BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM DUKKAN GODIYA DA YABO YA TABBATA GA ALLAH SARKIN KOWA DA KOMAI MAI SAMAU MAI KASAI DA ABINDA KE CIKIN SU. YA ALLAH MUNA GODIYA DAKA NUNA MUNA WANAN LOKACIN LAFIYA UBANGIJI ALLAH YADDA KA BAMU DAMAN FARAWA LAFIYA KA NUFE MU DA GANI KARSHEN LABARIN NAN LAFIYA ALLAHUMA AMIN. YAN UWA ZOMU ZAUNA ZO MU SABA MUYI HAKKURI DA JUNA GA DUK WANDA ALLAH YABA IKON GANIN KUMA YA SHIGA GROUP DON ALLAH MUYI HAKKURI DA JUNAN MU, , , YAR UWA LITTAFI DAI NA KUDINE DARI BIYAR NE KACAL DON ALLAH KI DAURE KI BIYA KAFIN KI KARANTA DON GUJEWA SHIGA HAKKIN WANDA BAKI SANI BA, , , , Misalin karfe biyar da rabi na yamma amma kuma yanayin garin ya juye kamar karfe bakwai da rabi na dare zuwa takwas. Don gagarumin hadarin daya taso a lokacin ya hade garin ga baki daya baka ganin komai sai masu abin hawan dake gittaiya da masu sauri a kasa don kada ruwa ya fado a lokacin. Cikin hakane kuma wata katuwan jeep dark blue sai sheki takeyi ta keto titin da gudun gaskeda alama mai shi sauri yakeyi ya kai inda zai tafi kafin ruwan dake barazanan fadowa ya sauko Titin shiru don unguwan ko ba hakan bai faye yawan mutane sosai ba wani gida a layin motan ta tsaya tana horn sai maigadin gidan yayi saurin bude mashi kofan. Motan ta tsaya a daidai inda ake parking din motoci a gidan wani dan dattijo ne ya taso shima da saurin shi zuwa inda motan ta tsaya yana faman duke duke tun na cikin motan bai bude ba ya farayi mashi sannu da zuwa. Wani kyakyawan matashin saurayine ya fito daga motan ya zuro kafab shi daya bayan ya bude motan ya daukan wani abu a cikin motan. Wanan dattijon cikin girmamawa a gare shi yake fadin sannu da zuwa Alhaji karami barka da hanya. Karasa fitowa yayi gaba daya yana dauke da yar wata jakka dake nuna na laptop ne tare da wasu muhinman takardun shi a ciki. Shekaru shi zaikai kimanin ashirin da bakwai zuwa takwasa yana saye da wandon jeas blue na maza sai riga mai kwala fara da dan ado kadan a tsakiya ga kamshi na tashi ta ko ina duk da iskan dake kadawa alokacin. Kallon mutumin daya nace da gaishe shi yayi yana fadin malam mudi baka samu wuri ka labewa ruwa nan ba har yanzu kada fa ka jike kajawa kanka ciwo kasan ruwan sama yana tafiya da dan sauri yake magana da wanan mutumin . Dan jakkar da ya riko din mutumin ke kokarin amsa daga hannun shi ya dakatar dashi da fadin No ka bar shi kawai ya shige cikin gidan. Kamar ana jiran shigan shine aka sako da wani irin ruwan sama mai karfi lokaci guda abinda yasa garin ya kara yin tsit kenan Allah yana nasa ilon a lokacin. Yana shiga babban falon gidan ya dauke hanya zuwa part din shi kai tsaye duk da yana jiyo dan hayani a falon alaman akwai mutanen dake zaune falon lokacin. Babu abinda ke tashi sai kida duk da ruwan saman da akeyi a lokacin ya ja tsuki ya nufi dakin nasa yasa key ya bude ya shige ciki kai tsaye. Ruwan saman da ake zugawa a lokacin bai hanashi shiga wanka ba don dan tafiyan da yayo daga jos zuwa kano a mota. Ya fito wanka da alwalan shi duk da yasan akwai sauran lokacin sallah magariba kwanciya yayi saman kujera yana bin dakin da kallon yadda ummin su tasa aka gyara mashi dakin sai kamshi ke tashi don tasan shi din ma,abocin son kamshi ne sosai a rayuwan shi. Mikewa yayi da niyar zuwa dakin hjyn nasu daidai lokacin wayan shi da yai saiitin lokacin sallah ya dauki kara. Ba zai iya fita masalci ba a lokacin don haka ya tsaya daki ya tayar da sallah har saida yai isha,i yayi abinda zaiyi ya nufi dakin mahaifiyan nasu don su gaisa don ba wanda yasan ya dawo gidan a lokacin. Har lokacin kannen nasa suna zaune a falo ba wanda ya mike don zuwa sallah sai dararakun su da sukeyi a wurin. Kwatsan lokaci daya suka ganshi tsaye a kansu kamar an jefoshi daga sama nan suka dan shiga kame kame cikin rawan murya suna gaida shi da dawowa. Wani tsawa ya daka masu hadi da zazzare masu idon shi wanda kan firgitasu dashi don sun san inya juye idon ba wasa a wanan lokocin yaya ashe ka, , , Yace shut up tsupid girls ana ruwan ma ba zaku natsu ba anyi sallah kuma duk kuna zaune . Mai dan girman tana da dan kama dashi a cikin sune tace wallahi yaya yanzu nake, , , , Shiru tayi don yadda ya watsa mata kallo a wurin yana nuna masu hanyan dakunan su da hannun shi haka yasa kowan su mikewa da sauri suka bar falon yaja tsuki ya shige auri ummi din. Zaune take saman sallaya yayi sallama ya shigo tana ji ta dago tana fadin yanzu na gama tunanen ka ai. Na dauka wanan hadarin ya hanaka tasowa da wuri don nasan ka da tafiyan dare . Zama yayi yana fadin mun dawo tun dazun ai ummi don na tsaya sauke abokin tafiyane ne har iskan nan ya taso ban karaso gida ba ina hanya amma ai nan ruwan ya sameni ina shigowa. Ka dai daina wanan tafiyan daren na fada ma yanzu hanya baida kyau ko kadan kowa na tsoron hakan. Wai ummi meyasa baku sakawa yaran nan ido wurin ibadane ace wai yaran nan duk ruwan nan da akayi har magariba yayi suna zaune falo suna shan kida kamar gidan yan coci damu . Kai uwar ta kada tare da fadin kai Allah ya sawaka da halin yaran nan na dauka sun tafi daki yin sallah tun dazun ai. A dai saka masu ido don su yanzu babu a binda ke ransu sai duniyanci da shakiyanci Allah dai ya shirya muna su uwar ta fada. A dai kula mami ya fada za a akulan ta sake fada a cikin rashin damuwa da abinda yake fadi din akan yan uwan shi din. Yaushe ne zaka koma lagos ta tambaye shi ya nisa tare da fadin sai idan daddy ya dawo daga tafiya ya bata amsa. Amma idan bai dawo karshen satin nan ba zan tafi hakana ba tare da mun hadu din ba amma naso ka bari ya dawo ku hadu don wanan damuwan da yake ciki ko zaka gano abinda ke damun shi a yan watannin nan. Na rasa me yasa Alh ya koma hakan kamar bashi ba ga daya ya canza ya daina walwala da mu,amula da kowa a cikin mu har yaran nan duk ya daina sakewa dasu a yanzu. Kaita dago tana duban dan nata da yai zurfi a cikin tunane yana nazarin abinda mahaifiyan nashi ke fadi game da mahaifin su a lokacin. Kafin wayan shi dake aljihun shi yayi kara alaman kira ya shigo mai a lokacin ya dan dago da sauri yana daukan wayan tare da karawa a kunnen shi yana sauraren abinda ake fada mai. Bayan ya gama saurare ne yake fadin tomorrow morning in sha Allahu i will be in lagos sai mu duba shi. Bayan ya gama wayan ne ya nisa yana mayar da wayan cikin aljihun gaban rigan dake jikin shi ummi din ta dago tana fadin gobe ke nan zaka koma lagos din ashe ? Fuska ya bata kafin yace dole hjy kin san aikina ba nazama bane ya zama dole gobe inbi jirgin safe zuwa lagos din abinci fa mahaifiyar ta tambaye shi ? Fuska ya bata kafin yace sanyin nan ba zai bari na danci wani abu zan sha tea kafin in kwanta kadai kula da cin abinci ta fada. Yace insha Allah zava tsare ummi sun dan taba hira kafin ya fito yayi mata sallama don goben ba lalai bane ya samu ganin ta da safen kafin ya fita don asubancin da zaiyi a goben. Ya fito zuwa part din shi don hankalin shi naga wayan da akai mai gaba daya hankalin shi ya koma can. Bai zauna ba ya fara shiri ko tea din da yace zai sha din bai samu sha ba biyar da rabi na asuba ummi taji fitan shi gidan an bude mai get ya fita. Addua tayiwa dan nata na Allah ya tsare ya kare mata shi da sauran yan uwa a lokacin don ganin kakanta shi ga aikin da yakeyi a yanzu din. Wanda a gaskiya sai take ganin shekarun shi baikai ya fada wanan aikin ba haka don aikin nasu akwai kasada sosai a cikin sa. Karfe goman safe jirgin su ya sauka a filin jirgin inda abokan aikin shi ke jiran shi don daga nan zasu wuce inda suke son zuwa din don basu da wadattacen lokaci don kamar ma sun dan makara a lokacin. Kafin su gama da can su dawo karfe biyu saura ga ruwan sama daya sauko a lokacin ba tare da wani alamun hadari zai zubo ruwa ba kamar yadda nan arewa yakan tsaya nuna muna alaman zuwan shi. Ga wani irin go slow da ya cika hanyan sai hasken fitalan motoci kake gani da mutanen dake zirga zirga a kasa da sauran abin hawa don su haka bai damesu ba sun saba da hakan a rayuwan su . Tana tafe da sauri har tana tuntube don dan yayafin da aka fara tasan ruwane ke shirin saukowa a lokacin. Amma haka bai hanata sauri ta nufi titi mafi kusa inda tasan zata samu mutane a wurin . Saidai kafin ma takai titin ruwa mai karfi ya gwauce haka ta dinga tafiya ta hango jerin motoci da ke saman titin sun jera dogon layi don go slow din ya hadu a lokacin . Haka ta fara bin motocin tana bara tana neman taimako gana Allah da wanda yaji kyanta ya bata don Allah a cikin wanan ruwan. Glass din motan shi ta gefen shi yaji ana kwankwasawa ya dan dago daga abinda yakeyi da sauri yana kallon wurin. Mace ya hango a tsaye duk wanan uban ruwan tana cikin shi hankali kwance wanda suke tare ne yace dashi a cikin harshen turanci wa yan nan mutanen ne yan bara . Bara a cikin wanan ruwan haka yace kana mamaki ne su ai damane ya samu masu ga wanan lokacin yadda aka hafa go slow din nan haka. Dayan gefen ta koma tana kwankwasawa a hasale ta miko hannu ta inda aka dan bude din tana fadin Wahidu oga . Give me something oga even small Allah will reward you with , , , , kai innalillahi wanan mutanen suna da kaskantar da kai wallahi ya fada a hasale. Ta kara mika hannu tana fadin Wahidun Oga give something to eat a hasalw zai rufe glassa din na tare dashi yace a, a yana bude wani wuri yace bari mu bata don in ba bata mukayi ba haka zasu damemu da wanan baran . A lokacin ya dago kai yana kallon ta tana sharce ruwan daya kwanta mata a fuska da alama karfin ruwan yana damun ta itama a lokacin dubu biyu yayi niyar zarowa sai ya zaro kusan hudu haka takai hannu ta wafta duka a hannun mutumin tana jiyawa da sauri bayan godiyan da tayi mai . Binta da kallon mamaki yayi kafin yace innalillahi wanan yarinyace karama da wanan halin banza iri sune ma yan iskan gari. Dan murmushi na gefen shi ya sake yana girgiza kai tare da fadin indai wanan erea din ne zaka sha mamakin su ko wani yare zaka samu a nan tundai hausawan ku yan arewa sun fi yawa ga wanan harkan na bara yaja tsuki yana kawar da kai. Tare da jin haushin hakan a zuciyar shi ga yarinya har yarinya amma ta tsaya tana wanan kazantar sana,an dayafi tsana ko a arewan su. Balle lagas da yake ganin hanyoyin sana,a sun fi a kirga ga neman kudi idan mutum ya tashi nema din. Har suka kai gida a na sheka ruwan sama a lokacin suka fito daga motan a cikin ruwa hakan yasa suka dan jika kayan jikin su din. Kallon kudin dake hannun ta taji wani irin farin ciki ya kamata da sauri ta juya don barin wurin har tana dan hadawa da gudu gudu don tunawa da tayi tun safe basuci abinci daga ita har kanin ta Amar da duk suka dogara da ita a yanzu. Tun daren jiya batayi barci da dadi ba idan ta tuna babu abinda zasu ko karya dashi a gidan haka yasa bata kaunan komai nasu ya kare. Tasan wanan din zasu samu su danyi amfani dashi har zuwa dare in yaso sai ta fito ta nema masu abinda zasu ci. Da sauri ta karasa wani shago mafi kusa ta sai duk abubuwan da zasu buka mai saukin ci sai a lokacin ne ta kula ashe kudin yafi yadda take zaton ta samu. Wani irin shu,umin murmushi ta sake lokaci guda nan ta kara sayen komai wadatace da zai ishe su har karshen jibi da safe . Har ta isa gida ba,a kare ruwan saman da akeyi ba haka tsamo tsamo ta samu ta isa kazamin unguwan nasu da babu abinda ke tashi banda warin kwata da bola a lokacin. Cikin rashin damuwa da hakan saboda sabo da tayi da hakan a yanzu yasa bata ji kazantar komai ba a lokacin Kowa na gidan yana dakin shi ya labe ganin yadda yawancin kayan gidan suke iwo a cikin ruwa ganin haka yasa ta tuna da dakin su dake zuban ruwa sosai ga mahaifiyar su ba lafiya duk kwanakin nan wanda tasan ba komai bane ya kawo hakan sai aikin wahalan da takeyi kullun don saman masu dan abinda zasu kaiwa cikin su. Da sauri ta tura kyauren dakin, dakin ya bude can ta hangosu a takure wuri daya ga yan tsumakaran su duk sun jike da ruwan da ke diga daga saman kamar indararo a dakin. Da sauri ta karasa inda mahaifiyan nasu take labe tare da dan kanin su karamita dauko wani babban bargo suka kare kansu su ukun gaba daya a ciki. Duk da halin da sule ciki haka bai hanata dauko masu abinda ta sawo suci ba a takure a wurin suka ta mike ta dauko ledan pure watar daya daya rage masu a dakin ta kawowa mahaifiyar nasu da kanin ta su sha, . Kai mahaifiyan ta kada tana fadi da kyar kusha keda dan uwan ki ni zan dan samu ruwan saman nan da akayi insha. Wallahi Umma ba zan sha ba don ban ma jin kishin ruwa a yanzu din ta fada don hankalin uwar nasu ya kwanta tasha ruwan ta sauke wani irin ajiyan zuciya ta juya ta kalli uwar nasu tana mata sannu umma . Muryan mahaifiyar ne ke fadin kece da sannu da ubangiji ya hore mune ke kike samo muna abinda zamu sakawa cikin mu a cikin karfin ki. Sahiba ban da kwankwanto a kanki don nasan irin tarbiyan dana taso maki dashi tun farko naki dogara da karfin ki ki tallafi kanki ba sai kin zubarda mutuncin ki da kimarki ba ga maza a karshe ki koma abin kyama a garesu . Sahiba yadda kike muna Allah ya biyaki da mafificin alherin sa a rayuwan ki Allah ya baki masu rama maki irin abinda kikai muna. Kin kula dani da kanin ki tun kina mitsitsiyar ki har zuwa yanzun duk wani wahalan mu da dawainiyar mu duk a kanki yake yanzu Sahiba. Allah kadai zai iya biyan ki don Allah yasan komai daya jefa rayuwan mu a cikin wanan halin da gatan ku a duniya kun koma mabukata karfi da yaji kan wani dalili nasu can na rashin imani. Da sauri yar ta dago kai ta kalli mahaifiyar nata don wanan ba farau din ta bane wurin fadin da gatan su amma wasu sunyi dalilin komawan su hakan. Duk da nasan Allah ba zai kyalesu ba suma a kan wanan abin da suka aikata muna a rayuwan mu na shiga kunci da wahala irin haka a yanzu . Ina alfahari da samun ku a matsayin yaya a gareni Sahiba don da wuya a wanan zamanin a samu ya data fiki tausayin iyayyenta da yiwa mahaifiya biyayya irin haka. Sahiba a kullun ina maki adduan Allah ya baki kyakyawan sakamo arayuwan ki don a yau in munci munsha duk a dalilin kine Sahibat a duniyan nan. Hawaye suka silalo a hankali daga idon Sahiban dake sauraren uwarta kan ta na duke a kasa . A hankali ta lumshe idon ta tana tunanen yadda rayuwan su zai kasance a nan gaba dan sanin yadda suke fuskantar rayuwa a yanzu. Ga tambayan fam a zuciyar su amma babu mai bata amsan hakan duk mutanen da tasan umnan su na zaman arziki dasu tun farko tabi ta tambaye su ko daga ina suke amsa dayane basu san garin su ba ko yan uwan su suma dai ganin su sukayi kwatsan a lagos. Abinda suka sani shine daga dai arewa sukazo lagos din da goyon sahiba da cikin kanin ta kuma a jikin umma din amsan da take samu ke nan a gurin wasu da suka san su a baya. A kullun ta shiga irin wanan tunanen ko wani matsin rayuwa irin kalaman umma gareta ke kara mata karfin gwiwa . Har ta ji hankalinta ya kwanta da rayuwan su a nan din don ta fahinci inda umman nasu tabaro yan uwan su da mahaifanta yana da zafi da ciwo a garesu ke nan da zama can din. Don haka takan kwanmacewa rayuwan su a nan lagos duk da irin gwagwalmayan tashin hankali da fitinan da suke gani yanzu a rayuwasu. Indai hakan da umman nasu tayi na nisanta su da yan uwan su har take ganin shine mafita a garesu. Idonta ta bude da suka ciko da hawaye ta nisa tana sharewa a hankali tare da tunanen yadda zata bada hinma ga rayuwan su dana mahaifiyarsu din duk da tasan abune mai kamar wuya a gareta a yadda suke nan. Ganin ruwan saman ya tsaya cak ta mike daga inda suke zaune ta fara gyara dakin don su sami wurin kwana a ranan saboda haka suke a yan shekarun nan idan ana ruwan sama bata da huta a rayuwan ta. ZAINAB IDRIS MAKAWA ANA DARA GA , , , , , , BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAIJIN KAI YAN UWA BARKAN MU DA JUMM,A ZAINAB IDRIS MAKAWA SAHIBAT yarinya ce matashiya yar kimanin shekaru sha hudu a duniya sahibat doguwa ce kyakyawan gaske. Tana da wani irin halitta na daban da ba a faye samun irin su ba da yawa a cikin mutane sune ake kira ace mutum kamar shi ya zauna ya tsara kanshi don kyau. Haka launin fatan jikinta yana da haske da sheki ga jikinta a murje yana walkiya wanda hakan baiwane da kuma gado a bangaren mahaifin ta. Ba zaka san baiwa bane hakan sai kaga irin wahalan data taso a cikin shi amma wahala da wanan rintsin bai hana fatan jikin ta sheki ba. Duk da Sahiban ba fara bace irin sol din nan sai kuma dole a sakata a cikin farare ko a hakan sai dai kuma ko a hakan samun mai kyaun fata irin nata yana da wuya hakama mahaifiyar ta duk da wahalan da suke fuskanta na rayuwa. Yadda Sahiba take da kyau a baiyane haka kuma take da kyau hali a boye don akwai kyakyawan zuciya da kyakyawan hali a tare da ita. Haka idan maganan hakkurine idan anzo gun sahibata azon gidan hakkuri da juriya duk tsanani da wuyan al,amari bai wuce Sahiba ta kalleshi tayi mai murmushi ba. Amma fa ba kowa yasan da hakan ba sai irin su iya Muluka da maman Bisi da suka kwashi shekaru a tare ne suka san wanan halin nata na boye. Don idan ka ganta tayi shiga na bat da kama ga mazan zamani mayaudara a wurin neman abincin su ba zaka taba cewa ita keda wanan halin ba. Amma idan mutum yana son ya gane waye sahiban na gaskiya to yazo gidan su a lokacin tana gida zai san da hakan dana fada a yanzu. Kowa na yabon hali irin na Sahiba har kaga yarbawa nawa diyan su kwatance da ita da irin halinta na taimakawa uwarta da dan uwanta tun tana yar ficiciyar ta kuwa. Tun tasowan Sahiba a duniya ta bude ido a cikin talauci da wahala da kunci irin rayuwa tun tana karama har dan tasowan ta din nan bata taba ganin wani abin jin dadi na zamani a tare dasu ba. Daga fannin abinci sutura ko wani abin jin dadi komai zasuyi a rayuwan su sai da kyar da sudin goshi zasuyi shi tun dai a fannin abinci ba karamin wahala suke sha ba kafin su hada abinda zasu ciwa ransu gasu har su ukku kuwa. Don hakane ma basu damu da wai wani dafa abinci ba donko ko sunce zasuyi din abinda zai dafa abincin a garesu shine aiki kuma. Don hakane suka kwanmace a sayo garin kwaki da dan mangyada a yamutsa aci a tashi sai idan sun gaji da ci ko ranan data samo kudi da dan yawa wurin yin buga bugan ta zata dan sayo masu wake da bread da iya bisi ke dafawa a kofan gidan suci. Kamar yadda Sahiba ta bude ido ta tsunci kanta a cikin kangin talaici da kakanikayin rayuwa. Don haka ta bude ido data fara wayo taga mahaifiyarsu tana faman yawon bara dasu a cikin birnin iko din. Har izuwa yanzu da ta karbi uwar nata ta dauke mata duk wanan wahalan don ciwo dake son ya nakasa masu mahaifiyar nasu a yanzu. Don ga ciwo ga rashin gatan dake damun umma din yasa tun bata karasa kai hakan ba take iya kokarinta wurin fita ta nemo masu abinda zasu ci ga kanin ta karami ne sai kafa kafa sukeyi dashi don yanayin garin n a iko da ba kyau. Tsakanin Sahiba da mahaifiyar su akwai shakuwa mai yawa don bata taba yin komai sai da yardan mahaifiyar nata takan fita yawon buga buga abinda zasuci din. Sahiba ita ta saka kanta karatun boko na addinine ta dan samu a wurin mahaifiyar ta a gida don yanzu hakama har takai jss two a makaranta gwaunati na diyan tallakawa irin su dake can dan kasa da unguwar su kadan. Da hakan ma yanzu ta saka kaninta Amar irin wanda take zuwa din duk a cikin dan abinda take samowa suke wanan hidiman a rayuwan su a wahalce. Karan wayan ta dake ruri daga gefen tane ya ankarar da ita da sauri ta mika hannu ta dauki wayan tana fadin dan halas yanzu nake maganan shi a raina fa sai gashi ya kira. Kallon ta yarta Nabila dake gefen ta tayi cikin ya motse fuska yar tace halan ya Abubakar ne ko tana danna daukan wayan take fadin shine dai. Yar ta wani kara tabe fuska tana kawar da kanta gefe daya ta dauki wayan tana fadin ni har ka ban tsoro da banji kiran ka ba tun jiya nasan kuma ku ba kiran ku akeyi ba idan baku kuka kira ba. Yace wallahi tun jiya kina raina aikine kawai da yai min yawa da gajiya kuma ya hana in kira ku jiyan. Sai kuma ya juya yana gaida ita da kwana tare da tambayan ta mutanen gida tace duk suna lafiya sun raka hjy karima unguwa dagani sai Nabila ce a gidan yau. Yace dama abinda suke so ke nan fita yawo aje unguwa basu da wani abin yi sai gulma a rayuwan su. Kai Modibo har yaushe ka zauna kasan abinda yaran nan suke so yanzu kai da kullun kana faman yawon bin jirgi zuwa kasa kasa. Dariya abin ya bawa Abubukar wanda mahaifiyar shi ke kira da Modibo don sunan kakanshi yaci ta wurin uba. Ni fa yanzun ba abinda ke damuna kamar inga ka tsaya da gaskiya kan zamcen auren nan naka shine muradina a kullun. Hajja Addah har nawa nake da kike min zancen aure a yanzu duka duka fa ban ko kai talatin ba balle in fara zancen aure. Zancen banza ke nan me kake nema a duniyan nan da baka samu ba a yanzu kudi ilimi duk Allah ya baka fiye da yadda ake zato. So kake duniya ta samu a baki dagani har mahaifinka da abokan shi kema tayin yayan su ka aura ? Ganin ran mahaifiyar nasu kamar ya baci abinda yaki jini ya gani ko yaji ke nan yasa a cikin wasa yace yanzu ni hajja Addah ina nake da lokacin neman wata yarinya can sai ki nema min ai wace ta dace dani ko ?. Cikin jin dadin zancem shi uwar ta sake murmushi ta yadda har yake jiyo ta a waya tana fadin to kokai fa modibo ka tsaya kana wahal da kanka dana mutane. Aure fa shine cikar kamalan mutum yanzu kana aure darajan ka zai kara hauhawa ko ga mutane zasuyi ma kallon cikkaken mutum a idon su sabanin hakan da kake zaune kai kadai. Dariya yayi kafin yace da ita wai daddyn mu ya dawo kuwa ko har yanzu yana can ? Wanan zance kakeyi ai sai lokacin da muka ganshi yanzu kuma don dama ya fada muna wanan karon zai dan dauki lokaci a can idan ya tafi. Allah ya dawo dashi lafiya ya fada tace amin kadai kula da kanka a cikin arna kun nan don Allah. Insha Allahu hjy Addah babu abinda zasuyi dani sai Allah na zauna ma acikin wa yanda suka fisu zama arna Allah ya fito dani lafiya balle nan da suke da surkin musulmai a tare dasu ga hausawan mu ma ko ina a garin kamar kana arewa. Allah ya tsare tayi mai kafin suyi sallama dashi tana jin tausayin dan nata da son shi yana karuwa mata a zuciya. Idan bata manta ba haka mahaifin su ya tashi shima ya fara dan buga buga har yakai yanzu yana ketarawa waje ya saro kaya. Shima a bangaren Abubakar din yana aje wayan nisawa yayi yana shafo kanshi zuwa fuska kafin ya furzo da iska mai zafi daga bakin shi. Yana ci gaba da tunanen matsalan gidan su din da yayi yawa a yanzu koba a fada ba yasan iyayyen nasa mata suna hakkuri da halin mahaifin su a yanzu da can din ma da sam daddy din baida lokacin su sam sai idan yaso. Sanye take a cikin kayan makarantar da suka amsheta masu ruwan blue colour buje da riga babu batun dan kwali ko hijjabi sai dan hular bareti da ke saman kanta wanda ta dunkule gashin kanta ta cusa a cikin hula yasa dole don yawan gashin hulan ya dan dago ta baya kamar tayi a cuci maza dashi. Bujen ya tsaya mata iya gwiwanta sai takalman da data sawo masu ita da kaninta wurin yan gwajon su na lagos masu kama da kwabattan maza take jansu hakana don kwarin su. Bata damu da kanta ba ta dauko kulanda take sayawa kanin ta abinci don tara kada yaga sauran yara naci ya saka kanshi a damuwa . Yasa a kullun bata yarda kanin nata yaje ba wani abinci a tare dashi kallon mahaifiyar su dake zaune ta kura masu ido kan duk abinda sukeyi na shirin fita makarantar tayi tana fadin. Umma mun shirya zamu tafi uwar ta dan nida tare da fadin to dahiba ubangiji Allah ya tsare mun ku Allah ya bada sa,an abinda akaje nema a rayuwa. Suka amsa gaba dayan su da amin don inda sabo sun saba da hakan a kullun idan zasu fita daga gidan zuwa wani wuri. Suka fito tana binsu da kallo tausayi ga yayan nata kafin ta mayar da idonta tana cigaba tunane rayuwan data baro a baya gida har ta saka yayan nata a ciki wanan halin kangin talauci a yanzu. Eh dolene yasa hakan a garesu don ta tsaretar da rayuwan su ga baki daya da ake nema a halakasu kan abin duniya. Hakan yasa tayi nisa da gida nisan da ba wanda ya zata ko ya tsamaci har zata kai wanan garin mai nisa haka da bata da kowa a cikin shi. Hawayene suka zubu mata a fuska lokaci daya don wanan tunanen da tayi na dan lokaci daya tasa hannu a hankali ta share ta dauki abin karin da Sahiba ta sayo mata don ta karya dashi. Bayan ta gama ta mike zuwa wajen gidan don tasha iska kamar yadda ta saba yi a akullun ta zauna tana kallon mutanen gidan suna gittaya tunda rashin lafiyan nan ya kamata. Duk da tasan ta makara hakan bai hanata kai kaninta har makarantar su ba har bakin ajin su ta kaishi kafin ta juya da sauri ta nufi nata wurin karatun . Tafe take tana sauri kada malamin lissafi ya shigo bata ajin don tasan yau dashi zasu fara darasi a jin nasu gashi kuma mugune don dole saboda halin shi ta koyi lissafi har ta iya yanzu. Bata ankara ba taji an watso mata irin ruwan dake kwanci a gefen hanya da sauri ta daga kai ta kalli drivern motan dake tafiya a hankali kafin ta sake dago kai ta mayar ga tufafinta daya baci da ruwanba lokaci guda . Rantane taji ya baci don ganin yadda kayan nata ya baci cikin lokaci guda haka bata san lokacin data bude baki tana fadi a cikin harshen yarbancin daya zauna mata a baki yanzu radau . Tana fadi a hasale Abi wareni ? Olesi omo buruku noses ta hada da turanci cikin daga murya da karfi ta yada har mai jan motan zai iya jin muryanta. Gani mai motan yaja ya tsaya sai can ya bata daina zagin a cikin harshen yarbancin ba sai can taga ya fito daga motan ya tun karo yarinyar daya batawa jikin nata don bada hakkuri shi kanshi bai so hakan ya faru ba har a ranshi hakan ya faru bane wajen kaucewa hanyar da yaje yi ya watso mata ruwan a jikinta gaba daya ya baci . Ganin haka yasa ya yanke shawara fitowa ya bata hakkuri don sanin zafin abinda ya aikata mata din a lokacin. Saidai tun daya tunkaro ta din yana jin muryan ta cikon dan hasala ta sake fadin you, you no desi road, see d way you skarter my cloth ? Mumu man wen no get sense ta fada da karfi tana juyawa ta fara tafiya ta bar wurin don ta makara sosai a lokacin. Tsaye yayi ya kasa karasowa inda take tsaye din sai faman kakaban kayanta da takeyi rana ta a bace kafin ta ja tsuki da karfi kafin ta soma tafiya rai bace tana fada kamar sabuwar mahaukaciya da ita. Yana tsaye har lokacin yana tunanen ina yasan fuskan yarinyar nan ne sai kuma ya tuna ina fa zai santa wanan yar kabilan yarobane fa shi kuma baida wani alaka dasu saina aiki. Ganin ta wuce batama tsaya ba yasa shima ya juya ya shiga mota yana jan tsuki a fili ya ja motar shi ya bar wurin yana fada a cikin zuciyan shi ya koma motan ya shiga ya tayar ya bar wurin zuwa lokaci shima ranshi ya gama baci da abinda yar yarinyar karama tayi mai don rashin mutuncin da ake fada yan lagos basu dashi dama. Yana fada a zuciyan shi tare da jan tsuki fili yana cewa wani irin garine wanan marasa mutunci da rashin sanin girman mutum. Har yakai inda zai tafi ransh yana bace har lokacin yana fada a zuciyan shi kafin abokin aikin shi ya jashi da fira duk da ya fahinci ran shi a lokacin kamar ya baci sai bai kula da hakan ba gare shi sosai don ya dauka dare fuska na dayaga cikin dabi,un shi don ko yaushe shi fuskan shi a daure yake. Haka yasa yaci gaba da masa bayani har ya manta da komai na bacin ran da yake ciki da farko sukaci gaba da tsara yadda zasuyi su cin ma abinda ya fito dasu a lokacin har zuwa yamma kafin su rabu ya koma masaukin shi. Sai dai duk abin nan hankalin shi naga abinda ya faru dashi da safe don ranshi ya baci da zancen abin daya faru din dashi na yadda yarinyar ta zage shi tsab da safe. Don haka ya zama mai dole a yanzu yayi taka tsantsan da kowa a garin saboda ya karanci halin sune rashin mutunci dai. Sahiba kuma dai a nata bangaren ta kasa suke jiki a makaranta don haka tun shiganta ajin take zaune a cikin class sai faman cika take tana batsewa ga banza tana fada a zuciyanta ita kadai. Har ta dawo gida tana zaune tana cire takalman dake kafatan da safa ta take labartawa mahaifiyar ta abinda ya faru da ita dasafe a hanyarta na zuwa makarantan ta Nan uwar take mata fadan ta daina zagin mutane haka tayi mai uzuri wata kila shima basan rashi ai ya watsa mata ruwan kwata ba da gagan sai dai idan yanayin hanyar dake kwancin ruwane yasa har motar ya watsa mata ruwan bai sani ba. Da yarbanci take fadin umma shi makahone da ba yaganin mutane a kasa suna tafiya, kawai dai wullakancin sune na masu kudi shiyasa yayi min haka . Ai da naga ya fito a fusace na gudunayi ai kada ya sameni a wurin ya dakeni a banza umma tace dako kin tsaya abinda zai maki ke nan ya dakeki ya daki banza. Iya wale dake jin hiran su ta juye baki tana fadin kin san kuwa baku da kudin zuwa police station yin kara. Jin ta tsoma baki kuma sun san hakan neman fitina kawai takeyi dasu irin nata yasa da ido umma tayi ma yar nata signal da tayi shiru. Suka kyaleta don zasu iya cewa dasune kawai iya wale bataje police station ba wurin sharia a gidan duk da yawan da gidan ke dashi na yan haya tallakawa irin su masu karamin karfi a garin suke dandazon zuwa wanan unguwan don kama haya acikin saukin kudi. Karshe dai mahaifiyar sune tayi masu nuni da su tashi subar wurun jin iya walen bata bar zancen ba har lokacin. Suna shiga daki Sahiba ta fara shirin fita uwar na kallon ta yadda take sauri tace yau ina zaki ke na ? Ta juyo tana saka hula a kanta tace kati zan sara in kai titi in gani ko za a dace don yau na makara da fita taba mahaifiyar ta amsa tana mikewa daga duken da take tana daure igiyan takalman da zata fita dasu. Dukawa tayi gaban uwan tana fadin zata fita sai ta dawo ta kalli yar nata tana mata adduan kariya da samun sa,a ga wanan fitan da zatayi din kamar kullun. Shagon da suke sarin kati su yawata a cikin gari ta nufa da farko mai shagon ya hana mata yace yamma yayi a lokacin. Sai dai yawan rokon shi da magiya data dinga yi yasa ya ji dan tausayin ta don sun saba dashi tana yawan zuwa shago yasa ya dauko suka kirga na dubu biyar ya bata katin don yasan yarinyar tana da kwazo sosai ga wanan sana,ar. Ba nawa da sauri ta yanke shawaran a ranta ta bin layin motoci tana sayar da katin don idan an hada go slow wani lokaci suna ciniki a wurin sosai. Nan ta fara bin motocin a gurguje da dan sauri tana fadin buy credit mtn or eirtel glo yin ko, inda wasu suna saye wasu kuma su koreta akan ta damesu da yawan talla din a lokacin suna cikin uzuri. Har karfe shida ya buga ba tare datayi cinikin kwarai ba don ko layi daya ba ta kai ga sayarwa ba a lokacin. Ganin hakan sai jikinta yayi sanyi hankalin ta ya tashi sosai ga yamma sai kara karatowa yakeyi a lokacin. Hakan ya kara tayar mata da hankali sosai a hankali taja jiki zuwa gefen titi ta zauna don duk motocin dake jere a titin tabi ta tallata kantin basu saye ba . Gashi tasan da cewa abincin su ya kare idan sunci yau dan cinikin da tayi ba zai ishe su shiga makaranta da safe ita da kanin ta. Duk tunanen da takeyi bai hana idan mota tazo wuce ta gaban ta tace dashi buy credit Oga five hundred, two hundred own or one by credit na all services we have . ZAINB IDRIS MAKAWA ANA DARA GA, , , , , , , , BY ZAINAB IDRIS MAKAWA BISSIMILAHI RAHAMANIN RAHIM ALAHAMDULLILAHI RABBIL A,LAMIN, , , , , , LITTAFIN NAN NA KUDINE YAR UWA KI BIYA DON ALLAH KADA MU RIKE JUNA DANI DAKE AKWAI GOBE YAR UWA, , , , Kanta yana duke tana faman kirgan katin dake hannun ta idan bayi missing din wani ba a cikin su biya ya hau kanta ke nan don mai shago baida hasara shi. Card seller aka fada a cikin wata bakar moto da baka ganin wanda ke cikin ta sai idan ya bude zaka ganshi. Irin wanda mu hausawa muke kira da motar muggan mutane don ba,a faye yarda da masu irin wanan bakin glass din ba. Da sauri ta dago zuwa wurin da taji kiran ta tsaya saidai window motar kuma a rufe yake bata kaza ba tana tsaye kafin a kara bude glass din a daidai lokacin da take fadin. Hurry, up Oga i wan, go nd pray is time for pray now ba tare da ta dago kai ta kalli wanda ke cikin motan ba da gani kuma tana a cikin sauri ne a lokacin. Don yadda take dan girgiza jiki alaman sauri dai takeyi da gaske taji daga cikin motar ance. Give me ten thousand mtn card da sauri ta dago tana fadin sir pardon you means mtn card only for ten thousand naira. Sai kuma ta dan ruga da gudu kafin ta juyo tace i dey come oga i wan go nd bringam now zata ruga da gudu aka kara fadin and eirtel for ten , , , , Ai bata tsaya ba ta ruga a guje don tasan duk dadewan ta ba zasu wuce go slow din nan daya jeru a layi ba zata samesu ko gaba ne. Tana zuwa bata tsaya magana ba ta figo roll din katin don tasan a yadda yake zuwa ta hado dana glo dana etisalat ta juyo da gudu mai shago na ihun fadin you you . You abi you de crazy today play with my money like that ai bata tsaya sauraron shi ba ta tafi da gudu kai katin wurin motan. Kamar yadda ta tsamata haka dinne ko sunyi nisa a lokacin haka ta bisu a guje tana kwala ihu har ta samesu ta dan kwankwasa glass din tana fadin here is d card oga all is for ten ten thousand making Fourty thousand Naira. Ta saka a cikin motan saman jikin mai shi da sauri yace you be mad who ask you to bring all dis daga gefen shi aka miko kudi yana fadin ya bari ta wuce kawai ga kudin ta. Godiya ta fara sake mai tana fadin oga tank you may god bless all your family and protect dem tana daga masu hannu . Yau itace farar rana a gareta cinikin dubu arba,in da dan kai haka tasan tana da kudi da yawa ke nan a yau sai lokacin tasan ta gaji sosai ta fara dan jan kafa a hankali zuwa wurin mai shagon data dauko katin ta iske shi ya cika fam yana zaran ido yaga ko zata dawo gareshi. Sai gata ta bullo gaban shi tana washe baki tare da fadin oga don bese with me na market matter isee that is why a run to catch d money now now i sell fourty thausand own. Beautyful girl you good wor ya fada yana washe baki a take ta hade rai tunda ya fara fadin hakan ta katse shi da fadin . Oya give me my share, i wan go home now my mama are wetin for me at home to come with something. Haba beauty u no go livan till tommorow to get more money than dis one wen i go give u now. No give me my money today ta fada cikin kara tsuke fuskanta gareshi don ta gane wayau zai mata ga hakan don yana iya fadin ba haka bane idan har ta bari goben yayi. Don dole ya bata kada ta tara mashi mutane a shago don haka ya debo kudin ta ya bata bayan sunyi lissafi ta tafi. A hanya sallah ya risketa don haka ta tsaya a wani masalaci nan bakin layi tayi sallah maimakon ta nufi gida wurin da ake sayar da masara sari ta nufa don taga kamat za a caba a wanan sana,an zata gwada ta gani ta dan hada da sayayan dan abinda zasuci ta nufi gida. Koda ta isa ta samu ana hayani a gidan fada ya hada mijin wata matar gidan tare da iya mulika suna cacan baki kamar zasuyi danbe ga wasu hausawa suna girke a part din su tayi masu sannu ta shige zuwa nasu dakin dake can kurya da gidan. Ta samu umma da Amar hankalin su a tashe don karo na biyu ke nan umma tana tura Amar zuwa kofa ya duba idan zai hangota dawowa gidan. A gurguje ta shigo ta gaida mahaifiyar nata kafin ta juya ta fita da sauri alwala tayi a wajen ta gabatar da sallah isha,i dake kanta . Sannan ta zauna a gefen su tana bude kayan data dawo dashi din ta zaro abincin da tasan mahaifiyar su tafi so tuwo shimkafa da miyan taushe saidai ita da Amar basu damu da tuwo din ba sosai. Nan umma tashiga tambayanta take bata labarin komai suna cin shikafa dafa duka a cikin take away tare da Amar. Umma gobe idan Allah ya kaimu masara zan gasa da safe ba zan shiga schoool ba ta fada tana kai shikafan dake shakesu a bakin ta. Masara Sahiba ina kuma kika kwaso masara tace da kudin dana fada maki na samu a yau di naga an fara wanan sana,an ko ina yasa zan gwada in gani ko akwai samu a cikin sa. Karatun ki fa Sahiba uwar ta tambaye ta fuska ta bata a lokaci guda kafin can tace umma na dan lokacine wanan tallan ai. Kaga wanan unguwar mazauna cikin ta yan kazo nazo ne shine mafi hatsarin unguwa a cikin garin nan kaf don in kana neman yan iska a ko wani irin yare kazo nan zaka samesu . Ya juyo yana kallon mai maganan daga gefenshi sai alokacin ya dan nisa ya juyo yana fadin naga alaman hakan tun shigowan mu ai. Meye sunan unguwar kai tsaye yace dashi AJAGULE sunan unguwar ai kaga baida wani nisa damu amma yanayin su yasha bambam sosai Don shi gaba daya erea din yayi kama dana yan duniya tun daga yanayin shigan su zaka gane hakan ai . Shi yasa ka gani ban faye shigo wanan erea din ba idan ba aiki ya kawoni nan ba sam bana yarda in shigo don sai su nakasa mutum a nan ga banza ba wani aiki bane garesu . Ai kuwa dai da alama ga zancen ka don yanzu na fara nazarin yan unguwar a hankali simo ya juyo da sauri yana fadin dama kasan wani ne a wanan unguwar ? Kai ya girgiza yace ai na fadama wanan ne karo na na biyu danazo aiki a lagos yace i see. Saidai ka shirya gobe iwar haka zamu saje a cikin su don dole mu aje wanan kayan da komai namu mu zama daya da yan unguwar. Hakan na da kyau ya fada yana lumshe idanu har suka kai inda zai sauka sukai sallama ya fita ya shige masaukin shi dake cikin APAPA. A gagauce ya samu wuri yayi sallah cikin sane dake kugi ya tuna masa da abinci don tun karin safe yana office suna tsara yadda zasu kamo mai laifin dayazo kamawa din. Yana zaune a wurin yayi odan abinda zaici wanda ba wani abu bane illa dan ruwan zafi da kayan shayi har aka shigo da abincin yana zaune yana nazari. Babu abinda yake a zaunen sai nazarin da tunanen ta yadda zai fito wa wanda yazo kamu tun daga wani kasa kuma suke tuhumar yana nan Lagos ya boye. Gwaunati ta saka hannu ga aikin nasu don a yanzu ne idan yai nasara ga kamun wanan mutum din sunan shi zai yi fice a cikin aikin sa sosai. Sanin inane lagos yasa ya zauna yake nazarin komai yadda ya dace yasan kowaye zai kama da irin alakarshi da wasu manyan kasan shi yasa akai komai a asirce ba tare da kowa yasan da hakan ba. Don hakane yake son shiri na musanman akan wanan aiki don ko simo abokin aikin nasa na nan bai san wani shiri da yakeyi ba. Don simo din ma dan adam ne zai iya juyawa a barshi a ciki tako wani lokaci kuma gashi dan kabalan yarbawa kuma dan kabilan zasu kama ke nan dolene yayi taka tsantsan da hakan. Mace mace ce ta fado mai a ranshi don haka ya zama dole ya hada da macen to ina zai samota agarin nan ya tambayi kansa ? Da wanan tunanen ya kwana a ransa yana faman nazarin ta ina zai fara gashi baison Simo yasan komai akan shirin shi din a yanzu. KADUNA Hajja Addah ta fito don jin gidan shiru da tayi babu motsin kowa daga cikin yaranta a lokacin gashi har karfe shidda da rabi na safe. Dakin ta tura taji shi a bude suna kwance dukkan su suna barci hankalin su kwance kamar ba su ke fita karfe bakwai da rabi na safe ba zuwa school. Hjy Addah ta tsaya cak ta rasa abin da zatace don takaici a fili ta furta wai ya zanyi da yaran nan a rayuwana ? Wanan wani irin rashin hankaline haka ace ko sallah safe babu wace ta tashi a cikin ku tayi shi kan lokaci balle kuma har kuyi shirin makaranta. Tana fada dasu cikin hasala sai Nabila ta dago tana fadin mommy har gari ya waye ne haka ashe shine ba,a tashe mu ba tun dazun . Wani harara Addah ta watso mata kafin tace a hasale ai to ku jarani kullun nazo na tayar daku kada ku saba da lokacin sallah a zukatan ku ta juya zata fita daga dakin Sai kuma ta juyo tana fadin wani albishir da zan maku shine kada ku manta yau kune zaku mana abin karyawa a gidan nan don talatu ta tafi kauyen su tun safe a can zata kwana. Ba shiri kowan su ya mike daga yadda suka lafe da farko suna hada baki wurin fadin mene mommy talatu tayi tafiya ? Ta juya tana fadin idan kunga dama kada ku tashi ku gaida Allah sai ku gyara kwanciyan naku ina daki in an gama abin karyawa kukaiwa hjy karima nata a part din, nikuma ku tayar dani nima in karya ta fita abinta daga dakin ba tare data kara sauraren su ba.. Ba shiri suka mike suna rige rigen shiga bandakin a lokaci guda dan gaba daya yau sun san nasu ya samesu dan sauki shima karfe takwas zasu shiga lecture kuma yau uku zasu dawo gida. Sun halin mahaifiyar nasu kan abinda ta fada ba fashi koda hakan yana nufin zasu rasa karatun sune na ranan ba zata janye abinda ta fada aiki kan sai sunyu shi a gidan ranan. Sunyi dabaran raba aikin a tsakanin su su ukun mai gyaran gida da mai fere dankali da wace zata dora ruwa da sauran aiyu ka har Allah ya taimaka suka hada komai. Addah batayi barci ba koda ta fadi hakan tana zaune tanaci gaba da azzakar don neman gafara da dacewa ga ubangiji tare da neman kariya da tsari ga iyanlanta ga baki daya. Suka shigo suna fada mata sun hada komai yana danning din ta kai kawai ta gyada masu taci gaba da abinda takeyi. Uwa ta gari ke nan idan yaro yayi ba daidai ba a cikin hikima zaka hukuntashi gobe da kanshi zai gyara kuskuren shi kan abinda ya aikata din idan ya gane hakan. Wayan tane yai kara ta dauka tana duban mai kiran ta da safe haka dan murmushi ta sake kafin tace modibo da safe haka. Ta dauki wayan da sallama ya amsa mata yana a cikin shagwaban daya saba yana fadin uwata mai sona da kaunata antashi lafiya ya kuke ya gida da sauran yan uwa. Ta dan lumshe idon tare da fadin lafiya ya aikin anyi nasara ko har yanzu da saura mami aiki ai bamu ko fara ba tukun nan dai yai mata bayani a gurguje tayi mai adduan nasara dana kariya tare da fadin ya kula da kanshi kamar kullun. Yau tun safe babu abinda nakeyi sai shirin fita da masara da zan gasa a bakin titi duk da alaman hadarin da ake hadawa a garin sam wanan bai daga min hankali ba ko kadan. Umma daga daki take fadin Sahiba idan masaran nan ba zai baci ba ki bari har zuwa gobe don yau kinga yadda garin ya tashi da hadadi haka. Ga wuri ya koma tankar gari bai waye ba umma ko kin manta nan lagos ne ba ruwan su da hadari ko ruwa don wanan baya hanasu harkan gaban su. Dole tana kallo haka diyan nata ta shirya ta fita zuwa vakin titi da kayan gasa masaranta data ara wurin iya wale data bata aron kayan da gaiya bisa rijejeniyar bata dari biyu idan ta dawo daga tallan. Dukko da tasan ko ita riban da zata samu ba zaifi dari uku ko biyun ba ga dan masaran data saro din don gawa a bakin titi. Don kyata da ganin iyakarsu tayi hakan don kawai ta samu hanyar da wani fitina zai hadusu ta kware masu zani a kasuwa don sunfi kowa zama matalauta a gidan hayan nasu. Tun fitowan Sahiban taga yadda hadin yagame baka ganin komai sai duhun ruwa mai shirin tsunkewa a kowani lokaci. Amma saukin abin haka mutane suke zirga zirgansu ba tare da andamu da yanayin da garin yake ciki ba. Wuri ta samu a gefen titi tabi jerin masu sayar da kaya saman titin itama sai dai tana dan nisa dasu kadan don kiran kasuwa kowa a wurin kusan haka ake tsayi a wurin. Sai da ta gama shirya komai yadda ya dace ta zauna tare da aje ledan da zata rufa idan ruwan ya gwauce ta fara hura wutan gason masaran. Dan yayafi aka fara a hankalin a daidai lokacin data dago kai tana wani tsaye a gefe dan tako kadan ta ita yana kallon duk abinda takeyi a wurin. Ta dago don daukan leda ta gyara koda ruwan zai zo da karfi ta rufa suka hada ido dashi daga inda yake tsaye din. Tun data zauna din take kula dashi tsaye a wurin ci gaba tayi da abinda takeyi na gaso tana fadin azo a saya. Ruwane mai karfin gaskene ya dauko lokaci daya hakan yasa kowa ya gyara kayan sana,ar shi a wurin hakan kuma bai hana masu son saya su tsaya ba. Wani ne yazo kamar zai saya sai kuma ya tsaya yana son ya kawowa Sahiban iskanci a wurin ta dinga masifa dashi . Ganin haka yasa ya dan matso daga inda yake tsaye din a cikin turancin shi dake nuna shu din ba mazauni lagos bane na gidi ya kore mutumin a wurin ta. Jin dadin hakan yasa ta dan cewa dashi ta gode taci gaba da abinda takeyi a wurin na sayar da masara din ba tare data kara kulashi ba. Kallon yarinyar yake daga nisa ta bashi matukar tausayi don wanan bata koyi sa,an hafsa babban yar hjy karima ba balle su Nabila da suke ciki daya davewa kannen shi dake gida. Ya lumshe ido gami dajin tausayin tallaka yana ratsa mashi a zuciuyar shi shidai wanan yarinyar Allah na yawan hadasu da ita tun shigowan shi garin lagos din. Muryan ta yaji tana yare a cikin yarbanci tana kallon shi kafin ta juya da turanci tana tambayan u no sebi yaruba ? Kai kawai ya gyada mata tace o i see if no worry meka help u stay under my ledda . Kafada ya dan daga don wanan din ma mai kama da yare da tayi sai da kyat ya iya gane me take nufi da hakan. Haka suka dan shiga ledan kusan duk haka wasu suka samu suka dan laba ga ledojin masu talla a gefen titi din wa yanda basu son ruwa ya tabasu ke nan. Hankalin shi naga titi yana kallon masu suce a surin ita kuma tana faman gyaran kayan ta kada su jike da ruwan saman. But u are new here ba ta tambayeshi ya gyada mata kai kaiwa don duk a kage yake ya gaji da wanan yanayin da suke ciki gara da itama a dan tsugune take saman wani roban penti karami. Wuta ta dan taba da hannun ta a take ta furta subbahanallah wai Allah na da sauri ya dan kallota kafin yace kin iya hausa ne dama ? Ita fadi take lah kai bahaushe ne kaima saidai yanayin hausan nata duk da ta iya yana dan surki da harshen yare alokacin. Mamakine ya kama shi sosai na yadda ta saje da yan garin har ba a iya bambamta ta dasu ya kara dan satan kallon yanayin yarinyar ba inda tayi kama da hausawa ko kadan. A nata dabi,an shine idan taga bahaushe kamar taga dan uwanta najini ne a garin don haka ta dauki masara daya mai zafi ta mika masa. Kai ya girgiza mata don bai saba da irin wanan ciye ciye din ba tace take zakaji dadin shi ya karba dole yana fadin nagode. Ba damuwa taci gaba da abinda takeyi fuskanta a dan sake ke yar inace ya tambaye ta ba tare daya sake kallon ta ba. Ni nidai hausace amma ban san sunan garin mu ba amma umman mu tace garin mu arewa ne . Arewa wani gari ke nan a cikin arewan tace ban sani ba tana dan jera masaran data samu ta gasa a lokacin . Mamakine ya kamashi shi ya sake jefo mata tambaya mahaifin ku fa take fuskanta ya sake a lokaci guda har saida gaban shi ta fadi. A zuciyar shi yace ko dai irin shegun yayan nan da ake shigowa bariki a haifane su tashi a garin lagos din a wahalce karshe su zama yan daba masu batawa arewa suna. Don yanayin ta da yaga ya canza da tambayan da yayi mata din sai can ta bude baki tace umman mu tace tun kafin a haifi Amar kanina mahaifin mu ya rasu iya abinda ta fada min ke nan kawai. Allah ya jikan shi yace ya mayar da kanshi gun masu wucewa harkan gaban su yana kuma kula da yanayin su don abinda yazo nema wurin. Meye sunan garin ku ta jefo mashi tambayan sunan garin mu kaduna kin taba jin kaduna ko tace kwarai kuwa a cikin history ko ba a stete din queen Amina take ba ? Tambayan yaso ya bashi dariya don yadda ta fada din sai a lokacin ya kara kallonta ya fahinci iya shekarun ta. Wata rana zaki kai ziyara ke nan tace umman mu tace akwai nisa sosai a nan kaga kuwa bazanje ba tunda kudin motan shi ba da yawa da naje naga garin da tayi mulki da ake fada. ZAINAB IDRIS MAKAWA ANA DARA GA, , , , , , , , BY ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , , BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AR, RAHHAMANIN RAHIM, , , , , , , , , , LITTAFIN NAN NA KUDINE YAR UWA KI BIYA DON ALLAH KADA MU RIKI JUNA DON TSORON ALLAH A ZUCIYA YAKE BA A BAKI BA, , , , Idan ke me tsoron Allah ce zaki gane hakan da kanki don zuciyar ki ba zai barki ki aikata abinda ba daidai ba yar uwa Allah yasa mufi karfin zuciyar mu Amin. Kada ta halaka kanta ta halakaki don kawai karatun da ba,a zuwa dashi lahira iyakar shi nan duniya abarki da nauyi wani a kanki. Mamakin ikon Allah yakeyi wai yar arewace ita kuma bata san komao game da arewan ba amma tana kurin ita bahaushiyace don yadda ta nuna data ganshi kamar taga wani dan uwanta na jini. Yanzu idan nace zamu tafi arewa nida umman mu da dan uwana kamar nawa zan kashe ta tambaye shi tana kallon shi ido da ido. Shima dan kallon ta yayi duk da wahalan da take ciki hakan bai hana shi ganin irin halitan da Allah yaiwa yarinyar ba wanda ba boye yake gareshi ba. Gaban shine ya fadi ras ras don bala,in kamar da sukayi da Batula diyar baffa kabiru dake karatu a waye. Haba shi dai yarinyar tana yi masa kama da wani fuskan daya waye dashi da farko amma ya rasa a ina yasan wanan fuskan nata ne ? Bakaji ba nace nawa zai kaimu arewa mu uku a musali ? Yace zaku je arewan ne ? Tace yanzu kan banda kudi tunda umman tace kudin yana da yawa sai dai idan na girma zanta tara kudi sannu a hankali wanda zai kaimu arewa din nida mahaifiyata da dan uwana. Ji yayi muryan ta yi tankar na diyan gidan su da dan diple din ta dake lutsawa sak irin nasu wani iri yake ji a kirjin shi lokaci guda zuciyar shi ta shiga balaguro a tsakanin iyayyen shi din da ya sani amma ya kasa gano ko yar waye ita kanshi yaba amsa ba kama daine irin na ikon Allah amma hakan bai yuyuwa ai ina sam kamane kawai. Dagowa yayi yaga hankalinta na gun mai sayen masaran ta a lokacin suna cinikin da baifi naira hamsin zuwa dari ba kallon tarin dan masaran da take gasawa yayi sai yaji wani tausayinta ya kara kamashi lokaci guda. Ya tuna yanzu yan uwan shi suna can a cikin sanyin AC da jin dadi ita wanan boyar Allah gata a cikin ruwan sama yana dukan ta. Dan saba,in din da taiyi cinikine take washe baki tana fadin yau na fito a sa,a gashi har na fara ciki a cikin ruwan nan sai kuma ta sauke idon ta ga hannun shi kallon wanda ta bashi tayi baiko ciza ba tace. Bakaci ba ko wanan din bai maka bane in canzama wani tana kallon shi yace No yayi min zan tafi dashi ne inci anjima. Leda ta fara nema a cikin kayan ta, ta miko mashi ya saka a cikin zuwa lokacin ruwan saman ya tsaya cak don haka ta yaye ledan data rufamasu din. Ya mike yana yi mata godiya akan zai tafi tace au baka fada min kudin motan ba zaka tafi yace dubu hamsin zai kaiku har abincin da zakuci ko wani garine zaku a cikin arewa din. Ido ta kwalalo waje kafin yace ko kuma a jirgi zaku tafi jirgin sama zaki kashewa kowan ku dubu hamsin din akala dai ko kuma a jirgin kasa saidai zaku dan jima a hanya baku kaiba ta jirgin kasan amma yafi saukin kudi gaskiya. Kila sai idan na girma na fara aiki ko na samu babban shago zan dauki umman mu muje arewa ina son in san yan uwana ina son in san garin mu kuma da kowa nawa. A ranshi yace idan kina da uba ko amma a fili sai cewa yayi idan kin tara kudin ashe zamu ganku arewa ke nan duk lokacin ya gaji da wanan zuban da take mai maganan dole yake mata don yarinyar na bashi tausayi sosai a cikin dan hiran da tayi mai din yanzu. Sai anjima yayi mata ya juya zai tafi tace dashi har zaka tafi ke nan ko sana kazo yi kaima a nan kamar yadda yan can ke zuwa nan neman kudi don haka kawai taji ya kwata mata a rai yadda yake magana shi da yanayin shi ya nuna natsuwa a gareshi. No nazo neman wanine a nan ya fada ta dago a cikin mamaki tana fadin a wanan erea din namu yake da zama tambaye shi. Ban sani ba ina dai neman shi ko zan dace Allah yasa ka dace ya fada tace amin ya juya ya tafi ita kuma ta dago kai wani uban hadarin aka kada hadawa har yafi na farko haduwa a yadda ya taso din. Oni yau na shiga uku da iya wale a gidan mu ina zan saka kaina da fitinan iya wale ke nan ta fada tana gyara kayan sana,anta don bata da niyar barin wurin. Tausayin ta ya kara kamashi don haka ya dan taka zuwa inda take sai gani kawai tayi an miko mata sabbin yan dubu daya zasu kai ashirin ga nata lissafin. Da sauri ta dago kai tana kallon shi kai ya kada mata alaman ta amshi kudin ya nuna mata hadarin a cikin alaman maganan kurame yayi maganan. Ga mamakin shi ga yarinyar data fito neman kudi a cikin wanan uban ruwan haka ai zata karbi wanan kudin sabbi haka dasu kar . Amma sai yaga ta gyada mashi kai tana fadin a,a kabarshi nagode ummana ta hanani karban alherin zama don ba don Allah suke ba mace abin hannun su ba sai da dalili. Cikin mamaki ya tambaya yana fadin su mazan tace kwarai haka umman mu ta fada kuma umman mu bata taba fadan abu ba daidai ba. To ki karbi wanan din kicewa umman ku din wani bawan Allah ya baki su sadaka don yaga kina wahala a ruwa haka idan kuma baki yarda da hakan ba sai muje wurun umman naki in bata da hannun ta. Ai zata karba ko idan ita na ba a hannun ta din sai ta dan tsaya tayi tunane kadan kafin ya ji tace to barin paka kaya sai mu tafi din yace karbi kudin ki rika idan munje sai ki fara bata kafin ta fito din ta karba ta cusa a cikin wani katon aljihu a rigan jikin ta da bai kula dashi ba sai lokacin. Gidan kusane ko don ni zan wuce na cigaba da duban wanda nazo duba din tace dashi nan kusa ne kadan yace to mutafi don haka ta dauko kayan buuuu tana gaba yana binta a baya yana karayiwa yanayin ta kallo . Koda tace gidan bai da nisa sai tafiya yaga sunayi a cikin ruwan cabo ga kazanta ko ina irin na lagos amma haka take takawa a cikin rashin damuwa ita. Shine ke dan tsayawa kaucewa yana kin wani yanayi na bacin rai a gare shi don haka tayi mai nisa sosai dabara ya fado mai yayi kamar yana waya ya hango ta ta shiga wani lungu hakan ya bashi daman jada baya daga nan ya sulale mata ya gudu. Kamar kullun ta shiga gidan da sallaman ta a baki kamar yadda ta saba shiga idan ta dawo duk da sanin su musulmai basu da yawa a cikin gidan sosai. Amma hakan bai hanata yin sallama idan zata shiga aiko iya wale na zaune a kofan ta duk wanan sanyin ruwa da sabon hadirun da aka hada din a lokacin bai hanata kasawa ta tsare ba tana sakin habaici ga umma dake dakin su labe ba. Tana ganin shigowan Sahiba dauke da kaya da sauran tarkace tasan batayi wani ciniki ba don ruwan ranan yaki bari aji dadin sana,a a ranan. Nan ta miko hannu tana fadin Oya give me my renting money and my property i wan go inside. Kallon ta sahiba tayi tana fadin i dey come now i no forget with your money now. No be now i nter d house, i no even see my mama self, your money de for my mind since i cary ur tins. Look Omo, me i no wan wahala woo just give me d money u promies me. Dan tsayawa Sahiba tayi da mamaki hali irin na iya wale da son kudi da fitina tace . Oya cary d money, u tink sey i me no get d money to give u now, if give u dis money now i no go baro your tins again. Iya wale tace eh make u no baro wan again naw, just qui qui give me d money first. Duk da uban kayan dake saman kanta a lokacin haka ta tsaya ta tura hannu ta zaro dari biyu ta mikawa iya walem tana jin haushi a zuciyarta ta wuce zuwa dakin su da sauri don abinda ke gabanta. Allah nagode ma Sahiba kin dawo ke nan nikan nasan wanan hadarin yau da wuya ya barki kiyi wani cinikin kirki a garin nan yau. Umman mu tare nake da wani mutum a waje ya ban kudi dayaga hadari yace in dawo gida shine naki karba don kin hanani karban kyautan maza shine yace wai muzo wurin ki tare dashi kinga kudin nan yana waje yana jiran ki fito. Zuwa yanzu fuskar uwar ne ya canza a sanyaye tace Sahiba kin san shi ko kinsan koshi waye. Da sauri tana girgiza kai tace a,a umma wallahi ban san shi ba asalima ban taba ganin shi bani nidadi kawai tausayi ya bani da ruwa ke dukan shi nace ya shigo ledana ya fake . Da zai tafi yaga an kara hada hadari ya ban kudi yace in koma gida ruwa yayi yawa yau a garin. Sahiba yaushe kika fara magana da mutane irin haka har ki fara karbo kayan wasu zuwa gidan nan duk da irin huduban da nake maki a kullun. Hasbunalah hasbunallahi wani,imal wakil umma don Allah kada ki zargeni ga hakan kada kiyin zato kan abinda ba zan taba aikatawa ba koda a bayan ki. Jikin uwar ne yayi sanyi lokaci guda don abinda diyar nata ta fada sai dai bata yarda ta nuna sarewan ta akan hakan ba na fada maki kiyi hankali da maza ke dama kowa a cikin garin nan dake din da dan uwan ki amna kuke a wurina duk danice na haife ku. Ko banza gari irin wanan bariki dole sai ka kula da kanka sahiba yau kaji wanan ya samu wance . Gobe kaji ai wancen ga abinda ya sameshi shiyasa a kullun nake kafa kafa da rayuwan ku da nawa a garin nake zama wawiya mara wayau ga kowa a garin nan . Badon komai ba don kawai mu tsira da mutunci mu a garin nan yanzu kinje yau kin karbo kudin wanan mutum gobe kuma da wata zance zaizo maki don ba zai baki abinsa a banza ba. Yanzu zan fita in masa kashedi a kanki yayi nisa dake kema hakan ki nisance shi kada ki kara yarda da kalaman sa a gareki . Don dan adam mugun ice ne wanda ka yarda dashi ka amince masa shine zai dawo ya cuce ka akarshe. Koda kuwa dan uwankane a wanan zamanin zai iya cutama idan ba,yi dace da dan uwa na gari ba sai a hada dashi a cutama. Tashi mu fita naga maishi ta fada tana mikewa tsaye sahiba ce ta fara fita a dakin umma tabi bayan ta zuwa wajen saidai suna zuwa babu kowa a wurin sai mutane dake dan gittawa a lokacin. A nan na barshi fa umna na fada kafin in sake cewa na barahi a bayana tafe na shigo in fada maki nan dai ta kara kwashe yadda sukayi har ya bata kudin da tafiyan shi. Yazo neman wanine a garin nan umma ta sake tambayan sahiba wanan kalmam daga ida take tsaye da sauri a cikin yanayin damuwa da tsoro na,amsa da haka yace umma . Don dai ni bai min magana ba ban iyaka yaga wani zai mun rashin mutuncine yazo inda naken ya kori mai shi. Shige ciki mu tafi umma ta fada da sauri suna shiga suka hango Amar a tsaye yana kallon iya wale dake fada a kofan su ta dauki tsohon abin gashin masaranta data arawa sahiba din a cikin masifa irin nata maineman nayi a kullun. Bayan sun shi aka kara gwaucewa da wani ruwa mai karfi dole kowa ya nemi mafaka saidai hakan baisa sahiba ta zauna ba. Nan ta shiga gyaran dakin su da tara masu ruwan amfani ga yan kayan dake garesu na aiki sai yamma sosai aka dakatar da ruwan zuwa lokacin yunwa yaga halaka haka ta fito neman abinda zasuci a cikin duhun nan bread da shayi ta dauki kudin jiya ta sayo don wanan kan da aka bata ta gama tsorata dasu a zuciyan ta. Kodata dawo ta samu Amar har ya soma barci a lokacin ta tayat dashi suka sha suka kwanta bafon sun koshi ba. Washe gari bata so fita school ba amma umma ta gargadata dole ta tafi har lokacin data dawo bata sake jiki ba a gidan. Wajen gidan su ta fita ta samu dan karafuna tayi dubaran hada hada abin da zata gasa sauran masaranta na jiya ta fita dashi duk da umma bata so hakan ba sai dai don kada ayi hasaran kudin da aka saya ta barta ta fita dashi hakana . Allah ya taimaketa ta sayar da wuri don haka taje kuma ta sari katin waya tana bin motoci dashi har zuwa magariba ta dawo gidan da abincin data sayo masu don tasan ba wani abin kwarai a cikin su tun jiya. Bayan sun gamane suna zaune ta kwaso littafanta tana assignment din su na makatanta, Muryan ummane yadaki kunnuwan ta tana fadin ina kudin da mutumin nan ya baki taji gabanta ya fadi don tsoro a sanyayye ta dago kai tana fadin yana a cikin jakar kayana na boye. Dauko mu kirga nawane a gani ta mike da sauri ta dauko kudin suka kirga tayi wani irin zabura lokaci guda don ganin yawan kudin dake hannun ta a mike sabbi fil dasu. Dubu saba,in ne cif a hannun ta ta dago kai da sauri ta kalli mahaifiyarta dake kallon ta daga gefe itama a tsorace. Wanan kudin ya baki su duka zama guda Sahiba da alama wanan yana so ya shigo rayuwan mu da yaudara dole akwai abin da yake so a gurin ki. Tsorone ya kara kama Sahiban don zancen akwai abinda yake nema a wurinta da umma ke yawan fada din nan ko yaushe. Zaune yake bayan motan yana bin ko ina na unguwanin da kallo yana mamakin yadda garin yake bunkasa a kullun yake kara girma da fadi. Nisawa yayi kadan yana gyara kwanciyan balance din da yayi a lokacin a bayan motan driver najan shi zuwa gidan shi don dawowan shi ke nan kasan daga tafiya. Alh Ibrahim Nagwoggo tsohon ke nan tsohon jami,in tsaro da yayi ritaya ga aikin shi yanzu ya kama kasuwanci gadan gadan. Alh Ibrahim ustazu ne babba yasan addini sosai kuma yana amfani da sanin nasa a yanzu matan shi biyu bayan dadewan shekaru da yayi da matarsa daya hjy Addah. Dashi da ita duka yan uwane aure ne hadin iyayye a tsakanin su dukkan su din sun fito a tsatso dayane mutanen Adamawane Amma mazauna garin kaduna don a yanzu kowa nasu na kusa yana zaunane a cikin garin kaduna. Saidai duk da hakan basu bar gida ba don har yanzu suna kai ziyara a wurin yan uwansu dake can suma kuma suna zuwa idan sha,anin su ya tashi. Don iyayyen su basu rasu ba saida sukai dabaran aurar da wasu yayan su ga danginsu dake can don kada zumunci ya yanke a bayan su. Zaman hjy Addah auren hadi na dangi a gareshi baisa ya gaza nuna kaunata a gareta ba itama hjyn ta iya tattalin mijin ta don tasan abinda yake so da wanda baya so sai suka zauna lafiya saboda kiyayyewan da yakeyi din a kan hakan. Yayan su ukku yanzu dake raye a duniya don haihuwan ta biyar maza uku mata biyu amma mazan na farko sun rasu sai kan Abubakar da suke kira modibo diyan suka fara tsayawa a duniya. Kasancewan Abubakar da daya tilo garesu bai hana su bashi tarbiya isalama yadda ya dace ba dashi da sauran yan uwanshi mata Nabila da Aisha ke nan kanne a gareshi. Ya auro hjy karima shekuru goma da suka wuce ita din ma,aikaciyar jinyace a baya irin matan kaduna din nan yan kwalisa na kwarai. Daga baya ta aje aikin dataga abinda yai mata a gidan don gaskiya ba laifi akwai hutu sosai a gidan nasa. Da farko hjy karima taso ta wuce gona da iri ga zaman su da hjy Addah din sai shi Alh Ibrahim din ya nuna mata bata isa ba don dama maigida shike fara bada daman a raina masa matan da aka sama a gida wani lokaci. Ganin idan ta matsa daman ta zai tafi a banza yasa ta aje duk wani makaman data shigo dashi na yakar hjy din a gefe aka zauna lafiya a yanzu da har takai ga haihuwan nata yaran uku duka mata. Ita hjy Addah kusan iyayyen su daya za a ce don wa da kane suke da mijin nata Alh Ibrahim din don haka zumuncine mai karfi a tsakanin su. Duk da akwai kishi na boye a tsakanin su da hjy karima sin hakan bai hana hjy Addah rungumarta kamar yar uwa ba agareta don yayan ta gaba daya tana nuna masu kyauna har cikin ranta kuwa. Yanzu Abubakar shi babban da ga Alh ibrahim din yayi karatun shi na secondary ne a FGC porthercort dake kasan ibo don Allah ya bashi baiwan ilimi tin yana karamin shi. Yana gamawa saboda kwazon shi mahaifin shi ya kaishi waje yayi sauran karatu shi a can har ya zama yana aiki a karkashin malisan dinki duniya na tararyan kasa da kasa a matsayin dan leken asirin su dai wasu aiyuka a wurin. Sai Nabila da Aisha da yanzune suka shiga matakin farko a univesty kaduna suna karatun kimiya da fasaha dukkan su. Tarbiya iya tarbiya yaran gidan kaf dinsu suna dashi don iyayyen idanun su yana a kansu wurin ganin sun basu ingattacen tarbiyan daya dace da islama a gidan. Wanan ke nan daga dan cikin tarahin ahalin Abubakar dashi kan shi Abubukar modibo dayanzu yazo lagos neman wani mutum dayayo ta,asa a can waje din wurin shara da yaudaran mutane yana cin kudi tare da sayar da miyagun kwayoyi yana kuma safaran makamai a kasashen Africa. ZAINAB IDRIS MAKAWA ANA DARA GA, , , , , , , BY ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , , BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM MALIK, YUU,MMIDEEN, , , , KIBIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA DA AMINCI BA TARE DA DAUKAN HAKKIN KOWA AKANKI BA YAR UWA ALLAH YASA MUFI KARFIN ZUCIYAR MU AMIN, , , , , Motar dake dauke da Alh lbrahim ta danna kai shiga gidan nasa sai lokacin ya sauke ajiyan zuciya yana gyara zaman shi. Kananan yaran yan wirin hjy karima ne a waje su biyu suna saye da dogon wandon jean blue da riguna ja riga haka take masu shiga kamar su din tagwayene don ta hada kansu tun suna kanana a nata hikimar. Murmushi ya sake ganin yaran daga kofan glass din gidan suna yan tsale tsalen a waje gida ke nan da iyali sai a lokacin yaji dan farin ciki ya sauka mai a zuciyar shi. Hankalin yaran ne ya koma wurin motan mahaifin nasu da sukai kwana biyu basu ganshi ba, yana wurin yafiya. Ya kuma dawo a yanzu a daidai lokacin da kowa nagidan bai tsamaci dawowan shi ba a ranan tsaye sukayi suna kallon motan suna jiran suga wanda zai fito daga cikin motan a lokacin. Driver ne ya fara fitowa da sauri ya zagoyo dayan gefen ya budewa ogan nasa mota a cikin mutunci a daidai lokacin yaran suka sheko suna ihun eh daddy daddy da gudun su. Hakan ya ankarar da hjy Addah dake zaune falo tana waya sai su Nabila da suma a zaunen suke suna tsabgogin su a lokacin. Nabila ta dan zabura tana fadin kamar daddy suke kira fa zai yuyu shidin nema don ba abin mamaki bane son a cikin satin nan yace zai dawo dama. Jin dan shirun da yaran sukayine yasa su daukan wasan sune kawai sukeyi a lokacin don kewan shi da suke ji a yanzu din. Kofa a katuro driver shine yake kokarin shigo da kayan shi ciki shi kuma yana bayan shi tafe da yaran kanana daya rike daya ako wani gefen shi suna dan hira. Mikewa yan matan sukayi suka hari mahaifin nasu suna mashi sannu da zuwa dukkansu su uku da yar kanwar hjy da riko a yanzu. Hjy ta mike a cikin kwaliyan da take na atampan super tana murmushi take fadin kwatsam haka babu sanarwan zuwa. Gida yayi kira banda saurin uzuri bayan hakan sannu da zuwa tayi mai a cikin ladabi duk yayan nasa na baibaiye dashi ya amsa. Zama yayi yaran suka zube kasa kamar yadda suka saba suna gaidaashi a lokacin hjy ta juya tana fadin bari a kawo abin sha bata tsaya ba ta shige ciki. Wayan ta dake hannun ta ta kalla ta dan fara neman layi a gagauce ta samu layin hjy karima data fita gidan tun dazun. Har ya katse ba,a dauka ba bata hakkura ba ta sake kira a karo na biyu kusan ya katse aka daga tare da fadin hjy Addah lafiya dai ko ? Duk inda kike ki dawo gida yanzun nan don Alh ya dawo yanzu haka yana cikin gidan nan ko ta fada a dan gagauce tana katse kiran a daidai lokacin da hjy karima ke fadin dama yau zai, , , , Munafuka wai Alh ne ya dawo ta fadawa kawayen nata da suke tare ai dama yau zai dawo ne kika fito dayan kawar ta tambaye ta. Ina fa nasan da zancen dawowan shi a yanzu din na a gaban ta fa nafito bata fada min zai dawo ba don nasan tunda munafukine shima ba zai rasa fada mata zancen dawowan shi yau din. Wai karima me kike jira da wanan matar har yanzu baki taka mata burki ba tun farko saida nace a fitar da ita kafin ki shiga kice wai ita din me wanan tsohuwar ba zata zama maki matsala ba sai dai uwarshi itace matsalan ki. Yanzu gaahi tana son ta zama maki ciwon ido tsakanin ki da mijin ki don tana munafuka wai zata kiraki tana kashe murya hjy karima kiyi sauri ki dawo duk inda kike Alh ya dawo. Mikewa tayi tana fadin ai ki barni dasu sai nayi maganin su dagashi har ita din zasu gane kuren su dan shimfida nayi masu inga iya gudun su yanzu ko nagani. Tabe baki yar dogowan daga cikin su tayi tana fadin na yaushe kuma wai an cuci na kauye yanzu ai ki mike din ki daina kwana kina sake AC kega wace ta samu wuri. Alhalin mai miji tana can rike da mijin ta sai abinda ta fada kuma ta shimfida akeyi a gidan ke kin koma yar kallo kawai. Binsu tayi da kallo don suna kara mata takaicine kawai da wanan maganan a yanzu don takai iya kuluwa da zancen yau. Boyar Allah hjy Addah kuwa tana can tana kokarin kare kariman don da tafito dauke da kayan ta mufo falon har lokacin yana zaune da yayan shi suna surutu. Tana direwa yake fadin wai ina karima ne ban ganta ba me yuyuwa tana bandakine ko tana barci bata ji shigowan ka ba sai kawai taga ya dan saki murmushi a fuskan shi. A daidai lokacin ne kuma karamar yar hjy kariman dake saman cinyan shi zaune ta sake fadin daddy I told you she went somewhare tunda safe wanka ma anty Nabilace tayi muna. A take ya kara daure fuska a hankali ya sauke yarinyar daga jikin shi kafin ya mike ya dago kai yana fadin kin gani keda ke kareta zaki koyawa yara karya, Wai ma yaushe kika fara karyane Addah ya tambaye ta yana tsure ta da idonun shi kafin ya juya yana girgiza kai. Kayi hakkuri Alh fitan ne ya kamata in bashi ba babu inda take zuwa ai tana gida baiyi magana ba sai hanyar part din shi daya dosa kawai. Ya barta tsaye kafin ta juyo tana fadin Amira waya tambaye ki sai mamin ku ta murde bakin nan mai surutu idan ta dawo. Fuska yarinyar ta tabe tana make hannu alaman kuka a lokacin daga haka hjy tabi bayan shi cike da fargaba don sanin halin shi da tayi. Ta sameshi zaune saman gado ya kwabe babban rigan shi dake saman jikin shi kamar yana tunane a lokacin. Tashigo da sallama tana fadin Alh kayi hakkuri ya dago tare da dakatar da ita yana fadin ki fita a cikin zancen nan don nafiki sanin waye karima . Ba yau ba nasan tana wanan halin da zaran na daga kafa nabar gadin nan zaman gida ya kare a gareta ita kuma ko kina dauka bansan da hakan bane wai har zaki wani tare kina rufe min. Ku daiyi hakkuri kowa da halinsa ake zama dashi inda sabo aika saba da halinta tunda yanzu an zama daya. Hada min ruwa in watsa ya umurce ta kai tsaye don haka ta juya zuwa bandakin don ta hada mai ruwan wankan. A daidai wanan lokacin kuma hjy karima ta shigo gidan su Nabila ta sama a falo ko kallon su batayi ba sai Aisha da zakiya ke fadin sannu da dawowa Anty . Ciki ciki ta amsa ta nufi part din ta kai tsaye saida ta shige Nabila taja dan guntun tsuki tana fadin Allah ya kara ai gwai kuma da har kuka tare ta ai. Ta shigo ta kallemu ta kawar da kai kune masu wani taron ta can ai kun gani yanzu wa zata zo tana budawa taje can ta hadu da daddy yau yar rainin wayau kawai. Hjy karima tana shiga dakinta ta wurgar da jakkan hannun ta da gyalen data yafa saman gado kafin takai zaune a hankali saman gadon tana tunanen abinyi. Yaran tane suka shigo dakin suna hayaniya mami kin sayo muna Sweet suna kokarin bude hand bag din ta su duba su gani. Hey Amira stop it bana hanaki wanan halin ba kina bude min jaka idan na dawo sai dayan ta biyun tace kada ki bata mami. Itace ta fadawa daddy wai kin fita tunda safe bayan mommy tace kina daki kina wanka ko kuma barci ya daukeki. Wani kallo ta watsawa yaran kafin ta kai hannu tana jan bakin yarinyar karama tana fada sai kuma taja tsuki tana fadin ita kuma munafukan wayace tace inayin wanka ? Ai daddy yayi fada yace wai ta fara karya ko yayi fushi ya wuce part nasa. Mommy ku tana ina yanzu tana part din daddy what ta fada tana mikewa yaushe ne daddy ku ya dawo ta tambayi yar babban dake magana ita kan Amira kuka ta saka. Don babban yarta tana makarantan kwana a lokacin tana jss one don ba babba bace sosai shikuma a ka,idan gidan shi makarantar kwana yara suke zuwa bai yarda da jekaka dawo ba a lokacin. Yarinyar kan bata san time ba don haka tace da uwar tun safe daddy ya dawo hakan ya harzuka karima din sosai watau tun safe ya dawo shine saida suka gama cin amanan ta yanzu zata kirata do munafunci wai tana fada mata dawowan shi a yanzu. Tamike tana fadin sai nayi maganin wanan tsohuwar banzan da bata san ta tsufa ba wallahi. Part din maigidan ta nufa da dan fushinta saidai tana zuwa dakin ta nemi fushinta ta rasa don yadda ya hade rai data shigo dakin ko sallama ya zama mai dole ya amsa ne ya amsa mata. Yana zaune saye dogon jalabiya mai laushi a jikin shi medan karmin hannu ya mike kafafun shi saman gadon dakin daya ya gyara. Alh sannu da zuwa ta fada da dan fara,an kissa a fuskan tare da fadin ashe kana hanya bamu sani ba ? Ke dakata fice ki ban wuri dan Allah banda lokacin wanan shirmen naki yanzu ya fada yana lumshe idanun shi don takaici yana maijin zafin wanan halin yan barikin na karima. Yanzu yake daya sanin kara aure da yayi yana zaune kalau da yar uwanshi wace aka gina su da tarbiya irin na islama tun a gida yanzun kuma itama tana gina mashi zuri,a da wanan dabi,an da suka koya gun iyayye da kakanni. Sai gashi kwatsam ita karima din ta shigo rayuwansu da rana tsaka tana batun tabarbare masa tarbiyan gidan shi da suka taru suka gina da yar uwarshi kuma matar shi a yanzu. Tsaye tayi tana kallon shi da mamaki a fuskanta kafin tace me kuma nayi Alh har kake korata haka a dakin ka yau ? Oh baki san kinyi komai ke nan da izinin wa kika fita daga gidan nan waya baki izinin fita a cikin gidan nan ya kara nanatawa gareta. Bafa wani wuri naje ba Alh na leka gidane in dubusu don an kwana biyu ban lekasu ba. Babu wayane da ba bazaki kirani ki tambayeni ba sai kiyi yadda kika ga dama ko to ki koma gidan naku har ki jini. Alh a kan wanan maganan kake fadin wai in koma gida to kayi hakkuri idan ranka ya baci ta fada tana zama a kusa dashi. A hasale ya juyo yana fadin watau fitan bada izinina ba shine dan magana ko lalai ya kara tabbatar da baki da hankali karima. Shiru tayi kafin ta mike ta fita daga dakin ganin baida niyar yi mata magana a lokacin yasa ta fice ta bashi wuri. Tana fitowa sukai kicibis da hjy Addah wace ta fito daga kitchen da sauri ganin hjy kariman ta ce a, a karima kin dawo ashe ina nan hankalina a tashe tun dazun. Eh na dawo ta fada a gadarance tunda bukata ya biya ai a ce yanzu wai an damu don bana nan to sai me iyaka dai yace inje gidan mu din. Kamar Alh ya sani tana fita daga dakin ya mike shima ya fito yana bayan ta tsaye yana jin abinda take fadawa hjy Addah din. Karima kanki daya kuwa meye laifina a cikin maganan nan ko da zaki fita kin fada min ne amma haka na daure na kiraki ki dawo Alh ya dawo kada hakan ya zama matsala a tsakanin ku. Ummhumm hjy ke nan sai ki samu yara gasu can ki masu wanan dadin bakin amma ai daya fada maki zai dawo baki fada min a lokaci ba sai daya dawo ya samu hakan. Yau wani iskamci kike jine a gidan nan karima Alh ya fada daga bayan ta ta juyo munafucine banso Alh . Ni baka kirani ba amma ita ka kirata ka fada mata dawan ka harta bari na fita bata fada min komai ba don munafuci sai a dinga nunawa mutum ana sin sa a fili. Alhalin zuciya tab da bakin ciki da hassada yakewa mutum a hankali ya tako yana fadin fice daga gidan nan kafin ranki ya kai ga baci yanzu cikin dakewa da nuna shi din tsohon dan kakine shi yayi maganan. Ya juya wurin hjy yana fadin ki hado min abin sha yanzu ya juya zuwa dakin shi din sai yaji tabe a bayan shi tana fadin aikin banza ta wuce. Kamar yadda ya dace a ranan karima din ce da girki wanan matsalan dai ne daya faru ya kawo hakan a yanzu. Ji abinda ya fada sai ta fada kicin a fusace tana hada mai abinda yake sha din daya umurci Addah ta hadomai din ta shiga hadawa da abinci ha baki daya nasa. Hjy Addah tana ganin hakan ta juya abinta zuwa dakinta cike da tunane da takaicin irin wullakancin yarinyar data tsiro ranan. Shima maigidan daki ya koma ya zauna yana bakin cikin abinda ya faru din bayan kamar rabin awa sai gata ta shigo dakin dauke da kayan abinci zata aje yace. Ke dakata waya umurce ki kikawo wanan ko dake nayi dana bukaci hakan ki kwashe kayan nan ki bace min da gani kuma dole yau sai kinje gida ba zaki kwana min a gida ba. To sai me ta fada a hasale tana mikewa tare da ci gabada fadin nasan makircin maza dama ka tayar muna da hankaline don a cuceni. Tunda kasan yau nice da girki ai amma da yake ba ita bace zaka kawo wani fitina kuma . Naji girkine idan ga da,a da biyayya amma tunda yanzu kin isa da kanki ba umurni na kike bi ba don haka yanzu ina da daman sauka a inda naga dama . Ai don ka fadi haka a yanzu banyi mamaki ba don nasan duk abinda kakewa a yanzu kakw hakan don kawai musguna min. Don ka dawo ta baka tsohon abu kayi yadda kake so a ciki zaka zalunceni yanzu ko don an mayar dani ban san abinda ke faruwa ba. Dan murmushin takaici ya sake ba tare daya dago a yadda yake ba yace ke kike ganin shi tsoho don ni a wurina sabone . Don ni tsohon nan yafi min na yar yarinya sharaf don ya wadatar dani komai karima sai ayau nake nadaman auren ki a ruyuwana walh. Tun sunayi suyi kadan kadan har yakai ta fara daga murya hankalin wanda ke gidan a lokacin ya dawo garesu muyi hattara mata fadan mu ya tsaya iya daki da mazajen mu. Yau kusan kwana biyu ke nan ina zama a wurin ko zanganshi in rokeshi ya karbi kudin shi sai dai ban gashi ba har wanan lokacin. Dole na daina fitowa tunda ya fada min dama wani yazo nema a unguwan don haka ba lalai bane in kara ganin shi kuma. Gashi yanzun ba wani ciniki sosai don ruwan dake hana mutane samun sukuni yin cinikaiya a garin. Don haka nake faman yin dan buga buga don mu samu abinda zamuci nida umman mu da dan kanina Amar da shima dai bai faye lafiya ba sosai. Ga wanan kudin da aka ban umman mu ta hana a taba ko abinci mu saye dashi mu danci irin na kowa ta hana sam nima dai da farko na tsorace da zancen kudin. Amma yanzu da ban kara ganin shi ba sai tsoro hakan ya fita min zuciya na koma harkokina na neman kudi kadan kadan don mu samu abinci da zamu ci kada mu kwana da yunwa. Yau na makara da fita don ban dawo daga makaranta da wuri ba don haka na yanke shawaran kawai na je sarin kati in hada da bara lokaci guda ko Allah zai bani sa,a Sai dai tunda na tunkaro wurin Indibisi dake bani sarin kati na hango shagon shi a rufe hakan na nufin bai nan ke nan a lokacin. Gabana ya fadi da tsoro da fargaban kada mu kwana da yunwa a ranan haka na karasa ina tambayan makwatan shi sai da kyar dayan ya kalleni lalace yace bai nan ya tafi garin su an masa rasuwa. Haka na juya da sanyin gwiwa ina tunanen ina zan dosa a lokacin gashi yamma tayi sosai don biyar da wani abu na yamma a lokacin. Come now indibisi customer maker give u for today naw ai indibisi yana bamu labari ki u are good customer now oya come meke u quic quic go and come back in time b4 eight. Tsaye nayi ina kallonta kafin ta kara fadin oya come naw ko ruwa zaki dauka gashi mai sanyi sun fara kankara a hankali na gyada kai tace da sauri tana mikewa taga kasuwa . Don ni da niyata in dauki kati sai in hada dayin bara ko zan samu abinda mukai sai abincin da zamuci ga Amar ba lafiya kwana biyu ke nan tunda ruwan sama ya dukeshi hanyan dawowa daga school. Allah da ikon shi duk da sanyin da akeyi sai gashi na sayar da daukan farko da nayi na dawo da murna nace zani gida ta bani share dina tace I beg me u cary anoda one now try u go sellam all please help me sellam . Matar ta ban tausayi na dauka nakoma titi na fara bin layin motocin dake dawowa daga wurin aiki wasu daga kasuwa ina fadin buy cool water, Pure water oga buy cool water daidai wata mota green dana tsaya ina kallon motan aka zuge glass din motan akace pure water. Da sauri na haro wurin motan kafin in karaso har masu ruwa irina sun kawo ko naji a na fadin No you how much is your money inji wanda ke jan motan yana nuna roban ruwan da nake dauke dashi. Nace da sauri three hundred naira i carry daga gefen shi aka miko kudi ana fadin in karba sai driver ya miko min daga haka ya motan shi suka tafi ina fadin oga u no carry d water naw. Tsayawa kowa yayi yana kallona ganin haka sai na soke kudin a cikin jikina don ba abu mai wuya bane yanzu wani ya kwace a hannu na. Na karasa yawata saura ruwa Allah ya kara ban sa,a na sayar na koma da sauri na mayar da kayan na hada da dan gudu wurin sayen abinci kada ya kare. Na biya chemist na sayo magani wa umman mu da Amir na doso gida da gudu duk da akwai mutane a wurin lokacin amma suma ba abin yarda bane ZAINAB IDRIS MAKAWA ANA DARA GA, , , , , 6️⃣ BY ZAINAB IDRIS MAKAWA BISSIMILAHI RAHAMANIN RAHIM IYA KA NA, ABUDDU WA IYAKA NAS, TA, IN, , , , , , , , LITTAFIN KUDINE KI BIYA KI KARANTA YAR UWA A CIKIN SALAMA, , , , , , , Zan shiga gidan nayi kicibis da wani mutum wanda ba yafita ko yaushe a gidan mu sai jefi jefi zaka ganshi koda darene ya fito. Hakama ba ruwan shi da kowa a gidan sai dai zaka ga manyan mutane suna sintirin zuwa wajen safiya da marance yana daki shi a can kuma zasu same shi dakin suyi duk abinda zasuyi a dakin wanda bamu sani ba mu. Na shigo da sauri don tunanen irin fadan da umma zatayi min don daren da nakai yau har misalin takwas da rabi nasan a lokacin hankalin su yana tashe da rashin dawowa na gidan da banyi ba akan lokaci. Don duk iya dadewana a waje shine bakwai na dare zan dawo ko ina nake da duk abinda nakeyi zan barshi in dawo gida a wanan lokacin. Sai gashi yau tunanen halin da muke ciki a dakin mu yasa nakai wanan lokacin a waje wurin neman kudi ban sanda shi tsaye a wurin ba ina zuwa da sauri ina haki don gudun dana danyo mukaci karo dashi har dan abincin da na sawo ya bare a kasa don zafin da naji ban san lokacin dana sake abincin ba wurin. Abi ware ni ? u no de si road u de warker wit ur eyes closed daya daga cikin yaran mutumin ke fadin haka da suka taso kamar zasu cinyeni danya a lokacin. Ina kasa ina bin abincin dake kasa zube da kallo da takaici sai hawaye ke zuba min daga idona a lokacin nace. Na dan dago a hankali daga duken da nake na soma fadin god go ponish u ina nuna wanda ya tureni din da yatsan hannuna ina hawaye. Na sake fadin god go ponish u wetin i go gibe my mama today na d food i buy for dem naw u push me with dis ur big bodi d food don fowl down all. Wani dan gidan bisi da muke kira iya bisi da sunan shi yana fitowa ya same mu a wurin yace ehh ya sayiba na d food wen your mama de wetin for nayin u puur ? Hungry go kill u nd ur mama today wani irin haushi na kara ji a raina na sake fadin na dis yeye push me down. Dayan da suke tarene ya daga hannu zai kai min mari sai wanda mukai karon dashi cikin tsawa yace mashi. Takwabe don't toch her give her dat money make she buy anoda one na kalleshi a fusace ina fadin . Me i no wan money my mama go beat me if i kwalet de money u wan give me na food i want na fada a gadarance. C dis yeye girl wen de talk rubush i beg mey u carry d money go don't west our time joo sai naji ogan ya kalleni yace carry d money first meke he bring food for u inside. Nan yacewa dan uwan ya dauko wanan abincin na dakin su ya kawo min shi dayan ya tura min kudin da yace a ban da karfi a jikina har saida na dan ja baya ya taka zuwa dakin da suke zama wanda gidan hayane ba ruwan wani da wani a gidan. Ina tsaye ina dan kakaban ledan maganin dana sayo wa su umma wanda duk mai ya bata yana tsaye yana kallona har dayan ya iso da irin ledan nan na abincin resturan mai sunan shagon a jikin ledan ya miko min a fusace na karba sai kuma na kalli kudin dake hannuna nace. Carry ur money back dis one is ok for me i go nak ur darty mouth if u no live dis place wanda ya ban ledan ya fada a fusace. Ganin zasu iya dukana na wuce ina fadin my mama d come now if i go inside na wuce da sauri na bar wurin. Ina jin shi yana fadin cary ur wahala go yeye girl u na disturb people for nothing hungry girl omo jagu. Ni dai na shige da sauri a kofa na hango umma tsaye tana diban ta hanyar da zan fito da daren nan . Ina karasowa take fadin Sahiba irin tarbiyan dana baki ke nan ki tsaya kina fada da maza a bainar jama,a haka yanzu fa iya wale ta kwankwasa min take fadin gaki can kina fada da maza a bakin kofa. Umma tureni yayi fa abinci ya zube shine nake magana a kai sai kika ce su biya ki ko ? Ta fada a fusace tana kallona a dan maraice nace ni ban ce su biyani ba sune dai suka bada kudin nan gasu na miko mata kudin da abinci . Ta kalla tace na meye shi kuma kudin bayan abincin da suka bayar sai mukaji muryan wanan daya dauko min abincin a daki yana fadi whare are u come carry you vein u be lucky girl today our oga have macy on u. Ya jefo min dan gyalen dana barshi a can da nake yafawa inyi sallah dashi idan sallah ya riskeni a waje. KADUNA Tsayawa Alh yayi saida yaga fitan hjy karima gidan don bai iya jure cin mutuncin da ta daukowa kanta a gidab nasa yanzu. Wurin motar ta ta nufa tana fadin Asmau kina ina wai kin san mutumin nan yau korata yayi a gidan sa kuwa ? Gani nan zan fito wallahi ban san inda zan dosa ba tunda ba gida naje ba dazun din kuma yace lalai dole inje gida a yau. To ki tafi mana wani wuri zaki ba gidan ku ba tace tana tayar da mota to idan naje gidan me zan fadawa iyayyena shi nake tunane a yanzu. Ki je gani tafe gidan naku asamu ta fada kai tsaye kafin tace yaran fa yace kada in fita da kowa a cikin su suna can na barsu ciki dole. Wanan mutumin fa sai munyi da gaske a kanshi wallahi inba haka ba wanan munafukan tsohuwar matar nasa zata fitar dake a gidan kina ji kina gani kibar mata yayan ki ta bautar dasu. Wallahi basu kai min can ba dukkan su kuwa ta fada a hasale kafin taja tsuki ga maganan da Asmau ta fada a karshe tana kashe wayanta. Taje gida sai ganin ta akayi kwatsam ta shigo da kukan muna funci hankalin mahaifiyar ta ya tashi sosai a wurin. Tana tambayan ke lafiya kike kin shigo kinawa mutane kuka haka ai sai ki tsorata mu ga hakan. Cikin kuka tace mama cewa yayi in zo gida uwar tace ya dawo ne ko daga can ya bugo waya yana fadin haka. Ya dawo umna don kawai bai sameni a gida ba naje aurin barka shine na dawo yace kada inyi girki inbar masa gidan sa. Wanan ai daji wani sherine aka kulla a hakan amma haka kawai daga dawowan shi don bai sameki ba zaice wai kizo gida kuma fa mama cewa nayi gida nazo amma bai yarda ba ta kalli uwar. Keko ya raina gidan namu mana ya manta a dai ya nemeki har ya aura kika hayayyafa dashi. Kai kai tir da wanan halin mahaifin hjy karima dake fitowa daga bandaki yake fadan haka da buta a hannun shi yana kallon su. Yanzu ke kande da zaki mata fada kan abinda ta aikata ba daidai bane tunda kin sani amma kike fadan wanan ga yarki da tayo ba daidai ba. Shin kinsan girman zunubin da kika aikata ga hakan ko karima malamai da masana sunce da mijin mace yayi tafiya ya dawo gida bai samu matar shi a gida ba . Gara ya samu gawan ta ace ta mutu da yasamu ta fita bada izinin shi ba ya fada yana binsu da kallo. Ba komai ke damun ki ba karima sai shegantaka irin wanda kikaga uwarki tanayi a gidan nan ya kawo hakan. Yanzu malam ni meye laifina a cikin zancen nan da zanka dauki laifin ka dora min nima ai idan nasan ita keda laifi nima ba zan kyaleta ba ai tunda mijin ta shine komai namu a yanzu. Don haka ba zanso ta saba ba saidai a kan wanan dan zancen kawai zai turo muna ya gida da yamman nan. Shine namijin kwarai malam ya fada yana kaiwa zaune bayab ya gama kallon iyalin nasa yaci gaba da fadin idan bai turota gida ba a yanzu ai ba zamun san abinda take aikatawa ba din. Tabar gidan mijin ta bada izinin shi ba ta tafi wani wurin da ba wanda ya sani koke kin san inda ta tafi ? Yarinya tayo laifi tazo gida ta kawo kara ba za a tsaya ayi bincke ba a bata laifin ta don gobe kada ta kara sai kawai a mara mata baya karshe auren ya mutu Sai daga baya azo ana da an sani mafi yawan auren dake mutuwa a yanzu sakacin kune na iyaye daga dan magana kadan sai zancen saki ya biyo baya an bata goma daya bai gyaru ba irin wanan hasalan banzan da yanzu kikayi. Yar kice mai laifin amma kina kokarin daukan laifin ki dora akan wani can da baiji ba gani ba har kina fadin wai ba banza bane wanan abin . Idan ba banza bane shegan takane ko me yanzu yarinyar nan bata rasa ci ba bata rasa sha ba a gidan mijin ta amma don jin dadi har zata sa kafa ta fita bada izinin shi ba. To ai malam ni ba nabi ta nata bane ganin zancen nayi dai ba wani zance bane wanan ya dago yana fadin agareki yake ba komai ba shi da yasan kansa ai kinga ya dauki matakin daya dace. Nan dai yayi ta fada har akai kiran sallah ya fita ya barsu a wurin kamar jira asmau keyi ya fita sai ga sallamanta ta shigo gidan. Da sallama sama sama tana fadin shi wanan tshon me yake nufi da zai turo ki gida a yanzu don kawai kin fita baya nan. So yake ya mayar dake matar gida matar kulle irin kidahumar matar shi ko me da zaizo ya tayarwa mutane da hankali haka ne. Nima shi nagani yar nan amma malam ya tatare don yana na miji dan uwanshi yace kada ai maganan wai karimar ce bata da gaskiya. Humm baba baisan komai ba wallahi mama idan kinji tarihin uwar gidan nan nasa sai kin san karima bata gane ma koma a gidan nan. A ko banji ba ai naga yadda take shimfida iko da idona don ko yayan data haifa iko take da abinta balle wani. Indai zaku tashi tsaye idan kuna son zaman ta gidan nan wallahi ku tashi don in ba haka ba kuna kallo zata koma bora da karfi da yaji a gidan. Aiko ba akai ga hakan ba don duk inda zan shiga in fita a gidan nan sai nayi don yata ta kafa nata gwaunatin a gidan. Mama ni ba wanan ba kinga wanan dan nasu da suke ji dashi kamar kwai duk ilahirin zurian su yanzu kowa jinsa yake idan yana wuri ba a kallon kowa bayan shi. Ba kinji ba mama dama irin matan nan ai ba kansu suke asircewa ba har da diyan da suka haifa sai sun nema masu farin jini. Amma idan kaji Allah a bakin ta sai kace yar wani shehi ce ita wurin kawowa mutum Allah kusa. Sallah da basuyi ba ke nan akan lokaci daga uwar harsu suna zaune suna kullin sheri a daidai wanan lokacin kuma hjy Addah tana can saman sallayanta ta mika bukatan ta a wurin Allah. Har aka kira isha,i ta tashi ta mike ta gabatar ta dan dade a zaune tana addua kafin ta fito don shiryawa maigidan abincin dare akan lokaci tunda tasan baici kome mai nauyi ba tunda ya shigo gidan. Saida ta gama shirya komai ta koma dakinta ta yi wanka ta tsula kwalliya kafin ta fito daga dakin. Lagos Ajagule ruwa sahiba ta mika ma Amar dake kwace ya hade maganin data bashi kafin ta juyo kan mahaifiyar nasu da ledan maganin da ruwa tana kokarin barewa umma din nata. Duk uwan na kallonta tana faman sake sake a zuciyar ta kafin Sahiban ta juya ta dauko ledan abincin da aka bata din ta fara budewa a gaban kanin ta data tayar dashi yasha magani ga abinci kuma duk da bata san wani kalan abinci bane a cikin ledan. Tana budewa wani kamshi ne ya daki dakin sai da kowa ya kai idon shi kan miyan kafin itama ta dago kai ta kalli mahaifiyar su tana fadin. Umma wanan abincin zaikai dubu biyar fa ko yafi haka ji irin girman naman dake cikin umma ta dago tana nunawa uwar miyan. Kallon da mahaifiyar ke matane ya dakatar da ita daga maganan da takeyi din Sahiba uwar tace sai diyar tayi kasa da kanta cikin ladabi. A tunanen ki idan naso mu rika cin wanan ko yanzu da banda lafiya na gaki ba nasan zaki iya kawo muna abinda yafi wanan din ma idan munso hakan. Sahiba bata gane inda uwar ta dosa da zance ta ba sai da taji uwar mu matane kuma cikin bariki muke rayuwa muna da hanyar yin hakan ko karfina ya kare ga naki a yanzu. Saidai ni ba abinda ya kawoni nan ke nan jin dadi na banzatar da rayuwaba da naku ba nazo nan ne nabaro yan uwa da kowa nawa don wani dalili mai karfi a garemu baki daya. Saidai me idan kin fara ganin irin hakan dole ne duk ki yarda wanan tsarin namu na baya tunda naga kinga wanan kina farin ciki a yanzu. A , da farko naso na hana ki cin wanan abincin amma daga baya da nayi tunane sai nagane gaskiya Allah ne ya tsaga hakan yau a garemu ya kawo muna wanan kyautar a matsayin abincin mu. Amma said, sa hakan bai kwantar min da hankali ba don na kula a yan kwanakin nan abubuwa sun soma faruwa dake Sahiba. Don tun ranan da kika zo min da kudin nan hankali ba a kwance yake ba yanzu dake don gaba daya na shiga rudani duk da ina da yakini kan irin tarbiyan dana taso dake a cikin shi sai dai dan adam ba ai masa sheda da sai ince ke din ba rokon shi kikayi ba don kinga halin da muke ciki. Ki tsare kaki ki tsare mutuncin ki tsare marta ban gidan da nawa don Allah kin soma girma sahiba ki kula da rayuwan ki sosai fiye da yadda kike tsare a da can baya. Jikinane yayi sanyi na kai kasa dabas na zauna ina sauraren umma din tana fadin garin nan duk yan kazo nazone a cikin sa kinga ba wani kwaba a nan . Ni kaina maza sun sha kawo min hari Allah na kareni da yake sun iya dadin baki idan suna da bukan mace sai i lokaci guda duk zokimmm.m..m. n da nakeyi inci wanan ..... mmm. abincin ya kuma fice min a raina. Sai da kyat na iya dan cakula muna ci umma na kara muna nasiha a bayanen akan zaman duniya a garin lagos din karshe na tsame hannuna a hankalin dan yanayin da nake jin kaina a lokacin. Hannu na tsame na mike umma ta bini da kallo sai a lokacin na tuna da zancen kudin dana samo wurin tallan ruwa. Tsorone ya kamani na yadda zan nuna mata wanan kudin dake hannu na a yanzu ba yadda na iya tunda ba yadda zanyi dasu na ciro kudin daga cikin aljihu tare da kiran sunan umma din sai kuma nayi shiru. Kudin dake rike a hannuna ta kalla kafin ta mayar da wanda bakon fuskan gidan hayan mu ya bani suna aje saman tabarma a gefen ta. Nan dai nayi mata bayanin komai akan kudin ta karba taba bina da kallo kamar na tuhuma hancin ta takai kudin kafin inga ta cire da sauri tana fadin. Wanda ya baki wancan kudin ranan shine ya kara baki na yau din kuma don kamshin turare daya sukeyi da wancan din. Cikin dan marairaice nace wallahi umma bashi bane asalima wanan din ba bahaushe bane kuma yana cikin mota mai kyau sukace na bayar da sadakan ruwan ga mai bukata . Ya akayi idan bashi bane kudin suke kamshin turare daya da wancan din daya baki dole maishi bibiyan ki yakeyi ke nan sahiba. Idan ko hakane ya zama dole mu bar wanan unguwan mu koma wani unguwa can mai nisa mu zauna ta yadda ba zai gane inda muke ba kuma. Bakina yayiwa umma wani tambayan da banyi niyar mata shi ba a lokacin take yanayin umma din ya canza a lokaci guda har cikin ta yana dan shock don tambayan don cewa nayi. Idan hakane umma ki kaimu Arewa gidan uban mu zaifi muna wanan yawon hayan muna zama da arna. Sai kuma na koma dana sanin yi mata wanan tambayan don ni kaina abindake cin zuciyanane ya fito fili a lokacin. Don legas din garin kazo nazone da ai daba haka ba da yanzu na fara shan gorin hakan a wurin mutane sunan babu abinda ya damesu da zancen wani ina ubanka can wa mutum. ZAINAB IDRIS MAKAWA ANA DARA GA, , , , , , 7️⃣ BY ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , , BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM IHHI, DINAS SIRATAL MUS,TAKKIN, , , , , , , , LITTAFIN KUDINE YAR UWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA, , , , , Kwana biyu kamar Amar yaji sauki sai gashi kuma mun wayi gari dashi ya kankame muna duk idanuwan shi baka ganin kome sai fari. Ganin hakan yasa nasa ihu lokaci daya ina neman taimako ga mutanen gidan mu saidai abinka ga yare ba wanda ya leko waje don agaza muna a wanan halin. Son kowa na gudun abinda zaiyi laifi ko ya jefa kanshi a cikin wahala a lokacin duk dai iya abinda suke gudu ke nan. Ganin ba wanda ya leko waje don ya taimaka muna yasa na fita da sauri zuwa wajen gidan sai yan mutane tsiraru dake fito wa a gidajen dake gaban mu kawai nake gani. Sai kuma motocin da na gani a kofan mu guda biyu ajiye da alaman dai bakine su don suna magana da wani dake tsaye daga waje yana duke a cikin motan. Olon maja somebody help me please na kara yanka ihun ina dora hannu a saman kaina a cikin gigicewa don na bar umma rugume da Amar a dakin. A hankali ya dago daga jikin motan a ciki irin shigan da yakeyi a kullun da ba a ganin fuskanshi gaba daya sai dai kasan fuskan shi kawai. Ya sauke kallon shi a kaina na dan lokaci yana kallon yadda nake ina tsaye ina kururuwa ina ganin hakan na nufe shi da gudu na fadi kasa ina fadin please oga serve my broda from death. A cikin wani murya na kasaita da nuna isa yace where is he now na nuna mashi da hannu yana ciki. Da sauri naga ya juya zuwa cikin bai tsaya jira na ba nima na mike nabi bayan shi da sauri ina nuna mashi dakin mu bai tsaya jiran komai ba ya fada dakin da saurin shi. Umma ya hango a zaune rugume da Amar dake cikin halin dana barshi har lokacin bai a cikin hayacin shi. May we go hospital ya fada kawai ya sungumi Amar din umma ma ta mike tsaye tare muka fita motan nan da yake a wurin dana samesu ya nufa yana fadin open d door for me da sauri na cikin ya bude kofan motan. Sai lokacin naga ashe mutum biyu ne a cikin motan zaune a lokacin yake magana dasu fada motan yayi rike da Amar din a hannun shi. Ya umurci umma ta shiga nima na fada motan duk da bata daukan mu a cikon hausa umma tace Sahiba ki koma ki tsare muna daki kin san halin yan gidan nan namu ai. Umma ba zan iya barin ku tafi ku kadai ba ban san halin da zaku kasance a ciki ba a can ? Ki barta a tafi da ita idan hakan zai kwantar mata da hankali ya fada shima a cikin turanci ban tsaya mamakin yadda ya iya hausa ba har yaji abinda muke fada don hankalin mu dake tashe a lokacin. Wani haddaden asibiti suka kai mu da sauri umma tace dasu we no get money to pay bill me we go d gonvement one . Don't mind d money naw, we should pray for his health now god bless umma ta fada yace dont mind. Su suka fita sukai dan cuku cuku har aka karbe mu a asibitin aka ba Amar gado ke nan an kwantar dashi haka ke nufi . Daga yanayin fuskan umma zaka gane abu da yawa ya taru mata a lokacin sai dai kawai abarwa ciki sauran zance. Gari na dan haskawa ya shigo dakin yana fadin mama we are going we pay for all his bill so don mind now nd collect din money, user, am for food nd trasport . Ya dan tsaya ta window dakin ya kalli yaron da aka sakawa abubuwa a bakin shi idin shi suna rufe lub kamar bai a raye idan badon numfashin da yakeyi ba a lokacin. Haka suka fita muka bisu da kallo kafin inji umma ta sauke ajiyan zuciya tana fadin kin koma neman taimakon su ne kuma sahiba. Umma a waje na gansu lokacin da nake neman taimako kowa na gidan yaki fitowa ya taimaka muna a lokacin sai shine yazo har dakin ko magana bai mun ba. Ki kiyayi wa yan nan ina fada maki don da ganin su akwai abinda suke shukawa wanda basu son mutane su gansu. Ni kan shiru nayi na mayar da hankalina a wurin amar dake kwance tare da abin nufashi a jikin shi muryan umman ke fadin. Akalla sun kashe muna kudin da zaikai daruruwa a take a wurin nan yanzu ba tare da sun damu da hakan ba. Akan wani dalili har za suyi hakan a garemu alhalin ba yan uwansu muke ba sahiba dole sai idan suna da manufa akan mu ga nawa wautan nace nima ban sani ba Umma. A gaskiya sahiba wayan nan mutane sun saka zuciya a zatgin hakan kwata kwata hankalina bai kwanta dasu ba ko kadan. Don yadda suke facaka da kudi akwai alaman tambaya a garesu kuma suka zo a cikin wani yanayi dake nuna su din wasu marasa gaskiya ne. Amma umma koma meye mu dai babu ruwan mu da su tunda sun taimake mu ai shike nan yanzu ba sai sun kara ganin mu ba kuma. To Allah yasa sahiba ta fada tare da nisawa ta kalli kudin da ya bata musai abinci umma tana fadin wanan kudin duk abinci zamu saya dashi kamar ba jinya mukazo yi ba a nan. Sai naga ta fara kirga kudin har ta kai karshe ta dago ta kalleni tana fadin kinga abin da nake fada ko dubu darine cif sahiba aikin me wa yan nan mutane sukeyi da har suka samu kudin nan a yanzu . Watau idan uwa ta mayar da yarta kawar shawaranta zata zauna tayi hiran komai da ita koda shekarun fahintar yar bai kai ba akanzancen da sukeyi din daga dan hiran har yar zata fara fahintar wani na rayuwa. Don wanan zancen na uwar yasa yar ta dan shiga zurfin tunane a lokacin ta fara hango abinda hankalin ta ya kasa hango mata a kan mutanen Zaune take tana lazumi saman sallaya bayan ta idar da sallah magariba wani kanshi ya ziyarci hancin ta ko ba a fada ba tasab kanahin turaren mijin sune wanan. Shi din ne ya shigo dakin yana gyara agogon hanunun shi ya dan kalleta yana fadin aroka muna da yawa don Allah . Ta dan dago kai ta sauke a kanshi tana dan murmushi tana fadin Allah dai ya karba muna wanan kamshin haka sai ina kuma haka ? Ya dan bata rai kafin yace zanje gidan su wanan mara hankalin ne karima don mahaifita ya dameni da kira tun rana hjy Addah bata bata rai ba shima kuma din bai zaci hakan a gareta ba dama. Shedab da yake mata na bata taba korafi akan karima din ba tun shigowan ta gidan shi ta zauna kuma a cikin su din a yanzu. Sai cewan da tayi Alh kaima ai ba zaka biyewa mace irin karima kuna sayar da hali ba haka zama da wanda rayuwan shi san ba kwabo sai sannu a hankali zata shiryu ta gane gaskiya. Amma irin wanan ina dadin sa ga yara a tsakanin ku, ace ka turata gida haka dolene hankalin mahaifanta ya tashi gaskiya. Hmmm haka kike gani don ita ai bata da alaman nadama kan abinda tayi din ko dazun an fada min an ganta a by pass su biyu a cikin mota . Da ace ta damu da hakan ne ai da ko idon fita bata gani ba a halin yanzu din tunda tasan akan shi muka samu matsala dani da ita. To ai kaji na fada maka sai fa hakuri don yanzu wanda duk ya ganta matarka dai za a ce ba matar wani. Sai na dawo yace da ita don baida amsan da zai iya bata a lokacin ya sakai ya fice daga dakin ya bar gidan zuwa amsa kiran dattijon dake neman shi din. Yasamu ankai ruwa rana a tsakanin mahaifan ta din da suka samu sabani a gidan akan yar tasu. Bayan gaisuwa a tsakanin su sai dan shiru ya biyo baya mahaifin hjy kariman ne ya fara magana yana fadin . Alh mun san kayi hakkuri da halin yarinyar nan kuma kana kanyi har yanzu don ni kaina ba macen da zata kawo min wanan shegantakan in kyaleta ace mijin ki bainan kisa kafa ki fita ba tare da sanin miji ba. Alh yace ni abinda ya ban haushi fitan karima baida lokaci duk sanda ta bushi iska fita takeyi tana bin abokan banza suna koya mata shedana. Yanzu meye laifin hjy Addah a cikin wanan zancen da zata nemi ta zageta matar nan har idona ta faka ta kirata ta dawo gida na dawo. Wai amma ita, ta dawo gidan tana zargi wai itace munafukanta kuma duk wanan abinda tayi mata din bata gani ba. Daga can kofan daki inda mahaifiyan nata take zaune tace ai dama na fada maka malam karka da da karka kara akan uwargidan yace tazo gida. Cikin mamaki Alh ya dago kai yana kallon mahaifiyar matar nasa da bata iya boye shigarwa yarta a fili ba haka. Shikuma ma haifin na fadin saudatu mena fada maki tun kafin mu zauna wurin nan kikace kinji don haka karki kawo muna zancen ku na mata nan. Yanzu dai hakkuri zamu baka Alh kayi hakkuri yarinyar nan ta koma dakin ta iidan kunne ya ji jiki ya tsira idan halin ta ne ta koma tunda haka taga matarka ta gida tanayi data shigo. Nan dai mahaifin yai mata fada suka tattaro suka dawo gidan tare da ita inda suka samu mutanen gidan kaf din su a falo suna murnan zuwan yayan su daya dawo . Amira tana zaune saman jikin shi cikin rashin damuwa da rashin uwar su a gidan sukai mata sannu da dawowa ta shige part din ta kai tsaye. Alh ne ya shigo karshe bayan ya gama sallaman driver ya samu dan shi zo wanda suka dade basu hadu ba sai wanan karon daya shigo wanan aikin. Na neman wanda suke zargi da aikata wani abu na daban sabanin wanda ni ya fada min din alokacin a baya daya fada min dalilin zuwan shi. Da kyat Abubakar ya iya budan bakin yana fadin sannu da dawowa bai tsanmani amsawan ta ba don haka yana fadi ya kawar da kanshi ga kallonta kamar yadda itama ta kawar ranta na kara baci da ganin shi yazo. Duk da yakan dan samu abinda ya bata idan yazo sai dai hakan bai mata dadi ita don tana rainawa ita tafi son ya bata daidai da na mahaifiyar shi. Yaranta ne suka nufo ta da murna suna fadin mami ta dawo mami oyo jin muryan maigidan a falo yanawa dan nasa kirari da sarkin aiki ina ka fito office ina zaka aiki sai hakan kuma ya kara batawa hjy karima rai sosai don yadda yake nunawa diyan shi so a fili. Sai kishi ya rufe mata ido take ganin ai nata yaran basu samun kulawan mahaifin nasu kamar yadda yake kula diyan hjy Addah. Kishi ke nan duk halarcin hjy Adda da diyanta kishi ya rufewa hjy kariman ido bata ganin wanan halarci karshe ma sai take daukan hakan da kishi wai na munafunci suke nuna mata.. Saidai duk da hjy Addah tasan da hakan kuma abin yana damunta sosai a ranta saidai bata yarda ta biyewa halin ta sun zama daya ba. Wanda hakan kuma ya kara haska ta ga mijin don hakkurin ta don shi mutum ne da yasan ya kamata. Sabanin wasu mazajen da zasuga hakan duk da uwargida tana hakkuri sai kuma subi amarya a taru ana musguna mata. Irin wanan ke uwar gida idan kinga hakan hakkurin ki zai jawo maki raini da koma baya abinda ya kamata kiyi na farko shine addu,a tare da sakawa kanki hakkuri akai. Saidai kuma dole ki tanka din shiru wani lokaci yankan kawo raini ga uwargida don haka a rika dan magantawa a cikin hikima. Nayi mamakin yadda umma ta yarda ana kashe wanan kudin duk data soki wanda ya bamu shi din a lokacin. Sai gashi naga tana zara ana sayo duk abinda Amar yace yana sonci don iya sayen abin kaiwa baki kawai muke saye a asibitin. Magani da allurai saidai muga an shigo dasu dakin ana masa amfani dashi ba tare da mun fitar da kwandalan mu ba anyi amfani dashi. Yamma yayi karfe hudu umma ta turani gida in dauko muna dan abin bukatan da zamu zauna dashi asibitin don irin fitowan da mukayi koma bamu samu dauka ba dakin muma a bude muka barshi. Inda Allah ya taimaka ga irin wayau na duk da rudewan da nayi a lokacin bayan naga umma ta fita da Amar a rude sai dana koma na kwashe dan kudin mu dake dakin a lokacin. Don nasan yadda akeyi a gidan da zaran dan tafiya ya kamaka kayi kwanaki masu dan tsawo baka dawo ba sai abi dare a fasa dakin a kwashe ma abin kwarai a dakin masu amfani . Wanda sanin hakan yasa farga na kwashe kudin na tafi dasu a cikin aljihun rigan dake jikina wanda sai wanan lokacin nake tuna hakan. Abinda na zata shine ya faru don na samu har dan raggan katifan da umma da Amar ke kwana a sama andaga a dakin kai ba katifan bama har ledan kasa an daga wanda nasan kudi ake nema a dakin don mu bamu da wani abin jin dadi na zamani a dakin na kudi. Fada na fito waje ina yi a cikin yarbanci ina zage zage ina hadawa da turancin brokin a bakina wanda su suka amshe bakina wajen gwanewa. Ba wanda ya tanka min don hakan ne wasu ma basu gidan basu dasowa a lokacin daga kasuwa da sauran wajajen balaguron su. Gidan babban gidane zai mutane saba,in zuwa tamanin ke rayuwa a cikin wanan gifan da baifi mutum goma su zauna suyi rayuwa a cikin saba a arewa. Na karaci fadana na tsunci yan raggadun mu da yan plate na jawo kofan don bamu da kwado na rufo na nufi titi. A hanya muka hadu da iya mulika take tambayana abinda ke faruwa na fada mata tace in gaiyar mata da umma da Amar din. Har take ban shawara tunda muje asibiti muyi kokari umma taga likita asan abinda ke yawan damun ta datake faman ciwo haka. Naji dadin wanan shawaran na iya mulika din don duk fadin gidan ita kade ta nuna muna damuwanta a kan mu. Na koma nake ba umma labarin halin dana samu dakin mu a ciki ta bugi kirji tana fadin aiko mun shiga uku dama tayi tunanen hakan tun dazun. Shike nan an kwashe dan kudin da mutumin can yabaki shekaran jiya kudin bai amfane mu ba na tsaya dogon guri dashi. Umma ban bar dakin mu ba saida na kwaso duk dan kudin dake garemu na hado da wanan din don nasan akwai matasa a gidan masu shiga dakuna idan mutum bai gida. Sahiba kin kyauta muna da baki bari an sace wanan kudin ba yau umma ina zan bari tunda shi nake son muyi amfani dashi wuri ganin likitan ki kadin mu bar asibitin nan. Sahiba yadda nake jin jikin nan yanzu ina mukaga kuflfldin da har zanga likita ko na yaron nan ai Allahne ya kawo muna mafita a kanshi. Gobe dai sai muje mu yanki kati umma kema a dubaki tunda gamu a cikin asibitin ko iya mulika yanzu saida ta kara ban shawaran hakan kuma tace na gaida ke. Mun bar wanan zancen a kan gobe zamu ga likita ashe likitan yakan zagayo duba marasa lafiya da dare da rigimana nan na jefo mai zancen umma din. Saida ya dan kalli umma inda take zaune din yake fadin sai mu yanki kati a goben mubi layi Allah ya kaimu umma ta fada da hausa. Nan ya barmu ya fita bayan ya gama dan dube dube da tambaya akan jikin Amar din dake kwance yana barci. Abincin dana sayo muna da zan dawo shi umma tace na diba naci kan na kwanta tunda tasan a gajiye nake dai umma ta mance irin jigilan da nakayi a duk wunin Allah. Ban kaiga tashi a wurin ba don na tsaya ba umma labarin yadda na samu an burkuce muna daki har ledan kasa. Wata yar nurse tayi sallama dauke da ledan abinci da abin sha ta shigo dakin duk muka bita da kalkon mamaki. Tace a cikin yarbanci iya Amar ko ? Umma tace ahmi tace ga wanan ance na kawo maku inji wanda ya kawo ku ta aje tana fadin manbo, wa ta fita sai gata dauke wani katon kwali mu dai muna binta da kallo kawai har ta aje. Tace duk shi yace na shigo dashi yana zuwa zaiga likita eh, kwale data juya umma ta fada don nikan nagama shan jinin jikina a lokacin don nasan wani fadan zansha kuma a hakan. Kodan ance wai yana zuwane bata furta komai ba sai bin kayan take da ido tana ajiyan zuciya ga tagumi data hada tana umm,, , , Shiru har dare ya soma yi alokacin nakai kasa na soma barci don yau gamu ga fanka a dakin zamu kwana dashi kamar kowa a dakin nan da nan jikina ya mutu na fara gyangyadi har nakai kwance. Umma ce ta tayar dani naci abincin duk da taji tsoron cin namu amma saidai kuma zuciya naso don lafiyeyen abincine koda ba a bude ba duk kamshi ya bure dakin ko a lokacin. Saida ta dan kira sunana kamar sau uku na amsa tace a cikin yarbanci na tashi naci abinci kada inyi barci banci abinci ba. Na tashi na shiga ban dakin na kurkure baki ba na fito na zauna na dan kali umma nake fadin umma ba zakici abincin bane ke ? Tace sai zuwa anjima kafin mun kwanta zanci na jawo kedan na fara fito da take away din nan mai tsada na dan kali umma tayi kamar ba kallona takeyi ba. Saida na debo abincin naji umma na fadin indaici da bisimillah don bzmu san manufar su akan mu ba. Hakan nayi da murna a zuciyana da yau banji umma tayi wani fada ko maganan da zai ban tsoro naji abincin ya fita min rai ba. Naji dadin sakwaran da miyan egushi da naman shi kamar yanka duk da yajin da miyan kedashi haka nayi taci don yaji kan mun saba dashi mun tashi a cikin cin sa tunda muna garin yarbawa. Aka turo kofan da sauri muka dago don ganin waya shigo wata nurse ce dauke da file tace umma ta bata cikakken sunan ta likita yace da safe akwai awon da za ai mata kada taci komai har zuwa safen. Har zata fita umma take tambayan ta kudi nawa za, a bayar tace maganan likita ne wanan ba nata ta fice ta barmu da mamakin hakan don sanin halin asibiti da mukayi muna jin rashin nasihan da akewa marasa lafiya idan basu da kudin ganin likita. Mu sai gashi anzo kawai wai umma ta fara shirin za ai mata aune aune zuwa safe din. Abincin ne yafita min a rai duk da son da nakeyiwa abincin don dadin shi amma haka naji komai ya tsaya min cak lokaci guda. ZAINAB IDRIS MAKAWA ANA DARA GA , , , , , , , , , , 8️⃣ BY ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , , BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM SIRA,ATAL LAZINA AL,AMTA ALAIHIM, , , , BARKA DA JUMMA,A YAN UWA PAID NOVEL BY MAKAWA, , , Tunda suka fito sallah asuba hankalin ta ya dauku ga wata macen bahausa da ta gani a dayan dakin dake kusa dasu tana jinyar dan ta. Sai kuma yanzu da suka sake haduwa da matar a bakin famfo zata dauraye cups da plate da sukai amfani dashi wanda itama shi din tazo yi a wurin. Yanayin shigar matar ne ya kara daukan hankalinta zani da rigane na atamfa a jikinta sai gyalen da keda ruwa da shigen kayanta data yafa ya rufe mata jiki sai shigan yaiwa Sahiba kyau ainun har ya dauke mata hankali. Ga kunshin a hannayen ta gwanin ban sha,awa zanen sun fito shar dasu a hannayen ta ga zobbuna dasa a yatsunta hudu a hannun da bangus sai walkiya takeyi shar da ita. Tana tsaye a gefen su tana kallon rigiman da akeyi a cikin yarbanci wanda bakin sahibace ke tashi tana fada da wace ta fara zagin ta a wurin. Dan dagowa tayi don ta gyara gaban rigan ta daya dan fado bata son aga tsiraicin ta yasa take ta faman gyaran don rigan Okirki dake jikin tana suka hada ido da wanan matar dake tsaye tun dazun a wurin. Har ta mayar da kai ta duka sai kuma taga rashin dacewan hakan don ko banza matar yanayin ta ya nuna ita din musulmace kuma bahaushiya. Gashi har lokacin matar bata motsa ba ga wasu tafe bayan su wanda tasan matar zata dade a wurin nan ke nan don ba mutunci kega mutanen nan ba sai ka nuna masu kaima ka iya zaku zauna daidai. Roban ta ta tara kafin ta juya zuwa wurin matar ba tare datayi magana da ita ba ta karbi kayan dake hannun ta tun dazun ta juya. Yanzu kan da aka juya harshe hjy halima taji me suke fada don taji suna fadin Ajayi so na house girl de do dis for us since. Sai Sahiban data kwarai da zama a cikin su tace eh even house girl na human ben if i no sebe do am , i no go do ta fada ta duka tana zubawa kayan morning fresh din wanke wanken data gani a cikin kayan ta fara wankewa a hankali. Har ta gama hjy Halima na kallon yadda ta wanke su tsab ta nufo ta dasu ta mika mata bata tsaya jin komai ba ta juya ta dauki kayan ta data riga ta wanke su ko. Don dokar asibitin ne haka kada a wanke masu komai a ciki akwai famfo a waje idan bukatan hakan ya tasowa mutum a lokacin zama asibitin. Hanyan daki daya suka nufa tare sai lokacin hjy ta samu bakin yiwa yarinyar da tunanen ta ya addabi zuciyar ta tana fadi a cikin zuciyan ta. Ga yarinya har yarinya da zubin irin na musulunci amma kuma da gani ba musulma bace ga kyau ga wanan yar kamar ita ta halici kanta sai dai doti ya hana komai ya fito fili. Sai gashi sun hada hanya da ita zuwa ciki tace da sahiban thank you very much for what you did for me. Dont mind tace tana tafiya sai dan kayan matar ya tashi barewa tace subbahanallahi ina can ina mamaki har zan fadi. Jin hakan yasa Sahiban dan tsayawa a cikin mamaki tana fadin hjy dama kema hausace a cikin hausan da baka saba yi kullun ba dole harshe ya juya saboda rashin sabo dayi din. Au shike nan ashe kina jin hausa ta fada cikin mamaki tana kallon yarinyar dan murmushi sahiba tayi tana fadin me na hausa sai dai ba sosai ba irin naku amma ina ji deye deye. Ke kice kina jin hausa kawai wallahi ni na zata kema irin suce ai danaji kun juya harshe a cikin su kunayi. Ta sake danyin murmushi da har kumatun ta suka lutsa lokaci guda yan hakoranta masu kyau da basu samun gyaran daya kamata suka dan baiyana a lokacin. Kuna jinyan wanine kuma a nan ta tambayi sahiban tace eh kanina ne baida lafiya shine muka kawoshi tare da umman mu tana ciki. Allah sarki nima kinga danane baida lafiya shine muke nan ta fada a daidai lokacin da suka shiga ta cikin dan dogon dakin dake dauke da dakunan kwana na majinyata. Daki dayane a tsakanin su dana su sahiban don haka sukai sallama kowa ya shiga dakin sa da yake. Umma na samu zaune bakin gado tana magana da Amar daya farka ina shigowa yaron ya bini da idanu na aje kayan ina fadin . Amar ka falka ya jikin naka na nufo wurin gadon ina dan duba jikin yaron muryan ummane naji tana fadin anya sahiba abinda mutumin nan ke muna baiyi yawa ba kuwa. Da sauri na kallo umma ina fadin umma anyi wani abune kuma yanzu da hannu ta nuna min baske din abincin dake gefen mu aje. Na juya da mamaki ina kallon wurin naji taci gaba da fadin yanzu likita ya fita dakin nan shi da nurse wai zasu dubani yadda ya dace an biya suyi min haka din. An biya umma na fada a cikin mamaki kafin in dora da fadin towa ya biya din bai fada maki wanda ya biya din ba umma ? Kai ta fara girgizawa kafin tace nima nayi wanan tambayan ai yace ai tare ya ganmu da maishi wanda ya kawo mune ya biya kudin. Umma karde zancen ki ya zama gaskiya akwai abinda yake son yi damu yake muna hakan don ni nafi tsoron sherin ojuju da komai a lokacin. Tace ban tsamanin hakan don likitan ya fada min wai yace mu din ai yan uwan shi ne musulmai . To kinga kenan shi musulmi ne koda yake musuluncin mutanen kasan nan baikai ciki ba ai koma meye Allah ba zai bashi ikon da zai cutar damu ba insha Allah. Dauki abincin kici kada haka ya zama barnan dukiya don mu da zuciya daya muka dauki ko waye a yanzu. Na nufi wurin abincin na fara budewa egede kwamo da dan kalin turawa sai kwai soyayye sune cike a cikin takewa din sai abin sha kuma a cikin kwalayen su. Har na mika hannu zan dauka mukaji sallaman wanan matar bahausan a kofan dakin mu tana fadin nace bari nazo na duba yaron nan a cikin hausa. Mikewa nayi ina wasan baki kamar naga ta gida a lokacin sallamanta umma ta karba suka fara gaisawa tana tambayan jikin Amar umma tace da sauki. Take fadi kamar yadda ta fada min da farko dantane baida lafiya suke jiyan shi a nan itama don yau kwanasu biyu kenan cikin asibitin . Umma tai mata ya maijikin ta amsa da sauki saidai yanayi na skilar sai a hankali don lafiya muka haifishi sai daga baya da yaki lafiya muka gane laluran dake damun shi. Oh subbanallah ubangiji Allah ya yaye masa ya bashi lafiya idan da rabo wata rana sai ya mike kamar bashi ba. Tace to Allah yasa umma tana kallona a fakaice don tana mamakin ko wacece don matar ta cika mata ido sosai da gani dai ita din watace ko matar wani. Kamar ta gane mai umma din ke kiystawa a zuciyar ta tace yar nan taki tana da mutunci sosai wallahi ta sanadin kirkin ta na gane kudin hausawa ne yan uwan mu ai. Nan taba umma labarin dan haduwan mu ina jin lokacin da umma ke ajiyan zuciya da jin hakan barin kawo maku abincin yanzu aka shigo muna dashi yayi muna yawa. Ai da ki barshi don ga wani nan wani bawan Allah da yake taimakon mu shine ma ya kawo mu asibitin nan yake daukan dawainiyar mu da komai namu a yanzu. Allah sarki dama haka duniya ya gada duk inda kake baka rasa na Allah ai nima ba gashi mutumiyar ta hadamu a yanzu ba umma tayi murmushi. Tace bari a kawo ko kadan ne kila shi mara lafiyan zai danci don abincin marasa lafiyane ga baki daya don mahaifiyar maigidana ne a tare damu itama dai sai a hankali. Kin san halin tsofin nan da jiki taki ta zauna gida saboda shakuwan da sukayi da dan nawa sosai Fita tayi tana dan dariya bayan ta fadi hakan na dukar da kaina kasa muryan umma naji tana fadin . Sahiba idan banyi hankali ba zaki dauko min magana a garin nan muna zaune cikin rufin asirin Allah. Umma taimakon ta nayi kawai don naga bata iyawa shine na taimaketa na fada a sanyaye kaina a duke. Taimako ke kadaine kika san hanyar taimako nace umma hausace fa ita din shine yasa na taimaketa. An fada maki duka hausawa ne yan uwan juna sahiba wani bai san garin wani ba wani bai taba jin yaren wani ba ko a cikin hausan. Ba zan kara ba umma na fada zaki kara don taimako a jininki yake sahiba ba zaki san lokacin da kikai hakan ba. Kawai abin da nake so dake shine ki san wa yanda a yanzu kike dauko muna kiyi hankali dasu sahiba ki kula da kanki da mutuncin ki a duk inda kika samu kanki. Nagode umma na fada sai ga nurse ta shigo dakin da file din umma tace ta taso su tafi da ita likita zai fara ranan. Umma ta dan kalkeni tana fadin ki kula ki zauna min dashi kada ki yarda kije ko ina sai na dawo don nasan halin ki da rigiman tsiya ki fita azo a sace min yarona. Na dago da sauri na kalleta kafin in mayar da kaina kasa suka fita umma na fita saiga matar hausa din nan ta shigo da katon kulan abinci da plate na tashi da sauri na karbe ta. Ina maman taki ta tafi tambayeni ni nace ta tafi ganin likita au itama ba lafiyane ko kan matsalan dan uwan kine ? Itace ba lafiyan za a dubata na fada na koma na zauna ta dan kali Amar tana fadin zakaci abinci ko ya kura mata ido saida nayi mai yarbanci ya dan kada kai kadan alaman eh. Hakan yasa ta kalleni tana fadin ki zuba mai kadan ya danci na mike don bin umurnin ta ina bude warmer din wani irin kamshi ya bugine dafa dukan anta ne don shi yafi yawa a cikin abincin sosai. Na dan debo na kawowa yaron a irin hikimar su na uwaye ta bashi yana karba a hankali har yaci sosai. Ta dan jima a wurin mu zaune tare damu tace sunyi barci kada ta tashe su ni kuma ban yarda na gusa a dakin mu ba don tsoron da umma ta bani da zata fita. Na kasa na tsare tare da zubawa wanan hjy idon da zaman datayi a dakin mu din kafin inji ta jefo min tambayan dayasa na dago da sauri. Cewa tayi dani meye sunan ki ne yata na dago ina fasin Sahiba ta kara maimaita sunan Sahiba kafin tace ok. Ku mutanen wani garine wai don yanzu hausan ku ya juye ya hade da harshen kasan nan kamar ku din ba hausawa bane don kun saje dasu tsab a yanzu. Sai dai kamanin ki dake nuna zubin fulani ko shine kawai za a yarda ku din hausawane da kuma mahaifiyar ku da nagani a yanzu ya kara yardan min da hakan. Kin san su fulani zubin su na daban ne tundai fulanin shiyan sokoto adamawa da da bauchi ta kalleni. Wallahi mama ban san mu ko daga ina muke ba umma dai tace a arewa muke mukazo nan tun ina karama kafin a haifi amar. Cikin mamaki tace kina nufin mamanku bata fada maki daga inda kuke ba har wanan lokacin da kika fara girma ? Kai na gyada a cikin dan damuwa nace ba a fada muna ba kuma ina son in sani amma umma tace sanin baida amfani a wurin mu a yanzu. Don me zata fada maku haka idan ma wani abune ya faru a can ta bargida ta dawo nan ya kamata ace ta fada maku. Moddibo halin matar nan yana damuna a yanzu ina gudun kada hakan ya saka min hawan jini. Ya dago kai da sauri yana fadin hjy na fada maki ki daina damuwa da zancen matar nan kada ta jefa muna ke a cikin wani hali. Zanwa daddy magana yayi maku iyaka da ita tun kan wani abu yazo ya sameki nan gaba kuma Da sauri ta juyo tana fadin karka soma tsoma bakin ka a cikin harkan mu na fada ma wanan bai shafeka . Ka barmu muyi ta abin mu a tsakanin mu saukina shi Alh yana da kula don bai yarda ya bata power da take son samu ba. Ranshi ya gama baci dan haka bai saurari sauran bayanin da uwar ke masa ba don a lokacin ya fara tunane kala kala. Don da yayi aure zai iya daukan mahaifiyar shi har yan uwan shi su zauna tare duk da yasan abune mai wuya mahaifin nasu ya yarda da hakan. Sai dai zai gwada hakan don ya samawa mahaifiyar shi sauki ga hakan don shi gaskiya sam hankalin shi bai kwanta da hakan ba a yanzu idan akwai abinda yafiso shine mahaifiyar su. Bayan ya fita daga dakin ta kai tsaye gun daddy su ya nufa ya gaidashi da kwana suka hade a kofa da hjy karima a tsatsaye ya gaida ita ba yadda ya saba yi ba dama bai faye damuwa da lamarin ta ba shi. Sai cewa tayi Alh bai tashi ba yana kwance har yanzu jin muryan da Alh yayine yake fadi daga ciki ba moddibo bane ki barshi ya shigo mana tunda idona biyu. Ta matsa Abubukar din ya shiga bayan yayi mata wani irin kallo na ke waye abin kulanan shine mata masu shiga gidaje sy iske maigida da manyan diya suce sai sun dauki power gida da karfi da yaji su kula . Shi girma yau idan akace wanan ce uwargida idan kin gane ki bita da hikima ba a cikin tashin hankali ba yadda wasu keyi. Don irin haka na kawo maki matsala ga yaran matar nan ta yadda baki taba daraja a idon su wani lokaci har abin ya shafi diyanki da suke kanana a cikin su. Ya kutsa kai ya shiga dakin mahaifin nasu a daidai lokacin daya mike zaune daga kwancen da yake yana gyara jalabiyan dake jikin shi. Har kasa yakai ya gaidashi kafin ya dago yana gyara zaman shi a kasa saman carpet mahaifin yace ga kujera zaka zauna kasa yace ban yayi min dadi. Mahaifin yace naji ance wani aiki kazo yi a iko ya dago kai don har lokacin yana jin haushin hjy karima a cikin ranshi yace. Eh daddy saidai har yanzu muna kan binciken wanda nazo nema din don shi din yahoo ne na kwarai babba ne a cikin su sosai. Modibbo kana ganin zaka iya kasan fa yadda lagos yake da girma da kuma wanan matsalan ya dan dago kai sai alokacin ya samu yin guntun murmushi yana fadin insha Allahu daddy. Addu,an ku nake bukata a yanzu fiye da komai insha Allahu zan iya indai har shi din mai laifine kuwa ina bin abubuwan a hankaline har na gane. To Allah ya kyauta Alh ya fada yace amin daddy ya jikin naka yanzu kuma dan murmushin manya yayi kafin yace jiki da sauki yanzu saidai abinda ba a rasa ba kwai tunda girma ya kama yanzu kuma. Hakane daddy kuma sai dai a rage yawan tunane din nan don koshi yana kawo ciwo sosai ya dan kalli mahaifin nasa. Kai yaro dai ho ai tunane ya zama dole a yanzu don kaga rashin sanin inda mutanen nan su, , , , Shigowan hjy karima yasa daddy din yin shiru ya fasa fadin abinda zai fadawa dan nasa ta aje kayan break din data shigo mashi dashi tana fadin yanzu zakai wankane a hada ruwa ? Kina iya ki hada muna magana ne da tsohon gida ya bata amsa da bataji dadin hakan ba don taso ta nuna mashi shi din ba kowa bane gun ubansa sai kuma Alh ya bayar da ita. Ta dan tsaya jim kafin ta juya ta fita daga dakin tana jin zafi a zuciyar ta wani zance kuma Alh ya dauko suka fita zancen da suka soma din. Ya dan jima a aurin mahaifin nasa suna hira kafin ya mike ya bar dakin yayun da hjy karima nacan cikin damuwa a lokacin. Har aka kira matar umma bata dawo ba sai bayan tsawon wani lokaci ta dawo dauke da ledan magungunan ta da aka bata masu tsada don abinda ke damun ta din. A lokacin har na fara barci don zaman kadaici ni kadai don Amar ya koma barci shi tun bayan cin abincin shi. Jin motsin umma din yasa na falka ina fadin umma kin dawo ashe tace wallahi da yunwa don na wahala. A zuba maki abincine kici don yanzu dankalin yayi sanyi nake gani ikon Allah shi mai nema ina ruwan shi da wani sanyi ganin dai abincin yasa kika fadi hakan. Mikewa nayi na dauko kulan abincin matar hausa din nan iina fadin ci wanan umma da gani zaiyi dadi. Ina kum kika samu wanan abincin nace matar hausa din nan ce ta kawo muna ban ci ba fa umma na fada ita daice ta bawa Amar yaci. Yaci na bata amsa takai zaune tana kallon yaron na bude abincin ta gani tace ki zuba min sai ki zubawa kanki . Wanan matar bata kara leko mu ba har yamma ni kuma ina fama da tunanen zacen da mukayi da wanan matar akan ya kamata ai mu san garin mu yanzu. Duk da nasan hakan zai iya kawo muna matsala da umma don ba son zancen nan takeyi ba tuna hakan yasa naja bakina na kyale ta. Da yamma sai gata dakin tare da tsohuwan data kira da uwar mijin ta sun shigo duba amardin da jiki sun dan jima kafin su fita su koma dakin su. A cikin dare har mun kwanta aga buga kofan a zaton mu ko likitane sai dai muna bude kofan tunanen mu ya canza don ganin wasu mutane da suka shigo muna dakin. ZAINAB IDRIS MAKAW .ANA DARA GA, , , , , , , , , , , 9️⃣ BY ZAINAB IDRIS MAKAWA BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM GAIRUL MAGDUBI ALAIHIM, , , , , , , , , YAR UWA PAID NOVEL NE DON ALLAH KI BIYA KISHA KARATUN DUNIYA A ZAUNA LAFIYA, , , , , Dagani har umma a lokaci daya muka mike zaune don firgita saboda yadda aka bugo kofan dakin da karfi aka shigo. Su ukune ko wanin su yana saye da bakaken kaya sai bin mu sukeyi da kallo kamar yadda muma muke binsu da kallon saidai bamu ganin fuskokin su a baiyane. A cikin karfin hali umma tace masu una de look for somebody here ba magana ko daya a cikin su illar takawan da na tsakiyan yayi zuwa bakin gadon da Amar yake kwance da karin ruwa ya tsaya yana kallon yaron kafin ya kai hannun shi saman ledan ruwan ya dan duba. Duban yan uwan yayi kafin su tako zuwa gadon su dan dubashi suyi wani magana duk muna binsu da kallo da mamakin hakan a cikin zuciyar mu. Can dayan ya dago yana fadin mama ur son will be fine very soon my oga say he go live d town today. May u colect dis money manage am with ur pikins take care of dem yana mikowa mama kudi a cikin wani bakin leda. Umma ta kalli hannun shi da kudin kafin ta dago tace dashi tellam say me no want his money naw. D tin wen he do for us is ok for us now, make he cary his money go, Allah will reward him for dat. Ai mun gode ko hakan wallahi Allah dai ya saka da alherin sa ta karasa fadi da hausa tana zama a bakin gadon don ganin ba cutar damu sukazo ba. So u servi hausa ma self ki karbi kudin nan don na baki wanan ba komai bane a wuri nayi niyar taimaka maku ne don jin halin rayuwan da kuke ciki a gida a bakin mutanen gidan. Don haka don Allah ku karbi kufin nan kiyiwa yaran amfani dashi Allah ya sada mu da alherin sa don ba lalai bane mu kara haduwa kuma saidai yarana zasu dinga duba ku lokaci lokaci. A gadarance gashi duk da bakaken kayane sai kyali sukeyi kayan sun hade da fatan jikin shi chakulete colour . Yana da tsayi gami da kirji mai fadi kiran zaki gashi da dan tsayi da alaman jiki kuma don Allah ya bashi kyau kira ga zati a gaban duk wanda ya tsaya. Ga wani saje da mazan zamanin nake ajewa yanzu da suke kira da one million a fuskan shi ya kara masa kyau. Basai ya fada ba duk wanda ya ganshi yasan shi din wani ko acikin dubu don zan iya cewa komai ya hada ban sanarwa na imani ba da bangani a fili amma kan kudi sun riga girma yawa a wurin nan. Duk maganan da yakeyi da umman mu idona yana a kansa ina karewa halittan Allah kallo don yawan kallona har saida na gano fuskan shi na ainihi duk yana ganin shi ya rufe don a duke nake har lokacin don haka zan iya ganin hakan daga kasa. Don da nasan kiyasta shekaru a lokacin wanan ba zaifi ashirin da wani abu ba a duniya don yarone a iya sanin matasan legos da nayi ko tsoho mai hurhura yana dabi,un yara sai in kira wanan din da yaro. Na sake fadi a raina kyau da kudi ga kwaliya da kwarjini duk Allah ya tarawa bawan Allah nan sai dai kuma ya kaza don miskilin karshe ne shi. Da gani ga girman kai nan a fili da jiji da kai da yake nunawa a fili yana nuna shi din wani ne a gaban kowa tun ganin farko da nayi masa. Har ya juya ya fara tafiya bayan ya umurci a ajewa umma kudin a gefen ta a inda take zaune ta zuba masu ido cikin tsoro da fargaban su don basu da tabas. Kowa yayi shiru umma na ganin sun soma tafiya tace na rokeka kada ka zama min sabon matsala a rayuwa . Wani irin juyowa yayi har zuwa gaban umma din ya dan kalleta ya sake dan murmushi kafin yace. Mama nayi domin Allah ne don abinda kike tunane ba hali mu bane iyaka mu muna neman na kan mu ne da zufan mu. Idan kuma munga mai bukata mu taimaka masa don ya sakawa harkan mu albarka don gaba Allah ya kawo muna sa,a a rayuwa. Me yuyuwa daga yau na fada maki kila ba zaki sake haduwa da muba balle har wani abu ya biyu baya na asha don haka ki saki ranki niba mugu bane kamar yadda kike zato. A lokacin ya dan cire hulan daya rufo a kanshi ya kalleta da kyau tare da hada hannayenshi wuri daya kamar mai rokon gafara kana yayi wani abu kamar bissalam da hannu tare da dan rankwafawa daga haka suka juya suka ffice sauran suka bi bayan shi da sauri. Ina ganin haka na mike da sauri na rufo kofan dakin tare da saka sakata na dawo inda umma tayi mutuwar zaune don ko motsi bata iya yi ba har lokacin sai bin kofa takeyi da kallo inda suka fita. Umma idan baki yarda dasu ba ki kawo kudin nan yanzu inbi bayan su dashi duk inda suka shiga a garin nan. Sai lokacin umma tayi wanin irin ajiyan zuciya tare da kallona tana fasin ke din Sahiba kike fatan in barki kibi wa yan nan da suka tsaya gabana kamar mala,ikun duniya. Maza ki samu wuri ki koma ki kwanta saidai muyi adduan nufin su yazama alheri a garemu amma ba zan barki ki bi bayan wa yanda bansan asalinsu ba ko daga ina suka fito. Umurnin umma din nabi cike da fargaba a zuciyana na samu wuri na kwanta a makure ina faman tunane sai gizo fuskan shi da ya tsaya min arai ya ke mun a lokacin. Ina ganin kyawawan maza ban taba ganun mai kyau irin nasa ba a rayuwana har barci ya daukeni a hakan. Washe gari nikan na makara da sallah saida umma ta tayar dani a gurguje nayi sallah namike ina gaida umma da kwana kafin na fara tattara kayan da muka dan bata na fita dasu wurin wankewa . Tunawa nayi dana hjy na shiga dakin da sallama na samesu a ciki na gaida su a cikin ladabi nake tambayan mai jiki suka amsa da sauki Nake fadi nazo na kwashi kayan na wanke masu ne don zan tafi na wanko namu a famfo. Allah sarki yar albarka wallahi keda ai jiya an tafi dasu gida a wanke a can saidai cup din nan da suka sha tea da dare dashi. Na duka na kwasa na fita yau kan ban dade ba son yanayin dana tashi cikin sa ba dadi don haka ban kula kowa wirin ba nayi abinda ya kaini na bar wurin. Yanzu ya kike so ayi don ban fahinci inda zancen ki ya dosa ba ya dago yana fadi tare da kallon inda hjy karima take tsaye. Eh akan zancen Abubakar daine nace kai masa magana idan zai bamu kyauta ya rika bayarwa ta hannun ka sai taja tayi shiru. Ya dan dago ya kalleta yace uhumm ina jinki cigaba mana tace a, a shine dama nace zan ma magana don ka kafa wanan dokan . Eh lalai karima tunda gani dattijon banza ko don kawai in farauta maki rai sai inyi bakin jini ga iyalina saboda ke kece ko ? Wai karima ina tunanen ki yake zuwa kwanan nan ne ko dai wani abu na faruwa dakene ba a farga ba ta jefo mai wani irin kallo tare da fadin . Watau na haukace ke nan ba a sani ba ake zaune tare dani hakan kalaman ka ke nufi yanzu Alh don kawai na fadi gaskiya shine laifi ? Hakan nake nufi kin taba jin inda akaiwa uwa da danta shamki don kawai wani ko wata yaji dadi a rayuwan Yau ko cewa Addah tayi ya daina baki kudin shi ga baki daya ai ban tambayan ta dalili don datane ita ta haifi abinta. Balle ya bada sakon har abaki kike ganin kamar Addah ta rage ko bata son a baki din ko wani abu don haka zaki zo wurun dattijon banza ki izani in saba masu ko ? Ai dama nasani nasan haka zaka fada Alh haka dinne ai har kin sani kuma kika fada min yanzu ? Ta wani mikewa tana fasin ni in ma kyautan ya zama magana daga yau a bari don Allah ai ba rasa kudi nayi ba a hannu na. Ina da aikina ko yanzu naga daman komawa sai in koma yace badai gidana ba keda aiki sai idan baki gidan nan. Don Allah yaga halinki na boye da kika boye min da farko ya kareni daga fita aikin ki tun farko kyautan kuma abarshi zan fadawa modibbo din. A daina sai me zaka wani lauyeni kace nace matar kana ragewa ko wani abu can don hadin fada ta fita daga dakin. Tafita tana dan kunkumi don dabaranta ba soici ba gashi kuma zata kulawa kanta tsiya a gidan kan hakan. Dama shawaran kawace data bata tace ta gwada duk ranan da maigida ya kwana da ita har ya nuna jin dadin shi gareta to ita kuma ta gwada sa,anta a wurin miji ga abinda take bukata . Acewar kawar a take miji ke biyawa mutum bukatan shi a wanan lokacin don kawai jin dadin kasamcewan su a tare da suka raya dare suna sunna. Shine tayi kokarin gwadawa gashi kuma ita batayi sa, a ba abin yana neman kwabewa da ita ga baki daya a yanzu. Dakin ta nufa kai tsaye wurin wayan ta taje ta kira kawar ta nan take labarta mata komai daya faru tsakanin ta da Alh. Wani irin tsukin takaici taja tana fadin Allah karima ke banza ce waya fada maki da safen nan ya dace kiyi wanan maganan dashi ? Ai tun jiyan ya kamata a daidai lokacin da abin bai gama fita masa kai ba ke kuma saiki sako zancenki ki gani. Sallaman da taji daga kofa yasa ta katse wayan tana amsawa tare da fadin waye hjy nice Talatu dama wai nazo na fada maki Alh karami zai tafi. To sai akace me to hjy babba ce dai tace nazo na sanar maki Allah kai lafiya mana ko ta fada adan hasale. Talatun ta amsa mata da amin ta juya ta tafi yana zaune kannen shi sun dan mane suna rokon shi kudin anko yana ja masu hankali da hakan talatu ta dawo. Yanayin fuskanta kawai hjy Adda ta kalla tasan da akwai bacin rai a lokacin saidai bata nuna hakan ba don cewa da tayi Allah saukeka lafiya zata shiga wankane yana jin hakan ya mike tare da fadin . To mommy ni zan tafi ke nan sai kuma Allah ya sake hadamu da alherin sa uwar ta mike da sauri a cikin yanayin rashin jin dadi da tafiyan da dan nata zaiyi a lokaci. Modibbo Allah ya tsare ya kare muna ku a duk inda kuka shiga ya dawo muna da kowa lafiya shi da kannen sa suka amsa da Amin. Sai lokacin ya kalli kannen sa yana fadin to ni zan tafi ko sukace aaaa yaya gaskiya ka ganmu kafin ka tafi. Wani gani kuma zan maku bayan wanan gaskiya mudai ka ganmu yana dariya ya saka hannu ya ciro kudi masu yawa mika masu suka hau murna da Allah ya tsare Allah ya kiyayye a cikin murna . Nabila ya kalla yace nasan su Amira ba barci yanzu basu tashi ba idan sun tashi sai ku basu wanan suma su sayi alawa suka ari bakin yaran suna mashi godiya. Haka ya karasa inda daddy ke tsaye yana magana dasu malam mudi ya dan kai rusunne yana fadin daddy zan tafi ke nan . Dafa kafadan shi mahaifin nasa yayi ya mikar dashi yana fadin ka gama da yan rikicin can ke nan yace wallahi daddy . Na dai sallamesu ai mun rabu lafiya yanzu yau su Amira basu fito ba ke nan eh daddy naba Amira nasu ta basu idan sun tashi. Dan murmushi mahaifin ya sake kafin yace ka kyauta dan ko yanzu nasan akwai rikici idan sun tashi sukaji ka tafi ai . Cikin dabara ya fara tafiya da dan nasa don su bar wurin dasu malam mudi suke tsaye ma,ana zaiyi maganan siri dashi ke nan. Ganin hakan suma suka ja suka dan tsaya daga nisa dasu kadan sai da suka danyi kamar tako biyar suka tsaya har lokacin hjy da yaran ta na tsaye daga kofa suna kallon su. Don jira suke suga tashin shi su koma cikin gidan haka ka,idan rakiyan su yake idan maigidan na gida iya kofa suke tsayawa. Yanzun lagos din kuma zaka koma ya dan murmusa kadan yana fadin can zamu koma daddy don yau akai min waya sun gano mai wanan sunan. Allah ya bada sa, a ya amsa da amin ya kara fadin ka kula da kanka don Allah irin wanan aikin nasan hatsatin dake cikin sa sai anbi a hankali. Daga yayi mai fatan nasara ya juya ya dagawa mahaifiyar shi hannu tare kannen shi ya nufi motar da za a kaishi airport dashi. Likita yazo round ya duba Amar din yaga ya samu sauki sosai don haka yace zai bamu sallama zuwa yamma idan yaga yadda jikin nasa yakara samun sauki. Ranan umma ta dan daure ta fita har ta shiga gaida hjy nan datake taimaka muna tun haduwan mu da ita. Sun dan dade suna hira tana jan umma da dan hira sai dai duk dabaran ta umma bata yarda ta fada mata komai daya shafi rayuwan ta har ta fito. Ta samemu zaune muna hira da Amar din dake zaune saman kujera tana shigowa dakin nake fadin umma kinji danki ko . Wai keke za a saya mashi idan mun koma gida da kudin nan wani irin kallo umma ta watsa muna kafin ta juya ta kalli kofa ta koma da sauri ta rufo kofan ta dawo wurun mu duk muna binta da kallon tsoro dan yadda tayi din. Ku saurareni kuji a binda zan fada maku dukkan ku a yanzu kada inji wanan zancen a bakin kowa duk tambayan da wani zai maku akan zancen yaron nan daya bamu kudin nan kuce baku sanshi ba. Mena fada maku muka amsa da bamu san shiba har muna kada kai kada ku nuna tsoro a fuskan ku ko kadan don nuna tsoron ku zaisa su dauka mun sanshine. Shiru mukayi gaba dayan mu na dan lokaci kafin can na dago ina fadin umma wani abune kuma yanzu ? Babu komai jikinane kawai ke bani cewa akwai abinda bamu sani ba a game dasu kawai nayi shiru ina tunane saidai na kasa gano komai a yanzu. Dakin yayi shiru na dan wani lokaci kuma kafin Amar ya mike ya koma saman gadon ya kwanta. Allah ya gani nice duk silan jefa umma a cikin wanan halin damu kan mu ma yanzu idan wani abu ya samu umman mu fa ina zamu saka kan mu na tambayi kaina. Dakin aka turo likitane tare da nurse suka shigo ya dan kara duba jikin yaron kafin yace zai bamu salama sai mu tafi gida. Najin dadin jin hakan don na matsu mu bargidan saida likitan ya gama bayani ya mikowa umma wasu kudi yana fadin canjin mu ne da suka rage ta bamu kudine kuma masu yawa. Saida muka shiga mukaiwa hjy nan sallama take tambayan umma lamban waya umma tace bata da waya ita ai. Tana mamaki take fadin har da ke nayi murmushi tace a kwatanta mata gidan mu wata rana zata kawo muna ziyara. Nan dai mukai mata kwantace ko ta gane ko bata gane ba muka kara gaba abin mu muka barsu a asibitin don sukan basu san ranan sallama ba sukace. Kamar ba asibiti muka fito ba don yan gidan ba wanda yai muna an dawo lafiya ya maijiki. Karshe mu muke gaidasu da u na weldone su amsa muna a gadarance da thank u jo mu wuce har muka kai dakin mu da har lokacin a hargitse yake. Umma taga yadda aka tone dakin wurin bincike ta tsaya nikan ban tsaya ba dole na shiga gyaran dakin namu don ba zamu iya zama haka ba dakin a hargitse. Nan dai har na gyara suka koma ciki ni kuma na dan tsaya waje ina wanke wasu kayan mu a lokacin ne naji gudu na dago don ganin me akewa gudu din. Yan sandane cikin wani irin kaya mai ban tsoro suka shigo gidan yasa kowa ke gudu zuwa dakin shi ashe. Nima na shige dakin mu na mayar da kofa da sauri na rufe suna shigowa gidan mukaji ana sanarwa kamaf haka. Mun san kana cikin gidan nan don haka ka mika wuya a cikin saukin kai a hankali na kalli umma ina fadin wa sukazo nema umma ? Bakina ta kaiwa duka tana fadin inyi shiru da surutun tsiya can mukaji na banke banken kofan muka kara make junan mu mu uku a dakin a cikkn tsoro har suka kawo dakin mu da ba wani kofan kwarai ke garemu ba dama. Wani dan sandane ya shigo yana fadin ku shigo kofan a bude take ya shigo babu dadin gani yana bin ko ina da kallo. Har kayan mu ya dan dadaga ya fita yana fadin bai wanan dakin karshe suka tataro kowa na gidan dayan su ke nuna muna photon wani guy yana fadin mun san wanan kowa yaba hirgiza kai mukace bamu sanshi ba. Wani tsawa ya daka kowa ya firgita yace a gidan nan yake har tsawon mako hudu yake nan ma shiriru akayi ba wanda yace ya san shi a gidan. Sunyi iya binciken su basu gane komai ba har suka aikinsu da yan tambayoyi akace ba a sanshi a gidan suka gaji suka tafi bayan sunce zasu sake dawowa ZAINAB IDRIS MAKAWA qANA DARA GA , , , , , , , , , , , 1️⃣0️⃣ BY ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , , , , BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM WA, LAL DALIN AMIN, , , , , YAR UWA PAID NOVEL NE DON ALLAH KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA DARI BIYAR NE KACAL YAR UWA. Hankalin mu bai kwanta duk da sun wuce sun bar gidan amma kowa na waje cirko cirko ana faman mayar da magana kan zancen. Dukawa nayi naci gaba da wankin kayan da nakeyi daga can bayana naji muryan wale na fadi. U sahiba wen wan trobe for ur self thank god that day d man no kill u sai kowa ya kallo ni na daga ina fadi. Wale, i beg , me i no wan wahala wooo, mey u no comfire me wit that men sha bi i no dem before ? De fall me down, nd my food dont fawl, nayi i say mey de pay, nd de pay me , de give me anoda food ogwa ? witin consen me with dem again ? Maman shi tace dashi, wale may u no cary ur wahala come rich me shabi u no say dat mater no be smol case wooo . Uwar ta kwaba shi tana koran shi daga gidan ya fita yana wani irin tako na yan iska tabi shi tana zagi. Na dauki kayan dana wanke na nufi wurin da muke shayi a nan idona yakai kan wayan dake kasan yashe bayan wani kwandon roba na kayan iya bisi dake kusa da dakin mu. Na faki idon mutane na duka na dauka na tura a aljihun dan rigan dake jikina da sauri na karasa shanyin na koma dakin mu har lokacin umma na waje na bi wayan da kallon mamaki ni kadai a dakin. Ko da ban san waya ba nasan cewa wanan wayan babbace kasancewa umma na waje har lokcin bata shigo dakin ba. Yasa na fita don zuwa in debo ruwa a inda muke diban ruwa fitana yayi daidai da sake dawowan yan sandan gidan. Suka zo neman wayan duk an tara mazan gidan da yan matasan mata kan wayan sai binciken su akeyi kan wayan. Don ya nuna a cikin gidan wayan yake kuma yanzu sunzo signal bai nuna wayan na gidan ba duk an bincika ba a samu wayan ba . Inda Allah ya taimakeni shine ba wanda ya kawo ranahi a kaina cewa wayan yana hannu na a gidan har yan sandan suka tafi don ya nuna an bar gidan da wayan lokacin. Hankalin shi ya tashi matuka na rashin ganin wayan nasa daya fado gurin mayarwa a aljihu bayan sun gama waya an fada mashi wanda suka zo nema baya gidan ya bar kasan ga baki daya. Yabi ta ghana ya fita har yabar kasan ghana din a lokacin shine dalilin da suka bar yan gidan mu din suka koma bincike ga landlord din gidan ta yaya ya bashi gida haya a ina kuma suka hadu dashi har ya bashi hayan ?. Ko dana dawo kowa na dakin sa wasu kuma sun gudu sun bar gidan a lokacin fita na sake yi na je nemo muna abinda zamuci duk da mun dawo da abincin da hjy ta bamu kafin mu bar asibitin. Sai dai shi Amar yace tea zai sha shi yasa nafita wurin nema kayan hada shayin a hanya ne wayan ya fara vibration a cikin aljihuna sai dan kara har hakan yasani firgita. Don sam na manta da zancen wani waya dana tsunta ga baki daya sai lokacin har kiran ya katse ban san yadda zan dauka ba ashe tun wurin diban ruwa ake ta kiran layin ban sani ba ina can ina daga bohol. Ashe hjyn su modibbo ne take kiran layin dan nata tunda ya bar gida basu samu wayan shi ba sai wanan lokacin shine hankalin su a tashe ta samu aka dauka kuma ya katse Aka sake kiran layin nayi sa,a na danna daidai na dauka naji muryan mace tana fadin haba modibbo ka daga muna hankali haka ? Nayi shiru ina sauraren hausan matar da muryab ta ta sake fadin wai bada kai nake magana bane ga daddy kuma yana ta kokarin neman ka tun dazun. Ba mai wayan bane na fada tare da fadi me ego hausa kosi hausa fa hausa kadan kadan mama don jin danayi tace daddyn ku. Who are you aka fada wanan karon muryan namiji ne nace iam d one who found d phone i don't know d owner self. Kinji me take fada aka fada a cikin wayan ina ganin wayan ta fadi maine watace ta tsunta nace eh na samune a cikin gidan mu dazun. Ke wacece ni ni sunana sahiba na fada kai tsaye a cikin hausawa gwari gwari mai kama dana yare wani unguwa na fadi sunan unguwa . Na karashe da fadin a fada mai yazo ya karbi wayan shi idan kun same shi nakarashe da nagode. Allah yayi maki albarka nace amin woo nagode kada ki kashe aka fada a kausashe nace oyah oda Yan tambayoyi ya dinga min ina bashi amsa a cikin irin hikiman su na tsufin ma,aikata har ya gane komai da yake son ji a wurina ban sani ba . Muna gama wayan dasu na kali wayan ina jin dadin jayi waya mai tsayi a cikin yaren hausa duk da bansan da wanda nayi wayan ba a lokacin. Shi kuma daddy su neman layin wani abokin aikin dan nasa yayi ya fada mai ya nemi moddibon ya fada mai yadda mukayi. Kodana shigo gida nake fadin ni bazan sha tea ba wanan abincin zanci wanda ya saura muna na rana. Har na fara ci na tuno nake ba umma labarin wayan dana tsunta din har iyayyen maishi suka kirani. Da farko kirji ta buga amma tana jin har nayi kwantancen inda za a sameni a karbi wayan sai ta dan sake take min fada dana tsunta me yasa ban bata ba a lokacin ? Nayi shiru kafin ince umma naga kowa a wurin ne lokacin kin san kuma gidan nan da tsunce. Modibbo yana kwance daki abin duniya ya dameshi na rashin ganin wayan shi gashi kuma bukatan abinda suke ganin zasu kawo karshen shi ba samu ba a garesu. Yaji anyi nocking din kofan dakin shi da alaman akwai wani a kofan lokacin dake son shigowa wurin shi . Ya mike daga shi sai dogon wando da fari singlet a jikin shi haroon ya gani tsaye a kofan mamaki ya kamashi. Sun gaisa ya bashi wuri ya shiga dakin suka kara gaisawa da shi yace oga yace na zo na fadama anga wayan ka a hannun wata yarinya Sahiba. Sunan ya maimaita a cikin mamaki Sahiba a ina ta samu wayan ya kwashe yadda mukayi da mahaifin shi ya fada mai. Nan ya nufi wurin dan jakkar kayan shi da sauri ya dauko riga ya zuru ya dauki bindigan shi ya soka a bayan shi suka fita a waje yake fadawa security din da su biyo shi anga wayan shi a wanan gidan hannun wata yarinya. Suka biyo shi da sauri baya suka shi shiga motocin su zuwa gidan mu basu samu isowa ba sai sha daya da wani abu duk yan gidan sun dawo a lokacin sai yan kalilan ne basu dawo ba. Mukan har mun kwanta sai jin jiniyan mukayi a kofan gidan naji umma na fadin kai innalillahi wanan masifa yau da me yai kama hakane ? Kamar mahaukata suka shigo duk abinda suka gani a gaban su suyi ball dashi ina yarinyar da ake kira Sahiba suka fada. Ga kowa ya fito hankali a tashe matan daga su sai daura gaba wasu kuma sai dan guntun wando a jikin su . Umma na kokarin budan kofan aka bamko kofan da karfi tace subbanallahi wetin we do again ? Sahiba are you ? Sukace wa umma ta girgiza kai kafin tace na my daughter be Sahiba sukace ina nake ? Sai gani na fito daga dakin ina mutsukan idanu aka tambaya a bayan su kun ganta eh ya bada amsa tare da fadin karamace fa ogo. Ku kawo ta nan ya fara tunkudani na juyo ina fadin na wetin i do ? i no be criminal woo stop pushing me like dat. Ai kafin yace me gulma ya fara tashi a gidan kowa da abinda yake fadi har gaban ogan nasu aka kaini naja na tsaya gaban shi kim kam. Where is my phone ya tambayeni nace saka hannu a cikin aljihun riga na dauko na mika mai ai sai gida ya dauka olusi omo buruku. Na dis smal rat stil d officer phone ? smol girl like u shame on u omo kowa dai yan gidan namu da abinda ke fitowa bakin shi lokacin . Wani tsawa ya daka duk aka natsu yace yarinyar nan ta tsunci wayana ba sata tayi ba don ta kira parents din na ta fada masu da inda zamu same ta. Kuma mahaifina yace nayi mata alheri don wanan halin nata na kirki data nuna ba wanda zai tsunci wayan nan ya maida min shi kamar yadda ta mayar min a yanzu ba tare dana sha wahala ba. Don haka ga wanan ki rika ya fada yana miko min kudin da sai lokacin ya kalleni ya gane yarinyar nan ne ranan ashe ? Yasan ban shedashi ba don irin yadda yayo shiga ranan ba zan taba sheda shine ba a yanzu gabana tsaye . Ya juyo ya kara kallona yana miko min kudi na gurgiza kai tare da fadin i no de colete ur money i just do wam becouse of Allah. Tsuki yan gidan suka fara suna fadin olopopo see d person wen no get any tin de reject d money now . Eh i no go coletem my religion no teach me like dis wani officer ne daga bayan shi ya amshi kudin a hannun shi yana fadin where ur mama. Na nuna mashi kofan dakin mu yace ur mama go colect d money naw yana dan washe baki. Shiko yana tsaye ya soka hannu daya cikin aljihu ya kura min ido a cikin mamaki hali irin nawa. Suko yan gidan namu sai fadin suke ehh givan to her mother she will colectam, suna wani bubuda mashi hanya don ya wuce. Su kuma na fadin haba dis enosent girl can do dat may she found it some where mafi yawan su haka suke fadi suna kallon yadda za a kwashe tsakanin mu dasu. Har guntun dan sandan yayi nisa a cikin muryan shi na kasaita yace dashi look Samuel called d mother for me first. Duk mama na tsaye a kofan mu a cikin tashin hankali tana jin abinda kowa ke fada lokacin kafin ma ya karaso itace ta fito suka juyo tare. Sunzo wurin ta dan tsaya a inda nake tsaye itama tana kallon yawan su duk wai a kaina suka zo can yace da ita. Yarki ta tsunci wayana ta kuma kira azo a karba shine nake son bata alheri don halin data nuna na kwarai taki karba. Ai domin Allah yata tayi hakan ka tambaya nan kaji idan mun taba rigima da wani tsakanin mu da kowa a gidan nan sai mutunci. Daga gefe suka shiga fadin gaskiya ne kwarai kuwa hakane don baka sanin ma suna gidan nan idan ba sun fito ba agansu. Oya ki karbi kudin nan don hakan umurnine na tabbatar da na baku alheri don yaba abinda kukai min don kinga wayan nan duk wani baiyanin sirina yana cikin sa kuma tunda ta dauka bata taba shi ba. Woman colet d money u be luck woman to born pikin like u knowadays with good heart wani tsohon iyamiri dake sayar da kayan part na mashin din hawa ya fada daga gefe inda suke tsatsaye. Woman colect de money now iyamirin ya kara fada sai umma takai hannu ta karbi kudin don iya shegen bariki sai suka ihu da tafe wai har sun manta wa yanda ke zagaye dasu a lokacin . Nan dai gulma ya kare bayan sunga sunyi godiyan hakan da akai musu suka shiga motocin su suka tafi. Tafiya sukeyi amma hankalin shi baya tare dashi duk da yana bin wayan shi da bincike a lokacib don ya tabbatar ba a taba mai ita ba bayan batar ta. Saidai hakan bai hanashi shiga zurfin tunanen da yakeyi ba tare da tantama ko a ina yasan wanan fuskan a baya. Haka nan a bangaren mu sai bayan wucewan shi ne umma takai kudin a hancin ta tayi saurin cirewa da sauri don irin kamshin da taji kudin nayi. Nima a daidai lokacin kwakwalwata ta hasko min kamar shi da wancan guy din daya taba ban kudi a cikin mota lokacin dana fita da ruwa. Umma na fada da sauri a cikin hausa nake fasin kamar wanda ya han kudi da nake tallan ruwa fa shine wanan mutumin. Tambayan da zan maki yanzu ke nan kika rigani ashe shi din dan sandane ke nan nifa Sahiba wanan abin yanzu ya fara bani tsoro gaskiya. Fada muka ji an rikice dashi a wajen gidan mu tsakanin yarabawan gidan da iyamurai da muke haya tare. Da sauri muka fito don hayaniyar yayi yawa duk dako darene wai wani iyamuri yace da ace yaran yarbawan gidan suka tsunci wayan nan ba zasu bayar don duk barayi ne son kudi yayi masu yawa sasai. Tofa ashe a gaban iya wale ya fada aiko nan ta saka kururuwa duk sauran yarbawan suka fito a cikin dakunan su ana fada. Saida kyat suka watse a lokacin nikan nayi barci ni da Amar sai umma dake zaune tana sallah take jin abinda suke fada a cikin fadan nasu. Washe gari kuma tunda asuba suka dasa fadan a inda aka tsaya a cikin zafi iya wale ke fadin wai e go say dat naw for yaruba becos sahiba mother na his ashawo. Inna lillahi naji umma ta fada da karfi na dago daga saka takalman da nakeyi na dan kalleta a inda take zaune din. Naji tana girgiza kai tare da fadin ni iya wale zataiwa kazafi a gidan nan kan wanan maganan yanzu kuma. We all know dat u are sleeping with her when your wife is not in d town shabi na lia i de talk ta tambayi sauran. Ai kafin umma tace me nakai waje ina fadin iya wale so ur tin don come to my mama again ? Na kalleta kallo a cikin fushi cikin turanxin su na lagos nace yau zan fadi abinda kikeyi da mazajen su a cikin dare idan suna barci basu sani. As from today u wil not tell lie for any body again in dis house no be u i see dat night with baba tunde on d floor ? An dat day again d same tin i saw u nicked baba Alaba de for ur back abi na lia i talk ? Swear if i tell lia for u naw, haba kai kace wani irin ruwan zafi na wasa matar shi yadda ta yanka ihu hankalin kowa saida ya tashi wurin. Ita ko iya wale dafe kirji tayi tare da fadin yeh Sayiba ehmi ? Yes u iya wale, na u a i saw dat day in d night with dem abi na lie i talk a wani irin maraice tace ah haba sayiba why why please ? Why u de telling dem lie sayiba ? Shabi lie no good wen u tell dem lie naw for my mama ai kafin tace zata bada amsa iya Alaba ta zo gaban ta tana girgiza tare da gyara danmaran da tayi tana fadin . Ai sai ihu ya tashi suna fadin sham sham on u iya wale , u no de feel sham sleeping wit somebody husband wuuuu. Danta wale yazo daga baya ban sani ba ya kai min duka sauran mazab gidan suka taso mai suna why , why go beat her ? Sai fadan ya koma a tsakanin su suka shiga zagin shi iya wale da yau taga masifa daga inda take ido yayi ja ta shiga surfawa wale din kuma ashar . Wanda da alama bata ma san abinda takeyi ba a lokacin don tashin hankalin data shiga a lokacin kan abinda na fada tayi. Nikan bayan na gama hada fadan na tatara na bar wirin cikin sulalewa na shige dakin mu na zata umma zatayi min fadan hakan danayi mata don tana babba sai naji shiru bata tanka min ba. Wayan shi ne yai kara daga gefen shi ya dago yana kalon mai kira daddy ya gani don haka ya daga da sauri yana fadin daddy yanzu nake batun kiranka na bari gari ya kara wayewane dama. Gari kan ai ya waye na yau sai kuma gobe idan Allah ya kaimu kuma sai yayi murmushi wa daddy nasa . Shi kuma yaci gaba da fadin masha Allahu dada waya dai ya shiga hannun ka ke nan tun jiya haroon ke fada min kun karbo. Ai tun jiyan uana zuwa muka tafi muka karbo wayan ya fadawa mahaifin nasa sai daddy yace a gaskiya yarinyar nan tana da mutunci sosai da wata ai duk abinda za ayi sai dai ayi ba zata bayar ba. Ta bayar dadi yarinyar tana da saukin kai matuka irin hausawan nan ne haihuwan can yarinya don ba hausan take ji sosai ba. Allah sarki ina dai kai mata alheri yadda ya dace ko don irin wanan akan ba mutun abinda bazai taba mantawa bane akan shi. Wallahi daddy na bata kuma sun gode don da farko sunki amsa sunce don Allah sukayi su. Saidai daddy wallahi yarinyar nan yadda kasan yar zuri,an gidan Namadi sak haka zubin ta yake ba zakace ba yar gidan bace sai idan tayi hausa. Kaji harshen ta zaka gane hakan gaban daddy sune yayi wani irn mumunan faduwa lokaci guda da kyat ya furta Allah mai iko. Shekarun yarinyar zaikai nawa yace karamace sosai dadi don da gani bata kai sha biyar ba ma haka mahaifiyar su ba wata babba bace sosai ga shekaru. Wayan ce ta mutu lokaci guda ya dago ya dan kalli wayan yaga ya katse ya kara kira sai computer kece masa wayan a kashe yake. Yayi mamakin hakan don yasan service baya katsewa a unguwar su su sai dai ya basar ya mike ya shiga bandaki yayi wanka ya fitone yayi odan abincin da zai karya kafin su shiga office su dan kara tataunawa kan criminal din su daya gudu bayan yayi nasaran shigo da kayan shi Nigeria ta barau niyar hanya da ba a san dashi ba. Yagama shirin shi tsab yana saka aninin rigan daya sa yaji wayan ya dauki ruri kuma ya nufi inda take saman gado ya dauka. My Mom ya gani a rubuce da sauri yakai hannu ya dauka yana mata kirari tace kai ni ba wanan ba wani zance kukayi da Alh ne haka har ya daga mashi hankalin shi haka. Sai da kyat aka samu ya dawo daidai saidai har yanzu baya magana don bai furtawa kowa komai ba sai ido da yake bin mu da kallo dashi da kalloyana jijiga kai. Inna lillahi yace nikan bamuyi zancen komai da daddy ba illa zancen waya na daya bace na gani shine kawai hiranb da mukayi din daga nan kuma naji shiru na kira kuma wayan ya mutu. ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , , DUK WACCE TAKARANTA MIN LITTAFIN NAN BATARE DATA BIYABA BAN YAFEBA Dakin Ammin shi yawuce, tana zaune as usual cikin shiga na alfarma kaman matan shugaban kasan Nigeria waya a kunnenta tana waya, kan stool na gabanta kuma fruits ne yankakku da spoon aciki da alamu sha take sai wayan ya tsayar da ita, zama yayi kusada ita sanan yadauki bowl na fruit din nata yafara sha abinshi wayanshi yaciro yana dubawa miss calls yagani like 9 daga number daya shiru yayi yanaji ranshi na baci baisan ya akayi Faisal yabama that Aisha girl number shi ba, bayan yabar Abuja lokacin da Mama tarasu daya koma baima sauka agidan ba hotel yakoma da zama dan he’s tired of yanda yarinyar keep stalking him school gida kaman zata haukace akanshi, he just had sex with once which he paid which infact ma bashi yama nemeta ba, Wanan halin datakeyi yasa kwata kwata bayama neman yaran naija, all babes dinshi achan turawa ne cus sunsan menene sex for fun not sex for attachment, dan tsaki yaja ganin tasake kiranshi ya ijiye wayan Ammi datagama call tace “kai lafiya kana neman fasa wayanka” ahankali yace “Ammi damuna wata mayyan yarinya take ne wlh” dan murmushi Ammi tayi tace “kai haka kakema yammata wulakanci ahaka zaka sami matan kayi aure, danni wlh tasaka zanyi agaba Kwanan nan zakai aure dan bazan barka hakama yaro kanada 36 kana neman 37 ace ba mata ina, akwai ma wata yarinyar kawata danakeso kaje kadubo bakaga yarinyar ba kaman baturiya” ijiye bowl na fruits din yayi yace “Ammi please don’t start niba yaro bane dazaki dinga nemomin mata ba I will get married but lemme take my time baaa rushing ayi aure, I still young bawai tsufa nayiba” tunda yake maganan Ammi ke kallonshi tace “wai kai Son na lura bamaka son Auren nan gabaki daya” murmushi yayi ya kwanta akan kujeran yana daura kanshi kan cinyanta ashagwabe yace “Ammi kaina kaikayi sosamin” hannu tasa cikin soft gashin nashi tana sosamai scalp tace “daga ina kake dan na aika dakinka bakanan” ahankali yana lumshe idanu yace “dakin Mom” tsayarda susan tayi tace “akanme zakaje gaida matan nan ita yaran datake zama dasu bata taba turosu sun shigo sun gaidani ba barinma Wanan mai idanun mujiyan Khairy” shiru yayi yana jinta baice komiba yace “ita tanaso yarana sudinga girmamata ita batasa nata sunyi hakaba” murya chan kasa yace “common Ammi nowww, yaran gidan nan waye baya tsoronki masifanki yasa babu wanda keso yashigo side dinki ya gaidake” ture kanshi tayi dagakan cinyanta tace “ni uwarka kake kira masifaffiya eh” maida kanshi yayi kan cinyanta yace “Ammi ok bazan kara zuwa ba cigaba damin bacci nakeji wlh” yanda takeson Zayn yasa shi kadaine bata iyawa masifa da wanine yau daya shiga uku, cigaba da sosamai kan tayi baidauki cikakken 4min ba yay bacci ahaka, ta tasashi gaba tana kallo ahaka Baffa yashigo side din yana kallonsu murmushi yayi yace “kin sangarta yaron nan dayawa wife” murmushi tayi tace “wai nan lallabashi nake yaje yadubo yar kawata idan tamai mu musu aure koya kagani dan wlh Alhaji na lura Zayn bayason yau aure at all” tunda tafara maganan Baffa yay gim yana kallonta, ganin yanda yayi yasa Ammi tace “tunanin me kake bakace komi ba” dan murmushi yayi yawuce sama sanan yace “idan bayaso karki takuramai” binshi da kallo tayi dan reply din Baffa seems strange, dan tabe baki tayi tace “zaimaje kuma zai sota atoh”. Wuraren 4 tana zaune adakinta tana waya da Aliyu da this is the third time yake kiranta tun bayan text datamishi dazu kan ta yanke duk yadamu harda cemata zai dawo tahanashi karya dawo dudda haka yaki yarda, turo kofa Batool tayi tawani fado gadon tace “Malama Ya Zayn yace kifito kuje” ahankali tace “kije kicemai nafasa zuwa” hararanta Batool tayi tace “wacece Yar aikenki ni kinga tafiyata wajen Mom bye” Aliyu dakejin maganan su yace “waye Zayn? Ina zaku”? Dan yatsine fuska tayi tace “gidan mu zani wajen Baba, Ya Zayn kamanta Babban yayanmu dandan Baffan mune” dan ijiyan zuciya taji yasauke kafin ahankali yace “go and tell him u are not going, gobe Adamu yakaiki” gyadamai kai tayi tace “tom bari naje” katse wayan tayi ta ijiye kan gado sanan taja wani gyalen Batool data jefar kan gado tadaura akanta dababu dan kwali tazura silipas tawuce tafita”. Yana zaune cikin mota yakafa black sun glasses a idanunshi kaman wani makaho yana kallon kofar flat din Mom, sai uban kamshi yake yasaka wani gizna mai ruwan toka ajikinshi kaman wani ango, bude kofan flat din Mom da akayi yasa ya gyara zama yana kallon flat din da kyau, fitowa tayi babu komi a hannunta sanye dawani pink bathroom slippers da kumbunan kafanta sukai Zara zara sukai kyau aciki, har lokacin tana sanye da gown din dake jikinta dazu, hannunta dataji ciwo saiwani kaffa kaffa take dashi kaman Yar yarinya daga ganinta kasan bata sabajin ciwo ba and she hates getting injured, fuskanta looks so innocent and so beautiful tana wani irin glowing idanunta subyi fari kal kaman tana wankesu da hypo, pink lips dinta ko daganan zaune amota da bakin glass dinan a idanunshi yana iya ganinsu, gani yayi ta tsaya takalli waya nan tsuntsayen dayagani anan barandan Mom acikin cage dinsu masu kyau dankoshi dazu dazai shigo saida ta tsaya ya kalli tsuntsayen dan sunyi kyau, murmushi tayi sosai da he could see all side dimples nata na lotsawa jerin gajejjerun white baby teeth nata sun fito tana kallonsu sanan ta tashi tajuyo tana saukowa daga staircase din, ahankali yakai hannunshi yadaura kan kirjinshi dayaji every step datai taking yana jinshi a heart dinshi, tunda yake shi he never baitaba jin haka on anygirl ba, shi baima taba tsayawa yakalli any girl kaman yanda yakalli Khairy yauba, he don’t know mesa kawai he just like how innocent she is, dan iska always know dan uwanshi idan yaganshi but anytime yakalli Khairy he sees yarinya that doesn’t know anything, yayi nisa acikin tunanin yaji tai knocking glass din motarshi wani irin daure fuska yayi batare daya saukarda glass din kasa ba yay unlocking car din hakan yasa tabude kofar motan kallo daya tamai sanan tadan sunnar da kai ahankali tace “Ya Zayn baranj…..” “you don’t talk to me daga waje get in kafin nabata miki rai” jitayi ranta yabaci ahankali tashigo motan tazauna zata fara magana yace “rufemin kofan mota” rufe kofan motan tayi ahankali kafin tai magana yatada motan yaja ana budemai kofa dasauri tace “Ya Zayn bazani ba shine abinda nazo nafadama” batare daya kalleta ba yace “idan munkai kidawo” dan jim tayi ranta nabaci, batare daya kalleta ba yace “sit belt Miss” jan sit belt din tayi tasaka sanan ahankali tamaida kanta tana kallon hanya. ANA DARA GA DARE, , , , , 1️⃣1️⃣ BY ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , PAID NOVEL YAR UWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA DA AMINCI KADA KI YARDA DA RUDIN SHEDAN KICE AI MUMA KARYA MUKE YI WANAN BA GASKIYA BANE, , , , , , , BISSIMILLAHI RAMANIN RAHIM , , , , , , Idan wani abu ya samu Alh a yau moddibo ne silan hakan don shi ya kashe shi ina tsaye suke waya dashi ban san ko suwa ya fadawa Alh ya gani ba iya dai abinda na sani ke nan a yanzu. Amma kuma kin san dai ba zai fada mai abinda zai halaka uban cikinsa ba da kansa don ke kanki da kike fadin haka yafiki son shi. Ran manyan mata ya baci don haka har takai hjy tayi magana a ranan kan irin izigili da iya shegen da hjy karima kanso ta kawo masu a gidan wani lokaci. Haka dai kikace don ko abin a zuciya yake ba a fili ba shi dai na gani don da kin san hakan ai ba zaki fadi hakan ba a yanzu ai. Don Allah hjy wanan wani abu kuke son kawo muna a yanzu kuma mijin ku yana a cikin wanan irin hali haka. Ku har kunga wurin fada a yanzu tsakanin ku makin ku taimaka mashi da addu zaku tsaya kuna sayar da hali haka. Dr bari abin na karima baida armashi wallahi duk yadda ka iya hakkuri sai ta kaika kull, daga inda hjy karima take tace eh tunda ba gaskiya kike so ba ke dole ki fadi hakan ai. Ya kara daga hannu yana fadin kunga don Allah kuyi hakkuri yanzu haka sai mun kai Alh asibiti don jinin shi ya hau sosai. Innalillahi suke fadi bayan hjy karima dake fadin kaji ba ko yanzu na fada duk ko meye ma modibbone silar tayar da wanan zancen. Nabila ce dake cikin shirin fita school sukaji kururuwan hjy karima tana neman agaji kan mahaifin nasu ta fice daga dakin rai bace. Don abinda hjy karima keyiwa mahaifiyan su a yanzu abin yana matukar damun su sosai a rai. Saidai babu yadda zasuyi ne don hjyn su ma ba zata bari suyi mata wani rashin kunya ba a cewan hjyn tasu ai kishiyar tace tana ganin a yanzu daidai suke a idon mijin su. Gashi a cikin yan kwanakin nan wani irin tsoro da fargaban ta suke ji don ta riga data dasa masu tsoron ta a zuciyar su. Basu Nabila kadai ba wanan abin yake damu a a yanzu ai duk wani wanda ke gidan kuma ya shaki hanyaki yai arba da ita a ranan data ai watar da sihirin shima abin ya shafe shi kamar yadda bokan ta ya fada mata tayi takuma yi din. Ya kuma fara tasiri a jikin su a lokacin sihiri ke nan duk da ita a ganin ta bata samu yadda take son samu a garesu ba . Don gashi duk da tana ganin tsoron ta a fuskokin su sai ya kasance kuma hjy din bata shakun ta a yadda taso ta kasance. Alh dake kwance ne ya dago kai jin wai za a kaishi asibiti yake fadi cikin karfin hali dr a barni a gida ba sai naje asibiti ba, zan iya kula da kaina a nan ma ya fada cikin yanayin tausayi. Ya kara da fadin idan har naji sauki ga goben nan in Allah ya kaimu nake son yin tafiya. Tafiya kuma Alh kana cikin wanan halin ciwo haka hjy Adda ta fada yace insha Allahu zan kokarta naga na tafi don abu mai muhinmanci zai kaini inda zani din. Duk da haka da ka bari har kaji , , , , a ikon Allah idan tafiyan baida muhunmanci a gareshi ai ba zaice zai tafi ba sai dai kawai idan ba a son ya tafi ga goben ne to amma mai abu ja mara abuja irin haka ? Allah ya kara lafiya Alh hjy Addah ta fada don ta gane me karima din take nufi a lokacin a zaton ta hjy na fada hakane kawai don ya kasance ranan girkinta ne goben shine bata son yayi tafiyan dayace zaiyi din don hakana. Dan murmushi Addah tayi kafin tace ikon Allah wani irn dare ne jemage bai gani a rayuwan sa saidai wanda ba,ayi yana raye ba kuwa hjy ta fada. Ko ya gani yana son kara gani don hakan bai ishe shi ba ai itama karima ta mayar da amsan gareta. Yanzun nan zaku bar wurin nan ya fada rai bace likitan yace shine abinda yasa nake son daukeka a gaban su tunda sun zama haka a yamzu. Ke hjy keda nake dauka mai hankali zaki biyewa wanan da kurciya ke dawainiya a kanta lafiyan mijin ku shine abin nema a yanzu ba wanan shiriritan ba gaskiya. Kyalesu dr nagane duk shirme da jin dadine ke rudin zuciyar su a yanzu idan na tafi sun huta ai da ganina. Hakan yasa duk suka ja bakunan su sukai shiru don yadda yai maganan a cikin bacin rai da nuna takaici a gare su. Bazan iya kwatanta dadin da yan gidan hayan mu sukaji ba a ranan yadda na kwayewa iya wale zani a bainan jama,a don su iyamuran suna tsoron ta wai tana da maita yasa takewa kowa har yarbawan su yadda taga dama a gidan. A yanayin rashin walwalan da naga umma a ciki tun faruwan abin yasa nasha jinin jikina na rage duk san guntun walwalan dake tare dani a yanzu. Gashi yau kwana uku da dawowan mu asibiti ban fara fita dan buga bugan samun kudin da nakeyi ba har wanan lokaci. Don muna amfani da dan kudaden da muka samu daga hannaye manbambata damu san da su Allah ya tsago muna rabon mu daga tsatson su muna ci. Ko yanzu ma abincine na sayo muna don duk da kudin a hannun mu bamu girkawa saidai mu dan sayo don sabo da dabi,an yarbawa da mukayi a can da kuma rashin lafiyan umma din da Asma ke baraza a kanta yanzu. Duk da yake taimakon data samu a zaman mu asibitin nan yasa ta samu lafiya yanzu sosai ba irin nadewan nan da takeyi ko yaushe a cikin ciwo da takanyi ba a baya, Abinci ta fitar ta zuba a plate din da suke ci a ciki ta mikawa umma nata ta kai nasu har gaban kanin ta don suci kamar yadda suka saba yi a kullun. Munyi nisa ga cin abin muryan umma ya dakatar dani daga kai loman abincin a bakina take fadin . Zamu bar gidan nan da unguwar nan ga baki daya zamu koma can nisa da kowa da yasa mu nan a baya son gaba daya hankali bai kwanta da zaman mu a nan ba kuma yanzu. Umman don fadan mu da iya wale zamu bar gidan nan a yanzu in hakane umma ai na rama maki kwatankwacin abinda tayi maki itama taji in da dadi. Bashi bane Sahiba ni na hango abinda ku baku san dashi ba a yanzu don kaucewa duk wani abinda ka iya tasowa nan gaba gareku zai samu tashi. Umma idan mun tashi ban karatun ma fa nida Amar duk da karatun bawai ya dameni bane a lokacin. Duk nayi tunanen hakan umma tace sai dai da yake ga wa yan nan kudaden a hannun sai muyi amfani dashi wurin canza makarantar naku ai. Fuskana na bata kafin nace yanzu umma idan mun bar nan ina zamu koma kuma tace na yanke shawaran mu koma can semi boda zaifi muna don shike nisa da nan sosai. Semi boda umma wa muka sani a can da zamu koma can din da zama umma ta kalleni fuska daure tana fadin . Nan din da muke zaune tare dasu yan uwan mu nesu ko mun san sune dama haka can din da sannu zamu saba da su ai. Fuska na tabe lokaci daya alaman ban dai so hakan ba tace na kula baki son tashin mu gidan nan don sabon da kika dayi dasu duk da ba taimako a tsakanin mu dasu. Saidai ki sani duk sabon nan na banza don watarana dole mu bar juna mu dasu na bar gida da mahaifana da yan uwana da waye ba zan iya rabuwa a yanzu ? Na dago ido na dan saci kallon ta tasan tambayan da zan tambaye ta a yanzu shine. Mu koma gida kamar yadda nakan fada mata kulun idan muka shiga wani matsi na halin kaka nakayi nakan ce umma mu koma gadin naku mana zaifi. Ba zan koma daku guda a yanzu ba Sahiba sai lokacin da zaku iya kare kan ku a cikin yan uwan ku ta yadda duk wanda ya kawo maku hari zaku iya kare hakan a lokacin. Tsam na tsame hannuna daga cikin abincin don gaba daya na rasa meke min dadi a lokacin haka na nufi hanyar fita waje in wanke hannu na. Umma ta bini da kallo kawai din tasan abindake damuna a lokacin shine sabo kawai a yanzu inba haka ba meye hadina da wa yan nan dana sawa kaina damuwa da rabuwa dasu a yanzu. Har na kwanta ina cike da damuwan zancen da mukayi da umma na tashi daga wanan unguwar mu koma can nisa dasu inda ba zasu kara jin duriyan mu ba gashi na nemi dalilin hakan da umma zatayi na rasa a yanzu din. Wayarsa ce ta katse masa hanzarin sa nan ya tura hannu ya zaro wayan a cikin aljihun shi yana dubawa sunan hjy Addah ya gani a screen din wayan rubuce. Ya kara a kunnen shi yana sallama tare da mata shagaba ta katse shi da fadin modibbo ciwon Alh fa sosai ne don yanzu gamu asibiti dashi an bashi gado.. Yace oh my god meke damuwan daddy haka jiyafa lafiya muka rabu dashi. Ka daure ka shigo ka dubi jikin mahaifin ka zaifi idan akwai lokaci a gareka yace insha Allahu mommy zan shigo da yamman nan idan na samu jirgi ko gobe da safe idan Allah ya kaimu. Tace lalai ya kamata ka shigo din don hakan na da amfani sai dai idan kazo zakaji komai. Okay mommy sai nazo din insha Allahu ya fada yana katse wayan gami da duban agogon hannun shi ya sauko daga saman benen da yake kai tsaye ya nufi wurin motar su. Ma saukin sa ya nufa kai tsaye bayan yayi waya acikin motan ai masa booking din jirgin yamma da zai tashi a ranan. Yana tuna rabuwan shi da dad din da yake ce masa mommy ku ta fada min hukunci daka yanke game da auren ka tun ina can. Baison yayi gardama ko nuna bai sani ba ya nunama dad din hakane mahaifin nasa yace dashi are you serious this time around. Nafa sanka da tsanar ko wace ya aka gabatar maka a matsayin dacewa dakai babu kuma wani zabin da kai kayi. Yace No daddy Allah indai tayi maku ko wacece nima tayi min ai iam serious zan aure ta don nasan ba zakuyi min zabin banza ai. To Allah yasa alheri a cikin wanan al,amarin yasa muce gumma da akayi sa yace amin daddy din ya dan bubuga mai baya kamar yadda yakan mashi sukai sallama dashi. Ya runtse idanuwan shi don tuna ko da safe ai sunyi waya lafiya lafiya dashi har yake masa nasiha akan kyautatawa a ko yaushe akan wanda ya dace . Inda ya ke bashi labarin yarinyar da yanayin zubinta dana yan gidan Alh namadi wan mahaifin daddy din da suke yan uwa na kusa dasu . Yayi sa, a an samu jirgin da zai tashi karfe biyar na yamman ranab don haka ya tura kudi ai masa komai. Na fito daga gida da roban diban ruwana ina sauri don kada in rasa layin gaba in samu mutane da dama a wurin da zai iya kaini wani lokaci ban debo ruwan ba a jarkokin mu. Wata dake makwabtaka damu na sama a hanya muka jera zuwa wurin take fada min zata canza makaranta don zasu bar wanan unguwar zasu koma Ikeja da zama gidan wani dan uwan su. Nace eh nima zamu tashi ai kwanan nan zamu bar wanan unguwar da sauri tace ina zaku koma ke nan nace Semi boda. Tace i pity u dat place na ijabu de stay dere u no go enjo yam at all sai naji gabana ya fadin amma na daure nace da ita. So u mean all d people de stay at dat place na ijebu people no fine fine people stayed dare if u go u will c what am sayin wahala de dare to much. Tafe nake ina tunane har idan haka wurin yakw meyasa umma ta zani mu koma can da zama da nan cikin gari da muke manejin a rayuwan mu. Na samu nagama deban ruwan a wahalce a gurguje na shirya zuwa makaranta har muka dawo babu walwala a tare dani ina faman tunane ya rayuwan mu zai kaya a sami din idan mun koma can. Kwana biyu tsakani kawai na dawo daga makaranta na samu umma tayi muna packing din kayan mu a wuri daya nan hankalina ya kara tashi da hakan ke nan tashi mu a wanan gidan ba fashi ke nan. Idan kun gama sai ku shirya mu tafi don yaune tafiyan mu da zamu bar gidan nan an sama muna wuri can a sami din inda zamu koma. Tana fadin hakan ta fita ta dan jima sai gata ta dawo tana fadin wai mu fito mu tafi mota yana waje haka na fara jidan kayan mu ina kaiwa aurin motan. Yan gidan mu din suna fadin why u go live dis hausa iya sahiba na bcos of dis mama wale who de acuse u dat day ? Tace me i no mind dat matter at all, we are living just becourse we have relative ther wonko. Motar yar kurkura ce ni da kaya ma a baya muka zauna sai wanan unguwar dake da a yanzu ya zama sabon uguwar mj a yanzu. Muna dosan uguwar hankalina ya tashi matuka don a gaskiya ban taba ganin unguwa iri wanan a rayuwa na ba. Don itatuwan bambo ne akayi gida jen dasu a unguwan sai gidan dajen da basu da yawa a cikin unguwan duk bambo yayi yawa a wurin. Ga kuma wayan cin koson jama,a da abin baima fada a lokaci shiko kazanta ba a ko zancen shi a wurin don yawa Semi boda ke nan da nake jin labarin shi a sa can baya yau kuma gamu a cikin sa tsun bul da zama. Ina bayan mota sai bin ko ina na wurin nake da kallon mamaki wai a nan zamu zauna cewan umman mu ni san ba zan zauna a wanan wurin mai yawa da cinkoson mutane ba haka babu security na fada a kasan zuciyana ni ka dai a bayan motan har lokacin. Motan ya tsaya a wani gida kofan gida da shima da irin itacen bambo akatyi shi driver ne ya fara fitowa daga cikin motan kafin umma su sauko ita da Amar. Kai tsaye asibiti yace a wuce dashi daga airport din daya sauka bai sha wani wahala ba son ya san asibitin ya nufi bangaren maza da yasan zai iya samun daddy din nasu a can. Hjy karima ya fara hangowa tsaye tana magana da kawar ta dataji attach da yawa a kanta kalan ja sai wani shining takeyi don man bleach da yai mata yawa a jiki sosai. Duk da ta ganshi tafe ta kuma sheda shi din ne batayi wani fara,a afuskanta ba son ganin shi haka ya daure ya nufe su. Yana masu sallama sai kawar nata ne ta amsa bai damu ba don a zatin shi yanayin mahaifin nasu ne ya saka ranta baci. Ya bude baki zaiyi magana aka bude kofan dakin wasu yan uwan sune suka fito suna ganin shi suke fadin ashe har ka iso karasa man suna ciki ai ya wuce ba tare daya amsa masu ba kai tsaye. Hjyn su tana zaune kusa da Alh ta babake wuri wanda ba komai yasata yin hakan ba sai don hjy karima da taso ta kawo mata iyayye iyayye tun zuwan su asibitin. Gaidashi aka fara shima yana masu ya mai jikin hankalin shi akan mahaifin su dake kwance sambal saman gadon asibiti. Ya karasa yana sake tambayan ya jikin nasa hjy tace da sauki a lokacin Alh ya juyo inda yake ce sun tayar mada hankali ko sai da sukasaka tasowa a cikin daren nan haka. Ya dan sake murmushi ya dan duka yana gaida mahaifin nasa tare da tambayan shi abinda ke damun shi din. Ya dan murmusa yana fadin ba komai jikin daine ya dan motsa kasan yanayin jikin daya fara girma ai. Ni yanzu haka a gobe idan Allah ya kaimu nake son cin maka can legos din sai gashi kai kuma kazo ashe. Daddy a hakan kake son yin tafiya ba lafiya a jikin ka wani abin zai kaika koma meye shi ai zaka bari ka samu lafiya tukan daddy. Murmushi yayi kafin ya mayar da hankalinshi kan ruwan da ake kara mashi din yana kallo aka turo kofan dakin suka mayar da kallon su ga kofan banda Abubakar da bai juyana balle yaga ko suwaye suka shigo din. Muryan gwagon shice yaji sai ya juyo da sauri don yasan halin gwago Altine din da masifa yanzu za a jisu a wurin. Itace da yaranta yan mata biyu suka shigo sai wani izza da takama sukeyi a wurin da basket din abinci a hannun su. Kafin a gama gaisawa din kuma sai ga Alh wada da matar shi gwago halira sai dansu guda daya tilo a bayan su shima yazo gaida Alh din. A, a wanan shi kuma saukan yaushe wanda ake tambaya ya danyi murmushin gefen baki yana fadin mommy mun sameku lafiya. A cikin iza da gadara da isa uwar take fadin ai kowa zai fada ina yanzj kaji da kunnuwan ka dai. Ido kawai Abubakar ya zuba a dakin yana kallon da sauraren kowa a cikin nazari kafin yaji gwagon nasa tace . Wanan kan yaushe shima yazo garin nan ashe duk kun shigo ke nan a wanan loacin da ta fada tana kaiwa inda dan uwan nata yake kwace saman gado. Shima dan nata ya bita a baya suka fara gaida mahaifin shi da dalilin shine suka taru nan a yanzu . ZAINAB IDRIS MAKAWA ANA DARA GA, , , , , , , , , , , 1️⃣2️⃣ BY ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , , , , PAID NOVEL NE YAR UWA DON ALLAH KI BIYA KADA MU RIKE JUNA DANI DAKE, , , , , BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM ALLAHU, , , , , , Ni dai nasan yar talkace talal da ma ban san asalina ba tukun a duniya saidai kuma duk da hakan Allah ya jarabceni da kyankyami a rayuwana. Don akwaini da shegen tsabta da kuma jin kazanta ko dan abu kadan ne yazu zanji shi har kasan zuciyana. Don hakane ma yanzu nake bin wanan guri da umma ta kawomu da sunan zama kuma da mafaka a wurin mu a cewan umma din. Sauka nayi daga cikin motan ina bin wurin da kallon tsana da kuma kokarin tara hawaye a idona don takaicin abinda ke cina a zuciyana. A daidai lokacin dana dira daga cikin motan lokacin ne wata yar kyamusassan datijuwa ta fito daga cikin gidan tana muna marhabin da zuwa. Da gani dai sun san juna da umma da dadewa don yadda suka nuna din ga junan su kuma itace na zarga da alhakin dawowan mu wanan wurin a yanzu. Ido ta dan kura min kafin tace dani Sahiba ce wanan nake gani wai kai amma girman dan mutum baida wuya wallahi wanan yar ne ta girma haka ashe. Aku,rele, nace da ita tare da danyi dukawan gantsara kadan wai ina gaida da ita tace aini nan yar kasace ba wanan gaisuwan gaidani da ina wuni zaifi don ban yarda in rike yaren wasu a bakina . Kayan da driver ke jibgewa a kasane yasa matar fadin kin gani ba mun tsaya muna daukin ganin juna haka muna yashe rabo ai muje ga dakin can daga baya inda zaku zauna din ta fada tana yi gaba. Muka bita shima dai din ginan icene kamar ko wani duk su aka jera aka fitar da daki a wurin saidai shi wanan din da ta nuna a matsayin sabon mazaunin mu ya tsufa sosai da ganin sa ba na yanzu bane. Don wasu har koren icen da aka saro na bamboo tree din yana nannkoreshi shar a jikin icen wanan ko ya kode ya rike zuwa brown ko. Ikon Allah kamar ma kiwon dabbobi ake a cikin dakin don alama ya nuna hakan a dakin Sahiba karbi wanan tsintsiyar ki kara sharo dakin da kyau kafin ku shiga matar ta fada. Na mika hannu na karbi tsintsiyar a hannun ta har na shiga dakin na fito da sauri ina fadin umma, A dakun fumi firthy naira i wan buy clean to worsh d room first . Ehyahh yar naki ashe ba kalar zama wurin mu bace har take zancen clean a yanzu daga inda umma ke zaune tana tura hannu cikin katon kwagirin ta tace kyankyami daine irin nata kawai kuma sabawa zatayi ai. Yo ai dole ta saba indai tana zaune a nan damu wataran kamar ba ita bace ai idan ta saje a cikin mu matar ta fada sai umma tayi dariya. Sai ga wasu mata sun fito daga wani sashe na gidan suna fadin ai yau ladi baki mukayi a gidan ne kuma ? Ta wani tabe baki kafin tace dasu to bakin ke nan amma da ai a nan take ta koma can Ajagule da zama yanzu kuma suka dawo nan din. Na dan dago kai ina kallon umman mu a ciki mamakin jin cewa wai da a nan muke zaune ashe muka koma cikin gari da zama. Ga mamakina umma sai murmushi take masu bata mussa hakan ba ta miko min hamsin din na sa kai na fita ba tare dana san gurin sayar da kayan tiredan ba a lokacin. Titi inda motar mu yabi namike don naga wasu shaguna da zamu shigo layin can na nufa sai Allah ya taimakeni na ci karo da wani dan cures a bakin kofan wani gida na tsaya na saye na koma inda na fito. Tas na wanke dakin na cire duk yanan dake cikin sa na dauko labulayan mu na sargafa a kofan dakin da taga sai gashi dakin ya tashi daga akulki ya koma dakin motane a hankali nayi ta jidan kayan mu ina kaiwa cikin dakin har na jidesu kaf nayiwa ko wani wurin zama lokacin har magariba yayi ruwa na nema inda zan samo na zuba muna kada mu tashi da safe bamu dako na alwala a wurin. Allah ya taimakeni ina fita na hadu da wani yai min kwatancen inda zan samu ruwa a sannu har na cika dan roban da muke tara ruwa a cikin na dawo na zauna. Umma ta ce dani idan na huta ga abinci nan in dauka inci ladice ta kawo muna shi dazun muci ni da Amar. Amsawa kawai nayi amma bada niyar ci ba na amsa mata da to na kawar da kaina gefe daya ina faman tunanen wanan rayuwan namu da muke ciki. Ba karya bane da masu iya magana ke fadin kada ka raina kanka a inda ka samu kanka da zama sai a yau na tabbatar da wanan zancen haka yake ashe. Sai satan kallon juna sukeyi a dakin an rasa wanda zaiwa wani magana a cikin su balle har su kai ga gaisuwa wa junan su. Waini kan moddibo ka gaisa da dan uwan ka kuwa tun da suka shigo dakin nan hjy ta fada tana kallon yan samarin dake zaune a gaban su kowa na busan iska a lokacin don isa da takama da suke ji dashi. Don kada ya bayar da mahaifiyan nasa a gaban yan uwata ya nuna masu shi dane maijin magana a take yake fadin ban ma kula dashi aka shigo ba ai. Yah kana lafiya ya fada cikin dakewa shima ya amsa masa da lafiya ya mai jiki thank god ya samu sauki ai ya fada yana mayar da hankalin shi gun wayan shi dake hannun shi. Ai wanan din ne babban bazan daya kasa gaida mutane a wurin ya shigo kamar wani dodo dashi yana tsoron mutane. Halin the boy ne baku sani ba kuma da kyaluwa shi haka Allah yayi shi shine kuma yake son biyewa halin nasa ai hjy Addah ta fada. Alh dake kwance yana jin su ne yace wai ba zaku daina kiran shi da boy din nan ya nuna diyan hjy Altine yana fadin jifa inda kanen sa suka kai yanzu da girma za,a wani saura kiran shi da boy. Murmushi wanda aka kira d boy din yayi ya mike daga inda yake zaune yana fadin uncle ashe ka tashi ke nan na zata barci kakeyi ai. Ya mike daga zaune da yake yana saye a cikin kananan kayan da sukai matukar mashi kyau a jikin shi zuwa bakin gadon da daddy yake kwance din a sama. Kamar yadda yakanyi da danshi modibbo hakan yakanyi da dan kanwar tashi ba ita kadai ba har hjy Atine dake da yan mata guda biyu suma suna samun kulawan kawun nasu sosai a cikin so da kaunan junan su. Yaushe ka dawo ke nan daddy ya tambaya yace yau da safen nan daddy nazo gobe kuma zan koma don yau naso in juya sai na samu bakaji dadi ba kuma. Dan murmushi ya sake yana fadin suka kwantar dani a nan ba badan naso ba don kawai dai banda yadda zanyi ne na yarda na kwanta din. Amma dai yaya ai kwanciya yana da amfani a gareka tunda kaji doctor yace sai ka dan kwanta din kwanciyan a yanzu shi yafi ga lafiyan ka. Kofan aka turo hjy karimace da wanan kawar nata suka shigo duk suka kalketa suka kawar da kansu gare ta don yanayin wayewan ta ya nuna yar bariki ce ita bata da isashen kamun kai sosai. Alh ashe jiki ya ki karima ta kira tana fada min tana magana tana wani kwarkwasa a gaban shi abinda ya kara basu takaici ke nan a dakin. Allah ya gani abinda tun farko suka guda a auren shi da karima ke nan abinka da namiji ga abinda ya gani yana so yace yaji ya gani sai yayi. Gashi har yanzu rabo ya ratsa a tsakanin su yan maya uku resas suka haifa bai kuma sa ta natsu ta daina wasu halaiyan da basu so a gareta ba. Da shima kanshi Alh da alama yaji nauyin hakan sai ya basar yana fadin ya gode ya juya yaci gaba da zancen shi da boy din yana tambayan shi yanzu kana wani kasane boy ? Ya dan yi murmushi yana fadin daddy ba inda bana zuwa saidai yanzu din nafi bada karfi a kasan Ukraine don shigo da alkama a nan kasashen muna Africa da muke karancin su sosai. Masha Allah ashe kana wanan harkallan hakan yana da kyau sosai ina dai fadama duk lokavcin da kake bukatan wani taimako a cikin sana,an ka ka nemeni zan taimaka maka insha Allahu. A daidai lokacin hjy karima ta wani tabe baki tana fadin muje ko kubura sai kawar ta juya tana fadin Alh ya ya kara sauki ta juya ba tarewa kowa magana ba a dakin ta fita. Boy da moddibo kawunan su yana kasa kowa da iri takaicin da yaji a hakan saidai kawai a shanye ba dan anso ba. Babu wuta a cikin hasken farin wata muke zaune sai dai ina can dan nisa dasu kadan ina jin hiran su da nake tsunta guda guda. Ko barci yarki keyi a zaune koko gajiyan aikin da tayine yasa ta shiru matar da umma ke kira da Ladi ta fada. Kawai dai nasan bakuntane ba wani abu ba tana tunanen wancan unguwar da muka barone don bata so tasowan mu ba can. Ikon Allah yarinya nan din ai zaifi maku saukin komai dama ai don hjy nana ne kuka koma can Allah kuma baiyi zaman naku mai tsayi bane a can din da ita aka rabu. Wacece hjy nana na tambayi kaina don ban taba jin umma na zancen ta ba a gabana har yau wama umma ta taba zance ni a gabana na ba kaina amsa da hakan. Mikewa nayu tsam na hankade labulen zuwa cikin dakin namu din na kwanta ga duhu ga kukan wasu kwari a bayanbdakin masu shegen kara a kunnen mutum da zasu hana mutun yin barci da dadi. Allah ya gani ganin farko da nayi wa wanan unguwar na tsaneshi ga baki daya a rayuwana a haka nayi barci sai dai banfi awa biyu ba dole na falka don yunwa ga kuma karan kukan wanan halittan dake ban tsoro. Duk da duhun dakin amma hakan bai hanajin muryan umma ba tana fadin nasan dole ki falka dama don babu komai a cikin ki tun karywan safe da kikayi kafin kije school. Gaskiya ba zan iya cin wanan abincin ba dana gani kamar ma bayin yau bane guntayen tuwon masara da miyar kubewa fari tas dashi an zuba miyan a ciki. Bana jin yunwa umma kukan wanan abine ya dameni na bata amsa a cikin duhun nima ina gyara kwanci saman tabarman da nake kwance. Shiru naji umma tayi bata kara tanka min ba har wani barcin ya kara daukana bayan na gaji da tunane ni kadai a cikin dare. Washe garima haka na tashi sukuku dani bayan na gama sharan fadin kewayen mu da aka mayar kamar juji a gidan wanda a yanzu duk na gyara shi tas da wanab safiyan. Na debi ruwa na watsa a jikina na dawo na zauna na shafa mai naji umma na fadin ki karbi ga dari biyu ki fita ku samo abinda zaku karya dashi kafin mu san abinda zamuyi nan gaba. Karban kudin nayi na fita na fara dan zagayawa ina kara kallon yanayin wurin da hausawane zube ashe kamar mutum yana a cikin arewa ne zaune. Saidai kowa kuma a wurin da irin sana,an da yafi kwaraiwa akai ga masu tallan abubuwan da ban san suba nan ina ta kallo na nufi wata mace dake soyar masa na mika kudin ta bani masan tana ta zuba duk sai naji kazantan hakan nayi dana sani banje gurin ta ba saye don akwai har maza dake wanan sana,an a wurin. Haka na dawo gidan da jan kafa na zauna tare da dangware kwanon abincin a gaban Amar na koma na rakube gefen kofan dakin nayi shiru ina tunane. Ba zakici abincin bane ke umma ke fadi tana bude kwanin dake rufe ta girgiza kai ta jawo kwanon zuwa gaban Amar yana gani yake tambaya na waitin bi dis ? I no sebi eat dis kind of food wooo u ko ta kalleni tana tambaya nace i no go eat now i don bele ful na fada ina kawar da kaina gefe daya. Tace no be u buy yam for breakfast ta dauki daya tana kaiwa bakin ta kagin tace eatam naw go enjo am is test good now. I no sabi eat dis kind of food before i will drink gari da gradnut later na fada ina mikewa tsaye don barin dakin na fito na tsaya ina kalle kalle a wajen gidan. Sai ga wasu tafe da ganin su mata da mijine zasu fita na bisu da kallo matar tana saye da hijab a jikin ta shigan ta ya banbanta sosai dana wanda na saba gani. Har suka fice a gidan na sauke ajiyan zuciya ina mamakin su a raina kafin naji muryan ladi a kusa dani tana fadin yanzu nake zancen ku ai a zuciyana ko kunyi dabaran neman abin karyawa nace ? Dan juyowa nayi ina kallon ta kafin na dan kago murmushi a fuskana ina fadin A karo ma tace adukwbe yar nan haka uwar ku tayi sakacin da yaren wasu ya shige maku harshe haka ? Tana inane ita uwar taku na nuna mata dakin mu da iska ke dan kada labule a hankali ta juya ta nufi can din da abu a hannun ta zuwa aurin umma din. Ta dan dade a cikin dakin tare da umma wanda bansan ko akan me suke tataunawa ba har tayi wanan dadewan haka a ciki. Ni kuma ban shiga ba tunda bansam zancen da sukeyi kada in shiga injiwa kaina haka din ne kuwa don ta shiga tawa umma zancen sana, a ne sai aka kira wayan ta ta tashi. Ganin ta fita din daga dakin yasa na koma dakin na samu wuri na dan kwanta sai barci a can cikin barcin nake jin muryan ladi na fadin. Ke yanzu ai ko baki fita kin nemo kudiba yanzu kina da jari don wanan yar zata iya nema maki duk wani abinda zaku bukata idan tana da kwazo da basira. Ga wanan unguwar namu cike yake da samari majiya karfi suna harbin iska ga banza balle sun kyala ido sunga wanan yar taki ai kakanki ta yanke saka ke nan ke. Haba ladi ni kaina bayi shanshamci ba tun barin gida danayi kin sani balle na saka yar mutane ga hanyar halaka. Kin dai fadi gaskiya kan da kikace gani da ita a gaba tunda ba issashen lafiyane dani a yanzu . Eh ko can din inda muka baro itace tsaye damu ga komai tana samo muna dan abincin da zamuci a cikin wuni da dan kwabon da zamu sarafa rayuwan mu a kullun. Amma sam ban yarda ta aikata abinda kimarta da mutucin ta zai zube a idon duniya ni banyi ba ita kuma bazab sakata ba son bamu da gadon yin hakan. Cikin dadin baki irin na Ladi din tace yo ai ba gado bane abun indai ka riga ka shigo bariki ai shike nan ka zama dan gida ga wanan harkan. Ladi ina da abinda yarinyar nan zata dan rika juyawa yana zama kudi a yanzu a hannu na muna samun rufin asirin mu a cikin sa insha Allahu ba sai mun zubar da kiman mu ba. Kin sani kuma kinmafi kowa sani yaran nan ba shegu na haufesu ba suna da ubansu da yan uwan ubansu nadai gudu da sune don sun rasa mahaufin su ana son a juya a kansu yanzu kuma. Yo ai shike nan dama ni abinda nake jiye maki ke nan a yanzu kuzo ku zauna kuna zuba ido sai anci an raga a baku shine banso daku . Ko a can ma idan muka fito basu san mu bamu san suba ban yarda mun zubar da kimar mu a can ba balle nan da yake kamar kasan hausawa a wanan wurin. Har ladi tabar dakin ban gama fahintar inda zancen su ya dosa ba sai daga baya na fara gane kan zancen su ina hada kalmomin ina fahintar zancen su dana ji din sunayi. A raina nace ke nan dai ya tabbata umma ta gudu daga gida damune don kada a cuta muna ke cikin wanan halin na wahala data kwanmace ma ganun mu hakan. Su waye suke neman rayuwan mu bayan sun ga na mahaifin mu har mu suke son su karasa ake nufi. Idan har hakane kuwa zan kara taimakawa umma wurin ganin mun kula da rayuwan mu kamar yadda umma ke tunanen yi akan mu ko yaushe. Likita ya shigo ya duba jikin Alh yaga yayi yadda yake so sai kawai ya rubuta mashi sallama don shima bai son su kwana a nan gara ya koma gida zaifi mai sakewa da wakwala don sanin halun Alh da yayi bai son kwanciya asibiti ko kadan sai in ya kama dole. Aka tataro aka dawo gidan dashi Modibbo ne ya jawo shi a hankali tare da matan shi su biyu suna bayan motan a zaune. Har suka iso gida motan shiru ba wanda yayi wani magana sai maigidan ne da dan sa ke dan hira jefi jefi a motan. Shiya kama mahaufin nasa har zuwa dakin shi ya zaunar dashi saman gado kafin ya kunna mai Ac da bai sake sosai yana kokarin fita. Ji mana modibbo sai ya juyo da sauri inda mahaifin nasa yake zaune yace tambaya nake son yi ma tsakanina da kai a yanzu. Daddy akan me ya tambayi mahaifin nasa yace akan wanan yarinyar dai ta lagas da kace kaman su yana zubi na diyań gidan baba namadi. Shikan modibbo da nai san kai ba yace wallahi daddy kamarta dasu har ya baci harda dan lutsawan nan na kuma tun su duk tana dashi a fuskanta. Sai dai ita wanan din ko hausa bata iya sosai ba shine maraban su da yan gidan kuma ita wanan din ta dara su haske sosai gaskiya. Kasan gidan ita wanan yarinyar a lagos din na sani don dani aka tafi karbo wayan gidan gidan hanya din nan ne mai girma sosai don mutanen gida suna da yawa sosai gaskiya daddy. Zaka kaini in gansu ya fada abinda yasa modibo yayi saurin juyowa ke nan yana kallon mahaifin nasa a cikin mamaki. Lafiya dai kake son ganin ta daddy don ba yar nan bace fa na fada ma ita din yar nan bace kama ne kawai da sukayi a fuska. ZAINAB IDRIS MAKAWA ANA DARA GA, , , , , , , , 1️⃣3️⃣ BY ZAINAB IDRIS MAKAWA YAURI, , , , , PAID ONLINE NOVEL YAR UWA DON ALLAH KI BIYA KAFIN KI KARANTA KADA MU RIKI JUNA DANI DAKE, , , , , BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM ALLAHU, , , , Dan kwana biyun nan duk a shiririce nayi shi ba walwala ga kuma yunwa na batun kasarani don tsanda na kasa cin wani abin kwarai a cikina yanzu tun zuwan mu semi din komai ya tsaya mun cak. Ina ganin yan iska da yan duniya saidai wanda nake gani yanzu a semi boda ya cunawa wanda muka baro a baya can. Zaka ga yarinya da shigan kafirai amma idan ta juye harshe tana hausa sai kin rike kanki don mamaki. Hakama diyan su maza duk wani iya shege ya kare a wanan wurin ko yan Agege da Alaba rago da can ne dalilin hausawa kamar kana arewa da zama sun dagawa yan seme boda kafa wurin iya shige. Haka yasa fitama bai ban sha,awa yanzu haka zalika banyi gigin fara wani sana,a ba can da zan dan dogara muna dashi inda kudi zai shigo muna. Ga wanan hiran da naji umma da ladi sunyi ya kara min wani irin natsuwa a yanzu ga baki daya na koma wata shiru shiru dani a nan din. Yau kan na kudiri fita in zaga ko ina na garin inga gari gari ya ganni in sama muna abinyi don sai dan kudin dake hannun mu ne umma ke zara muna dan sayen abinci dashi dasu sabulun wanki dana wanka. Wani dogon rigana mai kama da kaki na saka sai takalmana da na ciro a cikin kaya ina goge kuran shi don in saka. Umma ta kalleni yau yarbancin take ji tace dani enbelolo ma,ana ina zanki tafi sai dana dan bata fuska nace i wan worker round to see d town b4 i start bussines . Don mind ur self here uno go enjoy dis place well, na bad people de stay round d place . Umma why we come here now why choose d place dan stay there at Ajagule me i no pit stay here woo na fada ina mike wa tsaye. U don no anytin dat worry us at dat place since i no peole don familier wit u naw at Ajagiule. Na mike tsaye ina fadin na yim u carry us come dis yeye place when person go die for notin haba pity us naw umma. Wani tsawa ta daka min har saida na gigice tana fada a haka har na sulale bata sani ba na fita daga gidan na fara tafiya. Kamar yadda kowa ke tafiya a wurin haka nima nake tafiya ba tare da kula kowa ba balle ma ban san suba balle na tsaya kula su har nakai titin su na zaga ko ina ina bin garin da nazari. Ba laifi don garin akwai shegen girma kamar sauran unguwanin lagos din da cinkoson abin hawa sosai ga yare kala kala a wurin har nazo iyakan layin na zaga wani layun shima na kewayo da zan dawo na tsaya wani shago na auni filawa da sauran kayan hadi har roban da zan saka kayan a ciki duk na saya na juyo zuwa gidan mu ban wani sha wahala ba wurin gane gidan don na saka shedan da zan gane hakan. Na samu umma a cikin damuwan rashin sanin inda na nufa sai gani kwatsam da yan kayan dana sayo na shigo gidan . Suna tsatsaye dasu Ladi cirko cirko sukaga shigowana ladi din tace ai na fada yar nan tana da wayayyen kai ba zata bata a garin nan ba. Kinbi kin tayar da hankalin ki ga hakan, nikan gaidasu nayi ina kokarin shiga dakin mu da kayan naji ladi na fadin meta sayo ne take kokarin shiga daki dashi ? Kamar ban jita ba na shige abina dakin ina fadi may ur evil eyes back to u, uno de see dis tin today. Daddy ka bari zan ga yarinyar na bincke ta wasu abu kafin ka ganta wai duk yanayiwa mahaifin nasa hakane don ya kwantar da hankalin shi. Saidai mahaifin yaki don cewa yayi idan ba zaka kaini ba zan kira Haroon ya kaini tunda tare dashi kuka je gidan yasan wurin. Shike nan daddy sai mu tafi taren ya fada idan kaji sauki sai mu je lagos din a tare in hakan zai fi ma sauki zaifi Alh ya fada. Haka ya fita daga dakin cike da zargin mahaifin nasa don gaba daya abin ya kulle mai kai a yanzu ya kasa gane meye hadin shi da wayan nan mutanen da yake nemane wai har yake zatin yarinyar nan nada alaka dasu yanzu. Dakin mahaifiyar su ya nufa ya samu ta fito wanka tana gyara jukin ta ya shigo kallo daya tayi mai ta fahinci damuwa a tare dashi take fadin. Zaka sakawa zuciyar ka damuwa akan wa yan nan mutanen ni yanzu na bar sakawa kaina damuwa kan lamarin wayewar karima na shashanci. Mommy anty kuma ina ruwana da lamarun ta a yanzu tunda ba zamana takeyi a gidan nan ba shi daddy da yaji ya gani shi suke ba kunya ai. Ido uwar ta bishi dashi tana nazarin sa kafin tace ai dole muma mu damu da haukanta tunda ta sakamu gaba a gidan har ku. Don tsaban samun wuri karima zatace wai idan wani abu ya samu Alh kaine silar hakan don dakai kukai waya ya shiga wanan halin don haka kaine silar. Kai innalillahi haka ta fada yana kallon mahaifiyar nasu da wani irin kallo na mamaki kafin yace. Zato zunubi don koni bansan dalilin da yasa daddy din shiga wanan halin ba daya shiga yanzu. Har kuma da damuwa da har takaishi kwanciya asibiti kan wanan zancen da mukayi dashi kawai a waya din ban san hadin shi da wanan mutanen ba. Wasu mutane ke nan kake magana a kai wai hjy ta tambaya a cikin mamaki tana kallon dan nata da shima ita yake kallo. Wallahi hjy ban san ko suwaye ba su na dai san a lagos suke zaune daga kawai naba daddy din musalin su yace wai yana son ganin su. Matane ko maza hjy ta tambaye shi ya dago kai ya kalleta kafin yace da ita a sanyayye wata yarinyace da mahaifiyan ta da sukai bala,in kama da yan gidan malam na tudun wada. Wai malam mahaifin mu ko wa yace malam dai namadi naku hjy ya kara fada wani kallo tayi mai ta mike tsaye tana saka hijab din ta tare da fadin kana da photo sune a wurin ka. Ban dauki photonta ba tunda nidai nasan ba wani hadin da ake dasu kamane kawai na yanayi sukayi da yan gidan. Ikon Allah ashe har yanzu zancen iyalin Badaru na cikin zuciyar Alh don nasan su yake hasashen ko sune aka gani a can din. Wani ne hakana kanin mu mana daya bata har yau ba a samu labarun shi ba ita kuma matar da yarta an nemesu ko kasa ko sama ba asan inda ta shiga ba ga ciki koda ta bar gida har ya fara tsufa a jikinta don cikin zaikai wata hudu da dan kai a lokacin. Shiru yayi yana tunane kafin yace anya wa yan nan sune kuwa do naga uwar yarinyar kama wata yarece fa. Ina fa za,a gansu tunda tunda yanzu kusan shekara goma sha wani abu ke nan da batan su ya dauki zancen tsawon shekaru yasa a zuciyat shi. Shima dai Abubakar din yasa zancen a ransa yana faman tunane kala kala meyasa sai daddy ne zai damu haka bayan ga yan uwan su nan suna harkokin gaban su basu damu ba. Washe gari tun cikin dare na tashi na kwaba filawan yadda nake so don na iya kwabin washegari da safe ina idar da sallah na shiga soyan da wani murhun tsoho dana tsinto na gyara a bayan dakin mu. Take kamshi ya karade ko ina na gidan mutum zai gane ana suyan wani abin filawa a lokacin. Sai ga yan gidan dake fitowa suna wucewa wurin sana,oin su suna tambaya na sayarwane nake cewa eh. Sai gashi tun ban fita ba na sayar ga baki daya a wanan gidan har ma bai isa ba don ban samu aje muna ba don mu karya dashi. Daga wana ranan sai na samu sana,an yi idan nayi na safe ya kare saina kwaba na ran da zan fita dashi waje in sayar. Sai ya kasance ina suyan umma nabawa mutane masu saya ni kuma nakan mayar da hankalina akan suya . Sai gashi har wasu wure an gane shigo a saya, muka kwasa muka koma wajen gidan ga badaya don abinka da dan Adam. Sai gashi an fara nuna muna hasada ga sana,an tamu har mun samu wa yanda suka fara irin sa a unguwar duk da dama sunayi saidai ba a lokacin da muke namu ba din. Yau ina son zuwa cikin garine don da shirin haka na kwana a raina ba kuma komai zai kaini ba can don saro kaya da sauki don yanzu kan mun wuce sayan mudu mudu da muke saye a da. Sun shirya tafiyan kamaan yadda suka tsara bayan sati biyu a lokacin har Abubakar din yayi tafiya zuwa onicha ya dawo lokacin daddy ya murmure ga baki daya. Duk yadda hjy karima taso jin dalilin tafiyan su a tare ta kasa gane komai sai ta dauki hakan da wani abu zai kaisu can din tare. Tafiyan safe sukayi suka shigo cikin gari haroon ya dauko su daga airport din zuwa wani hotel inda zasu huta suci abinci. Bayan sun gama ne suka shiga mota sai tsohon gidan mu da muka tashi haroon dinne ya fada masu mu suka zo nema da cewa wanan shine mahaifina. Mamaki sukayi suke fada masu ai mun tashi daga unguwan yan makwanin da suka wuce mun koma wani wuri na daban suma bamu fada masu inda muka koma ba. Ran Alh ya baci sosai da jin hakan sai ya dauki laifin ya dora gaba daya kan Abubakar da yaki yarda ya kawo shi tun lokacin da yaso zuwa din. Basu gane komai ba legas kuma ba karamin gari bane da zasu saka cigiyan mu har a samemu a cikin sauki don haka suka bada lamban wayan haroon da yafi kusa idan an ganmu a kirashi akwai kyauta da zasu bayar. Haka Alh ya dawo gida ranshi a bace duk da bai tabatar da cewa mu din bane ko wasune a lokacin amma haka yaji rayuwan shi ya baci da rashin ganin wa yan nan mutanen. Kafin takwas na safe har na gama soyan bounce din na aje a cikin katon roba duk wanda yazo saya umma ke kidaya masa hamsin hamsin Na fito a cikin shiri na samesu tare da ladi a tsaye gurin da muke suyan waje umma i wan go naw na fada tace seb joni take care of ur self nace yes ma na juya na fita bayan na dan taba kan Amar dake mikawa wasu fanke. Mota a legas ba matsala bane don haka ina zuwa bus stop ji ana fadin my2 apapa ajagule agege ikeja da dai sauran wurare a cikin garin. Wanan hjy ta fado min a rai da muka taba haduwa a asibiti sai kawai na fada motan ikeja condaster din motan yace min dari biyar na zaro na mika mashi ba tare da damuwa ba. A inda suke saukewa na sauka na samu mai mashin nace ya kaini toyin road yace dari biyu ba haye tare da fada mai street din da zani. Ban manta lambam gidan data ban ba sai gamu a kofan gidan nabiya shi kudin shi na fara tafiya zuwa kofan gidan. Kwakwasa get din gidan nayi saubiyu kafin na mayar da hankali ina karewa unguwar kallo naji an bude get din gidan maigadine ya leko yana fadin. Who de nock nace nice who u de look nace hjy halima kafin kuma ince maman Bilal yace i de come ya koma ciki sai kuma ya sake lekowa yana fadin. Waitin be ur name nace tell her na Sahiba d girl she meet at hospital ya dab kalleni na dan lokaci ya juya ya shige ciki na gyara tsayuwana a wajen. Can naji an bude kofan sai na hangota tafe bayan maigadi tana tafe cikin takon kasaita irin na manyan matan hausawa. Fuskan ta dauke da murmushi tana fadin wai mafalki nake koko dai yau Sahiba kece a gidan namu yau kin tuno damu ke nannta fada a daidai lokavin data iso inda nake tsaye din ta riko min hannu tana fadin barka da hanya ya mamanki. Gaskiya nayi farinciki da zuwan ki don har na debe tsamani da ganin ku kuma a garin nan nayi dan murmushi muka karasa shiga cikin gidan. Falo muka fara samu ya tsaru iya tsaruwa da kayan alatun zamani nayi sallama tsohuwar gidan tana zaune tare da jikokin ta a falon saman dima diman kujerun daya zagaye falon. Ta amsa min sallamana fuskanta itama cike da murmushi fa tasbaha a hannun ta tana ja a dayan hannun ta nuna min wurin zama tana fadin. Ashe kun samu rabarin rasuwan mijin nawa ke nan kuma sai na kalli hjy da mamakin abinda tsihuwar ta fada naji hjyn tace ai bata sani ba mama ina zataji inba yanzu data zo ba. Ke yesmin kice a kawowa bakuwata abin sha ta fada tana kallon wata matashiya dake zaune a falon tana karatu gwanin ban sha,wa. Don dai taban sha,awa yadda naga ta zauna ta mayar da hankalinta ga karatu ba abinda ya dameta a rayuwan ta ita . Itama mikewa tayi bayan tayi min wani irin kallo na yatsuna ta shiga ciki bata dadeba ta dawo ta zauna tana fadin na fada mata anty. Ok hjy tace ta juyo gareni nace ina wanan dan naki da baida lafiya sai ta dan lumshe ido kafin ta jingina bayan ta da kujera tana fadin ai ya rasu sahiba. Bayan barin ku asibiti mun dan kara kwana a asibitin har an sallamo mu ranan cikin dare ciwon ya tashi kuma maka kwashe shi zuwa asibiti kafin mukai yace ga garin ku. Yeh na fada instead ince innalillahi nace u mean dat boy has pass away oh may his soul rest in piece tace amin aishi ya huta ya tafi ya barmu da duniyan nan mai wahalan zama. Lokacin mai aikin ta kawo lemon fivealibe da ruwa ta aje a gabana tana gaidani na amsa a cikin ladabi. Ta juya ta wuce a lokacin ne hjy ke fadin nasha don na kwaso ranan da zafi ga tafiya can kuma tace ai kuna Ajagule ne dazama ko ? Na dan kurba lemon kadan na aje ina fadin mun bar ajagule tun bayan barin mu asibiti da kwana biyu muka sake unguwa. Yanzu kuna inane ta tambaya tana kallona nave muna seme boada semi boda ta ambata a cikin mamaki tare da fadin yanzu daga can kika zo ke nan ? A cikin ladabi nace da ita eh daga can nake nazo sayen filawa ne da muke bounce dashi a cikin gari don a company yafi sauki sosai. Fuska ta bata tana fadin kai banji dadin jin hakan ba gaskiya har ina tunanen wata rana nakai maku ziyara ashe kun kara nisa damu din kuma yanzu. Akan me kuka tashi a nan inda kuke ajagule din nayi dan raurau da ido kadin nace nima bansan dalili ba saidai ina hashen ko umma taga kamar an fara gane muna nan ne zaune a unguwar oho. Gaskiya kin kyauta da kizo inda muke da ba haka ba ba zamu san inda kuke ba a yanzu. Na dan kara kurban juice din kafin in mike ina fadin zan koma kada dare yayi banje na saya ba a rufe wurin tun yanzun zaki tafi ta fada nace eh nagode. Daki bari agama abinci idan kinci sai ki tafi ai ke tafi da yunwa yaushe kika kasan layi zaizo kanki idan kin tafi. Na danyi murmushi ina fadin ban tare da yunwa hjy ko hakan ma nagode na kara fada ina kokarun fita daga falon . Tace dani tana zuwa mike zuwa cikin dakunan kwanan su tadan dade kafin ta kwala wa yarinyar nan data kirata da anty kira ta mike ta shiga dakin ta sameta. Sai gashi sun fito yarinyar na dauke da leda a bayanta ta nufoni cikin murmushi tana fadin na barki a tsaye ko Sahiba ga wanan sai ki kara ki sai filawa din. Wanan kuma kuyi amfani dashi dake da ummantaki daga yau dan Allah idan kin shigo ki dinga zuwa muna gaisawa don a sada zumucin. Dafe baki nayi a cikin mamaki abin alherin da tayi min ina fadin haba idan tana min haka ai ba zan sake zuwa gidan ba. Ko yanzu ma wallahi hankalina bai kwanta ga yadda muka bar yaron ta bane da jiki a lokacin shine naga dacewan shigowa in kara duba ahi ashema baya raye a duniya shi. Nayi godiya na karbi kayan ta rakani har bakin get din su mukai sallama ta dawo ciki ni kuma na tare wani mai mashin daya kawo wasu mutum biyu na fada mai inda zai kaini na haye. Na samu layi sai dai ba wani dadewa tunda a kwai kaya a kasa na saya lokacin biyar na yamma yayi kusa. Mota ya fara wahala don haka na dade a titi kafin in samu abin hawa a can other side din titin kamar ance ya dago kai ha hango wata kamar yarinyar nan da sukazo nema shida daddy . Da sausauri yayo turne zuwa in da nake tsaye saida irin nisan u turne din su na legas kafin yazo har na samu mai napwp munyi jinga zai kaini har semi din har na wuce na bar wurin. Tun yana iya bin mu har muka bacewa ganin sa ya daki sitiyarin motan yana jan tsuki don haushin da taji a lokacin. Kodana isa seme boda na iske hankalin umman mu a tashe suna waje da Amar duk da duhun daren dake akwai sunyi zugun suna jiran suga inda zan bulo sai ga my nape ya tsaya dani a kofan na fito. Dubu biyu ya cajeni banji haushin bashi hakan ba don dare yayi sosai a lokacin umma ta mike ta nufo ni tun nan ta hauni da fada kamar zata mareni a lokacin nayi shiru sai me nape din ne ke bata hakkuri yana fadin koshi ya tausaya min ne ya kawoni don ba mota dare yayi lokacin. ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , , DANA DARA GA, , , , , , , , , 1️⃣4️⃣ BY ZAINAB IDRIS MAKAWA YAURI , , , , , , BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIN AR-RAHAMAN, , , , , PAID ONLINE NOVEL NE YAR UWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA DON DARAJAN ANNABI DA KOYIN SA, , , , , Ganin irin kayan da driver ya jibge min a kofan dam gidan namu na ciro kudin shi na bashi yayi min godiya yana fadin daga yau na karbi lambam shi har in muna da sako a cikon gari sai mu baga ya sayo muna ya kawo mu bashi kudin shi tunda yaga mu mutanen kirkine shima bahaushe ne dan uwan mu mutumin jahar sakwato ne shi. Umma tayi mai godiya ta karbi dan katin shedan daya bata mai dauke da layin shi a ciki yaja keken shi ya wuce. Kayan na fara dauka naji umma tace dani Sahiba wanan uban kayan a ina kika samu kudin sayen shi don ba zan fara zargin ki akan wani hali da ban sanki dashi ba a baya har yan amin su amsa min. Wallahi umma duk abinda kikaga na sayo da kudina na sayo shi na sana,an nan sai kuma wanan hjy ta asibiti data ban kudi na hada na karo dashi don kayan ya dauke mu wani dan lokaci. Wani irin kallon mamaki tayi duk da duhun dake akwai saida na gane hakan muryan yan gidan ne da zasu shiga suke fadin ur daughter don come back ? Ta amsa a sanyaye tana fadin ehn she don come back naw thank u for d care suka shige abin su ni kuma na fara kokarin jan kayan zuwa cikin gidan don mai keken ya taimaka ya kai min buhu ukun ta dan cikin gidan kadan ya aje ya tafi. Haka nayi ta wahalan jan kayan zuwa cikin dakin mu har Allah ya taimakeni na kwashe su kaf nakai ciki na zauna ina haki. Muryan Amar ne ke fadin u no buy some tin for me sister i no eat anytin since i de wait for u to come back. Nasan da hakan don son junan da mukeyiwa juna guntun juice din da nasha gidan hjy tace in tafi dashi da naman data saka min a cikin ledan na ciro na bashi sai take away din da na hado muna idan na dawo muci duka na aje a gaban shi. Daga nisa Ladi data tun karo kofan tana fadin yar ta dawo ko umma data amsa mata daga ciki tana fadin gata nan ta dawo wai mota ne bata samu ba ashe sai yanzu. Ta karaso dakin ta hankade labule tana fadin sannu yar nan ya kasuwan da hanya ai dai an godewa Allah tunda kin dawo lafiya. Na amsa mata ina mikewa take fadin yar umma yau umman ki ta shiga wani hali na rashin jin inda kika shiga haka tun safe ? Daga ita har umma dariya sukayi umma ke fadin uhm ina da gaskiyana Ladi kada yar mutane ta bata a hannu na gashi ba mutunci ne ga yan uwan mahaifinta ba. Ladi tace lalai kan a raina nace komai rashin mutuncin su a haka nake son sanin su waye su na bude ledan dana dawo dashi na dauko mata take away daya na bata tare da dan sauran tsaraban dana sayo muna Ta karba tana washe baki tare da saka min albarka buta na dauka na nufi dan wurin da muka kewaye don wanka da zagayawa na yo tsarki nafito na fara alwala har saida nayi rabi ne naji suna wani zance daga dakin don haka na tsaya ina sauraren su Ina alwalan nake jin suna ci gaba da magana ladi na fadin amma dai kinsan yanzu ya kamata ace gida sunsan inda kika shiga da yaran nan don ko baki fada masu yanzu ba nan gaba dole su sani saboda yar nan taki. Don kinsan dai ta fara girma gata da zati kwana biyu zaki fara ganin maza suna sallama a kofan nan din ko yanzu sun fara yi min magana a kanta. Don haka gara ki san nayi tun lokaci bai kure maki ba abinda kike faman boyo a fassara maki shi a wani hanya na daban. Sauu nayi na kasa ci gaba da anbin da nakeyi don ina son inji amsan da umma zata bata a lokacin saidai umman a sanyayye tayi magana don haka banji me ta fada wa ladin ba a lokacin. Haka na shigo dakin jiki ba karfi suna ganina suka canza wani magana har na tayar da sallah nakai rabi ladi tayi mata saida safe ta fice a dakin. Bayan na idar ne na juyo ina gaida umma da wuni ta amsa min tare da fadin ke kinci abincin ne nace yanzu zanci ina son in baki sakon da hjy ta bayar a baki ne. Yanzu Sahiba gidan wannan matar kika je nace eh umma naje naji ya jikin danta don bamu samu komawa asibitin ba a lokacin. Sai na samu dan nata ya rasu ashe a take naji umma na salati a wurin tana fadin yanzu dan nan ya kare ashe Allah ya rahama masa yasa iyakar wahalan sa ke nan na amsa da amin a lokacin naji karfin gwiwan dauko ledan da ta ban na bude ina nunawa umma din kayane na jikin ta da na wanan budurwan dana gani a gidan suka hado muna sai kayan yaron nan daya rasu masu kyau nasan na Amar ne sai da suka ciko min ledan ghana most go baka da kayayyaki a cikin sa. Kayan umma ta shiga budewa tana dan haska dan tocin mu da baida haske sosai saidai haka muke amfani dashi wurin gani da dare koda asuba idan na tashin yin wani abu na sana,an mu rayuwa ke nan. Tun bayan komawan shi masaukin shi yake faman tunane a zuciyar shi wanan yarinyar kamar ba mutum ba duk inda zaka ganta sai tayi ma walkiya ta bata. Towai me ye hadin su da daddy ne ma dayake neman su haka ruwa a jallo ya juya ya gyara kwancinyan shi yana fadi a fili dole akwai wani abinda ban sani ba da su suka sanshi kuma suke boyewa a tsakanin su . Don ga sanin sa ai inma har yan uwane dasu yadda daddy yake zato sun fi kusa da hjyn su ke nan don hjy ce yar gidan ga baki daya bisa ga daddy din dashi su ukune kawai mahaifin su ya haifa kafin ya rasu. Kai abin dai ya daure mai kai a karshe ya yanke shima zai fara bincike alakan da wanan matar data bata da ya"yan ta wace daddy ke nema a yanzu ruwa a jallo. Wayan shine yayi kara daga gefen shi ya dauka hjy ce ya dauka murya a dakushe kamar mara lafiya yana fadin Allah ya bar min hjy ta . Ta lumshe ido tana jin dadin addu,an shi gareta tare da kiran sunan shi ya amsa ya fara gaida ita da wuni. Bayan ta amsa a cikin kawaici da alkunya irin nasu na fulani don a gaban mutane bata sake jiki tayi hira dashi don idon jama,a. Hjy tace mudibbo dama na kirakane akan zancen auren ka kamar yadda kace in duba in zabama wace ta dace dakai . To na zaba na kuma fadawa Alh zabin nawa yakuma yi na,am da zabin shima yaba da goyon baya ga hakan. Ya dakatar da mahaifiyar nasa da fasdin hjy ban fahinta ba don zancen ya daure min kai gaskiya. Uwar tace ai kasan halin family mu dama basu bari a fita a auro matar farko a waje sai a cikin gida don haka a cikin gidan na zaba ma yar wurin Alh Nuhu yayan mu dake zaune a nan kaduna ina dai kasanshi ai. Abubakar ya tsuke fuska kamar mahaifiyar nasa na kusa dashi yana fadin mommy na fada maku ni banson wanan auren hadin naku tun farko. Kuma ko zanyi irin sa hjy sai a rasa gidan da za a nema min mata sai wanan gidan da basu da tarbiya da hankali. Hjy Addah ta dakatar dashi tana fadin wanan ba hujja bane idan ma har bata da tarbiya idan ta shigo gidan ka sai ka koya mata mana. Mommy dan Allah ku bar wanan zancen ku bari ni zan zabo da kaina don ba tsarina bane yan gidan nan. Kai dakata hjy tace dashi don aikin gama yagama ko don Alh ya kira yaya din ya fada mai kuma ya amince da hakan . Don haka yanzu babu wani zancen da zaka bullo muna dashi mu yarda dakai indai ba kasa zaka watsa muna a idon jama,a ba kuma. Mommy ba zan taba hakan a gareku ba insha Allahu kawai dai kiyi tunane akai don yaran gidan nan sam basu dace dani ba. Don sam basu san girman mutane ba basu da tarbiya ko kadan gashi basu da addini na tabbatar ko auren yar gidan nan nayi ba zamuyi zaman lafiya dasu ba. Don abinda sukaga dama shi sukeyi a rayuwan su mommy kinga ashe ban isa in sata ko in hata ba ke nan wani riba ke nan zan samu a karshe ? Don yayan mu ba zasu samu kyakyawan tarbiyan daya dace uwa taba diyanta ba don ko ita bashi ke gareta ba. Mommy nifa ban damu da wayewa ko wani ilimi ba can nafi burin auren mai ladabi da biyayya da natsuwa tare da kamun kai. Jikin hjy ne yayi sanyi tana sauraren dan nata don tasan duk abinda ya fada game da yaran gaskiya ya fada ba karya ko kare kai acikin zancen shi din. Don yaran dan uwan nata sam basu da tarbiya ko kadan tunda tana zuwa gidan itama tana ganin irun rayuwan su da rashin girmama na gaba dasu. Don ko sunje gidan idan ya kama sai iyayyen nasu sun ce dasu halan bakuga wance ba zasu dan gaida mutum a tsaye kamar wani sa,an su can. Dama shi mahaifin nasu ne ya nuna yana son ayi wanan hadin a tsakanin su don itama sam bata da ra,ayin hakan a ranta itama. Ta numfasa har yana jiyo hakan a cikin wayan tana fadin yanzu kai dama wacece wace kake so kuma a ina take ? Duk da ya danji sanyi a zuciyar shi da alama zai iya shawo kan mahaifan nasa kada ayi wanan hadin da suke shirin masa a yanzu. Yanzu kan likafa taci gaba kamar yadda na fada maku mun samu abokan hamaiya a wurin sana,an mu sanin halin yarbawa umma tace na rike addua sosai a bakina kafun na fita. Haka din ne kuwa don dana tashi zan kwaba sai nayi addua idan kuma zan fitar da kayan sai na tsaya naja abinda umma ta koyar dani daga bakin ta na addua. Amma duk da hakan suna biye damu yauma din na tashi a makare don mafalkin da nayi gabanin asubahin. Sai mafalkin ya tsaya min a raina sosai haka na fita na fara share wurin kafin na fitar da kayan mu da dan tocina kamar ance na haska tsakiyan wurin da muke aje murhun da muke suya dashi. Sai na hasko tsakiyan daya nuna alaman an gina wurin anyi wani abu da sauri naja baya ina fadin back to sender may evils eyes rich his sender oba my deat bodi notin will happen to me insha Allah. Hakan ya jawo hankalin sauran abokan kasuwancina da suma sun fito a lokacin suna gyara wurin da zasuyi sana,an su din. What happen omo wata yar matashiyar dattijuwa da itama ta kama wanan sana,an na suyan fanken safen da mukeyi don ma,aikata da sauran masu samakon fita suna saye su tafi dashi don muna a saman hanyane sosai mu. Nace see di tin somebodi do for my place ta duba da sauri taja baya tana fadin eh wai holy ghost fire. Who send dis for u ? somebodi wan see ur down fall at dis place ta fada tana kara ja da baya insha Allahu d evil tin may go back to his sender, notin will happen to me , Wata ta karba da insha Allah ban san ya akayi ba har yan cikin gidan mu sukaji sai gasu sun fito Ladi na fadin. We will see notin insha Allah noti go rich our daughter we no put our eyes on person business, why somebodi will put his eyes on her ? Tazo dauke da wani sabon kwarya a hannun ta da wani ruwa a cikin sa tana ta zage zage tana yayyafa ruwan a wurin kafin ta dakata tana fada. Ranan dai sai da kyat na iya suya sai ummace ta ansa ta karasa min duk da ba lafiya hakan ke bata ba shiyasa ban yarda umma din tayi wani abu nike komai idan ina kusa dasu don yanayin jikin ta daba lafiya. Daki na koma na kwanta ranan banyi sana,an rana ba sai hakan ya tayar wa umma da hankali sosai. Addua ta fara min tana dafe da goshina cikin ikon Allah har na sami barci a lokacin . Ladi kan hankalinta ne ya daga saboda zama a cikin yarbawa duk tasaba da al,adun su nacan bale wa yan nan dake da akidun al,adun su kala daban daban na kauye zama dasu duk yasa ta iya wanan al,adan da akidun su. Ladi farace bakatsina da kalagun ta irin na katsinawa gata dai dattijuwace amma ko yaushe zaka samu tana busa karan sigari ko goro a bakin ta. Yarbanci ko abakin ta kamar zuban ruwa zakace a iko din aka haife ta kana ganin ta kaga tsohuwar yar dandi data sha bariki a zamanin kuruciyan ta. Saidai dadina da Ladi akwai ibada duk da wanan kallon da nakan mata in tsane ta wani lokacin sai wanan ya dan gusar min da abinda nakan ji na tsana game da ita. Ni dai na bude idanu naga umma zaune kusa dani har lokacin tana min addua ga kuma muryan Ladi daga waje yana tashi tana fadin . Turancisu na bariki any person who de try to inter my road i wil show dat person my juju pass am meke hi quick quick live my daughter to live in piece. Da kyar dai ranan na samu nasha tun wanan lokacin umma tace indai sana,a ce a nan na daina ke nan ayi da wani kuma suje suyi tayi. Ladi tace don su za aki neman kudi tun farko sakaci mukayi ai ba a barin irin yaran nan haka su fada gari kai tsaye ba a nema mata tsari ba. Tunda su shegen tambaye tambaye ke gare su da zaran sunga bako yazo cikin su yana samu sai sunyi tambaya a kanshi. Allah ya taimakemu yarki tana da wayau bata dora tunkunya a wurun ta fara suya ba ta farga da hakan wanda nasan karfin adduan kine a garesu Allah ya tsare da sai ta kwanta ciwon da sai Allah a yau din nan. Hankalin umma ya kara tashi ta kara miko min ruwan maganin da ladin ta kawo aka bani sai zufa nake karyowa a jikina. Wanan ne dalilin dana dakatar da duk wani sana,a a cikin semi boda ga baki daya don umma taki yarda in kara yin wani a garin kuma duk da na roke ta ko a cikin gida in dinga yi idan ladi ta yarda da hakan. Amma umma tace sam idan dai wani zaiyi ba bakin ciki ba kyashi amma nikan nagama wanan sana,an kuma. Ganin da umma tayi yau ciwo gobe lafiya yasa ta yanke shawara muje asibitin nan da Amar ya taba kwamciya . Don likitan yace muna da sauran kudi da zamu dinga zuwa ana dubamu a cikkn kudinganin da umma tayi taji sauki yasa ta tattara ta aje zancen asibitin a gefe daya. Gaba dayan mu muka shirya ranan wata alhamis da jikin nawa dai ya kiya muka tafi asibitin bayan likitan ya dubanine ya bamu magani har umma mun fito naji umma tace. Tunda akwai sauran lokaci in kaita gidan hjy na tayi mata gaisuwa tare da godiya ga alherin data aiko muna ranan danaje gidan. Mun sameta a gida tayi maraba da zuwan mu kallo daya tayi min ta fahinci banda lafiya take tambayan umma . Umma ta labarta mata komai daya faru dani tun lokacin nan dai ta tausaya min ta bamu wani maganin gargajiya in shaka nakafa atishawa a nan sai can ya tsaya sai barci. Ba yadda hjy batayi da umma ba kan mu kwana har washe gari mu tafi amma umma takiya haka muka fito bakin titi neman motan da zai kaimu semi boda bamu samu mota ba. Na who be dis iya sahiba na u aka fada a bayan iya bisi ne tana tallan kayan maganin agumo na yarbawa akai. Take fadin ah long time no see dat day one man come to our house e de look for u nd sayiba. He say e bi sayiba father d man look rich he even say he go give amount for person when bring ur torry. Where are liven naw ta tambaya kamar umma ta sani tace da ita we de obalade now we de sell food there. Zama nayi don ban iya tsayawa a lokacin na kurawa titi ido daga can gefen da suke tafiya ya hango mu wani irin burki yaja don shi ke jan motan. Saida na bayan shi yazo ya dakeshi abinda ya dauke mai hankali ke nan a wurin kafin ya juyo har mota tazo mun fada da gudu don kada mu rasa mun bar wurin. Matar da yaga muna magana da ita din ya sama yana tambayan ta ko ta sanmu take fadin eh sai kuma ta nuna shi tana fadin na u come to our house dat day looking for dem ? Yace eh nan dai ta fada mai kamar yadda umma ta fada mata ya ciro dubu goma ya bata ta wuce tana murna shi kuma ya koma masaukin shi saidai bai yadda ya kira daddy ya fada mai ba don so yake ya tabbatar da hakan kafin ya sanar da daddy din. Saboda ya kula akwai wani abinda bai sani ba a cikkn maganan don haka sai yayi bincike kafin ya taimakawa daddy nasa akan mu. Duk da sun kirashi da dare suna sanar mashi da irin haukan da Alh Nuhu yazo har gida yayi masu ya kuma ce ba za a fasa auren ba shi yayi kadan ya basu kunya a gari. Da wanan bakin cikin ya kwana har ya mantar dashi zancen yarinyar daya fara nazari akai dole washe gari ya shirya zuwa gida don ayi ta ta kare a lokacin. ZAINAB IDRIS MAKAWA .ANA DARA GA, , , , , , , , , , 1️⃣5️⃣ BY ZAINAB IDRIS MAKAWA YAURI, , , , , PAID ONLINE NOVEL KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA YAR UWA, , , , , , BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AR-RAHIM, , , , , , Mun isa gida hankalin umma a tashe ranan don na gane hakan ne ta yadda take amsawa mutanen dake cewa damu u are wellcome, ko u na don comeback ? Mun shiga gidan dayake muna farkon a gidan sauran na daga ciki don ni sau daya na taba shiga cikin gidan naga ashe gidane babba dake dauke da mutane kala kala kuma wai duk irin ginan bamboo tree daine ko a cikin gidan. Wasu zakaga nasu har AC akwai a ciki wasu ginan kuma katako da katako aka hada aka mayar dashi daki mai kyau a ciki. A haka muke zaune cikin sa saidai mu namu ya nuna tsohon yine don ya dade ya soma dan fadawa amma bai lalace ba. Nikan muna shiga wuri na samu na kwanta don wani iri nake jin jikina ba karfi yayin da umma tana aje gyalen ta ta dauki buta ta nufi ban daki a lokacin. Har ta idar da sallah ban ko iya motsawa ba a lokacin ina kwance inda nake kuma ba barci nake yi ba sai can na iya mikewa naje nayi alwala na dawo. Ina sallah Ladi ta shigo tana muna sannu da zuwa da alama daga unguwa take a lokacin don shigan danaga tayi ya nuna hakan. Bayan sun gaisa tayi min ya jikin an samu ganin likitan tace mun ganshi yace makariya ne ke damun ta ya bata magani har ni ya duba yace mu koma karshen wata dai akan nawa jikin a kara awo. To Allah ya sauwaka ladi ta fada har ta juya take fadin wai gajiyane hakan yasaki laushi naga yanayin ki ya dan canza kuma ? Ke dai uwar dakina bari kawai abine da daure kai wallahi wai neman mu akazo yi a wanan can gidan da muka taso. Ke ki bari don Allah Ladi ta fada tana dawowa cikin dakin namu umma tace bari ke dai yadda jaga iya Bisi na rawan jiki da ganin nasan akwai wata a kasa. Don har cewa tayi wai meshi babban mutum ne yace kuma shine mahaifin yaran nan shiyasa data tambayeni inda muke Allah ya rufa min asiri ban fada mata gaskiyan inda muke yanzu ba da zama. Na dago daga inda nake kwance dunkule tun bayan idar da sallah na na dan kalli umma din don jin abinda ta fada. Ladi tace anya ba wani ne ke bibiyan rayuwan ku ba dama, umma tace nima abinda ya daure min kai ke nan yanzu. In har hakane kuwa ya zama dole un bar kasan nan mu kara gaba wajajen shagamu ko zuwa kamaro ko ghana mu samu wuri a can mu zauna. Umma na fada cikin mamaki don ban san lokacin dana saka baki a zancen su ba akan mahaifin mu yazo neman mu zamu kara gaba ko me ? Ni gaskiya na gaji hakana umma na gaji inma kashe mu zaiyi ya kashe mu matukar dai zanga mahaifina a duniyan nan. Ke ar ke me kika sani Ladi ta fada a hasale an fada maki neman arziki suke maku a yanzu dole neman rayuwan ku suke maku su halaka ku ai. Halakawa kuma da mukai masi me zasu halaka mu kuma ni dai koma meye su halaka mu din ma mu huta zaifi. Duka umma tayi niyar kaimun daga inda nake kwance Ladi ta tare tana fadin kada kiga laifinta yarinyace ita bata san komai ba don haka kyale ta ai jiki magayi. Har suka karaci fadan su suka kare ladi tabar dakin ban kara dago kaina na kalli inda suke ba nan ta bar umma da tunanen a zuciyar ta nawaye mai neman ta kuma ita da diyan ta. Shin wa yanda ta bari arewa ne suka biyo ta ko kuma nan ne kuma ta samu wasu masu bibiyan lamarin su kuma ? Ya isa kaduna a cikin tashin hankali misalin magariba don haka kai tsaye dakin shi ya nufa ya bude ya shiga. Wanka yayi ya dauro alwala ya fito zuwa masalaci a nan ya hadu da mahaifin shi suka gaisa yasan yazo garin suka shiga sallah a tare. Sai bayan isha,i suka shigo gidan tare lokacin ne kuma kowa yasan da zuwan shi garin ranan suka shiga taron shi a cikin murna banda hjy karima da gaisuwan kazo lafiya kawai ya hadasu ta wuce. Abinci aka gabatar masu ya dace da hjy mahaifiyar sune da girki tayi masa irin abuncin da yake so tuwon alkama da miyan danyan kubewa da kassan rago yaji daddawa da kayan yaji ya sake don anaci a cikin taro yaci sosai. Hjy Addah kallo daya tayi wa dan nata tausayin shi ya sauka mata sosai a cikin zuciya don yanayin sa kawai da ta kalla tasan yana cikin damuwa. Har suka bar wurin tana satan kallon yadda dan nata ke ciki hakan sai ya saukar mata da damu kan abinda ke damun shi din balle zuwan da sadiqa tayi gidan da sunan wai tazo ta gaidasu kuma su santa a gidan ya kara saka hankalin hjy tashi. Iyayyen su na barin wurin Nabila da gulma yace ta matso kusa da yayan nata tana fadin ai yaya baka zo tun jiya bane da yau kasha kallon mamaki a gidan nan sosai. Dame ya faru ya tambaya cikin son ya san ko meye saidai har lokacin idon shi na awayan shi yana karanta sakon da aka turo mai wanda ya dauke mashi hankali. Wai ashe wanan Samiran zaka aura yar gidan kawu Nuhu din nan yau ai tazo gidan nan gaida su daddy, wai amma dai tasha mai gaskiya a jikin ta kamar a gidan su aka bude kamfanin bleching fa. Au baki sani ba a gidan nasu kamfanin yake ko bata kawo maki tsaraban irin sa bane da tazo ? Ta saki yar dariya tana fadin kai yaya bafa kushe mata nake yi a hakan ba daga fadin gaskiya naga ka hasala dani mana yanzu ? Daga fadin gaskiya Allah bana son na ana shafa wanan mai din ne yace ai amsa na baki zaki tambayeni nasan ko wacece kike zance akanta asalima yanzu naji zancen a bakin ki ai. Tana dariya ta sake fadin kai kaji yaya abin ya koma yar boyone yanzu kuma ai zamu ganta har mu gaji sai dai gaskiya akwai aiki kan gare ta yadda nasan halinka da tsanani din nan. Dama ai nasani mai shegen zuban nan sai ta tare ka da zancen nan tunjiya take mita a kai hjy ta fada daga bayan su tana karasowa a inda suka barsu zaune har lokacin. Kai ya dago a lokacin yana duban hjy din har ta karaso inda suke zaune ta zauna Nabila tace Allah mommy abin ne ya ban mamaki sosai yadda tazo muna da fitsara a gida bako kunya wai ita tazo nuna kanta gareku. Sai akace kuma ki fada mai hakan ko don shegen surutu irin naki hjy ta fada tana hararan yar nata tayi dariya tana mikewa tare sa fadin mommy abinda nagani fa na fada . Kallo Abubakar hjy tayi tana fadin malam ka koshine ko s zubama ferfesu ka kara dashi dan murmushi ya kakaro a fuskan shi tare da fadin . Mommy ins zankai abincin nan danaci yanzu haka ma yana damuna don shine yasa na kasa tashi a nan tun dazun. Wani abinci kaci bayan wanan dan cakulan da kukayi daga kai har Alh bakuci komai ba ta fada tana kallon shi dole in dan zauna ya fada min kafin naje na kwanta ai . Sai da safe mayi zancen da wanan fadi ba a tambayeka din data fara ma don yarinyar dazun an turo ta gidan nan da safe ta gaiyar damu. Suhaila tace mommy ki bar cewa ta gaida ku tazo dai tayi maku fitsara a gidan nan dai ita da yan uwanta. Kai kukan yaran nan akwai iya sa ido da shishigi da gulman tsiya ina ga sai dai na maku tsiya akan zancen nan. Mommy ai abinda suka ganine suka fada da bata zo tayi ba ai hakan ba zai damesu ba son basu saba ganin irin fitsaran su ba a gaban manya. Wallahi yaya zama fa tayi sosai suna hira da daddy da mommy a falon nan har tana tambaya wai yaushe zaka zo . Murmushi yayi na mugunta tare da fadin oh ni take son gani ma ke nan ya fada yana girgiza kai da sauri hjy tace kaga kada ka biyewa yaran nan kaje ka aikata abinda bashi. Mu zumunci muke son gyara mu hada a tsakanin don zumunta yayi karfi ba abinda zai sake wargaza kanun ba a hakan ta fada cikin dan bacin rai. Mikewa yayi yana dan buga cikin shi alaman ya koshi da yawa don ya kawar da zancen don ganin ran mahaifiyar nasu ya fara baci da zancen. Har ya shiga dakin sai mamaki da al,ajabin abinda sisters din shi ke fada mai yakeyi saidai abinda ya kula hjy tana son zancen ko don abinda ta fada a gaban shi yanzu a falonsu. Da wanan tunanen barci ya dauke shi sai washe garine days zo gaida daddy ya fito mashi da zancen dif ya dauke kamar ruwa yaci shi a lokacin. Don irin albarkan da daddy din ya dinga saka mai kan amincewa da zabin da mahaifiyar shi tayi mai kuma yabi irin al,adansu na iyayye da kakani da aka shimfidasu akanshi duk zurian su kuma suke bin hakan har yanzu . Saidai duk bayanin da mahaufin ke masa hankalin shi baya jikin sai lokavin da daddy ke fasin mun yanke shawara karshen wanan watan da zamu shiga za,ai komai har daura aure tunda duka bangarorin bamu da wani shirin daya saura akan hakan matace kawai dama kake jira ka tare a gidan ka ita kuma iyayyen sunce a shirye suke ko wani lokaci dama. Kaga shike ka zama cikakken mutum a yanzu don duk wanda yakai ga aje iyali girma ya haushi ke nan a rayuwa zakaga ko mutane suna mutuntaka fiye da lokacin da baka da aure. Don haka kafin ka koma inda ka fito sai kaje kaga yarinyar da idon kaga irin zaben da mahaifiyar ka tayi ma don suma suna son gani jiya har nan gidan take tazo gaida mu ita yarinyar da yan uwanta nima kuma bazan so har ka koma waje a yanzu ba tare da aure akanka ba kuma. Ya dago idanun shi da suka canza launi yana fadin zan shiga kafin na tadi daddy insha Allahu ya fada a gajarce. A gundure da jin zancen mahaifinasa ya samu ya mike tsaye yana fadin zaije ya karya don tashin ke nan daga barci yazo nan gaidashi. Bin bayan dan nasa yayi da kallo don ya fahinci akwai damuwa a tare da Abubakar din dole akwai wani abinda ke damun dan nasa. Ya dade a dakin hjy yana nuna mata rashin son wanan hadin da suke son mashi amma ta nuna mashi ai bakin alkalami ya bushe a yanzu don ba zai hadata fada da yan uwan shi . Mikewa yayi yafice daga dakin kai tsaye motan shi ya shiga ba tare da yasan inda zai nufa a lokacin. Daga wanan fitan sai mota aka dawo dashi gida shi ya wuce hakan ya kara sa daddy zargin akwai wani abu ke nan da dan nasa ke nufi. Wai sabo turken wawa nikan ai ban saba zama wuri daya ba gashi ina ganin dan abinda ke garemu umma ke zara munaci muna sha a cikin sa wanda nasan zara bai barin dami. Sai faman shawaran mafita nakeyi a raina na kasa cin ma mafitan abinda zamuyi don wanan ungywar kan kamar garine komai kake idon wasu ba akan ka tundai ace neman na kanka yanzune sun gama dakai kamar yadda naji ladi tana fadi da bakin ta. Hakan yasa gaba daya garun ma nikan ya fice min a raina ga baki daya yanzu zama dai nake a cikin sa ga ba karatu garemu dagani har kanina muna neman kwashe wata uku zaune a gida muna zaman banza. Duk da karatu ni ba damuwa na bane illa neman abinda zamu rufawa kanmu a garin shine kullun tunane. Zaki ce fa ko ni din wata babbace mai shekaru a yadda nake wanan bakan wahalan sha hudun dai nake ina harin sha biyar ga shekaru a lokacin . Hakanan kuma nake buga buga a cikin wahala don umman mu bata da lafiya da za tayi wanan wahalan a yanzu. Safiyane na gama muna abin karyawa na kaiwa umma na aje ba wani abu bane taliyane dai muka dan sulala da safen don ciki ya dauki nauyi ba komai a cikin sa sai manja da dan attah dana jajaga na dafa sai kamahin attah ke tashi a ciki kawai ba wani nama ko kifin ice fish da yai banza a can. Na dafa ya fita raina sai dan cakula nake ina kaiwa baki suko sai kwasan abin su sukeyi hankali kwance suna ci. Saida na daidaici umma ta kusan gama ci nace umma dama ina son muyi magana zaman nan ya isheni haka kudin mu ya kusa karewa a yanzu gashi bamu komai da kudi zai shigo muna a yanzu. Cire hannu umma tayi cikin abincin tana kallona tare da sauraren abinda nake fadi din sai da nakai karshe tace akwai Allah sahiba shi zai duba muna Insha Allahu. Nasan kina kokari sahiba baki gajiya da kula damu ga komai nima kuma ina wanan tunanen da kikeyi a yanzu. Sai dai na barwa Allah zabi akan hakan yanzu ke wani shawara kike ganin zamu bi don dai gaskiya ban yarda da sana,a acikin semi ba kuma. Zan dinga shiga cikin iko ina neman abinda zamu ci nayi maki alkawari duk inda na taka zan tsare mutuncina kamar yadda kike min addua a kullun. Sam ba zan yarda da wanan ba ki shiga cikin iko ke kadai ki yawats iko ba karamin gari bane sanan kiji ance akwai masu neman a can cikin iko din wanda bamu san suwaye ba kuma akan me suke neman mu din. Nasan ds haka umma kuma ba zan taba yarda in koma ajagule ba zan canza unguwane wanan karon . A lokacin naga umma tayi dan ajiyan zuciya tana fadin yanzu na danji sanyi zan iya yarda da hakan. Ta ina zaki fara da garin nace zan koma ikoyi na duba ko zan samu abinyi a can din daga gobe zan fara shiga insha Allah zan shiga da dubu biyar na duba nagani ko zan samu abin juyawa a wanan side din. Nayi murna jin umma bata hanani wanan shawaran dana kawo mata ba sai albarkan data saka min a karshe wanda naji dadin hakan har kasan zuciyata. Washe gari tun safe na fara shirin shiga gari in zaga inga abinda zan kama a cikin garin. Nayiwa umma sallama na dauki hanyar sai ikoyi kamar yadda nayi alkawarin anan zan fara gwadawa. Tafiya nake ina bin layi layi a cikin kasuwan ina kallon ko ina tare da nazari har naje na tsaya gaban wani shago sayar da kayan miya ciki na shiga na samu mai shagon akan ya ban sari. Ya gaya min dokokin sari a wurin nace na yarda ina dauka na nufi cikin unguwar gadan gadan na fara ihun buy fresh vegetables fresh tomotors . Sai gashi Allah yaban sa,a lokacin dama mutumin yaban in dawo dashi bai ko yi ba na sayar da wanda na dauka duka har ana nema. Ban koma ta kanshi ba na dauki pure water na zagaya inda motoci suke cinkoso sai gashi na sayar kwara biyu suka rage min na zauna a wani innuwa nasha daya na wanke kafa da hannaye da dayan na koma kasuwan nayiwa su umma sayayyan da zankai masu gida nakuma yiwa mai shagon dana dauki kayan miya don ba karamin riba na samu ta hanyan daukan kayan da nayi ba a wurin shi. Don jin dadi har diban min yayi nakai gida nayi godiya na wuce zuwa semi boda shidda na isa gida a cikin farin cikina su umma suka tareni suna tambayana ya kasuwa ina washe baki nake fada masu irin sa,an dana samu a ranan. Na fitar da abinda nasayo daki na shiga na sako dan guntun wandon da nakan saka idan zanyu aiki na dauko doyan dana sayo muna na zauna na fara ferewa kafin na tashi na hada suta ranan dai munyi girki da kanmu munci abinda bamu faye yi ba sai lokaci lokaci. Na kwaso na kawo daki kamshin ice fish yana tashi da danyen Attarudu irin dai miyan yarbawa din nan dan shi na iya shi kuma muka saba dashi. Haka nake fita a kullun kuma ina samo sa,an da umma ke kira min idan zan fita zuwa wurin sana,a na din. Sana,a sun kai kala goma da nakayi hakan zan wuni a wahalace wurin neman kudi inayi ina share zufa dake tarso min idan na dawo kuma nayi girki muci . Wani lokaci zan samu Amar ya danyi min jajage don yanzu bamu rasa kayan miya a dakin mu don haka yakan diba ya dan gyara min ya kuma hura wuta ya rage min aiki ke nan kafin in dawo din. Ga zancen makaranta dake raina ko wani lokaci nakanyi wanan tunanen koda ni banje ba Amar shi ya samu ya tafi ni din a yanzu ba dole bane karatun a gareni Bukin ya taso gadan gadan kamar yadda daddy ya fada don tako wani bangare sai faman shiri sukeyi don lamarin bukin . Wanda tun bayan wucewan Abubakar sau daya yazo gida koshi sai da daddy yayi masa fadan hakan bayan hjy ta fadawa daddy din dalilin fushin shi dasu da yakeyi. Cikin fushi daddy ya mike yana fadin wanan wace irin maganace bayan mun tsayar da zance yazo zai kawo wani magana daga baya. Dama kin san baku shirya hakan da dan naki ba kika bari har nakai ga zuwa na tsayar da magana gaban manya. Hjy a cikin lumana ta kalli mijin nata tana fadin menene na tayar da hankali haka Alh ina dai dani da modibbo duk a karkashin ka muke. Auren nan kuma haka akaiwa kowa shi ko yana so ko baka so aka kuma hakkura aka zauna mutum nawa a cikin family din nan suka nuna basa so daga baya kuma bayan anyi aure a zauna lafiya. Alh ya dago kai ya kalleta kafun ya zauna dakyau yadda yake zaune ada yana sauke ajiyan zuciya yana fadin shike nan ai na dauka kema zaki mara masa ne ku mayar dani mutumin banza a idon mutane. Tace ni na isa in hakan tunda nasan wanan abin ba fashi tunda yaki nemowa da kanshi a wuce wurin . Ya gyada kai cikin zafin zuciya har lokacin yace ki fada mai ya tabbatar da yazo garin nan kafin satin daurin auren yaji bukatan da suke dashi a bangaren yan matan dashi da abokan shi. ZAINAB IDRIS MAKAWA ANA DARA GA , , , , , , , , , , , , 1️⃣6️⃣ BY ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , , , BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AL- MALIK, , , , , , PAID ONLINE NOVEL YAR UWA KADA KI KARANTA IDAN BAKI BIYA BA DON GIRMAN ALLAH, , , , , , , Yar uwa ina bukatan adduan ku da bakunan ku masu albarka Allah ya yaye min duk abinda ke damuna dani daku duka baki dataya don Allah kice amin yar uwa Allah ya amsa muna tare dake. Ko kafin ya isa har anyu jere a sabin gida sa daya gina kuma daddy ya taimaka mai da wasu abubuwa. Wanda hakan ya kara jawo mai bakin jini a wurin hjy karima tun tana fadan hakan a lokacin a zuciyar ta dakuma aminta har dai yakai ta fito fili ta tukari Alh da zancen tana fadin moddibo fa bashi kadai bane akwai yan uwanshi suma suna da hakki a cikin dukiyan shi. Murmushi ya dan yi yana zaune kamar badashi take magana ba sai da yaji tayi shiru ya dago kai da hasals yana fadin kin gama abinda ya kawo ki ? Tace aini ba fada nazo yi ba gaskiya na fada don bashi kadai bane akwai wasu yace oh niki dabaran ke nan ke to ina wasu din suke ki nuna min su a yanzu ? Ta dago itama a cikin mamaki tana kallon shi don jin abinda ya fada yana huci yace nace ki fada min ina wasun suke a yanzu din don ni shina fara gani a yanzu. Itama a cikin fushi ta fara fadin wa yan nan matan daka raina don suma mutane ne ai kuma dasu nake alfahari. Amma kuma dake dasu dani gaba dayan ku kuke tunkaho a garin nan ko sai tayi shiru karima kina da matsala wallahi. Moddibo da kike gani wata rana ko ina raye ko ban raye shine gatan ku daga ke har diyan naki da a yanzu kikewa wanan fadan. Kuma kada ki manta ba rashi ko wani abu yasa nakewa yaron nan haka saudan shima yana da hakki hakan a kaina kamar yadda kikewa diyan ki fada a yanzu. Kin ban mamaki karima halaiyan ki na banza a yanzu suke kara fita fili ko can ace wani yana cin albarkancin wani da badon darajan mahaifin ki ba dana nuna maki ko wa nake nima kingani. Ai dama haka fadan gaskiya yake saukin abin dai yadda kowa ya iya shige da fice nima zan iya hakan ta juya ta fita tabar dakin cikin kunya ya bita da kallo. Zuciyan Alh kan cike yake da zafin wanan maganan da matar tasa ta sameshi dashi wai yana kashe zarahi akan mutum daya kamar shi kadai ya haifa. A karshe mikewa yayi yana kai kawo a dakin shi daya har hjy ta shigo ta sameshi hakan kallo tsoro tayi mai don ta fahinci akwai wani abu mai zafi dake damun mijin nata a lokacin. A haka hjy ta sameshi a dakin binshi ta fara yi da kallo don ta fanci akwai abinda ya faru da maigidan nasu na bacin rai a lokacin. Alh lafiya dai ta fada tana kallon inda mijin nata yake tsaye ya dan juyo ya kalleta tare da kawar da kai ba tare data iya furta komai a gareta ba. Ido ta kura mai na dan lokaci kafin ta nisa tana fadin Allah ya sauwa har lokacin bai iya bude bakin shi ya bata amsan abinda take so ba. Lokacin da hjy tashigo dakin shi bayan kwana biyu da hakan da turamen zani a hannun ta guda biyar tana fadin ga abin arziki Alh ta zube turamen a gaban shi saman table din dake gaban shi a falon shi din tace. Gashi hjy karima ta bada a zuba a cikin akwatin modibbo da za akai gobe Alh ya dago kai a hankali ya dan kalli hjy ya girgiza kai tare da bin kayan da kallo yace ita karima din tabada wa yan nan kayan ? Tace yanzu ina daki Ladi ta shigo min dasu sai kawai ya sake murmushi a fuskan shi yana girgiza kai yace angode ai. Tun wanan lokacin hjy Addah ta fahinci akwai wani abu daya faru mijin nasu yace hakan kan kayan don ta dauka hakan zaisa yai farinciki a fili. Sai taga sabanin hakan gareshi shiru hjy ta danyi na dan lokaci kafin ta mike tana daukan kayan data zube din a gaban shi. Haka ta fita gwiwa a sanyaye ta kasa furta komai saidai zuciyata yana cike tab da zargi kan haka. Bukin ya taso din hjy karima din ita ta jagoranci komai da akayi a ranan ta boye komai dake cikin zuciyan ta an tafi da ita a cikin sha,anin akan shawaran da kawayenta suka bata na ta daure a tafi hakanan da ita kada ta bari a gane akwai wani abu a kasan zuciyar ta. Ganin har za,a fara sha,anin buki Abubakar bai shigo ba baiyi waya da kowa ba kuma sai hankalin iyayyen shi ya tashi sosai. Daddy ya soma neman layin Abubakar din wayan ba ringing ba a daga va sai hakan ya kara tayar da hankalin daddy din sosai. Ya kara kira karo na biyu akaci sa,a ya dauka daman ya kewayane a lokacin. A cikin girmamawa ya fara gaida daddy din da daddy ina wuni, ya amsa da lafiya kalau shin ba zaka samu zuwa bane har za a fara buki. A dan maraice yadda yaji muryan daddy din a cikin fushi yace dashi aimun hakkuri daddy ina tafe akwai abinda ya tsayar danine a nan ne daddy zan shigo kwanan nan insha Allahu Daddy yace dashi a hasale zancen aure kafa akeyi nan da kwana biyu mai zuwa in Allah ya kaimu don haka idan kaga dama ka shigo idaman ba zaka shigo ba ruwan ka. Yace daddy ayi min hakkuri ina sane zan shigo insha Allahu kada ma ka shigo aure daine ba fashi a cikin zuwa jibin ya kashe wayan Abubakar din ya tsorata da fushin mahaifin nasa don baya fushi irin haka dasu har ya kashe mai waya idan suna sai gashi yau din ya kashe. Don haka ya yanke shawaran kiran abokan shi a lokacin ya fara sanar dasu halin da yake ciki don mutum daya ya kira yace afadawa sauran don shi ba tarun abokai yake dasu ba. Sai daren da aka fara sha,anin buki ne yazo da abokan shi da basufi uku ba suka diro garin a cikin dare a lokacin har hankalin hjy Addah ya fara tashi tana gudun dan ya aikata wani abin da zai bar masu abin fade ga mutane. WwYayin da hjy karima aakuma duk take sane da komai dake wakana wanda take ganin duk alhakintane dana diyanta Allah zai fitar masu a nan. Gida har ya fara cika da wasu yan uwan su da sukazo daga wasu auraren na daban a bagaren daddy ma shine tare da yan uwan shi dasuka tsure shi da korafi wai yaki hadin da suka so ayi a tsakanin yayan hjy Altine da Abubakar din. Ya biyewa hjy Addah ta hada da diyar dan uwanta taki nasu din yanzu ga yarinya ta shiga wani hali don ta kwallafa rai ga hadin su da Abubakar din a rayuwan ta. Daddy din yana zaune yana jin su kafin yayi murmushi ya kalli kannen nasa mata yana fadin kai kudai mata kuna da matsala. Yau kuma har muna da bambanci ashe a tsakanin mu da gidan babfa namadi ashe a wurin ku ? Yau ashe har kuna da bakin da zaku fadi hakan kuda bakin ku har kun manta da irin halalarci wanan tsohon a gare ku har zaku fadi hakan don kasa ya rufewa tsofin mu ido. Kallon juna sukayi kafin hajiya Asiya tace mu ba hakan muke nufi ba yaya kawai dai don ganin yadda in anyi da ita hamida zumuncin zai kara karfi a tsakanin mu ne kuma yanzu. Can din bazai kara ba ke nan ya fada cikin daure fuska kafin ya gyara zama yana dan dagowa saman kujeran tare da fadin. Ina sin ku saurareni da kyau kuji kada ku manta ba haka tsufin mu suka koyar damu ba kan zumunci. Har ma udan laifi shi Nuhu yayi aiba yar shi bane tayi laifin don kuma yar kuce yar Nuhu idan kun dauki hakan. Yaya yanzu dai ai zancen ya kare dama mun fada mane kasan abinda Addah tayi muna bata kyauta ba tunda tasan akwai soyayya a tsakanin yaran nan tun farko amma ta nuna muna sin kai ga hakan. To kuji nan wanan zancen shirmen ina son duk a barshi a nan kada inii wanan zancen ya fito idan da Allah ya nufi hamida ce matar modibbo. Babu fashi ita dince zata kasance matar ba wanan din ba don haka na kashe wanan zancen tun a wurin nan ya fada yana komawa saman kujeran. Dole ba fuska a wurin su suka bar falon yayan nasu rai bace don a yadda suka shirya sun so suba hjy Addah mamaki a wanan karon. Haka dai akai sha,anin bukin hjy Addah na tsaka mai wuya ita bata tsira ba a gurin yan uwanta dake ganin laifin ta kanta daurewa modibbo gidi yake kokarin kunyata su. A bangaren mijin ta kuma sun hade mata kai gaba dayan su taga canji a wurun su kan sha,anin bukin . Duk kan da namiji daya tilo da Allah ya bata ake mata wanan abun da take gani yanzu gun dangin nata. Anyi buki an watse lafiya kowani bangare sun nuna ba komai saidai na ciki na ciki a zuciyar kowan su a lokacin. Alhamdullahi taro ya watse lafiya an kai amarya dakin ta uwarta tanuna yar yar dangi ce ita don uwar tayi mata goma shatara bayan wanda mahaifinta yayi mata kuma. Kasancewan itace ya ta farko a wurin ta yasa ta nuna nata bajintan a dakin yar kowa nata sa albarka masu zagi kuma suna bi da zagi da gulma. Agege lagos yau can abin ya daukeni yakai na sari doya ina bin layi shiga biyu nayi sa,a kamar na kifar ganin rana yayi sanyi yasa na dauki kati da kudina ina bin masu motan dashi don nasan zan sayar ko da zuwa gobene idan na kara fitowa. Motace na hango lafiyayya a gabana sai walkiya takeyi na nufi wurin motan da sauri ina fadin buy credit buy rechage card . Aka zuge glass din motan a hankali maishi bai min magana ba sai ga wani dan mashin a baya yace rechage card na sheka da sauri nakai mai card din ya karbi mtn na dari biyar yace give me five hundred change na bashi sai yake kuma kokarin wucewa da card din da kudin duka nace. Olay give me my money nd my card u de call me thief becouse of ur money ? no be thief u are ? U own my card nd my money u wan run with ur nape sai fada ya barke a tsakanin mu dashi a wurin. Kaya kaya ya sauko ni kuma na fara gyara kayana da kyau ina shirin fada dashi murya mukaji a bayan mu ana fadin waitin de happen ? Na juyo da sauri ina fadin na my money he wan run with bayeraben ya kara fadin oga i go nak dis yeye girl if she call me thief again. No be thief u be na sake fada nima a hasale oya give her d money dan sandan dake da kayan kaki a jikin shi ya fada.. Mutumin ya kara kallona a shasale sai gashi ya miko min dari biyar biyar da sanda na bashi da kuma eani daga cikin aljihun shi yana nace olesi omo buruku, buruku dadani. Ina tura kudin a cikin katon aljihun rigana mai zip na fada cikin dan hasala akai horn daga cikon motan nan na farko duk muka juya muna kallon motan. Naji dan sandan nan yace bring card for my oga na juya da sauri zuwa wurin mitan farko data tsaya kwadayin ciniki ya kaini ga mai keken kuma. Na isa wurin motan ba tare dana tsaya na kalli na ciki ba na fara fadin mtn zain etisalat, an glo five hundred two hundred own de. Jin anyi shiru daga cikin motan yasa na dago kai a dan hasale don dama kaina yana kasa ina gyara katin dake rataye a wuyana. Don haka ban kalli na ciki motan a lokacin saida na gaba na dago ina fadin oga talk naw me i wan go ina dago kai sai mukai arba dashi na dan so in razana don na kadu da ganin shi saboda na sheda fuskan a yanzu . Sai dai gani biyu ne yasa ja she da hakan na farko zuwa kama mai laifi a gidan hayan mu sai na biyun da yazo karban wayan shi da ya fadi a hannuna. Shine dalilin gane fuskan shi a yanzu da nayi har na sheda shi a wanan ganin da nayi mashi a yanzu. A cikin dan rudewa nace oga u na good evening woo how much own u wan na dan fada a sanyaye yana zaune ido kawai ya kura min daga inda yake sin. Sai na dan tsargu da hakan ga kuma irin kallon da yake minnna mamaki nikan ina ganin hakan sai na juya zan bar wurin da sauri. Naji ance wait cak naja na tsaya a wuri daya ban kuma motsa ba ban juyo ba sai bayan yan dakiku naji murya na fadin come back my oga wan see u. Na sheda muryan mai magana a lokacin dan samdam nan ne na tare dassu wanda ya rabani da mai Nape fada. Na nuna kaina ina fadin emi ina tambaya ya kada min kai a hankali na fara dan takowa a hankali ina nufar su. Nace oga na di card mtn eirtel glo which one u want na fada ina dago kai na dan kallesu . Yace yana nunani da yatsa yace you where is your mother na dan kalli bayana da mamaki koda wani yake yi badani ba, a bayana . Sai naga dai dani din yake magana nace she de for house ya sake fadin where ? Nace In surelere side, yace from there you come here nace yes cikin gyada mai kai ya kura min ido na dan wani lokaci. Kafin yace oya inter d car now take me to your mother place i want to see her wani irin mamakine ya baiyana a fuskana lokaci guda. Nace a cikin rudewa da tashin hankali lokaci guda i de come let me pack my tins na fada cikin juyawa da sauri yana magana ai ban tsaya ba da sauri na shige cikin mutane kafin ai haka na shige wani kwarkwada na gudu . Har ya tura dansandan yabini sai kuma ya sa ya dawo ya barni don yaga alaman ba zai sameni ba koda ya bini yadda wurin keda cun koson mutane da yawa haka. Kai tsaye wani titin na bula na dauki shatan mai Nape sai gida duk da kayana da kudin wani dana dauki kayan shi ban sayar ba a lokacin. Sai gani na iso gidan da wuri har umma na mamakin hakan gareni sai dai naki yarda in fadawa kowa wanan zancen nabarwa zuciyana hakan. Sai dai na yanke shawara a raina cewa zan canza wuri ne nisa dasu yanzu sosai don ni sai nake ganin kamar kamamu har umma yake son yi kan wani laifin da bansam dashi ba a lokacin. ZAINAB IDRIS MAKAWA ANA DARA GA, , , , , , , , , , , 1️⃣7️⃣ BY ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , , BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AL QUDDUS, , , , , , , PAID ONLINE NOVEL YAR UWA KI BIYA KI KARANTA ACIKIN SALAMA DON ALLAH KI TUNA DA HAKAN NAUYI NE A KANKI BABBA, , , , , Addu,an ku nake nema ubangiji Allah ya yaye muna matsalolin mu Allahuma amin, , , Wanan yar ko aljanace dai ya tambayi kanshi yana zaune bakin gado cike da mamaki isowan shi ke nan daga garin don kiran gagawa da akaimai cewa ana tuhumar shigowan wasu kaya da yan fasa kwauri zasuyi da shi a cikin daren ranan yasa ya baro kaduna ya shigo lagos din a ranan. Duk da daddy yayi matukar fada da rashin zaman shi ta huta tare da amaryan shi da kwana biyu ke nan ras da kai mashi ita a gidan shi. Zai tsiro da wani zance na ana neman shi a cikin gagawa har daddy na fadan cewa aikin bai taso ba sai alokacin da kake hutun amarcin naka modibbo suna wanan zancen ne kwatsam aka sake kiran shi a gaban daddy din nauyin bayanin da daddy yaji sunayi ne ya barshi ya garzayo lagos din. Daidai shigowan su ne sukai kicibis da Sahiba wace yake mamakin ganin ta a wanan unguwan kuma har ta iya masu wayau ta bace masu lokaci daya haka. Lalai wanan yar tana da abin al,ajabu a tare da ita ya ba kanshi amsa yana mikewa tare da alwashin koma wa take sai ya gano ko ita din wacece dai. Kayan jikin shi ya fara cirewa a hankalin yayin da wayan shi ya dauki kara lokaci guda wurin sa yake tsaye ya baro zuwa bakin gado inda ya bar wayan nasa da sauri. Don a zaton shi ai yan uwan aikin nasa ne suke neman shi a wanan lokacin sai yaga bakon nomba ya dauka. Ya kara a kunen shi ba tare da yin sallama ba yaji muryan mace a cikin muryan kuka tana fadin ka tafi ka barni ni kadai a gida a daidai lokacin da nafi bukatan ka fiye da kowa a duniyan nan. Dan tunane ya tsaya yi kafin ya gano yarinyar nan ne amaryan shi ta kirashi sai mamakin inda ta samu layin shi na boye ya kamata don shi yasan ba kowane keda wanan layin nasa ba a kasan nan. Yana sauraren ta duk ta gama iya shegen ta lokaci guda tana wani shagwaba da maganganun da bai saba jin su a bakin mata yan uwan shi ba sai wanan lokaci. Abinka da wanda baida lokavin soyayya a tare dashi sai cewa yayi ki bari ai zan dawo ya kashe wayan nasa yana tsuki tare da fadin. Kawai an hadashi da wani nauyi a yanzu kuma yana fama da kanshi haka za a dauko laluran wata a dora mashi kuma cikin rayuwan shi. Don shi abinda ke gaban shi kawai yanzu shine aikin daya shigo dashi kasan nan na yan fasa kwarin kayan da kasa da hukuma basu yarda ana safaran su ba a ko wani kasa. Ina ganin na bace ma ganin su na dafe kirji ina furta thank god dey no cachi me waitin i do again dis solder wan cachi me again ? Ban yarda na koma gida ba duk da tsoron da naji sai da na samu na sayar da katina na nufi gida tare da yan tsarabun dana sayo muna na amfani dama kaddara ya kaini wanan unguwan kuma Allah ya kareni garesu na kara fada. Na shigo gidan wuraren takwas saura don yanzu yakai umma bata faye tayar da hankalin ta ba a kaina ban fada mata komai daya faru ba a lokacin. Saidai a ranan nayi saurin kwanciya barci don kada umma ta fahinci halin damuwa da tunanen da nake ciki a lokacin. Washe gari na falka tun asuba nayi sallah roban da nake diban ruwa na dauka na nifi famfo duk saida na cika kayan mu na debi ruwan na fara shirin barin gida. Zuciyana yana cike da fargaba don in akwai abinda dan lagos ke tsoro sune soja ko dan sanda ko malam bahaushe. Don su sojawa nan takene sun wullakanta mutum lokaci guda shi kuma dan sanda yanzu ne zai ja maka kashin kudi bahaushen mutum kuma dan takifene shi bai damu da duk abinda ya samu ya kare ba a wurin fitina. Da sauri na watsa ruwa kamar yadda na saba yin wankana idan na shiga na fito dan mai na shafa sama sama kafin na jawo wani bakin dogon riga na roba dake tsaya min iya gwiwana nasaka na jawo takalma mai belt nasa hula na figo daga gefena na kakabe na rufawa kaina shi. Kan da ya dade bai samu gyara ba sai dai na daba masa hula in fita kawai kitson duk a dankare don tsufa. Dan jakkar baco dina na figa yayin da nake gyarawa kwagirina wurin zama a jikina da kyau na kalli umma dake zaune ta kura min ido duk abinda nake idon ta yana a kaina nace zan tafi umma. O Allah Sahiba Allah ubangiji ya tsare ya kare muna ke kije lafiya ki dawo lafiya a cikin amincin ubangiji. Allah ya duba muna wanan wahalan rayuwa da muke ciki ya kawo muna dauki a rayuwan mu nace amin umman a sayayye idona kamar zai fitar da hawaye na juya na kalli kanina dake barci abinshi hankali kwance nace a gaida min shi idan ya tashi nasa kai na fice daga gidan ina tunanen inda zan dosa a ranan. Agege nan ya fado min a rai duk da ban faye son wanan wurin ba a rayuwana don haka nake shawaran zuwa Alaba ko agege din har nakai wurin bus stop ban yake shawara a raina ba a lokacin. Tun ban karaso ba nake jin ana ihun agege din bus ya cika don kada in batawa kaina lokaci kawai na fada bus din agege din da sauri na mika kudin bus muka kama hanya. Tun dana sauka bus nake bin ko ina da kallo ina nazarin abinda zan danyi a wanan yanki in samu kudin da nazo nema din. Wata mai shago na nufa dake sayar da kayan sanyi na tambayeta idan zata ban sari in dauka matar da alama tana da fada don yadda na samu tana jidali da wani wanda ya rigaji zuwa tana kafa mai dukoki tsarinta na daukan kayan ta. Amma haka na daure nace ta ban sari na bata kudin ta na dauki minerals din na hada da gyada soyayya na kama yawon tallata a kai. Buy miniras buy dry g\nut nake fada ina bi layi layi a saman hanyan naji ance miniras da sauri na juyo zuwa inda aka kirani din su ukune zaune cikin mota baka da alokacin ban san sunan taba. Dan nisa na tsaya dasu don duk yawon tallana idan ba akan go slow bane bana yarda in kai bakin mota mai maganan yace cock na juyo da sauri ina kokarin dauko goran cock din na kuma daga nace how many ? Bring two and one sprite na aje da sauri na dauko na dan nufesu ina mikawa aka miko min dubu daya nace i don't have change. U want me to go and find change for u nace na naw i start selling it oga i don't have one thousand naira change. Dan mai karamin jikin ne a cikon su muke magana dashi sai na tsakiyan da kanshi ke duke yana aiki cikin computer ya dago kai yace dashi ya amsa don Allah su wuce. Har ya duka sai kuma ya kara dago kai da sauri ya dan kalleni sai ya mayar da kanshi yana gyara hulan kanshi facecap daya dan rufo mai fuska. Ban damu da hakan ba sai cewa nayi make give u dry g\nut with d change oga it sweet i swer ina dan daga hannu banji abinda wanan din yace mai ba naji yace oya bring d nut we are in hurry ya fada yana kokarin tayar da motan kama suna a uzurce da sauri na juya na kirgo gyadan a leda na kawo masu ina fadin thank u oga my god bless, . Kai d nut is too much for us woo ya fada shi mai jan motan nace aina canjin kune duka na zuba maku yace dan dauki kullin da baikai biyar ba ya miko min sauran har na daga naga ana miko min kudi daga bayan motan na dago ina kallon mai shi dayan yace take naw, . Na mika hannu na rawa na karba suna tayar da motan yace gret ur mama nd ur broda for me na kara kallon shi da kyau ina tunanen ina na san shi nasan fuskan shi kafin na kuma mayar da idona kan kudin masu yawa dake hannuna. A daidai lokacin dana tuno shi har sun tayar da motan su ko a lokacin sun harba kamar walkiya sun bar wurin na busu da kallo ina tunanen idan nasan lalai shine shine naba kaina amsa a tsaye da kudi a hannu na masu yawa da ban san adadin su ba. Da sauri na cusa kudin a cikin kwagiri na na tura ina dan waige waigen mutanen dake wucewa a wurin bai fi minti biyar ba sai ga wata mota da sojoji da yawa sun tsaya. Suna bin mutanen wurin suna tambayan su game dasu nikan ina ganin haka nayi saurin bin wani hanya saidai duk yan sandane sun kewaye a wurin ga baki daya ashe. Duk yadda ka iya dabara sun hana kowa motsi a wurin suna nuna photo mota suna tambaya ina tsaye sororo da kayan ruwana a kai ina kallon ikon Allah har suka gaji suka fada motocin su ta gabana motocin ke tafiya ina binsu da kallo don mun saba ganin tashin hankalin dayafi hakan ma fitina a garin. A hankali shima ya dago ya bini da kallo saidai wanan karon da zance a bakin shi don hannun daya daga min irin na warning kada ki bari mu hadu din nan duk da sauran mutanen wurin da muke tsaye duk sun dauka dasu yakeyi a lokacin yana bada warning ne a kansu hakan. Muna tsaye har suka gama wucewa kowa ya shiga harkokin shi kai tsaye kafin ace haka nikan na canza wuri ga baki daya nabar shiyan zuwa wani gun na sayar a cikin lokaci don haka ban tsaya a agegen ba kuma sai kawai naji ranan inje gidan hajiya halima in kai mata ziyara. Na mayar da kayan dana dauka haya na yi mata sallama tana fadun bazan kara bane nace da idan zan tafi gobe zan dawo. Na samu hjy a gida tayi murnan zuwana mun gaisa a cikin dadin rai ta tambayeni ummana da Amar nace duk suna lafiya. Abinci tasa aka kawo min naci saida na koshi nace zan wuce take fadin tun yanzu nace eh da akwai kuma ida zan tafine yasa zan wuce din. Tace in jirata tazo ina zaune ne nake jiyo muryan maza suna shigowa gidan ban damu in san kosu waye ba har suka shigo suna dan hiran su na gaida su a cikin turanci suka amsa min tare da zama a falon duk sai naji na takura da hakan. Gashi ban taba matsawa daga falon ba ban ma san kan gidan ba ga baki daya don haka na zauna a takure suna magana akan zancen kayan da suke tuhuma din an shigo dashi. A lokacin kuma hjy ta fito daga ciki dauke da leda a hannun ta ja tayi ta tsaya wuri daya tana fadin wa nake gani nan kamar ango a zaune ? Ya dan dago kai tare da kallon ta yana murmushi ya fara gaida ita mijin ta na fadin wanan angon ai an kwareshi don baiyi hutun angwancin nasa ba a dole ya dawo bakin aiki ba shiri. Sin dan dade suna magana yayin dana shiga zurfin tunane don ina tsuntan wani abu a cikin zancen nasu da sukeyi da hausa. Naji hjy ta ambaci suna tana fadin sorry Sahiba mun barki a zaune ko gashi kina sonki tafi nayi murmushi ina mikewa tsaye. Take fadin gashi ki gaida maman ki zanzo wata rana idan Allah ya yarda ya kawar da kai da sauri kuma ya juyo inda nake tsaye din. Ya mike da sauri yana nunani a cikin mamaki tare da waro ido wajr yace you a razane nima na dan ja kusa da hjy na tsaye cikin tsoro suka bimu da kallon mamaki dagani har shi. Sai da hjy ta miko min leda take fadin kasantane a cikin hausa komawa yayi ya zauna shima tare da dan basarwa ai kafin suyi haka koda hjy zata juyo bana wirin har na fice da sauri ba tare da mun tsaya munyi sallama da ita ba a lokacin. Cikin mamaki ta kara kallon shi tana fadin kasan wanan yarinyar ne sai kuma ta juya wurin mijin ta haroon tana fadin itace muke baka labarin su da muka zauna asibiti tare. Abubakar yace itace daddy ya zo nema kwanaki garin nan duk su suka hada baki wurin fadin itace suna tambaya yace itace sai dai gaskiya a yanzu na fara tsorata da yarinyar nan gaskiya ko dazun fa a agege na ganta tana talla anya ma mutunce kuwa wanan din. Hjy tace mutum ce don nasan har mahaifiyar ta da kanwarta mun zauna a asibiti daya dasu ga kwanakin bayan kanin ta baida lafiya. Da sauri suka bi bayana saidai ko mai kama dani basu gani ba a wajen sun rasa hanyar dana bi na tafi sai mijin nata ne ke tambayanta kisan gidan da suke zaune ne ? Tace nasan dai inda tayi min kwantace a baya don yanzu sun ajagule sun koma semi boda a can suke zaune yanzu ta bashi amsa. Da sauri ya kawar da zancen da fadin yanzun dai sunyi nasaran shigo da kayan kasan nan ta haramtaciyar hanya illa iyaka abinda zamuyi shine musan su waye wa yan nan masu kayan kuma wani jaha aka kai kayan a yanzu. Sun dade suna tataunawa da haroon din kafin suyi sallama ya mike don zuwa gida zuciyar shi cike da tunane kala kala. Nima haka na isa same ina son fadawa umma komai ina tsoro fadan da za ayimin din a lokacin don nasan yadda umma ke fada idan ranta ya baci dani. Don haka na faki idon umma din na fice zuwa waje can na samu wuri na fitar da kudin na kidaya sai da gabana ya fadi ganin dubu dari cur din su ya ban ashe da kuma dubu dayan dake saman kudin da suka sayi abu wurina da dayan ya bani. Jikina har yana ciri na mayar da kudin a cikin gwagirina danayi dan mara dashi ko ina nake bana rabuwa da shi a jikina dama don tsaro. Ai kuwa ina shiga umma ke fadin ina nafito nake cewa na manta ban sayo muna maganin sauro ba da muma magani insha na shige kawai abina na kwata cike da tunanen mafita garemu. Tabbasa shine wanda ya taimaka muna da asibiti kan matsalan Amar da yanzu yaro ya samu lafiya haka kuma umman nawa itama tayi lafiya sosai do manyan maganin data samu tana amfani dashi yanzu. Wurin ya cika sosai da masu tashen arziki yan kasuwa da masu smogling din shigo da kayan nan Nigeria. Sune zallah a wurin suka taru don nasaran da suka samu kayan su ya shigo lafiya ba kamar yadda suka zata zasu samu matsala ga hakan ba. Tun daga wajen wurin zaka gane hakan don irin manyan motocin da suka cika a haraban wurin taron nasu da sukeyi a ranan. Don duk wani dan kasuwa daya amsa sunan shi shi a nan suke hadu suna taron su idan hakan ya taso. Gidane babba na gani na fada da kayan more rayuwa a cikin sa suka hada a wurin kana gani kasan kudi yasha kashi a wurin hada ginan nan. Ga security nan ta ko ina tun daga bakin layin a banza har mazauna unguwar sun da haka don idan zasuyi taron su kowa na wanan unguwar yana natsa kanshi ne. Don yawan security din dake zama wurin saboda tsaro da kariya ga ubangidajen nasu don wata rana fada kan barke a tsakanin su yasu yasun su har ajiji ciwo ko rasa rai duk da a yanzu sun shawo matsalan hakan a tsakanin su tun bayan shigowan yaro karami a cikin su yanzu wanda yake kamar jagora a garesu. Bayan wa yan nan katai din yan ko ta kwana din ga wasu tsalalan yan mata a wurun suna kai da koma suna raba abinsha dana ci da aka tana dan hakan. A yau din duk wanda ka kalli fuskan shi a cikin su a sake fuskan shi yake wurin duk dako zaman jiran mutum dayan da suke wanda ya jawo masu wanan nasaran da suka samu din a yanzu don kayan da suka shigo lafiya. Sannu a hankali suka koma jan tsuki a tsakanin su don bata lokacin da sukeyi a nan din har yakai dai sun soma maganan kan zaman banzan da sukeyi din a wurin duk akwai komai na more rayuwa a wurin har mata. Sai can suka fara hango mutanen shi na hannun daman shi dakan shigo suyi dan kuskus kafin ya shigo surin ke nan lokacin hankalin su ya fara kwanci da zaman nasu. Kamar yadda kowa ya shigo ta kofan gaba shi sabanin hakan don ta kofan dake baya na dakin taron ya shigo masu duk suka maida kallo su gareshi. Don Allah yaba yaron zati da kira na halitta duk inda irin su suka shiga ansan da suna wurin ga kuma kwazo da Allah ya bashi na neman kudi duk da gwaunati na ganin sana,an nasu haramtaciya ce ga kasa shigo da kaya a bayan idon jami,an tsoro ba kasa. Ga wani dan saje daya aje a fuskan shi wanda ya kara fitar mai da zatin shi a fili yayi masa kyau ainun a hankali yake takowa tako irin na kasaita da isa da izza da gani shi kasan abinda ya taka a hakan. Taken shi suka fara mai na young billoniear yana dan daga hannu a hankali yana jinjina masu a hankali zuwa wurin da yasan shine wurin zaman shi din. Bai zauna ba din sai da yaje gaban wasu tsofi biyu da suka girme masa yakai runsune kasa yadda ake gaida manya a cikin al,adan hausawa ya gaida tsofin kana yabi sauran da hannu yana mika masu suka gaisa. Kafin ya dawo wurin zaman nasa ya zauna bakin shi na cike da adduan don yasan komai sai bawa ya danganta da Allah yake samun galaba dama kuma ko can abinda ya dakatar dashi ke nan bai fito da wuri ba. Haka kuma yasan cewa lamarin nasu saida hakan don duk wanda ke daki toron nan yasan abinda ya taka kafin ya shigo wurin. Tun mikawa wani dan maiduguri hannu wani lokaci yaji kanshi yayi mai nauyi wasa wasa har abin yaso ya kayar da kasa sai gyaran Allah aka samu baikai kasa din ba shi wancan din ya kwanta a lokacin. Bayan shugaba mai suna shugaba yayi adduan bude tarone suka shiga tatauna abinda ya kawosu wirin a lokacin. Daya bayan daya suke tashi kowa kuma a cikin su yana da inkiyan sunan da ake kiran shi dashi a cikin su wanda kowa yasan da take nasa. Alh baba shine uban gungiya shiya fara magana sai Alh Rabi maliya mai bi masa sai shi Aliyu yayyayafi don yawan alherin sa ga mutane su suka laka mai sunan ko su kirashi da dollers boy. Shine na uku a cikin kungiyan tasu a yanzu dama duk wani kwaran shike karban su ya fiddasu a hanya har a cin ma nasara. Yaro ne da kudi abokin manya don shekarun sa baifi sha takwas zuwa sha tara ba a lokacin amma ya kerewa sa,anninsa dama wayanda suka girme masa ga shiga kasuwanci a yanzu wurin harkan kasuwancin su. Aliyu ga kyau ga kudi ga ilimi duk Allah ya hada mai uwa uba ga kyau ga kwarjini sai dai kallo daya zaka dauka shi din miskiline na gaske don yana da wuyan sabo da mutane. Sai dai idan ka ganeshi baida girman kai mutane ke masa wanan fasaran do rashin ganewa saidai sam Allah bai sako mai tsoro ba ko fargaba don irun mutanen nan ne da idan sun tasa abu a gaba sai sun sameshi. Yadda yake da kafiya da naci yasa yayi fice a cikin abokan harkan nasu dan shi Allah ya bashi tausayi da jin kan nakasa dashi sosai ga taimako idan yaga mabukaci har sukai ido biyu da maishi. Kudi kan zamuce gadon su yayi a wurin mahaifin shi da yanzu tsufa da ciwo ya riskeshi saidai sun raba hanya da mahaifin nasa don shi smogal ya zaba a yanzu don yaga yafi ci a wanan zamani Don haka ya fada harkan motoci da kaya masu muhinmanci da gwaunati ta hana a shigo dasu a cikin kasa saidai saukin abin shi baya yarda yayi abinda zai zubar da kimar mahaifin shi ko kadan. A wani vangaren kuma yana harkan zinare duk ta barauniyar hanya abinda ya kara bunkasa karfi shi da kudin shi ke nan a yanzu. Wanan yasa shi saurin fice a cikin abokan harkan nasa a yanzu sunan shi ya daga ko wanan haduwan akan wani sabon ma,aikacin da aka turo yabi didigin su a nan gida Nigeria. Alh baba yaci gaba da bayani shi kamar haka bayan yayi sallama yace kowa nan yasan abinda ya taramu a wanan wurin a yanzu. Wanan matsalan babban abune da zai iya kawo muna cikas a yanzu cikin harkan nan namu don a wanan karon idan badon dollers boy ba da yanzu kayan mu na wanan shekaran sun zama tarihi a rayuwan mu wanda hakan zai iya kawo koma bayan da yawan mu a wurin nan. Kai suka shiga gyadawa tare da yan kuskus a tsakanin su kowa na fadin albarkacin bakin sa kan irin fargaban da suke ciki a da kan kayan su din. Alh baba yaci gaba da jawabin shi yana fadin mun san cewa akwai aiki ja a gaban mu yanzu kan irin matakan tsoron da aka daukan muna ga wanan harkan. Na turo wakile daga cikin mu su gana da shugabanin wanan jami,an tsaron abin ya kiya don shugaban su wani karamin yarone ke jagorantan su. Don kwata kwata yaki yarda da tayin da mukai masa na goro asalima sai kokarin bincken da yakeyi a kanmu yanzu haka. Don yayi ikirarin duk wanda ya fada a hannun sako kayan sa ba zaiji dadi a wurin sa ba kun san yaro a yanzu shike da kafi da naci akan aikin shi don haka wanan yaron ya zama dole mu san abinyi dashi don musan yadda zamu zauna dashi don harkokin mu su tafi daidai yadda suka saba. Kowa yayi shiru a wurin yana nazari a cikin zuciyar shi na hanyar da zasu bullo ma wanan matsalan da yanzu ya kunno masu kai. ZAINAB IDRIS MAKAWA ANA DARA GA, , , , , , , , , , , 1️⃣8️⃣ BY ZAINAB IDRIS MAKAWA BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AS SALAM, , , , , , ONLINE PAID NOVEL DON DARAJAN ALLAH KI BIYA KI KAUCEWA SHIGA HAKKON WANI YAR UWA, , , , , Abu sun mai yawa lokaci guda na rashin nasaran kama wanda suke nema da rashin sanin koshi waye har yanzu don sunayen da maishi ke amfani dashi na bugi. Sai kuma case din yarinyar nan daya dauka yasa a ransa zaiyi bincike da kyau yasan meye tsakanin su da mahaifin shi don shi hat ya fara zargin ko dai yaran diyan daddy sune a yadda yaga damuwa a tare da daddy din. Hakan bai mai ba yayi saurin kawar da wanan tunanen a zuciyar shi da sauri ya koma wani tunane semi boda ya kira a fili inda hjy halima tace muna zaune yanzu. Kafi kuma yaja tsoki yace wanan wani rayuwane ku kaka gudu kuna canza wuri kamar marasa gaskiya dasu aiko fulani yanzu basu yawan canza wuri haka barkatai kamar ku. Dole yasan hanyar daya bullo wa yarinyar nan ya gano komai nasu kafin daddy ya sake juyowa zancen nasu koma meye idan ba mai yuyuwa bane ya yi maganin abin kafin a farga. Chuku ya fado mai a rai don shine kadai zai iya bibiyan lamarin ya gano gaskiya kamar yadda a yanzu ya gano masu dollers boy dake ta faman yi masu yawo da hankali saidai har yanzu din basu gane taka maimain ko waye shi ba sosai. Amma har kasan zuciyar shi ya fara zargin wani a tare da boy din yanzu wanda kuma yake fatan kada abin ya kasance hakan gaskiyane nan gaba. Waya ya daga ya kira chuku tare da mai bayanin komai yace ya gane yarinyar sosai kuwa kuma zaiyi aikin nan da gobe in jesus name yafada. Ya tura mai kudin zirga zirgan da zaiyi wanan aikin yayi ta faman yi masa godiya yana jin dadi har cikin zuciyar shi da wanan kudin daya turo masa haka masu yawa don wanan dan karamin aikin daya sashi kan mace. Ya mike daga wurin da yake zaune din zuwa gado don tunda yayi sallah yake zaune yana azzakar har ya fada tunanen duniya kuma. Bai dade da kwanciya ba wayan shi ya fara ringing ya ya mika hannun shi ya dauki wayan dan tsuki yaja don ganin mai kiran nasa a lokacin don ba wani bace sai Nazira amaryan shi daya bari gida kullun tana masa korafin ya tafi ya barta a gida ita kadai. Dauka yayi da sallama saidai muryan da yajine sabanin nata din ya bashi mamaki har ya dan daga hannu yana kallon lokaci tare da mamakin me ya kawo uncle Nuhu gidan a wanan lokacin takwas saura na safe. Wani gaisuwa ya shiga yi kafin Uncle din ya katse shi da fadin kai ba gaisuwan ka nake so bani dalilin tafiya kabar min ya zaune a gidan ka ita kadai nake son ji ? Idan ma aiki kake takama da ka tafi yi meya hana ka dauki matarka ku tafi tare don ka rainawa mutane wayau ne kome da bakatafi da ita ba can ku zauna tare. Shiru yayi yana sauraren mahaifin matar nasa kawu a gare shi har lokacin da yaji ya tsaya da magana yace kawu ayi hakkuri tun farko abinda na guda ke nan don kowa yasan yadda aikina yake. Dakatar dashi Alh Nuhu yayi a fusace yana fadin kai idan ka rainawa iyayyen ka wayo niba zaka raina min don na gane komai da kakeyi a yanzu da sanin su kake iskancin nan. Dan murmushi yayi kafin ya ja nunfashi yana fadin ayi hakkuri na kusa kamala abinda ya kawo ni nan zan dawo a cikin satin nan insha Allah. Ka saurareni Alh Nuhu yace na baka yau zuwa gobe duk abinda kayi ka dawo gida idan ba haka ba zamu saka wando kafa daya dakai a garin nan don naga nema kake ka mayar dani mutumin bamza a garin nan yanzu. Idan na gama zan dawo ya fada Abubakar din yana kashe wayan bai jira cewan kawun nasa ba ko yaji abinda zai kara fada gaba ya kashe wayan kai tsaye gaba daya ta dauke a cikin kunan rai yayi cilla ta gefen shi yana huci. Nagane mutumin nan sai nayi da gaske idan ba haka ba raina min wayau zaiyi a garin nan ya fada a cikin hasala ran shi yana baci sosai da halin son kai da Alh Nuhu ya nuna mai yanzu din. Daga nan ya wuce kai tsaye ya shiga bath room wanka yake yana faman jan tsuki shi kadai a ban dakin har ya fito ya fara shiryawa. Yau tun tashina nake jin raina na baci gaba na kuma yana dan faduwa lokaci lokaci wanda ban saba da irin wanan yanayin ba a baya sai ranan nake jin hakan. Ko umma ta fahinci halin da nake ciki na rashin walwala a tare dani don ta tambayeni lafiya nake kuwa nace lafiya ta kalau kawai dai yau bana jin dadin rayuwanane kawai haka na tashi. Koma meye Allah zai kare min ke don nima a yan kwanakin nan ina yawan yin mafalkin da baida kyau a gareni addu,a nakeyi da neman tsari a kan hakan . Dan murmushin yake nayi ina fadin balle ba wanda ya sani don ba wuri daya nake zama ba a garin nan ko ina ina shiga ina yawatawa gobe kuma na canza unguwa. Amma sai naki fada mata komai wani tunane nayi akan kudin nan ranan dai na bata kuma nasha fada sosai kan yadda na bari har muka kara haduwa dashi duk da alherin da yaiwa umma amma tayi min fadan hakan ni dai ban damu ba tunda na rabu da kudin a jikina. Kwana biyu ke nan bayan bata kudin nake jin yawan faduwan gaba a tare dani yau da zan fita amma don karfin hali haka na daure na shirya na bar gidan. Nayi duk wani shirin da zanyi don fita na zo gaban umma na rusunna ina fadin zan tafi a cikin harshen yarbawa tayi min adduan tsari na kalli amar dake kallona na nace me zan sawo ma yau idan zan dawo yace min nama dariya nayi nasa kai na fita ina tunane don mun kwana biyu gaskiya rabon mu da nama a gidan. Saidai muga mutane nacin nama muna kallo don umma ta saba muna da hakan zamu iya zama da dadi da wuya duk wanda ya samu a rayuwa zamu iya kasancewa a hakan. Kuma hakan yana da kyau sosai don uwa ta nunawa yaro jin dadi da halin wadata a kullun abune mai muni da iyayyen yanzu basu gane ba ka koyawa dan ka ba kullun ne ake zama a vikin daula ba koda kuwa akwai wadatan ga mutum ya daure ya koyawa dan shi zaman duniya a yanzu. Haka nabar gida ina tafiya kamar wace wani abu e damuna a lokacin har nazo bus stop na shiga motan Obalande duk da nasan yan wanan yakin yarbawane zallah a cikin sa sai yan yaruruka kalin dake zama a cikin su duk da hakan kuma ba jittuwa a tsakanin su amma haka na hau mota a ranan sai obalade din. Tunda na sauka nake bin ko ina da kallo tunda ba unguwar na sani sosai ba aharawa daya na fara yankewa shine in bi layin mabarata don yanayin da nake ciki ranan ba zan iya tallaba. Har na zauna na hango wani tsoho mai sayar da maganin gargajiya zaune na nufi wirin shi na dan dade tsaye ina nazarin shi kafin in ce ya ban ko kadan sari. Kallona yayi yana mamaki yace zaki iya nace eh zan koma wani side in zauna ba a wurin da yake zan tsaya ba a cikin gurbatacen hausa na nake magana haka dashi. Na dubu biyu na sara don ban yarda na sara da yawa ba tunda gwadawa zanyi ina murna har na daga yake fadin in tsaya ya bani wani siri da zanci kasuwa dashi na tsaya. Yace in miko hannu na mika mai yake fadin don su yarda da ke kinga wanan layin na tafin hannun ki guda uku nace eh . Yace don a gaskanta maganin ki sai kice wa mace ta baki hannun ta ki duba idan namiji ke bi mata a wurin haihuwa zakiga layin nan biyu sun hade dayan ya ware nakasan ke nan. Idan kuma mace ce wace ke bi maki a wurin haihuwa zaki ga daga sama basu hade ba sun dan rabu wanan kawai idan kinyi zasu gaskanta magabnin ki su dinga saya zaki dawo idan kin kokarta na fada maki. Har kasa nakai ina masa godiya na karba na fara tafiya ina dan waigen tsohon a cikin tsoro don taba min hannun da yayi tunda umma tace mu daina yarda ana taba mu . Idan an tabamu mubi mutum mu rama ko waye a haka ake daukewa mutum kurwan shi a cinyeshi ko a bashi wallaha gashi yau rigima yasa na amfakawa tsoho waini tallan mahani. Sai da nakai titin babba inda ake hada go,slow na tsaya na fara bin motoci ina fadin by local medecine for ur body medecine de here. Wata mace ce naga ta tsaya a tana kallona na je dan kusa da ita ina fadin buy medecine madam. Meka give u d one when ur ogo no go look anoda woman again tace dani (waire,) wai ni mahaukaciya tana fadawa na gefen ta wani magana suna dariya. Nace madam no be lie i talk woo na true true i de talk make show u something ban tsaye ba na figi hannun ta daga cikin yaga motan ina bude tafin hannun ta nace. Na woman de follow u for d birth abi na dago ina kallon ta ta dan fisge hannun ta tana cewa woman for where ? Nace emm after ur mama born u d one who de follow you its a girl abi ? Kallon yar uwar nata tayi tana fadin see dis small girl how d u know all this nace eh na my work naw even you can ask me sometin now apart from dis. Kallon juna sukayi kafin dayan dake gefen ta tace oya look here who de follow me na rike hannun nata da sauri kafin ince na boy naw. He naw tall dan u na kwatanta shekarun tane na fadin hakan da wasa ashe gaske ne haka dinnne kuwa. A wai see dis small girl no someti like magic kafin tace wani abu nace make give u dis for free ur hair go grow dan dis u will look anty yayalash if ur hair start growing. Ta farkom tace No give me d one my oga die for me, on bed, if we are making sex ido na dan rufe kafin in tuna da wanda ya ban yace na wanan harkan ne. Nace if u user am today, tomorrow u will, come back, to look for me, for anoda one, tace oya make u give me dat one, a daidai lokacin kuma motocin dake gaban su suka fara muna horn su basu hanya don haka muka dan gusa kadan suka sake kirana a takaice dubu goma na samu a hannun wa yan nan matan don wanan abin. Wasa wasa ina tallatawa wasu su zageni su koreni wasu kuma su kirani su saya sai gashi zuwa yamma na hada kudi mai yawa ga wanan tallan maganin. Jin dadin hakan yasa na ware dubu uku daga ciki don irin riban dana samu ta wanan sana,an naba wanan tsohon daya ban maganin na tallata . Shi kuma jin dadin hakan yasa ya zaunar dani yana min bayanin yadda sa,anan nasu yake da abubuwan da yake amfani na kwarai da wanda baida karfi.. Anan na shiririce wurin sa ina daukam ilimi ice da ganye wurin tsohon bahaushe din . A karshe nace ya kara ban sari don gobe ba zan shigo wanan unguwan ba wani wuri zan nufa shima kuma na bashi shawaran ya gwada hakan yace zai gwada insha Allah don nan kawai ya sani yasa yake zama a wurin har nomban wayan shi na karba don kira idan wani abu ya kakare min a rayuwa. Ga wanda ya ban yace nayi amfani dasu don tsari don sana,an sai kaci ka koshi ake sanin ka ni duk ban damu da hakan ba . Ni kawai naga wurin samun kudi na karba nayi godiya tare da sallama na kama hanyar komawa unguwan mu da yamma lis sai dare na isa gida da dan kumshin kayana a cikin buhun siminti. Duk da warim ganyen da sake saki da umma keji bata tsaya tambayana ko me na dauko ba a lokacin har saida na gama abinci da naman kai dana kwaso muna a gidan. Wanka na fara yi kafin in fito in zauna muci abincin sai bayan mun gama umma take tambayana abinda na dauko a cikin buhu. Hannu na tura a cikin kwagiri da ban yarda in ajeshi ko a dakin mune don masu shigowa dakin na fito da damin kudin da zaikai dubu ashirin da dan kai . Na fara bawa umma labarin duk abinda ya faru a ranan jikin umma yayi sanyi sosai take fadin bana tsoro nace da zuciya daya na karbi wanan sana,an nan dai da daren na fara yan hayakin da tsohon nan ya ban nasha nasha. Barci nayi ranan sosai har da makara saida umma ta tayar dani don makara agurguje nayi komai diban ruwa ne naso makara don layin dana samu a wurin. Nagama na shirya na fita haka nake samun alheri a wanan harka sosai don sukan sun yi amanna da maganin gargajiya so sai a garin. Har ya kai na hada da irin nasu dana sara a wurin wata mata da na yan ghana ina sayarwa ina kuma samun alheri ga hakan tsohuwar bayeraban cema taso kawo min matsala sai da zan tafi kome ta gani kuma ta ban sari na hada ina yawatawa ana saye kuma sosai. Duk ban sani ba tun ranan Chiku yana biye dani duk inda na saka kafa yana ba ogan shi bayani a kaina. Saidai ogan baya gari yasa baiyi wani kwakwaran motsin da zan iya gane hakan ba ina harkoki na don har gidan mu a yanzu ya sani yasan lokacin fitina da dawowa na gida. Haka rayuwa taci gaba da tafiya har na tsawon makoni ina hatkokina na sayar da magani da yanzu yafi min komai kawo kudi don har an fara sanina ga wanan harkan . Saidai inda nake samun matsala shine wurin sayar da maganin maza saboda wasu yan iskan zasu iya ma maganan banza amma haka nake matse fuska ina saida masu shi. Duk abindake wakana tana ji daga part din ta don Alh Nuhu har ciki ya shigo ya karewa hjy Addah fada dk bai samu miji su da yayi tafiya a gida ba lokacin. Wani irn shu,umin dariya ta sake dataji fitan shi yanawa kanwar tashi warning kan lalai dan nasu ya dawo gun matar shi watau yar su zuwa gobe in ba haka ba su hadu da fushin shi dukkan su. Son tun lokacin da yar tasa ta bugo mai waya tana kuka a cikin dare tana fadin Abba Abubakar ya cuceni yaci amanata ashe dama da gaske ba son auren mu yake dani ba gashi yana shirin mayar dani karamar bazawara a yanzu. Ke ke Nazifa ki kwantar da hankalin ki kimun magana yadda zan fahince ki Alh Nuhu ya fada cikin dakatar da yar tasa lokaci guda don duk son da yake masu bai hana inta baci ya tsawatawa diyan nasa kan abinda sukeyi. Ki kwantar da hankalin ki ki fada min abindake faruwa ya fada a dan hasale don kukan nata yana taba mashi zuciyar shi. Don akwaishi da son diyan shi har bai iya boye haka a gaban kowa waye don son kai da yake dashi balle ita Nazifa da yar yar gaban goshin sace sunga wurin ci ne ga Abubakar din suka dauki yar suka bashi. Lokacin da wanan zancen nason hadi da diyan shi yazo masa don shi bai amince da irin wanan hadin auren da iyayye da kakanni suka bar masuyi ba a yanzu. Don shi ya fara aurawa diyan shi bare na waje wanda basu da alaka na jini dasu don bai yarda da hadin nan ba a karshe yarinya taje tana wahala. Kuka take sosai rake labartawa mahaifin nata abinda ke faruwa tun bayan tafiyan Abubakar din wai ko wayan ta idan ta kirashi yanzu baya dauka. Ga dan iskan yaro Alh Nuhu ya fada yana fadin shi din me shi din banza ni ina da wani manufa akan shi tasa na yarda na bashi auren ki don kar ya dauka ko wani abu yake dashi da har zai fara wullakanta min ke a yanzu. Wani iri Nazifa taji da zagin da mahaifin nata yayiwa Abubakar din a yanzu don da Alh Nuhu yasan yadda a yanzu take son guy din da bai furta haka a gaban ta ba taji. Don tun asali tana son Abubakar din har kasan ranta ahiyasa ma tayi amanna da aure ba tare datayi gardama ga iyayyen nata ba. Don a yanzu data dandana ko waye Abubakar din jinshi take shine komai nata shine ma kamar rayuwan ta gaba daya a yadda take jin shi a cikin ranta a yanzu. Amma jin kalamin daddy su sai take ta dan sauko ba kunya take fadin daddy kayi mai magana kawai ya tafi dani ko ya dawo. Allah daddy gidan nan yai min girma da bashi a cikin sa kuma kasan ni ban saba da zama haka ni kadai ba. Abban nasu ya fahinci halin da yar nasu ke ciki a yanzu yasa ya dan sauko ga yadda yake jin zafin wullakanta masa ya da Abubakar din ke shirin yi a yanzu shine yaje gidan su hjy Addah tun da faran safiya ya buga gida suka tashi ya shiga yayi mata masifa ya fito sai gidan yar nasa kuma can yaje ya karbi wayan ta ya kira mijin nata ya zuba mai tunda safe. Dole hjy Addah ta kira dan nata cikin bacin rai tayi masa fada sosai tare da umuratan shi akan kome yake ya dawo gida zuwa gobe. Wanan dalilin yasa ya taso don ya fahinci ran mahaifiyar nasu a bace yake kuma koda bata fada mai ba ya gane Alh Nuhu yaje ke nan yayi mata barazana irin wanda yayi mashi shima da safe. Don haka ya shirya ya dawo kaduna din don mahaifiyar tasu ba don wani ba can yace a zuciyar shi. Yayin da hjy karima kuma ta shige sakewa hjy din arashi a yinin ranan kan auren dan nata tana fasin mutum ya daukowa kansa alalkakai don son kai ko tace gamu gani rashe ya na shirin juyewa da mijiya idan mutum yace son kai ya iya shi. Wanan dalilin tafiyan nasa yasa ua dakatar da duk wani shiri da yake dashi duk da kiran da chiku yayi mai ya sheda mai ya gano wasu abubuwa a tare dani a yanzu. ZAINAB IDRIS MAKAWA ANA DARA GA , , , , , , , , , , 1️⃣9️⃣ BY ZAINAB IDRIS MAKAWA BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AL MU,MIN, , , , , , PAID ONLINE NOVEL YAR UWA KI BIYA KI KARANTA KADA KI RAINA GIRMAN ZUNUBI, , , , , , , , Adduan ku nake nema ga bakunan ku masu albarka yan uwa Allah ya yaye muna matsalolin mu ga baki daya dani daku duka amin. Duk da ba wani sabo mai tsawo a tsakanin su har yanzu a matsayin su na ma,aurata a yanzu hakan bai hana ita ta kawar da komai ba a fili don irin tsananin son da take mashi har cikin zuciyarta ta nuna bata damu da yadda yake daure mata ba. Yanzun ma dakin ta shigo a cikin kwaliyan ta tun bayan fitan ta daga dakin misalin karfe taran safe ta shiga nata dakin waya tayi da yar uwarta kuma aminiyar ta na gidan su tana bata labarin irin gwarzon min mijin da Allah ya hore mata daga sama irin wanda suke mafalkin samu ita da aminiyar nata a kullun. Yau ma dai Nazifa bata barshi ba don itace mai neman shi bashi ke nemanta ba duk wanan a cikin wayen wata yake kuma take nuna hakan cikin rashin damuwa don tasan wata rana daina hakan zaiyi idan sun saba. Aure irin na fulani asali sukeyi a family su wanda kwatsam zakaji an daura auren wance da wani ba tare da sun san juna ko sabiba a tsakanin su kuma a zauna lafiya baka taba jin bakin su ga hakan. Ta shigo dakin a cikin takon izza da isa da gadara irin na yan gidan su da suke jin Naira na motsi a jikin su sun kuma tashi da wanan akidan kaf din su maza da matan su haka suke da nuna isar su acikin jinin su hakan yake masu. Da dan fara,anta a fuskan ta taja tayi tsaye tana bin shi da kallo tare da tsuke fuskanta lokaci guda tana kallon shi a gadarance tace dashi. Wanan jakar da kake hadawa fa na menene shi ta fada daga inda take tsaye fuska daure hakan yasa ya dago jin yadda tayi mai magana a cikin gadara yana kallon ta kai tsaye shima ya bata amsa da fadin tafiya zanyi yanzu. Babu wani shakunta ko firgici a fuskan shi ya bata amsa kai tsaye kana ya juya yaci gaba da abinda yakeyi din. Tashin hankali tace ina kuma zai tafi bayan Abban ta yace zai zauna da ita har na tsawon sati uku a gida yanzu ko sati daya bai rufe ba da dawowa har ya fara shirin wani tafiya can. Zip din dan jakar tasa yaja ya mike gabanta yana kallon firgitatun idanun ta da suka juye tankar tana cikin maye a lokacin. Cikin daurewa yace lafiya dai naga duk kin canza lokaci daya ko wani abune ya faru kuma ? So nake na gaskanta wai da gaske tafiya zakayi kuma a yau din nan bayan Abba ya fada ma sai kayi sati uku tare damu a nan ko zakayi wani tafiya a yanzu. Yayi murmushi tare da girgiza kanshi kadan da daga kafadan shi yace shi Abban naki ya fada maki hakan game dani ? Wata karfafan ajiyan zuciya ta sauke tare da fadin nasan kunyi hakan da Abba don Abba ba zai mun karya ba ka sani idan kuma kace zaka tafi yanzu zan daga waya na kirashi. Ya saki murmushi yana duban ta kafin yace a wanan karon kan ya fada maki ba daidai ba don ni bamuyi hakan dashi ba. Na shiga uku kana nufin ke nan Abba karya yayi min ko me ya Ababakar don haka maganan ka ke nufi a yanzu. Anyway duk yadda kikace haka din ne nidai nasan ba mace nake ba balle har a kafa min doka inbishi dole ina fatan kin gane. Ya sure jakar shi tare da wayoyin shi ya rataya yana fadin sai na dawo da sauri tayi kanshi a rude tana fadin. Wait wallahi ba zaka tafi ka barni ba ni ban gane wanan irin rayuwan ba kullun ace mutum na hanyar tafiya ni kwata kwata sam ban ganewa hakan ba. Hannu yasa ya jayeta a hanyar yayi ficewan shi rai bace bai ko kara waigo ta ba ya fice daga gidan yana jin wani iri a zuciyan shi a lokacin har zuwa lokacin da faruq yakai shi airport ya shiga jirgi suka daga. Duk da yasan ranan babu jirgin lagos haka ya daure zuwa Abuja daga can ya fada na lagos din din kiran da chuku yayi mai na gagawa akan mu. Yanzu kan sai ince faduwan gaba ya zama min jiki har na dan saba da hakan a rayuwa ganin ba abinda ya sameni tun ranan. Haka na fita daga gida sai ras ras nake ji lokaci lokaci ina dauke da dan buhun sassake na ganyanyaki sai garin magani a kule. Apapa na nufa kai tsaye inda nake zaton cabawa ga matan wurin don a gaskiya ina ciniki sosai a wanan erea din idan nakai kayana can. Wata hamshakiyar mace ce ta fito daga motan ta tana kullewa zata shiga wani botiq nake mata talla ina fadin, madam come buy local medecine for pink, Ta dan kalloni a yatsune taci gaba da tafiya nace madam try,am nd see ego work for u well,well sai taja ta tsaya wuri daya na sake fadin may try my medecine and see ma god go give u fine fine pikin i swear. Da mamaki take kallona na sai ta karaso har inda nake din tace dani how d u no, dat i no born ? nd i de looking for dis medecinen ? Emm, i just look at u and saw u problems in ur face na fada yadda masu magani ke fadi idan zasu sharota ga mutum. Tace Surprise u small pikin u know all dis tins in ur life ? d u have d that my ogo no look anoda worman again after me. Na shiga kiciniyar bude leda ina fadin if u use dis one e no go see any woman again i swear ina daga hannu. Mukai ido biyu da chukuma dana fara zargi a yanzu don sau uku ke nan ina yawan ganin shi a inda nake yawon tallana. Dan rudewa nayi na shiga yiwa matar bayani a gurguje ta karbi na haihuwa dana kama miji a cewan ta . Ta miko min kudi mai yawa na karba ina godiya tare da fatan maganin ayi nasara abinda ake nema tana fadin Amen ta hanyar daga hannuwan ta. Ina sauri nake tattara kayana in bar wurin naji muryan a baya na ana fadin i wan buy local medecine for my pikin. Ba tare dana juyo ba nake fadin i no go sella,am for men ina sauri naga an tare min hanya bayan wanda ke bayana din. Waitin u wan do for me now, comot for d road , or i will shout oley for u naw, na fada a dan hasale . Katin shedan su ya ciro ya nuna min ban fahinci na meye ba sai kayan kakin dana gani na gane me hakan ke nufi. Waitin i do for u, see me see wahala woo, me i no do antytin wain solder man wan cach me naw, . Motan dake gefen shi ya nuna min da hannu na dan saci kallon bindingan dake gefen shi da ido ba musu na nufi wirin motan ina waige ko zan samu mai cetona. Allah da ilon shi kuwa a take yan wurin suka taso suna fadin ogo waiti dis gurl do for u she no fait with any body here. Why you go arest her naw, waitin she do for u ? suna kallona suke tambaya daga inda nake tsaye da naji sun fara magana naja na tsaya inacewa , me i no do anytin for dem broda. I don't no dem, nd even who dey are ma self, still card din shi ya ciro ya nuna masu sai suka fara darewa daya bayan daya suna sulalewa daga wurin don ba mai son wahala ta ritsa dashi a cikin su. Tare da buhuna suka turani motan suka bar wurin kamar walkiya har mukai nisan tafiya ban kula da wanda ke kusa dani ba a lokacin. Duk ina sake sake a cikin zuciyana na yadda zan samu in kubuta a garesu shine kawai abinda nake yi lokacin. Don nasan idan Umma na bata ganin ba ranan zasu shiga wani hali na tashin hankali su dauka an sace nine. Duk a yanzun din ma ba zan iya cewa ga wa yanda suka dauke ni ba ma don ban san abinda nayi masu ba suka sakani motar su haka. Saidai idona yana kyankyashe ko dar din hawaye ban sake ba sai bin titin nake da kallo naji an jefo min tambaya da what is your mother's name ? Na dan juyo a dan firgice na kalli mai maganan saida na dan kadu da ganin shi lokaci guda haka a gabana . Shiru nayi don ko bindiga suka saka min ba zance ga sunan umman mu ba a rayuwana saida na bayan yace min u no hear he de asking u. Nace a cikin e,e niya i don't no her realy name we de call her with umma by name. Dan shiru ya biyo kafin yace which tribe are you nace, my mama told us we are hausa fulani by tribe. Okay yace ya dan gyara zaman shi kafin ya sake fadin, from which state nace she no tell me that i only know we come from north side dat what she told me. Yace so ke baki san sunan gari ku bama a rayuwan ki yana gyada kai na dan bishi da harara muka shiga go slow daya fara marance. Allah maijin kan bayin sa a haka yana min tambayoyin ina bashi amsa daidai gwargodon sanina wani yazo ya daki motan nasu sai wanda ke gefena ya fita fada da maishi. Ban tsaya jiran wani abuba na balle motar nima na fita na yanka a guje sai gani na bullo wani unguwa da ma ban taba shigan shi ba. Haka na tare me keke na hau zuwa wani titin ina zuwa na fada motar da zai kaini unguwar dake kusa da namu do ba,a samun mota daga nan . Har lokacin gabana sai faduwa yakeyi Allah yasa kudina yana jikina can na barsu da buhun maganina na gudo har nakai gida ina tunanen hadina dasu da suke min wanan tambayoyin haka. Sukuku na shiga gida har umma taso gane hakam nasan in na fada mata ba zan kara shiga gariba ke nan kuma ni ba zan iya zama a gida ba saboda sabo da fitan da nayi a rayuwana. Don haka na shatata mata karya na samu na kwanta tare da karyan kaina ke min ciwo a ranan ina faman tunanen inda zan canza ba tare dana kara haduwa da wanan mugun mutum da a yanzu yake son shiga rayuwata ba. Washe gari din na dai fitane ba zance ga inda zani ba kawai na sakai na bar gida na dade a bakin titi kafin na nufi surulere da niyan yin wani sana,a acan. Ance ido wa ka raina don Alh Nuhu ga hjy Addah ya sauke haushin danta don ya taso Nazifa gaba da uwarta har gida suka samu hjy. Sai abinda ya raga mata nacin mutunci hjy sai hakkuri da take bashi kawai a lokacin bayan haka bata iya furta komai ba. Har yana ikirarin ta kira danta yazo ya sake mashi ya don ba gadin gida ya kawo ta nan tayi masu ba a cewan shi. Hjy dai ta rasa na fada sai ayi hakkuri take fada jin abin yayi yawa yasa hjy karima fitowa daga part din ta kamar da gaske. Tana dan basu hakkuri tare da fadin haka yake tun farko ya kamata, ace sun sanda hakan don haka aikin shi ya gada. Nan dai ya kare masifan shi tare da jawa hjy kunne akan suyiwa dan su fada shifa bai daukan haka ga diyan shi ko kadan. Tun fitan shi hjy ta zauna tayi shiru abin duniya ya isheta akan wanan aure da ba koyi wasu watanni da shiba an fara samun baraka haka a tsakanin iyayyen auren kan yaran nasu. Abinda kowa ke gudu ke nan a yanzu yasa ba wanda ke sha,awan hada wani alaka dashi kan aure da diyan shi itama din dai kaddaran haka ya jata har ta furta a gaban yar uwanta cewa tana son zabawa dan mata . Budan bakin ta sai cewa tayi da hjy me zai hana ki zaba mashi a cikin yaran yaya Nuhu gasu nan kyawawa dasu mazan yanzu ai irin su suke so . Yan boka kuma ga wayewa wanan zancen ne yar uwan hjy din ta dauka kafin hjy takai ga yanke shawara takai gidan dan uwansu din. Matar shi uwargidan shi naji hakan ta dauki zancen da zafi takai gaban mijin su tare da kara gyara zancen tayi mai kwaskwarima har Alh din yaji shima yana sha,awan wanan hadin a tsakanin yaron da dayan yarshi . A take hjy ke fadin ai zasu fi dacewa da Nazifa nake gani don gashi dama shima din wayayye ne kuma dan gata kamarta. Don shi kadai ne da namiji a wurin mahaifin su a yanzu sai nake ganin kamar hadin nasu zai dace gaskiya. Shima Alh Nuhun a lokaci wani irin shu,umin murmushi ya sake don akwai abinda yake bukata a wurin wanan yaton nan gaba sai yake ganin ai wanan dama ne a gareshi ya samu. Wanan ne dalilin hadin auren su daya taso haka kai tsaye kuma Alh Nuhun ya matse aka daura shi a kam lokaci. Tun bayan daya gano cewa yaron yana son ya subuce masu a karshe yasa daurin auren cikin dan kankanin lokaci kuma akayi haka. Yawan son diyan shi dayasa a zuciyar shi yasa yanzu da Nazifa ta kawo karan mijin nata ya rufe ido yayi masu cin mutunci ya tafi. Tafiyan shi keda suya hjy Asiya ta shigo gidan a nan ta samu hjy a cikin tashin hankali da farko hjy ta boyewa kanwar mijin nasu amma saiga hjy karima ta fito itake labarta mata duk abinda ya faru da shigowan dan uwan nasu kan zancen diyan su din. Budan bakin hjy Asiya sai cewa tayi ai dama yaya Nuhu mutumin banza ne baida tunane sam a rayuwan shi idan idon sa ya rufe yana iya yiwa mutum komai kan yayan sa. Da alama kan yadda yazo gidan nan ido rufe shi da matar sa da yar tasu a gabanta ya fadawa maman Nabila komai da yake son fada. Hjy dai tana jin su bata iya tankasu ba sai maganan banza suke fada game da dan uwan nata tana sauraren su kawai don tasan dama irin daman nan suke jira su fada mata cikin zuciyar su game da auren na Abubakar. Don tana sane da son hadin yarta da hjy Asiya din ke so tun da dadewa kuma har ta gabatar da zancen gaban dan ta yaki yarda. Wanan wace irin yarinyace haka kamar yar daba yarinya tana abu kamar wata mai tabin hankali ? Anya ma kuwa wanan ba wahalan banza yakeyi ba akanta ita din kuwa yar uwasu ce kodai watace can na daban yake wahalal da kanshi akanta yanzu. Zama ya gyara yana fadin to amma kuma ai kamarsu ya baci da yan gidan don ma har ita wanan din idan ga gata harta zarta yaran gidan yake gani wurin yin kama da iyayyen su. Don da ganin ta kaga yar fulanin asali da ita saidai da ta bude baki tayi magana zakafi danganta ta yar wani kabila da ba hausawa ba. Koma dai wacece ita ya sha alwashin cewa zai taimaka masu tasan ko ita wacece tunda ta shigo rayuwan shi a yanzu. Haka kawai dan interview din da yayi mata da wanda ya hada tun farkon haduwan su sai ya gane yarinyar tana son tasan mahaifan ta da jaharta. Kai mutanen mu na arewa akwai kaskantar da kansu a irin wanan wuraren da ba, a san daranjan su ba. Ta yaya macen bahaushi zata zube yara kamar haka tana yawo a cikin gari wai tana tallan magani da sunan neman kudi. Dan murmushi ya sake don tuno da kayanta data sake a cikin motar su ta gudu ta barshi garesu in ba shirme ba nawa zata samu ga wa yan nan kayan da ya gani a cikin jakarta. Shawara da Nazari yaci gaba dayi shi kadai a dakin yaga dacewan bibiyan case din ya zauna mai a zuciyar shi yace koma meye tsakanin yau da gobene zai shawo kan matsalam su don zai binciko har uwan yarinyar nan yaji idan yaran ma suna da mahaifi. Gaban shine ya fadi ya dauko waya ya fara neman layin chuku yake sanar mai cewa zuwa gobe yake son su kama yarinyar nan suzo da ita don akwai tambayan da yake son masu ita da mahaifiyar ta. ALIYU MAKAMA THE BOY zaune yake a hadeden gidan shi dake Apapa Alabi street dake tall get . Yana zaune kasa don nan yake zaton zaiji dadin zama a wanan yanayin daya daure mai kai a yau don yau dai taron nasu ba,a watse shi da dadi ba. Don shawara yasha bambam a tsakanin da abokan kasuwancin nasu dake da shawara daban daban kan yadda suke son su canza arkalar su a yanzu. Shikan gaskiya a wanan katon yasan zasu raba hannun riga dasu don baida ra,ayin shiga wanan harkallan tasu tun farko. Don bai fara wani kasuwanci ba irin na mahaifin shi saida ya dan koyi wasu abu daga halaiyar mahaifin nasa na gaskiya. Shi tun farko dama bai yarda da wa yan nan kurayen kudin da yake tare dasu ba kuma bai taba zaton suna wanan haramtacen sana,an haka a cikin tafiyan su. Hannu ya mika ya dauki cup din dake gaban shi cike da lemo tattaciya ya dan kurba ya mayar ya aje a inda ya dauka. Don yadda yake jin kanshi a yau sai yaji kamar ya kurba ruwan guba ne a cikin sa lokacin don bacin rai. Taya yayyafi zai masa haka ya boye mai abinda ya saka a cikin kayan shi har yayi kasadan fitar mai dashi tun daga turai har nan kasan ba tare daya san hakan ba sai yanzu da yaron shi ya tsegunta masa hakan da sukai mai. Akarshe dai yasha alwashin zai masu yankan baya ta yadda zai iya fitar da kansa daga zargin da aka fara jefan shi dashi zai nuna masu shi din jan koma ne idan su kifaye ne masu kwakwalwa daskare. Da wanan tunanen ya mike tsaye daga inda yake zaune din zuwa dakin kwanan shi don yau baijin fita ko ina don yadda yake jin kansa din. Haba dole ashe yan sanda su nemesa haka ruwa a jallo don wanan abin yace a fili rai a bace dan guntun murmushi ya sake don shawaran da zuciyar shi ta zauna a kai lokacn. A haka barci ya dauke shi mai nauyi har da mafalkin sun hade da yan sanda ana gumu dashi kan wanan case din daya zauna mai a rai. ZAINAB IDRIS MAKAWA ANA DARA GA , , , , , , , , , , 1️⃣9️⃣ BY ZAINAB IDRIS MAKAWA BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AL MU,MIN, , , , , , PAID ONLINE NOVEL YAR UWA KI BIYA KI KARANTA KADA KI RAINA GIRMAN ZUNUBI, , , , , , , , Adduan ku nake nema ga bakunan ku masu albarka yan uwa Allah ya yaye muna matsalolin mu ga baki daya dani daku duka amin. Duk da ba wani sabo mai tsawo a tsakanin su har yanzu a matsayin su na ma,aurata a yanzu hakan bai hana ita ta kawar da komai ba a fili don irin tsananin son da take mashi har cikin zuciyarta ta nuna bata damu da yadda yake daure mata ba. Yanzun ma dakin ta shigo a cikin kwaliyan ta tun bayan fitan ta daga dakin misalin karfe taran safe ta shiga nata dakin waya tayi da yar uwarta kuma aminiyar ta na gidan su tana bata labarin irin gwarzon min mijin da Allah ya hore mata daga sama irin wanda suke mafalkin samu ita da aminiyar nata a kullun. Yau ma dai Nazifa bata barshi ba don itace mai neman shi bashi ke nemanta ba duk wanan a cikin wayen wata yake kuma take nuna hakan cikin rashin damuwa don tasan wata rana daina hakan zaiyi idan sun saba. Aure irin na fulani asali sukeyi a family su wanda kwatsam zakaji an daura auren wance da wani ba tare da sun san juna ko sabiba a tsakanin su kuma a zauna lafiya baka taba jin bakin su ga hakan. Ta shigo dakin a cikin takon izza da isa da gadara irin na yan gidan su da suke jin Naira na motsi a jikin su sun kuma tashi da wanan akidan kaf din su maza da matan su haka suke da nuna isar su acikin jinin su hakan yake masu. Da dan fara,anta a fuskan ta taja tayi tsaye tana bin shi da kallo tare da tsuke fuskanta lokaci guda tana kallon shi a gadarance tace dashi. Wanan jakar da kake hadawa fa na menene shi ta fada daga inda take tsaye fuska daure hakan yasa ya dago jin yadda tayi mai magana a cikin gadara yana kallon ta kai tsaye shima ya bata amsa da fadin tafiya zanyi yanzu. Babu wani shakunta ko firgici a fuskan shi ya bata amsa kai tsaye kana ya juya yaci gaba da abinda yakeyi din. Tashin hankali tace ina kuma zai tafi bayan Abban ta yace zai zauna da ita har na tsawon sati uku a gida yanzu ko sati daya bai rufe ba da dawowa har ya fara shirin wani tafiya can. Zip din dan jakar tasa yaja ya mike gabanta yana kallon firgitatun idanun ta da suka juye tankar tana cikin maye a lokacin. Cikin daurewa yace lafiya dai naga duk kin canza lokaci daya ko wani abune ya faru kuma ? So nake na gaskanta wai da gaske tafiya zakayi kuma a yau din nan bayan Abba ya fada ma sai kayi sati uku tare damu a nan ko zakayi wani tafiya a yanzu. Yayi murmushi tare da girgiza kanshi kadan da daga kafadan shi yace shi Abban naki ya fada maki hakan game dani ? Wata karfafan ajiyan zuciya ta sauke tare da fadin nasan kunyi hakan da Abba don Abba ba zai mun karya ba ka sani idan kuma kace zaka tafi yanzu zan daga waya na kirashi. Ya saki murmushi yana duban ta kafin yace a wanan karon kan ya fada maki ba daidai ba don ni bamuyi hakan dashi ba. Na shiga uku kana nufin ke nan Abba karya yayi min ko me ya Ababakar don haka maganan ka ke nufi a yanzu. Anyway duk yadda kikace haka din ne nidai nasan ba mace nake ba balle har a kafa min doka inbishi dole ina fatan kin gane. Ya sure jakar shi tare da wayoyin shi ya rataya yana fadin sai na dawo da sauri tayi kanshi a rude tana fadin. Wait wallahi ba zaka tafi ka barni ba ni ban gane wanan irin rayuwan ba kullun ace mutum na hanyar tafiya ni kwata kwata sam ban ganewa hakan ba. Hannu yasa ya jayeta a hanyar yayi ficewan shi rai bace bai ko kara waigo ta ba ya fice daga gidan yana jin wani iri a zuciyan shi a lokacin har zuwa lokacin da faruq yakai shi airport ya shiga jirgi suka daga. Duk da yasan ranan babu jirgin lagos haka ya daure zuwa Abuja daga can ya fada na lagos din din kiran da chuku yayi mai na gagawa akan mu. Yanzu kan sai ince faduwan gaba ya zama min jiki har na dan saba da hakan a rayuwa ganin ba abinda ya sameni tun ranan. Haka na fita daga gida sai ras ras nake ji lokaci lokaci ina dauke da dan buhun sassake na ganyanyaki sai garin magani a kule. Apapa na nufa kai tsaye inda nake zaton cabawa ga matan wurin don a gaskiya ina ciniki sosai a wanan erea din idan nakai kayana can. Wata hamshakiyar mace ce ta fito daga motan ta tana kullewa zata shiga wani botiq nake mata talla ina fadin, madam come buy local medecine for pink, Ta dan kalloni a yatsune taci gaba da tafiya nace madam try,am nd see ego work for u well,well sai taja ta tsaya wuri daya na sake fadin may try my medecine and see ma god go give u fine fine pikin i swear. Da mamaki take kallona na sai ta karaso har inda nake din tace dani how d u no, dat i no born ? nd i de looking for dis medecinen ? Emm, i just look at u and saw u problems in ur face na fada yadda masu magani ke fadi idan zasu sharota ga mutum. Tace Surprise u small pikin u know all dis tins in ur life ? d u have d that my ogo no look anoda worman again after me. Na shiga kiciniyar bude leda ina fadin if u use dis one e no go see any woman again i swear ina daga hannu. Mukai ido biyu da chukuma dana fara zargi a yanzu don sau uku ke nan ina yawan ganin shi a inda nake yawon tallana. Dan rudewa nayi na shiga yiwa matar bayani a gurguje ta karbi na haihuwa dana kama miji a cewan ta . Ta miko min kudi mai yawa na karba ina godiya tare da fatan maganin ayi nasara abinda ake nema tana fadin Amen ta hanyar daga hannuwan ta. Ina sauri nake tattara kayana in bar wurin naji muryan a baya na ana fadin i wan buy local medecine for my pikin. Ba tare dana juyo ba nake fadin i no go sella,am for men ina sauri naga an tare min hanya bayan wanda ke bayana din. Waitin u wan do for me now, comot for d road , or i will shout oley for u naw, na fada a dan hasale . Katin shedan su ya ciro ya nuna min ban fahinci na meye ba sai kayan kakin dana gani na gane me hakan ke nufi. Waitin i do for u, see me see wahala woo, me i no do antytin wain solder man wan cach me naw, . Motan dake gefen shi ya nuna min da hannu na dan saci kallon bindingan dake gefen shi da ido ba musu na nufi wirin motan ina waige ko zan samu mai cetona. Allah da ilon shi kuwa a take yan wurin suka taso suna fadin ogo waiti dis gurl do for u she no fait with any body here. Why you go arest her naw, waitin she do for u ? suna kallona suke tambaya daga inda nake tsaye da naji sun fara magana naja na tsaya inacewa , me i no do anytin for dem broda. I don't no dem, nd even who dey are ma self, still card din shi ya ciro ya nuna masu sai suka fara darewa daya bayan daya suna sulalewa daga wurin don ba mai son wahala ta ritsa dashi a cikin su. Tare da buhuna suka turani motan suka bar wurin kamar walkiya har mukai nisan tafiya ban kula da wanda ke kusa dani ba a lokacin. Duk ina sake sake a cikin zuciyana na yadda zan samu in kubuta a garesu shine kawai abinda nake yi lokacin. Don nasan idan Umma na bata ganin ba ranan zasu shiga wani hali na tashin hankali su dauka an sace nine. Duk a yanzun din ma ba zan iya cewa ga wa yanda suka dauke ni ba ma don ban san abinda nayi masu ba suka sakani motar su haka. Saidai idona yana kyankyashe ko dar din hawaye ban sake ba sai bin titin nake da kallo naji an jefo min tambaya da what is your mother's name ? Na dan juyo a dan firgice na kalli mai maganan saida na dan kadu da ganin shi lokaci guda haka a gabana . Shiru nayi don ko bindiga suka saka min ba zance ga sunan umman mu ba a rayuwana saida na bayan yace min u no hear he de asking u. Nace a cikin e,e niya i don't no her realy name we de call her with umma by name. Dan shiru ya biyo kafin yace which tribe are you nace, my mama told us we are hausa fulani by tribe. Okay yace ya dan gyara zaman shi kafin ya sake fadin, from which state nace she no tell me that i only know we come from north side dat what she told me. Yace so ke baki san sunan gari ku bama a rayuwan ki yana gyada kai na dan bishi da harara muka shiga go slow daya fara marance. Allah maijin kan bayin sa a haka yana min tambayoyin ina bashi amsa daidai gwargodon sanina wani yazo ya daki motan nasu sai wanda ke gefena ya fita fada da maishi. Ban tsaya jiran wani abuba na balle motar nima na fita na yanka a guje sai gani na bullo wani unguwa da ma ban taba shigan shi ba. Haka na tare me keke na hau zuwa wani titin ina zuwa na fada motar da zai kaini unguwar dake kusa da namu do ba,a samun mota daga nan . Har lokacin gabana sai faduwa yakeyi Allah yasa kudina yana jikina can na barsu da buhun maganina na gudo har nakai gida ina tunanen hadina dasu da suke min wanan tambayoyin haka. Sukuku na shiga gida har umma taso gane hakam nasan in na fada mata ba zan kara shiga gariba ke nan kuma ni ba zan iya zama a gida ba saboda sabo da fitan da nayi a rayuwana. Don haka na shatata mata karya na samu na kwanta tare da karyan kaina ke min ciwo a ranan ina faman tunanen inda zan canza ba tare dana kara haduwa da wanan mugun mutum da a yanzu yake son shiga rayuwata ba. Washe gari din na dai fitane ba zance ga inda zani ba kawai na sakai na bar gida na dade a bakin titi kafin na nufi surulere da niyan yin wani sana,a acan. Ance ido wa ka raina don Alh Nuhu ga hjy Addah ya sauke haushin danta don ya taso Nazifa gaba da uwarta har gida suka samu hjy. Sai abinda ya raga mata nacin mutunci hjy sai hakkuri da take bashi kawai a lokacin bayan haka bata iya furta komai ba. Har yana ikirarin ta kira danta yazo ya sake mashi ya don ba gadin gida ya kawo ta nan tayi masu ba a cewan shi. Hjy dai ta rasa na fada sai ayi hakkuri take fada jin abin yayi yawa yasa hjy karima fitowa daga part din ta kamar da gaske. Tana dan basu hakkuri tare da fadin haka yake tun farko ya kamata, ace sun sanda hakan don haka aikin shi ya gada. Nan dai ya kare masifan shi tare da jawa hjy kunne akan suyiwa dan su fada shifa bai daukan haka ga diyan shi ko kadan. Tun fitan shi hjy ta zauna tayi shiru abin duniya ya isheta akan wanan aure da ba koyi wasu watanni da shiba an fara samun baraka haka a tsakanin iyayyen auren kan yaran nasu. Abinda kowa ke gudu ke nan a yanzu yasa ba wanda ke sha,awan hada wani alaka dashi kan aure da diyan shi itama din dai kaddaran haka ya jata har ta furta a gaban yar uwanta cewa tana son zabawa dan mata . Budan bakin ta sai cewa tayi da hjy me zai hana ki zaba mashi a cikin yaran yaya Nuhu gasu nan kyawawa dasu mazan yanzu ai irin su suke so . Yan boka kuma ga wayewa wanan zancen ne yar uwan hjy din ta dauka kafin hjy takai ga yanke shawara takai gidan dan uwansu din. Matar shi uwargidan shi naji hakan ta dauki zancen da zafi takai gaban mijin su tare da kara gyara zancen tayi mai kwaskwarima har Alh din yaji shima yana sha,awan wanan hadin a tsakanin yaron da dayan yarshi . A take hjy ke fadin ai zasu fi dacewa da Nazifa nake gani don gashi dama shima din wayayye ne kuma dan gata kamarta. Don shi kadai ne da namiji a wurin mahaifin su a yanzu sai nake ganin kamar hadin nasu zai dace gaskiya. Shima Alh Nuhun a lokaci wani irin shu,umin murmushi ya sake don akwai abinda yake bukata a wurin wanan yaton nan gaba sai yake ganin ai wanan dama ne a gareshi ya samu. Wanan ne dalilin hadin auren su daya taso haka kai tsaye kuma Alh Nuhun ya matse aka daura shi a kam lokaci. Tun bayan daya gano cewa yaron yana son ya subuce masu a karshe yasa daurin auren cikin dan kankanin lokaci kuma akayi haka. Yawan son diyan shi dayasa a zuciyar shi yasa yanzu da Nazifa ta kawo karan mijin nata ya rufe ido yayi masu cin mutunci ya tafi. Tafiyan shi keda suya hjy Asiya ta shigo gidan a nan ta samu hjy a cikin tashin hankali da farko hjy ta boyewa kanwar mijin nasu amma saiga hjy karima ta fito itake labarta mata duk abinda ya faru da shigowan dan uwan nasu kan zancen diyan su din. Budan bakin hjy Asiya sai cewa tayi ai dama yaya Nuhu mutumin banza ne baida tunane sam a rayuwan shi idan idon sa ya rufe yana iya yiwa mutum komai kan yayan sa. Da alama kan yadda yazo gidan nan ido rufe shi da matar sa da yar tasu a gabanta ya fadawa maman Nabila komai da yake son fada. Hjy dai tana jin su bata iya tankasu ba sai maganan banza suke fada game da dan uwan nata tana sauraren su kawai don tasan dama irin daman nan suke jira su fada mata cikin zuciyar su game da auren na Abubakar. Don tana sane da son hadin yarta da hjy Asiya din ke so tun da dadewa kuma har ta gabatar da zancen gaban dan ta yaki yarda. Wanan wace irin yarinyace haka kamar yar daba yarinya tana abu kamar wata mai tabin hankali ? Anya ma kuwa wanan ba wahalan banza yakeyi ba akanta ita din kuwa yar uwasu ce kodai watace can na daban yake wahalal da kanshi akanta yanzu. Zama ya gyara yana fadin to amma kuma ai kamarsu ya baci da yan gidan don ma har ita wanan din idan ga gata harta zarta yaran gidan yake gani wurin yin kama da iyayyen su. Don da ganin ta kaga yar fulanin asali da ita saidai da ta bude baki tayi magana zakafi danganta ta yar wani kabila da ba hausawa ba. Koma dai wacece ita ya sha alwashin cewa zai taimaka masu tasan ko ita wacece tunda ta shigo rayuwan shi a yanzu. Haka kawai dan interview din da yayi mata da wanda ya hada tun farkon haduwan su sai ya gane yarinyar tana son tasan mahaifan ta da jaharta. Kai mutanen mu na arewa akwai kaskantar da kansu a irin wanan wuraren da ba, a san daranjan su ba. Ta yaya macen bahaushi zata zube yara kamar haka tana yawo a cikin gari wai tana tallan magani da sunan neman kudi. Dan murmushi ya sake don tuno da kayanta data sake a cikin motar su ta gudu ta barshi garesu in ba shirme ba nawa zata samu ga wa yan nan kayan da ya gani a cikin jakarta. Shawara da Nazari yaci gaba dayi shi kadai a dakin yaga dacewan bibiyan case din ya zauna mai a zuciyar shi yace koma meye tsakanin yau da gobene zai shawo kan matsalam su don zai binciko har uwan yarinyar nan yaji idan yaran ma suna da mahaifi. Gaban shine ya fadi ya dauko waya ya fara neman layin chuku yake sanar mai cewa zuwa gobe yake son su kama yarinyar nan suzo da ita don akwai tambayan da yake son masu ita da mahaifiyar ta. ALIYU MAKAMA THE BOY zaune yake a hadeden gidan shi dake Apapa Alabi street dake tall get . Yana zaune kasa don nan yake zaton zaiji dadin zama a wanan yanayin daya daure mai kai a yau don yau dai taron nasu ba,a watse shi da dadi ba. Don shawara yasha bambam a tsakanin da abokan kasuwancin nasu dake da shawara daban daban kan yadda suke son su canza arkalar su a yanzu. Shikan gaskiya a wanan katon yasan zasu raba hannun riga dasu don baida ra,ayin shiga wanan harkallan tasu tun farko. Don bai fara wani kasuwanci ba irin na mahaifin shi saida ya dan koyi wasu abu daga halaiyar mahaifin nasa na gaskiya. Shi tun farko dama bai yarda da wa yan nan kurayen kudin da yake tare dasu ba kuma bai taba zaton suna wanan haramtacen sana,an haka a cikin tafiyan su. Hannu ya mika ya dauki cup din dake gaban shi cike da lemo tattaciya ya dan kurba ya mayar ya aje a inda ya dauka. Don yadda yake jin kanshi a yau sai yaji kamar ya kurba ruwan guba ne a cikin sa lokacin don bacin rai. Taya yayyafi zai masa haka ya boye mai abinda ya saka a cikin kayan shi har yayi kasadan fitar mai dashi tun daga turai har nan kasan ba tare daya san hakan ba sai yanzu da yaron shi ya tsegunta masa hakan da sukai mai. Akarshe dai yasha alwashin zai masu yankan baya ta yadda zai iya fitar da kansa daga zargin da aka fara jefan shi dashi zai nuna masu shi din jan koma ne idan su kifaye ne masu kwakwalwa daskare. Da wanan tunanen ya mike tsaye daga inda yake zaune din zuwa dakin kwanan shi don yau baijin fita ko ina don yadda yake jin kansa din. Haba dole ashe yan sanda su nemesa haka ruwa a jallo don wanan abin yace a fili rai a bace dan guntun murmushi ya sake don shawaran da zuciyar shi ta zauna a kai lokacn. A haka barci ya dauke shi mai nauyi har da mafalkin sun hade da yan sanda ana gumu dashi kan wanan case din daya zauna mai a rai. ZAINAB IDRIS MAKAWA ANA DARA GA, , , , , , , , , , , , 2️⃣0️⃣ BY ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , , BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AL MUHAY,MIN, , , , , , , , PAID ONLINE NOVEL DON ALLAH KI BIYA KAFIN KI KARANTA KADA KI DAUKARWA KANKI NAUYIN WANI KI KWASHI ZUNUBI, , , , Yau kan da farin ciki na tashi duk da ina jin abinda yanzu ya zame min jiki ko yaushe har zan iya cewa na yau din yafi na kullun . Sai dai hakan bai dameni ba a yanzu don kamar ya zamo min jiki a yanzu din Nayi sallama da umma kamar yadda na saba a kullun idan zan bar gida na kama hanya zuwa neman sa, a a gari tare da tunanen ina zan dosa a ranan. Tsayuwana na gyara daga inda nake tsaye ina tunanen inda zan dosa naji murya a gabana a na fadin ekeja. Ban tsaya tunane ba ko la,akarin motan na going ya tsaya na shiga daga ni sai driver a lokacin daga shigana sanyi da kamshi ya daki hancina ban kara sanin inda nake ba sai dai na bude ido na ganin a cikin wani saki mai kyau dashi ga sanyin AC ga kamshi na tashi a dakin duk da dakin na da duhu a lokacin . Sai dai duhun bai hanani gane hakan ba abinda mutum bai saba dashi ba dole inga bambamcin ga hakan. Kokarin yunkurawa nayi don in tashi naji ban iya koda motsawa a lokacin innalillahi na fara fadi ina hawaye tare da tunanen shike nan na fada hannun yan mafiya ke nan a yau abinda kullun umma ke min addu,a kanshi ke nan yau na fada tarkon su ke nan Allah ka fitar dani hannun wa yan nan azzaluman lafiya. Ya Allah kada ka basu ikon cutar dani koda dingon kwayar zarah duk a cikin raina nake wanan adduan ni kadai a dakin kwace an dare min hannaye da kafa. Duk wani kokarin da zan iya don in kwance kaina saga daurin da sukai min nakasa yi gashi dakin shiru baka jin motsin kowa a cikin sa lokacin. Don zan iya cewa nikadai ne a wanan gidan ko daki zon rashin jin motsin komai da banyi tun lokacin dana falka din daga barcin dole dana tafi. Hawaye ya fara zubo min lokaci daya ba abinda nake tunane sai mahaifiyana da dan uwana irin halin da zasu kasance na rashi a yanzu. Kai hardai na gaji na daina kukan na koma ihu duk da banyi zaton akwai wani a wanan gidan da nake ba a lokacin ina nemam ceto da fadin. Somebody help me, help please, help help sai kuma na fashe da kuka mai tsuma zuciya lokaci guda. Nayi ihun na nemi taimako ba wanda ya lekoni dakin nagaji nabarwa Allah ikon sa na shiga yin addu,a ido rufe . Gaskiya tashin hankali baida dadi a rayuwa don nayi tunane kala kala lokaci guda har na rasa na kamawa a cikin tunanen nawa da nakeyi. A haka har dare ya riskene a wurin kwance a daure a cikin yanayin gala baita da tausayi ga duk wanda ya ganni a lokacin. Duk da ban san lokaci ba a yadda nake a dakin tun safe har wanan lokacin da nake tsamanin dare yayi a lokacin. Naji ana kokarin bude kofan tare da jin muryoyin maza a kokafan da alama kokadin shigowa dakin da nake din sukeyi.. Naji an turo kofan lokaci guda da yai daidai da shigowan wani dakin ke nan a lokacin nabi kofan da kallo tare da kallon wanda ya shigo dakin lokacin duk da duhun dakin nai bari inga fuskan maishi. Why d u tie her like dis naji an fada oga u no how dis gurl be criminal stop calling her with that name aka fada a cikin tsawa naji wanda akewa fadan yace sorry oga. Please don't cheat me sai kuma na shiga fadi da yarbanci suyi hakkuri ban masu komai ba idan ma nayi ban sani bane nayi na hada hannu a wuri daya ina basu hakkuri. Fita naga mai fadan yayi sai dayan yabi shi a cikin daga murya nake fadin su barni inje gida kada mahaifiyata ta shiga wani hali. Aka rufo kofan da karfi na sake fashewa da kuka mai karfi lokaci guda ina ihu duk hakan bai basu tausayi ba. Sai can cikin dare aka kawo min abinci ban ko kalle shi ba bayan maishi ya banye min hannu yake fadin ga bandaki nan ina iya shiga nayi alwala ga kaya nan nayi sallah. Yana fadin haka ya juya ya fita ya kulle kofan daga baya wasu hawaye masu dumi suka zobo min lokaci guda a wurin na samu na mike zaune da kyat duk jikina yayi min tsami sosai a lokacin. Haka na samu na sauka daga gadon da kyat na shiga bandakin daya nuna min din wuri ne lafiyayye ko da ganin yadda ban dakin yake . Bin ko ina nayi da kallo kafin na daure na dauro alwala na fito duk da naso nayi wanka amma tsoro ya hanani hakan don bansan a ida nake ba a lokaci. Ledan dake saman gadon na bude a hankali kayane irin na hausawa sai hijab babba da nake ganin wasu matan hausa dashi a jiki a ciki. Hijjab din kawai na dauka nasa nayi sallolin dake kaina don a gaskiya bana wasa da sallah a duk inda ya riskeni zan tsaya inyi shi don horuwa da hakan da umma tayi muna akan sallah. Ina nan dai dakin a zaune dare yayi don alaman daya nuna hakan a nan kasa na kwanta inata faman sheshekan kuka har barci ya sace ni a hakan ban sani ba. Sai gabanin asuba na falka naga alaman an shigo dakin lokacin ina barci don wani abincin da aka aje min gefe na duk banci ba. Kiran sallah nadan fara jiyowa sama sama haka yasa na mike na shiga bandakin na watso ruwa a jikina a gurguje don nasan wanan lokacin wanda suka kawoni nan suna can suna barcin su a lokacin. Hakan yasa na danyi amfani da wanan daman na watsa ruwa ko zan danji jikin nawa ya sake min a yadda nake jinshi lokacin. Sallah nayi na idar nake ta faman tunanen yadda zanyi in kubutar da kaina har wani dabara ya fado min. Plate din abincin nan na juye na rike a hannu na ban yarda nayi nisa dashi ba daidai kofan na tsaya lokacin da naji ana kokarin bude kofan. Maishi yana sawo kai na daga plate na kai mai duka ya tare na samu hannun shi nayi kokarin gudu ta hanyar kusawa ta bayan shi har nakai wajen dakin na hango dogon korido ba kowa waje a lokacin. Daga kafan da zanyi naji an jawoni an mayar a dakin da karfi ina jhu ina fadin help help somebody help me please. Ba wanda ya leko har lokacin tsuki naji anja an fita tare da turo kofan na sake wani kuka mai cin rai. Na dade a zaune ba wanda ya kara lekoni dakin idona nakai ga plate sin daya tarwatse a kasa da alaman na samu maishi sosai ga dukan dana kai mashi din. Har zuwa karfe daya saura yan mintoci ba,a shigo dakin ba haka yasa na mike zuwa bandaki na dauro alwala gashi lokacin na fara jin yunwa a cikina. Don rabona da abincin tun daren shekaran jiya da mukaci abinci da su umma kafin na kwanta koshi saida umma ta matsa min na daure naci don barcin da nake ji a lokacin. Shine har wanan lokavin a cikina don abincin jiya da aka kawo min ya lalace ba zai ciwu ba saboda irin hadin da sukai mai. Can naji anturo kofa an shigo su biyune wanan karon da yake akwai hasken rana a lokacin haka yasani gane fuskan maishi saida na mike ina fadin. What have i done to you? You kidnap me here god go punish u for dis sin u made na fada ina nuna shi da yatsan hannuna a cikin mamaki. Common shutup ya fada a hasale yana fadin idan kina da sako gun mahaifiyar ki kiyi magana don yanzu zan tura a fada mata kina nan wurin mu, mun kama ki. For what reason ta fada muna abinda muke son ji a wurin ta idan mun kamata an jima jin haka yasa na zube ina fadin No No mai mahaifiyana tayi maku zaku kamata. Wayo kada ku kama min ummana bata da lafiya don Allah ku rikeni duk laifin da nayi ni nayi ba umma na ba na fada ina kuka. Basu tsaya saurara min ba suka fice abinsu ina jin ana rufo kofan dakin da nake da makulli aka rufeni a cikin dakin. Umma kan suna van sun shiga tashin hankali kamar zata haukace fun a daren da ban dawo gida ba lokavin dana saba dawowa. Haka suka kwasa zuwa bus stop din unguwar inda muke shiga mota suna tambaya koda wanda ya gani a wurin tare da nuna masu photona . Sai wani tsoho dan kamisho ne yace ya gane ni kuma yaga na shiga wata mota da ba bus ba da safe maishi yazo ya dade a gefen titi kafin can yazo nan inda suke a lokacin dana karaso wurin. Ihu umma tasa lokaci daya tana fadin shike nan sun sace mata yarta yar aamana a nan dai umma tayi ta sake magana saida su ladi suka jata zuwa gida a cikin duhun dare. Ranan kan, kan umma ladi ta kwana dole tana bata magana da ban baki haka suka kwana zaune hanlali tashe. Washe gari tun safe sukai shiri suka bazama zuwa cikin gari har gidan hjy halima suka so zuwa sai basu gane gidan ba don rudewan da umma tayi sai bata gane gidan ba. Haka suka juyo zuwa semi a nan kuma suka samu wani rabarin tashin hankali don ko gida ba, a bari sun shiga ba aka tare su da fadin wai yansanda sunzo neman umma din. Yan sanda kuma Ladi ta tambaya sukace yansanda kuma ba masu saukin kaiba don har da sojoji suka zo da motocin su nan basu dade da wucewa ba duk sun shiga gidajen unguwan nan dazun. Ai basu fargaba sai ganin umma ta tafi suuu kasa ta some sukayi nan kuma hankali ya kara tashi sosai. Aka kwashi umma din zuwa cikin gida sai da kyat Allah ya farfado da ita duk hankalin ladi ya tashi ranan don ta shiga tashin hankali ba kadan ba. Ranan dai a nan dakin mu Ladi ta kwana da umma sai sambatu take sakewa na fitan hankali a lokacin Ladi tana faman bata baki. Jikin dai na umma yakiya shawara aka ba Ladi cewa takai umma asibiti dole haka suka shirya zuwa asibitin don a cikin sambatun umma tana fadin saida naja kunnen yarinyar nan. Akan mutanen nan da take gani kamar son Allah da Annabi suke mata ni nasan da wata suna neman rayuwan tane kawai ga hakan. Kinsan dan yau da rashin jin magana amma sai yar nan bata yarda da hakan ba take karbo abinda suke bata din. Jin hakan ya karawa Ladi karfin gwiwan su tafi asibiti suga likita kada wani abu yazo ya samu umma din a yadda take kwance haka. Sun fito yan gulman unguwa suka shiga fadin wai akan yarta budurwa take wanan haukan haka yanzu yarinyar nacan tana holewan ta ita tana nan tana hauka haka. Yanzu ma wa zai tsaya wanan haukan kan yarinya ta bata idan ba gawan ta aka gani ba tana can wurin wani ya dauketa suna jin dasin su ko kuma ta hadu da yan Yahoo ta jona dasu a cikin gari. Kowa dai da abinda yake fada akan wanan maganan a unguwar namu don halin da umma suke ciki na tashin hankali. Ladi kan dole itace ta tsayawa umma din tunsa ba kowa ke garemu a unguwan ba daga Allah sai ita ladi din muka sani. Suna adibitin kuma sai gasu sun sameta a can asibitin sun shiga sun fita sunga likitan da umma ke kwance asibitin nasa sun fada mashi dalilun zuwan nasu. Sai gasu an kawo su har dakin da umma din take kwance suka duba jikin ta a haka kuma suke mata tambayoyi kan rayuwan ta take dan basu amsa sama sama. Ganin ba zata basu hadin kaiba ne suka fito fili sukace da Umma din matukar tana son yarta ta dawo hannun ta sai ta fada masu duk wani abinda suke bukatan ji a wurin ta din. Dole umma ta natsu jin hakan ta fara fada masu dan wani abu game da abinda suke tambayanta din da suke son sani. Shi da kanshi ya nemi sauyin asibiti ga umma din ya sa aka kaita wani mai tsada wanda yafi wanan din da take kwance a lokacin. Sai abin kuma yabawa umma mamaki a karshe don yadda ake kula da ita gashi ance sai idan ta kwantar da hankali za a kawo mata yarta. Dole umma ta daure tana shan magani yadda ya kamata a lokacin don dai kawai na dawo gareta gashi har dan sanda aka aje a kofan dakin da take ciki kamar wata mai laifi babba can da aka tsare. Ko wata matar babban dan sanda ko soja a cikin kasan nan don irin yadda ake nuna mata a lokacin. Yayin da ni kuma na rame na koma kamar wata zarara a dakin da aka kullemi din duk da bamu da gata sai na Allah amma sai gashi Allah yasa mun samu kulla daga masu farautan mu din a yanzu da bamu san dalilim halan da ake muna ba. Hankalin shi kwance kuma duk yasan abinda ke faruwa damu din daga umma dake asibiti a kwance har ni dake rufe a wani dakin cikin hotel din da ban sani ba. Umma ta samu sallama don haka suka koma gidan Ladi inda muke da zama a cikin damuwa har lokacin zuciyar ta yake, Hankalin shi kwamce ya gama duk wani shiri da zaiyi ban tsaya jiran wani zance ba sai zancen zuwa gidan da zaiyi gobe din. Kuma da wanan yarinyar zai tafi aje a yita su kare a wuce wurin idan sunje zaiyi duk abinda ya kamata ace anyi akan zancen yaran nan a yanzu. Ya fahinci cewa ita kanta umma akwai wani boyayyen sirin da take boyewa wanda bata son wani yasani a yanzu. ZAINAB IDRIS MAKAWA ANA DARA GA, , , , , , , , , 2️⃣1️⃣ BY ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , , , , , BISSOMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AL AZIZ, , , , , , , , , , , PAID ONLINE NOVEL DON ALLAH KI BIYA KAFIN KI KARANTA YAR UWA KADA KI DAUKI HAKKIN KOWA A KANKI, , , , Umma kan abin duniya ya isheta yakai mata inda yakai don bata taba tsamanin za,a iya gano su din ba da sauri haka sai lokacin da yaranta suka isa idan girma ya kawo masu zata kwashesu su koma gida. A cikin wanan jimamin na umma ne kuma washegarin dawowan su gida daga asibiti sai kuma ga mota da jiniya har kofan gidan. Kai bayerabe bai iya samun abu ba a rayuwan shi don su basu raina abin gulma gashi kuma ko banza umma ta kasance ba yar kabilan su bace ita. Din wurin namu Ajata sunfi yawa wa yanda akewa kirari da (eleyele) ma,ana farar tatabara da harshen su na yaroba ke nan. Hakan yasa basu tsayawa umma din ba saidai su taru suna kallon abinda ke faruwa idan sun watse su samu abin gulma gun hausawa. Yauma suna jin motan ta tsaya a kofan dan gidan namu na icen bamboo tree sukayo wurin caaa suna kallo. Shugaban tawagan ya fito ya shiga wurin umma sun dan dade tare suna ganawa duk lokacin yan gulman na wurin tsaye sai kara yawa da sukeyi a wurin kowa da irin karyan da yakeyi a lokacin. Acan cikin gidan kuma ummace da Ladi a dakin bayan sun gaisa yana bin ko ina na dakin namu da kallo a cikin tausayi da jimamen yanayin rayuwan da muke ciki a gidan yake fadin a ranshi koda ya kasance basu bane nake nema din. Wa yan nan mutane abin tamakawane matukar ba harkan banza sukeyi a garin nan ba son yawancin hausawa abinda suke bata rayuwan su dashi ke nan idan sun bar gida. Sai gashi kafin yai magana ya fara tsuntar wani abu ga bakin ladi dake ffadin mairo ki fada mai koda ya kasance bakr din duke nema ba. Don ki ceto rayuwan yar ki daga ukuban nan da kuke ciki keda diyan don Allah ya gani yau kusan shekara goma sha da zuwan ku garin nan baki cikin kwanciyan hankali daga ke har yaran ki. Don ma Allah yayiki natsatsa daga ke har yaran kin kama kanki da mutuncinki Allah kuma ya tsaya maku yana duban ku tunda baku raina mashi ga dan abin da kuke samu ga rayuwa ba. Wahalan ya isa haka mairo Allah shike kashewa yana rayawa ba wani ba har idan Allah ya kadara rayuwan ki dana diyan ki a hannun yan uwan mahaifinsu yake ko nan ida kuke sai sun biyo ku sun kashe ku din. Wanan kalamin yasa ya dago kai ya kalli Ladi din dake magana yaga tsohuwar yar barikice ita rikakka da ita don tsoro ya mutu a idon ta ko a yanzu. Kai ya mayar wurin umma din dake duke ya dan saci kallon ta hjy maryam ya fada a zuciyar shi da sauri ya tunota ya gano ko wacece ita din a yanzu duk da wahala da girma yasa a yanzu kamanim ta yadan sauya sosai bisa ga yadda yasanta din. Ga mamakin ta taji yace babba maryam wai dama kece din kuma kuna raye yan uwa suka shiga halin kuncin rashin ku a kusa daku , ? Itama umma din kai ta dago tana kallon shi da alama har lokavin bata gane ko waye a gabanta ba har lokacin don koda ta barsu bawai ta wani sanshi bane sosai a lokacin. Itama kai ta dago tana kallon shi don jin yakira sunan ta kamar yadda yawancin yan gidan suke kiranta da wanan sunan . Duk da kasancewan ta karama sa,an yaran don da wa yandama suka haifeta a cikin su amma darajan kanin mahaifan su tace suke kiranta da wanan sunan a ko ina. Bam, , shedakaba ta furta kafin tace dashi kuma dan wajen yaya DCP ko yace nice baabba. Tace da kama nayi amfani na ganeka amma badon na sheda ka na gane ka ba ya dan murmusa ya gyara zaman shi tare da fadin. Baabba me yasa kika guji gida kika dawo wanan wurin nisa da yan uwa kika zauna anan cikin kunci haka ga talauci da gatan ki baabba? Har yau gidan ku na nan ba kowa a cikin sa kamar yadda kuka tafi kuka barshi ba wanda ya taba ko tsunke a gidan kullun ana duban zaku dawo ko wani lokaci. Kaiya dawowan mu ai yana da wuya a wanan gidan sai dai wani ikon Allah dai kuma idan Allah ya nufi komawan mu gida ta fada a cikin hawayen daya gama wanke mata fuska ko a lokacin. Wani irin ba dadi yaji har cikin ranshi don a matsayin shi na jami,in tsaro ga maganan umma din ya gane akwai wani abinda ta sani na boye da kowa bai gane dalilin gudun nata ba daga gida. Umma din tace dashi ya wajen mahaifana ko sun saura a raye yanzu ko suna wani hali. Kai ya dukar kasa don baisan amsan da zai bata ba a lokacin sai cewa da yayi duk kowa yana lafiya baabba. Sai dau yau gaskiya ba zan kara barin ku kwana a cikin wurin nan ba zamu tafi daku can inda nake in yaso idan kun huta sai muyi magana don naga har yanzu akwai sauran damuwa a tare daku. Amar dake gefen umma din a tsorace yace cikin yarbanci umma tsoron wanan nake ji sosai ya kallo yaron da yai magana yana fadin ya kake abokina yana mika masa hannu Amar din ya make yana labewa bayan umma din. Ladi dai ido ta zuba masu cike da mamaki a ranta na ashe umma din dai mai gatace haka tazo nan ta zauna a cikin rashin galihu. Kai koma meye wanan dalilinn yana da zafi da daure kai gashi sun dsakartar da zancen data so taji don umma taki furta komai ga kowa tun ranan da ta shigo lagos din ta zauna dasu har wanam rana. Yazun kan maggi ya kama kan zabo don hjy karima ta samu gidan a yadda take so don a dan kankanin lokaci ta samu kan kowa na gidan kamar yadda take son samu din. Yanzu kan daga ita sai diyan ta kaje ji bakin Alh din abu kadan ya hau hjy Adda da fada ko zagi ido rufe. A takaice dai yanzu gidan yana kamar under control din hjy karima ne a yanzu duk biye suke da ita a gidan abinda wasu mata da dama suke butin samu a rayuwan su ke nan saboda dan zaman duniya na lokaci kadan mace zata iya sayar da lahiran ta kan hakan a banza. Abida komai yawan shekarun ki a duniya ba zaki tsufa irin na duniya ba a rayuwan ki akan wanan dan zama na lokaci yar uwa zaki yarda ki halaka kanki da kanki don kawai huduban shedan da shedanun yan adam ? Ya Allah kasa mufi karfin zuciyar mu akoda yaushe mu tuna kidhin nan fa na dan lokacine don baki san abinda kika debowa rayuwan ki ba zaman ki na duniya. Shin yar uwa idan har kin mulki kishiya da miji da yayansu zaki fitane ki mulki duniya ko garin ku baki daya ? Kin gani muyi kishi irin na wayewan kai mai ma,ana da fahinta kada ki yarda a cutar dake ke kuma kada ki cutar da abokan zaman naki don rayuwan yar kalilance a tare dake. A irin wanan halin ne da daman da ta samu sa,a gun bokanta a yanzu take taka kambon ta a dakin tafito tana tako daya daya daga part din ta a cikin shirin kwaliyan ta na fita unguwa wanda a yanzu kusan kullun sai ta fita a gidan. Ga idan akace gari ya waye da sabon iya shegen da zata tsiro wa mutane na iskancin kada dai a zauna lafiya don kawai ta musgunawa yan gidan ta nuna ita din itace dai a gaban komai. Har yakai yanzu yan uwan miji da suke yan uwa ga ita hjy Addah suna kokarin juyawa addah din baya don sai su shigo gidan ba tare da sun shiga part din hjy Addah din ba harsu fita. Don kawai a nasu zaton ita zata iya sa mijin su yai masu abinda suke so ko ya biya masu wani bukatan da suke dashi da sauri. Saidai kaiya yan adam basu gane hakan ba don irin matan nan da kansu kawai suka sani sai yayan su akarshema sune masu hana miji yaiwa yan uwasa alheri din don tsaban bakim ciki dake cin su a jini. Wasu kuma zasu dinga amfani da yan uwan mijin suna tatsar dan uwan su wurin ya bayar idan an bayar din sai su rage su tura a aljihun su. Su Nabilane zaune da kawayen su da suka zo gaida dija da bata da lafiya satin nan duk bata fita school na don fever dake damunta a lokacin. Gaida ita suka fara a cikin dan shaku tare da fargaba suma dai kawayen hakan har ta dan wucesu tana karbawa sai kuma ta juyo taja ta tsaya tana fadin. Amma dai baku da hankali duba yadda kuka bata falon nan kamar anyi fada a gidan gala kalo kalo suka fara a tsakanin su. Ta sake fadin ke kuma Dija daga ke har uwar ku da baku san ciwon kanku ba yanzu kin zauna a gida kince baki da lafiya baki fita school . Amma gashi yanzu muryan ki yana tashi har kofan gidan nan don kawai baku san zafin kudin da ake kashewa a kan ku ba ko me ? Oya yanzun nan ku gyara falon nan tasa ku kuma ta juya wurin abokan nasu da fada tana fadin maza kuzo ku fice a gidan nan tunda ba gidan holewa bane nan din. Tashi sukayi a cikin fushi don zagin barnan sunan da tayi masu din ransu a bace Nabila ta dago kai a cikin takaici ta kalleta tana fadin. Anty sunzo gaida Dija ne ba wani abu suka zo yi ba dama nace su fita ta dakawa yar mijin nata tsawa don kawai ta disgasu a gaban kawayen nasu ta nuna su din ba kowa bane a gidan nasu. Nabila da zata bisu ta basu hakkuri itama wani ashar din zagi da ta samu a wurin ta din jin hakan yasa hjy Addah cikin dakewan zuciya ta fito daga dakinta dayafi kusa da falon tana tambayan meke faruwa ne hakan ? Saida tayiwa hjy din wani kallon raini take fadin wani abu zaki tambaya bayan baku iya tsawata wa yaran ku idan suna abinda ba daidai ba. Karima ni din kike fadawa hakan tace an fada kewa da baza a fada maki hakan ba wai dama daurin gindin ki suke samu ta zauna a gida tace bata da lafiya amma yanzu ta dawo falo da kawaye suna muna shewa a gida haka . Shewa kuma wani irin shewa ne da banjiyosu ba a dakina af dama ai ba zaki taba jinsu ba ai tunda da sanin ki suke komai da sukeyi ai. Anan fada yaso ya kara kaurewa sai su Nabila din suka ja mahaifiyar su a cikin takaici suka shige part din su ransu na masu zafi ga wanan disgawan da hjy karima din tai masu a gaban kawayen su Da kuma nema ta raina wa uwansu wayau da take son yi a gaban kawayen su din a yanzu don basu karasa fita gidan ba a lokacin. Duk da saurin da takeyi saida ta tsaya ta batawa kanta lokaci wirin fadan da baida dalili ko nasaba don kawai neman nayi a gidan. Irjn haka take masu koda kallo sukeyi duk da akwai kayan kallo a ko wani part amma basu isa su bushi iska su fito main falo suce zasuyi kallo ba a yanzu kamar yadda suka saba yi a baya yanzun ne zata korasu zuwa ciki. Su dai a takaice wanan ahalin a halin yanzu nasu ya samesu basu da kwanciyan hankali idan garin Allah ya waye suna sauraron da wace zata bullo masu dashi na bacin rai a garesu. Zaune nake nayi tagumi gashi na fada sosai a cikin dan kwana ukkun da nayi a kulle a dakin ina cikin fargaba da tashin hankali wanda ba zan iya musulta shi ba a lokacin. Hakan yasa na zauna nayi tagumi ina zulumin halin da umman mu zata shiga a wanan lokacin na kiyasta abubuwa kala kala a zuciyana kan hakan karshe kuma na shiga jero addua a bakina. Naji an tur kofan dakin duk da ban gane lokaci ga hakan amma ina iya amgani da lokaci in fahinci lokavin da ake ciki a wuni. Hakan yasa na fahinci cewa lokacin dai bayan karfe ukun rana ne la, asar bata karasa yi ba a lokacin. Kofan naji anturo nayi mamakin jin hakan don ba lokacin da ake budewa bane a shigo min da abinci don da safe zasu kawo min abinci lafiyaye da drinks sai kuma karfe dayan rana zasu kawo min shi da yamma kuma karfe bakwai daidai suke kawowa . Ban dagoba ban juya ba don ganin mai shigowa din ina zaune takure a inda nake azaune din muryan da ban taba zaton ji a wanan wurin ba shi naji a lokacin . Umma ce ke fadin mun gode daga kofan na juya a cikin wani irin juyi na firgice lokaci guda ina kallon kofan na mike da gudu zuwa wirin kofan da umma din suke suna shigowa dakin da nake ciki din. Umma i miss you dey carry me come here, i don no wetin i do for dem dey kidnap me here sai na fashe da wani irin kuka mai tsuma zuciya ina fadawa jikin umma din lokaci guda. Har lokacin yana tsaye a kofa tare da harde kafa yana kallon haukan da nakewa umma din sai da umma ta dafa ni tace stop crying he be ur brother Abubakar son of ur aunti nd his father is ur baba broda. Jin haka yasa na dago kai daga jikin umma da sauri na dan kalle ta kafin na juya gun da yake tsaye ina mashi wani irin kallo kamar na tsoro a lokacin. Ta kara fadin a cikin yarbanci da fatan baki masa rashin kunya ba dai na girgiza kai tare da fadin ban ma ganshi ba tunda suka kawoni nan sai mai ban abinci kawai ke shigowa dakin nan ya kawo min. Naji ta sauke ajiyan zuciya a hankali ta juya gareshi tare datin wani yaren da ban taba tsamanin umma jinsa a bakinta ba, ya amsa mata shima a cikin yaren irin wanda tayi mai din . Wurin shi na nufa na bayan umma din tayi min yaren yarabawa akan in gaida shi a matsayin dan uwana kuma yayana. Na duka har kasa a cikin ladabi na fara gaidashi yana mamaki ya amsa min a takaice yana fadawa umma shi zai dan fita don Allah mu saki jiki kamar muna gida a nan. Ya rufo kofan sai lokacin umma tabi dakin da kallo ta ko ina sai kuma ta fashe da wani irin kuka da ban san dalilin yin shi ba a lokacin. Saida tayi mai isan ta don kanta tabari tara fadin sahiba na rabaku da gatan ku da yan uwan ku kan wani dalili da na zabawa kaina daku hakan a rayuwan mu. Ko yanzu ina nadaman komawa a cikin dakin ku da zakuyi don ban san ko dukane suke da akidan dake rike a zuciyar su ba akan ku. Ku yaranane a yanzu fada maku wanan labadin baida amfani a gareku yanzu don ba zaku taba fahintar me hakan da nayi yake nufi ba. Suma din zasu dauka ra,ayunane na son in shakata wata kila ya fitar dani a cikin su bar kowa nawa zuwa nan inda bamu da kowa na jini a nan din. Kallon kaina nayi jin umma tace ba zamu iya fahintar abinda zancen ta yake nufi ba a yanzu idan ta sanar damu niko gani nake ai na girma nakai munzalin da zan fahinci wani abu yanzu ai . Yanzu ba zan iya cewa mahaifin ku yana raye ko baya raye ba sai dai ga maganan Abubakar din yanzu da muka hadu na fahinci dai mahaifin ku shima baya tare dasu. A kullun zancen mahaifin ku shine makomar ku a cikin yan uwan shi don hakane yake taka tsatsak da ke a lokacin baya yarda ki rabi kowa idan ba niba ko shi saiko wasu daga cikin dangina kuma. Yanzu wanan mutumin ya min alkawarin ba abinda zai samu rayuwan mu dagani har ku muddin yana a raye a duniya. Haka kuma ya ban zabi akan idan ba zamu iya zama a can gida ba zamu iya dawowa nan din mu zauna tunda nan muka saba dashi din. Wanan ya kara ban kwarin gwiwan da har na yarda na amince zan je gidan kodan naga halin da mahaifana da yan uwana sule ciki a bayan mu. Tana fadin haka tayi shiru tare da shiga cikin tunane kafin ta mike tana fadin inane ban daki zata kewaya tayi sallah nan ta barmu zaune munyi shiru shi dai Amar yana bin fakin hotel din da kallin mamaki. Kafin nace dashi ban san ko inane nan ba don bansan lokacin da suka kawoni wirin nan daga shiga mota na tsunci kaina a dakin nan. Na fara bashi labdin yadda abin ya farune umma ta fito bayin tace in tashi inje inyi sallah in roki Allah tsari ga duk wani abin ki a gare mu. Bayan mun idar ne umma nake tambayan umma yadda har ya gane cewa ni din yar uwarshine haka. Murmushi umma tayi kafin tace kuna da kama na asali da zai iya gane hakan idan dama yasa da bacewan mu kuma ina zaton ya sani din dama. Umma ban fada bane ya dade yana bibiyata tun baro wancan unguwar da mukayi har zuwa yanzun da Allah ya bashi sa,a akaina yanzu din. Dakin fada min da wuri zamu gusa daga garin nan muje can nisa dasu ko yanzu din bawai zan yarda in bishi haka kawai bane sai na kalli hankalin shi na gane manufan hakan a garemu da yake son yi. Umma idan hakane ni zan bishi naje naga yan uwanmu in yaso indawo in fada maki irin taron da sukai min a can din. Tsawa umma ta daka min tare da fadun ke yarinyace sahiba kina zuwa rayuwan ki zasuyi kokarin nema su kashe ki. Su kasheni umma na fada a cikin mamaki ina kallon umma din don mamakin abinda umma din ta fada game da zuwan namu wurin yan uwan mu din. Kafin umma ta bani amsa aka turo kofan shine wani na biye dashi a baya da wasu trolers guda biyu ya shigo dakin misalin biyar da rabi na yamma. Kaya sawa ne namu dana umma a cikin akwatin don mutumin ya koma ya dauko daya ya dawo dashi nan yake nunawa umma nata sai nawa da na amar yake fadin zamu iya amfani dasu din mu sa ya sayo muna su din don Allah mu saki jiki dashi don bai daukomu da niyar wani ya cutar damu ba a yanzu kuma. ZAINAB IDRIS MAKAWA :ANA DARA GA, , , , , , , 2️⃣2️⃣ BY ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , , , , , BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AL JABBAR, , , , , , , , , ONLINE PAID NOVEL YAR UWA KI BIYA KI KARANTA KI KARANTA A CIKIN SALAMA NA FADA MAKI NA FITAR DA HAKKIN HAKA GAREKI, , , , Ummace kawai ta iya budan kayan da aka shigo muna dashi din nikan ina zaune ina faman tunanen rayuwa a zuciyana. Ina tunanen wai wani irin kiyayyane tsakanin mu da yan uwan mahaifin mu haka da har yasa umma ke gudun mu dasu haka ? Idan ita ummace basa so aimu ba zasu kimu ba tunda sune mahaifan mu ai dole ko su so yayan dan uwan nasu ai na fada. Abinci mai lafiya aka kawo muna wanan daren kan naci nasha na koshi na kuma yi barci mai dadi a ransn duk da tunanen yadda zan ga yan uwana ganin farko a rayuwana. Asuba mun tashi lafiya bamu kara barci ba sai mudin ganin yan uwa da zamuyi mukeyi a tsakanin mu inda nake cewa Amar ai suna da kama da wanan boda din namu sosai. Umma dai dake jin shirmen mu kamar almara wai muna zumudin zuwa ganin yan uwan mu a cikin ranmu muke wanan shirmen haka don tasan shirmene sai anje can gida mun ganewa idon mu abubuwa zasu rikice muna a can din ai wanda bata fatan komai ya samu wani daga cikin mu kuma. Shiru shiru a ranan bamuga wanan boda din namu ba kuma bai leko mu ba tun hakan yana damun umma a zuciya har dai takai ga yin magana a fili game dashi. Nace umma ba zai manta da muba ai tunda kinga ya kawo muna abinci da safe munci don haka muna a ransa wata kila akwai abinda ya tsare shi ga zuwa ne. Wasa wasa har magariba babu almanan shigowan shi dakin da muke din har zuwa lokacin da muka shiga barci. Abubakar din ne zaune a dakin mahaifiyan su bayan sun gaisa sun dan taba hira ya jefo mata tambaya da fadin. Wai umma meye dalilin barin gidan iyalan Abba sambo ne da har yanzu naji ba wanda ke zance a kansu. Wani irn juyowa hjy din tayi kamar ta kadu da jin sunan daya ambata din yanzu a gabanta din tace ina ruwan ka da wanan zance na manya ta fada a cikin daure fuskan ta gareshi. Shiru yayi ya dukar da kanshi kasa kamar mai tunane muryan mahaifiyar nasa ne ya katse shi tana fadin kada ma ka kuskura kace zaka tsoma bakin ka a cikin zancensu a yanzu. Koma ka tsoma din dawa zakayi mutanen da da suka bata cikin duniya ga baki daya babu labarin su har yanzu ina ruwan ka da zancen su kuma. Tunda yake bai taba mamakin kalaman daga bakin hjyn tasu ba irin yau din nan don bai taba zaton zaiji hakan daga bakin ta ba ma. Sai gashi ita da kanta take masa warning kan hakan da ya fitar da bakin sa a cikin rikicin gidan su ya rufa masu asiri. Idan har yaya Nuhu yaji wanan zance ai sai ka lalata komai a tsakanin mu kuma a yanzu gashi Addah Dada daga ranan da tayi zancen su a gaban shi tun ranan ya rufe da ita dashi da wasu yan uwa namu sam basu sin zancen shi a cikin mu ko kadan. Ajiyan zuciya ya sauke tare da mikewa tsaye yana gyara rigan shi yake fadin nizan tafi don ba dadewa zanyi ba na dai shigone kawai. Don a yanzu ya kara tabbatarwa kanshi cewa akwai wani al,amari dake boye tsakanin wanan ahalin dasu yara basu sani ba. Haka ya tafi cike da mamakin yadda hjyn ta nuna mai nan take inda ya doshi gidan shi kai tsaye har ya shigo Nazifa na kan waya don bata dauka zai dawo a lokacin ba . Don shigowan safe yayi masu a bazata kuma hakan bai hana shi sauke mata hakkin ta ba dake kanshi a lokacin. Shine take waya da yar uwanta kuma aminiyarta tana fada mata irin yadda suka kasance a tsakanin da yazo din duk a kunnen shi tsab yaji komai haka yasa ya juya zuwa dakin shi ba tare da tasan da ya shigo gidan ba lokacin. Dakin shi ya shiga ya kwanta cike da takaici da jin haushin wanan yarinyar mai tonon asiri haka garesu. Haba abu yayi mai yawa a zuciyar shi da zancen hjyn su zaiji da shi da sukayi dazun nan ko da zancen wanan sakaran yarinyar da take wai matsayin mata a gareshi yanzu. Wani iri yake ji a zuciyar shi haka yasa ya dauko wayan shi ya kunna kira,a a cikin shi ko zai rage jin abinda yake ji a ranshi din lokacin. Cikin ikon Allah kuwa ya fara jin zuciyar shi tana sauka masa har zai iya yin tunanen mafita a kan mu a lokaci don duk wani zafi a yanzu ya daina jin shi kuma. Baida wani manufa a yanzu daya wuce ya tunkari daddy su da wanan zancen yaji ra,ayin shi akan hakan. Wayan shi ya dauko ya kira layin mahaifin nasa duk da yasan ba lalai bane ya sameshi a yanzu don yasan lokacin aikine a lokacin. Sai gashi cikin sa,a daddy din ya dauki wayan nasa suka gaisa bayan sallama dashi suka dan taba hira kafin ya jefo mashi tambaya da fadin. Wai daddy wanan zancen iyalan Abba sambo da suka bata a ina ya kwana yanzu ne don gaskiya bai kamata ace an fita batun su haka ba suna can cikin duniya suna wahala. Tun bayan da mukaje neman su din nan wanan zancen yake damuna daddy sosai wallahi ya fada cikin sanyin rai. Mahaifin nasa ya tare shi da fadin ka samu wani labarine game dasu a yanzu ya tambayi dan nasa cikin kaguwa Abubakar din yace. No daddy naji kawai ka daina wanan zancen ne kuma shine na tambaue ka ya fadawa daddy din a sanyayye kamar bai damu ba. Watau Abubakar idan har bamu taimaki ahalin nan ba nasan sai Allah ya tambaye mu gobe kiyama don yadda alhakin neman nasu ya rataya yanzu a kan mu . Sai dai nasan da yawa daga cikin mu basu damu da hakan ba ni kuma yanzu abubuwa sun hanani wanan binciken a kansu yanzu. Daddy ka ban baki tun ban bar lagos ba na nemo makasu a garin nan idan suna nan cikin sa don wanan yarinyar da na gani gaskiya tana mugun kama da jinin gidan namadi daddy sosai. Moddibbo kabi sannu kada wani yasan da wanan zancen koda mahaifiyar kane don sanin hakan yana iya jawo maka matsala da yan uwana a yanzu. Duk da nasan kai din namijine jan gwarzo zaka iya komai kace zakayi a rayuwan ka a yanzu saidai ina kara fadama da kabi wanan maganan a sannu har in zaka iya hakan . Don nasan ba banza suka bar duk wani wanda yayi yunkurin dawo dasu a cikin muba a yanzu din don muggan mutane masu amfani da al,ada bisaga addini shine kawai akidar da suka rike don jahilci. Kada kaji komai daddy a yanzu a kaina insha Allahu adduan ku yana amfani a gareni a kullun dan guntun murmushi mahaifin nasa ya sake mai don jin abinda ya fada a lokacin. Wai rikici ya fada a fili bayan ya kashe wayan yana mamaki kan wani shirka can zasu jefa wa yan nan mutane haka a cikin wanan ukuban rayuwa. Abu na farko da zai fara shine ya tabbatar da mun samu mun murmure kafin mu koma a cikin yan uwa din sai kuma zancen karatun yara idan bai manta ba ai ya taba ganin yarinyar saye da uniform a tsohon unguwar su da suka baro. Jin an shigo mai dakin yasashi kara daure fuskan shi sosai a lokacin don yau zai nuna mata ko shi waye don taji dadin gulma da tushe. Har kwana uku bamu ji duriyan shi ba a wanan lokacin gaskiya ba umma ba har mu din mun fara shiga halin damuwa ga hakan. Muna zaune dakin munyi shiru tv kawai da nayi karanbanin kunawa a dakin ke aiki don hankalun mu baya wurin saboda bamu saba da wanan kalle kallen ba a rayuwan mu. Shiyasa ko yanzun ma din muka barshi yana aiki shi kadai don amar ya fara kallo sai barci ya dauke shi a hakan. Sahiba tsoro fa kar mutanen wurin nan su kai ga koran mu nake ji gashi yaron nan tun shekaran jiya rabon shi damu a wurin nan. Kardai ace ya gudu ya barmu don nasani dama ba zasu barshi ya mayar damu gida ba kamar yadda muma gidan ya fice a ranmu ga baki daya. Idan ko har haka din ne har yanzu tsugune bata kare muna ba don gara mu tattara inamu inamu mubar wurin nan baki a lekum idan bai dawo ba gobe. Wani irin ba dadi naji har kasan raina saidai ba yadda na iya ga hakan shiru nayiwa umma din nake hango abin kamar shirine hakan sukai muna dama. Bana fatan goben yayi don abinda umma din ta fada a kan zaman mu a cikin wanan gidan da bamu san kanshi ba muna dai cikin sa zaune kawai ana kawo muna abinci muna ci ga kuma kulawan da muke samu din a wanan wurin. Haka din kuwa Allah yai dare gari ya waye ina ta tunane da zullumin akan zancen mukaji anyi sallama a kofan dakin namu za a shigo. A Yanzu kan na sheda muryan shi ko a ina naji don saurin fahintar da nake dashi din a kaina, ummace ta amsa mai ya karaso ciki ya samemu. Muna zaune a cikin kayan da dai ya san mu dashi har lokacin don ba wanda yai amfani da nasa kayan da ya sawo muna din. Da alaman baiji dadin hakan ba daya gani ya dai daure suka gaisa da umma yana bata hakkuri kan rashin ganin shi da bamuyi ba na yan kwanakin wai tafiya ya kamashi ya tafi kuma ga ba waya a hannun mu yasa bai sanar damu ba. Umma tana fadin ba komai ai tunda Allah ya dawo muna dakai lafiya nika har na yanke shawaran yau idan bamu ganka ba sai mu bar wurin nan a yau din. Haba umma ai ba zan kawoku nan in tafi in barku a nan din ba cikin hotel koda bansan darajan ku ba nikan hausan da sukeyi sai nake jin shi a kunne na wani bakon hausa ne ba wanda muka dan koya a wurin umma din bane muka iya. Sai lokacin na samu daman gaidashi da wuni ya amsa min a takaice yadda ya saba ba sakin fuska a gareni ko kadan . Magana sukeyi da umma din wanda bana fahinta kan me suke maganan yayin dana dan saci kallon shi da kyau a lokacin ne kuma na fara tunanen a inda nasan shi farkon ganina dashi. Sannu a hankali nake tunawa har na gane ai shine wanda ya zo wurun gasa masarana a lokacin wani tunane nayi nace watau ke nan tun a lokacin ya fara bibiyata ke nan. Nidai ko ma meye ya kaimu gida shine bukatana a yanzu don banda wani buri daya wuce in ganni a gaban yan uwana in san su su sanni abar kira muna da bamu da dangi. Muna yawan samun wanan matsalan tun dai zaman mu a Ajagule gidab su iya wale suna yawan yi muna wanan gorin kuma hakan yakan dameni sosai. Don haka na kwamacewa komawan mu gida a yanzu din wirin dangi zaifi muna ko dan tsare mutuncin muna zaman diya mata dagani har umma din da maza ke kawowa harin tayawa ko wani lokaci da sunan iskaci. Zancen kararun mu sukeyi da umma ta fada mashi komai kan dakatar da kararun mu din da mukayi a yanzu bama zuwa boko saidai neman abinda zamuciwa cikin da nakeyi a yanzu. Ya nuna rashin jin dadin shi ga hakan yake fadin ba zamu bar garin nan ba sai ya karbo muna transfer din mu ga hannun shi zamu tafi. Naji dadin jin wanan zance na karatun don a gaskya ina son yin kararu sosai a lokacin nan dai da yadda zanyi ne kawai yasa na daina zuwa din. Sun dan jima da umma suna hira kafin yayi mata sallama ya barmu sai a lokacin nake fadawa umma ko shi waye shine wanda ya ke ban kudin nan dana fara kawo mata a lokacin. Ummake fadin mena fada maki tun farko zuciyana ya bani run a lokacin cewa akwai abinda ke shirin faruwa damu a lokacin. Baki yarda da hakan ba yanzu ko kin yarda ko to hakana ma a can gidan da kuke son zuwa abubuwa zasu faru da dama kan komawan mu din cikin su da zamuyi a yanzu. Jikina nayi sanyu don na fara fahinta cewa dai akwai abinda umma ke nufi da hakan da take yawan fadi ko wani lokaci niko wanan wani irin matsala ne haka da zamu fuskanta gun dangin mu din kuma. Kwana biyu sai ga ya Abubakar yana fadin mu shirya zai tafi damu school din da muka bari mu an so transfer din mu. Dole muka bude wanan akwatin mu saka kayan daya saya muna din sai dai duka kayan bazan iya sakasu a jikina ba don ban saba da saka irin su din ba. Duk yadda umma taso in saka na kasa sakawa don ko zanin ban iya daurawa ba haka ya shigo ya samemu muna wanan rikici da umma din. Take fada mai yayi dan shiru kafin ya juya ya fita sai can gashi ya shigo da kaya masu yawa dogayen riguna masu kyau daidai size dina da wasu wando da riga sune daidai dani ba wanan daya sayo din da farko ba. Na saka wandon jeans da yar riga daya dace mai dogon hannu na kawo hijjab dina na dora sama sai naji wata daban can dani ga zafi da naji atake ya fara rufeni don hijjab din. Haka dai na daure muka tafi ba wani wahalan da muka samu don dan bayanin dayai masu kan rashin ganina din da basuyi ba . Sun taimaka sun bamu ba tare da yi min repeat ba din sun fada mai i can make it saboda ina da kokari sosai a karatuna din. A hakan muka barsu muka nufi makarantar su Amar can madin ba wani matsalan da aka samu sun bayar da transfer din yadda ya dace. Muka dawo inda yai muna masaukin dole din muka samu umma duk ta damu da dadewan da muka danyi bamu dawo ba a dakin. Kai zan iya cewa wanan bawan Allah yana da saukin kai don sai idan baka zauna dashi bane ganin farko zaka daukeshi wani maijiji dakai ko wani mugu can. Amma a gaskiya ba hakan yake ba sam don halin shi a sanyayye yake komai nasa don na dauka da umma tace dashi akwai abinda take son dauka a can dakin mu na semi na dauka ba zai yarda da hakan ba sam. Sai gashi tana fadi a cikin irin ladabi sa yace ba matsala zai kaimu mu dauko duk abinda mukeson dauka a can din kafin mu wuce. Wanan tafiyan ni yaiwa dadi don akwai inda nake ajiyan kudi a dakin ko umma bata san da hakan ba sai ni kadai nasan wanan abin. Haka aka kwashe mu zuwa semi din mukayi sallama da duk abokan arzikin mu na nan kan cewa zamu tafi muga gida wata kila mu dawo ko ba zamu dawo ba idan mun tafi din. An dan nuna jimamen hakan don sabon da muka danyi dasu nikan na faki ido na hako kudina da nake binnewa a dakin cikin kyalen da nake daurewa a cikin sa. Kudin na nan kamar yadda na barsu ba a taba ko kwandalaba a cikin shi duk da mun samu an dan taba kayan dankin an binciki dakin ga baki dayan shi. Duk da wanan halin ba bakon abu bane a wanan garin don da zaran kadan daga na kwana biyu hakane ke kasancewa ga mutum dama. Mukai sallama tare da amsan laban wayoyi idan munje zamu kirasu yadda mukace dasu ke nan a lokacin. Haka muka rabu dasu ba dadin rai don sabon da akayi da juna na dan lokaci. Mun dawo hotel din da muke ne da kwana biyu ya gama duk wani shirin tafiyan mu din zuwa arewa a daidai lokavin mahaifinsu daddy ke nan shima ya dawo kasan da kwana biyu. Zo kaga murna kan don ma umma ta hireni da abubuwa da dama kafin mu fito tayi warning dina sosai kan na kama kaina da kowa don kada a samu a cuta min ga hakan. Karfe shida na yamma muka bar lagos zuwa kaduna state din da nake jin labadin shi a cikin tarihi ashe dama nan ne state dinmu ashe. ZAINAB IDRIS MAKAWA ANA DARA GA, , , , , , , , , , , 2️⃣3️⃣ BY ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , , , , BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AL MUTAKABBIR, , , , , , , , , ONLINE PAID NOVEL YAR UWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA NA FADA MAKI NA FITAR DA HAKKIN RASHIN SANI A GAREKI, , , , , WASA YA FARA, , , , , , , , , , Bin ko ina na airport din nakeyi da kallo da yanayin wurin duk da garin ba zafi amma naji bambamci yanayi da can din don lagos akwai ruwa saidai akwai zafi sosai a can din idan an tashi yi hakan. Wasu lafiyayyun motocine guda biyu suka dauke mu daga airport din zuwa inda zamu don nan san ko ina ba ni kila gara umma idan bata manta ba ta sani ita. Unguwar su ya kaimu kai tsaye don motan mu daban ce da wace ya shiga shi saidai abinda na kula dashi tun shigan mub motan umma batai magana da kowan mu ba sai addu,an da take faman yi a bakin ta. Haka yasa nima nayi shiru ina yan adduan dana saba a bakina na neman tsari ga abinki da dan adam yakeyi don neman kariya. Daga can cikin motan da yaya Abubakar yake yake waya tare da tambayan daddy da fadin daddy na shigo kaduna kana gidane yanzu ? Daddy din ya bashi amsa da eh moddibbo ina gida ai kasan baja fita da dare ni bayan magariba ina gida ko wani lokaci. Na sani daddy zamu karaso yanzu mu sameka a falo ya fada kai tsaye yana kashe waya yabar mahaifin nasa da mamaki don sam bai kawo da mu din yake tafe ba saidai tunajen shi da wasu bakin abokan aikin shine kila yazo don yadda yaji yana masa magana a gurguje da alaman dai akwai wani abu. Don haka daddy din ya mike zuwa falo inda suke karban bakin su a gidan hjy karima da zata shigo da ruwan zafi a flask ta tsaya tana mamakin ganin ya fito take tambayan shi don a zaton shi wurin hjy zai tafi. Ina kuma zaka a wanan lokacin ta tambayeshi wucewa yayi inda zai tafi kai tsaye ta juya ta shiga da flask din dakin ta aje. Wani get da sojoji ke gadin gidan aka bude motoci suka shiga lokaci guda darene a lokacin don haka kowa na cikin gidan sa a lokacin. Saida yayi magana da umma kafin ya juya ya fara tafiya zuwa ciki muka fito daga cikin motan kai tsaye duk da tafiyan dadi mukayi ba mota muka bi ba jirgine kuma daga airport zuwa gidane a yanzu. A hankali muka fara bin bayan shi zuwa cikin gidan daya dosa din muna binshi a baya ya rigamu shiga ciki yake fadin daddy ashe ka fito falon ko ga bakin naka nan na kawo maka zasu shigo. Baki daddy ya tambaya a cikin mamaki don bai fahinci dan nasa ba sallama umma data daga labule tana shiga dakin tayi muna biye a bayan ta muka shigo. Da wanan bakon yaren da naji umma tayi nan ma din shi take magana dashi da wanan daddy din a cikin yaren filatanci. Naga ya daga kamar a firgice da mamaki karara a fuskan shi yana fadin Mairo kece ta hanyar nunata da yatsan shi har hamnun shi na rawa. Umma tace nice yaya ina wuni mun sameku lafiya ya bayan rabo takai kasa tare da dukar da kanta kasa tana hawaye. A cikin karfi hali na iya fadin good evening sir sai lokacin ya dan kalli inda muke ina saye da wando wanda ke hade da riga blue sai gyale fari da nayi rolling din kaina dashi. Innalillahi wa inna alaihim raji,un ya fada yana mai kura muna ido dani da kanina da muke tsaye kimkyam muna kallon shi muna na rike hannun Amar din koda taka taso a hakan. A hankali ya dago hannu yana fadin come to daddy kids da sauri kamar muna jiran jin hakan daga gareshi muka nufi inda yake tsaye din ya mika hannayen shi garemu muka fada mai sai kuka yazo min jin dumin jinina da nayi karo na farko da wayau na a jikina. Kuka sosai nakeyi shima Amar ganin inna kuka yasa ya barke da kuka daddy ma da ya Abubakar duk kukan sukeyi ba mai bawa wani hakkuri a falon. Jin kukan ne da iyalan shi daga ciki sukaji Nabila data fito zuwa kitchen taji ana koke koke a falon ta koma da sauri ta fadawa hjy yasa suka fito gaba dayan su. Anyi daidai itama hjy karima taji tafito duk sukayo falon gaba dayan su lokaci guda kowa yaja yayi turus a cikin katfin hali hjy din ta karasa tana fadin. Lafiya Alh suwaye suka zo haka ta fada don umma kanta yana duke tana rusan kuka don haka bata shedata ba a lokacin. Har lokacin da hjy ke maganan muna jikin daddy din muna kuka sosai shima yana hawaye maidan sauti kafin ya dago yana fadin . Addah kunga halin da rayuwan yan uwan mu diyan mu yau yake ciki saboda sakacin da son kai irin na wasu daga cikin dangin mu ko ? Jin an ambaci sunan hjy Addah da umman mu tayi yasa ta dago kai a cikin sauri tana kallon inda hjy din take tsaye suna kallon mu cikin tuhuma don irin hjy karima kan ta dauka mu din diyan daddy ne na cikin sa daya haifa da wata mace a ganuwar aikin sa a lokacin da yake fita garuruwa yin aiki. Hjy Adda ko ba wanan tunane tayi ba ita zuciyar ta yafi tafiya da cewa wasu ne dai can na daban da suke da alaka dashi daddy din. Dago kan umma sai a idon hjy Adda din wani iri tayi ta danja baya tana dafe kirji da fadin Mairo kece a gabana ko mafalki nakeyi. Sai ta kai zaune saman kujeran dake bayan ta tare da sake hawaye suna zuba mata lokaci guda. Da kyat ta iya budan bakin ta tace Mairo ina kika shiga haka tsawon wanan lokaci haka kin tafi babu labarin ki bana diyan ki. Hannu daddy ya dagawa hjy daga inda yake tsaye din hjy tayi shiru hannu daddy yasa ya dagoni daga jikin shi a hankali ya fara min magana kamar rada yana fadin. Stop crying my daughter daddy is with you now yasa hannu yaci gaba da share min hawaye kafin ya koma wurin Amar ya kara jan shi a jikin shi shima. Hjy karima dauke su ki kaisu part din can na ciki da babu kowa ku kuma ku dauki yar uwar ku kujata zuwa ciki . Yana fadin haka ya juya inda Abubakar ya ke zaune yana fadin jeka gida ka huta harda safe yana fadin haka ya mike shima dan nasu ya mike ba tare da yayi magana da kowa ba ya fice gidan zuwa gidan shi. Falon ya saura damu dasu hjy ana kalo kalo kafin hjy karima tayi karfin jalin fadin mujeku zuwa ciki ku huta. Da kyat umma ta iya mikewa har lokacin tana rusa kuka mai tsuma zuciya tabi bayan hjy zuwa ciki muma muka bita. Wani part din su dake can kuryan gidan aka kaimu kafin Asabe mai hirkin gidan ta kawo muna wani lafiyayyen abinci sai kamshin ke tashi na man shanu a cikin sa. Duk muna zaune a cikin dar dar har lokacin kafin hjy Addah din ta shigo dakin Asabe da yaranta na biye da kayan mu da muka bari a cikin mota. Hjy Addah din ce ta nuna inda za a aje muna suka aje suka fita yake fadin Asabe ki dauko abin shara ki gyara dakin nan don Allah. Kafin ta juyo tana fadin au har yanzu zaune kuke gara ki saki jiki ko yaran nan zasu sake nasu jikin ki tashi Mairo kishiga bayi kiyi alwala kiyi sallah kuci abinci lokaci yana kurewa. Tashi umma din tayi zuwa ban dakin data nuna mata kafin ta juyo inda nake zaune bakin gadon tana fadin . What is your name na dan dago manyan idanuwa da suka rine nace Sahiba ma ta nuna Amar tana tambayan shi yace Amar ta dan kura mai ido sosai kafin ta numfasa tace feel free tana dan taba kafada na. Dan murmushin yake nayi mata kawai na dukar da kaina kasa na dan lokaci saiga wanan mai aikin ta shigo take fadin yawa Asabe a canza masu zanin gadon nan a gyaro ko ina matar dan uwanane data bata da yaran da dadewa Allah ya baiyana muna ita. Aikuwa ga kama nan da diyan na gani sosai ta fada tana kallon mu tare da fadin sannu sannun ku da zuwa. Ai da alama wa yan nan basa jin hausa nake gani tare da dan kallon mu din kafin ta juya wurin Asabe din tana fadin don Allah fara da falon sai su koma can su jira har a gyara nan din. Daga haka ta juya ta fice dakin yadda tace hakan akayi don mun koma falo aka gyara bedroom din. Umma tayi muci abinvin mun kasa don wanan kamshin manshanun dake ciki bamu taba cinsa ba sai wanan ranan haka aka rufe abincin ko umma bata cisa ba. Haka muka kwanta a takure a dakin da muke din saman gadon dake dakin zan iya cewa ranan umma batayi barci ba don na falko da dare na sameta tana sallah. Na dawo na kara kwanciya sai barci don dadin barcin da nake ji a lokacin ban san a inda ma muke ba don ga gado ga sanyin AC duk a dakin. Washe gari koda muka falka gari ya waye umma tana zaune saman salaya din da tayi sallah a wirin tana dan jan tasbi ta tare da maida gaba gasbas tana kallo. Ban dakin na shiga na yo alwala nazo nayi sallah ina gamawa na gaida umma na shiga gyaran dakin da muke din har falo saidai ban yarda na leka wajen gidan ba don gidan ma tsit yake a lokacin kamar ba kowa a cikin sa. Bayan na gama na shiga wanka na fito na shirya a cikin dan wani gown baki mai dan adon walkiya a gaban rigan. Inda Allah ya taimakeni shine bai yarda ya dawo da mu gida ba saida muka zama mutanen arziki yadda ba za a gamu a raina ba idan anganmu a gida. Don haka kaina yasha gyara ban damu da dan kwali ba hakana na koma na kwanta saman gado sai wani barcin ya daukeni kuma. Muryan hjy Addahce ya tayar dani lokacin da take fadi mairo ya gajiyan hanya yaya yaran kuka kwana ta amsa da lafiya. Mairo ina kika shege haka tsawon wanan shekarun da kuka kwasa baku gida wanab dan kuma gashi da ganin shi shima dan gidane shi don ya debo kamar mazan gidan mu sosai. Banji me umma tace ba don ina mikewa na mike zaune ina fadin good morning ma ta juyo tana amsawa a cikin sakin fuska a garemu. Dole ne ya kasance ba zamu iya sakewa dasu ba koda kuwa mun tashi a cikin su balle al,adun su yanzun da muke gani bakon lamari a idon mu zama da hausawan. Naji tana tana tambayan umma din da cewa meyasa bamuci abincin da aka kawo muna ba da daren jiya din ko tabawa bamuyi ba. Umma din ne ke fada mata cewa munce bama cin manshanu ta dan kallo inda nake da mamaki tana fadin a ikon Allah dan filo ne zaice baya cin man shanu kuma ? Har saida ta fita nake tambayan umma da ita din wacece a wurin mu take fada min itace mahaifiyar Abubakar daya kawomu gida. Akan hjy Addah din ta fara min bayanin yan uwa take fada min yadda muke da ita maimakon inji dadin hakan sai naji wani iri a raina na ba dadi. Don su gasu a cikin wadata amma sun barmu ba tare da damuwa da muba a cikin duniya cikin wahala duk da nasan hakan akwai laifin umma a cikin hakan don itace ta tafi damu ai. Na koma tambayan kaina me zaisa umma ta bar yan uwanta irun haka har ta shiga duniya damu ta kyalesu na tsawo shekaru haka. Wanan zancen kan gaskiya abin dubawane ga duk mai tunane dole fa akwai wata a kasa da ya jawo barin umma din gida damu. Abincin da ladi ta shigo muna dashi nake bi da kallo tare da gaida ita da gurbatacen hausa na da sannu kawai ba tare da karawa ba. Son umma ta fada min kada in nunawa kowa cewa ina dan jin hausa dagani har Amar din mu boye dan hausan da muke ji a gaban dangin namu. Sai gashi ko farawa da iyawa Asaben ta fita tana fadin ikon Allah yara sun koma kamar wasu kabila haka dasu nikan idan kin kwana yi mun shegeb yaren ku ainba zan gane me kike fada na yarinya. Kallon umma din nayi tayi murmushi kawai mai nuna kin fara gane me nake nufi yanzu ke nan dai daukan abincin naga umma din tayi ta duba. Ta dade tana kallon cikin kulan abincin kamar tana nazarin wani abu kafin ta juyo wurina tana fadin in taso munci abincin da aka kawo muna din na dan bi abincin da kallo kafin in tashi zuwa inda abincin yake. Wanan kan munci sosai don shayi ne da bread sai dankalin turawa da kwai da kosai da koko aka kawo muna abin kari din. Mun gama misalin karfe gomana safe daddy ya shigo har dakin da muke din suka kara gaisawa da umma muma muka gaida shi ya amsa yake tambayan sunan mu muka fada mai sunayen mu. Hjy Addah ce ta shigo falon ganin haka a cikin yaren yarbancin umma tace damu mushiga daga ciki muka mu barsu a falon. Koda muka shiga din hankalina bai kwanta ba don haka na dawo kofa na make ina sauraron su duk abinda ake fada a kunnuwa ina jinsu naji daddy na fadin. Daddy sai a lokacin yake tambayan ta ya bayan rabo mairo ashe kina lagos duk wanan neman da ake maku ?. Kin shige cikin duniya da yara haka kinyi shiru kamar baki da gata haka mairo ai mutum bai yanke irin wanan hukuncin ya tafi shiru haka har wanan dan ma da kika haifa a can gasu yaran gaba daya basu san mu. Gara dai ka tambayeta tun kan zance yakai wirin yan uwa idan wanan yaron dan Sambo nd duk dai ya kwaso zubin gidan mu gaba daya shima don har ince kaf din jikokin baba babu wanda ya kwaso shi da komai kamar yaran nan wallahi. Gara dai da kika ba kanki amsa karshe don ko makaho ya laluba yasan yaran nan jinin gidan mine su don babu ida suka rage gida wirin kama. Da kuma kike zancen wani yace wani abu yanzu wa kike tunanen zan dagawa kafa cikin su a sake wullakanci ga zuri,an sambo kuma ? Wanda dai da akayi mai dashi da iyalan nasa ya isa haka sai dai yanzu a nemin hanyan tuba da gyara gaba kuma amma a yanzu ba mai kara hada kai dani ayi irin shirmen da aka tafka a baya. Ko wancan karon bani nan ne har haka ya faru suka bar kasan bada sani ba aida ina nan duk abinda za ayi saidai ayita amma ba inda zasu tafi a lokacin. Amma Alh ka san yaya Nuhu fa ka kuma san halin sa da kudirin shi akan duk wani wanda ma yai magana game dasu tunda ya dauki abinda zafi sosai haka. Da wani irin kallo ya juyo yana kallon ta a cikin takaci kafin yace shi din Allah ne waliyin Allah da zai saka wani dokan shi na banza yana amfani da mutane kamar wasu jahilai yana kaiku ga halaka. Yanzu din abar min su din a nan gidan zasu zauna tare damu babu inda zasu har sai mai rabuwa ta rabamu ina dai dukiyan daya rike a hannin shi ya zama nasa a yanzu duk yake wa wanan fadan haka ? Yaje yaci ko ince suje suci shida masu binshi a yanzu din Allah ya basu wani wanda yafi wanan din daya rike ina shike nan dai duk dai wanan abu akan abu daya akeyiwa fadan nan kuma sun karba basai a barsu su zauna lafiya ba. Ni dama ai ba wai ina cikin zancen nasu bane kasani amma su yaya din nakejiwa a yanzu don yadda suka dauki zancen nasu na gani. Kuma hakan zai iya jawo su kulla da kai kan hakan don ba kyau kega halinsu ba ka sani don, , , , ke dakata don Allah ya isa haka ya fada a kausashe. Alokacin kuma Abubakar dake tsaye a kofa ya karasa shigowa falon namu fuska a daure jikin shi yayi la,asar don jin abinda mahaifanshi ke fadi. Daddy bai dakata da abinda yake fadi ba a lokacin don ganin Abubakar din yaci gaba da fadin shi Nuhun Allah ne ? Ko yayi kaman Allah a garemu da Allah zai fadi abu saboda wani akidan banza nasa ya sauyawa mutane zancen su don jahilci ko a da can ke kifi kowa sanin bana cikin wanan shirmen ni. Abinda kikewa tsoro dai shine Nuhu ba Allah ba shi Nuhun kanshi ai ya sanni yasan koni waye don haka ne ma zasu zauna anan gidan tare damu babu ida zasu tafi koda ita mairo tace zata bar nan din ba zata zauna da muba yaran nan babu inda zasu tafi sun dawo gida ke nan har abada koda bana raye kai Abubakar karike min su ammana kamar yadda mahaifin su ya bar muna amanan su a baya. Allah ne ya karbi addu,ana har yai sanadin ta tsatsona zasu dawo a garemu da zancen nake kwana dashi nake tashi don nasan Allah zai tambayen mu kan sakacin da mukayi akan yaran nan. Nasan kuma zasu so ja da hakan don su a nan Allah ya ajesu akanyin hassada nima kaina aiba barina sukayi ba na sani duk da kuwa bana shiga zancen kowan su a yanzu. Wanda yace yasan ni inyi dashi wanda baisan ni ba kuma ya zauna lafiya nima in zauna sai zancen dukiyan yaran nan ya zama dole duk wanda yaci dukiyan su a yanzu ya fito masu dashi abasu abinsu. Wanan wani zance kakeson daukowa yaya don kasan yadda ko wurin raba dukiyan man aka samu matsala balle yanzu ace za a bawa masu hakki hakkin su. Allah ya fisu akan hakan mommy hakki kan dole su dawowa yara da hakkin su don sule da alhakin abinsu ba wani ba. Don Allah ku barsu da shi yaya matukar zasu ban min yarana a raye don sun fada sun kara fada a gabana ina jinsu sun fadawa mahaifin yaran cewa zasu kashe shi ko su batar dashi kuma suci arzikin shi. ZAINAB IDRIS MAKAWA A NA DARA GA, , , , , , , , , , 2️⃣4️⃣ BY ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , , , , , BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM, AL KHALIQ, , , , , , , , ONLINE PAID NOVEL YAR UWA KI BIYA KAFIN KI KARANTA A CIKIN SALAMA NA FADA NA FITAR DA HAKKI RASHIN SANI A KANKI ALLAH YASA MU CIKA DA IMANI AMIN, , , , , , , A satin da zan rasashine ya fara danyi min wasu bayanen da ban san ma,anan su ba yana fadin. Kin jaf takardun komai nawa suna a cikin ginan nan na boye su ya nuna min wani bari na kofan dakin shi yace a nan suke nan nake aje komai a cikin ginan nan. Kuma ina son kiibi yan uwana kaf a sannu koda bayanane mairo don har gobe ba kaunata sukeyi ba na sani suna da mumunan akida a kaina tun tasowana a cikin su Allah ne kadai ke kaunana yai min wanan daukakan akansu. Ban dauki maganan shi da wani muhinmanci ba raina don na saba jin hakan a wuri shi ko yaushe yana fada min hakan. Sai ranan da zasu halakashi ne da safe nake tayar dashi yake fadin idon shi biyu ai tunda ya idar da sallah bai koma barci ba don mafalkin da yayi da su yaya Nuhu suna binshi zasu halakashi. Jin haka a bakin shi yasa nabishi da kallon mamaki nakai zaune daga inda nake tsaye a cikin mamaki jin abinda ya fada min din. Karfin hali da jarunta ya nuna min kamar zancen bai dameshi ba shi a zuciyar shi ganin da yayi kamar na damu yake fadin kada wanan ya dameki fa mairo wata kila sherin mafalkine hakan. Ai ba yau ka fara fadin haka ba kuma abin ya tabbata suma sheri daga karshe abin ya zama gaskiya. Kedai ki dauka a mafalkine wanan koda ma hakan zai faru yar nan nake ji da abindake cikin cikin ki a yanzu yadda zasu kasance a cikin makiyan su nan gaba. Duk da nasan Allah ne gatan bawa kamar yadda ya rayani a cikin su nagirma na zama haka a yau duk da ba,a son inkai hakan din ba kuwa. Idan har hakan ya kasance ki dauki yaran nan kiyi nisa dasu da gida inda ba a jin labarin ku ki renan min yarana a can yafi min komai kwanciyan hankali. Hawaye umma tasake masu dumi tana sheshekan kuka a lokacin tace a karshe dai ya mayar da zancen kamar alamara a gabana ranan bai fita ba sai wajajen karfe hudu na yamma bayan sallah yace zai dan tafi unguwa. Bayan fitan shima ban iya aikata komai ba don jikina da yayi sanyi da wanan zancen daya fada min game da yan uwan shi da suke binshi da sheri haka kamar ba jinin su ba shi. Yarinyar dake gefena a kwance na dan kalla sai tausayin kanmu ya kamani har in abinda ya fadin ya kasance gaskiya yaya zanyi da yaran nan ke nan. A take zuciyata tayi matukar yin rauni nakai hannu na shafo dan dake cikina wasu hawaye naji sun zobo min daga idona shar a dalilin tausayin kanmu danaji lokaci guda. Lokaci mai tsawo na dauka ni kadai a dakin sai wanan yar dake barci a gefena ina kuka nayi nayi hawayen su tsaya min abin ya gagara hakan. Sai gashi ya dawo gidan bai wani jima da fita ba na ganshi ya dawo rai bace ya shigo falon yana fadin wai ki duba wanan mafalkin da nayi da mutanen nan ashe zasu fito min da wani zancen banzane haka kuma. Ja yayi ya tsaya yana kallona don yanayin da ya ganni a ciki na tashin hankali ya fara fadin me ya faru kuma wani yazo gidan nan a cikin sune yana tambaya tare da zuba min ido yana son jin amsa daga bakina a lokacin. Nayi kwal kwal da ido na kasa magana takowa yayi inda nake yana fadin ke daina kukan nan ki fada min me sukai miki ne ? Ganin yadda ya rude yasani fadin basu zo ba basu fada min komai ba maganan da mukayi da kaine ya tsaya min a raina nake tunane. Ya dan kauda kai yana fadin Allah ya fisu don ba zasu taba shefe tarihina a bayan kasa ba kamar yadda suke son yi. Yana fadin hakan ya tashi ya shiga daki ya barmu a falon saida ya dan dade a dakin kafin na sameshi a ciki zaune yayi tagumi yayi shiru yana tunane. Ban iya masa magana ba har na aje mai flask na fita daga dakin zuwa dakina duk da ba raba daki mukeyi ba ranan a dakina na zauna kada na dameshidon naga yana cikin damuwa. Wanan ne ranan da ba zan taba mantawa dashi ba a rayuwana ranan da kullun ina tunata a rayuwana kwakwalwata takan neme zaucewa . Raina yakan sosu zuciyana takanyi baki kamannina ya kan sauya numfashina yakan dauke har wani lokaci nakan ji da rayuwata gwanma na mutu na huta idan badon yaran nan ba dake gabana. Don na koma dakin ganin irin hadarin daya game gari a daren ranan yasa na koma dakin dubashi na samu ya idar da sallah magariba yana zaune yana addua. Na dan tsaya ya idar yajuyo yana fadin meye laifina a cikin su mairo don Allah ya azurta ni fiye dasy suka dauko canfi suka dora min akaina. Sunce ni din dan shege ne a cikin alhalin mu don kawai uwata ta sameni a bakwaini ni nasan ba da zina aka haifeni ba kuma sun koma sunce mahaifiyata itace mai kandun baka ta kwashe arzikin gidan su ta bawa danta. Wanan mairo wani irin camfine da jahilci a kansu sun manta Allah ne mai bayarwa da hanawa idan yaso. Kasa ci gaba da bayanin yayi ya dukar da kanshi kafin ya dago yana fadin bazasu barni ba subar diyana don wanan bakin akidar nasu na camfi da suka saka a zuciyarsu. Sunce ni din da jinina idan muna cikin su ba zasu taba arziki ba a duniyan nan sai ya fashe da kuka zaune nakai ina bashi hakkuri akan zasu soshi zasu dawo suyi da sun sanin hakan da sukeyi a karshe. Yace kaiya mairo baki san su bane su din fa jinin fulanine gaba da baya akwai riko da gaba garesu koda na shekara dubune kuwa. Yar nan data tashi tana kuka yasa na barshi a dakin zuwa wajen ta dan rarashinta nakeyi har barci ya daukeni ban sani ba a wurin . Can misalin karfe biyun dare a cikin barci naji wani kara kamar fashewan abu a gudan ashe karan bindigane nake jin . Kafin na fara jin murya na tashi kasa kasa a gidan suna fadin ai mun fada ma ba zamu barka ba ka dauka wasa ne kome ? Daukan yarinyar nayi na goya a bayana a cikin rawan jiki na fara sanda na fara fitowa daga dakina dake can dan gaba da nasa Allah ya taimakeni duk hankalinsu yana a kanshi lokacin gaba dayan su sun saka shi a tsakiyan su.. Naji muryan yaya Nuhu yana fadin ka fito muna da duk wasu takardun wanan filin dana bankin ka ga baki daya dana gida muddin kana son ka kara numfashi kaida iyalan ka. In ko ba haka ba wanan na nufin ka dade da kama gida a kiyama kaida iyalan ka ko don kashe ku zamuyi mu kashe banza muga yadda kuma zakaci dukiyan da kake muna kuri dashi din a yanzu. Gabana ya kara faduwa a hankali inajin hakan nayi kokari barin wurin Allah ya taimakeni na samu nafita daga falon ba wanda ya ganni a cikin su hudun da suke gaban shi. Da wautana dakin maigadin mu na samu na shiga shima baya cikin dakin a lokacin sai bayan na shiga ne na boye ashe maigadin ne na tsalaka yana kwance a kasa cikin jinin dake malala daga jikin shi. Goyon dake bayanane ta fara motsi na dan mike ina jijigata sai lokacin na kula da halin da tsohon dake gadin mu yake ciki na zubar jini daga jikin shi ashe shi suka fara kashewa da shigowan su gidan. Innalillahi wa,inna alaihim raju, un suke fada dukka falon lokaci guda jikin su duk ya mutu ga sauraren labarin da umma ke basu har nima daga inda nake a labe ina iya jiwo abinda suke fadi sai hawaye ke zuba min don nagane kan labarin da umma take fada taci gaba da fadin. Allah dai ya rufa min asiri yarinyar ta koma barci a lokacin ina wurin dana boye din a cikin tashin hankalin da bai musultuwa. Ba komai ya hanani fitowa ba a lokacin don irin yadda nake ji a zuciyana sai zancen daya fada min da safiyan ranan akan yana rokona dana boye idan sunzo din ke nan yasan da zasu zo din ke nan dama har yake fadin hakan na tambayi kaina ? Muryan yaya iliya naji yana fadin kun duba ko ina na gidan nan don nasan tana cikin gidan saboda bata je ko ina ba yau ai. Naji wani murya da bansan ko na waye ba yana fadin bata fito ba muryan wani kato yace babu wanda ya fito a cikin gidan nan don ina tsaye wurin nan tun shigan ku ba wanda ya fito a cikin gidan nan sai gawan wanan tsohon dake kwance a nan. Shima yaya Nuhun ya fito yana fada sosai dasu gaba daya yana fadin kada ku bata muna shiri mana wanan matar fa da yar ta dole ne suma su mutu kamar yadda shima ya mutu a yanzu. Don gaba daya nake son a share min babin tarihin su don gaba wa yan nan tsinanun ba zan bar ko a duniyan ba cikin su don barin su wani barazanane a gare mu. Don haka gara mu kashe su ga baki dayan su yadda ba wani wanda zai kawo muna cikas akan komai nan gaba. Takon su naji suna ta bincikena a cikin gidan kafin wani ladani mai zakin murya ya fara kiran sallah sauran masalataiyan cikin gari suma suka dauka alaman asuba yayi a lokacin ke nan. Na sake jin muryan yaya Nuhu yana fadin wanan yar takai shegiya yarinya irin kafiyan tsiyar dake ga uwarta ke nan take dashi. Don ance kar kowa daga cikin dangi ya bashi yarsa amma uwarta ta dauketa don kwadayi ta aura mashi idan tana ganin ta tsirane ga hakan ba zan taba barin ta a rayeba cikin duniyan nan har shegiyar yar da suka fara haifa din nan kuwa ku dauke shi mu tafi don tsayuwan mu a nan zai iya kawo muna matsala idan mutane suka fara fitowa sallah yanzu. Naji wani mai sanyin murya a cikin su yana fadin indan mun tafi dashi ina zamu kaishi yanzu a hakan ya Nuhu yace a hanzari rafi zamu jefa dan banza yaya Nuhu ya fada. Rafi hjy Addah ta fada cikin sautin kuka tare da fadin ashe shiyasa aka kasa gane gawan shi ruwa suka jefa shi ke nan. Sautin karan tashin motocin su na fara ji kafin can na fara jin muryoyin makwata mu da wasu mutane suna fadin sun tafi ai ga gawan maigadin sai alokacin na fito. Daga inda nake boye da yata a bayana mutane suna ganina sukayo kaina da tambayan meke faruwa a cikin zaucewa da rudani nake fadin shike nan sun kashe shi. Yan uwan shi sun kashe shi sun halaka min shi rayuwata ta mutu ke nan bani da sauran amfani a yanzu kuma . Haka nayi ta maimaitawa har yan sanda suka iso wurin suna bincike akan abinda ya faru a gidan ba bakin da zan basu amsa a lokacin. Wai kuma saiga yaya Nuhu na gani shine a gaba wurin bawa yan sanda labari saidai muna hada ido zai watsa min wani harara a fakaice wanda ni kadai nasan da yana min wanan kallon . Gaba daya naji ban son ganin kowa nasa har ku din nan don har lokacin da ka iso yaya ban fadi komai ba ga kowa don na koma kamar kurma mai tabin hankali a lokacin. Shine ana sallah magariba na sullace jiki na bar gidan da ba wanda ya ganni daga ni har yar tawa muka bar garin nan ke nan. Sai umma din ta fashe da wani irin kuka mai tsuma zuciya da sauri yaya Abubakar yace amma wanan mutumin anyi mara imani a duniya shine ya kakace komai da suka bari ayanzu. Daddy lalai ya zama dole a tuhume shi kan wanan zancen zan tafi inyi aresting nasa kan tuhuman shi da kashe dan uwan shi tare da batar da gawan shi tunda ga shedu mun samu a yanzu. Dakatar da Abubakar din mahaifiyar shi tayi tana fadin na fada maka ka fitar da bakin ka a cikin zancen nan don wanan zancen iyayyen ku ne ba naka ba. Daddy ya katse ta da fadin Addah ba zaki godewa yaron nan ba bisa ga namijin kokari da yayi na dawo muna dasu gida yanzu ? Ya dago kai yana kallon ta a cikin mamaki ta dukar da kai kasa tana fadin ba hakana bane yaya kasan fa halin wa yan nan mutane da sheri kai kanka kasan komai. Idan na sani shine me yara sun dawo yanzu sai su basu hakkin mahaifin su da suka taushe ba shike nan ba kowa ya kama gaban shi. Yara dai har uwar na fada maku a gidan nan zasu zauna don haka ko bayan raina ban yarda a kaisu wani gidan ba su zauna duk da nasan yin hakan zai kawo matsala a wurin, , , , , Dama ai tun jiya ina zargin hakan nasan yaran nan yayan kane da wanan matar da nake gani mahaifiyar yaran hjy karima ta fada daga kofa tana shigowa falon ranta a bace hankali a tashe. Amma wallahi anji kunya girma kuma ya baci ka haifa a bariki an biyo ka dasu nan yanzu don ga asiri ya tono a yanzu. Shine akazo nan a kulla yadda za ayi dasu ba tare da kowa ya sani ba to Allah yafi ku don naji komai a yajzu. Har kana fadin wai a gidan nan zasu zauna don diyan kane su halal malal ba wanda ya isa ya hanasu zama a gidan nan kuma ko bayan ranka watau shi ya rike makasu amana ke nan ko. To ai dadin abin basu dai da gadin ka tunda duniya basu sheda daurin auren ka da uwarsu ba ai kowa kuma a cikin dangi bai san dasu ba dama. Murmushin manya daddy din yayi ya kalleta yana murmusawa yace kwarai kuwa yara yayana ne uwar kuma kanwata ce ita sai me kuma ? Zaka dai fada tace tana huci tana kari don ranta ya ga ma baci da abinda zuciyar ta ya raya mata a lokacin game damu din. Haba hjy karima ina kuma wanan zancen ya fito haka a bakin ki hjy Addah ta fada a cikin mamaki sai hjy kariman ta juyo a hasale tana fadin kaji munafukar mace a nan. Idan ba yayan sa bane na waye har yake fadi yanzu a rika mashi su a cikin amana koda bayan ransa ne ? Don kin mayar da kanki wata bagidajiya can har zaki yarda a yi wanan aika aukan dake ke gaki mai son miji kina son a kiraki da salihan mace ko mai rufawa miji asiri saboda son yabo da kikeyi a wurin shi. Kaiya boyar Allah wanan mumunan zancen bai kamata kiyiwa bawan Allah nan shi ba don shi din yayanane na jini kamar yadda hjy take yar uwa a gareni itama. Yaya kuma su ba shegu bane diyan dan uwansu ne da baya raye a yanzu don Allah ki fahinci abin da idon basira kafin ki furta kalamanki. Abubakar daya gama cika a wurin ya mike yana fadin daddy sai kafito ni zan dan fita anjima zan dawo mu karasa zancen. Daga haka yasa kai ya fice a dakin cikin takaici wai a gaban shi yau hjy karima ke dakawa uwarshi tsawa haka don rainin wayau. Dama ba yau ba ya gama fahintar halinta matar yar bala,in rainin wayau ne sosai idan ta samu wuri haka kuma yaga karfin halin daddy da har tayi mai wanan mumunan shedan a yanzu bai dauki wani mataki a gareta ba. Yau dashine gobe ba zata kara gigin raina mai wayau haka ba a gaban mutane ya kara jan tsuki yabawa motan shi wuta ya tafi. Daga inda nake tsaye bayan labule na sulale a kasa ina hawaye tare da kare bakina da hannu kada suji sautin muryana a lokacin. Can naji muryan daddy yana fadin modibbo kada kace zakayi wani yunkuri a yanzu kan wanan zancen ka bari sai mun zauna mun gama tataunawa sai mu san inda zamu bullo masu ga zancen. Yace naji daddy ya figi mota zuwa gidan shi kai tsaye a falo ya kicibis dasu Nazifa a zaune da yan uwanta suna gaidashi da dawowa yayi kamar bai jisu ba ya shige dakin abinshi ya kyalesu yana maijin haushin mahaifin su duk ya shafesu a lokacin. Sintiri ya fara yi a cikin dakin yana nazarin labarin da umma tabasu a yanzu a kan mu yaje ya dawo ya kasa zama a dakin karshe ya nisa yana fadin. Wai imagin ace dan uwan haihuwan kane yai maka haka inaga wani sabba can bare na waje aida zai aikata wanda yafi haka ke nan gareshi duk saboda abin duniya sukaiwa dan uwan su haka. Shine mommy ta san da hakan har ta yarda ta aura mashi jinin wanan mutum da yayan da zata haifa dashi suna iya kasheshi ke nan ashe ? Hannun shi ya dunkule a wuri daya yana naushi kafin yace a fili na tsani wa yan nan mutane har cikin raina ga baki daya. Wait yace da sauri ya daga kanshi yana fadin what harda su kawu iliya ke nan duk wanan arzikin dama ba nasu bane suke ci ke nan ashe hakkin wasune suka gina kansu dashi ashe. To waye mai sanyi muryan data fada ya danyi nazari can ya girgiza kai yana fadin haka ba zai yuyu ba ace wai harda baffa Audu cikin case din nan. Ya fara girgiza kai yana fadin No No no no dukan su ke nan sun hudun duk baffanin mune sukai wanan aika aikan ko me Allah dai yasa bada daddy a cikin su ba ya fada da karfi gaban shi nata faduwa don yasan kusan kansu dayane ga komai da sukeyi Fadawa yayi saman gadon ya dafe goshin shi da hannun shi daya yana fadin daddy ya damu da zancen yaran nan sosai me hakan ke nufi ke nan a yanzu. ZAINAB IDRIS MAKAWA A NA DARA GA, , , , , , , , , 2️⃣5️⃣ BY ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , , , , BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AL BARI, , , , , , ONLINE PAID NOVEL YAR UWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA NA FADA NA FITAR DA HAKKI RASHIN SANI A GARE KI ALLAH YASA MUFI KARFIN ZUCIYAR MU AMIN, , , , , , Dakin namu yayi tsit a lokacin don ba me iya cewa komai a lokacin saboda kukan da kowan mu yasha ranan don tausayin abinda ya faru damu din da umma taba da labari. Asabe ce ga shigo da abinci rana dakin niki niki ta kawo muna har kuryan dakin ina kwance na kifa ciki a saman gadon daga ni sai dan guntun shortniker wando a jiki da yar rigan shi a lokacin ina kallon yadda dattijuwan ke satan kallo na saidai ban dauki hakan wani abu ba lokacin. Gaida ita umma tayi muma muka gaida ita a cikin turanci ta amsa muna da kada kai umma ke fadin mu tashi muci abincin mana nace na koshi. Kin koshi me kikaci nace bana jin yunwa umma ta kyaleni ba tare da tace dani komai ba taci gaba da abinda takeyi. Hjy Addah bata kara shigowa dakin na mu saida dare data shigo muna zaune dukkan mu kusan rabin jikin mu yana ga na ummane. Gaida ita mukayi ta amsa muna a dan cikin sakin fuska take fadin zancen karatun yaran nan mukayi da Alh dazun yace a wani mataki suke yanzu ne ? Umma tace da ita taoardun mu suna hannun ya Abubakar don ya karbo muna trasfer da zamu dawo nan din tace ya kyauta da hakan da yayi. Ta mike take fadin mairo sai kin saki jikin ki komai zai zo da sauki don yaran nan suma su saki jiki damu ki godewa Allah ba mai zuwa gidan nan a yanzu sai can ba,a rasa ba kinga har Alh zai kare shirun sa ba tare da wani ya sani ba. Umma tace har da wanan abokiyar zaman naki kuna ganin ba zata fadawa kowa cewa muna nan ba yanzu ? Bata san komai a kanku ba kema ki hori diyan ki da kama bakin su akan fadawa wani kafin lokacin sanin hakan yayi a garemu. Umma tayi mata godiya ta dan dafa kan Amar ta fice dakin nan umma ke muna bayanin komai sai a lokacin na samu bakin magana nake fadin. Umma kina ganin suma ba zasu cuta muna ba kuwa ni yanzu kowa daya shafi mahaifin mu tsoron shi nake ji don ban yarda da imanin su ba kuma. Ban amince inzo nan ba saida naji inda za a kawo mu mu zauna don shi din wanan maigidan shine kamar amini kuma yaya ga mahaifin ku don a wurun shi kawai yake jin sanyi yana fada min wanan ko wani lokaci. Umma akan me sukaki mahaifin mu haka a cikin su tace ba akan komai bane tun farko a kwai wani camfi da fulanin mu syke dashi shine dalili. Wani dalili ke nan umma na tambaye tace akwai wani al,ada da sukeyi kan yayan su idan kana da diya mace har ya kasance yar taka tana da halittan hakoran gaba masu yawa a bakin ta har suna fita fili. Zakaga maza suna rubibin ta kowa na son ya aureta don sun camfa da cewa mata masu irin wanan halittan suna da yawan arziki a jikin su. Idan ka aure ta arzikin ka zai kara hayayafa ninkin banin ki fiya da dacan baya shanun ka zasu karu suyi yawaka dara kowa a rugan ku ko a gidan ku. Wanan dalilin yasa mahaifin mahaifin ku ya shiga gasan neman auren kakarku mace kuma Allah ya bashi ita har ya auro ta. A dalilin hakan kishi da bakin cikin hakan yasa sauran matan shi suka dauki karan tsana suka saka mata a lokacin. Ganin haka yasa kowa ya daina mu,amula da ita a lokacin suka maida ita ware a cikin su bata gane komai a tsakanin su. Wanan yasa shi kuma mijin ya mayar da hankalin shi gareta sai suka dauka wai yafi son tane a tsakanin su ga kuma wana camfin da sukai mata ya fara tabbata gaskiya. Dukiyan kakan ku ya dinga habbaka sosai a cikin dan kankanin lokaci shanayen shi sai yawa haihuwa suke karawa a lokaci sa,an da yake na fatauci kuma yana kawo mashi kudi. Allah da ilon sa kuma tun da aka kawo kakan ku gidan batayi wanki ba ashe tun zuwanta ta samu ciki cikin na fita sai suka kara tsanar ta fiye da farko da suke mata. Har yakai sun cusawa yayan su mugun akida a kanta suma yaran basu kallonta a matar ubansu a idon su don sun tsane ta kamar yadda aka koyar dasu hakan har Allah ya nufa ta haifi mahaifin ku a wata bakwai duk da mahaifin ku karamine sosai kamar yadda ake haihuwan yan wata bakwai. Wanan bai hana suyi sheri da kazafin cewa wai da cikin shi ta shigo gidan don haka ta haifa masu shege a cikin gida zai rufe tauraron yayan su ke nan na suna. Lokacin haihuwan maigidan yana wurin fatauci don haka suka korata ta gida wai ta bar masu gidan su ko wanka basu yarda anyiwa dan a cikin gidan balle ita wai kada jinin shi ya diga masu a gida. Duk da maigari ya kirasu akan su bari har mahaifin yaron ya dawo aji me zaice amma suka badawa idon su tankwa sukace sam basu yarda da hakan ba garesu. Dole maigarin ya kualesu ganin fitinan zaiyi yawa a lokacin aka bar kakan ku a gidan su har zuwa lokacin da ya dawo ko yan uwansa basu yarda sunyi wa dan suna ba yadda al,ada yake da sati a radawa da suna a yanka dabba a ci yan uwa da abokan arziki. Har lokacin da kakan ku ya dawo ya samu wanan labarin daya tayar mashi da hankali don yadda aka wullakanta masa mata da danshi. Korar sauran matansa uku yayi suje gidajen su sani Allah sani ma,aikin Allah har zauren hardon su da yake duk gidane aka bashi hakkuri ya mayar dasu. Amma ya barta a gida ta samu wankan kwarai ta gasu ita da danshi ga kuma alherin da yake aika masu lokaci lokaci saima zaman ta a gida ya fi mata kwanciyan hankali don ita ta kasance mace ce mai hakkuri sosai a lokacin. Ya bukaci matarshi ta dawo anan iyayyen ta suka nuna basu yarda da hakan ba haka ya juya ya koma wurin fataucin shi da bacin ran hakan. Kaduna ya yada zangon shi bayan ya gama sayar da shanayen shi a gidan dan uwanshi wanda yake shi anan suke zaune da iyayyen shi. Watau mahaifin su Alh mai wanan gidan shiyabawa kakan ku shawaran mai zai hana ya dauko kakan zuwa nan tunda yana yawan shigowa garin sai su dawo nan dayani tunda iyayyen su suna nan dama cikin gari da yawan su. Shawaran da yabi ke nan shine mafarin kara lalacewan duk wani abu daya faru a lokacin don dai ya je ya dauko matarshi suka dawo nan kaduna aka basu masauki suka zauna. Kafin yasai masu wani babban gida mai kyau a nan unguwan rimi dun da iyayyen su suke zaune aka gyara suka tare a ciki nakatse umma tace sai da aka dauki lokaci mai tsawo suka samu labarin ai sunkoma kaduna da zama. Nan kishi ya tashi sosai har saida iyayye suka shiga aka dawo dasu duka kadunan a lokacin har shi mahaifin ku ya fara karatu suna zuwa tare da sauran yan uwansu na nan . Koda suka zo garin akai zancen karatun yayan sai uwayen su basu yarda ba wai su yaran su zasu lalace tarbiyan su ya baci don haka manyan yayan gidan kakan ku namadi a lokacin basuyi kararu zamani ba sai yawon bin motoci akarshe da sukeyi duk da arzikin dake akwai ga mahaifinsu kuwa sai suka taso kamar marasa ji a lokacin. Shiko mahaifin ku ance shida Alh gidan nan sun hade kamar uwarsu daya don yadda suka shaku duk da ya girmeshi . Kana mahaifiyar su Alh na gidan nan a karshe ta dauke shi ta mayar a gaban ta daya gama primary sai aka turasu karatu can FGC maiduguri ya gama ya fito da takarda mai kyau. Shine dalilin zuwan shi karatu kasan waje har ya zama babban dan kasuwa koda ya dawo ya samu labarin mahaifiyar shi ta rasu da hawanjini. Yayi kuka sosai aka fara zancen auren shi sai duk inda sukaji yana nema a cikin dangi dama gari zasubi su soke sai wata yar mahaifin sune ta hadashi da jikan ta nike nan. Ta nuna muna kanta nace ke nan kuma yan uwane dasu ke nan tace a wani wurin zaman kanwa nake a garesu ai. Taci gaba da fadin a takaice dai mahaifin ku wanan fitan dayayi waje karatune ya dawo da abun arzikin shi da suke gudu ashe boyon kurwa ya dinga yi a cikin yan uwa. Abin duniya baya boyuwa don saida suka gano yawan arzikin da ya tara dama kuma sun camfa hakan kuma ya zamo gaskiya a yanzu don ya zarta su ga komai. Sai kuma suka koma fadin ai arzikin mahaifin su dayai sanyi a yanzu sune yatatara ya mikawa mahaifin ku yake juyawa har yai wanan kudin su aka barsu. Wani fili Alh gidan da akasa sayarwa a lokacin ya bashi shawara ya saya tunda yace yana son bude asibitin kanshi a lokacin. Wanan sayen filin shine dalilin komai daya faru a lokacin don mahaufin su yana rasuwa da shekara daya suka tayar da kayan baya kan cewa lalai sai ya kawo dukiyan shi tunda na mahaifin su ne dukiyan shi duk. Bakin su daya a lokacin mazan su da matan su don mahaifi su da mahaifin su ya bari a duniya a yadda sukace. Duk wani abu daya faru gaba daya ya farune ta wanan dalilin don saida yakai sunga bayan mahaifin ku a lokacin ya tafi ya barni dake da cikin dan uwanki a jikina lokacin. Kuka nake sosai tare da fadin umma kuma mahaifin su daya kikace kamar yadda nake gani a gidan nan da mukazo tace kwarai mahaifin su daya kuwa saidai sun sheganta mahaifin ku a cikkn yayan mahaifin su din . Don ko wurin rabon gadon shi daya rasu din dan abinda za a raba yaya Nuhu tsaye yayi yace ba za a raba da mahaifin ku ba don shi din ba dan mahaifin ku bane da cikin shi uwarshi tazo aure gidan mahaifin su ai. Da malamai sukace ba a haka ai sai suke cewa ai duk rabin dukiyan mahaifi su ya kare ne a wurin shi don haka ba za, a raba dashi ba abin har yakai alkali ya tashi daure shi don tijaran da yayi a kotu din. Don shi wanan yaya Nuhu din haka yake da tijara dan duk a tasha yayi rayuwan shi gun shigowan su kaduna da zama. Shiya kowa a cikkn yannuwan su yake kafa kafa dashi don sun taba wani rikici da maigidan nan soka mai yuka har aka kulleshi akace suna yara a lokacin. Umma me i hate d man ma self before i see am wallahi na fada cikin kunan rai da takaicin jin wanan labarin nasa da nake ji yanzu. Umma tace kada in soma in nuna hakan koda wasa a gaban kowa idan nayi hakkuri wata rana zan kamashi a hannu ne don Allah zai daukan muna fansa a gareshi. Kwance makai ina hadiyan zuciya kowa yasan yadda bafulace yake wurin zuciya ina faman saka yadda shima zan halakashi da hannuna. Umma ta fahinci me nake tunane sai naji tace min ranan da duk naji kin nuna masa wani hali a yanzu ranan zan bar maki garin nan in barku a cikin su ga baki daya daga ke har kaninki. Jin hakan yasa nayi wani irin ajiyan zuciya mai karfi wasu hawayen suka kara zubo min ina tunanen ni yaya zanyi in ramawa mahaifina zaluntar shi da akayi. A sannu yan gidab suke dan jan mu a jiki muna sabawa dasu duk da ba hausa a bakin mu sai dan turancin lagos da mukeyi da yarbanci. Har kwana uku wanda ya kawo mu bai shigo gidan ba ko ya shigo ne dai bamu ganshi bane oho ? Gashi wani lokaci sai naji na tsani wanan matar da akace ai mahaifin su daya da mahaifina idan na tuna da abinda sukai mashi a jikin shi. Itama umma na kula ta dan sake jikinta a duk da ko yaushe tana daki bata dogon motsi a gidan baka ma gane cewa muna gidan da zama din daga can ciki muke zaune idan ba mun fito bane har wani ya ganmu. Zancen karatun mu ya taso muka koma makaranta duk da yanayin karatun ba daya ba saidai munyi sa, a don karatun can yafi na nan da muka sama don haka mun samu an sakamu ajin da daddy yace a saka mu din. Mun ake kaiwa da safe makaranta don muna riga manyan yaran gidan fita zuwa school don haka tare dasu Amira diyan hjy karima muke tafiya school din. Da farko ba wani abinda ke hadamu da yaran sai yaran suka fara kawo muna rainin wayau suna kiran mu da wani suna da bamu fahinta ba. Ranan na dawo na tambayi umma meye ma,anam kalman tace a ina naji nace da ita a bakin diyan hjy karima suke kiran mu da yan cin arziki. Salati naga umma ta fara tace dole mu bar gidan nan don zaman mu a wanan gidan ba zai yuyu ba kan wanan matar da yayanta. Nace umma ta barmu dasu don ko mun bar gidan nan cikin wahala zamu kara komawa kuma bamu san inda zamu dosa ba ai idan mun bar nan din. Bayan kwana biyu da yin tambaya gun umma din sai ga yaran sun kara kiran mu da wanan sunan nace na your mama be dat . Na kaiwa yar yarinyar duka tare rankwashe har muka dawo gida sai darzan kuka takeyi mota na tsayawa ta fita da gudu zuwa gidan ta rafka ihu uwar dake kwance tana barci ta fito a gigice ta na tambayan abinda ya sameta tace nice na doke ta ai kuwa nan fa tayo kaina ina shigowa ta tsare hanya a cikin sababi tana nunani da yatsa a cikin sababi. Na kyaleta ina kokarin shigewa ciki ta hankadone baya nayi tangal tangal kamar zan fadi na ja na tsaya take na fulanin suka kawo min nace a hasale dont beat me again if not i will show u my true clour now , , , , , Ayi hakkuri nagaji sosai ZAINAB IDRIS MAKAWA ANA DARA GA, , , , , , , , , , , 2️⃣6️⃣ BY ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , , , BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AL MISAWWIR, , , , , , , , , , ONLINE PAID NOVEL YAR UWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA NA FADA NA KUDINE NA FITAR DA HAKKIN RASHIN SANI ALLAH YA BAMU CIKAWA DA IMANI AMIN, , , , , , Baya nayi tangal tangal zan fadi Allah ya kareni na cire jakar dake goye a bayana na kalleta ina huci nace why u de push me like dat ? I push you , why the you beat her ? you want to kill her or what ? Me i no go kill any body, na ur daughter de abuse me, na yin i beat her , whu u no ask her wetin she do for me. Wanan yar iskan mai suffan kafirai sai nayi maganin ki gidan nan zaki shiga taitayin ki dani wallahi. Na ce me i no hear u ask ur daughter first wetin she for me daga bayana naji ana fadin hey daughter why do you beat her she is your sistee now. Hjy karima tace can dai gasu gada Allah ya tsari diyana da hada jini da wa yan nan matsiyatan da aka kwaso muna a gida. Haba dai hjy karima zaki raba tsakanin su ne suma din ai yan uwan sune na jini daya. Hannu ta daga tana fadin hjy ya isa haka ni dai na fadi a daina hada min diya da kalan dagi idan kuma ta kara dukan min ya sai nayi mata bugun a kawo ruwa a gidan in rama mata. Na nuna kai na tare da daga hannu na nayi round dashi na kada ina fadin god forbid wallahi omale, every day she de call us with cin arziki walahi talayi if she repeat dat neme for us again i go break dat her tieni leg before we come back. Sam ban kula da kowa na gidan yana waje a lokacin sun fito ba gaba dayan su sai umman mu data sha magani take barcine bata san da hakan ba. Sahiba naji muryan ya Abubakar ya fada a tsawace yasa na dan dago na kalli inda yake tsaye shida daddy din suna sauraren mu nace . Nace broda na dis woman come push me for notin, nd she is abusue me, bcos her daughter de call us wit cin arzki, nayim i beat her, she come dey cry, her mama come dey block de road for, i come de inter nayin de woman push me back, Karima ba yarinyar nan hanya ta wuce daddy ya fada yana kallon ta ido da ido tace au kama mara mata baya ke nan tayi iskancin data koyo acen ke nan ? Bata hanya ta wuce nace dake ko kuwa ta wani irin jan hannun yar ta suka shige tana fadin wallahi da sake don ba zan yarda da wanan iskancin ba. Juyawa nayi wurin daddy na dan rusuna nace tank u uncle ya daga hannu yana fadin dont faith next time nace yes sir nashige ciki Amar ma yabi bayana. Kai ya Abubakar ya girgiza yana fadin wanan baku san ko waye ita ba a wurin dabamci da kowa ya kama kanshi da ita a gidan nan . Yarinyar da gaba daya lagos kaf tasan shi sai ta zagaye shi da kafa fada a wurin ta kamar shan ruwa ne ita. Daddy daya juya yake fadin dole tayi tarbiya sai namiji duk kokarin uwar ba zata iya bata tarbiyan da namiji zai iya bata ba ai. Da sannu da lalami zata koya a nan insha Allahu wata rana hakan zai zama tarihi a gareta sai ka fara shirin koyar da ita hakan a yanzu. Hjy Addah kan mutuwan tsaye tayi a wurin tana kallon ikon Allah ga yar dan uwanta dake tujara haka a gaban kowa duk dani ina ganin ai nayi masu mutunci tunda na tsaya nayi warning din ta ban makale mata a jiki ba. Mun shiga mun samu umma a kwance falo muka tsaya na debe uniform din dake jikina wando da riga sai dan hijab din da ya zama mun alkakai don debeshi nakeyi idan mun fita tunda ban saba saka hijjab in dade haka ba sai idan zanyi sallah nake sakawa . Abinci na zubawa Amar ya zauna yana ci sai ga Amira ta shigo dakin namu da takardan ta a hannu tana assigment din da aka basu. Kwanciya yarinyar tayi a kasa ties ta kifa ciki ba wanda yai mata magana a cikin mu har lokacin nima dai a karshe hankalina sai ya dauku ga tunanen kalman da hjy karima ta fada game da mu da zata shiga gida. A fuskana yarinyar ta manna min littafin nata tana inyi mata in koya mata mana sai yarinyat ta ban tausayi na shiga koya mata tana ganewa. Nemanta akeyi a cikin gida ta ko ina duk uwar ta tayarwa mutane da hankali daddy da ya Abubakar dake alwala a waje har baya sukaje wurin tankin ruwa aka duba ciki babu yarinyar uwar ta kara tayar da hankalinta sosai. Daga karshe sai ga yarta ta bude kofan mu ta gamu zaune tare muna cin abinci gs littafi a gefen mu muna assignment din a ciki. Juyawa tayi ta koma da gudu ta na fadin mami ga Amira can daki ita da yan cin arziki suna cin abinci ana mata assignment din ta a cikin zabura uwar tace ina ? Daddy yaja wani irin tsoki yana fadin shirmen banza shirmen wofi kinbi kin tayarwa mutane da hankali haka kince kin duba cikin gida ko ina. Har ya juya zai bar wurin ya juyo tare da kiran sunan yarinyar da humaira idan naji kin sake kiran yaran nan da yancin arziki a gidan nan sai na bata maki rai. Arzikin da uwarki ke fadin anzo ci a wurin ubanwa na same shi kije ki tambaya wanda duk ya fada maki da kikirasu da hakan ni ubanki nace arzikin su nake ci har ku a gidan nan yanzu. Wurin gaba daya yayi tsit kowa na kallon daddy din da mamaki jin abinda ya fada tundai ita hjy karima din daddy yaci gaba da fadin. Da arzkin uban su na samu aikin da nayi a baya da nasa kuma har na fara business din da nakeyi yanzu don haka ke dasu fada min waye dan cin arziki a cikin ku yanzu ? Don haka wa yan nan yaran sun wuce a raina su a gidan nan musan maku da mahaifin ku ya daukeku kamar diyan cikin shi da ya haifa son yai min duk wani abu da dan uwa zaiwa dan uwan sa a rayuwa ke Addah kin sani idan su basu sani ba ai. Don haka ku girmamin yaya don ko shi ke raye na barku haka zai muka baku maraici da rashina a duniyan nan nasani. Daga haka suka bar wurin zuwa sallah ya Abubakar ya bin shi a baya zuwa masalaci unguwar da suke sallah. Jikin kowa yayi sanyi haka suka kwasa suka koma cikin gida kowa da zancen daya tsaya mai a zuciya shi suka shige part din su. A part din hjy Addah Nabila ce ke fadin yau wanan yarinyar ta mun daidai jifa yadda tayiwa anty a gidan nan. Sauran ma suka dauka da hakan muma ai tayi bala,in ban mamaki ke bakiji abinda yaya ya fada ba cewa yar geto ce ita ta iya dabanci kamar tsiya. Hjy ce daga kofa take fadin meye abin burgewa ga yiwa babba rashin kunya irin wanan amma mommy ai ita akan gaskiya ta fadi magana ba tsoro dole anty ta koma baya tayi shiru. Ina zata iya da wanan yar tsatsaye take fa dagani saura kiris ta iya sheke koma waye ya taba ta . Wai mami mai daddy ke nufi da cewan da yayi yaran nan suke da arziki hjy ta juya tana fadin kya iya zuwa kin tambayeshi a waje . Tafice ta barsu suna magana a kai kona fadin abinda ya fahinta kan zancen mahaifin nasu har suka gaji suka watse zuwa sallah. A dakin mu bayan mun gama umma tace muyi sallah la,asar yayi na idar na fito na samu Amira din tayi barci daykata nayi na dora saman kujera saboda sanyin ties na kwanta a kasa din ni sai barci. Anty ta shigo dakin da kanta ta duba don jin yarinyar shiru da tayi ta samu munyi barci sallaman ta da umma taji yasa ta ta fito falon daga ciki uwar daka tana amsa mata. Wanan nazo duba ta nuna yar nata a cikin murmushi umma ke fadin tayi barci sun gama karatu da yar uwan barci kuma ya dauke su zata dauketa umma tace aiki barta idan ta falka sai a kawo ta. Anty din bata so hakan ba son bala,in haushin mu da take ji a lokacin ta juya ta tafi bata ce komai ba umma ta tsaya tana kallon ta cikin mamaki. Kafin ta juya zuwa cikin dakin sai gab da magariba ne muka falka wanka nayi wa yarinyar nima nayi na shafa mata mai sai na riko hannun ta zuwa part din su duk ban taba shiga part din kowa a gidan ba. Don mun kasa sake jiki da kowa damama ni shi Amar ko banza haka yake baida sakewa ko kadan da mutane kullun yana daki ne. Nayi sallama tare da fadin gata nan barci tayi a aurin taje yin assignment a lokacin ina fadan haka na juya na bar part din na dawo namu. A ranan daddy sunyi fada sosai da anty a kan mu tace wai ya kunyatata a gaban iyalin shi yace a kan yaran nan idan kince zaki matsa masu a gidan nan zan iya maki abinda yafi wanan din ma nan sukai ta musayan yawu dashi har ya gaji ya kyaleta. Washe garine umma taji abinda ya faru a wurin hjy data shigo su gaisa umma tace a bata hakkuri sahiba fada ke gareta itama wanan halin yana damunta dani ai. Na fito na samu hjy da umma a falin a cikin shirin makaranta na suka har kasa na gaida hjy din kamar yadda umma tace mu rika gaidasu. Bayan ta karba ne ta fara min fada kan abinda nayi a jiya din tana fadi ita sin ai matar mahaifin mune udan ina haka shima ba zaiji dadin hakan ba ai. Shiru nayi banyi magana ba saidata gama na mike tare da fadin thank you ma na kalli umma ina fadin zan tafi umma ta juye baki a cikin yarbanci tana min fada akan kada na kara fada haka da kowa koso nake plain din mu ya rushe ne idan ina hakan oda nace na wuce abinna . Duk da naga yaran sun manta da hakan ban yarda na shiga zancen su mun dawo gida lafiya bayan mun taso zuwa gida suke nuna min assignment din da nayi taci su tana murna dayan tace nima na koya mata na ta yau nayi banza da ita. Haka yaran suka zo suka tare muna a dakin mu dole umma tayi min tsawa na zauna na koyawa yaran suka fice can kuma suka sake dawowa sai ga uwar na kiran su sun daje still suka dawo kuma sai dare sosai suka bar part din nice na rakasu zuwa part din mu. Haka dai zaman namu a gidan daddy yake tafiya kadaram kada ham wani abu da nayi notis a ranan girkin anty shine duk naci abincin ta haka zan zauna na amaye abincin tas a cikina sannan zan ji dama a karshe kuma kaina ne zai ta min ciwo sosai sai can ya lafa min. Ranan gashi ina ji yunwa sosai tundare har safe banci komai har sha biyun rana mikewa nayi zuwa kitchen din su na samu mai aiki da ita suna girki. Una weldone nace dasu tare dan raba ido ga kayan abincin dake kitchen din baga ko mai ba nace i wan cook indomie. Juyawa tayi ta kalli hannu na tana fadin whare is d indomie nace i tink say you have it here ta juya kawai ta kyaleni a wurin taci gaba da aikin ta a wurin suka fita batuna. Na juya na fita a hasale ban tsaya ba sai part din mu na dauko kudi na dauki dan gyalena na dora a kafada na dagani sai dan riga karami ya dan wuce gwiwana na fice daga gidan. Wani shago danake hangowa idan zamu tafi school a unguwan na taka na tafi na sayo duk wani abinda nake so na juyo zuwa gida da kaya a blue leda. Ban kallon kowa sai tafiyana nake a cikin dan rigana sabar sabar dani motar data wuceni ne ta dan dawo baya ta tsaya a daidai inda nake na zo na wuce ta ko kallon gefen ta banyi ba. Najji anyi horn hakan ma baisa na juyo na kalleshi mai shi ba sahiba naji an ambata na juyo da sauri cikin mamakin jin an anbaci suna a nan din. Mukai ido biyu da ya Abubakar a cikin motan yana zaune fuska a murde yake fadin from where are you ? Nace i go by indomie that shop what ya fada har yana dan kallon gefe idan babu wanda yaji abinda na fada a lokaci. Oya inter ya fada yana bude motan gaban shi na dan daga kai na kalli get din gidan da baida nisa damu lokacin. Nace No i can trake, no far from here, yace a cikin tsawa common inter d car jare jin hakan na fada motan daya bude da sauri. Ina shiga ya fara fada yana fadin babu abincine a gidan nace akwai saidai duk ranan da anty din nan tayi girki naci sai nayi ta mai kaina ya dinga min ciwo sosai tun jiya banci abinci ba yunwa nake ji . Kuma nayiwa anty magana a kitchen idan akwai indomie ta ban na dafa ta kyale ni shine na dauki kudi na sayo. Yayi shiru kafin yace na fadawa hjy nace ban fada ba don ban son na dame su na fada ina kawar da kaina gefe shima shiru yayi har muka shiga get din gidan. Yana bude motar yace dani wait for me there naja na tsaya wuri daya har ya fito daga motan bayan ya rufe ya nufi hanyar shiga gidan yana fadin follow me nabi bayan shi da sauri. Part din mahaifiyar shi ya nufa suna falon ta ita da yaranta da yanzu a nan suke zama muka shigo tare dashi yayi sallama suka karba mai. Ya juyo yana fadin na aje kayan dana sayo a gaban hjy na dan yi darrr don yunwan da nakeji a lokaci. Haka dai na aje din a gaban ta ta kalli kayan da mamaki ya nuna da hannu yana fadi a cikin hausa ga kayan nan yazu na hadu da ita wai ta sayo a waje zataci yunwa take ji. Amma wanan yarinyar da tonon asiri kike wallahi hjy ta fada tana harara na ya tare da fadin a, a mommy nasan halin yarinyar nan tace taje kitchen ta fada suka kyaleta . Yaci gaba da fadin ta fada min wani zance da ya kamata a zauna ai nazarin sa don idan taci abincin anty wai amai takeyi kamar zata mutu wanan maganan a duba mata ne. Aduba meye ta fada rai bace yarinyar nan bata son a zauna lafiya a gidan nan nake gani zan zauna da uwarta muyi magana tunkan ta hada wani fitina kan hakan. A a mommy wallahi nima kusan kullun naci saina amayar dashi saina daina ci dole Fa,iza ta fada daga gefen su. A dai duba din tunda haka ne kada azo rashin kulla da hakan ya haifar da wani matsala nan gaba. Jeka modibbo nace zan duba wanan zance naga ya da za,ayi ya juya wurin Nabila yace bata wani abu a nan idan akwai taci banda bread da butter ba wani abu a nan yanzu ok kawai ya fada ya fita daga dakin. Sai kuma ya dawo yana fadin Fa,iza dauko gyale kizo da ita ku sameni a mota yasa kai ya fita ba abinda uwar zata ce sai kallon juna da sukayi da diyan ta kawai nikan na duka zan kwashi kayana in tafi. Fa,izan tace dani in biyo ta mu tafi sai hjy din tace dani hakan nan zan fita ta nunani da hannu tana bata rai na danyi kasa da idanuna fa,iza din ta fito daga daki tana fadin mu tafi nabi bayan ta tsomai tsomai dani muka bar part din ban fita ba saida nakai kayan dakin mu na aje da sauri na biyo bayan su. Wani gidan abinci ya kaimu akai muna take away har leda biyar sai kayan drinks daya saya muna muka juyo zuwa gida. Muna sauka ya mika min ledan abinci biyu na drinks din daya na duka ina godiya na shige part din mu da sauri sai dai kash yuwa yacini a lokacin ban iya cin abinci ba Allah ya taimakeni akwai fura mai sanyi nasha sai barci. Bayan sallah magariba muna zaune su umma suna cin abincin da na shigo masu dashi don ban boyewa umma komai ba don ban iya karya ba a rayuwana. Sai ga mommy tayi sallama dakin ta shigo a falo ta samemu zaune muka shiga gaida ita ta zauna tare da kallon wurin da aka aje muna abinci bamu taba shi ba tace. Dazun yar nan ta tafi sayo abu suka hade da yayan ta take fada min wani magana daya ban mamaki wai idan taci girkin hjy Karima sai tayi ta haraswa . Wallahi hjy nima hakan yana ban mamaki don ranan har marinta nayi a dakin nan na tursasa ta sai da taci loma biyu saida ta kwata ciwo tun wanan ranan na kyaleta ai da abincin ko kamahin shi taji yanzu matsalane hakan . Ikon Allah wanan wani irin matsalane haka ya samu yarinyar nan kuma ta dan kura min ido na dan lokaci ZAINAB IDRIS MAKAWA A NA DARA GA, , , , , , , , 2️⃣7️⃣ BY ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , , , , , BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AL GAFFAR, , , , , , , , ONLINE PAID NOVEL YAR UWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA NA FADA NA KUDINE NA FITAR DA HAKKIN HAKAN RASHIN SANIN HAKAN ALLA YA SA MU FI KARFIN ZUCIYAR MU AMIN, , , , , Sahiba nada matsala ki barta a inda kika ganta kawai ni kaina wani lokaci ina tsoron wasu halaiyar yar nan don abinda takeyi bana kai sake bane. Shiyasa tunda tace dani bata ci idan ta hadiyeshi ya zauna a cikin ta akwai matsala ko dan uwanta ta hanashi ci nima kaina bata so ina danci din nan sai ta kama fadin idan naci duk abinda ya sameni ta fada min gaskiya. Kallona gwaggo Addah ta kara yi don umma tace mu daina kiranta da hjy ko mommy da muke fadi da mukirata da gwaggo Addah. Allah ya sauwaka tace tana mikewa tare da fadin yanzu taci wanan abincin da modibbo ya sayo mata ko ?. Taci kadan tasha hura shine take wanan barcin haka ai ni kaina bazan so a farga da hakan ba ba kuma zan matsa mata akan sai taci girkin nan ba a gaskiya don nasan abinda take nufi. Dole akwai wani abu a cikin wanan abincin da nasu baizo daya dashi ba don haka kinga cinshi gareta matsalane ke nan . Jikina yayi sanyi da wanan zancen hjy ta fada tana fita daga falon ba tare da ta iya furta komai ba ashe zancen ya tsaya mata a rai sosai fura hjy karima ta kawo mata don tasan tana shan fura sosai ta fake a nan take kawo mata da sunan taga tana so nan ko surukulle ke cikin furan . Hmmm kishi fa kishi ne don duk sunan su daya dana birni dana kauye tafiyan su daya ne a wurinyin shi ke dai kawai ki godewa Allah kuma ki rokeshi kada zuciyar ki tafi karfin ki har ki fada kishin kaucewa Allah ki fada shirka. Allah ya tsare ya kare shine addu,an da mu mata ko yaushe ya dace mu dinga yi kada sanadin kishi mu shiga wuta a gobe kiyama. Muyi hakkuri mu danne zuciyar mu mu fitar da idon mu akan kishiya akan mazajen mu kokarin mu shine muga muna da abin dogara da zamu iya tallafan kan mu dana yayan mu da iyayyen tare da yan uwa Allah ya bamu abin dogaro da kanmu amin. Ya sassauta muna zafin kishi a cikin zukatan mu ya rabamu da kyashi da hassada akan komai damu da zurian mu baki daya Allahuma amin don kishi akwai zafi koga macen da bata taba aure ba balleke dake dakin auren ki. Manya sunce yara basu taba wasa suce wanan ne kishiyana saidai suce ga mijina wanan ashe abin dashi ake haihuwar ko wace mace ke nan (KISHI) Shine abinda ya taba hjy karima tazo gidan ta samu miji da matan shi da yan yayan su har sun girma tace kuma ala dole sai ta kaita ko ta fita a gidan mata Allah yasa mufi karfin zukatan mu amin. Saman table hjy ta dora furan yana nason raba don sanyin daya dauka a fridge yau zan gwada yar nan hjy ta fadawa Nabila dake kusa da ita zaune tace Fa,iza jeki part din su yan uwa ki kira min Sahiba. Kallonta Fa,iza tayi ta mike zuwa part din namu ta shigo da sallama take fadin mommy is calling you sis . Na dago daga sharan da nakeyi falon you mean gwaggo tace yes ta juya ta tafi sauri nayi na karasa sharan na leka ciki ina fadawa umma tace inyi maza in tafi. Sallama nayi na shiga daga ni sai dan riga iya gwiwa mai dan hannu rigan silk ne yana da dan kwalliya a jikin shi ta gaba. Ina shiga nake gaida ita don duk suna falo suna kallo ita da yaranta mata tace min Sahiba i warn you wearing dis cloth with out putting hijjab. Sorry ma na fada ina kaiwa kasa nace sis said you are calling me tace eh zaku tafi unguwa gidan yayan ku anjima da yan uwan ki don haka ki shirya. Da sauri na dan kallota ta gane abinda nake nufi tace ba wani gida bane yayan ku na nan gidan zaku duba muna matar shi da bata da lafiya. Yes ma na sake fada kafin nace na now, we go go, tace after four prayer nace yes ma na mike zan tafi take fadin nazo na dauki fura gashi in sha rabi in bata rabi tasha tunda ina son fura har yarta Nabila na fadin sufa, tace baida yawa, na dauka da murnana ina murmushi. Budewa nayi bayan na dauko kofi na dawo da sauri na na dan bulbula a cikin kofin ina daga farin goran furan ina duban yawan shi. Na aje ina fadin ga shi na gode nayi azaman kaiwa a bakina da sauri na dawo da kofin baya ina sake wani irin ihu a firgice ina kallon su. Suma firgita sukayi da ihun dana sake din a razane da sauri gwaggo ke fadin dama gwada ki nayi ki natsu ki saurareni. Ina na firgita Nabila ta mike tazo ta rike hannuna zuwa kujeran data tashi sama tana fadin ki natsu ki jimu Anty ce ta kawowa mummy shi data fita ta dade tana kawo wanan furan idan ta fita shine mommy take son gwadawa a kanki. Ita hjy din cewa tayi maza a kira mata umma tazo yanzu da sauri Fa,iza ta nufi part din namu ta kira umma din sai gasu da sauri. Ina ganin umma ta shigo nake fadin umma shabi dey wan kill me naw umma din ta tsawata min tana fadin gaskiyane yar nan nada abubuwa a kanta Nan ta shiga bayani umma na fada min a cikin yarbaci ina dan gyada kai na fahinta har ta gama yi min bayani ohma binu na fada ina hada hannuna wuri daya. Na masu in bar part din don kaina dake juya min lokacin wurin kwanciya kawai nake nema a lokacin. Na koma dakin mu sai barci ban falka ba sai can dare sosai hjy tayi sintiri a dakin mu tana dubani sai barci nakeyi sosai a lokacin kafin na tashi ina neman abinci da zanci umma ta tashi ta dauko min. Ta aje a gabana na dago kai na kalli abincin na mayar da ido kan mahaifiyana saina ya motsa fuskana ina bata rai na kawar da kaina gefe daya. Gwaggon ki ta dafo maki wanan ta kawo mak ki dauka kici ki kiyi sallah sai ki koma ki kwanta sai dan kara bata rai ina fadin d food no get herbal inside. Ki dandana mana ki gani ta fada tana mikewa tabar wurin na sake kallon abincin sai na jawo bowl din abincin zuwa gabana da kyau na kura mai ido. Kafin na dan diba kadan ina kaiwa zuwa bakina hannuna bai rawa kuma banji komai ba na kai bakina kamar an tsure munafuka cin abincin haka nayi. A hankali na hade abincin dana kai bakina ina sauraren yanayin da zanji din sai Allah da ikon sa banji komai ba na kara diba na kara kaiwa bakina sannu a hankali nayi kamar spoon biyar na aje na mike na shiga ciki zuwa bandaki na dauro alwala na fito. Barci nayi sosai har na makara a ranan haka na kwanta nace banda lafiya ba zan iya shiga school ba don ko idanuwa sun nuna cewa banda lafiya a lokacin. Lokacin da mommy ta shigo gaida umma a dakin ta sameni kwance a hakana cikin ciwon kaina na dunkule a wuri daya. Har lokacin fararen idanuwana sun rikide mun sun koma ja dasu don wahala ta dan dade a part din kafin ta fito ta koma nata part din cikin mamakin hakan a zuciyar ta. Tsab ta labarta wa yaranta da yanzu sune abokan shawaranta tana cewa duk yadda akayi akwai abinda karima take zubawa ga abincin nan. Don haka kawai ai mutum ba zaiki cin abinci haka da gangan ba dole akwai wani abinda takeyi na boye wanda bai dace ba. Koma meye Allah ya mayar mata da aniyar ta ko menene mudai bamu bita da sheri ba amma nasan dole akwai abinda haka ke nufi ai. Sun dauki lokaci suna wanan hiran a tsakanin su kafin su kawar su dauko wani zance su kama duk dai zancen na tsaye a cikin ran hjy har lokaci. Ban samu kaina ba sai zuwa rana na iya dagawa nayi wanka na dawo normal dani duk da hakan kasala ne duk jikina nake jin hakan kwana kaman hudu tsakanin faruwa hakan muna zaune da yamma mukaji. Sallama anyi a part din namu na karba yaran mommy ne suke shigo muna da kwalayen abinci irin su taliya da sauran su har gas din dafuwa da tukwane saida aka kawo part dinmu suka saka a dan karamin kitchen din dake part din don ko wani part a ginan shi akwai dan kitchen da store makale da ginan sai dai bai kai wanan babban dake can ta kofan baya ba. Umma dai tana zaune tana kallkn su saida suka gama aje komai saiga mommy ta shigo daga karshe takai zaune tana fadin. Mairo wanan kayan abincin kune Alh yasa a kawo muku zaku dinga girkin ku a nan yanzu ba sai kun hada da kowa a gidan ba yanzu akwai shimkafa taliya indomei da garin alabo da na semo da sauran kayan girki sai ku girka abinda kuke son ci a kullun. Wanan kamar dawainiya muka kawo maku kuma umma da fada tace aiyiwa kaine don kamar kanmu muka taimakawa ga hakan Allah dai ya raya muna yaran nan rayuwa ya raka tace amin. Tana tashi daga wirin da take zaune ta dan kalloni tana fadin zuwanki garemu sahiba yana shitin zama muna alheri ga baki daya a yanzu shiyasa akace kada ka wullakanta bako ko yaya yake. Bayan fitan su na mike na nufi wirin kayan na dan tsaya ina karewa kayan kallo kafin na duka na dauki abin shara na sharo kitchen din tsab na fara jera kayan abincin. Abu daya nafi jima dadi kamar wanan garin elebo da suka saka muna mai yawa a cikin kayan saidai wai Nama da kifi zamu dinga dauka a fridge din cikin gida idan mun tashi girki don fridge din dakin namu ba freeze bane. Kaf har aka gama wanan wainar hjy karima da bata zama gida bata san wanan zance ba sai ranan ta gama girki Asabe na kallo ta diba kamar yadda ta saba a kullanta ta mika mata takai mata part dinta ta dawo tana fita ta dan labe ta ganta tana zuba abu ga sauran miyan ta motse don dama tunda taga anyi haka take zargin akwai wani abu kuma gashi hjy taja mata kunne kan ta saka ido sosai taga abinda hjy karima din take masu a girkin su sai gashi kuma ta gani. Da farko bata so yarda da hakan ba saida mommy din tace kin san dai nice na daukoki gidan nan da kuma a guna kike in ba yanzu da kuka hade ba idan har cutan mu take yi to harke ake cuta don duk abinda akayi tare dake muka ci shi a gidan nan. Wanan yasa jikin ta yai sanyi ta dawo hankalinta da ta kwadaitu da dan abin da hjy karima din kan mata ihisani dashi don kama bakin ta a kanta mata ku kula da yawan mutane badon son ransu suka juya ma baya ba. Sai don kwadayin abin duniya da akan basu a jaye su dashi hankalinsu ya raja,a ga amarya har su bar wanda suke tare dashi su hade kai da bakuwa sabon zuwa don zuciya bata da kashi. Saboda shi alheri bai bar komai don kyautatawa yana saka kaunan ka a zuciyan mutane har suji suna kaunan ka da zuciya daya komai munin halin ka kuwa. Gabanta ke faduwa sosai koda ta dawo hjy din ke fadin ki karasa zuba abincin akawa kowa nasa har wa yan nan bakin ki zuba masu miya mai yawa akai masu. Tace baki hjy jiya da mukai girki tace a daina saka masu abincin yanzu don nasu sukeyi a aurin su basai an saka masu ba su. Wani irin juyowa tayi da mamaki tana fadin a daina saka masu suna girkin su daban akan wani dalili ta tsareta da idanu. Tace nima ban sani ba gurkin nan daina hjy kaf ba,ayi dasu ba jin haka ta fita fuuuu zuwa part din mommy din ta fado masu ciki a fusace tana fadin. Duk ta samesu a zaune falon su ta soma fadin bako sallama yanzu Asabe ke fada min wai an daina saka abinci da bakin nan . Hjy tace eh saboda basa iyacin abincin mu kada abin ya zamo barna yasa aka sayo masu wanda zasu iyaci a wurin su. Din sufi mutane ko me don ni ban gane wanan fitinan ba haka wasukafi a gidan nan da za ace wai abincin su daban ne da namu yanzu. Ba haka bane kinsan bawai sun iya cin namu cimakar bane na nan yasa yaran basa iya cin abinci wanan ai masifane aka daukowa mutane. Wasukafi ko wa suka kai ta juya ta fita tana fada tare da fadin idan ba munafunci ba don me ba za a fadawa mutum ba ko banda hakkin sanin hakane a gidan. Ya fita suka hade da Asabe a hanya take gaida ita da dan girmamawa har lokacin jikin asabe ya rawa don abinda ta ganewa idon ta din game da ita a kitchen din. Nan ta shigo ta aje abincin suna gaida ita da aiki take fadin ga abinci an gama hjy saidai yau din na ganewa idona gaskiyan abinda kika fada min don ta zuba ta motsa miyan bayan ta gargadani zuwa kai mata nata da batayi hadi a cikin sa ba. Shine na dan tsaya na labe na kamata tana zubawa a cikin wanan din daya saura shi kuma tace na dibarwa bakin nan daku nan na kai maku. Ke nan wanan din tayiwa hadi ke nan bada nata ba ta tambaya tace hakane hjy ki gafarceni kusukurena ne da ban tsaya a inda kika ajeni na kula da komai yadda ya dace inyi ba. Koma me tayi muna Allah zai isar muna a kanta don da nufin cutan mu tayi wanan abin da takeyi har Allah yasa yarinyar nan ta gane hakan da badon haka ba haka zamuyi tacin mugun abu tana cutan mu a kullun. Ban faye shiga ko ina ba na gidan don ma umma ce data matsa na dinga shiga part din mommy ina gaida ita a can ba sai tazo nan ba ta samemu bamu je mun gaidasu ba. Yasa har nakan dan shiga kuma bana iya sake jiki dasu kona shiga din don kowama tsoron sa nake a nan arewa tunda akwai hassada a zukatan su. Zamu dafa abinda ramu ke so muci mu sha mai kyau amma hakan bai hana umman shiga cikin tunane ba don ita ko yaushe zaki ga ta zauna tayi shiru abin duniya yana damunta. Ba komai umma ke tunane ba sai yadda makomar mu zata kasance a karshe in lokacin haduwan mu da yan uwan mahaifin mu yayi. Sam ban da zuwan baki gidan ba ina kwance ne umma tace najie wurin mommy in samo mata paracetamol tasha kanta na ciwo. Na shiga falon da sallama sai naja na tsaya suma din dakatar da dariyan da sukeyi sukayi a lokacin suka zubo min idanu a kaina. U are wellcome ma nace dasu ina dan rusun nawa tare da fadin good afternoon ma suka amsa min kamar yadda na gaidasu din. Nace mommy do u have paracetamol tablet, my mother want to use it, har lokacin ido suka zubo min suna kallo na da mamaki. Tace go and check dat rober nd see na nufi wurin data nuna min din don nasan inda take ajewa sai naji dayan su tace . Ina kuma kuka samu wa yan nan haka kamar kabila sai mommy din tace dasu diyar aminn Alh ne suka zo . Daga ina dayan ta kara tambaya mommy din tace daga lagos suke aukuwa dai ga kama nan a fili wata ta fada a cikin su. Tubarkallah ma sha Allah wanan yar kamar ba diyar kabila ba idan ka ganta sai dai idan ka kalli shigan nata ko batayi magana ba zaka gane kabilace ita. Suma fa a cikin su dama ana samun kyawawa haka sosai wallahi kamar su sukayi kansu wurin kyau saidai kuyi mata magana mana wanan shiga haka ga yarinya haka da dirin daukan hankali. Dariya mommy din tayi na dauko maganin tare da dan rusunawa ina fadin thank u ma na juya na fita duk suka bini da kallo. Dayan mai kama da hamshakiya ta maya da bayan ta saman kujera tana fadin yarinyar nada shawa,a ga kuma irin ladabin su. A kwai ladabi kan saidai ni bazan iya aje irin wa yan nan a cikin gidana ba azo ayi barna wanan kyau tafa bana wasa bane don duk dirin da ake son ya mace tana dashi. Dadin abindai baku da yawan samari a gidan shine amma gaskiya tana da kyau sosai suka katse hiran da dauko wani hira kuma. Nakaiwa umma magani tashe ba, a dade ba sai ga mommy ta shigo part din mu tana tambayan umma din ashe bata jin dadine jikin ta ne Umma ta dan dago daga kwancen tana fadin kaina ne kamar ya fashe nake ji dazun shine na tura ta ta nemo min magani. Dazun su hjy Asiya sun zo gidan nan ai saidai babu halin inzo dasu nan ku gaisa don ina gudun Alh yai fadan hakan. Allah sarki aiko da mun gana dasu wallahi umma ta fada kafin tace yaushe rabona dasune wai Allah dai ya kyauta wanan al,amarin. Ai zan tura yaran nan gobe gidan su sai suje tare da sahiba suga wuri gobe idan Allah ya kaimu ta fada tana mikewa. Umma ta kalleta tana fadin fitan dasu bai kawo matsala kada daddysu ya dawo yai fada suja maki laifi. Tace daga fita kawai da suke zuwa school fa ai ba zasu san ita ko wacece bane tukun na sai ya gama shirin shi ta fada har gidan modibbo zasu tafi idan sun fita din gobe weekend ZAINAB IDRIS MAKAWA ANA DARA GA, , , , , , , , , , 2️⃣8️⃣ BY ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , , , , , , , BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AL QAH,HAR, , , , , , , , , ONLINE PAID NOVEL YAR UWAKI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA NA FADA NA KUDINE NA FITAR DA HAKKIN RASHIN SANIN HAKAN A GAREKI ALLAH YA GAFARTA WA IYAYYEN DA KAKANIN DA DIYAN DA YAN UWA MUSULMAI BAKI DAYA, , , , Bawai fita dasune bana so ba a, a yadda mutane ke fadan magana a kaina idan sun gamu tare tambayan farko da zasuyi a kaina shine amma dai wanan kafira ne kuka samo ko ? Idan sunce a, a zasuce tana shiga kamar kafira idan ka ganta a ina kuka samo wanan din zasu basu amsa da diyar abokon daddy mune tazo. Zakiga suna min wani irin kallo na kyama ko hattara a idanuwan su kai malam bahaushe dai akwai nuna bambamci koda kuwa sun yaba halittana sai naga wanan kallon a kwayan idon su kallon dana kasa fassara ko na meye suke min. Don ko ranan da mukaje gidan ya Abubakar na farko irin kallon banzan da matar tashi tayi min yasa naji bana son na kara zuwa gidan ga baki daya don tana fitowa fallo muna zaune na dauki wani takardan dana gani a kan table din dake tsakiyan falo ina karantawa ta fito. Suka mike suna gaida ita tana wani irin shan kamshi ban dago ba idon ta a kaina har ta kai zaune sai fa,iza ta dan dungureni na dago kai take fadin greet her now nace good morning. Bata amsa ba ta kawar da kai gefe daya tare da fadin ita wanan din wacece haka kuka samo kuma tana wani ya mutse fuska tana watsa min kallo mai kama da harara. Amsa daya ne dai shi suka bata ban kara kullata ba na mayar da kaina ga karatun da nakeyi kafin mai aikinta ta fito muna da abin sha. Na kula da yadda suke wani dari dari da ita kamar suna tsoronta dai sai wani magana take masu a cikin izza da isa da takama nuna wayewa a garesu. Ko kallon lemun banyi ba don duk inda nake a wani irin matsuwa nake da mubar gidan lokacin shiru shiru ba mai magana na dago kai ina fadin Anty Nabila may we go naw,. Tace dani not now dagawa nayi ina fadin i don tiear woo, if u no go now meet me at home na dago na fara shirin barin falon lokaci guda. Wanan kan yar iskace naji muryan ta tana fada kubar kwaso min irin yan iskan nan zuwa gida dan Allah ku barta ta tafi mana bata san hanya ba. Ban tsaya sauraren ta ba na sakai na fita sai a gida suka sameni don ko mommy bata san na dawo kai tsaye part din muna nufa. Saida suka dawo ne suke labari aka san na dawo shine mommy tazo tana maganan a part din mu wai ban kyaya ba ba gidan yayan mufa muka tafi na fito hakana. Su kuma su Fa,iza suka sakani gaba da fadin wai na taho ban tsaya na karbi turare data basu ba budan bakina nace dasu ko ta ban ma bazan karba ai don sam matar bata da maner tana kallon mutane a wullakance. Shine yau da mommy tacewa umma zamu gobe nake jin raina na baci umma ta kula da hakan yasa tace dani maza na shirya mu tafi kawai. Mun shirya tsab muka fito duk da baida nisa wai a mota zamu tafi muka shiga Nabila taja mu zuwa gidan mun samu kofan falon rufe mun dade muna nockig aka bude. Wanan yayan namune daya dauko mu ashe gidan shine wanan daga shi sai wata dogowar jallabiya mai ruwan makuba a jikin shi lokacin. Yana ganin mu ya jaye yana fadin ashema kune kuka tsaya kuna ta sallama haka ai kofan a bude yake kasa kasa Fa,iza tace min ba dole muyi sallama ba ranan da mukazo fa muka shiga kai tsaye koran mu matarshi tayi wai ba a bamu izini ba muka shiga mata gida. Baisan tare muke ba sai gani da fa,iza mun biyo bayan su mun shigo a karshe sai lokacin ya dan saki murmushi yana fadin u ? Broda na ur house be dis ? we come dat day i no see u, so that lady na ur wife be dis ? Ya danyi murmushi kawai muka karasa zuwa ciki tana zaune falon ta mike kafa saman dan table ashe duk wanan sallaman da mukeyi tana jin mu har ya fito daga daki yazo ya bude muna kofan duk tana zaune. Bayan mun kai zaune sukan a cikin dari dari suke sai da suka fara gaida ita suke fadin yaya kazo lafiya yace Alhamdullahi sai lokacin nace broda you are wellcome. Ya amsa da fadin Sahiba so now you are enjoyed d north side see how you look now sai na danyi murmushi yaci gaba da fadin ya umma da Amar suke suna lafiya ko ? Ba wani matsalan komai a yanzu ko, , , sai matar ta katse shi da fadin wai ya hakane don Allah ita kadai ka gani a wurin nan kome ? Ke ni kike dagawa harshe haka ko zaki hanani magana da itane kuma wanan fa kanwatace itama kuma yanzu kamar bakuwa take a cikin mu. Ni yarinyar batayi min bane tana wasu dabi,u na kabila ko kafirai innalillahi yace tare da fadin a cikin mamaki da Nazifa kin san wanan din ko wacece gare mu baki daya ? Da zaki danganta ta da kafira balle me yarinyar nan tayi na kafirci a yanzu ban son haka kuma kada ki kara don hakan zai iya jawo muna matsala a tsakanin mu sosai kuwa. Ba itaba duk wanda ke falon saida yayi shiru yana sauraren ta kafin ya juyo yana fadin ku tashi ku shiga ku dafa min abinci inci ya mike bai jira komai ba ya shige wani part da nake zaton nasa ne. Wani irin kallon tsana ta jefo min kafin ta mike tana fadin kada ku halaka min kaya ehhe ta shige tabi bayan shi Nabila ta bisu da kallo tana fadin Allah ya gani don mommy nazo gidan nan wallahi. Wanan yar rainin wayau din da kazo sai ta bata ma rai ta musgunawa mutum halan bamu taba ganin kaya bane da zamu bata wanan din. Ke ko ba tana takaman ba mai kudin ubanta bane kaf a dangi dole tayi muna haka mana yar rainin wayau kawai. Dole kuma suka mike zuwa yin girkin muna zaune falo da fa,iza mu muna kallon tashan da take kallo din muna kuma jiyo hayaniyansu ita dashi daga ciki. Fitowa tayi a fusace daga dakin a daidai lokacin da Fa,iza ta mike zuwa kitchen din ta duba sai ni kadai a wurin zaune na dan kame saman kujera. Tun kan ta karaso ta daka min wani irin uban tsawa tana fadin Ke tashi a nan nayi kamar banjita ba ban san me take nufi ba ta kara fadin. Stand, up f Who give you right to sit on my chairs don't ever and ever sit on this chair again look at you dity girl like , , , , Allah aka fada a bayan ta yana karasowa a cikin wani tako har ya karaso inda muke din tana tsaye ina kallon ta kafin yace lalai ashe ko hakan kuke dama ashe ba karya ake fada ba kan halin ku. Har ina kujeran yake a nan tunda ba kujeran zinare aka kawo ki dasu a gidan nan ba lalai babu dan uwana da zai kara hawa saman kujeran ki daga yau din nan . Sai dai ai zaki barsu dai su shigo gidan dan uwan su tunda gida na dan uwan su har su zauna saman kujeran dan uwam su ko ? Ya juyo ya kalli inda nake yana fadin Sahiba call your sister for me now nace yes broda na nufi hanyar da naga suna bi din sai na samesu a tsaye sunji hayaniya sun fito sun tatsaya dan nisa kadan dasu. Ina fada masu ne abinda yace ya hangoni kafin yace dasu kuzo in sauke ku gida yanzu zan dan fitane abincin fa yaya Nabila ta tambaya yace barshi kawai kuzo mu tafi. Haka kowa ya dauko gyaleshi muka bar gidan shi ya fara fitowa sai kuma ya koma ciki yana fadin yanzun za a kawo min kujeruna sai ki kwashe wanan din naki da kike hana yan uwana zama.. Tace aiga yan uwanka nan ka tambayesu idan na taba hanasu zama a kai ita wanan da kika hana a yanzu wacece tawa ki fada min ? Kaika sani don ni bansanta ba cikin dangi ta fada tana gyara zaman ta ya watsa mata wani kallon zaki gane kuren ki ya fita. Wani irin figan mota yayi don bamu bishi ba tunda munzo da mota da zamu zo gidan gaida ita ashe rabon tashin hankaline ke kiran mu. Gashi sai tambayana sukeyi a motan meya farune har hakan ya faru a tsakanin su Fa,izace tace wallahi ba abinda ya faru duk ina jinsu ta shiga daki ta samu yaya tace wai don me yake magana haka da Sahiba har yana dariya baiyi da sauran kannen shi ? Shine fa fada ya kaure sosai a tsakanin su suke wanan fitinan haka wai ko kishin sahiba takeyi ne ? Muka shiga get din gidan Aisha tace yar wahala ce kawai in bashi ba meya kawo wanan zancen haka wata sahiba kuma har zata tsaya kishi don kawai yaya yayi magana da ita yana dariya ba sabo bane a tsakanin su. Sai a lokacin Fa,iza ta tuna take fadin zancen zuwa gidan gwaggo Asiya din kuma fa ko an manta da zancen ne yanzu. Ina zamu gidan gwaggo a yau din nan wanan yar rainin hankalin ta bata zance don wani hauka nata can na daban nina rasa me yarinyar nan tayi mata. Don na fahinci sahiba idan baka taba, taba sam bata da rigima ko rawan kai ga komai saidai idan kaso raina mata wayau ne za a jiku yanzu da ita. A compound din gidan muka hango motan yaya ajiye saidai baya wurin motan shi hankan yasa muka fahinci yana cikin gidan ke nan. Saidai ko da muka shiga akace ai baishigo ba don su basu mansan yazo ba ai a ranan ashe yana garine mommy ta fada. Da yake yanzu ina dan shiga wurin su mu zauna sai banyi saurin komawa side din mu ba don don wayan Aisha dake hannu na ina kallon photuna a ciki. Nan nake jin Nabila na fadawa mommy abinda ya faru tana fadin ikon Allah yanzun me ya kawo hakan kuma tunda kunce Sahiban batayi mata komai ba. Kafin wani ya bada amsa kira ya shigo a wayan mommy din ta duba take fadin ga yaya Nuhu ya kirani jin sunan data ambata yasa na dago kai ina kallon mommy din da sauri. Naga yadda take girmama wanda ya kira din suna waya tana bashi girma kamar yana a gabanta lokacin. Suma sauran duk shiru sukayi suna sauraron mahaifiyar nasu dake fadin wallahi wallahi yaya ban tura su don wani abu ba son kawai kwana biyun na bata jin dadi shi kuma baya garin yasa nace suje su duba min lafiyan ta. Shiru tayi tana saurare kafin tace ai bai isa yayi hakan ba yaya tunda bashi ya haifi kanshi don me zaice ta kwashe kayan ta a nan zai saka nasa a falon. Wasa wasa dai sai ga kira kala kala na shigowa wayan mommy din kowa da abinda yake fadi idan ya kirata din duk hankalin mommy yabi ya tashi sosai a lokacin. Zamana yayi min amfani don na fahinci wasu abubuwa a lokacin saidai abinda na kasa fahinta shine yadda mommy din ta ke fadin zance na kasa raba daya biyun inda mommy din ta dosa a yanzu. Shin mommy tana bayana ne ko kuma tana bayan yan uwanta ne don ga bayanin ta sam bata yarda sun zageni ba haka kuma bata yaba ni ba don na fahincin hausan da sukeyi sosai a lokacin duk da hankalina na nuna bani tare dasu waya nake kallo kuma ban san me suke fada ba na nuna hakan. Karshe dai yakai har mommy din ta shirya ta fita zuwa gidan tun abin safe har sai dare don ko daddy dake wani kasan saida takai ya saka nakin shi a zancen a yadda naji bakin Fa,iza. Don ance yaya wai yayi odan wasu kaya masu kyau yakai gidan dole saida ta kwashe kayan ta a falon ya saka sabbi nasa bai saurari zancen kowa a cikin su ba a lokacin. Nan fa aka sakashi a bakin dangi wasu na fasin yayi daidai wasu kuma suna fadin bai kyauta ba don ance har Alh Nuhu yace Nazifa ta bar gidan ga baki daya sai da akai ta bashi hakkurine ya barta ta zauna. Waishi ba wani daga cikin dangi da zai fada ya musa mai bai dauki mataki a kanshi ba, da wanan na fahinci ya saka masu tsoron shi a zuciya yana ganin cewa zai iya taka kowa a cikin su yadda yaga dama. Abu dai har yakai daddy dawowa gida lokacin don yadda mommy hankalin su ya tashi kada ya halaka mata da a banza kan abinda bai kai ya kawo ba a lokacin. Dole daddy ya taso yazo har ya kaisu ga sa,insa kowa na fadi a gaban dan uwa sai yaga bayan dan uwan shi. Shi Alh Nuhu ya fara furta cewa Alh Aliyu dcp kasan nafika nafi karfin ka kada kaga don mun kulla wani zumuncin dakai kamar ban iya maka komai a yanzu. Daddy yayi murmushi yana fadin kafin ka iya min komai ni zan ma idan kace hakane zaka bullo min don komai naka a tafin hannu na yake kasani kasanni na san ka don ni komai nawa ga Allah na dogara dashi baga na wani ko abin wani. Aure daine ruwan mu muka saka ga gareshi Allah yayi cewa tun farko yar ka matar modibbo ce don haka kai koni bamu isa mu hana wanan auren ba a yanzu. Daya daga cikin wa yanda suke iyayye a garesu ne yayi magana tare da fadin kaicon ku kuma ji kunya ace iyayyen mu zariyan su guda kan auren yayan ku da girman ku ku zauna kuna wanan abin. Ina kai dake da diya mace aure kakaita tayi biyayya ta zauna lafiya da mijin yau maizai sa ka koya mata cewa itace ta auro shi bashi ke auren ta ba anya Nuhu idan mun kawu wanan hali naka ba raba kan zuri,an nan zakayi ba nan gaba. Kai kuma Aliyu kabawa yayan hakkuri ku yafewa juna wanan ai sai yaran su ji dadin yin fitinan dayafi wanan din gaba. Duk da kowa na kulle da dan uwan shi hakan bai hana a gaban iyayyen nasu suba juna hakkuri ba kafin a watse sai dai na ciki na ciki a lokacin ga kowan su. Don shi Alh Nuhu yana ganin Alh Ali dcp yana kokarin nuna shi din wani a gaban shi alhalin banza yake kallon duk da yasan yana da nasa rufin asirin don bai nema ga wani duk da yayi ritaya baisa ya koma baya ba. Daddy bai tsaya ba ya shigo motar shi ya bar gidan kanin mahaifin su din yana cike da bakin ciki tare da tunanen yadda Nuhu ya dauki kanshi da girma har yana ganun yana iya taka kowa a yanzu. Dan guntun murmushi ya sake a fuskan shi don yin wani tunanen da yayi a zuciyar shi tare da dan dukan sitiyarin motan da yake tuki. Tun jiya muke da labarin dawowan daddy din a bakin fa,iza saida bamu samun ganin shi ba sai da yamma suna zaune tare da ya Abubakar mun dawo daga islamiya muka ganshi. Wurun su na nufa nakai har kasa ina gaida shi kafin na juya ina gaida ya Abubakar din dake zaune a cikin bacin rai yayi dukun dukun da ranshi. Daddy ne yake tambaya muna karatu sosai ko nace muna dai tabawa don na kusa fita harufa zan iya hada kalma yanzu yace yayi kyau mu mayar da hankali nagode nace na mike zuwa cikin gidan. Yabini da kallin tausayi kafin ya juya yana cewa dan nasa komai ya kusa zuwa karshe don ba zan bar yaran nan haka ba ana kokarin aibantasu a cikin yan uwa. Gashima a cikin gida har karima tana zargina a kansu da uwarsu akwai abinda yakai wanan muni a rayuwan bawa a sheganta ka don wani dalili can na daban. Yaba zaune yadda yake ya kurawa mahaifin nasa ido don baison tuna wanan zancen ko kadan kafin yace . Daddy tun farko ban so ka boyewa kowa wanan zance ba tunda ba tsoron su akeji ba don baka san ko waye wanan yarinyar ba kake dauka ba zata iya kwato wa kansu yanci akan komai ba . Tayi kankanta ga yadda kake nufi amma yanzu ai dole in fasa kowa ya sani don nasan ko waye Nuhu idan ya fadi magana da wasa kada ka dauka wasan ne yake maka kaima don zai iya aikata abinda ya fada. Saidai kaima modibbo ya zama dole ka kara jajircewa a ko wani lokaci ka zamo kuma mai hankuri da matar ka don kasan irin da uwarka ta zaba ma. Kamar yadda muka saba dakin mommy mukan fara shiga mu gaida ita kafin na hjy karima karshe wanda yaga dama a cikin su yakan leka umman mu a part din mu ya gaida ita. Muna shiga a yadda muka samu mommy din yasa ban tsaya ba na fito zuwa dakin hjy karima na tsaya daga kofa ina gadai ita ta amsa min ba yabo ba fallasa lokaci daya muka shigo da diyanta. Don har babban tana gida an samu hutun makaranta a lokacin bayan fitanane suke fada mata ai nice na goya Amira da zamu tafi kuma na dawo da ita a goye don ta taka wani abu da zamu fita tana kuka. Da sauri take fadin taga kafan yarinyar sai babban take fadin wanan sahiba din cire mata shi kuma tayi mata addu,a a wurin. Mai karatu idan baku manta ba nayi tallan magani a lagos kuma matar da mijinta sun yarda danu sun ban nasha sin kuma fada min wasu ina kuma gwadawa yana amfani sosai a tare dani a yanzu. Bayan na shiga ban tsaya ba don na samu umma har part din ta gyara ko ina tayi abincin da zamuci. Wanka na shuga na fito na saka wani dongon rigan silk a jikina sallah nayi don magariba ya gabato sai bayan mun idar din muna zaune a falo ne da littafi a hannu don haka kawai naji bana son cin abunci a ranan. Sallaman hjy karima ne a kofan mu take shigowa dakin muka karba kallo daya nayi mata nikan na dukar da kaina naci gaba da karatun da nakeyi. Sai bayan sun gaisa da umma ne naji ta abanci sunana tana fadin sahiba yau meya samu kafan kanwaki ne haka. Na dago da sauri na dan kalli gurin da take tsaye din ina fadin ina ganin dutse ta taka ko wani abu kafan ya dan mata ciwo. Amma na lalasheta tayi shiru mantawa nayi i fada a gasa mata da ruwan zafi da muka dawo kada wurin yayi mata ciwo da dare. Amma ai da takalma a kafanta na gani ta sake fada nace kaddara idan zai sameka sai ya samu sanadi don ban san yadda akayi ba ta cire takalman ta tako da kafa shine har hakan ya sameta. Shiru tayi ta juya ta fita bayan tace dani ta gode ta barni zaune ina binta da kallo ta fita umma ta juyo tana fadin. Bana fada maki ki rabu da yaran matar nan ba son bata da mutunci a dan maraice nace umma suke biyoni ni kuma ban iya daina kulasu don daddy. Sallaman da akayine yasa umma fasa fadin abinda zata fada a lokacin tabi kofan da kallo kaina na kasa ban dago naga mai shigowa part din ba a lokacin. ZAINAB IDRIS MAKAWA ANA DARA GA, , , , , , , , 2️⃣9️⃣ BY ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , , , , BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AL WAHHAB, , , , , , ONLINE PAID NOVEL DON ALLAH YAR UWA KI BIYA KAFIN KI KARANTA NA FITAR MAKI DA ALHAKKIN RASHIN SANI NA FADA MAKI NA KUDI NE, , , , , , Mommy ce ta shigo da fuska a dare muka fara gaida ita bayan ta amsa ta samu wuri ta zauna take fadawa umma duk yadda aka kwashe da Alh Nuhu da take kira da yaya Nuhu da mijin ta daddy da modibbo . Ba karamin mamakin faruwan hakan umma tayi ba don ban fada mata komai ba a ranan da muka dawo din. Tambayana umma tayi abinda ya kawo hakan sai ban boye komai ba na fada masu kamar yadda su fa,iza suka mayarwa mommy din da zancen. Ta dai fahinci ba laifina bane don ban mata wani abin bacin rai ba ra,ayin yin hakan daine tayi taso ta muzantani kuma abin bai tsaya a kaina ba sai ya koma mata. Amma duk da hakan sunyi min fada wanda nake mamakin meye laifina a cikin hakan da har akaga laifina kan wanan zancen. Tun wanan wajen nasha alwashi a raina cewa ba zan sake zuwa gidan su ba ko idan na ganta in gaida ita na kula wanan a cikin zuciyana ni kadai na barwa cikina hakan. A fannin daddy da Alh Nuhu kuma shi Alh Nuhu yasan ko waye daddy din don sun sha buga irin wanan wasa a tsakanin shi Nuhun nakaiwa daddy hari baiyi nasara ba. Don daddy tsohon jami,in tsarone yasan kansa son bai zauna kamar mace ba don yasan halinsu fulani da bakin rai ga riko kan dan abu kadan sai a salwantar da mutum ba komai bane a wurin su. Lokacin da yan uwa suka watse daga gidan kanin mahaifin su sai duk hankalin su ya tashi da kakaman da Alh Nuhu din yayiwa dan uwan nasu mai taimakon su don sanin halin Alh Nuhu din da kowa yayi. Domin bai fadin zance da wasa shi idan ya fada har cikin ranshi yake nufin hakan don hakane hankalin su bai kwanta ba musan man yan uwan haihuwan shi dcp din da shine jigo a cikin su a yanzu wurin shi suke dan samun hasafin rayuwa. Daddy dake zaune yana lazumi bayan idar da sallah asuba yaji wayan shi dake gefe ya dauki kara kirirrr kirirrr daddy bai motsa ba saida ya shafa addua ya kai hannu ya dauki wayan daya kara shigo da sabon wani kiran da sallama . Ba suna sai nomba tun kan ya dauka ya gane kiran nada wani manufa gareshi a lokacin. Hello ya sake fada bayan sallamannda yayi din a kamar kausashe don ya fahinci kowaye ke kiran nasa amma ya daure cikin muryan izza da isa yace wake magana bakin shi fam da addu,a . Bai dace na fadama sunana ba domin fadin sunana a gareka kamar na kaskantar da kainane gareka aka fada a dayan bangaren. Dan murmushi manya da kamar ya zamawa daddy dabi,an sa ya sake tare da fadin nasan dama kana kufule dani nima sin jiran ka nakeyi a ko wani lokaci. Au ashe kasan da hakan dama koda yake ni ba bakon ka bane ka sani don haka kar kaga kamar kaci bulus a wurina kaida danka ka saurareni nan da yan shekaru ka gani muddin danka yace zai wullakanta min ya wallahi sai inda karfina ya tsaya a kansu. Don a iya rayuwana bana son rainin wayau da wullakanci balle har kaida danka kunemi takani ta hanyar auren diyana ku nuna wai ku mazane a gareta. Aiko daddy yace dashi ashe kai kasan gaibu ke nan har kasan da cewa rayuwan namu zata kai nan da yan shekaru ke nan kuma. Yana fadan haka kawai ya kashe wayan don baida likacin wanan bakin jahilin da jahilci yayi mashi katutu a zuciyashi yake kuma rudin shi a duniya don baida arabi da boko. Yayi recording din komai ya nade a wayan shi ya kuma turawa danshi komai daya dauka din ya Abubakar yana gama saurare ya mike yana fadin lalai wanan mutumin dole su dauki mataki a kanshi ke nan. Ya kuma kira daddy din suka kara tatauna maganan har daddy na fadin shu,umine na gaske shiyasa na turo maka koda yaka fito muna ta hanyar baya. Duk da nasan ba zai iya min komai ba da yardan ubangiji duk da nasan cewa kafin duk ya aiwatar da wani abu mun gama tara komai da muke son samu game dashi insha Allahu sai mu rigashi yin komai yadda ya dace. Wanan sakon da mahaifin shi ya tura maine yasa ya kara kaimi wurin hada duk wasu bayanan da yake son tarawa akan surukin nasa. Yayin da syrukin nasa shi kuma a nasan bangaren yake kokarin bin hanyar da zaibi yaga ya halaka Alh Ali dcp har lahira karshe ya dan san tilon dansane zai gaji komai nasa sai yayan shi mata. Daga baya kuma ya dawo ya halaka kanawar shi hjy Addah gadon dan nasu yayi yawa a karshe sai ya juyo kan Abubakar din da yasan yarshi ce zataci gadon shi tunda uwarshi da ubanshi basu raye idan diyan mata ta kama a kawar dasu suma sai abatar dasu a huta da banza kamar yadda ya shafe Sambo da iyalin shi a doron kasa har abada. Wani shu,umin murmushi ya sake don yaga plain din shi ya tafi daidai ga yadda ya tsara komai a zuciyan shi shida kanshi yayiwa kanshi kirari da Nuhu maciji baka ramin kan kan ka saidai ka kashe ka shige. Sun dauka wahalan bokon da sukayi shine sunfimu ko mai daya bayan daya zanga bayan yan iska daga su har iyalan su don ba fin kowa sukayi ba da zamu zuba ido muna kallon su a cikin daula. Daddy bai koma ba mun dawo daga school muka samu mutanen gidan tsaye a waje in ka debe umman mu dake faman boyo a cikin daki wai yuka ya yanke hjy karima zasuje asibiti . Muma da dawowan mu ke nan muka tsaya muna mata sannu a wajen har suka tafi kafin mu shiga cikin gida muna masu tausaya mata. Wanan yasa yan abokan hurdan ta ke zuwa gaida ita dama wasu daga cikin yan uwa mijin da suka samu labarin hakan. Da dare bayan magariba fatima yar ta na tsakiya ta shigo dakin tana fadin wai maman su na kirana a cikin mamaki na dan kalli umman mu kafin tayi min alama da inje nabi yarinyar zuwa part din su. Tana zaune saman dogon kujera ta tallabe hannun don zugin da yakw mata ga bande an daure hannun dashi da gani dai ciwo taji ba kadan ba a hannun nata. Nan na kara yi mata sannu na kai kasa ina fadin gani ta kalleni tana fadin na shiga wurun yaran don Allah in gyara masu shimfida . Allah ya gani ban son wuce falon su iyakana in tsaya a falo in gaidasu in fita har in shiga ya kama min dole a part din su ke nan . Saida na danyi jim kafin in iya daga kafa zuwa dakin na gyara ko ina na dakin tsaba duk da darene na wanko har bayin yaran da bai samun gyara na fito. Na samu Amira tayi barci a falon zan dauketa zuwa cikine daddy ya shigo ya samemu . Gaida shi nayi ya amsa min a cikin fara,a yana fadin mutumiyan tayi barci ke nan ashe na danyi murmushi na tafi da yarinyar fatima tana bayana ta nuna min inda Amira din ke kwanciya. Kafin in fito ita yarinyar ta rigani fitowa falon wurin iyayyen dake zaune take fadin yau mami baki ga yadda anty ta gyara muna dakin mu ba yayi kyau sosai sai gani. Ban tsaya ba nayi mata Allah ya sauwaka da saida safe na fita zuwa dakin mu ina shiga kuma umma ta aikeni nakaiwa mommy abinci. Na samesu zaune suna kallo Fa,iza ke fadin aita dauka nayi barci ne nace hjy karima ce ta kirani wai na gyarawa yaranta dakin su. A cikin hausa naji mommy tace ita suraiyya bata iya gyaran daki har yanzu ko me da sai an kiraki Nabila tace bashi bama mommy su dafa mata sata a karshe aishine ba kyau. Wanan kan idan sun dafa mata sata ashe zasuji tsiya ranan hauwa ta fadi tana gyara zama ni kuwa murmushi kawai na sake don jin abinda suke fada. Washe gari kuma still ta kara nemana wai na gyaro mata part din gaba daya sai na kira suraiyya din muyi tare har fatima diyan ta. Mun fara da falo muka gama muka koma ciki ban yarda nabawa yaran fuskan raini ba muna gab da karasa dakintane dake da uban gyara don ni ganin dakin yasa na raina da wayau anty din ashe iya tsabatan ta a waje ne kawai dan muhalinta bai kalluwa sau biyu don kazanta. Muryoyin sune ya karade falon suna fadi ina mara lafiyan take ne ko tana gun Alh ne don matar bata da dama . Anty ta mike ta fito tana fadin kudai kuka sani da safen nan haka, suka ina mukaga zama ance hannu saura kiris ya guntule ta dago masu hannun ta zauna ta fara basu labarin abinda ya faru. Muna gamawa nikan nafito gaba dayan su suka sako min ido irin anga bakon fuska din nan a inda ba a zata ba don dagani sai yar wando dogo da riga irin na exacirses din a jikina na kaina kuma da hula sai sock dake kafana da muke yawon cikin gida dashi don sanyin ties din kasan. Tsab suka kalleni ban damu da kallon su ba a yanzu don na saba da hakan tun shigowan mu arewa haka zasu zubo min ido suna kallona kamar sunga wani halitta can na daban. We na don fisnish anty na fada kafin na juya ina cewa welcome ma u na good morning wooo na sakai zan fita naji anty tace dani. Ibeg sahiba go and help dem to cook break fasat for us before u go na amsa da ok ma nabada baya naji daya na fadin wanan fa ita kuma kuka samota haka. Dayan kuma tace ke badai abuwar yar aiki kuka daukaba haka wanan tsaleliyar haka kai haba wace yar aiki kika san zan dauka sirina waje aini sam ban yardada wata yar aiki ba can a yanzu. Itace dai wace nake fada maku din nan sunzo au don Allah ki bari dai ke kice muna dai irin yayan ashawo din nan da turawa ko larabawa kewa ciki akazo maku da ita gida. Wanan kinyi gangancin barin ta cikin ku wallahi fuska anty ta tabe tana fadin ke dai bari nayi magana da uban da matar gidan har dansu sunce ina nafito . Wai yar aminin ogace daya rasu don haka suba zasu yarda in wullakanta suba lokacun fa Alh nunawa yayi kona bar gidan idan ban iya zama dasu. Kinga ko ya zanyi ga yaran nan kaf din su sun dauki son duniya sun dora a kanta kona hana suna part din su lake a wurun su . Idan kinga hakan sakin fuska suka samu aishi yaro haka yake kaman kare in yaga sakin fuska saidai gaskiya kiyi taka tsantsan da irin wa yan nan tsintattun mage din idan idon ta ya bude nan gaba ba zaku iyata gidan nan. Sai ta ukun su tace kai haba menene ba gashi yanzu tana more mata ba albarkacin zama tare meye wani abin tayi hankali a nan don Allah ku bar wanan zancen haka tunda yarinyar na taimaka mata jifa yau yadda muka samu part din nan tsab. Wani iri naji na wanan maganan da sykeyi naji kamar in saka masu magana saidai yin hakan zaisa a gane ina jin hausa. Tunda a zaton su har daddy din gidan mu bamu jin ko zo in kasheki idan an fada balle shi amar da har yanzu bako yake a gidan ga kowa. Sai dana hada komai cikin dauriya na na dan rage yawan gas din na fito don tunda daddy ya dawo wanan can karon akai rikicin girki kowa ya dauki girkin shi a gidan shi da yaran shi . Don anty ce ta tayarda fitinan don me za a bamu girkin mu daban a gidan su kuma a hade masu suci na yawa a gidan da yaran su. Allah ya kawo saukin kai daddy din yace ai sai kowa din ya dauki nasa ba komai bane idan sunga hakan yafi garesu dama shi don yaran sa su hada kansu yace hakan . Kuma abinci da suke gani bashi ke saya muna ba modibbone yace a bar masa wanan nauyin don yana kwadayin ladan da zai samu ga ciyar da marayu ya dauki hakan. Daga wanan ranan aka kaiwa kowa kayan girkinshi a part din shi har muka samu arzikin saka muna freeze a dakin mu muma da aka sawo wa kowa don aje abin amfani karya baci. Na fito ban ko kalli inda suke ba son suna yan dararakun su a lokacin nasa kai na fice a part din cikin kunan rai. Ina shiga wurin mu na zauna na fara cire safan kafana na nufi cikin dakin kai tsaye wanka na fada yi saida na fito ne nake ba umma labari abinda ya faru . Murmushi umna din tayi tana fadin wanan haka hakin matan mu yake ga kishi su a zaton su kada daddy ku ya dawo ya aure ki. Idan ma harta dauka haka din ne daga baya zatayi kunyar hakan don zata gane shidin ubane na kwarai a gareki kudin ba kalan dangi bane gunsa yadda suka dauka din. Fatima ce tayi sallama ta shigo dauke da abincin da suka dafa tana fadin ga abunci inji mami nakawo maki ina fadi da sauri koma dashi ga wanda umma ta girka nan banci ba ma . Zoki aje umma ta fadawa yarinyar ta aje abincin a gaban umma ko kallon abincin banyi ba karshe ma tashi nayi na koma daki na kwanta. Barci nayi sosai ban tashi ba sai karfe biyu saura na tashi don Allah koda na fito har lokacin kwanon abincin yana nan dakin mu ba alaman an tabashi. Fita nayi zuwa part din mommy nan samesu ga turamen zani masu yawa a gefen ta a zube bai shafeni ban kuma tsaya kallo ba nake gaida mami kafin in wuce zuwa dakin kwanan su don nasan mutumiyana fa,iza tana can dakin tunda ban ganta a falon cikin su ba. Tana zaune tana waya na shigo ta kalleni da murmushi taci gaba da waya har ta gama ina dan duke ina karanta wani takardan da nagani. Tace ina jiran ki tun dazun kinga kaya a falon mu anko ne aka kawo muna na yar kanwar daddy da zata aure. Ke ai kin santa wace sukazo ranan har take fadin ki bata kanki kuyi musaya da ita nace na gane ta. Itace zatayi aure kin san yayan modibbo taso kamar ta mutu amma yanzu zata auri wani dan uwan baban sune a jos shine . Jos na tambaya tace min eh ko kin san jos din ne ta tambayeni tana kallo na nace ban san ko ina a arewa, ba banda wanan garin. Zaki sani har idan mun dace za a tafi damu ai zakiga gari na danyi dariya ina fadin wa zai tafi dani bansan kowa ba ? Tace aukin san mu ko kuma tare damu zaki tafi don su anty Nabilace manyan kawayen bukin kinga kuwa ai damu za ayi komai taso muje falon mu duba ankon. Ta daga na bita a baya muka zauna ni dai ina a takure ta jefo min zanin daya a jikina tana fadin wanan nakine. Na nuna kaina da mamaki ina dagowa nace ni tace eh zaki koyi daura a tamfa ko, kome kuke kiran shi a can nace ankara. Tace akwai wasu da za,a kawo muna wani irn dinki zakiyi da naki duk a cikin turanci buga buga muke maganan mu din dasu. Kafin nayi magana mommy tace a cikin hausa ina tasan inda ake dinki ko tasan inda za a dinka din balle takai ayi mata ku kai mata ayi mata. Nabila ta dago tana fadin ni kin san aiba irin dinkin su zanyi ba don haka karma a dora min wanan nauyi ban iyawa . Tellana zamu kaiwa yayi muna dinki ta fa,iza ta bada sai hauwa tace dama kun fi kusa da ita sai kukai ai maku tare din. Mommy tace na rabaki da wanan halin Nabila yarinyar nan idan bata biku ba wata sani a garin nan yanzu zaki wani fara fadin maganan banza a kanta tun yanzu. Shiru sukayi ga baki dayan su a falon har mommy din ta kare ni ke tambaya me ake dinkawa ga ango zanine ko buje ko dogon riga ? Wanda ranki ya zaba idan muje gun maidinkin zai baki hotone ki zabi wanda yai maki kyau sai a dinka maki nace buje nake so ba zani ba ko dogon riga. Mun dan dade muna hira a dakin dasu har zuwa yamma na koma part din mu ina bawa umma labarin zance zanin da yadda akayi. Washe gari ko sai ga Fa,iza har dakin mu tace in shirya zamu kai dinkin ankon namu saida ta jira na shirya duk da ni ba wani kwaliya nakeyi ba mun fito ne sai muka hadu da ya Abubakar zai shigo gidan mukayi mashi sannu da zuwa. Ya amsa yake tambayan mu inda zamu tafi Fa,iza ta fada mai yace kada mu dade mu daina fita wuri mai nisa haka. Bada motan gida muka fita ba taxi muka shiga zuwa wurin akwai mutane a shagon dinki tayiwa tellan bayani ya kawo min photuna na zaba sai suka saka min dariya wai ai din kin iyamurai ne wanan dana zaba nace shi din dai nake so ni akai jinga ya fadi kudin shi. Mun dawo gida take basu labarin irin dinkin dana zaba sukai ta min dariya wai ni zan dawo ince ban shi wata rana aka shigowa masu da nama kallon naman nayi sai gabana ya fadi. Da sauri na fita zuwa part din mu har na zauna zuciyana yana tashi hankalina kuma bai kwanta ba da ganin wanan naman . Hardai hakan ya jawo min yin amai bayan na fitone na kasa daurewa na fadawa umma abunda nake ji game da naman . Sai hankalin umma bai kwanta ba da zancen dole ta kira mommy ta fada mata abinda ke faruwa game da naman da nagani a part din ta dazun . Sun ki ci zuwa safe naman yayi wani irin baki ba dadin ganin hakan ya kara tsora mommy hae umma ga lamarina ga buki kan sun fara a gidan sosai kullun cikin fita auke yanzu. ZAINAB IDRIS MAKAWA ANA DARA GA , , , , , , , , , 3️⃣0️⃣ BY ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , , BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AL RAZZAQ, , , , , , , , ONLINE PAID NOVEL DON ALLAH NA KUDINE KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA BA TARE DA DAUKAN NAUYI BA A KANKI YAR UWA, , , , , Wasa wasa buki ya fara kan kama zakace ko a gidan daddy ake bukin duk wanda yazo ba zaice yaga umman mu ba a taron nan saidai nikan dani ciki tsunbul ake komai ko banzo ba fa,iza saita kirani a lokacin. Anko har kala biyar akai muna ko wani da sunan shi inda Allah ya kara rufa min asiri akwai baki da suka zo masu daga illorin da ibadan kawayen gwaggo Asiya da diyan su. Duk da manyane sun girme ko anty Nabila balleni karaman su sai ya kasance sunji dadin hakan a tare damu duk inda na shiga zasu nemoni su fada min abinda suke so. Sai itama gwaggo din hakan yai mata dadi don na zama kamar ta gida a cikin su yanzu din tunda ba sanin matsayina sukayi a garesu ba. A gaskiya naga mutane masu son junan su da kaunan zumunci a wanan bangaren nasu daddy don har daddy din da kansa saida ya shiryawa amarya dakin guda nasa na kansa hakama gwaggo Hari itama tayi nata bajintan sosai a matsayinta na kanwar mahaifiya kuma mai buki. Duka gidajen nasu ga baki daya ya kicime da baki yan buki don haka ko ina ba masaka tsunke a gidan lokacin haka yasa tausayin umman mu da azzalumi Nuhu yasamu zama a cikin hijabi don tsoron sherin sa da halinsa sai naji tsanan wanan mutumin a lokacin ya kara shiga na sosai wallahi. Tundai da Fa,iza ta nuna min iyalinshi a wurin kamu take fadin ga iyalin gidan matan yaya modibbo can sune iyayyen matansa da yayan su. Na kalli wurin sai wani hura hanci da jiji da kai da sukeyi suko mutane yan uwa sai wani basu girma akeyi a wurin ana fadin wai buki yayi buki tunda har yan gidan Namadi sun halarci wanan bukin haka kwansu da kwarkwata. Wasu dake kusa damu suke fada daya tace don sun san su din masu bukin masu hali ne kamar su da ai basu zo ba yo gwaggo Hari ai itama tana nuna masu itace ki duba shigan ta ki gani wane nasu Allah dai ya cece ta kada kuma a sakata a baki don kinsan su basu son suga kafisu fitowa a wuri yanzu suna nakasa mutum ya koma baya . Keko dai kinsan fa sune kusan abokan karawan su a cikin family din nan anty hauwa ce ta kwala min kira daga wurin da yan gidan suke zaune nazo. Tunda na tunkari wurin suka zubo min idanuwan su banjin zan iya gaida kowan su don haka ina zuwa nake fadin gani tace jeki ki kawowa su mommy wasu kujera guda biyu. Nace me i don no, where to find chair now, people are sitdown on it, who igo weak here ? Ina fadin haka na bar wurin don idanun da suka zobo min din suna magana a kaina don naji daya ta fara fadin wai wanan yar ce dama ba bahausa bace gata da ka ganta zakace yar filoce ita. Waima me sukeyi a gidan har wanan lokacin basu koma bane daya ta fada sai lokacin dana juya zan wucene na farga da matar ya Abubakar a wurin na sakai na koma inda na fito. Duk da bukin ya kawatar dani saidai hakan bai hana zuciyana jin bakin cikin dake damuna ba na duba duk taron nan amma ummana na gida a kumshe ta dalilin su. Taro yai taro don bansan kowa ba ga iya yi dana koya a geto kuma tun ina karamana na bude idona a geto ne yasa suka ban raba kayan buki don su yan gida kada suyi laifi a wurin su. Aiko ido rufe tunda ba sanin su nayi ba nake ba kowa daya daya ko kin dawo kina min guntun turacin ki bazan kara maki ba. Har kowa ya samu da hannu wata yar gidan ta kirani kamar in shareta sai naje take fadin i beg give three servoner for our moms na dan kara kallonta kafin in tura hannu cikin buhun na ciro jakkuna guda ukun daidai na mika mata da sauri tana magana na bar wurin. Idan ka jawo rigana ta baya zan sa gwiwan hannu in buge inci gaba da tafiya bana waigen bayana balle inga waye ke jana yar Geto ke nan sai ido. Anty amaryan daddy ta yafotoni da hannu nazo wurin take fadin in ba bakinta da yan uwanta baida yawa na mika masu buhun duka na koma wurin motan da muke dauko kayan a nan na samu gwaggo hari tsaye. Tana ganina tace dani ance ba a bani sai kinzo ki ban na mutane na gasu can dan murmushi nayi karo na farko a warin gabanta ne yayi mugun faduwa saida ta kadu ita kadai tasan abunda idon ta ya hasko min a kaina lokacin. A sanyaye nace gwaggo how many a cikin murmushin da har lokacin kesa gabata faduwa tace give me firty, na bata ashirin ina dariyan daya daga mata hankali don su suka san mahaifina da tashin shi sosai don a dakin su ya tashi in kin tuna da labarin mu. Tun wanan lokacin take bin na da ido da kallon tsoro a zuciyanta tabbas yayan su ya boye masu wani siri duk yadda akayi ba zata taba manta dan uwa kuma abokin shawara a gareta ba sambo. Kai yar sambo fa da matarshi sunyi tambaya fun ana cewa suna raye har aka koma cewa indan sunje gun malamai duhu ake gani ba a ganin ma,ana ke nan mun mutu saida kama kawai don haka taba zuciyan ta salama a kan abinda ya fara raya mata din. A can gidan ta muka nufa bayan an tashi a taron kowa yana mayar da fadi ina zaune nayi shiru don hankalina ya koma akan umma lokacin. Muryan gwaggone dake fitowa tana fadin yau kun bamu wahala kun dauki rabon abu kuba wanan bobanyan da bata san nagida balle na waje. Da sauri na dago kai don wanan hausan yaimin tsaurin fahinta take fadin ai kunyi daidai don da an wawashe shi duka lokaci guda amma yanzu kunga kowa ya samu ai . Wallahi gwaggo idan ba haka mukayi ba ba zamu iya da mutanen mu ba amma kinga ta raba an zauna lafiya har yan gidan kawu Nuhu daya daya ta mika masu shine suke fada wai ba,a karamasu ba a wurin. Kyale yan sallo da jin kai ai na hangosu suna min wani kallo na fita batun su wa zasu dinga hankadawa su a dole ga matan mai kudi dole a bisu da ace ma mutum baisan asalin kudin nasa bane zasuyiwa mutane iskanci. Wani irun kallo nayi mata kafin nayi kasa da kaina lokaci guda ina duban wayan Fa,iza dake hannuna lokacin don ni banda waya ba a sai min ba. Wayan gwaggo ne yayi kara lokacin ta dauka tana waya sai na bita da kallo don matar nada sha,awa gashi tasan kanta sosai irin wayayun matan kaduna din nan ne da suka san duniya ta waye har ta gaji gidan ta tsab dashi babune kawai babu a gidan don tsaruwan shi. Da murna ta juya tana fadin ashe kace yau ina da bako ke nan barin fadawa driver yaje dauko ka kome na wayan yace naji tace kwarai kuwa abokin kane dole kazo bukin shi saika iso din banda dare kasani. Gwaggo halan ya Mustaphane zai shigo hauwa ta tambaya tace shine dan ka,ida aikinji yace kada azo taron shi sai na ganshi dai kin san sune angon ne ai. Sune fa ya modibbo ma daya koma shekaran jiya na ji matar shi na fadin yau ko gobe zai dawo dazun . Mikewa nayi tsam dayan yan ibadan din bakin nan tace dani enbalalo nace i wan go see my mother nasan yanzu tana can ta damu da rashin dawowana gida. Na kalli inda fa,iza take ina fadin tashi muje gida tace min da wani mota mujira anty Nabila ta kaimu ai yanzu zamu wuce. I go track na fada tare da daukan jakkana na fita banyi sallama da kowa ba a get na hadu da motoci suna shigowa gidan sun wuce niko na fita na fara tafiya don nasan wani hanya kawai zan dauke ya kaini unguwar mu don na gane hanyar. Na shigo gida a gajiye kamar walkiya don saurin da nakeyi suma suka shigo suna tambaya ko na dawo mommy yayi min fada sosai da na biyo kasa ban jira yan uwa ba. A part din mu na shiga na samu umma zaune tana lazumi ga tv an kunna yana aiki gaida ita nayi ta amsa da kai na shige daki na kwabe kayan da suka dameni a jiki don ban saba saka atamfa ba a jikina haka. Duk dasun bani kaya amma nafi son saka yar katin dogon riga ko yaushe ko wanduna nafi jin dadin su a jikina idan suna saka din. Wanka nayi nayi sallah ban fito fallon ba na kwanta tunanene barkatai na dinga yi har barci ya daukeni a hakan sai safe harda makara don umma na tayar dani ina kin tashi don gajiya. Sai bayan na hada muna abin karyawane daga baya aka aiko muna da abinci part din mommy da aka kawo muna an dafa don bakin da suka kwana gidan. Haka dai nake jin kaina ba dadi a ranan don bakin rai dana wayi gari dashi haka kawai na dunga jin raina yana baci ga komai dan haka ban fita ba ranan saida yamma koshi Fa,iza ce ta matsa min na fito mu tafi wurin event din da za a yi a ranan yasa na daure muka fita. Saidai muna kawowa wajen gidan daddy din matasa ne a wuri sun kai su biyar ga daddy a tsakiyan su muka fito da sauran yan matan da sukazo ta hanyar su Nabila da hauwa. Ya Abubakar da fuskan shi ke fuskantar cikin gidan ya dan tsura muna ido har muka fito aka fara gaida su na kawo wurin ina gaida da daddy jin yadda na amsa yasa wanda yaba kofan baya ya dan juyo don ganin me maganan. Saida na kadu sosai don ganin wanan fuskan da ba zan taba mantawa ba komai dadewa a idona don ranan nayi mai kallon tsab a asibitin duk da kusan shekara biyu ke nan yanzu da watani da faruwan haka . Shima dai din yaso kaduwa saidai a can kasan zuciyar shi saboda iya duniya da yayi wajen mu,amula da mutane ya nuna bai taba ganin fuskan ba ko sanina. Duk abinda ke faruwa ba wanda ya nuna yasan da haka a wurin in ka debe mutum biyu da suka gwane da aikin su na jami,an tsaro a lokacin. Yadda ya nuna min din yasa na gane ko bai ganeni ba ko kuma kuma wani abu dai amma yana da wuya yace bai shedani ba a yanzu gaskiya. Da sauri na bar wirin gabana yana faduwa don nayi bala,in kaduwa da ganin dan hayan gidan hanyan mu daya zauna na yan kwanaki a ikko s gidan daya damu yanzu a gaban daddy din. Muka bar wurin sai gasu kuma har yaya Abubakar din sunzo wurin event din matar shi sai wani jiji dashi matar shikeyi a wurin har akayi taron aka watse haka kawai na tsunci kaina da boyewa ina Allah Allah in dawo gida in fadawa umma gamon da nayi a ranan. Daga can nisa kadan damu suke zaune don a cakude ake a wurin maza da mata ana ciye ciye saman table din kowa da irin zancen da sukeyi a wurin su. Ya hango ni zaune na rungume hannayena saman kirjina kamar ina tunane kafin in juya ina magana da Fa,iza dake gefena. Har lokacin mamaki da tamtama yakeyi na ganina kuma a gidan su tare da yan uwan shi na kusa kuma alama ya nuna cewa sun saba dani a gidan. To udan nice yaya akayi nazo gidan su ga guma mun saje da yan uwan su mata don zubin mu daya dasu wurin kama saidai ni ina da haske da tsayi fiye dasu. Kai anya ba kama bane yake gani a hakan to ga wanan din ma da turanci ai yaji uncle yayi mata magana a yanzu a fili ya furta how comes haka ya faru ya dan kira yaron shi yana masa rada ya duba ya ganni a zaune yadda nake ina faman tunanen da nakeyi a lokacin. Duk da taron yayi kyau amarya da angon ta sun sha kyau sunji kayan alfarma a jikin su kowa ya yaba da hakan sai fadi ake an nuna hali a wurin sha,anin bukin gaskiya ba bangaren amarya ba bana angon ba kowa ba a barshi a baya ba . Amma ni duk wanan bai burgeni ba kwatsam naji wai ana kiran sahiban lagos da mansurat ibadan, da idayat da kubura illorin su fito su nuna farin cikin su a wajen nan MC yana ta faman nanata hakan . Atake ya furta impossible a fili how comes wanan yarinyar tazo nan kuma ? Kidan yarbawane ya fara tashi a wajen a daidai lokacin da nake fadin emmi ina karkada hanayena sai Nabila ta taso a fusace ta rada min idan ni yar gida banyi ba ai sauran ba zasu yi har bukin ya kawatu. Tana wucewa na fara takowa daga inda nake lokacin da kowa ya baza ido yaga su waye ake kira a filin yan kudu da suka. Nasan yadda rawan su yake tafiya da kidan don haka nake bin wakan ina juyawa a hankali suma sauran ukun suka fito da irin rawan dukan muna da ankon a jikin mu da suke kira da dinkin kabilu na zaba akai min sai gashi, duk dinkin dana sa sai ya zarta na sauran manyan yan matan masu ji da kai a wurin taron sai bina suke da kallo yadda dinkin ya dane jikina. Holl din ya dauki ihu don rawan da mukeyi din fuskana a daure nake rawa, dama rawa kan ai ya kare a wurin yarbawa don haka mukayi yadda suke rawa suna dukawa har kasa . Nan aka shiga muna mannin kudi daga abokan ango yan uwa da abokan arziki wasu suka fito suka tayamu rawan har da iyayyen su kubura din suna manni suna rawa don su a ganin su an karrama masu yaran sune a wurin. Kidan ya kare muka fito mc nayi muna godiya na nufi wurin da nabar su fa,iza a zaune na same su na zauna suka shiga min dariya wai ashe na iya rawa haka shine basu sani ba . Na danyi murmushi da shine halina sai dimple dina ya dan lutsa ina dariya dago kan da zanyi sai a table din su yaya Abubakar da yake min wani kallo mai kama da harara nayi saurin kawar da kaina gefen da suke din . Sai idona kuma ya sauka kan wanan bakon da ban san matsayin shi ba a gun su daddy tunda tare na gansu. Ni da kaina na tsawala da zama a wajen taron, na mike tsaye kamar zan tafi wani wuri na faki idon mutane na nufi kofan fita daga hall din taron ko zan samu idon sani ya kaini gida duk da dare ne a lokaci don indan ta nice zan iya bin duhun dare in kai kaina gida a wanan lokacin ba don fadan mommy da zatayi min ba. Don Allah kadai yasan iya inda na taka da kafa a cikin garin lagos kan talla dan neman abinda zamuci wa cikin mu nida dan uwana da mahaifiyamu. Zama nayi saman wani dankalin dake kofan shiga wurin taron ina bin mutanen dake shige da fice a wurin ko zanga idon sani da zai kaini gida . Duk da naji mutum ya zauna a kusa dani hakan baisa na dago kaina ba tunda nasan wurin taro ne muke dole akwai mutane da yawa a wurin dake cikin irin yanayina. Saida muka kwashi kamar second goma a hakan naji ance dani how comes you come to kaduna ? Na dago kaina da sauri na dan kalli gefena koda wani maishi ke magana banga kowa da yake magana dashi ba dama kuma ba sake murya yake kamar sauran mutane bashi. Nan ma din kanshi a duke yake kafin ya dago ya kalleni ido da ido gabana ya fadi rass tabas shi din daine a zaune a kusa da inda nake zaune daga gefena na kara juyawa naga wa yan nan yaran nasa dana san shi dasu a baya dan nisa dashi kadan suna tsaye kamar suna gadin shi. Bakiji tambayan da nayi maki bane ya fada a tsawace na dan kadu da tsawan da yayi min din sai na mike tsaye yace don't try that, or my guys take u out, of dis place now. Tsoro ya kara kamani don nasan zasu iya min abinda ya fada din saidai a irin karfin halina ban nuna hakan ba a fili nace dashi shabi u no me before ? Sai ranan nasan shi mutum ne don karfin halina daya bashi dariya a lokacin yasa shi dan murmushi mai sauti har ina jin sa mikewa yayi kafin yace. Well if u continue to pretend like u don no me before is good for u, and if you tell any body in this town about me. That i am d guy living in ur compound for some days, i will cut that ur yeye tongue, ya watso min wani kallo ya fara tafiya sauran suka bi bayan shi da sauri kamar walkiya suka shige motar su na bisu da kallo. Sahiba what are u doing outside muryan yaya Abubakar ne a bayana ya fadi hakan a cikin tsawa na juyo da sauri cikin dan kaduwa don na firgita tunda a tsorace nake lokacin. Duban hanyar da suka bi nayi kafin na kara juyowa gareshi ina fadi a cikin i,iniya da cewa i just come out to have some fresh air. If u are tiered, call some one to take u home, why are you staying here u alone ? Sai kuma naga ya fara dan dube dube kamar yana neman wani ashe tare da matarshi suke tafe ta tsaya magana da wasu yan uwan su a baya sai gata tana fadin honey na barka kana jiran, , , , Sai ta kasa karasa abinda zata fada din don maganan ya makale mata a daidai lokacin da ta gani tsaye dashi muna magana . Idan gida zaki sai mu sauke ki don gida zamu koma yanzu ya fada da sauri nace zan tafi nabi bayan su ina baya zaune shida ita suna gaba. Ya ciro waya a cikin aljihun shi yana neman layi kafin ya gyara zaman ear pods din shi yana fadin hello Nabila idan zaku gida kada ku nemi sahiba gata nan a tare damu zamu koma gida. Sai lokacin na gyara zama da dan kyau ya kashe wayan ya kada gaban motan yana fadin kada suje suna neman ki idan angama event din basu ganki ba hankalin su ya tashi. Dan tsuki Nazifa tayi tana kawar da kai gefe ya kallota ta sai ta dan wayance da fadawa saman kafadan shi tana fadin wallahi duk na gaji yace idan mun isa sai ki kwanta mana. Bai kaimu gida direct ba saida ya tsaya a wani wajen ya shiga ya barmu a motan waya Nazifa ta fara yi aka dauka take fadin mufa mun tafi gida meshi ta tambaya tace wallahi mun tafi me zamu tsaya jira mukan da auren mu bamu gama amarcin mu ba. Tace Allah gamu wata yar iskan kalan dagi nasu nason ai ta kwabsa muna wallahi sai nayi maganin yar iskan yarinyar nan idan bata fita min a ido ba kan mijina. Wallahi fa itace ta sake fada ko meshi ta tambaya a ina suka hadu dani take fadin ba yar bariki bane ki duba fa yar nan dufa bata fi sakina ba a shekaru har ta iya son maza haka. Bari zan kiraki idan mun isa ta fada da ta hangoshi daidai zai karaso inda ya aje motar shi din, damu a cikin ta muna jiran shi. Ledoji ne guda biyu ya shigo dashi motan yana zama ya juyo ya miko min guda a baya inda nake zaune take dis ya fada ita kuma ya mika mata daya. Naji tace dashi ka aje nan mana ya dan kalleta kamar zaiyi magana sai kuma yayi shiru baice komai ba ya tayar da motan muka tafi. Har suka kawoni kofan gidan daddy ba wanda yayi min magana a cikin su na sauka da ledana a hannu ina masu godiya na shige cikin gida. Da sauri na nufi part din in fadawa umma abinda nagani yau a garin wanda nake cikin mamakin hakan da zullumi. Muryoyi nake ji a part din mu a ciki harda na umma a cikin muryan don haka na shigo falon da mamaki ina sallama aka amsa min sallaman. ZAINAB IDRIS MAKAWA Too., ANA DARA GA, , , , , , , 3️⃣1️⃣ BY ZAINAB IDRIS MAKAWA BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM YA FATTAHU, , , , , , , ONLINA PAID NOVEL YAR UWA KIJI TSORON ALLAH A DUK LOKACIN DA AKA AMBACI HAKAN A GAREKI KI TUNA DA AKWAI GOBE . Har wani riba zaki samu a wurin abinda akace ba a yafe a kansa ba ki nace sai kin karantashi kamar wani zancen daya yafi karuwa akan addini iyakafa rayuwan zaman duniya ce labari. Allah yasa mufi karfin zuciyar mu mu gujewa duk abinda zai kaimu ga halaka Allahuma amin. Ba kowa banw a dakin Asabe ce mai aiki ta kawo wa umma hira sai fatima da bata da lafiya aka barta a gida wurin umma tana kwance tana barci a dakin namu. Gaidasu nayi na aje ledan da na shigo dashi na nufi hanyar bed room din mu kai tsaye ina jin Asabe na fadin an tashi ke nan tunda ga yar nan ta dawo. Ban tsaya sauraren ta ba na shige ciki kayan jikina na cire na daura zani kana na shiga bandaki na watsa ruwa don nayi sallahna a can. Fitowa nayi na samu Asabe ta fita ta koma part din da take sai fatima dake barci tana jin muryana kuma ta mike ta taso zuwa inda nake zaune tana kwanciya saman jikina. Hannuna nakai na dan shafa wuyan ta har lokacin da sauran zafi a jikin ta na tambaye ta ko taci abinci ta girgiza min kai alaman bataci ba. Na zauna a kasa na bude ledan nace ta taso taci takai idon ta a ledan sai ta dan bata fuska dana matsa sai ta sauko na fara bata drink din milk sai gashi tasha sosai umma dai tana zaune tana kallon mu na bude kajin da kamshin shi ya hade dakin yasha kayan hadi irin na sayarwan su. Yakai kamar sau uku data karba saiga uwar ta shigo ta dawo don yar data bari a gida mukai mata sannu da zuwa take fadin ashe sauki ya samu . Yanzu jin dawowan yarta ta tashi dazun ai har ta bamu tsoro don amai tayi sosai ga jikin nata yayi zafi sosai kuma . Nayi mamaki jin Anty na godiya kan abinda akaiwa yarta matar da take dagawa kowa kai a gidan tana nuna ita tafi kowa da komai kan yarta sai gashi tana muna godiya goran milk din gaba daya da naman na raba biyu na mikawa fatima din suka tafi . Mikewa nayi na rufo kofan dakin na dawo na mikawa umma kayan na zauna a gefen ta da alaman magana a bakina lokacin. Meya faru umma ta tambayeni tana kallona na nisa ina fadin umma na sake ganin shi a garin nan fa yau a gidan nan da zamu fita tare dasu daddy sai kuma a wurin wanan wasan da mukaje yanzu. Wa kika gani umma ta tambaya nace wanda ya kai Amar asibiti da soja sukazo nema a gidan mu rana wanda yake ban kudi idan mun gashi. Gidan nan fa umma ta tambaya nace wallahi umma kuma yau ma yace kada na kuskura na nuna nasan shi a baya idan nayi haka na kyautawa kaina. Innalillahi umma ta ambata kafin tace Sahiba ina tsoron lamarin ki wallahi tun ranan da za, a kashe mahaifin ku irin kukan fitinan da kikayi sai yanzu nake gane hakan nada dalili ashe. Yanzu abinda nake so dake kada ki kuskura ki nunawa kowa cewa kin sanshi kamar yadda ya fada koma me hakan ke nufi ubangiji Allah ya mayar muna dashi alheri. Amin na fada a sanyayye kafin in koma tunane take tambayana wanan fa tana nuna min ledan dana aje da kayan sanyi, nan na fada mata komai daya faru har wayan da naji Nazifa tanayi a motan game dani. Haukan kishi ne wanan shi din ai yasan abinda yakeyi duk da sheri gadon shi tayi abin a jinin su yake masu dama. Washe gari ma hakan na tashi babu walwala duk tunane ya dameni a lokacin bayan sallah asuba na koma na kwanta lokacin na farka da sauri don mumunan mafalkin da nayi na tashi a cikin damuwa. Daddy nayi mafalki dashi mota tanata turnbuling dashi saman hanya ga shi yana neman taimako a cikin motan ba wanda ya kawo mai dauki a wanan lokacin ne na falka nayi wani irin zufa sharkaf na mike zaune. Ina bin falon mu da na kwanta bayan sallah asuba na dawo nan na kwanta a nan na yi wanan mafalkin da daddy din da nayi ya kuma tsorotani. Mikewa nayi da sauri na nufi wajen gidan babu kowa a wurin sai yan aikin gidan dake aiyukan su a lokacin. Na dan bi ko ina da kallo idonane ya sauka kan mai,aiki dake faman wanke motan da nayi mafalki da daddy a cikin sa ya samu wanan hatsarin. Juyawa nayi na koma cikin gida har lokacin gida na tsit kamar babu kowa a cikin sa don kowa na daki yana barcin safe a lokacin. Part din mu dake can kuryan gidan na nufa na tura kofa na shiga sai naga umma a tsaye tana mamakin ina naje a lokacin don bana fita a irin wanan lokacin. Tambayana tayi a cikin harshen yarbanci da ina na fito nace na fita waje ne ina zama ta bini da idanu kawai. Bamuyi wani girkin abinci ba tunda aka fara sha,anin bukin nan daga gida gwaggo Asiya ake shigo da abinci don yan aiki dake girkawa. Don haka na koma nakai kwance a inda na tashi din umma zama tayi tare da kuna tv tana sauraren azkar din safiya da sukeyi a tv kullun . Barcine ya kara daukana a wurin na danyu nisa kuma na sake yin maka mancin wanan mafalkin da daddy din sai dai wanan karon wani mutum na gani yana kwasan dariya irin na kyata muryan shi babu dadin ji. Wani irin falkawa barci nayi tare wani irin zabura da har umma saida ta dan razana dani yadda na falka din fita nayi irin na dazun din . Saidai wanan lokacin motar an gama wanke ta sai sheki takeyi hasken ranan daya fara fitowa yana haskata . Juyawa nayi na koma cikin gidan da shigana part din mu nace umma suna son su kashe daddy a yau din nan. Sahiba kanki daya kuwa nace wallahi umma na gani har sau biyu a cikin mafalki sai akace maki mafalki kuma gaskiyane ko ? Wanan gaskiyane idan har daddy ya shiga motar shi baka a yau zai iya halaka subbahanallahi ta fada tare da mayar da hankalinta a wurina. Kada ki yarda kiyi wanan zancen da kowa ta fada min a cikin daure fuska idan banyi ba duk abinda ya samu daddy din kece da laifin hakan umma . Na fada ina komawa na kwanta tare da runtse idanuwana mafalkin yana dawo min kamar a lokacin nayi sa. Mikewa naga umma tayi ta fita daga part din namu na mayar da idona na rufe sai can naji muryan mommy a kusa dani take fadin. Sahiba meke faruwane wai dake idanu na bude a hankali nace mommy ban sani ba nima amma dai wani abu mara kyau zai samu daddy a motar shi yau idan ya shigeta. Kallon umma tayi jikin ta ya fara rawa umma ke fadin yanzu ya za,ayi hjy dole in fadawa Alh mommy ta fada kada ya dauki zancen da wani manufa amma ? Bari dai inje mommy ta fada ta mike da sauri ta fita zuwa part din daddy din ankai kamar awa daya sai gasu tare da mommy din har part din mu. Ina zaune a cikin damuwa nayi shiru na kurawa kasa ido ina tunaje yayin da duk kafana na dora saman kujeran na dunkule a cikin light pink din hijjab dina da yaya ya saya mun. Ummace da take zaune ta kurawa tv da ake bayani akan sallah ido tana kallon yadda malamin ke bayani ta amsa masu sallama. Tun daga kofa daddy ke fadin yau meke faruwane diyana ance kinyi mugun mafalki dani hankalin ki ya tashi ko ? No ba mafalki bane daddy gaskiya ne na fada mai ina dagowa a cikin damuwa zama yayi a kusa dani yana fadin meya faru fada min inji. Sai hawaye na kasa magana a lokacin umma tace tunda asuba fa ta fita ta dawo ina tambayan ta tace min ba komai. Ta kwanta kuma sai gashi ta tashi a tsorace tana firgita take fada min wai zasu kashe ka yau din nan idan har ka shiga motar nan taka Baka ta waje. Ba abinda zai samu daddy ki da yardan Allah kinji Sahiba yana dafa min kafada na na girgiza kai nace don Allah kada ka shiga daddy. Yayi murmushi irin na manya jin haka da sauri na mike tsaye na nufi dakin kwanan mu don bamu raba daki da uwata ba har yanzu a gado daya muke kwana tare. Wani ruwa na dauko na fito dashi hannun shi na kama na shafa mai ruwan yana dai kallona bai ce min komai ba suma duk ido suka zuba min suna kallona. Alh yarinyar nan fa akwai abubuwa a kanta gaskiya baiyana daine basuyi ba har a gane hakan don wallahi ranan itace hana muci naman nan dana kai ma ya canza kala . Sahiba din daddy ya tambaya mommy tace kwarai kuwa Alh tace kabar yar nan wurin nan kawai inda ka ganta abubuwa da dama wallahi in sahiba ta fada duk sun zama gaskiya zuwanta garin nan. Kin san maza da karfin hali don daddy din murmushi yayi yana mikewa yace ashe tarihi zai maimaita kansa ke nan don haka mahaifiyar Attu take ai itama sai bayan mutuwan ta aka samu galaba a kan zuri,an ta. Ba komai kada ku yarda da wanan abin kinji idan kana yarda da irin hakan imanin ka ne ke samun rauni ya fada a karshe ya fita mommy ta bishi da fadin kada dai ka shiga motar nan yau Alh gaskiya tunda har an fadi hakan. Bayan fitan shine mommy da hankalinta bai kwanta ba ta daga waya ta kira yaya Abubakar din tace bayan sun gaisa kazo yanzu ina neman ka ta kashe wayan nata. Sai gashi ya kira hankali tashe da alama a barci yake lokacin yake fadin mommy lafiya meke faruwane i hope dai kowa na lafiya a gidan tace kadai zo nace maka yace gani tafe mommy. Ba a dauki lokaci ba sai gashi su Nabila ke fada mai muna part din mu tare da mommy din ya nufo can. Sun gaisa ne mommy tayi mashi bayani tiryan tiryan tundaga farko kallona yayi tare da fadin Na, ur mamiyota tell u dis torry in ur dream, or what, sai kuma yayi murmshi yana fadin yanzu me daddy yace akan hakan ? Zaifa shigane idan ba an masa da gaske ba mommy ta fada a cikin damuwa ya mike yana fadin daddy ne baisan wanan yar tasa ba don har magani tayi talla a lagos, Don haka ba abin mamaki bane idan tana fadin hakan a yanzu ni ba abun mamaki bane a wurina don nasan waye Sahiba. Ya fita yana fita ya nufi wurin daddy suka gaisa yake tambayan shi matar shi yace tana lafiya bissimillah daddy yayi mai yace ban koyi brush ba na zo nan . Daddy ina key din garejin nan ya kallo dan nasa yace yana nan yace a dauko wancan dayan motan dake ciki a wankrshi kafin daurin aure sai a kai wanan din ciki ajeshi. Kaima ka yarda da zancen su ke nan ko yayi murmushi ya mike ya soma tafiya zuwa waje kana yace ba kasan yar nan taka bace daddy har yanzu . Bai yarda yabar gidan ba saida aka fito da wata motan aka fara wankewa yace zai tafi gida ya shirya kada ya makara sukai sallama . Mommy ne tazo take fada muna yadda akayi hankalin kowa ya kwanta saidai kuma mommy tace waye wanan mutumin da sahiba ta gani a cikin mafarki? Hakana na shirya muka tafi don ranan ne bukin gashi kuma hankalin mu ya kasu gida biyu kan wanan zancen. Muna gidan bukin aka bugowa su mommy waya motan daddy ta kama da wuta a cikin gareji sai da kyat aka samu aka kashe wutan . Gaba dayan mu muka koma gida tare da wasu yan uwa nasu abin dai baiyi kyau ba gaskiya don haka kawai akaga motar ta kama da wuta. Kusan motar muce ta karshen dawowa a gidan muna fitowa ido yayo kanmu caaa har saida muka tsargu da kallon da ake muna din ashe mommy ne ta fara fadin dama Sahiba ta fadi. Ashe abinda zai faru ke nan ya tsaya ga motan shine mutane suka sako muna ido da muka shigo gidan a take sai akaso a juya zancen wasu suce kila ina sikiro ne naso na cinye daddy din. Sai da daddy yake fadin ita kuma nata baiwan ke nan sanin abu a cikin mafalki abinda zai faru ke nan ta gani ta fada muna dazun ashe ? Haka kowa ya tafi yana fadin albarkacin bakin shi su Anty kuwa cewa akeyi yaya za ayi haka kawai mota tana ajiye ta kama da wuta idan ba wani kullalan da akayi masa su dai kan basu taba ganin haka a gidan su. Duk da naso komawa gidan bukin ban samu hakan ba don kaina dake min mugunciwon nan dai da yakan dameni idan haka ya faru dani. Kwantawa nayi sai bayan magariba umma ta tayar dani daga barci tana fada dole haka na tashi naje nayi wanka sanan na danji dadin jikina. Don maitan Fa,iza a kaina ina shirin kwanciya sai gata dakin mu wai ta dawone muje wurin dinner da za ayi mu tafi tare. Naso naki zuwa amma sai umma tayi min magana akan nashirya mu tafi wata kila idan na dan fita jikin nawa ya kara walwale mun a can . Dole haka na shirya muka fita zuwa wurin bukin inda ake dinner din wurin ya cika sosai da mutane har wajen wurin. Haka muka samu muka kusa muka shiga bayan mun nuna pass din mu dukko da anko din dina din dake jikin mu a lokacin. Alh Nuhu ya kasa ya tsare yana zaune falin shi bayan ya gama ganawa da babban yaron shi kuma aminin shi da yake turawa yin duk wani sheri nasa. Wayoyinsa duka hudu suna gaban shi ya tsura ido yaji ta inda za a kirashi a lokacin don bashi labarin abinda yake da tabbacin faruwan shi a ranan sai murmushi yake faman sakewa shi daya a zaune falon duk ya kori kowa a lokacin yace a bashi wuri har iyalin shi. Shiko babban yaron nasa yana barin gidan kai tsaye unguwar dasu daddy ke ciki ya nufa a daidai inda zaiga wucewan daddy din ya bisu a baya. Saidai kuma sabanin hankali maimakon ya ga daddy a cikin wanan motan da aka asirce sai suka ganshi a cikin wani motan da basuyi zato ba. Da farko ma bai dauka shi din bane ya wuce saida ya gaji da zaman jirane yake kiran Alh Nuhun shi kuma akayi sa, a yakirashi a fusace don har yazo wirin daurin auren sukayi musabu,a da daddy din yaji kamar wani abu ya sokeshi a lokacin . Kafin ya kai gida hannu ya kumbura sumdum baiko iya daga hannuwan shi haka ya samu yakai gida hankali tashe dakin shi ya shige inda bai yarda kowa ya shiga mai ya dade a ciki ba wanda yasan halin da yake ciki . Sai bayan wasu awanin ne ya fito yana jin kamar ya cire hannun ya huta don azaban ciwon da yakeji yana masa lokacin. Shine karfe uku bayan daddy ya dawo gida suna falon shi da wasu bakin da sukazo masu daurin aure daga yola sukaji yan aikin gidan maza suna ihun wuta wuta a lokacin. A wurin dinner din kuma muna shiga cikan wurin yayi yawa haka dole muka ratso taron jama,an muka nemi wuri muka zauna a can dan baya. Bamu dade da zama ba aka aiko yaro wai yacewa Fa,iza mu zo ga wuri a nan gaba mu biyo shi hakan kuma muka fara ratsa wurun zuwa gaban inda akai muna nuni ashe duk yan family din suna wurin azaune muka bi sahun su. Zaune kawai nake kowa na harkokin shi ko ruwa ban iya dauka a wurin na sha ba duk ina ji ba dadi gida kawai nake son komawa in kwanta a lokacin. Wayan Fa,iza ta miko min shi ya dan dauke min hankali har na mayar da hankalina a wurin wayan ban damu da abinda akeyi a wurin ba. Kamar ance in dago kaina sai mukai ido hudu da shi yana zaune ya kura min ido daga inda yake zaune da sauri na kawar da kaina zuwa kasa. Tun wanan lokacin ban kara yin wani yunkurin dago kai ko dogon motsi ba a wurin sai naji hankalina ya kara tashi sosai da zama wurin. Ana tashi na nemi motan yan gidan don su Nabila basu tashi ba na rigasu komawa gida ban yarda sun barni a wurin ba. Ina shiga gida part din mu na nufa kaya kawai na cire na nemi wurin kwanciya sai barci ai kuwa dai yau ma na sake mafalkin katon mutumin nan sai dai duhu bai bari nagane fuskan mai shi. Yana nunani dan yatsan shi yana mun kashedi a kanshi sai gani na fara addu,a aikin mafalkin ya fara ja da baya baya ya bace a cikin duhun dare. Yana bacewa ina falkawa daga barcin tsorone ya kamani sosai na rarafa na shige cikin jikin umman mu na dunkule ga barci bai kara daukana ba kuma sai wajajan asuba. Ban fadawa umma komai ba da gari ya waye haka nayi ta faman hadiyan damuwana ni kadai a zuciyana. Da yamma ne mommy ta aiko wai inzo zata aike mu zo mu dauko kaya a gidan gwaggo hari dole na tashi hakana muka tafi mun samu an gyara gidan tsab kamar ba ai taron buki ba ciki a jiyan don wasu bakin su duk a gidan ta suka sauka. Sai da muka dade a falon kasa kafin tace mu shigo suna sama mu samesu a nan muka shiga da sallaman mu katon photon sune ya taremu a falon ban samu tsayawa duban photo ba don gaisawa da ita da muka tsaya yi. Don har mijin ta yana zaune tare da wani dake duban waya banga maishi ba a lokacin sai dai naji Fa,iza tace ina wuni ya mustapha. Lokacin ya dago kai yana amsawa saida na mike zaune don gani shi a gidan ga kuma Fa,iza ta kirashi da yaya a gabana yanzu. ZAINAB IDRIS MAKAWA ANA DARA GA, , , , , , , , 3️⃣2️⃣ BY ZAINAB IDRIS MAKAWA BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AL ALIM , , , , , , , , ONLINE PAID NOVEL YAR UWA KI SAN ALLAH YANA GANIN KI GA KOMAI UBANGIJI YA BADA IKON BIYA AMIN, , , , Kin sanshi ne Gwaggo ta tambayeni daga inda take a cikin rudewa nace eh nasan shi da sauri na sake fadin eh a wurin bukin nan na hadu dashi a nan na san shi. Sai kuma nayi kasa da kaina ikon Allah don kin sanshi a wurin buki nan sai kuma ki kadu haka ko wani abu yayi maki daya baki tsoro dashi haka ? Lafin inyi magana naji yace yar kauyece don kawai mun tashi kadeta da mota shine taso ta kawo muna rainin wayau a wurin na gyara mata saiti. Kai ubbana indai ba dukan yar mutane kayi ba har yasa take kaduwa haka yanzu data ganka don nasan halin ka sosai da rashin son rainin wayau mahaifin sa ya fada . Kai haba Alh ai ba zai duketa ba ba kasan su yarbawa da shegen tsoron tsiya yanzu haka dan tsoro ya bata shine ya zama wani abu a wurin ta inji gwaggo din. Fa,iza shiga ki dauko wani leda blue a saman gado kizo ku tafi da wanan shirmen nata don Allah kar ta zo ta dami mutane a nan muna zaune kalau din mu. Fa,iza na shiga dakin ya mike uwar ke fadin ina kuma zaka ana hira yaushe rabonka damune wai , ? Yace No mama ba ko iba zani ba zan danyi wayane yanzu in dawo ai yau ba zan fita ko ina ba ina nan tare daku nayi alkawarin hakan. Yana fadin haka yasa kai ya fice a falon zuwa kasa Fa,iza ta dauko ledan ina ganin ta na mike tsaye da sauri zamu tafi. Sai gwaggon ke fadin kice idan na kara hutawa zan shigo muyi magana da ita zuwa jibi don boy na gari ba zan samu fita ko ina ba. Kasa na kai ina fadin sai anjima na juya wurin mijin nata ina fadin bye uncle yace nazo na ji gabana ya fadi saida naga yana saka hannu a cikin babban rigan shi ya ciro bandar din yan Naira dari ya bamu mukai mai godiya har muna hada baki muka kara masu sallama muka fita daga falon gwaggo na fadin Fa,iza ki turo min yayan ku a waje don Allah ta amsa da to gwaggo. Muna barin falon take fasin shiyasa nake son nazo gida na samu uncle a gida don akwaishi da alheri duk kazo yana gida sai ya baka kyauta. Amma kinga dan nan nasu kamar baison yan uwa yake don shi ko gaida shi akeyi bai son amsawa kamar yana jin kyamar mutane yake sam baida saki wallahi wai kuma haka anty hauwa ke mutuwan s, , , Ganin shi zaune saman three setter ya hade hannayen shi a wuri daya tare da dan kura muna idanuwan shi. Dan kaduwa tayi kafin ta fara wayancewa da fadin sai anjima yaya nikan ban juyo ba nayi gaba ya daka muna wani tsawa yana fadin kai ku tsaya nan inda kuke. Ban tsaya din ba na soma tafiya kafin yace zan balla yarinya a wurin nan yanzu fa,iza ta gane me yake nufi kafin tace dashi lah yaya ai wanan bata jin hausa sai yarbanci da turanci kawai. Allah ko haka ta fada maku cewa bata jin hausa amma ku da wani yare kuke mata magana ya tambaya a daidai lokacin da fa,iza ke kirana na tsaya tare da juyowa ina kallon su. Ba tsoro ko dar dar haka na tsaya ina kare mai kallo a lokacin kafin ya dan yi wani iri yace anyway ku tafi ma ba matsala. Mun juya ya ciro kudi yana fadin tazo ta karba tana washe baki you come here naja na tsaya kudi ne har lokacin a hannun shi ya miko min tare da fadin give dis to ur mother kamar kullun. Saidana kalli kudin kamar ba zan amsa ba sai kuma na mika hannu na karba tare da dan rusunnawa alaman girmamawa a gareshi. Allah ya taimaka fa,iza ta fara tafiya don murnan kudin nayi saurin tura kudin a cikin rigana na fito na samu harta sauka saman dan matakalan su ta fara tafiya. Nacin mata da sauri take fadin may ya tambayeni nace sunana kawai tace idan yaso yana dan magana amma ba ruwan shi da kowa a cikin dangi. Balle yaya Abubakar da basu shiri dashi ko kadan shine wai anty hauwa kuma take son shi a hakan. Shi kadai gwggo hari ta haifa duk da ance itama ta haifa a bayan shi basu tsaya ba lokacin don ance kamar abinsu daya da mommy ne. Ban bata amsa ba muka shiga mota driver ya jamu zuwa gida har muka iso tana ban labarin su har mahaifiyar shi din da mijin ta. Ban yarda naje part din mommy ba kai tsaye saidana fara zuwa namu din na aje kudin na fito na sameta taba mommy sakon nace mata mun dawo tace ashe mun samu mijin ta a gida . Ta miko min kudin da aka raba nace lah mommy dakin barshi ai a wurin ki tunda ba komai zanyi dasu ba. Daga van fa,iza tace mommy anko fa zamu saya na fada maki mommy ta aika mata da dakuwa da hannu ta noke karshe cewa nayi abawa Fa,iza din ta saya muna anko din. Ina fadin haka na fita anty Nabila tace ina sha,awan rayuwan yarinyar nan abin duniya sam bai dameta ba ita da watace ai bata tashi sai an raba an bata su. Mommy da kanta yake duke tace ni har abin kamban mamaki rayuwan su kamar ba tashin bariki ba idan suna wani abu sun samu tarbiya sosai wallahi. Ina komawa na zauna gefen umma tare da daga kujera na dauko kudin dana boye din nace yau ma yace a kawo maki su. Kuma shi din dan cikin gwaggo hari ce ashe sai dai ban san dalilin shi na taimakon mu ba da yakeyi don yana kama da mugu sosai. Anyanzu kan banda fargaba a gareshi don nasan koshi waye amma da farko nasha jinin jikina dashi sosai ganin irun alherin nan da yake muna haka. Tunda nayi sallah na kwanta barci don haka da wuri na kwanta a ranan ashe wai anyi rikici da yaya Abubakar da matan shi da sukazo gidan da dare su jajantawa daddy zancen motan shi data kone. Sai gashi an kira Nazifa din a gidan ana fada mata cewa mahaifin su ba lafiya tun jiya hannun shi ke masa ciwo suna asibiti dashi. Bata jira cewan mijin taba ta mike da sauri tana fadin gata tafe yace idan ta tafi ta tsaya can shine rikici ya barke a tsakanin su a gaban iyayyen mijin ta kuma saida kyat suka samu suka shawo kanta ta yarda da safe kamar yadda yace yanzu dare yayi ta bari da safe su tafi. Ban san anyi ba saida safe da Anty amarya ta shigo tana fadin zasu tafi asibiti su duba Alh Nuhu maifin matar modibbo ance haka kawai hannun sa ya kage ba a san meya sameshi ba. Ashine aka kira matar jiya suna nan ake fada mata ankai mahaifin su asibiti ta tayar da fitina ga mijin wai sai ta tafi. Kin san auren hadine mu iyakarmu kallo uwarshi ta sani cewa yaran basu samu tarbiya ba kuma mahaifin su da Alh nan kamar Annabi da kafiri suke ta yarda tayi wanan hadin a tsakanin don irin halin su dama ai duk haka suke nasa kawai ake gani shi daya tona zyciyar shi duniya tasan halin shi. Umma cewa tayi jam abin baiyi kyau ba Allah ya sauka sai kun dawo ke nan insha Allah ba zasu fita ko ina ba suna nan balle sahiba tana nan itama tare dasu. Ta fice ta barni da mamaki biyu a zuciyana na farko gulman mommy da yan gidan su da takeson yi a gaban umma don rashin sanin waye umma din ga mommy. Sai na biyu shine ban san dalilin da yasa bata kaunan yayanta suna shiga cikin yayan dakin mommy ta kwamace su zauna a wurin mu duk da muna baki a cikin su din. Mikewa nayi na dauko masu sauran sweet da biscuit daya rage na kawo masu suna ci saiga mommy ta shigo tana fadin zasu tafi asibiti da Alh su duba jikin yaya Nuhu haka kawai hannun sa ya rike bai iya motsasa. Mukai mata a dawo lafiya ta fita umma ta kalleni cikin yarbanci take fadin anya mutumin nan ba wani sheri yajeyi ba ya koma masa kuwa ? Shine mana naba umma amsa kai tsaye a cikin rashi damuwa duk lokacin da yace zai taba daddy ko wani nasa yanzu hakane zai faru dashi ai umma . Sahiba a ina kike sanin wanan abubuwan naki nace nima ban sani ba umma ta wani irin kalloni kamar zatayi magana tayi shiru kuma. Basu wani dade ba suka dawo din labarin baida daddy wai sun samu an dauko mai magani yazo ana masa magani. Umma tace a asibitin ake maganin mommy tace shi ai kin san ya iya wanan abubuwan dasu ya yarda ko asubitin kila fin karfin shi akayi ko zafin ciwo yasa ya yarda yaje din. Zaune yake yana breakfast amma hankalin shi bai kwanta ba yayi iya tunane ya kasa gane halakan wanan yarinyar da daddy da har suke zaune a gidan daddy din yanzu yarinyar daya sani da a logos suke ita da mahaifiyar ta da dan uwanta yanzu meye hadin su da daddy din. Shigowan mahaifiyan shi falon ne yasa ya dago kanshi ya dan kalle ta itama din kallon dan nata tayi kafin ta kalli abincin da ta zuba mai bai taba ba. Wai ya haka meke damun kane haka ka tasa abinci a gaba haka kana kallo ko wanan da aka dafa bai maka bane a dafama wani ? No bana dai iya karyawa da wanan yayi min nauyi da yawa da safen nan haka sai dai tea zan sha dan anjima kadan. Kujera taja ta zauna tare da jawo abincin zuwa gabanta tana fadin oya bude min baki wanan abincin ne zakacw yayima nauyi a ciki ban iya shiririta ba shiyasa kake rakewa haka yanzu ai. Murmushi yayi ya dan dago yana kalon maman nasa yace kai haba mama yanzu fa na girma wani yazo ya samu kina bani abinci ga baki a samu abin fadi. Haka yaran nan da suka shigo shekaran jiya suka fita suna gulmana basu san ina falo zaune ina waya ba. Su Fa,iza da wanan bakuwar bayeran ban na gidan ko au bayerabace dama ashe haka nake zato don ance wai diyar abokin shine na can. Ban san ko wani aboki nasa bane a can don ni ban yarda da wanan zancen ba don yarinyar sam batayi kama da yarbawa ba tafi kama da zuri,an gidan mu ma sosai don dai ita din farace sosai da tsayi kuma. Dole dai suna da alaka mai karfi dashi tunda suke zaune agidan shi amma ai ya kamata ace kunsan ko iyalan waye su din ai. Ban zauna bane ai ina son yin wanan zancen dashi koda yake ma ba abinda ya shafeni da zancen shiyasan inda ya samo su ai. Don ance baison kowa yayi maganan su a gidan saidai kawai yana nuna suna da muhinmanci a gareshi sosai abindana sani ke nan. Kawar da zancen tayi da fadin ance yaya Nuhu na asibiti a cikin wani hali tun jiya sai yau nake ji da mukai waya da mamanka Asiya. Meke damun shi ya tambaya tace wai ance kamar jifan shi akayi don hannun likitoci sun duba sunce basuga wani matsala ba su. Ina zasu gani mama tunda kila abinsa ne ya koma masa wai ki duba last da muka hadu yake fadin wai yaushe na fara wanan harkan business dina bai sani ba har na kai haka ? A cikin wani irin zabura tace kada ya soma yin gangancin shiga harkana wallahi iskancin shi ya tsaya a wa yanda ya raina ya bar ganina mace don zan iyaja dashi don shima ya sani ni ban tsorin shi . A,a mama kada wani abu ya hadaki dashi don ke mace ce ni ba abinda zai iya yi dani sai ta Allah kawai yana baraza nan shine ga masu tsoro ko kwadayin abin hannun shi. Sun dan dauki lokaci suna magana kan Alh nuhu din wanan ya sa ya mike yana fadin ni zan fita mami wata kila in shiga kano zuwa anjima indai tafiyan ya yuyu garemu. Yau din nan uwar ta tambaye shi tana kallon shi da mamaki yace mama kano nada nisane kuma da zan fita da anty Asiya don tace sai muje ganin yaya Nuhu din . Amma yanzu barin bari ka tafi sai mu tafi zuwa gobe din in Allah ya kaimu a, a mama ku tafi kawai sai zuwa yamma fa nace zamuyi tafiyan tace to shike nan ai har maje mu dawo baku tafi ba tunda ba tsayawa zamuyi ba a can don ance ba a ma ganin shi don bokan shi ya hana wai a shiga a ganshi kaji wani shirme. Mikewa yayi ya koma saman kujera ya kwanta ya mike tare da dora hannayen sa saman fuskan ya shiga tunane don a yanzu ba abinda yake tunawa sai hanyar da zaibi ya fitar da kanshi kan neman da jami,an tsaro suke mashi. Duk da yasan hakan abune mai wuya a gareshi ya iya fitar da kanshi a cikin wa yan nan kurayen yan duniyan abokan sana,anshi marasa imani da tawakkali. Don ba zai iya zama da wa yanda akan kudi zasu iya kashe rai don kawai bukatan su ya biya kudi ya shigo masu ta ko wani hanya. Yanzu mutum kawai ka barahi inda ka ganshi kada ka tona cikin sa don ba zaka kara mai kallo biyu don abindake boye nasa Allah ya bamu cikawa da imani yasa mufi karfin zuciyar mu AminAmin. A gidan daddy kuma yau dai da fitina aka tashi a gidan don fada ne tsakanin mommy da Anty tunda safe ya kaure inda anty ke fadan wai ana son a kashe ta aga bayan ta don haka aka bata abinda zai kashe ta. Kai tun mommy tana hakkuri hardai takai ga ta tanka suka fara musayan harshe a tsakanin su abinda ya jawo duk wanda ke gidan ya fito a lokacin. Kusan nice na fito a karshe na tsaya ina sauraren wanan zubar da kiman da suke yi a gaban yayan su suna kallo. Anty sai kira take wai su mommy da diyanta basu kaunan ta gashi ana son a kashe ta har diyan ta daga ida nake tsaye nace haba anty whichi can of kind pf talk be dis? No be belle sickness de worry u, which can of talk be dis, u cary belle for three months now, na him u go say mommy don send evils things for u ? Wurin yayi tsit ana kallona son abinda na fada ido kakafe ban ko juya su nace is better to go and see d doctor first, before u talk dis mes. Aikuwa tayo kaina da fada tana fadin ni har na isa in mata kazafin ciki ita bata da komai a jikinta saboda tasan cewa tayi planning don haka bata taba zaton ciki a jikinta ba a yanzu. Don tana bin duk ka,ida daya dace kada tayi ciki a wanan lokacin sai gashi taji ina kira mata ciki haka yanzu. Hannuna umma taja zuwa part din mu ta zaunar dani saman kujera ruwa ta debo min ta bani na girgiza mata kai alaman a,a nan na zauna ina ta faman hamma sai kafa da nake kadawa kamar wata basaraka. Sai abin ya zama bokon lamari a wurin umma don haka ta fita ta kira mommy suka shigo dakin a tare. Sai da kyat suka samu na kwanta ina dafe kaina a lokavin umma ta fara tuna abinda ladi da sauran mutane ke fada mata a lagos game dani. ZAINAB IDRIS MAKAWA ANA DARA GA, , , , , , , , 3️⃣3️⃣ BY ZAINAN IDRIS MAKAWA BISSIMILLAH RAHAMANIN RAHIM AL QABID, , , , , , , , ONLINE PAID NOVEL YAR UWA DON ALLAH KI BIYA KAFIN KI KARANTA NA KUDINE NA FADA NA FITAR DA HAKKIN RASHIN SANI, , , , , Gidanne ya koma shiru na dan lokaci kowa da abinda rayuwan shi ke raya masa kan abinda ya faru a lokacin . Don mommy kan rayuwan ta ya gama baci da halin hjy karima wace bata yarda da Allah kan diyanta ko ita ba dan abu kadan zai faru yanzu Anty amarya zatace ai ai mata ne ture kishiya tayi mata don kawai taga bayan ta. Yar uwa kokece a irin wanan rayuwan ki zauna ki binki imanun ki anya bakiyi zurfi ga shirka ga aikin sabawa Allah ba. Tunda baki yarda da kaddara da duk ya sauka a kanki sai ki manta da cewa Allah mai yi a duk lokacin da yaso hakan a gareki Ko ki koma kina dariya kan abinda ya samu wani na sheri karki manta wata rana kema yana tafe a kanki yar uwa don haka lamarin Allah yake . Anty ko tana part din ta sai faman tunane da tsuki take ja tare da fadin jimin wanan yar iskar yar da zata lauyeni a gaban mutane tana fadin wai cikine dani har na wata uku har yaushe na gama wanka da zata kira min ciki a jikina yanzu. Allah na tuba koda zanyi ciki ai ba yanzu ba dama kwadayin da namiji yasaka na haifo wa yan nan kai a kai don kawai ina zaton samun da namiji a lokacin. Haka kawai zan zauna ina zuba yaya ga wanan tsohon karfina yazo ya kare na koma jagwal a cikin abokaina. Tun tana yawan tunanen hakan har yakai ta daina zargin hakan ta gaji ta ba kanta shawara saidai washe gari saida takai kanta asibiti don bata yarda da awon da tayiwa kanta a gida ba. Suka kara tabbatar mata da cewa su basuga komai ba a jikin ta daya danganci ciki ajikin ta don haka ta dawo gida da yamma sai gata dakin mu daidai mun dawo islamiyan yamma ke nan ina zaune. Sallama tayi bata tsaya komai ba ta fara fadin wa umma nazo injawa yarki kunne a gidan nan kafin Alh ya dawo da ta shiga hankalin ta dani a gidan nan. Idan ba rainin wayau ba ta yaya kamar Sahiba zata saka baki a cikin zancen mu har tana kira min wai ciki ne a jikina idan cikine ta fini sanin yadda ake daukan cikine ko kawai ta nunawa mutane ita yar zamani ne bata da kunya tasan komai. Kamar ya tasan komai tace aiki tambayeta yadda har yakai tasan mace mai juna biyu da harta iya yanke min hukuncin ciki a jikina na dai fada maki ki mata kashedin hakan a kaina don bani da dadi idan na saka mutum a gaba tana fadin haka ta juya ta fita daga part din mu. Umma ta jiyo ta kalleni tana fadin na fada maki ki kiyayi wanan matar Sahiba na dago ina fasin umma menayi mata ni da zata zo tana fadin wanan maganan haka a kaina sai umma tayi shiru. Tun wanan lokacin sai naji kawai na tsani wanan matar na daina zuwa gaishe ta na daina kula diyan ta saidai hakan baisa yaran su rabu dani ba don dole na dan kama kula dasu saidai ba sosai ba. A bangaren Alh Nuhu kuwa abin ya fara bashi mamaki yana tambayan kanshi har Alh Ali zai gagareni duk da nasan shima a tsaye yake kamar shi . Don a zaton shi shima daddy irin abinda yakeyi daddy din keyi shima don ya kasa cin ma daddy din ya nakasa shi yadda ya saba nakasa duk wanda ya shiga mai hanci da kudundune. A wanan halin kumane ya koma gwadawa ta wani hanya da yake ganin itace mafita na karshe da zai iya gwadawa a kan daddy din. Yaron shi aminin shi kuma yardaden shi ya kira ya sameshi a gidan hutun shi a nan suka kulla abinda suke shitin aiwatarwa akan daddy din ya ciro kudi masu yawa ya bayar wanda abubuwan zasu kankama a gareshi yadda yake so da sauri. Ranan ko iyalin shi sun san yana cikin farin ciki don yadda yake masu idan yana cikin nishadi haka ya kasance dasu a gidan. Yau a falon da anty ta hanasu zama a baya a gidan, muke zaune tana dakin ta bata san da muna falin zaune ba har yakai anty hauwa ta kunna muna kallo sai hankalin mu ya dauke ga hakan. Fa,izace ta dauko zaren kitso na kama mata kai don haka muka fara duk da ni hankalina ba a kan kallon yake ba na mayar da hankali ga kitson da mukeyi din sai jin muryan Anty mukayi a daidai lokacin da fa,iza ke fadin kan ya fara mata ciwo na dan sasauta mata kitson nake fadin hakana iya nima. Ai yau kuma kun dawo da iskancin zaman naku nan falon ke nan ba na kashe wanan zaman naku a nan ba dama ta fada tana wani zare idanu a garesu. Ban kula da ita ba a irin sai dariyan da nakewa fa,iza a lokacin ta juyo gareni tana fadin ga yar iska ina magana kina dariya kin daukeni mutumiyar banza ke nan. Ni nice yar iskan na fada a cikin hausan da ba daidai ba nace look woo don abuse me with dat name again wooo. Da mamaki anty ta bude ido tana kallona kafin tace ke bude idon ki ki dubeni banyi kama da wanda zaki raina ba a nan . Duk barikin ki keda uwarki kar nake kallon ku gidan nan don ba zan dauki iskacin yancin arziki ba yan gida basu raina ni ba . A wurin ki ne nake yarcin arziki amma wurin daddy da mommy ni ba yarcin arziki bane don diya nake a garesu kamar kowa. Idan kika bincika har nafi diyan ki power a gidan nan don su din ba a san ya aka samesu ba ma a gidan nan . Muko da kike kira da yan bariki da asalin mu da kuma nasaban mu don nasan munfi wata yar a cikin gidan nan. Fa,iza zata tashi nace ina zaki bana zuwa ko ina a nan zan zauna tunda ba gidan uban wani naje ba a gidan uban mu muke zaune kuma daddy bai hanamu zama a nan din ba shida keda gidan sa. Na fada ina murguda baki son na fahinci matar kanta kawai ta sani sai diyan ta bayan shi kowa ba mai mutunci bane a idonta gidan yasa na rufe ido nayi mata hakan nidana saba fada da su iya bisi ko iya wale balle anty da albarkacin daddy ta samu a wurina dama . Sallaman gwaggo hari ne tare da danta suka shigo tun kan ta karasa shigowa gidan take fadin wai hayaniyan me nake ji haka yana tashi tun muna waje ? Gara da Allah ya kawo ki wanan tsuntattan mage din nan daba wanda yasan asalin su tazo ta samu wuri tana son fin yan gida iya shege. Kai hjy karima me ya hadaki da wanan kuma kike irin wanan maganan haka gaskiya haka bai dace ba don Allah ai wanan kamar yar mijinki take a wurin ki. Yau mutanen nan suke zaune tare daku a gidan nanb ai inda sabo an saba a yanzu kun zama daya dasu haka gaskiya bai kamata ba. Shiru falon yayi kafin gwaggo hari ta juyo kaina tana min fada nayi shiru a daidai lokacin ya shigo gidan aka shiga yi mashi sannu ana gaida shi. Yau kam shigar kayan hausawa yayi duk da rigan irin dinkin zamanin nan ne mai tsayawa maza iya cinya din nan yayi matukar kyau dashi. Don kwarjin shi ya fito fili ga wanan shiga da yayi don shigar ta karbe shi matuka. Gashi da ganin shi kasan naira tayi aikinta wurin don ko shigar gwaggo hari itama abin kallo ne a lokacin. Nan falon suka zauna daga shi har mahaifiyar shi mommy dake daki tana jin abinda ke faruwa a falon ta fito tana masu sannu da zuwa tare da gaisawa. Wayan shine yayi kara ya dauka yana fadin ya akayi arrow duk akai shiru ana sauren shi shima din dai shirun yayi yana sauraren abinda jibrin arrow din ke fada mai take yanayin shi ya dan sauya. Yace Okey kana jina kada kowa yayi yunkurin yin komai gani nan zuwa kana jina zan biyo jirgi yanzu inzo lagos din in sameku. Na fadama kada kuyi komai sai idan nazo din don dama nasan da hakan zai faru ai don haka ku jirani inzo. Yana fadin hakan ya kashe wayan shi yana dago kanshi ranshi a bace sai mahaifiyar shi tace dashi meya faru ne kuma, ? Yayi saurin dawowa daidai yana fadin wai kayan mu aka kama shine suke son su tayar masu da rikici nace su bari inzo dai. Gara daisu bari kazo don jami,an tsaron nan wani lokaci ba tausayi ke garesu ba anjima zan je inji meke faruwa ya fada kafin ya mayar da hankalin shi wurin mommy yana fadin. Mommy nacewa mama ta kawoni wanan karon ina jin nauyin korafin da kike min na rashin zumunci idan mun hadu . Mommy tayi murmushi tana fadin ka kyauta wallahi baba ko kaifa ace mutum ko yaushe kamar injin ku bakwa samun lokacin hutune a rayuwan ku wai kaida dan uwan ka kullun a zurce kuke kan aiki. Mommy kuyi hakkuri wallahi yanayin ne na yanzu ya koma hakan ya fada yana dan sune kan shi kasa saboda nauyi ya kasa ci gaba da magana. Amar ne dake fitowa daga part din mu ummace ta toro shi ya kirani idon the boy ne ya sauka a kan yaron haka ya kara tabbatar mai da ba karya nidin daice ya gani a kaduna. Tunda ga kanina ya gani a gaban shi yanzu da yarbanci yaron ke fada min na mike a lokacin ne kuma Amar shima ya juya zai koma part din mu. Alokacin na Ya mustapha din yace dashi ya abokina zo mana haka baisa ya tsaya din ba nace a harshen yaruba bakajin ana magana sai yaton yaje wutin shi inda yake zaune ga kamshin turaren shi har ya fara hawa min kai a lokacin. Ya rike shi yana mai dan magana kus, kus wanda ba lalai bane wani yaji me yake fada mai a lokacin ga falon yayi shiru kafin ya kai hannun shi daya cikin aljihu yana ciro kudi masu yawa ya mikawa Amar din. Mukan gaskiya munci gajiyan wa yan nan mutanen don ba zamuce mun shiga duniya mun dawo hannu sake ba ko yanzu aka bukaci wani abu a wurin mu za a samu sosai kuwa duk da ba kidayawa nakeyi abinda muke samu din ba. Kowa falon ya fiddo da ido yana mamakin wanan kyautan daya bawa yaron daga gani daya da yayi mashi a yanzu zai bashi wanan kudin haka. Muryan gwaggo hari ce ke fadin kai har yanzun dai kana nan da son yaran ka ashe saidai maza sune abokan shi ai mommy ta fada suka dan kwashe da dariya a iya nan na bar wurin banji sauran maganan su ba kuma na dai fito na samu sun tafi ya bada alheri mai yawa yace a raba. Har ni an cirewa nace lah dakun barshi ai tunda amba Amir mun gode na fada a karshe naji Nabila na fadin shi ya mustapha har yanzu ba zancen aure gareshi ga yan uwan shi duk sunyi aure a dangi. Idan lokaci yayi shima ai yi zaiyi ko ita uwar nasa data damu da hakan da farko ai yanzu naji ta sake sai a lokacin Anty Amarya ta fito kallon kowa batayi ba a falon haka tasa kai tafice daga gidan. Falon yayi shiru bayan fitar ta Allah da ikon shi ba wanda yai maganan ta a falon har ta gaji da tsayuwa tana saurare ko zataji anyi maganan ta sai taji shiru sai hiran hausana dana fara koyo sukeyi ana kwasan dariya. Su ukune a zaune a falon duk biyun sunyi shiru suna sauraren shi yana fada masu abinda yake shirin aiwatarwa ga dan uwan nasu. Karamin nasu ne ya fara magana a cikin su yana fadin kai haba yaya abinda mijin ta yayi muna ba matarshi ko danshi yayi ma haka ba . Kuma karka manta da matarshi ai yar uwan mu ne ta jini don uba daya ba wasa ba duk daba cikin mu daya dasu ba amma kuma ai uban mu guda kuma tana girmama mu tankar ciki daya muka fito da ita . Kai dakata Dule nifa ban dauki duk wani dan uwa a matsayin dan uwa ba a yanzu duk wanda yayi kokarin ketara layina saina saba mashi ko waye shi din kuwa. Amma dai yaya kasan in har kai haka har iyalinka ka saba masu don har da yarka zata cutu ga wanan shirin naka. Kai Dule dayan da baiyi magana ba ya fada ka bari tunda ya shigo hancin yaya ayi maganin sa su wullakanta a idon yan uwa su gane su ba komai bane a yanzu. Wanda ake kira da Dulen yace amma dai ni naga a duba tunda ba wani abu bane mai girma ya hada ku dasu karku manta akwai yarmu yanzu a cikin zurian su fa dole komai mu dinga duba a yanzu yaya . Shiru yayan nasu yayi baiti magana ba hakan na nuna cewa ran yayan nasu a bace yake sosai a lokacin kan maganan sai dai kuma yana nazari akai. Gyaran murya Alh Gyade, yayi kafin ya fara fadin kai Dule na fahinci kamar kana tsoron Alh Ali a yanzu don kana ganin kamar shidin wani ne to sai mun nuna maishi ba kowa bane a garin nan. To Allah ya kyauta ya fada yana mikewa tare da fadin ni dai shawarana shine ayi diba akai fadan zumunci ba karewa yakeyi ba idan yazo hakkuri akeyi a kai kada a maimaita abunda mukaiwa Sambo a baya yaso zama muna matsala. Sun san halin sa idan har ya fadi abu to gaskiyan zuciyar shine ya fada don haka yana nufin bada shiba cikin wanan shirin ke nan duk da sun san ba zai fada ba kuma. Yana fita sukaci gaba da zancen tare da dan uwan nasa guda yayin da yaton shi ya kawo mai labarin dawowan daddy a ranan. Sunji dadin hakan har suna kyalkyalawa tare da fadin dan iska yau zaka san ba a ja damu a cikin lamari har kana nunawa yaya yatsa waishi yaya kai waye da zaka ce fadan ka yafina Allah mu zai gwadawa Allah a baki. Ya gama hiran shi ya mike yana fadin shi zai koma sai dai udan sunyi waya ke nan duk yadda abin ya kaya zasuyi magana . Alh Nuhu yace ko sai mun hadu wurin makoki ba a gidan Dn filo suka sa dariyan keta kamar ba wada kani ba a lokacin. Tun zuwan gwago hari da danta gidan suke ta faman hiran su har na gaji dajin hakan kuma na tabbatar da son shi sukeyi su gaba dayan su. Daga Anty hauwa har Anty Nabilan don zancen su ke nan hiran shi da zuzutashi shida yayan su hakan ne ma ya dan rage min zargin su da nakeyi jin har yayan su suna zuzutashi sai na dauki hakan dai wani nau,in wayewa ne kawai irin nasu. Muna zaune Nazifa matar ya Abubakar ta shigo gidan kwatsam muka ganta kamar an jefo ta suke gaisawa da ita na dan dago nace da ita sannu kawai na kawar da kaina ta shige wuein mommy bayan ta tambaya tana ciki suka amsa mata. Sun dan dade a dakin tare da mommy sai gata ta fito ranta a bace suna mata sallama bata ko samu amsa mata ba duk suka bita da kallo. Yar matsala aure ba a ko haihu ba amma kullun a cikin matsala ake Nabila ta fada sai hauwa tace ta samu wurin yin hakan ne. Ni da nice mommy wallahi va zaki ta kawo min sukan dana ba ina kyaleki hakan sai ga mommy din ta fito daga dakinta tace . Au ta tafine ni wanan yar naga ranan da zata san aure takeyi a yanzu sai abinda aka tsara mata ba wai wanda take so ba ita. Wai yanzu tazone a nema mata yar aiki don yace shi bai yarda da yan aiki ba shi kuma inba tsiyarshi ba ta yaya zata zauna wanan katon gidan babu maitaimako kuma wai yace tafaye kazanta kinsan sanshi da shegen akidan tsiya. Ita kuma yanzu tazo tun bai yarda din ba da shegen sallonta wai in tabbatar yar talakawace lis wace kuma bata da kwadayi da saka ido za a samo mata. Wanan yar rainin wayau ce wallahi wai me Nazifa ta dauki kantane yanzu tunda tayi auren nan ta dauki girman kai ta sakawa kanta Allah. Yanzu mommy samo mata din zakiyi fa,iza ta tambaye ta mommy din tayi mata wani irin kalllo ba tare da yin magana ba ta shige dakin ta. Nikan na mayar da hankalina gun karatu na son cin jerabawan da zamu fara karshen sati don daddy yai min alkawarin kyau idan jerabawan nawa yayi kyawo. Haka yasa na dadage na mayar da hankalina kan abinda aka koya min din don daddy ya tsamini yai min register a wani makarantar wanda ba namu ba. Bakin sune ya kama Nazifa don yaya kan yace bai yarda ba yaki amincewa sam da wanan zancen. Alh Nuhu dake zaune yana zaman jiran jin labari mara dadi daga bakin yaron shi amin shi wayan shine dake gefen shi yai kara. Cikin rawan jiki ya dauki wayan yana fadin Gyade ya akayine ai har yanzu banji komai ba jiran su kira nakeyi. Malam mun kira mu fadama cewa mai wanan wayan yana hannun nu yayi hatsari dazun nan a nan hanyar by pass. Innalillahi ya fara maimaitawa zaiyi tambaya yaji an kashe wayan dabas yayi wani irin zufa ya fara keto mashi dole ya cire hulla yana dan fifita kan shi . ZAINAB IDRIS MAKAWA ANA DARA GA , , , , , , , , 3️⃣4️⃣ BY ZAINAB IDRSI MAKAWA BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AL BASIT, , , , , ONLINE PAID NOVEL YAR UWA DON ALLAH KI BIYA KAFIN KI KARANTA NA KUDINE ALLAH BADA IKON BIYA, , , , Daddy ya iso muna murna da dawowan shi lafiya sai layi mukeyi muna zuwa masa sannu da zuwa yana zaune da alaman agajiye yake a lokacin yake hakan kuma yake amsa muna. Mommy da Anty suna zaune daga gefen shi tare da yaran anty din dukkan su a cikin kulawa sai hakan ya ban mamaki. Ban taba jin kewan namu mahaifin ba sosai sai a wanan ranan yadda naga daddy din zaune tare da iyalin shi a falon shi sai tausayin mu dana umman ya kamani lokaci guda. Juyawa nayi zuwa part din mu na samu umma zaune tana shafa magani a kafanta dakan dan mata ciwo take tambayana ya dawo lafiya nace lafiya kalau umma na shige ta bini da kallo. Can ta fara jin kukana sama sama har yakai ta mike ta leko kuryan dakin da nake nayi rub da ciki ina barza kuka . A hankali umma ta tako zuwa inda nake ta kai zaune tare da tambayana tana kai hannu saman kadana tace ke lafiya kike wanan kukan ? Ban iya magana ba naji ta kara matsowa gareni tana fadin ba zaki fada mkn meke damun ki ba ko anyi wani abune kuma na gurgiza kai. Sai dai ba magana don yadda nake jin zuciyana tana min kuna a lokacin na rashin mahaifin mu a tare damu don ban taba sanin dadin mahaifi ba sai yanzu da nake zaune a gidan daddy din. A wana lokacin nasan muhinmanci uba a tare da iyalin shi wanda mu muka rasa wanan gatan tun muna kanana bamu san dadin mahaifi a tare damu ba. Mikewa naji umma tayi ta fita daga falon can sai gata dauke da goran ruwa da cup a hannun ta tana fadin ki karbi ruwa kisha komai ke damun ki Allah ya yaye maki shi kiyi bissimillah kisha ruwan ta fada tana tsiyayawa a cup din. Dole na karba na dan kurba kadan nasha na mika mata cup din har lokacin tana tsaye a kaina ta kasheni da idanun ta alaman tambaya. A dan maraice nace umma ba komai bane fa na koma na kwanta a yadda nake da farko din naji tace Allah ya kyauta ta fita. Ban kara fitowa ba kuma bata kara lekoni ba sai wajajen la,asar na fito umma na zaune a falo saman kujera two setter Ammar yayi filo da cinyar umma din yana buga game. Gaida ita nayi take fadin kin tashi ke nan ga abinci can ki dauka na bata rai tare da fadin umma banjin yunwa na kai zaune. Naji tana fadin Fa,iza ta shigo sau biyu kina kwance har na zauna sai kuma na mike zuwa wurin faiza din in duba me take nemana dashi lokacin. Ba kowa a falon nasu na bude dakin su na samu duk suna ciki anty Nabila zaune wurin mirrow tayi tagumi sai Fa,iza da hauwa dake saman gado fa,iza na kwance hauwa ta zauna ta mike kafa tana kadawa a cikin tunane nayi sallama na shigo ina kallon yanahin su da mamaki har lokacin. Saida nakai zaune na dan sake kallon su kafin ince lafiya anty Nabila a cikin turancin nageria ta dan muskuta tana fadin wallahi ke dai Sahiba ba lafiya. Mommy aka bugo waya cewa yayanta yayi hatsari dazun yana asibiti rai a hannun Allah shine kika ganmu haka. Ikon Allah sai gashi sam banji komai ba ga hakan sai cewa danayi Allah bashi lafiya na juya inajawa kawata kafa Sahiba. Ta dan dago kai ta kalleni kafin tace dani kin tashi ke nan sau biyu ina zuwa part din ku kina kwance nace shine umma ta fada min yanzu ai nazo. Muryan mommy ne ta shigo duk suka mike zuwa falon wurinta nima na bisu a baya muna gaida ita da dawowa . Ta dai amsa takai zaune zuciya ba dadi don yadda ta bar dan uwanta din a cikin wani hali mara dadi Nabila ce takai zaune kusa da uwar nasu take fadin mommy ya jikin nasa ? Tace bari Nabila saidai ace da dama don har yanzu bai farfado ba baima san wanda yaje kansa ba har wanan lokacin. Ikon Allah kawai wanan abin nan ne fama cikin gari daga badarawa zuwa unguwarsu ya fito gidan yaya Nuhu abin ya samesa motar tayi kaca kaca ba kyace mutum ya fita a cikin motar nan ba wallahi. Daddy ya dawone ta dan bata rai kafin tace yadawa tare muka dawo ai shikuma wai yake fada min in barwa karima girki yau tayi. Naga yaran sun kalleta da sauri Hauwa tace amma daddy din nan mommy me kikace masa ke tace umhumm hauwa ke nan mezan ce dashi tunda baya bukatan ni inyi. Gaskiya gaskiya abinda daddy ke maki baida kyau mommy kullun sai aita tauye maki hakkin ki don kawai ita taji dadi tanawa mutane iskan ci a cikin gida. Kyaleshi yana da daman fadin hakan tunda Allah yace in kayi tafiya ka dade ka dawo kana da right di kwana wurin wace kakeso a cikin iyalin ka ai. Amma mommy wanan abin fa gaskiya yayi yawa don da ba haka daddy yake ba ai koma me tayi din kanta kanta take daukarwa alhakin haka bata sani ba . Ni yanzu matsalan dan uwana yafi damuna don inda sabo ai yanzu na saba da wanan halin da suke min ba sabon abu bane kuma a wurina. Sun danyi maganganu ina jin su duk da bana fahintar wani abin amma kuma ina fahintar wani inda na gane akan abinda suke magana a kai. Na dago kai na dan kalli sama kamar mai tunane kafin ince itama din ai zasu samu matsala dashi ne ai . Da sauri Fa,iza ta kalloni tana fadin da Anty din nace eh mana kilama a yau din nan ai na mike na shiga dakin su na dauko takardan Fa,iza saman gado na fito ina fadin zanje nayi karatu don mun fara jerabawa a lokacin. Wait for me tace na tsaya tare muka nufi part din mu da ita muna can har dare bayan munyi sallah ta fito ta koma part din su. Mukan muka rufe dakin mu ashe bamu dade da rufewa ba fada tsakanin Anty da daddy ya rikice akan yarta Suraiya dake makaranta zancen ya taso masu. Har abin ya kaisu ga zage zage a tsakanin su ta fito rai bace har waje tana zage zage kowa najin ta a gidan mukan muyi barci a jikin umman mu a lokacin kamar yadda muka sabayi. Tun safe sai ga mommy a dakin mu tashiga tana saye da hijjab din sallanta da gani daga wurin sallah take sallamta yasa umma bude kofan mu ta shigo. Tambaya tayi ina sahiba gata nan ta koma kwanciya umma ta nuna mata ni tana fadin lafiya dai ko hjy ? Wallahi lafiya kalau yar nan daine da abin al,ajabi jiya fa muke magana a gabanta ashe wai tace da Fa,iza itama ai ba zatayi girkin ba sai gashi kuwa sunyi fada sosai da Alh har da tonon asiri a jiya din shine Fa,iza ke fada min abinda tace din. Umma ta nisa tana fadin ni lamarin Sahiba ya fara daure min kai sai kiga yarinya tayi magana kamar a cikin wasa sai kuma hakan ya zamo gaske ni wanan abin ya fara damuna gaskiya. Nata baiwan ke nan ita kuma mommy ta fada tana kallona sai sukai shiru can umma take fadin ai naga kamar kece da girki din mana idan ya dawo. Sai mommy ta nisa tana fadin hakane ni din ya kamata nayi amma jiya mun dawo daga dinan ya gyade yake fadin wai na barwa karima girki kai tsaye . Ya jikin Alh din umma ta tambaya to da sauki yanzu na buga masu waya kafin in fito sunce har yanzu dai bai farfado ba sai dai likita yace ba komai bane wai zai farfado da yardan Allah Allah ya sauwaka umma ta fada. Ina jin su na lafe banyi magana da kowan su ba don kada su gane idona biyu a lokacin naji umma tace kai ita kuma wanan kishiyar taki da takalan magana take wallahi. Don me zatace itace zatayi gitki bayan tasan kece da girki kuma nifa kinga abinda ke ban tsoro da kishiyoyin zamanin nan ke nan hjy. Kana zaune kalau da iyalin ka sai su shigo su bata zama a karshe su kuma din ba zaman zasuyi ba koda sun zauna din a cikin fita kowa na kusa dasu zai zauna. Bari ke dai Mairo wallahi da farko Alh baya biyewa iskancin ta amma a yan shekarun nan yanzu kan ya biye mata wallahi. Zama dai kawai nake a cikinsu ina hakkuri amma komai ban ganewa yanzu wurin Alh duk abinda nayi shi dai banyi daidai bane a wurin shi. Kiyi hakkuri hjy duba ma ga yadda yaran nan a yanzu duk sun girma hakkuri kawai yanzu ya rage kuma ai don mazan yanzu sun fison haka suma. Shine ai tunda dai ina zaune cikin iyalina ai ita ta rage da daukan nauyi a wuyan ta yanzu kumabarin je ina son a hada abin kari a aika masu asibiti ta fada tana mikewa tsaye. Na dade a wurin idona biyu bayan fitan mommy din daga part din ban kuma daga ba balle umma tasan idona biyu lokacin. Zaune suke falon yayi tsit sai Jibrin Arrow ke bayani kan abinda ya faru yake bayani aikai sauran suna sauraron shi shi kuma mustapha sai goshin shi yake murzawa kawai a lokacin. Don yadda yake jin zuciyar shi kamar ya buga saboda bacin rai ya yarda dasu sun cuce shi da yawa zai nuna masu shi din kifine ne mai ganin mai jar koma ya fisu sanin kan duniya a yanzu. Don shi da ilimi da siyasa yake tafiya da harkokin shi ba tare da duhun kai irin nasu ba da sukeyi yanzu a jahilce. Har Arrow din ya gama bayanin shi bai dago kai ya kallesu ba shuru yayi ya tsurawa ogan nasu ido duk da sun girme masa a shekaru haka suke bashi girman shi da Allah ya bashi a kansu. Yaro da kudi abokin manya ke nan mustapha boy din hjy hari don ita ke kiran shi da boy kasancewan shi dana farko a wurin mahaifiyar nashi bata kiran sunan shi na asali mustapha din. Jin Jibrin din yayi shiru yasa ya dago yana binsu da kallo da idon shi da sukai ja jajir a lokacin murmushin dole ya kakaro masu . Don ji yake falon na juya mashi da kyar ya iya budan bakin shi yadan lashi lebon shi da yaji ya bushe masa yana fadin yaushe ne kayan zasu iso ? Jibrin ya gyara zama yana fadin zuwa karshen wata insha Allahu kayan na Nigeria yadda suka tsara kayi kokarin da namu kayan zasu dakata a can ba,a zo dasu ba ya fada ya mike tsaye tafiyan shi kawai yasa suka gane abin ba na wasa bane wanan karon. Juyowa sukayi bayan sun rakashi da kallo ya shige suka hada idanun su cike da zargin junan su a lokacin. Koda ya shiga dakin kwanciya yayi yana runtse idanuwan shi ba abunda ke fado mashi a rai sai dan uwan shi abokin gaban shi tuna kurciya da har yanzu sun kasa sake jiki da junan su a matsayin su na diyan yan uwa da suke. Ya sani sarai dan uwan nasa yana farautan su a yanzu don so yake ya kamasu dumu dumu da laifin kan abinda ya shafi dokan kasa . Ke nan da hakan na nufin Abubakar midibbo din yayi wining akanshi ke nan da komai don indan har ya kaishi ya kulle yasan ya gama gamawa dashi ke nan a duniyan nan. Mikewa yayi daga inda yake kwance da sauri ya dauko Laptop dinshi duk bayanan da yake so suna ciki kamar yadda ya adana su a baya dan guntun murmushi ya sake a lokacin. Asibiti zamu wai zamu kai abinci daga nan mu gaida maijiki duk da ban san waye ba lafiya ba a lokacin . Saidai haka kawai nake jin ban damu da wanda akace din yayi hatsarin duk da ance maishi din dan uwan mommy ne kuma dan uwan daddy kuma. Saidai hakan bai dameni ba kamar yadda naga sauran sun damu suna jin hatsarin mutumin a jikin su. Bujene da riga na atamfa na saka mai kalar pink da adon filawa farare masu girma daga nisa zaka iya dauka lace ne sai idan nazo kusa zaka gane atamfane na saka. Bayan mommy ta muna fada kamar yadda take muna duk lokacin da zamu fita daga gidan akan mu kama kan mu mu kula da mutuncin mu muyi tarbiya da da,a ga wa yanda zamu sama asibitin. Na dauki basket din abincin nabi bayan su ina dan gyara gyalena da yake sabulo min a kafada don rashin sabo da yafa gyale haka . Gaskiya ba yabo ba kyau kam Allah ya zuba min tundai yanzu da nake samun gyara daya dace dani don na murje nayi wani irin haske da dan jiki. Ga kiran hallitana da yanzu ya fito a fili don na kai budurwa sosai kuma na iya gyara saidai har wanan lokacin shigana da nasu akwai bambamci sosai don kayan da nake sakawa su basu iya sakashi haka su fita. Niko ko a jikina don gani ma nake ai na fisu shiga na fita a lokacin akai sa, a kuma ba wani mai kyani don daddy baida tsanani ga iyalin shi shi. Nabila ce ta jamu mun isa ba wani wahala don gane wurin don dukkan su sun san asibitin tunda muka tun karo wurin na hango wani mutum mai karfi tsaye yana fada. Sai faman gyaran babban rigan jikin shi yakeyi a lokacin ga yan uwa da abokan arziki anyi shiru ana sauraren shi har wasu ma,aikatan asibiti din suna wajen. Ido suka sako muna duk da fadan da yake kwasa har muka karaso wurin muna gaida su shikan saboda masifa baiko amsa gaisuwan namu ba muka shige ciki asibitin don ganin wace mommy tace muba abincin bata wajen. Mun shiga mun gaida na ciki mun masu ya mai jikin bamu tsaya ba muka fito daga ciki saidai wanan karon baya wajen da muka barshi sai sauran mutane ke wajen. Suma mun masu sallama muka nufi inda motar take zamu shiga har mun fara shiga aka kiramu dole muka koma sai dai mun samu wata mata mai dan kiba tana bashi hakkuri kada yayi magana. Jikin shi na bari yana fadin a fito da basket din da muka shiga ciki dashi sauran yan uwa na fadin son Allah yaya kada ai haka mana abin zai zama abin magana ai. Muna zuwa yace kai ku dubeni da kyau ku koma ku fadawa munafukin uban ku cewa ni Nuhu nace baiyi abincin da zai kawo nan asibitin ba hakama uwar ku din. Ku fada mata ni Nuhu nace kada akara kawo abinci nan sallon yaudara ko mayar da mutane fakirai ? Wurin yayi tsit ana sauraren shi yasake fadin nan ma an biyo shine a kasara ko tunda anga bai mutu ba . Sai wani zare idanuwa yake a kanmu yana kare muna kallo kafin ya sake fadi cikin tsawa maza ku dauki munafki kayan ku ku bace min da gani. Waitin he talk na tambaya amma don tsoro Fa,iza ta kasa ban amsa gashisu sun duka har kasa suna saurareb shi cikin ladabi ni na kasa kaiwa kasa sai dan bending din da nayi ta bayan su kowa na kallon mu a wurin. Ashe gaba da gababta shima Alh yana da wani dan iskan yaro wanda bai tsoron shi , shine yace muna kai ku tafi abin ku haba daddy wanan bai dace ba wallahi. Yanzu idan mu, iyayyen su sukaiwa haka ai ba zakuji dadi ba wallahi su ina ruwan su cikin harkan maganan ku kuma fa gashi sunce gwaggo Addah ce ta bayar a kawo abincin nan. Kasan kuma sauran yan uwa duk suna kawowa do me ita zakayi wanan batacin a garesu haka yanzu kuma wani magana ya fara bullowa ke nan kuma. Nikan a lokacin na mikema tsaye ina kallon shi cikin tsana don saura kiris in bayana kaina a gareshi Allah dai ya gyara zancen a wurin. Kai ku tashi ku tafi kuce an gode ana gaida ita guy din ya fada nikan na juya na fara tafiya shima ya kalli dan nasa kamar zaiyi magana sai kuma yayi shiru ya fara tafiya. Yana huci har yakai kofa ya juyo yana fadin Wanan dayan yarinyar da suke tare wacece ita sai matarshi dake gefen shi tace ban san ko yar waye ba a gidan dai take zama saidai naga kamar zuwa takeyi ta koma ko kuma diyan makwabta sune nake gani. Yace amma fuskanta sai naga kamar nasan shi a wani wuri koda yake dai kamane kawai dai saidai yarinyar da gani bata da kunya naga. Baba ko hausa bata ji fa wanan yar ance kabilace ita a unguwar suke zama ta shaku da yaran gidan shikan ya fada ya shige dakin da dan uwan nasa yake. Motar yayi shiru sai Nabila dake shara gudu kafin hauwa tace kungani ko saida nacewa mommy bana son zuwa wurin nan yanzu ga abinda ya biyo baya. Kikace ko nace nabila ta fada tare da fadin ni wallahi na tsure wanan da akace ko hararanka yayi sai kayi ciwo balle gashi kamar ya cinyemu da ran mu kan fada. Ina bayan motan tare da Fa,iza kowan mu baiyi magana sai tunanen zuci da mukeyi kai ni wallahi tun farko ban son ko ganin kawu Nuhu a raina tun ina karama hauwa ta sake fada. Daga bayan motan Fa,iza tayi magana tace wai da yake kiran daddyn mu da mugu shi din meye shiba ace masa mugu ba sai shi zai kira daddy da mugunta. Kai ku bar zancen shi don Allah wallahi ance ko zancen shi akayi ya sani ko manyan mu suna tsoron shi balle mu. Me zaiyi babu abinda zaiyi muna riga damun gama dashi ko saidai yaiwa wasu mugunta bamu ba insha Allahu. Sai suka saka dariya muna shiga gida part din mommy din muka nufa gaba dayan mu ban suka fara mata bayani ta fara salati sai kuka. Tana fadin wullakacin na yaya har yakai can aini badon shi na bayar da abuncin akaiba don jama,an dake wurin suna jinya ne na bayar. Ganin da nayi tsayin bai mun yasa na mike nabar part din don yadda nake jin kaina a lokacin. ANA DARA GA, , , , , , , 3️⃣5️⃣ BY, , , , , , ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , , , , , , BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AL KHAFID, , , , , , , , ONLINE PAID NOVEL YAR UWA KI GUJE ABINDA ZAI IYA HALAKAKI KAN HAKKI NOVEL DON KUDINE WANAN, , , , , , Umma yau na ganshi ido da ido wallahi wanan mutumin lalai mugune mugune na karshe umma yau na fara ganin a yau din kuma ya nuna min koshi waye. Wa kika gani kika shigo min haka a razane umma wanan Alh daya kashe min mahaifina shina gani asibitin. Farine ba sosai ba dogo mai karfi da da dan gemu ga jajayen idanu maicin mutunci da zarafin mutane ko a gaban kowa. Yaci muna mutunci ya tozarta mu yau a gaban kowa umma akan abincin da mommy ta aike mu mukai yace mu dawo dashi mu fadawa daddy shi Nuhu yace daddy baiyi abincin da zai aika masa ba. Fa,izace ta shigo take fadin ana kirana a falon Daddy kallon umma nayi inda take zaune ta kura min ido kafin in mike umma ke fadin. Ina fatan ba rashin mutunci kikaiwa yayyun mahaifin ki a fitan ku ba da yarbanci babaren data fada shine yasa Faiza dan kallon mu kaina kada nabi bayan Fa,iza din muka fita. Suna zaune a falon har mommy din muka shigo wuri Fa,iza ta samu ta zauna na duka a gefen ta tare da dukar da kaina a kasa shima daddy din kanshi na kasa yana dan bubuga kafan shi a kasa. Kafin ya dago yana fadin ungo Sahiba waitin dat man talk at d hospital ? Nan na fara korawa daddy komai tun shigowan mu asibitin har fitowan mu nakare da fadin that,s all i know daddy. Ya nisa tare da fadin fine kinyi kokarin fada min komai saidai ku meya sa zaku boye min koda yake ba laifin ku bane laifin uwarkune gata zaune. Amma ina son ki sani duk da sudin yan uwanki ne na jini saidai a bangaren su yanzun ba haka suka daukeki ba su a wurin su don yanzu Nuhu da yan uwansa sun bata komai a yanzu. Saidai ina son don Allah ki nisanta yaran nan da shiga harkan wanan mutumin da baida tauhidi a zuciyar shi kada ya taba min yayana don wanan kam bazan kyaleshi ba idan nayi hakkuri akan komai. Allah sarki mai uwa da uba raye a duniya ya godewa Allah na fada a zuciyana ga Daddy duk abinda Alh yake masa bai ji bacin rai ba, sai yau da yakai ga yayan shi ranshi ya baci haka dasu. Saidai dama idan yana da wata manufa a kaina don kai abinci yau aka saba kaiwa harshi abinci asibiti idan ya kwanta. Eh mommy haushin bai samu kashe daddy da sukai niyar yi ranan ba ya komawa dan uwan shi shine yake jiwa haushi a yanzu. What daddy ya fada karfi. Nace a rude yes dad they atterm to murder you on that day. How do you know all dis ? Ya tambaya yana tsure ni da idanu hannu na ware tare da fadin i dont know . Amma dai haka din ne daddy i know haka din ne sunyi plain su kashe ka a ranan sai ya juya masu akan kanin shi yayi arziki bai mutu ba. Ke kinji hjy kinji wanan maganan kuma da yarinyar nan ke fada yanzu na sake fadin yes dad abinda suka shirya ma ke nan. Innalillahi suke maimaitawa a lokaci daya mommy na fadin dama akan ka Alh aikai wanan aiken kai ku bar saurin yarda da orin zancen nan balle a bakin yarinya karama irin Sahiba. Ya dago kai ya dan kura min ido na dan lokaci na wani huro iska a bakina tare da hade yatsun hannuna a wuri daya kamar ina wasa dasu suna dan bada sauti kas kas. Tashi kije Sahiba daddy ya fada ban jira komai ba na mike na fita daga dakin daddy ya kallo sauran yaran dake wuein yana sauke numfashi tare da fadin. Ku saurari abinda zan fada maku yanzu kuji kada inji wanan zancen ko a cikin gidan nan balle wani waje da fatan kunji abinda na fada suka amsa da eh daddy. Suka mike suka fice daga dakin suna jin wani iri a zuciyoyin su , don haka ba wanda ya iya magana a lokacin ga baki dayan su. Shiru dakin yayi na dan lokaci kafin hauwa tace waiko yarinyar nan dai yar securo ce ko me dai don nifa abin Sahiba ya fara ban tsoro. Meye na tsoro a nan kawai dai wani bauwane na daban Allah yai mata kila ba,a sani ba amma ai zamu gane hakan udan zancen cikin anty ya fito gaskiya lalai Sahiba watace na daban a cikin mu. Tsoro nake ji idan ba yar wani cult bane fa don kusan wanan haline na diyan kabilun nan su ba su daukeshi a komai ba kamar ma ado yake a garesu. Don Allah hauwa ki bar wanan zancen don ni kin fara ban tsoro akan yarinyar nan wallahi wanan maganan da kikeyi ya fara firgitani da ita yanzu. Kai don Allah ku bari da muguwace ai a kaina zata fara nunawa ni dake tare da ita akoda yaushe kuma ai da yar cult ce da ba zatayi ibada haka ba don sahiba badai a tuna mata lokacin sallah ba dai. Shine kuma fa gaskya ba cult takeyi ba kawai dai wata kila iskokai ne a kanta suke mata hakan . Bamu san ya daddy ya kwashe da mutanen sa ba saidai abubuwa da suke tafiya a boye don zancen manya bai shafemu ba. Karshe dai saida aka fitar da Alh gyade kasan wajen suka kwashe watani kusan biyu suka dawo dashi hakana don ha samu kariya sosai a jikin shi an kuma kasa shawo matsalan jikin nasa. Alokacin kumanecikin jikin Anty data shagala da bata da ciki yafito fili a jikin ta wanda da farko ta dauka girman tubine hakan sai ranan Asabe ke fadin hjy anyi nauyi haka ashe ? Saidai wanan karon abin yazo maki da sauki bakya amai ko wani laulauyi mai bada wahala har tayi murmushi zata tafi sai kuma taja ta tsaya a wurin. Ta juyo ta tsaya a ya tsune tana fadin wai me kike fadine haka Asabe yaushe har na fara wanan wasan dake ko wani ya aikoki ki zolayeni da wanan zancen. Zolaya kuma hjy ? Haba ni na isa nayi wanan wasan haka dake ko kuma wani ya aikoni in muzanta maki akan me ? Sam ban san bakya son asan da zancen cikin nan bane a cikin gidan nan aida ban fada ba wallahi amma kiyi hakkuri hakan ba zai sake faruwa ba insha Allahu. Ta wuce fuuu zuwa part din ta kwanciya tayi saman kujera ta shiga tunane kafin a wani irin shureta saida ta dan sake ihu kadan tana mikewa zaune a cikin mamaki. Kara jin wani motsi irin wanda masu ciki keji a cikin cikin su lokacin da yaro yake a ciki kwance taji. What ta fada tana mikewa tsaye kafin kuma ya koma wani gefen ya lai mata shuri again saida ta cije baki takai zaune kuma tana kiran sunan Allah. Yau me take shirin ji kodai wai mutanen nan mayu ne Asabe da wanan yarinyar Sahiba data fara kira mata ciki a yanzu da take kokarin maintening din kanta. Kai ina mikewa tayi ta fara kai hannu a saman cikin ta tana jin abin cikin cikin nata yana motsawa a hankali alaman yana canza gurbi sakamakon dan taba cikin da tayi a lokacin. How come ciki har ya girma haka a jikin ta har da na iya motsawa haka amma bata farga da cewa cikine a tare da ita ba a jikin ta . Ita duk da tana malam asibiti bata yarda dacewa mace zata iya nomal al,adanta ba kuma tare da ciki mai rai a jikin ta haka gaskiya. Kai ina ta fada tayi waje zuwa kofan daddy ta samu dakin a rufe bata yarda baya ciki ba saida ta murda kofan tajishi a rufe. Bata samu natsuwa ba harsai lokacin da daddy ya dawo suna falon da mommy yana cin abinci ta shigo da sallama kasa kasa . Da mamaki suka amsa mata ba bata lokaci ta fara fadi gaskiya Alh ka dauko muna masifa a gidan nan ka hadamu dashi. Subbahanallahi ya fada yana dago kai eh masifa mana don Sahiba tana kokarin zama muna kashin bakin tukiya a cikin gidan nan. Tun ranan datake fadin wai ciki ne a jikina ban dauki zancen ta gaskiya ba sai yau din nan da Asabe ta kara furta min hakan kuma na tabbatar abin nason ya zama min gaskiya a yanzu. Akan me zatayi min wanan furcin ita ta fini sanin cikine ko bayana take nema ta gani don ka auri uwar ta zauna makwafina. Acikon kunan rai ya dakawa anty tsawa yana fadin wai karima kinyi haukana ko kuwa ki san abinda kike fadi kan mutanen nan a gidan nan. Kamar yadda kuke zamana a cikin gidan nan haka Sahiba da uwarsu suke zamana a cikin wanan gidan . Meyasa ke baki da fahinta ne akan abu ko yadda nakewa yarinyar nan idan ke mai kulane zaki fahinci suna da muhunmanci a wajena sosai. Ga yadda na fahinta a yanzu har kinfi Addah cin moriyan yarinyar nan a gidan nan don da bakin ki ke fada min yadda yaran ki ke jin dadun ta dake kanki a zaman su gidan nan tare damu. Amma da dan abu ya hadaki dasu yadda kike nuna rashin hakkuri kan diyan cikina haka kike kokarin nunawa gun sahiba a yanzu. Zancen ciki a jikin ki har wani zance ne da zai kawo tashin hankali koda baki da aure balle kina dashi. A nawa ganin ai kamar taimakon ki tayi ta fargar dake hakan tundake likitace kin kasa fahintar hakan idan kuma baki yarda ba sai kije asibiti ki bincika kiji gaakiyan maganan. Idan suna da muhinmanci a gareka ke nan mu a yanzu bamu dashi ke nan a wajem ka su sunfimu kima da daraja ke nan ta fada. Haba hjy karima ki fahinci me Alh ke nufi mana kada bacin rai ya sa idon ki ya makance ga hakan don Allah. Zaki iya fadan haka ai tunda da hadin bakin ki ake komai ikon Allah komai kamar yaya mommy ta tambaye ta cikin mamaki. Ai tare da yaran ki take ko wani lokaci waya sani ko wani abin kikasa tayi min yanzu ta fada tana wani cicikaka da kada jiki. Au tanan kuma kika bullowa yarinyar nan amma kuma ai naga kinfi kusa da su don kema kina aiketa kina sakata aiki da sauran abubuwa sai ni ince me yanzu a kanta kuma ? Ya isa haka Alh ya fada a cikin tsawa yana fadin duk wace ba zata tsaya ta tayani rokanwa yarinyar nan Allah saukin wanan laluran ba don Allah ta rabu dani da zancen banza a gidan nan. Yarinya tana fama da lalura haka mai karfi har zaku zauna kuna sa,insa aikanta don ba wace ta haifeta a cikin ku ko ? Da yau zaku tona cikin uwarta kuji yadda take ji da halin da yarta ke ciki na wanan laluran da baku iya daukan hakan a zuciyar ku. Wanan ba karamin abu bane keson ya bullowa yarinyar nan don ko dubanta kayi ka kalli idunun sahiba kai kasan Allah yayi ajiyan shi a wurin. Wallahi Allah hakane Alh uwar kan na cikin wani hali a yanzu da abin ke son yayiwa yarinyar nan yawa sosai aiko kan wanan furcin da tayi maki nakai karanta take mata fada wallahi a gabana sai cewa ita ita yaushe ta furta maki hakan ? Yaushe ta furta min hakan ta tambayi mommy data fadin hakan tace wallahi Allah haka ta fada tace me kikai mata da zatayi maki rashin kunya har ta furta hakan a kanki. Kin gani wanan wani bakon lamari ne kila ya shigeta bamu sani ba kuma don haka sai an kai zuciya nesa a yanzu don ina ga abubuwan zagayota sukeyi ba zaune suke a cikin jikin ta ba ai Inma ance zaune suke ba a mussu da hakan mommy ta fada daga gefen shi jikin anty yayi sanyi takai zaune karshe sukai ta zancen dai har ana dan dariya a kanta. Sun fito ne Anty dakin mu tayo direct ta samu muna cin abinci har da fatiman ta da Amira sai Fa,iza dake kallo a gefe kwance. Gaisawa suke da umma na dago ina fadin Anty barka da yamma tace ban karba tunda kin min baki ya bini na dan dago kai a cikin mamaki ina kallon ta. Tace eh bakin ne ya kamani Sahiba har nayi ciki a lokacin da ban shirya zuwan shi ba gareni yanzu. Umma tayi saurin fadin haba aiba aiwa Allah wayau yar uwa ubangiji ya rabaku lafiya niko cewa nayi da ita ni anty ? Ta kawar da zancen tana fadin yaushe wa yan nan suka shigo tana nuna yaran ta dake kallonta suna dariya nan a kwance na barsu suna kallo fa na fita. Ai kuwa suna nan tun dazun umma ta bata amsa muna nan tare dasu yanzu yarsu ta matsa suci abinci suka zauna ci. Ban san meke damun yaran nan da basa son cin abinci ba na gedigedi de wory dem na fada a cikin rashin kulawa ina fadin give dem local medicine for gedi gedi. Tace me i no wan dat local medicine at all, but i will take dem to hospital nayi dan murmushi ba tare da nayi magana ba. Daddy ya kara tambayan mommy abinda ya faru mommy din ta fada mai komai shiru daddy yayi na dan lokaci. Kafin yace watau dai zancen yarinyar nan da gaske ne dai idan ta fadi magana ke nan kuma hakan na nufin da gaske ke nan nisu Alh Nuhu sukai niyar halakawa ke nan ashe ? Allah kaga nufin wa yan nan yan uwan nawa ya Allah na rokeka kada ka taba basu daman da zasuci galaba a kaina har abada. Hjy dake gefen shine ta amsa da amin tana ajiyan zuciya tare da fadin na dade da sanin yaya Nuhu yana da wani kudiri akan ka koma me suke nufi insha Allahu Allah bai basu sa,a a kaina. Rayuwa ke nan yau da dadi gobe babu amma haka muke zaune a gidan babu ne bamu rasa ba a gidan don komai muka nema akwaishi gaskiya. Haka yasa rayuwa ya canza muna a cikin dan lokaci ba zaka ce nice sahiban geto ba wace tasha gwagwalmayan duniyan lagos. Zama da yan matan mommy da karatun da nake shiga yan Arewa a yanzu ya kawo min ci gaba sosai a rayuwa don yanzu idona ya bude kitsuwa yazo min wanda kowa na mamakin hakan ga dan zaman mu a arewa din nan kuma gidan daddy din. Haka ya kawo min farin jini saidai tsiwana da izzana wanda tun farko idan baki manta ba na fada maki ina dasu talauci dai ya rufe hakan gareni. Wanan matsalan tsiwan shine ya dan rage min farin jini a gurin mutanen don suna daukan hakan da don ina da kyau nake daukan kai a garesy haka nake wullakanci don azaton su wullakancine hakan basu san halin nawa bane haka bana shiga harkan kowa yasa sai mutane su dinga shareni. Wanda niko sai hakan yayi min dadi don ban faye son yawan magana ba saidai idan na tashi ko waye kai kai tsaye zan fada ma gaskiya. Haka zalika na mayar da hankalina ga karatu sosai don ban son a wuce ni ga ko wani famni na karatun boko dana mahammadiya ina mayar da hankali a garesu. Gidan ya Abubakar tun farkon zuwan mu da muka tafi tayi min wullakanci har aka samu rikici tsakanin su ban kara taka gidan ba kamar yadda na fada a baya. Saidai abinda na lura shine su kansu yan uwanshi ba son zuwa gidan sukeyi ba saidai saboda shi da mommy suke daurewa su tafi. Sai gashi yau da kansa ya shigo gidan dama yasha tambayan wai ina nan kuwa indan yazo baya ganina a gida. Sai ace ina school ko ina barci wanan yasa bamu haduwa dashi don haka bai san cewa Sahiban da yasani a da ba ita bace yanzu. Yau a part din mommy ya rutsa dani jin muryan shi yasa muka fito muna gaida shi kusan nida Fa,izace karshen fitowa falon daga dakin. Wando bakine a jikina sai wata riga pink dana hada da rigar mai dan hannu dabai karasa sauka ba sai gyale baki dana rufe kaina dashi. Daga can bayan su na dan tsaya na dafa kujera ina fadin brother u are wellcome ya hanya har ya kawar da kanshi sai kuma ya juyo da sauri yana amsawa tare da jin wani irin faduwan gaba yadda na koma masa ga gani lokaci guda haka yake fadin har lokacin kallon mamaki yake min. Sahiba kece wai ? Long time no see u , nace ina nan broda ina dan dariya tare da noke kai zan juya ya sake fadin daddy ya fada min yasama maki addimition state university ko ? Nace eh na fara zuwa wancan satin any whare zanga mommy don zaku koma lagos da zama na dan lokaci jin hakan yasa na dago kai da sauri na kallesa saidai babu alaman wasa a gareshi lokacin. Da kyat na iya budan bakina nace dashi back to lagos again broda? True true talk me i no wan go back to that side again na bata raina yace kije zamuyi magana leter dani da ummaki daku ZAINAB IDRIS MAKAWA ANA DARA GA, , , , , , , , , 3️⃣6️⃣ BY, , , , , , , , ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , , , BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHAIM AR RAFI,E ONLINE PAID NOVEL YAR UWA KI BIYA KAFIN KI KARANTA DON ALLAH NA KUDINE KADA MU RIKE JUNA DAKE, , , , , Na kasa boye mamakina ga hakan sai kallon shi da nakeyi a lokacin ko banyi magana ba kasan abinda zuciya ke raya min a lokacin. Sam ba zanyi fatan komawan mu lagos da zama ba gara rayuwan mu nan cikin yan uwa sau dubu da zaman lagos da mukayi babu kowa namu a wurin. Sai kuma na dago kai na kalleshi kamar a firgice ba komai na tuna ba sai mai zai maishemu lagos da zama a lokacin ? Sahiba kyale yayan ku da wanan zancen nasa don ba a kai karshen maganan ba inji mommy ta juya wurin shi tana masa fada don me zai fito da zancen a gabana haka ? Juyawa nayi na bar part din nasu zuwa part din mu a cikin rashin kuzari a tare dani don nikan arewa tayi min yafi zaman lagos a gareni duk da da farko kamar na shiga matsi saboda zama wuri daya da ban saba dashi ba a lokacin na bude idona cikin motsa jiki da fita neman nakai a rayuwa. Haka yasa ko a nan in dai ina gida ba zan fita school ba nice a ranan zan gyara gidan ko inansa baki daya. Tun mommy na fadan hakan har ta kyaleni don ta fahinci zama a kazantane bana so yasa nake aikin da kaina don a yanzu yaiwa Asabe yawa duk aikin gida ita daya keyin sa ga gyaran gida ga aikin kitchen. Ban samu umma a falo ba sai Amar dake zaune yana kallon ball a tv na samu wuri na kai kwance ina faman tunane. Har umma din ta fito tana fadin Amar ya canza chanal ya damemu da zancen wanan kwallon tun safe. Ban iya fada mata komai ba har yakai an wuni sai da zamu kwanta barci ne damuwan hakan yai min yawa na fadawa umma zancen. Shiru tayi na dan lokaci kafin tace dani Alh ya fada min hakan ga kwanaki amma yace sai idan sun kai ga yanke shawara don yin hakan yana cikin shirin su da suke muna. Amma zasu nema muna inda zamu zauna da kuma karatun mu don karya tsaya a can din duk dai yanzu da zuwan mu nan din muna neman rufe shwkara biyu ke nan kuma duk lokacin umma tana boye ba fita takeyi ba ko a cikin gidan. Sai mu yara da ba,a iya boyewa ne muke dan fita muna zirga zirgan mu ba tare da takurawan kowa ba a zaman mu din kaduna gidan daddy. Naji umma tace aiko ba komai yanzu mun san yan uwan mu mun kuma san garin mu da gidan mu ko ba komai muna da madafa a rayuwan mu nan gaba. Shiri sosai ashe daddy yayiwa komawan mu lagos din kan abu biyu zuwa uku ya yanke shawaran yin hakan na farko zaman mu a nan ya fara kawo zargi a kanshi. Kan yawan tambayan shi da akeyi mu din su waye a gareshi don duk wanda ya ganmu sai ya tambaya saboda zatin da Allah yai muna daga ni har amar kanina din daban muke a cikin yan uwa. Haka ya fara daga hankalin daddy har ya nemi shawaran ya Abubakar a kan yadda za ayi . Sai na biyu yasan ko bai samu matsala da kowa ba dolene ya samu matsala da anty Amarya don abu ba abu ba zata kai kara a aurin shi kan mu ya fara fuskantar baraza daga wurin ta kuma. Sai kuma idan muna nan ba zai samu fitar da duk wani abinda yake son aiwatarwa din yadda ya dace dashi din ba shine dai dalilai masu karfi da yakai daddy yanke shawara a yanzu mu dan nisanta dasu. Don haka sai aka fake da fadin cewa mahaifin mu da yayi tafiya ya dawo don haka zamu koma lagos din da zama kuma. Hankalin kowa ya tashi da jin hakan har anty Amaryan don sabo abune mai wuya ranan rabuwa da yan koke koken mu ranan muka bar kaduna zamu koma rayuwan lagos da a lokacin nake jin kuncin hakan a zuciyana. Wanan karon ma jirgin muka bi zuwa lagos din muka sauka da yamma a local airport dayake duhu ne mun samu mota na jiran mu shiyazo ya kwashe mu zuwa gidan da zamu zauna a Apapa. Wanan ne mafarin canza komai a rayuwana da nake son baki labari a yanzu yar uwa. THIS IS LAGOS Tun lokacin da nayi arba dashi na runtse idanuwana nake jin wani iri a raina har muka kawo inda zamu ban bude idanuna ba. Jin an tsaya yasa na bude idona na ganmu a wani kofan gida me bene hawa daya da get da komai a gidan duk da garin ya dan canza min anyi wasu sauye sauye hakan bai hanani gane unguwar da muke ba a lokacin. Yana gaban mota zaune ya nazari a cikin wayan shi ya dan juyo yana fadawa Amar da cewa Amar dis is ur new house in lagos. Sai yaron ya dan kakaro murmushi a fuskan shi muka fito aka bara fitar muna da kaya har lokacin ina dan dunkule a cikin half cover din hijjab baki dana saka wanda naji ana kira da half sunna a arewa. Masha Allah umma ta fada tana fadin sai ku fita mu shiga daga ciki ko ta fada muna hakan yasa na dan motsa a yadda nake zaune da ido sunyi min ja a lokacin. Duk da ganin gida ya dan sa na rage jin abinda nake ji a zuciyana saidai hakan bai sakani jin farin ciki ba a lokacin don rabani da yan uwana da barci ne kawai ke rabani da fa,iza aminiyata kuma uwar dakina a gidan daddy ke nan. Ga ya Abubakar ya hanamu dauko kaya da yawa a cewan shi in munzo hutu ai zamu samu na amfani a nan fadin hakan yasa nasan zamu dinga ziyaran su ke nan lokaci lokaci. Ni dai Allah gani nayi har na gwamace abarwa Alh Nuhu da sauran mutanen da suka cuci Abban mu a lokacin dukiyan da daddy ke kokarin kwato muna a hannun su da dawowan mu nan lagos din. Saman ne namu donshi muka hau gidane irin ginan zamani komai akwai a cikin sa kamar daulan da muka bari a kaduna nan ma haka akai muna gata a gidan. Bayan yasa key ya bude gidan ya mikowa umma makule ya nuna dakin farko yana fadin umma wanan na farkon zaki zauna. Sai wancan Sahiba ta zauna a cikin da jin haka na dago kai na kalleshi ya juya ya nuna wasu biyun dake gefe yace Amar zai zauna a cikin wanan na farkon don shi namijine sai dayan da ba kowa shima akwai komai a cikinsa sai a jewa baki shi da fatan gidan yayi maku haka don shine nagani kamar zaku sake sosai a cikin sa a nan. Kasa din duk nakune da zaku iya komai da kuke so sai kasan idan kuna da bukayan dan haya nan gaba sai a samu wanda aka yarda dashi ya zauna a ciki. Sai lokacin umma dake zaune saman dayan kujeran dake falon tace dashi ai ba kowa a cikin sa yanzu ke nan ? Eh umma don ban san ra,ayin ku ba ga shaguna nan kuma koda zaki samu masu hanyan su nan gaba shima naku din ne zaku iya bada hanyan shi. Allahu akabar yanzun dai a takaice muke da alhakin duk wanan gidan ke nan a yadda na kula ga bayanin ka modibbo ? Ya dan gyada kai yana murmushi yace hakane umma ba,a samu babba wanda yafi wanan din kuma wanan a karshe sai yaban sha,awa muka saye sa. Ban san irin godiyan da zan maku ba a yanzu ubangiji ya dada rufa asiri yasa a gama da duniya lafiya muka amsa da amin. A sanyaye nace dashi yaya mun gode Allah ya kara rufa asiri yace amin amma daddy ya kamata ku kira ku kara gode mai da wanan din. Ya Amar komai yayi ma ko akwai abinda kake bukata kuma Amar din ya kada mai kai da a, a mun gode yaya. Yace to umma ni zan tafi zan tafi masaukina baida nisa daku nan sosai gaba da kune kadan sai idan na samu lokaci zan kara leko ku insha Allah. Kamar ince don Allah kada ya tafi don ina ganin ya tafi ke nan ya barmu a nan har abada ba zai sake dawowa garemu ba kuma idan ya tafi. Yadda nake ji din ne yasa tun kan yayo kaina na mike zuwa dakin dayace shine nawa na bude na shige ciki ina sake kuka. Tsayawa nayi kuma turus ina karewa dakin kallo don irin yadda aka kawata dakin da komai na dakin pink ne har gadon da wardrobe sai kuma na tsaya ina kallo. Juyowa na sake yi da sauri na fito na samu har ya tafi ko sai umma dana sama zaune itama tana kukan fadawa nayi a jikin ta ina fadin shike nan umma suma sun tabu damu ke nan ? Basa iya zama damu kuma umma kowa yana gudun mu ke nan a yanzu kada Alh Nuhu ya kasheshi ko ? Sahiba nima tunanen da nakeyi ke nan tunda naga ashe ba tare da modibbo din zamu zauna nan din ba ashe. Shike nan umma shikw nan sai kuma na sake fashewa da kuka don ba zan iya yin magana ba a lokacin don yadda wani abu ya tokare min zuciya. Jikin umma na fada ina kuka itama kukan takeyi Amar kan yayi zaune yai tagumi ya kura muna idanuwan shi bai iya yin komai ba. Saida nayi kukan ya isheni naji umma tana fadin mu je muyi sallah kada lokaci ya shige muna bamuyi sallah ba akan lokaci. Dakin daya kira dana umma din muka shiga tana gaba ina bayan ta gadone da wardrobe milk colour da surkin baki sai mirrow da ban dakin har tawul an rataye sabo a kofan bandakin. Sallah mukayi muka idar mun dade muna addu,a wanda wanan ranan addu,a na zuwa ga mahaifinane nayi shi sai daddy da sauran yan uwa da nahiwa. Bayan mun idar ne sai lokacin zancen abinda zamuci yazo muna jin Amar ya fara zancen abinci yasa namike nafita falon. Kitchen din dana gani na bude subbahanallahi nan ma dai basu kasa damu ba gaskiya don akwai komai a cikin kitchen din da zamu nema ga store din shi nan shake da abincin da zamuci. Fridge da freeze na a ciki don haka na bude ai kira na kwalawa umma tazo tagani itama bata tsaya ba jin kirana sai gata ta fito da sauri daga dakin. Ta sameni a kitchen din na nuna mata hawaye ke zuba daga idon umma din wanda ba zance ga dalilin shi ba a lokacin. Takawa nayi zuwa wurin gas din dana gani ina son in dafa muna koda indomei ne muci mu kwanta a lokacin. Sai kuma na bude warmer din abincin dana gani abuncine ciki maizafi har yana tururi a lokacin na juyo na dan kalli umma din itama ni take kallo. Abincine fa umma tace nima shina gani ai aikin modibbo ne nasani yasa a kawo kafin mu iso nan kila. Shina fito dashi falon muka zauna mukaci kukan waya nake ji da sauri muka dago kai muna kallon juna da umma. Wayace ke kuka a gidan haka yasa na mike da sauri ina bin kukan wayan inda yake fitowa a dakin umma har Allah ya taimakeni naga wayan a karkashin filo tare da kwalin shi a gefe daya. Na dauka don na iya a wayan su Fa,iza daya zama kamar wayana a lokacin don nike faman jagulan shi sai idan an kirata zan kai mata. Na dauko wayan nazowa umma dashi ina fadin wallahi umma wayace sabuwa har da kwalin ta a cikin dakin ki wurin pillow. Wani kiran ne ya sake shigowa na daga da bissimillah gami da sallama abakina aka karba min. Muryan mommy ne don bazai bace min ba tana fadin Sahiba kun sauka lafiya ? Ban iya karba mata ba sai kukan dana sake kawai a lokacin ina mikawa umma wayan ta karba tana fadin menene waye kuma ? Muryan mommy taji tana fadin nice mairo ya kuka sauka ya jama, a da yaran ta amsa da lafiya mun barku lafiya dai ? Ta amsa da Alhamdullahi kafin tace kun tafi kun barmu da kewan ku har yanzu sai umma ta danyi dariya tana fadin . Gasu zaune sun kasa sake jiki tun zuwan mu na kasa gane masu balle yartaki ai gaba daya a hankali tashe take a gidan nan. Dada hjy sai kuma mukazo muka samu dawainiyan dayafi wancan da muka baro a nan kuma. Layin ne ya katse mukai kira baya shiga a lokacin dole muka kyale haka muka bar zancen neman layin na mommy din. Mikewa nayi na duba kofan a rufeyake tunda zamu shiga sallah dama na rufe kofan don ina jin lokacin da yake fadin mu saba da rufe kofan kada a barshi a bude. Lokacin da muka shiga dakin ne na bude troler kayana dana shigo dashi in dauki kayan barcina bayan na ciro na saka wando da riga na saka hula a kaina. Sai naji in bude wardrobe din in ga girman shi ko jakkar kayana zai iya shiga ciki umma na fadin daki kai kayanki wanan can dakin dayace shine naki don zaifi kunga nan sai ku barmin ni kadai. Maganan ce ta makalewa umma don kayan dake cikin wardrobe din da aka jera a cikin shi. Nan kuma hankalin mu ya dauku ga kallon kayan fita nayi zuwa dakin na duba haka din ne kayan ane a ciki shima na fito kamar mahaukaciya naje dakin Amar shima hakane dai na sama a cikin nasa. Dole muka dawo fslon muna jin wanan karamcin nasu a garemu dare har Amar ya fara barci muka shiga zuwa cikin dakin muka kwanta. Washegari kan kusan makara ne don banyi barci da wuri ba saboda tunane yan uwa da kawaye da abokan arxiki da muka baro a kaduna. Bayan nayi sallah ban kwanta ba duk da gidan baida datti amma saida na gyara ko ina na cikin gidan tsab na koma dakin nan da yake a matsayin nawa nayi wanka na fito. Wardrobe na bude na tsura mai ido na dan lokaci kayan an bambamtasu a mazaunin su shiryawa nayi cikin wani simple material dogon riga na fito abincin danayi muna na breakfast na fito dashi falon. Na tayar da umma data dan samu barci a lokacin don saboda bata barci sai wajajen tara na safe zuwa goma sha dayan rana. Mun ci munsha Amar daya damu sai a kunna tv na kunnawa tv din yake kallo nikuma na koma saman kujera na kwanta don umma tace kada ayi abinci sai na dare tunda na safen ya rage da muka dafa bamu cinyewa duk da ba yawa wanda nayi din amma mun kasa cinyewa duka. Barci ne ya daukeni a wurin kuma na samu nayi barcin sosai harda mafalkina na yan uwa dana bari a can da sauran mafarku dai na dinga yi. Sallah azahar ne ya tayar dani lokacin bayan nayi sallah dinne muka zauna da Amar can umma ta fito ban san ya akayi nayiwa umma tambaya ba da fadin. Wai umma kafin Abban mu ya rasu shi mai kudine sosai irin daddy ko dai shima wanan filin da suke magana yake dashi kawai dama ? Sahiba ta fada a cikin mamaki yaushe kika koma haka ko zama arewa ya koya maki wasu akida na shiga cikin maganan manya ne ? I am sorry umma ban tambaya da wani nufi ba haka kawai tambayan yazo min a raina na bata amsa ta kawar da kai ga kallona. Nima din jinin jikinane nasha a lokacin don ban dauka maganan zai taba zuciyat umma haka ba mun dade a wurin zaune ba wanda ya sake wani magana a cikin mu kuma. Zama wasa wasa ya kama mu a unguwar har yakai na fita na zagaya unguwar nagani har iyaka duk yanzu nasan na wuce level din talla da nayi ada can baya a lagos din. Saidai kasuwancin bai fita raina ba son haka na kawowa umma sharawa akan mu dan fara sana,an drinks a dayan shagon mu huta zaman gida da mukeyi din. Da farko umma bata yarda da shawarana ba wai sai modibbo yazo ta tambaye shi idan yin hakan ba zai zama laifi ba garemu. Gashi shi kuma baizo din ba bai kira kuma wayan mu ba duk shidin ya aje muna waya a gidan don amfanin mu amma kuma sai gashi bai taba kiran mu ba har lokacin nan. Ranan na taso daga barci na dawo falo ina zaune na umma ta fito tana fadin ni sana,an zamu fara ne mu dan rika fita waje ko banza mu fahinci yan unguwan nan da muke cikin sa idan muna fita. Nadago ina fadin umma kardai tunena ya zama gaskiya mutanen nan hanyan rabuwa damu suka nema kada mu caza masu fitina a kansu suma. Eh to nima ina tunanem hakan wani lokacin jin har modibbon shiru yanzu bai kara waiwayo mu a nan ba. Koma sun guje mu sun muna gata a yanzu ai umma tunda sun muna sanadin sanin gida da yan uwan mu. Ga wanan gidan da yanzu muke zaune a cikin sa duk da bamu san matsayin mu ba cikin gidan nan shin hanya aka daukan muna ko zaman su yakeyi muke zaune a ciki ? Ban tsanmani a matsayin haya muke ciki duba ga abundaya fada ranan daya kawo mu gidan nan kawai mu zubawa sarautan Allah ido yanzu muga makomar mu nan gaba. Sai kuma naga umma din tayi shiru ta shiga tunane nake fadin umma don in kawar da tunanen data fada yi din nace umma akwai kudin da zamu fara wanan sana,an ne a yanzu. Akwai kudi mana a hannuna ko kin manta da kudaden dake ajiye a wurina tunda dadewa ne suna nan banyi komai da suba har yanzu. Jin hakan hankalina ya kara kwantawa tashi umma tayi ta dauko kudin muka zauna muka kidaya ko wani umma ta dauresu daban ta ajiye su a wuri daya. ZAINAB IDRIS MAKAWA ANA DARA GA, , , , , , , , 3️⃣7️⃣ BY, , , , , , , , ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , , , BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AL MU,EZZ ONLINE PAID NOVEL YAR UWA DON ALLAH KI BIYA KI KARANTA KADA MU RIKE JUNA DAKE, , , , Watan mu daya yanzu a logos ke nan ba wanda ya kara waiwayan mu daga fanin yan uwan mu don haka bamu san halin da suke ciki ba damu. Muma bamu san halin da suke ciki ba a can ga karatun mu ya tsaya a lokacin shine babban abinda yafi damuna a lokacin . Kudin hannun umma na karba naje company nayi odar drinks din dai danayi niyar mu sayar da nake ganin shine zai kawo muna samu a yanzu. Zuwa yamma ko sun iso muna dashi an loda a cikin shagon dake kallon wajen gidan nike zama a shagon ina sayar da kayan don mun samu har fridge mun saya mun saka a ciki. Haka kuma na budewa Amar dan qures karami na saida katin waya shima a nan yake zama a shagon shi din don yau da gobe bai bar komai ba tunda yaron ya fara girma a lokacin. Haka nake wahalace wurin ganin rayuwa ta inganta muna ni da kaina na sama muna addimition muka koma makaranta. Idan mun tafi umma muke bari a gida da yanzu mun saba da makwabta duk da ba ruwan wani da wani a can lagos din kowa tashi ta fidda shine a garin kowa ka gani yawanci kazo nazo ne ake zaune. Nasha wuya wurin samun nawa addimition din don har saida na danganta da sarkin hausawan agege ya kama min na samu gurbin karatun a inda nake so. Kamar yadda suma basu waiwaye mu ba hakane muma din muka gaji muka fitar dasu a cikin ran mu a yanzu. Lokaci baida wuya ga Allah , har karatun mu yayi nisa a yanzu ga Allah ya tarfawa garin mu nono sana,an mu tana ja sosai. Don haka bamu cikin damuwa ko fargaban abinda zamuci dama shine damuwa na a lokacin. Sahiba kan ta canza a yanzu natsuwa da wayewa yazo min don girma ya fara kamawa nakai sha tara ga shekaru a yanzu. Weekend ne don haka yau nake da burin shiga kasuwa in sayo abinci don bana wasa har in bar abinci ya fada a gidan. Na shirya tsab dani na fito a shago na samu su umma nake fadin umma na fito zan shiga kasuwa zan duba abinda bamu dashi a gidan. Umma tace dani kada in dade akwai alaman hadari yau nayi masu sallama na fita ba mota don haka na fara takawa zuwa inda nake tsamanin samun mota da sauki. Lagos market nacewa dan Nape din yance inter nashiga muka dauki hanya akwai mutum daya dana samu a cikin motar dana shiga din ban damu da maishi ba nima na shiga motan na zauna a ciki. Muyin nisa ga tafiya ina dan kallin gefen dama naji maishi yana kokarin yaba min wani bakin kyale a kaina. Iya abinda na tuna ke nan a lokacin sai bude ido nayi na gan ni a tsakiyan mutane a kaina sun rike ni wurin kamar a gefen titi muke dasu. A hankali nake dan tsuntar abinda mutanen wajan ke fadi suna cewa A, weee see d people when try to kill d girl with d ritular . Ita kuma ashe akwai tsari a jikinta ta mayar dasu haka suna zaune tufafun jikin su duk ya yage fuskan su da gani sun sha duka na fitan arziki sosai. Abin ne ya daure min kai bayan na daga kai na kalli gefen da mutanen suke zaune sai ga wani a cikin yarbanci ya miko min ruwa a gora yana fadin. Karbi ruwa kisha Allah ya kareki yau da sun halakaki sai Allah ya baki sa,a sune suka halaka daga mai Nape din har shi wanda kuke baya zaune kunzo nan kun tsaya dasu kuna ta dabe duk kin yaga masu riguna kince sai sun rufa da wanan bakin kyalen da suke son yafa maki a jikin ki suka ki yarda su yafa shine aka samesu wurin nan akai masu dukan tsiya. Hannu nakai saman dan kwagirin dana daura daga ciki na naji yana jikina na karbi ruwan na dauraye fuskana kawai dashi na mike tsaye. Kasuwan da ban yarda na karasa ba ke nan koda suka tambayeni unguwar mu nace a agege nake suka kwashe zuwa can . Naki yarda in fada masu inda nake don nasan lagos nasan mutanen cikin ta sosai da sherin su don haka nayi masu karyan unguwa suka kaini wani waje kusa da gidan sarkin zabarmawa nace nan ne unguwan mu din. Wani lungu na samu na labe a ciki saida suka wuce na fito na bulla wani titi na samu mai adaidaita ya kaini gida. Ban fadawa umma komai ba saidai a yanayin data ganni kawai tasan babu lafiya lokacin don haka ta biyo ni zuwa ciki tana tambayana ko lafiya ? Lafiya kawai nace na shige na samu gadon dakinta na kwanta naja bargo na rufe jikina daku sai lokacin tsoro ya kamani kuma. Ga lissafin ya Abubakar yau shekaran daya da watan shi shidda rabon shi damu gashi hankalin shi yana wurin mu amma kuma ya kasa yarda ya turo wani inda muke yana ganin yin hakan zaisa wani yaji a unguwar da muke zaune. Ashe tun bayan sati biyu da kawo mu wanan gidan da yayi tafiya ya kamashi zuwa can ma,aikatan su don haka baya kasan ga baki daya shi . Lokacin kan mu gaba dayan su muna dauka sun fita zancen mune yasa bamuji duriyan ko mutum dayan su ba kuma. Gashi yasan a wanan lokacin abincin daya aje muna ya kare ga karatu yasan mun bar zancen shi ke nan yake tunane. Yayi mamakin da mahaifin shi tun bayan tafiyan mu bai sake jin ya tuntubeshi da wani zancen mu ba kuma idan sunyi waya dashi. Hakama mommy mahaifiyar su ba wanda ke tambayan shi ko yana da labarin mu tun da muka tafi sai hakan yake bashi mamaki sosai. Allah ya gani yana jin tausayin wanan a halin sosai a zuciyan shi don yana ganin an danne muna hakkin mu sosai saboda son zuciya da tsoron wani yasa an kasa aiwatar da komai a kan hakan. Ciwo nayi sosai da faruwan hakan sai daga baya nake fadawa umma abinda ya faru dani hankalin umma din ya tashi sosai don haka ta kwashe sai wurin wani malamin yarbawa da ta dade da sani a tsohon uguwar mu din . Saidai mun samu tsohon yanzu ya dan tsufa sosai don haka ba lalai bane ya iya sheda ta sosai amma duk da hakan mun samu ya taimaka. A cikin bayanin shi naji yana kiran mamiwota wai ni din aljannun ruwa nake tare dasu don haka yana da wuya aci galaba a kaina ai. Sai gashi yana fadawa umma cewa mutanen da dukiyan mu yake wajen su har sukai sanadiyan zuwan mu nan yanzu wasun su susan muna raye hankalin su ya dan daga da hakan. Jin ya fara irin wanan zancen na tashi na fice daga wurin zuwa dan waje kadan na zauna nan na dinga ganin irin manyan motocin da ake parkerwa a wajen masu kudi suna zuwa neman isimi na kuma gane ba shi kadai ke aiki a wajen ba. Duk na gaji da zama ina jiran umma can kamar ance in dago idona wurin wata mota dake tsaye a wajen tun zuwan mu sai idona ya hango min wanda ban zata ba a lokacin. Yana waya ya bada baya bai kallon gefen da nake zaune din haka yasa na mike da sauri a daidai lokacin da umma da Amir suka fito daga dan wurin da nake zaton mutumin babalawo ne shi ba Alfa bane kamar yadda umma tace dashi da zamu zo. Dan karamin hijjab din dake kaina naja na gyara rufe fuskana da kyau dashi ta yadda ba za a gane ko wacece ba a lokacin gashi dole sai munbi inda yake zamu wuce. Allah Allah nakeyi inga mun bar wajen don yanzu gaba daya ban son in kara ganin wani wanda na sani a wanan bangaren na mahaifan mu ga baki daya naji kawai na tsanesu ma a lokacin. Bin mu yayi da kallon mamaki har wanda suke tare ya fito suka shiga mota hanyar da mukabi suka biyo ya hangomu mun tare mota zamu shiga. Cema driver yayi ya bi bayan mu a hankali yaga inda zamu har suka biyo mu har gidan sai da sukaga umma tasa ke ta bude kofan ta kuma rike min hannu mun shiga suka bar unguwan namu. Amma abinda mamaki yace a fili ga wanda suke tare din a kaduna ya barmu yanzun kuma ya ganmu a nan lagos har da gida me hakan ke nufi ke nan. Zancen su da mahaifiyar shine ya dawo mashi a rai da tace mudin yayan abokin kawun shi ne dake lagos yayi tafiya mai dadewa yasa ya kwaso mu zuwa gidan daddy din kamar yadda daddy ya fada mata a lokacin. Ke nan mahaifin namu ya dawo ne a yanzu ko kuwa kodai wani plan ne hakan dama aka shirya ne sai yaji hankalin shi sam bai kwanta ba ga zancen mu din haka kawai yaji yana son yasan wani abu game damu lokacin. Bayan kwana biyu shi kadai yazo ya hango umma zaune a shagon ta tana sayar da kayan sanyi da rechage card ya dan dade tsaye kafin yaja motar shi ya tafi. A wata yamma kuma weekend ne haka kawai yaji ai ya biyo titin namu ni ya fara hangowa tsaye da yaro a hannu na na fito daga shagon mu din yaji gaban shi ya fadi. Yaron wata nerboug din muce na dauka don ina da son yara zata fita zuwa kasuwa ta bar yaron a wurin mu shine yake kuka na daukeshi a lokacin ya ganmu tare da yaron. Tambayan kanshi yayi akan me ya damu da mutanen nan ne hakane kamar wasu yan uwan shi na jini ko yan uwan nasa ma yaushe rabon shi dasu yanzu. Nikan zaman gida yayi yawa jiki bai saba hakan ba don dole kuma in dinga fita mu samu abinda zai kara tallafa muna ga karatun da mukeyi mai tsada don su can ba free education sai ka biya kudin komai. Haka yasa na samu aikin dare yamma in taso goma na dare a wani babban shago dake unguwar mu din baida nisa da gidan mu sosai. Idan na dawo daga school zan saka uniform din aikin wajen in tafi aiki sai dare nake dawowa sai dai aikin ya fara fita min rai saboda wani lokaci koda zan dawo hanya ba mutane da yawa sosai. Shiyasa tun wanan abinda ya faru dani yanzu sai nake jin tsoron hawan Nape idan dare yayi yasa nake sin barin aiki a shagon. Manyan mutane yan kwalisa masu ji da kansu maza da mata ke zuwa sayayya wanan shagon da nake aiki din wasu suyi muna alheri wasu kuma musha disgawa a wajen su duk da muma dai neman kudine ya kawomu shagon ba wani abu ba. Gashi duk wanda ke shagon sai sun maka interview sun ga idan ka cancanci aiki dasu zasu daukeka aiki a wurin don tasare tsareb su saidai akwai kudi sosai yasa mutane ke neman aiki a wurin suyi. Nima wata kawata yar school din muce ta kaini wurin da wasa sai ko suka daukeni gashi suna jin dadin aiki dani don ina jin yaruka kala kala a bakina don yawon gidan haya da mukayi a baya tun ina karama. Yau ma duk da nagaji don mun dan wahala a makaranta hakan baisa na zauna na hutawa rayuwana ba a gida . A gurguje na shirya zuwa aurin aikin duk da nasan na makara a lokacin zasu iya korana inyi hasaran kudin ranan ke nan. Don sai sun cire a karshen wata a cikin abinda suke bamu din yasa ban son missing din ranan zuwa aikin don kada dan abinda suke bamu ya ragu. Tun a kofa ganin ogan gaba daya a waje yasa na sha jinin jikina duk da yana magana da wani hakan bai hana in tsaya in gaida shi ba a wurin. Ina fadin good day sir har ya amsa cikin daga hannu na dan wuce sai kuma naji yace dani wait wani lokaci kika zo aiki ke nan ? Sorry sir na samu dealy ne daga school ban dawo da wuri ba sai yanzu na dawo na kara fadan sorry sir ina dukar da kai. Sai ki koma yau baki da aiki ke nan ya fada yana kawar da kanshi gefe daya ka barta ta shiga tunda ta bada uzurin ta . Kai na dago na kalli wanda ke maganan farine sosai mai zubin iyamurai ga dan saje a fuskan shi yana saye a cikin suit baka data karbi jikin shi. Saidai kana kallon shi kasan boko ya ratsa jikin shi da yawa haka wayewa sai yake min zubi da yanayin wani wanda na sani. Ga shekaru kuma baikai ya Abubakar ba ko ya mustapha saidai do jin dadi da samun wuri zai iya kaisu ga gani idan mutum yayi mashi kallon tsoro. Thank u sir na fada ba tare dana tsaya jiran komai ba nashige daga ciki na barsu a wurin a gurguje na fara aikina don na samu har an kawo wata ta a madadina ta tsare bangaren da nake aikin ko. Tare suka shigo da ogan mu suna zagayawa na kara gaidasu ban kula ba ko sun karba min don dai naci gaba da zagaya wurin da nake din ina duban masu shige da fice a gefen wurin. Sun danyi tako baikai biyu ba wayan shine yayi kara yaja ya tsaya yana daukan wayan tare da fadin hello Didi, Tun suna magana da turanci har suka koma kamar larabci daga inda nake zaune na saka earpieces a kunne na ina bitan karatuna don ban yarda na yarda karatun dana samu a zaman mu na kaduna ba. Na hango wasu sun zo part dina suna duba kayan zasu tafi basu mayar da kyau ba nake fadin zaku jawa mutane hasara ga banza kuma ba saye zakuyi ba ku kuja min matsala ga mutanen nan da basu san kaddara ba. Ya juyo ya tsaya yana kallona a cikin mamaki na gyara kayan ina dan kara kakabesu na koma inda muke zama na zauna kafin custurmers su shigo wurin ga hasken a ko ina ya haske wurin ga baki daya ba zakace darene ba a lokacin do haka kalan wurin ya bada ma,ana sosai. Mun saba ganin irin su yan kwalisa suna shigowa shagon don haka ban damu da isan koshi waye ba na dai ganshi da oga suna zagayawa haka yasa na fahinci yana da muhinmanci a wurin ogan namu.q Har kusan lokacin tashi mun daga aikin suna tare da oga da sauran manyan shagon a lokacin ne na fito da abayana daga cikin jakkata na dora saman jan rigan dake da tabarin shagon da bakin bujen dake jikina. Nayi rolling din kaina da gyalen kayan ina irin wanan shigarne don kare mutuncina don ban yarda in fita hakana idan zan koma gida saboda bata garin dake akwai a garin. Duk dadewan shagon shine goma da rabi zuwa sha dayan dare mu mata goman ne namu sai dai wa yanda ke kusa da shago din ke zama har a rufe shagon su tafi. Jakkana na dauka inda muke ajewa ina fadin good night oga da cewa manyan mu dake wurin suka amsa min da cewa night miss Sahiba na fito ina gyara dan kwalin abayan da yake dan sabulowa a jikin nawa. Sai lokacin naga hadarin daya game gari yayi bakikirin yana shirin tasowa da iska ban damu da wa yanda ke haraban ba nake fadin ya subbahanallah Allah ka ceceni na samu abin hawa ya karasa dani gida kafin ruwan nan ya fado. Na dan tsaya na minti biyu lokacin har an fara iska a garin kadan kadan yasa na fara dan takawa da kafa don kada ruwan ya tsayar dani a wurin. Motocin dake fitowa nake dan waige kafin wata motar ubansu taja ta tsaya a gabana jan danjan bayanta yana dan haskawa kadan kadan har na tako ina kokarin wuce ta . Glass din motan aka zuge lokaci guda naji wani murya na fadin can i help you don akwai hadari ruwa zai iya fadowa ko wani lokaci a yanzu. Na duba da kyau na gane wanan guy din ne dana gani da shugaban shagon mu yake min magana no zan iya takawa ba nisa sosai na fada ina ci gaba da tafiya. Kada kiji tsorona niba mugu bane ya fada a cikin hausan shi pure saidai hausan akwai dan bambamci dana yan kaduna dana kara gwanewa yanzu dashi. Mamakine ya kamani jin hausa radau a bakin shi yasa naja na tsaya ina bashi hakkuri tare da fadin. Ba haka nake nufi ba don kada in bata ma lokaci na fadi hakan banda nisa sosai da nan shiyasa nace hakan . Kizo ki shiga na saukeki kada ruwa ya tsare mu banyi mussu ba ya bude gaban motan na shiga ya subbahanallah na fada a raina. Kamshi da sanyi ne sukai min maraba a motan sai kuma karatun malamina dan india ne ko balarabe dake kira,a a cikin motan. Saidana zauna nace nagode na gyara zama na takure a wuri daya kamar a tsorace idan ka ganni a lokacin don nasan ranan na shiga motan maya kan. Bai juyo ko sau daya ya kalli inda nake zaune ba sai tukin shi yakeyi a hankali don ina shiga na fada mai layin da zan tafi yace nayi mai kwatance idan mukai wurin. Layin nace ga wurin ko a nan ma ka saukeni ba nisa damu zan iya karasawa yace gidan nakune bakyason a gani nayi shiru har kofan gida ya saukeni ina faman yi mashi godiya yaja motarshi ba tare da amsa min ba ya tafi. Umma suna waje suna hada kaya don sai na dawo nakan hada mu rufe shagon mu shiga gida zuwa sha daya don masu zuwa sayen kayan sanyi a lokacin. Tun fitowa na daga motan umma ke bina da kallo har na karaso inda suke nagaidasu sukai min sannu da zuwa na karbi kayan dake hannun umma din don sun gama hada komai muka fara tafiya zamu shiga ciki. Naji umma tace dani ina kika samu mai motar nan daya saukeki yanzu na juyo da sauri ina fadin wallahi umma ban san shi ba taimaka min yayi kada ruwan nan ya dukeni . Sahiba kardai ince kin fara kula maza ne a rayuwan ki wani irin juyowa nayi na dakatar da tafiyan ina kallon umma din kafin incw maza kuma umma ? Wallahi nafada maki nansan shiba ban kuma taba ganin sa ba sai yau din nan kuma banda gaisuwa da godiya ba abinda ya hadani dashi. ZAINAB IDRIS MAKAWA ANA DARA GA , , , , , , , , 3️⃣8️⃣ BY, , , , , ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , , BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AL MUDHELL, , , , , , , ONLINE PAID NOVEL YAR UWA KI BIYA DON ALLAH KAFIN KI KARANTA NA FADA NA FITAR DA HAKKIN RASHIN SANIN HAKAN, , , , , , Ni kaina yau dana tsaya a gaban mirrow nasan kayan dana saka sun karbeni sosai don yadda suka mayar dani wata preety girl kamar wata cerlebrity din lagos dani saidai inda na rago su na dora dan hijab dina da nake sakawa iya kafada na. Turare idan an min biya shagon nan nake sayen oud a wajen don na koyo shafa turare zamana na kaduna idan ina kusa suka murza zasu miko min in shafa nima a lokacin. Rigan bakace har kasa ta sauka min sai dairin mai fitar da sharp din nan ce ya fitar min da surana fili na ya mace sosai duk da ban damu da hakan ba tunda a ganina ai na suturta jikina ke nan ni ina shiga ta musulunci ke nan a can. Jakkana na ratayo nazo nayiwa umma dake kokarin fita ta bude shago sallama ni kuma na leka dakin Amar na ce dashi mu tafi. Tare dashi muke jerawa mu shiga mota ya sauka a hanya ni kuma na wuce zuwa nawa wurin mun sauke shi ya taka ya dauki hanya muka tafi ina bayan Nape kamar ance dani in dago kai mukai arba da dan gwaggo hari a inda go slow ya tsare mu . Da sauri na kawar da kaina kamar ban ganshi ba lokacin, don wani irin faduwan da naji ga tsoro ya idda kamani sosai da ganin shi din danayi a wurin ina Allah Allah kada shima ya ganni . Duk da nasan ganin shi alheri ne a garemu saidai yanzu da nasan ko shi waye bana son haduwan mu dashi a yanzu gaskiya. Don haduwa zai iya saka ya tunawa mutanen kaduna damu har su dawo su nememu abinda kuma ban so ya faru a gare mu ke nan yanzu gaskiya. Don nafi son sai na fahinci meye dalilin su na sharemu da kowan su yayi don daddy ma bai ko gari da muka bar kaduna din kuma bai nememu ba yanzun da ya dawo. Allah ya taimake ni aka bayar da hannu motocin suka fara tafiya don barin wurin nace wa driver keken da nake yai sauri. Na sauka ina mikawa mai keke kudi naji ance a bayana hello ban juya ba don ganin dawa meshi ke magana balle insan koda ni yake maganan. Na juya zai wuce aka kara fadin hello miss jin hakan yasa na juyo don ganin mai maganan motar suce ta dazun da muka hadu a wurin yanzun ma a bayan mu ashe wani kallo kada ka raina ni nayiwa driver din . My oga de talk to u, wanda ke wajen yace min wani kallo na watsa mai kafin in ce who be ur oga ? Go tellam say , me i don't have business with him, nd i no be those gurl dey are chassing on d street sha . Daga haka na juya na wuce ban yarda na daga kai ko ido na kalli inda shi yake zaune ba din kada yasani zuwan dole wurin. Da dan sauri na bacewa ganin su na shege inda muke daukan lecture na nemi wuri na zauna abina ina dakon malami ya shigo. Har malamin ya shigo ina zaune ina tunanen me yake nema a wurinane wai da yake bibiyata a yanzu don bai rasa sanin dililin da yasa aka jafar damu nan inda muke yanzu. Ina murna na huta tunda nayi masu haka ashe ban huta dashi don kuwa ina sauka bus din school da nakan biyo mu sauka a jaction sai ga motar na sake gani kuma a wurin again. Inda Allah ya taimakeni driver ne kawai shi kadai a motar ba maigidan nasa madam my oga send me to pick you, i dey follow you since u no see me. Wani banza kallo na watsa mai ban tsaya bi ta kanshi ba na nufi wurin da yan nape ke tsayi suna shiga da mutane cikin unguwa direct nace ya wuce dani shagon da nake tsare kaya son kada inje gida ya bini har can. Exacuse na basu na rashin sako uniform dina kuma suka daukan min hakan basu koreni ba a ranan nayu mamakin hakan don basu yarda a zo masu aiki hakn. Na samu an kawo masu kaya shagon conteners suna ta sauke masu haja sai na dauka don shine suka barni na zauna haka ranan dai munsha aiki ga kyauta kuma da muka samu sai sha daya saura muka samu komawa gida da taimakon motan shagon daya kai kowan mu gida a lokacin. Nayi duba a hanyar banga wanan mai bibiyana din ba waishi driver don haka na sake raina na isa gida lafiya da yar jakar dake dauke a hannu na na kayan da aka bamu a wurin. Da shigana gida na samu umma a falo tana jiran dawowana hankali tashe nayi sallama ina cire takalmana tare da fadin umma na dawo sannu da gida umma. Ina kika tsaya yau haka sahiba umma ta tambaya rai bace tana kallona a cikin daure fuskanta gareni dama nasan hakan zai faru nace wallahi umma daga can kada in makara shago na tafi don nasan idan na dawo gida zan iya makara kuma basa son ana makara haka su. Amma ai ya kamata ki sanar dani kafin ki fita ba wai ki barmu haka hankali tashe ba tunda baki saba yin hakan ba. A dan marairaice nace umma kiyi hakkuri don Allah ba zan sake ba insha Allahu tayi shiru tana kawar da kai gefe daya. Anty ekabbo Amar ya fada na dan kalleshi nace dashi how are u Amar ya amsa da fine yana gyara kwanciya inda yake yana karatu ya zube littafi a gaban shi. Ledan shango da na shigo dasu na zube a gaban umma kafin na mike zan shiga dakina in cire kayan jikina. Muryan umma ke fadin yau yaron nan yazo gidan nan bakya nan da sauri na juyo ina fadin wani yaro ke nan umma ? Dan wajen hjy harira kanwar daddy ku na kaduna kece kika nuna masa gidan nan har yazo ? Umma wai ya mustapha kike nufin yazo gidan nan ko wa don dai ban taba nunawa kowa gidan nam ba wallahi ko abokan karatuna kuwa. Shi din nake nufi mana diya nawa kega hjy harira din idan bashi kadai ba shi nake nufin yazo nan muke zaune dashi a falon nan ya dan jima nan kafin ya tafi. Dawowa nayi na zauna nayi shiru ina dan tunane kafin can in dago kai ina fadin umma tun ranan da mukaje wurin wanan Alfa din idan kin tuna munga wani mota baka kusa da itaciyar dake wurin da mutane tsaye suna magana . To sune muka gani a wirin kuma ranan ce na fara ganin shi tun dawowan mu garin nan a ranan na fara ganin shi sai kuma yau da hold up ya tareni hanya mm a gansu suka bini har school din mu ban kuma tsaya ba. Don gaba daya bana son kowa daga wanan bangaren a yanzu gaskiya da kuma irin kashedin da yai min kada na kara nuna nasan shi a ko ina . Shi din ya fadi hakan nace kwarai umma shiya fada min da bakin shi ranan da a kai bukin dinnan diyan gwaggo Asiya din nan . Oh Allah kai kadai kasan dalilin halittomu a cikin wa yan nan mutanen da suke yan uwa a garemu kuma basu rike zumuncin nasu ba a kan mu. Ban iya ba umma amsan komai ba illa dai nayi shiru ina nazari na dade zaune a wurin kafin in mike zuwa ciki na cire kayan jikina nayi wanka. Ban fito ba saida nayi sallah na saka kayan barcina wando da riga sai bakin hula a kaina na cusa gashina aciki na dora zani a sama na fito kitchen na shiga na debo abinci na fito. Cibi biyu nayi sai na kaaa cin abincin saboda tunanen daya dameni a lokacin muryan ummace ke fadin yace zai dawo weekend don haka zaku hadu dashi ke nan kuma ai Saidai idan son samune umma mubar gidan nan kafin weekend din ko don ni yanzu tsoro mutanen nan suke ban baki dayan su . Gara mu kara gaba can inda babu wanda ya san mu, mu zauna kuma zai fi muna don na fahinci gaba dayan su ba kaunan mu sukeyi ba. Kallon da umma keyi mun saina dauka cewa shawarana ya karbu a zuciyarta na har zanci gaba da fadin kinga ai idan sun, , , , , Ashe har yanzu baki da wayau sahiba ban sani ba na dauki wayau na dora maki ashe ke har yanzu da sauran ki ban sani ba To bari kiji sahiba daga wanan gidn babu inda zan kara tafiya kuma sai dai yanzu duk abinda zai faru damu ya faru. Boyon ya isa hakana don na dauka yanzu lokaci ya kusa da zamu baiya a garesu su sanda sanin muna raye a duniya. Bukata na kawai dama ki samu karatun da idon ki zai bude ko kiyi wayau da zaki iya tunkaran su su gane koke waye a cikin su. Har idan ma basu nememu ba muda kan mu zamu nemesu nan gaba idan lokacin hakan yayi a garemu kedai kawai ki kara maida hankali kan karatun ki a yanzu kiyi hankalin da zaki iya tunkaran su akan hakkin ku. Zaman mu a nan shine rufin asirin mu don yanzu idan kin kula bana cikin fargaba irin baya daku haka shi kanshi wanda ya kawo mu wanan wurin nasan yayi hakan ne a bisa wani shiri da yake muna nan gaba . Bawai haka kawai ya kawomu nan ya zubemu ba dole da akwai shirin da yakeyi shima da zai samu mafita a cikin maganan nan. Kuma ina sane daya dauke mune daga can ya gudo damu nan da yake ganin shine maboya a garemu don nan din kusan zagaye muke da gidajen security duk unguwan nan idan kin kula da hakan. Dan nisawa nayi kafin na runtse idanuwana na dan lokaci Allah ya gani duk da tunanen umma na nufin haka ni dai sai hakan bai mun gaskiya. Abincin na dan fara cakula da cibi ina laiwa bakina badon dadi ba ko dandanon shi sai dai kawai don in kawar da yunwar dake damuna a lokaci. Banda aiki ranan Saturday amma hakan na kirkirowa kaina fita tun safe na shirya nacewa umma akwai screening da za ai muna a shagon da nake aiki . Kallona umma tayi tana fadin wani screening zaki kuma yanzu keda kikace zaki bar shagon wahala yai maki yawa yanzu zaki daina aiki dasu. Amma ai umma ban barsu ba tukun na kinga dole in je ayi min don sai karshen shekara nake son na aje dama lokacin sun bamu bonazan kaya yadda muma zamuci riban mu dasu. Allah ya tsare umma tayi min na fita Allah ya gani banyi niyar zuwa shagon ba amma haka na daure na fita duk wanda ya ganni sai yayi mamakin ganina a lkacin haka na daure nayi signing na fara aiki kamar yadda muka saba dasu ban damu da kallon mamakin da sauran ke min ba don ba fuskan da wani zai iya tambaya don ko matan ma,aikatan daga gaisuwa ba abinda ke hadani dasu kuma. Ni sam a rayuwana ban yarda da abokiya ba haka kuma bana sakin fuskan da zaka ga damana har ka samu shiga a wurina kowa ban yarda dashi ba haka Allah yayi min rayuwana ni. Wasu mata da mijine hausawa ta shigan su na gane hakan don sunyi irin shiga na arewa har yayayen su biyu suka zo part din kayan kamshi dana gyaran jikin mata. Matar ta daga wani set din man shafi take fadin su dauke shi mijin yace a cikin hausa nifa kin san bana son man da ke saka mutum haske ko ya canza mai kalan jikin shi. Matar tace dashi amm kuma ai naga wanan din na larabawa ne nasan zaiyi kamshi bawau don fari na daukeshi ba mijin ya sake fadin ki dai duba wani zaifi. Lah yayana daka barta ta dauka tunda tana so wanan baya saka haske sai dai ya gyara mata natural skin din ta zai kara kyau ne kawai nan babu kayan karin haske gasu can daga baya ku kun baro wurin wacan yarinyar. Bayani nake masu amma su sun tsaya suna kare min kallo a cikin mamaki har na kare masu bayani suna tsaye sororo suna kare min kallo. Ikon Allah matar ta fada tana murmushi yanzu ke din nan ashe kin iya hausa a bakin ki haka radau kamar jakar kano. Amma dai ke haihuwan arewace ko nace ni bafulatanan jalingo ce saidai a kaduna aka haifeni na kuma tashi a lagos kamar yadda kike gani na yanzu. Ta dan sake dan murmushi har hakoran makkan ta na gold suka dan bayana fili tana fadin aiko ga kama nan mun gani a zahiri da fulani. Amma ke bakuwace a shagon nan mijin ya fada daga bayan ta yana rike da hannun yaran su , nace a,a na dan dade a nan kuwa. Saidai da yamma nake aiki dasu na tashi da dare don ina zuwa makaranta da rana mijin ya dan taka ya barmu a wurin tana dan dariya kamar taga wata yar uwanta na gida. Mu muna nan Apapa ne zaune kusa da Olamide eyes center sai na danyi murmushi don Olamide yana bayan mu kadan nace kinga kuwa muma a ta gaban shi muke zaune ai. Zuwan wasu custemers yasa na barta na dan tafi wurin su ina masu bayani baisa matar nan ta barni ba sai ta tsaya tana jiran in gama dasu. Ban gama da wuri ba har mijin ya kirata suka nufi wani wurin na fita zancen su nikan na kama aukin gabana na saka ido ga kaya tare da jagoran masu zuwa sayan kaya kamar yadda akeyi. Na dauka sun tafi sai gasu sun dawo inda nake matar ke fadin kinga yar uwa har zamu tafi ban san sunan ki ba nace mu dawo don Allah na tambaye ki. Sunana Sahiba amma Fatima nake da Sahiba din ake kirana har a gida gaskiya kina da suna mai kyau shigowan wani ya dauke ma mijin ta hankali har ya barmu mukai musayan lamba da ita da kwatancen gidajen mu sai gasu sun tako zuwa inda muke daga bayan mu ana fadin. Kai madam yau kece da kanki kika shigo shagon mu ta waiga tana dan murmushi tare da fadin wallahi oga Sha,aban . Nice fa yau a shagon naku mai a lbarka nace bari dai yau na biyo shi nazo naga shagon naku don oga saidai yazo shi yana ban labarin girman shagon nan Good day sir na fada daga bayan matan inda nake tsaye na juya ban jira amsan shi ba nasa kai na bar wurin ga baki daya. Wani irin faduwan gaba nake ji wanan ne karo na biyu da muke haduwa dashi a shagon sai kuma ranan nasan ainihin masu wanan katon shagon haka. Zasu tafi wanan matar ta kara magana akaina don naga duk sun juyo gaba dayan su lokaci guda sai kuma sukaci gaba da magana don ina dan nisa dasu banji me suke fada ba a lokacin. Da hannu ta kirani nazo da sauri wanan karon don ganin su tare da wanda nake zaton a yanzu sune masu shagon nan da muke aiki a cikin sa shine kuma wanda ya kaini gida ranan idan baki manta ba don yanzu ankai wata shidda sai ranan kuma na sake ganin shi na kuma shedashi. Take care of her ya fada lokacin da suka dan fara tafiya da mijin matar sai matar tace dashi wanan ma ai kusan ta fika iya hausa zance. Yayi murmushi sukaci gaba da tafiya da gani suna wani magana ne mai muhinmanci a lokacin don yadda naga suna zancen daga nisa. Kin gashi can shike da wanan shagon a waje yake zama don rayuwan shi gaba daya a can yayi shi . Yadda ma,aruf ke fada min sunyi karatu tare dashi aminin shine sosai suna karatu saidai kasancewan shi dan masu hali suna gama karatu ya fara harkan business shi kuma ya fara aikin gwaunati a nan kasan. Shidin dan wani shararen dan kasuwa ne dan arewa saidai mahaifiyar shi ta kasance yar garin nan ne ita don haka yake ruwa biyu shi. Yana zama a kasashen labawa ne shi can yake harkokin rayuwan shi sai dai a yanzu naji Ma,aruf na fadin yana son ya dawo nan gida Nageria da zamane. Wanda nasan mawuyacin abune ya iya hakan Allah sarki azuciyana kuma nace wai fadi ba,a tambayeki ba ke nan mata da bakin zuba haka sai kace wata aku. Ni a tsarina ban son yawan surutu gaskiya haka Allah yayi min rayuwa na hannuna naji ta rike tana fadin zo mu zaga ki tayani zaben kaya dama ya hanani zabe shi kuma ba mace ba yar uwana. Ina mamakin wasu abin komai tsadan su zanga ta dauki biyu har dai takai mun gama a daidai lokacin da suma suka dan fito mijin na fadin idan ta gama ta sameshi waje. Sai bayan anyi komai an saka kayan a cikin leda ne kawai naga ta miko min dayan ledan tana fadin wanan nakine kanwata don yau kin debe min kewa sosai wallahi. Ga abokan aikina sai bina da kallin mamaki sukeyi har dai lokacin da suka tafi na dawo cikin shagon naci gaba da harkokina ban dawo gida ba sai dare lokacin dana saba tasowa daga wurin aikin na shigo gida. Umma har sun kwashe sun shiga ciki nayi mamakin hakan sai kuma nayi tunanen saboda sanyin da akayi ranan ne yasa ta kwashe da wuri haka zuwa ciki. Da kayana niki niki da matar nan ta saya min na shiga gida da sallamana umma na zaune a falo da gani hankalin ta a tashe yake. Ledan dake hannu na tabi da kallon har na aje ina fadin umma sannu da gida na juya wurin Amar ina fadin kai how far ya kake ? Ke gidan ubanwa kika shiga haka umma ta fada a cikin wani murya da ban san tana dashi ba nima dan tsorata nayi ina fadin umma na fada maki shago zan tafi ai dazun da safe. ZAINAB IDRIS MAKAWA ANA DARA GA, , , , , , , , 3️⃣9️⃣ BY, , , , , , , , , , , , , BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AS SAMI,E ONLINE PAID NOVEL YAR UWA KI BIYA KAFIN KI KARANTA DON ALLAH KADA KI SHIGA HAKKIN WANI CIKIN RASHIN SANI, , , , , , , , Sahiba yaushe kika fara karya hakane har yaushe kika zama haka ban sani ba kin maishe ni karamar yarinya ko me a yanzu sahiba ? Innalillahi na ambata a fili tare da kallon umma ina nuna kaina da hannu kafin na fara kada kai a hankali ina fadin. Wa iyazu billah umma kada ki soma don Allah kada ki fara zargina da irin hakan har idan zan iya aikata wani abin assha a duniyan nan dana fara aikatawa tun zamanin da nake yawon talla. Amma umma sai gashi yau ke da bakin ki kike kokorin furta abinda ban taba tunanen yinsa ba a rayuwana ba ko wani ya fadi hakan a gabakin umma ke mai iya shedatace ga hakan duk da ina yarki kuwa. Amma ba komai umma Allah ne shedana tun safe ina shago don neman kudin da za a ba Amar ranan monday don sunce shine dateline din da suka diba a kai kudin school fees din yasa nayi double din aikina a yau da gobe insha Allah. Amma umma don Allah kiyi hakkuri haka ba zai sake faruwa insha Allah sai na zube kasa alaman bata hakkuri hawaye na zubo min a idona. Ki shiga umma ta fadi na mike gwiwa ba lakka na nufi hanyar dakina wanka nayi ban fito ba duk ko da uban yuwa da nake ji a lokacin . Tunda na watsa ruwa ina wanka ina kuka na fito nayi sallah shafa,i da wutir nabi gado hakana na kwanta ban fito ba ranan a dakina na kwana banje na lakewa umma ba yadda na saba. Itace ma data jini shiru ta leko dakin ta samu na kwanta duk da lokacin banyi barci ba sai na lafe kamar ina barci zuciyata tana cunkushe da bacin rai . Ba fushi nake da umma ba sai abinda take zargina dashine yake damuna don ni a ganina ban taba tsayawa har wani namiji ya bude bakin shi ya furta min kalman so ba balle har in yarda in bishi yawon banza yadda take zargin na fara a yanzu. Wani tunane nayi dayasa na dan mike zaune kafin in koma na kwanta don bayanin a yanzu baida rana a gareni wurin umma din tunda har ra riga da ta saka zargina a ranta. Ba komai na tuna ba sai ledan kayan da matar nan mai suna zakiya ta saya min a shagon mu wanda na shigo dasu niki niki don umma bata saba ganin na dawo haka da kaya a hannuna ba gashi kuma na dade yau a wajen dole nasan damuwa ne har ya sakata fara zargina din a lokacin da ganin wanan kayan kuma dana shigo dasu din a lokacin. Da yake barci barowon gaskene duk halin da kake ciki sai yasan dabaran daya sace ka kona yan mintuna ne ko awani shine kadai yaceni a ranan don irin yadda zuciyana take ciki a wanan ranan. Washegari lahadi nayi sallah na idar na fara gyara dakina na fito na shiga kitchen don na dora ruwan zafi saman gas. Ja nayi na tsaya ina bin ko ina da kallo don na fahinci akwai sauyi a cikin kitchen din namu a lokacin na kara bude dan store din dake manne da kitchen din buhuhunan shikafane har biya gasu tumatur da jarkan mai biyu dana manya sai wasu irin doya manya manya a wurin da dankalin irish azube kasa. Mamakine ya kamani na ganin hakan saina fara tunanen ko ya Abubakar ne ya dawo garemu kuma yanzun. A hankali na rufo store din kafin na fito na fara gyara gida har lokacin dana gama banji motsin umma ba sai dai dakinta yana bude na juya na shiga dakin da sallama. Umma na zaune tana jan tasbaha a hannun ta na tsuguna yadda muke gaida ita na gaida ita da kwana kai ta gyada na mike na dan gyaro dakin na koma kitchen ban daki wani lokaci ba na hada muna abincin na gyara kitchen din na fito. Dakina na koma nayi wanka na fito na shirya cikin wani dogon rigan nealon idan na sakasu haka na nufin a gida zan zauna ke nan ranan bazan fita ba. Na koma gado na kwanta sai ga Amar yayi sallama a dakin don shima yanzu a dakin shi ya koma kwana don dan girman daya kara yi yanzu. Da littafi a hannuna na mike saman gado ina karatu ya shigo na dan dago kai ina kallon shi kafin in dan sake murmushi gefen fuskana a lokacin. Fadawa yayi saman gadon dakin yana fadin anty na naga tun jiya kina fushi da maganan da umma tayi itama umma din bayan tayi kuma daga baya naga ta damu da hakan sosai kuma. Bana fushi da umma kokai Amar ina dai damuwa ne da yanzu umma ta fara zargin zan iya aikata wani abu mara kyau a rayuwana bayan nasan koni wacece a cikin dangi mu. Idan ban yi abinda zai daga martaban mahaifin mu ba ba zanyi wanda zai sa ayi tir damu ba a rayuwan yan uwan mu . Fatana da butina Amar shine kullun inga na tsaya karatun mu yaci gaba inda zamu iya tallafawa kanmu basai wani daga dangi ya kara taimakon mu ba kuma mun koma abin tausayi. A yanzu na daina ganin laifjn kowa da nake gani a baya don yin hakan a garemu ya kara koyar damu abubuwa masu muhinmanci a rayuwan mu yanzu. Ya Abubakar yayi muna komai shima kuma yayi hakan ne don ya tsira da rayuwan shi dana iyayyen har da yan uwan shi bai fada muna bane amma yanzu na gano manufan shi nayin haka garemu. Kin daina ganin laifin shi ke nan a yanzu yaron ya tambayeni nace kwarai kuwa Amar don hakan yasa na kara gane ko mu din su waye a yanzu a cikin su don zama a cikin su zai iya sa mu shagala mu manta da komu suwaye amma kada ka damu lokaci na zuwa da komai zai zama tarihi a garemu da yardan ubangji. Jiya wanan dayan mutumin yazo gidan nan bai sakeki ba kuma duk dana gane wa yake nufi amma bai hana nani tambayan shi ba ko waye yazo din. Mai bamu kyautan kudin da babu mai bamu irin shi din nan jiyama ya baku kyautan ke nan na tambaye shi. A, a bai bamu kudi ba sai dai ai kinga kitchen din mu cike da kayan abinci ko to shine yasaya yazo muna dashi . Shiru nayi ina tunanen shi kuma dame yazo muna yake kokarin shiga cikin rayuwan mu a yanzu kuma haka don dole sai akwai wani bukata da zai sa ya shigo rayuwan mu din. Don yanzu nasa mutane basu shiga rayuwan mutum duk halin kuncin da yake ciki sai da wani dalili nasu na daban can. To yanzu shi din dame yazo muna ko shima din yana da wani falili nasa na daban ne da yake son aiwatarwa a kammu kuma na tabayi kaina ko kuma shidin ma maganan mahaifimu ya shafesu ne suma yake son yin amfani da dama hakan wurin jawo mu jikin shi yanzu. Amma naga sun dan dade da umma suna magana da ban san abinda suka fada ba Amar ya fada daga gefena shiya dawo dani daga zurfin tunanen dana shiga lokacin. Maganan su ce ta manya na fada don na kawar da zancen ya kara fadin monday din zan shiga school din ke nan ya tambaya yana kallon fuskana lokacin don son jin amsan da zan bashi. Zaka shiga insha Allah zanje na biya ma kudin da komai yadda ya dace in Allah ya yarda ranan monday din kamar yadda nake so Amar bana son karatun ka ya samu targada ko kadan. Da ace yauma na fita zuwa aikine da zan hada kudin gaba daya don in sun ban wanda nayi da rana tare dasu a hannu sai na hada dana jiya da dan kudin dake hannu zasu kai a biya ma sin amma yanzu zan kai masu abinda ya samu ko zasu yarda ka zauna dasu. Yay ba zaki fita ba ke nan ya tambayeni nace umma bata so don haka ba zan fita ba kayi hakkuri Allah zai kawo muna mafita da yardan Allah. Mikewa yayi ya fita ba tare da yayi min magana ba na bishi da kallo ina mamakin hakan har ya karasa fita na juya na mayar da idona kan takardan dake hannu na lokacin. Ba a wani dauki lokaci mai tsawo ba sai gasu tare da umma sunyi sallama a dakin na amsa umma ta samu wuri a gefe ta zauna tare da kiran sunana na dago da sauri ina kallonta. Itama kallona tayi ido cikin ido sai na dukar da nawa idon kasa da sauri kafin inji tace Sahiba duk da kinman bayani na gamsu da hakan kin kuma saura da zancen ne a zuciyar ki har yanzu don Amar ya sameni wai kince yau ba zaki fita ba zuwa shagon yau ? Dan murmushi na sake nace umma ba hakana bane naga kamar ranki baison hakan ne gara na bar fitan kawai a nemi wani hanya mai sauki da za a biya kudin gobe in Allah ya kaimu. Ke nan ke ba za,a lurar dake hanya ba ke nan don Allah umma kiyi hakkuri tunda har kokai magana hankalin kime bai kwanta umma kuma na fahinci me kike nufi da hakan. Bana zargin ki ga aikata wani abin daya danganci maza Sahiba saidai ina tsoron dadewan ki a waje ga abinda hakan zai iya jawo maki a rayuwa. Nagode umma na fada tace amma yanzu kona fita na makara zasu iya cewa ban fito da wuri ba tamike tare da fadin shike nan tunda haka kikace ta fita Amar ya bita da ido kamar zaiyi kuka. Kafin ya juyo kallon shi a gareni fuska ba annuri a cikon sa sam ina ganin haka naji ba dadi a raina na mike ina fadin kaga barin fita in gwada ko zasu barni in shiga nayi na yau din ba shike nan ba na mike ina sauka saman gadon. Ban dauki lokaci ba wurin shirin na fito har daki na samu umma a zaune tayi shiru na shiga ina fadin zan gwada fita umma ko zan samu su barni in shiga. Rana ya danyi don haka ban samu mota daga cikin unguwa ba sai nayi shawaran takawa da kafa nabi hanya jiki ba kwari don nasan zuwan banza kawai zanyi. Wata Jeep ce fara lafiyayya mai kyau ta wuce ni a hanya duk da basarwa irin nawa saida na yaba da kyau motar na dan bita da kallon basarwa . A kofan shagon na samu motan tsaye da alama maishi shagon yazo sayayya ke nan na dan kara kallon motar ina addu,a raina ina fadin Allah ka bamu wanda yafi wanan mai ita kuma Allah ka kara mar arziki. Dakata nan akace min na dago kai manajan mune tsaye a kofan ya fadi haka dama nasan hakan zai faru tun kan nazo din. Na dago kai tare da fadin sorry sir ban sona kai time din nan ba kayi hakkuri ka barni in shiga don Allah inyi wanan aikin for d sake of my brother . I want to paid his school fees tomorrow na dan hanna hannu wuri daya ina rokon shi yace dani. I beg de go before i call d security for u. U wan pai ur broda school fees, why u no come in time, u tink we de stay here for play or what ? De go jere , u tink say we be yeye here ? Banyi zuciya ba na dan tsaya na kalleshi da idona da suka ciko da dan hawaye don takaicin irin cin fuskan da yake kokarin yi min a wurin. Na dan fara ja da baya baya ina rayawa a raina gaskiya yau idan na bar wurin nan shine karshen zuwana wanan shagon na raya a zuciyana don na filanin yazo a makogorona lokaci guda (zuciya). Wani kallo nayi mai kafin in juya ina kokarin fara tafiya naji wayan shi yayi kara ya dauka yana yes sir ok sir sory sir. U girl ya fada da dan karfi tare da dan takowa har haraban wajen yana kwala min kira duk da nasan dani yake hakan baisa na tsaya ba ko in juyo. I am talking to u ya kara fada da karfi yana shan gabana na dago jajayen idona na sauke a kanshi cikin mamaki yake kallona yace. I dey talk to u , u no look ur back , wen u de warker , oya go inter, u be luck today ya fada . Da ace ni wata maishice ba zan kalli wanan shagon ba a yau koshi shigan da nayi don in cikawa Amar burin shine don tun ranan thursday yana gida zaune bai fita school ba gashi zasu fara exam. Ban ko tsaya gaisuwa ba na kwabe abayan dana sako a sama nakai inda muke ajewa tare da jakkana na nufi wurin aikina sai ga mai raba aikin yazo yace na koma wurin da ake kirga kudi na zauna saka ido shine aikina ranan a kusa da wani office din su da suke meeting manyan dake kula da wurin. Aikine ko a wurin sosai kasancewar wurin babban shagon kaya mutane tun dai yan kasan waje da masu kudi da manyan ma,aikata sai shagon yasamu karbuwa a wurin su . Ban saba da aikin ba duk da ba wani abu bane mai wahala amma yau sai najini daban da sauran ranakun aikin danake masu. Sam ban san akwai mutane a kusa damu suna meeting ba sai lokacin dana fara dan jin hayaniya na tashi a wurin a daidai lokacin kuma kaina ya fara sara min abinda ya dan dade bai mun ba . Har yakai an kai ga kiran wanda muke aiki dashi ya tashi saini na zauna wurin ina karban kudin abinda aka saya din kafin ya dawo . Hayaniyane sosai wa karedw wirin wanda kuma ni kadai ne ke jin hakan don wace muke tare tana saka kaya a leda bata ji komai ba a lokacin. Table din gabana na dan buga na mike sai wanan dakin na murna jin an shigo yasa duk suka dan juyo suna kallona a lokacin don ba wanda ya isa ya shiga wanan wirin. Kudine suka bata har miliyan hamsi da wasu abu akai ya kawo wanan muhawaran a tsakanin su, ina shiga sai kallona sukeyi suna mamakin abinda ya kawoni cikin su karamar ma,aikaciya dani haka. Don ban kai mataki na biyu ba a cikin ma,aikatan wurin sai kuma gani na shigo masu suna tsakiyan da tataunawa akan matsalan dasu manyan wurin kawai ya shafa a lokaci. Good day sir na fada kafin in juya ina fadin d money u are talking now, is with mrs Olanike nd mr Andrus house . Kaika sata ka bata ajiya a gidan ta on 27 karfe sha biyu na dare idan ba a dauki wani mataki ba sai ta fito dashi ku raba kaida ita ko karya na fada ? Ina fadi ina nuna Andy din dake zaune lafin na sake kallon su ina fadin tell him d man he is lookin for who battery him yesterday, is now in idi,eroko try to run away to oversea that,s mr Akani. Da sauri ya dago kai ya kalleni ina fadin haka ban tsaya jiran komai ba na juya na sakai na fita daga dakin taron duk suka bini da idanuwan su lokaci daya mamakin ya hana kowan su magana . Me yarinyar nan take magana a kai ne mai wurin ya kira waya yana tambaya sai wani Abdulhamid yake kara masa bayani abinda na fada. Sam ba wanda yayi zaton jin hakan don har ana batun kiran security daga waje su wuce da wayanda ake zargin sune da alhakin hakan lokacin. Gaskiya ta fada ko kuwa daku da ita duk mu mika ku wurin yan sanda yanzu kuyi bayani a can manager ya fada a fusace. Namijin yace shi sam bai san wanan maganan ba, bai ma san inda wanan zance ya fito haka ba ai. It look like wanan yarinyar tana da wani baiwa akan hakan don haka kawai ba a kirata ba a nan ta shigo ta fadi abinda ya faru haka . Har kuma tayi magana a kan mr Akani da suke rikicin kudi da oga a daren jiya sai gashi ta fada yanzu a nan yaya akayi duk ta san wanan din yanzu ? Dole maganan ta abin dubawa ne don ya akayi har ta san da zancen Akani da jiyan nan sukayi shi da dare oga ya kirani yana fada min abinda ya faru. Ya zama dole mu mikaku duka wurin hukuma idan kunje can kuyi bayanin abinda ke faruwa in yaso ta kara yi masu bayani a can ya fada yana kokarin daga wayan shi. Jin hakan da mrs Olanike tayi yasa da sauri tace zan fadi gaskiya bana son abu daya dangata da station ko wani abin juju ko kadan a rayuwana. Me, i no wan wahala woo, come collet d money wan you bring to me dat day abi, d same day, dat dis gurl talk about it? No be dat day, u bring d money they talking about it now? i no wan wahala wooo atoh! I ask u whare u getterm ? u say make i no ask u now. Ta mike tsaye tana fadin ita fa bata ciki shiri ajiya kawai ya kawo mata ta ajiye mai na dan wani lokaci kuma ta aje mai su. Manyan sukai kasa da kai na dan lokaci duk basuyi zaton wanan mailaifin shiyayi rub da ciki da wanan kudin daya shige ba haka masu yawa. Sun fi kai zargin su gun kananan ma aikatan su dake tura masu kudi sune suka kwashe kudin haka gashi kuma wanda ake zargin yana da alaka da mai wajen ke nan su din yan uwa ne najini yai masa wanan aikin. Ina barin dakin jakkana da abayana na dauka da zuman fita daga wurin don gaba daya hankalina baya a jikina a lokacin. Karo nayi da mutum haka baisa na tsaya ba don in bashi hakkuri yana tsaye ya zura hannayen shi a cikin aljihun wandon dake jikin shi duka biyu. Ido na dago kawai na kalleshi na ci gaba da tafiyana banyi magana dashi ba na nufi hkudin fita daga wajen ga baki daya naji an rikoni. Kaina kai nake fadi ga maishi ina fadin mu head wooo my wooo har nakai kasa durkushe a wurin rike da kaina dake min ciwo sosai. Ayoyin Allah daga cikin Al,Qur,an mai girma ya fara ja min lokaci hankalin mutane ya fara dawowa gare mu hakan yasa ya dan kara jana zuwa bayan wani kanta. Har dai ya kai karshe ya kira sunana na amsa mai yace masha Allah dan juyawa yayi yajana fadin dis is notin serious woo . We usualy have dis problem in our people so don't take is serious matter ya kuma juyo kaina yana fadin go home nd have a rest. Tafiya na fara yi kafin daga inda yake yayi mai magana sai Abdulhamid din ya dakatar dani da in jirashi yazo bayan na jirashi ne sai gashi da mota yazo ya kaini har gida. Umma ya sama yayi mata bayanin abinda ya faru dani tayi maigodiya tare da dan bayani nan yayi mata alkwarin akwai wurin wani alpha da zai kaini yana bada maganin irin matsalan nan tayi mai godiya kafin ta shiga gida ta sameni kwance har barci ya daukeni a lokacin. Ban falka ba sai dare na dan samu sauki naci abinci bisa tursasawan umma din na kuma watsa ruwa a jikina na sake kwantawa. Kwana biyu ina kwance ban fita ko ina abin duniya yayiwa umma yawa ana haka ranan da abin ya faru da kwana hudu sai ga yan shagon mu maza mutum ukku sun sallamawa umma tafito suka gaisa . Suke fadin sunzone kan abinda yafaru dani a dalilin su don haka mai shagon yace su kawo min alherin don jin dadin da yayi na fitowan kudin shi daya gane wasu kudin shima da suka fi wanan yawa a hannun Akani dana fada mai inda yake ya bishi. Manaja yasa hannu ya ciro key daga Aljihun shi tare da envelop ya aje a gaban ta yana fadin wanan key din motace sai kuma kudin mai a cikin wanan takardan ZAINAB IDRIS MAKAWA ANA DARA GA, , , , , , , , , , 4️⃣0️⃣ BY, , , , , , ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , , BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AL BASIR, , , , , , , , ONLINE PAID NOVEL DON ALLAH YAR UWA KI BIYA KAFIN KI KARANTA NA KUDINE , , , , , Sun tambayeni umma tace dasu ina barci tun ranan da abin ya faru bana ciki hayacina don lafiya bai isheni ba tun lokacin. Sun nuna tausayawan su ga hakan daya faru yayin da suke dan dube dube a gidan kafin su aje key din motan suna fadin ga wanan shugaban wurin aikin mune ya aiko mu muyi ma Sahiba godiya mukuma bata wanan a matsayin tukwaicin abinda tayi mai har kudaden shi suka fito gareshi. Yana fadin hakan ya aje dan makulin mota saman kujera tare da envelope yana fadin wanan kuma kudin mai ne ya bayar tasha mai muyi duba da zata shigo aiki sai dai bamu ganta ba tun wanan ranan a zaton mu abinda ya farune ya hanata fitowa aiki a wurin mu din. Bashi bane lafiyane bata dashi bayan haka kuma tun kan faruwan wanan abin dama tana da niyar barin aiki a tare daku nan gaba kadan. No no mama don do that please, we want to work with dis gurl now don Allah ayi hakkuri abi, ya kalli sauran yana tambaya idan ya fadi daidai a lokacin. Suma dai dariya suka kwashe dashi a lokaci daya don sunji irin hausan da yayi lokacin sai dayan yace ba karamin ci gaba muka samuba a sanadin wanan yarinya a yanzu. Don ayi muna barna mai yawa da bai dace ba wanda gaba dayan mu wurin nan da duk ya shafe mu saidai Allah zai cece mu kawai. Sai ga Allah ya jefo muna sahiba a ciki rayuwan mu ta warware muna wanan rikicin wanda hakan yai muna dadi ga Abdulhamid nan shi yayi muna bayanin komai muka fahinci baiwane Allah yayi mata a kan hakan mun gode mun gode kwarai da abinda tayi muna din. Makulin dake samandan table gaban umma ta dauka tana fadin muma mun gode da kuka fahinci hakan sai dai ku mayar masa da makulin motar shi a yanzu sahiba bata kai bukatan mota ba a rayuwan ta. Sahiba yarinya ce kara dake shirin rufe shekara ashirin a wanan shrkaran mai zuwa yayana marayune basu da mahaifi don mahaifin su tun sahiba nada shekara uku ya rasu ya barni da cikin dan uwanta ta sanadiyan kasheshi da yan uwan haihuwan shi sukayi don kawai kan abin duniya. A haka nake kula da diyana bayan na gudo zuwa nan dasu har zuwa yau din nan da kuka zo min da wanan maganan don haka ba zan karbi komai nasa ba . Sahiba nada wanan laluran tun tana yarinya haka yasa bana son tana shiga mutane sosai don abin zuwa yake mata a lokacin da ba,a zata ba idan wani yayi abin da bai dace ba ga dan uwan shi ma,ana dai ba,a cuta a gaban ta idan tana wuri zata fadi haka kai tsaye ba tare da anyi tsamanin hakan ba. Kallon juna sukayi lokaci guda kafin su juya ga umma suna fadin shi wanan kyautan ba komai bane daga cikin abinda yake da dan haka kada ki hanawa yar ki jin dadin daman da Allah ya bata a yanzu. Abdulhamid ne ya tare da fadin mama nasan me kike nufi da zancen ki insha Allahu hakan ba zai faru da yarki ba a rayuwan ta saboda adduan ki a gareta da kuma maraicin dake saman kansu a yanzu na rashin mahaifin su tare dasu. Wanan ba komai bane hakan wani budine daga Allah daya fara aiko mata a rayuwan ta a yanzu, adduan ki gareta shine abin bukata don haka kiyi hakkuri ki karbi kyautan nan a matsayin tukwicin abinda tayi muna ga baki dayan mu. Shiru umma tayi tana tunane a daidai lokacin suka mike suna fadin su zasu tafi sun gode kuma da taron da akai masu. Ban san wainar da ake toyaba a gidan ina dakina rufe ina barci ga don haka bana sanin abinda ke faruwa a cikin gidan lokacin. Ban fito ba sai karfe uku na rana na tashi nayi sallah bayan na kara watsawa jikina ruwan sanyi don na danji daman yadda nake ji a lokacin. Fitowa nayi falon bayan na idar da sallah umma na sama zaune a falon tayi shiru ta mike kafafun ta saman center carpet din falon mai jikin damisa . Sannu da gida nayi mata ta bini da kallo har na zauna take fadin me zanci akwai abincin data dafa a kitchen ta debo min naci. Nace ba yanzu ba umma ina kaiwa kwance ta kalloni tana fadin Sahiba zaki halaka kanki da yunwa na fada maki ki dinga daurewa kina dan cin abinci don ki samu sauki da sauri amma bakaci komai ba ya zaka gane kaji saukin jikin ka. Zan sha tea umma na fada ina bata fuska tace madara ya kare nace da lipton kawai nake so nasha don dama sai naga dama nake shan tea din da madara wani lokaci. Mikewa nayi zuwa kitchen din umma ta bini da kallo na hado ruwan zafi tare da litop da dab suga kadan don ban faye son suga ba ni haka dai nake na zauna ina dan tsoma ganyen shayin a ruwan zafi umma ta kura min ido daga inda take zaune. Kafin na dago na fara dan kurbawa ina hutawa zuwa can na dauka na kara kai cup din a bakina ina kurbawa naji umma tana cewa yan wajen aikin ku sunzo kina barci. Da sauri na cired cup din abakina har ina sarkewa wurin fadin gidan umma yaushe suka zo ? Yau din nan suka zo kina barci ga key nan da wanan takardan suka kawo a matsayin tukwicin aikin da kikai masu wai sunce a baki. Aiki kuma umma kuma sai kika karba kuma hakan na nufin ai na zama mai bada magani ke nan kuma umma. Nima abinda nakewa gudu ke nan naki karban wanan abinda suka kawo amma sai yaron nan na cikin su musulmi din nan yai min magana kan na karba wanan ba komai bane daga cikin dukiyan wanda ya baki koda bamu karba ba wani zai ba shi gara dai din mu karba yafi. Kinji dalilin da yasa na karba na kuma fada masu cewa zaki bar aiki dasu nan bada dadewa ba suka nuna bacin ransu ga hakan suna roko a barki ki koma aiki dasu don Allah. Nace dama kina da niyar barin aiki ko ba wanan matsalan ya faru yanzu ba dama akwai niyat yin hakan gareki zaki aje aikin ki dasu. Bazan kara zuwa aiki dasu ba umma wurin ga baki daya ya fice min a raina don ranan dana je karshe suka nuna min ba sabo ga aikin su idan ka saba masu zan dawo nan kofan gida ko snack na dinga ajewa da dare tunda wanan titin namu babban hanyane na kowa. Ko bakiyi wanan ba yanzu wanan kayan drinks din da mukeyi akwai kasuwa sosai a gareshi ana samu sosai a cikin sa matsala dai shine rashin jarin mai tsoka da bamu dashi a hannu da sai mu kara ya zamanto muna egent na company yadda za a iya sari a wurin mu. Shiru nayi ina tunane don umma ta kawo babban shawara a nan saidai inda zamu samu kudin yin hakan ne a yanzu shine matsalan. Dan shirune ya biyo baya kafin nace yanzu umma yaya zamuyi da wanan kayan tace dani wanan dai zamu jira yazo tunda yace zai shigo ya kaimu wurin wani da zai baki maganin matsalan ki. Umma ni banda wani matsala banda ciwon kan nan dake yawan damuna wani lokaci shine dai din matsalana a yanzu. Shidin dai ai ake magana do mutanen kanki suke haddasa maki wanan matsalan ciwon kan ai idan su taso maki gara tun wuri a nema maki magani a kanshi zaifi. Amma umma kin san matsalan masu maganin nan a yanzu shine irin kudin da suke tsulawa mutum tunda ba ko yaushe ne hakan ke taso min da a barshi kawai zaifi. Sahiba kin san matsalan nan naki ba karamar matsala bace fa yau da ace mutanen basu da fahinta kinsan abinda hakan da suka sakaki zai jawo muna kuwa ? Ban dauki key din ba bankumayi magana a kan komai ba karshe ma na mike na shige daki ina tunane na bar komai a wurin. Don ni almara naji zancen motan kamar a mafalki na dauki zancen waini sahiba ce da kyautan mota gun mutumin da ban san shiba ban kuma da wata alaka dashi. Da yamma Abdulhamid dinne ya dawo gidan mu sun tsaya a falo suna magana na fito maka gaisa dashi yake tambayana yaya jiki nace da sauki . Suka cigaba da magana da umma akan alkawarin gobe da yamma zai zo ya kaimu wurin mai maganin dayace din. Umma tace ab gode saidai da fatan ba wanda za a kaucewa Allah bane wurin ya danyi murmushi yana fadin. Shima baya shirin da irin wa yan nan mutanen sam inda za ai muna rukiya ne asan abinda suke so su rabu dani har abada idan hakan mai yuyuwane. Sai kuma ya dauko zancen inda za,a aje min motana don sabuwace dallailiya ashe don ma komai nata a leda yake tukun ba a bude shi ba. Umma tace akwai gareji a gidan nan sai dai ba a gyara shi ba yace ba matsala zai mayar da motar company ya kwana a can don akwai tsaro a wurin gobe zaizo dame gyara a gyara wurin da zan dinga aje motan a gidan. Ya dan dago yana tambayana ko na iya mota da sauri na dan girgiza kai ina bata fuskana da kawar da kai yace ba matsala matarshi ta iya mota sosai za a samu lokaci ta koya min. Hakan daya fada yasa na danji sanyi a raina ya mike tare da yi muna sallama umma na masa godiya yace tabar gode mai yana kwadayin ladan kula da marayu ne a garemu. Odaro na fada daga inda make zaune ban tashi ba don ni jin komai nake har lokacin kamar a mafalki don har lokacin zuciyana bata gaskanta min gaskiya bace motar tawa ce wai. Umma ta dan dade a waje saida ya nuna mata ko ina na motan kafin ya shiga yaja zuwa inda yace zaikai ta din ya tafi. Sai bayan ya tafine umma ta shigo sai kuma hankalin ta bai kwanta da hakan ba sai zargi yakuma shiga zuciyar ta duba ga yadda lokaci ya koma yanzu . Tun dai data tambayeni nace ni a wurin aiki kawai nake ganin shi bamu taba wani hurda dashi ba kona gaisuwa hakan yasa hankalin ta ya tashi kuma sosai da tafiya da motan da yayi din ni har ina mamakin hakan ga umma don ban zata itama ta sa motan a rai ba sai wanan lokacin ga nawa tunanen. Ganin ta damu har tana tambayana shi inda nasan shi nace umma idan ma har gudu yayi da motan ai kanshi yaiwa do dai duk inda yakaita sai ya dawo da ita nan da kanshi. Ina fadin haka na mayar da hankalina wurin kallon tv da nakeyi na fita zancen su itama umma din jin abindana fada yasa tayi shiru na dan lokaci karshe na mike zuwa dakina na kwanta na barsu a falon. Washe gari dana tashi naji saukin jikina sosai bayan na idar da sallah haka na fito na danyi aiyukan da nakeyi a gidan kafin muka shirya zuwa makaran ta. Bayan fitan muma umma bata zauna ba a gida don da zaran mun fita itama bata son ta zauna a cikin gida saita dawo shagon sayar da kayan sanyin mu ta zauna a nan. Saidai ranan haka ta zauna a cikkn damuwa dan ta saka ido har ta gaji ko zata ga Abdulhamid saidai har yamma da muka dawo babushi babu alaman shi. Hankalin umma ya kara tashi umma ta matsa sai naje ma,aikata na duba ko yazo inji dalilin rashin zuwan shi ban iya musa mata haka na shirya nabi hanya saidai banje can din ba. Na dawo na fada mata cewa bai shigo ba yau amma ta bari idan Allah ya kaimu gobe na sake dubashi. Umma tace ina ai mu tashi kawai muje can idan ba,a gane ba sai muyi karan shi kawai a station a nemeshi zafi. Ina jin haka nace tayi hakkuri har washe gari zan dawo school da wuri sai asan abinyi a kanshi haka dai ta hakkura ba dan taso ba. Washe gari ban dawo gida ba sai karfe hudu shima Amar sai uku da rabi ya iso gida mun samu umma a waje nan na zauna shagon wurinta muka gaisa. Na cire dan hijab din dake wuyana sai na zauna sai yar dogowan riga yellow daya tsaya min iya wuyan kafa muna hira ina bata labarin accident din daya faru a hanya. Umma ta matsu in gama bata labari ayi zancen daya dameta mota ya tsaya a kofan shagon ta da farko mun dauka masu tsayawa su sai kayan sanyi ne a wurin mu. Saida mai motan ya bude ya fitone mukaga ashe Abdulhamid din ne ina jin umma na sauke ajiyan zuciya har abin ya ban dan dariya. Yazon sun gaisa yake fadin umma tayi hakkurin rashin ganin shi a jiya wallahi matsala aka samu da Land lord nasu ya basu notis su tashi mai gida zai yi gyara na kuma bai basu notis din da wuri ba sai last week. Nan dai aka tausaya mashi tare dan magana kan hakan yace yazone a tafi gun mai maganin kada dare yayi in kuma sai zuwa gobe ne hakan baida matsala zasu iya bari aje gobe din. Umma tace ai ya dakata har hankalin shi ya kwanta zaifi tace ai ya bari harhankalin shi ya kwanta ya samu inda ya aje iyalin shi zaifi. Da hausa nake fadin umma mezai hana ya duba bangaren nan idan zai masa sai yazo ya gyara su shiga har ya samu inda suke so. Umma tace itama dai hakan ta gani idan wurin zai masa don zaman wurin haka ba kowa yana bata tsoro wani lokaci dakuna ukune da falo kitchen kamar yadda namu yake a sama. Dakin bakine sai aka debi garejin mota daga gefen shi shi baikai namu dake da daki hudu ba a sama. Umma tace dashi nace ba da wanan wurin zai maka ka duba ka gani sai ku dawo nan da iyalin naka har ka samu wanda kake so din idan kuma yayi ma shike nan ku zauna a ciki. Da sauri yake tambaya ina wurin umma ta nuna mashi ya juya tace bari ta dauko key a bude ya gani ya ma rasa me zai fada a lokacin. Ni ta tura na shiga na dauko mata key din ya bude ya shiga ya bude ko ina ya gani sai gashi ya fito yana wasan baki tare da fadin wuri yayi kyau sosai wallahi a nawa zasu dauka haya ke nan. Da sauri umma ta tare shi da fadin ba wanan ya kiyasata ya gani ai yasan yadda ya kamata sai ya fadi yayi shiru na dan lokaci kafin ya dago yana murmushi yace dadai za a fada mai zaifi don kada ya shiga hakkin mu da yawa ba zai so hakan ba. Shiru nayi ina sauraren su umma tace ai itace ya kiyasata yace to a raga mai ya bada dari biyu da hamshin a shekara idan bai tauye mu ba. Umma tace dashi kabada dari da hamsi a shekaran Allah ya kara rufa muna asiri ya shiga mata godiya ba adadi. A zuciyana nace ashe da tun tuni mun bada hayan wurin da mun dan samu mun rage ta wanan hanyar amma wurin yana kulle ba wanda aka bawa shi haya. Yayiwa umma godiya sosai tare da addu,a kamar wanda zaiyi kuka a lokacin don bai taba zato ko tsamani zai samu ko kwatankwacin hakan ba a wanan halin sai gashi Allah ya kawo mai daga sama a cikin sauki. Shiyasa kyautatawa yake da dadi koga wanda baka taba sani ba saboda baiga dai abinda yai muna ba har aka amince masa hakan. Washe gari tun kan in fita zuwa school sai gasu da iyalin shi sun shigo gyaran wajen nan na fita na barsu suna gyara. Ba abinda ya kara min dadi sai ganin su da yara maza nasan cewa Amar zai samu abokan wasa ke nan a yanzu yan uwan shi maza. Ai kafin mu dawo daga school har sun kwaso komai nasu sun tare a ciki sai gidan ya dan canza min kamar ba gidan mu ba ga haske ansaka a ko ina ya kara haske wajen. A gaskiya mutum dadi gareshi ko yayane don gashi mun fara ganin hakan tun yanzu nashiga gida umma ke fadin yau baki sun hanani bude shago sun tare aciki yau din nan. Nace umma naga an gyara wuri yayi kyau sosai wallahi Allah ya bamu hakkurin zama dasu tunda musulmai ne yan uwan mu su tace amin nima adduan dana gama ke nan a zuciyana. Wanan shine mafarin shigowan Abdulhamid a cikin rayuwan da ya shiga cikin labarin da zan baki nan gaba. Satin mu daya tare dasu gaskiya ba wani matsala a tsakanin mu duk da ba zama nakeyi ba sai da yamma idan na dawo yamman ma ina shago amma na kula da yadda takewa umma biyayya sosai sun dauketa kamar wata yarsu ko yar uwa duk da matan takan dan so zama muyi hira saidai ban saba da sakewa mutane haka ba. Ranan na takwas a gidan mu yazo da dare ya samu umma yana fada mata cewa mu fito muje don yayi magana da Alfa din yace yazo damu yau karfe takwasa. Ba yadda na iya haka umma tasani a gaba muka shiga motan shi zuwa wurin a hanya ne yake ba umma labarin cewa. Tun zuwan shi lagos yasan malamin sun zauna a unguwa daya dashi lokacin don shi dan lokoja ne ya shigo lagos wurun dan uwan shine daga baya kuma dan uwan nasa ya barshi ya koma cottono da zama. Har dai muka kai yana bamu labaein shi a takaice har matar nasa da suke yan gari guda da ita daya aura yaren su daya dashi sai dai ita iyayyen ta na nan cikin lagos zaune . ZAINAB IDRIS MAKAWA ANA DARA GA, , , , , , , , , 4️⃣1️⃣ BY ZAINAB IDRIS MAKAWA, BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AL HAKAM, , , , , ONLINE PAID NOVEL DON ALLAH YAR UWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA BA TARE DA RIKE HAKKIN HAKA AKANKI BA, , , , , Wani tsohone zaune a cikin fararen kaya da farin gemen shi mai tsawo sai wano katon casbaha daya rike a hannun shi yana zaune saman wani farin dadduma mao laushi dakin sai kamshin turare yake tashi a cikin sa kokai waye sai kanka ya sara a wanan dakin don kamshi irin turaren da ya game dakin. Muka shigo da sallama yana amsa muna da wa,alaiku mussalam da harshen yarbanci kafin ya juya wurin Abdulhamid yana fadin sune kazo dasu. Yace eh wanan ce diyar tawa dana fadama tana fama da matsalan sai kuma wanan yar uwan nawa itace ta haifeta su biyune kanin ta yana gida mun barshi. Dadtijun yace Allahu Akbar ya dago kai ya tsura min ido kuri kaman yana nazarina lokacin kallon shi nayi sau daya na dukar da kaina kasa don ba dabi,ana bane saka ido cikin na wani na dan lokaci mai tsawo haka. Allahu akabar ya kara fada yana gyara zama tare da jijiga kanshi yace lalai yarinya tana da abubuwa a kanta masu girma saidai ba masu cuta mata bane don su din kamar na gadon gidane suke a jikin ta. Zasu iya kareta a duk inda za,a iya cuta mata ko za a cuci wani sai kuma yai shiru kamar yana nazari a zuciyar shi sai can ya dago kai yana tambayana. Omoge na dago kai don nice dai yan mata kadai a wurin yace ko zaki iya tuna haduwan ki da wani tsoho da kikai mai tallan magani kuma idan kin bayar ana dacewa sosai da maganin naki. Umma na fadin wa Sahiba sam ai bata taba sana,a irin wanan ba yace ta dakata ni yake tambaya. Da sauri na dago kai ina fadin eh na taba a baya na hadu da wani tsoho na fito talla ban samu abin dauka ba muka hadu dashi. Shine ya bani sari kuma ya gwada min yadda zab dinga bayarwa in rudi mutane sai aka dinga saye sosai dana gwada din. Ya dan girgiza kai yana murmushi kafin yace daga baya fa na fada masu kaf abinda ya faru na daina yace ki godewa wanda ya dakatar dake wanan sana,an . Din sun so daukan ki zuwa ruwana kiyi kwanaki a wurun su da zaran kin fito zaki zama babban mamalawo don shi din ba mutum bane. Mutanen ki yan ruwa suna da yawa a jikin ki sune kuma suke aiki da kakan ki a baya shine suka so komawa wurin ki lokacin. Orishirishi Sahiba yaushe duk kikai wanan abin ni ban sani ba umma ta fada cikin damuwa tana kallona ta kuma juya ta kalli dattijun dake bayani. Ba zaki sani ba ai don ba zasu bari haka ya faru ba yar ki nada wani irin tauraro mai haske duk inda take za a sanda ita haka wasu zasu sota wasu kuma da basu da zuciya mai kyau zasuji basa son ta sam. Irin wanan ajannun na gode suna da wuyan sha,ani sosai koda ance za, a fitar dasu a jikin ta sau dai kawai su lafa amma basa tafiya suna tare da ita ko yaushe. Sai ya kalloni yana fadin dai a cikin yarbacin da ake magana yarinya dan fita zan gana da iyayyen ki akan haka zanyi magana da ya shifi jinin ta kin san duk yadda yan uwa suke suna da dadin sha,anin sosai koda kuwa tasan su din masu matsalane a gareta. Jin haka na bike gaba daya na bar dan dakin kafin su dade a ciki suna magana da umma ina waje na zauna ina faman bin mutanen dake zirga zirga a wurin da kallo. Sunzauna sunbi layi suna jiran a akirasu lokacin don wasu ma a nan muka samesu wurin suna jiran iso daga gareshi ga kuma su umma suna ciki basu fito ba don ina jin maganan su daga inda na tsaya din . Sai can suka fito din ran umma kamar a bace kallo daya nayi mata na kawar da kaina gefe daya haka muka shiga mota kowa baiyi magana a motan muka dawo gida. Lokacin har yamma tayi sosai mun samu Amar a shago yana ciniki muka tsaya wurin shi sai da magariba ya kusa na mike na shiga cikin gidan mu. Wanka nayi kafin lokacin sallah na kunna tv ina kallo kamar daga sama naji muryan ya Almustapha a gidan dan wajen gwaggo harin kaduna. Kafun in tashi zuwa dakina har sun shigo shida Amar da umma Allah ya taimakeni a lokacin sallah kawai nake jira a tayar in tada nawa sallah. Har ya zauna ban samu gaida shi ba saida ya zauna ya jawo Amar zuwa jikin shi suna hira da umma nayi mamaki yadda har umma ta sake dashi haka da sauri. Yana tambayan ta yaya jikin tayi amfani da maganin ko ni mamakine ya cikani saida na mike nake gaida shi da zuwa daga haka na juya zuwa dakina. Umma ta kirani tana fadin ban gane shi bane na girgiza kai na wuce ban tsaya ba na tayar da sallah har na idar ina jin muryan shi da umma din. Mamaki nake daga inda nake zaune mutumin daya umurce ni a gidan mahaifan shi cewa kada in fara in nuna cewa nasan shi koda wasa don me yanzu zai dawo ya dinga kokarin son kulla zumunci damu kuma ? Yarinya nake tabasa a gareshi amma zan gwada mashi don bamu da gata yanzu ba shine zaisa har su takamu yadda suke so ba. Ban fito ba saida zai tafi umma ta kwala min kira na ki amsawa Amar ya leko dakin da dokin shi ya samu na tayar da sallah da bansan kan shiba bama lokacin. Ina ji ya koma yana fadi wai ina sallah ne lokacin haka suka kwasa ta dan rakashi ta dawo ta tayar da sallah itama ban yarda na fito ba son nasan kwanan wasa dole sai umma tayi min fada kanshi. Sai karfe tara na fito a cikin shirina na kwanciya barci suna falo zaune inda Allah ya taimakeni kafin takai ga yi min magana saiga Muniya matar Abdulhamid ta shigo tana fadin . Tazone ta fadawa umma bakon da yazo yabawa yaran su dubu goma tafito da kudin tana nunawa umma tare da ajewa a gaban ta. Ban dago kai na kallesu ba na mayar da hannkalina a wurin wakan da akeyi a cikin tv din kafin can na mike jin suna hira tana fadawa umma maigidan ta da yaran sun fita zuwa asalatu wurin daukan karatu ke nan suke nufi da hakan. Abinci na debo na fito ban zauna falo din ba na shige dakina dashisun dan dade tare kafin mijin nata da yaran su dawo tayima umma saida safe ta shiga gidan ta. Haka yasa bamu hadu da umma ba a ranan sai washe gari na gama aiyukana da nakayi kafin in tafi school na dan zauna ina kurba rwan zafi don ga dabian bayerabe baka fita daga gidan ka ba tare daka saka wani abu a bakin ka ba koda kuwa kurbi dayane. A cewan su koda wani mugun abu zai sameka Allah zai kawo saukin abin da kariya bazai sameka yadda akeso ba ba ku koyawa diyan ku sabawa da dan cin koda wani abune kadan kafin su fita makaranta mata Allah ya tsare ya karemu baki daya amin. Umma ta fito daga daki tana gyara daurin zanin dake jikin ta tace dani bayan takai zaune tace sahiba na dago kai da sauri na kalleta. Abinda kikayiwa dan uwan ki jiya kin kyauta ke nan umma dan uwana wake nan ta watso min harara daga inda take na sake dukar da kai kasa. Ki matsa idan nuna kula shi a garemun da yakeyi shima laifine yin hakan kin dai san bamu da kowa a duniyan nan sai wanda ya tausaya muna yazo ya rabemi kafin shima kwana biyu ai masa aiki ya gujemu. Dan murmushin bakin ciki na sake a fuskana kafin ince umma kema kin fada da bakin ki yanzu bazan taba yarda da duk wani daya shafi wanan zuri,an ba kuma a yanzu. Balle wanan din da tun farko ya iya fada min kada in yarda in sake nuna cewa nasan koda a mafalki ni kuma zan nuna mashi cewa ba shegiya aka haifeni ba ai. Ina fadin hakan na mike ban tsaya sauraren ta ba na fita zuwa school ranan ko Amar ban tsaya jira ba na sa kai na fice a gidan ni kadai. A school ma ban sake jiki ba don abinda ya faru dani da umma da safe haka kawai zai zoya haddasa muna fitina a tsakanin mu. Dole akwai abinda abinda yake dashi a zuciyan shi game damu na nasa a raina amma ko me haka ke nufi wata rana zai fito filine ni dai komai umma zatayi min bazan taba yarda in nuna wai nasan shi ko muna da wani alaka dashi ma. Har na koma gida ban yarda na sake ba har lokacin haka itama umma din hakane ya faru da ita don nayi mata abinda take gani saboda na girma nake ganin har zan iya kin bin dokan ta akaina. Shima din dai haka ya koma yana mamaki yadda yarinya karama ta iya masa duk a lokacin bai gano cewa wai saboda wanan maganan bane daya fada min nayi hakan. Me yarinyar nan take nufi ne wai ko ta dauka takai wata mace ce da har zai nuna ra,ayinsa a kanta yaja guntun tsuki tare da daukan cup din glass din dake gaban shi cike da ruwan lemo ya kurba kafin ya aje cup din yana furzo iska daga bakin shi. Me yarinyar nan ta dauki kanta a yanzu yarinyar dake yawo kwararo kwararo a cikin garin nan da kayan talla a kanta. Da badan maman shi data matsa akan ya binciko wani alakane tsakanin daddy damu ba ba abinda zaisa ya sake kula wa yan nan mutanem ya fada a fili shi daya kamar mahaukaci a falonshi. Shi shi ya fada wai bata sanshi ba a lokacin ne kuma warning din da yai min a baya ya fado mashi a zuciya tabbas wanan maganan yar ficiciyar yarinyar nan ta rike. Da badon tafiyan dake gabab shi ba gobe daya koma yaciwa yarinyar nan mutunci ko a gaban uwar natane kuwa don shi baida shayin kowa idan ya tashi tsula tsiyar shi shi yasa bai kula kowa kaf dangin shi saboda bahagon zuciyar shi da take mai baudai shiru shirun muguntane gareshi don ya tsotsina fulani a jinin shi. Abdulhamid ne ya shigo har falon mu bayan sallah isha,i suka gaisa da umma ina daki ina jin muryan shi tunda yayi sallama don kwana biyu ke nan muna haka da umma. Bawai bama magana ba a,a kawai dai tana fushi dani sama sama ne dana ga haka na rage zama a kusa da ita nafi zama a dakina idan ina gida. Ina kokarin shafa maganin nan da suka amaso baki amfani dashi ba duk dare ina shafawa kafin in kwanta barci tunda saboda ni aka karbo Sahiba fa naji Abdulhamid ya ambata don ya kamata ta koma aikin ta hakanavnaji muryan shi yana fadi yaci gaba da fadin. Don yau sun tambayeni ita nace ta samu lafiya sosai don naga tana shiga school. Eh to Sahibace yanzu Abdulhamid ta dauko wani sallo kuma bari dai a kira maka ita kuyi magana idan tana ra,ayin komawa nan din. Sam banji dadin jin kalamin umma ba datayi mai a kaina don dai itace zance ta dauki abindaya faru da zafi ai kan almustpha din da yazo dawata manufa garemu yanzu. Amar ya shigo ya fada min umma na kirana nace gani tafe bai dade da fita ba na fito saye da dogon rigan barci na daura zani a sama sai yar hula dana daure gashina na dunkule a ciki. Gaida shi nayi kafin ya ce dani gobe ki fara fita aikin ki Sahiba don aikin yana da muhinmanci a kanki sosai sai dai ba lalai bane ki gane hakan yanzu. Idan kinyi hakkuru nan gaba zakiji dadin hakan da alama ya fada yana kallona dan shiru nayi kafin nace bawai bana son komawa bane sai dai yanzu irin kallon da mutanen wajen sasuyi min shine kawai. Ba wanda zai kalleki dawata manufa yanzu don duk su san ke din ta dabance so suna tsoron yadda zasu tunkare ki ko su wani tsaya a gabab ki balle mu manyane muka san da abinda ya faru din. Ganin yadda umma tayi yasa nace shike nan zan shiriya gobe na fara fita idan Allah ya kaimu na kara da fadan nagode uncle yace shima ya gode. Ya juya zuwa part din su ya fita daga part din mu sai naji wani iri a raina yadda na bi umurnin shi kuma yaji dadin hakan ko ba komai na fahinci suna kokarin maida mu wasu na jikin su . Duk da banyi mamakin hakan ba don irin halarcin da umma tayi masu a cikin yan kwanaki da sanin mu dasu wanda hakan na hango zai zama muna alheri nan gaba watakila Lokacin mai tsawo na dauka ranan banyi barci ba koda na koma daki ina tunanen yadda zan kasance da abokan aikina idan naje aikin . Ba komai nake guduba sai sanin da nayi masu akan camfa abu yanzun zasu iya cewa da wani juju nake aiki ko wani kungiya nakeyi nake gane abinda mutum yake ciki. Washe garin da zan fita gun aikine muke magana da umma kan Almustapha wai na daina abinda nayi mashi ranan don bashi nayiwa hakan ba kamar ita na tozarta a gaban shi ai. Umma kin manta da warning din da yayi min kan kada na nuna nasan shi ko a wani wajen umma nafa fada maki yadda mukayi dashi lokacin. Yanzu ma din da wata manufa yake zuwa nan umma sai kiyi hankali kisan yadda zaku zauna dashi ki kama bakin ki dako mu waye a wurin daddy don abinda yazo ya sani ke nan ina fadin hakan na dauki jakkana tare da gyara hijabina nace sai na dawo umma. Shiru tayi ta bini da ido kawai har nakai kofa na murda zan bude naja na tsaya na juyo ina fadin shi din kin sani mai laifine da yansanda suke nema ruwa a jallo a cikin su harda yaya Abubakar ki kula umma kar zuwan shi ya jawo muna matsala muma a nan. Kofan na bude na fita ta sake bina da kallo don jikin ta ya mutu da abinda na fada kafin na fita amma idan har hakan gaskiyane dole tayi taka tsatsan a wurin zancen ta yanzu. Na isa wurin aiki tun a kofa da zan shiga na fara haduwa da wani babban ma,aikacin a wurin yayi wani irin ja baya da sauri ya kauce min tun a nan na fara kaduwa da kalubalin dazan fuskanta a wurin. Nayi signging kamar yadda kowa keyi ina kokarin zuwa inda nake tsaro naji muryan Abdulhamid a bayana yana fadin ba a nan zanyi aiki yanzu ba . Sun canza min wuri zan koma wurin accounter muyi aiki tare dasu a a ciki mamaki da kaduwa ne ya kamani lokaci daya najin hakan. Nasan wurin don haka na nufi wurin da suke na samu suna bakin aikin su muka gaisa suka nuna min wurin zamana kenan zan zauna zaman saka ido a komai har kudin dake shigowa da jama,an dake zirga zirga muna gani a wurin. Gaskiya na sani matsayina da komai baikai in kai wanan matakin da suka ban a yanzu ba a wurin don kosassun mutane da suka kwarai da aikin suke wanan wurun suna aiki. Nawa dai saka idone idan suna aikin da sauran abubuwa don haka mai min bayani yana dagawa daga wurin na sauke ajiyan zuciya tare da bin wurin da kallo. Gashi su kaf duk da manyane amma bai hana suyi wani haba haba dani ba mu biyu ne mata a wurin saidai dayan gaskiya ta girme min ga komai irin wayayyun matan nan ne na lagos masu ji da kansu do haka take zuba wani sallo da yauki a wurin. Aiki kan ranan anyi an tashi lafiya lokacin tashi yana yi na fito daga wuein bam saba da zama a cikin irin wanan sayin haka ba. Ina fitowa muka hade da Abdulhamid yake fadin ni yake jira nazo na ya kaini wurin motana dake aje a waje don yasan ban sanma kalar motan ba har lokacin. Dan yajayin fuskana na sauya kafin nace ya bari watarana zan ganta na san hakan amma yanzu muje kiga motar kawai kafin mu saka ranan da zaku fara koyon motan. Irin kallon da yan wajen ke min suna kus kus a kaina yasa na fara tsarguwa da hakan zan tafine na bashi amsa na fara tafiya don fita daga wanan wajen. Ya sake fadin zaki jira mu koma gida a tare don yanzu zan fito mu tafi daga nan sai kiga motan sai kuma ya dan juya ya kalli inda nake kallo yayi dan murmushi yana fadin. Yana juyawa ya nufi inda suke aiki ya dago jakkar aijin sa ya nufoni muka fita bamu bar wajen ba saida ya nuna min motan dake matsayin nawa yana rufe a wuri sabuwa dal da ita. Mun kama hanya duk jikina yayi sanyi ga tsarguwa da tunane da ya addabi zuciyana a lokacin ya dan kalleni yana fadin. Wanan sai ya faru dama suna zancene kan yaushe kikazo nan kika samesu har a kaiki wanan wurin aikin wasu kuma kan abinda ya farune suke shakkan ki a yanzu. Saidai dole sai kin kara taka tsatsan da kowa mu saman wanan wurin da oga yace a mayar dake yanzu don duk wanda ke wanan wurin sun san kan aikin su sun kuma karanta aikin tun farko keko haye kikayi. Don haka ki kula ki sa ido dama ina zargin don hakan oga yasa akaiki wanan wurin ki aiki dasu don abubuwan da ake masa a wanan wurin ba kadan bane wallahi. Zaki canza yanzu dole zaki zama big girl a cikin dubu komai har dabiun ki dole ya kara canzawa a yanzu don hakane ma ya karasa ya bayar da wanan motan. Godiya nayi mai bayan hakan ban samu bakin kara furta mashi komai ba har muka kai gida inda muka samu su umma a waje tare da matar shi suna muna sannu da dawowa. Na tsaya mun gaisa dasu kafin na shiga ciki itama matar muniya tashi tayi tabishi zuwa nasu part din suka bar umma tana hada kaya zata rufe shagon don yamma yayi a lokaci. Ranan ban samu sukuni ba don ni abin kamar a mafaki nake ganin shi lokacin wai yau nice a wanan matsayin anya kuwa zan iya kuwa. ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , WwwANA DARA GA, , , , , , , , , 4️⃣2️⃣ BY, , , , , , , , , , ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , , BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AL, ADL, , , , , , , ONLINE PAID NOVEL DON ALLAH YAR UWA KI BIYA KAFIN KI KARANTA NA SAUKE HAKKIN RASHIN SANI A GAREKI, , , , , Akwana biyun da nake aiki a wanan wurin baifi sati biyu da fara aikin ba duk da ba fulltime nake zuwa ba sai yamma idan na dawo daga school in taso goma dare sai kuma gobe idan Allah ya kaimu zan fito. Amma hakan bai hana jikina canzawa ba don nayi wani itrn kyau na murje haskena na boye ya kara fitowa yanayina kanshi ga baki daya ya sauya a yanzu. Dole ina gilma mutane su bini da ido ga uniform din official din ya karbi jikina don bujena har kasa yake sai dan hijab da nake dorawa a sama.wanda iya fuskana zaka iya gani. Zan iya cewa a yanzu kam masha Allah zamana shagon nan don kudi baya katse muna gaskiya don akwai alwas da ake bamu don suturorin aikin mu kawai shine lissafi idan ko wani part na kaya sun shigo da kudin su. Anyi gulma anyi jininin hakan don ban isa wanan matakin ba tsakani da Allah sai manager yace wanan umurnin oga mai wurin ne dawa dani wanan part din. Don har kungiya akayi aka samu manager da zancen yayi masu bayanin irin umurnin daya samu daga samane dole sukai hakkuri suka saka ido don ba mai ikon zuwa wurin maishagon koshi manager da yake jin kanshi yana hura hanci idan yana gaban shi dole ya kwanta kasa don biyayya a gareshi. Bayerabe bai raina abin jifa dan uwan shi, kan dan abu kadan don hakan saida suka gwada sa,ansu gareni sai dai sun makaro don akwai tsarin Allah a tare dani badai mutum ba saidai Allah. Suit din aikin baki ke jikina na dufaro kamfani a cikin motana a karo na farko da Abdulhamid ya matsa min da hakan dole na koya na fara tuki har yakai ranan na fita school a cikin ta na dawo kuma na shirya zuwa wirin aiki duk a cikin motan. Umma kan tana jin dadin hakan ganin irin baiwan da Allah yayiwa yar ta irin wanda bamu taba zaton samun shi ba a rayuwa . Yau gashi Allah ya tarfawa garin mu nono Allah ya gwada mata yar ta a wanan matsayin da bata taba zato a garemu mu ba rayuwa ke nan inda ranka baka debe tsamani a wurin ubangiji. Na fito na kulle motar kamar yadda Abdulhamid yayi warning dina dayi akan in kula in dinga rufe kofa idan na fita daga ciki zan shiga wani wajen. Abinda nayi mafalki da darene na fara cin karo dashi duk yana cikin alamomin iskana zanga abu a mafalki washe gari kuma sai ingashi zahiri. Nasan akwai masu wanan baiwan da yawa a cikin al,umma duk alamane na farfarun mabiya ga mutum da wuya aiwa irin su asiri ya kama mutum irin masu wanan yanayin. Funke ne tsaye kamar dama ni take jira ina shiga sai gata da fara,anta ta nufoni tana washe min baki tare da fadin hello miss Sahiba. Na dan ce hi ina tafiya take fadin you about to let todaya sai kuma ta miko min hannu tana fadin good evening jere . Kallon hannun nata nayi na dan sake murmushi kafin na amsa mata da evening missFunke ina fadin hakan na girgiza kai na wuce zuwa sama inda office din mu yake yanzu. Da gudu ta kara biyo ni a dole sai tayi abinda tayi niyar yimin na taba jikina a lokacin saidai na fahinci hakan danaji muryan ta a bayana yasa ban dakata na haye zuwa office din da sauri na murda na shiga. Yeh tace tana bin kofan da kallo don yadda nayi mata din ban tsaya ba tana fadin i don dead wooo if i no touch dis gurl twoday. Ina shiga na gaida manyana dakr zaune office din kafin na hari wurin zamana ina addua a bakina lokacin nakai zaune takardun list din da aka tara min na shiga duba ina rubutawa . Kafin can naji rikici ya kaure a tsakanin manyan nawa na kudi akan lissafi har suna kokarin daga hammata a lokacin. Stop it na fada da karfi ina fadin ba haka aka bashi ba gaskiya yake fada an turo maida kudi kazane a ranan kaza da karfe goma na safe ya kuma tura a ranan banki har replay ya dawo gare ku a nan aka samu matsala kudin sun shiga cikin inda ba ayi niyar turawa bane mistakene. Tsaye sukayi kowa na kallona nace babban accounter din ya duba sakon wayan shi ai baka goge ba ko yana nan ciki ? Da sauri ya tura hannu cikin aljihun shi ya ciro waya ya shiga duba sakon daya shigo mai saiga bayanin a wayan shi ya dago kai da sauri ya kallo inda nake kafin ya sauke wani irin ajiyan zuciya ya dago kai ya kalli shugaban wurin ya mika mashi bayanan wayan shi. Lokaci daya suka dago kai suka kalloni inda nake tsaye nima na kura mashi ido ina sauraren abinda zai fada a lokacin. Fuskan su karara baiyane da mamaki a fuskokin su daidai lokacin na juya na koma na zauna tare da kifar da kaina saman taburina. Smart girl we have to be carefull with u in dis place Sahiba u are very talent girl . Ban dago kaina ba duk abinda yake fadi ina dai dan jin shi sama sama a lokacin na bude jakana na dauko maganin da Alfa ya ban in shaka idan naji alaman ciwon kai zai taso min cikin ikon Allah a hankali naji ya lafa min ba kaman yadda ya saba min ba. Sai office din yayi tsit bayan kowa ya natsu ya zauna manager ya shigo kan maganan a yadda ya samemu a office din kowa na aikin gaban shi yasa mamaki ya kamashi na ganin ba wanda ya damu haka ana fadin kudi sun shige. A kofa ya tsaya yana kare muna kallo a wurin kafin yace meke faruwa ya samu ba wani bincike da akeyi ? Ogan mune ya dago yana fada mashi cewa an gane komai anyi solving da taimakon Sahiba tayi muna lissafi har yadda kudin ya shiga. As how ya tambaya da mamaki akai mai bayani komai ya girgiza kai ya fita ba tare da yayi magana ba sai da muka dawo gida Abdulhamid ke fada min yana ganin fa zan bar aiki dasu abinda kawai ya fada min ke nan ba tare da bayanin komai ba. Nayi mamakin jin hakan amma kuma ban tambayeshi dalilin korana wurin su da za ayi ba kawai na fara tunanen abinda zanyi nan gaba a rayuwana. Jirgi Emerate ya sauke passenger daya dauko a Abuja daga cikin su harda Nazifa da yaran ta biyu daya yar shekara biyu sai karaman jaririyar yar wata biyu data haifa a lokacin. Yan gidan su ne da sukazo daga Kaduna don taronta suka tarbesu a gidan wani abokin baban su suka sauka saida suka huta washegari suka kama hanyar Kaduna. Bata sauka a gidan su ba gidan iyayyen ta ta sauka inda akai dafifi ana murna da zuwan ta don gabaki daya ta sauya ta kara zama wata babban mace yar gayu sai wani izza da isa takewa mutane. Yaran basa jin hausa basu ma yarda da mutane bata samu ganawa da mahaifin su ba sai washe gari da safe ta sakeshi a falon shi zaune. Yana saye da babban riga babu yar ciki a cikin rigan ya zauna ya baje saman kafet yana shan ferfesun kifi a gaban shi ta shigo da fara,an ta ga yaranta dauke a hannun ta. Fuska ya daure ganin yaran sai dai hakan bai hanashi ya tareta ba don an dade ba,a haduba a tsakanin su saida takai kasa take gashe shi ya amsa tare da tambayan ya hanya ta amsa da lafiya. Yake tambayan ta karatu tace ta hada a can bai tambayeta mijin ta ba kuma baiyi magana a kan haihuwan data samu a can kasan ba don bai iya tambayan ko daya don bakin hali irin nasa yana bakin ciki a zuciyar shi na hada iri da zuri,an daddy dayayi. Har zata daga take fafin baba gafa matan ka nan suna gaida kai ya kalli yaran a lalace yana fadin nagan su ai saidai kinsan bana maraba da zurian Aliyu gidana. Keda gwaggon ki kunja mun hada iri dasu don nacin uwarki badon ta nuna ra,ayinta kan son ki auri wanan dan iskan yaron ba ba abinda zaisa na hada zuria dasu a gida. Jikin Nazifa ne yai sanyi saboda maganan mahaifin nata ga yayan nata da take so kamar ta mutu a rayuwan ta hakama mahaifin su ya Abubakar yake kaunan yayan nasa sosai. Ganin yadda yanayin ta ya canza ya sake fadin nifa ban kaiki gidan nan aure don ki share kafa ki zauna har kina zuba masu yaya haka ba. Na fada maki tun farko cewa ina da manufa ga auren nakune shiyasa har na yarda da hakan idan bashi ba ba abinda zaisa in daukeki in mika wanan gidan da raina a duniya. Mijin ki da mahaifin shi sune ke son su ja dani a cikin dangi nayi alkawari kuma duk wanda yace zaija dani sai naga bayan shi a doron kasan nan. Shi Ali idan ba rigima ba har me yake takama dashi a duniyan nan me yake dashi meya tara da yake ganin wuyan shi ya isa yanka har zaice zaija dani akan dansa ya saba maki nayi magana shima yayi ? Wanan lokacin ta kasa rike kukan ta don Allah ya gani tana son mijin ta ita don ko huduban da yayi mata kancewa da wata manufa da yasa zata dan zauna a gidan nan ta dauka yanzu data hada zuria dasu komai zai wuya a zuciyan mahaifin nata ashe tunanen ta bai bata daidai ba. Yanzu ta fara shedawa gaskiyan mutane da suke fadin shi din maison kansa ne kuma mugune a cikin dangi dolene kowa ya bishi a yadda yake so. Yanzu kuma tasan ta kara sheda kowama ya shiga tarkon baban nasu sunan shi sorry ke nan do ko ita ya zama dole tayi taka tsantsan da yaran nan tunda har ya iya furta hakan a gaban ta yanzu. Muryan shine ya dawo da ita ga tunanen ta da yake fadin ina son ki sani komai dadewa sai na rabaki da gidan yaron nan nan gaba kadan idan na gama aiwatar da shirina a kan su. Wayan tane dake hannun ta ya shiga ruri shine kuma ya dakatar da mahaifin nata ga fadin abinda yake fadi a lokacin. Mijin tane yake kiranta a lokacin yaji saukan su don bai samu layin nasu ba sai wanan lokacin amma har wayan ya katse bata iya dagawa ba. Jin mahaifin nasu yayi shiru yasa ta mike zuwa don barin falon ranta a bace dakin mahaifiyar ta ta koma dake zaune ta hakince tana waya tana ba kawarta labarin dawowan yar nata. Kawar na fadin ai gara da kika nace aikai wanan hadin irin matasan da ko wace uwa ke burin taga yarta ta aura ke nan a duniyan nan ai yanzu. Saiga Nazifan ta shigo mata da kuka abinda ya dakatar da ita ke nan daga wayan da takeyi din lokacin tana tambayan yar nata hankali tashe abinda ke faruwa. Dakin ta shiga bata iya ba uwar nata amsa ba don kukan da yaci karfinta a lokacin ba zata iya furta komai a lokacin. Tashi tayi tabi bayan yar nata tana fadin ke lafiya ko mijin nakine wani abu ya sameshi baki fadi zaki dagawa mutane hankali haka ? Mama bashi bane fa ta fada a cikin kuka Abba ne yace baya son diyan nan don baya kaunan zuri,an uban su kuma in rubuta in aje zai rabani da mahaifin su nan bada dadewa ba. Zaune uwar takai tana salati tare da fadin abin na Alh har yakai can don wani bukata nasa ya mayar dake bazawara ko ya mayar maki da diya marayu don shi daukan ran wani a wajen shi ba a bakin komai yake ba. Nazifa din ta dago tana fadin mama zan tafi tunda har Abba ya iya fadin haka kada ya zo halaka min yaran nan don Abba zai iya ga yadda na fahinta yanzu. Dako na tona masa asiri a garin nan idan har ya taba min jikokina da Allah ya fara ban idan ma zasuyi abinsu shida mahaifin Abubakar ya tsaya iya su amma karya kawo gareku gaskiya ta mike da sauri yar tace mama dawo. Zuwan ki yanzu zai iya haifan wani matsala da zai kawo fitina don shima Abba din ya hau yanzu don Allah mamakiyi hakkuri kada ki masa magana yanzu kan hakan. Naji amma yasa duk abinda yake takama dashi nima din nasani don tafiyan duk gudane dani dashi idan yace zai taba min yaran nan yanzu sai inda karfina ya kare dashi wallahi. Abubakar kuma yayi kita bai shiga ba yasa ya bugowa hjy Addah waya yaji ko lafiya matar nasa bata daga waya ba. Don bai taba zaton wai gidan su zata tafi direct ba haka tunda yasa a gyara gidan su kuma tasani komai an saka masu sabo a gidan an kara gyara ko ina na gidan. Wani dalili ya hanashi zuwa tare da iyalin nasa shi sai karshen wata zai shigo ya don aikin daya taso mashi bayan sun gama shirin tafiyan su tare dole ya bari su fara zuwa kafin shi ya biyosu daga baya. Dauka tayi da sallama suka gaisa take tambayan shi aiki da iyalin shi sai mamakin jin hakan ya kamashi har yake fadin. Mommy ai suna Nageria kwana biyu ke nan basu zo bane nan ko baku da labatin zuwan sune ya tambaya cikin mamaki . Suna Nigeria fa kace yace kwarai kuwa mommy tun shekaran jiya suka taso kuma na tabbatar da tana kaduna yanzu haka. Lafiya har ta shigo garin bamu da labarin hakan yace shine abinda ke ban mamaki yanzu ke nan ai mummy don tasan na gyara gida don zuwan ta din ai. Kashe waya yanzu in kira mahaifiyarta muji idan tana gurin su yace tana can ma tunda bata zo nan gurin ku ba ai ya kashe wayan itama ta kalli nata wayan. Ta kira layin baije ba not reachable ake fadi lokacin ne kuma Faiza ta fito daga dakin kwanan su ta zauna tayi shiru tana jin abinda suke magana a kai. Ba wanan ne ke damun ta ba sai mafalkin da tayi shine ya tsaya mata a rai tayi shiru tana nazarin mafalkin a ranta . Hauwace ta kira sunanta ta dago tana fadin na,am Sahiba me kike fadi duk suka zubo mata ido suna kallon ta kafin suce wata Sahiba kuma kike kira yau ? Yau kuma kin tuno Sahibace a zuciyar ki ko me Sahiba kan ai sun manta damu yanzu sunci moriya sun manta kowa yanzu suna can suna bariki Nabila ta fada. Bariki kuma Fa,iza ta tambaya a cikin mamaki idan ba bariki ba me sukeyi a can lagos din dama ? Hjy dake jin su tana kokarin sake kiran mahaifiyar Nazifa ta katsesu da fadin uban wa yace daku haka wai ? Tayi sa,a a lokacin kiran nata ya shiga ta kara a kunnen su har aka dauka da hello ta amsa sai dan gaisuwa sama sama tace na bugo in tambayene idan su Nazifa sun iso gida ? Tace sun iso jiya da yammn nan gata kwance tana barci sai Addah djn tace Alhamdullahi dama mijin tane ya bugo yana tambayan isowar su din . Ashe ta taso ita bamu da labari Allah ya hutar da gajiya yaushe zata iso gida ke nan ta tambaya a karshe. Tace sai ta huta a nan an kwana biyu ko idan mijin ta yazo saita dawo hjy Addah tace amma ko in kunyi hakan bakuyi muna adalci ba gaskiya amma ba matsala zan turo yara su daukan min yaran nan ingansu ta kashe wayan ta. Zage zage hjy ta fara da fadin zancen banza zancdinnmmwofo ni Addah zata kira ta raina min wayau kan danta idan zatayi mulki ta tsaya iya danta kawai don ko yaran nan ba zan yarda su shige mata ba cewa da diyan Nazifa din. Me tace mama Nazifa dake kwance tana waye da kawayen ta ta tambaya ta dan dago tana kallon mahaifiyan nata sai ta fada mata yadda sukayi da Addah. No ba inda zasu tafi ta bari idan ubansu ya dawo mun koma zata gansu kowa ban yarda dashi ba ai yanzu ta fada tana komawa kwancen da take din da farko. Itama din dai Addah fada ta kamayi a nata bangaren tana fadin laiai ma yarinyar nan me take nufi da hakan wai da yin haka ? Amma zata dawo ai zata fada muna dalilinta na komawa gida ta zauna ga dakinta ta bari a nan sai kuma taja tsuki tana fadin shima dai daya turota zuwa gida ita daya haka don su basu raina dalili ai. Mommy yaran ba zamu gansu ba ashe yanzu don nasa ko anje daukan su ba zasu bayar dasu azo gidan nan dasu ba saidai idan yaya ya dawo kasan nan ke nan kuma. Zanje zanje duk abinda zamuyi muyi ta akan yaran nan kafin Alh ya dawo gidan na kuma ya aza min nasa jidalin ina zaune kalau. Wani irun nisawa Nabila tayi kafin tace solution dayane mommy kawai yaya ya kara aure zasu shiga hankalin su idan yayi hakan. Amma wallahu nasan idan kin dogara da wa yan nan jikokin ba zaki taba nunasu a matsayin jikokin na fanin yaya ba tunda kinga sun fara haka. Sun fasan yaran nan gidan nan ba wanda yasan su da ido saidai a photo kawai amma ta iya shigowa kasan nan dasu ta share kowa idan ba don shi din da ya kira yana fadin zuwan ta ba. Kinji ki da wani zancen shirme Abubakar din ne zai kara aure ko wanan din da yaya na samu yayi har aka kai haka din. Iskancin ta yayi yawa mommy haka ya dace ayi masu kawai don idan sun gashi da wata matar ai dole su kama kansu su daina kawowa mutane rainin wayau haka. ZAINAB IDRIS MAKAWA ANA DARA GA , , , , , , , , 4️⃣3️⃣ BY, , , , , , , , , , , , ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , , BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AL LATIF, , , , , , , ONLINE PAID NOVEL DON ALLAH YAR UWA KI BIYA KAFIN KI KARANTA DON NA KUDINE ALLAH, , , , Kwace nake ban da niyar zuwa aiki duk da yau ya kamata in fita full day nayi aiki dasu amma na gyara kwanciya naja bargona na kara rufa. Umma ce jin shiru ban fito ba yasa ta fito daga dakinta zuwa nawa tayi sallama ta shigo dakin ta sameni ina barcina hankali kwance ba niyar tashi a lokacin balle nayi shirin fita wirin aiki. Kwana biyu ke nan ban zuwa aikin ina gida idan na dawo tare dasu tunda Abdulhamid ya fada min hakan naga kafin su dakatar dani gara na dakatar da kaina aiki dasu din. Sahiba umma ta kira sunana tare da dan tabani kada na dan firgita ina falkawa na bude idona umma tace sahiba yau ba zaki fita aikin bane ga lokaci na tafiya ? Idona na dan lumshe ina fadin umma na daina aiki dasune don Abdulhamid ya tsegunta min kamar zasu koremu a ma,aikatan nan bada dadewa ba. Shiya fada maki haka na kada kai ta sake fadin koda zasu koreku ai zasu baku hakkin ku ko dkn haka ki tashi ki shirya ki fita bana son wani abu ya fito a bangaren ki gaskiya ki bari sai idan sun dakatar dake din tukun. Wani iri nayi da fuska saidai ba yadda na iya dole na dan yunkura ina fadin zan shirya na tafi umma tace Allah maki albarka na amsa da amin. Ban bata lokaci ba don ko banza naji umma tayi min abinda nake so a rayuwana don babu abinda yakai dadi ga yaron daya san kansa koda kuwa karamine yaji uwa ta saka mai albarka kamar yadda umma tayi min. Don yana karawa yaro karfin gwiwa da kuzari ya dinga aiki mai kyau a rayuwa koda kuwa babbane yana son jin kalman Allah yayi albarka daga bakin mahaifa. Wanka nayi na shirya a gurguje kafin in fito har Abdulhamid ya kira umma yana fadin ya ban fito ba kowa na wurin aiki don yau akwai baki da zasu zo muna ma,aikatan. Sai ga umma ina gaban mirrow ina shafa mai take fada min bata fita ba saida ta tsaya har na shirya na fito na samu ta hada min tea dole na zauna nasha na nufi wurin mota na tayar na dan bata wuta kafin inja in bar gida zuwa aiki. Tun daga nisa na gane gaskiya Abdulhamid don akwai alaman baki don motacin da naga iri daya a wurin an jera su har guda biyar manya manyan jeep sai walkiya sukeyi suna daukan ido. Haka na rabasu na shiga da sauri saidai na tsargu lokacin dana samu kowa a haraban wurin tsaye ga wanan matashin na kwanakin baya da akace shine wai mai wurin tsaye yana jawabi kowa yayi shiru. Baka jin komai sai sautin takalmana dake kara a lokacin na ratso wurin daga can baya naja na samu wurina tsaya ina sauraren abinda yake fadi. Turancin shima ko a cikin turawan abin kallone farine sol har yafi ya mustapha fari da kyau da komai saidai tsawone bakai mustapha din ban din shi mustapha har ya dan duka kadan don tsayin shi . Wanan din kam sune tashin falo tutube da remote na gaskiya don baima san wani abu zafin rana ba ko talauci kila a rayuwa. Ba wani abu yake fadi ba sai irin yadda ake sakaci da aiki a wurin ana samun matsala yake nuna baci ranshi da hakan sai a karshe da yace zai dauke wasu daga nan ma,aikatan ya kaisu sabon wurin da aka bude su koma can. Sai kuma ya kara da godiya kan yadda wasu ke aiyukan su tukuru musanman kananan ma,aikatan wurin su yafi yabawa ya kara da cewa su kara karfi ga aikin su yayi hakan ne don a rage zaman banza a gari tafe suka fara yi mai Allah bai ban ikon taba mashi ba ni a lokacin . Don na kagu da tsayin saidai ina dago kai yayi daidai yana kallon inda nake tsaye a takure din cikin shiga na na islama kamar kullun don zuwa kaduna a yanzu ya kara haska min hasken musulunci sosai a zuciyana ba kaman da danake sakaci da ibada ba don talla duk da alokavin ma ina sallah gaskiya. Don umma tana iya kokarin ta wurin haska muna ibada ko lokacin shiyasa bamu sha wani wuya ba a can da mukaje don mun koya a wurin ta. Sallaman mu yayi kowa ya fara tafiya ana kuskus da zantukan da yayi a wurin musaman na kara albashi da yayi alkawari gako wani ma,aikacin wurin har masu gadi don ya yaba masu sosai lokacin jawabin nasa. Nima gyara dan jakar dake kafadana nayi a lokacin naji muryan manager yana tsayar dani ta hanya kiran sunana naja na tsaya yake fadin in sameshi office din shi suna tsaye tare da bakin nasu lokacin. Yes sir na fada na juya zuwa office din mu na aje kayana da yar jakana na fito na zuwa office din su zuciyana cike da zargin dalilin kiran da yake min da safen nan. Har zuciya ta fara raya min cewa shike nan zancen korana din ya baiyana ke nan a yanzu tunda manager ya kirani har office din shi. Na isa na dan tsaya daga waje duk da nasan zasu iya ganina daga ciki tunda glass ne wurin ko wani office din dake cikin wurin. Shigo mana yace min daga ciki na dan tako na bude na shiga da sallama sabo da yin hakan ko ina zan shiga babu kowa a office din sai shi daya yana hada takardu a tsaye na karaso ciki. Kara gaidashi nayi ya amsa yana nuna min kujera in zauna nakai zaune din cikin mamaki kafin ya dago yace dani congrat miss Sahiba. Na dago kai da mamaki ina kallon shi don ban san abinda yake min murna akanshi ba a lokacin sai naga ya miko min wani farin takarda yana fadin. Nayi maki murna sahiba zaki bar wanan aikin damu na dan lokaci duk da dai ana tare din saidai zaman ki ba zai kasance nan na sidin din da kikeyi a yanzu ba. Don idan oga yana gari zaku kasance dashi keda Adnan na dan lokaci don, kun san shi ba mai zama kasan nan bane sai udan yazo bai kuma yin fiye da sati daya ya koma sai dai idan wani abu ya tsayar dashi. Saidai ba wani aiki mai yawa bane ke zaki koma a matsayin sakatariyan shi adnan kuma PA din shi zaku fara aikin ku a goben nan ko ince yau da company n an namu zaku fara zaiyi aiki damu idan kin duba takardan gobe kuma haka har jibi. Shiru nayi ina jin wanan bayanin nasa kamar a mafalki yake min wanan bayane din don gaba daya ban san me zance ba a lokacin. No kada ki shiga damuwa Allah ne ya zaboki ya baki wanan daman don kin cancanci hakan gaskiya mun yaba kwarai da irin kokarin da kike muna wajen warware muna matsalolin da sukaso taso muna har sau biyu muka samu saukin komai daga bangaren ki. Wanan shine ya bamu daman karfin zaboki daga cikin ku don ki taimakawa masana,antun shi da yake dasu a kasan nan . So congrat onces more again da wanan daman da kika samu da kowa yake fatan samun shi a rayuwa son zakiyi aiki da babban mutum a kasan nan kuma matashi. Innalillahi na fada don ga baki daya kaina ya daure ga abinda duk yake son fahintar dani a lokacin. Yanzu suna office don Adnan har ya tafi sun soma aiki a office din shi ko tun dazun a hankali na dago kaina na dan kalleshi zanyi magana ya sake fadin . Idan kina da wani bayani saiki bari daga baya zamu zauna muyi maganan daya dace amma yanzu akwai aiki sosai a gaban ki. Mikewa nayi a hankalin jiki ba kwari kamar kazan da kwai ya fashewa a ciki na fara takawa sai kuma naja na tsaya wuri daya tare da dan juyowa na kalle shi na bude baki da zuman tambayan shi. Ya dago yana fadin you can go now nasan yanzu sun fara aiki ko tundazun bai kai ga rufe baki ba sai ga wani ya shigo yana fadin wai ance ina new sectrery din take tazo ta fara shigar da komai. Muka kalli juna ni da manager kafin naji yace gata tafe yanzu ta tsaya ina mata bayani ne dole nabi bayan shi zuwa inda suke. Daddy ya jijiga kai bayan hjy Addah ta gama mashi bayanin komai yana sauke nunfashi kafan shi ya mike daga yadda yake zaune a kasan. Tsawon dan lokaci bai iya furta komai ba sai can yace yanzu me kike son nayi akan zancen nan ko kin manta da zancen mu na baya ne da mukayi lokacin da kika zo min da zabin yar Nuhu a matsayin matar da moddibo zai aura nace ki dai sake dubawa kikace ai itama din yar gidace ko ban son zumuncin ku da dan uwan ki ya kara kulluwane daga haka na goya maki baya ban kara furta komai ba. Don haka yazu ma runda a gidan kawun modibbo take zaune ai nan da can duka gidane sai ta zauna mana menen ? Wani irin kallo hjy din tayi mai na mamaki don jin abinda ya fada tasan zancen yana da ma,anoni masu yawa ke nan a zuciyan shi. Can yace dama shi modibbo ya kirani ya fada min komai na bashi hakkuri don haka kuma ina nason ku fita zancen ku kyale su a zuba masu ido aga me suke nufi da hakan. Sai lokacin hjy ta dan sauke ajiyan zuciya don jin abinda daddy din ya fada ta koma cewa saidai yaran da ba wanda ya sansu a nan bangaren fa Alh ? Murmushi daddy ya sake yana fadin yara ai dole komai dadin dadewa a kawosu gidan nan idan kunyi hakkuri da hakan. Don ta kan yaran ake son bi a aiwatar da nufin da ake kokarun aiwatarwa a kan mu yanzu nasan waye Nuhu nasan duk wani shirin shi na shirme da jahilci Kai innalillahi hjy ta fada na dauka wanan hadin zai kawo zaman lafiya a tsakanin ku idan anyi sai gashi kuma hakan yana son kawo wani babban matsala kuma. Daddy bai tanka ba yayi shiru kamar mai nazarin wani abu itama dai shirun tayi na dan lokaci kafin ta mike tsaye ganin baida niyar kara fadin wani abu kan zancen. Fitan mommy falon daddy din yayi daidai da shigowan hjy karima falon itama tare da yarta na goye ta zauna tana gaidashi. Ya amsa yake tambayan Amira ya jikin ta tace da sauki dama ai itace tajawa kanta ciwo idan ta tashi fitinar tsayan ta wai wani sabon iskanci Sahiba take kira tun wayewan garin nan data tashi sunan Sahibane a bakin ta. Sahiba kuma ita har yanzu bata manta da zancen su sahiba a rayuwan ta ke nan daddy din ya tambaya. Ai gaba dayan su basu manta da itaba a rayuwa kullun zancen su dai shine yaushe Sahiba zata dawone mami sai na masu tsiya suke barin zancen ta a gidan nan. Shiru daddy yayi wani abune ya fado mai a rai game da su sahiba dai wanda ya kasa saita zuciyar shi a kan hakan. Ban taba sani ko zaton akwai office a wurin ba haka kuma ban taba sanin cewa wanan wurin haka yake da girma ba sai wanan ranan. Ashe duk wunin da mukeyi a cikin sa iyakar mu inda aka ajemu ne don baka zawa wani part don kanka sai idan an mayar dakai wurin yasa bamu san kan wirin ba ko dai nice da ban damu da komai ba sai abinda ya kawoni ban sani ba. Wanda yazo kirana ya fara shiga ina biye a bayan shi muka shiga office din suna zaune kowan su ya kurawa computer dake gaban shi ido a lokacin. Na shigo na gaida su da aiki ba tare da sun dago ba suke amsa min gaisuwan mutumin yayi min nuni da wurin zama nakai zaune daga barin shina dama inda suke zaune. U are wellcome dayan ya fada min yana miko min takardan dake saman taburin shi na karba a sanyaye yake fadin nabi bayanan dake ciki na turawa chief sakon baiyanan dana gani a cikin takardan. Hankalina na kwantar na fahinci me ake nufi duk bayan kawai zan tura a dayan suein shi shine abinda zanyi nan take na fara turawa kafin dan lokaci na gama na dan dago da zumar fadin na gama idanun shine akan yadda nake aikin kamar wace ke tsoron laptop din ko kyama haka nake dannawa na hada komai har na tura mai. Kaina na dukar kasa yace cikin dan saurin maganan shi kin gama turawa na kada mashi kai alaman eh ya kara turo min wani takardan kuma aikin dai da muka wuni munayi ke nan har akai sallah azahar na dubi lokaci a wayana dake aje saman table din koshi wayan umma ne da nake amfani dashi duk ya tsufa yaji jiki sosai. Tsab na mike tsaye daga zaunen da nake suka dago kai lokaci daya suna kallon inda nake tsaye din asalat kawai nace dasu ina kokarin fita daga wajen kujeran. Sai lokacin ya dago kai ya kalleni jin abinda na fada kafin kuma ya kalli agogon dake daure a tsintsiyar hannun shi fari da gashin jiki yaiwa addo dasu ko ina. Dan magana yayi a cikin muryan ruwa naji wanan yace dani daga can na wuce restuaran din wurin akwai abinci an hada naje naci kafin in dawo. Ban iya furta komai ba na fice daga office din direct dakin da aka warewa mata don hutawa na tafi ban dakin na nufa nayi sallah kafin na fito na tayar da sallah har lokacin komai da nakeyi kamar a mafalki nakeyin sa nake gani don ban iya gaskanta hakan ba. Na dade zaune ina tunane barkatai ga umma ba waya a hannun ta balle na kirata in fara sheda mata halin da ake ciki kan na dawo haka dai na daga na koma office din ban samu kowa a ciki ba lokacin duk sun fita basa ciki. Hakan ya bani daman karewa ko ina kallo na dan lokaci kafin na mayar da kaina a waya na dauko earpiece dina na makala na fara shan free kira,a dana kan sha. Na daga kaina sama na mayar da kai bayan kujera na mike ina bin karatun a hankali ko zanji sasauci a zuciyana lokacin ga sanyin AC da aka sake yana ratsa ko ina na jikina sai kamshi ke tashi a lokacin. Har suka shigo banji motsin su ba saboda bakon yanayin dana tsunci kaina mai kama da mafalki a wurin har saida wanan din mai mun magana ya dan daki table din dake gabana na dago da sauri ina bude idanuwana da suke a lumshe kamar barci na son daukana a lokacin. Da sauri na kai hannu na cire wayan a kunnena na mika kuma ina kashe kiran da nake saurare din ina gaida su da dawowa. Wayan ya kara kallo karo na barkatai yana kaiwa zaune a mazaunin shi har lokacin bai magana da kowa a cikin su bamu muka bar wanan wajen ba sai gab da magariba. A gajiye na isa gida daga shiga na wanka na fada nayi na fito na tayar da sallah ban daga wajen ba saida nayi isha,i na fito daga dakin. Umma na sama falon tana sallah na samu wuri na kai kwance ina jiran ta idar ina gaida ita ta amsa min tare da tambayana ya aiki ? Saida na lumshe ido na dago daga kwance ina fadin umma idan na fada maki abinda nake ciki yau ban san ya zaki dauki zancen nan ba. Cikin damuwa take cewa dani Allah yasa lafiya ba wani abin bane ya faru kuma ba Sahiba ina jin tsoro da fargaba akan ki ako wani lokaci. Eh to umma abin kan da fargaba kuma da mamaki ace duk manyan matan da muke aiki tare sai nice kadai a yau na samu karin girman da ko mazan wurin basu samu ba shine abin mamaki a wurina kuma yake damuna. Nan dai na labarta mata komai daya faru ban raga komai ba na fada mata duk yadda abin yake har aikina. Shiru umma tayi na dan lokaci kafin tace dani Abdulhamid ya kamata yanzu mu nema akan wanan maganan idan ba wani makarkashiya aka kulla maki ga hakan ba. Amar ta kwalawa kira ya firo ta turashi wajen Abdulhamid din anyi sa,a yana gida bai fita ba ranan zuwa asalatu wurin daukan karatun da yake zuwa da yaran shi. Mikewa nayi zuwa kitchen na dan zubo abinci kadan na fito na fara ci ke nan yayi sallama part din umma ta bashi izzini ya shigo. Bayan sun gaisane take fada mai duk abindana fada mata yana jijiga kanshi har tagama fada mai komai yana sauranta kafin yace. Hakane umma komai data fada maki tabbasa haka ya faru ba kuma komai yasa haka ba sai cancantan Sahiba. Akwai masu takarda a hannu da suka karanci wanan fanin amma kuma sai Allah ya zabo sahiba a cikin duk dako ilimin nasu saboda gaskiyan ta da warware matsala irin nata tabbas nasan wanan shine kawai dalilin ba wani abu ba. Aikin nan alheri ne ga yar ki dake dama mu baki daya haka kuma sai kinyi hakkuri sosai kin sa yarda da Amincewa ga tarbiyan da kika ba yar ki a rayuwa. Don aikin ta yanzu zai iya kaita ko ina da Sha,aban yake a vikin kasan nan don gyin aiki tare dasu idan har bukatan haka ya taso. Jin abinda ya fada yasa na dago kaina daga cin abincin danake dan cakula da cibi na kasa cin abin kirki ina sauraren su lokacin. Barin gari akan aiki ita daya Abdulhamid yace kwarai kuwa don zasu iya tashi daga garin nan zuwa arewa ko kudu duk aikin zai iya kaisu wanan wuraren . Ina sam hakan ba zai yuyu ba gaskiya aiki idan ya wuce fadin lagos din nan gaskiya saidai a bari yaushe zan bar yar marainiyar Allah tana wanan gararin don kawai rashin gata. No no no anty ba haka bane ina sam na tabatar kuma na yarda wanan ba zasu cuta mata ba a nan Allah ma ba zai yarda wani abin kyama ya faru maki da yarki ba. Ki yarda dani don Allah ina rokon ki ki bar yarinyar nan rayi amfani da daman ta data samu a wanan lokacin wanda zai kawo mata cigaban rayuwa idan Allah ya yarda. Shiru umma tayi na dan lokaci tana nazarin kalaman shi kafin kome ta tuna tace na yarda dakai da imanin ka Abdulhamid don na tabbatar ba zaka taba barin yarinya na ta cutu ba ga hakan. ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , ANA DARA GA, , , , , , , , , 4️⃣4️⃣ BY, , , , , , , , , , , ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , , , , , BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AL KHABIR, , , , , , , ONLINE PAID NOVEL YAR UWA DON ALLAH KADA KI KARANTA MIN IDAN BAKI BIYA BA, , , , , Washegari a Ekoyi muka wuni ga wani girma da haba haba da mukr samu wurin mutane don kawai muna tare dasu da muke samu . Ban san kowa ba a wurin sai Adnan da muka fito company daya dashi koshi dan zaman aiki wuri dayane ya hada mu dashi ba wani sani nayi mai ba. Ban yarda idan lokaci yayi na ibada duk aikin da mukeyi zan aje naje nayi sallah sai suma masu sallah a cikinsu su mike zuwa yin sallah din. Aikin aikine kan tukuru don babu magana ko wani abu bincikene kan kayan da aka shigar da kudin su bisa riban da aka saka a sama. Muna gamawa da Ekoyi din wurine na sayar da babura masu kafa biyu sabbi fill din su a leda suna cikin kwalayen su na part. Magana suke a tsakanin su ganin an gama yasa na mike tsanman na suri jakkata wanan Felix din dake dan min magana yake tambayana ina zanje nace gida. Ba zaki jiramu ba nace ina saurine kada mahaifiyana taga na dade ban dawo gida ba wow babban yarinya dake maman ki zata tsaya maki fadan baki dawo gida da sauri ba ? Felix ya ambata daga inda yake ba tare daya juyo ba yake fadin ka dauketa ka kaita gida ka fada mata gobe zamu hadu a gidan mota na ebony dake idi,eroko kusa da bakin titin dake kallin custom office . Tsayawa nayi ina kallon su gaba daya din ko lokacin ina yawin tallana ai sau daya naje wanan unguwar ban kara marmarin komawa ba tun lokacin. Gani kamar ban gane ba Felix yace karfe takwas daidai in fito in jirasu a main road na Apapa zasu daukeni a wurin. Nace OK Sir na juya na fita na barsu ciki titi na nufa duk a gajiye nake ina neman abin hawan da zai kaini gida don bada motana nazo ba dama taxi na dauko drop. Na dan jima wurin a tsaye kafun su fito daga cikin comoany sunyi mamakin ganina a wurin Felix din ne dai ko wanan karon ya tuko har inda nake yana tambaya bada mota nazo bane ,? Nace drop na dauko zuwa nan din shiga muje yace dani yana bude min dayan gefen nasa na shi muka kama hanya. Ba abinda ke tashi cikin motan sai kidan turawa shi kuma yana bin sautim da wakan har muka dauki hanyar da zai hau damu titi da kyau. Motan yayi shiru sai shi dake bin wankan jefi jefi idan an kawo inda yake jin dadi kunsan kafirai da son wanka. Na tare da ya kalloni ba naji yace miss sayiba don't you know dat you're now different than before ? Why are u not used your car ? Bai kallo inda nake ba saidai jin ya kira sunana nasan dani yake magana lokacin yasa na dan juyo ina kallon shi. Our oga don base with you today. Don't ever repeat dis mistake again when we are going on mision, he's not happy with d way he is seeing your behaiviours. Saida naji yayi shirune nace dashi iam sorry i will not repeat it again but what have i did wrong in dis ? Murmushi yayi kafin yace baki san waye guy din nan bako shi mutum ne mai kirki kwarai baida kyatan na kasa dashi ko kadan. Shi mutum ne mai sakakwn hannu ga duk wanda yake tare dashi sai dai kiyi hankali don akwaishi da kaifin basira sosai da ilimi dan adam kallo daya zai maka ya fahinci rayuwan ka da abinda kake ciki. Don haka ki kara kulawa ki kuma ci gaba da kawar da kanki ga komai da yake kiyi aikin daya kawo ki nan tare damu baya son yaga baka da tsabta don wanan yana hadashi da mutum gashi da son kamshi aikon gashi dai shi yadda yake ko na gyada kai yace ki kula da abubuwan dana fada maki din. Jin yayi shiru nace nagode na kawar da kaina gefe ina cigaba da tunanen dan zancen daya fada min din. Ba komai nake tunane ba sai shi din waye wai da yake da wanan dukiyan haka mai yawa a cikin kasan nan. Gaskiya nasan kabila suna da arziki fiye da yadda muke tunane a Nigeria din nan sai dai ai yayi karami da mallakan wanan dukiyan haka. Muryan Felix din ne yake fadin kin san shi haka ya taso a cikin daula uwarshi hausace yar erewa sai dai yanzu ba zakice ita din hausa bace don yanayin larabawa da dabiun nan daya shige mata gaba. Ance mahaifin shi dan nan lagos shi saidai shima mahaifin nasa ya gaji dukiyan shine a wurin mahaifin shi kamar shi. Sunyi aure ne a can lardin labawa inda suka hadu da ita taje karatu shi kuma harkokin business din shi sun kaishi can . Kafin ya aureta yana da wasu mata yan yaren nan lagos din saidai bai taba haihuwa ba sai haduwan shi da itane Allah ya basu haihuwa. Haihuwan su biyu kafin shi basu tsayawa kinsan mutanen mu da canfi don har sun fara camfa mahaifin cewa da diyan shi dukiyan shi ke habbaka. Sai gashi sun haifi Sha,aban ya tsaya har ya girma yakai haka yana da kanwa mace daya sai yan uwa dake karkashin shi a yanzu. Duk da har yanzu yan uwan mahaifin shi ba wani shiri ke tsakanin su dashi dalili uwarshi ta kasance ba yar yaren mahaifin shi bane sai kuma kiyayya irin wanda ake samu gun yan uwa wani lokaci duk da kyautatawan da yake masu din. Daga nan yayi shiru ya barni da tambayan kaina ashe dama haka yan uwan uba sukan kasance a ko wani bangare ke nan ba mune kadai keda wanan matsalan ba ashe ? Saidai kinga duk wanan harkan da yakeyi a nan din yafi samu a can kasashen larabawan don sun fimu dukiya mai yawa fiye da nan din. Yanzu ma wanan aikin da mukeyi an samu matsalane da wasu manajojin dake son durkusar dashi a wasu bangaren yasa wanan binciken ya taso a haka yanzu da can bai haka a wuraren sana,an shi ai. Hango layin mu da nayi nake cewa dashi your right hand idan kaje wancan jection din yace ashe baki da nisa da ma,aikata dama na gyada mai kai don kaina daya daure a lokacin Allah Allah nakeyi na sauka ko zan samu dan sa,ida a zuciyana. Yana kawowa kofa mu nace yayi ina kokarin daukan jakata tun kan ya kashe motan nakara mai godiya na bude na fito yaja motan shi ya tafi. Watan su biyu a kaduna koda wasa bata taba lekowa kancewa zata gaida mahaifan mijinta ba ko zata kawo yara su gansu. Tun abin yana damun hjy Addah har ya koma bata mamaki akarshe kuma ta watsar da zancen kada ya zama mata ciwon zuciya. Har Allah yayi dawowan Ya Abubakar kasan bai fadawa kowa dawowan shi ba saida yayi kwana uku a cikin gidan shi yana hutawa kafin ya tako zuwa gidan su da safiyan jumma,a sai ganin shi kawai yan gidan sukayi suna karyawan su da safe ya fado masu. Da murna suka tare shi don an dade ba,a hadu ba har yasamu wuri ya zauna aka shiga jero mai abincin lokacin hjy karima ta shigo tana mai sannu da zuwa da yaranta baki daya gaba daya yaga sun girma mai lokaci guda sunyi tsawo ga ganin shi. Har sun gaida shi sun mashi sannu da zuwa zasu wuce Amirah tace ina anty Sahiba ? Gaba daya falon sukai tsit sabanin shi da gaban shi yayi mai wani irin faduwa lokaci guda don gaba daya ya manta da zancen wasu iyalin su sahiba a lokacin. Sai wanan zancen da yarinyar nan tayi yasa abin ya dawo mashi a rai baki daya lokaci guda sukuma sauran na fadin. La,ilah ji yarinyar nan ashe bata manta ba don tasan cewa shi ya tafi dasu lokacin yasa ta tambaye shi su a yanzu. Ta dauka suna wuri dayane yasa ta tambaya yanzu din hjy ta fada ya dago yana fadin basu zo garin nan bane tun lokacin mommy. Suzo wurin wa mu ko waya bamu tabayi dasu ba tun wanan lokacin don gabaki daya ma mun manta dasu wallahi. Take yanayin shi ya sauya yana fadin kun manta dasu hjy kun manta dasu fa mommy ya fada cikin manaki ? Au su basu nememu ba sai mune zamu zauna neman sy a kullun ? Daga inda hjy karima take tsaye tace dashi wanan ce ma mai karanbanin tunawa dasu ita da fatima can ba,a rasa ba. Innalillahi ya fada yana shafo kanshi daga sama zuwa sama a cikin damuwa irin na tashin hankali ya mike tsaye daga inda yake zaune din. Ina kuma zaka ya koma ya zauna hjy Adda tabi dan nata da wani irin kallo na ban mamaki ganin yadda duk ya rikice lokaci guda kan zancen su. Ko ni wani lokaci dan sabon da mukayi dasu zaman mu dasu a nan gidan nakan ji kewan su sosai sai dai baka da wani alaka da mutum kaga duk yadda ka damu dashi dole ka kyale. Hjy karima ce ke fadin wanan zancen daga inda take tsaye kafin ta juya tana fadin ai Amira kan naga ranan da zancen sahiba zai fita zuciyar ta gidan nan. Fitan hjy karima da yaran ta ya dago yana fadin gaskiya mommy ba a kyau ta ba da baku nemi mutanan ba sai su dauka wani abu hakan ai. Kai yaya kaci abinci ka karya ka tsaya kana zancen wata sahiba can da bata ko damu da kowa ba dama fa zaman dole sukeyi a nan dama. Ke kikasan abin fadi ya dago kai yana kallon nabila din dakw magana kafin yace zancen yan uwan ki akeyi bana wani ba ke idan haka ya sameki suna a matsayin ki zasu kyaleki ne ko me ? Ka tafi gidan kane ko nan ka sauka mommy ta tambaya tana kawar da zancen da yaran keyi a lokacin don kada maganan yai nisa. Don Allah ya gani ita dai bara son zancen ganin mutanen nan ta bangareta gara aje can ayi duk wace za ayi idan wani ya gansu ba ita ba. Ta sake tambayan shi da fadin kakai kayan ka gidanka ne yace tun shekaran jiya ai nake garin nan ya fada har lokacin fuskan shi a daure. Ba abinda yake tunane a zuciyar shi sai yaya muke rayuwa a can tunda ya barmu ne ga bai samu nemawa ko Amar gurbin karatu ba ya tafi. Yasan ko ba zamuyi azancin cewa muci gaba da kararu ba tunda shi bai dawo gare mu ba balle ya taimaka muna da hakan. Abinci fa ta yaya muke samu yasan wanan ba wani babban matsala bane don zanyi talla in tallafawa rayuwan mu yasan da wanan din. To amma abinda ya daure mashi kai shine, idan shi baya kasan daddy fa me zaisa daddy yafita zancen bayin Allah nan haka ? Shifa abubuwan nan suna daure mashi kai kan game da daddy akan wanan zance wani lokaci anya kuwa koshi ma din ya gano hakan ne don yana kwararen dan sanda irin mahaifin shi. Muryan hjy ne ya katse shi tana fadin ke nan Nazifa da yaran suna gidan ka yanzu haka ke nan uwar nasu ta tambayeshi tana mai tsura masa ido don son jin amsan da zai bata. Ban fada mata na dawo kasan nan ba kuma bazan fada ba sai idan taji ga wani kamar yadda tayi maku itama yana fadin haka ya mike tsaye. Kallon kayan abincin da aka aje a gaban shi tayi kafin tace ka zauna ka karya kafin ka fita shima ido ya saukar ya kalli abincin kafin ya ja dan tsuki yana fadin ba zan iyaci ba mommy. Akan me ko ka karya a gidan kane ya kada mata kai alaman a,a yana fadin ban ci komai ba tunda na dawo kasan nan. A razane ta mike tsaye tana fadin bakaci komai ba mekakeyi ka tsaya haka da cikin ka bakaci abincin har tsawon kwanakin nan modibbo ? Kawai bana jin cine mommy ai wanan ba komai bane idan akwai diyan icce sai mutum yaci na dan lokaci. Zancen matar ka kana ganin hakan zaifi ba zai jawo matsala gareta da mahaifinta ba kasan halin yaya Nuhu da daukan zafi da gangan. Mommy ku wanan ya dama ni bashine a gabana ba yanzu zancen Nazifa kuma banyi fada da ita ko wani sa,insa ba amma ta zabi taci wa iyayyena mutunci da yan uwana. Don haka mommy na rokeki da kada ki fada masu zancen dawowana don girman Allah ya hada hannayen shi a wuri daya yana rokon ta arzikin hakan. Yana fadin haka ya juya zai fita Nabila tace wanan shine daidai ai mommy wallahi ayi maganin ta ta gane kuren ta zaifi. Baidai juyo ba duk dayaji abinda kanwar tashi ta fada haka yasa kai ya fice yana jin zuciyar shi tana masa kuna. Gidan sa ya koma ya kulle kanshi a cikin dakin yana faman tunane shi yanzu ma da wani ido zai kallemu yacewa wayan nan mutanen me a yanzu shekara nawa yanzu rabon su da su waige mu an dauki lokaci mai tsawo haka da wani ido zai kalli umma da yaranta yanzu. Yayi shiru taci gaba da tunane can yace bayan wanan shi daddy dake kasan meya hanasa neman su ne ? Anya kuwa ba wani abu a boye da daddy don shima ya boye kan wa yan nan ahalin dake cikin ukuba da gararaba a cikin duniya. Duk dai yasan a yanzu basu saura gararanban gidan haya ba tunda ya sama masu wurin zama ya sani kafin ya wuce . Kuma yana da yakinin cewa ba zasu daga, daga inda ya ajesu din ba in bada wani dalili mai karfi ba da zaisa su bar wurin. Bai sake fitaba a ranan sai washe gari da yamma ya shirya ya fita zuwa wani super market don ya dan sayi abubuwan bukata na gida. Tunda ya tunkaro wajen da motar shi samarin dake tsaye suna hira suke satin motar tasa har yazo kusa dasu ya wuce. Daga cikin su dayan ne ya sake murza idanun shi ya duba da kyau idan ba idon shi ke masa gizau ba tabbas modibbone a motan yake tukawa . Da mamaki ya bishi da kallo tare da fadin yaushe guy din nan ya dawo garin nan ? Abokan shine suke tambayan shi ko yasan shine yake fadin mijin Naziface fa datake aure suke zaune a kasan waje dashi. Kai mutumina kace zaka dauko muna dani ke nan ashe wata rana mu faso gari a cikin sa yace ku bari kawai aisai na dana motar nan kota halin kaka duk shi din jan wayane shegen kanshine sosai shima. Har ya sawo abinda zai sayo din ya dawo ya wuce su a wurin bai shedama akwai mutane a aurin ba lokacin. Sai bayan sati dayane ya shigo cikin gida ya samu yar nazifa na kuka yake lalashin ta kafin can yace dasu ke nazifa ashe mijin ki ya sawo wata kafiran motane da zai dawo ? Da mamaki kowa ke kallon shi har mahaifiyar su yace Allah wata rana zai ban motan nan in dana ta don nima na faso gari zama cikin salebiritin garin nan. Mahaifiyar nasu tace kai ina kaga mijin ta a garin nan da naka shirmen kuma yace kai ji mama fa ? Shi modibbo din ne kuma ban sani ba ko me sau nawa ina haduwa dashi saidai kin san sbi da ahegen daukan kai yasa nima nake kyaleshi . Sai dai mota kan saina dana motan nan nasa komai jin kan shi kuwa don nayiniyar hakan a zuciyana. Na shiga ukku modibbo fa dan wajen Addah kacw ka gani yace tun yaushe nake ganin shi a garin nan. Hankalin Nazifa da uwar yai mugun tashi tana fadin mama ya dawo kasan nan ban sani ba ke nan ko me mama ? Bar dan iska daga shi har uwar tashi Addah idan ma wani makarkashiya suke kullawa ga hakan zasuyi kunya indai nice. Don wanan auren mutu karaba dake dashi a duniyan nan har udan mashi din zubairu ya gani din. Kira layin sa mu gani idan zai shiga mu tabbatar da zancen zubairu din idan da gaskene don shi ya faye shirme wani lokaci. Nazifa ta dauki wani layi tana kiran shi sai kiran ya katse don yayi blocking din layin ta ga baki daya ba zata sameshi ba lokacin idan bashi ta cire hakan ba. Kira barkatai yana mata haka ta kalli uwar tana fadin kiran yaki shiga umma kanwarta dake gefe tace da ita. Mama a gwada kiranshi a layina idan zai shiga mu gani ana saka layin aka kira sai kiran ya shiga saidai bai daga kiran ba har ya katse. Duk sun zuba mata ido ta dago tana fadin kiran ya shiga saidai bai daga kiran ba a lokacin don dama yana suspecting din kiran nasu ne ya shigo mai don ba mai kirashi da baida layin shi a wayan shi. Gashi kuma ba kowane yasan da yana kasan ba da zai kirashi washe gari kuma ya nada ya tafi abin shi bai dawo ba ko mommy bata san yayi tafiya zuwa Abuja ba wani aiki a lokacin. Washegari bayan sun gaji da zancen ne suka kira layin hjy Addah kira uku bata daga ba don in takirasu haka suke mata sai anga dama a daga mata kiranta. Gashi ta rama kuma sunajin haushin hakan da tayi suna fama zunduma mata zagi sai gashi ta daga kiran. Suka gaisa sama sama kafin suce da ita ashe moddibbo ya dawo garin bamu da labarin hakan hjy tace dasu oh baku da labarin dawowan shi ashe yanzu ko ai sati uku yake nema a garin nan ke nan. What sati uku Addah amma daga ke har dan naki baku da mutunci ashe haka in ba aure kaddara bane mai zaikai Nazifa auren modibbo har kuso ku rainawa mutane wayau haka. Kashe wayan mommy tayi don zuciyan ta ba zai juri jin wanan zagin da hjy din take mata ba alokacin . Don zata iya ramawa hakan kuma zai haifar da matsala sun yi ta kiranta taki daga wayan sai da suka hakkura suka kyaleta. ZAINAB IDRIS MAKAWA ANA DARA GA, , , , , , , 4️⃣5️⃣ BY, , , , , , , , , ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , , , , , BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AL HALIM, , , , , , , , ONLINE PAID NOVEL YAR UWA KADA KI KARANTA IDAN BAKI BIYA HAKKINSA BA DON NA KUDINE, , , , , , , , Allah ya nufa na zana exam dina na karshe a makaranta saura jiran jerabawa a garemu da fatan alheri yanzu kan sai kuma godiya a wurin ubangiji mai komai mai kowa daya nufeni da gamawa lafiya ba tare da samun wani tangarda ba a cikin karatun. Yanzu fadi barnan lokaci shiyasa ake son iyayye su dage sosai a wurin yiwa yayan su addu,a musanman ke uwa don addu,an ki karbabane a wurin ubangiji ga yayan ki. Tabbas ko rantsuwa nayi bana kaffara akai don adduan umma akan mune ko yaushe shine kuma ke bibiyan mu ba zama rokon abin duniya takewa rayuwan ta ba hakana. Sahibat kan ba sahiban da yan kaduna suka sani bace a baya yanzu wanan sahiban idon ta ya bude sosai ta zama first clasa ko a cikin lagos din a yanzu. Ba sahiba kawai ba har mahaifiyarta da dan uwan ta cigaban Sahiba suma ya jawo masi cigaba a yanzu. Shagon sana,an mu shi kanshi ya girma ya zama babban shago wurin sarin yan guwa don kudin da nake samu idan ogan mu yazo kasan na aikin yawo da mukeyi dashi ga shago da karatun mu sai abinci kuma idan mun saye da yawa abincin zai daukemu har wani lokaci mai tsawo din baci mukeyi ba. Yau ma ogan mu zai shigo kasan kamar yadda ya saba lekomu idan zai shigo din akan yo min aike a sabon wayana da yanzu ya canza min shi na ajewa umma nata ko ince na sai mata wanda yafi wanan sosai har Ammar. Don canza wayan ya samo asaline ranan da mukai wani fita zai gana da wasu abokan sana, an shi dole mota biyu akai amfani dashi zuwa wurin meetung din. Muna mota zamu tafi wurin ne aka kira layina naki daukan waya wani ya gani da kiran ya matsa na dauka yakai idon shi ga wayan . Ammarne ke nacin kirana wai nabar gida ban aje mashi kudin exam din shi da nace zan bashi ba a cikin hausa nayi magana kada wani yajime muke fadi a lokacin. Don in nayi turanci suna ji idan yarbanci nayi hakane zasu jini yasa na canza yarena da hausa ina fadin haba Ammar ka suba dakina karkashin filo suna nan na je maka kuma ka maida hankalinka wurin jerabawa kasan dai bamu da kowa Allah ne gatan mu a duniyan nan nima kaga karatu na dage nayi sosai Allah ya taimakeni ka daina wanan shegen game da kakeyi, karshe nace ka gaida umma kace mata mun fita ko, A gaban mota nakan shiga tare da wanda ke jan mota idan zamuyi irin wanan fita daya kama na gaba dayan mu idan zamu fita sai in koma gaba suna baya su biyu. Sam bai taba kullani ba ko ya nuna damuwan shi a kaina don da wuya inyi magana ma ya bani amsa direct yadda ya dace har na soma tsarguwan kaina da hakan. Abin mamaki sai naji ana fadi idan zakiwa yaro fada ba haka ya kamata ki nuna masa ba ai ki daina ce masa baku da kowa mahaifiyar ku da dan uwan ki suba kowa bane a gareki ? Saida na dan juyo nace dashi sorry sir a dan gimame daga hakan bai kara cewa komai ba tunane na lulayi na ashe duk lokacin dana canza harshe ina yaren hausa yana jina ke nan ban sani ba don bai taba nuna shi din ma yana da jinin hausawa a jikin shi don yafi shiga na kananan kaya ko ya saka irin jallabiyan nan mai tsada har wandon su na larabawa. Lagos ce fa duk yadda ka dauko karyan ka sai kaga abinda ya rinjaye ka ga gani a wurin wani yasa idanuwan su ko dan wanki da gugane su a bude idon su yake a can. Tunane na ya katse ne da yakecewa Felix ya tsaya wani shago sayar da waya ya fada mai ya fita ya zabo wayan mata iphone mai kyau ya sayo. Felix din ya fita ya shiga shagon ya dan dade muna zaune saukin abin bai kashe mota ba AC na bugun mu a lokacin don haka ba wani damu . Can sai gashi a lokacin har oga yaja tsukin dadewan shi yakai sau biyu sai gashi ya fito daga shagon rike da leda a hannun shi. Yana shiga motan zai mika mai sai cewa yayi No give it to her ina zata bini da wanan matacen gwagwanin nata wai waya abin kyama kawai. Mutuwan zaune nayi na kasa motsi kafin na mika hannu ina karba felix din yana min dariya don duk cikin su shine karami da Adnan sune kuma nawa yazo daya dasu. Da kyat bakina ya budo nayi mai godiya da addua irin na musulmin da akaiwa alherin da bai zata ba ga wanda yai mashi kyautan. Jin cewa zasu shigo aiki ranan tallata yasa na fito falo na samu umma a zaune nima zaman nayi ina saye da rigan barci mai sulbi sai zani dana daura daga sama sai hula baka iri mama cap din nan da akeyi a lagos yanzu a kaina. Baki barci ba ashe umma tace dani na danyi murmushi ina fadin banyi ba umma yanzun suka turo min da sako wai ranan tallata oga yana gari zamu fita. Tau aikin ya tashi ke nan wata uku yayi ke nan har zai shigo nace zai shigo umma ni aikin nan nasu ya fara fita min a rai yanzu umma. Da Allah zaisa na samu aikin gwaunati zan daina wanan din tunda ba na dindindin bane shi na kama na gwaunati din zaifi. Wanan din ma ai yana kokari sahiba ina laifin hakan da muke samu mutanen nan sun taimakawa rayuwan mu sosai a baya har ina zargin aikin da wani manufa kukeyin shi sai daga baya na gane aikine kawai dai na taimako Allah ya kawo muna a rayuwa. Hakane umma mun samu sosai a wanan fammanin shiyasa nake son kada in shagala dasu zan fara neman aiki na dindindin a yanzu gaskiya. Yanzu dai dole gobe in fita na samo dan rigunan da zan saka wanda zai fiddani nayi amfani dasu a wanan aikin ke nan don ban son tsarguwa ga hakan. Akwai kudi a hannun ki ke nan ko na dauko maki wanda ke hannuna ajiye umma ta tambayeni nace da ita a, a umma wanda ke wurina zai isheni ai don ba wasu masu tsada kwarai zan saya ba. Wani mai kudin idan kana tare dashi yana maka yafi son ka nuna yana maka din don haka ko kwara biyune dai ki sayo masu tsadan zaifi ummata fada. Washe gari na shirya da dan rana misalin shadaya da rabi na fita naso zuwa shagon mu nayi sayayya a can sai kuma na fasa na nufi wani sabon shago dake Agege na gown din mata wata bazabarma ce bude shagon daga ghana tana shigo da irin gown din nan na dubai dinkakku. Na shiga wurin suna haba haba dani aka ban wurin zama da drinks da ruwan gora yan matan dake tsaron kayan suka fara zuwa suna gaidani. Saiga wata mace gajera kamar ta taba ganina ta nufoni a cikin fara a tana fadin sannu da zuwa kanwata barka da shigowa gidan nan. Me za ai maki gyaran kai da kafa da yatsun hannu ko dress ga kikazo duba kawai na dan murmusa sai naji sha,awan gyaran kan ban san lokacin dana bude baki nace kai zan gyara da jikina sai dress din. Wasa wasa sai gani a shagon nasu har uku na rana suna min gyara an gama ta fara nuna min kaya tana fadin kinga ke mysulmace wanan zai fitar dake da addinin ki zaki haska sosai month dinga ne suka fito ba kowa yasan su ba a kasan nan. Kala hudu kawai na zaba a shagon na biyasu kudin su na fito har mota suka rakoni da kayana na shiga naja zuwa gida. Wasa wasa saida ya share wata kusan biyu bai dawo kaduna ba yana can aiki ya hanashi dawowa a kuma tsakanin an kwasa tsakanin iyayyen Nazifa da nasa don kowa ya hau a lokacin wanan ya kara bude sabon babin kiyayya a tsakanin su sosai a lokaci. A cikin wanan haklin ranan ya dawo gida duk daya gaji gidan su ya nufa kai tsaye an tareshi taro mai kyau duk da bai samu mahaifiyar shi a gida ba ta tafi barkan haihuwan kanwar hjy karima ita da hauwa da fa,iza sai Nabila ce kadai a part din don haka bayan ta bashi abincine ta kira mahaifiyar su a waya tana sheda masu zuwan yayan nasu. Hjy tace ya jiramu gamu hanya tafe yanzun nan kafin su dawone Nabila ta tsegunta mashi duk abinda ya faru tsakanin iyayyen su da iyayyen matan nasa . Amma kuma ta rokeshi kan kada ya nunawa mahaifiyar su cewa ta fada mai komai don zata yi mata fada saboda tace kada wanda ya fada mai wanan zancen idan ya dawo. Ko lokacin daya fada cewa zai dawo ba abinda zai fitar da mommy din a wanan lokacin koda suka dawo din ma ta fara zargin Nabila din tana tambayan ta yace ban san ida ta shiga ba tunda ta ban abinci ta shiga ciki. Zama tayi suka gaisa dashi da yan uwan shi kafin ta dauko mai zancen matar shi da cewa ka samu ganin ita Nazifa din kuwa. Hannu ya cire a goshin shi daya dafe yana jin zuciyan shi na masa kuna a lokacin yace da mahaifiyar su din daga airport nan nanufo direct. Basu san ka dawo ba ke nan yace yanzu ne fa saukana mommy ba sune a gabana ba dama a yanzu barsu can su zauba su huta nima a yanzu aiki yayi min yawa ai. Horon ya isa haka duk da nasan sai kakai kanka garesu sun fada ma abinda sukaga dama yadda suke so don sin dauka da zafi. Murmushi ya dan sake a fuskan shi ba tare da yayi mata magana ba ya mike yana fadin zan isa gida in watsa ruwa a jikina. Yaushe zaka tafi ka dawo dasu yace sai naje gidan ya fita ta bishi da kallon tausayi don tasan donta yake daurewa komai da ake mashi din. Haka ta zauna a wurin ta kasa komai don tunanen daya dameta kan auren dan nata daya dauko sabon sallo na son mulkan shi kota halin kaka shi kuma yaki yarda da hakan. Ya isa gida wankan yayi kamar yadda ya fada ya fitone ya dauki wayan shi ya fara aiki a cikin sa yana neman wani labarin da yake so a cikine yaga taron manyan yan kasuwan da za ayi a garin kaduna din ranan Laraba mai zuwan nan. Murmushi ya sake yasan zai samu dan haske ga abinda yake son samu da dadewa a wurin don haka ya hake wanan ranan yana murmushi. Tun a daren ya bugawa duk wanda yake bukatan aikin nan dasu ya sanar dasu shirin shi da zai aiwatar a wurin. Washegari shiru shiru mommy bata ji motsin shi ya shigo gidan ba har yamma ga wayoyin shi baya shiga a lokacin suna rufe. Hankalin mommy ya daga take zaton ko yaje gidan yayan nata ne kamar yadda ta umurce shi wani abu ya faru dashi a can don tsoron ta Allah yanzy tsoronta yayan nata . Tunda ya iya furta cewa a gaban ta yake fadin Aliyu kai ba komai bane kuma ba kowa ba kawar dakai da dan naka ba wani jan aiki bane a wurina. Cikin karfin hali shima mijin nata ya mayar maida amsa yana fadin Nuhu kayi sherin ka ka barni don ta Allah ba taka ba duk kace zaka tabani ko ahalina wallahi karyan ka ya kare a garin nan ke nan. Wanan hasumin mommy ta rike a zuciyar ta duk da manya sun shiga zancem sun sulhunta su an raba irin wanan fadan sunce sun bari. Saidai sanin halin yayan nata da tayi yasa tasan zancen bai fita zuciyar yayan nata ba duk ya ce ya sake komai ya wuce tasan yana rike dasu rikicin duniya da mairai akeyin sa. Ga dan uwan haihuwan shi Alh gyade ya nakasa yanzu baida wani moriya daga tsaye sai zaune bai iya komai anje asibiti da gurin yan tsubbo abu ya gagara tun lokacin har yanzu kuma ba a fasa ba don har kasan an bari dashi ba a dace ba. Hankalin hjy bai kwanta ba sai lokacin da suka samu wayan shi ya shiga ya sheda masu cewa shi yana Abuja a lokacin. Amma ka daina halin nan modibbo duk kabi ka dagawa mutane hankali har mahaifin ku na kira na sheda mashi bamu jika ba tun jiya. Haba mommy sai kace karamin yaro tace umm, umm bari wanan lokacin da ba a dauki rayuwa a bakin koma ba ba yaro ba babba a wurin yaudara. Yana dariya ya kashe wayan shi yana fadin a zuciyar shi ba inda zani mommy sai sun gane basu da wayau idan ma zai karbi yarsa ne ya karba wallahi. Fita yayi zuwa wani unguwa a can samarin gidan su Nazifa suka ganshi har gaisawa sunyi dashi yayi masu alheri sukai godiya suna jin dadi. Suka dawo gida suna murna suna da alherin da yayi masu din suna fada suna kari a cikin murna da farin ciki mamakine ya kamasu yan gidan abinka da gidan yawa take zancen yakai kunnen Nazifa. Aiko har wajen Alh Nuhu yaji kamar ya hade ranshi a lokacin don takaici da bakin ciki yana fadin watau yaron nan ni zai nunawa shi dan iska yake ko ? Shima kuma din yayi hakane don ya tura masu sako ta yayan shi su san su suka dauku Nazifan a bakin wata tsiya yayi alkawarin ba zai tafi ba sai ita data bar gidan don kanta ta gaji ta dawo. Nikan zance shawaran umma yayi min rana sosai don naga fa,idan shawaran a yanzu tunda na fara aiki dasu wanan ne karo na biyu da zamu bar lagos zuwa wani gari na farko muje abuja dasu mun dawo a ranan. Ga wanan katon kuma kaduna zamu tafi meeting mu dawo duk da bani kadai bace mace yanzu dake cikin su akwai Yemisi da ta dawo daga kasan waje tana jin kanta mu shidda ke nan ke tafiya yanzu wuri muna take mai baya kowa da aikin sa kuma. Sai shawaran umma din yai min dadi a lokacin don shiga ta alfarma shine ya dace da wanan shigan munyi da safe karfe bakwai zasu daukeni mu tafi. Sai ga zance ya canza aida karfe hudu zamuyi tafiyan ke nan wanan katon kwana zamuyi a can yaya zan tari umma da wanan zancen ta kwana tare da maza haka. Abdulhamid na sama a gidan shi bayan ya dawo aiki na fada mai abindake faruwa shima din saidai yayi tunanen abinda zai fadawa umma din kafin ni kuma yayi min nasiha da kama kai da mutuncina duk da yasan ba halina bane yin hakan. Saidai baisha wani wahala wurin fadawa umma din ba sai cewa da tayi ta kama kanta da mutuncin ta nasan halin sahiba amma duk da hakan ta tsare mutuncin ta dai a can don kaduna gidane gareta. Data shigo kuma take fada min yadda sukayi da Abdulhamid din ta min nasiha tare da cewa na leka gidan daddy koma na kwana a can din ba komai bane din sun watsar damu hakan mu sai mu bisu ai yan uwan mune su. Allah ya rufa min asiri karfe uku sai ga felix gidan yazo wurin umma yake fada mata don lokacin da suka kirani suna fada min nace ba zan tafi ba ni shine ya fadawa ogan shi kuma ya turo shi wurin umma din akan ya roketa zamu tafi aiki kaduna mu dawo gobe. Shima din rokon shi umma tayi akan akula mata dani don Allah kuma akwai yan uwa a can don mu din daga kaduna din muke ai. Karfe uku da rabi muka bargida zuwa airport don jirgin hudu zamu bi ba bata lokaci kuma jirgi ya daga sai kaduna garin gwauna damu. A wani katafaren hotel muka sauka kowa da dakin shi karfe takwas zasu fara taron nasu ke nan na dare don haka muna da sauran lokaci ke nan sallah nayi na zauna zaman lazumi. Kafin na mike na shiga nayi wanka a bayin na fito sallah na tayar na fara shirin barin hotel din shiga nayi sosai na alfarma da daya daga cikin rugunan dana sayo din baka mai duwatsu farin ado a jikin shi na zauna gaban mirrow din na daura dan kwali baka ganin komai sai zagayen fuskana sai turaren muzawa mai kwanci daya bi jikina yana tashi a gankali takalma mai hill ne a kafana sai jakka dana dauka shigen kayan jikin nawa kafin na dauko jakkar laptop dina daga baya. Ni kaina nasan ban taba shiga irin wanan din ba haka zaka rantse da Allah ni din wata balabiyace a lokacin Felix ne ya kwankwasa min kofa a lokacin na bude yake fadin suna jirana a waje fa nasan oga baison latti. Ashema har yemisi na cikin gidan lokacin tare muka jera mu ukun dukkan mu a cikin bakaken kaya . Mun samesu a cikin mota sai satan kallon motan nakeyi don kyau ya nuna min inda zan shiga na nufi gaban motan zan bude da sauri wani yace min baya dai na bude bayan na shiga. Budewa nayi ina mamakin sauyin ranan na shiga na dauka yemisi ma nan zata shiga naga ta nufi wani motan daban ta shiga. Ina shiga ogan mune a ciki a cikin rikicewa na gaidashi ya amsa min ciki ciki a takure na zauna muka fara hanya motan yana shiru saishi dake aiki a cikin computer din shi yace na bude nawa yana miko min wani abu . Ganin ba zan iya ba yace dani na miko mai photon mune mu da umma da mukayi ranan sallah na saka a screen din computer din . Saitin ta yayi min tare da dan fada min abinda zanyi ya miko min tafiya mai dan nisa sai gamu haraban wajen taron tun daga nisa zaka ga irin haske da yawan motocin dake wajen. Daga can dan nisa kadan muka samu wurin parking din motocin mu bamu fito ba sai da wasu security sukazo aurin aka bada umurnin fita. A ciki kuma kallo yake don matasan masu kudin zamani ne birjit a wurin sai tsofi da dattawa da kososhin gwaunati masu fada aji a cikin kasa. Wow ga sha,aban nan ya shigo da nasa tawagan wanan taro yayi albarka sosai da amsa gaiyatan matasan mu dake tasowa da kulada jin dadin kasa. Idanuwa sukayo kan mu caaaa yana dan daga masu hannu irin na sallama ga yan uwa har muka isa inda akai muna mazaunin mu a wurin. Daga can baya inda suke zaune da zasu iya ganin masu shigowa yake kallon fuskokin mu daya bayan daya sai dai ya tsayar da kallon shi ne a kaina zuciyar shi na bashi karya a lokacin. ZAINAB IDRIS MAKAWA ANA DARA GA , , , , , , , , 4️⃣6️⃣ BY, , , , , , , , ZAINAB IDRIS MAKAWA BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AL AZEEM, , , , , , , ONLINE PAID NOVEL YAR UWA KADA KI RAINA GIRMAN AIKI MAI KYAU DON HAKA KADA KI RAINA KANKANTAN ZUNUBI A GARE KI KIBIYA KAFIN KI KARANTA, , , , , , , Kina daukin a dauko ki karanta a banza bayan kinsan girma da nauyin hakki a wurin Allah kada ki raina girman zunubi a kanki yar uwa ki zama mai gujewa shiga hakkon wani komai kankantan abin Allah yasa mufi karfin zuciyan mu. Yanayin zaman mu daban dana saura a wurin bamu dade da zama ba aka fara gudanar da taron ba wani abu ake magana akai ba sai yadda abubuwa a yanzu suke tabarbarewa a kasa inda gwaunati ke neman hannun jarin yan kasuwa . Akan su saka hannu su bayar da gudun mawa a nasu bangaren mai bayani ya kara fadin babu babba ba karami a wurin wanan harkan don gaba daya ci gaban kasa ake nema. A karshe gwaunati ta kawo tallan wasu abubuwa da gwainatin ke mulka a wurin yan kasu don ya koma karkashin su ko abubuwan zasu gyaru nan gaba saboda gwaunati na ganin ba zata iya ba idan ba hannun yan kasuwan a cikin harkan. Ko wani abu aka gabatar zamu zauna muyi nazarin sa a tsakanin mu a cikin sytem din dake gaban kowanin mu a turawa juna wanda kusan ko wani dan kasuwa shima yana duban abinda ka fitar dashine a lokacin. Duk abinda akeyi daga inda yake zaune idon shi na a kan mu ya raba hankalin shi gida biyu zuwa ukku a wurin komai irin na yarinyar ne saidai wayewan da rayuwa ya hanashi yarda da abinda zuciyar shi ke bashi. Wanda ke bayani a lokacin ya fadi abin ban dariya duk dakin taron aka kwashe da dariya sabanin ni da hakan yasa na dago kai a lokacin ina bin mutanen dake wurin da kallo. Caraf idona ya sauka kan tsohon dake gefen mu dan nisa kadan damu daga inda muke zaune babu tantama shi dinne dai Alh Nuhu shine makashin mahaifin mu dana taba gani sau biyu a rayuwana don bazan taba mantawa da fuskanshi ba. Take naji duk ilahirin tsikan jikina ya tashi a wurin ba zan iya kara daga kai in kalli wurin hatare dana shakeshi ba a yadda nake jin zafi a zuciyana ba. Wurin ya dan kaure da hayaniya don dan hutun da akaje kan ambada dama ayi nazari kan zancen da gwaunati tazo dashi ga yan kasuwan da suka karba sunan su na yan kasuwa a kasa. Masu hida a wurin ne biyun suka kawo abin sha a taburin mu duk ina jin abinda suke fada sama sama don ban cikin hankalina sosai a lokacin. Adanan ne yake kokarin bude drink din dake gaban shi da sauri na dago kai ina fadin karku taba komai a cikin abin da aka aje a gaban ku. Kalloni gaba daya sukayi da mamaki nace kuyi saurin gagauta abinda mukeyi mu bar wurin nan kafin nan da minti talatin don yan kungiyan asiri sunyi yawa a wurin nan akwai abinda zai faru a nan gaba. Felix ne yace what sahiba are you a wizird how d u know all dis will happened next hannu oga sha,aban ya daga masa akan yayi shiru. Kafin inji suna zance da Jimoh babban na hannun daman shi ke nan da suke gudanar da aikin su tare don akwaishi da hazaka sosai yau sai gashi na tsoma masu baki ga zancen su ina fadin. Maida alkama din zasu kada ku canza wani daga wanan din idan kun yarda ba tare dana dago kai na kallesu ba na sake fadin sai semintin don shima ribane a gareku nan gaba baikai second ba sakon haka ya shigo a wayan mu daga gareshi. Ya fara rufe sytem din shi kafin da sauri gaba dayan mu muka rufe muka mike tsaye don barin wurin bayan ya aika da sakon shi. Yana gaba muna daga bayan shi gab da zamu fitane aka kwalawa sunana kira da Sahiba abinda yasa yaja ya tsaya cak ke nan ya dan waige . Ba shi kadai ya tsaya ba don gaba dayan mu munji kiran kafin kuma ya daga kafanshi ya soma tafiya don barin wurin muka bishi a baya . Zargin shi ya zama gaskiya don ta haka zai gane koni dince dai ya gani ba zargin yakeyi ba a lokacin sai dai ai kuma ban ko juyo ba a lokacin . Ganin mun fara takawa don barin wurin shima ya tako da sauri zuwa wurin mu din alokacin har mun shiga mota driver ya tayar ya tsaya yana kallon mu da hannu nayi mai wani alaman da bai gane me nake nufi da hakan ba. Ya juya don komawa dakin taron kafin yakaine ciki yaji fashewan wani abu har mu dake cikin motan a hanya don bamuyu nisa ba munji wanan karan fashewan abin. Daga can motan da jimo ke ciki ya bugowa oga waya yana fadin yaji abinda sukaji kuwa yace yaji shima direct masaukin mu muka koma daga nan. Bayan mun fito daga motan tsayawa yayi kamar yana nazari duk muka tsaya a bayan shi muna sauraren me zai fada. Baiyi magana ba sai kuma ya fara takawa yana tafiya tare da fadin jimo follo me Sahina you too yaci gaba da tafiya zuwa dakin da yake. Dan tsayawa nayi kafin da sauri nabi bayan su din nan muka bar sauran suka bimu da kallo kafin Felix dan duniya ya wayance da fadin yarinya yau kin taro much akanki tunda kika fara tsoma baki ga maganan manya haka. Yana tsaye tsakiyan dakin ya harde hannayen shi oga Jimo ya rigani shiga shima haka ya sameshi tsaye a wurin. Na shigo na bisu da kallo kafin yayi wani tako biyu zuwa uku ya juyo garemu yana fadin meke cikin drinks din da kika hanamu dauka a lokacin kuma meke faruwa a wurin? Bai tsaya kallo na ko saurare ba ya juya yaci gaba da abinda yakeyi din a yadda muka sameshi da muka shigo dakin. Shirune ya biyo baya ya kara takawa ya juyo yana fuskantana tare da fadin zanso jin mai farautan ran mu a wanan kasan. Baku kadai bane don ba a kan mutum daya suke keson nufin su ya kaiba ga kowa dake wurin suke son mallaka wanda ya fada tarkon su, Ba zasu so ku matasa ku sayi komai ba son a yanzu sun san akwai wa yanda suka fisu karfi a cikin ku shiyasa sukayi plan din da taron zai watse a hakan . Nayi shiru shima ido ya daga yana kallon Jimoh din na dan lokaci kafin ya dawo da kallon a kaina yana fadin you can go now na juya na fita har nakai kofa naji yana fadin. Take care of yourself nagode na fada na barsu tare da Jimoh din a dakin dakina na nufa inda na hadu da tawagan mu suna shigowa daga ciki. Dakin na saka key din dake wurina na shiga saman kujera na zube tare da dafa kaina na dan lokaci mai tsawa komai na kasa yi don ko tunanen yaki zuwa min. Hannuna na tura a cikin jakar dake gefena ina laluben abin da nake nema don a gaba umma ta saka min shi a jakkar dana bar komai ban dauko ba take tambayan na dauki maganina nace haba umma gobe fa muna gida war haka. Shakawa nayi kamar yadda Alfa ya umurceni dayi kafin naji na fara dawowa normal a lokacin sai bayan wani lokaci mai tsawo na mike na nufi gadon dakin na dan zauna na fara cire takalman dake kafana. Na jawo zanina nadaura na kwabe rigan dake jikina zuwa bandakin na dauro alwala na fito sallah nayi sosai na dade zaune a wurin kafin naji ana kwankwasa kofan. Ban bude ba na tambaya daga ciki naji muryan mace na fadin room services na bude abincine ta kawo min na bata hanya ta shigo dashi na gaida ita. Ta juya tafita na rufe kofan ina saye da hijjab din da nayi sallah a jikina na har lokacin ban cire ba na nufi cikin dakin lokacin wayana yayi kara alaman sako ya shigo min a wayana. Daukan wayan nayi na duba ogan mune mamaki nayi ashe yana da lanbana shi tambayan a yake yi game da abincin da aka kawo muna normal kawai na bashi amsa dashi na aje wayan daga gefena. Naci abincin sai dai ba sosai ba na gama abinda zanyi na kwanta zuciyana cike da tunanen abubuwa barkatai a lokacin. Bazance nayi barcin dadi ba a ranan don dai koda na danyi saina falka don mugun mafalkin da nakeyi a lokacin. Har gari ya waye nayi sallah tare da addakar din safe kafin na mike da wani itin barci a idona na nufi wurin tv dake dakin na kunna na rage damuwa a zuciyana. Yau rabo da naga wanan labaran hausa sukeyi a tashan da ke kai na koma na zauna ina lumshe idanuwa don ko na kwanta ba barcin zanyi ba a lokacin. Abinda ya farune a wurin taron jiyan da dare aka sanarwa anan tashan ashe har hakan yayi sanadiyar mutuwan wasu bayin Allah a wurin. Hankalina ya dauku ina sauraren labaran ne naji an kwankwasa min kofa na mike ina tambaya waye ta amsa min da fadin Yemisi. Na bude ta shigo tana bin dakin da kallo duk da komai nasu iri dayane da wanda take a ciki itama saida ta karewa dakin kallo ta juyo tana fadin A,a i tink say you de for oga room now, na dere you sleep with him ? A cikin wani irin mamaki na kallota take fadin why you no sleep with him naw ? i tink say, u de dare with him dat is why i no try my luck yesterday night ashe ke baki kwana dashi ba ni kuma banje na kwana a wurin shi ba duk mun tashi a zero. Ta fada tana bata fuska ta dafa min kafadana tana cewa kinsan na dade ina kwadayin kasancewa da ogan nan namu tun ranan dana fara ganin shi ga dama ya samu jiyan kuma ya wuceni. Me zance wa wanan mahaukaciyar ballagazan yar iskan inji sanyi a zuciyana sai kuma hankalinta ya karkata gun labaran take fadin caaye na d tin happen for dat place ? Umm na fada tare da kallonta ina fadin i wan go bap now don dai kawai ta fice min a dakin don wani irin takaicin ta da nake ji a raina yanzu don gaba daya ta zube min ga gani. Itako ko a jikin ta bata dauka ta fadi wani abu mai muni ba ga hakan sai kokarin jana da hira takeyi nayi shiru ban bata amsa take fadin wai kinsan irin tsadadun mazan nan kaza da kaza can abakin ta dai ita ta iya fadan maganan banzan ta. Gabin ba zata fita ba yasa na mike ina kokarin shiga bandaki take fadin naje na fito zata zauna ta jirani nan kan duk da ta girmeni da komai. Na rufe idona na nuna mata hakan ba zai yuyu ba ta fice dai kawai don ni bana yarda da irin hakan itama mamakine ya kamata take tambayana don ban yarda da ita bane ko me yasa na fadi hakan. Nace no sirinane haka kuma addinina bai yarda da hakan ba gaskiya don haka ta fice kawai zai fi na shiga wankana. Fushi tayi ta mike ta fice fuuu na mayar da kofana na rufe ina jin takaicin ta har kasan raina. Wankan na shiga nayi bayan nafito na shirya a cikin wani dinki half atamfa gaban kuma material ne sai duwatsun da akai kwaliya yana daukan ido ina jiran inji sunce mu fito mu tafi sai ga sako wai ba jirgi a ranan da zai tafi lagos sai gobe. Da sauri na dauki waya na kira umma muka kara gaisawa take tambayan ko zamu tasone nan dai na bata labarin abinda ya faru garin ta dafe kirji tana fadin mun godewa Allah bai shafemu ba ashe. A karshe sai cewa tayi dani sai ki shirya kije gida ke nan ki gaidasu don kada inja zancen nace to umma idan naje zan kiraki ai. Barci na kwanta nayi a dakin na kuma samu nayi sosai don sai bayan karfe biyu na tashi nayi sallah jin fita daga wajen wurin nayi na dan yafa gyalena na fita. Wurin shuke shuke na hango da farararen kujeru na nufi wajen hankalinane ya dauke a wayana dana zauna ina karanta sokonni. Naji ance dani a bayana hello na dan dago da sauri don ganin waye Adnan ne a tsaye ya saka hannayen shi duk biyu cikin aljihun wandon shi. Ashe kema kina nan ke nan ya fada na fito yanzu ne ina kallon garin garin yana da dadin yanayi sosai zanso na dan shiga garin na zagaya sai dai ban san inda zan tafi bane. Muje mu taka kaga garin na bashi amsa muka fito daga cikin hotel din muna takawa kawai sai na tare taxis yaji na fadi sunan unguwa nace a kaimu as a drop ina hausa da mai Napep din. Yace sai dubu biyu nace zuwa da dawowa 1500 idan zaka kaimu Adanan ya kura min ido har muka gama magana da mai a daidaita din muka shiga naji yace so you can speak that language abi nayi murmushi. Wani shago na hango daga nisa nace my adaidaita din ya kaimu can muka fito na shiga na sayowa Fa,iza fatima da Amira kaya kala bibiyu da kayan kamshi. Muna barin wurin na ciro memo na rubuta sunan kowa don haka kawai naji hankalina bai kwanta da in shiga gidan daddy din ba don ban san manufar su akan mu ba. Da kwatance har muka kai gidan daddy din gidan nan da kyaushi yarda na barshi a baya daga dan nisa kadan muka tsaya na sauka na nufi get din gidan na kwankwasa maigadin ya leko ba malam Adamun dana sani bane a baya wanan din. Mun gaisa nake tambayan shi don Allah ko Faiza tana gida Amira yace suna ciki nace ka karbi wanan sakon ka basu ina gaidasu ina saurine ba zan samu shiga ba. Na bashi dubu biyu sabbi nace ka karbi wanan ka rike ina gaidasu na juya yace boyar Allah ince waye idan an tambayeni nace kace Sahibace daga lagos. Muka juya muka wuce nace mubi ta gidan ya Abubakar gidan yaso bace min don sauyin da akai masa amma muma duk da haka na sheda gida. Kofan get din gidan a bude yake na ja gyalen kaina na rufe fuskana dashi ganin wata mota zata fito a gidan shima bin mu yayi da kallo ganin muna kallon gidan nasa ya fito ya nufi gidan su su gaisa da mommy da daddy. Nake cewa Adnan gidan blood brother dinane wanan gashi nan ma zai fito na fada shine kallon daya kamamu muna masa din. A can gida kuma daya isa ya samu duk ilahirin gidan a waje har iyayyen su mata suna mayar da fadi ya shigo da motan shi yai parking ya fito. Sin kasa hakkuri Fa,iza da hauwa da Fatima suka tako har inda yake suna fadin wallahi yaya Sahibace tazo gidan nan taba da sakon nan akawo cikin gida ba zata samu shiga ba ita. Kai nifa na fada maku kila fatalwane ko aljannun ta sukayi shige da ita suke son su rudemu kawai. Aljannun kuma mommy Sahiba dince dai tazo koni na ganta jiya da dare wurin comferences din nan da akayi har aka dasa bom a wurin. Saidai kawai a yanzu dahiba ba Sahiban da muka sani bane a baya gaskiya koni ta bace min kama dai nayi amfani dashi na gano cewa itace sai yanzu kuma da naji wanan din na kara tabbatar da hakan ita dai din nagani jiya ashe. Cabdijam Nabila ta fada daga inda take tsaye ta rike kugunta da hanayebta biyu tace hala yaya ta zama rikakkan bariki ne yanzu ko yasa har ka kasa gane ta. Dama na fada ai wallahi yar barikice sosai bata da kunya ko tsoro ko kadan wallahi daganin Sahiba irin yan iskan lagos din nan ne dama. Ke ja can da maganan banza kina zargin yar uwan ki ga banza to bari kiji indai sahibace a yanzu duk ta fiku aji da sanin duniya don banga wani abin asha a wurin ta. Mamaki na daya yanzu shine yadda akayi sahiba ta samu wanan matsayin haka babba na sakatariyar wanan mutumin da suke aiki dashi dana gamsu jiya don ba karamin matashi bane a cikin kasan nan shi . Ita Sahiba din mommy ta tambayeshi a cikin mamaki yace kwarai mommy wallahi sahiba a wani matsayi take yanzu dako mu maza sai anyi da kyar zamu kai hakan . Aikuwa dai don ga alama nan ya nuna hakan cikin wanan sakon jifa wanan uban kayan masu tsada data aikowa yaran nan yanzu dashi. Kada kayi mamakin hakan tunda mace ne ita kuma ko banza dama sahiba mace ce sosai idan ta samu wuri wahalane dama ya boye siffanta na kwarai. Kai haba haba mommy bai kamata aji irin wanan kalamin a bakin ki ba yanzu don Allah a kan yaran nan don kusan daya take damu ai a wurin ki. Yana fadin haka yasa kai ya shige cikin gidan ya barsu nan tsaye wajen kafin Nabila tace dashi mu kara ganin kayan Fa,iza tana karban ledan a hannun ta. Mommu kan ta juya ta shiga ciki ta samu danta da take nema ruwa a jallo akan maganan shi da matar shi da aka sake samun matsala akan fitinan su. A waje muka samesu tsaye suna neman mu don an duba dakunan mu bamu ciki sai gamu mai adaidaita ya sauke mu Adnan ne ya biyashi kudi yana godiya ya wuce. Mr Jimone ya tare da fadin ina muka fito ba tare da sanar da mutane zamu fita ba hankalin mutane ya tashi ga rashin ganin mu. Kai tsaye nace dashi sorry sir na tafi wurin yan uwana ne da mr Adnan dayace bai san gari ba lokacin kuma ba kowa a wajen da zamu fadawa zamu fita. Cikin mamaki yake kallona kafin yace yan uwa ke kina da yan uwane a nan kaduna din ya sake tambayana a cikkn mamaki yana kallona. Kafin inyi magana Felix ne yace ai ita din yar nan garin ce mahaifiyartace ta fada min haka jiya da naje daukata gidan su har tana fadin sai ta kwana a gidan su idan ba matsala. Shiru yayi ya juya cikin bacin rai yana fadin don't repeat dis mess again kun tayarwa mutane da hankalin kun kuma san garin ba lafiya ana ta fada a kafafen labarai tun daren jiya. Lokacin da muka juya muka hango ogan mu tafe wurin da muke yemisi tana bayan shi tana mashi surutu ya iso mr Jimo ke fadin sir wai ashe ita din yar wanan garin ce dama. Really kawai ya fada ya nufi wurin motar shi kai tsaye yana fadin zai fita ba zai dade ba zai dawo budan bakin yemisi sai cewa tayi sir can i follow you ? Bai ko kallota ba ya shiga mota ya fita mu kuma muka shiga cikin hotel din kowa ya nufi dakin shi don yin laluran shi. Sallah nayi na fito sai ga Felix ya turo sako akan mu shirya zamu wuce zuwa jos mu kwana a can daga jos zamu wuce lagos gobe da safe akwai jirgin lagos a can. Haka muka shirya a gurguje muka dauki hanyar jos da yamman nan wai ashe mahaifiyar ogan namu yar jos ce ita dama saidai tana waje a lokacin. Sai mahaifanta kawai ke zaune jos a yanzu wanan tafiya kan gaskiya an dai yishine ba a cikin dadin rai bakan don tafiyan yazo muna da akasi kuma bamu ba duk wanda yai tafiyan alokacin ya samu matsala arewa ke nan abinda suka sabayi a kaaashen yare ayi lafiya a watse lafiya an kawo arewa an watse baram baram kowa yana neman mafita a lokaci ya tsere. Mun isa jos ana sallah magariba kai tsaye wani gida naga mun nufa mun samu taro sosai a gidan wajen masu gidan da alokacin bamu iya tantance su. Mu mata cikin gida aka kaimu direct mazan bamu san isalin su ba a waje na daiji ana kwalawa wata kira da mallam gasu sha,aban din sun iso a cikin hausa. Daga cikin dakin akace au har sun karaso sannun ku da zuwa wace ta fito din tsohuwace sosai ta tsufa amma gata ya hana ta duka irin na tsufi. Ganin mu, mu kadai yasa taja ta tsaya tana fadin ja,irin shi yana ina shi kuka barshi wa yan nan kan yare ne aida gani dangi shine na oduduwa basa jin hausa. To shiga dai dasu ciki kafin ya shigo tsohuwan ta fada sai akace mu shigo ciki da harshen turanci muka shiga jikan na tsaya na kowane takalma daga kofa ban yarda na zauna ba saidai na gaida ita a cikin ladabi tana amsa min da yarbanci. Mallam kodai sha,aban ya kawo maki kishiyane ki gani dama ai daya kyauta irin wanan yar haka mai zubi irin nasa ai sai su dinga haifo maku zabaya. Duk suna dauka bama jin hausa ne ganin da nayi lokacin sallah na shigewa yasa nace dasu mama don Allah zanyi alwala nayi sallah. Lah ashe yarnan tana jin hausa ke nan kika barmu muna zuba haka a gaban ku zo muje na kaiki ta fada tana mikewa duk suka bimu da kallo. Na kwabe gyalena na nufi inda tabi ta nuna min ban dakin nayi alwala na fito daidai lokacin ya shigo falon ya kaure da hayaniya dashi jakkana na bude na fito da hijab dina har kasa na koma can gefe zan tayar da sallah. Da sauri suke salati suna cewa don Allah zo ga daki nan ku shiga kiyi sallah mana kyayi sallah a nan kuma yar nan na bita zuwa ciki dakin ban kara fitowa ba shida kanshi ya turo yemisi ciki ta sameni na idar ina nuke kayan sallah. Dakine mai kyau da komai na jin dadin rayuwan dan adam a cikin sa ga shimfida na alfarma anyiwa gadon dakin sai kamshi ke tashi tako ina a cikin dakin har falon nasu. Babban falone da zai iya cin baki ko mutum nawane kwa yaji saitin kujeru na alfarma irin na kasan waje din nan da kashi katon photunan sune iyalan gidan tsaye an aje a jikin bango kamar wa yanda ke ciki zasu fito suyi magana. Dan zaman da nayi a falon ne na kurawa photon wata mace ido da mijin ta dake cikin kaya saki irin na masu kudin yarbawa din nan nada can shekarun da suka wuce baya har wanan lokacin ma wasu na sakashi . Babu tamtama sune iyayyen ogan mu da Felix ya ban labarin su ranan ban kai karshen tunane na ba naji sallaman matar ta shigo ga wata biye a bayan ta da katon tire dauke da abinci cikin sa tana fadin yata ga abinci ku tashi kuci kinji kada barci ya dauke ku. Mun gode mama na fada ina mikewa zaune abincine mai rai da lafiya aka shirya muna munci mun sha kafin mu kwanta barci . Duk da banda sabo amma na dan sake da matar da naji kowa na gidan na kira da hjy Laraba na dan sake jiki da ita muka dan taba hiran abinda ya faru a kaduna din damu. Yemisi na kwance tayi waya tayi charting don na kula fushi take dani tun abinda ya faru tsakanin mu da safe nima na shareta. Bayan hjy ta fitane na shiga ban daki na watsa ruwa dana fito nayi duk wani shirin barcina tare da addua na haye gado na kunna kira,a na barta zaune ta mike kafa saman gado tana zuba yare. Washegari koda akazo tayar dani sun samu har na idar da sallah ina zaune ina addua ta juya tana fadi au ashe kin tashi ma. Bayan na idar wanka nayi na shirya don nasan tafiyan safe zamuyi don haka ina idar sallah nayi wanka na shirya na koma bakin gado na zauna. Ina turawa Ammar sako a waya a lokacin yemisi ta falka daga barci ta dan kalleni taja tsuki tana gyara kwanciya. Shidda da tabi nayi sai ga kira a wayana cewa mu shirya gasu nan zuwa su dauke mu zamu wuce airport ke nan a lokacin tana jin haka ta wani zabura ta sauko daga gadon ni kan jakkana na dauka na nufi falin gidan a nan na samu hjy din tsohuwar gidan zaune tana ba yan aiki umurni don su samu suyi muna abin karyawa kafin mu tafi. Gaba dayan su sukai sallama suka shigo gidan ana karbawa suka zube a gabab tsohuwan suna kwasan gaisuwa a wurin ta yana shigowa ya dubeni a inda nake zaune yana fadin ina yemisi din mu tafi mana. Mikewa bayi aiko ya dinga fada sosai kan ba zasu kara tafiya da ita ba daga ranan don baiga amfanin zuwa da ita bama. Badai tafiyan ke nan ba ya kalli agogo yana fadin hjy zamu makara a cikin hausa jirgi bakwai daidai zai tashi kinga in mun tsaya zamu makara mikewa tayi tana fadin haka ba zai yuyu ba ka kawo min kawata har gida kace ta tafi haka bata karya ba kuma. Kitchen din ta nufa can sai gasu tare da mama Laraba da ledojin take away a hannun su suka mika ma kowa nasa nawa kan ko ba a ce ba yafi na kowa yawa a ciki muka karba muna godiya tana fadin kwa karya a jirgin ai. Ta miko min wani warmer sabo yana kyali tana fafin karbi wanan ki rikawa ogan nasa kinji wanan in kunbi nasa baya cin abinci. Mukai masu sallama muka fito a gurguje yana can dan nesa kadan da tsohuwar suna magana mama Laraba kamar yadda ya kira ta tasamesu a wurin har mun shiga mota mun zauna ta dangwara min wani leda a jikina na dago kai a cikin damuwa na kara mata godiya. Mun samu jirgi da kyat da fudun tsiya da sukayi ba ai wani tsayawa ba jirgin namu ya tashi zuwa lagos . Allah ya taimakeni a can baya na samu seat na zauna na sake saidai har lokacin ban wani sake jiki ko in duba abinda ke cikin leda ba. Allah ya sauke mu lafiya mun sauka mu mata suka fara saukewa gidajen mu nice ta farko yaran Abdulhamid da Amar dake kwallo a waje suka sheko suka tareni. Naji mamakin ganin ana sauke buhun dankalin turawa da doya wani na kulan dana bari nasa a mota da nake kaya sai ga yara nagani dashi sin shigo sun bayar akawo min. Bayan yaran sun fitane muka zube a falo da umma da Amar ina basu labarin tafiya da abinda ya faru har hira da yemisi duk saida naba umma labarin komai. Amar ne ya jawo kulan yana tambayana meke cikin sa nake fada masu yadda akayi har kulan yazo gareni lokacin kuma muka bude babu komai a cikin sa sai sayayyen kaji da dan irish da manyan suyan kwai a cikin sa kajin daine masu yawa sosai saida kulan yacika duk girmansa kuwa. Mikewa nayi zuwa dakina daga nan ban fito ba na kwanta sai barci barci sosai nayi a ranan ban tashi ba sai bayan karfe uku da kwata na falka ma dubi lokaci. Aida sauri na mike zuwa bandaki na dauro alwala na fito sallah nayi kafin in fara jin wani irin yunwa na ziyarana lokacin. Falon na fito wanan abinci na sama din da alama basu girka komai naciba da rana don haka shina dauka nayi warming din shi naci nima. Bayan ya gama sauraren mahaifiyar shine yaji tayi shiru ya kwantar da murya yana fadin naji hjy zan tafi amma ki sani wallahi idan naje suka zageki ko daddy aurena da Nazifa ya mutu ke nan har abada. Da sauri hjy ta dago kai ta kalleshi yace kwarai mommy don haka tunda dai ba fada mukayi ba indai har tana sona har yanzu ku bari ta dawo dakinta da kanta yafi. Mommy tasan kwanan wasan don dai sai sun nemi suja masa rai zasu iya zagan masa mahaifan sa a gaban shi tundai yayan nata dayafi kowa hawa a lokacin. Budan bakin mommy din sai cewa tayi idan dai hakane kada kaje a bata goma daya bai gyaru ba abinda kawai zakace dasu ke nan. Ta dawo dakin ta tunda ba fada kukayi ba shike nan don dai nasan sai yaya yayi masifan hakan don kai yake son gani yacima mutunci son ransa. Da nayi masa me mommy dako ya raina kanshi ranan wallahi yara kuma idan zasu rike sune su rike din nasan dai idan muna raye sai sun nemeni. Shiru mommy tayi tana nazarin maganan su da fan nata shima dai hakan ne don mikewa yayi yana mata sallama ya fita ranshi a bace a nan waje ya samu sauran mutanen gidan a zaune inda ya barsu din Fa,iza tayi tagumi tana tunane. Amirace tana ganin shi ta mike tsaye tana fadin kakaini wurun ta yaya sai yarinyar ta bashi tausayi ya dan kakaro murmushi yana fadin zan kaiki ai Amira yanzu akwai inda zani daga nan ne. Sahiba din tana garin nan kenan yaya Fa,iza ta sake tambayan shi a karo na barkatai yaji tausayin yaran sosai saidai bai yarda ya nuna masu komai a fuskan shi ba sai murmush kawai da ya sake masu ya juya ya nufi motan shi ya shiga ya bar gidan. ZAINAB IDRIS MAKAWA ANA DARA GA, , , , , , , , 4️⃣7️⃣ BY ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , , , , , BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AL GHAFUR, , , , , , ONLINE PAID NOVEL YAR UWA DON GIRMAN ALLAH KI GUJI SHIGA HAKKON WANI KAN SON ZUCIYA KI BIYA KAFIN KI KARANTA NA FITAR DA HAKKINA NA FADA MAKI, , , , , , Kwana biyu ina gida ina hutawa banje ko ina ba don dan wanan tafiyan da mukayi na kwana biyu bama gida kamar wace tayi wani tafiya mai nisa saboda rashin sabo da hakan. Yau ma barcin Safe nakeyi nayi mafalki wai zan fita zuwa unguwa sai na fita wurin umma inda take a shagon ta zaine nasameta Nayi sallama da umma a shagon ta na fito na nufi wurin motana ina kokarin bude motan na hango wata mota ta dumfaro gidan mu. Sam ban damu da waye ba a motar har yakai na bude motan ina kokarin shiga naji an ambaci sunana daga bayana ana fadin Sahiba wai dama ke dai dince na gani a kaduna ? Na juyo ina dago kai don ganin waye idanuwana suka sauka a kan yaya Abubakar dake tsaye yana kallona a cikin mamaki. Saida na dan kadu lokacin kafin na jawo courage nasawa zuciyana lokaci guda ina dan sauke murmushin gefen fuska kafin nace dashi ina wuni yana amsawa na fada mota har na tayar yana tsaye yayi mutuwan kasko ga kallona na bar wurin duk yana tsaye ya zuba min ido ya karasa wurin umma din. Wani iri nake ji ina jan motan wani tunane nayi na dauki waya da sauri na kira umma yare nayi mata ina fada mata cewa kada ta kuskura ta fadi wani abu game da rayuwan mu. Daidai nan na falka daga barcin a hankali nakai ga bude idona ina bin dakin da kallo har nasan barci nakeyi nayi wanan mafalkin . Zama nayi a bakin gado karshe don mafalkin ya tsaya min a raina tun falkawana daga barcin kafin in mike tsaye na fada ban daki na watsa ruwa na dan dade a ban dakin kafin in fito na shirya cikin wani dogon riga blue mai dan karamin hannu sai hula dana saka saman kaina don banda niyar fita a ranan duk da har yanzu bawai na daina zuwa shagon mu bane don ban bar wirin ba nakai matsayi mai girma a cikin shagon a yanzu. Na samu umma na shirin fita wajen shagon ta don ina jin dadin yadda naga umma na son wanan sana,an nata sosai don yadda take kulawa dashi a kullun. Kin tashi ke nan umma ta tambayeni nace eh tare da kara gaida ita ina zama nake fadin umma na fada maki cewa naga yaya Abubakar a kaduna. Da sauri umma ta juyo tana kallona a cikin mamaki tare da fadin kin ganshi fa kikace na gyada mata kai a hankali kafin nakai hannu saman fuskana na shafo ina daga kafa na dora saman kujera ina fadin yanzun ma na gashi a cikin mafalkina nasan kuma zaizo gare mu bada dadewan nan ba. Zaizo fa kikace dama baisan inda muke bane sai yanzu daya ganki a wirin taron ya tuno damu umma bana zaton hakan akwai dai abinda yafaru haka ya faru umma. Don daga baya nayi tunanen sai na fahinci kamar shi kanshi an saka mai mantuwa a kan zancen mu kodai wani abu maka mancin hakan. Umma ta dago kai ta kalleni don jin yadda na kirata din saida na dago kai sai nayi shiru kuma take tambaya mene ? Nace barshi dai ba yanzu ba umma dama tambaya naso yi maki a kan daddy yanzu tambayan baida amfani don ba zaki fahuceni ba umma na fada. Har lokacin umma kallona takeyi da mamaki saidai ganin banda niyar magana yasa taja tsuki tana fadin zaki fara kakaro shirmen ki ke nan kuma sahiba. Umma dawa Abban mu ya fara shawaran filin shi da yayi sanadiyar barin shi duniya lokacin ? Me kike tunane kike wanan tambayan kuma yanzu gaskiya nake hangowa dole da akwai hadin kai cikin abinda ya faru umma . Bayan ansan da cewa su sukai kisan Abban mu kuma aka barsu suna harkokin su a cikin mutane a she ana haka a wanan kasan dama ? Ke kada ki shiga aikin da banaki ba Sahiba har ki fara zargin wanda baida laifi a cikin zancen ni a yanzu nabarwa Allah sanin sa akan komai daya faru damu a rayuwa. Umma ba zaki gane bane dama na fada maki tun farko ai bazaki fahinceni ba wani tsawa ta daga min har saidana dan kadu tana fadin kawai don kinyi mafalki da Abubakar sai kawai kiyi kokarin zargin wanda ya taimaki rayuwan mu a baya don nasan mahaifin shi kike kokarin jefawa zargi kuma yanzu. Yi hakkuri umma ba zargin sa nakeyi ba kawai dai ina hasashen hakan ne garesu tunda zuciyana ya fara nasa zargin wani abu akan haka. Ta dan tsura min ido na dan wani lokaci kafin naji ta mike ta fita daga falon zuwa kasa nasan shago zata bude a lokacin. Ni kadai na wuni zaune a falon don suna kasa basu shigo ciki ba inda nake nima din dai tunane ya hanani fita inda suke. Da yamma ma da suka shigo umma batayi wani sakewa dani ba a lokacin nasan duk zancen da mukayi da safe ne da ita yasa ta rashin sukuni. Washegari na tashi da shirin zuwa shago don har yanzu ina lekawa don wanan tafiyan namune ban tafi ba kwana biyu. Na fito a cikin shirina na dogon buje mai shara, shara green mai adon filawa fari sai farar riga mai dogon hannu da aninaiya har kasan shi dan half sunna hijab daga sama iya kafadana sai hular mata dana kafa irin na cow boy da ake yayinsa daga can saman kaina nafito. Inda na samu umma a dakin ta nake fadin bayan na gaisheta umma zan tafi wurin aiki sai na dawo ke nan hope ba wani matsala na sake tambayanta ina kallon ta. Ta dan dago tana min Allah tsare a dawo lafiya babu matsalan komai don sai yamma zamuyi abinci gashi har lokacin muna cin naman dana dawo daga jos dashi duk da mun dibama iyalin Abduhamid din. Ina fitowa nan muka hade da matar Abdulhamid muniya muka gaisa take tambayana umma nace bata fito ba tukun zan tafi aiki na fada tayi min a dawo lafiya itama. Gaskiya idan Allah ya tashi ikon shi ga bawan shi sai yabar yan Adam da mamaki don dai nikan naga amfanin adduan uwa da dogaro ga ubangiji a kaina a yanzu. Don nida nake karamar ma,aikaciya yau gashi ubangiji yai min daukaka da shi kadai yasan sanadin hakan gareni ya daukakani ta inda ba,a taba zaton min ba a lokaci daya. Sai gashi wai nice idan na shigo manyan mu nada a ma,aikatan yanzu suna kokarin gaidani a cikin girmamawa da kafa, kafa gareni don gujewa yin laifi saboda ina da matsayin da basu taba mafalkin kaiwa gareshi ba yarinya karama dani don yanzu ba inda nake aiki ba duk masana,antun Sha,aban dake kasan nan nasan abinda ke tafiya a cikin su a yanzu. Duk da ba wani daukan kai nake dashi ba ko a baya yanzu ma hakan baisa ina masu daukan kaiba zan tsaya mu gaisa a cikin mutunci da mutu kafin na wuce. Saidai har lokacin ban kai ga hada wani zumunci ba da kowa a wurin in ka debe Felix daba ma zama kasan yakeyi ba shi ya faye fita kasan waje lokaci lokaci sai Adnan da Abdulhamid da mukayi dan sabo dasu na zaman yau da kullun. Iyakata in shigo mu gaisa dasu sama sama sai na wuce naje yin aikin daya kawoni wurin ban damu da kowa ba kamar yadda muka saba dai yi dasu a baya. Kun san dan Adam da daukarwa kanshi zunubi kuma dole ne ai zargi ko tunanen hakan cewa wai kodai muna tare da Oga Sha,aban ne ? Har yasa ya bani wanan girman haka a cikin lokaci guda don zargi kawai irin na dan Kansas da yake dorawa kanshi idan yaga wani ya samu cigaba dayafi nasa. Duk da idan wasu sun kasa hakkuri sunje da tsegumin wurin manaja yakan fada masu gaskiya ba wani alaka a tsakanina dashi banda na aiki shima kanshi ya bincika hakan ya gane ba komai banda aiki dana sani kuma akeyi dani din shike nan. Morning miss Sahiba aka fada nasan muryan waye don haka na juyo ina amsa gaisuwan da fadin morning Adewale sai kuma na tsaya cak ina kallon wanda ke tsaye a bayan Adewale din cikin kaduwa da mamaki abinda yasa shi dan juyawa bayan shi shima yana kallon abinda nake mamaki din. Mazane su uku a cikin kayan motsa jiki daga gani dai fitowan safe sukayi daga wurin motsa jiki suka nufo nan shago din. Don ba kowa bane sai Ya Mustapha da muka dauki kusan shekara biyu da rabi bamu ganshi a idon mu ba don mun dauka ma gaba daya ya manta damune ashe wai baya kasan ne yayi tafiya a lokacin shima shine a gabana yanzu. Ganin yadda yake kallona a cikin mamaki yasa na juya da sauri zan bar wurin muryan shi naji yana fadin dakata Sahiba na juyo ya fara takowa zuwa inda nake masu binshi a baya suna biye dashi lokacin mutum biyune a bayan shi. Idan nace a zuciyana ina da abokin gaba gaskiya banda shi a raina hakama abokan aikina kuma saidai su a bangaren su na zama abin harin su a yanzu kuma don yan matan shagon yan kwalisa danazo na sama a wurin yanzu suke ganin nafisu ga komai sun dauki karar tsana da kyashi da hassada sun saka akaina har suna samin suna da yarinyar manya wai. Don wai manyan nan duk nema na suke da harkan banza don sun ganni yarinyar mai kyau suke daukana a boye suna iskanci dani. To ko a wanan lokacin ma dai Funke dasu Abeni na wajen suna gulma akan mustapha din da suka ganshi ya hadu sai gashi sunga ya tsayar dani ya nuna ya sanni dama a wani wuri sai kuma abin ya kara basu mamaki da haushi. Ya tako yazo har gabana ya tsaya yana yimin kallon mamaki na nan dukar da kaina kasa kafin nace dashi ina kwana a cikin yaren hausa. Ya amsa min tare da nunani yana fadin kece Sahiba ina mama da Ammar jin yadda yayi magana na amsa mashi da suna lafiya ya su gwaggo Hari da daddy ? Lafiyan su kalau ya fada yana lumshe idanun shi kafin yace wai dama kece dai din na gani a kaduna tare da sha,aban muyideeen ? Sam ban yarda ke din bace saidai mai kama dake a wurin don hakane ban yarda ke bace da zuciyana ke fada min ke din ce. Excuse me na fada na fara tafiya na bar wurin yana tsaye ya bini da kallon mamaki kafin yace wa na tare dashi su tafi suka bar wajen . Aiki na sama sosai don kwana biyun da nayi ban fito ba saidai haka nayi shi ina jin wani iri a raina ba dadi nasan haduwan mu da Al mustapha din ne ya jamin bacin rai din. Don haka nake duk ranan dana hadu da wani daga cikin su zan yini ne raina na baci saboda mun tashi a rayuwan kadaici da badan Allah ya bamu uwa ta gariba Allah kadai yasan yadda rayuwan mu zai kasance a ciki. Na taso daga a gajiye zuwa gida inda na dan tsaya lagos market nayi cefanen fresh vegetables da nama danya na koma gida dasu don zanyi girki dare ranan. Tun dana doso naga mota a kofan gidan na dafe kaina don nasan mafalikina na jiya ke son zama gaskiya haka dai na daure na karasa na parker motan ina dauko kayan dana sayo ne suka fito daga cikin gidan. Hankalina ya kwanta lokacin da naga Felix ya fito daga cikin gidan namu na dan sake murmushi yana fadin see you from where are you now ? Na share ina fadin Amebo olofofo inda ka aikeni na fito na kara da fadin na dauka baka kasan nan ai har kun tafi ko ? Yace ina oga na kasan nan ba zai koma ba sai munyi bukin zagayowan mutuwan mahaifin shi na shekara da yan dangin su suke yi a zuciyana nace wa iyazu billahi har dake kasan musulunci suna wanan dabi,an ashe ? Yanzun ma naje can office din ku ban sameki ba shine nazo nan don na kira layin ki bai shiga sai lokacin ma na tuna da tun kashe wayan da nayi a daren jiya ban kunnata ba ashe. Akan me kake nemana na tambaye shi yace aikine ya taso muna kan wanan shagalin da za ayi din don haka kinga muna da zama a gobe ke nan daku. Fuskana bata kafin na wayence da fadin Allah ya kaimu goben na dan taka mai zuwa wurin motan shi ya tafi na juya na shiga cikin gidan namu. Nazifa kan abubuwa nason su kwabe mata lokaci guda don in tabi ta mahaifin su shike nan ta rasa uban diyan ta tana ji tana gani don ya hana ta koma dakin ta. Ga abinda kuma mijin nata ya fada cewa ai basuyi fada dashi ba balle ace sai yazo zata dawo asalima da zata zo din yai mata goma na arzki don kada su shigo su wahala a lokacin shi bai kasan tare dasu kuma. Yanzu kuma abin ya koma mata ciki yadda mahaifin ta ya kafe kan wani dalili nasa da su suka kasa fahintar manufan shi akan haka. Yau dai ta rufe ido ta samu mahaifiyar su da zancen komawa ta tace ita zata koma dakin tane tunda tasan halin Abubakar tunda ya fadi hakan bazai taba zuwa ba kome za,ayi ko bazai zo ba tunda ya fadi ta fadi hakan. Kina ganin cewa komawan naki baizo ba shine mafita kinfa san halin mahaifin ku Nazifa haka zai iya jawo muna matsala dani dake a wurin shi. Mama idan na zauna kuma shima matsalan aurena zai samu don haka gara ki bari in koma kawai tunda dama ra,ayinane nazo nan na zauna a gida bayan ya kara gyara min gida kafin inzo. Yanzu ai kinga illan hakan don auren ki ya mutu ba komai bane ga Alh shi don bai daukeshi wani abin kunya ba haka. Ta kasa ba mahaifiyarta amsa sai hawayen da take sakewa kawai a lokacin don yadda take jin kanta kiris ya rage takai ga aikata abinda take ganin zai dace da ita a lokacin. Itama mahaifiyar nata a cikin wani hali take a lokacin don tasan mutuwan auren yar nata ba karamin hasara zai jawowa rayuwan au ba idan auren ta ya mutu a yanzu ta wanan dalilin. Don duk ilahirin diyan gida dake aure babu wace tayi dacen gidan miji irin yar nata shi kanshi majaifin nasu yasan da hakan bakin haline kawai dai irin nasa ya taso. Aikuwa da yamma mahaifiyar nata ta samu mijin nata a falon shi yana waya yana kumfan baki yana mazurai da idanu sai billahillazi bai isa ba shi waye har yaushe yazo kasuwa shi da zai kawo zancen sauke farashi. Wuri ta samu ta zauna a gefen shi har ya gama wayan yana huci tayi shiru bata tanka mashi ha har lokacin daya kare hucin nasa tace dashi sai hakkuri mutane. Yace aisun sanni sun san halina sun san kuma koni waye da abinda zan iya yiwa mutum idan yace zai ketare abindana sharadawa mutum. Jikin tane yai sanyi don jin abinda ya fada a lokacin don ba zata iya fito da zancen daya kawota wurin shiba na yarsu a lokacin. Jin tayi shiru yasa shi kallota yana fadin shi wanan karamin dan iskan baizo ba har yanzu ke nan ta gyara zama tana fadin wallahi baizo ba Alh shinema dalilin zuwana yanzu ai kan zancen. Don Nazifa tace tunda ya fadi hakan ba zaizo gidan nan ba kan maganan nan nasu tunda ba fada sukayi dashi ba tazo nan don haka kayi hakk, , , , Ke salma ki kama kanki da wanan maganan da kike kokarin fada min a yanzu idan baizo ba shike nan a kashe auren mana bashi ke nan ba. Alh har da bakin ka kake fadin auren yarka ya mutu bayan kasan akwai haihuwa a tsakanin su yaran ina za a kaisu idan ka kashe mata aure ? Yayi wani irin juyowa yana fadin yara yarafa kika ce salma yaran dasu taje gidan sa dama ta mayar mashi da tsiyar sa mana kowa ya rike nasa. Gaskiya hakan ba zai faru ba insha Allahu kadaiyi hakkuri kai mai diya mace ta koma dakin ta tunda dama duka daya ake matsalan ka da mahaifin shi ba zai shafi auren yarka ba. Wani tsawa ya jefa mata kafin yace kin ko san abinda kike fadi idan kin mata dako ni waye ya kamata kishiga hankalin ki kinatsu keda yar taki zaifi maku. Mikewa tayi rai bace ta fice falon nasa tana magana ciki ciki ya bita da kallon tsana har ta bace mashi da gani yaja tsuki yana kallon ruwan dake gaban shi. Dakin ta ta koma a cikin bacin rai ta rasa meke mata dadi a lokacin zama tayi tana kallon yar nata dake kwance dunkule a cikin damuwa. Mikewa tayi tafita daga dakin tare da wayan ta falon ta ta koma ta fara neman layin da take son kira har ta samu ta danna kira ba, a jima ba aka dauka. Sun dan dade suna magana da wace ta kira din a wayan kafin ta mike tsaye tana kashe waya tare da sauke ajiyan zuciya. Dakin metting din namu yayi tsit ana jiran aji me zaice damu a wurin game da kiran da yai muna na gagawa kan shirin da yake son ayi din. Shi ya fara gabatar da tsarin shi kafin sauran su kawo nasu shawara duk su dora akan nasa din sai da naji sunyi shiru na dago kai na dan saci kallin su lokaci guda kafin na mayar da kaina kasa ina rubutu. Sam ban yarda nayi wani magana a aurin ba don abinda nake son fadi bai yuyuwa a lokacin don a gauraye muke ga addini sannan kuma su ko musulmai sun dauki wanan da muhinmanci sosai. Har aka gama na tura mashi sakon a nasa sytem din ina jiran su mike nima na tashi Ausa girl you no say anything now ?. Felix ya fada yana mikewa na danyi murmushi ina tashi tsaye tare da kallon su ina fadin Allah ya sadamu da alherin sa na saba jakata na fita daga office din. Tun a mota na fara fada a zuciyana ina faman jin zafin irin dukiyan da suka ware na wanan shagalin kai ina na fadin shirmen banza shirmen wofi mutane ku dinga hauka haka wai al,ada tir da wanan bakin al,adan nasu gaskiya naja tsuki ina kada kai tare da fadin kai ina sam hakama bazai yuyu ba haka kawai ku karawa mamaci nauyi don jahilci. Shiyasa bahaushe ko yauahe yake rena addinin yare don duk yadda kayi dashi sai ya surka hakan da al,adanshi. Bayan na isa gida nayi wanka nafiti banci abinci ba kwantawa nayi don in huta saidai barci ya gagareni a lokacin. Gashisai juyi nake ina tsuki can nayi wani tunane take na mike zaune na jawo wayana don aikata abinda zuciyana ya bani a lokacin. Wayana dauka na zauna na tsara komai yadda nake so na tura sakon kai tsaye zuwa gareshi nayi saurin kashe wayan nawa don kada ma a kira a sameni a lokacin kan wanan karanbanin dayi a lokacin . Sai lokacin naji dan sanyi a zuciyana duk da nasan al,adan sune hakan shawarana ko magana ba shi zaisa su fasa abinda sukayi niyar yi na barnan dukiya ba ga wanda ya mutu din. Na fadakar dashi yin hakan da zasuyi katin wani nauyi ne gun mamacin su kamata yayi su bada sadaka gun mabukata da gidan marayu a cikin unguwa. Ko asai shimfida akai masallataiya da butoci da laspeakee gadai abubuwa nan da dama na rubuta mai na fadarwa garesu da wanan tunanen na koma na kwanta barci. Washe gari da safe ina barci ummace ke tayar dani na dauka zancen zuwa wurin aiki zatayi min har na fara fadin umma yau ba company zani ba. Sai naji tace kina da bako a waje yana jiran ki wai umma waye da safen nan kuma na tambaye ta banga maishi ba dan wajen Abdulhamid ne ya shigo yake fadi. Lokaci na duba a wayana tara saura na safe ashe lokaci har ya ja haka ina kwance na dan shiga bayi na fito na dauki rigan da nayi amfani dashi jiya na mayar a jikina sai hula akaina. Na sauko na hangoshi tsaye ya bada baya yana kallon titi har na karasa saukowa kan steps din ina mamaki a raina waye wanan mai sallaman dani wanan lokacin har na iso nayi sallama ya juyo yana amsawa . Gabana ya fadi tare da ambata sunan shi lokaci guda nake fadin yaya Abubakar kaine dama kana nan wai ashe dama akwai ranan da zaka tuna damu har kazo garemu ? ZAINAB IDRIS MAKAWA, ANA DARA GA, , , , , , , , , , 4️⃣8️⃣ BY, , , , , , , , , , , ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , , , , , , , , BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM ASH SHAKUR, , , , , , , , , , ONLINE PAID NOVEL YAR UWA KUKAN KURCIYA A KULLUN JAWABINE SAI MAI HAKKALI KE GANEWA, , , , , , , Yana tsaye ya zuba min idanun shi ba kiftawa jikin shi saye da farar shedata maza mai dinki iya cinyar shi da guntun hannu. Ga shaddan sai maiko takeyi alaman tsada da sabon taka a jikin shi agogon hannun shi silver sai kyali da yakeyi da takalma baki rufafu a kafan shi. Shiru yayi baiyi magana ba sai kallon mamaki da yake min naci gaba da fadin yaya na dauko ko duk dangi sun kimu kaida yan gidan ku ba zaku taba mantawa da muba ai yadda kuka nuna muna kauna. Sai gashi har kun din kun manta damu kun watsar damu a cikin kabila kun fita batun mu kun barmu a nan muna rayuwan kadaici. Haka baisa mun zargeka ba sam don kaima hawan abin kayi daga sama yaya dalili yana iyasa ka fita zancen mu idan kaga abin zai shafi wani naka don haka zaka iya mantawa damu, , , Sahiba ya fada da karfi a lokacin ne wani kuka mai karfi dayafi wanda nakeyi yazo min na dago ina fadin haka ya tabbatar muna da kissan Abban mu ya shafi duk ahalin mu ga baki daya ke nan, , , , , , Sake kiran sunana yayi a cikin tsawa a daidai lokacin da gaba daya yan gidan namu ke fitowa zuwa wurin ga baki dayan su umma har tana hadawa da dan gudu tana saukowa. Kilode sahiba na dago kai na kalleta a cikin hawaye ina fadin ko,sin kankan, ina nuna mata shi da mamaki a fuskan ta yadda manya kan rude wani lokaci idan sunga tashin hankali. Juyowa yayi don jin muryan umma din da magana ya makale mata lokaci daya duk abinda take da niyar fada nakinta yayi nauyi ta kasa fadi lokaci guda. Sai nuna Abubakar din da yatsa da takeyi can ta samu bakinta ya bude tana fadin modibbo kaine yau ? Ya dan murmusa cikin takaici yana fadin nice umma mun sameku lafiya yaya gida ya bayan rabuwa zoka shiga ciki umma ta fada ba tare data amsa mashi gaisuwan shi ba har lkacin kuka nake darza a wurin sosai . Amar na isowa yana sheda fuskanshi ya fada a jikin shi lokaci daya yana kiran sunan shi yana sake kuka mai karfi shima. Duk dauriyan ya Abubakar din ya kasa rike hawayen shi shima din dai kukan yakeyi sosai a lokacin hankali tashe. Nan umma tasa hannu tana fincike Amar din da shima ya rike shi a lokacin tana fadin ku barshi ya shiga ciki kun tsaya a nan kuna kuka haka kowa na kallon ku. Sai kuma ta juya wurin muniya tana fadin muniya broda din mune daya tafi shekara kusan biyar kenan rabon shi damu. Shine wanda ya saya muna wanan gidan da muke cikin sa tana nuna gidan dagani itama umma din a rude take a lokacin don bata cikin natsuwan ta idan kaganta. Inda nake tsaye na dafa mota dayazo a cikin ta ina rusa kuka ya nufa hannuna naji an riko wanda na gane ba hannun umma bane lokacin yasa na juyo da sauri. Shine a tsaye bayana yana fadin zo mu shiga daga ciki ku daina kuka haka gani na dawo da karfin Allah gareku wanan karon insha Allahu kunyi hakkuri ku saurari uzurina don Allah. Zomu shiga ciki ya fada yana mai kura min ido yana kallon cikin kwayan idona lokacin na mike nabi hanya ba tare da masa magana ba zuwa ciki. Shima din jan hannun Ammar yayi suka nufi hanyan cikin gidan namu yana sharewa kanin nasa hawaye tare da danyi mai magana a cikin kunnen sa. Ban tsaya falo ba daki na nufa na fada saman gado naci gaba da kukan da zance ga dalilin shi ba a lokacin dalili daya ya kawo shi shine zuwan yaya Abubakar wuein mu yau. Ina jin muryan su a falo tare da umma bai fadi komai ba shi ummace ke magana duk daba wani abu take fadi ba sai tambayan shi da tayi mutanen gida da sauran su. Barin zo umma ya fada ya mike tare da tambayan ina ciki ko aka bashi amsa da ina ciki ya shiga da sallaman shi dakin ya hangoni nayi rub da ciki kwance saman gado ina kuka. A kofa ya dan tsaya ya kura min ido kafin ya karaso cikin dakin yana kiran sunana jin ya zauna a bakin gadon kadan kusa dani yasani motsawa lokacin. Kara kiran sunana yayi yana fadin kukan ya isa haka don Allah nasan nayi laifi babba na tafi na barki da fama dasu umma da Ammar amma ki saurari uzurina kan haka. Mikewa nayi na fito falo wurin umma ya bini da kallon tausayi don yasan irin zafin da mukeji a lokacin ya dan kada kai ya mike ya fito daga dakin. Ummace ta kalleshi tana fadin sahiba badai rikici ba idan ta tashi yi yanzu murnan ganin shi kukewa kuka haka ko baku so ya dawo garemu bane yasa kuyin kukan nan. Barsu, suyi umma don a zaton su na tafi na barkune da wani manufa Allah ne shedana tafiyane ya kamani tun ranan dana aje ku a gidan nan. Gaba daya nida iyalina muka bar kasan nan sai kuma nayi kuskuren daukan layin ku a lokacin don azatona zan kara zuwa na dauki layin ku ko kuma lokacin ba bukata tunda zan dinga zuwa kai da kai ina ganin ku. Saidai gaskiya nayi mamaki kwarai lokacin dana dawo kasan nan naji cewa tun lokacin ba wanda ya neme ku har zuwa yanzu din. Bansan da haka ba a bakjn Amira yar hjy karima nasan basu tare daku ashe yadda na zata abinda ya ban mamaki kwarai ke nan a lokacin. Dakuma nayi tunanen cewa nima kaina gaba daya wani tunane a kanku ya gushe a zuciyana yasa na fara zargin cewa dole akwai wani dalilin hakan an matar damu ku an cire muna ku a zukatan mu ga baki daya. Saidai abjn mamaki ba a cire ku a zuciyae Amira da Faiza tare da fatima idan yai zan shiga cikin gida don mu gaisa zakaji Amira tace yaya ka kaini wurin sahiba. A sauri don Allah ita kuma Fa,iza zata labe tana tambayana yaya ka samu layin sahiba din ka bani wanan ya kara min karfi a zuciyana jiya tana tambayana na koma gida na kwana da shirin zuwa duban ku yau din nan. Karshema kuma kyautan da sahiba ta turawa yan uwan nata ya kara karfafa zancen ku a yanzu don yadda hjy karima ke fada min cewa saida takai ga dukan yaran kan tambayan da suke mata ko da acikin darene. Kunji abinda ya faru wanda nasan wani kulline akan hakan don Allah kuyi hakkuri da abinda ya faru banayi bane don wani manufa a gareku. Haba modibbo idan kana da wani munufa akan mu tun farko aiba zaka daukemu ka kaimu wurin dangi ba tsawon shekaru ba kuma zaka nema muna wurin zama a nan ks hanemu da yawon hayaba ai. Kayi muna hanyar da zamu dagora da kanmu nabada haya a dayan bangaren kudi na shigo muna ta cikin sauki a yanzu duk da yake hayan ya zama kamar gidane don wanda ke ciki a yanzu kamar dan uwa muka koma dashi a nan. Mutumin kirki muka samu don tun lokacin bamu sa wani a gidan nan ba yana rufene kawai sai lokacin da wanan mutumin ya shigo rayuwan mu a karshe kuma sai gashi ya samu matsala da gidan da yake haya shine muka bashi nan su zauna a cikin sauki don wurin aikin su daya da sahiba shine sabon mu dashi. Ya dago yana fadin Sahiba din aiki takeyi yanzu wani irin aiki takeyi a yanzu din kafin umma ta bashi amsa wayana dake gefe yayi kara na dauka. Felix ne da zolayan sbi ya fara mun hira yana ban labarin wai yau sun tashi oga na fada masu cewa sun danyi wasu sauye sauye taron da za,ayi don haka na shigo karfe hudu mu zauna kan sabon tsarin da akayi din. Kinsan masu kudin nan da wahal da tallaka ya dauka mu bamu da abunyi ne a garin sai nasa tsarin koda yake fa muna samu oga badai kirki ba kan don nasan bamu tashi a taron nan banza. Jin abinda yake fadi yasa na danyi murmushi daya baiyanar asirin kyawawan dumple dina a fili har suka dan lotsa kyawona ya baiyana a fili sosai. Daga inda yake zaune yana satan kallona ya lumshe idon shi yana ambatan subbahanallahi haka yarinyar nan take dama ashe ? Na sake dago kai lokacin da Felix din ke fadin kedai yarinya fito da katon jakarki gobe zamuji dumus a wurin ogan mu sosai na sani. Fararen idanuwan nawa da suke farare tas gashin ido dogaye don wasu na dauka ina saka eyes lashes ne a idona haka gashin gira na suma a kwance bakikirin dasu kamar an jera min su. Dariya nake sosai ina kara juyawa kamar da gaiyya nake juyasu a lokacin wanda ma ban san ina yin hakan bani sam. Ido ya kura min yana kallona tare da tunanen yadda na sauya ga baki daya ko magana na yanzu abin kallone don a cikin wayewa da isa nani watace nake wayan yana kuma jin kalaman mu da Felix din. Nan dai muka dauki lokaci a wayan ni da Felix din indan na dago kaina har fararen idanuwa suka sauka a nasa ganin zan kallo inda yake sai yayi saurin kawar da idon shi gefe da sauri. Subbahanallahi yake iya ambata don ganin yadda nake sauke idon ganin yadda wayewa da natsuwa yake a tare dani ga wani irin kwanciyar hankali daya hango . A take yaji wani irin faduwan gaba ya sauka masa tare da tsoro da fargaba yanayin nan da yake kallona a cikin shi zaune gaban shi lokacin. Don dai komai nawa har nasu umma din da Ammar a yanzu ya sauya muna ba kamar yadda muke a cikin wahalan rayuwa ba a baya. Saidai kuma yasan ba karamin kudine zaiyi wanan aikin ba a garemu haka dole dai da akwai babban madafan da muke dafawa a rayuwa daya sauyamu haka lokaci guda yanasa a zuciyar shi. Daidai lokacin da yaji ina sallama da wanda nake wayan ya mike yana fadin shi zai tafi sai ya sake dawowa insha Allahu zai shigo ya kara ganin mu. Wanda har lokacin ban kara masa magana ba ko kallon inda yake ya daga daga zaunen da yake umma ta kalloni tana min signal da ido nayi saurin fadin mungode ya Abubakar. Yace No kada ku damu wanan duty nane in kula da ku don ku din yan uwane sosai a gareni don haka ba zan kara barin ku ba kuma insha Allahu ya fada yana taba kafadan Ammar Hannu umma ta daga tana fadin amin wooo amin mun gode nikan hankalina na mayar kan wayana na nuna ban ma san yana falon ba a lokacin. Wanda sam bashi ba ko umma hakan da nayi sam bai mata dadi ba don ita a nata taso muyi haba haba da shine mu nuna ina aka saka dashi don zuwan dayayi wurin mu din. Niko a yanzu kaf din su a matsayin makiyan mu nake daukan su dan yadda suka barmu cikin diniya a watse babu kulawa lokacin da muke da bukatan hakan garemu. Bayan sun fita umma ta dawone aiko ta hauni da fada wai ban kyauta ba da ban rakashi ko nuna kulawana da zuwan shi ba . Shiru nayi ban dago kaina ba balle in bata amsa don nasan abinda zan fada ba zai mata dadi ba shine kawai nayi shiru a lokacin. Suna zaune a gaban tsofin suna mayar da magana bayan sun gama saurare dayan tsohon yace su barshi dasu kada masu nuna cewa sunzo wurin su don tasan halin mijin nasu karyazo ya zama matsala a tsakanin su kuma. Ta dawo gida Allah ya taimaketa ba wanda yasan fitanta har ta dawo don kowa na part din shi a lokacin don haka babu mai tseguntawa mijin nasu fitan ta. Duk da Allah ya dorata a kanshi yana dan daga mata kafa ita don yana son ta ita ba auren su na filani yayi da ita ba. Wurin barikancin su can ya hadu da ita ya auro ta don yaso kawai suyi zaman banza a watsene sai gashi har abin ya kaisu ga aure tsakanin su. Akayi kuma sa,a yana ji da ita sosai cikin iyalan nasa don tayi iya harka dashi yadda yake so saidai duk da hakan idan halin shi ya motsa yakan mata rashin mutunci sosai. Basu zo ba sai bayan kwana biyu da zuwan salma din gidan su saiga tsofin sunzo su sameshi a kan zancen yar shi din da dan wajen dan uwan nasa Alj Ali dcp. Da farko fada ya soma yi yana fadin shi za a kawo iskanci yaro yayi ba daidai ba zaice yana son ganin shi zaice aiba fada sukayi da matar shi ba balle yazo ya ganmu. Kai jam jam jam Nuhu wala hankali o da ace yau Namadine ke raye zai shiga zancen zurian ku har zaka iya musa mashi. Dayan kuma yace amma Nuhu ka ban kunya da mamaki ni da nayi bugun gaba ina fadin acikin kaf babu mai jin maganan mu da girmamu sai kai don haka ba zamu samu matsala wurin ka ba na bada wanan shedan a gaban yan uwanka. Son girma da yabo gareshi don haka tsohon na fadin haka kanshi yayi girma ya fara fadin ba hakana bane baffah yaron ne yake da girman kai da izza irin na uban shi yasa nake son nuna masa shi ba kowa bane wallahi. Shi kowane kuwa, dayan tsohon ya fadi yayi saurin kallo shi yace kwarai kana matsayin mahaifin shi kuma surukin shi zakace baida kowa shiko keda kowa a garin nan tunda har gaku iyayayyen shi da rayuwanku. Sai yayi shiru kamar yana nazari kafin can yace dasu naji baffah na kuma gode da zuwan ku gareni in Allah yaso zata koma idan na kimtsa. Haba Nuhu haba dai ai kamata yayi tunda har kaji maganan kuma ka yaba da zuwan mu a matsayin mu na yan uwan mahaifin ku ya kamata ne ka bamu dama yanzu mu mayar da yarinya dakinta tunda ba fada sukayi ba sukace. Ya kara yin shiru na dan lokaci kafi yace kada fa hakan ya jawo mata gori a wurin shi nan gaba yan tsofi har suna hada baki wurin fadin haba haba sam bazaiyi haka ga yar uwan shi ba ai. Nan dai sukai mai dadin baki da bashi girma har dai yaji ya zugu yace a shiga ciki ai mashi magana da hjy salma karshe ma dai shiya mike sai ganin shi kwatsam sukayi yana fadin Nazifa ta fito ta koma gidan ta gasu baffah a waje suna jiran ta yanzu. Komai dama ita Nazifa din ta gama shiryawa tana batun sulalaewa ta mayar da kanta gidan tane koda iyayyen nata basu yarda ba sai gashi Allah ya kawo saukin abin manya sun gyara zancen. Sun isa gida saida suka buga maigadi ya fito a bakin shi suke jin cewa maigaidan yayi tafiya a safiyan ranan ya tafi. Allah ya taimaka makulin daya bata da zatazo yana hannun ta shi tayi amfani dashi wurin bude kofan suka shiga tare da dan mata nasiha kan zaman aure ta daina daukan zance tana kaiwa mahaifan ta. Badon Allah ya gyara uwarta tayi dubaran tun karansu ba auren nan babu abinda zaisa ba, a rabashi a wanan lokacin tunda kowan su yahau haka. Ba gida suka nufa ba gidan hjy Addah suka nufa don sun san ba lalai bane su samu daddy a gida lokacin tundashi ba mazauni garin bane shi sosai. Sun sameta sun mata bayanin duk abinda ya faru sun kuma ce idan moddibo din ya dawo a yasamesu sukai mata sallama ta kawo masu abin arziki tayi masu sallama suka tafi a cikin dadin rai. Washe gari koda na tashi nayi sallah kamar kullun na dauko waya na samu sako daga Oga Sha,aban cewa na sameshi goma na safe. Nayi mamakin ganin wanan sakon duk da nasan hakan nada nasaba da sakon dana zauna na tsara mashi ranan . Saidai ina tamtama a zuciya ko hakan ya zama laifi a gareni ke nan a yanzu don haka korana ko warning dina zaiyi don da dukan mu yake nema dole Felix ne zai nemeni. Don haka sai tsoro da fargaba ya kamani lokaci guda a cikin raina daidai ba yadda na iya haka na tashi na shirya bayan na fadawa umma zan fita ana neman mu nayi mata bayanin kan bukin mutuwan da za ayi din asabar mai zuwa. Itama dai bata goyi bayan wanan dabi,an ba nasu saidai tace nayi taka tsantsan da aikina a gama lafiya kowa da nasa irin al,adan tunda na saba ganin yadda sukeyi lokacin da nake talla har pure water na leda dana gora muna kaiwa a wurin mu saida masu a ranan muna ciniki sosai idan ana taron. Nagama shiri cikin atamfa dana dinka buje da riga na dora hijab a saman dan kwalina kamar yadda na saba idan zan fita. Na isa katafaren gidan nasu ban samu wani matsala ba son a yanzu masu aikin gidan sun saba dani ko don ganin mu tare da sukeyi lokaci lokaci. Wanda ke tsaron kofab shiga falon shi na tambaya idan oga ya fito ya sanar dani cewa yana ciki yau tun safe yake karban bakin shi. Kafin in shiga saiga Felix ya iso wurin tun dags nesa yake washe min baki yana fadin wa nake gani kamar beauty don haka yake kirana idan ya tashi min sheri. Har ya iso inda nake yana fadin kai kai kai kinga yadda kika hadu kuwa kamar wace zata gasan kyau haka gaskiya kayan nan sun matukar karbi jikin ki sosai. Na watsa mai harara ina fadin kaifa baka rabuwa da zolaya ni bashi ba don Allah kiran me oga ke min a yau kuma ? Kafada ya daga tare da ware hannayen shi yana fadin ni ina zan sani yarinyar Oga na sani ko wani sirin zaku tatauna a yanzu wanda baku son kowa ya sani. Sake hararan shi nayi ina nufan kofan sai kuma naja na tsaya don ban yarda ya sakani gaba ba haka shi yana bayana ba. Muje mana ya fada yana nuna min kofan nace ka fara shiga kayi min iso sai na biyo ka a baya ya kwashe da dariya yana tura kofan. Bayan shi nabi muka shiga banyi zaton yasan ina bayan nasa ba saida nayi sallama cikin zazzakan muryana duk da bana ji koda ya amsa min saboda girman falon da nisan da muke dashi a tsakanin mu. Waya yakeyi ga wasu tsofin yarbawa guda biyu zaune a gefen shi da irin rigan sakin nan nasu nada a jikin su cikin natsuwa nake tafiya har na dan karaso inda suke suna bina da kallo a cikin harshen yarbanci na gaidasu suka amsa . Felix ya nuna min wurin zama nakai zaune shima ya zauna daga barin gefena na hagu har lokacin tunda yai muna kallo daya ya dauke kanshi bai sake kallo inda kowan mu yake ba. Kaina a duke yake ina kallon zanen kafet din da aka malala saman ties din falon mai ban sha,awa zakace hakine ba sakashi akayi ba idan ka ganshi don kyau. Jin yayi shiru ya gama wayan yasana dago kai don ganin me yakeyi muka hada ido dashi a daidai lokacin da yake mikawa tsufin nan kudi. Da sauri na dukar da kaina a cikin kunya kamani da yayi ina satan kallon shi shima idon nasa ya kawar yana magana da tsofin a hankali duk da muna falon ba zamu iya jin me suke fada ba a lokacin. Tsofin suka mike suna mashi sallama kafin su juyo garemu suna muna sallama nabisu da idanu har suka bacewa ganina na nisa ina juyowa gare su. ZAINAB IDRIS MAKAWA ANA DARA GA, , , , , , , , , , 4️⃣9️⃣ BY , , , , , , , , , , , ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , , , , , , BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AL ALIYY, , , , , , , , , ONLINE PAID NOVEL YAR UWA KUKAN KURCIYA JAWABINE MAI HANKALI KE GANEWA ALLAH YA BADA IKON BIYA, , , , , , Da inyi shiru gara ina tunatar daku gaskiyan abin ki biya shine ka,ida ki karanta don namu ba irin nasu bane namu ba takarda bane rubutune ta yanan gizo ki biya ki karanta shine ka,idan abin yar uwa kin biya ki karanta a cikin salama ba tare da shiga hakkin wani ba bawai ina magana akan nawa ba kawai a, a yar uwa idan ance paid novel ne son Allah kikai zuciyat ki nisa ki daurekibashi bayan don kariyan ma,aunin ki sai mai hankali da imani zata fahinci kalamina Allah yasa mufi karfin zukatan mu a matsayin mu na musulmai ku yafe min idan na fadi ba daidai ba gareku. Falon ne yai shiru na dan lokaci kaina na kasa duke ina danna wayana da ba komai nake duba a ciki ba lokacin don kawai na kawar da shirun da falon yayi ne a raina. Jin shirun yayi yawa yasa na dago kaina naga me yakeyi a lokacin kawai sai na samu niya kurawa ido ashe yana kallon abinda nakeyi da wayan. Nauyi da kunya naji lokaci guda cikin sarkewan murya na daure na kokarta na dan zamo saman kujera ina gaidashi cikin girmamawa. Saida yai dan jim ya amsa min da yaya gida da aiki nace Alhamdullah ina komawa saman kujeran na zauna. Shirune ya kara biyo falon na kamar minti biyu kafin yayi gyaran murya duk muka dago kai muna kallon shi lokaci guda. Yace a cikin muryan nan nasa mai taushi irin na ustazai ina fatan kin san dalilin kiran ki da nayi a wanan lokacin a cikin hausa. Na girgiza kai alaman ban sani ba ya dan murmusa a karo na biyu danaga murmushin shi na farko a jos da yake tare da kakan shi sai kuma yau dayai min a falon nasa. Naji yace OK menene ra,ayin ki akan bukin da za ayi sturday na mahaifina ko bake kika turo min da sako bane ya fada yana tsureni da idanun shi. Ban dago kai ba don nauyin shi da nake ji sosai saima wasa da nakeyi da yan yatsun hannuna da suke zara zara sun sha penti don fashin sallah da nakeyi na digasu da safen nan don kwaliya. Muryan shi naji yana fadin kinyi shiru ko bakya magana ne kece fa kika kawo wanan sharan yanzun kuma sai ki min bayani yadda ya dace inji a gaba idan zan iya. Na dago kaina fararen idanuwana suka sauka akan shi dana dan kalleshi kafin in bude bakina ina sake dan murmushi daya kara baiyyanar da asirin kyau na a fili ina fadin Sir . Subbahanallahi yace a zuciyar shi yana lumshe ido gaskiya badai kyau ba amma bata waye bane har yanzu don akwaita da sauran wayewa saidai akwai kamun kai da ake son macen musulma dashi kam gaskiya. Nasake fadan Sir saboda naga haka baya cikin tsarin musuluncine kaima ka sani don haka da wanan abin gara kawai ayi abinda Annabin Allah ya koyar damu game da mamatan mu da zaiyi saurin kai lada a garesu. Shine addua ta hanyan kai sadaka tare da abin sallah a masallataiya da sadaka a inda ya dace mai zai hana a aika da sadaka ga gidajen marayuwan na gaskiya da suke neman taimako irin haka a ciyar dasu da niyar ladan yakai ga marigayin. Masha Allah yace ba tare da sanin kalman zai fito a bakin shi ba lokacin don tunda na fara magana suke kallona dashi da Felix din suna kallon yadda hakorana farare suke jere kamar anjera min sune haka ga wani dan wushirya a tsakanin su daya dan kara min kyau idan ina magana. Mai akin shice ta shigo dauke da tire da dan kofi a cikin sai data gaishe mu ta aje mai tana bude kofin a gaban shi hayaki ya dan tashi daga cikin kofin mai nuna zafin ruwan shayin a lokacin. Bayan fitan ta dan shiru ne ya kara maye gurbin falon saida ya dauka ya dan kurba sau biyu ya rike kofin yana fadin . Ummm,humm ya ustaz ya fada a baiyane ke muke saurare ko kin gama bayanin ki ke nan kallon shi nayi na dan sake murmushi don jin sunan daya kirani dashi da ustaziya dan kawai na fadi ga yadda za ayi a addinan ce. Shiru nayi naci gaba da wasa da yan yatsuna ban dago kai ba bayan murmushin dana danyi da farko can naji muryan shi yana fadin. Kinyi shiru ko baki tsara komai bane game da hakan nawa kike ganin wanan tsarin naki zaici ko baki lissafa ba kika gabatar da shawaran ? Da sauri na dago kaina don jin abinda ya fada don na zaci a cikin fushi yayi maganan saboda shishigin da nayi masu nabada wanan shawaran. Kofin shayin shi ya kara kaiwa bakin shi ya kurba ya aje saman table din don ya fahinci ba zan fadi wani abu ba akan hakan . Ya aje yana fadin cikin mamaki ok kina nufin wani zan saka yayi wanan tsarin da kika kawo a yanzu ko me dole keda kika tsara abin kece zaki aiwatar da komai daya shafi hakan a yanzu shiyasa na kiraki a nan yanzu. Ya mayar da kansa ya jingina a kujera yana fadin ina fatan kin shirya yin hakan daga yanzu don yau wednesday babu wani sauran kwanaki garemu. Milayan nawa za a baku ki gudanar da wanan aikin da tsare tsaren ki ki fada yanzu a tura maki kudin sai a fara komai yadda ya dace ayi. Shi aikin Allah idan za a yi ba dole saida kudi mai yawa ba ko kudi kalilan sai su wadatar da wanan plan din ai. Sai naga ya bini da kallon mamakin jin abinda na fada sai kuma ya koma lumshe idanun shi kamar ba zaiyi magana ba a lokacin. Wani irin mamakine yake yi na yarinyar nan don ya gwadata da dama a fannin kudi tana cinye jerabawan shi da yake mata din. Felix ya ambata yayi wani amsawa da sauri yace ka miko min chack dina da biro a daki na rubuta mata yanzu felix din da bai san zancen da akeyi ba don shi baijin hausa kuma a cikin hausa muke maganan dashi a lokacin. Felix na shiga bai kara kallon inda nake ba sai zaman daya gyara yana lumshe ida da tokare haban shi da hannun shi daya ya dora fararen kafan shi saman dan table din gaban shi yana cigaba da tunane akan abubuwa. Na dago kai na dan kalleshi idon shi a lumshe sai kuma nakai kallona a inda tsufin nan suka tashi dazun da muka shigo naji gabana ya fadi lokaci guda. Sake kallon shi nayi yana zaune a yadda yake din nace Sir dai ko ba kudi mutumin kwaraine shi ga kyau ga kirki ga kuma kwarjini na fada a raina. Ido na tsura mai ina kare mai kallo dan gashine irin da matasa zamani ke bari yanzu a fuskan su zagaye a fuskan nasa bakikirin ya karawa fuskan nasa annuri sai dan baki karami hanci har baka farine kuma sol dashi kamar wani jinsi ne na wani nahiyar. Abinda nake ganine yasa nayi magana da ya maye gurbin shirun da falon yayi a lokacin ina fadin ya kamata ka dinga nisanta kanka ga duk wani wanda ya fito daga fannin mahaifin ka mace ko namiji don suna binka da mugun nufi a koda yaushe. Idon shi ya bude ya tsaya yana kallona har na gama fadin abinda zan fada din ya wani murmusa tare da fadin nasan da wanan tun ina karami basa kaunana sam gaba dayan su Yanzun ma da abinda suka shafama a kujeran nan idan da son samune lada ka yarda ka zauna a saman shi sai bayan gama bukin nan baki daya don manufan su su jefeka ka kafadi daga wanan bukin da zakuyi. Fitowan felix ne dakin dauke da abinda ya aikeshi yakawo mai ya mika mai shine ya hanamu cigaba da maganan. Rubutu yayi saman check din ya miko min tare da fadin gashi ki karba ayi yadda ya dace aikomai na taso daga inda nake zaune. Na nufoshi don na karba a cikin ladabi ina fadin Allah ya karba yasa haske yakai gareshi dashi da sauran mamatan mu ga baki daya. Ina isowa wani irin kamshine mai kashe jzuciya yaji ya daki hancin shi lokaci guda saida ya lumshe idon shi yana amsawa a cikin taushin murya da Amin ya Allah. Don gaskiya yaji dadin wanan adduan nawa don shi yana son yaji wani nama mahaifin shi addua irin haka. Har na juya naji yana fadin ki tabbatar da kunyi amfani da kudin sosai ga family din ki nina baki bakin hakan ki dauki iya bukatanki ki bada saura ga wanda kike so final. Ina fita ya kalli felix da ke kokarin mikewa tsaye lokacin yake fadin a samo wasu kujeru yau din nan a saka a falon nan ka kwashe wanan a fita dasu. Ya dago kai tare da fadin oga wanan fa basuyi ko wata uku ba da aka shigo dasu falon nan ko ka manta da hakan neya fada yana kallon kofan dana fita. Yace dashi a cikin dan tsawa do as i said felix ko ka manta da mahaifiyana zata shigo gobe da yan uwan ta ne kasan nan wurin adduan . Yace sorry sir ya dukar da kanshi kasa shi kuma ya shige zuwa ciki zuciyar shi cike da tunanen zancen da mukayi dashi a falon. Tun safe take tsaye tana faman aiki duk da ba wani aiki bane takeyi umurni ne ga abinda zasuyi mata don girki da gyaran gida saboda wayan da tayi da mommy ta sheda mata dawowan mijin nata a ranan da ita mahaifiyar ta tursasa mashi sai ya dawo gida matansa ta dawo dakin ta itama. Yayi mamakin jin haka don shi sam baiso haka baima cikin tsarin shi a lokacin don gaba daya yaso ya basu mamakine da sai sun girgiza dashi amma kuma aikin gama ya riga da ya gama mommy ta bata masa tsarin komai yanzu. Tana zaune ta tsala kwaliya daga ita har yaran ga wani irin kiba data zauna tayi a yanzu tun bayan haihuwan yar su na biyu ta fara wanan kiban daya kara munanta ta a yanzu. Tana zaune a falo tana jiran isowan shi koda taji tsayawan mota da hamzari ta mike ta kwashi yaran zuwa waje don su tareshi. Sai ganin su yayi a gaban shi girshi ba kunya wai tana mashi sannu da zuwa a cikin daure fuskan shi gareta ya fito daga motan ta kara gaidashi ya amsa a daure ya wuce har yaran ba tare daya taba su ba zuwa falon shi. Kamshine ya tare shi a falon zai shige yaji babban yar mai sunan mommy tana kiran shi da daddy yaja ya tsaya ya juyo yana kallon yarinyar tare da rage tsawon shi gareta yadda ya saba masu a can idan ya dawo. Ya sunbanci yarinyar a goshi tare da tambayanta yaya take tana masa gwalanci duk da ta fara mantawa dashi don watan su hudu ke nan basu tare dashi. Daga bayan shi inda Nazifa take tsaye ne yaji muryan ta tana fadin watau mu ba za ai muna wellcome ba da dawowa ba sai ita mai sunan hjy ku ko ? Bai mata magana ba sai mikewa da yayi yana karban yarshi a hannunta ya daukesu duka biyu zywa dakin shi driver daya daukoshi ya shigo mai da kayan shi ciki a lokacin Nazifa ta dauka zuwa dakin shi abinda bata saba yi ba ke nan a baya. Saida ya huta tare da yaran a dakin shi ya fito zuwa falon don kiranshi da Nazifa ta matsa dayi na ya fito yaci abincin da yasha gamin bokaye da malamai da mamanta tayi ta karbo mata shi don kawai a samun kanshi a dinga juya shi yadda ake so saboda kafiyan shi da taurin kai da yake dashi kuma yake nuna masu shidin shine fa. Saidai sun makaro don nacin ta yasa ya ankara da hakan don haka koda yana zaune sai waya yakeyi harda na iska tana zaune a cikin damuwan rashin cin abincin shi duk ta kagu taga yakai cokali a bakin shi. Can dai da taga ya gama wayan ta kirkiro murmushin kissa tana fadin wai ko fushi kake damune na abinda ya ffaru kaki cin abincin nan ? Ya kallota a lalace yana fadin fushi fushi akan me mekikai min da zanyi fushi aiku zance kuna fushi keda kuka koma gida ba tare da nasan laifin da nayi maku ba bayan mun rabu lafiya dake. Tace kayi hakkuri don Allah nagane kuskurena nayin hakan don ban dauka Abba zai canza abinda wani manufa ba haka. Ban san wani irin kiyayya ke tsakanin gidan ku da Abban mu ba har yake ikirarin shafan diyan da muka haifa dakai suma abin ya shafesu don sam Abba ya gwada min baya kaunan jinin ku ko kadan wallahi. Duk da mama ta dan fada min cewa matsala aka samu na rabon dukiyan wani dan uwansu maikudi da yarasu tun muna kanana wai kowa nason wani abu ya kasa barwa dan uwa a tsakanin su shine wai mafarin wanan fadan nasu har yanzu. A yadda naji mamana cewa har zargin duk suna da hannu a cikin mutuwan dan uwan nasu a lokacin da yake daddy na sama aka rufe zancen wai har yanzu kuma ba, a san inda iyalin dan uwan nasu suke ba gashi su sun raba dukiyan nasa a tsakanin su suda su baffah gyade da sauran su. Gaskiya abinda su Abba keyi baida kyau saidai kuma ai dukiyan dan uwan sune shine kawai amma aibai kamata ace har ya zama matsala a tsakanin su ba haka. Tayi shiru tana dago kai ta kalloshi don dama tana duke tana sharewa yarta dake shan nono bakine saita dago kai jin yayi shiru yana sauraren ta. Irin kallon da yake mata a lokacin shiyasa tasha jinin jikin ta ta fara zargin irin baran baraman da tayi ko katobara a gaban shi duk a wautanta nason su shirya dashi ya sake jiki da ita saboda kewan shi da sharenta da taga yanayi. Amma cikin labarin abu biyu yafi tsaya mai a rai na farko shine cewan da tayi mahaifin shi na cikin harkalan da akayi na kashe namu mahaifin. Sai kuma cewan da tayi mahaifinta har diyan da suka haifa baya kaunan su yana iya sabauta su don irin kiyayyen da yake nuna masu. Mikewa yayi a zabure saida gabanta ya fadi ganin yadda lokaci daya ya juye mata kamar wani zaki dashi yakai hannu ya karbi yar dake hannun ta ta rike tana kallon yanayin shi. Ina zaka da ita ya mika hannu ya fisgeta da karfin tsiya yana fadin bani yata in kaisu inda za a kulamin dasu don bazan barsu inda zasu tashi da rashin imani ba. Ganin da gaske yakeyi yana shirin fita mata da yaran yasa ta yunkura ta rigashi isa kofa ta kulle ta saka makulin a cikin jikin ta. Hakkuri ta fara bashi yana kokatin gyara yaran baida niyar bata su dabara ya fado mata ta dauki waya a cikin kuka ta kira mommy a cikin kuka take fada mata komai mommy din tace bashi wayan ta mika mai yaki karba tasaka handsfree tana fadin koma meye na fada ma kajirani gani nan zuwa yanzu gidan. Koda mommy ta iso ta samesu a cikin tashin hankali sosai don Nazifa tasha kuka har ta godewa Allah a lokacin don tashin hankali data gani a fili lokacin. Da umurnu ta fara bashi ya mika mata yar data fara kuka sosai a lokacin baiso ba ya mika mata yar ta zauna tana fadin meya kawo haka yau yau da dawowan ka ? Ina na fadama cewa komai ya wuce kada inji wani magana wani irin huci yayi da baki kafin yakai zaune yafara fadawa mahaifiyar nasa abinda ya faru tiryan tiryan. Hjy sai kada kai takeyi tana fadin Nazifa mai ya kaiki wanan katobaran haka a gaban mijin ki baki tunanen in mahaifin ki yaji wanan zancen dake da uwarki duk kun shiga cikin matsala ke nan. Nan dai mommy ta samu ta kwatar da fitinan har ya sauko kan dan bakin data bashi yace yaji amma yaran sa ba zasu taba zuwa wanan gidan ba a yanzu. Hakana ya kwana ranan yana faman tunanen wanan zancen biyu a zuciyar shi abunda ya hanashi barci ke nan a ranan. Saida na isa gida na duba abinda ya ban tunda na saka a jakka kafin in fito ban dauko na dubaba saidana gama cin abinci na dauko jakkana ina dubawa. Ba karamin kaduwa nayi ba lokacin da naga yawan kudin da yai signing a karbo gashi har ga Allah yace na zari kusan rabi muyi amfani dashi a gidan mu muma din ai marayune. Umma na kira ina fada mata abinda ya faru tayi shiru tare da mamaki cikin rike habanta can tace dani duk da hakan ki masa sadaka yadda ya kamata sai ki kwantata ki rage saura din Allah ya jikan musulmai ya gafarta masu. Na amsa da Amin zuwa la,asar na samu Abdulhamid a office na fada mai duk halin da ake ciki game da yadda mukayi da ogan mu din dashi muka fito tun a ranan muka fara bin masalataiya muna ganin limamai muna basu sadaka da abubuwan amfani a masalcin. Washe gari muka dora a inda muka tsaya don muyi yadda ya dace gaskiya mungama da masalataiya muka koma ba mabukata musulmai abinci sosai har labari yakai kunnen ogan namu. Ranan dayace din ranan mahaifiyan shi ta shigo suna falo sai ga wasu mata sunzo gaida ita da zuwa nan suke fada mata cewa sunga an saka hoton mijin nata babba ana mashi addua taji dadin hakan sosai kallon dan nata tayi don tasan aikin shine bana kowa ba. Murmushi ya sake mata taka tsantsan yakeyi da mahaifiyar nasa sosai da kanwarshi da sukazo don bai yarda wani mai aiki dan lagos ya dafa masu wani abinci ba da abinsu sukazo daga can don tsaro. Ranan da za ai taron bamu zauna ba tun safe muke faman shiye shirye da zirga zirgan komai ya kammala daidai yadda aka saba yi. ZAINAB IDRIS MAKAWA ANA DARA GA, , , , , , , , 5️⃣0️⃣ BY, , , , , , , , , , ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , , , , , , BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AL KABIR, , , , , , , , ONLINE PAID NOVEL YAR UWA KARFIN IMANI KE SAKA TSORON HADUWAN BAWA DA UBANGIJIN SA ALLAH YA KARA MUNA IMANI A ZUCIYAR MU AMIN, , , , , , , Tsatsaye muke duk kan mu a falon nasa daya ban mamakin sabon gyaran da naga anwa falo din a cikin kwana biyu haka har center kafet din nan daya dauke min hankali a ranan babu shi yau dana shigo. Dukkan mu farin tufafine a jikin don wanan sha, anin na dinka farin less da akai min dinkin buje da riga kuma dinkin ya karbeni don zamanin buje darigane abin yayi sosai sai kuma dogon riga wanda ni nafi saka dogon riga redmade ba wanda aka dinka ba. Takon ogane ya fito ya samemu inda muke tsaye muka shiga gaidashi ya nuna muna kujera mu zauna shima don ya kai zaune yana fuskantar mu. Jimoh ya fara kira ya dago kai yace kasan wanan abu yashafe ku dukkan ku tunda ya shafeni don haka zaka kula da komai dake gudana a wurin taron nan har abincin da za,aci ka kula da lafiyan shi you know you people are special from d other and kuma ba kowane yasan alakata daku haka ba a cikin family dina so take care. Oga Jimo din yace yes sir ya juyo kan Felix yace make sure u felix kana hankalce da duk wani motsi na kowa a wurin ka kula da abinci da abin sha wanda bakin mu zasu ci baida illa ko kadan yace yagane. Sai ke yemisi bakin mu mata su samu kulawa sosai ta hanyar directing din masu kula da bangare su yaza kina kulawa da wanan banda rawan kai ya kara mata hakan aka kwashe da dariya sabanin nida ban ko murmusa ba don nawa dariyan zai kona mata rai fiye dana saura. Kaima Adnan aikika kenan a bangaren maza a yau don Allah ku kula suka amsa da yes sir sai ya kallo inda nake yana fadin u Sahiba you will be with my family i mean my mother and my sister and others take care of their needs please kada ki yarda ki daga a inda muke komai taro zaki saje a cikin mu tare damu kamar yar family din kike kina saka ido a kan mu. Felix yace baby girl ke nan dai ya watsa mai harara kafin ya fara fada yana fadin ka kula ba aikin wasa nake so ba don nasan akwai makiya a wurin dole zai kasance da hatsari a wurin sosai don kaga wanan taron yafi na wanda mukayi a baya cika sosai . Ya amsa da zai kula kudi ya fito dashi ya mikawa kowa wrafer yana fadin a samu na badawa kunsan komai na bayerabe kudine shi don haka ya bamu namu rikon . Kowa ya mike nima haia ya juyo yana fadin Sahiba go inside now zaki samu mahaifiyana tare da yan uwanta suna shiri kufito tare. Gabana ne ya fadi lokaci daya idan na shiga wazance dasu nake amma a fili yes sir na amsa mai ban ko juyo gun yan uwa ba ma sakai na shige ciki. Cikin babban wurine sosai mai dakuna da yawa a ciki akwai kuma katon falo maidan girma daga ciki din na samu wuri na zauna bancewa kowa komai ba ina kallon zirga zirgan su da kowa keyi na shiri. Sautin wani waka ana salati na fara ji haka yasa nasan zasu fito daga cikin zuwa wurin taron ke nan son nasan komai akan taron na tashi naga anayin sa tun ina karama kuma duk wankan da zasuyi na iyasa sosai nima. Na mike na gyara na fara dan takawa na shige cikin su muka jera tare zuwa waje a falo muka sameshi nan ma tare da wasu yagama ya tako zuwa gaban uwan shi ya duka ta dafa kanshi tana mai addua sauran masu kurciya a wurin duk suka kai duke ana fadin Amin amin amin ya Allah. Lokacun da aka mike din ne na samu kustsawa nakai kusa dasu na tsaya har aka fito inda za a shiga mota motocine bakake wul dasu tunda zamu shigo an wankesu sai walkiya sukeyi suna sheki da daukan ido. An bubudesu da sauri ya nuna wanda mahaifiyar nasa zata shiga suka nufi wurin alokacin naja na tsaya ya kalloni da sauri nabi bayan su nima. Kowa ma yabi don ga masu kirarin su nan suna kirari har muka isa wurin motan suka shiga suka zauna uwar da kanwarshi a baya sai ya bude gaban a zaton kowa a wurin shine zai zauna sai juyo yana fadin in shiga gaban motan. Na shiga na gyara aka rufe ya koma baya tare da mahaifiyar shi suka saka kanwarshi a tsakiya sauran yan uwan su suka shiga sauran motocin dake wurin. Idona na lumshe tare da ajiyan zuciya lokacin da naji motan ya tashi ya fara tafiya damu zuwa wurin taron ke nan. Sha,aban waye wanan daka hada mu da ita ban gane ba mahaifiyar tasu ta fada abinda yasani bude idona ke nan lokacin. She is my new sectrary ya fada wanan karamar yarinyar haka aini na dauka ka hakkura ka samu wace kake sone yanzu but wanan ai tayi karama sister shi Aisha ta fada. Stop dat Aisha ya fada a kausashe ya zama dole sai ta kasance damu ke nan mahaifiyar su ta tambaye shi. Aikintane ta kula damu a wurin shine dalilin zuwa da mukayi tare ita don ta kula damu a wurin ya fada yana kawar da kai gefe daya. Shiru motan yayi har lokacin da muka isa wurin taron addua inda wani filine babba da aka ware dan shagulgula a garin banyi tsamanin taron zai tara jama,a irin haka masu yawa a wurin. Saigashi indama zamu aje mota ya zama aiki a wirin saida kyar felix suka samu a can ciki aka shiga da motan muka samu muka sauka. Dakyat suka samu kaiwa inda aka tanadarwa su iyalin shi don bayan su yan dakin su su biyu akwai wasu mata biyu da mahaifin nasa ya haifa mahaifiyar su yan yare dayane da mahaifin nasa. Yasha aure basa haihuwa ko kuma idan sun haihu diyan su mutu sai aka camfashi cewa da diyan kudin shi ke hafbaka don haka aka dinga tsoron auren shi. Lokacin daya hadu da mahaifiyar Sha,aban bai boye mata komai ba duk abinda ake zarga mashi din ya fada mata da yake bahaushe akwai karfin hali su hakan bai basu tsoro ba ya aureta ta haifa mai diya biyu kuma sunanan raye. Sai kuma suka juyacewa ai ba diyan shi bane su shiyasa yaran suka tsaya jin haka shikuma lokacin yana raye yace gaba daya duka iyalin shi za,aiwa gwajin jini sai sukaki yarda wacan da diyanta suje tun lokacin yaran suka fita rayuwan shi. Amma bayan mutuwa shi an raba gado dasu an basu kason su kamar yadda musulunci ya shimfida . Saidai Allah bai raba daya ba don yanzu su saidai sunan mahaifin nasu dasuke amfani dashi don na komai daga cikin abinda aka raba din nagadon su. Duk a wanan taron na tsunci maganganun a wurin matan dake gefena ta baya inda Allah ya rufawa Sha,aban da mahaifiyar shi asiri shine kamar su sak da mahaifi nasu har dabi,un shi duk na mahaifin nasu ne . Lokacin da aka kirasu zuwa wurin babban limamin don suyi addua ne, nabar jin me suke fada don na tashi na barsu a wurin suna hiran su na gulma. Lokacin da suka tashi din don zuwa gaban liman din banyi niyar tashi na inbi bayansu ba tunda iyalan mamacin akakira zallah. Amma tun da natuna da worning din da yai min yasa da sauri na mike nabisu a bayan muka fita tare dasu zuwa gaban liman din. Yadda suka rusunna haka nima na rusunna adan baya dasu kadan ana addu,an ina amsawa da amin amin har na gaji da duki can muka taso muna bin limaman dake zaune muna zuba kudi kamar yadda akeyi dai. Muka dawo wurin zaman mu muka zauna bamu dade da zama ba aka kawo masu abinsha dana taunawa gaban su aka aje nabi drinks din da kallo na dago kai muka hada ido dashi na girgiza kai alaman kada su taba komai fa. Zaune nake kawai amma na mayar da hankalina ga abinda ya kawoni tun lokacin da naga an fara yawo da abinci don kada a samu matsala a bangarena. Zakace hankalina yana gun program din da akeyine a wurin saidai a zahiri ina kallon abindake wakana dasu ne a fakaice a wurin. Can sai ga wata mata fara tas irin hajiyoyin lagos din nan itama mai jiki kama mahaifiyar oga din daganin ta da yanayin shiganta zaka gane itama hamshakiyace dai tazo ta rungumi mahaifiyar Ogan namu sun dan dade tare haka suna magana. Sai bayan tafiyan ta matan ta wuce ne na farga da abinda ya faru a lokacin saboda baka dauka yadda sukayi da junan su kadauka akwai wani na mugun nufi a tsakanin su. Na rasa yadda zan sanar dashi an samu matsala sai dabara ya fado min wayana na tura mashi text da fadin if possible kasa mahaifiyar ka ta canza gyalen jikin ta yanzun nan akwai sherin da aka shafawa gyalen kada ya taba jikin ta . Sai aka samu akasi bai dauki wayan ba a lokacin don mutanen da sukai yawa a gaban su suna kawo gaisuwa lokacin. Na rasa yadda zanyi kawai saina danna mai kira ba kakautawa na matsa da kiranshi ina kashewa har yakai ya ciro wayan nasa ya duba sai yaga sakon da sauri ya dan juyo na gyada mashi kai alaman eh. Rubutu na hangoshi yanayi ga wayan shi ya turo min What would we do now ya aiko min da sako na tura mai da fadin mu tashi zuwa resting room zan kawo mata gyale yanzu kada kowan ku ya bari gyalen ya tabeshi. Ya gyada min kai bayan na tura mai da sakon sai kuma na turawa Adnan ta wayana nabi bayan su zuwa dakin hutun da zasu jira din. Muna kai kofan nake jin uwar na masifa don me wai ya dago dasu zuwa nan sai da muka shiga ya kalleta yace akwai matsala don akwai abinda aka shafa maki a jiki ki a wurin rungumar ki yanzun nan shi muke son ki cire wanan gyalen da sauri ba tare da maganin ya taba jikin ki ba . What ta fada kafin tace Lalalala haram haram ta fada tana yare cikin larabci shima yaren ya fara mata jikin ta yayi sanyi sosai tana fadi kalas kalas yallah yallah. Ta juya turanci tana fadin shine tsiyata da mutanen nan wallahi baka zuwa sai wani ya nemi da yahalaka yaga bayan ka. Ganin zata kaiga barin abin ya tabi jikinta yadda take fada na taka zuwa inda suke a cikin ladabi nace dashi zancire gyalen a jikin ta yanzu sai ya yafa mata na jikina kafin akawo wani Adnan zaizo yanzu dashi insha Allah. Hakan mukayi yaja wanda ke jikina ni kuma na cire nata ya yafa mata nawa din tayi tagumi tana kallon ikon Allah gabanta sai faduwa yake mata anan ya fada mata cewa kada su yarda su taba komai naci a wurin. Adanan ya kirani ya dawo na fada mai inda muke yashigo ya mika min na walwale kai mata gyalen maikyau dashi ta yafa ledan mukai amfani muka saka wanan a ciki. Iya tunanen duniya yayi shi a rayuwan shi don ya gano gaskiyar maganan da yaji a bakin Nazifa matar shi don yana son ya dago wanan case din ba tare da sanin kowa daga cikin mahaifan shi ba. Abune wanda yake son binciken siri don haka gaba daya a yanzu sai bai yarda da yan ahalin shi ba don duk yana zarginsu dayin rubda ciki a gadon uyan maruyun Allah da aka bari bayan kashe masu mahaifi da gangan . A wanan fanin yasan yana da evidence ko umma ta ishesu shedan komai ga irin bayabar da tabayar a lokaci don an kashe mata miji a gabanta ta kuma san ko suwaye sukayi shi. Saidai ta ina zai fara wanan binciken nasa yanzu karshe dai yayi tunanen zuwa police station ya binciko wanan case din saidai hakan ba zai yuyu a gareshi ba sai a sirce zai gudanar da komai yadda ya tsara din. A gidan sa kuma duk wani dabaran da nazifa zatayi mai yaci abinci ya kaucewa wanan zai fita yaje waje ya hada take away ya zauna a motan shi yaci don kada wani ya ganshi girman shi ya fadi. Yauma zai fitane da safe yana shiri tana zaune gefen gado ta zuba mai ido tana ba yar ta nono take fadin. Nasan a gidsn hjyn ku kake cin abinci yanzu don baka yarda da girkina ba kana nufin za a hada kai danine a cuta maka ko me koda yake ma ba kaine mai laifin ba mommy din ai tasan hakkina ne yanzu in baka abinci ba ita ba amma take baka don kawai a kuntata min. Dakatar da abinda yakeyi yayi yana kallon ta tare da fadin Nazifa kanki daya kuwa koda a can nake cin abincin ma laifi ne idan naje can naci abincin ? Ai kin fi kowa sanin cewa mommy ce mahaifiyata don baki da kunya zaki bude baki kina fadin wanan banzan maganan haka a gabana yanzu. Ta tabe baki tace dama ai haka akeson ya kasance a tsakanin mu shiya ake kirkiro abubuwan da akasan zanyi magana a kanshi. Saukin abindai mutum bai iya rabumu saidai yayi sherin shi ya barni wallahi indai nice. Ya rasa abinyi sai ido daya zuba mata wai uwarshi take fadawa wanan maganan haka yana mamakin rashin iya maganan Nazifa haka Wace ma bata iya boye sirin uwarta da ubanta ba wajen katobara wa zata ragawa ga duk abinda ya fito a bakin ta wautane ko rashin tarbiya ke damun ta ? Wani haushi ya shigeshi nata ta ya juya yana saka talkama a kafanshi a cikin kulewa da ita yaji muryan ta tana fadin wai fitan zakayi baka karya ba da gaske ? Don kawai na fadi gaskiya bai kulata ba sai tura wayan shi da yayi cikin aljihun ya dan juyo ya kalleta a cikin takaci yasa kai ya fita yana jin ta tana mashi masifa har ya bar jiyo muryanta don nisan da yayi da ita lokacin. Haka muka wuni a wanan wuri Allah ya taimakeni ina fashin sallah a ranan don haka na biyewa abinda sukeyi har aka gama muka kwasa zuwa gida bayan anyi rabe raben gift masu tsada da jawabai daga yan uwa da abokan arziki da suka san mamacin a baya. Dole saida muka koma gidan nasu tare dasu don haka nakai yamma sosai a ranan ban dawo ba sai dare na shigo gida na samu umma a cikin damuwan rashin dawowa gashi na wuni ban gida a ranan. Koda nayi sallama a kofa na tsaya ina cire takalmana a cikin gajiya na jingina jikina ga bango ina kallon umma dake amsa min sallaman yaran Avdulhamid ne a falin tare dasu suna kallo suka dago suna kallona tare da yi min sannu da dawowa. Na karba na nufi cikin dakina ina fadin umma ina zuwa don a matse nake na watsa ruwa don yanayn da nake ciki a lokaci. Na dade a cikin bayin na fito na zauna na gyara jikina ba zancen yunwa sai barci a tare dani don haka na dai fita naje muka gaisa da umma ban dade ba nayi mata saida safe na dawo dakin na kwanta. Washegari ban tashi da wuri duk da nasan gidan Oga zan koma a ranan aiki kuma an fada muna mu fito da wuri akwai abinda zamuyi da safe. Sai dai gaskiya gajiya bai barni nabi umurnan ba a ranan nafito na samu umma tayi alale wanda yaji kwai sosai cikin sa da kifin teku sai kamshi ke tashi suna zaune har yaran Abdulhamid suna ci yaban shawa sosai amma na kasa zama naci ko kadan saboda saurin da nakeyi a lokacin. Goma ya wuce da yan mintuna a lokacin haka nayi masu sallama a gurguje na fita daga gidan na samu abokan aikina har yemisi suna falon farko zaune muka gaisa suke fadin karfe nawa na fito nida akacewa mu fito tun safe. Wuri na samu na zauna oga jimone ya fara magana kan aikin mu na jiya da mukayi ya yabawa kowan mu daba,a samu wani kuskure a wurin kowa ba a lokacin. Yar aikin gidan ce ta fito tana fadi a cikin yaroba ance Sahiba tazo idan tana nan jin hakan yasa na mike nabi bayan ta muka shiga ciki tare. Bakin su nan nan basu tafi ba son haka gidan yake da jama,a cike gashi kayan aikine a jikina na saka bakin wando da riga fari ta ciki sai corth din mata dana saka baki a sama kayan sun matukar karban jikina sosai. Suna daki da hjyn shi ta sauka a nan na samesu zaune tare da wasu bakin su suna hira na gaida su a cikin mutunci na mike zan fita hjyn tace oh Allah sarki yarinyar jiyace ashe ? Na danyi murmushi zan juya in fita muka hade da Ogan mu da zai shigo dakin da suke din don yayi sallama da bakin da sukazo masu daga arewa zasu koma gida jirgij karfe daya na ranan. ZAINAB IDRIS MAKAWA ANA DARA GA, , , , , , , , , , , 5️⃣1️⃣ BY, , , , , , , , , , , , , , ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , , , , , BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AL HAFIZ, , , , , , , , ONLINE PAID NOVEL YAR UWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA BA TARE DA HAKKIN KOWA BA DON BIYA ZAKI TURO DA KATIN WAYA KO BANK TA 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK 08036959557 Hjy fatima farar macece sol saidai bata da tsayi sosai amma kuma ba za a kirata gajera ba kuma mai tsawo ba tana da kyau don kana ganin ta kasan tayi zamanin kyau irin nata Tana da dan fada sai dai ba irin sosai din nan ba can don inda tayi nan take barin zancen bazata rike a rayuwan ta ba. Nagane hakan ne don yanzu a tare dasu nake dan zaman su damu a kasan nan da zasuyi ya azamin nauyin fita dasu ko zama ina kulawa dasu a cikin gidan don ganin masu shigowa da kuma motsin su. Saidai gaskiya hakan ba a banza zance mukeyin aikin ba don akwai alheri sosai da muke samu ga hakan a kulun daga garesu kinga ko aikin bai zama na banza don baga albashi kawai muka dogara bake nan ai. Ranan danayi wanka zan fara sallah a gudan su sallah azahar ya riskeni ranan ana sallah na mike na shiga bandakin da nake kewayawa a cikin sa na dauro alwala nazo na tayar da sallah anan falon su Allah da ikon shi hjy ta gitto ta ganni ina sallah anan ta shiga tana mamakin irin halina haka babu sakewa ko zakewa ga sha,anina duk da yanayina ya nuna akwai hutu a tare dani amma ina nuna a karkashin su nake komai a cikin girmamawa zan masu shi. A, a kece kike sallah anan baki shiga daki ba ta fada kafin ta shige ta kara da fadin idan kin idar zamu fita dake unguwa dan an jima kadan ta fada a karshe. Na idan na dan zauna nayi addua kafin na jawo jakkana na fito da kayan makeup din dake ciki na gyara fuskana kadan koshi naga duk macen da zata shigo a cikin kwaliyan ta take a fuskanta yasa na dan fara yin make din haka ba dabi,ana bane yin makeup. Daga driver saisu biyu da yarta muka shiga motan zuwa wani unguwa mai nisa dasu munje gidan wata mata dana gani wurin addu,an ranan so close to her . Mun zauna a falon matar sun gaisa muma mun gaisa da ita suna dai hiran yaushe rabo a tsakanin a cikin hiran sun ne naji ranan da zasu koma. Kusan sau biyu muna hada ido da wanan matar sai tayi saurin kawar da idonta daga kallona saina fara zarginta don mugu bai hada ido da mai iska sau uku ko biyu. Can matar take fadin wanan kyakyawar yar dai tun shekaran jiya nake ganin ku tare da ita hala da ita kuka zo daga can ? Hjy ta dago ta kalleni tana fadin wai wanan yar a, a anan dai muka sameta danki ne ya hadamu da ita tun zuwan mu yanzun ma rakomu tayi nan kin san shi da rashin yadda . Haba wanan ai kyauta haka abin tsorone sosai dan tafi kama da yar ruwa saboda kamannin ta ai dariya hjyn oga tayi tana fadin mace maikyau sai ta zama wani abu kuma don kyaun ta matar tace nan lagos nefa hjy fatima. Sai matar ta kara kollona tana dan murmushi take fadin anya kuwa wanan ba sallon yan zamanin nan bane kuwa ya fito maki dashi don wanan ai batai kama da yan aiki ba sam. Hjy Fatima mahaifiyar shi bata gane mai matar ke nufi ba tace ai ba aikin gida nake nufi na dahuwa ko wani goge goge ba a ma,akatan su dai take aiki tare dasu. Yaran nan sun iya bata sau wallahi haka dai ya fada maki shi amma wanan ai ba haka yake ba kema kin sani sabo kawai ya turata kuyi kada daga baya ki nuna baki son zancen. Anya haka zancen nan yake kuwa don nasan halin sha,aban sosai ke dai mubar zancen matar ta fada saboda bata dauka na iya hausan da sukeyi din ba yasa ta juye yare zuwa hausa sama sama don bata iya yaren sosai ba. Mikewa tayi zuwa kawo mana wai abin tabawa duk da bata sanda zuwan mu ba haka ya ban daman kallon ko ina na falon nata don hankalina bai kwanta ba a lokacin. Can idona ya gano min abinda yasani mikewa da sauri don yadda na zabura saida suma suka fitgita dani don tsoro. We most live now before she come back with her evil act now now na fada cikin fidda idona waje ina umurtan su da hakan. Aishan tsoron yadda taga mayi taji ta fake a bayan uwarnata don saitin kafanta nake kallo sosai ganin basu tashi ba yasa na nuna abin da hannu ina fadin go back to ut owner don't try to touch any one here again. Ai Aishan saita mike uwar ma hakan suka fara tafiya ban fita ba saida suka fita nabi bayan su har sun shiga mota na bude na kalli gidan ina fadin back to ur send d evil sprit. People are saying dis to hajiya ban taba yarda ba har hjy zata iya cuta min duk irin taimakon da nayi mata a duniyan nan ashe. Mama i told you duk ranan da naganta ko zan ganta sai nayi mafalki da ita da wasu abu suna bina a baya zasu kamani kuma na fada maki tun kan muzo nan din. Driver kan sai gudu yake shararawa da motan har muka kai gidan nasu a waje muka samesu da Felix da Jimoh zasu fita. Fasa shiga motan yayi ya tsaya da mamakin ganin mu mun dawo lokaci yana kallon yaga hankalin su a tashe suna fitowa sai fada mahaifiyar su keyi abinda yasa ya fara takowa zuwa inda suke ke nan. Baku sameta a gidan bane ya tambaya farko mun ko sameta saidai zance ya juyane kuma uwarta fada meya faru tace ka tambayi wanan yar ita ta gani koma meye tasa mu tasowa yanzu mu bar gidan idon shi ya lumshe yana fadin ya Allah. Dama nasani nasani mama kada dai kice zan rabaki da kawarkine na yarinta don a tare na taso na ganku kike fada amma wanan matar yanzu ta canza saboda kudi. Babu abinda zai faru dasu mugun abinta ya koma akanta ya bita ita da yaran ta yanzu kin riga da kunfi karfinta ko a duniya. Duk suka tsaya suna kallona a inda nake tsaye kafin tayi karfin halin fadi No ki bari ke yarinyace baki san komai ba mun dade tare da ita mutane suna gada min wanan maganan gashi yau ya zama gaskiya . Mommy idan baki yarda ba zata kawo kanta gidan nan a yau din nan ta roke gafara don tana can cikin wahala yanzu haka mun barta abinta ya koma a kanta. Itace ta kiraki da safe kan kada ki wuce ba kizo gidanta ba kikai mata alkawarin zuwa din kafin kizo ta shirya abinda zatayi maki din taso amfani da jinin kune kawai ko naki kona yarki. God forbid bad things Allah ba zai bata sa,a ba har abada cool down mommy zata zo yau din nan ta sameku ai na fada na juya zuwa wurin da abokan aikina suke na barsu a nan suna kara tataunawa akan zancen. Karshe dai ogan mu bai fita zuwa inda zasu tafi ba din suka kwasa suka koma ciki don suna gardama cewa kodai firgitasu nayi kawai ba abinda na gani zan hadasu da mata yar tace ai a bari a gani tunda nace zata kawo kanta garesu ranan. Duk muna falon gidan a zaune har su wanan lokacin hiran kasuwanci ake da mr Jimo muna sauraren su, muka jiyo hargowa a wajen gidan. Felix ne ya mike yana fadin ihun meye haka yake ji a compound din gidan yana fita yake wanan maganan sai gashi baikai ga fita ba sun juyo da maigadi yana fadin. Hjy na dat that ur friend come de shout ebi like say she don be mad today wooo . U no here how she de shout ur name, saying dat make u na forgive am woo , d tin meke me surprisee amm woo, which one of my friend ta tambaya yace dat big Alaja who de always come dis house if u are around. Tayi wani irin tabawa tana fadin shike nan batu ya zama gaskiya ke nan shi ya mike da sauri suka bi bayan shi zuwa waje a cikin mamaki. Daga hjyn har diyanta duk sun firgice suke suna kallon kofa har yemisi dake wurin a tare damu don duk mazan sun fita a lokacin. Sai gasu sun shigo falon tare da ita lokaci guda tana faman soshe soshe tazo gaban hjy takai gurfane tana fadin kimun rai ki raimakeni. Nayi kuskure danayi kokarin taba ku nayi kuskure ba yau ba ina kai maki hari dake da yayan ki kuna kubuta daga track dina yau nayi niyar in gama daku gaba daya don haushin da nake ji naki na kin fini da komai diya ta nuna yaran kudi da gida da komai kin fini Fatma kin fini why zaki fini yanzu bayan nasan na fiki komai muna yan mata. Hannu bibiyu hjy ta dora a kai tana fadin mabinu da harshen yarbanci tare da fadin na shiga uku dama haka kike mansura ban sani ba. Ta kai ga cire dan kwali tana fadin ki min rai ki taimakeni nasan nayi ba daidai ba gareki don Allah ki yafe min ki yafe mun fatima tana hada hannayen ta wuri daya. Hjy din da yar ta suna ja da baya ganin haka na dan tako zuwa inda ogan yake tsaye ina fadin yace ta tafi daga yau ta fita hanyar su ga baki daya. Haka yayi sai tayi wani irin lankwasa can ta dago bata ko tsaya kallon su ba tafita daga gidan kamar mahaukaci duk wanda ke wajen lokacin jikin shi yayi sanyi sosai lokacin. Mommy kan ta gaji da korafin nan nasu a yanzu don har tsoron ganin kiran wayan Nazifa take yi don tasan karane zasu kawo mata a lokacin. Yauma din dai tana jin kiran ta saida gaban ta ya fadi tasan magana gudane dan kullun tana dauka ko sallama babu take fadin. Nagane kece ke daurewa Abubakar yake min wullakanci idan bashi ba don me zaki dinga bashi abinci a gidan ki yaki cin girkin mu a nan. Nazifa kinsan da wace kike magana kuwa nasani mana ba mommy bane ta fada a lalace tare da fadin kidai ja masa kunne kuma ki kiyayye mommy na fada maki don ni yake aure ba ke ba . Tana fadin haka ta kashe wayan tabar mommy din tsaye da mamaki da al,ajabin yar nata kota manta da bayan uwar mijin ta take ita din kanwar mahaifinta ne ita. A haka yar ta Nabila tazo ta sameta tsaye tana mamakin ta ganin mommy a haka take tambayan ta mommy meya faru halan dawa kike waya ? Ta sake kallo yar nata da mamaki tana fadin barni Nabila yau kan naji abin mamaki a rayuwana duniyan nan waini Nazifa zata kira tana warning dina akan yayan ku. Har da fadin wai idan ni yake aure sai naci gaba da bashi abinci gidan nan yanaci what mommy nazifa din ta fadi haka . Yar abu kazan kazan nan wallahi bata kai yar iska ba tunda bata fadi a gaban yaya ba shigiya mai gadon iskanci kawai. Ta shiga zage zage a dakin hjy din tace da ita tayi shiru kada wani yaji wanan cin mutuncin ko nabila din sai bayan ta fada mata taga yadda take fadan tayi da ta sanin fada mata ko meye. Saiga hauwa ta shigo dakin ganin su hakan itama tambaya take wanaji kina zagine haka tun ina waje ? Bar yar iskan nan Nazifa wai waya ta bugowa mommy na kai nabila kinga halin kike wallahi yanzu kun fara wanan zancen ke nan a gidan nan har hjy karima taji zancen nan. Karshe ta kama yadawa a gari gari ya dauka kunsan halinta kuma sarai kan urin zancen nan. Wai meta fadane haka hauwa ta kara tambaya tana kallon nabila tace wai cewa tayi fa idan mommy na auren yayan mune ta sani jimon yar iska wace bata samu tarbiya a gidan su ba kawai. Kuma uban nan idan banje gidan nan na casa Nazifa shegiya nake don wallahi ban yarda da wanan cin fuskan haka na wullakanci. Kada ki soma wallahi dama nayi take nema ita da iyayyen ta ba wani aiki bane yanzu mahaifinta yace zai sabauta rayuwan mutum kan an taba mashi ya kun sani. Mommy sai a barta ta dinga yiwa mutane irin wanan iskancin nan tanaciwa mutane fuska ko yaushe . Tsawa mommy din ta dakawa hauwa din ta hauta da fada sai hauwa din ta tashi ta fita daga dakin ta mayar da kallonta wurin Nabilan tana fadin kinsan hauwa fa tafiku zafi meyasa kika fada matane wai ? Mommy zagin yayi muni dayawane wallahi amma barta idan ta kara wallahi bazamun kyaleta ba Allah ta mike ta fita hjy na nadaman fadawa yayan nata mata a lokacin. Don tasan diya mace dajin zafi da kishin mahaifiya idan an taba maka uwa yadda kake ji a zuciyar ka. Hauwa,u ko tana shiga dakin waya ta dako ta fara turawa Nazifa zagi ta uwa ta uba ta zage ta tas ta tura mata nabila na shigowa ta ganta da wayan take tambayan ta tace zagi na turawa yar banza taji inda dadi. Idan anyi magana sai mommy tace wai a kyaleta don ubanta ubanta shi Allah ne da za a ji tsoron shi ? Zaune take a cikin fushi da dan jin sanyin yadda tayiwa mommy din yau itama ko banza taji zafin da taji haka kawai zata batamasu shirun su bayan sun kashe kudi mai yawa su tafi a banza. Hauwa aida kin barta sai mun hadu ba zamu hadu da itaba watarana sai mu nuna mata ai mun sani musan kai komai. Wai anty tsoron ta akejine wai da zataci bulus ta zagi mommy a banza a kyaleta koshi yaya yaji bazai kyale wanan cin fuskan ba ai. Ba fa zai kyale ba ni don mommy ne kada tace ta hanemu saida muka tayar da zancen kuma tunda bata son anty taji. Taji mana ke barin fada maki nifa yanzu ban tsoron kowa wallahi duk wanda zaiji yaji ta zagi uwana na zagi uwarta da ubanta ba shike nan ba. Waike har da ubanta kika zaga dama nabila ta tambaya tace me zan tsaya jira da yar banza cewa nayi ita tsafi uwar ta tsafi ubanta tsafi. Kai hauwa baki da kyau wallahi kin mun daidai iyaka dai mommy tayi fushi shike nan ai. Ranan kan sai waya na bugawa ummana kan cewa a gidan zan kwana har hjy ta karba ta roki umma din da kanta don yadda na nuna mata din na damu. Don abinda ya faru ina fita tare da abokan aikina muga tafiyan hjy mansura sai hjy fatima din tace Sha,aban tell me inda ka samo yarinyar nan haka mai abin al,ajabi ? A wurin aikin mu take hjy nan dai ya basu dan labarna daya sani da irin taimakon da nayi mai a rayuwa yake fadin she is tellent in dat way. But a nan suna fadin wai jinnune a kanta eh sudin ne sune aike irin wanan aikin dama mostly ana samun su sosai acikin al,umma amma sai a mayar dasu abin wani tsoro ko mugaye kuma is natural habit din su suna gani sun sai mai zaifaru dakai. Aisha ce take fadin amma dai a nan zata kwana tare damu yayana yace ina fa ita kuma gidan su fa idan ta kwana nan din. Ai gaskiya Aisha ta fada gaskiya takwana damu a gidan nan yau don bazan iya kwana mu kadai a cikin gidan nan ba. But mommy ba gamu ba a gidan ga Felix i beg idan ba zaka iya rokonta ba ni zan roka ya kara bata fuska shi ta yaya zaice ta kwana dasu bayan babu kwana acikin aikin su. And beside mutanen nan suna da kokari sosai dashi kada fa hakan yazo ya jawo mata wani matsla ga yarinyan nan kan hakan. Ita da kanta tasa Felix ya kirani take fada min bukatan su a take na bata raina Allah ya gani ba zan iya kwana ba tare dasu umma ba. Sai naji tana fadin ummaki kike tsoro ko Sha,aban ya fada min komai ki kira mahaifiyar taki in fada mata da bakina please ki taimaka muna gobe da yamma zamu bar garin nan zuwa jos daga can zamu koma insha Allah. Wayan na dauko na fara kiran layin umma din ta dauka tana fadin a sahiba na kira dazun baki dauki wayan ba. Umma ina lafiya zaki dawone yanzu ta tambaya sai na mikawa hjy din waya don irin kallon da takeyi min lokacin har lokacin umma na min addu,a Allah ya dawo dani lafiya. Tace hjy ba yarki bace nice mahaifiyar ogan su da mukazo addua don Allah ina son ki ara maki yarki na yau don gobe zamu koma ta kwana a wurin mu ta taimaka muna da shiri. Kai kai hjy idan bake ba sam ba zan yarda da wanan ba yata marainiyace ban son wani abu yazo ya same ta a waje. Insha Allah ba abinda zai sameki lafiya zata dawo gareki insha Allah ba komai don Allah a rike min ita amma ta fada tana kashe wayan. Sai wayan shi yake dakila bai yarda ya dago kanshi ba kuma yana jin abinda duk akeyi a wayan. Sai yamma muka fita tare dasu sayayya sukayi sosai har ni na samu shiga an samo min kaya kusan duk abinda Aisha ta dauka a wurin zatace nima indauka. Muka dawo gidan bayan anyi sallah ne mukaci abinci dakin su muka kwana duka mu uku a tare ranan. Washegari tun safe ake shiri karfe ukku suka dauki hanyar airport tare damu bamu dawo ba saida jirgin su ya daga muka dawo muna dawowa kayana a hade suke na shirya sai gida ban tsaya bako na minti biyu don dama na kagu in tafi gida. Yana zaune sai kai yake kadawa daga zaunen yana kara nanata sakon Hauwa,u din a cikin wayan matar shi din dake tsaye a kanshi tana girgiza jiki don ranta ya gama baci sosai lokacin. Meya kawo wanan zancen haka ya kara tambaya yana kallon ta tace na fada ma cewa ban sanni ba jin haka yasa ya mike da sauri ya tare da jawo rigan shi ya saka ya fita katfe takwasa na dare. ZAINAB IDRIS MAKAWA ANA DARA GA , , , , , , , , 5️⃣2️⃣ BY, , , , , , , , , , , , ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , , , , , , , , BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AL MUQIT, , , , , , , , , , ONLINE PAID NOVEL YAR UWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA BA TARE DA HAKKIN KOWA BA DON BIYA KI TURA DARI BIYAR 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK 08036959257 Ya is gidan suna zaune a falo suna kallo bai tsaya komai ba sai inda hauwa take zaune ya daga hannu yakai mata naushi ta gwauce bai sameta sosai ba ya kara kaiwa zai buga . Da sauri Nabila tace a, a yaya ka tsaya mana kaji ba,asi zaka kama dukan ta haka bayan matar kace ta zagi mommy don me ba za a zageta ba itama ? Da wani irin mamaki ya juyo yana kallon Nabila din tare da fadin ta zagi mommy fa kikace nabila tace kwarai yaya shine ita kuma hauwa ta tura mata da sakon zagi din. What ita Nazifa din ta zagi umma how comes har ta iya zagin mommy akan me zata zagi mommy din ? Kan abincin mana wai mommy idan ita ke auren ka taci da baka abinci idan basu saka kafan wando daya da ita ba. Ita Nazifan ta fadi haka ya tambaya a cikin mamaki yana lallon kanwar tashi Nabila tace wallahi yaya itace ta kirata ta fadi hakan a gaban mu. Yayi wani irin juyawa zai bar falo lokacin har mommy dake ciki cikin damuwa abinda surukar nata tayi mata yana cin zuciyarta tafito don jin hayaniyar su da tayi a falon. Wai meke faruwa ta tambaya daga inda take tsaye tana fito zuwa falon hauwace ta turawa nazifa zagi shine yaya yaji yazo yanzu. Na fada maku kada inji an tayar da wanan zancen ya fita baku jiba watau har saida kukayi yadda kuke so ko ? Au da gaskiya ke na ma ta bugowaya din ya sake tambaya cikin mamaki nabila tace ta bugo mana kai baka yarda bane dama yaya. Kai yasa zai fita daga falon mommy ta dakatar dashi da fadin kada kaje kace mata komai kyaleta iskancin kurciya ke cinta ai itama mace ce zata haifa. Baice da ita komai ba yasa kai kawai ya fita daga gidan ranshi bace ya shiga motarshi ya tayar ya bar gidan. A lokacin ne kuma hjy karima da suke jin hayaniya suka fito ta daiga fitan shi a cikin fushi amma bata samu jin kome ke faruwa ba a lokacin take tambaya meke faruwa ne wai ? Nabila tace a, a hauwace yaya yakewa fada ba komai bane me hauwan tayi mai ta sake tambaya ba wanda ya bata amsa tace to kuma ku daina rashin ji mana kullun aitama fada baka barin abu hardai ta juya ta tafi ta koma part din ta. Koda ya shigo ya samu har tayi barci irin matan nan ne dake barci suyi dadaya da cinyoyin su waje su sake tsirecin su don dadin barci. Duka yakai mata a cinya yana sake tsuki gata yanzu tayi wani irin kiba don dadin data kara samu a yanzu din hankalinta kwace a gidan mijinta. Ke tashi yace da ita a cikin takaici yana kura mata ido ta dan muskusa ta juya tana fadin au ashe barci ya kwasheni ? Yace ke me kika kira mommy kika fada mata dazun yana mai mata wani irin kallon tsana idanunshi a cikin bacin rai sosai yake kallonta din. Kaje an fada ma munafunci da makirci da gulma a kaina yanzu kazo zaka tsureni ko ta fada tana kokarin komawa ta kwanta. Ya wani irin fincikota daga filon data sa kanta dintace kada ka balla min habana don Allah a banza ta fada a fusace tana kokarin kwace jikinta daga rikon da yai mata din. Nace me kika fada wa mommy a waya tace au an fada mane don kazo ka hauni da fada bayan zagin da kanwarka tayi min kuma ? To ni zan iya dako wani munafuki wallahi tunda ba zaman lafiya ake so ganin munayi ba dama ai don haka anzugaka kazo kaci min mutunci don na fadawa mahaifiyarku gaskiya ko ? Tass ya dauketa da wani irin wawan mari saida ta koma kwance yadda ya sameta ya nunata da yatsa yana fadin wallahi ahir din ki da uwata wallahi. Duk iskancin da rashin mutuncinki da zakiyi ki tsaya a kaina nidake auren ki kada ki kuskura ki saka mahaifiyata a ciki don ban raina maki taki ba kema. Kodon kinga ina kyaleku bana kula wallakancin da uncle yake jifanta dashi don kina mara hankali bari kema ki fara jifanta dashi ko ? Mara hankali da tunane kawai ke idan kina da tunane kin taba ganin ina sa,insa da uncle ne duk abinda yake nuna min a fili. Sai kece don kin raina min tawa uwar baki dauketa a matsayin da Allah ya bata ba a gareki na kanwar mahaifinki don baki da tarbiya zaki nunawa duniya kalan tarbiyan da aka baku na rashin girmama babba ? Jin fadan da yake yine yasa yaran nasu falkawa a tsorace suna saka kukan firgita suna kokarin kankame jikin uwar nasu. Nazifa dake dafe da kuncinta tace ni kamara Abubakar kan uwarka da yan uwan ka yace an mareki ke wacece zan gwada maka ko na isa wallahi don sai an rama min marin nan dakai min sai ka raina kanka. Yace wallahi karya kike baki isa ba wallahi kuma banga wanda ya isa ba bayan Allah bata dadaraba ta kara fadin zaka gani wallahi kuwa. Ya daka mata tsawa yace saina tattakaki yanzun nan wallahi mara mutunci ya juya yana jinta taci gaba da yimai suratai tana fadin zaka gani zaka san ka mareni. Uwarta ta kira a cikin daren nan tana dauka ta fara fada mata abinda ya faru tun farko sai data gama fadi uwar tace rufamin baki sakarai kawai an fada maki duk son da yake maki sai ya bari ki zagi uwarshi ko yan shi a gaban shi ? Allah ya aikeki ki fadawa Alh wanan zancen sai kin raina kanki a duniyan nan wallahi don dama neman hanyar da auren ki zai balle ake bida shiko Alh ba ruwan shi rabaku zaiyi kada ki koyi kisa da kisisina irin na kowa zauna kina masa gadara da isa a gida idan shi zai fitar dake ta kashe wayan tana jin haushin wauta irin na yarta. Washe gari yana ganin kiran mommy yaki daukan wayan don yasan zancen ne zatayi masa shiko yanzu ko wanda yasan Nazifa baison jin sunan a gaban shi. Shirin shi ya gama tsab ya dauko dan jakar shi da yake tafiya dashi ya fito a falo ya hangota zaune a saman kujera duk idon ta ya kumbura don kuka. Ya iso inda take bata ko dago kai ta kalleshi ba ya dan tsaya tare da kiran sunan yarshi mai sunan mahaifiyarshi mairo . Saidai ita Nazifan ta juye tace wai sunan kanwarta ce dake bimata mairo ya saka don haka take kiranta da mairo din ba sakayawa don shi. Zanyi tafiya kinji saina dawo ya fadawa yarinyar tare da saka hannun shi cikin aljihun shi ya ciro kudi ya mika mata daga haka ya daga ya fita baiko jiyu inda suke ba yabar gidan ta bishi da kallo. Tun dana dawo nake barci na kashe wayana don kada a sameni kiran ya tayar dani daga barcin gajiyan dana samu din. Barci nayi sosai don ban falka ba sai yamma sosai gap da magariba na tashi gurguje ranan nayi sallolin dake kaina sai kuma yuwan da nake jin na fito umma basu ciki suna shago. Kitchen din muna nufa don samun abinda zanci duk da yunwan da nake ji bai haba in gane cewa akwai sabon abu a cikin kitchen din ba da nabi da kallo ina mamaki akwai miya saidai ba a kaiga dafa abinci ba lokacin. Saina yanke shawaran yi muna sakwara bayan na dafa indomie na aje na dora doyan dana fere na wankeshi na zuba a cikin tukunya. Na fara cin indomie din sai naji baimun ba na aje fara aikin sakwaran da zan daka din miyan na saka bayan doya ya dahu nayi hadin miyan egushi. Kafin a kira sallah na hada komai yadda nake son shi na gyara kitchen din naji ana kiran sallah magariba yayi har falo na gyaro na shige nayi wanka tare alwala . Ban fito ba duk da kafin in idar din naji muryan umma sun shigo cikin gida ma,ana ta rufe shago sun shigo gida. Saida nayi isha,i na fito ina gaida umma take fadin ashe na tashi har nayi girki tana fadin bari su shigo su girka abinci tunda ina barci. Murmushi nayi na zauna ina gaida ita tare da tambayan ta kasuwa take fadin sai hamdala kasuwan ya dan tsaya saboda zuwan dama yanzu ba ciniki sosai. Kasa na zauna na kalli Ammar dake ekujo anty mi na amsa mashi da yaya kake yace lafiya nace ga abincin ka nan na daka maka. Da sauri ya dago yana dariya tare da fadin da gaske sakwara nayi yana kokarin bude kulan abincin yagani. Sai ya kwashe da dariya ya nufi kitchen ya fito da plate biyu a hannun yazo ya zauna a gabana tare da jawo abincin ya bude yana kallona na dan kalloshi ina fadin ehhee mana ma,ana ya zuba muna muci. Har umma shiya zuba mata ina nan zaune hankalina ya dauku a wayata ina karanta sokon da aka tura min. Yace min bissillahi na dan motso muka fara cin abincin falin yayi shiru don yana cikin dabi,an mu hakan idan muna cin abincin. Dazun yayan ku yazo gidan nan saidai bai shigo ba a shago ya samemu muka gaisa ya kawo muna kayan abinci nayi shiru ina ci gaba dacin abincina ban dago kaina ba. Bakiji bane ta fada umma an fada mashi bamu da abincine daya kawo muna wani irin maganane wanan. Shiru na sake yi banyi magana ba yaran nan sune ke kulamu a cikin duka yan uwan mu da muke dasu ina laifin su yanzu don yazo ya kawo muna abinci. Sun san abaya mabukata muke ba zasuyi zaton a yanzu muna da dan dama ba duk da alama ma ya nuna a jikin mu cewa bamu tare da wahala. Amma ko muna dashi ai ba a hana alheri sanan yaushe rabo dayazo gidan nan wurin mu tun lokacin da kikai mai wullakancin nan bai sake zuwa ba sai yau din nan yazo ya kuma zo muna da alherin sa. Wani yayan namune ciki yazo umma ta kyaleni bata ban amsa ba sai Ammar ne yace mai bamu kudi din nan mana handsome din nan. Dan gwagon ku hari umma ta fada a daidai lokacin da aka turo kofan falon namu bayan anyi knocking za a shigo. Duk muka juya don ganin maishi yaya Abubakar ne ya shigo da sallaman shi falon muka karba mai ya shigo. Mun gaisa dashi ya amsa tare da kallon mu ya samu wuri ya zauna umma tana tambayan shi mutanen gida . Yace suna lafiya a ranan ma ai ya baro kaduna yazo lagos din aiki sai umma ke fadin intashi in kawo mai abinci da abinsha a dauko a shago. Haka na mike zuwa dauko na dauki key din shagon don zuwa na dauko mai drinks din yana fadin a barshi umma tace haba kamar bako dai dakai modibbo. Ko baka iya cin abincin mune kada a kawo maka da sauri yace No ba haka bane mama a koshe nake dama kafin nazo nan din. Ni dai ban tsaya sauraren su ba na nufi hanyar sauka daga benen sai Ammar ya biyoni a baya muka fita tare dashi. A can yake ba labarin zuwan mustapha da baiko tsaya don ya samu akwai custermers a wurin ta sunzo daukan kaya lokacin ya aje muna abinda yazo dashi ya wuce. Koda muka fito ya tsaya ya rufe sai a lokacin na kula da motar da aka sake ajewa kofan gidan munga mota a kofan gidan bamu dauka gidan mu maishi yazo ba don akan aje motoci a haraban namu wani lokaci don muna da filin parking sosai a wurin.. Muka shigo saida naja na tsaya don ganin su, su biyun duka a lokacin daya gidan namu kamar sun hada bakin zuwa a lokacin. Wani irin matsanancin faduwan gabace ya ziyarceni lokaci daya don ganin su a tare da nayi a falon namu suna gaisawa da umma. Tunda yayi sallama ya shigo suka gaisa da junan su kowan su ya mayar da hankalin shi kan wayan shi yana dakila. A sanyayye na bude baki ina gaidashi kafi yada kan shi ya amsa muna na aje drinks din a gaban ya Abubakar kafin shima na aje mai daya a gaban shi. Na juya na shiga kitchen na dauko plate na zuba miya na kawowa kowan su plate din na aje gaban su. Na juya na saka ledan sakwara bibiyu a cikin plate nakai gaban su na aje agaban kowan su sai shi mustapha din nema ya dago kai a hankali yake fadin thanks. Na daga ba tare da yin magana ba ruwa na koma na dauko masu har na wanke hannu ina ajewa na nufi hanyar dakina naji muryan umma na fadin . Ina zaki ga abincin kunaci da kanin ki zaki tafi kuma na juyo a hankali cikin harshen yarbancin ina fadin na koshi kuma bazan iya kara ci ba yanzu. Yayyun na ki fa da sukazo zaki shiga ki barsu a zaune ta kara fada naji wani iri ina fadi a raina wayyyoni Allah na umma zata kwafsa min a nan kuma. Da ace umma tasan yadda nakeji lokacin a raina da batayi min wanan maganan ba lokaci. Yanzun dai komai ta famjama famjan inji yan iya magana bani da masaniya akan zuwan su a lokacin banda kuma dalilin shin . Don haka zaman da banaso a wurin suna zaune ban kuma da dabaran da zanyi in shige ciki a yanzu don dole inbi umurnin umma din. Haka yasa na dan dago kai na saci kallon inda suke naga mustapha shi dan duniyan har ya fara cin abincin dana aje masu din a gaban su yana ci a cikin sukuni da kwanciyan hankali ba wani damuwa a tare dashi lokacin. Sabanin yaya Abubakar dako kallon abincin ma baiyi ba yana fama da wayan shi kodan yafi mustapha din zama bafulacen kidi ne oho. Bani da zabi a lokacin illa kawai in dawo in zauna a tare dasu duk da yadda nake jin feeling some,how a gaban su din a yanzu. Kodan saboda na girmane yanzu na fara sanin kaina ko kuma dai kawai don bana son wani halaka da yan zuri,ansu baki dayane a yanzu ban sani ba. Yadda ya sake jikin shi yana ci abincin shi sosai hankali kwance suna dan hira da Ammar dake gefen shi zaune da gani kasan sun dan saba da yaron shima sosai. Amma ya Abubakar uffan baice dasu ba yana ta faman dakilan wayan hannun shi kawai karshe ma wayan shi tayi ringing ya dauki kiran yana jin maishi. Kai sai a ranan na kara sanin shi din miskiline na karshen karshe don ba zakace shi din ya taba sanin Almustapha din wani wuri ba ko suna da alaka ta jini da junan su bah. Umma na a takure take zaune cikin su lokacin kawai dai ba yadda ta iyane ta zauna amma zuciyar cike yake fam da zargin su a lokacin. Saida ya gama wayan shine yana sakawa a aljihu a daidai lokacin shi mustaha din ya mike yana cewa umma shi zai tafi jiya ya zo lagos shine yace bari yazo ya gaida mu. Godiya sosai umma take mai tana saka mai albarka kan irin yadda suke kullamu suna zumuncin lekomu lokaci lokaci. Duk abin nan da sukeyi ko ya dago kai yaiwa dan uwan nashi magana asalima ko sashen da yake ya Abubakar bai kalla ba lokacin, duk da yana jin shi yana sallaman da umma din ko dagowa baiyi ba har ya fita. Nikan hakan sai ya ban mamaki sosai da tsaro tunda nasan yadda iyayyen su suke da zumuncin su ganin haka saina kara shan jini da zurian tasu ga baki daya. Yana zaune a inda ya barshi sun fita da Amar sai ga Amar din ya dawo yana fadin ya wuce sister wai mu shirya gobe zai zo ya kaimu beach. Umma ya akayi wanan ke zuwa maku gida haka har kuka yarda dashi baku san koshi waye bane halan har ku sake dashi haka ? A, a modibbo baka gaje dan uwan naka bane halan don nima mamaki nakeyi tun shigowan shi yadda kuka nunawa junan ku baku san juna ba. Saida ya dan murmusa ya dago kai yana fadin nasan shi mana mustapha dan gwaggo hari sister din daddy ko ? Wanan ba mutumin arziki bane kada wata rana ya jefaku a fitina azo ana maku buncike a gida kan laifin da baku aikata ba. Umma tayi wani iri da sauri ta kalli moddibo din a cikin mamaki tana fadin cikin sanyin murya Shidin ai yana zuwa nan ne saboda alakan iyayyen ku modibbo duk da ba sanin dawwan mu gidan nan mukai mashi ba da farko . Amma yanzu din da ya ganmu tare da mahaifinka zuwan mu kaduna shine karfin zuwan shi lokaci lokaci can ba a rasa ba yakan dan leko mu a gaisa. Kada ku yarda dashi Umma don Almustapha ba mutumin kirki bane dan smogal din haramtattun kayan da gwaunati ta hana a shigo dasu cikin kasan nan ne. Da sauri muka dago da wani irin kallon juna nan da umma lokaci guda yau ko ba komai munsan dalilin da yasa ake neman shi wanan can lokacin daya fake a gidan da muke haya. Yanzun don mutum na smagal ya zama abin kyama ga kowa ke nan umma ta tambaya cikin mamaki tana kallon modibbo din dake bayani Yace kwarai kuwa umma don yana cikin jerin mutanen da gwaunati ke hari sosai idan dubun shi ya cika zai rainawa kanshi ranan sosai saidai yana ganin shi mai wayau ne ba za a iya gane shi ba yake gani. Don haka ku nisanci hurda dashi don ni sam ban yarda dashi ba ko kadan da zuwa nan din da yake maku don sam bansan yaddama ya gane wai kuna nan ba har ya biyoku ya fada yana min wani irin kallon tuhuma. Banda alakan komai dashi banda na gaisu a tsakanin ga umma nan ka tambaye ta kaji asalima shida kanshi yayi warning din kan nuna na taba sanin shi a baya idan zaka tuna ranan dinner diyar gwaggo Asiya da mukaje tun wanan lokacin na rike wanan kalaman daya furta min gaisuwan ma sai da umma ta matsa min nake gaida shi idan mun hadu. Yace kun gani ba idan ya yarda da kanshi ai ba ai ba zai fadi hakan ba gareki muna fukin kasa don suna yaudara saboda suyi kudi sufi kowa suke wanan harkan mai hatsari a garesu nina san mustapha don kusan tare muka taso a zurian mu dashi nasan halinsa sarai da kasada. Ka yarda dashi don shi din ba wanda kuke zargi bane na tsunci kaina da fadi haka lokaci guda ina kallon yaya modibbo din da shima ni yake kallo da mamaki. Yayi min wani irin kallo nace kwarai kuwa yaya babu ruwana dashi bayan gaisuwa tun baisan mu suwaye a gareshi ba kuma har yanzu din ma bai sani ba don nasan kan abinda yake zuwa gidan nan ke nan a yanzu ya binciko alakan mu da daddy ku kuma ko hakan bawai ya dameshi sai ya sani bane. Yana dai zuwa nan ne kawai don nasu yazo daya da amar ya mustapha shi kanshi kuma ai baisan yaudaran shi sukeyi ba suna surka sana,arsu da miyagun abubuwa a cikin kayan su da sukai odan zasu shigo dashi kasan nan. Don haka suke amfani dashi don ya iya harkan suka lababa shi suna amfani dashi wuri saka kaya ya shigo masu dashi a cikin rashin sani. Sai dai amma yanzu din ai yasan komai don shi kanshi kyamar abokan harkallan nasa yakeyi sosai a yanzu suma din suna farautan shine kamar yadda suka san yana nasu. Kallona ya tsaya yana yi a cikin mamaki na mike nace kwarai idan baka yarda ba ka bincika kaji zaka gane gaskiya insha Allah duk dani banda wani business dashi kamar yadda kake zato. Abin harin ka yana cikin gidan yanzu haka hanya dayane duk asirin da ta dauko maka yana a cikin dakinta a kasan wardrobe din kayan ta cikin farin leda da zaka samu dama ka dauke zaku zauna lafiya duk da shirmen na mahaifiyar tane ba nata bane daga haka na wuce na barshi zaune da mamaki yana bina da kallo. Kafin ya juyo wurin umma yana fadin har yanzu wanan abin nasu bar kanta bane ashe umma but how comes har tayi wanan tsowon lokacin dasu haka basu jirkitata ba ? ZAINAB IDRIS MAKAWA ANA DARA GA , , , , , , , , 5️⃣3️⃣ BY, , , , , , , , , , , , ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , , , , , , BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AL HASIB, , , , , , , , , , ONLINE PAID NOVEL YAR UWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA BA TARE DA HAKKIN KOWA BA DON BIYA KI TURA DARI BIYAR 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK 08036959257 Nikan tunda na shige daki ban fito ba barcine ma ya daukeni don akwai gajiya a jikina dama ban gama warwarewa daga gajiyan dana kwaso a gidan ogan mu ba lokacin. Bana son shiga wurin aiki mu sai ranan monday don haka nayi zamana a gida ina hutawa kuma wayana a kashe don wanda ya kira yajishi kashe. Barci na samu nayi sosai natashi nayi sallah na gyara jikina don zan dan fita zuwa lasuwan kusa damu in sai muna kayan miya don yayi low sosai idan na fara fita aiki ba lokaci gareni kuma. Dogowar rigace dai har kasa a mutunce saidai zuwa kafadantace shakallo don idan zan sakata hakan sai dole dantsena sun fito a fili hakama gaban rigan irin mai nuna girman nonon mutum din nan ne a fili. Amma ni da nasaka sai nakawo yar cikin nan da ake yayi mai makuraren wuya da dogon hannu na saka daga ciki sai hakan ya bada kala mai ma,ana . Saidai ranan ban saka hijab ba son wata rana haka nakan fita sai hula a kaina hakan ba komai bane a wurin mu don dankwalin ne na daura kwai kamar daurin tura din ka yafashi kamar gyale a saman kan ki. Shagon umma na nufa na sameta da custermers gaidasu nayi na samu wuri na kai zaune ina kallon abinda zan kira akawo muna a shagon don na kwana biyu ban leka ba. Sallaman Felix mukaji a bakin shagon yana gaida umma da good day mah ta amsa mashi sai ya hangoni a cikin shagon zaune. Why d u swich up your phone today ? We de call u sinces morning we nerver reach u why now ? Oga don base with u today, true true ido kawai na zuba mai ina kallon shi kafin yace u no dey talk today ? Na dan mere baki ina fadin waiting i dey talk now call my phone nd it swich den ? U see na now now ogo live dis country travel to Dubai see d money he give us before he go ya fada yana taba aljihun shi don shi sarkin son barkwanci ne sosai idan ka saba dashi. Nace kun gode ina mikewa tare da fadin na market i de go now to buy some fresh vegetables and other tins . Ina kokarin fita daga cikin shagon umma din take fadin in sawo mata cheas idan na gani nace yes mah muka jera da Felix din zuwa wurin motan shi. Motan dake saukowa saman titin ne yana nufo inda muke muka tsaya muna kallo har ya iso ya tsaya muna ta magana daganin yanayin tsayin mu zaka gane mun san juna sosai da Felix din saidai hankali yana surin motan duk da na ciki bai fito ba a lokacin. Can ya sako kafa daya waje babu abinda nake gani sai bakin takalman maishi da bakin wando shi don sauran jikin shi na cikin mota a lokacin. Felix yai min sallama zai shiga motan shi ya tafi nima a lokacin nabar wurin zuwa motana dake parke a gefe na kwarai ke nan naji an ambaci sunana a bayana saidai kodana waigo naga mai maganan . Yar motana da bai taka kara ya karya ba shima yake kallo a cikin mamaki karara a fuskan shi nasan mamakin shi na dayan biyune bai wuce motar tawa bace ko na wani zan shiga dai ? Ya mustaphane a cikin shiga na suit a jikin shi bakake he look classique sai dai kyakyawan fuska yau a daure yake irin sanin farko da nayi mashi a baya. Na dan yi tsam wuri daya kafin na jingija jikina a motana don ganin yana takowa zuwa inda nake tsaye nakai hannu na zare dan glass din dake idona. Ya karaso a lokacin nima dai na gama daure nawa fuskan a gareshi kamar yadda shima nasa yake daure lokacin. Na dago kaina a hankali na dan kalleshi ina fadin ina wuni ya amsa yabi motan da kallo kafin ya juyo gareni yana fadin ina mama take na nuna mai shagon da hannu ba tare da nayi magana da bakina ba . I would like to see you now ya fada ya juya zuwa inda na nuna mashi umma din a cikin shago nabi bayan shi da kallon mamakin yadda yanayin shi yake yau nasan akwai matsala. Ban shiga ba sai kawao na shiga motana naja nabar wurin bakuma komai yasa nayi haka ba sai dan nasan idan daman ya wuce min ban shiga kasuwa ba zamu dan shiga cikin wani hali na yan kwanaki idan bamu da kayan girki da muke bukata. Hankalina kwance na sayo duk abinda nake da buka ban kuma wani dadeba na dawo gidan saidai ga mamaki har lokacin motar shi na nan a haraban gidan . Saidai wanan karon har umma bata shago suna ciki tare da ita yaran Abdulhamid ne suka tayani kwasan kayan zuwa ciki na shiga da sallamana a bakina. Zaune yake saman kujera kamar yadda itama umma din ke fuskanta shi suna hira akan sana, an ta . Amar ne ya mike da sauri ya karbi farin ledan dana shigo dashi a hannuna yana gaidani da dawo na amsa kitchen ya nufa da komai tare da yaran ciki suka barshi yana saka komai a inda ya dace a aje shi. Na fito ina sauri zan shige daki umma take fadin tun dazun yayan ku yazo yace kun hadu kince zakije ki dawo yana da magana damune. Kallo daya nayiwa inda yake ban iya maimaitawa saboda kwarjin da yai min don idon daya tsura min yaji me zance da umma din kan abinda ta fada. Au bansan ni yake son gani ba ai gani na fada a karshe tare da zagayowa na samu wuri na zauna shirune ya dan biyo falon kafin ya gyara murya yace umma zaso na danyiwa sahiba yan tambayoyine kadan don Allah ya kare magana yana kallon umma. Baida matsala yar uwakace ai zaka iya mata tambayan da kake son yi mata ba damuwa ga hakan don a zaton umma akan wani aiki zai tambayeni. Don Allah ina son ki fada min yadda kukayi da Abubakar modibbo a jiya da na barshi gidan nan wurin ku don ya sameni da wani zancen da yaban mamaki sosai yau din nan. Akan me zanyi zancen ka dashi tunda ban san komai a kanka ba na dai tare shi da fadi su daina zargin ka akan abinda bakai ka aikata ba suke zargin ka dashi. Kamar meke nan Sahiba kike nufi rana wata lokaci duk ban raga mashi komai ba saida na zaiyana mashi komai daya faru dashi bai iya magana ba bayan idon daya tsura min kawai yana kallona da saurarena. Sahiba waya fada maki wanan zancen ina rokon ki daki fada min gaskiya don na dade ina son sanin duk wani abinda kika lissafo min a yanzu. Nasani ne kawai yace hakan kuma bai taba yuyuwa dole wani ya sanar dake hakan na mike kawai nabar falon don yadda nake ji har cikin raina. Umma tace ka yada da hakan don baiwan da ubangiji yai mata ke nan a yanzu har idan kuma baka yarda da wanan ba zaka iya tambayanta wani abin na daban ka gani. Shiru yayi na dan lokaci kafin yace zan gwada don in kawar da zargin hakan a raina Amar umma ta tura ya kirani wani kallo da nayi mashi saida yaron ya firgita ya koma yana fadawa umma din a furgice. Me kake son tambayana a yanzu zancen kayan da kuka boye a cikin conteiner na Alh yayafi don kana ganin shine ke ma sherin haka. What ya fada ya mike tsaye yana fadin lalai umma na yarda don ba wanda yasan da nayi haka sai babban yarona na kasan waje gashi kuma sahiba ta fada yanzu. How come,s wanan ta koma haka yanzu yaushe wanan abin ya sameta haka mama ya sake tambaya yana fadin no warnder halinta keda wuyan sha,ani. Stop it aka daka mai tsawa ranan dai a takaice yaji tonon asiri na yan kungiyar su har da abinda bai taba zato duk na fallasa mai shi jikin shi ya dauki rawa sosai a gaban shi nasha wuya sosai don sai da umma ta shaka min wanan abin na samu kaina da kyat har magariba muna abu guda hankalin umma ya tashi sosai tayi data sanin faruwan hakan saida kyat suka lafa min na shiga wani irin barci mai nauyi. Sai washe gari na falka jikina a dake ko ina yana min ciwo muryan Abdulhamid naji a part din mu yana fadin idan mun shirya yana waje yana jiran mu. Abin duniya ya damu Nazifa gashi majaifiyarta ta hanata fadawa mahaifinta zancen ya daukan mata mataki akanta. Haka ta zauna tayi shiru bayan fitan shi tana tunane ita kaidai a katon falon nasu sai yayanta dake wasan su a gefen ta taji ana kwala sallama tun a waje. Duk da ta sheda muryan mahaifiyar nata saidai hakan bai sa ta yunkura zuwa taron ta ba don irin yanayin da take ciki a lokacin. Sallama ta kara daga murya tanayi da kyat ta iya amsa mata saidai ita hjy salma din muryan yaran da taji yasa ta nufi falon tana shiga ta hango yar nata zaune cikin wani hali na tashin hankali. Me zan gani haka nazifa me kike son mayar da kankine wai ko so kike dani dake mu koma abin dariya idan an kashe auren naki ne ? Hawaye ke zuba daga idanuwan ta tana fadin wallahi mama baki ga irin wullakancin da yayi min bane shiyasa kike ganin laifina. Ban gani ba kuma ba zan gani ba ke da idon ki da girman mu kina dai ganin irun wullakacin da mahaifin ki ke muna a gidan ku ai mun fita kowa muka fadawa hakan da yake muna. Ba hakkuri muke muna zama dashi ba wanda bai sani ba sai ya dauka wani dadin duniya muke kwasa a wurin shi. Gaban ku zai zagemu har iyayyen mu tas a gaban kowa zai dukemu da girman nan namu kuma kin sani ba baki sani bane. Mama baki dai son a fada ne kawai amma idan na zauna wanan dan iskan kasheni zaiyi don yaga ina son shi. Uwarta kwashi salati tana taba hannayen ta wuri daya tace mjin nakine dan iska Nazifa yaushe kika zama haka wai ban sani ba . Duk tantirancina da iya shege duk kuma irin cin fuskan da Alh zaimun kin taba jin na bude baki na zage shi ? Lalai dole kijawa kanki duka ki zagi uwarshin ki zageshi har kannen shi dan banzane da bazai dukeki ba ? To wai ma fada min meye yaron nan modibbo ya rageki dashi a duniyan ko kuwa cikin yan uwan ki kaf dake aure waya kaiki samun dakin aure haka ki fada min. Mama kin sani fa uwarnan nashi ba zata taha barin mu zauna lafiya dashi ba cikin tsawa uwar tace da ita rufa min baki wace tayi gadon rashin hankali a wurin ubanta. Ke da kina da hankali hjy Addah ba kanwar uban ki bane da zaki buga mata waya nacin mutunci irin haka. Wallahi mama kar, , , rufa min baki na kira hjy Addah din ta fada min komai kuma ta rantse min bata san komai ba akan wanan zancen don baya ko zuwa gidan nasu. Ke gaki sarkin marasa hankali da wayau kin kirata kin zageta ko kin manta ita ta haifi dan kuma ta aura maki shi da yardan ta . Idan ba yana bin umurnin mahaifiyar shi ba ko kusa dashi ke nazifa kina zaton zaki iya zuwa kon nunawa duniya tayi masa zaben tumun dare ke nan a kan ki. Gobe sai ki nemi wace zata gyara tsakanin ku dashi idan kun bata son ko tayi niyar taimakon ki diyan ta ba zasu bari ba. Idan kina dauka maganata wallahi kiyi gagawan gyara tsakanin ki da mijin ki idan kuma kinki har suka gaji dake karshe ba zaki sha da dadi ba. Dolene ki sauke girman kanki da wani fadin rai in kina son ku zauna lafiya da mijin ki dolene kuma ki masa biyayayya kamar yadda Allah yace ai masu. Abincin shi shimfidan sa dama yan uwan shi su kasance kin kiyayye hakan sai ki kamo su daga kasa an fada maki haka ake kama gida a cikin karfi da yaji kome ? Duk gatan ki da wani girma da kikaga yan uwan ki na baki a yanzu yau in akace auren ki ya mutu da yaron nan angama baki shi don mahaifin ki ba zai baki abinda mijin ki ke baki ba har ya hasakaki haka a cikin yan uwa ba. Fada sosai mahaifiyar tayi mata tare da nuna damuwan ta kan kada auren yar nata ya mutu asirin su ya tono don samun da sukeyi a wurin shi. Sam bata bata daman furta komai ba a gaban ta har ta gama tayi mata sallama ta fito zuwa gida ta bar yar nata na hadiyan rai. Sai fadi take kaji mun mama da wani zance ai hakan kukayi har baba yake ganin yafi karfin ku yake maku abinda yaga dama irin nacin fuskan da yake masu. Nikan babu da namijin da zan zauna yana min haka na kyaleshi don bai isa yace ya juyani yadda yaga dama ba har yan uwan shi su samu kafan rainani ina sam hakan bazai yuyu ba. Gabantane ya fadi ras don tunawa da kalamin mahaifiyar ta na karshe me mamake nufi da hakan tana nufin saki ke nan ko me ? Komawa tayi ta lankwashe a cikin kujeran da take zaune tana maida numfashinta a hankali tare da lumshe idanun ta. Ba komai take tunane ba sai tunanen rabuwan ta dashi don tasan idan fitinan su yakai fitina mahaifinta kai tsaye zai bashi rashin gaskiya shi kuma din ya saketa. Ta dade zaune ta nemawa kanta mafita saidai mafitan ne da kamar wuya a wurin ta don haka na nufin sai ta kwanta an hauta za a zauna daidai ke nan haka ke nufi. Tun bayan sallah asuba dana iya tashi nayi na koma na kwanta wani irin zazzabi da ciwon kai suka rufeni lokaci guda maganin dana sha na shaka yasa har barci ya dan daukeni lokacin. Yar uwa idan nace maki wanan abin baya damuna bata lokacine son in akwai abinda ke damuna a rayuwana lokacin danayi wayau din nan nasan duniya shine wanan laluran fadi ba a tambayeka ba din da yanzu yake son zama min babban lalura don har wasau nason amfani dani wurin cin ma bukatan su wanda hakan ya dan so kawo min matsala a rayuwana daga baya. Don ba kowa zai yarda da hakan lalura bace da akan jarabi bawa dashi kai tsaye musaman nida nayi zama a cikin kabilu da za a iya ganin kamar harkan wani cultisim na shiga acan nake haka. Shine dalilin daya sa na bakishi a cikin labarina don ki fahinci kan labarin cewa ina da wani lalura ko baiwa zan kirashi yadda bature ke kiran shi a turance da talents yan baiwa ke nan. Gani ba kawa ta kut da kut ummace dai komai nawa don da ita na bude ido da ita na tashi kuma nake rayuwa da ita sai dan kanina Amar dake tare damu shi din namijine kuma tunda ya kai secondry ya fara barin mu gida haka kuma ya samo asaline don yaran Abdulhamid da suke fita tare wurin buga ball. Ban san dadin kawa ko aminiya ba sai zuwan mu kaduna shakuwa na da Faizan daddy yasa nasan muhimancin mu,amula da sa,an ka. Abubuwa da dama nakan so in damu wata muyi shawara saidai wacece zan sama tunda ban shaku da kowa ba a rayuwana dan dama wani lokaci mukan zauna idan weekend ne ban fita ba tare da muniya matar Abdulhamid muyi hira . Saidai tsiyan abin ban yarda hiran yai tsawo don rashin sabo da mutane da bamuyi ba sai tsakanin mu kawai muke mu,amula mu kadai duk wanan kuma yana cikin tarbiyan da muka samune a wurin umman mu don kokarin nisanta mu da mutane da tayi. Ranan da ya Abubakar yazo umma ta sheda mashi na tafi wurin aiki yake tambayan aikin me nakeyine ta fada mai a wani company nake aiki kuma a na samu sosai ga aikin . Don yanzu dana kare karatuna akwai samu sosai a wurin Alhamdullahi gaskiya mama dama Sahiba tayi karatune ya tambaya a cikin mamaki. Ikon Allah umma ta fada ta mike ta shiga daki ta dauko mashi takardun karatuna ta bashi ya duba ya dade yana nanata karantasu. Ya dago kai yana fadin ikon Allah dama ashe ta tsaya har tayi karatu haka toshi yana ina har haka ya faru wai ? Gaskiya dolene yaran nan su ja baya da kowa a yanzu duba ga yadda aka watsar dasu haka a cikin duniya bayan kuma asan suna raye a doron duniyan kowa ya fita batun su har daddy din. Wai dai zancen Nazira ko yana da kamshin gaskiyane daddy na da hannu cikin wanan kisan da akayi yasa baya son a tayar da zancen yake ta fadin lokacin tayar da zance baiyi ba. Wani lokaci yake jira ayi wanan case din sai lokacin da wani daga ciki ya mutu ko sai lokacin da ba musu case din za ayishi. Ya gama tunanen shi ya dago kai yana cewa umma kai gaskiya mama wanan abin alfaharine ga kowan mu wallahi saidai bai kamata ace ta tsaya aiki a company ba don basu da tabbas ga hakan. A, a a kada kace hakan don wanan aikin mu mun samu rufin asiri sosai a cikin sa ta yadda ba zamu raina hakan ba a garemu. Na sani mama amma ina nufin tunda tana da takardu haka masu kyau me zai hana a sama mata aiki a karkashin gwaunati tayi zai fi wanan din da takeyi yanzu idan an samu. Koda kuma za,a samu din ya kasance dai a arewa za a samo mata don yanzu in son samune nafi son ku koma gida kusa da yan uwa ku zauna. Take annurin fuskan umma ya canza lokaci guda take fadin a, a ka barmu nan inda muke don zaman mu nan yafi min kwanciyar hankali da komawa can inda fitina da tsegumi zai hanamu zaman lafiya. Sai dai idan har kun yarda mu dinga kai ziyara muna ganin wanan baida matsala amma a yanzu hankalin mu ya fi kwanci da zaman mu a nan. Shiru yayi yana dan tunane kafin yace mama masan abinda kike tunane don matsalan ku dasu uncle nuhu ne hakan kuma a sannu an kusa kaiwa karshen zancen insha Allahu. Don ina bincike yanzu sosai akan matsalan ba tare da sanin kowa ba don bana son kowa yasan da ina wanan binciken gaba daya har daddy ban yarda da su san da zancen ba don na kula indan na yunkura kamar ana tosheni ga hakan. Idan har haka zai ja matsala a rayuwan ka modibbo gara a rufe wanan zancen mu hadu a lahira dasu Allah yai muna hissabi a gaban shi umma ta fada da sauri ta kara da fadin. A yanzu bamu da abinda zamuce sai godiya ga Allah da kuma gareku kai da dan wurin hjy harin nan dake zuwa wani lokaci haka kuma inda sahiba ke aiki a yanzu gaskiya banda abinda zan fada sai hamdallah. Jin an ambaci sunan mustapha ya bata fuska don baison jin hakan ba sam bai dau son mu,amulan mu da wanan guy din yasa yace na dai fada maku kuyi hankali dashi mustapha din. Ya kwana biyu ma baizo nan ba ai tun lokacin da yazo kan matsalan maganan da kai masa mutanen kan Sahiba suka taka tafada mai abubuwa da dama a game dashi tun ranan ban sake ganin shiba gidan nan. How comes mama har kuka yarda yasan da wanan matsalan nata har yaji komai a bakin ta ya fada a dan tsorace cikin mamaki yana buga hannun kujeran da yake zaune a kai. ZAINAB IDRIS MAKAWA ANA DARA GA , , , , , , , , 5️⃣4️⃣ BY, , , , , , , , , , , , ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , , , , , , , , BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AL JALIL , , , , , , , , , , ONLINE PAID NOVEL YAR UWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA BA TARE DA HAKKIN KOWA BA DON BIYA KI TURA DARI BIYAR 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK 08036959257 Duk yadda yaso yaja ra,ayin umma ta yarda da shawaran daya zo mata dashi umma taki yarda da hakan karshe sai cewa yayi idan na dawo tayi shawara dani taji. Don shi dai yana son komawan mu gida kaduna sai asai muna gida can mu zauna yafi zaman mu nan da muke mu kadai. Kallon umma nayi bayan ta gama fada min ina fadin umma me haka ke nufi dayazo dashi ko yana ganin nan din zama mukeyi cikin rashin kamun kai ne ? Ko kuma gidan sa daya saya muna yake son mu bashi idan ba haka ba muna zaune kalau zai fito muna da wanan maganan yanzu. Ina ganin dai wani abu yake hange ga hakan har yakawo wanan maganan don nima dai nayi tunanem dalilin shi na fadan haka ? Babu ida zamu saidai din in yakama watarana mukai masu ziyara a can amma yanzu gaskiya umma zancen su kaf ya fita a raina tunda sun nuna duk suna kyaman mu. Munjima muna zance da umma kafin kowan mu ya kama gaban shi don dare yayi a lokacin haka na kwanta da jin zafin maganan a raina sai fadi nake ina ruwan shi da aikina kuma idan ba hassada ba ko kyashin hakan. Naga dai hakan ai abin farin cikin ne ga duk wani mai kaunata da ci gaba in koma arewa in zauna yadda saura suke zaune ko me ? Tun safe aiki nake yi tukuru don haka ban diba wayana ba sai lokacin da nafito zuwa sallah azahar muna gaisawa da wasu daga cikin ma,aikatan mu lokacin na nufi inda muke sallah na gama daga inda nake zaune ne na jawo jakkata don gyara fuskana. Lokacin ne idona ya sauka a wayata na dauko don in kira umma inji lafiyan su don haka dabi,atace duk inda nake a daidai wanan lokacin zan kisu inji lafiyan su. Miscall din da nagani ne a wayan da bakuwar nomber ya ban mamaki sosai don nasan ban ba wani layin wayana da banda sunan shi ba. Umma na fara kira kafin na kira mai layin wayan dana sama an kirani dashi ringing uku aka daga nace sallamu alaikum who is on d line please ? Sahiba aka fada a cikin wayan nace yes its me Sahiba who is speak na tambaya a gagauce don jin muryan mace da dan hayaniya a wurin maimakon inji anyi magana sai ji nayi ance . Wayyo Allah na kuzo wallahi ga Sahiba ta dauki wayan jin hakan yasa naji gabana ya wani mugun faduwa sosai na kara fadin who is on the line please karo na barkatai. Sahiba Fa,iza ce daga kaduna take magana Fa,iza na kara maimaita sunan a cikin mamaki ina fadin who is Faiza is wrong number you dial bye. Da sauri tace your sister from kaduna so kon manta dani ke nan sahiba long time ? Wait Faiza where do you get my number first ? Bata bani amsa ba sai ihun da takeyi tana kiran sunayen yan uwa suzo ga sahiba yau a waya . A take naji wani iri a zuciyana duk yadda naso in kashe wayan da farko duk da nagane mai magana a lokacin amma sai naso in share su kamar yadda suma suka sharemu tsawon shekaru basu nememu ba shine yau zasu kirani. Sai naji kuma tana fadin kai itace kuwa wanan kamar ba muryanta bafa wallahi amma kuma daidai nasa number da yaya ya bani din ke Sahiba nice faizan mommy ina umma da Amar jin haka yasa. Na sake dan murmushi nayi karfin halin fadin it, is you Faiza long time ya kuke nan ta amsa da lafiya ina umma nace tana gida ina wurin aiki yanzu Ya kuke ya mutanen gida a cikon hausa da yanzu ya kara barkacewa don sai a gida gaban bako mukan juye harshe a cikin hausa don haka dole hausana ya fita daban a yanzu. W Faiza ce a ina kika samu layina na tambaya a cikin mamaki ina kallon kasan wajen da nake zaune ina saka safa a kafa don ranan kowa shigan suit yayi a ma,aikatan namu. Don haka nima shi din ke jikina da dogon bujena wanda ya banbanta da dinkin sauran don su dan karamine iya cinyar su suke sakawa nawa ko har kasa yake kai min ina dan banbanta kaina dasu. Hankalina ne yadawo lokaci guda don ganin yadda hankalin mutane ya dawo kaina don ganin yadda nake waya a cikin fara,a ina nuna jin dadin haka. Da sauri nake fadin i will call you back letter na kashe wayan ga baki daya don nasan zata dameni da kira idan wayan yana kunne yasa na kashe gaba daya. Saidai ina aiki ina kallon wayan zakace fa,iza dince a gabana lokacin Allah Allah nakeyi a tashi inje gida in ba umma labari. Tunda ya tun karo kaduna yaji kamar zuciyar shi ba zata daukeshi ba lokacin do bayan zafin da yake ji na ki yarda da zancen da yazo ma umma dashi ta nuna rashin amincewan ta ga hakan. Sai kuma na samun Nazifa da hitinan ta da zaizo ya sama a gida don yasan ba zasu kwashe dadi da ita don ba irin matar da miji zaizo ya samu yaji dadi a wurinta bane. Saidai a rabu da tashin hankali da fitina wanda duk itace kuma mai jawo hakan ya faru a tsakanin su yana kokarin yaga sun dan samu fahinta kodan mahaifiyar shi. Amma kuma ya lura hakan ba mai faruwa bane don yarinyar ta dauki girman kai da raini ta dora a zuciyar ta sam bata zo da zaman lafiya a gidan shi ba. Itace fada da yan uwanshi nuna kyama ga kowa nasa uwa uba ga rainin ta yanzu har ya kawo ga mahaifiyar shi don tana doluwa. Mace mai son mijinta ta hanyar uwan miji take fara neman zuciyar mijin ta da sauran yan uwan shi koda kuwa yana nuna cewa shi bai damu da yan uwan nasa ba a fili dole in an taba su yaji kishin hakan. Don haka ki zamo mai nunawa dangin miji kamar kece yar uwansu bashi ba a gaban su kada ki yarda ki dinga fada da dangin mijin ki haka na kawo ki fita ran mijin shi kansa watarana. Ko ya kasance ranan da aka kara maki kishiya duk sai su watse su koma gun sabuwar suna yayin ta dole kina kallo hatshi mijin gaba daya sai a sayesu. Amma Nazifa gaba daya bata tunanen hakan din batama taba wani tunanen ko zai iya karin aure ga mijin nata ba don tana ganin ita ta gama dashi ga wautan irin nata. Tsoki yaja lokaci guda yana gyara zaman shi don yasan takaici zaije gidan kawai ya sama a lokacin zama ya gyara daga inda yake zaune a bayan motan ana jansa yana mai lumshe idanun shi a hankali don yadda yake jin kansa. Bayan sun isa gidan ya sallami drivern shi bai shigo ciki ba sai daya dan zaga ko ina na gidan nasa don dai kawai ya rage tention din da yake ji a zuciyar shi.. Kafin ya samu ya dan saita kanshi zuwa ciki bai sameta a falo ba lokacin hakan ya bashi daman wucewa dakin shi ya kimtsa har ya dan kwanta don ya huta ba tare daya sanar da ita zuwan shi ba. Saida tayi batcin ta ta tashi koshi yaran tane suka tayar da ita daga barcin don hayaniyar da sukeyi sun gaji da kumshewa a cikin dakin su ga ba wanda yashigo gidan kusan kwana nawa ba wani daya leko su sukade a gida sai uwarsu suke rayuwa. Don ko makwabta bata taba shiga gidan su da sunan ziyara ba don gani take ita tafi karfin bin makwanci ai. Watace mama Abdul ta danso shige mata karshe dole ta jaye don ba fuskan hakan zata zo tayi ta sallama har ta gani dole ta juya ta koma ko idan ma ta amsa ta fito zata tambaye ta da lafiya ? Bata da laifi wurin yin hakan don a gidan su bata saba ganin hakan ba saboda har makwabtan su suna tsoron mahaifin ta kowa ya kiyayyi kanshi dasu su kadai ke rayuwan su da iyalinsu. Yayi juyi yagaji yayi tsoki karona barkatai a saman gadon kafin yaji turowan kofan ta shigo koshi saida ta jima zaune falon kafin ta kula da sautin karatun da yasa a dakin nasa dake dan fitowa zuwa falon. Shine ta tashi a cikin mamaki ta nufi dakin tana mamaki a fili har ta karasa ta hangoshi a kwance yaba kofan shigowa baya. Baban mimi yaushe ka dawo ta fada tana karasowa cikin dakin tare da mamaki karara a fuskanta lokacin. Saida ta fada kusan sau biyu gana uku ya juyo yana amsa mata a dakile don baisan da wace zata tare shi ba ga yadda suka rabu dashi da zai tafi. Na dawo ya bata amsa tun dazun nakai kusan awa biyu ai da shigowa ya fada har lokacin duk yana kwance bai mike ba kafin tayi wani magana yar babba ta shigo tabar karamar a falo zaune hakan yasa tayi mai sannu a tsatsaye ta juya ta fita. Ya jawo yar a jikin shi suna gaisawa can sai gata ta goyo yar da ruwa a gora gami da cup ta kawo mai saidai bai taba zaton hakan daga gareta ba gaskiya. Mikewa yayi zaune a karba baya ta tsiyaya mai a cup yakai baki yana fadin bissimillahi a fili ta yadda duk wanda ke kusa dasu zai iya jin hakan. Yako sha sosai don a gaban shi ta murda gora ya gani sabon budewa ne yasa yasha daba haka ba zaice ai yasha ruwa a jirgi kafin su zo. Zaune takai a gefen shi tana fadin shine koka sanar damu zuwan ka gashi ban dora girki ba a gidan don yau mai aiki ta fita unguwa ta fada dama matar zata zo tayi masu abinda zatayi zuwa karfe daya sai ta wuce don bata yarda wai ta zauna ba. Baida damuwa amma me kika bawa yaran nan sukaci tace aiba abincin sukeci ba cornflakes ne zan hada masu idan sun bukata. Fuska ya kawar don baida abin fada a nan tunda yasan koya fada din ba gyarawa zatayi ba take fadin kona shiga na girka yanzu ne yace barshi kawai ban tare da yunwa yanzu ya fada yana mika hannu ya karbi yar dake bayanta goye yana dan mata wasa. Daga inda take tsaye tana kallon su gwanin ban sha,awa bata san lokacin data lumshe idanun ta ba a hankali don sai yau data natsu ta samu kulawan shi take ganin ba macen data fita jin dadin miji ashe duniyan nan. Shiko dan duniyan duk da sun ya kasance da mace dake damun shi bai yarda ya nuna mata damuwan haka a bangaren shi ba ya daiyi kokarin sassauta natsuwan shi da kuma maida hankali wurin nuna kauna ga yaran shi har yaga iya gudunta. Kai ya dago ya kalleta itama dai din kallon su takeyi saita bashi tausayi a yadda tayi din hannu ya mika mata yana fadin zauna mana kin tsaya kina kallon mu kuma. Dole in kalleku kun maidani ta ware kana zance kaida diyan ka kawai kun barni to ayi hakkuri ya fada sai ta kai zaune. Bai samu leka gidan su ba sai washe gari da yamma ya kwashi yaran shi bayan ya zauna ya shiryasu da kanshi don ita madam din sai aukin barci da takeyi wai duk ta gaji shine ya shiryasu da kanshi zuwa gidan su su gaida iyayyan shi. Tunda yai sallama mommy ta ganshi tare da yara wani irin dadine ya kamata lokaci guda saidai tana mika hannu yaran sukaki zuwa wurin ta hakama kannen shi. A nan ya samu labarin mahaifin shima yana gari sai bai dade part din mommy ba ya je tare da yaran su gaisa da daddy din. Sun sameshi yana waya ya mika hannu su zo sukaki suka make a jikin mahaifin su daddy ya gama waya yake fadin ku ke nan baku san kowa bako ? Zasu sani ai dole modibbo din ya fada yana dora karamar saman cinyar shi daddy din ya juyo yana fadin sai kaji ina zancen aure summaya ko ? Wace summay ke nan kuma daddy ya tambaya yana kallon daddy din daddy yayi murmushi yana fadin har ka manta sunan baby Summaya ne kanwar ka na wurin karima dai. Baby dai ta gidan nan daddy kake nufi yace ita fa uwart tace aure zatayiwa yarta ba zata tsaya yin karatu ba sun sama mata miji dan uwurin Alh gyade. Wai Ma,aruf dai ko wa shi kuwa dai wai shine zanbin kanwar taka naso na hana uwar ta ta saka min tashin hankali ka barsu ayi tunda haka suka zaba da kansu ai. Nadai fada masu duk abinda ya taso babu ruwana don kada su kuka dani tace ta amince da sauri modibbo yace amma daddy gaskiya kasan akwai matsala sosai yaron da ko karatun kirki bai tsaya yayi ba za a dauki ya a bashi do kawai yana wani guntun sana,an shi kuma yarinya karama kamar baby ? Ai itama din bata yi ba kaga saisu karata can suji dashi tunda haka uwarta ke so don na nuna rashin yardana shekaran jiya nan taso rikita min gida da hauka. Allah ya sauwaka ya fada yana mikewa tsaye daddy zan kai su wajen anty su gaisa ban shiga can din ba ya amsa da haka nada kyau kafin ka tafi zan fito waje in ganka. Yayi ta sallama a falon hjy karima ba amsa ba ya juya zai tafine yaji muryan Fatima na amsa mashi daga ciki ya tsaya. Tana bude labule ta ganshi tsaye tare da yaran shi take fadin lah yaya kune ashe ta juya tana fadawa uwar dake fitowa ga yayan mu yazo. Ta wani tabe baki tare da fadin wani yayan ku kuma a lokacin ya shigo da sallama a bakin shi ta amsa mai tana fadin yaushe garin yace jina dawo anty. Ya gaida ita cikin mutunci ta amsa mai kadaran kadaham sai fatimane tayi kokarin karban yar bataki ba taje wurin ta kuwa sun dai dan gaisa ya daga zai fita take fadin ka shiga wurin Alh ne ko yace eh daga can nake yanzu ai. Yayi ma bayanin auren kanwarka daya taso ko yayi murmushi kafin yace ya fada min yanzun nan don nasamu yana waya akai yake min bayani. Amma zancen karatu fa anty tace tayi a can ai munyi magana dashi kan hakan yace toh Allah ya sanya alheri yasa wurin zaman tane tace amin amin nagode don jin baiyi wani korafin kar ayi ba bayan haka. Shima din yace hakane don yadda daddy ya fada mai sun kwasa da ita to tunda daddy ma bai iya da abinsa ba shi me zaice yanzu kuma banda fatan alheri. Ya mike yana fadin ina ita baby din take tace tana ciki tana washe baki ya kamata in ganta kafun intafi inji ra,ayin ta anty kada a saya mata abinda ranta baya so. Nan ma taji wani irin dadi sosai koba komai sa yaga a wurin shi dama dai rigimane bata shirya auren yar ba a lokacin zancen ya taso daga sama haka. Baby ta kwalawa yar kira ta amsa daga ciki sai gata ta fito da dan wandon jeans da rigan bubu ja a jikin ta tana ganin shi ta washe baki yace see you . Ta rakube tana dariya ya kara fadin amarya ke nan ashe zamu sha buki shine koki kirani ki sheda min ko ta dan boye fuskan ta ya miko mata hannu yana fadin zo mu saka labule kada anty ma tajimu dagani sai ke ta biyo shi suna rike da hannun juna suka fita daga dakin ganin haka sai kuma uwar ta dan tsargu da hakan tana gudun kada ya zugata Suna fita cikin ikon Allah a daidai kofan su yaja ya tsaya yana fadin kin gane ko duk wani abinda kike so sai kimun list din shi kada kiji komai har in kina so ki rubuto min komai ba matsala insha Allah zan saya maki shi Allah ya baku zaman lafiya tace amin a kunyace. Ya wuce yabarwa Fatima data dauki yaran ta shiga ciki dasu ya koma part din mahaifiyar su ya samu ta shiga dakin ya bita can suka zauna yana fadin ashe aure za aiwa baby ? Mommy tayi wani ajiyan zuciya tana fadin ashe sun fada maka kai yanzu ba wanda ya fada min daga uwar har mahaifin ku. Yin ma abin akeyi a boye kamar ba,ason naji ko idan naji bana bari ayi ko wani abu can dai indai wanan yaron ne ai gasu gashi ko. Suma wa yan nan Allah ya zaba masu na alheri masu addini da sanin ya kamata, yace amin lokaci ne baiyi ba idan lokaci yayi suma ai yi zasuyi insha Allahu. Hakane komai bai wuce lokacin sa ai saukin abindai ai sunyi karatu don haka naje na samu wai ashe Sahiba har ta hada digree dinta wanan shekaran harma tana aiki a wani company nan lagos din. Ka san inda suke yanzu ke nan uwar ta tambayeshi yace na sani mana dama nasan gidan da suke ai bawai ban sani bane barina kasan nan daine . Ita Sahiban har ta hada karatunta tana aiki ga wa yan nan zaune a gida aikin ya buwaya koda yake Alh ne dai bai yarda da wanda aka samu ba ai dama. Bawai aikin bane mommy kinsan zan iya sama masu inda zasu jona su tsaya suyi karatun ne yadda ya dace amma sun tsaya wasa. Ina yaran ta fada tana kawar da zancen kada yai nisa yake fadin suna gun su fatima na barsu suka zauna kuma ta kara tambaya ? Yace sun yarda da ita nan dai sukai ta zancen kan abinda ya shafesu a karshe sai ga yaran an dawo mashi dasu ya daukesu basu jima ba yayi masu sallama suka tafi. ZAINAB IDRIS MAKAWA ANA DARA GA , , , , , , , , 5️⃣5️⃣ BY, , , , , , , , , , , , ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , , , , , , , , BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AL KARIM, , , , , , , , , , ONLINE PAID NOVEL YAR UWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA BA TARE DA HAKKIN KOWA BA DON BIYA KI TURA DARI BIYAR 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK 08036959257 Nashigo gida na samu umma na shago don haka kai tsaye na nufi cikin gida na bude kai tsaye dakina na nufa kaya na fara cirewa ina wurgawa saman gado kafin na nufi bandaki. Wanka na nufa na fito na saka daya daga cikin rigunan da nake zaman gida dashi ina fitowa kitchen na nufa na dora muna abincin na fara gyaran gida wanan duk aikinane kun sani bana yarda umma tayi don ba lafiya ya isheta ba saboda asman dake damunta. Har na gama girkin nayi sallah kamar kullun sai lokacin na fara jin motson umma sun rufe shagon sun shigo cikin gida saboda dare yayi bata kaiwa dare a ka,idar zaman ta. Nayi sallah isha,i na fito da wayana a hannu ina masu sannu da dawowa suma din gaisheni sukayi haka muka sabayiwa junan mu kullun. Saida muka zauna cin abinci nan na fara labartawa umma zancen kiran wayan da Faiza tayi min ta kiraki fa yau kikace wallahi umma akwai wanda kika bawa layinane ? Dan shiru tayi kafin tace dani kwarai kuwa don naba Abubakar ranan daya tambayeni da bakya nan. Nace haba nikan nayi mamakin hakan wallahi don gaskiya bana bada layina haka barkatai saina yarda da mutum sosai. Abubakar din baki yarda dashiba ke nan Sahiba shikuma macucin mune kome yake biyan mu dashi na girgiza kaina da sauri. To shina gani don yaron nan yana da kirki da mutunci sosai ya nuna damuwa da kuma tausaya muna fiye da kowa da muka sani. Shiru nayi ban bata amsa ba don bana son tana fadin haka dukda nasan gaskiya take fadi amma ni zancen sune gaba daya banson ji. Ban kaiga karasa tunane ba wayana ta dauki ringing na dauka na duba lanban umma itace ko yanzu ta kirani dauka kila shine ya basu layin tunda yaran dama sun damu damu sosai ko zaman mu a can. Dauka nayi tare da sallama muryan Faiza ne tana fadin haba Sahiba ko bakya son magana danine wai tun dazu ina ta kira yafi ashirin wayan ki yana kashe saboda ni kaka kashe wayan. A harshen turanci nake bata hakkuri aina fada maki cewa aiki nakeyi dazun din sai yanzu na dawo gida yasu mommy dasu Anty Amarya ? Anty Nabila da anty hauwa ya su Amira da fatima baby da kowa na gidan tace kowa na gida lafiya kalau suna jin ki ya umma ? Gata ku gaisa na fada ina mikawa umma waya ta dauka itama da hausan ta daya fara rikedewa dana yare a yanzu . Suka gaisa itama tana jero mata tambayan yan uwa da sauran tana fadin ga mommy naga umma ta kashe wayan a nan nagane itama akwai haushin su a zuciyar ta ashe. Ga Mommy ita mommy bata sanda mu bane saida kika nemo yar uwarki zata wani karbi waya wanan zumincin zamani haka dame yayi kama ace yan mahaifi daya amma basu san zafin iyalin dan uwansu daya kwanta dama ba. Wallahi irin wanan nakan tuna a rayuwa har wani lokacin in zauna inyi kuka ina meyasa gwaggo ta zaba min mahaufin ku a matsayin mijina. Da wanine yau muna can cikin yan uwa a mutunce sun san darajan mu muma munsam nasu ana damawa damu amma wa yan nan kan abin duniya idon su da kunnuwan su ya rufe sun manta da cewa akwai ranan hisabi yana jiran kowa. Duk da maganan umma din ya taba min zuciya sosai don ma kusan nafi umma din jin zafin amsam wayan da mommy din tayi niyar karba a wurin faiza din. Sai gashi umma takai ga daukan mataki kafin nina dauka ban taba tunanen jin haka ba a bakin umma danaji din tana fada sai kima gata ta furta hakan yasa nasan ankai karshen umma ke nan. Na bude baki ina fadin kiyi hakkuri umma saukin abindai akwai hissabi ga kowa idan suna ganin haka ba komai ko sunfi tsoron wani Allah da Allah din ai mutuwar data rabamu da mahaifin mu bata bar kowa ba. Shiru falon yayi don tunanen da kowa keyi lokacin shigowan Amar daya sauka kasa bayan fitowana yasani dago kai ina kallon shi. Leda ya shigo dashi gidan yana fadin saida kyar na wanan uwan kamshin da kuma maganan dayayine yasani dago kai na kalleshi da kyau har ya zauna yana aje kumshin a gaban umman mu. Kallon ledan umma batayi ba don ranta da yake bace a lokacin ina ganin haka na bude baki da kyar ina fadin meye a cikin ledan Amar ? Ya sunkuyo ya buda min ledan wani kamshin suya meat irin na hausawa din nan ne ya daki hancina ga naman an masa manyan yanka gashi yana maiko yana fitar da suraci acikin shi kuma na zafi. Jeka kitchen ka dauko plate ka zuba a ciki umma dana san zaku saya ai tun dazun dana tsaya na sawo maku ai saidai nakan ji kunyar in tsaya a irin wuraren nan ne. Amar ya fito da plate dauke a hannun shi yana wani rawan jiki nace kaikan kamar ba bafalatani ba kana rawan jiki akan nama haka Ammar ? Abine yabawa umma dariya tace ashe kin kula dashi kema kamar nayi magana yadda naga yana wanan sabarin jikin haka kamar bayacin nama a kullun gidan nan. Amar yafi ganewa magana da yarbanci don haka yake fadi da yarbanci aiba irin wanan bane muke ciko ? Inda na kara godewa Allah ina jin fulanci saidai banyi don tun ina karama na bude baki dashine amma zuwan mu lagos din mu a sannu yarbaci da pidin ya shige bakin mu saidai umma bata yarda da hakan ba. Tsoka biyu na iya ci a ciki koshi don ta sake jiki na kokarta naci na tsame hannuna na dan shiga tunane kafin nakai ga mikewa ina fadin zan tafi na kwanta kada in makara da safe. Saida na lwanta din amma juyi da tsuki yafi yawa kafin barcin yayi gaba dani nine harda mafalkin su a ranan don kawai dan wayan da mukayi dasu din a ranan. Washe gari kodana kunna wayana text massage na sama a cikin wayan mai tsawo nata banbi ta kansa ba a gurguje na shirya na fito na samu Amar ma ya fita ko zuwa school shi. A gurje na fita gidan don ban son abinda zai ja min matsala a wurin aikina ko kadan don sun tsani wasa da aiki ina ganin yadda sukan sallami ma,aikatan su kan makara shiyasa nake kiyayye hakan a bamgarena. Saidai kash duk saurina kuma na makara a yau don nayi saurin banza saboda ogan mu sha,aban daya zo ashe ba tare da sanin kowa ba ya zo tun safe ya kawo muna ziyara bazata don ko Felix ma kanshi baisan da zuwan shi ba asalima a club ya kwana don harshi na rigashi zuwa. Allah yai min katari a daidai lokacin da ma,aikata ke halartan wajen da muke ganawa dashi na iso don haka nabi layi a tsarge duk da yana tsaye a cikin fararen kaya bai kallo wurin da nake ba amma kuma ai yaga shigowata ciki na nasa a raina. A cikin takon shi irin na mazan da suka waye suka san kan duniya suka kuma zauna da kafan su ya iso har inda muke yana fuskantar mu bai aje idon shi kan mutum daya ba don sai bin kowa na wurin yake da kallo. Kafin yayi gyaran murya wanda hakan ya kara karkato da hankalin kowa gareshi ya fara da sallama a cikon taushin murya irin nasa. Ya fara fadin i am disappoint yau yadda na samu a wirin nan ada kune kusan wa yanda nake alfahari dasu gaba daya out of fiyty five ma aikar da nake dasu wurin tsare aikin su sai gashi yau idona ya gane min kun fara zama kamar kowa ku din ma. Shiru wirin yayi kamar yadda shima yayi shiru yana dan bin kowa da ido kafin ya bode baki da kyar yana fadin why zaku zama haka har yakai na kasa alfahari daku kuma ? Sorry sir aka fara fada maza da matan don ganin yadda ranshi ya baci yake nuna bacin ranshi kuma a garemu baki daya. Jakkata dake rataye a kafadana na gyara kafin na mayar da hankalina inda shima yake kallo din Felix ne ke shigowa da ganin sa a rude yake ya karaso bai tsaya ba sai inda nake tsaye nima a tsarge. Yayi fada sosai ranan duk muna tsaye muna sauraron shi kafin yayi sallama damu a cikin bacin rai ya juya ya bar wurin aiki babba na sauke ziciyana ina nasa hakan. Ba tare dana tsaya kula Felix ba dake tambayana kasa kasa how come oga ya shigo kasan nan ba tare daya sani ba ya jefo min tambayan ko ke kinsan da zuwan shine ? Wani kallo nayi mai ina fadi yaya zan sani shima da yake kusa dashi yace bai sani sai nice zan sani ta yaya kuwa ? Har mun kusa kaiwa inda zamu hau masarrafin da zai kaimu sama naji ana fadin kubiyin nan guys oga yana son ganin ku yanzu. Na kalli Felix a cikin zaro ido shima hakan ya kalloni kafin na juya na shiga masarrafin zuwa sama din inda office offices suke a can sama din. A gidan su ya bar yaran don bai nufi gida ba daga nan ya wuce zuwa wani wuri yana a tsakiyan aikine saiga kiran Nazifa tana tambayan shi wai ina suke ne har warhaka ? Ina wurin wani aiki ya bata amsa a takaice yaran fa ta tambaya da mamaki suna gida wurin mommy na barsu ka batsu can fa kace yace eh da matsalane barin su can din? A,a saidai gaskiya kasan basu saba dasu ba ai kuma mimi nono take sha kasani eh na sani saidai ai akwai abincin ta idan tayi kuka yaran zasu bata. Ji yayi ta kashe wayan sai yabi wayan da dan kallon mamaki kafin ya daga kafadan shi irin alaman ko a jikinshi din nan. Tana kashe wayan na mahaifiyar ta takira bata sameta don haka ta kasa hakkuri don in akwai abinda taki jini a duniyan nan shine yaran ta su rabi kowa na gidan mahaifin su don wai basu son ta. Daki ta mike ta shiga ta fitone sai ga kannen ta haka yasa taji dadi suta tura suje gidan su dauko mata yaranta. Lokacin da sukaje harsu Nabila sun so su hana masu su amma sai mommy tace idan kun rikesu nan kuna da abincin basune ? Shi kuma lokacin daya gama yazo gidan daukan sune ya samu har ta turo an dauki yaran sai ranshi ya baci da hakan sosai ganin hakan da mommy tayine take dan gyara zancen don bata kaunan tashin hankali a tsakanin su ko kadan. Koda ya isa gidan haushi da kuma maganan mahaifiyar shi bai bari ya tada zancen ba sai wucewa da yayi dakin shi baiko tsaya kan yan uwan tana dasuke falon shi zube ba suna ta hayaniyan su. Tun a wanan lokacin ya dauki zafi da ita sosai a gidan don yasa a zuciyar shi cewa ko baiyi magana da fatan baki ba zai nuna mata ita bata isa ba a cikin hikima. Daga wanan ranan ya daina zama gida tun safe zai fita gidan sai yamma ya dan shi zuwa takwas kuma ya kitsa ya fita. Baya ko kallon yaran idan sun nuna sun gashi sai ya nuna ya barta da abinta ta kula dasu don yana son ta gane kurenta. Tun bata gane me yake nufi ba harta fara dagowa ta fara neman jin ba,asin hakan da yake yazun ta hanyan tashi da safe ta shiga dakin nasa ta sameshi yana shiryawa yana tsaye gaban mirrow yana daura tie a wuyan shi ta shigo. Gaidashi tayi da kwana ya amsa bai fasa abinda yakeyi ya juyo ya dubeta ba tace wai naga kamar kana fushi danine fa ? Yace ko da kikai min me tace toni na sani gani nayi ka daina wuni a gida ka daina cin abinci ka daina kulani dai har yaran ga baki daya ? Ya juyo yana fadin na daina kulaki kamar ya yanzun da kika gaisheni ban amsa bane zaman gida kuma da kike magana idan na zauna a gida ke zaki ciyar dani koda kika zo gidan nan ina kin sameni ina aikina. Ta dago kai tayi wani irin kallo bai kulata ba ya wuce wurin aje suit din ya dako yana sakawa kafin yace yara kuma ai yarankine dake da yan uwan ki don haka meye na damuwa don wani bai kulasu ba yanzu. Yarana fa kace yace eh ba yaran ki bane na waye yana fasin hakan yasa kai ya fita zai bar gidan tace na sani aidama nasani. Nasan don na aika an dauko mi su gidan ku kake wanan fushin haka don me zaka bar min yarana a can gidan haka kawai ina ji ina gani a sabauta min yara. Kamar zai fita sai ya juyo yana kallon ta yace idan har gidan ku ba, a sabauta maki suba babu gidan da za ayi masu hakan ko kin dauka kowa kamar sune da suke kirarin cewa basu kaunan su a fili don tsaban iya sheri har da yaran da basu san komai ba. Yana fadin haka ya fita ya bargidan ya barta zaune tana binshi da kallo tana mamakin zagin gidan su da yau yayi kiri kiri aitake tafara jin wani iri. Mikewa tayi zuwa dakinta fuuu har ta dauko waya sai kuma tayi wani irin tunane ta tsaya idan ta kira fa rigima ya taso tasan halin mijin ta zaice ne aiga abinda yasa ta fada. Hawayenane ya sako mata daga idanunta na bakin ciki da takaicin irin maganganun daya fada mata kafin ya fita a rana. Gidan su ya nufa ya samu gida tsit don haka ya nufi part din mommy kai tsaye a falo ya samesu wasu kuma suna kitchen suna girka abin karyawa. Nan suka shiga gaidashi yana amsawa ya zauna a falon yayi shiru hauwace ta shiga tana fadawa mommy zuwan shi amma kuma ta ganshi kamar yana cikin damuwane. Da sauri mommy din ta fito ta sameshi a falon zaune yadda hauwa ta barshi din mommy ta fito tana fadin a, a yaya dai modibbo na ganka haka da safe haka ? A jiyan zuciya ya sauke yake fadin nazo ganin daddy ne ina ganin kuma kamar bai bude part din shiba har yanzu don nags wurin a kulle yake. Mommy takai zaune saman kujera tana fasun basu fito ba ke nan har yanzu nina rasa wanan iskancin wai mutum da tsufan shi amma idan ya shige daki da mace sai yakai wani lokaci bai fito don iskanci. Mikewa yayi yana fadin ni zanje in dawo an jima idan ya tashi muryan hauce ke fasin yaya ga abin kari mana mun gama . Da sauri mommu tace dashi ya fada maki bai karya bane da zai fito ko jan magana dai kawai irin naku zaki kawo muna. Kawo min hauwa yace yana komawa zaune tare da fadin basu tashi ba koda na fito barin dan karya a nan din kafin in tafi. Mun shiga office din yana zaune yana dubam.takardan dake gaban shi jin shigowan mu baisa ya dago kanshi daga abinda yakeyi ba. Sai can ya dago kanshi yana aje takardan dake gaban nasa ya nuna muna kujera da hannu mu zauna mana nice na fara girgiza kai don sanin laifin da aka kamamu dashi na makara. Ganin haka shima felix din ya nuna bazai zauna ba ya girgiza kanshi yana fadin aina dauka koda bani nan kune zaku saka ma abina idanu sai gashi kuma nazo na samu ba daidai duk da na bincika an fada min ba haka kuka sabayi ba amma ku kara tsarewa don Allah. Da nazone da wani bukata a gareku da nike son ai aiki akansa sai kuma hankan da nagani yanzu yasa jikina sanyi ga abinda nazo dashi din. Kallon juna mukayi a tsakanin mu nida Felix kowa na tunanen wani zancene yazo muna dashi kuma da zamuyi. Kujera ya kara nuna muna mu zauna muka kai zaune kanshi a duke yana aiki kafin ya dago yana turo muna wasu takardu a lokacin aka turo kofa sauran mutum ukun mune suka shigo lokacin. Fara duban takardan nayi na dan lokaci bayani ne akan company shi na kaduna da kano dake batun durkushewa a yanzu . Nan yai muna bayani kan yana rokon zamuje can din muyi aiki dasu na dan lokaci mu gano mashi inda matsalan yake . Shiru office din yayi na dan lokaci don ni sam ban ma kawo kaina ga zancen masu zuwa amma kuma abin mamaki zancen farko nice ta farko daya fara kiran sunana a wurin. Na dago kai da sauri ina kallon shi a cikin mamaki yace na sani kina tare da mahaifiyar ki da kanin ki zaune haka kuma akwai masu iyali a cikin ku. Don haka na tadarwa kowa yadda ya dace akwai wurin zama akwai mota da duk wani abin jin dadi dazaku bukata a can na tanadar maku shi. Yanzu ina sauraren ku ku tsara yadda tafiyan zai kasance nayarda dakune na daukeku tankar yan uwana na jini don haka nake wanan shawaran daku yanzu saidai idan akwai wani wanda yaga hakan bai mai ba zai iya kawo nasa shawaran muji. Shiru office din ya kara yi kafin oga Jimo ya fara magana yana fadin shi a nasa ganin zaifi kyau a fara tura Adnan tare da Sahiba suje wurin a matsayin sabbin ma,aikata daka dauka daga nan sai su dauki rohoton abinda ke gudana a wurin daga nab sai musan abinda zamuyi nan gaba kano da kaduna din kusan abu dayane ke tafiya dasu don haka zasu iya fara da kano din sai kadunan. Hakan yayi Felix ya fada nasan Sahiba zata iya zata fimu sanin abinda ke gudana saboda kwazon ta bayan hakan ita mace ce kuma yarinya da zatayi saurin shiga ran mutane. Felix na fada da karfi take annurina ya canza lokaci guda naci gaba da fadin aiki zanje ko bayar da kaina ga maza so mind your language please. Hannu Sha,aban ya daga min da hausa yake fadin zancen felix ya dauka hakan shine daidai amma ni nasan zaki iya koba ta wanan hanyar ba Sahiba saboda kwazon ki na aiki da kike dashi ki taimaka min na gane abindake faruwa a can please. Ido na kura mai na dan lokaci kafin na kawar ina fadin banice da ikon kaina ba kun sani a katkashin mahaifiyana nake yace ya sani shiyasa zan baku duk wani abinda zaku nema a can idan Allah ya yarda. Hausan da yakeyi yasa basu gane me yake fadi ba a lokacin suka zuba muna ido suna kallon mu zanje gidan naku daga nan dani da jimo da Abdulhamid . Idan na bar nan don tafiyan naku zai kasance a cikin satin nan mai zuwa ne idan Allah ya yarda don haka na yanke shawaran zaku tafi dake da Adnan yemisi da Abdulhamid zai shigo yanzu. Jin su kawai nakeyi don ni zuciyana ya lula a duniyan tunane lokacin don sam bamma tare dasu don banji yadda zaman ya karasa ba a karshe. ZAINAB IDRIS MAKAWA ANA DARA GA , , , , , , , , 5️⃣6️⃣BY, , , , , , , , , , , , ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , , , , , , , , BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AR RAQIB, , , , , , , , , , ONLINE PAID NOVEL YAR UWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA BA TARE DA HAKKIN KOWA BA DON BIYA KI TURA DARI BIYAR 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK 08036959257 ALLAH SARKI AI RAINA BAYA BACI YANZU DON KIN FITAR DON NASAN AKWAI RANAN HADUWA SEE U👋👋👋👋 Bayan fitan su dole nina tsaya don dama hakane muke dan shirune ya biyo office din kafin can na dago kai da sauri ina fadin breakfast Oga ya gyada min kai alaman a kawo mashi. Ruwan tea ne sai cake na kawo mashi don nasan ko cake din sai kila yaci hakan da nayi mai yasa ya dan ji sauki a zuciyat shi sosai don rabon shi da abinci tun karyawan da yayi gida kafin ya tasone a cikin shi lokacin. Ganin ya kurbe dan ruwan shayin sai dan kadan ya gutsuri cake din ya barshi nan nake fadin na kara mai ruwan zafin ne yace no barshi da sauri yaci gaba da aikin da yakeyi a cikin computer shi. Jimo ya kara dawowa da wasu takardun dayayi aiki a cikin su sun dan dade tare suna magana kafin ya fita Felix ma ya shigo da nasa. Bayn fitan felix din ne na shigo na samu ya hada kanshi da tafin hannayen shi biyu ya dukar da kai da gani yana cikin damuwa sosai. Sai kuma hakan nima ya dameni don ban taba ganin shi a cikin irin halin nan ba haka mutum ne mai nuna jajircewan shi ga komai lalai wanan abin ba karamin abu bane a wurin sa. Dan satan kallon shi na sakeyi har lokacin bai dago kan shi yana a yadda na sameshi zaune din sai nayi tunanen ko barcine ya samu a hakan na juya zan fita naji yace kina son wani abune ? Ya dago manyan idanuwan shi ya sauke a kaina dama nace ko ayima odan abincine ka danci na fada cikin sanyin murya. Murmushi naga ya dan sauke irin na gefen fuska din nan mai nuna ina cikin wani hali yace tea din da nasha is ok don ban iya cin komai a yanzu suna son suga bayana Sahiba . Yau laifine don nakai abu a kasan haihuwan mahaifiyana suma su karu damu su samu ashe hakan yin laifine a garesu. Sun mayar da dukiyana abin wawaso an rasa gane inda kudin ya dosa ko ya shige har suna kawo min shawaran na sayar da wurin ga wasu ki duba min mutanen sahiba. Nayi mamaki kwarai da karfin hali irin na dan arewa a nan shiya nemesu da abin arziki don kasa ta karu dashi sukuma suna neman ganin bayan shi a yanzu din. Tausayi ya ban sosai ganin yau yadda ya tsaya yana ban labarin abindake damun shi kamar wata yar uwanshi naji a lokacin. Yasa har na kai ga bude baki ina fadin halin dan Adam ne oga ko naka sai a hada kai dashi a cutama indai dan arewa ne don haka sukaiwa mahaifin mu yan uwan shi na uba daya suka kashe muna shi kan dukiyan sa shine mafarin da mahaifiyar mu ta gudo damu zuwa nan lagos tun muna kanana basu san muna raye ba son kawai kada mu taso muce muna son dukiyan mu. Da yardan Allah zamuje muyi aiki sosai insha Allahu sai mun gano inda suka shiga maka da dukiyan ka su fito dashi idan mutum nason kansa da lafiya. Kodana gama magana na dago kallon da yake min na mamaki ne ya dan ban tsoro yace yes Sahiba na manta shaf da zaki iya sam raina bai kawo kan hakan ba da farko. Amma yanzu hankalina ya fara kwantawa sosai wallahi saidai kuma naji kin jefo min zancen sun kashe mahaifin ki akan dukiyarsa wanan maganan da gaske kuma haka yake ? Ban taba karya ba bazan fara ba yau abinda na fada ma hakan ne ya faru a gabanahaifiyata sukayi ta daba mai wuka har ya mutu su kuma suka handame dukiyan da baya. Yaya akayi kuka tsira nan ma na bashi labarin komai daya faru a lokacin kamar yadda naji umma tabawa daddy dasu ya modibbo labari a ranan. Shiru yayi ya zuba min ido yana kallo haka Yemisi ta shigo ta samemu kallona tayi kafin ta dauke ido ta mayar a kanshi tana mamaki. Zan iya shigowa tace tana kallon shi zaki iya mana ya bata amsa ko kinga wani abune ta dai nemi wuri ta kai zaune saida ta seta kanta ta fara maganan daya kawota office din. Nikan fita nayi na barta a ciki tana masa bayani aikina naci gaba dayi har ta fito tana dan watsa min harara a raina nace kinyiwa banza din ban san kinayi ba ma. Da dare bayan mun ci abinci na fara ba umma labari saicewa tayi ai sun rigaki zuwa nan sun rokeni da rana kuma na tausaya masa. Na nuna masa tausayi sosao kan hakan ubangiji Allah yasa hakan ya zamo silar fitan arzikin shi a gano inda suke a sanyayyena amsa da amin umma. Amma umma zuwan mu kaduna din ba zai kawo wani matsala ba tsakanin mu da yan uwa a can na tambayi umma din ina kallon fuskan ta. Sahiba aikine fa ya kaiki can ba wani shashanci ba sanan kuma kari da dadawa tare duk zamu tafi yadda sukai min bayani har Abdulhamid da iyalinsa meye na matsala a wanan kuma ? Wanan fa wani hikimane na ubangiji idan kin kula da hakan saidai kawai a barwa Allah nasa sanin yanzu don shi yasan abinda ya shirya ga hakan. Ba gidan kowa ko a karkashin wani zamu zauna ba kila har mamu kare wani baisan mun shiga garin kaduna din ba tunda ba sanin ki akayi ba a can dama. Dole muka fara shitin tafiya saidai umma ta dan koka da sana,anta saiga Abdulhamid ya kawo shawaran cewa kanin shine zaizo ya zauna tare da matarshi su kula muna da gida idan umma ta yarda sai a barwa matar shago su zauna muna. Yadda umma ta yarda da Abdulhamid ko dan uwantane ya tsaya a nan don haka a take ta amince da hakan. A shiga a fita kan tafiyan sirin namu ba tare da kowa yasab da hakan ba ranan mun kusa tashi aikine sai ga kiran oga ya samemu lokacin muda zamuyi tafiyan duk muka hallara . Office din yayi tsit kafin ya dago kai yace damu Alhamdullahi duk wani shiri ya kammala akan tafiyan mu din saidai matsalan daya fara hangowa a tsakanin mu yanzu kuma. Ba wani matsala bane sosai sao rashin hadin kan da babu shi a tsakanin yemisi da sahiba don haka zai iya kawo muna rashin nasara a can idan muje can muna hakan. Don hakane zai raba tun nan yemisi zata zauna kano tare da felix sai su zauna a can da sauri Filix ya dago kai yace ahh, why now oga ? Yace hakane zaman lafiya aida sauki don dole kamar a wuri daya ake tunda ba nisa sosai kuma a karkashin abu daya kuke dukan ku a can. Har ya kare zancen shi yemisi koni bamuyi magana ba an dai wayi gari kawai anga dukkan mu bamuzo aiki ba a ranan sai suka dauka mun fita wani aikine. Munyiwa kaduna shigan dare ne dukkan mu sai wanda yazo taron mu dinne ya dauke mu ya kaimu kwatas din a unguwar GRA. Tuncan kowa yasan nomban gidan shi don haka nuna muna kawai akayi nikan da umma mun tsaya addu,a hakama naga saura musulman sun tsaya addua. Amar tun shigan mu yake bin gidan da kallo yana fadin wai dama ace nan din shine gidan muna lagos daya dinga jawo abokan shi nan ai. Gidane madaidaici da dakuna hudu plat dai irin na zaman family din nan ginan shi maikyau an saka gadaje da kayan kitchen a ko wani gidan bamu da matsalan komai da zaman nan. Su Felix da jimo Adnan da Abdulhamid ne suka fara fita don ranan ni na tashi da ciwon kai ban fita ba ita kuma yemisi wai ta kwana gudawa. Zuwan su tare da gabatar da kansu a sabbin ma,aikata ya dan kawo tsegumi a wurin sosai hakan ya kawo cecekuce wai ya kwaso yarbawa daga kudu yanzu su zasuyi aiki a wurin kuma. A yadda suka dawo suna bamu labari komai na wurin ance ba tsaro mai karfi kamar yadda ya fada masu wurn ya samu matsala. Kwana biyu suna fita ga rana na ukune na samu fita duk da naso makaran fita din haka na shirya na daure na fita a cikin motan da sai ranan na fara shigan shi tunda aka ajemin shi a kofan gidan. Jikina yana saye da buje da rigan les pink maidan ado da blue din filawa sai gyalen dana saba saman kafada na da jakka shige da kayan. Kayan sun kara fito min da kyauna a fili sosai tun shigowana nake bin ko ina da kallo a wirin a daidai inda naga motar Adnan na parker nawa motan na fito. Na dan tsaya nayi nazarin wurin sosai sai hakan ya dawo da hankalin ma,aikatan dake waje a haraban wajen tafiya nakeyi a hankali ina waya da adnan dake min kwatancem wurin da zan samesu idan na shigo. Duk wanda na wuce ina jin abinda suke fada game dani wanan itama din tare da sabbin oganin take kai wanan yarinyar karama haka ? Kila dai ire iren yan matan su salman ne da suke daukowa aikun saba da ganin irin su a nan suna sintiri wani ke fadi. Na wuce kamar banji su ba saidai maganan ya tsaya min a raina lalai dole mu saka ido ga irin wa yam nan da suke maganan su din. Ina kaiwa tsakiyan wurin naja na tsaya wuri daya ina duban ta inda zaifito min sai gashi ya fito a sani dan karamin lungu yana min sannu da zuwa tare da nuna min hanya yana gaba ina binsa a baya na samesu a office din da suke ciki. Har gida taje takaiwa yayan nata dogon list din da uwar nata ta zauna ta tsara matashi waiduk abubuwan da takw bukatane duk. Duk daya gane sai ya karba yana fadin wai yan mata duk wanan ke kadai ke dashi da fatan dai kina iya amfani dasu bana son zancen daukan yar aiki ki zage kiyiwa mijin ki bauta ki samu ladan aure zaifi maki. Ta dan yi murmushi na yarinta tana kawar da kanta gefe daya tana dan jin kunyan abinda ya fada mata din mika mata takardan yayi yana fadin ki rike wanan a wurin ki ki fadawa anty saina shigo mu zauna da ita. Duk abinda suke fada Nazifa na jin su don tayu masu zaune a wurin taki dagawa tana son taji meya lawota wurin dan uwan nata. Mata a kula a dan dagawa maigida kafa a duk lokacin da yake ganawa da yan uwanshi na jini ko aminan shi irin wanan zaman da kikeyi yana ja maki bakin jini a wurin al,umma haka kuma yana hana maigida yayi alheri wa masu bukata idan yana kallo idanun ki don wata kila kin rokeshi bai samu baki ba har wani ya kawo nasa bukatan a lokacin daya dace ya bayar. Yar uwa kada ki zamo cilin silar hana alheri ki kasance mai karfafa kafan a yi zumunta don ki tashi da hasken hakan a goshin ki ranan gobe kiyama ubangiji Allah yasa mu dace amin. Nazifa bata so hakan ba duk data dan dauki haske amma kuma rashin ganewa ya hanata fahintan komai a lokacin. Itama hjy karima tana gida tana Allah Allah yar nata ta dawo taji yadda sukayi da yayan nata a lokacin. Bayan baby Summay ta gama labarta wa uwar sai cewa hjy karima din tayi burgan banza dama ai nasan ba zai iya bamu abin kwarai ba don wanan munafukan uwar nasu bata bari yayi alheri ko kadan dama ta kara jan tsuki tana fadin aikin banza da wofi idan ma sirina suke son ji basu taba gane hakan wallahi. Zato zunubi koda ya zama gaskiya da yamma sai gashi gidan direct part din ta ya nufa kuma Amira taga shigowan shi itake fadin ga yayan mu nan yazo. Fatima na fadin tare da yaran sa ne yazo Amira tace ban tsaya ba ina shigowa na ganshi basu gama magana ba sai jin sallaman shi a kofan su sukaji. Ya zauna an gaisa yake fadin anty baby ta sameni dazun a gida ta kawo min list din yanzu ga wanan sai ayi hakkuri dashi. Nan hjy karima ta fara fadin kai modibbo wanan kanwar taka ta azama lalura haka har ka biye mata kai kuma. Dan shafan fuskan shi yayi yana fadin hakan ai shine daidai anty ku godewa Allah daya nuna maku hakan kuna tare damu addu,an kune ke aiki a kanmu . Wani iri taji tana kai idon ta kan takardan daya basu din saida ta dago kai da sauri tana fadin anya modibbo kudin nan basuyi yawa ba haka ya mike yana fadin bakomai anty kayan gado dai da sauran su nayi magana da Fatima ventures zasu shigo da kayan da komai na sakawa a daki a haka mata su sai a duba dakuna nawane a gidan yanzu don sun tambayeni hakan . Shiru hjy karima tayi gaba daya jikinta ya gama mutuwa da bayanin ta sai ji tayi yana fadin na barku lafiya anty ya mike ya fita yana kadawa baby din data dago tana kallon shi hannu ya fice. Yana fita yaran sukayo kan uwar suna fadin mama nawa yabadane mu gani summaya din ta fisge takardan a hannun ta. Ihu ta sake tana fadin mama miliyon biyu fa ya bada tace bari kedai baby aini na kasa magana wallahi don na rasa mezan ce ga baban kunan muna kai ruwa rana dashi kan dan abinda na bukata. Ashe yaron nan yana da kudi hakane Allah sarki mama har kina zagin sa dazin gashi ya baku abinda bakiyi tsamanin samun a wurin sa ba fatima ta fada daga gefen su inda take kwance saman kujera. Harara uwar ta watsa mata tana fadin kaji yar baki na zageshi din duk cikin hakkin mune wanan din yaji dadin mahaifin ku cikin ku kamar shi ? A wani matsayi kuke yanzu a nan din tambayan dana jefo masu ke nan bayan na zauna na dan bi office din da aka ajesu din da kallo. Adnan ne ya dago kai yana fadin a cikin dariya ai shine muma har yau bamu gane ba madam don munyi tambaya bamu gane komai a nan din ba. Ba gaskiya bane na fada ina mikewa a nuna min office din manage din yanzu na fada ina barin kujera. Sahiba kibi wanan zancen a sannu don mutanen nan basu da kyau wallahi na fahinci hakan tun jiya da muka fara tambayan su Abdulhamid ya fada. Ai ban tsaya sauraren shi ba nasa kai na fito daga office din ina bin rubutun office din da kallo. Idona ya kai gana manager din ban tsaya jiran komai ba na nufi kofan zan shiga da sauri dan tsohon dake zaune a kofan ya taso yana fadin . Hjy ina zaki ba a ban ikon barin kowa ya shiga a wanan lokacin ba don manya ke ciki suna meeting na dan kalloshi na sake mai murmushi komey ya gani oho naga ya jaye min da sauri na shiga ya biyoni a baya. Jin an bude kofan an shigo yasa gaba dayan su su wurin goma suka juyo suna kallon wanda ya shigo office din. Binsu nayi da kallo daya bayan daya har nakai kan manager din na tsaya a hankali na tako baka jin komai a lokacin sai karan takalmana dake fitar da sauti. Good morning manager ya dan amsa min da sauri sauri files din dake gaban shi na kalla ina fadin zamu fara aiki akan wa yan nan now now. Da niyar wullakanci ya dago ya fada min magana ko me ya gani kuma sai ya kasa baba kazo ka taimaka min mu kwasa zuwa office din da aka bamu muyi aiki a cikin sa. Ina kallon tsohon nake magana shima dai ni yake kallo kamar kowa sai kuma na koma fadin zamuyi aikin da wasu daga cikin ku zasu taimaka muna . Af kuyi hakkuri fa ban gabatar maku da kaina ba nazo na fara aiki kai tsaye kada ku damu don haka nake ni ban wasa kan abinda ya kawoni a wuri. Kwana biyun nan ban fito ba saboda dan gajiya daya dameni sunana miss Sahiba daga lagos na fada tare da rokon su su yi hakkuri da shigowan da nayi masu kai tsaye. Zamu iya daukan files din kun gama dasu na juya ina tambayan shi tare da kallon shi na tsure shi da ido OK zan baku minti talatin a kawo muna muna jira na juya na fara tafiya suka bini da kallo. Har nakai kofa na juyo ina fadin saidai kada ka manta ka fito da wayan nan da kuka boye kai dashi na nuna mai dayan mutumin. Daga haka nasa kai na fita shiru office din ya kara daukan kafin manaja ya cire hullar kanshi yana fifita dashi a kanshi da fuskan shi. Yau naga shu,umar ya lalai mutanen nan basu zo muna da wasa ba a wurin nan saida suka shiryo muna amma barsu in sun san wata ai basu san wata ba. Kafin su rike baki na turo kofan kai dakai dakai a tare zamuyi aikin daku sai ku samemu da files din muna jiran ku yanzu. Wacece ita din wai wani dan kyamusasshe a cikin sune ya tambaya a cikin hausa azaton ba maijin ko zo in kashe ka acikin mu kaf, wa,iyazu billahi wanan mutumin ta nan ya biyo muna kuma yanzu ban taba kawo hakan ba wallahi ? Suyi duk abinda zasuyi mana kudi daine sun shige bamu san inda suka shiga shike nan mana fakat . Dayan su ya fada yana wani ware hannayen shi na dan sake murmushi daga inda nake tsaye din yaci gaba da fadin zai dauko muna kafirai suzo fitgita mu kome ? Alhassan kabi maganan nan sannu don Allah kai ka cika danye kai kada abin nan ya dawo ya juye damu fa kana magana haka. Ta kwabe din mana wake tsorin hakan yanzu duk iya binciken su dai ba zasu taba gano kudin nan ba tunda ba a hannun mutum daya suke ba yakarsa fadi a hasale na dan saci kallon shi da wutsiyat ido. Kai manager din ya fada har lokacin yana fitara da hular kanshi yana fadin su Alh dai yanzu ai dole mu nemosu su sanda zancen nan gaskiya. Office din na koma ban zauna ba sai bin ko ina na office din nayi da kallo suma abokan aikin nawa kallona sukeyi ba wanda yai min magana a cikin su. Widow officen kawai nake kallon haraban wajen a tsaye kafin muji an turo kofan office din an shigo wa yan nan mutanen dana nuna ne su ukku dauke da takardun company a hannsu su. Kallona abokan aikina suka fara yi kafin su shigo suna gaisawa dasu na nuna masu table din akan su zauna saidai kuma wurin ba zai ishe mu ba dole mu koma babban hall din taron cikin wurin da aikin mu na fada yes madam Adnan ya kara fada suma suka bini da kallon mamaki. ZAINAB IDRIS MAKAWA ANA DARA GA , , , , , , , , 5️⃣7️⃣BY, , , , , , , , , , , , ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , , , , , , , , BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AL MUJIB, , , , , , , , , , ONLINE PAID NOVEL YAR UWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA BA TARE DA HAKKIN KOWA BA DON BIYA KI TURA DARI BIYAR 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK 08036959257 ALLAH SARKI AI RAINA BAYA BACI YANZU DON KIN FITAR DON NASAN AKWAI RANAN HADUWA SEE U👋👋👋👋 Sallama yayi ya shigo part din mommy ce ta amsa take fadin a, a ina kuma ka tsaya ai na dauka ka tafine don yaran sun fada min kazo tundazun na dauka Alh kazo gani bai nan ka tafi. Ban tafi ba dama baby ce nazo gani ina part din anty ne tundazun din da sauri mommy tace me kuma ya kawoka wurin baby da uwarta ? Yana kaiwa zaune saman kujera yake fadin akan sha,anin bukintane don dazun ta sameni gida nace tazo zanzo na ganta shine yanzu nazo. Wani kallo uwar har yan uwanshi ke masa yace ba wani abu bane dai nine nace tayo min list don abinda take so shine ta kai min daga haka yaja bakin shi yai shiru bai kara magana ba kuma. Idon ta kara zuba mai tana fadin ka fitar da kanka cikin zancem nan don koni uwarka ba,a saka a cikin shi ba banga dalilin da kai zaka wani zake ba haka ? Ta manta cewa nima idan Allah ya kawo lokacin gani dasu har uku a gaba dama tayi hakanne don kawai ta kumsa min bakin ciki take tunane . Ta nuna yaran nan basu da farin jini gashi har yarta ta isa aure ta samu manemi su suna zaune a gida shine kawai sai kuma dan kudin da yaron ke nuna masu yana dashi yanzu kuma. Haba mommy ki daina damuwa da irim kananan maganganun nan don Allah suma din ai lokacine baiyi ba idan lokacin yayi yi zasuyi ai. Yana fadin haka ya mike yana fadin zan koma mommy sai dai gobe in Allah ya kaimu don zan tafi abuja din a goben nan idan Allah ya yarda. Ya kara mata sallama ya fita ba tare da ya fadi abinda yazoyi wirin su hjy katima dinba yana fita Nabila tace aiso nayi mommy ki tambaye shi muji ko wani abu ya basu ai. Haba kema ai kin sani tunda kikaji ya fadi hakan aikin gama ya gama ko kwanan zakiga anfara sha,anin bukin nan gadangadan ke nan ashe hauwa ta fada daga inda take zaune. Tsuki mommy tayi tare da fadin koma me zai basu indai wanan matarce ba zai taba haske ko ta wani so shiba indai itace. Mommy shifa yaya ba don ta yayi ba ai kinji abinda ya fada baby din ce ta tafi wurin shi dazun ta ganshi yayine kawai don zumunci hauwa ta kara fada uwan taja wani irin tsuki tana jin wani iri a zuciyar ta. Office din yai shiru dan dakikun mintina ba zamu zauna a yau ba don lokaci ya danja yanzu sai dai gobe idan Allah ya kaimu yanzu a samu wanda zai bude mana da addu,a bayan nan sai mu fita ga baki dayan mu zuwa cikin kafanin muga abinda mukazo zama a kanshi na fada. Kallon kallo aka fara a tsakanin mu dasu jin abinda na fada wani daga cikinsu mai dan tsawon gemu ya fara da sallama. Takardan dake hannuna nake karantawa har lokacin da suka shafa nima na shafa din na kallo inda felix yake nace yai muna addua ya dan kalleni ya fara. Gaba daya muka mike muka fita wanan da yai muna addu,a shine ya jagorance mu yake nuna muna wuraren ai kafin kace me har an samu wanda yaje ya rsuguntawa manager ga abinda aka hangomu munayi a lokacin. Don me ba zamu takawa yarinyar nan burki bane rankayadade haka kawai mu zauna karamar yarinya tazo tana kokarin juyamu muna zaune. Nima abinda na gani ke nan ai gara mu nuna mata nan fa arewane ta shigo ba kasan su ba ita din me don Allah oga bala. Kyautane zai rudemu ko shigarta na banza me akayi akayita ma da har take batun bude muna zani a kasuwa muna kallon ta in abin nan yayi nisa fa duk kan mu nan zai shafi kowan mune wallahi. Shafa kai don duk masu laifi muke ai manager ya furzo iska waje daga cikin bakin shi yana fadin don me ba zamuyi wani dabara na sallon sayenta ba mu gwada mu gani idan hakan zai yuyu. Da nawa kake ganin zamu saye ta a wuce wurin daga milliyon daya zuwa sama zamu fara kaftawa mu gani amma muddin muka bari wanan abin yai boosting wallahil azeem kowan mu nan sai ya raina kan shi cikin mu yanzu meye abin yi ke nan. Abin yi na farko shine duk wani wanda ke da hannu a cikin harkan nan a sanar dashi ya kwana a cikin shirin kota kwana don fitana idan an san farkon shi ba a san karshen shi ba. Tunda nake ban taba kawo sense ko yarda akwai wani abu a kaina sai wanan ranan tawa ta farko dana ziyarci company nan kai rayuwan nan ina zaki damune wai. A yanzu yan Annabi a baki Fir,auna a zuciya sun fi yan son abi a zukatan su yawa don zaka ga mutum har mutum amma kada ka tona kaji aikin da yakeyi a bayan kasa. Meyasa tsoron Allah yai karanci a wanan zamanin hakane har kafiran masu bautan wanin Allah suna sun sufi musulmi gaskiya. Nace hakan ne don zamana a cikin su ina rayuwa sai kadan dinsu ne ke saka ransu ga abin wani idan kaji sunce dakai i swea to god iyakar gaskiyan ke nan suke fada lokacin. Amma a yau sai dan musulmi ya rantse ma da Allah bisa kan karya koda kuwa yasan gaskiya yake karyatawa a kan karya saboda rudin duniyan nan ubangiji Allah kasa mufi karfin zuciyar mu Amin. Don naga abinda basu zata ba a filin Allah saidai zan bisu a yadda suke son mu tafi din har mukai karshe dasu hakana. Kaci nawani ka raya kanka da iyalan ka yaya kake zaton diyan ka da ka tayar a cikin haramun zasu kasance suma zakaga mutum yana kwalliya da haramun yana tunkaho a cikin ta kamar ba ranan haduwan mu da Allah. A gajiye muka gama zaga ko ina muka dawo office din mu zaman mu ke nan saiga abin sha an kawo muna masu sanyi da cake. Yemisi na zama take fadin duk ta gaji ta mika hannu zata dauki drinks din nace don't ta dago kai ta dan kalle ni kai na kara kada mata alaman a, a dai tayi saurin ajewa ta daga. Sabbin abokan aikin nawa suka zuba muna ido don rashin fahintar abinda ke gudana a lokacin. Harshe na juya da yarbanci ina fadin duk wanda zai sha ko yaci ya fita nisa da wanan wurin yasai duk abinda yake bukata don wanan din hanyar dauremune aka dauko haka. God forbid ta fada tana fadin iam testing let me go and find something to drink . We can go home now sai gobe don Allah kowa ya fito da wuri na fada na juya wurin wa yan nan mutum uku din ina fadin mun gode da lokacin su da suka bamu da fatan zasuyi hakkuri a cin ma manufar wanan aikin a tare dasu. Tare muka fito zuwa haraban aje motocin company ina kallon yadda mutane sukayi gungu gungu suna gulman mu a lokacin kowa ya shiga motar shi muka nufi gidajen mu. Da yake azahar tayi tun muna hanya muke jin kiran sallah a wurare don haka ina shiga gida gaisawa kawai mukayi da umma na shiga dakina nayi shirin sallah. Na idar ban fito ba karatun alkur,ani na soma yi sosai cikin daga murya duk wanda ke gidan zai iya jina a lokacin. Har lokacin la, asar yayi na mike nayi sallah na shafa na fito na samu umma zaune tare da maniya suna hira muka gaisa da ita take fadin ashe ba barci nakeyi ba don shi maigidan ta tun shigowan shi ya kwanta barci wai yau ya gaji da yawa yace. Murmushi nayi ina fadin na dauka zai fitane zancen karatun yaran nan amma yanzu yamma tayi ni zan fita gobe kafin in shiga office mu nema masu inda ya dace dasu. Abinci fa umma ta fada muniya tace bakici abinci ba tun lokacin da kuka dawo Sahiba ai ita wanan yemisi din nan gidan mu tazo ta karbi abinci taci. Tausayi yemisin ta bani kamar ba ita ba yadda tayi laushi a yanzu tun zuwan mu nan arewan don itama taso tazo tare da mahaifiyar ta sai sukai shawara kan ta fara zuwa taga yanayin wurin ita. Abincin na debo na dan fara ci a lokacin kuma muniya ta fita daga part din mu tsakuran abincin nayi na kai na aje a kitchen waje na fita don kallon yanayin sabon wurin namu. A hankali nakai hannayena saman kirji na sauke ina lumshe ido tare da shakan iskan dake kadawa mai sanyi a lokacin. Dan takawa nayi na jingina jikina kan dan adon da akaiwa kofan shiga gidan namu wanda kusan ko wani gida akwashi a wurin. Bin gidajen wajen nayi da kallo sabon wurine da gani saboda ba mutane sosai a gidajen kusan ma mu din ne nake ganin farkon shi gidajen da aka gina su ko muzo na biyu don yaran dana hango dan nisa damu sun fito a cikin shirin islamiyan su lokacin sai kuma naga wani ya fito ya bude mota sun shiga . A gabana sukazo suka wuce na dan bi yaran da kallo hakan yasa na nasa a raina cewa zan samu lokaci in masu magana game da karatun su Amar don yanzu yana secondry ne a matakin farko. Na dade a wurin don har nakai ga kaiwa zaune ina nazarin wurin kafin magariba yayi in shiga ciki don sanyi ya kara saukowa sosai a lokacin. Sallah nayi na samu wuri na kwanta kasa a falon ina tunanen mai gobe zai haifar garemu in Allah ya kaimu gaskiya karatu yana da dadi ga dan adam sai dai idan Allah bai nufi bawa da yinsa ba. Da badon jajircewan da Allah ya nufeni da yinsa ba na dage har na cin ma wanan manufan da ko wace uwa take gurin ganin haka ga abinda ta haifa da muna can wullakace ina faman tallah da neman dakon abinda zumuci. Rana na farko ke nan danaga aikin alherin da ya Abubakar yayi min a rayuwana don shi mutumin daya dorani a matakin farko tunda da har na dakatar da karatun nawa ne. Koda ina da baiwan sani idan banda ilimi baiwan ba zai kaini ko ina ba a duniyan don komai da ilimi yake tafiya zamanin nan. Na shirya a cikin buje da rigan aiki don in batar da sawu fula kawai na dunkule gashina na cusa a ciki ban saka dan hijjab dina ba da nake sawa iya wuya. Zan shiga mota ke nan na hango wanan miji da mata din hausawan zasu fita ashe matar ma,aikaciyar asibiti ce ita mijin daine ban san a ina yake aiki ba shi. Tattataki nayi zuwa inda suke suna ganin na doso wurin suka dan kuro min ido na karaso Ina masu sallama suka karba gaidasu nayi a cikin harshen turancin kafin na fara fadin. Don Allah ina son su taimaka min ne da yaran mu ko inane keda makaranta maikyau da zamu iya saka yaran mu a ciki. Nan dai nayi masu bayani sai matar ke fadin tana shiga mota ashe suna da yarama to ka taimaka masu mana idan zaka iya kai. Yace ai kinji Allah ta hadamu dashi don me zaki taimaka masu tunda muna wuri daya zaune dasu bamu san inda zasu taimake ba ai. Nan dai muka aje magana dashi zai dawo ya dauki yaran a kaisu ko za a dauke sun don yanzu second term ake ga karatu. Yadda yai muna alkawari hakan ya cika don ya samu Abdulhamid sun kai yaran da takardan da muka karbo daga lagos nasu an saka su azuzuwan da suke can din ranan mun riga Abdulhamid zuwa wurin aiki kan wanan matsalan sai lokacin hankalina ya kwanta ganin Amar ba zaman banza zaiyi a kadunan ba shima. Yau kan ma,aikatan ya cika da ma,aikatanta duk masu zaman banza a gida suna karban albashi a banza sai gasu sun fito aiki a ranan. Tundaga get din nake kallon irin mutanen dake wajen har nakai motana inda zanyi parking na ajeta ban fito ba don wayan dana tsaya yi da Abdulhamid sai hakan ya dan bata min lokaci ga ido sun zubawa motan suga wanda zai fito a cikin taba. Kafana fari sol daya sha takalma mai tsawon duduniya na fara sakowa kasa na tsaya ina dauko jakkar laptop dina dana aje a gefena. Na fito ina gyara dan yalalon gyalen dana yafa a kaina iya wuyata a hankali na fara tako a cikin irin tafiyana maikama data tarwada . Tafiya nakeyi ina gyaran gyalen dake zamomin saman kaina din ina dan gyarawa ga waya inayi a cikin harshen yarbanci a daidai wasu mata dake tsaye nayi sallama dashi. Wai aikin banza wanan abarce tazo har aka rudamu haka ku fito ku fito wasu yan zafin kai diyan kwari aka turo yin bincike wanan kan Allah na tuba ai bata ishe mu komai ba wallahi. Salamu Alaikum na fada a daidai lokacin dana dan wuce su ban tsaya ba kuma duk me suke fada kunne yake. Au wai musulmace a hakan sai dayan tace yo aikin kin san haka suke su ba a gane musulmi a cikin su don duk shigarsu dayace ai. Wurin da muka shirya zama nan nanufa na samesu a zaune suna duban tulin takardun dake gaban su. Gaida kowa suka nuna min inda zan zauna nace su tashi daga wurin gaba daya ku dawo nan na nuna wurin da zamu zauna a barin dama saitin taga da yake haska wurin sosai. Mun zauna mun fara aiki bamu jima ba kamar an turo da wani abu a cikin siling din wurin da muka tashi din wani ihu yemisi ta sake tana fadin jesus da karfi kowan mu ya mike tsaye a cikin tsoro suna bin wurin da kallo. Allah ya ban ikon fadin innalillahi wa inna alaihim raji,un Allahuma ajirni fi masibati wa,akkalibli hairan min ha. Auzu bikallamatilllah min sheri man halak may d evils of dis place back to his sender. Ina fadin hakan na koma na zauna cikin ko in kula naci gaba da aikina saida nayi da gaske na samu suka samu natsuwa har suka zauna a tsorace baki sai addu,oin tsari nake karatowa a cikin sa. Ganin yadda na sake jiki ina aikina yasa suka dan sake nasu jikin saidai a tsorace suke aiki a wurin wai suna tsoron aikin malam. Wasu files na rike a hannu na guda uku kafin na dago ina fadin ina son ku gane cewa rayuwa mu a nan yana cikin hatsari sosai kuma kun sani. Saidai alkawari muka dauka kan cewa zamuyi wanan aikin komai rintsin shi da zuciya daya don haka nake ganin duk wani aiki da zamuyi a nan sai idan mun hada kan mu wuri daya kamar yadda muka saba. Files din hannuna na daga masu nake fadin duk abinda muke nema ya farone daga cikin wanan files din na hannu na don daga kanshi ne abubuwa suka rikece a wurin nan. Na kalli sabbin abokan aikin mu suma tsarguwa sukayi da yanayina sai dana dan juya idanuna nace na dawo gareku. Na zabo ku cikin mu don ku taimaka muna da wasu abubuwan da suka shige muna a dahu daga abinda zamu aiwatar a nan din. Na yarda da gaskiyan ku da nagani a fuskokin ku lokacin dana shiga wurin taron ku yasa na aminta muyi wanan aikin tare daku a yanzu. Zamu fara da wanan file din dake hannuna na daga masu wani tsohon file daya sha jiki ya fara tsufa komai da muke nema yana cikin nan na dan bubuga file din dake hannuna. Sun dauka shi suka boye suka dauki wanda bashi ba a matsayin wanan din na hannuna don haka kada wanda yai masu zancen wancan din da suka boye. Suka kada min kai alaman haka yayi daga haka nace dasu mu tashi da dan murmushi makale a fuskana na bar wurin don gano wani abinda nayi . Wani girma suke ban na musan man badon komai ba sai don abu biyu na farko suna ganin cewa kamar nafi kusa da oga gabadaya. Sai na biyu don baiwan da suka fahinta Allah ya ban na sanin abubuwan dasu basu sani ba idan na fada yakan zama gaskiya wani lokacin. Sam ban kula a yadda muka fito daga office din ba don hankalina yana ga wayana da nake duban sako a lokacin. Sun sakoni a gaba suna bina a baya kamar dai wata oganyar su a gaba saida na juyo naga a yadda muken ne naja na tsaya ina makain hakan. Dole sai mun hada da yin hakan zasu saka shakun mu a zukatan su Adnan ya fada min acikin yare na kada mai kai. Wurin motanna na nufa na bude na saka kayan a ciki suka tako min saida na bude na shiga suka shiga nasu motan saidai na dan dade ban tayar da motar ba kamar yadda nayi dana shigo wurin. Caaaa akai min da ido sun zobo min ido suna kallon kowa da abinda yake fada kan zancen mu masu fadin ai gara da akazo bincike wasu na fadin me zasu gane su oga balane fa. Karshe izza keyan su zasuyi su sallamesu da kudi su tafi basu gane komai bai ai indai su oga balane sun saba da irin wanan bincike haka bai basu tsoro. Waya na tsayi da oga jimo na tura mai duk bayan aikin da muka yi ranan kafin in tada motana in bar haraban ma,aikata zuwa masaukin mu. A daidai lokacin ne suka kalli junan su daga inda suke tsaye suna fadin lalaima yarinyar nan zata gane kurenta na shigowa hancin mu da kudundune da take shirin yi yanzu su oga bala ke nan da suka tsargu da shigowan mu a cikin company da sunan bincike a wurin su. Tun dare yake kiran layin umma baya shiga ya gwada nawa sam bai zuwa shima don wayan a kashe yake idan zamuyi aiki. Allah ya taimaka yanzu yana fitowa daga inda ya gama bincike ya lalubo wayan ya kara gwada kiran umma sai kiran ya shiga lokaci guda ya lumshe idon shi ya nufi motar shi ya shiga yana kara wayan a kunnen shi. Bayan sun gaisa ne yake fadin yayi ta trying wayan baya zuwa sai yanzu ya samu tace Allah sarki kwana biyun nan wayan yana kashene ai dazun Ammar ya saka min ita a caji. Baiji abinda take fada ba yasa ya dan dago ya kalli wayan location din da network ya bashi ne nata ya bashi mamaki don ya nuna a kaduna yake waya da maishi kaduna kuma ya fada a zuciyan shi. Zan sake kira anjima yanzu ina saman hanyane idan na isa gida zan kiraku da dare akwai tambayan da nake son yi makine akan uncle marigayi. Allah ya kaimu ta fada sukayi sallama ya kashe wayan ya kara dubawa still dai kaduna ya bashi ya kira kaduna how comes zai nuna mashi tana kaduna matar dake lagos ya fada a fili shi kadai a cikin motan. ZAINAB IDRIS MAKAWA ANA DARA GA , , , , , , , , 5️⃣8️⃣ BY, , , , , , , , , , , , ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , , , , , , , , BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AL WASSE,E, , , , , , , , , , ONLINE PAID NOVEL YAR UWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA BA TARE DA HAKKIN KOWA BA DON BIYA KI TURA DARI BIYAR 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK 08036959257 Har yakai gida yana mamakin hakan a cikin zuciyar shi bayan ya parker motar ne yaja tsuki yana fadin shirmen banza ya fito ya shiga gida. Falo ya samu Nazifa yau ba laifi tayi dan kwaliya da alama dai ta fitane ko tayi wasu baki mm a musanman a gida ya nasa a zuciyar shi. Gaidashi tayi yayi da yaran suka shiga murnan ganin shi daga nisa ya dan daga masu hannu ya shige dakin shi ya barsu a wurin uwarce ta bushi da kallon mamaki mutum haka da riko har ga diyan shi abinda ya faru ne ya fado mata a rai lokaci daya. Izuwa yanzu daya horasu din idan tayi tunane akan abinda ya jawo masu matsalan takan tuna da hudubar uwarta datace mata. Wai Nazifa kinsan darajan mahaifiya kuwa kinsan yadda wa yanda suka dauki iyayyen su da muhinmanci sukeji yayin daka taba masu ahali. Mutum ko dan banza ne akayiwa nasa wullakanci ya sani balle wanan da shawarashi da komai nasa yana a iyayyen shi. Kinyi kokarin nisanta diyanncikin shi da jinin shi shi kuma ya nuna maki ya barki da yaran ki kuje kuyi tayi dasu akwai abinda yafi wanan zafi a wurin mace ace yau uban yaya ya yafe maka yayanka aiko da wasa ya furta maki hakan idan kina da wayau dole ki damu. Tunda nayi sallah ina dakina ina nazarin wanan files din haka ya hanani fitowa don aikin da nakeyi a falo din sai sallah kawai yake tayar dani lokacin. Ummace ta leko dakin tana fadin yau wani irin aiki kikeyi hakane ya dauke maki hankali kai na dago bayan na zana arrow kamar yadda nake saka sheda a wuri idan naga tambaya. Ina murmushi nace umma da alama aikin mu yazo da sauki don wa yan nan files din da kike gani a gabana ya kumshi duk wani bayanin da muke nema. Saidai nayi mamakin ganun haka saboda wasu fliles din da suka boye suna zaton wa yan nan ne a wurin sauri ikon Allah gagara musali ta fada . Kafin ta nisa tace baida alhakin sune shiya sosu da alheri sun nuna masa halin yan Adam yanzu gashi abinda basu zata ba yana shirin faruwa dasu kuma. Bawa akwaishi da matuwa sosai akan dukiya sai ya shagala ya manta da komai balle dukiyan daba nakaba yau ina laifin wanda ya jawoka cin arziki a karkashin shi ? Nisawa nayi ina dagowa tare da aje takardin a gefen wurin sallah na nasan don ban fito naci abinci bane yakai har umma ta biyoni dakina dan tun zuwan mu bata leka dakin da nake zaune a cikin sa ba sai ranan. Tare muka fito zuwa falon nako samu an jera abinci saman dan karamin dining table din dake aje a gefen falon Amar yana kwance yana kwashe rubutu a littafi shi yana jin motsin mu yake gaidani na amsa na zauna umma ta zauna a gefena. Muka fara cin abinci cibi uku nayi na wani irin zabura na mike tsaye da sauri kamar an tsikareni lafiya umma ta tambaya banyi magana ba nasa kai na fita daga falon kai tsaye na nufi hanyar get din shigowa haraban gidajen namu. Ganin haka hankalin umma ya tashi sosai Abudulhamid ta kira hankali tashe tana fada mashi ya fito daga shi sai dan gajeren wandon daya saka a jikin shi na zaman gida. Ina kaiwa kofan na tsaya na dan lokaci kafin na duka na dauki duwatsu kwara uku nayi addu,a na jefa a ta wajen get din duk kusurwan wurin hudu nayi haka na juyo na dawo part din mu duk su umma da Adnan da Abdul suna bina a baya. Daidai tsakiyan gidajen naja na tsaya na dade a wurin ina dan waige waige kafin nayi tako biyu na tsugunna a wurin na dade kamar ina ginan wani abu kafin na mayar da kasan na rufe. Tare muka koma ciki dasu a lokacin ina shiga falon na fada kan kujera basu ankara ba sai ji sukayi ina barci cikin abinda baifi mintuna biyar ba da shigowan mu. Abdul ne ya kallesu yana fadin nasan ba ita bace dama akwai matsalan da suka hango sukai wanan abin haka duk yadda akayi. Ke nan dai tana da sprit a kanta masu karfi Adnan ya tambaya kwarai kuwa ya bashi amsa sun dade a wajen gidan mu suna magana kafin suyi sallama da umma su shige gidajen su don dai suna mazane amma sun dan firgita don basu san meya kawo hakan ba. Washe gari jumma,a ban iya fita da wuri ba don sun dauka ma bazan fito ba a ranan sun fada da aka tambayeni cewa banjin dadin jikinane. Abin yai masu dadi sosai da sauri Inusa ya nufi office din manager ya samu malam bala a ciki ana faman kulawa yake fada masu abinda yaji a bakin abokan tafiyana. Suke fadin mu din dama na wasane an fada mata mu yan iskane da zatayi wa kutse kudi daine munci ba yadda za ayi damu fakat yana wani bude hannayen shi biyu yake magana a cikin isa da izza. Zubur na mike ganin lokacin a gurguje na fada ban daki nayi wanka na dauro alwala na fito na tayar da sallah. Shiryawa nayi cikin bakar abaya nagyara tsab zaka dauka balarabiyace ni din na fito na dauki files dina da laptop na shiga motan sai ganina kawai sukayi na shigo wanda yakai gulman banda lafiya ranan shiya kawo masu tsegumin zuwana kuma. Kallon juna sukayi da mamaki kafin suce ga yar iska shu,uma kada fa yarinyar nan taso juyamuna hankali fa. Ban zauna ba sai yawatawan da muka kama dasu Adnan bayan inda ya rifto muna jiya na nufa tare dasu ba abinda ya faru da saman rufin din wurin to amma ya akayi cikin ya rusa Adnan ya tambaya. Wurin na dan kurawa ido na dan lokaci na sauke ajiyan zuciya muka koma ciki bayani na fara yi masu kan abinda nayi nazari kowa ya duba abin yadda ya dace sauran zancen zami barshi sai monday mu karasa nace dasu. Da biyu nayi hakan don nasan zasuji wanan zaman namu na ranan don haka nake son hanin kullin da zasuyi muna kuma nan gaba. Motana na nufa don tafiya gida saidai tun kan na kaso inda take in shiga naji gabana yayi wani irin faduwa sosai addua nayi na sa kai na shiga don zuciyana ta ban na shiga kawai . Hakana tuka zuwa gida ba abinda ya sameni saidai ina fita ban jima ba ake fadin akawo agaji motar na fitar da hayaki a cikin ta. Aka dai samu aka tsayar da taimakon mazan site din namu abin yabawa kowa mamaki Amar yabi Abdul da Adnan tare da iyalin shi zuwa sallah jumma, a sai ya rage dagani sai umma a gidan ban yarda na kwanta ba don kada sallah ya wuceni. An sako jumma,a ke nan ya fito ya shiga mota ya dauki waya kira layin umma muna zaune kiran ya shi ya shigo a wayan umma nike kusa don umma na sallah na dauka don ganin shine mai kira. Haka kawai naji yanzu ya kamata na daina nuna mai komai tunda yace ba laifin shi bane hakan don shima baiso haka din ba da aka kyalemu din. Sallamu Alaikum na fada ya amsa min tare da fasin so you are at home Sahiba nace eh yaya good afternoon ya amsa da afternoon. Ya kuke ya mama nace lafiya tana sallah ne yace ok kuna dai lafiya ko kwana biyu ban zo na duba kuba aiki yayi min yawa a nan ina kaduna. Ayyah yasu Faiza dasu Amira na tambaye shi yace lafiya suke suna tambayan ki sosai da alama shima yaji dadin yadda na sake ranan muna magana dashi din. Idan mama ta idar zan kira ki gaida Ammar ya fada yana kokarin kashe wayan dake hannun shi din ina fadin umma ta idar amma ya kashe wayan baiji ba. Umma na idar da sallah take fadin Abubakar ne ko na gyada kai tace ya kirani jiya yana fadin akwai tambayan da yakeson yayi min bansan ko na menene ba dai don bai fada ba tukun. Mwku yake son tambayan ki kuma na fada shigowan Amar yasa muka bar wanan zancen da mukeyi din yana bamu labarin wai yaga hanyar da muke zuwa school da muna gidan daddy zaune. Ni dai kallon shi nayi umma ko cewa tayi dashi haba Amar koni bazance ga hanyar da zamubi zuwa gidan daddy daga nan ba don gaba daya garin nan ya juye min ban san a wani barin muke ba. Dariya abin ya ban nace bamu da wani nisa sosai dasu a nan don muna New GRA ne nan kinga ba nisa sosai dasu ba daga nan. Wayan tane ya sake daukan kara ya kira ko ta fada ina mika mata wayan dake hannun nawa ta karba bayan tayi receive. Sun gaisa yake fadin ko kin san filaye nawa Uncle ya bari a duniya kafin ya rasu mama don naga kamar ba wanan case din a cikin case din shi yadda wani makwabcin shi yaba da shedu shekarun da suka wuce. Shiru umma ta danyi kafin tace ba zance na sani ba gaskiya amma dan littafin da yake rubuta komai na samu daman daukan shi yana wurina kafin na bargida . Wata kila zaka iya ganin komai a cikin sa da kake so yanzu ban baku bane a baya don ganin zancem bai tashi ba lokaci. Da kyau mama haka yayi yana nan a hannin ki yanzu haka ko tace yana wurina yanzu haka bana yarda nayi nida dashi ko kadan ai. Zan shigo lagos wani sati zanzo har gida na karba in duba don Allah a ajeshi da kyau don nasan akwai bayanan da zan iya samu a cikin sa. Basu gama wayan ba layi ya katse lokaci guda kallon umma din nayi ina fadin bana son su san cewa muna garin nan umma. Dama saida nayi wanan tunanen hakan zaizo bai samemu a nan din ba kawai a kyaleshi mana idan har ya samu zuwa din bai samemu ba zaiyi zaton mun tafi wani wurine don ba zai taba zaton muna garin nan ba ai saboda Abdul dai yayiwa kanin gargadi kada ya fadawa kowa ga inda muka tafi. Shiru nayi ina tunane a raina yadda abubuwa ke son tikice muna kuma gana aikin da mukazo yi na gane zamu kwasa dasu sosai inba gyaran Allah ba. Shi kuma yanzu yaya ya fito da wani zance wai akan matsalan mahaifin da kawai ya share zancem kamar yadda kowa ma ya share har sai an je gaban ubangiji. Olawede ya kira waya yana min bayani kan sai an buga waya a kawo mai kaya nace ya bari idan kin dawo zan fada maki. Sai lokacin na nisa ina fadin yaushe ya kira umma wallahi banso ya kai ga kira ba naso na tura kudine a tura masa kaya tun bai nema ba. Sai kuma zancen aikin nan ya dauke min hankali umma kinga mutanen nan basu tsoron Allah sam wallahi wai yanzu kokari sukeyi su koremu da asiri ko su shafa muna mantuwa mu bar garin nan a rikice. Yaushe tsoron Allah zai shiga zuciyar mutanene sun Allah ba karya bane wai mutuwan nan fa kullun yita akeyi ana nunawa mutane ishara akan shagala da duniya. Amma maimakon tsoron Allah ya shiga zuciyoyin yan Adam sai kuma kara dulmiya da son duniya akeyi musanman musulman mu na wanan nahiyar na yanzu. Waya na dauka na turawa wa kamfani kudi tare da kiran su nayi masu bayanin abubuwan da zasu kawo muna. Mikewa nayi na kwaso takarduna ina dubawa kafin nayi wani zabura da sauri don ganin sunan wanda ban zata ba a cikin jerin sunan da nike lissafowa a lokaci. Kafa ma sunan ido nayi na dan lokaci kafin na saci kallon umma inda take zaune na kara mayar da kallona kan sunan ina kallo. Jikina ne yayi sanyi sosai na kasa aikin da nakeyi din na zurfafa a cikin tunane mai nisa lokaci guda. Barci na shige da wuri ranan umma tana daukan duk hakan gajiyane a nasu fahintar basu san abinda na gani bane a takardan yasani a cikin damuwa don sunan wanda ban taba zato ko tsamani ba da nagani a cikin wanan jerin sunayen. Saidai kuma zuciya na taki yarda da hakan cewa shi din ne saidai idan mai kama da sunan shi ne na gani din acikin masu ruwa da tsakin maida kamfanin baya a yanzu. Sam zuciyar shi bai yarda da abinda yake gani a wayan shi ba don haka washe gari ya dauki wayan ya saita shi ta yadda zai kaishi har inda yake bashi location din wayan umma din. Ganin inda ya kaishi a GRA din na kaduna ya tsaya yana mamaki hakan kuma signal din yaci gaba da nuna mai green kundunbala yayi ya shiga compound din wurin yana bin ko ina da kallo. Har inda computer din nasa ya tsaya wuri daya yana dan halbawa ya dago kai ya kalli kofan gidan da kyau mamakine ya kamashi lokaci daya amma cikin karfin hali irin nasa yasa ya fito don tabbatarwa kanshi ganin dalilin kasancewar hakan. Gyara tsayi yayi tare da dan gyaran kwalan rigan shi nocking din kofan gidan yayi tayi lokaci guda kusan sau uku ba wanda ya bude gidan. Kallin gidan ya kara yi na dan wani lokaci kafin ya juya ya na kokarin shiga motan shi jin an bude kofon yasashi juyowa ya dan waigo don ganin ko waye ya fito. Nice tsaye dagani sai dan rigan barci mara hannu har kasa duk dantsen hannuna sun bai yano a waje. Sai gashin kaina dana daure daga baya yay dan tuntu babu hula a saman kan nawa din. Sunan shi na dan kira ina fadun sannu da zuwa kayi hakkuri barci mukeyi bamuji nocking din kofan naka ba tun dazun. Tsaye yayi ya dan kuramin ido na dan lokaci kafin yace wai Sahiba kece din dama kina garin nan bamu da labarin hakan ? Ehto tafiyan ne dai yazo muna a hakan bawai munzo nan din bane da shiri bare mu fadawa wani zamu zo din . Bissimillah mana shigo umma na ciki barin tayar maka da ita na fads ina shigewa ciki shikan imanine ya kasheshi a wurin lokaci guda. Umma na sama a daki na fada mata zuwan shi mamakine kwarai ya kama umma ban tsaya mata wani bayani ba don sallaman shi da mukaji ya shigo falon lokacin . Haka yasa ta fito daga dakin a cikin hijab din ta mai ruwan siminti har kasa tana mashi sannu da zuwa ya amsa ta nuna mai kujera ya zauna. Sun gaisa duk umma tana a kunya da ganin shi tunda bata samu fada mai cewa muna kaduna ba ita da bakin ta saida ya gano hakan da kanshi. Dan shirune ya biyo bayan gaisuwa kafin can ya kawar da shirun da fadin gaskiya mama banji dadin hakan ba ace kuna cikin garin nan banda masaniya saida na,urana ya nuna min hakan ta hanyarshi har nazo nan inda kuke yanzu ? Bayan munyi waya dake mama koda ka sani ai sanin baida amfani yaya don ba lalai bane bayan kai wani dan uwa ya neme mu a garin nan tunda ba ruwan kowa damu . Juyowa yayi ya kallo inda nake fitowa ina maganan wanan karon na dora jacket din rigan a sama na daure a tsakiyan kwakwasona . Ba tsoro ko wani darr dinshi a fuskana lokacin ga wani gogewa da wayewa irin na matan goggagu da ya baiyana a fuskana alaman dai jiya ba yau bane a wurina. Amma ta yaya yarinyar nan idon ta yai sauri budewa hakane ya tambayi kanshi lokaci daya kuma ya ba kanshi amsa da fadi ba abin mamaki bane kuma ga yarinyar data tashi lagos kuma tayi karatu a cikkn sa ga aiki kuma duk a lokaci daya haka. Sahiba ni kike fadawa wanan maganan haka na dan kai zaune ina murmushi na kara fadin sorry to say tun jiyan da kuke waya na hana umma ta fada ma hakan. Don aikin daya kawomune kawai zamuyi mu koma inda mukafi karfi da wayau don haka ba lalai bane sai ka sani. Dan murmushi bakin ciki ya sake kafin ya dago kai ya dan kalleni yana fadin, , , , , , ZAINAB IDRIS MAKAWA ANA DARA GA , , , , , , , , 5️⃣9️⃣BY, , , , , , , , , , , , ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , , , , , , , , BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AL HAKIM, , , , , , , , , , ONLINE PAID NOVEL YAR UWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA BA TARE DA HAKKIN KOWA BA DON BIYA KI TURA DARI BIYAR 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK 08036959257 ALLAH SARKI AI RAINA BAYA BACI YANZU DON KIN FITAR DON NASAN AKWAI RANAN HADUWA SEE U👋👋👋👋 Don haka kawai naji gara in fada mai hakan don su sanda sanin cewa bawai surin su mukazo ba lokacin namu ne ya kawomu garin. Masangalin kujera na dafa ina kallon shi kanshi ya dan dukar a kasa kamar yana nazarin abinda na fada mai a lokaci. A kujara na zauna gami da ciro wayata dake ringing a daidai lokacin dan basarwa nayi har kiran ya katse na dago kai ina fadin . Wallahi ninace kada umma ta fada ma haka kada mu sakaka a cikin matsala kuma don aikine na yan watani ya kawo mu nan ba wai munzo zama bane nan kaduna kaji dalilin dayasa nace kada umma ta fadawa kowa muna nan. Abin mamaki ya bashi yadda na zauna nake maganan zakace wata babban mace ce a lokacin. Kafin ya juya wurin umma din yana tambaya tun yaushe kuks zo garin nan ke nan umma har ban sani ba ? Kafin umma ta fada mai nace shekaran jiya nan a takaice ya dan kara kallo inda nake saini kaina amsar bata bada ma,ana a gareni ba amma kuma hakan ne na shirya dama tun baizo gidab namu din har idan sun gano muna cikin kaduna. Kanshi kawai ya girgiza cikin wayancewa don yanayin yadda yaga ina masa a yanzu yace I na Ammar yake ? Wayata ta fara kara kafin ni ko umma mu iya cewa wani don idon daya zubo min na mamaki komai da nakeyi a yanzu din. Daga kano suka kirani suna min bayanin irin abinda suka sama a wurin da wullakancin da manager da suka sama yayi masu don bai ko yarda an zauna dashi ba bama balle har su fara aikin da sukajeyi a can sun kira oga sin fada mai yace su sanar muna nan kaduna. Ku dawo nan kaduna kawai kada ku kara kwana a kano din zan shiga da kaina next week in Allah ya yarda. Yemisi ta karbi wayan tana maganan banza da dan sauri sauri nake magana dan haushi kawai sai na katse layin. Na dago kai na kalloshi sau biyu muna hada ido dashi yayin da nake wayan don haka ina gamawa na mayar da hankalina a wurin shi. Daga umma ke zaune take fadin sun samu matsalane acan din ko na gyara zama ina fadin dama nasan hakan zai faru tunda mutane basa son gaskiya yanzu . A sake ya dago yana fadin suwa ke nan umma kaida gani kasan a cikin dauriya yake maganan tasa lokacin. Umma ta fara zuba mai labarin abinda ke faruwa duk da daure fuskan danayi lokacin amma haka ta labarta mashi komai game da zuwan mu din. Kanshi ya kara girgizawa kafin yace dani wani company ne a cikin kuke bincike a kai ya tambaya yana kallona. Madaidaitan idanuna na lumshe kafin nace dashi na maigidan mu dake garin nan tare da yi masa kwatance yadda zai gane su. Kina ganin zaku iya da wanan aikin kuwa da kuke rainawa a yanzu don nasan masu hurda a wurin a baya can shu,uman mutane sosai don haka yawancin baki masu masana,anta a garin nan suke kuka dasu. Na sani yaya saboda hakan ne ai na zabi nazo nan din don sanin irin halinsu danayi tun kan muzo din. Kibi a hankali don yanzu mutane sun baci sosai balle suna ganin ki karamar yarinya haka dake zasu nemi illanta maki rayuwan ki. Nasan komai yaya a kansu har dama abinda basuyi tsamanin zan sanshi ba game dasu don haka zan gwada sa,a na a kan su yanzu. Haka nada kyau idan kuna da wani matsalan da sai kun nemi taimakon mu zaki iya kiran layina insha Allahu zan taimaka maku dashi. Nagode yaya Allah ya kara girma amma nasan basu shirya yin lalama akan matsala ba don tun yanzu sun fara kawo muna hari akan aikin sun gamu duk yarane ba wanda yakai shekarun su a cikin mu. Mikewa yayi yana fadin mama ni zan tafi dama wanan tracker din ne ya jawoni a yanzu sai na sake juyowa da fatan baku da matsala a yanzu dai a nan ? Bamu da matsalan komai a na gaskiya don komai kawo muna shi akeyi basai mun saya ba ta fada mai cikin kulawa. Ok ni zan tafi ya fada lokacin kuma na mike tsaye nima ina fadin mungode ya tare da bin bayan shi dan dan kallona da umma tayi lokacin. Har bakin motar shi na rakashi ta juyo a yana fuskantana a cikin karamar murya ya kira sunana yana fadin . Kuyi hakkuri nasan abinda akai maku mm a banza daku a cikin duniyane yanzu yake maki zafi har nake ganin kamar shima ya dawo gare mune don ya cuta muna yanzu. Banyi magana ba sai wasan da nakeyi kawai da yatsun hannuna lokacin a karshe dai ya kara da bamu hakkuri har yake fadin yanzu haka a kan case din mune yasa bai koma ba don akwai binciken da yakeyi a asirce ba tare da kowa nasa yasan yanayi ba. So yake ya gama kafin ya fito masu da zancen a banza shine dalilin daya kira umma din har ya gane muna kaduna a lokacin. Idona ne ya kawo kwala kafin nace dashi ai dama kabar wanan zancen inda suka aika muna mahaifi gaba dayan su can zasu tafi ai idan anje lahira Allah yai masu shari,a a can. Don wani tone tone a yanzu sai nake ganin baida amfani tunda sin riga da sunci dukiyan ko nake gani a yanzu tunda Allah ya fitar damu daga kangin wahala da a bar zancen kawai zaifi a yanzu kada rayuka su baci don naga akwai wa yanda basa son zancen. Shiru yayi ya dukar da kan shi kafin ya ce dani sai anjima idan kuna da wani matsala ki nemeni a waya zan taimaka maku dashi in Allah ya yarda. Yana fadin hakan ya shiga motan ya tayar ya bar unguwar namu a hanlali na jawo kafana zuwa ciki ban zauna a falo ba don umma ma bata falon na shiga ciki. Wanka nayi kafin na fito na hada muna abin karyawa muka karya dashi na koma daki na kwanta. Gwago Hari ce da kanta taje airport ta dauko dan nata cikin jin dadi da nuna kulawa a gareshi sai wani haba haba takeyi dashi lokacin kamar dai karamin yaro. Agida kuma tarbo na musan man ya sama an shirya mashi duk saboda dawowan shi wanan wahalar da kai din da sukeyine yasa baison fadawa mami din nasa dawowan shi saidai su ganshi kwatsan ya shigo garin. Bai tsaya falon su ba kai tsaye bayan gaisawan shi dasu gwaggo Asiya dasu mommy da aka gaiyato suzo taron dan lelan kai tsaye ya shige part din shi ya barsu zaune a falon. Wanka ya shiga duk da baida wani datti amma yana jin kansa a takure lokacin son haka yake ganin watsa ruwan zaifi mai sauki. Bin bandakin yayi da kallo na dan lokaci kafin ya fito ya dan sauya kaya wanan karon zuwa riga da wandon yan Pakistan mai laushi har farin singleting shi na maza yana haskawa daga cikin kayan. Yasan suna jiran shi a falo aci abinci don inda sabo ya saba da irin rayuwan mami din nasa kan yadda take nuna masa rsagwaran so zalla a gaban ko wayema zata gwada hakan. Ya samu ma sun karu a yarda ya barsu a baya faifan Nazifa suka bude a gidan kan iskacin da tayi masu a gidan buki da sujaje. Har gwaggo Asiya tayi mata magana bata ganesu bane halan ta zaune yadda take take fadin na ganeku mana ba su gwaggo Asiya bace bata kuma gayar dasu din ba ta kyalesu. Wanan yasa duk ta kara fita cikon ransu shine yanzu gwaggo Asiya din ta tayar da zancen suke mayar da magana akan abinda ya faru a ranan. Fitowan Almustaphane yasa suka dan sassauta muryoyin shi daya karade falo gaidasu ya sskeyi kafin uayi kokarin samun wuri yana kaiwa zaune. Gwaggo Asiya tace zaka zauna kuma bakaci abinci ba dan murmushi ya sake yana fadin a koshe nake yanzu mama sai zuwa dare zanci wani abu. The boy kayi wanan uwar tafiyan mai nisa kace ba zakaci komai ba yanzu maza muje danning ko wani dan abu ka taba a ciki. Tashi sukayi zuwa cin abincin shikan zaune yake kawai a wurin yana kallon uban abincin da aka zuba mai cilin plate a gaban shi gashi bai iya mussa hakan. Ya dan yi spoon uku da kyar ya dauko abin goge bakin shi yana gogewa da sauri uwar ta dago kai tana fadin boy zamuyi fada yanzun nan . Murmushi yayi yana mikewa tsaye tare da fadin zan ci anjima mami idan na dawo yanzu ina son hutawa ne kadan ya dan rungumi uwar tashi. Nan ya barsu zaune sukan suci abincin su sosai basin sun rasa a gidajen su ba sai don marmari da kuma haduwa da juna. Basu bar gidan ba sai da akayi sallah la,asar kowansu ya kama gaban sbi cikin jin dadi da kasancewa da junan su a lokacin. Daga gidanshi yaje gidan su ya dubasu ya samu mommy bata gida Nabila ke sheda mashi inda ta tafi din ranshine yaji ya baci sosai. Ya rasa meyasa suke bata lokacin su akan wanan mara tarbiyan da gata yayiwa yawa har baisan abinda yakeyi ba bai kallon kowa da daraja yana ganin kamar yafi kowa. Bai zauna ba yayi masu sallama suka suna masa magana yake fadin zaije ya dawo ya gansu ya fice daga gidan . A get motan su ya hade dana mommy din dake dawowa ita da gwaggo Asiya yana gani su ya bata rai a tsatsaye ya tsaya ya gaidasu ya wuce. Mommy ta fahinci dalilin sharesu da yayi a lokacin don haka ta danji ranta ya baci a lokacin yadda ya nuna masu din. Ta shiga cikin gida su Nabila suke gaida da ita ta amsa tana zama tare da tambayan Nabila din yayan ku ya shigo gidan nan ko ? Me kuka fada mashi daya shigo gidan nan mun fada mai inda kika tafi gidan gwaggo Harira wurin dawowan ya mustapha. Dariya sosai Fa,iza ta kwashe dashi lokaci guda duk suka juya suka dubeta suna mamakin abinda takewa dariya a lokacin. Wallahi ba komai bane sai Sahiba dana tuna ranan da mommy ta aikemu wurin gwaggo muka samu yaya a gida mun fito muna gulman shi ashe yana falo a kwance yana waya. Ya jiku Hauwa ta tambaya yajimu mana tana surfa mai zagi da katon banza a saman jikon maman shi ya kwanta gashi da wani geme kamar sai gashi gaban mu. Dariya suka kwashe dashi dukkan su lokaci guda me yayi mata ko bai nuna yajiku ba ai kin san halin Sahiba mana anty karasa tayi duk da yana jinta kuwa. Wanan yatinyar ai yar iskace ta kwarai Allah yaga abinda ya gani ya barta a cikin tsiya da suke ciki yar iska kawai. Wallahi ni yarinyar bana son zancen ta kodan ta faye zama fayau ne duk inda kaje da ita sai ansan da tana wurin zakaji wai mutane fa sai su dinga tambayan ka diyar waye ita din shiyasa ban son fita da ita wallahi. Wani kallo Faiza ke mata daga inda take zaune kafin tace kai kai mutum ya dinga aibanta dan uwan shi haka don kawai tafiki tsari. Waye tafi tsari din Nabila ta tambaya har tana dagowa don bacin rai tana fadin mommy wallahi kiwa yarinyar nan magana kona fafasa mata baki yanzu a wurin nan. Kaji min yar iska ni ta ina Sahiba yar kabilu waccema ba a san asalinsu ba sun zo su danganta da uban wasu har zaki wanice dani tafini. Sahiba din ce bata da asali uwar ta dago kai tana tambayanta a cikin mamaki sai ta bata rai kafin tace mommy to waya san ubanta din. Ni mommy ta fada rai bace duk suka kallo inda take a cikin mamaki taci gaba da fadin na karaji kin dangata yar nan da mugun suna zan bata maki rai a gidan nan wallahi. Wai mommy dama kin san mahaifin su ashe shine Anty Nabila take fadin wai basu da asali kila daddy suke kokarin lakawa ita yasa aka koresu. Salati mommy ta fara yi tana tafa hannayen ta a wuri daya kafin tace yanzu sherin da kuke kokarin kulawa mahaifin ku ke nan akan yaran nan dama ? Da sauri Nabila tace a, a mommy nima ji nayi ana fada wallahi cikin dangi yasa nazo ranan ina fada masu abinda naji din amma bani na kawo zancen ba. Kasa magana tayi a lokacin din bata san me zata fada ba ga yaran nata sai mikewa tayi ta shiga dakin nata ta barsu a wurin zaune. Nabila ta kalli faiza cikin dan kwantar da murya ta kada mommy tajisu tana fadin na fi karfin sahiba kema kin sani duk kika kara hadani da yar matsiyata din nan mai kama da yar wanke wanke wallahi saina balbala ki a gidan nan ranan don ta dan sayo maku gwajon lagos ta aiko maku kike wani rawan jiki akansu haka. Nayi shirina ranan monday na fita wurin aiki tunda na tsayar da motana udanuwa suka dawo akaina na mutanen dake ma,aikatan . Sam ban damu da irin kallon da suke min ba don inda sabo a yanzu na saba hakan a wurin su. Ban yarda na shiga office din da muka saba zama don yin aikin muba aranan don haka na zaro wayana na fada masu zamuyi aikin yau a cikin office din babban accounter din ma aikatane. Don haka nasan a nan zan samesu na fito yadda na saba ina saye da wandon jeans na yayi sai yar riga fara mai dan ado daga gaban riga daya tsaya min iya gwiwana kaina yana saye da hula baki kalan wandon dake jikina zakace tare akayi su. Na wuce naji wasu na fadin kai ga mace dai kan har mace amma kuma kafira bata sallah ina wayana na wuce su ina mamakin dan adam da daukarwa kanshi fitina yake. A daidai shiga na hadu da oga bala da sauri zai fito yana waya yana ganina yadan razana ya daburce don gani din da yayi a bazata. Gaisawa ya tsaya mukayi dashi sama sama kafin don ban tsaya ba ina tafiya muka gaisa din da dan murmushi gefe a fuskana na wuce zuwa ciki. Suna zaune ina tsaye ina karanto masu abinda nayi nazari a file din farko dana bude tare da bayanin abubuwan da na gano a cikin sa. Kafin na dauko computer na daga inda nake tsaye din ina tura bayanan da muka gani acikin sa aka turo kofan office din. Oga bala ne tare da manager suka shigo a dan rude duk muka dago muna kallon su a cikin mamaki kallo daya nayi masu na mayar da hankalina wurin computer da nake tura sako ciki. Bayani yakeyi a rude yana fadin sunzo don Allah akwai wani files a ciki da basu dabganci wanan zaman naku ba zamu dubasu cikin nan. Ba tare dana fago kaiba na fadi a cikin yarbanci su basu su duba din naci gaba da aikin da nakeyi ban dago kaina ba. Ban dago kai ba still ganin suna damuna nace dasu wanan kuke nema ku dauka ai mun gama dashi zaku iya tafiya dashi yanzu. Lokaci daya suka dago kai suna kallona kafin su juya su kalli junan su kuma suna mamakin hakan. Manager ne dan fara ja baya kafin ya juya ya fita daga office din oga bala yabi bayan shi ba tare da sun tsaya amsan file din ba don sun san komai yagama tonuwa a cikin shi ke nan. Kallon su nayi ina fadin zamu shiga kano gobe idan Allah ya kaimu da safe Adnan zamu tafiya da motar kane dana Abdul zuwa can don haka ku sha mai da wuri da zaikaimu ya dawo damu a yau din nan. Sai mun hadu goben na fada daga haka na fita don ban iya tsayawa hira a rayuwana har yanzu sabo da rayuwan ujula dana tashi a cikin sa har banda lokacin da zan tsaya yin dogon hira da mutane. Basai mun tambaya ba don da ganin wurin hankali a tashe yake nikan ban tsaya ba wurin motana na hara direct na bude zan shiga. Da sauri Bello ya karaso inda nake ya tsayar dani yana fadin wallahi madam akwai matsala don suna son su hada kan mutanem wajem nan ai muna bore a koremu. Nothing will happen insha Allah na fada na bode motana na aje kayan dake hannuna tare da juyowa gareshi ina masa godiya. Na shiga na tayar da motar na halba aguje nabar haraban wajen suma suka shiga muka fice zuwa inda masaukin mu yake. Haka yasa suka dawo da hankalin su wurina har na bace kowa na fadin albarkacin bakin shi a kan mu yarinya yar firit kara sai bakin wayau da fitinan tsiya haka. Wasu suce da ganin wanan yar ta karantu sosai tayi ilimi tun tana karama irin tashin turai din nam ne kana ganin ta kasan ba tashin kasan nan bane ita. ZAINAB IDRIS MAKAWA ANA DARA GA , , , , , , , , 6️⃣0️⃣BY, , , , , , , , , , , , ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , , , , , , , , BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AL WADU,D, , , , , , , , , , ONLINE PAID NOVEL YAR UWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA BA TARE DA HAKKIN KOWA BA DON BIYA KI TURA DARI BIYAR 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK 08036959257 ALLAH SARKI AI RAINA BAYA BACI YANZU DON KIN FITAR DON NASAN AKWAI RANAN HADUWA SEE U👋👋👋👋 Zaune suke sun kura mai ido sai harkan gaban shi yakeyi kamar baisan dasu a wurin ba zaune ga lokacin da suka bata a waje kafin su samu shigowa wurin shi falon. Saida ya gaji daja masu rai suna zaune shiru don zakace ba wani mahaluki bayan shi a falon. Gyaran murya yayi ya dago yana fadin kai yanzu manaja har akwai wani hallita da zaizo garin nan ya tayar maka da hankali irin haka ? Kuma kace mace ce yar karama ke maku wanan karanbanin barazanan da rayuwan ku yaya akai sake kabari har haka ya faru dakai kamar ba namiji ba ? Zama manaja ya gyara ya dan shafo fuskan shi kafin yace wallahi Alh yarinyar watau shu,umace ta gaske fiye da yadda kake zaton ta. Don ka duba fa wanan file din Bala ya fada muna cewa shida hannun shi ya cire shi kuma ya boye shi amma yarinyar nan sai gata da files din nan a hannun har kuma ta zakaloshi cikin yan uwa tasan dashi. Koda muka shiga muyi yadda kace sai cewa tayi damu me muke nema wanan nan din ta na hannun ta saita miko muna tana fadin gashi ai ta gama dashi ko mu dauka. Ke nan ta kwashe komai na cikin sa ke nan ta dawo muna dashi din muyi abanda zamuyi dashi wallahi Alh yarinyar fa kada kaso ka ganta duk batafi shekarun yata ta biyu ba da haihuwa. Dan shiru yayi kamar yana nazari can ya dago ya gyara babban rigan shi dake saye a jikin shi daga shi sai ita dama kana ganin jikin shi daya fito daga cikin . Yace yanzun dai manaja a takaice ba zaka iya ba ke nan da wanan yarinyar manaja ya gyara yana fadin gaskiya kusan hakane Alh dole sai kun saka hannu a zancen nan. Zamu saka ita sin me ko oduduwa kakan yarbawa ya shigo gonan mu a yanzu ai zamu kawar dashi ne kamar kauda kara ba wani aiki bane kubani yau da gobe ki gani sai ta nemi agaji ta bar garin nan a gagauce nina fada maku. Godiya suka shiga mashi cikin nuna jin dadin su ga hakan nan kuma sai hira ya barke a tsakanin su oga Bala na nuna masu yadda nake turanci wai nasha mai nayi fari kamar baturiya nazo zan masu barazana da fari a nan shiko yace su za a nuna ma farin shago suda sukaga yan matan kano bila,adadin mai zai basu tsoro kafiram banza kawai. Alh na jinsu kafin ya dago yace meye sunan yarinyar ne koba ta fada maku sunan ta bane ta fada ya dago yana kallon manaja shi oga bala dake ta faman zuba lokacin. Gaskiya na manta don sunan dai gashi kamar na yarbawa kamar na hausawa haka ko larabcine oho ? Sa,ba ko me kusan haka dai ta fada koma waye ai zamu sani ya fada ku bani lokacin dana fada daga gobe zaku ban labari da bakin ku yadda za a kwashe da ita. Godiya suka karayi kadin su bar falon nasa ba tare da sunyi wani maganan akan dawo da abinda ke hannun su don har lokacin zancen haka baizo a zukatan su ba. Shi Alh ma shirme da haushin su yake gani yadda suka wani tsorace akan mace macen ma yar cikin su kwaranya da ita. Tsab na shirya a cikin wando da rigan aikin mu na can mai daukan hankali ga duk wanda yaga kayan namu na fito daga daki zuwa da yar jakar tafiyana ina fadin umma zamu tafi ke nan. Tace har zaku tafi baki karya ba dauki ga tea nan nasan dama haka zaki ce zaki bar gidan nan bakici komai ba. Dole na dan kai zaune nayi bissimillah na kafa kai na dan fara kurbawa saboda akwai dan zafi umma ta kura min ido daga inda take zaune . Nagama nace to umma zamu tafi ina mikewa tsaye tace Allah ya tsare ya kare Allah ya haushe ku a saman su ya sa a dace da abinda akaje nema. Na amsa da amin kofa na tsaya hakan kusan dabi,atace ban fita gida ba tare da addua ba bani ba kusan dabian yarbawane hakan da yawan su haka suke wanan dabian nagama na shafa nafita umma tana bayana. A kofan mu ta tsaya tana min sai mun dawo na amsa na tafi bakin motan Adnan nan na shiga muka dauki hanya mu hudu a nasa motar shida felix a gaba zaune nida yemisi abaya. Felix ne ya fara magana yana bada labarin irin wullakancin da akai masu a can din yana mamaki sosai na yadda suka nuna basu san aikinsu subama sam. Yaja hausa hausa are terreble people ya fada dan gyaran murya Adnan yayi yana masa signal da ido gani nan fa yace. Ainikan yarobace don ban san komai ba ga hausa karshema kila bana jin yaren sosai suka kwashe da dariya nidai murmushi nayi masu kawai. Allah da ikon shi mun isa da wuri kai tsaye muka nufi cikin ma,aikatan kamar dai yadda wacan din ya mutu sai ince wanan din ma kamar ya fishi mutuwa ga ma,aikatan a warwatse wani wurima na hango dabbobi suna kiwo a cikin wurin mota ya tsaya a gaban ginan daidai inda Felix yace ya parker da sauri na dago kai nace ya kara gaba gadan ya tsaya a barin dama. Sun rigani fitowa dukkan su a cikin motar har na dayan motan sukazo suka tsaya a daidai inda motar mu yake tsaye suma suka fito daga cikin motan. Hankalin wa yanda ke ma,aikatan ya dawo gare mu ganin mu a cikin bakaken kaya lokacin ganin Felix da yemisi . Kafin na fito ina bin ko ina da kallo na haraban wajen yadda ma suka bamu lavarin dai naga basu fadi daidai don gaba daya wurin ya lalace sosai. Bamu shiga ba sai zaga ko ina da mukayi har idona ya kyallo min an cire injin biyu dake sarrafa alkama a wurin. Mun shiga muna dan gaisawa da wanda muka gani nice baya ina waya da umma da harshen yarbanci muka kai kofan muna tambayan manager wurin. Wai yau bai fito ba suka bamu amsa naja na tsaya daga baya suma din kamar can da muka barone don gulman sukeyi suna ina kwarin nan suka fito hakane wai ? MD da da sauran manyan wurin muka sama sun kira chairman din wurin shima wai baya gari wani ya gama waya dasu ya juyo yana muna bayani cewa wai yace ace yayi tafiya sai next week zai dawo. Har abokan aikina sun fara maganan kan yanzu ya zamuyi ke nan sai sukaji nacewa mutumin excuse me can i have his number please ? Sai naga sun kalli juna sun juya da hausa suna fadin wa zai yarda a koreshi idan oga ya dawo ya gane nina bayar gaskiya bazan basu ba nikan. Ba zasu bayar ba fa yemisi ta fada tana fadin ranan wallahi ba karamin wullakanci sukai muna ba a wurin nan saida kyar muka samu suka fada muna koshi wanine ya nuna muna tabaya lokacin zai fita ya haumu da fada sosai a wancan wurin. Muje kawai nace dasu suka biyoni baya na bi hanyar matakalar benen zan hau da sauri wancan daya buga waya ya biyo mu da waya yana fadin gashi ya kara kiran layin kuma yana mika muna wayan sai Abdul ne yakai hannu ya karbi wayan a wurin shi. Yz miko min na dauka kuma ban tsaya ba har muka hau saman na kara a kunnena ina ji wai bayanan shi don haka sai kubar, , , , No problem koda baka nan ai company na nan zamuyi aikin daya kawomu mu wuce kada ka damu ai na fada ina mikawa wancan mai wayan wayanshi. Tsarin ginan nabi na gane offince din da nake nema din na nufi can murda kofan nayi yana bude sai nadanyi nocking tare da sa kai cikin officen ga baki daya. Saura suma suka biyoni a baya waya yakeyi a lokacin jin yadda aka shigo mai yasa ya dago a fusace yaga ko waye sai mukai arba dashi ya mike da sauri. Sannu da zuwa yayi muna kafin ya tambaya mudin su waye Adnan yayi mai bayanin daga inda muke da abinda mukazo wurin su yi kuma na bincike kan company. Nan ya fara muna inda inda yana fadin ai tun da suka samu labarin muna kaduna suke kokarin shirya files din saidai basu hada ba har yanzu. Baida matsala ai tunda mun sameka zaka iya debo muna wanda ke nan sai mu fara dashi na fada bayan na kare bin office din da kallo. Yace gaskiya ba zai iya bayar da komai ba shugabanin sa basa nan don haka muyi hakkuri har su dawo din. Kana tsamanin bamu san shirin da kukeyi bane a kai yau din nan da muke son su a hannun mu inyaso saiku cinawa wurin wuta kamar yadda kuka shirya yi din da daren nan ko ? Na fada na kallon shi tare da dan sake mai murmushi har dimple dina ya dan lutsa a lokacin bashi ba kowa na office din saida ya kalloni na dan duka kadan ina aje computer na dana fitar tare da fadin files guda dubu biyune ko da dari takwas da muke dasu a nan a cikin shekara goma sha hudu dayin wanan masana,antar . Yanzu kuma kuna kokarin fitar muna da guda dubu da dari takwas sauran fa malam idan kun boyesu koda yake no need ku fitar muna da wanda kuyi niyar fitarwa din ba matsala zamu samu komai a cikin wa yan nan din na hannun mu. Sorry mah ya fada da dan rawan jiki ba laifina bane yin hakan nima umurni akabamu muyi hakan daga saman mu waya kawo wana idea din na tambaye shi ina kallon shi ido a cikin ido. ( Mai karatu zaki iya cewa wanan shirine don labarin yayi dadi haka Allah sarki ranan da Allah ya hada ki da wani dan baiwa mai abin mamaki zaki tuna da ni Sahiba ashe labarina ba karya a cikin sa. Ni kaina haka dai Allah ya haliceni nake gani banda matsalan ciwon kai gaskiya bansan ina da wani matsala a jikina ba . Bana bada magani amma zan iya kallon ki in abin ya biyo a kaina zan fada maki komai game dake kuma hankalina bai bace a tare dani ba.) In takaice maki dai ranan bamu daga a surin ba saiga manaja mai tafiyan sati daya ya dawo garin ashe baije ko ina ba yana garin dama. Wani bakine mai dan jiki da tsawo sajen fuskan shi yana gauraye da baki da fari da tsaga uku uku a bakin sa. Yo don me zasu shigo muna babu sanarwa haka kawai suce sunzo aiki damu ana ce masa yallabai kayi hakkuri a bisu a sannu tunda sun zo ko ba abinda zamuyi yanzu. Saina ci musu mutumci na nuna masu nan arewane ba ai muna kutse haka shi idan ba yana mutumin kawai ba bazai nemu mu sulhunta a tsakanin mu ba. Sai kawai ya turo muna comitten bincike haka suzo su wani cika muna wuri da guntun turancin su iya wuya don Allah ku bari in shiga muyita yanzu dasu yana fadin haka ya fado offince din inda muke kai tsaye. Kowa daga inda yake zaune yana aiki suka dago kai suna kallon shi Bellone cikin wanda muka dauko daga kaduna yake fadin malam lafiya dai. Bin kowan mu da kallo yayi kafin yace ance kuna nemana kuma kun shigo baku fada muna zuwan ku ba kun fara aiki bada masaniya ta ba? Who is he na tambaya ba tare dana dago kai daga abinda nakeyi a cikin naurata ba yace iam the chairman of this place. And then so what na fada idona kan laptop din na dago ina mikowa na kusa dani takarda yana tsaye ya kura min ido a cikin mamaki. You can go now mr chairman you are not invet here ka barmu muyi aikin daya kawo mu mubaka wurin ka daga inda Adnan yake ya taso zuwa inda nake zaune yana nuna min abu a computer shi nayi masa bayanin komai ke ciki. Ina kokarin dukar da kaina inci gaba da aikinane Felix ya jefo min tambaya na bashi amsa duk yana tsaye kamar an dasa shi a wurin ya kasa fita. Ku bashi kujera ya zauna wanan tsayin yayi yawa haka jin haka ya bashi daman fita yana fadin yana zuwa ya fice da sauri. A kano suna jiran fitowa mu yau su sha kallo kamar yadda Alh ya fada masu cewa zaiyi maganin mu su bari suga abinda zai faru damu a kwana biyu ras. Suna zaman saka idon ganin fitowan mu shiru har sha dayan rana babu alaman mu sai suka dauka ai abinda akace zai faru damu din ne yafaru din. Suna mayar da zance ne kiran chairman din can ya shigo masu a wayan yana sanar dasu muna wurin su munyi kaca kaca muna musu binciken kwakwaf. Yan iska a can suka dura maku yau kuma ashe akwai ta kuwa da wanan shu,uman yarinyar mai kwakwaf da isa. Sundan jima suka kashe wayan suna murnan can kuma iskan namu ya kadamu ke nan mun gama dasu ke nan ashe dama me zamu iya dasu . Abinda basu sani ba shine Alh na can ya shiga wani hali don ya kira bokan su ya fada mashi komai yace ya bari zai kirashi idan ya bincika. Ya binka din ya kumaga abinda bakin sa bai iya fadawa Alh kada su raina mashi wayau ga aikin shi abincin shi ya dakile a wurin su. Yasa yace dasu gaskiya subi aikin nan a sannu don mutanen nan sun wuce yadda ake tsamani don me basu fada mai da wuri ba su san abinda zasuyi a kai. Yanzu aikin gagawa ba zaiyi tasiri akan su ba dole sai an dan bada lokaci kafin a samu yadda ake son samu. Su bashi shanu ayi yanka da bakaken busurai guda uku da kudin da za a sai turaren da za ai aikin dashi yace zai aiko masa zuwa yamma. Ankan sayo shanu wai a hanya haka kawai shanun ya mutu a cikin mota haka kawai ba a san me ya sameshi ba. Jin wanan labarin ya sa Alh shiga cikin wani yanayi na tashin hankalin don ba kudin shi bane shi kadai shi yanzu me zai fadawa sauran abokan harkan nasa akan haka. Bawai shanun yafi karfin shi bane kawai dai bakin haline irin na wasu don yana ganin idan ya sai wani shanun kamar shi kadai ke nan ya biya masu aikin amma yasan abinda zaiyi . Adaren ne kuma yayi mafalki da wata fitsitsiyar yarinya a gaban shi tana bashi warning kan abinda suke shirin aikatawa din a cikin tsawatawa ya ganta tana mashi kashedi. Hannu ya daga yakai mata mari takama hannin wai har hammun shi ya kare a cikin ya falka a firgice yana maida numfashi lokacin ne kuma yaji baya iya daga hannun da yaga an rike masa din a cikkn mafalkin . Duk yadda yaso ya motsa hannun abu ya kiya gareshi tun yanayi shi kadai dole ya bidi taimakon iyalin shi kan hakan. Abu wasa wasa har gari ya waye aka nemo mai duba kariya yazo har gida ya duba yaja masa hannu ai sai abin ya karu mai fiya da yadda yakeji da farko ma. Dole aka danganta shi da asibiti can ma sunyi iya duban su basu gane komai ba suka saka mashi ruwa da alluran kashe zafi don ya samu dan sassauci amma ina . Awanan halinne Oga Bala ya kirashi don ya sheda mai halinda ake ciki babban dan Alh din ya dauki waya yana masa bayani halin da mahaifin nasu yake ciki. Takawa yayi ya kira chairman da manager ya fada masu abinda ke faruwa da Alh din ranan kallon juna sukayi kafin shi oga balan ya basu shawara cewa su isa asibitin suga halinda yake ciki daga can suyi masa bayanin komai. Saidai sunje din abinda idon su ya gane masu babu dadi ga Alh dole sukai mashi sannu suka kama bakin su suka tafi. A hanyane manaja ke fadin anya anya kuwa ba wanan dalilin bane ya jawowa Alh wanan fitinan karo da yarbawa fa ba banza bane. Kai ina sam Alh fa da kuke gani shima shegen kanshine na gaske indai wurin wanan harkan ne yaci gaba da cika bakin sa kan Alh suna sauraren shi. Yanzun mommy wanan abinda kukewa gwaggo baku sakata a hanya ba sai biye mata kuna dulmiyewa shine daidai mommu ku baku sakata a hanya maidaidaiciya ba. Me kuma mukayi don kawai mun je nuna mata farin cikin mu shine laifi kuma yanzu ? Ok kiyi hakkuri mommy idan ranki ya baci amma ni gaskiya na fada maku ai don kawai yana shi kadai sai a diga yin wanan abin haka fissabilillah ? Tau ubana nida abu ke samuna su zo min din fa shiba laifi bane yin hakan ko tunda ni akaiwa ko na fada ma kadaina raina min wayau irin haka. Don ko banza kasan dai hari yar uwatace kuma tare muka tashi da ita kamar kawaye sai yanzu kuma kan danta in kita. Ya mike yana fadin zan tafi dama kayan yarinyar nan da nayi odane suka iso nazo in fadawa daddy dasu din zanje yanzu in samu daddy din. Yana gadin haka ya mike tsaye ya fita zuwa part din daddy din yayi sallama ya shiga don hango daddu din da yayi zaune kasa yana waya hjy karima zaune a gefeb shi.. ZAINAB IDRIS MAKAWA ANA DARA GA , , , , , , , , 6️⃣1️⃣BY, , , , , , , , , , , , ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , , , , , , , , BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AL MAJID, , , , , , , , , , ONLINE PAID NOVEL YAR UWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA BA TARE DA HAKKIN KOWA BA DON BIYA KI TURA DARI BIYAR 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK 08036959257 ALLAH SARKI AI RAINA BAYA BACI YANZU DON KIN FITAR DON NASAN AKWAI RANAN HADUWA SEE U👋👋👋👋 Karfe goma na dare muka fito don nema inda zamu kwana ga yunwa dake cin mu lokacin don ma munyi dabaran odan abinci aka kawo muna har inda muke banci abincin ba don inada matsala a rayuwana. Bana cin kifi ko wani iri kuma bana zama a indama ake cinsa sai gashi anyi rashin sa, a sun kawo masu ferfesun kifi a cikin hadin haka yasa na dan fita daga waje don warin shi da aka bude yake son sani amai. A inda na zauna bayan ginan nake jin ana kuskus waya akeyi da wani kan cewa ya tabbatar ya shigo cikin dare yayi yadda aka umurce shi dayi. Fotowan da nayine ya ban dama samun lokacin don jin abinda suke shirin yi anyi yan wasu abubuwa a wurin. Aikin ne damuka dan dakata ya kaimu dare gashi shawarma da dan ruwan lemu naci shine a cikina har daren. Bello ne ya nema muna wurin kwana don gaskiya yana da kirki sosai ga kwazon aiki don ya iya computer sosai irin talent din nan ne shi. Wanka nayi tare da alwala nayi sallah na dade zaune ina addua kafin nashafa na mika hannu na dauko wayana dana makala a canji na kira umma nayi masu bayanin ba zamu samu daman dawowa ba a ranan. Addua tayi na Allah ya tsare ya kare na amsa da amin daga man na shiga duban sakon da aka turo min. Sakon farko daga oga jimo ne yana min fatan nasara da godiya kan aikin da mukeyi ya samu labarin yadda aikin ke gudana. Sai sako na biyu daga Faiza idan da sabo na saba da ganin sakon nita tana min fatan sake ganina a rayuwa a karshe tace kada nayi mamaki ganin ta lagos wurina wata rana. Sai na uku sakone daga oga Sha,aban shima din fatan alheri ya turo min da godiya sai tambayan umma . Dan murmushi na sake a fuskana don jin dadin wanan sakon kamarni mutum irin sha,aban zai tsaya ya turowa godiya irin haka ? Nagaji daga inda nake ni kadai ina faman tunane don haka na mike zuwa bandaki na fito nayi adduan kwanciya nakai saman gadon. Wasa wasa aikin da muke ganin na kwana biyu muka shigo yi sai gaya yakaimu har karshen mako a nan kano din sanam muka koma kaduna. Yayi sallama ya shiga fallon ya samu wuri ya zauna yana sauren wayan da daddy din keyi akan rashin lafiyane har yana fadin a kaishi waje idan nan din ba su gane komai ba. Daddy din ya gama waya ya juyo yana fadin kai duniyan nan wai Alh Bubane wanan aminin Alh Nuhu ya samu matsalan tashin lafiya da rana tsaka hannu ya rike mai. Allah ya sauka ya bada lafiya ya fada kafin ya zamo yana gaida daddy din sunyi kafin yace nazone kan zancen Summay baby don a tuntubi gidan mijin aji in sun gama hada inda zasu sakata a kai kayanta can don kayan sun iso ko a yanzu. Nan hjy karima ta fito daga uwar dakin Alh din datake ciki tana gyara sai taji abinda modibbo din kr fadi kafin daddy yace dashi kamar wasu irin kaya fa yana tambayan dan nasa. Ya dan gyara yace kayan dakine nayo mata odan su kuma sun iso dama nayi hakane don kada kayan su jima suzo daidai bukin ya kusa. Shine banda masaniyar hakan Abubakar bayan wancan kudin da tace ka basu a baya har kayan daki kuma ka hada mata ? Zaune hjy karima takai don ta rigada ta gama magana akan wanda zata sayawa yarinyar har hakan ya hadasu fada da mijin nasu sai da ban baki aka shawo kanshi ya fara bada rabin kudin kayan. Wayan shi yake duba don haka hankalin shi baikai ga kowa ba a cikin su balle yaga irin kallon junan da sukayiwa juna na zargin kin gani ko ko kuma don me zai mata haka a bangaren hjy karima din. Wayan shi ya mikawa hjy karima dake zaune a gefen mijin ta yana fafdin ga kayan sunce kalla biyune milk da purple suka shigo dasu shine na zaba mata purple din kamar zaifi. Wayan ta tsurawa ido tana kallon kayan da suka saka zuciyar ta kusan bugawa a lokacin yau yar tane da wanan kaya haka masu uban tsada. Ta mikawa Alh wayan shima ya dade yana kallon kayan ya mikowa dan wayan shi ta fara din modibbo wanan irin dawainiya haka mai yawa ? Ni zan koma dama abinda ya kawo ni ke nan ga takardun kayan sai idan an shirya aje da wanan idan za a kwaso yayi masu sai anjima ya fita ya barsu da mamakin shi. Mommy aka kira koda tazo dan nata ya fita falon lokacin sai mijin da hjy ta sama zaune zugun zugun ta zauna a cikin tsarguwa tana fadin gani Alh. Yace modibbo ne yazo da wani zance yanzu koya fada maki ta dago tana fadin zancen me Alh don ni bamuyi maganan komai dashi ba ya fita. Takardun photunan gadon ya mika mata ta dago ta karba ta fara dubawa kafin ta dago kai ta kallo shi. Modibbone ya sayawa kanwarshi kayan daki murmushin dadi mommy ta sake a daidai lokacin da ta dago don taga yanayin da fuskan mommy zai nuna a lokacin. Mommy ke fadin amma ya kyauta haka akeso babba ya zama babba a wuri ya fara daukan girman shi ke nan a yanzu. Nan suka dan taba zance irin haka kafin ta mike zuwa part din ta ta barsu a falon hjy karima tabita da kallo. Yau na tashi ina son sawo abin bukatan mune na gida don haka na shirya tsab cikin doguwar riga mai tsaga har gwiwa sosai sai dan gyalen dana yafa a kaina dayasha gyara. Nida Amar muka fita nake jan mu a motana dayasha wanki yana walkiya muka dauki hanyar cikin gari da zan iya cewa wanan ne karo na farko dana taba shiga gari da sunan wani bukatana. Tafe muke mun sake kida dake tashi na yarbawa aikin Amarne wanan yawo kawai mukeyi don haka kawai muke dan shakatawa kuma na fitone don Amar din lokacin. A daidai traffic muka tsaya magana nake a wayana hankalina yana saman traffic din dukda wayan dake kunnena a lokacin. Hannu aka bamu na ja motan da sauri kamar ance in dago kaina in dan kalli gefe Almustaphana ya kura min idanu na kawar da sauri ina kallon hanyana. Shi dine tabbas na gani don jikinane ya ban ana kallona na dan kallo wurin na ganshi a cikin wata mota fara. Mamakine ya kama shi don zuciyar shi bai gaskanta mai abinda idon shi ya gane masa ba harko in kamane wanan kaman yayi yawa sosai wallahi. Har motan ta wuce yana binta da kallon mamaki ta cikon glass yana fadin anya wanan ba sahiba bace kuwa ? Inhar itane tun yaushe take garin nan ke nan har yakai gida cike da wanan tunanen a zuciyar shi dabara ya fado mai yaron shi ya kira ya bincika mashi har in itace ko tana lagos din tunda yasan gidan yasan kuma motana. Wani shago muka shiga Amar ne zai zabi kaya a cikin sa shida kansa ya zabo abinda yake so muka juyo zuwa gida lokacin shidda na marance tayi ko. A wajen gidan mu muka samu umma zaune tare da muniya suna hira a nan na tsaya sai Amar ne wanda ya shiga da kaya cikin gida lokaci. Umma ke fada min yayan mu yazo bai samemu ba da sauri na juyo ina tambayan wani yayan namu a ciki tace Modibbo mana. Na sauke ajiyan zuciya don a zatona shima mustapha din yasan gidan nan ke nan don ko sun sani ba zan je gidan kowa ba a cikin su na raya a raina. Saida akai kiran sallah muka bar wurin zuwa ciki kowa ya shiga dakin shi don gabatar da sallah a lokacin. Ban fito tunda na idar din ina daki ina aiki har dare yayi sosai kafin na fara jin haushin karnuka daga wajen mu can nisa kadan damu don ina jin haushin da dan nisa da mu. A can kuma na dinga jin dan hayani kafin a fara kwankwasa muna kofan gida na taso da sauri na zura hijjab dina a jikona. Falo muka hade da umma tace waye a cikin daren nan haka karfe ukun dare yake kwakwasa kofa a yanzu ? Ba lafiya dai duk yadda akayi ta kara fada kofan na nufa da sauri umma ta tareni tana fadin waye daga ciki. Bude mama ya fada da hankali nine Abdulhamid jin hakan yasa na bude kofan da sauri ina budewa suka fado cikin gidan mu shida iyalin shi baki daya lokaci guda. Umma ta mayeastar da kofan da karfi ta rufe lokaci guda take tambayan shi meke faruwa ne wai ? Yace ki saurara kiji tun dazun ake wanan ihun hakan daga bayan layin mu nace ina sauran yace baisan halin da suke ciki ba a gidajen su. Mikewa nayi na nufi hanyar fita daga gidan da sauri suka tareni nace dole na dubasu ina fadin haka na fito shima ya biyoni a baya yana fadin su rufe gidan. Wurin yemisi na nufa ita da take mace bugu daya ta kara zabura nace nine sahiba saita bude tayi kuka har ta godewa Allah. Fitowa tayi ta rufe gidan jin cewa da nayi nice sahiba yasa su Adnan da felix dake tsaye a bayan mu bude kofan suma da sauri suka fito daga gidajen su nan sauran makwabta suka dinga fitowa daya bayan daya jin karan bude kofunan sauran gidaje da sukeji a lokacin. An hadu wuri daya ana shawaran zuwa duba abin ko a kira yan sanda suzo nace me zai hana muje mu duba kada ku manta bamuji motsin masu gadi ba kuma ya kamata a duba halin da suke ciki su ma. Kowa ya fara kallon dan uwa an rasa wanda zaiyi kundun balan zuwa ga karan abin kamar dabba yana ci gaba da kugi a cikin wahala sosai lokacin. Kallon Abdul nayi ina fadin yakai yemisi gidan mu wurin su umma ya dawo da sauri suka wuce don duk a tsorace take lokacin. Tafiya na fara yi ba tare da sun farga da hakan ba sai wajen kofan masu gadin get dakeda dan tazara da inda gidajen namu suke. Kofan na bude saidai basu cikin daki ga takalman su nan a kofan da alama sun gudu ko an daukesune muka fara zargi . Tambayan sunan su na fara yi aka ce Lukas da Barau suke ba wani tsoro a zuciyana ko fuskana sabanin sauran jama,an wurin da suke a firgice lokacin. Hasken wayan dayan mutumin na karba na fara bin inda abin ke kuka na fara karanta addua a bakina ina tafiya zuwa wurin da kukan abin ke fitowa. Innalillahi wa, inna alaihim raji,un wani mugun halittane a wajen kamar an masa tarko shi bai shigo compound din wurin ba kuma bai tafi tankar kafeshi akayi. Dabba zan kira abin da suna ko dodo gaskiya idan na tsaya fada zan bata lokaci haka yake kamar kosassan karya amma yafi karya girma da abu najen kasa kamar nono a jere har kasa. Bindin shi kawai yakai kaurin wani katon kare fuskan shi kamar hallitan alade amma a sabule zakace tsokane kawai baida fata ya wani irin walkiya na tashin hankali. Mutum biyun da sukai karfin halin biyoni a baya sukai saurin juyawa da sauri acikin tashin hankali sukuma sauran na ganin su suka arta cikin compound din a guje har wasu na ihu. Kowa yace a zamanin nan ba dodo ya tubawa Allah don har gobe akwai sauran halittan boye da Aljannu masu rikida su koma irin don tsafi. Daga inda nake na fara fadin kayi ko kiyi gagawan komawa gun wanda ya turo ka daga yau kada ka kara dawowa aike a cikin garin nan har abada. Kamar mai jiran a bashi umurni ya fara tafiya yana wani irin kugi da numfashi ya nausa yayi yamma ya bace a cikin duhun dare. Saida suka kai basu ganni bane wasun su suka juyo dan dubani din a hanya muka gamu dasu ashe sauran makwabtan unguwar tamu duk suna tsatsaye cikin tashin hankali. Washe gari kan ace kwabo labari ya karade ko ina a cikin gari ga wanda Allah ya nufa ya ji wanan labarin . Kowa da fassaran abinda yake fada wasu suce ai dodo aka gani wasu kuma suce masu maita ko tsafine da suke rikida suka zama hakan suka fito yawon dare. Rana ta baci masa ua kafe a wurin nikan tunda ba a fita office weekend ne barci nayi sosai ranan abina. Sai daya na mike nayi wanka tare da alwala nayi sallah umma ne ta lekoni ina addua take fadin in fito naci abinci saidana shafa na saka kaya na fito daga dakin. Na zauna na zuba abinci na fara ci ke nan mukaji anyi nocking din kofan gidan Amar ne ya amsa yake fadin waye yana bude kofan. Ganin mai nocking din yasashi dan sake murmushi yana fadin wellcome broda tare da dan rusunawa kadan ya shigo da sallama rike da hannun Amar din ciki yana gaida umma. Ta amsa mai da dan fara, a tare da tambayan shi iyalinshi ya amsa cikin jin dadin hakan kafin na dago ina gaidashi ya amsa min. Ya su mommy da yara shima din ya amsa da lafiya kalau yana juyawa wurin Amar tare da tambayan shi ya yake yana zuwa makaranta ko ? Ya amsa da eh mun fara zuwa a nan har an fara muna test kuma naci dukka, gaban shine ya fadi don kama da Amar a yanzu yayi da mahaifin mu sosai don duk zuwan da yakeyi wurin mu bai taba ganin wanan kamar namu da mahaifin mu ba irin yau. Don gaskiya duk wanda yasan Abbah mu yasan duk muna kama da Abbah mu sosai saidai shida yake namijine yafi kama da Abbah din sosai. Umma yanzu nake karantawa cewa wai jiya an samu dan matsala a wanan unguwar wani abin firgita ya ziyarci shiyan nan da fatan wanan matsalan bai shafeku ba dai. Bai shafemu ba kuma bana zaton akwai wanda ya shafa a cikin wurin nan Allah ya kare kowa dake cikin nan wurin dama wasu makwabtan unguwar nan. Saidai hakan ba karamin daga muna hankali yayi ba don gaba daya jinyan ba wanda yai barci da dadi saboda tashin hankali. Idan wurin nan babu security daya dace gaskiya ya kamata a canza maku wuri kada sani abu yazo ya sameku a nan din. Daga inda nake zaunen na sake kallo shi naji yaci gaba da fadin ina tsaron kada wani abu ya sameku ne umma don garin nan baida kyau yanzu kaduna ba kamar da can bane. Ba abinda zai faru da yardan Allah don akwai hadin kai sosai a cikin wurin nan kada ka damu da hakan. Kafin tace dashi wai da gaske ne zancen auren yar uwarka ko shirmen Faizace kawai irin da sukeyi ? Kwarai mama zasu aurar da ita ga dan gidan uncle gyade yayan mommy, yaya gyade dai gyade dana sani zasu ba yarinya karama kamar wanan din. Allah ya kyauta amma shi Alh ina nufin yaya mahaifin ku yasan wa yan nan mutanen kuma ya yarda ayi wanan hadin ?. Eh yace min uwar ce ta nuna ita dai tunda yarta naso abashi ita har hakan yaso saka rikici a tsakanin su da farko. Fuskana da hannayena ne kawai a wayan da nake tabawa din lokacin amma hankalina yana wurin zancen da sukeyi Waye wanda zata aura ke nan don ba gama sanin yan uwan namu dama nayi ba tunda a boye muke a cikin su lokacin kamar mujiya. Sahiba aikin ku na tafiya kamar yadda ya dace dai ba matsala ko sai lokacin na dago daga inda nake saman kujera a gaban dinning din na dan kallo shi ina murmushi nace. Ba matsala saidai halin mutane ne sai an fito masu a inda basu zata ba don basu da niyar bamu hadin kai muyi aikin daya kawo mu. Kenan sai kun hadasu da hukuma ko wani abu makamancin hakan zasu dauki abin serious sosai haka nake tunanen yi a karshe . Baida matsala tun farko na fada maki ai idan da abinda zan taimaka maku dashi dai ki nemeni na danyi murmushi ina fadin lokacine baiyi ba na neman ku idan yayi zamu neme ka mun gode. Nidai ban yarda na fadi komai ba cikin zancen su don sai naga zancen manya ne bai shafeni ba ai. Mikewa tsaye ya don tafiya bayan ya dan duba agogon sau barkatai umma tayi maigodiya da kulawan shi a kan mu ya fice daga gidan har saida ya tayar da motan shi na sauke ajiyan zuciya a hankali. Bayan tafiyan shi zancen su da umma ne na auren baby ya tsaya min a raina akan me za ayiwa baby aure ga su anty Nabila da anty hauwa a gida. Amma sai baby din ce zatayi aure toshi wanda zata aura din waye shi waye mahaifin ta kuma danaji suna magana akan shi. Shi kawai nake son sani dan haka naji kawai duk yadda za ayi zan halarci wanan bukin da zasuyi a gidan su saidai ta yaya zan tunkare su gida. ZAINAB IDRIS MAKAWA ANA DARA GA , , , , , , , , 6️⃣2️⃣BY, , , , , , , , , , , , ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , , , , , , , , BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AL BA,ITH , , , , , , , , , ONLINE PAID NOVEL YAR UWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA BA TARE DA HAKKIN KOWA BA DON BIYA KI TURA DARI BIYAR 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK 08036959257 ALLAH SARKI AI RAINA BAYA BACI YANZU DON KIN FITAR DON NASAN AKWAI RANAN HADUWA SEE U👋👋👋👋 Zaune nake da tulin takardu a gabana ina aiki yayin da hankalina ke kan Laptop dina ina ina tura sako a cikin sa muryan oga Balane a office din yashigo a gagauce yana fadin anzo za a ganmu a lokacin. Ban dago kai na kalle shi ba sai aikin da nake faman yi haka sauran duk wanda ya dago ya samu ina aiki sai ya duka yaci gaba da abinda yakeyi kada ya samu kuskure a cikin aikin sa. Ya sake fadin Alh da muke hurda dasune a wanan company sukazo su ganku ayi maslaha a tsakanin mu dasu don sun samu labarin hakan. Ka fada masu cewa ba kawo kansu ba a yanzu idan lokacin hakan yayi ai zamu gaiyaci mai hannu a cikin harkan nan yanzu muna tattara bayanai ne shine aikin mu. Wanin kallo yayi min na banza kafin yai kwafa ya fita yana fadin yarinya baki san wuta ba sai kin dafa an gaya mamaki su Alh wasa ne komu don dole muke biye dasu ai. Daga waje ina jin yadda suke surfa min zagi na ashar da cin mutunci murmushi na sake a fuskana ina godewa Allah a kullun. Ita wacece waye ubanta a cikin kasan nan da za mu tako har nan tace bata shirya ganin mu ba a yau sai lokacin hakan yayi zata ganmu. Bello dake jin hausa da sauran biyun suka dago kansu suna kallona don sun san danaji irin zagin da Alhazawan ke min dole zan tanka masu. Don ago bala da zai fita yabar kofan a bude yadda zamu iya jin komai da ake fadi a wajen hakama suma zasu iya hango wasun mu daga cikin wurin. Mikewa nayi kawai na nufi kofan kai tsaye su hudu ne manyan mutane saye da manyan riguna a jikin su dukkan su. Daga bayan su sukaji muryana a daidai lokacin da oga Bala ya shake murya yana kara zugasu suko suna hawa ga mutane sun taro dan nisa kadan kowa na kallon ikon Allah. Niyar ubanace da aka haifa a hanyar halas kamar ko wani dan suna na kwarai lokaci daya dukkan su suka juyo suna kallon inda nake tsaye ina fitowa daga office din. Kallon mamaki kowan su ke mun don a cikin hausa nake magana gani saye a cikin suit kai da hulla daya boye gashin kaina a lokacin zakace no din wata kabilace da ban taba jin ko zo in kashe ka ba da harshen hausa. Ba zamu ganku ba yau din nan don bamu tsara hakan daku zamu zauna daku ba sai idan bukatan hakan ya taso a garemu don haka idan kunga zaku iya tafiya sai ku tafi. Dukkan su hudun kallon mamaki suke min na karanta da ganina na cewa nanjin hausa gashi inayi naku kama da ruwan fulani don da ka gani kasan yar wani nake a cikin kasan nan na hausawa. Juyawa nayi na shiga office din na zauna naci gaba da aikin da nakeyi saidai banjin zan iya karasawa don yadda zuciyana yake hasala. Daka zagan min uwa ko uba gara kayi ta zagina sau ba adadi zan iya hakkuri da hakan amma idan ka tabo min iyayye yanzune zaka jini. Ai kafin mu fito labari ya gama karade ko ina na ckkin company cewa ashe yarinyar nan tana jin hausa kamar jakar kano don yau ta wanke su oga bala dasu Alh Buhari sosai. Ni dai mun fito naga ido yayo kan mu caaa don inda sabo mun saba da hakan ai don sun nuna muna tsarguwa da kyaman kasancewa dasu wurin a filin Allah. Figil figil nake tafe a cikin saurina da yar jakat laptop dina sai dan wayana dana riko a hannu na mun nufi wurin da motan Adnan yake don shi ya dauko mu har yemisi zuwa aiki yau. Saiga manaja ya biyoni da sauri shida oga Bala a baya da waya duk mukaja muka tsaya lokaci guda muna kallon shi. Yake fadin madam na dole badon yaso ba ga waya don Allah ki karba Alh ne ke son magana dake a wayan kallon wayan nayi kafin sauran abokan aikin nawa su kalleni. Waitin concer me with him bada wani hadi da kowa a garin nan na fada mashi kuma nasan na cikin wayan yana jin mu a lokacin da nake zancen. Alh kaji abinda ta fada ai yace yi kokari ka bata wayan yanzun nan kada ka bari ta daga baka bata ba don jin hakan yasa nakai hannu na karbi wayan tare da fadin . Assalamu Alaikum, ba oga bala ba duk wanda ke wurin saida ya kadu lokacin don nuna alaman ni din musulmace ashe ? Kada kadamu Alh ka dai kara shiri don zamu hadu da yardan ubangiji dakai lokacin hakan baiyi ba a yanzu sai anjima na mika mai wayan shi. Figil na wuce shi na bude gaban motan na shiga na zauna tare da gyarawa naja kofan na rufe zuwa lokacin idanuwana suna canza kalla badon komai ba sai jin muryan wanda nafi tsana a cikin duniyan nan. Wanan wani sabon masifane haka ke shirin faruwane yarinya karama nason tayi muna yawo da hankali haka a cikin garin mu. Naga ko lagos indai akace harka damune suna tsoron hakan amma wata banzan yarinya can yar isk, , , , tarine ya sarke Alh a lokacin bai samu kai karshen maganan shi ba da zai fada. Sai mika hannu yake faman yi wurin goran ruwan dake aje da sauri suka miko mashi goran ruwan ai yana kai bakin shi kamar an kara mai tarinne lokaci guda. Rudewa wa yanda ke falon sukayi sai sannu suke masa yana amsawa da hannu koda kai sai da kyat ya lafa mai ya koma yabi kujera yana mayar da numfashi guda guda ga wani irin zufa yana karyo masa a goshin sa. Ganin ya samu sauki yasa su masa sallama suka tafi sai kanin sa Buhari da babban dansa ne suka zauna a tare dashi basu tafi ba lokacin. Sai bayan mintuna ya dago kai ya kalli kanin nasa yana fadin anya Buhari wanan yar bata zo muna da shiri ba kuwa yau nice yarinya karama haka ke fadawa magana haka. Dan nasa ne dake kawar da goran ruwan a gaban shi ya juyo ya kalli uban yana fadin wace yarinya ke nan baba ? Hannu ya daga mai yana fadin sanin hakan bai shafeka ba yanzu Dan hjy zancen sana, an mune yazo da matsala shi mukeyi. Au daka nayi yar harkace take son ta kawo maku matsala ai yanzu nayi yaga yaga da ita cikin garin nan jeka nace uban ya fada wa dan a fusace ya fita badon yaso ba. Kallon kanin shi buhari yayi yana fadin yaron nan ya kawo zance fa a nan buhari kasan ni ba a shiga hurumina a fita baki alaikum sai kasan ka shiga zance na ka raina kanka da kanka wallahi. Yaran nan yan daba zan hada da yarinyar nan su hake mata zata san muna ba a kawo muna zancen banza a zauna lafiya. Eh to gaskiya shawarane maikyau hakan amma kuma ni sai naga gara dai abi zancen nan sannu a kare lafiya ban faye son irin abubuwan nan yanzu sam wallahi. Lokaci yayi garemu da za ace mun daina wasu abubuwa da zasu hanamu kwanciyan kabari lafiya gara dai muji da irin barnan da muka tafka na kurciya a tubawa Allah zaifi. Allah bashin mu samu maslaha dasu idan ma biya su kudaden su zamu a zauna a san ta yadda za a basu kudin su tunda hakkin sune muma mun sani. Kai tir da halinka buhari yanzu wanan dalilin yasa yanzu ban komai dakai wallahi dadin gyade ke nan da badon kafan nan nasa da makiya suka lalataasa shi yaki lafiya gareshi ba wallahi baka ma sanin halin da muke ciki. Wai kai ko ka manta da zancen inna ne da ta tayar damu dashi takan fada muna kowa ya shiga gaban kada mu tausaya masa ko muji kanshi mu buge ko kashewa idan yakama mu kashe din. Kai haba yaya zaka hada lokacin su inna da wanan zamanin da musulunci yayi karfi a ko ina a dai duba zancen don Allah abi sannu. Kallon kanin nasa yayi yana gyada kai yace eh lalai buhari ka nuna min ka shiga izzala yanzu kan ashe ba karya bane da ake fadin kakai yaran ka makaranta masu dagagen wando karatu hakan ko gaskiyane ashe ? To yaya baka ganin komu irin wahalan da mukeyi na rashin karatu da bamuyi ba yanzu zamanin nan fa da ilimin addini dana bokon yake tafiya dashi a rayuwan mutum. Eh to yanzu kan na gane inda ka dosa buhari saidai kada ka manta ba a sakewa tuwo suna a duniyan nan yayi murmushi don gane me yayan nasa ke nufi yace Allah gafurul rahimun ne ai yaya abinda aka aikata a baya ya wuce yaya ? Harda kashe yan uwa da mukayi a tare a baya kana ganin zai yafu a garemu ne ga Allah ya dukar da kanshi kasa jikin shi yai sanyi yayan nasa yaci gaba da fadin ko kana ganin wanan din baifi komai barna a cikin abinda mukeyi ba yo na kashe nawa nahau dukiyan shi waye zan bari a yanzu kuma ? Dago kai kanin nasa yayi yana fadin da ace zanga iyalan Sambo a yanzu zan duka in nemi gafaran su tare da fada masu gaskiya in kuma basu kason da kuka ban a ciki koda kuwa ya kama na mallaka masu dukiyana a baki dayane yanzu in koma banda komai a hannu na. Ido ya kura mai na dan lokaci kafin yace dashi yau daba kai bane buhe da wanine yayi wanan zancen haka a gaba ba abinda zai hana in halakashi a duniyan nan. Sai dai kuma kai dinne saukin abin kuma ina zaka gansu a yanzu mutanen da boka ya fada muna sun dade da mutuwa a hatsarin mota wurin gudun mu ina kuma zaka gansu a yanzu baki nawa ya fada muna hakan cewa sun dade da mutuwa ko. Har itama mairo din yan uwanta a yanzu sun gaji da nemanta dole sunyi hakkuri da hakan ai tunda abinda mukai masu ka manta dako suna raye ba zasu taba waiwayan gidaba ma balle ka gansu a yanzu ? Mikewa yayi yana fadin shi zai tafi amma dan uwan nasa yadai kara dubawa kan wanan shawaran daya kawo a karshe. Bai dago kai ya kalleshi ba kawai yasa kai ya fita sai lokacin ya bishi da harara yaci arzikin uwarsu daya da kuma abinda inna ta fada da zata mutu da ranan yasan koshi waye shima. Dan nasa ya dannawa kira a waya tare da tambayab kana inane yace gani nan zan tafi tudun wada kazo ina son hanin ka ya fadawa dan nasa. Idan mun fita umma takan kunna kira,a ya tayata hira tana bin karatun haka na dawo na sameta ita kadai a gidan . Gaida umma kawai nayi na fada saman kujera tare da dafe goshina da hannuna daya na lumshe idanuna ina tunane. Ganin haka umma ta kira sunana na dago kai na dan kalleta kafin na cire hannun ina kaiwa kwance nace umma yau nayi waya da wanan mutumin . Wani mutumi kenan fa umma ta tambayeni na sake fadin wanan Alh Nuhun wan mahaifin mu a ina kika ganshi ta tambaya cikin mamaki ? Dagowa nayi daga kwancen da nake ina fadin kusan kudin company da muke nema yana a hannun su sun rike haka bincikena ya nuna min. Saidai ban yarda munyi magana dashi a yau na fada mai ya jira har lokacin haduwan mu dashi yayi. Haka kikace dashi nace kwarai umma ban shirya haduwan mu dashi a yanzu don haka ba zan tsaya magana dashi ba ko mai zai fada min kuwa. Kibi a sannu don mutanen nan basu da kirki ko kadan sanin koke waye a garesu yanzu zai kara saka masu tsanarki a zukatan su . Da ace tun farko nasan suna cikim zancen nan babu abinda zaisa na yarda ki fara aikin nan mai yawan kasada a rayuwan ki yanzu. Nasan da hakan umma nima saida muka zo din nafara bincikene na gano dasunan shi da wasuma da bamu zata ba a cikin wanan harkan. Allah dai ya shige muna gaba nace amin muka dayi shiru kafin ta dago tana fadin dazun yayan ku yazo ya kawo muna goro da alawan bukin Baby da za ayi. Na dago ina fadin yaushe yazo tace dazun nan bai dade da tafiya ba kuka dawo ya karbi takardan nan dayace zai duba ranan dake waje na. Da sauri na dago kai ina fadin umma ya tafi dashine tace a,a yadai duba ya ban ajiyan zuciya na sauke tare da lumshe idanuwana . Kafin in dago ina fadin umma ban takardan in duba in gani yau din nan ba bata lokaci ta mike ta dauko min ta kawo min. Mikewa nayi dashi zuwa dakina na kwanta na fara karantawa a tsanake ina bin rubutun mahaifin namu da kallo da yadda yake tsara rubutun shi. Da gani basai an fadama mai ilimi bane shi don irin turacin dake cikin takardan lokacin idona lumshe saiga hawaye sun zobo min a hankali nagoge. Bayanin irin rayuwan da yake ganine a cikin yan uwanshi sai bayani kan rayuwan shi har neman gwago hari da hanashin da akayi ita kafin ya dawo ya samu tayi aure. Sai kuma irin ci gaban daya samu da aikin daya fara da CBN tare da business din da yakeyi kafin in budo wani shafi daya rubutawa rayuwa mai kunci da takaici . A wanan shafin kafin na karanta nayi kuka nayi kuka mai tsuma zuciya sosai ni kadai a daki don abinda na karanta a cikin takardan sharfi ne kan irin barazana da matsi daya fara gani daga yan uwan haihuwan shi. Ban fito dakin nan ba saidana karanta wanan kudin sai tsakar dare na fito neman abinda zanciwa cikina lokacin. Babu kowa a falon don dare yayi sosai a lokacin haka yasa nayi amfani da wayan hannuna wurin ganin haske a falon har na samu na debo abincin na dawo na fara ci a cikin duhu. Naci kamar cibi hudu na dagata don motsin dana faraji a haraban namu duk da suna da nisa sosai da inda gidajen mu suke amma hakan bai hanani jin takon suba kuma na gane an shigo wurin namu lokacin. A hankali na taka zuwa inda window falon mu yake numfashina naja sai na zabura kafin a mayar dani na furta wani abinda bansan na furtashi ba lokacin. Na koma na kwanta abincin da banci ba ke nan kuma saida safe don kwanciya nayi dan wani irin barci daya ziryaci idona a lokacin mai nauyi. Kamar a cikin mafalki take jin ihun yar ta dake dakin ta kwance kusa da ita zabura tayi don jin ihun yar natane dai ba wani a lokacin daga ita sai daura gaba a jikin ta tanufi dakin a gigice take lokacin. Tura kofan tayi da karfi a daidai lokacin da sauran mutanen gidan suma suka fito don jin ihun daya karade gidan nasu a lokacin shima kanshi maigidan a rude daga shi sai dan short irin na maza katon cikin sa a waje ya karaso dakin a gigice . Abinda kowa yagani nr yake sasu komawa baya da sauri suna salati ga makwabta a lokacin har sun fara fitowa don ba karamin ihu yarinyar takeyi ba yana bin dare. Innalillahi Alh ya ambata tare da fadin Sanda kanka daya kuwa da hankalin ka kuwa kasan abinda kake kokarin aikawa ga kanawarka a yanzu. Baya cikin hankalin shi don haka bai jin tsawan da mahaifin nasa da sauran yan uwanshi ke masa a lokacin. Ganin zasu tsaya ya illanta mata yarta yasa uwar yin kundunbala ta fada ciki ta fincikoshi da karfi hakan yasa yaranta maza biyu suma suka taimaka mata wurin bambare shi sukaja yar uwansu tare da yaba mata zani da sauri a jikin ta. Aiko binta yayi bayan mahaifiyar nata yana kokatin jawota ala dole sai yakai a jikinta kamar yadda aka umurce shi yaje yayi din. Alh da baisan matakin dauka ba a lokacin nufar dan yayi ya kifa masa mari uku masu kyau rai bace ya fara magana yana fadin. Don ubanka ka shiga hankalinka mana ko nan cikin gidana aka turaka kayi wanan aika aikan da zakazo kana neman hakewa yar uwanka haka ? Jajjayen idanuwan shi da suka rine suka sauya halita don kana ganin shi kasan baya a hayacin shi gabaki daya yayi wani irin gumji ya juya yana kokarin cakumo yar dake makale a jikin uwarta yan uwanta sun masu kariya a lokacin. Kai ranan nan dai ahalin gidan sunga tashin hankali don haka ya koma kamar mahaukaci saida aka ja yar a cikin dubara zuwa wani daki aka boye ta shi kuma maza sukai waje dashi don a samu natsa shi . Alh ne yace a kawoshi falon shi kafin ya shiga wani daki ya debo wani abu da hayaki yana yayyafawa dan nasa dake rike ahannun mutane. Haka gari ya waye kafin kace meye labarin hakan ya fara karade unguwa zuwa cikin gari har aka samu masu kari a zancen suka gyara labarin tare da kwaskwarima don zancen yayi dadin ji da bayarwa. Irin barcin da nayi ranan bana kau sake bane don da kyar na iya tashi nayi sallah kuma na kwanta a wurin sai karfe daya saura na falka na shiga wanka tare da dauro alwala na fito. Tsab na shirya na fito umma tayi mamakin hakan nace zan leka na dawo don ban san irin barcin da nayi ranan ba. Na isa wurin aiki sai bina da kallon akayi niko ko in kula da irin kallon da suke min din kai tsaye na shige inda muke aikin mu. Duk Sunyi mamakin ganina a lokacin niko ko in kula da hakan na zauna na bude laptop dina na fara aiki a cikin sa bayan gaisuwa ban kara magana da kowa ba a wurin sai kai da nake kadawa idan wani yayi min wani tambaya. Aiki nayi sosai a ranan don har kusan biyar na yamma ina cikin ma,aikatan lafin na nade nu,uran na fito zuwa gida. Ko a gidan ma bana magana Abdulhamid umma ta sama take fada mai halinda nake ciki shida matar shi suka biyo umma zuwa gidan. Duk yadda sukaso nayi magana banda bakin hakan karshema na barsu a falon na shige ciki don kallo daya zakaimun kagane ba a cikin hayacina nake ba lokacin. Hankali tashe aka kira Nazifa da sassafe ana sheda mata abinda ke faruwa a gidan kan yan uwanta. Kukata saka a wajen hakan ya jawo hankalin mijin nata dake execise a lokacin ya fito yana tambayan ta abinda ya faru take wanan kukan haka. Kasa fada mashi tayi don bata san me zata fada maiba a lokacin don maganan nada nauyin fada a bakin ta. Daya matsa sai cewa tayi dashi gidan mune ba lafiya wai suna asibiti da safiya da ya umar cikin mamaki ya kara tambayanta da meya samesu haka lokaci guda tace saidai idan naje zanji. Ga mamakinta sai taji yace da ita ki jirani muje tare mu gano su yanzu Allah dai yasa ba wani abu sukaci da yajawo masu kwanciya asibitin ba haka lokaci guda. Ai kuwa dai taren sukaje suka samu yan gidan cirko cirko a haraban asibitin kowa ransa a bace ana ganin su hanlalin kowa ya koma garesu. Bayan sun gaisa dasune yake tambayan su cikin son jin abinda ya samesu din sai kowa yayi shiru yana dukar da kanshi kasa lokaci guda. Da yake yasan kanshi bai matsa masu ba ya wuce zuwa ciki ya kai tsaye don ya tambayi likita abinda ke samun su din ? Saidai baikai ga shiga ba a bayan filawan dake wajen yaji muryan kawun nasa na waya yana fadin wallahi akwai matsala babba Alh ina fada maka. Gaba daya hankalina a tashe yake don wanan abin ana ganin shi karamin magana yana son ya zamo muna babbba a garin nan. Don gaba daya yarinyar nan tana son juya muna hankali tayi muna wasa da hankali wai yaron dana tura ya gama da ita jiya shine ya dawo ga kanwarsa haukace yana neman aika abinda na umurceshi dayaje yai mata a can. Sahiba kawai ya anyana a zuciyar shi lokaci guda haka yasa ya juya bai shiga ba don ya gama jin komai a inda ya dace yaji gaskiyan maganan. Sai waya ya bugawa matar cewa shi ya tafi idan ta gama ta dawo gida ya barta can ita da yaranta gidan ya dawo ya karya kafin ya fice a gidan zuwa gidan su. A can ma labarin komai ya riski mommy ya samu tana waya don haka ya zauna kamar baisan akan me take wayan ba. Saida ta gamane ta juyo tana fadin daga gida kake halan ta dan bata fuska kafin yace eh daga can nake. Ka ji abinda ke faruwa ke nan ko yace namefa mommy tace zanceb gidan yaya Nuhu mana da basu gajiya da sake muna abin kunya a gida ko yaushe ? Naji mommy don naje can din nida Nazifa saidai na fahinci reshene ya juye da mujiya ga zancen shine dalilin dawowana na barta can. Me kake nufi da wanan zancen yace eh mommy don abindaka shuka shine zaka girba dan haka ANA DARA NE YA FARU DASU, , , , , ZAINAB IDRIS MAKAWA ANA DARA GA , , , , , , , , 6️⃣3️⃣BY, , , , , , , , , , , , ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , , , , , , , , BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM ASH SHAHEED, , , , , , , , , , ONLINE PAID NOVEL YAR UWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA BA TARE DA HAKKIN KOWA BA DON BIYA KI TURA DARI BIYAR 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK 08036959257 ALLAH SARKI AI RAINA BAYA BACI YANZU DON KIN FITAR DON NASAN AKWAI RANAN HADUWA SEE U👋👋👋👋 Wasa wasa hakana kwashe har kwana hudu a zaune ba umm, ba umm,umm agida zaune saidai inta bin mutum da idanu saidai kallo daya zakai min ka fahinci ina cikin bakon yanayi. Hankalin umma ya tashi sosai da hakan dole ta daga waya ta kira ya Abubakar tana sheda mai halin da nake ciki a yan kwanakin. Yaji hankalin shi ya tashi don zaune suke falo lokacin shida Nazifa da yaran su saiga kiran umma ya shigo wayan shi ya dauka da sallama yana gaida umma din. Abinda yasa Nazifa dan juyowa ke nan ta kalleshi don jin mama daya ambata bata gane ko wace mama bace alokacin suke waya da ita. Yadda ya zabura yasata fadin lafiya wacece kuke wayan sai lokacin ya dan saita kanshi yana fadin gani zuwa mama yanzun nan insha Allah . Ido Nazifa ta kura masa har lokacin daya kare wayan nasa idon ta na a kanshi don bata fahinci dawa yake wayan ba. Mikewa yayi a daidai lokacin da yake kokarin saka talalman shi dake gefe yana daukan makulin motan shi daya aje saman table gaban shi don dama yana da niyar fita a lokacin. Wacece ta jefo mai tambaya tana kallon shi a tsorace don sanin cewa yan gidan su na asibiti har lokacin don haka takai zuciyar ta can ko wani abune ya samu yanuwan nata . Mamace ya fada kawai yana kokarin fita daga falon wace mama ke nan fa ta sake tambayan shi kai tsaye yace maman su yusuf da cewa Ammar kanina don yasan ba zata gane ba yana fadin haka ya fice daga gidan ya barta zaune tana maimaita sunan maman yusuf wace maman yusuf kuma ? Sai kuma taja tsoki ai tunda ba yan gidan su bane shike nan ko wace mamace su karata can yanzu kila wani case din shinecan har ya dan ruta da hakan taci gaba da kallonta kamar ba kanwata ciki daya ke kwance asibiti ba a cikin tashin hankali. Tuki yayi na tashi hankali yan mintuna kadan ya sadashi da gidan mu ya fito zuwa ciki misalin karfe biyar na yamma a lokacin. Yana shiga falon dani yai arba a zaune na hakince irin zaman da manyan mutane keyi a da can baya na sarkuna kafafuwana biyu suna lamkwashe a tsakina duk da sama kujera nake zaune. Ummace data fito kitchen rike da plate din dake shake da apple a cikon shi suka hade ta dan saki ajiyan zuciya tana fadin Abubakar har ka karaso ke nan ? Yace eh mama fuskan shi a kaina yake gaisawa da ita kafin yakai zaune yana fuskantana umma ma zama tayi bayan ta aje plate din a gefena tana fadin gata nan wallahi yau kwana hudu ke nan na rasa meke damunta haka ? A lokacin Abdul dayaga shigowan shi shima ya shigo don shi ya ba umma shawaran a fada mashi kada su barni a hakana don har yayi waya da oga Sha,aban yace su mayar dani lagos saidai ta yaya zasu daukeni a haka Abdul ya tambaye shi ? Don hakane shi Abdul din yaga garafa su fadawa yan uwana tunda ina dasu a garin koda shawaran da zasu bayar a kan matsalan nawa don sun fahinci akwai sabon sauyi sosai a cikin lamarin. Idon shi har lokacin yana a kaina koda yake amsa sallaman Abdul din ya shigo ya zauna shima idon shi dai har lokacin yana gareni. Umma taci gaba da fadin mun rasa gane meke damun ta sai bakon yanayin da take muna komai a hakince ko a kwantace zatayi muna magana baki yaki budewa har yanzu. Gaban shine ya fadi ras ras ya fara ambato innalillahi a fili tare da fadin dama nasan wanan aikin zai iya jawowa Sahiba matsala sosai don wallahi shu,uman mutane ne mutanen nan sam banu Allah ga al,amarin su ko kadan. Su dai burin su shine suga sun gina kansu sun halaka mutum ko da gaskiyan shi don nayi bincike na gane wa yanda sukazo aiki a kansu a yanzu. Abdul ne daba hausa yakeji sosai ba yake fadin yanzu meye abin yi ke nan yana tambayan su sai ya gyara zama yana fadin kuma gata da lafiyan ta balle muce aje asibiti ko ? Abdul yace munce zamu tafi tayi muna kashe din hakan tun shekaran jiya ya kara zakudawa yana fadin innalillahi baya ko kitbta idon shi a kaina. Yace gara kubar aikin nan nake gani don yana da hatsari sosai ga yinshi idan ta dan samu sauki sai a koma can lagos din zaifi. Sai a lokacin Allah ya bude min baki a cikin wani irin muryan daba nawa ba kamar na maza na fara fadin a kansu zamu dakata ai basu ida ba basu isa suyi min komai ba don suna tare dani. Shifa sarki ne gaba daya yake zaune haka a kaina sun taba ganin inda sarki yaja baya da yaki hutu kawai suke son nayi su tafi ba abinda zasu iya indai an yarda da Allah da kuma aljanni akwaishi to sune tare dani. Kuka umma ta sake lokacu guda mai ban tausayi tana fadin shike nan yar nan abin nan ya tabbata gaskiya a kanki ina daukan hakan kamar dai baiwane ashe da abubuwa saman kan ki. Baiwane mana shi shifa ba a kowani kazami yake saukaba sai a inda ya dace kuma ya kama yazo da kanshi ai da yaran shine saman kaina amma yaga ya dace shi yazo yanzu da kanshi. Zakace wani babban sarkine a zaune yake magana da isa da izza kafin na juya na dauki apple din har cizawan irin na sarakuna nayi shi na aje a gefena. Falon yayi shiru tsit kafin muryan Abubakar ya amayo yana fadin Abdul ya biyo shi akwai inda zasu tafi wanan ba abin su zura ido bane kawai sai lokacin da sukaga daman sake ni din. Nan suka fita suka barni da umma zaune wacce ta kura min ido na lokaci guda tana mamakin budan bakina a yau din don ko ba komai zuwan Abubakar din ya taimaka mata ai tunda yazu tasan magana na yana nan bai dauke ba. Gidan wani malami suka tafi can cikin kabala sai gasu tare dashi sunzo gidan da yar jakarshi bayan sun gaisa da ummane suka dan fita don yin sallah lokacin magariba ya kawo jiki. Sun dawone lokacin duk munyi don ina sallah na daidai saidai murya a bayyane irin ta maza nakeyi a lokacin saida suka jira na idar malamin ke fadin da sauki lamarin don gashi har tana ibadan ta saidai inaganin kamar namijine a kanta yanzu idan kun lura da yanayin sallahta a yanzu. Dama ya fada muna shi na mijine ai kuma sarki Abubakar ya fada don shi har lokacin mamaki yakeyi a zuciyar shi yadda yaji muryana ya canza a lokaci guda. Jakkar dake gefen shi ya dauko ya ciro kur,anin shi tare da wani turare ya dan yayyayafa a gefen shi ya fara bissilah da sauri na daga hannu ina fadin ba sai kajaba malam. Suratul sulaimana ko barin ja maka ya kalli littafin da nisan dake tsakanin mu ya girgiza kanshi kadan yana fadin kwarai. Amma duk da haka barin dan ja kaji abinda Allah ya fada ya fara jawo ayah uku falon yayi shiru ana sauraren shi ya dago kallon shi nakeyi a natse . Yace tunda kai musulmine muna son jin meya kawoka jikin boyar Allah nan kuke bata wahala haka yace wahala haram muke dai bata hutu a yanzu don ana son cuta matane. Muyi hakane don masu son cutawan su dauka ko sunyi nasara a kantane malam yace na,am amma ai koda baku shiga jikinta ba zaku iya taimaka mata din. Yace malam ba yau muke tare da ita ba tun ranan da aka haifeta muke tare da ita don haka idan zamu cuta matane da mun cuta mata tun lokacin. Mahaifiyar ta bata da ganewa data gane tun a lokacin irin kukan da takeyi tana karama wanda hakan alamane wani abu zai faru dasu ai. Ko ranan da aka kashe mahaifinta ya kasance watan azumine bamu aiwatar da komai a watan ibada saidai duk da hakan mun nuna mata alama saidai bata gane hakan ba. Lokacin magariba a lokacin da ko wani mugu yake samun sa,anshi ke nan ya aiwatar da nufin shi a kan wani ko ya aika da sheri akn abin nufin shi. Mun saka tayi ta kuka sosai har dare amma sam basu bar gidan basu kuma gane akwai kulli tafe a kansu ba sunyi nasaran hakane don irin sharadin bokan su ya basu a kan lalai su tun kareshi a wanan ranan . Sauran basuje da niyar a kashe shi ba saidai a turasasashi a kan dukiyan daya tsone masu ido wanda suke ganin bashi ya dace ya mallaki wanan dukiyan ba a cikin su. Malam yace umm,umm yana kada kai nan dai ya basu labarin komai tiryan tiryan sai lokacin da suka fara baiyana a kaina ya kare da fadin cewa yanzu duk wanda yace zai tunkareni a kwai aiki a gaban shi sosai. Har yanzu da Nuhu ya turo danshi yazo ya illanta rayuwan Sahiba din da suka mayarda aniyar hakan a kanshi shine mafarin baiyanan su a yanzu don Nuhu shu,umine sun zauna a jikinane koda yayi aikima ba zai gane koni wacece ba a yanzu. Dama nasan da hakan ya Abubakar ya fada don ni naji da kaina yana waya nayi kuma tunanen hakan tun lokacin kai kuma a kwai aiki Abubakar din a gabanka ya nunashi da yatsa ya nuna kanshi yana fadin shi shikan ai bai tare da wani aiki a yanzu mai yawa. Dan murmushi na sake yace abinda kake nema nasu yana karkashin kulawan mahaifin kane don da hannun shi akai komai. Wani irin zabura ya Abubakar din yayi lokaci guda yace kwarai kuwa amma idan na fada maka zaka yarda ka je office din su na tsohon ajiya bayan bakar kanta can kasa layi na uku daga barin hagun ka idon ka zai sauka a wani tsohon jan file zaka samu duk abinda kake nema kake wanan wahalan haka. Yace ya gode ba don ya yarda da hakan ba har kasan zuciyarshi ya dauki abin shirmene shi amma a fili ya amsa da to kawai. Don yana ganin mahaufin shi ba zai taba wanan badalan ba shida ke kawowa mutum ayah kan komai da mutum zaiyi zai sa hannu ga wanan aika aikan haka amma zai gwada don ya tabbatar da gaskiyan lamarin. Sun dauki lokaci a tare dashi gaba dayan su ya fadawa kowan su matsalan shi wurin ita umma akan yan uwanta akai mata magana kan lalai tayi gagawan zuwa garesu tun lokaci bai kure mata ba sai Abdulhamid shi kuma an fada maicewa yan uwanshi sun masa abinda kada yayi arziki don suma basu tara ba sai don haka idan yana son kanshi da arziki ya daina nuwa ko matarshi yana da budi ko wasu abu suna shigo mashi a lokacin. Malam akace yayi gagawan komawa akwai mara lafiyan da suka zo daga nisa dake son taimakon shi duk da sun san ba zai iyaba amma ya nemo wani suka fada mai inda zai sameshi wai shine keda makarin ciwon maralafiyan dake jiran shi dain agida lokacin. AKarshe yayi masu alkawarin cewa zai fita bada dadewa ba in Allah ya yarda hutu kawai suke ba godiyan su a yanzu. Abu wasa wasa har suka kai goma da rabi a gidan mu ana abu guda zuwa lokacin an kira malam yakai sau biyar wai yazo yayi baki daga katsina. Haka dai sukaiwa umma sallama suka tafi kowan su cike da mamaki abubuwan daya wakana a wurin a mota malamin ke fadin lalai akwai manyan abubuwa masu karfin gaske akan yarinyat nan . Nisawa yayi daga inda yake tukin motan din shi tunanen zancen mahaufin shine ya tsaya mashi a rai da baisom ya gaskanta hakan kada ya zamo gaskiya da wani ido zai dubi wa yan nan mutanen idan hakan ya zamo gaskiya. Bayan ya sauke malam sunyi sallama ya kawo abinda zai bashi ya bashine ya tafi ya samu sunyi barci a falo ya rufe gidan ya tayar dasu haka ya kwana yana tunanen maganan aljanin har yana jan tsuki. Washegari bayan sallah asuba ya koma ya kwanta don barcin dake idon shi bai falka ba sai bayan tara yayi wanka yana shiryawane umma ta kirashi a waya a daidai lokacin nazifa zata shigo dakin taji yana fadin yaya jikin nata mama da sauki dai ko ? Bataji me aka fada ba hakan ya tsaya yana sauraren umma dake fada mai yanayin jikin nawa a lokacin yana fadin masha Allah zai shigo anjima idan ya fito. Sunyi sallama da umma din ya juya yaci gaba da shirin shi jin batayi magana ba yasa shima bai juyo gareta ba tunda bata iya gaidashi da kwana kullun yana mata fadan hakan. Wai wata mamace kake wanan wayan da ita tun jiya hakane ta tambayeshi tana mai tsureshi da idanu ya juyo a cikon mamaki yana kallon ta tare da tambayanta wata mamace ? Ina ruwan ki da sanin ko wata mace ko banda ikon waya da kowa sai kin san wanda nake waya dashi kiji da abinda ke gaban ki kafin ki shiga hurumin wani. Wani kallo tayi mai tana fadin bangane wanan na kamar ya naji da abinda ke gabana meye a gabana din ta sake tambayan shi. Wani kallo yayi mata tare da fadin ohh ke yanzu halinda yan uwanki ke ciki duk garin nan ya dauki zance ba abin damuwa bane a gareki ko ? Koda yake banyin mamaki don banga shitin hakan a gareki ba dama ko kadan yaja tsuki kuka ta fashe dashi tana fadib dama shike nan kuma da abin ya shafa kai min gorin hakan balle wani na waje. Wanan muma ke kika daukeshi a gori tunda suke asibitin nan kin dafa abinci kin kai masu ko ki sai wani abu akai masu daga tambayan dawa kake waya zaka fada min wanan maganan haka. Ina ruwan ki da wace nake waya kije duk abinda zuciyarki ya naki shine din ya fada ya dauki hular shi daya dora saman gado yakafa a kai tare da daukan agogon shi ya daura a hannun shi yana nufar hanyar fita daga dakin. Itama mikewa tayi tabi bayan shi tana fadin wallahi idan ma da watace kake waya in fada ma kayi kadan wallahi kace zaka kara min kishiya a yanzu. Jin hakan yasa ya tsaya a kofan yana kallonta a cikin mamaki yace haka zuciyar ki ya baki dama to haka din ne don kin canka a daidai ya fice daga gidan ga baki daya. Gidan su ya nufa har lokacin yana jin rashi a bace yake mai sun gaisa da mommy yake tambayanta mahaifin shi tace da safen nan yayi tafiya zuwa ghana daurin auren yar abokin shi. Ok kawai yace yayi shiru kafin ya kara fadin yaushe zai dawo ke nan tace zuwa jibi nasan don bukin baby ya kawo jiki yanzu ina zai tsaya can kuma. Hakane ya fada yana mikewa tare da fadin shi zai tafi sukai sallaman da mommy din ya kawo falon sune yaji muryan Faiza na fadin yaya na daina samun sahiba a waya kwanan nan. Wallahi naso tazo wurin bukin nan ko zan ganta inga yadda ta koma yanzu wallahi yaya naso ace zata zo din. Murmushi yayi daga inda yake tsaye yana fadin kinsan lagos akwai nisa da nan din kuma aiki takeyi kin sani yanzu. Kamar wani buki can ta damu mutane Allah yasa sahiba tazo idan sahiban tazo ma waya damu da zuwan ta kin damu mutane. Ban daiyi dake ba idan ma kowa bai damu da itaba nina damu da ita hakama nasan akwai wa yanda suka damu tazo don nan bayan ni. Ba wani buki bane bukin yar uwan naki Nabila kadafa ki manta baby yar uwar haihuwan kice look ban son inji ko inga wani abu ya fito daga wurin ku har a kare bukin nan ya nunasu da yatsa duka ukun cikin daure fuskanshi garesu. Ba zakaji ba brother insha Allahu hauwa ta fada daga inda take zaune cikon ko in kula da zancen da sukeyi mai tun shigowan shi. Mommy ne tafito daga dakin tana tambayan meya faru kowan su yayi shiru na dan lokaci saishi ne yace na fada masu kada naji wani tashin hankaki daga wurinsu kan lamarin bukin nan da za ayi. Mommy takai zaune tana fadin me zaikai bakin yaro a ciki iyaka dai ayi a watse lafiya shike nan bukin da ajirace ake damu mu tanka a sauke muna abinda akeson fadamuna dama me zai kaisu fitina nadai fada masu gaskiya ai. Nima abindana fada masu ke nan yanzu ya fada yana kallon mahaifiyar nasa kafin yai mata sallama ya nufi inda yake son zuwa kai tsaye tsohon office din ya nufa. Bayan ya nemu izzinin shiga an bashi don sanin koshi waye a wurin su din kwatancen da akai mashine yabi zuwa wurin kantan komai bai mantaba yadda aka fada har yakai daidai wurin files din . Idon shine ya sauka saman jan file din na kasa ya jawoshi yana kakabe kuran da takardan kedashi yaga an rubuta murder case da kwanan wata da komai a cikin sa. ZAINAB IDRIS MAKAWA ANA DARA GA , , , , , , , , 6️⃣4️⃣ BY, , , , , , , , , , , , ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , , , , , , , , BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AL HAKKUM, , , , , , , , , , ONLINE PAID NOVEL YAR UWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA BA TARE DA HAKKIN KOWA BA DON BIYA KI TURA DARI BIYAR 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK 08036959257 ALLAH SARKI AI RAINA BAYA BACI YANZU DON KIN FITAR DON NASAN AKWAI RANAN HADUWA SEE U👋👋👋👋 Ranan kan na samu barci sosai yadda na fara hakama saukan shi yazo min don saidana shaki barci kusan wuni daya ina abu daya sai yamma na tashi. Gidan ne yayi min shiru na mike zaune ina duban wayana da ban gani ba a gefena dana san ina ajewa din a hankali na fito zuwa falon sai dai banji motsin umma ba a falon na bude labulen dakin ta a nan ma bata cikin dakin lokacin. Haka yasa na nufi kofan gidan namu na bude dagani sai dogon wando light brow da riganshi kala daya kaina a hargitse duk da na daure shi da ribon ta baya. Ummace a tsaye tare da Abdul suna magana jin budan kofa yasa su juyowa suka kallo inda a cikin mama umma ina wayata na fada. A cikin dan tsorata da i,iniya take fadin wayan wayaki na wuri a dakina na saka maki chagi jin hakan yasa na juya na barsu tsaye suna mamaki. Ba komai sukewa mamaki sai tun farkon faruwan ciwona na umurci da adauke wayan a kusa dani bana son ganin ta yasa umma ta boye wayan a wurin ta duk tsawon kwanakin tana kuma saka caji a cikin ta. Dakin nata na shiga na dauko wayan dake saman filon ta nafito zuwa falo ban zauna ba na nufi kofan sai gasu sun shigo nace umma yunwa nake ji sosai a cikina. Kallon inda Abdul yake tsaye shima din ni yake kallo a cikin mamaki wai yau nice ke tambayan abinci da bakina wace kwana da kwanaki bana cikin komai sai diyan icce a cikina. Da sauri umma tace abinci bari a dauko maki abinci kici ta wuce zuwa kitchen da sauri ta hado abinci ta kawo min. Sune zaune sun zuba min ido har na kusa tashi da leda daya na sakwara da miyan yauki dsyaji nama manyan yanka a cikin sa. Saida ya saura kadan na dauki goran ruwa na kwankwade shi saura kadan shima na aje tare da lumshe ido sai lokacin ne na tuna da suna tsaye a kaina dan murmushi na sake a cikon kunya kafin kuma na mike zuwa dakina da sauri fitsari nayi sosai a lokacin naga ai gara na watsa ruwa naji dadin jikina a lokacin. Wanka nayi na dauro alwala kodana shirya na fito nasamu Abdul baya gidan sai umma zaune a falo tana ganina tayi min sannu na amsa Ammar dake kwance shima ya dago yana gaidani. Wai umma wani abu ya farune halan ina barci kadin umma ta girgiza min kai tana fadin ba komai Ammar ya dago yana fadin . Baki da lafiyane fa almost one week ke nan yau ni na tambaye shi da sauri sai umma ta mika mai dakuwa da hannu tana zagin shi. Maida kaina nayi jikin kujera ya dan lumshe idona ina tunane saidai na kasa tuna komai a lokacin yadda ya dace in tuna din. Ammar dauko min laptop dina a daki na fada don sam bana jin karfin jikina ko kadan ya mike da sauri ya dauko min tana da full charge don haka na fara duba abinda nake son dubawa. Date din ranan na duba da sauri na dago kaina don ya nuna min rabona da yin aiki ga lokacin kafin in magana muniya ta shigo dauke da cool abinci tana ganina ta washe bakin jin dadin ganina zaune ina aiki. Ta shigo da murnan ta tana fadin oh mun godewa Allah sahiba kin tashi ogana yayi kuka sosai kan rashin lafiyan nan naki ranan shida Adnan a gidan mu. Barin aikin nayi na dago kai ina kallon ta cikin mamakin jin abinda ta fada sai kuma na juya na kalli umma na dukar da kaina. Daga inda yake tsaye yaga yana neman faduwa kasa a lokacin hakan yasa yakai kasa zaune saman dandaman wurin tun baiyi nisa ga karanta abinda ke cikin ba ya fara cin karo da tashi hankali. Tsab ya gama karanta komai yanayi yana share gumin dayake tartso mashi saman goshin shi da hannu daya kafin ya mayar da file din ya daure kamar yadda ya sameshi a wurin saidai wanan karon bai bar file din haka yadda ya sameshi ba a wurin saida yayi itin nasa dabaran ya musaya komai ya canza wurin sallon ajiyan. Ya fito ana sara mashi sanin koshi waye a wurin daga nan yayi sallama dasu yafito ya shiga motar shi yabar wurin hankaki tashe Allah ne ya gyara ya isa lafiya don baya ko ganin hanya da kyau a lokacin, Haka ya shiga gidan suna falo a zaune don uinin ranan bata leks asibiti taga yan uwanta ba acewan ta tagaji da zuwa mutane suna nunata. Don haka tayi fushi ta daina zuwa da rana a cewab saida dare zata dinga lekasu da niyar yau tayi masu dafuwa taje dashi ko don gorin da akai mata a safiyan yau din. Saiga mijin nata ya shigo a yanayin data ganshi ta fahinci ba lafiya gareshi amma hakan baisa ta tashi ta bi bayan shi taji meke damun shi a lokacin. Sanyine ya rufeshi lokaci guda jikin shi har yana karkadawa don tashin hankalin daya tsunci kanshi a ciki ranan. Yana kwamce shi kadai a dakin sai rawan sanyi yakeyi shi daya yana kuma faman tunane abinda ke karasa hauhawan zazzabin jikin nasa yake kara karuwa a lokacin. Lalai duniya baki da tabas don mutum gaskiya ba abin yarda bane ashe ko kadan a zamanin nan koda kuwa kun fito tsatso daya dashi kada kayi saurin aminta dashi kai tsaye sai ka fahinci shi waye a zuciyar shi. Idon ya kara rintsewa lokaci guda yana maijin wani irun zafi a zuciyan shi bayan na jikin shi dake fita a lokacin. Ba ita tashiga dakin ba sai bayab isha,i data fito wai zata asibiti a lokacinne ta sameshi a dakin ya rufe ruf a cikin wani yanayi na tashin hankali. Amanatace ta raya hakan a zuciyar ta kafin ta kirashi tare da fadin zan tafi asibiti na dubosu dakyat ya iya budan baki yana fadin. Don Allah kashe min Ac din nan gaba daya ta wani kalleshi shekeke kafin tace tou fa a cikin wani yanayi ta nufi wuri makunnin wutan ta rage Ac din har ya rufe jikin shi ya kuma bude a daidai lokacin da take fadin na tafi yaran suna gun mai,aiki idan kafito ba tare da nuna damuwa da halin da yake ciki ba a lokacin. Dan miko min ruwa mara sanyi ya fada a wahalce nan ma saida ta dan kalleshi kamar zatayi magana sai kuma ta wuce tana fadin kada dare fa yayi min ban fita ba. Takawo ruwan saman table ta dangware mai tun bai dago ya kara fadin wani abu ba ya tsayar da ita don haka ta fice a gidan kai tsaye. Acan asibitin ma samun mahaifiyar ta tayi ta cika da ita tana jiran zuwan ta don rashin jinta da kuma rashin kirasu su san halin da take ciki kamar ba yar uwan haihuwanta matsala irin haka ya sama ba a lokacin. Idan sauran yan uwan nata sun nuna ko in kula suna goyon bayan dan uwansu itafa da suka fito ciki daya da yar uwan nata. Iein fadan da uwar ta dingayi ke nan lokacin tana zaune tana taunan cingan tare da duban wayan ta jin uwar tayi shiru ta karasa da Allah dai ya sauwa irun wanan abin haka kamar masu bakin uwa aka. Mama konazo din da haka mutane zasu dinga gulma suna nunani ni kuma haushin hakan nake ji wallahi. Kuka kanwar dake saman gado ta sake lokaci guda don jin zafin abinda yar nata tafada a lokacin ita ke nan taji kunya a nunata a matsayin yar uwanta inaga ita kanta ke nan. Kiyi hakkuri Allah zai kwato maki hakkin insha Allah in suna ganin kamar kece kika gaiyatoshi zuwa wurin ki kamar yadda suka juye zancen a yanzu gaba dayan su. Bata kai wani lokaci ba don tagaji dajin irin wanan zancen dake kara mata takaici a zuciyarta ta mike tana fadin tau mama zan tafi nabar yara a gida da mai aikina. Cikin makoshi uwar ta furta Allah bamu alheri tafice suka bita da kallo alokacine kuma uwar tasake kukan takaici haka yayi daidai da shigowan yayanta maza suke tambaya. Lafiya mama wani abune ya faru kuma tace ba komai sai kanwar tasuce ke fada masu abinda yayan nasu tazo tace a wurin. Saida ya falkane yaga goran ruwan data aje masa a wurin duk yadda yaso tashi ya dauko jikin sa yayi masa nauyi ya kasa tashi a lokacin haka ya mayar da barcin a wahalce sai cikin dare ya tashi daya dan lafamai ya samu rama sallolin dake kanshi dabai samu yiba. Anan kuma ya zauna yasha tunane akan abinda ke addaban shi a lokacin ya dade yana rokon Allah da neman yafiya daga Allah kafin ya samu ya rarafa ya hau saman gadon ya koma kwance ringingine yana faman sakawa da kwancewa. A haka gari ya waye masa baikai ga mafita ba da kyat ya iya samu yayi sallah ya koma ya kwanta yana jin zazzabin na neman ya dawo mai a lokacin. Washe gari yakama asarbar ne don haka babu zancen fita aiki a wurina hakan ya ban daman samun gyaran gidan mu duk daba wani dattin dake cikin sa amma na daure na gyara don jikina ya kara sake min. Ammar ne yake labarta min abubuwan da suka faru dani da yadda na kasance ba magana wani iri naji a zuciyana take hawaye ya fara silalowa daga idanuwana. Sai tunane nake menayi suka zaune akaina duk yawan mu sai nice nake da wanan laluran mai matsala da batarwa a cikin yan uwa. Muryan ummace data fito daga bandaki take fadi to mai surutun tsiya watau dana hana ka fada saidai ka faki idona ka fada mata komai tana kokarin kai mashi rankwashe a kai nace umma don Allah ki barshi. Idan bai fada min ba waye zai fada min umma shi kadai nake dashi a yanzu shinake gani yake ganina a matsayin dan uwa na shikiki a gareni umma. Dole duk abinda ya shafeni ya shafeshi shima umma kada ki hukantashi kan abinda ya dace yayi yayi din kuma zaki hukuntashi kan hakan. Zama umma ta koma tayi tana ajiyan zuciya tare da fadin ban hana ya fada maki ba amma zai bari ai sai kin karasa murmurewa nan gaba sai ya fada maki haka akeyi. Yaushe ne bukin baby umma na tambaya don in kawar da zancen ta dan sake ajiyan zuciya tace inaga wani satine ko shine bukin ko baifi dai kwana goma ba yanzu abinda ya rage. Ok nace na gyara zamana da kyau zamu tafine amar ya tambayeni daga inda yake zaune nace ina ganin hakan zamu tafi insha Allah. Naga ya dan sake murmushi a fuskan shi don jin dadi abinda na fada kafin na juyo ina fadin amma akai sai ranan daurin aure zaka tafi da yaya Abubakar ko ? Wayan dana kirane aka dauka na fara magana kan ina son a turo min da kayan da nake bukata na dauki lokaci muna wayan kafin na kashe wayan . Shiru babu ya Abubakar gidan mu har weekend din ya kare muka koma aiki ummace ma dai naji tayi maganan shi har sau biyu na rashin zuwan shi din saida dare muna cin abinci ranan monday ya kira waya yana shedawa umma rasgin lafiyan shi. A nan muka karbi wayan duk muka jajanta mai tare da fatan Allah ya bashi lafiya ya amsa da amin. A wurin aiki kuma an fadawa mutane tafiya nayi yasa basu ganni ba sai suke zaton na dawone a lokacin suke min sannu da zuwa ina karbawa. Muna tsaka da aiki kwatsam ba zato ba tsamani ranan tuesday saiga Ogan mu gaba daya ya ziyarce mu shidasu oga jimo. Ba wanda keda masaniyar zuwanshi a ranan sai ganin su mukayi sunzo kwatsan mun dan zauna dasu anyi bayanin da korafe korafe kafin su fito don gaba zasu tafi zai tafi kasan Niger republic shine ya tsaya yaga jikina don an masa bayanin komai daya faru dani a takaice. Bayan mun fito ne muka dan kebe dashi ya kalleni yana kara yi min godiya tare da tambayana karfin jiki nace jikin da sauki. Yace yazone ya duba idan aikin zai jawo min matsala mubar aikin a barsu da Allah abinda yasani sakin dan murmushi ke nan wanda ke nisa damu sai yayi zaton wani zancen soyayya mukeyi a lokacin duba ga yadda muka tsaya a jikin motan muna fuskan sauran jama,an da sukaja baya suna jiran mu gama tataunawan dashi. Wanan matsalan bai shafi aikin nan ba na fada ciwone kawai lokacin zuwan shi yazo min i am OK now na fada godiya ya kara min bayan min fatan alheri da zai tafine mun taka zuwa inda suke yake fadin a gaida umma yaso ace ya samu ganin umma sun gaisa da ita. Bakomai zan fada mata na fada da dan guntun murmushi dauke a fuskana yayi sallama da mutane bayan ya bada alheri ga kananan ma,aikatan dake bakin aiki a lokacin Wanan zuwan nasa ne ya jawo tsegumi ga mutane kowa da zancen da yake fada a wurin ranan bamu dade ba don zuwan shi da tafiyan shi yasa muka bar aikin dake gaban mu din a ranan. Hello mommy na kirakine in fada maki baban su maryam baida lafiya kwanan sa biyu bai iya fita ba . Mommy din ne ta kalli wayan a cikin mamaki da karfin hali tace Nazifa kina da hankali kuwa a rayuwan ki wanan wani irin maganane haka kike fada min kai tsaye haka. A gidan ku ba a koua maki sallama bane ko gaisuwa balle girmama na gaba kada ki kawo min diban albarka a gabana dif taji ta kashe wayab tabi wayan da kallo. Daga Nabila har hauwa dake gefen ta suka kalleta da mamaki jin yau yadda mommy ke fada da sarakuwan nata haka hauwace ta kasa hakkuri take fadin mommy meya faru ? Barni da mara hankalin yarinyar nan duk yadda ka iya hakkuri da lamarin Nazifa sai ta kaika karshe watau. Wai yayan kune baida lafiya ashe kwana biyun nan shine takirani haka kai tsaye take fada min ba sallama ba komai. Yayan mu mommy suka hada baki shifa ni wanan kaddarareb auren da bason nayi sabo ba danace da ba, ayi shi ba wallahi. Don yarinuar nan bata da ranan canzawa a rayuwan ta abin nata ma sai gaba yake yi a yanzu kamar mara hankali. Mommy din ta shige dakin ta tana ci gaba da fada da sarakuwan nata dabata masan tanayi ba a lokacin don itama tana can tana mita akan wai mommy din tayi mata cin fuska a kan dan ta. Sam ta manta da cewa a daidai kofan shi take tsaye take wanan maganan saida taji muryan shi yana fadin kedawa ke wanan maganan haka ? Ta wani irin kallo kofan kawai ta wuce yana kwance yake mamakin wanan hali na matar nasa da bata data ido sam kowa ta samu yanzu take wanan sababin haka yaja tsuki yana gyara kwanciyar shi. Don likitan data ganine yazo har gida ya dubsshi yai masa allura yasa ta dan nuna damuwanta akan rashin lafiyan nasa lokacin har taga tayi abin arziki ta kira mommy . Gashi kuma mommy din ta watsa mata kasa a ido har tana kokarin zagin gidan su ita nata gidan daban ne ko yarabta sun fisu tarbiyane ?. Ba,a kai awa daya ba mommy din ta dira gidan ita da yaran ta biyu don lokacin Faiza tana school bata dawo ba yasa basu je da ita ba gidan. Sunyi sallama kusan sau biyu ba a amsa masi ba da alama kuma suna ciki don ga tv na aiki ssidai babu kowa a falon lokacin. Basu ankara ba hauwa ta kirashi a waya sai ji sukayi tana fadin yaya kana cikine gamu a falon ku da mommy duk suka kallo inda hauwan take. Ba a dauki tsawon lokaci ba sai gashi ya fito yana saye da jallabiya a jikin shi kallo daya zakai mai ka gane ya rame sosai a lokacin da alaman yaji jiki sosai ke nan. Gaidashi suka fara a lokaci guda a vikin kulawa da nuna damuwan su a kanshi ya zauna da kyat yana amsawa don alluran da akaimai a lokacin. Bayan sun gama gaisawane mommy ke tambayan shi abinda ke samun shi yace zazzabine kawai mommy ya wuce kawai ai wanan uban raman da layi lokaci guda haka tun yaushe ne ka fara ciwon , ? Ya dan shafo fuskan shi yana fadin tun ranan da naje gaida ku last nadawo da wanan zazzabin kana cin abinci kuwa yadanyi murmushi yana mayar da kanshi a makarin kujera yake fadin bakin nawane ba dadi mommy. Nan dai ta danyi mai fada akan yaci wani abu ya kalli inda Nabila ke zaune yace dan dafa min wani abu naci mai ruwa ruwa . Wanan maganan da yayi sai yaba uwar tausayi take fadin matarka fa tana inane ita yace ban sani ba ko tana gidan nan don banji duriyan ta ba dai. Sallati hjy ta fara ta kalli hauwa tace ke kira min Nazifa a part din ta yanzun nan da sauri hauwa ta mike ta nufi part din Nazifa din. ZAINAB IDRIS MAKAWA ANA DARA GA , , , , , , , , 6️⃣5️⃣ BY, , , , , , , , , , , , ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , , , , , , , , BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AL HAQQ, , , , , , , , , , ONLINE PAID NOVEL YAR UWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA BA TARE DA HAKKIN KOWA BA DON BIYA KI TURA DARI BIYAR 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK 08036959257 ALLAH SARKI AI RAINA BAYA BACI YANZU DON KIN FITAR DON NASAN AKWAI RANAN HADUWA SEE U👋👋👋👋 Allah sarki duniya duk yadda ka raina kanka dole kana da makiyi a cikin dubu. Ni zainab nasan ban taba novel in zagi wani akida na islama ba rayuwana ba don rayuwana bai taba kaiwa can ba ban kuma taba nasa inyi hakan a zuciyana ba harga Allah. Ban tana nuna akidana ba a duniya darika, shi,a,tijjaniya ko izzala kadariya duk addinine masu mutunci a idona don sun sheda Allah dayane Annabi mohammad kuma manzon sane masoyin mune. Shine mutum mafi daraja a cikin mutane why zaki nemi ki bata min suna kan abinda harga Allah ban taba nasa hakan ko a fili ga wani . A wurina duk wanda ya sheda babu sarki sai Allah Annabi mohammad manzonsane mai shi ya zama dan uwa a gareni. Akan me zaki hada da mutumin da ake fadin yana cikin duhun kai baida ko sani akan addini gidahumin jahili kawai, shi dai muna musuluncine shi wanda ake nuni da halin jahilci a kanshi da dogaro da wanin Allah ko baki fahinci me labarin yake nufi ba. Don haka ki fahinceni ba wani akida dana ambata akan wanan mutumin labarine na gaskiya ko me labarin bata fada min akidan ta ba balle na wani. Ba jahila nake ba da zan tsaya ina sukan dan uwana musulmi mai sallah biyar a rana da ambato Allah. Ke yar uwa ki tubaga Allah da wanan sherin da kike son yiwa kanki kina ganin kamar ni kika kulawa hakan. Babu inda na ambaci hakan ki koma ki duba ki karanta da kya ki fara istigifar ga Allah. Haba yar uwa me nayi maki haka zaki min wanan abinda ko a fili da zaki tambaya ko ni wace akan addinina zaki gane hakan don Allah don son da kukewa Annabi ku barni in zauna lafiya da kowa da wanan sherin da kike kokarin kullawa kanki waini. Ni dai na sheda babu sarki sai Allah Annabi mohammad manzonsane ki koma ki karanta da kyau idan na fadi hakan da kukace. Ku dinga yiwa mutane uzuri don Allah ban taba samun wanan matsalan da yan group dina da yanzu mun zama yan uwa dasu tun akan tarko balle ke da aka dauko maki na Allah ya isa aka kai group din ku kuke kokarin min sheri shi fitina idan kayi sanadin kuna shi baka san a inda zai tsaya ba. Kuyi hakkuri idan na bata maku nikan wallahi ban fada hakan ba har ga Allah cewa wai kai abin ma ba dadin fada can ga bakin wanda ya nasa hakan . Ikon Allah mommy ta fada tana ajiyan zuciya takai kallon ta ga hauwa data aika tana zaune har lokacin ki kira min ita nace dake da sauri hauwa ta mike don zuwa kiran Nazifa din a kofan ta suka hadu hakan yasa hauwa ta juyo. Kusan tare suka iso falon da Nazifan don batayi mata magana ba itama haka ta iso tana fadin sannu da zuwa ashe harkun karso ta samu wuri ta zauna saman kujeran dake fuskantar na mommy din. Idon shi ya lumshe cikin jin kuna da zafin rai bayan na ciwon dake damun shi a zuciyan shi yace bai ci komai ba tun safe mommy ta fada tana kallonta wai abu mai dan ru, , , , Ke baki iya gaida babba bane ko bako ya fada yana kallonta ido jajir a lokacin saida ta wani kalleshi kamar tana mamaki da maganan shi kafin tace. Nima ai naga ba a gaidani ba kuma ni akazo aka sama a gidana ai nagani wani irin zabura yayi daga saman kujeran zakace bashi bane mara lafiya dake takawa da kyat ya fito a lokacin. Wa kike fadawa hakan mommy dince zata gaidake ko wa a cikin su ke kin gaida mahaifiyar sune balle kiyi mutumcin da za a gaidake ? Har kina fadin ke aka sama a gidan ki inane gidan naki ki fada min yau idan na hada kudi da wani naki nagina wanan gidan ? Modibbo mommy ta fada da dan karfi cikin bacin rai ya kallo mommy tace koma ka zauna tana da gaskiya don gidan ta muka zo ba karya ta fada ba ta mike tsaye tare da duban yaran tana fadin ku taso mu tafi Allah ya baka lafiya. Mommy ina kuma zaku akan wanan da ko dabba yafita sanin darajan dan adam a wurinta yaja wani irun tsukin takaici da bakin ciki wanda shi kadai yasan zafin da yake ji a zuciyar shi lokacin. Eh ai gara mu tafi irin hakan ke hana ko yaran nan in turo gidan nan wallahi bana son diban albarka ke kuma ki sani wuri daya na fito da mahaifin ki don haka na wuce raini a wurin ki ko wanin ki. Ni yanzu me nayi kawai sai mutum na zaune kalau za a samu sherin da aka lakaka mai nima ai hakan yasa bana zuwa gidan naku. Kada kije mana dama wake son ganin ki ko zuwan yanzuma don dan uwan mu mukazo gidan nan idan bashi ba wa zaki gani a gidan nan Nabila ta fada. An daiyi hasara a koma gida a koyi ladabi wurin gyatuma hauwa ta bada a daidai inda zata wuceta cikin kashe murya ba tare da kowa ya jita ba. Bani nayi hasara ba sai ku da kuke zaune a gida ko kare bai taya ba kece kika buda muna hanya indai kwantai ne saida aka roki yaya ya daure ya dan jona ki jaka. Fau taji ta gwauce dukan bai sameta sosai ba mommy ce data dawo da baya bayan jin fada ya kaure a tsakanin su takaiwa hauwa din duka ta noke ta samu bayan kanta har dan kwalin kanta yana batun faduwa kasa. Ke kuma Nazifa zaki biye mata ku zubarwa kanku mutunci idan ita bata da hankali aike kina da hankali ko ? Saidai ta zubarwa kanta da mutunci don ni tasan nafi karfin ta ga komai takoma can tayiwa wa yanda ta saba yiwa bani ba nan don ba zan kyale yarinya ba. Mommy ta gane metake nufi hakan yasa ta juya rai bace tana fadin Allah ya sauwaka kai kuma Allah ya baka lafiya tafita daga gidan sai bayan sun shiga motane suka hango shi ya dab tako yafito daga kofan falon ya rike da hannun sa daya . Saida yaga tashin sune ya koma zuwa cikin gidan har lokacin Nazifa tana tsaye tana yankan kauna bata da niyar bari daga kofan ya dagata yana fadin ke ma yanzun nan basai anjima ba ki fice min daga gida. Akan wanan maganan zakace na fice ma daga gida ba inda zan tafi dama abinda ya kawo su ke nan yanzu don suja min matsala tsakanina dakai kuma sunja din don haka babu inda zan tafi. Haka kikace yau idan kika bari na fito na sameki a cikin gidan nan sai rayuwan ki yayi bala,in baci fiye da tsamanin ki yana fadin hakan ya sakai zuwa dakin nasa . Ba zai iya kwanciya ba a lokacin din haka kai tsaye ya bude wardrobe din shi ya ciro kaya daga ciki yana sakawa a jikin shi. A can ko yar aikin tane take fadin hjy tunda kinji abinda ya fada gara ki sameshi ki bashi hakkuri son ba,a hakan da kikayi din . Kamar kinci masa fuskane fa ga mahaifiyar shi a tsaye kike jefawa yan uwan shi wanan kalamin haka kiyi hakkuru ki bisa daki ki bashi hakkuri zai fi. Wani irin kallo ta watsa mata kafin ta kawar da kanta takai zaune bata hakkura ba dai ta sake fadin hjy yi hakkuri ki sameshi a dakin shi don Allah. Idan namiji ya fadi hakan yana nufin haka har cikin ranshi ne mikewa tayi zubur ba tare data kalli matar ba ta nufi dakin shi. Agajiye na dawo gida bayan wucewan ogan mu na zauna ina cin abinci ina ba umma labarin zuwan shi da abinda ya fada game dani. Yaushe zai koma ai ya tafi ko ba kasan nan dama yazo ba kawai ya ratso yaga aikin mune dukan kofan da akeyi ne a lokacin ya dakatar damu duka. Ammar ne ya mike don hankalin shi na kallon ball da yakeyi ga kuma littafi a gaban shi nasan ko nayi mai magana hankalinshi zai kasu biyune a lokacin yasa na kyale don nasan da an gama ball din zaiyi abinda ke gaban shi. Yana bude kofan ya Abubakar ne tare da yaran shi a kofan da sauri ya kara ja baya daga kofa yana basu hanyan shigowa ciki. Nima dai da mamaki nake kallon shi daga inda nake zaune umma ne ta samu bakin fadin a, a yau da baki kake muna tafe ashe ? Yayi murmushi yana kaiwa zaune tare da dora yaran saman jikin shi ya fara gaida umma tana tambayan shi ko lafiya ? Ya dan dago yana murmushin dole tare da fadin bana jin dadin jikina wallahu mama shine kuma kafito hakan yace wallahi umma. Inda nake ya kalla yana fadin Sahiba ko zan samu abu mara nauyi in ci yanzu ? Umma ke fadin tashi maza ki duba a samu abinda akai masa yaci na mike zuwa kitchen din na dan tsaya ina duban kayan dake kitchen din kafin na dora ruwa saman gas. Abincin mai sauki nayu mai hade da kunun gyada na kawo mai a dinning da kyar ya dago zuwa dinning din tare da yaran da nake satan kallo yan mata su duka biyun . Ba laifi gaskiya yaran kama da yan uwa sukeyi suma sai dai na kasa tuna fuskan Nazifa balle na tantance fuskokin nasu kowa suka biyo ga kama. Muryan shi naji yana fadib kizi ki dauke su a nan zan barsu in zan tafi da sauri na juyo ina kallon shi da mamaki umma sai cewa tayi lafiya ko modibbo ? Dan murmushi ya sauke kafin yace lafiya mama nakawo su nan ne kawai dai ya fada sai ya mayar da hankalin shi wurin cin abincin dake gaban shi faten wake yaji kayan hadi a cikin sa dama mun jika wake kamar yadda mukan jika shi yayi awani idan zamu dafa saboda saukin dahuwa a saukake. Da alama yaji dadin dahuwab sosai don idan kin jiki yafi dadi a wurin ci da daukan kayan hadi bai kara magana ba saida ya gama. Ya dawo saman kujera ya zauna yana fadin mama a nan zan bar yaran nan su kwana biyu tare daku don nasan babu wanda zaisan suna gidan nan. Meke faruwa umma ta sake tambayan shi nan ya fara jero mata irin cin mutuncin nazifa dabai tsaya a gareshi ta hada har mommy da yan uwan shi. Nima dai sam banji dadin hakan ba gaskiya don nariga da nasan ko waye Nazifa akan kujeran ta taci min mutunci a baya don haka ba zan manta da ita ba a rayuwana gaskiya. Sai kuma yaran suka ban tausayi don laifin uwarsune yanzu yake kokarin shafan su ke nan saidai naji umma na bashi baki yana fadin yana son ya horata ne umma tayi hakkuri don Allah. Zai tafine yabada kudi wai a saya masu abin bukatan su sai idan ya dawo da sauri nace no ka barshi kawai yaya zan saya masu komai insha Allahu. Har yakai bakin kofa nace kira sunan shi yaja ya tsaya wuri daya ba tare daya juyo ba nace ya Abubakar kana ganin kawo yaran nan gidan nan yin hakan ba zai jawo wani matsala daga baya ba ? Saida yaji nayi shiru ya juyo yana fadin Sahiba shin akwai wanda yasan kuna garin nan ne bayan ni ? Kai na girgiza mashi yace OKey ta yaya kike zaton wani zaiyi tsamanin a nan suke ga gobe zanyi tafiya nima don haka kada kiji komai a ranki saidai idan zasu damekune a nan din in canza masu wani wuri. Kafin inyi magana umma tace haba dai koba diyan ka bane modibbo ai zamu rike ma balle diyan cikin kane wa yan nan kada kaji komai a kan zaman su a nan din. Yace yagode yasa kai ya fita muryan yarinyar ne yayi sanadiyar juyowan mu ga barin kallo mamakin da muke mashi na ya tafi ya barmu da yaran a gidan take fadin. Ina daddy mu ta fada kamar bata magana da farko irin haka idan kaganta don karantan su ita dai karaman har lokacin tana jikin umma a lafe da alama bata da rikici. Fuska kumshe da murmushi nace daddy yaje ya sayo maku alawa yanzun nan zai dawo na fada ina mika mata hannu tazo wurina. Kin zuwa tayi ta makale a jikin kujeran daya tashi a kai tana wasa da hannayen ta mikewa nayi daga inda nake na shiga dakin umma na dauko masu biscuit da sweet din amar masu dadi na kawo masu. Abin mamaki sai naga ta fisga daga hannuna kamar mai fushi ko fada na mikawa dayan kafin in juyo gareta ina fadin ba zaki ce min thank you ba na karbe abina yanzu. Kamar ba zatace ba ganin na mika mata hannu zan karba sai naji ta fada ciki ciki nace good girl ina shafan kanta a hankali. Na koma na zauna a inda ya tashi din ina lumshe idanuna a hankali nasan yaran ba a koya masu komai daya shafi tarbiya a addinan ce. Don shi kanshi godiya wata kallamace da yakamata a fara koyawa yaroshi a don yanada ma,anan da ke nuna yaro yana da tarbiya don yana mutunta wanda yayi maka hidiman ka gode mai. Bayan ta gama shan alawan taso ta tayar muna da rikici na mata wanka na goyata a lokacin maniya ta shigo wurin umma. Ganin yaran take fadin a anan babasu ya barsu ashe don naga zuwan su ina ciki kuma naji fitan shi kai yaran masha Allah kudai zurian ku suna da kyau. Ina kyau a nan na fada ina juyo mata yar dake goye a bayana don yarinyar uwarta ta biyo yanzu na gane hakan danayi nazarin su da kyau. Ta zauna tana mikawa yar dake jikin umma hannu ta lafe jikin umma taki zuwa mukai dariya ina fadin umma kin samu ya ke nan ashe ? Jikokina ne kin sani don dai zumuncin ya koma hakane ina yar yaya Nuhu da dan hjy Addah ai duk nawane ko indaga zumunci don dukkansu a matsayin tobasai na suke ai don ni na kasance yar mace ce a cikin su. Shiru nayi na fada tunane don fadin hakan da umma tayi a sanadin su baffa Nuhu umma ta rabu da yan uwanta hayatan hayatan. Hankalin umma naga muniya bata kula da halin da nake ciki ba lokacin don na zurfafa ga tunane a lokaci fitan muniya nake fadin umma. Ta juyo gaskiya ya kamata ace mun ziyarci yan uwan ki kafin mu bar kadunan nan da mukazo gaskiya saboda wani Alh Nuhu can har ki jefa kanki a cikin halakan alhakin zumunci. Dukiyan nan suje suci ba shine a gaban mu tunda har ubangiji ya rayamu muka kai wanan lokacin ba tare da arzikin mu ba. Umma tayi shiru tana saurarena kafin tanisa tace naso hakan don duk kwanakin nan hankalina yana wurin su gaba daya. Ko barci na kwanta mafalkin gida da yan uwana nakeyi abin yana damuna sosai a rai nima zamu sa lokaci mu tafi na fada ina mikewa don yarinyar da tayi barci a bayana tayi min nauyi sosai a lokacin. Yaushe rabona da goyo tun zaman mu kaduna ina goyo Amira sai kuma yau dana goya yar yaya Abubakar din badon uwarta ba sai don ubanta kawai. A ranan kan bamuyi barci ba don yaran dukkan su suyi rikici tundai babban ina da maganin mura shi muka dinkirawa yan banza barci mai nauyi ya dauke su har safe na fita wurin aiki basu falka ba a lokacin. Ina wurin aikin amma bini bini nakan kira umma inji halin da yaran suke ciki tace suna wurin muniya da suka fara tikici ta daukesu ta fita dasu zuwa wurin ta. Sai lokacin hankalina ya kwanta na sauke ajiyan zuciya ina fada a zuciyana cewa haka kawai a dorawa mutane wahala don wani dalili. Can kuma ashe abinda ya faru bayan barin mommy din da rikicin ya barke a tsakanin su bayan yar aikin ta matsa mata taje ta bashi hakkuri taje. Tana shiga dakin ne ta zauna yana ci gaba da shiri tace wurin kafa nazo ganin baiko juyo ya kalleta ba a lokacin don yadda yake jin takaicinta a lokacin. Kikazo yi me a nan na fada maki wallahi yau ba zaki kwana min a gida ba son haka ki fice tun muna sheda juna dani dake kan ranki ya baci kamar yadda kika batawa mahaifiyata rai kema. Dama ai haka akeso idan kuma mutum bai fada ba ace baya da kirki sai lokacin ya juyo da kyau yana fuskantar ta yace dama kina dashine ashe rashin mutuncin naki yakai haka ban sani ba ? Get out of my side ya fada da karfi ta fito yana fadin na baki minti biyu kacal wallahi idan baki fita a gidan nan ba komai zai iya faruwa ki kuka da kanki wallahi duk abinda ya faru kuwa. Jin hakan yasa tayi fushin zuciya gyalen ta kawai sai jakka ta dauka da makullin motanta ta fice gidan da niyar ai tasan hakan ba zai yuyu ba dole za a dawo da ita. Saidai tana fita ya fito ganin mai aiki tare da yara a cikin damuwa yasa ya tambaya a kausashe da ina take ne ? Tace ta fita yanzun nan har ya dan taka ya juyo yana fadin OK kefa tace in bari ta dawo na tsare yaran yace OKey kina iya tafiya yanzu kema ya fada cikin daure fuska don zan kulle gidanane in fita. Dakin shi ya koma ya fito saiga mai aikin ta fito tana kokarin daukan yaran yace barsu a nan dasu zan fita. Tare suka fito daga gidan yasa yaran a motashi ya ya koma ya kulle gidan yashiga yana magana da maigadi itama ta tafi tana mamakin hakan. Gidan mommy yaso kai yaran kafin kuma ya canza tunanen shi ya juya zuwa unguwar mu a yakai muna yaran ya kuma ci abinci a can yana fita hotel ya nufa ya kama daki a can ya kashe wayan shi kuma. Nazifa ko gidan su ta nufa ta samu mahaifiyar da jiya suka dawo daga asibiti ta sanar mata da komai wani kallo uwar ke mata kafin takai karshe tayi shiru. Nazifa kasheni kuke son yine a gidan nan kome ? Don ku nake zaune gidan nan ina hakkuri ina bin umurmin shi duk da irin takuran da muke fuskanta a aurin shi. Farko dana gane halin shi naso fita gidan nan saidai kaddara ta riga fata don na samu cikin ki dole na zauna na haihu bayan haihuwan ki kuma komai bai canza ba lokacin amma mahaifiyata tace na zauna nayi hakkuri in sama maki abokan shawara a gidan nan. Har yau da kuke ku biyar hakkuri nakeyi kin sani don kunfini sanin mahaifin ku baudaden rayuwa ke gareshi. Balle ke da dadi yayi maki yawa don iskanci da rashin sanin ciwon kai kin kasa zama ki natsu a dakin ki ko zamu samu salaman rayuwa a wurin ki. Yau har iskancin naki yakai kiciwa uwarshi mutunci a gaban shi haka bako bayan idon ta ba kin dauka kowa irin kine da zai zauna don kina zinariyan mata kiciwa uwarshi mutunci yana kallon ki ? Wallahi kiyi maza ki koma tun wani baiji wanan badalan da kika aikata ba a gidan nan yanzun nan gasu Tasi,u nan su rakaki ki koma su bashi hakkuri dacewa kannen ta dake zaune sai tsuki suke ja a gefen su. Shigowan yar aikin ne ya hana uwar magana nan ta gaisa dasu ta fara rabtabo masu bayanin komai a karshe dai kowa zabura yayi jin ya rufe gidan ya kuma tafi da yaran. Ina yakai min yara ta fada a zafafe wurin mommy mana kaninta ya bata amsa taji ranta ya baci sosai lokaci guda. Uwar tace kin gani ko kinga abinda kike kokarin ki jawowa mutane yanzu kuma in ba ai hankali ba sai zancen nan ya fita kowa yaji. Wallahi kiranta zanyi ta aiko min da yarana yanzun nan ba zan bar yarana a can suko kwana tare dasu ba akan me zai daukan min yara yakai min su can ? Ta fara kiran layin mommy din uwar tace miko min wayan wawiya yanzu zaki bata komai don baki da wayau ko kadan ke . Kiran har ya tsuke mommy bata daga ba don a zaton ta cin mutunci zata kara masu saiga nabiyune ta dauka sai taji muryan mahaifiyar Nazifa din tana sallama. Nan dai suka gaisa take fadin haka kuma wanan mara hankalin ashe tayi maku ni bansan meke damun rayuwan Nazifa ba wallahi. Ba komai ai taci albarkacin haihuwa saidai ta bari don gaba in ta dauki hakan zata sha wuya harni Nazifa zata kalla ta zaga a gabana meye laifina a cikin dubu dana zabota tazo mu zauna tare ashe yin hakan kuma laifine hjy salma ? Gaskiyane hjy Addah don Allah kiyi hakkuri idan na samu lokaci zanzo har gida in kara baki hakkuri kan hakan baki da laifi wallahi. Don yar banzan bata san yadda na samu akayi wanan hadin bane kwarai da ba hakan ba don da ta zama muna ya kuwa taba mara da kunya. Ba komai ai ya wuce nikan a wurina hjy Addah ta fada tona gode inji hjy salma din ta fada kafin tace yaran dai basu yi maki fitina ba dai ko ? A cikin mamaki hjy Addah ke tambaya yara kuma wasu yaran ke nan su mimi wai tace ai basa nan ba a can na barsu ba gidan. Kallon juna sukayi a cikin mamaki suka hada ido basi wurin ki fa tace wallahi ba a zo dasu nan ba ai ko an fada maki suna gidan nan ne. Ga Nazifa nan yace ta fice masa gida tafito tabar yaran karshe kuma bayan tazo yanzu saiga yar aikinta tazo tana fadin ya dauki yaran ya rufe gidan shi ya tafi dasu. Ina yakaisu hjy Addah ta kara tambaya aine nima nake mamakin hakan don inba nan ba ina zai kaisu ke nan ? ZAINAB IDRIS MAKAWA ANA DARA GA , , , , , , , , 6️⃣6️⃣ BY, , , , , , , , , , , , ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , , , , , , , , BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AL WAKIL , , , , , , , , , , ONLINE PAID NOVEL YAR UWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA BA TARE DA HAKKIN KOWA BA DON BIYA KI TURA DARI BIYAR 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK 08036959257 ALLAH SARKI AI RAINA BAYA BACI YANZU DON KIN FITAR DON NASAN AKWAI RANAN HADUWA SEE U👋👋👋👋 Ina bara adduan ku da bakunan ku masu albarka ga wanda Allah yaba ikon tunawa yayi min nagode. Muniya naba kudi ta sayowa yaran abin bukata daga tufafi permppers da alawa da biscuit har magani don yaro baka rabashi da ciwo. Kwana biyu kawai nasan mun samu matsala da yaran bayan shi mun zauna lafiya dasu babu wani matsala gaskiya ganin haka sai na daina damuwa akan yaran Don muma yayi muna shine silar mayar damu cikkakun mutane a yanzu har na tsaya nayi karatu da taimakon Allah ga har Amar shima yana karatun don da karatun lagos natsaya nayi sai yanzune zan shiga jami,a a lokacin. Amma gani a mataayin dako makiyina baiyi tunanen hakan ba gareni koda a mafalkine cikin kuduran ubangiji . Wanan yasa nakeji da diyan ya Abubakar din na kawar da tsanan uwarsu a zuciyana tunda basu sukai min laifi ba uwarsune da kakan su. Ina jin yaran har cikin zuciyana sosai dan zaman mu dasu dama kuma in baki manta ba haka nake da yarani har yaran Abdul sun saba idan na dawo su tareni bazan shiga gida ba sai na raba masu dan abinda na tsaya hanya na sawo masu ranan da ban sayo ba kuma kudine zan basu ince suje school dashi da safe. Yauma shiryawa nayi zamu fita kasancewan weekend ne ranan zamu fita sayayya don washe gari sunday ne yawancin shaguna basu budewa a ranan. Nida muniyace a gaba ta dauki yar ya Abubakar karaman a jikinta babban kuma rabin jikinta yana akan jikina ina tuka motar . Wani babban shagon sayar da kaya na tsaya muniya ta kalloni tana mamaki na sake mata murmushi kafin ince zan dan duba abune na juya wurin samarin dake baya su hudu ina fadin banda garaje sun san nan ba wasa yanzu a yankewa mutum hannuwa idan ya taba masu kaya. Daga cikin motanshi ya kura muna ido sosai har muka fito muka shiga shagon shima fitowa yayi yabi bayan mu zuwa cikin shagon. Yar banci mukeyi a lokacin yana tsaye yana mamakin ina na samu diya saidai abinda ya tsayar mai da mamakin nasa shine gabnin yarinya tana son zuwa wurin . Ajiyan zuciya ya sauke ganin uwar yarinyar ta karbi abinta daga hannuna sunyi gaba sai lokacin ya iya motsawa daga inda yake tsaye din. Kayan yaran nake zabe mata kaina a duke naga hannu ya tabo wani daga bayana yana fadin ki zabi wanan yana da kyau sosai. Ya sallam na fada a raina ina lumshe idanuna duk da ban juyo ba nasan muryan dake min magana a lokacin don muryan Almustaphane a bayana yake maganan. Gane hakan baisa na juyo na fuskance shiba naci gaba da abinda nakeyi wurin dubawa karamin yaron muniya kayan sakawan shi. Sahiba dake nake don nasan kin sheda ko waye a bayan ki ke nan wanan kin juyowan naki da kikayi a yanzu ya nuna min hakan. Kwarai na shedaka kokai waye saidai bai zama dole gareni ba in nuna nasanka a ko ina na ganka kona ji muryan ka din. Murmushi mai sauti naji ya sake tare da gyara tsayuwar shi da kyau yana fadin har yanzu zancen haka na cikin zuciyar ki ashe ? Magana daya zanyi da mutum na rikeshi har mutuwa ta bana mance Alheri hakama bana mance gargadin ko wani zancen danayi da wani. Ina munyi wanan zancen dake a baya na dauka komai ya wuce a yanzu ai na dago kai na watsa mashi wani irin kallo da dukkan idona. Murmushi ya sake yana saka hannayen shi cikim aljihun wanson shi dukka biyu yace ba wanan ba me kika zoyi a kaduna yanzu ? Kwanaki na ganki a by pass sai na dauka bake bace don ban taba zaton cewa kedin bace a kaduna a wanan lokaci daga baya kuma sai banyi mamakin hakan ba don tunawan da nayi cewa kedin dama kin taba zama a nan din. Me ya kawoki nan ina kuma mama da Ammar suke ban rufe baki ba saiga yaran sun dawo hannayen su dauke da alawan da nace kowa ya zabo a lokacin. Amar yana ganin shi ya dan so zuwa wurin shi sai kuma ya tsaya yana kallona a cikin dan shakkan hakan a fili. Zo mana abokina ya fada yana kallon Amar din da murmushi a fuskan shi ya sake mikawa amar din hannu nayi mai alaman ya tafi inda yaken. Da sauri ya karasa wurin shi banda wani dar din komai akan Amar din don mun riga da mun koyar dashi abinda duk wani zai tabayeshi game da zuwan mu din. Gaba daya yaran suka bishi a baya yake tambayan shi yaushe kukazo garin nan yace this week muka zo muna zuwa ganin likitane mu koma lagos. Har a ranshi ya gamsu da hakan da yaron yace don ba wani shaku a fuskan yaron na fadin hakan ya sake tambayan shi wani unguwa kuke yace a hotel a can muka hadu da wa yan nan suma sunzo bukine sukace. Daukan yaran yayi yaci gaba da yi masu sayyayya har na fitan arziki mu dai muna jiran su a madakata muka fito tare dashi. A bakin motan mu ya tsaya nayi dabaran ba muniya makulin motar tun kan mu fito akan itace zata ja motar kada ya gane hakan don tun wurin biyan kudun Amar yai min signal da cewa ya fadamai hakan. Duk sun shiga motar sun zauna saini naji yyace gaskiya sahiba baki da kirki kin shigo garin nan keda Amar amma baki nemi yan gida sun san kina nan ba. Ba wani abu nazo nan nema wurin wani ba asibiti mukazo kawai kuma jirgin safe zamubi gobe din wanan makwabciyar tamuce ta matsa mu shigo ko zamu dan saki jiki dama Amar ya fada min yace. Ka gaida gwaggo na fada ina kokarin shiga motar dana bude tako kije da kanki idan kin damu da ita ya fada. Nashige mota bance dashi komai ba a lokacin mukaja muka tafi muka dauki wani hanya don batar mai da sawu saida naga bai biyo mu bane na sauke ajiyan zuciya. Mun koma gida nake ba umma bayanin haduwan mu dashi lokacin muka bude abinda ya sayo ma yaran muna mamakin hakan. Ammar kuma ya bamu bayanin duk yadda sukayi dashi lokacin dayaja su yana masu sayayya. Wai yar nan kinyi dubara tun farko kamar kin san hakan zai faru din nace na sani tunda munzo garin su man ai dole mu hadu da wanin su gashi ko duk mun hadu dasu din. Kayan da nayi oda lagos don halattan bukin baby suka iso gareni a daidai lokacin da kuma nake wasi wasin zuwa bukin yanzu don ni kadai nasan shirin da nakeyi a bangarena yanzu boyo dai ya isa hakanan kuma garemu na fada a raina. Shiri nayi sosai da ba tare da kowa yasan da hakan ba sai wa yanda na shirya hakan dasu da zamu tafi tare. Shiru dakin yayi lokaci guda ba wanda ya iya magana a cikin su bayan mahaifiyar nasu tagama wayan da hjy Addah. Tasiu ne ya kawar da shirun falon yana fadin ba shike nan ba tunda wurin kakansu suke yanzu meye na damuwa kuma ? Kai dan Allah rufa min baki in yaran na wurin Addah ita fa me yake nufi da ita ko a nan kake son ta zauna muna a samu abun fada kan mu. Ban fita wani ba yanzun kuma wani na shirin tunkara duk a kan yaya wanan abin dame yai kamane wai ? Ni Abba ma nakejiwa wallahi don idan yasan da zacen nan komawan ki yanzu sai Allah gidan nan. Wa zai fadawa Abba ina gidan nan ta fada tana dauko wayanta tana neman layin mijin nata lokaci guda. Ai dole Alh ya san kina gidan nan ke kin dauka zancen wasane wai kinyi wauta babba da kibar yaran nan a gidanshi koda baizo donke ba dole yazo don yayan shi ai. Dolene mana Nura ya fada yana mikewa tsaye yace ita anty ma duk mata suna son dangin mijin su amma ke kullun kina cikin fada da naki ko banza ai gwaggo Addah kanwar mahaifin mune kuma muna jin dadin ta duk wanda yaje daga gidan nan. Ya fada yana gunguni ya fita daga dakin rai bace uwar nasu ta kwala mashi kira don kada ya fita ya fadawa wani. Da kyat yaron ya dawo dakin ya zauna yana cicika yana batsewa har lokacin yana jin zafin yar uwan nasu sosai a zuciyar shi. Ya kara fadin ke baki tausayin mamace ki duba dan iskan nan idan baida hankaline ai suna da yan mata a part din meyasa baije can ba sai nan don suna jin haushin mu mana su barna muna suna ga banza. Kan uwar na suke abin duniya ya dameta lokaci guda kafin tayi magana uwargidan su tayi sallama ta shigo da sunan gaida Aina,u da jiki. Amma tana ganin Nazifa sai kuma ta buge da fadin kina nan ne ashe ta juya ta kalli mai aikin nata tana fadin ina yaran suke ? Suna gida tare da baban su ta fada Allah sarki sai basu biyo kuba kuma ashe sun saba da uban nasune har haka. Aina ya karfin jikin naki tace naji sauki a wani irin yanayi na nuna rashin jin dadi a lokacin. Ta juya tana fadin idan kun tafi a gaida muna su ta fice a cikin tsarguwa ganin yadda suke zaune zugun zugun a falon kamar an masu mutuwa. Dole dai yadda ba a son din hakan akayi don an nemi wayan Abubakar din ba, a samuba don baya shiga yana fadin a kashe wayan yake. Dole uwargidan nasu tafadawa halinda ake ciki ta samu mijin nasu da zancen bayan ta gama yiwa nazifan fada sosai na irin rashin jankalin da takeyi. Har tana fadin idan baki hankali ba sai iyayyen shi ko shi sun saka ya kara aure mace da zatazo ta mamaye mKi gida kina ji kin gani kuwa. Shi kuma Alh ya gama jin tana gida modibbo y kwashe yaran ya rufe gida ba a san inda yaje da yaran ba yanzu haka ko an kira wayan nasa baya shiga sam. Dago kan Alh din sai cewa yayi to shine me ke nifa sam bani son zancen yaron nan a gabana kwata kwata wallahi na tsani wanan dan iskan yaron a rayuwana mai kafiya kamar irin na ubansa. Hakkuri za ayi Alh tunda aure ya hada harda zuri,a uwargidan nasa ta fada a sanyaye ya mere baki yana fadin to tunda ya hada ai sai ta koma can wirin su baffa Amadu su mayar da ita. A daiyi hakkuri Alh abi abin a sannu zaifi hannun ka baya ruba ka yanke aure ya riga daya gama yanzu kuma kaga dama kuma ga zumunci a tsakani. Bai kara magana ba don bacin rai har ta karasa zaman ta tashi ba tare daya iya furta komai ba a lokacin don yakai wuya makura da zancen. Wasa wasa sai gashi ana share kwanaki ba wanda ya biyo bayanta daga can gidan shima ba, a jishi balle a san inda suke da yaran. Wanan ya tayar da hankalin mommy sosai ga zancen bukin su daya doso kai sai abin ya taru ya zame mata biyu lokaci guda. Anty Amarya taji komai amma tunda ba a fada mata ba sai ta share saida tana gulma da mutanen ta idan sunzo su kuma in zasu fita hjy Addah na falo zasu sake mata haibaici da cewa aikin huta ki aurar da yarki ki huta ba sai ta girma maki a gida kuna gwada sa, a ba. Wanan irin zancen yakan dagawa mommy hankali sosai saidai bata nuna tasan dasu akeyi don kada ta biye masu a tafi da ita ana yadawa a gari. Daddy ko a waya mommy ta kirashi ta fara fada mai abindake faruwa da Abubakar din tun cikin wayan ya fara sababi dasu . Daya dawo kuma ya dora a inda ya tsaya inda yake shiga ba nan yake fita ba dama uwa itace mai daukan kwaram ko yaushe. Bukin kan an farashi gadan gadan ba kama hannun yaro saidai kuma dan cikasa din da aka samu daga bangaren ango don yaki sake hannu yadda uwar yar keson ayi a bukin. Gidan baffa Abdullahi kanin daddy za, ayi kamu ban samu zuwa ranan ba yadda naso saboda na dade a wuein aiki sai washe gari da za ai mother's day a gidan gwaggo hari ne na samu halartan taron . Mun isa musalin biyar da rabi duk girman gidan ya cika da mutane tun daga waje har cikin shi da jamma,a wuri na samu nayi parking din motana na fito tare da Ammar da babban dan Abdul sai muniya da mukazo tare. Dogon riga ne dark blue har kasa yaji duwatsu daga sama zuwa kusan cibiyan rigan muniya ma ba a barta a baya ba tayi shiga na abaya mai kyau sosai. Shigan mu kawai zai nunawa mutum cewa mun banbanta da yanayin yan wurin dole wanan idan na gitta a sau anjuyo ankara kallon mu karo na biyu don shigan yai min kyau sosai a ranan don ko takalmana da jakkana abun tsayawa a kallane a wurin. Wayata na jawo iphone thirty ina kiran layin Faiza dake can cikin taron jama,a a lokacin sai can taji ana kiranta ta dauki wayan tana dubawa taga sunana da mamaki take kallin kiran ta fita daga wajen taron zuwa cikin gidan tana daukan kiran. Kwana biyu sahiba ina ta kira bani samun ki nace ayyah kina ina yanzu tace kin san an fara bukin baby muna wurin mother's day yanzun haka . Ki fito gamu a waje ki shigo damu nace mata a takaice don bana jin ta sosai a lokacin kai abin sherine aida nasan hanyar lagos wallahi da kin gani watarana. Ki fito mana na fada a dan tsawace ta sake fadin wai iskaci sheri wai zaki min don kinki zuwa ko ke wata iri ce wallahi zan koma donke fa nazo wurin nan . Waida gaske kikeyi ko wasa nace ke bakiji kidan wurun nan na tashi a wayana ba aiko inaga taji din don wani irin ihu data sake lokaci guda. Baifi yan mintina ba tafito waje tana raba ido gamu a gabanta ta wuce tana basarwa na kara danna wayana nace wai kinyi haukane zaki wuce duk a cikin turanci muke magana don shi na shirya yi a wurin . Juyowa tayi inda muke ta kara kallin mu saida ta tsaya tayi min kallin tsab kafin ta yanko da gudu ta rugumeni nima din rugumeta nayi muna murnan ganin juna. Wai sahiba kece nan ko gizau idona ke min kece kika koma wata lady dake haka don Allah ? Murmushin cikin aji wanda a yanzu ya zame min jiki na sake mata ganin hankalin mutane yana dawowa garemu muniya na gefe tana muna murmushin ganin yadda mukeyi. Ina Ammar da umma na nuna mata Ammar a gefena dake tsaye Ammar kaine ta fada tana nufar shi ta rugumeshi gaisuwa irin na yaran lagos yayi mata. Goodevening ya fada tare da dan rankwafo kai yana dan daga kafa daga baya itakan mamakin wanan sauyin namu takeyi har kasan ranta. A tare muka jera zuwa cikin wurin taron da ita sai hankali ya dawo garemu don yadda aka jera kujerun na zaune zasu iya hango masu shigowa gidan. Tun kofa naji an fara tambayan ta su waye wa yan nan faiza sister din mu ce take fadawa mutane kawai. Murna yayiwa faiza yawa bakinta bai rufuwa a lokacin sai yankawa mommy kira takeyi alokacin cikin taro tana rungume dani mommy ta juyo tana fadi mommy ga Sahiba. Fatima dake can tana magana taji ana fadin sahiba ta juyo ai muna arba ta sake kara ta kama bangaje mutane tayo wurina tana ihu jin dadi tare da kiran sunana. Hakan saiya kara jawo hankalin mutane garemu sosai kowa na kallon mu Amira ce tasani kaiwa da dan sasarfa muka rungume juna a wurin . Mommy ta taso anty amarya ma taso ina binsu muna rungumar juna ina gaidasu saiga Nabila da hauwa muka rugumi juna gaba daya yan gidan sun nuna inada ma,ana a wurin su. Kafin muka dan zauna na dan lokaci dana dago kai zanga yadda mata ke kallon mu suna magana muka dan juyowa nayi ina fada mata muje motana su kwaso kayan gift suna a bayan mota mu zamu tafi. Ina zaki ta tambayeni nace inda muka sauka fatima ce aka tura ta fadawa Anty Amarya sai gata da kanta lokaci guda muka mike don barin wurin idone ya bine caaaa. Takawa nayi inda mommy suke zaune tare dasu gwaggo hari har kasa nakai ina sallaman su don ladabi ban damu da idon mutane dake kanmu ba a lokacin. Hakan ya kara nunawa taron cewa suna da ma,ana a wurina sosai yadda nayi masu din lokacin kuma anty Amarya ta iso tana fadin Sahiba kuyi hakkuri ance zaku tafi ba a gida zaku saukabane ?. Kaina girgiza ina fadin akwai inda muka sauka ko tunda nan za ayi yawa ta kara fadin fatima tace kince azo a kwaso serbeniya ko nace eh Anty na kara juyawa nayiwasu gwaggo sallama muka tafi harda anty din son rashin yarda da bata dashi. An bude ta cika da mamaki sosai manyan kwalaye ne na jug masu kyau tun gida umma tasa na ware ma mimmy nasu da yanzu naga kunya a idon ta karara don ganin mu da tayi. Faiza na dankawa nasu naba mommy saura haka aka kwaso zuwa cikin gidan gwaggo hari gaba daya don anty tace basu rabuwa a wurin lokacin. Ido caaaa suna tsaye har na tayar da mota muka barsu cike da mamakin ganin mu a ciki bakon yanayin da mukai masu na bazata lokacin. ZAINAB IDRIS MAKAWA ANA DARA GA , , , , , , , , 6️⃣7️⃣ BY, , , , , , , , , , , , ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , , , , , , , , BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AL QAWAIE , , , , , , , , , , ONLINE PAID NOVEL YAR UWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA BA TARE DA HAKKIN KOWA BA DON BIYA KI TURA DARI BIYAR 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK 08036959257 ALLAH SARKI AI RAINA BAYA BACI YANZU DON KIN FITAR DON NASAN AKWAI RANAN HADUWA SEE U👋👋👋👋 Ina tuki ina sharan hawaywn daya cika min idona da bakomai yasani yun shi ba a lokacin sai ganin yadda taron yan uwa basu san mu ba alhalin muna jinin su. Wanan wani irin zaluncine haka dan uwa uba daya ku rabashi da duniya ku wofintar da iyalan daya bari a cikin duniya cikin rashin damuwa ku kuna zaune daz naku cikin jindadi da kulawa duniya ina zaki damune haka ? Muniya datayi shiru a gefena take fadin kiyi hakkuri nasan abinda ya sakaki kuka ganin yan uwa haka a wuri daya dole kaji ranka ya sosu sosai . To amma kuna da yan uwa haka ashe Sahiba meyasa baku ziyaran su alhalin naga suna son ku sosai ji yadda yarinyar nan data ganki ta rude gaba daya wallahi don jin dadin ganin ki. Amma daga ke har umma har Ammar kamar baku damu dasu ba why kuke nuna kamar baku da gata hakane sai wanan dan uwan naku kadai naga yana zuwa wurin ku shima baku ke zuwa ba ? Murmushin dole na kakaro a fuskana lokacin na kara kai hannuna ina share hawayen dake fuskana bandaiyi magana ba itama nisawa naji tayi kawai lokacin. Haka muka isa gida umma dake zaune tare da yaran suna zaman jiran dawowan mu ta fito tana muna sannu da zuwa na amsa a cikin rai kawai na shige ciki zuwa dakina. Gado na fada na sake wani kuka mai ban tausayi rashin Abban mune ya dawo min sabo a zuciya sai nake ganin gaba daya ahalin namu basu kaunan mu ne wanda ya mutu ya mutu ke nan dai. Nakai wani lokaci kwance a wurin kafin naji muryan maryam tana fadin tare da dan bubuga min jiki in tashi in tashi kawai take fadi ganin ban tashiba ta hawo gadon ta kwanta a jikina. Sai lokacin ne na sauke wani irun ajiyan zuciya naji kamar yarinyar ta lalasheni a lokacin ina jin wani natsuwa na sauka min a zuciyana lokaci guda. Nakai wani lokaci a hakan ban motsa ba kuma ba barci nayi ba a lokacin jin nauyin yarinyae yai min yawa a jikina yasa na dan juyo naga halin da take ciki ashe barci yarinyar tayi lokacib a jikina na gyara mata kwanciya nima na juya rigingine ina kallon darking din dakin. Sai can na tuna banga umma ta biyoni daki ba hakan ya sana mike da sauri nafito daga dakin na nufi dakin umma ganin bata falo a lokacin yasa na nufi dakin nata. Zaune take a inda ta idar da sallah a cikin wani yanayi na ban tausayi jin na shigo dakin ne yasa ta dago idanunta daya sha kuka ta sauke a kaina lokacin. Zaune nakai bakin gado kafin ince komai da ita ta dago tana tambaya maryam na wurin kine na gyada kai tare da fadin tayi barci. Nan take tana damuna tun fitan ku shine na turata wuri ki ta fada a kasalance nasan zaki take son sha zakin nan kuwa ba zai basu lafiya ba idan ya tashi tambayan su. Sun saba da shan sa ne tun gida tunda kikaga shi kadaine a bincin su tace bata ko koyawa diyan ta alheri ba ai duk uwar da tasan kanta zata nisanta danta da wanan kayan kwalaman na turawa saidai uwayen yanzu suna ganin kamar hakan wayewa ne amma da illan da yakewa yaro a jiki sosai kuwa. Ai kinga yarbawa da sauran kabilu basu yarda sun yar da gargajiya ba kodama sugar zasu sha saidai mai kololo kuma bai wuce kwara biyu a wuni don sun san illan hakan ga jikin dan Adam abin ba manya kawai yake shafaba har da yara kanana a wanan zamanin. Shiru nayi ina nazarin abinda umma ke nufi kafin inji tana fadin ashe kun samu taro sosai a airin yan uwa da kukaje ? Na nisa tare da dago kai na dan kalleta nace eh umma gaskiya sun nuna muna jin dadin su sosai da ganin mu a wurin saidai mun barsu da mamakin mu sosai a zukatan su. Nan dai na fara bata labarin abinda ya faru a wirin damu har dawowan mu din tayi shiru tana tunane mai zurfi. Zaune suke a falon su sun tasa kayan a gaban su suna kallo a cikin mamaki kowa yayi shiru sai hauwace tace nifa wanan kafiran motar da kuma irin shiganta shine ya tsaya min a rai wallahi. Jiki don Allah da wani zancen banza ace maki mutum ya fito lagos don me zaki tsaya mamakin arzikin ta lokaci guda sai dai idan kinso. Shi dan lagos meye bai iya aikatawa don kawai ya tara kudi nikan banyi mamakin hakan ba tunda dai kinsa Sahiba kyakyawace ta karshe dama . Wai kina nufin ta kallo Nabila din bata karasa ba tace kwarai kuwa ke nifa ban wani mamaki ko maza sukaje neman kudi acan ai kinga yadda suke dawowa nan Amma ai barikin ta dai baisa ta canza ba yanzu ko tunda tarbiyan nan nata naga yana nan ji yadda taje gaban su mommy ta gaidasu a cikin taron nan ni shine ya burgeni da ita a wurin wallahi ko duk ko yadda ido yake a kanta ba. Sahiba ta koma ubanta sak a yanzu muryan mommy datayi tagumi ta fada cikin nisawa da nauyi kafin ta fadi hakan duk suka kallota. Wallahi yau ganin yarinyar nan ya daga min hankali sosai bani ba son duk wanda ke wurin nasan abinda ke zuciyar shi ke nan idan ya tuna. Muryan yayansune yayi sallama duk suka kalli kofan shigowa falon nasu lokacin guda ya shigo suna mashi sannu da zuwa. Saida yagaida mommy a cikin mutunci ya samu wuri ya zauna ya fara amsa gaisuwan kannen nasa a lokacin. Yana ce masu ya bukin ashe har an fara ke nan ko hauwa ta amsa mai da kai kafin tace tun jiya yaya muna ganin bukin yan gayu ai. Faiza ta fito daga dakin cikin murna take mai sannu da zuwa ta zauna a kusa dashi ta fara fadin yaya mu Sahiba fa tazo garin nan wallahi. Sahiba ya fada a cikin mamaki yace ina kika ganta tace cikin fara,a wallahi wai bukin ne ya kawo su tace amma bata sauka gidan nan ba kuma ta karasa fadi cikin bacin rai a fuskan ta. Ita dawa tazo da mama da Amar kanin ta ya tambaya yana boye razanan shi a fuskan shi lokacin. Kai ina kakai yara nan ka tayarwa mutane da hankali haka anya kana son ganin farin cikina kuwa yanzu modibbo ? Yara mommy wasu yaran ke nan ta watsa mai harara kafin tace ai sainace yaran ka zaka gane ko ? Ya dan shafo fuskan shi kadan zuwa kasa yace suna Abuja gidan abokin aikina na kaisu tunda ita bata damu dasu ba. Baka da hankali ina gani yanzu modibbo da har ka tsaya biyewa matarka mara tarbiya ka aikata hakan bayan kasan hakan zai jefamu a wani hali na tashin hankali. Kuyi hakkuri mommy nasan a lokacin idan na kawo maki sunan zakice ne a mayar dasu wurin ta a lokacin ni kuma ina son nuna mata ita ba kowa bace yasa na dauki matakin hakan. Yanzu kai wani irin yardane tsakanin ka da wanda kakaiwa yaran har ka yarda zai rikama yaran tsakani da Allah ku dinga yin tunane kafin aiwatar da abu wallahi. Abinda za aje a dawo ana da ansani a kansa bayan lokaci ya kure baida dadi duk da dai itama din Nazifan halinta sai Allah ne amma wanan matakin baiyi ba wallahi ta karasa cikin bacin rai sosai ta mike ta shige dakin ta. Suka bita da kallo kafin hauwa tace dashi kayi hakkuri yaya har daddy saida suka samu matsala da mommy kan wanan zancen don shi daddy wai laifin mommy yake gani yanzu . Amma dai ita mommy ai bata kula mashi ba tunda neman abinda zai tunzurata ta cikin taron nan yanzu yakeyi . Wani kallo yayi wa yarinyar yai shiru bai kara cewa komai ba yashiga dogon tunane mai zurfi kafin ya furzo da iska daga bakin shi yana fadin. Naso a ginawa mommy gida ta bar su nan amma kuma hakan ba abinda zai yuyu bane don shi kanshi daddy ba zai yarda da hakan ba sam. Kaima yayan mu kasan ba zai yarda da hakan ba ai don yasan duniya zata zageshi kawai dai mommy tayi hakkuri da sabon sauyin data samu a wurin shi yanzu don anty da kuke gani ba karamar shu,uma bace. Kai ku daina irin wanan zancen zargine da camfi irin na mutane sai mutum ya daukarwa kanshi zunubi a banza irin haka. Yaya kai namiji ne baka ganewa wallahi amma muda muke zaune a cikin gida mun san abinda ke gudana ai Nabila ta fada cikin bacin rai da damu kan irin cusgunawan da mahaifiyar nasu ke gani yanzu a gidan. Bai kara magana a kan zancen ba sai tambayan daya jefowa Faiza data zauna a gefen shi itama cikin damuwa don irin rayuwan cin fuskan da mahaifiyar tasu take gani a gidan yanzu abin yana damun kowan su a rai. Yace Sahiba din tace zata kara dawowa nan ne ko sun tafi ke nan tace zata gobe da yardan Allah don bamu ko zauna da ita ba a gidan gwaggo hari inda akai event din muka hadu da ita tazo da Alheri sosai yaya taba kowa mamami bakaga irin kayan rabo da takawo a wurin bane yaya . Na fada maki sahiba ta canza a yanzu don babba ma,aikaciyace Sha,aban comoany ga baki daya inda yake da reshe cikin kasan nan itace mai kula da shige da ficen komai a kasa. Sahiba din kwarai kuwa ita din ba karamar mace bace a yanzu gaskiya duk abinda kukaga tayi kada kuyi mamakin hakan tanada oppotuniy din yin hakan gaskiya don ta wuce sanin ku a yanzu. Kinji ina fada maki kina cewa wai maza takebi kila in bashi ba ina zata samu kudi irin haka take wanan abin yanzu kinji ke nan da kunnuwan ki hauwa ta fadawa Nabila din. Kallon mamaki yayi mata kafin yace ke yanzu ashe ba mai tsayawa kiyi fada bane idan wani ya fadi haka akan yar uwarki ashe ? Kai yaya wai idan an tashi zancen yarinyar nan kai da mommy sai ku dinga fadin cewa yar uwanmune su ta ina muka hada dangi da jikan yarbawa wata kila dai mahaifiyarta ce yar uwan su daddy ta can wurin dangin danga kawai ace wai muna da hadi da wanan mai zubin larabawan don dai yanzu na daina kiranta da jikan Oduduwa ai . Jiya Allah yaya don baka ganta bace ta fito kamar yar wani kasa ba yar nan Nigeria ba shigan da tayi jiya din kasan mutane da gulma ina jin wasu na fadin ko yar abokon business din daddymu ce sukazo kara. Nabila da bakinki kike fadan haka kan Sahiba koda yake ba laifin ki bane yanzu don baki san yaya alakan ku yake da ita ba shiyasa . Amma ki daina don watarana zakiji kunyan hakan da kanki wallahi idan kin san su din ko suwaye gare mu da kuma abinda kike takama dashi a yanzu zakiji kunyan kanki a ranan yana fadin hakan ya mike ya fita kawai ya barsu suna binshi da kallon mamaki. Tsuki nabila taja tana fadin shike nan don ta zama dan wani abu a yanzu sai ayi kokarin danganta alakan mu da ita kawai haka ranan naji Mommy ta fadi hakan har da muna fada a kanta nifa na tsani yarinyar ne kawai wallahi. Don tafiki kyau yanzun kuma kinji ance ga cigaban data samu a rayuwa ko me hauwa ta fada daga gefenta me zata nuna min wurin kyau nima inada nawa dirin sai me kuma ? Shi arziki yanzu yin shi ai baida wuya idan kana aon yi ga hanyoyi nan na samun arziki lokaci daya ga mutane bila,adadin ba sai kayi wani wahala ba can. Suka hada baki suka kwashe da dariya lokaci guda suna kawar da kansu gefe daya lokaci guda don sanin halinta da sukayi wurin yaba kanta da nuna ita tafi kowa aji. Daddy yana zaune a kasa saman kafet ya mike kafafuwan shi yana amsa waya lokacin ne anty amarya ta shigo falon ta zauna don ganin waya yakeyi a lokacin mai muhinmanci sosai. Ya dago kai fuska ba yabo ba fallasa a cikin fuskan nasa ya juyo inda take yana sake dan murmushin dole da baikai cikiba yace . To ya taron naku na yau dai an watse lafiya ko ta gyara zama tana lumshe idanu tare da fadin wallahi Alhamdullahi Alh jama,a sunyi kokari sosai wallahi. Wai kasan har da Sahiba tazo daga lagos kuwa saboda bukin nan ai bansan yarinyar nan tana kaunan mu haka ba sai yau wallahi bakaga irin alherin data kawo muna ba ni ai takara jamin girma a garin nan sosai wallahi. Tarin daya sarke mijin a lokacin shine ya hanata karasa maganan da take son fadi a lokacin shi kuma sosai yake son tarin ya tsaya mai lokacin ya tambaye ta wai wace Sahiba take magana a kaine ? Ruwa ta mika mai ya amsa da sauri ya kurba kafin yadan ji sallama itako ta tsugune a gefen shi ta kura mai idanu cikin mamaki. Sannu ta kara mai bayab taga ya samu saita numfashin sa a lokacin tana kokarin kawar da kayan abincin da yaci a gabashi. Ta kara fadin wai sannu Alh irin wanan sarkewan haka wata kila yajin ne yayi ma abincin yawa don naji su hjy suna korafin hakan yace umm,umm. Saida ya dauki yan mintina suna shiru a falon kafin ta mike tana fadin zan koma wurin baki dama nazone in fadama zancen sahiba din ne. Wai wace Sahiba dai kike maganane tun dazun haka ta koma ta zauna tana mamaki tare da fadin a, a Alh akwai wata Sahiba da muka sani da wanan sunan bayan Sahiban maman Ammar na lagos da suka zauna gidan nan shekarun baya. Ita nake nufi wallahi sai gata kwatsam a wurin taron Alh wai kaga Sahiba ko yanzu kuwa wallahi idan bata fadi ba kokai daka santa baka ganeta yanzu Allah ko. Ni ai yau naga abin mamaki sosai kuwa Alh duk yaushe Sahiba tabar nan ne amma gata da gani a cikin daula take rayuwa yanzu gaba daya komai nata ya canza wallahi saita fadama itace zaka tuno da fuskanta na baya can. Sallaman modibbo ne ya katse maau hiran ya shigo falon don ya gaida mahaifin nasa anty Amarya ke fadin a, a ashe ka dawo ke nan masu tafiya babu sallama kabar hankalin mutane a tashe. Ya danyi murmushi yana kaiwa tsugunne tare da fadin mun samemu lafiya ya taron jama, a Allah ya sanya alheri yasa wurin zamantane har abada suka amsa da Amin anty baki har kunne tana washe shi don dadi. Sam sam a gidan basu kula da abinda aka rubuta ba a cikin jug din da kofunan sai ga kira a lokaci daya ya fara shigowa a wayan daddy kiran baffa Abdullahi ne kanin daddy ya dauka . A zaton daddy zance zai mai akan daurin aure amma sai yaji Baffa din na fadin yaya kana gidane wai ? Eh gani nan zaune a falo ya bashi amsa yace kajirani gamu tafe da salau yanzun nan muna hanya ya amsa da to ya kalli modibbo yace dashi . Tsarin da kuka dauko dakai dame dakin ka baku dauki tsarin kwarai ba ace mutane kullun babu zaman lafiya an fada maku kowa ba hakkuri yake da iyalin shi ba yanzu ina amfanin biye matan da kayi ka kwashe yara ka tafi dasu ka kuma kashe wayan ka ba a samunka ka tayarwa mutane kawai da hankali haka ? Kanshi na kasa yana sauraren mahaifin nasa ne yaji sallaman kanin mahaifin nasa a kofan falo har lokacin Anty Amarya tana wurin a zaune. Kowa kallon kallo aka fara a tsakanin su ganin yadda suka shigo falon a lokacin kamar a firgice ina yar uwanki Baffa ya tambayi anty Amarya tana ciki ta bashi amsa yace kira min ita kizo da wanan abin bukin da kika ba matana dazun a gidan hari. Ta dago tana mamaki kafin tace wani ciki yace wanan anbin me kamar flask ma da akace watace tazo dashi kika basu akan sai gobe zaki raba saura. Oh nagane jug din da Sahiba ta kawo ke nan a raba gaban daddy ya bada ras ras haka na modibbo din yace ko bata nuna maka abinda muka gani a jug din rubuce bane ? Yanzu dai take fada min an kawo mata gudunmawa sai ga wanan ya shigo shiya hana ta karasa fada min to bari a kawo kaga abinda muka gani a ciki na firgici. Kai bamu wuri Daddy ya fada da cewa ya Abubakar ya fice ya basu falon sai baffa yace inafa zashi tunda wanan abin a yanzu ai ya shafi kowa a nan nake gani sai ga hjy karima ta shigo dauke da samfur din jug din dauke a hannun ta tana bude ledan tare da fadin. Koba wanan ba ai Sahiba ta kashi kudi a nan wallahi shiko ya Abubakar sai fadi yake a zuciyar shi me sahiba ta aikatane yanzu ? Mikawa mijin ki Baffa yace da hjy karima daidai mommy na shigowa falon ke nan suke wanan magana tana gaida su hannu kawai baffa ya daga mata yana nuna mata wurin zama . Kafin ya juya yanacewa daddy ka duba daidai kasan inda akai rubutu zakaga me aka rubuta a jikin kofin nan na hannun ka COURTESY, SAHIBA SAMBO NAMADI & AMMAR (YUSUF) SAMBO NAMADI, , , , , , , , , , ANA DARA GA , , , , , , , , 6️⃣8️⃣ BY, , , , , , , , , , , , ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , , , , , , , , BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AL MATIN, , , , , , , , , , ONLINE PAID NOVEL YAR UWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA BA TARE DA HAKKIN KOWA BA DON BIYA KI TURA DARI BIYAR 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK 08036959257 ALLAH SARKI AI RAINA BAYA BACI YANZU DON KIN FITAR DON NASAN AKWAI RANAN HADUWA SEE U👋👋👋👋 Tafe yake cikin tako irin na mazan zamanin da suka san kansu a cikin isa da izza ba sai ya fadi koshi wani bane a wajen wayewan don kallo zaka mashi kawai hakan zai nuna kansa. Ba komai yasashi cicika da shakan iska ba a yau sai zancensu da maminsa data tare shi dashi da safe na wai ga Nabila nan ita take son a hadasu don zumuncin ta da dan uwanta ya kara karfi a tsakanin su bayan na diyar gwaggo Asiya da muka sha biki a baya. A cikin mamaki yake fadin wata Nabila dai mami yana tambaya a cikin mamaki don shi indai Nabilan daddy ce sam bata taba burgeshi ba yarinyar yaji mami din tace Nabila dai yar wurin yayana Aliyu mana daka sani ita nake nufi kasan dai mutane suna fadin dani take kama ko sosai kaima kasani ? And so what mami don kuna kama ai bake din bace don ni bata taba burgeni ba a rayuwan duk da kaman da ake fadi ta dan kwaso ki. Asalima dai ni ban taba jin kowan su yan dangin nan acikin zuciyata ba gaskiya mami na fada maki idan na tashi aure ni da kaina zan kawo maki yarinyar har gidan nan insha Allah amma ni ban faye son wanan aure na hadin da kuke son ayi ba garama idan kai ka gani kace kana son abinka. Jin hakan mami tayo kanshi tayi mai kaca kaca a lokaci har hakan yasa ya guda ya dauki key din motarshi ya fita zuwa hotel yaje can ya kama daki ya wuni a ciki yana barcin shi hankali kwance don sanin gidan nasu yau da taron jamma, a. Sai yanzu daya dawone kuma ya samu iyayyen nasu dukansu biyu kamar hankalin su a tashe yake don yaji mami dake rike da wani flasks a hannun ta tana juyawa take fadin gaskiya Alh abinnan yana da mamaki sosai amma haka kawai yaya sunan zaizo daya da nasu haka. Idan ba diyan marigayi brother bane ta yaya zasu rubuta sunan shi da Sahiba Sambo namadi da Ammar sambo shima dayan ? Jin sunan da mahaifiyar tasu ta kirane yasa ya dago kai yana kaiwa zaune saman kujera ya dago a cikin girgiza don jin abinda mami din ke fadi lokacin yana mata kallon mamaki. Kasa hakkuri yayi yana fadin wace Sahiba dai kuke magana a kansune yanzun mami badai Sahiba dake lagos zaune da kaninta da mahaifiyan ta ba wace tayi zama nan garin gidan daddy shekarun baya ? Wani kallo iyayyen nasa suka jefo mashi mai dauke da tambaya uwar tace kasan sune dama ? Ya dan kada kai kafin yace kwarai kuwa sanima na sosai tun tana karama tana talla a lokacin nasanta a lagos. Sai kuma yai shiru kan abu biyu daya tuna na farko kallon da iyayyen nasa suke mashi sai nabiyu yana son sanin akan me ake maganan su yanzune wai ? Wai dama mami kin sansune wai ? Ya tambaya a cikin mamaki kamar ya nasan sune kake min wanan tambayan hauka a yanzu kuma ? Indai wace kasani ne abaya din itace yanzu ta bullo muna da wani zancen daya dade da shudewa a garemu cewa wai ita din diyar marigayine yayan mu dan gidan Baffa namadi marigayi ne ita. Da wani irin mamaki a fuskan shi ya dan dago daga saman kujeran da yake kai zuwa bakin kujeran yana fadin . mene mami kika fada Sahiba dai da kaninta diyan uncle dai dana sani wanda aka kashe aunguwar mu na farko sai kuma ya koma ya mayar da jikin shi saman kujera da kyau yana lumshe ido kafin can ya budesu yana fadin ? No wander nake ganin yaron nan Abubakar ko yaushe tare dasu wani lokaci ashe yasan irin halakan dake tsakanin sune amma aini basu taba fada min komai ba kan hakan. Kuma is hard inshaga lagos banje wurin su ba don haka kawai Allah ya hada jina dasu don suna da kirki sosai kuma suna ban tausayi abinda ya hadani dasu ke nan tun farko ba wai nasan kosu suwaye a gareku ba. Zuwa lokacin da yake zancen wani irin kallo iyayyen nasa ke mashi a lokacin na mamakin jin abinda yake fada mai kama da almara a bakin shi. Hakan bai dameshi ba yaci gaba da fadin ashe gaskiya duk haduwa uwar da yaran zasu tambayeni ke suce a gaidake sai na dauka kulawane hakan kawai suke nuna min ba tare daya damu da canjin yanayin mahaifiyar tasa ba a lokacin. Wani irin kuka mami din ta fashe dashi tana fadin yanzu dama mairo tana raye ashe su yaya sun sani basu fada muna ba ? Gara da bai fada ba din don karshe sanin ba zaiyi dadi ba a lokacin yanzu ko sunyi sake da alama dan zaki ya girma don ANA DARA GA DARE YAYI NE A YANZU KAN A WANAN GARIN. Gidan Alh Nuhu da shima iyalan shi sun samu kyautan a wurin hjy karima don yan uwa masu ido da kwali ta rabawa kyautan a ranan ba, aba yaku bayi ba wai sai gaba. A babban falon gidan matan shine da yaran su suna rike da gifts din a cikin jimame sai nanata sunan da maida magana kan yadda sunan yazo daya haka. Don su abinda yasa basu yarda wasu nasu bane sunan Ammar din a sanin su ai ya dayace a lokacin kuma sunanta Fatima sunan mahaifiyar shi Sambo din ke nan aka sakawa yar ana kiranta da maamah. Wanan kuma ance sahiba take da Amar shine ya dan rudasu a lokacin don haka basu yarda ba sunane kawai yazo daya dai amma ina aka samo Namadi din kuma shi suke muhawara a kai yazu. Yo idan ita dince ma sai me tunda su basu kula da mutane ba mune zamu bisu haka kawai ai akace sun bar gida muguwa mata kawai duk a ance basu ma raye a yanzu ai. Hjy salma bakanuwace mahaifiyar Nazifa matar ya Abubakar itace ke wanan zancen don a watse a bar maganan don sunyi har ya ishesu a lokacin ta gaji. Guduwa fa tayi don sheri mutuwan mijin ki da yan kwanaki ki kwasa ki gudu ai ta gamu data Allah a can ta mutu a wullakance cikin duniya. Inma yarce bata mutu ba ta dawo wa zai yarda da ita a yanzu tunda bata da shedan hakan kumama ai bata san komai ba yarinyar dake karama sosai a lokacin me zata karas a lokacin. Gyaran muryan maigidan da yakeyi naku natsu gani tafe yasa wasu suka kwasa da gudu wasu kuma suka zauna a tsorace sun kasa gudu lokacin. Sannu suka fara mai suna mikewa bai tsaya ba basujin kuma ya amsa masu ya shige zuwa part din shi kai tsaye. Matan nasa ne suka kalli juna lokaci guda suna fadin kada dai ki fada masa wanan labarin yau son ba zamu sha da dadi ba gidan nan kin sani laifin daba namu ba ya shafemu mai suna Ladi din dake da girki tace waya aikeni aiken fadin mutuwan sarki ba a bakin Ladi ba kan. Daddy ya gama karantawa ya dago kai yana kallon yan uwan haihuwan nasa da matan shi kafin yace tabbas nagani diyan Sambone ba karya sukayi ba . Kafin ya dukar da kai na dan wani lokaci ya dago yana fadin ku koma dakunan ku wanan zancen mazane ai bai shafeku ba. Baffa Abdullahi yace wai naga saboda su akace yar tazo wirin taton a yadda mata suke fada min kafin inzo don ma ban tsaya sauraren suba nayo nan. Su tafi daga baya saji duk yadda akayi daddy ya fada cikin daure fuskan shi lokaci guda haka yasa suka mike hjy karima zuciyar ta na cike da tambayoyi akan hakan banda mommy da tasan komai wanan ranan takejiwa gashi ya fara tunkaran su a yau din nan . Allah ya gani wanan hanin da taiwa yarinyar a ranan dama ya daga mata hankali sosai tunda gabanta ya fadi har lokacin take jin kanta a wani irin yanayi na daban. Modibbo ma ya mike zai bi bayan mahaifan nasa yaji muryan uban na fadin ina kuma zaka ai sai ka tsaya kai masu bayani don shi ya san komai akan ganin su din can Ikko. Ikko suke suka tambaya yace kwarai amma yanzu bansan a inda suke ba tun bayan da nasan ganin nasu ba alheri bane ga ahalin mu ga baki daya nasa ya mayar dasu a lokacin baki a laikum basan yadda akayi ta dawo ba yanz. Baffa Abdullahi ya gyara zama yana fadin af tunda tasan gida me zai hana ta dawowa kuwa a yanzu ni a ganina tunda sune ai sai a nemesu kawai yanzu zaifi. No ku bari ku gama da jama, a zaifi sauki modibbo ya fada a kausashe ga iyayyen ido tar ba tsoron komai a lokacin mahaifin ya kura mai idanu . Ya mike yana fadin nasan ba zata sake dawowa ba ko wanan don Faiza da Amira da fatima tazo amma rayuwan ta yanzu ba a nan yake ba kuma. Yai masu saida safe ya fita don shima hankalin shi a tashe yake lokacin da abinda ke shirin faruwa a ahalin su don yasan mutum dadaya ne kawai rigiman bai shafa ba a yanzu. Ni kaina nasan na kashe kudi ba kadan ba don kudin dana taba din ina kokarin muna tanadine a lokacin amma ciki nayi karfin halin tabawa na labta wanan uban sayayya da nayi din na bukin. Bin tarin kayan falon na sake yi da kallo ina fadin ba zanje wurin yinin bukin nan ba umma amma da dare zamu halarci dinner da za ayi don lokacin ne nasan yan family din maza da mata suna zaune wurin . Ki dai bi a hankali don kowa ya rigaka kwana yana rigaka tashi sun fiki sanin ta kan duniya zasu iya yin abinda zai shafi lafiyan ki ko mutuncin ki kin sani. Ban fito ba umma saida na nemi sa,ata a wurin Allah don haka Allah yana tare damu ko yaushe tunda bamu da hakkin su akan mu tace wanan haka yake Allah ya kara tsaya muna na amsa da amin. Nasan Faiza ta zuba ido kuma zata kira waya bata sameni ba da yake ranan Friday ne ban jima a wurin aikin muba dana kammala komai a ranan a bangaren mu yanzu sai sammaci da za a turawa ko wanin su da dakatar da wa yanda zamu dakatar ne a wurin aikin ranan monday kawai ya rage muna kuma mun shirya yadda abi zai kasance a ranan. Tun bayan magariba muka fara shiri don ban son zuwa da wuri sai wajajen goma na dare tare da duk abokan aikina na da muke tare na gaiyace su don haka su zasu mara min baya a wurin an kuma tsara ga yadda abin zai kasance damu tunda rana. Yadda nake shiri haka aka wuni da kuskus a wanan wunin a gidaje da dama saidai abinda ke daure masu kai bai wuce tambayab kansu da sukeyi har in mune toshi dayanyaron fa dan waye ? Gabin ban zoba yinin bukin sai aka fara share zancen wasu sun manta da maganan amma manya kan yana a cikin zukatan su fam. Annoucement din da aka farane a wurin ya jawo hankalin mutane inda Bello ya samu sayen mc din da kudi mai yawa ya fara shelan sanar da mutane dake wurin zuwan mu hakan yaja hankalin duk hall din a lokaci guda. Ga sanarwa ta musanman ga amarya da ango cewa kanwar ango kuma yaya ga Amarya miss Sahibat Sambo Namadi yar uwa ga ango da amarya ta iso wanan wurin da tawaganta daga lagos zasu shigo don taya amarya da ango murnan wanan ranan. Ya Abubakar dake zaune shi da nazifa da sai ranan daddy yasa yaje ya dauko ta ba wani musu yaje gidan yayi sa, a Alh Nuhu baya gida ta biyoshi suka dawo har lokacin da suke zaune wurin dinne din ba wani sakewa a tsakanin su. Yayi wani irin juyowa shi tsorin shi a lokacin kada inzo da yaran shia san suna wurina yaji amma bana shigowan mu ba don yasan a yanzu zan iya yin fiyema da hakan ai yasani a yanzu. Cool music aka saka na hakan ya kara jawo hankalin mutanen wurin kowa na baza ido yaga wanan da aka fada an bude muna hanya sosai don aikin kudine bamu shigo ba saida aka shirya komai na shigan namu. Mazan saye suke a cikin suit mata mu hudu matar Adnan muniya da yemisi saini sai mazan majiya karfi wurin su goma a bayan mu dauke da manyan sacks dake dankare da kayan rabo. Kallo ya koma kanmu ina tsakiya sai walkiya nakeyi don bakin kayan dake jikina dare ne suna da shining dake sasu walkiya dinkin rigace daya matseni sharp din cock cola dina ya fito a fili kaina yasha ado shima ga sarka mai dan karen kyau a wuyana yana walkiya. Murmushi na fara duk table din da yan uwan mu suke kamar an fada min sai na dagawa mutanen zaune hannu hakan kuma baisa na tsaya sai nufar inda amarya da ango suke nakeyi sauran na bina a baya. Ganin na hau steps din inda suke zaune yasa suka mike Baby ta haroni da sauri ta fada saman jikina na dan bude idanun ta ina share mata fuska kafin inji muryan angon na fadin sannu da zuwa yar uwa na juyo gareshi har lokacin ina rugume da yarinyar a jikina tana dan kukan da bansan ko na meye ba a cikin harshen turanci nayi mai magana dashi kadai yaji menace ya danyi murmushi na nuna mai abokan aikina suka fara gaisawa dasu itama nasa ta gaisa da matan abin da muka shigo dashi yan matan dake tare damu da samar suka fara bi table table suna ajewa nan take wurin ya rude da hayani har muka samu gaba dayan mu muka sulale daga cikin wurin ta kofan baya ba bata lokaci muka bace wa kowa dake tare da mamaki. Kuwa bayan yaki don an turo wai abi bayan mu saidai ko kuran motocin mu ba a gani ba har na masu rabon kayan da aka raba din wanda shi ya dauke hankalin mutane suka hargitsa wurin jakkane wani dauke da kayan wanka wani kuma kayan shayi wani riga mai hoton amarya da ango haka kayan sukazo launi launi duk abinda ka samu shine rabon ka. Gara kafito kaji meke faruwa don abune daya shafi Sambo namu marigayi dai daka sani jin hakan ya tsaya sauran wayan har ya fito a gigice cikin dakin suke zayyana masa abinda ke faeuwa wai ashe tun jiya yarinyar ke barazana a ahalin mu amma an rasa wanda zai fada muna wanan zancen. Kai Sani kaga yarinyar ne da idon ka wanda aka kira da sanin ya gyara zama yana fadin umm,humm bari yayace wallahi naganta buhari ma ya ganta kama da uban su sak saidai don ita mace ce kawai ta dan bambamta da uban amma namjin kan ai kakine kawai na Sambo din. Kayan dake gabanshi ya kalla kamar mune kayan irin kallon da yaiwa kayan lokacin kafin ya nisa yace aikin banza ke nan har inma gaskiyane kowan ku nan ai yasan Sambo baida da namiji ko ? Alh ba wanan zancen a yanzu kamata yayi mu fara sanin waye wanan yarinyar wai kuma a ina take zaune amma kafin nan dole muga Ali dcp muji komai. Kuna bani mamaki wallahi matar nan da yarta fa wurin malamai bakwai sun sheda muna sun mutu kuma malaman nan ba wai hadin baki bane sukayi tunda ba wanda yasan wani a cikin su kuna nufin hakan karyane ke nan. Saidai dama idan ya zauna da watace acan daban irin zaman bariki tunda kunce yarinyar kamar kabilace ai haka yake don gaskiya shiganta kamar na kabilune nagani buhari din ya fada a sanyaye kafin ya fada cikin tunane. Falon ya kara shiru na tsawon lokaci karan wayan Alh sani ne yasa kowa ya daga ya kara wayan a kunnen shi yana amsa sallama tare da sauraren bayanin maishi din wanda ya kirashi a lokacin. Abinda ya fada tun kafa wayan a kunnen yasa su kara mayar da hankalin su wurin Sani din da yake fadin dama nima nayi zargin shi dcp Aliyu din don in bata da alaka dasu tun farko me zaisa har tazo bukin yar su yanzu? Ya kashe wayan bayan ya gama sauraren na cikin wayan yana fadin kuji a yadda ake fada yanzu wai yarinyar ta zauna a gidan Ali dcp na wani lokaci kafin su koma inda suka fito. Yanzu kuma wata babbace ake gani ko wani babban mutum a can kudu take aure amma dai za a binciko min ko yar Sambo dince ta asali. Shirmen banza ke nan shirmen wofi nifa duk wanan zancem a shirme na daukeshi a wurina sam ba zai yuyu ba son wanan rudani da kuke nuwa sai a gane da wata a kasa . Idan har yar Sambo dinne tazo mana mu kawar da ubantama balle ita me zata iya yi damu yanzu kuma ? Ina abinda dai kuke tunane ke nan sannan shi Alin har in shiya kulla wani makarkashi na zuwan wanan yar aiko shi bai tsira ba a cikin zancen Alh Nuhu ke wanan maganan rai bace. Falon yai shiru yaci gaba da fadin yanzu dare yayi koma me ke nan sai a bari har zuwa safe ba sai muga shi Aliyun muji gaskiyan maganan a bakin shi ba. Kallon shi Buhari yayi don jin abinda ya fada na a gaja dashi Aliyun aji me zai fada game da zancen don su san matakin da zasu dauka. Karfe biyu saura sai alokacin suka fito kowa ya shiga motar shi ta alfarma da sukazo gidan dashi zuwa gidajen su ciki da zargi da tunanen wani ne keson ya kulla masu shiri kaqai da hakan. Yadan dade a zaune yana tunane kafin ya mike zuwa wani daki dake part din nasa ya rufo kofa ya fara abinda yake sonyi a dakin lokacin ZAINAB IDRIS MAKAWA ANA DARA GA , , , , , , , , 6️⃣9️⃣BY, , , , , , , , , , , , ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , , , , , , , , BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AL WALAIE, , , , , , , , , , ONLINE PAID NOVEL YAR UWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA BA TARE DA HAKKIN KOWA BA DON BIYA KI TURA DARI BIYAR 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK 08036959257 ALLAH SARKI AI RAINA BAYA BACI YANZU DON KIN FITAR DON NASAN AKWAI RANAN HADUWA SEE U👋👋👋👋 Bayan mun firfito daga motan na tsaya nayi masu godiya sosai tare da basu abin rabo ba tare da sun san abinda ke faru ba don Abdul ya fake ga fadin ba,a son asan inda nake zaune yasa zamu nuna hakan a wurin. Kowa ya nufi bangaren shi kafin na juya muka shiga ciki nida Amar muka rufo gida su umma suna falo yaran duk sunyi barci saman jikin ta muka samu wuri muka zauna har lokacin sai sannu da zuwa take muna. Ammar ne ya fara bata labari yana tambayan ta da umman mu duk taron nan ana nufin su din yan uwan mune wai ? Haba dai na fada daga inda nake zaune ina cire sarkan wuyana don na riga na cire dan kunne ko alokacin . Nace duk wanda kaga na gayar sune yan uwan mu na jini saura kuma abokan arzikine da suka zo tayasu murna kafin na juyo ina fadin amma umma nayi mamaki da daddy ya aura wa karamar yarinya kamar baby wanan mashayin haka ? Jam ta fada mashayi kuma nace kwarai umma don har ta hudashi ma zaki gane hakan a jikin shi kinsan ni bana shiri da maishan wanan abin sam don haka naganeshi da sauri. Allah ya kyauta ta fada a karshe muka amsa da amin sai tace yanzu dai saura mu saurari abinda zai biyo baya ke nan don nasan dole su nememu yanzu kan ruwa a jallo. Zasu nema sosai ma amma ba yanzun ba sai an daura aure gobe wanan zance zaiyi boosting ga kowa don zasu hadu a wurin ne za a fara wanan maganan daya shafemu din don kowa yanzu haka yana cikin wasiwasin ne a zuciyar shi kan mu. Waya ta na mika hannu na dauko daga cikin jakata na kunna sako suka fara shigo min da sauri na dauko na duba ina karanta sakon da nagani daga oga sha,aban ce yasa na bude sakon da sauri ina karantawa. Katin gaiyatane na bukin kammala karatun kanwarshi tilo daya da yake da ita wand za ayi a Oxford. Wanan kan ai sai manya zuwan shi na fada a fili meke nan fa umma ta tambayeni tana kallona jin abinda nake fadi a loka nan nake fada mata abinda sakon ya kumsa. Shiru tayi kafin tace dani au a can ke nan zasuyi taron nayi mata bayani dalla dalla yadda zata fahinta a daidai lokacin ne kuma wayana ya dauki kara lokaci guda. Na duba ya Abubakar ne a layin yana gab da katsewa nadaga da sallama ya amsa yana jefo min tambaya kuna inane nace gida sai naji ya sake wani nauyayyan ajiyan zuciya. Kafin yace OKey kawai ya amsa dashi yayi shiru sai kuma naji yace ki kula don kin tayar da hankalin manya sosai a wurin nan yanzu haka nemaku suke ruwa a jallo. Karo na farko da zaice yaji farin cikina har nayi dariya a fili haka yadda yaji a lokacin tun bayan dawowan shi garemu kafin nace sai su matsa idan suna son ganoni a yanzu ai da safe zan shigo gidan ki gaida umma. Don sam baiyi zancen yaran shi koda yake yadda yake magana yanayin ya nuna cewa shima dai hankalin shi a tashe yake a lokacin. Daddy tun safe ya fita daga gidan gidan amin sa ya nufa kai tsaye wanan fitan shine sauki a gare shi ranan don bai dawo ba sai gab da daurin aure Abubakar da suke waya dashine ya gudanar da komai har aka gama tsara komai yadda suke so. Hankali kan ba a kwance ba don duk taron yan uwa da zaka gani a gidan bukin suyi gungu gungu kowa da abinda yake fada inda a nan hjy karima take tsuntar wani zance ga jama, a. Hakan sai ya lankwasar da ita ga gagarumin shirin da tayi don taba mommy da diyan ta takaici a ranan don itama hankalinta bai kwanta ba ai a wurin. Saidai duk da hakan yan uwa da abokanta sunyi dan kide kide da raye raye wanda sukasa niyar yi don turawa mommy haushi da yayan ta. An daura aure an tashi lafiya baki suna watsewa ne baffan su nan biyu suka kira taron gagawa a tsakanin su yan family din. Bayan kusan duk wanda aka gaiyata sun isone sai yan kalilan ne basu wurin aka fara da addua kafin ya fara magana da fadin. Tau sallamu Alaikum jama, a duk da nasan wasun ku da dama nan sun san makasudin wanan kira na gagawa da ya hadamu nan wasu kuma basu sani ba dai. Kamar kullun kusan sai wani abu na muhinmin ya farune na musanman muke wanan haduwan irin haka a nan . Daidai lokacin Alh Nuhu ya tura hannu a cikin Aljihun shi na riga ya ciro kwankwan shaken shi ya balle ya diba ya tura a duka hancin shi biyu yana turmuzawa da kyau don ya dauki caji. Jiya zance ko shekaran jiya baiyanan wata yarinya da wasu a nan cikin ku suka kawo muna labari tazo da barazana a gare mu cewa ita din da kanin ta yaya ne ga dan mu kuma dan uwanku marigayi sambo daya rasu a shekarun baya daya shude. Nan aka fara dan hayani a falon tsohon lokaci guda kowa da abinda yake fadi a lokacin don wanan bakon lamarin da akazo dashi din. Ko tana da hujjan fadan hakan ko baiyanar da kanta da take kokarin yi yanzu a gaban mu idan tana da hujjan hakan sai tazo muna dashi don mu gamsu da bayanin ta Alh Nuhu ya fada a kausashe. Yana bin kowa dake falon da kallo idanun sa sun kada sunyi ja sosai a lokacin kowa yai shiru a falon yana sauraren shi don bai magana wani nayi ko don dole a kyaleshi ya gama. Yaci gaba da fadin wanan zancen banza da wofine ai ta bijiro muna yanzu wai ita din yace ga dan uwan mu a sanin nan kowa yasan Sambo ai ya dayace gareshi sai matar daya bari daya. Ita kuma akarshe tabi dare ta gudu a ranan da abin ya faru yasa muka fara zargin ko itace ta kashe shima ta gudu kuma. A iya bincke mu gano inda take har malamai bakwai mun gani kan hakan wurare daban daban suna sheda muna duhu suke gani ma,ana dai bata duniyan nan daga ita har yarta kuwa. Don me yanzu wata yarinyar banza can yar duniya ga yadda akace ai wanan din kamar kabilace ma ita to a waje ya haife ta ko me bamu sani ba ? Wanan kuma ka fadi ba daidai ba yaya don ba zamuyi saurin sheganta yar nan a yanzu sai idan mun tabbatar da hakan baffa Hamza ya fada wani mai ra,ayin rikau ne shi ba ruwan shi da kowa a cikin su. Wani kallon shi Alh Nuhun yayi kafin yace duba Hamza kada kayi kokarin kawo muna zancen da baida hujja a nan ko kadan abinda muka sani shine Sambo dai ya rasu haka kuma iyalin shi duk munsan basu raye a yanzu. Wanan ba gaskiya bane kan don har in kana tunanen hakan ka daina komai mai iya yuyuwane a yanzu idan yarinyar nan tazo da hujja mai karfi ya tabbata ita din da kanin ta din yayan marigayi din ne ke nan. Ta kawo hujjan mana ko ta baiyana nan agaban mu idan ta isa ita din tsagerace muna sauraron ta ya sake fada rai bace kowa dai nan yasan mairoce matar sambo yau ina mairo din take. Zata ko zo har mairo din baffa Abdullahi da tun dazun yake son yin magana yana shakkan abinda zai fada din a wurin sai yanzu Allah ya bashi ikon fadin hakan kowa ya kallo shi. Kwarai zata zo har mairo din da kuke fadi a yanzu mairo bata mutu ba tana raye don ance kwanakin baya suna cikin harin nan ita da yaran kusan shekaran biyu a nan kaduna gidan dcp zaune. Meka fada yace kwarai yau da safen nan Addah ke fada min komai don tayi shirune da bakinta bisa bin umurnin shirin mijinta da yace kada ta nuna kosu din waye a gare su taja bakin ta tayi shiru bata fada ba. Ta fada muna duk yadda a yanzu kuke tsamanin wasan ya wuce nan sin ashe mairo ta tafi da ciki a jikin ta wanan cikin shine wanan yaron da kuke tantama akan shi. Ita Addah ta fada maka hakan yace kwarai da gaske kuwa bani kadai ba dani da Hamza da sani da Hari da Asiya yau da safen nan a falon ta. Lalai kuwa zamu zauna da Addah kai zancen nan fa yafi shafuwan mu a nan nake gani baku kadai ne zaku nuna damuwan ku a kai ba kawai. Amma dai muna da hakkin cikin wanan zancen kuma kamar yadda kowan mu nan idan ya mutu ya bar baya kowa zaiyi hakki a kai don kula da abinda dan uwa ya bari hamza din da yake karami cikin su ya fada. Kwarai kuwa baffa Buhari ya fada wanan maganan haka shike hamza don haka yanzu ya kamata ace mun samo ita mairo da yaran nata don samun gamsashen sheda a wurin ita mairon. Abinda nagani ke nan baffa Abdullahi ya fada don zancen manya sunyi shiru sun bar matasan kannen su suna magana a lokacin. Samun su yanzu shine shawara na gaba baffa hamza ya fada sai Abdullahi yace baida wani wahala don wanan yaron moddibo da dan wajen hari sun san da ida suke zaune a can ikko. Ikko fa Alh Nuhu ya fada a cikin mamaki yace kwarai a ikko suke zaune ashe duk wanan dadewan haka tana ikko zaune ashe. Amma indai hakane Ali dcp ya munafunce mu ai ba haka mukayi dashi ba ya fada a cikin subutan baki baffa hamza ne ya dawo mai da tunanen shi yace yaya kukayi dashi muji ? Wani banzan kallo ya jefawa kanin nasa yace baka isa ba kuma in fada maka don kai hamza da nake gani nake hango zallan bakin ciki a idon ka baka isa ka titsiyene nan in fada maka ba yanzu. Dan dariya hamza din da suke daki daya da hjy Addah ya kwashe dashi don shi lectura ne a A b u zaria a lokacin boko ya gama ratsashi ko sosai shi yasan abinda yakeyi sosai. Maganan shi sam baiyi wa wasun su dadi ba amma kuma manyan sun tsaya ga maganan shi hakan yasa Alh nuhu rufe kowa da fada har yana fadin shine dai babba a nasu zauren don haka ko anki anso dole abi anbinda ya fada don haka bai yarda da zancen wai mairo ta dawo da iyalin ta ba ai dama ba wanda ya koreta don kawai tana zargin kanta ai tagudu ta shiga duniya. Jin hakan matasan daga cikin su suka mike suna fadin maganan shi zancen banza ne shima ai ina ya taba jin haka idan diyan cikan kane zakace mu wofintar dasu a cikin duniya ne ? Ranan dai an fara kaiwa inda ba a son akai don dama matasan hudu sun dade suna jin zafin irin cin zarafin da yakeyi a cikin Family. Ranan kan gaskiya an tashi wanan taron ana kaiwa kaiwa abinda bai taba faru dashi ba ya fadi har wasu tsageran kanansa suna mayar mashi da amsa bako manyansu ba a cikin su. Haka sukayi wanan satin a cikin rigima sai kus kus sukeyi a tsakanin ba wanda ya isa ya fito fili ya fadi don basu samu kan daddy da iyalan shi ba balle suji wani abu a wurin su suna fama da sallaman bakin su da sukazo buki lokacin. Safiyan litini kuma a wurin aiki tun safe bello yana get din ma, aikatan dake shigowa yana sane dasu idan zaka shiga sai kayi signed idan sunan ka na cikin wa yan da aka dakatar ya baka takardan dakatarwa ba bayanin komai sai idan kaje ka karantane zakaga abinda aka rubuta ma a ciki. Karfe tara saiga Oga Bala ya shigotun daga nisa yake mamakin ganin an rufe get din ma,aikatan yau haka ya karaso har get din zai hau maigadin da fada yaga bakon fuskane a ranan don bai sanshi bama kwata kwata a cikin ma,aikatan nasu. Malam ka fito ka duba can indan an yarda ka shiga sai a bude ma ka shiga mutumin ya fada cikin rashin ko inkula da abinda ya fada. Fitowa yayi daga motan yazo yana kokarin bude get din a cikin fada sai ga wasu majiya karfi sun mike mutum biyar dole yaja da baya yana fadin meye hakan wai ? Meke faruwane a cikin nan yau ne ni zaku hana shiga ciki ubanwa yasamu wanan aikin duk garin nan ? Yallabai barka da zuwa aka fada daga gefen shi Bello ya kuma shedashi wurin barka da kwana rankai dade bai tsaya amsawa bellon ba yake fadin kai me ke faruwane wirin nan har banzan mutanen can suna min barazana da shiga ciki. Rankaidade ba laifin su bane umurnin hakan aka bayar daga sama cewa duk wanda sunan shi bai fito a wanan takardan ba kada yashiga ma,aikatan . Me ake nufi da hakan ya tambayi bello din a wani irin yanayi na bacin rai rankai dade gadai takardan ka karanta zaifi kyau nake gani. Zuwan chairman ne ya hana su karasa zancen shima basu yarda ya shiga ciki ba don sunayen su bai fito a ciki ba. Kafin wani lokaci kofan wurin ya koma kamar kasuwa da jama,a wasu su shiga wasu kuma a dakatar dasu daga aikin. Manyan da abin ya shafa sunyi kiran layin duk wani wanda ya kamata ace sun kira a lokacin sai dai basu samu layukan su ba a lokacin. Alh Nuhu yana zaune a falon shi suna waya da kanin sa gyade akan matsalan daya shafesu suna zagin daddy har gyade din na fadin da yau lafiyan kalau ba abinda zai hanashi zuwa gidan Ali dcp yaci masa mutunci sosai wallahi. Yaron shine ya shigo yana fadin Abba wasu mutane suna maka sallama a waje harda yan sanda a tare dasu. Yan sanda ya tambayi yaron yace kwarai don da matan yan sandan me zasu shigo gidan sai gani na iso suka turo ni. Fada ya tashi yanayi akan me zasu zo min har gida idan ma wani abu aisai su kirani inzo in samesu ya fada a cikin gadara. Yana fita a fusace hango taron da yayi ne ya bashi mamaki lokaci guda yana isa suke fada mai sunzo tafiya dashine don anyi karan shi a sha,anban company. SHA,ABAN ya maimaita sunan a cikin mamaki sunan manager din na chairman ya kira yana fadin sune sukai karana kowa ? Alh idan kaje can zakaji yanzu mu wanan ba case din mu bane case yana hannun Oganin mune can wanan ai wullakancine da rainin wayau zasuce sunyi karan mutun haka. Alfarma daya sukai mai don kasamcewar shi babban mutum yasa suka kyaleshi ya shiga motarshi zuwa headquater din su inda ake neman shi a can. Saidai yana zuwa yaga ashw bashi kadai bane mutane da dama ne a wurin case din ya shafa yaso ya nuna masu halin shi amma basu bashi daman hakan ba don sun fada mai umurni suka samu daga sama. Muna zaune kiran ya Abubakar ya shigo yake tambaya muna nan gida na amsa mashi da eh ba a dauki wani lokaci ba mai tsawo sai gashi gidan namu. Yaran nasa na ganin sa suka shiga murna saidai ya mika hannu karamar ta lafe a jikin umma tana mashi dariya babban ma tazo ta kwanta min a jiki tana boye fuskan ta. Gaidashi mukayi kafin ya fara magana yana fadin umma nasan duk kinsan abinda ke faruwa a yanzu kan gabatar dasu da Sahiba tayi ta hanyar da kowa bai tsamanin ta haka zata fitowa kowa ba lokaci guda haka ta girgiza kowa na ahalin lokaci guda. Da wanda ya dace ya sani wanda bai dace ba duk sun sani a lokaci guda abin kamar an fasa kwaine a gari don kowa zancen da yakeyi ke nan a yanzu. Saidai a gaskiya umma ba zance hakan baiyi daidai ba ko yayi daidai duba ga sanin waye Uncle Nuhu a cikin garin nan dama kasa baki daya. Uncle dai basai na fada maku ba shu,umine na gaske wallahi naso ace ta bari sai zuwa lokacin da muka shirya tunkaransa mu tunkareshi alokacin da muke da shirin mu. Amma yanzu aikin gama ya gama ko don yasan kuna raye an fada mashi kuma hankalin su a yanzu duk a tashe yake don wanan abin ya jawo rabuwan hankali da baraka a tsakaninsu sun kashi gida biyu. Nan dai yaiwa umma data sansu bayan duk abubuwan dake gudana a tsakanin yan,uwa na tashin hankali kan zancen cewa mu din diyan marigayi ne dan uwansu. Ikon Allah wanan hakikancewar haka umma ta fada a cikin mamaki yace eh saboda sun san basu shuka gaskiya bane ya jawo hakan ba komai ba. Idan ba wani abinku a hannun su ai duk wanan tayar da jijiyoyin wuyan ba za ayi shi ba ayanzu asalima ba zasu damu daku ba ai sam don kun baiyana din yanzu. Dago yarinyar dake jikina a kwance nayi don gyara zama da nake son yi inyi magana a lokacin sai naga yarinyar ashe tayi barci ne a hakan data lafe a jikina wai. Abinda ya jawo hankalin shi garemu ke nan yake fadawa umma mommy ta dameni kan indawo da yaran nan hakana don ma bukin nan ne ta daga min kafa da zancen nace dasu Abuja nakaisu gidan abokina. Uwar tasu ta dawo ke nan umma ta tambaya yace ta dawo don mommy kawai na dawo da ita saboda naga mommy tana shakun mahaifinta sosai a rayuwan tane. Dolene aji shakan wanan shu,imin mara imani don kawar da rayuwan kiyashi yafi girma dana mutum a wurin shi sam bashi da imani ko kadan. Amma umma banda ya Abubakar na fada ina jawo yar ina gyara mata kwanciya a kujera wayan shi ya dauki kara ya ciro yana dubawa sunan Nazifa ya gani ya dauka cikin basarwa yana amsawa. Hankali tashe take fada mai wai yan sanda sunzo har gida sun tafi da Abban su yace akan wani dalili tace yasir yace wai akan wani company ne na SHA,ABAN sukai karan su daddy din shine ake neman ka a yanzu gida. Daga inda yake zaune ya dago kai ya tsureni da idanun shi shanyayu masu kamada yana jin barci ko wani shauki yace kunyi karan wasune yau din nan yana mai kura min idon nashi har lokacin ? Kai kawai na iya gyada mai a lokacin don yadda yake kallona a cikin mamaki ba zan iya yunkurin fadan komai ba a lokacin. ZAINAB IDRIS MAKAWA ANA DARA GA , , , , , , , , 7️⃣0️⃣ BY, , , , , , , , , , , , ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , , , , , , , , BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AL HAMID, , , , , , , , , , ONLINE PAID NOVEL YAR UWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA BA TARE DA HAKKIN KOWA BA DON BIYA KI TURA DARI BIYAR 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK 08036959257 ALLAH SARKI AI RAINA BAYA BACI YANZU DON KIN FITAR DON NASAN AKWAI RANAN HADUWA SEE U👋👋👋👋 Hankali ya daga sosai lokaci guda don zancen kama Alh Nuhu da abokan harkallan shi ya bazu ko ina iya abinda ya sani a lokacin shine cewa. Wata yar kabilace take son ta shiga masu hanci a kundundune a lokacin take kokarin kawo masu cikasa ga harkokin su ta bata masu suna akan abinda aka riga aka saba dashi na kasuwanci da hadawa da bashi . Da akarshe dole mai bin bashi yagaji ya kyalesu dashi da taimakon hadin kan manyan ma,aikatan wuri idan sun dosheshi sai sunyi raga raga da wurin kafin su canza alkibila zuwa wani sabon wuri. Wanan yake kawo muna koma baya a cikin arewa duk wanda zaizo aiki bada sunan maishi ya karu dakai bane saidai kai ka debi rabonka kwana biyu harkan ya watse wuri ya zamo tarihi. Don haka banda kawai mu makasu kotu a lokacin babu abinda zamu iya yi don barnan da sukaiwa oga Shaaban tayi yawa sosai da har muke mamakin hakan don dole mukakai karan su kotu saboda mun fuskanci ba zasu basa hasin kai ba a samu maslaha a tsakani mudasu ba a lokacin don hakane muka yanke shawaran yin hakan ba tare da sanar da kowa ba balle a tare mu da ban hakkuri da daure bakin mu da asiri wanda kowa yasan shiyafi yawa a wanan karnin sosai a ckin al,umma. Don haka nasan zamu samu kalubali sosai kan wanan abin don haka sai naji dadin kwasan yaran da yaya yazo yi a gidan mu washe gari kawai muka bar garin kaduna zuwa lagos don karatuna da nake na masters a yanzu hutun da muke ya kare don aikin bai daukemu wani tsawon lokaci ba sosai yadda mukai tsamani zai dauke mu har tsawon wata ukun da mukai zato da farko. Mun isa lagos lafiya bayan mun gama daidaita komai anan kaduna da kano munyi warning din sabbin ma aikatan muna yanzu inda bellone zai jagorance su a yanzu. Kano kuma Adamu muka tura zai kula da can din don haka muka juya muka dawo kai tsaye lagos din bayan komai ya daidaita. Gidan mu banda dan kura da yayi ba abinda ya sameshi duk akwai aiki a gidan su manira amma hakan bai hanata zuwa ta tayamu gyaran wurin mu ba da umma tayi magana sai cewa da tayi ai mijin ta da yarane ke gyara yasa tazo nan din. Mun gyara ko ina kafin na watsa ruwa na kwanta don aikin da mukayu din na gaji sosai ke nan a yanzu watau jikina a yanzu har ya manta da wahalan daya saba dashi a baya ke nan kome ? Ban tashi ba duk da umma itama tadan runtsa amma ana azahar ta tashi bata kara kwamciya ba girki muniya tayi ta kawo muna shi su umma sukaci har aka dan aje mun don kayan freezer din mu gaba daya na kwashe da muke aiki muniya ta tafi dashi wurin su can part din su. Karfe hudu na kamala sallah na zauna na shafa mai tare da saka kaya a jikina dan simple makeup nayi a fuskana na fito abinci umma ta fara min tayi nace sai na dawo zan dan shiga lagos market in sayo muna wasu abin bukatan gida a lokacin. Ya dade a tsaye kofan namu yana danna bell tare da dan waige waige ko zaiji motsi a gidan Abdul kamar yadda ya saba ji don yana da wuya yazo wurin mu baiga wani ya fito daga cikin gidan su ba ya gaidashi ko matar ko diyan ne. Saidai ranan suma kofan su a rufe yake kamar yadda namu din yake kuma site din yayi wani irin shiru kamar ba mutane a wurin. Ya danna door bell kusan sau uku yasa shi mamakin hakan wayan shi ya ciro daga aljihun shi ya fara neman layina wayan na kashe yasa ya kira na umma din saida ya kusa katsewa ta daga da sallama a bakin ta. Tana fadin yi hakkuri ina kitchen waya na falo yasa banji ba a lokacin suka gaisa yake fadin yazo gida a rufe shine ya kira ta dan sake murmushi tana fadin . Wai a wanan gidan na kaduna ko nan lagos shima mamaki yayi sosai kafin yace lagos kuma mama kun koma lagos din ne ko ? Muna nan lagos tun jiya da safe ai muka dawo kayi hakkuri bamu samu sanar da kaiba hankali baya kwance a lokacin. Lagos umma kun koma amma bamu da labarin hakan mama naga ina gidan naku two days ago tace kayi hakkuri tafiyan ne ya taso masu haka a uzurce muka dawo nan din . Mama gaskiya banji dafin hakan ba gashi baku samu ganin juna dasu mommy ba kun bar garin koda yake da yuyuwan zaku dawo ai nake gani ko ? Banda masniya ga hakan koda zasu dawo wanan karon badani zasu dawo ba don aikin ba zai kai wanan da sukayi ba a yanzu nake gani. Shiru ya danyi kafin yace to mama Allah bamu alheri sai na sake kira ke nan ta amsa da Allah ya nufa ya kashe wayan yana bin wayan da kallon mamaki tare da furta me hakan ke nufi ke nan kuma ? Ya juya zuwa wurin motar shi ya shiga yabar site din yana jin wani iri a zuciyar shi ba dade a lokacin don sam ba haka yaso ya rabu da mutanen ba amma don me zasuyi mai hakane. Iska ya furzo tare da fasin Sahiba a fili don yasan a yanzu sai yadda nayi da umma kuma don nice ke tsarawa rayuwan mu komai a yadda ya fahinta a yanzu din. Wanan zuwan yazo wurin mune da niyar ya zauna damu ayu magana kan zancen zuwan mu gidan baffa su daddy da suka rage don su baffa hamza ne suka turoshi zuwa garemu suna son ganin mu su gana damu din. Saidai gashi yazo ya iske sabanin hakan a wurin mu wai mun bar garin muna lagos umma ke fada mashi yasan ba zanyi hakan ga banza ba dole akwai wani abinda na shirya a yin hakan ya shafo fuskan shi a karo na barkatai yana furzo iska yanzu me zai fadawa su Uncle din ke nan sun bar garin ko me ya fada a fili. Yaje ya samu su uncle din ya fada masu cewa mun tafi hakan yabawa kowa mamaki don me ana cikin wanan rikicin haka zamu bar gari kuma ba tare da kowa ya sheda zuwan mu yadda suke a kage da sugan mu din. Abubuwa da dama na sayo muna gidan ya koma kamar bamuyi tafiya ba a cikin kwana biyun da muka dawo cikin sa din. Sakon da Felix ya turo min nake zaune a falo ina faman juya tare da tunanen hanyar da zanbi in sullubewa wanan tafiyan a yanzu kuma. Tafiyace dai kika sani mai karatu dana fada maki a baya cewa muna cikin wa yanda zasu tafi labeno daga can zamu wuce bukin yaye sister shi a can england. Yar t-shirt farace ta zaman gida sai wando baki tied dake jikina na shan iska kaina ba dan kwali gashina yana daure da ribon baki mai kyau shima a kaina sai kamshin turare da nakeyi a lokacin don yanzu na saba ko bazan fita ba zan saka kamshi jikin rigan da zan saka lokacin. Tsuki naja daga inda nake zaune din ina aje wayan a gefena bayan na gama karanta sakon karshe da Felix din ya turomin a lokacin saboda list din dana karanta a yanzu. Don nasan banda wata mafita da zanyi a yanzu kuma don tabbas tafiya dani dolene ke nan duba ga yadda aka tsara sunayen mu a list din nice ta ukku a cikin list din tafiyan . Ma,ana dai dukkan mun ya committe din mu ke nan zamuyi wanan tafiyan ke nan hakan na nufin zamu fita yin wani abin ke nan a can kuma. Umma ce ta dago daga lissafin da takeyi tana fadin meye kuma nace zancen tafiyan mu daine wallahi. Tafiya akan kare karatun kanwar tashi ke nan ko me inaga dai a yanzu zancen ya sake ganin gaba dayan mune wanan tafiya din. Waya dana jefa a gefena ne ya dauki kara ina magana da umma nake kai hannu na dauko wayan ina dubawa cikin mamaki na dago kai ina fadin ya Abubakar umma cikin mamaki. Kiran ya katse nace ba kunyi magana dashi ba umma kin fada mai mun bar kaduna tace na fada mai saidau ya nuna baiji dadin hakan ba a yadda ya nuna min. Wayan ya kara daukan kara karo na biyu nayi mamakin hakan doshi baya kira sau biyu idan ya kira daya ko an dauka ko ba a dauka ba bazai sake kira ba kuma sai gashi yau ya sake kira a karo na biyu . Dauka mana kiji me yake son fadi umma ta fada daga inda take zaune na mika hannu na danna kiran tare da kaiwa a kunnena naji yana sallama na amamsa. A harshen turanci na fara gaidashi ya amsa tare da fdin uncle Hamza nason yin magana dani sunan na maimaita yadda ya fada yace eh gashi. Wani business nake dashi koma meye ya fada ma ba zanyi magana da kowan su a yanzu don basu san damu bayn kashe muna mahaifi da sukayi na kashe wayan dip. Kallon sauran yayi don wayan na a handfree a lokacin kowa dake wurin yana iya jin abindana fada mai lokacin. Eh ba mamaki idan tayi hakan tunda ba tarbiya ta samu ba dama jin wanan kalamin na baffa sani yasa Abubakar dan kallo inda yake zaune. Kai ya girgiza kafin yace duk ilahirin dan wanan zurian tamu banga wanda yakaisu samun tarbiya ba amma sai ka zauna dasu ka natsune zaka fahinci hakan . Yanzu akwai zafin mu a zukatan su don sun dauka gaba daya babu mai kaunan su amma a sannu idan an fahinci juna zaku gane cewa yaran sun samu tarbiya sosai a rayuwan su. Basu bar wurin ba saida suka yanke shawara kancewa zasu tafi lagos a karshen mako bisa jagorancin ya Abubakar da zaikaisu har inda muke zaune din. Saidai sunyi rashin sa,a a lokacin sunzo basu samemu ba ance munyi tafiya don har su umma sunje garin su muniya wurn buki don nasan bana gida yasa na yarda da tafiyan su din tare saboda hakan yafi kwantar min da hankali. Wani mamakine ya kama kowan su lokacin da wanda suka sama yake fada masu cewa ayyah ai basa nan sun tafi America tun jiya nan gaba dayan su. Kara maimaita sunan baffah Hamza yayi yana gyada kai yace America kuma yana kallon Abubakar dashi ma yake mamakin hakan . Ikon Allah yaushe har mutanen nan suka bunkasa haka kowa bai sani ba lamarin daga Allah ne Abubakar daya shiga motan karshe yake fadi. Baiwane kawai na ubangiji don Ita babban Allah yai mata wani baiwa a rayuwan ta wanda ba zan iya fadi ba a yanzu saidai idan kun ganta zaku gane hakan . Kallon juna sukayi sunzo da niyar kwana garin saidai rashin samu yasa suka koma a ranan basu kwana ba a can gida kuma suke jin labarin cewa ai yarinyar da tayi karan Alh Nuhun an nemeta don ayi sulhu ba sai anje kotu ba wai tayi tafiya zuwa kasan waje bata kasan. Baffa Abdullahine shi baffa hamza kallon juna sukayi tare da fadin kai anya ba yar nan tamu bane kuwa keda wanan aikin don yanzu haka bata kasan nan tayi tafiya itama zuwa America. Sun tatauna sosai haka labarin ya fara tafiya ai ana ganin dai yarinya dayace tazo tana juya su Alh din haka har wanan zancen ya shiga kunnen su Nabila dake zaune falon lokacin da mommy take wayan. America suka fada suna kallon juna ita da hauwa kafin suce wai Amerrica duk da ta samu aiki har wani girma da wani matsayine zaikaita wanan kasan. Mutane akwai karawa zance gishiri wallahi yanzu an shiga fadin zantuka ke nan barkatai har sai ranan da gaskiya zatayi halin ta ai Nabila ta fada tana jan tsuki a fili. Faiza dake zaune tana jin su haushi da mamakin su ya rufeta lokaci guda kasa masu magana tayi a lokacin sai mayar da hankalinta da tayi kan wayan ta sosai a lokacin. Mun samu taro na musan man a wurin su duk da hotel ne aka sauke mu a lokacin Turkeya mun huta sosai don tunda na shiga na rama sallolin dake kaina a lokacin nabi lafiyan gadon dakin da aka saukeni a ciki. Barci sosai nayi don har sunci abinci ogan mu ya shigo yagana dasu yayi masu bangajiya a lokacin sun gaisa dashi ya tafi. Washe gari kuma ya dawo da rana don ba hotel daya muka sauka dashi ba shida mahaifiyar shi a wani shahararen hotel na kasan Turkish ya saukashi . Zamu kwana biyu a garin don akwai abinda zaiyi a nan din kafin a kwasa zuwa wurin abinda ya kawomu na sister din nasa. Karfe hudu da rabi zamu halarci wani wuri da zamu gana dashi da mahaifiyar shi lokacin zamuyi liyafa tare dasu muci dinner a tare a yadda aka tsara aka fada muna kuma . Ba wani kwaliya nayiba na azo a ganiba, dogon rigace kawai kalan kakin soja a jikina gaban rigan yanada tsaga da filawowi zuwa gwiwan rigan sai igiyan daure shi dana daure tsakiyan kwankwasona sai dan kwalin shi a kaina saidai rigan gaskiya ba laifi don ta hadu wurin kyau dagani kasan na kashe naira a wurin sayen shi. Muna cikin motan daya dauko mu zuwa masaukin su inda suke suna jiran mu ashe tsakanin mu da idan suka sauka din baida wani nisa sosai da inda muke. Motar na tafiya a hankali saman titin ga ruwa daya kawata garin hakan nake bin garin da kallo ga gidajen wasu a tsakiyan ruwa da yayiwa garin kawanya ga gine gine iri iri sai inda kallon ka ya tsayama. Hakan yasa na raina kyan lagos duk da a kullun garin lagos a cikin cigaba yake fiye da sauran biranen Nageria da muke dasu Motan ya shiga wani kayattacen compound maikyau da ban sha,awa wanda kowan mu ya yaba da kyau wajen don wasu har magana sunyi. Kusan saida kowa ya gama fitowa daga cikin motar na fito a karshe ina dan gyara rigan jikina cikin kamewa don yanayi zaka kalla kasan bawai tafiyan ina jin dadin shi bane duk daulan da muke gani a wanan tafiyan. Wani mutum ne dake jiran mu a wajen wurin ya taremu yake muna sannu da zuwa shi yai muna jagora zuwa inda suke wurine mai kyau da aka kawata shi da sosai da kujeru na alfarma masu kyau da daukan hankali aga wani babban table din cin liyafa wurin ga manyan kayan cin abinci nan saman shi a jere. Alaja kamar yadda naji yan lagos na kiranta dashi itace muka hango cikin shiga na alfarma zaune tare da danta a gefe saman wasu kujeru na alfarma a wurin. Fuskanta ba yabo ba fallasa lokacin data hangomu kusan lokaci daya muka iso tare da wasu da nake zaton yan uwansune na jini kungiya biyu wasu daga arewa wasu uku kuma daga kudu suke. Muka hade a tare dasu gaba dayan mu sun nuna farin ciki da ganin mu suke muna sannu da zuwa ba bata lokaci bayan gaisuwa aka nufi saman dinning table din don cin abincin. Gaba daya a takure nake a wurin don nice karama cikin su gaba daya da muke zaunen addua akafara wanda shida kanshi ya jagoranci adduan . Kafin abawa daya daga cikin kiristocin shima yayi addua a lokacin aka shafa jimoh ne ya fara magana yana fadin sunyi maraba da kowa daya samu halartan wanan tafiyan yadda kowa yazo lafiya Allah ya maida kowa gida lafiya. Sai abokan aikin mu ya nuno mu a inda muke zaune yana fadin wanan gaiyatan da biyu maigida ya shirya maku shi don kuzo nan ku huta na sati biyu saboda ci gaban da kuka samowa company a yanzu. Nan dai aka dauki tafen jin dadi bandani da dan guntun murmushi na sake kawai iya fuska da baikai ciki ba a lokacin don jin har sati biyu zamu kwashe a wanan tafiyan da in mun dauko yarsu data gama karatu zamu wuce Dubai daga can muyi sati daya mu dawo gida Nigeria daga can. Muryan Alaja ne ya dawo dani daga tunanen da nakeyi inda yemisi dake kusa dani zaune ta dan zungureni na dawo firgigit daga tunanen da nakeyi a lokacin. Tana fadin yata ya kuma kamar bakya farin ciki da wanan albishir din da kukaji a yanzune na dauka kowan ku nan zaiyi farin ciki da wanan karamawan da dana yai maku a yanzu. Don muma kun jawo muna cigaba sosai a cikin harkokin mu a wanan lokacin don gaba daya ma,aikatan da muke dasu sun mayar da himma wurin kawo muna dukiyan mu yadda ya kamata a yanzu. Dan murmushi na kara sakewa ina fadi a cikin yarbancin da itama din tayi muna cewa nayi murna da jin hakan Allah ya kara rufa asiri aka amsa da amin lokaci guda. Nan aka fara cin abinci ni dai na zubane amma sam banji dadin abincin ba sin haka cibi biyu kawai nayi na kurawa cup din dake gaba cike da ruwan lemo mm a ainihi idanu. Daga inda yake zaune shima ido ya kura min babu ko kiftawa haka Alaja dake magana dashi ta dago tana kallon shi jin yayi shiru a lokacin ta kalli inda dan nata yake kallo din taga na kurawa cup idanu ina tunane. Let me feed you by myself oyyah come close to me ta fada tana tayar da wace ke kusa da ita zaune a lokacin wace sai alokacin na shedata wanan kanwar natane dai da muke haduwa a sha,anin su. Dan murmushi nayi na dauki cibin na dibi abinci da sauri don jin abinda Alaja ta fada a kaina don nuna damuwan ta kan rashin sake jikin da nakasa yi dasu. Matsa min tayi akan na dawo kusa da ita din inda tasa wata tashi don dole na mike na dawo inda take na zauna. Ana cin abincin ana hira da dariya ganin hankalin su ya dauku ana surutu yasa na mike daga wurin na nufi can inda muka samesu da farko na zauna ina bin wayana da baida amfani da kallo don katunan wayan mu basu da amfani a kasan yanzu. Hankalina ya dauku ga wayan ban san zuwan felix inda nake ba sai muryan shi naji yana fadin meke damun kine haka yan mata ? Kaina dago na dan kalleshi kafin in ce dashi nothing meka ganine kawai ina tunanen mahaifiyatace dana baro a gida. Don ban taba tafiya haka mai nisa ba tare da ita ba asalima idan ba tafiyan da muka tabayi da oga ba yayi saurin fadin wanan da bom ya tashi ko kai gaskiya mutanen ku they are wicked. Felix kazo kabi mutanen nan kayi muna odan abincin dare ya fada daidai lokacin da yake karasowa wurin namu. Haka yasa muka dago kai da sauri muna kallon shi kafin ya karaso inda muke zaune ya zauna na yunkura zan mike ina fadin felix ya jirani zanga yadda wurin yake yace no in zauna magana zaiyi dani. Felix din ya wuce inda ya aikeshi a lokacin ya kai zaune yana fuskantana kafin ya fara din miss Sahiba bansan irin godiyan da zan maki ba in nuna maki jindadina ga abin da kukai min. Gaskiya na yaba nakuma gode sosai da wanan aikin da kuke gabatar min ko nawa zan baku sai dai kawai in baku badai kudin ladan aikin ba a gareni. Aikine na kasada babba kukayi wanda ba kowa zai tsaya yai makashi ba don ni kaina da farko da Jimoh yace a baku aikin na tsorata matuka ina gudun wani abu mara kyau a sanadin aikina yazo ya sameku Don na bincika naji labarin mutanen nan bashi da kyau sosai akan dukiya zasu iya salwantar da rayuwan mutum. Kai na dago tare da murmushi ina kallon shi don jin abinda ya fada nace kome zasuyi nasan cewa Allah ba zai basu sa, a akan mu ba asalima ai sune suka taba abinka don haka kome zasuyi a kansu zai koma yanzu. Gaskiyane sun kawo muna hari da dama dan zaman da mukayi dasu saidai Allah bai basu sa, a akan mu ba don muna tare da tsarin Allah hakane yace yana gyara zaman shi tare da fadin ina da labarin komai daya faru daku a can don nima nan ban zauna ba a kanku. Daga ida suke zaune suna hango mu ta cikin glass din da yai muna katanga dasu saidai ba zasuji abinda muke fadi ba don dan nisan dake akwai a tsakanin mu. Don haka sai suka dauki hakan da wani zance na daban mukeyi a lokacin kowa da abinda yake rayawa ga wanan zaman a zuciyar shi. Sam ni ban dauki hakan da wani manufa ba tunda nasan akan abinda muke magana lokacin dashi. Alajace da kanwarta tayi mata magana a rada ta mayar da idon ta a kanmu lokacin a cikin zargi zuwan felix wurun yana masa bayani ne yasa ta taso daga inda take zaune din zuwa wurun mu a lokacin. ZAINAB IDRIS MAKAWA. 2ANA DARA GA , , , , , , , , 7️⃣1️⃣ BY, , , , , , , , , , , , ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , , , , , , , , BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AL MUHSIH, , , , , , , , , , ONLINE PAID NOVEL YAR UWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA BA TARE DA HAKKIN KOWA BA DON BIYA KI TURA DARI BIYAR 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK 08036959257 ALLAH SARKI AI RAINA BAYA BACI YANZU DON KIN FITAR DON NASAN AKWAI RANAN HADUWA SEE U👋👋👋👋 ALAJA macece tsayayya mai kiran karfi don garsakace yadda malam bahaushe ke fadin mace mai irin zatin ta zamu iyacewa kuma tsayin nata yayi mata kyau sosai gata farace ita jajir ga jiki daidai tsayinta sai abin ya hade ya bada ma,ana a gareta. Ta karaso wurin tana fadin a a sha,aban wai kayi waya da Walida kaji ya jikin nata kuwa a yadda yake zaune ya mike kafafun shi saman dan stol dake gaban shi. Takai zaune a kusa dashi jikin ta yana gugan nashi tana fadin ya kamata ace la kirata kaji yaya ta kara ji da jikin nata ai don kasan da tana nan a tare damu yanzu haka dukda mahaifiyarta tace zamu hadu dasu can england din. A cikin harshen larabci yayi mata magana ba tare daya dago kai ga abinda yakeyi ba sai ita Alajan ta juyo tana dan murmushi take fadin. Wai laifine ka kira matar da zaka aura kaji lafiyanta tunda da ita muka shirya wanan tafiyan rashin lafiya ya kamata . Murmushi Allah ya ban ikon sakewa ina dan kallon shi jin an ambaci aure a gareshi nace sir gaskiya maama ta fada yana da kyau kakira kaji lafiyan ta. Da mamaki ya dago yana kallona kafin yace I don't no who she is talking for kin dai san bansan wacece ba kuke zance a kanta ba na fada maku ba wanan zancen a zuciyana yanzu. Don haka ummi ki bar zancen nan tun wuri ya karasa fada yana tanke fuskan shi a cikin harshen larabci da bama ji. Dacewan hakan mama ta gani a gareka mune yanzu zamuyi hakan kai muna fada mutum musulmi bai cika cikkaken mutum a idon jama, a sai yana da iyali a gida. Da kyau yata haka nake son ki da fadin gaskiya koda yaushe gara dai ku fada mai ta fada a cikin yanayin damuwa a fuskan ta lokaci guda. Na rasa meye hakan yakeyi kai ba musulmi bane da baka yarda da kaddara Sha,aban nima ai mijina ya mutu danayi hakkuri ba gaku ina kalko ba to kai waye zaka kalla ya debema kewa a rayuwa kowa fa yana son barin baya a duniya ko banza zasu tuna dakai suyi ma addua. Wana maganan da mahaifiyar shi keyi yasa jikin kowan mu yayi sanyi lokaci guda karshe sai mikewa yayi ya barmu mu uku zaune fita yayi zuwa wajen wurin yana shan iska rike da cup din lemu a hannun shi. Felix har yanzu na kasa samun kan yaron nan na dauka zaiyi maraba da wanan dun da muka zabar mashi don yarinyar akwai kyau ga ilimi sanan gata yar manyan mutane a can Nageria din. Nan Felix din yai magana yana fadun mommy kin fa san halin ogana kan wanan magana ko wancan ma kece kika matsa sosai akayi shi a lokacin. Har kuma rasuwan ta bawai wani shiri bane sosai a tsakanin don kin san irin rayuwanta baiyi daidai da nasa ba kinfi kowa sanin haka. Kai kabar wanan zancen don wacan ta riga data rasu ko yanzu wata nake son na nema mashi yana kuma bultse min akan zancen gashi na riga dana fadawa mahaifiyar yarinyar kuma sun yarda da hakan a yanzu. Don haka kuyi min kokarin hakan gareshi ku biyun nan tana nuna mu da hannunta naga ke ya yarda dake sosai a rayuwan shi har wanan abin yana ban mamaki. Yadda ya amince dake haka kina mace koda yake hakan ba abin mamaki bane ga wanda ya sanki kuma yasan kina tare da juju zaki iya juya kowa a yadda kike so. Saidai ina ina rokon ki da kada ki shiga cikin rayuwan dana don Allah duk abinda zakuyi ya tsaya iya aikine kawai kamar yadda da farko shine ya hada ku ta kare tana hada hannayen ta a wuri daya alaman rokona. Duk girma da nauyin Alaja da nakeji sai naji lokaci daya ta zube min idona ya rufe na kirata da sunan ta da Alaja me zancenki ke nufi a kaina yanzu ido babu nauyin ta ko tsoro a lokacin itama din kallon mamaki ta bini dashi a idonta. Ni sahiba ba dan ki ba duk wani da namiji dake duniyan nan ban taba jin wani abu so ba ga kowa don ban taba soyayya da kowa ba a rayuwana balle na fara akan danki . Na mike daga inda nake ina fadin idan ma har zuciyar ki ko wani ya fada maki haka yai maki karya don ni yanzu ba wanan bane a gabana ba. Aikine da danki daga yau din nan na daina tunda har kike zargin wani abu ga hakan ba komai tsakanina da oga sai zalla biyayya da mutunci iri wanda shi ya nuna min hakan. Kada kiyi zaton aiki da nakeyi a katshin danki zai baki daman hasko wani zaton dani koshi bamu tabayi a zukatan mu ba akwai dubun shi da suke jiran hakan ni ba matsalana bane a wurina aikine ya hadamu shi kuma nakeyi dashi ko yanzu din da kika ganmu a zaune. Ina rike mutum ne yadda ya rikeni tun farko danki ya daukeni kamar yar uwanshi nima hakan yasa na daukeshi hakan kamar yadda shima ya daukeni din. Don haka ki kwantar da hankalin ki kije kai tsaye ki nemawa danki yar shugaban kasan duniya wanan bai shafeni ba ni. Kuma ki sani daga wanan ranan komai ya kare a tsakanin mu dashi na fada ina mikewa tsaye fuuu nabar wurin ina jin Felix na kiran sunana ban tsaya naji abinda yake son fada min ba lokacin. Sai muryan ogan naji yan fadin meke faruwane felix mai kukai matane hakane wai ? Sai kuma ya sake juyowa rai bace yana fuskantar su kafin kuma ya juyo da sauri yakai kallon shi inda nake ina kokarin fita daga inda muke tare dasu din wurin da suka gyace mu din . Wani tsawa ya dakawa Felix a kan ya bini ya dakatar dani kada in bace a cikin garin mutane nashi ya sameshi. Na fada maki gada kiyi wa yarinyar nan komai idan sunzo garin nan ummi saida kikai mata wani zance a yanzu ashe ya fada rai bace yana bin bayan felix din. Sun kai su goma ko fiye da goma a police station din tun safe suke wurin a tsaye su shiga su fita sun kasa yin komai daya dace a wurin don suna neman bellin shine a ranan. Bayan ya kwana har biyu a hannun hukuma nan garin Abuja wanda da kyat suka iya nemo inda yake lokacin kafin su fara wanan shige da ficen na neman bellin shi bisa jagorancin babban abokin shi wanda shi din dan majalisnane a lokacin wanda yaci zabe da taimakon Alh Nuhu din. Sai fada yake da yan kakin wurin kan basu san matsayin shi bane ko basu shedashi bani suke mai yawo da hankali. Dan sandan ya dubeshi cikin girmamawa yana fadin wanan case din Alh daga sama take don haka sai kun koma can kun gyaro don mu kamar ajiyan shi aka bamu nan ai. Nan ya matsawa dan sandan yake fada mai ai case din daga office din sakataren gwaunati ya fito don haka su koma a gyaro komai. Fitowan shi office din yasa sukayo ruuu a kanshi don suji halinda ake ciki, saboda shi kadai ya samu ganin IG din lokacin ko shi dun kuma don mukamin shi da yazo dashine aka barshi ya shiga. A daidai lokacin kuma sauran yan uwanshi Alh Nuhu din da suka biyo mota daga kaduna zuwa abuja suka iso wirin a gajiye. Basu samu labari mai dadi ba a wurin don haka hankalin su sai ya kara tashi fada sosai sukeyi suna fadin haka kawai za a kawo mutum a tsare shi kan kudi a ina zai samu kudin da zai biya yana daure ? Kallon su baffa Hamza yayi a cikin takaici kafin yace nifa na dauka wanan abin anyishine da wata manufa don yarinyar da tayi aikin files din nan harta zakulo su yaya din ba wata bace yar mu ce yar dan uwan mu kuma na uba daya wanda ya rasu shekarun baya . Wani kallo suka jefa mai kafin dayan Alhazawan yace yar kufa kace malam Hamza yana tambaya a cikin mamaki tare da kallon baffah hamza din da yai magana. Kai ya gyada yace kwarai don kusanma ba tantama nakeyi ba don itace tazo daga lagos tayi wanan aikin har hakan ya faru. Yar waye ke nan Alh gyade ya dan tako da sandan da yake dogarawa ya samu ya dan shiga mutane yace yar waye ke nan kake nufi wai ? Baffa hamza din yace yarinyar nan dai yar wurin yaya sambo marigayi data baiyana wancan satin ai itace ashe tayi wanan aikin a company sha,aban din. Wai kana nufin cewa wanan yar da gaske yar samboce ita toshi da namijin fa to ? Shima kwarai danshine don ance kamar su daya da yaron sosai yaron ya kwaso mahaifin shi fiye da ita macen ya fada yana gyada kai. Kai wanan abinda daure kai yake gaskiya a lokacin wani daga cikin abokan su yake fadin tazo da wani manufa ke nan yanzu dai ? Kwarai ba kadan ba sanan tayi tafiya zuwa england sai nan da sati uku zasu dawo kasan nan a yadda mukaji. Duk Alh yana tsare har wanan lokacin sai lokacin data dawo za a jirata ko me ? Shi muke kokari yanzu mu sameta ai saidai wayan ta baya shiga don yaron nan Abubakar da dan wurin harira suna da layin ta su. Kaji matsala babba ke nan yanzu bullowan wanan yarinyar da uwarta har kuma gada namiji ya fada a tsorace hankalin shi a tashe. Meye matsala don sun bayana a yanzu din tunda dama dauka ake sun mutu ne kuma ashe suna raye ba shike nan yanzu abinda ya rage kawai mu jawosu zuwa cikin mu ai shike nan. Shike nan fa kace hamza kai hamza nafa gano me kake nufi daka matsa mutanen nan yanzu su shigo cikin mu bayan wofinta kansu da sukayi a baya can. Ba komai kake kokarin nunawa ba gare mu yanzu sai zalla bakin ciki da jin haushi irin na yan uba da kake kokarin nuna muna. Haba Alh gyade wanan zancen haka a nan ai bai dace ba a tsakanin ku muyi abinda ya hadamu yanzu a nan shine mafita kan Alh a yanzu baffa buhari ya fada rai bace. Daga can gefe daya kuma baffa hamza na fadin meye abinjin zafi a cikin nan yanzu don haba don Allah haka bai dace ba abinda kukeyi yanzu baffa Abdullahi ya fada a harzuke. Tafiya nakeyi duk da sunana da Felix ke ihun kira haka baisa na tsaya ko in juyo in kalleshi ba don yadda nake jin idona ya rufe a lokacin sam na manta a wani kasan muke ma. Kai tsaye masaukin mu nakai kaina saidai kowan su yayi mamakin hakan zakace na san garin ne na kuma taba zuwa kasan . Bansha wahala ba wurin kai kaina dakunan da aka saukemu a cikin sa, ina elevator karshe da zai sadani da dakunan suka iya nasaran cin mun a cikin sa. Do u want to kill your self Sahiba ki duba yadda kike ratsa motoci haka ba tare da damuwa ba a zuciyar ki . Idan kin kashe kanki ko wani abu ya sameki me kike son in fadawa yan uwan ki ko mahaifiyar ki ? Kallon shi na dingayi kawai lokacin da yake magana yaci gaba da fadin don ummi ta fadamaki magana zaisa kiyi wanan abin idan wani abu ya sameki fa ke baki tunanen hakan ne ? Kaina na dukar kasa saiga hawaye takaici ya zobo min yana sauka a fuskana nake fadin a cikin karfin hali don kukan daya zo min din nace. Kasa a mayar dani Nigeria don ba zan iya ci gaba da zama haka mahaifiyar ka tana min wani zargi ba na daban don kawai ni ba yar kowa bace ina aikine a karkashin ku. Elevator din ne ya bude lokacin mun kawo inda zamu sauka ke nan zuwa wurin dakunan namu fita mukayi gaba dayan mu sai ya juya ya kalli Felix yana fadin ka koma can ka dauko min briefcase dina yanzun nan daga haka ya biyo bayana a daidai lokacin dana bude dakin da aka kama min na hotel din da muke a ciki. Shima lokaci daya ya biyoni zuwa cikin dakin mamakin hakan ne yani sosai sai tunane nake me nayi na rashin gaskiya ko nuna wani halin da Alajan zatai min wanan mumunan zato a kan danta da bamu taba tsayuwa ko na minti talatin ba dani dashi. Muryan shine a bayana yake fadin nasan wanan ba plan din ummi bane nasan daga inda zancen hakan ya fito. Don ko jiya mun dade muna magana a kanku tare da ita bata nuna min akwai wani jin zafin ki a zuciyar ta ba saima kara yabawa da kwazon aikin ki da tayi min duk a jiya din nan da kukazo. But why yanzu ummi zata fito min da wanan matsalan haka tana kokarin rushe min farin cuikin dana rasa na shekaru da dama kan wani bukata can nasu na daban. Watau da gaske mrs kubura keyi bazata daina abinda ta shirya min ba irin wancan karon ita burin ta ke nan ta assasa kiyayya da bakin ciki ko yaushe tsakani da ummi ? Look Sahiba duk da nasan ba zaki gane inda zancen nan ya dosa ba a yanzu ina rokon ki wani alfara kiyi min koda sau dayane kawai a rayuwan ki . Sai lokacin na sake dago ido na kalloshi inda yake din tsaye a cikin bacin rai ganin na kalloshi yace yes ki taimaka min koda sau daya ki taimaki rayuwa na please . Kada ki bari suyi nasara akan ummi dani sai kin daure da wanan taumakon da zaki min a yanzu ki nuna wanan zancen da ta turo ummi ta fada maki bai dameki ba haka kuma zaton su a kan mu din gaskiyane ki barni da sauran plan din zan karasa da kaina insha Allah. Ganin irin kallon tuhumar da nake maine yasa ya kara fadin please kada zuciya ya hanaki irin taimakon da kike muna a baya nasan zaki iya hakan ya kara marairaicewa kamar zaiyi kuka a lokaci guda cikin tashin hankali. Hakan yasa naji tausayin shi sosai naji wani irin ba dadi a lokacin don ko banza shine wani haske na rayuwana da ayanzu nake amfana dashi don haka shima dole in taimakeshi kamar yadda ya taimakawa rayuwa don nasan dai ko ya amfana dani shima ya taimake ni ai. Yana batun zube min nayi saurin fadin please Sir i can help you yadda kake so zan daure in shanye duk wani bacin rai da zan gani a wurin mahaifiyar nasa da sauran yan uwan shi don bansan manufarshi ga niyar yin hakan da yake son in masa ba a yanzu. Felix ne ya kwankwasa kofan ya shigo don a bude kofan yake har lokacin ya shigo dauke da briefcase din oga din a hannun shi. Yana mika mai ya karba yana maigodiya don oga badai godiya ba kan gaskiya ko dan karamin yaro kake kayi mashi abin kyautatawa sai ya godema. Wanan wani haline nasa na daban don gaskiya ni kan ba zan iya kiyasta maki halin salihanci da kirki irin nasa ba don shi mutum ne na daban zakaita magana yana shiru kamar baya jin ka. Sai can idan yaji inda ya dace ya dan bada amsa zai dago ya fadi kalma daya zuwa biyu shike nan iya zancen shi. Laptop din shi ya dauka ya danyi abu a ciki duk muna tsaye a cikin ladabi muna kallon shi kafin ya dago yana fadin zamu fitane ya aikawa jimo sako suna jiran mu a waje yanzu. Felix ne ya fara fita daga dakin kafin ya juyo kamar rada yana fadin plan din mu zai fara aiki daga yanzu sai ki kula ki daure sosai ya fada a hankalin cikin kalman hausa da dukan mu kinsan hausa ba zama yayi sosai a bakin mu ba. Wasu shaguna muka tafi an yace kowa ya dauki abinda ranshi ke so a wurin a gaban idon kowa da muke tare yaja hannuna muka nufi wani sashe na wurin . Kaya ya fara jidan mai yawa irin na matan musulmai na kasan inda ina kallo yemisi sai cika take tana batsewa ta dauka wani sabon gani ba bazata tayiwa idon ta akan mu ba yemisi ba kawai duk wanda ke tare damu hakan ya dauka lokacin. Sai dare sosai muka dawo masaukin mu da kaya niki niki shida kanshi kamar gaske ya taimaka kama min kayan zuwa dakina. Ban tsaya jiran komai ba bayan fitan su bandaki na fada nayi wanka tare sa alwala na fito nayi sallolina sai barci don banjin cin komai a lokacin. Washegari kamar yadda yace karfe takwas duk mun shirya zuwa airport mukai ban kwana da wanan kasan mai dadin zama da ni,ima dukda zaman kasan yazo min da akasi saidai hakan bai hanani jin wani iri ba lokacin. A nan airport tun nufar mu wurin muka hagoshi suna magana da wasu mutanen kasan na Turkeya su biyu suna tsaye . Yana saye a cikin suit dark blue clour daya kara haska farin shi ya fito mashi da kurciyarshi a fili ba zakace ya haura talinta da dan kai ba lokacin. Mutum akullum shekarun shi gaba sukeyi yana kara canzawa amma shi sai ka rantse da Allah a kullun kara masa kuruciya akeyi idan ka kalleshi. Ganin muna tun karo inda suke tsaye din ne yasa ya juyo yana kallon mu da alama cikin mutanen akwai wanda yayi magana a kan mu. Wani iri naji lokaci guda faduwan gabane ya ziyarceni a lokacin ga tsikan jikina da yai wani yarrr har zuwa yatsan kafana ganin yadda yake sako min murmushi daga nisa. Kafin mu karasa sai ganin Alaja da mutanen ta su shidda din nan a tsakanin mu dasu don haka sun tare muna hangoshi da mukeyi . Haka yasa a hankali na sauke ajiyan zuciya tare da ja na tsaya a wuri daya don dan tako kadan ne ya saura dama tsakanin mu dasu. ZAINAB IDRIS MAKAWA ANA DARA GA , , , , , , , , 7️⃣2️⃣ BY, , , , , , , , , , , , ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , , , , , , , , BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AL MUB,DI , , , , , , , , , ONLINE PAID NOVEL YAR UWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA BA TARE DA HAKKIN KOWA BA DON BIYA KI TURA DARI BIYAR 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK 08036959257 ALLAH SARKI AI RAINA BAYA BACI YANZU DON KIN FITAR DON NASAN AKWAI RANAN HADUWA SEE U👋👋👋👋. Yana ganina ya bar mutanen da suke tare lokacin tsaye haka ya wuto mahaifiyar nasa yana tafe yana murmushi dauke a fuskan shi har ya karaso inda muke tsaye gab dani yaja ya tsaya har muna dan hada kafada dashi. Nayi saurin dan ja da baya kadan yayi murmushi yana fadi kamar rada kada ki yarda ki nunawa kowa dake wurin nan wani abu please. Kamar gaba na ya tsage a lokacin don nauyi hakana daure na biyewa yadda yake so muje ko ya fada yana nuna min hanya da hannu tare da dan wani dukar da kanshi kasa. Wani kallo suke bin mu dashi yayin da Alaja taji wani irin tukukin bakin ciki ya kara rufeta a lokaci guda as a mother to him ba zata taba barin dan ta ya rabi wanan yarinyar mai tattare da sihiri ba a fili haka ta fada a ranta. Sam ba zai yuyu bama ace dan ta da daya tillo datake alfahari dashi a duniya ya auri yarinyar da bata da background ba yar kowa ba yarinyar da ko da nacikin cikin uwar shi ta kalla tasan me yake fadi. Ba kyau baje abin duba nasaba da dacewa sam wanan yar bata cancanci zama surukarta ba ta kara dago kai ta kalle mu a daidai lokacin da muka karaso inda take tsaye tare da mutanenta gaba dayansu duk sun sha mur a fuskan su lokaci guda. Da alama hakan bai dameshi ba shi ya nuna masu don muna isowa wurin su yaja ya tsaya yana gaisawa dasu sama sama tare da fadin ya suka kwana ? Daga inda nake tsaye na gaida Alaja da ekkaro mah da yatsune a fuskan ta ta amsa da karo joo tana kawar da ido a kaina take fadin ya bai jirasu ba ya wuto zuwa airport. Yake fasin yana sauri ne kada mu iso baya wurin Nabil ne ai ya dauko shi zuwa nan din bai dagakata ba ya juya ga fadin Sahiba meet my friend Nabil living in turkiya. Muka gaisa da wanda ya kira da Nabil din ya kara fadin she is Sahiba by name a cikin dan murmushi Nabil din ke fadi nice name is she the lucky girl that charm your heart ? Shima sin dariya kawai yayi mukayi gaba muna jere da juna gashi duk wani iri nake jin kaina a wurin don gaba daya sun zubo muna idanun su a kan mune felix ya yafuto yana fadin mu shiga kada a bata lokaci ka tabbatar da kowa ya gama kafin ka biyo mu. Ya fada har munyi gaba kadan ya tsaya kuma yana fadin idan da wani matsala ina ciki sai ka sameni suka dan tsaya da abokan nasa suka dayi magana da larabci sanan muka nufi ciki. Mazaunin mu daya da oga da tun zamana ban dago kai ba balle in juya inga na bayana da gefen mu shima kuma bai min magana ba sai zama dayayi ya harde kafafun shi. Barcine ya daukeni wanda nasan rashin yin shi da darene da ban samuyi sosai ba a lokacin don tunanen zancen Alaja da na kwana fassarawa a lokacin ban gano manufar Alaja din ba gareni. Tafiya ganin gari akace muna jin england da labarai a kanshi yau sai gamu a kasan cikin hukuncin ubangijin mu Allah. Ba zan tsaya mamaki ba akan abubuwan da mukaga su Alaja da danta nayi don shi kudi babu abinda bai saka bawayi idan suna dashi. Yammane muka isa masaukin da zamu zauna lafiyayyen daki irin na manyan mutane shi aka kama min don ashe wanda muke ciki iri dayane da nasa da Alaja sai sauran suna a cikin wanda baikai wanan din kudi ba. Tun shigana ban fito ba ina cikin dakin bayan ramuwar sallah dake kaina sai kuma na haye gado da niyar barci a lokacin kararawan dakin naji yana kara na tashi naje na bude inga kowa waye. Room service ce tsaye dauke da dan abin turo abinci tana min murmushi miss sahiba ko na gyada mata kai abincin ta shiga dashi bayan ta gaya min wanda yace a kawo min abinci din. Na jaye ta shiga daga ciki ta ajemin nayi mata godiya ta fita abincin nabi da kallo abu daya ne daga cikin abincin ya dauki hankalina watau fruits salad din dake nade a cikin wani bowl mekyau dashi. Fasa kwaciya nayi na zauna na bude na fara sha da bissimillah a bakina sosai naji dadin abin don yasha hadi na kayan lanbu sai lokaci nake karewa dakin kallo da ada ban damu da ko a ina nake ba. Idona na lumshe ina mai hamdala ga ubangiji daya nufeni da ganin irin rayuwan da ko wace mahaluki ke fatan ganin kanshi a ciki. Sosai na sake na kwashi harka a dakin don na manta rabona da tsayawa naci wani abu irin haka don na wancan kasan da muka baro tafarnuwa da wasu sanadaran girkin kasan ya hana in tsaya inci wani abin kirki. Saida na dade zaune kafin i mike na nemi wuri na kwanta ina sake ajiyan zuciya wayana na lalubo ina duban sako kamar da wasa na kunna datana sai naga sakkon ni na shigo min a lokacin. Mamakine ya kamani yasa na danna kiran layin umma da damuwa da rashinta a kusa dani ya addabi zuciyana a yan kwanan kin nan da mukayi ba tare dasu ba. Saidai sam wayan nasu bai shigaba yasa na fara duban sakon nina saiga sakon ya Abubakar mm a gani a wayana yana fada min sunzo basu samemu a gida ba ya lissafo min sunayen wa yanda sukazo tare din nan lagos wurin mu. Amsan dana bashi shine ayyah Allah sarki see u next shi kawai na rubuta mashi a lokacin karshema wayan na kashe na fada tunane. Barcine ya daukeni a hakan yasa na manta da komai dake gabana don dama kuma barcin dai nake ji gaskiya don a takure nake sosai a lokacin. Bude wayan yayi bayan ya kammala komai yana duba sakon nam shi dake shigo kamar a sama saiga amsan dana bayar ya baiyana mai ya soma karantawa. Baiyi mamakin hakan ba don abinda yafi wanan ma din zan iya rubuta mai a lokaci idon shi ya mayar ya lumshe a hankali yana tunanen yadda abubuwa zasu kashe a karshe. Naziface ta shigo dakin motsinta da taji yasa ya mayar da idanun nasa ya rufe a hankali yana ci gaba da nazarin abinda ke cikin zuciyar shi. Saida ta zauna a gefen shi ta hau gado da kyau take fadin yanzu shike nan haka Abban mu zai zauna a tsare sai ranan da yar iskan yarinyar nan data tsaresu ta dawo daga balaguron ta ? Wacece yar iskan ya juyo yana tambayanta a cikin mamaki tare da tsareta da idanun shi mai alaman mamakin abinda ta fada karara a lokacin. Ehmana idan ba yar iska take ba gantalala har Abbane zata sa a kama don kawai su nuwa mutane su yan barikine basu san daraja da girman babba ba. Shi kuma babban daya tabawa yara kayan sufa shi kuma meye ko wanda bai taba an kamashi duk idon shi na a kanta yana mata wani kallo na tsana. Kafin ya kawar da kai yana fadin koda yake banga laifin ki ba don kin fadi haka yanzu don ke yarinyace baki san komai ba a zancen. Wai shigar mata ke nan zakayi ko me ko dai ka shigan mata ai bata kaini a gurin ka ba kome ko Abba yayi ma da kake jin zafin shi yanzu. Dama nasan ba wai ka damu da wanan abin bane tunda kowa yasan kaika nemisu ka kawo su garin nan har take ganin kamar ita din watace can. Au ashe kin sani ai ban san abinda kuke fada ba ke nan nako godewa Allah da yasa nine silan dawowan su cikin yan uwan su a yanzu . Ashe ku haka a wurin ku laifine ban sani ba to kije gun wanda ya fada maki nace ya dauki matakin hakan a kaina idan zai iya. Tsuki taja tana juyawa baya taci gaba da fadin saukin abindai wallahi Abba yafi karfin hakan duk ko me zatayi ya riga da yasha gaban ta ko wallahi ai tazo zata hadu damu kowa na jiran isowan ta ai. Za ko tazo din kuma zaku ganta sai muga wanda zai taba ta idan kun shirya mata don ma ki sani karewa a gidan ku zata zauna tunda nan ne tushen ta na asali. Wanan kuma fadane kawai kayi a yanzu amma ko ubanta yayi kadan yace zai zauna muna gida balle ita don haka inma haka aka shirya gara tun wuri a bari tunda ba gidan ubanta bane. Au ke na ubanki ne ya fada a hasale lokacin da baisan hakan zai fito daga bakin shi ba duk da hakan bai daina zancen ba yaci gaba da fadin ki koma ki tambaya wanan gidan na waye tun farko ? Yana fadin hakan yaja tsuki ya juya baya tare da lumshe idanun shi kamar yadda ta sameahi dakin da farko shiru tayi na dan lokaci kafin ta mike fuu ta fice dakin tana fadin mutum kullun kazo mashi da zancen arziki sai ya nemi ya bata ma rai shi. Washegari ya shirya bai tsaya karyawa ba don yasa tea sai bread zai samu kawai yasashi fita zuwa gidan daddy da safe don ya karya a can duk da yasan da wuya mommy ta bashi abincin don gudun zuciyar matar shi da takeyi. Babu kowa a falon sai faiza dake karyawa a gurguje kada ta makara zuwa makaranta a lokacin. Gaidashi ta fara yi a gurguje kafin tace mommy na ciki barin kira maka ita yace no barshi hada min abin breakfast in karya sauri nakeyi yanzu nima zan tafi abujane. Da sauri ta juyo tana kallon shi Abuja yaya yace eh yi sauri ki ban ta nufi kitchen din part din su da sauri tana aje mai ita kan ta fita tana mashi Allah ya kiyayye hanya. Saida ya kusa gama cin abincin mommy dake jin motsi a falon ta dauka faiza ce bata fita ba har lokacin ta fito. Ja tayi wuri daya ta tsaya tana kallon dan nata da ya bata tausayi lokaci guda mutum magidanci ace bai samun kulawa yadda ya dace haka ga iyalin shi waima mai aikin meye ranan ta a gidan ne ita ? Kai kuma ya haka ta fada a fili wai wama ya baka abuncine gidan nan yanzu kai tsaye yana daukan kofin ruwa yace faizace kuma ta fita. Zaune ta karasa kaiwa tana fadin kai yaran nan basa ji saida fa na gargadesu da hakan su daina baka abinci bana son fitinan matarka wallahi don bata da kunya. Mommy don Nazifa kikace su daina bani abinci ai kasan halinta dai wuri rashin kunya ta fada tare da daure fuska lokaci daya. Ni zanje Abujane yanzu ya fada ko daddy ya tashi yanzu da wuya idan sun tashi tunda yara ba makaranta suke zuwa ba saidai ka duba in ya fito. No indai ya tashi ki fada mai nazo bai tashi ba zance kan case din uncle Nuhu mu gani idan zasu ban belin shi. Allah yasa su baka wanan abu dai baiyi dadi ba wallahi yanzu ita sahiban tasa dai aka rufeshi ke nan . Mommy ko itace ai bata da yadda zatayi tunda baida niyar biyan su kudin da company ke bin shi kinga ai yanzu yasan da gaske sukeyi tunda shi komai yace aikin suhiri zaiwa mutum. Sahiba ko ba ai mata wanan idan ya sani munyi magana da ita da safen nan tace ya fadi lokacin da zai bada kudin sai a bada belim shi shine zan tafi in ganshi yau din ko hankali zai kwanta. Ni dai bana son kana saka kanka cikin wanan zancen gaskiya da zakaji ta tawa kabarsu can su karata a tsakanin su zaifi. Bani kadai zan tafi ba tare dasu uncle hamza ne zamu tafi so ni zuwa kawai zanyi inga manya a can final. Alh yasan da zuwan ku daddy bai sani ba ina ji amma ai yasan da zancen neman bellin don shima ya gwada ba a bashi ba. Wayan shi ya dau kara ya dauka yana fadin gashi tafe yana tare da mommy ne daga haka ya kashe wayan yana mata sallama ya fita tana mashi addua. A ranan kan basu dawo gida ba saida Alh nuhu din wanda ya fada sosai da dare suka shigo kaduna suka wuce dashi gidan shi kai tsaye nan iyali suka shiga murna kowa da abinda yake fada. Bayan sun sauke shi gida ya nufa ya samu basuyi barci ba yaran ne da suka ganshi suka tare shi a cikin murna itako tana zaune a hakince tunda ta juyo ta kalle shi sau daya yana shigowa bata kara juyowa gareshi ba. Dakin shi ya shiga ya watsa ruwa kafin ya fito yana tambayan abincin shi sai lokacin tayi magana tana fadin nasan ina kaje tunda safe ni banyi abincin dare ba yau naka na rana mukaci. Kallonta yayi kafin ya juya ya koma zuwa dakin shi cikin takaici shirin kwanciya yayi kafin kira waya ya shigo mashi sun dade suna waya da wanda ya kirashi daga Abujan kafin suyi sallama yana kashe wayan a lokacin. Iska ya furzo daga bakin shi tare da shafo kanshi yana gyara kwanciyar shi don abinda sukai magana a kai din yanzu. Bai saba mata haka ba yanzu ma din daya share ta yana jin bai kyauta ba hakan yasa ya mike zuwa dakin da mahaifiyar nasa ta sauka. Yako samu Alajan ta hau dashi iyakar hau don yana shiga tunda taga shine taci gaba da wayan ta da ya sama tanayi a lokacin. Daga tsayen kaiwa yayi zaune saman gadon yana kishingidewa tare da zaro wayan shi daga aljihun shi yana latsawa. Har ta gaji ta kashe wayan taci gaba da tsabgogin gabanta lokaci guda ya fara gaida ita bata juyo ba balle ta kalleshi. Ummi wani abu ya farune ya tambaye ta a lokacin ta dago tana fadin sha,aban ban san me kake nufi dani ba a yanzu watau ban isa in ma magana ba kaji. Magana ummi wace magana ke nan ya tambaya cikin mamaki kamar bai san abinda take nufi ba a lokacin. Kada ka maidani mahaukaciya mana shaaban kana nufin gayatan yarinyar nan da iyayyen ta da nayi haka zasu zo ka nuna masu ban isa da kai ba ? Har a gabana kake rike hannun yarinyar nan kana laluba wai ka nuna min ban isa da kai ba kome da har gaban kowa ka nuna min kai ga zabin ka. Haba ummi kiyi min adalci wan can karon nayi maku biyayya ga abinda kuke so ya kamata wanan karin kuma ku bani dama nima in gwada sa,ata mana na fada maki bana son wanan hadin da kuke son yi yanzu . Ya kamata this time ki bani chans nima in nemo abinda zuciyana ke so da sauri ta kallo shi tana fadin badai wanan zabin naka ba mara amfani a garemu . Ko don jujun ta kake sonta ne sai ko kuwa don kyau da take dashi bayan nan fa ka fada man wani abu da yarinyar nan zata gwada wa wace na zabo ma yanzu. Kai ya girgiza yana fadin ko daya ummi saboda halinta na gaskiya da sanin ya kamatane kawai nake son ta. Gaskiyan ta na banza da wofi dama don ta kamaka haka yasa ta nuna maka ita mai gaskiyace ai . Dama nasan abinda zai faru a karshe ke nan tai maka jujun da zaka mutu da sonta umiportant love zakayi don abinka take so ba kai ba. Lalala haram Alaja ita ba yadda kike zato take ba asalima ni din ke son ta ba itace ke sona ba don haka ita na yanke a zuciyana zan aura final. Yana fadin haka ya mike daga inda yake zaune ya gyara kayan shi da sukai dan squzing yana kokarin fita daga dakin ta kira sunan shi ya tsaya cak ba tare da juyowa ba. Tace udan tace hakane zan nuna mata ita bata isa ba ko juju din gaba da gabanta wani jujun yafi karfin nata. ZAINAB IDRIS MAKAWA ANA DARA GA , , , , , , , , 7️⃣3️⃣ BY, , , , , , , , , , , , ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , , , , , , , , BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AL MU,ID, , , , , , , , , ONLINE PAID NOVEL YAR UWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA BA TARE DA HAKKIN KOWA BA DON BIYA KI TURA DARI BIYAR 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK 08036959257 ALLAH SARKI AI RAINA BAYA BACI YANZU DON KIN FITAR DON NASAN AKWAI RANAN HADUWA SEE U👋👋👋👋 Wurin taron ya cika makil da yan kasan dama baki irin mu itako Aishat ganiya sai murna da farin ciki takeyi da zuwan yan uwa duk wanda ya taka a dalilin ta zata har kasa tasa gwiwa bibiyu tayima sanu da zywa irin na al,adan yarbawa don girmamawa. Wanan abin da naganine yasani sake yan kwala watau dai gata wani abune nace a raina wata kila yanzu da ace mahaifin mu yana raye muma zamu iya samun wanan gatan da Ganiyat ta samu. Ranan da na kare karatuna ko kaza bata biyoni ba balle dan mutum ni daya kwallin naje na dawo duk ko da nuna min kauna da wasu abokan karatuna keyi a lokacin gaskiya naga dabam a wurin saboda rashin kowa a tare dani. Ganiyat zata iya girme min da shekara biyu ko ukku gaskiya amma shirun ta ita yai yawa sosai da kuma ba mutum girma. Tunda muka gaisa da farko haba haba da ita mahaifiyar su da bakinta sukaja ta bata kara tako inda muke ba saidai tana daga muna hannu idan ta biyo ta wurun mu. Yemisi da muke zaune a tare kusa da juna naji tayi tsuki tare da fadin Olon magge yasa na juyo ina kallon ta naji tace what a stupid tin be dat as dis gurl come here ke bakiga yadda ta mutatuntamu ba da farko amma ina kallo Alaja ta fada mata wani abu game damu nasan ko a kanki ne tayi magana. Kaina kum na tambaya a cikin mamaki yes bake ke dating din danta ba dawa zatayi kuwa a daidai lokacin ya juyo yake fadin kinga waccan da suka shigo yanzu itace Alaja ke fada dake a kanta. A hankali na dago kaina zuwa duban inda su Alaja suke zaune wata matashiya nagani a tsaye suna gaisawa dasu kallo daya nayi mata na kawar da kaina gefe daya. Kamar sun san da hakan sai ga Aishat ganiyat, ta riko hannun ta a cikin murna zuwa inda muke zaune tana fadin brother meet mansurat . Ya dan dago kamar da mamaki a fuskan shi ya furta who is she a take naga tsarguwan kalamin shi a fuskanta kafin ganiyat tashiga mashi dan bayani da cewa ai ita din diyar kawar ummice dake Manchester. Oh sorry by the meet my Pierce Sahibat from Nigeria ya fada kai tsaye a wurin ba tare da jin komai ba ya dan gyaro wuyan rigan shi kafin ya daga hannu yana duban lokaci a agogon hannun nasa. Dan dukowa yayi kamar yana min rada yake fadin ki mike tsab mu bar wurin nan yanzu yau din nan zamu wuce zuwa Dubai da dare. Kaina gyada ina kakaro murmushin dole a fuska saidai daya san kiris nake a lokacin inyi cikin shi da masifa akan bata min suna da lokana danaga yana kokarin yi yanzu kaina don kawai wani plan nasa zaita nunani a matsayin piance din shi ceni. Wanda ni kadai nasan wanan karyane shirine tsakanin nida shi kawai amma kuma shirin nason ya suce wuri a yanzu na fada don kula da yadda yake son batawa mahaifiyan shi rai a bainan jama, a. Haka yasa na dan kallo Aishat Ganiya tare da bakuwan a cikin fara,a ina fadin kai sannu da zuwa fa kun biyo hanya mai nisa duk saboda Aishat Ganiya sannun ku da kokari Allah ya bar zumunci. Sai lokacin na danga murmushi a fuskokin su naci gaba da fadin ga dan uwan naku nan ina mikewa zamu taka zuwa wancan wurin mu mike kafan mu na dago tare da hannun yemisi da yanzu don dole muke shirin dole da ita sama sama. Wayan ta yai kara a daidai lokacin da take shirin tashi zuwa dakin ta har lokacin tana cike da mijin nata da jin haushin shi sosai kan zantukan daya fada mata daren jiya ta manta da cewa itace ta kawo mai zancen har ya bata amsan daya dace da abinda ta fada sai kuma ta dau zafi dashi. Number mahaifiyar ta tagani take mamaki tana dauka take fadin lafiya mama babu ko sallama mahaifiyat nata tace mijin ki ya fada maki sun dawo da Alh ko ? Abba ya dawo ta tambaya a cikin mamaki tare da fadin nidai yanzu naga ya shigo ya shige part din shi baicewa kowa komai ba. Waiko Nazifa kin san abinda kikeyi kuwa kinsan me ake nufi da aure to mama ya fita bai fada min inda zai tafi ba ya dawo sai nace mai me ? Tsuki uwar taja mai karfi tana fadin zaki shukawa kan ki tsiyane wata rana ji yadda su Alh gyade suke bada labarin yadda aka kai ruwa rana dashi sai da kyat da sanin koshi waye suka ba da bellin Alh yau. Nikan bai fada min ba son haka ban san yayi ba yanzu ina Abba din yake ta tambaya yana nan gida mana tare suka dawo dashi ai. Zan iya kiran shi yanzu ta tambayi uwar cikin nuna ta gaji da wayan lokaci ki kira din ko zai dauko yanzu dai ya shiga wanka don mutane sunyi yawa saida aka rufe gida ya samu ya huta. Barin bari sai gobe na kirashi kada ki soma don nasan halin ki da sakaci ko goben sai lokacin da kikaga daman tashi da barci zaki zo don haka ki gwada kiran shi a yanzu ko zai dauka. Tace zan gwada barin bada minti biyar nan gaba amma fa ina ganin tsiyan da mukayi da baban maryam ne a daren jiya yasa ya tafi yau din. Shirmen banza shirin tafiyan da sukeyi yau kwana hudu ke nan zakice wai kunyi tsiya dashi kan haka yasa kila yaje indai zaki gyara ki gyara don iskacin ki ba inda zai kaiki . Kallon wayan tayi bayan uwar ta kashe taja tsuki tana ajeshi a gefe daya kafin ta dan fada tunane na san lokaci tana nazari can ta kalli me aiki tana fadin haule ki kwashi yaran nan zuwa daki gani tafe yar aikin ta amsa da to hajiya. Dakin ta shigo a dai lokacin data sameshi ya zuba ruwan tea din daya dafo a kicin tana waya bata ji fitan shi ba har ya gama ya dawo dakin shi kuma ya tsunci wani abinda take fadi a lokacin daga inda yake. Yana tsaye daidai saitin window dakin dake bude iska na shigo mashi yana tsiyaya ruwan shayin tashigo da sallaman ciki ciki. Dan juyowa yayi ya kallota kafin ya mayar da kanshi ga abinda yakeyi a lokacin ta karaso tana fadin ashe tafiya kayi yau din baka sanar muna ba. Eh tafiya nayi lokacin dana fita baki tashi daga barci ba a lokacin OK ta fada tana kaiwa zaune can tace dashi kuma ashe anyi nasaran fito da Abba yau din ke nan. Eh anyi don munyi magana da wace ta tsare shi tace a sakoshi ya nemi kudin idan babu su ya biya company abinsu . Wai saima data saka baki ke nan ashe aka sako Abba din ta fada cikin mamaki yace eh dama ba abinsu ya taba ba. Shiru tayi tana binshi da kallo ganin cewa duk maganan da sukeyi bai juyo ya kalli inda take ba yake bata amsa. Mama ce ta bugo min take fada min cewa kaine kayi kokari har aka sakoshi din eh hakan ai rufin asirin kowane banyi don wani ko wata ba ni kaina nayiwa hakan ai. Bata kara tanka mashi ba sai nazarin da takeyi a cikin zuciyar ta kafin can ta nisa tana mikewa tace dashi saida safe Allah bamu alheri ya fada shima. Washe gari sai goma ta isa gidan nasu ta samu har mai aure abuja ta iso a lokacin duk suna falo tare da mahaifin su ta shigo falon kowa ya bita da kallo. Gaban mahaifin nasu taje ta gaidashi ya amsa take gaida shi tare da mai Allah ya kara tsare gaba ya amsa cikin rashin walwalan data sameshi a ciki . Wai Abba ita din waye dahar take da iko haka da zatace zata wullakantaka mu kyaleta haka kawai wata banza can tazo ta batawa mutane suna wani dan shi saurayi ke fadin haka. Shiru mahaifin yayi kamar baiji shiba ya share zancen dan nasa don koda ya dawo jiya duk yana cikin tashin hankali sosai matarshi ta biyune ta shigo tana fadin wai Alh Inusa suna falon ka na baki suna jiran ka. Sun iso ke nan ya fada yana kokarin mikewa da sauri nan ya fice yabar yaran nasa a cikin damuwa suka fara mikewa zuwa cikin gida inda uwayen su suke. Mommy ne tashigo falon daddy din da sallama ya amsa mata tana binshi da kallo don taga yana shirin fita haka da sassafe kuma hakan ba dabian shi bane sai idan wani abu ya faru yake fitan safe haka a cikin garin. Ina kwana tayi mai ya amsa don irin kallon mamakin daya kula tana mai yasa yace gida Nuhu zamu don ya dawo jiya cikin dare akace. Wallahi nima hjy salma takirani tana fada min har na kirashi mun gaisa dashi tun jiya din yace OK yanzu ni zan tafi can din. Ya kafa hula akanshi ya dauki waya yana mata sai ya dawo tayi mai Allah ya tsare a tare suka fito daga falon don bata ko zauna ba ya fita. Tana komawa part din ta yaranta ne a zaune falon ta samu wuri ta zauna kallon su tayi don ta fahinci akwai maganan da sukeyi suka ganta suka shiru. Daddy bai tashi bane Nabila ta fada ya tashi mana ya dai fitane zuwa gaida yaya Nuhu daya dawo jiya. Au yadawo ashe ya dawo jiya ance yayan kune yaje ya fito dashi wai dama jiya yanzo nan da safe yana sallaman mu zasu tafi wurin shi. Mommy wai kinji kuma hauwa ta fada sai sauran suka kalleta da sauri me akayi mommy din ta tambaye ta ? Wai aahe Sufynu yana shaye shayene da gaske yaba baby kashi har ta dawo gida jiya saida wanan yar ta anty tazo ta mayar da ita. Subbahanallahi mommy ta fada da sauri har da duka tace wallahi wai ya farfasa mata jiki ya korata kai Allah ya kyauta har yaushe akai aure da haka ya fara biyowa baya ? A mommy dama ai sun sani suka yarda baki nawa ya fada masu cewa baida hali amma saboda kudin da yake basu ya rufe masu ido har da cewa anty tayi ana masu bakin ciki da hassadane da nakin ciki don anga yarta tayi saurin samun miji. Indai yan gidan uncle ban hana wanan Isma,il din nan ba shine mai dama nidai ga yaran gidan nake gani jinan mommy ta fada duk suka dago suna kallon ta . Bana son jin irin wanan maganan a bakin ku da baby din da shi Sufynu din duk yan uwan kune don haka kowa matsalan shi ya shafe ku ku kama bakin ko kuyi masu addua. Shiru sukayi wanan yasa tun farko basu son mommy din taji zancen a bakin su hauwa kuma ta fada mata yanzu don haka basu so ta fada mata ba. Yaushe ne hakan ya faru mommy ta sake tambaya hauwa ta kalli Faiza tace ga wace ke fada muna yanzu mu. Faiza ta bata rai tace nima Fatimace ai ta fada min tace wai mommy ta kora su waje don baby tazo mijinta ya duketa sai take ban labari. Shiru mommy tayi bata kara magana ba bayan Allah kyauta data fada ta dauki remote din tv tana canza chenal Faiza ta mike zuwa daki. Falon cike yake da ire iren su ana hayaniya daddy yayi sallama ya shigo suka amsa banda Alh Nuhu daya kawar da kanshi gefe tun shigowan daddy din falon. Gaisawa ya fara yi da mutanen daya sama a wurin suma suna amsawa a cikin girmamawa mutuntashi don girmanshi da irin darajan shi. Har kasa ya duka a gaban shi yana bashi girman shi na matsayin shi babban yaya a garesu a family su. Hakan ya kara fasa kan Alh nuhun dole ya juyo yana amsawa babban mutum kamar daddy ya bashi girma haka a gaban kowa aishi babu kamarshi ya sani. Yaya ina can ina jin yadda abubuwa suka dinga gudana yace a cikin basarwa eh abune mai kama da an shirya shi dama saidai ai zai koma kan duk wanda ya shirya haka don baisan Nuhu ba dakyau yasa aka kulla hakan don kawai a tozartani a idon jama,a. Shi abu idan yazo a daina sa zargi a cikin shi don duk nan mun sanda haka na iya faruwa da kowa a kan harkan shi ba komaine muke samu yazo muna daidai ba yadda muka tsara. Kwarai kuwa wanan haka yake Alh Bello ya fada daga inda yake zaune yaci gaba da fadin kai kasan idan ba kaddara ba har yaushe wanan yarinyar me kama da yar tsana zata zo tayi nasara haka a kan mu lokaci daya. Kada kai mamaki Alh bello ina fada ma wanan abin kamar wani shiri ne akai muna akan hakan don kawai aga mun tozarta a idon jama, a. Ban dauka yadda kake tunane bane Alh hakan dai kamar wani al,amari ke shirin faruwa haka na dauki zancen idan kayi zurfin tunane . Me kake nufi da hakan daga fada Alh Nuhu ya tambayi Alh Bellon abokin shi yana mai tsure shi da idanuwan shi. Eh ko ka manta da kowa nan abinda kake tunane ya shafeshi sallaman wasu abokan sune ya dakatar da faaa kwan da Alh bello ya tashi yi a lokacin. Mikewa daddy yayi yana masu sallama da niyar tafiya yana furta Allah ya tsare shi zai koma idan ba damuwa zamu iya ganin juna karfe hudu a gidan gonana Alh nuhu ya fada. Ba damuwa Allah ya kaimu lokaci lafiya ya fada ba tare da damuwa da komai ba ko darrr yadda wasu keji idan ya furta hakan. Daga inda muke tsaye muna hangosu kan shi a duke Ganiyat nayi mai magana kanshi yana a duke can ya dago ya tura wayan shi cikin aljihun shi. Kai tsaye ya taka zuwa inda Alaja suke zaune da mutanen ta yai magana dasu na dan second ya juya yayiwa Jimoh alama da hannu jimoh ya taso da sauri ya sameshi. Mun hango dai jimoh na kada kai kafin ya juya zuwa wurin yan uwan tafiyan mu yai masu magana shi kuma ya nufo inda muke tsaye din kai tsaye. A nan ya same mu mu tafi yace damu kawai yai gaba muka bishi a baya zuwa wurin da aka tanadar muna motocin da muke amfani dasu kasan. Kai tsaye wurareb tarihi muka nufa ranan munsha yawo shikan sai aiyu kan shi yake a cikin computer din shi dake lake dashi Jiddadun Alaina. Mun dawo masaukin mu a gajiye sai shirin tafiya kamar yadda ya fada muna zamuyi gaba a ranan su alaja zasu biyo mu baya idan Aishat Ganiyat ta karbi kayan ta daga makaranta. Karfe goman dare na ranan muka daga zuwa Dubai muka sauka da safe ana a can ma mun samu masu taron mu kamar yadda aka shirya. Masauki maikyau ga nagarta da jin dadin rayuwa nikan tun bayan sallah dana kwanta barcina nayi sosai sai uku na rana na falka koshi don sallah dana tuna yana kaina banyi ba. Na idar na zauna ina addua tare da jan lokaci don la,asar daya gabato a lokacin saidai kafin lokacin cikina ya fara kiran ciroma . Gaskiya a wanan tafiyan mun sheda cewa Oga Sha,aaban ya nuna jin dadin shi ga aiki mu kamar yadda ya fada din don a gaskiya mun ga gari gari ya gan mu. Shin shi mai hali Allah kan ga zuciyar shi yai mashi zarafi duk da ba duka masu halin Allah yaiwa halin kwarai haka ba akwai irin su baffana Nuhu da suka riki arziki abokin tafiya lahira a garesu. Wani kuma mai kudin Allah kan bashi basira da zai gane cewa yiwa wasu shine abinda zai tsira ya samu daga cikin arzikin shi a gobe kiyama. Samun irin su kalilan masu kafin basira da tunane a wanan zamanin zakaga wani a cikin daula kamar ba gobe gare shi wanan yasa ya shagala imanin shi baya kaishi tuna halin da rayuwan wasu suke aciki. Amma saidai cikin dubu akan samu goma da zukatan su fal yake a wurin taimako taimakon da zai zama silar dagawa wani dagawan wani da shi kuma fiye da mutum dubu zasu karu a dalilin shi nan gaba duk ta dalilin mutum daya ubangiji Allah ya karawa mai arzikin taimakon tallaka arziki na duniya da kiyama Allahuma amin. Nayi wanan bayanin ganin yadda ogan mu ya tallafawa rayuwa cikin rayuwa da yayi sanadin dagawan wasu da dama a dalilin shi bawa ya tuna idan har Allah ya bashi ikon aikata hakan wani irin lada zai tara a wurin Allah wanda ya samu a sanadin tallafawa rayuwan mutum daya rayuwa itama ta ceci rayuwan dubu nan gaba ? ZAINAB IDRIS MAKAWA ANA DARA GA , , , , , , , , 7️⃣4️⃣ BY, , , , , , , , , , , , ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , , , , , , , , BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AL MUH,YI , , , , , , , , , ONLINE PAID NOVEL YAR UWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA BA TARE DA HAKKIN KOWA BA DON BIYA KI TURA DARI BIYAR 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK 08036959257 ALLAH SARKI AI RAINA BAYA BACI YANZU DON KIN FITAR DON NASAN AKWAI RANAN HADUWA SEE U👋👋👋👋 Kamar yadda suka aje din hakane ya kasance da daddy don da yamma ya shirya zuwa gidan gonan da Alh Nuhu ya gaiyace shi zuwa da sunan zasu gana. Saidai yai masu bazata ga zuwan don ranan ya fito masu dsp din shi sak don mota biyu yazo dashi da wanda yake ciki driver yana jan shi sai dayan motan da security uku a cikin shi sun mara mai baya. Tun tsayawan su wurin hankali ya dawo gareshi har yafito a motan yana bin motocin wurin da kallo don ya sheda ko motocin su waye a wurin. Har ciki security din suka rakashi a kofa ya tsaya ya daga masu hannu su dakance shi wurin suka ja baya suna jiran shi. Kallon juna na tsayen sukayi lokaci guda kafin su mayar da idon su akan daddy din da yashigo a gadarance yana binsu da kallo ya samu wuri ya zauna bayan ya basu hannu sun gaisa. Alh Nuhu Sai wani cika yakeyi yana batsewa kafin ya bushi iska daga bakin shi yana sauke ajiyan zuciya yace Ali dpc kai muke jira duk nan daka ganmu kan zancen mu dakai na shekarun da suka shude a baya. Don nasan ganin iyamu ne zaune a wurin nan mu da wanan abin ya shafa zai iya tunama da ko wani zance nake magana a yanzu. Don haka ba sai na bude baki na fadama cewa ga dalilin gaiyatan ka nan da nayi ba a yanzu don kaida dan ka kunci amanan mu da kuka dawo da ahalin Sambo yanzu a cikin mu bayan tsawon lokacin da suka dauka da bace a cikin duniya . Yana kaiwa nan ya ja yayi shiru a cikin hasala yana wani irin mazurai da ido kamar zai kama da wuta lokaci guda. Jin yayi shiru daddy dake dan motsa hannayen shi daya harde a cikin yan uwa yana wasa da yantsun hannun nasa yana kuma sauraren abinda dan uwan nasa ke fadi a lokacin. Ya dago kai yana gyara zama tare da gyaran murya kafin ya fara fadin Alh Nuhu wanan ne dalilun da yasa kuka gyatoni a nan yanzu ? Don kuna ganin ko zaton na aikata wani abinda bai dace ba zuwa gareku sai kuma ya girgiza kan shi alaman takaici gami da sauke murmushi a fuskan shi yace. Idan ma har abinda da kuke zargina dashi a yanzu gaskiyane haka din ne eh hakan ne don tun farko aina fada maku ni duk ranan da akaga mutanen nan a shirye nake da in rungumesu in kuma danka masu abinsu dake hannuna a lokacin. Bai gama rufe baki ba Alh gyade daya kai iya hasala yace dashi billahillazi karya kakeyi Ali kayi kuma kadan a yanzu. Kai kai kai Gyade aika bari mu gama jin shi tukuna ayanzu kafin wani ya furta wani kalami a gareshi don dama ai gaskiyan zancen muke son ji daga bakin shi tunda ance tun farkon maganan nan yaki ya furta komai a kai har yanzu. Au da me kuke son in furta bayan nasan gaskiya cewa su din daine a yanzu ubangiji ya dawo muna dasu cikin mu ta sanadin dana daya gan su ya daukosu zuwa gidana har suka zauna tare damu na shekara kusan biyu kafin kuma nayi nadama da bakin ciki akan abinda ya faru a tsakanin mu dasu abaya. Ban fada maku cewa yasan komai dake gudana ba shiya yai shiru yaki magana da kowa kan wanan zancen a yanzu. Saidai ai sauki abin dai da hannun mutum.aka aiwatar da komai don haka ba wani hujja da mutum zai kawo a yanzu yace shi ya tsame kanshi yanzu. Murmushin daddy yayi don jin wanan kalamin na Alh Bello babban aboki kuma aminin Alh nuhu tun na kurciya dashi kuma aka shirya komai a lokanlcin har zuwa yanzun da ake fadin wai sun dawo din. Kwarai yasan da sanin hakan zai faru muddin suna raye suka baiyana sai dai tun a lokacin shi jami,ine dayasan kan aiki shi tun lokacin kuma ya shiryawa zuwan wanan ranan. Kwana hudu a Dubai banga giccin Oga Sir Shaaban ga idona ba tun zuwan mu kasan saidai dadin kan muna samu shi har nake tunanen wai dagaske ko hutun da yace din mukazo yi ke nan ashe ? Kai gaskiya idan kana dashi dai ka huta a rayuwan ka don bakajin kyashi ko zafin yiwa wani na kasa dakai idan Allah ya horema zuciyar alheri don irin wanan halin dace ne. A rana ta biyar ne a garin don munsha hutu har mun fara jin zaman dakin ya fara isar mu don bama komai daga kallo sai charting ko karatu. Sai hakan yai min dadi nikan don wanan wasan kwaikwayon da Oga keyi dani gun mahaifiyar su shi da nasan yana matukar biyayya gun mahaifiyar shi. Don duk abinda zai mata wanda zai bata mata zuciya nasan baya so a dan zaman da nayi dasu a gidan su lokacin bukin tunawa da mutuwar mahaifin su. Amma yanzu na rasa ko meye dalilin shi nayi mata hakan ga wanan hadin da Alaja din keson yi a tsakanin shi da yar aminiyar ta yanzu. Yanzu kuma da Alaja bata tare damu bai kara nemana da nuna irin kulawan da yakan nuna min agabata din yanzu ko ina cikin dakin da aka sauke mu din ina tsabgan gabana. A haka muka samu sako kan cewa mu shirya zamu shiga cikin gari muga yanayin gari da tsarin sa. A zuciyana nace wani garin zan gani a yanzu makka kawai ya rage naje gani tunda naga england da ban taba zaton zuwan shi ba a wanan lokacin yanzu saurana makkan kuma. Sai dai ina fatan umma ta fara zuwa kafin ni shine nake kokarin tara kudi a yanzu in kaita ga dan abinda muke samu daga aikina da kuma shagon mu insha Allahu shine burina kawai a yanzu gaskiya. Don ni babu zancen soyayya ko wani mu,amula da wani da zai dauke min hankali balle ma ban taba bada fuskan da wani namiji zaizo ya nuna min soyayya ba sai wanan karon da muka nuna hakan da Ogana hakan kuma sai yake min bambarakwai don rashin sabo da hakan. Haka muka shirya don fitan a daidai lokacin da suka aje muna time din fitan kafin lokacin kowan mu ya shirya don fitan da zamuyi din. Sai a wanan lokacin ne kuma na sanya Oga a idanuna tun ranan da mukazo da ban kara ji ko ganin shi ba ko inji wani abu gareshi ba. Yana tsaye a haraban wurin da wasu yan kabilan chana suna magana muka fito zuwa wurin motocin da zamuyi amfani dasu bisa jagorancin felix da ya fito damu zuwa wurin. Gaidashi muka fara yi a cikin ladabi bayan ya iso inda muke ya fara umartan Felix da ya kula damu tare kuma yi muna bayanin cewa zamu dan shiga garin mu zaga muga gari muga yadda al,amura kasan ke tafiya a nan din. Duk wanan bayanin da yakeyi kaina na kasa ina kallon wayana da nake charting da ya Abubakar a lokacin don haka ban yarda mun hada ido dashi ba. Yayin da duk second shi sai ya dago ido ya kallo inda nake tsaye ina saurarenshi a lokacin da yake bayanin nasa har dai ya kaiga kiran sunana yana tambayan ina ko tare dasu ? Sai lokacin na dan dago kai ina fadin yes Sir a gajarce har muka dauki hanya zuwa wuraren daya fada zamu kai ziyara din shi felix ya saba zuwa don kusan shida oga din akwai dan dangantaka saboda mahaifin felix din shine babban yaron mahaifin Ogan mu a lokacin da yake raye . Yanzu ko mahaifin Felix din ya tsufa sosai shima ya koma kasan su na igbo a kauyen su da zama . Wanan yasa yanzu shi kuma yajowo Felix din suna harkokin su a tare don yaci gaba da tallafawa rayuwan ahalin nasu Felix din. Don haka kusan shi felix din yasan komai akan ogan namu saidai baya zama can Labeno a tare dasu yana zama a gida Nigeria ne sai in bukatan tafiya waje ya taso yaje. Shine dalilin zaman Felix din na hannun daman shi sosai kamar yadda shima oga Jimoh suka hada halaka tun na kurciya idan sunzo Nigeria duk da Jimoh ya girmeshi amma suna tare koda yaushe dashi kasancewan su makwabtane a lokacin suna yara. Shine abokin shi nakusa a nan Nigeria bai kuma manta dasu ba har wanan lokacin da suke komai a yanzu yana zaune tare dashi a karkashin shi. Saida muka dawone daga fitan da mukayi nasan Alaja da Ganiyat sun iso Dubai din don ganin su tare da mukayi a haraban hotel din muka hade dasu sun fito shan iska. Nan dai aka shiga gaisawa dasu ana masu bangajiyan taro da muka barsu sunayi a can tare da bakin ta data gayyato a bangaren ta. Kamar yadda ta hade rai muna hada ido nima hakan na hade nawa a lokacin sai Ganiyat din ne ke fadin Oni wan kweb wa ! Tani ? yemisi ta fada tana kallon ta don son jin wanda yake magana dashi din a cikin mu don kanshi yana duke baka dauka ma yayi wani magana a lokacin. Tace boda me wan kwebwa Sayiba na dago na dan saci satan kallon shi a inda yake tsaye a cikin fararen kaya irin na yan, kasan Pakistan kayan su mashi matukar kyau sosai a jikin shi. Yemisi ta dan zungureni tana fadin ke ake kira nace no ke dai amma ai yasan ba zanzo ba wanan wurin ga uwar Alaja a tsaye yadda ta saka min ido haka. Ganin ko gezau banyi ba daga inda muke din yasa shi ya dan tako zuwa inda muke din tsaye zaikai tako biyu zuwa uku tsakanin mu dasu tun bayan gaisawan mu da Alajan . Sai dai ina mamakin rashin ganin mutanen ta da sukazo mata ma,ana abokan tafiyan mu wata kila sun komane daga england su, sun juya zuwa Nigeria. Kara gaida shi mukayi daya karaso wurin da muke din ya amsa a cikin sakin fuska yana fadin. A kwai meeting da zamuyi a nan gobe karfe goma na safe ki tabbatar da kun shirya ke da Ad,nan da Jimoh nake bukatan muje tare don akwai abubuwa masu muhinmanci da zaku sani. Allah ya kaimu goben lafiya na fada a cikin girmamawa daga hakan ya dan yi magana da yemisi kafin ya juya ya bar wurin. Ajiyan zuciya na sauke tare da bin bayan shi da kallo na juyo ina kallon yemisi da niyar fadin mu shiga ciki sai na samu itama shi din take bi da kallo. Tafiya na farayi ganin haka ta biyo bayana da sauri muka shige ciki a nan muka bar sauran suna magana da Alaja da su jimoh. Kowa a falon yayi shiru yana sauraren abinda da daddy din ke fadi bayan ya gama sauraren shima inda ya soma da fadin yana kallon fuskunan su a daure yace. Da ace kusan kowaye wanan yarinyar da kuke zancen ta haka a kanta da ko wanen ku a nan ya kama kanshi a yanzu ko kuma dai ya dawo mata da duk abinsu daya karba a baya. Ko kuma mutum ya tozarta a idon jama,a kamar dai yadda ta soma maku a yanzu kan dukiyan wani hakan kuma zatayi a kan nata koma fiye da hakan. Au kai zaga zugota ke nan tazo taci muna mutunci ashe idan ba haka ba har ina zata ji abinda ya faru a baya waye zai bata shedan wani abin da sai mu kadai muka san yadda ya faru ko kai daka shigo daga baya baka san yadda abubuwa suka kaaance ba a lokacin don gudun irin hakan muka rufe maka gaskiyan zancen. Murmushi yayi wanan karon ya mike yana fadi ni zan barku saidai shawarana shine kowa ya hado masu dukiyan su baki alaikum mu basu. Ba za a bayar ba Alh Nuhu ya fada a fusace yau kaci arzikin abu daya a wurin nan da ba haka ba da fita wurin nan gareka yau sai Allah . Nasa zaka iya saidai ku sani mutum baya mutuwa idan kwanan shi bai kare ba koshi wanda muke zance akan iyalin shi yanzu kwanan sa ne suka kare a lokaci. Don haka ni dai yau ashirye nake a duk lokacin da suka bukaci komai nasu in basu don dama ba karba nayi don naci ni kaina ba. Ni na barku lafiya ya fada yana juyawa karya kake wallahi kayi kadan kace zaka juya muna baya a yanzu wanan ba mai yuyuwa bane a wurin ka yanzu don ya zama dole kamar yadda muka rufe komai a baya mukayi shi tare yanzun ma hakan zaka nuna baka san komai ba a wanan zancen. Murmushi yayi ya gyada kai kafin ya juya yana tafiya tare da godewa Allah da yabi shawaran da zuciyar shi ta bashi kan yaje da security din shi. Da Allah kadai yasan yadda zasu kwashe dashi a wurin nan tunda ba imanine dasu ba don su sam basu tunanen sun girma yanzu su koma ga Allah. Ido ya lumshe yana tunanen wautan daya tanka a baya duk dama dai yasan yayi hakan ne da wani manufa wanda suma basu san da hakan ba. Gidan sa ya nufa kai tsaye sai dai suna shiga get din gidan nasane ya hango hjy karima ta fito daga cikin gidan da sauri tana kokarin shiga motar ta sai gashi. Kallon ta yakeyi a cikin mamaki inda zata fita haka hankali tashe bata fada mai ba itama din ganin shi ya dawo yasa ta dakata daga kokarin shiga motarta da takeyi. Ta dagakata har motar nasa ya tsaya ta karaso wurin da yake fitowa daga cikin motan ta sameshi ya daure fuska lokaci guda tare da tambayan ta ina zaki haka yanzu kuma ? Alh ba lafiya fa baby ce ta bugo min waya yanzu a cikin tashin hankali wai yaron nan yayi mata tsinanen duka ko tashi bata iyayi. Kallon ta yayi cikin mamaki sai kuma ya fara takawa don ya bar wurin ja yayi ya tsaya yana kallonta yace sai ke kuma zaki tafi yin me gidan nasu yanzu ? Ah zuwa zanyi muyita dashi wallahi tunda tace yanan gida yanzu zanje in sameshi in nuna mai karyan iskanci yakeyi shi. Ki sameshi fa kikace ke da kanki karima keda kanki zaki fada gidan suruki haka idan kinje kice masa me to ? Kallon mamaki itama tayiwa mijin nata tace in fada mai duk anin da yayi min dadi a cikin wani irin haushinta da takaici yace ke da dan karfi ta juyo yace koma gida. Yanzun ne baida hankali ko mashayi ai kaqai ku koma ko kin manta da kikace kunyi bincike kun gano duk sheri akai mai kawai. Kuyi gakkuri din Allah sai a hankali wallah ANA DARA GA , , , , , , , , 7️⃣5️⃣ BY, , , , , , , , , , , , ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , , , , , , , , BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AL MU,MIT , , , , , , , , , ONLINE PAID NOVEL YAR UWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA BA TARE DA HAKKIN KOWA BA DON BIYA KI TURA DARI BIYAR 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK 08036959257 ALLAH SARKI AI RAINA BAYA BACI YANZU DON KIN FITAR DON NASAN AKWAI RANAN HADUWA SEE U👋👋👋👋 A ranan nasan anci gaba sosai a hanyar kasuwanci son komai yanzu a zamanance akeyi shi kamar yadda muke dan kwatantawa dai a Nageria saidai gaskiya a can su kan aun muna fincin kau ma,ana an barmu a baya dai. Mun fito dakin taron na karaw juna ilimi a cikin farin ciki da kwanciyan hankali sai faman binsu a baya nakeyi duk jikina ya mutu da abinda na gani . Sai yaushe mu Nigeria zamuci gaba koda rabin haka abinda nayi ta tunane ke nan har muka fito gashi wurin dai matasa ne masu dan matsakaicin shekaru don tsofi daga ciki basu da yawa sosai. Waya na hngoshi yanayi can dan nisa damu sosai kafin ya tako zuwa inda muke tsaye din suka fara magana da jimoh a cikin yarbancin da idan yanayi zakace wani yaren yakeyi ba yaroba ba. Adanan ne yayi magana daga bayana yasa na juyo ona kallon shi yake fadin ya dai yan mata kingani tun a ciki nake ganin alaman hakan a tare dake. No ba komai tunanen gida kawai nakeyi don ban taba tafiya ba irin haka ba tare da mahaifiyana ba. Suma din basu taba zuwa wani wuri nisa dani ba sai wanan karon nan dai ya dan taba min hira har na sake muna wurin har suka kare tataunawan da sukeyi suka tako a tare inda muke tsaye nidashi. Sun karaso boda jimo ke fadin yawa Adnan sai kazo mu tafi tare dakai ita Sahiba zata wuce tare da Oga daga nan zasu wuce wani waje suyi signing. Sam ban kawo komai a raina ba tunda aiki muka fito a lokacin dukkan mu baya muka shiga don naso shiga gaba tare da driver da zai jamu ya dan daka min tsawa a cikin yarbanci da kada in bashi kunya mana wanan fa driver ne aikin sa yakeyi. Dole na dawo baya tun zaman a motan ban dago kaina na kalli inda yake zaunw din ba shi ga kuma motan a hankali yake tafiya saman lafuyayyen titin dake shimfida a kasa ko ina na garin tsab yake sukan gaskiya sunci gaba ga komai na zamani sosai sun barmu a baya. Eh mun je wani waje muyi signing ashe kayan da za,a shigo mai dasu wa yan nan company din da mukayi aikine a kaduna da kano zai kara farfado da wurin kuma sosai har yafi da can baya dayayi shi. Daga nan zuwa karfe hudu da rabi muka bar wajen duk da agajeye muke hakan baisa mun nufi masauki ba don a kasalance naji yana fadawa driver inda zai kaimu kuma. Kai Dubai kan taci gaba wani irin kantine na sayar da kaya tufafi da sauran abubuwa muka ziyarta tare dashi a zatona na dauka nan ma wani abin yazo yi sai da muka shigane na gane ba komai yazo yi ba a wurin don abinda naji yana fada da muka shiga ciki. Zaki iya yin tsaraban komai da kike so a nan don ba lalai bane ki kara shigowa wanan wuri nasan ba zasu iya shigowa nan dake ba indan kun fito tare. Na rasa me zan fada mai a lokacin don lissafi ya kwance min ba zan iya yin komai ba don kaina lokacin naji ya kara fadin har mama da brother din ki ki saya masu kayan wurin nan zaifi. Tsaye nayi kawai ina kallon shi ban iya cewa dashi komai ba OK idan baki san me zaki dauka ba muje na tayaki kada mu bata lokaci don gobe nake son in bar kasan nan zuwa Cairo. Lokacin ne na iya dago kai na kalleshi ido da ido ina mamakin jin abinda ya fada ke nan har mu zamu bar kasan ke nan yake nufi ko me oho ? Kamar yasan me nake tunane naga ya fara tafiya yana fadin gobe zan koma Cairo zan barku a nan ku karasa hutun ku ranan tuesday zaku koma Nigeria. A daidai lokacin da ya isa wurin kayan maza yake wanan maganan nan ya fara duba saidai hankalina baikai kan irin da naga yana zaba ba a wurin. Yana jefawa cikin wani dan keken da muka sama a gefen wurin sai jidan kayan yakeyi kafin ya tura kekan zuwa wani bangare kuma da alama dai yasan kan shagon sosai nake gani. Ina biye dashi a baya kamar zonbi da wata da muka sama wajen ma,aikaciyar wurin yake magana ta dan juyo ta kalle ni kafin ta fara zabo kaya tana jefawa a cikin basket din muna binta a baya can dai takai ga daga wani tana gwada tsayin shi a jikina saidai bana jin yaren da takeyine. Wani irin mahaukacin sayayya yayi a wurin abin har ya ban tsoro amma kuma sai nasa a zuciyana cewa wanda zamu kara zubawa a shagon mune na lagos lokacin. Don haka naye tsaye duk inda mukaje ina binshi a baya har muka kusan gamawa sai riga daya na iya zaba a wurin saboda tsadan kayan dana gani a rubuce. Muka fito zuwa wurin biya ya basu card dinshi aka cire kudin nan sukai packed xin su aka kai muna a motan da mukazo da ita bamu muka isa masaukin mu ba sai tara na dare a gajiye naga an iso masaukin namu. Tunda moton ya tsaye yake fadin karfe bakawai na safe zan bar garin nan ba lalai bane mu sake haduwa daku nan din don haka ku kula da kanku har lokacin tafiyan ku yazo. Zaku zauna tare da Alaja a nan din don sai kun tafi kun barsu idan na dawo zamu wuce gida tare dasu lokacin sun gama hutun su da zasuyi. Sai kuma ya dan juyo ya kalleni sosai yana fadin nagode da kokarin komai da kikai min Sahiba wani iri naji a raina na dago kai na dan kalleshi ina fadin. Ba sai ka gode min ba ni ya kamata na godema ga irin kokarin da kake muna a rayuwa da badon kai daka tsaya min ba har rayuwana dana mahaifiyana ya inganta a yanzu da bamu san inda rayuwan mu zai kasance a yanzu ba. Wani irin lumshe idanun shi yayi lokaci guda sai kawai naga ya yunkura zai fita daga motan tare da fadin is OK nasan pain din ku a yanzu take care daga haka ya rigani fitowa a motan. Nima na fito tsayawa yayi yana saita kanshi kafin ya daga kai ya kalli saman benen dake gaban mu na dakunan kwanan bakin hotel din. Naga ya juya yana magana da driver daya dauko mu din a cikin larabci lokacin ne kuma muka jera zuwa ciki inda zamu kai dakunan kwanan mu. Alaja da yar ta dake tsaye saman suna kallon dawowam mu suka kalli juna suka tabe baki suna jiran hawowan shi saman na karasa inda masaukina yake na shige ciki. Ban san ya akayi aka shigo da wanan kayan da muka sayo ba dakina nidai na fito wanka danaje don yin alwala na samu an shigo min dasu a dakin. Da mamakin hakan na tayar da sallah ina gamawa a lokacin abincina yana ajiye naci sai barci ranan ban ko tsaya duba sakon wayana ba don gajiya. Har naso makara gayin sallah washe gari don a gurguje na fada ban daki nayo alwala na fito sai da na idar ne na fara tuna ko yanzu ya wuce a lokacin na dubi wayana karfe takwas saura yan mintina. Idona na lumshe ina tunanen abubuwa da dama a raina kafin na girgiza kai a hankali na dan jingina jikina da bangon dake kusa dani na dakin. Zubur na mike ina bude idona daga rufen da suke na daga na nufi wurin kayan da na gani a dakin ko an kwashe na samu kayan suna nan a inda suke ajiye har lokacin. Binsu nayi da kallon mamaki tare da tuna irin makudan kudin da ya kashe wurin sayen kayan don irin kudin da naga an rubuta a jikin kayan. A lokacin idona yakai saman takardan dake makale a gefen kayan na dauko da sauri ina karantawa a hankali na koma baya kadan daga wurin na kai zaune. Ban dago ba ina wurin cikin zurfin tunane yanzu duk ni ya sayawa wanan kayan ashe dama kayane fa da aka kashe kudi masu yawa wurun sayan su don ni na dauka ma a shagon mu nacan zamu saka. Tunane nayi to ni yanzu wani irin godiya ma zanwa wanatn mutumin ne wai na dade a zaune ina tunane gashi bama zan iya cewa ga irin kayan dake cikin packed din ba lokacin. Tun ina dan tunane har na fara gyangyadi a wurin haka yasa na mike na koma na kwanta barci nayi sosai a ranan ga abokan tafiyana suna son ganina gashi ba layin kasan a wurina. Saida nayi barcina na gaji sannan na tashi nayi wanka sai lokacin na nemi abinci na danna masu kan a kawo min abinci a dakina. Bayan naci na koshine na kara watsa ruwa a jikina na zauna a gaban mirrow ina kallon kaina a ciki yadda naga sauyi sosai a jikina. Fatana yayi wani lub lub dashi a yanzu tankar dai dama can a cikin daula na taso ban taba wahala ba a baya. Ashe ko wani jikin dan adam hutu yake son samu dan lokaci kankani zakaga fata ya murje saboda samun hutu da haka harna shirya a cikin wani dogon riga baki mai laushi mara hannu saidai rigan dinkishi har kasa ya sauka min xinkin wani mai shara shara dashi haka ta kasa na dan dira bakin gyale a kaina dake daure ba kitso. Wanda duk da rashin kitso bai hanashi cikowa ba a lokacin don mai masu kyau da nake amfani dashi a kaina din. Dakin yemisi na nufa don mu gaisa don tun shekaran jiya rabon da muga juna nan na samu bata nan don nayi nocking ba bude ba yasa na juya don komawa nawa dakin. Amma kuma sai naji na gaji da zaman dakin ina bukatan in dan zaga cikin wurin in mike kafana na mike don fita haraban wajen. Karaf muka hade da Ganiyat data fito itama daga nasu part din a cikin wani irin shigan da bai dace ba ace tayi shi don kawai tana a wurin da ba garin su ko kasanta ba don na tabbatar da ba zata taba shiga lagos a cikin wanan shigan ba ko dan yayanta ya tafine baya kusa dasu. Saidai kuma naga ita ko ta damu da haka duk da kallon da yawan mutane suke mata a wurin baisa ta ji wani darr ba a lokacin muka hade ta dan rugumoni tana fadin a, a Sahiba ashe kina nan baku tafi tare da brother dina ba na dauka tare zakuyi tafiyan dashi ai. No team din mu suna nan ba tare damu ya tafi ba sai naga tayi murmushi kafin ta kalloni da kyau tana fadin aiba dole saida team zaki tafi ba don ke yanzu ogan su ce. Don me ba zakibi shi ba wai, ina cutship kukeyi a yanzu ke dashi kuna son ku fahinci juna a tsakanin kafin auren ku dashi don haka ba wani abu bane idan ya wuce dake ai a yau din don kowa yasan soyayya kukeyi a tsakanin ke dashi yanzu. Jin kalamin ta yasa na dago da sauri na dan mata kallon mamaki ta gyada min kai alaman eh tare da fadin kada kibi zancen Alaja ko wasu can masu gulma. Duk da nasan mommy mu bata son alakan ku kedashi tace ke din baki dace da brother ba sam, saidai ni banga rashin dacewan da mommy ke fadi ba a kanku nan. Don gaskiya brother na ya iya zabe sosai wallahi saidai kawai abinda mommy din take fadin a kanki shine kawai yanzu matsala a wurin ku. Kina da kyauki da kyau diri da tsari duk da ake nema a jikin mace, ta nunani da hannu tace komai naki alhamdullahi gaki da ilimin ki sosai don naji yayana na fadin kina da ilimi sosai a both side a kanki. So ni banga laifin a nan ba dan ya zabeki a matsayin pience din shi da har zaisa ita Alaja tace wai bata yarda ya gabatar dake a matsayin wace zai aura ba a yanzu. Tunda harke yake son ya aura don kina bashi tausayi da kuma kaunan ki da yakeyi right ta dan daga gira tare da kara kura min idon ta sai kuma ta nisa tana fadin. At this age da kike ya kamata ki huta hakana sahiba, ke din baki cancanci wanan rayuwan wahalan ba kamar wani namiji ko yaushe kina kan aiki nasan abinda yayana ke kallo a gareki ke nan yanzu don nasan halin shi. Amma mommy bata gane me yake nufi ba har tana fadin bata yarda ya kawo mata ke a matsayin sarakuwa ba ke mai juju ce a kanki. So ni ban damu da duk abinda kike dashi ba a kai tunda yayana yana son ki a hakan da kike, meye matsalanta tunda bada ita zaki zauna ba. Don nasan yayana nasan halin shi yana da ilimi da hankali da hangen nesa gashi da tausayin na kasa dashi duk da mahaifiyar mu bata son hakan tace halin daddy din mu da haka akai poisining din shi da goro a kauyen su. Ni nasan idan ba yaga dacewan ki dashi ba daba zai taba yarda ya nuna mata haka ba don ita wanan dai yar yuhanus taso ya aura a yanzu amma ni sam batai min ba. Shi kuma ya nuna mata kece ya yanke zai aura don haka yana da right da zai zabowa kanshi abinda zuciyar shi ke so a yanzu. Amma taki ta gane hakan ita duk da shita samu da nice nan kingan ni da kawai zan fitar zancen tane in yi abinda nake so a rayuwana tunda ita tayi nata zamanin. Na kallo ta cikin mamaki don na sandare a lokacin ina jin abinda ban taba zaton jin shi ba daga bakin ta itako ta dauka zancen nata yai min dadin saurarene a lokacin. Taci gaba da fadin wai kin san me yasa mommy keson ko yaushe ta dinga zabawa brotherna mata ya aura ? Kai na girgiza mata kamar zombi tace ba komai bane fa don ta dinga juya matar yadda take sone kawai ne daga ita har brother dina. Kin san Mum nada wani hali da baida kyau ita burin ta a ko ita taga ta mallaki kowa da komai yadda takeso shine kawai dalilin ta nayi mai zaben matar da zai aura ko yaushe kada ta auro mai wace zatafi karfin ta. Ke din nan tace akwai juju a kanki ba zata taba yarda yayana ya auri mace irin ki ba a cewanta don zaki dinga fada mai halin da kowa yake ciki da abinda zai faru ga rayuwan kowa don tun lokacin a lagos ta tsorace da lamarin ki. Nan kan dan munafukin murmushi na sake a fuskana tace ai kin san matar shi ta farko itace ta nema mashi ita yar abokin daddy muce ita. Haka ta dinga juya ta har mutuwar ta bata isa ta sake da mijin ta ba mommy bata bari sam yanzu ko da wuya ta kara samun irin ta kuma. Haka bayan mutuwanta ta aura mashi wata a America saidai ita kan wanan mommy bata san ta fita wayau ba sosai don haka auren bai kai ko ina ba suka rabu a cikin wata shidda dayin auren nasu. Don haka ba kowane yasan da zancen wanan auren nasa ba don ko Nigeria bamu tafi da ita an ganta ba don hakama wasu basu sanda auren ba . You know what ta tambaye na girgiza kai tace ke mai sa,ace gaskiya kinsan abinda yasa nace hakan na dan kalleta sai tayi murmushi. Tare da fadin idan na fada maki brother dina bai taba soyayya ba zaki yarda da hakan wallahi shiyasa nake son shi dake don abinda zuciyar shi ke sone ke. Murmushi na sake kafin nace nima ina son ki saidai ina son ki sani tsakanina da yayan ki babu wani soyayya ko wani zance makamancin hakan gaskiya. Aikine kawai ya hadamu tare bayan haka ba wanan abin da kile zato a tsakanin mu na zancem aure ko wani abu can. Idan Alaja taso ta kwantar da hankalin ta ni aikine ya hadani da danta ba wani zancen soyayya ba can kawai dai ni taimakon juna mukeyi dani dashi. Sai zancen juju da take fada saukin abin ba zuwa nayi na saya ba wanan kyautane daga Allah daya nufeni da hakan don haka ko ita bata wuce wanan matsalan ba a wurin Allah. No kada ki damu ko ki dauki hakan da zafi sonda nake makine yasa har na fada maki sirin mu gaskiya . Kada ki damu Ganiyat wanan ba wai na dauki abinda zafi bane kawai dai ina son Alaja ta gane cewa ni danta baya gabana don haka ta hada shi da d uk wace take so . Ina fadin hakan na juya zuwa dakin da aka saukemu a cikin sa da ace a Nigeria nake ko kusa da gida ranN babu abinda zai sa kara kwana . ZAINAB IDRIS MAKAWA ANA DARA GA , , , , , , , , 7️⃣6️⃣ BY, , , , , , , , , , , , ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , , , , , , , , BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AL HAYYU , , , , , , , , , ONLINE PAID NOVEL YAR UWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA BA TARE DA HAKKIN KOWA BA DON BIYA KI TURA DARI BIYAR 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK 08036959257 ALLAH SARKI AI RAINA BAYA BACI YANZU DON KIN FITAR DON NASAN AKWAI RANAN HADUWA SEE U👋👋👋👋 Mun fita da tawagan mu don yo sayayyan tsaraba a lokacin na dan sawo abinda nake bukata a zuciyana daidai wani har umma da Ammar da yaran Abdul makwabcin mu don sune yan uwa na kusa a gareni yanzu da nake ji dasu. Har lokacin sosai nake jin zafin zancen Ganiyat a zuciyana wanda ba ita nake jin zafi ba sai ogan mu da mahaifinyar su da suka dinkeni ta baibai ba gyara ba dalili zasu dora min wahala a kaina. Ni sam ba zancen soyayya a zuciyana don banma taba jin son wani ba balle harkan soyayya ya wahalal dani haka yadda ta dauko min din. Sai ranan da zamu tashi da rana ne an fitar da kayan mu gaba daya zuwa airport kowa yana mamakin irin kayan dana saya bance da kowa kala ba muka fito a nan muka hade da Alaja data fito don yin sallama damu gaba daya sun hadu a reception din wurin a lokacin ne muka fito ni da yemisi a karshe. Tun kan mu karaso wurin mukai arba nida ita haka kawai naji gabana ya fadi abinda ban saba jiba ga kowaye na kalla kuwa bana jin komai ga mutum ni. Amma haka na daure na karasa wurin har kusan inda take zaune muka gaida ita a cikin ladabi ta amsa ba yabo ba fallasa tana juyawa wurin jimoh taci gaba da fadin abinda suke fadi lokacin. Mu zamu tafi na fada kai tsaye ina mikewa a lokacin Aisha Ganiyat ta iso wurin itama a cikin fara a aka shiga mata barka da fitowa tare da sallama . Mun tsaya mun gaisa da ita kafin naji muryan Alaja na fadin munji dadi sosai da wanan ziyaran taku bisa ga aiyukan da kukaimuna shima kuma din ya biya kowan ku hakkin shi dake kanshi. Me yuyuwa wasun ku daga wanan zuwan shine na karshe a garesu wasu kuma zasu iya dawowa da fatan ba zaku manta da halarcin dana ba a gare ku. Don ba karamin kokarin bane daukan dawainiya haka ga mutum ga tallakawan shi harku shida kai tsaye don haka sai ku gudewa Allah ku kuma tsaya a matsayin ku na cin arziki a wurin mu kada mutum yace zai wuce gona da iri don yaga wuri. Saboda hakane tun farko bana son mu rabi tallaka don su ko yaushe gani sukeyi kamar a banza mutum ya samu dukiyan shi . Sai kaga sun rabi mutum sun shige mai jiki kwana biyu sai su bullo mashi da wani hali na daban sabanin yadda sukazo a cikin talauci ka mayar dasu mutane. A lokacin zasu nuna ai dakai dasu din duk daya kuke a yanzu don haka duk maison aikin shi ya kiyaye ya tsaya a matsayin shi na dan aiki ko ba haka ba ? Tana kallon Jimoh take karasa maganan kai haba mama i don't think a cikin mu akwai irin wa yan nan mutane don haka abar zancen nan zaifi. Idan kasan kanka kasan wanine Felix ka bari kawai in fadi maganata don in akwai mai niyar yin hakan ya bari yemisi tace gaskiyane sai dai bana tsanmanin cewa akwai masu irin wanan halin a nan gaskiya. Mu nan ai yarda da sanin ya kamata ne ya kawo mu wanan matsayin bawai on contrac muke ko wani abu ba so banga inda wanan zancem ya taso a cikin mu ba. Aka sari irin tallakan nan anfi samun su a cikin students ko wasu masu zuwa yin safara na kasa da kasa sai kiga sun samu wani mai kudi ko wani kusan gwaunati sun makale suna ha,intar shi ai amma mu nan mun san meya kawo mu na fada. Kai gaskiya kika fada Sahiba Ganiyat dake bayana ta amsa aka sari students haka suke sosai kuwa nace kwarai ma kuwa da sunga mai kudi zasu like su nace tundai mata koda ba kabilan su daya ba saboda kwadan abin duniya zasuma iya auren su don kawai su mallaki kudin shi suci su zama wani abu nan gaba su dawo suna raina mutane kamar da farko suma din abin tausayi bane. Shiru kowa dake wurin yayi lokacin da nake wanan maganan ido rufe Abduhamid ne yazo ya kama hannuna yana fadin ai bakiji ba Sahiba wai saida muka shirya mutumiyar ki ta bugo waya na sayo masu sarka. Da hannu yayi signal sai ga yemisi ta biyo bayan mu da sauri a tare muka fita da ita zuwa inda motocin da zamu bar haraban suke. Karshe ashe a can basuyi sallama da dadi dasu ba don yadda Alaja ta fara zage zage dole a bar wanan abinda yanzu yake ikirarin yasa aiki a gaba yana barnan kudin shi ga wasu. Sai zancen ya koma tsakanin ta da yarta dan a gaban kowa ta fadawa uwar cewa abinda takeyi bai dace ba tayi fada sosai har ran uwar ya baci itama ta fara mayat da amsa a gareta. Bamu dade a airport ba jirgin mu ya daga zuwa Nigeria kai tsaye har lokacin ina dai zaune ne banyi wa kowa magana ba saukan dare mukayi . Don haka saida safe muka isa gidajen mu kamar yadda ya umurci akai kowa har kayan shi gidan shi idan mun sauka mun gama clearence din kayan mu. Ni da Abdul ne zaune a baya sai Adanan a gaban motan tare da driver dake jan motan mu muna zaune a baya tunda naga na sauka kasa na lumshe idanuna a hankali don murna. Ban kara jin dadin hakan ba saida muka tun karo unguwar mu na hango gidan mu wani dadi sosai ya kumeni lokaci guda. Safiyane yara sun fita zuwa school sunyi resuming a wanan satin ya kasance unguwar ya kara yin shiru a lokacin kamar wani brack din sojoji. Motan ya tsaya a kofan gidan nikan tunda muka sauka na sauke ajiyan zuciya da har yasa Adnan juyowa yana min sheri dayin hakan nan na barsu zuwa ciki sai ganina kwatsam umma tayi na shigo gidan. Sun shiga muna da kaya cikin gidan har lokacin ina manne a jikin umma na ban iya yin komai ba sai da suka gama hawowa da kayan nayi godiya suka tafi. Mikewa nayi na shiga dakina dana sama a gyare tsab kamar ina kasan dama don kullun sai an gyara min dakin an saka kamshi a cikin sa kamar ina nan. Wanka na shiga na fito banko saka kaya a jikina ba na nemi wuri mm a kwanta sai wani irin barci mai nauyi koda umma ta lekoni ta samu nayi barci a lokacin. Fita tayi zuwa gaida Abdul da dawowa suna dan hira har take fada mashi cewa ai nayi barci ko a lokacin yace Allah yasa koda zata tashi abubuwan nan sun fita kanta. Nan dai yake ba umma labari sama sama sai kan umma din ya daure don ta kasa fahintar me ya kawo haka tsakanina da mahaifiyar ogan namu. Barci nayi sosai a ranan don sai bayan la,asar na falka nayi alwala na dan saka riga a jikina zuwa falo. Shidai a iyakan binciken shi ya kasa gano dalilin mahaifin su mm a boye wanan file di a lokacin yasa ya kara yarda dole akwai wata a kasa dai tsakanin daddy din da su yan uwan nasa. A hankali ya jawo mota zuwa gida sai dai bai samu Nazifa a gida ba kuma bata fada mai cewa zata fita zuwa wani wuri ba da zai fita. Har ya gama abinda yakeyi ya fito gidan bata dawowa ba restaurant ya nufa yaje yaci abinci inda sabo ya saba da hakan kamar wani gwauron da baida galihu. Yasan dalilin yi mashi hakan don sun kwasa da safe da ita da yake tana son kudi a wurin yau sammako ta buga mai a daki ta sameshi yana shiri take fadin tazo ne taji guduwan mawan da zasu aikawa Abban ta dashi. Do yan uwanta sun fara kawo mm nasu za a saka ido aga ita me zasu kawo a nasu bbangaren jin yayi shiru har ta kare zancen ta baiyi magana ba yasa ta kallo shi tana fadin kana ko jina. Indai jine ina jin ki mana tunda ba kurma Allah yayini ba ke yanzu bakiji kunyar tunkarana da wanan zancen ba ? Kallon shi tayi cikin mamaki tana fadin kunya a kan me don kawai ka taimakawa Abbana kome aida wanine a can gidan ku ko banyi magana ba zaka bayar. Wanan kalamin nata yasa bai kara tanka mata ba sai yaga magana ma zai tsaya ta kara bata mashi raine a banza don haka yai shiru kawai ya kyaleta. Karshema fita yayi daga gidan kai tsaye ya wuce headquater din su wurin aikin da yake son yi a cikin file din nan ranan haka kuma yasa ta fita zuwa gida don su tattauna da mahaifiyarsu. Tako samu a jirace mahaifiyar take da ita nan ta fara mayar mata aikuwa bata kai karshe ba tayi cikin ta da sababi sosai ta zage ta tas tare da mata fadan fitar arziki. Ta kuma umurce ta dace ta koma tayi mai magana a cikin lalashi da ban hankari don idan bai basu kudi mai tsoka suka ba Alh ba wallahi akwai matsala a surin su sosai. Shine ta dawo bayan la,asar ta samu ya fita baya gida kuma taga alaman ya dawo gidan saidai bai dadeba ya fita kuma. Zaman jiran shi ta zauna yi bai dawo ba sai gab da magariba ya shigo kai tsaye dakin shi ya nufa don yana son ya raba jikin shi da kayan daya saka lokaci. Saidaya gama duk abinda zaiyi ya hau gado ya kwanta yana tunanen duniya don shi yasan idan ba gaskiyan zancen nan ya sani ba baida sauran shakat a zuciyan shi don alkawarin daya daukan wa kanshi kan haka sai ya gano gaskiyan maganan. Duk da yana fargaban ace da hannun daddy su dumu dumu a cikin kisan baffan nasa da dawani ido zai kalli ahalin sa a matsayin dan wanda ya kashe masu uba. Ido ya runtse a lokacin yana maijin zuciyar shi tana mashi zafi sosai mutumin da duk wanda zai fadi wani zance akanshi na alherine da yabo. In ka debe wanan matsalan da yan uwa suka dora mai na cewa shi ya hanasu yin arziki saboda sun camfa mahaifiyar shi har shi din da wanan mumunan zaton nasu. Shigowan Nazafi dakin ne ya katse mashi tunanen sa bita yayi da kallo har ta karaso tazo ta zauna a gefen gado yana yadda ta sameshi a rigingine bai motsa ba har lokacin. Baban maryam na dawo ban hakkura ba ta fada a daidai lokacin da yaji wani irin zafi a zuciyar shi na yadda take kiran sunan maryam gatsau haka a gaban shi . A cewan ta ta juye sunan mahaifiyar nasa zuwa na kanwarta da kakanta wai ai sunan sune ya saka bana mahaifiyatshi din ba. Nan ma dai shiru yayi mata shi kadai ke jin yadda yake ji a zuciyar shi lokacin a kanta ta sake fadin bb maryam don Allah kayi hakkuri ka saurareni . Kada kayi fushi don Allah dani kace ba zaka ban kudi ba in kaiwa Abba don wallahi duk yan uwana sun kawo masa nasu gudun mawar nice da hafsat muke rage bamu bayar ba a yanzu. Nan kan ya dan muskuta yana fadin me kudin makiyi zai karashi dashi a yanzu tunda a matsayin makiyin shi nake nida kowa na gidan mu a zuciyan shi. Shine kuma zan dauki kudina yau in bashi ai kema kin san ba zai karba tunda ni da diyana jinin makiyin shi muke. Wanan zancen da kakewa Abba yanzu kan ko wanda bai hada komai dashi ba ya kawo mashi kudi ai karba zaiyi yadda yake neman kudin nan ido rufe. A yadda naji har filincan nasa na hayin malali ya saka a kasuwa wai ba a taya filin da kudi me yawa ba yasa bai sake shi ba. What ya fada da karfi yana dagowa daga kwancen da yake ya kara maimaita tambayan da badai filin nan daya fara gina company atamfa a cikin sa ba ? Ta dauka ya damu da jin hakan ne sai tace a cikin marairaice wallahi kasan mutane da son banza suka dinga taya masa shi a wullakance shine ya fasa gashi ance lokacin da aka basu ya kusa cika dole yaje da wani abu mai dan tsoka da zai fara biya. Umm,mm ya fada ya koma ya kwanta yana jin wani irin a zuciyar shi lale wanan mutumin da karfin hali yake sosai watau filin marayu din daya mallakawa kanshi da karfi da yaji shine zai saka kasuwa yanzu da yake ganin filin zai iya fita hannun shi duk da basu yarda da cewa iyalan mai filin suna raye ba . Ba abinda ya kara daga masu hankali kamar jin wai harda da umma tazo masu wai dan dan uwan sune shima din wanan ya fi daga hankalin su sosai don a mota da zasu dawo daga karbo Alh Nuhun can abuja yake jin su baffa hamza na wanan firan. Muryan Nazifa ne ya katse mai dogon tunanen da ya shiga din lokaci guda tana fadin kaji dalilin dayasa akai shawaran tara masa kudin a bashi. Ok naji sai na duba ya iya fada don baison maganan ta kara masu nisa a tsakanin su yana son yin dogon nazari a lokacin. Shine washe gari ya dauki waya ya kira umma yaji yaushe zamu dawo don asan abinda za ayi kafin Alh Nuhu yakai ga kadar da filin ya salwance a dauki mataki. Bayan sun gaisa da umma ya tambayi lafiyan sune yake fadin ya labarin Sahiba umma yaushe zasu dawone daga tafiyan ? Sai umma tace a cikin murmushi ai gata nan a gaba da safen nan suka dawo masha Allahu ya fada tare da fadin an dawo lafiya ko ya aiki kuma ? Na amshi wayan ina fadin yaya mun sameku lafiya ya su mimi da maman su karo na farko tun farun matsala a tsakanin a baya . Duk suna lafiya ya fada OK zan barki ki huta zan shigo zuwa jibi akwai maganan da nake son zamuyi daku na muhinmin idan nazo din. Ok yaya na fada a lalace ina mikawa umma wayan dake hannu din ta karba ban san dogon bayanin da yake mata ba a lokacin na dai ga umma ta bata fuskan ta sosai lokaci guda. Sai bayan sun gama wayan ne umma ta sauke ajiyan zuciya tana kallona take fadin wai filin mahaifin kune da Alh Nuhu ya mallaka har ya fara gina a cikin sa yasa a kasuwa zai saida ya biya basusukan da ake binshi yanzu. Au filin yana nan ashe na fada cikin mamaki ina kallon umma tace haka dai yake fada min yanzu wanan akwaishi da karfin hali da iya cin amana. Ya kai karshe don wanan ko ya sayar saiya dawo hannun mu na fada ina komawa kasan kafet na zauna tare da kallon ammar wanda nasan ni yake jira na bude kaya ni kuma naki bude mai. Murmushi ya sauke a fuskan shi yana fadin anty please na nuna mai kayan da hannnu ya dauko muka fara budewa don ni kaina ban san meye a cikin sayayyan nasaba tunda bani na saya ba. Allah da ikon shi kayan umma ne muka fara budewa kalla bakwai irin dunkunan Dubai din nan na manyan mata tun a jakkar na gane haka don an rubuta a harshen larabci da ~umma~ . Nan muka duba mukaga komai na ciki harda wani handbag mekyau sosai na manyan mata na Ammar na jawo na duba suna na tura mashi gaban shi ya bude. Komawa nayi na jingina kaina saman kujera tare da dan mayar da kan nawa baya ina lumshe idona ba komai nake tunane ba sai zance biyu na farko zancen sayar da filin Alh Nuhu sai kuma zancena da Alaja. Ihun Ammar ne yasani dan dagowa ga yadda nake zaune ina kokarin ganin abinda yakewa ihun wasu suit ne size din shi masu kyau gaske irin da yaran su can ke sakawa ya dago yana fadin Antymi wanan rigan yai min kyau sosai wallahi ya fara min godiya. Bani na sayama ba na fada kai tsaye don ban iya karya ba na kalli na umma da nawa nace ogan mune ya sayo wa yan nan duka a dubai. Wani kallo umma ta jefo min mai alaman tambaya nayi saurin fadin wallahi umma ban san zai saya ba yanzu ma mamakin hakan nakeyi yadda ya iya zabe haka kamar an auna tsayin ku. Wayana ne ya dauki kara na mika hannu saman kujeran na dauka ina dubawa don ba wanda ya kirani tun shigowana gida har washe garin nan. Sabon layi na gani na kasan waje daga kasan Germany da mamaki a fuskana na dauki wayan ina daukan wayan a bangarena. Irin sallaman dana tashi dashi a bakina na dabi,an yarbawa nayi a wayan muryan da aka amsa min sallaman ne a lokacin yasa gabana faduwa lokaci guda duk da na sheda muryan me kiran nawa a lokacin. Kun isa gida lafiya ya kuka samesu duk ya fada a lokaci daya da kyar na samu cikin kyarman murya na hada dace masa Alhamdullahi. Masha Allah ya fada sai kuma yai shiru kamar yadda nayi shiru a nawa bangaren bayan dan second na tsinkayi muryan shi yana fadin. Ina Germany na samu contrac dasu zan shigo masu da wasu kaya daga Labeno sun yarda sun saka min hannu wanda hakan zai jawo min dagawa sosai da yardan Allah. Masha Allah nafada tare da mashi fatan gamawa dasu lafiya na nuna murna a fili kwarai ya dan kara min bayanin yadda abun zai kasance mashi kafin ya dan sake yin shiru na wani lokaci yace. Kiyi hakkuri da abinda mahaifiyarmu tai maku sahiba musanman ma ke kasancewa na bana wurin lokacin da hakan ya faru a tsakanin ku. Murmushin dole nayi ina fadin haba dai wanan ba komai bane don muma ai tana a matsayin mahaifiyace a garemu na tsunci kaina da fadin hakan. Nasan hakan Ganiyat da Jimoh sun fada min komai daya faru don haka kiyi hakkuri tunda mun san dalilin yin hakan a gareki. Na fahinci yaji komai daya faru a dubai din nace kuskure fahinta ne aka samu duk wani mairai idan abu yazo masa a lokacin da bai zata ba zai iya aika kome yake gani a matsayin kariya a gareshi. Nagode ya fada yana sauke ajiyan zuciya a hankali har ina iya jiyoshi ku zauna ku huta na mako daya kada ku fita gun aiki murmushine ya dan subce min nace. Oga ai mun huta zaman yayi yawa hakana gara mu koma bakin aikin mu don nema ya kaimu wurin ka ba hutu ba don haka dole mu koma muci gaba da aiki hutun ya isa hakana. Ke baki kama da wace zatai ta aiki ko wani lokaci ba hakana shigan ku office officialy ne yanzu sai idan bukatan hakan yataso a garemu. Wani nauyi da kunya naji lokaci daya nace nagode yace kada ki damu nike da godiya a wirin ku ki mika min godiya ga mama ya kashe wayan. Na dago muka hada ido da umma data tsura min idanu budan bakin umma tace min kiyi hankali da irin mutanen nan da suke yawan son diyan su maza . Kallonta nayi cikin mamaki tace kwarai saboda data kula da cewa wani abinda batayi tsamani ba yana shirin faruwa a tsakanin ki da danta yasa ta fara bullo maki da haka. Batayi karya ba don ko wani tsuntsu kukan gidan su yakeyi tana ganin ke bakiyi daraja da mutuncin da za a ce danta ya nemeki ba don kedin ba yar kowa bace take gani kuma ga wanan matsalan dake a kanki. Sai lokacin nayi magana jin umma tayi shiru nace umma ki gafarceni ban taba saurayi ba a tarihin rayuwana. Saidai a tunanen ita Alaja din tana ganin kamar muna soyayyane da dan nata wanda ba hakabane a wajen mu nasan dai ya bukaci in taimaka mashi in nuna kamar soyayyan mukeyi a gabanta. Nan dai na labarta mata abinda ya faru a can kaf ban boye mata komai ba saida na gama take fadin wanan gangancin fa Sahiba ? ZAINAB IDRIS MAKAWA ANA DARA GA , , , , , , , , 7️⃣7️⃣ BY, , , , , , , , , , , , ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , , , , , , , , BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AL QAYYUM , , , , , , , , , ONLINE PAID NOVEL YAR UWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA BA TARE DA HAKKIN KOWA BA DON BIYA KI TURA DARI BIYAR 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK 08036959257 ALLAH SARKI AI RAINA BAYA BACI YANZU DON KIN FITAR DON NASAN AKWAI RANAN HADUWA SEE U👋👋👋👋 Washegari tunda safe na fara shirin don samako nake sonyi zuwa inda na kwana ina kullawa a raina. Koda na fito su umma basu tashi ba a lokacin ko Ammar dake fita school bai tashi ba na bar gidan Allah ya taimakeni na samu mai taxi irin masu sammakon nan na safe nace ya kaini airport. Already Felix yayi min bucking din jirgi tun karfe bakwai na yammacin jiyan na godewa Allah don yan mintuka kadan suka rage jirgi ya tashi na iso. Karfe sha biyu na shigarda kara da taimakon Bello ma,aikacin mu da yazo ya daukeni a airport mukai duk wani abinda zanyi ya juya dani ya kaini airport jirgin karfe biyu muka shiga lagos karfe hudu da rabi ina cikin gidan mu a zaune ba zakace na tafi kaduna a ranan na dawo ba. Gaida umma nayi da gida don a shago na sameta na hausama zuwa part din mu wanka nayi na fito na tayar da sallah ban tsaya neman abinci ba nabi lafiyan gado na kwanta sai barci. Baifi awa daya ba na falka don wayana dake gefena daketa ringing na mika hannu na dauka a jagule a cikin muryan barcin dake idona a lokacin. Harshen yarbanci ya zaunu a bakina na dauka ina tambayan wake magana a cikin yarbanci saida gabana ya fadi lokacinn da naji muryan Daddy a kunne na. Hausa yake min na nuna mai banji me yake fadi ba na kashe layina kai tsaye har wayan a lokaci guda ina jifa da wayan gefe daya. Ido na mayar na lumshe da niyar barci sai kuma barcin ya gagareni don tunane ya rinjayi zuciyana a lokacin don babu abinda yazo min sai mamakin kiran da daddy yake min a wanan lokacin. Shigowan umma dakin ne ya hanani ci gaba tana fadin Ngwa Sahiba yau ki tafi kadunane ko me ta miko min wayan tana mamaki tare da fadin yayan mune ke magana dani. Na karbi wayan a hannun ta na kara a kunnena ina jin dan hayaniya a wurin koda yake min sallama don haka na gane cewa bashi kadai bane a wurin lokacin. Mikewa nayi zaune da kyau ina karba mai sallaman sai gaisuwa daya biyo baya a lokacin kafin yace wani abin mamakine yaji don gasu nan the all family sun hadu ana neman iyayyen su a kotu ranan Monday . Wai nice nake kalubalantar su akan dukiyan mahaifin mu shine daddy ya kira layina ban ganeshi ba an nema daga baya wayana akashe. Sai Umma suka samu yanzu wai ya wanan zancen yake ne ko ina da masaniya nace idan munje kotu zamu hadu a can suji komai amsan dana bashi ke nan kawai a lokacin. Kace ubanta dake kwance a cikin kasa koshi ya taso yayi kadan yace zai wullakantani naji muryan baffah Nuhu na fadin hakana sai dan hayaniya daya biyo baya a lokacin. Recording din wayan na dana tun karbana haka yasa na sauke wani irin murmushi tare da fadin if he insult my father again i know how to handle him i swear will turne dat his folish mouth to his toes. Alh wallahi ka daina don yarinyar nan da ji bata data ido kaji abinda take fada yanzu a cikin waya naji wani murya na fadin hakan ashe baffah hamza ne lokacin rike da wayan daya karba a hannun ya Abubakar din. Ko uwarki mairo tazo nan bata isa ta tunkaremu haka ba hujja ba, , , , , subbahanallahi na fara ji a cikin wayan sama sama iya abinda zan iya karasawa ke nan a lokacin. Ku kamashi mana kada yakai kasa subbahanallahi innalillahi kagani ba kunga abinda nake fadi wallahi yarinyar nan bata tun karo mu ba saida data shirya muna . Duk sun manta wayan yana kunne ake ta wanan hayaniyar wasu na fadin ku kamashi a kaishi asibiti zaifi kada a barshi gida haka don Allah. Dif umma dake sauraren su taji wayan ya mutu lokaci guda gidan baffa Amadu kanin mahaifin iyayyen mu kuma sai ya dauki salati da tashin hankali. Hanklin kowa a tashe yake a lokacin dole asibiti aka nufa da Alh din fitowa magariba labarin komai ya isa kunnen yan uwa don a gaban kowa lamarin ya faru. Bakin shi bude ya shiga common nan iyalin shi sukaji meke faru aka fara fada masu abinda ya faru baffa gyade yana fadi a cikin hasala Saida baffa buhari yace kai gyade ka kama bakin ka wurin nan kada naka ya sameka yanzu kana fama da kafafun ka. Shiru yaran sukayi suna sauraron abinda iyayywn nasu maza suke fadin wai wace yarinya wanan wanda ya kawo min hari ya juya masu a kaduna ya sake tambaya. Baffa gyade yayi mai bayani yace kut wanan yarinyar shu,umace ta gaske yoooo ai shegiyace ta gaske don a shirye take da kowan ku nan ya nuna su da yatsa har yan uwanshi naji haushin shi. Yace ni tsoho ya tura aiki kwanaki wurin ta yasin nayi wata daya ina ganin suranta a mafalkina duk na kwanta barci itace fa wanan, , , Kai ya isa haka don Allah bari muji da abinda ya damemu a yanzu yace alkur,an idan itace tsoho ya kara tabowa yanzu kuma sai kun lalubeta na rantse maku. Idan kuma kun dauka wasane toh ku gwada ku gani aishi tsoho yasan ko ita waye don ya gwada duk sa,anshi a kanta karshe saida ta laishi makargama. Aiko take wurin hayani ya fara tashi wasu na masa kallon mashayi wasu kuma kallon tababe ake mashi baffa hamzane ya ratso tsakiyan dakin yana fadin. Yanzu kun daiji abinda yaron nan kalla,mu ya fada saboda haka a gwada don kallamu yafi mu sanin Alh da komai nasa kun sani. Aiko a gwada din zaifi ya kara fada daga kofa shi kallamu din yana fadin wanan shegiyat kila a indiya take zuwa tsafin ta tunda bata tsoron kuna. Mata gungun su daban mazan ma haka ga matasan diyan su a gefe daya suma suna nasu a daidai wanan lokacin da ake wanan maganan daddy da mommy suka shigo cikin dakin dake shake da yayan fulanin asali na kurnan kaya a can cikin jahar yola wanda suke surkukin daji daba kowa yasan dasu ba sai yan asali. Daddy sun sama baffah hamza na fadin tsiyan abin yanzu ko an kira wayan bata dagawa idan ba wayan modibbo bane. Meke faruwa daddy dake kallon yanayin Alh nuhu din dake kwance shirim saman gado baki bude ya juye ya koma gefe daya sai ya baka tausayi a lokacin don bai san wanda duk ke wurin ba sai numfashi da yakeyi sama sama a lokacin. Yace kun dauka wanan ne dalilin ne yasa hakan faduwane kawai don damuwa da yai mashi yawa amma ai ita yarintane kawai ke cin ta harta furta hakan. Wanan zancen da daddy yayi yasa suka dan lafa amma zagi kan ranan na shashi a wurin wa yanda suke dauka kazafi nayiwa iyayyen nasu a lokacin. Duk yadda daddy ya kira layina kona umma a ranan muki dagawa har na dan nasu Abubakar din ba a daga ko daya kwatsam sai ga kiran dan hjy halira a wayan umma lokaci guda. Nice na daga wayan a lokacin kwana biyu da faruwan hakan tsakanina da Alh nuhu da har lokacin yana kwance a yadda yake. Ina sheda muryan shi na mikawa umma wayan tare da fada mata mai kiran ta din ta dauka suka gaisa da umma lafiya yake tambayana tace gani kusa. Yacewa umma din mahaifiyar shice take magana da umma tace a cikin mamaki hjy hari yace ita gata zasuyi magana. Muryan hjy hari din ne da sallama suka gaisa da umma akayi yaushe rabo don inaga har kuka saida tayi a lokacin kafin ta fara magana akan karan dana saka yan uwan ubana kan gadon mu. Dan murmushi umma ta sake kafin tace wanan zancen sune da yarsu kinsan ita ta gado komai na kakanin ta itakeda karfin halin iya tunkaran su kan wanan a yanzu. Hjy hari tace bazance kada ta nemi dukiyan su ba a yanzu amma komai nason sulhun gida kafin a kai ga hakan. Naso nazo lagos din wurin ku kodan in ganku in saka ahalin yaya marigayi a idona wallahi Allah da ace nasan kuna raye da ba haka ba wallahi. Don haka ku shirya ku zo nan kaduna duk ayita ta kare a zauna a sulhunta wanan zancen don magana ya gama karade garin nan kowa da irin abinda yake fadi akan zancen. Zamu zo ai a cikin satin nan da za,a shiga kotu insha Allahu muna kaduna zanso idan kunzo na ganku kafin kowa don da abinda nake son mu tatauna daku. In son samune zaku iya sauka a gidana idan babu takura kada ku zauna hotel ko wani wuri a,a ki barshi yarki nada gida a nan kaduna da muke zama a cikin sa bamu da matsalan wanan ko kadan. Sunyi sallama an barta da mamaki ashe wai har kaduna din muna zama da sunan aiki amma duk basu da labarin hakan ? A cikin satin sau daya nafita aiki ido yayi min yawa na canzawan da nayi sai kuma ga tafiyan kaduna ya riske mu haka muka shirya tafiyan yamma mukayi muka isa goma na dare don juye mun da akayi a abuja sai muka kara bin wani jirgi zuwa kadunan Belli ne yazo ya dauke mu zuwa gida a lokacin. Ya Abubakar ne ya gano duk kwana biyun nan ina cikin kaduna don haka ya tunkaro gidan namu daya sani kai tsaye tundaga nisa ya hango wuta gidan a kunne alaman akwai mutum.a gidan lokacin . Bai shiga ba ya juya zuwa yayi ya fadawa su baffah hamza da uncle Abdullahi sai gasu tare sunyi sallama muna zaune mun idar da sallah suka shigo. Sau daya na daga kai na kallesu ban sake kallin inda suke suna gaisawa da umma ba sai kokarin shiga daki danayi a lokacin. Ummace ta hanani take min yarbanci idanuwan su tar a kaina suna min kallon mamaki ina saye da dan t-shirt fari mai rubutun da manyan haruffa i wander why na kamfanin Nike sai dan bakin wandon jeans daya tsaya min iya idon kafa ya matseni kaina daure kawai da ribon da hulla mai raga . Nima cikin harshen yarbanci nake fadin zan shiga cikine kawai aiba wurina sukazo ba don kiris ya rage a lokacin na sako hawaye a idona lokaci . Kai haba hjy mairo baki koyawa diyan mu yareb mu ba sai yaren wasu kabilu can na daban baffa hamza ya fada yana kallona har lokacin a cikin mamaki. Umma dai batace komai ba son fuskanta a daure yake lokacin sai naji baffh Abdullahi na fadin suna jin fulacin kila wanan yaren daine yafi karfi a harshen su don zama cikin su da sukeyi. Ya Abubakar kuwa duk yana jin su baice komai don gaba daya na kula dashi baya cikin hayacin shi a lokacin sam. Dan shirune ya biyo falon bayan na dawo na zauna din baffa Abdullahine ya fara magana yana fadin Mairo da farko zanso na kara maki gaisuwan rashin dan uwan mu kuma shakikin mu wanda bamu samu natsuwan maki ba tun a wancan lokacin mai tsawo daya wuce zuwa yanzu. A hankali na dago kai na dan kalleshi kafin in mayar da kallona a wurin umma a lokacin da take fadin hakkurin namune ai duka Allah yayi mai rahama suka amsa da Amin. Ya Sambo ya tafi ya huta saidai ya bar baya da kura akan dukiya munga abubuwa da dama mairo wanda har muka fara tuhumar ko hakan na daga cikin abinda yasaki barin gida dake da yarki a lokacin ? Kafin umma tai wani magana Ammar ne ya fito daga dakin shi yana saye da wando three quarter na maza fari sai riga mai photon zaki a jikin shi light blue clour daya dauki jikin shi suka bishi da kallon a cikin mamaki. Falin yayi shiru shima din dan kaduwa yayi da ganin su sai daya dan nuna razana a fili kafin ya gaidasu yana fadin good evening sir yayo inda nake zaune ya zauna a gefena rabin jikin shi na a jikina. Ammar kuna garin nan baka kirani ba ashe sai lokacin ya kula da ya Abubakar din ya dan mike a cikin mamaki yana fadin broda welcome i no see u shaaa. Suko mamakin kamar yaron da mahaifin mu ya hanasu ko motsi a lokacin sai can baffa Abdullahi ya nisa yana fadin ikon Allah kunga wani ikon ubangiji a nan wurin kuma ke nan ? Bari kaidai ina ganin kamar gun wanan macen sai kuma shi wanan din yace ai ga inda kaman yake dashi sak. Watau dai lamarin nan kawai saidai a barwa Allah ikon sa don zance ya kare a nan yanzu illa kawai yanzu mu tunkari baffa Amadu da wanan zancen. Ammar din ya mike zuwa wurin ya Abubakar yana tambayan shi yaran shi sai baffa hamza ya ce kai ku tashi mu tafi sai gashi yana share hawaye daga fuskan shi dake zubo mashi yana fadin wanan alhakin dame zamu amsa shi gaban ubangiji. Da kuka suka fita daga gidan mu dai muna zaune a inda suka barmu sai ammar ne yabisu suna rike dashi da yaya Abubakar din can ya dawo yana kulle gida yake fadin sun tafi ai tare da tambayan masu kukan nan suwaye su wai ? Su baffane zaune a gaban kannen mahaifin su suna kuka wi wi wi kamar mata tare da fadin anyi sakaci baffa sakaci ba karami ba wanda na tabbatar da sai Allah ya tambaye kan hakan. Ace diyan dan uwan mu suna raye haka a cikin duniya sun koma kabila zaka rantse baffa na diyan mu bane idan kagansu. Zama tsohon ya gyara yana fadin to kai banda abinka Hamza a cikin kabilu fa uwarsu ta tayar dasu koda a nan arewane yau akace mace ce zata ba yaro tarbiya ba tare da mahaifi ba ya kuke tsamanin tarbiyan nan. Hakane baffa ya gyara zama yana fadi tare dayin fifita da hularshi daya rike a hannun shi kafin ya kara gyara zama yana fadin kai jiya munga ikon Allah Baffa kamar yaron sak dana ubanshi har tafiyan nan na marigayi din. Yanzu dai karfe biyu idan an fito daga sallah sai a hadu a nan din a fadawa kowa kamar yadda aka sabayi harsu din sai a fada masu. Saidai kan yana da wuya ace sun amsa wanan kiran naku nake gani don gaba daya suna nuna kamar basu yarda damu bane ga baki daya mu nake gani. Dole a yanzu su nuna hakan amma idan an fahinci juna komai zai koma yadda yake don haka a kara hakkuri baffa Amadu ya fada sukai mashi sallama suka tafi tun a mota suka fara waya suna gaiyatan yan uwa har mata wurin wanan haduwan. Kamar yadda umma tayiwa hjy hari alkawari nice na tuna mata ta kirata tare da mata kwatancen inda muke sai gata da safen sun shigo da dan nata. Ina daki kwance sai kulawa da kwancewa nakeyi wanda har lokacin ban gama tsara yadda nake so ba naji sallaman su har fitowan umma daga dakin ta. Tayi masu sannu da zuwa bayan sun shigo sun zauna akai yaushe rabo da juna naji muryan Ammar daya fito yana gaidasu . Kuka naji gwaggo hari din tanayi tare da wasu maganganu hakan yasa na fito daga daki a lokacin daidai kujeran dake saiti da inda zan shigo falon daga dakina na tsaya tare da dafa kujera ina gaidasu. Naji tace zo gareni yata ku gafarce wanan duk sherin su yaya Nuhu ne kedai kin san komai dama mairo sai yanzu na kara yarda da cewan da akeyi suna da hannu a cikin kashe muna dan uwa dayawa mutane sun fadi hakan lokacin da sukaga ba a dauki lokaci ba an wawashe abinda ya bari kuma ba a nuna damuwa da bacewan ku ba. Ba wani nuna damuwa da akayi a lokacin haka ana kallo bayan kowa yasan irin makircin su yaya nuhu har suka rabe dukiyan ku iyasu ba wanda ya iya masu magana duk da asanshi da iya salwantar da rayuwa ba wani aiki bane a wurin shi shi yanzu. Kitchen na nufa don ban iya jin wanan zancen nasu bansan abinda yasa ba ko sau daya ni ban taba jin wani darrr akan shi ba yadda naga mutane na nunawa koda sunan shi sukaji. Wai a cewan su ko sunan shi ka kira ka zageshi yana ji ko a wani garine kuwa don haka mutane suke yawan tsoron shi sosai. Daga kitchen din ina jin abinda suke fadi a lokacin naji muryan gwaggo hari tana fadawa umma a cikin damuwa cewa ayi hakkuri tunda Allah ya dawo damu cikin su lafiya a janye wanan karan da yarinyar nan tayi a sulhunta komai a gidan kada daga baya hakan yazo ya jawo muna matsala wani abu yazo ya samemu kuma don halin su baida kyau har gobe zasu iyayin komai don dukiyasu. A fusace na fito daga kitchen din na tsaya a inda zata iya ganina gaba daya yanayin fuskana ya sauya raina ya baci bakikirin idanuwana duk sun kankance na fara fadin . Kuna ina a lokacin da aka watsar damu a cikin duniya ko lokacin da suka kashe muna mahaifin mu a kan abin duniya wani mataki a ka dauka a lokacin har batan umma damu da ba,a san ida tashiga ba na tsawon lokacin nan. Yanzu lokaci yayi da komai zai baiya kara muradin mu a yanzu ba karban dukiyane kawai ba don nemawa mahaifana yancin sune da aka tauye a lokacin na dawo yanzu koda nan karbi komai nasu ba dolene abiwa mahaifana hakkin su a yanzu kan duk wanda ke da hannu a cikin cuta masu. Na kare magana ina jefa mata wani irin kallo na ke kinsan koni waye kuwa a yanzu ? ZAINAB IDRIS MAKAWA ANA DARA GA , , , , , , , , 7️⃣8️⃣ BY, , , , , , , , , , , , ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , , , , , , , , BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AL WAJID , , , , , , , , , ONLINE PAID NOVEL YAR UWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA BA TARE DA HAKKIN KOWA BA DON BIYA KI TURA DARI BIYAR 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK 08036959257 ALLAH SARKI AI RAINA BAYA BACI YANZU DON KIN FITAR DON NASAN AKWAI RANAN HADUWA SEE U👋👋👋👋 Kallon mamaki suke bina dashi don abinda na fada yanzu a gaban su kafin gwoggo hari ta koma ga kallon danta tana fadin . Kaga abinda yasa tun farko nace dakai mu fitar da bakjn mu a cikin wanan zancen ke nan ka matsa min saina gamsu na taushi zuciyan su yanzun dai kaji wani sabon fitinan da suke son su jawo a cikin ahalin mu kuma wai su yaya Nuhu suka kashe masu mahaifi. To ke banda abinki mairo ai naga a lokacin da abin ya faru kina cikin hayacin kuma tare dake akai komai baki fadi hakan ba sai yanzu. Wani murmushin takaici umma ta sake wanda ban taba ganin tayishi ba a fuskan ta cikin yan dakiku ta koma kuma ta daure fuskan ta murtuk kamar wace bata taba yin dariya ba. Tace ga dalilin rashin fadan yanzu kin bada amsan shi da kanki hjy Hari kallon ta gwaggo hari din tayi na bam fahinceki ba fa ? Ehh lalai na yarda dangin miji dangin mijine a yanzu harira don wanan abin da kuka nuna muna keda yayan ku yau da ace nice yar uwan ku bashi ba da dole zaku tsaya ku fahince mu. Amma gashi gaba daya ku kafan kun kasa fahintar gaskiya a yanzu inka debe wanan dan gidan dcp daya yarda da gaskiyan mu ya amince damu har ya dauko mu wancan lokacin ya kawo mu nan kaduna muka zauna gidan mahaifin shi na kusan shekara biyu. Amma a karshe ba ai komai ba saima na fahinci akarshe kamar yasan da kome ya faru a lokacin don yadda ya tura keyan mu da rana tsaka muka bar mashi gidan shi ba zaton haka ba tsamani a gare mu. Kai mairo ke nan wanan kuma sabon sherin dashi kikazo yanzu ke nan har yaushe wani mai hankali zai yarda da wanan zancen. Dakata mami don Allah wanan abin fa abin tsayawane a duba masu shi idan bata da hujjan fadan hakan ba zata fada ba a yanzu. Ina tsaye sororo kamar wata wawuya a inda nake ina kallon mamaki tun yanzu ke nan dama kuma saida na zaci hakan zai faru don ba zasu taba yarda da wanan maganan ba. Gwaggo na fada daga inda nake ta waigoni gami kura min ido na fara fadi a cikin kakkausan murya ina kallon ta nace. To ina son kowa ya sani ni nan ban tashi zuwa da wanan zancen a yanzu saida na shirya wa hakan don duk wanan zancen nasan da yawan ku zakuyi shi dama a shirye nake da ko waye a cikin ku yanzu kotu sai muje shi ba a kan komai sai kan biwa mahaifana hakkin su don ina da shedu mai karfi akan hakan. Mami ki tashi muje yanzu na fahinci wanan zancen zance ne da duk wani mai hankali zai zauna yayi duba a cikin sa bisa ga abunda suka fada a yanzu. Mama mun gode da bamu lokacin ku da kukayi a yanzu na fahince ku na gane me kuke nufi kuma ina bayan ku har gobe dari bisa dari idan bukatan haka ya taso a gare ku. Mun gode da fatar mu daka dade kanayi tun kafin kasan ko mu suwaye agare saidai kamar yadda mahaifiyar ka ta bukata ka fitar da bakin ka cikin wanan zancen don zaman ka lafiya a cikin yan uwa. Murmushi yayi ya dan kalli umma din kafin ya juyo ya kalli fuskana a inda nake sosai fuskanshi dauke da alaman tambayoyi bila,adadin yana fadin zamu tafi saidai kuyi tunane me kyau akan hakan. Haka zalika nima na tsura mai manyan idanuwa da a yanzu suke min bushe suke kuma matukar firgita mai kallon su a lokacin. Da kyat na iya budan bakina da yai min nauyi saboda kuncin da zuciyana ke ciki a lokacin da kyat na iya furta mungode da kulawa kawai na juya na koma kitchen. Ban tsaya naga fitan su daga gidan ba saidai naji tashin motar su subar kofan namu sai lokacin na sauke ajiyan zuciya ina runtse idanuwana a hankali cikin kunci. Karan wayan umma naji ta dauka suna gaisawa har lokacin itama bata sake ba don yanayin da take maganan ya nuna hakan. Naji tana fadin Allah ya kaimu anjima din to shike nan zamuzo din insha Allahu nagama hada muna breakfast na fito dashi falon na dora saman dining ban tsaya ci ba na koma daki nashiga wanka. Kodana fito na shirya ban dawo falon ba zama nayi a daki ina kara bin dairy din Abban da kallo ina kara tara irin bayanan da yayi a cikin dan littafin sirin nasa. Kafin inji muryan ya Abubakar ya shigo suna gaisawa da umma lokacin yana kara mata bayanin abinda ke faruwa a lokacin. Sahiba ta fitane ya tambaya yana son ji idan ina ciki umma tace dashi ina ga ta kwantane tun fitan hjy hari daga gidan nan ta shiga dakin. Mikewa nayi zaune saida nayi kamar minti uku a zaunen sanan namike naje gaban mirrow na dan gyara kafin in fito ina saye da wani dogon riga baki rigar jallabiyan matane irin mai sharp din nan na zaman gida wanan tafiyan da mukayi ne na dawo dashi sai dan gyalen daya daura a kaina nasa kamshin turare oud na matane ke tashi a jikina. Sallamu Alaikum na fada daga bayan shi ina fitowa a cikin dakin yayi firgigit kafin ya juyo yana karba min tare sakin wani zazzafan ajiyan zuciya da har nake iya jin shi a lokacin. Saida na zauna na fuskance shi na fara gaida shi cikin dakewa ya amsa min yadda ya saba don ko yaushe shi fuskanshi baka taba ganin fara,an afuskan shi. Kullun kamar yana a cikin damuwa zaka ganshi ko wani ujula dake gaban shi bayan ya amsa min ne ya soma fadin . Kiyi hakkuri domin jiya nazo maku da baki haka kwatsam babu sanarwa nima hakan bayin kaina bane daurowa hakan ya kama don in wanke kaina daga zargin da suka fara yi min akan ku. Cikin lokaci daya yayi min duk wanan gajeren bayanin lokaci guda ido na dago na kalleshi nace zuwa dasu nan din a yanzu baida wani illa tunda aiki ya fara a yanzu ai. Ok yace yana dan zakudowa daga kujeran yaci gaba da fadin yau akwai meeting da za ayi a can gidan kakan mu mallam Amadu inda kowa zai hadu kamar yadda suka bukata. Shine nazo na sanar maku don na kira mama a waya na fara fadamata saidai kamar bayanin da nayi mata din ba zaku gane ba. Sai kuma naga ai ba zaku san wajen ba shine yanzu nazo da kaina in baku addres din wajen inda gidan kakan namu yake ko zaku iya zuwa . Don by all means ina son ku kasance a wanan wajen don hakan zai kara kwantar wa mutane da hankali don wasu da dama sun dauka cewa shirine dai akayi akan hakan. Amma sai yadda kuka gani idan zaku iya zuwa wajen shine yanzu nakewa mama bayanin komai kika fito. Saida na janye daga kallo shi kafin ince dashi whu not idan har kana bukatan muje wajen zamu zo ai da umma ne ko nida Ammar kawai. Yes dole saida mama zaku ai don itace shedan komai a yanzu zaku sameni a wajen don haka kada kuji komai zan kuma kawo jimi,an tsaro don kada hakan ya jawo wani fitina a wajen. Ok hakan yayi zamu zo insha Allahu na fada na fara laluban wayana ina turawa bello sako don kada in matan da addres din gidan har lokacin duka na tura mai. Bayan tafiyan shi na dubi lokaci kafin inkai kwance sai lokacin naji umma tayi magana tana fadin. Yanzu kina ganin cewa zuwan mu wajen bazai jawo wani matsala ba ke nan nace umma zuwan mu din yana da amfani tunda har ya fadi hakan zamu umma ba abinda zasu iya muna a yanzu don mun riga damun kafa sheda a kansu magana yana hannun security . Dakin taron ya hadu sosai kan wanan kiran na gagawa da aikai masu har ma wanda ba,a zata zasuzo ba sun zo a wanan ranan. Addua tsohon yayi ya fara gabatar masu da zancen ya kare da fadin kowan ku nan yanzu dai yana da labarin baiyanan iyalan Sambo da suka dawo a yanzu. Sun kuma dawo da wani sabon zancen cewa tana karan Nuhu da yan uwan shine kan kashe masu mahaifi da kuma wawashe masu dukiyan shi. Nan take wurin ya kaure da maganganu kowa da abinda yake fada a lokacin don wasu dai sam basu yarda da zancen da mukazo dashi ba wai wanan sherine da kazafi don kawai a batawa iyayyen su suna. Tsohon yayi ta bada hakuri akan suyi shiru suji karshen maganan shi saidai kus kus yayi yawa a wurin abinda ya fada ne yasa su shiru wasu har da waige a lokacin. Don cewa yayi yanzu haka zancen nan da akeyi suna cikin garin nan zaune sanan abinda bamu sani ba shine ashe sun dade garin nan zaune yarinyar tana aiki a nan. Su Daddy da gwaggo hari a kusan lokaci daya suka iso wurin don sun iske kowa ya cika yana batsewa a lokacin. A hankali na danno kan motana wajen motan data kara daukan hankalin wa yanda ke saitin window din da kofan cikin wurin dake wagale don yawan motocin dake shigowa haraban a ranan. Motan ta dade ba a bude ba har yakai sun kagu da suga wanda Allah yaiwa ci gaba a cikin ahalin su ya mallaki wanan motan haka. Can na bude lokaci guda da Ammar dake dayan gefen don umma a baya ta zauna ita Ammar ya zagayo ya budewa umma side din da take zaune ya karban mata handbag din ta ta fito. Imnalillahi wa inna alaihim raji,un baffa ya fada tare da fadin shike nan ma gasu sun iso dada shike nan ma yanzu zance ya kare ke nan tunda sunzo. Gaba daya wanda suke wurin suka mayar da hankalin su kan fararen Alhalin dake shigowa daga get din suna kallon ikon Allah. Nan surutu ya fara tashi suna fadin wallahi mairoce kuwa lalai da gaskiya ita din ce kai amma akwai kama duniya haka. Muka karaso nikan wallahi banji komai ba sai ummace nake jiyewa yadda ta saka damuwa tunda muka tunkaro wajen duk da nace da ita ta dake don Allah. Assalamu Alaikum na fada tare da daga masu hannu kafin mu karasa inda manya suke zaune a lokacin muka zube kasa muka fara gaidasu wuri ya kara kaurewa da surutu lokaci daya. Umma dake gurfane a gaban su baffa Amadu suna gaisawa a cikin mutunci muka mike tsaye tsaye kerere a a tsakiyan wurin bayan umma ina bin kowa na wajen da kallo. Suma din kallon nawa sukeyi a cikin mamaki sai magana sukeyi kasa kasa akan mu kujerun roba farare aka bamu muma mu zauna muka dago umma muka zauna a tare lokaci guda kafin tsohon ya samu wurin ya natsu ya fara magana. Sannu ku da zuwa tsohon ya kara fada tare da sake murmushi a fuskanshi haka yan uwa ke zuwa suna gaisawa da ita muna zaune hankalina ya koma a wayana da nake turawa felix sako a lokacin. Kiran Adnan ya shigo na dauka bluetooth dina na gyara na fara magana ina masa bayanin da har ya kaini ga tashi tsaye na dan gusa daga can ina magana. Eh shegiya tasan abinda ta taka wanan da ganin tama kila a turai take zaune ko irin rikkakun yan daban nan na lagos take zaune dasu. Gungun wasu samarine ke fadin haka daga gefe daya daga cikin su har da diyan su Alh Nuhu dasu Alh gyade da sauran su. Bayan tsoho ya samu wurin yayi shiru da kyat ya kallemu yacewa Umma Mairo baki kyauta muna ba da kika shige cikin duniya haka shiru baki kara waiwayan gida ba tsawon lokaci haka har muna daukan ko kun mutune mairo ? Bayan nan kwanan nan kuma mukaji bayanan ku wurin bukin yar gidan Ali dcp sai kuma mukaji shiru sai kwanan nan muka sake jin wai yarki tayi karan yan uwan mahaifinta a kotu kan wasu dalilai. Umma tana shiru sai faman goge hawayen dake zubo mata a fuskanta da takeyi Ammar yana dan lalashin ta ta hanyan dan buga mata kafada yana mika mata abin gogewa. Tambaya tsohon ya kara jefowa umma dake kurum bata bashi amsa ba sai hawayen da take sakewa . Can na dago kai na dan kalleta ina magana a harshen yarbanci nake fadin ta tashi mu tafi zaifi da wanan hawayen da take sakewa haka. Baffa hamzane ya taso daga inda yake zaune yaje wurin tsohon sukai magana kus kus dashi na dan lokaci kafin ya dago yana fadin. Mun san a yanzu gaskiya ba zata iya magana ba duba da a nan duk an hadu kuma a duba yawan shekarun da aka dauka ba a tare dole yau din nan a fama mata mutuwar mijin ta gaskiya. Don haka a barta ta huta daga baya sai a zabi wasu da zasu zauna da ita su fahinci dalilin ta da tsoho ya tambauye ta don haka ayi hakkuri har su sauko. Wanan ai ba zai yuyu ba, ba inda zata tafi tunda har taso ta wullakanta muna mahaifan mu don wani bukatan ta can na banza datazo dashi . Wani kuma daga cikin su yace wani yasata barin gidan dama da,a yanzu dawowan nasu zai jefa zukatan mutane da dama cikin tashin hankali. Kawai tunda an hadu yau din kuma tazo tayi bayani kawai kowa yaji tayi magana shine abin ji don ba zamu yarda mahaifin mu ya halaka ba saboda su. But na mike ina kallon mai maganan na nunashi da yatsa na fara fadi a cikin harshen turanci kada kayi kokarin sukan mahaifiyan mu a nan. Don mahaifiyan mu ba sa,ar yin ka bane idan kana son jin wani abu ka bari sai ranan da kotu ta bukaci zuwan mu kaji. Lokaci daya suka fara tayar da hayani wurin ana tattaresu don kaucewa fita sai shar suke faman zubawa kamar zasu zo su duke mu. Tafawa nayi na sake mikewa tsaye don naji suna fadin yau ko mu ko su a wurin ba wani sanaya ko duban halaka a tsakani yasa na mike na fara tafawa a hankali ina zagayan su . Good, ku kawo inda nake son kuke au ashe ku har kuna da uban da kuke gani kuna jin dadi bayan mu naku uban ya mayar damu marayu ya kuma jefamu cikin duniya wullakance. Kowa wurin yayi shiru yana kallona don abindana fada din naci gaba da jefa masu kallon tsana ina tsaye kyam a tsakiyan dan filin taron Innalilllahi manyan ke fadi masu jin turanci daga cikin su, a harzuke baffa Hamza yace kunga ku bari abi abin nan yadda aka tsara shi yanzu kunji abinda ke shirin faruwa a nan kuma duk ku kuka ja. Tare guy din da yafisu zafin nama akeyi yana tun karoni nace ku barshi ya tabani daga yau ba zaiyi gigin kara taba wani ba da sunan zuciya. Muddin ka iso nan ida nake zaka kare rayuwan ka a daure gidan maza wallahi kowa yai maka tsaye a kasan nan kuwa . Wurin yayi tsit lokaci guda sai muryana da akeji in hada da turanci in hada masu da yarbanci na zamo masu yar daba ta asalin da suke jin labarin su a Getto. Unbagarborn kai idan kasan kuya har zaka iya budan baki da sunan fada yau ka kallemu bayan mahaifin ku shine yayiwa mahaifin mu yanka na rago a wuyan shi a gaban yan uwanshi bayan sun sakashi saka hannu a kan kaddarorin shi. Carb naji an rike min hannu ta baya nayi wani irin juyowa a kausashe ina shirin illanta maishi baffa hamza ne da ya Abubakar suka rike ni sai dai a lokacin har na fita hayacina ko lokaci guda. Don Ina sun makara ihun dana sake don bacin rai saida duk tsikan jikin wanda ke wurin kuma dan asalin jinin ahalinmu ya tashi kowa yace babu Aljani a duniya karyane. Ai kafin suyi haka nayi cikin taron nan na cakumo wuyan wanan dake maganan fitsaran babu wanda zaice ga yadda akayi na kai garshi a lokacin na shakoshi nayi wani irin girgizashi idanuwan shi suka firfito waje lokaci guda. Duk mazan dake wurin taron nan sunyi sunyi su bambareni daga jikin shi sun kasa da kyat umma da yaya Abubakar suka iso gareni a cikin tashin hankali. Shiya karbi wanan guy din a hannuna da kyar don kalama daya kawai daya fada a lokacin na sakeshi yanzu dai kun gani idan dabanci ko wani iskanci kuke ji tsohon ya fada rai bace. Wanan da kuke gani a gaban ku ko ubanku ya taba ta yanzu ina yake yana can cikin wahala kukuma gaku kuna son tayar muna da zaune tsaye. Daddy dake zaune yayi mutuwan wacin gadi ne ya nisa tare da mikewa zuwa inda nake sai kyarma nake ina jijiga a cikin wani irn tsuma yazo gabana yace. Sahiba ki kalleni nine daddy ki bar zancen nan har a natsu ayishi hankali kwance zaifi don mun san kinsan komai harda abinda mu bamu sani a yanzu. Kallon daddy din nayi cikin wani irin yanayi kafin na girgiza kai tare da kutawa ke da kingani kin san abin bana kai sake bane a lokacin. Ai kafin a samu yaya Abubakar su fitar dani wurin tuni wur ya rikece da surutu kowa na fadin albarkacin bakin shi kan abinda na fada a lokacin. Kamar wata gwauna suka rakani zuwa gidan gwaggo hari da umma tace can za a kaini don umma bata yarda a san inda muke ba ma,ana dasu kawai ta yarda yanzu ke nan. Ranan kan gwaggo ta sheda irin abin dake kaina sai dare sosai na samu kaina nayi barci sosai gashi koda wasa ba wanda ya sheda masu ai iskane sai suka dauka duk turjin yan iskane kawai da jigalanci irin na yam dabam lagos dana koyo. Saidai zancen cewa uban su yayiwa namu uban yanka irin na rago shi abinda ya dagawa kowa hanlali don haka yaran nasa suka shiga motan da suka ciko da sunan iskanci da turji a wurin suka koma cike da kunya da fargaban abinda sukaji din. ZAINAB IDRIS MAKAWA ANA DARA GA , , , , , , , , 7️⃣9️⃣ BY, , , , , , , , , , , , ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , , , , , , , , BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AL MAJID , , , , , , , , , ONLINE PAID NOVEL YAR UWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA BA TARE DA HAKKIN KOWA BA DON BIYA KI TURA DARI BIYAR 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK 08036959257 ALLAH SARKI AI RAINA BAYA BACI YANZU DON KIN FITAR DON NASAN AKWAI RANAN HADUWA SEE U👋👋👋👋 Gaba dayan su sun taru a falon kowa sai mayar dana zuciyar shi yakeyi a fili iyayyen su mata sunyi zaune zugun zugun abin duniya ya damesu. Ku lokacin data sheke hadi meyasa baku tarar wa yar iskaba kun nakasata muga karyan dabbancin nata Nazifa ta fada rai bace. Ke wallahi na raba ki don duk yadda kike tsamani ta wuce nan wallahi ki dubafa mijin ki dasu baffa hamza bayadda basuyi su bambamare ta a jikinta ba amma sun kasa. Shi kuma muna fuki dama ai haka yakeso dam iska da sauri mama Ammo uwargidan Alh Nuhu din ta kallo yar tasu tana fadin akul na karajim kin zagi mijin haka a gabana saina saba maki. Kowa shiru yayi a falon yana kallon su don fadan da Ammo din kewa Nazifa ido rufe ts juya ga sauran yaran da kaf din su suna gida a lokacin in ka debe mutum uku dake aure wani gari a cikin su. Dama nasan komai daren dadewa wanan ranan yana zuwa garemu don shi alkawarin Allah bai tashi abin bakin ciki da kunya ne a yanzu yake shirin tunkaran mu gidan nan kuna hauka baku sani ba. Gaba daya kan yanzu sun mayar da hankalin su kan Ammo suna kallon ta da sauraren mai take shirin fada masu haka mara kyau da rashin dadin jine ? Baiyanan ahalin Sambo a duniyan nan yafi komai muni garemu da baci gami da tonon asiri ku kun sani ta kalli sauran kishiyoyin nata. Dama abinda nakewa Alh gudu ke nan a baya yace ina nafito ni ban isa in fada mai gaskiya ba kuma ba wanda ya isa to yau ha otin sa nan ya fara faruwa. Da Allah zai nuna muna sai ya dawo da yarinyar nan da karfi karfi kuma na iko da fin karfin duk wani yanzu dake cikin Alhalin mu a raye. Yanzu sai ku shirya fuskanta kyama da tsana da gori daga kowa bawai yan zuri,an mu kadai ba duk garin nan sai an nuna ku a matsayin yayan Alh nan gaba. Tana kaiwa nan ta fashe da wani irin kuka tana fadin In Boni Hande da mike tabar falon da sauri suma kishiyoyin nata sai kuka sukeyi na tashin hankali. Wa zai basu amsa a yanzu babu amaryan su ce bata kuka ba itama ido ta zubawa sauran tana sauraren su don koda aka aurota wanan case din ya mutu ta shigo gidan. Umma Salma ce ta dan kallesu tace tun ina goyon kane Sanusi abin ya faru ai ya kamata ku gane me Addah Ammo ke fadi a yanzu don masu girma a cikin ku yaci su gane ko wanan gidan kanshi da muke zaune cikin shi a yanzu na wanene ? Kwarai kuwa ummu salma na tuna gidan marigayi ne dan uwan Abba daya rasu baida kowa Abba yayi gyara muka tare a cikin sa hakane ya kalleta a zabure don tunawa da hakan. Tace to ka tuna ke nan yanzu kowan sun dawo shi Addah Ammo ke son ku gane kuyi nazari a kan shi ai . Wai yay buba wai a nufin wanan gidan da muke ciki a yanzu dama na chikas din nan ne ko me ? Karfe bakwai nayi sallah na mike ina kallon umma nace umma mu tafi gida akwai aikin da zanyi a ma,aikatan mu don kaya zasu iso yau din nan su Adnan sun taso yanzu daga lagos zasu zo nan na fada a sanyayye. Ai ki bari gwaggon naki ta fito kada taga munyi mata butulci jiya fa kusan kwana raye tayi a kanki shigowan hjy hari din ta ga yanayin mu kamar muna wani zance. Take tambaya umma ke mata bayani cewa zan tafi gun aikine wai juyowa tayi ta kalleni tana fadin haba aiki saida lafiya akeyin shi ai ? Ki bari sai ta kara samun lafiya ki fita ni kaina wallahi saida nasha magani da asuba din nan na samu mikewa haka balle ita da tayi wanan abin haka. Yarbanci nayiwa umma na hari gadon dakin na kwanta rub da ciki suka bini da kallo kafin hjy hari din tace wallahi mairo idan nace dake jiya nayi barci a gidan nan karyane. Abin nan da kuka fada min ya tsaya min a zuciya na kasa barci wai meye gaskiyan zancen nan don Allah. Murmushi irin na takaici umma ta sake kafin tace gaskiyan ne kikaji hari a bakin mu shine kuma muka fada yanzu din. Kuka ta sake a hankali tana toshe bakin ta tare da fadin yanka fa mairo yankan rago kayiwa dan uwa ka don dukiyan shi haba haba tana kuka take wanan zancen. A gabana wallahi Allah ya nuna min lokacin da yaya Nuhu ke yankashi yana fadin idan kun kasheni ku kula min da iyalina don Allah sai naji muryan wani na fadin iyalin ma naka ba batin su zamuyi ba ai balle su kawo muna matsala kinji abinda yasa na bar gida ke nan lokacin da shigan cikin yaron nan naje nisa daku. Kuka sukeyi sosai harni dake lafe saman gadon kamar nayi barci a lokacin umma taci gaba da fadin hari nasha wahala sosai a rayuwana har na haifi yaron nan shi kuma yanzo ba lafiya haka nayi ta fama dashi ko yanzu kika kalleshi kinsan Ammar ba lafiyeyye bane a ido . Sai fa da Allah ya turo muna rai biyu rai biyun nan sune suka fara fitar da rayuwan mu kangin wahala sune dan wajen yaya Ali da dan wajen ki . Kafin sahiba yanzu ta hadu da wani bawan Allah wanda ya daga darajan mu da kimarmu a rayuwa haka tana aiki a karkashin su. Wallahi komai akace yaya Nuhu sunyi zai iya batan ki ko shekara ba ayi ba ya fara gyaran gidan ku ya tare da iyalin shi suka rabe komai naku iyasu kowa na kallo ba wanda zai iya furta komai akan haka har yaya Ali kuwa da ake ganin zai iya dashi lokacin. Ance sunce koda kin dawo baki da wani gado don ya mace ke gareku da marigayi don haka suna hakkin cin arzikin dan uwan su yadda wasu ke fadan sunce fa. Murmushin takaici umma ta sake lokaci guda tana fadin ai Allah yafi su yansan komai kuma yanzu da Allah ya dawo damu din sai muji me zasuce. Gwaggo hari tace baki ga shi ya buhari jiya saida aka daga shi ba a wurin shiko yayya gyade fadi yake karyan bamza da wofi kawai a cikin kunya yana muzurai. Nidai har barcin gaskiya ya daukeni suna zancen don maganan su kara tunzurani yakeyi a lokacin ina jin zan iya kashe kowan su dake da hannu a cikin kissan mahaifin mu din. Barci na samu nayi sosai a lokacin a cikin barcin nake jin ana tayar dani wanda umma ke dan kiran sunana a hankali na samu na bude idanuwana da kyat lokaci guda. Ki tashi gasu sun zo suna falon gidan wai mu zo alwai maganan da suke son yi damune kaina girgiza ina fadin umma barsu ba zamu kara zancen komai dasu ba sai an hadu a kotu. Tunda na fahinci basu son sulhu ko girma da arziki akan zancen tashi zakiyi muje muji abinda suka zo muna dashi tunda su din sune magaba tan mu. Dole na mike badon naso ba na fada ban dakin dake cikin daki fuskana na daurayo na fito kayan da umma ta tura Ammar ya dauko min a gida na saka. Wani rigane dogo mai Short hannuwa sai filawan kwakwwa dake jikin rigan an masa ado daga cibiya kuma dan tattarane ya sauka kasa rigan yayi matukar karban jikina sosai. Gwaggo Hari ce a gaba umma na bayan ta sai nida Amar dake biye a bayan su muka shigo falon wanan karo su kaman gomane suka zo ba a irin taron nan mai yawa sukazo ba. Yadda naga su umma da gwaggo sun zauna sun zube a kasa yasa nima zubewa a kasan lokaci daya aka fara gaisawa a tsakani. Kafin wanan tsohon na jiya ya fara magana mai kama da ban hakkuri ko nasiha kan a taushi zuciya kada abar abin kunya cikin duniya duk daya ake ayi duba kan lamarin banda bata suna. Sam maganganun da yakeyi a lokacin basu shigeni ba yasa na mike kawai da niyar barin wurin lokaci guda umma tace dani ina zani na dan bata fuska ina fadin zan shigane ciki tunda mun gaisa dasu. Kallona sukeyi ina tsaye kerere ba wani gyale ko hijjabi don ban saba da sakawa ba sai dan half sunna da nakan saka shima din yanzu ba ko yaushe ba. Muryan daddy naji yana fadin na zauna a gama abinda ya kawo su suna son mu janye kara a sulhunta komai a gida . Wanan ba zai yuyu ba na fada ido bushe gida zaku saka su yanke kawunan su kamar yadda suka yanka min mahaifina lokacin da yake rokon su. Kada ki kawo muna zancen banza munan iyayyen kine a matsayin yan uwan uban ki mukazo wurin ku. Wai wai wai kamar ya daba min mashe a zuciyana lokacin din abinda wanan ya fada tabe nayi da hannuwana ina kallon shi ido da ido nace. Oh realy kai dan uwan mahaifinane ashe ai ban sani ba sai yanzu da kake fada amma lokacin da muke cikin wahala ban ganka kazo da zumar kwatar min hakkina ba a lokacin. Masu girgiza kai suna girgiza masu budan baki sun bude don mamaki na kalli tsohon ina fadin look baba ka daina wanan sulhun da kake son yi a yanzu don hakan ba zai yuyu ba. Gaba dayab su suna da hannu a cikin kissan mahaifina dakai baka sani ba amma zakaji a nan gaba don hakane suke kara nisanta mu dasu basu son mu rabe su basu son a nuna mu a matsayin diyan mahaifin mu balle duniya tasan muna raye. Daddy dukar da kanshi yayi kasa yana dan murza hannayen shi don ya gane abinda nake nufi bayan baffa hamza ya gama fassarawa tsohon abinda na fada. Kai naga ya kada ya nisa tare da fadin Allah ya kyauta sai kuma yace yanzun dai kuna da hujja akan hakan ke nan ko .? Na gyada kai yace zancen baffah ki Nuhu da ake fadin kokuwan kine yasa yake kwance muna rokon a sassauta mashi idan hakane . Ni ni ai ban masa komai ba a yanzu zagin mahaifina yayi muka dakatar dashi don yasan ba abinda zai iya babu babu . Amma baffah kun ban mamaki da kuka zauna kuna kallon yadda yarinyar nan ke kokarin zuba muna rashin mutunci kuna zaune kuna kallon ta wai iska ko iskancin . Kaita kanka tukunna kafan ka idan bakai hankali ba har abada ba zaka tashi ba shine ajalin ka shi zai kaika kamar yadda kuke kai mutane lahira. Ka tuna shi kukaje kashewa a ranan kaida yaron ku dake kwance a yanzu an rasa meke damun shi akan fadan baki kukaso kasheshi a ranan. Kaf na basu labarin shirin su a lokacin Ya Abubakar ya shigo falon shida su baffa Abdullahi kaf nabasu labarin komai dake aike daga bangarena. Har kisan Abban mu da sukayi da rabon komai da sukayi iyasu da abinda suka tsorata daddy dashi a lokacin har ya karbi abinda suka bashi daga ciki. Aradu yarinyar nan manyace baffa gyade ya fada lokaci guda kai kai ka daina fadin hakan a fuskanci abinda ke gaban mu yanzu tsohon ya fada. Kai ina wanan yarinyar ta gama damu ta shuci rayuwan mu ke har kin isa ki muna wanan tonon silar idan da a bayane shan. Kun dai yarda kun aikata ke nan baffa hamza ya tambaye shi a fusace yace in Nuhu yashe ya yarda ba idan bai sheba muma ba zamu sheba don ya fita sheri kun sani. Daga bayan su baffah Buhari yace nikan na yarda na kumayi nadama kai Ali dcp ka sani ba yauba na fada maka komai ko a lokacin barazana da rayuwana sukai min kuma da kurciya a lokacin na fadama komai ai ? Kallon daddy modibbo yayi yana fadin why daddy why ka aikata haka akan dan uwan ka sai yayi shiru don hawayen da yazo mashi a lokacin. Kafin yace nasan komai daddy na sani tun lokacin dana dawo na samu kafita wanan zancen nake kwankwanto a kanka har yakai naje na bincika file din case din wanda mutanen kan sahibane suka fada min inda zan sameshi. Ikom Allah dayan tsohon ya fada yana kara kallona yace wallahi tsoho su suka fada min inda zan dauko file din don wanan yarinyar da kuke gani ta wuce yadda kuke kallo ayanzu kan komai. Wanan case ne daya shafi hukuma don haka dole abar yarinyar na akan karan da tayi baffa hamza ya fada idan munce a rufe wanan magana a gida haka dole dai zancen nan fita zaiyi waje ku sani. Haka su masu bin hakkin su ai kunga bamu kyauta ba idan an kyalesu a haka ana kallonsu su kansu zasuga rashin adalcin mu a nan don haka wanan zancen bana gida bace bafa a yanzu. Hamza nasani ba yauba kake son ganin bayan mu wanan zance nata ina shedun ta idan haukan ta ya bata haka tana shara karya har kuna yarda muma ba kyalesu zamuyi na bana muna suna da suke son yi tunda bata da sheda kan hakan . Ya yun kura tare da daukan sandan shi ya mike tsaye ya kallo inda muke yana fadin zaku gane ba a taba mu a wayen lafiya gaba daya sai nayi karan ku kotu kan kokarin bata muna suna da akeson yi har kai hamza da nake ganin kana kokarin mara masu baya su bata muna suna. Au haka kace to jeka kayi karan don Allah Allah ya kaika kaje karan su ke kuma zaki san kin tamu a garin nan karshen iskanci kikeyi yanzu. Idan uwarki ta shiga bariki dake kin tashi a gaban yan jagali kin kwaso hauka kinzo muna kina barazana nan kaniyar ki zakici wallahi yana kainan ya fita fuuu kowa ya bishi da kallo. Lalai zance na kasa don hauka na damun wa yan nan jahilan da suka dauki hukuma wasa baffah Abdullahi ya fada a cikin mamaki kafin ya juya kan Alh buhari yana fadin . Yanzu kaima binsu zakayi kuyi kara ke nan kome ya nisa yana gyara zama yace gashi nan ku tambaye saunawa ina zuwa wurin shi kan wanan maganan. Don haka wallahi ni yanzu a shirye nake da duk irin hukuncin da za ayi min muddin shine zai zama yafiya a gareni kan kuskuren da muka aikata duk da nasan bani cikin kashe shin da sukayi. Amma kuma nasan sune ban fada ba don tsoron su da nake ji a lokacin kuma sun bani rabo na karba daga ciki ina amfani dashi. Nuhu ne da shi gyade sai abokan shi mutum biyu Alh Shafi,u da Alh bello su suka aikata hakan ina waje ina jiran su a lokacin . Don na dauka abinda suka kace zasuje yi wurin shine ya kaisu sai washe gari labarin mara dadi ya zo muna na mutuwan Sambo din. Hankalina ya tashi sosai a lokacin don wanan abinda suka aikata ga dan uwan mu tun lokacin naso in fadi gaskiya amma sai suka kulleni a dakin bello sukai min barazanan kasheni nima idan na fadi gaskiya har kawo wa yau din nan kulun a cikin barazana suke min duk lokacin dana yunkuro masu da zancen. Ko lokacin da yarinyar nan ke fadi daya tura a kashe mai Alh Ali nayi iya kokarina don inga na haja faruwan hakan amma basu saurareni ba. Daddy hular shi ya cire ya goge zufan dake tsiyayo mashi daga cikin kanshi don tashi hankalin abinda kunuwan shi keji mai a lokaci. Zuwa wanan lokacin duk wani wanda ke falon kuka yakeyi wiwi hankali tashe tsohon yace tir tir da hali irin na Nuhu da gyade. Alh wanan maganan dole sai anje ga hukuma don ita kadai zata warware wanan manakisa nasu kai tsaye idan ba hakaba ko yanzu tsugunne bata kare muna ba a nan. Ganin suna kan tataunwa akan zancen na mike zuwa ciki don ba zan iya zama ina sauraren wanan abinda ke kara daga min hankali ba haka. Ya mustaphane zaune saman dining ya dafe kanshi da hannuwan shi bibiyu shima a cikin tashin hankali don duk abinda ake fadi daga inda yake yana jin su. Yana jin motsi ba tare da yasan ko waye ba ya dago nice ya gani naji ya kira sunana a wani yanayi hakan yasa na tsaya a inda nake ba tare dana juyo na fuskance shi ba. Mikewa yayi ya tako zuwa inda nake tsaye din ya yazo ya tsaya har muna iya jin hucin numfashin juna a lokacin don irin kusantar juna da mukayi . Hannuwan shi ya fara hardewa fuskan shi ya nuna alaman damuwa a cikin sa sosa yasoma fadin nasan an cuta maku sosai a rayuwan ku. Ban san ma da wani ido zamu kalleku ba a yanzu a matsayin mu na yan uwanku alhalin muna dashi muka bar rayuewan ku a cikin wahala haka. Saidai ina son ki sani duk wani abinda za ayi a kotu don muga an hukunta mutanen nan ki sanar dani wanan zaluncin nasu ba zai tafi a banza ba insha Allahu. Kaina dago na kalleshi tare da dan sake murmushi ina fadin mungode saidai duk wani shiri da zanyi kan hakan na riga na shirya a yanzu ba sai an taimaka min ba. Oright hakan yayi kyau ya fada har na fara tafiya naji yace saidai ki sani dis is arewa not lagos ko yayane sai kin nemi taimako a wani wajen. Ba damuwa na fada ina shigewa tare da fadi a raina da kasan dalilina kin kowa ya jefa kanshi cikin wanan fitinan da kowa yanzu ya fahinceni. ZAINAB IDRIS MAKAWA ANA DARA GA , , , , , , , , 8️⃣0️⃣ BY, , , , , , , , , , , , ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , , , , , , , , BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AL WAHID , , , , , , , , , ONLINE PAID NOVEL YAR UWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA BA TARE DA HAKKIN KOWA BA DON BIYA KI TURA DARI BIYAR 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK 08036959257 ALLAH SARKI AI RAINA BAYA BACI YANZU DON KIN FITAR DON NASAN AKWAI RANAN HADUWA SEE U👋👋👋👋 Da yamman ranan muka koma gidan mu duk da aiken da daddy yayowa yaya Abubakar wurin mu cewa yana son ya gana damu a ranan hakan baisa mun je gunshi ba. Don umma ta hana muje a cewan ta me zai fada muna kuma yanzu bayan baiso haka ya kasance da muba ya boyewa yan uwa baiyanan mu don rufuwar asirinshi shi. Gashi tun faruwan hakan gaba daya ya Abubakar ya sauya kallo daya zakai mai ga duk wanda ya sanshi ka gane cewa yana cikin wani halin damuwa a zuciyar shi . Don ya fada hasken nan nasa na gado ya dan dushe yayi baki ga gashi daya bari kadan a fuskan shi ko kana magana dashi sai ya tafi tunane ya barka nan. Rashin zuwa dani aiki ranan yasa oga yaji halin da nake ciki inda sukai mai dan bayani briefly yasa yaji tausayin mu a zuciyar shi. A can ma dai gidan Alh nuhu da suka kwaso shi daga asibiti cewan shi ciwonshi ai bana asibiti bane yasa suka dawo gida kowa na zuwa wurin malamai da bokaye ana karbowa ana dura mashi ko a shafeshi ko a turara mai yaki yayi ta tari. Yau ko da uwargidan shi ta shiga dakin don duba halin da yake ciki don sunje sallah sai samun shi tayi ya falka yana bin ko ina da kallo na dakin. Yana ganin ta yaso ya yun kura ya tashi a cikin mamaki sai kuma ya kasa don jikin da sauran nauyi a lokacin sai binta ya kamayi da kallo. Juyawa tayi a guje ta fita a kofan falon ta tsaya tana fadi cikin daga murya tana fadi ku fito Alh ya tashi Alh ya bude idon shi. Ai a guje kowa ke fitowa daga dakin shi zuwa wajen su har yaran dake wajen suka cika dakin lokaci guda ana faman mashi sannu da jikin kowa da mamaki a zuciyar shi. Waya aka fara bugawa yan uwa da abokan arziki cewa Alh ya falka nan aka shiga shati fadi cewa maganin da akayi mai na karshe ne ya karbeshi. Sai zuwan Alh gyade ne zancen ya canza don yana shigowa dakin dan uwan nasa dake makil da mutane ya tsaya a kofa yana fadin . Ehh lalai kuwa ya tabbata yarinyar nan manyace ta gaske ashe don gashi ya tabbata a zahiri mun sheda . Haka yasa kowa na dakin yake binshi da kallon mamaki karara a fuskan shi yaci gaba da fadin cewan da tayi muje ai ya tashi ko zancen gashi ya tabbata. Haka baffa buhari daya iso shima cewa yayi tabbas babu sarki sai Allah Annabin mu Annabi mohammadu manzon shine . Lalai Allah da Annabin shi suyi gaskiya koce babu Aljani a duniyan nan yai karya wallahi yanzu zancen yarinyar nan ya tabbata gaskiya ashe ko gaba da gaban ta a cikin wani aikin ke nan. Nan kuma zance ya fara tashi kus kus a cikin yan uwa da abokan arziki an dai samu ya tashi har yai wanka yaci abinci sosai saidai jikin nasa da ba karfi har lokacin. Sai lokacin ya samu zama da yan uwan shi har aminan shi biyu da matan shi yana tambayan su abinda ke faruwa suka fara fada mai abinda suka sani ya faru. Har zuwa irin rikicin gida da nazo akayi dani da kuma zancen zaman su dani a safiyan jiya din da komai dana fada masu a falin mijin gwaggo hari har cewan nice sabbabin rike masa kafafun shi gyaden. Shiru Allah Nuhu yayi yana sauraron abinda kowan su ke fadi a lokacin har suka gama yace akwai aiki a gaban mu sosai ke nan saidai nan na sheda yarinyar nan bata tunkaromu ba saida ta shirya muna tsab kafin tazo garemu. Sai kuma ya murmusa kafin yace waini ce karamar yarinya a yanzu take shirin challanges dina don tana takama da guntun sihirin ta ko ? Alh nidai tunda kaga haka wallahi abi abin nan a sannu uwargidan ta fada ya hararo ta don sai lokacin suka kulla da cewa ai suna kusa irin wanan zancen ba ayin shi a gaban mata. Juyowa yayi cikin su a fusace yana fadin ku me kukeyi a nan da zakuzo ku wani zauna muna muna magana kan abinda mu ya shafa. Biyun kan mikewa sukayi sai uwargidan ne da hjy salma a zaune da take binshi da wani irin kallon tsana da Allah waddan halin ka. Can ta mike tana fadin lalaikan kai ya shafa Alh don ka shafa muna kashin kaji a jiki duk inda muka bi da yaran mu sai an nuna mu a matsayin naka yanzu. Tana fadin haka ta juya ta fara tafiya yace ehh salma kikai kuwa yanzu tunda har zaki iya mayar min da martani haka kuwa amma zanyi maganin ki ita dai bata juyi ba ta fice. Sai bayan fitan sune suka fara bashi labarin abinda ya daga mai hankali wanda bai dauka wani ya taba sani ko zaiji ba sai gashi a bakina yanzu yaji. Kai ya girgiza yana lumshe idanuwan shi cikin takaici kafin ya bude idanun karo na biyu da a yanzu sun rikede zuwa ja ya furzo da iska daga bakin mai dan sauti yana fadin. Yanzu na gama fahintar yarinyar nan kaf saidai ance wanda ya rigaka barci dole yake rigaka tashi ita yanzu ta soma muko min dade muna wanan. Dadai mun barta mu bata dukkan abinda take nema kawai a rabu lafiya zaifi ina amfanin wanan tonun silar da mukeyi a tsakanin mu dasu. Wani kallon zargi yake jifan dan uwan nasa dashi kafin yace ashe kai sakaran banzane yarinyar nan fa tazo da zuman kota halin kaka saita kaimu kasa a cikin garin nan. Don muna sakarkkaru sai muyi zaune muko mu zuba mata ido ke nan tayi galaba a kan mu muna kallo kome kake son fada yanzu ? Gaba dayan ku kubani kunnuwan ku kuje me zan fada maku nan ya kitsa masu duk yadda komai zai kasance idan anje kotu ga jibi banda goben sukace sun gane komai don dole haka zasu bishi din sai abinda yace dasu dole zasu bi. Wanka na fito ina zaune gaban mirrow ina shafa mai a jiki wayana dake saman gadon ya dauki kira mikewa nayi na dauko wayan a inda yake aje saman gadon. Duban layin nayi Abdul ne makwabcin mu kuma abokin aikina a lokacin mun gaisa yake tambaya su umm da ammar nace lafiya suke yake fadin gasu sun sauka kaduna a wanan gidan namu dai muke zaune ko nace eh. Kaya mukazo saka hannu zamu kwana a nan nayi masu sannu da hanya don nasan aikin sane hakan saina dauka shi kadaine ko su biyu a lokacin saidai ban tambaya ba. Bayan na fito ne nake fadawa umma zuwan shi take fadin gashi kuma ba zasu samemu a gida ba don yau fitan mu kotu na farko don haka dole muje cikin lokaci. Karyawa mukayi tare da duk daukan wani abinda zamu bukata muka fito zuwa kotun a karo na farko da zamu shiga ke nan. Har nakai bakin mota na juyo nacewa umma mu taka zuwa titi ba zamu shiga wanan motar ba sam a yanzu kallona umma tayi ina tafiya ina waya muka fita get din mu bamu dade da tsayuwa ba saiga mota an turo muna muka shiga. Tun daga nisa na hango yadda wanan wurin ya cika da motoci wanda nasan na yan uwan mune mafi yawan motocin dake wanan waje duban lokaci nayi saura minti uku a fara yasa nace muyi zaman mu a motan kada mu fita. Gashi ba mai ganemu don motar mai duhun glassce har wasu samari sukazo suka wuce wa yanda ba zan iya shedasu ba suna fadin wai ance ai kamar yarinyar nan taji tsoro ba zata zo ba kuma. A to kai baba Alh na wasa ne ya gama ta da allon karfensa ya saka mata razana ta gudu kila itama ai rashin sani ne ya cuce ta. Allah ya taimaka driver ya bude kofan shi yana shan iska muke tsinkayo zancen su daga inda suke tsaye a kusa damu . Lokacin yana cika nace mu fita muka fito daga cikin motan muka nufi hanyar shiga wurin a lokacin har alkalin ya fara magana kan shari,an namu ko muka shigo don wani shari a akeyi kafin namu zaman. Muna neman Sahiba sambo namadi da tai karan Alh Nuhu Allah gyade da buhari namadi duk yan uwan mahaifin ta. Ko Sahiba na kusa ta gabata gaban mai shari,a na amsa da na,am gani sai lokacin kowa yasa muna wurin suka juyo a cikin mamaki karara a fuskokin su suna kallona. Alh Nuhu da wanan ne karon shi na farko daya fara ganina shi ido ya kura min har nazo inda ake tsayi na tsaya ina kallon kowa idanu bushe. Jikina dogon rigace a lokacin na yan kasan Mexico kinsan irin rigunan su ga kyau amma kuma dole akwai nakasu a dinki da bai dace da yar bahaushe ba. Hakana saka don nasan zasuyi magana don kawai in nuna masu nifa ni dince da akwai bariki da komai a tare dani. Mai gabatar da kara ya fara fadin abinda karan ya kunsa aka nemi su Alh nuhu da sufito sai gasu da babban riga ruuuuu sun fito suna fuskantar mai shari,a din sai wani cicika suke suna batsewa in ka debe mutum daya da fuskan shi ya nuna damuwa karara. Tambayan su aka fara suka gabatar da sunayen su sai mai magana yake fadin ko sun san da wanan kalubalin da ake tuhuman su dashi ? Alh nuhu yace su basu sanda hakan ba asalima basu san nidin ko wacece ba don haka basu san zancen da nake magana a kanshi ba yanzu. Aka juyo wurina ana tambaya a daidai lokacin da yan tawagan mu suka karaso cikin kotun hakan ya mayar da hankalin mutane wurun kallon su din kowa sai yake zaton lauyoyine ko wasu bakin yan sa ido. Mai maganan ya dan je wurin alkalin sukai kus,kus dashi kafin a juyo da zance a wurina suna fadin naji ko ina da lauya da zai kareni ? Kafin nayi magana can ya dago hannu yana fadin gashi tare da gabatar da kanshi shine lauyan da zai kareni . Aka juya wurin su Alh suma nasu lauyan ya mike yace shine mai kare bangaresu nan kotu ya fara aka bawa mai kareni dama mutumin da bansan inda ya fito ba sai a wanan ganin da nayi mai don har yaya Abubakar yazo da lauya wani abokin shine da ya kware shima wurin sharia. Jin babban lauya da kasa ta sani a bayana yada har Alkalin ya fara kama kanshi a lokacin tambayan su yayi da cewa ko sun san dan uwan su daya mutu shekara goma sha biyar daya wuce ? Mai karesu yace wanan tambayan ai batayi daidai ba gaskiya Alkali yace a barshi yayi ya kara maimaita tambayan sukacw sun sanshi dan uwan sune mahaifin su daya saidai uwa kowa da nasa uwar. Yace da kyau shin ko kunsan yana da mata da ya a lokacin suka kalli juna kafin da sauri Alh gyade dake dan dogara sandan shi yace munsan da hakan. Au to kuma kukace da farko baku san wanan zancen ba mai karesu ya daga don nema masu kariya a wurin shi yace an bashi a bar wanan tambayan shima aka bashi dama ya juyo gareni. Ke kin taba ganin su kin san su a matsayin su na yan uwa gun mahaifin ki kema kuma ya a garesu nace na sansu mana amma da yake su basu nemeni ba kamar yadda mahaifina ya bar masu amanan mu nima kuma din ban nemesu ba kamar yadda suka sheremu a cikin duniya. Au to baki nemesu ba tsawon wanan lokacin yanzu kuma da zaki nemesu sai kika nemesu a kotu ke nan ko ? Hannu mai kareni ya daga kai an fafata sosai wanan yace wanan wanan yace wancan a karshe aka ce meye hujjana na tuhuman su da kissan mahaifina da kuma neman dukiyana da ban tunkaresu ba sai kotu ? Nan suka tsaya ja inja har Alkali ya dan doki gudumar shari,a yayi gyara yana fadin kotu ta dage wanan karan sai nan da sati biyu mai zuwa tare da bani daman zuwa da hujjana na fadan hakan. Nan aka fara fita daya bayan daya ga text din Adnan cewa kada in nuna ai tare muke haka yasa na fito muka koma wanan motan su kafin ma in fito har sun riga da sun shiga motocin su sun bar haraban kotu din lokacin. Mun tsaya mun gaisa da yan uwan da basu da tsoro wasu kan tuni suka karawa talkaman su mai suk bace a wurin don sanin halin Alh nuhu din wurin iya baraza da rayukansu din. Zagi kan nasha shi a motan da suka shiga sai can suka samu lauyan su da fada wai su ai sunso ya gama komai daga ranan nan alkali ya sallami karan namu ne. Waiko kai Alh bello ka tabbatar da kaga Alkalin nan kuwa ya juyo yana kallon shi don son jin amsan da zai bashi a lokacin . Yace komai kamar yadda ka tsara haka na shimfida mashi saidai kila wani hikimace nasu haka yasa ya daga karan a yau din. Wayan shi ce tayi kara kamar kada ya dauka amma kuma ya daure ya dauka don sanin halin da suke ciki din ko wani zancen ne zaiji a kaina. Muryan da yajine ana gargadin shi kan gobe ya tabbatar yana Abuja don case din dake can yana jiran shi. Wani irin tsuki yaja tare da fadin anya yarinyar nan zan iya mata hakkurin wani abu a rayuwan ta kuwa din na tabbatar idan nayi wasa zata shige min hanci da kudundune a garin nan. ZAINAB IDRIS MAKAWA ANA DARA GA , , , , , , , , 8️⃣1️⃣ BY, , , , , , , , , , , , ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , , , , , , , , BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AL AHAD, , , , , , , , , ONLINE PAID NOVEL YAR UWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA BA TARE DA HAKKIN KOWA BA DON BIYA KI TURA DARI BIYAR 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK 08036959257 ALLAH SARKI AI RAINA BAYA BACI YANZU DON KIN FITAR DON NASAN AKWAI RANAN HADUWA SEE U👋👋👋👋 Mun nufi gidan na samu su Abdul gaba suna jiran mu dole mukaja muka tsaya muji abinda zasu fada muna. Zasu tafi company suyi aiki idan sun dawo zasu shigo don lauyana zai so ya ganmu akwai maganan da yake son yi damu. Bani cikin yanayin dadin rai don haka amsa masu dai kawai nakeyi don suma sun kula da hakan a lokacin yasa suka barni balle umma dake kukan bakin ciki tun fitowan mu kotu din. Gida muka dawo kowan mu ya shigo ranshi bace bamu dade da shigowa ba Abubakar ya iso gidan namu shima yanashi har lokacin bai a cikin walwala. Ya zauna andan tattauna ya kawo shawaran cewa mu juya mu koma lagos don zaman mu a kaduna yanzu akwai hatsari sosai saboda ya kula mutanen nan basu son gaskiya ga al, amarim su sam. Nace nima nayi muna tunanen hakan ko banza kuma ga Amar dake karatu kada hakan yazo ya jawo mashi matsala saidai yanzu tunda Abdul yazo gobe zai koma zasu tafi da Ammar din ya zauna a wurin su . Ni zanso muje da umma wurin danginta su ganta su san tana raye kamar yadda suke ji yace shima yayi tunanen hakan sai dai a yanzu dole mubar arewan nan mu koma can inda basu da ikon shiga suyi wani abu. Don shi jikin shi ya bashi cewa da akwai matsala da wani shiri da yanzu sukeyi na kawar damu su hutu don ba wani abu bane mai wuya hakan a wurin anyi hakan yafi dubu ba a dauki wani mataki ba. Jin hakan yasa na dan shiga dogon nazari kafin na yanke shawara a raina kawai dai mu tafi din yau ga baki dayan mu mu koma lagos din zaifi don nima na zargi hakan. Dole da yamma muka bi jirgi zuwa lagos muka sauka goma na dare sai gida ba zancen barcin gajiya don dagani har umma tunane ya addabi zuciyar mu a lokacin. Idan na zauna shiru zanyi ina tunane haka ko aiki na fara yanzune tunane zai shigo cikin haka nayi rana dana fita aikin saida irin hakan ya faru dani a nan suka gane ina cikin matala har saida nayi masu bayanin halin da nake fuskanta a yanzu din. Shine Felix yayiwa ogan mu bayani da cewa na tafi kaduna a kan case din mahaifina shine ya tambaya na nemi lauya ne sukace zasu bincika. Bayan sun bincika dinne kuma suka gane cewa banda wani lauya mai karfi shine shi ya dauki wanan lauyan da yazo daga Abuja don yana kokari sosai akace. Kwana uku da dawowan mu lagos lauyan yazo har gida muka gana dashi bayan ya gama jin komai na labarin daga bakin umma. Sai ya kara tambayan mu ko muna da wani sheda har munce a a sai na tuna da wanan dan littafin siri na Abban mu na dauko mashi bayan ya gama dubawane naga ya saki dan murmushi a fuskan shi. Yana fadin wanan ma kawai zai isa sheda har in zamu samu wanda ya sheda rubutunsa a kotun akalla a samu mutum uku ko biyu da zasu sheda muna rubutun na marigayin ne. Dan tunane nayi mai zurfi a lokacin kafin na amsa mashi a raunane da eh za a samu insha Allah yace good ki sa a ranki kamar munyi nasarane akansu da yardan Allah. Kai kawai na iya gyada mai a lokacin don yadda nake jin zuciyana yana tafasa akansu babu tsoron Allah ko nadama a cikin zukatan su yadda suka iya kallon mu suka musanta maganan da sun san gaskiya anyi shi. Haka ranaku ke zuwa suna shudewa har dai yakai saura kwana uku da zamu koma kaduna din shiryawa nayi tunda safe na fita zuwa makarantar su Ammar na sake daukan permition akan shi. Don washegari ko safiyan tafiyan zamu bar lagos a yadda ya Abubakar ya tsara muna tafiyan namu na wanan karon da zamuyi zuwa shiga kotun. Ina barci umma take tayar dani wai Falix ne a kofan gidan mu nayi mamakin hakan na dai shirya na fito na sameshi muka gaisa ya miko min envelope yace ogane yace ya kawo min zamu sauka a gidan shi don yafi wanan da muke ciki security sosai naso nayi gardama amma kuma Felix din ya ban shawara sai na yarda na karba. Mun isa kaduna a ranan motocin shi sukazo suka dauke mu guda biyu sai kotun da ake sharian damu yau ma zance yafi wancan karon na farko cika. Sharian muce ta farko a ranan don haka muna shiga aka fara kiran mu gabata a gaban kantan alkali suka fito a cikin shaddodin su sai maiko yakeyi suga alhazai masu fada aji a gari kowan su sai cicika yake yana mazurai a wurin. Mai magana da yawun Alkali ya bukaci lauyana da ya taso ya fara gabatar da shedan shi na masu wanan zargin. Ya mike yayi gaisuwa irin nasu kafin ya fara magana yana fadin Alh Nuhu kusan kaine shugan wanan tawagan naku a yanzu dama lokavcin aikin ku. Shin ko za ka iya tuna kiran da kayiwa marigayin a waya landline na gidan shi ranan akan zancen alherin daya sameshi yaje a matsayin ka na dan uwan shi yana fada bayan dawowan shi gida kai kuma ka kirashi a waya . Objection my lord mai karesu ya fada kotu kuma ya dauki kananan maganganu lokaci daya saida mai sharia ya buga gudumar shi wurin yayi tsit lokaci guda. Ya kalli barister din yace yaci gaba da abinda yakeyi yanayi yana gyara glass din idon shi yana kallon bakin fuskokin da suke zaune wurin wanda yanayin su kawai ya nuna su din bakine daga wata nahiyar sukazo don wanan shari,an suma. Sake maimaita masu tambayan farko dayayi masu yayi yace ko zai tuna da yadda sukayi a wanan ranan yace shi sam basuyi wani zance da marigayin ba. Murmushi mai tambayan yayi kafin yace ko cikin ku akwai wanda zai iya tunawa a nan don kila Alh shiya mantane don an dade wanda kuma wanam zancen kasani Alh shine mafarin komai daya faru yanzu. Kai Alh ya girgiza cikin dakewa da daure fuskan shi tamau a lokacin suma sauran aka tambaye su suka nuna basu sani ba basu ma san wanan zancen ba ai. Hannu baffa hamza ya daga aka nunoshi don ya taso yazo ya tsaya ya gabatar da kanshi koshi waye da alakan shi da wanda ake sharia din dasu. Yace a ranan attani goma ga watan biyu na alif dari tara da tamanin da biyar yayan nawa mai suna Yusuf wanda akafi sani da Sambo danmadi. Ya dawo kasan nan da kwana biyu ya nememu mu yan uwan shi kaf akan nasara da Alherin daya samu a kasan turai na taron da yaje. Inda ya malam hamza ko zaka gaya muna koku dasu waye a wurin lokacin da yake maku wanan bayanin? Yace nida yan uwan haihuwan mu da mahaifin mu ya haifa kaf din mu maza mu tara a lokacin ina makaranta nazo hutu akai wanan abin. Sunayen ku nan ya fara zano sunayen su kaf sai barister din yayi murmushi yace muna sauraron ka yace bayan ya gama muna bayani yace yana son wanan kudin filin shi na kusa da filin sukuwa na da yana son ya gina katon kafanin yin sugar dana filawa indan Allah ya yarda. Saidai ya taramune don mu bashi shawara mukuma fahintar dashi saboda shi ba sanin mutane sosai yayi a nan ba ya bukaci yayan mu Nuhu da ya jagoranci komai da za ayi lokacin. Amma budan bakin yayan namu sai cewa yayi a gaban kowa don ka mayar dani fakiri mabukaci zaka zo min da wanan zancen banzan. Halan bamu san silar arzikin naka bane wai da dukiyan mahaifin mu ka samoshi don haka ba zamu yafe maka duk hakkin mu dake kan kaba ka sani yana fadin hakan ya mike ya fita yana kiran yan uwan shi. Nan kotun ya dauki kace nace aka shiga mayar da zance kuma saida aka tsawata wa hakan kotun yayi shiru mai tambayan a lokacin yace bayan nan fa me zaka iya tunawa kuma ? Yace eh bayan fitan su sai ya rage iya mu hudu a lokacin yayan mu mudi shima ya rasu a yanzu shine yace dashi yayi hakkuri yasan halin yaya Nuhu din da saurin fushi da zuciya. Yace ai inda sabo ya saba don ma yau din bai furta mai Sambo sai naga bayan ka kaida kowa naka . Barister din dake kare su Alh ya dago yana fadin bai yarda ba aka daga mashi hannu ya koma ya zauna . Baffa hamza yaci gaba da fadin littafi wani brown yaciro yana rubutu kafin ya dago kai yana ce muna shi yana ganin duk abinda yaiwa yan dakin su ba zai taba yin haske a wurin su ba in ka debe buhari shine nakewa alheri ya dawo da baya yana min godiya. Wanan ma ya isa mai tambayan ya fada yace angode idan bukatan sake neman shi yayi za a nemeshi kuma. Ya dakata mai kare su Alh ya fada yana mikewa ya koma ya tsaya a inda yake yace malam hamza kace kake ko duk da yasan shi yasan komai nasa don har matar shi nada alaka dashi barister din dake mai wanan tambayan a lokacin. Yace naji ka fadi wani zance yanzu cikin maganan ka dake nuna cewa shi mamacin yana hake da yan uwan nasa dama dake nuna cewa ashe shiyasa zargin iyalin mamacin a yanzu ya karkata a kansu su kadai ? Dan murmushi baffa hamza ya sake kafin yace abune ai wanda bawai ahalin mu ba kadai kowa yasan da wanan zancen a gidan mu bako mamacin ba kowama idan ya taso zaifi su basu taba yarda wanan akidace ta wasu fulanin mu tun tele tele kun sani. Mu bamu sani ba sai ka fada muna yanzu yace to koni nan dana sayi sabuwar moto waya ya bugo min kan cewa na bar ganin ya kyaleni ido ya saka min kada naga ina rike guntun ali na dauka nakai kowa ne yanzu idan nayi wasa zai batar dani a doron kasa yanzu haka ina da record din a cikin wayana kaf yadda mukayi dashi. Yace basai kasa muna wayan ka ba tunda ba sharian ka mukeyi yanzu ba ai zaka iya tafiya ka zauna yace ya gode ya juya zai tafi sai mai karemu yace dakata ko zan iya samun record din inji don zai min amfani nan gaba kadan idan abinda nake nema yazo daidai. Ya shiga laluban wayan shi yace gashi ka dan kuna muna nan kuma gardama ya kaure a tsakanin su lokaci guda har wasu daga can yan bayan fage na fadin ai aji irin furcin shi shiyafi. Aka kawo wani na,uran kara sauti aka hada muryan shi tarara yanawa hamza din kashedi kafin barister din ya shiga tafa hanayen shi yana godiya ya mikawa baffa wayan shi. Alkali ya bada lokacin hutu ya mike nan kowa ya samu daman mayar da zance ga nakusa dashi shima mai karesu din ya mike suka dan fita daga gefe a tare dasu. A can kuma dakin hutu alkaline a zaune ya kwabe hular kanshi suna maganan siri da babban yaron shi kan wanan case din yaron yana fadawa alkali abinda ya gano a cikin case din. Duk yadda akayi yarinyar tanada wani mai fada aji a kasan nan a yadda na fahinta gara kawai muyi abinda zai kara muna daraja da daukaka a indon mutane zaifi in yaso shi sai a mayar mashi da kudin shi. Wayan alkalin ne yayi kara ya dauka yaji mai magana na fadin shin kasan sharian da kakeyi kuwa a yanzu ya fara yawo a kafafen labarai na kasan nan don haka ka gagauta yin abinda ya dace kada kasa son kai a cikin zancen nan. Wani abokin aikin shine na wani jaha ya kirashi yana gargadin shi yace wai na tambaye ka man ita wanan yarinyar a karkashin wa take aiki a yanzu ? Yace da gani dai yarinyar tana da daurin gindi sosai a wurin wani kusa a yanzu dai na kasa gano gaskiyan zancen ina dai kan binciken hakan. Koda Alkali ya dawo lauyan su baffane yayi magana shima yana son ya samo hujjah don zargin da akewa wanda yake karewa din. Aka daga karan sai karshen daya ga sabon wata mai zuwa za a kara zama lokacin sun gama fahintar inda zancen yake kafin nan su yanke hukunci. Saida aka fito ne muka samu gaisawa da wa yanda sukazo wurin mu daga cikin yan uwa muka gaisa dasu suke muna fatan alheri akan Allah ya tona asirin maishi ko waye . Mukayi sallama dasu a rana muka juyo zuwa lagos saidai ba kamar ranan ba don yanzu mun fara samun hujja mai karfi daga yan uwa. Da daga farko suke tsoro da shayin bada sheda don kada a halakasu da tsafi ko wani abu nadaga cikin sherin Alh nuhun da suka shede shi dashi din. Ni sai bayan mun dawone ma na tuna da envelop din da Felix ya kawo min washe gari ina kwance na mika hannu na dauka. Katin fatan alheri ne maikyau dashi sai kalaman fatan samun nasara da akewa mutum a cikin katin da kallo shi kawai zaisa ka gane yana da tsada sosai. Dan murmushi na sake a fuskana a karo na farko tun dawowan mu lagos din mikewa nayi na dauko wani takarda ina dubawa ni dai Allah ya gani a yanzu kaf yan uwan mu inka debe mutu hudu zuwa biyar har dana sanin fitowa a cikin su nakeyi. Mutum biyar din kuwa sune ya Abubakar wanda Allah ya jefoshi a cikin rayuwan mu da alheri domin ya tallafa muna sai baffa hamza sai kuma gwaggo hari da danta sai baffa Abdulahi da shima yake nuna muna kulawa sosai a zaman kotun. A can kaduna kuma yau gidan nasa makil yake da yaran shi da wasu yan uwa da abokan arziki dake ganin kazafi akai masu don kawai a bata masu suna a gari. Falon na cike da mata wata mai zakin murya a cikin matan dake falon take fadin kai wanan zamanin dame yayi kama haka ? Wai ace yar dan uwanka daya mutu ya bari itace wai zatayi karan ka ta zauna kotu dakai tana sharia don lalacewan zumuncin zamani. Yo keko dai akan kudi maye mutum ba zai iya yi a yanzu ba hjy hafsa wata karba daga gefen ta ni sai na dauka kamar hadin bakine don kawai anga suna samu bari a tsiyata mutum a huta a koma daidai. Wanan yar ai ta bushe fitilan tako don ance ma ko shigarta kawai kagani kasan ta rika ta kuna bata taran kauri don idanuwan ta a bude suke. To aini yadda naji ance tare da manyan kasa take kinga kuwa dole ta dauka zata iya can wata daga cikin yan uwa ta amsa su da fadin . Ni har taysayi take ban bata san waye Alh bane ta kawo kanta Alh ai ba, ayi mashi wanan haukan yama kyaleta dai don tana yarinya ne karama kila ? Nan dai suke ta shaci fadi dinsu har suka gaji sukai sallama suka tafi ba don sun gaji da gulma daga gefe wata yar gidan ta kalli nazifa tana fadin niko wanan shigan da za ayi har kotun zanje naga wanan yar iskan yarinyat dai a idona. Baki nazifa ta tabe tana fadin kiga haushi dai kan din ance wallahi karamar yarinyace sa,an su manir kinga kuwa ai karamace sosai wuri ta samu kawai tana iya shegen ta kawai indai Abbane ai kar yake kallon ta. Toshi mijin kiku fa da akace shi yazo da ita daga lagos din ya nuna mata gida fa tace wanan dan iskan ranan naji mahaifiyan shi na masa fada yace shi ina ruwan shi cikin wanan case din tunda bai shafeshi ba. Ai baima zuwa kotun ina gani don ko wanan zaman ma yana Abuja aka zauna bai gari ai shiyasa na kyaleshi. Da zai tafi na bugi cikin shi ina fadin gobene fa zaman su Abba kotu yace dani ina ruwan shi da zaman su shi wanan zancen ba nasa bane don haka zaije yayi mai fiddashine. Shi zancen biyan wanan kudin company din yanzu ke gaban shi suga inda kudi zai fito a biya su kudin shine a gaban shi. Kai gaskiya Abba yana da makiya wallahi ki duba fa Nazifa idan haka ba shiri bane ina Abba ya taba fadawa hannu irin wanan gashi lokaci daya . Allah ya fisu ai kome kuwa zasuyi ba zasu taba cin nasara ga Abba ni shiyasa abin baya damunama sam wallahi don a shirme nake daukan zancen. Wai ace anyi karan Abba haba kai jama,a da kuma laifin yin kissan dan uwansbi fa ? Nifa har yanzu zuciyana ya kasa tsayi wuri daya wallahi tun maganan da mama tai muna ranan nake jin kamar wani abu zai farune dasu Abba din . Don fa yarinyar nan ta shirya sosai wallahi ga ta ba tsoro ko shayin kowa haka zata tsaya tana fuskantar kowa a cikin kotun. Ni yanzu so nake kawai naga an kare wanan sharian wallahi saina fadawa baffa hamza magana daga yau alakan namu ta jini ta bare ai yaga yadda nayi mashi dazun da muka hadu dashi wani kanin su ke wanam zancen a cikin takai . Wai tace a bata dukiyan mahaifin nata kuma abi mata hakkin halaka mata uba dasu Abba sukayi idan ba tsoro ba uwar nata tazo ta tunkari su abba mana idan bataji tonon asiri ba a wajen su. Saida suka kare barikancin su sanan yanzu suzowa mutane da wani zancen bamza cN ZAINAB IDRIS MAKAWA ANA DARA GA , , , , , , , , 8️⃣2️⃣ BY, , , , , , , , , , , , ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , , , , , , , , BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AS SAMADU, , , , , , , , , ONLINE PAID NOVEL YAR UWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA BA TARE DA HAKKIN KOWA BA DON BIYA KI TURA DARI BIYAR 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK 08036959257 ALLAH SARKI AI RAINA BAYA BACI YANZU DON KIN FITAR DON NASAN AKWAI RANAN HADUWA SEE U👋👋👋👋 Abubuwa sun rikice sun rabtabe a tsakanin dangin an kasu kashi uku kowa da bangaren da yake zargi wasu na ganin mune da laifin komi. Wasu kumana ganin ai yadda mukayi din shine daidai don suma wanan sun san zaluncine ba dai yadda suka iyane kawai. Yayin da wasu kuma suke ganin a,a laifin baffa hamzane tare da modibbo dasu baffah Abdullahi suke kulawa yan uwan su sheri. Duk wanan ni bashine a gabana ba kawai ni burina naga mun samu freedom kamar kowa mu daina wanan boye boyen da muka taso a ciki umma na faman boyemu garesu . Sun sa tabar yan uwanta da garin su duk saboda su komai namu ya fita daban da sauran yan uwa dake harkokin su a fili babu boyo a garesu. Kome za ayi dai yanzu ni ba dukiyan dake hannun sune a gabana a dai gane gaskiya a inda take masu zargin umma suna dora mata laifi kan abinda basu sani ba su sani yanzu. Don har yanzu ba ako soma shiga inda nake son akai ba din ummace ta turo kofan dakin nawa tana cewa dani na fito naci abinci don tun safe ban leko falon ba abinci yana ajiye. Na amsa mata da zan dan watsa ruwa a jikina kafin in fito ta juya ta tafi bayan na fito wanka na zauna na shirya nafito abincin na nufa na bude har lokacin yana da zafin shi sosai da zan iya ci. Zama nayi na dauki remote na kunna tv na fara cin abincin dana zuba din badon yunwa ko jin dadin bakina ba. Wayana ne yai kara na dauka ina duban mai kirana a lokacin ya mustaphane dan gwaggo hari nabi wayan da kallon mamaki kafinnin kai hannu in dauki kiran. Ina karawa a kunnena tare da sallama ya amsa da fadin hi baby ya kuke ya kuka isa gida dan jim nayi kafin in iya amsa mashi da fadin who is speaking ? Dan murmushi naji ya sake kafin yace nufies dan gidan gwaggon hjy hari from kaduna i hope yanzu kin gane daidai ko ko a kara maki bayani yadda zaki ganeni. Forget about that why are you calling me now ? What a surprise question ne wanan bazan kira kanwata naji lafiyan ku ba sai ina da wani dalilin kiranki ko wani abu zan kira ? To nakira kawai inji lafiyan kune a yanzu in fada maki kuma zan shigo kafin zaman ku na gaba da zakuyi don a kwai, , , , Bama bukatan hakan a yanzu ko menene Allah zai tsaya muna insha Allahu OK idan ke baki son jin me zai kawo ni umma tana so jin don zai karata a gaba. Look mr don Allah ka tuna kaida kanka ka gargadeni da bani warning kada in nuna wani sananya a tsakanin wanan maganan ka tuna kaman a yanzu ka bani warning din a wurina. Ok nagode naji ya fada a dan sanyayye cigaba da fadin sai dai ki sani wata rana keda kanki zaki janye wanan maganan a zuciyar ki. Yana fadin hakan ya kashe wayan shi duban wayan nayi naja tsuki ina lumahe idanuwana a hankali don tunawa da wanan lokacin daya fada min hakan. Yana ganin a yanzu zan jaye zancen a zuciyanane kome Allah ya gani shi din bai cancanci haka ba a wurin mu don ya taimakawa rayuwan mu alokacin da muke ciki bukatan taimako don haka bai dace da yadda nake mashi yanzu ba . Saidai kuma yin hakan ya zama dolene don na fuskaci iyayyen su basu son diyan su jefa kansu a cikin wanan rikicin don gujewa fadawa halaka da tsoron abinda ka iyaje ya dawo nan gaba a garesu. Wanan ne babban dalilin dayasa nake jan baya ga kowan su don ina ji masu tsoron da iyayyen su kejiye masu daga wani sheri saboda mu. Saida darene muna zaune mun tare dasu umma da suka rufe shago don dare da yayi abinci mukaci bayan mun gama cin abinci ana dan taba hira a tsakanin mu. Nake fadawa umma ya kira waya saidai umma ko kin kula cewa iyayyen nasu basu son mu,amulansu damu suna kokarin ko yaushe su yakinci diyan su akan kulamun da sukeyi. Mommy tasha warning din haka a gaban ga ya Abubakar haka in zaki tuna itama gwaggo hari tayiwa danta wanan kashedin a kan mu ranan. Haka na nufin dukkan uwayen biyu basu son wani abu yazo ya samu diyan su ke nan ta dalilin mu don hakane nake kokarin ganin na nusantasu da zuwa wirin mu ko shiga lamarin amma bayan wanan ai ba zan taba kin su ba don sun taimaka muna lokacin da muke bukatan taimako a garemu. Shiru umma tayi kamar tana nazarin abinda na fada kafin ta nisa maidan bada sauti tana fadin nasan da hakan kwarai Sahiba nima nayi wanan tunanen a baya ai. Amma kuma tunda su yaran basu nuna hakan ba a tsakanin mu dasu sai naga idan kina nuna masu haka zasuga kamar mu din masu butulci ne a garesu. Nan dai muka dan taba hira a tsakanin mu kafin na mike na shige dakina zuciyana cike da tunanen irin maganganun da mukayi da umma kan hakan. Wanan karon ma kamar wancan tafiyan mukayi shi da niyar kwana daya kawai zamu mu juyo idan an tashi daga kotun . Mun shiga a kan lokaci ina sayene a cikin suit baki na mata wando da riga dinkin zamani sai takalma tom daya shiga da kayan. Sosai shigan ya karbeni ya kara fito dani a yadda na koma yanzu wata classic sai dan jakar dake makale a kafadana karami. Kotun kan ya cika makil da jama,a masu son jin wanan badakalar da ake gwabzawa a cikin ahalin namu na tonon asiri. Dayawa nunani sukeyi a wurin har lokacin da aka bukaci da nataso mu gabata gaban mai sharia na mike na taso aka bini da kallo ke zakice diyar wani pastor ne ni in kin debe dan bakin half hijab dana dan saka daga samana ya rufe min kaina kawai. Suma sukazo suka tsaya kamar yadda akeyi idan an shiga koto mai bayani ya fara karato dalilin zuwan mu da kuma inda aka tsaya ranan ga sharia. Lauyan su ne aka fara ba dama ya mike tare da ban girma ga Alkali kafin ya fara fadin shi a matsayin shi name kare bangaren su.. Yau yana maganane da cewa yanzu dai a bisa bayanin baya da sheda na farko ya bayar sun gane cewa akwai hadin bakin wasu yan uwa a ciki da suka tunzura maganan. Har suka turoni nazo nayi kara don kawai a tozarta su Alh din don haka zaiso yayi min wani dan tambaya. Kotu tace an bashi dama ya juyo gareni yana murmushi ga mamakin shi nima murmushin yaga na mayar mshi a lokacin yace da kyau yarinya zaki gane kuren ki a zuciyarshi. Sahiba ko ya tambaya nace that is my name yace good ko kina da shekara nawa mahaifin ki ya rasu ya fada yana wani kada kai nace dashi shekara biyar yace U see . Kina da shekara biyar a lokacin ke yaya kikayi kika san da cewa hakan ya faru su Alh nuhu ne suka kashe mahaifin ki ? Nan kotun ya dauki kus kus na jama,a shiko yana gefe ya zuba min ido na dan gyara tsayina kafin nace dashi kai tsaye. Nace saboda ina da shedan hakan ga wace akayi abin a gaban idon ta , sai kuma sheda na biyu ina da littafin da mahaifina ya rubuta bayani shima a cikinsa a yanzu. Yayi min wani irin kallo na gyada mashi kai zaiyi magana mai kare bangaren mu ya karba da fadin wanan ai ba hurumin ka bane kake kokarin shiga yanzu. Alkali ya daga mai hannu ya mike ya karaso yana fadin kamar yadda kotu ta nemi da mu gabatar da shedu kan zargin mu a yau munzo da wace komai ya faru a gaban idon ta itace hjy maria matar shi marigayin uwa kuma gasu masu karan sai wanan lokacin sunan Amar ya fara shigowa a cikin sharian. Kotu tabada daman fitowan umma din da sai a ranan mutane suka sheda fuskanta don basu ganin ta sai ni da Ammar ta shigo a inda take tsaye . Kotun ya dauki surutu lokaci guda don ganin umma yadda ta sauya a yanzu ta murje tayi kyau sosai da ita. Aka fara tambayanta sunan da matayinta ta fada Alh gyade sai gyara tsayuwa yakeyi nan aka fara mata tambaya tana bada amsa. Abinda ya faru ranan ta fada tun kafin yaje ya gansu din ya fada mata da dawowan shi ya koma ba lafiya da wayan da sukayi da Alh nuhu. Dakata hjy lauyan namu ya fada yace zan maki yar tambaya lokacin da hakan ke faruwa ke kina ina a lokacin ? Tace duk muna tare rabuwana dashi shine dana kai yar mu daki wanan sahiba din na bata magani nima nasha wanda ya sayo min don ina da shigan karamin ciki dana dawo dashi lokacin ba kowane yasan dashi ba sai nida mijina din. Na koma na kara samun shi cikin tashin hankalin dayafi wanda na barshi a cikin ina shiga yake ce min idan kuji ankasheni kada a zargi kowa yan uwan haihuwana ne su Nuhu suka kasheni. Kai har takai da tabada labarin yadda kisan ya kasance da komai ya faru har fitowan su ai ga baki daya kotun ya dauki salati kowa na fadin albarkacin bakin shi. Har saida alkali ya tsawata aka samu akai shiru taci gaba da fadi lokacin kuka ya rinjayi karfin ta lokacin da baffa buhari yake tambayan su sun samu ganin shi sunyi maganan dashi ? Lauya ya tambayeta ke nan shi buhari baisan kasheshi akazo yiba kike nufi tace hakan nake tunane don daga inda nake labe a dakin maigadin ina jin yadda yake tsuki yana fadin wanan ai sai a zargi wani abu a garemu bayan sun fito yake tambayan su yaya ya yarda zai bayar ko nasan bai zaiyi gardama ba ai yadda kuke nufi. Sukace ai zance ya kare tunda ya zama tarihi yanzu kuma komai ya dawo hannun mu ga baki daya da irin neman da sukai mata din a cikin gidan shi baffa buhari na fadin akan me zata gudu don ta ganku. Har zuwa kashedin da Alh nuhu yai mata washe gari akan saura ita a gaban mutane yake fakan idon su ya nuna zai yankata itama haka ya sata dauki yarta ta gudu daga garin baki daya ke nan har taje can tayi renon cikin dake jikin ta tare da diyanta duk a can ta karashe a cikin kuka kotun ya dauki salati lokaci guda. Haka masu raunin imani a kotun ma suma kukan suke taya umma na labarin data bayar din a lokacin mai taba zuciya Ina gefe a zaune na hada kai da kujeran kotun dana zauna akai ina faman kuka sosai duk da kamshin da naji na turaren shi hakan baisa na dago kaina ba na daiji mutum ya zauna a kujeran kusa dani ya miko min handcarchef in share fuskana. Bayan na gogene na dago da niyar inwa maishi godiya idona ya sauka ga ogan mu zaune a kusa dani daga bayan mu kuma sauran jama, an mune a zaune. Dan zabura nayi dan mamakin ganin su a wanan lokacin yace be cool kada ki damu, damu a yanzu mu saurari mai wanan alkalin zai yake nan gaba. Kai kawai na iya gyada mai a hankali naci gaba da goge hawayena dake zubo min muryan lauyane ya dawo damu kallon gaban kotun yana fadin. Ya mai sharia wanan shine shedan mu ta biyu dake nuna su alhaji nuhu sune suka kashe dan uwan su saboda wani bukatan da sukaje wajen shi dashi a ranan. Objection my lord wanan ai bai isa sheda ba don za a iya tsara mata fadin hakan tazo nan tana muna kukan karya don tana ganin ba zamu gane hakan ba. Lauyan su ya fada namu zai tare alkali ya daga mashi hamnu ya koma ya zauna wanan ya tunkari umma. Yace hjy mairo munji shirin da kika tsara muna a yanzu saidai abin mamaki ke a lokacin kina ina har haka ya faru baki sani ba . Tace na fada ai jikin yarmu da yayi zafi a lokacin ya turani dakina in bata magani nima nasha maganin daga nan na tsaya na shimfide ta shine barci ya dan daukeni ganin shi yana ta faman rubutu a cikin littafin shi na siri yasa na zauna dakin kada mu dameshi don nasan inya gama zai nememu ai ko don yaji lafiyan yar shi. Shine a cikin dan barcin daya daukeni na fara jin kamar kakarin shi na fito zuwa dakin shi da sauri a nan na samu sun gewayeshi su hudu Alh Nuhu ya dora mai yuka a wuya shi ya ganni sai dai su basu ganni ba da hannu yayi man nuni da in gudu. A daidai lokacin da shi Nuhun ke fadin dama kai kadai ka rage bakin irin a cikin mu yanzu sauran basu dameni ba kawar dakai shine yafi a garemu ya fara yanka mashi yuka yana rokom shi idan kun kasheni ku kula da matana da yata da ciiii daga nan sai salatin shi naji da karfi alokacin na dauko yar muka fice ta kofan kitchen ta baya na nufi dakin maigadi don babu kowa a wajen . Sai bayan na shiga ne na dinga ganin innuwan mutum a cikin duhu yana zirga zirga a wurin yana tsuki tare da fadin wai daga magana sun nemi wuri sun zauna. Kuka ya hana umma karasawa shima lauyan komawa yayi ya zauna yana dan caka biron dake hannun shi saman takardan shi . Alkali kuma sai faman rubuce rubuce yakeyi a nasa takardan lokacin kukana ya tsananta sosai yasa ban iya jin komai. Hannun Ogan mune naji saman nawa yana fadin be strong ba a cin yaki da ragganci ki zama mai karfin zuciya ko yaushe da zafi amma ki daure. Kai kawai na gyada a lokacin don ba zan iya fadan komai ba duk lokacin da ake bada wanan labarin nakaji wani iri a cikin kasan zuciyana nakan kwantanta irin zafi da radadin da mahaifin mu yaji a lokacin. Muryan lauyan mune yake fadin ya alkali mai sharia zanso ganin buharin da ake zance a gaban kotu yanzu ya amsa min wasu tambayoyi kafin nan ga wanan mai sharia ya gani bayanin dashi marigayin yayine a cikin nan din. Aka karba aka mikawa Alkalin ya gyara zaman glass din shi ya fara duba a hankali nan akai cigiyan buhari ya fito a gaban kanta ana neman shi. Kowa ya bishi da kallo har ya karaso ya tsaya gaban su hayaniyane ya fara tashi lokaci guda a tsakanin su Alh nuhu da yan kallo da kyat alkalin ya samu ya saita mutane akai shiru lokaci guda. Sai a lokacin na dago kai na kalli wanda ake kira da buharin nayi mai kallo na tsana da ki shima din yana da zubi hallita irin nasu saidai baikai su shekaru bane kawai shi. Lauya ya fara magana Alh buhari ko ya amsa da eh yace sunan ka ya fito a sharian nan kusan sau biyu ke nan ko zaka fadawa kotu abinda ka sani game da abinda ake tuhuman yan uwan ka da aikatawa ga dayan dan uwan ku da Allah ya karbi rayuwan shi a baya. Fuskan shi ya dan shafo kafin ya soma fadin eh to gaskiyan abinda na sani dai shine shi dan uwan namu ya dawo daga tafiye tafiyen da yakanyi a kasashen ketare . Sai wanan kayon ya bukaci daya ganmu a nan bayan mu hadu a gidan mahaifin mu yake fada muna cewa wanan tafiya ya samu haske da yawa a cikin shi. Nan ya bukaci da mukawo ya shawaran abinda zaiyi har muma mu karu da yaga ba wanda yai magana yake fada muna nasa kudirin a lokacin . To sai abin baiyi tasiri a zukatan sauran yan uwan mu ba bayan mun bar wurin shine suka bukaci damu hadu muyi wani shawara a lokacin. Lauya ya tareshi da fadin ku nawa ke nan fa yace iya mu yan dakin mune a lokacin amma kuma da mukazo taron sai naga Alh bello da Alh tanimu dinne ma suka tsara duk yadda za ayi a tunkar shi sambo din lokacin. Kamar wani irin tunkara ke nan lauya ya tambayeshi yace eh to a gaskiya shawarane kan yaya shi da yake karami a cikin mu don mahaifin mu ya dauki nauyin karatun shi za ace yanzu shine zai juyamu. Ma,ana ya fimi arziki inma arzikin ne aida kudin mahaifin mu yayishi tunda shanun da dukiyan mahaifin mu aka batar har ya samu ilimin nasa. Don haka dole ya kawo dukiyan da yake ikirarin ya samu a kasa aba kowa nasa ko kuma muyi karan shi akwato muna hakkin mu. Na basu shawara kan mu barshi da abinshi shi Allah ya zaba a cikin mu sun nuna min ba hakan ba nace to ba laifi nizan tafi. Sai na manta da dan ledan dana shigo dashi wurin na dawo daukane na samu sun canza maganan shi Alh nuhu na fadin sai in halakashi in halaka banza ba zan sa ido ina kallon takaiciba hakana. Nace kai haba dan uwankane fa ina laifi dai kuyi mai maganan da kukace zakuyi zaifi nabar wurin hankalina bai kwanta ba na samu yayan mu Ali dcp da zancen sai cewa yayi in barsu suyi mai magana ai sambo dukiyan nasane abin tambaya. Nikan lokacin dana bar wuri Ali dcp ina mamaki saina nufi wurin sambo din na fada mai komai dake faruwa akan ya dauke iyalin shi yaje wani wajen. Sai ya nuna min in yan uwan shi na haihuwa sunkishi ina zai tafi ke nan da yamma sai naga yazo wurin nuhu da yake lokacin duk gidan muna gado muke bandashi daya sai gidan kanshi bai zauna a ciki ba. Nan suka dade da nuhu suna magana kafin ya fito ya tafi ranshi a bace daga inda Alh nuhu yake tsaye yace munafuki dama nadade ina zargin ka a raina. Murmushi yayi yaci gaba da ba kotu labarin dashi ya sani Alkali yana rubutawa har aka sallamishi aka dawo kan wanan dan littafin da akai rubutu akai. Inda mahaifinamu ya rubuta idab na mutu a tuhumi nuhu gyade da Ali dcp aminina donshi yasan sirina ya fadawa nuhu komai. Ga inda ya tsara kaddarorin da yake dashi an karanta kowa yaji nan dai Alkali yace aje a rufe su Alh har haduwa na gaba kan zargin da ake masu din na kisan dan uwan su a shekarun daya gabata a baya. Kotu ta tashi na dade zaune ban motsa ba a inda nake ina jin wani iri a zuciyana kafin can in dago kaina. ZAINAB IDRIS MAKAWA ANA DARA GA , , , , , , , , 8️⃣3️⃣ BY, , , , , , , , , , , , ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , , , , , , , , BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AL QADIR, , , , , , , , , ONLINE PAID NOVEL YAR UWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA BA TARE DA HAKKIN KOWA BA DON BIYA KI TURA DARI BIYAR 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK 08036959257 ALLAH SARKI AI RAINA BAYA BACI YANZU DON KIN FITAR DON NASAN AKWAI RANAN HADUWA SEE U👋👋👋👋 Kowani bangare ka kalla fuskan su babu dadi ko kadan gashi ranan sun fito kwansu da kwarkwatan su anzo kotun . Don Alh nuhu daya fada masu ranan ne za, akai karshen sharian sai mun kwashi kunyar mu a hannu mun gane kuren mu a wurin shi. Sai gashi ranan reshe ya juye da mujiya shari,a ya hau kansu yanzu nayin kisa da salwantar da dukiyan marayu da sukayi a tsakanin su. Saidai daddy da kotu ta nema ance bai kasan yana waje amma harshi baffa buhari an rufeshi ranan don shima za a tuhumeshi kamar yadda shari,a ya tanada. Mutanene gun gun haraban kotu din kowa na mayar da zance akan sharian na yau kusan mune na karshen fitowa daga cikin kotun yayin da aka zubo muna idanuwan tausayi wasu kuma na tsana. Kasancewan da oga Shaaban a wurin sai ma aikatan mu suka koma bayan mu suka sakomu a gaba hakan ya kara sa mutanen wajen mayar da hankulan su a kan mu. Har lokacin kuka nakeyi sosai gwoggo hari da danta da mijintane suka haro inda muke din sukazo wajen mu gaisawa aka farayi dasu kafin tace Sahiba kibar wanan kukan in Allah yaso gaskiya ta fara halinta kowa ya sheda hakan a nan yanzu. Yaya Abubakar ne ya karaso wurin kallo daya zakai mai ka gane baya cikin hankalin shi suna magana da mijin gwaggo hari din da mustapha. Ogane dake gefe yana waya ya taka zuwa inda suke shida Ammar da zuwansu Ammar ya nuna ya Abubakar din yana fadin dis our big brother and his like a father to us now . And dis our uncle too and his wife sai ya riko hannun ya mustapha yana fadin dis too is carryin with us too he means alot to us. Kallon ya Abubakar din da uncle din yayi kafin ya kai kasa yana masu gaisuwan sarakuta tare da fadin yaji dadin daya gana dasu yana neman auren yarsu Sahiba a wajen su idan ba damuwa. Duk wanda ke wajen kallo ya koma a kansu lokacin yasa da sauri ya Abubakar ya dago shi yana fadin wanan zancen banayi bane a wajen nan sai anje gida an zauna tare da sauran iyayyena zaizo. Adnan ne yake nuna min ogan namu lokacin da yake tsugunne na juya da sauri tare da mamakin ganin hakan a garesu a yadda na sanshi babban mutum dai. Dariya aka kwashe dashi lokaci guda naga Abban ya mustapha yana dan bubuga mai baya ban san abinda suke fada ba a lokacin. Sai dai duka fuskan yan uwan nawa biyu a lokacin baida dadin kallo bayan dan zancen da sukayi a tsakani ya juyo zuwa wurin mu fuska a sake ya umurcesu da su kawo motoci mu wuce zuwa airport daga nan. Takawa mukayi inda su ya Abubakar dasu baffa hamza suke tsaye suna hira wanda bai wuce akan oga mu ko sharian suke magaba ba lokacin. Gaisawa mukayi dasu kafin muryan ita gwaggo hari tace ke yata ashe tafe kike muna da suriki yau yanzu yake gabatar da kanshi a garemu ai. Da mamaki nake kallon ta don ban gane abinda take magana a kanshi ba lokacin wanan ai shirmen banzane mutane na cikin wanan tashin hankalin zai wani zo ya gabatar da kanshi wai a matsayinshi na wanda ke son ya auren Sahiba. Mahaifin shi ne da baffa hamza suka idan ya gabatar da kanshi garemu yanzu laifine yaushe zamu kara ganin shi ne wai ? Tunkan mahaifin nasa ya rufe baki ya juya ya bar wurin mahaifiyarsa ta bishi da kallo kafin ta juyo tana kallon mu dan dariyan yake tayi a fuskan ta kafin tace damu yau din zaku koma ke nan ? Umma tace yanzun kuwa daga nan sai airport zamu tafi jirgi karfe biyar na yamma zai tashi wai mukai sallama zamu tafi umma ta kira ya Abubakar sun dan jima suna magana kafin ta juyo muka tafi. A cikin motan da mukazo da ita muka koma don mun samu duk sun shiga motocin su saidai ba wanda ya iya maganan komai a cikin mu lokacin har muka kai airport din. Nan ma ba bata lokaci muka kama hanyar lagos don dama lokacin tashi ya kusa har muka isa gida lafiya ina jin wani zazzabi ya rufeni tun a cikin jirgi da kyar na samu nakai kaina gida a lokacin ban tsaya komai ba sai kwanciya a yadda nake jin kai . Duk yadda suke shiga tashin hankali a gidan wanan yafi daga masu hankali sosai don gaba daya gidan ya rikice da kukane lokaci guda. Yadda makwabta suka saba shigo masu idan wani abu ya faru dasu sai yau din babu kowa daya shigo masu gidan a ranan. Cikin manyan mazan diyan shine suka shigo a lokacin suma kallo daya zakai masu kaga bacin rai fuskokin su don rayukan su babu dadi ko kadan lokacin. Sun zauna ana masu sannu sai daya daga cikin matan ke tambaya kun gane inda aka kaisu kuwa ko har yanzu ? Mun gano da kyar mama saidai ba a bari a gansune don wuri mai tsanani aka kaisu don laifin da ake zargin su dashi din mai karfine sosai. Kukane kuma ya dawo masu sabo kowa na fadin abinda yazo mashi a baki a lokacin dayan matasan ne ya yanka wani ashar sai Addah wuro take ce mashi. Na fada maku ku daina zagi don mahaifin ku shine da laifin komai ninasan abinda ku baku sani ba akan wanan maganan. Tunfa ba ai wata biyu ba Alh ya rabe kayan Sambo sambo mutum mai kirki mai zumuci kaf a cikin yan uwanshi amma suka dauki karan tsana suka samashi a dalilin mahaifan su kawai. Ina laifin wanda ya samu yace kazo kuci da wani dan uwane ai bazai ko tuna dasu ya jawosu a jiki ba amma shi duk lokacin daya sauka kasan nan kowa sai ya sani dangi kaf kuwa don zaibisu daga daga yana sauke masu alheri a gida. Kukun sani basai na fadi komai ba ta nuna kishiyoyin nata dake zaine sukace kwarai kuwa kayan sallah mu dana yara a lokavin duk shine ke muna tun baiyi aure ba kuwa. Ko a lokacin da ace yabi ta Alh wallahi ba zai muna wanan din ba kuma bamu ba gaba dayan mu yan uwa hakan yake masu wanan alherin amma wai ace yau su Alh ne sanadin barin bawan Allah nan duniya duk wanan alherin da yake binsu dashi kan abin duniya kawai. Addah wuro ki daina fada don Allah don aikin gama yariga daya faru wanan babban dan ya fada ni ba komai nake jiwa ba a yanzu sai kaddarorin Abba da kaf za a kwace a mayarwa masu dukiya da abinsu ne abin ji ai. Kai kuma yaya ka fara zancen ka ke nan a kan me za a kwace dukiyan duka saidai a basu nasu a bar mashi nasa ai. Mekega Alh din dama hjy salma ta fada tana kallon su tace ai zancen gaskiyane ya fada shiyasani idan zai tuna ko wancan gidan da muka fara zama a cikin sa na waye gadon shi sambo dinne ai da aka raba tunda su sun sayar da nasu a lokacin sun raba kudin da sunan zasu ja jari dashi ya karye. Kowa yayi shiru yana tunane wayan Nazifane yayi kara a lokacin ta dauka tana jan suki da muryan ta daya dushe don kuka tana fadin muna gidane mana har yanzu. Can kuma tace sai mun gama zan dawo mana bana fadama ina gida har yanzu ta kashe wayan tana jan tsuki kajiki da wani shirme ke kuma. Wani dan uwanta ya fada daga cikin su mutumin da tun dazun muna tare dashi wurin neman inda aka kai su Abba a dalilun shine fa har muka gano inda suke. Dayan yace balle idan akace yau bawan Allah nan baiyi kuka ba da wuya wallahi yadda hankalin shi yake a tashe din nan koda muka rabu yace zazzabi ma yake ji sosai. Toki tashi kije gida kinji mijin ki ba lafiya uwarta ta fada idan kin zauna nan din me zakiyiwa mutane tunda ba wani abin kukeyi a nan ba gobema aisai ya barta tazo a cikin dadin rai amaryan gidan nasu ta fada karshe. Badon taso ba tamike zuwa gida haka ta isa gidan ranta a bace ta samu babu kowa a falin part din ta ta nufa ta shiga ta yada jakar hannun ta saman kujera. Kayan jikinta ta fara cirewa don tasha iska ta kafin kuma ta fara kwalawa mai aikinta dake dakinta da yaranta kira ta kawo mata abinci. Bayan ta kawone ta aje mata ta koma ta dauko ruwa lokacin ta samu ta fito daga bandaki tayi mata sannu da zuwa. Yauwa don Allah ki koma ki dauko min wani drink don ban faye son wanan din ba zata dauka sai kuma tace ki barshi mana ki dauko min wani. Ba,a jima ba sai gata ta dawo mata dauke da wani da kuma wani leda a hannun ta tana fadin hjy wanan baban su maryam ya dawo dashi dazun da zaishigo ya bani. Ok meye a ciki ta tambaya nuna mata tayi bata bude ba bayan ta bude ta dibi rabonta don tasan ba zata samu ba idan uwar dakin ta dawo ta amsa a hannun ta. Sun dan taba hira a tsakanin su tana tambayan ta yaran idan basuyi fitina ba dan bata nan tace sun dan taba sai kallon uwar dakin nata takeyi yadda take hankada abinci a cikin ta kamar ba gidan su tafito ba har dare haka. Nan dai suka zauna harta kare abincin tas ta mike ta kwashe kayan tare da mata saida safe ta tafi tana mamakin hali irin nata ko yaranta bata tuna dasu ba wurin cin suyan data tasa a gaba sai kwara uku data bari wai taje dashi. Saida ta gama komai da zatayi har charting kafin ta mike ta shirya zuwa part din shi ta murda kofan taji shi a rufe baki ta mede ta juya ta koma dakin ta. Washe gari tun safe ya shirya zuwa gidan su don duk jiyan bai samu lekasu ba asalima ba zaice sun sanda wani labari dake yaduwa a gare ba don mommy bata nemoshi ba. Yayi mamaki kwarai daya shigo ya samesu gaba dayan su dukkan su a falon gidan tunda safe haka yakaroso da sallama a bikin shi yana gaida iyayyen nasa kafin kannen nasa su fara gaidashi suma. Make faruwa ya tambayesu tin kan ya kai zaune yana kallon fuskokin su yaji hjy karima na fadin wai cewa akayi yau jami,an tsaro zasu zo gidan nan bincike . Haba dau anty waya fada maku hakan ya tayar maku da hankali akan me zasu shigo har cikin gidan nan bincike ? Kai bakaji sherin da yarinyar nan take kokarin yi masu bane a koto ya tambaya cikin mamaki da wace yarinya ke nan mommy ? Tace wace in banda Sahiba dai da idan anyi maganan ta kace tana da kirki tana da gaskiya to yanzu kaji dai inda sherin ta yakai gun su Alh kuma. Amma mommy ita sahiban ce ta ambato sunan daddy a ciki aka fada maku ko masu laifin ne suka ambace shi har sunan shi ya shiga ciku ? Dama yanzu nabila ta gama fada ba zaka taba yarda da hakan ba ka dauki sahiba tankar wata a zuciyar ka . Gaskiyace kawai bata faduwa Anty ya yarinyar nan bata saka sunan daddy a karan ta ba kuma tasan yana da hannu a ciki kamar yadda mahaufinta yabar komai a rubuce. Nina sani shi kanshi daddy na sameshi kwanaki da wanan zancen tun baikai haka ba yace wanan zancen banza ne itama ta sani amma bata nuna min hakan ba. Inba hadin baki bane wanan maganan yaya za ayi sahiba tasan zancen da akayi tun tana goye a bayan uwarta mommy ta fada a hasale. Mommy amma ai uwarta na raye ita a gabanta akai komai ko don haka sahiba tana da wurin ji wanan abin dai sam baiyi dadi ba don gaskiya wanan mutumin bai cancanci haka ba a wurin su gaskiya. Ke nan yanzu kai baka da wani abinda zakayi kafin shi Alh ya dawo ke nan ya kallo uwar cikin mamaki kafin yace amma mommy kinsan casene fa na kisan kai wanan ? Innalillahi uwarta fada cikin tashin hankali sai anty amaryane tace cikin karfin hali yanzu dai sai an kaishi kotun ke nan yace dole sai dai in ba hannun shi a ciki kinga shi yayi free ke nan . Yanzu ma ba wanan ba so nake daddy din ya dawo duk wani abu daya san nasune in yana hannun shi ya hada a mika masu abin su tun wuri tunda yasan yadda sharia take dai . Tunda wancan zuwan da sukayi naji ya taba fadan cewa duk wani abu nasu yana nan hannun sa ya ajiye da sunan su shine nake son ya yarda yanzu lokaci yayi da zai mika masu shi. Nima mun shayin wanan maganan dashi don wani lokaci idan ya zauna yai shiru ka tambayeshi meke faruwa sai yace hakkin marayun dake a kansa ne yake tunane. Ni wanan yasa ban wani tayar da hankalina ba sosai da wanan zancen don nasan abune mai wuya daddy ya yarda har hakan ya kasance dashi. To waini shi wanan bawan Allah wani irin dukiyane ya tara haka mai yawane da har ya jawo wanan rikincin haka kowa da hannu dumu dumu a cikin case din har wanda baka zata ba Anty Amarya ta tambayeshi. Hjy karima ke nan bakizo kin sameshi cikin mu a raye bane yasa kike wanan tambayan a yanzu haka. Shi tun yana karamin shi haka Allah yai masa baiwa a cikin yan uwa don ko dabba za a sake a gidan mu saika mika masa ya sake ma zata dinga hayayyafa idan kuma har ka sake da sunan ka wallahi a karshe salwancewa dabban zatayi kota mutu ko ta bata ko kuma ta tsunbure. Kai akwai dai camfi a da can baya wanan duk a yanzu wa zai tsaya yin wanan to ai irn wanan abin ne har ya kawo hassada ya shiga cikin sa sun kasa gane Allah bai raba daidai ba koga yatsun hannun mu. Aiki yake a kasan saudiya wurin danyen mansu can har ya kasance ya fara aiki da wasu kasashe yana samu sosai tun baiyi aure ya aje iyali ba yan uwa kuma suna amfana dashi sosai. A lalai akwai abin duniya ko da a yanzune balle da can baya da abin duniya yake madara Allah dai ya kyauta wanan shigowan naka yasa hankalin mu ya dan kwanta yanzu ta fada tana kallon wayan ta miscall din diyar ta baby ta gani. Kai wai naga tun dazun sai wani cicika kake kana batsewa ga banza wani abin akai maka kome ta tsaya a kanshi tana kallon shi. Wa zai mai wani abu a yanzu mahaifin shi dake shigowa ya fada ya samu wuri ya kai zaune yana kallon iyalan nasa ya mike kafafuwan shi saman dan karamin table din falon. Hjy hari ta kara fadin tun dazun ko abunci yaki yaci tun dawowan mu daga kotun nan sai lokacin ya dago yana fadin mommy na fada maki ba komai bane. Kawai dai bana jin cin komai ne a yanzu idan naji zancine ai murmushi mahaifin nasa ya kara sakewa yana fadin . Kaga zama gwauro ke nan uwarka na fadin kayi aure kana fadin ba yanzu sai yaushe zaka kawo mata tayi ma auren da take so. Fada mashi dai da ace yana da matane yanzu ina zanga ma wanan fushin nasa yana can yanawa matarshi shi kadaiyi wa kanka fada tun ba a fara kiran ka da tsoho ba. Ka duba fa modibbo yanzu yaran shi biyu daya haifa ko banza dai ai a kallesu ace ga iyalin modibbo nan ko ? Kai mommy ana zance sai ki dauko zancen wanan yaron mai fadin ran tsiya kina hadawa da mutum sai ya dauka koshi din sa,an mutum ne ai ni bana son zancem yaron nan sam kamar yadda shima bai son nawa. Na dai fada ma ku daina haka tun muna raye yau irin wanan abin kunyar da aka tafka a kotu ina dadin shi yan uwa zariya daya saboda hassada sun kashe dan uwan su akan dukiyan banza. Irin wanan da kuke fara nunawa shine ke girma har yazo ya zama babban magana a cikin zukata mudai kun gan mu da yan uwa sai sam barka a tsakanin mu. Mikewa yayi tsam ya fice daga falon yana masu saida safe ya nufi part din shi kai tsaye ya barsu falon suna binshi da kallo. Danki aure yake so ke kuma kinki kwantar da hankalin ki ki gano hakan ki kula dashi tun lokacin da akai zancen auren yarinyar nan a kotu yake wanan fushin haka . Da sauri ta juyo inda mijin nata yake zaune tana fadin wace yarinya wai kake zance yace wacan yar taki dai ta lagos din da kika sani da alama yana son yarinyar nan saidai fadane baiyi ba kawai . Wani irin abu taji ya soki zuciyarta lokacu guda tace da mijin nata don Allah Alh mu bar wanan zancen a nan kada wanan zancen ma ya fita waje. Yace cikin daga kafadan shi zakice na fada wata rana amma ki bincike shi ki gani zakiji da kunnuwan ki kuwa wanan maganan. Kai ina sam wallahi hakan ba zai taba yuyu ba wallahi wace wanan yar din da idanun ta suke a bude haka sam wallahi. Amma dai ai yar dan uwan kice ita din idan yace ita din yake so zaki hana ne ko me don kin san dai yace ba tsarun shi bane a hadashi da mace sai wace ya gani yace yana so. Ti badai wanan din da bata samu tarbiyan daya dace ba don Allah Alh mu bar wanan zancen don har naji zuciyana ya baci sosai yace kidaiyi tunane kada ki dawo kina jin kunya wata rana. ZAINAB IDRIS MAKAWA ANA DARA GA , , , , , , , , 8️⃣4️⃣ BY, , , , , , , , , , , , ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , , , , , , , , BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AL MUTAQDIR, , , , , , , , , ONLINE PAID NOVEL YAR UWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA BA TARE DA HAKKIN KOWA BA DON BIYA KI TURA DARI BIYAR 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK 08036959257 ALLAH SARKI AI RAINA BAYA BACI YANZU DON KIN FITAR DON NASAN AKWAI RANAN HADUWA SEE U👋👋👋👋 Wa iyazu billahi marubuta muna halaka kan mu akan wasu don kawai neman suna sai mu shagala da yin fasadi da badala wurin rubuta labari. Shin yar uwa kina tuna cewa duk kallama daya sai mun tsaya masa a cikin ramin mu inda ba mai gyara ko wani dadin baki. Saboda zon zuciya kin zauna kina batsa kin shagala da rudin shedan hakan bashi zaisa a soki ba ko ki samu daukaka shi so da daukaka daga Allah yake. Kin fito kina shiga hakkin al,umma da yiwa shedan kanfen tambayi masu auren. Ko a tsakanin su da mazajen su akwai hijjabi akan wanan baiwan da Allah ya saka a tsakanin jinsi biyu na mace da namiji. Shi Alkalami fa yafi takobi kaifi wurin isar da sako ga alu,mma tundai a wanan zamanin da muke ciki Don haka nake kiran yan uwana marubuta da muryan musulunci yaku yan uwa marubuta mu hankalta da abinda muke rubutawa a cikin labarin mu yin batsa bashine ke jawo daukaka a sanka ba . Idan bamu gyara ba kada mu bata al,umman annabi a sanadin alkalamin mu yan uwa idan na fadi ba daidai ba don Allah ku yafe min amma a kulla yan uwa wallahi abin yana son ya wuce musali mufa ba yahudawa bane da ke fayece sirin boye marubuci kuma da gyara aka sanshi cikin al,umma. Kwance nake shiru na kurawa rufin dakina ido ba abinda ke min yawo a yanzu sai kalamin ogan mu gasu yaya Abubakar da kuma zancen gwaggo hari a gaban mu. Juyawa nayi don zuciyana da naji yana mun zafi sosai a lokaci daya a gaskiya kaina ya daure sai tambayan kaina nakeyi nan din ma wasan yake so nayiwa yan uwana da hakan ko me ? Idan har wasane wa zamuyiwa wasan a nan kuma idan can muyiwa mahaifiyar shi don wani dalili nasa dayace in taimaka mashi a wuce wurin. Jin yadda ruwan sama ke sauka a lokacin yasa na ja abin rufa don nasan sanyi za ayi a lokacin na lumshe idona daga haka har barci ya daukeni ban falkaba sai safe. Washe gari ma hakana tashi da kyat na samu na fito falo don zazzabin dake damuna a lokacin hakana fito na karya kamar yadda umma ta bukaci in fito din in karya tunda banci wani abu tun tafiyan mu. Bayan na samu na dan sha ruwan tea din dana hada da kyar na samu na kurbe shi duk da rashin yawan shi kuwa. Na koma na jingina jikina a kujera ina dan kada kafa a hankali ummace ta fito daga dakin ta da sako zata ba kanin Abdul da yanzu shine karfin zaman shagon namu sosai. Don umma bata da issashen lokacin zama kamar da yanzu yasa ta barshi da shagon shi yana zama yana dan samu shima tunda yana da amana. Ta dawo ta zauna ta kalli kofin dana sha shayin a cikin sa kafin tace dani wanan din ya isheki ke nan na kada kai ta zauna take fadin dazun baffan ku sun kirani. Jin hakan yasa na dago kai da sauri ina kallon ta tace sun kirani kan wai ana neman bellin su iyalan su Nuhu da sauran tun jiya sun damesu da suna masu zariya a gida. Amma nace dasu duk abinda sukayi mai kyaune ai suna da daman yanke hukunci a yanzu don suma dan uwansu aka kashe yakin ba namu bane mu kadai ai. Hakan yayi umma a yanzu ko ance a kashesu ko a kwace dukiyoyin su a mayar muna sun dai da sunriga sun cuce mu ko don haka Allah ne kawai zai isar muna a kansu dama bukatana shine. Kowa yasan muna raye asan abinda su suka aikata kuma kowa ya bar maki zargi kan abinda mutane basu sani ba. Don idan ba hakan mukayi ba ba ranan da wanan zargin na mijin ki ya mutu kin shiga duniya da yarki don wasu cewa suke muna barikancin mune a nan. Hawaye naga yana zuba a idon ta nima din hawaye nake sakewa zuwa lokacin umma tace mutum akawai daukan wa kanshi zunubi. Kai zakaga mutum daga sama yayi abu wanda ba halin shi bane amma sai ka dauko wani zargi ka dora mai kana zargin shi dashi. Allah ne shedana tun ranan dana bar gida har zuwa wanan lokacin ban taba aikata wani abin assha ba da zai zubar muna da kimar mu a idon jama, a. Don haka shi yasan dalilin yin hakan a garemu nidai na shigo lagos ne don tserar da rayuwan mu daga cutarwan su ban kuma taba kai raina da cewa zan yi wani abinda ya kaucewa mahaliccina ba. Na kuma san wanan abin da kikayi maikyaune don haka kawai zamuyi nasaban mu ya dawo garemu lokaci guda. Shiyasa banyi wani yun kurin hanaki hakan ba daidao da rana daya don nasan irin tarbiyan dana tayar dake a cikin sa . Idan iyayye suna da yakini akan diyan su a zamanin nan sai mutane su dauka ko diyan sun fi karfin iyayyen ne suke kyalesu suna abinda sukaga dama har sai kaji ana fadin wani ko wance yafi karfin iyayyen shi ai . Abin ba haka bane yakine ne wani lokaci da iyayyen ke dashi kan tarbiyan da suka ba yaro idan ba,ayi dace bane sai kaddara wani lokaci ya afkawa dan don yawan bakin dan Adam akan yaro baki mugun dafine sosai ga dan Adam, . Addu,an mu ga yaya a yanzu shine neman kariya daga idon hama, a ko yaushe bawai neman abin duniya ba kawai ina ma,anan yin addua ga abin duniya kazo kuma abin ya zamo ma fitina a karshe. Umma na kalla nace umma abinda baki sani ba shine tunda na taso ba a taba fada min magana mai zafi ba irin wanda Alaja mahaifiyar ogan mu ta fada min na cewa wai ni din ba mai nasaba bace yar mace ce ni. Murmushi naga umma tayi a fuskan ta tana fadin ban tsamani ta kaiki nasaba ko tafiki nasaba a rayuwa don yanzu ita kanta kawai tasani bata san abinda Allah zaiyi maki ke nan gaba ba. Ban taba jin son kowa ba a zuciyana tun ina karama balle zancen da Asabe ta tabayi a gabana lokacin muna semi boda wanan maganan ya tsaya min a rai yana a cikin dalilaina na jajircewa a rayuwana. Wayan umma ne ya kara kara a lokacin ta dauka ya Abubakar ne a layin bayan sun gaisa naji tana tambayan shi baida lafiya ne taji muryan shi wani iri a cikin wani yanayi? Yake fadin kawai dan zazzabi nake fama dashi tun jiya amma da sauki sosai sai ya fara mata zancen da yake son suyi da ita karshe yace ta dan dakance shi anjima zai kirata ai. Ganin har kwana biyu bai kira ba yasa ranan muka tuno dashi nake fadin umma ai kamata yayi ki kirashi ki masa ya jikin nasa da kika jishi shiru. Ina da niyar hakan a raina sai dai Allah bai ban ikon kiran nasa ba tana magana ta daga waya ta kirashi abin mamaki wayar shi a hannun nazafa yake ranan don muryan tane radau a wayan. Hakan yasa na daina abin da nakeyi na dago kai ina kallon inda umma take zaune don tana dauka ba sallama sai cewa tayi waye wanan kuma ? Ke wacece na fada daga inda nake kutumar uba kikira min miji ki koma tambayan ni wacece au idan ke mijin kine ni kuma brother dinane and so what ko wa kike gareshi don ban sanki a cikin dangin sa ba. Kece zakifi kowa shedani kuwa don Allah malama ki bashi wayan kinji na fada a hasale ni kuma kara haukatata nakeyi ko banza muna da azzaza da ita da dadewa dama. Daga inda yake kwance ya bude idon shi yana fadi da kyar ke ban wayana nan ita kuma tana kokarun surfa min zagin cin mutunci shi kuma sai fadin yake da hankalin ki kuwa kikewa yar uwan ki wanan zagin haka nazifa ? Yar uwata ta ina me muka hada da ita kaima maye hadin ka da sune wai don ban gane me haka ke nufi ba wai kai kadaine a cikin dangi halan da komai sai kai ? Ganin sunan ummane a screen din wayan yasa yace umma zan kira dan anjima kadan to yana asibiti uwar bin didigi sai a barshi ya huta. Wani iri naji har cikin raina umma kuma na fadin don me zaki biye mata kuyi haka wanan ai shi zaku tayarwa hankali shida baida lafiya. Umma wanan matar ko tana da hankali kuwa daidai baki biye mata ba kunyi wanan don shi kike gani bana son kiran shi idan bashi ya kiramu ba son gujewa irin hakan. Zanko dinga kiran shi sai tayi abinda zatayi din idan na kira na fada ina haran gefe kamar itace a tsaye wurin. Kinji wai asibiti ciwo ya kaishi gashi taki bari muji meke damun shi saboda bakar kishi irin nata na hauka rai bace umma ta kalleni tana fadin a, a banga laifinta ba akan mijinta take hakan ai. Nikan kodana ce zan kira tun wanan ranan bankara komawa takan wayan shi ba kuma amma nakanji suna waya da umma tana masa ya jikin ? Mun shirya zamuje kauyen su umma amma sai mun tsaya kaduna mun gaida ya Abubakar dan kafin mu dawo sai lokacin shiga kotun mu hakan zaisa yaga badon shi kanshi muka zo ba. Mun shirya tafiyan mun isa kaduna a cikin dare don haka saida muka kwana washegari muka nufi gida daddy duk da bamu san irin taron da zamu samu ba a lokacin wurin su. Sam nika bamji komai a raina ba don wanan ne karo na biyu da zan shiga gidan daddy kuma da ranan da ya Abubakar yazo damu daga lagos daga baya aka mayar damu kan wani dalili dabamu sani ba a lokacin . Sai yau kuma da zan shiga don kaina ba kawoni wani yayi ba don ko yanzun din kan bin umurnin umma ce da tace a nunawa ya Abubakar bamu rike da mahaifin shi tunda ita umma tasan komai. Karma yadda mukasani gidan nan kamar yadda muka sanshi a baya komai ba a canza mai ba in kin debe fenti shima din nasan lokacin bukin baby ne akayi shi. Tun kan mu shigo muke jin muryan su a falon gidan babba suna dariya a daidai lokacin da mommy ke fadin kai hari wallahi baki da dama wallahi. Wallahi Addah haka kawai ai gara in fada mai gaskiya kan wata wai Sahiba can daga sama dama ace mahaifinta yana raye ne har yanzu . Ko kuma ta tashi a nan cikin mune kinga ka shedi tarbiyan yaro amma ni da nake son ya banbaro min yar gidan wani babban kusa zai kawo min zancen wata wai Sahiba can ana zaune kalau ? Abin ko dadin ji babu fa yaro ya gigice min shiko mahaifin shi har da son mara masa baya akan karya wai meye ga Sahiba din ? Mommy tace Allah dai ya sawake ai hanyar jirgi dabam ta mota daban dariya suka kara kwashewa dashi mommy na fadin aini tuni na kakabe shi da wanan zancen haukan modibbo zai kalli idona yace min shifa daya sani da sahiba ya aura tun farko. Dafani naji umma tayi a bayana ta kada min kai sai na dan hade bakin cikin daya tokaremin makoshi lokaci guda. A take nayi sallama daidai da shigowana falon nasu umma suna bayana har lokacin suka juyo a razane suna amsa muna a cikin rikicewa dukkan su daka gansu kasan a rude suke da ganin mu alokacin gidan. Hjy mairo wai kune a tafe haka suna mikewa tsaye lokaci guda, mune fa umma ta fada har da fadin ikon Allah yanzun nan kuka saukane ? A,a anan dai muka kwana jiya mukazo da dare zamu yola ne muka ratso nan mu gaida modibbo da jikin sa. Ayyah aiko kinyi zumunci hjy hari ta fada tana wani dan kame kame a, a Ammar kin koyi waya da mutumin naka kuwa ? Yace No a cikin turanci don shi yadda nake dan jin hausan baya ji sam sai guda guda yakan fada kuma ba daidai ba . Zaune dai nake a inda na zauna sai mamakin su nakeyi don abin nasu ya kara kulle min kaina sosai lokaci daya. Yanzu kan nasan tabbas wa yan nan mutanen ba zasu taba son mu ba kenan a rayuwan su gwaggo hari matar da muke ganin mutuncin ta sosai. Don ta nuna muna so har da kauna a fili yanzu take fadan wanan maganan haka a kan mu mara dadin ji can da sauraro ga kunnuwan masu ji. Ke ku fito ga Sahiba mommy ta fada a cikin waya nasan da yaran ta take wanan wayan lokacin ba dauki lokaci ba kuwa saiga Faiza da gudunta ta fito. Muka rungume juna da ita ana yaushe rabo duk da raina yana bace a lokacin amma ganin Faiza din sai na dan sake jikina da ita. Yan jan ajin saida suka dauki lokaci suka fito sun fito da fara,an su da farko amma lokaci daya fuskansu ya murtuke. Don sun tsorata sosai da ganina wani irin kyau da dress cikin shiga ta alfarma irin namu na manyan yan matan lagos. Su kansu yanayina kawai ya nuna masu a yanzu ba ajin su nake ba mun gaisa dasu a cikin girmamawa kamar yadda aka saba a can baya ban nuna masu komai a fuska ba suka samu wuri suka zauna. Faiza ke fadin kwanaki kikace zaki dawo baki dawo ba Sahiba nace sorry my dear wallahi tafiyace ta kamani zuwa england daga can na wuce dubai mukayi kwanaki. Na fadi hakan ne kuma da gangan a gaban su mommy din da diyan ta kice dai har fita kikeyi yanzu abin dai ko sauku babu ashe. Nace kin san yanayin aikin namu haka yake muna shiga kasashe da dama ko yaushe da wuya ki sameni a lagos yanzu ai. Dan guntun tsoki Nabila taja daga baya dukda taki sake sautin shi amma nasan ko umma taji wanan sautin na dago ina fadin Anty Amarya fa ? Oh sun fita wallahi dasu Fatima dazun ana buki walima a gidan babban yayarta duk a cikin harshen turanci muke magana. Diban lokaci nayi ina fadin umma mu tafi a cikin yarbanci gwaggo hari harda fadin ba zaku tsaya akawo maku abin sha ba yanzu ta aika yar aikinsu ciki ai No abarshi kawai zamu tafi jirgin karfe biyu zamu bi zuwa yola yau . Amma muna son don Allah idan ba damuwa Faiza ta nuna muna gidan Abubakar din mu je can kallon juna sukayi don ita kanta gwaggo hari rikicin shi da matar shine ya kawo ta gidan. Eh to ko yana gidama yanzu waya sani eh zamu daije gidan mu gaisa dasu koda baya nan idan tazo za a fada mai mun gaida ku ai umma ta fada tana mikewa. Tare da fadin idan Alh yazo muna gaidashi suka amsa kamar ba komai a zuciyan su gaba dayan su kuma suka rakamu zuwa waje din ganin kwan koda me mukazo. Rudewa sukayi lokacin da sukai arba da rantsatsiyar motan oga da muka shigo zuwa gidan nasu wanda nice kuma ke ja bamuzo da driver ba. Umma ce tabawa su Nabila kudi har suna musawa tace bazan baku alher ku karba ba Nabila ko kuma kuna cikin masu zargin muna aikata wani abinda bai dace bane a can. Da saur har suna hada baki wurin cewa yaran nasu su karba nidai na bude motar na zauna sai lokacin na kalli Nabila nace anty ya aiki kuma ? Kallon juna sukayi kafin suyi magana Faiza tace cab aiki a yanzu ana dai nemane ai kaina na dan girgiza daga cikin motar nace ko zaku iya aiki a company nan garin. Yanzu kan naga fuskan su sosai don washewa sukayi lokaci guda zamu fadawa daddy suka fada nace OK idan kun shirya saiku hada takardun ku zan tura akarba. Daga haka Faiza ta shiga muka dauki hanyar gidan yaya Abubakar muka barsu a tsaye suna bin mu da kallon mamaki da al,ajabi. Aiki fa yarinyar na ta fada gwaggo hari ta fadi tana sauke ajiyan zuciya nima wanan zancen barazanan ai nake mamaki yanzu. Ku hada takardun naku koda yaya baisani ba idan yayi magana kuce dashi ninace ku bata muka karyan arzikin nata inda ya tsaya wanan kuma wani sabon sallo wai asan ita watace komai ? Tasan cewa daddy ba zai yarda da wanan zancen ba yasa ta fadi hakana amma ai zamuga karyan ta a lokacin muna kwanan gidan ya Abubakae kiran su ya shigo ta wayan gwaggo hari take fadin. Zancen aikin yaran nan a ina zasu sameki da takardan nasu ok za a aiko a karba ranan Monday din nan mai zuwa sai su fara fita . Mun gama wayan ban tsaya wani abuba na kira malam bello na fada mai komai yace an gama har inda nake son a jemin su koba komai nayi hakane mu rama alherin dan uwan su garemu. Suna ko gida ko awa daya ba akai ba aka sallama anzo karban takardun su da komai nasu ga opper din aikin guda uku an kawo masu har albashin da za a dunga biyan su a company sugar din dana filawa. Waya mommy ta dauka ta kira number gwaggo hari da imani ya kasheta tana dauka take fadin me kika samu kuma ko daki ban shiga ba fa yanzu na iso gidan. Bari ke dai yar uwa abin mamaki zai kasheni yau wallahi wai kin san yarinyar nan da gaske takeyi an kawowa yaran nan takardan aikin su har gida da albashi su da komai a wata. Ke don Allah ki daina wanan zancem zolayan ina Sahiba taga wanan daman mustaphan ta dake zaune ya dago jin an ambaci sunan sahiba . Mommy tace wallahi Allah zancen wasa ya wuce ga takardan a hannuna imani ya cikani nan zaune hari. Wai ya akayi wanan yar ta samu wanan daman hakane waya tsaya mata take wanan iskancin da take so hakane . Addah waiko kin san kila irin wanan baiwan na mahaifinta ta kwaso don in baki manta ba shima haka yake fa duk abinda ya dafa sai yayi albarka sosai wallahi. To yarshi shita gado a yanzu ke nan kome don kaina ni ya daure ga baki daya don wallahi, , , , sai taji ta kashe wayan ashe Anty Amarya ce da yaranta suka dawo a lokacin. Lafiya dai na ganku haka Anty Amarya ta tambaya saida ta nisa take fadin aiki yaran nan suka samu yau aiki kuma a ina aiki ya fito haka tsawon wanan lokacin da ake neman sa. Wallahi ikon Allah daine idan rabon ka ya rantse sai maishi Sahiba ce tazo gidan nan itace daga tambaya sai ga opper mun gani har gida na company tauraro. Sahiba fa a gidan nan tana ina ta sake tambaya tana dan waige waige sun tafi ai suna gidan modibbo dama shi suka zo gayarwa. Mama don Allah mu bita can mu ganta Fatima data dan fara tasawa yanzu ta fada tace kuje ku gani ko zaku samesu a can din. Yana da wuya su sameta don sauri sukeyi tace yau zasu tafi yola suyi sati daya a can jirgin karfe biyu zasu bi. Yaran suka mike da sauri suka fita har sun manta su karbi kudin Napep saida uwar ta kirasu ta basu kudin suka kama hanya suna Allah Allah su samenu a can. ZAINAB IDRIS MAKAWA ANA DARA GA , , , , , , , , 8️⃣5️⃣ BY, , , , , , , , , , , , ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , , , , , , , , BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AL MUQADDIM, , , , , , , , , ONLINE PAID NOVEL YAR UWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA BA TARE DA HAKKIN KOWA BA DON BIYA KI TURA DARI BIYAR 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK 08036959257 ALLAH SARKI AI RAINA BAYA BACI YANZU DON KIN FITAR DON NASAN AKWAI RANAN HADUWA SEE U👋👋👋👋 Haba mami kin ko san abinda kike fada ayanzu akan yar marainiyar Allah yarinyar dako lafiya bata dashi na kula maza har kike kokarin aibanta ta da irin wanan kalamin. Me kaji na fada akanta yanzu na aubantawa gaskiya kawai na fasa game da ita shine kuma wani abin aibanta don kawai baku son ana fadin gaskiya idan an ganta. Mami barun fada maki wani abinda baki sani ba akan yarinyar nan yau wallahi mami koda kikaga ina tallafawa rayuwan sahiba da suka fada maki tun kafin hakan . Sahibace ta ceci rayuwana ta wankeni daga mugun zargin da ake min har gaskiya yanzo ya baiyana suka daina harata da sun kamani a wanan lokacin wallahi daurin rai da rai zasuyi min a lokacin. Alh mahammoud da kanshi yake duke yana karatun jarida saidai yana jin su abinda ke wakana a tsakanin su yace. Au itace yarinyar da ka fada min ke nan ashe data boye sani ka ta boye akan bata taba ganin fuskan kabama din da itama suke zargin ta. Yace Daddy wallahi itace tana karama sosai a lokacin ko yanzu ma ai karaman yarinyace girman daine Allah ya bata a cikin lokaci. Kafin ya juya wurin gwaggo hari din da tayi suman tsaye tana sauraren makusantan nata lokaci guda kan bayanin da bata taba sani ko jiba sai yau data tsunci zancen a bakunan su. The boy kai ta nunashi da yatsa yace wallahi mami nafi karfin shekara uku muna wanan case dasu modibbo da kike gani kike tambayan shi abindake hadamu wanan matsalan ne ya kafe akan sai ya kamani ya danka a hannun hukuman su an kaini kasan biyu da suke zargin mu. Labarin komai ya bata har zuwa wanke shin da nayi da fada mai wanda sukai mashi sherin ya kuma bincika har aka gano gaskiyan hakan gareshi. Yanzu ga irn sakayan da take binku dashi ko ranan ina jinku da Addah a gidan kuna mata irin kazafin nan ke ga naki itace silar fitar muna dashi cikin wahala. Yanzu kuma yaran Addah din duka uku ta sanadin ta sun samu wurin da zasu dogara da rayuwan su. Irin wanan halin da kuke nunawa shine yaci yan uwan ku a yanzu dama shi sherri ai dan aikene don komai dadewa watarana sai ya dawo kan maishi yanzu me gari ya waya garesu don Allah ? Don shi Nuhu ya dauka arzikin kota halin kaka yin sa akeyi a zauna lafiya baisan tarin nauyi da wahalan daya daukarwa kanshi ba ga hakan . Idan baku daina hakan ba wanan halin karshe a kanku zai dawo har ita Addah dake da diya mata har uku a gabanta dakema mai da daya tilo ki jawa kan ki fitina a sanadin hassada irin na dan Adam. Shiru tayi na dan lokaci tana kallon su kafin ta kai hannu ta share zufan dake karyo mata a goshin ta duk ko da sanyin Ac daya karade falon a lokacin. Sahiba in banda wayau da suke mata suna amfana da basiranta da Allah ya bata ba wani hakalan iskanci ko shashanci a tsakanin ta da kowa idan tace eh ga mutum ita sheke nan a gurin ta eh din Wai modibbone yaso ya kamaka daurin kuma daurin rai da rai dama ashe har akayi hakan ban sani ba ashe mami ta fada cikin mamaki ? Kallonta dan nata yayi yana fadin wanan kuma kada ki zarge shi don aikin shi yakeyi shi, kowa kuma yasan haka ka,idan aikin su yake tunfarko. A kan me zata zargeshi ma mijin nata ya fada shiba rantsuwa yayi akan aikin shi ba cewa ko mahaifin shi yai abu zai fada . Faizace a gaba muna binta a baya tayi sallama a bakin falon nasu da kamshin girgi da yar aikin gidan keyi a lokacin ya karde gidan tun daga waje. Waya takeyi yarsadan wanda hakan bai bata daman karba sallaman mu ba lokacin sai dai bin mu da tayi da kallo muna shigowa a wanan lokacin ne kuma shima ya tsaya da motan shi kofan gidan. Yaran suna wasan su a falon koda muka shigo babban ce ta dago kai ta kalle mu ta sheda mu sai tayo gun umma tana muna oyoyo kafin ta sake umma ta dawo gareni har Ammar. Wai amma kukan kunci da fari da har yar nan ta yarda daku haka kamar ta sanku dama ai ba wanda ya isa taje wajen shi banda mamanta da baban ta. Wayan ta aje tana cewa yar ke maryam jimun yarinya daga ganin baki sai kiyo kansu da gudu haka kamar ta san su tana zarewa yarinyar ido a daidai lokacin da karamar tazo ta fada jikin umma dake zaune duk da ba,a bamu wajen zama ba munyiwa kan mu matsugunni mu. Su waye wa yan nan kuma ta fada tana kallon faiza don son jin bayanin mu bakine sun zo gaida yayane da jikin shi. A, a umma so you're on the way ? I don't know that you people a coming yanzun nan na fita zan tafi office din mu wani aiki dama. Kafin ya juya akan mu yana fadin Sahiba you are welcome Yusuf how far now ta sake juyowa da kyau ta zuba min ido don jin sunan daya ambata a lokacin. Wai wanan din ce Sahiba dama ta fada tana watso min wani kallon tsana da nima na bita dashi jin ta ambaci sunana ya jiki mukai mashi kafin ya juya yana fadin ina matar nan mai aiki sa a kawo masu abin sha mana yana kallon matar nasa. Wace tayi kamar bata jishi ba lokacin umma tace a, a abarshi dai wallahi a koshe muke mu kan ba kishi ba yunwa an gode ta fada tana murmushi a fuskanta tare da dan shafan yarsu data kwanta mata a jiki. Uban yace kinga mama ko Aimana sai umma tace ashe bata manta damu gaba dayan su sun shedamu hakan ya bani mamaki sosai wallahi. Wani kallon mamaki takewa kowa na falon na yadda muka san yaran nata haka bata da labarin komai ita shine ya daure mata kai hakan. Muna cikin magana ya bamu labarin rashin lafiyan nasa yaran anty Amarya suka shigo gidan da sallaman su ai nan na manta da ita muka buge da hira sosai dasu kamar a baya. Mikewa mukayi zuwa waje don sunce suna son muyi hotuna a tare dasu kafin in tafi har umma suka fito suka sakemu a wajen hakan ya hana muyi sallama da ita har muka tafi bayan nayiwa su Fatiman har Faiza alheri daga jakkana muka kuma sauke tsaraban da mukazowa yaran ya modibbo din dashi. Mun isa Yola kamar yadda aka shirya cewa zasu zo su taremu daga gidan babban wan su umma dake cikin garin yola yanzu zaune. A wanan ranan na sheda ashe muna da yan uwa raye a duniya irin so da kaunan da suka nunawa ganin mu don mun samu gidan nasa a cike da yan uwa da sukaji zuwan mu sukazo don ganin umma din damu. Nan kuma aka zauna ana jajanta mata abinda ya faru tare da adduan samun nasara a kansu sun dai sha tsina da mugun fata a wurin dangin umma din. Kwanan mu uku a yola cikin jin dadi da nuna muna karamci muka nufi kauyen su umma din kai tsaye a ruggan su mukaya da zango . Nan ma munga kauna da so a wurin su sosai anan na sheda idan asalin kyaumu ya fito duk zaka gansu zubin daya dogaye farare masu kyau da zubin filanin farko dasu har saika rantse su din wasu yare ne na waje. Saukin abin dai nama ne don haka ina cin abinda aka sarafa muna naman dashi ba wani kyama amma duk abinda ya danganci abin ruwane shi ko menene kuwa ko kamshin naji zan bar wurin idan ba Allah ya gyara ba har amai nakan yi wani lokaci. Idanuwana sukan juye su canza kalla zuwa ja jajir kaina ya dinga ciwo tsawon wani lokaci wanan yasa a yanzu dana fara wayau nake kiyayyewa bana yarda da abinda zai jawo min matsala kuma. Saidai ashe wai haka yan uwan mu na gefen umma dana gefen mahaifiyat mahaifina suke dayawa din su suma basa cin abin ruwa saidai ba duka ba suma don akwai irin su umma da kan danci itama din ba damun ta yayi ba sosai. Tsaraba sosai mukaje dashi kwanan mu biyu a wurin su kuma muka kara gaba zuwa wajen dangin mahaifin mu ta fanin mahaifiyar shi. Naji dadin wanan tafiyan na kuma san muna da gata ashe a duniya mmuma kuma muna da yan uwa na jini dake matukar son mu a duniya. Nakan ji manyan su na fadin kamata sak da wace ta haifi mahaifiyar Abban mu da tsayina da komai wai har yatsun kafa nata ne na kwaso suke fadi. Ana gobe zamu shiga kotu muka koma laduna badon mun so rabuwa dasu ba suma din hakan tare da muna alkawarin wasun su zasuzo har idan muke su gane mu suma. Tunda muka shiga kaduna barci nakeyi ban falka ba sai yamma lis don gajiya da kewan yan uwa ina faman rayawa a raina cewa yanzu kan naga inda yan uwa suke masu son mu. Bayan sallan magariba ne muna zaune falon gidan wayan umma yai kara ya Abubakarne ya kirata yana tambaya ko mjn dawo ko muna yola din. Muna cikin kaduna dazun nan da yamma muka dawo umma ta bashi amsa yayi muna sannu da zuwa yake fadin. Gobe insha Allahu za a shiga kotu daddy ma yana nan ya dawo sati daya ke nan watau tun tafiyan mu yola ya dawo shima kasan. Washe gari mun dan so mu makara a lokacin don zuwan kotu har mutane sun dan fara kus kus akan rashin halarta mu din sai gamu. Hakkuri lauyan mu ya bada aka fara shari,a yadda ya dace ayi din inda alkali ya nemi daddy daya ba umurni dawowa kasan don tuhuman da ake masa yazo ya kare kan shi a kotun. Dadi ya fito cikin kamala da shiga na jallabiya mai ruwan madara sai yar hular dara ja akanshi daya saka don kare mutuncin shi duk wanda ke zaune ya bishi da kallo. Kamar yadda akewa kowa tambaya a kotun haka akaiwa daddy din shima tambayan bayan an karanto mashi laifin da ake tuhumar su dashi din. Ya dan girgiza kai na dan lokaci saida ya danyi dan shiru irin na manya kafin ya dago kanshi yana fadin zan bayar da sheda akan abindana sani iya gwargwado in Allah ya yarda. Kamar yadda kowa ya sani marigayin abokinane sosai kuma kanina aminina haka muka taso dashi a gidan mu yai rabin rayuwan shi kaf kafin ni na fara aiki shi kuma saboda kwazon shi gwautin jaha a lokacin ta turashi karatu waje. Bayan ya kammala karatun kuma yazo ya samu aiki a can sai rayuwan shi kancan kaf ya koma can waje saidai kaf din mu yan family din mu dani yafi yarda . Don haka yana turo kudi nan ina masa tanadi kamar yadda kowa ya samu akeyi har wani tafiya da yayi ya samo wasu mahaukatan kudi ya turo na sai mai filaye manya kudu uku masu girma. Wanan ne abinda ya fara jawo muna matsala a tsakanin mu nidashi don yace zai yi manyan gidajen mai irin na waje na nuna mashi ba haka ba komai a sannu ake binsa. Duba ga yadda yake matashi a lokacin ko aure baiyi ba tun daga wanan lokacin ya fita zancen filin kuma bai kara min maganan shi ba har sai bayan yayi aure har matar ta haihune yayi wani fita sai gashi wanan fitan ya dawo da mahaukacin kudi irin na wancan shekarun. Sai a lokacin ne ya samu waiwayan filayen shi ni kuma duba ga yadda muke dashi lokacin har na taba filin nayi amfani dashi wurin nawa bukatan. Na nuna mashi lokacin kwara daya ya rage a cikin filayen kuma shine mafi girman aka a ciki take ya nuna min nacin ranshi ya dai wuce a hasale abinda bai taba min ba. Nima nasan ban kyauta ba gaskiya sai hakan ya dan fara jawo matsala a tsakanin mu dashi ya daina kulani ya daina dai yi dani kamar farko. Wata rana ina maiduguri nazo weekend da yamma yan uwan haihuwan shi su Nuhu suka sameni bayan mun gaisane suke fada min ai sunzone su kara ji a bakina wai ashe Sambo shike da wanan katon filin na hanyan fita gari nace eh ai wanan bashi kadai bane ma akwai wasu filayen bayan wanan kuma manya ne suma . Nan muka buge da fira dasu abinka da dan uwa nan nake ta labarta masu irin dukiyan daya samu da abubuwan da yake dashi. Allah ya gani ban fada don wani abu ba lokacin amma bayan kwana biyu sai ga Sambo din yazo min rai bace yana fadin bai taba zaton zan masa hakan ba. Don me zai bani amana kuma inci inje ina fadan duk wani siri nasa ga jama, a a lokacin dai dukkan mu kurciya yaci mu don nan muka rabu baram baram dashi kowa na fadawa dan uwa bakar magana duk irin hakkurin shi ranan bai raga min ba. Bayan munyi hakan dashine da kwana biyu muka wayi gari an kashe shi saidai amatsayina na dan sanda binciken farko na gano cewa yan uwane suka halakashi lokacin. Nayi yunkurin yin wani abu sai ga batar matan shi abinda ya kara daga hankalin kowa na ahalin mu ke nan kuma . Shiru har wata uku babu labarin ta sai ranan sukazo suka sameni da zancen tunda Sambo ya rasu iyalin shi kuma sun bata abinda zaifi a raba dukiyan shi kawai tunda dukiya bai azuwa tunda ba, a san ranan dawowan iyalin shi kaduna. Haka yasa na kara zargin su na kirasu a sirce nayi masu magana sai suka so su mussanta hakan karshe dai da sukaga na gane gaskiya duk da basu fito filin sun amsa laifin su ba lokacin. Sai cewa sukayi in ma son dukiyan shi dake hannunane banson in bayar in tafi da dukiyan in rike amma sai na basu wanan filin ko kuma dukkan mu a tuhumeni nima. Inda ni kuma naga hakan ba karamin banan suna bane a wurina yasa naja bakina nayi shiru a lokacin tare da fatan duk lokacin da wanan case din zai taso ya kasance ina raye a yishi . Don a yadda na kula Nuhu dai gashi nan tsaye idan bai ci arzikin nan na Sambo ba zai iya samun matsala lokacin don yadda yabi ya zare kan abinda dan uwan nasu ya bari kuma a yanzu bashi da wanda zaici sai su din don diya mace ce ya bari a duniya a zaton mu. Sai dai duk da rufe wanan case lokaci zuwa lokaci nakan tuno da wanan nauyin dake saman kan mu don haka na samu lokaci na ware daga cikin dukiyana iya abinda nake ganin nasune a wurina na debe masu shi. Amma kuma daga baya sai kuma na fara wasu harkala da kudin sai dai ban yarda na hadasu da nawa ba har lokacin . Kwatsam wata rana saiga iyalan marigayin sun sauka a gidana dana daya gano su a lagos yazo dasu. Nayi iya kokarina wajen yin shawara da zuciyana in baiyana din na boyesu ga kowa a lokacin suma kuma din na hanesu da baiyana kansu ga kowa. Nayi kokari a lokacin naga na hada kan dukiyan su in basu saidai na kasa hakan a wurina gashi lokacin na fahinci su Alh nuhu kamar zasu gane su kashe su ni kuma bazan so in zama sanadin hakan a garesu ba lokacin. Yasa na umurci dana da na shirya wa plan cewa ya kwashesu ya mayar can lagos din har zuwa lokacin dani zan shirya fitar masu da dukiyan su in danka masu a hannun su . Sai kuma rai da dukiya wanan yasa na sha,afa da zancen su gaba daya don kudin da yanzu nake juyawa sai ga wanan zancen ya taso don haka naaan za a kawo kaina yasa na tsaya saida na cire masu komai nasu na dawo da shirin danka masu abin su a yanzu. Humm, umma dake gefena ta fada tana dan jijiga kafanta a cikin takaicin jin wanan cin amanan da tasan duk shirin magana ce kawai don ya kare kan shi a yanzu daga tuhuma. Saukin shi dai dayane shine baya cikin kisan amma makushe dukiyan harda shine don ai bai taba fadawa kowa wanan zancen ba haka sai yau. ZAINAB IDRIS MAKAWA ANA DARA GA , , , , , , , , 8️⃣6️⃣ BY, , , , , , , , , , , , ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , , , , , , , , BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AL MU,AKHIR , , , , , , , , ONLINE PAID NOVEL YAR UWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA BA TARE DA HAKKIN KOWA BA DON BIYA KI TURA DARI BIYAR 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK 08036959257 ALLAH SARKI AI RAINA BAYA BACI YANZU DON KIN FITAR DON NASAN AKWAI RANAN HADUWA SEE U👋👋👋👋 Taben da lauyan mu yayine ya dawo da hankalin kowa a kotun aka dan rage surutun da akeyi a lokacin kowa na fadin ra,ayin shi. Kallon su akeyi yana kallon daddy yana murmushi har ya isa wurin shi ya tsaya yana dan jijiga kai. Ya kalli daddy din yace well Alh kotu taji bayanin ka a yanzu saidai idan ba damuwa akwai dan tambayoyin da nake son in maka. Yana fadi fuskan shi a wurin alkalin dake zaune yana dan rubutu a lokacin a farar takarda daya dauke mai hankali ya gyada kai alaman an baka. Ya dubi Alh yace Alh a cikin bayanin ka naji kace kun sami sabani da marigayin akan wani abu nasa lokacin ko zaka iya fadawa kotu abinda ya jawo maku wanan matsalan. Sai a lokacin ne aka san ya shigo dame kareshi a kotun ya daga yana gabatar da kanshi tare da fadin wanan tambayan ai an wuce wurin tunda yayi bayani ko . Alkali ya daga mai hannu alaman ya bari a tambayi daddy din ya koma ya zauna shi kuma yaci gaba da kallon daddy din yana sauraren shi. Daddy ya gyara tsayi yana fadin eh to a lokacin dai daya ban ajiyan ya kawo min shawara naji rejecting to ba wani abu bane illa nayi amfani da kudin wurin gina wani wuri a garin lagos a lokacin. Inda ya nuna min don me zan masa hakan bayan ga kudirin shi nason ya gina gidajen mai shine burin shi. To mu a nan marigayin yayi bayani a takardan sirin shi cewa ka bashi mamaki don ka dauki kudin shi da yake da buri ka gina babban hotel a garin ikko na kanka dashi. Haka abin yake ko kuma kana da abin fadi a nan dan murmushi daddy ya sake a fuskan shi yace shine dalilin fadan namu dashi. Dama nasan idan na fada mai hotel zan gina don yafi wanan burin nasa da make ganin shirmene a lokacin ba zai taba yarda da hakan ba. Don shine ma ya nuna min baida ra,ayin gina hotel a rayuwan shi don irin abubuwan da za a aikata a ciki. Amma sai naga rashin wayaushi nabi baya nina gina a kashin kaina sai wanan yayi matukar batawa shi sambo din rai sosai har yakai ga furta min kalami da fadin. Brother kana ganin kamar ka cuceni ne ni kadai to kasani kanka ka cuta da wanan abin dakai min don bani kadai ka cuta da hakan ba. Fadin hakan sai naji raina ya baci dashi nace yau ni kake fadawa haka sambo akan dukiyan ka sai ya kalleni yayi murmushi bayan ya mike yana fadin. Ka bani mamaki sosai brother ban taba zaton kai zaka iya yin wanan abin na sonkai ba gareni . Anan lauyan ya tare shi da fadin sai kace dashi me kai kuma kallon lauyan daddy yayi kafin yace naji haushi sosai a lokacin yasa nace dashi akan kudin da bamu tabbatar da ida ka samoshi ba har kake kokatin min rashin kunya. Idan bakai hankali ba sai na saka an bincike ka inda kake samun dukiyan ka haka sai me kuma ya baka amsa lauyan ya tambaya ? Daddy yayi shiru idan ba laifi zan fadi abinda marigayin yace maka lokacin ya kalli alkali ya daga mai kai alama go ahead gareshi. Kaika sani duk inda haram yake bana wajen kada kudi ko dukiya ya rufe ma ido ka dawo kana dana sanin hakan a baya. Hakane ko Alh lauyan ya tambayi daddy din shiru daddy yayi yana fadin yaron nan abinda yai min ke nan lalai hurda damai ilimi yana da wahalan fahinta yafada a ranshi. Na fada daidai ko lauyan ya tambaye shi sai kai kuma kaji haushin mayar maka da hakan da yayi yasa ka dauki alkawarin baiyanawa yan uwan shi duk sirin shi daka sani ko. Wanan ke nan ya wuce wurin ya koma fadin sai zance na biyu shine ko Alh zai fadawa koto inda wanan dukiyan na baya suke yanzu bayan mutuwan mai ita ? Eh to gaskiya zance ni kadai nasan inda kudin sambo yake a lokacin amma sanin kowa yasan ya dawo da wani abu mai muhinmanci wanan tafiyan. Shine na fadama sun sameni a gida kan wanan kudin muka bincika kudin suna nan yadda ya ajesu a bankin shi . To a wanan lokacin muka fito da kudin muka rabashi a tsakanin mu har wurin rabon yaso ya kawo muna rikici a tsakanin mu wanda har wanan lokacin muna rike da wanan zancen. Ko Alh zai iya fada muna abinda kowa ya samu a cikin kason objection my lord dayan lauyan ya fada lokacin dana gimtse idona dake fitar da hawayen bakin ciki. Wanan wani irin rashin kaunane da rashim imani sukaiwa mahaifin mu haka yan uwanka na jini bako bare ba sai kace basu san inda ya fito ba wanan irin son kai da suka nuna mashi. Ashe gaskiyane da ake fadin kiyayya ta asali bata goguwa a zukatan makiya kome ko zakai masu sai ranan da sukaga kanka a kasa koshi idan yana motsi basu barin ka sai ya daina matsin. Saidai su wa yan nan sun kashe macijine basu samu sare kan shiba da ace sun sanda hakan duk inda muka shiga cikin duniyan nan Allah nuhu sai ya nemo umma damu ya halakamu a lokacin. Dukda abune mai wuya irin nisan shakon da umma tayi zuwa semi boda Allah kadaine ya gyara bata tsalaka kwatano damu ba a lokacin. Ko can din take zai iya zuwa ko ya tura akashemu da ace yasan da hakan a lokacin Allah ne kawai zai kwacemu a hannun shi. Duk yadda lauyan mu yaso yakai daddy makura saboda yasan logon sharia ya kasa kayar da daddy a ranan don iya duniyama. Sai rokom kotu da daddy yayi kan cewa yana son kotu ya bashi dama ya halartawa iyalan mamacin dukiyan su a hannun su dake wajen shi tunda yanzu lokacin hakan yayi. Jin hakan yasa na dago idona ina kallon daddy din wanda ni kaina bazance ga irin kallon da nake masa ba lokacin kamar ance na duba gefena ya Abubakar ne zaune dasu baffa hamza a kujera guda. Idona a cikin nasa alaman daga kai yayi man wanda ban fahinci nufin shi ba a lokacin sai muryan mai bayanin kotun dake fadin ko zamuga wace ke kara muji na bakin ta a yanzu. Duban inda nake mutane keyi ranan dai shiga shigen na hausawane duba da inda muka fito yola yasa nasaka atamfa amma buje da riga matsatsu da suka kame jikina sosai. Gyalen dake saman cinyana na dauka na dora a kafada don gaskiya babu wani zancen hijjab a gareni don ban saba sakawa ba tun ina karama. Wanan yasa ko a yanzun niko a jikina hakana tashi tinkis tinkis dani suka bini da kallo masu tausayi na tausayawa masu jin haushi naji hakama masu mamakin mu a wurin. Daga yanayina zaka gane a gajiye nake ko kuma cikin wani yanayi na daban can mai nuna rashin jin dadi a gareni nazo na tsaya a inda ake tsayawa din lauyan ya kalleni yace dani. Shabi u hear what he said now ? Waitin he talk na sake jefo mashi tambayan nima a wahalce yace dani kan dukiyan mahaifin ku dake hannun shi da yake son ya danka maku su a yanzu. Which kind of wealth he dey talk now i beg may he forget about dem shaaa. Ni a yanzu kawai bukatana garesu shine su sakar muna mara muyi rayuwa kamar kowa ina son kotu ta kafa muna sheda damu dasu akan duk abinda ya shafi rayuwan mu a yanzu sune. Aiko nan kotu ya dauki hayaniya masu dariya nayi irin yadda nayi maganan zakace ni din wata tsohuwar bayerabiya dani ga kuma na nuna ba dukiyan bane a gabanmu mu. Shima kanshi lauyan dariya na bashi sosai yayi dan murmushi yana girgiza kanshi dan abin ya bashi mamaki matuka nace yes now. We no wan de money and erverything daya fito a wurin kowa daga garin nan tunda ba zasu dawo muna da mahaifin mu ba su rike komai mun yafe mu. Aikuwa kamar mutane su cinyeni danye don abindana fada ina kuka ina share hawaye har alkali yaita dukan gudumar shi wurin yai shiru ya dukar da kanshi yana rubutu kafin ya dago yayi gyaran murya aka kara natsuwa sosai ana saurarenin. A nazarin kotu a bisa tsarun da doka ya shimfida ya zama dole wa,yanda ake tuhuma su gagauta dawo da duk abinda suka wawasa na daga dukiyan mamacin ba tare dako kwandala ya bata ba a cikin shi kamar yadda ya rubuta dukiyan shi a tsare ya bari. Nan aka shiga jero masu abubuwan daga ciki har da gidaje da filaye kiwon shanu motoci da sauran abubuwan amfani na gida. In boni handi yoooo Alh gyade ya fada yana zubewa kasa tare da fadin Nuhu kai shushe mu ka shuci rayuwan mu kace muci ba a komai ya gashi zan tashi ko kwandala bandashi a duniya. A take kotun ya rikice da koke koken diyan su dana yan uwa kowa da gefen da yake bi a cikin su yayin da Alh nuhu yayi tsayuwan da baisan inda yake ba a lokacin. Alkali yaci gaba da bayani bayan haka kotu ta yanke hukuncin Alh Ali dcp taran naira miliyan ashirin ga magadan don kamashi da cin amanan mamacin da kuma sassaucin dauri na shekara daya ko taran naira miliyan biyar ga kotu. Haka kuma zai iya daga karan idan hakan bai mashi ba yaje gaba iya abinda kotu zata yanke yanzu ke nan kan Ali dcp. Sai su Alh nuhu da zasu mika komai da suka mallaka ga ko magadan su haka kuma zasu fuskanci daurin mara sassauci da tara ga kotu kan kisan dan uwan su da sukayi. Shi buhari ya wanke kotu ta bata kamashi da laifi asalima an yaudare shi anyi amfani dashi anje kissa an kuma boye mashi hakan. Jarrr kaniya Alh nuhu ya fada da karfi kowa dake cikin kotun hankali ya koma akanshi lokaci guda ya fara fadin akan Sambo za ai min daurin rai da rai a gidan wakafi. Kana da daman daga kara idan sharian mu bai gamsheka ba a nan aka fada Alkali na dagawa daga kujeran shi da yake zaune don an dade a wurin zaune ranan. Koke koke ne ya tashi a kotun lokacin guda wanda yan uwa keyi na tashin hankali ya dai tabbata ke nan cewa sune suka kashe dan uwan su ashe. Ga iyalin su kuma suna fadin an tauyesu ba a basu daman kare kansu ba ga kuma cin zarfi wai za a kwace komai da suka mallaka a dankawa yaran nan shine wani sabon tashin hankalin su a lokacin. Daga nan wurin sharian ko gidan kowa bamu leka ba aka wuce damu airport zamu bi jirgin yamma da zai tashi duk ko son ganin mu da aka turo text cewa daddy yana son yi a lokacin hakan baisa mun dawo ba muka bar masu garin suna a cikin tashin hankalin halin da zukata suka shiga lokacin. Saukan dare mukayi Abdulne yazo ya dauke mu daga airport ya kaimu gida tun a hanya suke hira da umma ban saka masu baki ba har muka kai gida. Daga shigan mu dakina na nufa na kwabe kayan jikina da suka dameni na shiga wanka na fito na tayar da sallah don rama sallolin dake kan mu. Karfe goma da rabi na gama komai duk da banci abinci ba amma wurin kwanciya nake nema in kwanta lokacin don yamayin da nake jin kaina abu ya tsaya min a makoshina lokacin. Abinci muniya ta kawo muna amma ban iya dagawa naci ba har barci ya dan daukeni ban kara sanin inda nake ba kuma a lokacin. Washe gari hakan yasa na tashi ina jin yunwa sosai a cikina na fita neman abinda zanci din nan na hada cooker orth na zauna nasha lokacin umma ta fito daga dakin ta zuwa wajena a falon. Sai bayan ta zauna nake gaida ita ta amsa take fadin wai mutane basu da kunya yau daddy kune ya kirani yake tambayana muna ina zaizo ya same mu. Kin fada mashi munbar kaduna tun jiya na tambaya a gagauce tace na fada mana nace muna lagos mu tun jiya ai daga kotu airport muka nufa ai. Wai sai yake fadin don me zamuyi haka bayan ga yadda aka aje magana damu ido na tsurawa umma dake min bayani sai cewa nayi amma yaji abinda kika fada a kotu ai don haka ya rike komai shiri tsakanin shine da mai dukiyan na kashe waya. Dan murmushine ya baiyana min a fuskana ganin yanzu umma tsoro ko nauyi ya fara fita a idon ta a yanzu. Mun dan taba hiran abinda daddy ya fada a cikin kotu din kafin mu sauya hiran namu zuwa na yan uwan umma dake yola. Irin yadda suka nuna muna karamci da jin dadin ganin mu da sukayi a lokacin jin nayi shiru lokacin da take min bayanin yadda suke da kowan su yasa ta dan kura min ido tare da dakatar da maganan da take min din tana kallona . Nayi zurfi sosai a cikin tunane a lokacin don haka ban gane hakan da wuri ba sai dana sauke ajiyan zuciya na dago kai nake tambayan ta da cewa. Dama wanancan kauyen shine asalin kauyen iyayyen mu maza da suka fito tace kwarai kuwa kusan duk abu daya ake ai kinsan bafilace da son zaman daji ai. Badon komai ba ya jawo hakan saboda dabbobin sune suke bin wuraren dake da sanyi don haki saboda dabbobin nasu su koshi kada suyi rama . Don shi bafilace na asali a rugga aka sanshi da zama ba a cikin gari ba amma cikin garin akwai su idan idon su ya bude zakiga sun baro daji sun dawo gari da zama to alokacin sun camfa idan ba Allah ya gyara ba mutum yakan shiga wasu halin dabana kwarai ba ga hakan. Asali dai bafilace shi a daji aka san rayuwan shi ba acikin gari ba duk da a cikin garin akwai fulani yan asali da asalin sune garine suma. A can kaduna kuma an wayi gari kwatsam kotu ta tura a kargame dukkan gidanjen su har wanda iyalan su ke rayuwa a ciki ashe. Abin bai tsaya a nan ba don duk wani kaddara na Alh nuhu dai na mahaifin mune ashe don haka kotu ta bayar da daman cewa a kwace komai daya mallaka ayi kudin su ko zasu kai adadin abin mu dake hannun shi. Zancen gidan shi yafi daga hankalin kowa a cikin ahalin namu don har ya Abubakar shima a karshe hankali a tashe ya kira yana fada muna abinda ke faruwa. Don yanzu shi kanshi sharian namu yana bashi tsoro sosai don ya gano akwai wanda ke izza wutan abin daga sama kuma maishi ya tsaya muna saidai ya kasa gano ko ta inane. Don dai Alkalin ya fada mai case din babbane sosai don an bashi umurni tundaga sama akan yayi sharia yadda ya dace idan ba haka ba a bakin aikin shine. Saidai kuma yayi mamakin jin yadda mukai mamakin faruwan hakan don sam bamu sanda wanan zance ba a lokacin mu sai a wurin shine muke ji lokacin. Ko dai waye wanan din yana da wani alakan hakan daku ko kuma dashi marigayin ke nan tunda yan jarida sun yadda zancen kowa yaji a yanzu. Ya barmu da mamakin hakan don muma munyi bincke a bagaren mu mun kasa gano ko waye mai wanan danyen aikin yanzu kuma. Gashi sai waya ke zuwa yana dawowa na yan uwa dake neman mu a layin su don wai a roka mu yarda iyalansu zauna a ciki kafin asan abinyi garesu. Saida kyat suka samu layin na na dauka mun gaisa su babbaf hamzane suke fadin haba Sahiba bai kamata kiyi hakan ba idan sunyi maki su. Idanuwa na lumshe a hankali ina rauraren baffah hamza din don abinda yake labarta min lokacin na halin tashin hankalin da kowa ke fuskanta a cikin su. Baffa ban san waye ya bada wanan umurnin ba don na tambaya a nan bangaren mu babu wani daya saka ai hakan na bashi amsa a sanyayye. Mukai sallama na fara jin digon tausayin su a kasan zuciyana don wanan yawan iyalan nasu ina zasu zauna wanan korar kai tsaye haka lokaci guda ba zato. Da sauri wani zuciya ya gargadeni da har kin manta da naku bakin cikin rayuwan da suka jefaku ciki na maraici bayan kisan gillan da sukaiwa mahaifin ku ? Ko har kin manta da irin kunci da kadaicin rayuwan da kuka kasance na tsawon shekuru masu dama ? Daga inda yake zaune da sauri yake sarrafa computer din nasa yana son gano abinda yake nema a lokacin koda zargin shi zai iya zama gaskiya . Idonshine ya sauka ga wani rubutu na shafin mutumin farine dogo saidai ya girmey masu sosai ga shekaru yana tsaye a cikin bakkaken suit da suka karfi jikin shi. Shigan shi zaka dauka dan shekara ashirin da wani abune lokacin nan ko shekara talatin da biyu yake ma,ana zai iya kaiwa sa,an ya Mustaphan gwaggo hari a wajen shekaru ke nan. Ga wasu baiti da yayi kasan photon nasa da wanda ke nuna halin kunci takaici suyan zuciya bakin ciki dayayi na rashin ubangida aminin shi a baya . Sai ya dawo kasa yana nuna cewa duk da kuncin da zuciya ke ciki a yanzu hakan ba zai hanamu tunawa da Allah ba kan amsan adduan mu na tsawon shekaru kan Allah ya baiyana muna azzaluman da sukai maka kashin gillah. Lokaci yayi da zasu fuskanci hukunci daidai da abinda suka aikata a gareka suma a yanzu sai wani photon da ya sake yana mai murmushin mugunta. .ANA DARA GA , , , , , , , , 8️⃣7️⃣BY, , , , , , , , , , , , ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , , , , , , , , BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AL AWWAL, , , , , , , , , , , ONLINE PAID NOVEL YAR UWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA BA TARE DA HAKKIN KOWA BA DON BIYA KI TURA DARI BIYAR 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK 08036959257 ALLAH SARKI AI RAINA BAYA BACI YANZU DON KIN FITAR DON NASAN AKWAI RANAN HADUWA SEE U👋👋👋👋 Zubur ya mike tsaya lokaci guda ya fara zagaye dakin shi kadai yana tunanem inda yasan wanan sunan ko fuskan wanda yake kallo a screen din laptop din tsawon awa daya da rabi. Wani irin abu yaji a zuciyan shi lokaci daya yaja ya tsaya yana sauke numfashi a lokaci guda ya dan furzo iska mai zafi daga bakin shi kana yakai hannun shi akanshi ya shafo zuwa fuskan shi. MUKHATAR USMAN MARWA fittacen dan kasuwan nan mai harka da ma,adanai na kasa kasa matashin da yai saurin fice a wanan harkan lokaci guda kuma yana matsayin basarake daya fito daga nahiyar gabas mai fada aji akasa saboda sun kawowa kasa cigaba sosai ake damawa dasu sosai. Mukhatar dai kowa yasan ba mutum bane mai lokacin kanshi balle na iyalan shi ko yan uwa mutum ne wanda a yanzu ganin sa ma aikine. Yayiwa harkan shigan wuri harkan kuma ta karbeshi yashige cikin turawa ya saje dasu ana gwagwalmayan rayuwa tun tasowan shi. But why ya tsoma kanshi a cikin wanan harkan a yanzu yake tambayan kanshi saidai a halin yanzu ba amsa a gareshi. A gurguje ya shiga bathroom ya watsa ruwa a jikin shi ya fito ya shirya yana kokarin daura belt din shi a kwankwason shi ta turo kofan da kuka wiwi . Hakan yasa ya juyo yana kallon ta duk da bata bude baki tayi magana ba yasan kukan ta bai rasa basaba da abinda ke faruwa a gidajen su a yanzu. Juyowa yayi a fusace yana fadin ke meye hakan meye zaki shigo min dagi a wanan yanayin na tashin hankali haka kuma ? Haba modibbo kaji wai a kan wanan case din yarinyar nan wai anje gida an fitar dasu mama fitarwan wullakaci gaba dayan su gidan, suna titi a watse da safen nan fa suka dira masu a gida sukai masu wanan wullakacin. Uhummm ya fada ya juya yana kara saka wandon jikin shi da kyau ita kuma tayi tsaye sororo tana binshi da kallo cike da takaicin ganin rashin damuwan da bai nuna ba ga abinda ta fada mai din. Wani irin kuka mai sautin tausayi ta sake lokaci guda har ya kare shirin shi yana jinta saida ya fesa turare bayan ya gama tsab ya juyo yana ce mata. Yanzu kukan nan naki shi zai saka wani abu ko kuma kijawa kanki wani matsala nima kuma ki tayar min da nawa hankalin ? Dole inyi kuka saboda nina nasan zafin da radadin hakan dana ke ji don kai naga abin bai shafeka ba ka nuna min yanzu. Kome zaki fada ki fada yanzu don kina da daman fadan hakan saidai kada ki manta da cewa nima abin ya shafeni ai ko kin manta da hakan ne. To ba laifina ya kamata yanzu ki gani kiga laifin iyayyen mu da sukabi son zuciya suka aikatawa bayin Allah irin haka a baya yanzu lokacin namu fuskantar tashjn hankalin ne yayi. Da ace basu bi son zuciyarsu da kuma hassada ga dan uwan sy ba da yanzu kowa na zaune kalau a cikin salama amma yanzu ba yadda muka iya don zakanya ta girma ko tsakiyan daji ni kaina abin a yanzu na kara gaskanta sakaiyane kawai ke bin iyayyen mu na abinda suka aikatawa dan uwan su a baya. Yana kai nan ta dago kai da sauri tana mai wani irun kallo kamar zata cinyeshi danye ya gyada mata kai kawai ya figi suit din shi dake saman gadon daya gama feshewa ya fita nan ya barta zaune tana mai matsakancin kuka cikin tashin hankali. Gidan su ya nufa don yana son ganin daddy a wanan lokacin kan binciken dayayi din saidai yayi rashin sa,a daddy din baya gida a wanan lokacin. Yana tsaye yana mamakin inda mahaifin nasu yajene don yasan baya sakkon fita irin wanan lokacin haka sai idan wani abu mai muhinmaci sosai ya taso gareshi. Bai kaiga karasa isa wurin motar nasa ba wasu mutane suka iso ya sheda su dan yasan wasu daga cikin su kusan irin aikin su daya saidai ba a ma,aikata daya suke aikiba don kowa da nasa bangaren wurin aikin ne. Nan dai suka sameshi suka gaisa dashi suke fada mai sunzo neman maigidan nan ne don basu dauka daddy shine mahaifin shi ba a zaton su wani aikine ya kawoshi shima wurin daddy din . Yake cewa dasu shima ai wurin shi yazo saidai baya gida OK babban nasu ya fada zamu dawo munzo ne mu tafi dashi dama don ya amsa muna wasu tambayoyi da muke so daga gareshi . Basu tsaya mashi bayani ba suka juya nan suka barshi a tsaye cikin jimame a lokacin hjy karima ta fito zata fita unguwa zuwa gidan yarta don haka a gabanta aka fadi komai. Itama dai hankalinta ne ya tashi sosai a lokacin jin abinda jami,an suka fada take fadin wanan tashin hankali haka dame yai kama ? Haka jiya bamuyi barci da wuri ba a gidan nan don su hamza da yara su ya Nuhu sun dade a gidan nan tare dashi wanan abin gaskiya baidai yi dadi ba wallahi . Mutum yanzu in kai masa rana sai yayima dare in ba shi ba wai yau Sahibace da kanta takewa Alh haka a garin nan. Murmushi yayi yakai bakin motarshi ya jingina jikin shi da motan yace me Sahiban tayi kuma anty da ake mata wanan zargin haka yanzu. Modibbo kai yanzu bakaga rashin kunyar yarinyar nan ba haka meye Alh bai mata ba zaman su garin nan don Allah ? Anty idan yai mata ai yayiwa kanshine don wata kila da wani manufa yai haka din garesu mutanen da dukiyan su yana hannun daddy da Allah kadai yasan adadin abinda aka bar masu sai shi wanda keda dukiyar nashi kuma baya raye a yanzu. Tsaye tayi cikin yanayin mamaki da rudewa yadda modibbo da bakin shi yake fadin ha tana kallon yadda yake fadin magana haka ranshi a bace. Abinda bata taba ganin ya faru dashi ba yau ta gani a fuskan shi lokaci guda ya rikede ya koma wani kala dashi lokaci guda zaka fahinci tsananin tashin hankali ne yake ciki a lokacin. Nan dai yayi mata bayanin komai yadda zata gane sai ga hjy na komawa bayan mota takai har tana kai ga jingina jikinta a motan . Lailai muna cikin halin tsaka mai wuya a yanzu don nima wanan fita da zuwa zanyi can gidan mijin baby ance duk yan uwan nasa suna nan gidan a yanzu. Zaki iya zuwa ki duba muna halin da take ciki in yaso sai a san abinda za ayi nan gaba don ba zasu zauna masu a gida haka gata gasu ba. Har hjy ta fita daga gidan da motar ta yana tsaye yana waya da wani abokin shi daya bugo mashi wayan a lokacin. Yana cire wayan an kunnen shi yana kokarin turawa aljihu motan daddy ya danno cikin get din gidan suna tafe tare dasu baffa Abdullahi da baffah hamza da wasu mutum biyu daga cikin yan uwan su. Yana tsaye har suka gama fitowa daga motan ya karasa wurin su yana gaidasu a cikin ladabi suka amsa mai ganin shi baisa dakata da zance da sukeyi ba. Daga can inda ya danja ya harde hannayen shi saman kirjin shi ya jefe masu tambaya daddy waye mukhatar usman Marwa ? Mukhatar usman marwa baffa Abdullahi ya maimaita sunan cikin mamaki daga gefe baffa hamza yace wanan matashin ne da yai arzikin fice a harkan ma,adaina da sauran su. Ai dan asalin kasan maidugurinr shi kuma yana taimakawa matasa sosai akace musan idan yasan sana,an ka kuma kana da sheda kan hakan zai iya tallafa maka ka daga kaima. Wait amma kamar nasan mai wanan sunan a baya duk da ina tantaman cewa shine a yanzu don an dade ban kara jin duriyan shi bama ni. Wanan dai dan maidugurine oh wanan kuma da nake fadi kamar a wurin sambo na sanshi a baya yazo dashi lokacin muna maiduguri har gidana wai ya hadu dashine yaje karatu ya samu matsala ana son aimai wullakanci a can shine ya taimaka mashi. Shi din daine shine wanda a yanzu ya dauki wanan karan da karfi shine case a yanzu ya koma hannun shi kan wasu abu da yake tuhuma garemu sai ya gyara zancen. Salati suka dauka lokaci guda baffa Abdullahine yake tambayan wa ya sanar mai da wanan maganan yanzu sai daddy ya dan yi murmushin manya yace mai yuyuwa su Sahiba dine ko? Don idan basu ba wa kake ganin yasan dashi ko yana tare da marigayin a baya sai su sai ko ni da Allah yasa zan sani din a lokacin. Sam basu bane don su na fara tuntuba koda sun san wani daya daukaka wanan maganan haka suka nuna min basu san komai su. Zasu fada ma gaskiyane daddy ya fada kai modibbo ya girgiza mashi yace tun zamana da su ban taba jin sahiba ta fadi karya ba ko abinda ba daidai ita fa kai tsaye take abinta . Daddy bayan wanan din jamin yansandan siri sun zo gidan nan neman ka na fada masu baka nan sunce zasu je su dawo dan anjima. Ni ni suka zo nema akan wani dalili kuma zasu zo har gida suna nemana ko wanan zance kotu dinne kuma suka biyoni gida kanshi. Ban tsamanin hakane gaskiya don su sai idan ana tuhuman mutum kan wani abu mai girma shine zasu baiyana ai. Nasan da wanan amma kuma zuwan su din shine ya daure min kai a yanzu bai gama rufe baki ba motan su ya danno ya tsaya a wajen gidan basu shigo ba . Ashe motocin har biyune ma bakake sabbi dal dasu suna sheki ga rubutun shi daga federal government suka zo Abuja can babban headquarters din su ke nan na Abuja. Har suka karaso aka gaisa nan suke tambayan waye Alh Ali dcp a cikin su ya dan murmusa jin wai basu sanshi ya nuna masu kanshi. Ok you're under are rest suka fito da takarda suka nuna mashi da sauri modibbo ya karaso yana fadin for what ? Sorry sir ya fada da alaman sun san mukamin shi sukace umurnine daga headquater din mu kan supect da ake mashi. Kafadan shi daddy ya dafa yana fadin kyalesu mu tafi amma ku dan ! da baya suma hankali a tashe a lokacin ne modibbo ya fito da wayan shi yana neman layin umma. Daddy daya shiga ciki kuwa rudewa yayi ya kama kwalawa matan shi kira sai mommy ce ta fito take fadin hjy karima ai ina ga bata gidan nan don yara sunce tafita. Ya manta data kirashi zata tafi gidan baby din ta duk da baiso ba dole saida ya barta ta tafi din ta cikin waya don ba yadda ya iya da fitinan ta alokacin. Yace to zamu tafi don anzo tafiya dani Abuja a razane mommy tace Abuja lafiya Alh suwa zasu tafi dakai ? Jami,an tsaro ya bata amsa da gani baya cikin hankalin shi a lokacin kuka ta sake tana fadin akan wanan case din ne kuma za a tafi dakai ko me baffah Abdullahi ne ya bata amsa da shine dai ya taso kuma yanzu saidai bamu san akan me bane kuma yanzu ake neman shi can. Nan dai modibbo da ya shigo yana waya da basu san dawa yake ba a lokacin yake fadin wallahi fa yanzun nan gashima zasu wuce ai dashi yanzu haka ya tsaya yana sauraren wayan tare da fadin to shike nan hakan za ayi don umma tace ya bari na dawo na fita aiki dazun nan zata bincika yasa yace hakan. Bai samu kanshi ba sai wajajan karfe dayan rana ya samu shigowa wurin mahaifiyar nasa dattijuwace baka amma ba sosai ba da zubin irin na kunuri. Tana saye a cikin lafaya mai laushi kana gani kasan mai tsadane ga kamshin turaren su na asali dake tashi a falon tun har waje idan zaka shigo gida kamshine na asali zai tare ka. Da murmushi a fuskan shi ya karaso falon sukai arba da mahaifiyan nasa yasa ya sake mata lalausan murmushin dake karawa fuskan shi annuri. Saidai ya zube a kasa daidai saitin kafafuwan ta yana fadin ya salam tare da dora kanan shi saman kafafuwan ta ya sauke ajiyan zuciya kafin yace. INDA, WATTU UMMI, ta sauke murmushi tare da shafo kanshi daya dora saman jikin ta tana fadin WATTU KILLEFIYA ya dan murmusa cikin jin dadi ya kara noke kanshi saman cinyan nata yana dan sauke ajiyan zuciya karo na barkatai. Amma sun san da zaka zo yaudin ne ko wanan dandazon taron dana gani a waje haka nan ya dago yana fadin nima abinda ya ban mamaki ke nan dana tun karo gidan nan wai hakama a cikin siri na shigoma. Tashi kaci wani abu kafin komai lokacin sallah ya gabato kada wani kuma yazo ya hanaka samun lokacin haka da dare ma zauna idan ka samu kanka. Jin zata mike yasashi dagowa don yasan abinda take nufi shima tashi yayi suka nufi dinning inda abinci ke jiran shi aje alokacin da kanta ta zuba masu abincin ta dawo kusa dashi ta zauna. Kin yin magana tayi a lokacin donshi kawai sai hakan ya bashi daman samun lokacin dayaci abincin sosai tana kallon shi. Har saida ya kusa gamawa take fadin yanzun dai asirin su ya tono ke nan ya tabbata din zargin da kakeyi na shekaru su din ne suka kashe bawan Allah nan ashe ? Sai lokacin ya dago kai ya dan kalleta yace wallahi ummi sune sune da kansu sukai mashi wanan aikin kuma suka tura iyalan shi nisa da gida don barazanan da sukai masu lokacin. Salati dattijuwar ta sake tare da fadin kai duniya ina zaki damune haka wai yau har mun kai dan uwa ya kashe dan uwan shi don saboda dukiya. Mutum mai kirki mai mutunci ga addini da sun barshi ya rayu dasu da Allah kadai yasan abinda zai zama yanzu a kasan nan yau ba gakuba kuma na kasa gareshi Allah ya tsayawa rayuwan ku tai albarka. ZAINAB IDRIS MAKAWA ZAINAB IDRIS MAKAWA ANA DARA GA , , , , , , , , 8️⃣8️⃣BY, , , , , , , , , , , , ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , , , , , , , , BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AL AWWAL, , , , , , , , , , , ONLINE PAID NOVEL YAR UWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA BA TARE DA HAKKIN KOWA BA DON BIYA KI TURA DARI BIYAR 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK 08036959257 ALLAH SARKI AI RAINA BAYA BACI YANZU DON KIN FITAR DON NASAN AKWAI RANAN HADUWA SEE U👋👋👋👋 Sallaman hjy ghana da yaran ta mata a falon ya dakatar dasu daga hiran da suka dauko a cikin fara,a suka amsa masu sallaman tare da nuna jin dadin ganin su a lokacin. Hjy ghana dake tafe tana fadin ashe ko shawaran autana yaci gashi ko mun sameshi a cikin gidan kamar yadda ya fada. Nan dai suka karasa shigowa aka gaisa a cikin raha da nuna jin dadi daganin juna hjy din ke fadin dayaya muka samu shiga gidan nan ? Mukhatar sai mu kara godewa Allah da wanan baiwan da yai maka a yanzu lumshe idamuwan shi yayi a lokacin zuciyan shi naso ta tuno mai da wasu abubuwa da suka wuce a baya amma yana tausan zuciyar nasa don kada ya tuna hakan a wanan lokacin. Yare ya barke a tsakanin su wanda kowa ke ji a cikin su hjy ghana babban yayace ga mahaifin shi mukhatar din na uwa daya uba daya. Suma suna da nasu rufin asirin tun can baya amma yanzu nasa ya taushe nasu har suke ganin suba komai bane a yanzu kinsan halin mu yan adam da hangen nisa. Bamu waigen baya kullun idon mu a samane muna hango wa yanda suka zarce mu maimakon mu dinga kallon wa yanda muka fi don haka zaisa mi dinga godewa ubangijin mu kullun. Zancen autan tane da suka fara dashi a baya ya kawota yanzu sai kuma yaran ta mata dake son su gana dashi kan wasu bukatu nasu. Yaya kamar yadda suka saba kira a bakin su don yadda mahaifiyan su ke kiranta ke nan suma suka dauka ya tsaya masu a bakin su kuma. Ban manta da zancen autan ki ba idan yadda nake so ya samu nan da dan lokaci autan ki zai bar kasan nan ga baki daya zamu zauna dashi acan inda nake zama a yanzu. Wani irin dadi dattijuwar taji don wanan albishir din da yai mata duk da tasan a baya basu kyautawa yaron ba amma shi sam ba rikesu da komai ba asalima sai nuna yake kamar wani abu bai taba faruwa dasu na rashin mutunci ba can baya. Abinda basu sani ba shine yana iya danne zuciyar shine baison ya tuna da wanan abin daya zama mai sanadin alheri a yanzu don su nashi sun kishi wani bare yazo ya daga rayuwan shi. Nazone nagane ku a yau din nan kuma zan juya don na bar tarin aiyuka a gabana jin hakan yasa mahaifiyar shi ta dago kai da sauri tana kallon shi cikin mamaki. Yace eh ummi yau din nan da yamma zan wuce lagos ina son a yau in gana da iyalan marigari na gansu su san ina nan ban manta dasu ba a raina inda taimakon da zan masu sai in masu kuma. Taimako kan ai kayi masu shi yanzu tunda ka taimaka dukiyan su yana fitowa hannun azzuluman mutane a yanzu. Ummi zan daiyi ni yanzu wancan din su sukayi kokarin koma da kansu har gaskiya ya baiya saidai zaluncin ya hana su fadi inda suka shiga da kudaden shi na baya wanda yafi komai yawa kuma don shi suka kashe din. Wai wa kuke zance haka akanshi hjy ghana ta tambaya cikin rashin fahintan su a lokacin sai ummi din tace wanan bawan Allah daya tallafawa rayuwanshi da aka kashe shi a kaduna wancan lokacin . Dan tunane hjyn ta tsayayi kafinta tunoshi tace duk tsawon wanan shekarun dama ana bincike a kai ? Dama hjy ai baka kashe mutum ka zauna lafiya komai daren dadewa sai Allah ya tonama asirin kan Alhakin dake kan ka Allah dai ya tsare ya karemu daga miyagun kaddarori kawai babban yar nata daga cikin su ta fada. Abin takaici ma wai ace yan uwan haihuwan kane sukai ma haka kuma suka wawashe dukiyan nasa iya tsakanin su basu tuna da iyalan shi va ummi ta fada Yana jin su idanuwan shi a lumshe ba abinda yake tunowa sai ranan daya fara haduwa da Abba lokacin da suka amshe visa ga koran wullakaci. Kan laifin data san cewa dasune ya aikatama uban laifi amma aka dora akanshi don yana matsayin dan cin galihu a wurin su. Jin yayi shiru bai magana sai faman tunanen da yake yi yasa wace ake kira da anty shuwa take cewa dashi dan uwa nazone kan zancen muna baya dakai. Sai lokacin ya bude idanuwan shi yana dan kallon ida suke zaune din cikin kokarin son ya tuna da alkawarin da take nufi sunyi dashi. Nan dai suka dan tatauna abinda ya shafi rayuwan ko wanen su da irin taimakon da suke nema a wurin shi yace daya koma ummi ta tuna mashi . Bayan tafiyan sune ya kara yiwa mahaifiyan shi bayanin abinda yake son zuwa yi lagos din da irin taimakon da yake sonyi din idan yaga halin da muke ciki a can. Karfe biyar yabar maiduguri zuwa lagos bayan ya gama ganawa da duk wani wanda ya samu ganin shi saura kan hakkuri ya basu kan hakan. Hjy karima ta dawo ta samu abinda ya faru hankalinta a tashe kafin kuma ta fara sababin cewa an munafunce ta tunda ba a kirata ba tun lokacin. Ba dai wanda ya biye mata don bashine a gabansu ba su yanzu dole kuma ta dawo aka hade kan jin yaya za ayi dole su baffah ne da modibbo zasu biyan shi. Anan kuma suke jin labarin cewa suma din su Alh Nuhu har baffah buhari ma ashe an tafi dasu Abujan ga gidajen su da aka kulle zance ya gama bazuwa cikin gari ko ina ko a lokacin. Da farko sun dauka zancen wasane duk kazafine ko barazana don mahaifin nasu zai iya fitar da kanshi kan ko menene ya tasa haka kuma su basu yarda cewa wanan laifin shi ya aikata ba dukda wa yanda suka san lokacin sun fada masu gaskiya kan hakan. Hankali yakai kololuwan tashi kowa ya nufi inda yafi mai sauki ya zauna inda mafi yawan su a gidan gadon su suke don matan ga baki daya nan suka nufa suka zauna a nan diyan nasu da suke ganin basu iya zama cikin wanan gidan a yanzu suke samun su ayi maganan da za ayi din a lokacin wanan rikicin. Sauri nakeyi na isa gida dan hold on daya tsayar dani a hanya don nasan lokacin umma tana can ta tayar da hankalin ta ganin ban saba kai hakan ba gashi kuma na kasa samun layin umma din. Ina mamaki tun lokacin dana sawo kai na hango motoci a kofan gidan don motocin kawai kansu abin kayar da gabane saidai sanin dan filin namu in baki mata ba na fada a baya cewa motoci na yawan parking a wurin don hilan dake akwai garemu na parking. Haka na karaso a gajiye na parker motana dab da gidan mu inda nakan aje motan in shiga gida har Abdul duk a nan yakan aje motanshi. Haka kawai na dinga jin gabana yana yawan faduwa ban yiwa wa yanda na sama tsaye wajen magana ba . Ila dai nafito da ledan dana sayo masu tsaraban idi,iroko dana tafi din ledan a shake yake da kayan marmari sai dayan da tsaraban Ammar ne a cikin sa daya dameni in sayo mashi unders na maza . Tun daga dan matakalan steps din mu wani kamshi ya daki hancina amma haka na daure na karasa ina mamakin wanan wani irin kamshine kuma ko maniyace ta saka a part din su. Na turo kofan da sallama kamar yadda na saba shiga da sallamana gidan umma i am back na fada tun turo kofan don nasan ranan zansha fada sosai a wurin umma kan rashin kiranta in sanar da ita inda nake a lokacin. Saida maganan ya makale min don hango umma zaune tana sharan kwalla da nayi ga wasu mutum biyu a zaune tare da ita . Saidai sam basuyi kama da iyalan jinsin mu ba don mu din ba bace muke ba don daga hancin mu da giran idanun mu haka manyan idanuwa. Ban damu da ko suwaye a zaune ba lolacin na karasa da sauri zuwa wurin umma din ina tambayan ta da yarbanci su waye me sukazoyi me sukai mata kuma ? Kabo anty sahiba Ammar ya fada daga inda yake zaune a takure na amsa da Ele wooo sai na juya da pigin ina tambayan shi . Waitin dey come do here sunyiwa umma wani abune maimakon umma din ta ji dadin damuwan da nayi da ita din sai kuma ta juya fada dani kan in natsu mana. Wanan shine wanda yasan komai na mahaifin ku sai yanzu ya gane inda muke da wanan maganan ya taso ya dade yana neman mu sai yau ya samu zuwa inda muke. Oda na fada ina mikewa don ni na gaji da burgan mutane a yanzu garemu basu nememu ba a cikin wahala sai lokacin da dadi yazo muna kowa ya taso yana fadin shi shine . Duk bina sukayi da kallo yayin da umma ke fadin ba zaki gaida su da zuwa ba wai meyasa kike hakan wani lokaci. Sai lokacin na dago kai na kallo inda suke daga inda nake tsaye nace you are wellcome ina wuce wa abina . Cikin kunan rai umma din ta kara dakatar dani lokaci guda cikin daga murya lokacin har nakai kofa ina daga labule zan murda handle din kofan dakin. Na juyo ina fadin e dakun umma bafa wurina sukazo ba wa yan nan asalima ban taba jin ko labarin su ba don haka me zan tsaya nayi duk a cikin yarbanci muke magana suna kallon yadda muka juye a yanzu muka zama yaren karfi da yaji ba zakace mu din jinin Abbamu bane mutum mai turaci da rike kabilan shi na fulatanci. Yau sai ga iyali shi sun gani sun gani sun rikide sun koma wasu kabila ko al,adanmu sun juye mun koma kamar kabilun kudu sak. A take idanun shi suka kawo ruwa lokaci guda ya fara magana da tun da ya gabatar da kanshi gun umma basu samu daman yin wani magana ba suke kuka daga shi har ita kuwa din. Look miss Sahiba munzo nan kan pieces ne ba wani abinda kike tunane bane ya kawo mu asalima munzo ne don mu roke ku gafaran abinda ya faru mukayi maku gaisuwan rashin mahaifi dan uwa jigo a garemu watau mahaifin ku. Wani kallo na jefo mai dan yan kan na kiris su tashi min a lokacin badon gyaran Allah ba jifa wai gaisauwa sukazo yi muna na mahaifin mu a yau din nan. Kamar yasan abinda nake kallon su dashi naji yace don a lokacin da abin ya faru munzo daga can Hong Kong inda ya barmu da niyar zaizo yayi aiki a nan sai labarin mutuwan shine ya rikemu. Munzo mun nemi dcp Ali lokacin don shi mukafi sani a cikin yanshi amma sai ya dauka wani abune na daban ya kawomu gareshi lokacin . Don ya zaci munzo kan wani zancen kudine ko wani abu da zamu karba a wajen marigayi din mun nemi mu ganku sai aka fada muna kuma wai kun bata. Wanan zancen ya daure muna kai a karshe dai haka muka gaji muka koma ba tare da mun gane komai ba akan ku wurin su sai gashi lokacin da kuka fara wanan case kwatsam labari ya riske mu. Yasa na turo a tsayawa case din sai kuma naji ance wai ke kince kin yafe komai daga garesu illa fili kawai kuke so a baku. Ni kuma nace ban yarda ba a yanzu komai da suke ganin sun sameshi a yanzu sai sun mayar dashi ko kuma su hadu da mumunan fushi a garemu. Musan wanda ya mutu lokacin sane yayi amma ta sanadin su ya tafi don haka mu a wurin mu sune suka kashe shi don haka muma iyalan shi ba zamu kyalesu ba a yanzu da gaskiya ya fito. Fuskan shi ko muryan shi nake kallo a lokacin na rasa wani daga ciki ya dauke min hankalina haka ? Saidai maganan shi na karshe da yayi cewa su iyalan Abban mu ba zasu kyale a yanzu ba yasa naji wanan kalamin a wani bambarakwai. Su iyalin shi ta ina ya akayi suka zama iyalin shi din yanzu don haka duk wanda zai kiraku akan waye ya daukaka kara a babban kotun Abuja kuce dashi. Babban yaron shine mukhatar usman marwa ya daukaka kara a yanzu don ku kungama naku fanin an gani yanzu nawa fanin ne wanan . Ku gafarce zance a karshe dani da abokina na rashin zuwa gareku a lokacin daya dace ace munzo mun taimaka maku alokacin da kuke cikin wahalan rayuwa. Duk da hakan ba laifin mu bane an boye muna komai daya shafe kune a lokacin don haka kada ku zargemu da laifin hakan gare ku. Da fatan zaku fahince mu don Allah ku yafe muna kan abinda son zuciyar wasu yasa muka aikata maku na rashin zuwa gareku na tsawon lokaci. Saiya dukar da kai yasa kyale yana sharan hawayen dake zubo mai lokacin a idon shi ganin hakan yasa na juya zuwa dakina da sauri. Saman godo na fada ina wani kuka mai tsuma zuciya kafin na koma tunane alokacin don ina ganin mu munfi kowa matsala aduniyan nan. Daga wanan zuwa wanan matsalan sai yaush ne zamu koma kamar kowa mu shiga yan uwa muma mu san muna da dangi kamar kowa a duniya ? Sallaman su na fara ji suna ma umma sallama hakan baisa na fito ba har yakai na daina jin muryoyin su a falon namu haka yasa na gane cewa mu kadaine a gidan lokacin. Ban fito falon ba sai safe na tashi don zuwa wurin aiki har lokacin akwai rashin walwala ga umma dole na tsaya naga ta karya kumallo. Bayan mun gama karyawa ne na mike naje na shirya sallama nayiwa umma na fita zuwa aiki misalin sha daya rana sai ga wayam umma ya shigo mmin ZAINAB IDRIS MAKAWA ANA DARA GA , , , , , , , , 8️⃣9️⃣BY, , , , , , , , , , , , ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , , , , , , , , BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AL AKHIR, , , , , , , , , , , ONLINE PAID NOVEL YAR UWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA BA TARE DA HAKKIN KOWA BA DON BIYA KI TURA DARI BIYAR 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK 08036959257 ALLAH SARKI AI RAINA BAYA BACI YANZU DON KIN FITAR DON NASAN AKWAI RANAN HADUWA SEE U👋👋👋👋 Kira bisa kira haka muke samun kira a lokacin saidai amsa dayane shine bamu san wanan zancen bamu don haka dole mutum ya kyale mu. Karshe ma kashe layukan wayan mu nayi sai can dare nake kunnawa in shiga median naga sakonin da suka shigo min a yinin ranan. A irin hakane har ya Abubakar ya samu ganina a online yai min magana na bashi amsa da muna kalau ga dalilin kashe wayan namu a lokaci. Yake fadin cewa hankalin shi ya tashi kwarai da rashin jin layukan mu a kunne sun dauka wani abun kuma ya faru damu don shi a yanzu hankalin shi baya kwanci. Muna kalau na bashi amsa tare da tambayan shi iyalan shi dasu Faiza ya amsa a gundure da alaman akwai abinda yake cin zuciyan shi a lokacin. Yake tambayana wanan din ya kara dawowa ban san wa yake magana a kaiba yasa na tambaye shi yace wanan dai da umma tace yaron baffah marigayine shi daya bullo yanzu a kan case din ku. Banda time din wanan a yanzu don ban san meya kawoshi gare mu ba a yanzu din don haka bai a gabana na bashi amsa. Cikin mamaki yace dani sister kin san ko waye wanan mutumin a yanzu kuwa duk da mahaifin kune ya dagashi a baya har ya zama haka a yanzu . To shidin shine mai ma,adanai fiya da lissafin a cikin kan nan shine Mukhatar usman marwa da kike ji nima cikin mamaki din nace shine wanan din yace kwarai kuwa mahaifin kune ya dagashi har ya zama haka a yanzu din. Ashine dalilin shi na son shiga zancen ku a yanzu din a iya binckena a kanshi na gano bada wata manufa yazo gareku yanzu ba. Illa son da yake ya rama alherin mahaifin ku a gareku yanzu din sai dai ya dauki zancen kashin baffa da akayi da zafi don haka yake son a gano kaomai daga wanda ya hada plan cewa a kashe shidin yake son sani yanzu. Sai naji yayi shiru na sake fadin hello yace ina jinki sai dai ni jikina na bani cewa daddy a wanan katon ba zai iya tsalake wanan sharian ba shima idan ya tsalake na kaduna. Brother ban gane may kake nufi ba yanzu yace eh wanan karon kinsan tunda case din yakai su Abuja shariace za ayi sosai ba irin na kaduna ba. Wanda a karshe zai iya shafan kowa gaba daya nasan zasu durkushe ba zasu rage dako allura ba a hannun su. Wait a minutes nifa zan kirashi in fada mai wanan abin ya isa haka a yanzu sunan family din mune zaici gaba da baci ko yaushe a karshe kuda ke tasowa daga baya mutane zasu zo basu yarda da kuba ma. Kai ya gyada min yace masha Allah da kike da wanan fahintan haka kike da tunane irin na maza kike da tausayi da jin kai irin na mahaifin ki. Duk wanda ya kashe wani zaisu hadu a gaban Allah wata rana don shima bazai zauna gadin duniya ba ai dole yaje inda ya tura dan uwan shi. Yau dukiyan da sukai haka don kanshi idan an nema babu ko rabin shi a hannun wasun su don ba dukiyan Allah da Annabi bane don haka Allah ba zai barshi a hannun su ba . Da ace na tsaya na saurari wanan mutumin da na karbi lambashi a lokacin nasan zai mun amfani a yanzu zan kirashi in fada mai abar zancen haka ya bar duk mai hannu a ciki da Allah. Saidai ko umma ina jin bata karbi layin shi ba har ya tafi ranan au yazo wurin ku ke nan ma ashe nace yazo ranan da dare na dawo na sameshi a gidan mu tare da umma. Indan hakane zan tsanata binciken nomban shi ko zamu samu zan turo maki ki gwada yi mashi magana aji ko zai yarda ya janye zancen a yanzu. Duk da ya kamata ace na dauka don mahaifin modibbo yana cikin zancen ya kara ban wanan shawaran sai sam ban dauki hakan a zuciyana ba. Illa kawai yadda naga iyalan su suna cikin wani hali a lokacin yasa wani imani da tausayin hakan nasu ya kama zuciyana don nasan zafin irin hakan tun ina karamata. Kawai nasan wanda ya mutu ya mutu ne wanan sharian tsakanin su da Abban mune gobe kiyama don ko ance su dawo da wanan dukiyan a yanzu ba samun shi za ayi duka a hannun su ba. Haka dai mukayi sallama da ya Abubakar din da yake faman ban hakkuri kamar kullun yana kara tausan zuciyana kan abinda akai muna din. Mun gama na kashe wayana saidai maimakon in kwanta in huta sai barcin ya gagareni na fada tunanen duniya kuma. Wata zuciya tana izani kan me zance abar zancen a yanzu bayan su da farko basu tausaya muna ba sunyi son ranau sun rabamu da mahaifin mu. Su suna tare da nasu a cikin jin dadin rayuwa wanda mu sam bamu samu hakan ba don bamu san dadin mahaifi ba a yanzu. Iya abinda Allah ya debowa Abban mu ke nan a lokacin wata zuciya nawa ya fada min don mutum bai wuce lokacin shi ai. Washegari na fadawa umma kaf yadda mukayi da ya Abubakar din tayi dan shiru kafin tace yana da wuya yanzu mukhatar ya janye wanan zancen yadda ya dauke shi da zafi haka. Saidai a gwada yi mai maganan amma abune mai wuya yanzu ya yarda don irin amanan dake tsakanin shi da mahaifin ku a baya don marigayin ya daukeshi tankar wani dan uwa da suka fito ciki daya dashine. Amma mu munfi kusa da Abba din a yanzu hukuncin Allah muke so a kansu bana mutum ba tun farko ma da ansan wanan abu zai shafi har inda ba a zata ba da anbar zancen dukiya iyaka su dai san muna raye a duniya bamu mutu ba. Yanzu ko gashi Ana dara ga dare yayi don shi ma modibbo dayasan da hannun mahaifin shi cikin case din nan da bai yarda tun farko ya tazzara zancen haka ba ko don rufin asirin mahaifin shi din. Umma kike ganin bai sani ba yayi hakan yasan komai shidai mutum ne mai tsayawa yayi aikin shi da gaskiya kawai don ko yanzu bawai ya damu da abinda zai faru kan mahaifin nasa bane ai tunda yayi ba daidai ba ai kinji abinda ya fada ranan kan daddy. Yace yana ganin daddy yasan komai shine dalilin da baison a daga zancen nan a yanzu to kowa keda hannu a cikin case din nan dolene ya fuskanci hukunci daidai abinda yayi don haka a bari ayi sharian daya dace. Har na shirya na fita zuwa wurin aiki muna zancen da umma nan muka barta gida ita kadai kowa ya fita zuwa nasa tsabgan. Saidai ina isa zan shiga office dina idona yayi arba da oga sha,aban tsaye suna magana su ukku haka yasa nagane ashe yana kasan ke nan. Office dina na shiga direct ganin hankalin su ya dauku ga maganan da sukeyi a lokacin na shiga na zauna na fara aikin daya dace a lokacin Banfi minti biyar da zama ba oga Jimo ya shigo office din da wasu takardu yana min bayani akansu wanda ya kasa gano shigewan kudin. Bayani komai yadda yake har zuwa karuwan da aka samu akan yadda abin ya gudana nayi mai sai gashi yana washe bakin shi don jin dadin hakan. Don dama ya rikece shi a zaton shi kudi ya shige wani hanya da bai fahinta ba sai gashi na walwale mashi komai a saukake. Ya juya zai fita a lokacin oga sha,aban ya shigo office din idanuwan shi tarr a kaina har ya karaso inda muke nan oga jimoh ya fara rawan jiki don ganin shi. Mikewa nayi na gaidashi da zuwa ya amsa min tare da jan kujera ya samu wuri yakai zaune a cikin office din nawa. Fita jimo din yayi da sauri daga office din ya barmu mu biyu a lokacin shiru nayi bayan na koma na zauna ina dan kallon fuskan laptop dina. Sai jikina ya bani cewa kallona yakeyi a lokacin haka kawai naji in dago kai don jin shirun wurin yayi yawa a lokacin. Ina dago kai zargina ya zama gaskiya don ni din yake kallo a lokacin da sauri nayi kasa da idona cikin jin nauyin shi don idon daya tsura min din. Muryan shi naji a lokaci guda saida gabana ya fadi yana fadin idan ba mutum ya kira layin ki ba Sahiba ke baki taba kiran mutum kiji lafiyan shi. Abinda ya fito bakina lokaci daya da dago kaina shine iam sorry sir na fada cikin wani irin murya mai rauni a lokacin. Sorry for what ya tambayeni ya tsureni da idanuwan shi nima nayi kasa da kaina don bazan juri irin kallon da yake min ba a lokaci. Mikewa naga yayi ba tare da yai magana ba ya juya zai fita a office din saida yakai kofa ya juyo ya dan kalleni nima kallon nasa nakeyi lokacin. Ya fara fadin i will call you letter don ina son muyi magana dake mai muhinmanci sosai kafin na tafi yanzu naga akwai aiki a gaban ki yana gama fadin hakan ya juya ya fice daga office din. Tun bayan fitan shi wanan wunin aikin ma dai tunane yaso ya rinjayeni lokacin don ina tunanen me yake son muyi magana akai dashi kuma ? Shin a kan aikine ko akan sharian mu zaiso yasan wani abu kai ko kuma wani zance ne na daban ya taso kuma ? Sai dai kuma lokaci guda na share komai na shiga yin harkan gabana a lokacin don tunanen ba zai fitar dani ba a wanan lokacin. Kamar kullun lokacin tashin mu wurin aikin yayi don haka kowa yana rahaman zuwa gida na hada dan abinda na shigo dashi office na fito don zuwa gida. Sama sama nake amsa gaisuwan da ake jefo min ina sauri in fita don ina son in watsa ruwa a jikina don yadda nake jin jikin nawa a lokacin yana son yi min nauyi. A kofan fita muka kara hadewa dashi cikin tawaga saidai wanan karon akwai bakin fuska da ban sansu a wurin ba gaisuwan sama sama nayi masu na nufi wurin motata dake aje. A fakaice yake satan kallon yanayina nayi dan duhu na rame ga yadda yasanni a baya duk da yanayina ya nuna akwai damuwa a gareni daka kalleni. Karfe da tsiya duk saurin da nakeyi sai gashi na shiga taki tashi kuma lafiya kalau nazo da ita wurin aikin ganin yadda nake fama da motan ya turo min wani kan cewa na fito nabar motan a duba min za a sameni gida dashi idan an duba. Dole motan shi nafito NB a shiga drivern shi na nan lagos ya kaini gida saidai isata gidan kuma na samu wani labari mara dadi wai an kulle su daddy a abuja daga sunan yi masu tambayoyi aka rike su a can gaba dayan su. Banji dadin jin wanan labarin ba duk da sun cancanci hakan koma fiye da hakan kawai dai barin su a yanzu shine karin rufin asirin family din mu baki daya duk da duniya ta riga tasan da komai. Don haka zaisa a karshe yan uwa da yawa daga cikinsu su koma marayu kamar yadda muma muka taso marayu din a yanzu wata sharian sai a lahira. Ni kaina yanzu idan ina wani abin har mamakin kaina nakeyi kamar ba Sahiban dana taso da hayakin kai bace a baya yanzu. Tun zuwan ganin gida yola danaga irin halin rayuwan da suke ciki a can da kuma irin hudan da suke muna ga kuma taimakon laluran dake kaina da wani kakan mu ya bani nayi amfani dashi tun can sai abubuwan da nakeyi na rawan kai yanzu suka rage min sosai. Yanzu kan hankalin kowa kusan a tashe yake don ko ta fanin daddy wanan tsare shin da akayi din har ana masu rade,radin cewa suma za a zo a rufe nasu gidan hakan ya kara tayar da hankalin iyalin daddy din sosai wanan lokacin. Ga bangaren hjy karima yakai baby ta dawo gida don fitinan da sukayi da kanwar mijin ta kan abinci mijin kuma na dawowa gida bai tsaya bincike ba ya hau baby din da duka . Wai don me zata hanawa yan uwan shi abinci tayi masu wullakamci kan abinci shida gidan shi. Ko ubanta Ali dcp bai isa ya hanashi yiwa yan uwan shi abinsh ba balle ita yar gadon mugun abu kawai ita kuma tace ai duk su dine yan gadon mugun abu. Shida mahaifin shi suka yanka dan uwan su yakan rago saboda rashin imani nan suka taru dashi da kanen shi dake gidan suka linkida mata kashi da kyar ta samu makwabtan su suka shigo suka kwace ta daga hannun su. Shine ta dawo gida don jinya saboda taji jiki sosai hjy karima a yanzu tayi data sanin hada zuri,a dasu abinda daddy ke mata gudu ke nan ashe ta kasa fahintar shi. Sai yanzu take gane abin bayan an makara kuma ga karamin ciki dake jikin ta yanzu babu yadda zasuyi yanzu da ba cikin nan ita kawai data kashe auren kowa ya huta hakana yarta ta koma makaranta a yanzu tun bai batawa yarinyar lokaci ba. Saida kyat modibbo ya lalashe ta tayarda don da tace duk abinda za ayi ayi sai ta zubar da cikin jikin baby din cikin hasala. Can gidam gwaggo hari kuma ta kasa gane kan danta sai dai idan ta tambayeshi yace mata babu komai gashi bai walwala ko kadan a lokaci. Ana haka ya tarkata kayanshi da rana tsaka yace zai tafi shi sam gwago din bata so hakan ba amma ba yadda ta iya dole ta saka mai ido ya tafi. Saidai a zaton ta kafin ya dawo ya manta da komai yasa ta kyaleshi a cikin yanayin da yake din ya tafi kai inbanda abin maza da basu raina mace idan suna aonta. In bashi ba ina zaI kai wanan yarinyar Sahiba da idanuwanta suke a bude karr da duniya haka don haka taja bakin tayi shiru don kada zancen ma ya fita har wani yaji shi. ZAINAB IDRIS MAKAWA ANA DARA GA , , , , , , , , 9️⃣0️⃣BY, , , , , , , , , , , , ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , , , , , , , , BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AZ ZAHIR, , , , , , , , , , , ONLINE PAID NOVEL YAR UWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA BA TARE DA HAKKIN KOWA BA DON BIYA KI TURA DARI BIYAR 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK 08036959257 ALLAH SARKI AI RAINA BAYA BACI YANZU DON KIN FITAR DON NASAN AKWAI RANAN HADUWA SEE U👋👋👋👋 A hankali na tako zuwa inda wayan ke jone a jikin chargi dana shigo na samu akwai wuta a lolacin na makala wayan a caji na shiga bandaki. Kallon layin dake kirana a lokacin nakeyi don ban san wanan layin dake shigowa dakiran a lokacin. Na dauka da sallama ina karawa a kunnuwa na a daidai lokacin da me kiran nawa yayi sallama shima a bangaren shi jin muryan na mijine yasa na kara mamakin haka ina sauraron maishi lokacin. Gaisawa mukayi da harshen turanci saidai duk da hakan ban sheda muryan maishi ba kafin maishi din yake fadin nasan baki san mai kiraki ba ko nace eh a sanyayye. Ok kina magana da mahaifin Al,mustaphane mijin gwaggom ki harira daga nan kaduna da fatan kuna lafiya. Fadin hakan da yayi yasa na kara mai wani sabon gaisuwa na mutunci da girmamawa lokacin guda don ina ganin mutuncin mutumin a idona gashi duk kotun da muke shiga tare dashi muke zuwa kotu din. Da zaran mun fito kuma zamu gaisa yayi muna bangajiya tare da bamu kwarin gwiwa akan abinda muke tunkara a gaban mu. Tambayana yayi ina umman mu da dan uwan mu nace dashi suna lafiya kalau ya furta masha Allah kafin dan shiru ya sake biyowa baya. Kafin kuma yace Sahiba dalilin da yasa na kiraki akan zancen danane mustapha dan uwan ki da fatan zaki natsu ki saurareni. Wani abu ya farune da mustaphan na tare shi da tambaya a dan razane yace no no na yana lafiya saidai ba lau ba saboda ke sahiba. Mustapha yana sonki yana kuma ra,ayin auren ki a matsayin matar shi ku zauna tare wanda idan hakan ya kasance zamu fi kowa farin ciki da hakan. Shiru nayi ina jin abinda dattijon ke fadi a lokacin wanda yazo min a bazata idan danshi yana sona shine zai fada min ba dan nasa ba ko haka su sukeyi a nasu al,adan koko son danne yasa shi ya tunkareni da zancen haka kai tsaye. Ban iyacewa komai ba sai lokacin da naji yaci gaba da fadin zamuyi maraba dake a cikin family din mu zamu rikeki tankar irin rikon da mukewa dan mu mustapha dan daya kuke dashi a garemu. No uncle ida kace kai zan yarda da hakan don zuciyat ka akan mu me kyaune da kaida danka nasani amma ita gwaggon mu akwai wani fassara da tayiwa rayuwana da take kallona dashi a idon ta. Saidai kamar yadda ka fada din ni yace a wurin ka uncle na sheda hakan a gareka gara dai in zauna a hakan a matsayin ya a wurin ka wace ko yaushe matsala ya tunkaromu zaka iya tsaya muna akanshi. Amma aure ko wani alaka irin haka ban taba jinshi a zuciyana ba face kallon dan uwa da nake masa akoda yaushe a idanuna. Shiru yayi kafin yace dani ki dai kara tunane akan maganata don yanzu haka akan wanan maganan a halin nan da ake ciki mustapha yana fuskantar barazan sonki a zuciyar shi sosai kuwa. Aiko ya daina uncle don shi din yayane kawai a gareni wani abu mai kama da so ko wani so uncle na gode amma wanan bamai yuyuwa bane ka tambayi matarka abinda suka fada ita da mommy ta gidan daddy a kaina ranan. So nagode da kulawan ka garemu da fatan wanan maganan bai bata ma rai a yanzu ba sai anjima na kashe wayana ina sauke numfashi don mamakin daya cika min zuciya a lokacin. Wayane a hannunta tanayi a lokacin da gani wayane mai muhinmaci sosai a gareta don yadda ta maida hankali tana sauraron wayan a lokacin. Har yarta babban tazo ta bugeta tana fadin maza mai aiki ta wuce dasu zuwa garden din gidan kafin ta fito yaran suna kuka haka mai aikin ta kwashesu. Amma bai taba nuna min alaman hakan ba sam saidai nasan da cewa yana yawan kulasu don kusan ma shine wanda ya dawo dasu gida suke fada ta a bangaren ta . To ki kula ki mai da hankali don abinda zuciyana ya fara zarga min ke nan a yanzu duk da yanzu din ba komai a tsakanin su. Zaune kawai take tana jin wani irin masifa yana taso mata wanda bata iyama controling din kanta a lokacin don yadda take jin kanta din. Wayan ne ya katse ba don sun gama fadan zancen da sukeyi ba lokacin hankalinta ya tashi ta mike daga zaunen da take ta fara yawo a dakin a cikin masifa. Abincin ranama gashi tana kallon an dafa irin abinda take son ci amma ya gagareta ci a lokacin sai faman kutawa da takeyi tana hadawa da tsuki. Wanan wayan na mahaifiyar ta ya tayar mata da hankali sosai a ranan duk da tasan cewa shi din mutum ne da baida ra,ayin yin mata biyu a rayuwan shi yasha fadan haka tanaji. Idan wani abu ya hadata dashi yakan ce da ace nime ra,ayin kara matane a rayuwana Nazifa da yanzu na dade dayi maki kishiya a gidan nan . Wanan kalamin yasa take masa duk wani iya shegen da takanyi wani lokaci tunda taji yana furta hakan tasan ta rufe kofa ke nan babu wata shegiyan da zata shigo mata gidan mijin ta a lokacin kuma da sunan aure. Tsuki taja a karo na barkatai a inda take din kafin ta dauki waya tana laluban layin yarta dake aure abuja kuma abokiyan shawaranta. Ta samu layin ya shiga sun gaisa suka dan taba hira akan mahaifin su inda yar nata ke fada mata cewa ke dai jiya an barmu munga su baba wallahi. Au wai dama ko ganin su ba,a barin ayi ne ta tambaya cikin mamaki sai yar nata tace wai keko kinga irin matakan da aka daukane akansu kuwa ? Kissa fa ake zargin su dasunyi tare da hamdame dukiyan mamacin mu dai kan ai su baba sun bar muna abin fade a cikin rayuwan mu. Gashi zancen ya karade ko ina don har wata yar mijina ta kirani don iskanci tana fada min wai ashe abinda ya faru da mahaifin mu ke nan ana zargin shi da kisan dan uwan shi. Inko hakane gaskiya dai munyi hasara sosai ace mahaifin mu yayi kisan dan uwan shi saboda arzikin shi, , , , Naziface ta katse ta da fadin keme kikace da ita anty tace Nazifa me zan fada kuwa tunda sun ja muna wanan bakin sunan a duniya kuma. Mu dai yar iskan yarinyar nan ita da uwarta ai sunja muna tsiya yanzu yan iskan mutane kawai da basu san mutuci ba a rayuwan su. Haba nazifa don me zaki zagesu akan gaskiyan su suke fa su don su babane basu kyauta ba kema kin sani a kaddara mu akaiwa hakan zaki iya kyalewa kiga suna cun dukiyan mahaifin ki suda iyalin su kiyi shiru alhalin kikai lokacin da zaki iya ja dasu. Kuma jiyan naji ai su baffah hamza na maganan cewa ita madam din tace zata kira a sassauta akan yadda aka dauko tsarun ai kinga kuwa intai haka ta kyauta muna gaskiya. Wai wata madam ke nan nazifa ta tambaya cikin son jin amsa tace yarinyar mana ai haka ake kiranta da madam sahiba . Wai kinsan ko akanta dama na kiraki yanzu wai ashe son baban su maryam takeyi yasa ta lake mashi haka ashe soyayya suke dashi ban sani ba ? Ke nazifa waya fada maki wanan maganan kuma yanzu ana wanan halin wake ta batun wani soayya can kuma ? Anty ke nan dama aiba mutuwan mahaifim nasu ya damesu banesu bane su zancen dukiya ya damesu a yanzu don haka a sake muna mahaifin mu suje suci dukiyan su daya dama. Idan fa gaskiya tazo ana cire son kai a cikinsane nazifa kindai san su Abba basu kyautawa zumunci ba gaskita koda ace sun jawosu ajiki kuwa suna kyautata masu ba su watsar dasu irin hakan da sukayi kai koma ace din suna a hannun su basu dai kyauta ba gaskiya sai dai kawai ayi sha,ani a yanzu kawai . Anty kardai ace kin fara yarda da lamarin wanan munafukan yar iskan yarinyar nan a yanzu har kima tausayin su nifa har yanzu ban yarda cewa su baba suka kashe masu mahaifin ba Allah ko. Amma kinsan baba zai iya aikaya fiye da hakan dai ko to don me yanzu zaki tsaya kina wani konkonto a zuciyar ki akan haka . Sun dauki lokaci duk inda ta fito sai yar nata ta hasaka mata saidai hakan baisa ta yarda da abinda yar uwar nata ke fada mata ba a lokacin. Mommy ne zaune bayan fitan yaranta daga dakin da kowa ya dawo daga aiki ya shigo mata da dan tsaraban da sukan kawo mata duba ga ranan ayi albashi yasa ko wace ta shako mata leda da abubuwan bukatansu wanda suka san zasu nema a ranan. Dama tana tunane akan hakan sai yanzu gashi yaran sun shigo mata da abin arziki irin haka wasu hawayen tausayi yazo mata lokaci guda. Ashe akwai ranan da zatazo masu irin haka duk irin dukiyan da take ganin sun tara a gaban su amma sai gashi ba aje ko ina ba har rayuwa ta fara juya masu baya haka ? Yau badon yaran sunyi tunanen irin haka ba ai da bata san yadda zasuyi a rayuwan su duk da modibbo na iya taimaka masu sosai tun ranan da mijin nasu ya tafi. Saidai duba ga yanayi da kuma yawan su ba lalai bane komai ya wadatace su a yanzu yadda suke so don dole kudin da yake bata tayi wani lalura dashi ai. Gashi kamar yadda sukayo mata sayayya haka suka dan kwatanta suka sayowa hjy karima da yaranta itama suka kai mata. A zaton mommy din hjy karima ba zata karba sai gashi sun dawo suna fada mata cewa ta karba a cikin jin dadi kuma har da godiya ga hakan da sukai mata. Da alama kuma sun bata kudi duk da basu fada mata hakan ba amma tunda suka iya aje mata kudi itama tasan zasu kwatanta hakan ga abokiyar zaman nata. Ashe ko wani mutum da Allah ya hadaka dashi yana da ranan shi a duniyan nan yau itace ta sanadin Sahiba alheri ya shigo mata ya part din ta haka ta juya tana kallon kayan dake gaban ta a cikin babban leda guda hudu wanda sayayyan Faiza yafi yawa daga ciki. Sahiba yarinya ta kwaso halin mahaifin ta ke nan da halarci za a ce bata fahinci irin rikon da nake mata a zuciyana ba ? Wayan tane yai kara ta dan juya a kasalance tana duban wayan da wanda ke kiranta a lokaci guda sunan hjy harira ta gani da hjy Hari ta mika hannu ta dauki wayan tana karawa a kunnen ta. Gaisawa sukayi tare da jajanta zancen rashin dawowan daddy cikin su har tsawon mako biyun nan kafin hjy hari din a bangarenta tace wai kinsan me tace sai kin fada. Yarinyar nan Sahiba fa ina ganin ranan duk abinda muke fadi a kunnen tane saida ta gama sauraren mu tayi sallama ta shigo gidan ku. Meyasa kikace haka hjy hari ta fada tana gyara zaman ta tace bari kedai sako ta bani ta wurin Alh cewa ya tambayani abinda na fasa kanta da the boy ranan a gidan ku ? Ita sahiban ta fadi hakan da bakin ta hjy hari ta amsa da wallahi abinda ya fada min ke nan yau da safen nan don gaba daya yaron nan yaki daukan wayan mu sam tun ranan daya bar kasan nan. Shine shi Alh yace yasan abinda zaiyi nasan ya kira layin ita sahiban ne sukai magana kan shi boy din ta nuna masa hakan. Idan ko har haka wallahi abinda ake fadi kan yarinyar nan na shu,imanci gaskiyace hjy hari wai kode da gaskene ta mugun kungiyan mayu ne irin na kudu bamu sani ba ? Yarinya kamar aljana kowa yasata a gaba sai taga bayan shi hjy hari tace aina gani don ni abin ya ban tsoro sosai wallahi. Wai mema muka fada a ranan game da itane wai don ni har na mata da anyi wanan zancen shi nake son tunawa a yanzu ? Ba wani abu bane illa man ta kara tuna mata abinda kowa ya fada game da sahiba sai kuma suka koma kame kame a tsakanin su. Bayan na gama shiri na na juya zan filo wurin umma wayan ta sake daukan kara na juyo zuwa inda take na dauka Sir oga Shaaban ne a layin lokacin. Sai lokacin na tuna da yace zai kirani da kuma zancen motan dana bari da sauri nayi receiving din wayan karya katse. Muryan shi naji a dan sanyaye yana mun sallama na amsa tare da fara gaidashi ya amsa har lokacin muryan shi yana a yadda najita da farko. Bayan mun gaisa dan shiru ya gitta a lokacin kafin yace dani naso nazo da kaina saidai hakan bai samu ba don nazo family house din mune da yamman nan. Ya zancen maganan mu ya tsaya dake don ina son yin aure a cikin dan kwanakin nan kada koda yake wanan ba zancen yi a cikin waya bane zanzo har gida in sameki muyi shi don aure nake son yi dake Sahiba. Nervetheles motan ki na a waje yanzun nan a kofan gidan ku idan kin fito zaki gani zan saka subada key a hannun Abdul. Ok nace a cikin wani yanayin dana shiga saboda zancen daya gama yi yanzu daya zo min a bazata don sam ban taba tsanmanin irin wanan maganan ba a bakin shi. Wai dama da gaske sir Shaaban yakeyi ne da wasan da muka hadawa mommy shi a can kasan da mukaje komu ita din ta dauka kusan gaskiyane zance. To wai ko a kanshine yanzu yake son juye abin ya zama gaskiya a idon jama, a ko kuma wani abin ne ya sashi haka gareni. Don sam ban taba jin wani mahalunki da namiji a cikin raina da sunan so ba har wanan rana ta yaya zancen aure har mutum biyu zaizo min a rana daya kusan lokaci guda kuma. Fitan da banyi ba ke nan zuwa wirin umma na dinga jin bacin rai a zuciyana dole na samu wuri na kwanta na share zancen ga baki daya don ina son natsuwa. ZAINAB IDRIS MAKAWA ANA DARA GA , , , , , , , , 9️⃣1️⃣BY, , , , , , , , , , , , ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , , , , , , , , BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AL BATIN , , , , , , , , , , ONLINE PAID NOVEL YAR UWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA BA TARE DA HAKKIN KOWA BA DON BIYA KI TURA DARI BIYAR 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK 08036959257 ALLAH SARKI AI RAINA BAYA BACI YANZU DON KIN FITAR DON NASAN AKWAI RANAN HADUWA SEE U👋👋👋👋 Affuwan yan uwa kwana biyu bakujini ba wallahi ba laifina bane matsala wutan neper ne da muka samu har tsawon kwana hudu dan Allah ai min affuwan yan uwa. Ina zaune sakon ya Abubakar ya shigo min na duba naga lambane da sunan maishi na dade ina maimaita sunan a raina kafin na aje wayan don nasan a lokacin dare can a kasan da mai layin wayan yake yanzu. Don akwai wanda zan iya samun shi a nan idan yana Nigeria saidai ban gwada kiran wanan layin ba tunda yace baya kasan yanzu yana kasan waje. Washegari kan kona ce ina da karfin gwiwa a tare dani nasan karya na fada don bana jin wani lakka a tare dani har yakai umma ta fahinci hakan a gareni . Take tambayana abinda ya sameni nace nima haka na tashi ina jin raina yana baci sosai a ranan gashi kuma dama na boye mata zancen wayoyin kowa da nayi jiyan don fada mata zai iya saka umma tace zata ban wani shawara dagane da hakan. Kallona umma tayi ta sake fadin anya kuwa ba abinda ke damun ki ga haka don yanayin ki gaba daya ya nuna kina cikin damuwa gaskiya. In kuma wacan zancen ne kika saka a ranki haka ai gara ki fitar da rai zaifi don su yanzu suke fuskantar nasu hukuncin abinda suka shuka din. Ba zancen su bane a raina kawai dai hakan na kwanta na tashi ina zama lokaci guda nake fadin hakan kafin na tambayi umma Ammar ko ya fitane lokacin ? Ta dan dago tana fadin koya fita bai wuce ya shiga part din Abdul bane don yau ba school ake zuwa ba balle ya fita haka da safen nan. Bata rufe baki ba ya turo kofan ya shigo falon mu nan ya fara min ina kwana na amsa a kasalance yake fadin jiya ban fito ba mun yi hira da dare lafiya nake kuwa ? Nace kalau jin suna yawan tambayana hakan yasa nayi kokarin nakai kwance a daidai lokacin da wayana ya dauki kara kira na shigo min a lokacin ke nan. Hannu na mika daga kwancen ina gyara kwanciya na dauki wayan na kara a kunne na ina fadin morning brother jin haka yasa Ammar ya matso kusa dani. Bayan mun gaisa ya tambayeni gida nace suna lafiya lokacin Ammar yace na bashi waya zaiyi magana dashi shi kuma din yana tambayana yadda mukayi da mutumin da alama zancen tsare daddy din yana damun rayuwan shi sosai a lokacin. Zankirshi ai na bashi amsa tare da fadin na bari time yayi daidaine da yadda nake son na kirashi kada muyi mai girshi. Ok kawai ya amsa min dashi nan ammar ya cabe wayan ya mike zuwa waje suna magana da bansan kona maye ba a lokacin. Saida suka gama magana da Ammar din kafin ya dawo min da wayan hannuna na karba naci gaba da magana yake fadin in ba Ammar kudi kafin yazo yayi registration din football team yake son shiga. Hararan inda Ammar yake nayi ina fadin shi da bai faye lafiya ba zaije shiga wasan kwallon kafa a yanzu. Nan dai ya din ya kara min magana na amsa da zan bashi nayi dan mamakin abinda ya hana ya turo maahi din ya amma kuma sai dan tunane yazo min lokaci guda na kodai ya dan shiga matsalane rashin daddy din nan na dan lokaci sai kuma shi ya Abubakar din naji tausayin sa sosai kan hakan. Bayan gama wayan mu na dannawa wanan layin kira har sai dayayi ta ringing ya kusa katsewa aka daga a cikin wani muryan maza mai amon wani sauti dake kada zuciyan ya mace lokaci guda. Hellow2 yake fadi daga ban garena na amsa nima da kya kafin nace i am Sahibat from lagos calling now. I know miss sahiba where d you get my number nace daga wani na sama kafin na juye zancen da fadin ya kake ya family din ka. Well, anyway duk muna lafiya nagode ya fada a gurguje kafin yake fadin ya mahaifiyar mu da dan uwana nan ma na bashi amsa da suna lafiya. Sai dan shiru ya biyo baya kafin yace dani anything else miss sahiba na nisa kadan tare da fadin nothing much dama akan case din su yan uwan mahaifina dakasa aka tsare a Abuja yasa na kiraka yanzu. I know saboda shi kika kirani din don idan bashi ba ba zaki kirani don mu gaisa ba ai ina da labarin cewa wanan dan iskan yaron yana neman layina ninace a bashi ai. Amma ban dauka take zaibi yai amfani da layin ba na dauka shida kanshine zai kirani kan barawon mahaifin shi da baida imani idanuna na dan runtse don jin zagin da yakewa iyayyena din da a yanzu su nake gani a matsayin iyayyena a duniya kaf. Enough mr mukhatar wanan matsalan mu ya shafa family din daddy mu bakai ba banga dalilin da yanzu zaka saka kanka a cikin family issue din mu ba. Dan murmushi ya sake kafin yace good ashe kuna da family yanzu har kin sanda dasu suma sun san dake da kike ikirari a kansu. Amma suka wullakantaku suka barku a cikin duniya kuna yawo ba wanda ya tausaya maku sai yanzun ne da sukaga bayi suke son ku har kike ganin su a yan uwanku yanzu ? Good idan wanan ne ai basu kade bane da irin laifin nan naga wa yanda ma sukeda karfi fiye dasu basuyi yunkurin neman mu ba sai wanan lokacin. And beside mu musulmaine musan cewa bawa bai wuce kaddaran ubangijin shi dan haka mun yarda da wanan a yanzu munyi imani da hakan. A takaice dai na gane kamar neman jin dadin yan uwa a yanzu ya rufe maki idanu har kina ganin kowa mai laifine a wajen ki don kawai , , , , Look mr ban kiraka don dogon zance ba a yanzu kawai kayi abinda ya dace kasa a sako masu mutanen su final mu mun barsu ga Allah understand na kashe wayan. Duk da umma bata jin turanci amma ta fahinci ba maganan dadin rai mukeyi da sunan wanda taji nakira din wanda tun lokacin ta dago kai ta mayar da hankali garemu. Meya hadaki dashi koba mukhatar din maiduguri bane kuke waya dashi yanzu na gyada kai alaman eh shidin daine . Maimaita tambayan ta gareni tayi ta sake jefo min tambayan da tayi min da farko meya hadaki dashi yanzu kuma ? Akan case din su daddy daine ya Abubakar ya matsa sai nayi magana dashi don a san abinyi don hankalinsu a tashe yake nan dai na fada mata yadda mukayi dashi din a cikin yare yadda zata gane. Wanda tun kan na kai karshe nake ganin wani irin kallo a fuskan umma din da take jefo min na takaici da jin zafin abinda nake fada mata din. Yanzun Sahiba kinga kin kyauta ke nan yadda kike kokarin watsa mai kasa a ido haka kan kokarin da yakeyi don mu ? No umma idan ba hakan nayi maiba a yanzu ba zai dauki maganan da muhinmanci ba sosai don kinga ya Abubakar a yadda ya daukemu bai dace muki nuna mashi goyon bayan hakan ba. Dan shiru tayi kamar tana nazarin zancen nawa kafin tace nasan da hakan amma shima bai kamata ace kin masa magana haka tsatsaye ba a yanzu. Shiru nayi don an riga an gama ko yanzu saura naga ranshi zai baci ya fitar da hannun shi a case din ko kuwa don yadda naji ya kira daddy da macuci yana da wuya idan bai saka anyi masu wullakanci ba fiye da yadda bamu zata ba ma. Shiru falon yayi kowa da abinda zuciyar shi ke raya masa lokacin kafin wayana ya dauki kara lokaci guda banyi saurin dubawa ba sai kusan ya katse na dauka ya Abubakar din ne ya kara kira wanan karon muryan shi da rauni yake magana wanan karon. Sahiba wanan guy din ya kirani kece kika bashi layina nace bani bace dama ya fada min yasan kana neman layinshi shi yace a baka. A zaton shi kaine ka turoni nayi masa magana sai naji ya Abubakar din ya dan sake murmushi kafin yace dani yace zai saka a daure ga baki dayan mu idan bamu fitar da baki cikin wanan zancen ba a yanzu. Ko muka kara matsa maku kuka kirashi zaici muna mutunci fiye da zaton mu kawai dai shike nan yanzu ai ku barshi yayi abinda zaiyi a yanzu din. Kada ki kara kiranshi a kan zancen ki barshi tunda har yake zargin mune muka turoki wai kici masa mutunci muna ganin idan munyi hakan zamuyi nasara kanshi don baida karfi kome a cikin zancen ko ? To mu sani ba wani barazana da yanzu zai dakatar dashi kan matakin da yake shirin dauka ku kyaleshi shida bakin shi zai furta ya janye akan zancen. Ok kawai ya iya ce min lokacin naji ya kashe wayan don wani murya dayazo wurin shi suna magana tunda na kwanta na juya ban kara magana da kowa ba don raina daya baci da maganganun dayayi din gun su yaya. Kai duniya bata da tabbas abinda baffah hamza ya fada ke nan kafin ya kai zaune yaci gaba da fadin dama na fada maku ai da wuya yadda mukayi da yarinyar nan ta canza magana kuma yanzu. Eh yanzun dai ai gara da mukaji daga bakin ta kaga mun fitar da zargin komai nasu a zuciyan mu, dama ai nasan Sahiba ba zata fada mai komai ba. Ya dai yine kawai yaji idan mun tursasatane kan haka kawai kowa ya kyaleshi yanzu a zuba mai ido. Ayi hakan mu dai dan saurara mu gani nan da dan wani lokaci kafin mu kara tuntubanshi da kan mu wanan karon. Da wanan shawaran har suka isa Abuja da yanzu zuwa abuja ya kamasu a cikin mota don dole ya Abubakar da bai saba da wanan harkan tafiya da mota ba ya kowa don dole. Saidai duk yadda sukayi don a bari suga su daddy din sun kasa ganin su don tausararan matakan da aka dauka a kansu. Wanan yasa dole suka juyo zuwa gida duk rayukan su a baci zuwa wanan lokacin sun saduda da cewa lamarin a yanzu yafi karfin su. Wanan dawowan ya kara tayar da hankalin kowa a family din mu kowa da irin abinda yake fada yanzu kan zancen wasu suce aima har an sa ranan kashesu. Wasu kuma suna fadin cewa a a ai yanzune ma za,a fara sharia dasu don wani cargo na kayan zinare da suka dulmuye a tsakanin su na dan uwan nasu da suka kashe. Hakana dai wanan zancen yayi ta yawo a tsakanin ba wanda ke fadan daidai da abinda ya faru dasu don ko wanda suka tafi don ganin su Abujan ba zasuce ga halin da suke ciki ba. A bangarena kuma dai duk da naso na kyale zancen na kasa hakan ranan da faiza ta kira wayana tana kuka take fada min wai ashe su daddy ance rateyesu za ayi ? Naji wani iri a lokacin amma tausayinta yasa na daure nake fadin ba gaskiya bane hakan don ko mu ba a nememu ba har yanzu kan zancen don ko nasan ba za ai wani sharia da bamu wajen ba a lokacin. Koma meye nasan ba zasu rufe sati biyu a can tsare ba don haka ku kwantar da hankalin ku ku daina jin jitajita hakana. Abinda ya daure min kai shine yanzu sam bana jin alaman mutane kaina a tare dani kamar da can da nake yawan jin su ko suke taso min haka kawai kamar ila har na gama komai da zanyi zan kwanta. Sai nayi wani tunane kawai na mike na nufi wardrobe din kayana na dauko wani jakkana na koma saman gado dashi na shiga laluben abinda nake nema a lokacin. Har nayi sa, a na lalubo abinda nake nema na bude kwalban na dan shaka kadan kafin na rufe na mayar ai ban kaiga dawowa bakin gadona ba tun lokacin na fita cikin hayacina. A wanan daren jumma,an dai abubuwan kaina saida suka taka min saida kyat umma ta samu suka dan lafa min ba tare da wani hayaniya ba kuma. Washegari ma sai ummace ta kai min dan ruwan tea nasha da kyat na koma na kwanta ba,a dauki lokaci ba wayana ya dauki kara ummace ta dauka tana sallama. Wanan mutumin mukhatar usman ne a layin yana jin muryan umma ya shedata suka gaisa yake tambayan ta lafiya mu tace Alhamdullahi sai dai Sahiba din ce take fama da laluran ta na jinnu da kan dameta wani lokaci. Ya danyi shiru na dan lokaci kafin yace dama tana da wanan laluran ne ashe umma tace dashi tana dashi don yanzu sun kai shekara kusan goma data fara irin haka. Dama nima a nan nayi wani irin mafalkine da ita shine yasa na kiraku yanzu inji idan kuna lafiya don mafalkin ya ban tsoro sosai da sauki umma ta fada. Bayan dan shirun da yayi can kuma ya sake tambayan ko dai duk a kan case din nan ne don abinda mafalkin ya nuna min ke nan saboda mutanen nan shu,uman mutane ne sosai wallahi. Umma tace anya zasu iya cin galaba akanta kuwa sai dai abinda ya fito daga Allah amma nina san ba dai suyi mata wani abinda zai iya kamata ba dai da sunan sihiri. Amma hjy sai nake ganin kamar ba a banza take wasu abubuwa ba a yanzu Allah ya nufa umma tace don hjy da ya kirata da shi a lokacin. Da zasu iya wani abu da ita da ba a kai wanan lokacin ba kawai dai tana da nata dalilin ne a yanzu na ganin bai kamata duka a hukuntasu a kan laifin da bai shafi wasun su ba dai. Ok na fahinta yanzu a dan bani lokaci na kara dan bincke wanda ba a kama da wani laifi ba sosai a cikin su zan sakoshi insha Allahu nagode da kuma na sameki mukai maganan fahinta dake. Ba komai umma ta fada sai dai kunyi hakkuri da wanan yanayin na Sahiba don haka abubuwan suka mayar da ita yanzu sam bata da tsoro ko fargaban komai idan ta tashi magana. Murmushi ya sakeyi yana fadin ya fahinta kafin ya kashe wayan cike da fargaba da tunanen wani zance da suka tsaya mashi a rai cikin dan maganan da sukayi da umma din na dan lokaci. ANA DARA GA , , , , , , , , 9️⃣2️⃣BY, , , , , , , , , , , , ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , , , , , , , , BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AL WALI , , , , , , , , , , ONLINE PAID NOVEL YAR UWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA BA TARE DA HAKKIN KOWA BA DON BIYA KI TURA DARI BIYAR 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK 08036959257 ALLAH SARKI AI RAINA BAYA BACI YANZU DON KIN FITAR DON NASAN AKWAI RANAN HADUWA SEE U👋👋👋👋 Yau na tashi da wuri don aikin da muke dashi a office yasani sakkon tashi don zuwa wurin aiki na samu na gama da wuri nayiwa umma sallama na fita. Don dan kwana biyun da nayi ban fita ba koda naje na samu aiki ya taru yana jirana a lokacin bayan na gama gaisawa da duk wanda ya kamata na zauna na fara duba aikin dake gabana lokacin. Sosai na natsu Ina aiki kafin tsawon wani lokaci wayana ya fara kara ban kula da in dauka ba don aikin dake gabana a lokacin har yakai ga tsunkewa kafin wani lokaci kuma kiran ya sake shigowa again. Dan tsuke naja a daidai lokacin dana mika hannu cikin jakata ina dauko wayan son duba wanda ke kirana lokacin . Saidai ganin bakon lamba yayin kasan wajene kuma ban san mai shiba yasa na dana ina karawa a kunne na. Muryan mace ce yasa na tsaya ina sauraren ta a daidai lokacin da nake kokarin yin sallama ita kuma take fadin ehhe na sahiba a dey talk too? Naso sheda muryan maishi amma na kasa tuna inda nasan wanan muryan taci gaba da fadin ba zan tsaya wani dogon magana ba dake a yanzu saidai ina son ki fita hanyan dana da kika sihirce min shi saboda arzikin shi. Dama haka irin ku suke diyan tallakawa da zaran kun kyala ido akan dan mai kudi kukaga yana da arziki lokaci kankani sai ku juye mashi kai ku sace zuciyan shi. Na fada maki tun farko dana ba ajin ki bane aiki kawaine a tsakani ku aikin ma a yanzu zanso a barshi don nasan izuwa yanzu kin samu karuwa sosai a wurin shi wanan ma kawai ya isheki in kina da godiyan Allah. Wai waye wanan mara sanin mutunci da adam sai zancen wani dukiya da danki dama ban sani ba kike faman yi min a waya ? Koke wacece baki da kirkin ko imani dan baki san Allah ba balle Annabi a cikin lamarin ki an fada maki kowaye danki aiki dashi danki din da kike fadi,kina tunanen anayi anaci masa kudin . Za ai masa aikin banzane ko an fada maki mu bayin shine ko haihuwan mu yayi da zamuyi masa aiki kyauta ? Ki koma ki tambayi dan naki idan wani abinshi ya taba hadashi dani har kike min wanan zancen daki baya gabana ko waye shi don haka ki dafa abinki kice idan Sahibace . Mamakine ko me ya hanata ban amsa don ni kaina nayi mamakin jin yadda tayi shiru don da farko tayi niyar cimin mutuncine sosai a kan dan nata saina tare ta da baki na wanke ta tas a wayan. Tsuki naja naci gaba da aikina raina a bace lokaci guda naji tsanar aikin ga baki daya ya kamani don nasan ba kowa bace sai Alaja zata kirani taso raina min wayau ga danta ji nayi kamar kada na karasa aikin na mike nabar office din a lokacin. A dadafe na samu na karasa komai office din na mike tare da tattara duk wani abinda nasan cewa nawane na bar office din rai bace. A sabuwar motana na saka sai bayan na shiga na zauna na dago kai na kalli haraban ma,aikatan lokaci guda na sauke ajiyan zuciya. Don Allah ya gani banso na daina aiki dasu ba saidai hakan ya zama min dole don in samawa kaina dashi Sha,aban din salama a gun mahaifiyar shi dake nata haukan a kanmu yanzu . Motar nasa key zan tayar wata zuciya tace bar masa motarshi shima a nan to idan na bari ai taci banza ke nan naba kaina amsa ni kadai . Jan motar nayi a hasale kamar Alaja din tana tsaye tana kallona a lokacin nake jan motan haka nakai gida zuciyana yana tafasa. Na dan tsaya mun gaisa da umma dana sama a shago kafin na shige ciki na tube kayan jikina na dan watsa ruwa na fito mm a shiga kitchen abincin dare na dora muna lokacin don dai kawai naga na zama busy na fita zancen dake cin zuciyana lokacin. Saidai hakan bai samu ba don ina aikin abin yana fado min a rai ina jan dan tsuki daga inda nake har na karasa na kawo falo na ajewa su umma na shige dakina zuwa lokacin an kira sallah magariba ko. Bandaga wurin ba har saida na idar da isha,i na mike wanka na sakeyi na dawo na kwanta zuwa lokacin lekowan Ammar sau biyu a dakin nawa yana ganina busy. Har sai lokacin da yazo karona ukku ya sameni kwance ya zauna a bakin gado yana tambayana meke faruwa dani ? Notin na bashi amsa wayana dake gefe ajiye ya dauka ya bude ya fara latsawa sai naji yace dani you have nine miscall in your phone. Da sauri na juyo inda yake ina tambaya daga waye yace new number ne yana miko min wayan dake hannun shi din. Kallon number nayi na wani kasane ba wancan da akakirani dashi bane da farko banza nayi da kiran muka kama hira da brother din har ya dan mantan dani abinda ke damuna din a lokacin. Muryan ummane ta kira Ammar yazo ya daukan muna abinci idan ba zamu fito zuwa falo ba lokacin muci. Jin hakan yasa muka fito kamar ana jiran zaman mu a falo wani kiran ya kara shigowa saidai wanan kiran na ya Abubakar ne yasa nayi saurin dagawa. Gaisawa mukayi yana tambayan lafiyan mu nace dashi duk muna kalau kafin yace yau dai daddy da uncle buhari they free yanzu haka suna gida dazun nan suka dawo daga Abuja. Thank god na fada tare da fadin yaya sauran kuma saida ya dan nisa kafin yace dani kinsan yadda sharian kashe mutum yake fa. Ko su din bawai an sakesu ga baki daya bane an dai yardane ayi bellin su a yanzu din kafin lokacin shiga kotu yayi. Idanuwana na lumshe kamar yana gabana lokacin ina maijin wani iri a raina sainaji muryan shi yana fadin ki fadawa mama duk yadda akayi mun gode duk da munsan ba,a kyauta maku ba ga hakan. Mukai sallama dashi don akwai hayaniyan da nakeji yana tashi a wurin hakan ya nuna yana wurin jama,ane lokacin ya kirani. Nayiwa umma bayani kamar yadda yayi min bayani babu wani fara,a a fuskanta ko nuna jin dadi ga labarin sai Allah ya kyauta data fada kawai ta dan nisa a lokacin. Loma biyu kawai tayiwa abincin sai ta kasa ci gaba da cin abincin dake gabata din a lokacin nima a bangarene hakan ne ya faru dani. Don na kasa kalon abuncin da sunan ci sai wayan da nake faman dakila a hankali bada niyar yin hakan ba nakeyi don dole. Shima dai Ammar ya dan taba saidai baci kamar kullun ba don irin yanayin da yaga mun shiga a dan lokacin na damuwa wanda ba zamuce ga dalilin hakan ba a lokacin. Gidansu daddy kuwa sai shige da fice jama,a keyi suna mashi murnan wai sherin da ake kokarin kula mai don a bata mai suna. Ai yanzu gashi gaskiya tayi halinta an gane an sakoshi tunda part din anty Amarta hjy karima ba abinda sukeyi sai faman surfa muna zagi iya son ransu. Wai mun dawo da talauci a haukace munzo mun hargitsa masu kwanciyan hankalin su lokaci guda mun hana mutane zaman lafiya. Sai goma na dare aka samu rufe gidan daddy din sanan mutane suka tsagaita shigowa badan sun daina zuwa don murnan dawowan nashi ba a lokacin. Washegarima haka aka dora tun fitowan shi a masalaci jama,a suka dunga shigowa a lokacin nan kuma gidan ya sake dinkewa da jama,a har ma sunfi na jiyan da sukazo mashi tunda shi mutumin jama,ane ga kuma ta fannin matan shi suma don labarin ya bazu gari kowa yaji. Daddy daya fito gaisawa da gungun wasu maza da mata da sukazo daga fannin anty Amarya bayan sun gaisa din ne akai mashi barka da arziki. Sai kuma aka shiga jefa min zagi suna aibantani tare da jefa muna mumunan addu,a da sauri daddy din ya dagawa mai maganan hannu lokaci guda. Tare da fadin haba malam meye laifin yarinyar nan a nan ka kwantata akan ka idan kaine yau aka kasheka yaya iyalinka zasu dauki a bun a zuciyar su. Ba dadi mutumin ya bada amsa cikin sanyin murya yana gyara zaman shi a hankalin cikin muzanta don wanda yakeyiwa ya katseshi ta hanyar daure jikin shi. Daddy din yaci gaba da fadin haka din dai nasan zasuyi koma fiye da hakan amma kaga jiyan nan ba,a sakini ba don wani matsayina kona wani saidai don ita wanan yarinyar da kake zance akanta yanzu. Itace tayi tsaye saida taga an fito damu a yanzu din don wanan kamun bada sanin ta akaimuna shiba yanzu wanine can kuma da yake da alaka da wanan case din yasa akamomu din shari,an da akai a nan wai bai gamsheshi ba. Au haka zancen yake yace kwarai kuwa babu laifin iyalin marigayin ko kadan a wanan kamun namu na yanzu . Wanan tsakanin mune dashi wanan mutumin a yanzu ita kuma ta bayar da nata taimakon ta hanyar da zata iya bayarwa din a yanzu kan hakan. Kowa falon yai shiru dukda tunanen kan wanan zancen na daddy sukeyi a yanzu har dai aka dauko wani zancen suka kaiga watsewa wurin. Modibbone ya shigo gidan cikin kamala dashi da matarshi nan suka shiga gaida mutane da suka sama kafin ta samu wuri daga kujeran dake da dan nisa da inda daddy din yake zaune ta zauna itama. Kallonta mommy ta danyi kadan kafin ta mayar da kanta inda take kallo da farko tana maijin zafi a zuciyarta na yarda Nazifa din bata da kunya ko kadan a rayuwan ta. Don idan tana da kunya ta yaya su suna zaune saman kujera zata shigo itama ta zauna a sama haka wanan ai nuna rashin tarbiyane garesu. Fuskanta a cikin damuwa yake itama daddy dakewa yan jikokin shi ba a ne ya dago yana fadin suma dai su Alh din muna sa raicewa abin zaizo masu da sauki insha Allahu saidai yadda shari,an ya tsaya dai a yanzu. Hawaye ta fara sakewa duk kokarin da tayi kada su fito din wurin taushe zuciyarta saiga kuma zancen da daddy din ya karasa dashi a yanzu wanda ya kara tayar mata da hankali. Dama kuma zuwan nasu saida mijin nata yayi da kyar ta taso sukazo gaida daddy din don a cewan su ana son a nuna masu son kaine a fitar dasu daddy din su kadai abar mahaifinsu a ciki maganan da suka gama da yarta kenan a waya. Sai gashi kuma yanzu daddy din yana fadi da bakin shi cewa fitowan mahaifin nasu saidai addua ke nan kuma watau dai ba tabbas a garesu. Bayan sun da jima a zaune an bata hakkurine ta tsagaita kukanta ta turawa mijin waya da su tafi hakana ya sauketa wurin mahaifiyar ta. Bai tashi a lokacin ba saida ya dan kara lokaci suna magana da mahaifin shi sanan ya tashi ya sauketa a gidan da uwayen nata ke ciki yanzu nan ya tafi inda zai je ya barta wurin su. Washegari har goma ban leka office ba ga aiki na ugent na jirana haka yasa suke ta kirana daga Felix har oga jimo saidai wayan nawa baya shiga. A haka dai har karfe biyu ban leko ba har hudu felix daya fito ya biyo ta gidan namu akace dashi na fita lokacin. Haka kuma washegari shiru har kwana uku babuni babu wayana don idan ban samun zuwa zan bugowa oga jimoh waya in sanar dashi dalilin rashin fitowana ranan. Gashi ko oga Abdul da muke gida daya ban fada mai dalilin rashin zuwan nawa office din ba dan bamuma haduwa dashi ko a gida. Hakan yasa daga wurin aikin suka nufo gidanmu su ukku sunyi sa,a ina gida na gama gyaran gida da jikina ina kokarin in fita shagon umma in zauna. Sai gasu sun shigo tare da umma da suka sama a shagonta na fito muka gaisa nan Filex ke min wasa bayan mun natsu oga jimoh yake tambayana ko lafiya har kwana ukku basu ganni ba. Dan shiru nayi kafin nace dasu na jaye daga aikina bazan kara shiga aikiba kuma gaba daya suka kalloni don basu zaci jin hakan daga gareni ba lokacin. A cikin wani yanayi oga jimoh yace ko saboda mey nayi wanan maganan nace ra,ayine hakan ganin ba zan kara magana ba akan hakan yasa suka mike sukai muna sallama suka tafi. Umma bata dawowa tun fitan su don tasan da dalili dana fadi hakan don haka tasan idan na samu natsuwa zan fada mata ko meye. A nan gidan kuma komawa nayi saman gado na kwanta ina faman tunane tunda ina son aikina ina samun rufin asiri a cikin sa kuma basumin komai ba wurin. Saidai dole in barshi don kare mutunci da kima da Alaja ke son ta nuna min ina bin danta da mugun nufi saboda wani manufan da nake dashi kanshi na daban . Dole haka zan daure in saba duk da nasan nayi rashi sosai a yanzu din amma haka zan daure in bar aiki karkashin danta ga baki daya don taron mutuncina kawai. Ba,afi minti ashirin da fitan su ba gidan mu saiga kiran oga Shaa,aban ya shigo wayana har ta katse ban daga kiran nasa ba. Bayan wani lokaci kuma ya sake kirana din wanan karon kan na daga mun gaisa sama sama yake fadin yanzu jimoh ke fada mai wani magana akan me zan aje aikina haka kawai. ANA DARA GA , , , , , , , , 9️⃣3️⃣BY, , , , , , , , , , , , ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , , , , , , , , BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AL MUTA, ALI , , , , , , , , , , ONLINE PAID NOVEL YAR UWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA BA TARE DA HAKKIN KOWA BA DON BIYA KI TURA DARI BIYAR 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK 08036959257 ALLAH SARKI AI RAINA BAYA BACI YANZU DON KIN FITAR DON NASAN AKWAI RANAN HADUWA SEE U👋👋👋👋 Dan shiru nayi kafin na bashi amsa nace is my wish na bar aiki daku a yanzu haka zaifi kwanciyan wasu na kusa dakai dake ganin ba aiki bane ya hadamu dakai a yanzu. What a noses talk kike min haka akwai wani wanda ya ban shawara na daukeki aiki lokacin dana daukeki da har zaki aje aikin ki don jin dadin maishi ? Hakan yafi min sauki na riga dana aje aiki dakuko ba zan kara shiga ma,aikatan ka da sunan aiki ba kuma hakan shine kwanciyan hankalina nima a yanzu. Saidai na gode da duk irin taimakon da kayi min a baya Allah ya hada fuskokin mu da alheri amin na kashe wayan . Duban wayan yayi yana mikewa tsaye don jin dadin tunanen da nazarin dalilin wanan maganan daya zo mashi a bazata. Dole akwai wani abu a cikin magana na don nace nayi hakan ne don farin cikin wasu na tare dashi . Toh waye har zan iya sadaukar da nawa farin cikin haka saboda maishi tunda yasan banda wani aiki bayan wanan da nakeyi a karskashin shi din yanzu. Idan hakane ya zama dole ya kara bincike tsatsaura yaji a inane wanan matsalan da nakeyiwa barazana haka ya fito ? Sam baiyi tunanen ya fara binciken Alaja dake kusa dashi kan haka don yasan banda wani matsala dasu da zaikai har ta kirani irin haka muyi magana da ita din. Saidai hankalin shi ya tafine kodai akwai wani abu dake faruwa a cikin company daya hadani da wani dake kusa dashi har ya jawo haka ? Jimoh din ya kara kira bayan sun gaisa yace ina son ka bincika min abinda ke faruwa koyi fada da wanine a cikin ma,aikatan mu ya jawo hakan. Gaskiya banyi tsamanin hakan ba ga mis sahiba don ko kawa ko wani aboki bata dashi asalima kaika sani idan ta shigo aiki bata tsayawa kula kowa saidai ta wuce zuwa aikinta. Yanzu taki fadama matsalan da aka samu ke nan ko me don nima nayi da ita ta fada min meke faruwa taki fadin komai sai cewa da tayi tadai dakatar da aiki damune don kanta. Nisawa yayi a hankali kafin yace ni ta fada min ta dakatane don farin cikin wasu na tare dani kaga kenan akwai matsala ke nan a cikin maganan. Lalai kan dole akwai abinda ya faru wanda bata son ta fadi dalilin yanzu saidai gaskiya barin ta tafi ba alheri bane a wajen mu don samun mai aiki tukuru kamar sahiba yanzu sai an tona gaskiya. Abindake damuna yanzu ke nan akan wanan maganan don dole mugano inda matsalan yake a gyara haka kawai ba zata yanke wanan shawaran kai tsaye ba. Haka suka aje maganan suka kashe wayan kowan su yana cikin damuwa lokacin shikan Jimoh bincike ya fara yi sosai ko mun samu matsala da wani a ma,aikatan saidai bai gano komai ba. Dole a karshe ya nemi Abdul akan ya taimaka masu ya zauna dani asan abinda ya faru har nake ikirarin barin aikina dasu. Daukan wayan yayi lokaci guda don yasan tun bayan aikin daya bashi yauce rana na farko daya kirashi a waya haka gaisawa sukayi mai kiran na bashi girma suka gaisa kafin ya fara fadin. Yallabai yau kusan sati ke nan yarinyar nan bata fita zuwa wurin aikin taba kuma lafiyan ta kalau don ina ganin tana fita zuwa cikin gari yin tsabgogin gaban ta ta dawo gida saidai sau biyu ke nan naga ta fita . Amma takan dan leko mahaifiyarta a shagon su na kofan gidan ta dan zauna lokaci lokaci saidai abinda na kula kuma su ma,aikatan aikin nasu manyan ma,akatan sunzo gidan kusab sau biyu ke nan. A yadda na samu labarin cewa wai ta aje aikintane don karankanta kawai don hakane ma,aikatan ke binta ta dawo. Guntun murmushi ya sake har wanda suke wayan yana jinshi kafin yace good dama irin daman da nake jira ke nan a samu daga wurin ta zan kiraka idan na kare shirin da nakeyi nan gaba kadan. Sukai sallama a gurguje yace zakaji sako daga gareni ka kara saka ido ga komai nasu dake gudana kamar yadda ka dauki alkawarin yi da farko yace insha Allahu yallabai za ayi yadda kace. Bayan sun gama wayan dashi kasa ci gaba da aikin da yakeyi a gaban shi yayi ido ya lumshe a hankali yana tuno suran daya ganta ciki a ranan. Ta ina zai fara ya tambayin kashi yana mai bude idanuwan shi lokaci guda ya sauke a saman laptop din shi dake bude a gaban shi. Aiki zan jawota tayi ya ba kanshi amsa da sauri yace Nop ba zancen aiki a tsakanin mu sam dolene in fito fili in nuna masu kudirina a kansu yanzun kan. Kaima kasan da wuya su iya tattarowa su dawo gareka kai tsaye haka yadda kake nufi dole sai ka juye zancen a cikin siyasa wanan lokacin. Don yarinyar tana da balain wayaun tsiya irin na matan zamani idanuwan ta da gani a bude suke ba irun su bane akewa farat daya a kamasu ba. Yaya zaiyi ke nan hakan yasa ya dan kishingida ya tokare haban shi da hannun shi daya dake rike da biron da yake rubutu dashi yana dan juya kanshi saman kujeran. Kafin can ya sake wani malalacin murmushi a fuskanshi lokaci guda yana aje biron wanan karon hannayen shi ya hada wuri biyu ya tokare haban nasa yanaci gaba da tunane. Wayan shi ya danna yana gyara tsayuwan bluetooth din shi a kunnen shi ya soma magana cikin bada umurni ya fadi abinda yake son fada a daidai lokacin da matarshi hamida ta shigo office din nasa na gida da yake zaune. Har ta karaso wurinshi yana zaune yadda yake saidai zaka dauka ita din yake kallo a lokacin sai lokacin da tazo ta zauna a hannun kujeran ta dan shafo jikin shi ya dan sauke siririn ajiyan zuciya yana dago kai gareta. Ya na ganka kamar kana cikin damuwa dan murmushi ya kara sakewa kafin ya shafo fuskanshi da tafin hannun shi yana fadin. Ba damuwa bane hakan nasarane nasarane akan rayuwan mu ga baki daya na hango na gane yanzu lokaci yayi da gurina dana maigidana zai fara cika. Tsaman ta cire hannun ta saman suman kanshi da take dan yamutsawa tun zamanta gefen shi tana mikewa tsaye tare da dab takawa daga inda yake zaune din takai wurin window ta tsaya tana kallon haraban wajen. Allah ya gani a rayuwanta taki jinin yai maganan wanan ubangidan nasa dashi da mahaifiyar su duk magana suce da badon ubangidansa marigayi ba da yanzu suna cikin wahala tsunbul ko. Yaushe Allah zai hadashi da iyalinshi ya rama masu Alherin shi gareshi Allah ya gani a wurinta wani tunawa da ubangidanshi ko wani zancen tausayi yanzu duk bai taso ba a gareshi. Su iyalinshi ya kamata ya duba ya ginasu kamar wasu yayan lu,u,lu,u ta zama abin kwantace a duniya ita da yaranta biyu da Allah ya basu. Saidai kassh koyi da wanan mugun ubangidan nashi da bata sani ba da yace yanayi a yanzu shine mafi girman abinda keci mata rai a rayuwa. Duk da yana sake mata hannu yana kuma kyautata ma yan uwanta duk wani bukata nata ya tsare saidai ita kan ba hakan takeson shi dashi ba. Taso ace ta sameshi a hannu tana juyashi yadda takeso sai abinda tace dashi zaiyi a rayuwa ko kuma ta hanashi ya hannu. Duk da hakan ma ba laifi tasan tayi dace tabada tazara ga sa,oin tashin su ana kuma kwatance da ita a cikin matan da suka isa suka kai a yanzu din. Dan tunane tayi da sauri ta washe don tunawa da tayi idan ta nuna hakan a fili akan wanan zasu iya samun matsala dashi don ta taba gwadawa bata sha da dadi ba. Hamida ta kasance irin matan nan ne da basu son mazansu suna alheri don a cewanta yawan alherin shi kamar ita da diyantane yakewa illa da hasaran dukiyan su don shi bai iya alheri kadan ba. Wanan yasa sam bata son kowa ya mameshi shima din zuwa yanzu ya gama fahintan waye ita don haka bai zama dole tasan komai nasaba a yanzu. Shida ita aurene kamar na gida duk da ba wani zumunci bane a tsakanin iyaka dai alkawarine tun na kurciyana da akan fara soyayya iyayyen su mata kuma kawayene shine ya kara kulla alakasu har ya kaisu ga aure duk a lokacin mutane na fadin tama girmeshi amma shi yasan bata girmeshi iyaka dai yan sa,a guda suke da shekara ma ya darata da aji. Koshi don ita an mayar da ita bayane a lokacin yasa ya fita da ajin haka kuma bayan bin wan mahaifin shi da yayi zuwa waje da sunan za a sama mashi gurbin karatu a can inda suken. Saidai suna zuwa labari ya canza inda yazama yaron gida shine aike da duk wani sauran aiyuka nagida a lokacin cikin haka babban dan wan baban shi da yake hannun shi ya kwashe wa mahaifin nasa wasu makudan kudi a karshe aka laka mai duk da iyayyen nasa sun san bashi ya dauka ba dansu na cikin sune ya hada gagarumin party da turawa da kudin . Bayan sun rufe ido sun mashi bugun tsiya tare da kora gashi baisan kowa ba a kasan passport dinshi kuma yana hannun su sun rike wanan duk muguntan matar wan baban nasa ne wace take yar uwa a gun mahaifiyarshi a gida . Amma take nuna mashi tsana da tsangwama kasancewan shi a cikin yayanta da sam.bata son hakan ya kasance dashi tunda saida ta hana mahaifiyar shi auren dan uwan mijinta taki yarda a lokacin. Ya Abubakar ne zaune a kasa gefen kafan mahaifin nasa da suke ganawa na siri dagashi sai dan nasa a lokacin don maganan da dan yazo dashi tanada muhinmanci sosai a rayuwan su. Ba wani magana bane illa gaba da gaba da Abubakar din yayi da mahaifin kan lalai ya fada mai gaskiyan maganan dake tsakanin shi da dan uwanshi marigayi da tuhuma yai yawa akan mahaifin shi din. Don wanan dan takifin mutumin mukhatar din da gaske yakeyi a kansu kan duk abindaya sani sai an tsaya a kotu sun fada. Daddy idan baka fada muna a yanzu mun san komai ba zaiyi wahala mu iya kwatoka a hannun wanan mutumin a yanzu don yana da burin kargameka a gidan maza. Nasan yana da gurin yin hakan don da gaske yazi lauyoyi a can sun fada muna duk wani tuhuma da ake muna wanda mamu nan mun manta da anyi hakan . Daddy ya gyara zama yana fadin watau mudibbo na dade da sanin wanan lokacin yana tafe son zuciyana yana bani cewa da akwai wani wanda yasan komai na Sambo bayan ni. Don hakane na zauna na tsara komai amma kuma kasan dukiya da shiga rai da ace nayi dubara lokacin da kakawo min iyalin sambo da farko na mika masu dukiyan su a hannun su da duk haka bai taso a yanzu ba. Hakane daddy modibbo din ya fada tare da fadin ko zan iya ganin takardan a yanzu inda ka rubuta komai din don asan inda za a fito masu. Dan shiru daddy yayi kafin yace da dan nasa inaga basai an duba wani takarda ba nima a yanzu nafi bukatan na dakawa mutanen kayan su a hannun su ko hankalina zai kwanta ga komai. Daddy idan kayi hakan yayi kyau sosai ga al,amarin amma kuma anya duniya zata yarda da mika masu komai haka tsakanin ka dasu kuwa ? Bandamu da zancen mutane akaina ba yanzu abinda nayi niyar aikatawa shi zan aikata akaina dasu final. Kai ya gyada cikin gamsuwa da abinda mahaifin nasa ya fada lafin yaje bakin shi yayi shiru lokaci guda yana nazari kalaman mahaifin nasa. Kafin ya daga kanshi dake duke yana fadin daddy zan koma Allah yasa mu dace mahaifin nasa ya busar da iska yana fadin amin zan kokarta naga hakan ya faru. Part din mahaifiyar shi ya nuna bayan sun gaisa da kanin shi da a yanzu sauyin rayuwa ya samesu na dan aikin da suka samu suna biyawa kansu wasu bukatu nasu da ba sai sun roka ba an ja masu rai a yanzu. Hankalin shi ya mayar gun mahaifiyar shi ya kara gaida ita a natse kafin ta jefo mashi tambaya kaje kakai masu abincin kamar yadda mukayi dakai zaka kai ? Na dai tura ankai masu don ni banje da kaina ba kamar yadda mukayi mommy don ko naje gidan da kaina ba lalai bane in samu shiga ciki mu gana dasu. Kana ganin hakan yayi maka ke nan kowa ya ganka yasan abinda ya kawo ka ai donme zaka damu sa zancen wasu can a kan ka ? Shiru yayi babu amsa a lokacin don yasan ba zai iya shiga gidan ba a yanzu gaskiya saboda gidan babbam gidane mai tarin mutane da yawa a cikinsa. Don haka ba zai shiga ya dinga faman gaisawa da tarin matan da zai sama a tsakar gidan ba gungu gungu ya dinga gaidasu. Hauwa ce ta taimaka mashi ta jefo mai tambaya akan aikin ta ya tsaya bata amsa har hankalin mahafiyar nasu ya dauke ta shiga daki ya samu ya sulale daga gidan ya nufi nasa gidan kai tsaye. Zaune muke da umma da muniya har matan kanin mijinta da suke zaune dasu a yanzu a wajen gidan mu muna hira mukaga dawowan mijita daga wurin aiki. Itace ta tashi ta nufi wurin shi sai gasu sun samemu a tare dashi zuwa inda muke ya gaida umma dagida dake mai sannu da zuwa. Sun dan taba hira kafin ya juyo kaina yana fadin eh sahiba na your eyes be dis i no see u all dis days. Na dan sake murmushi ina gyara zama tare da fadin i dey wooo bani dai son fitowa wajene koda yaushe na bashi amsa a takaice kafin na dukar da kaina ga wayana lokacin. Zanso ganin ki anjima idan na dawo daga magariba ya fada sai lokacin na kara dagowa ina fadin OK. Basu dade da shiga part din su ba namike na shige namu part din yan aikace aikacen gida nayi a lokacin na dora muna girkin abinda zamuci. Nagama tsab dama ga al,adan bayerabe kafin ya dora girki ya tanadi duk wani abinda yake bukata ga abinda za a girka din muma zama a cikin su haka muka sabadayi. Shiyasa da mun dora girki yan lokaci kadan sai kaga an gama shi a cikin lokaci haka kuma abincin dai bawai wani dahuwa ake bari yayi sosai ba don haka suke girkin su dama. Bayan isha,i saigashi yayi sallama falon ya shigo suna gaisawa da umma na fito muka gaisa yake cewa dani dama ba wani abu bane don Allah tambaya yake son yai min. Zagayowa nayi na samu kujara na zauna ina fuskantar shi yace ya dauka a matsayin da muke yanzu dashi mun zama yan uwa mu dashi. Saidai ashe abin ba haka yake ba mu a wurin mu don inda na daukeshi kamar yaddashi ya daukemu ba zan aje aikina ba tare dana fada masa dalilina ba nayim hakan. No kada ka damu da wanan ni a wurina wanan ba wani abu bane da zan dinga bin mutane ina fada masu dalilina shiyasa ban fadawa kowa cewa ga dalilina ba ai. Amma ai ko bamu fada ba ansan mun daukeka a matsayin dan uwa yanzu don mun wuce makwabtaka damu dakai. Wanan amsan da kika ban yanzu Sahiba bashi zai sa na gamsu ba har sai naji dalilin kina barin aiki din da kikayi. Jin hakan yasa na dan lumshe idanuwana na dan lokaci kafin na bude ina fadin brother matsalan mahaifiyan oga shaabance ta kira waya tana fada min wasu maganganu da har zuciyana ta kasa daurewa nakai ga bata amsa tare da alkawarin zan bar aiki da danta kamar yadda ta bukata har abada din. ZAINAB IDRIS MAKAWA ANA DARA GA , , , , , , , , 9️⃣4️⃣BY, , , , , , , , , , , , ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , , , , , , , , BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AL BARR, , , , , , , , , , , ONLINE PAID NOVEL YAR UWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA BA TARE DA HAKKIN KOWA BA DON BIYA KI TURA DARI BIYAR 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK 08036959257 ALLAH SARKI AI RAINA BAYA BACI YANZU DON KIN FITAR DON NASAN AKWAI RANAN HADUWA SEE U👋👋👋👋 Kai ya fara dan juyawa yana fadin unbelieveble da ace a bakin wani naji wanan zancen da zance karyane don ita Alaja tafi kowa sanin muhinmancin zaman danta dake a yanzu. Wanda ke kanki baki san suna amfana haka dake ba dan karacin shekarun dakeki don mutanen mu suna karin magana da suke fadin sai arziki ya hadu akanci gaba irin amfanin da danta ke samu a yanzu tasan bai taba samun irin sa ba ai. Idan ban bar mata danta ba duk abinda ta fada min nan gaba kuma fa duk dashi nasan yana kyautata min sosai fiye da tsamani ma. Gaskiyane ya fada a sanyayye kukan umma da mukaji shine ya sakatar damu daga maganan da mukeyi muka juyo hankalin mu tashe . Ta daga hannayenta biyu sama a lokacin tana fadin oho Allah mun tuba ka yafe muna laifin da mukai maka bada sanin mu ba ya Allah. Sahiba idan kika bar aikin nan yanzu ina kuma zamu dafa muna cikin rufin asiri da aikin nan naki wanan matar kuma yanzu ta kawo muna matsala. Duk a vikin harshen yarbanci umma ke wanan maganan duk da naji wani iri har kasan zuciyana fiye da yadda ma nakeji da farko. Amma haka na daure ina bawa umma hakkuri tare da irin abinda na hango zama a karkashin oga Sha,aban zai iya jawo min nan gaba don nasan halin su na yarbawa da rashin yarda da Allah. Shima Abdul din dukda baiso hakan dana yanke ba da farko a karshe dana nuna mashi matsalan da hakan zai iya jawo min sai ya yarda da zancena din . Yayi min adduan Allah ya kawo min wani mafita a cikin gagawa shima yanzu zai taimaka min da addua da kuma neman min inda zan dan laba in samu aiki tunda zaman gidan haka baiyi ga mutum. Haka kawai na shirya washe gari nacewa umma zan tafi unguwa sai bayan fitana ne ashe na manta da wayana gida lokacin na jona a caji. Unguwar su Asabe na tafi semi boda duk da wurin ya dan canza a yanzu anyi gine ginen zamani da benaye sosai amma na gane gidan na Asaben. Gidan yana nan da ginan shi na tallakawa zan iyacewa tun bayan barin mu kaduna da muka dawo lagos wanan ne karo na ukku da nakawo mata ziyara. Tana waje gidin iccen dake kofan gidan nata tsufa ya kamata a yanzu gaskiya amma hakan ta shedani bayan dan tambayan da taimin na wacece ? Sahiba na bata amsa zan ci gaba da bayani tace a, a, a, sahiba dai ina maman ki ina dan uwanki nace duk suna lafiya gashi duk ta rude da murnan ganina lokacin. Na fito da dan tsaraban dana kawo mata yanzu babu kowa a gidan kamar lokacin da mukai zama gidan da yake da mutane dayawa sosai don masu zuwa cirani sunfi son irin gidajen nan da yafi saukin kudi su zauna a cikin shi. Sai mutane kalilan ne kuma yare ke zama da ita a gidab dako kamar gidan zai dinke da jama,a don haka yanzu ban san kowa ba a unguwar sabbin fuska nake gani. Saidai halin dan adam da gulma yasa suna ganina da mota haka lafiyayya sai suka fara zuwa muna gaisawa dasu itako tana fada masu ai jikantane tazo wurinta. Muka shiga gausawa dasu gaskiya a ranan nayiwa ya Abubakar addu,a yafi a kirga kafin na kawo gida yadda ya tsamomu daga wanan rayuwan kaskancin har ya nuna muna ahalin mu . Yayi muna kuma sanadin fita cikin kangin irin na rayuwan talauci da wahalan rayuwa tare da rashin galihu haka yasa na kudurta a raina insha Allahu zan zauna da Asabe ta fada min garin su itama in sadata da danginta na jini koba dadi irin namu dai ansan da tana raye a duniya ai. Saidai kuma ina dawowa gidan labarin yasha bambam da wanda na baro wurin Asabe dashi din don na dawo na samu umma a gida tana murna da farin ciki. Nima na shigo da murnana gida tun kan umma ta shigone Ammar ke ban labarin cewa ai wai wanan mutumin da akace yaron daddy mune yayi waya da umma tun dazun take jin dadi. Waya sai kuma na tuna da zancen wayana dana bari a gida yana caji lokaci guda na mike da sauri zuwa dakina wayan na dauko na samu miscall har sha na dinga dubawa daga office din mune yafi yawa sai kiran shi oga shaaban da kansa sai number wanan mutumin kuma da Amar ke fada min. Ban kira kowan su ba don a gajiye nake lokacin ga yunwa kuma dake cina duk da hakan wanka nayi don sauke gajiyan kafin na fito na nemi abinda zanci. Ummane ta shigo take fadin kin fita kin manta da waya yana ta ringing tundazun ake kiran layin saidai ba wanda ya daga saina Abdul ne Ammar ya daga yake fada mai kin fita wayan yana gida kin barshi a caji. Sanan wanan mutumin fa ya kirani yau din nan yana sheda min cewa zamu tafi umar a satin nan mai zuwa gobe zai aiko aimuna komai har ya tambayeni idan kin taba fita waje nace masa kwarai kuwa. Kinje dubai da wasu kasashe na duniya harma sai kuma tayi shiru ganin irin kallon da nake mata mai kama da tuhuma a lokacin. Itama dai shiru tayi tana kallona kafin na girgiza kai ina fadin gaskiya umma ki bar saurin yarda da mutane haka yanzu. Don yanzu duniya abin tsorone shi yana nufin zaizo muna da yaudarane ya koma muna wani cuta ko me ? Ni sam hankalina bai kwanta da wanan mutumin ba yabar abin shi ina da wanan plan din dama a shekaran nan insha Allah dake cikin makkan bana da za ayi. Makka fa kikace sahiba nace insha Allahu abinda naketa tara kudina ke nan tun wancan shekaran naso kije Allah bai nufa ba sai bana insha Allahu har an gama komai na tafiyan saura yan abubuwan da zasu kiraki nan gaba kiyi. Hannu ta daga don yanzu ta saba da dabi,an yarbawa tana godewa Allah cikin jero min albarka muna amsawa da Amin. A fannin oga shaaban kuma tsab oga jimoh ya fada mai kamar yadda na labartawa Abdul komai hankalin shi yai matukar tashi yake fada mashi yanzu basu tare da Alaja shi yana asia sai idan ya dawo zuwa wani sati zai shigo nageria din a zauna. Oga Abdul ya dawo yana fada muna abinda yace din sam banji komai ga hakan bani don har a bada na daina hurda dasu zan nuna mata tallakama mutum ne mai mutunci daya san zafin kan shi. A can kaduna kuma dai daddy ne ya kirasu uncle hamza dasu baffah Abdul da tsofin nan biyu da suka rage cikin iyayyen su yace yana da magana dasu. Bayan sun zaunane din anyi abinda ya dace a tsakani ya kora dalilin kiran su din da yayi nacewa yanzu lokaci yayi da yake son ya mayarwa magada da dukiyan su a hannun su shi dama bai rike da wani manufa ba yana gudun ne ya bada a hamdame komai mu rasa a lokacin da aka gane mun bayana ya zamanto babu komai da zamu gada. Nan yan uwa suka fara fadin albarkacin bakinsu kan abinda ya fada din baffah hamza dai yana kurum harsai da yaji anyi shiru ya dauka da gyaran murya yana fadin. Amma sai naga bai dace ace irin wanan halin da aka fito akan wanan maganan yanzu ace wai a gida za a mika masu gadon nan daga mu sai mu ba wani shedun hakan na gwaunati daya shigo cikin zancen. Shiru falon yayi na dan lokaci kafin baffah Abdullahi yace wanan kuma shawarane mai kyau hakan ka kawo muna don mu nan idan munyi shedan hakan karshe komaina iya tasowa mu jefa jan mu a cikin wani rikicin kuma. Nan suka fara fadin albarkacin bakin su daddy dai yana kurun baiyi magana ba hakama modibbo da zuwa yanzu abinduniya ya dameshi kan fahintar waye daddy din nasa a yanzu da yayi. Don ko wanan taron daya tara din saida ya kara tuntubanshi kan zancen yayi wanan kiran da yanzu suke zama a kanshi din. Muryan daddy din ne yayi gyaran murya yake fadin hamza don na fahince ka yanzu kamar baka yarda da abinda zan basu ba ko hakan bai maka ba da zanyi ? Eh to gaskiyane baffah hamza din ya fada yace kasan sha,ani na gado wuyan lamarine a cikin sa balle duba ga yadda yanzu na fahinta cewa mutanen ban sun ba duk wani abu da yanzu ake magana akanshi baya. Ma,ana kamar sun yafe zancen dukiyan dake hannun ku dama su bukatansu kawai a daina farautansu din da akeyi su fito fili kowa yasan dasu a cikin dangine. Daddy ya bude baki zaiyi magana ta hanyar kiran sunan baffah hamza din yana fadin watau hamza baka fahinta ba. No daddy maganan uncle gaskiyane fa dole sai hukuma sun sanda za ai hakan kaima kasanda hakan don haka maganan uncle ba wani abu bane ai yanzu nagani modibbo ya fada daga can inda yake zaune a takure. To shike nan tunda haka kukace sai a gaiyato wanda zaku gaiyato din shike nan ko a zauna lafiya ba wani wanda zamu gaiyato a nan baffah hamza ya fada wanan karon a tsatsaye don ya hasala zuwa lokacin. Can dai kotun da akai maku sharia dasu za a koma a zauna a tsara komai yadda sharia ta tanada final ya mike don barin wurin saboda kirkiri ya hango an shuka rashin gaskiya ga al,amarin a filin Allah lokacin. Dakata mana hamza tsohon guda ya dakatar dashi ya koma ya zauna yake fadin idan kai haka yanzu kamar ka dauko wani barakane kuma a tsakanin ku ai da dan uwanka. Kallon inda daddy din yake zaune dagashi sai babban riga babu yar ciki a cikin ta ya zauna ya mike kafafuwan shi saman kujeran. Kafin yace no ba wani barkan da zai faru a tsakanin mu aishi yasan halina niko yaushe a bayan gaskiya nake ba zan yarda na goyi bayan karya ba har abada. Da akwai inda zanje daurin aurene dama ai su sun sani yana nuna su baffah Abdullahi da wuyan shi tau zaka iya tafiya don na zata fushi kayi dama zaka fita. Ya mike tare da kallon su yana fadin to ni zan tafi Allah ya bamu alheri sai yadda aka shirya din inji yasa kai ya fita suka bishi da kallo lokaci guda. Kafin tsohon ya kada kai yana fadin kai hamza watau dai wanan halin nasa sai abinda ya karu dashi yanzu kuma . A toh ya kara karfi yanzu dakuma matsayi tsohon dan bokone fa haukan boko na dukan shine ai daddy da sai yanzu ya samu daman yin magana yace tsohon mahaukaci dai ko anje kotun da yace din meye zasu iya wai ? Mikewa modibbo da bai iya jin karasan zancen na mahaifin shi yayi yana fadin ni zan tafi tunda ba wani abu zakuyi ba a yanzu din. Baffah Abdullahi yace tsaya sai ka saukemu a gida dama da aikin da nakeyi a can nafito shima ya mike yabi bayan dan nasu modibbo. Nan aka barsu da sauran suna kulla yadda abin zai kasance don yasan basu danacewa ga duk yadda ya tsara masu don dole subi shi don yana da karfin fada a cikin su. Dukan kofan da akeyine ina kitchen ina hadawa Ammar abin karyawa kada ya fita bai karya ba zuwa school yasa nake fitowa tunda safe idan na idar da sallah saina dora abinda zan hada mashi din. Tsam na wanke hannuna na fito zuwa kofan ina fadin who is on the door kafin na bude din nake tambaya daga ciki don ban yarda na bude kofan haka kai tsaye ba. Yace shine sakone daga mukhatar usman ya aikoshi jin hakan yasa na bude kofan wani mutum na gani a waje gajerene baida haske sosai yana rike da wasu takardu a hannun shi. Good morning yace dani you're welcome nace ya kara maimaita abinda ya fada da farko cewa an aikoshi wurin mrs Sambo da danta da za ai masu passport na visa. Ko zai iya ganin ta ya fada yana dan leka bayana daga ciki ashe umma ce ta fito yake kallonta zanyi magana naji tace talloni da yarbacin nan ya juye harshe yana fada mata sakon da aka aikoshi tace aitace danta kuma Ammar yana cikin dakin. Umma wai baki ganewane yanzu fa duniya ya canza umma kada ki saurin yarda haka da mutane lokaci guda ina fadin hakan saina juya na koma kitchen inda nake aiki ban san ya suka kwashe dashi ba dai a nan don aikina na ba hinma na gama na koma dakina a lokacin Ammar yazo ya sallameni bayan ya gama shirin shi na bashi kudin breakfast din ya tafi. Barci ne ya fara fisgana lokacin da wayana ya dauki kara don dole na tashi ina mika hannu na dauko wayan ina dubawa wanan sabon layine kamar na share sai na dauka oga sha,aban ne a lokacin na kara a kunne na. Yan mata barka da warhakan ya fada kai tsaye a cikin hausa wayan dana kara a kunnena na dan daga ina kallon layin da aka kirani dashi kafin na mayar ina fadin who is on the line please ? It,s me mukhatar usman your new boss now ya kuke ya hjy na turo yarona ya kawo takardan da zasu cika kin hanna hjy cikawa. Idanuwana na dan runtse muryan shi na dukan dodon kunnena sautin yana kayar min da gaba numfashina yana wani irin sauka da sauri sauri a lokacin. Hello din da ya sake fada yasa na tattaro natsuwa nasaka a zuciyana lokaci guda ina fadin no ka barshi already na riga dana biya mata makka zata tafi this year don haka mun gode. Masha Allah ya fada a bangaren shi tare da fadin da alama kina son kwaso halin mahaifin ki wurin kyautatawa sosai naji dadin jin hakan a gareki Allah yasa a fi hakan. Ba zan kuma so na hanaki samun lada a wurin Allah ba a yanzu saidai don haka zaku je umarah kuje makka daga baya no ita kadai dai zata tafi don haka yanzu no need taje umurah a yanzu. No Saidai shi umurah ba zuwa makka bane ai don haka zamu tafi a yanzu muyiwa mahaifin ku addua kamar yadda na saba zuwa ina masa lokaci lokaci zanso wanan lokacin muje tare daku da mahaifiya da iyalina muyi addua a tare insha Allahu . I hope ban takura maku ga hakan ba in a kwai wasu da kuke son muje tare dasu zaku iya bamu list din su a cikin lokaci mata biyar maza biyar bayan ku saidai ki tabbatar da masu imanine da mutunci a cikin family din . Don haka zan barki ki huta sai naji daga gareki shawaran da kuka yanke din zuwa anjima. Wayan nabi da kallo ina mamaki da al,ajabi ni kadai a dakin yau ina Alaja mai son nisanta danta damu yau ga wani na rokon a zaba mashi mutane masu kirki da zasu kai ziyara kasa mai tsarki don yin addua. Ni yanzu me zancewa umma kan wanan maganan ta dauka sai yadda nace a yanzu ina kokarin juyata yadda nake so ko me ? Da haka na mike zuwa wurin ta shago don naji fitanta daga gidan kafin barci ya fara daukana nasan zancen nan ne ya hana tayi min sallama. ZAINAB IDRIS MAKAWA ANA DARA GA , , , , , , , , 9️⃣5️⃣BY, , , , , , , , , , , , ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , , , , , , , , BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AT TAWWAB, , , , , , , , , , , ONLINE PAID NOVEL YAR UWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA BA TARE DA HAKKIN KOWA BA DON BIYA KI TURA DARI BIYAR 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK 08036959257 ALLAH SARKI AI RAINA BAYA BACI YANZU DON KIN FITAR DON NASAN AKWAI RANAN HADUWA SEE U👋👋👋👋 Na rasa me zancewa umma a lokacin don haka na zauna kawai ina sake sake a raina kafin na nisa na dago kai ina fadin wai umma kinji mutumin nan ya kara bugo min waya cewa ki tafi ai maki visa ke da ammar har ma da wasu mutum goma a bangaren mu. Don za a tafi aiwa mahaifin mu addu,ane a saudiya wai kuma tare dani zaku tafi har mahaifiyar shi da yan uwan shi za ayi wanan tafiya. Kafin in gama fadi umma takai gwiwan ta biyu a kasa tana addu,a ga Allah tare da daga hannayen ta biyy sama fuskanta yana kallon sama ga hawaye na zuba tana godiya ga ubangijin talikai taci gaba da jeru addu,a a cikin harshen yarbanci . Dole muda muke wurin muke amsawa amin amin ya Allahu har takai ga mikewa tsaye zakace ita din haihuwan kurciyan lagos ne a yadda ta juye yanzu zuwa al,adunsu . Bayan gama adduan ne nikan na tashi na shiga daga ciki falo na zauna na kunna tv saidai ba kallon nakeyi ba don tunanen daya rinjayeni a lokacin. A kan wa zamu zaba a cikin dangin mu ke nan don banga na zaba nikan a idona a iya sani na dai danayi masu a kaduna saidai idan mamaki zan basu a dauki wasu tsofi uku na nan da ba ruwan su mata yan uwan mune na sosai su din sai dai kamar ba a cikin dangi suke ba don talauci. Amma na kudurta komai ritsi dole inje da faiza da Amira ko fatima daya dai daga cikin su dolene saboda kaunan da suka nuna min a zamana dasu kaduna har yanzu kuma. Haka a bangaren maza zamu dauki baffah hamza da baffah Abdullahi Abdul makwabcin mu sai wasu biyu daga can yola yan uwan umma. Jikina na mayar bayan kujera ina sauke numfashi tare da fadin anya umma zata yarda da wanan zabin nawa kuwa ko zata sauya idan ta shigo. Matsala dayane na sani akan su faiza da Amirah amma in anyi duba da dubina sun cancanci tafiyan bayan dubana su din adduan su da alaman haske a yanzu. Idanuwana a lumshe suke umma ta shigo ta sameni hakana a zaune na mike kafafuwana idona a rufe bina tayi da kallo kafin tace dani lafiya nake kuwa ko wani abin kuma ya faru ? Ba komai na furta lokaci guda ina bude idona na sauke a kanta dakinta ta nufa ta dan dade a ciki nasan ta kewayane lokacin. Tana fitowa tun daga kofa take fadin nayi nazarin wanda ya dace ace mun tafi dasu din nace eh to ina dan dagowa tare da fuskantar ta nace . A kwai dai maza din na shiga lissafo mata su tare da dalilin sakasu din tana dan gyada min kai a hankalu alaman gamsuwa. Kafin na dawo wurin mata ina lissafo mata su din suma tare da mata bayani ko zata iya tunawa dasu tsofin dana saka din da ban tantance sunayen su ba a yanzu. Saidai kamar yadda nayi tunane haka din ne ya faru akan su Faiza din dana kawo kansu don taso ta musa din nayi mata bayanin dalilina ta gamsu aka aje maganan a haka. Bayan fitan umma zuwa shagon ta na fara neman layin ya Abubakar wanda yake jigo a garemu cikin family yanzu don in sanar dashi . Kiran ya katse bai kira ba ashe lokacin suna gun daddy ana wanan maganan da sukayi din a lokacin bayan ya fitone yaga miscall dina a lokacin ya dauka. Bayan mun gaisa nake fadin idan ba damuwa zan iya samun passport din uncle hamza dana uncle Abdullahi faiza na dai lissafo mai sunan su kaf . All dis peoples da kika lissafo min me zakiyi da passport din su haka ko zaki kaisu makka ne ya fada a cikin gatse da zolaya. Eh gaskiyane umurah dai zamu tafi tare muyiwa Abbah mu addua a can masha Allahu wai da gaake kikeyine wallahi da wasa da na fadi hakan da farko. Ashe abindana canka din gaskiyane yanzu haka muna tare dasu uncle hamza din ma zanyi magana dasu insha Allahu ba zai wuce yau din ba. Ba a kwana ba a ranan saida suka turo min passport din da duk wani abinsu nan dai na tura mai kamar yadda yace din. Haka ban garen ya Abubakar dai baiyiwa kowa bayanin komai ba akan photunan daya karba din don haka ba wanda yasan da wanan zancen . Haka kuma shima din tun rana dana tura sakon banji shi ba don bai kira ba akan yaga sakon ba sai wajajen tara na dare ya kira wayana da vedio call ina online a lokacin muna hira da Felix da yemisi da suke rokona na dawo wurin aikina na kyale Alaja bata san me takeyi ba a yanzu. Har felix din ke fada min cewa Aisha ma ta kawo mai karan zata bar Alajan ta dawo nigeria ko wani kasa. Da kyat na lalashe ta har ta bari yayanta ya dawo daga tafiyan nan da yayi kada hakan ya kara daga mai hankali don ana fama da naki case din yanzuma haka. Alaman ina ruwana na tura mashi karshe sai ga kiran wanan mutumin ya shigo min dama kuma ina mamakin rashin kiransa kada ya buda muna kasa a ido muzo muji kunya a karshe da banga kiran nasa ba na fara tunanen hakan a zuciyana saida na samu su yemisi muna hira na dan sha,afa da zancen lokavisa Na dan dade ina bin wayan da kallo tare da mamakin kirana da vedio call a wanan lokacin don me ba zaiyi kirana ba sai vedio call yana kallona. Sam babu damuwa a gareni don rigan barcin dake jikina ganin kiran zai iya katsewa a lokacin yasa mm a daga da sauri sai ga photon shi ya fito a wayan. Yana dauka yace mai tsiwa ya kika wuni ko har kin kwantane ko na kiraki duk da nasan yan mata kamar ku samari basu barin ki kwanta a wanan lokacin. Fuska na bata nake fadin sakon ya shigo dazun don su nake ganin sun dace a tafi dasu din a wanan lokacin. Dan murmushi yayi yana shafo fuskan shi alaman gajiya a tare dashi yace nagani saidai kamar har da yara a ciki kuma addua zamujeyiwa marigayi ai ? Eh shi zasuje suyi suma don suma din musulmaine adduan su kuma zaifi na wasu manya din nake gani alright as you wish. Bari na barki kici gaba da charting din ki kada saurayin ki ya tuhumi ko kin samu sabon saurayine ya zargeki. Zaki jini zuwa gobe zan turo da duk wani abinda zasuyi visa dashi inaga hakan zaifi sauki sosai har na umma din saiki turo min da account number dinki yanzun nan idan kin sauka daga hakan yace good night ya kashe wayan . Nan ya barni da guntun tunanen maganganun shi gareni kwanci nayi ban dauki hakan a komai ba na dauki hakan dai kamar yana son ne sabo ya dan shiga tsakanina dashi a yanzu. Har aka turo min da kudin da zasuje suyi visa har da dori wasu a sama kudin don nasan wanan kudin yafi karfin wanan laluran suma din na basu daidai gwagwado don ban kyataci kowa a cikin su ba lokacin. Sai lokacin labarin tafiyan ya bazu a dangi daddy kan mamakine ya kashe shi don bai san ta ina kudi ya fito muna haka da wanan alherin ba. Gashi ba lokaci don baifi kwana hudu ya rage yanzu ga tafiyan namu don haka ba lokacin wani kwana kwana ga kowa ko wani nazari don baffah Abdullahi yayi tsaye kan yaran zasu tafi tunda tare dashine. Haka suka shirya muka hadu a logos din don tacen muka tashi sai kasa mai tsarki gaba dayan mu zamu kai ziyara a ka,idance . Wanda nake tunanen wata kila iya mune tafiyan dama badashi ko wani nasa ba ko lokaci zama dasu Faiza bamu samu ba lokacin don da yamma suka iso sai batun tafiya wanan yana cikin shirin ya Abubakar ne don kada a dora muna wahala yace. Shigan safiyane ana asalatu muka sauka birnin jiddah inda baffah hamza ke jagorantan mazan a lokacin don wayewan shi a cikin mu duk da nidashi ne muna a tsaye lokacin. Har motar da zata kwashe mu zuwa masauki mu huta kafin mu wuce zuwa madina washegari kamar yadda suka tsara muna din a cewan wanda yazo daukan mu din. Ba laifi mun samu masauki mai kyau da nagarta gaskiya don munji dadi sosai a ranan don haka tun jidda mun sauke gajiyan mu a nan. Mun bar magana caaaa a kaduna don kowa da irin yadda yake fassara zancen tafiyan namu don wasu na fadin nice ai na kaisu umurah din da kaina don nayi karfi yanzu na rika sosai. Wasu kuma na fadin a, a gadon ne ai aka fara bamu muka fara banzatar da kudin dama ai kudin gado haka yake komai yawan shi a banza da wofi yake tafiya. Wasu kuma na fadin idan ba kudi yai muna yawa ba na rasa wanda zan kai umurah sai su iyan Amina da dije da inna ma,u. Inda wasu kuma suke ganin dacewan abinda nayi din don inbada su faiza da fatima babu wanda bai bukatan zuwa wannan kasan dama a cikin su basu samu mai kaisu ba idan ba uncle hamza dake da karfin zuwa ba sai idan bai so ba dai. Haka dai zancen yai ta yawo kowa na fadin albarkacin bakin shi kan tafiyan namu lokacin a gidan daddy kan basu da bakin magana yanzu don kowa dai na dauki dan dakin shi sai kaji baki ya mutu murus. Basu da abin fada sai saka albarka tundai anty amarya dake fadin kai yarinya ba abinda ya dameta ai an mata ha,inci ta saka muna da alheri yanzu don bata mace halarci ba. Washe gari kuma sakko mukayi zuwa birnin madina a can ma wanda zamu hadu dashi yazo ya taremu ya kaimu masaukin da zamu sauka. A wani katafaren hotel ne mai kyau da tsada komai na wurin sam barka sai a lokacin muka samu kwarin kiran yan gida don a gaisa dasu su faiza suka shiga photuna suna turawa gida. Mukan sai kallon su da mukeyi son wa zamu kira yayin da Ammar yake tare da Abdul makale tare dashi suke komai don muna zuwa masauki bamu zauna ba su uncle sukace mu fito mu mika gaisuwa gun manzon rahama don haka muka dunguma zuwa masalaci a lokacin. Bamu dawo masauki ba sai tara na dare don haka kowa ya gaji ya nufi dankin shi don hutu a lokacin ida muke daki daya mu ukku da faiza da fatima. Ba wani hira sosai yanzu mukeyi kamar da can baya ba dasu saboda dan dedewana da akayi yanzun ba a tare yasa akwai dan shakku a tsakanin don sai wani ban girma sukeyi ko kuma idan najasu da hiran zasu dan sake muyi hiran. Diba kuma a yadda yanzu wani irin natsuwa da kamala yazo min ba sahiban da wagar wagar suke gani ba don ko a da dai masifa da fitina yafi min yawa sabo da zaman geto yanzu ko duk ba wanan komai a cikin kamala suke kallon ina yinsa. Saida Nagama duk duk wani shirin kwanciya da zanyi a lokacin na hawo mamaken gadon alfarman dake dakin na kwanta dancan karshen gado da suka barmin. A lokacin ne wani irin natsuwa tare da tunanen daya haifar min da ajiyan zuciya yazo min lokaci guda ina sauke shi wanda ba komai ya jamin hakan ba sai ganin Fa,idan wanan tafiyan da yanzu mukayi. Don addua kan mahaifin mu ya samu a ranan wurin yan uwa sosai duk wanda muka hada ido zai dinga kwararo mai addua da fatan dacewa da rahaman ubangijin gareshi. Ido na lumshe a hankali ina jin kaunan wanan mutumin da yayi sanadin yin hakan a garemu yanzu din don ba karamin kokari yayi muna ba kan hakan. Idan fa nace kauna baiwa kauna na son shi ba a, a kauna dai wanda ke nuna kanayi da mutum sosai a lokacin wanda kake jin wani abu har kasan ranka akanshi don ya zama masoyin mu na gaskiya kamar yadda muke jin ya Abubakar a yanzu. Mun bar lagos laraba alhamis oga sha,aban ya diro lagos din da zuman zama dani da wasu daga cikin ma,aikatan a sulhunta tsakanina dasu. Son haka ya baro daulan larabawa dayaje last ya nufo Nigeria saidai tun a airport Felix ke fada mai ai ban kasan mun tafi umurah duk family din mu lokacin. Mutuwan zaune yayi da mamaki yace ita sahiba din yace kwarai jiyan nan suka bar kasan nan nima a wurin oga jimoh na samu labari. Don har da Abdul suka tafi a cewan shi itace ta biya mai tare da wasu yan uwanta su goma ga mahaifiyar ta da kanin ta kuma. Har oga jimoh yasa ayi bincike ko kudin company ta kwasa ba a sani ba tayi wanan abin haka mai bam mamaki ya kare fadi yana kallon fuskan shi don son jin me zaice shima a game da hakan. Da sauri ya girgiza kai yana fadin no no ba zata taba yin hakan ba na sani dole dai akwai wata kila dai dukiyan nasu ne ya fito suka fara da hakan. Har suka kai gidan shi da yanzu yasha gyara sosai ta ko ina don kullun cikin canza mashi tsari ake koda yaushe. Ga abinci an tare shi dashi amma zaune yake ya kasa wani motsi ya kurawa kasan ties ido kawai yana tunane ya rasa me Alaja take nufi dashi a rayuwa. Shigowan felix tare da oga jimoh falon ya katse mai tunanen da yakeyi din nan suka gaisa oga jimoh din ya kara fada mai yadda mukayi dasu a fili inda yake fadin . Yayi iya kokarin shi sosai kan na hakkura na dawo bakjnn aikina amma na kafe bazan dawo ba tunda har mahaifiyar shi tana ganin cewa cutar shi nakeyi ina amfani dashi dan naci dukiyan shi. Kai ya girgiza wanda hajan rashin yawan maganan shi sosai ne yasa ya zama mashi dabi,a a jikin shi idan yaji maganan da bai gamsheahi ba lokacin. Ya dan zakudo ya gyara zama yana fadin i know who is that girl kudi ko wani abin ba zai rude ta ba idan zatayi abune zatayine idan kuma tace a barshi an barshi ke nan. Don haka ba zamu tsaya muna binta ba tunda kun bita da farko taki a dan saurara mata har zuwa lokacin da Allah zaisa ta sauko ko zata dawo. Don haka ayi gagawan maida wani a matsayin ta yanzu kada aiyukan suzo su tsaya a samu matsala ya fada yana mayar da bayan shi ga kujeran daya dan dago din don yayi magana. Ya dora hannun shi daya saman goshin shi yana dan murzawa a hankali tare da lumshe idanuwan shi daya rufe su lub a lokacin. Wanda ba komau yake tunane ba sai irin matakin da yakamata ya dauka yanzu kan wanan abin na Alaja ya kaishi makura ta yadda ba zai iya kyale hakan yaci gaba ba. Da ace Alaja tasan irin matsayin da yarinyat nan take dashi a cikin zuciyan shi da batayi gangancin daukan wanan shawaran da zuciya ta yabata ba. Tana da kirki tana da mutunci haka tarbiyan ta yayi daidai da irin tarbiyan da yake son samun mace dashi ga aiki tukuru babu ha,inci da cutarwa a cikinshi kuma a duk lamarin ta. Ai baki sani ba Addah ni har yanzu wanan abin bai daina ban mamaki ba kai abin abin daure kaine fa ace wai wanan yarinyat ta kwashi mutane haka zuwa umura kawai gaskiya da sake. Dagowa yayi ya dan kalli mahaifiyar nasa daga inda yake kwance ya mimike saman kujera ko zaiji dadin jikin shi. Don daren jiya ya sauka kasan tsawon wata biyu ke nan baya Nigeria don haka akwai gajiya a jikin shi ga kuma gwaggo hari data tayar dashi wai sai ya fito ya saka wani abu a bakin shi tunda tun shigowan shi yake kwance yana barci. Daga inda yake kwance yana sauraron wayan da sukeyi da mommy hjy Addah baisan me Addah din ta fada ba a lokacin ya dai hasaso zancen don yaji mami din shi na fadin. Kwarai kuwa irin halin sa ta kwaso na son yan uwa Addah saidai ina jiyo masu abinda zai biyo baya gaba sun samu dukiya yanzu sun fara banzatarwa a banza shifa kudin gado haka yake kamar an kyasta mashi ashana dama kafin yazo hannun magada. Sai a lokacin ya fara fahintar ko kan wa suke zancen su saidai bai tabbatar da hakan ba a lokacin kafin yaji tana fadin. Ni fa yanzu a kan wanan maganan ko waya mun daina yi dasu yanzu nikan ai yafi min ma don kada azo ace dama don gadon nasu nakeyiwa wanan rawan kan a kansu . Sun dai jima suna magana inda a karshe ya fahinci a kan wa suke zance bayan sun kashe wayan ne ya kalli mahaifiyar nasa ya jefo mata tambaya da fadin. Mami suwa Sahiba ta daukane kuma ina suka jene da mutanen da kuke magana a kai saita juyo tana fadin kaidai bari the boy. Kaga abinda dama nake gudu ke nan tun wuri ku kuma baku fahinceni ba mutane su fara fadin don naga kudine nake kokarin cinna maka ita ka aura. Kasan ko zasu fada irin wanan facakan arzikin da suka fara haka wai ace sahiba ta dauki mutum goma zuwa umurah lokaci guda haka kai tsaye ai wanan abin akwai ayan tambaya a cikin shi. Shima jin tayi shiru ya jefo mata tambaya da har an mika masu dukiyan nasu ne ko haka ya tambaya yana kallon fuskanta ? Wanan kuma ban sani ba har in an basu gaskiya banda labari kuma da an basu din aida naji kuma koba gaskiya ba wanan abin nasu aiba a boye yake ba kowa yasani. Haba mami kin gani gashi kin ba kanki ansa yanzu cewa ba a basu ba amma kuma kuke masu wanan zargin haka why don Allah mami kika canza hakane yanzu ? Ya kamata ku tausayawa mutanen nan da ace kunsan irin kaskancin rayuwan da mutanen nan suka gani a rayuwan ba zakuyi masu wanan abin ba yanzu. Kudai maza haka kuke ga gaskiya mutum na gani amma sai ko rufe kuce mutum baiyi daidai idan bashi ba ba za a tsaya aji inda kudi ya fito ba sai a hau murna cewa wai tayi kokari. Na fahinci yanzu don na furta ina son yarinyar nan kika taane su hakan ga amma idan ba haka ba ai da can naga kina tausayin su sosai ba kamar yanzu ba. Duk abinda zaka fada ni ina nan bisa kan zance na ba zakasa mutane su zage a banza ba ko ka dauko min magana a cikin zuria ta. KLlin mamaki yake jifan ta dashi don ya kasa gane mai take nufi har yanzu don kawai yace yana son sahiba din ne wanan abin ko kuma wani zance ne a kasa daban ? Shiru yayi ya mayar da hankalinshi wurin tv dake aiki saidai zuciyar shi fam yake da tunanen me hakan ke nufi har zan dauki mutum goma zuwa umarah. ZAINAB IDRIS MAKAWA ANA DARA GA , , , , , , , , 9️⃣6️⃣BY, , , , , , , , , , , , ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , , , , , , , , BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AL MUNTAQIM, , , , , , , , , , , ONLINE PAID NOVEL YAR UWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA BA TARE DA HAKKIN KOWA BA DON BIYA KI TURA DARI BIYAR 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK 08036959257 ALLAH SARKI AI RAINA BAYA BACI YANZU DON KIN FITAR DON NASAN AKWAI RANAN HADUWA SEE U👋👋👋👋 Sallah asubah a haram mukayi don tun karfe uku da rabi baffah ya tayar damu don zuwa masalaci. Duk sakkon mu mun samu har masalacin ya fara cika mun daiyi sa,a mun samu shiga ciki mun zauna. Bayan nafila da muke tayi bini bini zamu mike mu gabatar da nafila kuma gaba dayan mu saidai Fatima da take dan kwantawa tayi barci ta dago kuma ta bi sahun muba wanda ya matsa mata don mun san cewa ita din yarinyace a cikin mu. Har karfe goman safe kafin mu dawo masaukin mu a gajiye kowan mu yake a lokacin wanka mukayi kowa yabi lafiyan gado ya kwanta don karfe sha biyu kawu yace zamu koma masalacin. Muna da kwana biyu ba abinda mukeyi banda ibada tukuru babu kakautawa kowa na fadawa Allah zuciyan shi. A rana ta ukune munje masalacin an idar da sallah sai ga baffah yazo inda muke zaune da abincin daya sawo muna saboda yace mu daina zuwa gida mu wuni a nan sai bayan sallah mu tafi masauki. Bayan sun karba ne don ni ina addua a lokacin kai na samu daga mashi kawai a lokacin don banson katse azzakar ddin a lokacin. Karfe tara muka iso masauki ba zancen tsayawa hira a yanzu gare mu don kowa a gajiye yake lokacin cikin mu. Daga umma har sauran tsofin uku da suke tare basu shigowa dakin da muke a cikinsa dan gara mu din mukan shiga mu gaisa dasu ko mu dubasu wani lokaci idan muna a masaukin. Wanka na fito lokacin don nice na shiga farko suna zaune suna dan ciye ciye kasa saman kafet ga sanyi AC ta ko ina a cikin dakin. Umma ta turo kofa ta shigo daga inda nake tsaye ina kokarin saka riga a jikina jin suna gaida ita yasa na juyo da mamaki ina kallon ta. Yarbanci muke yi don haka ba lalai bane suji me muke fadi a lokacin wanda kuma umma zuwa tayi tana fada min tsohuwa guda bata da lafiya tun a masalaci bata fadi ba murane ya kamata ya haifar mata da ciwon kai da zazzabi jikita yayi zafi. Cikin nuna damuwa nace subbahanallahi duk suka kalloni suna son jin me ya faru da hausa naso yi masu bayanin cewa bata da lafiya sai kuma na kasa dole na juya da turanci ina fada masu abinda ke faruwa tunda hausan ya kiya lokacin . A gurguje na saka riga a jikina muka fita zuwa nasu dakin dake kusa damu a kwance na sameta ta nade a cikin katon bargon su . Yadda na gantane ya tayar min da hankali na karasa ina dadin mama meyene ya sameka zamu asibiti ko a dan yanayin tashin hankali nake magana. Don Allah ya gani na tsorata da hakan a wurin yarbawa zasu camfa suce dama da wani manufa na kaisu saudiya don nayi kudi dasu ko wani abu. Fita nayi a gigice daga dakin na fita zuwa waje don in samo magani a wanan lokacin Allah ya taimaka muka hadu da wani dan Nigeria ina masa bayani yace gaskiya ba wani phamacy a nan kusa amma barin taimaka ga wanan ku bata gobe sai ku kaita asibitin. Dan jakkar dake bayab shi ya bude ya fito da wasu magani ya bani tare da bayanin yadda zata sha din nayi mai godiya na juya da sauri zuwa lifter. Ina kokarin rufewa ne aka dagatar dani wasu mutane zasu shigo mazane ni kadaine mace a cikin su har suka karaso suka shiga tare dani duk hankalina bai a kansu ina can ina tunanen halin da mama take ciki kwance. Mai tsiwa meke faruwane haka dake naga hankalinki a tashe yake is anything wrong somewhere ? Duk wanan maganan da yakeyi a cikin harshen hausa yayi shi sai na karshen daya fada da turancine na fahinci dani yake magana lokacin. Yasa na sauke fuskana a saman nasa ina dan kallon shi tabbas shine shine wanda yai sanadin zuwan mu saudiya da har muka fara zargin ko ba zai cika alkawarin da yayi muna bane yazo shima kamar yadda yace din. Sai kuma na kara kai idona kan kayan su duk da ba wani kaya bane dan jakane irin na maza matafiya sai sauran jama, an dake ciki wanda na fahinci wani ban girma da suke mashi na musanman. Manyan idanuna na dan kada don mayar da kallon gareshi saina sama nidin yake kallo har lokacin cikin daurewa nace you're welcome. Lumshe ido yayi a daidai lokacin da kofan elevetor din ya bude aka fara fita nima yunkurin fitan nayi na bar wanan din daya taimaka min da magani yana masa bayani abinda na fada mai. Wait sahiba ya fada daga bayana kafin suka karaso zuwa inda nake yana fadin na bari wanan zai dubata doctor din shine da yazo dashi dama don irin hakan . A tare muka isa dakin su umma din na fara shiga nayi masu bayanin zuwan shi amma a cikin harshen yarbanci na fadawa umma din. Nan umma ta shiga washe baki tare da daga hannu sama tana godewa Allah da zuwan shi kafin nace ta daina hakan mana kada su dauka wani abune hakan. Na dan juya na fada masu da akwai wa yanda zasu shigo yanzu su dubata na fadawa faiza ta fada masu saida suka nasu na fita na sheda masu su shigo. Da sallama yana rataye da cout din shi daya saba a hannun shi ga alaman gajiya a tare dashi gaisuwa na mutunci sukai masu kafin shi likitan ya nufi aurin da mama Amina take kwance din. Nima takowa nayi nazo bakin gadon ta gefen shi ina dan kiran sunan ta ta dan yaye abin rufan ta amsa za a dubaki na fada a cikin hausana da ke dan sarkewa. Har dai ya dubata ya gano cewa murane ya jawo mata matsala ya haifar mata da zazzabi haka mai zafi nan take ya bude dan jakkarshi ya fito da allura yai mata sukai mata sannu suka fita dakin zuwa masaukin su. Mun dan jima a dakin har saida barci mai nauyi ya dauke ta kafin mu fito zuwa dakin mu mu kwanta da asuba kuma muka tashi zuwa masalaci yin sallah. Sai bayan mun dawo ne su baffah suka shigo suna gaida mana da bata samu zuwa yin sallah ba lokacin. Nan baffah yaso ya fada muna zuwan mukhatar da tawagan shi har da mahaifiyar shi a cewan baffa din ya shigo nan jiya har yasa anwa mama Amina allura umma ta fada. Au kai wanan mutumin ai akwai mutunci a daidai lokacin na fita daga dakin zuwa dakin mu inda muke . Ban tsaya ko wanka ba na fada saman gado don gajiya sai barci nayi barci sosai har da mafalkin naga ana wani taro wanda bansan kona meye ba lokacin. A daidai lokacin da ban kaiga sanin ko taron me nagani ba na falka daga barcin kuma taron ya tsaya min a zuciyana. Wanka nayi a gurguje don kada mu makara ga fita don sukan basu kwanta ba tun dawowan mu kuma harsun shiya ko . Gaba dayan mu har su umma da mama Amina da yanzu taji sauki sosai don treatment din data samu muka fito don fita zuwa haram din. A wajen haraban hotel din muka hade dasu sai a lokacin na tabbatar da maganan baffah din lalai da mahaifiyat shi sukazo umurah din ashe. Don ya rike mata hannu suna tafiya tare a hankali tawagan shi suna biye a bayan su suma a hankali naso mu share amma zuciyana ta haneni da hakan. Dole naje su umma zuwa wurin da suke don basu farga damu ba a lokacin sai jin muryana sukayi ina fadin salamu alaikum. Haka yasa shi ya dan juyo da sauri ganin mu gaba dayan mu yasa yaja hannun mahaifiyar nasa suka tsaya. Nan muka fara gaida mahaifiyar nasa a cikin girmamawa ba wata tsohuwa bace sosai saidai ta dan manyanta gaskiya amma da sauranta a rayuwa. Ohh hjy yace kafin ya shiga yi mata bayani a cikin yare yana fada mata mune iyalin mariganyin ke nan da yan uwanshi. Da sauri a wani irin yanayin tausayawa take fadi cikin hausanta itama da bai zauna mata a baki ba kamar mu a yanzu. Tambaya takeyi tare da nunani tana fadin kai wanan kan ai tayi kama dashi sosai shima dai daga inda yaken ido ya kura min kamar yana son gano kamar data gani a jikina din. Su kawune suka iso a daidai lokacin data rugume ni a jikinta tana dan buga bayana tare da jefawa Abban mu adduan samun rahama. Sun gaisa dasu baffah suma tayi masu gaisuwan rashin Abba din tare da adduan albarka ga iyalan shi gefe na koma don wayana da yai kara na dan ja gefe ina amsa kira saidai hankalina yana wurin su duk da bana jin abinda suke fadi a lokacin don wayan daya dauke min hankali. Ba a dade ba sai ga wani dogon motan kwasan mutane yazo nan baffah ke fadin wai muzo mu shiga motan a, a ba zamu shiga ba baffah Faiza ta fada zamu taka da kafa mukan tunda yafi lada ku tafi kawai zamu karso. A nan dai din bayan bafdah yai masu bayani suka tafi suka barmu da kafa muka karasa zuwa ba wani abu da akeyi sai ibada tukuru. Duk da muna tare mun hade da tasa tawagan a yanzu don dama signing din tafiyan duk tawaga guda muke dasu . Haka yasa tun a ranan muka dan fara sabawa tundai wasu yan matasan mata da mukazo muka hade dasu su uku inda na dauka dai sudin kannesa ne na jini. Shakuwa sosai ya shiga tsakanin mu dasu don kunsan mata da saurin sabo lokaci guda saidai na fahinci biyu daga cikin su matan aure ne su dayace bata da aure. Haduwa dasu yasa muka fara dan sayayya a madina din don cewan su wai kayan madina sunfi na makka zama quality jin hakan yasa su faiza suka biye masu suna jibgan kayan tsaraba duk da su bafdah sun hanamu sayan kaya a madina din. Ni dai iyakata in rakasu ban faye sayen kayan ba har suna min sherin hakan gashi munyi sa,a zamu kai kwana goma shabiyu a birnin madina don rashin zuwan shi da wuri ya jawo hakan. Ina yawan ganin su tare dasu baffah sosai a ko ina zamu hadu suna tare dasu banda gaisuwa ba wani abinda ke hadamu dashi don yawan kallon da yake min idan mun hadu har na fara tsarguwan shi. Ban faye zuwa inda yake ba idan suna tare dasu baffah zan tsaya daga nisa dasu ranan dai har nakai ga jan tsuki don na manta tare da yan uwanshi muke ina fadin kai nina tsani kallo wallahi. Waye ke kallon ki faiza ta tambayeni wancan mutumin mana har bana son mu hadu yanzu wallahi sai ya dinga bin mutum da kallo haka kamar , , , , Faiza ce tayi min nuni da su cewa dan uwansune fa naja tsuki ina kawar da kaina gefe daya hankalina ya koma kan wasu yan kasan chaina na bisu da kallo. Banyi aune ba sai jin muryan shi nayi a bayana kusa sosai yana fadin sun baki sha,awane kike kallon su haka ? Firgigit na juyo inda muryan nasa yake yana kusa dani din kamar yadda nake zargin gaida shi nayi cikin basarwa kamar banji abinda ya fada ba da farko. Ya gyara tsayuwa yana fadin kuna kokari sosai dake da yan uwanki uncle ya fada min irin kokarin da kukeyi ai saidai ku dan rika ba kanku hutu umurah ba aikin hajji bane dake da dokoki da yawa nayin sa. Nagode kawai na fada ina kokarin wucewa muryan shi ya dakatar dani da yake fadin zanso ki samu lokaci mu dan tattauna dake kafin mu bar kasan nan don akwai abinda nake son muyi magana a kai daga ke sai ni a nan din. Kallon ido da ido nayi masa wannan karon a cikin mamaki nake fadin a kan me ke nan zaka so zama dani fa ?. Saida ya dan murmusa yace wani abune daya shafi rayuwan mu a yanzu duk da mun fara magana dasu malam hamza amma zanso naji ra,ayin ki kema kan hakan. Idan ya shafi rayuwana ai ko a waya zamu iya maganan don ban faye son tsayi haka da mutane ba in public gashi kuma kace su baffah sun san zance ai is OK tunda shi baffah hamza yana da wayewan kai sosai ina fadin haka na juya na tafi. Na barshi yana bina da kallo tare da mamakin baudaden halina nan kan sam ban biyo mahaifina ba ga hali ya fada cikin zuciyar shi. Washe gari da darene bayan mun dawo masauki kwana biyu ya rage mu wuce zuwa makka sai ga kiran ya Abubakar ya shigo min. Na dauka muka gaisa ya tambayeni yan uwa nace duk suna lafiya yai muna ya ibada har na bashi kowa su faiza suka gaisa dasu. Kafin ta sake miko min wayan yace akwai wani abinda ke gudana ne dama tsakanina da mukhatar usman ashe don dazun uncle hamza ke fada mashi. Da sauri na tare shi da meke nan fa no ni ba wani abu jiya madaine yake fadin yana son yin magana dani ai dadai ya fahinci ban san komai sai cewa yayi is OK zai kira gobe sai muyi magana don ya fahinci yanzu darene a wajen mu. Bayan muyi sallama na kashe wayan zuciyana yana cike da tunanen wani magane wai gashi su baffah basuyi min wani bayani ba. Muna kuma tare dasu dazun da zamu dawo masaukin mu ai kawai saina share zancen ni naci gaba da tsabgogina na kwanciya na kwanta. Washe gari ya kama jumma,a da wuri muke shirin fita zuwa masalaci don mu samu sallah a lokacin cikin masallacin. Kowan mu yana shirin umma ta shigo dakin da wani leda mai kyau ta miko min tana fadin yau jumma,ane mu saka fararen kaya mu fito. Na bude ledan wani dogon rigane mai kyau da daukan ido kafin ma nayi magana take fadin in saka ba lokaci idan mun dawo zatai min bayani ta fita. Ni dai na bita da mamaki faiza ta bude rigan tace na saka yana da kyau sosai gashi yau jumma,a dama ban so ba amma na daure na saka don umma. Saidai ina jin don me zata kashe kudinta ta saya min riga haka ni ban saya mata ba haka muka fito dole motan dake kwasan su zamu shiga mu bisu kada mu rasa sallah a haram din. Har mun zauna cikin motan na hangoshi ya fito shi da wasu mutum biyu shima fararen kayan ne na yan Pakistan a jikin shi sun karbeshi sun masa kyau sosai. Suka shigo motan ya tashi ban yarda na dago kaina ba a lokacin don kada mu hada ido dashi tun kallon dana jefa mai lokacin da suka fito din na kawar da kaina gefe ina karatun wani addua a cikin wayana. Har muka isa masallacin muka nufi wurin mata suma maza suka nufi nasu wurin har dare muna ciki muna ibada kafin mu dawo masaukin mu. Duk dai gani nan banjin dadin kaina a ranan gaba daya tun safe ina jin bakin rai muna sauka mota su mama Amina suka tareni da fadin yar nan ashe abin arziki ya samemu haka yau ? Ban fahinci me take fadi ba a lokacin don haka murmushi kawai nayi mata na wuce zuwa ciki na barsu suna tafe bayana suna fadin wanan abin da mamaki yake babu abinda bai iya faruwa ga bawa idan Allah ya nufa dama ? ZAINAB IDRIS MAKAWA ANA DARA GA , , , , , , , , 9️⃣7️⃣BY, , , , , , , , , , , , ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , , , , , , , , BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AL AFUWW, , , , , , , , , , , ONLINE PAID NOVEL YAR UWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA BA TARE DA HAKKIN KOWA BA DON BIYA KI TURA DARI BIYAR 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK 08036959257 ALLAH SARKI AI RAINA BAYA BACI YANZU DON KIN FITAR DON NASAN AKWAI RANAN HADUWA SEE U👋👋👋 A hankali yake saukowa daga matakalan ya na tsikayo muryan mahaifiyar shi a waya tana yanka salati tare da fadin aure fa wani irin aurene haka kowa bai san da shirin saba ? Kafin ya karaso wurin yaji tayi shiru tana saurare wanda suke wayan dashi lokacin har ya iso ya zauna ba tare da yayi mata magana ba yana dan tunanen shi. Kalman data fada yasa shi dago kai da sauri yana kallon ta taci gaba da fadin dolema ai ita Sahiba din tasan da shirin auren ta dama sukaje can watau sun raina damu nan har zasu gwada muna mu bamu isa ba ko bamu kaiba. Da ansan abindata shirya ke nan da aiko su hamza din kada su tafi balle su dauki wanan rainin hankalin nata. Nina dauka a yanzu muna da kima da darajan da zata kawo miji nan a daura mata aure amma don ta gwada muna bariki auren ma a can saudiya zasu daura shi. Wai sahiba ce tayi aure kowa mami yake tambayanta da zalla tashin hankali a idon shi karara don wanan zuwan ya dawo da niyar yin yadda ya dace dashi da mahaifin shi koda mami din bata soba kuwa. Sai gashi tunda faran safiyan ranan da yake saka ran dawowan mahaifin shi suyi zaman karshe da mami din kan kudirin shi kunnen shi ya tareshi da wanan zancen a bakin mahaifiyar shi. Zubur ya mike yana fadin sahiba fa kika ce mami Sahiba din itace tayi aure a can saudiyan dama aure sukaje yi a can bata sanar da kowa ba sai kuma ya juya ya fita kafin ta bashi amsa. A rude ta kashe wayan tana kwals mashi kira saidai ko juyowa baiyi ba balle ya amsa kiran da take mashi da the boy boy fa dakai nake bakaji bane wai. Don sam ta manta da wani zancen so da yake min abaya motan shi ya nufa kai tsaye bai tsaya ko ina ba sai gidan ya Abubakar da yake zaton da sanin shi akai komai. Wanda baisan shima sai bayan daurin auren da baffah suka nuna isa sukai min ya samu labari ba duk da su baffah sun fada mai yadda zancen ya kasance amma yaji ba dadin rashin sanar mai da kuma rashin tambayan ra,ayina da basu samuyi ba. Don ya fada masu cewa su fara tambayana ra,ayina kan hakan da mahaifiyar mukhutar din tazo masu da bukatan tana son hadin iri a tsakanin mu dasu don abinda danta kawai zai muna ke nan ya rama halarcin mahaifin mu gareshi a cewan ta. Yace su tambayeni suji ra,ayina don yasan halina fiye dasu zan iya tara masu jama,a a can ayi yadda ba,a so a tsakanin amma kuma da suka zauna dasu umma sai a karshe shawara ya tsaya kan cewa gara dai ayi din kamar yadda suka bukata tunda su sun isar min ai suke gani. Da wanan shawaran suka tafi masalacin bada niyar daura aure a ranan ba amma sai kanin mahaifin shi mukhutar din dake cikin su yace ga sadaki gaba daya tunda suna wuri mafi tsarki a duniya a lokacin ai gara kawai ayi komai daga baya sai ayi duk shagalin da za ayi in an koma gida. Wanda ba bata lokaci kuma bayan idar da sallah suka gaiyaci mutanen dake wurin aka tsaya aka daura aure akan sadakin dubu dari kacal a musulunce. Horn ya dinga yi da karfi saida maigadin gidan ya fito a gigice yazo ya bude mai zan iya cewa wanan ne zuwan shi na farko duk tsawon zama shi dan uwan shi a lokacin baisan yadda gidan shi yake ba . Don abinda ke tsakanin su na rashin jittuwa da basayi ra,ayinsu yasha bambam dana juna a yanzu din ma magana yazo ya fadawa dan uwan nasa akan burin shi ya cika sai ya zuba ruwa a kasa yasha. Horn din motan yayi ta dannawa hakan yasa ya Abubakar din fitowa dagashi sai dogon jallabiyan dake jikin shi a lokacin. Yayi mamakin ganin Al, mustapha din gidan shi sam bai kawo akan wanan zancen yazo mashi gida ba a lokacin sai gashi yana dan kakaro murmushin dole a fuskan shi don ganin dan uwan nasa a gidan sa duk da baisan abinda ya kawo shi gidan ba lokacin yasan dai dole akwai wani dalilin zuwan shi gidan wurin shi. Haka ya karaso zuwa inda yake kokarin fitowa a cikin motan shi a fusace shima sai ya daure fuskan shi yadda ya ganshi din. Salamu alaikum ya fada tun kan ya karasa isowa inda yaken rike wanan salaman munafuncin nazo nayi murnane kan sherin da kake bina dashi. Har ya fito a fili haka kayi nasaran rabani da Sahiba a wanan karon saidai ba zaka iya raba zumuncin dake tsakanin mu ba ai. Kaifa baka da hankali duk da nasan ba yinka bane wata kila a buge kake ma yasa har ka fadi hakan in bashi ba nine zan rabaka da sahiba ko wanda ya aure ta a yanzu . Juyawa yayi ya kalli yan sandan dake kofan gidan suna gadi wanda suma din su suke kallo daga inda suke kafin ya juyo yana murmushi ya kalli dan uwan nasa yana fadin. Kaci arzikin a gidan ka na sameka da ba haka ba yau dana nuna ma dan drugs nake na gaske saidai ni shana ba kowa ne yasani ba ai don banyi shan da nake zuwa mashaya kamar na wasu tsofin a baya ba. Ido Abubakar din ya runtse tare da hade dantsen hannun shi kamar mai alaman shirin kai masa naushi a lokacin. Ashe kana da wanan labarin kaima saidai wanda ya fadama koya baka labarin cewa tare suke zuwa da manemin matan da har tsufa ya kasa daina gara wanda yayi da kurciya ya daina yanzu ai. Wa kake nufi da hakan ke nan yace wanda ka fada abokin cin mushen sa nake fada na kurciyan da sukai sha,shanci tare ya daina shiko yana ruwa har yanzun. Wani kallo ya kureshi dashi kamar zai dukeshi kafin ya kuta ya juya ya bude mota zai shiga sai kuma yaja ya tsaya yana fadin . Kaci bashin wanan kalman daka fada a yanzu sahibs kuma ka rubuta ka aje cewa saina aureta muddin ina raye. Shirme ke nan don a yanzu Sahiba tafi karfin ka fiye da yadda kake zato don wanda ya dauki garabasan ba sa,an jan wanda ma kake takama dashi bane balle kai a yanzu. Shima jan idon shi ya zubo mai kafin ya kuta yana kokarin murda key din motan ya kara fadin zancen bashi kuma ni Abubakar bana cin bashin kowa a rayuwa. Nan yaja mota a haukace Allah ya taimaka ba kura a gidan dake malale da inter lock a ko ina na haraban gidan daya bata mashi jiki a lokacin da kura. Binshi yayi da kallo tare da furta mahaukacin banza kawai da wofi ka dauka zaka zo min da hauka na kyalekane . Ya shiga ciki yana mai jin zafin kalaman dan uwan nasa a kansa inda yake nasa irin matakin da zai dauka kan mustapha din nan gaba da sai ya raina kanshi. Da sauri saurina dawo dakin mu don haka kawai naji jikina ya mutu kwanciya nakeso kawai gomama batayi ba na bi lafiyan gado tare da kashe wayana na kwanta sai barci. Can cikin dare ba mike na tashi ban daki na shiga na fito da alwala nazo duk suna barci basu san ma na falka ba a lokacin. Na dade zaune ina sallah a wurin kamar yadda na saba yi ko a gida tun lokacin dana samu dakin kaina ina yawan yawaita nafila da dare kamar yadda naga umma na yawan yi a baya can da muke kwana daki daya dasu. Har na idar na dan kishingida a wurin ina tunanen mafalkin da nayi har ya falkar dani lokacin ido na mayar na rufe saiga hawaye yana zubo min a hankali. Yauni da bansan Abbana ba a fili nice ke mafalki dashi har na samu albarka daga bakin shi nasan akan dai zancen yadda na dage na bankado asirin yan uwan shi har na ganshi a cikin mafalkin nawa na yau. Har lokacin da zamu tafi sallah yayi alam ya buga hakan yasa na dan dago na bubuga gado su faiza suka tashi mikewa nayi nima na kara yo alwala zuwa lokacin da muka fita gashi washegari zamu bar madina ina jin wani iri a raina wanda bani kadai ke jin wanan din ba lokacin. Munje an taso kamar kullun inda maza sukazo suna fadin mu shirya kayan mu karfetakwas na safe zamu dauki hanyar zuwa makka da faiza da fatima duk a kage suke aje makkan a lokacin. Kowa sai faman har hada kayan shi yakeyi lokacin su sister kamar yadda suke kiranta har manyan su suka shigo dakin namu. Kallon inda nake kwance ta fara yi tana fadin a, a ina dake akace za a fita yanzu kuma na ganki a kwance haka hankalin ki kwance. Tana kallona take wanan maganan idonta a kaina har ta zauna faiza ce take fadin wai dani take magana fa na dan juyo ina dan murmushi nake fadin. No bani ba sai kuma na juya da turanci ina fadin ba inda zan sake fita sau anjima idan mun fita sallah dai na fada ina gyara kwanciya. Kai matar yaya ba dai izza ba da takama kin kumayi dace kinzo inda ya dace zanso ganin ki keda Anty Battula a gidan ku. Waitin she talk na tambayi Faiza ina kallonta kafin takai ga ban amsa aka turo kofan umma ce ta shigo suka gaisa kafin ta juye min harshe da yarbanci tana fadin . Wallahi wanan tsohuwar ne tazo wai zata fita dake yanzu tana son zaki rakata zaban kaya a wani shago ki daure ku tafi kuma banda , , , Haba umma ga yayan ta nan ai babu zaben da bazasu iya ba daba sai naje bani nifa ban son shigewa mutanen nan na fada ina bata raina don Allah ya gani hakan bai mun dadi ba. Ki tashi kuje tunda ta roka dake zata tafi kina son in fada mata bazaki bane ko in mata rashin kunya kikeso nace ban yarda kije ba tunda kina yata. Zan tafi naba umma amsa a takaice tace tagode amma kada ki dade ki fito tunda ta shirya tace ta sake fadin in kula da kaina don Allah. Haka na tashi na shirya raina a bace don dai babbace zan raka din haka kuma umma din da tayi min tsaye sai in tafi yasa na shirya don dole na fita . Har nakai kofa ina jin wanan din dai da suke kira da sister ita matar auren kenan tana fadin Amarya ke nan a dawo lafiya ban kawo komai a raina ba na dauka don katon hijjabin dana saka take min sherin hakan. Dakin su umma na fara zuwa muna cikin magana aka turo kofan wanan budurwan yar wancan tawagance ta shigo tana fadin waini suke jira gasu a waje. Tare muka fita da Rukkaiya din zuwa dakin su sai gasu su fito shine a gaba uwar tana baya tana gyara mayafin jikin ta a cikin hausan da bai zauna mata ba take fadin au ga yar tawa ta fitoma ashe yanzun muke niyar bin bayan ki. Kafin ta rufe baki nakai kasa irun gaisuwan mu na yarbawa na bar girma gaba dayan naje kasa ina gaida ita da sauri ta dagoni tana fadin kai kai haba dai ke yatace fa yanzun mun kara zama daya sosai daku ki daina hakan kinji. Yi nayi kamar ban ganshi a wurin ba muka jera muka fita na dauka da Rukkaiya din zamu fita dukan mu ashe dagani sai sune kawai fitan. Wani motane lafiyayye a waje muka sama ita muka shiga shida driver suna gaba muna baya da tsohuwar sai yaren su sukeyi da banji aikina kawai bin garin da kallo yadda aka tsarashi. Wani katafaren ajen sayar da gwala gwalai mukaje motan ya tsaya muka fifito muna kallo wajen amma shi baiko damu da kallon da mukeyi ba din. Yake fadin bissimillah hjy mu shiga ko zamu shiga din ta juye mai da yare ya dan juyo ya kalleni yana min guntun murmushi. Nan muka shiga wajen har kasa a kwai gina na shagunan gwalagwalan gasunan kowa na kira kazo ka saya sai binshi mukeyi zuwa wani babban waje. Bayan an bamu wajen zamane mun zauna suka shiga kawo irin kayan da suke dashi a wajen muna dubawa da kudin su . Wanine ya dauke min hankali na rike na dan juyashi har bayan shi zubin shi yaimin kyau sosai ga gani da nice zan saya wanan din zan zaba saidai ban san ra,ayin maishi ba. Ban kuma san wace zasu saiwa ba a lokacin muryan shi naji yana tambayana da wanan dai yana da kyau ke nan ko naga kin rikeshi. Kamar ba zan bashi amsa ba sai can nace eh yana da kyau sosai design din yayi min baida girma ko nauyi saidai kudin shi yayi yawa sosai nake gani. Idan yana da kyau kawai a dauka ya fada ba tare da damuwa ba sai kuma yakai hannun shi ga wani shima dai zubin shi gaskiya kamar yafi wanda na zaba din yace wanan fa ? Sai lokacin zaice yaga murmushina kadan har diple dina yana dan lutsawa nace kamar yaso yafi wanan din ma kyau din ban gashi ba sai yanzu duk a harshen turanci dole muke magana. Ai is ok uwar ta fada shida kanshi ya zabo wasu awarwaro ya hada da kayan sai mamaki su nakeyi a raina don nasan uban kudi suka tara a wana wuri lokacin. Bayan yan canza magana kawai naga ya tura masu kudin su a take muka fito zuwa lokacin ashe har yamma yayi ke nan na fada a raina ba zamu samu zuwa sallah ba a haram ke nan. Wanda banso hakan ya kasance dani ba a lokacin muka dauki hanya a zatona masalaci zamu ko gida sai gamu wani wajen kuma nan kan sayayya sukayi sosai ina mamakin tana da wasu yara ne dai haka ashe bayan su sai gab da sallah magariba muka nufi masalaci a can muka hade da yan uwa. Bayan mun dawo ne faiza taso bugun cikina da ina kayan da muka sayo nace suna wajen masushi a can na barsu dashi. Washe gari kan da dawowab mu sallah aka daura tafiya zuwa makka na dauka tafiyan wasa ne ashe tafiyace mai nisa a tsakani dukda motocin lafiyayyune amma sai wani tsawon lokaci muka isa birnin makka din kusan tafiyan yini guda a hanya. Duk na Annabi ya roka Allah ya karawa Annabi daraja dashi da sahabban sa da mu duka musulmi na duniya amin don tafiya mai nisa mu gamu a mota munga nisan tafiyan ballesu da a kafa sukai wanan tafiyan saman dabbobin su. Ranan muka isa masalacin makka mukai dawafi dukko da tarin gajiyan da muka dauko din kamar yadda sunna ta koyar ayi. ZAINAB IDRIS MAKAWA ANA DARA GA , , , , , , , , 9️⃣8️⃣Y, , , , , , , , , , , , ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , , , , , , , , BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AR RA"UF, , , , , , , , , , , ONLINE PAID NOVEL YAR UWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA BA TARE DA HAKKIN KOWA BA DON BIYA KI TURA DARI BIYAR 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK 08036959257 ALLAH SARKI AI RAINA BAYA BACI YANZU DON KIN FITAR DON NASAN AKWAI RANAN HADUWA SEE U👋👋👋👋 Sai asuba muka dawo masaukin mu kowa a cikin gajiya yake lokacin barci mukayi sosai a ranan don haka bamu samu zuwa masalaci ba sai asuba. Karfe ukun dare muna cikin masalci nafila muka fara gabatarwa sai muka dora da dawafi mun gama daidai lokacin da aka fara kiran sallah asuba muka sake dauro alwala don jiran sallah asubahi. Koda muka dawo masaukin mu dake wani hotel a kusa da masalacin ba nisa sosai da wurin wanka mukayi a daidai lokacin da room service ta shigo tana gaidamu wata bakar fatace matar. Bayan mun gaisa take fadin itace mai kula da mu da duk wani bukatanmu har ranan da zamu bar garin muna tare da ita don haka idan wani abu ya shige muna kai mu nemeta zatayi muna bayani komai. Nidai kallon ta kawai nakeyi har ta kare bayaninta tafita bayan t tambayi abinda za a kawo muna muci lokacin suka fada mata. Ba a jima ba sai gata da irin abincin da suka bukata din ta kawo muna suke tambayana ko zanci abincin na dan bata fuska kafin nace da zan samu amala shi kawai nake son ci a lokacin. Ga mamaki sai naji tace baida matsala suna da duk wani abincin da muke dashi a can gida nageria a nan ai in bata yan mintuna zata dawo. Abu kamar wasa sai gata da abincin har miyar danyen ewedo da nama manyan yanka da ake mashi ta kawo min har dakin su umma saida sukaci wanan abincin. Saidana koshi nak kafin na ture abincin a wani masalacin unguwan mukai sallah azahar har da la,asar sai dare zamu koma haram kamar yadda aka tsara muna komai. Illa ranan jumma,a ne zamu jecan mu wuni sai dare zamu dawo namu masaukin mu huta hakan yake a tsare kowan mu ya sani kuma. Yau bayan nayi barci na falka na shiga na dauro alwala nazo na tayar da sallah a dakin da muke din don ban sauka zuwa masalaci ba. Bayan na idar na dauki wayana ina dubawa daga inda nake zaune saman sallaya duban startturs nakeyi indona ya sauka ga abinda ya Abubakar ya rubuta. Masha Allah finaly my sister got marrige in madina Alhamdullilah wish you happy marrige life. Sai Felix daya rubuta Suprase friend dina tayi aure bada saniba ba abin mamaki yana nuna alaman ba ruwan shi. A a mamakine ya kamani a lokacin to kowa sai habaici akan aure akan suwa suke wanan maganan hakane ? Idona ya sauka kan na Muniyat data rubuta komai ke da farko yana da karshe yar uwa muna maki fatan alheri da dacewa a gidan auren ki zamuyi missing dinki . Muniyat kuma again akan zancen aure itama na fada ina dagowa a daidai lokacin da Faiza ta turo kofan ta shigo da kaya niki niki a hannun ta sunje sayayya sun dawo ke nan lokacin. Tsayawa tayi tana kallon yanayina don a rude nake a lokacin na dan fita hayacina sai kuma na juyo na tsaya ina kallon ta kafin nace look Faiza tell me something you know ? Akwai wanda zaiyi aure ne dama a cikin yan uwan ku kamar ya ta tambayeni nace wani abu naga ya Abubakar ya rubuta a wayan shi na bude ina nuna mata. Saida ta dafani tace haba kila watace can yake tayawa murnan hakan kin san maza ai yadda suke. Ban tsaya jiran wani abuba na kara nuna mata na felix din na nuna mata na muniya sai cewa tayi ai yanzu lokacin aure ne dama a Nigeria zai yuyu yazo masu lokaci gudane kuma. Shigowan fatima dakin dauke da kaya itama yasa muka juyo muna kallon ta take fadin wai wai yau naga iyakar yawo ta fada saman gado lokacin faiza ta samu ta sulale ta shige ban daki itama. Na rasa abinda zanyi lokacin sai kuma hankalina ya dauku kan Fatima dake nuna min irin tsaraban data sawowa yan dakin su da daddy sai mommy . Tambayan ta nayi ina nasu anty Nabila da anty hauwa sai na yaran ya Abubakar ta dan dago kai ta kalleni kamar zatayi magana sai kuma tayi shiru. Look kiyi kokari ko yayane ki saya masu dan wani abu na fada na juya zuwa bangaren da nake zama nakai zaune tare da maida bayana a jikin gadon. Ina tunanen rayuwan hausawa wanan halin wai dashi ake haihuwan sune ko dai daga sama suke tashi dashine kusan abinda ya jawowa family din daddy din mu matsala ke nan har yakai ga sunyi kisan shi da hannun su . Anya kuwa zan iya aure a North side na fada irin wanan abubuwan yayi yawa sosai don dai namiji da wuya ya zauna da mata daya irin kudu koda sunyi biyun ba a zama wuri daya nake ganin sunayi don haka ba lalai bane dan uwa yasan halinda dan uwa yake ciki duk da akwai masu karamin karfi dake hadawa wuri daya saidai ban taba zama dasu nasan irin rayuwan da sukeyi ba suma a can. Kofan dakin aka turo sisterce ta shigo dakin da alaman a gajiye take lokacin itama don tare suka fita dasu Faiza din. Nayi matuwa a wancan shagon da muka fito karshe cabdijam Faiza dake yarfe hannun ta ta fada yanzu komawa zakiyi kuma gaskiya kuma ya mukhutar yana tayi muna fada wai mun daukeku munje yawo daku tun safe. Au ashe yana nan ni tun a wurin dawafin farko ban sake ganin shi ba ai faiza ta fada sister din tace ina zai tafi keko ba a kare abinda ya kawomu ba duk da shi ai yaci riban umurah tunda gashi da galleliyar amarya a kusa dashi tana dan kama bakin ta. Ba zata dagoki ba ai wanan Faiza ta fada saina kallota sai kuma sukayi shiru wai meye amfanin a dinga boyewa anty Sahiba wanan zancen tunda an daura aure ni gaskiya fada mata zanyi tunda dole tazo ta sani kuma taga mun munafunceta muma Fatima ta fada. Jin ta ambaci sunana yasa na mayar da hankali a kansu don su a zaton su bana jin hausan da sukeyi sosai lokacin don haka bazan gane ko me suke fadi ba na kuma ji saidai in tsaya in mayar ne ba zan iya ba lokacin. Fatima ki maimaita zancen ki na fada a cikin hausa duk suka kalloni sai takai zaune tana fadin dama dama wai ba wani abu bane fa anty Sahiba dama aure ki aka daura da wanan mutumin tun a madina. Shine wai kada a bari ki sani ni kuma naga idan munyi hakan bamu kyauta maki ba gaskiya gara mu fada maki ki sani cewa su baffah sun daura maki aure zaifi. Tunda aurene ba wani mugun abu ba da za ace kada a fada maki irin kallon da nake jafa mata harda dagowa a yadda nake yasa yarinyar tayi shiru ta kama bakinta lokacin. Na nuna kaina nace ni aure No bakiji dai da kyau ba aure fa na fada ina mikewa tsaye a fusace kamar walkiya nakai kofa na tura dakin su umma. Suna zaune abinci sukeci a lokacin yadda na fado dakin da yanayin sallamana yasa umma din dago kai da sauri ta kalleni . Nima ita na kafe da ido tambaya suke lafiya kuwa ai kamar jira nakeyi nace abinda naji yarancan na fada yanzu gaskiyane ? Ni Sahiba aka daurawa aure da wanda ban sani ba ko me kamar ya baki sanshi ba umma ta fada kafin na aje magana ta tana fadin. Shi mukhatar din ne wanda baki sani ba kome ko kuma zamuyi maki abinda zai cutar dake kike gani haba mairo kada ki mata fada a yanzu haka mama kudidi ta fada tare da fadin ba a bugun mutum kuma a hanasa kuka don kusan da kwanan zancen haka dama gun yarinyar nan. Tunda anyi abin nan ba,a shawarace ta aji ra,ayinta ba aka nuna mata isa da fin karfin iko aka aiwatar da hakan don haka yanzu lalashi ya dace da ita ba daga murya ba. Sai kuma ta kallo ida nake tabar kallon umma din tana fadin zo yata ki zauna in fada maki yadda komai ya zo muna har muka aikata maki hakan bada sanin ki ba. Kallon hannun nata nayi da take miko min kamar mugun abu ta rike kafin na juya da sauri zuwa dakin mu na fada saman gado lokaci guda batare da nasan abin yi ba a lokacin. Don kuka ko wani abu yaki zuwa min a lokacin sai runtse idanuna da nayi kawai ina ganin duhu a zuciyana. Shi mukhatar dinne baki sani ba ko me wanan kalamin na umma ne yake min yawo a kwakwalwana a lokacin . Me haka ke nufi dayi don ban fahinta ba ban kuma yi da wani cewa na tashi aure ko ina neman miji ba balle har suce su zarga min aure bada sani ba . Aure aure fa ina impossible na fada ina mikewa zaune da zuman fita daga dakin mama kudidi da mama Amina suka ahigo dakin namu. Hankalin su a tashe mama Amina kamar yadda su faiza ke kiranta dashi don ni a wajena gwaggonace ita don mahaifinsu daya da mahaifina saidai ita wanda take aure mai karamin karfine shi don haka ba a jinta a cikin yan uwa hakama gwaggo kudidi duk dakin su daya tana auren wani malamin makarantane itama tana kuma koyarwa ita din saidai karfi bai kaiba haka. Sahiba yata ta fada tun daga kofa ki natsu ki kwantar da hankalinki ki ki saurare mu munyi waya da ya Hamza yace yana shigowa yanzu don Allah ki natsu kin ji sahiba ta fada a tausashe. Dan guntun murmushi mai kama da yake na sake a fuskana ina fadin haba mama why da zakuyi min haka why now why please sai lokacin naji hawaye ya zubo min. Dukkan su biyu kasa daurewa sukayi suma hawayen suke sakewa a lokacin don yadda na nuna din ina mamaki ya nuna yanayin don mahaifina baya raye yasa sukai min hakan. Sallaman su baffa hamza tare da umma yasa kowa ya juya garesu suke kallon su suka shigo dakin shima fuskan shi a kaina tun daga kofa ya fara fadin . Haba haba Sahiba why now na dauka mun isa dake kina daukan mu kamar mahaifin ki kin san darajan mu a wuyan ki shiyasa har muka yanke wanan shawaran haka ai. Tunda kin san dai ba zamu taba cutar dake ba kan hakan, yayi mamaki kwarai lokacin dana daga mai hannu a cikin wani irin yanayi ina . Tare da fadin stop that nonsense talk uncle hamza da ace kai ubanane na gaskiya baza ka taba daura min aure da wanda kowa bai sani ba sai cikin dan lokaci. Haka ba zaka taba aurawa diyar cikin kaba aure da bata sani ba yadda kai min din nan a yanzu Sahiba umma ta fada da karfi daga ida take tana matsowa gareni. Ko gezau banyi ba na dago kai na kalli umma din da a yanzu itama komai ina ji zan iyayi kan wanan abinda sukai min din. No kyaleta mairo na fahinci irin zafin da takeji a zuciyar ta a yanzu idan an matsa mata komai zata iyayi baffah Abdullahi ya fada a tausashe daga inda yake tsaye yana kallon abinda ke faruwa. Nima abinda na fahinta ke nan ko kadan banji zafin zancen taba gareni baffah hamza ya fada daga inda yake ya fara takowa zuwa bakin gadon da nake zaune. Ya kai zaune a kusa dani ya dafa kafadana yana fadin yaushe kika taba ganin uba zai iya cutawa yarshi sahiba ? Idan kinyi tunane irin wanan baki kyauta ma son da kaunan da muke maki ba a yanzu mun barku kuda mahaifiyan ku a baya lokacin da bai dace ace mun barku ba. Yanzu kuma kun dawo garemu muna fatan mu baku soyayyan da mahaifi ya dace yabawa yarshi ko irin kauna na uba da yarshi . Da ace mukhatar mutumin banza ne ki sani mune mutane na farko da zamuki yarda dashi koda kuwa kece kika kawo muna shi a matsayin zabinki gareki idan bai muna ba ba zamu taba yarda ki aure shi ba. Saidai ki sani cewa bamu maki wanan zabin a banza ba sahiba munyi hakane don mu nunawa duniya cewa ke din yar albarkace mai bin umurnin iyayye . Duk da wayewan da mutane suke ganin kinyi a yanzu munyine mu nuna masu cewa wayen wanki da rashin tashin ki a cikin da bakiyi ba. Bai hana kiwa na gaban ki biyayya yadda ya dace ba duk ko da irin abinda wasu yan uwan mu suka aikata ga mahaifin ki bai hana kiga girman mu a idon ki. Kwarai kuwa sahiba mutane da yawa suna dauka yanzu baki kallon mu a iyayyen ki sun dauka kin watsar damu kamar yadda muka watsar dake a baya. Saidai har gobe ba duka aka taru aka zama daya ba dole a cikin zuria akwai na gari akwai baragurbin don haka yanzu damu dake zamu taru mu kara dawo martaban gidan mu dana iyayyen mu da wasun mu suka zubar a baya a idon duniya. Shiyasa da tsohuwan nan tazo muna da bukatan son hada iri a tsakanin ku dasu mu kuma mukaji nauyin ta nacewa mu nuna mata bamu yarda da hakan ba tunda duk abinda sukeyi suna yinshine don darajan mahaifin ki a idon su. Sai mukaga idan bamuyi hakan ba wa zamu basu kamar yadda suka bukata tunda shi ammar dana mijine ba zancen aure a gareshi yanzu. Kiyi hakkuri idan muyi maki ba daidai ba sahiba a madadina dana yan uwana harda mahaifiyan ki muna neman gafara akan hakan da mukai maki. Jin maganan shi ta karshe yasa na sake wani irin kuka mai gumji wanda duk ke wurin saida yafitar da hawayen tausayi yadda nake fadin how can stay with this man ? Ba tare da nasan komai daya shafi rayuwan shi ba ba wani nawa wanda yasanshi don ko ya Abubakar ina ganin bai sanshi ba haka kuma sai a yanzune kuka sanshi. Wanan karon baffah Abdullahine yai magana yana fadin indan wanan ne daughter ki kwatar da hankakinki . Bamu daura maki aure da mukhutar ba saida mukai bincike muma mai tsanani a gareshi muka gano shi mutumin arzikine mai mutunci da kima a idon jama, a. Tun bamu san zamu hadu dashi ba ta sanadin ku muka san waye mukhatar a bakin jama, a don haka ba wani abu na muni da aka sanshi dashi gaskiya na zahiri. Ya kare da fadin kodan yadda mahaifiyar shi ta nuna maki kauna da taki mahaifiyar da tayi na,am da wanan hadin kiyi hakkuri ki daure ki zauna dashi. Kodan ki fitar damu kunyan yan uwan mu da suke shirin muna dariya a kanki sahiba ki daure ki zauna da wanan mutumin insha Allahu zakiyi alfahari dake da kowa naki kan wanan auren nan gaba. Umma ta dawo ta saitin kaina tana fadi a cikin yarbacin in rufa mata asiri kada wanan zancen kukan da nakeyi ya fita har zancen ya koma kunnen su taji kunyar hakan tunda yan uwan ubana sunyi bugun gaba dani a yadda al,adansu yake. Kuma basu bayar dani a wurin banza ba insha Allahu zanyi alfahari da wanan auren don Allah kada in yarda in nuna masu ban yarda da irin tsarinsu ba na fulani. Haka dai tayi ta maganganu a cikin harshen yarbanci da baji sukeyi ba har dai na dan rage sautin kukan da nakeyi a lokacin . Dukkan su sunyi shiru a lokacin da alaman rayukan su baida dadi kamar yadda nawa yake a ciki faiza da fatima kuma sun rakube a gefe daya a cikin damu suna kallon abindake wakana a wurin har kowa ya manta da suna wajen ma lokacin. Maganganun su mama kudidi yasa jin zuciyana ya dan sassauta min a lokacin har na dago ina kokatin sauka daga gadon inda nake kwance. Kowa ya bini da ido ana kallon kome zanyi a lokacin gyalena dake saman gado na dauka na yafa kafin na taka zuwa inda kafan baffah hamza yake na tsunguna tare da fadin uncle ka yafe min insha Allahu zan yi maku biyayya kamar yadda al,adan ku yake na gida. ZAINAB IDRIS MAKAWA ANA DARA GA , , , , , , , , 9️⃣9️⃣BY, , , , , , , , , , , , ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , , , , , , , , BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM MALIK AL MULK , , , , , , , , , , , ONLINE PAID NOVEL YAR UWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA BA TARE DA HAKKIN KOWA BA DON BIYA KI TURA DARI BIYAR 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK 08036959257 ALLAH SARKI AI RAINA BAYA BACI YANZU DON KIN FITAR DON NASAN AKWAI RANAN HADUWA SEE U U👋👋 Ba yadda na iya don abu biyu zuwa uku na farko yin biyayya gun uwata sai nabiyu zanyi biyayya gun magabatana kamar yadda umma tace dani haka al,adasu yake gada na yarda na karya ga hakan sai kuma don ita mahaifiyar shi mukhatar din da sukace ta roki hakan kada in nuna bata isa ba a gareni. Gashi abu kadan zakaji tana faman yabon mahaifin mu ta mashi adduan samun rahama a wurin ubangiji duk muka hadu da fatan muyi koyi da irin halin mahaifin namu. Nima zan nuna mata yace kamar kowa zan nuna masu na gado mahaifin namu a wani fanni na rayuwa saidai kwakwalata da zuciyana ta kasa daina shi mukhatar din a wurin yaya nake ke nan ? Na gyara kwanciya badon naji dadin shi ba lokacin ina tuna irin alkawarin dana gama daukarwa iyayyena a yanzu suna saka min albarka. Akan wanan auren shina tuna na lumshe idona cikin takaici da kunan zuci ban taba kawowa kaina wani laluran aure ba a yanzu kusa. Asalima ban taba kallon wani da namiji naji ina son shi ba da sunan aure amma sai gashi kaddara ta a yanzu tazo min da abinda ban shirya mashi ba a lokacin. Hawayene masu zafi n aji suna bin fuskana a lokaci guda daidai lokacin da wayana sako ya shigo min ke nan ban yi yunkurin dubawa don yanayina daba dadi a lokacin. Jin sako na biyu ya kara shigowa lokaci guda yasa na dan juya ina kallon wayan nawa sunan ya Abubakar nagani rubuce ya turo min sakon. Nakai hannu na dauki wayan na bude gaisuwane tare ban hakkuri yana tausan zuciya na yarda da kaddara duk yadda yazo mi n shine cikan musulmi mutum na gari a wurin ubangiji yana da tabbacin mukhatar zai rikeni amana da mutunci kuma kada in yarda a samu matsala a bangarene har ya daukeni mara tarbiya. Baki na dan mere don jin kalamin shi na karshe don kaman yasan na shirya yiwa wanan mutumin daya biyo ta baya don kawai ya hadani fada da iyayyena a yanzu. Don haka na shirya rashin zaman lafiya ko kwanciyan hankali a bangarene da wanan mutumin da ya wuce sa,an aurena a yadda na dauka. Idan ma aurene sir Sha,aban nake iya aure a yanzu koda yin hakan ya taso min a yanzu idan banda zancen Alaja da ya bata min rai da dukkan su a yanzu. A rayuwa naki jinin kai min gori kan abin hannun ka ko wani abu daya shafi dai ka nuna abinka yasa nake tare dakai shiyasa ban shiga mutane don nasan mu ba masu shi bane sosai don haka daga aiki sai gida saiko wani wuri na musanman. Idan nace nayi barci a ranan karyane don haka ko da asuba da zasu tafi sallah ban bisu ba ganin haka itama fatima tace su tafi kawai ba zata tafi ba. Faiza da tafito ban daki ta samu fatima kwance take tambaya sai cewa tayi bazanje nabar anty sahiba a cikin wanan halin ba haka ku tafi kawai. Ita kuma sai tace a,a ku dai tafi nina zauna da ita zaifi zaman kike tace ba zan iya wuce na barku ba gaskiya gara dai mu zauba din dukkan mu a nan hankalina zaifi kwanciya. Duk sai sukaki fita karshe sai mama kudidine ta shigo tana fadin mufa ake jira a waje sukace su tafi kawai yau ba zamu tafi ba. Duk abinda sukeyi ina jin su amma ko motsawa alaman najisu banyi ba har mama ta fita daga dakin suma suka koma suka kwanta suna jiran lokacin sallah suyi a daki. Felix ne ya kira Sir Shaaban yana fada mashi abinda dake faruwa zaune yake tare da mahaifiyar shi da duk kwanakin suna dan sama sama da junan sune da shi da ita. Nan ya fara maimaita Sahiba fa kace tayi aure a madina yace kwarai Abdulne yake fadawa oga jimoh jiya da dare. Kuma ya turo mai photunan daurin auren a yau ya gani shike nan yanzu shike nan abinda ya fara fada lokaci guda. Wanda ba wani abu bane illa dabian su na yarbawa daya tsaya mashi a rai kuma ya rikeshi a gaskiya. Cewan da malamin shi yayi mai arzikin mu yana hade dashi idan muna tare zaiga arzikin shi yana bunkasa zaiga komai yasa a gaba zai sameshi a saukake zai zama mai albarka. Da farko bai dauki hakan gaskiya ba sai zuwan mu kaduna yin wanan aikin da kuma irin cigaban da yaga yana samu a yan shekarun nan . Sai ya dauki wanan zancen da gaskiya ya rikeshi a rai saidai bai taba fadawa kowa wanan zancen ba har ranan da ya samu labarin barina aiki dasu a lokacin hankalinshi ya fara tashi yazo kuma ya samu wai bana kasan tun lokacin hankalin shi ya fara tashi. Yanzu kuma ga felix yazo mai da wanan zancen yasan na salwanta daga gareshi ke nan na fita hannun shi haka yasa yana kashe wayan ya mike ya bar abincin dake gaban shi. Alaja da tadan fara saukowa ta bishi da kallo don ganin yadda lokaci daya ya shiga cikin rudani kuma gashi ya ambaci sunana a wayan. A lokacin ta dan mere bakin ta tana gyara zama sai kuma taga ya mike rai bace yabar falon Aisha ce tace dashi a, a brother why are you living now ? Tana fadi tana kallon abincin daya tashi ya bari a wurin ga mamakinta ko juyowa baiyi ba a lokacin balle tasa ran samun amsa a wurin shi dukko da hakan ba halin shi bane. Sai hakan bai kwanta mata a raiba mikewa tayi tabi bayan shi har dakin kwanan shi zaune ta hangoshi a bakin gado ya dukar da kai kasa kamar yana tunane mai zurfi hankalishi a tashe. Takowa tayi har zuwa bakin gadon ta samu wuri ta zauna a kusa dashi na tsawon dan lokaci kafin ta dauki hannunta ta dora a nasa tana fadin . Meke faruwane dakaine haka brother ta tambaya tana kallon fuskan shi hannun nata ya dan rike da karfi kafin ya dago kai yana kallonta da idanuwan shi da suka rine sukai ja don tashin hankali. Da sauri tace subbanallahi brother tell me please what is going on ko sahiba din ce ta kara jefa mai tambaya cikin tambaya. Murmushin dole ya dan kakaro a fuskanshi kafin yace sahiba ta tafi ta tafi daga gareni yanzu har abada Alaja taji dadi yanzu shike nan Aisha . Nasan daba don wanan matsalan nata da Alaja ba ba abinda zaisa sahiba aure a yanzu at dis time tayi surprise din mutane haka lokaci guda. Wai da gaske kakeyi miss Sahiba tayi aure at dis time da kafi kowa bukatan ta tare dakai kuma tayi ma hakan lokaci guda ? Idanuwan shi ya runtse yana fadin you can live now bana bukatan dogon magana a yanzu zata kara magana yace please Aisha live me alone. Jin hakan yasa ta mike tsam ta bar mashi dakin ko kallon Alaja dake zaune saman kujera mai zaman mutum ukku ta mimike tana waya tazo ta wuce ta. A zuwa lokacin yar nata laifin ta tagani don gani take itace taja komai a lokacin har hakan ya faru da dan uwanta ya rasani. Bin bayan yar tayi don tasan hakan sukan hade mata kai idan ta taba mutum dayan su sai dayan shima ya nuna bacin ranshi ga hakan shiyasa bata son wani matsala irin haka a tsakanin su. Bata san meyasa ba Sun kasa fahintar gata take son masu ko yaushe akan me zata yarda ya auro mata yar tallakawa a zuri,an ta. Sam bata yarda da hankalinta ta rabi talauci talakka banda wahala meke cikin hada halaka dashi banda tsiya don ko yayane dole dashi zasuti amfani su tofo suma. Da ace yarinyar dan wani hamshakine ko mahaifinta baida mukami zata iya yarda danta ya auri yarinyar don sahiba ba inda take da matsala banda na rashin background. Gwaggo harice zaune gefen daddy ranta a bace daddy din yai shiru yana kallon ta kafin ya furta kai yaran nan sun girma amma basu san sun girma ba su. Yanzu kema din ga irin abinda suka aikatawa jinan su na bace bace kina son ki aikata hakan a gabana da alama goyon bayan danki kike son nuna min don dole akwai abinda yasa modibbo ya fada mai hakan shima. Dama nasan haka zaka fada a karshe ba zaka dauki maganan da muhinmanci ba ai amma dama ai sai kuma tayi shiru. Kallonta yadan yi kafin ya mayar da jikinshi saman kujera ya dan shafo goshin shi yana murzawa kafin ya mika hannu ya dauki waya. Danshi ya kira yace a takaice kazo yanzu kome kakeyi ka barshi kazo yanzun nan daga bangaren modibbo din yake tambaya lafiya dai daddy ? Lafiya ke nan kazo yanzun nan da sauri ya mike don cika umurnin mahaifin nasa cikin yan mintuna ya isa gidan saidai tun daga nisa ya hango motan gwaggo hari a waje alaman tana gidan itama a lokacin. Tambayan kanshi yayi meke faruwa hakane wai ko a kan zancen auren sahiba din ne sukaji hankalinsu suma ya tashi da hakan. Da sallama ya turo kofan falon ya kai kallon shi ga iyayyen nasa biyu dake zaune a lokacin yanayin su ya kalla ya gano ba lafiya a wani bangare. Daddy lafiya ya fada tunkan ya zauna samu wuri ka zauna ya fada yana nuna mashi da hannun shi ya kalli wurin yakai zaune a hankali ya kara maimaita tambayan shi wanan karon gun gwaggon nasa. Dake zaune tana cika tana batsewa don yadda take jin kanta lokacin jin tambayan daya jefo mata yasa ta dan harareshi tana fadin. Kaji mun mara kunya sakon daka bayar ne ya sameni yasa nazo gun mahaufin ka tunda nika rainani a yanzu har zaka iya fadawa boy wanan maganan ido da ido. A, a gwaggo Allah ya baki hakkuri amma shi mustapha din ai ya fada maki dalilin fadin hakan danayi ko ? Me zai fada min bayan wanda kake ganin yanzun wuyan ka yayi kauri kai ka isa zagin mu a yanzu akan Sahiban banza wace , , , , A, a hari me kuma ya kawo zacen sahiba a yanzu nan don Allah ku bar yarinyar nan da abinda ya isheta daddy ya fada rai bace. Kafin ya juya wurin dan nasa yana fadin kai meya hadaka da dan uwanka har yakai ga batanci ga iyayyen ku ? Shiru modibbo din ya danyi kafin yace wai fa daddy samuna yayi har gidana dacin mutunci aai akan zancen aure sahiba nine duk na kullashi. Nan dai ya kwashe yadda sukayi tiryan tiryan ya labarta masu saiga gwaggo hari tayi shiru kafin tace shi boy din ya fada ma hakan ? Gqaggo zan maku karyane naci riban me a hakan idan na fadi ba daidai ba daddy ya kalleta yace kinji ke ku dinga bincike kafin ku auwatar da abu don Allah. Yanzu waya fara zagi a nan daga zancen baki kawai kuma ya koma ya fada maki kekin hau haka ni ai na dauka duk daya suke a wajen ki ashe ba haka zancen yake ba. Wallahi yaya rainane ya baci idona ya rufe wai ace modibbone ya fadi hakan garemu ashe shidin mara kunya ya fara fada bai nuna ba. Ba zai nuna ba yanzu dai kun girma kusan ya kamata ku kun fadi hakan kamar yara me wasu zasu fada kuji zafin sa ? Kai daya fadama meyasa ka biye masa kuka kai ga hakan wanan ai fada mata ko yarane su aka sansu dashi haka baku maza haka magidanta ba. Ayi hakkuri munyi kuskure gwaggo kuyi hakkuri don Allah ranmune ya baci har muka kai ga hakan ya fada yana dukar da kanshi kasa cikin ladabi. Toh yanzu dai in zaku daina ku daina don mu ba tabbata zamuyi tare daku ba a nan in kun rike zumuncin kun kyautawa diyan ku nan gaba idan kuma kunci gaba da hakan kundaiga yadda abubuwa suke a yanzu. Bayan fitan shi gwaggo hari ta shiga wurin mommy sun dan jima a tare suna tatauna wanan matsalan na diyan su kafin danta ya isheta da kira ta bar gidan. Kwana biyu cur bamu fita dan gara su sun dan fita zuwa wurin sayayya ni dai kan ko kofa ban leka ba ina dakin kwance sai faman tunane dake cin zuciyana. Ba komai bane ya tsaya min a raina lokacin sai yadda rayuwana a yanzu zai kasance min da kuma yadda zan barsu umma na tafi wani uwar duniya da sunan aure kai ina nace a raina. A daidai lokacin da akai nockig din kofan tare da turo kofan lokaci guda jin hakan baisa na dago don ganin mai nocking din kofan da zai shigo ba. Wani kamshin ne ya daki hancina lokaci guda wanda yasani dago kai ina kallon kofan shine a tsaye kaina ya zuba min idanu kamar ranan ya fara ganina na farko. Da sauri na lalubi hijabin da nayi sallah dake gefena na rufa a saman dan rigan dake jikina dogo ya matse min jiki har zaka iya ganin suran jikina a fili. Wani dan guntun murmushi ya sake wanda har ina iya jiyoshi a lokacin Sahiba meke damun ki haka kinbi kin sukurkuce kamar ba Sahiban mommy ba dana sani mai kwazo. Ko duk a kan cikan alkawarin ubangiji akan mu yasa kike kokarin nuna butunlcewan ki a hakan ? Wani kallo na jefamai mekama da tsana do your wish kayi amfani da daman da kake zaton kana dashi a yanzu a kaina. Kada kayi tsamanin a yanzu kayi nasara ke nan ko ka dauka wanan damane da zakayi amfani dashi a kan mu kan wani manufa naka don ka cin ma nasaran abinda kake nufi. Hannaye ya ware kafin yace Allah ne kadai shedana banda wani manufa ko daya akan family din mutumin da yayi silan zamana wani abu rayuwa na. Bani da komai a kanku sai alheri fatana mu rayuwa tare mu kara kafa kan mu a karkashin innuwa daya daku haka kawai zan maku nasan na taimakawa kaina daku farin ciki yakai ga mahaifin ku. Stop dat jork kana tsamanin ban san abinda kake kokarin yi bane a kan mu din sai yayi murmushi yana gyara tsayin shi yace idan ma har kin yaudari kanki a hankan zato zunubine . Allah yaga manufata a kan ku yanzu kuma kada zuciyarki ya yaudari wani ko zato akan shi Allah ya gani ban nuna kudi ko karfin iko akan kowa ba naki illa zallah gaskiya danazo masu dashi kuma suka gamsu da hakan gareni. Don haka ina rokon ki da ki cire komai a zuciyar ki yanzu ki natsu ki fahinci waye mukhatar a wajen ki da mahaifin ki . Ranan da naga natsuwa zan sanar dake koni waye nan gaba na barki lafiya dama nazo naga fuskan kyakkyawan amaryatane nakuma yi maki sannu da jiki duk da nasan ba abinda ke damun ki sai fargaban gamayya dani a yanzu. Karkiji komai ni nidin mutum ne mai saukin kai da sanin ya kamata ga duk wanda ke karkashin innuwa na a zaune har sai idan maishi ya fito da nasa manufan a kaina muke raba hanya dashi . Saidai ki sani ni da sahiba auren mu na mutu ka rabane insha Allahu da sannu zaki fahinci koni waye nan gaba. Ki kula da kanki don Allah kada wani abu yazo nan gaba yafaru dake please take care yaran ki sunce a gaida ke idan na ganki. Yara na dago kai ina sake kallon shi da mamaki yaranshi fa ke nan yana da mata kila ma mata don hausawa irin wanan a yanzu ba zancen mata guda a gareshi sai mata dai da yara kan. Ohni sahiba naga ta kaina a duniyan nan ni yaya zanyi da rayuwana ke nan da wanan kaddaran dayazo min a hakan ? ZAINAB IDRIS MAKAWA ANA DARA GA , , , , , , , , 1️⃣0️⃣0️⃣BY, , , , , , , , , , , , ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , , , , , , , , BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM DHU_AL_ JALALI WA_AL_IKRAM , , , , , , , , , , , ONLINE PAID NOVEL YAR UWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA BA TARE DA HAKKIN KOWA BA DON BIYA KI TURA DARI BIYAR 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK 08036959257 ALLAH SARKI AI RAINA BAYA BACI YANZU DON KIN FITAR DON NASAN AKWAI RANAN HADUWA SEE U👋 Kofan na tsurawa ido nabi shi da kallo har ya bace mun da gani kafin na sauke ajiyan zuciyan daya fito fili lokaci guda ina kawar da idanuwa ga kofan . Aka sake turo kofan kusan lokaci guda azatona shine dai ya dawo kuma wanan lokacin sai muryan Fatima naji tana sallama da alaman kamar a dan firgice lokacin. Yasa na juyo ina kallon su tare da fadin har kun dawo ke nan tace tun dazun muna waje an tare mu wai oga na ciki tare dake . Juyowa nayi na dan kalleta take fadin wallahi anty Sahiba baki gansu bane fa a waje wasu irin murda murdan kataine dasu zabban tsoro na zatama wani abin mukayi lokacin da muka shigo na gamsu tsaye a kofan. Banji tsoron komai ba tunda suka dakatar damu suna fadin wai oga yana tare da madam a ciki nasan shi suke nufi Faiza ta fada tana zama. And so what da zasu tare ku a waje kamar wasu masu laifi shi baisan kuna dakin bane ya shigo muna dakin mu ? Ai gara dai da suka tare mu ina zamu shigo ango da amarya suna ciki muzo muyi mugun gani a idon mu faiza ta fada tana kallo na tana dan dariyan shakiyanci. Take na daure fuskana na hayayyako mata ina fadin Faiza ki dubeni da kyau nayi maki kama da wace zata wani shiririta da namiji can ? Shi wanan din ai yanzu na daban ne ba dan i love you bane mijin kina don haka yana da right din da zai kebe da matar shi ai. You are crazy faiza koda kuwa sonshi nake har cikin raina ba wanan daman a gareshi da zaizo min da irin wanan zancen a yanzu. Ke kuwa kin san me aure yake nufi Sahiba mijin kine fa na sunna kike fadin haka aida zaran an daura aure a tsakanin ku shike nan komai ya wajjabata a tsakanin ku kuma. You de craze har yaushe kika san irin wanan abubuwan da sai manya ya kamata su sani har kike wani kashe ido haka ? Kinsan how old nake kuwa yanzu da ace nice na samu wanan babban daman da kika samu a yanzu kada kiyi mamakin ki nemeni baki ganni ba wallahi. Wani kallon mamaki nabita dashi ina kallon ta tace kwarai kuwa sahiba dama da sa,a babba kika samu a rayuwan ki kuma naga kina son wasa dashi ke kamar baki san kin taki sa,a haka a rayuwan ki ba kekan ? Ido na kurawa Faiza din tace Allah da gaske nakeyi sahiba gani nake sam abin kamar baki daukeshi da wani ma,ana ba a zuciyar ki. Ban kara sanin ko waye mijinki ba sai jiya da sister ke kara bamu labarin shi matar shi daya da yaran su biyu yan mata tace bata son haihuwa da yawa tana planning. A cewar ta matarshi ta girme maki nisa ba kusa ba da tare zasuzo nan sai tace bata shirya ba da tafiyan ya tashi don zata kai yaranta hutu Australia. Ita din shi wai aurene na hadin iyayyensu mata da wani iri na kallo ta tace koya girmeta da kadan zai girme mata a shekaru don haka kinga ke nan dai ba yarinya bace dai ita din. Saidai kinyi sa,a amma har idan kin daina wanan tsiwan naki na tsiyan na rashin nuna kulawa ga mutane don ita din ance. Sam bata son yan uwan mijinta ko kadan don hakane ma yan uwa ke gudun su rabeshi a yanzu sabanin shi da yakeda son yan uwa birni da kauye nasa. Yanada taimako tallaka sosai akace ga kula da iyali da duk wani wanda yake karkashin shi zaune yana jin dadin shi saidai idan har matan ta gane haka ba a daukan lokaci dole ka rabu dashi. Matar shi shu,umace ta karshe yadda suke fadi din dukiyan shi da komai har ana zargin cewa suna hannun wanan matar don yadda take facaka da arziki ita kanta. Auren shi dake sunce za a kirashi da mukkadarine don ba wanda ya taba kawo aure gareshi a rayuwan shi don yan mata da yawa suna son shi saidai babu dama garesu. Akwai watama a cikin yan uwan su da kamar za, ayi aure tsakanin su ana sati daurin aure ayi komai yace ya fasa haka kawai har yau ance tana nan batayi aure ba tana jiran shi. Yaran shi ko bai hadasu da komai ba a duniyan nan don yana ji dasu sosai akace duk abinda sukeso shi yake masu. Kinga kota yaran kika nuna masu kauna nasan zaki kwasoshi a tafi yadda ake so keda shi don wanan mace dole sai an hada da siyasa lamarin ta. Faiza do you know what you're saying me sahiba inbi ta yaran shi ko matarshi in sosu don kawai ya soni nerve ba Sahiban ummana nake ba ke nan ko kin manta da nice na girgiza kai tare da dan sauti da bakina ina fadin nerve. Ki daibi sannu don irin wa yan nan matan dake kakace gida da wuya ake iya inmasu har kaima na baya ka samu ka kafa naka gwaunatin a zuciyan miji. Who want the gorvenment ? i beg may you no west my time jooo all dis na rubish you de talk. Sahiba wallahi kinsan fa yar maidugurice ita ni tsoron da nake ji ke nan wallahi koda yake kema din dai idon ki a bude yake amma duk da hakan dai ki kara natsuwa don Allah. Juyawa nayi da niyar kyale zancen nata lokacin naji fatima na fadin ai ance wai tana da wasu hasabiban kannenta da take zaune tare dasu. Wai yan iskane har shi basu raga masa itama din kamar dai tana tsorin sunema suke aiwatar da komai a gidan. Yanzu ma haka tana can tana fitina dashi duk da yake yana nan don an samu wanda ya tsegunta mata zancen auren ki dashi. Har hjy mahaifiyarshi takira ta zaga duk da itace mussababin hadin auren shi da ita amma ance yanzu duk ta manta da wanan ita kanta da yan uwanta kawai ta sani. Yauwa kinga na mata faizan ta fada ko a nan saikiyi kokarin kafa gwaunatin kin tun yanzu a wurin hjyn tasa tunda muna tare a nan da ita yanzu. Haka kawai fadin hakan da fatiman tayi sai naji ina son irin wanan drama din dasu haka yasa na juyo da kyau ina sauraren ta. Har suka kare zancen su banjin zan dauki ko daya daga ciki don mutumin da yai min dole a kainshi ya bata min duk wani tsari da shirina a yanzu akan rayuwata. Karfe uku kamar yadda muka saba fita nice na tayar dasu ranan da barci don ba abinda yafi min yanzu banda nakai kukana kan wanan sabon rayuwan da zan tsunci kaina a cikin sa daga sama a daidai lokacin da ban shirya hakan ba. Farkon abinda ya dace dani ke nan a rayuwana na mika kukana a wurin ubangijina kan wanan matsalan a yanzu gani gaban maganin komai inji mafada. Suna da gajiya a jikin su amma haka na matsa masu saida suka tashi muka tafi tare dasu ranan kan na mika kukana sosai a wurin Allah don babu kamar ubangijin mu gare mu. Karfe goma muna masaukin mu na debo gajiya sosai a lokacin sai wurin kwanciya nake nema in kwanta har na kwanta din barci ya soma fisgana sako ya shigo min a wayata hakan yasa na bude idona. Shine ya turo min sakon da Amaryata hope kin tashi lafiya ya karfin jikin naki ? Naso sai na koma naje turai na kwaso maki kayan lefen ki don naga irin suturan su kike sakawa amma hjy ta damu da na fara saya maki tun a nan . Don haka ki bani time da zamu zagaya zuwa cikin gari ki duba shine sakon daya turo min kawai naja guntun tsuki tare da wurga wayan bayana na kwanta sai barci. Ban falkaba sai azahar na tashi ban kuma tsaya bin ta kan wayata ba wanka nayi tare da sallah kafin na hau abincin dana sama daci don yunwa nakeji sosai kwana biyun nan duk ban tsayawa naci abincin kirki saboda tunane. Amma a yau kan jin kaina nake sakayau dani kamar an gafarta min dukkan zunubaina a ranan. Bayan mun gamane kuma sai fira har muka gama mukai sallah la,asar na kara komawa gado na kwanta tare da jawo wayata. Wani sakon shi na sama na bude tuni yake min kan sakon farko ga abinda na rubuta masa nima a lokacin. Ayyah hjy nagode da kulawanta ga yar amananta saidai ka bata hakkuri ni din ba ma,abociyat tara sutura bace wanda ke gareni sun isheni rayuwa. Bayan ya karanta murmushi ya sake bai kara min wanan maganan ba har sai ranan da muka hade dasu a wurin dawafin bankwana a nan ne muka hadu har da mahaifiyar shi. Ba yadda na iya dole naje muka gaisa dasu din tana ganina ta fadada fara,anta tana miko hannu tare da fadin diyata na dauka har mu tafi ba zanganki ba ai zo nan ki zauna tana nuna min wuri a kusa da inda take zaune din. Bayan na zauna taci gaba da fadin naso ace sun banike daga nan mu wuce can maiduguri dake yan uwa su ganki. Amma iyayyen ki sun roka cewa muyi hakkuri har ku koma sati biyu da komawa su gama fadawa yan uwa sai ki tare ga baki daya. Gabanane yayi wani mugun faduwa lokaci guda don jin abinda ta fada din lokacin da badon kaina a duke yake ba da zata iya hango irin razanan danayi a lokacin. Sai magana takeyi bata kula da hakan ba taci gaba da fadin saidai yana da wuya ya barki ki dan zauna damu a maidugurin . Don yace yanaga da wuya ki tsaya a nan don zaku wuce ga baki daya a can inda zaki zauna saboda wai ba a kasa daya zaku zauna da ita uwargidan naki ba yace. Saboda yanzu harkokin shi ya koma singerpor ga baki daya da Dubai yace a cikin daya yake son ajeki a can . Ba matsala duk inda kuke insha Allahu zan sameku a can din saidai ki riki wanan ibadan naki saosai diyata addua shine takobin mumuni Allah yasa albarka a cikin rayuwan ku ga baki daya. A hankali na samu kaina da amsa mata da amin mama nagode ta kara da Allah yai maki albarka na amsa da amin again. Komai yai farko yana da karshe akace yau gashi mun kare lafiya zamu tafi washegari kowa zuciyar shi cike da zumudin hakan. Don tafiyan namu an kara kwanaki saboda yan kwanakin da yayi bai iso ba haka yai cuku cuku aka karawa tawagan nageria din kwanaki yakuma bi kowa da alheri mai tsoka a wurin. Ban so sake haduwa dashi ba har mu bar kasan amma da gajiyan nan muna dawowa masauki sai ga uncle hamza ya kirani . Wai mijinane yake son magana dani lokacin nayi mamakin jin hakan a bakin baffah din shi ba zai iya min magana ba ke nan komai da zai hadani da baffah a lokacin. Wani wawan tsuki naja bayan mun gama wayan dashi lokacin na wurgar a gefena suka kalloni dafa inda suke zaune don wayan har yacin ma faiza lokacin. Lafiya ta tambaya tana kallona idona daya cika da kwalla na sauke a kanta cikin takaici ina fadin jimun wanan mutumin fa wai uncle ya fadawa yana son ganina a yanzu zamuyi ban kwana dashi zai aiko a tafi dani masaukin shi. Masauki ta fada tana kwalalo ido waje nace rainin hankaline nafishi iyawa yanzun nan zan gwada masa kuwa. Da sauri na mike kanar ina shiryawa saida nagama tsab ne har faiza tana tayani tana fesa min turare . Sai suuu na koma na kwanta saman gadon tare da dafe kaina ina fadin washh ina fadawa na fasa kara mai firgitarwa duk suka rude lokaci guda . Yaren yarbanci na fara yi da sauri fatima ta nufi kofa sai dakin su umma take fada masu abinda ke faruwa. Ai sai gasu tare hankali tashe sun shigo dakin namu tundaga kofa umma ta fara jin abinda nake fada tace dasu. Ai mutanen kantane suka taka mata ashe har a kasa mai tsarki suna hawa kan mutum haka nan ta shiga shafana sai wani sauti nake sakewa kas kasa gaba daya duk wanda ke dakin zai iya jin hakan . Hankali tashe mama ta kira su baffah tana fada masu yace yanzu fa muka gama waya da ita saidai dama naji muryanta ai wani iri can. Sai gasu dakin suma a cikin tashin hankali sun shigo don baffah yazo da niyar ya fatatake ni ne sai ya samu abinda yafi karfin shi a dakin. Sai gasu sun koma ban hakkuri jin har abinda bai taba fadawa wani yana da niyar yiba ana zakalo mashi da kaf labarin wurin aikin shi . Da sauri ya shiga bada hakkuri yana fadin ba karya mun yarda daku mmdon munsan a kwaiku kamar yadda akai dan adam shima. Nan ake fada mai ai yarsa na can kwance don shi ya tabo su ya batawa godiya rai ummace ke fassara masu duk abinda na fada a cikin harshen yarbancin wani kuma in yazo da turane suna jin abinda suke fada. Text ya turawa mukhatar din yana fada mai abinda ke faruwa shima yaso daga hankalinshi amma baffah din ya kwantar mai da hankali. Abinda basu sani ba shine turarena na shaka suka taso min don gaskiya na dade wanan matsalan bai taso min ba haka don gaba dayan su dakin ranan sun gaskanta hakan. Sai dare sosai suka samu ya lafa min amma gaskiya koni nayi dana sanin yin hakan aiko da sassafe sai gasu har hjy tashi sun shigo gaidani ina kwance sharkaf dini don jikin da naji din. Hajiyan tasu ke fadin kai tana da wanan matsalan ne haka dama umma tace ai yanzu ma yai mata sauki ke nan sosai sama ga da can baya. Don tana kai sati daya tana fama da wanan laluran idan ya taso mata daga gefe baffah ke fadin ni ai na sheda yanzu. No Wonder yarinyar nan take tsatsaye haka ashe manyan abubuwane haka saman kanta zancen yata data fada wallahi na kira suke fada min sati ke nan suna fama da ita sai jiyan nan suka baro asibiti. Haka dai kowa ke fadan albarkacin bakin shi a wurin suna tsaye sun kura min ido kowa da abinda yake sakawa a cikin su. Murya a sanyayye yake fadin uncle ko zamu daga tafiyan nan ne har taji sauki da sauri umma ke fadin yanzu data falka insha Allahu zata ji dama. Zuwan daine na yanzu suka zo mata da karfi sai hjy nasu tace ai da kawai a dage idan sauran zasu tafi tunda sun shirya sai su tafi su. Nagodewa umma data kafe da ai kawai a bari mu tafi zaifi koda an tsaya din ma duk abin dayane a can kuma za a samu a karbo min magani inda ake karba ai. Da haka suka yarda da zancen umma har muka samu a ranan muka baro kasa mai tsarki zuwa gida nigeria. ZAINAB IDRIS MAKAWA ANA DARA GA , , , , , , , , 1️⃣0️⃣1️⃣BY, , , , , , , , , , , , ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , , , , , , , , BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AL, MUQSIT , , , , , , , , , , , ONLINE PAID NOVEL YAR UWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA BA TARE DA HAKKIN KOWA BA DON BIYA KI TURA DARI BIYAR 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK 08036959257 ALLAH SARKI AI RAINA BAYA BACI YANZU DON KIN FITAR DON NASAN AKWAI RANAN HADUWA SEE U 👋 Kwance nake tun dawowan mu bawani karfi a jikina abubuwa da dama suka hadu suka sauke min rashin kuzari lokaci guda haka. Saukin abin dai shine saukan dare mukayi washegari kuma da safe su baffah suka dauki hanyar kaduna basu kwana ba sai muka koma mu kadai a gidan kuma. Idan badon tafiyan mu da Abdul bane ba wanda zaisan mun je har kuma mun dawo din yanzu saidai ganin shi da mutane sukayi yasa yan wa yanda muke hurda dasu suka san da zancen dawowan mu kasan. Daga ciki ko har da abokan aikin mu na ma,aikatan mu dama wasu makwabtan gidan mu har suke muna sanu dazuwa a lokaci. Tun bayan dawowan mu kasan wayana yana kashe ban kunna ba son banda aiki sai faman barcin gajiya da nakeyi lokacin. Da farko na dauka ai wanan matsalan nawane dana dade banyi ba saida wata makwaciyar mu ta shigone take fadin ai haka akeyi don sai lokacim da mutum ya dawo gidane yake sauke gajiyan daya kwaso a can dama. Ta wagan ma,aikatan mune sukazo don gaida mu da zuwa wanda a gaskiya badon ni suka zo ba sai don Abdul da yake ma,aikacin su a yanzu shi. Amma saboda mutunci sai wasu suka zamo suka shigo namu part din daga ciki kuwa harda Adanan da Felix sune suka shigo part din mu don mu gaisa. Umma ta shiga ta tayar dani jin sune yasa na fito daga dakin saye da wani fashion hijab dashi da babu dayane don kamar riga yake ya matseni ko ina amma a hakan wai mace ta rufe jikinta ke nan dashi a yadda sukayishi. Tunda na fito Felix ya fara min ba,a da Amarya so na your eyes be dis ? See how you look fresh you, na de enjoy wooo ? Daidai ina zama nake fadin who be amarya ? i beg de go joo, carry dis your amebo talk and go. Gaskiya kin kara wani fresh dake fa wai da gaskiyane zancen auren ki gashi kin jefa min ogana cikin tashin hankalin tun da yaji cewa wai kinyi aure bai kara daga wayan kowan mu ba kuma a nan. Na, so you hausa people de do your marrige no any cerlarbration or gathering ? Why you too de talk about that da nayi aure zaka ganni gidan mu zaune a yanzu saboda wanan matsalan muharamin na kasan saudiyane fa na fada masu hakan don kawai ya bar zancen. Ya dan bata rai tare da fadin haka mukaji ku musulmai kuna da ka,idoji masu yawa dama don a kawar da zancen nake tambayan su yaya office din su suke fadin office yana nan saidai yan canje canjen da aka samu a yanzu kawai. Nan nakejin wai yanzu Adnan da Abdul din gidan mune a matsayin aikina su biyu saidai abubuwa da dan dama sun faru bayan barikink wurin felix ke fadi har oga saida ya shigo kan matsalan barin mu da kikayi haka kuma da yan matsalolin da aka samu. Saidai yazo ya samu kunyi tafiya gaskiya baiji dadin hakan ba ashe ke matsala kuka samu da Alaja haka baki fada muna ba ? Alaja mace ce mai yawan son kanta sama ga kowa ko mu hakkuri muke da al,amarin ta har muka kai wanan lokacin a tare dasu felix din ke fadin hakan. Mikewa nayi zuwa daki ba tare dana bashi amsa ba na dauko masu tsaraban daya dace dasu irin na maza saidai da dan banbanci don na Adnan shida yake musulmi na dan banbanta masu. Har kofa na rakosu sai wanan lokacin na fito daga gidan tun bayan dawowan mu daga kasan dana shiga gida. Don hakan sai naji kawai gara na dan tsaya na sha iska a wajen kafin na juya zuwa ciki ban koma daki ba na tsaya na gyara gida don ganin yadda gidan ya dan hargitse min a idona. Bayan na gamane na shiga wanka na fito ina shafa mai wayana dana kunna da safe yana caji a power van. Na mika hannu na dauko wayan sai na samu miscall har hudu a wayan daga Faiza sai kuma shi mukhatar din da yai min kira uku ina falo banji ba yanzu kuma a kan meya kirani din na tambaya. Faiza na fara kira don jin kiran da tayi min din dukda nasan dan sabon kwana biyun da mukayi ne a zaman mu kasan saudiya ya motso mata. Aikuwa ina daukan wayan abinda nayi zato shidin ne haka kuma abinda nafi tsana shine ta fara fada min kalman amarya amarya!!! Idona na dan runtse a hankali tare da fadin Abi waireni ? Ko kin haukacene wai ? Sai naji ta kwashe da dariya tana fadin keko boyar Allah kinbi waya haka kin kashe ko samun ki ba ayi ? Ga maigidanki nason jin muryanki tare da sanin halinda jikin ki yake ciki ba a samun ki ba,a samun umma sai Abdul makwabcin ku shi kuma yace yazo garin su . Eh ya dawo jiya tare da mahaifiyarshi da bata da lafiya ayyah Allah ya bata lafiya ta fada na amsa da amin kafin tace ke gulma kecina tun jiya fa. Akan me fa na tambayeta saida taja kafin tace akan kishiyan ki fa Sahiba jiya sister ta kirani tana fada min cewa sunyi fitina sosai da mijin ki har yakaisu da batun saki saidai Allah ya gyara ba ai sakin ba . Don hakane ita kuma tace tunda a kanki komai da bai taba faruwa haka ba tsakanin su ya faru yanzu sabodake ba zaki taba tarewa a gidan shi ba da sunan aure. Faiza na katseta ina fadin ki daina irin wanan maganan ina ruwana da matalan shi da matarshi matsalan sune can tsakanin su bai shafeni ba. Ya shafeki sahiba waiko kinsan me ake nufi da kishiya mu sanma ma irin taki din nan da ta tsare ciki ta tsare waje a gidan mijin ku yanzu. Koma meye matsalan ta ni bai shafeni ba na bata amsa ta tareni da fadin keko ya shafa a yanzu sahiba don kece zaku zauna a karkashin innuwa daya da ita abinda bata taba zato ba a rayuwan ta . Sam bai fada mata zancen auren shi dake ba sahiba idan ya fadi abune daba zai yuyu ba akace dole kuma tasa hakan don hjyshi ta hana ya fada ma kowa a lokacin tunda itama iskancin matar ya isheta zuwa yanzu. Enough faiza enough please kin dameni da zancen wa yan nan mutanen kwata, kwata basu a raina balle zancen su ya dameni suje can suyi duk abinda zasuyi wanan ba matsalana bace hakan. All what i know shine idan har ta shiga gonata sam ba zataji dadin hakan ba final amma ni zancen su a yanzu ba matsalan daya shafeni da hakan understand ? Sahiba nasan da hakan amma kiyi tunane kema ki gane saboda wa take wanan haukan hakan a yanzu duk saboda kece fa ? don kawai kin auri mijinta, Shi nake son ki gane don Allah ki sa umma ta nema maki tsari a jikin ki please kafin tarewan ki tunda babu isasshen lokaci a yanzu. Katseta nayi da fadin Sahiba ni in nemi tsari bayan wanda Allah ya hore min a jikina ga kuma adduan dana sani a bakina ? Idan wanan kike jima faiza kada kiji komai a zuciyan ki ni ina tare da tsarin ubangijina komai ba zata taba yiwa yar uwarki a duniyan nan ki sani. Don zuwa yanzu na gama fahintar me faiza take ji ga hakan da taji a game dani gashi nikuma sam banji komai a zuciyata ba game da wanan labarin da take fada min din a cikin tashin hankali. Don da gani yadda take maganan hankalinta a tashe yake sosai da abinda taji amma ni sai banji wani abin tashin hankali ba a lokacin. Haka dai muka gama wayan da ita don sam bata fahinceni ba ita damuwanta shine muyi wani abu a cikin yarbawan mu da muke zaune dasu tunda ance suna da asiri muma kada wanan matar ta samu galaban illanta min rayuwana take nufi. Har muka gama wayan da ita na kashe ina mamakin maganganun faiza din sai nasawa nake a raina watau yanzu dai a kasan hausa idan zakayi aure dakai da mahaifiyar ka ko yan uwa baku da shakat a zuciya saboda irin wanan dalilin musanman ma idan mai mata zaka aure sai irin zantukan nan ya biyo baya a karshe. Ni yanzu ba shine damuwa na ba a yanzu abindake zuciyana yakuma tsaya min shine makomar mahaifiyata da inda zan bar dan uwana shine abin damuwa a gareni yanzu. Don sam ba zan iya ketare kasa ba da sunan bin wani in bar mahaifiyata da bata cikin kosasshen lafiya hakama kanina Amar ince nabi wani namiji a yanzu. Wanan dalili yana cikin abinda ya hanani kula wani namiji a bangarena bansan na boye ba don sam nikan bana kallon namiji da sunan aure a rayuwata. Hakama yasa da oga sha,aban ya fito min da zancen naga ya zubemin a idona irin yadda na daukeshi kamar dan uwa a zuciyata. Idan kana son mu zauna lafiya dakai kada ka gwada min wani tsagan soyayya a fili don yanzu ne zamu bata dakai. Ban kaiga idda tunanena ba kiran mukhutar din ya shigo layina lokaci guda wayan ya dauki kara ina kallon wayan na kasa dauka don haushin da nake ji a raina. Saida ya kusa tsunkewa na daga ina sallama naji wani irin ajiyan zuciyan daya sake yana fadin Alhamdullahi Sahiba i hope lafiya kuke haka da ba a daga wayan ki bayan sallama ya fadi hakan da yaji na amsa mai. Lafiya muke bana kusa da wayane ina falo ina aiki nabar wayan a falo na basa amsa da hakan ya kara sauke dan guntun ajiyan zuciya kafin yace. Aiki kuma ke da kanki da baki da lafiya a jikin ki aiki yanzu ba naki bane hutu ya kamata dake a yanzu kiyi barci ki huta gajiyan dawafi da zaman jirgi jinin jikinki ya dawo fresh a yanzu. Idan na kwanta sai umma tayi aikin ke nan da kanta da sauri naji yace no no no ba haka nake nufi ba amaryata ai yanzu nafi son hutun mama sama da taki sosai. Idan akwai abinda na tsana shine ya kira min kalman amaryata da yanzu yake yawan fada min daga bakin shi. Amarya for where idan nayi aure a yanzu na dauka kaine mutum na fatko da zakai min fada don barin uwata da dan uwana da basu cikin koshin lafiya nace nabi wani da sunan aure. Jin zancen yayi wani bambarakwai a kunnuwan shi kafin naji ya murmusa yana fadin a ina zaki bar mama din dama kina zaton zamu barsu a logos ne mu mutafi wani kasan daban ? Idan nayi hakan naci amanan zaman amanan da nayi da ogana da ace tun lokacin mutuwan shi nasan abinda ke faruwa daku wallahi Allah da ba zaku taba zaman kuncin rayuwa ko kwatankwamcin wanan da kukayi ba a rayuwan ku. Sahiba kin san zama na amana da mahaifin ki yayi dani a rayuwata kuwa banjin zan iya kara barin ku a wanan halin baku dawo kusa dani ba sai idan nayi hakan sanan hankalina zai dan fara kwanciya bisa ga irin abinda nake ji. Na rike wa yanda basu san ya akayi na samu dukiyana ba har kowa nasu balle ku da kune silar komai nawa a yanzu. Da ace kinsan yadda nakejin zafin Ali dcp a rayuwata da ko wanan zancen baki dauko ba a yanzu don komai daya faru daku shine silan hakan a gareku don shi ya boye min gaskiyan zancen ya rufeni. Enough that Ali dcp da kake kira he is my reletive shine uba a gareni shine dan uwan da yai silan komai nasani amma wanan sharia ne tsakanin shi da wanda suka zalunta. Bana son in rasa kowa a yanzu cikin su kamar yadda na rasa nawa mahaifin a baya shiyasa na roki Allah ya cire min duk wani zafi da takaicin su da nakeji na barsu da Allah zaifi. Ba zanso suma iyalinsu suji irin zafin da mukeji ba a zukatan mu don Allah baiyi zukata iri daya ba idan mu mun iya daukan wanan halin wani ba zai iya ba shi a zuciyan shi. Sai zumuncin yaci gaba da lalacewa har abada ba za a samu zaman lafiya a tsakanin mu dasu ba a rayuwa wanda ba zamuso mu zama silan hakan ba don bamu san me gobe zai haifa a garemu. Don haka bari ga Allah shine mafita suje idan don dukiyane da komai mukan mun yafe masu mun barsu da Allah final. Masha Allah ya ambata a cikin wani tsiga na ajiyan zuciya tare da fadin naji dadin jin wanan kalamin daga bakin ki a yanzu barin shine mafita . Ba zaku karbi komai nasu ba ninan na isheku na mayar maku da duk abinda zasu ba ku a rana daya don haka kwarai maganan nan naki abin dubawane sosai Sahiba na fahinci me hakan ke nufi a cikin zancen ki yanzu. Mun dauki lokaci kan dashi muna magana ta fahinta a wanan ranan kuma ya goya min baya ga hakan akan duk abinda na fada inda ya nuna min amincewan shi . Da zaiyi magana a sassauta sharian don kawai diyan su da matan su amma kafin hakan zaije da kanshi ya zauna dasu su san cewa nice na yarda da hakan a garesu. Don haka duk wanda keda wani abu a zuciyan shi a game damu ya fitar a zauna lafiya zaifi sauki ga mutum ba don tsoro kuma akai hakan ba. Nagode idan kayi muna hakan ka gyara komai tabbas sahiba ke yar halak ce na yarda don zuciyan ki daya da mahaifin ki. Da ace sun san da abinda yazo masu lokacin da suka kashe shi da basuyi hakan ba a lokacin don yazo masu da tarin alheri a rayuwa inda zai kafa kowan su ta yadda zurian su zata karfi a cikin duniya. Saidai kadara ta riga fata kwana sun kare a lokacin sune sanadin barin shi duniya a lokacin babu wani mahalukin da ya isa hana kaddara a kan bawa . Zan barki ki huta zan kara tunane mai zurfi akan komai na kuma gode da lokacin da kika bani a yau din nan har na kara fahintar yadda rayuwan ki yake a fili. Sai yanzu zance ya taja jin sautin murmushina a fili tsakanina dashi don abinda ya fada din nace kada kace hakan a kaina yanzu don baka san wacece sahiba ta gaskiya idan an tabani na sani. Shima din murmushi ya sauke tare da fadin hakane amma idan mun zauna a tare zan karasa sanin komai ina alfari da kasancewan ki daya daga cikin a halina koba komai nasan zan samawa gidana mace tagari wace tasan ya kamata ga kowa sai anjima ya kashe wayan kafin na furtawani kalman a garshi sai nabi wayan da kallo ina sauke ajiyan zuciya lokaci guda. Muryan umma ce ke tambaya dawa nake waya tsawon hakane ta shigo tun dazun ta samu ina waya haka Abubakar ne ? Bashi bane umma na bata amsa da mukhatar muke waya yanzu na fada mashi ya janye zancen kwace gidajensu da yai niyar yi kuma a bar wanan sharian a zauna lafiya. Sai gani nayi umma ta zauna tana fadin kinyi daidai yar albarka kamar kinsan da wanan zancen nake kwana a zuciyana nake kuma tashi dashi. Yadda su kudidi suka fada min halinda iyalansu suke ciki a yanzu don har yakai wanan yar da akai auren hadi da dan wurin gyade sun samu rabuwa a tsakanin su duk a kan wanan fitinan . Wai baby kike nufi umma itafa bamu bari yan uwan nata sunji bane a can don kada su tayar da hankalinsu kan zancen Shi kanshi Abubakar yanzu idan kin kula yana dari dari damu tun bayan da zancen mahaifin shi ya fito kowa yasan da hakan sam yanzu ya rage irin yadda yakeyi damu a da can. Idona na lumshe don nina dade da sanin hakan kuma nasan abinda yakeyiwa ke nan ashe itama umma ta gano hakan da yakeyi din. Ban tsaya mata dogon bayani ba don hakan kawai zamuyi mu zauna lafiya da yan uwan mahaifin mu har karshen rayuwan mu. Karba ko daurewa jan wani sabon fitinane a tsakanin mu dasu tunda Allah ya hore muna abin da zamu tallafawa rayuwan mu a duniya don yanzu ko shagon da umma ke zama cikin sa kawai zai shemu muci musha har mu ba wani. Kwana biyu tsakani na samu kira daga kaduna kan abinda ya faru inda yanzu aka gyara zancen kan cewa wai ai an gano gaskiya ba laifin su bane. Amma kowa a cikin dangi yasani cewa su din daine sukayi kisan kuma suka wawashe mashi arzikin shi suka wofintar da iyalanshi da komai nasa daya bari. A can wurin mukhatar kuma yana samun kalubali sosai gurin matarshi data kafe kan cewa ita sam bata yarda da wanan auren daya sakeyi ba a yanzu. ZAINAB IDRIS MAKAWA ANA DARA GA , , , , , , , , 1️⃣0️⃣2️⃣BY, , , , , , , , , , , , ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , , , , , , , , BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AL, JAMI,E, , , , , , , , , , , ONLINE PAID NOVEL YAR UWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA BA TARE DA HAKKIN KOWA BA DON BIYA KI TURA DARI BIYAR 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK 08036959257 ALLAH SARKI AI RAINA BAYA BACI YANZU DON KIN FITAR DON NASAN AKWAI RANAN HADUWA SEE U 👋 Zaune nake falon mu na mike kafafuwana saman dan table dinnda muke cin abinci koyin wani abu wanda yake aje a falom da tun zuwan mu gidan a nan muka sameshi. Tv ke aiki a lokacin amma hankalina bai wurin abinda akeyi a tv din don na lula cikin tunane a lokacin don yanzu sam rashin fitina aiki ya fara damuna zuwa yanzu. Wayata dake gefene ya dauki karan kira na shigo min kallon wayan nayi sunan ya Abubakar ne saman screen din wayan nayi mamaki hakan tare da mika hannu na dauka ina mashi sallama. Ya amsa a cikin wani murya me nuna yanayin damuwa a gareshi lokacin a hakan muka gaisa dashi kafin yace dani sahiba sai baffa ke min bayanin yadda sukayi da maigidan ki kuma. Na danja numshi kafin nace akan meke nan kuma yaya na tambaye shi cikin sonjin akan me sukai magana kuma yanzu ? Yanzu kina ganin abar zancen nan ba tare da daukan wani mataki ba a kansu kamar yadda mijin ki ya fadawa baffah shiyafi sahiba ba tare an tsaya yanke masu sharian irin abinda suka aikata ba ? Dan guntun murmushi na sake a bangarena ina fadin hakan zaifi yaya don haka shine kaanciyan hankalin kaf family din mu. Abban mu dai sun kashe shi ba zai dawowa ba don haka mun barsu da Allah ya sakamuna kan abinda suk aikata muna din. Bari ga Allah shine saukin mu a yanzu da muke son shiga yan uwan mu muma kamar yadda kowa yake cikin su zaune lafiya. Idan ka lura mu biyune mahaifin mu ya bari a cikin ku sai kuma mahaifiyar mu dake tare damu a yanzu kayi duba ka auna yaya idan munja da yawa yaya makomar mu zai kasance a cikin ku nan gaba. Ku din duk kun fimu yawa ku yan,uwa na kusa dana nisa suka sani muma fa jinin kune amma ana wasan boyo damu a cikin ku . Barin wanan zancen a yanzu shine kawai saukin mu ba kaina nake dubawa gaba ba don Ammar nake duban abinda zaije ya dawo a garseshi cikin ku shina miji. Wani iska naji ya furza tare da tareni ga fadin abinda zan fada yace na fahince ki sahiba na kuma gane dalilin ki yanzu nayin hakan. Idan suna da kunya da tsoron Allah ko tunane da kansu ya kamata su dawo da komai dake hannun su yanzu ba sai kun tambaye suba kuma. Sai a saka masu ido a ga irin nasu tunanen tunda kin tula masu kasa su zauna a cikinsa har in akwai tunane zamu gani duk da nasan yana da wuya yanzu suce zasu iya dawo maku dashi tunda daddy ma ya kasa hakan. Ka bar zancen daddy don ko yaci ya kula damu bana mance alheri komai kankantashi gareno gidan kune silan dawo damu cikin mutane har muka kai haka a yau ga idon mutane ko wanan wani abune mai girma daya kamata abawa maraya ai. Kun bamu wurin zama kun bamu ilimin da muke amfana dashi a yanzu aiko kaga daddy yayi muna komai a rayuwa ina fadi hawaye yana sauko min a idanuwana. Burina daya shine in samu dai kawai a zauna lafiya damu dasu don yin hakan shine saukin mu a cikin su. Ba babban bakin ciki garemu kamar ace yan uwa duk sun gujemu sun juya muna baya duk akan wanan maganan daya mu kasance bamu da kowa da zamu kalla a matsayin dangi a garemu ai kaga hakan ba zai muna dadi ba nan gaba. Shiru yayi yana saurarona har nakai aya kafin ya nisa yana fadin akan hakan zaku hakkure da abinda yake mallakinkune sahiba kowa yasanda dukiyan kune a hannun su. A cikin wata murya kasalaliya na kira sunan shi da brother Abubakar please abar wanan zancen kamar yadda nace zaifi sauki ga kowan mu. Yace OK amma ki kara tunane sai nayi murmushi kawai ba tare danace komai dashi mukai sallama na kashe wayan ina tunane. Sahiba wanan wani irin sunane haka ita din yar wani yarene wai data iya wanan karfin halin manewa mijina haka ta fada a fusace tana kallon babban yaron shi data tsare a falon ta tana mashi tambaya a lokacin. Kasa yayi da kai kafin yace a gaskiya ba zance ga yareta ba saidai nasan ita din a lagos take zaune da kowa nata shine iya abinda na sani a yanzu. Kyaleshi tayi ta zurfafa a cikin tunanen dayasa har ta manta dashi tsaye wajen a lokacin shine ya kawar da shiru da fadin may i ? Ta gane me yake nufi tun bai kaiga karasawa ta nuna mashi hanya da hannu a hasale ya samu ya fita da sauri ya barta a zaune ita da kannen ta. Wai kinji bayeraniyace fa a ina ya hado yar yaruba kuma kai maza sai a barsu inda aka gansu yar uwan nata datazo don maganan ta fada. Zaiganta mana tunda munafukine duk inda zai shiga ya gano ta tunda yayi niya ai zai iya ganin tunda jaraba ke cinsa har da yan yare ya jajibo dashi da ita duk zasu gane kuran su a gidan nan. Amma naji ance ba a kasa daya zaku zauna bai da ita wai a can Hong Kong ita zata zauna ko Dubai ke kuma kina nan paris. Zancen banza yake wallahi ai inda duk ya ajeta a tare zamu zauna da yakw munafukin namijine ai kinga bai fada min komai ba har yau a kan zancen. Inba ni dana fito mai da zancen ranan muka kwasa dashi ba har ni yau mukhatar zaiyiwa barazan saki akan wata arniya can. Wanan ne ya daga min hankali wai yau mukhatar ne akan wata yake ffadin haka har zance ya bazu a cikin munafukan yan uwansa sai yawo suke da maganan. Ban taba sanin basa son ki ba haka a tare dashi saida wanan zancen ya taso maku kaf dinsu sun zube min a yanzu wai murja har yawon rabon anko take da kanta tana fadin auren yayan su da amaryan sa zata tare ne. Injin bata kai gidan ki ba ta juyo tana tambaya yar uwan nata da sauri ita kuma tace da ita haba dai ai ko tasha giyan wake ba zata nufoni da wanan shirmen ba iyasu suke haukan su ai. Zan gwada masu nice kuwa ai yanzu gani na dira a kasan duk mai iya shege sai yayi mu gani don koshi basai zanzo ba wanan zuwan. Ai hakan yafi gara da kikazo ayi komai a gaban ki zaifi duk wani mai shirin iya shege yanzu zai shiga hankalinshi yan iskan banza kawai . Kafanta dake mike saman tintin din dake a gabanta ta dan ja tana gyarawa kafin wasu yan uwan shi mukhatar din su shigo gidan da sallama. Sun sheda muryan su don haka kowan su yai shiru ba tare da amsa sallaman nasu ba sai ita suwaiban ke fadin munafukai su hansai ne fa suka shigo don gulma. Sunzo su samu na karasawa dayan dake mike daga dan nesa dasu tana jin duk abinda suke fada haushi ya hanata tankawa take fadi. Wai koba kowane a gidan suka kara fada da dan karfi akwai mana kun shigone bakuga kowa ba zaku damemu da sallama haka don Allah dayan budurwan ta fada a hasale. Ikon Allah tau, aka fada daga wajen ai muna sallamane munji ba a amsa muna ba suka karaso ciki da wani sabon sallama din. Wani kallon banza ake watsa masu ba yadda suka iya don hjy ce surukarta ta turosu tunda sunji labarin isowan ta kasan duk da ba haka suka saba ba dama da tazo zata aiko a sanar da sarakuwar nata ta bayat da dan abinda sukazo mata dashi a lokacin. Saidai wanan karon abin yasha bambam don ji kawai tayi ana fadin anga gidan bude ko dan nata ya shigone ko ? Tsohuwar tayi mamakin hakan saida tasa a bincika ake fadin ai matar gidan ne ta sauka a daren jiya saida tayi mamakin jin zuwan ta kasan don basu saka ran zuwanta ba a wanan lokacin. Nan dai tayi masu irin wullakancin da takeso ita da yan uwanta saidai sun kyaleta don irin gargadin da mahaifiyarsu hjy tayi masu kafin zuwan su gidan yasa suka kyaleta. Zaman shirun yai min yawa yasa na mike don yin wani abu a gidan don na saba da jagaliya yanzu da ban fita sai a gida nake kai da komona ina wasa jini ga aiyukan gida. Wayana dake gefe ne ya dauki tsuwa hannuna na dauraye na dauki wayan Fatimace muka gaisa tana tambayan su umma nace duk lafiya suke sai Amira ta karbi wayan muka gaisa tace ga anty baby nace tazone don sam na manta da zancen sakin da akace anyi mata. A sanyayye yarinyar ke fadin ai ina gida anty Sahiba mun rabu da D salati na saka tare da tambayan yaushe haka ya faru ? Anty Sahiba manir baida hali ko kadan nan dai take fada min matsalolinsu na cewa ba abinci ba kula gashi yaki bari taci gaba da karatu. Karshe kuma yan gidan su kaf suzo sun tare a gidan su sai wahala take faman yi dasu amma basa ganin hakan harshi manir din har hakan yayi sanadiyar barewan cikin ta, don wahakan da mami tai magana sai suka nemi zagin ta maganan dai gashi nan . Don da ji matsene yaron ya shiga ciki ashe dama da inuwan mahaifin shi yake yanzu kuma ba mahaifin nasa komai ya jagule masu yanzu ga baki daya. Har hakan yazo ya faru aikin da ban iya karasawa ba kenan ina tunanen zancen ya Abubakar lokacin da za ai auren da yake korafin cewa rayuwan yarinyar zasu lalata kawai basu sani ba. Amma ita uwarta dadi takeji yarta ta samu maidan abin hannunshi har tanawa su Nabila da hauwa shagube a kan hakan. Yanzun kuma ga yadda abin ya kasance masu a karshe dai ba dadi yadda babby din ke fada min rabuwan nasu sai yarinyar ta ban tausayi. Koba komai iyalan gidan daddy sun nuna muna kauna don haka ba yadda zan iyawa mahaifin su wani cin fuska haka don su har gobe a yar uwansu na jini suka daukeni fiye da kowa a cikin dangi. Shima haka modibbo tun bayan wayan mu dashi kalamaina suke damun shi a rai don shi baiga abinda zaisa muce mun yafe dukiyan mu alhalin hakkin mune a hannun iyayyen su. Da suka kwace da karfi da yaji daga manalakinshi kowa ya sani don me yanzun zamuce mun barsu dashi me hakan ke nufi kenan a yanzu. Da wanan damuwan da yake ciki ne har yashigo gaida mommy data kula dan nata yana cikin damuwa a lokacin ba zato yaji ta jefo mashi tambaya . Hira take mai na sabon saurayin da Faiza tayi Bello dan zaria duk yan uwan nasa na zaune a falon don hakan dabian sune zama a cikin falo tare dashi idan yazo saidai har in wani abu na muhinmin zasu tattauna da uwar yan uwan nasa zasu daga su basu wuri ko idan sun san da zancen ba zasu fito ba ma . Yayi kuri ya rike haban shi da hannayen shi yana kallon kasan dakin da idanuwan shi a lokacin yaji muryan mommy na fadin wai kai lafiya kake kuwa ana ma bayani ka yi shiru haka meke damun zuciyar ka kuma ? Har lokacin bai dago a yadda yake ba saida hauwa tace yayan mu dakaifa mommy take magana sai lokacin ya nisa da dan karfi ya juyo yana sauke ajiyan zuciya lokaci guda. Lafiya kake kuwa ta sake maimaita tambayan ta tana kallon fuskanshi tare da kara nazarin shi lokaci guda. Fuskan shi ya shafo a cikin yanayin damuwa kafin yace wallahi mommy zancen su daddy ne dai yake daure min kai wai mutanen nan suce abar zancen har su daddy su yarda da hakan ? Ma,ana fa sun barsu da Allah kuma sun yarda da hakan ya fada a cikin wani irin yanayi na damuwa sosai a lokacin a fuskan shi har zuciyar shi. Wai su Sahiba kake zance dama yace wallahi mommy to nima nayi ta tunanen hakan ai saidai ba yadda zakayine tunda mahaufin ku yanzu na kula ko zancen baison ajemai dashi. Nima abindana gani ke nan mommy toba sai mu saka mai ido ba nidai yanzu nasan mutanen nan basu rikemu da komai ba wallahi. Ko mutumin nan daya fito neman Faiza ta dalilin tane faiza tace min ya santa har suka kulla dashi to akan me zata faman rike bayun Allah a raina su suna bin nawa da alheri. Jiyan nan hjy karima ke fada min ko tana ganin nasani ne tunda nafi kusa da su oho ? Wai sunyi waya da sahiba din akan zancen baby dake gida ko haka bai ishi mutum ba don Allah ? Ta juyo tana kallon dan nata amma mommy ai daddy yayi masu shima akace inji Nabila da tunda aka fara zance ta hade fuskanta wuri daya. Babu abinda ke cin zuciyar ta sai zalla bakin ciki da takaicin jin an ambaci wanan yar rainin wayau sahiba don hassadan Sahiba ya fara yawa a zuciyar ta har yakai yanzu tana kokarin cusawa yan uwanta wanan akidar. Saidai a kullun ta dauko zancen batacin riba a wurin yan uwan nata don sai su nuna su basuga wani illa ga Sahiba ba gaskiya wanan yasa yanzu take yi iya ita don kawai Sahiban da sunan nata a yanzu yake yawo a cikin dangi dama wa yanda ba dangi ba duk sun fara sanin ta. Shiyasa yanzun ma da taji an dauko wanan zancen yasa ta saka bakinta saidai bata sha da dadi ba a gurin mahaifiyan nasu da yayan su don sun zageta tas. Abinda yasata tashi a cikin fushi ta shige zuwa cikin daki tana magana ciki ciki don katsetan da akayi kan hakan a yanzu ta rasa meyasa mommy din ke ra,ayin duk wani zancen daya shafi sahiba a yanzu. Meya kawo haka ta tambayi kanta tana jan tsuki tare da kara jin tsanar yarinyar a zuciyar ta aai meya dama haka wani lokaci abu ks kasancewane ? Wai yau sahiba ce take taka duniya yarinyar da abaya can saima sun bata wani abubuwan take amfani dashi wai itace yanzu ta koma haka lokaci guda. Ba abinda ya kara ja mata takaicin yarinyar sai irin yadda har iyayyen su a yanzu suke nuna ita din fa ai watace don kawai suna takama da cewa dukiyan hannun iyayyen su nasune kome ? Tsuki taja tana lumshe idanu tare da fadin shiyasa tun farko sam yarinyar bata kwanta mata a raiba ita balle yanzu data koma wata yar kabila sosai ga ba nauyi ko kunyar kowa a idon ta sam. Saidai shi Abubakar modibbo na fitowa daga cikin gidan ya samu motan baffah hamza danasu baffah Abdullahi sun shigo ashe suna wurin daddyn su lokaci. Bai tsaya ta kansu ba yaja motanshi ya fita gida bai dade da fita ba sai gashi suna neman shi an kira wayan shi yace yanzu yabar gidan gashi ya kama hanyar zuwa kano. Sun nemi ya dawo don haka dole ya juyo ya dawo don amsa kiran su saidai yana shiga falon ya samu basu biyu bane tare da daddu din kamar yadda ya zata ya samu harsu baffah buhari dasu baffah gyade sunan gidan wurin daddy din a falonshi. Yan mintuna bayan shigowan nasane baffah hamza ya fara magana kan haduwan nasu yana fadin duk da wanan tarom a yanzu kai modibbo bai shafeka ba namene mu iyayye zallah. Amma a wanan zaman dole mu nemoka don kai kasan abinda ya dace ga abinda muke tattauna a yanzu din wanda ba komai bane sai zancen auren yar uwanka tace lagos watau sahiba. Duba ga yadda abin ya taso haka lokaci guda ba tare da masaniya ba ko wani shiri don haka mukeson a bangarem mu mu iyayye musan irin gudun mawan da zamu taimaka dashi a wurin wanan sha,anin duk dashi mijin ya nanata muna cewa shifa matar shi kadai yake so baison wani abu daga garemu. Dan murmushi kusan kowa ya sake kafin tsohon nan yace don ya raina da kuran mu ko me ya fada a dan bacin rai. To nima dai na fadi hakan a gaban shi amma saiya nuna min koda bashi bane yana da hakki da nauyi akan yarinyar shima. Baya ga haka zai zama kamar barnan dukiyane tunda shi sam baya zama a kasan na kuma duk da haka gidan ko yaushe a cikin canza sauyi ake mai. Don haka don Allah kada muce zamu wahal da kanmu wurin yin wani abu yanzu din haka kuma itama yarinyar da mahaifiyar ta na dan tuntubesu kan hakan uwar tace basu da damuwa a wanan don irin bukin suna lagos zasuyi kawai a can shike nan. Lagos kuma ba a nan zasu kawota ba ke nan daddy ya tambaya sai baffah hamza din yace dashi kudidi ma tayi wanan maganan. Shine mairon tace a dole gida ai za a kawota daga nan sai a wuce zuwa maiduguri din da ita bayan sun gama nasu abinda zasuyi ke nan acan . Kai kowa ya gyada tare da gamsuwa da abinda baffah din ya fada yaci gaba da fadin yanzu kai modibbo mun kirakane muji mu a nan me yakamata muce munyi mata yanzu ? ZAINAB IDRIS MAKAWA ANA DARA GA , , , , , , , , 1️⃣0️⃣3️⃣BY, , , , , , , , , , , , ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , , , , , , , , BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AL, GHANAEI, , , , , , , , , , , ONLINE PAID NOVEL YAR UWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA BA TARE DA HAKKIN KOWA BA DON BIYA KI TURA DARI BIYAR 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK 08036959257 ALLAH SARKI AI RAINA BAYA BACI YANZU DON KIN FITAR DON NASAN AKWAI RANAN HADUWA SEE U 👋 Kamar yadda su baffah suka shirya duk da cewa ba zancen kashe kudi ko wani abu ga auren mu duk shi mukhatar din ya dauke nauyin hakan. Saidai wanan shawaran bai sa sunyi sanyi a gwiwa ba don suma a nasu bangaren iyayyena sun tanadi irin abinda zasu kai koda shiba zaiyi amfani dashi ba yan uwansa su raba a tsakanin su. Don hakane suka yanka kudi a tsakanin su aka hada har da shanu biyu a matsayin garan da za a kai sai buhuhunan abinci na hatsi da sauran abubuwan daya dace. Sai kuma wani shanun da zasu yanka a nan don daddy sun tsayar da cewa a nan kaduna din za, a daukeni zuwa maiduguri don kowa yasan asalina hade da waliman da duk su suka shirya yin shi. Lokacin da labarin wanan shirin ya fara zagaya danki wasu sunyi na,am da hakan da za aimun wasu kuma sin nuna hassada da bakin ciki a ciki kan cewa ai sunsan inda suke abinsu. Nan lagos dai ba wasu kawayen kirki nake dasu ba sai su yemisi ne da saura abokan hurdana da sauran mutane aka danyi buki irin na al,adan yarbawa nan ma dai anci ansha daidai gwargwa don kima tare da raba abubuwa. Kafin a dauka zuwa kadunan inda muka samu rakiyan abokan arziki na mutunci zuwa kaduna din a gidan daddy muka sauka inda a nan za ai duk wani abinda ya dace kagin ranan tafiyan. Zuwa lokacin zuciyana ya gama dakewa sosai da komai na falwala Allah al,amarin ina bin kowa da kallo su faiza suke kai da komo sune yan buki. Ida naji dadin abin shine duk manyan matan da sukayo min rakiya daga lagos wanda yawancin su ta dalilin Abdul muka sansu masu rikon addinine sosai basu wasa da ibada ga su kuma kamilai ba wani zancen watsewa a tare dasu kallo daya zakai masu kasan cewa su din hamshakai ne na fada. Wanan yasa bakuna suka kara mutuwa a cikin dangin mu kuma sun nuna hali sosai yadda ya dace dama su suna girmama buki ko wani irine. Munyi kwana biyu a kaduna ana bidia irin na hausawa ga kumshi na musanman da aka dauko maiyi tundaga maiduguri da gyara irin nasu hjyn su mukhatar ta turo ta nan. Saboda ta samu labarin irin gyaran da uwargida keta faman yi a bakunan mutane wanda mu nan da mai kunshin ke muna hira na dauki hakan ga shirme a wurina. Amma da dare yayi na kwanta ina nazarin zancen saina fahinci ashe abinda su muniyat da wata Aisha da muke shiri sosai tun dawowan mu unguwar mu ta lagos da muke zama sukewa ke nan har kasan ghana Aisha taje ta kwana biyu ta dawo min da wasu abubuwa saida kyat suka samu na danyi amfani dashi. Hakama nan tun zuwan mu kullun safe da yamma sai mommy ko anty amarya sun tsureni nasha wasu abinda ban san kona maye ba saidai suna cewa na daure nasha abin amarene dai. Kai duniya abin tsorone don a cikin yan uwa aka samu wanda ya tseguntawa wata dangin uwargida cewa tayi hankali dani don ni din rikakkan yar sikiroce ta kwarai. Don sun kawo lefe na bazata da ba wanda ya taba tsanin itin sa don komai ya zama na kallo a ciki saboda an nuna bajinta da nuna halin akwaishi sosai inda zan tafi din. Yan uwa sai sam barka da tubarakallah sukeyi wasu kuma fidin na bakin su sukeyi wai dama irin mu ai hakane muke samun maza mu cafke lokaci guda irin su Nabila and coo. To a nan ne aka samu wata munafukan ta samu ta tsegunta masu wanan zance aiko kafin ace meye sun baza labarin cewa ai matar da ya auro din yar tsafice ita. Har dai labari ya dawo kunnen yan uwar mukhatar din a yadda suka zauna suka tsara komai zakace aida gaskene labarin. Haka dai suka dauki zancen wasu na fadin duk sherin kishine idan ma har manyace ita ai itace daidai da Falmatan tunda itama bin bokaye da malamai take sai su kara a tsakanin su yanzu. Falmata ko haukan karya ta hauwa maigidan cewa wurin bakin jaraban shi gashi ya dauko masu wace zata kasheta ita da yaranta harshi din. Dariya kawai yai mata don shi zuwa lokacin fitinan Falmatan ma ya isheshi a gidan don gudun hakan ne baiso tazo ba kuma gashi duk mutane basu yarda da zancen da suke yadawa din ba sai cewa ake zafin kishine kawai suke fadan hakan. Suma din kwanan su daya a kaduna anyi dinner da aka shirya yi dasu washe gari kuma zamu kama hanya zuwa maiduguri saidai sauki abin jirgi zamu bi zuwa Maiduguri din. Karfe tara muna gidan ya Abubakar da mukai mai diran bazata wanan umurnin ummace da tace dole akaini gidan shi shi matsayin jigona bayan iyayyen mu din. Kowa yayi mamakin hakan don irin girman da mukeba shi yaya Abubakar din na musanman ne don a wurin yarbawa haka abin yake dama idan kaine babba. Haka umma tabi wanan al,adan data koyo a can din sai suke ganin hakan a sabon lamarine a wurin su don ba kowa yasan ma,anan hakan ba lokacin. Durkushe nake kasa a falon nasa inda gwaggo kudidi gwaggo Amina dasu anty Amarya da sukai min rakiya suna zaune saman kujerun falon gidan nasa . Inda sai bin ko ina suke da kallo suna mede baki don yadda aka bar komai na gidan ba gyara ko kulawa wanda wanan aikin macen gidane gyaranshi . Kota gyara ko tasa a gyara din amma ga komai dai an saka na alatun zamani a falon amma ba kula yadda ya dace duk kura ya rufeshi na hammatern da akeyi a lokacin. Yana zaune suna gaisawa dasu gwaggo din sunawa juna yaya dawainiya da baki da sauran abubuwa kafin can ya juyo inda nake zaune ya dan kura min ido na dan lokaci. Kaina yana kasa ni kadai nasan halin da nake ciki a lokacin ko macen da tayi auren soyayya ta kwatanta dani da akaiwa auren hadi na bazata kwatsam banda masaniya a wanan lokacin. Muryanshi naji can cikin kunnena dawani irin kasalalen murya ya kira sunana da sahiba wanda hakan yasani runtse idanuwana a lokacin. Ban iya amsa mashi ba amma haka yaci gaba da fadin yanzu zaki bar umma zaki barmu zaki shiga sabon rayuwa a cikin mutanen da baki taba sanin suba a rayuwan ki. Wanan yasa ni sake wasu irin hawayr masu dumi a lokaci guda karo na farko tun bayan dakewa da bushewan zuciyana kan wanan zancen auren. Ya kara fadin althoug sahiba a wanan fanin nasan baki da matsala saidai shi rayuwan aure wani rayuwane dake tafiya da ilimin zamani na lokacin da ake ciki a karnin da kai aure a lokacin. Mace bata samun riban aure kin sani sai akwai fahinta a tsakanin ta da wanda zata zauna dasu musanman mijin data aure da yan uwan shi. Daya daga cikin matan da mukazo daga lagos dasu da aka hadomu da ita cikin wanan tafiyan tace kwarai kuwa (Na true you talk ) Idoshi ya lumshe a hankali kafin yaci gaba da fadin kina da hakkuri da hangen nisa ga tausayi saidai duk wanan sai kin kara ga wanda kike dashi don shi zaman aure abune na daban ga masu yinshi. Abinda mijin ki baya so kada kiyishi Sahiba wanda yake so ki kara sama da yadda kika iya nayi bincike mai zurfi mijin ki baya da matsala ko kadan a cikin tarihinshi. Don haka ki kwantar da hankalinki ki natsu ki zama dasu na tsakani da Allah don ki samu riban auren ki ki zauna lafiya da kowa kiyi biyayya ga al,adun gidanshi matukar bai kaucewa addinin ki ba. Zuwa yanzu kukana na kasa danneshi don sautin shi ya fito fili wanda shima yanayin muryan shi a yanzu din ya sauya ga yadda yake magana da farko a lokacin. Kije ubangiji ya albarkaci rayuwan auren ki da komai naki ai ba rabuwa mukayi ba tunda zamu dinga waya dake lokaci lokaci. A lokacin na kara karfin kukan nawa ina son in magana saidai ba zan iyaba a lokacin amma sai naji muryan shi yana fadin zamu baki Amirah ku tafi tare na dan lokaci kafin ki bar kasan nan. Don ance zaki dan zauna da mahaifiyar shi kwana biyu kafin ki tafi muma kuma zamuzo insha Allah don muna son zamu dan zauna dasu a kanki insha Allahu. Bayan hakan bai kara fadin komai ba naji yayi shiru da kyat gwaggo Amina dake kokatin dagoni daga zaunen da nake ta iya daga ni sai lokacin na bude dan guntun gyalen dana rufe fuskana kafi suyi aune na fada saman jikin ya Abubakar din daya riga ya mike shima a lokacin ina sake wani irin kuka mai ban tausayi. Tare da fadin brother na fasa wanan aure bana so bana iya barin umma da dan uwana in tafi i don't want dis marrige at all. Bayana naji yana dan bubugawa tare da fadin you most to marry Sahiba haka shine cikar imaninin ki a cikin al,umma aure dolene ga musulmi don sunace mai karfi garemu. Ba abinda zai samu umma ko Ammar don suna tare damu nayi maki alkawarin kara saka ido ga duk wani lamari nasu daga yanzu. Kai na girgiza ina sake fadin No i don't want zamana a gida yafi min wucewa na barsu idan na wuce wani wajen dawa za a barsu yanzu nice komai nasu a rayuwa Ammar ba lafiyane sosai dashi ba hakama umma din. Saida kyar suka samu na yarda na barshi a lokacin muka fito tare dashi yana kara min nasiha jin su kawai nakeyi don takaicin daya rufe min zuciyana. Nazifa dake tsaye bayan kujeran da yake zaune saida taga fitan mu daga falon nasu ta sauke ajiyan zuciya tare da fadin yar iska. Ashe iskancin naki iya nan ya tsaya aje a iske kanuri can suci muna magininki da kyau ai zaki gane kuren ki yar iska kawai ance maki aure wasane dama. Daga gidan ya Abubakar gidan tsofin nan biyu aka kaini dake zaman iyayyen su a yanzu kannen mahaifan ubanan mu ke nan daga nan muka dawo gidan daddy din . Mun samu yan maidugurin sun iso wai yan daukan amarya bayan wa yanda suka kwana a nan mazansu da mata nagodewa Allah na kuma godewa yan uwa da suka taru suka fitar dani kunya suka nuna nidin yar dangice gaba da baya. Don yan uwan umma ma da dangin mu na kauye ba,a barsu a baya ba duk sunzo daga kauye din don an aika masu suma kuma sunzo. A yadda suka buga anko wai duk sabodani din ya kara sana fashe da kuka ga ko ina ya cika makil da dan mutum anci ansha sai sam barka ga kowa lokacin. Yan kai amarya mutum ashiri aka bukata saura yan uwan ango ne da abokai wai ashe shima mukhatar din yana kaduna a ranan. Jin cewa tafiyan na jirgine yasa su gwaggo hari da tawaganta dama wasu da ban zata ba duk suka shirya yimin rakiya don su karas da komai yadda suke jin labari. Mommy ce akace su zauna su sallami baki a gida daga baya zasuzo tare da ummana da wasu sauran yan uwa ganin daki wanan alkawarine da akai masu. Haka gwaggo Amina ta fito rike da hannuna zuwa falon daddy dake cike da yan uwa da abokan arziki kan inyi sallama dasu lokacin. A tsakiyan falon aka zaunar dani bayan wasu daga cikin iyayyen mu mata sun rikoni zuwa falon nidai sai binsu nakeyi don ban taba sanin al,adan hausa fulani haka yake da akidu masu tarbiya ba idan bawa yabisu daki daki. Daddy ne ya soma magana bayan budan taro da addua ya fara min nasiha saidai ince ya dora inda aka tsaya don nasiha kan nasha a wurin yan uwa dama. Har yakai akaba baffah hamza dama shida wa yanda suke yan sa,oi kusan baffah hamza din shine ba karshe a lokacin. To Sahiba Alhamdullahi mun godewa Allah daya bamu iko tare da lokacin sauke wanan nauyi da dan uwan mu yabar muna. Alhamdullah don zan iya cewa kinyi dace da miji wanda yasan darajan ki tare da kimar ki kuma da tausayin ki a matsayin kina marainiya a yanzu. Don Allah sahiba kije ki zauna tsakani da Allah a dakin mijinki kada ki yarda wani abin asha ya fito daga gareki ko wani hali da baida kyau damu bamu sanki dashi ba. Kirike Allah da mairaicin ki Allah yai maki jagora da haske ga almarin ki ya baki zuria masu albarka yasa ku gama lafiya ki kara hakkuri shine maganata ta karshe dake. Haka suka fito dani ga yan uwa nan kan sunzo bila,adadin gaskiya nidai kodan me sukazo naji dadin ganin hakan daga garesu. Bayan mun shiga motoci airport aka nufa har yan rakiya sai a nan ne naji ana fadin aiga angon can ashe harshi sukazo suna gaisawa da mutanen mu. Ba,a tsaya jiran komai ba aka fara kidaya masu zuwa dama sun fito da shirin su na tafiya har wa yanda ba,a kidaya zuwan dasu ba. Nidai ina biye da gwaggo har zuwa cikin jirgin ba,a dade ba jirgin ya tashi wanan karon tare da anty Amarya hjy karima nake zaune. Tun zaman take kara lurar dani abubuwa wanda hakan yakara sa kaina daukan hasken zaman kishintaka da mata keyi muna jin labari. Yan uwane da abokan arziki sukazo taron mu zuwa gidan hjyn shi inda su gwaggo suka bukaci a kaini a cewan su sai na fara kwana wurin ta taimin masauki kafin zuwa gidan da zan zauna din a ciki. Nan ma mutanene sosai muka sama anci ansha duk a gidan mahaifiyar nasa wanda ba haka ita uwargidan taso ba don hakan ya bata mata wani daga cikin tsarin ta da sukayi. Don basu da kunya har gidan hjy sukazo wai don me za a ajeni gun hjy din ace sai gobe ko wani abu can su sam ba haka tsarin al,adansu yake ba. Su gwaggo hari dasu Anty Amarya suka hayayakosu da fada suma kan cewa mu tamu al,adan fulanin mu haka muka gada sai amarya ta sauka wurin surukarta an bata girman ta kafin a kaita gidan mijinta inda zata zauna. Kiri kiri suka nuna su basu yarda da hakan ba don sun shiryawa tarona gidan don me za a bata masu tsarinsu da sukayi yanzu zakace sune iyayyen miji a yadda suke kafa doka da fadi idan kana wurin a tare damu. Nan su gwaggo hari suka nuna masu bafa su kadai suka iya iskanci ba suma da nasu a boye gwaggo harine ta fara fadin wai ku suwaye da zakuzo muna da wanan hayaniyan hakane ? Munce ga yadda al,adan mu yake kunce sai mubar al,adanmu dole mubi yadda kuke so to mu ba hakan al,adan mu yake ba dole sai ta zauna a hannun uwar miji kafin ta shiga zuwa dakin ta itama ta saka mata albarka. Ji mun mata da kafewan tsiya wata ta fada daga gefe to har in zaman lafiya kukeso a aiwatar dolene taje dakin ta a yau din nan kamar yadda kowa yasan anayi din, kuma wanan sallon uwargida kanta bata yarda dashi ba don ba haka aka san anayi ba ko ina. Au uwargida ta aura ko mijin su da mahaifiyarsa sune muka sani a jigon aure babu abinda ya damemu da damuwar uwargidan a nan mu . Kowa ya tsaya a matsayin shi don bamu kawo gareta ba mu har yanzu don haka kada ki jefo muna zancen ta a nan ki zo zaki kafa muna doka haka tsarin mu yake ga al,adan mu. Kallon gwaggo hari din matar tayi ba laifi don a tsare take da gani itama watace mai fada aji ga yanayin ta don haka ta dan daure ta sake fadin . Au naku sallan da kukazo dashi ke nan munan kujerane daidai muke da mazaunan kowa don haka zamu zuba daku ga haka. Zakuyi kunya kuya kuwa wanan karin dan yar mu na daidai da kowa ta kara binsu da wani kallon yare dayan tayi mata suka fice daga dakin a fusace kafin hjy karima tace kai nadai gode da hanza ya tsara hakan baki ga wani kallon wullakanci da suka shigo muna dashi ba da farko. Sai bin mu da kallo takeyi daga sama har kasa tana wani mere bakin ta sun shigo da niyar wullakanci sin zo gida ai kodame suke takama kuwa gwaggo harin ta sake fada. Lalai za ai zama a wanan wurin kuwa gwaggo Amina ta fada sai hjy kafima tace in dai wanan ne zasuyi daidai dan banjin komai a gun Sahiba ni. Karamci kan mun gashi karfe takwas na dare an gama shirin dinner din da aka shirya za, ayi harni din na gama duk wani shiri don nasan da hakan kada a girsheni yasa wanan custermer din nawa ta hada min kayan dinne na gani na fada tun daga dubai aka kawo min su a hade. Duk wani wanda ke wajen saida shigana ya burgeshi don zakace nidin wata yar sarkin yarbawane a yadda nayi ado da tsara jikina don ba doguwar riga bace a jikina lokacin, zanine da riga na wani lace dinkin buba irin na yayi daya sha haduwa wurin kyau. Don duk inda na juya walkiya nakeyi wal wal daurin zaninma na yarbawane nasan yadda suke komai dan haka tsarin yarbawa na tsara a komai nawa wurin. Kowa ya zuba ido zan shigo aga fuskana a lokacin don duk basu sanni ba auren ma a bazata yazowa mutanen shi da yan uwan shi. Saidai lokacin da muka shigo din fuskana yana a rufe da dan wani mayafi dayai shige da kayan sai walkiya yakeyi ba mai iya ganin fuskana lokacin. Kamshi kan shi angon sai da abin ya hau kanshi balleni da kamshin yake a jikina yana hawa min sosai ina jinshi aikin anty amarya da gwaggo hari ne wanan din. Cool music suka saka na oldscul a wurin na wani mawaki nan abokansa suka dauki tafe da shakiyanci gareshi wasu yan mata masu kaya iri daya suna gaba da bayan mu su hudu. Daga inda hjy Falmata take zaune da tawaganta tace wanan ai iskancine ashe dama haka suka shiryawa abin ban sani ba har suna fadin wai yazo a kuraren lokaci haka ? Bana fada maki naga suna shiri ba lokacin a bayana su anty hawauce faiza hamida da zainab yar wurin gwaggo Amina sune a matsayin yan matan bukina. Ba irin zagin da anty Nabila bataiwa hauwa ba da gwaggo hari tace sune za a dasu ba a yarda wani dan waje ya shigo yaci da cewan sauran yan uwanmu dake wajen bukin wai. Nan yaren kanuri ya tashi don ganin su don ba wace bata hadu ba a cikin su wurin sai nasu adon ya bambamta dana gaban mu din. Bayan mun zauna aka dan gabatar tare da bayanai nan shagali ya fara masu bayanan da sharhi suna fitowa sunayi. Gwaggo hari ta karbi abin magana ta soma magana tare da gabatar da kanta a matsayin gwaggona take nan ta fara fadin tau yan maiduguri. Ga amanan uwargijiyan ku nan Sahiba bafulatanan asali sai wurin ya dauki hayaniya kowa da abinda yake fadi tana dariya, . Tace OK duk da dai gida tazo ba wani waje ba don nan gidane gareta ango kuma uncle dintane yanzu kuma mijinta. Kiji min abinda wanan matar ke fada wata daga gefen uwargida ta fada tace haukane kawai irin nasu kafin ta gama zance taji gwaggo hari na fadin. Nace hakane don shi mukhatar kamar wani jigo yake gun yar mu koda bai aure taba ga kuma aure a tsakanin su yanzu Allah ya hada. Don haka zan kira garesu da a zauna lafiya uwargida muna mai baki hakkuri tare da kara danka amana a gareki dan nauyin bana mukhatar bane shi kadai a yanzu nan dai taci gaba da bada shawara kan zaman lafiya tare da dan barkwanci ta fita wata kawar gwaggo din darta rakota ta shigo tayi bayani itama kafi ta fara bayani . Inda ta bukaci hankalin mutane kan za ayi budan kai a lokacin daga can hjy falmata da kungiyan ta suka soma fadin wanan ai iskancin yan kadunane zasu kawo mutane a nan su nuna wayewa da iyayi kowa wasukafi wayewa suke gani oho ?. Kowa na kallo aka kawo kujeru biyu yadda ta buakata aka bukaci ango ya fito ba bata lokaci ya fito ya zauna a zaton mutane nice za a kira sai kawai ta kira dj dama ta fada mai sai ya saka mata kidan uwargida rangida don Allah jama,a ku tafawa uwargida hajiya falmata mukhatar wurin ya dauki tafi lokaci guda. Yatsine ta fara daga cikin su wata wace ta fisu shekarune ta taso tayi mata magana kafin ta mike sauran suka biyo bayanta suna tafe da ihu suna zuba mata kudi. Nan su faiza su fatima suka fito suna kwasa don wanan fagen amaryane wai shine hikimar su gwaggo don wani idan ya wuce ba zai bada komai ba. Ta isa a cikin izza ta zauna don gaba take da maigidan don haka ko kallon inda yake batayi ba ta samu wuri ta zauna kafin a bukaci su kauwace amarya zata fito fili. Nan ta fara fadi a cikin yare tana fada tana fadin na fada maku bazan fito ba wurin wanan iskacin amma ya hafsi tace sai nafito waya sani ko sabon iskanci zasuyi min a nan kuma. Shidai murmushi yayi yana jin abinda take fada baidai yi magana ba iyakan shi ido kallo daya zakai mai kasan yana cikin damuwa a lokacin. Bayan sun fice daga ita sai shi a tsakiyan filin zaune kowa yayi shiru ana kallon su sai kuma hasken wurin ya dauke aka saka dum light wakan fulani ke tashi a cikin cool music zabayen ke kirari ga amarya. Gudan da wanan hjyn tayi yayi daidai dana cikin kidan su faiza ce suka hawo sukai min rakiya har zuwa inda suke zaune din ina zuwa gaban su na tsugun na duk hankalin jama,a yana wurin mu ana kallon me zanyi a lokacin Amira ce ta iso da cup's biyu a hannun ta saman ture ta miko min. Na dauka na tsiyaya ruwan madaran dake cikin kwali na mika wa mukhatar din ya karba sai tare da dan matse hannuna a cikin nasa sai dai na danji zafin na daure na sake tsiyayya wani na mikawa uwargida kin karba tayi naji yayi mata yare ban dai san meya fada mata ba lokacin ta karba. Gurfane nake gaban su sai ihu ke tashi holl din ina nan a yadda nake mai magana tace Alhamdullahi amaryan mu da alama mai ladabice ga shugaban nin ta . Yadda ta gurfana haka a gaban maigida da uwargidan ta tana neman zaman lafiya a tsakanin su sai muyi masu fatan alheri dangin ango kuma su fito tare da abokan arziki da masoyansu suzo su taya uwargida da ango sayen bakin amarya . Wuri ya dauki ihu da sowa dangin shi suka fara fitowa suna jefa kudi kafin na abokai su shigo suka cika wurin da takardun dolers na kudi. Har lokacin gurfane nake a gaban su sai kokarin bude min fuskana wasunsu keso na hana suga fuskan suna fadi ai sin biya don haka in bude har anty hauwa tazo tafitar dani a cikin taron tunda mutanen ba karewa zasuyi ba lokacin. Amma har aka watse kaina yana saye da wanan gyale da bazaka iya ganin fuskana ba sosai hakan ya fara saka zukatan su wasi wasin ko yaya yanayina yakene oho. Gashi dai a jiki ya nuna ni farace sol ga tsayi ma daidaici alaman dai zubin fulanice ni kuma ance masu ai bayerabiyar lagosce ni da farko. Da dabara muka sulale dan ba wani dadewa akayi ba a wurin dagani har angon kowa zuciyar shi yana cunkushe da abubuwa. Ko sha biyu mu bamu kaiba muka dawo gida ba tareda kowa yasan da barin wajen namu ba sai su gwaggo da na dan rubutawa text a waya lokacin. Suka sanda mun bar wurin zuwa gida hakama shima ya turawa wasu abokan shi da uwargidan shi cewa ta tafito zai tafi gidashi . Ta dauka ina cikin wurin taron take fadawa kawayen ta wai ango fa yace ya gaji shi zai tafi gida ai dama tasan irin wanan taron ba damuwan shi yayi ba shi shirin yan uwanshi ne kawai. Bayan tace ya tafi zata zo tare da kawayen ta ai shine kuma wata yar uwarta ke fada mata cewa ai amarya tabar wurin tun dazun itama. Sai kuma ranta ya baci dajin hakan nan suka fara fada wai ana munafuntar ta ance amarya ba ranan zata zo gidan ba kuma gashi sin tafi da maigidan gida akace. Nan take ta mike a fusace makarrabanta suna mara mata baya itama tabar wurin zuwa gida saidai ta samu gidan a rufe da alaman ma bai karaso bashi. Mamakin hakan kuma taji zuciyarta na azalzalanta ta shiga danna mashi kira taji yana inane yace gashi karasowa dashi dasu maina ta kashe wayan. Tana maijin zafi a zuciyar ta na kishi yana azalzalanta lokacin suka shigo katafaren gidan nasu bata ko son yin magana sosai a lokacim don kishi. Karshema ta haye sama ta barsu a falon ana mayar da fadi tun bayan fadin da wata yar uwanta tace da alama dai amaryan tana da kyau a fuskanta don yadda naga yan uwata din suma. Daga haka tamike tsam tare da fadin wai ni mukhatar yau yayiwa kishiya har ana kiranshi tsakiyn fili yana fitowa kamar wani karamin yaro can dashi tana kaiwa nan taja wani irin uban tsuki . Shigowan mu gidan kai tsaye na shiga cire kayan jikina da alokacin sun dameni da nauyi bayan uban kudin dana kashe wurin hadasu iyakar aikin su ke nan wanan ranan don ni a rayuwana banson saka lace ko atamfa nauyin su nakeji a jiki ko don ban saba bane oho ? Wanka na shiga na dade a cikin bayin koda na fito na samu su gwaggo sun shigo an dawo dasu gida suma lokacin. Sai hiran bukin sukeyi a tsakanin su kafin anty Amarya tace amma wanan uwargidan kan da alama tana jin wani abu wai girman kai da izza ko madaran da sahiba ta zuba mata fa bata ko kurba ba. Daga can inda gwaggo hari take zaune take fadin ai irinsu dama sai anyi takai dasu tunda bai taba mata kishiyaba dama yanzu zatafi jin abin a zuciyar ta sosai. Kinsan idan an maka a dan tsakatsakiyan nan yafi sauki da ace saida aka kwashi shekaru irin haka za aima balle wanan kan gaskiya akwai aiki. Shine ni ban gane ba wanan aikin da suke faman kira ko wani lokaci a iya tunane na kasa gano aikim da suke nufi dani har yanzu gareta ? Sallama akayi aka shigo muna da wasu manyan kulolin abinci tare da plate dakin nan su gwaggo suka shiga gaidasu da aiki suna fita wasu kuma suka shigo dauke da kayan shayi dakin. Gwaggo hari ce ta kalleni tare da fadin diyata me zakici ko shayin za a hada maki tana bude kulan abincin ferfesu ne a cikin dayan na kayan ciki. Shi kuma dayan kuma na soyayyan naman kazane shake a cikin shi sai plates masu yawa da aka kawo dan bukata. Nan wasu suka fara ci wasu kuma suka shiga wanka tea mai kauri anty amarya ta hada min ba tare da bread ba ta zauna a kusa dani saida na shanye na miko mata cup din. Karba tayi ta aje kafin tace dani saura wanan abin ta miko min wani dan cup dake cike da fresh milk na karba ina bata fuskana don dole nasha sai a lokacin ta dan fara min bayanin amfanin sa dayasa suke ban tun a kaduna kuma yanzun ma zata bar min saura na karasa sha. Fuska na kara daurewa lokaci guda kafin nace da bata ban ba gaskiya duk wanan ban dauke shi da wani amfani ba . Zakizo ki nema a guna wata rana tafada tana dan dariya na girgiza kai tare da fadin ku daina wahala da kanku ga wanan din koda yake dai kun yarda dashine don nayi saidashi ina karama a lagos na fara bata labari yadda akayi na fara wanan sana,an har mata suka gane suna saya a guna sosai lokacin . Tayi mamaki kwarai ga labarin dana bata din take fadin kai sahiba gaskiya an auna arziki da basu sakin bacewa mutane ba tun lokacin. Don irin hakan sai a nemi mutum a rasa sun daukeshi tunda suna son shi har zai iya ganin su dan zaman da mukayi da Anty Amarya a yan kwanan kin nan yanzu. Yasa na kara fahintar ko ita waye a yanzu mace ce mai saukin kai da saurin fahinta amma kuma bata son sam wani ya zo ya nuna shiya fita mussanman a gidan mijin ta ma,ana dai macece dai mai kishi ita da jajircewa wanda hakan wasu mata suke. Wanan yasa naji na yarda da ita har zan iya maganan abinda ya dami zuciyana da ita din kafin su tafi su barni koba komai yadda suke nuna min kulawa da kauna kai tsaye ita da diyanta a yanzu yafi min wanda mommy ta nuna min a baya. Sai naji kawai na aminta da ita tambaya na farayi mata akan zaman auren hausa tana ban amsa tare da bayani daki daki ina gamsuwa da hasken da take kara min din a lokacin. Na kuma gamsu din da abinda ya daure min kai din sosai a yanzu ta walwale min su ta yadda na fahinci yadda abin yake. Munkai wani lokaci bamuyi barci ba muna hira kusan mutanen duk sun shige dakunan da zasu kwanta sin kwanta ko a lokacin mukasha hira yadda har banso tace zata kwanta din ba. A nan take fada min zamu zauna da fatima don Amira tana da jerabawa in yaso idan ta gama sai fatima din ta dawo ita ta zo ta zauna dani. Nayi godiya don gaskiya hankalina ya tashi da ganin irin mutanen da zama ya hadani dasu a yanzu suma din dai kamatace don ba hausa sukeji sosai ba yare yafi karfi a harshen su gaskiya . Don haka nasan zaman za,a dan sha wuya a tare dadin abin dai akwai matsala gaskiya duk da dai nasan ba wani kasancewa a tare zamuyi dasu ba dama. Washegarima abin arzikin bai kare muna ba don abin karyawa ne aka dinga shigo muna dashi a daidai lokacin da wasun mu suke barcin gajiya wasu kuma suke wanka a lokacin. Ni dai tun kan gari ya gama haskawa nayi nawa wankan na shirya na koma na zauna a can kuryan dakin da muke ni dasu Faiza da sauran yan uwa ina bin kowan su da kallo tare da nazarin su da abinda suke fadi lokacin. Sai bayan sun gama karyawa ne su gwaggo Amina suka shigo suke fadin in saka mayafi zamu gaida hjy mahaifiyar su mukhatar din. Buje da rigan atamfane yar super a jikina da akaiwa dinkin buje da riga fetet daya dane jikina ya fito da shekaruna a fili sai kamshi dake tashi ko ina a jikina. Mayafi na yafa daya shiga da kayan sai flat shoes a kafana simple makeup ne a fuskana da nayiwa kaina don nasan abinda zai min kyau a fuskan nawa. Tsakiyan su nake sun kewayeni mukayi sallama a kofan falon da zai sadamu da dakin hjy din idan mun shiga daga cikin part din gaskiya ginan ya hadu duk da kaina a dan duke yake amma ina ganin yadda ginan ya tsaru. Tana zaune falonta tare da bakin su da gani basu jima da gama karyawa ba suma a lokavin don anata fita da kayan abincin da akai amfani dashi a falon. Sallaman mu yasa su kara dan natsuwa suke fadin sannuku da zuwa muka shiga muka zauna su gwaggo suka zauna a saman kujera yayin dani da yan matan muja zauna a kasa daga gefe aka shiga gaisawa. Nan su gwaggo suka dora da fadin toh hjy ga yarki nan mun kawota gareku amana yo ai wanan gida tazo don nan gidan sune itama. Kada wanan yasa kuji komai a rayuwan ku kan zaman ta a tare damu ni dai bukatana a zauna lafiya su bawa mijin su kwanciyan hankali da natsuwa. Don shi din dan ujulane da balaguro yau yana nan kafin gobe zakajishi a can haka sana,an shi ya kumsa hjyn ta fada. Don haka Sahiba ban son naji komai ya fito na rashin hankali a wurin ki ki godewa Allah kin samu yabo sosai daga bangaren ki nima din shedane ga hakan. Da sauri hjy halima ke kallon wadda aka kira da sunan data dade da sani tana kwankwanto a ranta kafin a natsu tace wai Sahiba dai dana sani a baya ko watace wanan din ? Kaina dago a hankali ina kallon wace ke magana din nima din na shedata hjy Halimace dai dana sani a logos shekarun baya idan baki manta ba. Matar da muka hadu asibiti da ita tana jinyar danta har tace muna ai dan nata ya rasu itace yanzu nagani a gabana dakin sarukata din tare dasu. A zabure take fadin lalai kuwa Sahiba ina kuka shiga duk wanan dadewan haka ina mahaifiyar ki da kanin ki take tambayana a cikin mamaki tana min kallon bazata. Nan ta shiga bada labarin haduwan mu da ita shekarun da suka wuce kowa saida ya tausaya muna nan suke fada muna cewa ai mijintane dan uwan mukhatar din ne. Don da mahaifiyar mijinta da hjyn su mukhatar ya da kanwace suke nan aka shiga gabatar muna da yan uwan mahaufiyar nasa da suke zaune a falo din . Mukaji kuma ashe su zamane yakai iyayyen su can suka zauna suka saje dasu an dai dan kara tataunawa kafin mu bar su zuwa wanan dakin muka barsu gwaggo tare dasu a part din. Sai bayan dawowan sune suke fadin wai karfe hudu zasu kaini dakina sam ban taba zaton hakan zai sani fargaba ba sai wanan lokacin don wani iri naji a zuciyana tunda suka fadi hakan. Suke fadin ance gidan a gyare yake basai munje munyi wani gyara ba a cikin sa komai an zuba kunga ko tunda har sun nuna kamar suma sun isa da itane ai sai suga kamar muna kwankwanto akai. Nasiha sosai suke min tare da kara lurar dani a dakin da suke idan kinga yadda gwaggo Hari da yar uwanta gwaggo Asiya suka zake suna min fada zakice basu bane masu min bita da kuli a baya. Yanzu sun nuna cewa ni din kan tasuce yar uwasuce ta jini dole yan uwan mahaifina suka dan rakube a gefe wanda saini din ke nuna sune nawa don komai zanyi ko nakeso su nake kira in tambayesu. Nasan hakan yana dan taba zuciyar su saidai basu nuna min a fili ba amma suna kebewa suna gulma don anty Amarya ta rutsasu suna gulman a tsakanin su tazo tana fada min. Kai mutanen halinsu saisu wallahi suwa ke nan na tambayeta wanda ba halina bane tsoma baki a maganan manya. Su gwaggonin nan naku dai hjy hari man da tawagarta yanzun na samesu a can dakin suna gulma cewa Allah yasa dai ki iya zama yadda kika saba da harkan bariki. Gadai gida kan kin samu amma bariki ba zai barki ki zauna a ciki ba dama watace a cikin diyansu ta samu wanan aida su tasu ta yanke ke nan. Jimun fa mutanen nan wai har hari na fadi saboda idon ki daya bude da barki yasa ta shiga tsakanin ki da danta tunda wuri don ba zata yarda ki rabi danta ba. Hakama modibbo shima ya nuna ra,ayinshi gareki amma sam ba zasu taba yarda da hakan ba a tsakanin ku don kin bude ido a bariki. San nan kuma ai gashi ya tabbata kan camfin da akai maku tun kakannin duk inda kuka shiga sai kun dara kowa lokaci guda kema dake bariki za ace wai kece kika samu wanan daulan hakan amma nasu diyan suna zaune a gida. Jimjn mutane da son kai haka don Allah ko me zakiyi da danta balle shi modibbo ma dayake da matarshi a gida harda yara. Kawai dai son kaine irin nasu na banza da baida dalili su a ko ina saidai sufi mutum badai kafisu ba da zaran suga Allah ya doraka akan su shike nan a dauki karan tsana da sherin duniya a dora ma saboda hassada. Lokacin nan shiyasa na rufe ido nayiwa baby aure saboda irin yadda suka fara nuna min waiga su Nabila gida amma zaice baby yake so shi. Yanzu kuma da Allah yakawo rabuwa a tsakanin su ba abinda basu fada ko yanzu din nafi bukatan ganin ta koma dakin ta ta zauna don dai kawao badai aikin yine a yanzu din. Don haka sahiba ki daure ki rugumi auren ki da hannu biyu kibi mijinki ku zauna lafiya daduk wanda ke kewaye dashi don Allah. Nisawa nayi kadan ina fadin nagode anty insha Allahu zanyi yadda kikace din zan zauna lafiya da kowa insha Allah. Kada kibi takan wanan uwargidan naki ki barta da halinta idan ba tashiga harkan ki intashiga kan ki nuna mata kema kin iya sai a zauna lafiya. Yanzu bakiga gidan mu ya dan samu sauyi ba don yanzu na gama fahintarsu abudai ne idan yazo ya kama nabawa kowa hakkin shi na bayar idan mutum yabi shike nan. Idan nace banji haushin zancen su gwaggo ba gareni karya nake fada maku don gaba daya nikan sun kara zubemin a idona. Antyko taci gaba da fadin wai ga dukiya har dukiya amma bai samu mata ba sun san indai kece kwana biyu zaki fito ki koma barikin ki da kika iyane ai. Jifa wai dan dan uwanka kake wa wanan fatan haka murmushin karfin hali nayi ina fadin ba komai tace don Allah sahiba ki daure ki zauna a dakin ki. Kinga dai yadda Allah ya rufa maki asiri a cikin makiyan ku har gobe kune sama garesu ni yanzu na gama fahintar kowa wallahi. Su mutanene masu dan banzan son kansu da mugun hassada a zukatansu basu son suga wani ya karu yafi ko yaushe su dai ace sune ke samu ko sune a gaban komai. Wallahi kaf din su indai ba na bayan nan ba sune zance maki suna da dama a cikin su amma kusan manyan nan wallahi duk halin su dayane gaba dayan su saidai na wani yafi nawanine kawai a cikin su. Wallahi shiyasa nake son modibbo Allah kinganshi sam bai kwaso wanan akidarba ko kadan yanzu ki duba duk da ake cewa komai ya wuce a zauna lafiya a tsakani. Kinga dan gidan Alh nuhu a nan ko daya ko dan kidan Alh gyade bafa wanda yazo ko dayan su ai idan gaskiyane ko yadda kikai masu din nan zasuzo ko diyan su su turo amma mugun nufi ya hana . To wallahi kaf dinsu kusan haka suke sai ka zauna dasu zaka san halinsu sosai shiyasa sam bamn dagawa Gwaggon ku kafa koshi Alh. Nisawa nayi tare da fadin Allah ya shirya dama naga yadda take kallona idan mun hadu da ita tun a kaduna nayi mamakin ganin tazo har nan din duk da tasan kwana biyu za ayi kafin a koma. Wanan ai sunyi ne da biyu wa yan nan da sai hannu mai mai suke bi idan baka dashi basuyi dakai . Idan ko kafisu kaida su zaku koma kamar Annabi da kafirine a fili zasu nuna maka kiyayya ba gaira ba dalili don kawai hassada dasa abu arai irin nasu. Anty amarya harta gama tafita ban samu abindana fada mata ko daya ba lokacin bayan nisawa da nakeyi ina tunanen zumuncin zamani yadda ya koma yanzu ga mutane. A gaskiya bazan lamunci zancen wai ummana ta dawo cikin su kaduna ta zauna ba a yanzuma . Don naji sun fara fadin wai ya kamata tunda nayi aure saita dawo gida itama su zauna a gaban yan uwa zaifi watau dai a can din sun dauke mu bariki muke shekawa kawai a zaman can din. Haka har karfe hudu yayi kowa ya shiga shirin tafiya zuwa gidan da zan zauna din a cikin sa wanda ba kowa yasan da sanin cewa ashe ba gida daya zamu zauna da hjy falmata ba dama har danginshi basu sanda hakan ba sai lokacin da aka dauki hanya daban ba wanda suka sani ba zuwa wani sabon gida nashi dake gaban unguwar da mahaifiyarshi take kadan nan nawa gidan na Maiduguri. Gidane na gani na fada wanda shine wanda ya gina a baya bayan nan don ba kowa yasanda cewa gidansa bane a garin . Tsarinshi da komai ginan kasan wajene ba irin fasalin ginan mu bane na nan da aka saba gani ina jin gwaggo hari na fadin dankari saidai muce Allah yasa mu cika da imani kawai masu kudi na inda suke kasan nan ashe. Aikuwa ciki taga mun shiga kai tsaye nan ta suma zaune tana raban idanu har motocin sukaja suka tsaya aka soma fita ga guda yana tashi a ko ina. Bin gidan kowa keyi da kallo kafin wata mai zakin murya ta sake sake guda da habaici lokaci guda da sauri wanda ke tsaron gidan ya garzayo yana fadin sannun ku da zuwa. Ikon Allah gwaggo ke fada tana fitowa yayin da suka zagayo a bangaren da nake zaune cikin motan gwaggo kudidi ta karaso ta bude bangaren da nake zaune naji gwaggo amina tace dakata da ita. Wanan gidan fa kamar babu kowa a cikin sa kudidi sai nake ganin kamar ba nan bane ai kuwa nan daine gidan nata wata daga cikin yan uwanshi ta fada daga bayan su. Inaga a nan zata zauna ita wancan dayan gidan kuma uwargida ke ciki tare da yan uwanta koni na dauka ai a gida daya zasu zauna tare sai naga an nufo nan yanzu. Bin gidan sukayi da kallo kafin gwaggo Asiya tace dankari gwaggo haro tace bari kedai anty na aini nayi shiru ga baki daya wallahi. Da sauri daya daga cikin yan rakiyan mu daga lagos ta iso dauke da buta a hannunta tare da sabon kafet din sallah magana tayiwa su gwaggp akan zanyi alwala nayi nafila kafin na shiga gidan ga yadda al,adansu yake. Allah ya taimaka sai mere baki gwaggo sukayi don jikin su ya mutu a lokacin suka kauce na fito daga motar da taimakonta nan suka nuna min gefe na tsuguna na daura alwala kafin na gama sun shinfida carpet din na hau na tayar da sallah din raka biyu . Kafin na daga hannayena biyu sama inayi suma sunayi da dan karfi duk wanda ke wajen yana amsawa da amin don sunsan addua sukeyi duk da hakan ya zama bakon lamari a wajen su kuma. Kafin na shafa tare dasu sai lokacin wani kuka yazo min suka fara addua tare da rike min hannu kaina a kasa ina kuka wiwi zuwa cikin gidan da aka riga aka budeshi ko tun shigowan mu get din gidan. Duk wani wanda ke wajen a lokacin na bashi tausayi dan yadda nake kuka wiwi zuwa cikin gidan a daidai shiga kofan suka tsayar dani . Kafin su fara da hasbunallahu wani, imal wakil kamar a waka baka jin komai sai muryoyin su a haraban gidan lokacin. ZAINAB IDRIS MAKAWA ANA DARA GA , , , , , , , , 1️⃣0️⃣4️⃣BY, , , , , , , , , , , , ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , , , , , , , , BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AL, MUGHNI , , , , , , , , , , , ONLINE PAID NOVEL YAR UWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA BA TARE DA HAKKIN KOWA BA DON BIYA KI TURA DARI BIYAR 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK 08036959257 ALLAH SARKI AI RAINA BAYA BACI YANZU DON KIN FITAR DON NASAN AKWAI RANAN HADUWA SEE U 👋 Da haka sukaja hannuna zuwa cikin gidan wanda kamshi da sanyine suka bugi fuskokin mu lokaci guda su anty amarya sai masha Allah nake jin suna fada. Ke kan sahiba kin gama da duniya saidai ki nemi lahiran ki kuma kai wanan daulan duniya haka kamar kana kasan masar azziki ya nuna kamshi wurin nan gaskiya. Nasan da biyu take wanan maganan a lokacin sister ce ta iso da sauri tana waya tare da fadin ehh tagane take fadin ku shigo ga dakin amarya daga nan . Subahanallah Walhamdullilah Allahu Akbar shine abinda yarbawan ke kira kamar da waka a bakin su wasu na amsa masu cikin yan uwana da nasa da sukai muna rakiya dayan kanwarshi duk tana vedioting komai da akeyi lokacin. Nan dai suka kaini dakin daya bugawa soster waya cewa shine nawa dakin ya hadu komai na cikin gidan ga baki daya na wajene don haka tsayawa bayani bata lokacine gaskiya gida dai tubarkallah masha Allah. Daga nan suka fara fita kallon yanayin gida sai aka barni da su faiza da saura a dakin sai lokacin na bude idona ina bin ko ina nagidan da kallo,. Tirkashi yayi da uwargidana hjy Falmata ke can wancan gidan nasa suna ta buki da mutanen ta ana kisa yadda komai zai wakana idan mun iso . Sai kuma labari yazo masu a nazata cewa ai amarya ta tare a ko da sauri hjy Falmata dake waya lakacin da yaranta tace mene kike fada ta tambayi wace kebada labarin tarewan a lokacin. Tace ta tare a gidan ta mana tun karfe hudu da rabi suka kaita dakinta tana can gaba daya dakin yayi shiru na lokaci guda kowa da irin abinda yake tunane a zuciyar shi. Mikewa tayi daga zaune sai wanan yatta din hafsat tace ina zaki koma ki zauna yanzu idon kowa yana kanki aga yaya zakiyi. Zama tayi ba dan taso ba lokaci guda sukaci gaba da fadin shi kuma haka yaiwa mutane dama bai fadi inda amaryan nasa zata tare bane. Kubar wanan zancen yar nasu ta kara fada don a bar maganan a bainan jamma,a saidai falmata din ta kasa controling din kanta a lokacin don jin zancen take kamar a mafalki. A cikin hasala take tambaya wani gidan nasa ya kaita ke nan sai mai bada labarin take fadin naji ance kusa da gidan sarki nan dai unguwar nakune mana ba niss naji suna fada. Katseta yarta da take biwa ga haihuwa tayi da fadin waike a ina kika samu wanan labarin ne ina nan daine yake nan kuma za a kawota wancan dayan part din ko ? Ya canza shawarane dai wata daga cikin bakin kawayen ta ta fada ta bude baki da kyar tace ya canza ne kan don ko jiyan nan saida yan uwansa sukazo aka kara gyara part din ai. Gyara ko na sosai don har mun leka ai komai a kwai ciki eh wanan makircin suka shirya yasa suka hana ta tare jiya din ai. Wanan bashi zaisa na fasa komai a kanta ba tunda tayi gigin shiga harkan mijina zan nuna masu ni din nice don ba irin mu ake hawa a taka ba. Falmata bakya ji a irin wanan lokacin kike wanan zancen haka haba dai ta fada a dan cikin daure fuska tana mai jin zafi da kuna a kasan zuciyarta na wanan sabon zancen da yazo mata. Lamarin na mijinta a yanzu ya fara bata mamaki don yana abubuwa kamar ba mukhatar dinta data sani a baya ba. Don a zamanta dashi sam baya boye mata duk wani lamari nasa koda kuwa yasan zata iya yin wani abinda ba daidai ba duk da tasan bawai ta kyaleshi hakana bane don ko yaushe cikin kara kammala abinta take don gudun irin haka. Ba abinda ta tsana kamar kalman kishiya sam bata taba sarai cewa zai taba mata kishiya a rayuwan su ba duba ga yanzu yadda shekarun auren su yaja zuwa yanzu. Amma sai gashi da rana tsaka yan uwa sun tasashi gaba a cewan ta har yakai ga sunyi galaba a kansu sunsashi ya kara mata wata a gida da sunan kishiya. Ita tasan ba yinshi bane don yasha fada baida ra,ayin yin mata biyu a yanzu sam haka yasa ta kara sakankancewa da bai taba mata kishiya ke nan. Ido ta runtse cikin takaici tare da fadin ina tausaya maki yar yarbawa ko yar filoce don zama gidan mukhatar saiya koma mata tankar zama cikin kabari. Tasan irin taron data shiryawa zuwan amaryan wanda manyan malaman dake mata aiki suka tabbatar mata dashi kuma ta amince da aikin su dari bisa dari don sunsha mata ai kuma ta gani ta yaba da aikin nasu don hakanema akan wanan din bata da matsalan komai a yanzu don tasan karshen yarinyar waje road zata nufa . Nan dai kowa ya shiga fadan abinda ke cikin zuciyar shi kamar yadda al,adan mata yake in iri haka ya faru suna goyon bayan bangaren da suke suna ganin ba ai masu daidai ba. Komai an saka a gidan babune kawai babu cikin sa hatta abinci kusan na wajene da komai na bukatan mace . Ranan ma a gidan yan uwa suka kwana amma da shirin su kan tafiya komawa kaduna Allah kadai yasan yadda nake ji a zuciyana a lokacin. Suko sai hidimar gaban su sukeyi kowana kokarin hada kayan shi wuri daya don an fada masu karfe takwas na safe jirgi zai tashi su zauna da shiri . Wani zazzabi zazzabine nakeji don haka na kwanta bayan na idar da sallah na ranan saidai ba barci nakeyi ba ina dai kwancene kawai ina kallon yadda yan uwa ke shiri amma badani da fatima ba lokacin. Anty Amaryane ta shigo dakin lokacin gani kwancen da tayine yasa ta fadin lafiya dai ko Amarya ?. Sanyi takeji Fatima ta fada kafin na samu bata amsa kallon Faiza tayi tana fadin kun samu abinda kuka bata tasha ko ? Anty kinsan halin yar nan taki fa ni wallahi tsoroma nakeji kada yazo yai mata yawa haka a jiki ta kasa komai sai kuma ta kama baki kota tuna da anty take maganane oho ? Au kema kinbi zancen gwaggonin ku ke nan ashe Faiza da suke fadin wai yau ango ya shigo ya kwana a nan duk da sun san muna nan don gulma. Wanan wai wani haline haka su gwaggo keyi ne don Allah wai haka dazun fa suka kama diban kayan kitchen wai zasu samu simple a sayo masu idan mun koma gida har saida dayan matan yarbawan nan tayi masu magana kan haka bai dace ba ai. Anty hauwa ce ke maganan a lokacin ta kara fadin ko a gida naji mommy na fada wai sin dibi kayan cikin akwatunan nan masu tsada. Don Allah ki bari hauwa anty tace wallahi ai shiyasa kikaga mommy ta dauki kayan ta mayar dasu dakin daddy. Watau dai mutanen nan sun tabbata yan son banza ke nan dai wanan wani irin haukane haka wai don sunga abin kamar banza suke yin hakane wai ? Wayana dake gefena yayi kara na kai hannu na dauka sokone daga Felix yasa na bude da sauri ina karantawa. Da farko murna yayi min tare da addua, sai na biyu da yake sheda min wai sunyi gobara a shagon su na Idi,iroko dake lagos sunyi hasara sosai a wajen. Ban bata lokaci ba na tura mai da sakon jajen kan hakan ina tayasu bakin ciki da abinda ya faru din shima ya turo min daya gode. Wanan labarin daya ban ya tsaya min a zuciya dan nasan wajen sosai wurine babba da ake aje kaya idan an shigo dasu kafin a raba zuwa garuruwan da za a kaisu. Tun jin wanan labarin na dunkele a wuri daya ba abinda nake tunawa sai irin dukiyan dake makare a wajen a gaskiya na tausaya kwarai da wanan abinda ya faru din. Ina kiran ummana da Amar dako wani lokaci yana kirana kai da kai mu dan yi hira ko ya fada min wani abu don ban bar gidaba saidana canza masu waya ga baki dayansu. Hakan yasa yanzu yana kirana sosai don suna kaduna suna jiran mutanen lagos da zasu tafi tare zuwa gida duk da Faiza ta kwarmata min cewa wai ance ai a nan kaduna su zasu zauna yanzu. Nasan umma ba zata yarda ba dan garama da ace ina gidane har yanzu mukazo idan nace zamu zauna a nan zamu zauna din tare. Waya take ta faman kira amma ta kasa samun shi don haka ta kara hasala dashi sosai a zuciyarta don saita dauki hakan ai rainin wayau ne yake mata at list ya kamata ya kira yaji lafiyan ta ai kamar yadda ya saba yi a baya. Bata samu jin labarin shiba sai baya karfe tara daya dawo gidan zuwa lokacin ta gama kuluwa dashi sosai a lokacin. Watau sai daya gama rawan kanshi ga amayarshi da yan uwanta ya dawo gida kilama ko yanzu din wani abu yazo dauka ya shigo tunda tasan dole ranam a gun amarya zai kwana tunda ta tare. Yawan mutanen dake gidan a lokacin bai hanashi shigowa part din nata ba haka ya fara gaisawa da mutanen da suka rage basu tafi ba har yakai kofan dakin nata yaja ya tsaya don muryan mutane da yakeji daga cikin dakin hakan ya tabbatar mashi da ba ita kadai bace a dakin lokacin. Kamar sun san yana tsaye wata ta bude kofan zata fito a lokacin hakan yasa ta san da yana wurin tsaya da sauri ta fara gaidashi cikin dan daga murya don naciki su sanda zuwan shi a kofan. Nan matan dama su hudune a dakin kuma suma da safe zasu tafi bakine abokanta da sukazo daga nisa sai yan uwanta mutum biyu suma. Ya dan dauki lokaci kamar yana duba wayanshi kafin yasa kai ya shiga dakin da sallama yana duban inda suke zaune. Tare da wata matar abokin shi da tazo daga Niger republic aminiyar ita hjy falmata dince sosai kuwa tun shigowan shi ta fara mai ba,a da ango ke nan Ashe amaryan zata bari mu ganka kafin tafiyan mu dan murmushi ya sake yace ai a marya bata rikeni ba kafin yai magana ne yaji hjy falmata din ta lailayo wani ashar tana fadin wane uban ta da zata hana a ganshi har ita din me ita din banza. Murmushi yayi gajere daya tsaya iya baki da gefen fuska kafin kuma lokaci daya ya daure fuskan tasa yace. Meya kawo zagi a nan kuma yanzu falmata ina hanaki wanan zagin dake son ya zauna maki a baki yanzu fa bazan lamunci wanan ba a gidana. Jin ya yarfata a gaban mutane a zaton ta duk a kan amaryan tasa yayi mata haka ta sake fadin don an zagi bayerabiyar taka kake wanan halakon haka wai ? Zagi kan ai yanzu na fara tunda kun fara min da munafunci ta tare kunce sai yau yau din ma da zata tare din saika dauketa kakaita wani gida kuka barni nan zaune. Da wanan gidan da wancan din duk ba nawa bane ya tambaya da mamaki don me zaka dauketa ka kaita wani gida na daban ? Mukhatar yaji an ambata daga bayan shi sai kuma lokacin ya farga da tana dakin ashe can daga baya tana lazumi don haka kuma ya sheda muryan anty hafsat din da tazo daga Cameron yartace ubansu daya uwane suka raba da Falmata din . Macece kamila mai addini mijinta ya rasu da dadewa tana zaunene a can ne don dangishi sun hata wucewa . Saboda zaman mutunci da sukayi da ita tana da hakkuri da sanin ya kamata bata da yawan hayaniya sosai ita kamar sauran gata kuma malamace ta addini sosai don shine aikin mijinta dama malunta yazo maiduguri a nan ya auri hjy hafsat din yatafi da ita kasan su. Ka dawo ashe ta fada ta kawar da zancen yace eh naje duban wani aikine garin Calaba sai yanzun muka dawo ya fada a dan ladabce. Jeka ka huta daga baya mayi wanan zancen amma ba a nan ba yanzu duk a cikin yare suke fadawa juna magana a lokacin. A sanyayye ya juya ya fita bayan yayi mata godiya don a wanan lokacin yakai iya makura da matar nasa dake abu kamar bata da hankali. Har ya kai dakinshi a gajiya da kana kallon shi zakaga zalla bacin rai a tare dashi da damuwa kuma yana kallon kannen ta dake zaune gidan shi amma basu iya gayar dashi ba lokacin suma suna taya yar uwarsu bacin rai ke nan a hakan. Tun shiga shi dakin ya fara kokarin cire kayan dake jikin shi lokacin yana maijin zuciyan shi ba dadi haka ko dan bai saba da irin wanan hayaniyar bane ya zo mai a hakan. Ita falmata tasani ba yayi aure bane don damuwa da mace shi sam ba irin mazan nan bane dake lakewa a jikin mace ita ta sani yana aurene don ida sunna ma,aiki S, A, W ne. Don me zata biyewa zancen wasu a yanzu ta bata tsakanin su bayan tasan yayi mata iya kokari a rayuwan zamanta dashi don kawai ya dauko wanan yarinyar yanzu a cikin su zata fito mai da wani hali na daban da bai santa dashi ba yanzu ? Tsuki yaja ya karasa cire yar cikin dake jikin shi tare da fadin zan koya maki hankali ki gane kuren ki idan kin matsa wanan haukan haka . Wanka yayi ya fito yayi sallah har lokacin ba wanda yai mai tayi abinci duk da uban yunwan dake cikin shi kuwa tun safe haka ya wuni hana rantsuwa ya dan sha juice a can da zaisha maganin shi. Shiryawa yayi tsaba ya fito daga dakin da bai san ina zai nufa a lokacin bai yarda wani ya bishi ba shiya ja mota da kanshi zuwa gidan mahaifiyar shi. Tsuki yaja don ganin ko nan akwai sauran mutane har lokacin amma haka ya daure ya kutsa kai ciki falon ya fara gaisawa da mutane sama sama. Hjyn tasa tana daga cikin don haka ya kutsa zuwa cikin don zaifi mai sauki a lokacin nan ya samu ta idar da sallah suna zaune ita da kanwarta a lokacin. Bayan sun gaisa din ne ta fara tambayan shi yaya jama,a yake fadin Alhamdullahi shima baya nan ya danyi tafiyane ya dawo yau din kuma. To amaryan ka dai ta tare a gidan ta sai muce Allah ya bada ikon rike amana da hakki a tsakanin ku yanzu sai kuma kayi hakkuri da matar ka kasani don zataga an mata ba daidai ba duk ko da tasan gaskiya. Ai wanan ba komai bane zan zauna da kowa da halinshi insha Allah ya fadawa yar uwan majaifiyar nasa a ladabce tace nasan zaka iya amma kuma sai ka kara hakkuri duk da hakan. Don ita falmata ta manta da halarcin kowa da akai mata a baya yanzu ta koma kallon mu a makiyan ta tunda mun goya maka baya kayi mata kishiya a yanzu. Kaga a nan idan bata kwantar da hankalinta ba zata koyawa na bayan rashin zama lafiya ke nan gidan ya rikice ma ga baki daya lokaci guda. Nima abinda nake gani ke nan gareta yanzu don ko yanzu dana koma gida saida yatta ta rabamu wai nakai amarya wani gida na daban mun munafunceta ita . Nan ma ta kira sai abinda ta manta a bakinta shine bata fada ba a lokacin ita duk ta manta da irin halarcin da akai mata a baya kan auren ku da ita. Murmushi yayi don baida abin fada a nan tunawama barnan raine a gareshi yanzu maida kanshi yayi saman kujera yana dan lumshe idon shi a hankali. Ita dai mahaifiyarshi bata iya fadan komai ba a lokacin don itama ba abinda zata iya fada a yanzu kan wanan hauka na falmata da yan uwanta da sukeyi a yanzu. Waya ta dauka ta kira layin yar aikinta tana dauka take bata umurni data kawowa mukhatar abinci a dakinta lokacin, ba a jima ba sai gata ta shigo dakin har lokacin suna zance shida ummin shi akan abinda yake faruwa a gidan nasa. Inda take kara lurar dashi nauyi da karfin ikon da yanzu ya kara rataya akanshi har lokacin daya kare cin abinci kafin ya bukaci su sister dasu fito gashi gaban shi ta zube kayan a falo ta fara mashi bayanin komai kamar haka . Duba ga irin abinda suka kawo yasa zamu basu kowa turmi daya da dubu ashirin ya dago kai a cikin razana yace what ? Samira haka mukayi dake don Allah cewa nayi me alokacin da zan baki kudin kayan nan na fada maki cewa ina son su san abu mai daraja a rayuwana suka kawo min bawai abin wasa ba. Koba komai suka kawo min mace ai tukwaicin da zan basu yafi wanan balle kinsan muhinmancin yarinyar nan a wuri haka kuma da yanzu take a matsayin iyalina . Zaki hada masu turmi biyu da dubu dari a matsayin tukwaici sai tsaraban kayan buki kiba ko wace haka ma mazan zakiyi masu final ya mike yana fadin Allah ya bamu alheri yafice gidan kai tsaye. Gaskiya ban so brother yayi hakan ba amma yanzu ya zama dole a basu mutanen da basu san darajan taba sune za,ayiwa haka ? Akul, na sake jin wanan furcin a bakin ki ke bake bama ko a bakin wani na sake jin wanan furucin mara dadin ji wallahi saina sabawa maishi fiye da tsamani. Dukiyan kiki ko nasa shi bai manta da mafarin arzikin shi ba kuma yafiki sanin abinda yakeyi ai babu ruwan kowa da abinda sukai masu. Ko kuwa duka suka taru sukai masu laifin da kike nufin sunyi din ko kuma ta nuna tana da wasu yan uwane bayansu din ko kinga wani bare ya kawota wurin mu yanzu ? Yadda taga uwar nasu na fada da gaske yasa ta dukar da kanta kasa tasan abinda tayi ya batawa mahaifiyar tasu rai sosai hjy ce mahaifiyar su ta fito take wanan magana. Bayan tafiyan hjyn daki ta mike ta dauko turamen zannuwan kamar yadda yace a lissafa a basu ko wani ta dora mai kudinshi a cikin envelope dauka sukayi suka fita zuwa gidan da aka kaini din dashi. Ina nan a yadda nake kwance din mukaji sallaman shi a falon gidan suna gaisawa dasu gwaggo da sauran mutane, kafi kuma muji sallaman shi a kofan dakin . Anty hauwace ta fara mikewa dan ta fita zuwa lokacin yasa kai zuwa cikin dakin ko mu hudune ciki a lokacin su suna hiran su ina kwance ina sauraren su lokaci. Ya shigo suka fara gaisawa suna ce masa ango don yasan su tun a saudiya sukayi ba,a da Faiza tace itace yata yace basu yarda ba nice dai babba gareta. Yanzun ma daya shigo hakan suka fara dashi yace a, a kanwa kune a ciki amma a nan zasu barki kada ku bar min matana ita kadai dole dai kema ki tsaya don Fatima kawai ai bata isheta ba yana magana yana kallon inda nake kwance. Ga dai amaryan ka nan tun dazun take muna raki wai ita bata da lafiya kila dama ciwon son ganin fuskan ka takeyi ta damemu sanyi takeji tun dazun. Gaskiya mukhatar mutum ne mai yawan ambato Allah a bakin shi don ko yanzun ma cewa a ouzubllahi meke damun ta faiza shine baku kirani a waya ba. Duk da ban gari dazun nan na dawo daga calaba cikin mamaki Faiza tace dashi calaba fa yace wallahi tun safe na tafi calaba kinsan sha,anin aiki irin namu ai. Zuwa lokacin ya kawo inda nake kwance din yakai hannun shi yana dan taba wuyana a lokacin duk suka fice daga dakin suka barmu dagani sai shi a dakin. What is wrong with you ya kara tambayana tare da dan zama a daidai tsakiyan inda cikina yake zuwa marana. Wani iri naji lokaci guda don hakan yazo min a bakon yanayi da ko ganin hakan ban taba yi ba balle hakan ya faru gareni. Dan kokarin ja da baya nayi saidai jikin shi na saman dan abindana rufe jikina din dashi lokacin ya gane hakan da nake da niyar yi amma sai ya basar ya nuna kamar bai fahinta ba. Muje kiga likita ya fada jin hakan yasa da sauri nace no nasha magani jikin yai min sauki yanzu ai nagode na fada ina lumshe idona lokaci guda. Yana yuyuwa streas ke damun ki tunda baki huta ba tun last week kuke event kinga hakan zai iya jawo maki ciwon jiki a yanzu daki daure muje din likita ya duba min ke ? No don't worry your self iam OK now na fada a kasalance sai ya bini da kallo kawai kafin naji yace wanan ne dalilin da zaisa na barki ki huta nan na dan lokaci sai daga baya zan dawo in tafi dake. Nima zanso a barni nan na zauna zaifi min zuwa wancan kasan don na zaifi min zama kusa da mahaifiyata da dan uwana a saukake. Sau nawa zan fada maki cewa ba zan barsu su zauna a nan ba suma ko kina daukan hakan wasane zamu tafi da farko daga baya zan turo a dauke su lokacin kin saba da can. Kara lumshe idona nayi a hankali kafin nace dashi kana ganin hakan ba zai jawo wani matsala gun mutanen ka ba ina nufin yan uwanshi ya kuma gane me nake nufi din yasa yace. Ina ruwan wani da family dina yanzu ko mahaifiyata itace ta zabi zama nan kasan nasan kuma saboda sister dinane dake nan zaune. Don haka kuma ba zan tauyewa wani daga cikin kuba hakkin zama da kowa nasa tunda Allahbya hore min abinda zan ciyar dasu din . Ban kara magana ba illa matsua da ya tashi ya bar min dakin dana matsu yayi lokacin saidai kuma naga baida niyar yin hakan shi asalima kamar dadin zama yaji a dakin shi. Saima naji yana fadin da safe zasu tafi an riga da anyi masu bucking din jirgi karfe takwas na safe shine nazo na sallamesu saidai zanso a bar Faiza da wata babba a nan tare dake idan hakan zai samu . Faiza tana aiki a kaduna na fada don haka dole ta koma aiki saidai Fatima da zamu zauna tare da ita zasu bari ina gani dan shiru yayi kafin yace anyway zanyi magana da uncle hamza idan na fita yanzu asan abinda za a yi akai. Sai kuma yakai hannun shi saman goshina yana fadin don't be a lazy tun yanzu kin fara rakin barin gida umma will be with you soon nasan shine damuwan ki dai yanzu. Dan lumshe idona yayi banyi aune sai naji yakai min kiss a gefen fuskana yana fadin take care zan tafi saida safe ya mike tsaye ya fita da sauri daga dakin. Nan ya barni cike da mamakin wai meyasa maza basu da kunya ne wai mutumin da yake a matsayin yaya a gareni ko mahaifi amma shi sam ba kunya ko wani nauyi a idon shi sam a kaina. Har barci ya daukeni bangama tunanen zantukan mu dashi ba ga kum yan uwana sun shiya barina da farko ban dauka zanji komai ga tafiyan su ba amma yanzu dana tabbatar haka dinne sai nashiga damuwa. Haka su sister suka kawo masu alheri har dakina suke suna min ba,a haka baisa nayi magana ba lokacin suka tafi. Barci barawone shine ya daukeni har na rage jin irin yanayin da nake ci washe gari kuma aka tashi da wuri kowa yayi haraman tafiya duk da sammakon mu amma saida aka kawo abun karyawan su daga gidan mahaifiyar mukhatar din. Bayan sun karyane mota tazo ta kwashesu hardani a rakiyan su don mukhatar din da nake kira da Uncle a yanzu don na rasa sunan da zan kirashi dashi wanan lokacin. Ga manyana nata karfafa min cewa nayi biyayya na girmama duk wanda ya dace nabashi girman shi haka in zama mai tausayi da taushin zuciya ga kowa koda maigadin gidane. Wanan huduban abokan arzikin mune na lagos da sukayo min rakiya su hudu har maiduguri daga cikin su tare da muniyat da makwabciyan mu Aminat suke yawan fada min hakan damun kebe dasu. Dagani saishi a motan muna baya driver yana jan mu a gaba sai motar dake bi muna su faiza ne kadai a cikin ta ko wani mota biyar biyar aka dauko su a cikin lafiyayyun motaci masu kyau da tsada. A gaskiya ko don wanan karamawan danaga gun mutanena ya isa zuciyana ya sassauta abinda nakeji anty muniyat ce ke wanan maganan lokacin da muka fito zamu shiga motar dan bamu san shima zaizo mu tafi tare dashi ba. Gaskiya kan an karamamu sosai anty Amarya ta fada na dan yi dariyan yake wanda shine dabi,ata kawai ba yawan magana. A daidai lokacin Motanshi ta shigo gida ta tsaya daga dan nisa kadan damu ya fito da sauri da alaman yaso makara yake gani. Inda su gwaggo suke ya fara isa da sauri yakai kasa gwiwa bibiyu a wurin yana gaidasu suka amsa mashi suma a cikin mutunci da girmamawa zaku tafi ke nan ya fada a cikin gurbatatcen hausan shi don ba hausan yake ji sosai ba yare ya amshe harshen shi sai turanci. Eh mukhatar sannu da dawainiya mun gode kwarai Allah yayiwa aure albarka ya baku zuria masu albarka ya amsa da amin nagode kafin ya mike. Wurin su faiza ya nufa suna ba,a tunkan ya karaso yake fadin kedai badake za a tafi ba sai kin kwana muna biyu a nan zaki koma . Bayan ya gama dasune ya nufo inda nake tsaye tare dasu muniyat din ya gaidasu nan manya suka sake addua daga inda su gwaggo suke tsaye gwaggo kudidi tace ashe mutanen nan haka suke da yawan ibada ? Suna da ibadan kan saidai shirme yafi yawa a cikin sa don dai suna hadawa da al,ada sosai idan ba yanzu suke gyarawa ba. Shine yasa ai nasan ba wani aikin banza su mairo suka aikata ba can da diyanta don dan zaman umuran da mukayi da ita na fahinci tana da rikon ibada da kamun kai sosai wallahi gwaggo Amina ta fada. Aiki a zahirance ai bashi bane zuciyar mutum wayasan abinda suke aikatawa a boye tunda ba mijine dasu ba can rayuwan lagos fa idan ka shigeta sai a hankali gwaggo hari ta fada tana yamutse fuska. Kai haba hjy hari koma meye ai tunda sun samu sheda haka ya wadatar don Allah ki iya bakin ki akan mutanen nan yanzu tunda Allah ya wanke muna su yar uwanta hjy Asiya ta fada. Shiru tayi bata tanka ba don ta fahinci me yar uwan nata ke nufi da zancen ta akan ta daina maganan haka kada zancen ya dawo kunnem mu ba abu mai wuya bane yanzu inji. Yana isowa inda muke tsaye ya dago ya kalleni tare da daga min gira yana fadin yaya jikin ya kika kwana ? Not bad na bashi amsa ina gyara rufin lafayan dake saye jikina lokacin don shi anty amarya ta ban shawaran na dinga yafawa tunda an zuba min su da yawa a kayana. Lafaya din yayi min kyau sosai a jikina sai kamshin turare da nakeyi wanda yanzu kan ya fara zama min jikina duk da rashin son kamshi da ban so ada. Kana yin abinda baka so don ka kyautata rayuwan na tare dakai don kawai farin cikin maishi haka anty amarya ta fada min a karshe da take bin jikina da kamshi. Zo naji lafiyan jikin naki kunnena yaji lokacin da banzata yana fitowa dags bakin uncle mukhatar din lokaci guda. Yi nayi kamar banji me yake fada sai na basar da fadin antashi lafiya ya mutanen gidan suka kwana lafiya ya fada yana cusa hannayen shi a cikin aljihun shi ya kara kallona yana fadin mu karasa airport din kada su makara. A nan kowa ya shiga motar kamar yadda sister ta tsara komai don tana wajen shine muka rakasu airport din ko a motan ma da zamu hannun shi yana sagale a cikin nawa yana dan matsa min su a hankali har muka kai airport din yana dan jana da fira ta hanyar tambayoyi su masu tafiyan ina masa bayanin wanda na sani. Saida muka tabbatar tafiya ya kankama don muna zuwa aka kirasu muka fara sallama lokacin ne naji wani irin yanayi kamar kuka zaizo min saga muniyat ta fara abinda yasa nawa saukowa ke nan. Rugumoni naji yayi a jikin shi tare da kama hannun fatima dake tsaye a gefen mu don mu kadai muka rage sai sauran yan uwanshi da suka rakosu suma da sauran mutanen shi a wajen. Bai bari munga tashin su ba muka dauki hanyan wurin da motan take aje ya shigar damu muka koma gids har lokacin kuka bai tsaya min ba. Muna shiga dakina nayi kokarin shiga kai tsaye sai naji ya rikeni ta baya haka yasa dole naja na tsaya na fada a jikin shi naci gaba da kukan da nakeyi fatima ma ganin ina kuka yasa ta fada saman kujera ta makure tana nata kukan. Bayana ya dan fara bubugawa yana dan murmushi kafin yace why are you crying ko zama nan ne bakyaso na mayar dake kaduna yau din nan, idan zama can ne yafi maki nan din ?. Kaina girgiza ba tare dana furta komai ba nayi kokarin zare jikina daga nasa amma sai naji ya kara rikeni tam a jikin nasa ya kwatar min da kai saman fadadan kirji shi. Na dan lokaci ina lafe sai sheshekN kuka nakeyi a hankali ki duba fatima ma kin sakata tana kuka kamar ke don tags kema kinayin abu kamar karamar yarinya. Sai kuma naji yayi murmushi anyway kina da right na kuka a yanzu nasan irin pain din da kike ji a zuciyar ki game da hakan don bakya so na ko Sahiba ba zaki iya zama da tsoho kamana ba. Hakan baisa na dakatar da kukan da nake danyi ba a lokacin sai ma kara dan sautin shi danayi a lokacin haka ya rike hannu zuwa part din dake gefen nawa din. Key ya dauko daga wani wuri da bazaka san akwai ma,adana a wajen ba ya bude kofan sai lokacin ya dan sassauta rikonnda yayi min din yana fadin key din part din ki na wanan waje but is a secret kada ki bar wani ya sanda hakan don tsaro . Yana budewa wani dan karamin falone ya baiyana a gaban mu shima dai kusan komai da akwai a nawa a kwashi nan din saida kala daya banbanta don nan din komai na cikinsa farine kal sabanin na part dina da yake milk colour. Zaunar dani yayi ya nufi wurin abin sanyin dake dakin sai gashi dauke da goran ruwa da cup a hannun shi yazo ya zauna a kusa dani ruwa ya tsiyaya ya miko min kaina girgiza masa alaman a, a. Open your mouth ya fada yana kai cup din a bakina zaki samu relief idan kin kurba ruwan kisha ko kadan ne ya fada yana kallon fuskana. Kai hannu nayi zan karba daga hannnun shi kai ya girgiza min yana fadin a, a karbi kisha kawai ba musu na dan kai bakina na kurba dan ruwan kadan tare da lumshe idanu. Good girl ina son mutum mai saukin kai kamarki yanzu fada min komai ya wuce ko mu shirya zuwa kadunan ne muna a yau din nan ? Kai na dan dago na kalleshi yace yes saina kaiki a yau din nan na fada masu kukan banza kike min don sun wuce sun bar minke a nan don baki yarda dani ba. Irin kallon da nake masa yasa yace yes koba haka babe baki yardani ba baki kuma daukeni a matsayin mijin ki kuma dan uwan ki ba har yanzu why zaki dinga kuka haka sahiba ? Kina son kijawa kan ki wani matsalane kuma yanzu ki tashi ki dan kwanta nasan akwai gajiya har yanzu a tare dake idan kin samu barci a yanzu komai zai wuce a zuciyar ki duk a cikin harshen turanci yake min magana don dole sai dashi zamu fahinci me muke nufi. Ta fito dan yau itama bakin ta zasu tafi duk da tasan yayi sallama dasu a daren jiya din kuma ya bada mota da za a kaisu airport. Amma zata so su kara sallama saidai tana nufar part din shi ta hango wurin a rufe a zatonta yana ciki har lokacin bai tashi ba. Saidai tana nufa kofar a cikin kasaita sai gaida ita masu aiki ke faman yi taji dayan na fadin hjy oga ya fita tun dazun da safe ai . Cak ta tsaya tana sauraron me maganan tace mene tare da kallon shi tana son karin bayani daga bakin shi yace eh oga ya fita dazun nan . Ina ya tafi da safen nan ta tambayi kanta tana juyawa don barin wurin haka ta koma part din ta har bakin suka tafi bata daina tunanen inda mijin nata ya tafi ba tare daya sallameta ba. Duban lokaci tayi idan ba karya idon ta ke mata ba yanzu shabiyu da wani abu na rana ji tayi ranta ya kara baci fiye da farko sai lokacin ta mike zuwa falo har lokacin abinci na ajiye haka ya karasa ranta baci karo na barkatai. Zama tayi don taci abinci idan ya dawo sai yaci nasa da sauri dayan matan yar aiki ta karaso ta fara zuba mata hannu ta daga alaman ya isa hakana. A hankali ta fara ci bayanta jawo abincin zuwa gabanta saidai da kyat ta iya hade spoon din farko data saka a bakinta tana taunashi kamat maicin magani. Ina mukhatar ya tafi haka koda gidan hjy ne zai tafi atlist zai fada mata cewa zai tafi gaida hjy balle wani wajen . Waya ta dauko dake gefen ta ta danna masa kira ya shiga saidai bai dauka ba har kiran ya katse yana kallo kuma bai dauki kiran nata ba a lokacin. Tsuki taja tare da kai hannu zata dauki spoon din da take cin abincin dake gabanta sai zuciyar ta ya hasko mata ke kodai yana tare da amaryashi ce . What ta fada karda ace mukhatar ya samu kebewa da wanan yarinyar ke nan a yanzu wait ta fada tana kada yatsun hannun ta suka bada sauti. Impossible ta fada tana mikewa tare da daukan wayan nata ta shige part dinta a hasale a nan tabar abincin bata damu da rashin karyawanta ba na ranan. Kira ta sake danna mai wanan katon ma ba,a dauka ba har kira uku bai daga ba abinda ya bata mata rai ke nan zuciyar ta kuma ya kara tabbatar mata da lalai ya samu kebewa da amaryan sa ke nan duk da a gidan ta ya kwana ranan kuma tasani . Me hakan da mukhatar yai mata yake nufi yanzu yana nufin har ya fara juya mata bayane kan yarinyar nan ko me hakan da yai mata yake nufi yanzu ? ZAINAB IDRIS MAKAWA ANA DARA GA , , , , , , , , 1️⃣0️⃣5️⃣BY, , , , , , , , , , , , ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , , , , , , , , BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AL, MANI ,E , , , , , , , , , , ONLINE PAID NOVEL YAR UWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA BA TARE DA HAKKIN KOWA BA DON BIYA KI TURA DARI BIYAR 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK 08036959257 ALLAH SARKI AI RAINA BAYA BACI YANZU DON KIN FITAR DON NASAN AKWAI RANAN HADUWA SEE U 👋 Zubur na mike zaune don tunawa da inda nake kwance a lokacin jin motsin mutum a bayana yasa na juya da sauri shine azaune saman gadon nasa da nake kwance a dakin. Yana zaune ya tasa laptop a gaban shi yana aiki a cikinsa kokarin tashi nayi zaune naji yace lokacin sallah bai karasa ba da saura a nan. Don haka kwanta ki huta kinada sauran lokaci har yanzu na hutu is just past twelve now duk maganan da yakeyi hankalinshi nakan aikin da yakeyi a lokacin bai daina ba. No i want to easy myself na fada a dan kunyace naji yace you can go ga bandaki nan a nan kaina girgiza masa tare da fadin zan tafi wurina in kewaya daga nan na duba fatima. She is OK here so kada ki damu da ita but you can go don naga you are not safe here yadda kika tashi a firgice din nan . Kunyan kaina naji don nagane ya kula da yadda na lalubi jikina bayan na waiga na ganshi zaune yana aikin da sauri nakai hannuna saman jikina najini nade a cikin lafayana dana kwanta har lokacin dashi. Kunyan kaina naji ga fahintar abinda nayi din saidai na basar haka na mike ina gyara jikina kafin na waigo ina fadin nagode na fita zuwa waje. Gidan shiru babu kowa a main falo din da zai sadaka da sauran part din gidan sai karan nauran dake aiki a lokacin gashi kuma an gyara ko ina sai kamshi ke tashi duk illahirin gidan baki daya. Fitana yayi daidai da sake danna mashi kira da hjy falmata tayi a lokacin wanan karon ya dauka kafin ya katse babu sallama sai cewa tayi mukhatar ina ka shigane tun dazun na kira kuma baka dauki wayan ba ? Kai tsaye ya bata amsa da fadin ina gidan amaryane ba tare da jin wani nauyi ko kauce kauce ba ya fada. Ashar ta lalaiyo ta kundumawa gaba dayan mu lokaci guda duk da mamakin hakan ya kamashi amma haka bai hanashi sake dan murmushi ba tare da fadin mun gode ya kashe wayar. Nan kuma wani haushi ya sake kamata lokaci guda ranta taji ya baci ga baki daya idon taya rufe wani bala,in kishi ya danne mata zuciya. Mikewa tayi da tare da figan dan gyalen kayan jikinta da zumar ficewa gidan zuwa gidan da akai mata kwatancen nan ne gidan da nake. Kannenta na ganin yadda ta fito suka tsare ta da tambayan ko lafiya muka ganki haka hankali a tashe zaki fita ba tare da kowan mu ba ? Zanje gidan wanan yar iskan naci masu mutunci don naga tun yanzu suna son raina min hankali ganin irin kallon bamu gane wa kike zance a kaiba da suke mata yasa tace a hasale gidan Amaryan wanan munafukin mukhatar man. Ehyyah anty please kada ki badamu mana tun yanzu mutune su samu abin fadi a kanki jiyan nan fa ta tare a gidan yau kuma ace kinje kina masifa ? Koma meye ai dole ya dawo gidan nan ya sameki babu ruwanki da ita a yanzu don game din ai bai fara ba ko tunda baiko kwana a wirin ta an gani ba amma yanzu da kije an samu abinda ake jira a kanki ke nan ai. Wani kallon hasala ta watsa masu kafin tace dasu a fada mana na isane idan da ban isa ba aiba zasu fada ba tana magana a hasale cikin yaren kanuri. Kwat ba zamu bariki ki fita a yanzu ba karamarsu ta fada daga inda take fitan kina nufin zubar da kiman kine a idon mutane ai basai kinje kin sameshi a can ba dole dai ya dawo gidan nan komai tsiyan su eh,heh. Ranta ne ya kara baci sai kawai ta nemi kujera takai zaune don kafarta bazai iya daukanta ba yadda takeji. Shima brother wani irin zuwa gidan amaryane yanzu da ranan nan haka aina zata saida darene zai tafi can din yau ko ta kalli yan uwan ? Shine ai kawai dai halin maza yake son ya fara nunawa tun yanzu waishi ga mai amarya wanan farin fatan yake rudin shi kome a jikinta mace hakama ba wani fasali gareta. Kallonta yar uwan tayi sai kuma ta kumshe dariyan ta dake cinta kada yayan nasu dake zaune hasale tace bata damu da damuwarta ba ita . Amma da badon hakan ba data bawa yar uwan nata amsa da cewa ki kalli kanki keda kike baka kirin ba fasaline kike zagin wata haka wace duk da a rufe muka ganta alama ya nuna cewa ita din mace ce har mace fuskantane kawai basu gani da kyau ba. Gashi duk wani memo din buki iya hannayen su a hade kawai ake nunuwa babu fuskokinsu a jikin abubuwan da aka raba na bukin. Wanan kuma duk aikon sister ce don bakin sanin da tayiwa hjy falmata din ko a photo zata iya shanmatan mutum karamin aikintane wanan din. Sanin hakan yasa sister tasa komai da aka buga bata yarda anyi amfani da photun muba a ciki amma duk da hakan saida suka gane dalilin sister din. Da kyar dai suka samu ta koma daki bayan sun gama surfa muna zagi ta uwa ta uba cikin ma wai basu da tarihina ke nan amma duk da hakan saida nasha zagi iya inda suka tsaya. Shima a nasa bangaren abinda ya guda ke nan tun farko bai daga wayan ba tunda ina dakin ina barci lokacin yasan zatayi mai fitina sai bai dauki wayan ba don kada injisu. Hakana rai bace ya fito zuwa sallah daga masalacin bai dawo nan ba gidan mahaifiyarshi ya nufa suka gaisa nan take fada mai su gwaggo sin bugo waya sun isa lafiya suna godiya kan karamcin da akai masu . Alhamdullahi ya fada dan jin sun sauka lafiya kafin ya mike yana fadin zai karasa gida tun safe daya fito rakiyan su bai koma gida ba. Har ya bada baya yaji hjyn na fadin kadai san yau a wurin sahibs zaka kwana ko dan ina tsoron halin da falmata ta fito dashi yanzu kan auren nan. Yanzun ma daga gidan ta nake ya fada tare da dan juyowa yana fuskantar mahaifiyar nasa yaci gaba da fadin tundana raka bakin nan airport ban koma gida ba har yanzu shine ta bugo waya tana surfa min zagi waini dan cin amana azzalumi tun yanzu na fara da hakan dukkan mu zatayi maganin mu ai dagani har sahiban . Ka gani ko wanan dalilin yasa banso zuwan falmata wanan sha,anin ba tunda bata kasan nan sai gata kamar an jefota saukin abin ma dai anyi an gama lafiya bata tada wani fitina ba a gaban mutane. Murmushi ya sauke a fuskanshi yace Allah dai ya sauwaka dadin abin ma anty hafsat tana wurin itace ke hanata yin wani abin idan tasoyi. Nima zuwan hafsat din yayi min daidai tunda na ganta sai naji dadi a raina amma bayan ita ai duk sauran irin su daya da falmata din kamar ba Lamice ta haifesu ba. Ni zan karasa yacewa mahaifiyar nasa kada ka biyewa shirmen ta don yanzu an tabata komai zata iyayiwa kowa musanman ma kai da kaimata laifin. Ya kara dan murmushi yana shafo fuskanshi a hakan ya fice daga gidan mahaifiyar nasa tabishi da kallon tausayi don har ya fada ya danyi baki tasan shi shi mutum ne wanda baison yawan hayaniya dama. Suna falo har ita ya shigo tunda ya hangosu ya daure fuskan shi tafiya yake a natse yayin da duk suka bishi da kallo saidai ita madam din ko kallo bai isheta ba. Da kyat dayan kawar nata ta iya budan baki tace dashi sannu da dawowa ya amsa mata ciki ciki yana jin madam Falmata najan uban tsoki yasa kai yayi part din shi. Yana shiga kwanciya yayi a yadda ya shigo dakin takalma kawai ya iya cirewa a lokacin tace ba abinda ke yawo a kunnen shi sai kalman azzalumi data kirashi dashi. Ta ina ya cuceta har tayi mai furcin wanan kalman mai muni haka amma zai nuna mata tayi babban kuskure kan fadin hakan . Shi duk sauran babatunshi bai taba damun shiba a yanzu amma wanan kalman na azzalumi shine ya tsaya mashi a rai yanzu. Yaso ta bashi hadin kai a zauna lafiya a yadda ya fara fahintar sahiba da alama tana da saukin kai tare da biyayya ba kamar yadda ya zata zaisha wahala a kanta ba. Kofan ta turo a fusace yasan itace don ita kadai ta isa ta shigo mai daki a yanzu kuma koda bayab shine don ds farko ta dauko kannen nata su shiga amma ya takawa hakan burki sun daina a yanzu. Ka dawo daga cin amanan naka ai sai ka koma can ka karasa don kwananta ya fara ke nan daga lissafina bazan yarda a kawo min wanan cin amanan ba a ha,inceni kan wata can da bata da asali. Sai lokacin ya dago da mamaki karara a idon shi ya sauke a kanta kafin yace Falmata kada in kara jin kin kira wanan yarinyar da mara asali koda kuwa a gidan karuwai na dauko ta. Ai kinfi kowa sanin tana da asali asalin ma da yafi nakowa tunda ke din shedane da arzikin mahaifinta nz gina nawa a yanzu. Kin sanin kinsan gidan mau me nake dashi kome ke akwai a gidan mu dacan baya lokacin da kika fara guduna don bamu da komai ? Yanzu kan itama din da mamaki ta fara kallon shi kafin tayi karfin halin fadin au ashe don dukiyan mahaifinta ke nan ka aure ta ? Yes of course don shi na aure ta saboda itama din dorne ce tana da kudin ta tana da kaddarori ga ilimi kinga ashe ba don kudi ta aureni ba sai don biyayya ga iyayye. And by the way kalman azzalumin na kada in kara jinshi a bakin ki me na rageki dashi a rayuwa ko me na ha,inci rayuwan ki dashi don kawai na kara aure a yanzu shine zaluncin nawa kome ? Ko nayi maki alkwarin cewa zan zauna dake ke kadaine a rayuwana bazan kara aure ba me kike so a rayuwa da ban maki shiba. Nakai kowa naki makka na gina maku gida na bawa yan uwanki maza har wanda ban taba sani ba jari yau don na kara abinda zuciyana yake so shine zalunci a gareki ? Mukhatar yau ni kakewa gori haka akan yar yarbawan da baka san ko ita din wacece bama tukunna ? Koda bayerabiyace ita haka na ganta ina sonta kuma hakana balle kinga asalinta kin kuma ga yan uwanta kinsan ko waye ita. Wani kallo ta watsa mashi kafin tace ehh lalai mukhatar wata kila harta dandana maka agumon bujenta na yarbawane ko ka haukace haka lokaci guda ? Bata dandana min bako zata dai dandana min sai na karasa haukacewa ga baki daya ki kuma iya bakin ki don ba zan dauki wanan sakarcin da kika soma ba a yanzu. I want piece in my life da kowa kuma kada kiyi kokarin zubar da girman ki da kimarki a idon yarinyar nan don you will regret it later. Duk kan wanan yarinyar kake fada min magana hakaan fada maki haihuwana kikayi da bazan fada maki ba ki fice min daga daki ya isheki hakana ya fada a hasale sake kallon shi tayi taga da gaske yake a yau kafin ta girgiza kai ta juya ta fice daga dakin rai bace itama ta hau sosai a lokacin saidai ganin yau shima ya hau fiye da tsamanin ta, taba kanta salama. Jin karan yadda ta bugo kofan yasa yan uwan nata dake zaune zaman jiran jin yadda zata kaya a tsajanin su Jin yadda ta bugo kofan yayi kara yasa suka kallon kofan da sauri itace ta fito rai bace ko kallon inda suke batayi ba ta wuce zuwa dakinta fuuu a hasale. Binta sukayi da kallo kafin dayan ta daga hannu alaman meya faru sai dayan tace ni data barshi kawai tunda dole itama ai ya kulata. Zakice haka mana tunda kin likewa mai mata kada ai maki hakan ta fada tana hararan yar uwan ta mike zuwa dakin yar nasu suma sauran suka bita. A kwance suka sameta ta kafawa rufin dakin ido tana tunane jin sun shigone yasa ta daga masu hannu alaman su barta kawai a lokacin. Yasa suka juya suka fice a dakin suma zuciyoyinsu babu dadi a lokacin ganin yanayin da yar uwan nasu take ciki na tashin hankali kan kishiyan da aka kara mata yanzu. Suna isa falo babban tace wai meye abin yi yanzu ta tambayi sauran sai ta tsakiyan tace meye kuwa mu meye amfanin mu muje gidan kawai mu latsa shegiya tasan ba wurin zamanta bane nan din. Idan munyi haka fa yana iya shafan mu karshe muma yace zai kore mu kusan halinshi idan ranshi ya baci kodai bamu duke taba muyi mata warning akan antyn mu din zaifi. Ni dai ban goyi bayan hakan ba yanzu da kawai mu bari muji kan zancen kada muje muyi abinda ba daidai ba dama gashi dangin shi kaf sun tsanemu. Nan dai sukai ta shawaran yadda abubuwa ke tafiya a yanzu din tare da sgan alwashin zuwa gidan nawa suyi min warning nan gaba kadan. Bayan na fitone daga part dinshi na shiga daki banga fatima a ciki ba kayan jikina na rage kafin na kewayawa nayi tsarki tare da dauro alwala na fito nafila na fara kafin lokacin sallah na mike na gabatar da sallah farillah din. Kofa aka turo a zato ko shine fatima ce ta shigo tana ganina take fadin au kin shigo har kinyi sallah ashe yanzun nan fa nake fadin Allah yasa kunga time din sallah yayi ai. Barci nayi wallahi tun dazun na sani shiyasa na fara aiki a kitchen kafin ki fito aikin me ke nan na tambaye ta aikin abinci mana ba,a nan yau uncle zaici abincin dare ba ? Cikin ya mutse fuska ina mikewa nake fadin me i don now woo, i no sebi dis kind of wahala, may be na here he go eat ? Murmushi ta sake a fuskanta tana fadin nan ne mana tunda dama saboda bakine bai zauna nan tun jiya ba ai yanzun ko bakin sun tafi sai ku fara amarci ke nan tana dariya. Kyale ta nayi naci gaba da nade hijjabin sallah danayi take fadin tun safe fa bakici komai ba nace banajin cin ina kokarin dauko wayana a cikin jakka da tun da zamu fita na saka a ciki ban kara bi ta kanshi ba sai lokacin. Ina bude wayan misscall nagani ratata a wayan sunayen masu kiran nawa wanda kusan su gwaggone da suka isa gida suke kirana lokacin. Nan na fara kiran su ina masu ban gajiya tare da godiya suma suna dan kara min da nasiha ha zuwa lokacin da Fatima ta idar da sallah zata fita na kirata da hannu lokacin muna waya da umma. Tazo tambayanta nayi me take dafawane tace wai tuwo tayi da miyar taushe don taga darene za a fi son shi kai na gyada mata har ta juya zata tafi sai kuma ta juyo tana fadin . A kwai wata mace da tazo tun dazun tace hjyn su uncle ce ta turo wai ta kama maki aiki muna kitchen din tare da ita tun dazun na gyada kai. Mikewa nayi nabi bayan ta da wayan a kunne na muka karasa kitchen din dake da dan nisa da part din a nan na samu matar itama ta idar da sallah tana nade dankwalinta data shimfida. Tun kan mu gaisa da ita nace haba haba dai badai a nan kikai sallah ba ga falo can ga kuma dakuna a ko ina a gidan . Matar tana dan murmushi ba wata babba bace sosai take fadin nan ma yayi min ai ba laifi ai wurin tana kara kallon wurin kafin tace da Fatima din itace matar gidan ko ? Eh itace sai gata tana rusunnawa kasa ta fara gaidani da fadin ina wuni hjy da sauri nace da ita no kada ki sake daga haka na fara bude wasu kuloli masu kyau dana gani an rufe. Tuwone da aka mulmula a cikin farar leda sai nason zufan zafi yakeji gashi ya tuku da kyau gwanin ban sha,awa sun kai leda biyar a ciki. Sai kuma dayan da aka saka miyar da sukayi tayi kyau sosai kallon sukeyi duka suji me zaice sai ji sukayi ina fadin masha Allah yayi kyau sosai. Ga drikin nan da ferfesu munayi ta fada nace duk yaushe za a cishi din yau din nan ? Kusan tare dani suka karrasa girkin muka fito don la,asar yayi a dakin fafima dakin dasu gwaggo suka zauna ne a nan muke har me aikin sai bayan magariba ne naji waya na kira na dauko shine a layin yake fadin. Kuna lafiya ko lafiya naba da amsa yace ok da fatan an girka min abinci don nan zan kwana yau insha Allah. The food is ready na fada yace ok ganin tafe idan na fito wurin hjy da sauri naga fatima ta mike bayan na kashe waya tana fadin. Na tashi na kimsa kada ya sameni hakanan kallon mamaki nake mata sai naga ta dan marairaice tare da fadin wallahi haka akeyi koda zai shigo saiya yasameki a cikin kwaliya zaifi. Wanan mai aikin ne tazo min sallama wai zata koma gidan hjy don a can kayanta yake mukai sallama da ita nayi mata godiya ta tafi. A nan don dole na tashi din na shiga wanka ban jima ba na fito na samu fatima har ta fitar min da wasu kayan sakawa wani material ne mekyau yana dan kyalkyali an mashi dinki bubu . Tsab na shirya a cikin shi fatima tana gyara min sai mamakin yadda akayi tasan irin wanan abubuwa ina mamakin yaran hausa da komai a yanzu sun sani sai gani na fito tsab dani da gani dai kasan amaryace ni din. ZAINAB IDRIS MAKAWA ANA DARA GA , , , , , , , , 1️⃣0️⃣6️⃣BY, , , , , , , , , , , , ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , , , , , , , , BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AD,DARR , , , , , , , , , , , ONLINE PAID NOVEL YAR UWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA BA TARE DA HAKKIN KOWA BA DON BIYA KI TURA DARI BIYAR 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK 08036959257 ALLAH SARKI AI RAINA BAYA BACI YANZU DON KIN FITAR DON NASAN AKWAI RANAN HADUWA SEE U 👋 Ko ina na dakin tsab yake ba dakin ba har gidan duk Fatima tabishi ta gyara ta saka kamshi tare da taimakon wanan matar da hjy ta turo ta taimaka min . Don haka gidan ya kara haske ga nutsuwa ba wani hayani saina kiran da fatima ta kunna dake fitowa daga dakina a hankali, yana kuma karama mai sauraron shi natsuwa. Don duk dakin muyi shiru muna bin karantun a lokacin ciki ciki yayi sallama daga kofan tare da dan jira mu amsa mai don yasan ba ni kadai bane a dakin balle ya shigo ciki kai tsaye. Kamar sallama ko anty haka yasa na dago kai daga kallon wayan da nakeyi lokacin ina mai kallon kofan nima. Wanan karon nokin yayi don yana zaton bamuji sallaman nasa bane haka yai daidai da budan kofan da fatima tayi da sauri taja baya tana mashi sannu da zuwa. A cikin fara,a ya amsa yana fadin a a badai tsoro yasa kuka shige daki ba a wanan lokacin dare baiyi ba is just past nine yanzu fa ? Tana murmushi daga inda take tsaye take fadin muna dai hirane a nan shiko duk maganan da yakeyi a lokacin hankalinshi yana a kaina. Ya karaso ciki yana fadin idan zaku shige ku dinga saka key daga ciki saboda tsaro duk da akwai masu gadi dags wajen gidan amma hakan is not safe gaskiya. Da hausan shi yake maganan da fatima kafin daga inda nake zaune bakin gadon nake fadin nothing will happen koda masu gadin ma basu ai a cikin hausana dana iya. Kallo Fatima yayi a inda ya barta sai yaga har ta fita dakin ko alokacin yaci gaba da fadi cikin mamaki so you are hering the languege abi ? Not long na bashi amsa ya karaso har inda nake zaune yakai saman gadon kusa dani har jikin mu na iya guganna juna sosai a lokacin yake fadin. How far my Lady kada kiyi fushi dani please aikine da wasu baki suka zo min dashi ya hanani zuwa nan in time kiyi hakkuri da hakan don Allah. Haba haba don't say that to me again ko ba baki ai akwai iyali dole ka gana dasu and beside you are my elder you have the right to do whatever you like a rayuwanka bani da matsalan haka sam na fada a cikin ladabi da iyakar gaskiyana a fuskana. Murmushi yayi tare da kai hannunshi sama hannuna yana fadin nagode da kika zamo mai fahintar hakan amma yana da kyau na tsare maki hakkin ki koba haka bane? Ya tambaya yana kokarin son mu hada ido dashi sai dai sam ba zan iya hakan ba a lokacin don ni din jinin hausa fulanice ko yayane akwai wanan kunyat a jinina na addini dana al,ada. Dukar da kai nayi don na gane me yake nufi sai naji yayi murmushi tare da fadin anyway anything to eat ko sai an fita an sayo aci ? No mun riga mun yi girki for the first tima bayan hakan banda ra,ayin cin girki waje ga rayuwana nafi ganewa na girka muci. Masha Allah Alhamdullahi sahiba akwaiki da abubuwan mamaki na rayuwa ga wanda bai sanda hakan ba zai dauka ba abindata sani game da rayuwan duniya don tashin da sukayi a cikin bariki. Farko abindaya tuna shine yadda ya bar gidanshi a cikin tashin hankali da fitina kan zaizo gidan sahiba din ya kwana. Gashi yadda ita sahiban ta nuna mashi ba komai zai iya kasancewa da iyalin shi ba damuwanta bane hakan, shin wanan maganan nata gaskiyane akwai matar da zata yarda da wanan a tsakanin ta da kishiyarta ko ? Ko dai hakan na nuna cewa wanan yarinyar har cikin ranta har yanzu bata aminta da aurenshi da ita bane ga kuma zancen abinci da yanzu ta fada. Haka ya nuna cewa kuma tana shirye da ladabi akan auren su ko zama dashi ke nan donga Falmata haka kawai zata kwashi iska afima shekara sai abincin fizza da sauran ire iren su zata dinga sa akawo suci duk da tasan baida bukatan hakan a rayuwan shi . Shi mutum ne da yafi bukatan irin abincin mu na gida da al,ada ya koyar damu cin shi don hakane idan yana Nageria koda tare da iyalinshi yazo ya kwanmace da yaje gun mahaifiyarshi yaci abinci a can . Kokarin mikewa nayi tsaye sai naji ya mayar dani na zauna muna fuskantar juna dashi da sauri na mayar da kaina a kasa don kallon da yake min yasa gabana faduwa lokaci guda. Kin gaji da yawa ina zaki yanzu ya fada kamar me rada yana kokarin mayar da bayana saman katifa dan rutse idanuwana nayi kafin nayi karfin halin fadin zan tafi falone na hada abinci don naga kamar a bukace kake dashi yanzu. Murmushi yayi irin na manya kafin yace ban fada maki hakan ba don ina son kasancewa dake ne kawai a yanzu naji dumin jikin ki na saurari muryan nan naki a kunnuwana. Jin wanan yasa na dan saki murmushin iya baki na lumshe idanuna kawai don ni nauyin shi da kwarjinshi yanzu nake ji musanman ma ida yana agaban nawa haka ? Balle yanzu da yazo min da wani abinda nake hangowa a tsakiyan kwayar idanun shi lokaci guda tun bayan shigowan shi daki. Ji nayi yayi min rumfa da kirjinshi lokaci guda tare da kokarin kai bakinshi a cikin nawa da sauri na kawar da kaina gefe da sauri ? Dan bina yayi da kallo kafin naji sautin ajiyan zuciyan shi yana mikewa zaune daga yadda yake din kada Fatima ta shigo ta samemu a haka ko ? Tana da hankali sosai ba zata shigo nan ba yanzu tunda kana ciki na fada tare da mikewa tsaye ga baki daya bin jikina yayi da kallo don rigan yayi matukar matseni ya fitar min da duk suran jikina a baiyane. Kusan duk haka dinkuna na suke don haka ni ban dauki wanan a komai ba a wurina shiko wani iri yaji lokaci guda yana dan lumshe idanun shi. A tare muka fito zuwa falon yana rike da hannu na muka tako a cikin natsuwa fatima tana tsaye a gaban dinning din ta kara gyara ko ina ga candles ta kunna a tsakiya da akai decoretion dinshi a jikin wasu glass an kawata wurin sai gwanin ban sha,awa. Tun daga nisa ya fara fadin a, a Fatima wanan aikin bai maki yaba ke kadai haja keyinsa tana dan dariya naji tace a, a wallahi bani nayi karasawa nayi kawai anty Sahibace tayi komai tunda da kanta. Da sauri ya kallo inda nake wai yana mamaki kamar karamin yaro yace kune duk da wanan aikin haka gaskiya ku daina aiki haka yana kallon inda nake daga gefen shi. Dan murmushin yake na sake haka yaja hannuna zuwa bakin table din muka kai zaune ya nunawa Fatima kujera ta zauna sai cewa tayi a, a zanci a daki alaman nauyi da kunya. Shima murmushi yayi tare da fadin au na tuna fulanine ku ai kunya ko zaki daina idan kina gidan nan ki zauna muci matata ta ciyar dake irin abincin da baki taba ci ba. Da alama dai shi mutum ne mai son barkwancin da raha sosai ashe kada ka yankewa mutum hukunci a lokacin daka fara ganin shi sai ka gama nazarin shi zaka gane hakan amma ganin farko na dauka ko magana aikine a gareshi. Bayan mun zauna jin abinda ya fada yasa na mike na fara zuba masu abincin na zata irinane shi saina zuba kadan ina kokarin juyawa yake fadin. Har kin zuba min ke nan kome na kalli abincin dana zuba din yake fadin kara min nikan aini da tuwo muna gaisuwan mutunci sosai dashi. Dauko wani ledan nayi na bude na zuba a plate din na gyara cup din ruwan dake gefen shi da plate din miyan ina dan tusunawa nace bissimillah. Nagode ya fada na juya na zubawa Fatima itama kafin na dauki plate na dauko leda daya na rabashi biyu saidai daya yafi daya yawa sosai na saka karamin a plate. Sai duk suka bini da kallo lokaci daya kowa na kallon abinda na zuba meye wanan din ya tambaya yana kallon abincin da nake kokarin zama inci din gaz kuma cibi na dora a sama. Samun wuri nayi nakai zaune wanan ma ai yayi mata yawa indai anty Sahibace sam bata cin abinci haka kamar kowa . No ki dinga cin abinci zaifi yanzu ba daya bane da wancan lokacin ko kina son yan kaduna su Fatima su raina da kiwona ne ? So ki daure ki koyi cin abinci please ya fada yana jawo plete dinshi zuwa gaban shi da kyau kafin ya fara da bissimillah. Zance ruwan miya nasha da dan naman dana zuba abinci kan cibi biyu kawai nayi na ture sai wayana na jawo dake gabana na fara dubawa. A hankali ya dago kai ya dubeni kafin ya juya ya kalli fatima data soke kai tana murmushi a kasa kasa don ganin draman da mukeyi dama tasan ba zanci komai ba ita. Ankai kamar minti biyar sai tura loma yake yana kurba ruwa lokaci lokaci muryan shine ya dawo dani daga sakon faiza da nake karantawa a lokacin. Badai kinci abincin ba ke nan ya fada kai na dago ina dan bata rai nace naci ya isheni haka tsam ta mike tare da fadin uncle saida safe. Ya dan bita da kallo kafin ya juyo gareni yana fadin idan baki saba da wanan abincin bane aida saiki girka wanda zaki iya ci koma meye ni zan koyi cinsa. Amma ba zan barki ki dinga zama da yunwa haka na kallon shi nayi cikin ladabi nake fadin wallahi i am OK with diis haka nake cin abinci ko a gidama. A hakan shine ci ya sake tambayana yana kallon plate din dake gabana a lokacin sorry sir iam OK! Lumshe ido yayi yaci gaba da cin abincin shi hankali kwance yana ci yana dan kurba ruwan dake gefen shi a hankali. Sai mamakin yadda yake cin abinci haka nakeyi a zuciyana kafin ya kusa gamawa ya dago kai tare da fadin. Zanyi kwana hudu tare dake a nan kafin na juya zuwa London yin wani aiki zan kwana biyu a can naso in tafi dake saidai hakan ba zai samu ba . Don mahaifiyata ta riga ta shedawa kowa zaki dan zauna a nan kwana biyu kafin nazo mu wuce Hong Kong a can zaki zauna don can business dina ke tashi yanzu nafi zama a Hong ko Dubai. Saiki zabi inda zaki zauna daga cikin biyun ya fada yana kallona tare da sakale loman daya diba a hannun shi. Inda hankalinka yafi kwanciya dana zauna duk dayane a gareni koda a nan din ne ma banda matsala ga hakan na fada a hankali ina sada kaina kasa lokaci guda. Hong din yafi don a can nafi zama sosai beside dubai din falmata da yara suna yawan zuwa hutu a can lokaci lokaci kuma gidan gudane. Naso nace dubai din amma kada na nuna kalana a fili sai nace is OK ba matsala kawai na mayar da hankali ga wayana. Hannu ya tsame a ruwan daya wankesu daidai lokacin naji muryan shi yana fadin will you be my guest at dis night ? Maganan yazo min a bazata har yakai ga haifar min da wani ciwon kai lokaci guda amma haka na dake bandai bashi amsa ba sai dan yaken danayi kawai a fuskana. Wayan shi yai kara ya dauka sai naga ya share kallon wayan da yaga na dan kalleshi sai ya dauki wayan tare da mikewa yana fadin hello ya dago min hannu alaman yana zuwa ya tafi . Dan binshi nayi da kallo kafin na mike na fara hada kayan don babu mai aiki nima kuma ban dauki hakan aiki ba na tsaya na gyara wurin saida ziciyana yana tune da zancen daya furta min dan mintina da suka wuce. Saidai duk abinda nake ina jin wani irin kullewan da marana yayi lokaci guda kamar dutse ya danne min maran abinda ban taba jiba a rayuwana. Haka na daure na kawar da komai a dadafe nakai dakina ina jin kamaf abu zai fito min a gabana lokaci guda. Haka na samu na isa bandakin don na kewaya ina tsugunnawa wani jini ya zubo min mai yawa kamar saren nono ya fado min da karfi saida na zabura dan tsoro. Da kyat na samu na dawo dakin na fada samsn gado ina faman nishin wahala da haka na lalubo wayana na kira fatima saidai tana busy a lokacin . Bandade da aje wayan ba sai gata a dakin daidai lokacin ins dunkule abin tausayi dani ina wani gurjin nishi mai nuna wahala ga mutum. Da sauri take fadin innalillahi meya faru anty sahiba da kyat na iya daga kai na nuna mata kasan marana dake min ciwon bala,i a lokacin guda haka. Shiga toilets kigani na iya fada da sauri ta fada toilet din dan ihunta naji lokaci guda ta fito tana fadin anty meye hakan tana tambayana. Ban sani ba na fada da kyar harfa motsi yakeyi nake gani ta fada a dan tsorace tare da kallon kofan toilet din a firgice. Uncle yasan da baki da lafiya ta tambayeni tare da tsureni da ido na kasa kai alaman a,a akirashi ke nan gaskiya wanan ba abin wasa bane. Da sauri na daga mata hannu alaman a,a ta barshi kawai, can wani tunane yazo min da hannu na nuna mata ta dauko min jakkana a cikin wardobe da sauri ta juya ta dauko. Na lalubi abinda nake nema na gani haka na daure ba mike zuwa toilet din har lokacin abin na nan yana motsi kamar abu mai rai. Na dade tsaye ina kallon abin kafin na fidda kwalban turarena na shaka a hancina nasan matsala don haka na daure nayi duk abinda ya dace inyi a lokacin sai lokacin abin mai kamar tsokan nama ko anta ya fara narkewa a hankali ya koma jini duk ina tsaye ina kallo. Ina jin muryan Fatima daga dakin tana kiran sunana anty ko in shigone nace gani fitowa yanzu haka na fito daga bayin bayan na wanke wurin na gyara jikina zakace kona haihune ina wani irin zufa na samu wuri na kwanta tun tana min sanni ina karbawa sai barci ya daukeni ban sani ba mai nauyi. Har ya gama abinda yakeyi baiga na leko ba sai yaga rashin dacewan hakan don shi ya kamata ya biyoni for the first time ai haka yasa ya taso daga dakin zuwa nawa part din. Yana sallama Fatima ta amsa mai idon shi a kaina yadda nake kwance din da sauri yake tambayan ta ko lafiya nan ta kwashe abindata sani ta fada mai. Hankalin shine ya tashi sosai yake fadin shine baku kirani ba bari muje asibiti kawai fatima din tace ta hana in fadamane kuma sai ina ganin ba na zuwa asibiti bane . Ana ciwon da bana asibiti ba fatima kada yazo ya zama mata matsala fa nan gaba bari kawai muje asibiti a tayar da ita lokacin nayi wani irin mika a cikin barcin har suna iya jin yadda kassan jikina ke wani kara lokaci guda . Dole haka suka kwana dani ina wanan mikan sai zuwa asuba komai ya lafa na koma barcina norman kamar bani ba hankalinshi yayi matukar tashi sosai har fatima din. Washe gari ban tashi da wuri ba sai wajajen takwas da rabi na safe na falka ina tashi ba wanan duduken a tafiya na koma normal dani kamar bani bace haka ya faru dani ba. Shima barci yayi don barcin dabai samu ba suna tare dani a halinda nake ciki da daren sai karfe daya yaje gidan nasa. Hira ya samu sunayi kamar ba ita ba ta sake sosai da kannenta da wata bakuwa kana kallonta kasan matar yar duniyace ta gaske. Haka ya wucesu suna gaidashi da kwana ya amsa ya shige yana jin dariyar Falmata din kamaf da gayya tana fadin saike hjyta ina yinki sosai hjyn kare kukanki. Dan ja yayi ya tsaya kafin ya daga kafa ya shige dakinshi duk zuciyar shi babu dadi a yadda yake ji suna jin rufo kofan shi. Take fadin wasa kake da Falmata wallahi baka sanni bane a yanzu mukhatar mu zuba dani daku aga karshen wasan . ZAINAB IDRIS MAKAWA ANA DARA GA , , , , , , , , 1️⃣0️⃣7️⃣BY, , , , , , , , , , , , ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , , , , , , , , BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AN NAFI,E , , , , , , , , , , , ONLINE PAID NOVEL YAR UWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA BA TARE DA HAKKIN KOWA BA DON BIYA KI TURA DARI BIYAR 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK 08036959257 ALLAH SARKI AI RAINA BAYA BACI YANZU DON KIN FITAR DON NASAN AKWAI RANAN HADUWA SEE U 👋 Barci nayi sosai a ranan tun abin safe sai bayan karfe biyun rana dana tashi don saboda yin sallah a lokacin sauka nayi daga kan gadon zuwa bandaki na kewa da niyar na watsa dan ruwa a jikina kawai na fito. Tunda nasan bana sallah don irin jin dana zubar a daren jiya din daga jikina wanda haka na kwana yana zuba min duk da nasan ba lokacin period dina bane a lokacin. Saidai me gani nayi kamar da daids duniya bani bace nayi wanan jinin haka a daren na jiya din don babushi ba alaman shi sam. Sanan kuma babu wanan ciwon mara din daya hanani shakat a daren don ji nake tankar marana zai ballene lokacin don ciwon da yakeyi din. Amma yanzu sam babu shi babu alaman shi a gareni tankar a duniya banice a daren jiyan face face a cikin jini ba. Dole haka na daure cike da mamaki nayi wanka a dadafe zuciyana cike da mamakin ganin hakan a gareni din. Sallah fatima ta shigo ta samu ina yi taja tayi turus a cikin mamaki tana kallona har zuwa idarwana data kasa hakkuri tace yaya akai hakane anty tana kallona. Dan murmushin yake na sake a fuskana kafin nace mata nima dai hakan na gani yanzu nake mamaki don ba alaman wanan matsalan a tare dani kuma yanzu ya dauke kamar banyi ba. Zaune takai a cikin mamaki tana kallona kafinta nisa tana fadin na kawo maki abinci a nan ne kici ? Don uncle tunda ya fita dazun har yanzu bai shigo ba shima abincin dai is ready nasan zaku so don fried rice ne with Chick meat muka hada. Ke dawa na dago na tambaye ta ina kallon fuskanta tace wanan matar ta jiyace ta dawo yau ma tare mukayi aikin da ita yauma. Fuska na bata lokaci guda don jin hakan data fada don ni sam yanzu ban yarda da kowa ba a wanan garin kuma haka zuciyana ya fara nuna min. Wani abune ga hakan anty ta tambayeni tana kallon fuskana cikin sonta san komeye ya bata min rai a lokacin. Nace a dan kasalance no ba komai zan fito na bata amsa ta mike ta fita a take zuciyana ya fara kawo min wani tuhuma nayi saurin kawar da zancen a raina lokaci guda. Na dan jima ban fito daga dakin ba saida nayi sallah la,asar nafito a falo fatimace zaune ita kadai tana kallo lokacin dana fito din. Da sauri ta dan yunkura tare da dagowa daga kwancen tana fadin kin fito anty nace ehh fatika sannu da hutawa dan dariya tayi kafin tace ga abinci can a dinning table an gama zanci amma ba yanzu ba na fada. Hira mukayi sosai lokacin da ita wanda hiran ya shafi hiran gidan sune da yadda suke zama dasu anty Nabila sai banji dadin yadda take ban labarin ba a lokacin. A takaice dai na fahinci cewa akwai wanan akidar ta zama dan uba a tsakanin su wai me wanan halin yake nufi na yan uba ? Shine fa ya jawowa Abban mu rasa rai har saida yan uba sukaga sun rabashi da duniya ga baki daya saboda wani dalilin shirme nasu can akan dan uwa. Shin a ko wani kabila akwai wanan halin yan ubancin ne da ake samu a yawancin gidaje ko dai sai a fulanin mu kawai ? Dole in bincika in gano idan wanan halin a ko wani kabila akwaishi har ko idan hakane kowani kabila har haka suke to lalai kuwa ina da aiki a gaba kan irin mutanen dana shigo cikin su yanzu. Gabana ne ya fadi sosai lokaci guda don tunawa da nayi da wani abu, lokacin daya wanda ya shafi rayuwata dana yan uwana. Mikewa nayi zubur zuwa kitchen yayin da fatima tani da kallo kitchen din naje na samu matar tana aikinta tukuru kamar yadda ko wace mai aiki takeyi a gidan aikinta. Na dan dade tsaye a bayan ta ina nazarin ta alaman motsin mutum taji a bayanta yasa ta juyo da sauri lokaci guda. Dan razana tayi kafin ta kakaro murmushi a fuskanta tana gaidani na amsa saboda kusan itama naji ba hausane sosai a bakinta ba lokacin. Juyawa nayi na koma falon don ban samu abinda nake nema a wurinta ba lokacin fatima ta fara fadin lafiya dai anty ? Lafiya na dai mike kafatane da yai min nauyi a yanzu sai naga tayi murmushi tana fadin aida kina iyawa sai mu fita waje zuwa garden don a kwai garden babba a wajen gidan nan. Ba matsala muje mana na bata amsa ta mike tsaye muka fice tana min jagora ita data san kan gidan a lokacin. Wurin yana da kyau sosai da tsari ga kujerun roba masu kyau gefe gefen na wajen a jiye muka dan fara zagawa muna hiran yanayin wurin dana gane da kuma yanayin weather din garin. Shine muka hango a tsaye daga kofan baya ta inda muka fito din ya tsaya yana kallon mu a cikin mamaki kafin ya fara takowa a cikin mamakin ganin yanayina a lokacin. Muma juyowa mukayi muka nufi inda yake sai muka hade dashi har lokacin ya na a cikin mamakin ganin yanayi na ban mamaki don fuskanshi yanuna hakan kafin ya fara fadin. Sahiba kinji saukine har kin samu fitowa waje ina can ina tunanen irin halin yanayin dana barki a ciki kafin in fita. Anty kan taji sauki ai uncle don har sallah tayi dazun don nima abin mamaki ya bani wallahi ni har tsoro ta bani wanan abin haka da ban mamaki yake kamar ba ita bace jiya gwanin ban tausayi muka kwana da ita ba. Sallah ya fada a cikin mamaki tare da kallona yana fadin how about the blood ya daina zuwane kuma ko a yanzu ko me ya kara dan kura min ido a cikin mamaki. Ya daina ne ai tunda har tayi sallah fatima na magana kamar wata babban mace da tasan ta kan duniya din nan kamar zaiyi magana sai kuma ya koma fadin. Muna can munje wani waje amma hankalina yana nan tun dazun ashe Alhamdullahi sauki ya samu masha Allah. Dan sunkuyawa nayi irin yadda yarbawan zamani keba na gaba dasu girma a yanzu cikin stly ina fadin you're welcome . Thank you ya fada a sanyayye yana mai dan sake fuska da nuna wani yanayi har lokacin a fuskanshi dana kasa ganewa. Uncle Bataci abinci ba tana jiran ka tun dazun nayi mata tayin abinci tace ba yanzu ba nasan kai take jira ka dawo kuci tare fatima ta fada a cikin zolaya ya kallo inda nakw da wani mamaki a fuskanshi ya kalloni a inda nake tsaye yana fadin. Ba kici abinci ba kina jirana madam ya fada cikin mamaki tare da kara karasowa gab da inda ni nake tsaye cikin mutuwan jiki? Har lokacin idon shi na kaina ya sake fadin keda kika kwana baki da lafiya haka don kawai naga kin samu barcine sosai da safe yasa bamu tafi asibiti dake ba a yau. Yanzun ma na dawone naga yanayin ki idan zamu tafi mu samu wani likita a nan ya duba min ke da wanan niyar na dawo yanzu don naji tsoron yanayin dana ganki ciki jiya din. Na samu lafiya na bashi amsa ina dukar da kaina kasa don haka basai mun tafi asibiti ba nagode daga haka na juya na nufi cikin gidan na barsu tsaye suna min kallon mamaki a wurin. Nima naji tsoro kwarai amma kuma sai naga ita bata damu ba wata kila dai mutanen tane sukazo mata da wanan yanayin haka. Don gashi kamar ba abinda ya faru da ita yanayinta ya nuna fatima ta fadi hakan tana kallon shi bai furta komai ba sai kai daya girgiza kawai yabi bayana itama ta shigo zuwa falon gidan. Bai fita ba saida akai magariba ya tafi samujn jam,i a cikin jama,a muma sallah mukayi normal kuma nake har lokacin bayan ya dawone daga sallah muka zauna mukaci abincin dare tare. A wanan lokacin ne mai aikin nan tace zata tafi gida alheri nayi mata tare da umartan ta tafi da sauran abinci abawa mubukata kada ya kwana ya lalace a nan din. Tayi godiya ta tafi sai bayan fitan ta yake fadin a ina muka samo wanan matarne nace hjy ce ta turo muna ita ai. Dan shiru yayi kamar me nazari kafin yace well tunda hjyce a barta amma ni nafi son a samu namiji da zaifi koda a bangarekune . No banda ra,ayin me aiki sam a rayuwana don wanan din ma banga matsala a wurinta bane kuma tana da tsabata da kula yadda ya kamata. Don bakin mu da baifi na mutum goma zan iya girka muna abinci ai a kullun na fada sai ya kalloni da sauri yace No ba zakiyi girki ba sam wanan din ma da kikayi a yanzu na barkine don in dandana hannun ki naji kalar girki a yanzu ai . Meye amfanin dukiyana iyalina basu huta ba koda yaushe nafi son naga iyalina suna hutu suna jin dadi nima na zo garesu na sauke gajiyana a wurin su ya karasa yana min murmushi a fuskanshi. Sam ban fahinci me maganan shi ke nufi ba don haka ban dauketa da wani muhinmanci ba shima din kuma ya gane hakan gareni sai ya share zancen bai fita mun dan taba hira. Daya shafi mahaifina yadda suka hadu dashi har ya zama yaron shi saidai hiran bai kai ko ina ba don dan kukan dana fara a cikin kunan rai da jin daci a zuciya. Haka yasa shima jikin shi yai sanyi bai iya karasa min labarin ba ya barni sai kuma ya dauki waya daga wata kasa yana amsawa shine ya tayar damu a wurin na mike zuwa dakina. Lafiya kalau na kwana a ranan shima ganin banda lafiya yasa bai nemini ba ya share yadai leko dakin ina barci haka yasa ya gane ni kadai ke kwana a dakin ba tare da fatima ba. Washe gari bayan mun karya yake fadin karfe hudu in shirya zamu tafi gidan hjyn shi tare da hjy falmata dukkan mu ukun zamu hadu a can. Sam banji komai ba a raina sai cewa kawai nayi Allah ya kaimu ya fita don ana jiran shi a waje nagane dai koda yaushe shi busy yake da mutane da aiyukan shi dama na saba da ganin irin hakan tun wurin oga Shaaban . Ranan kuma nayini yin baki suna shigowa ganin amarya don haka ban wani zauna a daki ba lokacin saidai masu zuwa idan sun fita zasu fara fadin ance bayerabiyace amaryan gashi bamuga zubin yarbawa gareta ba ai. Akan lokaci nayi sallah na shirya har fatima don yayi min waya mu hadu a can din driver yana nan ko yaushe a gidan idan muna da bukatan hakan. Hudu daidai ba saba lokaci muka dauki hanyar gidan hjy har me aikin nan nawa da yanzu mun dan fara sabawa da ita. Gaba daya yaranta da yan uwanta suna gidan lokacin hakan yasa na gane abu mai muhinmancine ya kawomu gidan ke nan wanan zuwan. Mun shiga an kuma taremu a cikin mutunci tare da jagoran sister muka isa falon hjy suna zaune su hudune a falon har kasa nakai na gaidasu suka amsa muna gaisuwan a cikin mutunci. Kafin na samu wuri nan kasan na zauna da sauri suke fadin haba sahiba a kasa ga kujera dai kya zauna kasa kuma no nan din yayi Mah, na fada. Baifi minti biyar da zaman mu ba muna nan zaune cikin ladabi sai gashi ya iso nan naga irin so da kaunan da yan uwa ke nuna mashi sisters din shine su hudu suka sakashi tsakiya sai shagwaba suke zuba mashi. Haka harya zauna suma iyayyen kamar zasu lasheshi kowa dai mukhatar kaina na sade kasa shima idon shi a kaina yake duk hiran da suke da babban yarsu lokacin. Dan dago kai nayi na gaidashi fatima ma hakan ya amsa a cikin sakin fuska da jin dadi tare da tambayan mu ba matsala ko kai na dan girgiza mai alaman ba komai a lokacin. Sukaci gaba da magana da yan uwanshi wanda mu bamu san me suke fadi ba din ba yaren da muka iya sukeyi ba su can ya dan ja tsuki tare da fadi yana kai fuskan a kan Duban agogo yayi yaja tsuki tare da fadi a cikin yare ita falmata me take jirane bata karaso ba kuma na fada mata yanzuma da zan taho. Sai wajan kamar minti goma sha biyarne sai gata ta iso a cikin kasaita da isa da takama da izza suka shigo falon da yan uwanta dake mara mata baya. Kowa dake falon ya bita da kallo waya takeyi a cikin isa da takama ta kai zaune ba tare da gaisawa da kowa na falon ba, suma yan uwan suka zauna saman sauran kujerun suna gaidasu hjyn a cikin isa. Kaina nadan dago na kallesu kafin na sada kan nawa yadda nake zaune ta gama wayan ta dago tare da fadin gani yare ya fara yi wanda dagani har fatima bama jin me yake fadamata lokacin . Amma kana gani kasan fada yake mata itama amsa ta bashi tare da kallonsu ta gaidasu a cikin yare zaka fahinci akan gaisuwa ne wanan maganan idan kana da hankali yadda abin ya faru lokacin. Fatima ki fita ki jiramu a wurin sister na fada ta amsa da to da sauri ta mike zuwa waje din kowa ya gane me haka ke nufi a cikin turanci na fada. Falon yayi shiru na dan lokaci kafin ya kalli yan uwan nata yace dasu su bamu wuri zamuyi magana fuskan shi a daure. Kamar ba zasu tashi ba don sai wanan ta kalli wanan wacan ta wani ya mutsa fuska tana kawar da kai gefe daya sai karamar ta fara mikewa ta fita. Idona ya tsaya akansu duk abinda sukeyi ina kallonsu lokacin kafin su mike don kallon da yar uwan nasu taimasu suka mike da sauri suka fita ko a nan ma na samu wani hit daga garesu ke nan . Boyayyen ajiyan zuciya na dan sauke tare da dukarda kaina kasa a daidai lokacin muryan hjy mama ya ga hjyn su uncle take sallama ga kowa na falon. Aka amsa mata taci gaba da fadin mun taru a nan ne don murna da samun karuwa yar uwa a cikin kuma abokiyar zama tare da yin nasiha ga juna son a zauna lafiya a taru a rufawa juna asiri tare dayin zama na amana da juna. Excuse me ta fada tana mikewa da waya a hannunta da alama wai wayan zata karba da sauri ya dakatar da ita da fadin koma ki zauna. Wani irin kallo ta watsa mashi kafin tace zan karbi wayane a ban yan mintuna indawo shima a hasale yake fadin a magana kike fadin zaki karbi waya yanzu? Wanan ai abune da muka sani gabaki dayan mu ba tashigo cikin muba a yanzu zata iyane yasa ta shigo don haka meye na wani zaunar damu a nan kan wanan maganan da mama ta fada. Kowa nan yasan me ake nufi da zaman aure ai don haka ita ai ba yarinya bace idan tazo da zaman lafiya matsalan tane udan kuma tazo da wani manufa duk a daidai muke so ni ina da abubuwa a gabana yanzu . Wanan ba zai zaunar dani nan ba muna batawa juna lokaci tashigo gidan ka fine shike nan mu zuba kawai a kan ka nida ita . OK haka kikace tace na fada saita juya wurin yan tsofin tana fadin mama kuyi hakkuri ni zan tafi wanan ba maganan da zaku zaunar damu nan bane yanzu. Tunda baku iya zaunar dani ba kafin ayi auren ku fada min zai kara aure kuji ra,ayina ba yanzu da komai ya faruwa ba ace za a zaunar damu tare ai muna wani nasiha. Zaiyi magana kanwar maman shi ta daga mashi hannu tare da fadin barta ta tafi Allah ya bada hakkurin zama ke sahiba ki zauna lafiya da mijin ki jeki Allah yayi maki albarka ya baku hakkurin zama sauran aka amsa da amin. Kaina dago tare da fadin nagode mama na yunkura na mike tsaye tare da masu sallama na fito na barsu a falon. A yadda na samu su sister a wajen rayukan su a bace da alama sun ji yadda ta fadawa iyayyen su maganganun banza a falon. Gaidasu da zama nayi kafin nacewa fatima mu tafi mukai masu sallama muka fito zuwa gida wurin mota muka nufa kaina na a duke yake ina kallon hanya. Sai naji a dan firgice fatima na fadin gasu fa a wurin motan mu anty ta fada a dan firgice na dago kai sune tsaye suna magana a hasale. Saidai suna hangomu duk hankalinsu ya dawo garemu wani kallo suke muna tun daga nisa har muka karasa excuse me na fada don su jaye a wurin. Sai duk suka juyo suka kalleni lokaci guda a cikin rashin damuwa na karasa wurin jikina saye nake a cikin wani dogon riga ja baja sosai ba rigan kamar feated yake don yana da dan sharp da dogon hannu sai v neck da akaiwa aikin zare na yafa dan kwalin rigan a wuyana. Sai takalmana masu tsini sosai high hill mai tsawo da igiya kana ganina kasan nasan ta kan lagos da kyau ko daga shirina ya nuna hakan duk da gidan saruka danazo Kai tsaye na nufo inda suke din fuska ba sauki zan bude motar saidai basu jaye a wurin ba har lokacin, , , , , ZAINAB IDRIS MAKAWA ANA DARA GA , , , , , , , , 1️⃣0️⃣8️⃣BY, , , , , , , , , , , , ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , , , , , , , , BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AN, NUR , , , , , , , , , , , ONLINE PAID NOVEL YAR UWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA BA TARE DA HAKKIN KOWA BA DON BIYA KI TURA DARI BIYAR 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK 08036959257 ALLAH SARKI AI RAINA BAYA BACI YANZU DON KIN FITAR DON NASAN AKWAI RANAN HADUWA SEE U 👋 Bata wuri ta shiga mota ya fada a fusace daga bayan mu sai ta jaye da sauri tana kallon fuskanshi na bude motar na shiga Fatima ma haka ta shigo sai gashi ya iso bakin motan nan ya duko yana fadin. Ki kula da kanki sahiba zan zo gida yanzun nan idan na gama dasu a nan kai kawai na iya gyada mashi a lokacin driver yaja mota muka tafi raina ba dadi ga abinda nagano. Allah yaga zuciyana naso na zauna lafiya da kowa amma wanan matar ba zata bari hakan ya faru ba amma zan bita a sannu inga iya gudunta. A gidan hjy kuma andai kwasa ba dadi bayan wucewan mu dasu don nan ta fara kafa mai tujara wai ya kawota gidan sune dama suci mata mutunci ita da yan uwanta ko me ? Nan dai suka kwashi jidali bayan an samu da kyar ya tafi ance ya barta tunda taki shiga mota ta tafi ita da yan uwanta. Rashi bace ya bar gidan sai mugun magana take fadi da iya abinda zata iya min na sheri karshe dai har yakai saida hjyn su mukhatar din tafito da kanta ta tsawata mata don dole tabi umurnin ta ta wuce. Saboda hjyn tace mata matukar bata bar gidan ba zata nuna mata ita ta haifi mukhatar din kuma ta umurceshi daya aureta a lokacin. Shin falmata kishi haukane ba,a aure nasa shi don dole sai ya aureki ke dole kuma yabi umurnina har ya aure ki din don yanzu kina ganin kin samu wuri yasa zakizo nan ki muna diban albarka. Daga kuzo a sulhunta a zauna lafiya ba fitina kowa ya rike girman shi ya tsaya a matsayin shi mijin ku yakara samun kwanciyan hankali a rayuwanshi amma zakizo min gida kina diban albarka haka ? Falmata me kika takane kike takama dashi wanda banice asalin samuwan haka gareki ba ko kin dauka tsoron ki nake ji nake kyaleki kinawa diyana da yan uwa wulkacin wai ? To kishiga hankali daga yau aurene dai mukhutar yayi sai kije kiyi abinda zakiyiwa amaryan yanzu saidai ki sani kemafa ba kyaleki za,ayi ba haka. Ehh hjy dama ba yau ba nasan zamana da mukhutar yana ci miki rai kina bakin ciki da hakan yanzu saidai a yanzu babu yadda zakuyi don jini ya rigada ya gauraya da ruwa tun tuntuni kin makara a yanzu. Tana fadin hakan ta shiga mota da sauri yan uwanta suka shiga suma ta figi motar da karfi tabar gidan a cikin zafin rai. Mun isa gida ban tsaya falo ba a daki na nufa na cire gyalen kaina tare da rataye jakkana na fada bandaki don lokacin magariba daya gabato. Na idar da sallah har lokacin raina a bace saiga Fatima ta shigo tana fadin wai anty wanan matar akwai masifa. Ashe bayan wucewan mu an kwasa sosai da ita har yakai saida hjy tayi mata tas tana ramawa. Idanuna na lumshe tare da fadin nagani naga komai Fatima saidai wanan haukan nata bai dameni ba sam idan ba tashigo rayuwana ba ba abinda zaisa na kulata. Zan barta na manna mata karamin hauka da duniya zasu sanda ita sugane mai gaskiya a tsakanin mu. Haka naso mami tayi a gidan mu amma sai a barta tana fada a dinga dora mata laifi ko yaushe magana ya tashi da tana kyalewa itama tayi na karkashin kasa ko banza za a dan zauna lafiya a gidan da kowa. Amma yanzu mu daban su daban da kashigo gida zaka fahinci akwai matsala a gidan kenan mutane su fita damu a baki. Nan mukayi ta tatauna matsalan kafin muji dawowan shi mun fito falo baya falin yasa muka samu wuri falon muka zauna a nan. Saida ya dan dauki lokaci kafin ya fito da alama wanka yayi a lokacin ya fito jikin shi saye da jallabiya ta maza brown colour sai kamshi yakeyi jikin shi. Nan muka shiga gaidasu muna mashi sannu da dawowa ya samu wuri ya amsa muna kafin ya fara fadin. Iam sorry da abindaya faru daku dazun nagode da kuka bar wurin baku tsaya anyi wani fitina ba daku tunda haka sukaso. Nerve mind wanan ba komai bane ai na fada tare da kawar da zancen nake fadin ya Abubakar ya sameka a waya ? Kallon mamaki yayi min na shareshi don na fahinci baya son zancen ya Abubakar din daga bakina niko kaf din mu nafi sabawa dashi don shine mutum na farko daya jamu zuwa gida ya nunamu a dangin mu saidai daddy ya boye hakan. Don shi kuma nake ragawa duk wani ahalin mu tunda abin ya shafi duka bangarenshi idan nayi ba daidai ba dole ranshi ya baci duk da yana nuna muna rashin damuwa akan bangarensu din. Yanzun ma akan maganan su ummace da Ammar da yan uwa sukai shawaran waisu zauna a kaduna umma ta bugo min tana fada min shine nakirashi yace zan tambayi mijina yaji ra,ayin shi kan hakan shine na fada mai yanzu din. Bai kirani ba ya fada yana ci gaba da bata fuska dan lokaci guda nake fada mai cewa akan zancen su ummace wai ba zasu koma lagos ba shine takirani tana fada min na kirashi yace sai yayi magana dakai yaji ra,ayin ka. A kan me zasu hanasu komawa can din yanzu tunda a can suka saba da zama ko banza ba zasu yarda dasu ba aikuma yanzu don wanda ya kashe maka naka baka taba mantawa dashi ai. Ko suna ganin kun manta da zancen ne a rayuwan ku kawai dai ban san ra,ayinki na yafe masu da sauri irin haka ba shiyasa nabiki da hakan. Ba komai bafa na dai share zancen ne don kawai rayuwan na baya ya gyaru nan gaba don kada hakan yazo yaci gaba. Wanan halin da matarka ta nuna a yau a gabana irinsa ne ya jawo har wanan matsalan ya faru da iyayyen mu tsananin kishi ga uwa yana saka zuciyar diyanta ya gurbata su dauki dan uwa a mastsayin makiyi a garesu. Shine dalilin da yasa nake son zaman lafiya da kowa a yanzu gaba da kadan da kadan yake fara a zuciya har ya girma yashafi duk wanda ke kewaye da masu shi. Kallona yakeyi a cikin mamaki har lokacin da nayi shiru kana ya nisa hannu kawai ya miko min alaman nazo wurin shi. Kallon hannun nasa nayi kafin na rarafa zuwa inda yake duk da bamu da nisa dama dashi amma da dan sasarfa na karasa inda yake din ina zuwa ya karasa jawoni ya manna da jikin shi yana sauke ajiyan zuciya tare da dan murza bayana a hankali. Kedin karamace amma kina da zuciyar manya Sahiba zuciyarki tankar ta mahaifin kine akan imani da sanin yakamata saidai ina tsoron abinda hakkurin ki zai iya jawo maki nan gaba . Jin hakan yasa na dago kai na dan kalleshi lokaci guda na dukar da kaina kasa dan ban iya jure hada ido dashi wanan lokacin. A daidai wanan lokacin kuma wani irin ciwon mara ya soko min lokaci guda har saidana dan zabura na rike maran tare da fadin innalillahi. Da sauri ya tambayeni ko lafiya nace maratace ya rike min sai gashi wasa wasa abu na shirin zama babba a gareni haka yasa bai tsaya ba muka nufi asibiti Fatima tana daki sai jin yana kwala mata kira tayi ta fito a gigice ganin yanayin da nake ciki yasa ta rudewa lokaci guda itama. Tashin hankali da fargaba ne fal a ranshi har muka isa asibitin aka dubani a iya bincken su sam basuga wani aibu a jikina ba daya kawo hakan. Wanan yasa ya shi bai tafi ba a lokacin daya shirya tafiyan shi har ya cika min satin dayan da Allah ya wajabta akan budurwa ai mata amma babu abin daya shiga tsakanina dashi. Gashi na fahinci cewa matsalan yana faruwane idan mun kebe tsakanin nidashi a nawa fahintar ke nan a yanzu don haka matsalata bana asibiti bane na kuma hana fatima ta fadawa kowa a gida game da wanan matsalan nawa din. Zaune suke a falon su tunda ya dawo sai wanan lokacin yafito falon suka zauna da Aisha da mahaifiyar shi suna hira. Wayan shi ya dauki kara ya dauka ganin wanda ke kiranshi din a lokacin yana dauka da sallama saidai jin muryan me magana kamar yana kuka a cikin tashin hankali ya daga mai hankalin shi. Tambayan shi yake hankali tashe kome ke faruwa abinda ya jawo hankalin uwar da kanwarsa ke nan suke kallonshi suma. Oga we don die woo all our goods is lost nan ya fara mai bayanin cewa conteners sun nutse a ruwan cottono. What ya fada da karfi saida wayan ya fadi daga hannun shi bai damu da hakan ba sai kasa dayayi ya kai zaune kawai tare da dafe kanshi. Tambayen shi take a cikin yaren da takai kala biyar lokaci guda saidai ba amsa hakan sai can ya dago ya kalli Alajan dake durkushe a gaban shi. Mami shike nan kin rabani da silar dawowan arzikina na fada maki itace rayuwana amma kinki ki gane hakan saida kika rabani da ita mami ? Wana rabaka dashi daya kunshi arzikin ka ta kara tambayan shi shima ido cikin ido ya bata amsa da fadin Sahiba. Sahiba ta kara ambatan sunan yace yes mami malamai da yawa sun fada min hakan na lurar dake hakan baki gane nufina ba. Ita din zaman tadani alherine a gareni sosai mami yanzu rashinta a tare damu ga abinda yake samuna akai akai ina hasaran duk abindana tara. Komawa tayi zaune dirsha lokaci guda tana mai kallon mamaki tare da kura mashi idanu kafin tace dashi sahiba dince arzikin ka shaaban ? Kwarai mami mutane da yawa suna fada min hakan saidai ban yarda ba sai da naga yadda arzikina ya hadu da nata sosai haduwan mu da ita yasa na yarda da hakan. Yanzu kuma da kika rabani da ita na kara gaskanta hakan don irin abin dake bibiyata a yanzu din na hasara da rashi. Yanzu kinji jirgi ya nutse da kayan da muka odo na mashinu ko daya ba a tsira dashi ba wanda duk rabin arzikina yana a wurin kayan nan. Innalillahi ta fara tafawa da hannayen ta lokaci guda kafin ta fadi cewa Sahiba ta asirce min yaro da har ka iya yarda da hakan gareta. Haba haba Alaja wanan baiyi ba wallahi mutum yana a cikin halin gigita kan hasaran da yayi a yanzu kuma zaki kawo mai wanan irin maganan mai cin zuciya. Aishace daga gefen su take fadin wannan maganan a fusace tana kallon uwar kafin ta juya ta koma inda dan uwan nata yake zaune tana fadin. Yayana meye abin yi yanzu can inda abin ya faru zamu tafi ko kuwa sahiba din zamu fara nema ta dawo gareka by all means. Wani kallo ya jefo mata na kina da hankali kuwa Aisha kafin ya bude baki da kyar yace matar auren cefa a yanzu a ina zamu nemo ta . Idan ma mun samota muce da ita me a yanzu duk wanan zancen bata sanda shi ba ita ni kadai na sanda zancen yasa nake daukaka rayuwanta akoda yaushe ta yadda ba zata iya rabuwa dani ba sai gashi mami ta rabamu da rana tsaka a lokacin da ban taba zaton yin hakan ba. Ta kara juyawa inda Alaja take zaune tana kallon su a cikin mamaki don a yanzu tasan abinda zancen shi ke nufi don yarbawa basu zama ba tare da irin wanan bincken ba a rayuwan su. Balleshi mutum mai gwagwalmaya irin haka dole saida tambaya a lamarin su muryan yartane ya katse mata tunanen da tafadayi tana fadin. Kin gani Alaja kinga abinda kika jawo wa danki yanzu saboda son zuciya irin naki ki barshi yayi rayuwanshi a yadda ya tsara tunda ke kinyi naki a yadda kike so a baya ba a hanaki ba. Hannu ya daga mata da sauri kan tayi shiru ga abinda take fadi din dan kalamin yayi tsauri ga mahaifiyar su din. Dana sani da nadamane fam a zuciyar Alaja saidai bata son diyan nata su fahinci hakan daga gareta a lokacin. Shima ya fahinci ciwon nawa a yanzu saidai bai tsammani nima din nagane wani abu bane na sihiri ke damuna haka ba don ban yarda na nuna mashi komai ba har ya tafi. Saidai mun samu labari a wurin su sister cewa hjy Falmata bata koma ba kamar yadda mijinta ya fada zata koma itama can inda yaranta suke karatu. Wai ta tsaya yin wani abune a nan shine ya tafi ya barta nan din wanan labarin bai dameni ba a lokacin amma sai naga kamar ita fatima ta damu da hakan. Kwana uku da wucewan shi da yamma muna zaune a falo har mai aikin mu don tun bayan tafiyan shi sai aiki ya rage muna a gidan yanzu. Itama taji dadin hakan don ta fara sakewa tare damu har in ana kallona aika tazo ta zauna zata zo so yanzu ta daina yawan takurawa kanta da labewa sosai. Nocking din kofa akeyi yasa Suwaiba mai aiki mike zuwa duba ko yawaye saidai tana bude kofan aka turo ta baya da karfi har saida taja dan baya kadan zata fadi kasa. Abinda ya jawo hankalin mu ke nan muka maida kallon mu a kofan muga mai shigowa a lokacin sune su hudu kamar yadda sukaje gidan hjyn su mukhutar din a ranan. Suna cikin wani shiga na iskanci saidai sun samu shigan da yafi karfin nasu a jikina don dagani sai dan wandon jean guntu daya tsaya iya wuyan kafana. Sai riga yar karama mara hannu mai dan kwala a wuyan shi ta yadda zasu iya kare min kallo da kyau ke nan don nasan babu kowa a gidan kuma ba wanda zai shigo yasani wanan shigar sai gasu sunzo sun sameni a hakan. Ehh lalai tun ba a je turai din ba an koma yin shigarsu koda yake ba mamaki ga hakan don zaman mutum a cikin daban lagos zai iya yin komai a rayuwan shi. Haba don Allah zaku shigowa mutane gida a haka kuna fitsara fatima ta fada a dan hasale na daga mata hannu alaman ta bari. ANA DARA, , , , , , , , , BY ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , , , , , 1️⃣0️⃣9️⃣ BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM, , , , AL, HADI YAR UWA KIJI TSORON ALLAH KI DAINA FITAR MIN DA NOVEL DON KIN BIYA KI BARI WANI YA BIYA SABODA ALLAH👋👋 Komawa tayi ta zauna tana binsu da kallo basu zo inda muke zaune ba sai yawo suka fara a falon suna tabe tabe da yatsune fuska haka yasa nasan ba arziki ya kawosu gidan ba lokacin. Har zuwa lokacin da suka nufi dakunan kwanan dake cikin gidan suna iskanci in ka debe daya daga cikin su da taja ta tsaya a bayan su . Juyawa nayi na kalli fatima nace go and close the door for me, ki kawo min key nan ta juyo da sauri tana kallona bansan meta gani a kwayan idona ba ta mike da sauri ta wucesu zuwa kofan tayi abinda nace tayi din jikinta sai kaduwa yakeyi a lokacin don tsoro. Suna wani tafiyan isa da takama suna harare harare suka karaso tsakiyan falon suka tsaya. Ganin hakan yasa na mike tsaye remote na dauka na rage karan tv dake aiki kallona sukayi tare da fadin ehh lalai samun wuri anga komai abanza dole ayi yadda akeso ba a saba da ganin daula haka ba ba. Dan murmushi na sake a fuskana ina dan karkada farin kafana da duk rabinshi yana waje sai takalman zaman gida na roba shima pink kalar wandon dake jikina anyi mai addo daga sama kamar gashi an rufeshi. Dama kwadayin arzikin ne ya kawota cin banza saidai yarinya kin tabka babban kuskure da kika yarda kika shigo gidan mijin yar uwan mu da sunan kishi da ita. Ohh Realy na kalleta na fada naci gaba da fadin ita yar uwar taku diyar waye a kasan nan da ba,a shiga gidan mijinta itama din ba shiga tayiba. Ji wanan banza muna fadi kina fadi ke din yar waye diyar bararon daji kawai kilama rufa rufa akaiwa mutane ba a san asalin ubanki ba. Keko taga arziki ido ya rufe yanzu anzo aci banza dole ta dauka daidai take da kowa tanzu banza kawai masu bin arziki da gudu kinyi kuskure wallahi. Har lokacin wani murmushi na sauke tare da fadin No warder naga kowa da kowa naku kun maida gidan mijin yarku gidan ubaku har uwarku da kowa naku kun dawo kun tare a gidan mutumi kun hanashi shakat a rayuwanshi. Kun hana danginshi su morewa dan uwansu kun hana kowa nasa ya rabeshi yaji dadin a innuwarshi yanzun kuma kuna bakin ciki da hassada nazo nima naci arzikin nasa. Koda yake talauci yana saka hauka ba mamaki ga irin rayuwan da kukeyi na dabbobi ko wani dabban ma yafiku tunane da sanin ya kamata don dabba baya abinda kukeyi harda yar taku jaka. Ehh lalaima yarinya wanan kin tarowa kanki much yau, dama gargadi kawai mukazo muyi maki ashe kina takama da karamin barikinki a hakan kema. Kinyi gaskiya wanan dama nasan karamar yar iskace ta lafene kawai don ta samu shiga dayar ta fada daga gefe tana wani tafa hannu kamar taga abin mamaki har lokacin duk basu farga da mun kule kofa ba fatima da suwaiba mai aikina suna tsaye daga kofa a cikin tsoron abinda zai faru. Amma gaskiya kunsan in munyi wani abinda ba daidai ba a gidan nan ran ya mukhatar zai baci damu wallahi don Allah ku bari mu fita lafiya yadda muka shigo karamar daga cikinsu ta fada a dan tsorace ta kara da fadi a cikin yare Gila gila. Ayyah sorry sister ki barsu suyi abinda suka zoyi zasu samu duk kala abinda suka zo dashi gidanan a yau na fada sai ta tsakiyan datafi fitsara tayi wani shewa tareda tafi tana kara matsowa inda nake tsaye. Kamar ban san me take ba a lokacin ina kallon biyun dake gabana a lokacin tana zuwa kusa dani hannu na daga saijin saukan mari tayi kawai a kumatun ta saida ta sake wani kara da karfin Allah lokaci guda. Kafin suyi wani abu nasa kafa na tadiyo babban nasu sai gata a kasa ta buga goshi da baki a saman ties ya fara fitar da jini lokaci guda. Dayan tayo kaina kafin ai haka tayi kasa na bita na haye muka fara fadan mata biyun sukayo kaina duk da ina saman yar uwan ban kyalesu ba suma don ina kai masu nashi da shuri duk wace na samu sai dayan dake tsaye tana kurma ihu duk abinda muke wayana a kunne yake yana dauka tunda nayi saitin shi lokacin da suka shigo suka fara iskanci. Danbe sosai nayi dasu duka hudun lokaci guda amma Allah bai basu galaba a kaina ba lokacin jin wani irin karfi nayi yazo min sai bugun mai uwa da wabi nake kai masu a lokacin. Dukan kofa da akeyine yasa muka dan dakata saboda na sheda muryan sister ashe Fatima ce ra tura mata text massage suzo ba lafiya gasu sun kawo muna attack a gida. Duk yadda akayi na kyalesu na kasa sai binsu nakeyi muka fara zagayen gida cikin tashin hankali an rasa wanda zai rabamu a lokacin . Har yakai sun nufi wurin kofan nabisu haukace suka fara ihu a cikin tashin hankali suna neman taimako ranan kan basu ba duk wanda ke wajen yayi mamakin ya akayi na iya masu dukan wulakaci haka su duka uku. Dabara Fatima tayi ta samu bude kofan har aka samu shigowa gidan da kyar da bani aka samu kwatansu a hannu na da kyar aka jani zuwa dakina aka samu fita dasu. Sai kuma ga yar nasu hjy Falmata tazo wai a barta tashiga tayi maganina don me zanyiwa kannenta haka kuma ace wai mutum daya tayi masu wanan dukan haka kai ina gaskiya da sake. Kafin ace hakan har labari ya fara karada gari an fara fadin abinda ya faru ana kari a kai ga kuma video da fatima ta turawa Sister suka sake a median ya fara yawo nan zancen ya karade ko ina ko lokaci guda. Hankali a tashe ya shirya zuwa Nigeria sai hjyn su ta dakatar dashi akan kada yazo don in yazo ba za,ayi mai dadi ba wanan yasa ya fasa zuwa saidai munyi waya dashi ya bani hakkuri kan abinda ya faru. Tare da jamin kunne kan kada in kara irin haka da kowa na bari idan sunzo sai na kirashi yasan abinda zaiyi shi ko yanzun ma ba zai kyalesu ba. A haka dai har maganan yazo ya lafa bayan tayi barazanan ta da borin sai tayi karana kan wanan matsalan shi kuma da taji yace tana karana daga can ta tafi gidan su. Naje gidan mu fa kace baban yusura yace kwarai ki tafi gidan ku daga kotun sukai dan sa,insa dashi a karshe yace idan bata dawo ba ta zauna kuma kada ta dawo mai tare dasu gidan shi gaba dayan su. Tashin hankali da jidalin ya karu ta dauki haka da wasa suma sai hankalinsu ya tashi sosai da jin abinda ya fada nan dayan take fadin aina fada maku kada kuje gidan da fitina kukace aje a saka mata tsoron a zuciya. Yanzun ga abinda ya biyo baya mu din ai bamu san haka take yar daba ba da bamuje ba sun rasa yadda zasuyi gashi itama yar uwan nasu ta fara juya masu baya a yanzu . Don yarsu hafsat data zaunar da ita ta lurar da ita kuskuren da suka tafka daga ita har yan uwan nasu takuma bata shawara kan su yarda girman kai suje gidan da sunan sunzo ba hjy hakkuri kana su suce zuwa har gidana daga nan. Da farko sunso suyi mussun hakan har ita hjy falmata din amma kowa yace hakan dai zasuyi ai aidukawa wada ba rage tsawo bane ga mutum a faki gaba dani dasu ai yanzu aka fara wasan. Da wanan shawaran suka bi sai gasu har gidan da misalin karfe biyar na yamma a lokacin tare da ita hjy hafsat din data kawo su saidai ba hjy Falmata a cikin su. Wani tasha na yarbawa da nake bin season dinsu tun a tv duk ranan laraba ina zaune a falon gidan nake kallona hankali kwace sai ga sun shigo anyi nocking suwaiba ta nufi kofa ta duba ta samu ai sune sukazo. Don dama mun sanda zuwansu shiya kirani sister kuma ta kira duk sun sheda muna zuwan su ya fada zasu zo su ban hakkuri ne kan abinda ya faru tsakanin mu. Don haka banyi wani abu na nuna masu rashin hankali ba don mutuncin matan da suka shigo dasu gidan a lokacin muka gaisa dasu cikin mutunci da girmanawa. Ta fara koro magana na katseta da fadin do me, i do you so no base me i no wan wahala gyare . Duk kallona sukayi na nuna masu cewa banda tsoro ko fargaban fitina koda da namijine don haka fada dashi na bude ido da ban iya ba ban amsa suna yar geto ba a yanzu. Ke na nuna dayan ai kafin kuzo nan sai da friend dinki ta fada maki cewa kada kizo amma kika nuna kinfi karfin barin fada maku ko sister din ku aiken da tayo min yana nan dawowa gareta indai ni sahiba ce bata san ko wacece ni ba ta barni a inda ta gani kome tayi zai koma a kantane. Allah dai ya sauwaka yar nasu ta fada tare da kara bani hakkuri na nuna ai komai ya wuce a wuri suka fita bayan sunyi muna sallama. Kallon naji ta fita raina a lokacin don haka na mike na shiga dakina ban kara fitowa ba sai washe gari don ba yadda fatima batayi dani ba kan na fito naci wani abu naki fitowa a ranan. Haka hjy Falmata ta shirya ta koma inda ta fito tare da tawaganta da sukazo bayan taga duk wani abinda take ganin zatayi wanda zai min katanga da maigida. Data sani ta barwa Allah idan muka zulunce ta sai Allah ya isar mata tun a nan duniya amma ta kasa hakkuri ta barwa Allah lamarin tayi ta addua a gare shi. Sai ubangiji ya dorata a kaina idan nazo mata da wani cuta ko ha,inci a cikin rayuwana idan kuma babushi sai yasa mu zauna lafiya a tsakanin mu. Amma gagawa aikin dana sanine daga baya idan kana da rabo a wajen ubangijin ka sai kayi daka sani baka kaucewa Allah ba. Sai labarin tafiyansu naji a bakin Fatima ita da take waya dasu sister lokaci lokaci wanan bai dameni ba tunda dama ba a gida daya muke zaune tare dasu ba. Hankalina kwance nake rayuwana a gidan muna waya dashi lokaci lokaci yana kirana har mu danyi hira dashi ko ya rambayeni idan ba wani damuwa a tare damu nan maidugurin. Har yakai wata daya da sati biyu lokacin yazo maiduguri koshi daga South Africa ya wuto zuwa Nigeria muna nan da yamma bayan magariba muka gashi ya shigo unexpected. Ina dakina lokacin na idar da sallah ke nan ina shafa mai don nayi wanka lokacin dana shiga yin alwala dama na fito na tsaya yin sallah. Ganin mutum kawai nayi a bayana tsaye yana rataye da suit din shi a kafadan shi sai farar riganshi yar ciki da hannunshi ke sama yana kokarin balle bottom din rigan daga sama a lokacin. Dan juyowa nayi gareshi ina kokarin kama dan tawul din da nake da daura gaba dashi lokacin ina fadin you're wellcome ansan man dake hannuna yayi a hankali ya mayar saman mirrow din. Zagayowa yayi zuwa gabana inda nake zaune kallon juna mukayi na dan lokaci na sada kaina kasa cikin nauyi da kunyarshi. Kokarin mikewa nayi sai naji ya rikeni lokaci guda na dan kara kalloshi zaiyi magana na rigashi ina fadin let me dress my self first. Sautin murmushin shi naji yana fadin ko kin manta cewa ni mijinki ne a yanzu haka nake son kallonki ya fada yana kokarin son mu hada ido dani dashi amma sai naki hakan. Sai yakai hannu kamar zai kama ma daurin tawul din na jikin nawa da sauri na mike zubur sai ya rikoni gaba daya zuwa jikinshi lokaci guda yana sauke wani irin ajiyan zuciya tare da fadin baby i miss you. Jikinane ya fara rawa lokaci guda ina kokarin janye jikina daga gareshi don a zatona irin wancan yanayin zai dawo min na ciwon mara da zuban jini shi nake gudun kada ya faru a yanzu din kuma dani. Saidai har muka gama tsayuwa mu a wurin ya sakeni banji wancan bakon yanayin nawa ba da nakeji idan mun dan hada jiki dashi saidai hawayen daya dinga fita min daga idanuwana kawai a lokacin. Wanda bansan dalilin zuwanshi ba a lokacin amma har yafita daga dakin hawaye bai daina zuba mi ba nasan bai kula da hakan bane a lokacin. Da kyar na samu na saka riga a jikina na koma nayi rub da ciki kwance gashi ina son tashi naje koda falone amma na kasa yin hakan a lokacin. Haka ya dawo ya sameni a cikin wani yanayi na daban da bai fahinta ba zaune yakai a kusa dani yana fadin na dauka akwai abinda zan samu indanci a yanzu. Jin nayi shiru banko motsa ba a lokacin a yadda nake kwance yasa ya dan dubani da kyau saiya fahinci ai barci ma nakeyi a lokacin. Dan bin dakin yayi da kallo bayan ya dago ko ina na dakin tsab yake kamar ba a amfani da dakin koba mutum a cikinshi dake rayuwa. Ajiya zuciya ya sauke kafin ya mike ya fita ya hado tea da kanshi ya dawo dakin ya sameni yarda yabarni a kwance har lokacin yasha tea dinshi ya fita ya dan jima ya dawo ya rufo kofa tare da bissimillah a bakinshi. Kafin ya jiyo ya dan tsaya tare da karato adduan tsari masu nauyi da tsayi yana tofawa a ko wani kusurwa na dakin nawa a hankali. Duk kunnuwanshi sunji mashi kamar anja tsuki da dankarfi ko a hasale baisa ya dauki wanan wani abu ba a zuciyar shi. Bissimillah ya kara tare da dan rage wutan dakin yana kaiwa zaune daga gefena tsukin ya kara ji anja da da karfin sauti tare da jin motsi kamar an taba handle din kofan dakin daya rufe din da da karfi da sauri ya dan kallo wurin saidai babu komai daya gani a wurin illa duhu a lokacin. Wayan shi ya dauko a aljihunshi ya bude page alkur,ani mai tsarki ya fara karantawa a hankali yayi nisa sosai a cikin karatun shi sai ji yayi nayi wani irin mika da nishi lokaci guda tare da juyawa a yadda nake kwance da farko. ZAINAB IDRIS MAKAWA ANA DARA, , , , , , , , , BY ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , , , , , 1️⃣1️⃣1️⃣ BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM, , , , AL, BADI YAR UWA KIJI TSORON ALLAH KI DAINA FITAR MIN DA NOVEL DON KIN BIYA KI BARI WANI YA BIYA SABODA ALLAH👋 Tsukin dai bai kare ba saidai a yanzu ya fahinci badaga bakina wanan sautin da yake ji yake fitowa ba haka yasa yakara kaimi a wurin daga sautin karatun nasa. Sannu a hankali ya fara jin numfashina yana komawa normal haka yasa ya fahinci cewa bani kadai bane a lokacin yayi mamakin hankan sosai a zuciyanshi dama ashe da gaske akwai wanan matsalan ashe ga al,umma ? Bai daina karatun da yakeyi a lokacin ba sai gabanin asubahi sosai shima barci ya daukeshi saidai lokacin sallah yanayi ya falka ganina mane a jikin shi na dunkule a wuri daya da alama sanyi ko tsorone a tare dani lokacin. A cikin dabara ya zare jikinshi daga nawa ya mike zuwa bandakina nan ma ya tsaya yana bin ko ina da kallo kafin ya daura alwala ya fice zuwa sallah. A daidai lokacin da aka tayar da sallah lokacin na falka a cikin mamakin ina duban yanayin lokaci na biyar saura na safe a lokacin mikewa nayi da sauri kada in makara ga sallah. Sai bayan na idarne na lura da alaman mutum ya kwana a dakin nawa lokacin don waya da jakkashi na laptop dake saman gado a lokacin ga wasu takardu da agogonshi duka a wurin. Mamaki naji sosai da ganin haka har yaushe ya shigo dakina ya aje wanan abubuwan kodai a nan ya kwana na tambayi kaina ganin ba amsa yasa da sauri na juya na kalli inda zan samo ansa din sai naga alaman dai mutum biyu sun kwana a wurin. Da sauri na mike na isa zuwa wurin da nake zargin an kwanta din babu abinda ke tashi lokacin sai kamshin turaren da yake amfani dashi. Mamakine ya kara kamani lokacin how comes har ya shigo dakina ya kwana a nan ban sani ba me yasa ya kwana a dakin kuma ranan ? Ban kaiga karasa tunanena ba sai gashi ya shigo dakin da sallama shi fuskanshi kuma yana nuna mamakin gani a tsaye a laman har na idar da sallah ke nan a lokacin. Ahankali na juyo na sauke kallona gareshi tare da kaiwa kasa ina fadin good morning uncle morning ya bani amsa tare da fadin how was your night Alhamdullahi na fada ina dan jada baya kada jikin mu ya hadu da nasa. Zama yayi a bakin gado tare da daukan kafanshi daya ya dora saman gadon ya dan bubuga gefenshi da yake zaune tare da nuna min inzo in zauna. Dan jim nayi kafin na iya dago kafata zuwa bakin gadon nakai zaune a gefen shi dan shiru yayi yana duban wayanshi kafin can yace ki fada min abinda kike gani a cikin mafalkin ki inji ? Cikin mamaki na dago na kalleshi kafin in maimaita tambayan da fadin in my dream ? Ya lumshe idanuwan shi yana fadin yes akwai abinda nake son in gane a game dake yanzu dan shiru nayi don ban san ta ina zan fara fada mai abinda yake sonji din ba. Mafalkin me kiyi a daren jiya daya baki tsoro kika firgita suwaye suke binki haka a cikin mafalkinda ya zamo ba mafalki bane zahirine ? Da sauri na dago kaina na kalleshi yace yes zahirine ba mafalki bane kawai kikeyi haka don tareshi nayi da fadin I know wanan yanayin da nake gani sabone a gareni. Amma duk da hakan ba nasara ga maishi son muna buga fada sosai da abinda nake gani din a yanzu barshi kawai maishi zai koma mashi insha Allahu a kwanan kuwa. Kallona yakeyi har na kare zance na ba wani alaman tsoro a tare dani lokacin kara maimaita min tambayan yayi nan na shiga fada mashi abinda nagani yana bina da kokarin son daukan wani abu a cikin jikina da karfin tsiya. Shiru yayi na dan lokaci kafin ya nisa yana fadin insha Allahu komai zaizo karshe ina jin dadin yadda baki fadawa kowa matsalan dake damunki din a cikin haka har mu sha karshen abin. Duk da a yanzu na fahinci sabon matsalanki shine da zaran mun kebe dani dakene kike shiga wanan halin kenan haka na nufin akwai abindake faruwa dake a wani wurin yanzu kuma. Kallon mamaki nake mashi don jin kusan yasan komai dake faruwa dani a yanzu saidai ta yaya yasan da hakan ke nan ? Kada ki damu ya fada yana kai hannunshi saman kafadana ya rugumoni zuwa jikin shi idona na lumshe lokaci guda don jin saukan hannun nashi da nayi a jikina lokacin. Yana kuma fadin nikaina nasan matsalan ki tun farko sanina dake sahiba bayan haka kuma ina bibiyan komai sannu a hankali nasa daga ina zan fara da matsalan nan naki tun yanzu. Hawaye naji yana zo min wanda bansan kona meye ba a lokacin gwaggo hari ashe tana da gaskiyanta wazai ga ramin maciji da rana yazo da dare ya taka bakin ramin da kafanshi. Babu mai hakkuri da wanan irin matsalolin nawa danima ya sameni da rana tsaka tunda da farko ba haka nake ba nima ai. Hada jikinshi yayi sosai da nawa ta yadda har nake iya jin saukan numfashin shi a lokacin a cikin gangan jikina har banyi aune ba naji saukan hannayen shi saman jikina yana yawo a hankali. Jikina na kankameva wuri daya tare da kara runtse idanuwa da suke rufe a lokacin don jinda nake kamar ana watsa min ruwan zafi masu zafi nake ji a lokacin. Banyi aune ba naji yana kokarin kwantar dani saman gadon a cikin wani irin karfi da bai taba tsamanjn jinshi gareni ba kasancewata yar firit dani ga idonshi. Yasa yayi saurin jada baya yana zuba min ido tare da kallon yadda jikina ya dauki rawa lokaci guda saina fara jin ina zuwa baya suuu lokaci guda idona yana kara rufewa Kafin hankalina ya karasa gushewa ina iya dan jiyo sautin karatun daya fara yi shi kadai zan iya karaswa a lokacin wanda naji a lokacin. Nidai a karshe na bude ido na ganni wujuga wujiga kwance saman gadon dakina da sai warin hayaki dake tashi ko ina na dakin ga baki daya. Yunkurin tashi nayi zaune bayan nagama bin ko ina na dakin da kallo lokaci guda na yunkura na mike zaune murya hjy su uncle ce dake zaune da a gefena tare da kanwarta. Sannu yar nan suka kara fada lokaci guda sannu kinji sannu da fama wanan abu haka yaki guda tun safe ana abu guda. Ai Allah ya kawo saukin abin nata mabiyan manyane fiye da wa yannan da aka turo matasu yanzu gashi sun fada da bakinsu cewa sarki ya tare wuri yana wahalal dasu da basu azzaba. Aini jikina duk ya mutu idan ba ko aikin aljani ba har yaushe yar nan tasan wa yannan labarun data bamu a yanzu ? Bashi bama ba abinda yafi ban mamaki shine kamar wai yadda zancen gonan gadon su yaran nan ya fito a bakin wanan yar har take bamu labarin shi tas kamar a gabanta akayi komai alokacin. Jinsu kawai nakeyi don ina son kewayawa bandaki a lokacin kuma suna zaune a dakin nawa haka yasa ina mikewa suke tambayana da turanci nayi magana na fito daga dakin suna ganin haka a zatonsu bana cikin hankalinane yasa nake kokarin fita daga dakin gashi sai wani irin zufa nake tarsowa a jikina lokacin na wahala. Ina zaki tafi gaba dayan su suka fada lokaci guda na dan juyo na kallesu ina fadin zan shiga bathroom ne aiga kofa nan dakin Fatima zan shiga na fada. Jin hakan yasa sister ta tashi da sauri tabi bayana zuwa dakin har na kewaya na fito sallah nake kokarin yi a lokacin haka dai na daure nayi sallah dake kaina a lokacin. A nan na kara kwanciya don banson hayaniya ido na lumshe duk da ba barci nakeyi ba lokacin amma saika dauka nayi barcine a lokacin yadda na lafe. Kokarin bude kofan da akayine yasani bude ido shine ya shigo tare da wani tsoho sosai mai farin gemu gajere da dogon tasbaha a hannun ga warin turareshi yasa kaina hawa na fara jin wani iri lokaci guda. Da sauri uncle mukhatar yazagayo zuwa inda nake ya tallafoni lokaci guda na fara shakuwa ina gyatsa duk lokaci guda ga hamma da nake sakewa ba kakautawa . Kai tsohon ya fara kadawa tare dan matsowa inda muke din zaune sai kokarin kankame jikina nakeyi don kada ya kara tabani. Ido sosai tsohon ya kafa nan ya fara karatu yana tofa min tare da umartan uncle da yadafe min kaina sai girgiza kai nakeyi hawaye na zuba min a idanuwana. Ya dan jima yana karatu kafin ya fara fadin wanan babban kayane a kanta sai baki gasunan sunsha fama sai sun shiga jikinta suma amma hakan bai yuyuwa . Karatu yaci gaba dayi abin mamaki yaren su na farayi na kanuri ina fadin abar karatun nan nan muka zuba yare dashi nan abinda naki fada a farko na fada cewa anturosune su hanani zaman aure da mijin wata. Sai sukai rashin sa,a sarki mai karfin iko yana jikina do haka ba wani wanda ya isa ya rabeni a wanan lokacin su kuma sunyi alkawari har sun amshi jini a matsayin hadayansu ko. Salati dakin ya dauka daga can kofa muryan sister ne ke fadin waya turoku wanan aikin haka gareta wani kallo aka watsa mata kafin ace wace ta turosu ta riga datafi karku dukkan ku banda wanan godiyan da aikin mu baya iya tasiri a jikin ta ko kadan. Mun gwada ko wani hanya bamuyi nasara ba ga hakan gashi kuma yanzun ana kona mu ba zamu yafe ba dole mu koma jikin wanda ya aikomu zuwa wurinta. Sai wani Ihu da kowa dake wurin ya razana da hakan dajin ihun maishi yana wahala a lokacin an dauki lokaci ana wanan yakin kafin su ce sun fice su tafi nayi lankwas kamar bani da rai a wurin. Allah ya taimaka tunda nayi barci ban falkaba sai washe gari na tashi da ciwon jiki da kasala haka yasani kwanciya ko falo ban iya lekowa ba a ranan. Yayinda shi kuma yake ta faman sintiri dayin hayaki da shafa abubuwa a jikina hardasu shakawa haka sunin ranan suka wuni dani da dare kuma tare dashi din muka kwana duk da akwai mutane a gidan da dole suzo su zauna dani din. Ranan kan ba abinda ya faru bayan kunyan hakan da nake danji duk da ina kwance ba lakka a jikina hakan bai hanashi gwada rungumana ba a Darren kamar yadda malamin yace su gwada hakan a gani. Dole haka ya barni ya koma don dama zuwan banana shirin bane yazone ya dan Kwan daya sai gani gani kwana uku don Lauren daya sameni bayan Susan nasa din. Fabian morrow nake ina kallon kaina yarda na rame na nayi duhu don abinda ya faru din dani lokacin a wurin Fatima nake jin abubuwan daya faru dani lokacin naji komai daya faru dani daga bakinta bata boye min komai ba. Yanzu kunne aka kasa ashe don sun ce zasu koma gun wance ta turosu su zo gareni su bata min jin dadin aure da farin cikina da sauran sheri . Na daina ji nauyin shi da kunya ayanzu don yakan bugo waya mu dauki lokaci muna hira har yakai na dan fara sakewa dashi sosai yanzu din. Ina da wata daya da kwana biyu a garin maiduguri muna kuma zaune lafiya da kowa kullun kuma ina waya da umma har Ammar ina jin lafiyan su sai hakan yazo min da sauki don kamar muna tare a gari dayane dasu sai kewan nasu ya rage min a raina lokacin. Kwatsan ya fado muna kamar wancan zuwan saidai wanan zuwan na safe yayi muna tunda ya shigo yayi wanka bai leko falon ba. Don hakane muka samu daman yin aiyukan mu wanda nida kaina na tuka mashi tuwon amala miyan ewedo da tantakwshi sai kuma naman dana watsa kamar yadda mukeyi a can. Bayan mun gama an shirya komai wanka nafada yi na fito na gyara jikina tsab cikin wani shadda kamfala milk colour dake ta maikon sabontaka a jikina. Part din nasa na nufa a kwance na sameshi ringine ya kwanta ya dora hannu daya a goshin shi kamar me tunane jin sallama na yasa ya dan dago daga yadda yake. Yana kallona na karaso ina fadin good day sir how was your jorning saida ya dan dago tare da mikon hannun shi zuwa gareni na karasa takowa a hankali har Inda yake kwance din jawoni nayi na fada a saman jikinshi. Ya maida hannun shi ya rufe yana sauke ajiyan zuciya lokaci guda sam wanan karon banji komai da nake ji ba a lokacin shima sai ji nake yana dan sake ajiyan zuciya na dan lokaci. A haka yaso wasan ya canza lokaci guda amma sai nayi saurin mikewa ina fadin your food is ready na barshi a kwance . Murmushi yayi ya bini da kallo yana fadin ya kamata by now a tausaya main hakana a barni naji dumin amaryana ko zan samu relief a zuciyana. Nima dan guntun murmushin na sake cikin kunyan shi nace ai ko yanzu kaji dimin jikin nawa me kuma ya rage a yanzu din. Ohh realy ban iya bashi amsa ba Allah ya taimakeni wayanshi ta dauki kara haka yasa na samu na fice daga dakin zuwa nawa dankin. A gaba mirrow na tsaya ina kallon kaina tare da sake ajiyan zuciya ina bawa kaina shawaran abinda zanyi a lokaci don kawai na nunawa wanda ke bina da sheri a kan auren sherin shi baicini ba. Yaji dadin abincin sosai har yana rokon aje mashi ya kakara da dare gidan hjyn shi ya tafi bayan fitan shi mun zauna da fatima a dakina muna hira tana ta kara nausar dani yadda ya dace na dinga yi idan yana gari wanda sai kallonta kawai nakeyi ni. A ranan kan komai ya wakana tsakanin mu saidai kafin hakan ya faru shi kanshi yasan abinda ya taba don bani kadai bace naji jiki gaba dayan mu kowa ya ji nasa . Abubuwane dake dukkan bangaren mu sai dai da taimakon ubangiji har aka samu kadarin abin ya karye inda a wani bangare kuma faruwan wani abu ya faru don the massage back to sender now. Badon komai ba sai dan yawan alherun mu da tsare ibada da bada sadaka da Allah ya hore munayin shi gaba dayan mu nida shi duka. Wanan yasa duk wani sherin da mugun nufi da aiken sheri na sihiri baya tasiri a kaina gashini alherina gun kananan yarane da bukata na sosai haka zan aiki yaron dake zama damu ya bi hanya yabawa mabukacin daya hadu dashi alheri ko nasaka aimun kosai da manja ko na sayi gishiri mai yawa na bayar akaiwa mabukata unguwar tallakawa . ZAINAB IDRIS MAKAWA ANA DARA, , , , , , , , , BY ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , , , , , 1️⃣1️⃣2️⃣ BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM, , , , AL,BAQI YAR UWA KIJI TSORON ALLAH KI DAINA FITAR MIN DA NOVEL DON KIN BIYA KI BARI WANI YA BIYA SABODA ALLAH👋👋 Duk yadda yaso na sake jiki dashi da safe naji kunyar hakan kwana shi biyu ya juya ya koma daga sunan zuwa ghana aiki ya kwasheshi kuma zuwa Australia daga can sai a waya mukai magana dashi. Haka naci gaba da rayuwa ni da fatima sai yan abokan arzikin da a yanzu muka samu a garin dake dan zagayo ana mu,amula arziki dasu. Ba fita mukeyi ba don haka bamu da labarin komai dake faruwa sai wani shigowa da sister tayi a wurinta muke jin labarin ashe hjy falmata bata da lafiya kusa wata biyu ke nan duk labari har ya baza gari muna cikin gida bamu sani ba. Ba tare da jin komai ba nayi mata faran samun lafiya na canza topic din hiran mu saboda ban dauki zancen a komai ba har a zuciyana. Mun wayi gari da mumunan labarin da anty Amarya ta bugo muna tunda safe cewa an kama ya mustapha a kasan waje tare da wasu abokan harkallahshi su shiddah. Wanan labarin sai baimun dadi ba sam danaji amma sai naga ita Anty kamar ma murna rakeyi da hakan don tana fadi tana kwasan dariya a lokacin. Haka na wuni ranan a cikin damuwa don wanan labarin daya riskemu maradadi ga ya mustapha din a ranan ina jin yadda Fatima take waya da aibanta shi . Nakira umma munyi maganan amma nace ta kyale idan ba gwagwo hari ta kirata da kanta ta fada mata ba don kada su dauka muna bibiyan bayan sune saboda mutum wuyan sha,ani gareshi. Dole muka daiyi Dan zance kan abinda ya shafi zancen kafin my kashe wayan cikin tausayawa a halin da abin ya shafa ballema da take dan son ga iyayyen shi kasancewanshi shi kadai a garesu. Ba anty ba kawai had Faiza data kirani iron abinda take fada min me nan cewa wai asirin shi ya tuno dama yana wandaka da kudi son ranshi, ashe kallar sana,an da yakeyi ke nan. Gashi yanzu asiri ya tonu gwaggo hari tana cikin tashin hankali tana bin manyan kasan su taimaka afito mata dashi suna fama kashin kudi. Don babu Wanda zai iya fito dashi akace son laifin nasa babbane sosai na katseta da fadin har in baida laifi ba zasu sakeshi ba ? Yana da laifi kan don ashe dama sana,arshi kenan sayar da kwaya ga anty Nabila dake faman jiranshi taki kula kowa akanshi yanzu. Kuma shi yace baya sonta dan dama dama Fatima gwaggo hari kuma ta hana halakan shi da Fatima din wai bata hada zuri,a da anty Amarya don ba mutanen kirki bane. Tay tayin maganganu da dama nidai said umm nake amsa mata had zuwa lokacin da muka gama wayan da ita hankalina ya tafi ga zancen ta sosai. Yanzu na yarda da cewa kowa kanshi yasani a fannin ubanne na don na fahince su tsab kowa basu bari ba me nan don' ai ba anty amarya kawai ta haifi Fatima a gaskiya camfinsu yayi yawa sosai wallahi. Wasa wasa wanan maganan har ya kai gwaggo hari ta kirani da kanta kan case din tana kuka take fada min na taimaka mata nayiwa uncle magana ya tsoma baki ko Allah zaisa a sako ya mustapha din don shi yana hurda da manya sosai. Nayi mata alkawarin zan mass magana na kuma jajanta mata kan matsalan tana godiya muka gama wayan na kashe ina fadin olesi, olopopo. Yanzunne tasan ina da rana run ranan da suka tafi bata kirani taji lafiyata garama in na kirata a lokacin ina masu yaya hanya har sau biyu. Na kira umma na sheda mata yadda mukayi da gwaggo hari din tace idan ba matsala nayiwa uncle din waya na sanar dashi halinda ake ciki koda akwai taimakon da zai iya mata a kan case din. Banki ba nayi sa,a ranan ya kira waya saboda haka nake kwance jiki ba lakka said ga kiranshi bayan sallah la,asar na dauka muka gaisa dashi jin muryana da yayi wani iri yasa yake tambayana meke faruwa ? Dan jim nayi kafin na amsa da babu komai yace your voice sound like kamar baki da lafiya na danyi murmushi kafin nace dashi kawai dai iam not in good mood ne yau din. Ya tambaya da sauri akan me fa nace kawai labarin wani cousin brother din mune ya samu matsala sai naji yace wanan da aka kama a abroad ? Cikin mamaki na tambaya kasan da zancen ne yace kwarai kuwa nasan komai saidai laifin ai babbane sosai don hakane kowa baya son saka kanshi ciki. Amma aiba laifin shi bane asalima kayan da ake tunanen nasane ba kayan shi bane sheri akai mashi kuma sunki bari yayi bayani. Yaya kikasan da hakan ke ya tambayeni Dan murmushi na sake tare da fadin na sanine mana haka zancen yake yanzu haka wa yanda sukai mashi sherin suna kokarin barin kasan ta ruwa . Nan na kara mai bayanin komai tare da rokonshi a kan ya taimaka muna please son case din ya zo da sauki da sauri yace ta yaya zan jefa kaina a wanan case din mai karfi haka ? Akan mutanen da har gobe nasan ba sonki sukiyi ba fatima tareshi nayi da fadin koda basu sona sune dai yan uwan nawa dana sani kuma nake bearing din sunan iyayyena a yanzu. Dan ajiyan zuciya ya sauke yana fadin yanzu ya kike son ayi ke nan don dole risk zan dauka na jefa kaina a cikin wanan case din don ba karamin case bace tunda ba a Nigeria aka kamashi ba. Bayani nayi mai yadda zai gane yayi shiru yana saurarena har saida na gama kafin yace anya kuwa Sahiba ba kina ganin har hanji ba ? Wanan irin bayani haka kamar a gabanki akai komai yanzu na gamsu indai hakane abin ba zaizo da wani matsala ba sosai insha Allahu. Shirun da yajine ba amsana yasashi kallon wayan shi muryan fatima yaji tana kwallamin kira kamar a cikin tashin hankali bai kashe wayan tasaba yanajin duk abindake faruwa alokacin wurin. Innalillahi ya ambata hankali tashe kafin yayi dabaran kiran layin fatima din yayi mata bayanin abinda zatayi min a lokacin. Wanan karon ban wani sha wahala sosai ba na mike don yanzu abin nawa akwai sauki sosai ba kamar dacan da mm nake wahala sosai ba idan ya tashi min. Barcin nan dai da nakan yi shinayi alaman sun sauka min a kai kenan lokacin kodana falka magariba tayi a lokacin. Duk yadda yadda yan uwa sukai tsamanin zancen ya wuce hakana yanzu a garesu don labari yazo masu cewa ai har an kashesu ko don an kamasu da babban laifi maigirma a kasan don haka aka halbesu. Ranan wayan gwaggo hari ya tayar damu barci karfe hudu da rabi na safe da kukanta take fadamuna cewa sun samu labarin cewa an halbe su boy don Allah na bincika masu gaskiyan zancen suji. Nima salati na saka a rude kafin na jawowa kaina natsuwa ina bata hakkuri tare da fadin gwaggo ki natsu wanan maganan ba gaskiya bane don ko jiyan nan munyi waya da uncle ya fada min ya samu ganin shi. A cikin wani irin karagi tace ya ganshi fa nace kwarai kuwa gwaggo don insha Allahu da alaman nasara sosai a case din. Sai naji ta sake wani irin shesheka kuka lokaci guda wanda nima yasani sake hawayen da suka taru min a fuskana lokacin. Wanan labarin ya dan karfafa mata gwiwa har yan uwa sun fara cika mata gida da sunan makoki da tayata jimame kan matsalan sai gashi ta fito tana fadin insha Allahu boy yana nan dawowa don ko jiya mijin sahiba ya ganshi har sunyi magana dashi. Nan take aka dauka zancen ya tabi zuciyar tane harta fara sakin magana haka taci gaba da fadin insha Allahu sahiba tace zai dawo gida da yardan ubangiji. Nan yan gulma suka samu nayi don basu yarda da abinda take fadi ba sun dauka zancen ya fara taba mata kwakwalwanta ne haka. Sai sam basu yarda da abinda take fadin ba wasu nacewa ina wani mijin sahiba can zai iya fitar dashi a wanan hatsarin daya fada ? Ya Abubakar duk da yadda suke da mustapha din yaji zafin kamashin da akace anyi munyi waya dashi yake fada muna sai dai ta Allah amma yana da wuya a fito dashi sai ban gaya mai zancen kokarin da uncle keyi ba a can din. An dai sha wuya hankali ya tashi sosai Allah da ikon shi watan su hudu a can sai gashi anyi nasaran fito dashi din ta hanyar kamo masu laifin aka wankeshi. Uncle da kanshi ya dawo dasu Nigeria bai fadawa kowa zuwan su ba sai ganin su gwaggo tayi tare baikai awa biyu ba ya juya zuwa Maiduguri. Ganin mustapha din ya fito ta hanyar uncle mukhatar ya kara daga darajan shi dani a idanun su tunda sunga yayi abinda basu taba tunanen zai yuyuba ga mustapha din. A sai zuwa barka da arziki akewa gwaggo hari kowa yana fadin albarkacin bakinshi a lokacin irin yadda a yanzu nayi masu rana a cikin su bayan sun wofintar damu a baya. Don ba,a dade ba da nayo masu aiken abubuwan azumi dana aikowa dangin mu ga baki daya har wa yanda ke yola dana nan garin kaduna daga ciki kuwa har da na Family din Alh Nuhu da Alh gyade da suke tsare har lokacin a gidan wakafi amma haka na aiko masu da kayan shiga azumi. Suma lokacin da baffah hamza ya kai masu kayan abincin dana tea din saida suka so su nuna bore wai ba zasu karba ba inji yaranshi. Amma iyayyensu mata da wahala ya gama kamasu zuwa lokacin sukace ai ba a haka tunda har na nuna kulawa a garesu kada suga laifina su dubi laifin iyayyensu maza kawai. Shima baffah hamza ya dora masu da nasiha kan tunda har ban nuna komai ba duk da irin laifin da akai muna amma ina nuna su yan uwanane na jini ya kamata suma su sauke makaman su hakana a kan mu. Su kwatanta idan sune mahaifinmu ya raba mahaifinsu da duniya yaya zasuji a ransu a kan mu sai jikin su yayi sanyi inda akai masu mm asiha sosai har wasun su suka nuna nadaman su sosai. A Wanan zuwan munje har lagos wurin su umma mun gaidasu mun kai masu dan abin azumi inda umma tayi ta murnan ganina a lokacin. Sai bayan mun samu kebewa da itane ta kallani tana fadin sahiba naji dadin yadda kika kwantar da hankalin ki haka sahiba don da farko hannuna a gaba yake yadda akai auren nan. Amma yanzu ganin ki haka hankalina ya kwanta sosai wallahi gashi ina ganin har da rabo a jikin ki idan ba karya idona ke min ba kila ? Dan murmshi na sake kawai Allah ya taimakeni fatima uwar baki bata jin yarbanci data kaini inda banso don ni cikin jikina bai hana min yin komai kamar yadda na saba ba haka kuma ina cin komai da nake ci a baya . Nafi da son sai cikin ya fito da kansa a gani bawai na dinga fadawa mutane ba don wanan camfin yarbawane haka don baka san bakin wani ba. Haka mukai kwana biyu tare dasu ummu a lagos muka dawo Maiduguri a wanan lokacin ne tawagan yan uwan mu maza da mata sun kai su ashirin sukazo mashi godiya kan tsimakon da yaiwa ya mustapha tare da abin alheri iya karfin su da sunan sun kawowa yarsu garan taron azumine. Yace ai ba sai sun taso ba don sunci albarkacin yai masu hakan a wurare da dama don haka ba sai sin wahalal da kansu ba illa iyaka dai ya kara kula sosai tunda ana binshi da sheri irin haka dole yana da makiya a wani wajen da bai sani ba. Gwaggo hari kasa ne kawai bata kaiba wajen mashi godiya a lokacin na dauka zasu kwana sai gashi sunce a ranan zasu dawo kaduna. Nagode Allah ba wanda ya farga da cikin dake jikina wanda zaikai wata biyar ko shidda a lokacin a jikina amma ya shafe ba a ganin shi sam. Har shi maigidan baisan da cikin ba Inda uwargida falmata duk da abinda ya faru haka baisa ta saduda ba don kullun a cikin barazanan fadi take ba aiwa diyanta yan uba ita. Yadda nazo haka zan koma don kullun a cikin sabon shiri take a kaina duk da bata samun nasara hakan baisa ta daina ba ita. Gashi a yanzu duk wani kafa da zata samu labarina a toshe yake tunda bana hurda da kowa in kin debe yan uwan mijina na kusa su kuma ba zataji komai a wurinsu ba don ba yarda a tsakanin su. Gashi dole zamu bishi zuwa Hong Kong saboda azumi da za a fara haka muka bar Nigeria zuwa kasan amma mun tafi da fatima da har yanzu itace zaune tare dani. Mun isa lafiya an kuma tashi da azumi saidai saboda wahalan tafiya kuma ga laluran ciki da zan iya cewa wanan ne wahalan farko dana farayi kan cikin jikina gaskiya. Wanan yakai saida mukaje asibiti dole aka bani gado na huta don ina bukatan hutu a lokacin barci sosai nakeyi yayin da yabar komai nasa ya dawo jinya ta asibitin. Ina bude Ido shine naga a zaune yana karatun kur,ani ya saka glass a idanunshi hankalinshi ya dauku ga karatun da yakeyi a lokacin . Haka yasa na samu daman kare masa kallo sosai a lokacin don banyi motsi ba shima bai dago kanshi ba a lokacin yana duke yana karatu. A hankali na mayar da idanuwana na rufe lokaci guda ina sauke ajiyan zuciya a hankan na tsukayo muryanshi yana sadakallahullazi. Jin hakan yasa na bude idona muka hada ido dashi yace kin tashi na dan gyada kai ya samu wuri mai kyau ya aje littafin ya mike tare da zare glass din daya manna a idon shi na karatu. Ya karaso zuwa inda nake kwance yana fadin sannu ya jinkin naki yanzu Alhamdullahi na fada ina lumshe idanuna lokaci guda. Yanzu ina ke damun ki yana kai hannunshi a saman wuyana a lokacin ba ko ina na fada a hankali ga abinci nan ki tashi kici . Fuska na bata lokaci don sam yanzu ban son cin komai a cikina duk kwanakin nan ga baki daya duk da ina kokarin wurin ganin ban zauna da yunwa ba. Baki isa ba ya fada yana kokarin jawo basket din abincin tare da fadin kina son ki wahalar da kanki ne da abinda ke cikin ki ku wahala ? Da dan mamaki a fuskana na dan kalleshi sai kuma na dan turo baki lokaci guda ina kawar da kaina gefe abincin ya fara zubamin har lokacin ban kalli inda yake ba. Aje min yayi a gabana sai na kalli abincin wanan dahuwan nasan na fatimane don yadda akayishi ya hadu ba irin da yan aikin gidan da muka sama suke muna ba. Mikewa nayi ina kokarin sauka saman gadon da nake kwance sa sauri ya kalloni yana tambaya ina zaki bandaki na bashi amsa. Bayan na dawone na zauna bakin gadon ya miko min abincin na karba cibi biyu kawai nayi na aje spoon din cikin plate ina kokarin komawa na kwanta ya sake fadin. Likita yace idan baki cin abinci akai,akai zaku samu matsala dake da abinda ke cikin, cikin ya fada yana kallon fuskan nikan dukar da kaina nayi. Banda abinda zance dashi tunda ya riga da yasan abinda nake boyewa a yanzu shi yasa nayi shiru a lokacin cikin jin nauyin hakan da kunyanshi. Kaina na kawar gefe daya na sake jin muryan shi a kusa dani yana fadin akan wani dalili kika boye min alheri da ubangiji ya azurtani dashi tsawom wanan lokacin.? Nasan dole kina da dalili naso ba kaina hakkuri in biki a yadda kike so amma zuciyana ya kasa daure hakan a yanzu don farin cikin da nake ciki duk da kin rage min hakan . Ciki a jikin ki fatima har tsawon wata shidda ban sani ba sai wanan lokacin daya rage saura kiris ki haihu ? Amma banyi mamakin hakan ba don koshi likitan da kyar ya iya gano hakan don da farko ya nuna babu komai a jikin ki. Forget about that yanzun me kike son kici ya sake tambayana yana kallon fuskana dake daure tamau a lokacin kamar banson zancen. ZAINAB IDRIS MAKAWA ANA DARA, , , , , , , , , BY ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , , , , , 1️⃣1️⃣3️⃣ BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM, , , , AL,WARITH, , , YAR UWA KIJI TSORON ALLAH KI DAINA FITAR MIN DA NOVEL DON KIN BIYA KI BARI WANI YA BIYA SABODA ALLAH👋 Kwana biyar nayi asibiti ina hutawa kafin na dawo gida nan ma sun bani doka kada inyi wani dogon motsi don yanzu cikin yana barazanan zubewa ne daga jikina. Wanan yasa yake kara nuna min wani irin kulawa da kauna yana kuma kafa kafa da zancen cikin kamar yadda na gargadeshi tun a asibiti da kada ya sake yayi wanan maganan ko a gaban fatimane sai idan bukatan haka ya taso ayi din .. Wanan kuma ya samo asaline kan sanin halin hjy Falmata da nayi don kasancewar ta shu,uman mace mai karfin hali da shige shige akan duk abinda tasa a gabanta. Tunda har ta iya tura min asirin da yayi tasiri a jikina ya zama dole in kiyayye duk wani siri a yanzu duk a kanta kuma don babu abinda bata iyawa a rayuwa. Anyi azumi lafiya inda nagodewa Allah har Allah ya ban ikon samu nayi fiye da rabin azumin shine baya zama wuri daya ko yaushe a cikin tafiye tafiye yake wanan ya ban dama idan bai gari sai na dauki azumina in kuma kaishi lafiya. Kamar yadda na rabawa dangi kayan azumi wanda daga wurin shi komai ya fito don dama haka dabian shi yake zai bawa hjy falmata abinda zata rabawa dagjn da mabukata a wanan lokacin amma sai ta soke kudinta taki rabawa kowa. Yadda ya bata haka ya bani nima hakan kuma na aikawa baffah hamza ya rabawa yan uwa zanuwa da shadda masu kyau da kudin abin sallah kowa yana samin albarka. Har cikin Maiduguri na aika da alheri wa yan unguwan mu ta hanyar wata malama da muke dan hurda da ita nan ma sun saka min albarka sosai tare da addua dama shi nake nema a wajen mutane addua a wanan lokacin. Babban sallah a duk inda yake gida yake komawa yayi sallah shine kuma watan haihuwana ga Fatima ta fara karatu dole sai su kadai sukazo Nigeria sallah duk da yaransu. Saidai kafin su dawone Allah ya saukeni lafiya a daren ranan sallah din na haifi yarana duk maza tagwaye sai lokacin na gane hikimar sayen abu bibiyu da yakeyi idan zai sayo kaya a duk kasan da yaje aiki. Watau ashe tun kwaciyana asibiti likita ya fada mai cewa yan biyune a cikina yake yin hakan labari ya riskesu na cewa na haihu a bazata banda shi da yasan da zancen cikin a lokacin. Duk wanda aka fadawa haihuwan nawa saiya musa hakan yace sahiba fa ta haihu cikine da ita dama wai har labari ya samu hjy falmata a lokacin suna tare da kawayen ta gidan nasu yana cike kamar ana buki wata yar uwanta tazo. Bayan sun gaisa take fadin barka fa ashe amaryanki ta sauka kuma yanzu nake ji nima na biya gidan su mariya take fada min. Wacece hakan take tambaya a yatsine tana wani bata fuska lokaci daya don daukan mara hankali tayiwa matar duk da tasan tana da hankali amma kuma baya bayada kadan ai. Da sauri matar data fahinci katobaran da tasoyi ta dan wayance da fadin au jini bafa abinda naso fadaba ke nan dama ? Sai kuma ga wani kanin ta ya shigo shima bayan sun gaisa yayi mata murnan sallah yake fadin ashe maigida ya samu karuwane haka amarya ta haifi tagwaye maza ? Zaune take saida ta mike tsaye ta fara fadin wai a ina kuka samo wanan zancen banzan haka dazun nan wacan tazo min da wanan zancen karyan yanzu kuma kai kazo dashi mutane sai ku dinga kirkiran labaran karya kawai kuna yaddawa. Shigowan kaunanta da waya a hannu falon a kuma gigice yasa ta dakata da zancenta a cikin yare take fadin dubi abun mamaki nan anty. Ta karbi wayan ina zaune a gadon asibitin dana haihu saye da rigan asibitin a jikina sai hularsu a kaina ga yaran biyu sun sha kayan sanyi masu tsada likitoci farare biyu sun da duko mukayi photon dasu. Aikin fatima ne data turo wanan photon a lokacin dama abinda nake gudu ke nan tun farko yasa na boye zancen cikin yanzu kuma ba zancen boyo ga kowa. Duk da sanyin Ac biyu dake falon bai hana goshinta tartso da zufa ba a lokacin yayinda ta kafawa yaran dake hannuna ido wa yanda kamar ubansu yayi kankisune don kama. Photocopy ke nan wata kawarsu ta fada daga gefe sai lokacin ta nisa kafin ta fara ganin duhu duhu ta lumshe idanunta a hankali tare da fadin mukhutar. Bata gudun abin kunya don haka nuna react dinta bai dameta ba lokacin ta fara fadin ni zakayiwa haka ka boye min zancen cikin matar ka ? Ku rage a falon nan yarta ta fada kafin su fara fita daya baya daya sai aminanta mutum uku suka rage ta kalleta tana fadin zaki fara haukan ki ? Zaki hanashi abinda Allah ya halasta mashine falmata ki natsu ki dinga daukan girman ki duba yadda yaranki suka fara girma yanzu fa. Wani malolon bakin ciki ta hade lokaci guda da taji ya rufe mata kan zuciya har bata iya ganin kowa a lokacin don bakin ciki wai ita falmata guda a gidan mukhatar yau akaiwa yaranta yan uba ? Bama kishiya da takewa fathting din ta fita ta bata wuri ba har da karin wasu yara maza biyu da yanzu suka shigo cikin file dinta. Amma mukhutar ya shammaceta ya gama da rayuwanta da har yaiwa diyanta yan uba a yanzu dama shi take gudu kuma ya faru. Wanan abin kunyar da zubar da mutuncin dayaja mata ina zata kaishi a cikin kawayenta dake mata kallon ita ogace ta tare gaba ta tare baya a gidan mijinta bayan cika bakin da tasha yi masu a baya ? No warnder ya fita da yaranta yau tunda safe da sunan zasu ziyara ashe yasan abinda ya shuka ke nan dama. Lalai wanan yarinyar takai shu,uma itama tunda har ta gagari rayuwanta ta kwana mata da miji har da samun rabo a hakan ? Muryan daya daga cikjn matan ya katseta dake fadin waiko ita ta haifesu ko kuwa sunyi aducting dinsune da sunan haihuwansu donsu batarwa mutane da hankalin su ? Da sauri ta juyo tana kallon matar itako matar saicewa tayi yes kina mamakin hakane meye ba za a iya yiba a yanzu aikibar mutum kawai da makircin shi. Shiru tayi tana nazari kafin ta mika hannu ta sake karban wayan tana nazarin fuskokin yaran kafin ta nisa ta fara fadin wanan zai iya zama gaskiya. Saidai akwai inda zan gane gaskiyan hakan don duk illahirin zuri,an su suna da dan cindo a karamin yatsan hannunsu idan hakane ko dole ya kasance suma a sameshi a hannunsu. Kwarai kuwa da kyau mun samu abinda zamu dogara dashi na farko da zamuyi challanges dinsu dashi bayan haka dole mu kara samun wani evedence da zai nunawa duniya yaran ba diyan mukhatar bane . Ni duk ba wanan ba a gabana duk suka mayar da hankali suna saurarenta lokaci guda din suji meye damuwanta dake ci mata rai. Ta nisa tana gyara zama tacesai wai ace yauni Falmata mukhutar yakeyiwa wanan irin halayen haka kan wata mace macen ma karamar yarinya. Au bakisan mazaba ke nan hajaju ai idan kina son kiga true colour dinsu ki bari sai sun kara maki kishiya kiga tabara da tsiyataku a wajensu kala kala dama abinda matakewa gudu da karin auren ke nan ai. Kina zaune kalau da mijinki daga sama wata tashigo ta bata maku tsarin zaman ku Idan baki kai zuciya nisa ba har a aikata abinda ba, a so a karshe. Falmata ki natsu ki yarda da kaddara kinga irin abinda yasa tun farko suka boye maki wanan zancen cikin ke nan don irin wanan halinda kike nunawa. Ke yanzu duk abinda ya faru dake a baya kin manta ke nan a yanzu keda aka samo rayuwan ki da kyat daga ballewan jini da ki kasha fama dashi. Ace wai mutum dan musulmai, amma baya tawakkaki da duk kalan kaddaran da Allah ya aiko ma bawa dashi. Mikewa tayi fuuu ta wuce zuwa sama inda dakunan kwanansu yake tabar kawayen nata tare da yan uwanta a falon. Yadda kowa yaji zancen haihuwana yake shiga mamaki kwarai don sam ba wanda zaice yana da labarin cikin jikina hakanema yan uwana har ummana dukda tasan akwai cikin saidai bata san yaushene watan haihuwan nawa ba. Lokacin daya kirata yana sheda mata zancen haihuwa da ace wanine ke fada mata wanan maganan ba mukhutar ba da ba wasa a tsakanin su. Da sai tace maishi wasa yake mata ko yana zolayanta akan hakan wai Sahiba ta sauka lafiya ta samu babies twin's maza haka maganan yazo mata a bazata . Har yaushe Sahiba din tayi cikin daya isa haihuwa ke nan koda mukazo sallamanta zamu tafi cikin na ajikina har ya tsufa a lokacin. Gashi ya fada matacewa zuwa tuesday zasu tafi daga ita har Ammar da gwaggo kudidi sai gwaggo Amina wanan tafiyan nasu ya kawo muhawara sosai a cikin yan uwa. Don sun fara fadin yanzu ke nan su gwaggo kudidi nafi dauka a matsayin yan uwa a gareni fiye da sauran yan uwa don me komai ya taso nawa sai ace su gwaggo kudidine kawai zasu tafi ? An rigada an masu komai na tafiyansu a yanzu don haka dole kowa yayi hakkuri da zancen zuwa tunda su ta zabi zuwansu tun farko don haka ke hari da Asiya dake Addah sai kuyi hakkuri a faki gaba kuma, ai yanzu aka fara. Don dole suka jaye zancen tafiyan don sun kula cewa sune zasuyi wanan tafiyan donsune ya cancanci sujeshi sai gashi waisu gwaggo Aminane zasu tafi irinwuce an wajen dasu ya dace ace sunje. Ranan kuwa suka shirya zuwa lagos inda a can zasu hadu dasu umma su wuce a tare dasu zuwa Hong Kong din su samemu kamar yadda aka tsara tafiyan. Akwai kanwar mahaifiyarsu da kuma wata dake zaman gwaggon shi daya da zasu tafi tare nan ma gida maiduguri an kashe kudi sosai ma anan don taro zasuyi tankar maijego da yaran suna kasan. Ana gobe zasuyi taron suna Maiduguri hjy falmata ta shirya da tawaganta suka bar kasan ta koma inda ta fito ko maigidan baisan zata koma wanan lokacin ba. Sai labari ya samu cewa sun tafi ita da diyanta da kannenta da sukazo gida yin babban sallah kamar yadda suka saba zuwa duk shekara a wanan lokacin sukan yi ziyara su gana da yan uwa suyi masu alheri . Sai gashi wanan karon haihuwana ya hanashi tsayawa don tun washe garin da yamma ya koma ya barsu a nan su. Sai gashi taji cewa itama hjyr tasa ta juyo ta dawo turai a wanan lokacin gashi ba zaman lafiya tsakanin shi da ita tun lokacin dayayi aure suke kwasan fitina da ita sai hakkuri da juna sukeyi tsakanin su. Wanan yasa ko zancen haihuwa sai a waya ya kira ya fada mata ya kuma kashe wayan shi gudun kada bacin rai ya biyo baya tsakanin su. Sun iso lafiya sun samemu kuma lafiya inda yara sukaci sunan mohammad da Ahmed sunan mahaifina da nasa zuwan su umma yasa yanzu na samu hutu sosai banda aiki sai barci ko wani lokaci. Haka yasa jikina yayi kyau sosai da alaman jegon ga karbi jikina idan ka shigo ba zaks taba cewa nice na haihu ba sai idan ka samu ina ba yaran nono. Yanzu ma barci nake tun safe dana shige daki bayan mun gama karyawa sai wajajen karfe biyu gwaggo Amina ta tayar dani in basu nono shine fitowana lokacin. Kowa na falon zaune suna hira mukaji ana nocking Fatimace ta fita duba ko waye muryan hjy falmatane a kofan take fadin kauce ki ban wuri don Allah. Fatima ta kauce da sauri ta basu wuri ta tun karo inda muke zaune din ni inabawa yara nono a cikin yare na fara fadin su boye min yaron dake hannun gwaggo kudidi tun kan ta karaso haka akayi . Suna mata sannu da zuwa ko kallon arziki basu samu ba sai kokarin shigewa takeyi zuwa dakin shi suna kallon ikon Allah. Suka shige sai gata ta dawo tana tafiya takalmanta na basa sauti tun kan ta karaso take fadin (ke ina makulin wancan part din ?. Ban kallo inda take ba naci gaba da abinda nakeyi ke bakya jin ina magana ne ta kara takowa zuwa har inda nake zaune a cikin wani isa da takama. Mrs may i know who are ? Kin shigo gida bakiwa kowa magana ba yanzu kuma kina tambayana key din gida haka kai tsaye ? Itama din kallon mamaki take min kafin tace samun wuri ni kike tambaya ko wa nake nace kwarai kuwa son banga alaman hankali ba a tare dake. Naso baki girmanki na shekarun ki da matsayinki na babba a gareni gidan miji amma naga sam ke baki san girman na gaba dake ba balle harni mm a girmamaki. Don haka ba zan bada key din gidana ba don bai fada min cewa zaki zo nan ba nima kuma ba zuwa inda kike zanyi ba don haka ki fice min daga gida yanzun nan kafin rayuka su baci. Au ashe har gidan ya zama naki ko ban sani ba ko dan yaran da kike takama kin kwaso sun zama naki a yanzu kike son ki fara mallake gidan ? Zaki iya mayar dasu inda na kwaso su ai tunda shine bakin cikin ki dama kada na haihu da mijinki gashi kuma na haihu din kamar yadda baki so haka ba. Haba Falmata ana zaune kalau zaki zowa yarinya da fitina haka tana fama da jegon ta kanwar mahaifiyar shi ta fada . Kune baku sani ba don babu mai labarin cikin wanan yar iskan saijin haihuwa kawai akayi don ta rainawa mutane hankali taje gidan marayu ta dauko rainon diya . Salati matar ta saka tare da fadin falmata sherin har yakai nan kina son batawa yara suna ga banza kiwa Allah ki bar wanan sherin tun bai fita ba . Yara kowa yasan na mijinkine don gasu kamar kakinshi wurin kama har wanan cindon dake dan yatsan shi duk basu ragoshi ba a wurin kama. In ma wani abu ya kawoki sai ki zauna har maigidan ya dawo saiku yita a gabab shi zaifi amma haka ba daidai bane gaskiya. Zama kan ai dole inyi a gidan nan har na kare kwanakin da zanyi kasan nan amma saina tonawa wanan yar iskan asiri kafin in wuce. Bako a cikin gidan nan ba don ko yini bakya yi a cikin gidan yau balle kwana sai ta jefo min wani kallo nace kwarai kuwa In kina musu ne mu zuba dake ga key nan na mika mata ina kallon ta. ZAINAB IDRIS MAKAWA ANA DARA, , , , , , , , , BY ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , , , , , 1️⃣1️⃣4️⃣ BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM, , , , AL, RASHID, , , , , , YAR UWA KIJI TSORON ALLAH KI DAINA FITAR MIN DA NOVEL DON KIN BIYA KI BARI WANI YA BIYA SABODA ALLAH👋 Kallon fuskana tayi itama da kyau wanda da alama mamakin karfin hali irin nawa take mamaki wai har itace karamar yarinya ke fadawa irin wanan gatsen a gidan mukhutar yau gidan mijinta da take da iko da ko ina na gidan. Hannu takai da niyar figar key din daga hannuna amma sai taji kamar wani abu ya soketa a kafadanta haka kuma hannunta ya rike a wuri daya taji bata iya mikashi. Acikin mamaki ta dago kai ta kalleni kamar zatayi magana sai kuma ta kara kai hannu da niyar ta karba da sauri naga taja baya ta juya da sauri ta tafi tana dan sauri a lokacin. Binta kowa yayi da kallon a cikin mamakin abinda ya hanata karban key din daga hannuna a yadda tayi niyar fisganshi da karfin dole. A lokacin muryan mama kanwar hjyn su mukhatar ke fadin duk iya shegen mace da shu,umancinta ai tazo karshe yanzu. Duk yadda akayi akwai abinda tagano kukaga ta juya da sauri haka mama din ke fadi cikin takaici da bacin rai ga irin halaiyan falmata din. Idan kaga Allah yayi halittanshi ga bawa to kabarshi kawai da abinsa ko kabi shi da addua don Allah kadai yasan dalilin yin bawanshi a hakan daka ganshi. Naga biyu ke nan a rayuwana wana matsalan jinnun na sahiba ga inda zaiyi ranan nasa a yanzu haka a baya kuma ya taimaka mata wurin kareta daga sherin yan uwan mu. Yau, da,ace badon mutanen dake saman kan yarinyar nan ba masu karfine haka da yanzuma an share tarihin ahalin yaya sambo ga baki daya a duniyan nan gaskiya. Saboda ko irin sherin dasu yaya Nuhu suka shuka a doron kasa ko littafi baya daukan shi kai tsaye haka don a lokacin har muna ganin ta tarowa kanta mutuwa sai gashi yau sune suka kare a tsare a gidan wakafi suna daure don kawai son abin duniya da suka kwallafawa rayuwan su. Ga na biyunshi yanzun ma na gani a gabana don wanan matar tana ganin kawar da sahiba ba aiki bane a wurinta yasa tazo har nan da niyar tozarci da kazafi a gareta. Sai gashi farat daya ta fara raina kanta da abinda ta taka lokaci guda don tsafinta baiyi tasiri akan sahiba ba kenan a yanzu yadda alama ya nuna hakan nidai na fahinta . Don kila dama da shirinta tazo garin nan don kawai tayi tashin hankali da fitina ta batawa mutane zukatansu don irin su haka suke da jan fitina ga abokan zaman su dama dan kada a zauna lafiya. Allah sarki aida tasan kanta kawai su zauna lafiya shine alheri yanzu a gareta don ba kowane sihiri yake kamawa ba don wasu baya tasiri a jikinsu amma tsafi ko wani shirka da takeyi can sam ba zai taba tasiri a wurin yar mu ba gwaggo ta fada. Abinda hjyn mukhutar ke nan ta fada itama har ta dage saida akai auren nan nasu gashi yanzu kuwa abin yazama alheri a yanzu tunda har ga rabo an fara samu na diya. Falmata ta shuka tsiyataku iri iri a gidan mukhutar tana ganin ba wanda ya isa yaja da ita tako ina saiga Allah ya kawo yar nan a cikin rayuwan su a yanzu. Har yakai hjy da kanta data haifeshi bata isa ta tashi taje gidan danta da sunan ziyaran kwanaki ba haka kuma bata isa a kawo mata diyanshi gidanta ba kai abubuwa dai da dama na nuna isa da gadara boyar Allah nan ta fuskaceshi a wurin falmata . Yanzu kinji sherin da tazo dashi bawai murnan arzikin samun yaran nan bane ya kawota, tazone da wani sheri da zata kafa don tayar da hankalin mutane kada a zauna kalau, shine tazo wai yaran rikonsu aka dauko a gidan marayu ba haihuwan yaran sukayi ba. Wanan kan da hankalinta kuwa gwaggo Amina ta sake tambaya don mamaki daya cikata lokaci guda a wurin tana kallon al,ajabi a filin Allah. Tsab take shedanane irin nata tana ganin uban kowa tana iya yiwa wullakanci balle wanan da take kallo a makiyiyar ta a yanzu fiye da kowa. Umma dai suna daki da yara ita da Fatima duk wanan abinda akeyi a katon falon gidan su basu sani ba don haka duk yadda hjy falmata taso taga yaran a lokacin abin bai yuyu ba gareta. Da yake gidan babban gidane bamu san wainar da suke soyawa ba a inda suke sai gashi mun gansu sun fito sun tafi ko magana basuyiwa kowa ba a lokacin. Lalai kin haifu Sahiba a cikin iyayyen ki yau Falmatace tayi saurin saduda haka har ta iya barin gidan nan kamar yadda kika fadi ba zata kwana a nan ba ba tare da wani hayaniya ba haka. Zaune yake a office din shi suna aiki wayan shi yayi kara ya dauka yayi mamakin ganin kiran yar babba yasa a lokacin da sauri yakai hannu ya dauki wayan. Yana ambatan sunan ta yake cewa ya suke ? lafiya daddy ta fada kafin ta soma fadin na dawo na samu mommy mu wai ta tafi Hong a yau din nan da safe ita da Anty Nafy. Hong ya ambata hankali a tashe yana fadin ina office yanzu zanje gidan na duba idan sun shigo OK daddy ta fada tana kashe wayan yasan yarinyar bata da hayaniya kamar ba falmatace uwar data haifeta ba. Yadda ya shigo gidan zaka gane hankalin shi a tashe yake lokacin haka ya karaso yana kallon fuskana ko zai gane wani abu ga yanayina. Bai fahinci komai ba don kamar kullun yadda na saba taron shi na taryeshi da sannu da zuwa ina gaidashi da aiki kafin na gabatar mai da abinci duk da nasan baya cin na rana a gida. Baiki ba yace yagode bai zauna ba su gwaggo ya duba suka gaisa yayi masu ya gida kafin ya juya zai koma falo yaji muryan kanwar mahaifiyar shi tana fadin. Falmata tazo yau din nan da wani sabon zance da mukaji a bakinta wai yaran nan ba diyan ku bane daukosu kukayi gidan marayu don ku tayar dasu . Daga inda yake tsaye yake ambato sunan Allah har yakai ga dafa bango yana fadin wanan wani irin zancen banzane haka mama ko dai falmata ta haukacene wai ? Shina gani don kishin ya koma mata kamar hauka yanzu kuma mama sunana falmata take son batawa kome don wanan ba fatima tayiwa sheri ba ni kaina tayiwa sheri ai a idon mutane don ta sheganta min yaya ko me mama ? Ina tsaye bakin dinning din ya fito da yanayinshi da gabadaya ya kara sauyawa a lokacin fiye da yadda ya shigo da farko gidan. Zama yayi ya kurawa waje daya idanu na dan lokaci kafin yace ya kukayi da Falmata data zo ? Kallon shi na danyi kafin nace nothing naci gaba da abinda nakeyi da wayana nothing bayan yanzu mama ke fada min abinda tazo tayi a gidan nan ina son jin komai daga bakin ki yanzune. Ban boye mashi komai ba har abinda na fada na kwashe tas na fada mai yana saurarena har na gama fadi ya jawo wayanshi da sauri na dan rike hannun shi ina girgiza kai. Kallona yayi nace kada ka kirata don Allah ka barta wanan fadan tunda bata sakaka a cikiba fadane namu na mata so ka barni da ita kawai. Falmata bata da kirki don hakane nake son nayi mata iyaka akan diyana duk Iskancinta zan iya hakuri na daure da komai da take min a kaina amma wanan sam ba zan lamunci hakan ba. Ina son diyana fiye da komai dana mallaka a rayuwana don haka zan iya sabawa kowaye yake son sheganta min jinina zufana da nayi wahala a wurin samun su. Kaina yana duke duk yake wanan maganan ina nazarin abinda yake fadi watau dai ko ya kuke dashi zai iya sabama idan ka taba mashi diyanshi. Jin yayi shiru yasa na dan dago kai na kalleshi yana zaune ya hada hannayen shi biyu saman kanshi ya dafe sai naji tausayin shi ya kamani lokaci guda haushin matar nasa zanji kome a yanzu ? Don na fahinci ashe ba karamin zance bane ta fada sai a lokacin nake nazarin zancen na gane me hakan yake nufi mikewa nayi daga inda nake zaune a hankali. Na taka zuwa inda yake zaune din cikin yanayin damuwa hannuna nakai a hankali saman kanshi ina fadin uncle kayi hakkuri mu bita da addua a yanzu. Da sauri ya dago kanshi ya dubeni idanuwanshi nagani sun kade a lokaci guda sunyi jawur dasu alaman bacin rai karara a idanun nasa. Da kyar ya bude bakin shi yace Falmata ba iri mata nan bane masu saukin kai hakana tana da matukar wuyan sha,ani sosai sam bata da fahinta abinda tasa a gaba shi take gani daidai a gareta. Ina mata ragowa da farko don mahaifiyatace amma daga baya saina fahinci su basu san hakan ba don a yanzu suna ganin kamar sunfi karfinane bata san ina raga mata bane a yanzu don hjy din da kuma yayan mu a yanzu. Bana son yarana su shiga cikin damuwa idan na sabawa mahaifiyarsu dolene abin ya damesu amma sam ita bata duban hakan tana ganin kamar duk abinda tskeyi fin karfina tayi yanzu din. Ta manta da cewa nine sillar mayar da rayuwanta haka cikin inganci ta manta cewa a innuwana take shan iskan rayuwan da take taka kowa dashi yanzu. Idan kayi hakkuri ka lalabata zata daina wanan tanayin shine yanzun a cikin zafin karin auren da kayi mata don haka ka lalaba ta ku fahincin juna ku zauna lafiya. Shiru yayi yana saurarena kafin ya nisa yana fadin fatima you are wonderful and best among the best mm agode da baki kasance irin matan nan masu hali irin nasu falmata da ace wanan halin kike dashi yau nasan sunana zai baci a idon jamma,a. Babu macen da za a zo har gida a batawa diyanta suna haka kuma har ta shanye hakan ba tare da ta dauki wani mataki ba haka . Idan ma na dauki matakin ba zaikai wanda Allah zai daukar min ba idan na kyaleta da halin ta idan kuma tana da rabon shiryuwa Allah ya shiryamu baki dayan mu amin muka fada. Nayi hakan ne a gaban shi don kada yasan kalar kishina don ba karamin tausan zuciyana nayi ba a lokacin har na nuna ba komai a zuciyana game da wanan haukan nata da tazo tayi muna a gida. Saidai nasha alwashin cewa zanyi kokari nayi ta daurewa ina nuna sanyi a zuciyana kamar yadda matan yarbawa suke taushe zukakatan su akan kishin mijinsu wanda kai bare ba zaka taba gane hakan ba garesu. Saidai zan manna mata karamin hauka a kaina ta yadda zan sace zuciyar mijin na rike a hannuna na juyashi yadda bata son ganin shi da ko wace mace a duniyar nan. Tayaya zanyi hakan ba wani abu bane me wuya tunda kowa yasanshi zanyi kokari na yaki zuciyana bazan yarda na taba zancen abinda ya shafi hjy falmata ba a gaban shi. Haka koda wasa ba zan taba nuna gazawa da yan uwanshi ba ko wani mutum da wata halaka ya hadashi dashi har na sanshi koda kuwa masu aikinmune irin maigadi da mai waki ko cookers da sauran su zuwa abokan hurda da yake girma da arziki dasu. Fanin gyaran jikina koda yaushe na koma kamar yarinya wanan ya zama wajibi a gareni ko yaushe jikina gidana ya kasance min a gyare. Haka kyautatawa a tsakanin mu ba gazawa ko kissa balle cutarwa tunda ni bai cutar dani ba ya zama dole nafishi son diyanshi da duk wani nasa a yanzu idan na dan kwatanta haka ina ganin na wadatar da yadda nake so. Sun gwaggo satin su biyu a can suka dawo gida inda suka barni tare da ummana da dan uwana Ammar wanan shine sillar dawowan ummana a tare dani. Hakan ya batawa yan uwan mu na kaduna rai sosai da suka fahinci cewa umma ba zata dawo Nigeria ba kuma ta zauna a nan din. Don wai da har ana shirin cikin baffah Abdullahi ko baffah hamza daya ya nemi umma ya aureta sai gashi na dauke uwata na tafi da abata can inda mukai masu nisa. Haka bai hanani yo masu aike ba lokaci lokaci sanan kuma zan bisu daga daga na aiko masu da sako mai ingaci a garesu wanda hakan ya jawo min farin jini da kauna garesu. Zuwan mu na farko Nigeria mun zone lokacin da Fatima da Ammar suka samu hutu a makarantarsu a lokacin har yarana sun iya tafiya don suna da shekara uku da haihuwa a duniya. Don haka ba wanda yasan yanayin su koda mukazo din dasu lokacin sallahne don haka a Maiduguri muka fara sauka . Mun samu an gyara muna gidan mu sosai ba kamar yadda muka barshi ba a baya can yanzun an kara gyarashi yayi kyau sosai ga ganin mutum. Hjy Falmata tazo a wanan shekaran don bukin sallah din duk da ita tana zuwa duk shekara nima don kawai ga irin yadda muke da yan uwanane yasa bandamu da zuwa ba na share kowa na zauna can tunda ga mahaifiyata a kusa dani yanzu. Hjyn su mukhutar ta kara dan tsufa amma da yake akwai kulawa ba zaka gane hakan ba gareta sosai tare sukazo da uwargida falmata daga Paris don haka sun rigamu shigowa Nigeria su don mu sai washegari muka iso . Amma bai zo gidan namu ba sai safiyan sallah ya kama ranan jumma,a za,a hau idi a Nigeria, ba wani aiki a gidana don sister tace kada muyi komai zasu kawo muna daga gidan hjyn su idan an girka a can. Da safe ina daki kwance ya shigo kafin aje mosque yana cikin shirin shi na babban kayan day saka a jikin shi wanda ya fito mai da shekarunshi a fili kana ganin shi zaka hango kamalla da kasaita a tare dashi ga kwarjinin shi a fili. Daga inda nake zaune nayi mai ina kwana duk da banji dadin rashin nuna kulawanshi da bai nuna muna ba lokacin da mukazo, duk da na kirshi bayan mun sauka din. Sai baizo ba bai kira ba don haka na danji zafin hakan a raina, kisan halin namiji mijin mace biyu baibar kowa ba don haka yanzunma shima a tsarge ya shigo din yana dan kame kame amma haka na daure na nuna ba komai a zuciyana kamar yadda na saba yi mai duk daya fahinci hakan gareni a fuskana. Bayan na gaidashi yana min ya hanya na basar tare da fadin har zaku tafi mosque ke nan yanzu ina duban lokacin a wayana. Time ya kusa ya fada a kasalance yana gyara tsayuwan shi lokaci guda ba tare dana kalleshi ba nace sai a tafi dasu babami suma suje su hau sallah idi yace OK idan zasu yarda ai saimu tafi nima zanso hakan ya fada har lokacin yana kallon fuskata. Mikewa nayi daga inda nake da sauri na fita na barshi dakin tsaye ya bini da kallo tare da mamakin hali irin nawa yana girgiza kai. Na samu umma ta saka masu kayan da wani kanin mukhatar din ya dinka masu don hawan sallah idi don tun muna can ya turo min photo kayan a waya. Dan Allah ya dorawa yaran farin jini sosai ga wanda ya gansu sai yaji yana son su a tare dashi kaunarsu yana shiga zuciya farat daya ga wasu . Ida mai karatu baki manta ba farko labarin mukhutar din na fada maki wanan guy din sunzo wurin shi tare da mahaifiyan shi kan a taimaka mashi da sana,anyi a lokacin. Mahaifan shine wanda suke mahaifan su daya dana mukhutar din kanin mahaifin mukhutar dine da har yayi sanadiyan daukan mukhatar zuwa kasan waje dashi sai suka samu matsala dasu a lokacin kuma ya hadu da mahaifina. Yanzu muna zaune tare dashi a can shima yana zuwa yana dawowane don international business sukeyi dashi ta haka nake samun daman turo kayana zuwa Nigeria wa anty Amarya da mommy dasu gwaggona Amina da kudidi suna sayar min. Ina kuma turawa sisters dinshi suma sai gashi Allah yasa muna albarka sosai ga harkan suna samu ina samu sosai ayanzu ga aikin company da nakeyi a can tare dasu. Wanda koshi saida akasha fama sosai da jidalin hjy Falmata don tace itama sai tayi aikin irin nawa karshe ma dai yace to tafito itama ta fara aiki irin nawa din tace kuma bata yarda da hakan ba tunda bata iya ya sani. Sai dai ya dinga biyanta albashi da kudi daidai wanda company ke biyana a bata itama hakana . Don yace bai yarda ba shine sukai jidali kanshi sosai dole tazo ta hakkura ta barni ina aikina da nake jin dadin yinshi sosai araina. Wanda hakan yana kara dauke min hankali ga komai ina kula da yarana da mahaifiyata da yan uwana dake tare dani sosai da kuma aikina shi maigidan idan yana kasan mijine idan kuma ya tafi sai Allah ya dawo dashi lafiya kuma aikina dai inayin abina yadda ya dace ban dorawa kaina wahalan duniya akan namiji ba. Yaran na riko daga dakin umma muka fito zuwa part dina sai muka hade dashi a falon tun daga nisa yake sakar muna murmushi har lokacin dana karaso dasu inda yake tsaye. Mamaki ya fada har yaushe akai masu wanan dinkin haka ya fada yana mamaki nace Abba ne ya dinka masu kafin muzo kai ya jinjina ya mika hannu sai yaran sukaki zuwa gunshi. Murmushi nayi a cikin harshen yarbanci nayi magana dasu suka dan kalleshi lokaci guda da kyar suka bishivdon basu saba dashi ba sosai saboda zaman da bayayi damu sosai. A sauko lafiya daga masalaci ya wuce da yaran gidan sarki daga gidan sarki suka nufi gidan shi a can ne suka kwasa da hjy falmata wai don me zaizo mata da yaran gidan ta. Sun danyi sa,insa dashi inda ya kwashe duka har da yaran ita falmata din suka wuce zuwa gidan mahaifiyar shi ancen yake fadawa hjy abinda falmata din tayi kan yaran yake fadi wana zai kawo masu babban matsala a tsakaninsu. Sai gasu gidana lokacin duk muna falo a zaune har Ammar taro na mutunci suka samu a wurin mu ina jin yaran na tambayan shi who is she Dad ? Your stepmother ya basu amsa sai dayan tace but mum told us that she is wicked and,and also a witch she is too dangerous i mean mun said. But she is nice dayan ta fada to nima shinagani ai amma mum tace muyi hankali da ita ta fada tana dan satan kallona inda nake tsaye ina cirewa yarana kayan jikinsu da yai masu nauyi ajiki. Wani tsawa ya dakawa yarinyar lokaci guda har ta dan kadu yake fadin she is my wife yaranta kuma sune blood brothers din kune nan ya shiga yi masu bayani suna kada kai. Dakina na koma don yayi baki a lokacin saidai raina yayi matukar baci jin yadda matar shi ta batani a wurin diyanta duk saboda kishi . Kinshin da ba a gida daya muke zaune tare da ita ba a lokacin amma saboda tsananin kishinmuna mata ta batani haka a wurin yaranta da haka suma zasu taso kishin su ya girma a zukatansu. Na gama fadawa umma komai ta nisa tare da fadin ai yadda ya nuna shine daidai tunda yatsawata masu atake kuma yayi masu nuni da suso yan uwansu na jini a zuciyar su. Da dare ya dawo gidan mu a nan zai kwana saida na gama hada mai komai da yake bukata kafin ya kwanta na juya zan fito. Naji muryanshi yana fadi ina zaki naso muyi dan magana dake yanzu ya fada hankalinshi akan laptop din dake gaban shi tun shigowana dakin yana aiki a cikinsa. Zan ba babami magani naji kamar mura nason kamashi OK baida matsala ya fada tare da dan dago kanshi a lokacin na juya na fita har lokacin bawai na sake bane hakana. Nasamu yaran suna barci a jikin umma na shiga dakin take fadin kiba yaron nan magani kafin barcin shi yayi nisa na amsa da shina dawo in bashi a yanzu. Da taimakon umma na bawa yaron magani kafin naji ta ambaci suna na juyo take fadin kada wanan zancen yasa ki sauyawa mijinki a yanzu sahiba. Idan kinyi duba ga irin halin abokiyar zaman ki meye laifin shi a cikin zancen nan tunda bashi ya haliccetava haka ba. Yana iya kokarin shi wajen gani hankalin ku ya hadu wuri daya musanman yaran nan nasa kinsan bada son ranta bane ai ya kwasosu zuwa gidan nan yau . Don data sani bazata taba yarda da hakan ba tunda tana da mugun akida a zuciyanta na rashin fahinta. Don haka kada ki dauki wanan zancen wani abu har ta hanaki jin dadin rayuwa keda mijinki dama abinda takeso ke nan tsakanin ku ko yaushe ya faru. Umma naga ban damu da zancen taba ban kuma sa kaina cikin sha,anin yaranta ba don me ba zata barni ba na zauna lafiya a inda nake ? Sahiba kishin matan arewa daban yake dana sauran mata idan kinyi tunane wanan ne ya jawo matsala maigirma a tsakanin mahaifinku da yan uwanshi duk a saboda dalilin kishine hakan ya faru. A yanzu zakifi maida hankali wajen ganin cewa yaranki sun san yan uwansu kikuma koya masu kaunar suso su a zuciyar su kamar yadda mahaifinsu ke kokarin yi a yanzu. Nasiha sosai umma tayi min kafin muyi sallah na tafi na shirya a dakina zuwa turakan maigidan duk da na samu ya hada har ya kwanta a lokacin. A hankali naje na kwanta daga gefen shi a zato barci yakeyi a lokacin don haka nayi adduan kwaciya na kwanta a hankali don kada na tayar dashi. Minti kamar uku tsakani naji muryan shi yana kiran sunana a hankali na bude idona dana fara lumshewa zan fara barci. Iam sorry idan zancen yarinyar nan na dazun ya bata maki rai kinsan halin Falmata bansan ko yaushe zata fahince mu ba nasan kina kokari wurin yin hakkuri da halinta don haka ina rokonki da kici gaba da hakurin da kikeyi ko dan sabodani. Bazan iya canzata ba saidai ina addua a ko yaushe gareta damu duka baki daya koda bata gane gaskiya a yanzu ba dole watarana zata gane hakan insha Allahu. Nisawa nayi a hankali na gyara kwanciyana kamshin jikina yakai ahancin shi lokacin ya lumshe idon shi cikin wani yanayi zanyi hakkuri da duk abinda hjy zatayi min amma ban iya wani hakkuri da wullakancin da kai zakai min saboda wata. I don't now why da zamu shigo garin nan na buga maka waya mun iso tun wajajen two na rana amma kika zuwa gidan nan a jiyan na dauka yanzu ko bakazo bacdon ni da yan uwana zakazo kaga saukan mu don diyan ka yanzu. Na sani mu muna iya hakkuri da duk wani halin da zaku nuna muna tunda mun shiga rayuwan ku da rana tsaka tana ganin munzo a lokacin da bai dace ba cikin ku. Duk da bawai so ko kauna yasa ka aureni ba don in zauna tare da kai sai tausayi zalla namu da kakeji yajaka kwadayin aurena a lokacin da sam aure baya cikin rayuwana a lokacin. Ka tursasani akan dole kaida iyayyena kuka tilastamin adole nashiga rayuwan ku da ayanzu nake ganin kamar mun zama dolene. Innalillahi haba Fatima keda bakinki kike fadan haka yau don kawai andan samu akasi a wurina jinyan nan koda kuka iso ina tare da emirate muna ganawa dasu. Ban samu kaina ba wallahi sai goma da rabi na dare har lokacin wallahi kuna a raina saidai nasan a lokacin kunyi barci don kun gaji amma kiyi hakkuri insha Allahu hakan ba zai sake faruwa ba damu. No ka daina bani hakkuri don mu da yan uwanmu suka gujemu ka tallafe babu nuna kyama a garemu ai kai ya kamata mubawa hakkuri idan mun saba mane ? Murmushi naji ya sauke kafin ya mirgino zuwa inda nake ya rugumeni a jikinshi yana sauke numfashi tare da fadin kada ki taba tunanen irin hakan gareni. Don in ban rikeku ba haka ina raye Allah bai hana mun ba sai Allah ya tuhumeni gobe kiyama kuma ki sani matsayi biyu kike dashi awurina . Ke mamatace a yanzu kuma amana a gareni daga ke har mahaifiyar ki da dan uwanki duk zaman amana kuke a wajena yanzu. Hawaye na fara sakewa masu dumi daga idona ya fara lalashina don jin sheshekan kukana dana fara a lokacin. Sallah da kwana biyu rana da zan fita girki muka shirya umma da yara muka tafi gaida hjy mahaifiyar mukhutar a cikin rashin sa,a mun samu falmata ma taje da nata iyalan a lokacin gidan. Nan aka fara kallon kallon a tsakanin mu dasu don shigar mu da yanayin mu ya fara firgitata don an dade ba,a hadu ba ga yadda yan uwan miji ke wani haba haba da ni da yarana suna ba umma wani girma na musanman a wurin. Ganin hakan ya tayarwa hjy falmata din da hankali sosai bata dauki lokaci ba ta mike tana fadin su tafi mukarrabanta suka mike sukabi bayanta a fusace. Tun a mota ta soma fada tana fadin you see kunga yadda ya daukaka rayuwan mutanen nan suka canza ga baki daya haka. Yaran ga baki daya ai ya mukhutar suka dauko ga kama sai farine kawai na uwarsu dayansu ta fada shiyasa na rufawa kaina asiri da wanan shawaran da geshuwa ta bani da farko wai nace ba yaranshi bane. Akan hakan wancan lokacin yayi min saki daya kan wanan zancen shiyasa yanzu bana daukan ire iren shawaran nan na banza don ko makaho ya laluba yasan jninshi yaranan. Kai jisu farare tas kamar ka dauke karamar ta fada wa yan nan bakaken da kika rainane naku ta fada a fusace don sai taga kamar yar uwan ta raina nata diyan ke nan . Shiru tayi kafin ta fada afusace waya sani ko mai ake shafa masu don su burge mutane wanan farin aiyayi yawa haka ga yara tunda ba diyan turawa bane su ? Haka suka kai gida yan uwan na bayan mota suna tsunkular junansu suna mata dariyan kyata don sunsan gaskiya saidai suna tsoron su fada a fili ta hausu da sababi. Sai dare muka dawo gida daga gidan hjy din don washegari zamu tafi kaduna don bandauki hutu maiyawa ba sati biyu kawai zanyi na koma Hong . Don haka saida muka shirya tun kan mu fita zuwa gidan hjy mukhutar din komai na tafiya mun tanadeshi lokacin. Washegari samako mukayi don a mota mukai tafiyan saboda zamu tsaya yola wurin yan uwan mu shine ya bamu manyan motocinshi uku kayi tafiyan dasu. Mun isa yola da dan sauran lokaci mun bisu daga daga muka kwana biyu daga nan muka dauki hanyar kaduna . Mun samu tarbo na mutunci wanda ban taba zato haka ba daga wurin yan uwan namu ko wanan karon a gidan daddy muka sauka inda mommy sai wani haba haba takeyi dani da diyana da umma. Hakama anty amarya ta rasa inda zata sakamu a lokacin don jin dadin ganin yadda rayuwan yarta ya koma a hannuna gashi kuma da Amirah zamu tafi itama zata karatu awurina . Muka fita zaga dangi don na samu anyi auren Faiza da Bello a lokacin ita da Anty hauwa sai anty nabilace batayi aure ba gamu har gidan baffah nuhu suka taremu a cikin mutunci har wasu yaransu munyi gaisuwan mutunci dasu lokacin da sukaji nazo . Anan suke min korafin baffah nuhu din baida lafiya a can prison din don kwanaki ma saida aka kirasu ana sheda nasu wai ya rasu ashe dogon suma yayi sunje an kwantar dashi asibiti. Yanzu dai ya dan samu kafiya amma jikin sai a hankali har yanzun dai gashi ba,a barin aganeshi koda anje wurinsu saboda irin tsaron da ake masu a wurin. Naji badadi dan jin hakan saidai banyi wani abu ba a lokacin daga nan gidan ya Abubakar muka nufa mun sameshi a gida. Matarshi taso ta share mu da muka shigo tana wani kwasan iska damu saidai kome ta gani sai gata ta dan sake har tana tsoma baki a cikin hiran mu dashi. Don sosai shikan ya nuna kulawanshi garemu ya nuna kamar kanwarce ta ciki daya nake gareshi ya dauki yara ya dora a saman jikin shi sai zolayana yake a kansu. A nan wurinshi nake jin ashe suna hurda sosai da uncle yanzun, ban sani ba don a bakin shi nake jin wai uncle ya gina wasu company da sunan su babami ana gab da karasasu yanzu haka. Kallona Nazifa tayi da mamaki nayi kamar ban ganta ba lokacin zamu wuce sai gata tana fadin na bata number na mu dinga waya. A wurin mota ma mun dade da ya Abubakar din muna magana dashi akan su baffah nuhu dake tsare su kuma su gefe dasu umma suna dan taba hira . Kwanan mu biyar a kaduna muka barsu cikin dadin rai ana haba haba damu kamar wasu kwai a lokacin don kowa naji damu. Nan muka barsu cike da alhinin mu don dan hakin da suka raina gashi a yanzu mun dawo mun tsone idanunsu yanzu kuma. Abinda dai basu so yana biye damu don Alkawarine na Allah garemu arziki daga Allah muka gajeshi don nayi abubuwa da dama a kadunan kafin na koma maiduguri. Ban bar kasan ba saida uncle ya shiga ya fita aka sako su baffah nuhu da yan uwanshi da alokacin suyi nadama yafi dubu na kashe mahaifina. Gashi mun barsu da nauyin don munki karban ko kwandala daga garesu haka kuma ko maganan bamu karayiwa wani ba. Uncle mukhutar kuma ya rike mu tsakani da Allah ba cutarwa nima ban matsa masu ga shiga harkan iyalanshi yanzu akarshe dai fatima ta auri ya mustapha duk da mahaifiyar shi bata son haka amma Allah ya zana hakan garesu mukazo Nigeria aka sha buki. Yarana hudu a lokacin gidan uncle maza uku mace daya ina kara godiya ga Allah da ya nuna muna rayuwa ingantace dani da mahaifiyata da dan uwana Mai karatu nagode da lokacin ki da kika bani muka kai ga karshen labarin sahiba da yan uwanta Allah yasa mu anfana da duk ilimin da muka samu a cikkn labarin sabanin hakan Allah ya gafarta muna Allahuma amin. ZAINAB IDRIS MAKAWA