da ita tsaye, suka fuskanci juna cikin ido, ita kallon haushi take masa shi kuma kallon I beg your pardon. Ta ce, “Me ye haka?â€? Amman can karkashin zuciyar ta hucewa take yi, tana kuma kara son mijinta a kowanne dakika, duk wata hanya da ya san zai bi ya wanke laifin shi a zuciyar ta ya san shi, duk da ta san kaunar da ita take masa ta rinjayi wadda yake mata, amma yana kokari a koyaushe ya nuna shi din mai son ta ne, mai gudun bacin ran ta ne. Bare yanzun da ta yi kewarsa, fiye da yadda bakin ta zai iya fassarawa, sai ta bada kai bori ya hau. Sun dade cikin farantawa junansu tamkar suna gidan su koko bakin beaches na Miami, kafin su zauna su fuskanci juna, jikin ta a barin kafadun shi na dama, ta soma share hawaye da bayan hannu duk ya bi ya rikice ya ce, “Me ye kuma?â€? Ta ce, “Anya Al’ameen ba ka gamu da wata kana so ba a dawowar mu? Wace ce Halimah da ka ke kirana da sunan ta yanzun?â€? Ya ji gabansa ya fadi damm! Kwata-kwata ya manta da wa yake tare, ya mance a inda yake, ya mance abin da yake yi, ita kadai ke yawo a ransa, ita kadai ke yi masa gizo a kowanne kiftawar ido. Amma ai namiji ne, tuni ya waske ya sha kunu ya ce, “Da aka yi me fa?â€? Ta yi tsaki ta ce, “Nufin ka ba na ji sosai ko me? You ‘ve both changed, u ren’t my real Ameenu (Gaba daya ka canza kai ba Aminuna da na sani ba ne). Ya ce, ‘Ashe? Baki na yi ko fari?â€? Ta ga yana neman ya raina mata hankali, sai ta yi murmusin takaici ta ce, “Man, kada ka yi fooling dina man? Be frank, duk ka canza, ka yarda ko kada ka yarda, na ji ka ba a yadda na saba jin ka ba, na rantse I’m smelling something trouble (Ina sunsunar wani abu mara dadi a tare da kai). Inda Allah ya cece shi shi ne kafin ya motsa bakin shi don shirya amsar da zai ba ta, Ann ta yaye labule ta shigo, shi ne ya matsa gefe cike da haushi, me ake da kafiri? Babu ko sallama balle neman aminci ga wanda ka taras? Ita ko Ihsan ba ta ko motsa daga yadda ta ke ba don ita kanta ba ta ji dadin abin da mahaifiyarta ta yi ba, ai ko bature yana kwankwasa kofa, ta san halin Al’ameen din ta sarai daga yau baya kara girmama ta, don ya sha ce mata babu dabba kamar mai shiga waje babu sallama. Ann ta dade tana kallon su cike da haushi kaman ta rufe Ihsan da duka ta ce, ‘Get out stupid.â€? Sum-sum-sum ta fice tana sharar hawaye, ita fa tana son Aminu, ba kuma za ta yarda a kashe mata aure ba, ita kadai ta san wahalar da ta sha kafin ta same shi. Sai dai a yau ma kamar kullum tana shakkar kaunarsa gare ta, amma na yau ya fi na kullum. Duk da cewa bai nuna mata wani abu ba ita dai zuciyar ta na ba ta yakinin a lokacin da suke tare hankalin shi baya tare da ita, musamman saboda sunan da ta ji ya fito cikin kuskure daga bakinsa, da kyar in ba wata ya gano yana so ba, sai ta kara barkewa da kuka. Ta samu kujerar da ke fuskantar shi ta zauna ta ce, “I’m sorry, na dauka wajena ka zo da babanta?â€? Ya ce, ‘Oh yes, Ma’ama, me too, am sorry, ni da Ihsan mun yi missing juna ne sosai.â€? Ta dube shi a lalace, sai dai fa ita kanta na mamakin wai wannan tsalelen ne mijin Ihsan din ta? Ko ita ta samu miji kamar shi ba haukan da ba za ta yi ba a kansa, sai ba ta ga laifin Ihsan ba ko kadan, amma Addinin shi ne ba ta ra’ayi, kuma tana son Ihsan da auren manyan mutane ne irin baban ta ba wai yara professionals irin su Aminu ba, yo me na sama ya ci bare ya bai wa na kasa? Ta zuki iska ta fesar ta ce, ‘Haka ne? Ni ko sai na dauka ba ka son ta ne.â€? Ya ce, “Ki yi hakuri Ma’ama, na dade ne rabona da gida, shekaru goma sha biyar, na dawo na tarar da uzururruka da yawa da suka sha gaban kaina, in kin duba fa kwata-kwata ko sati biyu kwarara ba mu hada ba a kasar, ita kan ta Ihsan ta sani ni ne babba a gidanmu, so kin ga ko family dina bai isa a ce na gama da su within a week ba, ku yi mun uzuri, rashin zuwana baya nufin tozarci ko izgili a gare ku don ko jiya babana ya samu Dr. A ofis, so ki yi hakuri.â€? Ta gyada kai cikin gamsuwa da wannan ta ce, “Na lura dai kana son ci gaba da zama da Ihsan bayan wanda ku ka yi a Miami bai isa ba, to ina da wasu sharudda da zan gindaya maka a gaba, idan har ka amince da su to ko a yanzu sai in kira Ihsan ku tafi.â€? Ya ce, ‘Ina jin ki Ma’ama.â€? Aminu fa daurewa kawai yake yana bin ta da yadda take so, ba don komai ba sai don nuna yes, yana son Ihsan, ya kuma san bai kyauta masu ba, amma shi ne za su gara shi kamar wata taya don kurum ya ce yana son ‘yarsu, su din banza? Ya dai kanne bai nuna ba a fuska. Ann ta gyara zama ta dube shi sosai ta ce, “Da farko dai ni Christian ce, karewa ma Babana Pastor (priest) ne babba a sanda yake raye. To a bisa tsarin mu tun Ihsan na karama tana bina church kuma har ta tafi America ba ta daina ba, ba zan ce Ihsan Kirista ba ce tun da kuwa baban ta ya dage ta yi Addininku, kuma nima na ga tana so sosai, don haka ba ruwana da wannan. To yanzu da ta dawo ma lallai ne duk Lahadi kabar ta ta je chochi ta ji wa’azi, ba zan ce kada ta yi sallar ku ba, wannan bai shafe ni ba, amma chochi dole ne ta je duk ranar Sunday. Abu na biyu kuma shi ne na san ku Hausawa ba ku dauki mace da wata daraja ba, da kun yi ‘yan shekaru da ita shi kenan ta gama amfani, sai a auro wata a wulakanta ta, to Ihsan ita kadai ce da mu, ba mu da wani kwai a duniya sai ita, kenan ba za mu zuba ido mu bari a wulakanta ta ba a ko’ina, dole mu kula da farin cikin ta, don sai tana farin ciki ne mu ma za mu kasance cikin dawwamammen farin ciki da kwanciyar hankali. Don haka in har kana son ci gaba da zama da Ihsan sai ka rubuta min a rubuce ka yi alkawari tsakaninka da Allahn ka daya cewa ba za ka kara auren wata mace bayan ita ba, ban hana ka harka da mata ba don na san matashi kamar ka ga sura uwa-uba naira, ba za ka lamunci rayuwa da mace guda ba. Sharadi na karshe shi ne ban yarda ka hana Ihsan yin duk abin da take so ba, don tana son ka, tunda mu ma ba ma hana ta yin son ranta, idan har ka amince yanzu rubuta min in kira ta ku tafi. Ganin baban ta bai zama lallai ba, don bai isa komai ba.â€? Al’ameen na zaune tamkar sassakakken gunki yana sauraron yadda ake tsara mai rayuwar kafirci ziryan a gidan auren shi. Tab, ba zai taba amincewa ba, don bai tashi ya ga ana hakan a gidansu ba, bai ga inda Daddy bai isa komai ba a gidansu, au shi ne shi ma za a nuna mai bai isa komen ba don kawai ya ce yana son ‘yar su? Niyyar shi da kawai ya mike ya tafi ya kyale ta sai sun neme shi don kan su, sai kuma ya yi tunanin ai kunyar marar kunya asara ce. Ya ce, “Am, Ma’ma, bana nufin izgili, raini ko kaskanci ga maganarku, illa ina son in miki bayanin da maybe, ita Ihsan ba ta yi miki ba. Da ni da Ihsan, duk mun hadu a Jami’ar Miami ne ko kuma na hadu da Ihsan na karuwancin ta ne ko ko in ce, dukkanin mu watsewar rayuwar turai ta hada mu, ba wai cikin mutunci na aure ta ba a hannun iyayenta da za’a kafa min wasu sharudda marassa madafa bayan auren da muka yi ba da sanin ku ba ko wasu specific hujjoji, da abin mu ku ka gan mu. Zan iya cewa ma na taimaki Ihsan ne daga gurbatacciyar rayuwar da ta jefa kanta a Florida, ashe in ba a gode min ba, ba za a wulakanta ni ba, a kan me yanzu don mun dawo cikin ku za a nunan iko da matar da na biya sadaki, a gaban shaidu? Maganar zuwa church ma kwata-kwata ban amince ba, yaya tana sallah za a ce min ta je chochi yin wa’azi, sai dai in itama Ihsan Kiristar ce short and simple, amma ba a hada Addinin mu da kowanne addini sai dai in completely ta koma addinin ki ne? Sai maganar aure. Ni dai Aminu Bello Makarfi, Musulmi ne gaba da baya, Addinin mu ya ba mu damar auren mata daidai har hudu in har muna da hali za kuma mu iya adalci a tsakanin su, domin kare kan mu daga dattin zina. Don haka ba zan iya wannan alkawarin ba, idan na yi niyyar in kara aure zan yi. Na ji kina cewa wai ina da chance na neman mata a waje alhalin ina da aure, to a Addininmu babu wannan damar, ko na Kiristan ba san inda ya baku wannan damar ba. Na karanta bible din ku ciki da bai din sa ban ji wannan nassin ba, (adultery)? Wancan ma da muka yi a turai mun tuba, duk rudin kuruciya ne da rudin shaitan, amma a yanzu dube ni am a perfect gentleman (cikakken mutum ne) na wuce stage na wannan shedanar. Maganar in bar Ihsan ta yi son ran ta? Like how? (Ta yaya?) Ban gane ba! Kada ki manta ina auren Ihsan ne fa ba fa ita ke aurena ba, don haka tilas in ta yi ba daidai ba in gyara mata. Mu a Musulince namiji ke ruling matar shi ba wai matar ke ruling din shi ba.â€? Ya yi shiru idon sa ya kada ya yi jazur alamun bacin rai. Ta ce, “To who ‘re you telling all these rubbish? (Wa ka ke gayawa wannan maganar banzar?).â€? Cikin bacin rai ya ce, “Am not talking rubbish, I only told you the fact (Ba maganar banza nake ba, gaskiya kawai na gaya miki).â€? Ta ce, ‘Sai ka sake ta kuwa, yanzun nan kafin ka bar falon nan, ana aure dole ne?â€? Ya yi murmushin takaici ya ce, “Bana jin kaina sai ‘yar ki, idan na sake ta sai kin gwammace mutuwar ta da rayuwar ta.â€? Ta ce, ‘Then divorce her and see (ka sake ta ka gani), me zai same ta?â€? Ya ce, a yayin da yake mikewa tsaye, “The worst thing you‘ve never imagine.â€? Wato abin da ba ta taba tsamamni ba. Ita ma ta mike ta ce, “Tun da na ce ka sake ta ta ruwan sanyi ka ki, to ka je, amma Ihsan ba za ta gidan ka ba.â€? Har ya kai bakin kofa sai ya juyo, “Kada ki kara cewa in sake ta, ba zan taba sakin mace ba a rayuwata. Ba don komai ba sai don daraja da girmanta da nake gani da tausayinta, amma ba wai don son ‘yarki ba. Da wannan nake cewa, in za ku iya ci gaba da ba ni auren Ihsan, idan na dawo daga tafiyar da zan yi a gobe zan zo in tafi da ita, in kuma kuna ganin akwai cutarwa ko takura a gare ta, duk ya rage na ku, sai in ce da ku, Salam!â€? Sai ya russuna mata da hannuwan shi biyu tamkar wani Ba’indiye, alamar girmamawa kenan da ake yi wa iyaye a Miami, ya juya ya yi ficewarsa. How much do you like this story? 5/7/22, 13:10 - Ummi Tandama😇: ____________________________ *âœðŸ? SIRADIN RAYUWAâœðŸ?* Book one *@Takori* Page7ï¸âƒ£ Tafe yake a mota zuciyarsa na faman tafasa da kuna, tunda yake ba a taba humiliating (Cin mutuncin) shi irin yau ba, ba a taba yi masa wulakanci irin na yau ba. Don haka maimakon sautin Khusairi kira’ar Mahmood Khaleel yake bi cikin Suratul Ma’idah. A ran shi kamar ya yi zagi, sai dai dadin kira’ar da yake sauraro na sanyaya masa zuciya, ya ce, ‘Ihsan din me har da za a daga wa mutum hankali kan auren ta? Ita nan har wata mace ce da za a tada hakarkari a dagawa mutum murya a kan ta mts! In da sun san a yanzu babu wani gurbi da yake jin zai iya jogana son wata diya mace a zuciyarsa, bayan HA-LI-MAH, da ba su yi masa wannan jan ran ba, da ba su yi masa wannan wulakancin ba, in ba don ma Hajiya da ta hankado shi ba zai zo ne? Ya yi kwafa shi daya ya ce, “Allah za su sha mamaki.â€? Daga nan harkokin sa ya wuce, ya duba ginunnukan shi ya ga yadda ake aiki tukuru cikin fasaha da kwarewa irin ta Malam Bature, abin ya burge sa, haka tsakanin shi da hukumar lafiya komai na tafiya daidai, ya biya ‘Sahad Storesâ€? da ke kan titin Benghazi Street ya yi wa Halimarshi sayayya masu firgitarwa duk na kayan ciye-ciye da lashe-lashe, mayukan gyaran kai da shampoos, dryer zuwa sauran tarkacen kayan gyaran gashi, haka ya ciko mata kit da kayan shafa duk set din neutrogena collection kamar wani mai hada lefe, ya san da kyar ne za ta yi amfani da su, ba burinsa kenan ba, illa ya ga dan murmushin ta mai gigita shi. Haka ya koma boutikue na kayan kanti ya saya mata riguna da skirt zuwa dogayen riguna (Designers) masu karshen tsadar. Gaban sa baya ko dar na za a iya tambayarta ina ta samu? Idanuwan shi sun makance cikin wata irin soyayya mai gigitarwa, tunanin shi ya gushe, ita kawai yake gani a gabansa. Ya riga ya shirya tunkarar kowa da maganarta, auren ta zai yi cikin watannan da son ran wani ko babu he did not care (Bai dame shi ba). A dai kamfanin ta kicin ya same ta tana yankan danyar kubewa da Hajiya ta ce a yi wa Daddy da busasshen kifi da daddare, ‘yar zulunbuwar rigarta ta sha wanki da omon Aerial ta yi fes. Nadadden gashin kanta a cure wuri guda kamar gammo as usual (kamar kullum), duk da wahala da ta tsotse ta ta kuma kwalmade ta still ita kyakkyawa ce kullum kuma kamar ana kara mata kyau ne. Ya hade hannuwan shi bisa kirjin shi bayan ya aje ledojin da ke hannunsa bisa marbles, duk wani acting din ta cikin yauki na halitta sha’awa yake ba shi, haka duk wani motsin ta burge shi yake, ya ce, “Ha-li-mah.â€? Da muryar da ke dauke da sakonni da dama. Ba shakka gangar jiki da ruhin ta duka sun amshi sakon da ke tattare cikin muryar Al’ameen, sai ta yi murmushin da yake son gani, ba kuma tare da ta dube shi ba ta ce, “Ni fa na gaya ma Al’ameen ba sunana Halimah ba, ka daina ce min Halimah.â€? Ta kasan idanun ta ta dube shi don ita yanzun wata masifar kunyar shi take ji, tun maganr su ta daren jiya. Aminu ya kasa magana, tuni ya bushe a tsaye, ji yake kamar ya jawo ta ya rungume, amma ya yaki zuciyarsa da aikata hakan. Tunda yake, bai taba jin wanda ya furta kalmomin nan uku sak, Al-A-Min, ya yi mai dadi ya kuma iya fadi tamkar ita ba. Sai ya zari mayafin daya cikin dogayen rigunan da ya saya mata ya karasa ya nannada mata aka, still ba ta dube shi ba ta ce, ‘Shukran.â€? Wato na gode. Ya ce, ‘Yunwa nake ji sosai, tun safe ban ci komai ba, na fito bikon matata ga shi ba su ba ni ba, ni kuma don haushi na ki cin abincin su, don Allah ko kin yi ragowar na rana ki sammun?â€? Ba ta san san da ta tuntsire da dariya ba, yadda ya karya murya ya rausayar da kai sai ya tuna mata da Patch Adams, jarumin fim din America na fim din (Brilliant) sai ta girgiza kai ta ce, “Ko ka san Patch Adams?â€? Ya ce, “Humour is the best medicine, shin ke kin amince cewa humor is the best medicine? (Ban dariya shi ne babban maganina kowacce cuta).â€? Suka koma tattaunawa a kan fim din inda ya lura ita dai tana son fim din sosai. Ta ce, “Me yasa suka hana ka matarka?â€? Ya zuba uban tagumi abin dariya hannuwan sa a kan freezer ya ce, “Oho! Masu, Kiristoci ne sai ana hakuri.â€? Da haka ta ja bakinta ta tsuke, ta jawo babban food flask na Daddy ne da ta je daukowa domin wankewa ta taras ko budawa ba a yi ba, niyyar ta in anjima ta ci idan Hajiya ba ta nema ba, a nutse ta dauki babban plate ta juye abin da ke ciki, farfesun kayan cikin rago ne irin mai sa yawun mutum tsinkewar nan tun bai sa a bakinsa ba, sai farar macaroni a babban flask din, ta bude wani fadi ka mutu, wani abincin Larabawa ne shartoum da ake yi da naman kaza, kwai da waken gongoni, ga kuma farfesun kifi ragon ruwa fari sol da shi, ta hada duk a katon tray ta dora mai akan freezer inda yake jingine a jiki ta ce, “Ko za ka iya cin wannan Al’ameen kafin in kammala tuwon dare?â€? Ya dube ta cikin ido da idanun shi masu kama da an diga masu silver saboda sheki, ta kawar da kanta da sauri domin ba ta iya jure kallon nan nasa ta ce, “Ka ci kafin in kammala wannan, Al’ameen ka fiya kallon mutum Allah.â€? Ya yi murmushi mai fidda sauti, ya dubi abincin ya ce, “Yanzu duk ke ki ka sarrafa wannan Halimah, a ina ki ka san Shartoum?â€? Ta wani irin juyo ta dube shi a ranta ko cewa take, “har ni za a tambaya abincin Larabawa?â€? Ta ce, “Allah ka rage kallo, domin haramun ne.â€? Ya sake murmusawa a karo na biyu ya ce, “In banda Halima ba mutumin da ya ishe ni kallo.â€? Ta dan juya kadan ta ce, ‘Ah! Matarka fa?â€? Ya ce, ‘Ihsan sunanta.â€? Ta ce, “Ni ai ba sunan ta na ce ka gaya min ba, cewa na yi ita ma haka ka ke takura mata da kallo?â€? Ya kai lomar farko na macaroni cikin bakinsa, dandanon girkin da komai ya yi masa dadi har kunnuwansa sai da suka motsa ya ce, “To wai ke, ina gamin ki da matata ne, are u jealous?â€? Ma’ana kina kishi? Ta juye kubewar da ta kammala yankawa cikin tafasasshen ruwan miya mai rai da motsi da ta hada ta ce, “Wa, ni?â€? Ya ce, “Yes, ke Halimah.â€? “A kan me ka ce haka?â€? “A kan na ga kin damu da ita, ita ba ta ma san ki ba.â€? Ta zobara baki gaba yadda takema Faisal in ya ba ta haushi ta ce, “Na yi zaton sai ana son mutum ake kishin sa?â€? Al’ameen ko ya nuna damuwa da shaguben ta, sai zuba abincin shi yake cikin tumbinsa santin dadi na dibar kununwansa, ya ce, “Oho! Haka nima na ji?â€? Su duka ba su san sanda suka sa dariya ba. Ya ce, ‘Zan tafi Niger yanzun nan sai wurin jibi zan dawo, na zo miki sallama ne, ga kaya ki yi amfani da su kafin in dawo in gayawa mutanen gidan nan bukata ta ta auren ki halimah. Ina fata ko me za a yi miki, Halima za ki kasance a baya na?â€? Ya kafe ta da ido, ta yi shiru ba tare da ta juyo ba, amma ta yi sanyi da juya miyar da take yi. Anya za ta iya aure ba da yardar iyayenta ba? Duk ko da yadda take jin Al’ameen a zuciyarta, ruhin ta da kasusuwa, bargo da gangar jikin ta gaba daya? Ba ta jin za ta iya zartar da wani al’amari ga rayuwar ta ba tare da sani ko amincewar wadannan iyayen nata biyu ba, ina! Balle aure dungurungum, tukunna ma shi Al’ameen waye ne? Bata da wani sani a kan shi, dabi’a, sana’a da uwa-uba asali. Ba ta san komai a kan shi ba, in ban da so makaho ne. Haka kawai fa rana daya suka ga juna, guguwar mahaukacin so ta fyade kowannensu, duk da bata jin ko barawo ne za ta fasa son shi da kaunar shi, amma aure? Sai ta kada hafizin harshenta ta ce, “Idan har Daddy ya amince ba?â€? Ya ce, “Idan kuma aka samu akasin haka?â€? Ta girgiza kai da sauri, ‘Nima ba zan amince ba!â€? Ji ya yi kirjin shi yayi wani irin bugawa da karfi! Ya hadiyi wani makalallen miyau da ya tokare a makoshin sa da kyar, ya zuki iska ya fesar cikin takaici ya ce, “Kenan you don’t love me Halimahhh?â€? (Ba ki so na Halima?). Ta ce, “Sam, ba haka ba ne Al’ameen…â€? Ya riko hannuwan ta duka biyu cikin zafin nama a zafafe ya ce, “To yaya ne?â€? Ta daga lumsassun abnormal idanunta ta dube shi, shi ma duban ta yake impatiently (A kagauce) ta ce cikin raunannar murya. ‘You said so many things to make me happy, and try your best to make things work out okey for me. If I could describe your kindness, I would be describing an angel. If I should describe your love, I would be describing my whole heart. U are a gift Al’Ameen, from Glorious God to me, you are an angel! How could I say I don’t luv U (Ta yaya zan ce ba na son ka?) Illa iyaka ana son duk abinda dan adam zai gabatar, ya yi kokari kada ya saurari ra’ayin shi, ya saurari ra’ayin na gaba da shi. Ka ga kaman shi Daddy ya girma har ya kusa tsufa, ya yi edperiencing wasu al’amura na rayuwa, musamman auren da aka gina a kan soyayya, wanda mu da muke kasa da shi ba mu yi ba.â€? Al’ameen duk da cewa maganar ta ta farko ta yi mai dadi, ta kuma wanke shakkun da ke zuciyarsa, amma ya kasa fahimtar ko me take nufi da wannan murdaddiyar magana? Bai san san da ya ce, ‘Shin me ye tsakanin ki da Daddyn gidan nan?â€? Anan ne ta fuskanci shirmen da take shirin tafkawa, da sauri ta ce “Babu, sam babu, illa a dan zamana tare da su na fahimci cewa shi mutum ne irin sauran mazan jiya masu kaifin tunani da hangen nesa.â€? Ya ce, “To magananniya, kina ganin wrong choice (Zaben tumun dare) za ki yi wa rayuwarki kenan a hada rayuwa da Aminu?â€? Ta ce, “Kash! Ana baka kana kin amsa, na riga na amince da Al’ameen-Al’ameen ne100%, illa just what my sociology told me, ka yi hakuri a bar maganar sai ka dawo din?â€? To Al’ameen ya tafi Niamey da kwarin gwiwa da dukkan goyon baya na zuciyarsa kan amincewa da yarinyar da ko sunan ta bai sani ba, dari bisa dari zuciyarsa ta amince da ita. Ya lura bayan nutsuwa, yarinyar mai hankali ce da sanin abinda take yi uwa-uba kyakkyawan tunani da hangen nesa she leave no stone unturned tamkar ba karamar yarinya da ba ta kai shekaru ashirin ba. Hakan nan akwai wannan kalmar ‘classâ€? a tare da ita ba daya take da sauran matan da ya sani ba wannan daban ce, ta san mutuncin kanta, ta san baiwar da Allah ya yi mata na ‘ya mace mai darajjah. Duk rudewar da mata ke yi a kan shi a Miami, ita ba ta yi surprised! (Don Allah mata mu dinga jan mutuncin mu a komai). Ya yi duk abin da zai yi a Yamai cikin kwanaki uku rak ya turo kayan shi ta jirgin ruwa. Ranar da zai dawo ya shiga kasuwa a Yamai don bude ido kawai, ba abinda ya dauki hankalin shi irin kayayyakin matan su da ya tabbatar za su yi kyau da Halimar shi tun da itama tana yanayi da su, ya ciko akwatuna masu kyau da kayan matan Zindar, Niamey, Maradi da Damagaram da niyyar in sun yi aure da Halimar shi zai bata ta dinga yi mai kwalliya yana ganin ta kamar ‘yanmatan Niger. Hatta necklaces da duwarwatsun adon su ya saya mata, su wannan da niyyar su zai ba ta a matsayin tsaraba da zarar ya koma. Ya tsaya a wani kantin turare ya saya wa Hajiyar shi saitin Givenchy (for women) da take amfani. A ranar ya sauka a Abuja. Masu aikin fenti ya tarar suna ta yi a kowanne sako a gidan. Khaleel ke gaya masa wai Aunty Saratu ce za ta dawo sati mai zuwa. Har ran shi ya ji dadi, amma sai me? Ya shiga sashin Hajiyar domin ya sanar da ita dawowarsa, ya kuma bata tsarabar ‘givenchy’n da yayo mata, ya ji shi a kulle gam da mukulli. Ya kwalawa Furkan kira ya ce, “Kai Hajiya ta je anguwa ne?â€? Furkan ya ce cikin rashin jin dadin al’amarin “Ya Aminu rabu da Hajiyar mu kawai, wallahi tana bin shawarar su Anty Suwaiba ne kawai, suna kai ta su baro. Yanzun wai ta koma Kaduna saboda Daddy ya ce da ita Maman Intisar za ta dawo, ba ka ga irin zagin da ta yi wa Daddy ba a gabanmu har mu da muka goya masa baya.â€? Al’ameen ya rasa me ma zai ce? Ba tun yau ba wasu halayen na Hajiyar shi ke ba shi kunya da takaici ba, yanzu da girman ta a ce ta yi yaji ai ba karamin abin kunya ba ne a garesu, bai taba ganin mace mai kishin kishiya irin ta ba, wanda a shekarun ta ya isa a ce ta bari, ta kame girman ta, amma ashe wasa farin girki? Ko zama bai yi ba a lokacin ya zari mota ya nufo Kaduna cikin unguwar Kabala Custain, ainahin gidan kakanin su na wajen uwa. Tun daga get maigadi yake sanar da shi duk gidan babu kowa sun tafi hutu Dubai har Hajiyar. Ya girgiza kai a daren ya dawo Abuja, amma bai koma gidan su ba, gidan sa da Daddy ya ara masa wanda cikin ‘yan kwanakin babu abin da ba a zuba a ciki ba na jin dadin rayuwa, sai su da suka ki zaman gidan, anan ya kwana. Ya kira Hajiyarsa a washe gari, yana ba ta hakuri ta dawo ko don darajar su, amma sai ta sa masa kuka wai su da uban su so suke su taru su kashe ta. Ya ce, “Amma dai Hajiya ko za ki Dubai ba yanzu ne ya dace ba, sai a ce bakin ciki ya kore ki, ai kamata ya yi ki bari sai ta dawo tukun duk in da za ki sai ki je. Ya ya za ai mu kashe ki da bakin cikin mu bayan ke ce wadda ba mu da ya ita a duniya? Ki yi hakuri ki dawo don Allah.â€? Ta ce, “In dai ni ce uwar ka Aminu, to ba kai ba Saratu ko ta shigo gidan, in har kana son in dawo.â€? Ya ce ya amince, amma fa in har ta dawo din. Ban da abin Hajiya shi ina ma ya zauna a gidan balle ya shiga harkar su (sai ka ce wani lokacin kuruciya). Shi dai har ga Allah lallaba ta yake yadda take so don kar ta zubar da kimar ta a idon mutane, tunda kowa ya ji ba ta gidan ya san me ta yi wa tafiyar, shi kuma ba zai so zubewar mutuncin uwarsa a idon kowa ba duk lalacewar ta kuwa, duk da cewa ita din halin ta sai ita. Karfe goma na safe, ya shirya cikin danyen boyel navy green, haka motar da ya hau a yau ‘Kiaâ€? ce, lemon green, koren takalmin fata ne a kafar shi kirar Italy. Daman Al’ameen ba dai iya cool dressing ba, ya yi amfani da farin mudubin ido don ado kawai, ya nufo gidan su cike da nishadi. Ya saki kan motar a shararren titin Atiku Abubakar, har ya tadda katafaren gidan su yana bin sautin Alicia Keys, iskar damuna na kara armasa masa hantsin tare da gudanar masa da wani bakon nishadi, in da duk ya motsa kamshin turarrukan sa Ultraviolet da Vanderbilt da yake yawan amfani ke tashi. Al’ameen kenan. Ya duba kicin bai gan ta ba, ya leka dakin da suke kwana nan ma ba ta nan, ya leka dakin Dela babu alamar ta, gabansa yayi mugun faduwa, sai ya tsaya a kofar kicin din cikin zakuwa rike da ‘yan makullan shi yana zuba idon ganin ta inda za ta bullo. Zuciyarsa fes, take a yau domin hakika ta azabtu da rashin ganin Halimarsa for long four days (Tsayin kwanaki hudu). Daga can lambun gidan ta bullo rike da ribdediyar goba koriya shar da za ta hadawa Daddy guava juice sai ta ga bakon da bata zata ba, tsaye kofar ofishin ta. Ta saki baki galala! Da gani na jin dadi ne ta ce, “Lah! Al’ameen saukar yaushe?â€? Idanun su ke kallon juna tamkar sun hadiye junan su don so da kauna. Ita kanta ta yi kyau a yau, domin ta yi wanka kenan ta sanya daya cikinr iguna da skirt din da ya sayo mata kalar su black and pure white, sai doka kamshin brut (body spray) take, hakan nan curarren gashin ta mai kama da gammo yau ya sha wanki ya ga mayuka kala-kala da ya shekara bai gani ba sai sheki yake a cikin sassanyan hantsin na Litinin. Ta yi mai tufka daya kwal murtukekiya jelar sai yawo take a gadon bayan ta, she look so cute kwarai cikin kayan. Ita kanta ba ta san nishadin me ta tashi da shi a yau ba? Haka kawai tun da Dela ta ce da ita Hajiya ta yi balaguro Kaduna ta tashi ta fetse kwalliya, ashe rabon gwarzon masoya Al’ameen ce. Ya bude mata dukkan hannuwan shi amma sai ta noke ta cilla mai katuwar gobar da ke hannun ta, ya mika dogon hannunsa ya janyo jelar gashinta da karfi, don zafi ba ta san sanda ta fada jikin shi ta yi maza kuma ta ture shi ta ce (Dela da ke makale jikin kofar dakin ta, tana leken su, ta daura hannuwan ta a ka ta ce, “Na shiga uku ni Dela, kar dai yarinyar nan ba ta san Aminu ba? Za a aikata da na sani! Ko da yake duk laifin uwarsa ne…ikin ta babu inda baya rawa saboda kaduwa, yau kam ta yi dana sanin sa masu idon da ta yi, da bata ganowa kanta wannan kayan takaici ba, wai an ce ka bar abin da ba ruwanka izuwa abinda bai shafe ka ba, sa-ido sana’ar banza). Sai ta ja bargo har kanta ta kudunduna tana rawar dari. Ta ce cikin fushi, “Aminu, ba na so, kada ka sake, wannan haramun ne, idan kuma ka ki zan gaya wa matar ka ta ja ma kunne.â€? Ya tuntsire da dariya ya ce, ‘Ita har ta isa?â€? Ta gyada kai, ‘Har ta yi yawa.â€? Ya tura hannun shi a aljihun shi ya ce, ‘Zo ki ji?â€? Ta harare shi cikin haushi ta ce, “Ba’a zuwa.â€? Ya mannawa wani gefen daban ido ya ce (ba tareda ya dauke idonsa daga gefen da ya mannawa idon ba), “Ashe kadangaru ma na son kafar fararen mata? Dubi yadda yake lasar farar kafar ki cike da so da kauna.â€? Haba! Da ta daka wani tsalle, sai gata makalkale jikin Al’ameen tana ihun rokon sa, “Don Allah cire min shi, don girman Allah! Sai hawaye sharrr! Jikinta na kyarma. Ya fiddo hannun shi daga aljihu rike da necklaces da zobba, abin hannu da kafa na duwarwatsun matan Niger da ya sayo a Niamey, ya russuna ya daura mata a kafa, ya daura mata a hannu, ya mike ya daura mata a wuya. Ya bula hancin ta da kwambalelen abin hancin su mai kama da awarwaro, sai da ta feso wasu hawaye don azaba, amma ta yi kyau! Ta yi kyan har ta gaji!! Ta bishi da ido galala! Kana hannayen ta da ke cikin nashi. Da jikin sa data makale. Ta sauke idon ta ga kafafun ta, wani hawayen ya zubo. Ya kai hannun ya shafo hawayen yana murmushi ya ce, “Haba Halimah! Ya ya ki ke min asarar hawaye a kan kadangare? Ba kadangare ba, ko Zaki bai isa ya taba ki ina gani in kyale shi ba, sai dai ko ni ko shi. I luv u Halimah!â€? How much do you like this story? 5/7/22, 13:10 - Ummi Tandama😇: ____________________________ *âœðŸ? SIRADIN RAYUWAâœðŸ?* Book one *@Takori* Page8ï¸âƒ£ 1 Rabi Al-Thani (Hijriyyah) Wata Biyu Bayan Dawowarsa Al’ameen da Halimar shi (Kamar yadda ya nace da kiranta) sai aka soma shimfida ingantacciyar soyayya mai ban mamaki da ban sha’awa. Barin yanzu da ba su da shamaki, Hajiya kishi ya kore ta don har kwanaki suka shura tana Dubai ta ki dawowa. Su Khalil tun safe in sun tafi makaranta sai karfe shida na yamma suke dawowa don haka ba su ma san me Al’ameen ke yi a gidan ba, kai ko a mafarkin su ba su kawo ya ma san hanyar kitchen din gidan ba, to ya je ya yi me? Ita kuwa Dela tsoron shi take, da ta gan shi za ta soma bare-baren jiki ta gaishe shi ta wuce ta bar su. Tana kakabin abin a zuciyarta ita kadai amma ba ta ce da yarinyar komai ba. To ta ce mata me? Me ke tsakanin ki da Aminu ko me? Ta gaya masa ya ce tasa mai ido a yi mata asarar abincin ta yadda duniyar nan ta zama uhm-uhm, ba ruwanta su karata. Daga ita har Al’amin sun dauka da ba son juna suke ba, sai yanzun. Tun tana jin kunyar sa har ta gaji ta bari, domin ban dariya irin na Al’amin Allah ya yi yawa da shi. So, shakuwa da yarda da junansu su ne muhimman tubalan da suka gina soyayyar su a kai. Haka amincewa da junan su kullum sai kara karfi yake a zuciyar kowannensu. Ji suke, daya bai iya rayuwa ba tare da dan uwansa ba. Ba ta san me ye so ba a rayuwar ta amman Al’ameen ya koyar da ita wata irin soyayya mai shiga rai a lokaci daya, ya koyar da ita yadda za ta so shi, ta kaunace shi shi kadai a zuciyarta. Ba ta taba jin son wani da namiji a duniya irin yadda take ji yanzun a kan Ala’meen ba. To haka shi ma, tuni ya mance da Ihsan kwata-kwata a babin rayuwar shi watakila ta zama tarihi. Wadda a lokacin ta rasa nutsuwa kwata-kwata na rashin sanin makomar ta; ‘yar rakiya? Ko matar Al’ameen? Ita kam da ta san cin amanar da kasar haihuwar ta abin tunkahon ta, Nigeria, za ta yi mata kenan da tun farko ba ta takura su dawo ba. Haka Ann ta ce da ita muddin ta name shi bai kawo kansa ba ta bar ta da Jesus ya bi mata hakkinta na haifar ta da ta yi da wahalar da ta yi ta yi da ita. Ya tabbatar mata da amaryar Daddy ta tare zai kai masa bukatar su, kasancewar sa gwarzon uba, mai son duk abin da ‘ya’yan shi ke so ko da shi ba ya so in har bai sabawa tarbiyya da Addini ba, ya tabbata ba za a samu wani mushkila daga gare shi ba, sai dai ko daga gare ta, don ya lura son shi take amman auren baya gaban ta sam. Duk lokacin da ya yi zancen aure ya kan lura ta shiga wani zuzzurfan tunani, sai ya ta’allaka hakan da tunanin mahaifiyar ta da ta ce ta rabu da ita tun tana karama ba ta san inda take ba. A irin wadannan lokutan ya kan gaya mata zai zamo mata Uwaâ€?, zai zamo Uba a gare ta. ‘Yan uwan shi za su maye mata gurbin nata ‘yan uwan, su nuna mata kauna ta jini da bata samu ba a rayuwar ta. Zai zamo mata miji kuma aboki, zai zama komai nata, zai kauna ce ta muddin ransaâ€?, zai nesanta ta da Hajiyar da ke kin taâ€?, zai bude mata duk wasu kofofin farin ciki da dan adam ke burin samu! Ta kasance cike da tunanin wa Daddy zai aura? Ta je daki ta kwanta a dandaryar kasa ta yi ta kuka. Ta tabbata ta rabu da mahaifiyarta kenan har abada! To amma kauna da kulawa irin wanda Al’ameen ke nuna mata, wani abu ne dake rage bakin ciki da takaicin da zuciyar ta ke ciki. Ta kan tambayi kan ta yaushe ne wannan daukin da Najib ya kwadaitar da ita zai zo ne? Ko ko Al’ameen ne? Shi yasa ya dage su yi aure? Allah Sarki! Tana matukar tausaya masa, bata taba ganin mai son ta bayan Faisal, irin Al’ameen ba, ai ko ita shegiya ce ya kyautu ta aure shi hakan nan. To amma a matsayin da take kai a yanzu wa zai mata auren? ***** 12 Jumada Akhir (Hijriyya) Rana Mai Dimbin Tarihi A Gare Ta Faisal Bello Makarfi ne ke saukowa daga jirgin MEA International, ranar sha biyu ga watan Jumada-Akhir. Gaba daya Engineer Faisal B. ya canza tamkar ba shi ba, yana sanye cikin bakaken suit ya kuma daura thick coat saboda matsanancin sanyin da ake tsugawa, bakin takalmi sau ciki ne a kafarsa kirar Italy, hannun shi na hagu daure da agogon Rado yayin da na daman ke rataye da matsakaiciyar jaka irin wadda matafiya kan zuba passort da sauran kayan amfani na gaggawa. Bai fara tozali da kowa ba sai Ya Ameenu da rabonsa da shi shekaru goma sha biyar. Ya karasa da gudu suka rungume juna suna juyi kafin su soma hawaye. Abubuwa da dama sun faru, na farin ciki da na bakin ciki, na bakin cikin shi ya fi yawa. Bai taba zaton zai kara ganin Al’ameen ba a rayuwar shi, har suka iso gida kuka suke wiwi. Ya rasa mai yasa bai kullaci Aminu ba? Amsar shi ne don yana son shi, ko a cikin ‘yan uwansa Aminu daban ne. Kuma tunda har Daddy ya yafe masa shi a kan me ba zai yafe masa ba? Bai fara tambayar kowa ba sai Inteesar dinsa, Aminu ya ce, “An ce tana makaranta amma daman kwanan nan za mu kai mata ziyara tunda ga ka ma ka dawo shi kenan.â€? Ya yi shiru cikin tunani, shekarun da suka gabata suna da yawa, ya ci a ce yanzu ta yi nisa a jami’a in har lissafin da yake daidai ne. To ko a jami’ar take? Ya so kwarai ya tambayi Al’ameen sai ya share, ko da can Al’ameen na shiri da Intisar ne balle yanzun? Ya sauke shi a kofar gidansu ya juya ya tafi gidansa don yana da abin da zai yi da yawa. Haka kuma a ranar ne motar Daddy ta sauke Aunty Saratu, Zarah, Goggo Jumami da aminiyar ta Jami a harabar gidan, sabanin da su kai da motar Al’ameen na mintuna uku ne kacal, Aunty Saratu again a matsayin matar Daddy Makarfi. Ta kara kiba, ta kuma yi haske sosai na samun hutu da kwanciyar hankali. Baben ta Zarah na kwance a kafadun Jami tana barci suka shiga sabon sashin Aunty Saratun wanda da farko sun dauka ba a Nigeria suke ba, babu abin da Daddy bai zuba mata ba na jin dadin rayuwar duniya irin abin nan dai da ake kira Aljannar Duniya. Dakin Inteesar kadai abin kallo ne don a naira miliyan biyu cif Daddy ya sa kamfanin edcel interior decoration suka yi wa Intisar da yake tsammanin tana makarantarsu a Riyadh. Tun kafin ta zauna ta ke kwalawa Intisar kira tun karfin ta, sai Khalil ya shigo yana toshe kunnensa haka su Goggo suna “Kar ki lahanta mana dodon kunne.â€? Khalil ya ce, ‘Anty ki yi hakuri, ba jiyo ki za ta yi ba, don tana can sassan ‘yan aiki, bari in je in dauko miki ita kawai aka, don in na ce ta zo ko kallo na ba za ta yi ba.â€? Hawaye suka fitowa Saratu sharr! Wai Saratun ta ce a sassan ‘yan aiki? Ta daura hannuwa aka ta fasa kururuwa ta ce, “Amma Allah ya isa tsakanina da ke Haj. Nafi.â€? Da haka ta kwasa da gudu babu ko dankwali tuni ya yi nasa waje, ta bi hanyar da zai sada ta da sashin ‘yan aikin. Khalil na bin ta yana kira shi ma kukan yake, a daidai lokacin da Faisal shi ma ya fito daga cikin gidan bangaren Hajiyarsu ko jakar hannunsa bai aje ba saboda kururuwar da ya ji ta gigita shi na muryar da ya tabbatar Antinsu ne, ganin Antin tana gudu babu ko mayafi bai san san da ya yar da jakar hannunsa ba ya rufa mata baya, yana “Aunty Saratu ki tsaya!â€? Ta ce, ‘In tsaya, uwarku ta karasa kashe min ‘yar? Ban san me Saratu ta tsarewa Hajiyarku ba haka Faisal, wannan karon ba zan taba amincewa ba!â€? Bata kuma tsaya da gudun da take ba, hakan nan hawayen ta ba su bar ambaliya ba. Tana tsaye tana farke buhun semovita don zubawa cikin ruwan zafi tafasashshe, Aunty Saratu ta rungumeta ta baya, yayin da hawayen ta da ke ta kwarara suka dinga sauka a kirjin Inteesar! A fusace ta juyo, a zaton ta Al’ameen ne ta ce, ‘What a nuisance, Aminu?â€? To amma sai ta ga mamarta, da ko a mafarki ba ta zaci sake gani nan kusa ba. Idanuwanta suka bubbude gaba daya tamkar sa fado. Ta kai hannu ta shiga tattaba ta a gigice ta dai tabbatar ita din ce hanci, ido, baki fuska, babu abinda ya canza a jikinta. Ta bude baki kamar mai son yin magana amma sautin ya kakare ya ki fitowa sai dai labban ta da ke motsi yanayin motsin na nufin, “Mamana?â€? Aunty Saratu ta janyo ta ta rungume tsan-tsan a kirjin ta cikin yanayin fita hayyaci ta soma cewa. ‘Saratu? Haka Nafi ta maida ke? Allah ya isa tsakanina da Hajiya Nafi, ba zan taba yafe mata ba haka duk jinin ta, in Allah ya yarda sai ya ga tozarci a rayuwa…â€? Faisal ya yi saurin toshe kunnensa yayin da gaba daya suka rikice da kuka. Yana ji yana gani ana bin su da mugun al’kaba’i, a kan laifin da ba nasu ba, a kan abin da bai shafe su ba, a kan abin da in da yana nanâ€? ba zai taba faruwa ba! Yasa hannu ya matso kwallar da ta tarar masa a kwarmin ido, kafin ya ankara tuni sun fice daga kicin din, ya mara masu baya tamkar kazar da kwai ya fashewa a ciki. zuciyarsa cike fal da nadamar zuwa Najeriya. Shin me ya yi zafi haka? Me Hajiyarsa ta yi wa Intisar din sa haka da zafi? Ya san Aunty Saratu mace ce mai dumbin hakuri, tabbas yau an kure ta an kuma kawo ta bango, tunda har ta kai ga furta wannan kalami. A babban falon Anty Saratu kuka diyar ta Saratu ma kuka, maimakon farin ciki. Tun suna ba Goggo Jummai tausayi har suka koma ba ta haushi ta mike ta na gyara daurin zanin ta tace, “Jami, na fasa kwanan gidan nan, tunda Saratu da Saratu ba su san yarda da hukuncin Allah ba.â€? Jami ma ta ce, “Kya fada dai Hajiya Jummai, kuma tunda komai ma ya zama tarihi, ni ban ga amfanin zubda hawayen ba. Dubi irin wannan duniya da Bello ya shirya masu amma duk ba su gode Allah.â€? Intisar ta rike hannun Goggonta ta ce, “Ki yi hakuri Goggo don Allah, daga yau ba za mu sake kukan nan ba, ban taba zaton Mama za ta dawo ba ne, ko a mafarki.â€? Ta share hawayenta. Goggo Jummai ta shafi kanta suka koma suka zauna tana kara yi masu nasiha kan muhimmancin yarda da kaddara mai dadi ce ko mara dadi. A yau kam Antin da diyar ta kwanan bakin ciki da farin ciki suka yi a zaune, in suka ce idanun su sun runtsa ko na sakan daya to sun yi karya, kowanne na bai wa dan uwan shi labarin bayan rabo. Intisar rungume take da kanwar ta Zarah da ba ta san an haifa ba, tamkar ta tsaga kirjin ta ta sanya ta don so da kauna. Amma sam yarinyar nan ba ta gayawa mahaifiyar ta irin azabobin da Hajiya ta rika gana mata ba ta dai ce ita ke yin girkin gidan kawai, wannan ya dan sanyaya ran Antin. Daddy ya je meeting Lagos sai a washe gari zai dawo, duk da haka ya yi wa Antin waya ya ji yadda suka iso ta ce sun iso lafiya cikin alkhairi, ya ce idan ya iso a goben sati mai zuwa za su tafi Riyadh su dubo Saratu karama. Ta ce, “Wace Saratun kuma ban da wannan da muke a kwance tare?â€? Daddy ya yi shiru cikin dogon tunani, can ya ce, ‘Aminu ya ce da ni Saratu na Riyadh?â€? Ta kara tabbatar da abinda Mal. Sidi ya ce da ita, na cewa Daddyn baya cikin hayyacinsa a duk tsayin lokacin sai ta ce, ‘Shi Aminu ba bako ba ne? Yaushe har ya yi zaman da zai san me ke faruwa cikin gidan?â€? Ya ce shi kenan tunda ga Al’ameen a gida, ya kamata a sake mata glasses a kirawo masa ita. Ita dai a tsorace ta gaishe shi, amma wai sai yake ce da ita wato tun tuni ta zo hutun ‘yar boye take yi mai a gidan ko? To ta yi asarar tsarabar da ya yi niyyar kawo mata…â€? ta jingina da bango, hawaye na karshe na zubar mata ta ce, “Ni dama na san wancan mutumin is not my real Dad (Ba shi ne babana na hakika ba), ban kuma taba kullatar Daddy na ba, even once (ko da sau daya). A kullum ina yi masa uzri, gare ni duk yadda rayuwa ta zoâ€? a karbetaâ€?, ayi mata uzuri da abubuwa guda biyu; Faisal da Daddy Makarfi.â€? Aunty Saratu na share mata hawayen da hannunta ta ce, ‘Kin ga Faisal ya dawo?â€? Ji ta yi tamkar an kwara mata ruwan kankara, ta zaro ido ta ce, “Haba don Allah! Allah Sarki Brother!! Wallahi ban gan shi ba sam.â€? Antin ta ce, “Ni dazu da na kusa haukacewa saboda bakin cikin uwar su ko kulasa ma na yi?â€? Ta ce, “Ayya Mamar mu! Ina laifin Hajiya zai taba shafar Ya Faisal, ina!â€? Sai wasu hawayen sharrr! Ta ce (cikin rarraunar murya), “Ni don farin cikin dawowarku ma ke da Ya Faisal, domin Faisal, na yafewa Hajiya har cikin raina.â€? Sai Antin ta bi ta da kallo, zuciyar ta cike da mamakin sanyin zuciya irin na yarinyar, bata daukan al’amuran duniya da zafi, ba ta da daukar kunci ko kadan, yanzu ne za a yi mata abu yanzun ne za ta manta tun tana mitsitsiyar ta. Amma ba ta manta alkhairin da mutum ya yi mata ko yaya yake. Saidai ta manta batancinsa gareta. Tana mamakin irin kaunar da take musu, tana mamakin irin kaunar da take wa Daddyn ta da ‘yan uwanta mazaâ€? ina ma a ce wannan shi ne bakin cikin yarinyar na karshe a rayuwa? Wannan tunanin ya kara mata kauna da tausayin yarinyar, ya kuma dugunzumar da zuciyar ta duk a lokaci daya, ta yadda duk wani farin ciki da ta zo da shi sai ya dushe zuciyarta ta koma bakikkirin. Ta roki Allah kada ya nuna mata ranar da Saratu-Intisar za ta fahimciâ€? me za ta fahimta? How much do you like this story? 5/7/22, 13:10 - Ummi Tandama😇: ____________________________ *âœðŸ? SIRADIN RAYUWAâœðŸ?* Book one *@Takori* Page9ï¸âƒ£ Karya Fure Take Al’ameen na gidan shi tun jiya bayan ya sauke Faisal yana faman aikin takardun tsare-tsaren ginin asibitocin su da fasalin da yake so a yi wa gidansa, wanda zai kasance cikin asibitin. Wayar Ihsan ta katse shi, da ya duba ya ga lambar ta ne sai kawai ya kashe ya ci gaba da aikinsa. Karfe shida na yamma ya baro gidan ya biya ya yi wa Halimar shi sayayyar su ice cream da dangin sa kana ya wuce. A harabar gidan ya ga bakin motoci da dama lambar Enugu tabbacin yau gidan a cike yake da ‘yan uwansa, a ransa ya kudurce yau sai sun gaya masa ko fushin me suke da iyayensu. Ya ratsa ta lafiyayyen falon Hajiya zuwa babban falon gidan ya shiga da sallama cikin muryar sa ta kasaita nan ya tadda su (complete family as earlier). Ba karamin dadi ne ya ziyarci zuciyarsa ba, domin ganin su a hakan ya tuna masa da abubuwa da dama da suka gabata cikin rayuwarsu. Najib, Faisal, Bello mai sunan Daddy, Faruk, Yasir, Nasir samarin Daddy da sauran kannen da ke bin su sun cika falon sun kawata shi, kowannen su ji yake da boko wanne-ne-ba-wanne-ne ba! Bai san da ya murmusa ba, sai baiwa Daddy labari suke na abin da ya shafe su, to amma me? Abin ne ya bala’in daure masa kai, ya rikita kwakwalwarsa, ya kasa tantance me yake gani? Halimar sa ce kwance rashe-rashe bisa doguwar kujerar da Daddy din shi ke zaune, ta yi matashi da kafafusna yana karanta mata labarin kwallon kafa cikin jaridar Punch da su Najib suka shigo da ita. Kamar sun hada baki suka ce, “Gaskiya gobe za a je bikon Ihsan wa Dr. Al’ameen, mun matsu da mu ganta.â€? Daddy ya aje jaridar bisa ruwan cikin ‘yar lelensa, ya dube shi ya ce, ‘Ku kyale shi dai, nake jin wata ya gano yana so ‘yar doguwa kyakkyawa anan din, don kwanaki har man gashi da ‘dryerâ€? ta gashin mata na gani a wata leda da ke hannunsa bai san na gani ba.â€? Gaba daya suka kwashe da dariya har ita da ba ta san takamaiman da wa ake cikin su ba, don a kwance take, ta juya masa baya tana fuskantar Anti Saratu da ke shayar da baby Zarah. To amma shi bai yi dariyar ba, maimakon haka da kyar ya iya daga kafa ya karasa har saitin kanta ya ce, “Halimah!â€? Da wata irin murya mai sanyi da rashin kuzari. Da sauri ta mike zaune ba tare da ta juyo ba, ta san dai ko ba jima ko ba dade dole zai san matsayin ta na hakika a gidan, kuma dama ita hakan take jira kafin ta iya yarda su yi aure, wato sani da amincewar Daddy da Mamarta! Ba ta iya ta dube shi ba, amma ta san duk duniyar nan babu mai kiran ta Halimah, sai shi, kuma ko a cikin mafarki ta ji lafiyayyar muryar shi cikin muryoyin maza dubu za ta iya fidda ita. Ta dai sunkuyar da kai kawai (feeling guilty) a ran ta tana cewa, yau dai Daddyn da kansa zai gayawa dan uwan su Al’ameen abin da ya dade yana son ya ji, ba za ta iya hada ido da shi ba, saboda dunguma-dunguman karerayin da ta shishshirga masa, amma ai Allah ya gani kuma shi shaida ne kan cewa ta yi ne don mutuncin Daddyn ta a idon dan uwansa har ga Allah kuma dalilin ta kenan. Aunty ta watsa masa harara ta ce, “Yaushe Inteesar din ta koma Halimah?â€? Idanun shi suka soma kankancewa su kadai cikin tsananin mamaki, ta’ajjibi da tashin hankali ya ce, “Inteesar kuma?â€? To wai an ce suna linzami, ba ta san sanda ta ce, “Na’amâ€? ba. Ya dubi Daddy gaba daya ya rikice ya ce, “Don Allah Daddy, wannan ba Halima mai aikin Hajiya ba ce ne?â€? Muryar sa kamar an shake shi, Aunty Saratu kallon sa kawai take kamar ta ga mahaukaci sabon kamu, yau ga likitan kwakwalwa ya samu tabi a kwakwalwa, haka Daddyn, ta ce cikin halin ko in kula, “lallai ai ban san Aminu ya yo guzurin shaye-shaye daga Miami ba.â€? Najib mai bin Faisal ya tabbata dan uwansa Al’ameen lafiyar sa kalau, ya kuma yi tsamamnin watakila Al’ameen ya manta Intisar ne yana dai ganin ta a kicin tana girke-girke da rayuwa a sassan ‘yan aiki saboda rashin imani irin na Hajiyarsu, sai ya ga ya dace ya yi mai cikakken bayani. Ai Al’ameen bako ne har yanzun kwata-kwata watannin shi biyu a kasar bayan shekaru goma sha biyar, ya san watakila don yana ganin ta tana jera abinci a dining in an gama ta kwashe ta yi sharar gidan gaba daya ta yi wanke-wanke, ta gyara masu dakuna ta kuma wanke masu bandaki. Ya dubi dan uwansa da idon rahama ya ce, “Ya Ameenu wannan Intisar ce fa, da ka ta fi ka bari tana karama. Wani labari mai tsawo ya faru a bayan ka, da ya yi sanadiyyar jawo faruwar al’amura da dama cikin rayuwarmu da har ya hana ta komawa makaranta shekaru biyu cif. Bayan Daddy ya rabu da Anti Saratu, Hajiyarmu ke sata ayyukan da ka ga tana yi don Daddy ya ce Antin ba za ta tafi da ita Makarfi ba, ka kuma san tsakanin su da Hajiyar tun tuni.â€? Al’ameen ya soma fiddo ido da murya ya ce, “C’mmon, wai kana nufin Inteesar diyar Aunty Amarya da na illata wa ido?â€? Najib da sauran suka gyada mai kai dukkansu alamar “Eh, ita din ce dai.â€? Ita kam girgiza kai kawai take, ta dafe kanta da hannuwan ta biyu tamkar mai ciwon kai, Shin wa ye ne Al’ameen? Ba dai Aminun Daddy ba? Yayan ta da ke karatu a Miami? Ta dubi mahaifinsu cikin yankewar buri bakinta na rawa ta ce, ‘Daddy wannan shi ne Al’ameen din ka na Miami?â€? Tana nuna masa shi da yatsan ta Ibham, ya gyada kai tababcin shi din ne. Ta dubi Al’ameen bakin ta a bude ta kasa cewa komai, shi ma din kallon ta yake haka duk jama’ar da ke falon kallon su suke. Ya kara matsowa gaban ta sosai cikin shakakkiyar murya ya ce, “Me yasa ki ka yi min karya?â€? Anty Saratu ta dubi Aminu ta ga yadda ya rikice, ta dubi Intisar ta ga yadda ta susuce tamkar wata kwarya-kwaryar drama ake yi a gaban ta, ta yi tsaki cikin takaici da tasowar wani tsohon bakin ciki mai tokarewa mutum a kahon zuci har ya rasa salama sai ya amayar da shi tukunna, irin wanda har abada mutum baya mantawa balle Uwa da ake cewa wai in maye ya mantaâ€? Ta ce, ‘Al’ameen ko? Wannan Intisar ce, Saratu ce, diyata da ka yi ball da ita idon ta ya fashe, ka tuna? In kuma ka manta ne na ke tuna maka. Har yanzu bata gani sosai. Ke kuma Saratu wannan yayanki ne Al’ameen, tun kina karama ya tafi karatu shi yasa ba za ki gane shi ba, ko kuma ba ki san shi ba ma kwata-kwata.â€? Intisar ta fasa kara mai firgitarwa ta ce, “Wayyo Daddy, shi ne har muke shirin aure? Aminu fa harâ€? ya ke yi…â€? Muryar ta ta kakare, sauran maganar makalewa ta yi a makoshin ta ta kasa fadin abin da ta yi niyya saboda wani makoko da ya zo ya tokare ta a makogaro, sai ta sulale daga kujerar da take kai bisa carpet a sume. Ba abinda ke yawo a kwanyar Al’ameen kamar abu daya “…alkawari daya zan iya yi miki Hajiya ta, ba zan taba son ta irin son da Faisal ke mata ba!â€? Ya kama kansa da hannunwan shi biyu yana girgizawa da karfi, ji yake abin tamkar a mafarki don haka yake fatan Allah ya taimake shi ya farka daga wannan mugun mafarki. Ya kasa daina gano ranar da ya dawo, ga Hajiyarsa a gabansa, yana yi mata wannan alkawarin, kalamun sun ki daina amo cikin kwakwalwarsa da karfi. “Ba zan taba son ta irin son da faisal ke mata ba!â€? Wai me yasa har kullum yake gamuwa da nadama mara amfani ne a kan Intisar? Kafafuwansa sun kasa daukar nauyin gangar jikinsa haka duk wata gaba a jikinsa ta rasa garkuwa, sai ya fada jikin Faisal yana fidda numfashi daidai. Kafin wani dan lokaci ragowar numfashin ya dauke kwata-kwata. A guje Daddyn ya yi kan shi ya dago shi ya rungume a kirjin shi ya ce, ‘Al’ameen, don Allah kada ka mutu, me ya faru? Me ke tsakanin ka da Saratu? Eye, ka gaya min mana?â€? Sai kuma ya sungume shi ya yi waje ‘yan uwan na mara mai baya suka sa shi a mota suka nufi babban asibiti. In banda Faisal ba wanda ya bi ta kan Intisar. To kowa nasa ya sani, don haka Anti Saratu diyar ta ta dauka tasa a tata motar Faisal ya ja suka nufi wani asibitin daban. Tana rungume da Intisar din ta tana kuka. In dai soyayya ta hada wannan abu, to ta tabbatar rabuwar ta da Intisar din ta ne ya zo! Ta san Daddy ko don kada ya rasa dan da ya fi so a duniya sai ya gaya wa kowa akwai aure tsakaninsu, tsintar ta ya yi a daji ba su san ko ‘yar waye ba. Ba ta tunanin komai illa rayuwar Intisar a gaba, da ta tabbata za ta kare cikin bakin ciki da takaici. Babu abinda ya kai rashin asali ciwo. Tsoron ta Allah, tsoron ta kada Saratu ta ce za ta tafi neman iyayenta. Tunanin hakan ya sa ta kara rikicewa da kuka. Likitoci biyar ne a kan Intisar suna kokarin ceto numfashin ta, to haka shi ma Al’ameen oxygen ne makale a fuskar shi ga kuma likitoci rankatakaf a kan shi. “Yau ga likita a gadon likitoci kenan?â€? In ji babban likita Alfared don sanin waye Al’ameen. Farkon Labarin Brigadier Bello Makarfi, ke kwance a bayan mota ‘Land-cruserâ€?, sanye yake cikin korayen kakin sojoji hakan nan ya saya kwayar idanun shi cikin bakin gilashi mai duhu ainun. Ya bude wayar shi ‘Thurayaâ€? ya shiga aikawa da sako hedikwatar sojoji da ke Jos, a kan hanyar shi ta zuwa Kano daga Kaduna, domin halartar seminer da karfe uku daidai na yammacin ranar a can Kano din. Ya kammala maganganun shi ya rufe wayar ya maida aljihu kana ya dubi direban shi ya ce, “Karo mun karfin A.C Sam.â€? Sai da ya kame kana ya karo, can ya kuma cewa, “Sam.â€? Direban ya sake kamewa tamkar wanda aka yi wa allurar zuke jini ya ce, “Yes Sir.â€? “Idan ka fita kauyen nan ka tsaya a nemi wuri in yi sallahn Azuhur, ga shi har biyu na neman shiga.â€? Yana magana cikin harshen Turanci ne a gurguje. Direban da ya kira Sam ya amsa a ladabce, a zuciyar shi yana mai jinjina tsantsenin Addini irin na ubangidansa ko kadan baya wasa da lokacin sallar sa koda a filin daga yake. Daidai hanyar na fita wani kauyen Fulani wai shi Shanono, direban ya tsayar da motar karkashin wata bishiyar darbejiya sassanya ga ‘ya’yan ta yalo shar duka sun nuna sun zuzzubo kasa abin sha’awa sun cika wajen, sai suka kawata wajen kwarai. Ya bude but din motar ya fiddo katuwar darduma kana cikin zafin nama ya budewa Ogansa kofar owner side, shi ma ya fito rike da doguwar tazbahar sa koriya. Sam ya nemi wuri zai shimfida dardumar a karkashin bishiyar amma sai me? Tsalle ya buga gefe daya cikin matukar razana a gigice ya ce, “Ogaâ€? Ogaâ€? na bebâ€? baby.â€? Ya ce, “Kai wane irin shashasha ne, me ka ke cewa?â€? Ya ware iyakacin katuwar muryarsa ya ce, “I said there’s baby here, come and see for urself, nawaho!â€? Brigadier ya kara taku, ya isa ga yaronsa ya ga yadda ya bi duk ya firgice har ya manta dawa yake magana yake kuma yiwa tsawa. Kana ya dubi inda ya mannawa ido tamkar sa fado, da gaske yake, jariri ne ko jaririya jazur da shi kwance cikin zanin saki, yatsun shi duka biyun cikin baki yana tsotso tamkar ya samu nonon mamarsa, alamun hakuri kenan, yana wutsil-wutsil da hannayen shi cikin koshin lafiya da gani ka ga haihuwar Fulanin usli, domin ko’ina a jikinsa jawur yake. Ya kira yi sunan Allah Alâ€? Aleem kana ya russuna ya dauki jaririn da Bismillah a bakinsa don shi kansa ba karamin kaduwa ya yi ba, don dai jarumin soja ne kawai. Sam ya kwalla kara don bai ga dalilin da ubangidan sa zai yi wannan kasadar ba, idan kuma dan aljanu ne fa? Karar da ta firgita jaririn ya tsandara kuka mai firgitarwa, cikin tsawa ya ce da Sam. “Shut up!â€? Tuni ya koma cikin nutsuwar shi, ya rungume jaririn tsan-tsan a kirjin shi ya dubi gabas, ya dubi yamma, kana kudu, sannan arewa. Ba motsin wani mahaluki in ka dauke karar tsilli-tsillin motocin da ke giftawa a kan titi jefi-jefi. Mutanen yanzu, anya suna son gamawa da imani? A zo dajin Allah, ba gida gaba ba gida baya a ajiye jariri, wanda bai san ma abinda duniyar take nufi ba, a gudu, don kurum son cimma wata manufa ta duniya ko ko don gudun abin kunya? Shin kunyar duniya har ta fi ta lahira? Ai shi kenan. Da ai na kowa ne, don haka ni ina so, zan kuma rike tsakani da Allah. Kai Sam dauko dardumar nan mu koma Kaduna.â€? Magana yake shi daya tamkar zararre, takaicin al’umma ne cike da ransa har bai san yadda zai kwatanta ba. “Oga da tsintaccen baben?â€? ‘Yes?â€? ‘Oga Seminar fa?â€? Cikin tsawa da gajiyawa da banzayen tambayoyin da yake ta jero masa ya ce, ‘Na fasa ko dole ne?â€? Bai kara magana ba, amma duk jikin sa babu inda baya rawa tamkar ana kada masa gangi. Sam kam ko za a kashe shi ko yana hauka ba zai dauki dan da bai san ko na waye ba! How much do you like this story? 5/7/22, 13:10 - Ummi Tandama😇: ____________________________ *âœðŸ? SIRADIN RAYUWAâœðŸ?* Book one *@Takori* Page🔟 Ya saki layin unguwar Sarki, ya dauki wanda zai kai shi Gwaman Road GRA. Ya tsaya a gida mai lamba dari da hamsin mai dauke da rufin jan kwano na zamani. Sojoji biyar ne suka bude kofar gate din cikin zafin nama yayin da direba Sam ke sulala motar mazaunin ta a hankali, tun kafin ta ida tsayawa sun bude murfin motar Oga ya fito cikin kakkarfan takun shi rungume da bebi. Cikin su ba wanda ya furta ko umh, illa idanun Sam direba da ke cike da gulma nata walainiya cikin na abokan aikin shi. Ai kuwa Oga na matsawa ya shiga tsurkun ta masu. “May be Oga gone crazy, ya tsinto baby a daji.â€? Hajiya Nafi, ita ce uwar gidan Brigadier, gajera ce kyakkyawa mai masifar kibar hutu. Ta kawata hakoran ta biyu da hakoran Makkah na gwal masu sheki tana da yalwar idanu manya. Hutun da take ciki shi ke boye zahirin shekarun ta, amma a kalla ba a kasara ba ta baiwa talatin da takwas baya. Sanye take cikin shudiyar atamfa Super mai zanen ruwan hodar furanni da ratsin kore kadan. Cikin sassarfa take ratsa falullukan da za su sada ta da sassan magidan da ke ta ruda ta da kira ta intercom. Mai aikinta Asbi ta tsayar da ita tana cewa. ‘Hajiya, na fa gama aikina na yau zan bulla gidan wannan ‘yar in mata sallama, kin san hutu na gobe ne zai fara ko kina da sako Sokoto? Don ni wannan hutun kusan don ke na yi shi, don kuwa na ji labarin zuwan wani sabon hatsabibin boka a Talata-Mafara, an ce aikin sa kamar yankar reza.â€? Hajiya ta ce, “Ke da Allah rabu da ni, irin wannan kira na Brigadier mai barazanar fasa dodon kunne kamar an ce na yi cikin ‘ya mace?â€? Asbi ta yi guda ta yi dariya ta ce, “Ai kiran ma alheri ne, kuma sai mai matsayi ake kiran, kin ji a kira wannan funkason ne? ‘Ya mace kuwa sha Allahu kin haifa kin gama don yadda Malam Arzai ya ce ba ta isa ta aje kwai a gidan nan ba, hakan ne ba kuskure. Tun da ta ki fita don sharri, asiri da makirci ai ta fita don rashin haihuwa, kinibbbiyar yarinya kawai sai kafirar kissa kamar Bakatsina. Ai yadda ta zo ita daya haka za ta sa kafa ta fita salin-alin, sha kurumin ki Hajiya Nafi, gagara gasar mata uwar gidan Brigadier, ke daya rai da ajali, uwargida kan gidan in kin so gida ya zauna lafiya, in kin bijire gida ya hautsine, Maman Aminu mai tumbin gwal ki ba ni doller.â€? Hajiya ta yi dariya, irin wannan washin na su Asbi da ire-iren su ba karamin kai yake fasa mata ba. Ta sosa keya ta gyara daurin dankwalin ta ta ci gaba da taka matattakalar da za ta sada ta da sashin maigidan tana cewa, ‘Duk kin bi kin cika ni da washin ki da bai karewa, kin hana ni amsa kiran maigidan. Jira ni in sauko komai ki ke so zan ba ki Asbi na.â€? Sai safa da marwa yake a kayataccen falon rugnume da jaririn da ke ta tsala kukan wahala da yunwa, yana hura masa iska cikin kunne shi bai yarda ba lallashi yake, falon cike yake da duk wani nau’in kayan jin dadin rayuwa na zamani. Hajiya Nafi ta ja da baya. “Subhanallah! Ran ka ya dade ina ka samo baby?â€? Ya ce, ‘Samu wuri ki zauna tukunna, ai maganar ba ta ja da baya ba ce.â€? “Dole in ja da baya, na san ina ka dauko shi?â€? “Allah ne ya ba ni, kuma ina so kwatankwacin su Aminu, ina fata za ki ji kai, ki amshi amanar da Allah ya danka mana? Ki rike tamkar su Khalil, Nafisa, ina neman hadin kan ku kamar kullum?â€? A wannan karon kam kallon shi take tamkar ta ga mahaukaci sabon kamu. ‘Daddyn su Khalil anya ka san abin da ka ke fada kuwa? Dan tsuntuwa, in rike? Ni?â€? Ya juyo gaba daya da murmushin da ya san ya kan kwantar mata da hankali, domin a da ya juya mata baya ne, sanin kan shi ne ita rudaddiya ce don haka baya son ganin rudanin da fuskarta ke ciki. Ya dube ta cikin ido ya ce, ‘I know, u’ll be shocked, amma kin sani, da dai na kowa ne kuma amana a wurin mu iyaye, ban so ki ki fahimtar abin da nake nufi da gangan, wato mu yi taimakon ceton rai don Allah, ba tare da tunanin abin da gaba za ta haifar ba.â€? Hajiya Nafi ta gama harzuka ta tabbatar shi mutum ne kaifi daya, tunda ya ce hakan mai raba shi da wannan jaririn da take gani shege ne sai Allah. Ta sake ja baya. “Wallahi dan tsuntuwa ba a gida na ba, ba dai cikin tsarkakakken zuri’a ta ba. Haka kawai, muna da ‘ya’ya ba rasawa muka yi ba, daidai har goma, ka dauko mana dan tsuntuwa? Wa ya sani ma ko uwarsa shegensa ta yi ta yar don gudun abin kunya shi nemu za ka kwaso mana?â€? A lokuta da dama Hajiya Nafi kan mance zuciya irin ta tsohon sojan, tsawa ya daka mata mai gigitarwa ya ce, ‘Get out! Stupid, idiot.â€? Kafin ta farga kuma har ya rigata fita daga dakin, shi da ya ce ta fita, ta yi tsaki ta yarfar da hannuwa cikin kakabin yau ita Brigadier ke kira idiot abin da bai taba yi ba, shekaru daidai har ashirin da biyar sai yau a kan wannan tsintattar magen, wannan ya kara mata tsana da tsangwamar jaririn da ba ta ma san ko wane jinsi ba ne a rai. Lallai in ta bar jaririn nan tare da shi tana shirin ganin wulakanci da tashin hankali, don shi in ya so abu ya so shi kenan, haka in ya ki shi ko duniya za ta taru a kan shi ba zai so shi ba. “Haka kawai ina zaman â€? zamana a kwaso min jidali, ai sai ka kaiwa munafukar matar ka tunda dama da ita ku ke kulle-kullen munafurcin ku, sai yau don rana ta baci za a kira ni? In ma kai ka yi shegensa aka kawo ma ai in ta yi wari ma ji.â€? Ta yi waje fuuuu! Kamar guguwa tana kwalawa ‘yar koren ta Asbi kira. Kishingide take cikin (3 seater) tana nazarin jaridar TIME takun shi kadai ta ji bisa marble din da ke shimfide a gidan ta san cewa shi ne, kasancewar shi, maigidan ta, Brigadier Bello Makarfi, mutum ne mai takin kansa. Duk da ya kwana biyu, kakkarfan mutum ne mai tsari, ga masifar saukin kai, musamman a cikin iyalinsa. Ta aje numfashi da jaridar gaba daya ta maida hankalin ta ga kofar shigowa, Sanye take cikin jajayen English wears riga da siket na zaman gida, a kunnen ta jan dankunne ne na barima dan mitsitsi, ta matse gashin kanta cikin jan hair-bound sai kamshin turaren ta Sandara ke tashi a falon. Saratu Sani Makarfi kenan. Ta mike cikin zumudi ta amshi babyn, “Ikon Allah, Baban su Khalil baby daga ina?â€? Ta kai duban ta gare shi, kyawawan idanun ta na masu bidar bayani, ‘yan bakaken lebban ta makale da lallausan murmushi. “Allah ne Ya ba ki, short and simple.â€? Ta fadada murmushin ta zuwa dariya-dariya. “Kada ka zolaye ni da abinda har abada ba zan samu ba.â€? Ta rungume babin a kirjinta idanunta suka ciko da kwallah, ya janyo ta gare shi ya ce, ‘Na taba yi miki wasa kwatankwacin wannan?â€? Ta girgiza kai da sauri. ‘To I mean what I said (Ina nufin abin da na ce). “In kuwa haka ne sai in ce Allah ya biya ka da Aljannar Firdausi Baban su Khalil, very cute baby girl, (kyakkyawar jaririya). Don Allah Daddyn daga ina?â€? “Daddy ko Darling?â€? Ta yi murmushi ta ce, “To Darling din, Allah ji nake kaunar ta na karuwa a raina, har bana jin zan iya baiwa uwar ta, ka taimaka ka karba min riko baban su Khalil.â€? Ta kwantar da kanta bisa kafadun shi kamar ta saki kuka, ya janye zuwa ga kan wayarsa da ke ta faman tsuwwa ya amsa ya ce, “Hello.â€? ‘Wato Daddy ka mance da mu a school ko ka ce da Sam ya zo ya dauko mu ko?â€? Faisal ya ce. “Kuma ka san yunwa ta matsa min amma ba ka damu ba koâ€?.â€? Cewar Najib. “To da ka je Kanon, ka sayo min Gurasar?â€? Yasir ya tambaya. “Wai me ya same ka ne Daddyn mu? Muna ta Magana ka yi shiru. Ko Hajiyar mu ta sake bata maka rai? Faruk ya dora na shi tambaya. “U keep silent Daddy, what’s the matter (Ka yi shiru me ke faruwa)? Inji Furkan. “Wai ma tukunna ka bawa bindigata bullets din da na ce ka sa mata kafin in dawo?â€? Bello (Daddy) ya ce. Ya yi murmushi cikin rashin gajiyawa da jerin gwanon tambayoyin su, don in akwai abin da ya saba da shi to wannan ne. “To shin nawa zan fara amsawa ne my cuties, irin wannan tambaya haka, yaushe ku ka koma ‘yan jarida daga sojojin da na sani?â€? Gaba daya suka rude, kasancewar duk suna jin sa a tare, shi ma hakan handsfree. “Nawa-nawa za ka fara amsawa Daddy.â€? “To ku yi mun uzuri my dear soldiers, Antin ku ce ‘in labourâ€?, so ku bari in ji da zuwan our newly born baby.â€? “Eho!!! Daddy Anti amarya haihuwa za ta yi? Amman mace za a haifo mana ko?â€? “Ga Sam nan na turo shi ya dawo da ku in kun zo kun gani.â€? Ya rufe wayar ya dubi Saratu da ke ta faman lallashin baby ya bude mata hannuwan shi duka, ta tafi da sassarfa sai kuma ta kara da gudu-gudu ta shige, ya maida ya rufe su ruf, ita da babin ya shiga rada mata cikin kunnuwanta. “A kullum shi yasa nake dada son ki Saratu, duk abin da ni ke so kina so. In an batamin sai ki shayar da ni farin cikin da ke mantar da ni ni tsoho ne. Allah ya yi miki albarka ya kuma sakawa Baffa Sani da ya yi tunanin hada mu aure da alkhairin duniya da lahira. Wannan yarinya Allah ne ya ba mu.â€? Ya kwashe duk yadda ya tsinto babin gaba daya ya fada mata har yadda su ka yi da Hajiya kafin ya shigo sashin ta ya fada mata bai rage komai ba. Ta yi salati ta kara kankame jaririyar gaba daya ta ce, “Amman Hajiya ta yi wauta, da ai na kowa ne, kuma ba ka san wanne ne zai ji kan ka ba. Ni kam Allah bai nufe ni da haihuwa ba da kai Baban su Khalil, amma na gode masa da ya kawon ta inda ban tsammani ba. Na yi alkawarin rike yarinayr nan tsakanina da Mahaliccina ba kuma zan taba nuna mata ba ni na haife ta ba. Abin yi yanzu shi ne ka je ka rufe bakin wanda duk ya san al’amarin don gujewa bacin rai a gaba, sai in ce Ubangiji Allah ya taya mu riko da amana.â€? Ya yi mata kyakkyawar sumba ta nuna kauna da yarda, hadi da godiya mai tarin yawa. Ko a yanzu kimar amaryar shi Saratu ya dadu a idanun shi, hakan nan ya kara ba ta wani matsayi na musamman a zuciyar shi. “Ni za ni in biyewa shirmen su Furkan, sai ku je Mother’s Delight ki hado mata duk abin da za ta bukata. Daga naira daya zuwa million na yarje miki Saratu ki je ki hado a kawo min bill din.â€? Ta yi murmushin da ya fidda siririyar wushiryar ta, “Har yanzu ban ji sunan Baby na ba?â€? “Ai yanka za ai Saratu sati mai zuwa idan Allah ya kai mu, haihuwa fa muka yi, kuma haihuwar ma na ‘ya mace da muke mafarkin samu a gidan nan, kenan dole a yi shagali ko don rufe bakin mutane?â€? Ta yi ‘yar dariyar ta mai ban sha’awa ta ce, “To ai kowa ya san ba ni da ciki, the worst part din ma yadda ku kai da Hajiyar su Aminu, yi tunani?â€? Ya yi dan jim, “Idan har za ta dagawa mutane hankali ne kan abin da aka yi domin neman mafificin lada a wurin Ubangiji, wallahi sai dai ta bar gidan nan, don ba ta isa ta sani ko ta hana ni ba.â€? Ta girgiza kai ta yi daki rungume da babyn ta da ta samu barci. ***** “Magana ce nake so mu yi?â€? ‘Ba ni da lokaci.â€? “To ki aro, ki karkade kunnuwan ki ki ji ni. Dukkanin mu ba yaro a nan, kuma na yi zaton shekarun ki da tunanin ki ya isa ki zama mutum, amma kina halin dabbobi.â€? Ta gwalo ido cikin mamaki, “Yau ni ka ke kira dabba Baban su Khalil, a kan tsintacciyar ‘yar ka?â€? ‘Ni ban ce miki dabba ba, na ce ne kina irin halin su na rashin tunani. To ki ji ba da wai ba, ranar da duk ki ka bude baki ki ka furtawa wani yarinyar nan ba ‘yata ba ce, tsinto ta na yi, babu igiyar aure ko daya a tsakanin mu.â€? Ta fashe da kuka, “Au! Ci min mutunci za a yi saboda ka je ta tsafe ka shi ne za a tozarta ni? Ba ka cewa ka sake nin kai tsaye?â€? Ya juya zai fita ta sha gaban sa fuskar nan jage-jage da hawaye, “Na ji ba zan fada ba, amma ina fada ma gaskiya, ba ruwana da yarinyar nan, na tsane ta, Allah tun ranar da ka kawo ta, na fada na kara.â€? ‘Wannan kuma matsalar ki ce, gafara nan ban hanya in wuce tun ban babballa ki ba.â€? ‘Ai ban gama ba ne, mijin karuwa, kada shegiyar ‘yar ku ta sake ta shiga sabgar halatattun ‘ya’yana.â€? Ya nuna ta da dan manunin sa ya ce, “Nafisa, ke Nafisa ki fitar min a ido in rufe. In ki ka kara kira min mata karuwa, za ki dandana kudar ki, karuwanci har aka fi ki? Ko ba kina karuwancin na aure ki ba? ‘Ya’ya kuwa ‘ya’yana ne babu fitinanniyar da ta isa ta raba mini kan su. Kin san tsintsiya ko? To haka zan maida su. Ki kiyaye zugugun bakin nan naki.â€? To kwana biyu dai suna badakala da yin ta ba dadi da maigidan. Ta dai tabbatar Brigadier gab yake da ya guntile tsohon auren su a kan shegiyar jaririyar shi. Yinin ranar zungur kukan bakin ciki ta wuni yi musamman da ya kori ‘yar koren ta Asbi ya ce kuma ko gaisuwa ta sake yi da matar shi sai ya harbe ta ya ba ungulu naman ta, don ya lura sun kukkulla munafurcin su da suka saba. Sam direba da sauran sojojin da ke aiki a karkashin sa duk ya tura su Lagos ya dauko wasu sababbi daga Porthacourt. Brigadier Bello Makarfi kenan, namiji saura mazan jiya, hadari sa gaban ka, guguwa mai fyade wanda ta so, sojan arewa mai watsa shashashai. Wannan ne kirarin sa. How much do you like this story? 5/7/22, 13:10 - Ummi Tandama😇: ____________________________ *âœðŸ? SIRADIN RAYUWAâœðŸ?* Book one *@Takori* Page1ï¸âƒ£1ï¸âƒ£ Wane Ne Brigadier Bello Makarfi? Bello Isyaku Makarfi, mutumin garin Makarfi ne ta jihar Kaduna, Bello ya tashi maraya gaba da baya hannun Baffan shi Mal. Sani ya girma. Lokacin da aka tura shi NDA garin Jos, shekarun shi ba su fi ashirin da biyar ba. Kwazo, himma da sadaukar da kai irin nasa ya kai shi matsayi iri-iri a soja cikin ‘yan shekaru kalilan. Ya auri Nafisa diyar wani shahararren dan siyasa mai neman kujerar gwamnatin Kaduna na lokacin wai shi Magaji Doller ne tun auren saurayi da budurwa, don dukkansu so ne ya hada su lokacin tana ajin karshe a sakandire, sai bayan auren ne ya fahimci Nafi watsatstsiya ce, irin ‘ya’yan nan da iyaye suka jika da naira, babu kwaba babu hantara kasancewar ita kadai suka Haifa, sai daga baya ne Allah ya nufa ta zauna gidan auren, da taimakon kaunar da take masa. Gidan iyayen ta yana nan a unguwar Kabala Cutain, cikin garin Kaduna wanda a halin yanzu mahaifiyar ta ce kadai a ciki (shekarun baya ne mahaifin ta ya rasu a hatsarin jirgin sama a kan hanyarsa ta zuwa birnin New York). Wannan ya ba ta damar zama millionnaire domin daga ita sai mahaifiyar ta kadai suka gaje mahaukaciyar dukiyar da ya bari. Kusan Nafisa ta fi mijin ta kudi don shi ma’aikacin gwamnati ne na kasa, sai dai za a kira irin su top-millitary a yayin da ita kuma ke harkar cinikayyar gwalagwalai daga kasashen Africa daban-ban da sauran kasashen da ke ketaren mu. Akwai babban shagon sayar da gwalagwalai nata na kashin kanta da ta bude a babbar kasuwar Kaduna, wanda ta sanya wa sunan first born din ta Al’ameen Jewellaries. Akwai matsananciyar kauna tsakanin ta da babban danta Al’ameen wanda ya ci sunan marigayin mahaifinta ne. Hakan nan sun bude wani a Lagos sai dai na hadin gwiwa ne tsakanin ta da aminan ta Haj. Suwaiba matar gwamnan Kaduna na lokacin da Haj. Badi’a ministar kudi ta lokacin. Sun yi aure yana matsayin Laftanal-kanal a shekarar da suka haifi Mohd. Al’ameen, yana major din shi ta haifi Najib, Faisal da Yasir. Shekarar da mahaifin ta ya rasu ne ta haifi Nasir da Bello mai sunan Daddy da suke kira (Daddy Karami). Daga Bello ta haifi Faruk sai ‘yan biyu duk maza Idris da Furkan. Dan ta na karshe shi ne Ibrahim Khalil da bai fi shekaru uku ba a lokacin. Kusan duk yaran sun fi shakuwa da Hajiya Saratu fiye da ita ba don komai ba sai don ba ta da lokacin su, harkar kasuwancin ta ya fiye mata komai muhimmanci, ke dai bar ta masifar son ‘ya’ya da kashe masu kudi, amma babu lokacin kula da tarbiyyantar da su. Duk wata kulawa da ta dace uwa ta kwarai ta bai wa ‘ya’yanta yaran nan sun same ta ne daga Aunty Saratu, tana iya kokarin ta kwarai wajen ba su kulawa ta musamman da ingantacciyar tarbiyya, kai ba ka ce ba ita ta haife su ba, ba ta ko damuwa da habaicin da Hajiyar ke yada mata na “a ci a yi kashi kadai.â€? Ita ko rurrutsa ma take wato kwanika, don duk shekara take haihuwa, sai daga kan Khalil ne haihuwar ta yanke mata, don haka kusan gaba daya yaran dukkansu daya, ba za ka iya bambance wa ko kani ba in har ba su suka gaya ma ba da bakin su. Brigadier Bello kakkarfan mutum ne na sosai, wankan tarwada mai kyakkyawar sura. Da wuya ka yi masa kallo daya ba ka maimaita ba saboda cikar zati da kamala. Mutum ne mai tausayi da jin kai, ya sha fadawa hadarurruka iri-iri a zamanin kuruciyarsa irin dai na kowanne soja, amma juriya da maida kai irin nasa yasa har kullum cikin promotion kan promotion yake. Bai damu ba don ya sadaukar da ransa kan cigaban kasar shi, Nigeria. Jaridu da mujallun Kaduna kan so buga abin da ya shafe shi saboda yadda jama’ar Kaduna da kewayen ta ke son shi. Ba shi Kaduna, ba shi a Lagos, kuma ba shi Abuja inda duk aiki ya wulla shi anan yake shi da iyalin sa, ayi ta famabn canjin makarantar yara. Rayuwar su abin sha’awa ce ga kowa barin ‘yan mazan ‘ya’yansu masu tsabar kama da juna. Duk da kasancewarsa ba mazauni ba baya sake da tarbiyyar ‘ya’yan shi. Islamiyya dole ne su je ta da yamma haka da dare ya aje masu malamin Addini da ke karantar da su littattafan Addini irin su Kawa’idi, Ishmawi, Sirah, Arba’una Hadith, Nurul-Mubeen da sauran su. Idan kuma sun tafi makarantar boko ba su dawowa sai karfe hudu na yamma, domin akwai special edtra lesson da yasa ake masu after school hours. Don haka duk cikin yaran Hajiya Nafi kaf babu dakiki kowanne kwaro ne wajen karatu, idan har ka ji su suna tafka musu to a kan karatun su ne, don kowanne ji yake ya doke dan uwansa a hazaka. Haka lafazin da ke fita bakin su a shekarun su zai ya ba ka mamaki, babu wanda ba za ka ji shi da ma’ana ba. Ga hadin kai, ga baiwa babba girmansa koda shi ke binsa a haihuwa. ‘Ya’yan Brigadier ba su san wani abu wai shi yawo ba ko raini ga na gaba. Basu iya zagi ba, basu iya karya ba, basu san yaya ake yin su ba. Haka idan sun dawo daga lesson din dare, kafin su kwanta karatun su ya koma wuyan Anti Saratu. Saratu, diyar Baffan Brigadier ce, auren zumunci ne a tsakanin su, zumuncin ma irin wanda aka zama daya din nan kamar wa da kanwa na ciki daya. Ta kammala digirin ta na farko daga Jami’ar (Edeter) da ke U.K, inda ta karanci Insurance zallah. Wannan kuwa daurin gindi ta samu daga murdadden dan boko dan uwan ta Bello, wanda ya dauki nauyin komai na karatun ta shekaru hudu cif a matsayinta na kanwarsa wadda nauyin komi nata ke kansa tunda ba’a yi mata aure ba. Ta dawo gida tana da shekaru ashirin da hudu da haihuwa. Rikicin auren ta da Alhazai biyu shi ya yi sanadiyar auren ta da yayanta, ko ko in ce daga gatse. Da fari Baffan su ya kira Brigadier ne ya ce, ‘Ka ga karatun nan dai kai ka daurewa Saratu gindin yinsa, ga shi ta dawo kowa ya zo ta ce ba ta so ga illar shi, kana nufin auren ma ka daure mata gindi ta ki yi?â€? Ya ce, ‘A’a Baffa, Saratu na son yin aure, ba ta samu wanda ya kwanta mata ba ne har yanzu. A yi hakuri a kara mata lokaci.â€? Baffan ya yi salati ya ce, “Shekaru ashirin da hudun za a karawa lokaci? To wallahi ba a gidana ba sai dai ka dauke ta ka kai can gabanka ta zauna. Duk kun ja min surutu a gari, ban isa in je wajen daurin aure ba sai an nuna ni ana zundena ga wanda ya aje uwar mata a gida wai boko. Idan ba kya son shi Alhaji Saminu saboda mata uku, shi wannan ministan fa mai mata daya saboda Alah me ye laifin sa?â€? ‘Yar auta Saratu sai ta kwabe fuska, ‘Gaskiya Baffa ya fiya tumbi, rundumi, ina zan kai wannan kayan jigida?â€? Brigadier ya yi dariya shi ko Baffan sandarsa ya dauka zai buge ta Bello ya tare, ya ce, “Ni za ki kawowa fitsara don ki nuna min ke kin je turai kin fetsare? In gaya miki Mungo-Park ma kakan-kakan ku mun ga iyakar sa balle ke, kuma tunda ba kya son Alh. Aliyu sai ki tattara ki bar min gida ko a daina ganin ki a garin nan ana nuna ni a wajen daurin aure.â€? Ya soma kuka. Brigadier ya ce, “Baffa duk abin bai yi kamarin haka ba, kash…â€? ‘To, to na ji bai yi zafin haka ba, ai sai ka gaya min me kuma ku ke nufi? Ka ce karatu, an kare, sai kuma me? A sani a bakin duniya ko me? Ba kwa auren junan ku kowa ya huta? In kuma shi ma tumbin gare shi to don uban ki zo ki fice min a gida ki koma can turan ki auro bature sardidi sannan ne ki ka burge ni.â€? Dariya ce ta kama su dukkan su, ya yi murmushi ya tausasa murya cikin rarrashi, ‘Allah ya ba Baffa hakuri, abin bai yi zafin haka ba sam, Saratu kin ji me Baffa ya ce? Me zai hana ni ki aure ni?â€? Kunya ta kama ta, ta sunkuyar da kai ba ta ce komai ba. Sai dai a ranta hakika ta yi na’am da auren Yayan ta, don dama tuni ta dade tana sha’awar yiwuwar hakan, don duk duniya ba ta ga namijin da ke burge ta kamar shi ba. Sai dai me? Tana masifar tsoron Hajiya Nafi, don ta san ta kwarai kamar yunwar cikin ta kan azababben kishi a kan mijinta da suma da suke dangin sa balle sun aure shi? Baffan ya ce, “Za ki amsa ko sai na yi kwallo da ke?â€? Ta zabura ta fake a bayan Yayanta, cikin tsoro ta ce, “Baffa to Hajiyar su Aminu fa?â€? Brigadier ya yi murmushi, “Ke manta da ita, ba abin da za ta yi miki, kin amince ko Saratuna?â€? Duka suka yi wa juna lallausan murmushi har suka bai wa Baffan kunya, ya mike yana karkade buzun shi ya yi cikin gida. Ba karamar badakala aka kwasa da Hajiya Nafi ba kan auren Saratu, don cewa ta yi munafurci ne su Baffan suka kulla mata don dama sun tsane ta, amma in ban da haka a rasa wadda za a kakaba masa duk cikin dangin nashi sai yarinyar da suka tashi gida daya? Kwanan ta goma a yaji babu wanda ya je bikonta da ta ga abin ba na wasa ba ne, dolen ta ta dawo ta tadda amarya a rufaffen sashin da ba kowa, kamar ta yi hauka, ta hana kanta ta hana kowa a gidan nan sakat da bala’i. Da ta ga wannan ba zai mata ba, domin kamar tana zuga su ne su kara likewa juna sai ta koma bin malamai da ‘yan tsibbu, ta mance Saratu kanta ‘yar malam ce, ba kowanne karabitin asiri ke kama su ba. ‘Ya’yanta ke ta tausar ta da cewa ta kwantar da hankalin ta har Najib na cewa, “Maman mu in ta zo me za ta yi miki? Maman mu ba a kan ki za ta zauna ba.â€? Shi ko Faisal cewa ya yi, ‘In dukan ki ta yi Ya Aminu zai rama miki.â€? To sai ya kasance ita Saratun mace ce mai ilmi na zaman duniya ta san yadda take tafi da abokiyar zaman ta cikin lumana. Amma har inda nan ke motsi, Hajiya Nafi kafarta ba ta bar gidan ‘yan tsibbu ba da ‘yan bori ba a hana Saratu haihuwa. To sun ci nasarar wannan kam, tunda ance abin gaskiyar mai shi ne. Amma kullum mijin su kara son ta yake saboda hankalin ta da tunani. Rashin haihuwar ta ba su danganta shi da kowa ba face Allah. Su kan ce lokaci ne har yanzu bai zo ba. Shekarun ta biyar a gidan wadanda in kin dube ta ba za ki ce ta hada ashirin da taran ba. Tana aiki da Insurance Company na Kaduna. Haj. Saratu baka ce bakin da akan kira black beauty. Mace ce da ta lakanci kalmar ‘gayuâ€? duk da shekarun ta still ita ‘yar gayu ce komai kuma cikin gayun da bokon take yin sa. Rakiyar Brigadier aiki duk ita ce haka in za shi abroad domin hutu ko aiki duka Aunty Saratu ce mai rakiya. Ita Hajiya son ‘ya’yanta ta sani sai maida kobo ya koma dari. ***** Ta sanya baby a ruwa ta yi mata kyakkyawan wanka, tana mai tazbihi ga Al-Khaliku Sarkin kaga halitta ta yadda ya suranta wannan yarinya tamkar diyar Larabawan Masar. Wani irin so ne ke huda bargo da tsokar jikin ta na ‘yar da ba ta san ko ta wa ye ba! Ta ciro bebin daga ruwan tana nannadewa a tawul kenan su Khalil suka shigo, wani na ture wani, kowannensu na cewa shi zai fara goyon bebin da Daddy ya ce ta haifa suna makaranta. Dadi ne ya kamata ta ce, Najib ne zai fara goyawa tunda duk ya fi su karfi. Najib shi ne da na uku a ‘ya’yan Hajiya, yaro ne mai kunya sai ya sadda kai a ransa yana cewa yaya ma za ai ya goya mace? Ya ce, ‘A’a Anti ai mace ce, da dai namiji ne sai in goya.â€? Faisal da tun shigowar su yana durkushe gaban jaririyar ya yi farat ya ce, ‘Gafaracan da Allah malam ni in goya, anti ni za ki na goyawa baby kullum.â€? Ta sa masa bebin a baya tasa zani ta kulle masa. Najib da yake duk ya fi su wayo har Faisal din da ya girme shi ya dubi bebin sosai ya ce, “Antin mu a haka wani sai ya ce bebin nan ta yi wata uku?â€? Gaban Antin ya bada dam! Sai kuma ta yi dan jim, kafin ta ce, “Ai su dama lafiyayyun babies haka ake haifan su da girman su.â€? A ranar kwata-kwata Faisal bai bar Anti da raino ba, shi ya zabi kaya overall na babies masu kyau cikin kayan da Daddy ya jibge mata ya sanya mata ya shafe mata jiki da olive oil. Haka Antin ta ce da su nonon ta ba ya da lafiya don haka doctor ya ce a dinga shayar da baby da madarar NAN. Faisal shi ya sanyawa babyn feeder a baki yana ta zuga ta wai ta yi sauri ta shanye ko ta yi saurin girma su dinga tafiya makaranta tare. In sun dawo ta bi su Islamiyya kafin su kwanta ya koya mata ABCD. Su kuwa sauran sun zagaye ta in ka dauke Al’ameen da ke makarantar kwana, suna ta yaba kyawun kanwar su, a cewar su ba su taba ganin baby mai kyawu kamar ta ba, ji suke tamkar su lashe ta don so, babu kamar Faisal, da kyar suka bar ta gun uwarta, don sun dage sashin su za ta kwana ko sauro ba za su bari ya taba ta ba, sai da Antin ta ce da su cikin dare za ta yi masu kuka sannan suka hakura. A daren Hajiya Saratu kwana ta yi rikon Allah ya raya mata bebin ta, ya kare ta sharrin dukkan abin ki, ya rufe bakin Hajiya Nafi kada ta fadawa ‘ya’yanta bebin ‘yar tsintuwa ce. Da sati ya zagayo raguna har biyu Brigadier ya kayar a kofar gidan si ya radawa yarinya suna Saratu, don kawai ya nuna mata godiyar shi kan karamcin da ta yimasa da kuma matsayinta a zuciyar shi ya zarce na kowa. Domin shi kan son bebin nan yake bilhakki, son da yake jin baya yi wa wani cikin ‘ya’yan shi bayan Al-Ameen. Unguwar Gwamna Road irin unguwar nan ce ta masu fadi ajin garin Kaduna da babu ruwan kowa da rayuwar kowa, balle har tsegumi ya bullo, don haka Brigadier ya yi wa yaran shi kawai Walima wadda ya hada da birthday din Khalil na 3 years. Da alama jinin Faisal da babyn Saratu zai fi haduwa, don kacokan Faisal ya tare a sashin Antin yana taya ta rainion babyn da yake kira Intisar. Shi dai haka nan yake son sunan, tuni duk yaran suka kama Intisar, Intisar. Antin kadai ke kiran ta da Saratun ta sak. Tun Hajiyar su na duka da zagi kan ya fita hanyar su har ta gaji ta zubawa sarautar Allah ido ta yi watsi da al’amarin su kamar ba ta san Allah ya yi ruwan tsirar su cikin gidan ba ma, ta rungumi kasuwancin ta kadai. Kuma dama yanayin sashin su sai mutum ya yi wata guda bai ga dan uwan sa ba in har ba shi ne ya neme shi ba (tamkar tafiya ce ta layi guda). Babbansu Al’ameen dama tun da fari bai kaunar Anti Amarya, a dalilin yana ganin a kan me Daddyn baya shawara da mahaifiyar shi akan komai na gidan dama rayuwar shi gaba daya sai ita da ta zo daga baya? Don haka ko da ya dawo ya tadda haihuwar Anti amarya bakin ciki bai sai an fada ba. Aminu kawai masifar jin kai da takama sabanin su Faisal da suke friendly ga kowa, ga miskilanci kamar tsohon kuturu, sai dai fa natural brain wannan shi ne nick name din shi a makaranta, Aminu yaro ne mai kwakwalwa a karatun lissafi tun yana karami. Sun dauki Intisar sun kai Makarfi sun warwarewa Baffan su da ya rage masu a duniya da Goggo Jummai mahaifiyar Anti Saratu komai. Abin da suka ce shi ne Allah yasa Saratu ta yo halin mai sunan ta kuma mai amfani ga al’umma. Baffa ne dai ya ce mai ya sa bai tuntubi hukuma ba tun da fari? Ya manta Bellon kansa hukuma ne tunda kuwa babban kusa ne a soja, sai ya ce kawai shi dai hakan nan Allah ya daura mai kaunar Saratu har bai jin dadai duniya zai taba rabuwa da ita. Malam ya ce, “hakika Ubangiji Yana jin kan bayin sa masu jin kai. Allah yasa Saratu ta yo halin mai sunan ta, ta kuma zamo ‘ya abin alfahari a gare suâ€?, yadda kuma abin yake sirri a tsakanin su haka suma za su rike. How much do you like this story? 5/7/22, 13:10 - Ummi Tandama😇: ___________________________ *âœðŸ? SIRADIN RAYUWAâœðŸ?* Book one *@Takori* Page1ï¸âƒ£2ï¸âƒ£ Cikin ‘ya’yan Hajiya Nafi kaf, Aminu ne ya debo halin ta na keta da kekasashshiyar zuciya. Da ta lura shi ne kadai mai taya ta kishin su Saratu, mai kuma son duk abin da take so, duk yaranta sun tare a gindin Anti Saratu sai ta shiga zuga shi ya ki Saratu karama, ya kuma dinga gana mata azaba a boye. Dama kuma duk cikin yaran gidan kaf ba maras kirki irin Aminu, amma Daddyn bai ganewa, wannan ya samo asali ne da kasancewar Aminu lumbu-lumbu wutar kaikai, sunkuru macijin sari ka noke, a fuska Musa a zuci Fir’auna, don a fuska mutumin kirki ne. Daddy na son Aminu ne saboda hazakar sa wanda kullum cikin dauko kyaututtuka yake a makaranta, bai taba yin na biyu ba a gaba dayan shekarun sa na sakandire. Hakan nan Aminu na da shiga ran iyaye da sauran jama’ar duniya ma baki daya. Shi kan sa ya san shi kyakkyawa ne, wannan na sa shi kara homa cikin tsararrakin shi duk da haka yana masifar gudun bacin ran Daddynsu. Shekarun Intisar uku cif, amma hikima da basirarta sun fi karfin shekarun ta, ko kadan ba ta da wayo sai dauke abinda duk aka koyar da ita nan take, don haka Aunty Saratu ta tuntubi Daddy da shawarar ya dace a sanya ta ajin rainon yara. A lokacin an yi posting din Daddyn jihar Lagos dukkan su sun tare a sabon gidan su da ke Victoria Island, wani azababben gini da Daddyn ya yi shekaru yana zubawa kamar ba ba za a mutu ba. Faisal ne ya kawo shawarar a kai baby Intisar Links International School, makarantar rainon yara da wata Baturiya mutuniyar Russia ta zo ta bude a Lagos. Satin baby kwata-kwata hudu a Links shugabar makarantar ta zo ta samu Daddy a ofis, bayan sun gaisa ta ce ita shugabar makarantar da yarinyar shi Saratu ke karatu ne, ya ce, ‘O.k, Links ko?â€? Amma can a karkashin zuciyar shi cike yake da tunanin ko laifin me? Saratu ‘yar shekaru uku da doriya kacal a duniya ta yi? Matar ta ce, “Wato abin da ya kawo ni shi ne in shawarce ka, gaskiya basira irin ta yarinyar ku ya wuce nursery, don haka na kawo ma shawarar in da hali kawai a kai ta (primary 2) a Turkish da aka bude kwanan nan, sai dai makarantar akwai tsada, amma I’m sure, Saratu za ta sami sound background (tushe na kyakkyawan ilimi) a gaba.â€? A nan ne Daddyn ya ja numfashi ya kuma saki murmushin jin dadi, “Ku kai Saratu duk makarantar da ku ke ganin ta dace da ita. Kada ku dama da kudi, daga naira daya har million zan biya, ni dai burina kasar mu ta amfana da ilimin ‘ya’yana.â€? Baby Intisar na aji uku a Turkish, amma fasaharta da kwazon ta kan ba malamanta tsoro. Ba ta da magana ko kadan sai tsabar karatu a cikin kanta tamkar wadda ake wankewa kwakwalwa da ruwan zam-zam. Kyawun ta kadai ya isa yasa mutum ya so ko da ya ki Allah. Sai kuma aka yi sa’a ya hadu da ‘yar gayun uwa; Aunty Saratu kullum cikin wanki da gyaran sumar Intisar take da mayuka masu kyau da tsada, don haka ne kullum za ka ga kan yarinyar yana wani sheki da kamshi, baki sidik kuma a kanannade (curl). Fara ce sol, siraran labban ta jazur da su, hancin ta matsakaici tamkar ansa ruler an ja shi an daidai ta shi a tsakanin idanunta. Wasu irin lumsassun idanu kullum kamar tana jin barci, fasalin su na ‘ya’yan itacen Almond (Almond eyes). Akwai tawwadar Allah a gefen hancinta na dama. Shape din fuskar ta oval (Tamkar zanen kwai), akwai gazar-gazar gashin gira, yalwatacciyar suma ta Fulanin usli, ga kyawawan yatsun kafa da hannu Tubarkallah. A kullum shakuwa mai tsanani na kra shiga tsakanin ta da yaran gidan musamman Faisal da Khalil da yake kusan tsaran ta. Rannan Antin na ofis aka sanar da ita tana da baki kafin ta yi masu izinin shigowa kasancewar ta nemi (transfer) zuwa nan Lagos, suka gaisa, sai suka ce su Malaman su Saratu ne, sun zo ne kurum su ga Mamar ta, su gaya mata Allah yai mata baiwa da ya bata ‘ya kamar Saratu. Aunty Saratu sai ta yi dariya, wannan complain (korafi) na jama’a ba yau ta fara jin sa ba, tun ranar da ta soma fita da Saratu mutane suka gan ta. Ta tambayi sunan su, dayan ya ce suna shi Mr. Victor shi ke koyar da Saratu lissafi. Dayar Mrs. Risikat malamar Turancin su Saratu ce. Tohaka ko kanti suka shiga sai an ba baby sweets zuwa biscuits an ce da Anti Saratu ana son ‘yar ta. Rannan Faisal ya ce, “Anti amarya ba za ki wa baby layar baki irin wanda Hajiyar mu ke mana ba in zamu shiga mutane?â€? Maganar Faisal ta ba ta tsoro. Don haka a washegari Makarfi suka yi sallar Azahar ta kwashe abinda Faisal ya ce ta gayawa Baffa. Baffan ya ce, Faisal ya yi tunani, kuma tsari tun yanzu zai soma yi wa Saratu. A wannan shekarar ne Aminu ya kammala karatun shi na sakandire a FGC Abuja, with flying colours (da sakamako mai ban mamaki). Aminu ya sha albarka a wurin Daddy, gata kuma ya karu sai abin da ya ga dama yake yi a gidan. A falon Hajiya ake hirar wai budurwar Ya Aminun, Bose ‘yar yarbawa Aminun ya kai mata katunan happy-Xmas masu kyau. Yasir ke baiwa Hajiyar labari, ta fusata ta ce, “Kai ina ka san Bosen?â€? Ya sosa keya yana dariya ya ce, “Ki rufa min asiri Hajiya, Allah in Daddy ya ji harbe ni zai yi, kin san Allah kanwar abokina David ne, in suka zo masa visiting sai ta yi ta kawon kaya wai tana sona, ‘yar wannan General Benga Delsun abokin Daddy da suka shirya coup (juyi mulki), a shekarar baya suka fasa?â€? Hajiya ta kwabe baki ta ce, “Kai nan har ka isa yin budurwa dan nan, oh, duniya ina za ki da mu?â€? Ya yi murmushin da ke lotsa gefen bakin shi na hagu (beauty point), ya kuma lotsa tsakiyar habar shi (cleave). “Kai Hajiya, ita har ta isa in yi budurwa da ita? Ba ki gan ta ba fa baka mummuna, ga warin Yarbawa, romantic eyes din ta kawai nake so.â€? Hajiya ta yi salati yayin da gaba daya yaran suka kwashe da dariya, ta ce, “Miko min wayar can Faruk ka gani, in zane dan banzan nan.â€? Ya mike yana murmushi ya ce, ‘Fada kawai ki ke Hajiya ta, amma na san ba za ki iya ba, ni din Al’ameen dan Hajiyarsa?â€? Faisal ne ya shigo rike da hannun kanwarsa Intisar da ta ci ado har ta gaji, sanye take da ruwan bular riga da siket din jeans, gashin kanta an yi kananun kalba an makalkale su da kyawawan ribbons kala-kala. Faisal ya ce, “Ya Aminu ka je in ji Daddy yana falon Anti Amarya.â€? Aminu ya mike ya tura hannuwan shi aljihu, ya dube shi cikin haushi ya ce, “Kai dai la’ananne ne, kullum kana gindin wadannan miyagun ko? Ko da yake na san ba laifin ka ba ne, ba mamaki kai ma an kai sunan ka wurin mai buzun nan na Makarfi.â€? Hajiya ta tuntsire da dariya, amma su yaran hankalin- su bai kai su gane ko da wa yake ba, ya mikawa baby hannu ya ce, “Come on beautiful baby.â€? Sai ta saki hannun Faisal ta tafi gare shi cikin yaukin ta na halitta, don wannan kira ne da ba mai yi mata sai Daddyn ta, kira ne da Daddyn ta ke mata. Ya kalli Hajiya suka kifta ido, (za a yi mugunta kenan), ya dauke ta cancaras kamar ya dau kofin shayi, Hajiyar na cewa, “Kai dai Yayan kobo ne, kawo min babyn nan, kai Faisal je ka ce masa yana zuwa.â€? Ya juya jikinsa a sanyaye cike da rashin jin dadin barin baby tare da su, don azaba tun tana rarrafe Aminu ke gana mata kala-kala, amma ta ki ta gane ta guje shi, sam-sam ba ta da wayo, yanzu ne za a mata abu yanzun ne za ta manta in har ba karatu ba ne. Aminu ya yi hanyar kicin din Hajiya dauke da baby a kafadun shi ya fiddo markadadden tattasai danye cikin firji ya cika kofi ya bude bakinta ya shiga dura mata bayan ya daura ta a saman deep freezer din tana ihu tana zillo, hawaye ya hade da majina shi ko cewa yake. “Sha maza beautiful baby, ko kya koyi magana, pepper soup ne.â€? Sai da ya dure mata tattasan nan duk a cikinta, ya cika ruwan kankara a cup ya sake dura mata, ya wanke mata baki tas, ya sake ta a kasa sai ta fadi talau, ya yi dariya ya kama gabansa. Faisal ya koma daukar baby, ba kowa a falon sai Hajiyar, ya ce, “Hajiya ina kanwata?â€? Ta ce cikin halin ko in kula, “Nan na ga ta yi hanyar kicin.â€? Duk da shekarun Faisal a lokacin ya san mahaifiyarsa bata kaunar Intissar yadda ba ta kaunar mutuwar ta. Ya kan tambayi kansa ko me yarinya karama kamar wannan ke mata? A guje yake kiran Intisar har kicin, abin tausayi, sai ya gan ta kwance bisa tiles din kicin din idanun ta a rufe tana fidda wani irin miyau tsinkakke, ba alamun barci take ko idon ta biyu sai wani irin nannauyan numfashi take a wahale, ya sungume ta ya sa a bayan shi yana gudu har yana faduwa ya nufi sashin Anti Amarya. Yana kuka yace, ‘Anti Intisar ta mutu! Ban san me ta ci a kicin din Hajiya ba.â€? Antin ta amsheta ta tabbatar ba mutuwa ta yi ba, sai dai jikin ta da ya yi wani irin jagab, kamar an yi mata duka. Ta yafa mayafi ta fito ta kira direba ya kai su wani private hospital nan kusa da su. To likita ya yi wa baby allura ta amayar da tattasai tsurar sa, ya basu gado don ta huta, nan Daddyn ya isko su Aminu na biye da shi, ya tambayi abinda ya faru da Saratun, Antyn na share hawayen da suka cika mata ido ta ce, ‘Oho ni na kasa gane wannan abu! Na ke jin firji ta bude ta sha ruwa kuma ta sha tattasai? Amma a shekarun baby duk da ba ta magana da kowa, ya isa a ce ta san ruwa wallahi, koma wa ya ba ta ai Allah yana gani.â€? Aminu ya kau da kai, shi ko Daddy bai ce komai ba, don bai san ma me zai ce din ba. Ya tabbata duk cikin ‘ya’yansa babu mai kin Saratu sai ko uwar su, ita din ma yanzu ba ta nunawa, abin da ya dauka kawai ko dai baby ta dauka lemu ne kawai. Wannan ta wuce. Rannan direban yara bai zo ba har bakwai da rabi ga shi ranar Litinin ce, Hajiya ta iske Daddy tana ta fada wai Emma bai zo ba yara duk sun matsu su tafi kar a duke su, to saboda baya son mitar ta ya kira Aminu ta wayar hannun shi ya ce ya kai yara makaranta. Sauran yara na baya, Khalil da Intisar na gaba, kan ka ce me ye wannan fada ya kaure tsakanin Khalil da Intisar wai sai ya biya ta littafin ta da ya cika da zanen biro. Aminu ya cire lafiyayyen hannun shi ji ka ke kau! Ya wanke ta da marin da ba a taba yi mata ba, ya ce, “Ko uwar ki ba ta isa ta yi surutu ina tuki ba.â€? Ta gigice ta sa kuka da karfin gaske, ya ce, ‘Lalala! Ki yi min shiru, shegiyi mai zakin muryar tsiya.â€? Ba ta yi shirun ba sai ma kara tsananta kukan ta har da ihu, ya kai hannun shi na dama ya ciro ta daga mazaunin ta, na hagun kuwa yana murza steering wheel cikin gwaninta, ya tura ta inda yasa kafafun shi, idan ya taka totur ita ma ya taka ta, duk yaran suka yi tsit kamar ruwa ya cinye su cikin kaduwa. Faisal kuwa da ba zai iya jurewa ba tuni ya soma yi wa Ya Aminun kuka ya daga Intisar kar ta mutu, sai da suka zo makarantar ya kashe motar, ya juyo ya dube su ya fiddo manyan idanun shi ya ce, ‘In ji wani mai tsautsayi cikin ku ya ce na mari Intisar ko na yi mata wani abu, uhn, sai na babballa yaro, ya kuma yi kwanan store Bismillah.â€? Yana fadi yana hada kan Faisal da Bello yana gwarawa don wai su ne manyan munafukai, gaba daya suka sa kuka har wadanda ba a daka ba, ya ce, ‘To ku yi shiru, ai in ba ku fada ba ba zan saku a store ba.â€? Duk suka yi shiru, ya ciro ta fuskar nan ta yi suntum da kuka ya zaunar ta cinyar Faisal ya ce, ‘Lashe hawayen ki I said!â€? Da sauri ta sa harshe tana zukewa. Ya bude masu kofa suka fice, ita ko baby kafa yasa ya cillo ta ya ja motar shi ya tafi. Ranar wata Alhamis Malamin Islamiyyar su ya zo, duk suka fice har sun fara daukar darasi, ita ko baby ta make a bakin kofa ba ta tafi ba tana so su gama ficewa ta sha majinar ta ta koshi tukun, ta yi can hanyar baskwata ta soma fyace majinar a hannun ta tana lashewa tana kuma zakulo tasono tana dannawa a baki kamar an ce da ita juya can, sai ta hangi Aminu tsaye jikin balcony (baranda) yana zukar sigari abin shi yana danna waya, ta saki baki galala! Don ta sha jin Daddy yana yi wa su Faisal hudubar cewa duk mai shan sigari dan iska ne, kuma cikin su duk wanda ya sha sigari ba shi ba shi. Jikinta ya yi sanyi lumus, yau ga dan iska ta gani a zahiri. Jikin shi ne ya ba shi wata kila ana kallon shi ya juyo da sauri suka hada ido, ta juya za ta gudu kafin ta yi taku uku ya danko ta ya ce, ‘Wai ke munafuka ko, au majinar taki ki ka zo sha to yau kuwa za ki dandana kudar ki, kin zo ganina ina shan rothman ko?â€? Cikin kuka ta ce, ‘Allah ni majina na zo sha.â€? Iyakar firgita ta firgita da shi ya kama kunnuwanta ya murde da karfi ya manna mata wani azababben mintsini a wuya ta kara tsananta kukanta, ya ce, ‘Ina shan rothman?â€? Cikin gigicewa Ta ce, ‘Eh.â€? Ya shiga daldalle mata baki da yatsun shi biyu, da karfi ta ce, ‘A’a, ban gani ba Ya Aminu.â€? Ya sassauta rikon da ya yi mata ya ce, ‘Daga yau na sake ganin ki kina lasar majinar nan sai na yanke hancin kowa ya huta, kazamar banza mai shan majina. Wane yaro ki ka gani yana shan majina a gidan nan ko don ke uwarki ‘yar kauye ce, za ku taru ku mayar mana da gida matattarar ‘yan kauye.â€? Ta ce, ‘Allah ba zan sake ba.â€? Ya sake cewa, ‘Kin gan ni ina shan Rothman?â€? Ta ce, ‘Allah ban gani ba.â€? Muryar ta har ba ta fita saboda kuka da razana. Ya yi murmushi ya sakar mata kunnen ya ce, ‘Tafi wurin malam.â€? Ai tun kafin ya karasa rufe bakinsa har ta kusa kaiwa, ya yi dariya ya shige cikin gida yana baiwa Hajiya labari, a fusace ta ce, “NI da Allah rabu da ni, tun yaushe na hana ka shan tabar nan, in ba zaka bari don komai ba ai ka bari don lafiyarka, tunda aka fara haka wata ran ai Daddyn da kanshi zai kamaka, na kuma tabbatar maka duk ranar da hakan ta faru ba kai kadai ba har ni uwarka sai mun kasa kurbar ruwa a gidan nan, me ye amfanin taba ga rayuwar dan Musulmi ban da cutarwa, wallahi ko bayan raina ka kara shan taba ban yafe maka ba!.â€? Yasa hannu ya dafe kai ya ce, “Haba my dear Mum, ki ji tausayina, ki janye wannan furucin naki a kaina, Aminun ki ne fa, insha Allah daga yau na daina amma ki sa mun albarka.â€? Ta yi murmushi ta ce, “Ai don ka san lagona ne, to Allah ya yi maka albarka.â€? Aminu ke koya masu assignment amma baby tana kwance jikin Mamarta ta ki tashi, ta dube ta, ‘Baby yau ba ki da assignment ne?â€? Ta ce, ‘Eh.â€? A dan tsorace don ba ta saba karya ba. Antin ta lura karatun ne yau ba ta so, ta ji ba dadi a ranta, ta shiga daki ta bude jakar ta ta fiddo littafin Maths din ta da yake shi aka fi ba su aikin gida, ta ga aiki na jiya da na yau duk ba ta yi ba, ta fito rike da littafin a hannunta ta ce, “Babyna, me yasa yau ki ka yi min karya?â€? Duk ta dabarbarce, umh, ita kadai ta san azabar da Ya Aminu ke gana mata wajen koyar da karatun nan, duk magana daya ya falla mata ‘ya’yan carbin karfe wai ta fiya jakanci, bayan kuma har ga Allah tafi Khalil fahimtar karatun, amma shi baya dukan shi,ta yi shiru ba ta ce komai ba sai da ta kara tambayarta a karo na biyu, sannan ta ce, “Ki yi hakuri Mamana, cikina ne yake ciwo.â€? Ta ce, ‘To ba sai ki fada min baby na in ba ki magani, sai ki yi shiru ki zauna ciki yana ciwo? Abinci ma ba ki ci sosai ba ya za ai ciki ba zai ciwo ba, tashi maza ki ci sausage rolls din ki ne na yi miki ki tafi wurin Ya Aminu karatu, ko kina son gobe Anti Magret ta buge ki?â€? Ta girgiza kai, ba da son ranta ba ta ci kadan ta dan kurbi ruwa ta dau littafin ta da fensir ta tafi babban falo inda ake karatun. Abin da ta fara ji da shigar ta shi ne. “Kin yi latti, kazama mai shan majina, kneel downâ€?. Ta shagwargwabe fuska tana duban Faisal tamkar mai neman taimako, ya rausayar mata da kai shi ma kamar ya yi kukan alamar su duka zai doke su. Ya ce cikin tsawar da ta sa ta sakin dan fitsarin da ya fara tarar mata. “Ur hands up, ur kneels down?â€? Wato ta tsugunna a kan gwiwoyinta ta daga hannuwanta sama, ta yi yadda ya ce don tsira da lafiyar ta, amma duk da hakan ba ta tsiran ba, ya tsula mata carbi ya ce in ta yi kuka mai sauti sai ya ci uwar ta, ta kunshe baki, kuka kamar ya kashe ta, duk yaran jikin su ya soma rawa, don idan ya soma dukan mutum daya to kowa ma sai abin ya shafe shi, suka ci gaba da karatun a haka duk suna tsorace da shi, sai da ya ga dama ya ce ta zo ta zauna ta yi nata. Yana nuna mata tana shan tsala, to kuka bai bar ta ta gane komai ba, sai ya zuba mata rankwashi kwaf, a tsakiyar ka ya ce, “Uwar ki ne ta ce da ke tara a tara da daya sha biyar (9 +1 = 15)?â€? Ta nutsu, ta hada daidai, ya ce “To ko ke fa, daga yau ki ka sake kuskuren lamba ko daya ba zan gyara miki ba sai dai in dura miki fitsarin Bombino.â€? (Bombino sunan karen da yake kiwo kenan). Da haka karatun ya kare. How much do you like this story? 5/7/22, 13:10 - Ummi Tandama😇: ____________________________ *âœðŸ? SIRADIN RAYUWAâœðŸ?* Book one *@Takori* Page1ï¸âƒ£3ï¸âƒ£ Juma’a 21 Jumada Thani Abinci ake ci bisa dining table kamar yadda yake a al’adar gidan. Furkan ne tsakanin Intisar da Aminu, Hajiya ta kiftawa Aminu ido za a yi mugunta kenan, ya ce da Idris ya miko masa ketch-up (tumatirin kwalba) sai ya faki idon kowa ya janyo har da kwalbar pepper irin attaruhun nan da Larabawa ke sarrafawa cikin kwalba ya zazzaga ketch-up kadan kafin ya zazzaga yajin pepper din kusan rabin kwalbar a plate din shi ya cakude shinkafar ‘fried-riceâ€? din shi, yau kam ya kudire Saratu ba za ta ci abincin ranar nan ba. Hankalin ta na kan T.V inda ake watso shirin da take matukar so na Tom & Jerry, ya faki idon kowa ya sauya masu plate ya janyo nata ya ci gaba da ci hankali kwance, ta cika cokali ta kai bakinta ba tare da ta dubi abincin ba ta tauna ta hadiye, ba shiri ta furzo shi waje cikin plate din Daddy da Hajiya ta zazzaro ido abin dariya ta ture plate din ta mike tana tsalle da ihu. Daddy ya mike ya kamo ta ta fincike ta yi bandaki da gudu, ji take tamkar ta tsige fatar bakinta ta huta da wannan azaba da ba ta taba ji ba. Hajiya ta fusata da abincin da aka furzo mata ta ce, “Dubi sangartar banza don Allah, yarinya ba kwaba ba tsawatarwa da can tunda ta fara cin abincin ba ta ji yajin ba sai yanzu da ta koshi?â€? Ba wanda ya tanka mata sai Anti da ta mike ta bi bayan Intisar din ta, Faisal ya janyo plate din Saratu ya dibi kadan ya kai bakin shi, ba shiri shi ma ya furzar ya ce, ‘Wuh! Allah masifar yaji, ci ka ji Daddy?â€? Aminu ya harare shi ya ce, ‘Wa ya sa ta ta zuba? Ina kallonta tana ta zazzagawa kamar ‘yar kauyen da bata san mene ne a ciki baâ€? Daddy ya dago a hankali ya dube shi na dan lokaci, kamar mai son fahimtar wani abu a tare da yaron, bai ga komai ba illa tarin kuruciya fal a cikin kan shi. A yau kam ya nuna masa bacin ran shi a fili ya ce, “Ko kadan bana jin dadin yadda ka ke mu’amala da kanwar ka Aminu, kai ba ka ganin Saratu karamar yarinya ce ne? Kai da ka ke babba da ya dace a ce ka hada kan dukkan kannen ka ka rungume su, sai ya zamo kai ne ka ke nuna bambanci? To su kuma kannnen na ka su koyi me kenan daga gare ka? Jiya ina ji fa kana tsula mata carbi wai ba ta iya karatu ba, to ba haka ake koyar da karatu da azaba ba, idan har ba za ka koya mata yadda ka ke koya wa sauran ba, ka bari na gode. Amma daga yau sai yau, kada ka sake taba lafiyar Saratu da sunan duka, don uwar ta na maku kawaici ba zan zuba maku ido ku illa ta yarinya ba, once and for all, ka kiyayi Saratu Ameenu!.â€? Hajiya ta aje cokalin da yake hannunta ta dubi Daddy a yatsine kamar za ta yi magana, ko me ta tuna? Oho! Ta maida bakin ta ta tsuke, can kuma ta ja wani dogon tsaki tsuuu! Ta ce, ‘‘Tashi mu bar wurin nan Aminu, maigida ya zo mai tabarma a bakin kofa ai sai ya nade kayarsa, mu nan ba wurin zaman mu ba ne na masu uban ne.â€? Ta fada cikin yi wa Daddyn gatse, amma shi din bai tashin ba, kwantar da kai ya yi ya yi ta bai wa Daddyn hakuri har da kwallah. Sai da ya tabbatar masa ya yafe masa tukunna. Wannan na daga cikin halayyar yaron da har kullum take sayo masa mafificiyar kauna a zuciyar mahaifin shi. Zai yi komai, zai bata wa kowa, amma ban da wadannan mutanen guda biyu; Daddy da Hajiya. Mutum ne da ya iya takun rayuwar shi, da wuya ka fahimci abinda yake ciki. Yana da taka-tsantsan cikin dukkan al’amuran shi mawuya ci ne ka ce yau ga ta inda ya kuskuro ka, sai dai da yake an ce wai zuciyar mutum birnin sa. Haka ne Al’ameen mugun mutum ne na karshe ga wanda ya tsana, sai dai muguntar sa tafi yawa a kan Intisar. In kin san wata kalma wai ita ‘yan-ubanci, to Al’ameen Bello ne shugabanta. Yana son uwarsa, yana son kannensa, baya son kowa ya rabe su saboda matsananciyar kaunar da yake wa Daddyn shi. Yana da ra’ayin rikau na Malam Bature kan single nuclear family life, bai ga dalilin da Daddy zai bata masu family ba ta hanyar kawo wasu can. A da, kafin Dady ya auri Saratu yana matukar shiri da ita, haka ko san da take karatu a Edeter musamman ya kai mata ziyara har sau biyu a matsayin ta na kanwar ubansa, yana jin dadin mu’amala da ita, kasancewarta mace mai ilimi irin yadda yake so, kuma wadda ta rage masu cikin dangin ubansu kaf, sai Baffa da Goggo. Amma tunda ta zabi zaman kishi da mahaifiyar shi shi ma ya ce to mu buga, in ya so mai sa’a ya kwaci Daddyn. To haka Aminu ke ta azabtar da baby Intisar kullu nau’in azabar yau daban ta gobe daban. Har sai da ya zamanto Baby in ta hango Aminu a bakin gate a guje take komawa dakin Mamarta tana haki kamar ranta zai fito, ko kuma wadda ta ga dodo, sai dai ta bude baki ta ce ga abin da yake mata ina! Tana masifar tsoron sa, tun Anti Saratu ba ta ganewa har ta fahimci baby na gigicewa in ta ga Aminu, haka ko muryar shi ta ji daga waje ta nutsu kenan, tun kuma ranar da ya hana ta shan majina ba ta kara ba, majinar ma kanta tsoron ta take ji, bini-bini tana yawo da tissue tana cewa da ‘yan uwan su goge mata, kada Ya Aminu ya yanke mata hanci ko ya ba ta fitsarin Bombino. Shi ko in ya ga Anti Saratu a wuri ya soma yi mata wakar come on beautiful baby kenan ko taso tambayar baby sai ta fasa, ta kan dauka don yana matsanta mata wurin karatu ne. Ranar wata Asabar ba aiki daga Aunty har Daddy suna gida ba su je ko’ina ba. Hajiya ce dai ta tafi Cape-Town can South Africa harkar gwala-gwalan su, kafin ta tafi sun shirya a nakasta Intisar yadda mutane za su daina sha’awar ta ta hanyar gurgunta wadannan kafafun nata ta zama gurguwa ta daina wannan tafiyar tata kamar ta mage, ita kuma za ta taho mai da mota End of Discussion (da ‘ya’yan gata ke yayi a lokacin) da ta yi masa alkawari. Aminu yana matukar tsoron Babansu yana kuma masifar son Hajiyar shi ta yadda duk abin da ta nuna ba ta so shi ma daga ranar ya tsane shi kenan. Rashin imanin da yake ganawa diyar Aunty Saratu ba wai halin shi ba ne domin dai shi mutum ne mai son kananan yara da son wasa da su shi yasa yake son Khalil. Komai yake yi yana yi ne don farin cikin Hajiya, don Hajiyar shi ta ji dadi, domin ta ce da shi ba irin wulakanci da tozarcin da Daddy bai mata ba a kan Intisar lokacin yana makarantar kwana shi yasa shi ma ya tsane ta, don komai yake so ita ma Hajiyar naso, komai yake so ta na yi masa, ko damuwa ya shiga Hajiya ba ta kuma samun kwanciyar hankali ba kuma za ta huta ba sai ta ga ta gusar masa da wannan damuwar. Abu daya ne har zuwa yanzun ta ki mara masa baya wato ra’ayin shi na son tafiya karatu Miami (Miami gari ne na ‘yan hutu cikin U.S.A) don tana ganin duk cikin ‘ya’yanta ya fi sonta, ya fi su kaunar ta, ya fi kaunar abin da take so. Idan ya tafi wa zai taya ta kiyayyar su Saratu? Tsaye yake jikin Volvos 6 din Hajiyar shi, yana ta faman murza ‘yar karamar kwamfutar aljihu pocket computer, sanye yake cikin Kaftani na wata jikakkiyar shadda-rini ‘yar Mali. Sai ga Intisar da Khalil tana rungume da ribdediyar teddin ta, daga inda yake tsaye yana iya jiyo muryar Khalil na cewa, “Baby ki je ki kwantar da ita a karkashin mota zan je in dauko mata filon ta.â€? Ya juya ya koma cikin gida yayin da ita kuma ta nufi karkashin motar da Al’ameen ke tsaye ba tare da ta lura da shi ba, domin ya ba su baya ne. Sojojin da ke gadi a harabar gidan ba wanda ya ba su hankalin shi kasancewar sun riga sun saba wasansu a wurin kullum ta Allah. Ta sunkuya za ta shimfide teddin kenan, sai ya sa kafa iya karfin shi ya yi (bull) da ita, ta hantsila ta wulwula har sau uku, kafin idanunta da goshinta su hadu da wani karfen pipe ta gigice ta dimauce ta saki wata irin razananniyar kara da amsa kuwwar ta ya ratsa illahirin gidan, gaba daya ma’aikatan gidan har shi Aminun suka yi kanta a guje. Jikinsa ya yi sanyi da ganin jini na gudu daga idanun yarinyar hade da wani irin ruwa. Ya saki Computer da ke hanun shi ya dauke ta a gigice yana. ‘Emma bude mini mota, wayyo Allah na shiga uku! Na yi kisan kai!â€? Abin da yake ta nanatawa kenan, har suka isa asibiti. Mummunan labarin ya riski Aunty Saratu ne tana cin abinci, ta saki cokalin ta ce, ‘Inna lillahi wa inna ilaihi raji’unâ€?.â€? Don Khalil da ke bayar da labarin cewa ya yi idanun Baby sun tsiyaye. Shi kan shi Daddy jikin shi babu inda baya rawa, da kyar ya kulle Aunty Saratu yabi bayan su saboda yadda ta fita daga hayyacinta cewa kawai take, ‘Yanzu baby shi kenan idon ki ya tsiyaye?â€? Likitocin ido kwararru uku ne a kan Intisar suna kokarin ceton ‘eye-bullsâ€? dinta (kwayar idonta). Sai bayan awanni uku babban likitan ya nemi ganin Daddyn a ofis din shi, ya fara da kwantar masa da hankali, don ganin yadda duk ya fidda rai ya kuma ba shi shawarar a kai baby asibitin kwararrun ido na Kaduna, in an yi sa’a a ceci lafiyar idonta, amma he’s sorry to say, ko da Saratu ta warke ba za ta ci gaba da gani da naked-eyes dinta ba. Inda duk hankalin Daddy yake in ya yi dubu to ya tashi, bai tausayin Baby kamar Aunty Saratu, da ta ci duk wani buri da fatan ta a kan Inteesar! Amman a yau a ce ta makance! Duk kwazon ta, duk himmar ta da ke sawa ana yi mata hangen zama wani abu a gaba. Bai san san da wasu zafafan hawaye suka shiga yi masa lugulgude a fuska ba tamkar ba Brigadier na soja ba. Yasa habar babbar rigar a ya share kafin ya sa hannu a tura su Kadunan. A jirgin (bell-view) da suke ciki, Aminu Bello, tafukansa yasa ya rufe kyakkyawar fuskarsa. Ya sha jin Malamin su na Islamiyya na cewa, ‘Ku roki Allah ya kare ku daga nadama mara amfani.â€? Bai taba sanin mene ne nadama mara amfani ba sai yau. Tausayin mahaifin su kadai ya ishe shi na wahalar da ya jawo masa. Ya san Daddyn na son shi, amma a yau yana shakkar, idan son da Daddy ke wa Inteesar diyar Aunty Amarya bai dame wanda Daddyn ke masa ba. A asibitin Kadunar ma sun ce ne idan Daddyn na da hali to ya gaggauta fitar da diyar sa asibitin kwararrun ido da ke Jiddah, nan suka bar Intisar karkashin matsananciyar kulawar likitoci su suka tafi neman visa. Masu abu da abin su nan da nan suka samu. Karfe tara na dare an shigar da Baby tiyatar ido. Mu karasa a littafi na biyu. Taku Takori How much do you like this story? 5/7/22, 13:10 - Ummi Tandama😇: ____________________________ *âœðŸ? SIRADIN RAYUWAâœðŸ?* Book two *@Takori* Page1ï¸âƒ£ Ameenu kishingide cikin lallausar kujerar asibitin Saudi-German, nadama goma da ashirin ji yake kamar ya farkewa Daddyn shi komai, in ya so ya nemi gafarar shi, ko ya samu saukin wannan dumbin hakki da ya dauka na rayukan al’umma da dama, na kuma yarinyar da ba ta ji ba ba ta gani ba, ba ta kuma tsare masa komai a rayuwa ba. Lokaci daya ya ji ya tsani kan sa kai da duk ‘ya’ya masu irin halin shi na taya iyayensu mata kishi. Amma tsoron hukuncin da Daddyn zai dauka a kan shi ya hana shi, gani yake kamar ma ya san shi ne sanadiyyar shigar diyar shi cikin wannan azaba shiru kawai ya yi masa, watakila ma kuma idan ya fada masa shi din ne ya tsane shi, hakan kuma ya yi sanadiyyar jawo masa bacin ran Hajiyar shi. Ya yi tunani iyaka tunani, ya rasa mafita cikin al’amarinsa, tunda kuwa ya zama fitina kenan ga iyayen shi? Daga karshe ya yanke abinda yake ganin shi ne mafi dacewa a gareshi shi ne ya bar su kwata-kwata ya fita daga tsakanin su, ya yi nisa da rayuwar su, ya bar masu kasar baki daya ya je ya ginawa kansa sabuwar rayuwa mai amfani. Me ye amfanin ‘ya’ya irin sa masu sanya iyayensu cikin halin ha’u’la’i? Babu. Kada ma ya je Hajiya ta angiza shi ga kisan kai, don ma abin ya zo da sauki? Da ta mutu fa me zai ce da Ubangijinsa? A kan wani kishin su na mata wanda shi bai shafe shi ba. Tunaninikan da yake ta yi kenan har aka fiddo Intisar daga dakin tiyatar da karfe biyu da rabi na sulusin dare agogon su na can. Ya tsaya a kan ta yana ta muzurai ganin yadda aka nannade dukkan idanunta da bandeji, jikinsa ya saki gaba daya. Washe gari likita Doctor Khair ya tabbatar wa Daddy Saratu za ta gani da taimakon medical glasses kanana da za su yi mata. Bayan sati biyu da yin aikin aka cire bandejin da addu’o’i na musamman a bakunansu don Daddy har Dawafi na musamman ya yi a kan lafiyar Intisar kadai. To Alhamdulillahi Saratu na gani daga kusa-kusa, sai dai ba ta iya gane abin da ke nesa da ita tangaran abinda a turance suke kira short eye-sight. A ranar Dr. Khair ya manna mata farin siririn medical glasses tamkar gidan biro don siranta garai-garai da shi kamar na ado, wallahi kada ki so ki ga yadda ya karawa yarinyar nan wani irin kyau da kwarjini, da aka sa mata sai ta kama dariya. Daddy ya kashe kudi ba kadan ba, amma wannan ba shi ne damuwarsa ba shi dai burinsa kada a ce Saratu ta rasa ganin ta kwata-kwata. Don haka da ya tabbatar tana gani tar da gilashin in an cire ne take gani dusu-dusu sai ya gode Allah. A ranar da suka cika sati na biyar suka dawo. Anti Saratu duk ta rame ta yi duhu saboda zullumi. A guje Intisar ta rungume Mamarta suka shiga juyi a tsakar gidan har suka bai wa kowa da ke wajen tausayi. Tana gaya mata labarin Daddy ya saya mata gilas mai kyau, za ta ke ba ta aro tana danawa, yaya Aminu yana ba ta abinci a baki baya tsula mata carbi a unguwar da suka je. Yayin da Ameenun ya yi tsaye harde da hannunsa bisa kirji yana kallon su cike da jin nauyi ko kadan bai bari sun hada idanu da Antin ba, tunda suka dawo. Antin ta dube si ta watsar ta ce, ‘Al’ameen kenan. Kai ma sannu da kokari.â€? Yanayin yadda ta fadi maganar cikin gatse, dole ta sa shi ya yi murmushin dole har cleft din ya lotsa, ya kuma sha jinin jikin sa, ji yake kamar ya ce da kasar ta tsage ya shige, ji yake kamar Anti Saratu ta san shi ne sanadiyyar nakasar diyar ta. Haka kurum Daddy ya aika takardun retire (murabus daga soja) Abuja. Ko kadan Al’ameen bai so ba, domin yana tunanin Daddyn ya yi hakan ne domin ya yi joining su Benga Delsu da ke son yin juyin mulki cikin ‘yan shekaru kalilan. Bakin ciki biyu kenan ya hadu ya tarar masa. Ga nadamar abin da ya aikata, wadda ta sa har ya tsani kansa da kasar haihuwar shi baki daya, ga kuma bakin cikin Daddyn su zai zubar da mutuncin su a idon duniya. Ran shi a masifar bace ya sake bijiro da bukatar shi na tuntuni, wato na son tafiya karatu Miami, ba tare da ya tambayi Daddyn dalilin shi na yin ritaya ba. Daddyn ya ce ya je duk abin da suka shawarta da mahaifiyarsa shi ba shi da ta cewa. Da kyar Al’ameen ya shawo kan Hajiyar ta amince da tafiyar shi sai dai ba ta amince mai zuwa America ba, duk wani Musulmi na kwarai yana neman tsari daga sharrin wannan kasa, amma ba wai ya yi marmarin kai kansa ba, ba mamamki ya mance kasar haihuwar shi Nigeria ce, birni irin Miami? Birni ne na hutu zallah, yana daya daga cikin biranen da kasar Amurka ke takama da su, saboda kasancewar shi wani bangare na kara bunkasar tattalin arzikinta (tourist attraction) sabida yadda al’ummar duniya suka zabeshi a matsayin wajen hutun su (Miami resort) ga kuma kashe Musulmi da kasar Amurka ke yi a lokacin. Ta ce ko dai (ELT Banbury) wato Ealing Tertiary da ke England ko Hull Unibersity (duka Britain ne), hankalinta zai fi kwanciya, in kuma duk ba su yi masa ba to ya tafi jami’ar Abuja. Ya amince zai tafi Hull ne kawai a fatar baki amma can a karkashin zuciyar shi ya kudurce a Miami zai karaci gaba dayan sauran rayuwar shi har mutuwa, ba don jin dadin da ke cikin birnin ba sai don wani specific reason (kayyadadden kuduri) nashi na daban. Duk wasu shirye-shirye na tafiyar Al’ameen, shugaban kasa na lokacin wanda aminin Daddy ne na kut da kut tun suna NDA shi ya yi wa Al’ameen, ga inda Daddy ya ce a kai shi, amma Al’ameen ya zage ya ce da shugaban Miami ne. Akwai kudi na musamman da kasa za ta ke tura masu duk shekara a matsayin su na ‘yan kasa masu karatu a waje da alkawarin dawowa su yi wa kasar su aiki. Ran Al’ameen a masifar bace ya bar Nigeria zuwa U.S inda daga nan ya nemi hanyar birnin Florida, a inda ya sami gurbi a babbar jami’ar Miami inda aka yi admitting din shi into lebel 1 Medicine. A shekarar shi ta biyu a Miami rannan ya ji a tashar BBC cewa an yi juyin mulki a Nigeria. Tunanin Al’ameen kawai shi ne har da Daddy din shi wanda yana ganin wannan karshe zubar masu da martaba da daraja ne Daddyn ya yi tunda har abada ya bar masu abin fadi, ba kuma ya cikin tsari na abin da ya koyar da su. Aminu ya yi kuka ya yi kuka har ya gode Allah, kukan da bai taba tsamamnin zai taba yi ba a rayuwarshi. Ya alkawartawa ransa shi da gida Nigeria har abada! Ko ya gama karatun shi nan zai nemi aiki ya yi aure ya yi zamansa. Ya manta Allahu shi ne mai juya al’amura yadda ya so. Ya je ga kwamfuta ya zanowa mahaifin shi sako yana fitar da zafafan hawaye (sanda na rubuta wannan littafi ilmin yanar gizo bai yi sauki da yaduwar da yayi a yanzu ba haka sadarwa ta kwamfuta ba kowa ke yin ta ba) na dalilin da yasa ya bar Europe zuwa U.S shine don kar suke samun koda labarinsa, a ganin sa ba shi da sauran amfani a gare su. Ya yi matukar nadamar wani gagarumin laifi da ya yi wa Daddyn shi ne zamowar shi sanadiyar nakasar Inteesar diyar Anti amarya. Ya kuma nuna karin dalilin shi na yin nisa da su saboda bakin cikin abin kunyar da yake tunanin Daddyn ya jawo masu. (Kaico! ‘Ya’yan yanzu har mun fi iyayen mu tunani da sanin abin da ya dace su yi? Mun fi su sanin abin da yake mai kyau a gare su? Anya Aminu bai yi kuskure ba?) A karshen sakon sa ga abin da ya ce duk dai mai nuna tsantsar nadamar sa kan abin da ya aikatawa Intisar ko ko nadamar shi da ya kira mara amfani. “Now, plz, don’t think I feel I’ve overcome all these regrets, I’ve not. I am one of those people that have to-day-to-day job on myself. But gradually, by trying to follow your teachings, I’m learning to control myself and be less critical of my fellow human being. And, it’s like being released from a prison. I just never dream that life could be so full and wonderful as earlier. Sincerely. (Sai ya yi signing din shi a kasan signing din ne ya rubuta). Mohammad Al’ameen Bello. Ma’ana: A yanzun haka kada ku dauka ko na yi nasara ne a kan dumbin nadamar da na yi, ban yi ba. Ina daya daga cikin mutanen da ke duba rayuwar su ta yau da kullum a kan-kan su. Amma a hankali, nan gaba ina kokarin in bi koyarwarka, ina koyon yadda zan ke sarrafa rayuwata in kuma zamo mara kushe da hassada ga kowanne dan adam dan uwana. Sai kuma hakan ya zamto tamkar fita ne daga kurkuku. Na san dai rayuwa ba za ta taba zama cikakka kuma mai dadi ba kamar da. A ranar Anti ke da Daddy, yana bisa kwamfuta yana duba sakonnin shi, yawanci abokan aikin shi ne ke yi masa korafi da nuna rashin jin dadin su na ritaya da ya yi da wurwuri, da sauran karfin sa da komai ga wadatacciyar lafiya. A kuma lokacin da ake mai hangen isowa matakin General, cikin ‘yan shekaru kalilan. Shi ko Brigadier Makarfi ko kadan ba su san tsarinsa ba, baya da wani nufi illa ya samu lokacin kula da iyalin shi da sa ido sosai a kan tarbiyyar su, tare da fantsamawa mahaukacin kasuwanci don neman abinci, wannan shi ne kadai dalilin shi na yin ritaya, amma ba wai don wani dalili na daban ba. Kwatsam sakon Al’ameen ya bayyana jikin screen , ya karanta ya maimaita fiye da cikin carbi amma bai fahimci abin da yaron ke shirin bayyana masa ba. Ba inda suka ce ya je ba ya je, kuma shi ya yi sanadiyyar nakasar idanun Saratu? Ya kai duban sa ga sashen da Aunty ke kwance tana karatun littafin addu’o’i na Al’ma’asurat da take karantawa duk dare kafin kwanciyar barci, ta kare tana kishingide jikin tuntu da alama cikin dogon tunani take, ya ce, ‘Saratu kin yi barci ne?â€? Ta muskuta kadan don ta gyara jin dadin kwanciyar ta ta ce, “No, ina tunanin secondary din da ya dace a kai Saratu ne. Sanin kan ku ne Brigadier dole Saratu ta ci gaba da samun ingantaccen ilimin da ta faro da shi, to makarantun nan na Lagos duka babu na yarwa, amma tarbiyyar Saratu nake ji. Duka makarantun cakude suke maza da mata kenan hakan nan za ta tashi girman Lagos? Abin nufi, ba tarbiyyar Musulunci ba tsarin Addini balle al’adun mu na Hausa?â€? Ta yi shiru kadan ba tare da ta dube shi ba, can kuma ta ce, “Brigadier, ni dai don Allah ina neman alfarma, ina da account mai nauyi, amma dole sai da taimakon ku. So nake in kai Saratu makarantar kimiyyah ta harshen Larabci da ke Riydh ne.â€? Daddy ya yi shiru bai amsa ba, tsawon lokaci yana nazarin zancenta, ya kama kan shi da ke faman sarawa tamkar ya rabe gida biyu ya ce, ‘Zo nan Saratu, ki karanta min abin da Al’ameen ke cewa da kan ki watakila na fi fahimta.â€? Jikinta ya yi mugun sanyi da ganin Brigadier hawaye yake fitarwa, ita ma ta karanta sakon Ameenu a fili cikin nau’in turancinta (British accent) da ta samu a shekarunta hudu a Edeter, ita ma ta kasa cewa komai, sai dai bata dimauta ba kamar mijinta. Daddy ya share hawayen da ke bin kwarmin idon shi, tausayin Intisar ne kurum da karin kaunar ta tattare da shi. Tun da yake da ‘yar yarinyar nan babu abinda ba ta gaya masa, amma ko sau daya ba ta taba budar baki ta ce da shi Aminu ya ko dungure mata kai ba. A tun ranar da ya dauko ta, ya ga alamun hakuri a tare da ita, yatsun hannayenta duka cikin bakinta tana tsotso, irin su ne ake kira ‘damo sarkin hakuri.â€? Hakuri ne da ita tun tana tsumman goyon ta. ‘Anya zan taba yafewa Aminu? Mene ne dalilin kashe Saratu da ya so ya yi? Me yake nufi da kin bin umarnin mu ya tafi inda ransa yake so? Anya Al’ameen jini na ne kuwa? Yau dan cikina ke zargina da abin da ya san ko a mafarki ba zan taba aikatawa ba? Duk kaunar da nake masa a yau sakayyata kenan, ai shi kenan in dai duniya ce ya je ga shi nan ga ta, wanda bai zo ba ma tana nan tana jiran shi. Allah idan har akwai hakkina akan Alâ€?.â€? Aunty Saratu ta yi sulu ta rufe mai baki da tausasan yatsun ta, ‘Kada ka yi haka Baban su Khalil, kada kai ma ka yi abin nadamar. Ni dama tuni na san Ameemnu ne ya yi kwallo da Saratu a bakin Emma, lokacin Aminun bai san yana durkushe yana wanke tayoyin mota ba, amman ban ce komai ba. Ba don komai ba sai don na san komai Al’ameen ya yi sa shi aka yi, kome ya yi, ya yi ne a dalilin son Mamarsa, a kuma cikin taya mamarsa kishi, amma ba halin shi ba ne. Ba tun yau ba na san Al’ameen shi kadai ne ya gado Babansa a wurin tausayi da jin kai. Tun da har ya yi nadama da ta dame shi irin haka baka yafe masa? Mu fa iyaye har kullum da afuwa aka san mu ga ‘ya’yanmu, domin fushin mu a gare su ba karamin nakasu ne ga rayuwar su ba. Lallai ne a yau Ameenu ya nuna ya cika Al’ameen trustworthy, wato (Mai gaskiya). Kuma tafiyar shi Miami ni a ganina ba wani abu ba ne, abu ne na kuruciya. Ina da yakinin cewa Ameenu zai dawo a lokacin da ka ke tsananin bukatarsa. Dama can Allah ya rubuta Aminu zai gama da kiyayyar Saratu a rayuwarsa, za kuma ta hadu da lalurar ido ta dalilinsa. Amma ka sani, sai dai in tunatar da kai, Daddyn Ameenu, wani baya dorawa wata rai abin da Allah bai daura mata ba.â€? Ta yi shiru, don ganin irin tasirin da maganganun ta suka haifar, ba shakka ta ga tasirin su sosai a tare da shi. Kanta ta daura bisa kafadun shi ta ce cikin ‘yar karamar murya, “Brigadier, me ka ce game da karatun Saratu a Riyadh?â€? Budar bakinsa sai ya ce, “Ai ni kin gama da ni Saratu, banida wani tunani sai naki, ba ni da wani hukunci sai wanda ki ka zartar don nasan ba za ki taba yanken gurbatacce ba. Ba ni da wani buri sai na yau a ce Saratu ta yi ilimin da al’umma za ta amfana da ita, ba don komai ba sai don in nunawa wadanda suka yasar da ita a daji muhimmanci da darajar da Allah ya yi wa dan adam, amma suka wulakanta shi. Fatana, Allah ya ba ni tsawon rai, ba ni son ku wahala ko kadan a rayuwa.â€? Ita kam Antin ba ta ga dalilin maganar da Daddyn yake yawan yi mata ba, na baya son su wahala, tana ji a jikin ta har su mutu ba za su taba wahala ba, to me ma zai wahalar da su? Kudi, suna da su kamar su tada kai da kafa da su, kwanciyar hankali kuwa sai dai su samma wani. Saratu ta yi kuskure, komai na rayuwa mai canzawa ne, akwai wanda ya wuce jarrabawar Ubangiji a wannan duniyar? A kuma cikin wannan rayuwar mai siradi iri-iri? To bari mu bi su mu gani, don kuwa an ce ‘gaba ta fi baya yawa.â€? How much do you like this story? 5/7/22, 13:10 - Ummi Tandama😇: ____________________________ *âœðŸ? SIRADIN RAYUWAâœðŸ?* Book two *@Takori* Page2ï¸âƒ£ Shekara kamar kwana. Baby Intisar ta zana Common Entrance Exam dinta ranar Asabar. A ranar ne kuma Najib da Faisal suka sami admission a jami’ar Ilorin (Unilorin) inda dukkaninsu za su karanci fanni daya wato Engineering sai dai Faisal na Chemical, Najib na Electrical, Yasir da Bello ba su samu first choice din su ba, wato Ilorin din sai second din, shi Yasir OAU (Obafemi Awolowo Unibersity), sun dauke shi sai dai a maimakon course din Banking and Finance, da ya nema Entrepreneurial Studies suka ba shi. Bello kuwa LASU sun ba shi kwas din da yake so Marketing, don shi rago ne, ya fadi dama bai son karatu mai wahala. Haka Nasir ya samu Jami’ar Abuja inda zai karanci Pol. Science, Faruk yana ajin karshe a sakandire yayin da ‘yan biyun gidan Furkan da Idris ke ajin SS II, shi ko auta Khalil ranar da Intissar ta zana Common Entrance (jarrabawar shiga sakandire) ranar ne ya zana Placement wato jarrabawar gama karamar sakandire. ***** Intissar ‘yar shekaru takwas da haihuwa, a yau tunani goma da ashirin ya dame ta, ba ma yau kadai ba, tun ranar da aka fara shirye-shiryen tafiyar su Riyadh ita da Khalil wanda makarantar su Turkish ta nema masu da kanta saboda hazakar su, a karatu a yau, babu irin ‘ya’yan gidan Bello Makarfi. ***** Dakin ta na jikin na Anti Saratu, dan karami ne da ke zagaye da fararen labulaye. Tun daga kofa za ka ji kana nitsewa cikin lallausan chinese carpet da ya malale dakin, dan karamin gadon ta na silber cike yake da taron teddy bears din ta wadanda su ne abokan rayuwar Baby Intisar a kullum, barci ko zuwa anguwa baya raba ta da su. Katifar gadon ta ruwa ce duk gidan ba mai irin ta sai ita ‘yar lelen Daddy, akwai tebir da take hawa karatu da bed side lamp bisan shi. A kullum dakin Intisar cikin raba yake, ga wani sassanyan kamshi na air freshner din raspberry, da Anti ke sawa a kai akai. Akwai tangamemen hotanta window size da ta dauka cikin snow wato kankarar Switzerland sanye da thick coat baka doguwa har gwiwa da farar doguwar safa, sai takalmin shiga kankara baki da farar hular sanyi da ta rufe har kunnuwanta ruf rungume da teddin ta, sai murmushi take kai ka ce kafafun nan ba su taba taka kasar Nigeria ba. Sun je ne Arm-forces Remembrance Day da ake yi a can duk shekara da Daddy da Mamarta. Ta yi tagumi kamar wata babba ta zubawa kifayen da ke gudu zuwa can karkashin ruwa a akwatin talibijin ‘yar karama da ke aiki a dakin, rungume da teddin ta da take kira ‘Luluâ€? daga can bayan ta aka lallaba aka cire mata gilass kallo ya koma dusu-dusu. Ta kumbura suntum ta bi shi suka soma tsere cikin dakin tana korafin “Ba ni gilass dina Ya Faisal, ka ga bana so.â€? Matsanancin tausayi ta ba shi har bai san yadda zai kwantanta ba, ya yi dariya ya maida mata, kamar kullum sai ta kara kyau, ta yi ajiyar zuciya ta soma jifan sa da teddin daya bayan daya yana karewa da hannunsa yana cewa, “Haba baby na, wai ke ba ki san wasa ba ne? Allah na rike Lulu ba zan baki ba sai na yi flushing din ta tabi tutu (kashi).â€? Anty ce ta raba fadan da kyar, ya fiddo sabon Math-set daga aljihun wandon jeans da ke jikin shi ya cilla mata, nan suka koma shirin su. To kusan kullum haka suke, ita Baby ba abinda ta tsana irin a cire mata glass lokacin barci bai yi ba, shi ko ya dage sai ta cire ta dinga hutawa, me ya yi zafi? Allah Sarki, ita ta san me take gani, dusu-dusu yana-yana, Ubangiji Allah kada ka taba dora mana matsala a ido, domin wani abu ne da idan babu shi rayuwa take zamowa mara amfani. Ya zauna bisa lallausan carpet din ta, hannuwan shi bisa gadon da take zaune yayin da ya zuba mata ido yana murmushi, ta yi filla-filla da math-set din tana dubawa da dukkan attention dinta, ina ruwan sarauniyar lissafi ya ce a ransa, amma a fili sai ya ce, “Ke kam kina jin dadin ki Intisar.â€? Cikin halin ko’in kula ta ce, ‘Dadin me?â€? ba tareda ta dauke kanta daga math-set din ba. Ya ce, ‘Ga ki nan kuwa, ba abinda ya dame ki, daga Antin ki sai teddin ki, muku yanzu karatu muke mai matukar wahala, karatun akwai wahala sosai.â€? Ta tura dan bakin ta gaba, wanda ke kara mata kyau da yarinta, “Bacin nima Daddy ya ce za a kai ni wani garin, kuma idan na tafi shi kenan na daina ganin ka da Mamana, kuma kasan Khalil cin zali na yake amma wai tare za mu tafin?â€? Faisal ya juya hular kaboyi da ke kan shi baya ya ce, “Ai in kun je ya ga ba ku da kowa ba zai doke ki ba, sai dai ma in ya ga ‘ya’yan Larabawan sun dake ki ya rama miki, kin san shi ba daga nan ba wajen karfi ba irin ki ba ne da kowane banza da ko wane hofi yake kayar da ke.â€? Ta tura mai baki gaba tabbacin ya kular da ita, ya kyalkyale da dariya, amma ita yanzun ba wannan ne a gabanta ba, ta kuma cewa, ‘Shi kenan na daina ganin ka Ya Faisal?â€? Sai hawaye a guje wani na bin wani, ya ce, ‘Oh! No Intisar, duk shekara za ku zo hutu gida, mu ma kuma za mu ke zuwa musamman muna duba ku, Riyadh gari ne mai dadi, you’ll enjoy it in a little while (Za ki ji dadin zama cikin ta cikin dan lokaci). Ya yi mata murmushinsa mai kyau, ya daga mata gira cikin tsokana ya ce, ‘Ba ki yarda ba ne?â€? Ta girgiza kai bata ce komai ba, “So what do you have to worry about (Me kuma zai dame ki)?â€? A daidai lokacin da Anti ta dawo rike da kofin da ake kira mug cike da madarar shanu fresh milk ta nufi bakinta da shi amma sai ta ture, Faisal ya yi kiran ta da hannuwan shi ya ce “Come on beautiful baby!â€? Sai ta mike cike da yauki da yangarta ta nufe shi, kafin ta karasa gare shi ya yi mata nuni da Anty Saratu da ke tsaye ta harde hannuwanta a kirji rike da kofin madara tana murmushi, sai dai da gani na rashin jin dadi ne, yau ta ba Babyn ta madara ta ture, ya ce, ‘‘Maman?â€? Bayan ya dan fiddo ido kadan alamar mamaki, sai ta karasa da gudu ta amshi kofin a hannunta ta kafa kai ta shanye, ta rungume kugun Aunty Saratu ta yi ajiyar zuciya ta ce, “Mamar mu ki yi hakuri, tafiya ne bana son in yi in bar ki.â€? Tana shafa kwantanccen gashin kanta ta ce, ‘Na hakura baby na, nima ina jin tafiyar nan ta ki har cikin raina. To amma ina so ki yi ilimi ingantacce wanda zan dinga alfahari da ke Saratu.â€? Ta ce, “I promised you Maman, I’Il try my best to make you proud. (Na yi miki akawari Mamana, zan yi iya kokarina in ga kin yi alfahari da ni).â€? Faisal ya sasa masu tafi mai karfi wanda ya janyo hankalin Daddy da ke dakin Antin shi ma ya zo, gaba daya suka taru suna lallashin ta sai da ta tabbatar masu ba ta tare da damuwa, sannan suma suka ji dadi. Intisar kenan.â€? Aunty Saratu, Faisal da Daddy su ne ‘yan rakiyar Saratu da Khalil makaranta. Kingston College, makaranta ce ta kimiyyah zallah a Riyadh (Capital din Saudi-arabia). Ba a hutu sai karshen shekara kadai, ta hada dalibai daga ko’ina cikin duniya musamman ‘ya’yan Larabawan Morocco, Pakistan, Egypt, Istanbul, da Syria. Ba kowa suke dauka ba, duk kudin ka kuwa sai ka ci interview din su. To Saratu da Khalil sun ci har sun side a darussan lissafi da Ingilishi. Ilmul-Kimiya’i wato (Science) shi suke koyar da daliban su zallah tun daga ajin su na karamar sakandire. An sa Khalil aji daya na babbar sakandire (SS), ita kuma Intisar aji daya na karamar sakandie (JSS). Tana sanye da riga da wandon Pakistan ruwan madara (milk colour), ta yane kan ta da siririn mayafin kayan, ta zuba yatsun ta duka biyu a baki tana tsotso kamar kullum, kafar ta sanye cikin wani rufaffen takalmi baki kirar Andalus. Tana kallon Faisal, Daddy da Mamar ta suna fita daga harabar makarantar cikin (Tadi) din da ta kawo su suna ta daga masu hannu. Sai ta ji wasu dumammun hawaye (warm tears) na zirarowa ta karkashin gilashin ta suna diga kan takalmin ta. Tsakanin Antin ta da Ya Faisal bata san wa ta fi kewa ba. Rayuwarta A Riyadh Saratu Bello Makarfi, yarinya ce daga cikin irin yaran nan da ake kira gifted wato ‘yan baiwa. Hakika Allah ya yi mata baiwa a ilimin Chemistry, fasahar ta tafi karfi a nan. A duk san da suke practical lokacin da ta isa babbar sakandire, akwai wani malamin su Balaraben Turkiya wai shi Dr. Alhassan a duk lokacin da take leke cikin ‘microscopeâ€? da ‘stethscopeâ€? sai ya ce, ‘Saratu is doing research to improve the quality of our lives. Ma’ana (Saratu na yin bincike domin gyara karkon rayuwar mu).â€? A duk san da ya fadi hakan ji take kanta ya kumbura, burin ta ya karu kan son gyara rayuwar al’ummah! Tun a shekararta ta farko a makarantar sunan ta ya yi tambari a set din su, ta yi sadikai (abokanai) da dama, ‘ya’yan Larabawa bila-adadin saboda farin jinin ta da shiga rai. Harshen ta ya juye da larabci ziryan. Larabci na hakika kuwa ba kala daya ba, ba kala biyu ba, tun daga na Hijaz, Maghrib, Yemen, kudanci da arewacin Istanbul babu wanda ba ta yarawa saboda cakudo da mu’amala da jinsi-jinsin dalibai ‘yan asalin kasashen. A shekarar ne kuma aka bata Nakeebatul-fasl wato (class monitress), shugabar ajin su saboda duk tafi ‘yan ajin focusing a hankali a hankali malaman su ke gane hakan don a komai ita ce a kan gaba. Uniform din su farar shirt ce sol da bakin tie, hade da bakin skirt sai farin ribbon da bakin sandal kirar Turkey. Ba kasafai suke haduwa da Khalil ba da ke bangaren maza in ba wani taro na makarantar ya hada su ba kamar quizzes ko debates da makarantar ke shiryawa a kai akai. A shekarar ne ko kusan karshen shekarar aka kawo wasu yara mata guda biyu daga France, hostel din da take, daya a saman gadon ta daya a gefen gadon ta ke da ganin su kin ga half-cast wato ruwa biyu, suna magana da harshen Faransanci a junansu, maimakon Larabcin Saudiyyah da ya fi yawa a makarantar. Yara ne da ko za ta girme su da kadan ne, kyawawa amma farin su mai duhu ne, hakan nan ba su da yawan gashi cancan, wanda ke nuna ‘yan asalin Ifrikiyyah fatar jikin su da irin maganar su shi ke nuna girman Faransa ne ko kuma dai sun zauna a France na lokaci mai tsawo. Sai da daddare ta kwanta ta shige cikin bargo bayan ta yi addu’o’in da take yi ta shafe jikinta, amma barcin ya ki zuwa, tana ta tunanin wadannan yaran da ta ji sun shiga ranta farat daya tana kuma tsoron ta kula su su yi mata wulakanci don da alamun su ‘yan jin kai ne sai me? Kawai ta ji sun juye harshe zuwa zallar Hausa kamar jakan Kano, ta ji ta saman gadonta ta ce, ‘Hunainah kin yi barci ne?â€? Ta ce, ‘A’a, Allah na kasa barci Yaya Hidayah, wannan Balarabiyar ta kasan gadon ki kawai, haka kawai na ji ina kaunar ta don kamannin su da Mamin mu in kin lura har ya yi yawa. Amma kalli ko kallo ba mu ishe ta ba, ko ta gane mu ba Larabawan ba ne oho.â€? Wadda aka kira Hidayar ta cafe, ‘Kamar kin san abin da zan ce miki kenan. Amma Allah ya kai mu gobe duk inda Larabci yake zan koye shi a gobe dole mu zama kawayen ta Allahâ€?.â€? Dariyar da take ta faman babboyewa ce ta kubuce, ta rasa dalilin da yasa mutane da dama basa gane ita Bahaushiya ce a makarantar, don su ba su san ma wata kabila wai ita Hausa ba, hatta malamanta sunanta ne kurum yake fallasa ta domin sukan ji shi banbarakwai har ba su iya fadi dai-dai, su kan tambaye ta nationality dinta a kullum amsar ta ita ce, “Ana Nigery (ni ‘yar Nigeria ce).â€? Daga haka ba ta kara komai a kai. Dariyar ta tasa duk suka tsorata suka yi shiru kamar ruwa ya cinye su ta ce da su, ‘Ma’ana Arabi, (Ma’ana ni ba Balarabiya ba ce), nima Bahausa ce kamar ku, ku sauko mu yi hira.â€? Duk suka dirgo gadon ta suka dubi juna, sai kuma suka tuntsire da dariyar gane ashe dukkan su tushen su daya. “Sunana Saratu Bello, na zo daga Nigeria.â€? Hidayah ta ce, “Muma duk ‘yan Nigeria ne. Amma an haife mu a France. Sunana Hidayah Bashir Sambo kanwata Hunainah. Baban mu ke aiki anan sai kuma aka cilla mu Russia, daga baya ne aka turo mu nan, nan din ma an ce ba da dadewa ba ne za mu tashi, saboda aikin da zai yi anan temporary ne. Sunan garin mu Shanono a cikin Kano, ke kuma ya sunan garin ku?â€? “Mu a Kaduna muke, daga baya kuma muka koma Lagos yanzu duk gidan mu suna can Lagos.â€? “Mu ma muna zuwa Lagos wata unguwa Bictoria Island akwai antin mu Hajjo mu kan je hutu wurin ta.â€? ‘To ai mu anan arear ma gidan mu yake, in kin wuce gidan Major General Shitu Allazi.â€? Karamar wato Hunainah da ta zuba mata ido kawai tunda suka fara surutun su ta ce, “Allah kamar ki daya da Mamar mu, end of the year, wato karshen shekara za a kai mu gida hutu, za ki bi mu Maman mu ta gan ki?â€? ‘Idan school ta amince min sai mu je mana kafin mu tafi gida, amma akwai yayana Khalil yana bangaren maza sai dai in tare za mu je?â€? Gaba daya suka hada baki suka ce, ‘Ba sai mu je taren ba?.â€? Daga ranar fa kawance ya kullu, inda duk ki ka ga Intissar kya ga Hidayah da Hunainah, dakin cin abinci, wajen daukar darasi, dakin karatu da wajen wasannin motsa jiki duk tare suke zuwa. Su ci mai kyau su sha mai kyau su zauna a mai kyau, kada ki so ki ga yadda suke wani irin girma cikin shekara guda kacal.kamar kajin gidan gona. Ga Hidayah da shegen tonon fada da ‘ya’yan mutane sai su taru su shigar mata wani lokacin kuma ta zame ta bar su a ciki don duk ta fi su wayo, ba ‘ya’yan Larabawan kadai ba har ‘ya’yan manyan Saudiyyah yaran nan ba sa kyalewa kamar kasar ta uban su ce. Hakan nan kowacce na ji da basira da kwakwalwar da Allah ya hore mata komai su ne higher ita Hidayah a fannin sport ta fi kauri kasancewar ta doguwa sosai. Kwanci tashi ba wuya gurin Allah kuma dama masu iya magana suka ce wai shekara kwana ce. Yau ga ranar tafiyar su hutu ta zo, an jinkirta tafiyar ‘yan Nigeria saboda babu jirgin su zuwa washe gari. Da taimamkon Dr. Alhassan kasancewar shi mutumin Intissar aka bar su bin su Hunainah da kuma kasancewar gidan gidan Jakadan kasarsu ne, ita da Khalil suka bi direban su Hidayah da cewar mota za ta je har can washe gari ta dauke su zuwa airport. Gidan su Hidayah na Shariâ€? Palastine ne a cikin birnin Riyadh. Tun daga gate Saratu ta tabbatar su ‘yan gata ne, amma gatan da ta ga ana gwadawa su Hidayah ya dame nasu ya shanye. Har a jikin kofar shiga falon gidan an mammanna card na Larabci da Turanci da Faransanci, masu dauke da rubutun “U’re highly welcome kids.â€? Wani kuma an rubuta “Marhaban bikum ya bunayyah.â€? Ta yi tsaye hannu a haba tana kallon Mamar su Hunainah na katantanwa (juyi) da su a tsakiyar falo tamkar ta maishe su ciki ta sake haifo su don kauna, shekara guda ba ta gan su ba. A ranta ta ce, “Nima dai insha Allah gobe I yanzu ina jikin Antina, nima ina jin dumin Mama na.â€? Ba ta ankara ba ta ji Mamar su Hunainah ta rungumeta ta baya, ta sumbaci kuncin ta na dama wani dadi ya ratsa ta irin wanda bata taba ji a duniya ba, ita ma ta maida mata da irin hakan, gaisuwar garin kenan “Marhaban bi kum asdi’ka’lâ€? wato barkan ku da zuwa abokan mu. “Ya Rabbi!â€? Haka ta fadi tana ja da baya. Wannan kama da yawa take tamkar ta yi kaki ta tofar. Tunaninnika daban-daban take sakawa tana warwarewa a ran ta amma ta rasa na kamawa. Su ko su Hunainah sai dariya suke abin su suna kyakyatawa suna fadin dama sun kawo Saddikar su ne (kawar su) Inteesar don ita ma Maman ta ji irin mamakin da suka ji da ganin Saratu. Jikin ta ya yi sanyi kalau, tuni ta jike kashirban da gumi. Tasa masu aikinta suka yi entertaning ’ya’yan ta da bakin su domin ta nemi duk wani tunani da kuzari da ke tare da ita ta rasa. Su kan su masu aikin da suka dubi Intisar, suka kuma dubi tangamemen hoton uwargijiyar su da ke kafe a falon sai suka ce ‘Subhana Rabbiyallazi iza ya kulu li shai’in kun fa ya kun.â€? Ma’ana tsarki ya tabbata ga Ubangijin da in ya ce kasance, sai ya kasance. Domin wannan kama da yawa take. Ambassador Bashir Sambo, shi ne mahaifinsu, baya gari a wannan lokacin. Duk kokarin Haj. Hadiza na neman layin shi abin ya ci tura a wannan daren, duka wayoyinshi a rufe, kamar ta dora hannu ta ce Wayyo Allah! Jikin ta har wani irin rawa da kyarma yake. Ita kanta ta kasa tantance me ke damun ta game da bakuwar ‘ya’yanta? Haka ta kwana cikin zullumi da ci da zuci, wani abin takaici kuma da sassafe sai ga motar Kingston College a kofar gidansu ta zo tafiya da su airport tana kwance a daki wani matsiyacin zazzabi ya rufe ta, Khalil ya ja hannun kanwar shi ko wanka ma ba su yi ba balle karin kumallo suka shiga motar suka tafi. Karfe goma na safe suna cikin jirgin Mea International wanda zai sada su da kasar su ta haihuwa, Nigeria. How much do you like this story? 5/7/22, 13:10 - Ummi Tandama😇: ____________________________ *âœðŸ? SIRADIN RAYUWAâœðŸ?* Book two *@Takori* Page3ï¸âƒ£ Ko kafin a dawo hutu, lokacin aikin su a Riyadh wanda dama na wucin gadi ne ya cika, an cilla Bashir Sambo kasar Korea aikin Jakadanci. Su Hunainah sun yi bakin ciki ba kadan ba na rashin sallama da kawar da suke so kamar ran su ga shi kuma basu taba tunanin yin musayen lambar waya ba. Hajiya Hadiza, ta roki Allah ya cire mata wannan tunanin da ke addabar zuciyarta yake kuma neman wargaza mata farin ciki, tunanin cewa wai diyar ta Fatimah ta gani. Shi maigidanta ma da ta fada masa dariya ya yi ta yi mata wai tasa abin a ranta ne ba dole ya yi ta yi mata gizo ba? Dama duk ‘yar farar yarinyar da ta gani ta ce tana kama da ‘yar ta Fatimah yau kuma kacokan ta ce ‘yar ta gani dungurungum. To amma wane mai hankali ne zai yarda cewa yarinyar da aka rasa shekaru goma a kauyen kayau, ita ce za a ce an gani a babban birni irin Riyadh? Birnin da ya tara al’umma iri daban-daban. Ban da abin Hadiza ai fararen ‘ya’ya gidansu ta zo. Hutunsu Saratu a Abuja suka yi shi inda Daddyn ya komo da zama kwata-kwata. Burin Aunty Saratu kusan ya cika ganin yadda Baby ta kwantar da hankalinta ta tsaya tsayin daka tana karatu. Babban bakin cikin baby da har za ta koma hutu ba ta sanya Ya Faisal din ta a idanun ta ba. Aunty Saratu ta yi mai waya cewa ga su Saratu sun zo hutu har za su koma ba ta ga yayan da ba ta da kamar shi ba, lokacin shi Faisal yana tsaka da jarrabawar wucewa (200 lebel), sai ya ce Aunty Saratu ta budewa Baby kwanfutar ta zai turo mata sako ta e-mail din Antin karfe shidda daidai na yamma, don a ayanzun zai shiga dakin jarrabawa ne sai ya fito. Inteesar na dakin ta a lokacin, komai yana nan yadda yake sai ma gyara na musamman da Daddy ya kara yi mata, saboda ya ce ita yanzun ta tashi daga 0-lebel. Kuka take sosai hawaye ya hade da majina, a kan me Ya Faisal ba zai baro kowane irin karatu ba ne ya zo ya ganta ba? Tsawon shekara guda basa tare? Amma just once throughout a year? (Sau daya kacal a shekarar baki dayan ta). Ba yadda Anti ba ta yi da ita ba ta amshi wayar sa su gaisa amma ta ki, me waya za ta yi masu, yadda ta yi kewar shi din nan? Ta kunso labarun su Hunainah fiye da cikin ‘ya’yan carbi tana Allah-Allah ta sanya kafa a Nigeria ta ba shi ya sha, shi ne zai yi mata haka, wai ba shi da lokacin zuwa? Antin ta kara tunzurata ta hanyar yi mata gwalo da fadin wai Faisal bai damu da ita ba, ai kuwa sai ta fashe da kuka na gasken-gaske, ta rungume kugun Mamar tana mata ihu da gunjin kuka ba na wasa ba, a dole tausayin ta ya kamata domin ta damu da Faisal sosai fiye da kowa a duniya haka shi ma, tunda ta tafi bai bar zancenta ba, bai daina tuna ta ba a kowanne dakika, harshensa bai bar ambaton sunan ta ba. Abu kadan sai ya ce, “Allah Sarki Baby na ana can, ko me ake yi yanzun?â€? Antyn sai ta yi dariya ta ce, “Ai sai ka bar naka karatun ka bi ta can ku yi tare.â€? Sai ya ce, “Bari in samu hutu ki gani, Aunty nima Riyadh zan tafi.â€? Ta kamo hannun ta suka zauna cikin kujera ta ce, ‘Saratu wai ke ba kya girma ne? Faisal da gaske yake jarrabawa yake yi, kuma ba a barin jarrabawa a jami’a a fito. Ke in kina taki jarrabawar kin taba tahowa baki gama ba? Idan kin kwantar da hankalin ki da kafafun shi za ki gan shi da zarar kun koma, don ba ki san yadda ya damu da ke ba ne.â€? Sai tayi murmushin da ba ta shirya ba. Antin ta kara da cewa “‘Taso ma ki ga wani abu.â€? Tana lalube cikin shafin yahoo-mail wani katon zanen zuciya kalar shi ja mai haske ya bayyana a jikin screen din kwamfutar, a kasan ta wani boyayyen rubutu ne da aka dunkule sa cikin tsari mai kyau da daukar hakali, Saratu-Intisa! Drop my picture into your mind Sis, allow it to dissolve in consciousness, and it will spread a healing balm over your entire soul. This is one of the simplest processes to feel me beside you. Read hard and make us proud. Faisal Bello Makarfi. Ba ta san sanda ta yi dariya ba kamar ba ita ce mai kuka wiwi yanzun ba. “Shin Mamana ta yaya zan sa hoton Ya Faisal a raina?â€? “Shi ne sai ki dauko fuskar shi a zuciyarki, ki sama ranki cewa wannan Faisal ne ku ke tare, yana kallon ki yana miki hira, yana kuma yi miki wannan kyakkyawan murmushin nan nasa. In kin yi hakan ba za ki ji haushi ba don ba ki gan shi a wannan shekarar ba.â€? To Saratu ta koma makaranta cike da farin cikin kaunar da Mamar ta da ya Faisal ke mata. Ba karamin bakin ciki ta taras a makaranta ba da ta ga ta shafe sati daya, biyu har uku su Hunainah ba su dawo hutu ba. A sati na hudu ne ta kasa daurewa ta je ta tambayi malamin da ke kula da shige da ficen hutun dalibai da suke kira Sayyid Ridhwan game da su. Ya dade yana bincike kafin ya samo mata detail din su, cewa ya yi da ita dama aikin jakadanci mahaifin su yake yi, inda kuma duk ya tashi nan suke komawa da karatu, yanzu kuma an yi posting dinsu kasar Korea. Ta samu wani kututturen icce ta zauna ta yi kukan ta mai isar ta; kukan sabo da kewa, kukan rashin amini, (to lose a friend is the greatest loss of all losses). Sai ta ji rayuwar makarantar ya zamo mata wani irin salam, musamman in ta tuna hirarraki da ban dariya irin na Hunainah masu cike da hikima a ciki, da kuma tonon fada irin na Hidaya da a kullum ke sanya su zama busy wato dai ba za su zauna shiru ba. Ta yi kuka har idanun ta suka shiga zafi da radadi. Daga baya ta rugnumi kaddara ta sanya wa ranta salama, don malamin Islamiyya ya sha gaya masu imanin mutum ba ya cika har sai ya yarda da kaddara mai dadi ce ko mara dadi? Kenan Allah ya kaddara iyakacin rayuwar da za ta yi da su kenan, shi yasa har ya nufe ta da zuwa gidansu, ta watsar da komai ta rungumi karatun ta kamar da, barin ma da ta yi sabuwar kawa Raadhah, mutuniyar Jeruslaam, tana fatan wata rana Allah ya kara hada ta da su ko da a mafarki ne. Sun ci gaba da karatu sosai Saratu Bello na kara yin fice. A wannan shekarar sau biyu ta fita debate a kan lissafi har Abudhabee (Dubai), dayar a Oman dukkansu UAE ne wato United Arab Emirate, ana kuma nunawa a tauraron dan-adam, ta kuma daukowa makarantar su kofin zinare, wannan ya kara bata damar zama ‘yar lelen malamai da hukumar makarantar gaba daya. Kingston College, na hangen bata shugabar dalibai in ta iso ajin karhse, wai ‘yar Africa! Africar ma kasar da suka fi gani da kaskanci, Nigeria ce? Wata ranar Litinin ta fito daga library tare da wata yarinya Rabikha, aka ce da ita principal na kiranta. Ta zo shiga kenan suka ci karo da Khalil, tsoro ya kama su, don wannan shi ne karo na farko da wani kira makamancin wannan ya ratsa da su a tare. Tsoron ta Allah, tsoron ta kada ta yi laifin da zai sosa ran Daddy a rayuwar ta. To amma me? Ta dade da sanin wani kamshi da ba ta jin shi a jikin kowa a duniya sai mutum daya, ba ta jin shi jikin kowa in baâ€? Ji ta yi an sure ta an yi sama da ita ana juyi da ita tamkar a hadiye ta, sai kuma dariyar mamar ta, ta dubi mai rike da itan, Ya Faisal ne. Tuni ta saki ihu, ta rukunkume shi tamkar ta sume don dadi ba ta ko ta Mamar ta. Kaunar Faisal da Intisar wannan cikin jininsu ne, kuma daga Indallahi take. A duk san da suke tare da juna, mantawa suke da kowa a duniyar sai junan su. Da Principle ta ga ofishin ta ya kacame da hayaniyar wannan family masu matukar kaunar junan su sai ta fita ta bar masu ofishin. An yi hira an yi dariya, amma baby magana daya, biyu za ta ce ina Daddy na? Sai Faisal ya ce, “Ba ki san Daddy ya tsaya takarar President ba?â€? Ba su tafi ba sai yamma lis. Washe gari suka zo suka yi masu sallama suka tafi. Dama sun zo aikin Umrah ne. To haka karatun ya kasance masu, duk shekara suna zuwa gida su yi wata guda suma kuma mutanen gidan na zuwa masu a kai akai, musamman Faisal, ka’ida ne duk karshen semester Daddy ya biya mai kujerar dubo Intisar. Wannan wani alkawari ne da ya yi wa rayuwar shi cewa ko Daddyn ba zai biya ba, zai san duk yadda ya yi ya kai wa Intisar ziyara ko da hakan na nufin ya ciyo bashi ne. Kwanci tashi ba wuya a wajen Allah, yau ga Saratu Bello ta kammala ajinta biyar na secondary a shekarun ta goma sha biyar a duniya. Shi kuma Khalil ya kammala, don ma sun maida shi baya ne saboda faduwa darasin lissafi da ya yi, amma da tun shekarar baya ya gama, daga wannan hutun shi ba zai koma ba, ita ce dai za ta koma ta yi final year din ta. An danka mata dankwalin shugabar dalibai. Wayyo! Ashe daga wannan hutun, mafarkai da burirrika ba za su taba zama reality ba. Saratu ta dawo hutu cike da farin cikin abu biyu, first of all, alkawarin da ta yi wa Daddy na kwato (1st Position) din ta daga hannun Amra Rushd abokiyar takarar ta mutuniyar Katar, da ta kwace mata a zangon baya ta cika shi, ta kwato (1st position) din ta as usual. Sai na biyu za ta ga farin cikin Mamar ta a fili, watakila ma har ta goya ta da zani duk da girman ta kuwa. A wurin Mamar har abada ita BABY ce, ta kan ce, har sai ranar da ta samu kani. Haka take yi mata duk san da ta yi na daya, wato ta goyata tayi ta zagaye daki da ita, in kuwa na biyu ne ta shiga korafi kenan. “Saratu kina wasa, Saratu alkawarin mu da ke kenan? Saratu where is your delegence (Ina kwazon ki), I dare you!â€? To yau dai duk ba ko daya, ga na dayan ta ta dauko, saura tukuicin Anty da Daddy. Ashe labarin bakin ciki da tashin hakali ke nan yana tsimayen su su fito daga jirgi, wanda daga jin sa Saratu sulalewa ta yi nan take a kasa sumammiya. ***** Cyril Stober ne tare da sabuwar Newscaster Hawwawu Gebi, ke karanto kanun labarun yau daga gidan talbijin na kasa (NTA Abuja), inda ya ce, “An kama wadanda suka shiryawa kasa juyin mulki a ranar 5/5 wanda Benga Delsu da Bello Makarfi ke jagoranta. A yayin da aka shiga hasko fuskokin su daya bayan daya, kafafuwan su da hannaye duka daure cikin ankwa abin babu kyawun gani. Suka kafawa Daddyn su ido kuriiii, abin tausayi tamkar sa zuko shi daga akwatin talbijin din. Cikin kwanaki biyu kacal ya rame, ya yi baki, ga wata kasumba ta tashin hankali da ta baibaye fuskar shi mai zati da kamala, kan shi a sunkuye, tun suna kuka kasa-kasa har suka rikice gaba daya da kakkarfa, Faisal ne ya mike ya finciko wayar T.B din ya hada ta da garu. “Allah Daddy ba zai yi haka ba, wannan sharri ne, sharrin..â€? Ya ma kasa karasawa saboda takaici da kunar zuci. Duk gidan ya koma tamkar gidan mutuwa, Inteesar tun zuwan ta da ta riski labarin, ta fadi ta sume, aka samu ta farfado har lokacin kudundune take cikin bargo tana rawar dari, zazzabi da masassara suka rufe ta, hakoranta sai karo suke da juna kawai ji ka ke kaf-kaf-kaf. A ranar Najib da Bello suka iso, washe gari sai ga Nasir da Yasir su ma a gigice, Nasir mai raguwar zuciya nan falon Hajiya ya zube yana kuka riris shi da kananan kannen shi, ita kanta Anti ta fita hayyacin ta ba kadan ba, bata ko iya rarrashin su. Najib ya ce, ‘Me zai sa Daddy ya sanya kan shi cikin wannan bala’i?â€? Shi ko Faisal rantsewa ya yi da Allah ya tabbata Daddy ba zai taba aikata abinda ake zarginsa da shi ba, saboda president aminin Daddy ne na kut da kut tun suna NDA a Jos suke tare har girman su har tsufan su ba a taba jin kan su ba balle a same su da wani sabanin ra’ayi, ya ya za a ce an hada baki da shi a kashe shi? Sun rasa ya za su yi? Sun rasa wa za su kai wa kukan su a yanzu ya dube su, yadda kasa take cike da su Daddy a wannan lokacin. Sai Saratu ta share hawaye ta ce, “Ya Najib, ni ina ganin mu taru mu yi ta addu’a da kan mu kawai, in Daddy ba laifn shi sai ka ga sun sako shi da kansu a lokacin da ba mu tsammana ba, amma duk inda za ku je a halin yanzun ba wanda zai saurare ku.â€? Sai a yau Hajiya Nafi ta taba daga ido ta dubi Intisar a rayuwar ta, duba na mutum dan adam, ta ce, “Yarinya karama ta fi ku tunani, amma kun tsaya kuna ta koke-koken banza amfanin me ke gare shi?â€? Washegari Najib ya nemo bisa din mutum biyar da shi da Faisal, Yasir da Hajiya sai Anti, suka dunguma kasa mai tsarki domin yin dawafi na musamman kan Allah ya fiddo mijin su/mahaifinsu cikin ruwan sanyi, suna addu’a fuskokin su jike da hawaye, tuni an manta da wani kishi, to ina wanda ake yin kishin domin shi? Gidan farin ciki gidan Brigadier Bello Makarfi, komawa ya yi tamkar gidan makoki, dukkan harkoki da walwalar su sun karkatse. A satin Saratu da Nasir suka kamo hanyar kauyen Makarfi. Kallon fuskokin su kawai Baffa Sani ya yi ya tabbatar babu lafiya haka goggo Jimmai. Nasir ba ya ko iya magana sai Saratu ce ta yi mai bayanin halin da ake ciki hawaye na bulbular mata a guje. Malam ya shiga rarrashin su yana tunatar da su duk wani soja haka ya gada, shiga hadarurruka ba yanzu Babansu ya fara ba, ya ma fi na wannan a baya lokacin da rikicin sojojin Amurka da Saddam Hussaini ya ritsa da shi a Baghdaza, da lokacin da aka kashe Major-General Aguiyi Ironsy ya kuma fito sumul kalau. Tun a ranar ya tara malamai bila adadin ya raba masu abin sadaka suka dukufa rokon Allah. Duk wani shahararren malami da ya kwana ya tashi a garin Makarfi da wajen ta Malam Sani ya kai abin sadaka a taya su rokon Allah ya fiddo Bello, gudan jinin shi kuma bango abin jinginar su. Nasir ya bude account din shi ya karowa Baffa kudi masu yawa. Watan su Hajiya guda a Saudiyyah kafin su dawo. Gidan ya kuma komawa tamkar gidan mutuwa harkokin su suka kara katsewa, na makaranta sun kasa komawa, masu aiki su kasa komawa bakin aikin su, kowa na ji da yadda ya ke ji a zuciyarsa. Najib ya yi trying wayar Aminu, kwata-kwata ya daina amfani da layin, ya aika mai ta e-mail babu amsa. Da yamma ya shiga dakin Hajiya sai ya tarar da ita tafukan ta cikin fuska tana ta razgar kuka. A sanyaye ya zauna ya sunkuyar da kai ya ce. ‘Hajiya duk fa abin da ya yi zafi maganin sa Allah ne.â€? Hajiya Nafi ta ce, “Na san da haka Najibullahi. Tunanin Al’ameen ke damuna, baya ko tunawa da mu balle halin da muke ciki. Mun yi da za shi Hull Unibersity, cikin ajiyana na banki na tattara na tura Ali dan kanin mahaifina ya binciko min Aminu a England, address din da ya bar mini ka san me ye? An ce kwata-kwata babu mai irin sunan shi a cikin shekarun da muka ambata da ya zo daga Nigeria. Na rasa inda zan sa kaina in ji sanyi. Idan na rasa Aminu na rasa ubansa ina zan sa kaina?â€? Sai ta kara tsanannta kukanta. Najib ya lankwashe kai abin tausayi ya ce, “Amma dai Hajiya kin san dai cikin kowanne hali Ya Aminu zai iya kula da kansa a ko’ina. A ganina bai dace kisa damuwar inda yake a ranki ba har ya zo ya dame ki, hakan yana iya zamo miki illa, kuma a cikin wannan halin da muke ciki na kewar mahaifin mu ke ma mu rasa farin cikin ki akan ya Aminu shi kadai ransa? Tunda dai kin san ko ba dade ko ba jima zai dawo ne?â€? Ta ce, “Ya kuwa bazan damu da inda Al’ameen yake ba, alhalin duk cikin ku babu mai kauna ta tamkar shi? Babu mai gudun bacin raina tamkar shi? Babu mai son abin da nake so tamkar shi? Ba mai damuwa da bakin cikina tamkar shi? Ya ya kuwa ba zan damu da inda yake ba?â€? Najib dai ya yi ta lallashin ta har ya samu ta yi shiru. Washe gari ya zauna ya zanawa Aminu duk halin da suke ciki ta cikin yanar gizo internet yana rokon shi ya zo su taru su san hanyar da za su kubutar da mahaifinsu da ya tabbatar da ba ya da laifi. Ya tunasar da Aminu yanzu ne fa ya dace su nunawa ubansu kaunar da ya wanzar da rayuwar shi a nuna masu. Ya tabbata ya kammala koma wane irin karatu yake yi cikin wadannan dumbin shekaru amsu yawa da suka gabata. To amma me? Daga Ameenu no reply har tsayin sati guda, wannan ya kara tunzura ‘yan uwan. Sai a kwana na takwas ne ya cillo wani matsiyacin rubutu don a ganin sa ai abin da ya jiyewa Daddyn kenan tun farko da ya yi ritaya amma shi bai jiyewa kansa ba. Rubutun Al’ameen Bello, ya nuna bai damu ba, bai kuma da ranar barin inda yake, domin America, ta zama wani ginshiki na farin ciki da kwanciyar hankali a gare sa, ta yadda har bai jin wani abu da ya shafi gidansu zai sa ya baro ta. A takaice dai ga abinda Ameenu ya rubutowa dan uwansa Najib. America teaches the cultivation of peace of mind to me, not as an escape from life into protected quiescence, but as a power center of which comes driving energy for constructing personal and social living. One is responsible for the outcome of what would be sealed. Al’ameen Bello How much do you like this story? 5/7/22, 13:10 - Ummi Tandama😇: _____________________________ *âœðŸ? SIRADIN RAYUWAâœðŸ?* Book two *@Takori* Page4ï¸âƒ£ Najib ya fashe da kuka, ‘Faisal, anya wannan Yayan mu ne da na sani mai so da kaunar Daddy?â€? Shi ko Al’ameen ba su san a halin bakin cikin abin da ya ke tunanin mahaifin su ya aikata ne ya furta wadannan kalaman ba, a ganinsa me Daddy ya rasa a rayuwa da zai tsunduma kan shi cikin irin wannan masifa in ban da rashin godiyar Allah? Har nawa duniyar take da zai bari neman mulkin duniya ya rinjayi imanin shi? Kudi dai na gwamnati albarkacin aikin soja bai san wane iri yake so kuma ya yi ba. Ya manta cewa, “Kalmomi da alkawarirrikan da aka yi su cikin fushi, kamar cin wuta suke, ba za ka taba iya maida barnar su ba.â€? Daga Faisal har Najib sun ce a kyale Ya Aminu ya yi yadda yake so. Allah zai fidda Daddy ne ba sai da taimakon sa ba. Ranar Asabar Baffa na Makarfi ya zo da malamai kimanin guda goma aka bude masu nan sashen baki, sati guda suka share suna saukar Alkur’ani mai tsarki, an yanka raguna har ba iyaka an yi sadaka haka sauran abubuwan sadaka iri-iri iyalin Brigadier ba mai jin kyanshin bada ko mene ne. Sai da Aunty Saratu ta zamo babu ko sisi a account din ta ta hada da saida bungles din ta na danyar gold. Haka samarin nan na Brigadier ba sa barcin kirki kowannensu kamar bai taba mallakar kwandalar kansa ba, duk sun jeme abin gwanin ban tausayi. Hakika Bello Makarfi ya gina iyalin shi a bisa tubala na so da shakuwa da shi, ta yadda rashin sa ya zamo masu tamkar rasa rayuwar ne dungurungum. Mutum ne da ya iya zaman duniya kuma mutum mai nuna wa ‘ya’yan shi da matan shi kauna da kobo, lafiya da karfin shi. Ya tsaya tsayin daka domin iganta rayuwar su ta yadda har sun fi kaunar shi a kan-kan su, dama duk wani abu da suka mallaka a duniya. Malamai iri-iri na karya da na gaskiya haka suke zuwa suna cin kudin su da sunan wai kafin sati an sako shi, amma shiru ka ke ji wai malam ya ci shirwa, sai ma sabon bakin mummunan labarin an dauke su daga Kiri-kiri Prison zuwa South Africa. Intisar, dama gwana ce wurin kai wa Sarki Allah kukanta a komai, to balle wannan matsala da ta shafi rabin ranta ‘Daddy Makarfiâ€?. Yarinyar nan ‘Halwaâ€? ta shiga, idan ka ganta a wancan lokacin sai ka amince ta fi kowa damuwa da Daddynsu. Jar fatarta ta yi duhu ainun, idanun ta sun fada ciki, sai kwayar idanuwan nan da karan hancin kadai. Ba a zancen komawa makaranta, aljihun kowa ya masifar girgiza, hatta Hajiya Nafi ba karamin faduwa ta yi ba a wannan shekarar, sabida cin kudin kawai ake ba’a inbesting din su, sai da ta kai ta kawo abinci wannan ya soma karanci a gidan Makarfi. Wani abin mamaki duk wasu abokan arzuka na Brigadier da abokan aiki wadanda cikinsu babu wanda ya taka matsayin da yake kai a soja ba tare da taimakon Makarfin ba, babu wanda ya yi tunanin ya taimaka masu ko da da kwayar shinkafa ne sai jelen jaje da ake ta yi masu ana Allah ya kiyaye gaba amma naira daya wannan babu wanda ya dauka ya ba su da sunan wai yana amintaka da Daddyn su. Ganin haka Faisal ya tara ‘yan uwansa kaf a falo ya ce. “To Assalamu Alaikum ‘yan uwa. Ku sani fa (La yukallifullahu nafsan illa wus’aha) Ma’ana: Allah baya dorawa wata rai abin da ya san ba za ta iya dauka ba. Saboda haka a abar komai a hannun Allah, mun yi addu’a daidai karfi daidai iko da gwargwado, we’be to wait for the outcome, wato mu jira ijaba a barwa Allah komai, mu koma makaranta masu aiki su koma bakin ayyukan su. A yau ku duba ku gani yadda aminan Daddy suka watsar da tallafin mu da shiga al’amuran mu bayan cikin su babu wanda ya taka matakin da yake kai ba tare da taimakon Daddyn mu ba. Wannan bai ishe mu ishara ba? A yau in cewa akai Daddy ya fadi ya mutu, ba za su taimake mu da komai ba haka za su bar mu mu tagayyara, da kyar su ce ‘Allah ya jikan rai.â€? Ashe kenan wannan karatun nan namu da ayyukan mu su ne madogarar mu sai kuma Allah gatan kowa? Karatun nan shi ne gatanmu, da shi za mu rufawa iyayenmu da kannin mu asiri. Ga shi kowannen mu ya yi asarar shekara guda wadda da tuni wasu cikinmu sun kammala har sun fara aiki. A gobe kowa ya koma inda ya fito, mu ci gaba da addu’a hakika ita addu’a ba ta faduwa kasa banza, kuma wanda ya fawwalawa Allah lamarinsa ba zai taba tabewa ba.â€? To nasihar dan uwansu ta ratsa su dukkan su. Saratu kam sharban kuka kurum take kashirban. Hajiya ta ba kowannen su isassun kudi ya koma makaranta. Ka ji ‘ya’yan Hajiya, to Saratu da diyar ta Saratu fa? A ranar baby kwana ta yi lallashin Mamar ta ta koma aiki ita ma, don Hajiya tuni ta koma harkokin ta, da yake ba ta son ganin bacin ran Saratun shi yasa kawai a wayewar garin Litinin ta shirya ta tafi. Allah Sarki! Wani ta taras a mazaunin ta, Insurance Company, ba su san wasa da aiki ba. To su sai abun duniyar ya taru ya yi masu yawa. Ta dai aika da takardun neman aiki kamfanoni da bankuna da dama a nan cikin Abuja, to amma aiki a Abuja sai ga masu uwaye a gindin murhun. Ba abin da ya dame ta kamar yankewar karatun Saratu a shekarar ta ta karshe, dama ta kammala ne da da sauki sai ta nema mata public unibersity wato ta gwamnati, ta tafi. Yadda Hajiya ta yi komai nata-ya-nata ta tabbatar ta nuna mata ranar NAIRA ne. Khalil din ta ya gama, to ita yanzun ina za ta nemo makudan kudaden da za ta maida Saratu Kingston College? Sai ta hada dukkanin gwalgwalan ta na ado gaba daya ta tattara ta sa a kasuwa, an yi masu sayen daraja kuwa. Ta dade da amsar mota cibic hannun Daddy wadda take zuwa aiki a ciki, ita ma ta yi gwanjon ta wani makocin su ya saya a wulakance. Ranar Laraba suka biyo motar haya zuwa Makarfi abin da ba su taba yi ba a rayuwarsu, don direban gidan tuni ya kama gaban sa tunda ya ga an yi watanni har shida ba wanda ya tuna ya ba shi ko sisi, ba shi kadai ba duk ma’aikatan wajen sun gudu in ka dauke maigadi, shi ma tabbas don ba shi da wajen kwana ne in ya tafi watakila shi yasa ya zauna amma hatta ‘yan aikin Anti Saratu sun yi tafiyar su tuntuni, sai ko ma’aikatan cikin gida su Dela da ke bangaren Hajiya da yake ita tana biyan su amma na Anti Saratu ko wata ba a yi ba da kulle Daddyn suka kama gabansu. Wannan bai damu Hajiya Saratu ba abinda ya dame ta ya dame ta. Sun iso Makarfi karfe uku da minti ashirin na rana lokacin Malam yana cikin gari, Goggo Jummai ta yi masu kyakkyawar tarba, bayan sun ci abinci sun yi kat, sannan Saratu da Saratu duka suka hada kai da gwiwa suka yi shiru. Goggo, ta ce, “Ku yaran nan, da kuruciyar ku za ku sanyawa rayukan ku cututtukan zamani masu wuyar magani? Mu ma tsofai-tsofai da mu rashin Bello bai hana mana rayuwa mai kyau ba sai ku? NI na san Bello na sarai tun yana a tsumman goyon sa babu abinda zai sa ya aikata abin da ake tuhumar sa da shi. Kuma ko don albarkacin addu’ar da ake ta yi gaskiya za ta bayyana, ko ba dade ko ba jima.â€? Aunty Saratu ta ja numfashi, Intissar kuwa kuri ta yi da jajeyn idanun ta kan tururuwan da ke ta yawo a kan malalen suminti, a ranta ko cewa take su babu abin da ya dame su, yanzu haka suna tare da Daddyn su, sabanin su da aka kame nasu aka garkame a kurkuku! Suka zama matsiyatan karfi da yaji sai tafkeken gida. A daidai lokacin da Baffa Sani ya shigo, shi ma nasiha ya shiga yi masu mai sanya nutsuwa da kwantar da hankalin mai imani. Har yana gaya masu ya yi Istihara ya ga Bello lafiya lau. Ya kara da cewa. ‘Saratu hakika Ubangiji yana duba izuwa zuciya, daga biyayya tasa, gwargwadon tsarkakewarta ko kebantuwar zuciya zuwa imani da shi, daga ambaton sa Madaukaki. Ki yi duba ga abin da ya cakuda zuciyar ki ki ambaci Allah da shi. Abu-Yazidal Basdamy ya ce, ‘Madallah da wanda bakin cikinsa ya kasance bakin ciki guda daya, abin da ya gani da idanun sa (na wannan bakin cikin) bai shagaltar da shi daga kai wa Allah kukan sa ba, haka abin da ya ji da kunnuwansa shi ma bai shagaltar da zuciyarsa ba.â€? Saratu ki yi tawakkali mana? Duk wani cikakken Musulmi mai imani wanda ya yarda da Allah daya ne, dole ne fa ya yarda da kaddara mai kyau ko akasin haka. Idan har imanin mu ya cika, to bai yiwuwa mu zauna lafiya. Akwai wata mace a zamanin Annabi (S.A.W) da suke tare da mijin ta lami lafiya, tunda suke tare ko ciwon kai bai taba yi ba. Anan ne take da wasiwasin cikar imanin shi. Rannan sai ta ce da shi su tashi su je wajen Ma’aiki mai tsira da aminci, ya tambaye ta laifin da ya yi mata ta ce babu, sai ya amince suka tafi, don ya san in har ba ta da wata hujja haka kawai (S.A.W) ba zai raba masu aure ba. Kafin su kai sai ya yi tuntube danyatsan sa ya fashe jini ya fito, sai ta ce mu koma dama shi kenan. Musulmi cikakke dole ne ya dinga gamuwa da jarrabawar Ubangiji a cikin al’amuransa na yau da kullum. Bai yiwuwa mu zauna lafiya har karshen rayuwarmu. Saratu da Saratu ku kwantar da hankulan ku da sannu zu ku ga nasibi daga Allah!!!â€?. Sai suka share hawayen a tare su ka ce, “Haka ne Baffa.â€? Aunty Saratu ta kwashe matsalar karatun Intisar kaf ta fada masa da kuma hukuncin da ta yanke. Baffa Sani dattijo mai zurfin tunani da hangen nesa bai katse ta bar sai da ta dasa aya, ya yi shiru cikin nazarin zancen ta a bisa ma’auni na hankali. Ya ce, ‘Amma Saratu ba ki yi tunani ba, idan kin kadar da dukkan abin da ki ka mallaka Saratu karama ta koma Riyadh, wanda bai zama dole ba, ba kya tunanin halin da za ku iya fadawa a gaba?â€? Gaba daya suka yi wa Baffan kallon rashin fahimta, ta ce da mahaifinta, “Uhm, Baffa ban gane ba?â€? Ya yi murmushi, “Kai yaro dai yaro ne, kuma tashi kyau take amma ba ta karko. Abin nufi me za ku ci, me za ku daura ke da diyar taki? Da me za ku ije lalurorin ku na yau da kullum? Alhalin babu wanda ya san ranar dawowar Bello sai Lillahi? Kun saba da ku ci mai kyau ku daura mai kyau, ranar da ku ka wayi gari ba ku da komai ya za ku yi? Kin san dai uwar su Aminu ko za ku mutu ba za ta taba daga ido ta dube ku ba, gamu ni da mahaifiyarki da Allah da taimakon da ku ke mana ke da Bello mu ka dogara, ga shi kin ce ke ba aiki ba to me ki ka gani?â€? Daga Inteesar har Mamanta suka yi wa juna kallon gane hangen Baffan su, to amma Saratu ta bar kyakkyawar turbar da ta fara gini a kai na ingantaccen ilimi? Idanuwan Anty Saratu suka ciko da hawaye. A yau kam ta kara tabbatar wa Allah ne gatan su, sai kuma Brigadier Bello Makarfi. Baffa ya ce, ‘Karatun Saratu abu ne mai kyau da muhimmanci, amma yadda Allah ya tsara al’amari, haka ya kamata bawa ya yi hakuri, ya danne nashi tsarin ya bi shi. Kana naka ne Allah yana nasa, kuma nashin shi ne gaskiya. A tsahirta da karatun a ga abin da Allah ya shirya a gaba. Ku zauna ku ci abinci, ba tare da kun zubda mutuncinku ta hanyar roko a idon kowa ba, balle a samu abin goranta maku. Na san yanzu an sa ido ne a ga kasawar ku. Amma in kun kame mutuncin ku baku kuma je neman taimako wurin kowa ba, ban da Allah, babu wanda zai wulakanta ku. A yau neman taimakon ya zamewa talaka abin wulakanci, don haka ku tashi ku je ku kwanta, gobe in Allah ya kai mu ki koma dakin mijin ki, ku ci gaba da addu’a, Allah ya kawo mana dauki da gaggawa.â€? Washe gari suka kamo hanyar Abuja cikin bus din haya kamar yadda suka zo, zuciyoyin su cike da taraddadin wannan masifa. Ko a mafarki Saratu ba ta taba kawowa iyayen ta da ita kanta za su taba fadawa irin wannan SIRADIN RAYUWAR ba. Saratu ta yi kuskure, babu wanda ya ke sama da jarrabawar Ubangiji. A yau ta tuno da wata waka da ta kan ji a bakin kawarta Hidayah, da haka kawai in tana wani abun za su ji tana waka tana cewa: “The rich also criesâ€?.â€? Ma’ana: ‘Mai kudi ma yana yin kuka.â€? Lallai Uba, shi ne jigon rayuwar ‘yan adam. Uba shi ne farin cikin iyali, shi ne bango abin jinginar su, shi ne rufin asirin su, in ba shi rayuwar iyali abin tausayi ne. Wani abu da ya ba su mamaki da suka iso Khalil ke gaya masu Hajiya da Mama Suwaiba sun tafi Johannesburgh (Saro gold dinsu). Madadin zaman hakan nan ta samawa Intisar makarantar koyon na’ura mai kwakwalwa a layin su inda za ta yi (DIT) ta kuma dauko daya cikin dakin Brigadier ta aje mata bisa tebirin karatun dakin ta sannan ta hada mata Internet, duk don ta debe mata kewa duk da yarinyar ko kadan bata nuna mata wata damuwar ta ba sam. Ita ce ma mai karfafa Antin da ta saki ranta, in don makaranta ne ko nan da shekaru biyar in Allah ya ce za ta koma ne a cikin yardarsa. Ta dage da fafutukar neman aiki da kafafunta. Saratu ta share komai ta maida hankali kan koyon kwamfutar ta, cikin watan ta na farko da farawar Diplomarta ta kware sosai. Yammacin wata ranar Juma’a zaune take bisa kujerar na’urar ta, tana zanawa kawarta Raadhah sakon yadda al’amuran rayuwa suka cude mata, suka yi sanadiyar rashin dawowarta makaranta. How much do you like this story? 5/8/22, 09:59 - Ummi Tandama😇: _____________________________ *âœðŸ? SIRADIN RAYUWAâœðŸ?* Book two *@Takori* Page5ï¸âƒ£ Sanye ta ke cikin danyar atamfa Super English, ruwan kwai da aka yi wa ratsi da shudi da jaja-jaja, atamfar ta yi matukar amsar dan kyakkyawan jikin ta, an yi mata dinki zani da riga fitted kanta babu kallabi, maimakon haka ta daura shi ne a kan cinyar ta, gashin kanta wanda yake curl a sake yake bisa dogon wuyan ta, sanyin air-condition ya kara taimakawa ainun wurin kara kwantar da shi lub-lub a wuyan ta kamar ba abin da ya dame ta. Sai dai ta yi ‘yar rama wanda hakan ya kara mata kyau, fuskar ta fes, da ruwan hoda chiristian dior da take amfani. Sai kawai ta ji an rufe mata ido daga baya, ta lumshe ido ta yi ajiyar zuciya ba ta bari a kasa ba ta ce, “Daga jin kamshin 5000 Doller na san Ya Faisal ne, wani Bayarabe mazaunin Illorin.â€? Faisal ya yi dariya, ya dube ta gaba daya yana kiyasta adadin ramar da ta yi, hannuwan shi a cikin aljihun wandon shi, ya ajiye gwiwoyinsa a carpet ya zaro hannun shi daga aljihu ya tallabi habar ta ya ce, ‘Baby, are you stillâ€? still at home?â€? Hawayen da take ta tattali ne suka kubce sharrr! Haushi ya ba ta kamar ta doke shi, ta kai hannu ta sauke hannun shi a habarta ta maida hankali ga abin da takeyi. Ta tabbatar sakon ta ya tafi ga Raadha, tana yi tana share hawayen da suka jika mata kundukuki da yatsun hannun ta. Ba wanda take tunani a wannan lokacin sai Daddy. To bata san kuma me za ta ce da Faisal ba, ba za ta iya gaya masa mai dadi ba, shirun shi ne mafi amfani. Ai ko albarkacin makwabtaka, bar ta kasancewar ta kanwar ubansu, ba ma na uban da ya hada su a gidan ba, sa dinga taimakon Aunty Saratu. Su ‘ya’yan Hajiya uwar su mai gwal, don haka duk suka koma makaranta suna batar da kobo yadda ransu ke so, turaren Faisal kadai ya isa su shekara suna cin abinci ita da uwar ta. Ba a maganar agogon diamond da ke daure cikin lafiyayyar fatar hannun shi wanda ya isa ya maida ta Riyadh har da canji! Su ko Allah Sarki, ko abinci sai sun je kasuwa da kansu sun sayo. Amma shi ne wai don rainin hankali yake tambayar ta har yanzu tana gida? To sun ba su wani abu ne ko da cikin dukiyoyin Daddyn da Hajiya ta tattare ta boye? Tasa dankwalin atamfar da ke bisa cinyar ta ta share ido, a sanda ta jiyo Najib na gaisawa da Aunty, wai ga buhun shinkafa nan za a shigo mata da shi, tana jiyo sanda Antin ta ce cikin fara’a, “Lah! Ku bar shi kawai, don can da yara muku nan mu biyu ne kacal, ba zamu rasa abin da za mu ci ba don ba Alhaji.â€? Ta sake tunzura, ta mike ta kashe kwamfutar ta yi daki fuuu! Har tana tuntube da kujera. Ita dukkanin su ba ta son ganin ko daya duk selfishes take ganin su wato masu son kansu kadai. Faisal ya zamo wani irin pale (Mara kuzari) tamkar ya mtu, ya kasa motsa ko da dan yatsansa, da kyar muyarsa ta fita can kasan makoshi. “Intisar na so ki tsaya ki fahimci ba wai…â€? Tuni ta fice. Faisal bai yi wa kowa sallama ba a ranar ya koma Ilorin. Bai ko ji tsoron tafiya mai nisa haka cikin daren ba, a hanya ya kwana, kar ki so ki tona zuciyar wannan aminin Intisar. An sanar da Anti tana da baki sati biyu bayan faruwar wannan. Ta sha lullubi ta iske su a sassan baki su biyu duka maza, ta sha mamaki da ta ga Larabawa ne na usil bakin nata. To an yi sa’a ita ma ta dan iya larabcin a bakin Intisar, nan suke gaya mata su shuwagabannin shashen da diyar ta ke karatu ne a Kingston da ke Riyadh. Sun zo Nigeria ne musamman don abu biyu, na daya kafa reshen makarantar su tare da Jami’ar Bayero da ke Kano, na biyu, sun yi amfani da adireshin su Saratu don su zo su ji ko lafiya, suka katsewa hazikar yarinya kamar Sarah da ake wa hangen great achiever a gaba karatu? Ya kare da cewa. “Saratu in ta kammala karatu, ba ma nufin kasar Saudiyyah ta amfana da ita, face kasar ku da za ta sami dumbin amfani daga gare ta.â€? Aunty Saratu ta gode masu, for their concern kan al’amarin diyar ta, kuma hakika ta ji dadi, sai ta ce, da su ko Saratu za ta koma Riyadh to ba yanzu ba, saboda ba za ta iya affording cost, din ba. Babanta yana kulle. suka nuna matukar juyayi, dayan ya ce shi da Saratu tamkar diya da ubanta suke a makaranta, shi ne Dr. Alhassan As-Sayyid malamin Chemistry din su, don haka zai ci gaba da daukar nauyin karatun Saratu daga sakandire har jami’a amma fa in sun amince. Aunty Saratu ta dade da daukar wata wasiyya ta mahaifinta kan ‘dogaro da kai, shi ne babbar siyasaâ€?, amma bata nuna masu ba. A karo na farko ta yi sha’awar gwada hankalin Saratu, sai ta yi ta yi masu godiya ta ce amma bari ta je ta ji ta bakin Saratun tukunna, don bai yiwuwa ta ari bakin ta ta ci mata albasa, suka ce alright. Inteesar kwance tsakiyar ni’imtaccen gadon ta tana mai fuskantar ceiling idanunta a rufe ruf kamar mai barci, zuciyar ta cike da kuncin Ya Faisal da Najib. Aunty ta tsaya a kanta ta yi murmushi ta ce, “Har yanzun haushin Faisal din ne? Alhalin sam ba shi da laifi Saratu, kudi fa uwarsa ke da su ba shi ba, a kan me za ki dauki laifin duniya ki dora masa? Sata kike so ya je ya yo ya maida ki makarantar ko me? Bayan ma Allah ya yi mana ludufi?â€? Ta juyo ta dube ta cikin ido, “Daddy ya fito?â€? Ta fadi da wata irin shanyayyar murya. ‘Tukunnah, ki san wani Dr. Alhassan a makarantar ku?â€? Ta zabura ta zauna daidai, ‘Chemistry teacher na da nake ba ki labari mai yi min wakar Saratu is doing research, kin tuna? Ya kula da rayuwata sosai a duk zamana na shekaru biyar a Riyadh.â€? “To shi ne ya zo yanzu tare da wani Abraham Shaikh, sun ce ki bi su ku koma makarantar zai ci gaba da daukar dawainiyar karatun ki har zuwa mu ga abin da Allah zai yi.â€? Saratu ta yamutsa fuska ta ce, ‘Kash! Ya kawo taimako a sanda ba ni da bukatarsa. Dama dai ya ce zai taimaka ne a fiddo mana Daddy, Akbar min zalik (abobe all) Mamar mu ba zan iya tafiya in bar ki lonely cikin irin wannan halin da muke a yanzu ba, ba zan iya karatun ban san halin da Daddy ke ciki ba. Don Allah Mamar mu ki ba malami na hakuri, ni wallahi ba zan bi su ba……â€? Sai tasa mata kuka da baya mata wuya tun farkon faruwar al’amarin kamar sun ce za su ja ta ta karfi ne. Aunty Saratu ko so da kaunar Intisar ke kara tofo a zuci da gangar jikinta. Ta gode Allah da bai ba ta dan kanta ba, mai yiwuwa da ba zai ji kanta kamar ‘yar da ba ta san ko ta waye ba. Da kyar ta lallabi Dr. Alhassan amma ya ce duk san da suke neman taimako kan karatun Saratu a shirye suke da su taimaka ta kowanne bangare. Har adires din sa ya basu na Riyadh, inda yake aiki da Turkey kasar haihuwar shi inda yake zaune da iyalin shi. Ga yadda Antin ta karanci zuciyar Dr. Alhassan ma kadai ta fahimci matukar kaunar Saratu yake, kauna ta hakika kuwa, ba ta malami da dalibi ba. Bello ya zo ya yi week-end a Abuja wannan watan. Ya ba baby wasikar Faisal da ya ce shima ta zo mai ne daga post. Da ta ki karantawa, sai da ta ga bacin ran mamar ta tukunna. “To Mama dauko min gilas dina.â€? Hajiya Saratu ta yi dariya ganin yadda ta zobara baki gaba (hakan take yi idan Faisal ya ba ta haushi), ta je ta dauko mata gilashin da kanta, ta sa hankici mai tsabta ta goge mata kwarmin ‘yan lumasassun idanun ta, kana gilashin, kafin ta manna mata farin siririn medical glass din ta. Broken heart! Na sani, duk bayanin da zan yi ba zai gamsar da ke ba Intisar, amma kafin nan, ina farawa da baki hakuri, Allah shi ne shaida, na fi ki damuwa da rashin komawar ki karatu. Ni kaina abubuwan da Hajiyar mu ke yi bana son su, to amma kin san ba yadda zan yi, tunda Hajiya mahaifiyata ce. A da ban yi niyyar gaya miki ba, sai don gani da na yi kin yi min wani fassara na daban a zuciyar ki. I try my best (na yi iya kokarina) in samu ko da takardar motar Daddy guda daya in saida, ki koma makaranta. Hajiya ta hana, har tana ikirarin tsine mini, idan na sake sa baki kan harkar karatun ki. Intisar abin da ban taba tsammani ba (ko a mafarki) wai Baby ki ka ki saurarena a kan wani (matter) da ki ka san ba ni da iko. Amma kin san Allah ko da zan yi yawo ‘in nudeâ€? (tsirara) ne, sati mai zuwa za ki koma makaranta. Daga Yayan da baya da laifi. Ta lumshe ido abin tausayi, tausayin kanta ne ko ko Ya Faisal? Ita kadai za ta iya kiyasta halin kuncin da zuciyar Faisal ke ciki a yanzun kan wannan al’amari. Ta sani idan da abin da Faisal ya ki jini a rayuwarsa ba kuma zai iya jurar sa ba. To bacin ranta ne. Ta san a duniya daga Daddy, Mamar ta, sai Ya Faisal a masu kaunar ta. Ta kai duban ta ga Aunty Saratu da ta yi tagumi tana kallon ta, ta yi murmushin karfin hali. “Kin ji abin da Ya Faisal ya ce? Cewa ya yi ko da a ce zai yi yawo tsirara ne, wai sati mai zuwa zan koma Riyadh, kuma wai kin ji ashe Hajiya ce ta hana su ba mu komai na gidan nan? Shin Mama me na yi wa Hajiyar su Khalil ne ta tsane ni? Me na ke mata? Kin san Allah tunda nake a rayuwata, ban taba gaishe ta ta amsa ba, ban taba shiga sashin ta ba ta zage ni ba, banâ€?..â€? Sai ta sa kuka. Aunty Saratu ta rasa ma me za ta ce? Tunani goma da ashirin ya yi mata rubdugu. Me za ta ce da Saratu wanda ya jawo mata kiyayyar Hajiya Nafi? Ta tsane ta don tsinto ta aka yi? Ta tsane ta don kaunar da Daddy ke mata sama da ‘ya’yanta? Ina! Ko za a daura mata bindiga a wuya ba za ta taba furtawa Saratu ba ita ta haife ta ba! Ba tun yau ba ta san Saratu tana da zuciya a kan komai. Da suke yara in Khalil ya ba ta abu, daga baya ya dawo ya ce ta ba shi, sai ta cilla masa ta ce, ‘GA tsiyar ka nan. Ni ma Allah zai ba ni.â€? Ba kuma za ta kara duban abin ba ko da ya yar daga baya balle ta dauka. To haka abin yake har girmanta. Duk wani abu da ta san zai taba mutuncin ta tana gudun shi tana kyamar shi tana yin nesa da shi balle rashin usli? Ta girgiza kai cikin jin wata sabuwar kaunar yarinyar da ta ratsa ta, ta kada harshe ta ce, ‘Saratu in Maman Khalil na bada rahma, don Allah in ta zo kan ki kar ta baki, in ce ko karshen ta kenan?â€? Ta yi murmushi tana share idon ta da hankici ta ce, “Karshen ta kenan fa Mamar mu.â€? Ranar Juma’a bayan an sauko sallar Juma’a, Faisal ya iso Abuja kamar yadda ya saba. Sanye yake cikin ‘yar ciki da wando ga kuma babbar riga ya ratayo a kafadun shi na babbar shadda Wagambari ruwan sararin sama mai haske (sky blue) wadda ta taimaka ainun wurin kara fiddo gogaggiyar choculate colour fatar shi mai sheki. Duk ‘ya’yan Hajiya Nafi haka suke kamar half cast kasancewarta usli Shuwa ce. Kira kamar well-fed Americans ga tsayi ga zati tamkar Babansu. To shi Faisal karan hancinsa har wani rankwafawa ya yi kadan saboda tsayi. Kowannensu ya mallaki diggunan beauty point biyu in ka dauke Al’ameen mai guda daya a gefen kuncin sa na hagu kawai kuma shi kadai ne da cleabe wannan dan digon na tsakiyar haba yayin magana ko murmsuhi. Faisal akwai son turare (5,000 Doller), inda duk ya yi za ka ji daddadan kamshin na bibiyar shi. To haka yau ma. Ya kalmashe cikin ‘yar lallausar kujerar computer Intissar yana kallon ta sai fama take da dogon gashinta mai santsi, ita a la dole sai ta yi kalba, ta yi ya warware, ta sa roba ta matse bakin ya sabule kamar ba ta san Allah ya yi halittar shi a dakinta ba ma. Ba don ta girma ba, da ya amshe ta, don wannan aikin shi ne, tun tana goye, sai da ta kai aji uku shi da kansa ya bari. Ko ta yi ta yi ya gyara mata sai ya ki, ya ce shekarun ta sha biyu ta gyara abun ta. Shi kadai ya san me yake ji tun lokacin game da Baby. To balle a yanzun da ta zama cikakkar budurwa ‘yar sha bakwai, komai ya ji Tubarakallah, komai na ta ya kai ya kawo, ya yi wa fuska da zubin halittar ta daidai. Ga ta nan dai tamkar kwalbar nan ta coca-cola mai sanya kan duk wani hadadden namiji juyawa. Kan shi kuwa ke juyawan ta ko’ina, wani irin abu ne ke ratsawa tun daga kwakwalwar shi har yatsan kafar shi game da Saratu a yau, barin yanzun da take sanye cikin wata jar matsatstsiyar riga fara sol da ratsin baki-baki samfurin (Dolce & Gabbana) da bakin dogon siket din jeans, to amma wannan kanwarsa ce fa da suke uba daya? Sai ya yi saurin korar shaidan a zuciyar shi ya rintse ido yana jan Hasbunallahu wa ni’imal wakeel, ni’imal maula wa ni’imal naseer, allahumma ajirni fi musibati hazihi wakhlif ni khairan min haâ€? har ya samu hakan da zuciyar shi ke yi ya lafa. How much do you like this story? 5/8/22, 09:59 - Ummi Tandama😇: _____________________________ *âœðŸ? SIRADIN RAYUWAâœðŸ?* Book two *@Takori* Page6ï¸âƒ£ Daidai lokacin da Anti ta turo kofar ta shigo dauke da jug cike da tatattun ‘ya’yan itacen tuffah da tambulan mai garai-garai. Ya mike ya karbe ta, ta tsiyaya masa ya sha suna gaisawa ta ce, “Bayerabe saukar yasuhe?â€? Ya yi dariyar da ya lotsa beauty point din shi, ‘Ke ma Anty tsokanar baby za ki lankaya min?â€? Ta ce, ‘ina suka yi posting din ka NYSC?â€? Ya ce, ‘Ai ni na shiga uku da kasar Yarabawa, nan Ilorin din suka bar ni.â€? Ta kyalkyale da dariya nan suka shiga hirar makaranta. Ya ce, ‘Aunty gobe fa Intisar za ta koma, ga bisa din ta na amso, yau ko darajar kallo ban samu daga Intisar dina ba, duba ki ga yau ko gaisuwa babu? Ni na rasa me kuma zan ce da Baby ta fahimci ba ni da laifi?â€? Yanayin yadda ya yi maganar ya bala’in ba ta tausayi, ta kai idon ta ga stool din da Saratu ke zaune tana ta aikin kalbar ta. “Wai da gaske Saratu ba ki gaishe shi ba?â€? Ta saki jelar hannunta, ta juyo kadan ta cira lumsassun idanun ta a gicciye ta zube su a kan shi, cikin sassanyar muryarta ta ce, ‘Ina wuni ya Faisal?â€? Ji ya yi tamkar ta ja shi da wutar lantarki, abin da bai taba ji ba a rayuwar shi. Gaba daya ya karasa kidimewa, kwayar idon shi na neman bacewa, ya yi kokarin saisaita tunanin shi ko don saboda Anti da ta kafa masu ido, cikin jarumtaka amma da kyar sautin ya fito daga makoshin sa da ya bushe rayas, ya ce, “Ba na amsawa, alhalin sai da na roka?â€? Ta yi murmushi kawai cikin halin ko in kula, ta juya ta ci gaba da kalbar ta. Anti ta yi mata fada sosai amma ba ta ce ko kanzil ba. Ta samu gefen gadon Intisar din ta zauna ta ce, ‘Maganar tafiyar Intisar Riyadh a gobe, ina ganin a bar ta kawai Faisal.â€? Maganar ta yi mai kama da saukar kibiya a kahon zuciyar dan adam, duk gwiwoyin sa suka yi sanyi, ya yi dagwalo abin tausayi, a ransa ko cewa yake me zai yi ya farantawa wadannan murdaddun uwa da ‘ya? Ta ce, “Da farko dai ina son sanin inda ka samo million biyu Faisal?â€? Faisal bai iya karya ba, kazalika duk ‘ya’yan Brigadier. ‘Hajiya ce ta ba ni in kai mata banki, ni kuma na ga da a kai kudi a aje a banki hakan nan kawai, ba gara na maida Baby makaranta da su ba?â€? Aunty Saratu ta yi murmushi, yau kam ta kara tabbatarwa kanta Faisal yaro ne danye da gigin kuruciya ke diba, “Yanzu saboda Allah Faisal, idan ta je banki daukar kudin ta, ta tarar baka kai ba, me mahaifiyar ka za ta dauke ka? Mara amana. Da mai cutar mahaifiyarsa wanda ni bana maka fatan hakan. Zafin rai ba shi zai sa Saratu karasa karatu ba, komai na rayuwa yana tafiya ne da lokaci. Idan Allah ya ce iyakar abin da Saratu za ta karanta kenan a duniya babu dan adam din da ya isa ya kankare. Har yau, har gobe Faisal ba mu fidda rai da releasing din Baban ku ba. Don haka yanzu-yanzu ka je ka saida bizar nan ka mayar mata kudin ta inda ta ce. Idan fa Allah ya yi hukunci Annabi sai ceto. Ita Saratu ba wai tana jin haushin ka don ku kun koma makaranta ita bata koma ba, illa ba ku damu da ni ba da kuma tunanin me ta yi wa Hajiyar ku ta tsane ta? Wanda na gaya mata wannan tunanin ba zai amfane ta da komai ba. Don Allah kan halicci mutum ya kimsa rashin jituwa tsakanin sa da wani ba tare da wani dalili ba. Bai yiwuwa mu samu soyayyar kowa a rayuwa . Na tabbata kana kaunar mu Faisal, kauna ba kadan ba. To albarkacin kaunar nan Faisal do as I said, ma’ana yi yadda na ce.â€? Sai ya mike, duk jikinsa ya yi sanyi lakwas. Ya maida passport din aljihun gaban rigar shi. Wasu hawaye suka tarar masa a kwarmin ido, amma ya yi kokarin maida su. Tausayin Aunty Saratu da Intisar ke narkar da jijiya mai bada jini a jikin sa! ***** A Korea A cikin babban birnin Seol din kasar Korea, Hajiya Hadiza ke kwance masu yawa, ta juya a hankali gami da dafe kirjinta domin samun sauki cikin sofa idanun ta a rufe, zuciyar ta cike da kuncin da ta kasa rabo da shi tsayin shekaru daga tafarfasar da zuciyar ta ke yi tamkar ta faso allon kirjin ta ta fito. Wasu irin hawaye suka biyo lallausar kumatun ta masu zafin dake kara zafin da zuciyar ta ke ciki. Cikin dan lokaci zazzabi mai zafi ya rufeta, jikinta ya rude sosai, zazzabin ne, ciwon kai ne, kirjinne duka ba wanda cikin su bai mata ligi-ligi ba, daga kwancen da ta ke ta fado kasa tana mirgin-mirgin, a sabili da wani irin zafi da tukuki da kirjinta ke yi. Ambassador Basheer Sambo, ya fito wanka ya zuba suit bakake ya na daura ‘linksâ€? din hannun rigar shi, cike da tunanin me ya tsayar da Haddizah? Tunda suka yi aure kimanin shekaru goma sha biyar a baya, dai dai da rana daya bata taba barinshi da daure tie da botirin riga ba in ba da wata muhimmiyar lalura ba, sai ko yau din nan. Ya shiga danna mata kira ta intercom har ya gaji, babu Haddizah babu tattausar muryar ta. Yana shirin fitowa ne bayan ya dauko briefcase din shi suka yi wani uban karo da babbar diyar shi Hidayah, a zahiri a firgice take, ga hawaye na zuba a idon ta, kira ta ke cikin tashin hankali “Mummy ta mutu Daddy…â€? Wadannan sune kalami mafi muni da ya taba ji a rayuwar shi, suka kuma hautsina ‘ya’yan hanjin sa duka a lokaci daya. A guje ya soma hada matattakala uku-hudu har ya tadda falon shan iskar su, inda a nan ne ya baro ta tana sallar asubahi. Rigingine ta ke kurum, babu alamun tana motsi haka babu alamun numfashi a tare da ita.Ya kai hannu cikin sanyin jiki ya juyo da fuskar ta gareshi yace “Ha-di-zah!â€? Ya kira sunan yafi sau goma cikin rawar murya kakkaura, amma bata amsa ba, kamin yayi ta maza in ji mata ya fiddo wayar shi cikin aljihu ya kira likitan su, cikin mintuna ashirin likitan ya shigo. Ya jima yana aune-aunen sa a kanta yayin da uban da ‘ya’yan suka yi sukutiiiâ€? suka zubawa sarautar Allah ido, kowanne zuciyar nan ba sai an tona ba da tararradi. Tuni Hunainah ta soma kuka, likitan ke lallashin ta yana gaya mata Maman ta ba mutuwa tayi ba, ya daura mata drip yayi mata allura guda daya yace idan ruwan ya kare zai dawo. A ranar ta sha allurai har da na jijiyoyi kamin ta soma shaida wanda yake kanta. Kwananta uku a kwance. Rannan da daddare sai ta ji ta narke cikin laima, ta yi salati ta runtse ido, babu ko tantama, dan yaron cikin da take dauke da shi ne, ya fice. Sakamakon binciken kwararren likita Norman, Hajiya Hadiza jinin ta ya hau sosai sabida wani damuwa da ta sama ranta tun da dadewa. Ambassada ya kama kai, “hypertension, Haddizar? Shin me ke damun Hadiza? Meye matsalan ta a rayuwa? Duk wani so, duk wata kauna ya mallaka mata ita da ‘ya’yan ta. Bai taba barin su cikin bacin rai ba dai-dai da rana daya sai ko cikin ajizanci irin na dan adam. Bai yi zaton akwai wani buri da take da shi ba kuma bayan wannan. Ba abinda ya gaza yi masu a rayuwa, to shin ta ina ya kuskurota da har ta ke neman rugurguza masu kyakkyawar rayuwar da suke ciki? Me ke damun ta, da ke neman ya cuce shi? Dan cikin da ya ke begen ta haife mashi da namiji, ta bari ya bi rariya a hofi da tunanin da ya ke ganin na banza ne. Satinta kwata-kwata daya a kwance, amma in kaga muguwar ramar da ta yi tsammani za kai shekararta guda tana jinya. Tayi duhu, idanun ta sun fada sosai kullum kuma bata umh bata umh-umh ko sannu su kai mata bata amsawa sai dai ta bisu da na mujiya kawai. Ambasada ya shiga matumkar damuwa kazalika ‘ya’yan ta ko makaranta sun kasa zuwa. Koda ta sami sauki ma jiya I yau, kullum tana kwance kawai (flat) tana kallon (ceiling) ita kadai tasan me ta ke sakawa tana kuncewa a zuciyar nan tata tamkar bata taba gamuwa da wani abu wai shi farin ciki ba a gabadayan tsayin rayuwar ta. Duk kuwa da kakkausan gargadin da likitanta ya yi mata na nesantar tunanin da take yawan yi don tserar da lafiyarta daga kamuwa da ciwon zuciya. A yau ma kamar kullum, ya dawo daga ofis ya taddata rigingine hawaye na bi ta gefen kuncinta, wani haushi ya kama shi amma ganin ‘ya’yan sun tasa ta a gaba suma kukan suke, an rasa mai lallashin wani, ya ji babu dadi. Dukkan jikin sa ba lakka, ya zame ya zauna gefen ta dai dai saitin kanta cikin rarraunar murya yace “Hadizah, in kina kaunar Ubangijin da ya halicceki, ki gaya mana me ke damun ki? Ki tuna fa daga ni har ‘ya’yan ki, muna da hakki mai girma a kanki da ya zamo dole mu san damuwar ki. In kina ganin bana iya magance maki ita, akalla babu abinda kudi basa yi a duniya, ni kuwa in har kudi zasu yi min maganin wannan damuwar da kike ciki, ban ga amfanin su gareni ba. Duk fa wani hakilo da na ke yi a duniya domin dauwamar farin cikin ku ne, da kokari na na cika alkawarin dana dauka akan ku ke da Hajjo. Idan kuma ni ke bata maki ki gaya mun don in gyara, don shi dan Adam har kullum ai ajizi ne?â€? Hadizah ta girgiza kai alamun ko daya babu cikin abubuwan da ya lissafa. Ya ce “to ko zaman kasarnan ne baki so mu nemi sauyin aiki?â€? Nan ma Hadiza tace “lalaâ€? yace “kenan aure na ne ya ishe ki, ko kuma kin gaji da zama da ni sabida wani illa ko nakasu da nike da shi, wanda ni din ban sani ba, kike kuma jin nauyin ki gaya mani? Idan haka ne ki fada mun man, ni har kullum Bashir mai kaunar ki ne da farin ciki da duk abinda kike so, zan iya sauwake maki domin farin cikin ki, ni da ‘ya’yan ki mu dauki danganar rashin ki, in har hakan zai maido maki da rayuwar ki ta baya…â€? sai ya fiddo biron shi daga aljihun gaban rigar shi, ya ja littafi ya yagi takarda, ya aza biro kamar mai shirin yin rubutu. Bata san yaushe ne ta samu kanta a gabansa ba tana magiyar kada ya rubuta, da wanne zata ji? Haka Hidayah da Hunainah sun rirrike hannun shi tamau da suka fuskanci aika-aikar da yake shirin yi wadda ko giyar wake ya sha yasan shima ba zai fara ba, komai rintsi. Suka ce “Daddy in ka saki Mamar mu Allah muma bazamu zauna da kai baâ€? yace “to ya kuke son in mata? Hidayah-Hunainah Mamin ku bata kauna ta. Baka taba boyewa wanda kake kauna damuwar ka ko ta mecece balle mijin ka, abokin rayuwar ka na har abada! Ku duba ku ga cikin da muke neman samuwar shi shekara goma da doriya, ta bari ya salwanta a banza, ba ruwan ta da mu balle damuwar da muma zamu iya kasancewa a dalilin tata damuwar, a dalilin rashin walwalarta garemu, shin wannnan shine zaman iyali na hakika da suka fahimci juna suka kuma yarda da junan su? No matter what ke damuna, ba zan taba boyewa mahaifiyarku ba…â€? Ya mike ya bar su nan ya fice. Hajiya kuka ‘ya’yan ta kuka. Tun da suke, basu taba fadawa halin kunci irin na yau ba. Gabadayan rayuwar su cikin farin ciki da fahimtar juna ne eben once, yaran nan basu taba ganin wani sabani makamancin wannan ya faru tsakanin iyayen su ba balle har a kai ga musayen ra’ayi ko tankiya. A ko’ina, Ambassador Bashir da Hadizah, masu nuna suna kaunar junan su ne. Amma a yau wai za’a rubutawa Maman su saki? Hidayah da Hunainah, cewa sukai a ran su kada Allah ya kuma nuna masu wata rana makamanciyar wannan. A fili kuwa rokon Mamin su suke ta gaya masu me ke damun ta???? Tushen Labarin Suna na na asali Hadiza-Kubra, amma a rugar mu DIJE a ke kira na. Ni mutuniyar wani kauye ce wai shi Shanono, karamar hukuma ce a cikin birin kano Nijeriya. Koda yake asalin mu ba Kanawa bane matafiyan fulanin daji ne. Mun billo daga wani jeji a yankin Adamawa muka dira a Gongola, muka dawo Dukku ta Gombe, muka sake tashi muka koma zama a Alkaleri ta Bauchi. A kan hanyar mu ta isowa Medile daga Yako, mahaifinmu wanda shine shugaban ayarinmu ya mutu, sai kanin sa Baffa Lalajo shi ke kula da mu kuma shi aka nadawa rawanin mahaifin mu. Bayan rasuwar sa ne muka lula cikin nahiyar Kano, a wani jeji bayan garin Shanono muka kafa bukkoki, muka saki dabbobinmu muka yi zaman mu anan cikin kwanciyar hankali. A can duk aka haife mu ni da kanwata Hajjo, da Baffa ya mutu ya bar Innar mu da tsohon cikin ta, kushewar ‘yan uwa da kakannin mu har yanzu suna can. Malam Ibrahim sarkin noma shine Sarkin Noman kauyen Shanono, mutum ne mai arzikin gaske, a garin Shanono bakidaya, babu wanda ya kai shi nome amfanin gona mai yawa, ya mallaki tafka-tafkan gonaki sama da goma ya kuma fi duk manoman garin samun amfanin gona mai albarka. Dabbobi garke-garke da gidajen gona da wannan mutum ya mallaka har ba zasu lissafu ba, a takaice abinda za’a ce shine duk fadin garin babu wanda ya kai shi arziki. Abin tausayi da wannan bawan Allah shine bai taba haihuwa ba, har shekarun girma suka riske shi. Shekarun su ashirin cif da matar shi ta ladan noma Shatu amma ko batan wata bata taba yi ba. Daga baya ne ya shiga neman auren karamar yarinya budurwa, tare da Addu’ar Allah ya sa karshen wahalar sa ta zo na samun Magaji daga gareta, wanda ya ke kwana rokon Allah ya bashi kamin ya dauki ran sa. Shekaruna goma sha hudu Baffa na ya ce ya ba sarkin noman Shanono aure na. Na yi kuka nayi bakin cikin kiyayyar auren tsoho sa’an Baffa na kaman in mutu, amma sai Baffa ya daga ni ya jefa a katuwar tukunya, ya zane da tsabga, sai da ya yi mun tabban da har abada ba zasu goge a gadon bayana ba kana ya kyale ni, ya kuma ce idan na sake tada hankalina kan auren sarkin noma sai ya kore ni daga rugar mu, mahaifiyata da Yafendo na babu yadda suka iya, haka suka wanke ni suka ba sarkin noma. Sarkin Noma ya dauki son duniya ya dora a kaina, wannan ne ya sayo mun bakin jini a wajen kishiya ta, Shatu, kullum cikin yadar mun da magana ta ke kan yarinya ta dani na auri tsoho sabida tsabar kwadayin abin duniya, na juye kan tsoho kinibabbiya, har sai da ta kai ko tsakar gidan bana iya fitowa in har ba Sarkin Noma na gidan ba, bana umh bana umh-umh kullum sai sakar auduga. Ba sai na fadi ba ku ma shaida ne a kan irin kyawun da Allah yai min, kyawun da akan ce duka rugar mu babu kama na. Da na lura Shatu ba kishiyar kirki bace sai na shiga yiwa kaina addu’o’in tsari daga sharrin ta, tare da yin taka-tsan-tsan cikin duk wasu al’amurana da ita. A zamana na shekara guda kacal da Sarkin Noma na fahimci shi mutumin kirki ne, mai alheri mai saukin kai da taimakon talakawa, duk garin kowa na kaunar shi da girmamashi suna kuma taya shi Addu’ar Allah ya cika mishi dadadden burin rayuwar shi kamin mutuwar sa. A hankali-a hankali sai na ji nima ina kaunar shi sabida kyawawan halayen sa. Shatu kan ce ta san na zo ne in haihu da Sarkin Noma, in kashe shi in kwashe dukiyar sa in gudu, to kuwa na haihun ta gani, domin ita tana cikin sahun matan nan da ake kira (juya). Yafendo na da dangina da ke ruga kan ziyarce ni lokaci-lokaci. Shekara ta daya a gidan Sarkin Noma sai ga ciki ya billo, amma da ya ke ni doguwa ce babu wanda ya farga har sai da ya shiga wata bakwai, ni kuma dama ba baki ne da ni ba balle in fadiwa wani. Ko shi kansa Sarkin Noma bai kawo a ransa wai ciki ne da ni ba duk da kibar da na yi, to abu ne da duk an fidda rai. Rannan Aliero (Yafendon mu) ta zo duba ni kamar yadda ta saba, na tashi don in debo mata ruwa a randa sai cewa tayi “yaki Dije, ikon Allah, ashe juna biyu gareki baki fadi mun ba? Ke dai Aradun Allah zurfin cikin ki wataran sai ya kahe kiâ€? nace “juna biyu? Yafendo me ar juna biyu?â€? tayi tsaki ta fito soro ta tadda Sarkin Noma, tace zasu dauke ni rainon ciki, ba kuma zan dawo ba sai na haihu. Farin ciki a wajen Sarkin Noma kema kin san fada ma bata baki ne. Ya daga hannu yayi godiya ga Allah ya shiga rabar da dabbobin shi da kadarorin shi masu yawa sadakah, ya kuma kara kyautatawa Malaman da ke taya shi rokon Allah kan su kara dagewa da Addu’ar Allah ya sauki Dije lafiya. How much do you like this story? 5/8/22, 09:59 - Ummi Tandama😇: ______________________________ *âœðŸ? SIRADIN RAYUWAâœðŸ?* Book two *@Takori* Page7ï¸âƒ£ A rugar mu na haife sankaceciyar diyata mai kama da ni a komi. Tun daga yatsun kafa, nannadaddiyar sumar kai har zuwa baki na jaririyar nan bata bar komi ba illa digon tawwadar Allah da ke gefen hancin ta na dama wanda ni bani da shi. Ranar suna Sarkin Noma sa da rago ya kayar ya rada wa yarinya suna Fatimah. Ban koma gidan Sarkin Noma ba sai da diyata tayi watanni uku kaman yadda ya ke a al’adar mu. Iyaye na sun yi mun gara mai yawa da burgewa. Ranar da daddare Sarkin Noma ya dauki Fatima ya tsaga mata uku-uku a tsakiyar kirjin ta na family din shi. A ranar mun yi kwanan farin ciki da Fatima a tsakiyar mu, amma sai me? Wayewar garin Litinin muka shafa babu jaririyar mu babu dalilin ta. Sarkin Noma ya yayi salati ya buge ni yace “ke Dije, ina kika aje Fadima?â€? Na mike nima ina mutstsike ido nace “ina ko na aje ta banda nan tsakiyar mu?â€? Ko kamin in kai karshen magana ta na soma kuka, aka caje gida kaf ciki da bai babu Fadima babu alamar ta. Shatu tasa hannu aka ta rafsa ihu tace “yanzu ‘yar daya jal, da muka samu aljannu sun dauke?â€? Jin abinda tace a take na fita hayyaci na ko jin su ba na yi na zame kasa a sume. Shi kuwa Sarkin Noma tuni hankalin sa ya gushe dama kuma ga rudu irin na tsufa, cewa ya ke “ina! Ina za’a ace aljannu sun dauke mun ‘yar guda daya da ban samu ba sai a tsufa na?â€? Yayi titi a guje mutane suna rike sa yana fizgewa yana kara nausar titin. A can gefe kuma mota ce akori-kura ta taho cike da tumaki da gudun gaske, irin motocin nan na kauye da basa jan birki sai sun je tasha. Abin ne ya zo da karar kwana in ba don haka ba ‘yar turewar da motar ta yiwa Mal. Ibrahim Sarkin Noma, bai isa a ce ya mutu ba, amma ko shurawa bai kuma yi a wurin ba. Da na komo hayyacina iyayena suka zo suka dauke ni na yi takaba kaman yadda Addini ya tsara. Baffa na babban malami ne, masani kwarai a cikin ilmin Alkur’ani. Ya dage da binciken Allah ya nuna masa musabbabin batan diya ta cikin Istikhara, cikin kudurar Allah kullum kishiyata Shatu yake gani. Rannan mafarki yayi wai ta haka rami tana neman bizne Fadima sai wani bawan Allah ya fizgeta yayi sama da ita, wanan kadai ya isar mishi gane cewa Shatu ce musabbabin batan diyata. To bafillace bai iya fushi ba, balle Baffan mu tun can zuciyar shi bata da linzami. Yasa samarin rugar mu suka haka mai wani wawakeken rami a jeji, manyan ‘ya’yan shi Leko da Kallamu yasa suyi fakon Shatu in ta dawo daga rafi su rufe mata ido da baki da bakin kyalle su dauko mai ita. Hakan kuwa aka yi. Kamar kullum Shatu ta dawo daga rafi da tulunta a ka, tana tafe tana ‘yan wake-waken ta hankalin ta kwance, duniya tayi mata dadi domin ita ta mallake komi na Sarkin Noma ko allura bata bari an bani ba, don a cewar ta yayi wasiyya tun yana raye cewa komi nashi ita ya mallakamawa, sabida tare suka tara abin su, sai ji tayi an kayar da ita an yi sama da ita, iyakar rudewa kam ta rude sai salati ta ke tana kiran iyayenta da kakanninta, bata zata ba bata tsammana ba ta ji ta kif, cikin rami, bayan ta da kasusuwan ta babu wanda bai amsa ba, tuni ta dauka mutuwa ta yi aka kawota kabarin ta. A lokacin duhun dare ya mamaye sararin samaniya, sai Leko da Kallamu suka gudu suka buya. Baffa na ya fito daga maboyar sa, nannade cikin farin rawani, ga farar auduga duk ya bi fuskar shi da ita, hannun shi na dama rike da kafceciyar addar saran bishiya, ya tsaya a bakin ramin yace “baiwar Allah, yau taki ta kare idan baki gaya mun inda ‘yar kishiyar ki take baâ€? Shatu tasa kuka ta ce, “wallahi ba cewa nayi su kashe ta ba, cewa na yi su kai ta dokar daji su yar, amma ba dajin nan kusa ba, cewa na yi ma su kaita wajen shiyyar nan kwata-kwata inda hankalin wani dan adam bazai taba kaiwa ba, sai in gaje gonaki da shanun Sarkin Noma ni kadaiâ€? Baffa yace “su waye suka taya ki wannan danyen aiki?â€? Tace “’yan sholisho ne na kira a tasha, yanzu ko zan sake rayuwa ba zan ce ga kamannin su ba balle inda sukeâ€?. Sai Baffa na ya mika mata hannu ta kama ya fito da ita yace “ki je ki ke da Allah, mun barki da fitowar rana da faduwar ta, idan Allah ya yarda sai kin ga sakayyar Allah ta sauka a kanki tun daga nan gidan duniyaâ€?. Ashe Baffa ya fadi da bakin mala’iku, Shatu na tafiya tana waiwaye ko gaban ta bata gani sabida tsoro da razana, ta afka wata korama da ke gudanar da ruwa, ruwa ya tafi da ita ba’a kara jin duriyar ta ba har yau din nan. Labarin nan da Baffa ya bani na yadda sukai da kishiyata Shatu, sai na fadi, ban kara sanin inda kai na ya ke ba. Tun daga ranar yau ciwo gobe lafiya amma ban kara rayuwa mai dadi ba. Jike-jiken saiwoyi babu irin wanda ba’a mun a rugar mu amma ciwo kullum kaman ana kara iza shi, sai dai a kwantar a tayar. Cikin wannan halin Allah ya aikowa rugar mu farin rashin ruwa, tumaki da shanun mu suka shiga mutuwa, gonaki da koramun mu suka bushe kyamas, hatta ciyayin mu da shanu ke ci sun bushe kyamas kamar ba’a taba amfana da su ba, wanda hakan ya kara taimakawa wajen kashe dabbobin. Aka dage da Addu’ar rokon ruwa ko ma fita daga wanan masifa sai Allah ya aiko da wani irin kakkarfan ruwan sama hade da cida mai karfin gaske. Ya yaye bukkokin mu, ya kashe tsoffi da marassa karfin cikin mu, ya tafi da kayan amfaninmu, marassa karfi ciki har da Yafendo na da mahaifiyata! Baffana kuwa garin gudu yumbu ya tade shi ya fadi ko shurawa bai yi ba. Ni da kanwata Hajjo kadai muka kubuta, inda Hajjo ta goye ni, tana gudu da ni, Hajjo ta sha faduwa tana tashi duk gwiwoyinta sun kwaile, hawaye take cikin ruwan tamkar wadda ake zarewa ciwo har ta fiddo mu bakin titi. Ni kam ban san ma me ake ba don tuni na suma. A nan bakin titin da zai kai ka gidan Hakimin Shanono mutane suka gan mu, aka je a ka gayawa Hakimi, yasa aka dauko mu, ni aka kai ni asibiti, Hajjo kuma ta rakasu rugar mu washegari suka ga inda Allah ke ikon sa, har ruwa da cabi ya rufe wasu, tumaki da shanun mu mafi yawa sun mutu, kalilan sun tsere, aka dauko gawar mamatan aka yi masu suttura aka kaisu gidan su na gaskiya. Hakimi ya cigaba da kula da lafiyata a asibiti Hajjo kuma na tare da ni, bata iya barci bata rungume ni ba mun yi barcin tare, tana wanke mun jikki tana kuka tana kiran Innar mu, domin Hajjo yarinya ce karama ‘yar kimanin shekaru goma sha biyu a lokacin, a yayin da ni kuma na ke da sha biyar, kin san girman jeji akwai karfi shi yasa har ta iya ta goye ni zuwa waje mai nisa haka. Wata na guda a asibiti ina jinya kamin in sami kaina. Hakimi ya tausaya mana kwarai da gaske yace mu zauna nan a gidan sa har zuwa sanda Allah zai bamu mazaje yayi mana aure. Kwamfa, matan Hakimi hudu suka ce dawa Allah ya hada su ba da mu ba? Haka kawai zai dauko ‘yan mata tsala-tala ya aje masu to zaman me za mu yi banda muyi masu bauta? Daga ranar duk uban girkin gidan Hakimi mu muke yinsa safe, rana da dare. Shara, wanke-wanke ke har wankin kayan su dana ‘ya’yan su, surfen masara da dawa da tatar koko kuwa wannan kananan ayyukan ne. Cikin wata guda kacal sai ga kanta ribda-ribda a hannun Hajjo cikin farar tsokar hannun ta sabida surfe. Farin mu ya dushe sai idandunan da karan hancin kadai. Suttura sai in yaran su sun yar mu ke samu mu dauka mu saka. Hajjo da wuya ta isheta ta ce mu gudu, mu tsirar da kuruciyar mu. Nace da ita darajar bawan Allahn nan Hakimi zata diba, ya dauke mu kamar ‘ya’yan cikin sa duk wata kulawa da ta dace uba na kwarai ya yiwa ‘ya’yan sa Hakimi yana yi mana, duk abinda ake mana cikin gidan bai sani ba. Ni kuwa dama tuntuni Allah bai daura min yawan magana ba balle tsegumin da har zan yi tunanin gaya mashi, wannan sai Hajjo, to amma ita ma surutun nata na tsoron Inna Kwaire, haka muke wuni ba mu ce da kowa ko ‘umhâ€? illa in sun ce mu zo mu yi masu kaza mu tashi jiki na rawa mu yi masu don mu kwana lafiya. Hakanan nace da ita. “Hajjo in mun gudu ina zamu? Mun san irin hannun da zamu fada a gaba? Kada ki guji mutanen da kika taras da farko domin irin su ne zaki taras a gabaâ€?. Shekarun mu biyu a gidan Hakimi muna bauta. Ba zan taba mancewa da ranar da Basheer kanin Hakimi ya dawo daga jami’ar Nsukka inda ya ke karatu ba. Basheer shakikin Hakimi ne da Hakimi ya rike tun yana karami bayan rasuwar iyayen su. A nan garin yayi firamare ya ci makarantar kwana ta FGC da ke Kano ya je ya kammala da sakamako mai ban mamaki. Hakimi ya danka mai gadon iyayen su da ke hannun shi ya ce ya je yayi ta karatun har ya gaji sabida hazakar shi. Tun da Basheer ya wulwula kudu ba’a kara jin duriyar shi ba sai ranar nan. Gabadayan karatun Basheer yayi shi ne a kan (Diplomacy), tun da ya bar Shanono bai dawo ba sai ranar da ya hado digirin shi na biyu, ya watsa takardun neman aiki a (Nigerian–Embassy) na kasashe har ukku sabida International Studies ya danganci aiki da kasashen ketare ne. Ranar kwatsam sai ga Bashir, ‘ya’yan Hakimi da matan shi duka suka debi murna babu babba ba yaro kowa baki a washe har muma da ba’a san da mu ba muna ta dariya, kasancewar Bashir mai faram-faram da barkwanci kowa son shi ya ke a gidan. Ban taba ganin Hakimi na far’a, irin wadda ya rika yi a ranar da Bashir ya dawo ba. Rannan ina shara Bashir ya zo wucewa dakin amaryar Hakimi, ban ga tahowarsa ba na sharo mai sharar da na sharo a kafa cikin wasa yace, “ke ‘yar fillo, ba kya gani ne? Koda yake na gane wayonki, don in rasa mata ne, to ai ni kyakkyawa ne a Nsukka kar kiso kiga yadda ‘yammata ke bibiya na, ni nan da kike gani ‘yammata jaka-jaka gare niâ€?. Hajjo da ke gefe tana wanke-wanke ta ce “ka yi hankuri, bata sani ba neâ€?. Ya kai duban shi gareta domin da fari bai lura da kasancewarta wurin ba, sannan ya dube ni, a kidime yace “ikon Allah, ke Hussainarta ce ko, koko ‘identical twinsâ€? kuke?â€? Duk sai muka yi murmushi a tare, kumatunan mu suka lollotsa gwanin sha’awa. Bishir ya bushe a tsaye, yace “ku ‘ya’yan makota ne?â€? Hajjo da ya ke Allah ya zuba mata magana, a komai ma da ba’a tambaye ta ba balle wannan mai dalili? Wani zubin surutu har tsunkulin ta yake, ko ni aka tambaya abu in har tana wurin ita ke aran baki na ta ci mun albasa, tayi narai-narai da ido ta rausayar da kai gefe ta ce , “ai mu marayu ne, Uwa da Uban mu duk sun mutu, ruwa ya tafi da Yafendon mu, Baffan mu kuwa garin gudu yumbu ya kayar shi ko shurawa bai yi ba…â€? sai ta koma kukan da ta ke kwana da wuni ta na yi. Bashir ya matsa gare ta ya russuna a gaban ta cike da tausayi yace “ayya kanwata! Duk wani mai rai mamaci ne, muma nan duk zaman jiran ta muke. Nima Bashir tamkar ku din nake, har gara ku kun san Innar ku har kun yi rayuwa mai dadi tare da ita, ni ko tana haifana ko fuskana bata gani ba ta tafi ta bar ni. Bani da kowa a fadin duniyar nan sai Allah, sai Yaya na, amma ba na kuka, don haka kema ki daina kuka. Daga yau na zame maku Yaya, kin ji?â€? Hajjo ta gyada kai alamun ta ji abinda ya ce. Ya sanya hannu cikin aljihu ya fiddo hankici fari sol da shi ya mika mata yace â€? share hawayen ki maza-maza, zani cikin gida yanzu zan dawoâ€?. A wurin uwar gida Kwaire ya nemi jin labarin mu tace “haka kawai ya je ya kwaso mana masifa rana tsaka, don sun gudo daga daji, ka gansu nan in ban da bauta ba abinda suke mana, kaima in kayan ka sun yi datti, ka dinga dankara masu har gugar takalmi daga yau kar ka kara yi, tsuntsu ne Allah ya kawo mana daga sama gasashsheâ€?. Da Hakimi ya shigo gidan bayan sallar lisha Bishir ya ke tambaye shi labarin mu. Hakimi ya kwashe komi ya gaya mishi har ciwon da nayi kamar ba zan rayu ba. Ya kare da cewa “ni kam don Allah ni ke rike da yaran nan, na kuma san sakamako na na gareshi. Duk ma mai cutar su cikin mata na ai ita da Allah, Allah yana kyale hakkin maraya ne?â€? Sai da Bashir ya fiddo hawaye don tausayin mu ya kuma ce da Hakimi zai aure ni koda bamu da iyaye balle muna da su. Hakimi ya sa mai albarka mai yawa amma sai ya ce tunda shi saurayi ne ya auri Hajjo ita ce budurwa, amma ni na gaya mishi na taba aure har na haihu mijin ne ya mutu aka kuma sace diyar. Bishir yace shi ba budurwa ta dame shi ba, hakannan tun da ya ganni ya ji bai iya rayuwa ba tare da ni ba, Hajjo kuwa zai rike yadda zai rike diyar cikin shi har zuwa sanda itama Allah zai bata miji ya yi mata aure. Ya roki Hakimi da ya bar sirrin nan a tsakanin su ko muma kada ya bari mu ji bare matan shi da ke kin mu tamkar mutuwar su, har zuwa sanda takardun shi na aiki zasu fito, kamin nan yana so ya ja ra’ayinmu mu saba da shi musamman ni da ya ga ko magana bana yi da kowa. Shima Hakimin tunanin shi yayi dai-dai da na dan uwan shi, ya kara karfafa shi da cewa abin da yayi jihadi yayi, da sannu zai ga budi da nasara cikin rayuwar shi. Don duk wanda ya taimaki wani babu shakka Allah zai taimakeshi. Yayi masa Addu’ar samun aiki mai tsoka wanda zai tallafe mu har mutuwa ba tare da gazawa ba, ya kuma kara tunatar da shi hakika yayi riko da sunnah, domin Manzo mai tsira da aminci ma ya fara ne da auren Nana Khadijah a lokacin tana bazawara, ta ma girme mishi nesa ba kusa ba. Kuma mata irin Dije sai wanda Allah ya nufa da samun rahmar aure domin daga halaye, dabi’u zuwa surar ta duka babu mummuna, ta kowanne fanni ma na fi ‘yar uwata nutsuwa. Tun daga ranar Bashir bai barin mu mu yi wani aiki mai wuya sai ya amsa ya yi. In wanke-wanke ne sai dai ya wanke mu dauraye haka in surfe ne sai dai ya surfa mu tankade, in kuwa wankin kayan su ne sai dai ya saba mu dauraye mu shanya. Ga shi da raha kullum cikin sa Hajjo dariya ya ke don ni da wuya duk ban dariyar sa ya ga hakorana. Rannan ya ce da Hajjo mai yasa ni bana dariya ne? Hajjo yadda suka saba da Bishir komi fada mai take bata boye mishi komi da ya shafe mu, haka kawai zan ji tana bashi labarin yadda muke rayuwa a ruga tare da Innar mu. Rannan ma ji nayi tana koya mai yadda ake tatsa harda cewa “Kawu na, Saniya fa sai da shafa a ke tatsar ta.â€? Ya tintsire da dariya ya ce, “kenan nima Hajjo sai da sannu zan samu So daga Yayar ki?â€? Ta ce “meye so kuma Kawu na?â€? Ya daura hannun sa bisa kirjin sa ya lumshe ido yace “So, is a feeling for deep affection, a bery strong feeling of affection…â€? ta yi sukutiii…â€? tana sauraron shi da dukkan hankalinta da iyakar fahimtar ta, tace “magana kake ko yare?â€? Yace “tunda baki ji ba shikenanâ€?. To a yau ma sai ta gyara zama, ta kalmashe ‘yan kafafunta kyawawan idanuwanta cikin na Bashir, na tabbatar wani babban sirrin zata kwaye masa, da haushi ya isheni sai na kai mata mangara da hauri da kafa, Bashir ya yi hamzarin rike hannuwana duk sai naji jikina ya yi sanyi, yayi saurin saki na ya dube ni cikin ido, wata irin kunya ta lillibe ni, wani abu ya daki kahon zuciya ta irin wanda ban taba ji ba nayi saurin sadda kai, yace “ko da wasa, kada ki sake dakar min kanwa ko bana nan ban yafe ba, Hajjo na gaya mun, mai yasa Hadizah bata dariya?â€?(Don shi bai taba cewa Dije ba, ita ma Hajjo ya hana ta har ta saba da fadin Haddizar), ta dube ni tayi murmushi kana ta maida duban ta ga Bashir, ta kalmashe ‘yan idanun ta tace. “Kana ji ba? Can-can an mata aure, an sata a lalle ta je gidan miji, ta haifo sankaceciyar jaririya, hancin ta irin wannan (sai ta ja nata), bakin ta irin wannan (sai ta ja nawa), gashin ta curi guda. Sai barayi suka lalabo cikin dare suka dauke ta suka ranta a na kare…â€? (tana yi tana gwada irin gudun da barayin suka rika yi da ‘yan yatsunta). “Tun daga ranar bata kara yin dariya ba, sai ciwo, ta yi ta ciwo kaman ta mutu, ka san kowa yana son dan sa Kawu na, kamar yadda Innar mu ke son mu, tamkar yadda Addar nan gidan ta ke son Salisun ta muku ta ke zagin mu. Rannan tace mun watakila ‘yar ta ta mutu yanzu tunda ba wanda zai ke bata nono…â€?. Bashir yayi shiru ya juyar da kai, bai son su ga hawaye ya ke fitaswa. Ya sa hankici ya dauke hawayen idanun shi da suka kada suka yi jazur kamar gauta, shi kan sa bai san ya akai ya baro wannan maganar ba. “Hadizah, Insha Allah za mu ga ‘yar ki Fatimah, mu hada da wadanda zamu haifa a gaba mu sa su a makaranta, suyi karatu irin nawa. Mu mun rasa soyayyar iyaye tun muna kankana, amma su Insha Allah zamu rungume su da dukkan so da dukkan kauna har zuwa ran da muka daina numfashiâ€?. Sai ya tashi ya fice. Matan Hakimi fa suka maida idanun su kan Bashir da duk wani takun shi cikin gidan. Wasu cikin su suka ce dakin mu yake zuwa cikin dare yana lalata da mu shiyasa ya tare a gindin mu, wasu suka ce a’ah, ai har da ranar ma abinda muke yi kenan cikin daki. Rannan har yana gayawa Inna Kwaire magana don ta ce da Hajjo tsintacciyar mage, yace da ita sanda Yayan shi ya aureta, aka dauko farin kyallen da ake shimfidawa amare fari kwal aka same shi, don haka gara Hajjo da aka tsinto daga daji ta san mutuncin kanta, itako da aka tsinto gaban iyayen nata ai basu ga mutuncin ba. Ai kuwa a ranar data kama Hajjo da duka sai da ta targada ta. Da Bashir yaga abin nasu bana kare bane sai ya zuciya, ya sami Yayan shi yace ya ja ma matan shi kunne ko dukkansu yayi masu dan banzan duka. Hakimi yayi murmushi yace yanzu kai Bashir, in aka kyale ka sai ka daki matan aure da ‘ya’yan su da jikoki da surukan su suna kallon ka?â€? Ya ce “to sabida Allah ina ruwan su da yaran nan ne don Allah tun da dai ba zaman su suke ba koko akan su suke zanne?â€? Hakimi yace “in kana son komi ya zo karshe, gobe a daura auren ku da Dije, ku zauna anan dakin da suke har zuwa ranar da Allah zai yiwa aikin fitowaâ€?. Bashir ya amince. A ranar ne kuma ya samu sakon kiran (Intrebiew) daga Abuja ana kiran su a safiyar washegari, ya gayawa Hakimi kar a fasa daurin aure amma shi za shi Abuja ya san maganar aikin ne. Karfe goma na safe Hakimi da Liman suka daura aure na da Bashir akan sadaki naira dubu biyar. Duk wasu kayan lefe da ke yiwa ‘yar gata a garin Shanono Hakimi yayi mun ni da ‘yar uwata. Har gobe, bani da abinda zan ce da Kawun nan naku Hunainah, domin yayi mun abinda ko mahaifana da suka haife ni iyakacin abinda za su yi mun kenan. Babban alkhairin sa gare ni shine da ya hada ni da miji irin Bashir, daya zamo jigo ga rayuwata, bango abin jingina ta kuma abin alfahari na. Don haka har kullum bana tashi daga inda nai Sallah ban nema masa rahma da gafarar Ubangiji ba. Sati na zagayowa sai ga Bashir cikin farin cikin da ba zai misaltu ba tare da wani abokin sa Hassan cikin motar Hassan din. Yana gaida kowa shi da Hassan suka shigo dakin mu, Bashir ko kulawa da su Hajjo da Hassan bai yi ba ya sure ni ya shiga juyi da ni a tsakar dakin. Hajjo ta ja mayafinta ta rufe ido tana laluben bango tana cewa “bako-bako boye ni, kada Kawu na yace na yi rashin kunyaâ€? ta shige cikin babbar rigar Hassan gabadaya suka sa dariya. Bashir yace “Khadijah tabbas ke alkhairi ce a gare ni, kamar yadda takwarar ki Nanah Khadijah ta zamo alkhairi ga Manzon mu?â€? Bashir bai taba tsayawa tambaya na ina son shi ko bana son shi? Abin da ya sani shine in har sai ya san wannnan za mu yi aure, ashe kuwa zamu mutu ba mu yi ba. Tunda dai ina bashi girma ina kuma tsananin jin kunyar sa, yasan alamun so kenan a wancan zamanin. Ya samu Hakimi ya gaya mishi sati mai zuwa zamu tashi zuwa kasar Faransa in da zai fara aiki da ofishin jakadancin mu na kasar. A ranar da aka kira su Abuja aka danka mai takardun shi na daukar aiki shi da Hassan babban aminin shi da wasu abokan karatun su da dama. Ya tsaya ne shirin ‘pass-portâ€? da bisar mu ne ni da shi da Hajjo. Hakimi ya sa wa abun albarka, ya kuma kara dankawa Bashir amanar mu, yace ya ke tunawa a kullum bamu da kowa, Allah shine gatan mu sai ko shi, Basheer. How much do you like this story? 5/8/22, 09:59 - Ummi Tandama😇: ______________________________ *âœðŸ? SIRADIN RAYUWAâœðŸ?* Book two *@Takori* Page8ï¸âƒ£ Da ranar tafiyar mu tazo ni kam sabanin ‘ya’yan gata da ake rakasu da nasiha da Addu’a ni da zagi da gori da habaici ‘ya’yan Hakimi da matan shi suka raka ni wai mu mayu ne, mun lashe kurwar Bashir da ta Hakimi to su kurwarsu ta fi karfin kankarar mu. Hajjo yarinyace ba hankali ga maida martani inda duk aka tsokalo ta sai ta yi masu gwalo da zata shiga motar Hassan ta ce, “Alalalo! Zamu shiga jirgi dai ba ke Inna Kwaireâ€?. Daga Bashir har Hassan dariya su ka yi, ni ko har muka zo Abuja kuka na ke na tunanin iyayen mu da batacciyar jaririya ta. A filin jirgin saman Abuja muka kwana tsimayen jirgi mai zuwa France ana ta cike-ciken takardu, da asuba muka bi jirgi ‘directâ€? (kai tsaye) zuwa babban birnin Paris. Gidan da muka zauna yana nan a jerin gidajen ma’aikatan jakadanci na kasar. Ba anguwa daya muke da Hassan ba don shi yana cikin gidajen ma’aikatarsu ne amma kullum ya taso aiki gidan mu zai yada zango su ci abincin rana tare da Bashir har dare. Shakuwa mai tsanani ke shigar su shi da Hajjo. Da girman Hajjo da komi Bashir ya dauketa ya dankara a aji daya. Hajjo ta sha tsiya wurin ‘ya’yan Faransawannan don tace mun har kungiya-kungiya suke yi zuwa kallon ta (katuwa a aji daya) ga wani sunan shakiyanci da suka lika mata (Mère) watau Mamar su kenan. A rayuwata ban taba halartar makarantar boko ba, amma na yi karatun Addini mai yawa a wurin Baffan mu sanda ya ke da rai. Sai Bashir ya kashe muhimmin lokacin sa yana koyar da ni karatu da rubutu haka Hajjo komi ta koyo haka zata zo ta yi ta koya mun Bashir na aiki ya koma karo karatu (PhD) babbar Jami’ar Faransa yana kara zurfafa ilimin sa. Shekara na zagayowa na haife ki Hidayah, asalin sunan ki Rahmah, sunan mahaifiyar Bashir ne kika ci, Hajjo ne ta sa maki Hidayah to sai muma din muka kama. A shekarar Bashir ya halarci kwasa-kwasai da dama a kasashe daban-daban, da ta kai har a ka yi mai karin girma daga matsayin da ya ke da shi a wajen aikin su zuwa (Consultant) na kasar Nijeriya a Faransa. Hassan bai taba furta mana son Hajjo yake ba har ta kare makaranta, kwazon ta da basirar ta yasa Bashir yayi cuku-cukun da ya nema mata aji biyu na karamar sakandire ta kuma lashe gwajin duk da suka yi mata tas. Sai da ta kai aji hudu a sakandire ne Hassan ya fito karara ya gaya mana shi fa kamun Hajjo ya ke. Daga ni har Bashir mun yi matukar farin-ciki ko da yake dama tuni mun dago shi, bini-bini kaji shi yana “kanwata, me ya hada ki da wancan karmasashshen Bafaranshen? Ke fa yarinya ce har yanzu, baki isa yin abuta da maza ba. Babban farin-ciki na shine na kasancewar Hassan 100% ya cika kamilin mutum dan babban gida a jihar Borno, don mahaifin shi sanannen malamin Addini ne, duk da zaman shegiyar kasa irin France, ya canza wasu daga kyawawan dabi’un shi duk da hakan ni da Bashir ba mu ji ko dar na wanke Hajjo mu ba shi auren ta ba tun kamin kammala karatun ta na sakandire don mun san Hajjo na da wayo dole ta canza Hassan, barin ma yanzun da kanta ya bude da rayuwar turai. Idan kin gan mu a lokacin zaki rantse bamu san wata aba miyar kuka da kalkashi ba don gabadaya sajewa muke da mutanen kasar, duka harshen mu ya juye da Faransanci zallah sai ma Bashir da ya ke baki shi ke tona mu, amma ko Hassan fari ne sol. Ranar da nayi haihuwata ta uku a duniya wato ke Hunainah, ranar ne Bashir ya kammala Ph D din sa in da muka kara samun ‘promotionâ€?. Mun dawo gida anyi gagarumin auren Hassan da Hajjo a garin Biu ta jihar Borno da Shanono ta jihar Kano, biki irin wanda ba’a taba yi a Shanono ba. Bashir Uban amarya kuma babban aminin ango an ba Naira kashi haka Hassan, sun nuna basu da abin so da kauna kamar kanwar su Hajjo. To ni ma komawa na yi kamar sarauniya wurin matan Hakimi ko numfashi ji suke kaman su min. ‘Ya’ya na kuwa ko makota basa bari su dauke su wai kar su shafa masu datti, ni ko na balle bakin jaka na kara jike su da ‘yan yanzu, ai sai na kara zama kamar kwan da kaza ta nasa yanzu-yanzunnan, ko motsi nayi a ce “Hajiya Hadiza, me kike so?â€? An sa Hajjo a lalle akayi sunan Baby, inda Bashir ya wanken dattin rai na ya mayar mun da sunan Innar mu (Hannatu), ke Hannatu Baban ki ke kiran ki Hunainah har yau din da ta bi ki. Bakar fatar Bashir da farar fata na ya mai da ku kalar coffee mai haske da har ake maku kallon ruwa-biyu, ya kuma sanya ‘nationalityâ€? din ku ‘in doubtâ€? (cikin shakku) bayan a zahiri gaba da baya ku Fulfulde ne ziryan. Da Hajjo ta kare sakandire suka zo Borno gaida Abban su Hassan da baya da lafiya, ai kuwa fir ya hana Hassan komawa aiki France kasancewar shi babba a gidan su kuma shi kadai ne da namiji. Duk kannin shi mata ne a gidan auren su ga tsufa mai wahala da ya kamashi. To Hassan da Hajjo ke ma kin san takaici ba sai an fada ba wai an katse masu rayuwa. A nan Maiduguri Hassan ya sayi kankareren gida na garari suka tare, inda Hajjo aka rufe bakin mahaifa kif aka afka Unimaid inda ta ke karatun (linguistic) harshen Faransa da Barbarci ziryan. Daga baya ne aiki ya cilla su Lagos inda Hassan ke aiki da ma’aikatar ilmi ta kasa wato Federal Ministry of Education. Shekarun ki Hidayah shidda, Hunainah biyar aka yi wa Baban ku Ambasada a kasar Russia, bamu dade ba aka canza shi zuwa Jordan inda a nan ne kuka kare firamare. Muna da shekaru uku a nan Allah ya yi wa Ambasadan kasar Nigeria a Saudiyyah rasuwa, aka sake yi mana (transfer) na wucin gadi zuwa Saudi-Arabia kafin a fidda sabon Ambassada, inda muka zauna a birnin Riyadh. Aka kai ku makarantar sakandire ta kwana. Ba zan manta ba, ba kuma zan taba mancewa ba, a dan tsukin na yi ta mafarke-mafarken wai na ga jaririya ta da aka sace. Kuka zo hutun ku na farko a aji daya da kawar ku idan baku mantaba, yau shekaru biyar kenan da faruwar al’amarin da har yau yake damuna a rai domin na tabbata wallahi Fatimah diyata na ganiâ€?. Hajiya Hadizah ta yi shiru hawaye na bulbular mata, jikin ta ya hau rawa. Hidayah da Hunainah, da suka yi jigum suna sauraron ta da dukkan hankalin su, suka juya suka dubi juna a gigice, cikin tsananin mamaki da ta’ajjibi mara misaltuwa suka hada baki, wanda su kan su basu san su yi ba suka ce “Saratu Bello Makarfi???â€? Dubawar nan da za su yi Mamarsu numfashi dai-dai ta ke fitar wa ba kuma ta ko iya shaida wanda ke kanta alamun hawan jinin ta ya tashi kenan. Hidayah ta fashe da kuka tace “Mamar mu don Allah kar ki mutu ki bar mu, Mamar in kin mutu ya za mu yi?â€? Karamar wato Hunainah ita ta yi hankalin kiran mahaifin su, masu aikin gidan mata suka taimaka wurin sanya ta a mota aka nufi asibitin da suke zuwa da ita. A daren nan Ambasada da yaran shi ba su rintsa ba, suka kwashe labarin data basu kaf suka gaya mishi, shi kansa ba karamin girgiza yayi ba yace idan yarinyar na makarantar ku ta Riyadh har yanzu, mai zai hana mu je mu neme ta? Idan har hakan zai dawon da farin-cikin Hadizah? Kawanaki uku bayan nan jirgin safe ne ya sauke su a birnin Riyadh, garin da rabon su da shi shekaru biyar kenan cif. Motar musamman aka tura ma Ambasadan daga Saudi-Embassy ta kwashe su zuwa Kingston College. Su Hidayah sun ga makarantar su ta da ta samu sauye-sauye ta fannoni da dama musamman ta fuskar cigaba, hatta ‘principalâ€? din da suka sani a da ba ita bace yanzun an canza a an kawo wata daga Asia maimakon Ayyush Siddiky da suka sani mutuniyar Madina. Ita bata san ma yarinyar da su ke nema ba ta dai hada su da wani tsohon malami, malamin shine Sayyid-Ridhwan mai kula da shige da ficen dalibai ya kuma dade yana aiki a nan. Ga abinda yace da su, “ayya! Yarinya mai hazaka irin Sarah, ban san maiyasa iyayaenta suka katse mata karatu ba a shekararta ta karshe. Inda duk kuka ganta ku baiwa iyayenta shawara su maido mana ita koda basu da ko sisin kobo ne, domin Saratou ‘yar baiwa ceâ€?. Daga Ambasadan har ‘ya’yan shi ji suka yi kamar su daura hannu a ka su rafsa ihu, Hunainah bata san sanda hawaye ya ziraro mata ba tasa hannu ta share. Su kanyi tunanin kaunar da sukewa Saratu Bello, a sanda suke makaranta, sun dauka kauna ce kurum ta haduwar jini daga Indallahi, da kuma ‘kualitiesâ€? na ita Saratun da ke sawa kowa ke sonta a (Kingston), to ashe Saratu jinin su ke gauraye dana juna shiyasa suke jinta har kasusuwa da bargon jikin su, barin yanzun kuma da suka ji wai ashe diyar Maman su ce? Ba abinda ke damun su kamar lafiyar mahaifiyar su da ke ta walagigi, tayi-bata yi ba Allah masani. A gidan saukar bakin da aka yiwa ambasadan masauki cikin su ba wanda ya rintsa, kowanne abinda ya ke sakawa daban ne dana dan uwansa, zuciyar kowannen su cike take da alhini da taraddadi. Hidayah dake kwance cikin kilishi tana kallon sama sai ta mike a gaggauce ta takarkare kamar gyare ta shiga jerawa ‘yar uwarta kira, duk ta rude sai rawa jikin ta yake kamar mazari. A gigice uban da ‘yar suka sauko daga bene inda garin sauka Hunainah ta sulmiyo daga matakala ta biyar amma bata kula ba ta gyagije ta mike, don sun dauka wani mugun abu ne ya faru da ita, a tare suke tambayar ta “lafiya?â€? Tayi wata irin ajiyar zuciya kamar an ce ga Saratu a gaban su ta rungume ‘yar uwar ta tace “na tuna ne Daddy, Saratu ta taba gaya mana ita da iyayenta suna zaune ne a Lagos, kuma nan anguwar su Aunty Hajjoâ€? Hunainah ta ce, “kwarai anyi haka nima Daddy mantawa na yi.â€? Ambasada Bashir sambo, bai yi barci ba a ranar sai da yayi masu ‘bookingâ€? din tikiti na jirgi mai zuwa Lagos din Nigeria a washegari. A yau kam sun samu sunyi barci cikin natsuwa har da minshari, sun tabbata wahalar da Mamar su ke ciki ta yanke daga yau tunda kuwa za su kawo mata Saratun ta har asibiti. (Anya kuwa?) Dawowar Hajjo kenan daga Ajaokuta inda take bautar kasa, ta tadda baki ba zato ba tsammani amma ba tare da Uwar su ba. Hajjo uwar ‘ya’ya ukku biyu maza da ‘yar auta mace, tuni ta hau tsallen murna kaman yarinya karama don har girman Hajjon bata bar wautarta ta kuruciya ba. Hassan ya je Maiduguri gabatar da wani aiki a ranar take tsammanin shi. To amma me? Daga uban har ‘ya’yan fuska babu annuri, duk ta bi ta tsargu, abinda ta kawo ma ranta kawai Yayar ta ta rasu wajen haihuwa dan tuni ta san tana da ciki, tun bata nemi bayani ba ta soma kuka tace “yanzu shikenan ni daya na rage a duniyar Kawu Bashir?â€? Duka sai ta basu dariya, daga kawun har ‘ya’yan sai da suka murmusa. Hakika Hajjo na kaunar Yayar ta fiye da kowa a duniya bata hada matsalar ta da ta kowa “a’ah Hajjo, Hadizah ta dage taga diyar ta Fatimah a Riyadh, shine muka zo mu bincika, don yarinyar wai ta taba gayawa su Hidayah a Lagos gidan su yake kuma a nan Bictoria Islandâ€? ta dafe kirji tace “anya? Yanzu haka ‘yar farar yarinya zata gani tace ‘yar ta ce, tunda tasa abun a ranta har ya dameta, ta jawo mana rikici da mutane ana zaune lafiya. In banda neman tada zauna tsaye ma irin na Ya Hadizah, ta yaya ‘yar data bata a kauye za’a ce an ganta a babban birni irin Riyadh?â€? Yace “Uwa ce, kada ki musa mata?â€? Hidayah tace “kuma dai Anti Hajjo kin san babu inda Allah baya ikon sa. KUN-FA-YA-KUN ne fa, wanda in yace ‘kasanceâ€? sai ya kasance. To in banda iko da kudurar tasa ta yaya kuma kuka tsinci kanku a France daga kauye ko ruga kamar yadda Mama ta bamu labari? Wallahi ni kaina daga ganin da naiwa Saratu da farko na san jinin Mamar mu ce, ko ke kika ganta za ki yi mamaki, in banda haske da ta fi Mama, da digon tawadar Allah dake gefen hancinta ba abunda ba irin naku bane a jikin ta sai ko ‘beauty-pointâ€? da bata da shi irin naku, ko yau kika ga Saratun wallahi sai kin dangantata da Mamar mu. A yadda na ji ta cikin raina a sanda na fara ganin ta, babu banbanci da yadda nake jin Hunainahâ€?. Maganar yarinyar ya ratsata kwarai, ta dage kai sama kamar mai irga ‘ya’yan taurari tace “shin ya sunan mahaifin ta?â€? Hunainah tace “Baba Makarfi ne ko Bello I’m confused?â€? Hidayah tace “Bello Makarfi, exactly sunan kenanâ€?. Hajjo ta dafe kirji, ta mike ta soma safa da marwa a kayataccen falon ta, bakinta na mai kakabin sunan da ya karade talbijin da rediyoyin gida Nijeriya tace “Bello Makarfi, kuna nufin Brigadier Bello Makarfi? Dan takarar kujerar shugaban kasar nan da suka shirya juyin mulki a shekarar baya? Ya zauna ne a wancan gidan dake kallon nawa, a sanina baya da wata diya mace, duk ‘ya’yan sa maza ne su goma cif, in ma ya haifa ban taba ganin ta ba, amma na san manyan ‘ya’yan sa su Faisal da Najib, don na kan gansu sun wuce a mota ko kuma tsaye a harabar gidan sai dai ko gaisawa bamu taba yi ba, a bakin Hassan ma na ji sunan su. Mutane ne ‘unsocialâ€? watau wadanda basa shiga shirgin kowa. Ba zan karyata ku ba tunda ban san gaibu ba amma Makarfi yana kulle tun bara, don haka kuzo muje gidan Bello Makarfi. In Allah yasa Fatimar mu ce zan ganeâ€? “ta yaya?â€? Ta juyo ta dube shi tana murmushi “jini baya boyuwa Baban su Hunainah. Yaya ta sha gaya mun a ranar da aka sace Fatimah, Baban ta ya tsaga mata biyu-biyu a tsakiyar kirjin ta na family din shi. Hakannan Fatimah nada tawwadar Allah a gefen hancinta da diga-digan ta tun tana jaririyaâ€? Bashir ko magana baya iya yi, ta sake yin murmushi. “In kuma duka wannan bai yiwu ba, akwai shari’ah, akwai kuma likita mai auna jini, balle ma nasan ba yadda za’ai su ce ‘yar su ce in dai da gaske tsintar ta su kai iyayen ta kuma suka gantaâ€?. Hidayah da Hunainah duk sun yi tsit ne kamar ruwa ya cinye su. ‘Yar dan takarar shugaban kasa? Kada su je a harbe masu Aunty da Daddy in sun ce Saratu ‘yar su ce. Saratou ta sha gaya masu yadda iyayen ta da Yayyun ta maza ke son ta kasancewar ita kadai ce mace a cikin ‘yan uwan ta maza goma ris! Rana daya su kawo masu wannan magana mai rikitarwa? Ita kuwa Hunainah sabanin tunanin ‘yar uwar ta ne. Ita tunanin da ta ke shin wace irin runguma zata yiwa Saratu a yau a matsayin ta na shakikiyarta ta jini? Ta sha kimanta nedt haduwarta da Saratu Bello by destiny or phenomenaâ€?., (cikin wata kudura da irada na Ubangiji) tun bayan rabuwar su a Kingston. Da da ne, a guje zata ruga ta rungumeta amma yau har bata san irin wadda ya dace ta yi mata ba. Gidan da ta nuna masu kadai tace nan ne gidan Makarfi ya firgita su don ko a turai da U.A.E da suke zagawa samun mai irin wannan mahaukacin ginin kaman ba za’a mutu ba sai an tona. Baban su bai biyo su ba tukunna yana can masaukin sa don haka Hajjo tasa ‘ya’yan ta biyu a gaba suka doshi gidan Brigadier Bello Makarfi. Rashin sa’a! Lallai ya tabbata gare su, ‘what was eben more unfortunate (babbar rashin sa’ar ma) get din gidan a garkame ya ke da wani irin azababben kwado, shi kansa kwadon yayi kura futuk tabbacin yayi shekaru biyu a hakan. Kafafuwan su sun sage, yawun bakin su ya kafe kat, tunanin su ya kare haka dabara ta kare masu. Shin me kuma za su yi su ceci rayuwar mahaifiyar su? Wani kabila ne ya shawo giyar shi yayi tatul yana tafe yana tambele kamar ya kife, daya zo gabansu sai ya ja birki, ya dakata ya zaro ido yace “wowâ€?, gorgeous!â€? wato kyawawan yara. Ya dubi Hajjo yana washe baki ya sake cewa “Madame, will u dash me dat rose Babe, plz?â€? Ya nuna Hunainah, wadda idon ta yai jage-jage da hawaye ta manna mai harara. How much do you like this story? 5/8/22, 21:04 - Ummi Tandama😇: ____________________________ *âœðŸ? SIRADIN RAYUWAâœðŸ?* Book two *@Takori* Page9ï¸âƒ£ Abuja, Ranar Litinin Karfe Hudu Da Rabi Na Yamma Intisar ta tashi da matsananciyar damuwar da bata san ko ta mece ce ba a safiyar yau Litinin. Wani irin kunci ke damun ta a zucci da bata san ko na mene ba kamar koyaushe wani sabon al’amari zai faru da ita mai dadi ne ko mara dadi? Ta rasa meke damun ta kwata-kwata, don haka ne ma ta langabe a gado tun safe har yamma ko falon su bata leko ba, bata ko so Anti Saratu ta ganta, don ta san muddin ta ganta cikin wannan halin to ita da kwanciyar hankali sun yi hannun riga kenan. A lokacin ita kuma Antin cike take da farin-cikinn samun ‘appointmentâ€? da ‘Afribank,â€? don haka ne ma tun safe bata nemi Intisar din ba tana ta aikin takardun neman akinta, sai da ta gama tas ta ankara da rashin Intisar din a falon tun bayan da ta karya kumallo. Tasa murya daga falon tace “Saratu!â€? Ta yi doguwar mika gami da dan tsaki cike da jin zafi, amma ba da Antin take ba, na damuwar da ta cuzguna rarraunar zuciyarta ne, ta mutstsike ido gami da tattare curarren gashin kanta cikin bakin ‘hair-boundâ€? ta zura kyawawan kafafun ta cikin farin takalmin bakin gado (bed-side shoe), ta murda marikin kofar dakin cikin matsananciyar kasala ta fito ta tadda Antin, saye da doguwar riga ruwan makuba mai hade da hula, amma bata sanya hular a kanta ba. Ta dube ta cike da murmushi irin wanda rabon da ta ganta da shi tun kulle Daddyn su tace “kin san meye ne? Wani abin alheri ne nan ke shirin samun mu, amma na gan ki rather-moody today, wani abu ne ya faru ban sani ba?â€? Ta zauna bisa kafafun Mamar ta, ta kwantar da kai bisa gwiwoyin ta tamkar dai zamanin kuruciya, kodayake ita har girman ta baka rabata da yaro dan shekaru uku, son jiki kuwa ko mage haka ta ganta ta kyale. Muryan ta a karye tana dibar bangon dakin tamkar mai tunanin wani abu tace “nima na kasa gane meke damuna, amma Mamar mu, mafarki fa na yi yau wai an tafi da Daddy za’a harbe…â€? Kafin Antin ta samu damar cewa uffan, itama Babyn ta karasa zancen ta sai dirin motoci suka ji, mota ba daya ba babiyu ba, hakannan ba uku ba, Intisar ta nufi bakin taga ta leka da sauri, abinda ta gani ya gigita ta (Daddyn su ne ke fitowa daga mota). Ta kwalla ihu tace “Daddy!â€? Anti Saratu ta mike a gaggauce zanin ta na kuncewa tayi sa’ar riko shi, da gudu itama ta leka ta tabbatar Saratun ba karya ta ke ba sai tayi waje. Ita ko Intisar sai taji hawayen dadi da farin-ciki na kwararo mata, ta jingina bayanta da bangon tagar idanun ta a rufe. In har tana da wani buri daya saura a rayuwar duniya to a yau, ya cika. Ta daga hannuwanta sama ta shiga kwararo yabo da godiya ga sarki Allah jikin ta na wani irin kyarma da karkarwa tamkar wadda aka sanya cikin sanyin kankara. Daga bayanta Khalil ya zungureta yana dariya kamar bakin shi ya tsage ya ce, “To ki je, ke kadai yake nema, ke kadai yake kira, ke kadai yake tambaya Inteesar!â€? Ta nufi sassan Daddyn da sauri faram-faram kamar zata tashi sama, Khalil na biye da ita a baya, amma ji ta ke saurin da ta ke dinnan ba zai sadata da Daddyn a yau ba, sai ta kara a guje. Shima Daddyn ya taso ne ya je nemanta da kansa don yana ganin ta ki zuwa ne sabida tsoron Hajiya Nafi. A bakin kofar shiga falon sukai karo da juna, a guje ta rungumeshi tana hawaye ta ce, “Daddy kai ne, ashe dama akwai ranar da zaka dawo?â€? Ya kalleta. Ya ce, “Saratu, ke ce kika lalace haka! Ina Al’amin Hajiya da ya tafi ya bar mun iyali cikin wannan ukuba?â€? Ya saki Inteesar ya juya ga Hajiya tamkar ita ce ta boye mai Aminun, ta sunkuyar da kai bata ce komi ba sabida zuciyar ta dake kuna, don ita kanta bakin-cikin da Al’ameen ya kunsa mata yana da yawa amma bai tambaye ta ba sai akan tsinanniyar ’yar sa? Idan ma yana nan din shi bawan su ne da zai nemo masu abincin? Duka yaran gidan basa nan sai Khalil kadai ya ce, “Daddy, muma tunda ka tafi, bamu kara jin labarin sa ba. An aika mai cewa an kulle ka amma ya ce wai ba ruwan sa.â€? Brigadier ya zame ya zauna akan kilishi yana girgiza kai ya ce, “babu laifiâ€? ya tambayi Anti Saratu su Bappa Sani da su Najib tace kowa yana lafiya, su Najib kuma kowanne yana makaranta. Yace ita Saratu me ta ke a gida bata koma makarantar ba? Sai kawai Antin ta rufe zancen da cewa ai sun gama makarantar ita da Khalil don bata son zancen yayi tsayin da ran ta zai baci, ya tambayi Hajiya ko ina motocin gidan bai ga ko daya ba? Daga nashi har na amfanin gida? Anti Saratu ta ce, “Don Allah Babansu Khalil ka tashi ka kintsa ka huta, ba yanzu ne lokacin wadannan kananun maganganun ba.â€? Bai ki ta tatan ba, sai ya mike ya nufi sassan shi. Hajiya na jifan ta da harara, lokaci guda kuma tana lallatsa nambobin su Najib tana gaya masu su zo gida ga Baban su Allah ya fito da shi. Intissar na ganin ita ya dace ta yi wa Faisal wannan muhimmin albishir ko don ta gyara zumuncin su data wargaza. Ita kadai zata iya bada labarin halin kuncin da ta tabbata zuciyar Yayan nata na ciki a dalilin yin biris din da tayi da shi. A hankali ta shiga danna nambobin shi wadanda suke tamkar karatun sallah a cikin kanta, zuciyar ta cike da farin-ciki maras misaltuwa. Kai tsaye ta samu bugu daya layin ya shiga to amma me? Muryar mace ce take tambayar ta ko wane ne akan layin? Ta yi dan jim, kirjin ta ya soma harbawa da sauri-sauri, muryar ta wani iri, cike da zargi ta ce, “Plz, ba layin Faisal Makarfi ne ba?â€? Ta ce, “Shine dai, amman ya shiga wanka yanzun nan, ko zaki sake kira anjima?â€? Saratu ta ji wani abu ya zo ya soke ta a kahon zuci, zuciyarta ta cunkushe kwakwalwar ta kasa rungumar abinda kunnen ta ke son ta fahimta. Me kenan Ya Faisal ke yi a kudun? Ba dai neman matan banza ba? Ta yi jifa da kan wayar ta hadu da garu wanda hakan ya haifar da darewar ta gida biyu, kafin wasu hawaye masu gudun gaske su zubo a kundukukin ta, tayi saurin sanya bayan hannun ta ta goge dai dai lokacin da Anti ta turo kofar dakin ta shigo, ba tare da ta lura da yanayin da Intisar din ke ciki ba tace “Saratu, Baban ku yace ki hada mai ‘vegetarian-mealâ€? mai kyau (abinci wanda babu nama a ciki sai ganye) bai son girkin kowa a yau sai naki, gashi na ganki sai kumburi kike kina neman fashewa?â€? Taja wani dogon tsaki, “Tsuuu!â€? ta girgiza kai ta sunkuyar, Anti Saratu ta kama baki “Ke Saratu, lafiyar ki kuwa?â€? Sai ta kara tsuga tsakin, ta mike tana niyyar shiga bayi domin adana hawayenta, bata san me zata ce da Antin ba. Anti Saratu duk da cewa ranta ya sosu da wannan sabuwar halayya ta Intisar da koda wasa bata taba yi mata ba, wai tsaki? Ta danne nata bacin ran don sanin halin ‘yan kayan nata sarai ba’a jin damuwar ta sai da dabara, don haka Faisal ya sabar mata. Sai ta kada kai ta juya ta ce, “Ai sai ki ce in je in ce da Daddyn ba zaki samu damar yi mai girkin ba, sabida wasu can sun bata maki rai, amma ba ki yi ta tsuga masa tsaki ba.â€? Tasa kai zata fita. Da sauri ta kamo hannunta, gaba daya ta fiddo abnormal idanunta waje, zaka iya ganin matukar razanar da ta yi cikin kwayar idon ta, ta ce, “Wallahi-wallahi Mamar mu ba haka bane, kai umh, ni abin ne ma na kasa ganewa Allah.â€? “To menene in ba shi kikewa tsakin ba?â€? Ta ce (kaman za tai kuka), “Haba Mama, haba don Allah Mamar mu, yaya za’ayi na yiwa Daddy tsaki ‘eben if I run mad (koda na haukace)? Wai Ya Faisal ne ke da budurwa? Kuma ba ki ji ba har tana ce mun ya shiga wanka? Ko a ina suke oho, da har zai shiga wanka a gaban ta?â€? Anti tayi jim, ita dai wannan closeness wato (kusancin) na Faisal da Intisar na bata tsoro, na kuma tayar mata da hankali, domin abun har ya so ya zarta na wa da shakikiyar kanwar sa, kar dai Saratu kishin Faisal ta ke? Ta ja dogon tsaki itama tace, “To ke ina ruwan ki? Kina tsammanin Faisal bai isa yin aure bane da zaki ce ba zai yi budurwa ba? Kina nufin ba zai yi aure ba kenan don yana matsayin yayan da ke son ki? To ke din zai aura koko in kin yi naki ne zaki sa shi a gaba ku je gidan mijin tare? Kin ga ni bani cikin shirme, ta so mu je?â€? Intisar data auna maganganun Antin cikin ma’auni na hankali da tunani sai ta ji Antin tayi gaskiya. Sai dai ita kam a duniya bata taba kawowa kanta yin aure ba tunda kuwa zai rabata ne da Ya Faisal da Mamarta. Bata kuma jin zata iya har abada! Ita kanta ta rasa maiyasa budurwar Faisal ta tsaya mata a rai ya ciwon makogaro. Sakwara ta shirywa Daddy da miyar egusi da aka wadatata da ganyen alayyafu sosai da gandar fatar saniya wadda ta dahu tai lugub, sannan da busashshen kifi, ganyen yaji sosai miyar tayi shar gwanin sha’awa musamman da yake da manja tayi amfani, sannan ta shirya faten dankalin turawa shima da ganyen a ciki da ruwan tumatur zalla. A karshe ta shirya farfesun hanta wanda shima ta wadata da ganyen alayyafun, kana ta shirya salad da ruwan salad cream, heinz-beans da mayonnaise (kalb) wanda ta fara cakudewa da kifin gongoni nikakke na (starkist) da bineger, tabi samanshi da adon cucumber, tomatoes, karas dafaffen kwai da sauransu. Duk da dai Daddyn ‘vegetarian-mealâ€? ya ce ta shirya lafiyayyen farfesun macen tolo-tolo mai rai da motsi, irin wanda ya dahu lugub din nan har tsokar ta salibe da kanta, tace a ranta in Daddyn bai son wannan ai Mamarmu zata so, har ila yau, tayi dafa-dukar spaghetti wadda carrot, greanbeans, kabeji da hanta yafi taliyar fitowa sannan ta matse mai ruwan guava kamar yadda ya fi so a kullum ta sanya a firji. Tayi wanka ta shirya cikin atamfa (exclusive) fara mai ratsin shudi kinsan irin wannan ‘colourâ€? a jikin farar mace karkiso kiga yadda ta kara haskaka ta, ta nannade gashin kanta kamar kullum cikin shudin ribbon ta jerawa Daddyn abincin a inda ya saba cin abinci. Saratu ba sangartacciya ba ce, ta iya komi a wurin Mamar ta, don tun tana shekaru sha biyu suke shiga kichin tare tana kallon yadda Mamar ke hadawa Daddy ‘deliciousâ€? don haka ne in ta tsaya ta tsarama abinci ko na Nicon-Noga albarka. Daddy na cin abinci suna mai hirar abubuwan da suka faru baya nan amma ba su gaya mai me sosa ran ba. Hajiya ta tashi fuuu ta fice da ta ji Daddyn na tambayar Saratu ‘glassesâ€? dinta sun tsufa ya dace a je Jidda sabon wata mai kamawa a canzo wasu. Ya tabbatar Hajiya ta saida gabadayan motocin sa da yayi magana tace lalurorin karatun yara ne, yace amma larurorin har sun kai na wadannan miliyoyin nairori sai cewa tayi itama gani tayi an fara shiyasa ta bi layi (tana nufin Anti Saratu da ta saida ‘yar motar ta bayan kuma tana da masaniyar cewa shi Daddyn ne ya mallaka mata da kansa), bawan Allah, bai son maganar tayi tsayin da har zata janyo bacin rai, sai ya ce Allah ya mayar masa da alkhairi. Kan ka ce meye wannan gida ya cika da jama’a masu taya Daddy murnar kubuta, wani abu da ya basu mamaki duk wasu tsofaffin abokan sa na nesa dana kusa wadanda rabon su da kofar gidan tun ranar da aka ce an kulle Makarfin sai gasu wai duk sun zo taya murna, dan adam kenan. Malam Sani da Goggo Jummai ma da yamma suka iso garin, kada ki so ki tona zuciyoyin wadannan dattijai, su Najib ma duk sun iso ana ta hamdala. Nasir ne ya gayawa Faisal ta waya shima yace Insha Allah gashi nan tahowa. Daddy bai samu kubuta daga mutane ‘yan taya murna ba sai karfe goma na dare, don haka bai samu damar fayyacewa iyalin shi komai ba na daga zargin da ake mishi Allah ya kubutar da shi sai ko Allah ya kai mu wayewar garin. Washegari da safe kuma sai ga ‘yan aikin gidan da suka gudu suna dawowa daya bayan daya suna aikowa wai a gayawa ranshi ya dade ga mai ban ruwa da mai tada inji nan sun dawo bakin aikin su, Aunty Saratu na jin sanda ya leka yace a gaya masu wanda suka yiwa iyalin shi da baya nan ma ya isa ya gode sai tayi dariya. Da aka taru ana karin kumallo kamar yadda ya ke a tsarin gidan kowannen su matse ya ke da son jin yadda wannan ijaba ta Ubangiji ta sauka kan mahaifin su, zuciyar kowanne fari kal kamar an mai bushara da Aljannah. Furkan ne ya kasa hakuri ya bara, “Wai Dad, ya aka yi ne?â€? Brigadier yayi murmushi, ya san abinda suka matsu da son ji kenan musaman Saratu karama da ta kura mai ido kamar mai gadin sa kada a sake kame masu Daddy a kulle. Fuskar shi ta yi fayau don duk wata kasimbar wahala ya shareta tas da kyakkyawan saisaye, sai dai ba karamar rama yayi ba tabbacin ya wahala kwarai da gaske. Ya dubi iyalin shi daya bayan daya kana tsoffin shi Baffa Sani da Goggo Jummai, sannan agogon da ke manne a falon, ya ce, “Ya isa a ce Faisal ya iso, don ya gaya mun ya biyo jirgin kasa tun daren jiya sabida tafiyar dare tafi dadi a jirgin kasa sai dai bata lokaci.â€? Ya kai duban sa ga Hajiya ya yi murmushi ya ce, “Dan ki, naso a ce yana nan.â€? Ta sunkuyar da kai kawai don tasan Al’amin yake nufi, ita kanta a yau tayi kewar shi ba kadan ba, tuni idanun ta suka ciko da hawaye. Abubuwa da yawa na faruwa a bayan Al’ameen masu dadi da marassa dadi. Taso a ce yana tare da su a yanzun tamkar sauran ‘yan uwan shi, ta tambayi kan ta ko maiyasa Al’ameen ya gujesu, baya ko tuna su? Bata sani ba, duk a kan nadamar abinda ya aikata ne ga ‘yar da ta tsana fiye da kowa Al’meen ya guje su, har kullum har kuma zuwa lokacin ya kasa daina ganin kansa a matsayin azzalumi akan Saratou. Ya cigaba da cewa, “Don abinda zan fada ya zamo darasi a gare su. Bana nadamar zamowana soja mai kare kasarshi takowannne fanni, kamar yadda har gobe ba zan yi ba. Abinda zan fadi muku yanzun ina so ne ku dau darasi kan cewa a wannan zamanin da muke ciki, babu aboki nagari, babu wanda zaka amincemawa, abokai sai su kai ka su baro ga fitinar da bazaka iya fidda kanka ba, su tsundumaka cikin masifar da baka san farko balle karshenta ba.â€? Ya mike tsaye, hannuwan shi ya sarke a bayan shi ya juya masu baya cikin tuno tsohon bacin rai na wani abu daya taba ma mutum zuciya matuka, dukkannin su sun yi tsit ko tari kwakkwara babu wanda yayi, su dai kawai so suke su ji me ya kai Daddyn su ga abinda suke da tabbacin ba laifinsa bane, to me ya tsunduma shi? “Rannan ina zaune a falon Janar Benga, ina sauraron fitowar sa a sabili da kiran gaggawa da yayi mani, sai na iso kuma a dai-dai lokacinda aka ce yana ganawa da baki, na kishingida cikin kujerar falon farko da zummar in jira shi, to amma sai na rika jiyo tashin muryar sa yana cewa da bakin sa shifa ya gaji da tsarin mulkin president (mai ci a yanzu) sabida yadda ya hana masu yin yadda suke so kamar yadda suka yi tsammani, suka kuma yi yarjejeniya da shi kafin su tsaya masa ya samu ya haye, su shirya juyin mulki kawai su turani in maye gurbin sa domin ni ina da sanyi, zan bar su su yi yadda suka ga dama da kasar mu, amma muddin suka bijiro min da bukatar su naki basu goyon baya, zasu shirya min tuggun da zan yi nadamar shiga na soja. A lokacin na fito, ko ganin abinda yake gabana bana yi sabida tashin hankali, don nasan su Benga sarai kamar yadda nasan yunwar cikina, masifaffun sojoji ne da babu abinda bazasu iya ba in har suka sa kansu don su suka san yaddda sukai suka raba president da Marshall Damijo duk irin matsananciyar amintakar dake tsakanin su kuwa, na shiga mota direba ya dawo da ni gida. Ke Saratu in zaki iya tunawa a ranar babu yaddda ba ki yi ba ki ji abinda ke damuna naki gaya miki har kika yi ta kuka. Na kwana ina saka yadda zan yi in fidda kaina daga wannan tsaka mai wuya da suke neman turani, wanda a lokcin da za’a rantsar da ni, na yiwa kasata alkawarin bazan taba yin wani abu ba bisa doka ba, ba zan taba cin amanar kasata ba, idan kuma har na nuna hakan na tabbata Benga Delsu da jama’arsa ba zasu kyaleni in zauna lafiya ba, sai na yankewa kaina shawarar yin ‘retireâ€? in koma kasuwanci cikin ruwan sanyi in barwa Allah al’amura na, na kuma amince cewa duk wata cuta ko daukaka da zata sameni to da sani da yardar sa ne. A washegari na aika takarduna na yin murabus daga aikin soja kwata-kwata, ai dai na fita daga kowanne irin shirin suma. Ashe dai tuya nayi na mance da albasa, don kwata-kwata sati daya a tsakani na ji su Benga ma sun yi ritaya, a dalilin an soke mulkin soja a lokacin, amma manya-manyan su irin su Marshall Shu’aibu Damijo, Shitu Allazi da Janar Delekonkwo duk basu yi ba, ban kawo komai a raina ba, don ban zaci zasu waiwayeni bama tunda sun ji na bar ‘militaryâ€? ashe dai kuskure nayi. Don a dai-dai lokacin aka soke ‘military-ruleâ€? Ranar wata asabar ina hutawa a gida aka ce dani Benga da Shitu na son gani na (seriously private) wato cikin tsananin sirri, nayi Addu’a kan Allah ya raba ni da sharrin wadannan miyagu kamin in je. Bayan mun gaisa, sun kuma gamsu da matakan tsaron da ke falon, suka gaya min bukatar su na cewa su Shittu zasu shirya kashe president ta hanyar sa masa guba a abinci da za’a sa kukun sa ya aiwatar akan wasu adadin biliyoyin nairori, in yaso ni sai su tsaida ni takara a jam’iyyyar da zasu kafa mai karfin gaske in samu ‘by all meansâ€? (koda ta magudi ne) sai in barsu su tsara min irin mulkin da suke so a yi. Hankalina ya tashi, cikin zafi na zazzagesu na kuma gargadesu kan cewa wallahi babu ruwana, idan kuma suka sake sako sunana cikin al’amarin su, to kuwa zan tona musu asiri duk da kakkarfar abotar dake tsakanin mu kuwa. Sai suka yi murmushi suka bani hakuri, tare da tabbatar min zancen ya wuce har abada, suka tafi. Kawai sai ji nayi har a bakin Faisal wai na tsaya takarar shugaban kasa? Duk an bi an manna posta na a ko’ina, president da kansa ya neme ni a waya yace a she takara na shiga haka ba sanarwa? To yana mun fatar alhairi. Sai ma na rasa me zance. Na kira Benga a waya nace ban ji dadin cin mutuncin da su kai min ba, wannan ai kazafine, suna sane da tsakanina da president ya za suyi min kage kan abinda bani da masaniya a kai? Sai cewa yayi su ba su bane, basu ma san anyi ba, don shi a lokacin ma yana Cameroun, amma inyi hakuri zai bincika ko su Marshall Shu’aibu ne. Abinda yace da ni kenan. Ranar da suka shirya wanzar da komi sai kukun da suka damkawa amanar abin ya kira president ya tona masu asiri, har kudin da suka bashi ya danka mai da takardun yarjejeniyar cewa ni za’a tsayar. Ni da nake amininshi tun muna NDA, nida ya taimaka ta kowanne fanni a soji, hatta karatun Al’ameen a turai shi ya dauki nauyi har yau kwandala ta bata taba yin ciwon kai ba, amma wai dani aka hada baki za’a kasheshi har lahira, (a tunanin shi fa), an ce mun president har kuka yayi kan cin amanar da yake tunanin nayi mishi, a take ya bada oda da shelar a kame mu duka. Rannan ina magana da Najib a kan hanyata ta dawowa daga Makarfi dibo jikin ka Baffa, motocin soji suka yi mana dabaibayi, nace da direbana ya tsaya amma saboda rudewa sai ya karawa motar wuta, nayi mai tsawa maimakon ya tsaya sai ya kara gigicewa ya kara gudun motar fiye da (300), ba sai suka sakarwa tayoyin motar (bullets) ba, motar ta hantsila ni na fado bisa titi cikin jini, shikuwa tuni ya dagargaje a ciki. Duk irin rauninnikan da ke jiki na haka suka kakaba min ankwa a ranar suka tafi damu Kiri-kiri. A Lagos aka kaini asibitin bariki nayi jiyya ta tsayin watanni uku kafafu da hannayena duka daure da ankwa jikin karfen gado, ban taba zaton zan rayuba, sai dai da yake wuya bata kisa sai in kwana ne ya kare. Bayan na warke aka tafi damu Enugu daga ni har su Benga ba mai ce da kowa uffan don takaici. A daren ranar abinda ya sani kuka tun farkon al’amarin shine da aka daura min camera daga gidan talbijin na kasa NTA, CNN da BBC domin watsa labarun cewa an kama mu dumu-dumu kan son yiwa kasa juyin mulki, karkashin jagorancina ni Bello Makarfi. Nayi kuka irin wanda ban taba yi ba a rayuwata, sharri ciwo ne da shi balle irin wannan dana tabbatar za’a harbe ni ne a banza a inda ko gawata baza’a yi mata sallah ba, sai dai ta zama ta ungulu da tsintsaye. Bana kuka don zan mutu, sai don mutuncinku da zai tafi terere, a sanadiyyyar wulakantacciyar mutuwar da nayi! Aka dawo damu (Imo State prison) da abin yayi kamari aka cilla mu South-Africa ta jirgi, inda aka cigaba da bamu tsatstsauran tsaro. A wannan dan tsukin na fidda rai da rayuwa kwata-kwata sai na maida al’amurana ga Allah, dare da rana ina rokon shi yayi mun rahma ya inganta rayuwar ku bayan raina. Mun shiga kotu ranar Alhamis inda aka tafka mahaukaciyar shari’a, shaidu suka tabbatr da sa hannun mu duka nan da nan ka yankewa Benga Delsu da su Shitu hukuncin kisa da bindiga. Ni kuma da babu kwakkwarar shaida a kaina, ban kuma amsa laifina ba, haka shi kansa kukun ya tabbatar babu ni a sanda aka kirawoshi, duk da irin kokarin da lauyana yayi suka san yadda sukai suka zurmani aka yanke min hukuncin life â€? imprisonment (daurin rai da rai), sai na daga hannu nace Allah yasa hakan shi ya fiye mun alkhairi da ku baki daya. Shekaranjiya ina kwance aka ce in taso, a gidan gwamnatin Delta, dayake an maido ni jurun din Delta State, President ne na gani tare da mukarrabansa wato gwamnonin Nijeriya gabadaya, ya debo su don su zo su bani hakuri an gane bani da laifi kwata-kwata a yau za’a maido ni gida. Na tambayi yadda abin ya kasance aka gaya min cewa Shitu da Marshall da za’a harbe su suka roki alfarmar a basu lokaci su farke komi, ba kuma nufin su a yafe musu bane, illa su fadi gaskiyar yadda Benga ya turani cikin al’amarin, don ya nemi hadin kaina na yi mai barazanar tona musu asiri, suka fadi inda za’a samu shaidar komai akan hakan a gidajen su, suka kuma roki da a kyaleni ko hakkin da ke kansu ya ragu, sun tabbatar alhakina ne ya janyo masu tonon asiri. An bani hakuri, an kuma bani tarar bata mini suna da sukai ta biliyoyin nairori tare kuma da sabon albishir din cewa sati mai zuwa in shiga (presidential office) a matsayin mai baiwa Shugaban Kasa shawara kan harkokoin Mulki.â€? How much do you like this story? 5/8/22, 21:04 - Ummi Tandama😇: _____________________________ *âœðŸ? SIRADIN RAYUWAâœðŸ?* Book two *@Takori* Page🔟 Gabadaya falon ya dauki tsit inka dauke karar bugun dakika na agogon bango mai nuna karfe sha biyu na rana dai-dai sanda Daddy ya kawo karshen labarinsa. Najib ne ya fara magana yana murmuhi ya ce, “Wannnan shi ake kira ‘narrow â€? escape (tsallake rijiya da baya)â€? Kowa yayi murmushi mai fidda sauti. A nan ne aka shiga baiwa Daddy labarin halin kuncin da gidan ya shiga a bayan shi, yadda karatun su ya dinga watangariya da yadda malamai suka rinka cin kudin su na karya dana gaskiya, Hajiya ta ce, “Wata rana wani mutum yazo mini ya sha farin rawani, ga doguwar tazbaha yana ja yace in bashi dubu arba’in in har ba’a sako ka cikin wannan satin ba zai maido mun kudina. Ni kuma jin haka jiki na rawa na kirgo kudi na bashi ya tafi. Yana fita Khalil ya shigo yace wallahi karen mota ne ya san shi a tasha har yau dinnan kuma ban kara jin duriyar sa baâ€? Gabadaya aka sa dariya har Daddyn ya ce, “Dana karyar, dana gaskiyar dai duk sun yi, kuma Allah ya amsa, sai mu roke sa ya kare gaba.â€? Faisal ya iso gidan su yamma lis, sanye yake da farar shadda ‘getznerâ€? babbar data dauki dinkin Mohammed Abacha, kafafunshi sanye cikin budadden takalmi kirar Italy, bakin agogon ‘swissâ€? ya lafe cikin lafiyayyar farar fatar hannun shi wadda bakin lallausar gashi ya baibaye. Kamar yadda yake dogo ba can ba, shi kansa ya san shi dan gayu ne na hakika mai ginannen jiki irin na Daddy Makarfi. Kallo daya zaka yiwa dukkan samarin nan na Brigadier ka amincewa ranka lallai abubuwan nan guda biyu masu tafiya a tare da juna sun masu mayafi wato naira da tsantsar boko. To haka Faisal Allah ya halicce shi da wasu ilhamomi daya zarta na ‘yan’uwan shi nesa ba kusa ba. Yana da kakkarfan taku mai jan hankali da idanuwa tamkar maganadisu, da ke fizgar hankula da dama garesa ba tare da shi din ya sani bama musamman ga ‘ya’ya mata. Ta ko’ina, Faisal Bello bai da makusa, shi kansa ya san hakan. Ma’abocin wani ni’imtaccen turare wai shi 5,000 Doller, inda duk yayi idan mutane sunyi dubu zaka fidda shi da wannan lallausar kamshin koda ya wuni ne da barin wurin kuwa. Don haka kamshin sa kadai daya baibaye ilahirin gidan ya tabbatarwa da mutanen gidan cewa ya zo, musamman Intisar din shi da Hajiyar shi. Ya sallame dakin Baban su cikin sanyin murya, kamar yana tababar ko karya aka gaya masa, tamkar wani yaro karami, sai ya fada jikin Daddyn hawayen farin ciki na ziraro mishi Daddyn yasa yatsun shi biyu yana share mishi ya ce, “Komi ya wuce Faisal, Allah shine abin godiya, mu rokesa ya kare gaba.â€? Abinda yace da shi kenan. “Daddy wai ya akayi ne?â€? Ya tambaya a dokance, sai ya sake mayar mai da labarin kamar yadda ya baiwa sauran ‘yan uwan shi, Faisal kuka yayi sosai na tausayawa mahiafinsa ya ce, “Na fadiwa Ya Aminu, Daddy ba zai taba aikata abinda a ke zargin shi da shi ba.â€? Amma a zuciyar shi. Sun dade suna tattaunawa akan al’amarin kamin ya tashi ya nufi sassan Hajiya. Allah-Allah yake ya sallami Hajiyar ya je ga Saratun shi, kanwar da baya da kamar ta duk fadin duniya, ya ji tayo waya ta kuma aje ba tare da ta fadi sakon da tai niyya ba wanda ya tabbata fitowar Daddyn su ne, to akan me ta aje? Shine abinda ke damunsa yake kuma matukar son ya ji. Ita kuma Hajiyar da ta fahinci a cusgune yake hirar da ita, ji yake kaman yayi fiffike ya fice sai tayi ta jan hirar da tsawo, tace kuma bai fita dakin sai ya cinye tarin abinciccikan data sa aka shirya dominsa tunda ta san inda za’ayi mai barbade-barbade zai je yaci sai yayi murmushi. Yana ci yana shan zagi da alkaba’I iri-iri daga bakinta wanda in har da sabo ya saba da jin ire-iren su, har ya zamanto basa damunsa a yanzun ta ce, “Na taba ganin maye irin ka Faisal? Shin me Saratu da Saratu ke baka ne da kake tarewa a gindin su?â€? Yai murmushi sosai da ya motsa dukkannin (beauty-point) din shi hagu da dama, yana taunar abincin yana cigaba da murmushin ya ce, “Hajiya, maita kuma? To a ina na tsotso?â€? Ta ce “a nonon Ubanka, can nonon su Saratu, in banda maita kai kenan baka da burin komi daya wuce Saratu da Saratu kai! Allah ka raba ni da irin maita, wannan alaka Allah Ka wargaza ta, shin uwar me kake daukowa ne jikin su Saratu?â€? Ya ce cikin muryar nutsuwa da rashin jin dadin kalamunta, “Hajiyar mu, kina bani mamaki. Bana dauko komi sai dai kar ki manta jinin mu ke gauraye da na juna, kenan ko ban bi su ba, wannan jinin na bibiyar jinin jikina?â€? Ta ce, “A gidan uban wa jinin naku ya gauraya?â€? Kome ta tuna? Tayi saurin fizgo dankwalin ta ta toshe bakin ta da karfi, yayinda shi din ya bita da idanun mamaki, a ransa yana cewa ko sai yaushe Hajiya zata girma? Ko sai yaushe bakin Hajiya zai iya magana? Ita kam babba ce, amma tunanin ta da maganganun ta na kananan yara ne, abin nufi, babu kawaici da jan girma a cikin su. Ta yi fatali da tebirin abincin komi ya kwankwatse, ya wanke masa jiki, ya rine farar sassalkar shaddar dake jikin shi ta soma nuna shi da yatsar ta sabbab, tana ja da baya tace a kaurare, “Wata rana zaka yi nadamar cewa da kake kun hada jini da Saratu!â€? Ya so yace da ita “irin wadda Aminun ki yayi akan ta ya nisanceki shekaru goma sha biyar?â€? Sai kuma ya tuna wannan uwar sa ce, da ta dauke shi cikin mahaifar ta tsayin watanni tara cif, ta haifeshi bayan nakuda da wahalhalun da harshe ba zai iya bayyanawa ba, ta raine shi shekaru dai-dai har ashirin da bakwai bata taba gazawa akan hidimomin shi ba. Kenan ko ba komi tana da wannan matsayin, amma da ba ita bace, a yau da ya gaya mata bazai taba nadamar hada jini da ko mai gugar takalmin Saratu ba balle ita, kuma har gobe zai cigaba da kaunar ta, tun kaunar nan da yake mata a sanda take a tsumman goyonta; ba mayya ba, ko ‘yar mafiya ceâ€? Tayi mamakin yadda har ya kwana ya wuni cikin gidan bai nemeta ba, duk da tasan ba zai wuce ya gamu da fushin Hajiyar su bane a kanta, kamar yadda ta saba a duk zuwansa garin, to itama dama haushin sa take ji don haka bata ko nemeshi ba. Washegari da safe tana dakin da su Goggo ke sauka tana kintsawa Goggon kaya don a ranar ne zasu koma Makarfi, ta dibeta cike da tsantsar kulawa da kauna irin ta kowacce kaka ga jikanyar ta, tace cikin zolaya “Saratu Baba ya dawo, mu da ganin ki kuma sai Baba ta ganiâ€? tayi ‘yar sassanyar dariyar ta ta ce, “Kai Goggo, yanzu sabida Allah sai ba Daddy nake zuwa Makarfi? Kin san ma yanzu ba zai yi wata bai aiko mu kawo maku kayan amfani ba musamman yanzun da ya san kun wahala kwatankwacin mu?â€? Goggo tace “hakane, wai ke sai yaushe zaki kawo min maigidanne?â€? Ta tintsire da dariya tace, “Kin san Alllah Goggo bani da saurayi.â€? Ta ce, “Haba dai, bari fadar haka, maza bari, babu ko dadin ji. Duk kyawun nan naki kaman aljana, ki ce baki da masinsini? Ki ce zama bai samemu ba, sai mu fara yo miki rubutun farin jini, watakila duk farin nan naki jinin ki bakikkirin yake a idanun maza.â€? Ta sake sakin dariya har da dan guntun hawaye, dai-dai lokacin da Faisal ya yane labulen dakin ya shigo tare da sallama. Bai zauna ba sai da ya dauki (remote) ya kunna A/C yana hararar Intissar ya ce, “Shin kema ‘yar kauyen ce ne Goggo da ba zaki kunna A/C ba duk uban zafin nan da ake?â€? Ya samu kujerar zaman mutum daya cikin (cushion) farare sol da suka mamaye dakin, ya zauna ya harde yana karkada ‘yan mukullayen shi dake like jikin wani ‘key-holderâ€? mai tsinannen kyau, ta tura baki gaba yadda take mai in ya bata haushi, ta mike zata fice sai ya dan zamo daga cikin kujera, ya mika dogayen kafafun shi suka tadeta ta fadi kif, bisa kafet da baka, ya ce, “Good, gobe ma ki kara zumburan baki, Allah Goggo Intisar ta raina ni.â€? Goggo ta ce, “Wa ya janyo? Duk ba ku kuka so ba.â€? “Da muka yi me?â€? “Kun fini sani ai don Allah shashashun wofi.â€? Intisar ta mike tana karkade kayan jikinta tana yatsuna kamar wadda aka tura cikin yumbu, ya ce “To Goggo bakya yi mata fadan turan bakin da ta ke yi?â€? A hasale kamar ta rufe shi da duka ta dago daga gurzar goron ta data keyi tace “Bana yi din, nace baku kuka so ba? Tana ganin ku kai daya har marin ku bazata yi ba, shin in tambayeka, sai yaushe kuka shirya kawar da Saratu ne?â€? Faisal yayi wani iri da fuska alamun bai gane hausar ba. “Ban gane mu kawar da ita ba Goggo don Allah yi min bayani, mu kawar da ita sai kace wata kaya? Ko mu kasheta kike nufi?â€? Intisar bata san lokacin da ta saki murmushi ba, wasu al’amuran na Faisal kan bata dariya, yafi kama da dan fari fiye da da na biyu, Goggo ta kara gyara bayanin ta da cewa, “Ina nufin sai yaushe ne zaku yi mata aure? Ga yarinya kafada daya da uwar ta, amman har yanzu kun taru kuna ta wani lailayarta Baby-Baby (tana yi tana kyabe baki irin yadda suke yi din) nan ko uwar mata ce. Wai naga kai ne na hannun daman ta shiyasa na tambayeka don ita uwar har da yi mun fuskar shanu don nace a yi mata aure. Kuna nufin saka muku ido za’ai kuyi ta ajiye yarinyar sai ta zama kwantan ‘yammata tukunna?â€? Intisar daga inda take tsaye ta dinga dariya ta ce, “Goggo menene kuma kwantan ‘yammata, ai mace bata kwantai komi girmanta, zata samu kato dai-dai girmantaâ€? Faisal sai ya juyar da kai, bai san san da yaja tsaki ba, yayi kicin-kicin da fuska, ya ce, “Wai ke Goggo baki da zance sai aure-aure, to har nawa Babyn take? Ko sakandire bata gama ba fa, ita wannan kifin rijiyar ma tana fita ne balle wani mummunan ya ganta yace yana son ta?â€? Ta harare shi a ranta tace bari in tura ma haushi nima, kaima ba kana da budurwa ba? Ta ce a ladabce. “Wa ya ce ma bani da saurayi Ya Faisal?â€? Faisal ya fiddo ido cikin barazana ya ce, “Eh, Baby kin san abinda kike fada kuwa?â€? Ya kara bude baki kaman zai kara cewa wani abu, kafin ya bara cikin kada ido ta sake cewa, “Allah Goggo ina da saurayi, amma balarabe ne mutumin Turkey, shine malamin chemistry din mu a Riyadh sunan shi Dr Alhassan, ya taba zuwa nan ma kuma ki tambayi Mama.â€? Ta kara duban Goggo da dukkan idanu, tana murmushin da ke kara mata kyau da kwarjini, lokaci daya tana satar kallon Ya Faisal da wutsiyar abnormal (marassa lafiyan) idanunta don ganin irin sukar da kalamin ta ke yi. Ba shakka ta ga sauyawar fuska da idanuwan shi bakidaya irin yadda bata taba gani ba, taci gaba da cewa, “Baki gan shi ba Goggo, dogo kyakkyawa jawur da shi, idanun nan kamar na Ya Najib, hancinsa zirit irin na Ya Faisal, muryar shi.â€? Haba! Faisal ya gama zuwa wuya tun kamin ta karasa, tun can fa sauraron ta yake ‘absent-mindedlyâ€? da tunanin ba Saratu-Intissar ke wannan maganan ba, yarinyar da har kullun yake gani ‘as a kidâ€? bai san yaushe bakin ta da idanun ta suka bude har haka ba, ita ce har take yabon kyawun namiji, abin mamakin ma har a gaban sa! Bai san sanda ya cafko hannayen ta duka biyu ba ya yana kallon ta cikin ido da idanun shi da suka rine ‘completelyâ€? har wani (blue-blue) suka koma suka rine da abin da bata taba gani ba, ya durkusar da ita gaban Goggon, shima binta yai suka durkushe yana huci kaman yunwataccen zaki ya ce, “Maimaita abunda kika fadi yanzun Intisar, Goggon bata ji sosai baâ€? ta tsorata, ta razana kwarai da yanayin sa haka tsatstsauran rikon da yayi mata ya gigitata, sai tasa kuka. Goggo ta yi salati ta ce, “Sakar ta, sakar mata hannu, sake ta nace, idan ka karyata fa?â€? Da alama bai jin ma abinda Goggon ke fadi domin gabadaya baya a hayyacin sa yace “In an karya ta sai me Goggo? Yanzu wannan tsakuwar yarinyar ce take yabon kyawun maza, ina ta koyo wannan fisarar?â€? Ta ce, “Na fada din, Goggo shekaran jiya waya na yi mishi, in gaya mishi Daddy ya dawo, wata Inyamura ce ta dauka tace min wai…â€? ya kara tsananta matsar da yayi wa hannun ta tare da murje yatsun kafar ta da karfi da nashi yatsun, ta saki kara don zafi amma bakin ta bai mutu ba, hakannan bata yi shiru ba da gaya wa Goggon yadda sukai da yarinyar shi a waya. Ya ce, “Nace da ke na santa?â€? “Ya santa mana Goggo, cewa tayi fa wai ya shiga wanka, idan bai san ta ba, ya za ai har ta san inda yake wanka? Wa ya sani ma,…â€? Faisal ya soma daldalle mata baki da yatsun shi da karfi nan da nan dan bakin ya haye, dai-dai lokacin da Najib ya shigo, koda yake ya dade yana kallon su yana son tirsasawa zuciyar shi rashin amincewa da abinda kwakwalwar shi ke son fahimtar da shi, ya shiga tsakani ya janye kanwarsa ya ce, “Wonderful! Abin mamaki, abinda cikin gidan nan ba wanda ya taba gani, abinda ko a tunani ba’a taba kuskuren tunanowa ba, wai Faisal da Intisar yau aka gani a rana?â€? Su kan su sun ji kunya ba kadan ba, don haka ba wanda ya amsa mishi kowanne sai huci yake kaman ya cinye dan uwan sa, Goggo Jummai ta kyabe baki ta sunto wani goron a habar zanin ta, ta kwashe wanda ta gurza a magogi da farko ta hambuda a baki tana mamulawa ta ce, “Ai kai kadan ka gani, baka ji ba har tonon asiri sukewa junan su,â€? Faisal yayi tsaki ya fice har zuwa lokacin idanuwan nan suna rine a (blue) kamar na wanda ya kama matar shi da kwarto, ita kuwa ta cigaba da gaya masu yadda suka yi da yarinyar shi a waya bata ko sanya comma, (wakafi) balle fullstop (aya) zuba kawai take kaman ‘ya’yan kanya Najib ya daga mata hannu “wait, excuse me please Inteesar, for Allah ’s sake, ina ruwan ki da budurwar Faisal, kin isa ki hana shi yin budurwa ne?â€? Ya zazzaro mata manyan idanun shi, ta sunkuyar da kai cike da matsananciyar kunya kafin ta daure ta ce, “To Ya Najib shima ina ruwan sa don nayi maganar saurayina sabida Allah sai ya murmurde ni yana neman balballa ni?â€? Najib yayi murmushi ya juyar da kai, kwakwalwar shi kaman ta tarwatse, yanzu kam ya tabbatarwa kansa abinda tun shigowarsa zuciyar shi ke gaya mishi yana karyatata da gangan, amma sai ya basar tunda mai ilmi ne, ya juya ga Goggo da son wanke mata nata zargin ya ce, “Goggo da ganin Saratu kin san anyi irin kannen mijin nan ne, masu kishin son da Yayun su ke nunawa matansu, masu so a raba musu kauna da matan Yayyunsu ‘equalâ€? (dai-dai wa daida) wanda kuma wannan ba zai yiwu ba. Mata fa matsayin ta a zuciyar mijin ta ya zarce yadda duk kike tsammani, kasancewar ta wani bangare na gangar jikin sa, zuciyar sa da hutun sa, zata bashi abinda ke kanwa bazaki taba bashi ba, zata kula da shi da rayuwar sa ta hanyar da ke kanwa baza ki taba yi ba. Hakannan daga jikin ta ne zai sami ‘ya’yan da zai yi alfahari da cewa nashi ne, mallakin shine, ta yaya matsayin ku zai zo daya? Kazalika shima Faisal yana tsananin kishin ki so wani fiye da wannan ingantaccen son zumuncin da kukewa juna, yaya za kuyi rayuwa da haka? Don haka dole ya ji zafi da farko, amma daga karshe dolen shi ya dangana ya danka ragamar rayuwar ki ga abokin rayuwar ki na har abada bayan shi, don kuwa shi ba auren ki zai yi ba ko a garin gaba-gaba muke bare gari na Addinin muslinci, so kusa ranku a inuwa sassanya, ku yayyafawa zuciyoyin ku ruwan sanyi, dole kowannen ku zai sami abokin rayuwa na daban. Ba rarrashin ki nake ba, gaskiya kawai nake gaya miki. Do u get me (kin fahimce ni?)â€? Sai ta mike tana kunkuni na alamun rashin yarda, sai dai wannan Yaya Najib ne bai yuwuwa ya fadi ta fadi, yanada wata kima mai yawa a idonta, amma da ba shi ba ne da tace da shi; Idan har auren kowannen su na nufin kawo sauye-sauye da canje-canje ne cikin rayuwar so da kauna, shakuwa da ingantaccen son zumuncin da suke wa juna ne ita da Faisal, to ita ta yafe nata! Zata zauna haka tare da Ya Faisal a gida daya, a gaban Daddy Makarfi, matsayin yayanta kuma nata abokin rayuwar har abada!! Ita dai bata son zancen budurwar Faisal ko kadan, za kuma su ci gaba da fada har da ba hammata iska idan ta sake jin zancenta. How much do you like this story? 5/9/22, 09:56 - Ummi Tandama😇: _____________________________ *âœðŸ? SIRADIN RAYUWAâœðŸ?* Book two *@Takori* Page1ï¸âƒ£1ï¸âƒ£ Su Goggo Jummai basu tafi a ranar ba sai washegari Laraba, Baffa yace Intisar ta shirya su tafi tare ta karbowa Daddy rubutun da za’a fara yi mai na tsarin jiki duk sati, in yaso sai su dawo ita da direban da zai kai su. Suna ta jiran Ado da ya tafi cefane har shabiyun rana bai dawo ba sai Daddyn ya kira Faisal yace ya je ya kai su. Ko kadan ranta bai so tafiyar nan da Faisal ba, ita yazu ko hanya bata so ta hada su sabida haushin sa da ta ke ji akan budurwar sa, har Addu’a take garin Allah yayi ya sake wayewa ya koma inda ya fito. A motar Hajiya (bolbos6) aka yi tafiyar, Baffa da Goggo na gidan baya suna taunar goron su suna hirarrakin su tamkar wasu yara sabbin aure ga sanyin A/C na ratsa su, Goggo har da su aje mayafi a gefe da ganin su dai kinga ‘yan gatan tsoffin da ‘ya’ya suka hucewa takaicin duniya, jikokin su Faisal da Intisar na gaba. A yau dressin din sa (bery-simple) wato sanye yake da caftan na shudiyar shadda ‘yar mali kalar ta kama sosai (dark-blue) kansa ba hula, silipas ne ‘chipsâ€? a kafar sa yana murza sitiyari cikin gwaninta, kamar kullum parmanent (tabbataccen) kamshin sa na (5,000 Doller Perfum) ya na tashi a hankali cikin motar cooly, wannan kamshin dake sa mutum gyangyadin da bai shirya ba. Ita ko ‘yar lelen gidan Makarfin sanye take da kamfala shadda ghanilla baka da aka yiwa dinki senegalese, maimakon dankwalin kayan ta yi amfani ne da siririn farin mayafi da yake dinkin babba ne sosai, baka ganin komi nata sai shacin kayatacciyar fuskarta dake manne da farin (medicated-glass) dinta sai ko santala-santalan yatsun hannunta farare sol kaman ka taba jini yayi tsartuwa data kawata da zobba na farin zinare wato (white-gold) kwaya biyu rak, ba abinda ke tashi jikin ta face sassanyan kamshin turare ‘zandariaâ€? bakin ta cike da chingum mai tsananin kamshi (hubba-bubba) tana tauna (bery-gently). Daga ita har Faisal kowanne shan kamshi yake wa dan uwan kaman bai taba sanin sa ba dadai duniya. A haka yake (speading) har suka fice jihar Neja ba wanda yace da dan uwan sa uffan, ya mika hannu ya karo karfin na’urar sanyaya mota domin Faisal Allah ya halicce shi mutum ne mai son ya ji shi jike cikin raba, ko kadan bai son zafi don haka fatar shi har wani santsi take irin na mazauna kasar sanyi nan ko tsabar hutu ne kawai, ya danna kaset na wakar Sani Aliyu ta (Shehu Kangiwa Jagoran Jihar Sokoto) yana kada kai cikin nishadi, yana rangaji da dogon wuyan shi yana buga sitiyarin da hannun shi daya, dayan ko yana cigaba da tukin sa hankali kwance yana bin wakar da ‘rhythmâ€? din da mawakin yayi amfani sak. Inteesar ta kama kanta da hannu bibbiyu, tuni kan ta ya soma sarawa, ta tsani ‘melodyâ€? na wannan wakar domin ciwon kai yake haifar mata ba tun yau ba, ta sha gayawa Faisal duk cikin kasusuwansa ba wanda ta tsana irin wannan kaset din, tun kuma daga ranar bai kara sawa ba, to yau ko don yana jin haushin ta ne? Oho! Sai ta kwantar da kanta cikin cinyoyin ta tayi shiru, kanta na cigaba da sarawa. Sun yi nisa sosai kuma ya gyara murya ya kure sautin sosai ta yadda su Goggo da ke baya ba zasu iya jin me yake cewa ba yace “wayyo Ronke, nayi missing dinki amma ‘by the way, gobe I’yanzu da yardan Allah ina Ilorinâ€? tayi tsaki baya ga wani tukuki daya zo ya tokareta a kahon zucci, ashe ma kabila ce Yayan da bata hada shi da kowa a duniya zai auro masu? Tuni idanin ta suka cicciko da kwalla, ta dago ta dubeshi da wutsiyar ido kana ta maida duban ta a tsirrai dake tsere a gefen titi tace. “Ai sai ka aje mu, ka koma can garin naku wajen Rakiyar tunda kuwa kuna wanka tare ba dole kayi kewar ta ba?â€? Yayi dariya sosai sabida Rakiyar da tace ya bala’in bashi dariya yace “ke Sis wanka da Ronke shine ya dameki, ni ko kyakkyawar fuskar ta nake kewa, da kissable-lips dinta, gata da iya dressing dan kuwa shigarta tana burgeniâ€? ta kuwa shaka, ta kule ta haye suntum, fiye da tsammanin sa ko numfashi da kyar take furzarwa, wai a gaban ta? Ya Faisal ke baro wannan kazamar magana? Amma Allah wadaran wannan Ronke data gurbata mata tarbiyyar dan’uwa. Shi ko Faisal ko a jikin sa, har wani lumlum yake da ido wai yana tunanin Ronke. Basu bata lokaci ba a Makarfi suka karbi sakon su suka fito sai ta bude kofar baya ta kame abinta domin bata son kuma jin zancen wofinnan na Ronke. Faisal ko ya kudure zancen Ronke yanzu ya fara, ya kai hannu ya shafi kyakkyawan saisayen kanshi zuwa dokin wuyanshi, ya dubeta idanuwan shi sunyi kasa sosai kaman suna neman rufewa don kansu yace “nayi maki kama da Ado direba ne? Allah ko Ronke dana ke mutuwar so bata isa ta kame a ‘owner-sideâ€? in tukata ba, Allah wallahi kuwa baki isa ba don haka cikin biyu dole zaki zabi daya. Ko dai ki koma gidan tsoffin da kika fito, ko kuma ki komo mazaunin mai zaman banza don kowa ya ganki ya san zaman banza kikeâ€? sai ta gyada kai kamar kadangaruwa, zuciyar nan ba sai an tona ba don takaici, ta fito ta banka kofa ta fada gidan. Goggo na sharar tsakar gidan da yayi kura futuk sabida kwankin da sukai basa nan ta ganta ta jawo kujera ‘yar tsugune ta zauna daga can gefe tana cika tana batsewa, kiris take jira ta fashe tace “ke lafiya? Me kuke jira tun dazun baku tafi ba, anya ‘ya’yan nan kuna jiyewa kanku tafiyar daren nan da ake jiye maku?â€? Tace “a’ah Goggo ba laifina bane, Ya Faisal ne yace in dawo a bani kudin mota in je ni tasha in shiga motar kasuwaâ€? Goggo ta ce “akan wane dalili? Ki ga mun dan nema, bari inje In tadda shiâ€? taja mayafin ta data rataye a jikin kyaure ko tsayawa yafawa bata yi ba tayi waje. Kafar sa daya cikin motar daya a waje yana bin wakar Hassan Sarkin Dogarai ta Dacta Mamman Shata, don shi Faisal wadannan wakokin namu na gargajiya sune (hobby) din shi, ya kan ce yakan tsinci kansa cikin nishadi a duk lokacinda yake sauraron su, musamman cikin halin kunci, damuwa, confusion, ko a yayin da ya rasa sanin hakikanin abinda ke damun zuciyar sa. Goggo ta tsaya a kan shi na ‘yan dakiku ba tare da ya sani ba, ta nazarci abubuwa masu dama a tare da shi cikin ‘yan dakikai, sai ta koma lallashi tamkar mai magana da yaro karami ta ce “wane irin neman magane ne wannan Faisal, wai maiyasa kuke hakane kai da ‘yar kanwallen kuma ai sai kowa yayi maku dariya, na dauka tun jiya zancen ya mutu? Ban san ka da riko maras dalili ba.â€? Ya rage sautin radiyon yace “sai ki tambayeta dalilin ta na kamewa a baya in tukata, an ce da ita ni direban gidan su ne?â€? Goggo Jummai tayi dariya irin tasu ta manya, amma zuciyar ta tayi nauyi, har yaushe zasu dauwama suna boyewa jinin su da sauran jama’ar dake tare da su wannan boyayyen sirri, musamman yanzun data fahimci yana neman zama cutuwa ko kwara ga Faisal da ita kanta Intissar? Har yaushe za’a dauwama a hakan? Ko makaho ya shafa idanun su zai bada tabbacin soyayya suke su kan su basu sani ba. Ita kam tana ganin da Bello yayi tunani da bai dauki matakin boye wannan al’amari ga kowa ba tunda ko watarana, Saratu za tayi aure, zancen duniya baya taba boyuwa koda kuwa a karkashin gado aka sanya shi. Auren daya cikin ‘ya’yan shi shine gata na karshe da zai yiwa rayuwar yarinyar in har kaunar da yake ikirarin yi mata ta gaskiya ce. Su kadai suka san asalin ta suka san ciwon ta duk tabon dake jikin ta baza su taba kin ta ba, to boyon na mene ne? Idan babu wannan akwai mutuwa, zai iya mutuwa a sanda komi zai bayyana garesu suzo suna cewa ashe da bai mutu ba da bazasu sani ba ina amfanin haka? Ita kadai take tunanin ta, tama mance a inda take tsaye, da wadanda take tare da su, duk suka dubeta, kamin Intisar din ta kai hannu ta bude murfin kofar bayan motar, karar kofar ne ya maido ta hankalin ta ta dubeta tace “a’ah, shiga gaban ku tafiâ€? ta dubi Faisal tayi murmushi tace “Da abokan wasa kuke sai ince son junan ku kuke, amma duk wannan ce-ce-ku-ce banga dalilin sa ba, sai aka ce wani abu zai ragu a jikin ka don Saratu ta zauna a bayan mota ka tukata?â€? Yayi saurin cewa “Allah Ya so ba su din bane, ko su din ne Allah Goggo ban ga me zan ci da wannan kodaddiyar yarinyar baâ€?. Intisar ta kai hannu a hankali ta shafo dogon karan hancin ta, ta kare masa kallo tsaf cikin ‘yan dakiku, ta so ace akwai makusa tattare da Faisal a yau ta rama wannan cin fuskar amma BABU! Komai nasa yayi masa dai-dai ya kuma dace da yadda Ubangijin halitta ya tsara mishi abinshi kai kace shi ya zabawa kansa, tako’ina, Faisal Bello bai da makusa. Ita ko tasan fara ce jazur, kenan farin ta yayi yawa har ta kode? Wasu kwalla suka zubo sharr, tayi saurin sharewa da bayan hannun ta. Goggo ta rasa ma abinda zata ce tace “oh ni Jummai! Allah kayi mun maganin abinda yafi karfina, ka iya min abinda bazan iya ba, nace shiga gaban ku tafi Saratu jayayya ba ta da amfani, Allah ya kiyaye hanyaâ€?. ***** Tafe suke tamkar tafiyar kurame, to ba wanda yace da dan uwan sa ci kanka, har suka fita shiyyar Kaduna kwata-kwata, yace a ransa bari dai ya kara tsokanota. Ya dibi yanayin ta kana ya maida hankalin sa a titi yace, “kin san meye ne baby? Abinda ke kara sawa in so Ronke, shine murmushin ta, tamkar na ‘yammatan hurul-eeni yake, tafiyar ta ko kin san catwalk to haka take. Idan tayi dariya jerarrun hakoran ta masu haske kamar kankara na sawa in mance da kowacce ‘ya mace a duniya, muryar ta tamkar sarewa na kwantar da hankalina. Tana kishina kamar mijin ta, ranar da kika yo mun waya kwana tayi tana kuka. Idan ta rungume ni Intissar mancewa nake da kyawun kowacce diya mace a duniya sai ita Ronke Adeyemi Olayemi…â€? Sai a lokacin ya lura Saratu kuka take haikan, kuka take tun karfin ta baka da zuci. Zuciyar sa ta tsinke hadi da wani mummunan faduwar gaba da ya sameshi duka a lokaci daya, komi ya tsaya mishi cik. Duk wani haushin ta da yake ji sai ya kau, tausayin kansu ya maye tunani mafi rinjaye cikin zuciyar sa har bai san shi kansa Faisal yake tausayi ba ko ita Saratun? Shi fa ba mahaukci bane, hakannan a shekarun sa, tunanin sa da matakin ilminsa, ya isa ya fahimci irin kaunar da sukewa juna daban take da wadda ‘yan uwan jini daya ke yiwa junan su. Kar dai ya kasance Allah ya jarrabcesu da son junan su alhalin suna uba daya? Mai yasa Ubangiji zai jarrabce su da wannan musiba? Yayi saurin jan istigfari ga sabon da zuciyarsa ta bijiro tare da kokarin kawar da wannn bahagon tunanin. Idan yasan zuciyar sa, ya san abin da ke damun ransa, ya san nata ne? Yanzu haka ma ita a binda ke damun ranta daban ne,. to in ba haka bane mai yasa suke kishin juna? Bai sani ba! Ba kuma ya son ya sanin, don sanin baya da amfani. Idan kuma ya dage sai ya sanin ba abinda sakamkon binciken nasa zai haifar face (bakin-ciki) tunda ko ko a garin gaba-gaba ake ba za’a taba barinsu su auri juna ba, to suma suna hauka ne? Kai Allah ya sauwake su ce suna son junan su, yaya ma hakan zai taba kasancewa? Ba komi ke kimsa masu wannan halakar a zuci ba face Iblis dan lis, (diabolical feeling). Don haka ya rage gudun motar ya safka a titi yace da karfi “A’uzu billahi minash-shaitanir-rajeem!â€? To bata zaci wannan kalamin ba daga bakinsa ba kwata-kwata a dai-dai wannan lokacin don haka ta tsorata, a tsammanin ta hatsari suka kusan yi, idanuwanta suka firfito cikin firgita dai-dai sanda ya kashe motar a gefen titi. Ya kwantar da kansa bisan ‘steeringâ€? suka kurawa juna ido yayin da kowanne ke kokorin fahimto boyayyen sirrin da ke zuciyar dan uwan sa, to amma ba wanda yayi nasarar hakan, ita ta fara kawas da kai ta maida duban ta ga motocin da ke gudun fanfalaki bisa kwalta, zuciyar ta cike fam da kuncin da bata san dalilinsa ba. Cikin karfin hali yace â€? Inteesar, baby, haba Sis, na hada ki da girman Allah kiyi hakuri, ni wasa nake Allah, amma da alama naga kin maida abin gaske?â€? Daga Intisar no response (ba amsa) kai kace da zaunannen dutse yake magana, yayi shiru, yama rasa ta inda zai faro, ya langabar da kai jikin ‘seatâ€? din shi abin tausayi don dai ta tabbatar yayi nadamar, cikin tattausar muryar shi yace. “Yanzu ke Sis (sister) in aka ce dake ina aikata abinda nake fadi sai ki yarda? Nayi zaton ke ce mutum na farko da zai shaideni a bisa norms and status (akidu da tsayayya) na Daddy Makarfi, ke ce (first) da zaki shaide ni (no matter what) al’amarin ‘may beâ€? (koda a wane irin al’amari ne kuwa)?â€? A nan ne ta dubeshi da dukkan idanuwan ta da suka kada suka yi jawur, wasu kibbau masu tsananin kaifi yaji sun gilma cikin zuciyar sa, ya runtse idon shi gam da karfi, baya iya jure kallon cikin idanun Saratou, baya son jin wadannan ‘feelingsâ€? din da yake ji game da ita a kullum amma a koyaushe ya dubeta tamkar ana linkawa ne, wayyo! Ya kai hannu saitin kirjin sa ya matse da karfi idanun shi a rufe, shi kadai ya san me ya ke ciki? Ji yake Saratu na huda bargo da tsokar zuciyar sa wani ‘feelingâ€? ne da ba zai iya suffantawa ba, ba tun yau ba, ba tun jiya ba, a tun ranar da ya dawo Abuja, sanda mahaifin su ke kulle, Inteesar taki gaishe shi don sun yi biris da tallafin Mamar ta, sunyi watsi da taimakon karatun ta. Abin ya cigaba beyond edpression (fiye da kimantawa) da har zuwa gidan ya gagaresa, yana ganin idanun Saratu sune magnet da ke jefa zuciyar sa cikin halaka da kaka-ni-kayi. Ya sha tambayar abokan sa masu kanne mata su gaya masa yadda suke a zuciyar su don ya kwatanta da nashi amma bai taba jin mai irin nasa ba. Akwai wani abokin sa Sagir da yace “ni kanwa daya ce da ni, duk sauran kanne na maza ne, amma yadda nake son su haka nake son ta ba wani banbanci, yo wane irin so ne zan mata da ya wuce in sa ido akan tarbiyyar ta? A kan me zan yi tunanin ta ina makaranta ko wani waje sai kace wata budurwata? Kai Faisal, gaya mun gaskiya, Inteesar, kanwar ka ce da kuke UBA DAYA?â€? Sai yace wallahi Allah kanwarsa ce. Sagir yace “to sai a nemi tsarin Allah kada ya kasance aikin Shaitan neâ€?. To kamar kullum, ya soma rokon sauki cikin zuciyar sa har ya samu ya dawo hayyacinsa, bugun da zuciyar sa ke yi ya lafa, sai da ta gama shan kamshin ta tace. “Ya Faisal ni ina ruwana ne? Me ka ji na ce? Kai kadai fa kake ta maganar ka, kake kidan ka kake rawarka ba matse ma baki nayi ba, in ma kayi din meye? Ba Mama tace lokacin ka ne ba?â€? Yayi murmushi a ransa ko cewa yake yaushe Saratu zata girma ne, komi nata akwai kuruciya a ciki, at 27, ya bata rata na akalla shekaru goma don haka lallashin ta ba zai yi wuya ba, ya ce, “Alright, na amsa wannan, ni dai so nake kiyi hakuri na san ranki ya baci, gashi mun kusa isowa gida, bana so Mamar mu ta ganki haka ‘bery-upsetâ€? (a birkice) don zata tambayeni ko? Gashi kuma ban san me zan ce mata ba.â€? Ta tura baki sabida matukar haushin da ya bata, ta soma motsi da bakin ta a hankali cikin tadin zuci, bata san har maganar ta subuto ta shiga kunnen sa ba. “A wane dalili raina zai baci? Sabida Yayana yayi budurwa? This is sheer nonesense!â€? (Shirmen banza ne kawai). Ta girgiza kai da sauri sai kuma hawaye suka zubo. Ya lakato hawayen yana murmushi ya ce, “you see, ranki ya baci. Hawaye su kan zubo a dalilai guda biyu ne kawai Intisar; bacin rai ko tsananin farin ciki. Saratu da ki zubar da hawayen ki a domina, gara kisa dorina ki yi ta duka na har ki huce bacin ranki. Your tears mean a lot to me, (zubar hawayenki na nufin abubuwa da dama a gareni) amma bazaki gane hakan ba a yanzun. Share hawayen nan maza-maza, don Allah ba don ni baâ€? muryar ta na rawa, kasa-kasa cikin rishin kuka tace “najiâ€?. Yayi murmushi yace “ba haka nake son amsar ba, cewa zakiyi shikenan Ya Faisal di na, komi ya wuce, na hakura, sa’annan ‘regain your mood (dawo da yanayin ki) Inteesar di na?â€? Ta shafi goshin ta zuwa siraran labbanta da ‘yan yatsun ta na dama, ita dai har yanzu RONKE na ranta, Ronke na damun ta, ta hana ta hadiyar miyau, da kyar ta hadiyi wani makalallen miyau daya bushe mata a makoshi, duk da taji matukar kunyar yadda yake mata magana a yau (lobing and romantic) tamkar ba Yayan ba, ta daure tace “shin wacece Ronke tukunnah?â€? Ya riga ya tsammaci tambayar, don ya san abinda ya tsaya mata a rai kenan don haka tuni ya shiryawa amsar ya ce, “kin san Allah Ronke class-mate (‘yar ajin mu) ce, ina koya mata karatu bayan wannan ba wani mu’amala tsakanin mu…â€? “wane irin ba affair (mu’amala) tsakanin ku to me ya hada ta da wayar ka?â€? Ya murmusa kadan “dauka tayi, tun kan in kai hannunaâ€? “to amma tace da ni wai kana wanka?â€? Yayi dan jim, yana tattara amsar daya dace ya bata, sai ta sake jeho mishi wata “kuma karatun ba’a makaranta ake yi ba, in haka ne ya akai har tazo inda kake wanka?â€? Ta kafe shi da nakasassun idanunta dara-dara farare kal, sai yace cikin kosawa tare da kokarin kaucewa kaifin idanun ta. “Amma dai kin san binciken abinda ya wuce baya da amfani, kuma rayuwa irin ta karatun jami’a cudanya da mata dole ne, abobe all ma Ronke kawata ce, tana zuwa gidan Major T. Ekiti inda nake zaune. Ta zo ne in koya mata karatu ina wanka, ta zauna jirana in fito a sanda ke kuma kika kira ta dauka, dama anan falo na ajiye, that’s all I know (wannan ne kadai abinda na sani).â€? Yadda ya fitittike yana bayani da sauri-da sauri duk sai ya bata tausayi, ya kuma bata dariya duka a lokaci daya, da gani zancen ya isheshi kuma iyakar gaskiyar shi ya ke fadi, amma sai bata nuna tausayin ba, ta sha mur sosai tace “ina na taba jin mace da namiji suna kawance? Wannan haramun neâ€? Yace “ni dai nace kiyi hakuri ko, komi ya wuce, daga yau nayi miki alkawarin ba zan sake kula ta ba tunda ranki baya so, ke da duk wasu matan duniya ma. Mace daya nake so, mace daya ke burge ni, mace daya nake so da kauna da dukkan ruhi na, mace daya nake sha’awar in aura amma ba zan taba iya auren ta ba. Don haka kar ki kara sawa ranki wai ni Faisal ina son wata diya mace bayan ita, ba kuma zan sake kula wata mace da sunan ina son ta ba har sai kin yi aure intisar, beliebe me or not, (ki yarda da ni ko kada ki yarda) ba zan kuma bata miki akan Ronke ba.â€? Yasa ma motar giya aguje suka harba kan titi basu sake ce da juna uffan ba. Maimakon zuciyar ta tayi sanyi da gane wasa yake zancen Ronke, kuma Yayan nata na masifar gudun bacin ranta, a’ah, sai ta kara yin bakikkirin ninkin ba ninkin kishin Ronke Adeyemi da kishin wannan da yake son bazai iya aure ba, don ta san koma wacece wannan son ba kadan bane ba kuma na wasa bane, he really mean it (yana nufin abinda yake fadi), ta gane hakan ta hanyar gesture (motsi mai nuna zahirin abinda ke zuciya) dake zane baro-baro cikin kyawawan kwayan idanun sa. How much do you like this story? 5/9/22, 09:56 - Ummi Tandama😇: _____________________________ *âœðŸ? SIRADIN RAYUWAâœðŸ?* Book two *@Takori* Page1ï¸âƒ£2ï¸âƒ£ Sai dai ko ba komi, ta yi farin ciki, farin cikin kasancewar a yau ta san tana da wani dan matsayi a Faisal, da ya wuce na Ronke Adeyemi. Alkawari na karshe da tayi da zuciyar ta shine bazata sake yin wani abu da zai sosa ran Ya Faisal ba, tunda kuma shima bai son tayi zancen wani (wanda dama ita wasa take) to hakannan zata kari rayuwar ta single ba aure don ma kar tazo auren ransa ya baci. Ita dai ta kasa gane irin wannan abu, ta kasa gane meke damun dukkannin su? Wannan kishin masifa kamar wasu mata da miji? Suna haukane? Wai shin a duniya akwai wasu ‘ya’yan da suke Uba daya da ke wa junansu irin wannan son? Cikin wannan dare mai kunshe da tarihin al’amura da dama cikin rayuwar su, daga Faisal har Saratu ba wanda ya rintsa sai juyi a kan gado. Tabbas son junan su ke dawainiya da zuciyoyin su yana yamutsa duk wani tunanin hankali da suka mallaka, wannan wace irin masifa ce? Daga Faisal har Intisar ba wanda ya taba kawo wannan a ransa ko a mafarki cikin shekarun da suka gabata, sanda take Riyadh har zuwa yankewar karatun ta sai ko yanzu da Shaidan ke neman kaisu ga halaka in har basu yiwa zuciyoyin su linzami ba. To ta yaya? Ba abinda zasu iya illa daukar gingimemen dutse su danne abinda ke neman tunkudowa daga kirjin su. Faisal Bello, matashi ne da tashen kuruciya, gami da jin dadin da yake ciki basu sa shi watsi da Addini. Don haka cikin daren ya mike ya gabatar da nafilfili na musamman yana rokon Ubangiji daya daura mishi wannan bala’I da ya yaye mishi, yo bala’I mana? To amma me? Tamkar ana kara iza wutar so da kaunar Saratu ne a kalbin shi. Ya durkushe bisa sallaya yayi kukan sa mai isar sa, kuka riris kaman ba namiji ba, namijin ma, Da ga Daddy Makarfi, kuka irin wanda rabon sa da yi tun wani duka da aka yi mai yana ajin karshe a sakandire daya zanawa wata yarinya jarrabawar lissafi, sai ko yau da son Saratu-Intisar ke neman narkar mai da zuciya. Hukunci na karshe daya yankewa kansa shine yayi nisa da Saratu, nisa ba kadan ba, wanda zai mantar da shi duk wani abu daya shafeta, tunanin ta, rayuwarta da matsayin da take da shi a zuciyar shi, ya tabbatar in har suna tare dole ne watarana abinda suke fakewa da ‘yan uwantaka ya bayyana zahiri ga iyaye da ‘yan uwan su da jama’ar duniyar ma bakidaya. Duk da yasan kasancewa ba tare da Intissar din ba, na nufin rugujewar rayuwar sa gabadaya kuma wani gibi da cike shi ba zai taba yuwuwa ba. Anya zai iya? To in bai yi hakan ba yaya zai yi? Tunda gashi har Goggon su na cewa (da su abokanen wasa ne da an musu aure), kenan ta fahimci duk fadan da suke takalar junan su duk cikin sigar SO ne? Son ma irin wanda ya fi karfin boyuwa a zuciya aka rasa yadda za’ayi da shi ya fiddo kansa kowa ya gani. A take ya amince da shawarar da zuciyar shi ta bijiro na tafiya (Birmingham) zurfafa ilmin sa (Masters) amma shi ba zai je soja kamar yadda Daddy ke so ba, ba don komi ba sai don kada ya mutu, ko a harbe shi bai ganewa idon sa wane irin (lucky man) ne zai sami Intisar a matsayin matar aure ba. Shi kam ina ma ba’a gidan su yake ba? Ina ma shi ba dan Daddy Makarfi ne ba? Ina ma shi dan Wa, ko kanin Daddy ne? Tunaninnikan da yake tayi kenan marasa kai da gindi har aka yi kiran assalatu a kunnuwansa, ya mike yana layi tamkar bugagge ya sako alwalla ya shiga nafilfilin da bai san iyakar su ba yana rokon mai canza al’amura daya canza mishi da mafi kyau. Karfe shidda dai-dai na safiyar ranar wadda ta kasance Talata, ya dauki diary din shi yayi wasu rubututtuka masu matukar muhimmanci a gareshi da Saratu, yana yi yana zubar da kwalla tamkar ba Faisal ba, ya hade duk wani abin amfanin shi da yake bukata cikin katuwar trolly ruwan bula mai duhu, ya shirya cikin suit baka da ratsin toka-toka sunyi masifar amsar shi, ya matse wuyan shi da bakin tie ya barwa al’ummar gidan (note) cewa yayi sammakon tafiya ya kama hanyar Ilorin inda yake hidimar kasa. Tunda Faisal ya tafi Ilorin ko waya bai yiwa kowa ba har tsayin watanni ukku cif, Daddyn na yi mai cuku-cukun tafiya Unibersity of Birmingham dake UK inda zai hado MSc dinsa wata kila ma har Ph D. Admission din bai fito ba sai a watan Mayu daga can ya tafi ko sallama bai zowa kowa ba, alhalin su Najib duk suna zuwa gida a duk karshen wata. Hajiya ta damu sosai. A watan Najib, Bello, Yasir. Nasir da Faruk suka sami aiki a garin Enugu inda suka yi bautar kasa, aiyuka kuwa masu gwabi (tsoka), shi Najib a (Petroleum Refinery) na Enugu, Bello (mai sunan Daddy) a kanfanin Inshora, Yasir da Nasir a NITEL sai Faruk a bankin (Inland) da gidajen zama da motocin hawa da komi. Sai gidan ya dade sai su Idris kananan dake makaranta suma basu faya zuwa ba sabida suna shekarar karshe karatun yayi masu zafi sosai. Haka kawai Intisar ta rika jin ranta na baci kamar koyaushe wani bakon al’amari zai faru da ita mai dadi ne ko mara dadi? Sai da Faisal ya cika watanni ukku cif yana karatu a Birmingham Daddy ya kira Hajiya yace da ita Faisal fa ya zarce UK yin M Sc din sa, in ya ga dama bayan shekaru biyun ya dawo, in yaso kuma ya zarce har Ph D ba zai takura mishi ba. Brigadier na girmama Faisal duk cikin ‘ya’yan sa a sabili da abubuwa guda biyu: juriya da karfin zuciya. Faisal ne a duk cikin ‘ya’yan sa zai ce mai yayi abu yayi koda ransa baya so, sannan duk cikin ‘ya’yan sa ba mai hakuri, nutsuwa da sanyin ran Faisal, yana da daukan komi na rayuwa da sauki, (sabanin Ameenu mai zafafawa akan al’amuransa). Don haka duk abinda Faisal din ke so yana kokarin yaga yayi mishi, in har bai fi karfin sa ba, baya son ya bata masa ko kadan kamar yadda shima yake mai biyayya da zuciya, gangar jiki da duk abinda ya mallaka yaron baya da kwaramniya ko kadan kwatankwacin su Najib, hakannan kome zai yi in ka auna sai kaga hikima a ciki, baya yin abu kai tsaye sai ya tabbatar yana da hujja na yin hakan. Don haka ko kadan bai damu da makudan kudaden da ya narkarwa Faisal yayi M. Sc a turai ba, shi dai burin sa ya sanya shi farin ciki kamar yadda yake sanya shi a kullum Hajiya ta gunduma ashar ji kake abu kazan uban nan…don me Daddyn bai gaya mata ba sai bayan ya tafi, kan me ba’a shawara da ita kan harkokin ‘ya’yan ta sai kace ba ita ta haife su ba? Ta tsuguna ta haifo dan a cikin ta a ce Saratu ce mai tsara mishi yadda take so? Yace tayi hakuri kada ta dauki hakki, Saratu bata ma sani ba balle ‘yar ta. Faisal dai dan sa ne, kuma shi ya roke shi alfarmar baya son kowa yasan zai tafi, sai bayan ya tafin, tace ai don ya san zata hana ne shi yasa ya hana a gaya mata, duk an tarwatsa mata ‘ya’ya cikin duniya an hana mata jin dumin su, alhalin ba’a san yadda tayi ta haifo kayan ta ba, ba komi yasa Daddyn yake barin su suna tafiyar ba sai don bai son ta ji dumin abinta, yana bakin ciki don matar sa bata da su a fake da karatu, to wane irin karatu ne da bai isa a yi shi a nan cikin kasarmu da manyan jami’o’in da mu ke da su ba? Ko su da basu yi ba karatun ba wani abu ya ragu a jikin su? Daddy Makarfi sai yayi dariya ya kamo hannun ‘yar rigimar yace “bai ragu ba kam, amma ai gaki nan kina abu kamar rudaddiyar tsohuwa ko ni nan na fiki wayewa.â€a kara kuluwa ta fige hannunta ta nufi kofa tana kunkunin Daddy ya gaya mata magana don ya nuna mata matar shi na aikin banki, har ita za’a gayawa wayewa, ita da take fita kasashen duniya saro zinarai take ciniki da matan manyan kasa bakidaya aikin kawai, ta sani dai baya shawara da ita kan harkar ‘ya’yan ta, to dai ita ce uwar su, wanna sunan (Nafi Uwar su Aminu) ba zai taba canzawa ba, kuma da tsohuwar zuma ake magani haka duk warin daddawar, ita ta gyara miyar (tana nufin ita da bata yi karatun ba, ita ce ta tallafi gidan a sanda aka garkame shi a kurkuku ba masu karatun bokon ba), fiye da wannan ma matsayin ta na mahaifiyar su ya dace a dinga neman yardarta kamin zartar da komi a kan su koda karatun ne. Shi kansa Daddy ya san ya bata mata kuma tana da ‘yar gaskiyar ta sai yayi ta lallashin ta, yana nuna mata menene don Faisal ya tafi Turai? Ita da kullum take hantara da kyarar shi ai jin dadin ta ne, sai tayi murmushi ta huce, ta fi kowa farin ciki. Tafiyar Faisalâ€? na nufin al’amura masu muhimmanci a gareta, tafiyar Faisalâ€? na nufin farin cikin ta, farin ciki ba daya ba, ba biyu ba hakannan ba uku ba, tafiyar Faisalâ€? na nufin cikar dadadden burin ta. Ko ba komi, Intisar za tayi bakin ciki, watakila har yayi sanadiyyar katse duk wani farin cikin rayuwar da take ciki a yanzu. Ita ko mai farin ciki ce da duk wani bakin cikin su Saratu a rayuwa. Saratu da Saratu zasu daina amfana da dan ta, zasu daina morar sa wanda wannan ba karamin nakasu bane ga rayuwar Intisar kuma cigaba ga wani specific (kayyadaddden) kudurin ta a gaba, wanda bai wuce na raba Saratu Da Saratu da duk wani farin ciki dake cikin rayuwar duniya. Sai tayi murmushi ta sawa abun albarka, tace da Daddy Allah yasa kada shi ya mancesu, ya guje su ya nisancesu tamkar Al’ameen. Daga Intisar har Antin ta sun ji tafiyar Faisal ne kamar daga sama. A falo Anti Saratu tayi ta kakabin abin Intisar na jin ta bata ce komi ba, hakannan bata juyo ba domin a lokacin tana wasa ne da kwamfutar antin tana ‘gameâ€? din ‘Mabis Beaconâ€?. Ashe wannan shine trauma din da take sunsune tun watannin baya; Rabuwa Da Ya Faisal! Idon ta suka yi rau-rau sai kwalla suka zubo masu zafin gaske, tasa bayan hannun ta ta share da sauri don kar Anti ta gani. Antin ta zauna shirim, cikin ‘leather seatâ€? din da suka yiwa falon kawanya tace “Saratu shine ko ki gaya mun Yayan naki zai tafi Birmingham?â€? Da Antin ta san kunci da tukukin dake nukurkusar zuciyar wannan baiwar Allah, hakika da bata yi mata wannan tambayar ba, amma Anti ce, bai yiwuwa ta kyaleta duk yadda taso yin hakan, duk kuma irin rashin son maganarta a lokacin, tace “Mamar mu babu abinda zan iya boye miki, in da ya gaya min zai tafi, abinda na sani kawai shine brother is in love (yana cikin soyayya) amma yace wai ba zai taba iya auren yarinyar ba, nake jin abinda yasa ya bar gida kenan. Amma ni ce shaidar cewa Ya Faisal ya tsani karatu ‘abroad (kasar waje)â€?. Anti tayi jugum, kallo daya zaka yi mata ka tabbatar tafiyar Faisal ya taba zuciyar ta, fiye da zaton Hajiya, ya takaita farin cikinta, fiye da yadda Hajiyar ta kintata a zuciyar ta, ta ce, “Oh ni Saratu! Ban da abun Faisal maiyasa ba zai fadi ba, sai ya bar kasar? Bana jin ko diyar wanene a garin nan da Babanku ba zai iya aura mishi ba. Allah to ya sa hakan shine mafi alkhairi.â€? Da daddare tayi shirin kwanciyar barci kamar yadda ta saba amma me? Idanuwanta sun ce basu san wannan ba. Tayi kukan ta mai isar ta, da ta kasa gane musabbabin sa. Ba zata ce son Faisal take ba, don bata san ma hakikanin menene son ba. Amma da tayi tsam da ranta ta fahimci kishin yarinyar da ta sa Faisal barin Nijeriya ne! Haushin tafiyar sa ya shafe kewar sa, mafi rinjaye shine irin matukar sabon da su kai da juna. Akwai wani kebantaccen al’amari game da Faisal a tare da ita, da ita kanta bata san menene ba. Abinda zata iya cewa shine Faisal, wani mutum ne precious wato (mai darajja) da kima agareta da muhimmancin sa da kimar sa ya zarta na kowa in ka dauke Daddy da Mamarta. Kenan mancewa da shi a tarihin rayuwar ta ko barin tunanin sa, wani abu ne da ba zai taba kasancewa ba!!! Mu karasa a littafi na uku, Takorin ku ce. Wa billahi taufeek! How much do you like this story? 5/9/22, 21:00 - Ummi Tandama😇: ____________________________ *âœðŸ? SIRADIN RAYUWAâœðŸ?* Book three *@Takori* Page1ï¸âƒ£ Lahadi/Jumada-Awwal Watanni Biyu Bayan Barin Faisal Satin Daddyn kwata-kwata biyu da fitowa ya shiga sabon ofis din sa a gidan shugaban kasa. Cikin watanni biyu rak arziki ya ci uban nada, rayuwa a gidan Brigadier Makarfi ta dawo sabuwa ful arziki wane shekarun baya. Sai da hankali ya natsa aka mance komi Aunty Saratu ta farkewa Daddyn gaskiyar Saratu bata kammala karatu ba. Daddy yayi ta fada har yana haki kan don me tuntuni bata gaya masa ba, da yanzu bata yi zangon karatun ta na farko a aji shidda ba, gashi shekara ta zo tsakiya tilas abarwa sabuwar shekara mai kamawa in Allah yayi tsawon rai. Amma kam ran shi ya matukar baci inda ya dauki duk laifin ya daura akan Anti Saratu. Ranar Lahadi, cikin sabon watan Jumada Awwal, ta shirya cikin wani lallausar material baki wuluk mai yarfen jajayen furanni. Curarraren gashin kanta ta nade shi tsaf cikin dankwalin kayan ta yadda baka ganin ko sili daya, kafar ta sanye cikin (bed-shoe) watau takalmin bakin gado, sannu a hankali take sauka daga benen sassansu tana bin matattakala cikin nutsuwa da yaukin ta na musamman da Allah ya hore mata. Tayi amfani da sassanyan turare (Week-End Burberry) sanyin kamshin na tashi daga jikin ta kadan-kadan inda duk ta gifta har ta iso falon hutawar Daddyn, da yake ranar Lahadi ce, ya kan kasance ne a falon yana ‘browsingâ€? tun safe har bayan karfe hudu na yamma baya zuwa ko’ina. Ta sakko ne musamman da niyyar bashi labarin Hidayah da Hunainah Bashir Sambo, kawayen ta na makaranta da suka shaku, bata taba yi mai zancen su ba, shi ko Daddyn komi nashi ita yake fara gayamawa kafin kowa a gidan har matan sa kuwa, tana ganin Daddyn zai taimaka ya binciko mata inda suka koma a Korea da adireshin su, kullum da tunanin da take kwana take tashi kenan, don dai hankalin su bai kwanta bane sai ko yanzun da take ganin ya dace Daddyn ya san da su Hidayah, har abada bazata taba mancewa da su ba. Yaran Sun zauna cikin kwakwalwar ta (like the screen saver of her imagination) Musamman Hunainah, kauna ce mai karfi take masu da har ta kan tambayi kanta, da su da Ya Faisal, wa ta fi kauna? Ta same shi da ‘laptopâ€? din shi ne kamar yadda tayi tsammani, sai ta ja kujerar da ke fuskantar shi ta zauna, suka dubi juna suka yi murmushi ta ce, “Daddy an tashi lafiya?â€? Ya ce, “Tunda ki ka ganni a nan ai zance ya kare, kin san tambayarki itace amsarki Saratuâ€?.â€? Magana yake amman hankalinta baya tare da shi, yana ga allon kwamfutar. Wani kayataccen rubutu ne Daddyn yayi, yayi mai ‘designâ€? mai kyau, da gani yayi ne don ado kawai cikin kwanfutar ba don ya aikawa wani ba, kalolin da aka kawata rubutun da su masu daukar ido ya dubesu ne koda bai yi niyya ba. A gurguje ta shiga bin rubutun bata sani ba ma a fili takeyi ba. “Although he refused to assist me when I needed his assistance most, I should, however, forgive him wholeheartedly.â€? Ma’ana “Duk da cewa ya ki taimakamin a sanda nake tsananin bukatar taimakon sa, duk da haka zan yafe mai da zuciya dayaâ€?. Cikin ‘yar karamar muryar ta ta ce, “Daddy waye wannan?â€? Yace “Yayan ku Al’ameen ko kin manta shi?â€? Ta kai hannu ta zare gilashin ta a hankali ta ce, “Al’amin kuma? Waye haka?â€? Cikin tsananin mamaki, zaka iya karantar hakan karara cikin abnormal (marassa lafiyan) idanun ta. “Muna da wani Yaya ne Aminu Daddy ko dai cikin dangi ne ta Makarfi?â€? Mamaki ya kama Daddy, ya ce, “Sanda Aminu ya bar kasar nan bakiyi wayau ba, Aminu ne ya janyo maki laluran ido, har da shi muka kaiki asibiti a Jeddah ba mamaki da baki san shi ba, abin mamakin shine ko sunan shi baki sani ba?â€? Ta ce, “Kwata-kwata ban taba ji a bakin kowa ba, ba wanda yake zancen shi daga Ya Faisal, Ya Najib har su Mamar mu ban taba ji ba.â€? Yayi murmushi ya ce, “Su Najib ai haushin sa suke ji, sunce sun fidda shi a layin ‘yan gidannan.â€? Abinda ta lura da shi shine idanun Daddynsu cike suke da kaunar dan shi Al’ameen da bege mai tsanani. Ta gyara zama ta ce, “Daddy a bani labarin Ya Ameenu?â€? Ai kamar mai jira ta tambaye shi, ya shiga bata labarin Al’ameen tun daga rayuwar shi ta kwaleji, hazakar shi irin nata, da yanayin mu’amalar shi da mutane. Ya ce, “Mutane da dama na mai mummunar fahimtar girman kai da wulakanci, amma ni nasan Al’ameen dina (gentle) ne kawai. A ‘ya’ya na ba mutun irin Al’ameen Saratu, domin shi din genius ne (mai madaukakiyar iyawa). Al’ameen nawa, yana kaunata sosai Intisar, ban taba zaton jin dadin turai da kyale-kyalen ta zasu sa ya mance ni ba balle…â€? Bai iya ya karasa ba sakamakon hawaye da suka shimfido mai a guje. Ya juyar da kai don bai son Sartun ta gani amma ta ganin. Tuni itama nata idanun suka cika da kwallah, tayi azamar mai da gilashinta tasa tissue tana share hawaye ta kasan gilashin. Tsana da haushin wannan Yaya Al’ameen ya dirammata tunda kuwa har zai sa Daddy kuka da azabar kewar shi, bata san sanda bakin ta yayi subul da cewa “Daddy maiyasa kake son Al’amin har haka?â€? Yayi murmushi ya ce, “biyayyar sa. Ban taba ganin yaro mai gudun bacin ran iyaye a duniya irin Al’ameen ba. Yana jin maganata yana yi mun biyayya, ban taba cewa ya bar abu yaki bari ba sai a kanki. Ya gaya mun sabida nadamar abinda ya aikata gareki ne ya bar mu kwata-kwata don aganin shi bashi da amfani a gareni…â€? Ya kwashe labarin komi ya gaya mata, bata yi wani mamaki ba, tunda kuwa dan Hajiya Nafi ne, ba illata ta ba, ta tabbata ko konata ne Hajiya zata iya sawa a yi. To amma albarkacin wannan son da ta ga Daddy na yiwa Al’ameen sai taji itama tana son shi, bata kullace shi ba ko kadan. Tabbas a lokacin zai kasance yana yaro ne cikin gigin kuruciya, tana da tabbacin da zai zo a yanzun he’ll be a caring brother (dan uwa mai nuna kulawa). Tace “Kaayi hakuri Daddy, ni na tabbata Al’amin zai dawo a lokacin da bamu zata ba.â€? Ya ce, “Kayya Intisar, Aminu fa har gaya mai akai an kulle ni, akan laifin da ya tabbatar ba zan taba iya aikatawa ba, amman yace wai zaman Amurka ya fiye mai kwanciyar hankali bazai dawo ba. Koma menene laifi na ne da tun farko na amince mai ya tafi. Ban taba kuka akan son dan da na haifa ba sai a kan Al’ameen. Ameenu yaro ne mai matukar shiga rai don haka fidda tunanin shi a lokaci guda, abu ne da bazai yiwu ba. Tunanin sa na azabtar da ni Saratu Ina kokari ina dannewa ne kawai don bana son kuma ku shiga damuwaâ€?. Inteesar tayi zuruuu tana sauraren Daddyn duk tausayin sa ya nannadeta, amma a ranta cewa take Allah ya isa tsakanin ta da wannan Ameenun, kuma wannan Al’ameen anyi tsinanne, tunda kuwa har zai iya sanya rayuwar Daddyn su a wani hali bayan wanda ya fito, kuma akan sanin kansa, suna murna duk wata matsala ta kare? Shin shi Ya Al’amin din nan bai tsoron hakkin Daddy ya hana shi kwanciyar kabari?â€? Ta tausasa halshen ta ta dukar da kai cikin matsanancin takaici ta ce, “Ba dai biyayya Al’ameen yake maka ba Daddyn mu? To na yi alkawari tsakanina da Sarki Allah zanyi ma biyayya Daddy irin wadda Al’ameen bai taba yi maka ba! Zan maye maka gurbin Al’ameen. Zan wanzar da rayuwa ta a biyayyar ka, zan dauwama a cikin umarnin ka in har bai sabawa mahalicci ba, bazaka taba sani abu in ki yi ba koda ya fi karfin lafiya, rai da abinda na `mallaka; sai dai in mutu a cikin umarnin ka Daddy!â€? Kalamun ta sun matukar bashi mamaki, hakannan sun girgiza shi amma bai nuna ba, sai yai murmushi ya shafi kanta da hannun shi na dama. Shi kansa ya san hakan a tun ranar da ya daukota cikin tsumman goyonta a dokar daji. Ya ga alamun hakuri, biyayya, kyautayi da jin kai tattare da ita. Yana kaunar ta, kaunar da baya yiwa daya cikin ‘ya’yan sa bayan Al’ameen. Ta ce “Wai shin ba’a bin sawun Yaya Aminu ne?â€? Ya girgiza kai, “Ba wai kudin ne babu ba Saratu. America kasa ce mai girman gaske, (It’s the greatest country of the world). Abin takaicin shine yana birnin Miami yana buya a cikin Florida kar mu gan shi ko kar mu san inda yake. In banda adireshin sa na e-mail ban san komi game da shi ba a yanzu. Kuma ke a tunanin ki yaron da ya watsar da iyayen sa akan kansa, bai son ganin su kina ganin ya dace iyayen su zubar da darajar da Allah yai masu ta iyaye su nemeshi? Ai har kullum da ke neman albarkar iyaye ba iyaye ke neman albarkar da ba. Yaran yanzu ne ka haife su amma baka haifi halin su ba. Duk in da uba ya kai ga gwada masu kauna da nema masu farin ciki su sai sun sashi kuka. Ba zan nemi Al’amin ba koda zan mutu ne ban gan shi ba, koda na mutu, Saratu ki gayawa Yayanku Aminu, son nan da nake mishi tun yana gudan jininsa, ina zumudin a haife shi in samu magaji, da kasancewar shi buri na ba abin da ya canza har gobe sai ma abinda ya karu. Kuma har cikin raina na yafe mashi kuncin daya dasa mani na shekara da shekaru.â€? Sai ta rufe bakin Baban su da tafukan hannun ta, kamar tace wayyo Allah! Sabida bakin cikin Al’ameen da mutuwa da Daddyn ke ambatawa kansa. Ta ce, “Insha Allahu Daddy ni da kai, zamu gayawa Ya Ameenu wannan. Daga yau zan fara Addu’a duk inda Al’ameen yake, Allah ya karkato da hankalin shi gida Daddy.â€? ***** Wani muhimmin abin farin ciki daya samesu bayan kubutar Daddy da ‘yan watanni shine bayyanar matashin ciki jikin Anty Saratu, farin cikin Inteesar a wannan dan tsukin kema kin san ba sai an fada ba. Daddy don farin-ciki makullin mota KIA ya danka mata fara sol ta fara zuwa sabon aikin da ta samu da (Afri-Bank). Gabadaya sun kirayi shekarar da watan Jumada-Awwal; ‘Cikar Burin Shekara Da Shekaru.â€? Dukkan Farin-Ciki Na Tafiya Ne Da Bakin-Ciki Laraba/Ashirin Ga Watan Jumada-Thani Ranar wata laraba, da saratu ta kira LARABGANA a gareta, ya kama ranar girkin Antinne don haka tayi mata sallama ta nufi sassan Daddy, duk ranar girkin ta haka suke wa juna, babu zancen kunya tsakanin Saratu da diyarta Saratu. A lokacin cikin ta ya shiga watanni uku duk wasu alamomin mace mai juna biyu sun gama bayyana a jikin ta. To bayan fitar Antin har goma na dare Inteesar na falo kwance cikin (rest-chair) dake falon tana sauraron labarun ‘networkâ€? daga gwanin ta Cyril Stober da Hawwa Baba Ahmed bata san sanda barci mai nauyi ya dauke ta ba, sabida a yau wuni sukai girke-girken Daddy ita da Mamarta ko na minti biyu ba su huta ba. Ba ita ta farka ba sai karfe ukku na sulusin dare shima sakamakon masifafffen sanyin da taji yana hurata ne, ta yayibi bargo ta ji wayam. Ta mike taga yadda ta bar komi a kunne ta kashe talbijin da ke ta shuuu! Da sauran kayan wutar da ke falon. Ta daga labule da niyyar kashe fitilun falon ta je ta kwanta kenan taji motsin ana taba kofa. Cikin ta ya hautsina ji kake kulululuuuu! Musamman data tuna bata rufe ko kofa daya ba bayan fitar anti, a guje ta shige bayan labule ta sandare ko kwakkwaran numfashi ta kasa shaka balle ta fesar. Ba abinda ta kawo wa ranta a lokacin face gaggan ‘yan fashi ne suka kawo masu ziyara, amma wannan ba karamin abin mamaki bane in akayi la’akari da irin sojojin da ke gadin gidan Bello Makarfi tuni ta soma hawaye, a lokaci guda kuma fitsari ya kulle mata mara. Bata san sanda ta sakeshi daga tsayen ba.Tsoron ta Allah, tsoron ta kada su taba lafiyar Daddyn ta. Ko wannan shine dalilin yin zancen mutuwa da Daddyn yayi mata a kwanakin baya? Daga inda take rakube a bayan labule, tana iya hangen kofar shigowa falon su kasancewar labulen shara-shara, kuma dakin gauraye yake da hasken da Allah bai bata ikon kashewa ba. Tana ganin sanda aka turo kofar falon cikin nutsuwa da sanda, ba abinda ‘yan idanun ta basu gane mata ba kasancewar akwai wadatar hasken kyandir kamar safiya. Sanye da bakar zulumbuwar riga, kanta a tsefe, tana rike da bakar kwarya a hannun ta na dama, wata bakar tsuntsuwa ce da ake kira mujiya matacciya rike a hannunta na hagu; Hajiya Nafi ce. Kanta tsaye ta murda kofar dakin barcin Antin ta shiga, tafi karfin awa daya kamin ta fito, tuni numfashin Intisar ya dauke. Ashe bata gama razana da mamaki ba? Da ta fito daga dakin Antin dakin Intisar din ta afka gaba-gadi. Ji tayi kamar tayi ihu amma sautin ya dauke kakaf. Me wannan baiwar Allah ke yi masu haka a dakuna cikin irin wannan talatainin dare? Nan ma tafi awa biyu kamin ta fito. Ta diba gabas, yamma, kudu da arewa bata ga kowa ba, sai kurum ta fice ta jawo kofar. Daga kwaryar har tsuntsuwar, sun bace bat. Wai a wauta irin tata, sai ta sheko da gudu ta lelleka dakunan ko zata ga in da ta aje masu kwaryar da mujiyar? Tunaninnika iri-iri ke shigar ta. Mafi rinjaye shine Hajiya na bakin ciki da cikin da Anty Saratu ke dauke da shi, shine tazo tayi mata wani mugun abu? Ta sha jin ana cewa Anti Suwaiba aminiyar Hajiya matsafiya ce ta kuma dade tana son sanya Hajiya a turbar tsafe-tsafe Hajiyar na ki, don ita Hajiya na daga cikin irin matan nan da basu yarda cewa asiri shi zai kwato masu miji ba sai power din su da kaifin bakin su. Wato yanzu cikin Anti yasa ta bi layi kenan? Har aka yi kiran assalatu tana rakabe a bayan labule cike da tunani da tsoro. Ba ita ta fito ba sai karfe biyar na asuba a lokacin da ta ji masallacin da ke makwabtaka da su ya kira sallah, jikin ta ba inda baya rawa ta shiga toilet din dakinta ta dauro alwalar sallar asuba, ta fara da raka’atainil fajr kamin ta bada farali. Ta kara da nafilfili na musammam tana mai rokon Allah ya kare su daga duk wani mai nufin su da mugun abu. Ta cigaba da karanta Suratul Kahfi har zuwa wayewar gari. Nan akan sallayar barci mai nauyi ya sureta. Da safe ta fita baiwa ‘yan aikin su umurnin abinda zasu hadawa Daddy da Anti karin kumallo, sai ta jiyo motsin Antin a daki, kamar tace wayyo Allah! Taso ta gayawa Antin abinda ya faru a daren jiya tun kamin ta shiga dakin gashi ta riga ta shiga. Tayi tunanin fadar ma bashi da amfani tunda yake ita din ma ai ta shiga, ko ta fada sai dai kurum ta tayar mata da hankali a zo a bata tara daya bata gyaru ba, don tasan halin Mamarta sarai cewa za tai sai anyi abinda za’ayi a gidan kuma kenan ita ta tayar da tarzoma ana zaune lafiya? Ta amince ta kuma hakkake cewa a duniya babu wanda ya isa yayi masu abinda Allah bai masu ba, to akan me zata dami kanta? Sai kawai tayi watsi da al’amarin. Sati daya da faruwar wannan rannan Daddy na sassan su, a lokacin tana kwance a dakin ta tana nazarin wani tsohon littafin larabci na Alfu-Lailah (Dare Dubu Daya), kamar a mafarki, sai ta jiyo Daddy na zagin Anty Saratu yana cewa, “Ke har kin isa ki gaya mun magana, naki in maidata makarantar, ko an gaya maku tono kudin nake? Idan bazaki maidata FGC Kazauren ba da kudin ki, kar Allah ya sa ta je, an gaya maki na damu da harkar ku ne matsiyatan banza da baku san ku taimakawa mutum ba koda kwandala sai dai ya baku, mts!â€? Ya ja wani dogon tsaki ya fice a fusace. Kirjin ta ya wani irin buga, jikake dammm! Me kunnen ta ya jiyo mata haka? Daddy ne yake cewa bai damu da su ba balle karatunta? Kai, wannan mafarki ne it’s only a bad dream (mugun mafarki ne kadai) bazata taba amincewa da abinda kunnuwanta suka jiyo mata a yau ba. Tayi saurin yasar da zancen shiyasa akace sauraron hirar mutane ba kyau, don wata rana bazaka jiyo wa kanka alkhairi ba. To Allah ya gani dai ita ba saurara tayi ba shi Daddyn ne yake yi da karfi. Ta kudurce daga yau koma waye yake magana da karfi, in har ba da ita yake ba to zata toshe kunnuwan tane. To sai me? Ta hadawa daddy abincin rana na Dolmah Stuff Cabbage, Fried Beef da Stuff Atomy a washegarin ranar. Duk gidan ya karade da kamshi a lokacin yana sassan Hajiya, to ta saba inda duk yake nan take kai mai abincin duk ranar girkin Antin in tayi ko antin tayi. Daddy da Hajiya na bisa tebur suna cin abinci, tayi sallama amma ba wanda ya amsa bata kawo komi a ranta ba cikin dariya tace “ayya Daddy, nayi latti ko?â€? Dai-dai sanda ta aje tray din a gabansa. Wani uban kallon tsiya da ya bi tangarayen da shi ya tsoratata ya ce, “Ke daga yau ke da uwar ki kada ku sake wahal da kanku wurin dafa min abinci, don na gaji da gishirin da kuke cika min, right?â€? Idanun ta suka ciko da kwallah, gwiwoyin ta suka sage, ta tuna tun tashin ta kullum ta yiwa Daddy abinci yabawa yake ya sa mata albarka, haka anti Saratu. Dai-dai da rana daya bai taba cewa ga abinda bai mishi ba a girkin su sai girkin Hajiya. Rannan ya ce inda ba’a kan idon shi anti Saratu ta karanci ‘Insuranceâ€? ba da ya ce nutritionist ce, ko yaushe suke cika gishirin oho! Abinda ta ji kwanaki ke neman zama gaskiya. A tsukin ta lura kwata-kwata Daddy ya dauke kafar sa daga sassan su haka Aunty Saratu ta daina girki amma dai-dai da rana daya bata taba nuna mata hakan a fuska ba. Data gaya mata abinda yace kwanaki game da girkin su sai tace wai itace tayi kuskure ta sanya mishi gishiri (3-spoon) kwanaki a dankali. To amma me? Kwanaki ta shiga dakin Antin sai ta tadda ta tana wani rubutu da ‘chalkâ€? a bayan kyauren bandakin ta, tayi abinda ya shigar da ita ta fito. Da ta tabbatar antin ta shiga wanka sai tazo ta karanta, ba komi bane illa (off-duty 29/9) wato Daddy ya dakatar da ita girkin sa a ranar ashirin da tara ga watan tara. A da, kullum ta Allah masu aikin gidan kan shigo da kayayyakin abinci iri-iri daga katon na juices zuwa na sauran kayayyakin bukatar yau da kullum amma yanzu kwata-kwata ‘storeâ€? din su ba komai duk na Hajiya Daddy ke cewa su kai. Rannan taga Antin ta debo kudi ta kira direban cefanen gidan tana lissafa mai abubuwan da zai sayo mata. A daren ranar ta shiga dakin Antin ta gaya mata kawar ta Hajiya Zainab na kiran ta a waya, sai ta taddata rub da ciki tsakiyar gadon ta tana girzar kuka. Tayi saurin komawa da baya ta kife wayar ta kifa kanta a jiki itama tayi ta kuka har Allah ya gajishsheta. Ta tabbatar Anti na cikin matsananciyar damuwar yadda Daddy ya yi watsi da su. To amma maiyasa bazata gaya mata ba su taru suyi ta kukan tare? A rayuwar ta, bata taba ganin Anti tana kuka ba. Mace ce tamkar da maza; zuciyar ta mai tauri ce, ba kowanne kankanin abu ke sata kuka ba. Shin ko wannan shine gaskiyar abunda kunnuwan ta suka jiyo mata kwanaki? Me yasa su basa dauwama a farin-ciki ne? Ta tambayi kanta wai meyasa rayuwar su ke juyawa ne tamkar a majigi? How much do you like this story? 5/10/22, 09:39 - Ummi Tandama😇: ____________________________ *âœðŸ? SIRADIN RAYUWAâœðŸ?* Book three *@Takori* Page2ï¸âƒ£ Alhamis, 1 Ga Watan Rajab Da Karfe Bakwai Dai-Dai Na Safe Ya shigo sassan su kamar abin arziki, ga dukkan alamu yayi shirin ofis ne yana magana a waya. Dadi ya kama Inteesar don rabon ta da ganin sa ma har ta manta. Kacokam komi nashi ya maida shi hannun Hajiya. Itama Antin tayi shirin tafiya aiki, ya zo ya wuceta fuuuâ€? kamar guguwa ko kuma wanda aka tankado tana zaune a falo ko dubar sashen da take zaune bai yi ba ya fada dakin Antin.Tana zaune tayi tagumi da hannuwa bibbiyu cike da damuwa, sai ta jiyo hayaniyar su, Daddy na cewa. “Wannan lalataccen aikin daga yau na soke shi, don ba mutunci na bane, na kuma gaji da maganganun da ake yada mun akan na bar matata tana aiki alhalin ban rage ku da komi ba. Meye amfanin ni in fita ke ki fita waye mijin? Sam da sake, ba kuma zai yiwu ba sai a sake lale, wannan ba tsari na bane. Don wa nake nemowa ba don ku ba ina na gaza a bukatun ku?â€? Tace “da da ne ka ce in bar aikin a sanda kake mijina sai in bari ba a yanzu da kake Mijin-Hajiya ba. Da baka san ci na ba balle shana, uwa-uba bani da hakkin matar aure don ni ba mutum ba ce koko don anga ina shiru kuma sai a sa bakin ciki ya kasheni in ban fita na nemowa kaina abinda zan ci ba, kokuwa mu dabbobi ne ka daure? Ita matar ka da ke fita kasashe kwana da kwanaki tana cinikin ta ita ba’a kawo ma gulmar ba sai ni mai zuwa aiki in dawo?â€? Ya soma nuna ta da dan alin shi “idan zaki yi rainin ki, da dibar albarkar ki, ki tsaya a kaina, don in kika tabo uwar ‘ya’yana sai in kakkaryaki baras-bas irin yadda ake karya karan raken takanda, ki na ji ko?â€? (Yana nuna irin baras-bas din da zai yi mata da hannayensa). “Ashe dama baki da kunya Baffa ya rufe cikin mayafi ya bani, duk wannan sunkuye-sunkuyen kan naki na munafurci ne?â€? Tace “oho dai! Dadin ta dai ba cewa akai tilas ka aura ba, tayi aka yi mana dukkanin mu muka amsa, ni banyi nadamar tsohon da aka lika min ba ina gabar kuruciyata sai kai? Ka sani dai ko yau kasuwar ta watse dan-koli ya ci riba, zan kuma iya auren kamar dan ka AMINU wanda yasan darajar aure ya kuma rike ni da mutunci ba kamar kai shanyayyen tso…â€?.â€? Fauuuu! Ya dauketa da mari yace “ni kike gayawa wannan maganar? Idan ba aure ni ba Yayanki bane? Banza gantalalliyar turai dama auren irin ku (kwantan ‘yammata) ai sai mu din. Amma tunda kin ce zaki auri kamar da na, to je ki na sakeki ki auri kamar Aminun in gani, ina kuma jiran katin gayyata…â€? tana murmushi tana zare shimfidar gadon ta tana cewa “in ma gantalin ne ai kai ka dauren gindin yin sa, da kwabon ka da nairar ka babu ko kwandala ta a ciki? So what in an sake ni dama banga banbanci ba da wannan zaman mahon da nakeyi, baka san cin mu ba, baka san shan mu ba above all ma bani da hakkin aure ai akuyar daure ce ta samu sake, ba sai gantali ba? Aure kuma da yardar Allah Brigadier zaka sha mamaki, ke Saratou! Hado kayan ki maza-maza mu bar masu gidan su (Ardhullahi-Wasi’a) duniyar Allah ai tana da fadiâ€?. Har ya kai bakin kofa ba tare da ya kara kulata ba, amma jin abinda tace sai ya komo da baya, ya dubeta sosai da idanuwan shi da suka kada suka yi jazur kamar gauta “ta je ina? Sai ki gaya min in ke kika haifeta, ko ke kika kawota gidan?â€? Kirjin Anti Saratu ya bada wani irin hargagi. Ta rude ta rikirkice ta kasa cewa komai. Duk wata tsiwa da ta ke ji a dole jikin ta yayi sanyi. Tun zuwan Intisar hannun ta bata kara tunawa cewa ba ita ta haifeta ba. Tsoron ta Allah, tsoron ta kada ya kasance Saratu da ke falo ta ji abinda mutumin da ta rika a matsayin mahaifin ta da bata hadashi da kowa a duniya ya fada. Sai ta zube ragwaf a kan gwiwoyin ta ta kasa magana sai hawaye shar-shar! Ke zubar mata. Bai tsaya sauraron ta ba yayi tsaki ya juya abin shi don kuwa rokon shi take kada ya gayawa Inteesar ba sune iyayen ta na hakika ba. Yayi ficewar sa ba ko waiwaye yana kara jaddada mata kada tayi rabin awa bata bar mai gida ba, ko allurar ta baya so a dakunan sa. Inteesar tsuma take tamkar mazari ita kadai a falo. Duk hayaniyar da suke akan kunnenta ko kalma daya ba wadda bata ji ba. Cikin dan lokacin zazzabi mai zafi ya rufeta kafafun ta suka kasa daukar nauyin ta, ko wani kwakkwaran motsi ta kasa tamkar sassakakken gunki. Ba abinda ke ta amo a kwakwalwar ta kamar wai Daddy ya saki Mamarta kuma wai bazata bita ba? Kwakwalwarta bata fahimci me Daddy ke nufi da “ita ta haifeta ko ita ta kawo ta gidan baâ€? illa tana tsammanin Daddy na gadarar shine Uban ta kawai, hakannan bata ji irin rokon da Antin ke masa ba don muryar Antin ya dushe gabadaya a lokacin. Bata gama dawowa hayyacin ta ba sai gani tayi Daddy na (ball) da komi na falon su, yana hada crystal da marble karar babu dadin ji tamkar wani mahaukacin kare. Ya daga t.v da hannu daya ya hada ta da garu, gilassan na kwarara a kasa cewa yake “ba dai ni na saya ba? To bazaki tsira da komi nawa ba Saratu including ZUCIYA ta mallakin watan ki ce. Cikin jikin ki ma bana so kije ki bawa kamar Aminun! Yadda kuma kika karya zuciyana sai wani ya baki (hundred %). ‘History will Insha-Allah repeat itselfâ€? (da yardar Allah tarihi zai maimaita kansa). Ina nan ina zuba idon ganin mijin ki yaro KAMAR AMEENU!!!â€? Daga ji zaka san kishi da bakin cikin wannan kalma shi ya fi komi bakan ta mai rai. Gabadaya ya koma tamkar wani ‘lunaticâ€?. Itama Intisar din hankadata ya dinga yi da kafa da hannu har sassan Hajiya. Gidan ba kowa duk suna makaranta. Hajiya na tsaye a falonta cikin shiga ta alfarma tana saitin eriyar talbijin, ta daure fuska sosai ta nufe su tana tada Inteesar din “haba Alhaji, in taku ta hado ku da Saratu ita Intisar meye laifin ta?â€? Hawaye yake sosai yana cewa “kyale ni Nafi, daga ita har uwar ta bakikkirin nake ganin su wallahi. Daga yau zan sallami duk ‘yan aikin gidannan, gata nan (ya nuna Intisar) da ke yashe a kasa cikin yanayin fita hayyaci) ita zata dinga yin komi na gidannan. Idan kika tausasa mata ban yafe ba, idan kika dai-daita matasayinta da na ‘ya’ya na cikin gidannan Allah ya isa tsakani na da ke! Ki kaita dakin ‘yan aiki yanzu-yanzu ba sai an jima ba.â€? Hajiya tayi salati tace “Alhaji duk me yayi zafi haka? Me Intisar din naka tai maka?â€? Ya ce, “Ashe yarinyar nan Saratu bata da mutunci, ta dubi tsabar ido na ta zaga da girmana da mutuncina da komi. Wai Saratu ce za ta ce da ni zata auri kamar Aminu? Don ta ga ina bautuwa a kaunar ta da ‘yar ta shine zata farke mun laya aka? Allah ko zumuncin mu da Baffa zai watse bana auren! Ta je ma duk inda zata Umma ta gaida Assha…â€? yayi sama kamar kububuwa yana ta fadace-fadace tamkar ba Brigadier Bello Makarfi ba, mai sanyin hali kamar ba soja ba, wanda ko hantara wannan bai taba hada shi da iyalin shi ba. Inteesar tayi tsammanin wannan mutumin da ke tsaye ba Daddyn ta bane wani ne dai mai tsananin kama da shi. Ta kasa yardarwa kanta da gangan cewa wannan juyayyen mutumin Daddy ne! Wani abu mai tsini kamar kibiya ta ji yana sokar ta a kahon zucci, yana keta tsakiyar kirjin ta don bakin-cki, takaici da mamaki. A hankali taji idanuwanta na rufewa don kansu ba tare da ita din ta san hakan ba. Tun tana ganin dakin dusu-dusu har duhu ya mamayi ganin ta. Bata kara tsinkayar me ke faruwa a duniyar ba. ***** Ruwan kankara ne ya farkar da ita daga dogon suman da ta yi. A hankali idanuwanta ke washewa tsayin minti goma kamin ta fahimci a dandaryar dakin Dela take kwance (mai aikin Hajiya). Sannu a hankali ta kai hannun ta ga goshin ta wanda take ji yayi mata matukar nauyi, to ba abin mamaki bane da taji shi ya haye yayi suntum sakamakon watsota da Hajiya tayi dakin da ka. Ta motsa da kyar, kasusuwan ta suka bada wata matsiyaciyar kara a sa’ilin ne ta fahimci a dandaryar marbles take kwance kasancewar ciki da wajen gidan Brigadier da marbles aka yi shi. Lokaci guda zuciyarta ta shiga tariyo mata abubuwan da suka faru tamkar a majigi. Ta tabbata kyakkyawar rayuwar su ta da ta zama tarihi kenan. Ta rabu da MAMAR TA, bata kuma da halin tadda ita, hakannan Daddy ya juya masu baya tamkar bai taba sanin su ba tsayin rayuwar sa. Daddy ya dankata a hannun Hajiya, matsayin ‘YAR AIKIN TA ba shi kuma da bukatar ganin ta kwata-kwata. Zata so kwarai ta ga Aunty Saratu a wannan lokacin, su rungumi juna su koka abinda ya same su. Ita kadai zata iya fassara zuciyar Antin a yanzu, ta tabbata tana cikin kunci ninkin ba ninkin wanda ta ke ji. Bata taba tsammanin zasu kuma gamuwa da wani bakin-ciki ba a rayuwar su bayan na kulle Daddyn su, ita wai me yasa rayuwar ta ke da SIRADI iri-iri ne? Ta tuna yadda tun tana mitsitsiyar ta Hajiya ta tsaneta, take fadi a gaban kowa ta tsaneta take gaya mata gaba da gaba cewa ta tsaneta fiye da kowa a duniya to balle yanzun da ta dawo karkashinta, karkashin ikon ta, matsayin bolar daddy ta san ita kam tata ta kare. Dama dai Faisal na nan ne ta san bata da kaico. Yau ne ta ji kewar Faisal fiye da kowacce rana ta kuma ji haushin sa duka lokaci daya don tana ganin kamar dama ya riga ya san duk abinda zai faru da su a gaba shiyasa yayi tafiyar sa ya bar masu kasar su karata su kadai tun kamin faruwar abin. Tayi tunani iyaka tunani me suka yi wa Daddy haka da zafi ya sanya su cikin irin wannan ukuba? Iyaka tunanin ta bata gani ba domin a kullum cikin tattashi da tattalin Daddy su ke, da aikata duka abinda yake so da gujewa bacin ransa ita da Anty Saratu. Dai-dai da rana daya bai taba cewa sun bata masa ko sun yi masa ba dai-dai ba in ban da jinkirta maganar karatun ta da Antin ta yi bayan fitowar sa inda duk ya daura mata laifi. Bayan wannan bata san wani ba. Ta ji matukar haushin Maman kan rashin kunya da cin fuskar da tayi-tayiwa Daddy har ranshi yayi bacin da ya gwammace yanke masu wannan hukuncin, amma da tayi wani zuzzurfan tunani sai bata ga laifin ta ba don itama yayi matukar bata mata kuma shi bacin rai ba abinda bai sawaâ€? Tunanin ta bai kare ba taji an murdo marikin kofar dakin an shigo. A hankali ta cira kai ta dubeta, Hajiya ce. Sanye cikin tsalelen lesi ‘jackardâ€? in banda wani masifaffen kamshi ba abinda ke tashi jikin ta, ke da gani kinsan anyi wa maigida kwalliyan dare ne sai taunar cingam take kas-kas-kas kamar wata budurwa. Ta ja kunshin kayan Dela ta zauna sosai ta dubeta ‘thoroughlyâ€? tana murmushi ta ce, “Saratu mai sunan Saratu, jikar Goggo Jummai!â€? Idan kunshin kayan da take zaune a kai ya amsa, to itama Saratun ta amsa, ba kuma don komi ba sai don wani masifaffen tsoron Hajiya da ya kara cikata. Jikin ta ya soma kyarma amma bata ce komi ba. Hajiya ta ce, “Karkade jajayen kunnuwan ki ki ji ni don kalma daya ta subuce maki cikin wadanda zan furta, kikayi watsi da ita, kamar kin yi watsi da lafiyar ki ne. Kin ji dai yadda babanki yayi da ke, ba don ma ya roke ni alfarmar kada in gaya maki wani sirri da zai narkar maki da zuciya farat daya ba dana gaya maki ko don in samu zuciyar ta buga ki mace kowa ya huta don banga amfanin rayuwar ki ba a halin yanzu, bata da maraba da ta gawar da ta ki rami, to amma duk ranar da kika kawo ni bango zan farke miki ne yadda bakin-ciki zai kayar da ke in tura ki ramin koda ta karfi da yaji ne. Na rasa dalilin da ya sa kika shiga rayuwata kika yi kane-kane a zuciyar ‘ya’ya na, bayan ni na tsane ki don haka dole nima in shiga taku in kacaccalata in dai-daita ta, yadda kika dai-daita min ta iyali na kasa jin dumin su, kema kin bar jin dumin uwar ki kenan har abada. Naga abinda Aminu ya rubutowa Alhaji, cewa nadamar abinda ya aikata gareki ne yasa ya nisance ni, na kuma fahimci Faisal ma don ke ya bar ni. Kodayake bana bakin-cikin wannan tunda ko ko ba komi, na tabbata kin dandani bakin-cikin tafiyar sa fiye da ni, ni ko mai farin-ciki ce da duk wani bakin cikin ki Saratou! Saboda haka ina mai tayaki murnar wannan sabuwar rayuwar da kika shigo, kin san sunanta?â€? Ta dubeta sosai tana murmushi ta kanne ido daya ta sunkuyo dai-dai kunnen ta ta ce, “SIRADIN RAYUWA! Daga tsallake siradi sai me? Sai makoma. Kin san makomar ki Saratu? (ta nuna can cikin kasa da dan yatsan ta), ba kuma kashe ki zanyi ba, don bana kisa, ko kyankyaso ban taba gwada kashewa ba, wani daddatan labari ne kunshe a dan bakinnan nawa zan baki, shine gubar ki, kina sha zaki mace, don nasan rarraunar zuciyar nan taki da Daddy da Mama suka yi kane-kane a ciki, bazata iya jurar sa ba. Ba wannan ne makasudin zuwa na ba, na zo ne in tsara maki sabon zaman gidan Daddy Makarfi. Da farko dai dama can kin san na tsaneki Allah abin haka yake har gobe na tsaneki Intisar, kin san wannan farin sani ba sai na maimaita ba, to balle yanzun da Allah ya kawon tsuntsun daga sama gasashshe, ba sai in yaga ba son raina, ko ya kika gani?â€? Ta kafeta da dara-daran idanun ta, bata san sanda ta ce “haka ne Hajiyaâ€? ba. Tayi murmushi ta cigaba tana irgawa da ‘yan yatsun ta daki-daki. “Da farko a kullum in kin tashi da Asuba ba bu zancen komawa barci sai kuma na washegari in Allah ya kaimu, zaki dauki tsintsiya da injin shara ki share falullukan da dakunan hutawa da na barcin gidannan gabadaya ciki da bai din su, banda na Daddy, daga yau ba ruwanki da rayuwarsa, abin nufi, manta kin taba sanin wani Daddy a rayuwarki ya zama tarihi! Ko gaisuwa tsakanin ku ta kare!! Ki share dakin baki da garejin motoci, sai ki tattara kayan abinci ki wanke ki hada mana karin kumallo, duk gidan cin mu da shan mu ya dawo wuyanki, Allah ya so takaita miki wahala yarana duk suna kudu sai ‘yan biyu na da dan auta da girkin gidan kadai ya kashe ki, dama gaki nan a fige ya kazar mayu ‘ya’yan mutsiyatan kauye kawai, ki gyara dakunan su Khalil da sauran kusufa-kusufa da sako-sako na gidannan, ki kula da ‘kitchenâ€? kar in ga komi (out of order). Haka ‘diningâ€? din gidannan in son ganin shi yana yana sheki da walkiya kamar kullum, ki kula da goge ‘sliding doorsâ€?, tagogi da kayayyakin wuta, idan naga kura ko yaya take wannan kinibabbiyar uwar taki ta kauye zan ci. Bandakuna (toilets) din gidannan ina son a kullum su fi ki fari su kuma fi Faisal dina kamshi. Abinci kullum in ji shi da taste (dandano) irin wanda kika saba yi wa Alhaji a sanda yake Babanki, don cewa zan yi ni na yi, kin ga ai bai dace ya ji shi ba dandano ba ko?â€? Hawaye na mata lugulgude a fuska tace “haka ne Hajiyaâ€?. “Yauwa, ashe kina fahimta na. Wannan gilashin da kike mannawa safe da yamma, kina zama tamkar ‘yar India don kyau a fake da laluran ido, daga yau na kwashe su na farfasa na karkarya na zuba a masai. Ba makanta ba, buri na dama ki nakasa, to akan me zaki sami dan jagora ina ji ina gani? Dama don karatu aka yi su, to karatu ke da shi sai ko a lahira in ana yi, kin ga kuwa ai ba su da amfani ko?â€? Cikin sheshshekar kuka tace “haka neâ€?. Tayi murmushi “ka ji yarinya mai ‘chemistryâ€? komi aka ce kya amsa, ko ba haka na ji tsohon Babanki na cewa kin kware akai ba?â€? Tace “shine Hajiyaâ€? ta tintsire da dariya tace “wai meyasa kike son ‘ya’ya na ne, bayan ni na tsaneki? Har kullum mutum kan yi nisa ne da jinin makiyin sa, ban da ke. Don naji an ce komi Faisal kike ambato, har kuka kika yi da ya bar kasar, yayi miki kama da ‘ya’yan mutsiyatan kauye ne?â€? Ta girgiza kai cikin dimuwa. Hajiya ta ce “yauwa! Daga yau kika sake koda kallar min’ya’ya sai na sa wuka na tsokale wadannan lumsassun makafin idanun munafurcin, kina ji na?â€? Tace “ina jin ki Hajiyaâ€? a ranta ko cewa take …ba Faisal ba, ba Najib ba, ba Khalil baâ€? duk wani jinin ki ma idan na sake daga ido na dubesa ba da kiyayya ba ki ce ni shegiya ce na amince.â€? Hawayen da ke surtu bisa kundukukinta basu katse ba haka bugun bakin-cikin da zuciyarta ke yi bai tsagaita ba, ta dago ta dubi Hajiya Nafi, Hajiya Murmushi kawai ta ke tamkar gonar auduga “karki manta da wanke ‘fridgesâ€? din gidannan dukkan su kullum ranar Allah, ki farke katon-katon na lemuka ki jera mana, randa naga kin sha ko daya sai na maida ke mummunar da babu wani da namiji da zai taba dubarki a duniya da sunan so. Daga rana mai kamar ta yau ko kofar gareji kada ki sake fita, ke sharar garejin ma na soketa, iyakacin ki cikin gidannan nan dakin Dela ga bandakin ta nan shine na amfaninki. Idan zaki shiga gyara cikin gida tabbata asuba ce, lokacin da ba wanda ya fito sai dai mu fito muga komi a kintse. Dakunan su Khaleel ko gyaransu ki tabbata sai suna makaranta. Dukkan ‘yan aiki an salleme su sai Dela da zaku zauna tare, itama aikinta shine kula da diba duk wani motsin ki a gidannan don ma kar kiyi tunanin bin uwarki kauye, kin gane ko?â€? Kanta cikin cinyoyin ta tana girza kuka tace “na ganeâ€? Hajiya tace. “Abu na karshe shine, abincin ki Saratu shine wanda Khaleel, Idris da Furkan suke rage, sai ko karshen tukunya. Idan kika ci wani bayan wannan, kin san wannan?â€? Sai ta nuna mata jajayen wayoyin lantarki a bude (ma’ana shocking) “shi zan hada miki, har sai ya zuke wannan farin jinin naki da kowa ke cewa yana son ki. Kin san kuma in na kasheki na kashe banza, tunda Babanki cewa yayi idan na sassauta miki bai yafe mun baâ€? ta dubeta sosai tace “Saratu ko Intisar ki ke, bai dameni ba. Daga yau sunan da na san ki da shi shine jikar Jummai, duk wadannan sunayen naki guda biyu ina gaba da su. Na farko shine Saratu, sunan makiyyata ne da bani da makiyi ya ita a duniya aka lankaya miki, na tsani Saratu, na tsani sunan Saratu da duk wani mai irin sunanta ma har ke. Shi ko dayan, ba Babanki ya yanka rago ya rada miki ba, da na ne. Faisal ne ya sa miki suna ‘Intisarâ€? don haka na kwace tunda mallaki na ne. Saura me? Ke jikar Jummai ce, Jummai uwar Saratu. Daga yau duk wasu kaya da kika san mallakin ki ne, na ba ‘yan aikina da zan sallame su. Daga rana irin ta yau, ga kayan sawarki na har abada! Ina fatan kina fahimta na?â€? Sai ta watso mata wasu dogayen riguna guda ukku, baka, ruwan madara da ja, babu wani ado a jikinsu haka suke zulum, kamar na masu sharar titi. Ta cigaba da cewa “ba zan hanaki wanka ba, don tsaftar abincin mu, don haka zaki dinga wanka da wani sabuhu wai shi ‘Auraâ€? da na gani a hannun su Dela, shi zan dinga aje miki sinki-sinki kiyi ta yi, har da brush da maclean don kar ki fesa mana warin baki cikin abinci. Kar kiyi zaton irin maclean din kin na da, sam, wannan wani ne wai shi ‘madamâ€? da na gani a dakin maigadi, bayan wadannan Saratu komi sanyi komi zafi ko (Vaseline) ba za ki shafa ba. Na ke jin kin fara jinin Haila, don haka ga panties guda biyar da auduga katon-katon na ajiye miki don kar ki bata mana kitchen, sannan ga Hijabi ki dinga Sallah don nima Musulma ce bazan hanaki Sallah ba. Wajen kwananki shine dandaryar dakin nan nasu Dela. Zan yi miki mutuncin tabarma da Babanki bai ce a baki ba, kin ga ai ni na fishi mutunci ko?â€? A wannan karon batace mata uffan ba, don zuciyarta ta gama zagwanyewa. Ta mike tana cewa “Shikenan dama sabuwar rayuwar ki, ‘yar baiwa, ko ba haka naji Faisal na ce miki ba? Idan kunne ya ji. To jiki ya tsira. Sai mun sake saduwa. Kodayake da kyar ne zaki dinga gani na, don zai kasance koyaushe ina tare da maigidana, babu shirmen rabon girki ko? haka sauran ‘yan uwan ki a da. Ranar duk da kika manta ki kai dogon barci ranar ne zaki ganni. Gobe da asuba zaki fara bautar ki. Saratu mai sunan Saratu, Jikar Goggo Jummaiâ€? ta fita tana murmushi. How much do you like this story? 5/10/22, 09:39 - Ummi Tandama😇: ___________________________ *âœðŸ? SIRADIN RAYUWAâœðŸ?* Book three *@Takori* Page3ï¸âƒ£ A takaice sabuwar rayuwar da Saratu Bello (Inteesar) ta tsinci kanta kenan a gidan tsohon Brigadier Bello Makarfi. Kullum aiki take tukuru kuma bil hakki, tun safe har dare hakarkarin ta bai ganin kasa, ta zo kwanciya baya yace bai san wannan ba, ta kuma kwanta a dandaryar kasa, ga sanyi da ake mai tsanani a lokacin kin san kuma sanyi irin na marbles, abinki da yarinya ‘yar hutu, bata dauki wata guda ba cikin wannan aikatau din kakkarfan ciwon kiriji da matsiyaciyar mura su kai mata mugun kaye, saida ta galabaita tsahon sati biyu kamin Dela ta watsa mata kwayar maganin da ta amso a (chemist) hakannan Hajiyar tace aiki ba wanda zata rage sai dai ma ta kara da wankin kayan Khaleel. Khaleel hankalinsa ya tashi da ganin azabar da ake ganawa Intisar a gidan su, shikansa yana mamakin wai Daddyn su ne kuwa anya yake biyewa Hajiya yanzun? Yayi fiki-fiki kamar bai taba sanin kowa ba sai Hajiya, bashi da tunani sai na Hajiya. Ya kira ‘yanâ€? uwan sa a waya dukkan su ya gaya musu abin mamaki, don shi har zuwa lokacin ya kasa yarda ba shirin (film) ne yake gani ba yana faruwa cikin gidan, wai Intisar din Daddy? Ita ne ta zamo bolar Daddy? Kuma Daddy ya saki Anti Amarya, to a kan me? A satin su Najib sukayiwa gidan zuwan bazata, kowannensu cike da mamaki. Najib na kuka ya shiga tambayar Daddyn su shin me Saratu ta yi masu shi da Hajiya? Idan rigima ta hadasu da Anti Amarya ne ina ruwan Inteesar, naîve and innocent? Daddy ya daka masu tsawa yace “ku bana son zancen banza, ku fice min a gida ku koma inda kuka fito, ni za ku gayawa ya kamata? Wani cikin ku ya sake yi min zacen Saratu babu ni babu shi har abada! Duk son da kuke mata yayi wanda ni da na yi cikin ta na haifeta nake mata ne? Na maida ta ‘yar aikin, kuma baiwa, idan wani cikin ku ya isa to ya maisheta cikin sa ya haifo ya ‘yanta ta ta zama ‘ya, tunda ni ban san darajar ta ba.â€? Daga Najib har sauran ‘yan uwansa sun yi zaton Daddy ya gamu da ‘mental imbalanceâ€? ne, tunda har ya iya ya saki Anti Saratu, ya kuma maida ‘yar da suke kishin kaunar da yake mata baiwa, to amma fa an gaya masu yana yin komi cikin hankali a office, duk yadda aka yi gamo yayi, sai su dage da yi mai Addu’a. Ba yadda basu yi su ga Saratu ba cikin gidan Hajiya ta hana, tace kuma in suka dameta zata dagawa kowannen su nono. Sai Najib ya rubuta mata takarda a madadin su duka, hawaye na zuba masu sharrrr, sun san tabbas da Faisal yana nan da an yi wacce za’ayi, to su ya za su yi su taimaki Inteesar tunda kuwa ga abinda lyayen su suka ce? “Gaisuwa mai yawa Sister mu. Ba zamu ce ya kike ba, don mun san ba za ki amsa ba. Amma ina so ki sani cewa mun yi duk iya kokarin mu Inteesar kan al’amarin ki, kamin mu fahimci ‘all our efforts are futile (duk wasu kokarin mu na banza ne), ba za su fidda ke daga halin da su Daddy suka sanya ki ba. Amma ki kudurce a ranki duk wani kunci yana tare da sauki, haka duk wata daukaka tana tare da jarrabawa. Ki kaiwa Sarki Allah kukanki, shi kadai ya san me yake nufi da hakan cikin rayuwarki, hakannan muma abinda zamu dage da yi miki kenan, domin al’amarin ya wuce tsammanin ki da duk yadda mu kai tunanin shi. Sai dai ina so ki fahimci wani abu daya, wallahi ko kadan kada ki kullaci Daddyn mu, don na lura kwata-kwata ba a hayyacin sa yake ba, har yana ikirarin rabuwa da mu muma, in muka sake sa baki a maganar ki. Ki tuna son da Daddy ke miki, fifitaki da yake a cikin mu, ki tuna ke ce abokiyar shawarar Daddyn mu kuma ‘ya mafi soyuwa a gareshi, tabbas wannan son, ba zai taba rikidewa ya koma kiyayya ba. Inteesar jikina na bani ke wata ce a cikinmu. Kada rashin komawar ki karatu ya sanya zuciyar ki karaya. ‘When there’s life there’s hope, so always edpect success no mater how worst things seem to be in your daily life.â€? Ni na tabbata wani babban alkhairi da farinciki ne zai sameki, har nan inda kike, har (kitchen) din da aka zabar maki rayuwa. Don haka ki cigaba da hakuri Allah zai kawo miki ‘daukiâ€? Insha Allah. Da wuya mu sake zuwa gida nan kusa, sabida idanuwanmu ba za su iya jurar kallon irin ukubar da kike ciki ba, kuma daga mahaifiyarmu wai ido da kunya. Amma Insha Allah za mu nemi Anti don tattauna mai yiwuwa. With much sympathy from your brothers. (To amma su kansu fada suke, sun san bazasu iya dosar Antin su gaya mata halinda Intisar din nata ke ciki ba). Kamar ko yaushe, sai ta kifa kanta cikin cinyoyinta ta shiga jera kuka mai tsananin ban tausayi. Wai haka kowa ke rayuwa? Ko ko ita kadai din ce? A duniya akwai wanda rayuwar sa ke da obstacles kaman ita? Koko ita bata da dauwamammen farin-ciki ne a rayuwar ta? A ina ta kuskuro Daddy, me tayi masa haka da zafi? Bata sani ba. Kenan dole ta rungumi kaddarorin duk da zasu sameta in har da gaske ta amince ita tana son daddy har kuma karshen rayuwar ta tana kaunar sa duk da a yanzun shi din ya tsaneta fiye da kowa a duniya. Da yamma ta shiga dakin su Khaleel kamin lokacin dawowar su makaranta tasa injin shara tana sharewa tare da killace masu takardunda suka wargaza. A lokacin Khaleel ya shigo, ya aje file din da ke hannun sa ya zauna bakin gado yayi jugumm yana kallon ta kaman yace wayyo Allah! Amma ita din bata ko dube shi ba aikin ta take tukuru cikin gwanin ta da sabo, ya mike yace ta bashi ya karisa yafi sau goma in injin sharar ya amsa to itama Saratu ta amsa. Alkawari ne ta dauka tsakain ta da Allah da kuma Hajiya cewa daga ranar da Hajiya tace ba ita ba ‘ya’yan ta to har ta mutu, in Allah ya yarda babu abinda zai kuma hadata da su koda gaisuwa. Juma’a, 1 Ga Watan Sha’aban Tun da duku-duku ta tashi ta soma shara da goge-gogen gidan. Ta zuba Omo Aerial cikin ruwa zata goge gidan bata san robar ta fashe daga kasa ba ruwan yana zuba, santsin Omon ya kwashe kafar ta ta fadi da fuska kafafun ta suka bada wata irin kara mara dadin ji, tsautsayi dai da baya wuce ranar sa, tun daga lokacin bata kara sanin inda kanta yake ba. Sai da safe Hajiya ta sauko daga sassan Daddy ta diba ko’ina ta ga ba inda aka gyara, ta lelleka kichin, jakar tasu ba abinda ta daura masu na karin kumallo. Ta kwantsama ashariya tace “Saratu!â€? Tayi kiran fiye da sau biyar bata ji ta amsa ba. Ta kira Ado direba tace “maza-maza samo mun kebur ka ganiâ€? cikin mamaki yace “Hajiya wane irin kebur?â€? tace “irin wanda ake daure Itace da shiâ€? bai tsaya tambayar ta me zatayi da shi ba ya tafi, amma zuciyar sa cunkushe da zargin ko matar na da tabin hankali ne? Da kyar ya samo don sai da ya shiga kanyen wasu Gwari tukunnah, ta yi mai godiya harda bashi kudi, ta shiga neman Inteesar kusufa â€? kusufa cikin gidan, a tsakiyar falon yara ta same ta a kwance, tsammanin ta barci ta ke don ta yi aiki ta gaji, ta shiga tsula mata daurin kebur tun tana ihu tana motsi har ta kasa hassala komi. Sai ta juya tana murmushi ta ce, “Saratu mai sunan Saratu, jikar Goggo Jummai!â€? Dela mai aikin Hajiya, duk akan idonta Hajiya ke dukan Inteesar, duk da cewa wata babbar lalura ce ke damunta, da ganin irin kwanciyar da ta yi ka san bata lafiya bace. A da, Dela bata damu da harkar yarinyar ba tana ganin ko ba mahaifiyarta ai akwai Ubanta cikin gidan da yakamata yasa ido a kanta, amma a yau sai ta ke tambayar kanta ko me ‘yar kyakkyawar yarinyar nan ke ma Hajiya? Ko ma meye da laifin Maigidan, ko ba ‘yar sa bace bai kamata yayi mata irin wannan rikon wulakancin ba don ba uwar ta balle ‘yar sa ta cikinsa. Ta ciccibeta tasa a baho ta jika tsumma cikin ruwa tana matsa mata jiki, inda duk ta sa tsumman sai tayi kara kaman ranta zai fita. Ita Dela a ganin ta taimako ne take yi bata san azaba take kara mata ba, tunda kuwa tafasasshen ruwa ne take danna mata cikin tsokar ta da ta bubbude, a ranta ko tausayi ne fal, tana mai yaba kowacce kankanuwar halitta ta Intissar tare da koro tasbihi ga Allah Al’khaliku daya kaga halittar yarinyar. Ko fatar jikinta mutum ya gani yasan akwai hikimar Allah a ciki, irinsu ne ake kira matan manya; ga tsayi ga zati. Yadda Hajiya ta ruda mata jiki da kebur duk jinni ya taru ya kwanta yarab, abinki da farar fata jazur kar kiso kiga yadda ta koma kamar jini zai feso ta yi wani irin jazur, hatta idanuwanta da kyar take iya bude su sabida yadda suka kumbure sukayi luhu-luhu amma ba su fasa fidda hawaye ba. Tunda ta ke, wani abu makamancin wannan bai taba sauka jikinta da sunan duka ba, lebbanta keta motsin da ke nuna ‘kafa taâ€?, Dela ta fahimci targade ne ta samu a kafarta ta dama, tana gyara mata tana kara amma muryar bata fita sam, bata san sanda itama ta soma hawaye ba ta ce “‘yar nan, shin ina mahaifiyarki ta tafi ta barki da wannan azzalumar mace?â€? Wannan kenan. Sati biyu bayan wannan tana tsaye tana kankarar abincin kasan tukunya kamar yadda Hajiya ta tsara mata. Duk dokokin data kafa mata tana kokarin ganin bata tsallake ko daya ba musamman hurda da su khaleel. Saratu tana da ‘zuciyaâ€?, babu abinda ta dauka da zafi kamar cewa da Hajiya ta yi meyasa ta ke son ‘yayan ta, bayan ita ta tsaneta? Don haka har kullum take kaskantar da kanta ga su Khaleel da nuna cewa ita ba kowa bace face ‘yar aikin mahaifiyarsu. Ko gaisuwa bata sake bari ta hadasu ba duk da su suna iya kokarin su wajen nuna mata kauna da jawo ta a jiki, hakannan karbar mata aiki amma duk bata kulawa. Furkan ne ya shigo kichin din rungume da ledoji shake da mayuka, sabulai, kayan gyaran gashinta zuwa su biskit din ‘digestiveâ€? da take yawan ci, ya rausayar da kai yadda dai zata ji tausayin sa ta amsa ya ce, “Inteesar, ki yiwa Allah ba don ni ba, ki amshi wannan, kudi na ne halali na, Allah kin ji na rantse.â€? Ta yi tsaki ta aje tukunyar ta dauki abincin ta data kankaro a murfin kwano tayi gaba tana cewa. “Idan dayan ku ya sake shiga harkata to Hajiyar ku ce zata raba mu.â€? Amma can a karkashin zuciyar ta wani gefene ke ta amon tambayarta “Saratu har Faisal?â€? Wasu mulmulallun hawaye suka mirgino mata a guje. Tsayawa neman tabbacin wannan amsar kan iya haifar mata da psychological depression. Aikin karfi da wahala, rashin kula da rashin gyara, kar ki so kiga yadda ya taru ya maida Saratu Bello, dalibar kimiyya a Riyadh, wadda ada baka banbance ta da mutanen Abu-dhabee ko Kuwait, a yanzu Saratu bata da maraba da ‘yan aiki Fulani ko irin Bararojin nan da ke aiki gidan masu kudi. Gashin kanta dankare wuri guda rabon da ya ga ruwa ko (kumb) har ya manta balle uwa-uba man gyara. Farinta ya dushe kamar yadda zuciyarta a kullum ta ke a cunkushe da bakin-cikin da ba za ta taba rabo da shi ba. Bata nadamar kasancewa diya ga Bello Makarfi, kuma har abada ba za ta yi ba. Bata bakin-cikin irin abinda ya yi mata matsayinsa na Ubanta mahaifi, kamar bakin-cikin rashi da rabuwa da mahaifiyarta. Tana taya Mamarta kishin rabuwa da soyayyar Daddy Makarfi, don ta san har abada ba zata sami makwafinta ba. Ita kadai ta san me ta ke ji a zuciyar nan tata sai dai komi tana danganashi daga Allah ne, ta kuma san ko ba dade, ko bajima in Allah yayi zasu sake ganin juna to za su sake a cikin kudurori da yardarsa ta amince bai manta da su ba. Bata bakin-cikin bautar da take yi a gidansu, don zata iya yin komi domin Daddy Makarfi. A yanzun ma ta kan sa a ranta ne cewa Daddy ne ke cewa “yi min kaza Saratuâ€? ranshi na mai dadi yana sa mata albarkar nan da baya gajiya da yayyafa mata, to akan me zata yi bakin-ciki? A da, Daddy ya nuna mata matukar kauna da bai nunawa daya cikin ‘yanâ€? uwanta ba, ya daukaka darajja da martabarta bisan ‘ya’yansa bakidaya, a yanzu kuma ya tsaneta; kenan yanzu (it’s her turn) yanzu ne ya dace ta nuna mai tata kaunar ta hanyar yiwa matar daya ke so biyayyah? Yanzu ne zata cika wannan alkawarin da ta yiwa Daddy na kasancewa a cikin umarninsa muddin rai? Yanzu ne ya dace ta yi masa biyayyar da cikin ‘yayansa babu wanda ya taba yi masa ta hanyar daya zabar mata, watau aikatau din gidansa? Ta tabbata Ameenun da ya ke alfahari da biyayyarsa, ba zai taba yi mai wannan ba, bai kuma taba ba, kenan yanzu ne ya dace tacigaba da yi mai biyayyar da tayi alkawarin yi mai wadda Ameenu bai taba yi mai ba? A ganinta ta ragewa Daddyn ta nauyin dubbunnan da yake biyan masu aiki sama da goma dake cikin gidanne, a yanzu ta zama makwafin su, to a kan me zata yi bakin-ciki? A lokacin ta fidda jin dadin rayuwa kwatan-kwata daga tsarin rayuwarta, ta amince da zabin Daddy ne dauwama a matsayinta na Jikar Jummai ‘yar aikin Hajiya. Ta amince haka Allah ya tsara mata tata rayuwar. Wata kwalliya ta kece raini da ‘ya’yan masu kudi ke yi ita dama tun fil azal ba ra’ayinta bane, tafi tafiyarda tsarin rayuwarta bisa tsari na larabawan data yi rayuwa a cikin su, balle yanzu da take ‘Yar Aikin Gidan Su? Tunda dai zatayi wanka ta wanke baki shikenan. Bata Addu’ar Allah ya fitar da ita daga halin da take ciki illah Addu’ar Allah ya dai-daita tsakanin Daddy da Anti Saratu. To in baku mance ba a littafi na daya, cikin halin da bakon Miami, wato Al’ameen Bello ya diro gida Nigeria kenan ba zato ba tsammani, tare da matarsa Ihsan, dawowar da ta kunshi canjin sabbin al’amura da dama cikin rayuwarsu baki daya. Sauran abubuwan da suka biyo bayan dawowar duk kun ji su kaman dawowar Faisal da Mamarta. To amma ya akayi Maman ta dawo? To bari mu bisu mu gani. How much do you like this story? 5/10/22, 09:39 - Ummi Tandama😇: ____________________________ *âœðŸ? SIRADIN RAYUWAâœðŸ?* Book three *@Takori* Page4ï¸âƒ£ Lagos/ Talata 25 Ga Watan Shawwal Dr. Hajjo Hassan Biu, kodayake da yawan dalibanta a LASU sun fi kiranta da Dr. Biu, sunan Biu ta sameshi ne daga mijinta Hassan wanda yake mutumin garin Biu ta jihar Borno. Ta baro ofis da karfe hudu dai-dai na yamma a matukar gajiye cikin motar ta Legend (One Door), sauri take data kai gida ta yi ‘freshen-upâ€? wannan gajiya da ta kwaso ga Maigidanta da yaranta tasan suna nan suna tsimayen ta ne ita kadai, dai-dai (junction) din da zata dauki titin Victoria Island danja ta tsaidasu, ta yi tsakin takaicin bata mata lokacin da za‘ayi a ranta ko tana tsinewa wannan traffic-congestion na garin Lagos, tsayin minti ashirin ba’a basu hannu ba, ta sake tsuga tsaki ta bugi sityari tace “damn itâ€? kana ta sake duba agogon hannunta dana motar baki daya, yanuna karfe hudu dai dai na yamma dai-dai kokacin da wani Bayerabe ya zuro mata tulin jaridun mako ta tagar motar ta. Ta harareshi cikin takaici amma me? TELL Magazine ta wannan ranar dauke take da wani ‘headlineâ€? da ya sa jikinta tsuma, da hamzari ta dauka ta bashi kudinsa, tabi rubutun a gurguje da mamaki “INNOCENT-MAKARFI, RELEASED!â€? Ma’ana “an sake shi a matsayin mara laifiâ€? a shafi na gaba kuma “Makarfi celebrated his sixtieth birthday, at Nicon Noga, on 2/2…â€? watau Makarfi yayi bikin cikar sa shekaru sittin a hotel din Nicon-Noga dake Birnin Tarayya ranar biyu ga watan biyu, sai kanun labaran yadda kowanne ya kasance. A dai-dai lokacin da danja ta baiwa bangaren da take hannu, tasa ma motar giya a guje. Ta yi parking a inda suka tanada domin adana motoci kana cikin sassarfa ta fito, bakar ‘after dressâ€? dinta rataye a kafadunta haka Jakarta na sakale a yatsunta biyu ko file dinta bata tsaya dauka ba tayi cikin gida, karar horn dinta ya fiddo ‘ya’yanta a guje suna “Mummy oyoyo!â€? Ta daga karamar ta café ta ce “my dear Dijah, ince ko kinci abinci sosai?â€? Ta daga mata kai alamar eh, don bata fara magana ba amma tana gane duk abinda aka ce da ita. Ta kama hannun ‘first bornâ€? dinta Bishir tace, “Kawu na, Daddyn ku na ciki ko?â€? Ya ce “Eh, tun dazu ya dawo, amma yace yau sai anyi miki bulala, kin dade baki dawo baâ€? Ta bude baki, “Wayyo ni Hajjo, ka ce yau sai buzu na.â€? Ya ce, “Ai boye ki zan yi cikin rigata Mummy.â€? Tana dariya ta ce, “To na gode Kawu na, nasan bazaka bari Daddy ya duke ni ba.â€? A haka suka karisa falonsu tamkar wadanda suka shekara basu ga juna ba. Da sassarfarta ta tura kofar ‘bed-roomâ€? din shi, baya nan. Tayi murmushi ta dan saurara don ganin ta inda zai bullo, sai ta jiyo karar zubar ruwa a famfo kadan tabbacin yana bandaki, ta karisa jikin kofar ta kasa kunne ta ce “can I come in? â€?(Na iya ya shigowa?). Ya ce, “Noâ€? Ta yi dariya ta murda kofar tana cewa, “Ai ni mazaunai ce, dole a zauna da ni.â€? Ya ce, “Idan duwawun ya zama kakkausa, sai a yanke shi shi asa na roba.â€? Yana tsaye ne jikin ‘sinkâ€? saye da gajeren wando kadai yana wanke hannunshi da kamkamsan sabulun ‘cleopotraâ€? bai ko juyo ya dubeta ba, ita ko jikinta ba inda baya rawa rike da jarida, ya juya mata baya ya soma cuda farin hankicinsa cikin ruwan da ke zuba daga famfo ta ce, “Pls, Baban Bashir dubar ni, Allah ba wasa cikin lamarina.â€? Bai dubetan ba dai ya ce, “Ni kuma nace bazan dube kinba, tunda kin zama kakkausa ba sai in cire in sa mai laushi ba?â€? Ta ce kaman zatayi kuka, “Be serious, don Allah?â€? Ya ce, “Idan mutum ya dauki al’amarinki da muhimmanci Hajjo shine gaula, to naji zan dauwama a gaula na bana bukatar zama serious, dubi agogonki karfe nawa?â€? Awoyi nawa kika kara kika barmu cikin yunwa nida yara bayan na gaya miki a daina basu abincin masu aiki?â€? Ta langabar da kai gefe guda, kana ta janyoshi ta baya, fuskar ta bisa kafadunshi ta ce, “To bakwa shiga kitchen din da kanku Baban Bishir?â€? Ya dan juyo ya dubeta da wutsiyar ido, Hassan ya san Hajjon shi sarai, har yanzu tana shimfida mai wautarta ne yadda ta ga dama, uwar ‘ya’ya biyar a yanzun amma in ta kwaba mai wani shirmen ko dan ta Bashir baya yi ba, ya juya ya cigaba da abinda yake ba tare da ya ce mata komi ba. A ran sa ko cewa yake, “Allah dai ya shirya min ke.â€? To har gobe haka Dr. Hajjo ta ke, malama a sashen Harsuna a (Lagos State Universisty) tana karantar da harshen Faransa zalla. Ta cigaba da magiyar yayi hakuri ya saurareta, ya fito daga (toilet) din zuwa dakin barcin su inda duk ya aje kafa nan zata mayas, tana tirjiya cike da shagwaba. A dakin barcin su ne ta russuna ta kama tafin kafarshi ya ce, “Wai ke wace iri ce ne?â€? Ta kakalo wani guntun hawaye can karshen idonta tace “Allah Babansu Basheer traffic congestion ne ya tare ni, kayi hakuri ka yafe don Allah ?â€? Ya tintsire da dariya ya dauki jaridar ta yana dibawa. Dr. Hassan Biu har kullum ba mace a idonsa tamkar Hajjo, wautarta kuwa kullum sai abinda ya karu shi dai hakannan yake son kayar sa. Daukaka kan daukaka suna gani a rayuwa don a yanzu haka Dr. Hassan Biu shine Ministan Kariya na kasa wato (Defence Minister), ‘ya’yansu biyar cif maza uku da mata biyu, Bashir mai sunan Babansu Hidayah kuma Kawun da bata da ya shi a duniya sai Hakimi (Abubakar) da Hafiz, Hannatu mai sunan mahaifiyarta kuma (name-sake) din Hunainah tana ce mata Maama, Dijah itace auta ta kan ce mata (Yaya Dijah) don sunan Yayar ta Hadiza ne. Ya zauna bakin katafaren gadonshi ta zauna bisa carpet tace, “don Allah bude jaridar nan mana? Allah na kasa karantawa duk jikina rawa ya ke,â€Ya dubeta sosai ya ga yadda ta susuce ya dan dubi shafin jaridar ya ce, “Shin ina ruwana da (birthday) din Janar Makarfi?â€? Ta ce, “Wai wane Makarfin su ke nufi?â€? “Yace “Tsohon Brigedier General Bello Makarfi, kin san ya fita sharrin ‘coup d’étatâ€? (juyin mulki) da su Janar Delsu suka tura shi, a yanzu shine mai baiwa president (shugaban kasa) shawara kan harkokin Mulki.â€? Ta ce wadanda suka zauna nan ‘oppositeâ€? (gida mai kallon) na mu shekarun baya?â€? Ya ceâ€? eh, ai tun kan a kamashi suka tashi daga nan, wai ke kin san shi ne? Kin ce don Allah in karanta kuma kin isheni da tambaya kin hanani karantawar, kin san kina son ki karanta ki karanta abunki manaâ€? ta ce “Baban Bashir, be serious don Allah, shin a wane gari Makarfi ya ke yanzun?â€? Hassan ya cika da jerin gwanon tambayoyin matarsa kan Janar Makarfi, kishin ‘yan mazan ya motsa ya ce a hasale. “So what in na gaya maki Abuja ya koma da zama? Sai ki dau mayafi ki yafa ki tafi, isn’t that good?â€? Hajjo ta kwantar da kai tace “Alasabbinani, maida wukar, ba abinda ya hada ni da shi baya ga Yaya Hadiza da tace diyarta da aka sace tana jaririya, su Hidayah sunyi makaranta daya da yarinyar a Riyadh, har suka kaita gidansu ta ganta ta gane ‘yarta ce Fatima, kuma wai yarinyar ta taba gayama su Hidayah cewa anan Lagos gidansu yake, gidan Bello Makarfi na nan Victoria. Wancan zuwan da Ambasada dasu Hunainah su kai ai kan maganar ne, muka je gidan a lokacia yana kulle. Ashe iyalinsa sun tashi…â€? ta kwashe komi dai ta gaya masa tun farkon al’amarin, ta kare zancen ta da cewa, “Abinda yasa tun tuni ban gaya maka ba, zancen ne naga ba wani ‘logicâ€? (makama) ba, to amma yadda ta dage ‘yar ta ce ta gani, sai duk nima naji jikina na bani yakinin cewa hakanne, ka san UWA fa a kowanne hali dan ta-dan-ta ne, ba kuma zai taba boyuwa gareta ba walau girma, tsufa ko kuruciya. Kana sane da cewa har yanzu lafiyarta gata nan ne kurum sabida nasihohin mutane, Hassan ka taimake mu ka kuma ceci rai don Allah?â€? Jikinsa yayi sanyi lakwas har bai san abinda zai ce ba. Hajjo ta daura hannayenta bisa kafadunshi tace. “Baban Bashir, farin-cikin Yaya fa shine nawa, bani da kowa a duniyar nan sai ita, ina boye maku damuwata ne kawai akan lamarin nan don bana son tayar da hankalin ku kamar yadda Yaya ta tayar da na Ambasada, ‘pls do somethingâ€? (kayi wani abu) manaâ€?. Hassan ya dubi matar shi yana kallon yalwatacciyar sumarta ta filanin usli, idanuwanta duk sun cicciko ya ce, “Hajjo, ji ni nan don Allah kar ki min kukan nan naki, I’ll try my best (zanyi iya kokori na) amma kin san mutane haka ‘top militaryâ€? irin su Makarfi dosar su da wani al’amari makamancin wannan sai anyi kyakkyawan shiri, hakannan uwa-uba shaidu, shin wacce shaida muke da ita na cewa ‘yar shi tamu ce? Wannan kwata-kwata baya a tsarin shari’ah kuma ya haura doka mai kare ‘yancin dan-adam tunda bamu da wata sahihiyar shaida. Abinda yafi yanzu ni zan fara zuwa Abuja inyi bincike in tabbatar in ma har yana da ‘ya mace a gidan, don a sanin da nayi wa Makarfi sanda suke makotan mu ya’yansa tara ne duk maza ba mace ko daya. Kai mata ma dai da rigma kuke kuma dole a biku da yadda kuke so ana so ko ba’a so, in ba haka ba yarinyar da aka ce ta bata cikin tsumman goyo, a kauye, itace za’ace an gani a birni irin Riyadh, birnin da ya tara al’ummar cikin duniya, ko dayake kamar yadda kika ce din ne UWA ce bazan musa mata ba. Amma da wani ne Allah ba ma zan sa bakina ba cikin wannan al’amari mai rikitarwa. Idan na tabbatar da komi zan shirya mana ‘visaâ€? zuwa Korea sai mu taho tare da su gabadaya, ni ina cikin hutun sati biyu, ke kuma na san kwanannan zaku shiga ‘long-vacationâ€? (dogon hutu na Jami’a) ko? Sai a shirya mai yiwuwa, hakan ya yi miki?â€? Tayi murmushin jin dadi, tabbacin ya faranta mata ta ce “nagode kwarai, Honey. Allah ya kara dankon kaunaâ€?. Minister bai yi sanya ba, a washegari ya bi jirgi zuwa Abuja, saida yasa akai mai kwakkwaran bincike kamin da suyiwa gidan tsohon Brigedier Bello Makarfi tsinke shida ‘yan rakiyarsa, amma cikin sa’a basu sami ganin sa ba yana dakin ‘meetingâ€? tare da shugaban kasa. Duk da haka Hassan ya baiwa sakatariyar shi ta gida katin shi wa Advisern, ya kuma bar daya cikin yaranshi yayi masu bincike kan ‘ya’yan Brigedier cikin siyasa irin tasu. A washegari ya tabbatar mai akwai Inteesar ‘ya mace daya kwal cikin ‘yan mazan ‘ya’yan shi amma a yanzu haka uwarta bata gidan tana hannun kishiyar uwarta ne. Ya ce shima ya yi nasarar samun wannan cikakken bayanin ne daga bakin Ado direban gidan, ta hanyar hilatar shi da cewa ‘ya’yan Birgediyan ne suke birgeshi da da mace a cikin su da ya aura, shine yake gaya mishi hakan. A ranar Hassan da jama’arsa suka baro Abuja. Yana cike da dokin ganin farin-cikin Hajjon shi, cikin wautarta watakila tace goyon shi zata yi har da majanyi da juyi. Ya ko gani, har ya gode Allah. Da wannan suka durfafi kasar Korea don kulla mai yiwuwa. Zuciyar Hajjo dai bayan farin-ciki cike ta ke da taraddadin kada Allah yasa su je su kwaso mutane kasa-ya-kasa a zo a ce Bello Makarfi ya sake canza garin zama. Kauyen Makarfi, Cikin Garin Kaduna Aunty Saratu tun bayan rabuwar su da Daddy tana gidansu a Makarfi, kullum kuma idanunta basa rabuwa da tsiyayar da hawaye duk kuwa da kulawar da lyayenta ke gwada mata. Baffansu cewa yayi Allah yasa hakan shi yafi alkhairi agaresu duka ya kuma kawo mata mijin aure kurkusa, (ya ma manta ciki ne da ita). Hakan kuma bai bata tsakanin shi da dan dan-uwanshi ba daga matsayin da ya rikeshi watau Da. Duk da cewa shi Makarfin ya watsar dasu gabadaya don ma kar suce ya maida Saratu, don shi yanzu ko mai irin sunanta baya son ji, kafafunshi kuwa rabon da su taka garin Makarfi shekara guda da doriya kenan. Shi ko Baffan musamman yake nikar gari ya je har offishinsa yace yazo ne su gaisa kurum ya ga lafiyar shi tunda shi ya watsar dashi akan abinda bai shafeshi ba. A irin wadannan lokutan Daddy kan ji kunya matuka. Tun yana dari-dari da Baffan har ya dawo ya saki jiki dashi suka koma kamar da, don ya lura Baffan mai kaunar shi ne don Allah ba wai don wata tsiyar hannunshi ba. Don kuwa ko kwandala baya tambayarshi in har bashi ya dauka don kashin kansa ya bashi ba bare har yace ya maida Saratu dakinta. Daga baya kuma ya wanke kafa ya soma zuwa Makarfin don kansa, amma baya shiga cikin gidan, iyakacin sa falon soro da ya ginawa Baffan don bakin kunya. Hakannan tun bayan fitowarshi yasa an rushe gaban gidan anyi mai zubin zamani an kuma wadatashi da komi na jin dadin rayuwa. Tun rabuwar shi da Anti ko naira biyar bai taba dauka ya aika mata ba a matsayinta na me dauke da cikinsa. Wannan bai dami Hajiya Saratu ba, don ita kanta mai kudin kanta ce a halin yanzu, a sabili da aikin da ta fara bayan fitowar Daddyn a sanda kuma duniya ta dawo masu sabuwa, sai kawai ta shiga tari, ga wanda Daddyn ke basu ita da Hajiya naira dubu dari-dari duk wata, don haka yanzu ‘accountâ€? din ta cike yake da (millions) gashi kuma ba abinda tsoffinta basa yi mata. Koda wasa Baffa Sani bai taba daukar carbi da niyyar wai Allah ya gyara auren Saratu da Daddy ba, sai dai Allah ya zaba mata abinda yafi alkhairi a rayuwarta. To amma Goggo Jummaifa? Kusan kullum sai sun kai ruwa rana da Baffan kan don me ba zai mike ya nema masu makarin asiri ba bayan yana da tabbacin wannan duk aikin tsafin su Hajiya Nafi ne? To in tsafi suke ita Addu’a ta ke, kuma ko gonakin gadonta zasu kare sai Saratu ta koma dakinta. A irin wadannan lokutan sai Baffa yace “kema tsafin zaki tafi nena kenan? To ki dinga yi dai kina tunawa duk matar da taje wajen boka ya bayyana mata wani sirri da Allah ya boye ko ya biya mata wata bukata da take ganin Allah ya gaza ko jinkirta biya mata, sai anyi kwana arbain ba’a karbi sallar ta ba, hakannan tayi shirkaâ€?. Goggo Jummai bata tsinkawa don tasan bata nufin kowa da mugun nufi face nemowa diyarta farin-ciki wanda yake a wuyan su iyaye, hakannan ta san boka ta san Malam. Shi kansa abinda yasa yaki tsoma baki don yana ganin da Saratu da Bello duk daya ne a wajen shi ba wani banbanci, kuma da suyi zaman aure tare da kar su yi, duk sunansu ‘ya’yan sa. Idan ya yi Addu’ar Saratu ta koma gidan Birgedier yana bukatar abin hannunshi da ya rage basu kenan, wanda shi ba don haka yake kaunarshi ba. Ya rungumeshi a sanda yake maraya; ba Uwa ba Uba balle dangi, ya zame masa komai nasa a lokacin shi bai taba haihuwa ba, ya wahala ainun wajen daukar nauyin karatunsa. Ya shiga kwanan kurkuku yafi a kirga akan bashi, don Bello ya zama soja, ya sha zagi gun mutanen kauyensu kan ya daurewa dan Wansa gindin zama dan fashi da makami, a lokacin kai bai waye da ilmin zamani ba, to akan me a lokacin bai ki shi ba sai yanzu don ya saki kanwarsa kan ta ci mai mutunci? Wane irin tallafi da girmamawa ne bai yi masa ba da ya soma daukar albashinsa na farko a soja, tun kafin a haifi wata aba Saratu? Ba zai ki Bello ba cikin kowanne hali, dukkansu kuma bai ga laifin kowanne ba. Ya san halin Saratu sarai, raina na gaba da ita balle mijin ta ba halinta bane sam tabbas akwai dalilnta na yin hakan, duk kuma dan-adam yana tare da ajizanci, sannan shi aure rai ne da shi, duk ranar da Allah ya kawo karshen sa zai mutu, ana so ko ba’a so. Hakannan hakuri da wahalar da suka sha ita da diyarta lokacin da yake kulle, sun cancanci mafificiyar kauna daga gareshi ba wulakanci ba. Dole watsar dasu din da yayi yayi mata zafi. Ya san in aka kawota bango kamar mara tunani take. Ita ko Goggon tunanin ta sabanin na Baffan ne, cewa take so-so-ne, amma son kai yafi. Da yardan Allah sai Daddy yayi nadamar wulakancin da yayi wa diyarta lokacinne ita kuma zata nuna mishi Nairarshi bata da amfani agaresu. Ta fannin ita Saratun kullum tunaninta na bisa halin da ta baro Intisar a ciki ne. Ta tabbata Allah ne kadai zai ceceta a hannun Hajiya. A duk sanda tayi rin wannan tunanin ta soma kuka kenan har Allah ya gajishsheta. Sau da dama ta kan yi tunanin kawai taje ta dauko ta shine mafi a’ala amma tunanin barazanar Makarfin da gudun abinda hakan zai haifar, na tonon abin tausayin da ke rufe daga Daddy ko Hajiya game da Intisar din shine ke tsorata ta. A watan Najib yaje Makarfi, sun jima suna hira da Antin iyakar kokarinsa yayi wurin boye mata zahirin halinda ‘yar ta ke ciki, yace ne kawai tana nan lafiya koda yake shi ba zaman gidan yake ba yana Enugu. Wannan ya dan kwantar mata da hankali don lafiyar ta tafi ji ba damuwarta ba. Ta tabbata dole ne zata kasance cikin damuwa kamar koma fiye da ita. Amman komi mai wucewa ne da yardan Allah. Bata tausayin kanta kamar yadda take tausayin Intissar don haka ta dage da Addu’ar Allah ya kawo masu mafita cikin al’amuransu. A watanninta na biyar da zaman Makarfi, ta haifi sankaceciyar diyarta a safiyar wata litinin. Yarinyar bata debo kamannin kowa ba sai na Faisal. Kamar su daya da faisal a komi. An aikawa Daddy a ranar ba yabo ba fallasa yayi hidima dai-dai gwargwado don Baffa kadai amma ba wai don ya damu ba. Da aka tambayeshi sunan jaririya sai yace su sanya duk wanda yayi masu mana? A nan ne ran Baffa ya baci yace a sawa yarinya suna Fatima â€? Zahra. Su yasir duk sun baro Enugu sunzo sunga kanwarsu dukkansu sai kururuta tsabar kamanninta da Faisal ne babu kuma wanda ya leka Abuja a cikinsu har suka koma. Anti Saratu kanji haushin Goggonta kan yadda taki hutar da kanta ta zauna wuri daya ta dangana da kaddarar rabuwarta da Daddy. Ita a yanzu ma chairman na Makarfi ke son aurenta tun bayan aifuwarta. A ranar wata alhamis Goggo da aminiyarta Inna Jami suka dawo yawonsu goshin mangariba kafafun su futu-futu da kura duk sai suka bata dariya. Jami tace “Au, dariya ma kike mana Saratu don muna nema maki ‘yancinki da aka bi aka bibbinne? Ni bani ruwa inyi alwallah inyi Sallah ki ji labari. Ai dama aka ce mai nema yana tare da samu, in Allah ya yarda nanda sabon wata mai kamawa kina dakin mijinki, kaikayi kuma koma kan mashekiya zamuyiâ€?. Saratu tayi tsaki, ta mike ta ciccika masu butoci da ruwa a randa a lokacin zarah keta tsala ihu amma ko waiwayon inda take batayi ba. Jami ta dauketa tana cillawa tana cafewa ta ce “yi shiru ‘yar ikon Allah, daga wannan watan kin bar zafin kauye In sha-Allahu don nasan shi ke damunki sai Habuja, ke da kauyen Makarfi sai ko gaisuwar Sallahâ€?. Goggo Jummai tayi dariya ta ceâ€? ai gobe har ita zamu tafin ko? “Jami tace “kwarai kuwa, don gara a soma yi mata rigakafi itama, baki ji Malam na Kafanchar yace itama an maida ta kamar mijiya a idon Mahaifin ba? Tunda aka haifeta kin ji yace a bashi ita ya gani? Ai gobe Saratu da kin ki da kin so kafar mu kafarki bukkar Mallam Sidi Fariâ€?. Ita kam jinsu kawai take a ranta ko cewa take ko Sidi Baki ne ba inda zata. Haka kawai don B-Bello shine autan maza? Itama bakikkirin din take ganinshi babu kuma koda birbishin son sake zama dashi ko kankani a kalbinta, zumunci ma don ya zama dole ne. Har sun kwanta da doddare Goggo ta kasa hakuri ta kirayi sunanta a hankali tace “Saratu, duk fa hakilon nan da muke yi don ke muke yinsa da farin-cikin ki ba don wani abu daban ba. Amma na lura ke haushin mu ma kike ji bakya godewa. Dazu ina ji Jami na ce miki gobe ki shirya mu tafi Kafanchan kin yi shiru baki amsa ba har da bin ta da tsaki. Shin ko yanzu ba kya son mijin ki ne?â€? Aunty Saratu ta gyara kwanciyar Bebinta dake barci tana fidda numfashi sannu a hankali cikin koshin lafiya. Tabbas tambayar Goggo itace amsarta. Ko a lahira bata fatan su hadu da Birgedier yanzu (kaji sharrin kishiya). Ta muskuta cikin tsananin bacin ran tono ma mutun abin bakin-cikin da ya manta dashi tace “Goggo ni fa tunda na bar gidan ban kara tuna wani Bello da sunan so ba, sai ko Yaya na Uban ‘ya ta. Yadda kika san bakin kumurci haka nake ganin sa ko muryarsa bana son ji wallahi. Wannan ‘yar ma kan dole nake shayar da ita, amma duk sanda na tuna wai kanwar su Aminu ce kamar in shake shegiya wallahiâ€?. Goggo ta yi salati ta sanar da Ubangiji tace “Ba zan musa miki ba Saratu don tabbas kema tsafin ya ci ki, amma a kalla gobe ki bimu addu’o’I ne Malam Sidi zai baki na neman zabin Allah ba wai wani abu baâ€?. Ta amince zata amma ba don ranta yaso ba sai don bata son yin musu da Goggonta ne kawai. A soron Sidi Fari wanda Sharifi ne a garin Kafanchan kuma dan uwan Inna Jami, ya amshi Babe-Zarah yana kallonta yace “Shin Saratu zaki iya bayyana mun yadda kike jin tsohon mijin ki a ranki?â€? Ta mayar mai kamar yadda ta fadiwa Goggon ta a daren jiya, duk ta matsu ta tafi don ita ba wannan aka ce zai hadasu ba illa Addu’a, ya girgiza kai ya dubi Jami yace “Hajiya Jamila, a jiya nayi bincike naga duk matsalar yarinyar ku amma Insha-Allahu komi ya zo karsheâ€?. Ya mika mata Zarah ya umarceta da ta shiga cikin gidan shi ta basu wuri, ita dama so take ta tafin, don haka cikin hamzari ta saba ‘yarta a kafada tayi cikin gidan. Malam ya ce “Jamila yarinyar nan duk wani mai imani dole ya tausaya mata, kuma ku godewa Allah daya nufe ku da mikewa tsaye kan al’amarinta, don Ubangiji shi yace tashi in taimake ka, kuma a gaskiyance sai mun mike tsaye in ba hakaba itada aure har abada kenan. Bakin asiri ko ince tsafi ne aka bizne mata a dakin aurenta wanda aka hada da idanu da gangar jikin matacciyar mujiya, da gashin kan ita Saratu d farcenta, shi ko mijin ta firraku a kayi masu ta yadda ba zai taba samun kwanciyar hankalin kanshi ba in har ba gani yayi ya rabu da ita ba. Akwai wata yarinya ma dana gani a gidan itama abinda aka yiwa Saratun da mijinta shi aka yi mata dashi Maigidan, kodayake na gani tana cikin gidan duk da haka, sai dai Maigidan na ganin ta kamar mujiya ya tsaneta kwata-kwata. Wannan tsafin a tsibirin Okeremor aka sameshi ta yadda karyashi kadai shine tono abinda aka bizne aka koneshi kurmus. Sabida haka zan tura wani Musulmin aljani dake min aiki wai shi Salmanu ya aiwatar da aikin. Daga wannan zan yiwa Bello kiranye, ai gyaran sunnah ne, shi da kansa zai zo neman a maida mishi matarsa, kada ku tsaya ja masa rai ku maida auren don kwata-kwata baya da laihiâ€?. Goggo Jummai ta gaya mai yarinyar diyar Saratun ce yace “ba komi, da tsarkin Alkur’ani kamin kwana uku zai warware komi. Itama Saratun ya kirata ya bata addu‘o’I da Nafilfilin da zata rikayi har tsawon kwanaki arba’in, da rubutun da za’a dinga rubutawa suna wanka suna sha ita da Zarah. To Anti Saratu taji dadin wannan, daga Goggon har Jami babu wanda yai mata zancen da Malam yayi. Tunda ta fara Addu’ar sai taji zuciyarta na sanyi a kullum. Duk wani kunci dake tattare da ita ya shiga yayewa sannu a hankali. Tabbas babu maganin da Al-Kur’ani ba ya yi kuma lallai shi (Shifa’un-Linnasi) ne wato ceto ga al’ummah. Kaunar diyarta ke shigarta sosai kamar na kowacce uwa ga dan da ta haifa. Kuna wai har ta sami kanta tana mai tinano irin kyakkyawar rayuwar da sukayi da Bello Makarfi da diyarta Inteesar. Da Goggon ta fahimci haka sai ta daga hannu tayi godiya ga Allah ta kuma garzaya Kafanchan ta tadda Mallam Sidi tare da abin sadakar da ya nema, harta dada ninka mai amman shi din sai yace ba zai anshi karin ba, yayi masu ne domin Allah da neman ladan gyaran aure da kuma kasancewar Jami kanwa agaresa, sai tayi godiya, ta kuma shiga kara jan hankalin Saratu tana nuna mata gidan Daddy shine kadai kwanciyar hankalinta ita da diyarta da Inteesar. Ko bazata koma don komi ba ta koma don Intisar da Zarah. Don ko tayi wani auren hankalin ta ba zai kwanta ba tunda bazata kasance tare da su ba, ina amfanin badi ba rai? Sauran abubuwan da suka biyo baya duk kun ji su cikin littafi na daya, wato dawowar Antin da barin garin Hajiyar. Dawowar Faisal da gane ainahin wacece Intissar kuma wanene Al’ameen? Suman da tayi ne har yanzu ban san musabbabinsa ba; na gane hakikanin waye Al’ameen ne? Na bakin-cikin kasancewarta dumu-dumu a soyayyar dan Haj. Nafi ne? Koko na tunanin ta rasa Al’ameen ne shima kaman Faisal tunda yake shima uban su daya? Ban sani ba. Yau ga likita a gadon likitoci kenan, in ji babban Likita Alfred, don sanin waye Al’ameen? How much do you like this story? 5/10/22, 21:33 - Ummi Tandama😇: _____________________________ *âœðŸ? SIRADIN RAYUWAâœðŸ?* Book three *@Takori* Page5ï¸âƒ£ Adai-dai lokacin da duk wannan ke faruwa, a lokacin ne kuma wata mulmulalliyar mota baka sidik kirar (Bently) mai kofofi hudu ta yi ‘parkingâ€? a harabar gidan Makarfi. Tun kafin motar ta ida tsayuwa Maigadi ya karasa ya shaida masu cewa babu kowa a gidan duk suna babban asibiti, yarinyar gidan da yaron gidan ne suka suma. A gigice Hassan Biu ya baiwa Direban dake jan su umarnin su nufi General Hospital. Tun kafin su isa Hajiya Hadiza ta fara kuka, ta narke Jikin Ambasada tace “ashe ma Allah ya rubuta gawar ta zan gani, Bashir?â€? Yasa hannu ya rufe mata baki ya ce “C’mmon Hadiza, cool down mana? Wa yace dake ciwo mutuwa ne? Ki tsaya ma mu tabbatar ita din ce tukunna?â€? Dr. Alfred ya fito daga dakin da Al’ameen yake, sauran likitoci biye da shi, ya isa har falon da su Daddy ke zaune jigum-jigum cikin zaman jiran tsammani, wasu na jan carbi wasu na safah da marwah. Ya russuna alamar girmamawa ga Daddy yace ya biyoshi ofis minti biyu. A kayataccen falon likita Alfred, ya dubi Daddy a nutse ya gaishe shi tukunna, duk sai suka yi shiru. Daddy yai karfin hali, duk ya fita kamanninsa dan lokaci kalilan saboda tashin hankalin rashin sanin makomar gudan jinin sa Al’ameen. Cikin taraddadi yace “shin ya cika ne Alfered ka kasa gaya mun?â€? Alfered yace “a’ah, Illa rayuwan M.A.B yana cikin matukar hatsari. Jininsa ya hau sosai fiye da kokarin mu. Sannan (I’m sorry to say) Dr. Al’ameen ya gamu da ciwon zuciya (Heart Stroke), duk da haka M.A.B yana numfashi, duk wani kokari da zamu iya shine yaji sauki amma ba ya warke ba (I’m Sorry)â€? Daddy ya soma share hawaye da bakin babban rigarshi. Alfered yace “wani mugun abu ne ya gani ya tayar mai da hankali haka, koko wani abu yake so ya kasa samu? Ko wani abu ke damunsa tun da dadewa ba’a farga ba?â€? Daddy in banda hawaye da zufa ba abinda yake, ya dubi likita idanunshi jazur ya yi mai bayani a takaice na iya abinda ya sani, yace “Ni na kasa gane kan wannan abuâ€? Alfered yace (cikin murya mai kwantar da hankali) “a yanzu M.A.B na bukatar magana mai kwantar da rai daga gareku, magana mai tausasawa da farantawa, ko mun samu jinin da ya hau ya safka kadan, a kuma samu kwantar da ciwon zuciyarshi ya kwanta cikin sauki. Ba zaka iya taimakawa M.A.B. ya samu rayuwa ta dai-dai ba a sanda kowa ke da bukatar sa ba? Ina nufin ba zaka iya taimakawa M.A.B ya samu sauki ba?â€? Daddy ya sake rikicewa, yace “in zan iya ta yaya? Ni ne kuwa mai matukar bukatar Al’ameen a yanzu, bana jin in na rasa Al’ameen nima zan sake rayuwa lafiya. Ta yaya? Ta yaya zan taimaka likita?â€? Alfered ya zare gilashin idonsa a hankali, ya dub Brigedier cikin sassanyar murya ya ce, “Ka je ka bashi hope, koda na karya ne!â€? Daddy ya mike, idanun sa basa ko ganin abin da yake gabansa, ya nufi dakin da aka kwantar da Aminu. Me zai ce da Al’ameen? Ya fadi sirrin da ke boye don samuwar lafiyar dan sa, ya kuma sanya rayuwar ‘yar wani cikin garari? Ya tabbata ya kuma amince So ne ya kada (Aminu-Amintacce), a rashin sani, to amma ai ba wani shamaki da zai hana wannan son kaiwa ga ci, ma’ana, ba abinda zai hana Aminu auren Intisar, tunda ba wata dangantaka ta jini a tsakaninsu. Shi kam zai fadi a yau, Allah ya ba Saratu da Saratu hakuri. So-so-ne, amma son kai ya fi. A yau zai fadiwa Aminu “Intisar ba ‘yar saratu ba ce balle shi.â€? A sannan ne kuma su Hajiya Hadiza suka fito daga mota suka yi wa harabar asibitin tsinke. Hidayah rungume da ‘yar uwarta Hunainah da fargabar halin da zasu sami ‘yar uwarsu ciki ke neman kayaswa, bata ko iya daga kafa sai jan kafa. Hassan da yake ya san Daddy shi ya nunawa Haj. Hadiza shi zai shiga wani daki na musamman wanda a ka’ida ba’a barin kowa ya shiga sai likitoci da malaman asibiti, ya ce “nake jin itace a can dakin Hajiya, don ga Makarfi can zai shigaâ€? this is Brigadier Bello Makarfi…â€sai kawai ta kwasa a guje tun basu ankara ba. Kusan a tare suka shiga da Daddyn tana haki kamar ran ta zai fita. Daddy bai kula da ita ba don shi kansa ba’a hayyacin sa ya ke ba, ya ji dai wani ya shigo tsammaninsa Hajiyarsu Aminun ce, ya dubi fuskar Al’amin cikin (Oxygen) wato abin janwo numfashi yayi mamakin yadda Allah ya mayas da halittar shi cikin dan lokaci kalilan, ya kara imani da mulki da ikon sa kodayake ba’a mamaki da ikon Allah, wannan wace irin masifa ce? Ya soma sheshshekar kuka kasa-kasa kafin ya tuno da abinda ya shigo da shi. Ya karisa dai-dai kunnen Al’ameen ya ja kujera ya zauna, ya kai hannu bisa sumar kanshi yana shafawa a hankali ya fara magana, muryarshi na rawa da karkarwaâ€? Hajiya Hadiza bazata ce ga wanda ke kwance a wannan gadon ba, don ko gani bata yi sosai, ita dai kawai tunaninta ya bata diyarta ce ‘Fatimaâ€? fakat, za kuma tayi ko menene don tserar da rayuwarta in dai zata iya koda hakan na nufin a zuke jinin jikinta ne bakidaya a sanya wa Fatima. To sai kuma maganganun Bello Makarfi, suka dauki hankalin ta kwarai, suka kuma warware duk wani taraddadi dake zuciyar kowannen su. “Al’ameen ka gafarce ni, na san mun yi kuskure ni da Saratu wajen boye maku ainahin kowacece Intisar, ba mu yi hakan domin mugunta ko wata manufa ta daban ba, illa domin tserar da ita daga kuncin da zata iya fadawa a girmanta inta fahimci ita ‘yar tsintuwa ce, sanin kanka ne ba abinda ya kai rashin asali ciwo. Aminu ka taimake ni ka mike ni kum in aura ma Saratu-Intisar! Wallahi ba ‘yata bace, tsintar ta nayi a daji na kawowa Saratu. Hajiyar ka zata tabbatar maka da hakan. Al’ameen don Allah ka mike! Ka mike!! Ba abinda ya hadaka da Saratu da zai hanaku aureâ€? Kuka yaci karfinsa da ya ga Aminu ko gizau. Ya kifa kai jikin karfen gadon yana ta yi kamar ba tsohon soja ba. Tausayi da dadi ne ya rufe Haj. Haddizah, wasu siraran hawaye suka ziraro mata, hawayen farin-ciki da tausayi duk a lokaci daya. Ta dibi yadda Allah Al-mussawwiru ke juya masu al’amuran cikin ruwan sanyi, ta kara amincewa lallai shi buwaya ne, gagara mithali. Sai ta matsa jikin gadon Al’ameen ta dubshi sosai. Tausayin shi da kaunar shi babu inda bai bi jini da tsokar jikin ta ba. Wai fa wannan kaunar diyarta ne ya kayar dashi haka? Ta russuna ta barin hagu, kanta jikin gadon a kife tace. “Kwarai Al’ameen Saratu, Intissar kuma Fatima ba kanwar ka bace kamar yadda kake tunani, ka tashi don Allah ka tausayawa Intisar da Babanka bisa halin da zai shiga in ya rasaka. Ni ce mahaifiyar Intisar. Mahaifin ta ya rasu ne tun tana Jaririya a dalilin bakin-cikin sace mana ita da a kayi aka kai daji, shine Babanka ya tsinta. Wannan shine gaskiyar al’amarin. Idan ka mike Al’amin ko a gobe sai mu daura maku aure, in ce ko shikenan? Ba fa abinda ya hadaku da Intissar!â€? Ta fadi da dan karfi cikin gunjin kuka. Maganganun har tsakar kwakwalwarsa amon su ke yawo, ya motsa kadan alamar sun dameshi, Alfered ya janyesu yace “ya isa hakananâ€?. To Hadiza da Daddy sai aka koma kallon-kallo. Kallo daya yayi wa Haj. Hadiza yasan yaga mahaifiyar Saratu a yau, in banda nauyin shekaru ba zai yarda ba Saratu-Intisar din su ce wannan tsaye a gabansa ba. Kwanaki goma abinda iyaye da ‘yan uwa ke ta gayawa Al’ameen da Intisar kenan. Har ita kanta Anti Saratu ta gigice rannan da Intisar tayi wani dogon suma kamar bata dawo ba ta shiga fada mata ba abinda zai hanasu aure don babu alakar jini a tsakaninsu. Malam Sani da Goggo Jummai ma ba’a barsu a baya ba wurin nunawa ‘yan gatannan kauna. Haka Hidayah da Hunainah dake kwana rungume da ‘yar uwarsu a cinya, suna rokonta ta tashi ta auri Yaya Al’ameen, ta basu kulawar da yayye ke baiwa kanne, ta ji dumin Mamarsu itama. Su nuna mata kulawa da kaunar da bata samu ba na kanne mata. Fatan Anti Saratu kawai samuwar lafiyar Intisar da likita ya ce, ‘Shockâ€? ne kadai ya gigitata ya wargaza mata tunani. Amma a hankali tunaninta yana saisaita kuma tunda ga komi yazo da sauki, danginta sun bayyana a sanda ake tsananin bukatar su. Ita da Hajiya Hadiza kwana suke bakin su bai yi shiru ba kullum dai zancen kenan. Cikin wannan halin Najib ya kira mahaifiyarsu a waya ya ce, “Hajiya, kin ce zaki dawo har yanzu kaman an aiki bawa garinsu, amma yanzu ina jin ya dace ki dawo, tunda ga Aminun ki kwance a gadon asibiti ba yadda yake, bai kuma san wanda ke kansa ba?â€? Ta ce cikin shesshekar kuka “Idan ka gan ni a Nigeria to na zo ganin ku ne, amma ni da gidan ubanku har abada! Sai dai ya zaba ko ni ko Saratu da tsinanniyar ‘yar sa. Idan nazo zan baiwa Aminu lafiya ne? Allah ya bashi sauki.â€? Najib ya so yayi mata bayani yaga ma bayanin baya da amfani, shin yaya zata ji idan ta ji cewa ‘yar da tafi tsana a duniya ce Dan da tafi so fiye da kowa ke so har ya kamu da ciwon zuciya? Ashe dalilinta na kin Intisar shine don tsinto ta aka yi, kuma tana tsammanin shegiya ce? Wane bayani zai mata ta fahimta a waya? Sai yace “Hajiya ki daina illata Intisar hakannan, don zaki sha mamaki. Don Allah ki gyara halin ki, ki dawo ki ji me ke faruwa cikin rayuwar ‘ya’yan ki?â€? Faisal tunda ya fahimci abinda ke faruwa ya bar asibitin, bai kara waiwayar kowa ba, babu kuma wanda ya kara jin duriyar shi cikin asibitin. A lokacin da ake tsammanin shine mutumin da zai fi kusantar Saratun fiye da kowa. Iyayen na mamakin irin wannan masifaffen so na Intisar da Aminu, gashi ba wani dogon lokaci suka dauka tare ba. So mai neman salwantar da rayuwa kamar a birnin Hindu ai abin mamaki ne. To Al’ameen da ‘feeling hopesâ€? din da Daddy da Hadiza ke ta bashi ya soma shaida mutane. Ga Addu’o’in da su Baffa ke tayi har Mallam Sidi ya zo Abuja ya kwana yi masu addu’o’in samun saukin Ubangiji. Ranar wata Juma’a ya mike zaune yace zai sha (tea), farin-cikin mikewar sa wurin Daddy da suaran ‘yan uwa kema kin san ba sai an fada ba, jiki na rawa Haj. Hadiza ta hada shayi mai kauri ta mika mishi. Kai ciwon Aminu harda na shagwaba don ya dade da samun sauki ko don Allurai da magungunan da ake dirka mishi kadai masu tsadar gaske, sai ya rufe ido yana jinsu kurum. Ba abinda yake son ji irin ya ji Daddy na yi masa ‘yar murya yana rokon sa don Allah ya tashi shi kuma ya aura mai Saratu a gobe. Har president da sauran abokan aiki da abokan arzikan Daddy sun zo duba Al’ameen, haka Dr. Argungu da sauran abokan Daddy na (aikin soja). Daga Miami, Florida, da duk inda Al’ameen yai aiki ko karatu abokanshi likitoci sun barko don nuna mishi kauna, duk kuma sun ji to bakin Rehab ne da ya kira wayar Aminu Najib ya dauka yace yana kwance a babban asibitin birnin tarayya ba lafiya, kai wannan Asibiti yaga taron jar fata da bai taba gani ba, haka ta bangaren Daddy kusoshin Nigeria sai barkowa suke daga ko’ina cikin kasar mu mai dimbin albarka. Wani abin dariya sai suyi ta cewa M.A.B na ciwon kirji ne. Idan an fadi haka Haj. Hadiza tayi ta dariya. A ranar Ihsan tazo a gigice, Babanta ne ya gaya mata Aminu na kwance Asibiti. Ko gayawa Ann bata tsaya yi ba ta zari mota ta taho. Tana sanye da atamfa Holland koriya dinkin Niger, kanta yane da dan mayafi. Ta isa ga gadon Al’ameen bata ko kula da tarin iyayenshi balle ‘yan uwa ba ta janyoshi ta soma kuka a lokacin yana barci. Haj. Hadiza ta tambayi su Nasir ko wacece? Suka ce suke jin itace Ihsan matarshi, don suma basu taba ganinta ba. Tayi ta bata baki tace Aminu yaji sauki sosai a hakan ma sai karfin jiki kawai. A can Asibitin da Intisar take, su Hunainah na tare da ‘yar uwarsu suna jiyya har ta soma taka kafafunta, kar kiso ki ga farin ciki a wurinsu da Anti Saratu. Maganar farko da Al’ameen yayi shine akan me Haj. Hadiza ta bari aka sace Intisar? Haj. Hadizah tace “kai da baka da lafiya ina kai ina tone-tone? Amma kasan dai babu uwar da zata dauki Da na halal ta kai Daji, duk wahala, duk talauci balle babu daya kanwar biyuâ€?. Sai yayi murmushi. Ranar Asabar aka sallami Intisar, ita, Anti Saratu, Hunainah da Hidayah suka zarce gida, shi Al’ameen Alfered ya rikeshi yace bai gama farfadowa daga ‘Luv-sickâ€? din nashi ba, kullum tsiyar da yake tayi mai kenan sai yayi biris ya kyaleshi kamar bai san yanayi ba. Washegari ya mike da safe ya zare masu ledar ruwan ‘dripâ€? da suka makala mishi ya aje bisan gado. Ya dubi inda Ihsan ke ta sharar barci ita da Haj. Hadiza (‘yan jinyar shi kenan kowa na tare da Intisar) a ranshi yace “mun hadu a gabaâ€?. Kafarshi ko takalmi babu ya fita wajen asibitin ya tari machine yace ya kaishi Addis Ababa Crescent. Masu gadi zuwa ma’aikatan gidan kadan ya rage dariya ta kufce masu ganin Oga ko takalmi babu dare a bayan achaba, ya sauka kuma sai yasa kai zai shige, mai babur yace “Sir, kudina fa?â€? Gabadaya ya juyo ya shafa aljihunan wandonshi zuwa na gaban riga bai ji ko sisi ba, Major mai baiwa shukokin gidan ruwa bai san sanda ya tintsire da dariya ba, a nashi aljihun ya biya mai machine. Al’ameen ya juya yace da mai babur ya jira shi, mintuna goma a tsakani ya dawo da mukullan mota (Peugeot 505 Station Wagon) ya dankawa Major yace ya fitar da ita a rumfar adana motoci ya bashi, ya katse dimbin godiya da fatar alkhairin da mutumin ke ta kwarara mishi da cewa, “kayi mun Addu’a, Allah ya bani Halimahh! Malam Sani Daddy ya umarta da ya bude taron da Addu’a. Bayan an shafa ya dubi Haj. Hadiza yace in Ambasada yayi izni ta fadi labarinta da yadda ta rabu da ‘yarta Fatima har ya tsinta. Ambasada yace ta fada. Tiryan-tiryan ta fadi tun aurenta da Sarkin Noman Shanono, yadda kishiyar ta Shatu tasa aka sace Saratu suka kai daji. Abinda ya faru da ita bayan wannan har zuwa sanda su Hidayah suka kawo ta gidansu na Riyadh, wahalar da suka sha kan nemanta da ciwon data kwanta kamar bata rayuba har zuwansu Bashir Lagos a lokacin Daddyn yana kulle, sun kuma baro Lagos zuwa Abuja shida iyalinsa fiye da shekaru biyu, su kuma basu san inda suka koma ba har zuwa sanda Hajjo ta sami labarin cewa shi Makarfi ya yi bikin cikar shekarun haihuwarshi sittin a jarida, ta matsawa Hassan ya bincika suka je Korea suka taho da su. Zuwan su can gidan Daddy da shaida musu da akayi suna Asibiti. Shigowar ta dakin da Daddy ya shiga da kuma abubuwan da ta ji yana fade. Shima Daddy ya kwashe duk yadda ya tsinto Saratun a dokar daji a kan hanyarsa ta zuwa Kano daga Kaduna domin halartar (Seminar) ya kawowa Saratu, rokon shi da tayi su rufe sirrin a ce ‘yar ta ce har illa Masha-Allahu. Yadda suka gayawa ‘ya’yan shi cewa haihuwa tayi haka uwar su saida suka yi alkawarin cewa duk rintsi ba zata fada ba. Brigedier yai shiru na ‘yan dakikai kana ya cigaba. “Bayan wannan ban san komai ba. Na yi zaton Saratu karama na Riyadh, ashe wai tana gidan tana aiki a sassan masu aiki. Allah ya gani ban taba sani ba har zuwa dawowar Saratu gidana, da yake mun sami sabani na lokaci mai tsawo hakannan ni ba mazauni bane kwata-kwata. Na dawo daga tafiya muna hirar fahimtar juna da iyalina kamar yadda muka saba, a lokacin Saratu ce min tayi Intisar tazo hutu ne daga makarantar da muka kaita a can Riyadh, inda har kika ce kin ganta Haj. Hadiza. Aminu ya shigo, yadda ya nuna kwata-kwata bai taba sanin Intisar ‘yar gidan bace. Ita ta rika fadar wasu maganganu da dukkanmu bamu gane ba amma…sai ya dubi Intisar da murmushi, ta kau da kai ta sunne fuskarta da karfi jikin Antinta. Shi ko gogan sai ya kara lumshe ido yana dubarta da dukkan so da duk wata kauna da da namiji ke iya mallakawa diya mace, ba abinda ya dameshi da iyayen su dake zazzaune, suruki zuwa matar shi ta aure. Daddy ya cigaba da cewa “amma ke Intisar na ji kin ce ne wai ashe Al’ameen ne nawa na Miami? Amma har kuke shirin aure? Sauran duk ban ji ba don haka daina jin kunya. Kai kuma Al’ameen kace Saratu ta maka karya, daga nan kuma duk kuka susuce kuka susuta mu. To kuma bayan kun ji ana cewa duka babu alakar Jini akwai aure shine ko kunya babu kuka karkade riguna kuka taso daga gadon asibiti, wato mu zo muyi muku auren ko? Sannan kai Aminu karyar me Saratu ta yi maka?â€? Gaba daya falon aka sa dariya, Hunainah har da hawayenta jage-jage inka dauke Faisal da ‘yar Argungu. Shi kansa Dr. Argungu yayi murmushi kuma hakika labarin ya tsuma shi. Baya shakkar wadannan mutane masu cikar mutunci nada nufin cutar ko cin zarafin ‘yarshi illah al’amarin Intisar da Aminu Allah ne ya tsarashi. Aminu ya dubi Haj. Hadiza da girmamawar da bata kwatantuwa yace “Maman su Hidayah karyar da yarinyar nan ta shirya min har ta wuce hankali. Wai Babanta ne ya siyarwa Haj. Ita tayi mata ayyuka, nace yana ina? Wai yana fita ranar da ya kawota mota ta bigeshi ya mutu, uwar ta kuma bata san inda take ba wai dama foreigner ce, wai talauci ne ya ishesu suka sayar da ita. A hakan kuma sai gata tana min karatun kimiyya mai inganci, tun daga nan na sinsino karya take, na dai bita ne kawai da yadda take so don a zauna lafiya. Akwai sanda haka kawai na yi tunanin ko gudowa ta yi daga garin su akan maza? Don ko sallama nayi mata bata amsawa amma in mai aikin Hajiya ce (Dela) sai ta amsaâ€?. Nan ma aka sake yin dariya. Ya ce “Na taba ganin hoton Hidayah da Hunainah a hannun ta, ina gani nace wadannan kannen ta ne, domin kamar ta isa. Amma a rashin sanin dukkanmu, tace da ni makaranta kurum ta hadasu amma ko Mamar su kamar an tsaga kara sukeâ€?. A nan kuma murmushi aka yi. Al’ameen ya yi shiru na dan lokaci cikin wani tunani, a lokacin sautin muryar shi ya karye gabadaya. Ya dubi Anti Saratu yayi murmushi ya sadda kanshi kasa cikin jin nauyi ya ce, “Na taso da kiyayyar Intisar diyar Anti Amarya, a dalilin son da Daddy ke mata, ban ga wanda akaiwa hakan ba cikin su baki daya bayan ni, amma wannan son ya zarce nawa. A da, Daddy na sona fiye da kowa a gidan, amma tunda aka ce an haifi Intisar a kuruciyata sai nayi tsammanin Daddy ya daina sona. Babu wani nau’in azaba da ya zo min a rai da ban gana mata ba, amma Intisar so na take bata kuma guje ni ba, kullum sai ta yi ta leke na. Idan na juyo muka hada ido sai ta zura da gudu dakin Mamarta. Nayi ball da ita domin ta karye, ko ta targade ta daina wannan tafiyan nata kaman ta mage tun tana mitsitsiyar ta amma ba don ta makance ba. A kuruciyata, ban taba tsanar kaina irin ranar ba. Na bar gida a dalilin bakin-cikin abinda nayiwa Intisar haka agabadayan tsayin rayuwata 15 years a Miami, Intisar nake tunawa da halin da na barta ciki. Yana daga abinda ya dugunzumo zuciyata ga son dawowa, don kawai in ga Intisar in nemi gafarar ta. Abin haushin, Hajiyata ta boye min gaskiyar inda take, don kar inje ko don kar ince tayi ba dai-dai ba? Haka su Najib ban san dalilinsu na boye min ba, kodayake ban tambayesu ba, suma kuma basu ce min ba. Hajiya ce tayi sanadin da naje kitchen (Madafi) kamar yadda tayi sanadin da na nakasta ta. Zuwan da yayi sanadiyyar kasancewana dumu-dumu a kaunar yarinyar da ban sani ba, kawai na sa mata suna halimah, ashe intisar ce kanwar Faisal diyar Anti Amarya, kuma ‘yar wasu? Kai abin da mamakiâ€?. Kowa sai murmushi. Dr. Argungu ya dan zamo daga cikin kujerarsa yayi gyaran murya duk hankali ya koma kansa aka nutsu ana sauraron sa yace. “To a madadin kawun Al’ameen ina nemawa dana Al’ameen alfarmar auren Intisar a hannun ka Daddyn Intisar koko a hanun su Bashir Sambo ne?â€? Hajjo ta yi karaf tace “Ina! A hannun Daddy Makarfi ne, har yanzu wannan sunan “Saratu Bello Makarfiâ€? babu mai kankareshi. Mu kam Ameenu shine namu, don haka mun bayan alfarmar Dr. Argungu.â€? Daddy ya sunkuyar da kai tabbas nauyin Argungu yake ji, amma a zahiri yafi kowa farin-ciki. Ya dade da wannan burin a rayuwar sa don dai ba yadda zai yi ne. Kamin ya sani abin furtawa Ihsan ta fasa kara mai firgitarwa ta soma yiwa Babanta kuka tana masifar baya kaunar ta ita dama Ann ce kadai mahaifiyarta. Kuka take wurjanjan tana neman fita daga falon amma Anti Saratu da Hajjo suka riketa tamau. Intissar ta mike sauran kannenta suka mara mata baya kamar wasu ‘body-guardsâ€? dinta, harta kai bakin kofar fita falon ta juyo Idanunta sun kada tamkar an watsa masu dakakken barkono, wani tukuki yazo ya tokareta a kahon zuci, kallon da tabi kowa dashi tamkar ba ita ba, ba kowa take tunani ba a wannan lokacin face kuruciyarta da al’ameen dan Haj. Nafi. How much do you like this story? 5/10/22, 21:33 - Ummi Tandama😇: ____________________________ *âœðŸ? SIRADIN RAYUWAâœðŸ?* Book three *@Takori* Page6ï¸âƒ£ Ta zargi kanta ta tsani kanta duk a lokaci daya ta kuma kalubalanci zuciyarta da so da kaunar Al’ameen. Idanunta gab suke dasu tsiyayo da kwallar da ta kasa kwarara balle taji sanyi-sanyin azabtuwar da kirjinta keyi¸duk da haka tayi murmushi ta girgiza kai ta koma ta russunawa Dr. Abubakar Argungu ta ce, “Don Allah Baban Anti Ihsan kada ka kara fadin wannan maganan. Alkawarine na riga na yi tuntuni ba abinda zai kara hadani da Jinin Haj. Nafi ko a Lahira balle aure? Da nasan ma Al’ameen dan ta ne wallahi ko gaisuwa…â€? sai ta rushe musu da matsanancin kuka. Duk falon yayi tsit sai da tayi mai isarta tukunna ta nayi tana share hawaye da majina da gefen mayafinta. Tamkar anyi masa allurar karfi, Al’ameen wanda ke sauraronta cikin rashin fahimtar me take cewa, ya isa gareta tamkar wanda aka fizgo daga kujerar da yake zaune, ya figi hannayenta duka biyu ya mikar da ita daga durkuson da tayi kamar na mai neman gafara sukayi facing (fuskanci) juna tamkar zakarun dake shirin dambacewa, yace cikin karyayyar murya “Kika ce mene Intisar? Say it again!â€? Ta dube shi cikin ido, babu tsoro ba fargaba balle kallon nan nata cikin kunya dake gigita shi, babu komi cikin kwayar idon dake birgeshi face kallon tsana da tsabar kiyayya tsagwaro, da karfi ta ce, “Nace ko zan mutu ba aure, bazan aureka ba! Ka je ka tambayi mamarka ya mukai da ita? Tunda dan ta shine ‘daâ€? to taje ta nemo masa ‘yaâ€? ba bayi irin mu ba (slaves). Aure nace ba zanyi ba, Al’ameen ko ana doleâ€?.?â€? Kamin ta kare ya falla mata kyakkyawan marin da ya gigitata, in batayi kuskure ba ta ce har ta ga wuta. Aunty Saratu ta saki Ihsan ta ce, “Ah ah! Al’ameen, bayan lahanta mata idanun kuma again za’a kurumtata? Wallahi bazai yiwu ba. Ta ce batayi din ko tilas ne? Ga matarka nan ta dawo dakinta ita kuma a bar mana ita haka ta sarara. Wanda uwarku tayi mata bai isa ba sai ka kara mata? Al’ameen akan idona? Ke Saratu shige mu tafiâ€? Ta juya ga Ihsan ta ce, “Ihsan kiyi hakuri ki zauna a dakin ki, indai a kan Intisar ne kin ji tace bata yi, in ce ko shikenan?â€? Gaba daya suka fice. Daddy ya ce, “Ku dai mata duk shekarun ku tumaki ne.â€? Dr. Argungu ya ce “Hakane, yanzu kuma da kansu zakaji sun dawo maka da maganar, kaga Ihsan don Allah. Daga cewa an fasa aure ta shige daki ko kunyar idanun mutane, koda yake duk Amerikar ce ta kwashe masu albarkaâ€? Dukkansu suka sa dariya. Wannan ta wuce. ***** Ihsan kwana tayi kuka Al’ameen kuma kwanan takaicin da bazai fadu ba. Kin dai san Aminun Halimar, Halimar ta ce bata auren? Ya rasa ma takamaimai takaicin me yake? Sai da yayi tsam da ransa ya fahimci takaicin abin da ya aikata ne. Yaya za’ayi ya bugi ‘yar mutane a idon mutanen da basu da ya ita a duniya a lokacin da suke cike da doki da farin cikin ganinta suna lailayarta tamkar kwai? Kuma bayan tana da gaskiya. Abinda Hajiya tayi mata in yayi tunani kome tace dasu daidainta ne, ba kuma abinda ba zata ce dasu ba, don ma dai tana da dimbin hakuri, to amma for God’s sake su ina ruwansu kuma meye nasu a ciki? Ina laifin wani ya taba shafar wani? Shi bai guji tashin hankalin da zai gani daga Hajiyar ba ya furta yana sonta? Koda yake yana tsammanin tsoro ne ko tausayin Ihsan ya sata furta hakan. Bai sani ba, ta fadi ne heart and soul (baka da zuci). Ya juya ya dubi barin da Ihsan ke kwance, shi din ma tausayinta ya kamashi. Rana daya tak tashin hankalin daya jefata ciki ya ramar da ita. Barci take amma ga busassun hawaye nan a gefen fuskarta. Tun safe bakinta ko ruwa bai gani ba balle abinci, gara shi ya samu yayi karin kumallo mai kyau. Ya nemi zuciyarsa shawarar abinyi? Ya tabbata in har za su cigaba da rayuwar aure da Ihsan dole hakkinta ya kamashi, domin zuciyar bazata taba iya wannan adalcin ba, na son wata diya mace a yanzu bayan Halimah, (Intisar diyar Anti Amarya). Shawara ta karshe da ya yanke da zuciyarshi shine na ya rabu da Ihsan taje ko Allah zai hadata da mai sonta fiye da shi, ta kuma zauna da uwarta lafiya, shima ya sami saukin matsalolinshi. Ya zuro kafafunshi kasa a hankali ya janyo lokar gilashin da ke jikin gadon ya fiddo wani dan (memo) da yake amfani don kananan rubuce-rubuce, ya zari biro ya daura bisa. Kamar an ce da Ihsan ta bude idonta, a hankali ta bude ido ta dubeshi ta mike taga rubutu yake cikin wannan talatainin dare, ya rubuta sallama kenan ta fizge biron tasa kuka. Ta san ba abinda zai rubuta a dai-dai wannan lokacin in banda saki agareta, don yana ganin hakan shine kadai hanyar samuwar kwanciyar hankalinsa ya samu ya auri wadda yake so. Ta kifa kai bisa cinyoyinsa to shiga rera kuka mai karya zuciya. Yayi shiru yana kallon ‘ceilingâ€? shi kadai yasan me yake sakawa a zuciyar nan tashi mai cike taf da rudani. Ihsan ta san Aminunta, ta san tausayinshi da jin kai. Yana iya fasa komi don tausayi da jin kai. Ta sauka daga gadon gaba daya ta durkusa a gaban shi tana kuka hawayenta masu dumi na diga bisa farar kafarshi, tace a cikin muryar kuka “Wallahi Aminu in ka sake ni na gwammace in kashe kaina in huta, don bazan iya rayuwar ba. Tun da har ina son ka Al’ameen akan me bazan so abinda kake so ba, ko mene ne shi balle kanwarka ta da, Intisar?â€? Ta dago ta dibeshi cikin ido, babu komi ciki kwayar idonta face gesture (motsi mai nuna zahirin abinda ke zuciya) ta ce, “Al’ameen ka tuna son Saratu ne fa ya kwantar da kai kamar ba zaka rayu ba, baka tunanin nima in na rasaka ba mamaki irin halin da zan tsinci kaina ciki kennan? Zuciyarka ce ke ciwon da har abada bazaka warke ba saboda tunanin ka rasa wadda kake so. Imagine yadda kake jin Saratu a rai haka nima da baka so nake jin ka. Na jure huldar ka da mata bila-adadin a Miami, akan me bazan iya jure wannan kalilan ba? Don mace daya? Ni dai ko ukku zaka karo in har zaka barni a matsayinda nake, to zan iya jurewa. Abinda ma nayi dazu wallahi zuciyace ta ciwo ni, don ina ganin Babana da ya haifeni bai damu da farin-ciki na ba. Amma yanzu na gane ‘So daga Allah neâ€?, babu kuma wani abin halitta da ya isa yayi yadda yaga dama da shi sai ko Ubangijin daya assasa mana shi a ruhi, don haka bana kishin son da kake wa kanwarka illa in roki Allah nima ya sammin ko gutsire ne daga cikin wannan son na Intissar a zuciyarka Ameenu.â€? Ya kai hannu ya dagota daga durkuson da tayi bisa kafafunshi ya zaunar ta gefen shi ya ce, “Ihsan ba haka bane, ba wai bana son ki ne ba, bana sonki zan aureki? Illah don dukkanmu mu samu kwanciyar hankali. Ki diba kiga tun dawowarmu gida muke cikin matsala, ke matsalata da ke na farko Babar ki bata sona. Na biyu kina da azababben kishi. Irin rotsen da kikewa mata a turai a kaina yana tsoratani, kar in hadaki da yarinyar mutane ki kashe musu ‘ya ni kuma bazan juri wannan ba, iyayenmu ma bazasu yarda ba, bayan haka ma nasan Saratu akan haukar da taga kina yi ne ta furta abinda ta ce. Ba abinda zai sa in hakura da Intisar yadda kema bazaki iya hakura da ni ba, ba yin kaina ne ba wallahi daga Allah ne. Kiyi hakuri I don’t meant 2 hurt u amma ko daya ban taba tunanin akwai macen da zan so ba haka a rayuwata har muka dawo. Tun ganina na farko da ita ban kara tunanin kowa ba, ban kara tunanin komi ba sai ita, ban kara dubar wata mace da sunan so ba sai ita. To mai wannan son idan ya sami abin nan da yakeso Ihsan ina zai iya adalci? In zo Ubangiji ya azabtar dani kan danne maki hakkoki? I’m sorry to say, ko a yanzu bana jin zan sake samun nutsuwa ban sami Intisar ba, ina tsoron danne maki hakokki da ke kaina, don haka kiyi hakuri Ihsan mu rabu, don hakan shine kadai hanyar samuwar peace of mind na kowannenmu, watakila hakan na nufin wani kebantaccen al’amari garemu duka? Sai kiga Allah ya musanya maki da mafi alkhairi na.â€? Ihsan kuka take tukuru, ba abinda take fadi a zuciyarta face la’ana da Allah ya isa ga duk ma wata mace mai sunayennan uku: Saratu, Intisar da Fatima. Tsakaninta da Intissar Li’ilafi dubune Allah ya isa kwando-kwando. Cikin dan lokaci duk ta mallake mata zuciyar miji tun kamin ya aure ta, Allah sarki! To ina ga ta shigo gidan? Ashe lokaci yazo da zata koma gefen Aminu tayi kallon rayuwarshi da wata? Ita kuma haka Allah yaga dama da ita? To amma yaya zatayi, tunda ta amince son shi take da zuciya daya. Ta tsinewa kasar haihuwarta da tayi mata wannan cin amana. Inama batace su dawo Nigeria ba! Shin a duniya zata ki wani dan adam kamar yadda ta tsani Saratu-Intisar? Ta tsani sunan, bata son ji, to amma me? In har da gaske tana son Al’ameen Bello, kenan dole ta tursasawa zuciyarta kaunar Saratu Bello? Tunda ta rigaya ta zamo wani bangare na gangar jiki, Jinin jiki, ruhi da kalbin Al’ameen? Sai ta matsa sannu a hankali ta kara shigewa jikin Al’ameen kamar yadda yake a al’adarta, tamkar magen da ke jin sanyi, kanta ta kwantar bisa kafadunshi, cikin low and weak voice (mara amo kuma rarraunar murya) tace “Aminu, ni fa na amince ina sonka, to akan me bazan so abinda kake so ba? Na rantse da Allah na amince ma auren Intisar da zuciya daya, ni ce ma zan je in rarrasheta, tunda akaina tace ta fasa aurenka. Zan kuma yi kokarin danne wannan kishin da baka so, in kuma maganar Ann ne Allah ta saduda don ita tace in je in yi jiyyar ka a asibiti, na baka hakuri ta gane batayi dai-dai ba, don haka ka fidda shakku akan mu, don ta adalci ai ni ce mai karfafaka da kayi, kuma hakkina ne in shiga yi maka addu’ar yin adalci a tsakaninmu. With my 100% go ahead (da goyon bayana dari bisa dari) ka je ka rarrashi Intissar ku shirya, kuma kada ka kara marar mun (little sister) na Al’ameen bana so..â€? da haka ta juya akalar hirar ga wadda yafi so suyi, tun suna Miami. Tuni Al’ameen ya mance da duk wata damuwa da yake ciki, kuma hakika sunyi missing (kewar) junansu ba kadan ba, tun ranar da suka baro Miami basu kara samun kwanciyar hankali ba. Don haka kowanensu cike yake da kishirwar dan’uwansa sun ma mance da matsalar data shiga tsakaninsu a baya. Sai Al’ameen yaji ranar tamkar irin renakun amarcinsu a beaches da resorts din Miami cikin bikini. Daga baya ma tausayi Ihsan ya rika ji, da yadda yaga jikinta na rawa, ya dubi irin cuzgunawa da maganganun soyayyarshi da ya yaba mata yanzun amma bata damu ba, burinta kadai ta nuna mishi kauna. Sai ya janyo matarshi shima aka barje, ya kuma alkawartama ranshi ko ya samu Intisar ko bai samu ba, ba zai taba wulakanta ta ba, don ya amince Ihsan mai kaunar shi ce tsakani da Allah ba don wata tsiya daya mallaka ba, mai kuma kaunar duk abinda yake so. A washegari wayar Ann ce ta fara tada ita daga barci, ta gode Allah Al’amin din ya shiga wanka tana cewa “Helloâ€? Ann to shiga zaginta da cin mutunci na fitar hankali ta ce, “kuma kin bani kunya Ihsan, mace kamarki, da gata da ilmi da aji ta dinga bin namiji daya yana garata kamar gare-gare abin wasan yara? Wallahi kin zubar da mutuncinki, kamar yau ne ina nan a zaune ranar daya wulakantoki da kafarki zaki nemeni tunda baki sayawa kanki darajjah ba, ana nema a siyo miki kina watsarwa.â€? Ta ce, “To Ann, ya na iya? Ina sonshi, ya zanyi?â€? Ta kara kular da Ann to kwantsama mata ashariya ta ce, “Son banza? Idan so cuta ne shi hakuri ba magani bane, har wata tsiyace Aminu Bello? Yana likita kina likita ki tsaya yana kada miki bindi?â€? Ta ce “lala! Ann, Aminu fa Malami na ne, ko a (ST. Bathalomew), daga gareshi na soma koyon psychology da psychiatry bafa wai likitan kwakwalwa ne kawai ba, koko wanda za’ace ga iyakacin field din shi kamar ni ba Malami ne a jami’o’in Miami. Kina ganinshi haka dan yaro Allah ilimin shi ya zarce tunani.â€? Haushi ya ishi Ann, Ihsan ta yi nisa bazata taba waiwayowa ba. Luv is overall! Ta ja dogon tsaki ta ce, “Kin yi asara dai, banza.â€? A lokacin yana tsaye ya sakarwa kanshi shower amma bugun da zuciyarshi keyi ya tsananta, zafin da ke azalzalar kirjin shi ke neman kayas da shi, sai a lokacin ya tuna rabon da ya sha magungunan shi tun safiyar jiya. Duk wata dibara da yake jin zai iya, a matsayin shi na likita yayi domin isa ga dakin barcin su inda ya aje magungunan cikin lokas, hannunsa na dama dafe da kirjinshi hakannan bugun zuciyar na kara karuwa fiye da farkon farawarshi, yana bin bango sannu a hankali da taimakon Allah ya isa ga lokar, yayi amfani da hannun hagunshi wurin fiddo magungunan. Ihsan ta shigo, ganin halin da yake ciki bata san sanda ta saki flask din shayin da ke hannunta ba da tray din gaba daya, ta karasa da gudu ta tallabeshi, ta ce, “Aminu, wayyo! Kirjin ne? Ka ga tun jiya baka sha magani ba, ka manta me Alfered ya ce, wayyo ni Ihsan na banu.â€? Ya yi mata alamar ta kawo mai ruwa, ta jinginar dashi jikin gadon ta tusa mai filo a baya ya jingina sosai, da gudu ta sake yin kichin ta fiddo ruwa mai sanyi da tambulan ta dawo ta mika mai kana ta cicciri magungunan ilahirin jikinta babu inda baya rawa, tasa mai abaki tasa mai kofin ya kora magungunan da ruwa, daga shi har ita sunyi wujiga-wujiga idanuwansu sunyi jazur. Ta ce, “I’m Sorryâ€? ya dubeta da jan idon yayi murmushi itama tayi karfin hali ta kakaro iya fatar kyakkyawan bakinta tace “You’ve to rest, pls Aminu, I don’t want to lose u, ka dinga kula, don Allah?â€? Wasu hawayen suka silmiyo ta gefen idonta. Ya kallet cikin jimami bai san me zai ce mata ba. To ba zai iya fadar mai dadi ba, da yace da ita yadda bata son ta rasashi haka shima baya son rasa Intisar. Tausayinta ba inda bai bi tsoka mai gudanar da jinni a jikin sa ba, to amma ya zaiyi? Kamin ta ankara barci mai nauyi yayi awon gaba dashi, ta sauka gefen gadon ta zuba mishi ido kuri, tana mai kara kaunar kowacce halitta a jikinsa. Haka kawai taji gabanta na faduwa lokaci-lokaci a duk sanda ta dubi Al’ameen, ta kai hannu ta share mai gumin da keta yankowa daga goshinsa, da taga wannan bazai mata ba, sai ta mike ta dauro alwalla da ada bata damu da ita ba, ta bude Al’kur’anin shi dake aje bisa durowa ta soma karanto mai ayoyin neman sauki data koya daga gareshi. Karfe hudu na yamma ya mike tangarau cike da kuzari tamkar wanda bai da wata lalura, cikin hamzari ya fada toilet yayi (freshen-up) ya dauro alwalla kamin ya fito Ihsan ta shigo rike da kofin tangaran cikke da danyar madarar shanu mai sanyi wadda shanta ya zame wa Aminu lazim a duk yammci, ta aza bisa ‘centre tableâ€? ta koma ta shiryo reduced fat and salt meal bisa dan madaidaicin tray wato abincin masu cardiac/hypertension problem. Ta zauna gefen gadon tana kallonshi yana sallah, zuciyarta cike da jin dadin ganin samun saukinsa, ya shafa Addu’an ya juyo ya sakar mata lallausar murmushi ba tayi nawa ba wajen mayar masa, yaja yatsar kafarta dake kusa dashi ya daga gira cikin tsokana yace “Kai Ihsan, irin wannan tagumi haka, ranar da na mutu ashe ke sai asibiti…â€? ta yi sulu ta rufe mai baki da tausasan yatsunta, kamin ya ankara sai hawaye sharr! Wani na korar wani. Ya janyo matarshi tsantsan yana dariya ya ce, “I’m Sorry, haba Ihsan kamar ba likita matar likita ba. Ni na isa in mutu, ban aje masu yi min Addu’a ba? So take care of urself b’cos I care!â€? Ta dago ta dubeshi cikin rauni da karaya. “Ka manta ne mahaifan ta lalace already? Are u dreaming? (kana mafarki ne) Ban ki ba dai daga Little Sister Intisar zamu samu masu yi mana Addu’a a gidan nan.â€? Ya girgiza kai cikin rashin kulawa da maganarta, ya ce, “Ai ni yau Baban Babe ne, to Maman ga bakina a bamu abinci…â€? ya bude baki har ya bata dariya, ta dauko kofin madararshi sai ya girgiza kai ya maida hannunta inda ta dauko kofin yana cewa “I need only you (ke kadai kawai nake so).â€? Tai kasa da murya, sai in har ka kasa kunne ne zaka ji cewa da tayi “U are always welcome!â€? Ita dai al’amuran Al’ameen Bello, daga jiya zuwa yau na bata mamaki. Haka kawai ta ji jikinta yayi sanyi, kuma so da tausayin Al’ameen na kara dawainiya da ita, second bayan second, minti bayan minti, awa bayan awa da bazata ce so da tausayin Al’ameen ne ba. How much do you like this story? 5/11/22, 08:13 - Ummi Tandama😇: ____________________________ *âœðŸ? SIRADIN RAYUWAâœðŸ?* Book three *@Takori* Page8ï¸âƒ£ A kalaminshi na karshe, wadanda kuma suke kalmomi na karshe a littafin da alama ma yanzun ya rubuta; ‘To in haka ne shi meye ribar sa a rayuwa? Da me ya yi riba da me ya tsira? Bai gani ba! Bai ci riba da son Intisar ba, bai ga amfanin ilmin daya nema don ta huta da shi ba, tunda Al’ameen billonnaire ne, baya bukatar a agaza masa, bai ga ranar da son da ya shekara yi mata yai masa ba. He is but a real loser! To amma tunda don ita ya nema, shi mai mallaka mata duk abinda ya mallaka a duniya ne koda kuwa ta auri Aminu ne ko waninsa, tunda dama tunda fari ya alkawartawa ransa hakan.â€? Ragowar bata iya ta karasa ba, saboda kwakwalwar ba zata iya ganewa ba…â€?.balle ta fassarawa zuciyar ta! Inteesar ta daga ido sama tamkar mai kididdiga adadin juyawar fanka, wasu irin hawaye ne marasa dandano bare launi ke tsere ‘one after the otherâ€? (bi-da-bi) kan kyakkyawar farar fuskar ta. Abubuwa da dama ta tuna a wannan lokacin, wato kuruciyarsu da Faisal can baya. Ashe dama abinda take ji game da shi a lokacin itama ‘sonâ€? ne? Gaba daya jikinta ba inda bai diba ba cikin kaduwa, dimuwa da razana, a take zazzabi mai zafi ya soma kokarin rufeta, saboda karkarwa da ilahirin jikin ta ke yi littafin ya zame ya fadi kan kafarta, dai-dai lokacin da Faisal ya murda kofar bandakin ya fito gabadayan sa. Daure da towel faffada iya kungushi yana ‘combingâ€? sumar kanshi sai ya daskare cikin matsanancin mamaki, suka dubi juna a gaggauce idanunta face-face da hawaye, tayi saurin juya mai baya, kana ta doshi kofa tana cewa. “Dama Daddy ne yace in kirawo ka, kada a kara zama cin abinci kana gida baka zo baâ€? ta sheka da gudu zata bar dakin abin tsautsayi, sai gilashin ya fado ta kuma taka shi da kafarta hannun ya lankwashe amma saboda quality (karkon) gilashin bai fashe ba, kamin ta russuna ya isa gareshi sai suka russuna a tare, hannunshi ya riga isa bisa gilashin don haka natan sai ya sauka akan nashin, shi yai nasarar daukowa, yasa karfi wajen gyara lankwashewar da yayi, a yayin da ta jingina da bango idanunta a runtse, hakannan hawayen basu fasa kwarara ba kamar an sunce fanfo. Ba komi take tunawa ba a lokacin face ranar da ya cire mata gilashi ta baya, lokacin ana shirye-shiryen tafiyarsu Riyadh ita da Khaleel, ta dinga bin inuwarsa a hasale tana “bani gilas dina Ya Faisal, kaga bana soâ€? haka dukan da ya sha da filo da wakokin da ya kanyi mata na “come on beautiful Babe, Maman?â€? Cikin nutsuwa ya maida mata gilashinta, suka sake dubar juna a susuce sai ta kara da gudu. Ya dade anan tsaye yana tunanin me ta gani ya sata kuka? Me ta gani ya gigita ta haka? Bai yi tsammanin zata sake kulawa da al’amarinsa ba a yanzun dai da ta ke cikin son Yayan shi Ameenu? Intisar dakinta ta nufa agigicenta ta maida kofar ta rufe ta murza key. Ta jigina da kofar ta sake runtse idonta da karfi, tamkar mai son farkawa daga mafarki. Abubuwanne ke tariyo mata can baya tamkar a majigi. Ta tabbatar Faisal shine mutumin da ta fara so a rayuwarta kuma mutumin da bazata taba samun mai kaunarta a duniya tamkar shi ba. Tausayinshi, yagama narkar da duk wani tunani da ta mallaka. Ta zargi kanta da cin amana ta kuma kirayi kanta da ‘butuluâ€? dan adam mai manta alkhairi. To amma wani bangare na zuciyarta ya kalubalanci hakan da hujjar cewa, a lokacinta da Faisal tsammani suke su ‘yan uwan junane sabanin haduwarta da Al’ameen. Hakannan Al’ameen shi ya koyar dai ta son shi, shi ya kimsa mata son shi karfi da yaji, bata san so na soyayya ba sai akan shi, don haka bata jin Allah zai kamata da wannan hakkin na Faisal sai dai kaso mafi rinjaye na zuciyarta na karfafata da cewa, yanzu ne ya dace tayi wani abu, yanzu ne ya dace ta sadaukar da kanta da soyayyarta (son da takewa Al’ameen) don nunawa Faisal wannan kaunar da ya wanzar da rayuwarshi nuna mata, tun tana a tsumman goyo. To wai ma ya akai ta so Al’ameen? Bata sani ba, illa may be because he is unikue (watakila don shi din na daban ne). Ta yaya? Ta yaya zata nunawa Faisal din kauna bayan a yanzun ya nuna baya da lokacinta ma? Ta tambayi kanta, lokaci guda ta bawa kanta amsa da cewa ta hanyar auren shi mana Intisar? Amsar tayi mata nauyi a baka da zuci, wai Intisar matar Faisal in banda Allah mai juya al’amura ina wannan abu zai taba zuwa masu a rai? A lokacin ne kuma ta tuna shima fa Faisal dan Hajiya ne! Wannan zuri’ar da tayi alkawarin ba zata sake kulawa ba! Wannan zuri’ar data nuna mata kiyayyar da ba wani mahaluki a doron kasa da ya taba nuna mata! Wannan zuri’ar da idan ta aura, ta sake jefa kanta cikin bala’I da masifa ne watakila ma fiye da na baya. Bayan yanzun da cikakken gatanta, ga Aunty, Daddy, uwa-uba dangi da uwa mahaifiya masu so da kaunarta. Zuri’ar Haj. Nafi? Ta girgiza kai da karfi, ire-iren maganganun Haj. kadai ke dawo mata wasu na bin wasu. “Wai me yasa kike son ‘ya’yana ne, bayan ni na tsaneki? Har kullum mutum kanyi nisa ne da jinin makiyin shi, Saratu banda ke! Don naji ance komi Faisal kike ambato, har kuka kika yi da ya bar kasar, yayi maki kama da ‘ya’yan mutsiyatan kauye ne? So nake bandakin nan ya fiki fari, ya kuma fi Faisal di na kamshiâ€? Faisal ne ya sa miki suna Intisar, kuma da na ne, mallakina ne, don haka daga yau na kwaceâ€?. Ke Jikar Jummai ce, Jummai uwar Saratuâ€?. Daga yau kika sake koda kallar min ‘ya’ya, sai na sa wuka na tsokale wadanna makafin idanun munafurcin, kina jina? Ta tuna amsar da ta baiwa Hajiyar a lokacin. A yau ma sai ta samu kanta da nanata su, sai dai sabanin sunayen da ta kira a wancen lokacin a yau cewa tayi…ba Faisal ba, ba Aminu baâ€? duk wani jininki ma idan na sake daga ido na dubeshi ba da kiyayya ba, ki ce ni shegiya ce na amince! Ta kudurce a ranta daga yau dukkansu ko gaisuwar dayansu bata so. Aure kuma in har sai da ‘ya’yan Haj. Nafi ne, to ita Saratu ta yafe! Ba irin bugun da su Hunainah da Anti ba suyi ba amma Intisar bata bude ba. Wuni tayi cin kuka da nadama mara amfani. Ta rasa meyasa rayuwar ta ke da matsaloli iri-iri tun tana jaririyarta. Dagabaya kuma tayi tunanin akan me zata bari soyayyar ‘ya’yan Hajiya ya wargaza mata rayuwa? Komi fa mutum ke daurama kansa don Allah baya daurawa rai sai abinda zata iya. Ta yankewa kanta ‘solutionâ€? na karshe tayi murmushi ita kadai. Ta san cikin Iyayenta kakaf, babu mai matsa mata akan wannan kudurin nata. Sai ko Mamarsu Hunainah ita ko bata jin ta don ta tabbata Daddynta zai bata goyon baya dari bisa dari. Ba ita ta fito ba sai karfe hudu na yamma, shi din ma azababbiyar yunwa ta fiddota. Su Hunainah na magana da Anti Hajjo a waya ta ce, “Gata nan ma ta fitoâ€? ta mika mata wayan ta ce, ‘Hello Auntyâ€? Hajjo ta ce, “Ba wani Yello Aunty, nikan baki dauke ni Antin ba, da ko menene ke damunki da kin kira ni kin gaya mini, Saratu shin me yayi zafi ne haka? Na ji an ce tun safe kin rufe kanki a daki kina kuka. Na dauka kasancewar mu kusa da ke, da tabbacin da kike da shi na iyayen kwarai ya isa ya sanyaya maki zuciya? Wannan kuntata duk na menene?â€? Tayi shiru, Idanuwan ta sunyi rau-rau kaman ta saki kuka. In da Anti Hajjo ta san yadda take jin zuciyar nan tata, da bata zargeta da kuntatawa kanta ba. Ita ba sauyin Iyaye ya dameta ba, damuwarta daban ne, daga ita sai Ubangijin ta suka santa. Hajjo ta ce, “Koda bakya kaunar mu Saratu, mu ne dai iyayenki, kuma ba’a sake iyaye sai iyayen daki. Wannan rashin sakin jikin da kike damu ban sani ba ko don ki na ganin bamu isa mu zamo iyayen ki ne ba?â€? (Aunty Saratu ce ta koya mata, ba’a jin damuwan ta sai da dabara) Ta sa kuka da karfi tace “Aunty Hajjo me ya kawo wannan maganar? Na rantse da Allah ba haka bane, ni abinda ke damuna daban ne.â€? Hajjo ta ce, “Don kin ce kin fasa auren Al’ameen? Ke, yarinyar ki da ke kar ki bari ciwon hawan jini ya kamaki akan soyayya. Shi Al’ameen din yace dake ya damu? Yana can tare da matarshi Allah kadai yasan farin-cikin da suke ciki sai ke ki bi ki kuntatawa ranki?â€? Ta share hawayen da ke zuba mata da bayan hannu, dai-dai sanda dan halak din ya yiwa falon tsinke, matarsa na biye da shi tamkar ta shige jikinshi don tsatsiba, ya zarce kai tsaye har inda take, ya ja tebur inda take ya daura kafa daya, dayar kuwa na kasa tamkar mai son jin kwakkwafin abinda ke sata kuka a waya. Ihsan ta bisu da kallo kana tabi bayan su Hunainah da sukayi cikin dakin Anti. Intisar ta bude baki domin ta bawa Antinta amsar da tai niyya amma kwarjinin Al’ameen ya katse komi. So ta ke tace har wata tsiyace Al’ameen din da zata kuntatawa kanta akansa? Ita ba shine damuwanta ba. Hajjo ta ji tayi shiru ta cigaba da cewa, “Ni dai shawarata a gareki Intisar, ki fidda damuwar komi a ranki, ki koma makaranta. A shirye muke damu nuna maki kauna ta kowanne fanni. Na san kina son Al’ameen, so bana wasa ba. Tunda har kika kusa salwantar da rayuwar ki akan tunanin bazaku iya auren juna ba. Amma abinda na ke so ki gane shine, ki yi tunani, ke yarinya ce karama har yanzu cikin shekarun (teenage), wannan gigin son duk na dan lokaci ne, da anyi auren an haihu shikenan ya zama tarihi sai zaman hakuri da juna. Abinda nake so da ke shine ki tsaya ki gina rayuwarki a bisa tubala na kwarai, in ba hakaba ba mamaki bada jimawa ba soyayya ta ruguzata. Al’ameen ya fiki wayo, daga shi har matarshi ba tsaranki bane a budewar kai da ilmi. Don haka ki tsaya ki nemawa kanki madogara mai kyau tukunna, wanda shine wannan ilimin mai matukar wuya. Idan kika sameshi samun Aminu ba zai maki wuya ba haka in kika barshi ke da banza a cikin su daya kuke, don sai kin raina kan ki a cikinsu. Ni in son raina ne ma Allah bana son ki auri mai mata irin Ihsan, ki dubi yadda take hauka akan mijinta fa, ke ‘yar nan, mind yourself (ki shiga taitayinki)â€?. Ahaf! Ai kamar Antin ta shiga ranta taga abinda take shiri komawa makaranta, tayi murmushi tare da saurin rufe ido, maganganun Antin take aunawa abisa sikeli daya bayan daya, wanda dama duk tayi tunaninsu, babu wanda bata ga gaskiya a ciki ba, ta ce a raunane. “Na gode Aunty.â€? Ta rufe wayar, sai yanzu ya fuskanci da wa take magana, bata ko dubeshi ba ta murda kofar da zata hadaka da dakin ta daga falon Anti, yayi hamzarin murda keys ya zare ya tura aljihun bayan wandon ‘basachiâ€? dake jikinsa ya ce. “Me Anti Hajjo ke gaya maki a waya, kike godewa kina kuma kara yi mun asaran hawayen da nake ganin daraja da kimar su fiye da na kowa?â€? Wasu ubansu harara da ta watso mai ya bashi mamaki don bai taba ganin tayi ba, ga idanun sunyi jawur sai ta kara kyau a idon shi, ko da yake so ne hana ganin aibi, ya ce, “Inteesarâ€? da muryar nan da ke karya lagonta, ta kassara kuzarin ta, amma a yau ko gezau, har yanzu hararar shi ta ke ba kakkautawa. Ya soma taki har inda take tsaye tamkar sassakakken gunki, ta soma ja da baya kamar wadda taga abin tsoro da kyama, ta san ba karamin aikin shi ba ne ya kamata da kokawa kawai don ya sata yin magana, cikin tsiwa da yatsina ta bude dan bakinta tana mai nunashi da dan manuninta ta ce, “Wallahi Al’ameen ka sake ka tabani yau zan fasa ma kaine, in bar inyamurar matarka da jiyyar da baka taba yi ba.â€? Bai fasa dosarta ba ya ce, “Jinya kuma wacce ce ba’ayi ba? Sai dai kar a kuma, idan jinya ta ciwon son halimah ce, to ayi ta yi kar a tashi. Kar ki kara kira mun mata inyamura, yadda kike musulma diyar musulmi, haka itama take.â€? dai-dai lokacin da ta dangana da bangon karshe na falon, shi kuma bai fasa bin ta ba, ta ce, “Wallahi zan kirawo Anti, tayi ma kashedin shiga harkana, ka nemo Halimar ka can amma ni Intisar ce, ka manta ka taba sanina a rayuwarka, ina gaya maka, ina kara gaya makaâ€? ya toshe mata baki. Ya ja hannunta na dama da karfi har bisa seater dake tsakiyar falon, ta karfin tsiya ya zaunarta ya ce, “Ke in ma Daddy zaki kirawo babu laifi. Amma sai na gama maganar da zan yi. Kin san me ya kawo ni? Zuwa nayi in gaya maki ranar da duk wannan maganannen bakin ya kara kuskuren cewa bazai aureni ba don uwata, wallahi sai na kakkarya ki.â€? Cikin tsiwar da bai san ta iya ba ta ce, ‘Ka karya ni? To ka ji ka sani ko da can da ka makantani, don ban da wayo ne, amma yanzu wallahi sai dai ayi ‘yar bibbiyuâ€? saura kadan da dariya ta kwace masa, to amma shi kansa yasan bai kyauta ba, jiya ya mareta yau ya gaya mata kakkausar magana, shi da ke neman wanke dattin da Hajiya ta yayyaba masu daga idanunta. Ya dire gwiwoyinsa bisa carpet abinda bai taba yiwa wata ‘ya mace a rayuwarsa ba, a yayinda ita kuma take zaune cikin kujera ta cika fam, kiris take jira ta fashe. Ya langabe kai gefe guda gwanin ban tausayi, yayi kamar ya share mata hawayen da suka soma surtu, sai kuma yafasa. Ya ce, “Inteesarr!â€? Yadda ya kira sunan cikin murya mai karkarwa da kauri (husky) kadai ya birkita Saratun, bata jin ko dan yatsanta zata iya motsawa. Ya ce, “I ‘am sorry, terribly sorry! Wallahi ni, wasa nake maki, in karya ki in ce na karya wa kenan? Jiya kuma zuciya ce ta debe ni, kin san bata da kashi, abinda kika fadi cikin mutane ya bata mun kwarai. Ni kaina ban san ya akai ba, Pls, 4 give me…â€? Ya karasa a raunane, kana ya matso ‘yar kwallah, ya maida ta bisa kujerar ya ce, “Wallahi Intisar nasan Hajiya ta bata miki, to amma ni meye laifina? Ni ban ji tsoron abinda hakan zai janyo man ba daga gareta na furta ina sonki? Sannan kuma bakya tausaya mun halinda zan shiga in na rasa ki kwata-kwata, ki tuna baya?â€? Ta sadda kai kawai, bata son jin wannan abun da take ji game da Aminu, bata son wadannan ‘feelingsâ€? din da take ji game da shi masu tada tsigogin jikinta a duk lokacin da suke tare, to amma Al’ameen din kamar wani mayen karfe ne, wuyarta yayi mata magana da wannan muryan nashi mai jan mutum uwa lantarki duk wani ‘weaknessâ€? din ta ya gama samunshi. Ta tabbata nisa da shi shine abu mafi a’ala a gareta in har tana son cimma kudurirrikanta akan Haj. Nafi, wadanda daga ita sai zuciyarta sai mahaliccinta suka san na mene, amma ba don bata son shi ba. Karya ne ko fatar bakinta ta fada, to bacin rai ne. Shi kadai take so har cikin tsokar zuciyarta, har gangar jiki zuwa kwakwalwarta babu inda baya girgiza da kaunar Al’ameen da sha’awar komi nashi, ita kadai ta san me take ji da yakin da take yi da zuciyarvta a duk lokacin da yai kuskuren kai hannunshi gareta koda yatsar hannunta ne kuwa amma ta rantse, ta kuma ta rantse ko son sa zai kasheta, ko duk duniya zata taru a kanta, bazata aure shi ba! A ganinta ta hakanne kadai zata rama abinda sukai mata shi da mahaifiyarsa wanda har abada bazata manta ba, ba zata yafe mata ba kuma ba zata daina tunawa ba. Bata san wannan hukuncin da ta yanke yai tsauri ba, domin son da Al’ameen ke mata Allah kadai ya san iyakarsa; ba na wasa bane, ya wuce ayi ramuwar gayya akansa yayi masa tsauri bazai iya dauka ba. Da kyar in bata yi kuskure ba, da kyar in hukuncinta ba zai zamo nadama mara amfani a gareta ba. Ya cira hannunta ya aza bisa kirjinshi, tana iya jin nannauyan bugun da zuciyarsa ke yi akai-akai, jikinta ya soma sanyi, ya ce, “Ki ji Intisar, kiji irin bugun da zuciyar nan ke yi a domin ki, saboda ke ne take ciwon da har abada bazata daina ba, ba kya tausayi na Intisar ba kya sona yanzun? Allah na rantse, in muka cigaba da tafiya a haka wata ranaâ€?. Wata rana bugawa zatayi gabadaya ta fashe kowa ya huta, ki taimake ni ki agaje ni, ki daina la’akari da laifin da ba nawa ba kina hukunta ni dashi don Allah?â€? Ita dai ta zamo ‘paleâ€? ko motsi ta kasa balle tayi kokarin yin wani abu, ta rasa abinda ke mata dadi shi kuma bakinshi bai yi shiru ba da gaya mata irin halin da zai shiga in ya rasata. Har ya kai ga kwantar da kansa bisa kafadunta. Cikin wannan halin Faisal ya turo kofar falon ya shigo, fes idon shi a kan su, ya juya da sauri yana cewa, “Excuse me plz. Ya Aminu ban sani ba!â€?. Ta mike a gigice ta banka dakin Anti, ta kifa kai bisa gado ta soma rera kuka sabo fil. Ina rowan mai neman kuka an jefeshi da dunkulen kashi. Gabadaya suka zubo mata ido Anti da Ihsan suka yo kanta Anti ta ce, “To kin gani Ihsan mijinki kullum sai yasa min ‘ya kuka, don haka ki je ki ja kayan ki ku tafi.â€? Ta sake kuluwa ta shaka ance Al’amin mijin Ihsan, ta sake tsugewa da kuka. Ihsan ta matsa jikin gadon ta dago kanta ta aza bisa cinyarta tana murmushi tace “Haba little sister na, kin hana mun miji sakat ko tausayinshi ba kya ji, jiya saura kadan ya sakeni, don Allah kiyi hakuri ki bamu hadin kai ko na samu kan Al’ameen nima…â€? Ta soma fidda kwalla itama, wani tukuki na cinta a rai, wai yau itace da kanta ke rokon wata ‘yar ficikar yarinya ta so mijin ta, Aminunta data gama shan bakar wahala a kansa, ta sadaukar da komi nata dominsa, take son sa tamkar ta fidda zuciyarta, ayya rayuwa! Ta daure ta share wasu azababbun hawaye da suka biyo kumatun ta a guje ta ce, “Intisar, Al’ameen ya gaya mun bazamu taba samun kwanciyar hankali ba in har baki yarda da maganar auren ku ba. Don Allah Intisar ki taimake ni.â€? Aunty ta juya ta fita, bata iya jure ganin wannan abin tausayi. Ita Ihsan din ce ta ke bata tausayi, ta tabbata ba karamin so takewa mijinta ba, abinda tayi mata da yawa baza su iya ba, dazu akan idonta Aminu ya turo kofa ya rufesu har da mukulli amma sai cewa tayi. “Allah dai yasa ya shawo kanta. Don na lura Intissar akwai zucciya.â€? Intisar ta dago don babatun Ihsan ya isheta, fuskar nan jike sharab da hawaye ta dubeta sosai ta ce, “Ina ganin mutuncin ki, don haka don Allah don Annabi Anti Ihsan ba ruwan ki, ki rabu da Al’ameen kawai, shi bai ji tausayi na ba sadda yake kwallo dani har na zamo nakasashshiya? Hajiyarsa bata ji tausayi na ba a sadda Daddy ke kwallo da ni ba a gabanta, da sadda take fyaula mun kebur? Take sa min shocking? Ke har da kan ki kike son in auri mijin ki ashe karya kike ba son shi kike ba. Baki sani ba, ni fa tunda fari ba son mijinki nake ba, kaddarar Allah ta hada mu a kichin kuma kaddarar ta raba, don haka ki tafi don Allah ina bukatar hutu, ina maku addu’a Allah ya baku kwanciyar hankalin ba sai tare da ni ba, ke ni ba wani aure da zan yi, da din ma dana amsa masa rashin galihu ne da rashin abin yi, yanzu kuwa ina da abinyi ina da galihu, ba wanda ya isa yayi kwallo da ni ban yi karar sa an fitar mun hakki na ba, ki je ki lallashi abinki ke daya ko ke ba mace bace baki ishe shi ba?â€? Ta fiddo mata ido cikin barazana kamar gaske, bayan a zahiri ji take kamar ta makureta ta huce. Ihsan tayi murmushi ta mike, a ranta ko cewa take lallai wannan yarinyace, danya (fresh), kalaminta kadai zaka ji ka tabbatar kurucci dangin hauka na dawainiya da ita, har akwai wata ‘ya mace mai cikakken hankali ta kuma san abinda takeyi da zata budi baki tace wai bata son Al’ameen Bello? Ta mike ta na rataya jakarta ta nufi kofa ta ce, “Ki dai kara baiwa zuciyar ki shawara Intisar, Al’ameen mai matukar son ki ne tsakani da Allah. Ba fata nake miki ba, amma ba zaki samu miji da ke son ki tamkar yadda ya ke son ki ba.â€? Intisar ta bita da hararar haushi, kar ta samu din, wannan dan iskan mijin nata? Yau kam kunya da tozarci tagama jin shi a rayuwar ta. Da wane ido zata dubi Faisal? Wane kalami gareta na wanke kanta daga sunan mayaudariya, maciyiya amana, butulu kuma mai manta alkhairi a idon Faisal? Sai ta kara jin tsanar Al’ameen ninkin baninkin na da, dubi yadda yake wa matarshi don wai kurum tana sonshi. Itama idan ya aureta wata rana ya sami wadda ya fiso fiye da ita ba mamaki ya turota lallasar yarinyar da yake son, tab! In ita ce ai za’a yi kata’i. Bata san wannan duk yana cikin wayewar Ihsan da duniya ne ba, ko ba komi zata sayo ma kanta daraja da soyayya a zuciyar mijinta, gaskiyar Hajjo ne Ihsan da Aminu sun fita wayo, ba kuma tsaranta bane a budewar kai da Ilmi. How much do you like this story? 5/11/22, 08:13 - Ummi Tandama😇: ______________________________ *âœðŸ? SIRADIN RAYUWAâœðŸ?* *@Takori* Page7ï¸âƒ£ Su Inteesar bayan sun baro gidan Al’ameen da aka tashi taron har suka zo gida kuka take. Ba kukan komi ba ne face na nadama da tsanar kanta! Amma su ‘yan uwan basu san haka ba, sai tausarta suke da kalami masu dadi. Wai ashe Al’ameen din Hajiya ne take ta wannan hakilon akansa, amma Al’ameen ya yaudareta kuma har abada bazata taba yafe masa ba! In ya ce tayi masa karya itama ai yayi mata karyar. Hajjo da ba’a rabata da abin dariya tace “kai ni Haj. Saratu Al’ameen ya burgeni. Fau, gaskiya jan kumatu yau yaga wuta. Ai ko ni ce Aminu abinda zanyi miki kenan. Ciwon zuciya ya kamani akan ki, in samu kaina da kyar kice bazaki aureni ba kan wani shirmenki da bai shafeni ba.â€? A ranta ta ce, “Allah sarki! Baki san ko wace uwar sa ba, da ba zaki ga laifi na ba! Baki san ya nake da uwar sa ba, da in banda zuciyar muslunci ba zaki ce in gaishe shi ba balle aure.â€? Hajiya Hadiza ta ce, “Ai wannan ma bazata sabu ba, wannan irin butulci dame yayi kama? Anti Saratu ta juyo ta dubesu sannu a hankali kana Intissar din ta dake ta rasgar kuka. Ita kadai tasan kukan me Intisar take, halinda zuciyarta ke ciki da nadamar da ke tattare da ita. Tayi kwafa ta ce, “Tunda dai tace batayi don Allah a bar zancen nan, wai Haj. Hadiza da me Instisar zata ji ne? Sabon sauyin zuciyarta ko maganar Aminu? Ba ciwon zuciya ba in ma ciwon mutuwa ne Aminu yasa Intisar fiye da wannan kuma sun cancanci dubun wannan daga gareta, duk da ba laifinsu bane. Kar ki manta Aminu ne ya makantar da Intisar da hannunsa, da Allah ya tashi saka mata sai ya saka mata ta hanyar daura mai masifar sonta, don haka mu kyale Intisar taji da abinda ya dametaâ€? Har suka kawo gida zancen kenan. Haj. Hadiza ta ce, “Haba Mamar Intisar, maimakon ki lallasheta sai ki dada tunzurata? Ai babu ramuwar gayya tsakanin wa da kaninsa kuma abinda Allah ya kaddara to sai ya faru. Ba Aminu ne ya jawo mata laluran ido ba illah Allah ya kaddara zata gamu da laluran ido ta dalilinsa, kuma Allah ya haramta rumuwar gayya, sannan abinda ya wuce shekara goma sha biyar ba’a tada shi ba sai yanzu don Aminu yana son ta? Kome Babarsa tayi mata ai ba sa’ar ta bace da zata ce zata rama! Da ita mai hankali da halarci ce bazata bude baki a gaban Brigadier tace bazata auri jininsa ba, koda kuwa ace yankar naman jikinta Hajiyar Aminu ke yi a kalla yaci darajar mahaifinsa da ‘yan uwansa dake sonta. Mutamin da ya daukota a daji bai san ko ‘yar waye ba. Ya hada da nashi ya rike bai kyamaceta ba duk da cewa bai sani bama ko shegiya ce, ya sota ya kaunaceta ya kula da dawiniyar rayuwarta shekaru goma sha takwas! Sai don wani dan gajeren sabani ya faru da bai taka kara ya karya ba tace bata son jininsa balle dansa na cikinsa, don ta tabbata shegiyar! Ai idan ni na haifeki, na shayar dake mamana to baki da miji sai Jinin Bello Makarfi sai ko in sune sukace basa so to wannan kuwa. Ni dama ba kowa bace ke ‘yarsu ce, sai yadda suka ga dama da ke. Wata rana irin ta yau bazaki ganmu ba sai ki san inda kuma zaki je tunda in kina da kunya bazaki cigaba da zama a gidan ubansa ba!â€? Anti Saratu ta ce, “A’aaah! Ya isa haka nan, sai ko in ikon haihuwa da shayarwa zaki nuna min Haj. Hadiza, amma in ba hakaba ni Saratu na rantse in har Intisar bata so bazata auri Aminu ba.â€? Inteesar ta kara fashewa da kuka a ranta cewa take “Ni Saratu na shiga uku, tsakanina da Al’ameen Allah Ya isa, yau ina zansa kaina gashi ya janyo su Mama suna fada a kaina?â€? Hidayah da Hunainah kuwa rungume suke da ‘yar uwarsu suna tayata koka abinda take kokamawa, da baza su ce ga hakikaninsa ba, ba suce ko uffan ba don baya daga cikin tarbiyyarsu tsoma baki a maganar manya in har ba an nemi jin ta bakinsu ba, amma kam da sunbi bayan Mamarsu da Antin su Hajjo don a duniya ba su ga wanda ya dace da Yayar su kamar Al’ameen ba. A ranar mutanen Makarfi suka koma, Daddy yayiwa Minister Hassan da Ambasada masauki a gidan saukar bakin gidan shugaban kasa su da matan su. Ba yadda Anti Saratu bata yi da Intisar ta bi Hajiya Hadiza masaukinsu ba amma ta kiya, gani take kamar zasu gudu da ita su rabata da Mamarta, gani take in ta yi hakan ta yiwa Antin butulci, ba don bata son uwarta ba illa a yanzu da komi ya bayyana gareta take tausayin Anti Saratu, wai ashe ba itace mahaifiyarta ba amma tayi mata irin wannan rikon da wata uwar bazata yiwa dan cikinta ba, take jin ciwonta, ciwon da uwa mahaifiya zata jiwa dan ta. Matsayin data riki Anti Saratu na uwa, bai ragu ba ko kadan a zuciyarta sai ma karuwa da yayi, haka matsayin uwarta shima daban. Ba wani sakar mata fuska Haj. Hadiza takeyi can ba shiyasa tafi shakuwa da Hajjo cikin dan lokaci, su dama su Hunainah ba bakinta bane, haka Baban su yadda yake janta a jiki, sai take kwatantashi da Daddy. In ka ganta cikin kannen ta kamar ‘yan uku, sun zamo tamkar wasu tsoka daya kowanne ji yake da dan uwan sa, motsi kadan daya zai yi ta tambayeshi menene? Su su Hajia Hadiza ma sun ce nan da kwanan uku zasu tafi saboda shirye-shiryen tafiyar su Hunainah makaranta. Sun sami (admission) a Jami’ar Al-Azhar dake Cairo ba kuma sun zo ne don su tafi da ita ba, ta ce da Aunty Saratu har abada Intisar tana nan a diyarta wannan shi yasa Anti Saratu kukan dadi. Zarah kuwa ta zamo ‘yar Haj. Hadiza don ko nono Zahra taki amsa koyaushe tana jikin ta tun kwanakin da Antin tayi tana jinyar Intisar bata kula da ita ba Haj. Hadiza ke bata madara suka saba, da hankali ya natsa ne ta bata kememe ta ki amsa, sai ta lafe jikin Haj. Hadiza. Anti ta ce, “Tunda kin yaye kanki ai shikenanâ€? suma su Hunainah na matukar son Zahra da kula da ita, har fada suke akan daukanta da girmansu da komi. A daren ranar Intisar na kwancea falon Anti duk yatsun Al’ameen sun fito rada-rada a farar fuskarta, haushi da takaici duk ba wanda babu a zuciyar nan, ga tunanin Ya Faisal, ta rasa abinda yasa yanzu ko gaisuwa bayaso ta hadasu, hakannan duk inda ya san zasu hadu a gidan to yana kokarin yaga cewa ya kaucewa wannan hanyar, in kuma guri ya kure sun hadun to ba dai ya daga ido ya dubeta ba, ya kuma bi ya daure wannan lallausar fuskar da a kullum ke tarairaya da sata nishadi tamkar bai taba sanin ta ba dadai duniyar. Sa’annan bayan sun shigo su Najib duk sun shigo sun mata sannu da jiki anyi raha da ‘yan dararraku na abinda ya faru tsakaninsu dasu Hidayah amma banda shi. Ta rasa wane irin laifi ne tayi mishi haka da zafi, ta dauka a yanzu ne ya dace dangantakar su ta fi ta da. Ko zata ki kula ‘ya’yan Haj. Nafi don Babarsu, ta kula su darajar kaunar da su ke nuna mata, amma ba don uwarsu ba. Don Ko da suka ji gaskiyar dangantakar su a yanzun sai ma suka kara dagewa wajen jan ta a jiki, basa hada son ta da na kowa cikin kannensu maza, banda Ya FAISAL din ta kadai. Shi a ranar ma ya fara zuwa aikin da ya samu a NNPC na nan Abuja kasancewar shi trained din kasar Ingila don haka bai sha wahalar samun aikin ba. Don haka ne bai zama sam, in ya fita tun safe sai dare. In ranta yayi dubu to a dugunzume yake da damuwa. Hakikah ta damu da Faisal can baya fiye da kowa a duniya. Wannan dadaddar kaunaar mara algus tana nan har inda yau ke motsi, illa sauya matan da yayi farat daya ke damunta. Zarah ta rarrafo ta kama kafafunta tana kallonta, bata kula taba sai Hunainah ce ta miko hannu zata dauketa tana cewa “My sweat Zarah, share wannan kada ta make ki.â€? Dai â€? dai lokacin da Hidayah ta fito daga toilet din dake makale da falon, da alama wanka tayi, kanta cikin “shower-capâ€? tana daure da faffadan towel, fatar nan lub-lub tamkar masu shiga wankan inji ga dogon wuya tubarkallah kamar barewa sak Yayarsu. Ta fannin kirar jiki kam basu da maraba illa fasalin fuska kowa da zubin tashi, haka complexion ya banbanta. Intisar doguwace siririya, fara tas, tamkar kirar larabawan Muritania ko ko mutanen Sirreleon. Shape din fuskarta oval mai kayatattun idanu da wadatar gassun gira, ido da sumar kai. Komi nata tamkar ita ta zaba caras-cas, kuma zam-zam ya dace da ita, tana da labba jazur sirara tamkar yankar reza, wanda in tai murmushi sai ta zama tamkar ‘yar flower (rose) yayinda Hunainah take doguwa kakkaura, kalar coffee, irinsu ne ake kira doguwar mace alkyabbar mata, ga tsayi, ga zati, duk tafi Yayun habewa da cika ido kai sai kace itace Yayar, nan ko girman kasar larabawa ce kawai kunfi shekarun ku buloras, kwata-kwata bana zata cika shekaru goma sha shidda, tana da kyawun da kai tsaye za’a kira manyan kyau, komi a waje, idanduna dara-dara farare kal, in tana kallon ka sai ka dauka hawaye zatai saboda wani sheki da kyalli da kwayar idonta keyi tamkar an diga masu mai me maiko. Sabanin Intisar shiru-shiru mai sanyi, ita Hunainah ‘yar yi ce zakakuwa, da ba’a takalanta ta kyale, duk gemun mutun baya bata tsoro haka duk rawanin sa in ya shiga hancin ta zata fyato shi, ko da suke makaranta itace mai tare masu fada idan Hidayah ta tsokalo, da bakin rashin mutunci wa ‘ya’yan larabawan da duk suka kawo masu wargi. Tafi Hidayah son Intisar kuma jinin su yafi gamuwa ko sanda suke makarantar ma sun fi jituwa, duk da halin su ya babanta. Hidayah dabance a cikinsu, domin dai ita yarinya ce mai jin kanta, ‘yar gayu kuma wayayya mai son hulda da kawaye masu ilmi, don ita takan ce bata a layin kucaki (su Hunainah), ko larabawa da turawan ma da suke tare dasu sai masu aji take kawance, akwai kuma son yawon bude ido garuruwan kawayenta dai-dai ne bata jefa kafarta ba, don haka duk ta fisu budadden ido, idan ta juya harshe zuwa larabci sai ka rantse tsatson King Abdul-Azeez ce, haka in ta murda turanci bazaka ce ba Afro-America bace, haka in ta juya Faransanci, yaren manyan kasashe dai-dai ne bata iya ba. Hidayah Bashir kenan. Tana da matsakaicin tsaho da dogon wuya kuma tafi Hunainah haske, amma bata kai Intisar ba, gatanan dai mai sheki kamar tarwada. Ta zazzarewa kanwar ido “kawota nan, ko in make ki wallahi, ban ce da ke in ta tashi ki gayamin ba, ina jin ki wani ‘your sweat Zarahâ€? banza mummuna, bakauya. Kamin Hunainah ta mayar da martani Najib ya shigo cikin takunshi na kasaita na ‘ya’yan Daddy ya coge jikin kofar shigowa, ya zuba hannuwa cikin aljihun shudin Jeans dake jikinshi yayi dariya a cikin kallon Hidayah ya ce, “Uh, su seniority manyaâ€? ai da ta daga ido taga shine sai ta saki Zarah jikin Hunainar ta falla da gudu dakin Anti. A yadda ta fado mata dakin sai data firgita ta mike a hanzarce sukai cirko-cirko, ta ce, “Ke lafiya, sai kace wadda aka jeho ko sallama kamar wadda ta ga dodo?â€? Ta cira kai ta dubi Anti Saratu ta mayar wani gefen bata san me zata ce mata ba, ta sauke sassanyan numfashi ta ce da ita me? Najib ya ganta cikin kayan wanka bayan dama can ya takura mata da kallo tun a asibiti da shigar mata hanci da kudundune? Ta yi ajiyar zuciya ta ce, “Barshi ma dai kawai Antiâ€? cikin murya mai kwantar da hankali da sassauci Anti ta ce, “Hidayah, wani abin tsoro kika gani?â€? Taceâ€? Lalah, actually nothing. Tambayar ki zanyi ki bani wet-lips.â€? Anti ta saki dariya ta juya mata baya tana cewa. “In kin duba kan mudubin Saratu, babu nau’in kayan kwalliyar da babu. Bayan haka na ganki da ‘kitâ€? mai cikke da kayan kwalliya ‘wet-lipsâ€? kala-kala. Wai meyasa ‘ya’ya na suke firgita ‘yan mata ne? Saratu ta taba sharce dan yatsa da wuka tana firan dankali saboda firgitar ganin Aminu na, to ke, karki zare don Allah.â€? Ta bude baki galala! Tana kallon Antin kamar wawuya, Anti ta fita da gudu-gudunta amma bata motsa daga inda take ba. Hunainah ta shigo tana mata dariyar shegantaka ta ce, “Yaya Najib yace ya soke ‘seniorityâ€? dinki daga yau, in kika sake takuramin zamu taru muyi miki dan banzan dukan da zaki kasa motsi.â€? Ta kyabe baki tana zira doguwar rigarta tana cewa, “In seniority ne yanzu na fara, ki je ki gaya masa.â€? Ba yadda bai yi ba ta fito taki, duk Anti Saratu na jin su, da ya gaji da magiyar har dakin ya bita ya tarkatota falon yana cewa, “Nima balaraben ne da za ai mun gaye ko na miki kama da shasahashun samarin Faransa, wadanda mata ke masu yanga koko donni ba fari bane, da dai ba’a san asalin balbelar bane sai tace daga Makkah ta zo, da wasu idanun ki fiki-fiki kina wani lallankwasa harshe wai ke balarabiya nan ko fillo mai tallen nonon shanono ce.â€? Dukkansu har ita basu san sanda suka tintsire da dariya ba har Intisar da ke ji da abinda ya ishe ta ta murmusa iya fatar baki, da suka dameta sai ta tashi tsam ta bar masu falon, daga baya Anti taji su sun sarke da hira ana ta darawa, tayi murmushi a zuciyarta tayi fatan abinda take zargi yazan tabbatacce. An hadu har Daddy washegarin ranar ana karya kumallo kamar yadda yake a al’adar gidan, amma Najib da Hidayah sai aikawa juna kallo ake ana murmusawa duka Antin na hankalce da su tana dariyarsu, ta tabo Intisar ta nuna mata Najib da Hidayah na magana da ka, kamar kadangaru, da alama Hidayah rokonshi take ya daina kallonta Daddy na kusa da shi, shi kuma ya dage kai tare da dage gira alamar sai me in Daddy na kusa da shi? Haushi ta shake Hidayah, sai kuma ta ga to me yayi mata zafi? In dai ‘ya’yan Hajiya ne gata nan gasu, wadda ba’a Haifa ba ma suna nan suna jiranta, ta harareta ta gyada kai ta cigaba da cin abincinta. Daddy ya aje kofi ckin natsuwa yana walainiya da idanunsa bisa makeken teburin cin abincinshi da Iyalinshi da yake ji incomplete har sai da yayi nasarar gano wanda bayanan, ya ce, gasu, wadda ba’a haifa ba ma suna nan suna jiran ta, ta harareta ta gyada kai ta cigaba da cin abincinta. “Wai ina Faisal ne a gidannan?â€? Nasir ne ya amsa ya ce, “Na ke jin bai fito ba, kwanannan na rasa meke damun Ya Faisal Daddy, duk ya zama wani calm, cool and introvert (Shiru-shiru, sanyi-sanyi kuma mara son magana) ko murna ba yayi da samun aikin sa, har matsayin mataimakin D.G, kasan ba wai don qualification din shi ya kai bane illa kasancewarsa trained din England kuma ya nema a dai lokacin da shugaban NNPC yai retire mataimakin shi ya hau kujerar shi kuma aka bashi (Ass.Director) amma banga alamar yayi farin-ciki ba.â€? Daddy yai dan nazarin maganan Nasir kana ya maida dubanshi ga Intisar data sunkui da kai, ita kadai ta san yadda take ji, ita kadai tasan halin da zuciyar ta ke ciki kan sauyawar rayuwar Faisal. Ai ita zata gayawa kowa Faisal ya canza, mutum mai far’a, raha, da hada-hadar jama’a (cheerful and passionate) shine a yanzu ya maida kansa bare a gidan ba tare da shiga harkar kowa ba. Bata kai karshen tuninta ba ta tsinkayi muryar Daddy can tsakar kanta na cewa “Saratu-karama maza–maza kirawomun Faisal, ki gaya mai na ce kada a kara zama cin abinci a gidannan yana cikin gidan bai zo ba, ba na so!â€? Ta mike tsam tamkar wadda kwai ya fashewa a ciki, tamkar mai tafiya bisan kaya kafafunta na harhardewa don sanin duk jama’ar falon ita suka zubowa na mujiya, haka kawai taji gabanta na faduwa fat-fat tana dosar sassan su bugun kirjinta na kara tsananta tamkar koyaushe wani bakon al’amari zai faru da ita mai dadi ne ko mara dadi? Hakan dai ta daure ta tsaya kofar dakin tai sallama ta yane labulen ta leka kanta kadan, don tunda take bata taba shiga dakin Faisal ba tun bayan tafiyar ta Riyadh, kuma koyaushe ta zo hutu yana makaranta, sadda ta same shi agarin kuma ana cikin tashin hankalin rashin Daddy wama yake ta wani neman dan’uwansa. Da hankali ya natsa kuma ta dauki buhun fushi ta aza masa shida ‘yan uwansa kaf bakikkirin take ganinsu, bata kula su tunda kan su kadai suka sani sai Hajiyarsu, bayan fitowar Daddyn kuma ga abinda ya faru, inda Faisal ya bar kasar, to sai yau, don haka tana ta kissima me zata gani a dakin Faisal? Karar zubar ruwa a toilet ya tabbatar mata Faisal na wanka ne, a hankali ta karasa shigowa da gangar jikin ta har tsakiyar dakin, sai kuma ta juya zata koma har ta kai bakin kofa kawai ta juyo ta karewa dakin kallo tsaf, haka kawai taji tana son yi mai kwa-kwa. Tangamemen hotonta (window-size) tun tana shekaru takwas cikin ‘snowâ€? wato kankarar Switzerland irin wanda ke dakinta na kuruciya, shine abinda zaka fara tozali dashi a gabas maso kudu na dakin. Dakin babu wani shirgi komi tsaf cikin tsari da burgewa, dan matsakaici ne shimfide da marbles sai dan karamin chinese-carpet siriri a gaban gado (medium Italian-bed), da centre table na ‘row-glassâ€? a gefe. Ba kujeru ko daya sai wadda ke jikin tebirin karatu da tulin takardu da jaridu zuwa magazines. Ilahirin dakin gauraye yake da parmanent watau tabbataccen kamshinsa na 5,000 dollar perfume tamkar kwalba guda aka rotse a dakin, nan ko tsabar kama komi nashi ne da turaren yayi, ma’adanar sanya kaya ta jikin bango da labulaye shara-shara farare sol sai sanyin raba ke kwarara harda kankara-kankara, don son sanyi irin na Faisal split biyu ce a dakin ta sama da ta kasa, ba wani kayan kallo sai allon kwamfuta har (Desktop, Mini, da Laptop) dake can wani corridor akan tebur na musamman makale da ‘yar kujerar kushin mai juyawa. Cikin tafiyar nutsuwa ta iso jikin gadon inda ta hangi DIARY din shi da ya aza biro a tsakiya, da alama yanzun yai rubutu, sai ta zauna bisa (centre-table) ta soma bude shafukan cikin zakuwa. Shafin farko wani dan karamin hotonta ne (pass-port size) shima tun tana kankanuwa, aji daya a makarantarsu ta Riyadh. Shafi na biyu maganganun da sukayi ne can baya kan Ronke Adeyemi. A kasan su yayi wasu maganganu da suka gigita ta inda ya rubuta; Ya bar gida domin kar abinda ke ranshi game da ita Saratu ya tonu. Itace hakikanin yarinyar da yake so, yake kauna, take burgeshi yake kuma son ya aura da dukkan ruhi da zuciyarsa amma ba zai taba iya aure ba tana matsayin kanwar shi da suke uba daya? Bayan wannan abubuwan da ya gamu da su ne a Birmingham, nasarorinsa da matsalolin da ya gamu dasu. Mu’amalarshi da wata yarinya Jean, saboda kamanninta da Saratun na sawa ya so ta. Duk ta wuce wannan a gurguje jikin ta ba inda baya rawa zuwa inda ya rubuta matsalar karatunta, inda ya rasa kudin maidata Riyadh! Irin mawuyacin halin da ya shiga har Allah yasa Haj. Ta bashi kudi ya kai mata banki, yadda ya samo visa da su da yadda sukayi da Anti Saratu. Tun daga lokacin ya kudurce wa ran shi neman nashi: (neman na kan sa) don Saratu ta huta, don Saratu tayi karatu mai kyau irin wanda Mamar ta ke so tayi, don Saratu ta samu ingantacciyar rayuwa tamkar tasu, don Saratu ta samu rayuwa mai kyau koda mijin da ta aura baya da shi, shi ya zame masu komi. Ya alkawartama ranshi rashin dogaro da dukiyar Hajiya, dukiyar da Saratu bazata amfana da ita ba, bai ga amfaninta ba. Akwai inda ya rubuta wahalhalun daya sha a Birmingham domin kokari da son fidda son ta. Amma abu kullun sai karuwa. Abinda ya kai shi ga kurba ‘giyaâ€? domin neman ‘reliefâ€?. Tuni hawaye ya wanke mata fuska. Ya cigaba da rubuta yadda giya tayi masa wata illa a huhu, babu wanda ya kula da shi sai Jean. Hakan dai a daddafe yayi-baya-yi-ba ya kammala karatun M. Sc bai ma tsaya yin Ph D din ba. Dawowarsa babu abinda ya fara karo da shi sai maganganun Anti Saratu masu kama da saukar mashi a kahon zuci. Cewa da ta yi, “Insha Allahu duk wani jininsu sai ya ga tozarci a duniya.â€? Tun daga lokacin ya yanke shawarar yayi baya da ita, don ya san Hajiya ta riga ta gama illata mutuncinsu a idanunsu. Idan ya cigaba da nuna mata kauna ba mamaki tsohon gyambon ya bare. Abin mamaki, Yadda yayi nadamar dawowashi Nigeria ranar da Inteesar da Aminu suka fadi suka suma akan idonshi wai a matsayin suna son juna unknowingly ba tare da sani ba, yadda labarin ya gigitashi, tun daga lokacin ya ji ya tsani dan uwansa Al’ameen don yana ganin yaci amanarsa. A ganinsa shine mutum na farko da zai bada shedar so da kaunar da yakewa Intisar tun tana jaririya. Ashe shima kansa Aminun bai san wacece yarinyar ba, bai san Intisar ce diyar Anti Amarya ba! Bai san yarinyar da yafi tsana fiye da kowa ce ba. Sai ya ta’allaka suman Aminu da cewa ‘shockâ€? ne ba ‘soâ€? ne ba, kuma daga ranar bai kara son ta. Da zance ya bayyana cewa Saratu ba kanwarsu bace ya gigice, a lokacin ne kuma ya lura maimakon Aminu yayi dana sani sai ma warkewa da ya soma, wannan ya tabbtar masa da cewa Al’ameen na “love-sickâ€? ne ‘rather than shockâ€? kamar yadda ya tsammana, farin cikin ganin cewa zai mallaki Intissar din sa, daya shekara yana jiyyar soyayyar ta, (kura da shan bugu, gardi da amshe kudi), sai ya gwammace yin nisa da asibitin kada bakin ciki ya kasheshi kwanan shi bai kare ba. Duk da haka ya zauna ‘in hopeâ€? ma’ana cike da burin sauyawar al’amuran, kaman yadda yake tsammanin shi kadai yafi kowa so da sanin ciwon Intisar diyar Anti Amarya. Amma a kwayar idon Al’ameen ya ga so tsantsa, ninkin-ba-ninkin na shi. Ya san Aminu Mai-nasara ne, ba kuma abinda ya taba sawa a rai bai samu ba. Ya san Saratu ta furta kin amincewa da auren Al’ameen ne only in frustration din (cikin bacin ran) kiyayyar mahaifiyarsu a kanta. Amma duba daya yayi mata ya gano babu inda bai amsa son Al’ameen a zuci da gangar jikinta! How much do you like this story? 5/14/22, 09:25 - Ummi Tandama😇: ____________________________ *âœðŸ? SIRADIN RAYUWAâœðŸ?* Book three *@Takori* Page8ï¸âƒ£ A kalaminshi na karshe, wadanda kuma suke kalmomi na karshe a littafin da alama ma yanzun ya rubuta; ‘To in haka ne shi meye ribar sa a rayuwa? Da me ya yi riba da me ya tsira? Bai gani ba! Bai ci riba da son Intisar ba, bai ga amfanin ilmin daya nema don ta huta da shi ba, tunda Al’ameen billonnaire ne, baya bukatar a agaza masa, bai ga ranar da son da ya shekara yi mata yai masa ba. He is but a real loser! To amma tunda don ita ya nema, shi mai mallaka mata duk abinda ya mallaka a duniya ne koda kuwa ta auri Aminu ne ko waninsa, tunda dama tunda fari ya alkawartawa ransa hakan.â€? Ragowar bata iya ta karasa ba, saboda kwakwalwar ba zata iya ganewa ba…â€?.balle ta fassarawa zuciyar ta! Inteesar ta daga ido sama tamkar mai kididdiga adadin juyawar fanka, wasu irin hawaye ne marasa dandano bare launi ke tsere ‘one after the otherâ€? (bi-da-bi) kan kyakkyawar farar fuskar ta. Abubuwa da dama ta tuna a wannan lokacin, wato kuruciyarsu da Faisal can baya. Ashe dama abinda take ji game da shi a lokacin itama ‘sonâ€? ne? Gaba daya jikinta ba inda bai diba ba cikin kaduwa, dimuwa da razana, a take zazzabi mai zafi ya soma kokarin rufeta, saboda karkarwa da ilahirin jikin ta ke yi littafin ya zame ya fadi kan kafarta, dai-dai lokacin da Faisal ya murda kofar bandakin ya fito gabadayan sa. Daure da towel faffada iya kungushi yana ‘combingâ€? sumar kanshi sai ya daskare cikin matsanancin mamaki, suka dubi juna a gaggauce idanunta face-face da hawaye, tayi saurin juya mai baya, kana ta doshi kofa tana cewa. “Dama Daddy ne yace in kirawo ka, kada a kara zama cin abinci kana gida baka zo baâ€? ta sheka da gudu zata bar dakin abin tsautsayi, sai gilashin ya fado ta kuma taka shi da kafarta hannun ya lankwashe amma saboda quality (karkon) gilashin bai fashe ba, kamin ta russuna ya isa gareshi sai suka russuna a tare, hannunshi ya riga isa bisa gilashin don haka natan sai ya sauka akan nashin, shi yai nasarar daukowa, yasa karfi wajen gyara lankwashewar da yayi, a yayin da ta jingina da bango idanunta a runtse, hakannan hawayen basu fasa kwarara ba kamar an sunce fanfo. Ba komi take tunawa ba a lokacin face ranar da ya cire mata gilashi ta baya, lokacin ana shirye-shiryen tafiyarsu Riyadh ita da Khaleel, ta dinga bin inuwarsa a hasale tana “bani gilas dina Ya Faisal, kaga bana soâ€? haka dukan da ya sha da filo da wakokin da ya kanyi mata na “come on beautiful Babe, Maman?â€? Cikin nutsuwa ya maida mata gilashinta, suka sake dubar juna a susuce sai ta kara da gudu. Ya dade anan tsaye yana tunanin me ta gani ya sata kuka? Me ta gani ya gigita ta haka? Bai yi tsammanin zata sake kulawa da al’amarinsa ba a yanzun dai da ta ke cikin son Yayan shi Ameenu? Intisar dakinta ta nufa agigicenta ta maida kofar ta rufe ta murza key. Ta jigina da kofar ta sake runtse idonta da karfi, tamkar mai son farkawa daga mafarki. Abubuwanne ke tariyo mata can baya tamkar a majigi. Ta tabbatar Faisal shine mutumin da ta fara so a rayuwarta kuma mutumin da bazata taba samun mai kaunarta a duniya tamkar shi ba. Tausayinshi, yagama narkar da duk wani tunani da ta mallaka. Ta zargi kanta da cin amana ta kuma kirayi kanta da ‘butuluâ€? dan adam mai manta alkhairi. To amma wani bangare na zuciyarta ya kalubalanci hakan da hujjar cewa, a lokacinta da Faisal tsammani suke su ‘yan uwan junane sabanin haduwarta da Al’ameen. Hakannan Al’ameen shi ya koyar dai ta son shi, shi ya kimsa mata son shi karfi da yaji, bata san so na soyayya ba sai akan shi, don haka bata jin Allah zai kamata da wannan hakkin na Faisal sai dai kaso mafi rinjaye na zuciyarta na karfafata da cewa, yanzu ne ya dace tayi wani abu, yanzu ne ya dace ta sadaukar da kanta da soyayyarta (son da takewa Al’ameen) don nunawa Faisal wannan kaunar da ya wanzar da rayuwarshi nuna mata, tun tana a tsumman goyo. To wai ma ya akai ta so Al’ameen? Bata sani ba, illa may be because he is unikue (watakila don shi din na daban ne). Ta yaya? Ta yaya zata nunawa Faisal din kauna bayan a yanzun ya nuna baya da lokacinta ma? Ta tambayi kanta, lokaci guda ta bawa kanta amsa da cewa ta hanyar auren shi mana Intisar? Amsar tayi mata nauyi a baka da zuci, wai Intisar matar Faisal in banda Allah mai juya al’amura ina wannan abu zai taba zuwa masu a rai? A lokacin ne kuma ta tuna shima fa Faisal dan Hajiya ne! Wannan zuri’ar da tayi alkawarin ba zata sake kulawa ba! Wannan zuri’ar data nuna mata kiyayyar da ba wani mahaluki a doron kasa da ya taba nuna mata! Wannan zuri’ar da idan ta aura, ta sake jefa kanta cikin bala’I da masifa ne watakila ma fiye da na baya. Bayan yanzun da cikakken gatanta, ga Aunty, Daddy, uwa-uba dangi da uwa mahaifiya masu so da kaunarta. Zuri’ar Haj. Nafi? Ta girgiza kai da karfi, ire-iren maganganun Haj. kadai ke dawo mata wasu na bin wasu. “Wai me yasa kike son ‘ya’yana ne, bayan ni na tsaneki? Har kullum mutum kanyi nisa ne da jinin makiyin shi, Saratu banda ke! Don naji ance komi Faisal kike ambato, har kuka kika yi da ya bar kasar, yayi maki kama da ‘ya’yan mutsiyatan kauye ne? So nake bandakin nan ya fiki fari, ya kuma fi Faisal di na kamshiâ€? Faisal ne ya sa miki suna Intisar, kuma da na ne, mallakina ne, don haka daga yau na kwaceâ€?. Ke Jikar Jummai ce, Jummai uwar Saratuâ€?. Daga yau kika sake koda kallar min ‘ya’ya, sai na sa wuka na tsokale wadanna makafin idanun munafurcin, kina jina? Ta tuna amsar da ta baiwa Hajiyar a lokacin. A yau ma sai ta samu kanta da nanata su, sai dai sabanin sunayen da ta kira a wancen lokacin a yau cewa tayi…ba Faisal ba, ba Aminu baâ€? duk wani jininki ma idan na sake daga ido na dubeshi ba da kiyayya ba, ki ce ni shegiya ce na amince! Ta kudurce a ranta daga yau dukkansu ko gaisuwar dayansu bata so. Aure kuma in har sai da ‘ya’yan Haj. Nafi ne, to ita Saratu ta yafe! Ba irin bugun da su Hunainah da Anti ba suyi ba amma Intisar bata bude ba. Wuni tayi cin kuka da nadama mara amfani. Ta rasa meyasa rayuwar ta ke da matsaloli iri-iri tun tana jaririyarta. Dagabaya kuma tayi tunanin akan me zata bari soyayyar ‘ya’yan Hajiya ya wargaza mata rayuwa? Komi fa mutum ke daurama kansa don Allah baya daurawa rai sai abinda zata iya. Ta yankewa kanta ‘solutionâ€? na karshe tayi murmushi ita kadai. Ta san cikin Iyayenta kakaf, babu mai matsa mata akan wannan kudurin nata. Sai ko Mamarsu Hunainah ita ko bata jin ta don ta tabbata Daddynta zai bata goyon baya dari bisa dari. Ba ita ta fito ba sai karfe hudu na yamma, shi din ma azababbiyar yunwa ta fiddota. Su Hunainah na magana da Anti Hajjo a waya ta ce, “Gata nan ma ta fitoâ€? ta mika mata wayan ta ce, ‘Hello Auntyâ€? Hajjo ta ce, “Ba wani Yello Aunty, nikan baki dauke ni Antin ba, da ko menene ke damunki da kin kira ni kin gaya mini, Saratu shin me yayi zafi ne haka? Na ji an ce tun safe kin rufe kanki a daki kina kuka. Na dauka kasancewar mu kusa da ke, da tabbacin da kike da shi na iyayen kwarai ya isa ya sanyaya maki zuciya? Wannan kuntata duk na menene?â€? Tayi shiru, Idanuwan ta sunyi rau-rau kaman ta saki kuka. In da Anti Hajjo ta san yadda take jin zuciyar nan tata, da bata zargeta da kuntatawa kanta ba. Ita ba sauyin Iyaye ya dameta ba, damuwarta daban ne, daga ita sai Ubangijin ta suka santa. Hajjo ta ce, “Koda bakya kaunar mu Saratu, mu ne dai iyayenki, kuma ba’a sake iyaye sai iyayen daki. Wannan rashin sakin jikin da kike damu ban sani ba ko don ki na ganin bamu isa mu zamo iyayen ki ne ba?â€? (Aunty Saratu ce ta koya mata, ba’a jin damuwan ta sai da dabara) Ta sa kuka da karfi tace “Aunty Hajjo me ya kawo wannan maganar? Na rantse da Allah ba haka bane, ni abinda ke damuna daban ne.â€? Hajjo ta ce, “Don kin ce kin fasa auren Al’ameen? Ke, yarinyar ki da ke kar ki bari ciwon hawan jini ya kamaki akan soyayya. Shi Al’ameen din yace dake ya damu? Yana can tare da matarshi Allah kadai yasan farin-cikin da suke ciki sai ke ki bi ki kuntatawa ranki?â€? Ta share hawayen da ke zuba mata da bayan hannu, dai-dai sanda dan halak din ya yiwa falon tsinke, matarsa na biye da shi tamkar ta shige jikinshi don tsatsiba, ya zarce kai tsaye har inda take, ya ja tebur inda take ya daura kafa daya, dayar kuwa na kasa tamkar mai son jin kwakkwafin abinda ke sata kuka a waya. Ihsan ta bisu da kallo kana tabi bayan su Hunainah da sukayi cikin dakin Anti. Intisar ta bude baki domin ta bawa Antinta amsar da tai niyya amma kwarjinin Al’ameen ya katse komi. So ta ke tace har wata tsiyace Al’ameen din da zata kuntatawa kanta akansa? Ita ba shine damuwanta ba. Hajjo ta ji tayi shiru ta cigaba da cewa, “Ni dai shawarata a gareki Intisar, ki fidda damuwar komi a ranki, ki koma makaranta. A shirye muke damu nuna maki kauna ta kowanne fanni. Na san kina son Al’ameen, so bana wasa ba. Tunda har kika kusa salwantar da rayuwar ki akan tunanin bazaku iya auren juna ba. Amma abinda na ke so ki gane shine, ki yi tunani, ke yarinya ce karama har yanzu cikin shekarun (teenage), wannan gigin son duk na dan lokaci ne, da anyi auren an haihu shikenan ya zama tarihi sai zaman hakuri da juna. Abinda nake so da ke shine ki tsaya ki gina rayuwarki a bisa tubala na kwarai, in ba hakaba ba mamaki bada jimawa ba soyayya ta ruguzata. Al’ameen ya fiki wayo, daga shi har matarshi ba tsaranki bane a budewar kai da ilmi. Don haka ki tsaya ki nemawa kanki madogara mai kyau tukunna, wanda shine wannan ilimin mai matukar wuya. Idan kika sameshi samun Aminu ba zai maki wuya ba haka in kika barshi ke da banza a cikin su daya kuke, don sai kin raina kan ki a cikinsu. Ni in son raina ne ma Allah bana son ki auri mai mata irin Ihsan, ki dubi yadda take hauka akan mijinta fa, ke ‘yar nan, mind yourself (ki shiga taitayinki)â€?. Ahaf! Ai kamar Antin ta shiga ranta taga abinda take shiri komawa makaranta, tayi murmushi tare da saurin rufe ido, maganganun Antin take aunawa abisa sikeli daya bayan daya, wanda dama duk tayi tunaninsu, babu wanda bata ga gaskiya a ciki ba, ta ce a raunane. “Na gode Aunty.â€? Ta rufe wayar, sai yanzu ya fuskanci da wa take magana, bata ko dubeshi ba ta murda kofar da zata hadaka da dakin ta daga falon Anti, yayi hamzarin murda keys ya zare ya tura aljihun bayan wandon ‘basachiâ€? dake jikinsa ya ce. “Me Anti Hajjo ke gaya maki a waya, kike godewa kina kuma kara yi mun asaran hawayen da nake ganin daraja da kimar su fiye da na kowa?â€? Wasu ubansu harara da ta watso mai ya bashi mamaki don bai taba ganin tayi ba, ga idanun sunyi jawur sai ta kara kyau a idon shi, ko da yake so ne hana ganin aibi, ya ce, “Inteesarâ€? da muryar nan da ke karya lagonta, ta kassara kuzarin ta, amma a yau ko gezau, har yanzu hararar shi ta ke ba kakkautawa. Ya soma taki har inda take tsaye tamkar sassakakken gunki, ta soma ja da baya kamar wadda taga abin tsoro da kyama, ta san ba karamin aikin shi ba ne ya kamata da kokawa kawai don ya sata yin magana, cikin tsiwa da yatsina ta bude dan bakinta tana mai nunashi da dan manuninta ta ce, “Wallahi Al’ameen ka sake ka tabani yau zan fasa ma kaine, in bar inyamurar matarka da jiyyar da baka taba yi ba.â€? Bai fasa dosarta ba ya ce, “Jinya kuma wacce ce ba’ayi ba? Sai dai kar a kuma, idan jinya ta ciwon son halimah ce, to ayi ta yi kar a tashi. Kar ki kara kira mun mata inyamura, yadda kike musulma diyar musulmi, haka itama take.â€? dai-dai lokacin da ta dangana da bangon karshe na falon, shi kuma bai fasa bin ta ba, ta ce, “Wallahi zan kirawo Anti, tayi ma kashedin shiga harkana, ka nemo Halimar ka can amma ni Intisar ce, ka manta ka taba sanina a rayuwarka, ina gaya maka, ina kara gaya makaâ€? ya toshe mata baki. Ya ja hannunta na dama da karfi har bisa seater dake tsakiyar falon, ta karfin tsiya ya zaunarta ya ce, “Ke in ma Daddy zaki kirawo babu laifi. Amma sai na gama maganar da zan yi. Kin san me ya kawo ni? Zuwa nayi in gaya maki ranar da duk wannan maganannen bakin ya kara kuskuren cewa bazai aureni ba don uwata, wallahi sai na kakkarya ki.â€? Cikin tsiwar da bai san ta iya ba ta ce, ‘Ka karya ni? To ka ji ka sani ko da can da ka makantani, don ban da wayo ne, amma yanzu wallahi sai dai ayi ‘yar bibbiyuâ€? saura kadan da dariya ta kwace masa, to amma shi kansa yasan bai kyauta ba, jiya ya mareta yau ya gaya mata kakkausar magana, shi da ke neman wanke dattin da Hajiya ta yayyaba masu daga idanunta. Ya dire gwiwoyinsa bisa carpet abinda bai taba yiwa wata ‘ya mace a rayuwarsa ba, a yayinda ita kuma take zaune cikin kujera ta cika fam, kiris take jira ta fashe. Ya langabe kai gefe guda gwanin ban tausayi, yayi kamar ya share mata hawayen da suka soma surtu, sai kuma yafasa. Ya ce, “Inteesarr!â€? Yadda ya kira sunan cikin murya mai karkarwa da kauri (husky) kadai ya birkita Saratun, bata jin ko dan yatsanta zata iya motsawa. Ya ce, “I ‘am sorry, terribly sorry! Wallahi ni, wasa nake maki, in karya ki in ce na karya wa kenan? Jiya kuma zuciya ce ta debe ni, kin san bata da kashi, abinda kika fadi cikin mutane ya bata mun kwarai. Ni kaina ban san ya akai ba, Pls, 4 give me…â€? Ya karasa a raunane, kana ya matso ‘yar kwallah, ya maida ta bisa kujerar ya ce, “Wallahi Intisar nasan Hajiya ta bata miki, to amma ni meye laifina? Ni ban ji tsoron abinda hakan zai janyo man ba daga gareta na furta ina sonki? Sannan kuma bakya tausaya mun halinda zan shiga in na rasa ki kwata-kwata, ki tuna baya?â€? Ta sadda kai kawai, bata son jin wannan abun da take ji game da Aminu, bata son wadannan ‘feelingsâ€? din da take ji game da shi masu tada tsigogin jikinta a duk lokacin da suke tare, to amma Al’ameen din kamar wani mayen karfe ne, wuyarta yayi mata magana da wannan muryan nashi mai jan mutum uwa lantarki duk wani ‘weaknessâ€? din ta ya gama samunshi. Ta tabbata nisa da shi shine abu mafi a’ala a gareta in har tana son cimma kudurirrikanta akan Haj. Nafi, wadanda daga ita sai zuciyarta sai mahaliccinta suka san na mene, amma ba don bata son shi ba. Karya ne ko fatar bakinta ta fada, to bacin rai ne. Shi kadai take so har cikin tsokar zuciyarta, har gangar jiki zuwa kwakwalwarta babu inda baya girgiza da kaunar Al’ameen da sha’awar komi nashi, ita kadai ta san me take ji da yakin da take yi da zuciyarvta a duk lokacin da yai kuskuren kai hannunshi gareta koda yatsar hannunta ne kuwa amma ta rantse, ta kuma ta rantse ko son sa zai kasheta, ko duk duniya zata taru a kanta, bazata aure shi ba! A ganinta ta hakanne kadai zata rama abinda sukai mata shi da mahaifiyarsa wanda har abada bazata manta ba, ba zata yafe mata ba kuma ba zata daina tunawa ba. Bata san wannan hukuncin da ta yanke yai tsauri ba, domin son da Al’ameen ke mata Allah kadai ya san iyakarsa; ba na wasa bane, ya wuce ayi ramuwar gayya akansa yayi masa tsauri bazai iya dauka ba. Da kyar in bata yi kuskure ba, da kyar in hukuncinta ba zai zamo nadama mara amfani a gareta ba. Ya cira hannunta ya aza bisa kirjinshi, tana iya jin nannauyan bugun da zuciyarsa ke yi akai-akai, jikinta ya soma sanyi, ya ce, “Ki ji Intisar, kiji irin bugun da zuciyar nan ke yi a domin ki, saboda ke ne take ciwon da har abada bazata daina ba, ba kya tausayi na Intisar ba kya sona yanzun? Allah na rantse, in muka cigaba da tafiya a haka wata ranaâ€?. Wata rana bugawa zatayi gabadaya ta fashe kowa ya huta, ki taimake ni ki agaje ni, ki daina la’akari da laifin da ba nawa ba kina hukunta ni dashi don Allah?â€? Ita dai ta zamo ‘paleâ€? ko motsi ta kasa balle tayi kokarin yin wani abu, ta rasa abinda ke mata dadi shi kuma bakinshi bai yi shiru ba da gaya mata irin halin da zai shiga in ya rasata. Har ya kai ga kwantar da kansa bisa kafadunta. Cikin wannan halin Faisal ya turo kofar falon ya shigo, fes idon shi a kan su, ya juya da sauri yana cewa, “Excuse me plz. Ya Aminu ban sani ba!â€?. Ta mike a gigice ta banka dakin Anti, ta kifa kai bisa gado ta soma rera kuka sabo fil. Ina rowan mai neman kuka an jefeshi da dunkulen kashi. Gabadaya suka zubo mata ido Anti da Ihsan suka yo kanta Anti ta ce, “To kin gani Ihsan mijinki kullum sai yasa min ‘ya kuka, don haka ki je ki ja kayan ki ku tafi.â€? Ta sake kuluwa ta shaka ance Al’amin mijin Ihsan, ta sake tsugewa da kuka. Ihsan ta matsa jikin gadon ta dago kanta ta aza bisa cinyarta tana murmushi tace “Haba little sister na, kin hana mun miji sakat ko tausayinshi ba kya ji, jiya saura kadan ya sakeni, don Allah kiyi hakuri ki bamu hadin kai ko na samu kan Al’ameen nima…â€? Ta soma fidda kwalla itama, wani tukuki na cinta a rai, wai yau itace da kanta ke rokon wata ‘yar ficikar yarinya ta so mijin ta, Aminunta data gama shan bakar wahala a kansa, ta sadaukar da komi nata dominsa, take son sa tamkar ta fidda zuciyarta, ayya rayuwa! Ta daure ta share wasu azababbun hawaye da suka biyo kumatun ta a guje ta ce, “Intisar, Al’ameen ya gaya mun bazamu taba samun kwanciyar hankali ba in har baki yarda da maganar auren ku ba. Don Allah Intisar ki taimake ni.â€? Aunty ta juya ta fita, bata iya jure ganin wannan abin tausayi. Ita Ihsan din ce ta ke bata tausayi, ta tabbata ba karamin so takewa mijinta ba, abinda tayi mata da yawa baza su iya ba, dazu akan idonta Aminu ya turo kofa ya rufesu har da mukulli amma sai cewa tayi. “Allah dai yasa ya shawo kanta. Don na lura Intissar akwai zucciya.â€? Intisar ta dago don babatun Ihsan ya isheta, fuskar nan jike sharab da hawaye ta dubeta sosai ta ce, “Ina ganin mutuncin ki, don haka don Allah don Annabi Anti Ihsan ba ruwan ki, ki rabu da Al’ameen kawai, shi bai ji tausayi na ba sadda yake kwallo dani har na zamo nakasashshiya? Hajiyarsa bata ji tausayi na ba a sadda Daddy ke kwallo da ni ba a gabanta, da sadda take fyaula mun kebur? Take sa min shocking? Ke har da kan ki kike son in auri mijin ki ashe karya kike ba son shi kike ba. Baki sani ba, ni fa tunda fari ba son mijinki nake ba, kaddarar Allah ta hada mu a kichin kuma kaddarar ta raba, don haka ki tafi don Allah ina bukatar hutu, ina maku addu’a Allah ya baku kwanciyar hankalin ba sai tare da ni ba, ke ni ba wani aure da zan yi, da din ma dana amsa masa rashin galihu ne da rashin abin yi, yanzu kuwa ina da abinyi ina da galihu, ba wanda ya isa yayi kwallo da ni ban yi karar sa an fitar mun hakki na ba, ki je ki lallashi abinki ke daya ko ke ba mace bace baki ishe shi ba?â€? Ta fiddo mata ido cikin barazana kamar gaske, bayan a zahiri ji take kamar ta makureta ta huce. Ihsan tayi murmushi ta mike, a ranta ko cewa take lallai wannan yarinyace, danya (fresh), kalaminta kadai zaka ji ka tabbatar kurucci dangin hauka na dawainiya da ita, har akwai wata ‘ya mace mai cikakken hankali ta kuma san abinda takeyi da zata budi baki tace wai bata son Al’ameen Bello? Ta mike ta na rataya jakarta ta nufi kofa ta ce, “Ki dai kara baiwa zuciyar ki shawara Intisar, Al’ameen mai matukar son ki ne tsakani da Allah. Ba fata nake miki ba, amma ba zaki samu miji da ke son ki tamkar yadda ya ke son ki ba.â€? Intisar ta bita da hararar haushi, kar ta samu din, wannan dan iskan mijin nata? Yau kam kunya da tozarci tagama jin shi a rayuwar ta. Da wane ido zata dubi Faisal? Wane kalami gareta na wanke kanta daga sunan mayaudariya, maciyiya amana, butulu kuma mai manta alkhairi a idon Faisal? Sai ta kara jin tsanar Al’ameen ninkin baninkin na da, dubi yadda yake wa matarshi don wai kurum tana sonshi. Itama idan ya aureta wata rana ya sami wadda ya fiso fiye da ita ba mamaki ya turota lallasar yarinyar da yake son, tab! In ita ce ai za’a yi kata’i. Bata san wannan duk yana cikin wayewar Ihsan da duniya ne ba, ko ba komi zata sayo ma kanta daraja da soyayya a zuciyar mijinta, gaskiyar Hajjo ne Ihsan da Aminu sun fita wayo, ba kuma tsaranta bane a budewar kai da Ilmi. How much do you like this story? 5/14/22, 09:25 - Ummi Tandama😇: _____________________________ *âœðŸ? SIRADIN RAYUWAâœðŸ?* Book three *@Takori* Page9ï¸âƒ£ A lokacin ne hankalin ta ya kai ga Hidayah da Hunainah wadanda ke hada komatsansu cikin ‘trolliesâ€? din su basa ko dubarta. Hankalinta ya tashi, ta ji babu dadi ta ce, “Ku kuma ina za ku?â€? In jakunkunan su sun amsa, to suma sun tsinka mata. Ta ja jiki ta sakko daga gadon fuskarta jike da hawaye taje ga Hidayah da Hunainah, ta kama kowacce da hannu daya ta rungume a jikinta ta cigaba da kuka mai tsuma rai su kansu basu san sanda hawaye ya cika idon su ba. Tace cikin kuka “Don Allah ‘yan kanne na ba sai jibi zaku tafi ba?â€? Hidayah ta tureta tana share hawayen ta da bayan hannu. “Ai zaman mu baya da amfani, tunda ke ba kya jin shawarar kowa kuma ba’ajin damuwarki. Yaya zaki sa Ya Aminu kuka akan idon matar sa? Mu bazamu iya jurar ganin wannan wulakancin ba, so hauka ne? Kuma idan yanzu ba kya sonsa ba zaki aure shi ba ai ba haka ake abun da wulakanci ba.â€? Ta ce, “Hidayah, Kome zan gaya miki a yanzu bazaki gane baâ€?. Baki san Babar Al’ameen ba neâ€?.â€? Ta katseta, “Ba bu abinda na tambayeki, ban kuma ce ki gaya mun ba, ban santa ba ba kuma na so in santa, to amma ta yaya zaki hukunta shi da laifin uwar sa wanda ba nashi ba ai har ga Allah kin dau hakkin shi…â€? Ta ce, “Hidayah, ba wannan ne kadai baâ€?.â€? sai kuma ta kara sa kuka, to tace mata me? Bata da abinda zata ce da ita ta fahimta game da Faisal Bello Makarfi, daga Anti sai Daddy ne zasu fahimce ta akan hukuncinta amma su Hidayah baki ne basu san komi ba. Dai-dai lokacin da Anti ta shigo tana rike da Zarah, tun kan ta zauna Zarah ke mikawa mutuniyar ta Hunainah hannu tana zillo daga jikin Antin, ta amsheta yayinda Antin ta samu gefen gado ta zauna ta dibesu dukkansu tace “duk mi ya janyo wannan?â€? Hunainah ta ce, “Tafiya zamu yi Antiâ€? ta ce, “Ina?â€? Su duka suka hada baki suka ce “Can inda aka sauki su Maman mu.â€? Ta ce, “Akan me?â€? Duk suka yi shiru ta ce, “Nasan sai jibi zaku tafi Korea, mun yi da Hajiya sai zasu tafi zasu biyo ku tafi, to a kan me yanzu zaku ce zaku tafi, ku bar ‘yar uwarku cikin irin wannan halin da ta jefa kanta don bana ce wani ya jefa ta ba.â€? Hunainah ta ce, “To Aunty yaya zamuji dadin zama alhalin tana kuntatawa kanta? A ce mutum bashi da aiki sai kuka kamar wanda ya rasa iyaye da dangi, mu bamu da amfani a gareta kenan. Muna iya kokarin mu don kawo ma Saratu canjin rayuwa amma bata gani. Damuwar ta bamu isa mu ji ba, bamu san hakikanin kuma me ke damun ta ba. Ni ban ga meye abin bakin ciki duk a cikin maganar nan ba, tace ta fasa auren Yaya Al’ameen waye yace dole ta aure shi? Sai kuma tasa mutane gaba tayi ta kuka in ta canja shawarane ba sai taje ta sameshi ta bashi hakuri ba?â€? Ta share hawayenta da yatsunta biyu ta ja ‘tissueâ€? ta fyace hanci ba tare da ta lura da hararar da Intisar din ta wurgo mata ba, dai-dai lokacin da Najib ya yi sallama ya shigo. Da ganin yanayin da suke ciki duk ya bi ya rikice, ya zube a gabanta bai ma kula da Anti dake zaune ba ya ce, “Hidayah, tafiya, why?â€? Sai ta sake barkewa da kuka. Ya fiddo ‘handkerchiefâ€? a aljihun don share mata hawayen da ke zuba ya na tambayar su me ya faru? Aunty ta ce, “Najib ya zan yi in san damuwan Saratu ne don Allah?â€? Ya kai dubanshi ga Intisar, cikin kwanaki kalilan rak wai har tafi can baya sanda take cin bakar wuya lalacewa, yayi murmushi ya ce, “Aunty, wait a minuteâ€? (jira ni minti daya).â€? Ya juya ya fita da sassarfarshi, ya fi rabin awa kamin ya dawo Faisal na biye da shi. Idanun shi jazur da gani shi din ma yana cikin tsananin tashin hankali kwatankwacin koma fiye da na Intisar din, don dai shi namiji ne, sannan akwai juriya. Kallon kyama kawai yake bin kowa da shi da tsanar duk wani al’amari dake cikin duniyar. Najib ya ce, “Zaunaâ€? ya ce, “Bana bukata.â€? Ya tsaya kikam a bakin kofa ya harde hannuwanshi bisa kirji, idanunshi akan Inteesar tamkar mijin da ya kama matarshi da kwarto. Najib ya zauna jikin Hidayarshi, cikin kwanciyar hankali ya dibi Anti cikin basira ya ce, “Dibe su Anti.â€? A mamakance Anti ta dubi Faisal, kana ta maida dubanta ga Intisar ya ce, “Anti me kika fuskanta?â€? Ta ce, “Dukkanin su, suna cikin yanayi daya.â€? Ya kuma cewa, “Anti ba ki tuno can baya?â€? Cikin rashin fahimta ta ce, “Ban gane baâ€?. Ya bugi Jakar Hidayah da kafarsa ya ce, “To cut the long story short! Na fahimci daga Faisal har Intisar suna son junansu ne tunda dadewa, duk wani da ya san kuruciyarsu zai gane hakan sai dai in baya da lura. Na dade da sanin Intisar kishin Faisal take har zazzabi sai da nayi na kwana bakwai don mamaki. Intisar na cikin damuwar yaya zata bar Faisal akan Al’ameen? Ko da taso Al’ameen ta so shi ne a rashin Faisal, ta so shi ne domin ya mallaki wasu ‘qualitiesâ€? da ‘appearancesâ€? na Faisal kaman murya, taku, da sauran su, yayin da Faisal ke jin haushin jinkirin shi na kin fara furtawa cewa…â€? A fusace Faisal ya katse shi, “Dakata don Allah Malam abin naka ya koma sharri, for God’s sake, yaushe na taba ce ma ina son Intessar, irin son da kake nufi? Yaushe ka zama predictor? Zuciyar wa ka shi ga a tsakanin mu har ka gano hakan?â€? Najib ya dubeshi a lalace ya ce, “To canzawa juna da kuka yi na mene ne?â€? Kamin ya rufe bakinsa kawai sai suka ji Faisal ya ce, “Hidayah zaki iya aurena?â€? Hidayah ta dago a razane, ta girgiza kai da karfi tace “A’ah, wallahi ba ruwana, ni ina da wanda nake so kada a kara sani a ciki.â€? Yadda ta fada da sauri da gigita saida ta ba Najib matsiyaciyar dariya, ya kuma ji nadamar abinda ya jangwalo ga abin na shirin juyewa kansa, shi ko Faisal wani dogon tsaki tsuuuâ€? yaja ya juya ya fita har yana tuntube da dokin kofa. Hunainah ta sunkuyar da kai cikin alhinin wannan cukurkudadden al’amari. Anti ta dubi Najib ta mike tsaye ta ce, “Ni dai ina ganin Saratu ki sassautama ranki hakannan, Allah ya zaba abinda yafi alheri gaba daya.â€? In banda Najib ba wanda ya ce, “Amin.â€? Ta fita ta ja masu kofa yayin da Najib ya cigaba dayi mata nasiha mai sanyaya rai. Ya ce, “In da nine ke, Saratu ba kuma wani abu da zai sake sa ni bakin-ciki. Kamar yau ne nake gaya maki cikin wasikata sanda akai mana katanga dake cewa; ni na tabbata wani babban al’amari ne zai faru dake anan gaba, kuma hakika ke din wata ce a cikinmu. Ga shi a yau kin zamo mabudi kuma sityari mai juya zuciyoyin ‘ya’yan Hajiya, sai inda ki ka garasu. Duba ki ga nima shakikiyarki bata barni ba. Kun zamo mana barin jiki, bango abin jinginar mu mu ji sanyi sai yadda kuka yi da mu. Don a yau Hidayah tace bata so na, ina jin haukacewa zanyi. To haka daga Ya Aminu har Ya Faisal na tabbata babu mai tsira daga takobin kaunarki, duk da nasan Al’ameen bai san Faisal na sonki ba da duk matsalar ta warware. Duka wannan matter bai yi kamari yadda kika daukeshi ba, don Allah, ki maida walwalarki ki, ki bude sabon shafin rayuwar farin-ciki da ‘yanci tamkar kowa, ina kara gaya miki ba fa mai yi miki dole kan abinda ba kya so.â€? Tasa gefen dankwalinta ta share idon ta tas, eh, gaskiya Najib ya fada, yanzune ya dace ta budewa kanta sabuwar rayuwa mai ‘yanci, tamkar sauran ‘ya’yan gata, ciki kuwa har da neman ‘yancin kanta na rama abinda uwar su ta shekara yi mata! Wasa farin girki! Tun kowa na tsammanin Intisar wasa take maganar rashin amincewar ta kan aurenta da Al’ameen har suka tabbatar da gaske take. Duk wasu hanyoyin sadarwa tsakanin su ta toshe su, bata daukar wayar shi hakannan in zai wuni cikin gidan bazata bari ya ganta ba, ko dai ta kulle kanta a (toilet) ko ta shige cikin (store) har ya gaji ya tafi haka Anti tace ba ruwan ta, ta tsame hannun ta a al’amarin duk abinda Intisar din ta zabawa rayuwar ta tayi dai-dai. Al’ameen duk ya sukurkuce ya rasa inda zai tsoma ransa, bashi gaban Daddy bashi gaban Anti, wurin Hajiya Hadiza kadai yake samun sanyi to ita din ma mijin ta daga baya ya gargadeta ta fita harkar su, tunda tare ta gan su, bata da wata (power) in dai akan Intisar ne. Su Hidayah kam bakin-cikin da suke ji kan Yayar su da hukuncin ta har kuka suke tausayin Al’amen kadai ya ishe su, duk ya rame ga wata kasimba ta babu gaira babu dalili ta cika kyakkyawar fuskar sa, duk son gayu da kwalisa irin na Al’ameen Bello, a yanzu babu ya kau. Babu komi gaban sa kamar Intisar din da ke neman kufce masa karfi da yaji yana ji yana gani. Babban abinda yafi damun sa shine wani kululu ko katutu dake tokare shi a kahon zucci, in ya tuna wai yau Halimar sa ce ke gudun sa sabida Hajiyar sa? Yayi dakacen kasancewar sa Al’ameen dan Hajiya Nafi, ba tun yau ba, a yau ma yana karawa. Ya kuma tabbata wannan tabon data yaba masu har abada bazai gogu a zuciyar yarinyar ba. Yayi ban hakurin, yayi ban bakin yayi lallashin duk a banza. Yo ina ya ganta ma? Ta haramta masa ganin kyakkyawar fuskarta da ke sa shi nutsuwa balle dan murmushin ta dake gigita shi, duk sun zama tarihi, na wani zamani can daya shude, zamanin da yake ganin ba zamanin da ya samu gata a cikin sa kamar sa, wato zamanin rayuwar ta a Kitchin. Ya kan zauna yayi tunani, iya kokarin sa ya rasa mafita cikin al’aamarin sa, karewa ma, bai san me take nufi da shi ba; tana son sa ko ta daina son sa? Kai bashi kadai ba babu wanda ya san nufin da ke kunshe cikin zuciyarta a gidan. Cikin wannan halin Faisal ya samu Daddy ya gaya masa ‘transferâ€? da ya dade yana nema zuwa NNPC na Lagos ya fito. Daddy ya nemi dalilin ‘transferâ€? din yace hakanan yake son yanayin garin Legas, ya kuma dade da burin aiki a nan to sai ga yadda al’amarin ya kasance, wato samun aikin da yayi da wurwuri anan Abj. Daddy yace ya je Allah ya sanya albarka amma yayi kokarin zuwa ya ga lafiyar gida duk karshen sati ko bayan sati bibbiyu. Ba kuma tare da ya kara bi ta kan kowa ba ya yai tafiyar sa, inda ya rungumi aikin sa cike da karfin zuciya. Yau kam Al’ameen ya kudurce bai barin gidan sai yaga Intisar ko da hakan na nufin ya kwana a gidan ne. Yana ta zarya falon Anti zuwa sassan Daddy har dare bata ba alamarta. Shi kam duk ya fi daura laifin komi akan Anti don a tsammanin sa da sanin Antin Intisar ke yi masa duk abinda ta ke yi. Bai sani ba, Antin ta fishi takaicin abinda Intisar ta yanke a kansa, don dai bata son matsanta mata ne. Ta tabbata ita yarinya ce, amma mai sahihin tunani da hangen nesa, tabbas tana da kwakkwarar hujjar ta ta yin hakan. Ita kadai tasan azabar da ta kwankwada a hannun Hajiya, sai dai tana matukar tausayin Al’ameen har hawaye take masa kamar su Hidayah amma a bayan idon sa. Karfe daya da rabi na sulusin dare ta fito daga maboyar ta, wato cikin store, ta san dai duk nacin sa zuwa yanzun ya hakura ya tafi amma me? Ta zauna gefen gadon ta kenan ya murdo kofar ya shigo. Ba karamar razana ta yi ba amma sai ta cije, ta yi kamar bata gan shi ba. Ta cigaba da kokarin gyara wajen da zata kwanta. Hakikah zuciyar ta ta girgiza da ganin muguwar ramar da yayi fiye da sanda ya kwanta ciwo, ga sumar da ta cika kyakkyawar fuskar sa kamar ba Al’ameen din da ta sani ba, mai tsananin kwarjini, gayu da kwalisa, ilhama da cikar zati. Fuskar shi ba annuri sam kamar yadda zuciyar sa ke wani irin zazzafan bugu da sauri da sauri. Ya dubeta da lumsassasun idanun sa cikin fidda rai da al’amarinta, ya karisa har gaban mudubin ta ya ja (stool) ya zauna yana fuskantar ta, cikin raunanniyar muryar da bata taba ji daga gare shi ba yace “Inteesar!â€? Ta dago ta dube shi, amma ta kasa magana, sabida zuciyarta dake neman bayar da ita. Ji ta ke kamar ta ruga ta rungume shi tayi kukanta mai isar ta, ta gaya mishi tayi kewarsa ita ma fiye da yadda harshe zai iya furtawa, fiye da yadda kwakwalwa zata iya fassarawa kuma fiye da yadda tunani zai iya kintatawa. Ta ji ta a marainiya, duk kuwa da tarin iyayen da suka zagayeta a yanzun. Ta fi jin ta a mai cikakken gata, a sanda suke tare a (kitchen) fiye da yanzun da take da Daddy da mamar ta. Ta azabtu da rashin ganinsa fiye da yadda shi yake tunani. Ya dubeta ya gani, ta fi shi ramewa da lalacewa, ta fi shi ciwon zuciya illa ita mai iya ‘controllingâ€? zuciyanta ne ba kamar shi da zuciya ke juyawa ba. Ta fishi jin ciwon abinda take masa da hukuncin da ta yanke masu, kuma ta fishi azabtuwa daga hukuncin. Ta fi shi tunanin yaya rayuwarta zata karasa batare da shi ba? Ya fiye mata duk wannan gayyar dangin da suka zagayeta! To amma wannan alkawari ne, alkawari ne tsakanin ta da zuciyar ta da Ubangijin da ya halicceta ta yaya bazai gane ba ya taimaka mata wajen cikar alkawarinta da burin da ta dade tana ciwa zuciyartaâ€?. Sheshekar kukan Al’ameen ya katseta da digar zafafan hawayenshi bisa tafin kafarta, dubawar nan da zatayi sai taga Al’ameen ne durkushe a gabanta, yama rasa kalmar da zai yi amfani da ita wajen rarrashinta da nuna mata muhimmancinta a gareshi. Me zai gaya mata ta yarda bazai iya jinyar zuciyar nan baâ€? me zai gaya mata ta san ya manta komi, ya manta kowa, ya manta ko shi wanene saboda rashin soyayyar ta? To itama kukan take mai tsima zuciya an rasa wanda zai rarrashi wani a tsakanin su. Ta ga dai inta biye masa zasu kwana ne a hakan, wanda ita bata fatan hakan. Ita kadai ta san yakin da take yi da zuciyarta a duk sanda take tare da Al’ameen, balle a irin wannan halin da zuciyoyinsu ke gab da narkewa saboda azababben son da fada ma bata baki ne. Ta sauka daga gadon itama tayi tsugunne bisa carpet a gabansa tamkar yadda yayi, don tana ganin it’s a disgrace agareshi ya durkusa mata, cikin muryar kuka da nadama tace “Ni, niâ€? dama cewa nayi sai in har Hajiya ta rokeni gafarar abinda tayi mun, ta kuma furta amincewa da ni a matsayin matar ka, sannan ne zan yarda.â€? Ya dago a hankali ya dubeta, yayi tsai da ransa yana nazarin zancenta. Tamkar kuma wanda aka yiwa allurar kuzari kuma sai ya mike tsaye, ya zauna a gefenta yace “Har ga Allah Saratu wanan shine uzrin ki?â€? Ta gyada kai tana hadiyar zuciya. Yayi murmushi, ya ce, “Intisar, idan na kawo Hajiya na gaban ki da Daddy da Aunty, ta nemi gafararki, ta kuma ce ta amince muyi aure, shikenan?â€? Ta kara gyada kai da sauri. Ya sake yin murmushi ya mike, jikinsa ba inda baya rawa ya ce, “Keep your promise.â€? Ya soma ja da baya-da-baya har ya tadda kofar fita idon shi na kanta, yana mata murmushin da har abada ba zai gushe daga zuciyarta ba, cikin karfin hali itama ta mayar masa, sai kuma duk suka kyalkyale da dariya ga hawaye sosai a fuskar kowannen su. Ya daga hannunshi ya sumbata kana ya huro mata iskar. Da haka ya bar dakin gudu-gudu sauri-sauri, zuwa inda ya adana motarsa. Akan idon Daddy dake kallonshi ta taga ya ja motar ya bar gidan. Daddy da Aunty Saratu suka yi ajiyar zuciya a tare. Duk kawaici irin nasa a yau ya yanke shawarar dosar Intisar a washegari don jin inda ta sa gaba, abin ya isa. Washegari ta je gaida Daddyn da safe kamar yadda ta saba a ‘mainâ€? falonshi, yana rigingine cikin kujera da ‘yar karamar rediyon shi inda yake sauraren ‘Voice of Americaâ€? shigowar ta yasa ya kashe rediyon kwata-kwata ya bata hankalinshi yana murmushi tun kamin ta zauna ya ce, “Saratu, gobe fa in Allah ya kaimu tare da su Hunainah zaku tashi, daga Korea zasu rakaki makaranta don duk wasu shirye-shiryen komawar taki ban san sanda Al’ameen yayi ba. Dama abinda yasa aka daga tasu tafiyar kenan nima ban sani ba sai jiya yake gaya mun. Sai dai kuma naga alamar bakya son sakin jiki da Haj. Hadiza, Why?â€? Ta yi shiru, yayi zaton bata ji ba sai ya sake maimaita tambayarshi. Ta dan kada kafadu alamun zancen bai dameta ba ta ce, “ba komiâ€? ya ce, “Ba komi, na nufin komi. Duk inda kika ji ance ba komi, to anan koman takeâ€?. Ta ce, “To Daddy itama bata kula ni sai ‘ya’yanta (Su Hidayah) to ni ma ba sai in zauna inda na fi wayau ba?â€? Ya girgiza kai cikin murmushi “a’ah, ba zaki zauna inda kika fi wayau kadai ba. Uwa-uwa ce, matsayinta ya wuce duk yadda kike tsammani, ko ita bata kula ki tilas kuma wajibi ne ke ki kulata, ki dinga nuna mata kauna. Above all, Hadizah bafillatana ce usul fillanci take maki, wannan kunyan na dan fari na nan tattare da ita ga kuma rashin shakuwarku, wanda wannan sai a hankali. Ke zaki taimaka ku shaku. Idan bakya kusantarta yanzun ba zaku taba sabawa da juna ba tunda yake ke mace ce, gidan aurenki zaki cikin dan lokaci, ki daure kiyi hutun karshen wannan shekarar tare da su. Don ba mamaki kamin ku dawo an daura auren ku duka.â€? Ta cira kai a hanzarce tana yi mai duban mamaki kana tayi saurin sadda kai, cikin siyasa irin tasu ta manya ya ce, “Wai yayane? Ke da mutumin me kuke ciki ne, na ganshi yana ta mana zarya kamar marayan da ya rasa uwa, me kuka yanke ne? Su Najib fa ku suke jira don tuni sun gabatar da bukatarsu suna son asa masu rana da wuri.â€? Yayi shiru yana nazarin irin karbar da tayi wa zancensa. Tayi lamo da wuyanta a masangalin kujera abin tausayi. Idonta ya kawo ruwa raw-raw cike da nadamar hukuncin da ta yanke akan Al’ameen, wanda tasan abinda bazai taba yiwuwa bane. Tayi kokarin maida hawayen don bata son Daddy ya gani. To amma shi Daddyn duk tsawon lokacin idanunshi na kanta, tsoron shi Allah, tsoranshi kada Intisar tace bata son Aminu. Da ina zai sa kansa da rigimar Al’ameen yadda jiya ya sashi gaba da magiyar a daura musu aure koda tace bata son shi! Abinda shi kuma ba zai taba Iyawa ba wato danne mata hakki don farin cikin nashi? To amma shi kansa yakan so kasancewar al’amarin ba don komi ba sai don cigaban zumuncin bangarorin guda biyu, hakannan zuri’arshi kadai ya taba yiwa sha’awar auren kamilallar mace irin Intisar! Balle gudan jinin sa Ameenu? Kwata-kwata tarbiyar Ihsan bai mishi ba, tun haduwar su na farko. Hakannan banda mutuncin Dr. Argungu da yake gani da tun zagin da Ann Hathaway taje ta yi mishi har ‘officeâ€? kan wai Al’ameen ya ci mutuncin Addininta don kawai ta bashi shawara kan zaman shi da Ihsan gaba daya suka sire mishi. Haka shigowa da Ihsan ke yi rungume da Al’ameen har cikin dakinsa abin na damun sa kwarai, don dai ba yadda zai yi ne. Cikin murya mai sanyi ya ce, “Saratu, ki gaya min saboda Allah ba kya son Al’ameen ko?â€? Ta shiga girgiza kai da sauri alamun ba haka bane, hawaye suka soma biyo kumatun ta. Tsohon Brigedier Bello Makarfi, ya mike zaune daga kishingiden da yayi, ya daura hanunshi na dama a kanta, ya ce, “Wannan hawayen da kike kwarararwa a kullum yana damuna, sai in ga ni ban kai ga taka rawar uba har yau a gareki ba. Bayan ukubar da na sanya ki cikin gidana, still na kasa share miki hawaye a shekarun farin â€? cikin ki, na kasa tsayawa in gina maki rayuwa ta kwarai tamkar yadda na gina ta ‘ya’yana, na zalunce ki, na bautar dake, ban baki kwakkwaran ilimi ba har yau, ban idasa da zaba maki miji na gari a girman ki ba. Idan bakya son Al’ameen kada ki ji nauyi na, ki kawo ko waye ni kuma mai share hawayen ki ne, in har ya cancanci ya amsheki daga hannuna, zan bashi. Ki bar la’akari da kasancewar Aminu da a gareni, ni duk daya kuke, sai ma in ce kin fi shi. Domin ke ‘ya ce da ban taba ganin mai biyayyar ta da son iyayenta tamkar ke ba. Na rantse, a cikin ’ya’yan da na haifa bakidaya babu wanda ya ji kai na ya ke kuma kaunata tamkar ki. Don haka don baki son Aminu baya nufin bakya son Daddyn Aminu, Illa shi Aminu ne ba kya so saboda wani aibinsa ko wani kuskure daya aikata miki kika kasa yafewa! Ni dai hakannan nake son ki da Al’ameen, ba don komi ba sai don masifaffen son dana lura yana yi miki mai gigigatarwa, mai neman fitar da shi daga hayyacinsa, mai neman raba shi da rayuwarsa. Duk kuma bakomi ba ne face sakayyar Allah garemu a kan ki. Ina son inda za’a so ki ne, har illa masha Allahu, ba inda za’ayi miki son wanin ki ba. Abin nufi, masu aurenki domin wani naki, kyawu ko dukiyarki. To sai naga Al’ameen ne irin mijin da ya dace da ke, irin mijin da na dade ina yi miki burin samu, zai kuma rike mana ke da dukkan kauna irin wadda muke so ki samu a gidan aurenki. Na kuma dade ina sha’awar yiwuwar hakan a raina tun kamin shi ya furta, tun a sanda yake cin zalinki naga abubuwa dayawa cikin kwayan idanun sa, na kuma san ko ba dade ko ba jima Allah na nufin wani babban al’amari a tsakanin ku. Amma in kina ganin na so kaina ne Saratu fada mini?â€? A gaggauce ta rarrafa gareshi ta gurfana a gabansa, ta girgiza kai da karfi ta ce, “A’ah! Har abada Daddy nasan babu mai kaunata a duniya tamkar kai, har kuma iyayen da suka haife ni. Ba kuma zaka taba yin wani abu da sunan son kai a gareni ba. Kuma ni baka taba bata min ba, dai-dai da rana daya balle ka sa ni cikin ukuba. Bana kuka domin kiyayyar Al’amin, kuka nake don so da kaunarsa, da suka yiwa zuciyata katutu. Allah Daddy, ban taba fada ba, amma Aminu na taba ji har ruhi da bargon jikina, nake kuma azabtuwa a zuci da gangar jiki domin kaunar sa! Kuka nake domin nadamar tsatstsauran hukuncin da na yanke a gareshi wanda na zauna nayi tunani akai na tabbatar ba zai taba yiwuwa ba, domin kiyayyarta gareni ba karama bace, da kiyayyata aka halicceta baza ta taba yin abinda na kudurta ba. Kuka nake domin sanin cewa na jefa Al’ameen dina cikin halin kaka-ni-kayi, halin da bazan iya fitar da shi ba, halinda zai iya janyo muguwar gaba tsakanin sa da wadda ta haifesa, ta shayar da shi mamanta, ta raine shi har ya girma ya kai munzalin da har na gani na ke bege, take kuma son sa fiye da kowa a duniya. Dama tace ni din mayya ce, yanzu zata kara tabbatar da zarginta cewa na mayancewa ‘ya’yanta, bayan ni kullum kokarina shine in nisance su, in yakice su daga cikin rayuwata amma na kasa! Ko nayi kokarin hakan bana cin nasara, ba don kaunar jini ba sai don cewa su wani bangare ne daga jikin Daddy Makarfi. Jinin da yafi karfin wulakanci da tozarci a gareni. Ina tsoron hukuncin da zata yanke masa, wanda ko menene ni ce zan zamo sanadi.â€? Daddy ya yi murmushi, yace “Gaya mun hukuncin da ki ka yankewa Al’ameen din ki?â€? Cikin hawayen dai tace “Cewa nayi yaje yazo da Hajiyar sa, ta nemi gafara ta kan kiyayyar da ta wanzar da rayuwarta nuna mini, ta kuma furta amincewa da auren mu da bakinta, sannan ne zan maido soyayya ta, in rungume shi matsayin miji na uban ‘ya’yan da nake burin samu daga tsatson Daddy Makarfi.â€? Ta cigaba da kuka sosai, ta ce, “Daddy daga baya nasan ban kyauta ba, nayi nadama, hukuncin yayi masa tsauri, don bazata taba amincewa ba, shi kuma ba zai dawo gareni ba sai da amincewar ta, tunda hakan muka yi alkawari. Ni kuma ba don komi nayi hakan ba sai don kwatarwa kaina da ‘ya’yan da zan haifa a gaba ‘yanci daga gareta. Ina guje masu halin da zasu iya fadawa a gaba daga ukubar ta. Ni kadai nasan ita ko wacece? Ku bar ganin wai don iyayena sun bayyana zata daina ki na, a’ah, kiyayyar ta gareni a cikin jinin jikinta take, bazata taba dainawa ba. Koda kuwa a ce ni ce mafi rinjayen iyaye a duniya. To amma ai shi Al’ameen na zalunceshi, na hukuntashi da laifin da ba na shi ba ko Daddy?â€? Tayi shiru tana maida lumfashi cikin zargin kanta. Ga Mamakin ta sai yayi murmushi, ya dora hannu bisa kafadarta, ya ce, “A’ah, ba ki zalinceshi ba, kin yi dai-dai. Ban taba ganin yarinya mai tunani, hazaka da hangen nesa irin ki ba Intisar! Ina ma a ce sauran yara mata zasu yi koyi da dabi’un ki da an daina wulakanta su a gidan aure. Soyayyar dake zuciyar ki bata rufe maki ido ga hango gaba ba, da abinda gobe zata iya haifarwa ba. Sadaukarwar ki da sanin ciwon kan ki bazasu tashi a banza ba!!! Abu ne da bazan iya gaya miki ba, Illa ni ma Haj. Nafi ta cuce ni ba kadan ba, wanda hakki ya koma mata. Ban saketa ba, amma ga gidan, ga ‘ya’yan nata kiri-kiri ta kasa zama a cikinsa, to tun a duniya kenan wata shari’ar sai a Lahira! Komi za kiyi Saratu ki sa Allah a gabanki, bayanki, hagunki da damanki. Kar ki ji tsoron mutum domin shi ba komi bane face abin halitta daga yunbu, mai yin komi daga kudirah da Iradar Ubangiji kuma bisa nufi da yardar sa. Magana ta karshe shine ina bayanki akan kudurinki na cewa sai Aminu ya kawo mahaifiyar shi nan a gabana ta nemi a fuwarki, bisa dimbin azabobin data gana miki, wanda ko Allah baya yafe hakkin wani kan wani. In kuma har baki yafe mata ba ai Allah ma bazai yafe mata ba. Ta kuma furta da bakinta cewa ta amince ki zamo mata a gareshi wannan tunani ne mai kyau. Ni kuma alkawari daya nake so ki min shine, daga yau bazaki sake zubda hawayennan haka kawai bada kwakkwaran dalili ba muddin ina rayeâ€? Ta sa hannuwanta duka biyu tana sharewa tace “Na daina Daddy, kuma in har hakan ta faru ni kuma na amince da auren Al’ameen koda a gobe ne, kuyi duk abinda kuke ganin ya dace.â€? Ya ce, “Ubangiji yayi miki albarka Saratu, ya zama jagoranki a rayuwa, ya baki aljannah mafificiya sakamakon biyayyar nan da kike yi mun a gidan duniya. Kada Allah ya nuna min ranar da Ameenu zai tozarta ni a idonki.â€? Ta sunkuyar da kai cike da kunya, a ranta ko cewa take ai ko Aminu kullum yankar tsokar jikinta zai ke yi yasa a miya, zata daure ba tare data gayawa Daddyn ba. Ya ce, “Abinda nake so dake a karshe shine ki ji abinda na ce da ke, ki bi mahaifiyarki su rakaki makaranta, ki maida hankali kan abinda ya kai ki, muma insha Allah zamu ke zuwa dibaku a kai-akai, in kun samu hutu ki zauna tare da su har mu ji me Al’ameen da Mamar sa suke ciki a san abin yi. Da dai za’a hada auren ku da na su Najib ne amma ina ga yanzu za’a fara yin nasun, har sai tazo tukun (Hajiyar), kuma ki saki jiki da ‘yan uwanki don Allah.â€? Cike da murmushi tace ‘I can do anything for your sake, Dad (zan iya yin komi domin ka Babana)â€? ya ce, “To Allah yayi miki albarka.â€? Mu karasa a littafi na hudu kuma na karshe insha Allahu. Taku har abada, â€? Sumayyah Abdulkadir. How much do you like this story? 5/14/22, 09:26 - Ummi Tandama😇: ____________________________ *âœðŸ? SIRADIN RAYUWAâœðŸ?* Book four *@Takori* Page1ï¸âƒ£ Alkawarin da ta yiwa Daddy bata karya ba. Ranakun da suka biyo baya, ta karesu ne cikin farin cikin da walwala ga kowa. Kowa a gidan yayi mamakin canzawarta haka farat daya sai dai babu wanda ya tambayi dalilin canzawar tata. Ko babu komi ta samu courage da relief daga rudanin da zuciyarta ke ciki. Alameen bai zo ba a washegari, ta tabbatar duk inda yake yana bisa hanyar neman Hajiyar sa, a Dubai ne ko a Kadunan ne oho su suka sani! Ta tabbatarwa kanta lallai wanda ya rasa abokin shawara abin tausayi ne, ita dama tun fil azal Daddy ne abokin shawararta sai ko Ya Faisal wanda a yanzu baya yi da ita, da wuya su bata shawarar da in tabi bata ganin yakini a ciki. Hankalin kowa ya kwanta musamman yan uwanta da basu san wainar da suke soyawa ita da Babanta ba, wadanda a yanzu sabon shafin soyayya ne mai karfi aka bude koko in ce ake kara kullawa tsakanin Najib da Hidayah. Wayewar garin litinin sukayi sallama da kowa har da Daddy da kansa a rakiyarsu (Airport) din Abuja, Najib da Hidayah dai kamar bazaa rabu ba illa sun yi alkawarin kasancewa a waya a kullum kamin a mallaka masu juna, hakannan shi Najib din za suke zuwa da Daddy. Zahra taki barin Haj. Hadiza kememe har shidewa ta shiga yi da Khaleel ya dage sai ya amsheta, kawai sai aka ji Anti Saratu ta ce, sai ku tafi da ita a yayeta, in ma zaku rike na baku halak malak. Ban sani ba dai ko Daddin Ameenu na da uzuri? Daddy yayi murmushi yace umh-uhm, Allah ya kiyaye hanya Zahrah, Zahrah Allah ya kai ku lafiya! Haj. Hadiza ta rungume Zahra tsam-tsam har da hawayenta, ta rasa bakin godiya bisa dimbin karamcin wadannan mutane, bata san me zata yi ta saka musu ba itama banda mallakawa yayansu tsala-tsalan yan matan ta, sai Ambassador ne kema Daddyn matukar godiya, su kadai suka san me suka kukkula kan auren yayan su ba tare da sanin yayan bama. Kwanan Intisar kwata-kwata ukku a gidan mahaifiyarta a kasar Korea, Abbansu ya maida ta Riyadh. Makarantar da fi so a rayuwarta, makarantarta ta baya, makarnatar da ta zamo silar warwarewar alamuran ta da gajarta bakin-cikin rayuwarta, tunda kuwa anan ne ta hadu da su Hidayah, har suka dangana ta ga mahaifiyarta. Makarantar da ko a mafarki bata kara yin na dawowa cikinta ba, don tana ganin bazata kuma samun irin wannan gatan ba. To haka alamarin Ubangiji yake, don haka yake cewa La Taknadu min Rahmatullah (Wato kada ku fidda rai da rahmar Allah) domin buwayar shi ta wuce mithali. Hakannan duk wani SIRADI a rayuwa da sannu in an yi hakuri zaa tsallakeshi, ba kuma inda hakuri da fawwalawa Allah alamura baya kai dan adam. Ta daga kanta sama a cikin ajinsu, kana ta sunkuyar. Ta yi duba ga rayuwarta mai juyawa tamkar a majigi. Ta kara jin tsoron Allah, tsigar jikinta ya tashi yarrrr! Ta kara tsarkake shi a zuciyarta, kadaitaccen sarki mai juya alamura yadda yaso. Tayi duba izuwa wahalolin da ta sha a rayuwa, wai yanzu duk sun zama tarihi. Ita kanta duniyar haka take, no condition is parmanent (ba wani yanayi da yake tabbatacce). Saratu ta watsar da tunanin komi ta rungumi karatun ta bil-hakki. Har yanzu burinta yana nan kan son gyara rayuwar alummah! Ta girgiza da labarin mutuwar mutuminta Dr.Alhassan, bayan auren sa da kawarta Rabikha. Ta jima tana yi mai Addu’ar Rahma da gafara wurin Ubangiji. An kai ta aji shidda ne, don haka bata wasa. Da yawan Malaman da ta sani a da, basu bane a yanzu, wasu an canza su, wasu an kara masu girma. Ita kanta shugabar makarantar da ta sani a da Ayyush Siddik ba ita bace a yanzu. Tace ashe ko ina ma haka abubuwa ke juyawa ba a kanta kadai ba! Bata kuma kara bi ta kan komi ba sai karatunta, ga wayar yan uwanta tana samu akai-akai, sai dai Alameen ko sau daya bai kira ta ba. Ranar da suka fara jarrabawar gwaji Haj. Hadiza da Ambassada suka je mata, ba karamin farin ciki tayi ba, don rabonta da ganin wani nata watanni bakwai kenan. Anan ne suke gaya mata Hunainah ta wuce Jamiar Alazhar Hidayah kuma an daura auren su da Najib suna honey-moon a can Al-kahiran, tayi mamaki kwarai da Hidayah bata gaya mata ba, gashi kuma suna waya. Daga baya ne ta tuna cewa Hidayah ta sha gaya mata bata son ta rigata yin aure, so take ayi komi nasu tare. In kuma hakan bata samu ba ita kam bazata ji dadin yin auren ba. Auren Hidayah da Najib ya tabbaar mata har yanzu Alameen bai dawo daga gun Mamarsa ba! Ko dai ta ja rayin sa kan nata, ko kuma wani mummunan alamari zai faru, wanda take gudu, take guje masa. Ko kuma kwata-kwata bata amince ba shi ya sa ya rabu da ita? Bata sani ba. Ba irin tunanin da baya zuwa mata a rai amman ta ki gasgata kowanne, kowanne tana yi mai uzuri ne da cewa Alamin zai dawo gareta komi rintsi ba zai bari Hajiya ta rabasu ba. Ramadhan 20/10 Hijriyyah Allah Sarki! Alameen Bello ne ke tafe cikin motarshi (ash colour Rio), sanye da Jamfa da wando na bakin yadin Filted. Ya saya raunnanar kwayar idonshi cikin bakin dark glasses akan hanyarshi ta zuwa air-port din garin Abuja domin dauko mahaifiyarsa da jirgin data shigo daga Dubai zai sauketa a yau. Yayi parking a inda aka tanada domin adana motoci ya karasa reception ya samu gefen wata kujera ya rage tsawo. Kada kaso ka tona zuciyar sa da ke bugu da sauri-da-sauri mai cikke da kunci, fargaba gami da igiyar so da ta yi mata dabaibayi. Idan har ka san Dr. Alameen Bello a da, to a yanzu sai ka wuceshi ba tare da ka shaida shi ba; gaba daya ya kare, sai tsayin da karan hancin gami da fararen idanun kadai. Yayi zaman akalla mintuna talatin kamin a fara shelar landing din jirgin. Tamkar kazar da kwai ya fashewa a ciki, ya mike yana mai dauriya da karfafa kansa da cewa akwai jin kai na uwa, akwai kauna ta Uwa ga dan ta. In ta kalleni ai zata tausaya mini, ita kanta tasan ba haka na dawo ba, tasan na zamo mara amfani, zan kuma kare rayuwa ta a hakan muddin bata bani abinda zuciyata ke muradi ba, zan gaya mata zuciya na ciwo, duk wani bugu da take yi Intisar ne a ciki, zan fadi, zata rasa ni muddin tayi min shamaki da Halimanaaa. Bai sani ba, ta dade a tsaye gaban sa, sanye da koriyar atamfa sufa, ta yane jikinta da yalwataccen mayafi, ta dade tana nazarin mugun zabgewar da yayi, kai da alama baya ganin abinda yake gabansa ma, baya jin taku balle gane abinda ke faruwa a gabansa. Ta mika hannuwa ta rungume shi ta soma kuka ta ce, “Ameenu mutuwa zaka yi ne?â€? A sannan ne ya dawo hayyacinsa, ya runtse ido cike da farin cikin saukar ta lafiya, ya russuna ya dauki Jakarta ya rataya yajata har zuwa inda ya adana motarsa. Ya bude mata gidan baya ta shiga ya rufe, ya aje jakar a gefe ya zago ya zauna mazaunin shi, ya kakaro murmushi mai kwantar da hankali ya ce, “Nayi fama da cuta ne Hajiya, amma alhamdulillahi naji sauki, nayi zaton an fada maki?â€? Tayi ajiyar zuciya tace ban zaci abin yayi kamarin haka ba, shin me ke damun ka? Ya lumshe ido yayi murmushi, ya bude su duka a kan ta ya ce, “Ciwon Zuciya!â€? Wadannan su ne kalami mafi muni da ta taba ji a rayuwarta, suka kuma diran mata tamkar kibiya a kahon zuci. Muryar ta na karkarwa tace kai ko meke damunka, da har ya janyo hakan? Me ka rasa a rayuwa da zaka sanyama ranka damuwa? Yayi murmushi yace in kin so Hajiyana, zan iya murmurewa kamar ban taba yi ba, haka in kin so, zai iya zama ajali na. Tace (tana mai girgiza kai da karfi) kada Allah ya nuna min wannan ranar! Daga haka ta ja bakinta tayi shiru. Ganin ya dau hanyar gidan Babansa ta daka mai tsawa mai firgitarwa ta ce, “Kai, ina zaka kai ni? Gidan Babana zaka kai ni! Ko baka ji ba?â€? Ya ce, “Na ji Hajiya na, kuma a bisa umarnin ki nake har kullum.â€? Ya karkatar da kan motar ya dauki hanyar Kaduna. Sai da tayi sallah, ta huta suna hira da mahaifiyar ta kan kayan da ta turo daga can Dubai din, ya shigo daga masallacin da ke kofar gidan, bayan ya samu jamin sallar laasar, duk suka dube shi. Babar Hajiya, wadda ta fara tsufa sosai amma yanayi irin na hutu da daular da take ciki ke son boye tsufan nata karfi da yaji, tana ta tsokanarsa yadda ta saba amma a yau bai iya ya tanka ba, taraddadin dake zuciyarsa kadai ya ishe shi. Ta dubi Hajiyar cike da alamar tambaya tace, “Shin me ke damun Mai gidana ne, duk ya lalace haka? Ciwo ko matsala? Hajiya ta kyabe baki tace umh masa! Ni ma haka na gan shi, munafurcin su can da su da uban su zai cinye amma ba ni ba, na fi karfin kurwar su Intasar Allah! Tunda ku sun lashe ku, to ku je kuyi ta bin su na yafewa Saratu, sai ta je ta kara jika malaminta, na yarda ita na haifawa ku, na amince yayan tara da nayi nakudar ku na haife cikin wahala da kaka-ni-kayi, duka nata ne, ni kuma ina rokon Allah ya bani masu jin kaina.â€? Ta soma sheshshekar kuka. Ya ji guiwoyinsa sunyi sanyi kalau, fiye da shigowarsa. Ya tabbata rashin nasara, ya tabbata garesa, Shi kadai yasan yadda kukanta ke girgiza zuciyarsa. Ya alkawartama ran sa idan ta hanashi zai hanu, shi kuma yayi jinyar zuciyarsa har sai ta mance da Intisar! Zai zabi Hajiyarsa akanta!! Zai zabi mahaifiyarsa akan soyayyarsa!!! Zai zabi farin-cikin Hajiya akan na shi, domin samun tsira a gidan duniya da tserewa daga azabar lahira. Duk da haka zai fadi, domin ta yanke masa hukunci. Ya zamo daga cikin kujera yazo har inda take, cikin kaskantar da kai da tsananin girmamawa ya ce, “Hajiyana, ba mayya bace Intisar, ki daina illata ta hakan nan, ki daina fadin muggan kalami akanta don Allah? In Iyayenta suka ji zasu yi kararki. A yanzu haka tana tare da Iyayenta bata gidan mu. Na zo ne neman amincewar ki, kan abinda zuciyata ke so da albarkarki. Ina mai neman yardar ki kan son auren Intisar diyar Aunty Amarya, a sabili da azabar sonta da ke neman hallakani. Ki ceci rayuwata Hajiya, ki ji tausayina. Ki daina laakari da hujjojin ki marassa madafa. Intisar ta ki ni, ta bujire wa ingantacciyar soyayyar da take mun saboda ke, saboda sanin halinki na rashin kyautayi da adalci a gareta. Ki taimake ni ki nuna masu ba haka bane, ke ma uwa ce mai tausayi da jin kai tamkar sauran iyaye, ke ma uwace da ta san ciwon dan ta, take kuma son duk abinda yake so. Bijirewar ki na nufin alamura da dama cikin rayuwata. Ba na nufina in tursasa ki bisa raayina ba, Illa ki ji kai na ki tausaya mun., ki yi min alfarma cikin dimbin alfarmomin ki da basa karewa a gareni. To a yau ma ina neman alfarmar ki irin wadda ban taba nema ba! Ina kuma mai tabbatar maki zan yi biyayya ga duk hukuncin da ki ka yanke a gare ni.â€? Ya sunkuyar da kai yana mai sauraron hukuncin nata. A zaune take kurum tana mai sauraron kowacce kalma da kowanne harafi dake fita daga bakinsa, tana kuma auna ta a bisa maauni na hankali da tunaninta. Ta kasa gasgata me kunnuwanta suke jiyo mata, ta dauki alamarin cikin irin mafarke-mafarken da take a dan tsukin game da yayanta da Intisar. Sun fi minti talatin shiru, babu wanda yayi koda kwakkwaran nunfashi balle hadiyar miyau. Sai a lokacinne wasu zafafan hawaye suke zubo mata, wadanda ita kadai ta san ko na menene, ita kadai ta san me take sakawa take kuma warwarewa a zuciyar nan tata. Bakin-ciki ne? Farin-ciki ne? Tausayi ne? Nadama ce? Ita kadai ta barma kan ta sani. Hukunci na karshe data yanke shine mikewa ta bar masa falon, ba tare da ta ce da shi komi ba. Alameen ya ji hantar cikin sa ta kada, yayan hanjin sa sun dunkule waje daya. Ya yi nadamar furta kalaman sa ga mahaifiyar sa, data daukaka kaunarsa a zuciyarta fiye da ta kowa a duniya. Wadda burinta a kullum shine dawwamar su cikin gata da farin-ciki. Amma a yau, sakamakon ta shine zabar wadanda ta ki jinni a duniya fiye da kowa a matsayin abinda yake so da kauna mai tsanani, yake burin ya zamo wani bangare koko ginshiki na rayuwarsa, kuma wai har yake gaya mata in har bata amince ba, zata yi asarar shi itama. Anya Hajiyar ta cancanci wadannan kalami? A lokacin ya ji ya tsani kan sa, ya tsani komi dake cikin duniyar kuma ya tsani ita kanta Intisar. A ganin sa duk ita ta jawo masa, samun sabani da Hajiyar sa. Yayi nadamar dawowar sa Nigeria a yau. Inama bai biyewa Ihsan sun dawo ba! Inama. Inama Sai ya ji wasu dunkulallun hawaya sun kwararo bisa kundukukin sa. Ya mike cikin yankewar buri da fidda rai da komi na rayuwar duniyar ya nufi dakin da Hajiyar ta shiga, yasa hannu ya murda kofar sai ya jita gam-gam da mukulli. Ya juya ga kakar sa Haj Iyami, wadda ke zaune cikin kujera tana kallonsu kawai cikin rashin fahimtar abinda suke ciki. Ya zauna a gabanta ya kama kafafunta ya shiga rera mata kuka mai matukar motsa zuciya, yana magiyar ta nema masa gafarar Hajiya, in ba hakaba bai san yadda zai yi da rayuwar shi ba. Ta kai hannunta kansa tana shafawa tace ya isa Maigida na, ko Nafi zata yi fushi da kowa a duniya bazata yi fushi da kai ba! Ta na sonka, son da kai din baka sani ba, na tabbata ba kai ka sata kuka ba, ita kadai tasan dalilin kukanta. Ka tashi ka tafi gida, dare yayi, gobe ka dawo lokacin ta nutsu sai mu zauna a yi maganar. Ina! Alameen ya tabbatar mata bai zuwa ko nan da can batare da ya san hukuncin da Hajiyar ta yanke a kansa ba. Ta kada ta raya harta gaji tace tunda kwana zaka yi, to ga makullan sassan baki can bisa T.V ni zan je inyi sallah. To a lokacin ne shima kunnen sa ya jiyo mai kiraye-kirayen sallar maghriba da ake ta yi a masallatai, ya mike ye fita, a masallacin ya samu dabinon da yai buda baki, ya sami jami a masallacin cikin gidan, bai baro masallacin ba saida akayi sallar Isha’i tare da shi, ya sake mikewa ya bade shafa’i da wutri. Ya dade cikin sujjadarsa, yana mai zubar da hawaye, cikin kai kukansa ga Allah subhana, mai juya alamura yadda yaso, yana mai rokon sa da ya fidda Intisar a zuciyarshi, tunda Hajiya bata son ta, ya karfafa masa raunanniyar zuciyarshi, ya bashi ikon yin biyayya ga mahaifiyar shi, ya karkato da kafaffiyar zuciyarta ta yafe mishi! Ta fahinci ba ya da nufin tozarta ta, kuma ba shi ya daurawa kansa kaunar Intisar ba. Abu ne da shima yafi karfin sa, yafi karfin iyawar sa, yafi karfin duk wani kokari da zai yi ya fidda ta a ran shi!! Ya bashi hakuri da dangana, ya sa yafi karfin zuciyarsa, domin shi kansa ya san yana cikin sahun mutanen da basa iya controlling zuciyar su musamman akan abinda ta ke tsananin so. Har zuwa sanda ya koma cikin gidan, Hajiya bata bude kofarta ba, abinciccikan da Kakarshi ta sa shi a gaba da su domin yayi buda baki, bai iya ya hadiyi ko loma daya ba. Ya kara ramewa, ya kara zabgewa, ya kara susucewa yini daya rak, fiye da yadda yazo garin. Sai da Assalatu Hajiya ta fito domin gabatar da alwallar sallar asubahi, ta ji wani abu ya tokare mata kofa sai rabewa tayi ta fito. Ba komi bane illa kyawawan kafafun Alameen da ke kwance a bakin kofar ta barci na dibarsa kadan-kadan, har ranta ta ji matukar tausayin shi. Wai Aminunta ne wannan? Mutum maabocin kuzari, fara, kwarjini, ilmi na kwatance da cikar zati ya koma haka, duk a dalihin soyayyar Intisar. Wasu hawayen takaici suka zubo mata. Ba shakkah, Intisar, mayya ce! Furucin da ta dade tana yi a kan ta yau taga tabbacin sa. Ta saki kurwar Faisal da Daddy Makarfi yanzu kuma ta dawo ta Aminun ta? Bazata taba amincewa ba!! Za tayi fito-na-fito da yarinyar nan a karo na biyu har sai taga karshen ta. Za tayi mata mai gabadaya ita da Saratu in ba hakaba, ta tabbata watarana daga ita har yayanta zuwa abinda ta mallaka, ba zasu tsira daga maitar yarinyar ba. Tasa kafarta ta zungureshi yayi saurin bude ido, tare da hamzarin gurfana a gabanta yace cikin dusashshiyar murya. Hajiya na, kin yafe mani? Tace kai ba na son zancen banza, tashin ka nayi ka je ka yi Sallah. Duk fadin gidan nan ka rasa inda zaka kwanta sai bakin kofa ta, salon ka jawo min magana ko me? Ya mike sum-sum-sum ya na fita daga falon yana waiwayonta, ta yi tsaki a ranta tace Allah ya isa tsakani na da wannan tsintattar mage. Sai a lokacin ta tuna abinda yace da ita, wai Intisar bata gidansu, tana tare da iyayenta. Tace ni zaa gayawa karyar banza ko ko ni zaayiwa dadin baki wai don in yarda, yarinyar da aka kawo min ita daga daji, tun tana tsumman goyonta, yanzu haka ma wasu mutane Saratun ta debo aka biyasu su ce su iyayen Intisar din ne, don ta yarda a kakabawa danta to bazata taba amincewa ba. Kwanan Alameen biyu kenan yana bin mahaifiyarsa tare da neman gafararta a bisa bacin ran daya lura bukatar shi ya sanya ta, amma taki ce masa komi iyakaci in ya dameta ta tashi ta bar masa wajen. A na ukun ne Haj. Iyami dattijiya mai tsananin hangen nesa, ta samu Hajiyar a daki rike da hannun Alameen da bakin ciki, nadama da tashin hankali ke neman zautawa, ta zaunar da shi a gefenta amma shi din sai ya zame daga bakin gadon ya zauna bisa carpet a gefen kafafunta kansa a sunkuye, hakannan hawayensa basu bar diga bisa tafin kafarta ba. Ta yi kira da kakkausar murya irin yadda bata taba yi ba. Ta ce Nafisa! Ke kam wace irin uwa ce? Na dade ban ga uwa mara tausayi irin ki ba. Ba haka ni da ubanki mu kai miki ba, mu kullum masu tausayi da kyautayi ne a gareki, tare da kaunar duk abinda ki ke so! A da, na rantse na daina shiga alamarin ki da iyalinki, domin dai kin girma, amma zuciyarki ta yara ce. Shin wannan so ne kike wa Alameen ko kiyayya ce? Wannan ba so ba ne. Ba soyayya ce ta uwa ga dan ta ba. Na tabbatar miki in baki yi hankali da rayuwar duniya ba za ki yi nadama, a lokacin da bata da amfani! Son kan ki yayi yawa Nafisa. Ita uwa har kullum hakuri take da son ranta ta barwa dan ta. Ba don a kan idona kika yi rainon cikin Aminu, kika kuma haife sa a hannu na ba, da sai in ce, ke ba uwar sa ba ce! Daga haka ta juya ta fita. Hajiya Nafi, ta dago sannu a hankali ta dubi Alameen, ta hadiyi wani daddatan miyau daya makale a makoshinta. Haka sheshshekar kukan Alameen ko daya bai sa zuciyarta ta russuna ba. Ya ce, “Wallahi Hajiya in kika hanani zan hanu, in kika yanke min hukunci bazan tsallake shi ba komi tsaurinshi. Na rantse da Allah wannan hukuncin da kika yanke a gareni na yin fushi dani ya fi komi tsauri da hatsari agare ni, fiye da rashin soyayyar Intisar! Ban san me na fada wanda ya bata miki rai ba, ban san laifi na gareki cikin alamarin nan ba. Idan kika ce in barta, daga yau na bar ta har abada! Ko hanyar da ta bi bazan kara bi ba, zan je in lallashi zuciya ta in runguni kaddara, in roki Allah ya cire min kaunarta, in rokeshi gafarar hawayen da kika zubar adalilina. Ni dai fatana ki yafe ni, ki daina fushi da ni, don Allah Hajiya. Ya karasa cikin rishin kuka.â€? Ta bude bakinta cikin kakkausar murya tace “Ameenu! Wane alkawari ka yi mun a dawowar ka daga Miami?â€? Ya dago cikin razana da dimaucewa ya ce, “Eye, naam, wane alkawari ne? Hajiya wallahi na manta.â€? Ta yi murmushi ta ce, “Ka je ka tuna, in ka tuna kazo ka gaya mun sannan ne zaka ji hukuncin da na yanke kan bukatar ka. Ya bude baki zai yi magana ta daga hannu ta daura bisa labbanta ta tace Shhhhhh, bana magana biyu. Na farko dai bazan hana ka aurenta ba akan-kaina, tunda sanda ka je inda take har kuka kulla soyayyar, ina cikin gidan baka yi shawara da ni ba. Dama kuma daga ku har ubanku ba ku dauke ni a bakin komi ba, baku dauke ni a cikakkar mai hankali ba. Na tabbata ba don ta bijire maka ba sai a yi auren ba da yawu na ba, sai dai a debo yayan shegiya a dire mini, a ce ga jikokina, in yaso ko in mutu, ko in yi rai, ba abinda ya dame ku bane. To a kan me zance ban yarda ba? rashin yardar tawa baya nufin komi tunda kuwa Bello Makarfi zai aura maka ko na yarda ko ban yarda ba? Saratu zata maye maka gurbina ko na dawo ko ban dawo ba? Ta yi shiru cikin matsanancin takaicin da ba zai fassaru ba, tana zukar numfarfashi da kyar tana fesarwa da kyar. Ya dago idonsa jike da hawaye yace wallahi wallahi Hajiya, bani da wadda ta fiki, bani da wanda zai maye mani gurbinki, bani da kamarki kuma ban taba kwatanta matsayinki da na kowa a zuciyata ba! Ni dai burina ki yafe mini laifinda na yi miki, wanda na sani da wanda ban sani ba. Tunda kuwa ba kya son Intisar daga yau nima zan daina sonta zan daina kaunar ta. Ki yafe mani ki sa mani albarka. Ki taya ni rokon Allah ya sa na fi karfin zuciya ta kuma ya yaye mun kaunarta. Ita kanta bata san sanda hawaye ya zubo mata ba, tayi saurin dauke su da yan yatsunta tun kamin ya gani. Ta mike tana nufin fita yayinda shi kuma ya bita da kallo, cikin rashin sanin abin yi kuma. Kamin ta kai bakin kofa ta ce, “Allah ya yafe mana baki daya, ka tashi ka tafi wurin matarka haka zaka tayar mata da hankali. Kuma ka yi kokari ka tuno shin wane alkawari ka yi mun a ranar da ka dawo daga Miami? Bana nufin in tursasaka bisa raayi na, illah in tserar da kai daga tozarta alkawari!â€? How much do you like this story? 5/14/22, 09:27 - Ummi Tandama😇: _____________________________ *âœðŸ? SIRADIN RAYUWAâœðŸ?* Book four *@Takori* Page2ï¸âƒ£ Tafe yake a mota amma hankalin sa baya jikin sa. Kuka yake kashirban kaman karamin yaro. Duk da zuciyar sa tayi sanyi da yafiyar da ya samu daga gareta wannan bai hanashi kukan tashin hankalin da kalamanta suka tsomashi ba. Wane alkawari ne yai mata? Ya kasa tunawa. Hajiya kin ce in koma ga matata, to ai gara in dawwama a nan kina azabtar dani daga hukunce-hukuncen ki, domin in na koma gareta bani da wani sauran amfani a gareta, me zan yi mata? Me zan ce mata? Rayuwata ta zamo impotent ba zata kara moruwa da ni ba, kowa ma ba zai kara moruwa da ni ba including Inteesar! Na dauka zaki fahimce ni, na dauka zaki ji kai na ki ji tausayi na, na dauka zakiyi tunanin soyayyar da nake yi mata bata shafi kiyayyar da kike mata ba, na dauka zaki yi min alfarma irin wadda ba ki taba yi mun ba, na dauka zaki ce je ka Aminu ka auri Intisar, Allah yayi maku albarka, ya sa hakan shine mafi alkhairi a gare mu bakidaya., amma kamar ba kya tausayi na, me zan yi miki ki fahimci ni mai gudun bacin ran ki da fushin ki ne? Ban zaci zaki yafe mun ba tunda na yi sanadiyyar zubar hawaye daga idanuwanki. Bana nufin in tursasa ka bisa raayi na, illa in tserar da kai daga tozarta alkawari ya tuno kalamanta na karshe. A lokacin zuciyarsa ta tariyo masa ranar da ya dawo, da kuma maganganun da sukayi shi da ita a dakin Faisal. “alkawari daya zan iya yi miki hajiya na, ba zan taba son ta irin son da Faisal ke mata ba!â€? Amsar da ya bata kenan a wancan lokacin, maganar ta cigaba da amo har cikin kwakwalwarsa, ta bi har cikin jijiyoyi da tsokar jikin sa, ta zagayo ta fito daga bakin sa. Eh nayi maki wannan alkawarin kam, nayi Hajiya na, kina da hujjar hukuntani da alkawari na. na gode. To amma ba kiyi tunanin komi ya faru a bisa rashin sani ne ba? Ban san Intisar ce diyar Anti Amarya ba. Na so ta a Halimar ta, baa Inteesar ba, Ban san san sanda zuciya ta rinjayeni ga son nata ba. Karar karon motoci sama da goma, tare da wuntsilawar da motar Alameen ta yi ta shiga katantanwa bisa titin, haka murje ta da wata kotuwar DAF mai cike da Hatsi tayi bisa titin da zai shiga da kai garin Minna kafin ya sadaka da Abuja, ya janyo hankalin alummar da ke wajen bakidaya suka ambaci. Inna lillahi wa inna ilaihi raji oun! Cikin dan lokaci jamian tsaro suka cika wajen tare da motocin ambulance abin dai babu kyawun gani. ***** UWA, MAHAIFIYA!!! Tunda ya fita ta kasa sukuni, ta rasa me ke mata dadi, ta rasa inda zata tsoma ran ta ta ji sanyi. Ta kai gwauro ta kai mari a tsakiyar kayataccen falon, can kuma ta isa ga taga tana lekensa, har ya tada mota ya fita daga harabar gidan idanuwan sa basu bar tsiyayar da hawaye ba. Ta koma cikin kujera ta zauna cikin mutuwa jiki, ji tayi tamkar ta zauna a cikin kaya, ta yi tagumi, zuciyar uwa! Haka kawai taji hawaye na zuba mata sharr-sharr. Ta san duk cikin yayanta babu mai son ta tare da yi mata biyyayyah tamkar Alameen, anya hukuncinda ta yanke a kansa tayi masa adalci? Gaskiyar Innar ta ne son kanta yayi yawa, kuma wannan ba so bane! Ita uwa kullum hakuri take da abu koda tana so ta barwa danta, ya roke ta, ya kaskantar da kansa gareta irin yadda wani cikin yayanta bai taba yi mata ba. Ya nuna mata fifiko akan bukatar shi. Ya ce alfarma ce ya ke nema irin wadda bai taba nema daga gareta ba! Ya zubar da hawaye irin wanda bai taba zubarwa a duniya ba, sabida tashin hankalin fushinta a gareshi. Koda sanda yake kankani bata taba ganin shi yayi kuka haka ba. Ya nemi jin kanta da tausayi amma bata nuna ko daya ba, duk da cewa ba hakan ba ne zahiri a zuciyarta. Ta nuna masa damuwar shi bata dameta ba, kiyayyar da ke zuciyar ta kadai ta sani, koda hakan zai zama ajalinsa bata amince masa ba, shin ita din wace irin mahaifiya ce? Ta kai tunaninta ga yarinyarda aka kira da suna Saratu-Intisar. A iya saninta da yarinyar, shekaru goma sha takwas da suka gabata, tun tana jaririya kawo girmanta, bata taba daga ido ta yi mata koda kallon banza ba, bata taba bude dukkan idanun ta tangaras ta dubeta ba, sabida tsananin girman ta da kimar ta da take gani. Bata taba fada mata abu tace da ita ba haka ba. Bata taba yin musu da ita ba balle ta kai ga zaginta, duk kuwa da irin kyara, tsangwama, ukuba da rashin kyautatawar da take mata. Ta dauki yayanta tamkar yan uwanta na jini, bata kula yayan kowa a duniya sai nata, sune ta mayar abokanta, yayyunta, kawayenta, abin gani ta ji farin-ciki kuma abin alfaharinta. Bata hada kaunar yayan ta da na kowa a zuciyarta. Bata dauki kanta a bakin komi ba face kaskantacciyar baiwa a gareta, duk da yakinin da ta ke da shi na cewa ita din diya ce ga Bello Makarfi. A duk iya fadin tunaninta, ta kasa tuno ranar da yarinyar ta kuskurota ko da sau daya, ta kasa tuno ranar da yarinyar ta yi mata ba dai-dai ba. Ta kasa tuno ranar da yarinyar ta hantari ko daya cikin yayanta, duk da fada mata da take tayi da babbar murya cewa ta fita harkar yayanta, domin ita din ta tsane ta. Ta kasa tuno inda yarinyar ta taba gayama wani abinda take mata koda da subutar baki ne kuwa, har kuwa mahaifiyar ta, bata jin ta gayawa Saratu irin rikon da tayi mata a bayan ta. Kai iyaka tunanin ta bata taba ganin yarinya mai hakuri da yakanah kamarta ba, shin maye laifinta don Aminu ya so ta? A kan me bazai so ta ba? Tana da qualities da dama da zaa so ta a kan su, me tayi mata ta tsaneta? Rashin iyaye? To ai kowa ma zai iya rasa iyayen sa, ko ita a yanzu mhaifinta ya rasu, da uwar ta take zaune, sai a tsaneta? Shegiya ce? To in shegiyar ce ma ai ba ita tayi wa kanta ba, ba ita ta jawa kanta ba, itama hakan ta budi ido ta tsinci kanta, kuma ko yau ta mutu zata shiga Aljannah kamar sauran halattattun yaya in har ta yi aiki na kwarai. Ko a yanzu ta tabbata da yarinyar zata fadi ta mutu, to bata da kaico a rayuwa! Uwar rikonta da uban rikon ta kullum cikin shi mata albarka suke, bata wasa da lokacin sallolinta guda biyar duk rintsi, duk gajiya, duk sanyi, duk ciwo sai ta ganta tana sallah da asubahi, sai ta ganta tana sallah akan lokaci har wani mulmule ne baki wuluk bisa goshinta sabida tsabar sujjadah, kullum Kaman ana kara tisa shi ya fito radas. Bata taba jin ranar da harshen yariyar yayi ashar irin na su Khaleel ba koda da kuskure ne kuwa. Bata taba jin ranar da wani ya budi baki ya furta wani kalami ga yarinyar, wanda ba na yabo da alheri bane. Zata rantse wannan yarinyar bata san meye iskanci da shaidanci na wannan zamanin ba, da yammata suka sa a gaba, batasan kallace- kallace da karance karancen banza na zamani ba, bata san bata lokacin ta a abinda bazai amfane ta ba, to meye laifin ta? Me ta yi mata? Ta tsaneta domin Daddy Makarfi na son ta fiye da kowa cikin yayan sa? To amma in tayi tunani duk wani da mai hakuri da biyayyah ya kan samu mafificiyar kauna a zuciyar iyayen shi. Idan Bello Makarfi bai tausasa mata ba, ina zata je ta a tausasa mata? Ina zata je ta ji dadin rayuwar ta? Bata da kowa, sai su sai Allah da ya halicce ta, ya dace tayi wa Makarfi uzuri akan wannan, in haka ne to meye hujjar ta na tsana da tsangwamar wannan baiwar Allah? Babu! Illa ita din mutum ce mai son kanta da yawa, mai biyewa sharrin shaidan da rudin zuciya, abinda Allah ya hore mata bai sa ta gode masa ta fuskanci abinda zai anfaneta ba, aah, ta wanzar da muhimmin lokacin ta wajen nuna tsana da kyara ga wata kankanuwar halittar Ubangiji da bata tare mata komi a rayuwa ba, ta biyewa sharrin kawaye da dukiyar da Allah ya hore mata, maimakon tayi aikin lada da su ko sadakatul jariyah, aah, sai ta bata su ga tsafe-tsafen banza, wanda aka ce gaskiyar mai shi ne domin a yau, babu ya wargaje! Ba abinda hakan ya kare su da shi, Allah ma kadai ya san irin farin cikin da Saratu da Saratu da Bello Makarfi suke ciki a yanzun. Ga dai gidan tana gani, ta sha wucewa ba sau daya ba ba sau biyu ba ta gabansa, amma ya gagareta shiga. Bai sake ta ba. Ta tabbata a zahiri ba kishi ko zafin ranta ne ya hanata komawa gidan ba, illa ita din ji ta ke ta kaskanta, ta wulakanta, hakannan bata da idon da zata dubesu, ko ma tace kwata-kwata ji take gidan yafi karfinta. (To tun a duniya kenan wata shariar, sai a lahira)! Shin ma anya ba hakkin su ne ya rikide ya dawo kan yayanta ba? Wannan soyayyah da Faisal da Ameenu ke wa Intisar, ta tabbata ba kadan ba ce, kwayar idanun su ya nuna, komai na jikin su ya nuna, ta tuna Almeen magana yake amma a zahiri fatar bakin shi ce kawai ke motsi, a sanda ya ke cewa zai daina sonta zai daina kaunarta, in har hakan zai sa ta yafe masa Wasu hawaye suka kara zubo mata, wannan shi ake kira nadama mara amfani. Inama ba tayi ba, inama bata aikata duk wannan ba! Wani bangare na zuciyarta ne ya tunatar da ita cewa ai akwai sauran lokaci, lokaci bai kure ba, da zaki gyara bayan ki, ki nemi gafarar kowannen su, dukkanninsu masu sanyi ne (musamman Alameen) tabbas zasu yafe miki, ba tare da wani jan rai ko bata lokaci ba, kuma hakika zasu yi farinciki dukkanin su, idan kika nemi afuwar Intisar din nasa zai yi farin ciki da hakan. Wannan tunanin ne ya dan sanyaya mata, ta mike domin dauko wayar ta, ba wanda tayi tunanin fara kira sai Almeen tana mai saka irin tausasan kalaman da zata yi amfani dasu wajen bashi hakuri, tare da tabbatar masa da amincewarta 100% kan bukatarsa. Kuma tace da shi a washagari yazo ya dauke ta ya maida ta dakin ta, ya danganata ga Intisar ta nemi gafararta ta sa mata albarka, ta nemi gafarar mijinta da abokiyar zamanta su koma zama na amana da aminci kamar yadda tun farko Saratu babba ke so su yi. A yayinda ta kai hannunta ga wayar, a yayin ne zuciyarta ta yi wani irin mummunan bugu irin wanda bata taba yi ba a rayuwar ta. Lokaci guda yawun bakinta ya tsinke, hakannan tsigar jikin ta ya tashi yarrr! Dai-dai sanda agogon dake makale a bango ya ke kada karfe biyu na rana, cikin daddadan sautin da yafi mata kama da wakar Bankwana! A Gidan Bello Makarfi Dawowarsa kenan daga sallar Jumaa da sassarfar shi, cikin takun sa mai karfi ya doshi sassansa, to amma tun safe yau haka yake sukuku ba kuzari. Aunty Saratu ta karaso ta amshi brief-case daga hannun shi da bakar suit da ya ratayo a kafadun shi, lokaci guda kuma tana loosing tie din shi tare da yi mai sannu da zuwa. Bai amsa ba hakannan dai ya wuce zuwa toilet, tayi zugudiii a falo da taguni da hannuwa bibbiyu, cike da tunanin me ke damun Daddy a yau ne? Daga can gefe wayar shi dake cikin aljihun suit din shi da ta aje ke ta tsuwwa, ta fiddota da nufin mika masa toilet amma ganin sunan mutumin da ke kiran ya dan kadata, Commissioner of Police Adams Stacy, kawai sai ta amsa ba tare da wani tunani ba. Ya fara ne da magana cikin nutsuwa cewa ta sada shi da Markarfi direct wato kai tsaye inda ita kuma ta nuna baya kusa, ya fada mata ko minene in ya fito zata fada masa, shi kuma ya dage kawai ta bashi Makarfi har ranta ya baci ta kashe wayar, ta cillata bisa kujera. A dai-dai lokacin daya fito daga toilet din, ba kuma tare da ya tambaye ta ita da wa take magana a waya ba kawai ya hau darduma ya zauna, can kuma ya mike ya fuskanci gabas ya tada sallah da ba zata ce azahar ce ko laasar ce ba, don kuwa dawowarshi kenan daga sallahr jumaa, kai da alama bama ya son magana kwata-kwata kuma baya cikin hayyacin sa, ta tambayi kanta ko rashin nutsuwar sa na da alaka da kiran da aka yi masa yanzun? Oho! A irin wadannan lokutan itama bata faya takura masa ba, baya-baya take da shi har zuwa lokacin da shi da kansa zai ware ya kulata, sai ta maida hankali bisa jera abinci bisa tebur. A sannan ne wayar ta cigaba da kara ba kakkautawa amma bata ko dube ta ba, ta tabbata mutumin dazu ne, ta tsani mutum mara yarda da kafiya. Sai da ya sallame sallar a lokacin wayar tayi burarin ta har ta gaji ta katse ta kama wani, ya mika hannu ya dauki wayar ya ce, Hello? Daga can bangaren mutumin ya ce, Your excellency, Stacy Adams ke magana daga ofishin yan sanda da ke Minna yace na gane ai, akwai lambar ka a waje na, ina fatan dai lafiya? Yayi dan jim, yayinda zuciyar Daddyn ta shiga harbawa da sauri da-sauri, ya tabbatar wannan shine sakamakon mugayen mafarke mafarken sa a dan tsukin, sai dai ya ambaci (Innalillahi) a zuciyar sa yafi sau talatin tun ma kafin ya ji mabbabin kiran. Yayi karfin hali ya ce ina sauraronka. Mutumin ya ce cikin tattausar murya Your edcellency, muna tare da gawar dan ka Dr. Alameen Bello Makarfi, ya yi mummunan accident akan hanyarsa ta zuwa Abuja daga Kaduna, wanda bincike ya nuna yafi minti talatin da sakin sityarin motar shi wanda hakan ya janyo hatsarin motoci fiye da goma akan titin, babu wanda ya tsira a cikinsu. So ku zo babban asibitin Minna ku karbe shi da kayayyakin da ke cikin motarsa da ke tare damu. Ina mai yi maka taaziyya, hakika rasa mutane irin su M.A.B, ba karamar asara ba ce, ba ga iyayen su kadai ba har ma ga alummar Nigeria bakidaya. Hawaye na kwarara daga idanunsa, irin wadanda bai taba zubarwa ba, har kuwa lokacin da aka yanke masa hukuncin daurin rai-da-rai da san da ya rasa iyayen sa! Ya ce, “Daga Allah muke, kuma gareshi zamu koma. Alameen Allah ya ji kan ka, ya sa mutuwar ta zamo hutu a gareka, ya baka Aljannar Firdausi madaukakiya, ya yafe maka kurakuranka, ya inganta aiyukan ka na kwarai, ya shafe zunubanka, ya sa ka zamo Da mai ceto ga iyayen sa.â€? Na yafe maka duniya da lahira. Ina rokon Allah yayi maka rahmah da gafara!. Wasu hawayen suka zubo, irin wadanda basa saukaka kunci da radadin mutuwar da a zuciyar mahaifansa! Balle da irin Alameen Bello! Ba iyayen sa kadai ba, duk ma wanda wata muamala ta taba hada shi da shi koda sau daya ne, dole ya girgiza da gushewar sa a doron kasa. A lokacin ne ye tuna wannan ba lokacin kuka bane, lokaci ne na karfafa zuciya, lokaci ne na nunawa Alameen din sa gata na karshe a rayuwarsa, wanda ba komi bane illa Addua da nema masa rahmar Ubangiji. Wani Imani ya zo masa. Ya yunkura ya mike ya doshi kofa ya manta babu ko kwakkwarar suttura a jikin sa. Aunty Saratu ta mike bata ko ganin abinda yake gabanta illa ta mika masa babbar riga da takalmi, suka fito harabar gidan a tare. Har zuwa sanda Daddy da mukarrabansa suka shiga mota suka bar gidan, bata ko motsa daga inda take tsaye ba, hakannan hawaye ko digo daya bai fito daga idanuwan ta ba. Ta kasa gasgata alamarin, ta kasa gaskata abinda kunnuwan ta suka jiyo mata, ta kasa amincewa da wai Alameen ya rasu! Ta dauki alamarin a matsayin irin mugayen mafarke mafarken nan da dan adam ke yi ya farka cikin dan lokaci. Allah kadai yasan tsawon awonnin da ta yi a tsaye a wajen tamkar sassakakken gunki ko gungumen itace. Har zuwa lokacin da motar da ke dauke da gawar Alameen tare da motocin da ke biye da ita suka cika harabar gidan. Ta daga ido taga wai yau Alameen ne ake fiddowa da sunan babu wata gaba dake motsi a jikinsa kuma babu numfashi. Abin mamaki, babu ko kwarzane a jikin sa, babu ko digon jinni a jikinsa tamkar mai barci kai baka ce accident yayi ba. Fuskarsa da a kullum ke cike da ilhama da cikar zati, tare da kwarjini na musamman a yau ma hakan ta ke, baya ga wani haske da annuri da ya kara tamkar a ce Alameen ya bude kyawawan idanuwan sa ya amsa. Ta dai tabbatar wannan zahiri ne ba mafarki ba ne sai ta yanke jiki ta fadi, yayin da jinni ya soma bin kafafunta ba kakkautawa. Babu ko tantama dan yaron cikin da take dauke da shi ne ya bi dan uwan sa nan take. How much do you like this story? 5/14/22, 09:27 - Ummi Tandama😇: ____________________________ *âœðŸ? SIRADIN RAYUWAâœðŸ?* Book four *@Takori* Page3ï¸âƒ£ Kamin wani dan lokaci labarin mutuwar Alameen Bello yayi tambari a cikin Abuja da wajenta ta kafofin yada labarai, haka gidan redion BBC tuni sun watsa labarin zuwa Jackson Memorial dake (Florida), da Meritime dake birnin Miami, haka sashen Hausa, redion Nigeria Kaduna, suma labarinsu a dan tsukin kenan. Kamin kace meye wannan gidan Bello Makarfi babu masaka tsinke balle dai-dai da isowar shugaban kasa da yan majalisar sa, gami da babban limamin masallacin Abuja wanda zai jagoranci sallar. Daya bayan daya samarin Brigedier ke isowa, wani ya samu sallar wani bai samu ba, (irin su Faisal da Najib da ke garuruwa masu nisa). Cikin wannan halin ne direbanta ya karaso da ita gidan cikin motarta (Volvos6) ko inda zasu tusa kan motar babu a layin, don haka tace da shi ya ajiye ta a nan farkon layin. Ta fito duk jikinta nade cikin laffaya koriya shar, idanuwan ta shabe-shabe da hawayen da ta ke jin har abada bazata daina zubar da su ba, illa a yau ta ji wani sabon imani ya shige ta, tsoron Allah da takwah ya karu a zuciyarta. Ta yi iya kokarinta don ganin hawayenta ko daya bai diga a kasa ba, kokari take wajen ganin ta maida su, Allah Sarki! Wai Aminun ta ya tafi, Aminun ta mai sonta, mai yi mata biyayyar da cikin yayanta kaf, babu mai yi mata kwatankwacin ta. Ya tafi, cike da bakin-cikinta na rashin kyautayi da tausayi a gareshi, ya tafi, cike da buri na karshe a rayuwarsa wanda bata taimaka masa ya cikashi ba, ya tafi, ba tare da samun wata daddadar kalma ko daya daga bakinta ba a lokacin da yake tsananin bukatar hakan. Ya tafi, yana mai rokonta wata alfarma wadda bai taba nema daga gareta ba. Dama ya ce rashin amincewarki na nufin alamura da dama ckin rayuwa ta. Da ma yace in kin so, zan iya murmurewa kamar ban taba yi ba, haka in kin so zai iya zama ajalina! Wasu hawayen suka shararo mata. A yau Aminun da take so fiye da kowa da komai a duniya, hada da rayuwarta kuwa, ya tafi, akan buri da soyayyar wadda ta ki jini, ta tsana ta ke kuma gaba da ita fiye da mutuwar ta. In haka ne ita dame tayi riba a kiyayyar da ta ke wa yarinyar? Ta na raye a doron kasa, za kuma tacigaba da rayuwarta tamkar kowa har zuwa lokacinda ita ma nata ajalin zai zo. Ashe duniyar ba komi ba ce? Ashe duniyar ba madawwama ba ce? Duk wata daukaka, soyayya, dukiya, ilmi, gami da gata basa hana mu komawa ga mai kowa mai komi? Ta ci burirrika da yawa a rayuwar ta a kan Alameen dinta, taci burin ganin jikokinta daga gareshi, ta ci burin ya mallake komi na Daddy Makarfi, ta ci burin ya biye mata su sake korar Saratu su gina kansu, su tsere ma saa, suyi wa kowa fintinkau. Bata so ya hada rayuwa da tsintacciya mara asali, bata so ya hada rayuwa da wadda ba kowa bace baa kuma san ko yar waye ba, bata so Saratu ta more shi, ba ta so Saratu ta rabe shi. To a yau ya tafi ya bar mata duniyar bakidaya. Cike da kuncin da soyayyarta ta uwa, bata yi kokarin yaye mishi ba. Cike da kucin da soyyar da take ikirarin yi mishi bata taimaka ba ko kankani wurin fidda shi daga halin ukubar da zuciyarshi ke ciki ba. Ta sa habar zaninta ta share hawaye da majina a tare, zuciyarta na suya da kuna, gangar jikinta na kaduwa. Ta russuna ta kai hannunta na dama ta yaye farin kyallen da yai mata shamaki da kyakkyawar fuskar sa. Fuskar shi fes, tamkar bai taba dandanar wani bakin ciki a rayuwarsa ba. Babu ko kwarzane a jikinsa. Karfin imanin da ya kara ratsata shi ya bata damar bude Alkurani mai tsarki ta shiga karanta masa tare da sauran yan uwansa da mahaifinsa. A lokacin Ado direba ya sauke Ihsan a gidan, ta soma dara mutane tana shigowa cikin falon, sai ta tsaya sororo idanuwan ta a kan Aminun ta, nannade cikin farin kyallen da idonta ke ganinshi bakkirin. Wata juwa da ta shiga kwasarta ta soma ganin mutanen sun zama bibbiyu uku-uku, har zuwa lokacin ta kasa gasgata abinda ake ankarar da ita. Hajiya ce ta mike ta kamo hannunta, ta mika mata wani bangare na Alkurani da a ke karantawa, a lokacin ne kowa ya lura da jinin daya yanke yake malala a kasa kamar da bakin kwarya, kana ta fada jikin makarar ta kankeme shi jikinta na wani irin kyarma ta ce yaya za kai min haka? Yaya zanyi da babyn ni kadai Alameen bayan kace tare za muke rainon sa? Yaya zanyi da rayuwar bayan na sha gaya maka in ka bar ni bazan kara rayuwa mai kyau ba? Bazan iya amfanawa kaina komi ba? Kai da kace min Kaduna zaka ka dawo, muje nemon auren Intisar din ka, na riga na gama yi muku shirin tafiya honey moon Miami! A cikin gidanmu na da Alameen yaya zakayi mana haka? A yayinne idnnuwanta suke shiga lunshewa da kansu, kamin ta bingire a jikin shi kamar mai barki. Babu wanda bata baiwa tausayi a wajen ba. Dr. Hajjo ce da Goggo Jummai suka kinkime ta suka sa a motan Hajjon suka yi asibiti da ita. Jinin da ke fita jikinta ya balain gigita Aunty Hajjo, rokon ta Allah, rokon ta kada Ihsan ciki gareta yake ficewa kaman Anti Saratu, don haka ta ke kwarara gudu kamar ta tashi sama bata damu da zagin da motocin da ke gabanta da bayanta ke aiko mata ba, yayinda Goggo Jummai ke rungume da ita a bayan motar zuwa National Hospital inda akayi admittin din Aunty Saratu. Yafiya ta uwa da uba, albarka ta uwa da uba tare da adduar neman Rahamar Ubangiji daga bakin da baya da kaico, bakin uwa, Alameen ya same shi daga bakin mahaifansa. Yo me yafi wannan dadi? Hajiya bata tashi tsinkewa gabadaya da alamarin Sarki Allah ba, sai da aka zo fita da Alameen dinta zuwa gidan sa na gaskiya. A nan ne ta ce bata san wannan ba. Ta ruga ta rike shi tamau da karfin da kowa ya tabbatar ba nata bane. Daga Najib, Yasir, Bello har Faisal, watsar dasu tayi bakidaya da sukayi kokarin rabata da makarar dake dauke da Alameen dinta. Ta shiga surutu wadanda kowa ya tabbata baa hankalinta take yin su ba. “Kana fitowa na dauki waya in gaya maka cewa na amince, kazo ka daukeni muje gaban mahaifin ka in nema maka aurenta. Shine ban samu layin ba. Na zauna da niyyar gobe in taho da kaina, sai kawai na ji a radio wai kayi hatsari. Don Allah ka dawo, wallahi da albarka ta da kake nema kaje ka auri Intisar. Na yarda, na kuma amince da abinda a da, naki amincewa da gan-gan cewa ita din yar baiwa ce, ba duk yayane irin ta ba, ba duk yaya ne Allah yayi wa nasibobin da yayi mata ba, ba duk yaya mata ne masu hakurin ta ba. Na yarda, na amince ta zamo uwar yayanka, na tabbata suma yayan zasu zamo nagari, kuma masu biyayya da yakanah tamkar ku. Ko asirin da nayi mata a baya, ba da son raina ne ba, illa Hajiya Suwaiba da ta tursasani wai in ba hakaba watarana akan ta Babanku zai rabu da ni. Yayana, zan daina jin diminku duk Saratu zata kwace ku da kinibibinta. Kuma ni bance ayi mata na mujiya ba cewa nayi kawai a farraka tsakaninta da ku da Daddy Makarfi Jin irin batutuwan da take na tozarta kai, wadanda tabbas bana mai cikakken hankali bane yayanta suka sake yunkuri cike da karfin zuciya suka bambareta daga jikin makarar aka fita da shi. Duk abinnan da ake, Daddy Makarfi, rike yake da tazbaha idanunshi babu ko digon hawaye, a sahun gaba, wurin raka Alameen gidanshi na gaskiya. Hakika mutuwar Alameen ta girgizasu, ta wargaza tunaninsu, ta takaita farin-cikinsu, ta azabtar da ruhinsu, ta dai-daita tunanin su, ta girgiza zuciyoyin su ta kuma nutsar da su ga kara kadaita Allah! A wani bangaren mutuwa ce wadda baa taba yi masu ba. Sun shiga yanayi na kewa, kunci da alhini irin wanda basu taba shiga a tarihin rayuwarsu ba, ninkin ba ninkin halin da suka shiga a sailin da aka kulle Daddyn su. Wai ance ba mutuwa ake wa kuka ba, sabo ne, to sun saba da Alameen. Yaya ne mai kyautayi da son jinin sa, da iya takun rayuwar shi. Mutun ne da ko hanya ce ta hadaku da shi a wuni daya, zaka so ka zauna da shi shekara daya. Idan zama ne na shekara ya hadaka da shi, zaka so cigaba da zama da shi muddin rayuwarka. Yana da dimbin kirki da dimbin alkhairi. Yana da tsananin kulawa kan abinda yake so musamman iyaye da yanuwan sa, yana kuma nuna hakan a fuska, aljihun sa da zuciyar sa. To balle kuma matar shi abokiyar rayuwar shi. Mutuwar Alameen sai ya zamanto tamkar wani girgijen gini na gidan ne ya fadi, ya ruguje. Walwala ta karanta haka zuciyoyi sun azabtu, babu mai iya yiwa dan uwan sa taaziyyah sai kallon-kallo. Ba abinda kunnuwan su suka tsana da ji kamar wani ya ce da su, “Ya hakuri?â€? Allah ya sani, da ka ce musu wannan gara kawai ka ce, “Allah Ya Ji kan sa!â€? Anan ne za ka ga wasu hawayen kauna sun zubo. Irin kaunar nan da har abada, bazata taba gushewa ba. Makarfi yaga kauna daga alummar Nigeria da wajenta kwarai da gaske. Daga shugaban kasa zuwa gwamnonin jihohinsa duka, kusoshi na mulkin soja zuwa na farar hula, likitocin Florida musamman daga birnin Miami da duk wani sako ko loko da Alameen yayi karatu ko wani aiki na wucin gadi sun barko domin jajanta masa wannan babban gibi da yayi a rayuwarsa, da cike shi abu ne da har abada ba zai yiwu ba! Yaya goma suka saura masa amma ji yake a yanzun kam bashi da ko daya a duniya. Ko dama can kaunar Alameen daban ce data kowa a zuciyarsa, baya hada son da yake masa da na kowa cikin yayansa. Yana son shi, ya na kaunar shi tun yana tsumman goyon sa, ta yadda har yake kiran sa BURI NA. Sai dai har kullum yana mai farin-ciki da irin mutuwar da Alameen yayi; ranar Jumaa, cikin watan Ramadhan, da azumi a bakin sa.Wani irin hatsari amma kamar Baben dake goye a bayan mamarsa. Albarka ta uwa da uba. Kykkyawar shaida daga duk wanda ke tare da shi. Dr Rehab gurfane yayi gaban shi yana kuka da hawayensa marassa launi yana cewa Na dade ban samu mutun mai kyakkyawar zuciya irin M.A.B (Mohammed Alameen Bello) ba! Na dade ban ga Musulmin da ya san shi Musulmi ne a turai irin M.A.B ba, na dade ban ga mutumin da ke tara halal batare da digon haram a ciki irin M.A.B ba, na dade banga mutum mai alkhairi da duk abinda ya mallaka a duniya irin M.A.B ba, ban taba samun aboki nagari mai amana kwatankwacin sa ba. Hakika kun yi rashi babba, amma wannan ba rashin ku bane ku kadai na alummah ne. Nafi kowa sanin dimbin alherinsa. Tabbas shi ya tafi, amma aiyukan sa na alkhairi ba zasu taba yankewa ba! Hajiya kam, daga baya saida aka dangana ga psychiatric Hospital na Kaduna da ita, domin a cewa gamu da abinda suka kira mental disorder. Iyaka kokari likitan Alameen wato Dr. Alfred yayi wajen ganin cikin wata ukku da wasu yan kwanaki da Ihsan ke tare da shi bai zube ba. Amma na Anti Saratu ya fita, sai dai fatan Allah ya bada musanye da alheri. Kwanan Ihsan goma kwance a gadon asibiti bata san wanda ke kanta ba. An yi mata karin jinni fiye da leda uku hakannan karin ruwa baya yankewa. A binciken kwararren likita Alfred ta gamu da ciwon hawan jinni. Don haka suka cigaba da rikonta a asibitin yayinda suka sallami Aunty Saratu tun a ranar sadakar bakwai, kuma a ranar ne Haj. Hadiza da Ambasada Bashir da diyarsu Zarah da ta zama buleliya jazur da ita suka sauka a birnin Ikko inda daga nan suka biyo jirgi zuwa Abuja cikin tsananin dimauta da gigicewa, suna masu mika taaziyya mai girma ga Bello Makarfi. Sai ya ce mu gode masa, mu godewa Allah, Allah na gode maka! Hakikah karfin imani irin na wannan bawan Allah na baiwa kowa mamaki. Shukrah yake tare da hamdalah ga Allah a koyaushe akayi masa taaziyyar gudan jinin sa Ameenu. Ya kama hannun Ambassada yana murmushi ya ce, Basheer? Don me ba zan gode masa ba? Sanda ya halicceni nikadai ya halitta, ban san kowa ba, bansan komi ba. A hankali ya koyar da ni in mike in taka kafafuna a doron kasa. Ya bani ikon yin aure, na haife su, amma ba nawa bane, amana ce ya danka mini ya ce in kula masa da su zuwa lokacin da zai karbi abinsa. A duk tsawon lokacin nan daga niimarsa nake ci, nake sha, nake numfashi, na ke neman abinda zan kula da su. In ciyar dasu in tufatar dasu. Yayi min falala da niima daga duk wani jin dadi na rayuwa. Babban niimarsa gareni shine yayo ni Musulmi, yayi nufin karbe Alameen daga gareni domin ya jarraba imani na, yaga cewa shin ni mai godiya ne ga dimbin rahmominsa da fadhalolinsa a gareni ko ko zan butulce? Sabida wannan jarrabawa kankanuwa da ya yi mini? Don haka har kullum nake gode masa, na tabbata ban fi shi son Alameen ba, kauna ta da shi shine in yi masa addua, na nema masa Rahman Allah, kuma ina rokonku ku taya ni nema masa gafara domin hakikah yana daga cikin nagartattun yaya masu shiga zuciyar iyayen su! Satin su daya a Nigeria suke juya kasar Korea, Aunty Saratu ta gargade su ta kuma gargadi kowa da kada a sake Intisar ta ji wannan labari, wadda a lokacin take zana jarrabawarta ta karshe a secondary. Gargadinta yafi zafi a kan Hidayah, wadda ke tare da mijinta a nan Nigeria tare da su. Ita Hunainah dama tana Jamiar Al-Azhar da ke Cairo inda take karanta physiothearaphy. Suma kan su, sun tabbatar babu mai iya dosar ta da wannan labari illa tazo ta gani da idanun ta, taji abinda kowa ya ji, koda yake ita din mai jin fiye da abinda kowa ya ji ne! Ranar kwanaki na arbain da rasuwar Alameen an yi adduoi na musanman da sadaka mara iyaka, a yayin ne kafafuwa suka fara daukewa, sai su isu, wayyo! Ashe wanda ya mutu shine ya mutu, rayuwar sai wanda ke raye? Jarrabawa ta karshe da ta zana ta kama ranar litinin. Bata farin ciki ba kuma ta bakin ciki duk da cewa kusan rabin burinta na rayuwa, ya cika, ta kuma ji tamkar an dauke mata wani nannauyan dutse ne aka.Ba don komi ba sai don tsananin damuwar rashin sanin makomar rayuwar ta a inda ta adana zuciyarta, wato rashin sanin hakikanin abinda Alameen ke ciki. Kwanaki sun shude sun zama satittika, satittika sun shude sun zama watanni bata kara ji daga Alameen ba. Ta dauki laifi duka ta azawa kanta, tare da kalubalantar baudaddiyar zuciyarta. Eh, ta kirayi zuciyarta baudaddiya domin raayin rikau irin nata shi ke zalintar ta a koyaushe. Juriyarta yayi yawa har ya zama cutar kai, ta tabbata in har bata yafewa zuciyarta ba, zasu yi hisabi da ita. Bata taba mallaka mata abinda take so ba! A kullum tana mai kalubalantar kaza saboda kaza, tana kin kaza saboda kaza, tana cewa aah a inda ya kamata tace eh. Ba ta laakari da uzrin kowa sai nata. Bata karbar uzrin kowa sai wanda zuciyarta ta yanke. Ta manta cewa kaza kan halatta kaza a inda babu kaza. To yanzu idan Alamin yayi fushi ne ya yakice ta azuciyar sa, ko kuma Hajiyar ta ja raayinsa ya fita harkarta ina zata tsoma rayuwarta? Yaya zata yi da wannan mikin da ke narke a zuciyar ta da har yau bata sami damar amayar da ko rabin-rabin sa ba ga wanda yake ciwon domin sa? Yaya za tayi da kuncin da zuciyarta ke ciki na nadama da dana sanin hukuncin da ta yanke masa? Burin ta kawai a lokacin ta koma gida, ta neme shi ta bashi hakuri, ta gaya masa ta fi shi azabtuwa da hukuncin ta, ta fi shi shiga tashin hankali akan hukuncin ta, wannan karatun da ta yi duk a cikin karfin hali ne amma second, minti ko awa tunanin shi ne a zuciyarta, tunanin halin da yake ciki ke nukurkusar ta illa ita din mai juriya da zurifin-ciki ne. Ta amince a yi masu aure koda Hajiya zata ke yankar naman jikinta sala-sala kullum ta Allah ne har sai ta karar da ita, in har suna tare, ba zata ji zafin hakan ba, kai in ta kama ta je ta kama kafar Hajiyar ta roketa ne zata yi, ta nema mata gurbi da zata raba rayuwar ta cikin inuwar muhimmiyar zuciya irin ta dan ta Alameen. Haka kawai ta ji hawaye sun zubo mata, ta daga kai ta dubi dakin barcin su da ke cikin makaranta Kingston College, dalibai yan uwanta ke ta hada kayansu cike da farin-cikin tafiya gida a washegari. Zaune take kurum a gefen gado tayi tagumi ta zubawa tickets din ta ido, wadanda a kayi mata booking daga Riyadh zuwa kasar Korea ta Kudu. Ba komi take tunani ba illa a yau kam zata sabawa Daddy, bazata iya tafiya wajen mahaifiyar tata ba, ba ta je ta ga me yayi mata katanga da Alameen ba! Bata je taga halin da Daddyn ke ciki ba, wanda rabon da su neme ta an fi karfin wata uku, kai ba Daddy kadai ba, hatta Hidayah da Hunainah ba wanda ya kara yi mata waya, ba wanda ya aiko mata da ko sakon best-wishes akan jarrabawar ta, wanda ba haka ne tsarin rayuwar yaran ba; duk wani abu na farin ciki ko na fatar alkhairi su kan taya junan su. Ta duba inbox din ta na e-mail ba bu sakon kowa sai na kawayenta yan sauran kasashe. Duk wayar da ta kira cikin danginta hagu da daman is not available me hakan ke nufi? A karo na farko tun bayan rabuwarsu a dakinta, ranar da ta zamo rana ta karshe da bata sake ganin shi ba, illa wannan murmushin da yayi mata irin wanda bai taba yi ba, kuma wanda har abada ba zai goge daga zuciyarta ba. Ta shiga lallatsa nambobinsa tare da tambayar kanta to in ma kin sameshi me zaki ce da shi? Alameen don me ka gujeni ko don me baka nemana? Don ka daina so na ko don na kasance azzaluma a cikin soyayya? Kamar kullum yau ma an ce da ita is not available. Ba ta hakura ba dai, ta budo dan guntun templete text kamar haka long time no see ta aika masa. Fiye da awa daya, bai dawo mata da (reply) ba. Ta kifa kanta cikin cinyoyin ta cikin yanayi na tashin hankali da matsananciyar faduwar gaba. A karo na biyu ta kara kokarin kiran layin Ambassada wannan karon ta samu ta shiga cikin saa, bugun farko ya amsa inda ya shiga bata hakurin rashin nemanta da baa yi yace alamura sun cudewa kowa, kuma suma sun yi tafiya sai kwanan baya suka dawo. Mamarta kuna bata da lafiya laulayin ciki ke wahalar da ita shi yasa ta rufe waya. Ta bukaci tana so ne a canza mata booking zuwa Nigeria. Ya ce maiyasa kike son maida hannun agogo baya? Ya an gama komi tahowa kawai ya rage ki ce a canza, kuma Daddy zai yi fada tunda shi ya ce ki zo ki zauna da mahaifiyar ki, har sai yace ki dawo da kansa. Sai ta saka masa kuka mai karya zuciya, ta ce don Allah Abban Hunainah ka taimake ni, ka yi min rai hankali na yayi gida, in ya so idan na je na ga Daddy sai in dawo koda kwana daya ne, ni dai hakannan na ke jin babu dadi, kuma hankali na ba zai taba kwanciya ba muddin ban je naga halin da Daddy ke ciki ba. Ka taimake ni kayi wa Daddy bayani yadda ba zai ce na ki jin maganarsa ba. Ni dai ji na ke a jiki na Daddy bashi da lafiya. Ya ji idanuwan sa sun ciko da kwallah amma yayi kokarin maida su. Ya ce alright, Saratu, zan kira Daddyn yanzu muyi maganar, in ya ce ki taho zan kira air-port din yanzu. Amma ki kwantar da hankalin ki Daddynki lafiyar shi kalau ko jiya mun yi hira da shi. Ta yi ajiyar zuciya mai karfi. Bayan kamar awa daya ya sake kiran ta, ya ce shikenan sai gida gobe Insha Allah, Daddyn ya ce da kanshi zai je air-port taryen ki. Sai ta yi murmushi. How much do you like this story? 5/14/22, 09:27 - Ummi Tandama😇: ____________________________ *âœðŸ? SIRADIN RAYUWAâœðŸ?* Book four *@Takori* Page4ï¸âƒ£ Hakan kuwa a kayi, ta fito daga jirgin MEA International sanye da doguwar riga kirar Oman, ta yane kanta da kankanin mayafin panorama kalar baki da ratsin toka-toka, yayinda abnormal idanuwanta ke saye cikin farin medicated din ta mai kama da gidan biro sabida sirinta. Kafar ta bakin takalmi ne mai tsayi sosai kuma mai tsari da ban shaawa, babu wani make-up a tare da kasaitacciyar fuskar ta, sai wannan kyawun ziryan mara algus da kyale-kyalen zamani Ta na rataye da matsakaiciyar jakar hannu, siraran labbanta dauke da murmushi kayatacce ga Daddynta data fara yin tozali da shi. Ranta yayi dadi da ganin wannan taron dangi da aka yi dominta. Ga dai shakikiyarta Hidayah rike da hannun mijinta Najibullahi, ga Antin ta, ga Aunty Ihsan, ga Bello, Nasir, Yasir, Idris, Furkan da Khalil uwa-uba babban Yaya Faisal Bello Makarfi. To amma duk wannan gayya ta hanga, ta duba bata hango zahran cikin taurarin ba, ba ta hango haske maganin duhun zuciyar ta ba (bata hango Alameen din ta ba). Duk da haka ta daure, ko a fuska bata nuna ba, tabi kowa da runguma, amma data zo kan Ihsan sai da ta dan dakata kadan kamar mai nazarin wani abu, kana ta daure ta rungumeta itama, sai ta ji wani abu mai tsini ya tokare ta wanda babu ko tantama ciki ne mai girma sosai. Ji tayi wani abu yazo ya tokare a makoshin ta. A yau kam ta samu kanta tana mai kishin Ihsan fiye da koyaushe a rayuwar ta. Ko kamin ta iso kan Faisal shi har yayi gaba ya bude mota ya shiga yana jiran su, daman shi ya yi driving dinsu cikin babbar mota Jeep baka mai tudu da tsayi. Hannunta cikin na Daddynta, hakannan kujera daya suka zauna. Sai a lokacin ta lura da muguwar ramar da kowannen su yayi, ba kuma wanda ya yarda ya kara hada ido da ita, kai ba ma wannan ya dame ta ba kamar muguwar hararar da Faisal ke jefa mata a duk sanda su kai kuskuren hada idanu ta cikin mudubin motar. Karewa ma babu mai yin ko kwakkwaran motsi a motar tamkar ruwa ya cinye su. Tun tana kai zuciya nesa tana tausar zuciyar ta da cewa ai koma meye tunda gani a gidan zan ji ne har ta kasa controlling tashin hankalin ta kawai sai ta fashe da kuka, cikin siririyar muryar ta mai tsuma zuciya tace ku sauke ni, ku sauke ni a titin nan tunda duk bakin-ciki kuke da dawowa ta, zan koma inda na fito. Daddy ya yi murmushi ya kama hannunta na dama yace, “Waye mai bakin-ciki da dawowar ki Saratu, gayamin sunan shi yanzu in sauke shi, ya nemi wani uban daban amma ba naki ba, umh waye shi Intisar gaya mun ki gani in baa sauke shi ba?â€? Ita dai bata bar kukanta ba, haka Ihsan da Hidayah kuka suke cikin mayafansu, kuka mara amo bare sauti sai radadi a zuci. Koda suka iso gida ma bata sake zani ba, kowa yayi nasa waje, Faisal ya wuce da Daddy office Najib da Hidayah sun wuce gidansu a Maitama, Ihsan ma ta wuce dakinda aka ware mata, inda anan ne take zanan takaba da rainon cikinta don Daddy yace bazata rabu da su ba har sai ta haihu, dan ta ko yar ta yayi wayo daga nan tana da zabi a rayuwar ta. Mahaifinta ya amince da hakan amma Ann cewa tayi wahala ce bata ishe ta ba. Dawowar Intisar gidan sai ya zama tamkar wani fami ne bisa ciwon da ya fara samun sauki ga kowa a gidan. Wai Antin ta mai tarairayar ta da rasa ina taka saka ina-taka aje da ita a duk lokacin da ta dawo hutu, ita ce yau mai kakalo aiki don kawai kada ta zauna da ita ko na minti daya ne a dakin, kai daga karshe ma da taga kukan da Intisar din ta soma na neman karya mata zuciya itama ta fashe da kukan duk irin kokarin ta kuwa, sai ta gudu sassan Daddy Intisar din bata kara ko jin duriyar ta ba. Aah, wai me ke shirin faruwa ne? Ta kasa baiwa kanta amsa, me ya kawo Ihsan gidan har daki aka ware mata cikin sassan Anti, ina Alameen? Sai a lokacin ne ta daga idanunta cikin gilashinta, ta kai duba ga katon hoton shi window-size da ke makale a falon tun kamin ta tafi, babu hoton an dauke shi. Ta sunkuyar da kai, haka kawai ta ji mummunar faduwar gaba ta same ta, jinni ya daskare daga gudun da yake yi cikin jikin ta. Kada Allah yasa abinda zuciyarta ta sinsina ya tabbata. Kada Allah ya sa a ce da ita a yau babu Alameen. Ka da Allah ya nuna mata wannan ranar! Ta kai hannu ta share kwarmin idanunta a dai-dai lokacin da Khaleel ya shigo, daga bakin kofa ya sanar da ita Daddy na kiranta, ba kuma tare daya kara ce da ita komi ba ya juya ya fita. Ta mike cikin rashin kuzari, tamkar kazar da kwai ya fashewa a ciki ta doshi main falon su. Kowa na zaune, da yawa kansu a sunkuye, kadan ne suka dube ta. Ta yi mamakin duk wannan taron da a kayi mata na menene? Ta kai dubanta ga Mamarta, domin neman Karin bayani, amma kamar dazu tayi ignoring hada ido da ita. Daddy ya mike da kan sa har inda take ya kamo hannunta, ya zaunar da ita a gefen sa. Ya ce mu karanta salati goma sha daya ga Annabi (S.A.W), mu karanta kulhuwallahu kafa (3) zuwa makwancin sa, mu kara godiya ga Allah da yayo mu Musulmi maabota Imani da yadda da Kaddara. Bayan sun shafa ya dubi Intisar da tashin hankali ke zane baro-baro bisa kyakkyawar fuskar ta tamkar ta daura hannu a ka ta ce wayyo Allah! Ya dubeta da sassamyan duba mai sa nutsuwa ga dan adam ya ce, “Saratu!â€? Ta dago ta dube shi da dukkan idanu amma bata amsa ba, idanunta fiki-fiki a warwaje. Ya yi murmushi yace zaki iya gaya mun me da me Ubangiji Allah yayi miki a rayuwarki, kama daga lokacin haihuwar ki zuwa yau da kika dawo? Ta shiga girgiza kai da sauri, hawayen ta na zuba bisa cinyar ta ta ce, “Aah! Ba zan iya ba, domin baiwar sa da fadhalolin sa masu yawa ne a gareni. I can’t express his infinite mercy! An yar da ni a daji amma bai bar ni na tozarta anan ba, bai ba wani mugu iko a kaina ba. Ya hada ni da uba nagari, mai so na da kauna ta tare da jin ciwo na kamar, ko ma fiye da uban da ya haife ni. Ya bani wata irin uwa, mai kyautayi da alheri, wadda a kullun burin ta shine farin-ciki na. Bakin-cikin ta shine bacin rai na. Ya bani yan uwa ba jinni na ba, amma masu jin kai da matukar kyautayi a gare ni. Ya yi mun rai, lafiya, ji da ganin da bai raba ni da shi kwata-kwata ba. Ya kuma bani lafiyayyun kafafun da na ke takawa da su a doron kasa in nemi Ilmi..ya yi mun komi.. ya yi min kowa, I can’t explain his abundant blessings, ai abubuwanda ya yi min baiwarwaki dasu ba zasu fadu ba.â€? Ta yi shiru cikin sheshshekar kuka da Imani da ya kara ratsata. Ya girgiza kai cike da gamsuwa da kalamunta ya ce, “To a yau idan aka ce Allah ya jarrabce ki da wani bacin rai, domin jarraba imanin ki da godiyar ki gare shi bisa wadannan niimomi da ya yi miki, ta hanyar dauke abinda kika fi so a duniya me zaki yi? Ya ya zaki karbi alamarin kuma me zaki ce da shi?â€? Cikin yankewar burin duniya bakidaya, kuma cikin matsananciyar kauna da bege ta ce, “Sai in yi tawakkali in gode masa! Hakan ba zai sa in fita daga Imani na ba. Ba tun yau nake haduwa da jarrobawoyinsa ba, ba kuma wadda na taba faduwa. Duk wadda yayi min in nayi hakuri daga baya alherin sa na ke gani. Ya ce madallah da wanda zuciyar sa ta kasance maabociyar bakin ciki guda daya. Abinda ya gani da idanunsa, ko ya ji da kunnuwansa (na wannan bakin-cikin) bai shagaltar da zuciyar sa daga rahmomin Ubangiji a gare shi ba. Intisar, Alameen ya amsa kiran mahaliccinsa, ya tafi ya barmu da kewa da ciwon rashin sa, ya bar mana gibin da mun tabbatar cike shi abu ne da bazai taba yiwuwa a gidan nan ba, kamar yadda mance shi ko shafe tunaninsa, wani abu ne da ba zamu taba iyawa ba!. Ta runtse idanuwanta da karfin gaske, runtsewa irin wadda bata taba yi masu ba, yayinda wasu hawayen suka kwararo da gudun gaske daga kyawawan abnormal idanun ta. To haka kowa a wajen kifa kai yayi a inda yake zaune ya shiga fidda nasa hawayen da ya dode bai fitar ba. Suna jiran wannan ranar. Ranar da zaa gayawa Inteesar Alameen ya rasu! Su kam basu ji dadin hukuncin Daddy ba da yace kar a daukota tun a wancan lokacin gashi yanzu ta dawo masu da mutuwar danya shakaf. Abinda ya riga ya faru watanni uku da suka gabata. Jikinta ne ya kama kaduwa, ta soma rawar dari duk kuwa da zafin da ake a lokacin. Kafin wani dan lokaci zazzafan zazzabi ya rufeta haka gabobin jikinta babu inda bai girgiza haka hakoranta ba wanda bai haduwa da dan uwansa ji kake kaf-kaf-kaf. Ta mike da gudu ta je ta rungume Mamar ta. A sannan ne ta samu damar yin kuka mai sauti. Kuka mai girgiza zuciya, kuka irin wanda bata taba yi ba a tsayin rayuwarta. Kuka na rasa abu mafi muhimmanci kuma mafi soyuwa ga rayuwarka. Kuka na nadama da da na sani mara amfani! Bata tabayin da na sani a rayuwar ta ba sai yau!! Bata taba tsanar kanta a duniya ba sai yau. Ba abinda ta ke tunawa illa irin rabuwar da suka yi da Alameen din ta. Ashe dama rabuwar kenan? Wannan murmushin, wannan, wannan hawayen nasa da dariyar da suka yi duk na bankwana ne, Allah Sarki! Ta tashi daga jikin Maman ta rarrafa ga Daddy, ta kama kafarsa cikin raunanniyar murya ta ce, “Kada ka taba yafe mun Daddy. Domin ni ce silar shigar Alameen cikin halin kuncin da ya shiga. Ai na gaya maka hukuncin yayi masa tsauri bazai iya cikashi ba. Da nasan hakan ne zai kawo ajalin sa, wallahi dana amince masa koda bata amince ba, ko da hakan zai zamo karshen abinda zanyi a rayuwa ta, koda zata haka rami ta bizne ni ne da raina. Nayi kuskuren hukunta soyayyarshi gareni a matsayin laifin da ba nashi ba! Na kasance azzaluma ga dimbin soyayyar da yake mini. Ban yi maka adalci ba ko kadan Daddy domin da da halacci, da duk wani jinin ka ma yafi karfin yarjejeniya a gareni. Da ni din mai halarci ce da ko kare ka haifa kace in aura, zan yarda ba tare da wani ja-in-ja ba. Balle shi mai kirki ne, kyautayi da soyayyah irin wadda ban taba gani ba. Yayi kokarin inganta rayuwata ta hanyoyi da dama, ta duk hanyar da ya san zai bi ya fidda ni daga halin da yazo ya sameni a ciki; da yawun bakinsa, da aljihunsa, da zuciyarsa da komi daya mallaka! Amma sakamakon sa, wani hukunci tsatstsaura, da nake da yakinin ba zai taba yiwuwa ba! Ba zai taba samo shi gare ni ba. Ban maida martanin soyayyata gareshi ba koda kashi talatin cikin dari (30%) na dimbin soyayyar dake tattare da ni. Maimakon haka, sai nayi amfani da matsananciyar soyayyar da yake yi min wurin hukunta shi da laifin da ba nashi ba…â€? Ta ci gaba da rera kuka mai matukar motsa zuciyar duk wani mai sauraron ta. Ita ba mutuwar Alameen tafi daga mata hankali ba, kamar irin rabuwar da suka yi, da kin amincewar ta da auren su, bayan ba haka bane zahiri a zuciyar ta. Ba don komi ba sai don sanin cewa irin su basu da kaico, mutuwa ba komi bace face hutu a gare su, halayen sa da dabiunsa duka masu kyau ne, tsarin rayuwar shi da muamalar shi da kowa mai kyau ce. Duk wanda ya san shi idan ya budi baki alkhairi zai fada a kan sa. Bata taba ganin mutum mai kirki da jin kai irin Alameen ba, don haka bata kokamawa mutuwar sa, sai rashin soyayyar sa, da rashin maida martanin tata soyayyar a gare shi, kuma a ganinta ta zalince shi, har abada Daddyn ba zai yafe mata ba. Tunda duk kawaici irin nasa, sai da ya zaunar da ita ya nuna mata kwadayin sa a fili kan son ta da auren Alameen, shin Daddyn da Aminun sun cancanci hukuncin da ta yanke masu? Wanda ya zamo karshen rayuwar Alameen din ta? Ta sunkuyar da kai cikin matsanancin tashin hankali, ji take har abada bazata kuma iya hada ido da Daddyn ba. Daddy Makarfi sai ya yi murmushi. Ya sa hannu ya dago ta daga durkuson da ta yi na mai neman gafara, kamar koyaushe ya aza ta a gefen shi ya ce, “A kan me zan ki yafe miki? Me kika yi mun? Ki daina cewa kin zalinceshi domin baki da hakkinshi. In ma da wanda ya zalinceshi to uwar da ta haifeshi ne. Ya tafi ne cike da kewa da begen ki. Ya tafi ne a bisa kudirinsa na son ki da kaunarki, a bisa son ki da ke neman tagayyara shi da tarin kaunarki daya illata zuciyar sa. Ki bar ganin kan ki a matsayin mai laifi illa masoyiya tagari, mai son fidda masoyinta daga kuncin da fushin uwa ka iya jefashi a rayuwarshi.. Albarkar Allah ta tabbata a gare ki. A wannan daren mai cike da sauyin sabbin alamura da dama cikin rayuwarta, ta kasa runtsawa, hakannan ta kasa tsaida hawayenta kamar yadda ta kasa yiwa Alameen addua. Har yanzu ta kasa daina ganin kanta a matsayin azzuluma a gare shi. Ta ma kasa gasgata alamarin kwata-kwata. Ta dauki komi as an optical illusion, Delusionâ€? Wai Alameen din ta? Ya rasu! Duk burin da suka ci wa rayuwar su, duk farin-cikin da take hangowa rayuwar aurensu ya zama tarihi? Shi kansa Alameen din wai a yau ya zama sai tashin zance? Ba zata kara jin daddadar muryarshi da ke gigita ta ba, sai a mafarki! Ba zata kara jin daddadan kamshinsa da duk duniya bata taba jin mai irin sa ba. Wannan korafin da ban dariyar sa, ba zata kara jin ko daya ba cikin kiran “Halima dube ni!â€? Wasu hawayen suka kara shararowa a kundukukinta zuwa cikin kunnuwanta, kasancewar a kwance ta ke rigingine bisa niimtaccen gadonta, tana mai tuna ranar da suka rabu a dakin, yana durkushe a gabanta yana kukan da bata son tunawa, domin ta yarda kawai da dimbin soyayyar shi gareta. Ta yarda shi din ba zai iya rayuwa ba tare da ita ba. Ta kai tunaninta ga alamuran ubangiji masu juyawa tamkar tayar mota ko gare-gare abin wasan yara. Ita kan ta rayuwar haka take; yau fari gobe baki. Ta na tunanin shin wace rana ne zuciyarta zata huta da bakin ciki a duniya? Wane lokaci ne zata samu dawwamammen farin-ciki a rayuwar ta? Wace rana ce zata tsallake SIRADIN RAYUWAR ta? Tamkar kuma wadda aka tsikara da allura sai ta mike ta doshi kofa. Karfe ukku na sulusin dare. Ta sanya takalminta ta dauki filo da gilashinta, kana ta yane kanta da yalwataccen mayafi, ta dauki tocilan tana haskawa, kasancewar an kashe dukkan fitilun gidan sai na cikin dakunan barci, ta doshi hanyar sassan Hajiya. Daga nan kuma ta nemi hanyar kitchen din ta. Ta murda kofa ta kunna fitila, komi yana nan yadda yake, illa kura da koina yayi. Ta koma dakin su da Dela wadda tuni ta dade da barin gidan, tun dawowar Antin ta sallameta. Tabarmar ta da Hajiya ta bata na nan a bayan kofa, ta fiddota ta karkade ta dawo kitchen din ta. Ta shimfida a inda ta saba ta daura filon, ka na ta kwanta. Sai ta ji wani sanyi ya sauka a zuciyar ta. Filla-filla tana mai tariyo rayuwarta da Alameen ta dan lokaci a cikin kitchen, wadda tafi tsayin shekaru a idanunta. Kalaman sa masu dadi da sanyaya zuciya na dawo mata tar-tar a sharp kwakwalwar ta, haka hoton kyakkyawar fuskarsa garai-garai a idanunta. Ta san idan ta ce ma ta yi barci a wannan daren, to karya ne. Ta kuma yaudari kanta. 5/14/22, 09:27 - Ummi Tandama😇: ______________________________ *âœðŸ? SIRADIN RAYUWAâœðŸ?* Book four *@Takori* Page5ï¸âƒ£ Bayan Watanni Biyu Dr. Rehab Mohammed, aboki nagari kuma amini na kwarai ga marigayi Dr. Alameen Bello, ya iso kasar Nigeria a safiyar wata litinin, tuni dama Daddyn ya san da zuwansa, don haka ya tura Yasir ya taho dashi da ga air-port. Ya samu Daddyn a ofis ne inda suka kara yiwa juna taaziyya. Ya shiga fidda takardu da file-file yana yiwa Daddyn bayanin su dalla-dalla, kama daga takardun gidan marigayin da ke Miami da wani fili daya saya ya fara gini a Florida, shares din shi (hannun jari) na bankuna, takardun asibitin shi Meritime na kwakwalwa da suke kokarin rufewa, zuwa takardu na kananan kadarori kamar bungalows guda biyu daya saya a Vienna, da dakin shan magani cikin meritime da wasu kudade da yake bin Baptist Health Care dake Miami. Akwai kuma kudi na musamman da suka tasamma naira miliyon goma da su abokanen aikinsa suka bawa iyalinshi sadakah, ba don komi ba sai don dinbin alherinshi da taimakon da yayi masu a rayuwar shi tare da su wanda a cewar su har abada bazasu manta ba. Daddy ya amsa ya yi mishi godiya mai tarin yawa, yace amma kafin ya tafi, ya jira ya yi shawara da matar shi tunda mahaifiyar shi bata da lafiya. An zauna da Ihsan a ranar wadda kanta ke sunkuye cikin abaya. Daddy ya shaida mata abinda kenan ya kuma danka mata komi na Alameen ya ce ya bar mata duniya da lahira ita da abinda zata Haifa, illa kason mahaifiyar shi da za a cire. Ihsan na hawaye tace ta amsa, amma itama ta barwa abinda zata haifan, bata son komi na Alameen domin bata taba tunanin ta ci gadon Alameen ba. Burin ta har kullum shine shi ya bizne ta. Don haka in an cire na Hajiyar Daddy ya cigaba da kulawa da jikarsa ko jikansa dukiyarshi a hannunshi. Alfarma daya take nema su yi mata shine Rehab yayi kokarin maido Meritime cikin Nigeria kamar yadda Alameen ya dade da wannan burin kuma har ya mutu da burin a zuciyar shi. Tace ya riga ya nemi iznin assasa asibitin daga federal ministry of health tun dawowar su, takardun komi suna nan a gidan su, tuni ginin yayi nisa, haka ko bayan rasuwar shi maaikatan basu daina ba, domin ya riga ya biya su kudin su. Tana so Rehab ya taimaka mata ya cigaba da jagorantar asibitin koda yana can Miami ne. Akwai karatu da zata karo na tsawon shekaru ukku kacal idan ta dawo zata cigaba da jagorantar Asibitin kamar yadda Alameen ke son yayi Allah bai bashi iko ba. Abinda zata haifa tana da burin in mace ne ko namiji? To zai yi karatu irin na Baban sa, ya jagoraci Meritime, tana fatan ko bayan ran ta Daddy ya taimaka mata wajen cikar barin ta, wanda Alameen ya dade da yiwa rayuwar sa amma rayuwar tayi mishi gaggawa. Rehab ya daga ido ta cikin farin mudubin idon sa ya dubeta. Yayi mamakin yadda cikin bakar fata aka samu irin wannan soyayya ta tsakani da Allah tsakanin mace da mijinta tamkar a kasar haihuwarshi (India). A da, ya dauki matan bakar fata a matsayin masu kwadayi da son abin duniya kadai; basu san mecece soyayya ta gaskiya ba. Amma a yau Ihsan Abubakar, ta shayar da shi mamaki. Ba shakka rayuwa ta kada Ihsan ta shigar da ita taitayin ta, ta yarda ita din ba komi bace face kyal-kyal banza, da zaka tafi ka barta ka shirya ko baka shirya ba. Ta zama mai tsoron Allah da gudun duniya abinda Alameen ya dade yana nusar da ita bata gane ba sai da ta faru a kanta. A karshen satin Faisal ya iso daga Lagos, sanye yake da kufta da wando na bakar lallausar shadda getzner. To tabbattaccen kamshinsa na (5,000 Doller) kadai daya gauraye ilahirin gidan ya sanar da mutanen gidan isowarsa as usual. Ya saya kwayar idanuwan shi cikin bakin dark glasses ta yadda baka iya ganin halin da kwayar idon shi ke ciki. Babu shakka mutuwar dan uwansa ta dokeshi inda duk ya dauki laifin ya daura akan baiwar Allah da bata ji-ba-bata gani ba, itama ta kanta ta ke Intisar. Inda abinda ya tsana da gani a rayuwarshi a yau to Saratu Intisar ce. Yana ganin ta as a wicked lover kuma har abada baya jin zai yafe mata. Baya ga tagayyara tashi zuciyar tare da daidaita farin cikinsa, ba kuma tare data kara waiwayar shi a rayuwarta ba don sanin shi din a mace yake ko a raye? Ta koma ga zuciyar dan uwan sa, ta illata ta gabadaya da ciwon da har abada bazai warke ba. Duk hakan bai ishe ta ba, sai da ta yi sandaiyyar danganar shi da karkashin kasa, inda baa dawowa. A yanzu kam ya na mai tantama da alamarin ta, tare da furucin da nahaifiyar su ta dade ta nayi a kanta na cewa, shin ko ita din, mayya ce? Ya samu Daddy zaune bisa kujera yana nazarin labarun da ake watsowa daga tashar CNN a akwatin talbijin din jikin bango (plasma) dake falon. Yar lelen na gefe rike da karamin Alkurani izfi sittin bugun Misra tana karantawa. Kallo daya ya yi mata ya kawar da kanshi haka itama, da ganin mugun ramar da kowannen su yayi. Zuciyar ta ne ya bata wani irin bugu, don sai ya zamo mata Alameen sak a ranar bankwanar su illa shi din yafi Alameen haske da kauri kadan. Tamkar bai taba sanin ta ba, bashi kuma da masaniyar kasancewar ta a wajen ya doshi Daddy suka gaisa, suka shiga hira ta abinda ya shafe su. Cikin karfin hali ta juyo tace ina wuni Ya Faisal? Da sauri ya amsa sabida dukan da zazzakar muryarta ta yiwa zuciyarsa, ba tare daya dubeta ba ya ce lafiya, yaya gida? Da haka ya maida hankalin shi kan zancen da suke da Daddy cewa ranar litinin zai tafi da Hajiya asibtin Meritime da ke Miami domin har zuwa lokacin babu wani cigaba akan alamarinta a asibitin kwakwalwa na Kaduna. A lokacin Daddy ya ji matukar kunyar dan nasa kan biris din da yayi da alamarin mahaifiyarsu, ko ya ta ke bai taba tambayar wani a cikinsu ba. Ya sadda kai ya ce kun yi maganar da Dr. Rehab ne? Ya ce Eh, shi da kansa mun je ya ganta, shi ya kawo shawarar mu tafi da ita can din in Allah ya yarda zasu yi iyaka kokarinsu. Daddy ya ce Allah ya taimaka, in akwai wani matsala sai kayi gaggawar sanar dani, ya ce babu wata matsala don shi Rehab din ne ya dau nauyin komi daga aljihunsa. Ta tashi ta bar masu falon cike da tukuki da kunar da zuciyar ta ta shiga yi kan irin wulakancin da Ya Faisal ya tsiri yi mata ba tun yau ba. A washegari takardun ta na karatu suka fito suka tadda Daddyn a ofis, sabida kyawun sakamakonta hade yake da gurbin karatu daga Jamioi har ukku sai wanda ta zaba. Jamiar (Ummul-Kura) da ke Madinah sun bata gurbi a fanning pure and applied chemistry yayin da (King Abdul-Aziz University) da ke Riyadh suka bata biochemistry inda (Al-Azhar) da ke Egypt suka bata (doctorate) gurbi a medicine and surgery. Duka cikin ukun nan babu na yarwa babu kuma wanda ba raayin ta ba. Don haka da Daddyn ya bata zabi tace ta bar mishi wuka da nama ya zaba mata wanda duk ya ga ya dace da ita. Ranar da Faisal ya daga da mahaifiyarsa kasar Amurka nema mata maganin tabin kwakwalwa data samu. Ranar ne itama ta daga Egypt tare da Najib da Hidayah da Daddyn ya wakilta suyi mata rakiya, bayan sun kammala duk wani shige da fice da ya kamata aka bata lokacin da zata fara shiga aji, wato daya ga watan Junairu na sabuwar shekara mai kamawa, kimanin watanni biyu kenan kamin lokacin. Sun hadu da Hunainah a can wadda tuni ta zama yar gari, don haka ita ta nuna musu garin suka ci shi. Najib da Hidayah kam wani sabon honey moon din aka bude. Yayinda ita kuma ke tare da Hunainah kodayaushe, tana koka mata rayuwar ta da ta ishe ta, komi bakikkirin take ganinsa, bata jin dadin komi. Ta gaya mata ita ta yanke rai da samun farin-ciki a rayuwarta, komi da ta ke yi tana yi ne cikin karfin hali da inganta Imani. Babban abin da ya dameta ya kuma kara dagula lissafinta da jin dadin ta shine gabar da Faisal ya daura da ita, ita ba yarinya ba ce, ta tabbata Faisal ya daura alhakin mutuwar dan uwansa da baya da kamar shi a duniya ne a wuyan ta. Ta ce cikin karyayyar zuciya da radadin zuci mara misaltuwa. “Hunainah a da na so Faisal, na so shi a cikin rashin sanin shi din ko me nene a gareni. Hakannan dai nike son shi sabida shi mai kyautayi ne da tausayi, kuma gwani wajen nuna kulawa da nuna kauna a gareni. To kin san zuciya an halicce ta ne a bisa kaunar mai kyautatawa a gareta, to hakan ne ya faru da ni a lokacin. Na so shi a sailin da ban san ma menene son ba, son shi nake, amma ban san son shin na ke ba, kawai na san ni mai tsananin kishi ce a kanshi ta yadda bana son ko da wasa in ji ko in ga wata mace ta rabe shi. Babu ranar da ta fiye min tashin hankali tamkar ranar da ya ke yi mun hirar budurwar sa Ronke Adeyemi. A ranar na tabbatarwa kaina ina son Faisal, so na soyayya a matsayin yana yayana da muke uba daya? Don haka na kalubalanci zuciyata na gargadeta da kakkausar murya a kan haramci da rashin dacewar abinda ta ke so! Haka na samu taimakon kiyayyar da mahaifiyarsu ke mun ya zagwanyar da 50% na soyayyar, kawai dai na bashi matsayin wani mutun precious a zuciyata (wato mai darajjah) kuma har yau, har gobe hakan ne ba abinda ya canza. Domin in har zan manta Faisal wanene a gare ni? To kuwa zan manta wane ne Daddy Makarfi. Yayi min dimbin alheri kwatankwacin na Daddy na, tun ban san kaina ba. Kawai na budi ido na gan shi tare dani, cikin karimci da ingantacciyar kulawa. Ko a sanda uwarsu ta yi min shamaki da su, na kuma alkawarta ma raina na rabu dasu har abada, na tambayi kaina a lokacin anya zan iya rabuwa da Faisal? Na bawa zuciyata amsa nan take da cewa, aah! Faisal wani mutum ne mai muhimmanci, kima da daraja a zuciyata da bazan taba iya rabuwa da shi ba. Haka lokacin da ya bar ni ba zato ba tsammani, na yi kuka nayi kewa na shiga kunci mara misaltuwa. A hankali na dinga sanyawa zuciyata salama tare da kokarin yakice shi a raina amma na kasa, sabida wata ingantacciyar kauna ce nake yi masa ta daban a zuciyata. A sailin ne kuma Alameen ya shigo cikin rayuwata. A lokacin da zuciyata ta rasa aboki, take cikin kadaici. Lokacin da nake mai tsananin bukatar taimako. Sai ya zo da wata irin soyayyah mai shiga rai ya shimfidata a zuciyata, irin wadda ban taba ji ba. Irin wadda ko a mafarki ban taba yin na tsintar kaina cikin ta ba. Soyayya ce irin wadda ko muryar sa na ji, sai na ji gabban jikina, zuciya zuwa kwakwalwata gabadaya sun amsa! Idan dosowa yayi inda na ke, babu inda baya girgiza da kadawa a jiki na. Na tambayi kaina ashe dai wannan itace soyyar ta hakika, waccan da nayi duk a cikin gigin kuruciya ne kuma sabo da shakuwa sune tubalan da suka ginata a birnin zuciyata. Wannan ita ce natural love kuma love at first sight wadda daya bazai iya rayuwa mai dadi ba tare da soyayyar dan uwansa ba, wadda kobo ko sisi ba zai iya sayen ta ba; saukakka ce daga indallahi! Kwatsam, kaddara da mutuwa suka yi mun yankan kauna, a lokacin da muke gab da cikar burin zuciyoyin mu. Duk da cewa ta wani bangaren zan iya cewa ni na jawo amma na amince kaddara gaba take da komi. Na ji ciwon rasa Alameen yadda harshena bazai iya furtawa ba, zuciyata bazata iya kwatantawa ba, ba don na yi imani da Allah da duk abinda ya saukar a gareni, mai dadi ne ko mara dadi? Da na tabbata babu abin da zai hana ni fita daga hankalina, sai dai komai ina dangantashi daga Allah ne. A duk sanda na tuna Alameen ina yi masa adduar neman rahma kuma na tabbata wannan ita ce kauna ta karshe da zan nuna masa. Ni kadai na san ciwon da zuciyar nan ke mun Hunainah, ni kadai na san kadaici da maraicin da nake jin ya sameni. Na dauka wannan ne lokacin da Faisal zai tausaya mun, ya waiwaye ni ya rungumeni, ya bani soyayyar da na rasa ta dan uwan sa mu debewa juna kewar Alameen, to amma abinda na fahimta shi a yanzu kiyayyar da yake mini da da hali, da ya koreni daga gidansu, da da hali, da ya dauki fansar dan uwansa a kaina. Yana gani na muguwa mayaudariya kuma maciyiya amanar soyayya. Na rasa yanda zanyi da zuciyata Hunainah, na rasa wanda zan fadi wa abinda ke damuna idan ba ke ba. Na san ke kadai kika san irin ciwon da nake ji ke kuma ce kawai zan iya gayamawa na ji sanyi a zuciyata Hunainah.â€? Hunainah kuka yar uwar ta Intisar ma kuka. An rasa mai rarrashin dan uwansa. Ita Hunainar da aka gayawa labarin don neman kwarin gwiwa da shawararta sai tafi victim din ma karaya da zub da hawaye. An rasa mai lallashin wani. Hakika tafi yar uwarta jin ciwon wahalolin da take fuskanta a rayuwarta. Tunda uwarsu ta haifeta kawo girmanta bata taba hutawa ba. Bata taba ganin mai SIRADI iri-iri a rayuwa irin Saratu-Inteesar ba. Daga wannan bakin-ciki ya gushe sai wannan ya bullo. Gaskiyarta ne tabbas ba don ta kasance yarinya mai karfin imani ba da ta fita a hankalinta. Kalaman Hunainah ga yar uwarta shine; “Ni na tabbata Ya Faisal na son ki. Wannan son da yake miki tun kina tsumman goyo ba abinda ya canza domin soyayya ta gaskiya bata taba gushewa kamar yadda bata tsufa, saidai masoyan su tsufa. Balle ku da yanzu nema kuke kan ganiyar kuruciyarku. Kawai dai zan iya cewa yana jin zafin ki wanda na san as time goes on zai daina ne, ki fidda damuwar komi a ranki, domin karatun ki bana wasa bane in bah aka ba zaki sha mamakin mugun kayen da zaa dinga yi miki. Ki bar komi a hannun Jallah mai kowa mai komai, wanda Ya halicci Faisal, Ya halicci Alameen, Ya halicci Inteesar ya sanya soyayyar juna a zukatan su. Ki bashi ikon zaba miki abinda ya san shi ne mafi alkhairi a rayuwarki.â€? Hakika nasihar yar uwarta ta nutsar mata da zuciya. Tayi damarar karfafa zuciyarta da kokarin yakice duk wata damuwa da ke damunta, tareda daura aniyar fuskantar karatun ta da dukkan iyawarta. Gabadaya daga Alameen har Faisal ta sanyasu cikin wani fai-fai na tarihin rayuwarta ta baya inda ta budewa kanta sabuwar rayuwar data tarar a gaba. Duk dai a lokacinne kuma tabi jirgi zuwa kasar Korea domin gano mahaifiyarta kamin lokacin da aka diba musu na fara karatun ya cika. Inda ita Hunainah hutu ne zata je na karshen semester wanda daga shi in ta koma zata shiga mataki na uku. Hidayah da maigidanta Najib sun koma gida Nigeria inda Hidayar zata fara karatu a jamiar Enugu inda mijin ta ke aiki kenan. Daddy ya zaba mata Al azhar dake Egypt ne sabida dadadden burin da ya dade dashi kan son Saratun ta zamo mai amfani ga dumbin alummah da fasahar da Allah Ya bata, wannan shine dalilinsa na zabar mata Medicine and Surgery. Hakika sun ji dadin hutunsu a Korea tareda mamarsu. Duk wani daddaurewa da takewa Inteesar a da, yanzu ta daina jan ta take a jiki fiye dasu Hunainah. Ita kadai tasan dimbin tausayin da yarinyar ke bata wanda ita din bazata iya maganta mata matsalolin da Allah Ya daura mata a rayuwarta ba. Gabadaya ta kare, sai tsayinta da farin kadai dama jikin ba wani jiki na azo a gani ba. Ta kan yi mata nasiha da ta kara dayanta Allah a alamuranta yana sane da ita, ba wai mancewa yayi da ita ba. Da sannu zata samu madawwamin farin-ciki a rayuwarta kamar kowa. Hakurin ta da kudurin ta na alkhairi a kan kowa, ba zai tashi a banza ba. A lokacin Haj. Hadiza cikin ta ya tsufa sosai, haihuwa yau ko gobe. Zahrah an sanyata a nursery tayi wayo sosai ba abinda bata cewa. Ta gaya musu Daddyn su Hunainah yayi retire suna jiran kwanakin da aka deba musu su cika su koma gida bakidaya. Su Inteesar sun ji dadin hakan sosai. Daya ga watan Junaiuru na sabuwar shekarar suka koma makaranta. Inteesar ta samu sauyin rayuwa ta fannnoni da dama, haka tsarin karatun Al-azhar yana burgeta komai cikin nutsuwa babu takurawa. Suka durfafi karatu babu kama hannun yaro, balle data fahimci abin na yi ne, mai wasa sai ya kwashi kashinsa a hannu sai ta kara dagewa tareda bada himma sosai. How much do you like this story? 5/14/22, 09:27 - Ummi Tandama😇: _____________________________ *âœðŸ? SIRADIN RAYUWAâœðŸ?* Book four *@Takori* Page6ï¸âƒ£ Bayan Watanni Uku Lallai babu cutar da Allah ya saukar a doron kasa ba tare da ya saukar da ita tare da maganinta ba. A yau Hajiya Nafisatu Bello Makarfi, ke sauka daga matattakalar jirgin KLM cikin filin jiragen saman da ke garin Kaduna. Dr. Rehab Mohammed tare wasu daga likitocin asibitin meritime su biyu sune suka yo mata rakiya daga Birnin Miami da lafiyarta da hankalin ta sumul kalau, inda yayan ta Faisal da Nasir suka zo taryenta, kar kaso ka tona zuciyar su mai cikke da godiya ga sarki Allah da ya baiwa mahaifiyar su lafiyarta sumul kamar ba ita ce ta tafi bata san abinda take yi ba. Suka rungume juna daya bayan daya cike da kewa da farin ciki, a yayin ne wasu hawaye marassa dandano suka zubo mata. Ba komi ta tuna a lokacin ba face ranar da Alameen ya zo ya dauketa a air-port zuwa gidan iyayen ta ranar da ta dawo Dubai, kuma ranar da ta kasance ta karshe a tsakanin su. Ashe wani bakin cikin na nan yana jiran ta, shine rasuwar mahaifiyar ta Hajiya Iyami. A nan kuka ya zamo mata sabo. Yayan ta sunyi nufin tafiya da ita gidan mahaifinsu inda ita kuma ta nuna aah, suje su fara rokar mata gafararsa tukunna, bazata koma masa gida ba da yawunsa ba, kuma ta san har ga Allah ta zahince shi kwarai da gaske, in bai yafe mata ba ta san hakkin sa kadai bazai barta ba. Baa maganar hakkin Saratu da Saratu da ke kanta. Ta roke su su nema mata gafarar wadannan bayin Allah kafin ta zo da kanta neman gafarar su. Ta tabbata hakkinsu ke ta dawainiya da rayuwar ta. Komawarsu gida suka tadda labarin duk suna asibiti, Ihsan ce ke nakuda tun shekaran jiya haihawar ta zo da tangarda, daga karshe dole mahaifinta ya sa hannu aka shiga da ita dakin tiyata bakunan su cike da adduoin samun saa domin hakika ta jigata, duk wani mai imani dole ya tausaya mata. To alhamdullahi an yi nasarar fiddo jariri katoto da shi lafiyyaye. Daddy ya amshi Babe da niyyar yi mishi addua da lankaya mishi kalmar shahada amma sai zuciyarsa ta buga da karfin gaske! Yayi tazbihi ga Allah ya tsarkake shi a zuciyar sa, ya kara imani da buwayarsa da isar mulkinsa akan komi. Babu ko tantama wannan Alameen Bello ne yake rike da shi a sanda mahaifiyar shi ta haife shi. In kasan photocophy na Alameen to wannan jaririn ne. A take ya lankaya mai sunan shi cikin kunnuwan shi wato Alameen Alameen Bello. Sai dare aka fito da Ihsan zuwa dakin hutu, duk tayi wani fiyat ta zabge sabida wahala. A wannan dan tsukin ne kuma taga kauna da karimci daga lyaye da yan uwan Alameen irin wadda bata taba tsammanin zata samu ba. Ta tabbata ita yar gata ce amma Alameen ya fita gata gaba da baya, kuma kaunar da iyaye da yan uwan shi ke mishi, duk dimbin arzikin iyayenta ita bata samu koda kwatankwacin ta ba. Ashe ba dimbin arziki da dukiya ne gata ba, aah, matsayin da kake da shi a zuciyar iyaye da yan uwan ka. Har aka basu sallama suka dawo gida bata san kukan Baby Alameen ba, koyaushe yana jikin Aunty Saratu da kannen mahaifin sa, iyakacin ta da shi shan nono kadai. Gaba daya sun dauki kaunar duniya sun aza bisan Alameen karami musamman Faisal da Najib da shiga goma fita goma sai sun ce a kawo masu yayansu. Bayan sunan Alameen ne suka doshi Daddy da alfarmarsu na ya yafewa mahaifiyarsu kurakuranta, domin hakika tayi nadama mara iyaka. Daddy sai ya yi murmushin sa mai nufin alamura da dama kamar koyaushe zai yi wata magana mai muhimmanci. Ya ce, “In don ni ne ai ba abinda tayi mun, ban da kaunata da take da ku yayan ta. Wadanda ta zalinta kam suna can inda suke, don haka ta je na yafe mata duniya da lahira. Amma maganar wai ta dawo dakinta bata taso ba, domin mai hali baya fasa halin sa. A yanzu kam girma ya hau ni, ina bukatar hutu, bazan iya jurar tashin hankali ba. Don haka ku je ku tambayeta idan har ta shirya zama na amana da zuciya daya da duk wanda na kawo cikin gidan nan na ajiye, to ana maraba da ita. Idan kuma akasin haka ne a zuciyarta to don Allah ta nemi wani gidan don wallahi a yanzu bazan iya jure halinta ba! To bayan dogon kai ruwa rana da kyar da sidin goshi Aunty Saratu ta shawo kan Daddyn ya yarda da komen Hajiyar da babu shakka ta darastu da rayuwar duniya. Har kasa ta tsugunna neman gafarar Saratun tare da alkawarta mata tazo ne su yi zama na amana da aminci na har abada. Saratu ta tabbatar mata duniya da lahira ta yafe mata domin yayanta sun gama mata komi a rayuwa. Ta nemi Intisar domin neman gafarar ta, inda ake sanar da ita tana Alkahira tana karatu. ***** Bayan Shekara Daya Faisal Bello Makarfi ke taka matattakalar da zata sadashi da falon Daddy Makarfi cikin sassarfa, sanye cikin farar shirt product din DKNY da bakin wandon Tokyo da misalin karfe shidda na yammacin ranar Lahadi. Isowar shi kenan cikin garin, kamar kullum, a yau ma ya saya kwayar idanun shi cikin bakin gilashi domin boye halin da kwayar idon shi ke ciki. Ya yi sallama a babban falon kana ya jinkirta har ruwa sanda Daddyn yayi masa iznin shigowa. Zaune yake ya tasa allon computer (Laptop) a gabansa bisa tebir inda suke musayen sako da diyarshi Inteesar tana bashi labarin karatun su a makaranta. Ba tare da ya dauke hankalin shi daga computern ba ya amsa sallamarsa tare da nuna masa wajen zama daga gefen sa. Aunty Saratu ta shigo dauke da babbar warmer da kofunan shan ruwa ta aza daga can kan dining tana murmushi tace aah bakin Ikko ne sai yanzu, kai da tun jiya muke tsammanin ka. Ya ce wallahi kuwa shirye shiryen tafiyana ne ya tsaida ni, kin san babu biza mai wuya irin ta U.K. A sannan ne Daddy ya cira kai ya bishi da kallo na mamaki. Sannu a hankahi kuma cikin dan kankanin lokacin yayi nazarin wasu muhimman abubuwa da dama a tare da yaron. Ya sa hannu ya fidda mudubin idonsa ya kara duban Faisal sosai. Ta fahimci uban da dan na bukatar privacy domin tattauna matsalolinsu sai bata matsa da tambayar me zai je yi ba ta ce Allah ya shige mana gaba. Daga haka ta ba su waje. Daddy ya ce cikin wata murya mai kama da umarni. Faisal ina zaka je? Yayi dan dawurwura na dabarbarcewa da rashin kwakkwarar hujja ya ce am eh, Daddy, admission dana nema tun shekarar baya a can Birmingham domin karo Ph D dina, har na manta kawai sai shekaranjiya suka aiko min, to shine nazo in yi muku sallama, zan ta fi. Daddy ya ce Faisal, me ke damun ka? Kana kallon kan ka a mudubi kuwa? Tun bayan rasuwar Alameen na ke lura da kai babu cigaba a alamarinka, kullum kara lalacewa ka ke. Wannan ramar da kake tayi a kullum kamar kudin guzuri ta mece ce? Yaji idanuwan sa sun ciko taf da hawaye amma yayi kokarin maida su. Cikin jarumtaka yace Allah babu komi Daddy. Yace to kaima Faisal ko dan uwanka zaka bi ne ku barni ni daya? A wannan lokacin duk jarumtakarsa saida hawayen suka balle. Ya zare gilashin sa a lokacin ne Daddyn ya samu damar ganin yadda idanuwan sa suka fada sosai, baya ga kadawa da suka yi sukayi jawur kamar gauta. Ya ce, “Ina adduar Allah ya bani tsawo ran da zan kula da kai a gaba dayan ragowar rayuwar ka, kamar yadda ka sadaukar da kuruciyarka wajen kulawa, hidimar mu da tarbiyyantar da mu.â€? Ya ce, “In haka ne Faisal me yasa zaka bar ni? Me yasa baka son tsugunawa a waje daya? Yau kana can gobe kana nan kamar wani tsuntsu. Ka kasa tsayawa ka ginawa kanka rayuwa ta da namiji. Ba ka ko tunanin yin aure! Karatu dai karatu kadai Faisal kaman alhuda huda? Duba kaga kanin bayanka matar sa tsohon ciki gareta, haihuwa yau ko gobe. Dubi Alameen ya tafi, amma ga Alameen Alameen nan na yawo cikin gidan nan yana tuna mana da shi muna yi mishi addua, ko ba zaka yi aure domin bukatar kanka da cikar mutuncika ba, kayi domin shi kansa ibada ce mai zaman kanta. Ban san me kake nufi da rayuwar ka ba, ban san meye planning dinka a rayuwar nan ba. Ina jiye maka tsoron kazo duniyar a banza ka koma a hofi. In kana ganin bani iya yi maka maganin matsalarka to a kalla zan baka shawara wadda kai a shekarun ka bazaka hangosu ba. Ko kuma mutuwar Alameen ce ta ke nukurkusar ka har yanzun? Take neman kayar da kai tun karfin ka bai kare ba?â€? Yasa hankici ya share idonsa ya share dogon karan hancinsa ya ce, “Aah Daddy, na riga nayi tawakkalin cewa ya tafi, ba kuma zai kara dawowa ba.â€? Ya ce, “Madallah, ni dai da zaka bi son raina da ka hakura da tafiyar nan ka rungumi aikin ka an kuma daura maku aure da matar marigayi Ihsan da ka faranta mini, ko ba komai yarinyar ta nuna mana ita mai kaunar mu ce ba wai abinda muka mallaka ba. na dade ina kissima yiwuwar hakan a zuciyata ba tun yau ba..â€? Ya dago cikin wani irin yanayi na firgici da tashin hankali ya dubi mahaifinsa, kana cikin nutsuwa yace “Daddy! Na rokeka alfarma, don girman Allah koda wasa kada ka kara tunanin zancen nan balle ka fada wani ya ji. Kada ka bari alamarin yayi tasiri a zuciyarka don Allah? Yaya ma zaayi ka yi wannan tunanin? Zaka karasani kwanana bai kare ba. Ka bar ni in ji da ciwon da zuciyata ke yi. Ba matar da Alameen ya aura akan yana so ya tafi ya bari ba don ba ya so ba, ko yarinyar da ya taba nema bazan iya aure ba balle matar sa. Kayi min uziri ka karbi hanzari na, in dai tafiya ce na fasa amma don Allah, kada ka kara ce min wani abu makamancin wannan. Daddy ya yi murmushi ya ce yaro dai yaro ne. To kaje ka kawo min yarinyar da kake so cikin kwanaki goma rak! Amma in ba haka ba zan daura aurenka da Ihsan a ranar da kwanakin nan suka cika. Na gaya maka na kara gaya maka babu wasa cikin magana ta. Cikin matsananciyar damuwa ya ce ni bani da wata yarinya da na ke so. Ban taba son wata ya mace a duniya ba. Alameen kadai na ke so!!! Don haka na baka wuka da nama ka zartar da duk hukuncin da ka ga dama a kaina, ka zabamin ko wacece amma ka taimake ni Daddy kada ka aura min matar Alameen. Wallahi zan gudu in bar garin, don ni Ihsan Yaya ta nake ganinta. Saura kadan dariya ta kwace masa amma ya cije ya daure yace shikenan, tashi je ka sai na neme ka. Sai dai ina mai gargadinka ka cire abinda ke damunka daga zuciyar ka domin tsira da lafiyarka. Babu wata cuta da Allah ya saukar a doron kasa da bai saukar da maganin ta ba. Ka kaiwa Sarki Allah kukan ka amma ba wannan damuwar da ka sawa ran ka ba babu gaira babu dalili. Ya mike kamar wanda kwai ya fashewa a ciki ya doshi sassan Anti Saratu. Tun daga hangoshi Alameen karami ya watsar da kayan wasan shi ya rarrafo da hamzari ya kama kafafun shi, shi kuma yayi gaggawar russunawa ya daukeshi ya rungume a kirjin shi. A lokacin ita Ihsan ta tafi asibitin Alameen Memorial da ake canzawa suna maimakon MERITIME. Ko ba don haka bama a dan tsukin bata samun zama sabida shirye shiryen bude asibitin da ya gabato, tana sa ran yaye Alameen karami ne ma cikin wannan watan mai kamawa domin hidimomin sun mata yawa, ga tafiyar ta karin karatu saura watanni (3) kacal. A kan Alameen bata da kaico ta san Anti Saratu na iya kokarin ta a kan sa, haka Hajiyar Alameen duk wani buri da tattalinta ya taallaka ne a kan dan yaron da bai ma san ko shi wane ne ba. Motsi kadan zata shigo sassan Antin tana ina maigidana ne? Ban ji duriyar sa ba tun dazu, wane shagalin yake yi ne? Kayan wasa kuwa na dubban nairori bata jin kyashin saya masa ko na nawa ne har ma wanda yafi karfin shekarun shi irnsu automatic motorbike da kekunan yara musamman take yo odar su daga Germany duk don Maigidannata. Inda shi kuma Daddy bashi da wani aboki kaman wannan Alameen Alameen Bello. In kaji shi yana bashi labari sai ka rantse da wani cikakken mai hankali ne yake magana ba da yaro dan shekaru biyu ba. Faisal ya zauna ya kifa fuska cikin tafukan sa, yayinda Alameen ke dabdalarsa a dokin wuyansa. Antin ta karaso rike da tambulan cikke da sassanyar madarar shanu fresh ta mika masa. Ba tare da yayi musu ba ya amsa ya shanye wata niima da sanyi suka sauka a zuciyarsa. Jijiyoyin kansa duk sun mike rada-rada a kansa haka tsigar jikinshi sai tashi yake, tabbacin zazzabi ke neman kama shi. Ba ta katse shi ba har saida ya samu nutsuwa don kansa, kana cikin sanyin murya ya ce, “Aunty, kin ji abinda Daddy ya yanke a kaina?â€? Ta ce, “Ya hanaka tafiyar ba? Ni ma ban ga dalilin tafiyar baâ€? Ya ce, “Tafiya ni na fasa da kaina, cewa yayi in kawo matar aure cikin kwanaki goma ko ya aura min maman Alameen karami. Sabida Allah Anti yaya ma Daddy zai yi wannan bahagon tunanin? Sabida Allah an yi mun adalci kenan? Cikin mu wa aka taba zabawa matar aure? Yaya zaayi in iya hada rayuwa da matar da Alameen ya mutu ya bari ba don baya so ba, sai don mutuwa da tayi mishi yankan kauna? Wannan ai cin amana ne da tozartawa. Wallahi ko yarinyar da Alameen ya furta ya na so, bazan iya aure ba balle matar sa. Komi son da nake mata kuwa zan iya jurewa. Don na tabbata in shine ya san ina son mace, da ko itace autar mata daga ranar bai kara sonta. Zai hakura ya bar mini domin shi dan uwa ne mai dimbin karimci da sadaukarwa. Na zo ne in roke ki alafarma ki hana Daddy wannan kudurin nasa, ni kuma nayi alkawarin yin biyayya ga duk matar da ya zaba mini matsayin abokiyar rayuwata ta har abada, amma ni ba zan auri Ihsan ba.â€? Ta yi murmuishi ta ce, “Na ji uzurinka Faisal, kuma da yardan Allah zanyi kokarin in ganar da shi. Amma da sharadin zaka amsa min wata tambaya guda daya da zan yi maka. Kayi min alkawarin zaka fada min gaskiya ni kuma na yi maka alkawarin ba zaka auri Ihsan ba!â€? Cikin sauri ya ce, “Wace tambaya ce Anti? Wallahi zan amsa miki iyakar abinda na sani.â€? Ta ce, “Shhhh, ka daina saurin rantsuwa akan abinda baka da tabbas.â€? Ya ce, “Wallahi Anti zan gaya miki.â€? Rantsuwar da yazo yana dana sanin yinta kamar yadda ta gargadeshi a farko. Ta tattara hankalinta gabadaya gareshi cikin murryar manyantaka da bada umarni tace menene hakikanin abinda ke damunka, tsakaninka da mahaliccin ka? Cikin juyayi da dana sanin alkawarinsa ya ce, “Anti soyayyah ce ta ke azabtar dani. Shekaru dai-dai har goma sha daya. Amma alhamdulillahi a yanzu ta kusa karasani nima in bi dan uwana in huta da azabar ta. To amma matsalata shine bana so tayi galaba a kaina, kamar yadda tayi galaba akan dan uwana. So nake in nuna mata banbancin mu na cewa ni mai iya controlling zuciyata ne sabanin shi da zuciyar ke juya alamuransa. Idan na barta ta yi galaba a kaina sauran yan uwana ma bazata kyalesu ba, haka zatayi ta bin mu daya bayan daya tana kashewa har sai ta karar damu. Don haka bazan barta tayi galaba a kai na ba.â€? Murmushi tayi ta ce, “Wace yarinya ce kake so shekarun da suka wuce, ba kuma zaka taba iya aure ba har ka bar mu domin ta?â€? Cikin kaduwa da matsanancin mamaki ya ce, “Anti wa ya gaya miki wannan maganar?â€? Ta ce, “Bai zama dole ka sani ba, ka yi alkawarin amsa min tambayata ne kawai amma ba kai ka dinga tambayata ba. Sabida haka ka ji tsoron Allah ka idasa cika alkawarin ka.â€? Ya sunkuyar da kansa kasa, in banda zufa ba abinda ke ketowa daga koina a sassan jikin shi, duk kuwa da A/C da fanka da ke ta aiki a falon. Ya yi dana sanin saurin rantsuwar sa. Nauyi da kunyar idanunta duka sun masa mayafi. Muryar sa can kasan makoshin sa tamkar ba tashi ba, ya ce, “Anti Inteesar din ki ce!â€? Ba tare da alamun wani mamaki ko girgiza da furucinsa ba ta ce, “To yanzun ka daina son nata ne?â€? Ya girgiza kai har yanzu bai dago ba, ji yake har abada bazai iya kara hada idanu da ita ba, a sanyaye ya ce, “Ya zaai na daina sonta? Ita din ce dai har yau bata bar ni na huta ba kuma har gobe ba zan taba iya auren ta ba!â€? Ta ce, “Hujjah?â€? Ya ce, “Hujjata a da shine kasancewar mu uba daya. Hujjata a yanzu kuwa Alameen ya so ta. Ni kuma bazan taba yin tarayya da shi a son komi ba ban hakura na bar mishi ba. Don na san da a ce ya san ina sonta, da tuni ya hakura ya bar mini.â€? Saura kadan dariya ta kwace mata amma ta cije, “Ta girgiza kai tana murmushiâ€? Ta ce, “Wannan ba hujja ba ce ba Faisal. Don haka tashi je ka. Cikin kwanaki goma ka yi tunanin abinda ya dace da kai. Ko dai samawa zuciyarka abinda ta dade tana so don dorewa rayuwa mai inganci ko kuma auren matar yayan ka. Ina mai tabbatar maka har yau, har gobe Saratu na son ka. Soyayyarta da Alameen wata kaddara ce daga Allah amma kai kadai take so tun tana mitsitsiyar ta. Ta damu da kai sosai, zata iya yin komi a domin ka. Gareta duk yadda rayuwa ta zo, a karbeta. Don haka ne ta karbi soyayyar Alameen.â€? Sau da dama tana yiwa komi na rayuwarta uzuri da Faisal da Daddy Makarfi. Ta baka wata daraja da muhimmanci a rayuwarta irin wanda bata baiwa kowa a duniya ba. Duk halin da kake ikrarin ka shiga a wancan lokacin, ina mai tabbatar ma itama ta shiga kwatankwacin sa koma fiye da naka. Ta damu da kai sosai. Ta na matukar kishinka fiye da yadda baka zato. A duk halin da take ciki, na farin-ciki ne ko na bakin ciki kai take tunawa tace Allah Sarki Ya Faisal! Da yana nan da kaza-da kaza, da kaza bata faru ba, da kaza ta faru. Ta fi kowa bakin ciki da tafiyar ka ni nasan wannan, amma ita tsammani ta ke ban gane ba. Ya girgiza kai har yanzu kan shi a sadde, ya ce, “Anti wannan kauna ce ba soyayyah ba. Intisar kauna ta kawai take, amma bata so na!â€? Ta ce, “Babban jigon soyayya shine kauna. Kai ba namiji bane? Baka san yadda zaka yi ka gina soyayyar ka a zuciyar matar da kake so ba? Sai ka zuba ido ka zama dan kallo kana muku-muku cikin daki? To zauna nan kallon ruwa har sai kwado yayi maka kafa. Ina mai tabbatar maka Intisar ta shigo wani matakin da take tsananin bukatar soyayyar da namiji a yanzu, komai na iya faruwa da rayuwar ta balle a inda su ke da babu kowa a tare da su sai Allah da ya halicce su. Bar ganin ta yarinya mai kamun kai, da yawan yaya mata basa iya tsallake wannan stage din (adolcence). A jiya da na lissafa jibi ne zata cika shekaru ashirin da haihuwa. Faisal me kaka jira da rayuwar ka? Ina ganin lokaci yayi da ya kamata ku fuskanci alkibla sahihiya.â€? Kwana yayi yana nazarin zantuttukan da suka yi da Anti a daren jiya. Sai dai har zuwa lokacin ya kasa tsayarwa da kansa wata sahihiyar shawara. Ya kasa daina ganin Saratu a matsayin mai dimbin laifi a gare shi. Laifin da yake jin har abada ba zai iya yafe mata ba! Hakan nan zuciyar ta ki bada goyon baya, ta ki daina bugawa a kowanne second da so da kaunar Inteesar, shi kam ya rasa inda zai tsoma rayuwarshi ya ji sanyi. Ya kasa zabarwa kansa komi cikin zabin da aka bashi. Abinda yake da tabbaci kawai shine ko zai mutu ba aure, ba zai auri matar Alameen ba, kamar yanda ba zai iya auren yarinyar da Alameen ya furta yana so ba kome zaayi da shi kuwa, balle Intisar din da har abada ba zai daina ganinta a matsayin azzaluma ba a cikin soyayya, mayaudariya mai son kanta da yawa kuma maciyiya amanar kauna. Laifuffukan ta gareshi basu da iyaka kuma tananinsu ma bata lokaci ne. Ya dai barta da duniya da abinda ke cikin ta kadai sun isa su koya mata hankali. How much do you like this story? 5/16/22, 07:35 - Ummi Tandama😇: ______________________________ *âœðŸ? SIRADIN RAYUWAâœðŸ?* Book four *@Takori* Page7ï¸âƒ£ Ranar litinin Ihsan ta tashi zuwa Miami inda zata halarci kwas na tsawon shekaru uku madadin karatun ta, yaronta Alameen karami ta bar shi ne karkashin kulawar kakanninsa. Duk wasu shirye shiryen tafiyar Ihsan Dr. Rehab ne yayi mata Allah kadai ya san kudurin shi na alkhairi kan wannan mace mai kyakkyawar zuciya ta marigayin amininshi. Zaman lafiya da a ke a gidan Makarfi tsakanin Hajiya Nafi da Anti Saratu abin sai ya burge ka, ya kuma baka mamaki tamkar ba wani sabani da ya taba shiga tsakanin su. Lallai duniya makaranta, ta koyar da Hajiya Nafi darussan rayuwa kala daban-daban. Hakannan harkokin kasuwancin ta daya fara durkushewa sabida rashin kwanciyar hankali a yanzun ya fara farfadowa. Yayinda Aunty Saratu ta a je aiki kwata-kwata ta rungumi auren ta da hannu bibbiyu, da fatan cikawa da imani kadai. Ambasada Bashir Sambo, sun dawo gida bayan ritayar sa a embassy. Katafaren gidan da ya kwashe shekaru biyar yana ginawa yana nan cikin anguwan Lamido Crescent dake cikin birnin Kano. Gida ne na gani a bada labari da duk fadin anguwar babu wanda ya kama kafar sa, tamkar an dauko shi ne kacokam daga kasar France an aza a filin wajen. A lokacin tagwayen data haifa duk maza suna da shekaru biyu da haihuwa sai Zarah da ke da shekaru hudu, wadda daga yaye dai ta za ma yar su kwata kwata, don daga Daddy har Aunty Saratu babu wanda ya kara magana a kan zaman yarinyar tare dasu. Tsarin rayawar gidan dole ya baka shaawa, babu hayaniya sam-sam, rayuwa ce kawai suke kamar a turai. Lokaci-lokaci suna zuwa Shanono duk da cewa dangin sun kare. Matan Hakimi tun bayan rasuwar sa duk sun kama gabansu, manyan yayansa maza kuwa duk Bashir ya dauki nauyin karatun su a manyan jamio’in mu, matan duk shi ya aurar da su tare da basu jari mai tsoka domin dogaro da kai. Haka duk matsalolinsu yana kokari a kai domin tabbatar da cikin su babu mai kukan rashi. Ba tare da yin shawara da kowa ba Hajiyar su Faisal ta shiga yi masu cuku cuka ita da Faisal, Najib da Hidayah domin tafiya Al-kahira, saida ta kammala tsaf aka sanya masu date din tashi kana ta samu Daddy ranar girkin ta a wani dare, ta sadda kai cikin matsananciyar kunya ta ce, “Babansu Khaleel, ina neman izninku zuwa wajen Intisar, ina matukar kwadayin afuwarta da yafiyar ta gare ni, har yau ji nake ban sauke wani nannauyan dutse daga kaina ba. Idan ka amince zan nemi rakiyar su Najib ko albarkacinsu ta dube ni ta yafe mani.â€? Tasa habar zaninta ta share idonta ta fyace majina ta ce, “Idan yarinyar nan bata yafe mun ba, bana jin Alameen ma zai taba yafe mini. Haka ubangiji na ma ba zai yafe mun ba, iznin ka kawai nake nema domin nagama komi, jibi ne zamu tashi.â€? Ya daga ido ya dube ta kawai ya ce, “Me yasa bakya shawara kafin gabatar da alamuran ki? Sai in ce kin yi asarar kudin ki domin kuwa jibin ne zata dawo hutun karshen shekara.â€? Ji ta yi kamar anyi mata bushara da Aljannah. Ta ce, “Ba komi ai, Allah ya kawo su lafiya.â€? A Egypt Saratu da yar uwar ta Hunainah, cikin wani boutikue dake cikin jerin kantunan Shaam-El-Sheikh da ke cikin birnin Al-Kahirah, dukkansu suna sanye da riga da skirt iri daya samfurin Dolce&Gabbana, sun kuma daura after dress bisa dressing din nasu kala daban-daban, na Intisar grey ne wato ruwan toka-toka yayin da ta Hunainah ta kasance baka sidik. Hunainar rike da kwando da suka cika taf da kayan shafa, (shopping) suke domin dawowa gida hutu a washegarin gobe in Allah ya kai mu. Ga dukkan alamu ita Hunainan cike take da farin-cikin dawowa hutun ko ba komi ta dade rabon ta da gida fiye da yadda ta saba yayin da a daya bangaren Intissar gata nan ne dai kawai. Kwata-kwata ta rasa me yasa bata farin ciki da wannan hutun duk da cewa kuwa rabon ta da gida shekaru biyu kenan cif. Hakanan dai take ji a ranta wani bakon alamari na shirin faruwa da ita a wannan tafiyar kamar yadda yake a aladarta, komi zai faru da ita mai dadi ne ko akasi takan ji bacin rai ne wanda ke kasancewa zane baro-baro a kyakkyawar fuskarta, duk rabin hirar da Hunainan ke mata kan tsohon cikin da Hidayah ke tare da shi, da bidirin da zaa sha wajen haife shi kasancewar Hidayar mai rakin tsiya ko kadan hankalin ta baya tare da ita. Gane hakan da Hunainan tayi sai itama ta ja bakinta ta tsuke, har suka koma makaranta basu kara ce da juna komi ba. Karfe tare na safe jirgin Egypt-Air ya dire su a birnin Kano. Kai da ganin su kaga yayan hutu na garari kuma yammata na kasaita, wadanda gabansu da bayansu, gata da hutu kadai ke magana. Zai yi wuya ka yarda haifaffun kasar Nigeria ne, sun fi kama da santala-santalan matan Mouritania ko kuma irin half-cast din nan da suka tashi a kasar sanyi. Akwai wata nutsuwa ta musamman da zuzzurfan ilmi ya kara ma fuskokin su. To haka makallalen saurayin da Hunainah ta yi tun a cikin jirgi ke biye dasu har zuwa reception inda duk suka a je kafa nan yake mayar da tasa. Ya kare ganin basu da niyyar kulawa ya sha gabansu, kyakkyawar fuskarshi dauke da kayataccen murmushi ya dubi Intisar ya ce Assalamu Alaikum Yayata, zuciya ce ta ga wani koren fure tana so shine take ta faman bibiyar sa, kada iska ta dauke shi ko kuma ya bace mata tana ji tana gani. Suna na Hashimu Ingawa, ki taimaka kar ki bari furen nen ya bace mani, don Allah? Yana magana ne cikin accent na Katsina, ya rausayar da kai gefan da Hunainah ta ke, ta cika ta yi fan har tana neman fashewa. Idan da abinda ta tsana a duniya to wani namiji ya ce yana sonta, duk dangantakar dake tsakaninsu daga ranar zata wargazata da rashin mutuncin da ko inuwar ta ya gain sai ya sauya hanya. Ta tura akwatin ta fuuuu! Tayi gaba kaman guguwa. Intisar ta yi murmishi, haka kawai ta ji gayen ya burge ta, tana son mutum mai fallasa asirin zuciyar sa da fidda zahirin kaunarsa gaban kowa ba tare da shayi ko haufin komi ba tamkar Alameen din ta. Ta dube shi tsaf yake baya da makusa, da ganin shi ka ga wanda ilmi da naira suka ratsa sai dai baki ne, amma bakin sa mai kyau ne tunda kuwa ya hadu da hutu da gogewa. Sanye yake cikin makubar suit da ratsin fari sol ya daura jibgegiyar rigar sanyi fara sol wadda tsawon ta yake har guiwar sa, ya zuba dukkan hannayen shi cikin aljihun rigar amma hakan bai boye hasken agogon diamond da ke walkiya cikin lafiyayyar fatar hannun shi ba. Ta ce mun gode Hashim, amma in gaya maka gaskiya wannan furen da kyar zaka same shi ya fiddo ido abin tausayi duk sai ya bata dariya, da gani maabocin raha ne shima kaman Alameen ya ce is she married (maana tana da aure?) ta girgiza kai tana murmushi tace uhm-uhm, tukunna dai, karewa ma dai wannan furen naka tsoron maza yake, da kyar zata tsaya ta saurare ka. Yayi wata ajiyar zuciya mai karfi duk sai ya kara burgeta, da gani ba kankanin so ya kamu da shi a lokaci daya ba. Ya ce ni dai Yayata, pls help me, ni na san yadda zan yi, kuma zaki yi mamaki Allah, bata samu Mr Right dinta bane yet, amma ni tunda na ganta a Cairo nasan we are meant for each other kuma naga matar aure, shin zaki iya ba Bakatsine auren yar uwar ki? Ta yi murmushi mai sauti har kyawawan hakoranta suka bayyana tace why not? Katsinawa sun dade suna burge ni. Don an ce akwai su da rikon aure da muhimmanci fiye da Kadawa da Kanawa. In har ya cancanci in bashi kuma tana son sa everything is possible wato komi mai yuwuwa ne. Ta fiddo katin Babansu mai dauke da adires na gida ta kuma fiddo biro cikin jikar ta ta rubuta mai nambar Hunainah a bayan katin, yayi mata godiya sosai, ya ce har abada ba zan mance da wannan taimakon da kika yi mun ba Yayar mu, na gode. Da haka suka rabu, ta doshi Hanainah da ke ta faman cikka, kiris ta ke jira ta fashe. Bata bi ta kanta ba ta fiddo waya ta cire layin ta na Cairo ta sanya MTN tayi lodin recharge da ta saya a gefe tana kiran Babansu, cikin minti goma sha biyar sai ga mota ya turo masu da direba, ya kwasheu zuwa Lamido Crescent. A cikin motar Hunainah ta kara cika ganin Mamar da Baban ba wanda yazo taryon su ga bakin-cikin da Saratu ta kunsa mata kuma ta ki bata hakuri sai hawaye sharrr! Intisar tayi kokarin maida dariyar ta don kar ta fito ta rufe ta da duka. Sai da suka shiga gidan ta sunkuya ta kwashi dariyar ta mai isarta tana bawa Maman labarin yadda aka yi da sabon saurayin Hunainah, ita ko tunda ta watsar da trolly din ta tayi sama bata kara saukowa ba, saida matsiyaciyar yunwa ta hullo ta. Sun hadu a dining karfe hudu na yamma suna cin abinci tare da Baban su, yan biyu a cinyar Intisar hagu da dama tana sanya masu friso cream a baki da dan kankanin cokali yayinda Zarah ke zaune bisa tata kujerar kusa da ta Babanta Bashir tana cin vicorian sandwitch suna bashi labarin makaranta da yanayin karatun su, ya ce nikam ban so kika dauki surgery ba, naso ne ki dauki gynaecology domin muna da karancin likitocin mata kuma mata yan uwan su a nan Arewa tace lah Daddy, ai Hidayah ce tace zata dauka bayan ta haihu, sai na ga da mu taru duk a abu guda, ai gara a rarraba kafa ya ce wannan shirmammiyar ce zata koma wani karatu, ba ki ji ba tun yaushe take wakar zata koman kin kara jin sun tayar da zancen, ki daina sata a layin karatu bar ta dai da mijin da giringidishin ta, amma ba wani karatu da zata koma balle idan ta soma zubo yaya. Gaba daya aka sa dariya. Yace Daddynki yace ki yi zaman ki sai ya neme ki, kuma kiyi shirin tarbar wasu muhimman baki gobe da zasu zo specially don ke ta yi murmushi ta ce, Daddy kenan, shi gani yake har yau bana son zama da mama ne bai san alkunya nakewa Aunty na ba ta fada tana kallon mamar cikin ido cikin sigar tsokana. Da ganin fuskar maman ka san ta ji dadin maganar ta amma sai ta daure fuska ta ce ke bana son rashin mutunci, Hajiya Saratun kike yiwa alkunya? Don ta kara bata kunya sai ta shagwargwabe fuska ta ce to “Mama ai so-so ne, amma son kai ya fi ko? Ni ma ina son jin dumin mamana da ta haife ni, don Anti Hajjo tace mun tunda aka sace miki ni baki kara dariya ba, sai ranar da kika gan ni ko Daddy?â€? Yayi dariya ya ce, “Kwarai Intisar, in na ce zan baki labarin irin suman da ta…â€? Hajiya Hadiza ta mike tana harhada tangarayen da suka ci abincin a kufule ta ce, “Bari in bar maku wajen, sai ka ji dadin sawa ta kara raina nin tunda ita dama ba kunya ce ta ishe ta ba.â€? Suka yi mata dariya dukkansu. Ba ta bi ta kan su ba ta dauki kwandon kayan abinci ta yi gaba, yayinda Amabassador Basheer ya shiga bata labarin rayuwar su tun daga ruga zuwa kauyen Shanono, har zuwa tahowar su kasar Faransa. Ba shakka ta ji tausayin maman ta sosai ta kuma kara jin kaunar ta a ranta. Sun yi shirin barci ya lura Hadiza dai fushi take da shi, tana tsaye jikin mudubi tana sharce kanta data wanke cikin kumfar pert plus ya zagaya ta baya, kyawawan fuskokin su suka koma cikin mudubin ya ce, “Wayyo ni Bishir ina zan sa kaina? Haddizana na fushi da ni a kan laifin da ban san na yi ba ta ce ba wani nan, kome kake yi mun kana sane, tunda ai na nuna maka bana so. Yarinyar nan fa kana mancewa diyar fari ce baa sakar masu baki hakaâ€? Ya tuntsire da dariya ya juyo ta gaba daya ya ce “Don Allah Dijangala, yaushe zaki shigo gari ne?â€? Babu inda wadannan kyawawan kafafun na Dije na basu taka cikin duniya ba, amma har yau tana abu tamkar tana cikin ruga ko kaugyen Shanono? Ta kara kumbura amma sai tayi murmushi, don yadda ya kirata da Dije rabon shi da hakan tun dawowar shi daga Jamiar Nsukka dake kudu, ta ce, “Ai ko Annabi (SAW) ma ya ce dan kauye sai yayi shekaru arbain a birni sannan ne zai zama dan birni. Ni ko yau shekaru na ashirin da takwas a birni, ka ga kenan har yau da saurana.â€? Ya yi dariya ya ce, “Naji-naji ni dai hakanan nake son Dije na, ko ta zama yar birni ko bata zama ba. Bana fatan abinda zai bata mata rai balle ya raba ni da ita. Neman alfarmar Dije na nake ta dinga sassautawa Intisar tana nuna mata kulawar ta tamkar sauran yayan ta, domin ba shakka ita din abin tausayi ne. Har yau bata kai ga samun cikakken farin ciki a rayuwar ta ba.â€? Washegari tun wajen karfe tara na safe Hajiya Hadiza ta shigo dakin da suke, a lokacin duk sunyi wanka suna shiryawa ta ce, “Me kuke shiri game da zuwan bakin?â€? Intisar ta ce, “Wai su waye?â€? Hajiyan ta juya tana ce wa, “Nima ban sani ba, amma tunda har Daddyn da kansa ya fadi zuwan su ai kin san masu muhimmanci ne. Akwai komi a kitchen in da abinda baku samu ba sai ku yi magana a tura direba kasuwar yan kaba don ni bana jin shiga kitchen din nan a yau.â€? Intisar ta ce a ranta ‘shiga kitchen ai sai mu manyan kuku.â€? Ta dauki mayafin Pakistan ruwan bula da ke jikinta ta yafa ta zura silipas ta fita tana cewa da Hunainah, “Yi kwanciyarki ki huta, ni nan da kike gani ingarma ce a wannan fanning.â€? Ta tuntsire da dariya ta ce, “Ah ah zan taya ki, ai in Allah ya ce ce ka huta sai ka huta, kuma tunda gani a yanzun ko mutuwa ce na ji na gani muyi ta tare.â€? Tayi murmushin da ya tuna mata da wasu alamura da dama da suka gabata ta yi gaba tana cewa, “nagode sister, balle Insha Allah sai na riga ki mutuwa, ko ba komi zaki dage wurin ganin kullum ranar Allah kin yi min addua, kin taya ni yiwa Alameen kin kuma taya ni ganar da Ya Faisal abinda yake tunani game da ni ba hakan ya ke ba, illa dai ba zai taba saurara ta ba, da ya gane wasu abubuwa da kowa bai gane ba. Kwalla ta ciko idon ta, ta yi saurin fita don bata son Hunainah ta gani, ta san halinta yanzun sai ta fita damuwa, Hunainah ta yi dan jim, can kuma tayi tagumi tace “Oh Allah! Ka dubi wannan baiwa taka, ka bata soyayyar nan da take nema mai barazanar raba ta da duk wani farin-cikin da take ciki.â€? Wayar ta da ke kasan pillow ta shiga kida cikin daddadan sauti, kamar ta kyale ta bi bayan yar uwar ta sai kuma dai ta daga, ganin bakuwar lambar mai layin glo kuma ta nan cikin gida Nigeria ta sha mamaki, ta san dai dawowar ta kenan bata hadu da kowa ba balle ta bashi nambarta, gashi ba lambar Hidaya ba bata su Najib ba. Cikin sassanyar muryar ta mai zaki da taushi ta ce, “Yello! Hunainah Bashir ce a kan layin?â€? Daga daya bangaren Hashim ya yi wata irin ajiyar zuciya, ya ce “Don Allah Hunnainah, ki saurare ni kar ki katse, Hashim ne da kuka gamu da shi a filin jirgi, pls Hunainah help me, zuciyar zata narke in kika ki sauraron ta?â€? Ta yi murmushi, muryar shi da yanayin maganar shi cikin nutsuwa su suka fi daukar hankalin ta, cikin kwantar da murya da ita kanta bata san ta yi ba, ta ce, “To Hashim, mai ka ke so?â€? Da sauri ya ce, “Hunainah! Hunainah na ke so don Allah!! Ta kyalkyale da siririyar dariyar ta da tafi zakin sarewa a kunnuwan shi, ya kara kwanciya sosai a doguwar kujerar da ya ke kwance, ya kankame wayar gam kamar mai tsoron kada wani ya fizge, ya cigaba da magana cikin shauki da bege. “Allah Hunnainah tun a Air-port din Cairo kika kwance mun kai, baki bar ni da wani tunani ba ko kankani sai naki, don Allah ki amshi kokon barana ki sammun gurbi a zuciyar ki ko yaya ne zan ji dadi in tsugunna a nan har zuwa sanda zaki bani babban gurbin. Na yi maki alkawarin Insha-Allah ba zaki yi dana sani a kaina ba, ba za kiyi da na sani da zamowa na uban yayan ki ba, zan yi kokarin zama masoyi mai amana. Ki bar hadani da sauran mazan da aka ce kina tsoro don wallahi ni ke na ke tsoro Hunainah, sai yadda kika yi da ni. Cikin kwana dayan nan rak ba ki barni da tunanin komai ba sai na kyakkyawar fuskarki da fushin ki da kame mutuncin kanki. Ki yarda ba duk mazan ne muka taru muka zama daya ba, akwai masu soyayyar tsakani da Allah, wadanda zasu iya bada rayuwar su da komi da suka mallaka a domin ki Hunainah. Ki yarda da ni you are very special (ke ta musamman ce) ko zaayi yaudara ba zaa yaudare ki ba.â€? Gaba daya ya kashe duk wata laka dake tare da ita, ta zamo pale duk wani kuduri da tunani da take da shi a kan maza, Hashim ya warware shi a yau. A tsaye take a da, amma bata san sanda ta kai ga kwanciya bisa rug-carpet dake gaban gadon ta ba. Tana murmushi rungume da wayar kamkam ta kasa cewa komi yayinda shi kuma Hashim ya cigaba da ragargaza mata zuciya da dadadan kalaman shi har ta yarda ta amince ta kuma tabbatar wannan dai na daban ne, kuma shine Mr. Right din da ta ke nema. Muryar shi ta yi kasa sosai ya ce cikin matsananciyar damuwa. “Plz Hunainah say something mana? Shin am I accepted? Ta ce cikin shagwabarta da ta saba yiwa kowa, “To ai kai ne dadin bakin naka yayi yawa, bayan nasan matarka ma duk hakan kake fada mata?â€? Ya kyalkyale da dariya ya ce, “Eh mana, matata ma Hunainah duk haka nake gaya mata, amma nafi son Hunainah akan Hunainah.â€? Ta ce, “Itama sunanta Hunainah?â€? Yadda furucin ya fito daga bakin ta cike da kishi abin tausayi bai san sanda ya kankame fillon kujerar ba, tamkar ita din ne ya kankame ya ce, “Sunan ta kenan Hunainah Bashir, I love her very- very much!.â€? Ta ja wata irin kakakarfar ajiyar zuciya, wani dadi ya ratsa shi cikin murmushi ya ce, “To ya, Hunny na, in zo Kano domin ki? Ba zaki haramta mun ganin wannan kyakkyawar fuskar ba, ba zaki yi mun rowar wanan daddadar muryar ba?â€? Ta yi dariyar ta mai ban shaawa duk da baya ganin ta ya ji ta har cikin ran sa, ya ji ta har cikin jinni da jijiyoyi, tsuma kawai yake cike da bege saida ta ja aji ta ce, “You are welcome.â€? Ya ce, “gobe-goben nan fa?â€? Ta ce, “Ahah sai dai next week ban gama hutawa ba tukunnah.â€? Yayi shiru kusan minti uku bai ce uffan ba, ta yi zaton ajewa yayi har zata kashe itama sai ta ji ya ce, “Kada ki yi mamaki kamin kwana bakwan da kika ambata kin ji labarin mutuwa na, kuma ke ce sanadi Hunainah.â€? Ta ce, “Me yayi zafi Hashim ko yau ne ka zo, am sorry.â€? Ya ji dadin saukin kanta da saurin amsa kuskuren ta, ya na son mace mai saukin kai da rashin amfani da soyayyar da ake mata tana azabtar da mai kaunarta, ya ce, “Na gode Hunainah, ki gayar mun da Yayar mu kamin in zo mata gaisuwar surukai, wai don Allah ya sunan ta ne?â€? Ta ce, “Saratu Intisar take, zata ji sakon ka yanzun nan, don ma ta fita ne da kun gaisa, zan je tana jira na.â€? Ta lura in don ta shi ne su kwana suna yi ba zai gaji ba. Ya yi murmushi ya ce, “Wai ke mai wayo, to ai ban gaji da jin sassanyar muryar nan ba Hunainah, ni ya za ki yi da ni to?â€? Ta yi muramushi ta ce, “Zan kira ka in na gama Hashim ka yi hakuri, baki ne zamu yiâ€? Ya ce, “Shikenan Hunainah, sai me zaki dan ce mun da zan rinka tunawa kamin bakin su tafi?â€? Ta yi dariya sosai tace, “Wohoho Hashim! Me kake ci na baka na zuba? In dai Hunainah ce ka samu, Im only yours!â€? Ya cillar da wayar ya rungume filon kujerar yana na gode, na gode Hunainah and Ill forever be yours too!â€? How much do you like this story? 5/16/22, 07:35 - Ummi Tandama😇: ____________________________ *âœðŸ? SIRADIN RAYUWAâœðŸ?* Book four *@Takori* Page8ï¸âƒ£ Da gudu ta fada kitchen din ta kankame yar uwar ta, ta daga ta cancaras tana juyi da ita a kitchen din ta ce, “Aunty Intisar sunan ki daga yau, kin yi mun abinda har abada bazan manta ba, me kike so in miki nima in faranta miki don Allah?â€? Ta ce, “To aje ni in gaya miki, kada kirjin ki ya bude?â€? Ta dire ta tana dariya ta ce, “Wallahi baki da nauyi, shafal kamar na dauki bokitin ruwa.â€? Ta bita da kallon mamaki ta ce, “Hunainah, dama kina da karfi haka?â€? Ta juya mata baya cikin jin kunyar abinda ta yi, ita kanta bata san inda karfin nan ya fito ba, karfin soyayya kenan? Ta dafa kafadarta ta ce, “Me ya faru ne sister, you look so happy than ever, whats the matter? (Da alama kina cikin, farin ciki fiye da koyaushe, me ya faru?) Ta juyo ta koma cikin nutsuwarta ta ce, “Ke share kawai, nayi passing papers dina in ji Saajid Marwan (abokin karatun ta).â€? Ta san halin Intisar sarai, yanzu idan ta ji zancen nan sai kowa a gidan ya ji, tsiya kuwa da zasu yi mata ita da Hidaya, sai ta kasa kurbar ruwa a gidan don ta sha ce musu ba wanda ya isa ta bata muhimmin lokacin ta a kansa, sabida duk mazan mayaudara ne balle Hidaya da tayi saurin yarda da Najib bata ko tunanin karatun ta, gata nan har yau ta kasa komawa karatun, Najib sama- Najib-kasa bata da wani aiki sai nasa ga tsohon ciki tun bata cimma komi a rayuwa ba (a tunanin ta fa). Intisar ta yi murmushi don ta sunsuno yar uwarta ta amma sai itama ta bagarar ta ce, “Shine kuma sai ka ce yau kika fara cin jarrabawa, idiotâ€? Ta sa hannu ta lakace mata hanci ta cigaba da kwabin da ta ke cikin mider, ta ce, “Je ki daki ki cigaba da hirar ki da Saajid Marwan din naki, ko dai da shi zaa yi ne?â€? Ta kyalkyale da dariya tace amman kin yanke ni, wannan abu dan kutuf ya kuttun tofa miyau? Ta ce, “Yi a hankali dai ke mace ce, kada ki haifo irin sa ko wanda ya fi shi muni.â€? Ta dubi yawan aikin da Intisar ta yi cikin dan lokaci tana can tana soyayya, ta jinjina kai ta ce, “Amma ni a ganina Hajiyar su Najib ba karamin taimakon rayuwar ki tayi ba, tayi miki horo na ya mace, abinda kike yi ni ko rabin rabin sa bazan iya ba, ke ko cake wannan wallahi ganin wahalar in zauna in kwaba na ke.â€? Ta yi murmushi ta ce, “Nima na sha tunanin haka, in banda dukan da take mun da kebur, da shocking din da take jona mini kamar wata barauniya, da zagin da take mun na fitar hankali da ni da Anti Saratu, da gorin da take mun a kan son yayanta, wallahi da na gode mata.â€? Hunainah ta fiddo ido ta ce, “Shocking fa kika ce? Ta girgiza kai cikin tuno tsohon bakin ciki ta ce, “Shi fa, ke dai kawai a share, ban taba gayawa kowa ba ko Antina sai Alamin, na barwa raina, na barwa Allah ya saka min abinda matar nan ta wanzar da rayuwanta a yi mun, na barta da fitowar rana da faduwarta, na bar ta da duniya da abinda ke cikinta, na bar ta da Allah!â€? Hawaye suka ciko idon ta, Hunainah ta ce, “Menene kebur? Ta ce, “Wani siririn karfe ne da ake daure itace da shi, yafi bulala zafi, ya fi kututturen ice shiga jikin dan adam, kada Allah yasa a doke ki da shi Hunainah. Ta janye rigar ta sama ta nuna mata gadon bayan ta ta ce, “Duba nan ki ga, wannan tabon har abada ba zai goge daga kafafuna da gadon baya na ba, kamar yadda har abada bazan yafe mata ba.â€? Hunainah ta dubi zanen da ke gadon bayan ta wani a kan wani, sai dai yabi lafiyar jikin ta ya fara bacewa, ta share kwallar idon ta tace ido na idon matar nan Unh! Intisar ta yi murmushi ta ce, “Kada ma ki fara wannan tunanin, don a yanzu ta zame maki dole, kakar dan ki da Hidayah zata Haifa, ni kuwa ta gama mun komi tunda ta haifa mun Alameen ta shayar da shi, ta so shi, ta kauna ce shi fiye da komai a rayuwar ta, ta haifa mun Faisal daya zamo ginshiki kuma tushen duk wani mataki da na taka a rayuwa. Ya so ni, ya kaunace ni yayi duk iya kokarin sa wurin gina mun rayuwa mai inganci. Ina tabbatar miki duk wani hakilon Faisal na rayuwa domina ne, ni yake nemawa, bai damu da kansa ba tunda yana daga tsatson Hajiya, bana jin ko jikokin jikokin su zasu taba wahala a rayuwa. Tana da arzikin da hankalin ki ba zai taba baki ba don haka ni yakema tanadin rayuwa amma ba shi ba. To don ta ki ni bata yi laifi ba, don ita zuciya an halicce ta da kishi a kan abinda ta ke so, ta na son yayan ta, su kuma suna so na, dole ta yi kishi dani.â€? Hunainah ta yi ajiyar zuciya ta ce, “Allah ya saka miki.â€? Ta ce, “Wannan kawai itace magana Hunainah, A bar wa Allah ya fi a ja Yasin. Yanzu me ta isa ta yi mun a duniya sai dai in mata in kwana lafiya, to amma ba zan yin ba, ko gobe na gan ta durkusawa zan yi har kasa in gaishe ta, don na san Alameen ko a ina ya ga Mamata ba zai yi mata kallon banza ba, zai tsuguna da guiwoyin sa ya gaisheta cike da girmamawa. Ya gaya mun cewa kiyayyar da take min bata da dalili Allah ne ya daura mata, ba don kuma wani aibu na ta ke ki na ba, illa kawai ta samu kanta a mai ki na. Sai in fidda ta cikin masoyana in rungumi masu so na. Bai yiwuwa mu samu soyyaya daga kowa don ko Annabin rahma Allah bai bar shi ba makiya ba. Kenan ya dace na yi mata uzuri. Uwa- uba tana auren mutuminda bani da kamar sa a duniya, tana auren Daddy Makarfi, da dadi ba dadi ta yi hakuri ta zauna da shi cikin kowanne hali. Ni kuma duk mai kaunar sa abin girmamawa ne a gareni. Don haka a ranar da kika yiwa Babar Alameen rashn kunya, a ranar zan lakada miki dukan da baa taba yi miki ba!â€? Ta rungumeta tana dariya ta ce, “Allah ya sauwake ki doke ni dukan haushi sai dai ki yi mini dukan kauna.â€? Ta ce, “To ko ke fa?â€? Cikin dan lokaci sun kammala aikin su mai ban shaawa, abinci kala-kala har kala bakwai Intisar ta shiryawa bakin ta da bata san ko su wanene ba, abin sha kala hudu, (snacks) kuwa baa maganar su kala-daban daban mai ban shaawa. Gabadaya abincin ta babu irin namu daga na Masar sai na Korea. Sai da kasusuwan bayanta suka amsa kas! Kana ta shiga wanka. Ta dade tana gyaran fatar jikinta da mayuka masu gyara fata da sanya taushin fata, irin su aveeno E45 da norwegian formula kamin ta shirya cikin wani tattausan lesi (cotton) baki mai kananan duwarwatsu, ta killace gashin kanta cikin hair bound ta mulke siraran labbanta da lip-balm mai sanyin kamshi, ta kuma feshe jikin ta da turaren cKIn2U. Iyakacin kwaliyar ta kenan a kullum cool don ko kwalli bata damu da ta sanya ba sai Anti Saratu ta matsa mata. Hunainah na gefen gado can a makure tana amsa waya cikin yar karamar murya don bata son Intisar din ta ji, da ganin yadda take kashe murya kasan da masoyin da a ke matukar so ake magana. Intisar ta yi biris da ita kaman bata san me take ba amma a ranta tayi dariya tayi har ta gaji. Ta na zaune a gaban mudubin bata mike ba tana fesa turare wani dan yaro da bai fi shekaru biyu ba ya yane labulen dakin ya shigo yana zare kyawawan idanun shi alamun bakunta, yatsun shi biyu duka a baki yana tsotso, sanye yake cikin caftan na purple shadda rini me tsadar, kafar sa daure cikin farin kambas. Da farko dai zuciyar ta ce tayi wani irin mummunan bugu kafin hawaye su biyo baya su bata mata kwalliyar fuskar ta, kirjin ta yana harbawa da sauri da sauri ta karasa ga yaron, ta zube ragwaf a gaban sa ta kama hannuwan shi da ke cikin bakin sa ta rungume shi sosai a kirjin ta, hawayen ta na zuba a gadon bayan sa. Ganin babba tana kuka shima sai yasa kuka, ta yi saurin share idon ta tana dariya ta cira shi zuwa gefen gado ta zaunar da shi a kan cinyoyinta ta jawo jakar Hunainah da bata rabo da choculate ta dauko kit-kat ta bare ta bashi, ta ce, Alameen Alameen Bello, suna na Aunty Intisar, ka na so na? Ya gyada mata ka kawai cikin halin ko in kula, ta ce wa ya kawo ka? Yace Uncle dina da Baba na. To ai uncle din nashi da Babannin nashi suna da yawa, don haka bazata ce wanne ne ba wanne ne ba. Ta ce ka ga shi wancan Alameen din yana sona, yana yi mun murmushi, kaima kayi mun murmushi don Allah? Gaba daya ya bude bakin yana yi mata dariya da kyawawan hakoran shi, beauty point din da cleave suka lotsa a tare, tayi saurin juyawa tana share hawaye. Hunainah ta kashe wayarta ta dauki yaron a cinyar ta, itama kwalla ta cika idonta tace Allah da girma yake, Intisar ashe akwai irin wannan kama ta da da uban sa? Intisar ba baki, tace Alameen ka ga ka sa Aunty Intisar kuka, ka bata hakuri ya kai dan hannunshi ya shafo hawayen ta, ya sauka daga cinyar Hunainah da gudunsa yayi waje, a hausar shi wai Baban shi zai je ya nunawa Antin tana kuka. Hidayah ce ta shigo Najib na biye da ita kaman jela, kafin ka ganta sai ka fara ganin tulelen cikin ta sabida girman sa, kafafunta sun kunbura haka ita kanta ta zama katuwa basu san sanda suka fashe da dariya ba. Ta juya cikin shagwaba, hannunta a ido tana kai karar su ga Najib. Ya ce, “Kyale su honey, shekara mai zuwa duk haka zasu koma suma, gara ke tare zamu yi nakudar mu mu biyu mu haife kayan mu.â€? Hunainah ta ce, “Tab! Allah ya nuna mun wannan rana, wallahi bayan taga zai koma ya na leken ki, ki na wayyo Allah Najib, ba ka ce tare zamu yi nakudar ba, ya zaka tafi ka barni ni daya? Tana yi tana gwada irin rike kwankwason da Hidayar zata yi gaba daya suka sa dariya har ita.â€? Najib ya ce, “A bar zancen wasa, ke Intisar bakuwa kika yi tana falo, Maman Hunainah ta ce ku je dukkan ku. Kin ga dan ki ko? Ta sukuyar da kai a hankali ta ce, “Eh, Alameen ya girma fiye da yadda na zace shi, kamannun shi da Baban shi har sun yi yawa.â€? Ya yi murmushi ya ce, “Kowa haka ya ke cewa.â€? Duk sai suka yi shiru dukkansu, babu shakka kowa Alameen din ya tuna. Najib ya bagarar ya dubi Hidayah yace zani cikin gari honey, take kia of yourself, pls, me kike son in taho miki da shi? Ta yamutsa fuska tace kafafunnan sun matsa mun Najib, ko asibitin zamu koma? Ya ce yana karasowa inda take kwance a gafen Hunainah, “Aah bari in gani, I can deal with them, messaging din su zan cigaba da yi zasu sace yanzun nan.â€? Gaba daya ya manta da su Intisar da ke wajen, ya debi kafafun ya aza a cinyar shi yana matsawa sannu a hankali. Cikin matsananciyar kunya suka zame daya bayan daya suka bar masu dakin zuciyar su cike fal da shaawar su, barin Hunainah da a take ta rinka kissima wai inama ita ce da Hashim din ta, ita kuwa Intisar tunanin ta shine Allah ya bata mai son ta kamar yadda Najib ke son Hidayah, har baya iya jurewa a gaban kowa nunawa yake bashi da abu mafi muhimmanci kamarta. Ta shiga falon da sallama, amma sai tayi turus, a bakin kofar bata karasa ba. Zuciyar ta na harbawa, kafafuwanta suka sage, jikin ta yayi sanyi; Hajiya Nafi ce, a zaune a falon mahaifiyar ta sai Khaleel da ke shan lemun Ribena. Ta juya da niyyar komawa cikin gigicewa amma muryar da ta ji daga can kofar shigowa ta katse gudun jinni a cikin jikin ta, ta warware tunanin ta kaf ta kasa koda motsa kafar ta balle ta idasa yunkurinta na komawa inda ta fito, muryar Faisal. Ya ce Intisar! Bata amsa ba, amma ta dakata kuma bata juyo ba, shima bai shigo cikin falon ba, daga can bakin kofa yake maganar kamar baya so, da gani don ta zame masa dole ne amma da ba zai yi ba. Ba kuma tare da ya kalli sashen da take ba ya ce (cikin murya ta girma da bada umarni). A matsayin Yayan ki, baa matsayin dan ta ba, ina ganin ya dace ki saurareta. Ba lallai ne ki yarda da abinda zata ce da ke ba, amma a kalla tunda gaba take da ke, ta kuma taso gari-ya-gari domin ki, ta kashe muhimmin lokacin ta tazo gareki, duk da kike kasa da ita, ta zo neman wata alfarma a gareki. Ashe kenan ta san cewa ke wata aba ce mai daraja da zata nemi wani abu daga gareki. Bai dace ki wulakantata ba tunda Manzon Allah (SAW) ya ce bakon ka annabin ka ne. Kuma ko a lahira wani kan ci albarkacin wani. Da haka ya juya yayi ficewar sa. Ya bar mata permanent (tabbataccen) kamshinsa na (5,000 Doller perfume) da har a mafarkin ta jinsa take yi. Hawayen suka idasa zubowa bisa kundukukinta. Cikin dauriya da jarumtaka ta juya ta isa gabanta, ta zube guiwoyinta a kasa hawaye na zuba a idon ta tace Hajiya ina wuni? Ita kanta Hajiyar kuka take yi, haka bata ji dadin kalaman da Faisal yayi amfani da su wajen yi mata magana ba, tamkar ya goranta mata kaunar da suke mata ne, su da suke nema. Ta kai hannu ta dafa kan yarinyar tana share mata hawaye da hannunta, ta kuma sauko daga kujerar da take zaune ta zube gwiwoyinta a gaban Intisar din kamar yadda ta yi, ta ce, “Ki yafe min don Allah Saratu, ki yafe ni Saratu, bani da kalaman da zan yi amfani da su wajen nuna miki dimbin nadamata kan abinda na yi miki. Abinda zan iya cewa kawai shine kiyi hakuri ki yafe min hakika nayi nadama, na yi nadama mara amfani a kan ki Intisar. Kada ki dubi tsakanin ki da yaya na ko abinda suke miki, wannan hakkin ki ne. Ki dubi girman Allah da manzon sa ki yafe mini. Kuskure ne nayi, nasan kuma babu wanda yake sama da shi. Kiyi hakuri da abinda Faisal ya ce da ke, ban san me ye ke damun sa ba. Hajiya Hadiza ta shigo, tana tura troller kwandon kayan abinci zuwa dining da ke gefe guda a falon ta ce wane irin abu ne haka Hajiya? Don Allah ki koma ki zauna. Ta ce, “Aah Hadiza, ki bar ni in roki gafarar Intisar kawai, ko kwanta mata ne sai in yi, in ba haka ba hakkin ta ba zai bar ni kwanciyar kabari ba. Intisar ta kama hannun ta ta maida ta bisa kijerar ta ce shikenan Hajiya, Allah ya yafe mana gaba daya.â€? Shiru ta yi tana mamakin sanyin zuciya irin na yarinyar, tana mamakin kaunar da take wa yayanta. Ta na mamakin hakuri da yakanar ta da daukar alamuran duniya da sauki. Bata zaci ko a mafarkin ta yarinyar zata taba yafe mata ba. Ta tabbata ko don wannan halayyar tata dole kowa ya sota, dole alumma su kaunace ta, dole ta zamo a bar so ga duk wani da muamala ta hadata da shi koda na second guda ne, hakika a yau ta kara tabbatar wa da cewa da a ke ita din yar baiwa ce. Ita kuwa Intisar ta yi laakari ne da fadar Ubangiji (SWA) mai cewa hakikah Ubangiji mai afuwa ne, kuma ya na son bayin sa masu afuwa. Bata duba Alameen ko Faisal ba, ta yafe mata saboda Allah. Ta yi tunanin to me ya sameta bayan kiyayyar da ta ke nuna matan? Babu komi sai alheri. Ita ce dai har ta dangana da asibitin masu hankali. Amma ita ai gata da lafiyar ta sumul kalau a gaban iyayen da aka tsaneta don bata da su. Sun hadu suna cin abinci gaba dayan su har Abban Hunainah, Najib da Hidayah da kuma Khalil da suka zo tare da shi. Hajiya Hadiza tace wai ina Faisal ne a gidannan? Hajiya tace rabu da shi mutumin banza, na rasa inda ya dauko wannan bakar zuciyar kamar tsohon kuturu, ni wallahi har fargaba nake Jumaar sa ta zo ya zo garin Abuja, ya zama wani masifaffen karfi da yaji, abu kadan su Furkan zasu yi ya rufe su da fada in banda Alameen karami babu wanda ya ke ragamawa a gidannan, ban sani ba ko gamo yayi cikin kabilun nan na Lagos don ba kyau ne da su ba. Hidayah ta tuntsire da dariya har tana kwarewa, Najib yayi saurin cika ruwa a kofi ya mika mata yace kin gani ko? Hajiya shiyasa baa son magana in ana cin abinci. Baban Hidayah ya dago ya dube shi yayi murmushi ya ce Najib ka na ji da matar nan ta ka, baka san tafi kowa fitina a gidan nan ba. Ka rage rawar kan nan da kake a kan mace, in ba haka ba zata raina ka. Daga shi har Hidayan sun ji matukar kunya Hajiya ta ce, “Umh-umh, kyale sa ya kula da matar sa, dubi halin da ta ke ciki fa ai dole a kula da lafiyar ta.â€? Hajiya Hadiza da bata san tsamar da ke tsakanin. Faisal da Intisar ba ta dube ta ta ce, “Ke tashi maza ki je waje ki nemo man Faisal, ya zo ya ci abinci.â€? Hajiya ta ce, “Ba zai wuce bencinnan na wurin masu gadi ba, ki ce da shi ya zo ina kira yanzun nan.â€? Sai da kirjinta ya harba kamar ta ce wayyo Allah! Ta mike talau! Juwa ta kwasheta saura kadan ta kai kas, Hunainah ta tallafe ta tace yi a hankali, kujerar nan zata tade ki Najib ya dago ya dubesu yayi murmushi kawai ya dauke ido a kan su. Ta fita cikin kasala da rashin kuzari amma sai ta labe a hanyar zuwa wajen bata je din ba, a ranta cewa take lallai ma ya Faisal! Har yau bai gama sani na ba, ba dai ni ce baya son gani ba, ni mujiyar sa ajalin sa to nima bana son ganin sa ko hanyar daya bi nima na daina bi. Hawayan da basa wuya a idanunta suka zubo. Ta sa gefen rigar ta ta share ta dawo falon ta zauna a mazaunin ta tace yace ya na zuwa. Shiru shiru babu shi babu alamar sa har suka kare cin abincin. Abinda kunnuwanta suke jiyo mata Hajiya na baiwa mamarta labari ta kasa gasgata shi, hakan nan ta kasa amincewa da abinda ta ke jin. Wai Faisal ya kawo wa Baban shi mata Bayarabiya kuma bazawara mai yaya uku da suke aiki tare a NNPC wai ita Ronke yace nan duniya ita ya ke so, su kuma sun ce wannan auren sai bayan ran su. Hajiya Hadiza ta yi dariya ta ce, “Ina ruwan kurucci dangin hauka. Kin san idan Allah yayi ma wata baiwa baka gani, sai dai wani ya gane maka. Amma ina mutum kaman Faisal ina auren bayerabiya?â€? Najib ya ce, “To yaya zai yi Hajiya? Wadda ya ke so bata son shi, ba sai ya je inda ake son shi ba?â€? Ya fada ne kamar da biyu, idanun shi a kan Intisar, wadda cikin sanyin jiki ta aje cokalin da ke hannunta ta tashi ta yi dakin su da ke saman bene. Ta sa mukulli ta rufe kofa ta tafi gaban taga ta tsaya kawai, hannayenta sarke a bayanta, wasu irin zafafan hawaye suka zubo a kumatun ta. Kamar an ce da ita juya nan; ta kalli harabar gidan ta tagar. Daga can ta hango shi cikin motar sa porsche kafarsa daya a motar daya a waje, sanye cikin lallausar shadda yar Indonesia ruwan kasa-kasa dinkin Tazarce, fatar agogon roled da ke hannunshi ma ruwan kasa kasar ce haka takalmin fata na kasar Italy dake kafarsa ruwan kasa ne mai duhu. Ya rame ainun hakannan kyawawan idanunshi masu narkar da zuciyar ta sunyi ciki sosai ya kara fari, haka lallausan fatar shi ta kara gogewa sosai fiye da sanin da ta yi masa a baya. Waya ce yake amsawa cikin lumshe ido, da gani zaka san kalaman da a ke gaya mai cikin wayar ba karamin dadi su ke mai ba, don har kwantar da kujerar motar yayi da alama dai cikin matsanancin nishadi yake. Zuciyar ta ce ta shiga harbawa da sauri da sauri don tuni ta fassarawa kanta koda wa yake maganar kawai Ronke Adeyemi. Ta ja murfin tagar da karfi ta rufe garam, tare da zuge labulen gaba daya, ta durkushe a nan ta yi kukan ta mai isar ta. Ta tabbata a yanzun kam Faisal ya daina son ta! Duk wani so, duk wata kauna daya ke mata ya zagwanye sakamakon rashin maida mishi martanin dimbin soyyayar da ya shekara yi mata. Ronke yake so tun-tuni har yanzu kuma bai daina ba, har ta zama bazawara uwar yaya uku still ya na son kayar sa. Ita kuma haka Allah ya so da rayuwar ta? Ba zata taba cin riba a soyayya ba. Allah Sarki! Wai yau ita Intisar ce Faisal ya ke neman maraba da ita. Ita din da a da, baya da abin so da gani tamkar ta. Ita din da a da, in bai gani ba baya iya nutsuwa amma a yau rashin ganin ta shine nutsuwar sa, kwanciyar hankalin sa kuma abinda yake matukar so. How much do you like this story? 5/16/22, 20:23 - Ummi Tandama😇: ______________________________ *âœðŸ? SIRADIN RAYUWAâœðŸ?* Book four *@Takori* Page9ï¸âƒ£ Hunainah ta dafa kafadun ta, ta dago a hankali ta dube ta, sai ta rungume ta da karfi tayi kukan ta mai isar ta a kafadun yar uwar ta. Ta ce, “Hunainah ni kuma haka Allah ya so da ni? Soyayyar yayan Daddy ne zata kai ni kabari na. Hunainah ya Faizal ya daina so na, leka ki ga da Ronke yake magana, ni kuwa ko gani na baya son yi.â€? Ta ci gaba da kuka sosai yayin da Hunainar ta shiga taya ta suka yi tayi kamar wasu yaran goye. Ta ce, “Ni wallahi zan je yanzu in bawa Ya Faisal hakuri, in gaya mishi hakikanin abin da ke zuciya ta. Idan ya auri Ronke din nan Allah Hunainah mutuwa zan yi nima in bi Alameen sai mu yi auren mu a can.â€? Hunainah ta yi murmushi duk da hawayen da ke zuba mata, ta tabbata yar uwar ta bata cikin hayyacin ta, soyayyah na neman zautar da ita ta ce, “Aah, baza ki je ki bashi hakurin ba, me ki kayi masa? Laifin da kasan kayi shine kake bada hakuri a kai amma ba wanda baka san ka aikata ba. Ai ko Allah baya kamamu da laifin da muka yi a bisa kuskure. Mutun mai laifi, shi yake kama kansa da kansa ta nuna cewa ya san da wannan laifin. Ki bar shi ya je ya aure tan mana, sai me? Sai aka ce daga kansu babu sauran mazan aure?â€? Ta share idonta tana murmushi ta ce, “Akwai maza da yawa a duniya. Amma a zuciya ta babu kaman Faisal! Ni kadai nasan shi ko wanene? Alkhairin sa da karimcin sa masu yawa ne a gare ni. Yafi karfin komi a waje na. Ina tabbatar miki Faisal ya fi so na da komi na duniya. Duk wannan son da kika ga Alameen ya yi mini, wallahi wallahi Faisal yafi shi so na. Illa cewa shi Alameen baya iya boye abinda ke zuciyar sa kuma baya iya controlling din ta akan abinda yake so. Sabanin Faisal da ya kasance mai juriya da karfin zuciya, ta yadda ko da a ce son zai kashe shi zai iya jurewa ba tare daya nuna ba. Ki taimake ni Hunainah in ganar da shi irin asalin kaunar da nake mishi yafi gaban duk wasu kananun zargi daya ke yi a kaina. Ko me zan fada niki game da ni da ya Faisal ba zaki gane ba, da dai a ce kinsan irin rayuwar damu kai a baya ne. Abinda nake so kawai ki gane shine Faisal, wani mutun ne precious wato mai darajja da kima a zuciyata da girman sa da darajar sa da na ke gani ya zarta na kowa in kika dauke Daddy da Antina. Ronken nan da kika da kika ji ana ambato ba son ta ya ke ba, zai aure ta ne kawai don ya rama tozarci da cin amanar kaunar da yake tunanin nayi mishiâ€? Ta sa gefen dankwalinta ta share idon ta, ta fyace hancinta ta yi murmushi cikin takaici ta ce, “Hunainah, a lokuta da dama wasu alamura na rayuwa kan zo wa mutum ba a yadda ya tsammana ba. Na so Faisal tun yana a yaya na jini haka a gaba dayan rayuwata son shi nake ni din ban sani ba. Soyayyar Alameen irin soyayyar nan ce da ke shigar mutum farat daya, ta rugurguza duk wani tunanin hankali da ya mallaka, kasancewarsa wani irin mutum na daban a cikin alumma, komi na shi ya kasance in style yadda babu zuciyarda ba zata kwadaitu da kasancewar sa abokin rayuwarta na har abada ba. To haka ta ragargaza min zuciya ba tare da tsammani na ba, wanda a lokacin ban taba tunanin zan so wani da namiji a duniya bayan wannan ingantaccen son zumuncin da na ke wa Ya Faisal wanda a wani bangaren ba haka ba ne; so ne na soyayyah, na shaawar komi na shi. Sabanin kaunar Alameen mai shigar mutun farat daya, soyayyar Faisal a hankali ta shige ni, ta bi jinni da tsoka, kasuwa da bargon jikina tun ban san kaina ba, ta yadda ko muryarsa na jiyo daga waje jikina ya fara tsuma kenan, haka zuciyata zata fara rawa ina dai kokari ne ina boyewa saboda Anti, da sanin cewa hakan ba dai-dai bane haramun ne, haramun din ma wanda Allah ya yi kakkausan hani a kai. Shima kamar ya san hakan, sai ya tafi. A lokacin ne na samu nayi jinyar zuciyata har ta warke. Sai kuma Alameen ya zo, shi kuma da wata irin masiffafar soyayya mai shiga rai a lokaci daya. Duk da haka ina kokarin in tuno Faisal da dinbin karimcin sa. Ko a sanda na shiga wannan daumuwar da kukan zuci, bayan fitowar mu daga asibiti, kuka kasa gane hakikanin me ke damuna har kuka yi fushi kuka ce zaku tafi? Wallahi ba komi bane damuwa da halin da Faisal ke ciki ne, damuwa da alamarin sa ne da ganewa da nayi ashe shima irin son nan da nake masa ya ke yi mun. A hakan sai na samu kaina cikin halin dimuwa da rashin abin yi. Duk da cewa kaunar Alameen ta fi rinjaya na alokacin amma na tuna Faisal, na tuna alkhairinsa, na tuna karimcinsa, na tuna kyautayin sa da jin kansa a gare ni. Babu abinda mahaifiyar sa bata ce da shi a kaina ba, babu irin wulakacin da bata yi masa a kaina ba amma yace ya ji ya gani shi mai kaunar mu ne da ni da Anti na. Sanda ya tambayi Hidayah cewa wai ko zata iya aurensa, baki ji yadda na ji a raina ba. Na ji tsoron in tace eh, to ni ya zanyi da rayuwata, yaya zan ji a raina? Sai na gode Allah da tace aah duk da nasan ni din bazan hada yanuwa biyu in aura ba. Ke Hunainah in nace zan gaya maki matsayin Faisal a zuciyata sai mu kwana mu wuni ban gama ba. To don Allah meye laifi na a nan? Ta ina naci amana? Yaya yake so in yi da raina? In banda ke ba wanda zan iya budar baki in gayawa zuciyata Hunainah, ki taimakeni in ganar da shi abinda ba zai taba ganewa ba, ba tare daya saurare ni ba. Ta cigaba da kuka mai motsa zuciyar duk wani mai sauraron ta. Hunaiah ta ce, “Duk na ji, amma wallahi baza ki je ki wulakanta kanki a gabansa ba. Idan kika gaya masa hakan a yanzu cewa zai yi don kin rasa Alameen ne ba zai taba yarda da ke ba. Ki barwa Allah alamarin ki roke shi zabin alkhairi cikin rayuwar ki.â€? Hakika nasihar yar uwarta tayi tasiri a gare ta, ta samar da nutsuwa a zuciyar ta. Ta ce Allah gani gare ka, na baka zabi ka zaba mun da mafi kyau. To a gaba daya kwanaki biyun da su Hajiya suka yi a gidan bata kara ganin Faisal ba. Akwai wani abokin sa Tajudden mutumin Kano a unguwar Yan kaba can wajen sa ya ke wuni, tun safe yake ficewa bai taba cin abincin gidan ba. In banda Najib, Hidaya da hunainah babu wanda ya san me su ke ciki. Haka Najib ya yi iyaka kokarinsa don ganin Faisal din ya zauna ko na awa daya ne a gidan don su dai-dai ta da Intisar din amma ya nuna baya bakata kai ko son ganin ta ma ba ya yi, ya matsu lahadin ta zo su tafi don dai baya son iyayen su tuhume shi ne amma da tun jiya ya yi tafiyarsa. Hidayah ta tabo Intisar da kafarta tana nuna mata Hunainah data rakube a gefe tana amsa waya sai kwasar dariya take cikin nishadi, ta ce cikin rada, “Wai wannan saurayi ta yi ne?â€? Ta yi murmushi ta ce, “Ke sai yanzu kika lura? Ai jiya abinda ta kwana yi kenan sai da na sa tissue na toshe kunnuwa na don dariyar ta ta hanani barci kamar wata shashashar madinaâ€? Hidayah ta ce, “Ina ruwan farin shigaâ€? Suka yi dariya suka tafa. Ta sha jinin jikinta, ta dan juyo ta kalle su suka juyar da kai suna wata hirar daban, ta juya ta cigaba da hirar ta. Intisar ta ce, “Tunda bata ce miki ba, kyaleta ki bita da hakan ita da kanta zata fada miki, ko ina zaa kai karatun likitan kuma oho! Wannan soyayar ta irin mai sawa mutum ya shiriri ce din nan ce, kwata kwata fa ko wani kwakkwaran kallo batai masa ba, a waya kawai ya wargaza mata planning to ina ga suna tare?â€? Suka kara kwashewa da dariya. Ta dai tabbatar da ita su ke, sai ta fita ta bar musu dakin. Baa jima ba kuma suka ga ta yi kitchen shiru-shiru bata dawo ba ashe girki take delicious, kamshi ya cika hancinan su a take yawun mai cikin ya fara tsinkewa ta ce, “Aa ah, wannan yarinya wa take wa girki? Don Allah zo muje tsurkuâ€? Intisar ta koma ta kwanta tana cewa, “Ni ba irin ki ba ce, kina abu babu jan girma shiyasa ta rainakiâ€? Ta ce “Ai wallahi sai na je, kuma sai na ciâ€? Tana taku da kyar da kyar ta nufi kofar fita sai taba Intisar dariya. Hunainah a kichin tare da Lami mai aikin su tana taimaka mata, ta hada abinci kala-kala irin su (Badadis, ruzz wa dajaj, ful wa tamis, mabkabkah, firakh, shawarmah da pizza) ta killace a cikin wermers. Hidayah ta shiga bubbude wermers din tana sa cokali tana kai loma, da gudu Hunainah ta zo tana rufewa, ta ce, “Me kike nufi? Ni bani da kwano a gidan ko me?â€? Ta ce “To dama ina kwanon yake? Na dauka tunda anyi miki kayan aure an sallame ki daga gidannan?â€? Ta ce “To wallahi sai naci abincin nan tunda ba ke kika yi ba, solobiyar banza ba fuss ba ass rakiyar mata duniya.â€? Intisar dake shigowa tayi dariya, ba tun yau ba fadan Hunainah da Hidayah na bata dariya, idan suka fara kamar sa cinye junan su fada dai irin na sakonnin juna da baya karewa. Ta zo ta shiga tsakani ta ce, “Ke Hidayah rabu da wannan ki debi wancan na cikin tukunya tace a kan me? Ga na saman tukunya zaa ce inci dandakakke? Shi wannan din na wanene na san dai Daddy baya cin abincin larabawaâ€? Ta ce, “To neman rigima kike, zan kai karar ki wajen mijin ki, haka kawai kizo gidanmu zaki fitine mu a wane dalili?â€? Hadayah dai ta rantse sai ta debi abincin nan don bata ga amfanin sa ba, kuma miyanta ya tsinke dan cikinta yana ta motsi yana tsunkulinta shima yana so ya ci. Ita kuma Hunainar kaman tayi kuka ta rantse baza ta diba ba. Rigima har kunnen Maman da Hajiya da ke zaune a falo, Najib bai yi magana ba kar ya yi a ce yayi rashin kunya, amma shi ma a ransa ya rantse sai matar shi ta ci abinda ta ke so. Dan haka suna falon ana ta mayarwa da maman zance ya zare jiki ya je ya kwashe warmers din duka ya yi dakin da aka sauke su shi da Faisal, kana ya fiddo waya ya kira matarsa ya ce ta ci son ranta. A can falo Hajiya Nafi ta ce “Don me ba zaa bata ba? Ku baku san rigima irin ta ta mai juna biyu ba ko tausayin ta bakwa ji?â€? Intisar ta ce, “Ai an ce taci na tukunya ta ki.â€? Maman ta ce, “To ku me za kuyi da abincin in kun hana ta ci? Ita da zata tafi gobe ta bar maku gidan?â€? Intisar zata yi magana Hunainah ta kyafta mata ido ta ce “Ai abincin ba namu ba ne, bako muka yi wa.â€? Hunainah tana ta kyafta mata ido da take yatsun kafarta alamar tace bakon nata ne, bata kalleta ba. Hajiya ta ce tana murmushi, “Suruki muka yi? To na waye a cikin ku?â€? Intisar ta yi murmushi kawai, cike da kunya ta mike ta yi dakinsu, wannan ya tabbatar masu cewa bakon nata ne kenan. Hajiya ta mike jiki babu lakka, kamar anyi mata duka ta nufi dakin da su Najib su ke, tayi sallama ya bata izinin shigowa, sunyi rashe rashe bisa carpet suna kwasar gara, fuskarta kawai ya kalla ya san wani abu mara dadi na damun ta, amma ganin Hidayah sai ta yi kokarin maida damuwarta ta ce Faisal nake nema, ina yake? Yace yana can cikin gari wajen Tajudden Alhaji tace kirawo min shi a wayar ka ya nuna mata wani gefe can bisa centre table ga wayar shi can, anan ya ke barin ta, baya fita da waya. Tace duk sanda ya shigo ka sanar dani, ko karfe nawa ne. Ta juya zata fita, har ta kai bakin kofa ta juyo tace amman baku kyauta ba, wannan abincin Intisar bako zata yi, ta zauna ta shirya masa. Don son kai irin naka shine ka satowa matar ka. Wannan ba dai-dai bane sukayi murmushi su duka, don sun dago abinda ke damun Hajiyar, (ta dauka bakon na Intisar ne) ya ce, “Hajiya kada ki damu, bari in je in yo masu take-away in kuma basu hakuri tace kayya! Ba dai kamar anyi a gida ba, kuma ka san wahalar da ta sha wajen yin abin ta? Kai dai ka daina son kai a alamuranka, domin yana jawo nadama mara amfani.â€? Jikin sa yayi laasar da kalamun Hajiyar. Tsam, ya tsame hannun sa daga plate din ya dauki mukullin mota yace da Hidayah yana zuwa. Ya nufi pounded yam da ke kan titin Audu Bako yayo wa Hunainah take-away na sakwara da miyar egusi da naman kaza mai rai da lafiya, ya biya Mr. Biggs na Beirut Road ya sayo snacks kala kala ya kuma je captano ya sayo dankwala dankwalan kaji gasassu ya dawo gidan. Da kansa ya je ya wanke warmers din data shirya abinta ya shirya mata kayanta yanda ta bar shi ba tare da su din sun sani ba ma, don su a tsammaninsu tunda aka yowa Hidayah waya ta manta da zancen abincin. Sai karfe sha daya da rabi na dare Faisal ya shigo gidan, ya soma hada kayan sa cikin jaka don karfe shidda na safiyar washegari zasu hau jirgi mai tafiya Abuja. Najib ya zare jiki ya je ya sanar da Hajiyar dawowar sa. Bai zata ba bai tsammana ba kawai ya ji gyaran muryar Hajiyar akan sa ta sallame a dakin ta samu gefen gadon dake dakin ta zauna, fuskarta babu alamun wasa ko kankani, ta fuskance sa sosai tai ce, “To Ba-Kano, wurin ka na zo.â€? Ya yi murmushi ya ce, “Ka ji Hajiya, har wani dadewa nayi a Kanon da zan zama Ba-Kano? Tace oh oh, naga wai kai kullun zaga Kanon ka ke ciki da bai din ta, ko gaishe mu baa yi.â€? Ya ce, “Wallahi wurin Tajudden nake zuwa, ai kin san shi wannan abokin aikin nawa da ya zo ya gaishe ku a sallar bara?â€? Ta ce, “Allah sarki! Ashe wajen sa kazo, ba wajen mutanen da kake kwana a cikin gidansu ba, ai da ka sani can wajenshi ka sauka, da masu gidan baza su san da kai bama balle har su dinga tambayar laifin da suka yi maka kake gudunsu ko maigidan baka gaisarwa, bayan kana kwana cikin gidan sa?â€? Ya yi shiru, kan sa a sadde ya ce, “Kuyi hakuri Hajiya, wallahi ni ba abinda sukai min, hakannan dai yanzu nake jin bana raayin hayaniyaâ€? Ta sakar mai dakuwa da duk yatsunta goma ta ce, “Su waye masu hayaniyar, ni Uwar ka ko Uwar su Hidayah, ko ko Uban da ya haife su?â€? Ya yi shiru bai ce komi ba. Ta ce, “To magana ta karshe data kawo ni shine bazaka har gidan nan ba sai ka nemi masu gidan ka gaya masu dalilinka na gudunsu kamar makiyan ka, ka kuma nemi Intisar ka bata hakurin gabar da kake da ita sai kace wadda ta dauki bindiga ta harbe danuwan naka, bayan ni uwar sa ni nayi sanadiyyar ajalinsa. Yau da a ce Alameen yana raye, zai so ganin wannan yarinya kullum cikin bakin ciki da baya karewa? Kullum idanun ta kamar na mai takaba, ba don komi ba sai don kaunar ku da Allah ya jarrabe ta da ita, in banda wannan yarinya a duniya wa zai kuma kallona da mutunci bayan irin rayuwar kuncin da na jefa su itada uwar ta, amma bata kullace ni ba, ta yafe mun dunguma dunguman hakkokinta da ke kaina ba tare da wani tashin tashina ko bin baa si ba. Uwar ta da yan uwan ta basu taba kallona da abinda na yi mata ba, sun sani ba wai basu sani ba. Ka sani, ba don ta rasa masoya ne har yanzu ta ke zaune a hakan ba sai don ku da ta kallafa soyayyar ta a kan ku, har bata jin zata iya kaunar wani bayan jinin mahaifin ku. Alameen ya yi kokarin ganin ya jefa yarinyar nan cikin rayuwar farin-ciki iyaka iyawarsa, amma hakan bai yiwu ba, mutuwa ta katse masa duk wani hanzari. Na rantse da Allah da a ce yana raye. Da tuni yarinyar nan ta daina kuka a rayuwar ta, ta daina bakin cikin da har yau zuciyarta bata rabu da shi ba, ta samu madawwamin farin ciki haka a rayuwar ta. Ashe idan baa tausaya mata ba bazaa kulla gaba da ita ba. Ni na san wallahi ba don kai ta yafe mun ba, illa kawai tana girmama ku, tana ganin kima da mutuncin ku fiye dana kowa a duniya, tana darajja ku tana kaunarku kaunar da bata yiwa yan uwan ta na jinni. Da ace bata kaunar ku, da wallahi har duniya ta nade bazata kuma kallon ku ba sabida abinda na ce da ita a can baya balle har ta so hada rayuwa da ku. Ina mai tabbatar maka ko bayan raina Intisar ta sake kuka a domin ka, Allah zai bi min hakkina na haifar ka da na yi da kokari na wajen ganin na inganta maka rayuwa da abinda kake so kake kuma gudu da gangan. Ta sa habar zaninta ta share hawayen da suka cika mata ido.â€? Faisal ko motsi ya kasa, durkushe kawai yake tamkar mai neman gafara. Zuciyar sa ta cunkushe da tunaninnika daban-daban. Ya rasa abinda ke masa dadi, ya rasa abinda ke sanyashi tsanar duniyar da abinda ke cikin ta, ya rasa abinda ke sanyashi nadama a kan Intisar. A ganinshi ai shi ya dace a tausayawa ba ita ba, shi da bashi da saa, shi da yake son maso wani? Shi da bai ci riba ba ko kankani a soyayyar daya wanzar da rayuwarsa a yi mata? Amma wai har shine uwarsa zatayi masa baki a kanta, bayan ita din nan ba abun tausayi ba ce; muguwa ce, mayaudariya ce, azzaluma ce kuma mai son kanta da farin cikin ta kadai? Ya girgiza kai wasu zafafan hawaye suka zubo bisa lallausar kumatun sa, ya ce cikin matsanancin takaici, “Yanzu Hajiya me kike so in yi?â€? Ta ce, “Ban sani ba, shashashan banza kawai. Kana zaune har wani zai aure ta baka cikawa kanka kowanne buri ba, baka cimma wani farin ciki a rayuwar ka ba, ka zo a banza zaka koma a hofi, kana ta kunci da dacin rai kai daya babu wanda ya san kana yi sakarai kawai. Yanzu yanzun nan ba sai anjima ba ka nemeta ku sasanta, ai na san son ta ke lalata ka ba wai ban sani ba, zuba maka ido nayi in ga iya gudun ruwan ka, amma naga abin naka bana kare bane, wanda bai san abinda ke masa ciwo ba. Ya yi murmushin takaici ya ce, “Hajiya, tunda muke a duniya, na taba ce miki ina son Intisar, so na soyayyah, da har kike cewa in aure ta?â€? Ta dube sa a lalace ta ce “Ai fa, shine naga ka bar kasar baki daya saboda tsoron, kada son daka ke yi matan ya fito kowa ya gane, sabida bakin cikin bazaka iya aurenta ba alhalin tana kanwar ka da kuke uba daya? Shi ne kake bata min domin ta, kake yin fito-na-fito da ni duk a kanta. Tun a lokacin na dago ka Faisal, kawai na godewa Allah daya bani ikon cika alkawarin da nayi wa Babanku na cewa bazaa taba ji daga baki na ba ita din ba yar sa bace, na tabbata a lokacin da sai ka aure ta, koda ni din zan ki amincewa. Wannan shine babban dalilina na kara boye maku maganar, don ina ganin bakin ciki na na karshe a rayuwa kuma wanda zai kayar dani a lokacin shine ka aure ta. To amma dubi yadda Allah ke juya alamuran rayuwarmu gaba daya ta yadda mu din bamu tsammana ba, bamu taba zato ba. Ina mai tabbatar maka idan ka bijirewa magana ta a yau Faisal zaka yi nadama mara amfani a gaba dayan ragowar rayuwar ka, irin wadda na yi, danuwan ka ya yi. Ka yi amfani da sauran damar da Allah ya baka a lokacin daya dace, domin in ta wuce, ba zata taba dawowa ba!â€? Ta fada tana kada yatsanta Ibham, lokaci guda kuma ta mike ta bar masa dakin idanun ta cike da hawaye. Ji yayi zaciyar sa ta karye, duk wani sauran kuzari da ke tare da shi ya kare. Ya mike ya fito daga dakin, shi kansa bai san inda ya ke jefa kafar sa ba, kawai ya tsinci kansa a tsakiyar falon gidan. To ina zai dosa cikin gidan nutane karfe goma sha biyu da rabi na dare? Ban da dai uwa-uwa ce kuma dole a bita da yadda ta ke so. Banda ma rigima irin ta Hajiya to ya je yace mata me? Shi fa ko nambar wayarta baya da ita. Above all ma yana ganin magana da ita ma bata lokaci ne tunda ba wani amfani ke gareshi ba. Na farko Intisar-Intisar ce har kullum a gare shi, the past memories will forever remain fresh in him, sai dai ai shi bata son shi, Alameen kadai take so. Shi ba komi bane face yayan da ta ke kauna. Me yasa Hajiya ba zata dubi wannan ba? Me yasa bazai cigaba da zama a matsayin da ta bashi ba ko don tsira da daraja da mutuncin sa da take gani? Tunanin hakan ya sanyashi juyawa, tare da kokarin maida kwallar da ke neman bayar da shi. Amma sai Najib ya tokare masa hanya da kafar shi ta dama. Ya daga ido ya dube shi fuskarsa babu alamun wasa hakan nan bacin ransa ya ninka na koyaushe, ya fito baro-baro cikin idanun sa. Najib din bai kalleshi ba don shi kansa ya razana da tension din da yaga Faisal din a ciki, wayar sa kawai yake latsawa cikin murmushi, cikin saa kuwa bugun farko ta shiga, ita din ce kuwa ta dauka da alama dai cikin magagin barci ta ke, cikin rarraunar muryarta kamar koyaushe tace Yello! Ya Najib ya aka yi? Ya ce ki yi mun afuwa, na katse maki barci. Ki sakko yanzu nan falo ina son ganin ki personally, is vital ki zo da sauri. Da haka ya katse wayar ya maida aljihu. Ya dubi dan uwan shi yai murmushi ya ce, “Gata nan zuwa, kayi hakuri da shishshigi na, I just dont want to loss you, as I lose Ameenu! (Bana son rasa ka, kamar yadda na rasa Aminu) kuma na rantse idan ka cigaba da azabtar da kanka kai ne da wahala, in ma dukanta ne ka yi, amma ka ke tunawa a kullum duk laifin da kake tuhumar ta da shi, bata aikata ko daya ba, zargi kawai kake kuma wallahi in baka yi wasa ba zaka yi nadama mara amfani. How much do you like this story? 5/16/22, 20:23 - Ummi Tandama😇: _____________________________ *âœðŸ? SIRADIN RAYUWAâœðŸ?* Book four *@Takori* Page🔟 Shikam ya shiga uku, wai meyasa kowa ya budi baki sai yace zai yi nadama a kan Intisar? Bai taba yin nadama a rayuwar sa ba, kuma har abada ba zai yi ba! Ita ce dai ya kamata a gayawa wannan. Intisar din wace ce? Wannan daya rike a hannun shi tun tana jaririyar ta? Wannan da ya ci kashin ta ya ci fitsarin ta, yasa mata feeder ya cire mata pampers itace wata mutum da zai yi nadama a kan ta? Yayi murmushi cikin takaici mara misaltuwa ya bude baki don baiwa Najib amsar da ta dace da shi, babu shi babu alamar sa. Nitsatstsen takunta ya jiyo tana saukowa daga saman bene, bai san daliliba kuma ya samu kansa cikin gigicewa da dimaucewa. Wannan tsohon son, wannan tsohuwar kaunar da an ka ce bata taba gushewa sai dai masoyan su gushe, to balle su da suke ras, a bisa ganiyar kuruciyar su. Wai wannan Intisar din Aunty Amarya ce yau ake lika mai yana cewa baya so! Intisar din shi da baya hada kaunar ta data kowa a rayuwar shi. Intisar din da ke zuwa cikin mafarkin sa, tsayuwar sa, zaman sa, tafiyarsa da duk wani alamari da yake gabatarwa. Intisar din da zuciya ke kuka domin son ta, gangar jikin ke azabtuwa domin kaunar ta, yawun baki ke kafewa, gudun jinin jiki ke daskarewa, tunanin shi da hankalin shi gabadaya ke gushewa a duk lokacin da yaji sassanyar muryar ta. Wannan murmushin, wadannan abnormal lumsassun idanun, wannan takun mai kamar na mage catwalk, wannan da wancan, kai everything about her that drives him crazy idan ya bar su a yau, shikenan? Sai ya juyo cikin wani irin slow motion da yafi kama da umarnin zuciya zuwa abinda take matukar so. To itama din kallonshi take, cikin wani yanayi na mamaki da rashin abin cewa. Suka yiwa juna kuri da ido, kowanne na kokarin gano boyayyen sirrin da ke cikin zuciyar dan uwansa. Ba shakka ta ga abubuwa da dama cikin kwayan idanun shi; bayan ciwon so da ya illata su, akwai rashin yarda, tuhuma, zargi da yanayin nan na yaya zan yi da son ki? Ta dai tabbatar bazata iya jure ganin irin wannan kallon na zargi da yake mata ba sai ta juya masa baya, a yayinda hawayen da take tattali suka samu yanchin kan su. Ta daga kafa da niyyar hawa bene domin komawa inda ta fito amma ina! Kafar tace bata san wannan ba, bata amince ba. Wannan Ya Faisal ne fa? Har yau, har gobe wannan Yayan ne da babu kamar sa, Yayan da zata iya sacrificing (sadaukarda) komi nata domin farin cikin sa including rayuwar ta. Shine yau cikin wani tsohon burin daya dade da shi, amma ta kasa taimakawa wurin samar da shi a gare shiashe kenan ita ta cika butulu, dan adam mai manta alkhairi, kaza ci ki goge bakin ki.. ta sake girgiza kai da karfi kamin ta samu kanta zube a gaban shi da dukkan guiwoyin ta. Kuka take na fitar hankali, kuka irin mai gigita duk wani mai imani, kuka take irin mai motsa zuciyar duk wani mai sauraron ta balle Faisal? Ya dira hannuwan shi duka biyu a bangon da ya ke jingine cikin muryar da ta razanata, ya ce, “Enough .. is enough Intisar! Ba tun yau ba ai nasan so kike ki kashe ni, kamar yadda kika kashe min Ya Ameenu? To amman wallahi ko zan mutu bata dalilin ki ba; baki isa ba, kin yi kadan ba a haife ki ba har yau ko wacece ke! Uwa ta ta ce idan kika sake zubar da hawaye domi na bata yafe mun ba, wato tunda kin kasa kashe ni shine zaki sa bakin uwa ya lalatani? Abinda bata taba gani ba sune suka zubo a yau. Yayi kokarin kau da fuskar sa don kar ta gani, don a ganin sa ba karamin ci baya bane Intisar taga hawayensa, hawayen ma domin ta. Kenan ta yi galaba a kansa, kenan shima ba zai iya controlling zuciyarsa ba kaman Alameen in dai a kan Intisar ne? Sai yayi saurin juya mata baya tare da saurin sanya hankici ya share idon sa amma ita din bata fasa kukan ta ba har da sheshshekar da ke kara kona masa zuciya. Ta kama kafarshi ta dama, wani irin karaya, da ya ji zuciyarsa tayi shi kansa yayi mamaki, hakannan kalma ko daya ta kasa fita bakinta, yace sakar min kafa da wata murya tamkar ba tashi ba. Ta ce in na sake ka ai ban gama cin ribar rayuwata ba, ni fa mayya ce, ko ba haka a ke ce muku ba? Don haka in kaga na sake ka Ya Faisal to nima bana numfashi. Kisa kuma tunda na rigaya na fara akan me zan bari? Bayan barin ba zai shafen wannan dattin na baya ba? Ya yi murmushin da bai shirya ba, ya ce haka ne? To ki je ki kama kurwar wasu man, dole sai tamu? Ta share hawayen da suke zubo mata tace ai baka sani ba, takun ce tafi ta kowa gardi. Kuma abinda baka sani ba shine mu mayu in muka fara cin daya a gida, bama hakura sai mun cinye sauran duk. Don haka kai ne babba a yanzu, ta kanka zan fara kenan? Sannan in gangaro Nasir, in iso Daddy karami, in gangaro in dawo Faruk sannan Yasir. Sai in koma kan Idris da Furkan. Shima Najib din ba don na koshi ba, sai don yar uwata da ke samu tana lasa sannu a hankali kamin shima ta kayar da shi gaba daya. Mutun daya kawai zan bari shine Khaleel shima a bisa dalilai biyu; Na farko kurwar sa ta mun kankanta, makale mun za tayi a makogaro. Na biyu kuma ina da burin saka masa abokantakar kurucciya; shi abokina ne, dan uwa na ne, abokin shawara na ne. Cikin halin kunci, dadi, farin ciki da ukuba da na kasance a raynwa, bai taba juyan baya ba, bai taba goranta mun ba. Bai taba daina so na ba kuma bai taba nunan ni bare ce a gare shi ba. Ta cika mishi kafar ta mike da gudu ta yi sama da hawayenta da basu bar ambaliya ba. Amma sabida zurfin ciki irin nata sai ta rakabe tayi kukanta mai isar ta ta share idonta, kana ta lallaba ta je ta kwanta a gadon ta. Idan tace barci ya ziyarci idanunta a yau ita kanta ta san karya ta ke. Wani irin masifar son Faisal da bata taba ji ba ke yagalgala zuciyar ta. Ta kudundune a cikin bargonta tamkar curin alkaki. Gaba daya jikinta kyarma yake kamar ana kada mata gangi, haka a take wani irin sanyi mai huda bargo ya shiga keta tattausar fatar ta zuwa cikin jikin ta, kamin dan lokaci wani zazzafan zazzabi ya rufe ta. Don haka koda tayi sallar Asubahi bata iya ta cigaba da lazimin da take yi ba har zuwa wayewar gari ba; lallabawa tayi ta koma cikin bargonta da take jin da shi da babu duk daya ne a gareta, domin bai taimaka ba ko kankani wajen rabata da wannan azababben sanyin da take ji. Wajen karfe bakwai na safe Hidayah ta shiga jan kafarta wai ta tashi suyi mata rakiya bakin mota zasu tafi. Cikin kankanuwar murya ta ce ki yi hakuri, akwai barci mai yawa a kaina Allah ya kai ku lafiya. Muma nan da next week na ke jin zamu taho Abujan, safe journey. Hidayah tayi murnushi kawai ta juya tana sauka daga matattakalar bene, tana ta korafin zurfin ciki irin na yar uwarta, ga dai damuwa fal a bakinta amma ba zata taba bude baki ta fadi ba. *** A Lagos A birnin Ikko, cikin maaikatar matatar mai ta kasa (NNPC) Engr. Faisal Bello Makarfi ne jingine jikin tagar ofishin sa yana kallon alumma cikin motocin da ke yawo bisa titi, freely, babu abinda ya dame su. Har yau ya rasa sukunin zuciyarsa ya kuma kasa yankewa kan sa hukunci. Babu abinda yake tunani kamar kalamun Intisar gareshi a daren jiya, da irin kukan da ta dinga yi a gabansa. Ya ji zuciyarsa a karo na farko tana mai kalubalantar sa musanman in ya tuna abubuwanda Hajiya, Aunty Saratu da Najib suka ce da shi. Ya dace ya yiwa Intisar uzuri cikin alamarin ta, me zata iya yi akai? Me ta yi na hakika wanda ya zamanto cin amana, ko yaudara? Na farko dai ta so Alameen a sanda bata da kowa, ya nuna kulawa da damuwa da rayuwar ta a zuwan dukkanin su basu san junansu ba. Baya da haka ma wace diya mace ce zata yi arba da Alameen Bello, har ya furta yana son ta tace bata son shi? “Babu! Wannan karya ne!â€? Shi kan sa ya sani wannan a cikin jinin Alameen ne, yana daga cikin baiwarwakin da Allah yayi masa watau farin jinin mata, tun yana sakandire babu irin damben da yammata basa yi a kan shi, balle a lokacin da yake cikakken mutum? Hakannan ya san Intisar tana da wani hali na girmama duk mai kaunar ta, da kaunar duk mai kaunar ta. Ta so Alameen a cikakkun shakarunta na teenage a lokacin da ta san menene so na hakika kuma mece ce kauna? Tana kaunar sa matsayinsa na Yayan ta mai sonta, mai kulawa da ita da alamarin ta, a matsayin sa na Yayan da suke uba daya. Sabanin Alameen da ya zo mata a matsayin wani bako da bata sani ba. Mutuwa dai guda daya ce, sai dai hanyoyin ta yawa garesu. To hanyar mutuwar Alameen ta kasance hakan, akan turbar cika burin zuciyar shi na so da kaunar Intisar amma ba Intisar ce ta kashe shi ba. To ta kashe shi a kan me? Bayan shine kadai wanda zuciyarta ke so da kauna? Wani kishi kuma ya zo ya tokareshi a kahon zucci. Dai-dai lokacin da Tajuddeen ya bankado kofar shi ya shigo. Ya juyo da sauri ya dube shi yayinda shi kuma ya watsa mai katunan da ke hannun shi a fuska, ya ce meye haka na ke shirin gani? Faisal are you in your full-sense? (Kana cikin cikakken hankalin ka) Ya russuna ya dau daya cikin katinan daya watso mishi, katin gayyatar auren su ne Ronke ta bugo take rabawa cikin maaikatar inda itama nan take aiki. Yayi murmushi cikin bagararwa yace to meye abin mamaki? Ba ni na ce ina sonta ba? Ya bishi da kallon ya ga mahaukaci ya ce ko ka san Ronke ita ta kashe mijinta da hannun ta, don kawai ta samu damar auren ka? Yayi dariyar shi mai ban shaawa data kara kular da Tajon ya ce to ai ka ji shi bata son sa, shi yasa ta kashe shi, ni ko akan me zata kashe ni? Ni da ta ke so shekaru dai-dai har takwas? Tajuddeen ya mike yasa hannun shi cikin aljihu yana girgiza kai yace alright, Allah ya baka saa Faisal ya fita bayan ya bugo masa kofar ji kake garam. Yayi tsaki a ransa yace kaga mun mutum da daukar dala ba gammo. A karshen satin ya iso gida cike da zullumi, ya kara ramewa, ya kara lalacewa alamun rashin cikakkar nutsuwa ya game koina a tare da shi. Babban zullumin sa yau ne rana ta karshe da Daddyn ya deba mishi don jin amsa ta karshe daga gareshi tun bayan fatattakar zancen Ronke da ya yi. Ya tabbatar mai daga ranar in bai zo mai da wata kwakkwarar madafa ba auren shi da Ihsan karshen satin ya tabbata, zai daura, duk da ita Ihsan din bata nan ya jirata ta dawo. Idan har akwai abinda yafi daga masa hankali a rayuwa to wannan maganar da Daddy ke ikrari ne. Yana zaune falon Aunty Saratu wadda ke ta fama da fitinar Alameen karami dake ta fatali da komi na falon wai shi a kai shi gidan Baba Najib, ko kallon inda yake bata yi ba, balle ta bashi lemu ko madarar da ta saba bashi idan yana cikin bacin rai don ita yanzu Faisal ya daina bata tausayi haushi kawai yake bata. Wai Intisar din ta, ita ce ake lallamin Faisal ya aura yana bijirewa kamar an ce da shi rasa masoyi ta yi? Tayi kwafa ta ce sai ka isa falon ya fito, tun dazu dama ya ke tambayar isowar ka. Ya mike tamkar wanda kwai ya fashewa a ciki, ya nufi sassan Daddyn zuciyar shi na harbawa. Gwarzon Uba, namiji sauran mazan jiya, na zaune cikin lallausar carpet din karamin falon hutawar shi yana sauraron labarum duniya daga muryar Amurka (Voice of America), a gefen shi Hajiya Nafi ce tana ninke wasu kayan Daddyn da aka wanke. Faisal yayi sallama cikin muryar shi mai cike da ladabi da rashin kuzari, gaba daya suka amsa mai sallamar tare da kai duban su gare shi. Cikin su babu wanda zuciyar shi bata motsa ba da ganin karin ramar da yaron ke tayi a kullum, ya kasa hutar da zuciyar shi, ya tsayar da ita wuri daya ta samu abinda ta ke so. Cikin yayan su baki daya basu taba ganin jarumi kuma mai fin karfin zuciya irin Faisal ba. Ga mamakin sa, abinda bai zata ba Daddyn murmushi ya sakar mishi mai kwantar da hankali ya ce bakin Ikko ne, sai yanzu aka iso? Ya dan ji dadi shima ya yi murmushin, kansa a sadde ya ce eh wallahi, an samu delay ne na isowar jirgi mai zuwa Abuja, da nace zan bari sai gobe to kuma sai naji duk hankalina yayo nan din suka cigaba da hirar su kan aikin shi da karin girma da ya samu, wanda Daddyn ya gani a (television) daren jiya cikin labarun NTA na kasa. Ko kadan bai sako zancen da Faisal din kewa dari-dari ba. Sai da Faisal din yace kwanannan Nigeria zata yi exporting crude oil (fitar da man fetur) zuwa Belgium kuma shine wanda alamarin ke hannun sa, don haka cikin sati na sama yake sa ran tafiya Belgium din zai yi a kalla sati biyu domin yin wasu bincike. Daddy ya maida fuskar shi ta koma ta manyantaka kamar yadda yake yi a duk lokacinda zai masu magana mai muhimmanci ya ce Faisal cikin babbar muryar da ta kada yayan hanjin sa ina maganar mu ta kwana? Ya kara sunkuyar da kai ya rasa bakin magana sai zufa da ke ketowa takoina a sassan jikin shi. Hajiya ta yi tsaki ta ce kaima da laifinka Baban su Khalil. Har yaushe zakayi ta biye mishi yana yi ma yawo da hankali sai kace shi din karamin yaro ne? Ya daga mata hannu yace babu ruwan ki, ai hakkin shi nake son in bashi kuma Allah shine shaida na Faisal ko a lahira bani da hakkin ka. Maganar wannan Bayerabiya na soke ta kwata kwata har abada, koda wasa kuma ko bayan raina kada ka sake tada ita. Dr. Rehab ya aiko neman auren Ihsan a hannu na don haka rana irin ta yau, Jumaa, Insha Allah zan daura auren ka da Saratu Intisar, Ihsan da Rahab, Hunainah da Hashim kamar yadda iyayen su suka danka mini. Don haka tashi je ka. Bana bukatar wata kalma daga gare ka, ba lallashin ka nake ba umarni ne, its order! Saratu nada watanni ukku dazata yi kamin ta koma makaranta don haka ba Belgium ba, in ma birnin Sin ne zaka tafi, amma kafarka kafarta. Duk abinda kuke ciki tun-tun-tuni na sani ba ban sani ba, illa bana so nake shiga personal life din ku ne. Na dauka kai da kanka watarana zaka kawo mun maganar kana son auren Intisar komai daren-dadewa? Ban sani ba, ashe kai tuni ka canza soyayyar da kiyayyah? To don Allah karewar kiyayyah Faisal idan na baka auren Saratu ka yanko min ita gunduwa gunduwa ka kawo min gabana, sannan ne zan san baka son ta! Ka gane ko? Yallah! Kana iya tafiya ka fara shirye-shiryen ka daga yau ko kwandalar ka bana nema. Bai ce komi ba, ya taso ya fito ko ganin gabansa baya yi, bai kuma kara kula kowa ba a gidan, washegari karfe sha daya na rana a Lagos tayi mishi, week-end da yazo da niyya ma ya fasa yi musu Intisar din tazo ta yi masu. To ai kuwa kamar ya sani, a ranar yar halak din ta dira a gidan ita da yar uwarta, murna wajen jamaar gidan abin baa magana. Ta kankame Mamanta tana dariya ta ce ke Baby na sai yaushe zaki girma ne? Dube ki kin zama cikakkar lady abin alfaharin kowacce uwa, shin me Maman Hunainah take baku ne haka? Ta kyalkyale da dariya ta ce, “Kin san Allah Mamar mu ba abinda take bamu sai dan karen fada, ni duk kewarki ta dameni, baki ji ba yadda nake ji na a yau very happy kamar na rabu da kaya ta kai mata dundu ta ce ba wani nan, ni zaki yiwa dadin baki, kin tafi kin ji dumin uwa ni kin mance ni ko waya bakya mun, sannan kizo kiyi min wani dadin baki?â€? Ta rungumeta gaba daya ta ce ayya Mamar mu, ai da tsohuwar zuma a ke magani, you are everything to me! Gaba daya suka yiwa juna dariyar kauna. Ta sake cewa Main Hoon Naa (Im here now) babu inda zan kuma tafiya in bar ki. Aunty tace sai gidan Faisal? Ta yi murmushi kawai ta juya mata baya. Ai ita wannan ta fidda shi a gabanta yanzu. Ko ita mayyar gaske ce ya dace ta sake shi hakannan. Duk da cewa shine wanda zuciya ke ciwo a dominshi, amma ai baya yi da ita yanzun wannan sai Ronke Adeyemi. Da daddare suna cin abinci (tuwon Acca miyar Shuwaka) ita da Daddynta a cikin kwano daya, bayan sun kammala ta je (toilet) ta dauko roba da sabulu da kuma ruwa a kofi ta dawo, ta tsugunna tana zuba mishi yana wanke yan yatsunshi cikin kunfar sabulun camay, suka hada ido suka yi murmushi. Ta kai ta zubar itama ta wanko hannunta ta dawo suka cigaba da hiran bayan rabo tana bashi labarin Al-Azhar ne da yanayin karatun ta. Ya dago ya dubeta da dukkan idanu ya maida fuska ta manyantaka kamar koyaushe zai yi magana muhimmiya a gare su, ya ce, “Saratu har yanzu lokaci bai yi ba ne da zan ga yayanki na gudu cikin gidan nan tare da Alameen-Alameen Bello?â€? Ta sunkuyar da kai, komi ya tsaya mata cik, idanunta suka cicciko. Har yau ta kasa sabawa da ambaton (Alameen Bello) da ake yi a gaban ta. Ta kasa daina zubda hawaye a duk ranar da aka ambaceshi. Ta ce cikin zazzafar murya A duniya akwai mai so na ne bayan kai da Alameen? Yayi murmushi, amma kalaman sun taba zuciyar shi, yace akwai ma wanda ya fi mu! Dukkan burirrikana a kanki Saratu, a yau sun cika, saura guda daya. Shine wannann dadadden burin nawa na in aurar da ke Saratu inda zaa so ki a kaunace ki muddin rai. Shin idan na kawo wani da nake tunanin shine wannan mutum da nake burin in mallaka ki gare shi, shine nake ganin ya dace da zama abokin rayuwar ki na har abada bayan ni, yaya zaki karbi alamarin? Wasu hawayen tausayin Daddy suka zubo mata. Tana mamakin kaunar da yake mata, tana jinjina dimbin son da ya ke mata fiye da yayan daya haifa ba tun yau ba. Wannan ne yasa itama take yiwa komi na rayuwar ta uzuri da Daddy Makarfi. Ta ce wallahi ko kuturu ne zan amince da zabin ka Daddy! Ya daura hannun shi a kanta ya ce albarkar nan da nake ta sa miki a kullun, a yau ma ina karawa. Na zaba miki Faisal a matsayin mijin auren ki, sati mai zuwa zaa daura maku aure. Nima a yau ina neman wata alfarma gare ki irin wadda ban taba nema ba! Ina neman alfarmar ki rike mun Faisal da kyau. Ki bashi farincikin rayuwa da bai samu ba a gaba daya tsayin rayuwar shi. Ki nuna mishi kaunar da yake shakkar ki a kanta, don na tabbata ba gaskiya bane abinda yake zargi a kanki. Na fi kowa sanin son da ki ke mishi. Nafi kowa sanin muhimmacin da yake dashi a wurin ki. Saratu yadda zan baiwa Faisal amanar ki, kema a yau ina baki amanar Faisal don Allah, ku kula da junan ku. Ta dage kanta sama a hankali tana duban ceiling yayinda wasu siraran hawaye suka fito daga idonta suna bin gefen fuskar ta zuwa cikin kunnuwan ta. Ta sauke idon a hankali a kan, Daddy, ta yi murmushi. Yau ce rana ta karshe da take jin ta rabu da bakin ciki a rayuwar ta, ta kuma tsallake SIRADIN RAYUWAR TA! At last, zuciyarta ta samu abinda take so bayan wahalhahu iri-iri. Wannan alfarmar nan kuwa da Daddy ya nema, wani alkawari ne da dama tayiwa rayuwarta tun-tuni koda a ce Daddyn bai furta ba. How much do you like this story? 5/17/22, 07:14 - Ummi Tandama😇: _____________________________ *âœðŸ? SIRADIN RAYUWAâœðŸ?* Book four *@Takori* Page1ï¸âƒ£1ï¸âƒ£ Idan kaga irin soyayyar da aka zubawa tsakanin Hunainah da Hashim dinta, abin sai ya burge ka, ita kanta Intisar ba karamin burgeta suke ba. Sai ka rantse da Allah sun fi shekara da fara kaunar junan su ba sati biyu ba. Duk wasu bincike daya dace a gabatar kamin gabatar da aure Daddyn ya gabatar akan Hashim. Shi Hashim asalin su mutanen Ingawa ne ta Jihar Katsina, aiki da siyasa ya kawo mahaifin shi cikin garin Katsina inda duk suka girma. Babanshi shahararren dan siyasa ne dake rike da mukamin kakakin majalisar wakilai (speaker house of representatives) na Katsina a yanzun. Shine babban dan sa sai kanwarsa Husna ko auren fari baayi mata ba. Gaba dayan karatunsa yayi shi ne a kan kimiyyar yada labarai (Mass Comm.) daga Jamiar Nigeria (Nsukka) a yanzun yana aikin ne da gidan talbijin na kasa. Ya je karo karatu ne a Cairo na tsayin shekaru ukku inda ya hadu da su a hanyar dawowar sa hutu na farko. Don haka Hunainah baza ta samu matsala ba kenan kamar Intisar, tunda in an kare bikin dukkansu tare zasu koma kowa ya nufi makaratar shi amma ai suna tare. Idan ta dubi irin bidirin da Hunainah da Hashim ke shiryawa bikin su sai tausayin kanta ya kamata, wani zubin kuma abin har mamaki ya ke bata. Bata san akwai soyayya irin wannan ba har yanzun a duniya (sai zamanin Alameen) kamar yadda bata san yaushe idon Hunainah ya bude haka ba. Tana tausayin kanta tace Allah Sarki! Ita dai Hunainah mai saa ce, ta samu miji wanda ke son ta yake nan nan da ita ya kuma damu da ita, sabanin ita da angon ke gudunta kamar ajalin sa don tun ranar da aka yiwa Faisal hukunci da aurenta ko keyarsa ba wanda ya kara gani haka ko waya bai kuma yiwa kowa ba. Hajiya ce ma ta damu ta nemeshi, ta taras kwata kwata ya rufe wayar shi ma. Tun abin na damunta har ta dake zuciyar ta ta saki jiki ake komai da ita. A ranta ta kan ce unh Ya Faisal da ni kake zancen, har yau baka gama sanina ba, in dai kiyayya ce to mu zuba amma tunda na amsawa Daddy ba ka isa ka sani in bata mishi ba, ya fi karfin komi a wurina. Idan kai bai isa da kai ba to ni ya isa da ni har yayi yawa. A washegari laraba wato ana i gobe kamun amare Ihsan da Rehab suka dira a gida Nigeria, Ihsan tayi kiba ta kara kyau sosai. Alameen karami ko ganeta bai yi ba yana ta gararin gabansa. Ta shigo falon Anti inda suke zaman lalle ta dungurewa Intisar kai ta ce, “Ke dai na rasa wace irin sister ce, dan (e-mail) da kike mun kin daina, haka yar gaisuwar wayar ma duka kin daina, ni in na kira a ce is switch off anya da haka zaa yi zumuncin?â€? Ta yi murmushi ta zare gilashinta ta ce, “Don Allah ki yi hakuri Aunty Iham, ni wallahi waya bata dame ni ba gaba daya rufewa nake, ga Anti na ki tambayeta Allah ko ita bana kira, kuma da yake na dade ban ziyarci (café) ba na taras sun yi condemning I.D dina, amma bayan biki zan gyara Insha Allah, a yi mun afuwa a karbi uzuri na big Auntyâ€? Gaba daya suka sa dariya. Ta ce, “To me kuke shirya mana ne don ku ne yammata. Mun gayyato bakin kunya da yawa daga MERITIME da Florida, ya dace ku tsara activities masu kayatarwa? Ta kyabe baki ta mike tana cewa oh-oh, wannan ba da ni ba, tambayi wannan masu auren soyayyar, ni da angon ke gudu na kar in cinye shi? Ai ni auren hakuri zanyi ba auren so ba.â€? Washegari aka yi kamunsu ita da Hunainah a Makarfi cikin dakin Goggo Jummai. Hidayah na asibiti likita yi bata bed-rest domin girman cikin ta abin tsoro ma ya koma, sannan ta shiga matakin karshe. Duka sun damu da condition din ta suna kuma tsananta addua kan Allah ya sauke ta lafiya. Washegari Jumaa bayan sallar Jumaa Daddy, Dr. Argungu da tsohon Ambasada Bashir Sambo suka daddaura auren yayayan su a babban masallacin Abuja a kan sadaki naira dubu goma-goma kacal domin neman albarka inda aka zarce da walima a fadar shugaban kasa. Ta koina abokan arzuka ciki da waje sun sake barkowa ta kowanne bangare domin nunawa wadannan mazan jiya na kwarai da suka bada gudunmuwa ta hakika a rayuwar su domin cigaban kasarmu Nigeria. To Faisal bai zo ba sai daren ranar da shi da Taju. Duk wasu abubuwa daya dace a ce shi yake yi Najib ke gabatar da su. Daddy da Hajiya sun hadawa Intisar lefe na gani a bada labari da Hidayah bata samu rabin rabin sa ba. Manyan sarkokin white-gold da duwatsu masu daraja da Hajiya ta dankara mata a kit kadai abin tsoro ne, cewa take in bata yiwa Intisar ba a yanzu wa zatayimawa? Shi kuwa Najib mota ce sabuwa dal a cikin tamfol ya danka mata kirar kia 407 haka sauran samarin Brigedier kowa da irin gudummuwarshi mai gigitarwa, shi kuwa auta Khalil dirkekiyar teddy ya danka mata yace akan kwantar da wannan teddin, kika zama mai gilashi. Sai da tayi kuka da wasu irin hawaye masu zafi amma a yau, zafin farin- ciki ne. Dr. Hajjo kuwa gudunmuwarta shine ta dage wurin gyara yayanta ta yadda zasu zamo ababen so ga mazajen su (ina ruwan yar Maiduguri). Duk wasu activities da Hunainah da Ehsan suka tsara da ita, ta soke kanta, tace walimar da su Daddy su kai ta wadaceta, albarka kawai take nema cikin rayuwar auren ta. Su kansu sai jikinsu yayi sanyi suka rage wasu abubuwan da basu zama dole ba. Ko kuda bata gayyato ba banda Raadhah, mutuniyar Jerusalaam (Israel) kawarta ta (Kingston College), uwar yaya biyu a yanzun kuma likita a asibitin (Doctoor Sulyman Fakeeh) dake Jeddah. Ranar asabar da daddare Daddy ya tara su ya yi masu fada sosai da nasihu masu sanya tsoron Allah. Ya dubi Intisar idonshi cike da kwallah, don ji yake kamar daga ranar ba zai kara ganinta ba, kai kace ba Faisal ya aurawa ita ba. Ya ce, “Biyayyar nan da kike yi mun, ban taba cewa eh, kin ce aah ba, a yau na roke ki, ki yiwa mijin ki ninkin wadda kike mini. Ina kara cewa Allah yayi miki albarka Saratu. Duk wasu burirrika na a rayuwa a yau sun cika. Saura in ga yayan ki na gudu cikin gidannan wanda na san da kyar ne, domin mu mazan jiya ne ba na yau ba, shekarun sun tura sosai. Ta kwaye laffayar da aka rufe mata ido da shi, idanunta jage-jage da hawaye, tasa hannun ta daya da ya sha adon kunshi ta toshe mishi baki, cikin muryar kuka, ta ce, “Insha-Allahu Daddy har jikokina zaka gani ba yayana ba.â€? Ta juya da gudu ta rungume Mamar ta, tace, “Mamar mu yanzu daga yau shikenen na daina ganin ki a karo na biyu? Ta cigaba da wani irin kuka mai karya zuciya, ta ce, “Mamar mu idan na taba bata muku, tun daga ranar da kuka tsinto ni, har zuwa yau da kuka aurar da ni a hannu nagari, na rokeku ku yafe mini kuyi min aikin gafara. Bani da bakin da zan gode muku sai dai in biku da fatar alkhairi da kyakkyawar addua har zuwa ranar da na daina numfashi. Kun shiga wahalhalun rayuwa iri-iri da bakin ciki kala-kala a saboda ni. Na rasa ku ko wadanne irin mutane ne masu karimci da dimbin alkhairi. Har yau, har gobe har kuma jibi, ban ga mutane masu kyautayi da kyakkyawar zuciya irin Daddy da Mama na baâ€? Duk kokarin da Aunty Saratu ke yi kada Intisar taga hawayenta ta kara rikicewa sai da hawayen suka zubo a kafar Saratun. Ita kadai tasan me take ji, ita kadai tasan irin kuncin da take ji na rabuwa da Babyn ta. Rabuwa bata zuwa makaranta a dawo karshen shek`ara ba, rabuwa bata a je Kano a dawo bayan sati daya ba, rabuwa bata tana Makarfi tana Abuja ba, aah, rabuwa ta har abada sai dai azo da yawo. In banda aure yakin mata wa ya isa yayi masu wannan yankan kaunar? A yau ma Hajiya Nafi matsowa tayi tana kara neman gafarar Intisar, tana kuka a gaban Daddy da Mamarta, don gani take har yau da sauran tabonta a zuciyar yarinyar. Bata sani ba, ita wata irin halittar Ubangiji ce (ba daya take da sauran mutane ba). Idan tace eh, bata taba dawowa tace aah! Bata taba yin abu da zuciya biyu; a kullum kalamanta na nufin abinda take nufi ne. Gidan da Daddy ya dankarawa Faisal a nan Maitama ne kusa da gidan Najib amma yace sai dai in ita zasu ajiye a nan, shi kam ba zai baro flat din shi dake cikin NNPC Krts. ba dake Lagos, akan wani auren da ba son shi ake ba. Hakan dai suke ta biye mishi suna lallabashi yadda yake so. lntisar na kara tausar zuciyar ta da danne bacin ranta. Washegari Ihsan da Rehab suka koma Miami inda zata karasa karatunta tsayin shekara guda, sannan su dawo su jagoranci MERITIME. Hunainah kuma an kai ta Katsina (family house) na su Hashim a unguwar Shaiskawa kamin su kare hutun su. Dr. Hajjo da Aunty Saratu sun kulle Intisar a daki suna ta kus-kus din su, Hajiya Hadiza na kofar falo tana latsa waya amma kunnuwan ta na kansu, tayi dariya a ranta tace har yaran yanzu ne zaa koyawa dabarar rike miji? Balle wadannan su Intisar da babu inda basa jefa kafa a duniya, suka kuma tashi da larabawa sarakan soyayyah? A ganin ta Aunty Saratu da Hajjo na bata lokacin su ne kawai amma su Intisar, sun fi su sanin sirrin soyayyah. Aunty Saratu tace ke gafara nan solobiyon banza, kin zauna kina ta asarar hawayen ki a banza kan wani shirmen Faisal! Kina mantawa Ya Faisal din ki ne fa? An ce da ke soyayyah ta gaskiya na fading (kodewa)? Dubi yadda Hidayah ke gara Najib inda ranta ke so kaman ba shi ba bayan ke kin fita komi ma, amma kin zauna kina kukan banza wai baya son ki, karya yake! Yafi kowa farin-ciki a yau kuma yafi kowa cika burin zuciyar shi kawai yana pretending ne. In kuma kina ganin ba dai-dai na fada ba kiyi karyar rashin lafiya ki gani. Hajjo ta kyalkyale da dariya amma Intisar kuka kawai take yi. Sun dauko hanyar air-port inda zaayi masu rakiya zuwa filin jirgi, motoci har guda goma a jere reras (in coboy). Faisal ya na tare da yan uwan sa cikin bakar Jeep din Daddy, ita ko tana cikin motar Haj. Saratu tsakiyar Maman da Hajjo, sai Goggo Jummai da Goggo Jami aminiyar Goggon a gaban motar yayinda Khalil ke jan motar. Ta dan dago ta dubi Anti Hajjo cikin muryar kuka tace Aunty Hajjo ina son zuwa Shanono, duk da an ce Babana ya rasu ina son ganin wani abu da ya shafeshi koda kauyen ne kawai. Hajjo tayi murmushi tace Mal. Ibrahim bai bar kowa ba, amma bazaa rasa Dattijan da suka san shi ba, kuma har gidan shi zan kai ki har gidan Hakimi mai ci a yanzu ya baki tarihin mahaifinki. Malam Ibrahim mutumin kirki ne duk wani dattijo da ya kwana ya tashi a Shanono ya san shi, zai kuma baki kyakkyawar shaida a kansa da yadda mutuwar sa ta taba zuciyar alummar Shanono. A filin jirgin saman Abuja, Daddy ya kamo hannun Faisal da Intisar yana murmushi ya dunkule su wuri guda, kana ya nuna masu hanyar matattakalar jirgin, ya girgiza kai ba tare da ya ce komi ba. A haka suka juya suka shiga taka matattakalar idanun su cike da hawaye, suna yi suna waiwayen su. Hawaye suka zubowa Anti Saratu, har ga Allah bata ji dadin yadda auren ya zo wa Intisar dinta ba. Murfi A cikin jirgi Faisal na karatun jarida, Saratu na karatun Alkurani, motsi kadan ta juyo ta dube shi tayi murmushi ta juya ta cigaba da karatunta. Amma shi tunda ya daura idon shi a Daily Trust bai sauke ba, balle ya san Allah ya yi ruwan tsirar ta a kusa da shi. Service ta zo ta aje masu abinci tayi gaba abinta. Intisar ta mike da zummar zata je ta rage mara bayan ta a je jikarta (channel) a kujerar ta, ta shiga toilet ta samu kan masai tayi zamanta tana tunani kawai, aranta tana kissima ko wanne irin rayuwar aure za su yi a hakan? Don ita kam ba wani fitsari da ta ke ji kawai dai tana ganin in tana zaune a wurin ba zai ci abincin ba kada ta samu hanyar da zata shiga sabgar shi shi yasa ta taso. Shiru shiru Faisal yaga bata da niyyar dawowa ya dan soma duba agogon shi locoste yana mamakin dadewar da ta yi a bandakin sai kace mai nakuda ko kallon abincin da aka aje masa bai yi ba. Idan yi duba agogo sai ya maida kai a Jarida, can anjima kuma ya maida idon shi bisa hanyar tahowa daga toilet har aka soma shelar a daura belt jirgi zai sauka a birnin Ikko. Yayi tsaki tsuuu, ya aje jaridar ya mike ya bi bayanta, nan yaga wani shirgegen Bayerabe a kofar (toilet) din da alama shima ita yake jira ta fito, wani haushi ya sake kama shi ya kwankwasa kofar da yatsun shi ukku da dan karfi sannan ne ta bude ta fito. A da niyyar shi ya balbale ta da fada amma ganin yadda idanunta suka kada suka yi jajir tabbacin ta ci kuka ta koshi sai kawai ya sake jan wani dogon tsakin, ya juya ya ce ba kya ji ne? Ana a daura belt kada Allah yasa ki daura ni meye nawa a ciki? Ta yi murmushi a ranta ta ce in babu naka, meye naka na tasowa daga mazaunin ka? Har suka fito daga jirgin babu wanda ya sake cewa da dan uwan sa uffan. Tajuddeen na jiransu cikin motar Faisal kirar porsche, ya debe su zuwa NNPC Ktrs. Tsarin gidajen ya burgeta kuma gidan su yafi duk gidajen tsari da sabunta. Tun daga (gate) ta yaba da tsarin rayuwa irin na Faisal mai cike da tsabta, hatta cikin shukokin sa babu rubbish na ganye ko daya koina tsaf-tsaf. Tsayawa ma fadin irin dukiyar da Daddy, Hajia, Aunty Saratu, Hajiya Hadiza, Hajjo da Amb. Bashir suka narkar a gidan Intisar abin ma sai ya zama kauyanci, duk da anyi mata babban jeren a gidan su na Maitama ne. Wannan komi a saukake yake (English Parlour) Koina an shinfide mata shi da marbles har jikin bango, wasu irin yan uban su leather seat (Chinese) da Daddy yayo odar su musamman daga China haka chinese-carpet din da ke malale a tsakiyar falon bata taba ganin irin shi ba a duk yawon da take cikin duniya. Nan ta cillar da jakarta ta zauna cikin kujera cike da gajiya, ga yunwa dake addabar ta. Ta kai hannun ta na dama ta dafe goshinta dake sarawa, yayinda tayi amfani dana hagun wurin dafe cikinta ko ta danne kugin da akuyar cikinta ke ta yi. Tajudeen ya shigo yana ta mata barkwanci irin nasa, jin sa kawai ta ke amma shi kansa biyu biyu take ganin sa sabida yunwa. Shima da ya ga ba fuska bai dade ba ya yi masu sallama ya tafi, da alkawarin gobe bayan ofis zai biyo Faisal ya yi mata hira. Faisal matattakalar dake falon yabi zuwa dakunan barci guda uku dake saman bene a ransa yana cewa wai Baby jira take yace da ita ga dakinta? Ai ko tana da aiki, sai dai in ta kwana a falon. Taga dai zaman haka ba zai mata ba, don in yunwar zata kasheta ba zai kulata ba, sai ta dauki Jakarta ta rataya ta bi hanyar da ya bi, wai ko ta samu kitchen a can, bata sani ba (kitchen) din ma kofarsa na nan cikin falon don dai labule ya rufe ta ne. Ta kusa kaiwa matattakalar karshe kenan dunduniyar takalminta ta makale daga matattakalar baya ta kuwa sulmiyo daga benen ta baya tana mirginowa (step-by-step) har tsakiyar falon, ta fada kan hannunta na dama ji kake kas, kashin Amarya ya targade. Da ta daddage ta zuba wata irin kara ba Faisal dake cikin gidan ba, hatta makotansu Franklyn da matarsa Chinyere sai da ta firgitasu suka kuma shigo gidan suna buga musu kofa don su ji ko lafiya? A lokacin yana tahiyya ne don sallame sallar Isha’i data riskesu a hanya, don haka saida yai sallama kana ya taho yana hada matakala biyu-biyu-hur-hudu, yayi wanka yana sanye da jallabiyya fara sol, ya ciccibeta ya aza bisa rest-chair kamin ya je ya bude kofar su Franklyn su shigo suna tambayar sa what happen with his bride? Ya ce cikin matsanancin tashin hankali shima bai sani ba, amma yana zatan zamowa tayi daga bene. Ita ko sai kuka take tana kiran hannunta, wayyo Mamana, wayyo Daddy kun kawo ni inda zan mutu! Kai abin na Intisar har da karawa aya zaki. Gaba daya ya rikice idan kuma ya kai hannu kan hannun da ake cewa yana ciwon a kwalla mishi wata matsiyaciyar karar da ke kara gigita shi. Chinyere ta ce taimaka mu kama ta Oga mu kai ta asibiti, wannan hannun da kyar in ba karaya ba ce (Faisal Makarfi, shine G.M watau General Manager na NNPC gaba daya da ke rike da reshen Jihar Lagos a yanzu. Gaba daya ya dauketa cancaras tamkar ya dau yar Baby, suka shiga motor Franklyn zuwa wani (private-hospital) da ke kusa da su. Nan da nan likitan kashi ya karbeta yana dubawa yace ba karaya ba ce, gocewar kashi ne. Nan da nan ya hau gyara tana ihu tana faman kiran Daddy da mama, yau har Hunainah ta sha kira wajen gyaran hannun nan Faisal ya rasa inda zai sa ransa sabida damuwa, bai san hawaye yake ba sai da ya ji dandanon gishiri a bakinsa. Yayi saurin sharewa da hannun shi kada Franklyn da ake baiwa (order) a ofis yaga kukan G.M gaba daya akan ciwon matar shi. Likitan yayi mata allurai biyu ya kuma umarci a siyo magungunan da ya rubuta yanzun nan a bata idan ta ci abinci. Sai a lokacin ma ya tuna rabonta da abinci a saninsa tun daren jiya daya shiga dakin Anti neman Najib ya ganta suna ci da Anti Hajjo. Franklyn shi ya tafi sayen maganin nan cikin asibitin inda Chinyere ta ja mota ta koma gida kawo abinci. Har zuwa lokacin kuka kawai takeyi mai cike da kissa, shi kansa kukan bana zafi bane na jin dadin ganin yadda Ya Faisal ya gigice da ciwonta ne, ashe dai still akwai wannan burbushin son ko yaya yake? Ba tayi tsammanin tana da sauran gurbi a zuciyarsa ba in tayi laakari da irin halin ko in kula da yake nuna mata. Ya zauna a gefen gadon da take kwance, yayi tagumi ya kasa cewa komi, can kuma ya sauke tagumin ya ja kujera dai-dai fuskar ta ya zauna, sannan yai karfin hali yace. Don Allah Baby kiyi shiru, kin san me Hajiya tace da ni kuwa? Cewa tayi in kika kara kuka a dalilina bata yafe mun ba, kina so bakin uwa ya lalatani? Ta girgiza kai da sauri, sannan ta kama share hawayen. Ya dafe kai da dukkan hannuwan shi biyu, zuciyar shi na wani irin bugu da sauri-da-sauri. Dai-dai nan Franklyn ya kwankwasa kofar yayi mai iznin shigowa, ya kawo magungunan cikin ledar asibitin da ruwan swan babbar roba, ya ce cikin harshen turanci ranka ya dade akwai masu sayar da gasassun kaji anan tsallake, ko a sayo ne? Ya ce aah, Chinyere ta ta tafi ta kawo abinci, mu bata minti goma mu gani Franklyn ya juya ya fita yayinda shi kuma ya maida raunannun idanun shi a kanta, har barci ya soma fizgar ta kadan-kadan. Ya so ace ta bude ido ya tambayeta yadda akai ta fado daga bene, amma itama kamar ta fahimci take-taken shi na neman a shirya shi yasa ta tamke idon ta a zuwan barci take, farin-ciki fal a zuciyarta. Ta godewa cokalelen takalminta da yayi sanadiyyar fadowarta daga bene da bata san yaushe Faisal zai kula ta bama balle har ya nuna damuwar shi a kanta irin haka, wato shine Aunty Saratu ke cewa ta kirkiri ciwon karya, sannan ne zata gane Ya Faisal din ya damu da ita ko bai damu da ita ba? Allah sarki Antinta, ashe itama abin ya dameta, kamar yadda ya addabi rayuwarta? Chinyere tayi nocking ta shigo rike da warmers din abinci kanana guda uku cikin Kwando, da leda cike da apple da lemun zaki manya manya, ta aje bisa dan tebir dake gaban gadon Intisar suna magana da Faisal cikin yarbanci, ta bi bayan mijinta bayan ta jawo masu kofar. Haka ya zauna shiru ya rasa abinda ke mai dadi, in ya kai hannu da niyyar ya tasheta taci abinci sai kuma ya fasa, don yana tsoron kukan nan nata mara sauti dake girgiza mai zuciya. Nan dai ya zuba mata ido wata irin kauna da soyayya na ratsa shi, ya rasa abinda zai yi. Gaba daya ya mance komi, sai kaunar Intisar din shi dake azalzalarshi a zuci da ruhi, wata da watanni, kwana da kwanaki, shekara da shekaru. Yau gata a matsayin mallakin shi amma ya bari Shaidan yana kada mishi gangi da wani shirme na banza wanda ita ya lura bai dameta ba; abinda ta san dai-dai da rayuwarta ne shi kawai take yi. Bai sanda ya bi ya kwanta a bayanta ba, ya rungumeta cikin wani irin yanayi mara fasaltuwa da bai taba tsintar kanshi a cikin irinsa ba. Ita kam in banda ajiyar zuciya ba abinda take yi, kamin wasu hawaye masu dumi (warm-tears) su malalo ta gefen idonta. Hawayen farin-ciki na karshe a rayuwarta. Ta bude idanuwanta farrr! A kanshi, ya juyo ta sosai suka dubi juna, yayi wani murmushi da rabon da ta ganshi yayi irinsa tun tana makaranta a Riyadh, ya lumshe idonshi ahankali, ya ce, “Please forgive me Inti na, ban san me ke damuna ba, ban san abinda ke min ciwo ba. Ba mamaki ina da tabin hankali a kan kaunarki shiyasa na kasa amincewa da ke tun bayan da kike son Alameen.â€? Ta toshe mai baki ta soma rero mai kukan da ke azabtar da zuciyar shi. Ya ce “Please please Inteesar na roke ki, don Allah in zaki azabtar da ni bata wannan hanyar ba, bata wadannan hawayen da kike ta zubarwa a dalilina ba, kuskure ne na san nayi amman kema ai da laifin ki, baki san yadda zaki baiwa matun hakuri ba balle ki nuna kin san abinda yake ciki, ko ki nuna dan I care, aah, ke kanki kawai kika sani. Amma ai kema dai Baby kin san I can’t do without you.â€? Ta lumshe idon ta a hankali, wani matsanancin farin-ciki da bata taba ji ba yana ratsa ta, ta ce, “Amma dai Ya Faisal sanin kanka ne ko zan so wani a rayuwata ba zan so shi irin yadda na soka ba? Kuma komai ai mukaddari ne daga Allah, rayuwar mu duka a rubace take a Lauhul-Mahfuz ba mu muke tsarawa kan mu rayuwa ba. Kuma na dauka da kai da Alameen duk abu daya ne, ba banbanci? Don haka idan na so Alameen ai kamar na so Ya Faisal ne tunda babu bambaci daga uwa har uba, har ma kamanni. Idan na so Alameen na so shi ne a rashin Faisal! Na so shi ne don wasu qualities nashi da sukai kama da na Faisal!! Na so shi ne don ya nuna kulawa da ni da alamari na irin yadda Faisal ke mini!. Naso shi ne don kasancewar shi jinin Daddy Makarfi. Ni kuwa duk jinin wannan mutum abin so ne da kauna a gareni. Amma duk cikin su na fi son Ya Faisal nafi kaunar Ya Faisal tunda duk ya fi su kauna ta. Wannan kaunar da ya nuna mini, tun ban san kaina ba, ita ta gina wani tsiro a zuciyata yayi ta girma har yau inda nake. Ban taba tunanin dai-dai da rana daya Ya Faisal zaka yi tunanin bana son ka ba, ban taba tunanin zaka taba zato na da yaudarar ka ba. To in yaudare ka in ce na yaudari wa? Na yaudari kaina? Tunda kuwa kai kadai ne zuciyata ta ginu a son ka da kaunar ka? Baka sani ba, tun kana a muharramina na sha kimantaka a matsayin miji a gareni. Na sha tunanin in da a ce kai ne zaka zamo miji na wace irin saa zanyi? Na sha tunanin idan ka auri wata ba ni ba ni yaya zan yi? Na sha zama in yi tunanin ni a rayuwata bazan taba yin aure ba, sai dai in zo gidanka da matarka in zauna. A wadannan shekarun zuciyata bata taba hutawa ba ko sau daya da tunanin ka. Haka gangar jikina bai taba daina azabtuwa ba da begen ka. Na sha yin mafarke mafarke na ni da kai a matsayin miji da mata, ga yaya zagaye damu, cikin wata irin rayuwar soyayya, ban taba fadawa kowa ba. A yau zan gaya maka wani sirrina da daga ni sai Ubangiji na muka san shi; na sha zuwa ina leken ka a dakinka in kana barci, a lokacinda ma na san cewa (uban mu daya). Na sha yin kuka kamar in fidda raina a duk sanda nayi tunanin ba zamu iya auren juna ba. Son da nake maka Ya Faisal wani iri ne da ni kaina ban san iyakar sa ba. Koda na fara jin kaunar Alameen a ranar da na fara ganinsa, na so shi ne sabida muryarku da take iri daya, na so shi ne domin maganganun shi na hankali da nuna kauna duk irin naka ne. Kana tsammanin mai irin wannan son zai taba canza shi zuwa zalinci ko kiyayyah? A ganina idan na gaya ma hakan a sanda kake zargina, cewa zakayi don na rasa Alameen ne, ba zaka taba yarda dani ba, zaka ce tausayinka kawai nake ji shiyasa nima na dake zuciyata na bika da yadda kake soooo Ragowar maganar makalewa tayi cikin makoshinta, domin Faisal yayi nisa wurin fiddo mata zahirin kaunar da yake mata bai ko damu da hannun da ke ciwo ba. Da wasu sabbin alamurada bata san dasu a nature din halittar biladama ba (physical relationship). Ashe ita kauna ta fatar baki ta sani, bata san mecece kauna ta sassan jiki ba. Banbancin yake nuna mata a farrake filla-filla between oral one and emotional one wadanda suka tabbatar mata har yau ita BABY ce, jaririya dake rarrafe a fannin soyayyah. Wadanda suka san so da kaunar kam tafiya suke da kafafun su; basa bata yawun bakin su wurin fassara ta; nuna ta suke emotionally and practically. Ta samu kanta a wata sabuwar duniya ta daban, da bata taba tsintar kanta a ciki ba. Ashe dai wannan itace soyayyar ita sobeka ta sani? Duk abinda take gani cikin mafarkinta (kamar yadda tace) a yau Faisal ya nuna mata a zahiri, har ma wanda bata gani ba, sababbi kar a cikin ledar su. Wasu hawayen suka kara zubo mata, wadanda ta tabbatar a wanan karon na farin-ciki ne! Hawayen da ta tabbatar sune na karshe a rayuwarta! Masha Allah- lakuwwata illah billah. Takorin ku ce, ke yi maku fatan alkhairi. How much do you like this story?