Ruɗin Ƙuruciya                               31 A hankali ya ƙaraso in da Farhan ke tsaye, yasa tattausan hannunsa ya riƙo nata, ya matse a hannunsa ya kalli cikin idonta. Hakan ya saukar mata da kasala ta sunkuyar da kai daga kallonsa saboda kwarjinin da yai mata. A hankali cikin wata irin murya da ita kaɗai take jin meyake cewa yace "A karo na biyu bayan neman soyayyar ki, zan nemi Alfarma a gurinki Farhan, dan Allah ki amince na gaji da abunda suke min akanki Please Farhan" Shiru tayi tana jin yadda zuciyarta ke wani irin bugawa, gumi keta keto mata kota ina, ba ta gama yanke hukunci ba, taji Sadik ya haɗata da jikinsa, ya haɗe bakinsa da nata. Wata irin tsuma jikinta yake yi, ta rasa gane a wani yanayi take, tsoro ko kuma haushin Sadik, duk da yadda Sadik ɗin ya riƙeta gam, amma ji take tamkar zata faɗi ƙasa, dan haka ta sa hannu ta rirriƙe shi karta faɗi. Wani irin ihu da shewa suka ɗauka a gurin nan Gaba ɗaya, seda mintuna uku suka cika cif sannan Sadik ya cika Farhan. Idanunta sunyi rau rau kamar za tai kuka, se ajiyar zuciya take kamar wadda tai gudu. Nan akaita tafa musu, Nas yace "Weldon gaskiya abokinmu da his wife to be, kun burge kun ƙayatar kuma ka tabattar mana da cewa kai....." Se kuma yaƙi ƙarasawa. Aka yanka cake amma sam Farhan hankalinta baya jikinta, ji take tamkar ta aikata wani gagarumin zunubi da Allah baze yafe mata ba, take taji nadamar zuwa gurin partyn ta baibaye ta. Da sauri ta silale ta tafi in da aka shiryata, ta cire rigar jikinta ta ɗau kayanta ta saka, wasu irin hawayen nadama suka shiga zarya a fuskarta. Ta fito harabar gurin tana ƙoƙarin fita Sadik ya biyota yana ƙwala mata kira, amma taƙi tsayawa, cikin hanzari ya koma ya ɗakko mota, yaja ta da gudu yabi bayanta. Su Nas kuwa dariyar mugunta suka dinga yi, Amin yace "wannan ne karonsa na farko da yayi, amma kamar ƙwararre dama can a matse yake, da haka da haka dai" Babba yace "Aiku kuka ɓata abun da kuka hana ai amfani da ƙwayar nan wallahi" "Dan ubanka idan anyi amfani da ƙwaya muyi yaya da su a gurin nan? Kuma ka san ba komai ake bashi ya karɓa ya ci ba, amma sannu a hankali se mun sa shi a layi" Amin yace "hakane, Amma a hakan ma muny nasara ai" Suka cigaba da dariyar mugunta. Wani wawan parking Sadik yai a gaban Farhan, ya sakko yana faɗin "Farhan meye hakane kikeyi? Ki tsaya in maida ke gida mana" Cikin kuka ta kalleshi tace "ba zan tsaya ɗin ba nika ƙyaleni" "Ba zan ƙyalekin ba, ki wuce mu tafi" "Bazan wuce ɗin ba" Fizgota yai da ƙarfin gaske ya dannata a mota, yaja motar da gudun tsiya ya bar gurin. Sosai Farhan take masa kuka iya ƙarfin ta, amma be saurareta ba, seda ya dangana da unguwarsu, sannaan yai parking. Ya kalleta yace "Farhan me nai miki hakane?" Wani irin mugun kallo tai masa, ta fara ƙoƙarin buɗe motar, amma yai saurin cewa "ok i understand, dan Allah kiyi haƙuri nayi kuskure amma hakan shine mafita kawai a gareni" Buɗe motar tayi ta sauka, ta nufi lungun gidansu da sauri. Sadik ya dafe kai ya jingina da motar yana dana sanin biyewa su Nas. Ta samu guri ta zauna ta sha kukanta, kafin daga bisani ta goge hawayenta, ta tashi ta nufi gida, tan daf da shiga gidan sega Sunusi, yana ganinta ya washe baki yace "me sunan larabawa, daga ina haka?" Ko saurararsa ba tayi ba, ta shige gida sedai tun a soro ƙirjinta ke bugawa, gani take tana shiga Asirinta ze tonu. Ta daɗe a soron a tsaye sannan tayi sallama ta shiga, Umma na tsakar gida tana tankaɗe, ta ɗaga kai ta kalli Farhan, ta amsa sallamar ta maida kai ta cigaba da abunda take yi. Dama hakan umman take mata tun a baya, amma wannan karon se ta tsargu ta ga kamar Umman na san karantar wani abu a tare da ita. Ta daɗe a tsaye sannan ta shiga ɗakinta, tana shiga ta nemi Guri ta zauna ta cigaba da kuka, wai yau ita Sadik yasa bakinsa a nata a gaban jama'a ba kunya bakomai, shikenan ya zama ɗan iska itama yana son ya maida ita. Duk da ta cire wancan kayan, amma natan ma da ta mayar ƙamshin turarensa suke, cikin hanzari ta tashi ta cire kayan, amma ta fuskanci ba iya kayan ne keyi ba, jikinta ne yake ƙamshin turaren nasa. Addu'a ta dinga yi akan Allah yasa kar Asirin ta ya tonu, a gane in da taje da abunda ya faru. Har zuwa dare, amma taƙi sakin jikinta ta kasa sukuni, ga damuwa da fargaba duk sun cikata. Ko yunwa ba taji balle taci Abincin dare, haka taje ta kwanta, hakan be damu Ummanta ba balle taji ba'asin dalilin ƙin cin Abincin nata. Sosai Sadik ya damu da yadda Farhan tai ta kuka, nadama duk ta bi ta lulluɓe shi da dana sanin biyewa abokai, ya dinga tunanin ko a wane hali take? Ko ta dena kukan Allah masani. Sedai wani ɓangare na zuciyarsa ya kasa tantance nishaɗi yake ji ko kuwa? Abunda ya faru tsakanin su yai matuƙar tsaye masa a rai, he really enjoys it, abunda ya daɗe yana kwaɗayi ne dama, sedai damuwar da ya ganta a ciki ya hana shi sakewa yaji nishaɗin yadda yakamata. 'Auta yau ina ka shiga ne, for the whole day ban ganka ba, ba ka zo inda nake ba, rabona da kai tunda ka tafi school" Beji shigowar Mother ba sam, se maganar ta da ya ji, a hankali ya ɗan gyara kwanciyarsa yace "bakomai Mother" "But it seems like something is going wrong somewhere, na ganka wani iri" "Bakomai kaina ne yake ɗan min ciwo, kuma na sha magani" "Naga Abincin ku a falo, kaɗan aka taɓa kaci kuwa?" "No, naje gurin friend ɗina bayan sallar juma'a a can nai lunch" "Anyway shikenan, idan kan be dena ciwo ba se a tafi Asibiti" Ya jinjina mata kai tare da lumshe idanunsa, ina ma ba weekend za'a shiga ba ya samu ya kuma ganin Farhan, ya rarrasheta. A ɓangaren gidan dr. Kuwa wato ango sha guɗa Usman, Amarya ta fara fuskantar ƙalubale daga gareshi, duk da irin tarin soyaya da sukai a waje, ta kasa gane kansa yadda yakamata. Usman wani irin mutum ne me murɗaɗɗen hali, gani take kamar ta dena burgeshi gaba ɗaya, da yawa wasu halayen bata san yana da su ba se yanzu, miskili ne na gasken gaske, idan har tai masa laifi ko zata mutu baze ce mata kin min laifi kaza ba, sedai tagavya canza gaba ɗaya ga zuciyar tsiya, nan da nan damuwa ta isheta, taga tamkar canza mata Ussyn a kai ba shine wanda sukai soyayya ba. Wayarta ta ɗakko ta fito falo ta zauna, ta buɗe ta shiga contact ɗinta ta fara duba lambobi, tana zuwa kan wata lamba da aka saka my other half tai ajiyar zuciya da alama, lambar take nema. Nan take ta dannan kira ta shiga sauraren a ɗau wayar. "Salamu Alaikum" Jidda tace "wa'laikum salam, ba dai bacci kike ba?" "Wallahi ba bacci nake ba, nayi aikin gida ne na gaji, ya akayi ne Amarya?" Jiki a sanyaye Jidda tace "Besty dama haka auren yake? "Kai Jidds, yaushe a kai Auren da kike wannan zancen?" "Besty na kasa gane kan dr. Gani nake kamar an canzamin shi, gaba ɗaya na dena burgeshi, duk rawar kan nan da yake a kaina babu, in yi kwalliya in tsuke, amma ko kallo ban isheshi ba na rasa meye matsalar" ta ƙarasa maganar cikin damuwa. Wadda ta ke kira da besty ta gyara zama tace "Jidda kenan, lokacin da nake miki gargaɗi ina ɗoraki a hanya gani kuke Kamar ban waye ba, ban iya soyaya ba, ta yaya ba zaki gundure shi ba, bayan tun kuna waje kan kuyi Aure kin saba tura masa hotunan ki da ƙananan kaya, har video Call kuke da sleeping gown a jikinki, to me zaki da zako burgeshi kuma? Muna school idan yazo hugging ɗin sa kike, you even kisses his cheeks, idan nai Magana se kuce ni 'yar ustazai ce, to ga abunda nake gaya miki nan, abunda zeyi ɗokin kin gama nuna masa a waje, to what next kuma?" Cikin sanyin jiki Jidda tace "hakane besty, wallna gani, kuskure dai na riga nayi shi, amma yanzu meye mafita, ke kaɗai na gayawa halin da nake ciki" "Mafita ɗaya ce, ke dama ɗabi'arki ce zama da English wears kullum kamar 'yar turawa, tunda he's no more appropriating ita, ki koma masa ƙabilarki ta Hausa Fulani, ki duba kayan lefenki ki dinga masa wankan atamfa da leshi, idan yaso ki dinga saka English wears ɗin lokaci zuwa lokaci, Sannan shaƙuwar da ku kai a waje kar ta sa ki dinga kallonsa kamar mate ɗinki, ko ki dinga masa magana ba wani respect, no matter how close you are to each other, he deserves a respect from you shi namiji namji ne, ki dena wannan maganar taki cikin gadara, ki fara da jarraba wannan mu gani, se muga meye next abun yi" "Ka besty i love You lodi lodi, ina yinki Sisyna, insha Allah zan jarraba Allah yasa a dace" "Ameen Allah ya daidaita, kice ina gaishe shi" "To zeji insha Allah" Jidda ta fara tunanin maganganun bestyn ta, wato duk abun nan da suke a school suna ganin wayewa ce ashe yana da negative impact a gaba? Dama duk abun nan da take dan burge Usman kuma a kirata wayayyiya ze zo ya dena burgeshi? In Kuwa hakane Lallai a rayuwar ƙuruciya ana tafka shiirmen da ze zo ya zamewa mutum abun dana sani a gaba. Daga Sadik har Farhan sukuku su kai Weekends ɗin, damuwar Sadik ɗaya kukan da suka rabu tana yi, ya dimga fatan Allah yasa karta rabu da shi a dalilin abunda ya faru. Sedai baze iya misalta zallar nishaɗin da tsananin shauƙin soyayyar da ya shiga ba, a lokacin da yake sumbutar Farhan, wani abu ya dinga ji from no where yana ratsa ilahirin jikinsa, dan gaba ɗaya mantawa yai da batun wani ƙyanƙyami ko wani abu me kama da haka, hakan ya ƙara kwaɗaita masa son Auren Farhan, sabida wani irin sonta da ya ƙara shigarsa. Amma ba ya jin ze kuma yadda ya aikata makamancin wannan kuskuren, dan shi kansa yayi nadamar biyewa su Nas ya aikata abunda be taɓa aikatawa ba a rayuwar sa. Duk yadda ta so jin tsanar Sadik a ranta saboda abunda yai mata amma abu ya gagara, sam ba taji ta tsane shi a zuciyarta ba, mussaman idan tai la'akari da shima be san abunda su Nas suka shirya ba, sedai a jikinta tana jin abunda suka aikata ɗin ba daidai bane, kuma kasancewar sun aikata a gaban mutane, ba za'a taɓa dena kallon su da abun ba. Ba zata iya misalta yanayin da ta shiga a lokacin da abun ya faru ba, dan Tamkar a mafarki haka ta dinga ganin lamarin, kuma ta kasa tantance halinda ta shiga, saboda taji wani abu da jikinta be taɓa bata ba a tsawon rayuwarta se a wannan karon da abunda ya faru ya faru, lokaci lokaci idan ta tuna abunda ya farun ta kanji ta tsani komai, sedai ƙarƙashin zuciyarta na hasaso mata wani yanayi ne me wuyar mantawa. Ranar Monday kuwa Sadik shirin Makaranta yake, amma cike da zullumin yadda ze tunkari Farhan ta saurare shi. Itama nata ɓangaren tunanin yadda zata shiga makarantar take tayi ido huɗu da wanda akai abun a gabansu, dan tana ji a jikinta ta rasa wata kima da daraja da take da ita a idon wasu daga cikin abokan karatun nata. Jibtaka tamkar ta fasa zuwa makarantar, amma idan ta fasa tasan se a tambayi ba'asin hakan, dan haka jiki a sanyaye take aiwatar da shirin makarantar. Seda aka gama Assembly sannan ta shiga makarantar, ta wuce ajinsu tana sussunkuyar da kai, duk wanda suka je gurin tsirarun mutane ne, dan a 'yan ajinsu Lilly ce kawai taje se wasu daga 'yan ajinsu Sadik se Khairat, du du du ba su fi su goma ba, amma gaba ɗaya ta rasa sukuni. Sadik na shiga ajinsu suka hau yi masa ihu da shewa. Be kula su ba yaje ya nemi guri ya zauna a mazauninsa, Nas da Amin sukaje suka zauna kusa da shi, Nas yace "Mazaa, ya ake ciki ne? Munyi ta kiran wayarka ba ta shiga, kuma ka barmu a gurin partyn ba ka dawo ba, ya kaji abun?" Sadik ya ɗago idanunsa ya kalli Nas, kallon da Nas ɗin ya kasa tantance kallon meye. Amin yace "wallahi you did it in the most passionate way, naji haushi da ka hana ɗaukar hotuna ku bada kala fa" Nas yace "ai mun tabattar da namiji ne yanzu, yanzu zaka fara soyayyar morewa ba irin wadda kake yi ba da, ta ƙauyanci, nasan ko yanzu ka samu chance you want do it again ko ba haka ba?" "Shut up!" Sadik ya faɗa da ƙarfi yana dukan benci. "Dan Allah ku ƙyaleni inji fa abunda ya dameni, ku tashi ku ban guri" Binsa su kai da kallon mamaki, meke damunsa hakane? Kasa jurewa yayi, ya tashi ya nufi ajinsu Farhan amma ya tarar Madam Joy na ciki na musu lesson dan haka ya koma ajinsu. Bayan fitar Madam Joy, Lilly taje in da Farhan ke zama ta zauna a kusa da ita tace "mutuniyar ya gajiyar taro?" Wata ƙwalla ce ta zowa Farhan, da tuna a gaban Lilly Sadik yai kissing ɗinta, ta san maybe Zuwa yanzu duk ta gama bawa 'yan ajin labari. Lilly tace "yana ga kamar zaki kuka? Meyafaru?" Aikuwa maganar Lillyn tasa hawayen da Farhan ke maƙalewa ya gangaro kan kuncinta. "Yasalam, Farhan menene?" Cikin kuka Farhan tace "bakomai" "Bakomai amma kike kuka?" Farhan ta jinjina mata kai. Lilly tace "anyway shikenan, bari in ƙyaleki kar in takura miki" Har Lilly ta miƙe Farhan ta riƙo hannunta, ta dawo ta zauna tace "ya akayi?" "Fatima dan Allah kin gayawa wani abunda ya faru agurin nan?" Lilly ta riƙe hannun Farhan tace "i understand you ƙawata, karki damu ni ba wanda na gaywa, ni ba haka nake ba, and is something common in this school, no one will cares, amma duk da haka ni ban gayawa kowa ba, in abunda ya saki kuka kenan ki kwantar da hankalinki" Farhan ta jinjina kai tace "Nagode sosai" "Bakomai karki damu" Ana haka, aka kaɗa jiniyar fita break, Lilly ba ta jira kowa ba ta ɗau littafinta, da kayan ciye ciyenta ta tafi ofishin malam Nazir, fan wata irin ƙishirwar ganinsa ke damunta, tun incident ɗin nan da yafaru, idan har bata sa shi a idonta ba, ba ta jin daɗi. Kan tai sallama yaji ƙamshin turaren ta "Assalam Alaikum" tai Sallama. Be ɗago ya kalleta ba ya amsa. "Good morning Sir" "Morning how are you?" "Fine Alhamdilillah" Ta ja kujerar da ta saba zama ta zauna, ta fara ƙoƙarin kwafar note ɗin ta, so take ko sau ɗaya su haɗa ido, amma yaƙi kallonta aikinsa kawai yake, wanda seda hakan ya ɗan bata haushi. Sir Nazir kam yana sane yaƙi kallonta, saboda ya kasa gane kansa akan 'yar ƙaramar yarinyar nan. Yayi rayuwar University cikin manya manyan 'yan manta, yai yawace ywacensa, amma be taɓa cin karo da wadda yake jin wannan bugun zuciyar akanta ba se wannan yarinyar me shegen iyayin tsiya. Yayi mata kyau sosai, ji take tamkar ta gaya masa yayi kyau, amma tai shiri da bakinta tana tunanin me za tai wanda zesa ya kulata? Can tai gyaran murya, tare da miƙa hannunta kusa da inda hannunsa yake ta ɗau biro. Ɗagowa yai suka haɗa ido, ta ɗanyi luuu da nata idanun cikin wata irin murya tace masa "Nawa biron ya tsaya, shine na ɗauka aron naka" A hankali ya jane idonsa daga nata, ya cigaba da abunda yake yi. Wayarsa ce ta fara ringing, ya kalli wayar sannan yasa hannu ya ɗauka ya kai kunnensa. "Assalam Alaikum" yai Sallama. Lilly ba ta iya jiyo me ake cewa a wayar amma taji yace "like serious, congratulations my dear, am missing you, very soon zan shigo nima insha Allah" Ya ɗanyi shiru Sannan yace "yadda kike so, idan ta idar ki bata wayar in kwashi gaisuwa" Tunda ya fara wayar Lilly ta ƙura masa ido harya ƙare, gaba ɗaya Annurin fuskar ta ya ɗauke bata san lokacin da tace "Sir fa wa kake waya?" "Da ƙaniyarki" ya bata amsa. Sunkuyar da kai tayi ta cigaba da rubutunta, haka nan taji haushi ya kamata. Mintuna kaɗan aka sake kiransa ya kuma ɗagawa, cikin wata nustuwa da girmamawa yace "Ina kwana Umma, duk kuna lafiya, ai insha Allah na kusa shigowa, Auta tace min ba ta da carryover a exam ɗinta, baki yaƙi rufuwa" Murmushnsa ya faɗaɗa yana shafar gashin kansa yana wayar, wata nustuwa Lilly taji da ta fuskanci da 'yan gidansu yake waya. Babban abunda ya bata mamaki da kusan dariya be wuce yadda yakewa Mamansa shagwaɓa a wayar ba, se taji ya wani ƙara burgeta sosai da sosai, ta dinga kallon sa tana murmushi. Yana Ajiye wayar ta kalle shi tace "Sir is she your Mum?" Ya jinjina mata kai alanar eh. Tai murmushi tace "Amma Babba da kai kake shagwaɓa" Murmushi ne ya ƙwace masa ya shafi gemunsa yace "Ai su iyaye ba a girma a gurinsu" "Eh hakane, amma kai kayi girma da shagwaɓa" Yace "Allah ko?" "Eh mana, ai mata ne kawai suke shagwaɓa" Murmushi yai ya cigaba da dannan System. "Sir kana da ƙanne mata ne?" "Eh ina da ƙanne mana, shiyasa bana don inga kuna rashin ji, idan na tuna da ƙanne na, bana jin daɗin ganinku kuja rashin ji, sedai ku kuma ba kwa son ace muku bari" "Sir ba haka bane ba fa?" "To yane Fati, ke kanki na san kina jin haushi na saboda hukunta ki da nayi ko?" Lilly ba zata iya misalta farin cikin da ta shiga ba, kasancewar Sir Nazir yana mata Magana cikin nutsuwa ba hargowa da zare ido. Ta ɗago idonta ta kalleshi, ta ga shima kallonta yake, ga wani cikar zati da kwarjini da ya sake yi masa ado. A hankali ta sauke ajiyar zuciya, a ranta tace "ohhh God" ta fara tunanin ko ba duka ba za'a samu Sir Nazir da Mafi rinjayen siffofi da ake kamanta mazan littafi da shi, ba abunda yake tsole mata ido irin sajensa da wannan faffaɗan ƙirjin da yake da shi, she wish to hugs him even once, ta shafa wannan sajensa kamar yadda take karantawa a littafi. "Fatima ya kira sunanta" "Wani irin ɗagowa tai da idanunta, wanda sukai mata nauyi saboda jinta da take a gajimare, sheɗan na ta buga mata gangarsa a kwanyarta. Kallon da tai masa ne yasa jin jikinsa yai wani irin sanyi, yaji gumi na karyo masa. Kuma ta tsatsare shi da idanunta taƙi ɗaukewa. Jin halin da yake shirin shiga ne yasa ya aro jarumta, ya haɗe rai yace "concentrate on what you are doing" A hankali ta janye idanunta ta cigaba da note ɗin, amma lokaci lokaci idan ya ɗago ido se su haɗa ido tana masa wani irin shu'umin kallo da be san dame ze fassara kallon ba. (Ƙalubale gareku iyaye da malamai, Annabi Sallallahu alaihi Wasallam ya hana keɓancewa da mace wadda ba muharramarka ba, a yanzu muharraman ma se ana sa ido sosai, saboda muna zamani ne computer age, wannan kallace kallacen fina finan wanda ya dace da wanda be dace dui matasan mu kallo suke, ga uwa uba litattafai wanda wasu suke taka muhimmiyar rawa, gurin gurɓata tunanin Young adults ɗin mu. Sannan mace duk in da take komai girmanta ko ƙanƙartarta duk girmanka duk ƙanƙantarka zata iya jefaka a bala'i, 'ya mace tana da hatsarin gaske, Allah yasa mu dace" Farhan tai zuruu da ido, kamar agola a rabon gado, gaba ɗaya ta kasa sakewa. Gefe ga su Haseen suna ta karatun littafin su, da fari hankalinta baya kansu, tayi zurfi a cikin tunani, sedai jefi jefi kunnuwanta na ɗaukar wasu abubuwan. Tana nan zaune aka tashi, kowa ya bar ajin amma ita tana zaune ba ta tashi ba. "Farhan" taji muryar Sadik ta daki dodon kunnenta. Haɗe rai tayi sosai ta ƙi kallonsa. Matsawa yai kusa da Ita, tai saurin matsawa daga in da yake. "Farhan meyasa kike guduna kuma? Fushin kike dani haryanzu?" "Dan Allah ni ka ƙyaleni" "Bazan iya ba Farhan, dan Allah kiyi haƙuri" "Dan Allah ka ƙyaleni" "Kema kin san ba abune me yuwuwa ba, tsautsayi ne baze sake faruwa ba insha Allah, ki tashi mu tafi gida Please kiyi haƙuri" "Bazan haƙurin ba, kawai kasa nayi abunda ban taɓa yi ba" "Nima ban taɓa yi ba, amma ai nace ba zan sake ba" Tsaki tai masa ta ɗakko jakarta, ta raɓa shi zata wuce. Riƙota yayi ya haɗata a bango yana kallonta, kamar yadda yaga anayi a Bollywood 🙄🙄🙄. "Farhan nike baki haƙuri kina min wulaƙanci, nasan nayi miki laifi but am sorry, dan Allah kiyi haƙuri" ya ƙarasa maganar a sanyaye. Kawai idanunta suka fara zubar da hawaye. Hannu ya kai ze share mata hawayen, amma ta riƙe hannunsa. "Shikenan na gane ba zan taɓaki ba, zo mu tafi" "Ni ba zan bika ba" "Baki haƙura ba kenan?" Ya tambayeta a marairaice. Gaba ɗaya ta rasa dalilin da yasa ta kasa jin haushin Sadik, yadda yake marairaicewa ne yasa wani irin tausayinsa ya shige ta, kuma tasan idan ta dena kulashi, bata da wanda zata cigaba da raɓarsa tana jin daɗi, babu wanda zata dinga raha da shi tana jin daɗi. Yasa hannu ya karɓi jakarta, yace "muje ko" Tabi bayansa suka fito, a harabar in da ake parking ɗin motoci, suka haɗu da Mubarak Babba, ya kalli Farhan yana wani kashe ido yace "A'a yarinya ta zama 'yar hannu, delay ɗin na meye haka baku fito ba, ko dai ana tisa wancan karatun ne da a kai ran Friday". A take Farhan taji wasu hawayen na silalowa daga idanunta. Sadik ya kalli Babba yace "Mubarak, ka sanni na sanka, ni da kai kar ta san kar ne, ko da wasa ba ruwanka dani da kuma Farhan, abunda ya faru ma tsautsayi ne, kar ka kuma na gaya maka" Mubark yace "hmm to shikenan, na dena" Yaja Farhan suka shiga mota suka tafi. Seda suka kaita har inda take sauka Sannan Sadik yace "dan Allah ina ƙara baki haƙuri Farhan, kiyi haƙuri" Ba tace Komai ba, tasa hannu zata buɗe motar ta fita. Ya kuma riƙo hannunta, ta waigo ta kalleshi yace "baki cemin kin haƙura ba" "Bakomai ya wuce" tai maganar tare da zare hannunta ta fice. Shikam direba a ransa yace "Allah yasa yaron nan ba wata watsewar sukai da Yarinyar nan ba, naji yana bata haƙuri. Sam Farhan ba taji wani abu ya ragu game da son da takewa Sadik ba, sema wani ƙara jinsa da take a ranta. Idan ta kwanta bacci ba abunda yake yawo a ƙwaƙwalwarta se tunanin Sadik ɗin. Tana cikin tunanin Ba tsammani taji wani irin yanayi yana bijiro mata, wanda ba ta san menene ba balle ta tantance baƙon yanayin da ke ji a jikinta! Faɗin cakwakiyar da ke cikin littafin nan ba ta faɗuwa, hanzarta zuwa AREWABOOKS dan samun naku. Or subscribe it at affordable price of ₦300 only. (Saura acemin mara kunya, labarin ne yazo a haka🙄) Mum Amnash ina godiya da sharhinki da kuma shawara, Nagode Allah ya bar zumunci 🙏 Domin gyara Sharhi ko shawara 07063065680.. SHIN KUNA DA LABARIN MANHAJAR AREWABOOKS KUWA? MANHAJA CE DA TAZO DA TSARIN DAN SAUƘAƘAWA MARUBUTA DA MAKARANTA SAUƘIN CINIKAYYAR LITATTAFAI. TA IN DA ZAKU IYA SIYAN KOWANE FEJI AKAN KUƊI ƘALILAN, DAI DAI DA ALJIHUNKU. INA FARINCIKIN SANAR DA KU CEWA, DA ZARAR NA KAMMALA FREE PAGES, ZAKU CIGABA DA SAMUN CIGABAN LITTAFIN RUƊIN ƘURUCIYA, AKAN MANHAJAR AREWABOOKS. KARKU BARI A BAKU LABARI, AKWAI TARIN DARASIN RAYUWA A CIKIN LITTAFIN.                                                  31 A hankali ya ƙaraso in da Farhan ke tsaye, yasa tattausan hannunsa ya riƙo nata, ya matse a hannunsa ya kalli cikin idonta. Hakan ya saukar mata da kasala ta sunkuyar da kai daga kallonsa saboda kwarjinin da yai mata. A hankali cikin wata irin murya da ita kaɗai take jin meyake cewa yace "A karo na biyu bayan neman soyayyar ki, zan nemi Alfarma a gurinki Farhan, dan Allah ki amince na gaji da abunda suke min akanki Please Farhan" Shiru tayi tana jin yadda zuciyarta ke wani irin bugawa, gumi keta keto mata kota ina, ba ta gama yanke hukunci ba, taji Sadik ya haɗata da jikinsa, ya haɗe bakinsa da nata. Wata irin tsuma jikinta yake yi, ta rasa gane a wani yanayi take, tsoro ko kuma haushin Sadik, duk da yadda Sadik ɗin ya riƙeta gam, amma ji take tamkar zata faɗi ƙasa, dan haka ta sa hannu ta rirriƙe shi karta faɗi. Wani irin ihu da shewa suka ɗauka a gurin nan Gaba ɗaya, seda mintuna uku suka cika cif sannan Sadik ya cika Farhan. Idanunta sunyi rau rau kamar za tai kuka, se ajiyar zuciya take kamar wadda tai gudu. Nan akaita tafa musu, Nas yace "Weldon gaskiya abokinmu da his wife to be, kun burge kun ƙayatar kuma ka tabattar mana da cewa kai....." Se kuma yaƙi ƙarasawa. Aka yanka cake amma sam Farhan hankalinta baya jikinta, ji take tamkar ta aikata wani gagarumin zunubi da Allah baze yafe mata ba, take taji nadamar zuwa gurin partyn ta baibaye ta. Da sauri ta silale ta tafi in da aka shiryata, ta cire rigar jikinta ta ɗau kayanta ta saka, wasu irin hawayen nadama suka shiga zarya a fuskarta. Ta fito harabar gurin tana ƙoƙarin fita Sadik ya biyota yana ƙwala mata kira, amma taƙi tsayawa, cikin hanzari ya koma ya ɗakko mota, yaja ta da gudu yabi bayanta. Su Nas kuwa dariyar mugunta suka dinga yi, Amin yace "wannan ne karonsa na farko da yayi, amma kamar ƙwararre dama can a matse yake, da haka da haka dai" Babba yace "Aiku kuka ɓata abun da kuka hana ai amfani da ƙwayar nan wallahi" "Dan ubanka idan anyi amfani da ƙwaya muyi yaya da su a gurin nan? Kuma ka san ba komai ake bashi ya karɓa ya ci ba, amma sannu a hankali se mun sa shi a layi" Amin yace "hakane, Amma a hakan ma muny nasara ai" Suka cigaba da dariyar mugunta. Wani wawan parking Sadik yai a gaban Farhan, ya sakko yana faɗin "Farhan meye hakane kikeyi? Ki tsaya in maida ke gida mana" Cikin kuka ta kalleshi tace "ba zan tsaya ɗin ba nika ƙyaleni" "Ba zan ƙyalekin ba, ki wuce mu tafi" "Bazan wuce ɗin ba" Fizgota yai da ƙarfin gaske ya dannata a mota, yaja motar da gudun tsiya ya bar gurin. Sosai Farhan take masa kuka iya ƙarfin ta, amma be saurareta ba, seda ya dangana da unguwarsu, sannaan yai parking. Ya kalleta yace "Farhan me nai miki hakane?" Wani irin mugun kallo tai masa, ta fara ƙoƙarin buɗe motar, amma yai saurin cewa "ok i understand, dan Allah kiyi haƙuri nayi kuskure amma hakan shine mafita kawai a gareni" Buɗe motar tayi ta sauka, ta nufi lungun gidansu da sauri. Sadik ya dafe kai ya jingina da motar yana dana sanin biyewa su Nas. Ta samu guri ta zauna ta sha kukanta, kafin daga bisani ta goge hawayenta, ta tashi ta nufi gida, tan daf da shiga gidan sega Sunusi, yana ganinta ya washe baki yace "me sunan larabawa, daga ina haka?" Ko saurararsa ba tayi ba, ta shige gida sedai tun a soro ƙirjinta ke bugawa, gani take tana shiga Asirinta ze tonu. Ta daɗe a soron a tsaye sannan tayi sallama ta shiga, Umma na tsakar gida tana tankaɗe, ta ɗaga kai ta kalli Farhan, ta amsa sallamar ta maida kai ta cigaba da abunda take yi. Dama hakan umman take mata tun a baya, amma wannan karon se ta tsargu ta ga kamar Umman na san karantar wani abu a tare da ita. Ta daɗe a tsaye sannan ta shiga ɗakinta, tana shiga ta nemi Guri ta zauna ta cigaba da kuka, wai yau ita Sadik yasa bakinsa a nata a gaban jama'a ba kunya bakomai, shikenan ya zama ɗan iska itama yana son ya maida ita. Duk da ta cire wancan kayan, amma natan ma da ta mayar ƙamshin turarensa suke, cikin hanzari ta tashi ta cire kayan, amma ta fuskanci ba iya kayan ne keyi ba, jikinta ne yake ƙamshin turaren nasa. Addu'a ta dinga yi akan Allah yasa kar Asirin ta ya tonu, a gane in da taje da abunda ya faru. Har zuwa dare, amma taƙi sakin jikinta ta kasa sukuni, ga damuwa da fargaba duk sun cikata. Ko yunwa ba taji balle taci Abincin dare, haka taje ta kwanta, hakan be damu Ummanta ba balle taji ba'asin dalilin ƙin cin Abincin nata. Sosai Sadik ya damu da yadda Farhan tai ta kuka, nadama duk ta bi ta lulluɓe shi da dana sanin biyewa abokai, ya dinga tunanin ko a wane hali take? Ko ta dena kukan Allah masani. Sedai wani ɓangare na zuciyarsa ya kasa tantance nishaɗi yake ji ko kuwa? Abunda ya faru tsakanin su yai matuƙar tsaye masa a rai, he really enjoys it, abunda ya daɗe yana kwaɗayi ne dama, sedai damuwar da ya ganta a ciki ya hana shi sakewa yaji nishaɗin yadda yakamata. 'Auta yau ina ka shiga ne, for the whole day ban ganka ba, ba ka zo inda nake ba, rabona da kai tunda ka tafi school" Beji shigowar Mother ba sam, se maganar ta da ya ji, a hankali ya ɗan gyara kwanciyarsa yace "bakomai Mother" "But it seems like something is going wrong somewhere, na ganka wani iri" "Bakomai kaina ne yake ɗan min ciwo, kuma na sha magani" "Naga Abincin ku a falo, kaɗan aka taɓa kaci kuwa?" "No, naje gurin friend ɗina bayan sallar juma'a a can nai lunch" "Anyway shikenan, idan kan be dena ciwo ba se a tafi Asibiti" Ya jinjina mata kai tare da lumshe idanunsa, ina ma ba weekend za'a shiga ba ya samu ya kuma ganin Farhan, ya rarrasheta. A ɓangaren gidan dr. Kuwa wato ango sha guɗa Usman, Amarya ta fara fuskantar ƙalubale daga gareshi, duk da irin tarin soyaya da sukai a waje, ta kasa gane kansa yadda yakamata. Usman wani irin mutum ne me murɗaɗɗen hali, gani take kamar ta dena burgeshi gaba ɗaya, da yawa wasu halayen bata san yana da su ba se yanzu, miskili ne na gasken gaske, idan har tai masa laifi ko zata mutu baze ce mata kin min laifi kaza ba, sedai tagavya canza gaba ɗaya ga zuciyar tsiya, nan da nan damuwa ta isheta, taga tamkar canza mata Ussyn a kai ba shine wanda sukai soyayya ba. Wayarta ta ɗakko ta fito falo ta zauna, ta buɗe ta shiga contact ɗinta ta fara duba lambobi, tana zuwa kan wata lamba da aka saka my other half tai ajiyar zuciya da alama, lambar take nema. Nan take ta dannan kira ta shiga sauraren a ɗau wayar. "Salamu Alaikum" Jidda tace "wa'laikum salam, ba dai bacci kike ba?" "Wallahi ba bacci nake ba, nayi aikin gida ne na gaji, ya akayi ne Amarya?" Jiki a sanyaye Jidda tace "Besty dama haka auren yake? "Kai Jidds, yaushe a kai Auren da kike wannan zancen?" "Besty na kasa gane kan dr. Gani nake kamar an canzamin shi, gaba ɗaya na dena burgeshi, duk rawar kan nan da yake a kaina babu, in yi kwalliya in tsuke, amma ko kallo ban isheshi ba na rasa meye matsalar" ta ƙarasa maganar cikin damuwa. Wadda ta ke kira da besty ta gyara zama tace "Jidda kenan, lokacin da nake miki gargaɗi ina ɗoraki a hanya gani kuke Kamar ban waye ba, ban iya soyaya ba, ta yaya ba zaki gundure shi ba, bayan tun kuna waje kan kuyi Aure kin saba tura masa hotunan ki da ƙananan kaya, har video Call kuke da sleeping gown a jikinki, to me zaki da zako burgeshi kuma? Muna school idan yazo hugging ɗin sa kike, you even kisses his cheeks, idan nai Magana se kuce ni 'yar ustazai ce, to ga abunda nake gaya miki nan, abunda zeyi ɗokin kin gama nuna masa a waje, to what next kuma?" Cikin sanyin jiki Jidda tace "hakane besty, wallna gani, kuskure dai na riga nayi shi, amma yanzu meye mafita, ke kaɗai na gayawa halin da nake ciki" "Mafita ɗaya ce, ke dama ɗabi'arki ce zama da English wears kullum kamar 'yar turawa, tunda he's no more appropriating ita, ki koma masa ƙabilarki ta Hausa Fulani, ki duba kayan lefenki ki dinga masa wankan atamfa da leshi, idan yaso ki dinga saka English wears ɗin lokaci zuwa lokaci, Sannan shaƙuwar da ku kai a waje kar ta sa ki dinga kallonsa kamar mate ɗinki, ko ki dinga masa magana ba wani respect, no matter how close you are to each other, he deserves a respect from you shi namiji namji ne, ki dena wannan maganar taki cikin gadara, ki fara da jarraba wannan mu gani, se muga meye next abun yi" "Ka besty i love You lodi lodi, ina yinki Sisyna, insha Allah zan jarraba Allah yasa a dace" "Ameen Allah ya daidaita, kice ina gaishe shi" "To zeji insha Allah" Jidda ta fara tunanin maganganun bestyn ta, wato duk abun nan da suke a school suna ganin wayewa ce ashe yana da negative impact a gaba? Dama duk abun nan da take dan burge Usman kuma a kirata wayayyiya ze zo ya dena burgeshi? In Kuwa hakane Lallai a rayuwar ƙuruciya ana tafka shiirmen da ze zo ya zamewa mutum abun dana sani a gaba. Daga Sadik har Farhan sukuku su kai Weekends ɗin, damuwar Sadik ɗaya kukan da suka rabu tana yi, ya dimga fatan Allah yasa karta rabu da shi a dalilin abunda ya faru. Sedai baze iya misalta zallar nishaɗin da tsananin shauƙin soyayyar da ya shiga ba, a lokacin da yake sumbutar Farhan, wani abu ya dinga ji from no where yana ratsa ilahirin jikinsa, dan gaba ɗaya mantawa yai da batun wani ƙyanƙyami ko wani abu me kama da haka, hakan ya ƙara kwaɗaita masa son Auren Farhan, sabida wani irin sonta da ya ƙara shigarsa. Amma ba ya jin ze kuma yadda ya aikata makamancin wannan kuskuren, dan shi kansa yayi nadamar biyewa su Nas ya aikata abunda be taɓa aikatawa ba a rayuwar sa. Duk yadda ta so jin tsanar Sadik a ranta saboda abunda yai mata amma abu ya gagara, sam ba taji ta tsane shi a zuciyarta ba, mussaman idan tai la'akari da shima be san abunda su Nas suka shirya ba, sedai a jikinta tana jin abunda suka aikata ɗin ba daidai bane, kuma kasancewar sun aikata a gaban mutane, ba za'a taɓa dena kallon su da abun ba. Ba zata iya misalta yanayin da ta shiga a lokacin da abun ya faru ba, dan Tamkar a mafarki haka ta dinga ganin lamarin, kuma ta kasa tantance halinda ta shiga, saboda taji wani abu da jikinta be taɓa bata ba a tsawon rayuwarta se a wannan karon da abunda ya faru ya faru, lokaci lokaci idan ta tuna abunda ya farun ta kanji ta tsani komai, sedai ƙarƙashin zuciyarta na hasaso mata wani yanayi ne me wuyar mantawa. Ranar Monday kuwa Sadik shirin Makaranta yake, amma cike da zullumin yadda ze tunkari Farhan ta saurare shi. Itama nata ɓangaren tunanin yadda zata shiga makarantar take tayi ido huɗu da wanda akai abun a gabansu, dan tana ji a jikinta ta rasa wata kima da daraja da take da ita a idon wasu daga cikin abokan karatun nata. Jibtaka tamkar ta fasa zuwa makarantar, amma idan ta fasa tasan se a tambayi ba'asin hakan, dan haka jiki a sanyaye take aiwatar da shirin makarantar. Seda aka gama Assembly sannan ta shiga makarantar, ta wuce ajinsu tana sussunkuyar da kai, duk wanda suka je gurin tsirarun mutane ne, dan a 'yan ajinsu Lilly ce kawai taje se wasu daga 'yan ajinsu Sadik se Khairat, du du du ba su fi su goma ba, amma gaba ɗaya ta rasa sukuni. Sadik na shiga ajinsu suka hau yi masa ihu da shewa. Be kula su ba yaje ya nemi guri ya zauna a mazauninsa, Nas da Amin sukaje suka zauna kusa da shi, Nas yace "Mazaa, ya ake ciki ne? Munyi ta kiran wayarka ba ta shiga, kuma ka barmu a gurin partyn ba ka dawo ba, ya kaji abun?" Sadik ya ɗago idanunsa ya kalli Nas, kallon da Nas ɗin ya kasa tantance kallon meye. Amin yace "wallahi you did it in the most passionate way, naji haushi da ka hana ɗaukar hotuna ku bada kala fa" Nas yace "ai mun tabattar da namiji ne yanzu, yanzu zaka fara soyayyar morewa ba irin wadda kake yi ba da, ta ƙauyanci, nasan ko yanzu ka samu chance you want do it again ko ba haka ba?" "Shut up!" Sadik ya faɗa da ƙarfi yana dukan benci. "Dan Allah ku ƙyaleni inji fa abunda ya dameni, ku tashi ku ban guri" Binsa su kai da kallon mamaki, meke damunsa hakane? Kasa jurewa yayi, ya tashi ya nufi ajinsu Farhan amma ya tarar Madam Joy na ciki na musu lesson dan haka ya koma ajinsu. Bayan fitar Madam Joy, Lilly taje in da Farhan ke zama ta zauna a kusa da ita tace "mutuniyar ya gajiyar taro?" Wata ƙwalla ce ta zowa Farhan, da tuna a gaban Lilly Sadik yai kissing ɗinta, ta san maybe Zuwa yanzu duk ta gama bawa 'yan ajin labari. Lilly tace "yana ga kamar zaki kuka? Meyafaru?" Aikuwa maganar Lillyn tasa hawayen da Farhan ke maƙalewa ya gangaro kan kuncinta. "Yasalam, Farhan menene?" Cikin kuka Farhan tace "bakomai" "Bakomai amma kike kuka?" Farhan ta jinjina mata kai. Lilly tace "anyway shikenan, bari in ƙyaleki kar in takura miki" Har Lilly ta miƙe Farhan ta riƙo hannunta, ta dawo ta zauna tace "ya akayi?" "Fatima dan Allah kin gayawa wani abunda ya faru agurin nan?" Lilly ta riƙe hannun Farhan tace "i understand you ƙawata, karki damu ni ba wanda na gaywa, ni ba haka nake ba, and is something common in this school, no one will cares, amma duk da haka ni ban gayawa kowa ba, in abunda ya saki kuka kenan ki kwantar da hankalinki" Farhan ta jinjina kai tace "Nagode sosai" "Bakomai karki damu" Ana haka, aka kaɗa jiniyar fita break, Lilly ba ta jira kowa ba ta ɗau littafinta, da kayan ciye ciyenta ta tafi ofishin malam Nazir, fan wata irin ƙishirwar ganinsa ke damunta, tun incident ɗin nan da yafaru, idan har bata sa shi a idonta ba, ba ta jin daɗi. Kan tai sallama yaji ƙamshin turaren ta "Assalam Alaikum" tai Sallama. Be ɗago ya kalleta ba ya amsa. "Good morning Sir" "Morning how are you?" "Fine Alhamdilillah" Ta ja kujerar da ta saba zama ta zauna, ta fara ƙoƙarin kwafar note ɗin ta, so take ko sau ɗaya su haɗa ido, amma yaƙi kallonta aikinsa kawai yake, wanda seda hakan ya ɗan bata haushi. Sir Nazir kam yana sane yaƙi kallonta, saboda ya kasa gane kansa akan 'yar ƙaramar yarinyar nan. Yayi rayuwar University cikin manya manyan 'yan manta, yai yawace ywacensa, amma be taɓa cin karo da wadda yake jin wannan bugun zuciyar akanta ba se wannan yarinyar me shegen iyayin tsiya. Yayi mata kyau sosai, ji take tamkar ta gaya masa yayi kyau, amma tai shiri da bakinta tana tunanin me za tai wanda zesa ya kulata? Can tai gyaran murya, tare da miƙa hannunta kusa da inda hannunsa yake ta ɗau biro. Ɗagowa yai suka haɗa ido, ta ɗanyi luuu da nata idanun cikin wata irin murya tace masa "Nawa biron ya tsaya, shine na ɗauka aron naka" A hankali ya jane idonsa daga nata, ya cigaba da abunda yake yi. Wayarsa ce ta fara ringing, ya kalli wayar sannan yasa hannu ya ɗauka ya kai kunnensa. "Assalam Alaikum" yai Sallama. Lilly ba ta iya jiyo me ake cewa a wayar amma taji yace "like serious, congratulations my dear, am missing you, very soon zan shigo nima insha Allah" Ya ɗanyi shiru Sannan yace "yadda kike so, idan ta idar ki bata wayar in kwashi gaisuwa" Tunda ya fara wayar Lilly ta ƙura masa ido harya ƙare, gaba ɗaya Annurin fuskar ta ya ɗauke bata san lokacin da tace "Sir fa wa kake waya?" "Da ƙaniyarki" ya bata amsa. Sunkuyar da kai tayi ta cigaba da rubutunta, haka nan taji haushi ya kamata. Mintuna kaɗan aka sake kiransa ya kuma ɗagawa, cikin wata nustuwa da girmamawa yace "Ina kwana Umma, duk kuna lafiya, ai insha Allah na kusa shigowa, Auta tace min ba ta da carryover a exam ɗinta, baki yaƙi rufuwa" Murmushnsa ya faɗaɗa yana shafar gashin kansa yana wayar, wata nustuwa Lilly taji da ta fuskanci da 'yan gidansu yake waya. Babban abunda ya bata mamaki da kusan dariya be wuce yadda yakewa Mamansa shagwaɓa a wayar ba, se taji ya wani ƙara burgeta sosai da sosai, ta dinga kallon sa tana murmushi. Yana Ajiye wayar ta kalle shi tace "Sir is she your Mum?" Ya jinjina mata kai alanar eh. Tai murmushi tace "Amma Babba da kai kake shagwaɓa" Murmushi ne ya ƙwace masa ya shafi gemunsa yace "Ai su iyaye ba a girma a gurinsu" "Eh hakane, amma kai kayi girma da shagwaɓa" Yace "Allah ko?" "Eh mana, ai mata ne kawai suke shagwaɓa" Murmushi yai ya cigaba da dannan System. "Sir kana da ƙanne mata ne?" "Eh ina da ƙanne mana, shiyasa bana don inga kuna rashin ji, idan na tuna da ƙanne na, bana jin daɗin ganinku kuja rashin ji, sedai ku kuma ba kwa son ace muku bari" "Sir ba haka bane ba fa?" "To yane Fati, ke kanki na san kina jin haushi na saboda hukunta ki da nayi ko?" Lilly ba zata iya misalta farin cikin da ta shiga ba, kasancewar Sir Nazir yana mata Magana cikin nutsuwa ba hargowa da zare ido. Ta ɗago idonta ta kalleshi, ta ga shima kallonta yake, ga wani cikar zati da kwarjini da ya sake yi masa ado. A hankali ta sauke ajiyar zuciya, a ranta tace "ohhh God" ta fara tunanin ko ba duka ba za'a samu Sir Nazir da Mafi rinjayen siffofi da ake kamanta mazan littafi da shi, ba abunda yake tsole mata ido irin sajensa da wannan faffaɗan ƙirjin da yake da shi, she wish to hugs him even once, ta shafa wannan sajensa kamar yadda take karantawa a littafi. "Fatima ya kira sunanta" "Wani irin ɗagowa tai da idanunta, wanda sukai mata nauyi saboda jinta da take a gajimare, sheɗan na ta buga mata gangarsa a kwanyarta. Kallon da tai masa ne yasa jin jikinsa yai wani irin sanyi, yaji gumi na karyo masa. Kuma ta tsatsare shi da idanunta taƙi ɗaukewa. Jin halin da yake shirin shiga ne yasa ya aro jarumta, ya haɗe rai yace "concentrate on what you are doing" A hankali ta janye idanunta ta cigaba da note ɗin, amma lokaci lokaci idan ya ɗago ido se su haɗa ido tana masa wani irin shu'umin kallo da be san dame ze fassara kallon ba. (Ƙalubale gareku iyaye da malamai, Annabi Sallallahu alaihi Wasallam ya hana keɓancewa da mace wadda ba muharramarka ba, a yanzu muharraman ma se ana sa ido sosai, saboda muna zamani ne computer age, wannan kallace kallacen fina finan wanda ya dace da wanda be dace dui matasan mu kallo suke, ga uwa uba litattafai wanda wasu suke taka muhimmiyar rawa, gurin gurɓata tunanin Young adults ɗin mu. Sannan mace duk in da take komai girmanta ko ƙanƙartarta duk girmanka duk ƙanƙantarka zata iya jefaka a bala'i, 'ya mace tana da hatsarin gaske, Allah yasa mu dace" Farhan tai zuruu da ido, kamar agola a rabon gado, gaba ɗaya ta kasa sakewa. Gefe ga su Haseen suna ta karatun littafin su, da fari hankalinta baya kansu, tayi zurfi a cikin tunani, sedai jefi jefi kunnuwanta na ɗaukar wasu abubuwan. Tana nan zaune aka tashi, kowa ya bar ajin amma ita tana zaune ba ta tashi ba. "Farhan" taji muryar Sadik ta daki dodon kunnenta. Haɗe rai tayi sosai ta ƙi kallonsa. Matsawa yai kusa da Ita, tai saurin matsawa daga in da yake. "Farhan meyasa kike guduna kuma? Fushin kike dani haryanzu?" "Dan Allah ni ka ƙyaleni" "Bazan iya ba Farhan, dan Allah kiyi haƙuri" "Dan Allah ka ƙyaleni" "Kema kin san ba abune me yuwuwa ba, tsautsayi ne baze sake faruwa ba insha Allah, ki tashi mu tafi gida Please kiyi haƙuri" "Bazan haƙurin ba, kawai kasa nayi abunda ban taɓa yi ba" "Nima ban taɓa yi ba, amma ai nace ba zan sake ba" Tsaki tai masa ta ɗakko jakarta, ta raɓa shi zata wuce. Riƙota yayi ya haɗata a bango yana kallonta, kamar yadda yaga anayi a Bollywood 🙄🙄🙄. "Farhan nike baki haƙuri kina min wulaƙanci, nasan nayi miki laifi but am sorry, dan Allah kiyi haƙuri" ya ƙarasa maganar a sanyaye. Kawai idanunta suka fara zubar da hawaye. Hannu ya kai ze share mata hawayen, amma ta riƙe hannunsa. "Shikenan na gane ba zan taɓaki ba, zo mu tafi" "Ni ba zan bika ba" "Baki haƙura ba kenan?" Ya tambayeta a marairaice. Gaba ɗaya ta rasa dalilin da yasa ta kasa jin haushin Sadik, yadda yake marairaicewa ne yasa wani irin tausayinsa ya shige ta, kuma tasan idan ta dena kulashi, bata da wanda zata cigaba da raɓarsa tana jin daɗi, babu wanda zata dinga raha da shi tana jin daɗi. Yasa hannu ya karɓi jakarta, yace "muje ko" Tabi bayansa suka fito, a harabar in da ake parking ɗin motoci, suka haɗu da Mubarak Babba, ya kalli Farhan yana wani kashe ido yace "A'a yarinya ta zama 'yar hannu, delay ɗin na meye haka baku fito ba, ko dai ana tisa wancan karatun ne da a kai ran Friday". A take Farhan taji wasu hawayen na silalowa daga idanunta. Sadik ya kalli Babba yace "Mubarak, ka sanni na sanka, ni da kai kar ta san kar ne, ko da wasa ba ruwanka dani da kuma Farhan, abunda ya faru ma tsautsayi ne, kar ka kuma na gaya maka" Mubark yace "hmm to shikenan, na dena" Yaja Farhan suka shiga mota suka tafi. Seda suka kaita har inda take sauka Sannan Sadik yace "dan Allah ina ƙara baki haƙuri Farhan, kiyi haƙuri" Ba tace Komai ba, tasa hannu zata buɗe motar ta fita. Ya kuma riƙo hannunta, ta waigo ta kalleshi yace "baki cemin kin haƙura ba" "Bakomai ya wuce" tai maganar tare da zare hannunta ta fice. Shikam direba a ransa yace "Allah yasa yaron nan ba wata watsewar sukai da Yarinyar nan ba, naji yana bata haƙuri. Sam Farhan ba taji wani abu ya ragu game da son da takewa Sadik ba, sema wani ƙara jinsa da take a ranta. Idan ta kwanta bacci ba abunda yake yawo a ƙwaƙwalwarta se tunanin Sadik ɗin. Tana cikin tunanin Ba tsammani taji wani irin yanayi yana bijiro mata, wanda ba ta san menene ba balle ta tantance baƙon yanayin da ke ji a jikinta! Faɗin cakwakiyar da ke cikin littafin nan ba ta faɗuwa, hanzarta zuwa AREWABOOKS dan samun naku. Or subscribe it at affordable price of ₦300 only. (Saura acemin mara kunya, labarin ne yazo a haka🙄) Mum Amnash ina godiya da sharhinki da kuma shawara, Nagode Allah ya bar zumunci 🙏 Domin gyara Sharhi ko shawara 07063065680.  Littafin nan ₦300 ne kacal. 0009450228 Aisha Adam Jaiz Bank KO kuje manhajar AREWA BOOKS ku siya.                          33 Daga Farhan har Sadik se sauke Gwauron numfashi suke, cikin kasala Sadik yace "Ko in kaiki clinic ki samu ki huta?" Ta ɗaga masa alamar eh, ta ɗaga shi suka fito daga ajin suka nufi Clinic. Se kuma kunya da jin nauyin abun da tai suka baibaye ta, ta fara tuhumar kanta garin yaya haka ta faru?. Clinic suka shiga, suka tarar da me kula da Clinic ɗin, cikin gurɓatacciyar hausar sa yace "Ahh Prince ke, ko shi waye ba lafiya ni?" Sadik ya nuna Farhan. Yace "eyya sorry, what's wrong with her?" Sadik yace "just Headache, I think she only needs rest" "Okay take her to female ward". Sadik yace "ok" Suka shiga Femal ward shi da Farhan, ta kwanta akan gado, Sadik ya kunna mata fanka, ya janyo kujera ya zauna a gabanta yana binta da ido. Kasa jure kallon tayi ta sunkuyar da kai. "Farhan ina ganin damuwa ƙarara a fuskar ki amma ba kya son gayamin, ba zan takura miki ba, saboda nima na kan tsinci kaina a irin damuwar ki, sedai ni muna da banbanci, wasu lokutan na kan tattauna damuwa ta da mahaifiyata, ko Yayana, samun wanda zaka dinga gayawa damuwar ka ko be maka magani ba, at least zaka rage zafin abun dake damun naka, amma Yakamata ki samu ko Mum ɗin ki ne ki gaya mata koma menene, tunda ni ban taɓa ganinki da wata ƙawa ba, a school ɗin nan ma ba ki da ƙawa, dani kawai kike iya sakewa kuma nima ɗin kin ƙi gayamin" Kawai se ya ga ta sake fashewa da kuka, har da shesheƙa. Kasancewar ta tuna halin ko in kula fa mahaifiyarta ke mata. Sadik Yace "Yasalam, na faɗi wani abu ne kuma?" Ta girgiza masa kai. Hannunta ya riƙo cikin nasa, yana murza yatsunta a hankali, sedai wannan karon da yake murza hannunta, wata nustuwa take ji, akan lokacin da Salma ta riƙe mata hannu, a wannan lokacin ma ita tsoro ne ya kamata. "Farhan, kin san yadda nake jinki a raina kuwa? Kina da gurbi me girma a zuciyata, wallahi kukan ki na ɗaga min hankali, da alama damuwar ki ba ƙarama bace" Ya cigaba da murza hannunta, hannu ɗaya kuma ya shiga share mata hawayen dake kwaranyowa daga Idonta. Haka ya wanzu yana mata harya fuskanci ta fara samun nustuwa, ta sassauta kukan da take akan lokacin da suka baro ajin su. Lilly kam tana Office ɗin Sir Nazir, se zuba masa shagwaɓa take da shirme kala kala, wani yai mata shiru wani kuma yai dariya, because she's very funny at times. Ta miƙe tsaye daga in da take, tace "Bari in tafi Class" ya ɗago da nufin ya bata amsa, Wata irin shu'umar miƙa tayi, se kace wata gogaggaiyar budurwa, wanda har seda rigarta ta ɗage cibiyar ta ta fito. Shikuma ya bita galala da ido kamar wani soko, cikin murya kamar me jin bacci tace "Sir se an jima" Ta juya zata fita ta hau tari, wanda yana daga cikin almun tashin ciwon masu Asma. Da sauri ya taso daga inda yake yana faɗin "Fatima, ya dai jikin ne?" Ƙoƙarin kwanciya take a ƙasa tana riƙe ƙirjinta, se faman tari take. Da Sauri ya zagayo ya riƙeta ya ɗagota daga ƙasa yana jera mata Sannu. A hankali ta tsagaita da tarin, tana lumshe idanu jinta a hannunsa. "Lilly' ya kira sunan ta. Ta buɗe idanunta a kansa. "Are You ok?" Ta jinjina masa kai. "Kina iya numfashi normal?" Nan ma ta ɗaga masa kai. Yace "sannu ko zaki tafi Class?" Ta noƙe masa kafaɗa. Ya tsuke fuska yace "meye hakane? Tashi ki tafi Class tunda ya lafa miki mana" "Uhmm, Allah jiri nake ji, kaina ne yake juyawa" "To bari in ajiyeki a ƙasan ki ɓata jikin ki" Tashi tai daga jikinsa ta jingina da jikin table ɗin da kujeru suke. Ya miƙe ya koma mazaunin sa ya ƙyaleta. Jacket ɗinta dake ta ƙamshin turare ta cire ta ɗora akan table ɗin sa. Ya ɗago ya kalleta "wai ke meye hakane, tashi ki barmin Office" ya faɗa a kausashe. A raunane tace "Am sorry sir, i need air ne, da ƙyar nake numfashi and i mean it" tai maganar tana jan numfashi da kyar. "Ok na gane, tashi ki lallaɓa maza ki tafi Class, su kai ki Clinic" Yadda yake gumi da yadda yake har haɗo maganar da kyar ta tabattar da tarkonta yayi kamu, kuma ta gazgata abunda take karantawa a Novels. Dama ba wani ciwonta da ze tashi, tayi hakanne dan ganin reaction ɗin sa, ta miƙe a hankali ta ɗau jacket ɗinta ta fice tana murmushi. Har ta bar Office ɗin kallonta yake, se da ta fita sannan yai ajiyar zuciya, tabbas ya fara jin wani abu yana masa yawo a game da Yarinyar nan, kuma babu ko tantanma son ta yake. But how comes will he falls in love with this little girl? Ya tambayi kan sa. (Nace Mun gama Yaya Ammar, @ WATA kissar sai mata🙄 if you know you know, if you don't get it look for the book WATA KISSAR SAI MATA) Seda Sadik ya tabattar da Farhan ta ɗan samu nutsuwa Sannan yace "zaki iya zuwa aji ko mu cigaba ds Zama a nan, kinfi son nan?" "Zanje Class" ta bashi amsa. "Ok" Kawai ya ɗagota da kwanciyar da take, Sannan ya ɗan tsura mata ido. A hankali yace "Sannu babyna, Allah ya baki mafita akan abunda yake damun ki" Yai Maganar yana goge mata gumin dake goshinta da hannunsa. Ta sakko daga kan gadon, ya rakata har Class ɗin su, Sannan ya koma aji, lokaci lokaci yana zagayowa yana dubata, tare da tunanin meke damunta haka a wannan ƙananan shekarun nata haka?. Da aka tashi daga Makaranta ma, suna tafe a mota ta jingina da kujera ta lunshe idanunta tai shiru, taji hannun Sadik a nata. Ba ta motsa tai shiru yana cigaba da wasa da yatsunta. A haka har suka je in da suka sauketa, yau ko sallama ba suyi ba ta sauka ta nufi layinsu. Da sallama a bakinta ta shiga gidan, sedai matar da tai karo da ita a tsakar gida ne, yasa Farhan yin murmushi tace "Adda kece kika zo?" "Nice na zo yarinyar kirki, Ohh girman ɗan mutum ba wuya, kalli yadda Yarinyar nan ta ganɗame ta girma" Farhan ta durƙusa har ƙasa ta gaisheta, matar tace "Farhan, gaskiya kin girma, yaushe rabonki damu?" "Adda hanya ba kyau, kuma kusan duk lokacin da Umma za ta je ina Makaranta" Adda tace "hakane kam, Allah ya taimaka" Farhan tace "Ameen, ina su Amina baki zo da kowa ba?" "Amina na can, na baro su a gida, an kawo mata kuɗin Aure wancan satin" Jimm Farhan tayi, Aminan sa'arta ce, dan ita Farhan ɗin ma ta bata watanni kusan bakwai, amma har za'ai mata aure, dama su iyakacin karatun yaran su primary ne. Umman Farhan na jinsu ba tace Komai ba, Farhan ta tashi, ta  shiga ɗaki ta canza kaya, ta ɗau bokiti ta shiga banɗaki dan yin wanka. A nan banɗakin ta tsaya tana ƙarewa kanta kallo, tana jin daga ƙasa yadda mararta ke ƙullewa, ƙirjinta kuma na mata zafi, ta kalli kanta ta lumshe ido hawaye na zuba daga idonta ta hau tunani 'Anya Sadik ze yadda ya aureta idan yasan ta kamu da Cancer Mama, babban abunda yake ɗaure mata kai da ciwon shine se lokaci lokaci, ida  ga kusa period take jinsa, gashi ita ba abun ta tafi Asibiti ba' Tana cikin tunanin ta jiyo Muryar Adda Hafsa tanawa Ummanta Magana da fullanci. "Ke Mairo, yanzu haka zaku cigaba da barin yarinyar nan tana Girma a gaban ku da sunan boko? Kalli ƙirjinta fa kalli yadda 'ya ta cika haka" Umma tace 'ni kaina abun yana damuna, babanta ne ke son tayi karatun, babban abunda ya ke bani tsoro shine watanni uku baya ta fara al'ada" Dafe ƙirji Adda Hafsatu tai tace "Al'ada kuma Mairo, kinga tun wuri ku kawar da Yarinyar nan, bokon me yarinya ta zanƙale haka a gida" "Ba laifina bane, na mahaifinta ne, shi kuma kin san ba'a tursasa shi, shine yake son tayi karatun nan, amma nima nafi ganewa tai Auren" "To ina fatan dai akwai manemi?" "Eh to, akwai wani a nan maƙwabtan mu, Almajiri ne, malaminsu yaiwa babanta Magana akan yana so a bawa Yaron, to yana da nustuwa dai, amma babanta yace karya fara zuwa se an kwana biyu, amma ya amince ya bashi ita" "Wane irin se an kwana biyu, ke ni in be yuwuwa, se in ɗauketa be sani ba in tafi da ita can ƙauye, baffa ya aurar da ita a can, haka akeyi? Mu munyi bokon ne, amma duk gashi an aurar da mu mun zauna har mun haife su, me za'aci da wata boko yarinya kina zaune kuna haɗa kafaɗa da ita, kalli yadda ta zama uwar mata fa" Farhan a hankali ta furta na shiga uku, ta toshe bakinta a banɗakin ta cigaba da kuka, bata taɓa bijirewa iyayenta ba ko akan mene, amma a wannan karon ba zata lamunci Aure Sunusi ba, ko ba zata auri Sadik ba, ba zata auri Sunusi ba gara ta haƙura da Auren. Ta daɗe a banɗaki sannan ta fito, Adda Hafsatu na ta binta da kallo tana "kinga Yarinya ta zama uwar mata" Da daddare har Lilly ta kwanta bacci, Nazir ya kirata, sabod haka nan zuciyarsa take azalzalarsa ya kirata yaji muryarta, dan zuwa yanzu ya tabattar da sonta yake. Sun daɗe suna waya da shi, yana mata ya jiki, ta zage ta dinga zuba masa taɓara, seda ta gamsu tarkonta yayi kamu, saboda duk wasu alamu sun fara nuna sonta yake. Zuwan Adda Hafsatu ta wani fannin Farhan taji daɗi, dan ta ɗan samu sakewa, ba kamar da ba, tana samun abokiyar hira, duk da ƙanwar mahaifiyarta ce amma, ta na janta a jiki saɓanin Ummanta. Da yake a ɗakin Farhan take kwana, suna hira sosai. "Adda, dan Allah meyasa Ummana ba ta sona ne, ba ta son kulani" "Kee, ta dinga kula ki kina 'yar farin?, So kike ai mata gori? Ai badan baban ki baze yadda ba ni zan ɗauke ki, ai al'adara mu ba ruwanka da ɗan fari" "Haba Adda, Al'ada ai ba Addini bace, kowa in ana hira yana hirar mahaifiyarsa, amma ban da ni, da na zo guri se ta tashi, ko Magana ba ta son yi min" Ta ƙarasa maganar cikin damuwa. "Ke ƙaniyarki, wato zuwa makarantar da kike shine har kike da bakin cewa Al'ada ba addini bace ko? To mu Al'ada ce me kyau a gurin mu,kuma muna girmama wannan al'adar a ƙa'ida ai nice Ummanki ba ita ba, da babanki ze yadda ai ɗauke ki zanyi mu tafi can mu zauna in miki Aure" "Aure kuma Adda, karatun fa?" "Shi karatun da kike faɗa Addini ne?" Farhan tace "Adda ai Addini ne yai mana umarni da mu nemi ilimi, ko daga nan zuwa birnin sin ne" "Amma ai ba boko aka ce ba ko?" Farhan tai murmushi tace "Adda, shi ilimi ai ilimi ne, tunda Annabi Sallallahu alaihi Wasallam ilimi kawai yace, to kowane ilimi ne in dai be saɓa da addinin mu ba" "Ke ya isheni haka, ki min shiru, Aure dai shine gaba da komai" Farhan tace "shikenan"  yana daga daɗin da Farhan ke ji shine, a wayar Addan takewa Sadik messages, se ya saka mata kati su raba dare suna hira ta saƙon message, Adda Hafsatu na can na bacci, wani lokacin har makarantar dare take tafiya da wayar, suyi waya a can ita ba ta damu ba sam. Se dai kan tafiyar Adda Hafsatu, ba yadda ba tai da Abban Farhan akan a ƙyale bokon nan tunda ta na da manemi Ai mata aure ba, amma ya nuna nata mahimmancin karatun 'ya mace. ************************************ Kwanci tashi asarar rai, lokacin zana jarabawar Karshe da Sadik zeyi da 'yan SS3 ta ƙarato, wato lokacin barinsa makarantar ya ƙarato sosai. A lokacin Farhan tana Jss3, ta ƙara girma abunta, ta cika Sosai. Sedai Farhan duk ta rasa nutsuwarta, da ta tuna Sadik ze bar makarantar ya barta se tai ta kuka, sauƙinta ma shida manyan 'yan iskan dake damunta ze gama makarantar su Babba da kuma Salma. Duk da sun cigaba da kawo mata farmaki ta ɓangarori daban-daban, ba tare da Sadik ya sani ba. Idan ta tashi kuka ya dinga rarrashi kenan, tare da Alƙawarin ze Aureta, Wannan shine babban dalilin da ze sa ya kammala secondary a shekarar. Batun irin kusanci da shaƙuwar da ke tsakanin Sadik da Farhan kuwa ba'a magana, Sunyi shaƙuwa me ƙarfin gaske, ji take idan ya bar makarantar ta rasa wani abu me matuƙar mahimmanci a kusa da ita. Yau bayan sallar isha'i, Farhan ta dawo daga makarantar dare, ƙaninta Imam ya sanar da ita cewar Abban su yana kiranta. Ta maida hijjabinta ta fito, ta nufi ɗakin Abban, ta shiga da Sallama a bakinta. Abba ya amsa mata, taga Umma a zaune a gefensa, ta durƙusa ƙasa tace "Abba gani" Abba yai gyaran murya yace "Farhan, waye yake kawoki a mota daga Makaranta?" Cikinta ne yai wata irin ƙara, gumi ya shiga tsatsafowa daga goshin ta, ya a kai Abba ya san haka, bayan a can baya ake ajiye ta?. "Magana nake miki, ki bani amsa waye yake kawoki a Mota, ɗazu Sunusi ya gayawa malam bara'u, shikuma ya zo ya sameni" Farhan ta sunkuyar da kai ba tace komai ba. Umma tace "kaga abunda nake gaya maka ko malam, ana miki magana ba kya ji ne?" Farhan ta ɗanyi jimm, ta karanto duk Addu'oin da zata iya sannan tace "Abba bani kaɗai ake kawowa ba, 'yar ajinmu ce ake zuwa ɗauka, idan ta tashi duk na hanya se a ɗakko mu tare, kowa a sauke shi se a ƙarsa da ita gida" "Kuɗin motar da nake baki ne baya isarki?" Abba ya jefo mata tambayar. "A'a Abba suna isata" "To meyasa sedai ki biyo motar yaran masu kuɗi?" "Babu komai Abba" "Farhan lalacewar zamani nake jiye miki, yaran masu kuɗin nan wasu ba Kirki ne da su ba, wataƙila a banza wataran za'a goranta miki, wanda babu daɗi, dan Allah Farhan ki kula da kanki ki tsare mutuncinki" "To Abba insha Allah" Abba yace "se magana ta biyu, da tuntuni yakamata in miki amma ban miki ba, malam Uba ya zomin da batun Yana son in bawa Almajiransa Sunusi ke, to na yaba da hankalin Yaron da nutsuwarsa, ba shi da wata damuwa, kuma an gayamin garinsu da suwaye iyayen sa, duk ba su da wata matsala dan haka gobe in Allah ya kaimu ze fara zuwa wajenki, ku fuskanci juna, dan Mahaifiyar ki ta nuna da wur take son ai miki Aure, tunda kinga mu dangin mu duk ba karatun muke ba, kuma baffan Ummanki har waya yayo yana mitar ance kin girma amma ba'a fara zancen Aurenki ba se karatun boko" Gaba ɗaya Farhan ta dena gane komai, se tsananin bugubda zuciyarta keyi, ta rasa meke mata daɗi sam. Abba yace "naji kinyi shiru" Cikin rauni Farhan tace "Abba karatu na fa?" "Ai ba yanzu za'ai Auren ba, a samu dai ku fuskanci juna, kinga Farhan gara ki auri talaka dai dai ke, ba zan so aurar da ke in da za'a wulaƙanta ki ba dan bamu da Komai, amma kinga wannan shima ba shi da koma, kin ga se kuyi arzikin tare" Farhan tai shiru ta kasa ko ƙwaƙwaƙwaran motsi. Abba yace "ko akwai abunda zaki ce?" Farhan ta girgiza kai alamar a'a. Yace "yawwa, tashi kije Allah yai mil albarka" Ai ko amsawa ba ta iya yi ba, ta tashi jiki a matuƙar sanyaye, ta nufi ɗakinta, ta na zuwa ta zube akan katifarta, ta fashe da kuka. Wata irin masifaffayar soyayyar Sadik ce ke bijiro mata, ga shi ba ta son yin duk wani abu da ze sa ta saɓawa iyayen ta, amma ya za'ai ta auri wanda ba ta so kwata kwata, bayan ga wanda zuciyarta ke so? Dole tajewa Sadik da wannan maganar dan samo bakin zaren. Tunda ta shiga ɗakin nan ba ta sake fitowa ba har gari ya waye. A Library taje ta samu Sadik, ya duƙufa yana karatu, ta sa hannu ta rufe littafin. Da sauri ya ɗago ya kalleta, se kuma yai murmushi yace "kefa kin fiye neman Magana, da na tashi a zuciye na make ki fa?" Tai murmushi tace "sannu da hutawa" "Hmm ina fa hutu, lokacin exams na ta ƙaratowa, gaba ɗaya kamar kaina ya fashe" "To ka dinga hutawa mana, ba naji ance expo ce za'a baku ba" Sadik ya harareta yace "me kika maida mijin nakinne? Daƙiƙi ko me? Dan abun kunya duk tsawon shekarun nan Abba na kashe kuɗin makaranta a ƙarshe ace se an bani expo wuce nan" Tai mit tace "kaga gifted, ni ban taɓa tunanin gifted suna karatu ba ai" "Waye yace miki ni gifted ne, ba wani gifted, yanzu dai meye labari?" Tai ajiyar zuciya ta kalli Sadik tace "labari babu daɗi" "Subhanallahi how comes? Meke faruwa kuma?" "An gayawa Abba kana kawoni a mota, jiya yai min Magana" Sadik yace "garin yaya, wanene ya gaya masa?" "Ba ma ita ce babbar matsalar ba, kwanakin baya ƙanwar Umma ta zo gidanmu, tana ta mita akan lallai wai se an min Aure, Abba yace se na gama makaranta, tunda ta koma suke kiran Abba a waya, akan lallai a fitarmin da miji, wai tunda 'yarta sa'ata ce ita ma Aure za'ai mata" Sadik yai mata ƙuri da ido yace "ina jinki" "Sadik Abba yamin miji" Dammm! Yaji ƙirjinsa ya buga yace "ina jinki" Cikin matuƙar rauni ta cigaba da cewa "Sadik i don't know what to do, you are leaving me soon, zaka tafi karatu, zaka barni idan ka tafi mahaifina ze iya yanke Kowane irin hukunci, dan Yanzu haka ya ba da ni, harya ba shi damar ya fara zuwa gurina, da na kammala secondary School yace ze aura masa ni". Ta ƙarasa maganar ƙwalla ta taru a idonta. Kasancewar suka ɗai ne a cikin Library, ya sa ya kamo hannunta cikin nasa, duk da wani irin azababben kishi da yaji yana taso masa, ga matuƙar tashin zuciya da ya shiga, amma ya dake cikin tattausar murya yace "Allah ne yake da nan da shekaru ukun, ke mallakina ce, duk wanna fafutukar da nake saboda mu kasance tare ne, kuma Insha Allah zamu kasance tare, dagaske nake sonki Farhan ba kamar yadda ake cewa RUƊIN ƘURUCIYA bane" "I know, but bana son bijirewa iyaye na" "Ba zamu bijire musu ba, zasu fahimce mu Insha Allah" Haka Sadik ya cigaba da lallaɓata yana kwantar mata da hankali, amma ƙasan zuciyarsa wata irin fargaba ce da tashin hankali mara misaltuwa. Da Sadik ya koma gida ɗakinsa na cikin falo ya tafi, sedai ji yake kamar yai kuka, yana son Farhan matuƙar so, idan aka aura masa ita ze iya riƙeta amma kowa ya kasa fahimtar su. Jiki a Sanyaye yai wanka ya fito falon, a falon yai karo da Mother, ya ɗan ƙura mata, ta dube shi tace "Lafiya kake min wannan kallon haka?" Yace "ƙamshin Abba naji" "Iyayi, Abban naka har wani ƙamshi ne da shi na musamman?" "Eh mana ya dawo ne?" Tai murmushi tace "ya dawo, amma yana hutawa ne" Yai murna yace "I know I guess it right, bari inje idan ya tashi na ganshi anjima" Mother tace "Abinci fa?" "Mother zan dawo ba yanzu ba" ya juya ya fita yana ta lissafin abun yi. Lilly Kuwa da ta koma gida ta tarar mamanta wai ta tafi Sokoto anyi haihuwa, dama babanta ba mazauni bane, daga ita se masu aiki kenan a gidan. Dama ba yau aka saba tafiya a barta a gidan ba, daga ita se masu aiki, Mum ɗinta ta maida zuwa Sakwatto bakomai ba, nan da nan taje ta dawo, wataran idan ta tafi se tai kwanaki ba ta dawo ba. Hakan ya ƙara bata damar sakewa sosai a gidan. Sir Nazir mutum ne me matuƙar aji da kwarjini, ba student ba har a staffs mata akwai masu son shi, amma tsabar kwarjininsa yasa ba su samu fuska a gurinsa ba, amma gashi a karon banza yarinya ƙarama ta samo kansa tana juya shi yadda take so, da tenakon ƙawayenta da kuma kallace kallacen fina finai da uwa uba karance karancen dake ƙara ruɗa tunanin yaran da ke tashen ƙuruciya. Sadik kuwa gidan su Khairat ya tafi, yana tunanin ko ze samu mafita Khairat ta bashi shawara, dan wasu lokutan duk shirirtar ta ta kan bada shawarar da ke ɓullewa. "Kace min magana za muyi kuma kayi shiru" Sadik yace "Khairat na rasa ta ina zan fara ne, abun ya cushemin da yawa" "To daure dai ka gayamin" cewar Khairat dake kallonsa. "Khairat, kin gane Farhan ai?" Khairat tace "ji wata tambaya, ganewa kai" "Khairat, ina matuƙar son yarinyar nan, a dalilinta na takura in gama makaranta a SS2, yanzu zancen da nake miki babanta ya bawa wani ita, nan da 3years za'a aurar da ita, ni Kuma lokacin ina level 3 kenan, bana son in rasata, na so yiwa Mother bayani, amma taƙi saurarata, na rasa yadda zanyi" Khairat tace "bro, lokacin mace fa da na namiji na ɗaya bane, idan kace se an jira ja gama karatu zaka aureta kasan shekarun da saura, kuma haryanzu yarintar ka ake gani" "Naji na gane, ai dama ba cewa nai yanzu ba, sonake a neman aurenta, ni ta jira zuwa kan ta gama secondary ina level 3 se muyi auren, na rasa wanda zan tunkara, Faruk ma ya ƙi fuskanta ta na rasa abunyi gaba ɗaya" Khairat tace "Nima kaina ya kulle wallahi, amma kayi magana ds Abba mana kaji me zece" "Khairat, Mother ma ba ta saurareni ba balle shi" "Kuma kaga ra'ayin su ɗaya da ko Daddy, da se ince ko shi za'a gayawa yaiwa Abba Magana, amma nasan ba zasu amince ba, cewa za suyi kayi yarinta da yawa" Sadik ya dafe kai yai shiru, kawai ya miƙe ya fice daga falon jikinsa ba ƙwari Misalin ƙarfe takwas na dare, Alhaji Abdullahi yana falon dake shashensa shi da kafatanin iyalan sa, ciki hards dr. Da matarsa Jidda suna cin abincin dare. Sedai Sadik se jujjuya spoon yake, ya kasa cin Abincin kirki. "My boy, ya akayi ne naga baka cin Abincin ina fatan ba matsala?" Sadik yai murmushi yace "bakomai Abba" "Yayi kyau, ya shirye shiryen exams kuma?" "Alhamdilillah Abba, mun kusa farawa soon Insha Allah" Abba yace "that's good, Allah ya bada sa'a, and ina nan ana nema maka admission, an duba min nan Lund University a swiden, Alhaji Ayuba yace ; makarantar ta na da kyau sosai, amma se nan da 6_7 months sannan zasu fara bada admission, kaga kan lokacin exams ɗinka ta fito" Sadik ya kalli Abba kamar yai magana, amma kwarjinin mahaifinsa ya hana shi yin Maganar, ya haɗiye maganar da yake son yi ɗin, yai murmushin fole. Aka cigaba da cin abinci, ana hira ban da Sadik da abun duniya ya addabe shi. Lilly na Office ɗin Sir Nazir, tana ta zuba taɓararta son ranta, shi kuma yana binta ido yana murmushin. "Sir yaushe zaka zo Gidan mu ne?" Ya ɗan zaro ido yace "kefa kika cemin gidanku akwai sojoji, so kike in zo su zane ni kenan?" Lilly tai dariya tace "ba abunda za suyi maka fa, kuma ma ba sa nan se guda ɗaya, ni ka ɗaice a gida, idan na koma kaɗaici ne ke damuna" "Kuma kawai se in zo muku gida?" Ɗan tsuke fuska tai tace "ba fa ka taɓa zuwa ba sedai muyi waya, ni dai dan Allah ka zo Gidan mu" "Kai Lilly, ina jin tsoro gaskiya" Yana son yarinyar nan matuƙar so, sedai yasan ko da wasa be isa ya tunkari gidansu yace yana neman Aurenta ba, dan zaren ba kalar yadin bane. "Au kenan baka damu dani ba ko? Nika ɗai nake sonka da nice ai zanje in da kake" tai maganar a shagwaɓe. "Common baby, you know i love you mana, but akwai risk inje gidanku Fatima, ban san wace karɓa za'aimin ba" "Nace maka fa ba kowa a gidan, kawai ka zo muyi hira ka tafi, amma shikenan" Ta juya zata tafi ya riƙo hannunta yace "haba Zahrah na, ba haka bane" "Dan Allah ka zo please" tai Maganar ta na kallon ƙwayar idonsa. Ajiyar zuciya ya sauke yace "in dai hakan ze saki farinciki, zan zo Insha Allah" "Yawwa I love You dear" tai Maganar tana kwanciya a jikinsa. Kamar gunki haka ya ƙame, yana kallon Lillyn. Ta ɗago ta kalleshi ta kai hannunta kan gemunsa, da ke matuƙar burgeta. Kasa ko motsi yai daga in da yake. Cikin wata irin kasalalliyar murya tace "Ban san iya farincikin da zan ba idan ka zo Gidan mu" Hannunsa ya kai ya ɗora akan nata tattausan hannun, yana jera ajiyar zuciya, tare da lumshe idon sa. Babu zato babu tsammani aka turo ƙofar, yanayin da suke ciki na kasala be basu damar yin zafin nama, gurin sakin junan su ba. "Innalillahi wa innalillahi raji'un!" Littafin nan ₦300 ne kacal. 0009450228 Aisha Adam Jaiz Bank Dan Allah a biya kan a karanta. Ayshercool 07063065680.                                   Wasa wasa ta cigaba da jin wannan baƙon yanayin yana bijiro mata, yanayi da bata taɓa shigarsa ba, a hankali take juyi akan katifarta, ta janyo pillown ta, ta rungume shi gam tana ajiyar zuciya, ƙasan zuciyarta tana karanto duk addu'ar da tazo bakinta. Sannu a hankali bacci ya kwashe ta, sedai baccin nata be je ko ina ba ta fara ganin Sadik a baccinta, yana sumbatar ta kamar yadda ya faru a gurin partyn nan. Baccin nata be tsayi ba ta sake farkawa, mamakin yanayin da ta shiga takeyi, harta fara tunanin ko wani abu ne ze sameta? Sedai ta kasa mantawa da mafarkin da tai da Sadik ɗin. Ɓangaren Sadik ma hakan ne ya kasance, juyi yake bacci ya gagari idanunsa, saboda abunda yake damunsa gashi ya rasa yadda ze iyayensa su fahimce shi, ko yanzu yai Aure yana da abun riƙeta, mahaifinsu ya gina ƙatuwar plaza me hawa uku, kowacce tana da shaguna goma sha biyu, kowa yana da hawa ɗaya, wato shaguna goma biyu. Banda sauran kadarori da yake siya yana ajiye musu, mahaifiyarsa yakamata ta fara fuskantar sa amma taƙi bashi goyon baya, balle ta taya shi neman izni agurin mahaifinsa, kullum zancensu da lissafin su, University ɗin da ya dace su turashi a ƙasar waje yayi karatu. Yana zuwa nan a tunaninsa yaji tamkar ya ɗora hannu a ka ya fasa ihu, haka wannan dare ya kasancewa Sadik, rabi bacci rabi tunani. Ƙarfe ɗaya da rabi na dare, amma Fatima Hakeem wato Lilly, tana kwance a kan gadonta, tasa earpiece tana sauraran Audion wani littafi. Babu wani cikakken ma'ana da littafin ke ɗauke da ita, face zunzurutun batsa yadda ake fayyece abubuwan da a shekarunta sun yiwa ƙwaƙwalwarta girman gaske. (Sedai yaran na ƙarshen zamani, ko ba a littafi ba sun san komai, yara ƙanana masu ƙananan shekaru, sedai rubuce rubucen mu na ƙara taka muhimmiyar rawa gurin buɗe Musu abunda be kyautu ace sun sani ba) Shiru tai tana lumshe ido, tana sauraran yadda me karantarwar shima ya ƙware gurin karantowar ba kunya ba tsoron Allah. Duk abunda take saurarar nan ba wanda yake mata yawo a zuciyarta irin malaminta Sir Nazir, saboda a siffofin zahiri da ake faɗa a littafin yana ɗauke da su. A hankali ta sake lumshe idanunta, tana ganinsa a cikin idonta lokacin da take zaune a Office ɗin sa, a hankali tai wani tattausan murmushi, tare da ɗan taune leɓɓanta na ƙasa. A haka gari ya waye, zukatan matasan yaran kowa da abunda yake saƙawa, da tunanin hanyar samawa kansa mafita. Assembly ground ya cika maƙil, an gama National Anthem, Madam Joy tai wa Prefects Umarnin yin inspection, suka fara kewaya ɗaliban suna duba wanda suka yanke farce da wanda ba suyi ba. Salma ce ke duba na 'yan ajinsu Farhan, ta zo kan Farhan, Farhan ta miƙa mata yatsunta dan ta duba, sedai Salman ta kama hannun Farhan ta riƙe tana murzawa a hankali tana mata wani irin murmushi. Mamaki ne ya kama Farhan, ganin abun banbarakwai, ƙoƙarin zame hannunta Farhan take, amma Salma ta riƙe kam, cikin murya ƙasa ƙasa tace "dagaske wancan yaron saurayin ki ne? Sadik yake ko wa?" Shiru Farhan tai mata ta cigaba da ƙoƙarin ƙwace hannunta. "Yarinya wancan ba abunda ze tsinana miki, yazo yana min ihu a kanki, ki fita a sabgarsa ni zan baki abunda be ze iya baki ba, Just be my lover" Wani irin kallon mamaki Farhan ta bita da shi, kamar ya lover tsakanin mace da mace. Ta sake murza hannun Farhan a nata tace "kina da kyau Baby, ina sonki" Ta ƙarasa maganar tare da sakin hannun Farhan. Bayanta Farhan tabi da kallo tana mamakin wannan baƙon lamari haka. Sir Nazir shima ya cigaba da zazzaga ɗaliban, ya biyo ta layin da su Farhan ke tsaye, yana doso in da suke Lilly ta Soma bin sa da wannan idanun nata, yauma ba ƙaramin kyau yai mata ba, yana cikin kayansa na Bautar ƙasa, wando da farar shirt ɗin nan, se ƙamshin turare yake, kasancewar safiyace yayi wani fresh da shi. "Face Your front" ya faɗa a hankali lokacin da ya ƙaraso in da Lilly ke tsaye. "You look good" ta faɗa lokacin da ya ɗan gota ta, ya waigo ya kalleta amma ta maze kamar ba ita tai maganar ba. Farhan Kuwa abun ya ɗaure mata kai, duk jarabar Sir Nazir da kwarjinin sa, amma Lilly take binsa da wannan kallo haka. Aka kammala Assembly aka watse, period ɗin farko Sir Nazir ne ze shiga ajinsu Lilly, dan haka kan ya shiga ta samu brush ta taje yalwatacen gashin girarta, ta ƙara mai a leɓenta, kamar me shirin tarbar wani. Yasmin ta kaalleta tace "ban gane ba wannan gyare-gyaren fa? Naga kina wani ƙara lip gloss" Lilly tace "tarko zanyi in hana wani nustuwa, kamar yadda......ta hana...... Nutsuwa a littafi......" Yasmin tace "shegiyar gari, Allah ya shiryeki" Lilly tai murmushi ta sake gyara zama sosai. Tun daga waje ta fara jiyo maganarsa, ta sake gyara zama ta nustu. Ya shigo ajin da sallama kamar yadda ya saba, suka amsa tare da gaishe shi. Ya amsa a nutse, ya fara ƙoƙarin gabatar da abunda ya kawo shi, sedai da ya ɗaga ido se yaga Lilly na kallonsa, nan da nan yaji yana neman rasa nutsuwarsa, ya rasa meyasa yarinyar nan ke masa haka. A hankali ya taka gaban White board, yasa blue ɗin marker, ya rubuta sunan subject da kuma kwanan wata, ya rubuta Respiration, ya ja layi, ya waigo ya fuskanci ajin, cikin turancinsa me iyayi yace "before we proceed, can someone Among you briefly remind us what we discussed, in our previous class?" Class captain ne ya miƙe, yai bayani ya zauna. Nazir yace "thank you Class rep, you really try, can anyone add something?" Tsit ajin yai kamar ruwa ya cinyesu. "Fatima Hakeem, stand up and said something" Gaban Lilly ya faɗi, dan ba ta da abun cewa, ga turanci ya zauna a bakinta, amma fa batun wani karatu a aji ba yi take na dan be dameta ba, su goma me a ajinsu, ta takwas ko tara take zuwa, ba wani damuwa tai da karatu ba. "Am talking to you" ya faɗa a ɗan hasale. Miƙewa tai tana kumbura baki, tai tsit. Ya sake maimaita tambayar, amma tai masa shiru. "Get out from my class, daƙiƙiya Kawai baki iya komai ba se ciye ciye da surutu" Abun ya tsaye wa Lilly a rai, tai ƙwafa ta juya ta fita ba tare da ko bada haƙuri ba. Seda ya kori Lilly sannan ya samu Nutsuwar gabatar ds lesson ɗin yadda ya kamata, sedai harya kammala lesson ɗin tana ransa. Seda ya cinye time ɗin sa cif, lokacin dai dai da buga jiniyar fita break, ya tattara litattafansa ya fita. Yana fita ya ganta a kan barandar Class ɗin. Ya kalleta yace "idan kika wuce mintuna uku baki zo ba, i will punish you" Murguɗa masa baki tai, ta juya ta shiga aji, yabi ta da kallon mamaki. Tana shiga ajin Yasmin ta hau dariya tace 'haba jaruma ya aka ƙarke da korarki?" "Ƙyaleshi dani yake zancen ai" Farhan kam se binsu take da kallo. "Sssssss" Ko ba a gaya mata ba ta san Sadik ne kuma da ita yake, ɗan murmushi tai amma taƙi waigawa. Murmushi yai ya shigo ajin ya ƙaraso in da take zaune, amma tai saurin kifa kanta akan benci tana murmushi. "Tashi ko in ɗago ki" Da sauri ta ɗago tana murmushi, ya ɗan ƙura mata ido, yace "ina son murmushin ki Farhan" Sunkuyar da kai tana murmushi. Sedai me ji tai yadda ya zauna a kusa da ita ɗin nan, wannan yanayin yana bijiro mata, ya zuba mata dukkan idanunsa, ita kuma ta kasa motsawa. "Tashi muje ajinmu, Yaushe rabon da kike in da nake, kullum sedai in zo" "Ni bana son Zuwa ajinku" "Meyasa, nima bana son zuwa nan, 'yan ajinku suyi ta kallona ko haushi ba kya ji, tashi mu tafi" Ba musu ta miƙe ta bishi. Suna zuwa ajin su Sadik Amin ya kallesu yace "A'a Amaryar Sadik, an gujemu, amma dai gashi nan ya ɗakkoki" Wani kallo Sadik yai masa, hakan yasa ya tsuke bakinsa. Suka zauna a gurin zaman Sadik, yace "me zamu ci ne My dear" Yadda yai maganar yana binta da kallo yasa taji ta duk wani iri, tace "bakomai" "A'a da komai ina zuwa, bari inje in dawo, ungo wayata ki game ko kallon hotuna kan in dawo" Ba musu ta karɓi wayar shi kuma ya fita. Yana fita Taslim da Meena suka shigo, suka samu guri suka zauna. Meena ta sa hannu a jakarta tace "Taslim Allah yasa wannan ƙwayar tafi wadda nake sha, ina son cakewa Sosai" "Mubarak baze baki abunda ba yayi ba, amma dai ki kula, dan kar su saki hauka wallahi dan naga baki da wani aiki se wannan" "To Taslim ya zanyi, kullum gida ba daɗi, baka da ikon ƙwaƙwaran motsi, idan na sha na shige ɗakina nai luf, ba wanda ya sani nikaɗai nake cakewa ta" Taslim tace "ke dama kince ba kya iya karanta littafi a waya, na samo Audion a gurin su Lilly, bari musa ki fara jin abunda yake wakana" Meena tace "to sa inji" Kasancewar daga su se Farhan a ajin yasa da suka kunna kowa yana jin me ake cewa a Audion. Abunda Farhan ke gujewa kunnuwanta ji a ajinsu, shi ake karantowa a nan, ita da take game a waya amma seta rasa ina ma zata taɓa tai game ɗin. Wannan karon kasa tashi tai dan tsira da kunnuwanta daga jin wannan Narkakkiyar baɗala, a hankali ta kifa kanta taji yadda tsigar jikinta ke tashi, numfashinta har wani sama yake. Sadik ya shigo hannunsa da leda, yazo ya zauna, yace "Sorry na daɗe ko?" Ta girgiza kai alamar a'a. "Ga Abinci juyo in baki a baki fa kaina. Noƙe masa kafaɗa tayi, yace 'sarkin kunya, ga naki nan in kin koma aji kya ci. Ya ɗakko wayarsa yasa earpeice ya hau kallon film. Ya barta da wayarsa ɗaya a hannun ta, sam hankalinsa be kai kan abunda su Taslim suke saurara ba, amma ita kunnuwanta sun jiye mata. Nan da nan tunanin Farhan ya nemi ya birkice, jin abubuwan da ko kusa ba ta taɓa kawosu ba, kallon Sadik tai taga ko yana jin me suke saurara, amma taga hankalinsa baya kai. Da ƙyar ta aro jarumta, ta ajiye masa wayarsa tace "zan tafi Class" Ya kalleta a shagwaɓe yace "haba dai, yanzu fa kika zo" "Ai karatu zanje inyi" tai maganar tana kallonsa. "Wai ya naga duk kin wani canza ne? Meyafaru?" "Bakomai" ta bashi amsa. "A'a da komai, kalli ƙirjinki yaddada kike numfashi fa" Hararsa tai tace "Nika matsa in wuce" "Aikuwa sedai ki tafi ke kaɗai bazan rakaki ba" "Eh naji ɗin" tai maganar cikin shagwaɓa. Binta yai da kallo yadda take tafiya jikinta na juyawa. Murmushi yai yace "i love Your dramas" A hankali take tafiya, cike da wata irin matsananciyar kasala, da ruɗanin tunani, Tana tafiyar kawai taji an riƙo ƙugunta, a razane ta waiwayo kawai ta ga Mubarak babba. 'beb ya akai ne?" "Meye haka ka cika ni" "Anƙi a cika ki ɗin, abunda ki kaiwa wancan banzan a gurin birthday zaki min nima, munafuka kiyi ta nuna ke ta Allah ce, ashe 'yar hannu ce" Mutsu mutsu ta fara yi "nika cikani bana so" Ƙoƙari yake ya haɗata da jikinsa kamar yadda yai mata kwanaki. Sedai dai gaba ɗaya ba ta da wani kuzari a jikinta, da ƙyar ta aro jarumta, ta kai masa yakushi a fuskarsa wajen idonsa, ba shiri ya saketa ta arta a guje zuwa aji tana haki. Lilly Kuwa yau har taje tana kwafar note ɗinta ba ta kulashi ba, shikam se satar kallonta yake, yadda ta cuna baki ne ma ya bashi dariya. Kamar yadda ya zamewa Nana jiki, ta fito daga wanka ta tsane jikinta, ta ɗakko humrarta me ɗauke da muski da alumun a ciki, wanda Inna ce take haɗa mata da kanta. Mudubi ta ɗakko ta tsaya tana haska hammatar ta. Ta window Inna ta hangota, tai gyaran murya. Da sauri Nana ta sauke madubin ƙasa. "Me kike dubawa a hammatar?" Cike da ƙuruciya Nana tace "Inna wai ni yaushe gashi ze fito min a hammata?" Inna tace "Rai dai 'yar nan wai an fillewa fara kai, ai ba sekin matsu ba, yana nan tafe da gaggawa, duk ga alamomin balaga nan a tare da ke shima yana nan tafe" "Haba Inna waike ki ta faɗar wannan kalmar dan Allah" "Au to kar in faɗa? Ke fa kika fara tambaya na baki amsa" "To shikenan dai a bar maganar" "Ai ba za'a barta ba, sena kai aya, shi wannan abun da kike burin ya fito idan ya fito ɗin ba kya gyarawa, to za'a samu gagarumar matsala, kinga idan yana fitowa ba kya askewa kina barinsa cunkus a ciki kamar gonar gyaɗa, duk wankan da zaki ba zaki dena wari ba, idan ke ba kya ji na kusa dake zeji, saboda da kinyi gumi ne lamari ze ɓaci, ko kin sa turare zakiji ƙamshin daban warin daban. Haka shima na ɗaya gurin idan ya fito ba'a kula da shi, abunda ze faru kenan" Nana ta kalleta tace "na wani ɗayan gurin?" "Na ƙasan mararki" Inna ta zage ta dinga bayani, seda Nana tai dana sanin ɗakko zancen nan, sam Inna ba ta jin kunya haka take buɗe zance. Ƙarshe Nana ta miƙe tasa kayan Islamiyyar ta tai sallama zata tafi. Inna tace "to a kula da kai, banda biyewa ƙawayen banza, kar wani ya tsaida ke a hanya ki tsaya, banda wasan banza da shirirta a makaranta ki kama kanki, karatu kika je yi, ki kula kar inji kar in gani" "Inna duk fa na haddace wannan karatun naki" "Ai gara in dinga tisawa, kar ki manta wani abun, Allah ya tsare" "Ameen" ta miƙa ta fita. Wasa wasa har zuwa tashi daga Makaranta, Farhan ta kasa sarrafa ƙwaƙwalwarta akan tunanin da Yakamata tayi, yau abubuwa da dama sun ɗaure mata kai, ba dan Soyayyar Sadik da ke da matuƙar tasiri a zuciyarta ba, da barin makarantar nan za tayi ta huta, abubuwa sun sakota a gaba da yawa, kuma ha ba abokin tattaunawa. Ta rasa meta tsarewa da dama daga cikin 'yan makarantar nan suke takurata haka, ga uwa uba abunda taji a ajinsu Sadik, da shi yafi komai dagula mata lissafi da ɗaga mata hankali. Da aka tashi jiki a sanyaye ta ɗau jakarta ta fara tafiya, sedai ta kasa sauri saboda wata irin kasala dake nuƙurƙusarta, so take ta tafi tun kan Sadik ya ganta yace sedai su tafi tare. Sedai me tana tahowa ta hangi Mubarak Babba ya tsaya a hanya, ya zubo mata ido, da gudu ta kasa tai hanyar ajin su Sadik. Cikin sa'a tai karo da shi a hanya. "Farhan gudun ne kike?" "Bakomai" ta bashi amsa. "A'a da komai, guje guje ba halinki bane, ki gayamin meke faruwa" "Bakomai fa" "Shikenan muje" ya sata a gaba suka tafi. Suna fita taga babba a waje a jikin tasu Motar shi da Taslim. Ƙura mata ido yai, ta ɗauke kanta daga kallonsa ta shiga Motar su Sadik. "Nifa na kasa gane kanki beb, what's wrong ne?" "Na fa ce maka bakomai". Yace "shikenan" dan baya son cigaba da matsa mata. Seda suka fara tafiya sannan ta samu nutsuwa sosai, sedai me kasancewar sun zauna daf da juna ita da Sadik, se take jinta wani iri. Kallonsa take ta ƙurawa fuskarsa ido, wanda seda hakan ya bashi mamaki. "Why are you acting so strange, me kike kallo a jikina kuma?" Kallon direban tayi ta kalli Sadik tai murmushi tace "ni ba kallon ka nake ba" "Ƙarya nake kenan?" Ta ɗaga masa gira, murmushi yai ya kwanta a jikin seat ɗin motar yana kallonta. Da haka suka ƙarasa in da take sauka, ko sallama ba tai masa ba ta sauka ta shiga layin gidansu. "Farhanatuwa 'yan makarantar bokoko" Waiwayowa Farhan tai ta ga Sunusi a tsallaken wata kwata yana wankin kaya, yasa wani koɗaɗen yadi. Ɗauke kai tayi zata wuce, ya tsallako ya biyota yana "waini kwanan nan me nai miki ne? Ko gaisheni kin dena yi?" Kallonsa tai take taji wani takaici ya mamayeta, se tsamin rana yake ga wani Mugun warin hammata da yake. Cigaba da tafiya tai ba ta da niyyar saurarar sa, harta shige gida, ya tsaya saroro yana mamakin yadda Farhan ɗin ta canza, da duk in da ta ganshi seta gaishe shi, amma yanzu ta canza. Yau ne dr. Ze dawo daga tafiyar da yayi seminar Abuja, Jidda tayi duk iya ƙoƙarin ta tai gyare-gyaren tarbarsa tana Addu'a Allah yasa ta burgeshi. Ƙarfe huɗu na yamma ya shigo, fitowa tai daga ɗaki tana masa murmushi, binta yai da kallo ganinta cikin rigar buba ta leshi, ta ɗaura ɗan kwali se ya ganta yau daban sosai, kamar ba ita ba. Ƙarasowa tai ta karɓi jakarsa, ya rungumarsa yace "You look so beautiful" Murmushi tai tace "Sannu da zuwa Ranka ya daɗe" "Yawwa uwargida" Suka ƙarasa tai masa jagora yai wanka, ta kawo masa Abinci, se kallonta yake, dan sosai tayi masa kyau yau ɗin nan. Dagewa tai iya ƙoƙarinta, take masa magana da girmamawa saɓanin da da take yaɓa ta yadda take so. Aikam taga yaita nan nan da ita, yana koɗa yadda tai masa kyau, ya saki jiki sosai suna hira, kamar lokacin aka kawota a amarya. A hankali ta nustu tana tunani, Usman yana matuƙar son girma, yana son yaga ana girmama shi, an girmama decisions ɗinsa. A zigar ƙawaye na school da blogs ɗin da take following a social media, ta yadda da Aƙidar cewa idan ka fiye yiwa namiji biyayya ze raina ka ne, ko ya dinga wulaƙanta ka, da ta nustu se taga itama akwai abubuwan da ta tsiro da su na yace ayi abu kaza ta nuna ita ba za tai ba, sedai yabi abunda take so. Shi kuwa idan yace ai abu sau ɗaya tace a'a, baze kuma zancen abun ba seya ƙyaleta da fari gani take ita ke galaba, seda taga yadda yake watsi da ita yana sabgarsa, ya nuna mata ko da ita ko ba ita ze iya rayuwarsa. Tana matuƙar son dr. Dan haka ta fara gano kura kuranta, tai ɗamarar gyarasu tun kan tafiyarsu tai nisa a haka. Nazir yana gidansa da yake zaune, ya gyara katifarsa ya kwanta message ya shigo wayarsa "Hi" Ganij baƙuwar lamba yasa yai reply da "wake magana?" "Nice" aka bashi amsa. "Ke wa?" "Fatima Hakeem" "Ina kika samu lambar wayata?" Yana mata reply ta kirashi, ba tunanin Komai Ya ɗaga yace "ina kika samu lambata kike damuna?" "Au hakama zakace ko?" Yace "Ya akayi?" "Ƙara na kawo maka" "Wace irin ƙara ce haka, baki kawota tun a makaranta ba, se yanzu?" "Ai ƙarar ka na kawo maka" "Hmmm" Cikin shagwaɓa tace "Shine ɗazu ka cemin daƙiƙiya, wai meyasa ka tsane ni?" "Ba daƙiƙiyar bace? Ba kya son karatu sam, shiyasa nake miki haka kyayi zuciya" "To kuma seka dinga dizgani a gaban 'yan ajinmu wallahi seda nai kuka ɗazu" "Haba dagaske" "Uhmm, uhmm wallahi dagaske nake, dan Allah ka dena min haka Please" "In dai ba zaki dinga karatu ba, nima ba zan dena ba" "Ina yi fa" "A'a banga alama ba" Shiru tai ba ta kuma cewa komai ba yace "Hello" Kawai ta sa kukan ƙarya, yace "Subhanallah meye na kuka kuma?" "Ba kaine kace ba zaka dena cemin daƙiƙiya ba" "Kinga ya isa haka, kar wani abun ya sameki ace nine" "To zaka dena?" ta faɗa a shagwaɓe. "Se nayi tunani, seda safe zanyi aiki" Tace "Bari in zo in tayaka" "No, kika makara gobe a school zaneki zan ba Punishing ɗin ki kawai zan ba" Kamar me raɗa tace "good night Sir" Ta katse wayar tana murnar yadda ya amsa mata waya da dukkan attention ɗin sa. Da alama ds wuri tarkonta ze Kama Nazir da wuri. Abu kamar wasa Farhan kusan kullum idan Farhan taje ajinsu Sadik, su Taslim kullum cikin sauraron Audion Novels suke, idan ba taji a can ba ma 'yan ajinsu su Yasmin koda Yaushe aikinsu kenan. Kan wani lokaci tunani ya fara yiwa ƙwaƙwalwar Fahan yawa, wannan litattafai suka fara tasiri a ƙwaƙwalwarta. Gashi a duk lokacin da ta kasance a kusa da Sadik, se taji wani baƙon lamari yana bijiro mata, ko kuma yayin da yaje gurin kwanciya, se tunaninsa ya addabi zuciyarta fiye da yadda take ji a farko. Gefe guda Lilly na ta ƙara shigewa Sir Nazir, ya zaman kullum lokacin break za taje Office ɗinsa suyi hira, tun yana korarta har ya zama idan ba taje ba ze aika a kirata. Farhan ta rasa abunda yake mata daɗi, ta tashi da ƙullewar gefen mara, kuma gashi ba lokacin period ɗinta ba, babban abunda yake ƙara tsoratar da ita be wuce yadda in ta je fitsari take ganin wani yana fita daga jikinta ba, wasu lokutan kan tai fitsari, wasu lokutan bayan tayi fitsari, mussaman idan gefen mararta ya ƙulle, sedai babu wanda zata tunkara tai masa bayanin abubuwan da ke damunta ɗin, a haka ta lallaɓa ta tafi Makaranta. (Akwai ruwa kala kala da suke fita daga jikin mace, a duka cycle ɗin ta daga zuwan ala'ada zuwa wata. Mata na mistake da zarar sunga abu na fita a jikinsu se suce infection ne, ba kowane ne infection ba. Ruwa da yake fita kwana 11,12,13-14 bayan gama al'ada me kama da zare ana jawoshi, wannan yana nuni ne da ovulation period, wato mahaifa ta shirya karɓar jariri. A wannan tsukin lokacin mace zata idan tai tarayya da namiji za ta iya samun ciki. Shine wasu lokutan gefen marar mace har ƙullewa yake, wani ma ya dinga fita da ɗan sirkin jini. Akwai wanda yake fita, normal kamar ruwa ya kan jiƙa pant wasu lokutan, wannan normal lubrication ne na vagina, shi wannan ruwan yana bawa gurin kariya, a hausance ana ce masa Ni'ima, wanda ya kan ƙaru lokacin feelings Wannan duk normal ne. Discharge kamar dusar awara, me wari da ƙuraje, wannan shi ne na cuta, wanda za'a nemi magani.A kiyayi shan magunguna barkatai, saboda lafiyar kayan cikin da ke tace magungunan, bayanin da yawa amma zan taƙaita a nan) Babu me zaunar da Farhan yai mata bayanin wannan, balle ta san takamaimai meke damunta. Da break ta tashi ta tafi gurin Sadik, dan ajinsu se hayaniya suke, a ganinta ko zata samu nutsuwa a can. Baya ajin sun fita ball, se matan ajin su, amma ba Tunanin komai taje gurin zamansa ta zauna, a hankali tana cigaba da jin mararta na ƙullewa, ƙarshe suma su Taslim suka bar ajin suka tafi nasu guri. Kamar an jefo Sadik se gashi ya shigo ajin, yana ganin Farhan yace "yaushe kika zo? Da kin zo filin ball ina can kallon ƙwallo, yanzu su Tasliysuka cemin kina nan kina jirana" Shiru tai ba tace komai ba, ya ƙaraso ya kalleta yace "ya dai ko ba lafiya?" Ta girgiza masa kai tace A'a ni dai ka zauna. Yace "to shikenan" ya nemi guri ya zauna a kusa da ita. Ba tace masa komai ba, ya tsaya yana kallonta, fuskarta ta nuna ta na da damuwa, amma yasan in dai ba ita tai niyya ba, ba zata gaya masa ba. Ya gaji da zaman shirun, ya ɗakko wayarsa yana dannawa, a hankali ta ɗora hannunta akan nasa. Can kuma ta tashi zaune ta kwanta akan kafaɗarsa. Mamaki ne ya cika Sadik ba kaɗan ba, ko matsarta ya fiye yi, se ta zumɓura baki ta hau mita, amma yau ita ce da kanta ta kwanta a jikinsa, a hankali yace "lafiya kuwa Farhan?" Ta ɗaga masa kai alamar eh. Ya gyara zamansa sosai ta samu ta kwanta sosai a jikinsa. Duk da ƙirjinta se bugawa yake da saurin gaske, ita kanta ta san abunda ta aikata ɗin ba halinta bane, kuma ba abune me kyau ba, amma hakan yasa ta ɗanji sassauci akan abunda ke damunta. Sadik ji yai tana ajiyar zuciya, yana dubawa yaga hawaye na bin fuskarta. "Subhanallah, Farhan dan Allah ki gayamin damuwarki, menene?" Kawai ta ƙanƙame Sadik tana kuka, bata san me za tace masa ba, damuwa kam tana da damuwa fal a zuciyarta, amma ya za tai masa bayani, wannan ba abunda za tai masa bayani bane, tunda ba hurumin sa bane, amma wayake bata dukkan lokacinsa da attention ɗinsa in ba shi ba, wa zata tunkara da abubuwan da suke damunta?. A hankali ya fara share mata hawaye yace "ban san meke damunki ba Farhan, amma ina jin damuwarki a raina fiye da yadda kike jinta, ina fatan Allah ya yaye miki abunda ke damunki, kiyi haƙuri koma mene Allah ze kawo mana mafita. Ya ƙarasa goge mata hawayen, ya kwantar da ita a jikinsa, ba tai musu ko ƙoƙarin ƙwacewa ba ta kwanta. Sedai a take Sadik ya fara neman nustuwar sa ya rasa........ 07063065680. Littafin nan ₦300 ne kacal. 0009450228 Aisha Adam Jaiz Bank KO kuje manhajar AREWA BOOKS ku siya.                              Farhan ce tsaye tana kallon su Lilly, ba abunda ya daki zuciyarta irin miyagun maganganun sir Nazir, da ya dinga jifan ta da su a baya, saboda tana tare da Sadik. Basarwa tai ra ƙaraso gaban teburin sa ta ajiye masa wasu takaddu tace "gashi inji Madam Joy, tace you should review it" Tana gama faɗin haka ta jiya ta fice daga Office ɗin. Jiki a sanyaye ya ture Lilly daga jikinsa, yace "kinga abunda ki ka janyo ko? Shikenan mutuncina ya zube a idonta, za taje tai ta yayata abunda ta gani" Lilly tace "ba zata faɗa ba, kawai kayi kamar ba abunda ya faru" Yace "ta yaya bayan ta ganmu?" "Ajinmu ɗaya da ita fa, kaima ka san halinta ba zata faɗa ba" Banza Nazir yaiwa Lilly, yana jin dana sanin biye wa Lillyn. A shagwaɓe tace "Dear fushi kayi ne? Am sorry Please kaji" Tsaki yaja ya tashi ya bar mata Office ɗin Gaba ɗaya. Abun ba ƙaramin ɗaurewa Farhan kai yayi ba, za ta iya dafa Alqur'ani ta rantse da wani ne ya gayamata, Sir Nazir zeyi haka ba zata yadda ba, saboda yake tsare gida, ga faɗar Allah yace Annabi yace, dan mutum ne me riƙo da Addini sosai, amma ba kunya ba tsoron Allah ta ganshi rungume da ɗalibarsa a cikin Office ɗin sa. Tunanin take tayi, taji an janyo hannunta, a fusace ta waiwayo dan ganin waye yai mata haka, kawai taga wanda ta tsana wato Babba. "Meye haka?" Ta faɗa a raunane. Yace "Ban gane meye haka ba? Kin san komai amma ki dinga mazewa wai ke ta Allah, duk keɓewar da ku ke da Sadik mun san abunda kuke ai" Wani Mugun kallo tai masa, tai nufin ta wuce ta barshi a gurin, amma ya sha gabanta yace "kin san yadda kike looking so attractive Kuwa? Idan kika taho jikin ki yana wata girgiza, idan kika bada baya ma wani abun kallon ne, dole ki haukata ɗan mutane, muma ko a na bati ai se a bamu mu taɓa" Wani mummunan ɓacin rai ne ya kama Farhan, wata muguwar tsanar Mubarak Babba ta kuma baibaye ta, ta juya da baya zata tafi, kawai ya taɓa mazaunanta. Seda ta yanke masa hukuncin mari, Sannan ta dawo hayyacinta tace "Allah ya isa ban yafe maka ba, mugu asararre" "Ke dan ubanki ni kika mara, 'yar matsiyata da ke?" "Eh an mare ka ɗin" "Ki sa a ranki bashi kika ɗauka, wanda se kin biya shi wallahi, kin san ki bar wancan sokon ya taɓa ki, amma ni kika mareni" "Eh na bashshi ya taɓa ɗin, ina ruwanka da ni, ka ƙyaleni ka fita daga harkata" Mubarak yai mamakin ƙwarin gwiwar ta, be taɓa tunanin zata mare Shi ba, saboda kallon sokuwa yake mata. Da sauri ta shige Mubarak, ta cigaba da tafiya, wasu hawayen baƙin ciki na bin fuskarta, wata muguwar tsanar Babba na kuma mamayeta. Tun daga nesa ya hangota tana tahowa, ya naɗe hannayensa ya zuba mata ido. Tana zuwa tai karo da shi a tsaye yana kallonta. "Sarkin kuka me kuma ya faru? Ki tai min asarar hawaye ba dalili" Ƙara kwaɓe baki tai tana kuka. "Au abun hadda shagwaɓa, zo ki gaya min menene kuma? Waye ya saki kuka, kowa yana class amma ke kika fito waje" Yai Maganar yana janyo ta jikinsa, ba musu ta kwanta a jikin nasa, amma ba zata iya gaya masa abunda Mubarak yai mata ba, saboda sanin halinsa, dan haka tace "faɗuwa nayi" Kawai Sadik ya kama dariya "wallahi kin fiye abun dariya, Garin yaya kika faɗi?" Tashi tai daga jikinsa tace "dariya ka ke min ko?" "Haba ba fa dariya nake ba, zo mu tafi muje ki gayamin waye ya taɓa min ke, garin yaya ma a kai matata ta faɗi" Ba ɓarin da take yake kallo ba, hakan ya bata damar kallon abunta son ranta tana jin son sa na ƙara ratsa zuciyarta, he's so much caring and funny. Yace "Princess, gaskiya wannan hijjabin da kike sawa yayi ƙanƙanta, wani zamu siya am so Much jealous" "To ai ka san idan na sa wanda yafi wannan girma ƙwacewa za'ayi" Ɗan ƙaramin tsaki yayi yace "kwata kwata wannan tsarin be dace da Addinin mu da Al'adar mu ba, kin ganki kuwa idan kina tafiya?" Kunyace ta kamata, dan ita kanta tasan kayan sun kama jikinta sosai. Kenan Babba abunda yake faɗa gaskiya ne. Bin sa take tayi kamar raƙumi da akala, wani ajin ya jata in da ba kowa, da nufin suje yai rarrashi. Suna zuwa Yasa hannu ya buɗe ƙofar ajin, sedai mummunan ganin da su kai ne ya razanar da su gaba ɗaya. Dan seda Farhan ta saka ƙara, ya janyo ta da Sauri ya toshe mata baki. Wata irin kyarma jikin Farhan yake, ba ita kaɗai ba, shi kansa Kamar zuciyarsa ta tsaga ƙirjinsa ta fito haka yake ji, saboda tashin hankali da fargaba. Duk iya shegen Sadik be taɓa mummunan gani ba kamar na yau ba. Bakomai suka gani ba face Salma da gangs ɗin ta suna sheƙe ayarsu, wata irin tsuma Farhan take kamar zata shiɗe, wannan wane irin bala'i ne haka?. Jan hannunta yai suka bar gurin, sedai ya rasa mema ze cewa Farhan ɗin, gaba ɗaya shima kansa ya kulle. Ya rakata ajinsu ta shiga shi kuma yai gaba, haka jikinta ya cigaba da kyarma, ta kasa mata abunda ta gani, wanda ya danne wanda ta gani a Office ɗin sir Nazir. Ko da aka tashi, babu fargabar Komai Farhan ta kuma bin Sadik a motar su, zuwa gida sedai ya kasa ce mata komai, ita ma kuma ta kasa ce masa komai har suka kaita gida, sedai yau a titi ta sauka ta shiga hanyar gidan su. Tun da ta sauka ta fara tafiya kanta yana ƙasa, sedai ta lura da yadda mutane keta binta da kallo, duk da kasancewar babban hijjabi ne akan Uniform ɗin ta. Sadik kam yana cike da damuwar yadda ze tafi ya bar Farhan a Makarantar nan, me cike da tarin ƙalubale, babu wanda ya damu da harkar kowa, ita Makaranta neman kuɗinsu ne kawai a gabansu, su kuma ɗaliban suna taƙama da kuɗin iyayen su ne ke aiki, dan haka ba wanda ya isa ya taka su, shiyasa kowa yake abunda ya ga dama. Yau gaba ɗaya kamar mara lafiya haka ta wuni, ta rasa meke mata daɗi, har zuwa taje Islamiyya ta dawo, tana tunani wato Salma abunda takeyi kenan shiyasa take mata wasu abubuwan da ta kasa gane kansu gab ɗaya ta dinga cewa wai ta na sonta?. "Farhan" taji an kira sunanta. Waiwayawa tai, taga wata babbar mace ce, maƙwabciyar su da tare kwanan nan, dan matar ta girmi Ummanta sosai. Farhan cikin girmamawa tace "Hajiya ina wuni?" Matar tace "lafiya ƙalau, zo nan Farhan" Ba musu Farhan ta ƙarasa in da mata ke tsaye a bakin gate ɗin gidanta, matar ta ja ta cikin gidanta ta kalleta tace "Farhan kina saka brezia kuwa?" Turus Farhan tai tana kallon matar, taji maganar ta tata wani iri. "Kinga ni uwace ba batun jin kunya kowani abu, kin zama budurwa, ba kya ganin yadda maza ke kallon ki? Duk da naga kina da ƙoƙarin saka hannu a hijjabi" Farhan tai shiru ta sunkuyar da kai, ita kanta abun na damunta, amma tunda ummanta ba ta siya ta bata ba, ba tai mata umarnin sakawa ba, ba ta san ya zata kalli abun ba idan ta fuskanci ta fara sawa ba da izinin ta ba, iya kaci sedai ta saka half vest ta kawo normal vest ta ƙara a kai. Hajiya ta jinjina kai tace "jeki, zan shigo gidan naku" Cike da jin kunya Farhan ta fito daga gidan ta tafi gida. Da daddare bayan ta kammala cin Abincin dare, tana ɗaki tana bitar Alƙur'ani, Abba yazo ya ƙwanƙwasa ƙofar ɗakin. Dama sanye take cikin dogon hijjabi, ta fito daga ɗakin tace "Abba gani" Abba yace "Yawwa, kije ga Sunusi can a ƙofar gida ya zo ku gaisa" Ji tai kamar Abba ya watsa mata wuta, jiki a sanyaye tace "to Abba" Abba yana juyawa ya tafi, Farhan ta fara hawaye, haka nan ta zura takalmanta, ta fita. Tun kan ta ƙarasa ƙofar Gidan, warin hammatar Sunusi yai mata sallama, cikin baƙin ciki da ɓacin rai haka ta ƙarasa guri ɗaya ta tsaya. Wandon jikinsa ta kai kwana uku tana ganinsa da shi, rigar ce ma ya canza. Ya ƙaraso in da take tsaye ya washe baki yana "manya manya maganin ƙanana" Haɗe rai tayi sosai, ta ɗauke kanta. "Hmm naga alamar miskilanci kike ji yau ɗin nan, dama malam ne su kai shawara da Abbanku, suka ce lokaci yayi da Yakamata in fara zuwa gurinki dan mu fuskanci juna" Farhan a ranta tace "ai kuwa ba zamu taɓa fuskanta ba har abada" "Nasan dai an gama gayamiki komai, kusan tun bara Malam yace min 'meze hana ya nema min Aurenki, tunda yaga ke yarinyar kirki ce, kuna haryanzu ba wanda yake zuwa gurinki, yace ko in ba damuwa ni ya nema min Aurenki, kuma cikin ikon Allah Abban yai murna da hakan" Wani baƙin ciki ne ya tokare zuciyar Farhan, wato ma anga ba wanda yake zuwa gurinta shine aka ce ya nemi Aurenta, son da takewa Sadik ne yasa ba ta bawa kowane namiji fuskar yi mata magana, balle yazo gurinta. Kwata kwata Sunusi be iya Magana ba, sqe wani soki burutsu yake, ya kama nan ya kama can, ga uwar dariya sekace wani kwantacce. Ita ko malamanta na Islamiyya da suke alarammomi mahaddatan Alqur'ani, a nuste take ganin su, Amma Sunusi ya fita daban gaba ɗaya. Har ya gama surutun sa, Farhan ba tace masa ci kanka ba, yai surutan harya gaji yai mata sallama, ya tafi. Wani marurun takaici ne ya ƙule zuciyar Farhan, ga Sadik me za tai da wani Sunusi? Ta dawo gidan ba daɗewa taji sallamar Hajiya, Umma ta amsa ta bata gurin zama suka zauna a tsakar gida. Hajiya tace "Maman Farhan, wani shishshsigi na zo nai miki, amma lamari na 'ya'ya shi ɗa na kowa ne ko ba haka ba?" Umma tace "hakane" Tace "yawwa, Magana ce game ds Farhan, duk da na ga ku al'adar ku ce ba'a bawa ɗan fari kulawa, amma 'ya'yan da a kaiwa wannan ban da na yanzu, Farhan ta zama budurwa ba ta da ƙawar da ta wuce ki. Ki duba yanayin jikinta, Allah ya bata garin jiki yakamata ace ta fara saka brezia saboda yanayin jikinta, Yakamata ta san mahimmancin kula da jikinta, duk da naga 'yar ta mu nutsatsiyya ce Alhamdilillah, amma saboda yanayin al'adar taku nace ni bari in zo da kaina in adana 'ya ta, da na kirata na mata magana ni da ita, amma naga ba haka yakamata ba, yanzu ina Farhan ɗin?" Umma tace "tana ɗakinta" taiwa ƙanin Farhan ɗin umarnin ya kira Farhan. Farhan ta fito tsakar gida, duk da takaicin da ke cunkushe a zuciyar Farhan, a haka ta gaida Hajiya. Hajiya ta miƙowa Farhan ledar viva tace "Farhan ga brezia nan ni na siyo miki da kaina, a adana wannan baiwat da Allah ya bayar, dan ba kowa yake bawa ba, a adana yadda yakamata Allah ya fito da danƙareren miji na gani na faɗa" Kasa ɗaukar ledar Farhan tayi, ta ɗaga kai tana kallon Ummanta, amma taga Umma na kallon wani gurin daban. Hajiya tace "Au ba zaki ɗauka ba, jira kike se ta baki umarnin ki ɗauka, maza ɗauki kije, idan Allah ya haɗaki da 'yan banzan samarin nan na zamanin, sukai miki ba daidai ba, ko wani ya taɓa kya nutsu ai tashi kije" Gaba ɗaya wat irin kunya ta mamaye Farhan da Umma, sam Umma ba ta ji daɗin maganganu nan da Hajiya ta faɗawa Farhan ba, wata irin kunya ta lulluɓe ta. Farhan tace "Nagode" ta ɗau ledar ta tafi. Tan zuwa ɗakinta ta zazzage ledar, taga brezia ce guda bakwai, sababbi ga turaren humra hadda su hoda da jambaki. Da sauri ta miƙe ta fara gwadawa, ta saka sannan ta kawo rigarta ta mayar se ta ga rigar ta ƙara zama a jikinta. Se kuma kawai taji kunyar kanta ta kamata, wai yau ita ce da saka brezia, farin cikin samun wannan kayan, yasa duk ta manta da wasu damu wowi da suka dameta. Washegari da taje school kuwa, Sadik ya dinga cewa "wani abu ya canza a tare da ke Farhan, amma na kasa gane ko meye" Ta bagarar da zancen, dan da sa idonsa ze iya ganowa, sedai tana ta so ta bashi labarin jiya Sunusi ya zo, amma ba ta son ta sa shi a damuwa. Amarya Jidda kam, tuni ta fara dawowa daga rakiyar ƙawaye, dan ta fara fuskantar wannan Aƙidar ta su hadda baƙi ciki a ciki, dan su basu samu damar yin Auren ba, amma duk lokacin da aka haɗu a group ko get together ana hira, suna nuna cewa yiwa namiji biyayya yana kawo raini da wulaƙanci. Tabbas namiji ya cancanci yabo da biyayya, duba da irin tarin ɗawainiya da ke kansa, duk dan ganin farincikin iyalnsa. Ganin ta fara dawowa daga rakiyar su ne yasa suke ta faman zunɗenta yayin da wasu ke zigata wai daga yin Aure duk ta canza. Yanzu ma chatting take, a group wata Friend ɗin su ta turo, yiwa miji girki ba dole bane, anayi ne dan kyautatawa, kuma ai cewa a kai miji ya ciyar da mata. Nan da nan topic ya ɗau zafi, yayin da wasu ke ta supporting ɗin topic ɗin. Jidda tai murmushi tace "haba ku kuwa, ya fita ya nemo rana, zafi, sanyi ya fita ya nemo sannan kuce girki ba dole bane, ai kuma ku gayawa kanku gaskiya" "Ke Jidda wai ko dai dr. Naki ya jiƙa wani abu ya baki ne yasa duk kika zama haka?" Jidda tace "ya jiƙa ya bani zumar soyaya mana" "Ke, mu zaki gayawa magana dan kin san Namiji, to muma muna hanya" cewar Abida. Jidda tace "dole in gaya muku magana mana, seku jira ku san namijin kuma kwayi bayani" Maryam tai Voice message tace "ba shakka kin shahara, ke gaki kin san daɗin miji, muma muna hanya dan ubanki amma batun sakarwa miji wannan maganar babu ita" Jidda tace "ki bari ki san daɗin mijin, se mu tabattar da hakan" Maryam tace "ɗan labarta mana meye daɗin mijin" Bestyn Jidda ce wato Sajida, tabi Jidda private tace "besty, a beg close that Chapter, ki rabu da wannan shashashan, suna bugun cikin ki suji sirrin Aurenki, dan Allah basar da su" Jidda tace "kuma fa hakane besty, kai shiyasa nake yinki tawa ta amana, bari in ƙyale su kawai" Kwana biyu Lilly ba taje office ɗin sir Nazir ba, kuma ya shishshiga ajin su, amma yaga bata zuwa kwana biyun nan. Abun seya ɗan dameshi, ya koma gida da daddare ya ɗau wayarsa ya kira ta. Ya kira ya kai sau uku, se a na huɗu ta ɗauka, da ta ɗauka ɗin kuma taƙi magana. "Baki ga kiran wayata bane kika ƙi ɗagawa?" "Na gani" ta bashi amsa. "Amma meya hana ki ɗagawa?" "Bani da lafiya" ta faɗa a taƙaice. "Meya same ki?" "Allah baby gani nake kamar ba sona kake ba, daga wannan incident ya faru, shikenan kake fushi dani duk na rame ko iya cin Abinci ba nayi, kuma ko a waya ka kasa kirana, ni wallahi ba ka sona" ta ƙarasa maganar cikin kuka. Ya kwantar da murya yace "haba Babyna, ke in wani ya gayamiki bana sonki zaki yadda? Kawai banji daɗin yadda Farhan ta samemu bane, kuma kika nuna baki damu ba shiyasa naji ba daɗi but am sorry please" Shiru tai taƙi Magana. "My Lilly kina jina?" Kukan shagwaɓa ta kuma sa masa, ya shafi gemunsa ya lunshe ido, ya furzar da iskar bakinsa yace "Babyna nace kiyi haƙuri dan Allah, ko nima so kike in fara Rashin lafiya ne?" "A'a bana son kayi rashin lafiya" "To shikenan, ki dawo school please, duk ranar da ban ganki ba bana jin daɗi" "Ai da ka damu dani, da in da nake zaka zo" "A'a Lilly ina jin tsoro ne, amma kiyi haƙuri ki dawo kinji tawan" "To shikenan, Zan dawo insha Allah" "Yawwa i love You so much" Tace  "Ummmm I love you too" Haka ya zage ya cigaba da zaro manya manyan kalaman Soyayya ga Yarinyar da ta kasance ɗalibar sa, wadda ba ta fi sa'ar Autar su ba. Haka rayuwa ta cigaba da tafiya, cike da ƙalubale, wataran farinciki wataran akasin haka. Lilly ta koma Makaranta suka shirya, ita da Nazir suka cigaba da rayuwar su kamar da. Mubarak Babba duk in da yaga Farhan se ya mata kallon warning, kallon zamu gauraya, dan ya tabattar mata da se ya rama marin da tai masa, kuma ko da tsiya ko da tsiya tsiya se ya keta alfarmar rayuwar ta. Kasancewar Farhan ta fara gogewa Sosai, duk da rashin maganar ta amma tana da ƙwarin gwiwar mayar masa da martani ta hanayar cewa "Allah ya fika, kuma ba ka isa kaimin abunda be min ba". Sunusi ya cigaba da zuwa gurin Farhan, sedai fa ba wata hirar kirki, shikaɗai yake surutunsa ya gama ya tafi, kanzil ba zata ce masa ba, sedai yayi ya gaji ya tafi, ƙarshe Ya kai ƙararta gurin Abba, Abba yace yayi haƙuri rashin sabo ne da ba suyi ba. MASOMIN RIKICI! A yaune ɗaliban SS3 na makarantar su Farhan ke kammala jarrabawar su ta ƙarshe, suna fitowa daga jarrabawar suka shiga yayyaga Uniform ɗinsu, yayin da wasu suka dinga rubutu da maka a Uniform ɗin, da gudu suka dinga tafiya in da aka aje manyan speakers na cashiya kawai saboda murna, wasu kuma litattafansu suka shiga yagawa suna watsawa sama, shakiyanci kala kala. Yayinda zuciyar Sadik ta cika da damuwa, ta kuma tsananta harbawa, sam ba ya farinciki zuciyarsa a cunkushe take. Cikin sanyin jiki yake takawa, Yayin da ɗalibai ke ta iface iface, suna tafiya filin rawa, gami da waƙe waƙe, kamar yadda yake bisa al'adar makaranta, duk lokacin da ɗalibai suka kammala jarrabawar ƙarshe ta fita, an dinga raye raye kenan. Ƙofar ajin su Farhan yaje ya tsaya, ya zuba hannu a aljihunsa, ya tsurawa ƙofar ido, cikin sanyin jiki ya murɗa ƙofar. Kamar yai tsammani, yana buɗewa sautin kukanta ya daki dodon kunnensa, yai dirar mikiya a zuciyar sa. Ajin ba kowa se ita kaɗai. Sannu a hankali ya ƙarasa, ya zauna a kusa da ita, ya ɗago ta ya tsura fuskarta ido yadda tai ja, fuskar duk hawaye. Cikin sanyin jiki yake share mata hawayen, yana girgiza mata kai, a hankali ya fara Magana "ki zama jaruma mana my wife, hakan ba yana nufin rabuwar mu bane, zan dimga zuwa ganinki kan in tafi fa" Wani kukan ne ya sake ƙwace mata, dan tana jin yadda zuciyar ta ke tsananta bugu, da wata irin mummunar faɗuwar gaba da ta tashi da ita yau, dan daren jiya ba ta rintsa ba. Rungumeta yai a jikinsa tsam, kamar ze tsage ta shige jikinsa, ya kwantar da kansaa wuyanta, yana jin yadda take sheshsheƙar kuka. Kasa jurewa yai, dan yadda Farhan ke jin faɗuwar gaba shima haka yake ji, a hankaliya lumshe idonsa, sega hawaye na zirarowa daga cikin idon nasa, tabbas abunda ze sa Sadik kuka, ba ƙarami bane, Farhan ta nai wani matsayi me girman gaske a zuciyar sa. "Princess, dan Allah ki dena kukan nan haka Please, zaki karyan zuciya" Ƙanƙame shi ta sake yi cikin kuka take cewa "ba zan iya denawa ba, gabana faɗuwa yake, ban san me ze faru ba, kuma bana son ka tafi ka barni" Shafa bayanta ya shiga yi, yace "ba abunda ze faru se Alkhairi, kuma zan dinga zuwa ina ganinki, kina da mahimmanci a gareni Farhan" "Dan Allah Sadik, ka riƙe alaƙawarin da kaimin Please" tai maganar cikin kuka tana zubar da hawaye. "Duk wuya duk rintsi, in dai ina raye sena tabattar wa da duniya, Soyayyar mu ba RUƊIN ƘURUCIYA bace, ba abunda ze sauyan ra'ayina insha Allah, ina sonki Farhan" "Nima ina sonka sosai Sadik, dan Allah karka barni" Karo na farko tun haɗuwarsu, da ta buɗe baki tace "ta na son sa" Ya ɗagota daga jikinsa yace "dan Allah ki maimaita abunda kika ce" Ɗan tura baki tai, sannan ta lumshe ido tace "Ai kaji me nace" "Dan Allah ki sake faɗa". "I love You" ta faɗa tana sunkuyar da kai "I love You too my princess" ya ƙarasa maganar tare da haɗe bakinsa da nata. Farhan ta kasa hana Sadik, sema riƙe shi da tayi sosai. Daga Farhan har Sadik ba zasu iya misalta duniyar da suka faɗa ba, sun shafe lokaci a haka, duk da yadda zukatansu ke matuƙar harbawa, saboda rashin sabo, jin  Sadik ya kai hannunsa ƙirjinta ne yasa tsoro ya shigeta, da sauri ta zame jikinta tana maida numfashi. A hankali ya kashingiɗa ya lumshe ido, yana maida numfashi, yana jinsa a wata sabuwar duniyar ta daban. Ita kanta Farhan jinta tai wani iri, ta shiga wani yanayi na musamman da ya kan bijiro mata lokaci zuwa lokaci. Ya zaci Farhan za tai masa mita ko ta haɗe rai, amma ya buɗe idanunsa yaga ita ma ta kashingiɗa tana sauke numfashi. Da alama ta shiga yanayin da ya shiga. Ya kai hannu ya kuma riƙo nata, yace "Farhan" ta buɗe ido ta kalleshi, amma se taji kunyarsa tai saurin sunkuyar da kai. Murmushi yai yace "tashi mu tafi gida, wannan kaɗe kaɗen ya cikamin kunne, ina buƙatar hutawa" Tace "to" Ta miƙe ta fita, ya zuba nata ido tun daga sama har ƙasa a ransa yace  "Allah ka bani yarinyar nan" Ta kalleshi tace "ka tashi mu tafi" A kasalance ya tashi, tai gaba yabi bayanta, ta tsaya ta waigo taga yana tafiya a hankali tace "meye hakane?, ka zo mu tafi, kace mu tafi kuma kana tafiya a hankali" Sadik yace "kece kika ja min ai" Share shi tayi taƙi kuma cewa komai. Ya biyota suka fito, 'yan Makaranta nata iface ifacensu da celebrating, su kuma suka tafi. Suna tafe a mota hannuanta na cikin na Sadik, direba kam yana hangowa ta mudubi, a ransa yace "shikenan yarinyar nan, Allah dai ya tsare yasa me afkuwa bata afku ba" Nazir ya tashi da matsanancin ciwon ciki da zazzaɓi, harta kaishi ga danganawa da Asibiti, seda aka masa ƙarin ruwa, dan haka ko Makaranta be shiga ba. Seda aka sallamo shi ya dawo gida, Sannan ya samu ya sanar da Makaranta, ga halin da yake ciki. Aikuwa malamai sukai tawaga guda duka je duba shi, kasancewar Makaranta na matuƙar ji da shi. Da labari ya samu Lilly, Nazir ba lafiya ta damu matuƙa, ta shiga tashin hankali. Ta kirashi a waya tai masa sannu, amma jin yadda yake amsawar yasa ta san yana jin jiki. Kasancewar Gidan ba kowa se ita kaɗai, yasa ta cewa masu gadi zata gidansu ƙawarta, ta kira Mummynta a waya ta gaya mata, ba musu suka bata hanya ta fice. Taje ta yo siyayyar kayan marmari, da abubuwan sha'awa ga mara lafiya, ta tafi gidan Sir Nazir, dan in suna hira yana kwatan ta mata gidan da yake zaune. Littafin nan ₦300 ne kacal. 0009450228 Aisha Adam Jaiz Bank KO kuje manhajar AREWA BOOKS ku siya. Littafin nan ₦300 ne kacal. 0009450228 Aisha Adam Jaiz Bank KO kuje manhajar AREWA BOOKS ku siya.  Da Lilly tabi kwatancen sa ba ta wani sha wahala ba ta gano gidan, ɗan ƙaramin gida ne, kusan shikaɗai ne a tsukin gurin, dan sabuwar unguwa ce duk ba mutane, ba wasu gidajen kirki se tsilla tsilla. Ƙaramar Ƙofar taje ta fara knocking, ta daɗe a tsaye dan har ta fara fidda ran za'a buɗe ƙofar, kawai taji an buɗe. Turus yai ya tsaya yana kallonta, kallo ɗaya tai masa taga yayi rama sosai, idanun sa sunyi zuru zuru, sanye yake cikin dogon wando baƙi, da vest fara ƙal. Duk da halin rashin lafiya da yake ciki, amma a haka ya daure yace "Lilly, me kike a nan?" Tace "Duba ka na zo yi, na kasa samun nutsuwa tun da aka ce ba ka da lafiya" "Shikenan, Nagode ki maza ki koma gida kar wani ya ganki a nan kinji" Kallonsa tai da mamaki tace "meyasa?" Yace "idan wani ya ganki za'a iya yi mana sharri fa" Aikuwa ta haɗe rai tace "dama na sani nina damu da kai, har in zo in da kake in duba ka amma ka min haka shikenan nagode" ta juya zata tafi yace "am sorry ba haka bane, ina jin tsoron abunda zeje ya zo ne, amma shikenan shigo kawai" Ya bata hanya ta wuce, kasancewar jikin sa ba ƙwari a hankali yabi bayan ta, suka shiga ƙaramin falon ya samu guri ya kwanta akan doguwar kujera. Ya lumshe idonsa. Ƙura masa ido tayi sosai ta na binsa da kallo, duk da yayi rama amma hakan be hana kyawunsa fitowa Sosai ba, wata irin soyayyarsa na sake fizgarta. "Sannu my love" ta faɗa cike da kulawa. ya jinjina mata kai ba tare da ya buɗe idonsa ba. Duk da ba shi da lafiya, amma ko ina tsaf da shi,a gidan a share, hadda ƙamshim roomfreshner. Ta miƙe ta ɗakko ledar da ta zo da ita zuwa gaban sa, ta zauna tace "ka tashi ka duba abunda zaka iya ci ka samu ka ci kaji babyna" Ya girgiza mata kai yace "bana buƙatar komai, bana son cin komai" Cikin shagwaɓa tace "haba dan Allah, ka daure ko yaya ne ka ci" A hankali ya buɗe ido ya kalleta, yaja numfashi yace "tashi daga kusa dani Lilly, ki tafi gida ma kar a nemeki" "Ni kake kora ko?" Ta faɗa tana nuna kanta. "Ba korar ki nake ba, kar a nemeki a gida, na san ba'a san nan kika zo ba" "Mummy ta na Sakwatto, an musu haihuwa fa, daga nan za taje ganin Daddy a Abuja" "Duk da haka dai" ya faɗa a hankali. "Idan ba ka ci ba ba zan tafi ba" Ya tashi zaune yace "bani abunda kike so inci, Nagode sosai da ziyarar nan, amma ki tafi gida" "Wai se korata kake shikenan, ni idan ka zo gidan mu ba haka zan ma ba" Nazir yace "Lilly is different ace ni na zo gidan ku, akan ace ke kika zo gidana, kin kasa gane me nake nufi" Ba tace komai ba ta ɗakko masa madara ta miƙa masa. Ya girgiza mata kai yace "zata iya sani amai, bani Ayabar in ci" Ta ɗakko ta miƙa masa, da ganin yadda yake ci ka san yana jin jiki. A hankali yace mata "miƙo min ruwa a bayan tv stand ɗin can" Ta tashi kamar yadda yai mata umarni ta kawo masa ruwan roba, sedai yanzu kusancin da ke tsakanin su yafi na ɗazu. Ya karɓa ya sha, se bin sa take da ido. Yana ƙoƙarin kwanciya, Amma  ta hana shi tace "guda ɗaya fa kaci, baka ci da yawa ba" Yace "na ƙoshi, zan iya amai" Ba tsammani taji ya kwanta a jikinta ga jikin sa da zafi sosai saboda zazzaɓi. Da ƙyar tace "jikin ne?" Maimakon ya bata amsa se sake ƙanƙameta da yayi a jikinsa, yana ta numfashi da kyar. A hankali ta dinga shafa bayansa zuwa sumar kansa, tana masa Sannu. Gefe kuma tana raya abubuwa daban daban a cikin ranta. Tabbas mace duk ƙanƙantar mace mace ce, Ruɗin ƙuruciya da kururwar sheɗan, silar lalacewar ƙarshen zamani, abunda ake rubutawa a litattafai ya taka rawa a ƙwaƙwalwar Lilly gurin hilatar malamin nata zuwa ga afkawa tarkon sheɗan, shikuma bisa ga jagorancin sheɗan ya biyewa son zuciyarsa, suka afka tarko me matuƙar muni. Ya aikata zina da ɗalibar sa, abunda ko a mafarki be taɓa kawo faruwar hakan ba. Ya kalli in da Lilly ke kwance, ko ƙwaƙƙwaran motsi ba ta iya yi. Dafe kansa yayi tare da ɗorawa kansa dukkanin laifin, kan sa cigaba da sarawa yai, ya zubawa Lilly ido da hawaye ke bin gefen idonta. A hankali ya ɗagota yana mata Sannu, amma ta kasa magana se kuka da take. A hakan ya temaka mata ta kintsa jikinta, sedai ko haɗa ido ya kasa yi da ita, saboda matsananciyar kunya da kuma nadama da suka shige shi. Duk da yadda take jinta a galabaice, haka ta fice ta bar gidan, zuciyarta a cunkushe da dana sani da kuma zubar da hawaye, shikenan ta rasa abu mafi kima da daraja a tare da ita, duk da yadda ta ɗokanta da son gazgata abunda suke karantawa a littatafai, da yadda zuciyarta ke ƙawata mata malamin na ta, amma ta gane Barno gabas take. Ta kuma ji nadamar abunda yafaru a tsakanin su da malamin nata. Ta na zuwa gida tun a falo ta zube, ta dinga rusa kuka kamar ranta ze fita, tayi asarar da ba zata taɓa mayar da ita ba. Ranar yau Sadik ya kasa bacci, shi kansa ya san jure rashin Farhan a kusa da shi ba abu ne me sauƙi ba, ya riga yayi matuƙar sabo da Masoyiyyarsa Farhan, yana jinta sosai a cikin ransa, sedai fargaba ta kan shige shi a duk lokacin da ya tuna wai mahaifinta ya mata miji, yana jin wani abu a ransa wanda ya kasa tantance ko menene. Da safe ba zuwa Makaranta, se ƙarfe goma na safe sannan ya tashi daga bacci, ya tashi ya shiga cikin gida dan gaida Mother. Tana ganinsa tace "Ahh, Sadik wai me ke damunka kwanan nan ne?" Sadik yace "me kika gani?" "Duk ka rame kayi wani iri, ance kun kammala exams amma ba wani alamar farinciki a tare da kai, balle a ɗan shirya maka wani abu na musamman, whats wrong ne my Auta?" Sadik baya son maimaita magana, ya san koya gayawa Mother damuwarsa ba abunda za tayi a kai, sema wataƙila ƙarshe suyi faɗa dan haka yace "bakomai kawai am not in mood ne" "Ban gane you are not in mood ba, gaba ɗaya fa ka dena walwala Sadik nifa bana son ganinka a haka" Cike da shagwaɓa da kuma ƙosawa yace "haba Mother, nace miki fa bakomai am ok, just a little stress, kuma shima saboda exams ne, but i will be ok insha Allah" "To shikenan, kaje Abbanku ya tashi ka gaishe shi" Sadik bece komai ba ya nufi sashin Abba, ya tura ƙofar ya shiga da Sallama. Abba dake shan tea ya ɗago ya kalli Sadik tare da sakar masa murmushi sannan ya amsa sallamar. "Abba good morning" "Morning dear, ka tashi lafiya" "Alhamdilillah" Abba yace "Masha Allah, director na makarantar ku ya kirani jiya, he tolds me that you wrote your last paper yesterday" Sadik yace "eh Abba mun gama" "Masha Allah My Son, Allah yayi albarka ya bada sa'ar jarrabawar, Insha Allah sakamako na fitowa zaka tafi karatun ka, kaje kai zamanka hankalinka kwance, idan ka kammala seka dawo" "Abba dan Allah, ni dai dama a bar zuwa ƙasar wajen nan a nema min kawai a Nigeria ko a nan Kano ne" Abba ya kalleshi yace "You Are not serious, Sadik da a zamaninmu shine a kai karatu na gaske a ƙasar nan, amma banda yanzu karatun da zaka kammala a shekara huɗu, se kai shekaru bakwai kana fama abu ya gagara, kullum cikin yajin aiki, yanzu idan kaje can kuwa ba ruwanka da wannan nan da nan ka kammala degree ɗinka, kayi Master's ɗinka a can, sannan ka dawo gaba ɗaya" Sadik kamar ze kuka yace "Abba wai sena gama masters zan dawo?" "To idan ka dawo ka zauna me zakayi, ka dinga zuwa mana hutu shiki, ka maida hankali ka gina rayuwar ka, duk da nasan ba zaka bani Kunya ba" "Abba, ba zanyi Aure ba sena gama Master's ɗin?" Saroro Aba yai, dan har damuwa ta bayyana a fuskar Sadik ɗin. "Wace irin maganace kuma wannan Sadik? Guda nawa kake da kake wannan batun, kai ka san nauyin dake hawa kan mutum kuwa idan ya ajiye iyali, guda nawa kake gaba ɗayanka, yayanka ba abun koyi bane a gareka, ya kammala Master's ɗin sa sannan yai aure, ai shi Aure lokacine Ɗan gidan Abba, idan lokaci yayi zaka yi" Ba fargabar Komai Sadik yace "Abba yarinyar da nake so ba zata jirani tsayin shekaru bakwai ba, kan in Aureta ba, Daddy wallahi ina sonta Sosai" Sadik yai maganar ƙwalla kwance a idonsa. Abba ya jinjina kai yace "Sadik, kasan dai ba zan maka Aure yanzu ba ko? Kai kanka kasan ba ka isa Aure ba, ina son ka cire wannan tunanin a ranka ka maida hankali akan karatun ka" "Abba ina sonta Sosai, idan na tafi zata iya Aure ta barni". Tausayin Sadik ne ya kama Abba, amma ya bar hakan a zunzurutun shirmen ƙuruciya. Ya dafa Sadik yace "Sadik, RUƊIN ƘURUCIYA ne ke damunka, kana tafiya karatu ya ɗauke naka hankali zaka manta da ita, sannan ina kai ina wata Soyayya? Shirmen ƙuruciya ne kawai, ka cire ta daga ranka ka fuskanci rayuwar ka kaji ko?" Sadik ya jinjina kai jikinsa a Sanyaye. Abba yace "yawwa my son, Allah ya baka ilimi me amfani, matso kusa dani muyi breakfast tare" Sadik ya girgizawa Abba kai yace "na karya" Ya miƙe jiki a Sanyaye, ya bar part ɗin, ɗakinsa na BQ ya tafi, jikinsa har rawa yake saboda tsabar damuwa. A falo ya wuce Faruk, yana shirin fita. "Sadik lafiya kuwa?" Sadik be amsa masa ba ya wuce ɗakinaa, yana zuwa ya faɗa kan gadonsa, ya ɗora pillow a kansa kawai yaji hawaye ya fara bin fuskarsa. "Sadik tashi muyi magana, meye haka kake ne?" Yaji muryar Faruk a kansa. Sadik ya tashi zaune, sedai abunda ya bashi mamaki be wuce yadda yaga hawaye a fuskar Sadik ba. Take hankalin Faruk yai mummunan tashi, saboda mutum ne me matuƙar son 'yan uwansa. "Sadik meke damunka ne, ka ɗagan hankali fa" "Faruk dan Allah ka gayamin meyasa kuke cewa soyayata RUƊIN ƘURUCIYA ce? Na gayawa Abba abunda yake damuna, amma shima yace min RUƊIN ƘURUCIYA ce, meyasa kuke cewa hakane?" Faruk yace "Sadik, ba ka ajiye batun nan ba ko? Ni da kai na gaya maka komai, kuma nace maka lokaci ne, zaka dena jin duk abunda yake damunka" Shiru kawai Sadik yai, Faruk ya cigaba da ƙoƙarin kwantar masa da hankali, amma sam baya jin abunda Faruk ɗin yake faɗa, har yai ya gama ya bar ɗakin. Yana cikin tunanin ne, Wayar Sadik ta far ringing, be ko duba waye ba ya ɗaga ya kai kunnensa. "Wato kai dan ka riga mu graduating har ka fara ja mana aji ko? Ji muka fito muka nemeka muka rasa, ana can ana ta celebrating muna nemanka muyi maka spraying kuɗi, amma muka neme ka muka rasa gaba ɗaya" Nasir ne yake ta wannan cakwaikwaiwar da ba Komai Sadik ɗin yake fahimta a cikin maganganun nasa ba. "Sadik kana jina kuwa?" Sadik yai ajiyar zuciya yace "ina jinka mana" "Amma shine kai mana banza? Wallahi har mun fara missing ɗin ka" Sadik yai murmushi yace "kune za kuyi missing ɗina?" "Wallahi Sadik dagaske nake, gaba ɗaya yau ajin ba daɗi baka nan, ko salama ba ka tsaya munyi ba jiyaka tafi" Sadik yace "na tafi kai mata ta gida ne shiyasa" "Lallai Sadik, yanzu yarinyar da ka haɗu da ita a 'yan watannin nan har ta fiye maka mu da mu kai shekara da shekaru tare?" "Kowa matsayin sa daban a gurina" "Bakomai, yaushe zaka shigo ne?" "Daga gama makarantar se in fara zuwa, se an kwan biyu tukuna, bana son in zo ta shiga damuwa" Nasir yace "Lallai, abun anku babba ne Sadik" Sadik yace "ƙwarai kuwa, zamu bawa wanda suka ɗau lamarin namu wasa Mamaki" Nas yai dariya yace "ai shikenan" Su kai sallama Sadik ya kashe wayar ya cigaba da tunanin sa. Ya barwa zuciyarsa ze jarraba cire Farhan daga rayuwarsa ko da gaske ne da ake cewa ba sonta yake ba, RUƊIN ƘURUCIYA ne kawai? Sir Nazir kuwa tun da abun nan ya faru, kusan kwanaki uku amma damuwa da masa yawa, hakan ya bawa ciwon zama sosai a jikinsa, ga ciwo ga damuwa, hawaye sosai yake idan ya tuna aika aikar da ya tafka, be san wani irin hukunci ze fuskanta ba, ko zata je ta faɗa azo a kama shi, ko ba zata faɗa ba be sani ba. Kasa jurewa yai, ya ɗau wayarsa ya kira layinta, beyi tsammani ba yaji ta ɗaga wayar. Da sauri ya tashi zaune yana faɗin "Fatima ya jikin ki?" Maimakon tayi Magana se sheshsheƙar kuka da take. "Lilly dan Allah ki saurareni, kuskure ne mun riga munyi amma dan Allah.... Be ƙarasa maganar ba ta sake rushewa da kuka, wanda yake bayyanar da tsantsar damuwa da take ciki. Kasa magana yayi daga ƙarshe ya katse kiran, wasu hawayen dana sani suka shiga zubo masa, shima yana da ƙanne mata, ƙannensa tara mata wasu an musu Aure wasu ba suyi ba, amma yau ace shine yai zina da 'yar da da yayi Aure da wuri, da ya kusa haifarta. Wani irin dana sanin zuwa makarantar nan ya sake baibaye shi, tun yana jami'a mata suke bin sa, tun yana da ƙananan shekaru ma kan ya shiga jami'a, Amma babu wadda ta taɓa cin galaba a kansa se Wannan tatsitsiyar yarinyar ɗalibarsa. Sosai ya dinga kuka kamar ƙaramin yaro, damuwa da dana sani suka haɗu suka sake baibaye shi. Kewa ta fara damun Farhan, na rashin abun ƙaunarta a kusa da ita, shikenan yanzu idan aka fita break bata da gurin wanda za taje suyi hira, sedai kullum ta na aji, wataran sedai ta kwanta tayi kuka, dan ba ƙaramin kewar Sadik ɗin take ba, gashi yai mata alƙawarin ze dinga zuwa yana ganinta, amma yau sati guda da barinsa makarantar bata ƙara jin ɗuriyarsa ba. Har abunda ya faru ya faru, Lilly ta warware Mummynta ba ta dawo daga garinsu ba, ta koma Makaranta dan zaman Gidan damuwa yake ƙara mata. Sedai tun da ta koma kallo ɗaya za kai mata ka san ta canza sosai da sosai, dan duk ta wani koma so silent. Yasmin ce ta fara lura da hakan tace "wai Lilly meke damunki ne? Kince mana baki da lafiya, amma na ga duk kin koma wata iri, baki da kuzari, ko dai duk dan Nazir ba lafiya ne?" Lilly ta girgiza kai tace "A'a, ni ba abunda yake damuna" Haseena tace "kinga yadda ki ka rame Kuwa? Kin rame sosai gashi kin koma wata saliha, waima meya sameki ne?" Kallonsu tai suna daga cikin wanda suka dinga ingiza ta duk me afkuwa ta afku, gashi ta rasa mutuncinta amma su suna tare da nasu. Tace "Ciwona ne ya tashi kawai, ga Mummy ba ta nan, shiyasa duk abun yai min yawa haka" "Eyya sannu Allah ya baki lafiya" Ta amsa musu da 'Ameen" Class rep ne ya shigo yace "Lilly, yau kamar haɗin baki, mutumin naki ma se yau ya dawo aiki, yana kiran ki a Office ɗin sa" Gabanta ne ya faɗi, dan ko haɗa ido ba ta sake son yi da Nazir, Haseena tace "Yawwa muje ma, ni ina da Matsala a test ɗinsa yai min ƙwauron maki" Lilly ba ta son su fahimci wani abu, dan haka ta tashi jiki babu ƙwari suka fita ita da Haseena. Tun da suka shiga Office ɗin idonsa na kan Lilly, wadda kallo ɗaya za kai mata ka ga duk a hargitse take. "Sir ya jiki?" Haseena ta faɗa tana kallonsa. "Alhamdilillah" ya faɗa a taƙaice. Haseena ta fara masa magana akan test ɗin ta, amma ya kalleta yace "can You please excuse us?" Haseena ta kalli Lilly, ta kalli sir Nazir taga yadda fuskokin su ke ɗauke da damuwa. A hankali ta janye jikinta ta fita daga Office ɗin. Nazir ya kalli Lilly, cikin sanyin jiki yace "Fatima zauna muyi magana" Girgiza masa kai tayi alamar ba zata zauna ba. Miƙewa yai a hankali yaje ya kulle Office ɗin, ya dawo ya tsaya a gabanta, ya zubawa kyakyawar fuskarta ido, wadda take ta koma jawur saboda kuka. Cikin rauni da karaya yace "Am sorry please, ban San meyakamata in ce miki ba, but.. Kasa ƙarasa maganar yai, ganin yadda jikinta yake kyarma saboda kuka. Riƙo hannayenta yayi a cikin nasa "dan Allah Lilly ki yafemin, ki rufamin Asiri" "You ruin my Life, ka cuci Rayuwata" "Na sani, kuma ba kowa nai ba kaina nayi wa, amma ki bani damar wanke laifin da na aikata, ina da ƙanne Mata idan a kai musu nima ba zan ji daɗi ba, idan na nemi Aurenki a gidanku za'a bani?" Turus tai tana kallon Nazir, dan ta san abune me wuya, dan iyayenta basa ƙaunar talaka mussaman mamanta, amma ita harga Allah tana ƙaunar Nazie duk da wannan abun da ya gifta a tsakaninsu. "You mean zaka Aureni?" "I mean it Lilly, na ɗauki abunda ya faru tsakanin mu a ƙaddara, amma in zaki iya Auren talaka kamata, ina sonki a hakan tunda dama aini nayi kuskuren" "Na yadda, na amince in dai zaka Aure ni" "Shikenan, tunda mun tsaya akan wannan yarjejeniyar, mu zama masu riƙe sirrin junan mu, kuma muyi ƙoƙarin kaucewa faruwar hakan a gaba" Ta jinjina masa kai tace "insha Allah, ba zan gayawa kowa ba" "Yawwa my love" suka rungume juna, yana ɗan shashafa bayanta alamar rarrashi (🙄🙄 anyi ba ai ba kenan). Farhan kam shirun da taji babu ɗuriyar Sadik yasa ta fara karaya, da fari ji tai kamar taje ajinsu ta tambayesu shi, amma ta fasa, dan 'yan ajin nan nasu se a hankali, yanzu za su iya kawo mata maganar banza. Sadik ji yake kamar bashi da lafiya, zuciyarsa se azalzalarsa kawai take akan son ganin Abincin ruhinsa wato Farhan, amma yana son tabattar da gaskiyar batun da ake masa akan Farhan ɗin. Farhan kam ta fara sarewa, dan in dai ta tuna da shi se tayi kuka, tana Addu'a Allah yasa yazo ta ganshi. Tana cikin tunanin sa Umma ta ɗaga labulen ɗakinta tace "kije kinyi baƙo" Farhan tace "to" Umma na juyawa Farhan ta ɓata fuska, dan ta san ba ze wuce wannan mannannen bawan ba, wato Sunusi duk abunda take masa na ƙin yi masa Magana idan ya zo, be sa ya fahimci in da ta dosa ba. Ta saka hijjabinta ta fito, aikuwa shiɗin ne ba wani ba, tana ganinsa taji kamar ta koma gida da gudu, dan ko ƙaunar ganinsa ba tayi. "Barkanki da wannan lokaci ya furen zuciyata" Idan akwai abunda Farhan ta tsana be wuce wannan banzayen kalaman ba da yake faɗa, dan sam basa burgta sema ƙara ɓata mata rai da suke. Ya sake cewa "ina fatan kin wuni lafiya cikin aminci kamar ni" Farhan a ranta taji kamar tace "A'a cikin tashin hankali na wuni" amma ta dake, da yake wulaƙanci ba ya cikin ɗabi'arta. Tace "dan Allah ko zamuyi sallama, zan tafi makarantar dare kar in makara" Sunusi ya gyara tsaiwa yace "Amma ai kya bari mu gaisa ko?" "Ai naga mun gaisa, idan na makara za'a iya dukana a makaranta" "Eh to kuma hakane, amma ba kya iya jure bulalar malam saboda ni ba?" Ba ta san lokacin da tsaki ya kufce mata ba, dan ji take kamar ta zabga masa mari. Tace "kaga se an jima, Makaranta zan zo in tafi" Ta juya ta koma cikin gida zuciyarta na mata wani irin tafasa. Tana shig gida Umma tace "harya tafi ne?" "Eh ya tafi, lokacin tafiya makaran yayi" Umma tace "naga se takwas kuke shiga, yanzu kuma bakwai da kwata" Farhan tace "eh dama zuwa yai kawai mu gaisa, kuma yai min Sallama ya tafi" Umma tace "shieknan, Allah dai ya tabattar da al'amrin nan, ayi ai Auren nan kowa ya huta, dan da babanki ze Amince tun yanzu a karɓi kuɗin asan da ƙwaƙwƙwarar magana" Farhan ɗakinta ta shiga tana ba Ameen ba a ranta. "Ya Allah karka tabattar da wannan lamarin, Addu'a iyaye ga 'ya'ya ba ta da hijabi a gurinka, Allah ka tabattar min da Alkhairi, Amma Allah ka rabani da wannan sunusin bana son sa, Allah kai ka ɗai zan iya gayawa, kai kayi unarni da bin Iyaye, ina musu biyayya daidai gwargwado, ya Allah ka rabani da wannan bawan" Haka taita Addu'a, muryarta ƙasa ƙasa tana goge hawaye. Takwas saura mintuna, ta saka hijjabinta na makarantar dare, ta shafa turaren humra me sanyin ƙamshi, ta shafa ta ɗau jakar Islamiyyar ta, daga  tsakar gida kawai ta iya cewa Umma na tafi, ta sa kai ta fita. Jefa ƙafarta kawai take, tana share hawaye lokaci lokaci, ba zato ba tsammani, kamar daga sama wai anwa wada ƙwace,se ji tai an janyo hijjabin ta ta baya da ƙarfi ta faɗa jikin mutum. Ware murya tai za ta ƙwala ihu, kasancewar ba kowa a lungun, ammma yadda ya toshe mata baki ya hanata yin hakan. (Mubarak Babba 🥺)! Littafin nan ₦300 ne kacal. 0009450228 Aisha Adam Jaiz Bank KO kuje manhajar AREWA BOOKS ku siya.  Littafin nan ₦300 ne kacal. 0009450228 Aisha Adam Jaiz Bank KO kuje manhajar AREWA BOOKS ku siya. domin kuwa ya fi sauƙi ta can. Ƙamshin turaren sa ne ya fahimtar da ita waye. "Matsoraciya kawai, komai seki fara ihu" Ture hannunsa tai, ta ƙwace tana tura baki. Fitilar wayar sa ya ɗakko ya haska fuskarta yace "ya naga kamar ma kuka ki kai" Yana faɗan haka kamar ya tuna mata, se ga wani hawayen na zubowa. "Farhan lafiya kuwa?" Cikin shagwaɓa tace "ba kaine ba, kace zaka dimga zuwa ka ganni, amma tunda muka rabu ranar ba ka sake zuwa ba, se damuwa nake". Murmushi Sadik yai yace "nima ai a cikin damuwar nake, tunanin ki ya hana ni sukuni, nayi tunanin zaki kirani a waya ma, tunda kince in ba ke kika kirani ba kar in kira ki, na ɗanyi rashin lafiya ne. Kuma yau tunda na tashi na kasa nutsuwa, ganinki kawai nake son yi, na daɗe a gurin nan ina sa ran ganin wucewar ki, in samu in ganki" Ta sauke numfashi tace "to kaji sauƙi?" Yace "Alhamdilillah, na warware kina lafiya dai ko?" Ta ɗaga masa kai tace "lafiya ta ƙalau, kawai ganinka nake son yi" "To ba gani ba nazo, ko dai haryanzu fushin ne?" Ta girgiza masa kai sannan tace "Mu bar nan gurin kar wani ya ganmu a gayawa Abba. Yace "ok, mota na ta titin bayan layin nan, muje can ba Wanda ze ganmu" Tace "Makaranta fa zani" "Ba daɗewa za muyi ba, ganinki kawai zanyi seki tafi" Tace "to" Ta bi Sadik zuwa Mota, suka shiga gaban motar da yake motar me tint glass ce, ba me ganin su, ya kunna musu fitilar motar. Ya dubeta yace "ya makarantar?" "So boring duk ba daɗi" Yai murmushi yace "nima fa ji nake dama ban gama yanzu ba, wallahi ba ki ji yadda kewarki ta dameni ba, gashi ke ba waya ba balle mutum ya neme ki a waya" "To ya zanyi tunda ba'a bani ba?" Sadik yace "da yadda za'ai" yai maganar tare da sa hannu a aljihunsa, ya ɗakko sabuwar waya me madannai(keypad) ya miƙa mata. Ta sa hannu ta karɓa tana kallonsa. "Ki ɓoye wannan, akwai layi a ciki, duk lokacin da kika samu dama ki kirani, amma ba zan iya jure yin nesa da ke sosai, ba tare da ko jin muryarki ba" Farhan tace "Tsoro nake ji, kar a ganta a gida fa" "Ki ɓoyeta Farhan, in da ba wanda ze gani please, ina missing ɗinki Sosai" ya ƙarasa maganar yana marairaice murya. Tace "shikenan, zan ɓoye Allah yasa kar a ganta ɗin, idan aka ganta ban san ya zanyi ba* "Babu ma wanda ze gani insha Allah, ki kwantar da hankalinki kinji my wife" "To Allah yasa kar a gani ɗin" Yace "Ameen, ko tex ne se ki dinga yi min, my lovely" Farhan tai murmushi tana jujjuya wayar. "Kinga ba dan a ɓoye na baki wayar nan ba, ai da Babbar waya zan sai miki ta manyan yara" "Manyan yara, ai kune manyan yara nikam ba babbar Yarinya bace" Sadik yai dariya yace "Babbar yarina ce ke Farhan, you are very beautiful, and at the same time kina da innocent soul kina da hali me kyau shiyasa nake ta kula, bana son wani ya ƙwace min ke, dan Allah Farhan ki dinga mana Addu'a, Allah yasa kar a rabamu, Allah ya tabattar mana da Alkhairi a tsakanin mu" A zuciyarta tace "Ameen" Amma a fili tai shiru. "Farhan ba ki ce Ameen ba, ko ba kya sona ne?" Noƙe masa kafaɗa tayi. Yace "ok faɗi Ameen in ji" "Nifa na faɗa a raina" tai maganar a shagwaɓe. "Ni ban ji ba ki faɗa inji" yai maganar yana kwaikwayon muryarta. "Uhmm ka bari" "My Lovely baby, wannan shagwaɓar taki is killing me" Ya ɗakko wata leda, cike da kayan ciye ciye na chocolate yace "ungo ke na siyowa wannan" "Ta ya zan shiga da Wannan gida? Idan aka ce a ina na samo fa?" "Kice mijinki ne ya baki, ai ba a shiga tsakanin miji da mata" Zare ido tai ta kalleshi. Yaxe "eh mana, tunda ke dai baki da wayo, ga jakar Islamiyyar ki nan ga ƙaton hijjabi, kisa a ciki mana" Ba ta san yawan yi masa musu, dan haka ta karɓa tace ta gode. Islamiyyar da Farhan ba taje ba kenan, ta zauna suka cigaba da hirar su a mota. Seda lokacin tashin su daga Islamiyya yayi sannan yace bari ya rakata bakin layin su. Suka fito daga motar, ya rakata har bakin layin, sannan ya juya ya tafi. Zuwan Sadik duk ya mantar da ita wata damuwa da take ciki. Sedai ta na zuwa gida ta fara fargabar kar a gane ba taje makaranta ba. Da daddare ta tura ƙofar ɗakinta, ta ɗakko wayar nan, ta saita komai a silent. Tana cikin saitawa se ga message ɗin Sadik "Hi sweetheart, kinyi bacci ne?" "No banyi bacci ba, ya kaje gida?" "Lafiaya ƙalau Alhamdilillah, meya hanaki bacci har wannan lokacin?" "Thinking of someone very important to me" "Wow, who is that lucky?" "Youuuuuuuu" Abun mamaki, Farhan ta zage suka dinga hira kamar ba ita ba, da yake ba a gabansa bane, ta dinga tura masa saƙonnin soyayya. Har kusan ƙarfe ɗaya na dare, sannan su kai sallama, ta je ta ɓoye wayar. Sedai bayan sunyi sallamar Sadik ya shiga aikin nasa na tunani, kullum sake jin Farhan yake a cikin zuciyarsa, sedai ya kasa tuna menene mafita akan wannan lamarin, ya rasa ta ina ze fara samun mafita, ga tafiya zeyi Gashi yasan ko giyar wake ya sha, Babu yadda za'ai Farhan ta jira shi tsawon shekaru bakwai ba tai Aure ba, ga ƙudurin iyayenta na son Aurar da ita da zarar ta kammala Makaranta, gashi ya rasa goyon bayan iyayensa akan abinda ke damun sa. Lilly kam tai ta ɗar ɗar ko Mamanta za tai noticing wani canji a tare da ita, amma taga sam mamanta ba ta fuskanci komai ba dan haka Kamar wasa, Lilly da Nazir suka koma suka jone kamar yadda suke a baya. Sema sake samun kusanci da su kai da juna fiye da baya. Farhan ta cigaba da zuwa Makarantar ta, wasu lokutan da wayar take tafiya makarantar, idan an fita break ta ɗau wayarta ta samu wani gurin, suyi ta waya da Sadik. Yau kamar yadda ta saba tai wayar ta gama, zata koma aji taga Mubarak Babba ya zo makarantar, wanda hakan ba ƙaramin ɗaga mata hankali yayi ba, dan yace in dai yana raye seya rama marin nan da tai masa. Aka tashi daga Makaranta, ta kasa ko fitowa daga aji saboda tsoron ba ta san meze mata ba. Da ƙyar ta samu ta fito daga ajin, tana waige waige da niyyar ta samu dama ta gudu gida, yau take sake ganin Ranar Sadik a makarantar nan, duk abunda ze faru ba wanda yake raɓarta saboda a na tsoron sa. "Leƙe leƙen me kike? Gani nan a bayan ki, dama ai dan ke nazo" A razane ta waiwayo taga Mubarak Babba, a tsaye ya zura hannayensa a cikin aljihun wandon sa. Razana tayi taja ta tsaya tana kallonsa. "Ke da kin ɗauka da wasa nake da nace sena rama marin da ki kai min, ko a zatonki ƙarya nake da nace sena samu abunda nake so a tare da ke?" Yai Maganar yana takowa gabanta, ita kuma tana ja da baya, har ta kai bango. "Yanzu ai gaki, ba wannan shashashan da kike taƙama da shi ze tare miki, ba abunda zan miki a yanzu, saboda nan be dace da gurin ɗaukar fansa ba, amma ko a jima ko a daɗe zamu gauraya, ina nan akan bakana, sena ƙetara abunda Sadik a kasa ƙetarawa" Yai maganar yana dariya da ƙoƙarin kai hannunsa fuskarta. "Kai Mubarak meye haka?" Da sauri Mubarak ya waiwaya, yaga Amin. Amin yace "meye haka kake ƙoƙarin yi ne?" Babba yace "ina ruwanka da abun da nake ƙoƙarin yi? Ina taya kaya ne" Amin yace "kaga Mubarak dan Allah ka bar wannan maganar, duk matan da kake bi a ciki da wajen makarantar nan be isheka ba, wannan dai ita Sadik ya ƙallafa rai a kai, dan Allah ka bar masa kayarsa, ka bar ganin baya makarantar, kasan halinsa ze iya nemoka wallahi" Mubarak yace "wallahi tunda na ƙyasa sena ɗana, kaima kasan bana ɗora raina akan abu in janye, and I will show her" yai Maganar yana kallon Farhan da ke zazzare ido. Amin yace "wannan amanar Sadik ce, ka nemi wata dai banda wannan, in ba haka ba kaima akwai sister ɗinka a school ɗin nan semu far mata" "Kutmar, karka kusakura wallahi kar kayi wannan gangancin" yai maganar yana nuna Amin. Amin yace "Ashe ba daɗi kake lalube na wasu, ai iya wuya Sadik namu ne, idan muka bari a kai masa ɓarna bamu kyauta ba, Farhan wuce kiyi tafiyarki" Farhan har da haɗawa da gudu ta bar cikin makarantar, ƙirjinta na dukan uku uku. Da godewa Allah ta tsira daga sharrin Mubarak. Farhan duk lokacin da suka so haɗuwa da Sadik, se su haɗa meeting point lokacim tafiyarta Makarantar dare, su shiga mota su yi hira sannan ya tafi. Gefe guda kuma tana ta fama da Sunusi, kasancewar sa mutum me nacin tsiya, wanda ba ya zuciya, yayi burus yaƙi nunawa Farhan yana jin haushin rashin saurarsa da take. Wasa wasa kusan kullum se Mubarak ya zo Makarantar nan, duk da ba uwar da take kawo shi, sedai zuwa yiwa Farhan barazana, gashi ta kasa gayawa Sadik saboda buyagin sa. Yau fitsarar Babba tasa har ajinsu Farhan ya bita, tana zaune tana solving Maths, 'yan ajinsu ana can gurin raye raye da support, kasancewar juma'a ce, seji tai Mutum ya zauna a kusa da ita. A zabure ta miƙe tsaye, amma ya tare mata hanyar fita. "Dan Allah ka rabu dani" ta faɗa muryar ta na rawa. "Yarinya kenan, haryanzu baki yadda da abunda na faɗa ba kenan, idan so nake zan iya sawa a kamo min ke, inyi yadda na ga dama da ke, sedai sonake a karan kanki zaki amince dani* Yasa hannu ya matse mata kumatunta da ƙarfi. Taɓa ta yake da hannun sa, tana buge hannunsa tana kuka, tana neman hanyar fita, sukaji an daki ƙofar ajin da ƙarfi. He was very shocked da ya ga Sadik, dan tunda suka kammala jarrabawa, Sadik be sake shiga makaranta ba. Be tsaya ba ya janyo Mubarak ya ɗura masa wata irin Ashariya. Jijiyoyin Kan Sadik duk sun ɗaɗɗaga, idonsa yai ja ya kalli Mubarak yace "kai dan baka da mutunci ka rasa wadda zaka bi se abunda nace nawa ne? Tunda muka bar makarantar nan ka fara bibiyarta ake gayamin, dan na ƙyale banyi Magana ba shine kake son zarce gona da iri, an gayamaka a banza zan bar makarantar nan in ƙyaleta? I already put my CID on her, me tai maka kake bibiyar ta? Ko abunda ke tsakanin mu ne ya shafe ta?" Sadik yai maganar yana hankaɗa Babba. Mubarak yafi Sadik girma sedai Sadik ya fishi siffar ƙarfi. Ya kalli Farhan a fusace yace "dan me kika ɓoyemin yana bibiyar ki? Yanzu ba dan an sanarmin ba nazo da shieknan komai ze iya faruwa? Farhan why?" Kasa Magana tai se kuka da take. Sadik ya kuma kallon Mubarak yace "wannan shine magana ta da kai ta ƙarshe, kar ka kuskura abunda ke tsakanin mu ya shafi Farhan na gaya maka" Mubarak yace "Ai kowa yaci tuwo da ni miya ya sha, ka rubuta ka ajiye idan har ina raye, sena wulaƙanta yarinyar nan, tunda ita ce abunda ka ɗora ranka a kai" Sadik be kuma cewa komai ba, ya fizgo Farhan da jakarta, sukai waje yana huci. A mota suna tafe se kuka take, "malama ki rufen baki, yanzu ba dan an gayamin yana bibiyar ki ba da komai ze iya faruwa, kin san halin Yaron nan kuwa? Meya haɗaki da shi ma tukuna?" Cikin kuka Farhan ta gayawa Sadik Komai, haka ya dinga mata faɗa yace duk lokacin da aka tashi ze zo ya dimga ɗaukarta, kuma ya na da masu yi masa CID a kanta a cikin ajinsu ba a wani guri ba. Haka ya kaita gida, sannan ya tafi. Farhan ta tsorata da lamarin Babba, amma ta rasa meye a tsakanin Sadik da Babba, saboda wasu lokutan tana ganinsu tare, kuma shi Babba yana zuwa sha'anin Sadik sosai, amma meye a tsakanin su haka?. Abba yana zaune a falo, yana kallon labarai, Mother na masa hira. Faruk ya shigo falon da sauri. Abba yace "Jarumin maza, saurin me kake haka? Ya akayi?" Cikin damuwa Faruk yace "Abba, yanzun nan aka kirani a waya daga gidan Hakimi, wai ba shi da lafiya, an kira wayar ka ba ta shiga, kusan sati biyu kenan ba shi da lafiya" Da sauri Abba yace "subhanallah, ai idan ina can layina baya shiga, amma ya akai ba'a kira gidan nan an faɗa ba?" Faruk ya kalli Mother, ya ɗauke kai Yace "Abba, ance min an kira wayar Mother an gayamata, amma ba wanda yaje duba shi a gidan nan, ni da na sani zanje" Abba ya kalli Mother yace "Yanzu Hauwa har a kiraki mahaifina ba lafiya, ba kije kin duba shi ba, ba ki tura wani daga yaran nan ba, kuma in dawo ki kasa sanar min?" Wani Mugun kallo Mother taiwa Faruk sannaan yace "Wallahi ban zaci abun ya kai haka ba, da mu ka waya cemin sukai kawai zazzaɓi ne ke damunsa, aka kwan biyu na kuma kira aka cemin jikin da sauƙi, shiyasa ban gaya maka ba" A fusace Abba yace "ya isa haka, dattijo kamar wannan ba lafiya, ai yafi ƙarfin ace is not that serious, ko daya ke tunda ba mahaifinki bane ai dole kice haka nagode" ya tashi ya bar mata falon ransa a matuƙar ɓace. Mother ta dawo da idonta kan Faruk tace "Sannu mara mutunci, ka tunzura shi yamin masifa hankalinka ya kwanta kaji ko, saboda tsabar rashin mutunci maimakon ka bar maganar a iya an kiraka ance ba shi Da lafiya, shine har da gaya masa ai sun gayamin ban gaya masa ba" Faruk yace "Mother ba haka bane, yanzu shi Abba se suga lafinsa, da aka kira aka faɗa kinga da koni kin aika naje na duba shi ai kinga da abun baze zo a haka ba" "Dallacan rufemin baki, sakarai kawai shiyasa nafi son Auta ai, da Shine da babu yadda za'ai yaimin wannan shirmen da kai min" Faruk ya girgiza kai yace "ai ko baki faɗa ba dama nasan ni ba sona kike ba, kinfi son Sadik, amma yadda muke ƙaunar ku haka shima yake ƙaunar su, Mother ba zaki ji daɗi ba ace yai koke ko Abba wani ba lafiya, amma ba wanda ya zo kanku a cikin mu, hakan ai ba daɗi but am so sorry Insha Allah ba zan sake aikata hakan ba" Ya juya ya bar falon. Duk cikin su ukun nan babu me biyayyar Faruk, shi dr. Dama ba magana yake ba, ko laifi yai maka sedai baƙin ciki ya kashe ka, in zaka kwaɗa shi ka cinye da faɗa wai ya ɓata maka rai, baze ma nuna maka yasan da shi kake ba balle ya baka haƙuri. Sadik kuwa ƙeƙe da ƙeƙe me ba'a tursasa shi, idan yai laifi kai masa faɗa ma se yai zuciya, koma ya bar maka gurin gaba ɗaya, baya son tashin hankali sam, shi ko laifi yai yafi som ai masa nasiha akan ai masa faɗa. Faruk ne kawai ko yayi laifi ko beyi laifi ba, dan a zauna lafiya zece ayi haƙuri, sam baya son yaga ya ɓatawa wani rai ace yayi laifi, sedai idan aka fusata shi kamar wuta haka yake, baya sakkowa ta daɗin rai. Duk da son da akewa Sadik a gidan, amma Abba yana wa Faruk so na musamman, saboda sanyin halinsa da rashin son hayaniya. Yau kowa a ɓangaren sa ya kwana daga Abba har Mother, dan yayi fushi sosai ga fushinsa ba sauƙi sam, Mother ta rasa in da zata sa kanta. Faruk ya koma sashinsu, ransa a ɓace ya tarar da Sadik da wayarsa a hannu, yana cin bredi. Messages ɗin Farhan yake kallo tana ba shi haƙuri, amma yaƙi tankawa dan soyake ya nuna mata yaji haushin ɓoye masa abu da tayi. Messages ɗin ta na ban haƙuri kala kala, amma yaƙi reply. Faruk yace "Autan Mother, Hakimi ba lafiya fa, ashe tun kan Abba ya dawo Hakimi ba shi da lafiya" Sadik ya ɗago ya kalli Faruk yace "Allah ya jiƙansa" ya maida hankalinsa kan wayarsa. Faruk ya buɗe baki yace "dan ubanka ce maka nai ba shi da lafiya, amma kace Allah ya jiƙansa" "Ohh sorry, na zi cewa nai Allah ya sawwaƙe" Gaba ɗaya Faruk ya lura, hankalin Sadik na kan wayarsa, dan haka ya ƙyaleshi kawai. Farhan ganin Sadik yaƙi kulata duk tarin messages ɗin da tura masa yasa ta haƙura, ta tabattar yayi fushi ne sosai haka, abunda be taɓa yi mata, yai fushi da ita haka. Ƙarfe bakwai na safe Abba ya shirya tsaf, da nufin tafiya ƙauye gurin mahaifinsa, yana ƙoƙarin fitowa ne sega Mother ta shigo, ta kalleshi tace "Yallaɓai dan Allah ka tsaya ko breakfast kayi seka tafi" "Bana buƙata" Abba ya bata amsa a taƙaice. "Dan Allah kayi haƙuri, ka karya kan nan gama shiryawa semu tafi tare" Be bata amsa ba ya raɓata ya wuce, ta biyo shi tana masa Magana, Amma yaƙi saurarar ta. Bawan Allah, Yana fita harabar Ajiye motoci, yaga Faruk ya shirya harya fito da mota. Abba yace "Faruk ya dai?" Faruk yace "Abba ai nasan yau zakace zaka, shine kawai na shirya da wuri na fito da mota, yanzu dama nake sa ran shigowa cikin gidan, inji da Yaushe zaka tafi in bika" Abba yai murmushi yace "to shikenan, mu tafi kawai na shirya" Ya buɗewa Abba mota ya shiga, ya zaga ya buɗe motar shima ya shiga sannan yace "Mother semun dawo" Ya fara jan motar sannu a hankali suka bar gidan. Wani marurun takaici ya tokarewa Mother rai, saboda tsabar abu da rashin hankali irin na Faruk, wannan ƙungurmin ƙauyen yabi mahaifinsa, abun takaicin ma wai shi ze ja motar har can, ta ja ƙaramin tsaki ta juya ta koma. Sadik ƙarfe goma ya tashi kamar yadda ya saba tunda ya gama makaranta, wayarsa ya fara ɗakkowa ya duba messages ɗin Farhan, murmushi yai, tare da kissing ɗin message ɗin yace "ina sonki Babyna, amma dole ina nuna miki rashin jin daɗi na akan laifin da ki kai min" ya ajiye Wayar ya shiga yai wanka ya fito ya tafi sashen Mother. Yaje ya tarar da ita a zaune tayi shiru, an kawo mata breakfast amma ba ta ci ba. "What's up Mom, Good morning" Ajiyar zuciya tai tace "ka tashi kenan?" "Eh Mother, wai na ganki somehow worried, meke faruwa ne?" Nan ta gaya masa abunda ya faru, da yadda Abba da Faruk suka tafi ƙauye. Sadik yace "to Mother meye abun damuwa a nan? Zaki zauna ki ƙi cin Abinci?" "Bari Sadik, nasan da kaine ba zaka min wautar da Faruk yai min ba, saboda tsabar shirme ya san halin babanku da ɗaukar zafi amma yaimin wannan kwaɓar haka, yadda kasan in mangare shi wallahi, yaita abu kamar ƙaramin yaro, wai a nan ya kammala degree ze koma masters, amma yai ta abu kamar wani mara wayau" "Easy Mother, ni wallahi idan kina masa faɗa haushi nake ji, bana son inji kina masa faɗan nan wallahi" Mother tace "Au goyon bayansa kake?" "A'a ba goyon bayansa nake ba, kawai dai bana som in ga ana ɓata masa rai ne, duk da nima wasu lokutan yana ɓatamin rai, amma haƙurinsa ne yasa yake ban tausayi, dan nafi sonsa akan wannan dukun dunkun ɗin" "Waye dunkun dunkun ɗin?" Sadik yai murmushi yace "ba kowa, amma dai na ari bakins na bada haƙuri, dan Allah ayi haƙuri a dena mai faɗa, ji nake kamar ni akewa" Mother tace "to me ɗan uwa, nima ina son abina ai, dan duk ya fiku hankali" Sadik kawai ya girgiza kai yace "Mother kina da abun mamaki, bari in zo in karya" Ya fara haɗa kayan tea da suke gaban Mother ya fara karyawa, ya barta da tunani. Farhan Alla Alla take a tashi, Sadik ya zo ɗaukarta ta kuma bashi haƙuri, sedai direba ya turo ya ɗauke ta shi be zo ba, ji tai kamar tace ba zata bishi ba, amma gudun karta kuma wani Laifin yasa ta bishi ya kaita gida. Abba wajen ƙarfe goma na safe suka isa. Sedai jikin Hakimin da sauƙi, amma dai yayi rama sosai da alama ya sha jiki. Inna tace "Allah yayi ka zo kenan Hakima ta barka ka zo duba shi?" "Inna ba haka bane, bana gari ne, shiyasa kuma itama ba ta da lafiya wallahi ban sani ba" "Eh ai dama ba za saka sani ba, tunda da ka dawo baka damu da kazo in da muke ba, ni ban damu lallai seka zo ba ma, ai ko ta waya ka kira kaji yadda muke, Abdullahi ka kiyaye ni fa" Abba ya kwantar da kai ya dinga ba da haƙuri. Faruk yace "Inna na Nana ne?" Inna tace "ta tafi Makaranta, se anjima zata shigo" Inna tai ta yiwa Abba faɗa, Faruk ya koma kusa da Hakimi ya ɗauki man zafi ya dinga shashafa masa a bayansa zuwa hannayensa, yana mammatsa masa yatsunsa cike da kulawa da tausaya wa. Hakimi yace "Anya ba za'a bar min wannan mutumin a nan ba, ya iya jinya fa" yai maganar cike da zolaya. Abba yace "ko Asibitin cikin gari za'a tafi da shi a duba shi sosai?" Hakimi yace "A'a, ga ƙaton Asibiti nan da ka gina mana, akwai kayan aiki sun min duk abunda ya dace, dama hawan jini ne, kuma sunce ya sauka Yanzu Alhamdilillah" Faruk yace "Ai can akwai ƙwararru fiye da nan, ka bari mu tafi da kai kawai, kaga daga nan semu riƙe ka, ka barwa Hajiya Inna karagar" Sosai Hakimi yai dariya, har seda wushiryarsa ta fito yace "waini ina Ango ne, da kuma shi wancan ɗaya abokin nawa?" Abba yace "Usman baya gari, shi kuma Sadik basu daɗe da kammala jarrabawa ba, muna masa shirye shiryen tafiya karatu ne" Tunda Abba ya fara wannan bayanin Inna ta ƙura masa ido, ya kai aya sannan tace "Ina ze tafi karatun?" Abba yace "ƙasar waje ne, kamar yadda 'yan uwansa suma su kaje, Faruk ma ya kusa komawa Master's" "Shi Wannan fitsararraen yaron zaka kai ƙasar waje karatun?" Abba yace "Inna ai ba wata damuwa, karatu kawai zeje yayi" Inna tace "gaskiya ne" Faruk ya samu fura da kilishi ya dinga ci, Abba yace "kaga kaci a hankali, in ba haka ba ze ɓata maka ciki, kuma ba banɗaki a hanya sedai ka yanki jeki kaje kayi" Faruk yace "Abba ai a can ba Fura me daɗin wannan" hira suke sosai, yayin da Inna ke ta maimaita batun tafiyar Sadik cikin turawa yayi karatu. Suna nan zaune se ga Nana ta dawo daga Makaranta, kasancewar tsananin soyayya dake tsakanin Hakimi da Nana, tunda ya fara rashin lafiya, duk in da taje ta dawo gueinsa take fara zuwa ta ga jikinsa, ko cikin dare se ta ɗau fitila taje ta haska taga ko yana numfashi. Ranar da jikinsa ya hana shi cin Abinci kuwa, ita ma ba zata ci ba. Shiyasa tana shigowa ta nufi turakar sa, tana faɗin "Inna ya jikin Kakana?" Inna tana daga ɗakin tace "ban sani ba, tunda ba zaki iya ƙarasowa ki gani ba" "To ai Inna takalmi na nake cirewa, yau ba abunda na gane a makarantar nan, duk hankalina yana gida ji nake kamar in gudo gida in ganshi". Ta ƙarasa maganar tana shigowa ɗakin, sedai tai turus ganin su Abba da Faruk. Murmushi tai da ta ga Faruk, ya miƙa mata hannu da nufin su gaisa, wani irin kallo Inna tai mata, wanda ya sa Nana tsugunawa tana gaishe su. Abba yace "Hajiya ta, ya makarantar?" "Lafiya ƙalau, ya aiki?" Abba yace "Alhamdilillah, ya me jiki?" "Da sauƙi Alhamdilillah" ta miƙe ta nufi gurin Hakimi, ta ɗora hannunta a goshinsa tace "Sannu ya jikin naka?" Hakimi yace "naji sauƙi tunda naga ɗana" Nana tace "Inna kin bashi Abinci ne?" "A'a babata ke nake jira ki zo ki dafa ki bashi, ke da ba'a iya miki daga ke har kakan naki" Ba ƙaramin dariya Inna da Nana ke bashi ba. Lokacin sallar Azahar yayi, Sukai alwala suka tafi salla, har da Hakimi. Bayan sun idar Abba da Hakimi suka tsaya a ɗakinsa na waje, in da mutane ke cigaba da zuwa dubiya. Faruk ya shigo gidan, ya tarar Nana tana cin Abinci, ya tsaya yana kallonta, ya shafi sumar kansa tare da yi mata murmushi yace "Shine kina kallona kika ƙi kulani ko?" Murmushi tai tana ɓoye fuskarta a tsakanin cinyoyin ta. Ya zauna a gabanta yace "Abincin ma baki iya yiwa mutane bismillah ba, bani cokalin muci tare" Ɗagowa tai ta zaro ido, taci Abinci da namiji, taɓ ashe yau zata sha terere a gurin Inna, kan ta yunƙura ta tashi Inna ta fito daga banɗaki hannunta riƙe da buta. 07063065680 Littafin nan ₦300 ne kacal. 0009450228 Aisha Adam Jaiz Bank KO kuje manhajar AREWA BOOKS ku siya. Littafin nan ₦300 ne kacal. 0009450228 Aisha Adam Jaiz Bank KO kuje manhajar AREWA BOOKS ku siya. domin kuwa ya fi sauƙi ta can. Zazzare ido Nana tai, Inna ta zabga mata uwar harara, sannan tace "me nake gani haka?" Faruk ya kalli Inna sannan yace "taƙi kulani, ta gaida babana amma ni tai min banza, kamar ba ta Sanni ba shine na zauna inji ba'asi, inji dalilin hakan" Inna tace "eh Lallai kam, gara kaji ba'asi" tai maganar tare da ajiue butar hannunta ta shiga ɗaki. Inna na tafiya Nana ta miƙe tsaye, Faruk yace "ina zaki kuma?" "Wanka zanyi in tafi makarantar Islamiyya" Yace "To shikenan, ki ɗauke sauran Abincin kije ki rufe" Nana ta ɗauka ta tafi ta ajiye sauran Abincin. Faruk ya shiga ɗakin Inna da sallama, ta amsa masa ya samu guri ya zauna. Yace "Inna dan Allah ki bar mana Nana, mu tafi da ita a canza mata Makaranta" Inna tace "Tofa wani sabon fi'ili, Nan ɗin ce maka aka yi bata karatu?" "A'a ba haka nake nufi ba, gidanmu ba 'ya mace ƙarama haka kamar ita, nifa wallahi ina son 'yar uwa mace, inji tana Yaya, ince na'am Sisto what do you want" Inna ta bishi da kallo tace "kai kam akwai ka da iyayi na gaske, ba naga wannan Yarinyar a gidanku ba ai itama ƙanwarku ce" Faruk yace 'Khairat ai ba ta zama a gidan mu, sannan dai ni Nana nake son ki bamu, in ga ina koya mata Assignment, in dinga kaita outing, in sai mata abubuwan da take so, i want pampered her" "Kai ka san me kake faɗa ni ban san me kake cewa ba" Yace "haba Inna, Ki bar mana ita dan Allah" Inna tace "wai ni ko san Nanan nan kake ne a Aura maka mu huta? Wannan magiya haka" Zare ido yai yace "Aure kuma? yanzu se aiwa wannan yarinyar Aure? Ai this is child abuse, ni ba Aurenta nake son yi ba, kawai so nake in ganta a gidanmu, ace ƙanwarmu ce" "To bazan bayar ba" Inna tai maganar tana hararsa "Inna dan Allah ki bamu ita" "Kai nace Ba zan bayar ba, babanka ma yayi nacin ya gaji,  zan iya bada komai da na mallaka dan a barmin Nana, idan ina ganin ta Kamar mahaifinta nake gani, kuma idan na baku ita shikenan ba wanda zan kalla a gabana, ku ba zuwa in da muke kuke ba, wannan ɗin guda ɗaya ai kwa barmin" Inna tai Maganar ƙwalla na taruwa a idon ta. Faruk yace "eyya, am sorry i understand you, na gane Inna, bakomai kiyi haƙuri, Allah ya jiƙan 'ya'yanki da kika rasa, ita kuma Allah ya rayata da Imani, dan Allah kar ki kuka, sannan in dai mune insha Allah kan in koma Master's zan dinga zuwa inyi kwanaki tare da ku" yai maganar cike da damuwa. "Inna tace bakomai kar ka damu, mahaifiyarku ba zata bari ku zo ƙauye ba, amma duk da hakan da ka faɗa naji daɗi sosai, Allah yai maka Albarka" tai maganar tana jin ƙaunar Faruk, yaron ba dai jin ƙai ba da tausayi, baya son yaga wani a damuwa. Suka cigaba da hira shi da Inna, yana bata labarin yanayin rayuwar turai. Nana tai shirin tafiya Makaranta ta zo ɗakin Inna tace "Inna zan tafi makaranta" Inna tace "to a dawo lafiya, ban da biye biyen ƙawaye, banda tsayawa da namiji a waje, a tafi ana sa hannu a hijjabi, banda kalle kalle ko ciye ciye a hanya, kar wani yace miki je kij, banda bin lumguna abi hanya sosai. Nana se signa ta kewa Inna akan ta ɗan tsahirta da zubo wannan jawaban, saboda ga Faruk a gurin, amma ba abunda yai mata zafi se zuba take, tana sake jaddada mata. Shi Faruk ma abun dariya ya bashi, wai wannan 'yar Nanan akewa wanna jan kunnen, Yarinyar guda nawa take, ana ta wani ta sa hannu a hijjabi, ɗan abunda ke ƙirjin nata be taka kara karya ba, yanzu yake fitowa. Faruk ya miƙe yace "muje in rakaki Makarantar" Nana tace "A'a Inna ta hanani jerawa da maza" Faruk yace "Ikon Allah, Inna duk kin takura mana ƙanwa, ni gashi ban gama ganinta bama, ai shikenan sekin dawo Allah ya tsare ayi karatu da kyau, zan bawa Inna saƙo ta ajiye miki" Nana tace "to ku gaida gida" Yace "Ba zaki ce in gaida Sadik ba?" Yai Maganar cike da zolaya. Nana tace "wallahi bana gaida shi" tai maganar tana fita daga ɗakin. Taje waje taiwa Abba da Hakimi sallama ta tafi makaranta. Se bayan la'asar sannan sukai harmar tafiya, dan Alhamdilillah jin Hakimi da sauƙi. Inna tace "ya dai kamata kaiwa kanka faɗa Abdullahi, ka nunawa iyalinka mahimmancin iyayenka, kakansu ko a daji yake yakama yaci darajar ya haifeka suzo su duba shi, amma ba su da uzuri ace su kasa zuwa suga jikinsa, dama ziyara ma su zo in da muke wannan mun yafe, tunda ba sa son Zuwa, amma halin rashin lafiya ai abune da Yakamata ace sun san yakamata" Faruk yai saurin cewa "Ayi haƙuri Inna zamu dinga zuwa Insha Allah" "Da kai nake Magana?" Inna tai maganar tana kllonsa. Faruk yace "Allah ya bada haƙuri" yai gaba abunsa yana murmushi. Seda Inna ta gama mitar ta sannan Abba yace "dan Allah kiyi haƙuri, insha Allah za'a gyara, kuma duk zamu sake dawowa mu duba shi haba ɗaya". Inna tace "ya dai kamata kasan abunda ya dace" Yai ta bata haƙuri, daga nan suka kama hanyar komawa gida. ko da Nana ta dawo daga Islamiyya ta tarar sun tafi. Nana tace "Inna har sun tafi?" Inna tace "eh sun tafi, ga sababbun litattafai can, Yayanki ya bayar a ajiye miki, hadda jakar Makaranta sabuwa fil me kyau" Nana tai murmushi tace "aikuwa nagode sosai Allah ya saka da Alkhairi" Inna tace "Ai nan ya zauna ya na min magiya akan lallai se na bar musu ke sun tafi da ke, ni kuwa ba zan iya ba, dan ban yadda da tarbiyyar wannan gidan ba, gidan nan nasu se a hankali" Nana tace "taɓɗijan, ni ma ba zan zauna a wannan gidan ba, ba zan bisu gidan su ba, wannan masifaffayar babar ta su, me wa mutane kallon banza, ga wannan wawan masifaffafe wanda be san darajar mutane ba" Inna tace "ke dan ubanki ba ki san kara ba? Ko dan yadda ɗan ta ke nuna miki so ai kyayi kara, yanzu idan yaji kina cewa uwarsu me yiwa mutane kallon bamza zeji daɗi? kuma ban hanaki faɗar mummunar magana akan wanda yake gaba da ke ba?" Nana ta ɗan tura baki tace "yi haƙuri na dena, gaskiya dai Faruk ya na da kirki ba kamar wannan me hura hancin ba kamar wani kasa" Inna tace "i taku dai ke da shi ɗin" "Ai wallahi Faruk duk yafi kirki" Nama ta faɗa tana murmushi. Inna tace "wai ni meye tsakanin ki da Faruku ɗin nan? Ko dai son sa kike? Ayi 'yar gida mu huta?" Nana ta zaro ido tace "taɓ Wannan ne ze Aure ni, kina ganin sa ɗan birni me kyau, me ze da 'yar ƙauye, ƙauyen ma na ƙayau?" Inna tace "in dai kina son sa ai shikenan, ba wata damuwa" Nana tace "Inna ya ake jin son ne to?" Inna tai murmushi tace "a bar wannan maganar, tashi kije ki karɓo zumar ki a gidan kuka, Hakimi ya bayar da kuɗi a kawo miki" Cikin murna Nana ta tashi tana Allah ka yiwa Kakana Albarka". Inna ta bita da kallo tana murmushi. Se bayan magariba sannan su Abba suka koma gida, suka tsaya a masallaci su kai sallar isha'i, Abba yace suje restaurant su ci Abinci, se kusan ƙarfe goma na dare sannan suka dawo gida. Faruk ya wuce BQ, Abba kuma ya shiga cikin gidan, kai tsaye ya wuce part ɗin sa ya rufe ƙofarsa. Romeo Sadik kuwa baban Soyayya, yaƙi kula Farhan se wanata yake, har kiran wayarsa tai, amma ya ƙi ɗagawa, amma ya sa hotunan ta a gaba yana kallo, yana murmushi. Seda Safe sannan Sadik ya san su Faruk sun dawo da suka haɗu da Asuba, Sadik yace "Ai na zaci a can zaku kwana da naga dare yayi baku dawo ba" Faruk yace "A'a ba'a can muka kwana ba, jikin nasa ma da sauƙi sedai duk ya rame sosai" Sadik yace "Aka bibiya ma ba wata cutar kirki bace, ake ta wannan kwaroroton ba shi da lafiya" Faruk yace "Wai Sadik Yaushe za kai hankali ne? Nan Abba yai zazzaɓi da mura, har kuka kayi saboda damuwa, yadda fa kake son babanka shima haka yake son nasa, hawan jini ne fa yake damunsa" Sadik yace "haba dai hawan jini kuma? wallahi na zaci be fi zazzaɓi ba" "To hawan jini ne, duk ya rame ƙafafunsa sun kumbura" Sadik yace "Subhanallah, Allah ya bashi lafiya, dole hankalin Abba ya tashi, dan naga hawan jinin nan shike kwashe mana tsofaffin nan, Allah dai ya bashi lafiya, shima ya tsufa ya haƙura da wannan Sarautar amma kamar da sarautar aka haife shi yaƙi haƙura" "Idan ya sauka daga sarautar kai zaka je ka riƙe masa?" Sadik yace "Allah ya kiyaye inje in zauna a wannan garin da ko ruwan roba babu, ba wata tsayayyiar wutar lantarki, gari duk se uban shanu da gonaki, ga ƙudaje ha warin kashin shanu, wai ma sarautar dole ce haba, ba abunda ya nema ya rasa da Abba ba ya ba shi, amma yaita wahala da ɗawainiyar mutane, wannan yace kaza wancan ma yazo da tasa matsalar, banda 'yan jarida da ke zuwar masa ba yau ba gobe, faɗan filayen magada duk fa haka Abba yake bada labarin wahalar da yake sha akan sarautar, sekace Dole ya haƙura mana" Faruk yace "dan ubanka kai meya hana ka ajiye sarautar da akai maka ta yariman Hausawa, har wani taƙama kake wai kai Prince, daga zuwa rakiya ba'a bawa dr. Ba se kai a kaiwa Sarauta, banga uwar da kake tsinanawa a sarautar da a kai maka ba ɗin" Sadik ya wani gyaɗa kafaɗa yana murmushi yace "ya ranka, You are talking to Prince, kayi magana da girmamawa mana" Tsaki Faruk yai tsaki yace "dalla ware, ni zan kwanta saboda a gajiye nake in ka rigani tashi ka shiga cikin gidan, ka miƙamin gaisuwa gurin Mother kan in shiga" Sadik yace "ok" Faruk yace "Aff na manta ban gaya maka ba, Inna na gaishe ka, da kuma Nana" Tsaki Sadik yai yace "Nifa bana son Maganar da ba shikenan ba, wannan tsohuwar yadda ta tsaneni ne za ta ce a gaishe ni, ai ko zan mutu ba zata faɗa ba, wannan Yarinyar kuwa me ɗan kai kamar an roƙo mata ita ma ba zata faɗa ba, ni harka ban haushi da kai zacen Yarinyar nan, dan na manta da ita ma a duniya" Faruk yai dariya ya wuce ɗakinsa, dama dan ya tsokani Sadik ya faɗa. Sha ɗaya na Safe Sannan Abba ya buɗe part ɗin sa ya fito cikin shirin fita, Mother ta tareshi tace "Yallaɓi jiya da kuka dawo kan in fito na tarar ka rufe ƙofa, ya me jiki?" "Ke kina da damuwa da me jiki ne? Ai mara lafiya na ne, dan haka ni ya shafa ba ke ba" "Dan Allah Abba ka bar wannan maganar, kuskure ne na yadda nayi shi, amma dan Allah kayi haƙuri" "Wane haƙuri kuma ban da wanda nake yi Hauwa'u, ai ba tun yanzu kike nunamin wariya akan dangina ba, kallonki kawai nake, dan haka kowa ya riƙe nasa, rashin lafiyar mahaifina ni ta shafa bake ba, dan haka ki ƙyale ni" Cike da ƙwarewa da iya kissa ta fara kuka tana faɗin "haba Love, dan Allah kayi haƙuri Hakimi ai babana ne nima, bekamata ka dinga nuna ai basu shafeni ba, lokacin da mu kai waya ba su gayamin abunda ke damunsa ba, shiyasa ban zaci babban ciwone haka ba dan Allah kayi haƙuri" Abba zeyi Magana ya ɗaga kai su kai ido huɗu da Sadik, dan haka ya fasa ya janyo ta jikinsa, ya fara share mata hawaye yace "is ok ya wuce" Sadik da ke tsaye yai murmushi, kawai ya nufi Kitchen. Abba ya san illar dake tattare da bayyanar da saɓanin ma'aurata har 'ya'yan su su sani, saboda hakan na haifar da matsala da rarrabuwar kawunan Iyali. Ma'aurata na iya faɗa su dawo su sasanta kansu, amma muddin 'ya'ya ko iyaye suka sani, ba sa mantawa kuma hakan ya na iya kawowa wannan Iyali matsala. Dan haka Abba ya wayance, ya bar Komai ya ƙyale Mother Saboda Sadik da ya shigo, dan baze so ya ga mahaifiyarsa na kuka ba. Se da Sadik ya shige sannan yace "bana son dinga yi miki faɗa, ko makamancin haka a gaban 'ya'yan ki, saboda ba na son martabata ta zube a idanun su, ba na son farincikin da na kafa a gidana in sa ƙafa in rushe shi, shiyasa nake kawar miki da kai, amma naga kin ɗau abun wani fanni daban, Yakamata ko yaya nima ki dinga kamanta yi min kara akan ahalina, ko ba komai nima zan ji daɗi" Share hawayenta tai ta riƙe hannunsa tace "insha Allah hakan ba zata sake faruwa ba, kuma zanje in duba sji insha Allah, amma dan Allah ka dena fushin nan dani ba zan iya jurewa ba" Abba yai murmushi, ya ɗan ja hancinta yace "ya wuce" Tai murmushi tace "to muje part ɗina in rarrasheka" Abba yace "Ai yanzu ma na rarrasu" A ɗan shagwaɓe tace "ni ban yadda ba, dan Allah muje, kaci Abinci ka canza wannan wankan da kayi" "Ke dai ba zaki Girma ba ko? Gashi kin ajiye sirika, wadda a kowane lokaci za'a iya cewa ta haihu amma kin ƙi girma" "Yaushe zan bari in Girma ka hango min wata, ai gara in ƙi girman" Murmushi sukai tare, suka nufi part ɗin ta. Rashin zuwan Sadik ba ƙaramin damun Farhan yai ba, ya sata a matuƙar damuwa, kullum direbansa zeje ya maida ita gida, amma yaƙi zuwa, kuma yaƙi ɗaga wayarta ko responding ɗin messages ɗin ta. Shima a ɓangaren sa hakan da yai yana damunsa, amma a ganinsa hakan shine matakin da ya dace ya ɗauka, dan ya zama gargaɗi kar ta kuma aikata laifin da tai masa. Mother ta fara noticing kusan kullum direba dai dai lokacin tashin Sadik daga Makaranta seya fita, ita dai ta san ba aikensa take ba, kuma Sadik ya kammala Makaranta, amma ta rasa ina yake zuwa. Yanzu ma kusan awa guda tana jiransa ta aike shi, amma ba ya nan ta rasa in da ya tafi haka, dan haka tace idan ya dawo ace ta na son ganinsa. Haka kuwa akayi, bayan ya dawo daga cika umarnin megida Sadik, ya nufi amsa kiran da matar gidan ke masa. Ya ɗan jira a falo kafin ta fito, cikin takunta na isa ta ƙaraso falon ta zauna, ta kalle shi tace "Yawwa, dama na aika a kiramin kai ne dan inji in da kake tafiya, kusan kullum seka fita, ni ba aiken ka nake ba, kuma dai ga Sadik ya kammala Makaranta, ina kake zuwa haka? Yanzu tun ɗazu fa ina zaune ina zaman jiranka zan aike ka amma baka nan, ina kaje?" Ɗan Jimm Direban yayi, yana ɗan nazari yana jin kamar ya gayawa Hajiya Hauwa abunda ɗanta ke aikatawa, amma wata zuciyar tace masa 'kul ɗinka, wannan matar da bata son laifin 'ya'yanta kana gaya mata zata iya cewa ƙarya kake, za kaiwa ɗanta sharri, koma shi yaron ya ƙaryata ka, dama dai mahaifinsa ne' "Ina magana kai shiru ka ƙyaleni" muryar Hajiyan ta dawo da shi daga tunanin da yake. Yace "Amm Hajiya, dama Sadik ne yake aike na" "Yake aiken ka ina?" Tai maganar tana tsare shi da ido. "Yake aike na, wani guri" "Wani guri ina? Gurin ba shi da suna ne?" "A'a Hajiya, amma dai sa da ze fi kyau ki tambaye shi da kan ki" Ɗan shiru tai sannan tace "shikenan, in kayi sallar azahar kaje gidan Mummy, kace ta baka saƙon ka kawo min" Yace "to Hajiya, bari in sallar in je" Daga haka Ya miƙe ya fice daga Falon, yana godewa Allah da ba ta titsiye shi tace lallai se ya gaya mata ba. Mother na nan zaune a falo, Sega Sadik ya shigo yana 'yan waƙe waƙensa, be kalli in da Mother take ba, ya nufi Kitchen. "Sadik zo nan" Mother ta kira shi. Juyowa yai ya dawo in da Mother take, ya nemi guri ya zauna yace "gani" "Ina kake aiken Malam Ayuba direba, da kusan kullum se ya fita?" Sadik ya kalli Mother yace "wani abun yace miki ne?" "A'a be ce min komai ba, na tambaye shi yace in tambayeka, tun ɗazu nake jiransa zan aike shi baya nan" Sadik yace "eh yana ɗan min wani aiki ne" "Wane aikin kenan?" "Mother, wata yarinya ce nasa yake kaiwa gida" "Ita yarinyar gidansu babu motar da za'a ɗauketa, ko se ubanka ne me arzikin banza na baitil mali?" Sadik ya ɗan tsuke fuska yace "dan Allah Mother ki dena, da suna da motar ai na zan sa a dinga kaita gidan ba, kuma kamar taimako ne, mu baga motocin nan birjik a gidan nan ba, gamu da ma'aikata, ba fa abun damuwa bane". "Kaga Sadik ka kiyayeni akan batun matan nan, duk makarantar ku babu wanda zaka ce min gidansu babu motar da ba za'a iya zuwa a ɗauke shi ba, bana son aikin rashin gaskiya fa" Haushi ne ya kama Sadik, Mother ba dai faɗa ba akan abun da be taka kara ya karya ba, tai ta mita akan abunda ta riga tafi ƙarfinsa. Miƙewa Sadik yai ya bar mata falon yana kumbure kumburen baki. A harabar gidan Sadik ya samu Ayuba direba yace "ka gayawa Mother in da nake aiken ka ne?" "A'a ban gayamata ba, cewa nai kawai ta tambaye ka" Sadik yace "ok, shikenan" Ayuba yace "Yawwa, Yarinyar dama tace min wai kar in ƙara zuwa ɗaukan ta, zata dinga tafiya da kanta" Sadik yace "saboda me tace hakan?" "Wallahi nima ban sani ba" ya bawa Sadik amsa. Sadik yai shiru yace "shikenan, bakomai nagode Sosai" Ya juya ya nufi BQ. "Sadik ka dena sona ko? Ka dena zuwa in da nake, ka dena duba saƙona, na baka haƙuri kaƙi haƙura ko? shikenan Nagode sosai" Message ɗin Farhan kenan, da Sadik ya ci karo da shi a wayarsa. Take se yaji tausayinta, yaga be dace ya wanata haka ba. Kiran wayarta yai, baiwar Allah ba tai zuciya ba ta ɗaga wayar, kasancewar tana makarantar Islamiyya. Tana ɗagawa ta sa masa kuka. "Wayyo Allah, am sorry my dear, na san ban kyauta ba dan Allah ki min Afuwa, wallahi ni kaina kewar ki ta dameni sosai" Cikin kuka tace "ba wani nan, ka dena sona wallahi ko Abincin kirki ba na iya ci saboda damuwa, Why are you playing with my emotion?" "Yi haƙuri am really sorry, kina jina?" "Ni ba abunda zan ji, ka dena sona na gane" ta katse kiran. Ajiyar zuciya Sadik yai, dole yaje ya ga Farhan yau, dan yana missing ɗin ta sosai da sosai. A ƙoƙarin kaucewa fushin Abba, yasa da Mother taji Abba da Usman zasu koma ƙauye dubiya, tace zata bisu taje taga jikin Hakimi, ko ta huta da fushin Abba. Ko da sukaje garin ƙin sakin jikinta tai, dan a fili ta dinga nuna ƙyamar garin, duk da irin tarin tsafta ta Inna. Nana kuwa dama tunda suka gaisa, ta fita ta basu guri, dan jininsu baya haɗuwa da Mother kwata kwata, dan ba zata manta yadda Mother ta dinga mata ba a ɗan zaman da su kai a gidan su ba. Shi Usman kam dama kamar yadda yake ɗabi'arsa, tunda aka gaisa yaiwa Hakimi ya jiki, ya koma gefe ya tsuke bakinsa, se idan Wani ne yai masa Magana se ya amsa. Abba yace "Alhaji jikin nan naka kamar babu wani cigaba fa, ni dai dan Allah ka bari mu tafi da kai a duba ka yadda yakamata" Hakimi yace "A'a, Asibitin nan namu baka ga yadda suke ƙoƙarin su ba, sunce hadda shekaru ma da suka ja, ka kalla fa cikin ikon Allah da ƙudurar sa naga Auren jikana namiji, ai Alhamdilillah ko yau muka tafi Allah yai mana ni'ima se fatan dacewa, ina Faruku ne wannan karon ba ka zomin da shi ba" Abba yace "ai ka san yana ta fama da shirye shiryen tafiyar sa, yaje yin clearance ne, ina ga a satin nan, ze tafi ƙaro karatu Insha Allah" Hakimi yace "to su haka zasu ƙare a yawon neman boko, baze Aure ba tukuna" Mother da ba da ita suke hirar ba tai farat tace "Ranka ya daɗe, ai haryanzu yaro ne, kallon dai babba kuke masa amma yarone ƙarami, gara tunda ƙuriciyar su suyi karatun kan nauyi ya hau kansu" "Eh hakane kam, to shi ɗaya abokin nawa fa, da yace wata shekarar zan koma ɗaurin Aurensa, kun masa Auren ne?" Abba yai dariya yace "Allah ya temake ka, yayansa ma be yi ba se shi? Ai shirme ne kawai irin na Sadik, nan da 'yan watanni shima yana Turai ƙaro karatu" Hakimi yace "ku dai naga kun bawa Boko mahimmanci sosai, ko da yake ai Ilimi abune me mahimmanci, amma Yakamata a dinga sara ana duban bakin gatari, ni karatun ma da ze yuwu suyi shi a gabanku kuna sa ido yafi ka kai yaro turai, baka san me yake ba" Abba yace "eh hakane, amma jami'oin namu ne na nan, kullum cikin yajin aiki da sauran matsaloli, shiyasa gara a can ƙasashen ƙetaren, nan da nan su gama su huta" "Hakane, amma ina fatan ze zo ya ganni kan ya tafi turan, dan babu lallai harya dawo ina raye" Abba yace "insha Allah ze dawo kana raye, ka dena wannan maganar, Ranar Asabar insha Allah, zan zo maka da shi ya duba ka" Hakimi yai murmushi yace Allah ya kaimu" Mother kamar a kan ƙaya take, dan Alla Alla take suyi su tafi, aikuwa da yin Azahar suka juya zuwa gida. Sadik yayi zarya a layin su Farhan dan ya samu ya ganta amma baya ganin wucewar ta, ya je Makaranta amma ya tarar wai kwana biyu ba taje ba, nan da nan hankalinsa ya tashi, ya kira wayarta amma ba ta shiga, ya tura mata messages amma babu reply. Tun magariba, har kusan ƙarfe tara yana unguwar su Farhan, amma be samu ganinta ba, Jiki a sanyaye ya koma gida, ya tarar da Su Mother sun dawo daga ƙauye. Sadik yace "wai ina kuka tafi haka, na shigo ba kowa a gidan nan, na kira wayarki ba ta shiga" Mother tace "hmm ƙauye mukaje duba Kakanku" "Wai haryanzu be warke bane?". "To jikin nasa dai da sauƙi, but he is seriously sick, Abbanka yace jibi in Allah ya kaimu ze koma, kuma tare zaku tafi, kaje ka duba shi, dan wannan tsohuwar ta fara mita" Sadik yace "nifa bana san zuwa garin nan, wannan tsohuwar ta sa mutum a gaba da masifa, tun da na masa Addu'a ba shikenan ba?" Mother tace "Ni dai ba ruwana balle ace ni nake ziga ka" Suna cikin maganar Abba ya shigo, tare da Faruk, Sadik ya kallesu yace "Abba sannu da zuwa" "Yawwa sannu, wato kai muka shirya mukaje dubiya babu kai, wai ina ma ka shiga ne?" Sadik ya ɗan sosa kai yace "bacci nake, ban san ma zaku ba" "Jibi in Allah ya kaimu zan koma, in gani in ba dama zan taho da shi nan cikin gari a duba shi, in ta kama a fita da shi ne a duba yadda za'ai, tare da kai zamu tafi kaima ka duba shi, dan haka ka shirya" Abba na gama Maganar yai gaba, dan be jira me Sadik ɗin ze ce ba. Shi ba zuwa ƙauyen ne ma yafi damunsa ba, illa halin Inna na shegen sa ido da masifa. Yauma haka ya kwana cike da tunanin Farhan, lallai da alama ita ma fushin take da shi, dan duk ta tosje duk wata hanya da zasu haɗu. Farhan kam ta ajiye wayar da ya bata, ta kashe ta ta ɓoye, ta cewa direban Sadik ya dena zuwa ɗaukan ta, gashi tana tsoron Babba ya cigaba da bibiyar ta. Dama an kusa fara exams, ba wani lesson ake musu ba, dan haka ta dena zuwa makarantar Gaba ɗaya, tace se an fara exams ta koma. Ga damuwa ta sa ko Abinci ba ta iya sakin jiki taci, kullum ta na ɗaki, Umma kuma ba ta damu da taji meke damunta ba. Yau gaba ɗaya zaman Gidan ya isheta, dan haka ta yanke shawarar zuwa Makarantar dare yau, ko ta ɗan samu releif. Tana fitowa daga gida, ta kusa barin layinsu, sega Sunusi, duk da babu wuta amma yana ganinta ya ganeta. "Hajiya Farhanatu, ance min baki da lafiya ya jikin?" "Na ji sauƙi" ta bashi amsa tana ƙoƙarin raɓa shi ta wuce. Sake tare ta yayi yace "haba to ki ɗan tsaya mu gaisa mana, kwana biyu fa bamu haɗu ba, haba tauraruwar zuciyata" Cikin rawar murya kamar tai kuka tace "dan Allah ka ƙyaleni Makaranta fa zan tafi" Ze kuma yi mata magana, ta raɓa shi tai tafiyarta. A duk lokacin da ta ga Sunusi ji take ta ƙara shiga matsananciyar damuwa, saboda shike barazanar rabata da farincikinta. Jefa ƙafarta kawai take yi, taji tai karo da mutum a gabanta, ta ɗago ido ta kalleshi, duk da lungun ba wuta amma hakan be hanata gane shi ba. Kewaye shi tai zata wuce ya kuma shan gaban ta. "Ni zakiwa wulaƙanci, kina ganina zaki tafi, waye wancan ya tsaida ke yana miki Magana?" Yai maganar a matuƙar kausashe. Haushi ne Yakamata, duk da a ƙasan zuciyarta taji daɗin ganinsa, cikin ƙwarin gwiwa da tsiwa tace "ban sani ba" "Ni kike cewa baki sani ba?" Shiru tai masa zata raɓa shi ta wuce, amma ya riƙeta gam yace "muje mota" "Ba zani ba, ka cika ni" "Ai ba abune ne wahala ba in ɗagaki in kai ki motar ba, sedai kome za'ace a ce ba ruwana" Ta san halin Sadik sarai, ze aikata abunda ya faɗa, dan haka ta haƙura ta bishi tana kuka, zuwa in da ya saba parking. Sun kwashi mintuna a motar, kuka kawai take kamar ranta ze fita, a hankali yace "kukan ya isa haka, ke kullum cikin kuka ko gajiya ba kya yi?" Shiru tai masa, tai me isarta sannan tai shiru. "Yanzu gayamin, ma tukuna kukan me kike?" Ko kallonsa ba tai ba, ta ɗauke kanta. Sadik yace "Hmm, dole inyi fushi a duk lokacin da naci karo da abunda yake barazana ga soyayya ta, banji daɗin ɓoyemin batun Babba na bibiyar ki da ki kai ba, baki san hatsarin yaron nan ba" "To shine zaka dena ɗaga wayata, ka dena kulani, shikenan tunda ka dena sona" Sadik yai murmushi yace "Taɓ, bana tunanin akwai wannan ranar, da zan dena sonki Farhan, yanzun dai ga Abinci na taho miki da shi naji kince ko Abinci ba kya iya ci" "Ni ba zanci ba" tai maganar tare da murguɗa baki. Yai murmushi yace "lallai nayi sake wannan bafullatanar ta raina ni, har nake Magana kina mayarmin, shikenan let me feed you" Ya takura mata harta haƙura ya dinga bata Abincin a baki da kansa. Aikuwa ta sake taci sosai, suka fara hira, yake gayamata washegari zeje ƙauye duba kakansa. "Amma ba zaka daɗe ba ko?" "Taɓ, ya za'ai naje wannan ƙauyen na zauna, a goben insha Allah zan dawo" "To shikenan, Allah ya bashi lafiya, amma dan Allah meya haɗaka da wannan Mubarak ɗin da yake nema ya shafe ni?" Sadik ya ɗanyi Jimm sannan yace "abun babba ne, amma karki damu idan na dawo zan baki labari" Tace "shikenan" ta kashingiɗa a jikin seat ɗin motar kamar yadda yayi. Ta ƙura masa ido, tana jin wata irin soyayyarsa na ratsa jikinta, ba ta san wani hali za ta shiga ba idan ta Auri wani ba Sadik ba. A hankali ya juyo da fuskar sa ya kalleta yace "Ya dai?" "Gabana ne yake faɗuwa ban san dalili ba" tai maganar wasu hawayen na bin fuskarta. "Please calm down, muna tare Princess, mucigaba da Addu'a duk yadda za'ai, idan naje ƙauye ina ga zan gayawa Kakana buƙatata ina ga su su fahimce ni" A hankali ta furta "Allah yasa" Fuskar sa ya matso daidai ta ta yace "wane irin so kike min Farhan?" "I don't know" ta faɗa tana lumshe ido, lokacin da taji bakinsa a nata. They really enjoys the moment, jinsu a wata duniyar ta daban, me cike da rikitattun al'amura. (Yau Sadik watsewa yake ji🙄, ga bani da lafiya, dan haka zan fice in bar ɗakko rahoton ban son harkar watsewa 😂😂) Sosai Sadik ɗin yake ƙoƙarin zarce tunani, duk da yadda jikinsa ke rawa idanunsa suka rufe. Rirriƙe hannunsa Farhan tai tana kuka, tare da girgiza masa kai. A hankali ya bar abunda yake, ya cikata ya jingina yana sauke numfashi. Yau har ƙofar gida ya rakata, ya kalleta yace "sena dawo, kimin fatan nasara, Allah ya cika mana burinmu, sannan shi wannan me gangancin zuwa in da kike, ya kiyayi abunda yake nawa, in ba haka ba ze mamakin abunda zan masa, ko ya rabuda ke ta daɗin rai, ko kuma in masa amfani da yaren da ze fi ganewa" Farhan bata iya cewa komai ba, se bin Sadik da kallo. Ya juya ya fara tafiya dan barin layin. "I love You, Please don't stay long, without hearing from you" Ya waiwayo yai murmushi yace "I love You too" Sunusi kuwa yana bakin layi, yaga wucewar Sadik da Farhan. Ya jinjina kai yace "dama wani ne yake hure miki kunne yasa kike wulaƙanta ni? Zaku gane baku da wayo daga ke har shi, zan hau buzu akan ku, sena rufe zuciyarki ruf, shi kuma in kife tasa zuciyar, ze gane ba'a takara da ƙolo" Kai tsaye ya nufi in da Sadik ke tafiya a cikin duhu!. Sunusi yace "Aminu, jirani mana" Sadik ya waiwayo yace "ba Aminu bane" Sunusi yace "dan Allah Aminu meye haka? Daga ina kake haka?" Sadik yace 'ba Aminu bane, Sadik ne" Sunusi ya jinjina kai ya maimaita "Sadik" INA ME BAKU HAƘURI NA JINA SHIRU DA KUKAYI, NAYI RASHIN LAFIYA NE, NAGODE SOSAI DA ADDU'AR DA KUKAMIN, I MANAGE TO TYPE FOR TWO PAGES FOR YOU, BUT I STILL NEED YOUR PRAYERS PLEASE 🙏🙏🙏) Ayshercool 07063065680 Littafin nan ₦300 ne kacal. 0009450228 Aisha Adam Jaiz Bank KO kuje manhajar AREWA BOOKS ku siya. domin kuwa ya fi sauƙi ta can. Littafin nan ₦300 ne kacal. 0009450228 Aisha Adam Jaiz Bank KO kuje manhajar AREWA BOOKS ku siya. domin kuwa ya fi sauƙi ta can. Jin Sunusi ya maimaita sunan Sadik yasa Sadik ɗin binsa da kallo, duk da cikin duhu ne, Sadik be damu ba ya cigaba da tafiyar sa. Har ya ƙule da lungun Sunusi yana tsaye yana kallonsa, seda ya ga Sadik ya bar layin sannan yai ajiyar zuciya ya jinjina kai yace "daga yau idan aka kuma cewa ka kalli in da take ba zaka ƙara ba, dani kake zancen sena muku farraƙu" Sadik kam a matuƙar kasalance ya nufi in da motarsa take ya ɗauka ya tafi gida, da ƙyar ya kai kansa gida, saboda yadda yake jinsa a gajimare. Farhan kuwa tana shiga gida ta tarar da Ummanta a tsaye a tsakar gida, seda gabanta ya faɗi. "Daga ina kike?" Umma ta tambayeta tana kallonta. "Umma daga Makaranta nake" "Ƙarfe nawa yanzu? Ƙarfe goma da rabi fa, ku da ake tashi tun goma, duk ƙannen ki sun dawo amma banda ke, har Amir na kuma aikawa Makaranta ya dubamin amma yace ba kya nan" Gaba ɗaya Farhan ta rikice, dan harga Allah bata san lokaci ya ƙure haka ba, uwa uba ma ko makarantar ba taje ba. "Ina tambayarki amma kin min shiru" Umma tai maganar a kausashe. "Umma nifa ba in da naje, mun biya duba babar su Naja ne, an mata aiki yaron ba rai, amma ba in da na tsaya. Umma tabi Farhan ba dan ta yadda da abunda ta faɗa ba, sema mamakin yadda yanayin maganar Farhan ɗin ke nuna ƙarya kawai take zabgawa. Umma ba ta kuma ce mata komai ba, ta wuce ɗaki ta barta. Farhan ta nufi ɗakinta jikinta na rawa. Sadik kam da ya koma gida se da yai wanka, sannan yai shirin kwanciya, sedai abunda ya gudana tsakanin sa da Farhan ya sa shi a wani mawuyacin hali, me wuyar fassara. Tashi yai daga kwanciyar da yai, ya fara zagaya ɗakinsa yana tunanin nemawa kansa mafita, tabbas yana ƙaunar Farhan, kuma a yadda yake jin kansa baze iya zama tsawon shekaru bakwai yana wata boko ba tare da yayi Aure ba. Wata irin iska ya dinga fesarwa daga bakinsa, ya shiga safa da marwa a bedroom ɗin sa. Ya nemi guri ya kwanta, ya janyo filo ya ƙanƙame ya runtse idanunsa, sedai surar Farhan ce ke dawo masa, yana kuma jin sa a wani yanayi. Wasa wasa bacci ya gagari Sadik kamar yadda dariya ta gagari kare, ba abunda yake se yarfe gumi. Wani tunani yai, a irin hirarrakin da suke da su Nas, yadda suke shawo kan irin wannan matsalar in sun tsinci kansu a ciki, sedai galibi duk ruɓaɓɓen tunani da su, dan duk ta hanyar saɓon Allah suke samun mafita. Tsaki yai ya miƙe ya nufi cikin gida, duk kowa ya kwanta bacci, ya lallaɓa ya shiga Kitchen, tea flask ya duba ya samu tea, ya zuba cofee sosai a ciki, ya zauna a Kitchen ɗin yana sha kaɗan kaɗan. A hankali ya kammala sha, ya koma ɗakinsa sedai babu wani canji sosai. Ɓangaren Farhan ma seda ta tsarkake kanta, dan yau sun zarce ƙa'ida, duk da fargabar tuhumar da ta fuskanta yau, be hanata jin ta aikata ba daidai ba na biyewa Sadik da tayi yau. Abunda ba ta taɓa zaton zata aikata ba, se gashi cikin lokaci ƙanƙani Sadik yasa duk wannan kunyar ta ta ta ajiyeta a gefe. A hankali ta furta "Yasalam, Astagfirullah, ya Ubangiji Allah kar kasa in rasa mutuncina saboda Soyayya, Allah ka yafe mana, Allah ka tabattar min da Alkhairi tsakani na da Sadik, Allah ka tsaremu aikata Zina ka nunamin Ranar da za muyi Aure" haka ta cigaba da Addu'a ƙasa ƙasa. Umma kam kasa zaune tai ta kasa tsaye, seda Abba ya dawo gida, ta bashi Abinci yaci ya nutsu sannan ta kalleshi tace "magana nake so muyi" Yace "ina jinki" "Game da wannan yarinyar ne" Abba yace "me kuma tayi?" "Nifa na kasa gane kan wasu abubuwa da ke aikatawa kwanan nan, kusan kullum seta gota lokacin dawowa daga Makarantar dare, yau se goma da rabi ta dawo, na tambayeta tace wai sunje dubiya, gaba ɗaya alamu sun nuna ƙarya take, nifa gaskiya tsoro nake ji" Abban Farhan ya numfasa yace "to yanzu meye abunyi? Ke ba wani matsarta kike ba balle ki tabattar da abunda kike zargi, amma meye abunyi a naki ganin?" "Abunyi ɗaya a haƙura da wannan bokon, wannan Yaron ya turo ayi Auren nan, yanzu har an fara yarmin da magana a dangi, na bar Yarinya a gida muna haɗa kafaɗa, dan Allah kayi wani abu a kai" "Banƙi ta taki ba akan Yarinyar nan, amma ni a jikina na yadda da ita, duk da ba'a shedar ɗan yau, tana da burin yin karatu a Rayuwar ta, dan haka bana fatan tauye ta, shiyasa nake son in bata dama, amma zan ga abunyi, idan Auren ne masalaha se ace ya fito ayi, amma nima kin jefa tsoro a raina, amma zanga abunyi insha Allah" Umman Farhan tace "Aikam dai ya kamata a gaggauta sanin abunyi, tun kan ta jawo mana magana, kwanan nan duk ta canza gaba ɗaya" ***** Se gefin Asuba sannan Sadik ya samu bacci ya kwashe shi, da ƙyar ya tashi sallar Asuba, itama a ɗakinsa yai sallarsa, ko azkar be ba ya haye gado ya cigaba da baccinsa. Ƙarfe takwas da rabi, Abba ya kintsa ya kalli Mother yace "Ina Auta ne?" Mother tace "ina ga be tashi ba" "Wane irin be tashi ba, ba shekaranjiya na gaya masa tare da shi zamu duba Hakimi ba? Faruk je ka taso min shi dan ƙaniyarsa" Cikin bacci yake jin maganar Faruk a kamsa "kai Sadik ka tashi fa, Abba yana jiranmu wai ka manta yau da kai zamu tafi ƙauye?" Wani uban tsaki Sadik ya ja, ya sake juyi ya cigaba da baccinsa. "Wai ba zaka tashi ba, Abba fa ya shirya kai kawai ake jira" Ai Sadik ko gezau beba, ya cigaba da baccinsa hankali kwance. Faruk ya ƙyale shi, ya koma falo in da ya bar su Abba. "Ina Sadik ɗin?" "Wallahi nayi nayi yaƙi tashi" Abba yace "yaƙi tashi, bari inje da kaina ina taso shi, ko daga shi se gajeren wando ne haka zamu tafi" Da sauri Mother tace "No baza'ai haka ba, yi hakuri bari inje in taso shi, yi haƙuri" Mother ta fita ta nufi BQ, aikuwa tana zuwa ta tarar da Sadik a kwance abunsa yayi ɗai ɗai, yana kwasar bacci. Ɗan ƙura masa ido Mother tayi, ganinsa take kamar jaririn da ta haifa jiya, haryanzu kallon abunta take wani ɗan ƙaramin yaro, da be wuce idan yana kuka ta rungume abunta ta rarrashe shi ba. Ta ƙarasa gaban gadon nasa ta fara bubbuga filonsa. Tura baki yai ze sake juyi. Mother tace "dan ubanka ka tashi, in ba haka ba Abbanku yace ko daga kai se gajeren wando ne haka ze tafi da kai ƙauye" A hankali ya buɗe idanunsa akan Mother, ya tura baki yace "ni wallahi Mother bana son Zuwa garin nan" Mother ta sassauta murya tace "to ya zakayi, tashi za kai ka rufan Asiri kar Ya ce ni nake zigaka, tashi maza kaje kai wanka" Sadik na tura baki haka ya shiga wanka, kan ya fito tuni Mother ta haɗa masa breakfast. Da kanta ta zauna tana bawa Sadik ɗin Abinci a baki, yana ci yana zuba taɓararsa son ransa harya ƙoashi. Ya saka ƙanan kaya, ya shafe sumarsa da mai sannan ya fito shi da Mother. Abba na ganinsu ya ƙurawa Sadik ido daga bisani yace "Sannu ko" Sadik ya sunkuyar da kai. "Nace sannu, barka da warhaka ranka ya daɗe, ka shanyani ina jiranka ko? Harna aika amma kaƙi tasowa, da nazo kanka da zaneka zanyi" Sadik dai bece komai ba ya koma gefe yana sosa ƙeya. Wata jaka Mother ta samu, ta zubawa Sadik ruwan roba, da tarkacen cookies a ciki, wai ta san ba iya cin Abinci zeyi a can ba. Sukai sallama suka kama hanyar tafiya. Suna tafe a hanya suna hira da Farhan, yana tura mata messages. "Beb kika hanani bacci jiya" "Ta yaya na hanaka bacci kuma?" "Through out the night am dreaming of you, gaba ɗaya na kasa bacci, gashi da sassafiyar nan Abba ya sa an tasoni mu tafi ƙauye" "Eyya sorry, Allah ya kaiku Lafiya ya tsare ku, ka kulamin da kanka Please" Murmushi Sadik yai ya tura mata "An gama Amaryar Sadik, Allah ya mallaka min ke Farhan" "That's my prayer always" "Dagaske kina mana Addu'a?" "Hmmm, ni gani nake ma kamar nafi sonka" "Ke 'yar Fulani Yaushe mu kai haka dake, kufa rigima ce da ku ga rinto, banda rinto ta ya kika fi sona?" "Nice me rinto ko?" "Eh mana kece, Yarinya dan baki san halin da nake ciki akan ki bane, ina sonki da yawa fa" "Ya kai cikin kofi son da kake min?" Kawai Sadik ya fara dariya, Faruk ya kalleshi yace "kai lafiyar ka kuwa?" Sadik yace "Meka gani?" "Gani nai kana dariya kai ka ɗai" "No wata beb ce ke bani dariya" Faruk ya girgiza kai yace "Allah ya shirye ka Sadik" Sadik yace "meye kuma Allah ya shiryeni? Haram na aikata?" "A'a ba haram ka aikata ba, amma gaskiyar Inna da tace be dace a kaika ƙasar waje karatu ba, zuwa za kai kai ta abunda Allah ya nufeka dayi, baka da wani zance sena mata da kuma Aure" Sadik ya waiwaya baya, dan yaga Abba na jin hirar ta su, amma yaga Abba sam hankalinsa baya kansu, waya ma yake. Sadik ya dawo da kallonsa kan Faruk yace "eh ɗin anyi zancen Auren, lafiya ce ta kawo hakan" Faruk yai murmushi yace "Ruɗin ƙuruciya kenan" "Kaga ka kiyayeni da wannan zancen RUƊIN ƘURUCIYA" Faruk yace "Allah ya ƙara lafiya Yariman Hausawa" Sadik ya cigaba da hira da Farhan, ta hanyar musayar saƙonni, yana nishaɗi. Da wuri suka ƙarasa garin, rabon da Sadik yaje garin nan harya manta Tsawon lokacin, dan gaba ɗaya garin nan be masa ba. Ranar Asabar ne, ya kama ba Makaranta dan haka Nana tana gida ba in da taje. Ta dawo daga aike taga motar su Sadik, fara'arta ce ta faɗaɗa, da taga Faruk ya sakko daga Motar. Ya zaga ya buɗewa Abba shima ya sakko, har ƙasa Nana ta durƙusa ta gaida Abba, ya amsa mata cikin sakin fuska. Faruk ya kalleta yace "Ina wuni" Nana tace "A'a ai zan gaisheka, ina wuni" "Ba zan amsa ba, tunda ni na fara gaisheki" yai maganar yana murmushi. Abba yace "ƙyale wannan yayan naki, ya me jiki?" A ɗan Sanyaye tace "jikinsa da sauƙi Alhamdilillah" Abba yace "lafiya dai ko?" Nana tace "eh Lafiya ƙalau" Duk wannan maganar da suke, se yanzu Sadik ya buɗe motar ya fito. Sumar nan se sheƙi take kamar gashin mace, ya ƙara fresh da shi kamar baya shiga rana. Yana sanye cikin ƙanan kaya, wando jeans da baƙar T shirt, ya ƙara kyau sosai. Ya ɗaga kai yana ƙarewa harabar in da suken kallo, ya ɗan kalli inda Nana take ya ɗauke kai. Itama wata uwar harara ta wurga masa, irin ko da wacce ka zo daidai nake da kai ɗin nan. Suka ɗunguma suka shiga gidan, Kai tsaye turakar Hakimi suka tafi dake cikin gidan. Suka sameshi a kwance, hannunsa riƙe da carbi yayin da Inna ke sallar walha. Hakimi ya yunƙura ze tashi zaune, Faruk da Abba sukai hanzarin zuwa suka ɗago shi. Ya kalle su yace "Masha Allah, sannunku da zuwa kun sha hanya, Bawan Allah ka sai hanya kana ta zarya, Yakamata ka dinga hutawa" Abba yace "Alhaji taya zan huta, ai duk inda nake hankalina yana nan baze kwanta ba, ka ƙi bari in tafi da kai" "A'a bakomai barni a nan ɗin, ina samun kulawa sosai" Alhaji ya kalli in da Sadik ya ƙame a tsaye yana binsu da ido, yace "Yarima, yau an zo da kai kenan, manya gatan wasa" Sadik ya ɗanyi murmushin gefen baki yace "ina wuni, ya jiki" "Jiki Alhamdilillah, ana dai yi mana addu'a ko?" Sadik yace "eh ana yi" "To madalla" Inna ta idar da sallarta, ta shafa Addu'a tace "Sannun ku da hanya" Abba yace "yawwa, yame jikin kuma?" "Jiki Alhamdilillah da sauƙi" Inna ta ɗaga kai tana ƙarewa Sadik kallo, irin kallon da ya tsana dan a haka take gano abunda za tai ta masifa a kai. Ya ɗan risina yace "Ina wuni?" Inna taja wasu seconds tana kallonsa sannan tace "hala kashi ne a gurin da baza ka zauna ba, ka ƙame a tsaye?" Hakimi yace "kin san saraki, ƙil shimfiɗar gurin ce ba ta masa ba, a samo masa Matashi" Inna tace "Sarakin wa? Wannan sarautar ba dashi ta dace ba, aka bashi ita, ba wani matashi da za'a bashi, im baze zauna ba yaita tsaiwa, soja" Sadik dai bece komai ba ya nemi guri ya zauna akan tattausar daddumar da ke gurin. Nana ta fita tsakar gida, ta samu Jug ta zubo ruwan randa, ta haɗo da kofuna, bisa ga koyarwar Inna, ta kawo Musu. Ta shiga zuzzuba musu ruwan tana miƙa musu, sedai taƙi zubawa ta bawa Sadik. Hakimi yace "shi wannan laifin me yayi miki da baki zuba kin bashi ba?" Sadik yace "No, am not thirsty bana sha" Ɗan ƙaramin tsaki Nana tai, tana hararsa. A ransa yace 'wannan shegiyar yarinyar ta fara rainin hankalin nata, in mata wani abun wannan tsohuwar ta ji haushi ta fara min masifa" Inna Kuwa tana kallonsa, yadda yaƙi shan ruwan nan, da yadda yake ta ƙarewa ɗakin nan kallo, kamar ya ganshi a wata duniyar daban. A hankali Sadik ya silale ya fita, ya tafi mota ya ɗau ruwansa na roba ya zauna yana sha. Mother ta kirashi a waya, sedai duk yadda ya so ya ɗaga wayar nan abu ya gagara saboda rashin Network, yai yai ya ɗan zazzaga ko ze samu Network amma abu ya gagara. Ransa ya ɓaci be san lokacin da yace "wannan banzan ƙauyen, Network ma babu dan masifa" "Wallahi ƙauyen mu ba banza bane, sedai me maganar ne banza" Sadik ya waiwaya yaga Nana a tsaye hannunta riƙe da wani ƙaramin kwano, da alama aikenta a kai. "Ke kuma nasa dake ne? Zaki fara bibiyata kina min rashin kunya, bar ganin gidanku nazo, wallahi se in tattakaki" "Wallahi baka da wannan ƙafar, babu ƙafar da zata iya tattakani in gaya maka, kuma wallahi a garinmu kake gidanmu, zan iya sa dogarai su zane min kai, dan nan ba gidanku bane balle ka ɗagamin murya" "Ni zaki sa dogaran su zane?" Yai maganar yana nuna kansa. "Eh kai ɗin zan sa su zamemin kai, gara ka shiga hankalinka" ta ƙarasa maganar tana hararsa tai waje. Binta yai da kallo, wata ƙwaila da ita se rashin mutunci fal cikinta. Gajiya yai da neman Network, ya koma cikin gidan yana tsaki da ƙanan surutai, shi ya gaji ma so yake su tashi su tafi, amma yaga basu da wannan niyyar. Lilly ce kwance akan makeken gadonta, se juyi take daga ita se underwear, ta rasa meke mata daɗi gaba ɗaya, wata irin kasala ke damunta, gashi wata irin wuta take ji a jikinta, babban burinta be wuce sake kasancewa da malamin ta b wato Nazir, ta rasa in da zata saka kanta, gashi sunyi nadamar abunda suka aikata, har yana iƙrarin ze Aureta, amma ita kaɗai ta san me take ji. Wayarta ce ta fara ringing, banza tai da wayar ta cigaba da juyi, daga wannan angle ta koma wancan, ta nayi tana ɗan jan tsaki lokaci lokaci. Wayarta ce ta sake ɗaukar ruri, a fusace ta kai hannu ta ɗakko wayar, ta duba se taga Nazir ne ke kiranta. Ɗagawa tai ta sa a kunnenta "hello my nazee" Ajiyar zuciya yai yace "Baby meyasa ba kya ɗaga wayata ne?" "Ba gashi na ɗaga ba" 'amma sau nawa na kira baki ɗaga ba?" "Nifa ban san kai bane shiyasa" "Shikenan, naji muryar ki wani iri, Lafiya dai ko?" "Lafiya ƙalau, Am just missing You Babyyyyy" Yace "Ummm, jiya fa muna tare, har kin fara missing ɗina?" "Yes, let's do a video call, I want see you" Yace "ok, as you wish my love" Ya katse kiran, ya kirata video Call. Sedai seda yai turus ganinta a screen ɗin wayarsa, cikin wannan shiga. Ko a jikinta ta fara yi masa magana "fita za kai hakane, naga kayi wannan kwalliyar haka?" Da ƙyar yace "wani ɗaurin Aure aka gayyace ni" "Ok, seka dawo, banda kallon mata Please, duk wadda ta ƙyasa kace mata kana da mata kaji Baby" "Wai ya naga kina wani ƙara fresh, kim ƙara ja kinga kumatunki kuwa?" "Haka kowa yake cewa nima kuma na gani" Nazir yace "kinga se an jima, karki hanani fita, gaba ɗaya kin sauyan yanayi bye bye" Murmushi tai ta kashe wayar, tace "ai gara yanayin naka ya canza, kaji abinda nake ji nima" Ajiyar zuciya Sir Nazir ya sauke, yana jin sa a wani yanayi na daban, na son sake kasancewa da ɗalibar tasa. A gidan Hakimi kuwa, Da Azahar aka yi funkaso da miyar taushe, ta sha naman kaji da man shanu, kallo ɗaya Sadik yaiwa Abincin ya ɗauke kai. Abba da Faruk suka zauna cin Abinci, amma banda Sadik da yake ta cin magani. Abba yace "Kai Sadik ka wanko hannu kazo kaci Abinci mana" Sadik ya girgiza kai. Abba yace "me kake nufi?" "Abba na ƙoshi" "Saboda me ka ƙoshi" Abba yai maganar yana kallonsa. "Abba ni ban zan iya ci ba, bana son wannan abun" "Aikuwa zaka zauna da yunwa, dan ban san me za'a nemo maka kaci ba" Inna tace "Yanzu meye aibun wannan funkason da ba zaka ci ba?" Sadik ya ɗan tura baki yace "ni ba naci" Inna tace "madalla, ka hutawa kanka, kuma babu me nemo wani abun ya baka, kar Allah yasa kaci ɗin" Tashi yai ya fita daga ɗakin, yana ƙunƙuni ya tafi mota ya ɗakko cake, ya dawo harabar babban soro, in da aka ɗure dawakai, ya shiga cin Abincinsa yana kallon dawakai. Harya gama cin abunda zeci, ya tsyaa yana jiran yaga fitowar su Abba dan su tafi, amma yaji shiru basu fito ba. Ya koma cikin gidan amma ya tarar da su a ɗakin Hakimin, ba su da niyyar tafiya ma, sedai ya tarar ana ta shashafawa Hakimin ruwa a jikinsa, alamar jikin ne ya ɗau zafi. Har la'asar ana fama saboda jikin Hakimi, Abba yace zasu tafi da shi yace be yadda ba, sedai a kira masa likitan da yake duba shi yazo har gida ya duba shi, amma su barshi a turakarsa, yafi son in mutuwa zeyi ya mutu cikin sutura a ɗakinsa ba tare da ya wahal da kowa ba. Inna dauriya kawai take, yayin da Nana ta dinga kuka kamar ance mata Hakimin ya rasu. Faruk ne ya biyo bayanta, yana rarrashin ta "haba Nana, ya zaki ɗaga mana hankali kema, ki dena kukan nan haka, insha Allah ze samu lafiya" Nana ta jinjina kai amma ta kasa dena kukan, yaita rarrashin ta. Shi kuwa goga Sadik ya koma mota yai zamansa, yana jiran a gama abunda za'ai azo a tafi gida. Likita yazo ya dudduba Hakimi, yai masa allurai ya bashi magunguna sannan ya ɗan samu sauƙi. Abba yace baze yuwu su tafi a ranar ba, saboda ko sun tafi hankalinsa ba ze kwanta ba, saboda ya tsorata da yanayin jikin mahaifinsa. Ai da Sadik yaji labarin a garin zasu kwana, ji yai kamar ance ya kwana a wuta, wani irin takaici ya turnuƙe Sadik, ji yake dama be biyo su ba. Cikin ikon Allah zuwa magariba Jikin Hakimi yai sauƙi, dan har yana iya miƙewa tsaye da kansa. Inna kuwa duk tana monitoring ɗin Sadik, yadda yake cika yana batsewa saboda zasu kwana a garin, gashi ya ƙi cin abinci, ruwa ma ya ƙi sha se wanda ya zo da shi na jarka ya Ke shan abunsa. Saboda rashin network, se message Abba yaiwa Mother, ya sanar mata a garin zasu kwana. Mother kanta taji haushin batun kwanan nan, dan ba abunda yafi damunta se Autan ta, ta san Sadik ba 'a masa gwaninta, kuma ba komai ne ke burgeshi ba, Abinci ma ba na ko ina yake ci ba. Da isha'i, Sadik yana alwala Nana ta fito daga banɗaki, ita ma tayo Alwala, tana fitowa ta fara yarfe hannu, aikuwa ruwan alwalar jikinta ya sauka a fuskar Sadik. "Ke wace irin Mahaukaciya ce ƙazama zaki watsamin ruwa a fuska?" Nana ta waigo ta kalleshi tace "kaine mahaukaci bani ba, kuma wallahi kar ka sake cemin ƙazama dan ban ma abun ƙazanta ba" "Wallahi idan baki kiyayeni ba sena tattakaki a gurin nan" "Kaga ka kiyayeni da batun zaka tattakani ɗin nan, sedai mu tattaka juna banza kawai" "Nine banzan?" Yai maganar yana nuna kansa da yatsa. "Eh kaine banzan, an faɗa banza" Aikuwa ya ɗaga butar da yake Alwala da ita, da ruwan da komai ya jefo mata. Aikuwa tai gefe tana kiran "wayyo Allah Inna" Ba shiri Inna ta sallame sallar da take, ta fito tsakar gida hakan yai daidai da shigowar su Faruk daga masallaci. Inna tace "lafiya meye haka?" Nana tace "dukana zeyi" Abba yace "Sadik wai kai meyasa baka girma ne?" "Abba rashin kunya fa take min, saboda tsabar wulaƙanci ta shiga banɗaki tai ƙazantar ta ta watsa min sauran ruwan kashi a fuskata" Nana tace "kut, wallahi ni ba kashi nayi ba, alwala nayi" Faruk ƙunshe dariya yai, yai waje dan abun nasu ƙuruciya ce da shirme kawai. Abba yace "kai yanzu ba ka ji kunya ba, idan ma hakane ba sekai haƙuri ba, kuyi ta abu kamar ƙananan yara,in dai zaku haɗu sedai kuyi faɗa" Inna saboda tsabar takaici, ta koma ta cigaba da sallarta, ba tare da tace uffan ba. Nana ma da sauri tabi bayan Inna, dan kar Sadik ya kuma yunƙurin dukanta. Da daddare Sadik yaita tsaki, gashi akan lintsumemiyar katifa, ɗaki irin na gidan sarauta, amma yaita mita da tsaki, wai ɗakin zafi ga ba wuta, ga missing Farhan da yake. Ƙarshe se message ya tura mata, ya sanar mata a garin ze kwana, yai trying lambarata amma inda yake ba network. Tun tara na dare ya tura mata message ɗin, amma se sha ɗayan dare ta ga saƙon, tana tsaka da tunaninsa. Zuwa gari ya waye, jikin Hakimi yai sauƙi sosai, ya samu ƙwarin jikinsa. Nana ta shiga ɗakin Hakimi ta gaishe shi, ta tarar yana bacci ba kowa a ɗakin se Sadik, yana zaune yana danna waya. Nana taje ta leƙa fuskar Hakimi ta tarar bacci yake, dan haka ta juya zata fita, ta kalli Sadik tai masa tsaki ba tare da yai mata komai ba. Kawai ya ɗau murfin kofin dake gefensa, ya jefeta da shi a ƙafarta. Ta waigo ta kalleshi tace "Allah ya isa na" Hakimi kam idonsa biyu, ya lumshe idonsa ne kawai yana jinsu, amma bece musu komai ba. Kunun tsamiya aka dama da wainar gero, Abba yana ta murna, dan yana missing ɗin Abincin gargajiya, yayin da Sadik ya sake cewa shi baze ci wannan abincin ba, shi kunun tsamiya gudawa yake sa shi, wannan baƙar abar kuwa baze iya ci ba. Tunda Sadik yake iya shegensa, Hakimi be tofa komai ba, se a wannan karon da ya bi Sadik ɗin da kallo shima. Nana ta fito tsakar gida, tana bawa magunan Inna Abinci, kasancewar Innan kamar kiwon su take. Sun kai su kusan bakwai magunan se tsalle tsalle sukeyi. Faruk ya zo ya sameta a gurin, yace "wannan magunan fa kyawawa Masha Allah?" Nana tace "Na Inna ne, nake basu Abinci, ni kaga nawa nan wannan farar da wannan ɗan beutyn" Faruk yace "Wow, gasky ne they are cute" Sadik na gefe, ya shirya Fitowar Abba kawai yake jira su tafi, yana zaune yana harar Nana da zarar sun haɗa ido. Nana tacewa Faruk "kaga wancan muzurun, me tsigaggen gashin nan, ya fiye fitinar tsiya, ga rawar kai gashi bashi da kunya, shiyasa gashi nan mummuna, ko fara'a ba ya yi, sunan sa Autan Mother" Faruk ya ɗaga kai ya kalli Sadik, wanda ya zubowa Nana ido, dan yasa wannan cin fuskar da shi take, wato muzuru ma ta sawa Autan Mother, hadda ce masa mummuna. Tunanin abunda zewa Nana yake dan ya huce, sega Abba ya fito a shirye, da alama tafiya za suyi, abun mamaki sega Hakimi ma da ƙafafunsa ze rakasu mota tare da Inna. Sadik yai saurin miƙewa, dan jinsa yake kamar akan ƙaya. Hakimi ya kalli Sadik sannan ya kalli Abba yace "Wannan abokin nawa a nan zaka barmin shi" Abba yai murmushi dan zatonsa Hakimi da wasa yake yi. Sadik kam ya fara zoma kai gaba, yana jiran su Abba su wuce ya biyo bayansu. Suna zuwa zaure na biyu, Hakimi ya kalli wani dogari yace "kar a bar wannan abokin nan nawa ya ɗaga ƙafarsa daga inda yake, a nan za'a barmin shi" yai maganar yana nuna Sadik. Abba ya kalli Hakimin yace "Alhaji kana nufin a nan ze zauna?" "Eh, ko ban isa bane?" Abba yace "wane ni ja da maganar ka" "A nan za'a barmin shi, kuma daga yau bana buƙatar ka sake zuwa, tunda naji sauƙi Alhamdilillah. Aikuwa Sadik ya gigice, ze taka yabi Abba, a kai sama da shi aka mayar da shi cikin gida, yana kurma ihu yana kiran Abba! Littafin nan ₦300 ne kacal. 0009450228 Aisha Adam Jaiz Bank Ko ku tuntuɓe ni ta wannan lambar Ayshercool 07063065680 KO kuje manhajar AREWA BOOKS ku siya. domin kuwa ya fi sauƙi ta can. Littafin nan ₦300 ne kacal. 0009450228 Aisha Adam Jaiz Bank KO kuje manhajar AREWA BOOKS ku siya. domin kuwa ya fi sauƙi ta can. Jiki a sanyaye Abba yai gaba, yana jiyo yadda Sadik ke ƙwala masa kira yana ihu. Duk da shi kansa Abba beji daɗin abubuwan da Sadik ɗin ya dinga yi ba a gidan, amma se yaji beji daɗi ba amma ba yadda ya iya. Shi kansa Faruk, se yaji tausayin Sadik ya kama shi, yasan yadda Sadik yake a sangar ce ba ƙaranar wahala ze sha zama a garin nan ba. Gashi Hakimi yace kar Abba ya sake zuwa garin. Se da wani ƙwaƙwalwa Dalili. Har mota suka raka Abba da Faruk, sukai musu Sallama. Nana kuwa da taga an saɓo Sadik a kafaɗa an dawo da shi, se abun ya bata mamaki. Inna na shigowa Nana tace "Inna wai ya naga an dawo da shi? Ba tafiya za suyi ba" "Kakansa yace a nan za'a barshi" Inna na faɗin haka ta shige ɗakinta. Sadik se kiran Abba yake kama wanibɗan yaye, ya kuma nufar ƙofar da gudu ze fita amma aka kuma hankaɗo shi aka hanashi fita. Hakimi ne ya shigo yana takunsa cikin nutsuwa, yaga yadda ake dambarwa da Sadik akan lallai seya fita. Ya kalli dogarin yace "ka ladabtar da shi idan ya kuma yunƙurin fita" Zare ido Nana tai jin abunda Hakimi ya faɗa, aikuwa aka ɗakko zumgureriyar bulalar dukan doki, Sadik na ganin wannan uwar bulalar ya shiga taitayinsa. Nana kuwa ta tuntsure da dariya tace "yau naga ƙarshen taurin kai da raina mutane" ta dinga dariya yayin da Sadik bata ta yake ba, yadda ze ya gudu kawai yake tunani. Daga Abba har Faruk su kai jugum jugum a mota, ba wanda yake magana, kowa da abunda yake saƙawa a ransa, can Abba yace "Faruk kaga abunda ƙaninka ya jawa kansa ko? Da ya daure beyi wannan ƙaƙale ƙaƙalen nasa ba, da babu lallai Hakimi yace a barshi amma kaga abunda ya jawa kansa" Faruk yace "wallahi kuwa Abba, Sadik yana da matsala halinsa se shi, ni kaina na nusar da shi amma yaƙi ganewa" "Ai shike nan, kaga gobe ba ya kuma ba, kuma idan yace ze rashin ji jikinsa ne ze gaya masa, ni rigimar mahaifiyarku nake tunani, yanzu idan muka koma babu shi haka za tai ta sababi" "Hakane kam, za tai mita sosai amma ai shine ya jawa kansa" Haka suka cigaba da tafiya suna maida zancen. Wasa wasa Sega Sadik yana hawaye, saboda shi ganinsa an zalunce shi idan aka ce ya cigaba da zama a nan, garin da babu wani abun more rayuwa a cikin sa. Ya nemi guri yai zaman direshen a tsakar gida, se lokacin salla, ze tashi yai alwalwa yai salla a nan tsakar gidan. Ba wanda ya kuma bi ta kansa, kowa sabgar gabansa kawai yake yi. Ganin ba kowa a tsakar gidan yasa ya miƙe cikin sanɗa ya nufi hanyar fita, amma yana zuwa ya tarar da dogarai a soro na biyu riƙe da manyan bulalai. Dawowa yayi kamar ya ɗora hannu a ka yai ihu, akai Abincin rana aka kawo masa, amma ya barshi a gurin be taɓa ba, har ƙarfe uku na rana yana tsakar gida a zaune kamar maye. Wajen la'asar sannan su Abba suka isa gida, Mother najin tsayuwar motarsu ta fito, cike da burin ganin yaranta da aka kwasa a ka kai mata ƙauye suka kwana, mussaman Annurin zuciyarta wato Sadik. Tana nan tsaye suka firfito daga mota, ta ƙarasa in da suke tana faɗin sannunku da zuwa, ina ɗan Autana?" Abba bece komai ba yai gaba abunsa, Faruk ma ƙoƙarin barin gurin yake, ta kalli motar ta tabattar ba kowa a cikin ta, ta kalli Faruk tace "ina Sadik ɗin?" Faruk yace "Ki tambayi Abba" 'ban gane in tambayu Abba ba, kai ka gayamin mana" "Mother am pressed, i want ease myself" yai maganar tare da nufar BQ. Mamakk ya kanainaye Mother tabi bayan Abba, tana zuwa yana shiga toilet ɗauro Alwala. Ta samu guri ta zauna tana jiransa, ko da ya fito kuma ya nuna mata salla zeyi ta ƙyale shi. Ba ta gaji ba ta nemi Guri ta zauna dan jiransa ya idar da sallar, taji ba'asin in da aka baro mata ɗa. Abba ji yai kamar kar ya idar da sallar nan, saboda be san ta yadda ze fara mata bayani ba, dan ya san ba ƙaramin haurawa za suyi ba. Aikuwa yana shafa addu'a tace "Abba nifa baku cemin komai ba, ina Sadik ne?" Abba ya kalleta yace "zan siyar da Sadik ɗin ne? Idan ma siyar da shi nai ai dai ɗana ne ko?" "Eh naji na kuma yadda ɗanka ne, amma Yakamata in san in da yake, kun tafi kun dawon ba shi dole in tambaya" Abba ya ɗan haɗe rai, cikin basarwa yace "mun baro shi a can" "Can ina?" Tai maganar tana zaro idanuwa. "Can ƙauye mahaifata, gidan Hakimi" "Amma meyasa zaka baromin yaro a can, kasan fa ba iya zama ze ba" "Saboda nima da na rayu a can ɗin kan ki haɗu dani a birni, ban mutu ba, dan haka shima baze mutu saboda zaman ƙauye ba se lokacinsa yayi" "Haba dan Allah, ai ba ka haɗa rayuwar da kai da wadda ze ba, haba Abba, Sadik be taɓa nisa dani na kwana biyu ba, duk in da yake muna tare, ni da Faruk ka bari ba zan damu ba, amma Sadik be saba ba baze iya zama ba, dan Allah in laifi yayi ka baro shi kayi haƙuri ka ɗakkon ɗana" Abba ya numfasa yace "bani yaiwa laifii ba, bana ce kai tsaye ga abunda yai ba, amma zan iya cewa koma mene shi ya jawowa kansa, tunda mukaje yake wasu irin abubuwa na nuna ƙyama ga garin, kuma bani na yanke wannan hukuncin ba, Hakimi ne yace a barshi a garin" "Amma maimakon ka basu haƙuri, ka san Sadik baze iya zama ba wallahi, ai seka basu haƙuri amm ba ka baro min shi a can ba" "Kinga Hauwa'u ki kiyayeni, ba zan bijirewa iyayena dan in faranta miki rai ba, yadda kike son ɗanki haka nima suke sona, kuma ba za suyi abunda zasu cutar da abunda na haifa ba" "Amma duk da haka se a duba yaron nan, tsakani da Allah baze samu yadda ya saba a nan a can garin ba" Ganin Mother na neman sake ɓata masa rai yasa ya miƙe, ya koma sashinsa ya rufe ɗaki. Wasu irin hawayen takaici ne suka taru a idon Mother, sam ba ai mata adalci ba, koma me Sadik zeyi ai bekamata ai masa wannan hukuncin ba, wannan uban ƙauye ina Sadik ze iya zama a cikin sa. Wayarta ta ɗakko ta kira Mummy, wato Maman Khairat, seda ta kusa katsewa sannan Mummy ta ɗaga Tare da faɗin "Afuwa Please, salla nake ne ya gida ya yaran?" "Gida lafiya ƙalau" Mummy tace "ya naji Muryar ki haka ne?" Cikin ƙufula Mother tace "kin san kuwa abunda Baban yaran nan yai min?" Mummy tace "to yau kuma ke da sweetheart ɗin ne? Meyafaru?" "Wai daga zuwa duba mahaifinsa a ƙauye, ya ɗaukar min Sadik ya tafi da shi, wai se dawomin yai daga shi se Faruk kawai, wai ya baro shi a can" "Kamar ya ya baro shi a can?" "Wai kakanninsa ne sukace a barshi a can, saboda yana nuna wa garin ƙyama, tsakani da Allah an min adalci kenan, inyi magana ace bani da haƙuri, ta yaya Sadik ze iya zama a garin nan fisabilillahi? Tsabar abu kuma ina masa magana ya tafi part ɗinsa ya rufe ɗakinsa" Mummy tace "Subhanallah, ai riƙon mahaukaci se sarki, waze iya riƙe wannan yaron naki ɗan hutu in ba ke ba, Sadii baya son wahala da takura, gaskiya ba'ai miki adalci ba, amma karki ce zaki matsa ki bi Komai a hankali, kiyi ta lallaɓa shi har ya ɗakko miki ɗanki, kar kice zaki fushi kin san zaki kuma janyowa kanki matsala ne, dan haka kiyi haƙuri na san ba'a kyauta miki ba" Mother tace "shikenan Yanzu a can ze kwana? Wannan wane irin abu ne, ni na san halin kayana wahala ze sha a garin nan wallahi be saba ba" "Na sani Hauwa'u, amma dai kiyi haƙuri dama kin san yadda Akuyarki tai kuka a dangin mijinki, dan haka karki ce zaki matsa ki ƙara baƙin jini" "Wallahi ji nake kamar in ɗau mota inje in ɗakko shi, sedai ai duk wadda za'ai" "Ke karki kuskura, garin son ɗa da neman gira ki rasa idanu, shi dai baban nasu zaki cigaba da lallaɓawa" "Shikenan Mummy, ki gaida su Khairat" "Bakomai za suji amma ki kwantar da hankalinki". "Shikenan se an jima" ta katse kiran. Mummy tace "Ikon Allah, wannan kakannin na su Faruk sun fiye Matsala wallahi" Khairat dake kusa da Mummy a kwance ta ɗaga kai ta kalleta tace "Wai Mummy Sadik aka kai ƙauye?" "Wallahi kuwa, baki ji muryar babarsa ba ina ga ma kuka take, kai Allah ya jarrabi Hauwa'u da son 'ya'ya mussaman Sadik" Khairat tace "gaskiya ba'a kyauta ba, wallahi ze sha wahala ne kawai amma kin san Sadik da son hutu" "Aikuwa yanzu se ta Allah, wannan ƙasurgumin ƙauye ina ze ga wani hutu". Wasawasa har la'asar Sadik yana zaune a tsakar gida, ya ƙi cin abinci kuma ya ƙi tashi ya shiga ɗaki, da fari Nana dariya ta dinga yi masa, amma daga bisani kuma se ya fara bata tausayi, ganin har taje ta dawo daga Islamiyya amma yana zaune a tsakar gida, haka kurum rana tsaka a bar mutum a in da be saba zuwa ba, alhalin da uwarsa da ubansa a raye, se taga ba'a kyauta masa ba. Idanunsa sunyi jawur, saboda tsabagen yunwa ga kuma baƙin taurin kai irin na Sadik. Aka yi sallar magariba, yai salla a in da yake ya nemi guri ya zauna, aikuwa sauro ya fara ɗawafi a kansa, saura ya fara zagaye baƙar sumarsa, ga yunwa dake sakatar cikin sa kamar ze ci babu. Nana ta fito daga ɗakin Inna, ta tarar da shi a zaune yana kore sauro da hannunsa, ga network ɗin wayarsa sam yaƙi harbawa. "Ka taso daga nan ka koma ɗakin da kuka kwana jiya, in ba haka ba sauro se ya kusa halaka ka a gurin nan" Banza yai mata kamar be ji me tace ba, daga ɗaki Inna tace "ke ina ruwanki da shi? Waye yace ki masa Magana se kunzo kuna faɗa ko?, Ki ƙyale shi yai ta zama a gurin, idan saurayen suka gama tsotse masa jini, ya tashi ya bar gurin, ai bari ba shegiya bace da ubanta. Sadik a ransa yace 'wannan tsohuwar yadda ta tsaneni ba ta ƙi in mutu a gurin nan ba' dan haka ya miƙe ya tafi in da suka kwana jiya ya kunna fitilar wayarsa yana sake haske ɗakin. Ɗakin ƙasa ne na gaske, an masa sumunti da ƙasa aka kawo farar ƙasa aka shafe ɗakin da shi. Se wata 'yar taga 'yar ƙut a sama kamar gurin kiwon tattabara, ɗakin ɗauke yake da ƙatuwar katifa da manyan matasai. Ga shimfiɗar buzu a gurin, wanda akeyi da fatar dabbobi, wanda warinsu kawai damun Sadik yake. Ya ajiye wayoyinsa akan katifar ya nemi guri ya zauna, yai tagumi yana jin yadda cikinsa ke wata irin juyawa. Ganin ba kowa a tsakar gida yasa Nana ta nufi ɗakin Hakimi. Ta tarar da shi yana kan sallaya yana jan carbi. Wata tasa taje ta buɗe ta ɗebi gurasa, har zata fita Hakimi yai gyaran murya. Ta waigo tace "Ci zanyi, yau ba zanci tuwo ba" Tana gama maganar tai waje, ɗakin da Sadik yake ta nufa, tana yi tana waige kar Inna ta kamata, ta ɗebo ruwa a kofin silba ta shiga ɗakin. Ta tarar da Sadik yai uban tagumi, kamar wanda yake jiran wani mummunan saƙo. Ta dire masa tace "gashi nan in ka ga dama kaci, in baka ga dama ba kai ta zama da yunwa bame lallaɓa ka yace se ka ci, sedai ka mutu da yunwa" Tana gama maganar ta juya ta fita, yayin da Sadik ko kallonta be ba, ya cigaba da taguminsa. Wunin nan guda yau be wanka ba, ya nemi guri ya kwanta akan katifar nan, ga tunanin Mother ga na Farhan, ga Faruk ɗinsa shima yana missing. Kawai yaji zuciyarsa na raya masa yaiwa tsofaffin nan Allah ya isa, saboda a ganinsa abunda su kai masa zunzurutun zalunci ne, saboda tsabar mugunta a dole se sun azabtar da shi. Jin sa da yake kamar ze mutu saboda yunwa yasa ya tashi zaune, ya janyo kwanon gurasar nan ya dinga danna ta haka gaya ba miya bakomai. Ya nayi yana shaƙewa yana korawa da ruwa, gashi ta fara bushewa, se yayi kokawa da ƙyar take haɗiyuwa, kamar yana cin takadda. Be tsaya duba wane irin ruwa bane, haka ya sha ruwan nan dan samawa kansa mafita. Da ya gama ci saboda tsabar takaici yai cilli da kwanukan a tsakar ɗakin yana huci. Ya hau kan katifar ya kwanta, zuciyarsa kamar ta tsaga ƙirjinsa ta fito dan baƙin ciki. Ba wuta, ba fanka ba sanyin AC, ɗakin se uban zafi, ga ba fitila se fitilar wayarsa da ya kunna. 'wannan ɗaki ko kabari ne se haka' ya furta yana tsaki. Ya dinga juyi amma ya kasa bacci, saboda ƙaiƙayi da jikinsa ya dinga yi, beyi wanka ba, ga sauro da uban zafi da ya addabe shi. Tashi yai zaune zaman dirshan, ya rasa abunda ze yi dan yaji daɗi. Farhan kam ta ɗan damu, dan yadda sukai da Sadik a Ranar zasu dawo, amma har yau Lahadi babu message ɗin sa tsawon wuni guda, tun saƙon da ya tura mata cewar a can za su kwana, tai ta kiran wayarsa amma ba ta shiga, haka ta haƙura ta kashe wayar ta maida ita in da take ɓoye ta. Tsakar dare Sadik ya kasa bacci sam, be san lokacin da hawaye suka fara bin idanunsa ba, hawaye ɗaya bayan ɗaya. Tsakar gidan ya fito yana ƙarewa gidan kallo, hasken farin wata ya haske ko ina, kawai se yaga gidan somehow look scary to him, toilet yake son shiga amma tsoro da fargaba suka hana shi hakan. Inna da take salla taji motsi a tsakar gida, ta ɗaga labule, taga yadda Sadik yake tsaye yana rarraba ido. "Me kake a nan gurin?" Maganar da Inna tai seda Sadik ya kusa zurawa da gudu, saboda jin maganar yai from no where. Se da ga baya ya fuskanci Inna ce, ya tsuke fuska yace "wanka zan na kasa bacci" "Wanka a tsohon daren nan, maza cigaba da tsaiwa a gurin kar kaje ka kwanta, akwai mayu idan suka fito suka lashe ka shikenan" Zare ido Sadik yai, be san takamaimai meye maita ba, amma dai yasan tabbas maita wani abune nau'i na tsoro, aikuwa cikin hanzari ya kwasa da sauri ya koma ɗakin da yake. Inna ta saki labule tace "ba dai kace kai baka ji ba, zaka ga tsiya ai ja'iri" Sadik sosai ya dinga kuka, kamar ƙaramin yaro me shan nono. Se wajen Asuba sannan bacci ya saci Sadik, Asubar fari aka zo aka tashe shi, yai Alwala zuwa masallacin cikin gidan Hakimi. Yana shirin ya miƙe yaje ya samu ya kwanta ya koma bacci, saboda rashin baccin da be samu ba jiya. Aka ce ba in da za shi za'a zauna karatun Alqur'ani. Aka rarraba Alqur'ani, amma Sadik ya ajiye nasa yace ko yayi ba lada dan be niyya ba, saboda haka baze ba. Ana ta karatun Alkur'ani, ya jingina da bango yana baccinsa, baccinsa ya fara nisa yaji an tsula masa carbi a ƙafa, ya buɗe ido a gigice. Wani dogari yace "ka buɗe idonka ka dena mana bacci" Tsaki Sadik yai, dan yaji zafin dukan carbin nan, dan se yace Allah ya isa. Haka Sadik ya zauna yai zuru yana rarraba ido. Mother kam baccin dare gagarar ta yayi, saboda tunanin halin da ɗanta yake ciki, ta san babu Lallai Sadik ya iya bacci a wannan garin, yadda ta ga dare haka taga rana, zuciyarta cike da tunani da tausayin ɗanta. Se kusan ƙarfe bakwai na safe aka tashi daga wannan karatun, Sadik ya tashi idonsa har mannewa yake saboda tsabar baccin da yake ji. A tsakar gida ya tarar da Inna da Nana, ba wanda ya gaisar ko ya kula a cikinsu ya wuce ɗakin da ya kwana. Ya haye kan katifa ya fara bacci, ƙafarsa na ta zugin dukan da aka masa da carbi. Ji yai an watsa masa ruwa, ya tashi firgigit. "Ka taso ana kiran ka" a hankali ya ƙarewa Nana kallo da take tsaye a kansa da kofin ruwa. A fusace yace "ke wace irin dabba ce zaki watsamin ruwa haka?" "Cewa a kai in tashe ka, kuma ahir ɗin ka da sake zagina" Juyawa yai akan katifar ze cigaba da bacci, yaji muryar Inna a kansa "zaka fito ne ko se an sa an fito da kai mara Kunya" Tashi yai yana kumbura baki ya fita tsakar gida yana tunanin wannan wane irin abu ne haka?" A tsakar gida ya ga An shimfiɗawa Hakimi dadduma, yana kashingiɗe, gefensa ga wasu dogarai guda biyu riƙe da bulalai, Sadik ya nemi guri ya zauna yana tura baki. Hakimi ya kalleshi yace 'ina kwana?" Shiru Sadik yai yaƙi amsawa. "Ya kai shiru baka amsa ba, can a gidan naku ma haka kake wannan rashin ɗa'ar baka gaida iyayen ka da safe ko?" Sadik ya sunkuyar da kai yaƙi Magana. Hakimi yace "a bashi Abincin safe" Nana ta kawo wani kwano ta ajiye. Hakimi yace "bismillah, maza ɗau Abinci ka ci" Sadik ya buɗe kwanon nan, tuwon masara ne a ciki da miyar kuɓewa ɗanya. Sadik ya gyatsine fuska yace "ni bana ci" Hakimi ya kalli ɗaya daga dogaran yace "A sashi yaci Abinci" Ai ganin da Sadik yai dogarin ya ɗaga bulala, ze zumbuɗa masa yasa Sadik a gigice yace "zanci dan Allah, a bani cokali" "Bame baka cokali, sa hannunka kaci da shi" Haka Sadik Ya janyo kwanon ya runtse ido ya kai loma ɗaya bakinsa, da kyar ya haɗiye saboda warin daddawar da ya addabe shi, sega ƙwalla a idon Sadik ya kai loma ta biyu amma ya kasa haɗiyewa se kakarin amai da yake. Hakimi yace "idan yai amai, ku zane shi sannan a ƙaro masa wani tuwon, zakaci ƙaniyarka, seka kwan uku kana cin gabza, saboda rashin ta ido har ayi Abinci a baku kace kai ba zaka ci ba ko, za'a ladabtar da kai ai" Haka A saka Sadik a gaba, seda ya cike gurbin Abincin da be ci na na jiya, seda ya cinye tuwon nan tas. Sannan aka kai masa ruwa banɗaki yai wanka, sedai shi kansa banɗakin tsoro ya bawa Sadik, ga wani soson wanka irin na mutan da ɗin nan me zafi a jiki, ga ruwan wanka a bucket ko abun zuba ruwa babu, masan dake banɗakin ma tsoro ta bashi, kar yaje yana cikin wankan ya faɗa ciki. sabulun kawai ya goga ya watsa ruwa ya fito da sauri, dan tsoro idan ya kalli rufin azarar nan se yaga kamar zega maciji a ciki. Da ya fito, Aka kawo masa wasu irin kaya over size, wanda ko Abbansa aka bawa kayan nan sun masa yawa, akace ya saka kayan. Sadik ya dinga kuka, hawaye shaɓe shaɓe yana tunanin wannan wane irin abune se kace zamanin bayi. Akai masa rawani kamar dagacin ƙauye, aka fita da shi zaman fada. Shigar da a kai masa tasa Nana ta dinga tuntsura dariya, duk gayun Sadik yau an maida shi ɗan ƙauye typical. Farhan duk ta damu kanta sosai akan rashin jin Sadik kwana biyu, ta kalli group ɗin su Lilly da suke kiran kansu da Sweet fifteen, suna ta shirmen su a ajin, sedai Lilly tayi shiru da alama tana tunanin wani abun ne. Haseena tace "ke Lilly, wai kwana biyu meke damunki ne, kullum cikin zancen zuci?" Lilly tai ajiyar zuciya tace "bakomai Normal" Yasmin tace "Ni sirrin Wannan glowing ɗin da kike zaki bani, kinga yadda kika ƙara ja kuwa, ga kumatunki sun sake girma" Banza tai musu suka cigaba da surutan su, Haseena tace "Yasmin zoki rakani Clinic in karɓi pad, a kowane lokaci zan iya ganin abun nan, kuna ban zo da pad ba" Yasmin tace "i thought you are pregnant ai" "Ke pragnent ɗin uban wa, ke kika min cikin dalla tashi muje ki rakani" Gaban Lilly ne ya faɗi jin hirar da sukeyi, cikin hanzari ta tashi ta tafi Office ɗin Sir Nazir. Sedai baya Office ɗin, ta nemi guri ta zauna tana jin yadda ƙirjinta ke bugawa da sauri da sauri. Ta daɗe tana jiransa se ga shi ya dawo, hannunsa riƙe da litattafai da maka. Yana ganinta ya fara murmushi yace "Baby yaya?" Ta kalleshi tace "Akwai matsala fa" Yace "subhanallah, matsalar me kuma Fateena?" "Am sick wallahi, bani da lafiya fa" Yace "eyyya sorry, ai baki gayamin bane, muje in rakaki clinic a duba min ke" Tace "Bafa yadda kake tunani bane" Yace "to yaya ne?" "Sir, wata biyu kenan ban period ba fa, kuma fa hakan na nufin ciki ne dani" "Innalillahi wa innalillahi raji'un, Lilly ya a kai kika san ciki ne da ke?" "Ina karantawa a Novels, kuma ka kanka ka mana lesson, ni gaba ɗaya hankalina ya tashi, ina jin tsoro idan babana ya sani ze iya harbeni wallahi" Cikin dirircewa yace "kinga, kwantar da hankalinki ki nutsu, haryanzu bamu tabattar da abinda kike zargi ba" Cikin kuka tace "meya rage wanda zamu tabattar ka sani a bala'i, duk wasu signs na ciki su nake ji a jikina, and kana cewa bamu tabattar ba" Nazir cikin tashin hankali yace "kinga calm down, yanzu bari in baki robar ruwa, kiyi fitsari a ciki, zanje in siyo pt strip dan mu tabattar se mu san abunyi. Ba tace masa komai ba ta cigaba da kuka. "Dan Allah Lilly ki nustu kar asirinmu ya tonu ki dena wannan kukan, bari inje yanzu zan dawo" Ya fita daga Office ɗin cikin sauri. Abba kuwa gani yai be kyautawa Mother ba da ya fita a sabgarta ba, tabbas an mata ba daidai ba amma yadda ya haƙura yai biyayya ita ma dole tayi. Sashinta ya nufa, bata falo ya wuce bedroom ɗin ta, aikuwa ya tarar da ita akan gado a zaune, tayi shiru ta zubawa guri ɗaya ido. Sallamar da yai ne ta dawo da ita hankalin ta daga dogon tunanin da take. A ciki ta amsa masa sallamar ta ɗauke kanta. Ƙarasowa yai ya zauna a kusa da ita, ya ɗan ƙura mata ido, yaga yadda idanunta su kai ja, da alama ba ta samu isashen bacci ba. "Barka da safiya" ya faɗa yana kallonta. Tura baki tayi ƙwalla na taruwa a Idonta. "Hauwa'u, nasan abunda a kai miki ba'a kyauta miki ba, amma tunda naiwa iyayena biyayya ya zama dole kema ki haƙura, nasan ba za su taɓa yi masa abunda zasu cutar da shi ba, dan haka kiyi haƙuri ki dena wannan damuwar, dan ban shirya yin musu ko jayayya da iyayena ba saboda ke" Ta ɗago ta kalle shi tace "Amma... Ya katseta ta hanyar ɗaga mata hannu tare da cewa "bana son sake jin wata magana akan wannan lamarin, na riga na rufe wannan babin, ki kai min breakfast ɗina part ɗina zan karya in fita" Ya ƙarasa maganar yana miƙewa tsaye, ya juya ya fita daga ɗakin. Wasu hawayen baƙin ciki suka shiga zubo mata, da ta san a can za'a baro mata Sadik, da duk yadda za tai seta hana shi zuwa garin, da wani aka bari a cikin yaran ba Sadik ba, da ba zata damu haka ba, amma Sadik tun tasowarsa be taɓa nesa da ita da kwanaki ba, har gara dr. Da Faruk suna zuwa cikin Family, har ƙasashen waje sunje karatu, amma Sadik baya zuwa ko ina ya zauna se in da Mother take, rana ɗaya ta ƙarfin tsiya an ɗauke mata shi. Lilly na nan zaune Office ɗin Nazir, se gashi ya dawo, kamar wanda zaki ya rarako, kallo ɗaya za kai masa ka san yana cikin matsanancin tashin hankali da zunzurutun damuwa. Ya shigo Office ɗin, ya rufe ƙofa ya kalleta yace "kinyi fitsarin?" Ta jinjina masa kai alamar eh. Ya karɓi robar, ya saka tsinken gwajin sedai yana zaro tsinken ba tare da jan lokaci ba ya nuna ɓaro ɓaro, Akwai ciki. Wani irin gumi ya shiga tsatsafowa daga goshinsa, ya ɗaga kai ya kalli in da take zaune ta ƙuro masa ido. Tace "Yana ga ka canza meyafaru? Me ka gani ne?" "You Are pregnant!" Ya bata amsa. Littafin nan ₦300 ne kacal. 0009450228 Aisha Adam Jaiz Bank KO kuje manhajar AREWA BOOKS ku siya. domin kuwa ya fi sauƙi ta can. 07063065680. Littafin nan ₦300 ne kacal. 0009450228 Aisha Adam Jaiz Bank 07063065680 KO kuje manhajar AREWA BOOKS ku siya. domin kuwa ya fi sauƙi ta can. Saurin toshe bakinta tayi, dan bata son abunda ihun nata ka iya haifarwa a tsohon daren nan ba. Bedsheet ɗin da take kai, duk ya ɓaci da jini, ga wani irin gigitaccen ciwo da marar ta keyi, se uban gumi take kamar me naƙuda. A hankali ta ja jikinta zuwa banɗaki, dan gyara jikinta, sedai abu ya gagara  ƙarshe ma ta zube akan gwiwowinta, jini na cigaba da zuba daga jikinta. Ita kanta ta firgita da jinin da ta zubar daga jikinta, yunƙurawar da tai zata miƙe, cikin ya faɗi gaba ɗaya. Ta dinga sauke numfashi, idonta har wani lumshewa yake saboda Azabar wahala. Ta daɗe a durƙushe a banɗakin, kan taji ya ɗan lafa mata, ta miƙe a durƙushe, ta gyara jikinta, ta cire bedsheet ɗin da ta ɓata, da kayan jikinta ta naɗe su ta ajiye su guri ɗaya, sannan ta koma ta kwanta. Sedai tun ba'aje ko ina ba ta kuma ɓaci da jini, saboda yadda take cigaba da zubda jinin ba ƙaƙƙautsws, haka ta dinga sintiri tsakanin ɗakin da banɗakin tana gyara jikinta, ga ciwon mara da ke cigaba da nuƙirƙusarta. Da ƙyar ta samu jinin ya tsagaita, sedai yana tsagaitawar kuma ta fara jin wani irin sanyi, ga jiri da ya fara kwasarta, da wani irin matsanancin ciwon kai, haka ta kwanta ta duƙunƙu ne, jikinta na cigaba da rawa. Sadik ba ƙaramin jin daɗin Alkaki da kilishin da Nana ta jefo masa yai ba, da gari banza ne se yai mata rashin mutunci saboda ta jefe shi da abu, amma da yake nema yake ba ƙorafi ba wani abu haka ya ɗauka ya ci. Mother ce zaune a gaban Abba, tana kuka wiwi kamar ƙaramar yarinya. "Dan girman Allah ka koma ka ɗakkomin ɗana, kana jin yadda yake min kuka a waya, wallahi yana cikin matsananciyar damuwa, dan Allah ka dawomin da ɗa na" "Wai dan Allah ya kike so nayi ne? Inyi fito na fito da Iyaye na, yau Sadik ko mutuwa yai a hannunsu na san ba zasu kashe shi da gangan ba, ko tunda kike haihuwa an taɓa ɗaukar ɗa ɗaya yaje garin ya zauna, meyasa kike hakane, kamar fa kina nuna sena nunawa iyayena basu isa bane ba fa" "Ni ba haka nake nufi ba, amma dan Allah ka basu haƙuri koma me yayi su barshi ya dawo gida, dan Allah ba danni ba" Abba ya kalli Mother yace "yanzu da yaron nan mutuwa yai fa? Ko kuma aka sace shi ya za kiyi?" "Wannan daban na san Allah ne ya karɓe shi, amma yana raye ina raye a nesanta ni da shi, ba zanji daɗi ba, dan Allah a dawomin da shi" Abba gyara kwanciyarsa yai, ya juya mata baya, dan ya gaji tun yana lallaɓata za ta sa su fara faɗa. Lilly da safe miƙewa ta gagareta se da ƙyar, da ta tashi se jiri ya dinga kwasarta, duk yadda taso ta fita falo ta kasa, se kwanciya tayi. Ganin har wajen sha ɗaya ba ta fito ba, yasa mamanta biyo ta taga ko lafiya, ta na zuwa ta tarar da ita a cikin bargo ta rufe kanta. A hankali ta kai hannu ta yaye bargon tace "Lilly, lafiya kuwa? Meya sameki haka?" "Mummy bani da lafiya" Lilly ta faɗa cikin karkarwa. "Yasalam, amma baki gayamin ba, meyasameki haka?" Seda gabn Lilly ya faɗi jin tambayar da Mum tai mata, amma ta basar tace "zazzaɓi nake da gudawa" "Amma baki zo kin gayamin ba, taso maza muje ki karya mu tafi Asibiti" Ta kamata da nufin ta miƙe, sedai tana miƙewa tai baya saboda jiri. Hankali a tashe Mummy ta riƙota tana salati, ta duba jikin Lilly taga jini tace "jinin meye wannan kuma a jikin ki?" "Mummy period nake, yana min rushing Sosai, tun jiya haka yake zuwa" Gaba ɗaya Mummy ta rikice, ta kama Lilly Zuwa banɗaki, ta taimaka mata ta gyara mata jikinta, ta sa kaya ta ɗauketa zuwa Asibiti. Idon Lilly harya nuna alamun ƙarancin jini, a yadda Lilly tai musu bayani, tace zazzaɓi tayi na kusan sati biyu se gudawar kwana uku, dan haka ba wanda ya kawo waccan ta'asar da tayi. Nan likita ya hauta da faɗa "ke dan shirme kina zaune ba lafiya kina nema ki kashe kanki, meyasa zaki zauna tsawon lokaci da larura ki ƙi faɗa" Mummy tace "nima abun ya bani mamaki, ya za'ai ace tsawon wannan lokacin, baki da lafiya ki kasa faɗamin, salon babanki ya dawo yace ina sane na barki ba lafiya" Lilly dai tai shiru, tana jin yadda kanta ke cigaba da juyawa. Nan da nan aka bata gado aka kwantar da ita, aka ɗebi jinita dan yin gwaje gwaje. Nan aka gano yadda jininta yai ƙasa, dan har tana buƙatar a ƙara mata jini, saboda yadda jininta yai ƙasa. Gashi duk gwaje gwajen da a kai mata sun nuna lafiyarta ƙalau, se 'yar malaria kaɗan a cikin jininta. Mummy ta fita waje dan kiran Mahaifin Lilly ta sanar masa halin da ake ciki. Likitan da ya duba Lilly ya shigo, ya kalli yadda ruwan da aka samata yake shiga jikinta a hankali. Ya ƙarasa gaban gadonta ya kalleta yace "Fatima, duk teses ɗin da akai miki sun nuna ba wani abu da yake damunki, malaria da ke jininki ma ba ta kai ace tayi tasirin da zaki rasa jini haka ba, ki gayamin tsakani da Allah, meke damunki?" Shiru tai tana binsa da kallo taƙi magana. "Magana fa nake miki" "Ni ba abunda yake damuna, kawai zazzaɓi nai da gudawa" tai maganar cike da ƙosawa. "Amma jinin da kika zubar yayi yawa, se fa an ƙara miki jini" "Nima ban san meya sameni ba" ta faɗa idonta na cikowa da hawaye. Yace "ok shikenan, Allah ya baki lafiya" Ta amsa da Ameen. Bayan fitar doctor, ta lumshe idanunta, ta tuna Nazir na can na hutawarsa, ita kuwa gata tana faman wahala tsakanin rayuwa da mutuwa. Me aikin su Lilly kuwa, ta shiga ɗakin Lillyn dan gyara mata, ta tarar da duƙunƙunen nan bedsheet da kayan Lillyn kaca kaca da jini, abun ban tsoro. Tai shiru tana tunani, ta san Lilly ta fara period, amma wannan Jinin yayi yawa ace na al'ada ne ya ɓata guri haka. Haka ta je ta zuba kayan a washing machine ta Wanke, tana cigaba da mamakin wannan jini haka. Nazir Kuwa tun daren jiya ya kuma kiran Lilly yaji bata ɗauka hankalinsa ya tashi, ya rasa in da ze sa kansa, bacci ma ya gagare shi yi, se kaiwa da komowa yana tunani, ya kira harya gaji amma wayar bata shiga. Da safe kasa zuwa makaranta yayi, dan yana cike da zullumin ko wani abune ya faru da ita, kar Asirin sa ya tonu. Allah ya temaki Sadik an ɗan rage wannan takurar da ake masa, mussaman akan cin Abinci, sedai fa babu hanyar fita, dan duk wani yunƙuri da ze ido na kansa ana kallonsa. Se dai ya auri zaman ɗaki, kullum yana ɗaki a zaune, idan ya fito to salla za'a je. Yau da daddare yana kwance yana kallon ƙaramar wayarsa, wadda gidan cajin yai ja alamar kowane lokaci zata iya ɗaukewa. Yau kusan kwanki huɗu beji muryar Farhan ko Mother ba, dan ma ƙaramar wayarsa akwai riƙe caji sosai. Gaba ɗaya ba bu lambar wanda take shiga. Ya duba agogo kusan ƙarfe goma da rabi na dare, amma zuciyarsa ta dinga azalzalarsa ya kira Farhan, ya Danna lambarta ya fara kira, yai ƙuri ya zubawa screen ɗin wayar ido. Be san wayar ta shiga ba, se jin muryarta yai yai can ƙasa ƙasa ta daki dodon kunnuwansa "Assalam Alaikum" Se da yai nannauyar ajiyar zuciya sannan ya ce "wa'alaikum salam" daga nan kuma yai shiru. Cikin sassanyar muryarta tace "kana lafiya?" "Kin manta dani ko?" "Ya za'ai in manta da kai, kasan wayarka ba ta shiga" "Hakane, ya Makaranta" "Lafiya ƙalau ya gidan, ya kowa da kowa" "Ƙyaleni da wannan gidan, meyasa baki bacci ba?" "Karatu nayi, kuma na zauna tunaninka" "Allah sarki matar Sadik, wallahi nima duk kewarki ta isheni, ina son in ganki" Murya a Sanyaye Farhan tace "nima ina son in ganka am missing you so much" "Kinga wayata ma ta kusa ɗaukewa saboda rashin caji, ban zaci wayarki zata shiga ba, but Alhamdilillah tunda na samu wayar ta shigo, ina fatan dai ba wata matsala ko?" Se da Farhan ta ɗanyi jimm, dan ta so tai masa maganar Sunusi, amma ta basar tace "ba wata matsala se guda ɗaya" "Matsalar menene?" "Ina so in ganka" Sadik yai murmushi yace "Nafi ki son mu haɗu, se in dinga jin kamar kafin in dawo wani ze ƙwacemin ke" "Ba wanda ze ƙwaceni, sedai ina fatan ka dawo da wuri, saboda idan kana nan zan fi samun ƙwarin gwiwa, rashin ka a kusa nima yana sani karaya" Haka kurum Sadik yaji wasu hawaye masu ɗumi, suna zirarowa gefen idonsa. "Farhan, ina sonki sosai, ni na san son da mukewa juna ba RUƊIN ƘURUCIYA bane, Allah ya cika mana burinmu" "Nima ina wannan fatan, bana son wata Magana ta kuma tasowa tsakani na da Sunusi, shiyasa na damu ka dawo" "Insha Allah ba wani abu da ze faru, ke tawace, wayata zata ɗauke Farhan se kuma in Allah yayi na samu caji, kimin Addu'a Allah yasa in dawo gida nan kusa" "Insha Allah zaka dawo nan kusa, I love You" Sadik yai murmushi yace "sake faɗa inji, in kika fadi kalmar nan ji nake kin tafiyar da mafi yawan damuwata, ina ma kina kusa dani kika faɗa, in kalli ɗan bakin nan son raina" Murmushi Farhan tai tace "good night" "Good night ko, am missing Your body warm and sweet fumes, just want kiss you again" Duk da matsananciyar kunyar da Sadik ya bata, amma hakan be hana ta jin wata kasala, da kuma jin yadda take missing ɗin sa ba. Farhan tace "Seda safe, kaga mun fara exams, gobe in Allah ya kaimu da wuri zan tafi makaranta" Sadik yace "Na sani, bari in zo mu kwanta tare" Seda Farhan ta buɗe baki jin abunda Sadik ya faɗa, bata san meke damun Sadik yau ba. "Ya ki kai shiru?" "To me zance?" Ta faɗa cikin shagwaɓa. "Ba kya son in tayaki kwanan? Aikuwa tare zamu kwana yau, hug your pillow, you will feel me with you" Murmushi kawai Farhan take, tana jin sabon salon soyaya a gurin Sadik, duk da yadda yake magana a hankali zaka san a cikin damuwa yake dan a muryarsa kawai taji yadda take ɗauke da damuwa. "Ba kice komai ba" "Naji, ka kwanta kai bacci" 'kona kwanta ba na iyawa seda kyar, kinga in da nake kwana kuwa? Haryanzu ban saba ba" "Zaka saba ne, lumshe idonka in maka addu'a kayi baccin" Be kai ga lumshe idon ba wayarsa ta ɗauke. A hankali ya lumshe idanun nasa, hawaye na cigaba da zirarowa daga idonsa, wanda shi kansa be san takaimaimai na menene ba. Ya ajiye wayar, ba tare da ya buɗe idon ba, yana jin yadda zuciyar sa ta cunkushe, ga matsanancin shauƙin son kasamcewa da Farhan da yake bijiro masa. A hankali ya janyo pillown da ke gefensa, ya rungume shi gam a ƙirjinsa, yana sauke ajiyar zuciya. Sunusi ke zaune akan wani buzu, se rubutu yake a jikin wani allo, gabansa wuta naci a jikin wasu ƙananun itace. "Sunsi wai akanwa kake wannan aikin ne haka?" Sunusi ya ɗago kansa yai murmushi yace "Haladu kenan, ai tunda ka ga nayi wannan zaman, aikin nayi ne, zazzafan aiki zanyi farraƙu zanyi" Haladu yace "wa za kaiwa Farraƙun?" "Wannan yarinyar mana da malam ya tambayar min aurenta, se nema take ta wahalar da ni, ashe wani ɗan tayin yaro take so, yake hure mata kunne, shine nake son in nuna musu ba a ja da ƙolo" Haladu yace "haba mutumina, a sassauta musu mana, kasan wannan aikin yayi zafi da yawa kai musu wani dai daban ba wannan ba" Sunusi yace "inaa, ai Wannan ɗin dai zan musu, naga kanta yana rawa ne, gara in saita ta tun da wuri, se tayi dana sanin wulaƙanta ni, kuma aikin da zanyi akan Yaron nan na gaske zanyi, yadda gobe in ance ya ƙara baze ƙara ba, zan kwashi kwanaki ina yi" Haladu yace "to ai shikenan, Allah ya dafa" Sunusi yace "Ameen" Lilly kam likita yace se ta kwana a Asibiti, saboda a cigaba da ƙara mata ruwa. Da yamma Mummy ta koma gida dan harhaɗo kayan da zasu zauna a Asibiti kafin a sallame su. Lilly tace a taho mata da wayarta, zata gayawa ƙawayenta dan su sanar ba ta da lafiya a makaranta. Haka kuwa akayi, koda aka kawo wayar Lilly ta duba, kusan missed calls goma sha na Sir Nazir. Tsaki tai ta ajiye wayar tana ƙunƙuni. "Dan Allah ni dai in ba zaka iya zuwa ba, ka barni inje da kaina in ɗakko Sadik" "Saboda kece sarauniyar 'ya'ya ko? Saboda rashin ta ido seki je ki cewa sirikan ki su baki ɗanki ko, to bari kiji in gayamiki wallahi Kika je garin nan da sunan ɗakko Sadik, ko kika ke ba tare da izina na ba wallahi a bakin Airenki!" Ras! Gaban Mother ya faɗi, dan Abba be taɓa makamancin wannan furicin ba, duk laifin da za tai masa, lallai wannan karon he is very serious on what he is saying. Kuma da ya gama maganar yai tafiyarsa ya barta a gurin, aikuwa ta zauna sosai tana kuka. Faruk ne ya shigo falon, ya tarar da ita zaune ta ma faman hawaye. Yasan tatsuniyar gizo ba ta wuce ƙoƙi, ya taka a hankali yaje kusa da ita ya zauna, ya fara share mata hawaye yace "haba Mother, dan Allah kiyi haƙuri da batun Sadik, ki kwantar da hankalinki ki dena wannan kukan, baze maganin komai ba" "Haba Faruk, dole in kuka Sadik yarone ƙarami, be taɓa nesa dani na kwanaki masu yawa ba, amma an baro shi a ƙauya, in da be taɓa zuwa ya zauna ba, kuma an hanani magana" "Hakane ba a kyauta miki ba, amma dan Allah kiyi haƙuri Mother, duk fa kukan nam da kike be canza Komai ba, kiyi haƙuri kukan ba shine magani ba, insha Allah in dai Sadik ne zasu dawo miki da abun ki" Haka yaita rarrashin Mother, yana cikin rarrashin nata sega Khairat ta zo Gidan, dan ta cigaba da taya Mother zama, dan ta ɗebe mata kewa. Da daddare bayan magariba tuni 'yan dubiya sun fara zuwa duba Lilly, ta samu Mummy ta tafi rakiya ta ɗaga wayarta ta kira Haseena a wayar mamansu. Maman Haseena na ganin Lilly ce ta bata wayar. "Hamshaƙiya, ina kika shiga ne yau kika ƙi zuwa school bayan kin san exams ake?" "Bani da lafiya ne" Lilly ta bata amsa. "Subhanallah, meya sameki ko Asmar ce ta ta shi?" "A'a zazzaɓi ne ina Asibiti anyi admitting ɗina, dan Allah ku sanar a school, duk da ma dai Mummy zata turo uncle ya sanar" "Eyya Allah ya baki lafiya, se munzo dubiya habibin naki kuma ya sani?" 'ke dalla ƙyaleni da wannan mutumin se anjima" Lilly ta katse wayar. Gaba ɗaya Sadik ya koma salihin ƙarfi da yaji, ba sawa ba fitarwa daga masallaci se ɗaki se zaman fada. Nana kam tausayi yake bata yanzu sosai da sosai, duk ranar da ta tabattar za a girka abunda ba ze iya ci ba, se ta nemo wani abun da zata bashi a ɓoye yaci, ze karɓa ya cinye amma baze iya godiya ba. Nana na cikin turakar Hakimi tana masa surutu, yace "je ki kiramin wancan Yayan naki" Nana ta miƙe tana faɗin "ni ba Yayana bane" tai waje zuwa ɗakin Sadik. Yana zaune yayi shiru yana zancen zuci Nana tace "kai ka zo ana kiranka" Ya ɗago ya kalleta ya maida kansa ya sunkuyar. "Da kai fa nake" "Ki ka kuma cemin kai sena ɓarar da ke a gurin nan" "An faɗa, kai kai kai ƙaton kai" Sadik ya tsani tsiwa, shiyasa Farhan ke burgeshi akwai girmama mutum ba wannan tsigaggaiyar ba. Yasan yanzu in beje kiran ba se ya janyowa kansa wata damuwar, haka ya miƙe ya biyo bayan Nana. A tsakar gida ya tarar da Nana, ta kamo kunnen wannan muzurun da take cewa Autan Mother. Ta riƙe kunnensa tana cewa "kai dai jarabarka tayi yawa, ga masifa ga ba'a maka gwaninta sena cillar da kai a waje, ɗan bantan uban me dogon kunne" Sarai Sadik ya san da shi take, Sedai ganin ba kowa a tsakar gidan, yasa ya ƙarasa in da take ya danƙota ya miƙar da ita tsaye. "Wayyo Allah na Inna!" Ta faɗa tana rarraba ido Sadik ya tsare gida sosai, ya ƙare mata kallo yace "Ni sa'anki ne? Ko na miki kama da abokin wasanki?" "Dallacan ni ka cikani, meye haka Inna wallahi ya taɓa ni" "Uban me zan taɓa a jikin naki? Shashasha ƙwailar banza da ta wofi, mara Kunya wallahi kika kuma cemin kai, ko na taho kika ɗau wannan magen kina zagi sena miki rashin mutunci sena kikkifa miki mari" Inna Kuwa a tare suka fito da Hakimi suna kallon ikon Allah, Sadik ya riƙe hannayen Nana, shi kam ko a jikinsa ya cigaba da yiwa Nanan warning. "To ni ka sakarmin hannu, ni ba 'yar Iska bace da zaka riƙen hannu" "To waye ɗan iskan? Wallahi idan ba ki kiyaye ni ba sena zubar miki da haƙora, stupid girl" "Wallahi ni ba stupid bace" bakin Nana yaƙi mutuwa, se zubo masa rashin kunya kawai take. Hakimi ya sake jinjin tsantsar fitsara irin ta Sadik, ganin idonsu ko a jikinsa balle ya cika Nana ko ya dena zaginta. Inna kam riƙe haɓa tai tana ganin ikon rabbi. Sannu a hankali Hakimi ya tako zuwa in da suke tsaye, ya cire hannun Sadik a na Nana. "Kai yanzu ka rasa da wa za kai faɗa se ƙanwarka? Kai ba abun kunya bane a gurinka?" "Allah ya rufan Asiri wannan ta zama ƙanwata, ni ba ƙanwata bace" "To mecece ita a gurin ka?" Hakimi yai maganar yana kallon ƙwayar idon Sadik. Sadik ya sunkuyar da kai, saboda tsananin kwarjini da dattijon yai masa. "Ni dai a ja mata kunne ta dena shiga sabgata, in ba haka ba sena ji mata ciwo" "Ahh kasheni za kai, ji min ciwo ai ba kai da yawa ba" Inna tace "dan ubanki ki biye masa yai miki illa, uwar marasa kunya" Nana ta tura baki tace "dama ai yace ya tsaneni, seya kashe ni ya huta kawai" "Eh na tsane ki" ya maimaita jijiyoyin kansa suna miƙewa, alamar ya zuciya ƙwarai. Hakimi ya kama hannun Sadik suka fita waje daga gidan. Suna fita Inna ta dirarwa Nana da faɗa "ki cigaba da masa rashin kunya, idan yai miki illa ke kila jiyo, kuma wallahi kika kuma bari ya taɓa jikinki sena miki dukan tsiya, 'yar banza shashasha" "Inna fa shine kawai ya riƙen....." "Zakimin shiru ko sena zo na tura kanki a cikin murhun nan" Nana tai shiru tana zumɓura baki. Wani ɗaki Hakimi ya kai Sadik, ya sa Sadik ɗin ya zauna yana ta huci, ya kalli Sadik yace "meyasa ba ka da ta ido ne? Kasa ƙanwarka ta raina ka, kuma a Gabanmu babu ko ta ido, su baka san mata haƙuri ake da su ba?" Hakimi yai maganar yana monitoring moves ɗin Sadik. Sadik yaƙi magana ya sunkuyar da kai yana huci. Yace "shikenan, ka zauna a nan ka baro musu cikin gidan, ka dena ganinta kana jin haushinta, idan ka huce zaɓi ya rage naka, ko ka zauna a nan ko kuma ka koma ciki. Amma kai baka san a cikin horon da nai niyyar yi maka, wani ƙasurgumin ƙauye na so kai ajiyarka ba, amma ta dage ta dinga bani haƙuri? Ita rayuwa ka kiyayi furta ka tsani mutum, mussaman a gaban makusantan sa in ba haka ba wataran za kai nadama" Sadik be ko gezau ba, har Hakimi ya gama nasihar sa ya baro shi a ɗakin. Baban Lilly da sassafe ya dira, dan an sanar masa Lillyn ba lafiya harda ƙarin jini. Dogo ne sosai, giant baƙi ne ga idanunsa jawur kamar gauta, alamun girma sun bayyana a tare da shi, dan lokacin retire ɗin sa ya kusa, kallo ɗaya za kai masa ka ga tsagwaron kwarjini a tare da shi. Yana zaune a bakin gadon Lilly, ya riƙe ɗan ƙaramin hannunta a nasa, hannu ɗaya yana shafa kanta yace "Sannu Mamana, ya kike jin jikin naki?" Cikin shagwaɓa tace "Daddy na warke ai, ni sonake a sallame ni mu koma gida, am tired na gajinda zaman Asibitin nan" "Ohhh sorry, amma idan ya kamata a sallame ki za'a sallameki ai, haryanzu jikinki ba ƙwari" Lilly tace "Daddy na gaji ne" Uace "ok shikenan, bari likitan ya shigo in masa magana" Ana haka se ga likitan ya shigo hannunsa ɗauke da file ɗinta yana dubawa. Baban Lilly yace "yawwa Doctor dama nemanka nake" Doctor yai murmushi yace "Ai gani nazo" "Doctor jaririyata fa ta gaji da zaman nan, ai discharging ɗin ta Please" Doctor yai murmushi yace "wannan ƙatuwar budurwar ce jaririya?" "Jaririya ce mana, aka ban zani ai goya abata zanyi, fifteen to sixteen years ai jaririya ce haryanzu" Doctor yai murmushi yace "in ba zaka damu ba yallaɓai ina son ganinka a office ɗina" Baban Lilly yace "ba damuwa muje" Gaban Lilly yai mummunar faɗuwa, saboda fargabar kar likita ya gano abunda ya sameta ya gayawa Babanta, ai take wasu irin hawayen tsoro suka fara zubo mata. Wayar ta ce ta hau ruri ta duba taga Nazir ne, a fusace ta ɗaga wayar tace "wai meye ne?" "Ban gane meye ba? Ina ta kiranki ba kya ɗagawa, ashe kina Asibiti harda ƙarin jini!" "Tabbas ina Asibiti harda ƙarin jini, babana ya dawo likita ya gayyace shi Office ɗin sa, dan haka ka shirya komai ze iya faruwa!!! Littafin nan ₦300 ne kacal. 0009450228 Aisha Adam Jaiz Bank 07063065680 KO kuje manhajar AREWA BOOKS ku siya. domin kuwa ya fi sauƙi ta can. Littafin nan ₦300 ne kacal. 0009450228 Aisha Adam Jaiz Bank 07063065680 KO kuje manhajar AREWA BOOKS ku siya. domin kuwa ya fi sauƙi ta can. Jikin sir Nazir ne ya ɗau rawa jin abunda Lilly ta faɗa. "Innalillahi wa innalillahi raji'un, Lilly yanzun meye abun yi?" "Nima ban sani ba, sedai kawai muyi ta Addu'a, ni kaina a tashin hankali nake wallahi". Doctor kuwa suna zuwa Office ɗinsa, Daddyn Lilly ya nemi guri ya zauna, ya kalli baban Lilly yace "yallaɓai, ba yau na fara duba iyalinka ba, mun daɗe tare muna wannan al'ammura na kula da rashin lafiyar iyalinka" Daddy yace "hakane, ina jinka" "To su dai 'ya'ya amana ce a hannun Iyaye, iya binciken da mukai bamu gano abunda yai dalilin rasa jinin Fatima haka ba, sedai shawarar da zan baku shine  a saka ido sosai a kanta, a kula da Abincinta sannan a kula da dukkan motsinta, da abubuwan da take yi" Daddy be kawo komai a ransa ba yace "dan dai wannan ai bakomai insha Allah za'a kula, tunda ta samu sauƙin jikin nata harta fara complain, a sallame ta haka, kar a takurata da yawa" Doctor yace "bakomai, yanzu zan sallame ta insha Allah" Daddy yace "to shikenan, na gama clearing bills ɗin mu ko?" "Eh, tun ranar ai an biya komai, se fatan Allah ya ƙara lafiya" Daddy yace "Ameen ya Allah, godiya nake doctor" Suka sake yin musabiha, sannan Daddy ya koma ɗakin da Lilly ke kwance. Ya tarar da ita a zaune, tayi zuru zuru, kamar mara gaskiya. Daddy uace "Baby na ya dai?" Tace "bakomai" Yace "nayi magana da Doctor, yanzu ze zo ya sallame ki, mu tafi gida zan kira Maman ki ba se ta dawo Asibitin ba tafiya za muyi" Lilly tai murmushi tace "Amma Daddy meya ce maka?" "Ina ruwanki da abunda yacemin? Bari ya zo ya sallame ki mu tafi gida. Duk da be gayamata abunda likitan ya gaya masa ba, amma ta samu sassauci dan ta sam da an gano abunda ya sameta, to da tabbas zuwa yanzu kashinta ya bushe. Washegari bayan an sallamo Lilly 'yan ajinsu suka dinga zuwa dubata, kowa yana mamakin abunda ya sameta da harta kaita ga ƙarin jini, ga fuskarta duk tayi wani iri ta kukkumbura. Kasancewar yau Juma'a, Sunusi yaci ƙarfin aikin da yake akan Sadik da Farahn, kasamcewar aikin ba kaɗan bane, bayan an sakko daga sallar juma'a, zuwa la'sar yasa wani yadinsa ruwan ƙasa, ya tafi zance gurin Farhan. Farhan kuwa tana ɗaki, tana lissafin yadda kwanaki suke ja, amma babu ɗuriyar Sadik ba ta san a wani hali yake ba, dama ya gayamata wayarsa ba caji. Cousin ɗinta ne me suna Hauzaifa ya ƙwanƙwasa ƙofar ɗakin da Farhan ke ciki. "Waye" ta faɗa cikin sassanyar muryarta. "Farhan kinyi baƙo" "Wane baƙon?" Huzaifa yace "Wannan Almajirin ne, wai in masa sallama da ke, dan ya raina min hankali ma wai ni ya aika" Tsaki Farhan tai, tayi shiru taƙi ko motsawa. Umma ce ta fito daga ɗakin ta tana faɗin "Huzaifa, kar ka sake ce masa Almajiri, ai ka san sunansa, kuma kasan shi ze Auri 'yar uwakka idan yaji kana faɗa masa haka baze ji daɗi ba" "Umma dan girman Allah ku samu mutum nagari ku aurawa Farahn, wallahi basu dace da wannan Sunusin ba, haba dan Allah yaje ƙauyensu ya nemi dai dai shi mana, se wannan masha Allah ga ilimin addini da na zamani ka.." "Kai Huzaifa ni kake gaywa haka? Shikenan dan mutum be ilimin zamani ba se ku dinga masa kallon be kai ba? Wace ita da ba zata aure shi ba? Masu ilimin bokon nawa ne sukai auren suke wahalar da matan, wannan da iliminsa da sana'arsa amma ka dinga kushe shi, kul kar ka kuskura in sake jin makamanciyar wannan maganar, ke kuma ki fito kije kin barshi a tsaye". Farhan ta sako hijjabi ta fito, sedai idan har idon Huzaifa daidai ya gano masa, kuka Farhan take yi. Gaba ɗaya yaji tausayinta ya mamaye shi, wannan wace irin rayuwa ce haka? Ace ba za'a bawa mutum zaɓin wanda ze rayu da shi ba sedai a zaɓa masa, hakan ba haramun bane amma babu tabbacin an tuntuɓi Farhan anji ta bakinta akan mutumin nan, kawai ake so a ƙaƙaba mata shi" Farhan ta fita jiki a sanyaye, tana zuwa ta tsaya ta ɗauke kanta daga kallonsa. Yace "Hmm babu ko gaisuwa 'yan mata?" Ko kallonsa ba tai ba ta cigaba da kallon Guri ɗaya. "Ki juyo mana in kalli wannan kyakykyawar fuskar tawa mana" Wani banzan kallo ta watsa masa, tana ji a ranta wannan kalaman daga bakin Sadik suka dace su fito. "Lokacin yayi da Yakamata ki kwantar da hankalinki, ki tsaya mu fuskanci juna, duk wannan haɗe ran da kike na ze canza Komai ba" Hawaye na zuba daga idonta tace "wai dan Allah me kake so dani ne? Me nai maka haka?" 'ban fahimci me kike nufi ba" "Meye dalilin da yasa kaje neman Aure gurin iyayena ba tare da amincewa ta ba?" "Saboda haka Shari'a ta ce ayi, in nemi izinin su kan in zo gurin ki" "Amma ko da shari'ar tace ai haka, ka san ba zan iya yiwa iyayena musu ba, kuma bani da niyyar wulaƙanta ka, amma zan gaya maka gaskiya wallahi Sunusi ka shiga hakkina, ba ka kyauta min ba" Murmushi yai yace "Allah ko? Aikuwa sedai kiyi yadda zaki, ko ki haƙuri ko karki yi, mahaifinki ya riga ya bani ke, dan haka gara ma ki haƙura, idan ma saboda wannan ɗan yaron kike min wulaƙanci gara tun wuri ki cire shi daga ranki, idan ma baki cire shi ba ni zan cireki daga ransa" "Ba zaka iya raba Soyayya ta da Sadik ba, saboda haɗin Allah ce, shi ka ɗai ze iya warware ta, idan kuma ka nace seka rabani da shi ka aureni, ni kuma zan barka da Allah yai ma hukunci dai dai da abunda kai mana" "Wannan kuma iyayenki zaki samu ki gayawa, bani ba" Wani irin malolon takaici ne ya tokarewa Farhan a zuciyarta, dan ba ta ƙaunar duk wani dalili da ze sa a ci mutuncin iyayenta. Juyawa tai ta shiga gida, ta samu soro ta zauna ta saka kuka. Huzaifa ne ya zo ze tafi, yaga Farhan a durƙushe tana kuka. Cikin tsananin tausayinta Huzaifa yace "Farhan lafiya kuwa? Wani abun yai miki?" Cikin hanzari ta ɗago, dan bata san Huzaifa ya zo gurin ba, tai saurin goge hawayenta tace "bakomai fa, har zaka tafi?" Huzaifa cikin damuwa yace "haba Farhan, duk da babu wata tazarar shekaru a tsakanin mu, amma ni ba wanda zaki ɓoyewa damuwa bane" Kawai ta kuma fashewa da kuka. "Kiyi haƙuri Farhan, na san ba kya son Sunusi ko?" Farhan ta jinjina masa kai da sauri. "Kiyi haƙuri, wallahi ni kaina bana ƙaunar wannan Sunusin, amma dan Allah ki dena kuka, insha Allah ba me miki Auren dole, dan sam baku dace da shi ba, amma ki dena kuka" Ta share hawayen ta tace "insha Allah na dena, Nagode sosai Huzaifa, ka gaida gida". Sunusi kuwa harya bar ƙofar Gidan, ya haɗu da Abban Farhan yana dawowa gida. Yana ganin Abban Farhan, ya zube har ƙasa yana gaishe shi. Abba yace "A'a Alaramma, kwana biyu ka ɓuya" Sunusi yace "wallahi Abba ina nan, Yanzu ma daga gidan nake" "Ahh to Masha Allah, kaje gurin Farhan ɗin kenan?" "Eh naje" yai maganar yana ɗan sosa ƙeya, alamar da Magana. Abba yace "ya dai ko akwai matsala ne?" "Eh to Abba kusan akwai ɗin kenan zance" "Subhanallah, matsalar menene?" "Eh wato Abba, ita Farhan ɗin ce na kasa gane kanta gaba ɗaya wallahi, da farko dai ta amince tana sona, to kuma katsam se naga wani ya kawota gida a mota, nai mata Magana amma naga kamar hankalinta yafi karkata kan shi wancan me hannu da shunin, kuma ma dai yarone ƙarami shine nace dan Allah Abba ai min rai, tunda an riga an bani ta dena kula wancan ɗin, ina jin ba daɗi a raina" Jimm Abba yai, dan gaba ɗaya jikinsa yai sanyi da jin wannan maganar ta Sunusi, Farhan ba ta taɓa nuna masa ba ta son Sunusi ba, ko akwai wanda take so ba, amma babban abunda yafi ɗaga masa hankali be wuce zancen wani na kawota a mota ba. Abba yai ajiyar zuciya yace "shikenan, bakomai ka kwantar da hankalin ka, zanje in shawara da mahaifiyar ta, zan ga abunda ya dace ayi haƙuri dan Allah" "Bakomai Abba, sannan dan Allah kar ai mata faɗa, bana son ranta ya ɓaci a dai nemi wata mafita daban" Abba ya murmusa yace "shikenan, kar ka damu" ya jiya jiki a sanyaye ya nufi gida. Huzaifa kuwa da ya fito ze tafi, ya hangi Abba da Sunusi a wajen ƙarshen layi, Sunusi ya gurfana yana Magana, hakanan jikinsa ya bashi, wani abun Sunusin ke kitsawa. Sunusi kuwa yana ganin Abba ya wuce yai ƙwafa yace "Ai naga alamar kan aikin nan da nake ya kammala se ina yi ina zagowa ta bayan gida, in ba haka ba Yarinyar nan za ta bani Matsala. Abba haka ya shiga gidan jikinsa a matuƙar sanyaye, dan be taɓa tunanin faruwar hakan daga Farhan ɗin ba, ya yarda da 'yarsa matuƙa da gaske. Umma daga yanaisa ta gane Akwai matsala, amma duk yadda tai ta tambayar sa Lafiya, ƙin gayamata yayi, dan be san ta in da ze fara mata bayanin ba, gashi ta fishi girmama abu irin wannan mussaman akan Farhan. Sir Nazir yana nan hankali ya kasa kwanciya, saboda fargabar abunda ze taso, gashi ta dena ɗaga wayarsa gaba ɗaya. A makaranta su Haseena suke zancen sunje sun duba Lilly, ta rame Sosai saboda rashin lafiyar da tai. Sir Nazir ya sa aka kira masa Yasmeen, ya tambayeta ya jikin Lilly, tace "jikinta da sauƙi, amma har ƙarin jini a kai mata, amma da jikin nata da sauƙi" Yace "ok to shikenan, jeki" Bayan tafiyar Yasmeen ya kuma ɗaukar waya ya kira Lilly, Amma ta ƙi ɗagawa. Yasan ba abunda ya faru, dan da tabbas in wani abu ya faru zuwa yanzu da an danƙo shi. Kasancewar an kammala jarrabawa, ya sa Farhan na gida, saboda hutu za'ai, ga damuwa tayi mata yawa, ga ba abokin hira balle ta ɗan faɗi matsalar ta taji daɗi. Jiki a sanyaye Farhan ta fito daga ɗakinta, zata ɗebi abun karin kumallo ta tarar da Hajiyar nan maƙociyar su ta shigo yiwa Umma sallama zata tafi umara. Farhan na ganin mutuncin Hajiya Sosai, har ƙasa ta durƙusa ta gaisheta Kamar yadda ta saba. Cikin sakin fuska Hajiya ta amsa tace "ke Farhan ko gaisheni ba kya ɗan shigowa kiyi, ni dama Ummanki ta barmin ke, 'yan jikokin nawa duk sunyi Aure ba me zuwa in da nake" Murmushi Farhan tai, tana ƙoƙarin miƙewa. Hajiya tace "Ni kam ko baki da lafiya ne naga duk kin rame" Farhan take taji kamar ta fashe da kuka, dan marabarta da mara lafiya kaɗan ne, amma tace "A'a Hajiya lafiyata ƙalau" Farhan ta ƙarasa maganar muryarta na rawa. Hajiya tace "tashi kije, naga ke ba son Magana kike ba, ni wallahi Umman Farhan da ina sauran ɗa da be Aure ba da nace muna kamun Farhan, ni ko a masu Auren ma in yi wani amarya da ita, ina son Farhan wallahi" Umma tace "Allah sarki, ai an mata miji, ɗan lokaci kawai ake jira a fara Maganar Aure" Hajiya tace "Allah sarki, ashe an rigamu to Allah ya tabattar da Alkhairi, na so ace cikin iyalina ta shigo, Farhan akwai nutsuwa" Suka cigaba da hirarsu da Umma, yayin da Farhan ta koma ɗaki ta zubawa kayan karin kumallo ido, ta kasa ci se zafi da ƙirjinta ke mata. "Yaya wai kije inji Abba" maganar ƙninta ce Amira ta dawo da ita hankalinta, haka nan taji gabanta ya faɗi, saboda wasu lokutan kiran Abban ba ya wuce zancen Sunusi. Kamar kasar da ta haɗiyi ƙwai, haka Farhan ta tashi ta tafi ɗakin Abba. Umma ma na zaune a ɗakin Farhan ta shiga ta zauna tace "Abba gani" Ya kalli Farhan yace "Farhan magana nake so muyi da ke, kuma ina son ki gayamin tsakani Allah" Gaban Farhan ya faɗi, tace "to Abba" "Farhan kwanaki an cemin ana kawoki a mota, amma kince min 'yar Makarantar ku ce, na ce miki bana son biyewa yaran masu kuɗi, Amma an kuma tarata ance min wani ne yake kawoki a motarsa. Gaban Farhan ya faɗi, wane munafukin ne wannan? Rabon da Sadik ya zo an do shi wata na biyu kenan bama yanan, amma an samu wanda ya samu Abba ya gaya masa. "Farhan waye yake kawo ki a mota?" "Abba Sadik ne" ta faɗa kai tsaye. "Waye Sadik" Abba ya tambaye ta. "Wanda suka zo suka kawomin invitation ɗin bikin yayan su, shi da ƙanwarsa, motar gidan su ce, idan anzo ɗaukar su ne muke tahowa tare, kuma na dena biyosu tunda kace min baka so, nika ɗai nake tahowa gida" Abba yace "to, ba a shedar ɗan yau, ba zan gazgata abunda kika faɗa ba, kuma ba zan ƙaryata ba, sedai ina sake jaddada miki Farhan kiji tsoron Allah, ki tsare mutuncinki, ki kula da kanki Farhan 'ya mace ce ke, kije shikenan" Farhan ta tashi jiki a sanyaye, ta bar ɗakin. "Nifa na fara tsorata da wannan lamuran, abu tun ana waiwai to maganin kar ayi kar a fara, kawai kacewa yaron nan ya fito, ni in babu hali ma kawai a haƙura da karatun nan, ka aurar da ita" Abba yace "Nima ina wannan tunanin, zanwa Malamin nasu Magana kawai su turo a kawo kuɗin, muga abunda yakamata ayi" Farhan kuwa tana tsaye a ƙofar ɗakin, a kunnenta taji Abba yana faɗin ze karɓi kuɗin Auren ta a hannun Sunusi. Jikinta na rawa ta ƙarasa ɗakinta, ta na zuwa ta durƙushe, ta nannaɗe a cikin hijjabi tana faman kuka. Kamar yadda Abba ya yanke shawara shi da Maman Farhan, washegari yaje ya samu malamin su Sunusi. Ya tarar da shi da Almajirai, Yana ganin Abba ya taso yana murmushi, suka koma gefe suka gaisa, Malam yace "Malam Mahmud, ina fatan dai lafiya?" Abba yace "lafiya ƙalau, dama ba wani abu bane, magana ce akan Farhan da Sunusi". "Eh to ya ake ciki?" Abba yace "ka san yanayin zamanin nan da muke ciki, da kuma halin ɗan yau, shine nace idan ba damuwa Sunusi ya fito kawai ya kawo kuɗin Aure" Malam yace "Alhamdilillah, amma gaskiya naji daɗin wannan magana ta ka sosai da sosai, ubangiji Allah ya ƙara girma, zanyi Magana da shi Sunusin, muje can garin nasu a tattauna da magabantasa se ya fito, Nagode ƙwarai da karamcin ka, Allah ya nuna mana lokacin Auren" Abba ya amsa da Ameen, daga nan su kai sallama. Fafur Abba ya fututtuke ya hana Mother Zuwa in da Sadik yake, tun tana damuwa tana kuka harta dangana ta saba, dan Sadik ya kusa watanni biyu a garin nan, ba tare da ta sake sa Sadik ɗin a idonta ba. Takanas su Nas sukaje har gida, dan kaiwa Sadik ziyara amma aka sanar da su baya gari, Faruk ne ya gaya musu, Amma be gaya musu in da Sadik ɗin yake ba. Allah ya temaki Farhan Tunda Mubarak Babba su kai arangama da Sadik ba ta sake ganinsa ba, dan haka ta manta da batun Mubarak Babba. Lilly kuwa ga warke sumul kamar ba tai rashin lafiya ba, dan har zata fara zuwa Makaranta cikin hutu ai mata jarrabawar da ba ta samu tayi ba. Ranar farko da t fara zuwa ta haɗu da Sir Nazir a makarantar, yana fama da marking ɗin takaddun Se da gabansa ya faɗi da ya ganta, duk ta rame sosai da sosai, sedai ta ɗanyi ƙalau da ita, ko in da yake ba ta kalla ba ta shiga sabgogin ta. A wani aji aka ware su, ita da wasu ɗalibai, wanda ba su samu damar yin jarrabawar ba. Se shiga yake yana fita yana son samun hanyar da ze mata Magana, amma abu ya gagara. Seda ta gama exams ɗin ta fito sannan ya samu ya biyo bayanta yana mata Magana. "Wai dan Allah Nazir me kake so ne? Me zan maka?" (Ashsha, ya rasa wannan darajar da girmamawa ta malami da ɗalibi saboda abunda ya aikata" "Haba Lilly, kin dena ɗaga wayata gaba ɗaya na biyoki kuma kin ƙi saurarata" Cikin tsiwa tace "in ɗaga wayarka in ce maka me? Bayan ka cuceni ka zalunce ni Allah ne yai da sauran kwanana na gaba da yanzu wani zancen ake ba wannan bax "Lilly ki dena ɗaga murya dan Allah kar wani yaji" "To wanin ma yaji mana ina ruwana?" "Lilly ni ki ke wa haka?" Yai maganar yana nuna kansa da yatsansa. Kawai kuma se taji tausayinsa ya kamata. "Koma me nai ai kai ka janyo min, se da aka samun leda biyu na jini, dole raina ya ɓaci" "Amma bisa amincewar ki koma mene ya faru, kuma ke kika bani damar nema mana mafita, se kuma ki dinga wulaƙanta ni dan ina binki?" "Ni ba wulaƙanta nai ba" "To girmamani ki kai?" Tai shiru tare da sunkuyar da kai. Cikin sanyin jiki yace "Tun da abun nan ya gifta a tsakanin mu nake jina cikin damuwa, amma kin kasa fahimtar hakan, nasan mun aikata Babban laifi, Amma dan Allah ki dena min haka" "Shikenan naji" "Shikenan kim ji kuma? Ba zaki ce Komai ba?" "To me zance?" Ta faɗa a ɗan shagwaɓe. "Nayi kewarki sosai Lilly" "I miss you too" "Ba wani ba ki missing ɗi na ba" "Wallahi nayi missing ɗin ka, wahalar da na shiga ce yasa naji haushin ka" Yace "to Yanzu fa?" "Ya wuce" tai maganar tana murmushi. "Yawwa Love, Allah ya ƙara lafiya muje restaurant mu ci Abinci tare mana" "Daga yin salaryn in cinye maka kuɗi, karka damu" "A'a kinga ban samu na zo duba ki ba, saboda ina tsoron ko kin faɗa a gida, muje mu ci Abincin kan azo ɗaukar ki" "Shikenan muje" suka jera suka fita daga cikin Makarantar. Khairat na zaune a falo, ta harɗe ƙafa tana kallon Bollywood, se ga wata 'yar makarantar Islamiyyar  su ta kawo mata ziyara. Khairat ta dinga murmushi, ta kalli ƙawarta tace "Yasmeen, waye ya gaya miki ina nan?" Yasmeen yace "gidanku naje, aka cemin kina Gidan su Prince, ni wai ina gayen nan, tunda ya bar school ɗin nan sau ɗaya ya zo, ko gurin budurwar ta sa ba ya zuwa?" Khairat tace "ke yana ƙauye fa" "Wane irin ƙauye kuma?" Yasmeen ta tambaya cike da Mamaki. "Yana ƙauye gidan kakanninsa, sun riƙe shi a can" Yasmeen tace "taɓ, Wannan gayen a ƙauye abun ba arziki, kin san yarinyar da yake so 'yar ajinmu ce" "Haba dai, Farhan ne sunan nata ko wa?" "Eh, haka sunan ta, wata 'yar talakawa sam bata waye ba" Khairat tace "Na santa, tare muka kai mata invitation ɗin bikin dr. Ya nace yace se ita yake so, in ya tafi karatu dai kowa ya huta" Yasmeen tace "hakane, amma meyasa ba zaki ba shi shawarar ya nemi budurwa wadda take tsarar sa ba, me ze yi da wannan?" "Ke kin san kuwa waye Sadik? So kike ya min rashin mutunci ko? Ko da wasa mutum ya kushe ta ba ki ga yadda ake kwasheta da shi ba, balle wata Shawara, ke nifa before am the one crushing on him, but now ya min yarinta kuma halinmu ba ze zo ɗaya ba, kawai na bar mata shi naga yadda yake hauka a kanta, ni ina jiran in samu wani handsome ɗin ne" Dariya suka yi, Faruk yai Sallama falon, suka amsa gaba ɗaya. Faruk yace "Khairat, Mother ta fitan ne?" "Eh tun ɗazu ma, ta daɗe da fita gaskiya" A hankali Yasmeen ta furta wow, ta kalli Faruk tace "ina wuni?" "Lafiya ƙalau ya kike?" Tace "Lafiya ƙalau" Faruk yace "ke Khairat baƙuwar taki ko ruwa ba zaki bata bane?" Cikin shagwaɓa Khairat tace "yanzu fa ta zo, zan bata ai" "Ba wani nan, baki iya saukar baƙo ba" ya ƙarasa Maganar tare da barin falon. "Wow, Khairat wannan ma ɗan uwan Prince ne?" "Eh ɗan uwansa ne ba kiga suna kama ba?" "Kai amma naga wannan fari, gaskiya yafi Prince kyau" Khairat tace "haba da faɗ kike, dan dai wannan fari ne tas, Sadik kuma be kaishi haske ba, amma duk 'yan gidan nan ba me kyan Sadik" Yasmeen tace "wayyo Allah, ammm da Allah kice ina gaise shi" Dariya kawai Khairat tai, ta canza hirar. Bayan tafiyar Yasmeen ne Khairat tai shiru tana tunani, tunda ta san ba zata samu Sadik b, Ai Faruk shi yafi dacewa ta sa a gaba, saboda shine nan da wani ɗan lokaci ze iya yin Aure. Sunusi ne a tsaye a bakin wani ruwa, da yake ta zuba gudu ga iska na kaɗa ruwan sosai, ga duhun dare se hasken farin wata da ha gauraye gurin. Ya ɗakko wata jar laya, ya jefata cikin ruwan, ruwan ya tafi da ita ya tsaya yana cigaba da kallon ruwan yana murmushi yace "yanzu aiki saura ƙarashe, ƙirisa ya rage in kammala aikin nan komai ya zama daidai. Sadik yana tsaka da baccin sa, yaji tamkar an sara masa wani abu a kansa, ya taho tun daga kansa zuwa ƙahon zuciyarsa, a kiɗime ya tashi zaune yana maimaita innalillahi wa innalillahi raji'un. Y dafe kansa yana jin yadda yake sara masa, zuciyarsa na ta bugawa da sauri da sauri. A hankali kuma ya furta "Farhan" take zuciyarsa ta tsinke, yaji babu abinda yake son gani sama da ita, dan rabonsu da waya kusan wata guda kenan. Kamar a mafarki haka ita ma Farhan taji an kira sunanta, ga wani irin sanyi da ya dinga ratsata, zaune ta tashi tana waige waige a ɗakin, kamar me neman wani abu. Ita kanta bata san me take nema ba, ga wata faɗuwar gaba da ta addabe ta. Miƙewa tai tayo Alwala, ta koma ta kwanta tana karanto duk ayar da ta zo bakinta. Se daf da Asuba Sannan Sadik ya koma bacci, sedai mafarkin Farhan ya dinga yi, mafarkan da ya kasa gane kansu ma gaba ɗaya, daga baya kuma ya koma irin mafarkansa da ya kanyi da ita. Mitar Inna ce ta farkar da shi daga bacci, "wai yau wane kalar rashin mutunci ne haka? Sallar ce ba zaka ba ko me, gashi can sun tayar da salla amma kana naɗe kana bacci" A hankali ya buɗe idonsa, ya miƙe daga kan shimfiɗar sa, sedai a yanayin da yake jin jikinsa, ba ze iya salla ba se yai wanka, ga wata irin wutar son ganin Farhan da ta addabi zuciyarsa. A hankali ya fito tsakar gida, yai karo da Inna tana salla a tsakar gida. Ɗan gajeren tsaki yai, a ransa yace 'yau kuma meya fito da wannan tsohuwar yin salla a tsakar gida?" Ko a jikinsa, ya wuce ya ɗau bokiti ya cika da ruwa, ya wuce banɗaki dan yanzu ya saba da wanka da ruwan sanyi. Yai wanka yai Alwala, Sannan ya fito ya wuce ɗakinsa. Tun da ya fito Inna ta bishi da kallo, duk da gari da sauran duhu, amma kallonsa take, ko a jikinsaya wuce ɗakinsa. Nana tace "ji wata masifa wanka da uwar Asubar nan, se kace kif... Ɗala mata duka Inn ai a baya yace "ban hanaki shiga sabgarsa ba? Se yazo yana zaginki ki buɗe maƙogwaro kina ihu ko?" Nana ta ja bakinta ta tsuke. Har zuwa safiya, jikin Sadik a matuƙar sanyaye yake, a hankali yake gudanar da komai. A tsakar gida ya tarar da Nana, ta zubawa maguna Abinci, ita kuma tana zaune tana saƙa da ulu da kwarashi. Gaban Nana ya ƙaraso ya tsuguna, ya zuba mata ido. A tsorace ta kalle shi tace "meye haka?" Ya ajiye mata wayoyinsa, yace "ina son caji a waya ta ne, zanyi amfani da su" "To na maka kama da wutar lantarki?" "Gurin masu caji zaki kai min" "Ajiye ba dan halinka ba, dan wani lokacin ina ɗan jin tausayin ka, da dan halinka ne wallahi ba zan kai ba" Kamar zeyi magana amma ya fasa, ya miƙe tsam, ya koma ɗaki. A jakar Islamiyyar ta ta saka wayoyin, ba ta gayawa Inna ba, da aka tashi daga Makarantar ta tafi kai masa cajin. Sedai gurin da nisan gaske, haka taje ta kai masa, wanda yai dalilin daɗewarta ba ta dawo da wuri ba. Inna ta dinga safa da marwa, tana tunanin in da Nana ta tsaya, amma Sadik na kallonta be ce uffan ba. An fara kiran sallar magariba sannan ta dawo gida. Tana shigowa kallon da inna tai mata ya sa ta sha jinin jikinta. "Zo ki gayamin in da kika je" Nana tace "wallahi Inna ba in da naje, caji na kai masa" Inna tace "shi wa?" Nana ta nuna Sadik tace "wannan" "Ƙarya kike ki gayamin gidan uban da kika tafi, ko wani ne ya tsare ki a hanya?" "Wallahi Inna ba wanda ya tsareni, wallahi caji ya bani na kai masa" Sadik yana zaune yana ji, ko kallonsu be ba, Inna ta kwakwkwaɗe Nana, ta ƙare mata zagi tsaf. Ba dukan Inna ne ya ɓata mata rai ba, illa yadda Sadik yaƙi ƙwatarta ko ya gazgata shine ya aike ta. Saboda tsabar baƙin ciki, ko Abincin dare ba ta ci ba ta kwanta bacci tana kuka. Da Asuba su kai clashing da Sadik, ta fito daga banɗaki, aikuwa tana ganin sa tace "wallahi ba ka da imani, kuma wallahi na barka da Allay, kai ka aikeni amma kana kallo, a ka dakeni a kai min faɗa, mugu kawai" Be ma nuna ya san yaji me tace ba, yai banza da ita, yai Alwala yaje salla. Se da gari yai haske, ya fito tsakar gida, ya ga Inna ta shiga sashin turakar Hakimi, Nana kuma ta fito daga banɗaki ta shiga ɗakin Inna. Ba tantamar komai, yabi bayanta, zuwa ɗakin Innan. Har Nana ta cire hijjabi, daga ita se ɗaurin ƙirji za ta fara cin Abinci, ta ɗaga kai taga Sadik a kanta a tsaye. Littafin nan ₦300 ne kacal. 0009450228 Aisha Adam Jaiz Bank 07063065680 KO kuje manhajar AREWA BOOKS ku siya. domin kuwa ya fi sauƙi ta can. Littafin nan ₦300 ne kacal. 0009450228 Aisha Adam Jaiz Bank KO kuje manhajar AREWA BOOKS ku siya. domin kuwa ya fi sauƙi ta can. Jikinta ne ya hau rawa, ta zazzaro ido ta furta "Na shiga uku, watan cin ubana a gida ya tsaya, wallahi baban mu ze iya kashe ni ya huta, Innalillahi wa innalillahi raji'un, ka cutar dani Sir" Shima cikin damuwa yace "Please calm down, ni kaina ban san haka zata faru ba, kuma da baki zo gidana ba da duk wannan abun be faru ba" "Au haka ma zakace ko?" "Bahaka bane, me faruwa ta riga ta faru, yanzu abunda nake so da ke shine, ki kwantar da hankalin ki kinji, zan san abunyi a kai" "Zaka san abunyi a kai Yaushe? For how long zan jira ka nemo mafita, idan kuma aka gano ni a gida fa" "Wait, ki dena wannan kukan dan Allah, babu me ganowa har ayi abunda za'ai, zanje in bincika abunyi zuwa gobe in Allah ya kaimu, amma dan Allah karki gayawa kowa Lilly" "Ni ba wanda zan gayawa, damuwata shine in rabu da cikin nan, zamansa a jikina kusanta ni da bala'i yake koma ajalina, dan babana baze barni da rai ba idan ya gano ni Allah" tai maganar hawaye na gangarowa daga idonta. "Nasani Lilly, dan Allah ki kwantar da hankalinki, ki shiga toilet ki wanke fuskar ki, seki koma aji dan Allah karki bari asirinmu ya tonu" Ta jinjina masa kai ta fice daga Office ɗin. Guri ya nema ya zauna, yana yakice gumi a fuskar sa, yana jin yadda zuciyar sa ke wani irin bugawa saboda tsabar tsoro da fargaba, be taɓa tunanin a karon farko haka Lilly zata ɗau ciki ba. Ajin su Sadik kuwa, an haɗu suna ta hada hadar su, wasu na ciye ciye wasu na danna waya. Nas ne yace "Allah sarki, wallahi missing ɗin abokin mu nake" Amin yace "kai dai bari bro, wallahi tun da Sadik ya bar school ɗin nan ta dena min daɗi, babu wani show na Musamman, gaskiya anyi missing wallahi" Taslim tace "ai ba'a cewa komai, Sadik duniya ne gayen yayi, he's very jovial yana bamu nishaɗi sosai" Amin yace "gaskiya Nas Yakamata mu kai masa ziyara gidan su" "Hakane, ni zata ma ze dinga zuwa school ɗin nan ko dan saboda beb ɗin sa, amma naga sau ɗaya ya zo daga nan be sake zuwa ba" Amin yace "kai Sadik ɗan bala'i ne, wallahi wani aka samu ya kira shi ya gaya masa Mubarak yana bibiyar Yarinyar nan, se gashi kamar an jefo shi, seda suka kusa bawa hammta iska fa ranar da ya zo, ni tsoro ma naji karsu dambace dan ka san Mubarak na yawo da makami" Nas yace "wallahi fa, kuma idan ya illata Sadik se yayi prison, dan babansa ba shi da kuɗin da ze ƙwace shi a gurin baban Sadik" Meenal tace "se cin mutuncin saurayin Taslim kuke a gabanta ya haka ne gayu" Taslim tai murmushi tace "saurayina na wucin gadi ba, ni ina ruwana dalili ne ya haɗamu kuma ya raba mu dan haka suyi ta zaginsa" Amin yace "kai Taslim, duk soyayyar da ku kai?" "Taɓɗijan, ai banda dalili ba abunda ze sa in saurari Mubarak, kai ka san suwaye samarina kuwa manyan kawuna ne wallahi?" Meena tace "wai dan Allah baki ji haushi ba da yake bin budurwar Sadik?" "Haushin me zanji Meena? Dama halinsa ne kamar ɗan Akuya haka yake, kuma naga ai ba mijina bane da zanji haushi" Nas yace "Amma kin san da haka kike biye masa?" "Yes saboda nima akwai abunda nake samu a gurinsa" "To gaya mana menene?" Nas ya faɗa cike da fitsara yana wani kashe ido. Taslim tace "kai dai Nas Allah ya shirye ka da gulma, budurwar Sadik da yake bi, dalili biyu ne yasa yake binta" Meena tace "wane dalili kenan?" Taslim tace "akwai tsama da ke tsakanin su, da ba kowa ya san meya haɗa su ba, dan haka yake son yin amfani da budurwar Sadik gurin rama abunda ke tsakanin sa da Sadik ɗin" Amin yace "Ni kaina ina mamakin yadda lokuta da dama na kanga ƙiyayyar juna a tsakaninsu, duk da suna pretending, amma meya haɗa su ne?" Taslim tace "ba za'a ji mutuwar sarki a bakina ba" "Kar Allah yasa aji ɗin, in tai tsami maji, nayi mamaki da duk zamnmu da Sadik be taɓa gayamana abunda ya haɗasu da Mubarak ba" Meena tace "ba abun mamaki bane, saboda yanayin halinsa, duk son nishaɗinsa, he has a private life, bakomai ze haɗaku yaje yana faɗa ba" Amin yace "gaskiya ne, Sadik yana da halaye na ban mamaki, masu kyau kuma abun koyi, a zaman mu na tabattar wallahi son da yake wa yarinyar nan da gaske yake sonta, ita ma kuma tana matuƙar son sa, sedai abune mawuyaci gidansu su bari ya aure ta, saboda 'yar talakawa ce sosai" Taslim tace "ni zan gaya maka 'yar talakawa ce, wallahi se an sa gidansu uku zuwa huɗu a gidan mu, ai ni naje na taho da ita ranar birthday ɗin ta" Nas yace "dama ai batun wani aure tsakanin sa da Yarinyar nan ba abune me yuwuwa ba, shiyasa ake bashi shawara kawai ya huta da ita a wuce gurin, amma ya tsaya yana shirme wai shi Aurenta zeyi kamar ba namiji ba, kalli da yadda aka sa yai kissing ɗin ta, daga baya kuma wai yazo abun ya dame shi, wasu lokutan yai ta abu kamar ba wayayye ba" Amin yace "ba haka bane, daga Yarinyar ne, da ya samu tantiriya, da zata gogar da shi sosai, da irin su Taslim ya samu, amma ita she's so innocent, shi yasa na koma jin tausayin ta dan da farko haushi take bani, amma daga baya naga idan Sadik ya lalata rayuwarta abun ze mata yawa, ga Talauci ga kuma lalacewa" Nas yace "kai tafi can, ka bibiya ba abunda ba ta sani ba, yaran nan na yanzu, kai yanzu in aka cewa iyayen mu muna zagawa square mu huta, zasu yadda ne? Kai dai kawai ai sha'ni duk rufa rufa ce abun" Taslim tace "kuma wallahi Yarinyar nan da zata shigo layi, zata ɗau haske zata gara manyan mutane, dan tana da kyau ga uban diri kamar babbar mace" Meena tace "ai abunda yake sake ruɗar Sadik kenan, wannan dirin nata" Nan suka cigba da gulmace gulmacen su. Seda aka idar da sallar azahar, sannan aka tashi daga fadar nan, Sadik yaga shirme a gurin 'yan ƙauye kala kala. Yadda suke kawo ƙara, wasu akan filaye wasu dabbobi, ba wanda yafi bashi takaici irin cases ɗin Aure. Wata mijinta na satar mata awaki ya siyar, wata yana cin mutuncin ta, hadda me kawo ƙara akan tana ciyar da dabbobin mijinta dusa yace ze biyata amma baya bayarwa. Shari'a kala kala, wasu abun haushi da takaici haka Sadik ya dinga jin su. Ƙarewa gidan kallo Sadik yake, yana tunanin ta ina ze fara haurawa ya gudu daga gidan? Sedai katangar gidan doguwa ce sosai. Sadik yana sha'awar kallon dawakan da suke burga, dan haka ya tsaya a gurin yana kallon yadda suke cin abinci suna huci. Kamar an mintsine shi, yasa hannu a aljihunsa ya ɗakko ƙaramar wayarsa ya kira layin Farhan, by luck yaji ta fara ringing. Murmushi yai ya gyara tsaiwar sa, yana jiran ta ɗaga. Sedai bata samu ta ɗaga ɗin ba, a ƙalla ya kirata kusan sau uku amma bata ɗaga ba, haka ya haƙura ya koma neman layin Mother, sedai shi kuma yaƙi shiga. Gajeren tsaki yai, ya waiga bayansa yaga wannan dogaran tsaye da bulalai kamar masu gadin bawa, haka ya juya ya shiga cikin gidan yana kumbura baki. Yana shiga ya cire wannan uban kayan da aka sa shi ya saka, ya zauna daga shi se vest da dogon wando. Ya zauna akan katifar nan yai shiru, gaba ɗaya jin sa hake kama a prison, ba wani abun ɗebe kewa, ba abokai ba kallo, ba yawo, ga wayarsa Babbar caji ya kusa ƙarewa, ga kewar Mother da yake yi, gaba ɗaya abun duniya ya dame shi. Farhan se da taje gida, Sannan taga missed call ɗin Sadik, gashi ta riga ta dawo gida, dama wayar kullum a silent take, shiyasa ba ta ji ringing ba. A gaggauce take komai, dan ta samu ta fita Islamiyya da wuri, ta kira Sadik, dan ba halin ta kira shi yanzu a gida, za'a iya jinta. Sadik ya zauna ba daɗewa yana jiran ya samu yai bacci, aka zo aka kirashi seda yai tsaki sannan ya fito. A turakar Hakimi aka sashi a gaba, da bulala aka kuma narka masa irin tuwon da yaci da safe. Sadik yana ci yana goge gumi, haka ya dinga cin tuwon nan, ji yake dama ya mutu ya huta da wannan jarabar. Seda yaci sannan ya koma ɗaki ya kwanta, zuciyarsa a cunkushe. Wayarsa ce ta fara ringing, ya tashi zaune da sauri ya duba yaga Farhan ce. Cikin hanzari ya katse kiran, ya kirata sedai ba ya jinta sosai, a haka yace "Baby ina kika je ne na kira baki ɗaga ba?" "Ina school ne, ka san wayar tana silent tun jiya nake trying lambarka taƙi shiga, se da na dawo gida naga missed call ɗinka, na bari seda na fito Islamiyya sannan na kira ka" Cikin damuwa Sadik yace "Baby ina cikin damuwa da tashin hankali wallahi" "Subhanallah, meyafaru ne?" "Kin ganni haryanzu ina ƙauye, ba kiji ba kya jina sosai ba?" "Eh naji abun ya bani mamaki" "Daga zuwa dubiyar nan aka hanani komawa gida, an barni a nan ina ta shan wahala" Cikin damuwa Farhan tace "meyasa to aka barka a ƙauyen?" "Kakana ne yace se an barni, baki ga yadda na koma ba, ba zan iya zaman garin nan ba, ina nan ina tunanin yadda zan gudu" Farhan tace "ya salam, ka dena batun guduwa karka ɗaga musu hankali, kayi haƙuri ka zauna zuwa lokacin da zasu bari ka tafi" "Farhan ba zasu bari in koma gida ta daɗin rai ba, se gana min wahala suke, ba ruwa ba wuta, ba irin Abincin da nake so tuwo fa ake bani, ga ina missing ɗin Mother, ga kema ba kya kusa dani, cajin wayata ma ya kusa ƙarewa, tunda na zo banga an kawo wuta ba, ba wanda na kira ba wanda ya kirani wace irin rayuwa ce wannan kamat wani bawa dan Allah" Tausayin Sadik ya mamayeta gaba ɗaya, cikin damuwa tace "ka kwantar da hankalin ka Dear, dan Allah kar kayi wani abun da ze ja maka ɓacin rai kayi haƙuri, kasan su iyaye ba'a jayayya da su" "Kakan ni na ne fa ba iyaye na ba, shima Abba ya tafi ya barni a nan, ban zaci Mother zata bari in kwana a garin nan ba ma" "Kakanni suma iyaye ne, kayi haƙuri zuwa lokacin da zasu bari ka dawo kaji my" "Hmm ba Zaki gane halin da nake ciki ba, duk yadda zan misalta miki ba zaki gane ba" "Zan gane mana, na sani zaman ƙauye babu daɗi amma kayi haƙuri ka kwantar da hankalinka kaji my love" "Lovely ya zanyi, but definitely se na bar garin nan ba zan iya zama ba, and am missing you sosai wallahi" "Am missing You too sweetheart" "Are you sure?" Yai maganar yana shafa sumar kansa. "Au ƙarya nake kenan?" Tai maganar a shagwaɓe. "Wane ni in ƙaryata Baby na, sonake in ƙara tabattar da abunda kike faɗa ne" "Hmm to ai shikenan, bari in ƙarasa Islamiyya" A ɗan shagwaɓe yace "ban gaji da jin muryarki ba Farhan" "Nima haka, amma kasan komai a ɓoye nake yi" "Hakane, kiyi fatan zamana a garin nan yai silar warwarewar matsalata" "Insha Allah, zanyi mana Addu'a sosai, Allah yasa su barka ka dawo" "Ameen, in ma basu barni ba zasu wayi gari suga na gudu, nace ya batun yaron nan ya kuma miki wani abu ne?" "A'a tun ranar nan ba ƙara ganinsa ba" "To shikenan, ki kula sosai duk abunda kika gani wanda baki yadda da shi ba ki sanar min, bana son ɓoyemin abubuwa da kike" "Shikenan insha Allah, amma baka gayamin meya haɗaku da shi ba" "Karki damu, idan na dawo zan baki labari, duk da ban taɓa gayawa wani ba, ni dai ki kulamin da kanki Farhan, kinji my wife". "Karka damu, Farhan taka ce kai kaɗai, as Sadik is for only me" Murmushi yai yace "hakane, naji daɗin wayar nan in kin rage min damuwa sosai, sekin dawo Allah ya kiyaye hanya" "Ameen ya Allah, have a nice day" Ta katse kiran. A hankali bacci yai awon gaba da shi, duk da ba wani jin daɗin baccin yake ba. Nazir ya kasa zaune ya kasa tsaye, tuna sakamako ya nuna Lilly na ɗauke da juna biyu, yanzu tsoron sa Allah tsoronsa Asirinsa ya tonu, ya san ya shiga uku idan Asirinsa ya tonu, dan kuwa ya kaɗe har ganyensa, gata 'yar gidan soja ga cin mutunci da zubewar mutunci da ze fuskanta. Ganin zaman tunani ba ze fishshe shi ba, yasa ya tashi yai wanka ya shirya, ya fita neman mafita. Abu kamar wasa, ko Abinci ya gagari Mother ci, saboda tunanin ɗan Autan ta, abun ya dameta ƙwarai amma Abba yaƙi bata fuskar da za tai masa ƙorafi. Duk da shima dannewa yake kawai, dan ya san Sadik ba ze taɓa jin daɗin zaman ƙauyen nan ba, amma ba ya son ya nuna dan kar Mother ta samu damar yin ƙorafi. Yauma Sunusi ya zo gurin Farhan taɗi, sedai ba ta sauya zani ba, taƙi kula shi balle ta tofa komai, shikaɗai yake ta zubarsa kamar an kunna tanki. Can ya nisa yace "Farhanatu, dan Allah wai meyasa idan nazo ba kya son sakin jiki dani ne? Da har gaisheni kina yi amma banda yanzu na rasa me nai miki" Haɗe rai tayi ta sake ɗauke kanta, daga barin kallon in da yake ma saboda baƙin ciki da take ji ba duk lokacin da ta kalleshi. "Ki kalleni mana ki min magana ko naji daɗi" "Aikuwa ka daɗe ba ka ji ba, ni dan Allah in baka da abun cewa ka bari in shiga gida bacci nake ji" "Haba Farhan yanzu maganar da nake miki bata da mahimmanci a gurinki? Ina son mu tattauna akan yadda zata kasance da bikinmu" Farhan ta ɗan murguɗa baki tace "Allah ya kiyaye" "Me kika ce?" "Ni bance komai ba, dan Allah kaga seda safe" "Saboda Sadik ne yasa kike min wulaƙanci?" Waiwayowa tai da sauri ta kalle shi, amma ta basar tace "waye kuma Hakan?" "Kin fi ni sanin waye hakan, sedai abunda nake son ki sani shine, ke tawa ce an riga an bani ke, ni iyayen ki suka sani dan haka ki fita sabgar wannan ɗan Yaron" "Kai ka san shi ni ban san shi ba" Sunusi yace "kin fi ni saninsa, tunda yake kawoki a mota, wato ni talaka ne shine kika ɗaura ɗambar wulaƙanta ni, to na dena lallaɓa ki in kin ƙi ji ba kya ƙi gani ba" Galala Farhan tabi Sunusi da kallo, ya akai ya san Sadik, kuma ya san shi ke kawota gida a mota. Guntun tsaki ta ja ta shige cikin gidan su, tana cigaba da tunani. Yauma Sadik cike da zullumin yadda ze bacci a wannan ƙungurmin ƙauyen ya kwanta, yana duba hotunan wayarsa, sosai ya dinga kuka lokacin da yaci karo da hoton Mother, yana missing ɗin babarsa sosai da sosai, ya rungume wayar yana kuka. Vibrating wayar tayi alamar saƙo ya shigo, ya ɗaga saƙon ya fara dubawa. "Am missing You hubby, i pray you come back soon, kar wani abu ya faru" Saƙon Farhan ne bana wani ba. Ya kira layinta, amma wayar taƙi tafiya, ya watsa wayoyin gefen katifa, ya fashe da kuka. Sir Nazir yana office ɗin sa, ya turawa Lilly saƙon yana son ganinta ta wayar salula. Kusan mintuna ashirin da tura mata saƙon se gata ta shigo Office ɗin. Yai sa'a lokacin corper George ya fita daga Office ɗin nasa. Ta samu guri ta zauna Sannan ta kalleshi cikin rauni tace "wace mafita ka samo mana?" Ya gyara zamansa sannan yai ƙasa da muryar sa yace "Mafita ɗaya ce Fatima, shine a zubar da cikin nan" Ta kalleshi tace "Amma ta yaya?" "Ga magani na taho miki da shi, ki fara jarraba magani mu gani ko ze fita" Lilly ta fashe da kuka tace "Innalillahi wa innalillahi raji'un, ancemin fa ana mutuwa garin zubar da ciki, ni tsoro nake ji kar Maman mu ta gane na shiga uku" "Ba zata gane ba ai, dan Allah ki kwantar da hankalinki, ki bi instructions ɗin da zan baki kiyi amfani da maganin" Lilly tace "wallahi tsoro nake ji" "Lilly idan ba ki yadda an zubar ba yaya zamuyi kenan? Ko so kike Asirin mu ya tonu?" Ta girgiza masa kai, yace "Yawwa dan Allah kiyi haƙuri, ki amfani da maganin ba abunda ze faru insha Allah, idan ba kya so a gane ki bari se da daddare kowa ya kwanta seki sha" Tace "to" Ya ɗakko wata ƙaramar kwalba wadda babu sticker bakomai a jikinta ya bata yace "ga shi nan, idan kin ci Abinci kin ƙoshi, seki shanye maganin duka, in Allah ya yadda cikin ze fita" Ta karɓa tare da zura kwalbar a aljihun rigarta. Ya share mata hawaye, yaita rarrashin ta harta ɗan kwantar da hankalinta Sannan ta koma aji. Kwanakin Sadik uku a ƙauye, ba komai yake iya ci ba, ta dole ya iya amfani da banɗakin su, saboda yadda wani Abincin ke ɓata masa ciki, har wata rama yayi saboda azabar damuwa, Nana kuwa yanzu yake bata sosai da sosai, ita kanta ta san an takura shi fiye da kima. Dama kusan kullum ana kawo kilishi ko tsire gidan Hakimi saboda Nana, ga tatattaciyar madarar shanu, ko fura da Nono da fulani ke kawowa duk dan saboda ita Hakimi yasa ake kawowa, saboda suna cikin abunda take matuƙar so. Sadik na zaune da safe, an dawo daga wannan tilawar da ake in an idar da sallar Asuba, ya duba wayarsa yaga saura kara ɗaya a ƙaramar wayarsa, babbar kam tuni ta ɗauke. Ba tsammani yaga kiran Mother ya shigo, cikin rawar jiki ya ɗaga kiran ya kara a kunnensa. "Auta na" shine abunda Mother ta faɗa cikin sanyin jiki. Ai take Sadik ya fashe da kuka yace "Mother, kin manta dani kun dena sona ko? Kin san ba zan iya zama ba amma ki ka bari Abba ya kawoni ya barni a nan, life is so hard for me here" "Sadik ba yadda zanyi da mahaifinka, fafur yace kar in kuskura in shiga maganar nan, nayi nayi da shi ya ɗakko min kai amma yaƙi, yanzu ya kake?" "Mother wallahi zan mutu in ba'a zo an ɗauke ni ba, na gaji wallahi, komai ba daɗi am missing You so much" "Am missing you too my love, dan Allah Sadik ka dena kuka zan cigaba da lallaɓa mahaifinka wallahi ko bacci bana iyawa" "Mother, am living for 3days without hearing from you, am missing home dan Allah Mother ki zo ki tafi da ni, wallahi bana son irin Abincin da suke bani, bana jin daɗin komai" Kawai Mother ta fashe da kuka, ji tai an zare Wayar daga hannunta, ta juya da sauri taga Abba ne a tsaye ya kara wayar a kunnensa yace "Sadik meyasa zaka ɗagawa mamanka hankali meye haka? Kukan me kake?" "Abba ka dena sona, ka barni a garin nan ni ba zan iya zama ba, am missing home dan Allah kazo ka tafi dani" Abba ya danne zuciyarsa a kausashe yace "Kai nutsu, da girmanka zaka dinga min kuka haka kamar wani ɗan yaye, me ka rasa ci ko sha? Ka nutsu ka kwantar da hankalinka ka zauna, idan lokacin da suka ga ya dace zasu dawo da kai, ka gaishe su" Abba ya katse kiran. Sadik ya ajiye wayar yana kuka yace "Abba Why" Nana na tsaye a bakin ƙofar ɗakin, an aiketa ta kirashi taji duk wauar da yayi, jikinta yai matuƙar yin sanyi da jin yadda Sadik ke kuka, a saɓule ta koma tsakar gida ta zauna tai shiru. Inna tace "yana ina?" Nana tace "bacci yake" "Wane irin bacci ba yanzu ya wuce ɗakin ba" Nana tace "to Inna yayi bacci fa" Inna ta ƙyaleta ta cigaba da aikin ta. Se can daf da la'asar sannan Sadik ya fito, idanunsa sunyi jajir sun kumbura, kana kallo ka san kuka yayi. Ya shiga banɗaki ya fito, ya kalli in da Nana ke kwance akan cinyar Inna, Innan na tsefe mata dogon gashin ta. Sadik yace "ke a ina ake cajin waya a garin nan"? Banza Nana tai masa ta cigaba da lumshe ido. "Ba kya ji na ne?" Yai maganar yana kallonta. Inna a ranta tace 'wannan ɗa ba dai tsarin ido ba' "Ni karka sake cemin ke, kuma in dai garin nan ne se sati sati ake kunna inji a gurin masu caji" Tsaki Sadik yai ya jiya ya nufi ɗakin da yake, Inna tace "ga alala can a ɗakina ka shiga ka ɗauka, na aika a taso ka tace min bacci kake" "Ni bana cin wannan abar" "Ka huta" Inna ta bashi amsa, sannan ta ɗora da "babu me sake takuraka kaci wani abu, in ka mutu da yunwa kai ka so" Be kuma bi ta kan Inna ba ya shige ɗakin. "Inna" Nana ta kira sunanta. "Na'am" "Inna dan girman Allah ku ƙyaleshi ya koma gida, wallahi har ya rame gashi baya cin abinci sosai, dan Allah ku bari ya koma gida" "Sannu me ɗan uwa, ai seki maida shi dan ubanki" "A'a ni ba ɗan uwana bane, amma Inna kuka fa ya ke yi ɗazu, wallahi ni tausayi yake bani, dan Allah ku barshi ya koma gidansu" Inna tai mata shiru, ta cigaba dai mata tsifa. Nana ba ta gaji ba ta kuma cewa "Inna nan fa Yayansa yace 'dan Allah ki ba dani su tafi dani kika hana, amma shi meyasa zaku riƙe shi?" Wani uban duka da Inna taiwa Nana a ka seda ta tashi ta zauna tana kallon Inna. "Sekije ki samu kakanki ki masa wannan tistiyen bani ba, mara kunya" Nana tai shiru tana sosa kai, ita dai ba taga aibun maganar ta ba. Ta faki idon Inna lokacin ta shiga banɗaki, ta ɗebo kilishi da Alkaki, cikin sanɗa ta shiga ɗakin da yake. Ta tarar da shi a kwance yayi rigingine, yana kallon rufin ɗakin. Ta jefa masa ledar kan katifarsa, ta juya ta bar gurin da sauri. Kamar yadda Sir Nazir yai mata bayani, da daddare bayan taci Abinci tai shirin kwanciya, ta ɗakko jakar makarantar ta, ta ɗakko kwalbar nan tai bismillah ta shanye ɗan ruwan dake cikin kwalbar, da ta shanye ta buɗe tagar ɗakin ta ta baya, ta jefa kwalbar waje. Ta dawo tais shiru tana jiran taji wani sauyi amma shiru. Tana nan tana saurare Nazir ya kirata hankali a tashe, tana ɗagawa yace "Fatima yaya, ya fita kuwa?" "Ni ba abunda naji" ta bashi amsa. "Kuma kin shanye duka?" "Eh na sha kamar yadda kace" "To shikenan, ze fita insha Allah, Allah ya tashe mu Lafiya yasa kar a samu wata matsala" Tace "Ameen" Wasa wasa har bacci ya kwashe Lilly ba taji komai ba. Cikin bacci taji wani irin azababben ciwo, tun daga kanta har yatsun ƙafarta, ga wani irin ciwo da mararta keyi kamar ana fizgo wani abu. A razane ta buɗe idonta, taja jikinta ta kunna fitilar ɗakin, gadon da take kai yayi kaca kaca da jini, wanda hakan ya tsorata matuƙa ta fasa ihu da ƙarfi! Littafin nan ₦300 ne kacal. 0009450228 Aisha Adam Jaiz Bank 07063065680 KO kuje manhajar AREWA BOOKS ku siya. domin kuwa ya fi sauƙi ta can. Littafin nan ₦300 ne kacal. 0009450228 Aisha Adam Jaiz Bank 07063065680 KO kuje manhajar AREWA BOOKS ku siya. domin kuwa ya fi sauƙi ta can. Zabura Nana tai ta miƙe daga kan kwanon gabanta, ta kalli Sadik a fusace tace "meye haka zaka shigo mana ɗaki ba sallama" tai maganar tana waiwayen in da zata ga hijjabi ta sa ta suturta jikin ta. Kan ta kai ga miƙa hannu ta ɗakko hijjabin, ya kai hannu ya danƙota, zazzare ido ta shiga yi ƙirjinta na dukan uku uku. "Ka sakarmin hannu meye haka? Idan Inna ta zo ta ganka fa, kalen ka jamin masifa?" Tai maganar ƙirjinta na bugawa da sauri, saboda rashin sabo kasamcewar sun samu kusanci Sosai a tsakanin su. Ba tare da yace mata uffan ba ya bata wasu irin lafiyayyun maruka guda biyu a kowane kunci. Wata irin gigitacciyar ƙara ta saki, Zani na neman kwancewa saboda Azabar zafi, da wayonta dai wani be taɓa marinta ba. Wani irin kuka ne ya ƙwace mata, tana wata irin sheshsheƙa tana neman ta shiɗe. "Kin ɗauka ƙarya nake da nake miki warning akan ki kiyayeni? Ni zaki kalla ki dinga zagi sa'anki ne ni? Ko dan kinga ina zaune a gidan ku shine zaki dinga gayamin abunda kika ga dama?" "Innalillahi wa innalillahi raji'un, me zan gani haka? Kai Sadik wane irin abu ne haka? Wannan wace irin fitsara ce a cikin ɗakina?" Hankaɗe Nana yayi, ta zauna a ƙasa daɓas, tare da dafe kuncinta da ke mata wani irin Azabar zafi, zanin nata ma ya gagare ta riƙewa, yana neman ya kwance gaba ɗaya. Inna ta kalli Sadik tace "me kai mata haka?" "Na sha gayamata ta kiyayeni, amma taƙi gani take ƙarya nake, shiyasa na dake ta" "Kuma shine dukan saboda tsabar rashin ta ido ka biyo ta har ɗakina daga ita se zani ka daketa saboda kain' dai fitsararrene ba ka da kunya, daga ita se zani fa, da zanin ya faɗi fa, ka ganga tsirara?" Sadik ya waigo ya kalli Inna yace "to meye a ciki? Wannan har mace ce? Aba kamar an daki gwangwanin madara, wannan ai bata wuce 'yar yaye ba, ƙwaila ce kuma ni ba abunda ya dameni kenan ba, zuwa nai dan in koya mata hankali" Baki Inna ta buɗe kamar wata shashasha ta bi Sadik da kallo, wato har ya san wata ƙwaila da wadda ba ƙwaila ba. "Allah ya sakamin, azzalumi mara imani, wallahi ban yafe maka ba, Allah yasa ai maka abunda ze baƙanta maka rai kamar yadda kai min" Ko a jikinsa, yana jin ta ya bar ɗakin,ko waigowa be ba, saboda atleast ya rage haushin da ke cunkushe a ransa. Nana kam sosai ta cigaba kuka, har fuskarta ta jawur saboda ta maru, ga shedar yatsunsa kwance akan kyakyawar fuskarta. Inna ta kalleta tace "ince ko dai be miki komai ba?" Cikin kuka tace "Inna fa marina yai har sau biyu" Inna tace "to ina ruwana da marinki yayi? Ban sha gayamiki ki kiyayi yaron nan ba? Sam ba shi da ta ido, da ya miki tsirara ai da ya gama cutarki" "Inna wallahi na tsane shi, dan Manzon Allah a maida shi gidansu kan ya kashe ni, ba wanda ya taɓa marina seshi wallahi Allah ya isa" "Ba zaki dena wannan surutan da kike ba, in kuma jin bakinki, ke ganinki ma da yai daga ke se ɗaurin ƙirji be dame ki ba" "Wallahi marin da yai min yafi zafi, ni Wallahi na zata ma zanin ya faɗi" Duk da yadda Inna take a ƙule, seda taji tausayin Nana, Saboda yadda fuskarta ta koma jawur kamar ɗanyen Nama. Riga Nana ta zura, ta fice daga ɗakin zuwa turakar Hakimi. Tana zuwa ta tarar da Sadik a turakar Hakimi a zaune, da alama Magana suke. Yana daga abunda Hakimi ba ya son gani, ganin damuwa a fuskar marainiyar jikar sa, saboda yana matuƙar tausayinta. "Ya akayi ne? Kukan me kike na zaki Makaranta bane?" Ya jero mata tambayoyin. Jikin Hakimi taje ta zube tana kuka. Sadik kuwa ya basar kamar ma be santa ba. Hakimi yace "Ke da kakar taki ne?" Nana ta girgiza kai alamar a'a. 'to meya faru?" "Dan Allah Alhaji ka maida Yaron nan gidansu" Wani shu'umin kallo Sadik yai mata, tare da maimaita kalmar yaro a hankali. Hakimi yace "wane yaron tukuna?" Ba Kunya ta nuna Sadik tace "gashi nan, wallahi na tsane shi, ko ganinsa ba na son yi" Take Hakimi ya haɗe rai yace "ɗan uwanki ne fa, meyasa kuke furtawa juna miyagun maganganu haka ne?" Cikin kuka Nana ta ɗago, ta nunawa Hakimi Fuskarta tace "kalli Fuskata, dukana fa yayi, da ni 'yar uwarsa ce ai baze dakeni haka ba kome nai masa" Hakimi yace "Ke me ki kai masa ya dake kin?" "Ko laifi nai masa seya dakeni haka?" Nana tai maganar wasu hawayen na zubowa daga idonta. Hakimi ya maida idonsa kan Sadik yace "me tai maka kai mata wannan dukan haka? Kalli shedar yatsunka a fuskar ta?" Kallo ɗaya Sadik yai mata, ya ɗauke kai yaƙi sake kallonta, kuma yaƙi Magana kamar gunki. "Magana fa nake maka" Sadik yai shiru ya sunkuyar da kai. Hakimi yai murmushi yace "Yanzu nan, ka zo ka sani a gaba, kana min magiyar in bari ka koma gida, amma na fuskanci haryanzu ba kai laushi ba da sauranka, tashi ka bani guri" Seda Sadik yai jimm kamar ba ze tashi ba, se kuma ya tashi yana kumbura baki ya bar ɗakin. Nana kuwa ta cigaba da kuka Hakimi na rarrashin ta, Inna ce da ta shigo ta koretaz tace maza taje ta saka Uniform ta tafi Makaranta a haka, gobe ta kiyayi shiga sabgar Sadik. Bayan fitar Nana Inna ta kalli Hakimi tace "Allah ya baka Nasara, nifa lamarin Yaron nan ya fara bani tsoro" Hakimi ya numfasa yace "ba ke kaɗai ba, ni kaina haka, amma hakan ya samo asali ne daga rashin kyakyawar tarbiyya da be samu ba a gidan su" "Tabbas ni zan faɗi wannan ma, kasan zuwa nai na tarar ya ritsata a ɗaki daga ita se ɗaurin ƙirji ya mareta, nai masa magana nace masa duk hukuncin da ze mata kamata yai ya bari se tana cikin sutura, a haka zata iyayin tsirara, Yaron nan ba kunya ba tsoron Allah yace min wai ai wannan ba mace nace ƙwaila ce, Yaron nan fa idan ba ai dagaske ba se abunda Allah yai, wai harya san ƙwaila ya san mace, ko da yake ba abun mamaki bane, tunda a kunne na naji yana gayawa uwarsa wai Aure yake so" Hakimi yai murmushi yace "Manya gatan wasa, to be isa Auren bane?" Inna tace "ya isa mana, da a zamanin mu ne ai tuni an masa mata, kuma jiya da Asubar fari ya shiga ya hau wanka, kaga kuwa ya tabatta ya isa Aure" "Amma shine mahaifinsa yake son turashi ƙasar waje karatu? Shi duk baya ganin abubuwan mu da muka gani?" Inna tace "wayasan masa? Yasa Aƙidar boko da yahudawa a zuciyar sa, gashi Allah ya haɗashi da matar da ita ma ba ta san abunda ya dace ba" "Lallai kam, shikenan zanyi abunda ya dace a kai, na san abunyi, ai da zuwa yai ya sani a gaba yana so in bari ya koma gidansu, da har zan amince wannan yarinyar ta zo tana kuka, tunda abun masa hakane nasan maganinsa" Inna tace "meye maganin nasa?" "Ki zuba ido zaki gani". Abu kamar wasa Lilly suka koma yadda suke ita da Sir Nazir, sedai haryanzu sheɗan na cigaba da hura musu wuta, tun da suka aikata son zuciya sheɗan ke ta sake ruru musu wutar fitina a tsakanin su. Gashi Nazir ya tuba, yace baze sake aikata makamancin abunda yai ba dama be taɓa ba se a kanta, kuma baya sha'awar sake aikata abunda yai ɗin. Sedai a duk lokacin da suke tare, se yai ta maza yake iya daure kansa, dan wasu lokutan idan a wayane ma ya dinga sakin layi kenan. Yanzu ma ta gama zana jarabawar da zata zana, kasancewar makarantar ba kowa ya basu damar sakewa sosai da juna. "Fatima" ya kira sunan ta. "Na'am" ta amsa tana kallonsa. "Babanki ze bani Aurenki kuwa?" "Wallahi sir ban sani ba, amma meyasa ka tambaya?" "Bana son mu sake aikata ɓarna ne, wallahi ina sonki da gaske, idan zaki iya Auren talaka kamata" "Nima ina sonka sosai sir, sedai ban sani ba ko Daddy ze yadda ba, kuma ai kaga baze yuwu yai min Aure yanzu ba, a Jss3 fa nake" Ya lumshe idonsa yana fesar da iska daga bakinsa yace "in my opinion, ina ga zan bar aikin nan in koma Jigawa kawai, ai dama na gama service ɗin naji daɗin zaman garin nan ne" Ɗan zare ido tai tace "meyasa zaka koma?" "Saboda in dena ganinki ko na samu nutsuwa, a baya ni babu wata mace da nake shiga wani yanayi saboda ita, amma idan har zan ganki da ƙyar nake samun saita kaina" "To seka tafi ka barni?" Tai maganar a shagwaɓe. "To ya zanyi Lilly, haka shine samun nutsuwa ta" "But i love You, Please kar ka koma dan Allah" tai maganar kamar za tai masa kuka. A hankali ya janyo ta jikinsa, ya ɗora hannunta a saitin ƙirjinsa, tana jin yadda zuciyarsa ke bugawa da sauri sauri, yace "kinji fa halin da nake shiga a duk lokacin da muke tare ko na ganki, ƙaddara ta kawoki cikin rayuwata, idan ban same ki ba, i better go back to my village" Gyara kwanciyarta tai a jikin Nazir tace "no ba za ai haka ba, zan san abunyi nima gaba ɗaya karatun nan ya fita daga raina, dama ba wani ja nake ba, gara aimin Auren in huta" "Karatun yana da kyau, amma idan munyi Aure zan bari ki cigaba, but Please help me" Ta ɗago tana wasa da sajensa tace "don't worry Baby" a nan ma dai Allah ne ya rufa Asiri basu watse ba ni dai nai gaba. Faruk na kwance a falo daga shi se boxers, yana kallon TV, yana missing ɗin Sadik sosai, se yaita kallon ɗakin Sadik ɗin yaga kamar ze ga Sadik ɗin ya fito daga ɗakin. Knocking ɗin ƙofar yaji yana ayi, ya miƙe ya nufi ƙofar dan ya buɗe, yana mamakin waye da tsakar ranar nan haka. Yana buɗewa ya ga Khairat a tsaye da tray a hannunta, seda gabanta ya faɗi ganin Faruk, jikinta ya ɗau rawa kamar mazari, ta shiga bin sa da ido, yadda gashi ya kwanta a jikinsa. Yatsunsa biyu ya haɗa ya murza suka bada sauti, a saitin fuskarta Yace "ya dai? Ya akayi ne?" Da ƙyar ta haɗiye yawu jikinta na rawa ta miƙa masa trayn da ke hannunta. "Meye wannan?" "Amm..dama nayi juice ne na cucumber na san kana so shine na kawo maka" Yace "Wow, aikuwa kin kyauta, shiga ki ajiye" Ta shiga cikin falon ta ajiye, tana cigaba da kallonsa, ba ta taɓa sanin kyan Faruk ya kai haka ba, gashi da ƙira me kyau, ga wani six packs a cikinsa. Bedroom ya shiga ya sako jallabiya fara ya dawo falon ya zauna. Se taji dama be saka ba ta cigaba da kallonsa a haka. Yace "yau me kuka dafa ne a gidan?" "Ai ba a gama girkin ba" ta bashi amsa. "Ai ba cewa nai ko an gama ko ba a gama ba, cewa nai me kuka dafa, ko ince me kuke dafawa?" "Ina ga shinkafa da miyar zogale" Yace "what? Shinkafa da miyar zogale kuma?" Tai saurin dawowa hayyacinta tace "shinkafa da miya ne" "It seems something is wrong with you, tashi ki tafi" Ɗan noƙe kafaɗa tayi, alamar ba zata tafi ba. Yace "ai shikenan seki ta zama" Ya maida idonsa ga tv, yana cigaba da shan juice ɗin. Wayarsa ce ta fara ringing, ya duba ya ɗauka tare da yin sallama. "Wa'alaikum salam Malam Faruku" Cikin sauri Faruk ya gyara zama yace "ranka ya daɗe barka da warhaka" "Yawwa barka, kuna lafiya?" "Lafiya ƙalau Alhamdilillah" "Ka manta da mu, tunda kuka tafi ba ka sake zuwa ba" "Ranka ya daɗe ai kai kace karmu sake zuwa, kuma wayarku ba ta shiga, saboda ba network" "Ƙwarai kuwa anyi haka" Faruk yace "Ya Sadik ɗin yake?" Hakimi yai murmushi yace "yana lafiya ƙalau, muma sa'a akai wayar ta shiga, tun jiya ake neman layin mahaifinka yaƙi, kaima da kyar naka yayi, amma duk matsalar network ɗin nan ne, muna muna ƙoƙarin ganin yadda za'a shawo kan matsalar" Faruk yace "Allah sarki, Allah ya temaka ranka ya daɗe" "Ameen ya Allah, nace baban naka yana gari ne?" "A'a ranka ya daɗe, kwanansa biyar da tafiya kuma ina ga se ƙarshen watan nan ze dawo" "To shikenan, idan kunyi waya ka gaya masa, lallai lallai idan ya shigo gari ya zo ya sameni a nan" "Insha Allah zan gaya masa ranka ya daɗe"  Faruk ya so tambayar Hakimi a bashi Sadik su gaisa, amma se yaji nauyin hakan, tunda shi Hakimin be bashi ba, kawai ya ƙyale sukai sallama, ya bawa Hakimi saƙon gaisuwa ga Nana da su Inna. Harya gama wayar Khairat kallonsa take. Faruk kam haka nan ya tsargu da kallon da take masa yace "can You excuse me please?" Seda ta ɗan tura baki sannan ta tashi, ta koma cikin gidan, a falo ta samu Mother tana Shan kankana, Mother ta dubeta tace "ya na ganki kina tafiya a hankali menene?" "Bakomai Mother, yanzu Faruk su kai waya da kakansu" Da sauri Mother ta ajiye kankanra da ta ɗauka take shirin kaiwa bakinta tace "meya ce masa?" "Na dai ji yace wai yana neman Abba ne, idan Abba ya zo ace yana nemansa" "Ko dai wani abun ne ya samu Sadik ɗin?" Khairat tace "Anya kuwa? Ni dai banji yace wani abu ya sameshi ba, dan da wani abun ya sameshi baze ce se lokacin da Abba ya dawo Sannan zeje ba" Mother ta girgiza kai tace "Allah sarki yarona" "To Mother tunda Abban baya gari, ki shirya mana kije garin da kanki, ki ɗakko shi" Mother ta girgiza kai tace "da ze yuwu ai da tuni nayi, zan fuskanci fishi da tashin hankali a gurin babansa idan naje, amma zan zuba musu ido in ga iya gudun ruwansu, fiye da watanni biyu an riƙemin ɗa an hanani ganinsa" Ta ƙarasa maganar tana jin ƙwallar baƙin ciki. Abban Farhan yana shirin fita aka shigo a kai sallama da shi, yace yana zuwa. Yana fita yaga malamin su Sunusi ne, ya tsaya suka gaisa Sannan malamin Yace "to kamar yadda mukai magana da kai, naje garinsu Sunusi na samu mahaifinsa nai masa Magana, yayi murna ƙwarai yayi farinciki da jin hakan, yace a basu lamuni nan da wata guda zasu kawo kuɗin Auren" Abba yace "Ahha Masha Allah, naji daɗi ƙwarai da gaske, nayi farinciki, ai nan da wata ɗayan kamar yaune a gurin Allah, Allah ya nuna mana ya sa zamu gani" Ya amsa da "Ameen" Abba ya nisa yace "Amma ina son idan anyi Auren nan, Farhan ta cigaba da karatun ta, saboda shine babban burinta a rayuwa, duk da shima Sunusin zan masa maganar" "Eh ai karatu abune ne mahimmanci, mussaman tunda da abunta aka ganta, wannan ma abune me kyau, zan yiwa Sunusin Magana Insha Allah, fatanmu Allah ya tabbatar mana da Alkhairi". Abba ya amsa da Ameen. Kusan sati biyu, Sadik be sake shiga harkar Nana ba, duk yadda take takalarsa wasu lokutan ko in da take baya kallo, ga wayoyinsa da ya bata ta kai masa caji, ko sau ɗaya be yi mata maganar wayoyin ba, shi mantawa ma yake da waya, kawai dai gashi nan yana rayuwa, se ya dinga jin kansa kamar ba shi ba. Farhan Kuwa sun koma zangon karatu na biyu, sedai jin makarantar take tamkar maƙabarta, gaba ɗaya ba ta da kuzari, ba abokin hira dama ita ba ƙawaye ne da ita ba, gashi ko a waya ta kasa samun Sadik fiye da wata guda, ga matsaloli sun taru sun mata yawa, hakan harya fara shafar karatunta, ya zamana ko excusing ɗin kanta tayi ta tafi Library karatu, ba ta iyawa, se tai ta kallon gurbin da Sadik yake zama yana tayata karatu. Tana matuƙar kewarsa, se taji gaba ɗaya ta dena gane karatun, bata iya maida hankali yanzu sam. Ga 'yan ajinsu lalacewa taci uban ta da, yanzu bayan karance karancen litattafan da suke, har memory suke bayarwa a turo musu abunda be dace ba, banda masu shaye shaye da sauran lalacewa, makarantar se ƙara lalacewa take. Dama Sir Nazir ne me tsawatarwar, shima kuma Yanzu ya faɗa tarkon RUƊIN ƘURUCIYA, dan haka kowa yake cin karensa babu babbaka. Bayan ta koma gida, ko Abinci ta kasa ci, duk ta rame tayi wani iri, tana kwance a ɗakin ta da Yamma, Taji Abba yana ƙwala mata kira. Cikin hanzari ta fito tsakar gidan, ta durƙusa a gabansa. "Yawwa, ɗazu malamin su Sunusi ya zo munyi Magana da shi, yace min in Allah ya yadda watan gobe za su kawo kuɗin Aure, dan tun kwanaki mu kai Magana zasu kawo kuɗin, amma yau ya tabattar min da watan gobe zasu kawo" Gaban Farhan ya yanke ya faɗi, taji ta dena ganewa na wasu lokuta, ko motsi ta kasa yi a gurin. Abba yace "ya naga duk kin canza, ko ba kya son Auren ne?" Za tayi magana ta ɗago ta kalli Abba, se taga yai mata kwarjinin da ba zata iya buɗe baki tace masa ai ba ta son Sunusi ba. Sedai cikin rauni da sanyin halinta tace "Abba karatuna fa?" Abba yace "karki damu da wannan Farhan, nayi magana da malamin su akan ze barki ki cigaba da karatunki, nayi niyyar Aurar da ke ne saboda wani dalili, amma zaki cigaba da karatun ki insha Allah, tashi kije yadda kike mana biyayya Allah ya baki 'ya'ya masu biyayya kema, Allah ya albarkaci rayuwar ki ya tsare ki daga sharrin lalacewar ƙarshen zamani, Allah yai miki Albarka" Farhan ta kasa amsawa, sedai ta miƙe akan ƙafafuwanta da take ji kamar an ɗaura musu duwatsu, ta koma ɗakinta. Zuciyarta ta dinga zafi, hawayen ta suka ƙafe ta kasa kukan se ajiyar zuciya da take tayi. "Sadik dan Allah ka dawo kar amin Auren nan, na kasa gayawa Abba bana son Auren, Kai nake so Sadik, duk wanda na Aura ba zan iya dena sonka ba" Tai maganar tana jin yadda zuciyar ta ke ƙuna, ga kuka ya gagareta. Wunin ranar Farhan ba tayi shi cikin kwanciyar hankali ba, haka da dare yayi shima bacci ya gagareta, dama kwana biyun nan dama baccin ma ba samuwa yake ta daɗin rai ba, balle ga wannan batun mafi dunguzuma mata zuciya, ko kusa ba ta ga yadda za ta iya zaman Aure da Sunusi ba, dan zuciyarta na tare da Sadik. Washegari da safe haka taje makaranta, babu kuzari sam a jikinta, dan har a kai lesson aka gama ba ta fuskanci komai ba, sedai lokaci lokaci ta kanji hawaye na ƙoƙarin zubowa daga idanunta, amma se ta neme su ta rasa sedai zuciyarta ta cigaba da zafi. Sam hankalin Farhan ba ya jikinta se da ta jiyo Muryar Yasmeen ta ambaci sunan Prince. Take hankalin Farhan ya dawo jikinta, ta tattara hankalinta akan Su Yasmin dan jin me zasu ce akan masoyin nata. Yasmeen tace "Ashe su Prince ana ƙauye, ni Wallahi ban taɓa tunanin gayen nan ze zauna a ƙauye ba" Mamakine ya kama Farhan, ya a kai Yasmeen ta san Sadik yana ƙauye? Amma ba abun mamaki bani, wataƙila a bakin abokan Sadik na ajinsu taji" wata zuciyar ta bata amsa. Yasmeen ta cigaba da cewa "gaskiya gidan su Sadik akwai zafafa Allah yai musu kyau masha Allah, kunga wani yayansa me kyau" Lilly tace "wai ke me ya kaiki gidansu ne?" Yasmeen tace "ina ruwanki da abunda ya kaini, ni da gidan sirikai na" Se da Farhan ta ɗago ta kalli in da Yasmeen take, aikuwa Yasmeen ta galla mata harara. Lilly tace "ba uwar da ta haɗaki da su Sadik wai gidan sirikanki" "Ahaaf kika sani" Yasmeen ta faɗa tana murmushi. Farahan taji jikinta har wani rawa yake, tana Addu'ar Allah yasa ba wani abun ne ya haɗa Yasmeen da Sadik ba. Seda wayar Sadik tai sati uku ba ta tare da shi, gaba ɗaya ya rasa meke damunsa, ya rasa tunanin ma meya kamata ya yi. Gaba ɗaya kamar deprssion ke nama ya kama shi. Ji yai an ajiye masa abu a jikinsa, ya ɗaga kai ya kalli Nana, ba ta ce masa komai ba tai waje. Ya ɗaga ya duba me ta ajiye masa, yaga wayoyinsa ne. Kawai ya bi wayoyin nasa da ido, gaba ɗaya wayoyin ma sun fita daga kansa. Ture wayoyin yai ya kwanta, yana ta ƙoƙarin yai tunani amma ya kasa. Kusan kwanaki uku da kawo masa wayoyin, sannan ya kunna ƙaramar wayarsa. Lambar Mother ya shiga dubawa, ya kira yaji ko wayar zata shiga, by luck yaji ta fara ringing, da Sauri ya tashi zaune yana gyara zama. "Hello Autana" Ajiyar zuciya yai Sannan yace "Mother kin manta da ni ko?" "Haba Sadik kai kana tunanin akwai lokacin da ze zo in manta da kai? Kullum kana raina, wayarka ba t shiga nayi kuka harna gaji, babanku ya hanani ko zuwa in ganka ba yadda na iya" "Shikenan Mother a nan zan cigaba da zama kenan?" "A'a ya ma za'a ce a nan zaka cigaba da zama, ai anyi wa Faruk waya ance ana neman babanku a nan gidan" Sadik ya ɗan taɓe baki yace "ni ban ma sani ba, Allah yasa idan ya zo ya tafi dani, Mother na gaji am tired wallahi" "Na sani Autana, amma dan Allah kayi haƙuri ka kwantar da hankalinka, kar kaje kayi wani abun da zasu hanaka tafiya, Abbanka yana nan yana nema maka admission a London, insha Allah da ya samu zaka tafi, naji ance an saki Waec ma, amma ban tabattar ba" "Amma ai Swiden Abba yace min ze kaini" "Ai Sweden ɗin ne, su se nan da kusan wata huɗu za su fara bada admission, su kuwa nan very soon, abunda ya sa nafi bada ƙarfin ka tafi London ɗin dan kayi ka baro ƙauyen nan" Sadik yace "shieknan, ina bro ko nemana ba ya yi, tunda suka tafi suka barni a nan, dama dr. Wannan da ina nan da ba na nan duk ɗaya a gurinsa" Mother tace "Wallahi Faruk yana Maganar ka, da zuwa ya so yi ma, amma yana tsoron abunda mahaifinku ze ce dan kwanan duk ya canza kamar ba shi ba" "Shikenan Mother" Jiki a sanyaye Mother tace "kayi haƙuri kaji Autana, ka kusa baro garin nan Insha Allah, Abban ma a satin nan ze dawo insha Allah" "To Mother Allah ya sa" "Ameen ya Allah" Su kai sallama. Messages sun kai goma a wayar, amma ya kasa buɗe ko ɗaya, ya Ajiye wayar ya murgina ya juya, ya lumshe idonsa. Yana jin yadda zuciyarsa ke masa wani irin bugu da sauri da sauri, ya rasa dalilin jin fargabar nan da yake yi. Da sauri Kamar an mintsine shi, ya tashi zaune, ya kuma ɗakko wayarsa ya shiga dubawa. Messages ɗin Farhan ne a wayarsa , se yanzu ya tuna da Farhan, a gigice ya shiga duba messages ɗin. "Am missing You so much, please ina kana lafiya ko message kai min" "Akwai matsala Please pick my call, or check my messages" Wayar Farhan ya shiga kira, amma a kashe, take wani irin gumi ya ding tsatsafowa a goshinsa, yayi mamakin yadda ya kwashi tsawon lokaci ba tare da ƙoƙarin sanin halin da Farhan ke ciki ba. Take Ya shiga tunanin meke damunsa haka? Har yake ƙoƙarin mantawa da abunda ruhinsa ke bege ba dare ba rana. Ya kira wayarta, ya kira ya kira amma ba ta shiga sam. Gaba ɗaya hankalinsa ya ƙi kwanciya, har kusan kwana biyu yana faman neman layinta amma ya ƙi shiga. Hankalin Sadik fa yaƙi kwanciya, kasancewar rashin samun Farhan a waya, abun duniya ya dame shi, ya cigaba da mamakin yadda a kai, tsawon lokacin nan be damu da sanin halin da take ciki ba. A rana ta uku ne, yaji wayar ta shiga, sedai taƙi ɗagawa sam. Sadik ya kirata ya kai sau ashirin, Sannan ta ɗaga sedai tana ɗagawa kukanta ya fara ji. "Farhan" ya kira sunanta a hankali. Bata amsa ba ta cigaba da kuka. "Ban san da wace kalmar zan fara miki Magana ba, Farhan ban san meya sameni ba" "Sadik har ka manta dani ko, Sadik kuɗin Aurena za'a kawo next month, Ina cikin matsala" "What the fucking shit are you talking about, ban gane kuɗin Aure ba" "Zan maka ƙarya ne? Wallahi Abba ze karɓi kuɗin Aurena, Sadik na shiga uku zuciyata kamar ta tsaga ƙirjina ta fito, wallahi bana son shi kai nake so" Wata irin nannauyar ajiyar zuciya Sadik ya sauke, yace "ba wanda ze aurar da ke ga wani, ke tawa ce, wallahi ko an Aura miki wani, sena biki har Gidan na ɗauke ki, kuma wallahi duk wanda yai gangancin Aurenki sena illata shi, sena masa tabo me muni, koma in sa a ɓatarmin da shi, ke tawa ce Farhan" ya ƙarasa maganar cikin ƙaraji. Kasa cewa komai Farhan tai se sheshsheƙar kuka da take, a hankali ta furta "Ina sonka Sadik, dan Allah kar barni, kar ka juyamin baya, ka riƙe alƙawari dan Allah, ina sonka sosai Sadik". Duk wuya duk rintsi Farhan, ke tawace kuma Wallahi duk wanda yai gangancin taɓa abunda yake nawa se na masa illa, ko waye shi. Yana cikin maganar be sake sanin in da kansa yake ba, seda Asuba tayi, ya buɗe ido cikin hanzari. Sedai yai yai ya tuna abunda ya faru, amma abu ya gagara, tabbas yasan bacci ko makamancin haka ya ɗauke shi, yana tsaka da wani abu me mahimmanci, Amma ya kasa tuna ko menene, ga abun yana ji a ramsa amma ya kasa tuna komai! Littafin nan ₦300 ne kacal. 0009450228 Aisha Adam Jaiz Bank 07063065680 KO kuje manhajar AREWA BOOKS ku siya. domin kuwa ya fi sauƙi ta can. Littafin nan ₦300 ne kacal. 0009450228 Aisha Adam Jaiz Bank 07063065680 KO kuje manhajar AREWA BOOKS ku siya. domin kuwa ya fi sauƙi ta can. Ɓangaren Farhan suna tsaka da waya, tana masa magana, kawai taji yayi shiru, ta kira sunansa amma taji kamar ya amsa cikin magagin bacci, zuwa can taji yayi shiru. Abun ya bata mamaki ba ta taɓa sanin Sadik da magagin bacci ba, ko ƙarfe nawa za su kai na dare suna waya ba ya jin Komai, wataran ita ce me cewa ma ita bacci take ji. Take taji jikinta yai sanyi ƙalau, ba ta da wani kuzari, se yanzu ta samu damar yin hawaye, amma da zuciyarta ta bushe. "Ohh Allah meke shirin faruwa ne haka?" Tai maganar tana sheshsheƙar kuka. Bacci kuwa dama wannan gagararta yai, ta kasa shi gaba ɗaya, se tarin saƙe saƙe da tunani. Da garin Allah ya waye, gaba ɗaya Sadik ya manta sunyi wata waya da Farhan, dan shi ya manta da ita ma gaba ɗaya. Ƙarfe kusan goma na safiya, ya fito daga ɗakin sa, a gefen ɗakin Inna ya hangi Nana tana watsawa tattabaru Gero, tana sanye cikin hijjabi, tunda ya zo Gidan nan, kullum cikin hijjabi yake ganinta, se Ranar da ya mareta ya ganta da ɗaurin ƙirji, amma duk zafin duniya Nana tana sanye da Hijjabi, ba ta taɓa rabuwa da shi, abun har mamaki yake ba shi. A hankali ya furta "Stupid girl" dan in za'a lissafo abunda ya tsana, to da Nana a ciki, duk da tarin Alkhairan da tai masa a zamansa a gidan, amma ba ya duba wannan se tsagwaron rashin mutuncinta da tsiwa da yake gani. Zancen zucin da yake ne, ya sa ƙureta da ido, ba tare da yasan yayi hakan ba, seda yaji saukar ruwa a fuskarsa sannan ya farga ya kalli Inda Inna take shirin yin alwalar sallar walha, ita ta watso masa ruwan. A hankali ya janye idanunsa daga kan Nanan, tare da goge ruwan da Innan ta watsa masa. A ransa yace 'yanzu fa wannan tsohuwar se ta zata wata tsiyar nake kallo a jikin wannan komaɗaɗɗiyar yarinyar, aba kamar taliya, dan ita ba wahala ta yiwa abu fassara, ko abunda kake nufi kenan ko ba shi kake nufi ba" Wayarsa dake cikin aljihunsa ce ta fara ringing, ya zura hannu ya ɗakko wayar, tare da nufar soro dan amsa Wayar. Muryar Amin yaji yace "Mazaaa, Allah ya temaki yarima namu" Murmushi Sadik yai yace "gayu dama kuna nan? Ba waya ba saƙo?" "Kai zamu tambaya ai, you just disappeared, mun zaci karatun ka tafi, har gidanku muka je amma akace baka nan wai kayi tafiya, ko a waya ba a samunka gaba ɗaya ko ta social media ba a ganinka" Sadik yace "ya ma za'ayi in tafi karatu baku sani ba, kuma ma ai Jarrabawar ta mu ba ta fito ba" "Ahh ta fito almost two weeks ago fa" "Haba dai, bani da labari ne sam, ya school ɗin?" "School Lafiya ƙalau, wai dan Allah ina ka tafi ne haka?" "Wallahi ina wani useless village ne" "Village as how? Babban yaro me kake a ƙauye kuma for whole this long?" "Kai bari kawai, daga zuwa garin nan dubiya Granny ya hanani tafiya, gaba ɗaya a takure nake, na rasa abunda yake min daɗi, sam bana jin daɗin garin nan, ji nake kamar ma bani da lafiya, kamar me jinya haka nake jina" "Amma kai kana me ka bari aka barka a ƙauye kamar ba Prince ba, sekace wani ɗan yaye kaine ma ka yadda" "Haba Amin, ka san da hankalina ba zan bari in zaunaa ƙauye ba, anfi ƙarfina ne kawai ba yadda zanyi, amma very soon insha Allah zan dawo, na kusa tafiya karatu" "Wow, ai gara ka dawo ɗin, haba a ɗanyi chilling before you leave the country, kai kaga wasu zafafan babies da aka kawo makarantar nan, kai Makaranta fa ana ta yi ba kai" Sadik yace "ai koma ina nan bani ɗin za'ai, tunda barin ƙasar zanyi" "Duk da haka school ɗin babu daɗi ba ka nan wallahi" "Please my regards to all, insha Allah kan in tafi zan shigo school ɗin" "To shikenan, ba ka tambayi ya beb ɗin ta ka ba?" Sadik be tsaya sauraron me Amin ɗin ke faɗa ba, ya katse kiran wayar. Tare da sakin ajiyar zuciya a jejjere. Farhan dai gaba ɗaya ta rasa nustuwar ta, a makaranta ma kiran Sadik ta dinga yi a waya, amma idan ya duba se ya manta lambar waye, kawai se yai ignoring ɗin kiran, ya cigaba da sabgogin gabansa. A gida Sadik ya saba masu aiki ne ke gyara musu ɗaki, wasu lokutan dan sangarta ko Abinci suka ci a gurin suke barin kwano, sedai a zo a kwashe, a gyara gurin amma yanzu shi yake fitar da kwanon da yaci Abinci da gyaran ɗaki. Gashi wataran yana tsaka da hutawa, za'a taso shi a haɗashi da dogarai suyi sharar burgarr dawaki, tun yana toshe hanci kamar ze amai saboda warin kashin dawaki har ya saba. Yanzu ma Har ya koma ɗakin da yake, ya kalli ɗakin kusan kwana uku be share ɗakin ba, duk da ɗakin ba wani datti yai ba amma se yaji duk ƙyamar ɗakin yake. Ya ɗakko kwanukan da yaci tun Abincin safe, da na rana ya fito da su, Nana na zaune tana wanke Wanke, yazo ya zube mata, dan kusan ta ma gama wanke wanken sannan ya kawo. Sheƙeƙe ta kalleshi tace "wannan wane irin wulaƙanci ne haka? Dan me ba zaka fito da kwanukan tun da Girma da Arziki ba, se sun gama bushewa, kuma kana kallon na gama Wanke wanken sannan zaka kawo min" Maimakon ya bata amsa yace "in kin gama, ki sharen ɗakina" "Kut uban kuturu ma yayi kaɗan wallahi, kai ka isa? Ni zaka kalli idona kace in share maka ɗaki saboda tsaurin ido to wall... Bata ƙarasa ba taga Sadik yai ball da robar wanke wanken gaban ta, kwanukan sun watse. Saroro tai tana binsa da kallo tare da mamakin jarabar Sadik. Da yatsansa ya nuna ta yace "idan kika kuskura kika min rashin kunya, yadda nai da kwanukan nan haka zan miki" Aikuwa ta miƙe zata fara zazzaga masa bala'i itama, taji gyaran muryar Hakimi, hakan ya tilasata mata haɗiye maganganun da suke cinta, take so tai amansu. Hakimi yace"In kin gama wanke wanken, ki share masa ɗakin ai yayanki ne gaba yake da ke, kuma ya isa dake" Seda Nana ta buɗe baki dan mamaki, ita ce ma zata sharewa wannan fitinannan ɗaki, shiru tai ta fara tattara kayan wanke wanken, tana jin yadda ranta ke mata ƙuna, tare da ƙudurce ramuwar gayya. Se da ta gama wanke wanken, Sannan ta tafi yin sharar, ta tarar da shi ya barbaje ƙafafuwansa a tsakar ɗakin, ya Ajiye pillow a ƙasa ya kashingiɗa. Ba ta ko kula shi ba, ta hau shararta facar facar, facar tana watsa masa datti a jiki. "Ke Mahaukaciya! Ba kya gani nee?" Ba ta ko saurare shi ba, ta cigaba da abunda take, tana watsa masa shara a jiki Sam Sadik baya son ƙura, dan haka ba shiri ya fita ya bata Guri ta cigaba da sharar tana ƙunƙuni. Ya zamana kusan kullum se sunyi faɗa, da abun nasa ya lafa amma yanzu kamar kaji, ko wasu abokan gaba haka suke yi. Da ne Inna take shiga ta tsawatar musu, amma yanzu kam ta ƙyale su. In zasu kashe kansu ko a jikinta, suyi tayi, sedai in ta gaji ta ƙarewa Nana zagi. Lilly ta rasa ta in da zata ɓullowa lamarin da ke tsakanin ta da Nazir, Sosai take sake jinsa a ranta, kuma ba iya Soyayyarsa ce ke damunta ba, har da muradin sake kasancewa da shi. Abu kamar wasa ko Abinci da baccin kirki suka gagari Lilly, kamar yadda take karantawa a Novels, haka ta auri shan Lipton da lemon tsami, dan samawa kanta rangwame. Abun ya fara damunta psychologically, gaba ɗaya ta koma wata irin shiru shiru, kusan kullum ta na ɗaki, se in waya take da Nazir, shine take rage damuwa, shima kasamcewar ita kaɗaice a ɗakinta, wasu lokutan wayar tasu ta kan zarce ƙa'idar Addini, su shiga wani fage daban. Kusan kullum se ya tambayeta, ya ake ciki tai maganar Aurensu kuwa a gidan su, amma tace a'a ita tsoro take ji. Yau da ita da Mamanta da Daddynta kasancewar yana gida hutu, suna Dinner da daddare, amma sam ya lura da yadda ba ta iya cin Abinci, se juya cokali da take, tai shiru tana zancen zuci. "Hey what are you thinking of?" Maganar mahaifinta ce ta dawo da ita daga tunanin da take, firgigit ta kalleshi tace "Nothing" Yace "No, akwai wani abu, ba kiga yadda ta rame ba? Gaba ɗaya kamar bata walwala" yai maganar yana kallon maman Lilly. Tace "Na gani wallahi, i even ask her tace min bakomai, shiyasa na ƙyaleta kawai. Yace "ko dai haryanzu jikin ne?" Ta girgiza kai alamar a'a. Yace "to meke damunki, Gayamin kinji Babyn Daddy" Ji tai kamar ta gaya masa, amma yai mata wani irin kwarjini da ta kasa ko ɗaga ido ta kalleshi, tace "bakomai fa Daddy" Yace "oya, maza ɗauki Abinci ki ci, ko in baki da kaina ne?" Ta girgiza kai tace "zan ci da kaina Daddy" Yace "oya maza ɗau spoon ki ci ina kallon ki" Haka nam ta ɗau cokali tana cin Abincin, ba dan tana jin daɗin sa ba. Farhan tunda su kai wayar nan ta ƙarshe da Sadik, ba su sake waya ba, ta kira wayarsa in ta shiga ma baya ɗagawa, jikinta gaba ɗaya yayi sanyi da lamarin, ga lokacin da za a kawo kuɗin Auren ta da Sunusi se ƙaratowa yake yi. Ta rame tayi duhu, amma hakan be sa Ummanta saurararta ba balle taji abunda yake damunta ba. Duk da lokuta da dama ko Abinci aka bar mata a Kitchen haka za'aje a tarar da shi ba ta ci ba, in kuma ita ta girka haka zata raba ga bawa kowa, amma ita ba zata ci ba, dan ɗaci Abincin yake mata a baki, mussaman idan yaje maƙogwaronta. Wata irin matsananciyar soyayyar sa ce take cigaba da nuƙurƙusa zuciyarta, mussaman lokuta masu hatsari da suka faru a rayuwar soyayyar su, her first kiss with Sadik, his romantic actions towards her, how supportive and protective he is, wata karaya ce ta sake baibaye Farhan, da tunanin idan ta rasa Sadik waye ze maye mata gurbinsa, Sadik ya koyar da ita abubuwa masu ruɗani, da tsayawa a zuciya, ba ta tunanin za ta so wani kamarsa. Sadik ya cire layikan wayoyinsa gaba ɗaya, ya ƙulle su ya saka a ƙarƙashin kilisan ɗakin, dan sam baya son wani ma ya kirashi a waya, sam ji yake wayoyin ma sun fita daga ransa, yaita ƙoƙarin tuna wani abu, amma ya kasa se dai ya haƙura. Wajen ƙarfe sha ɗaya na rana, yana kwance yai rigingine, kamar wanda aka tsikara, ya tashi ya fito ya nufi turakar Hakimi, abun mamaki yana zuwa ya tarar da Abba da Faruk. Turus yai yana binsu da kallo ɗaya bayan ɗaya, Abba ya kalli Sadik ya ganshi so calm, yai ƙiba yai haske saboda babu yawo, sedai kana kallon fuskar sa kasan a cikin damuwa yake, dan samu babu walwala a tare da shi. Tsayawa yana binsu da kallo, kamar be sansu ba, in lissafin sa daidai ne, yau watansa uku da kwana Ashirin da biyu kenan a garin nan, ba tare da ya ga wani daga gidan su ba, kuma ba tare da ya saka ƙafarsa a waje ba. Abba yace "to ba zaka ƙaraso ciki mu gaisa ba kenan?" Jiki a sanyaye Sadik ya shiga ɗakin ya zauna a kusa da Abba, amma be ce Komai ba. Faruk ya taɓa shi yace "meye hakan kake yi kamar wani ƙaramin Yaro?" Ɗagowar da Sadik ze yi sega hawaye a fuskar sa, take Abba yaji yana neman ya karaya, wani tausayin Sadik ya shige shi, ya san zaman ƙauye baze zama abu me sauƙi ga Sadik ba, tunda tun haihuwar sa a cikin gata yake, amma an ajiye shi a nan tsawon kwanaki ba tare da ganin kowa daga gida ba. Cikin dakiya Abba yace "meye kuma na kukan? Sekace wani ƙaramin Yaro?" Faruk ne ya rungume Sadik a jikinsa, yana duddukan bayansa alamar rarrashi yace "we Miss You Brother" Sadik yace "don't lie to me, you don't Miss me at all" "Who told you so? Zo muje waje kaji" Sadik ya yunƙura ze tashi, amma Hakimi yace "Uban naka ma ba zaka gaishe shi ba?" Ya kalli Abba yana son yai Magana, amma ya kasa se kuka. Abba yace "Ranka ya daɗe ƙyaleshi ma gaisa an jima" Faruk ya ja hannunsa suka fita daga turakar, Inna ta taɓe baki, banda sangarta kamar Sadik ya zauna yana wannan uban kuka haka kamar wani ɗan yaye. Hakimi ya maida hankalinsa kan Abba yace 'Amma Bawan Allah, nace ya batun tafiyar Yaron nan nemx Abba yace "muna ta shiri ranka ya daɗe, nan da abunda be fi sati uku ba insha Allah ze tafi, ana ta shirye shirye" Hakimi yace "yayi kyau, abunda nake so da kai shine, a sati ukun nan ina son a nemawa 'yar uwarsa Makaranta a inda ze karatu" Abba yace "Nana?" "Eh ita" Abba yace "Amma ranka ya daɗe, ai shi jami'a ze shiga ita kuma tana aji biyu a ƙaramar Sakandire" "Eh, ai ba a jami'ar nake nufi ba, Makaranta nake son a sakata daidai da karatunta" Inna tace "Amma Allah ya baka yawan rai, Nanan za'a kai turai karatu a wannan shekarun nata?" Hakimi yace "haka nace, umarni nake bayarwa ba shawara ba" Abba yace "shikenan, ai hakan baze gagara ba, insh Allah za'a nema mata" Gaba ɗaya kan Inna ya kulle, me Hakimi yake nufi da yin haka? Wannan wane irin hukunci ne? Yarinyar da ke kan ganiyar tashen balaga ita za'a kai ƙasar waje karatu? To waye ze kula da ita a can?' Sadik kam Faruk ne ke ta rarrashin sa, Sadik yace "Yanzu meyasa baku taho min da Mother ba? Shikenan an tsaneni an kawoni nan an ajiye kamar wani ɓarawo?" "Kayi haƙuri Sadik, yama za'ai ace ba'a sonka, Abba ne yace Mother ba zata biyo mu ba, amma ita ma tayi kewarka sosai, kai kasan kukan da tai saboda an bar mata kai a nan, amma komai ya kusa zuwa ƙarshe Insha Allah" "Amma tare zamu tafi ko?" Faruk yace "wallahi ban sani ba, amma bari muga zuwa mu tafi me zece" Shi kansa Faruk yai mamakin yadda Sadik ya zama wani shiru shiru. A hankali ya dinga ɗaukar Sadik da hira, har Sadik ya manta da damuwar da yake ciki suka cigaba da hira. Sedai ga mamakin Sadik yaji Abba yace Faruk ya tashi su tafi, gaba ɗaya zuwansu basu fi awa ɗaya da rabi ba zasu tafi. Sadik yace "Abba ni fa?" "Ban da kai Sadik, a nan zamu barka se lokacin tafiyar ka tukuna" "Abba saboda me?" "Saboda haka nace" Abba ya bashi amsa. "Abba yanzu ma tafiya za kai ka barni?" "Eh, zama guri ɗaya yasa ka nutsu ka ƙara kyau" Sadik bece komai ba ya juya ya tafi ɗakinsa ya rufo ƙofa. Gaba ɗaya jikin Faruk yai sanyi, shi kansa Abba ba haka ya so ba, amma ba yadda ya iya. Hakimi yace "Bawan Allah, ko baka faɗa ba, nasan zuciyarka da ta matarka babu daɗi na riƙe muku ɗa, amma banyi hakan dan muzguna muku ba, duk abunda kaga inayi da dalili nake yi, wanda base na zauna ina faɗar dalilin ba idan na isa, dan haka in anje gida a bata haƙuri, muna ɗaukar matakin da ya dace ne, Allah ya kiyaye hanya" Abba yace "babu wani dalili da ze sa ayi abunda za'a cutarmu, muna godiya duk matakin da aka ɗauka akanmu daidai ne, kai da kaya ai mallakar wuya ne" Hakimi yace "hakane, Allah yayi albarka" Abba da Faruk suka kama hanyar komawa gida. Suna tafiya a hanya, Faruk ya lura da yadda Abba yai shiru kamar yana nazarin wani abu. "Abba meke faruwa ne" Faruk yai maganar cikin ladabi. Abba yace "Bari kawai Faruk, ban san me Hakimi yake shiryawa ba, yace se an nemawa Nana Makaranta a London, abun tambayar a nan a ina zata zauna? Waze kula da ita? Kaga Sadik yana hostel ni kuma ba zanso ta zauna a cikin turawa ba, saboda addinin ta da tarbiyyar ta, da se ince ko gidan Steve zata zauna, ban san yadda a kai Hakimi ya yanke wannan hukuncin ba, duk da tarin tsantsenin sa akan tarbiyya, abun mamaki naga ita kanta Inna ma ba ta san zacen ba" Faruk yace "aikuwa duk wani hukunci da Hakimi ze ɗauka, baze ɗauka haka nan ba seda dalili" "Hakane, na so sanin dalilin amma naga baya son in fiye tambayar dalilin, shiyasa ban tambaye shi ba" "Amma Abba meyasa baka tambaye shi mu tafi da Sadik ba" Abba yai murmushi yace "kana son in ja wa kaina ɓacin rai ne? Bari dai in yi abunda yace in gani, samun Admission ɗin nan kusa abune me wuya amma dole zan bincika" Suka cigaba da tafiya kowa yana saƙe saƙe a zuciyar sa. Sadik zaman dirshan yayi, zuciyarsa ta bushe gaba ɗaya, ga kansa ya kulle ya rasa abunda yake masa daɗi gaba ɗaya. Farhan na tafe tana jefa ƙafa, kai kace bata da jini a jiki, tunani kawai take a ranta daban daban, haka kurum zuciyarta ke raya mata, anya Sadik ba Yasmeen ɗin ajinsu ya koma so ba, shiyasa yai watsi da ita ba, in ba haka ba meya kai Yaseen gidansu Sadik harta san yana ƙauye?. Dummm zuciyarta tayi, taji jiri na nema ya kwasheta ta faɗi ƙasa, da Sauri ta kauda wannan tunanin daga ranta. " 'yan Makarantar bokoko" da sauri ta waiga jin anyi magana a gefen ta. Haladu ne, abokin Sunusi, ba ta kulashi ba ta cigaba da ƙoƙarin tafiya, yace mata "Ina wuni" "Lafiya ƙalau" "Amm Farhan" ta waigo ta kalleshi. Ji yai kamar ya gayamata abunda Sunusi yake akanta, amma se ya kasa yaga be dace ya tona masa Asiri ba suna tare. Dan haka yace "An kusa kawo kuɗi ko?" Banza tai masa ta cigaba da tafiya, Haladu ya jinjina kai ya ƙara tabattar da Farhan ba ta ƙaunar Sunusi, dama ba su dace ba sam. Lilly ce zaune a Office ɗin Nazir, yana aiki suna hira ta zubo masa ido. Yace "ya dai wannan kallon fa?" "Yaushe zaka zo gidan mu?" "Lilly haryanzu baki cemin komai game da batun za'a bani ke ko ba za'a ban ba, ya za ai na fara zuwa?" "Maganar gaskiya nayi attempting faɗa a gida amma na kasa, yanzu shawara ɗaya ce kawai ka fara zuwa gidanmu" "Lilly se in zo gurinki ba iznin iyayenki? "Nifa haɗuwar nan da muke a school am not comfortable kawai ka zo gidan" "Amma idan aka ganni a gidanku hakan ba ze janyo mana matsala ba?" "Ba wata matsala, ai ina ga next week in Allah Ya kaimu zasu Sakwatto, se kazo Please" "Shikenan, Allah ya kaimu kin san bana son ɓacin ranki" Murmushi tai masa ta miƙe ta bar Office ɗin. Ko da Abba suka koma gida ya sha tuhuma a gurin Mother, dan yana shiga gidan ta miƙe tana faɗin "Ina Autan yake?" Abba yace "kamar yaya?" "Ba ɗakko shi kaje yi ba?" "Ni nace miki ɗakko shi naje yi? Kiran Hakimi naje" "Amma kasan a can zaka barshi, maimakon mu tafi tare in ganshi" "Ban niyya ba" ya bata amsa ya wuce ya barta a gurin. Mother ta fara ƙulewa matuƙar gaske, akan abunda ake mata akan Sadik. Tunda yaga sunyi haka, be yi gangancin gaya mata batun Nana ba da ita ma Za'a nemawa Makaranta a London ba, ya ƙyaleta. Cikin fargaba da ɗari ɗari Nazir ya shirya zuwa gidansu Lilly. Tun bayan sallar azahar tai wanka ta shirya tana jiran zuwansa, tai kwalliya ta sa masu aiki sun shirya masa Abinci. Daga nesa kaɗan da Gidan ya tsaya, ganin masu kaki a ƙofar Gidan. Ya kirata a waya, ya gaya mata ya zo. Mintuna kaɗan ta kuma kiransa a waya tace yaje Zasu buɗe masa ya shiga. Yana karanta fatiha da salati haka ya ƙarasa gaban gate ɗin, ba su ce masa komai suka bashi hanya ya shiga. Ƙarewa gidan kallo yake, gida kamar ba za a mutu ba, yanzu wannan gida dan dai rayuwar tsirarin mutane a ciki, da ana tuna mutuwa da ba a gina shi ba. Wayarsa ce ta fara ringing ya ɗaga Wayar. Lilly tace "ka miƙo hanyar da take facing ɗinka zamu haɗu. Haka ya bi hanyar yana rarraba ido. "Oyoyo" ya jiyo Muryar ta, ta taho da gudu ta rungume shi. Shima rungumeta yayi yace "Kinyi kyau sosai Baby" "Dama dan kai nayi, tunda ka yaba masha Allah" Yai murmushi tai masa jagora zuwa cikin wani haɗaɗɗen falo. Ta gabatar masa da kayan ciye ciye, ta zauna a kusa da shi, Kamar zata shige jikinsa, ga wani irin fitinanne ƙamshi da dukkanin su suke yi. "Baby a tsorace fa nake" "Meye abun tsoro kuma? Ba kowa a gidan fa, daga mu se maids da guard ɗin gidan nan" Ta dinga jansa da hira, yana cin Abinci Kamar wasu miji da mata. Sosai suke ƙoƙarin sake kauce hanya, da ƙyar Nazir ya aro jarumta ya ture Lilly, yana sauke numfashi. Yayin da tai shiru tana kallonsa. "Lilly alƙawari mu kai ba zamu sake ba, Aure zamuyi kar sheɗan yai tasiri akan mu, kuma kinga matsalar da aka samu wancan karon, bari in tafi" Ba ta ce masa komai ba, yabi hanyar da ya shigo ya fice. Nana ba ta san su Abba sunzo ba, kasancewar tana makaranta, sedai tunda ta dawo ba taga Sadik ba ko a tsakar gida. Ta kalli Inna tace "wai Inna ina wannan suƙundumin?" Inna tace "me kenan?" Nana ta nuna mata ƙofar ɗakin Sadik. Inna tace "wallahi idan ya fito ya dake ki, ki kaimin kuka sena ƙara miki" ba shiri ta tsuke bakinta. Seda daddare Inna take gayamata su Faruk sunzo tana Makaranta, amma ba ta sanar mata da batun tafiyar ta ƙasar waje ba. Tace "Amma Inna meyasa basu tafi da shi ba?" "Nima ban sani ba seki tambayi kakanki" "Ni duk da yana bani haushi, amma wataran tausayi yake bani wallahi, ya gaji da zaman nan, muma fa lokacin da muka zauna a gidansu gajiya nai da zama" Banza Inna tai mata ta cigaba da sabgarta. Nazir da ƙyar ya kai kansa gida, saboda halin da ya shiga, ita kanta Lillyn ta daɗe a gurin da ya barta a kwance, sannan ta tashi ta koma ɗakinta. Babban abunda ya bata mamaki be wuce yadda su Daddy suka dawo a ranar da daddare, bayan sunce zasu kwana uku sannan su dawo. Tai pretending kamar tayi bacci, taƙi fitowa, balle tai musu sannu da zuwa. Ta rufe ƙofarta da key, ta shige cikin bargo tana waya da Nazir, tare da nuna masa yadda tai kewarsa ba tare da kunya ko jin nauyin komai ba, shima haka ya saki baki su kai ta waya. Se Washegari da safe, sannan Lilly ta gaida su Daddy tare da mamakin dawowarsu a jiya, suna tsaka da karyawa Daddy yace "Lilly waye ya zo  min gida jiya da bana nan?" Gabanta ya yanke ya faɗi, ta kalleshi tace "Ammm.." "Kar ki min ƙarya, bayan tafiyar mu jiya wani yazo gidan nan, kuma ya shigo bisa umarnin ki, waye shi?" "Amm...mmm....Dadd..... "Karki kuskura ki min ƙarya! Ba a banza na saka masu tsaron gida na ba, uban waye ya shigomin gida jiya?!" Ya faɗa cikin kakkausar muryar sa. "Daddy saurayina ne" ta faɗa kamar za tai fitsari. "Whta! Saurayi Lilly?" Mummy ta faɗa tana kallonta. "Au ke yanzu nan har kin san kiyi saurayi ki kawo min shi cikin gida na? Lilly are you out of your sense? You are only fifteen years har kin san ha'inci" Lilly ta shiga girgiza kai tana rarraba ido, dan bata san hukuncin da ze ɗauka a kanta ba. "Waye shi kuma a ina yake!" Yai mata tambayar cikin tsawa. "Daddy wani corper ne? Cewa yai yana sona ze Aureni" Yace "good, kema kuma kina son sa?" Yai tambayar yana tsatsare ta da ido. Tai saurin ɗaga masa kai alamar eh. "A ina yake?" Tace "Nima ban san a in da yake ba kawai haɗuwa mu kai" Mummy tace "ke Aure kike so kenan?" Ba Kunya Lilly ta ɗaga kai alamar eh. Daddy yai murmushin takaici, ya kalli Lillyn da yake ganin ba ta fi ya kamata yai mata wanka ba, amma ita ke cewa wai Aure take so, me ta sani game da Auren da harya bata sha'awa take cewa za tayi. Ya sassauta zuciyarsa yace "shikenan tunda haka kike so, in dai dagaske yakw, kice ina son ganinsa" Wani irin farinciki ne ya ratsa Lilly ta gyaɗa kai. Mummy za tai magana amma ya girgiza mata kai, ya kalli Lilly yace ta koma ɗakinta. Bayan ta tafi Mummy tace, "kana nufin aurar da Lilly zakayi?" Yace "sekace bani da hankali, ai daga ji hure mata kunne yake, Allah ne kaɗai yasan tun lokacin da suke tare, sonake yazo in ganshi, in wanda zan yiwa warning n Kawai shikenan, in ma casa shi Yakamata in sa ayi zanyi wanda ya dace". Yau Friday, Nana na shirin tafiya Makaranta, Inna ta bata sallahun in an tashi daga Makaranta, taje ta karɓo mata saƙo a can wata unguwa, Nana ta amsa da to. Dan da farko ko makarantar ba tai niyyar zuwa ba, saboda yau jikin Hakimi ya motsa, jininsa ya hau ga zazzaɓi da tari yana ta fama da shi. Dan seda aka kira likita ya duba shi, ana tunanin ko Asibiti za'a ka shi. Amma inna tace Nana ba zata zauna ba ta tafi makaranta, dan in ta zauna koke koke za tai ta musu. Har aka tashi daga Makaranta, jikin Nana a Sanyaye yake, ji take kamar kan ta koma gida Hakimi ze mutu. A gurguje taje ta karɓo saƙon nan, tana tafe tana haɗawa da Sauri, saboda ta koma dan hankalinta yaƙi kwanciya sam. Sedai me tana shawowa kwanar gidan, ta tarar da cincirindon mutane a gurin, sunyi cirko cirko, duk da juma'a ce anyi sallar juma'a amma yanayin yadda taga mutanen hankalimta ya sake tashi. Nan take gabanta yai mummunar faɗuwa, jikinta ya ɗau rawa numfashinta ya shiga barazanar tsayawa. Da gudu ta nufi gidan tana ture mutane, hawaye na bin fuskarta. (RIP ALHAJI ALIYU MAMMAN RANO (HAKIMI) Littafin nan ₦300 ne kacal. 0009450228 Aisha Adam Jaiz Bank 07063065680 KO kuje manhajar AREWA BOOKS ku siya. domin kuwa ya fi sauƙi ta can. Littafin nan ₦300 ne kacal. 0009450228 Aisha Adam Jaiz Bank 07063065680 KO kuje manhajar AREWA BOOKS ku siya. domin kuwa ya fi sauƙi ta can. Kutsawa kawai Nana take tana kuka, yayin da dandazon mutanen ke binta da kallo, kamar wadda ta zare. Da gudu ta kutsa ta shiga, sedai tai turus saboda kasa banbance Alhini mutanen ke yi ko kuma farinciki. Turakar Hakimi ta nufa, ta shiga da sauri. Hango shi tai a zaune, ya sha fararen kaya da naɗi, sedai kana ganinsa ka san yana jin jiki ne. Runhumeshi taje tayi tana kuka tana faɗin Alhamdilillah, Ka ji sauƙi? Ka warke?" Yayi tari yace "Da sauƙi Alhamdilillah" ajiyar zuciya ta dinga saukewa, ta ɗaga kai ta kalli jama'ar da ke ɗakin. Se a yanzu ta kula da Abba, da Faruk a zaune, gefe ga Inna se Sadik dake zaune, idonsa yai ja kamar garwashi. Se da gabanta yai mummunar faɗuwa ganin idanun Sadik ɗin, kamar ba idon bil adama ba. Wani  irin matsiyacin kallo Sadik yaiwa Nana, wanda ya hadda sa mata ƙullewar ciki saboda razana. Cikin ƙullewar kai Nana tace "Inna wai me ake a gidan nan?" Inna tace "ba zaki gaida baban naki bane" Jiki a sanyaye Nana ta kalli Abba tace "Ina kwana" Jiki ba kuzari Abba yace "ina wuni dai ko" Nana tace "eh ina wuni" Yace "lafiya ƙalau Alhamdilillah" Hakimi yai tari, sannan yai gyaran murya yace "Alhamdilillah ala kulli halin, dukkan godiya ta tabatta ga Allah, Abdullahi" ya kira sunan Abba. "Na'am ranka ya daɗe" Abba ya amsa yana risinawa. "Ka sani ban yanke wannan hukuncin ba, se da na nasan ina da ƙwararan dalilai na, kar ka kalli abunda nayi a  matsayin cin zarafi ko nuna maka baka isa da iyalinka ba, Komai nayi nayi shine da dalili, ko bayan raina ban yadda wani abu ya samu Auren nan ba, Nana amana ce itama 'yarka ce, kuma marainiyar Allah, dan Allah a kula da Amana, sannan ka jawa ɗanka kunne a kanta" Ya kuma yin tari sannan ya kalli Sadik da ke ta ajiyar zuciya yace "Abubakar, na san na maka ba daidai ba, amma ka sani duk abunda babba ya hango ko yaro ya hau rimi ba ze hango ba, ban ɗau wannan hukuncin dan cuzgunawa rayuwarku ba, sedai ba zan zuba ido wani abu ya ratsa ta cikin iyalina mara daɗi ba, nasan ko bayan raina nan gaba zakayi Alfahari da hukuncin da na yanke, kaga kamar yadda kuke iƙrarin kun tsani juna, kaga se ku kashe kanku in kun ga dama, duk wanda ya ƙoƙarin raba abunda na ƙulla, ban yafe masa ba, Allah ya baka damar Auren mata huɗu, nan gaba in kana buƙata ka iya ƙarawa, amma ban yadda ka wulaƙanta 'yar uwakka ba" Zare ido Nana tai ta miƙe daga jikin Hakimi tace "Wai Auren wa akayi? Wa kaiwa Auren?" Inna ta daka mata tsawa tace "rufe mana baki ki, nemi guri ki zauna" "Inna a ina zan zauna, wai meyafaru ne?" Duk da jikin Hakimi ba ƙwari, haka ya janyo Nana ya zaunar da ita a kusa da shi, yace "kalli cikin idona" Ba musu ta kalli idonsa, take taga yai mata wani irin kwarjini, jikinta ya hau tsuma, Hakimi yace "Zaki bi Abubakar turai karatu, kema a can zaki ƙarasa naki karatun" Cikin rashin fahimta tace "Alhaji meyasa, ni fa bance maka zani ba" "Saboda na yanke hukunci, na Aurar da ke ga Abubakar Abdullahi Rano, ɗan uwanki" "Innalillahi wa innalillahi raji'un! Alhaji laifin me nai maka, meyasa zaka ce haka?, in bishi turai banda uwa banda uba se Allah se ku, idan ya cutar dani fa?" "Baze cutar da ke ba, muma kuma ba zamuyi abunda ze cutar da ku ba" Fizgewa tai daga jikin Hakimi jikinta na tsuma tai hanyar waje, Inna tace "ku riƙeta karta fita" ai kan ta gama Magana Nana ta kasa da gudu tai waje, Faruk yabi bayanta, tana zuwa babban soro ta faɗi ba tare da sanin in da kanta yake ba. Tunda garin Allah ya waye, Farhan ke wani irin matsanancin faɗuwar gaba, har idan zuciyarta ta buga seta dafe ƙirjinta, ta koma fizgo numfashi da ƙyar. A hankali take shirin Makaranta, tana yi tana jin wani irin tsoro da fargaba suna shigarta. A makare ta isa makaranta, gaba ɗaya har aka gama lesson ba ta fahimci komai ba. Sannu a hankali take tafiya, tana tafiya tana jin Kamar numfashinta ze ɗauke har ta isa gida, Umma sarai ta lura da yadda Farhan take komai sanyi sanyi, amma ba ta tambaye ta meya sameta ba. Farhan Ta ɗauro Alwala, ta zo ta tada salla, ta kai raka'ar farko da kyar, ta miƙe zata kawo ta biyu ta faɗi a gurin. Kasancewar duk ƙannenta sun tafi Islamiyya, Umma kuma tana cikin ɗakinta, dan haka babu wanda ya san meyafaru. Ko motsi ba tayi balle numfashi, tana ƙasa kawai a kwance. Su Amira ƙannenta suka dawo daga Masallaci, suka ci Abinci amma ba su ji motsin Farhan ba, kasancewar sun sa ba me son hayaniya ba ce, ga ta da son bacci dan hala suka ƙaddara bacci kawai take. Wajen la'asar Huzaifa ya zo gidan, a tsakar gida ya tarar da Umma suka gaisa, yace "Umma Ina Yaya, ta zo taga sabuwar wayar da na siya, ta sa mun Albarka" Umma tai murmushi tace "tana ɗaki" Hauzaifa ya shiga ƙwala mata kira yana "Waliyya zo kiga sabuwar wayata" amma yaji shiru. Yai knocking ƙofar ɗakinta yace "in shigo?" Amma shiru. Ya ɗaga labulen ɗakin, ya ganta a kwance akan sallaya kamar ba rai a jikinta. "Innalillahi wa innalillahi raji'un, Umman Farhan zo ki ga" yai maganar yana nufar in da Farhan ke kwance. Da Sauri Umman ta tashi tana faɗin lafiya. Tana zuwa ta tarar da Farhan a kwance, tazo ta taɓa ta taɓata amma babu alamar motsi a tare da ita. "Innalillahi wa innalillahi raji'un, Huzaifa kamar fa ta rasu ne" "A'a Umma ba ta mutu ba, tana da rai" Umma ta girgiza kai tace "kalli fa ba in da yake motsi a jikinta" Huzaifa ya fita da gudu, ya ɗebo ruwa yazo ya shiga shafa mata a gishinta zuwa fuskar ta. Tai yunƙuri Kamar za tai numfashi, amma ta kasa. Yace "Umma kin gani, mu kaita Asibiti" "Ni ina naga abun hawa, kawai ka kira baban ta a waya ka sanar masa" "Umma idan akace se Abba ya dawo ai abun ze zama worst, bari in fita neman abun hawa, kiyi tai mata fifita. Ƙannen Farhan suka kewaye ta suna kuka, Amira na mata fifita, Umar na karanta mata Alqur'ani. Kai tsaye gidan Hajiyar nan Huzaifa ya nufa, saboda yana fita yaga mota a tsaye a ƙofar Gidan. Sallama ya shiga kwaɗawa, ta amsa ta bashi iznin shiga. Tana ganinsa ta gane shi, ya tarar da ita da babban ɗanta, shine ya zo da mota Gidan. Nan Huzaifa ya gayamata abunda ke faruwa, nan da nan hankalinta ya tashi, ta ɗau hijjabi tabi Huzaifa. Tana zuwa ta tarar da Farhan, a mawuyacin hali. Hajiya ta hau faɗa tace "ni tun ba yau ba na fuskanci yarinyar nan ba ta da lafiya, tayi rama sosai ba ta da kuzari" Ta kalli Amir tace "maza jeka gida ka kiramin Daddyn Arham kace nace ya taho da motarsa ƙofar Gidan nan. Nan suka fara ƙoƙarin ɗaga Farhan, amma abu ya gagara saboda Farhan na da jiki, kuma gaba ɗaya jikin nata ya saki. Hajiya da kanta ta leƙa, tacewa ɗanta ya zo ya temaka musu. Yana zuwa ya ɗaga Farhan, Kamar ya ɗau karauni haka yai waje da Ita. Hakan yai daidai da zuwan Sunusi, dan ganin meke faruwa yaga mutane a ƙofar Gidan su Farhan. Yaga an fito da Farhan, hijjabin ta ya ɗage sam bata hayyacinta, amma babban abunda ya dame shi ba rashin lafiyar bane, illa ɗakkota da ya ga wani ƙato yayi. Maimakon Umma tabi su Hajiya, tace ba zata bisu ba, ta bawa Huzaifa kuɗi tace ko za'a buƙaci wani abun, ga kuɗi nan kan babanta ya dawo. Da sauri Sunusi ya ƙaraso, sedai kafin ya ƙaraso tuni sun ja motar sun tafi cikin hanzari. Amir ya samu a tsaye yana kuka a ƙofar gida, ya kalleshi yace "Kai meya samu yayarka?" Amir yace "ba ta da lafiya, suma tayi an tafi Kaita Asibiti" "To waye wancan da ya ɗakkota?" Amir yace "nima ban sani ba" daga nan ya jiya ya shige cikin gida. Sunusi yai shiru yace "ko dai shine Sadik ɗin?" Se kuma ya tuna Sadik be kai wannan jiki da tsayi ba, kuma a Muryar Sadik da ya ta ɓa ji, akwai yarinta a muryarsa, amma wannan babba ne sosai. Umman Farhan kuwa tai zuguum a gida, tana tunanin meya samu Farhan haka. Suna tafe a mota ɗan Hajiya yace "Hajiya wai meya samu yarinyar haka?" Hajiya tace "Nima ban sani ba wallahi" Huzaifa yace "ni a iya sanina ban ga tana rashin lafiya ba" Hajiya tace "Ai ba kusa ba nesa ga Allah, Allah ya bata lafiya" Kasancewar ɗan Hajiya wato Abbas likita ne, wani private Hospital ya kaita, Asibitin na abokin Aikinsa ne amma tare suke gudanar da Asibitin. Suna zuwa aka bawa Farhan gado, aka fara bata taimakon gaggawa, da alluran da zasu taimaka mata. Aka bar su Hajiya a reception, kusan mintuna Arba'in, sannan Abbas ya fito. Hajiya tace "Abbas ya jikin nata?" "Eh ta samu releif, mun ɗora ta akan drip, na rubuta teses an ɗebi jininta an kai lap, za'a duba". "To Allah ya bata lafiya, meye bill ɗin a biya?" Abbas yai murmushi yace "lallaima Hajiya, yanzu kawai seki biya" Tace "eh mana" Yace "to ni meye amfani na in har zaki biya? Wai ina mamanta ma, ina iyayenta naga wannan yaron ne kawai ya biyo mu, in sunzo se su biya kuɗin, an rage musu 30% saboda ke" Huzaifa yace "ga kuɗi Umma ta bani, nawa za'a biya" Hajiya tace "ƙyaleshi Huzaifa" Ta kalli Abbas tace "Ina tausayin Yarinyar ne, ai ita ce nake cewa da zan maka mata ta biyu da ita, amma a kace an mata miji, ai 'ya ta ce" Kawai Abbas ya hau dariya yace "wannan 'yar Yarinyar, da da wuri nai Aure ai na haife ta, wannan ai 'ya ta ce" Hajiya tace "wallahi Yarinyar akwai nutsuwa, ga tarbiyya she's first child of her Fulani parent, so ba kulawa Sosai, yanzu haka in ka bibiya ta daɗe tana rashin lafiya basu sani ba, kuma maybe ba ta faɗa ba, tunda ba ta da magana" Abbas yace "Allah sarki, Allah ya bata lafiya, tunda 'yar ki ce shikenan ba se kun biya ba" Se Wajen magariba, se ga Abba hankali a tashe ya isa Asibitin, ya tarar da Hajiya a Asibitin. Suka gaisa Sannan yace "Naji labarin karamcin da ki kai mana, ubangiji Allah ya saka da Alkhairi yasa ki ɗauka a gidan Aljanna" Hajiya tace "Ameen bakomai, ai yiwa kaine, bismillah muje ka ganta" Suka nufi ɗakin da Farhan take, tana kwance an sa mata Oxygen, hannunta ɗauke da drip, harta faɗa Sosai fatar ta tayi wani iri alamar oxygen ba ta wadatar jikinta. Ga SPO2 machine yana ta reading vitals ɗin ta. Ganin halin da Farhan ɗin ke ciki, seda Abbanta ya firgita sosai, ya ƙarasa gaban gadonta, ya shafi gashin kanta da yake a hargitse yace "Allah kai ka halicce ta ka ɗora mata, Ubangiji Allah ka tashi kafaɗunta in ciwon na tashi ne, in bana tashi bane Allah kasa ta tafi a sa'a" yai maganar ƙwalla na taruwa a idonsa. Hajiya tace "ka kwantar da hankalinka, insha Allah zata samu sauƙi" Abbas ya shigo da file ɗin Farhan, suka gaisa da Abba, Hajiya tace "Abbas ga mahaifinta' Abbas yace "Allah sarki, ai naga kama, Allah ya bata lafiya" Abba yace "to nawa ne aka ce kuɗin Asibitin, in biya mu maida ita na gwamnati, naga wannan Asibitin na masu ƙarfi ne" Hajiya tace "baka da damuwa da wannan, tayi sabon uba ai yace an mata kyauta" tai maganar tana nuna Abbas. Hajiya tace "sedai batun wanda ze kwana da ita, naga ka taho kai kaɗai ina Umman nata?" Abba yace "Ai ba zata zo ba, kin san ita ce ta fari, ina ga ni zan kwana a gurinta, zuwa da safe ƙanwata za ta zo se ta cigaba da kula da ita" Abbas ya jinjina kai yace "Baba ba kai ya dace ka kula da ita ba, a wannan halin da take ciki, tana buƙatar kulawar uwa ne" Abba yace "Ai da yake ita ce ta fari, kuma dangin uwar ba a garin nan suke ba, da za a samu me kula da ita, amma bakomai zan kula da ita" Abbas yace "No ba za ai haka ba, muna da Nurses, za suyi mata duk abunda ya dace, zamu kula da ita" Abba yace"haba ai wahalar se tai yawa, ba a ɗora muku nauyi da yawa bax Abbas yace "karka damu, aikinmu ne ai, ka bari zuwa an jima ka tafi kawai, zamu kula da ita, Hajiya tai min kyautar ta ai, 'ya tace nima zan kula da ita, muna da ma'aikata wanda aikinsu ne" Abba yai ta godiya, har seda Abbas yaji godiyar tayi yawa, ko Lafiya suka bawa Farhan iya godiyar kenan. Nana kuwa ana ta fama amma ta gagara farfaɗowa, se surutai kawai da take da fizge fizge, se da aka dangana da yi mata rubutu da Addu'oi sannan ta dawo hayyacinta, a hankali ta kalli Inna, ta rintse idonta tana faɗin Allah ya sa ba gaskiya bane. Inna tace "Nana kina jina?" Ta jinjinawa Inna kai alamar eh. Tace "to ɗago ki kalleni" Ta ɗaga kai ta kalli Inna, ta kalli ɗakin still ga Hakimi, ga Abba da Faruk sedai ba Sadik. Ta miƙe zaune ta kalli kayan jikinta, tun Uniform ɗinta ne da ta dawo da su, tai shiru dan tayi tunanin gaske ne ko mafarki tai, amma komai ya dinga dawo mata tiryan tiryan. Fashewa tai da kuka a gigice tace "dan Allah Inna kice min ba gaske bane mafarki nake, wallahi ban isa Aure ba" Inna tace "ki saurareni da kyau, kina jina, Kakanki ya riga ya yanke hukunci, An aurar da ke ga Sadik, yanzu Sadik shine mijinki, ina son ki karɓi ƙaddara a yadda ta zo miki, Allah ya riga ya ƙaddara haka zata faru, dan haka kiyi haƙuri ki karɓe shi a matsayin miji, gobe in Allah ya kaimu zaku tafi, wataƙila a satin nan ko na gaba zaku tafi can ƙasar" Kawai Nana ta fashe da kuka, tana wani irin sheshsheƙa kamar zata shiɗe, amma ta kasa Magana, se wani irin zazzaɓi ma da ya rufeta. Abunda ya faru shine, Ranar Juma'a Abba da Faruk suka ƙaraso, suka tarar Likita yana duba Hakimi, saboda jikinsa da ya tashi. Allah yasa zuwa sha biyun rana, aka samu ya ɗan samu sauƙi, Sadik yana ta murna yasan in Allah ya yadda wannan karon ze tafi gida, aka kawo masa sababbun kaya farare, aka ce su zesa, da farko abun ya bashi mamaki se yai zaton dan yau za'a tafi da shi ne. Bayan idar da sallar juma'a, akace za'ai ɗaurin Aure a Masallacin, Sadik Alla Alla yake ayi a gama abunda za ai, su tafi. Can aka fara ɗaurin Aure, yaji an ambaci Nana Asma'u, da Abubakar Abdullahi Rano. Da fari be san wa aka ɗaurawa Auren ba, se daga baya ya fara tunanin wannan ai sunansa ne?. Seda aka gama ɗaurin Aure, yaga Abba yana zufa, Faruk ya miƙo masa hannu yace ""burinka ya cika Auta, Allah ya Sanya Alkhairi ya baka wuyan ɗauka" Zaro ido Sadik yai yace "wa aka ɗaurawa Auren?" "Kai da Nana mana" ya bashi amsa. A gigice ya nufi in da Abba yake, yace "Abba da gaske ni aka ɗaurawa Aure?" Abba yace "Eh, kai aka ɗaurawa Aure" Gigicewa Sadik yai, ya fara zazzaro ido "Abba meyasa? Meyasa za'aimin jaka? Meyasa za'amin Aure ba tare da sanina na?" Ganin ze tada hayaniya yasa aka sa dogarai sukai cikin gida da shi. Nan da nan aka fara bushe bushe, Hakimi ya miƙe ze tashi, amma ya yanke jiki ya faɗi. Aka ɗauke shi aka shiga da shi cikin gida, ana tunanin koma ya rasu ne, nan da nan aka dakatar da wannan busar da ake. Se kuma daga baya cikin ikon Allah ya farka. Gaba ɗaya Sadik ya fita hayyacinsa, yai kuka yai kuka har idonsa yai jawur, shi a lokacin nan da Hakimi ya mutu ma ba abunda ze ji, ya rasa laifin me yai musu suka tsane shi haka, ko Auren za'ai masa ai a bari ya zaɓi wadda yake so. Magana ma ta gagari Sadik, se sheshsheƙa da ajiyar zuciya, wata muguwar tsanar Nana ta ƙara baibaye shi, ko ƙaunar jin an ambaci sunanta ba yayi. Tun saura kwana biyu Abba su zo garin, Hakimi yace masa in ya tashi tahowa, ya taho da Sadakin ɗansa. Abba sam ya zaci kawai barkwancin Hakimi ne, amma be taɓa zaton Hakimi zewa Sadik Aure da Nana ba. Ba shi da ikon ja da maganar mahaifinsa, amma sam be ga tsari a wannan Auren ba tsakanin Nana da Sadik waze tsawatarwa wani? Banda shirme da Yarinta babu abunda za'a tsinana a wannan Auren. A haka ma kullum ba su da aiki se faɗa, ina ga zaman Aure? Shikan sa Auren babu lallai sun san meye Auren balle suyi zaman Aure, ta guri ɗaya yaji sanyi a ransa, kasancewar Nana boarding aka samar mata, kafin dai ta gama Makaranta, su tare ƙil sunyi hankali. Ga Hakimi yai jan kunne sosai akan Auren, dan yace be yafe ba idan aka sake wani abu ya samu wannan Aure. Cikin dare kusan ƙarfe biyu da rabi na dare, Aka kaiwa Abbas sakamakon gwaje gwajen da a kaiwa Farhan. Ya sa aka kawo masa magunguna, ya tafi da kansa yai mata serving medication. Ulcer tai mata mummunan kamu, peptic Ulcer irin me riƙe numfashin nan, ga jininta yai ƙasa, ga kuma very high BP, nan ya shiga mamakin yadda a kai wannan 'yar ƙaramar Yarinyar ta samu wannan ciwuka haka. Ba yadda za'ai ace lokaci ɗaya duka wannan ciwukan suka kamata, sannu a hankali suka kaita ƙasa haka. Se da ya ja gajeren tsaki,da ya tuna yadda Hajiya ta bashi labarin yadda take zaune a gidan su. A fili yace "Wannan ai shirme ne, Al'ada ai ba Addini bace" Yai mata Allura ta cikin canula, yana yi yana monitoring vitals ɗinta, duk da an samu improvement ba Kamar lokacin da aka kawota ba. A hankali ya ga ta fara motsawa, dan haka ya tsaya ya zuba mata ido. Ƙoƙarin ta da kabbarar salla take, a cikin yanayin da take, harta fara ƙoƙarin tashi zaune. Abbas ya maida ita ya gyara mata kwanciya yace "Sannu" A hankali ta fara buɗe idonta, dishi dishi take gani, ba ta gane a ina take, ta kalli Abbas amma taga fuskar Sadik. A hankali ta kai hannu, ta riƙo hannunsa ta fara Magana "Sadik, Sadik dan Allah, dan Allah ka dena min haka, you are the only.. only...Sadik I need you....." Allurar da yai mata da ya shigo ce ta cigaba da ɗibarta, dan haka a cikin magagi take. Abbas yai shiru yana Nazarin ta, da abunda take faɗa. Ganin ta fara bacci, yasa ya fara ƙoƙarin zare hannunsa daga nata, amma ta riƙe gam tana tura baki. "Kowane Sadik ɗin nan ya na da alaƙa da damuwarta, wanda ya kai ta ga wannan rashin lafiya" Wata Nurse ce ta shigo za tai masa Magana, amma ya girgiza mata kai da alamar tai shiru, baya son mara lafiyarsa ta tashi. A hankali ya zare hannunsa daga na Farhan, ya fice daga Office ɗin. Nana tana ji ta na gani, da daddare Inna ta haɗa mata kayanta, ta na yai tana mata nasiha akan tayi haƙuri da abunda Allah ya hukunta akanta. Nana taiwa Inna banza, ta cigaba da sharɓar kukanta. Inna ta kalleta tace "Nana ba zaki dena kukan nan ba ko?" Cikin kuka Nana tace "Inna ya za ai in da ne kuka, bayan ba kwa sona, kun Auramin wannan Yaron, wanda a gabanki yake cewa ya tsaneni ni" "To Nana, Allah ya riga ya hukunta lamarinsa, ba yadda kika iya, sannan karki sake ce masa yaro, kiyi haƙuri ki kwantar da hankalinki, kiyi masa biyayya, duk abunda yakamata in gayamiki na sha gaya miki a baya, bake ba fito na fito da shi, matsayinsa a gurinki a baya daban, a yanzu ma daban, dan haka ki nutsu kiyi haƙuri" Ƙara rushewa da kuka Nana tayi, tana "Innalillahi wa innalillahi raji'un, nikam na shiga uku wallahi bana sonsa" Tun Inna tana rarrashin Nana, se data zageta tsaf a daren nan. Ita kanta Inna ba ta so Auren Nana ya zo mata a haka ba, taso Nanan ta ɗan tasa tai gagarumin bikin aurar da jikarta ɗaya mace da aka mutu aka bari, sedai wannan Auren da a kai na gaggawa shine mafita, akan samuwar abunda ze rusa farincikin ahalin gaba ɗaya. Sadik kuwa tunda aka ai ɗaurin Auren nan yaƙi magana, se ajiyar zuciya da yake tayi, wadda take nuna yana cikin damuwa. Sedai ta gefe ɗaya yana ji a jikinsa, babu inda Auren ne zeje, dan baze taɓa iya zama da Nana a matsayin matarsa ba, wannan kudahumar 'yar ƙauyen mara kunya, ya san ba yadda za ai Mother ta yadda da Auren nan ba. Dan haka dole ne a raba shi. Da safe da Abban Farhan ya zo, ya tarar Farhan ta tashi, har an taimaka mata tai wanka, sedai ta ƙi cin Abinci. Abba ya kalleta yace "sannu Farhan, ya jiki" Farhan tace "da sauƙi Alhamdilillah, Abba ina Umma?" Abba yace "tana nan Lafiya, tace a gaishe ki" Farhan tace "ba zata zo ta dubani ba? "Kinga Farhan, mu bar wannan maganar, Anty Uwani da Hauzaifa suna nan tafe tazo ta zauna da ke, amma haryanzu likitan be gayamana meke damunki ba" Farhan ta ɗan gyaɗa kai. Abba yace "Farhan Hajiyar nan tana da kirki, duk wannan ɗawsiniyar babu ko kwabon mu a ciki, Allah ya biyata da Gidan Aljanna". "Ameen" Farhan ta amsa. Suna cikin Magana ne sega Abbas ya shigo, da flask ɗin Abinci a hannunsa, suka gaisa da Abba. Farhan ta dinga kallonsa, tana tunanin a in da ta sanshi. "Gawa taƙi rami, ba magana?" Abbas yai maganar yana kallon Farhan. Babu Uniform a jikin Abbas, dan haka ba ta gane likita bane. Ya kalli Abba yace "Baba babu wata damuwa, zaka iya tafiya gurin Aikin ka, zamuyi ƙoƙarin ganin komai ya tafi daidai, Hajiya tana nan tafe" Abba yace "eh ƙanwata ma tana nan tafe anjima zata zo ta zauna da ita" Abbas yace "babu laifi" Ya Ajiye kular Abincin ya fita. Abba be jima ba sosai ya tafi, saboda shima yana jin kunyar azo a samu shike jinyarta a matsayin ta na babbar 'yar sa. Wata Nurse ce ta shigo, ta zubawa Farhan Abincin kular da Abbas ya zo da shi, ta takurata taci Amma ƙememe Farhan taƙi. Ana cikin haka zega Abbas ya sake shigowa ɗakin da Farhan take. Wannan karon da lap court ya shigo ɗakin nata, se a yanzu ta gano shine likitan, kuma taga kamanninsa da Hajiyar sa. Nurse ɗin ta miƙe tsaye cikin girmamawa tace "sannu da zuwa doctor" Yace "Yawwa ya patient ɗina?" "Patient gata nan, anma taƙi cin Abinci" Abbas yace "bakomai, jeki kawai" Nurse ta Ajiye Abincin ta fita, ya zauna akan kujerar, ya ɗakko plate ɗin me ɗauke da faten wake ya sha Alayyahu da kifi, ya kalli Farhan yace "Hajiya ce ta bani tace in kawo miki kan ta zo, ki karɓa kici" Ta girgiza kai tace "Na ƙoshi" "Ki daure kici ko ba yawa saboda ki samu ƙwarin jikinki" "Naƙoshi" ta faɗa a raunane. "Hey, karɓi kici nace" ya faɗa cikin tsawa. A gigice ta karɓa hannunta na rawa, ta fara kokawar cin Abincin, amma kunya take ji, saboda a iya gaban Sadik take iya cin Abinci. Abbas yace "Sorry kin sa na miki tsawa, daure kici kinji" A hankali ta fara cakalar Abincin, kamar ba ta so. Abbas ya ɗan kalleta yace "Mhmm hira nake so muyi" Haushi ne ya fara kama Farhan, dan mutumin nan ya takurata sosai. "Zan tambayeki wani abu, ina son ki gayamin gaskiya kinji?" Farhan ta jinjina masa Kai. "Waye Sadik?". Wata irin ƙwarewa Farhan tai, wadda ta haddasa sakin plate ɗin hannunta! (Me ze faru idan aka jewa Mother da Nana a matsayin sirikarta? Wace irin rawa Abbas ze taka a rayuwar Farhan, Ya Sunusi ze kaya da sauran al'amura keep following my pen Ayshercool) Littafin nan ₦300 ne kacal. 0009450228 Aisha Adam Jaiz Bank 07063065680 KO kuje manhajar AREWA BOOKS ku siya. domin kuwa ya fi sauƙi ta can. Littafin nan ₦300 ne kacal. 0009450228 Aisha Adam Jaiz Bank 07063065680 KO kuje manhajar AREWA BOOKS ku siya. domin kuwa ya fi sauƙi ta can. Abbas ya ƙurawa Farhan ido, ya miƙe yaje fridge ɗin dake ɗakin, ya ɗakko ruwan roba, ya miƙa mata. Ta karɓa ta ɗan sha kaɗan ta ajiye, ya ɗakko flask ɗin Abincin nan, ya ajiye mata a gabanta yace "oya, ɗau spoon ki cigaba da ci" Jikinta na rawa, saboda wani irin kwarjini da yai mata, haka ta dinga cakalar Abincin nan tana ci. Gani yai idonta ya cika da hawaye, da alama dai kamar ya takura mata, ya kalleta yace "ajiye in kin ƙoshi" Aikuwa kamar jira take, ta ajiye kwanon Abincin. Ya sake kallonta yace "Oya, gayamin waye Sadik?" Mamaki ne ya cikata, a ina ya san Sadik? Ya a kai ya san shi?. "Mhmmm ke fa nake jira" Ta sunkuyar da kai tana wasa da yatsunta, tana kokawar maida hawayen dake ƙoƙarin zubo mata. Yace "shikenan, tunda ba zaki gayamin ba, bari idan Abbanki ya zo na tambaye shi, ko in gaya masa Shi Sadik ɗin yana da Alaƙa da rashin lafiyar ki" Cikin sauri ta ɗago kai, hawaye na bin fuskarta tace "A'a, dan Allah kar ka gaya masa" "Meyasa kar in gaya masa?" "Bakomai" "Ban yadda bakomai ba, ki gayamin gaskiya ba wanda zan gayawa" Tai ajiyar zuciya tace "ɗan makarantar mu ne" se kuma tai shiru. Yace "ina jinki, se kuma akai yaya daga nan?" Ta sunkuyar da kai taƙi magana. "Ko dai yana takura miki ne a makarantar, yana miki abunda ba kya so?" Tace "A'a" "To gayamin, Why you don't want him to leave you?" Ta ɗaga kai ta kalli Abbas, tana mamakin yadda akai yasan wannan abubuwan haka. Yace "Anyway, tunda ba kya son maganarsa, Yaushe kika fara rashin lafiya?" "I don't know" ta bashi amsa. "As how? I mean Yaushe kika fara jin wasu alamu na rashin lafiya" "Ba zan iya tunawa ba, kawai ina yawan jin faɗuwar gaba ne, bana kuma iya cin Abinci, and i thinks am having cancer" Zaro ido yai yace "how do you know that? Ke kin san meye Cancer kuwa?" Ta share hawayen fuskarta tace  'ban sani ba amma ina tunanin ina da tabbacin haka" "Asibiti kika je aka gaya miki haka?" Yai maganar yana kallon ta. Tace "No, ina gani a tv, ana faɗar symptoms ɗin, and am having some of the symptoms" Yace "Well, a ina kike jin Symptoms ɗin? And wace irin Cancer kike tunani?" Tai shiru ba tace komai ba, sema sunkuyar da kai tana wasa da yatsunta. Yace "na gane, but for how long kika fara jin Symptoms ɗin?" "Almost a year" ta faɗa cike da kunya. "Karki kuma jawa kanki wannan masifar, is not a cancer, ba yadda zaki zauna da wannan ciwon tsawon shekara guda ba tare da kin fara shan magani ba, ace bata nuna ba, what You Are feeling is just a homonal activities, ki kanji ciwon a lokacin da kika kusa fara al'ada ko bayan kin gama da wasu 'yan kwanaki, is normal, Da kinyi Aure zaki dena ji, da zarar Sadik ɗin ya fito a kai Aure zaki nemi ciwon ki rasa, alamu sun nuna kina buƙatar Aure ne, da zarar kimyi Aure zaki dena ji, sedai maybe when you are pregnant in the first trimester zaki ji ciwon, ko makamancin haka" Farhan ji tai kamar ƙasa ta tsage ta shige, saboda tsananin kunya, kuma hankali kwance yake mata bayani. "Ko akwai wani abu da yake damunki deep down inside your heart bayan wannan?, a shekarun ki be kamata jininki ya hau Sosai ba" Ta girgiza kai alamar bakomai. Yace "Mhmm Yaushe Sadik ɗin ze zo dubaki ne?" Jin tambayar da yai mata yasa Ta ɗauke kai daga kallonsa, tana hawaye. A take ya fara gano matsalar Farhan, yace "he broke your heart ko?" Tace "No" Ya ɗan ƙura mata ido, tayi yarinta da Love Crises, she's very young, koma dai menene, akwai depression a tare da ita, Kuma da alaƙa me ƙarfi a tsakanin ta da Sadik. Yace "ajin ki nawa yanzu?" "Jss3" ta bashi amsa. Ya ɗanyi shiru, gaba ɗaya ba ta fi Shekara goma sha huɗu zuwa sha biyar ba, amma tana ɗauke da damuwa, Yace "Shikenan, bari in bari ki sake samun nutsuwa, ma cigaba da maganar, amma tabbas ina son jin a gayamin waye Sadik ɗin nan" Ba tace masa komai ba har ya fita daga ɗakin. Nana kam an haɗa mata akwatinta cif, dan har an kai akwatin mota, ta ƙanƙame Inna tana kuka tace "Inna meyasa zaku turani in da ban san kowa ba? Wallahi Inna bana son yaron nan, Inna ya akai kika dena sona, da kula dani kika yarda a tafi dani in da babu idonki a kaina? Haba Inna ta, da wa zan rayu babu ke a in da nake" Ai duk yadda Inna take dakewa se kuka, tace "kiyi haƙuri Nana, Allah ya baku zaman lafiya, ki bi mijinki ki samu aljannar ki, na so in samu isashen lokaci tare da ke, amma baze yuwu ba, kiyi haƙuri kiyi karatu da kyau Allah yai miki Albarka, ki kula da tarbiyyar da muka ɗoraki a kai" Nana tana turjewa tana kuka, aka kaita Mota, se kuka take kamar wadda aka gayawa ranar mutuwarta. Hakimi ya ƙarewa Nana kallo yace "zanyi kewarki jikata, ko a 'ya'yan da na haifa, babu wanda nakewa son da nake miki, sedai ba yadda na iya". Ya kalli Sadik yace "ga ta nan, Amana a hannunka, Nana Yarinya ce me tarbiyya, da muka raina nasan wa na aura maka, nasan na maka laifi, amma nan gaba zaka gane gata nai maka, ka kula da Amana, idan kaci Amana Allah yana kallonka, Abdullahi kar a bari inji wani abu mara daɗi game da Amanata, kuje Allah ya sauke ku lafiya" Nana tana kuka, haka aka ja motar nan suka tafi, yayinda zuciyar Sadik kamar wutar ƙira, saboda wata irin wuta dake ruruwa a cikin zuciyarsa, jin Hakimi kawai yake, amma wannan Amanar kam ba abar karɓa bace a gurinsa. Ganin kukan na Nana a ta da niyyar denawa yasa Abba yace "haba Nana, kukan ya isa haka, kar kanki yai ciwo kinji, ki dena kukan nan haka ya isa" Faruk yace "hakane, ki dena kukan nan kar kanki yai kafin muje can gida" ya ƙarasa maganar tare da miƙa mata hankici, dan ta goge hawayenta. Wani uban tsaki Sadik ya ja, dan ko motsin Nana baya ƙaunar ji, duk da yau ce kusan zece ranar 'yanci a gareshi, bayan takure shi da akai tsawon lokaci, aka hanashi walwala kamar wanda ya karya dokar ƙasa, sedai sam baya farinciki da hakan, dan da ya tuna yadda aka katse masa hanzari aka aura masa baƙauyiya, se yaji wani marurun takaici ya tokare masa zuciya. Nana ba ta sake tsinkewa da al'amarin ba, se da suka shigo gari Sosai, wata fargaba ta lulluɓeta, dan bata san wace irin karɓa Mother za tai mata ba, dan tun ainihi dama Mother ba ƙaunarta take ba, balle yanzu da aka aurawa ɗanta 'yar ƙauye da ta ke ƙyama, kuma ɗan da take ganin be isa Aure ba. Wajen ƙarfe tara da rabi, Hajiya ta zo Asibitin, tai murna sosai da ganin cigaban da aka samu akan jikin Farhan, dan ta farfaɗo sosai, sedai tayi rama sosai da sosai, ga leɓenta da ya bushe. Hajiya tace "Sannu Farhan, ya jikin naki?" Farhan tace "Jiki da sauƙi Alhamdilillah, Nagode sosai Allah ya saka da Alkhairi yasa kifi haka" "Ameen, bakomai Farhan Allah ya ƙara miki lafiya, Ummanki tace a gaishe ki" Shiru Farhan tai ta sunkuyar da kai, yanzu idan ma mutuwa tai shikenan, sedai ta mutu ba tare da Umman ta zo ta ga halin da take ciki ba. Zuwan Hajiya babu daɗewa, sega Anty Uwani, wato babar Huzaifa ta zo. Nan suka gaisa da Hajiya, ta kalli Farhan tace "Sannu Farhan, gaba ɗaya kin rame lokaci ɗaya, Allah yasa kaffara ne, ya ƙara afuwa". Kasancewar Anty Uwani mace ce me faran faran, hakan ya sa suka saki jiki da juna ita da Hajiya suke ta hirar su. Farhan tai farinciki sosai, jin Abbas ya gaya mata ba ta ɗauke da sanƙaran mama (Cancer), wanda ta daɗe a cikin matsananciyar damuwa, da kokwanton ciwon ne ya kamata. Amma idan har dagaske doctor Abbas yake, da yace idan tai Aure zata dena jin Symptoms ɗin, sannan ta dena damuwa idan har dagaske yake Aure take so, meyasa ba ta farinciki da ɗokin Aurenta da Sunusi? Tabbas ba Aure take buƙata a yanzu ba soyayya da farinciki take buƙata, sedai gashi me samar mata da su ɗin yai nesa da ita, nisan da bata san a wani hali yake ba, balle soyayyarta. Kenan ta rasa Sadik ne? Kokuwa haryanzu matsalar ƙauyene na rashin network ya hanashi nemanta? Wata zuciyar tace "ko dai gidansu zanje in tambaya in ji?' Da sauri ta kauda wannan tunanin, ita a wa, za taje gidan su ta tambayi in da yake? To ko dai abokansa zata tambaya, su Amin?. "Ke Farhan, tunanin me kike hakane?" Firgigit Farhan ta dawo hayyacinta, ta kalli in da Anty Uwani take mata Magana. Hajiya tace "tunanin me kike haka, ki kai shiru ba ma kya jin abunda ake faɗa?" Farhan tace "bakomai" "A'a da Komai, akwai abunda yake damunki da alama, wanda ya haddasa miki wannan ciwon naki" Farhan tace "bakomai fa" "A'a, to ma naji bakomai amma tunanin me kike haka?" Tai shiru ba tace Komai ba, nan dai dau kai tai mata faɗa akan koma meke damunta, ta cire shi a ranta, ko dan lafiyarta. Ita dai jinsu kawai take, amma ba ta ji zata iya hakan ba. Nana na ganin sun shiga layinsu Sadik, ta sake fashewa da kuka, dan ta tabbata shikenan ita da Ƙauyen da ta tashi, nan ta fara saƙawa da warwara akan irin karɓar da zata samu a gidan su Sadik ɗin. Tana cikin tunanin ne taji an tsaya, Faruk ne ya fito ya buɗe murfin motar, da yake tana baya ita da Abba. Tuni Sadik ya fita daga motar yai cikin gida, ba tare da ya jira kowa ba. Faruk ya ɗakko Akwatin Farhan, suna gaba, tana binsu a baya tana share hawaye. A falo Sadik ya tarar da Mother, ta ƙarasa da sauri ta rungume Sadik, hadda hawayen farinciki, tace "I miss You my son" Magana Sadik yake son yi, amma ya kasa se murmushi me haɗe da ƙunar zuciya da yake yi. Ta ɗago ta kalli Sadik tace "Kai sannu Sadik, duk kayi wani iri Allah sa ba rashin lafiya kai ba, naga idonka duk kai zur zuru" Sadik kawai ya sunkuyar da kai, wata ƙwallar baƙin ciki ta taru a idon sa. "Sadik meyafaru ne? Ka gayamin mana" Tana ɗaga kai sega Abba ya shigo, shida Faruk, taga Faruk da ƙatuwar Akwati, ba ta kai ga yin Magana ba sega Nana ta shigo, tana duƙar da kai kamar munafuka. Wani kallon banza Mother tai mata sannan ta kalli Abba tace "Sannu da zuwa" Abba yace "Yawwa" Sadik na ganin Nana, ya saki Mother ya juya ya nufi ɗakinsa da ke Falon Ya shiga ya rufe ƙofa. Abba ya kalli Nana da ta ke tsaye a bayan kujera tana rarraba ido yace "ya haka, ke da gidanku ƙaraso ki zauna mana" A ƙasa Nana ta zauna, tana share hawaye. "Abba ban gane meke faruwa ba, naga Sadik duk yai wani iri" Abba yace "An gutsuri wani abu a jikinsa ne?" Tace "A'a" "To me kike son ji, ba dai gashi nan an dawo da shi ba, ba su cinye shi ba ai" Tace "Allah ya baka haƙuri" Abba yace "Nana, ɗau Akwatin kije ɗakin da kuka sauka lokacin bikin dr., In ba a gyare yake ba, kiyi magana a gyara miki" Nana ta ɗau Akwatinta tai gaba, ita ta manta ma ko Mother ba ta gaisar ba, saboda tsabar tsoro da fargabar karɓar da za tai mata. Faruk kuwa tuni ya fice, dan baya son ganin dambarwar rikicin da za'ai s Gidan, dan ya san ba ƙaramar rigima za'ai ba a gidan. Ɗakin Sadik Mother ta fara zuwa, ta tarar da shi a kwance akan gadonsa, ya ƙurawa roofing ɗakin ido. Mother tace "Wai kai meke faruwa ne?" Sadik ya girgiza kai yace "bakomai" "Kamar ya bakomai, nagan ku duk wani iri, kuma me wannan yarinyar ta zo Gidan za tayi?" "Mother, I don't have answer for all this your questions, allow me to rest please" Mamaki ne ya cika Mother, musamman ganin hawaye na zubowa daga idon Sadik. "Sadik, meyafaru haka kake kuka?" Sadik baya son cigaba da Magana, dan haka ya miƙe ya shige toilet ya rufe ƙofa. Se kuma tai tunanin ko dan harya gama zamansa a garin ba taje ta ganshi bane, shine yake fushi?. Ƙofar toilet ɗin taje ta tsaya tace "kayi haƙuri Auta, nasan ba a kyauta maka ba, amma ba yadda ban ba Abbanka ya ɗakkomin kai amma yaƙi, nace zanje in ganka nan ma ya hanani, dama nasan ba jin daɗin zaman garin nan kai ba, amma kayi haƙuri kai wanka ka fito, zan kawo maka Abinci in baka da kaina" Har Mother ta gama surutunta, Sadik be tanka ba sema kunna shower da yai, dan ya dena jiyo sautin Maganar Mother, ya lumshe idonsa hawaye na zirarowa daga idonsa. Da tsananin Mamaki Mother ta nufi part ɗin Abba, ta tarar ya cire Babbar rigarsa yana waya, ta kalli bedside taga ya ajiye uban goro da alawa, ɗan taɓa baki tayi, ta shiga kawo masa Abinci. Be ce mata uffan ba ya fara cin abincin sa, ta kalleshi tace "Dan Allah Yallaɓai meke faruwa ne?" "Wai me kika gani ne?" "Ganinku nai gaba ɗaya wani iri, kamar wani abu na faruwa" "Ba abunda yake faruwa se Alkhairi" ya bata amsa. Can ya ɗago yaga yadda ta zuba masa ido yace "yawwa ina fatan an bawa Nana Abinci?" Ta ɗan yatsuna fuska tace "namanta ne, bari in magana a bata" Ta miƙe ta fita, tana zuwa falo Khairat ta dawo daga Makaranta, tace "Mother na dawo" "Sannu da zuwa, Sadik dai ya dawo" Cikin murna Khairat tace "Allah sarki bestyna, yana ina?" "No, karki je in da yake yanzu ban san me akai masa ba, naga baya walwala" "Amma dai lafiyarsa ƙalau ko?" "To gashi nan dai ban gane masa ba" Khairat tace "ina ga fushi yake, bari in bari zuwa anjima na je gurinsa" Mother ta manta da abunda ya fito da ita, ta ɗakko kwanukan Abinci ta shiga ɗakin Sadik, amma ta tarar da shi a kwance, ya lumshe ido ksmsr me bacci. Mamaki ya kuma kamata, yana jik motsinta, amma ya rufe ido kamar yana bacci, ta ajiye masa Abincin ta fita daga ɗakin. ta koma gurin Abba, ta tarar ya gama cin Abinci, ya kwanta. So take ta kuma masa magana, amma yaƙi bata fuska sam. Rabon Nana da Abinci tun jiya da safe, Inna tayi tayi tai kurarin amma Nana taƙi cin Abinci, har zuwa yanzu ba ta ci Komai ba, ga yunwa ga damuwa nan da nan kanta ya hau ciwo, har da zazzaɓi. Se bayan Abba ya idar da sallar la'asar ya shirya ze fita, sannan ya zauna a gefen gado, ya kalli Mother yace "Hauwa" Tace "Na'am" Yace "Na sani kin sani, Annabi Sallallahu alaihi Wasallam yacewa Sahabban sa, shin bana sanar da ku manya-manyan zunubai ba, Sahabbai sukace gayamana ya ma'aikin Allah, yace da su 'Shirka da Allah, saɓawa iyaye, da kuma shedar zur, Kin sani saɓawa iyaye laifi ne me girman gaske a gurin Allah, sannan kowane mumini ba ya zama mummuni se ya yadda da ƙaddara, me kyau ko akasinta, ɗa baya taɓa girma a gurin iyaye, kamar yadda haryanzu mukewa Usman kallon yaro ƙanƙani har muke zaɓa masa wasu abubuwan game da rayuwarsa, to muma haryanzu hakane, ba'a girma a gurin iyaye, kuma duk hukuncin da suka yanke akan ɗa, in dai be saɓawa mahalicci ba to tabbas be dace ga ɗa na gari ya bijire ba, dan Iyaye ba zasu Cutar da ɗan da suka haifa ba. Dan haka nake son ki tayani yiwa iyayena biyayya, Kamar yadda ban taɓa yunƙurin ganin kin saɓawa naki iyayen ba, nima ina so ki bani ƙwarin gwiwar da zan bi nawa iyayen, tunda iyayena naki ne. A dawowar mu kinga abubuwa da kike buƙatar bayani, na zo da Yarinya ba tare da na gaya miki meyasa na taho da ita ba, duk da hakan ba abun damuwa bane, dan ina da hurumin ɗakko duk wanda nake so ya zauna a gidana. Wannan goron da kike gani, na ɗaurin Auren ɗanki ne!!!" A zabure ta kalli Abba tace "ban fahimce ka ba, wanne daga cikin 'ya'yan nawa?" "Abubakar Sadik!" "What! Sadik ɗin akaiwa Aure?" "Eh shi ɗin, tun wancan Zuwan da nayi, Hakimi yace lallai in nemawa Nana karatu a ƙasar da Sadik zeje karatu, jiya kuma bayan sallar juma'a ya ɗaura masa Aure da Nana, ban san dalilin Hakimi na yin haka ba, amma koma dai menene nasan dalili ne me ƙarfin gaske, dan haka ina fatan ni da ku mu karɓi hakan a matsayin ƙaddara mu riƙe yarinyar nan kamar tamu, danni 'yata ce kin sani, Hakimi ya gindayamin hatsari me girman gaske, akan idan wani abu ya samu Auren nam be yafemin ba" Miƙewa Mother tai tace "Ya isa haka, wannan kai kanka ka san ba abune me yuwuwa ba, shikenan ni bani da iko ko martabar da za'a tuntuɓe ni kan a yankewa ɗa na hukunci? Wane irin abune wannan za'aiwa yaron da be san komai ba Aure? Me Sadik ya sani dudu guda nawa Sadik ɗin yake da za ai masa Aure, kuma a rasa wadda za'a aura masa se wannan yarinyar? Shikenan ni bani da iko akan yarana? Sedai ai duk hukuncin da ake so akansu, ko hakan yaimin ko be min ba? Da sake a wannan karon baze yuwu ba" Dama Abba ya san hakan zata faru, dan haka Abba yace "na biyo miki ta laluma amma naga baki gane yaron rarrashi, kiyi abunda kike ganin shine daidai, nima zan abunda ya dace" Fuuuu tai waje daga ɗakin, ta wuce ɗakin Sadik ta tarar da shi akan sallaya alamar salla ya idar, yai shiru yana tunani. "Kai dama abunda aka ƙullo kenen? Har nake tambayar ka menene kace min bakomai, wato kana sane kaje kace musu Aure kake so ko? Me ka sani a game da Aure? Shikenan ka gurgunta rayuwarka, kazo matsaloli su addabeka ka bi ka tsofe" "Haba Mother, tayaya kike Tunanin zance sumin Aure, in ma hakane ya za'ai ince A auramin wannan baƙauyiyar, tausyawarki nake buƙata ba wannan faɗan da kike min ba" Se kuma jikin Mother yai sanyi, ta zauna a kusa da shi tace "kana nufin baka son Auren nan?" ."Mother ya za ai ince ina so, na tsani Yarinyar nan ko ganinta bana ƙaunar yi" "Shikenan, ka kwantar da hankalinka, in dai wannan ne an gama, dole Auren nan ya mutu" "Amma Mother, Hakimi yace be yafe ba idan wani abu ya samu Auren" "Kana son Auren kenan?" "Mother dan Allah ki dena faɗan haka, wallahi bana so" Tace "in dai baka so ai shieknan, shi Hakimin ai ba ubanka bane da Allah ya isansa zata bika, tsabar son zuciya ne irin nasu, da kuma tasanar da suke min ta shafeku shiyasa aka maka wannan Auren, dan a cusan takaici, zan nuna musu nima 'yar yauce, dan an gaji da wannan abun nasu, ka kwantar da hankalinka kaci Abinci" Sadik ya jinjina kai cike da jin ƙwarin gwiwa, akan kalaman mahaifiyarsa. Da Yamma Abba yazo sake duba jikin Farhan, yaga da sauƙi sosai dan har hira sukayi. Abbas ya shigo ɗakin, yana ganin Abba yai murmushi yace "Baba sannu da zuwa" Abba yace "Yawwa, Sannu da ƙoƙari, muna ta godiya fa Allah ya saka da Alkhairi" "Ai bakomai, insha Allah zuwa gobe in Allah ya kaimu zamu iya sallamarta, muna monitoring ɗin hawa da saukar jininta ne, amma in ba zaka damu ba, ina son muyi magana da kai a Office ɗina" Abba yace "badamuwa" Kallon Abbas take, tana fatan Allah ya sa ba zancen Sadik zewa Abba ba. Bayan sunje Office ɗin, suka ƙara gaisawa, Abbas ya kalli Abba yace "wato Baba, a yanayin jikinta abunda binciken mu ya tabbatar mana shine, damuwa taiwa Yarinyar nan yawa, ko kai a shekarunka idan jininka ya kai kamar nata, dole a ɗoraka akan magani, tayi ƙanƙanta da fara shan maganin hawan jin" Abba ya dafe ƙirji yace "hawan jini kuma?" "Yes of course, hawan jini gashi shikansa jinin be wadaceta ba, saboda bata cin Abinci, abu na farko Baba Al'ada ba addini bace ba, babu in da akace dan ka haifi ɗa shine na fari kai watsi da shi da lamuransa, Yakamata mahaifiyarta ta ajiye wannan al'adar ta ja 'yarta a jiki ta san meye damuwarta, naso in bugi cikinta inji amma na fuskanci tana da tsananin kunya da zurfin ciki, ko kasan ta rayu tsawon shekara guda da tunanin tana ɗauke da ciwon Cancer wanda ba haka bane?" Abba ya zaro ido cike da Mamaki "Mahaifiyata yakamata ta san wannan, wanda in Asibiti ya kama a kaita a duba a kaita, amma babu wanda ya sani, Mutane masu hali irin na Farhan suna buƙatar ja a jiki da nuna musu soyayya, yadda zasu saki jiki har a dinga jin matsalolin su, idan aka cigab da tafiya a haka sakamakon da ze biyo baya baze daɗi ba, Mutane masu irin personality ɗinta are at risk of having depression, daga lokacin da ta samu depression ƙwaƙwalwata zatai ta gayamata abubuwa ba daidai ba, zata tsame kanta daga Mutane, da tunanin kowama baya sonta, in a kai rashin sa'a za'a iya wayar gari aga ta kashe kanta, ko a ganta a wata mummunar hanya wadda ba'a fata. Yanzu babban abunda nake ƙoƙarin yi shine, inga ta kwantar da hankalinta, yadda ko bata faɗi meye damuwar tata ba, a samu jininta ya sauka aita sa ido dan Allah" Abba yai ajiyar zuciya, dan yaji tsoron bayanin doctor Abbas, Abba yace "Nagode sosai da wannan bayanin naka doctor, Insha Allah za'a sa ido a kanta, Allah ya wuce mana gaba" "Ameen" Abbas ya amsa. Daga nan Abba ya tashi ya tafi yana tunani daban daban a ransa. Bayan fitar su Abba kuwa, Anty Uwani ta sa Farhan tai wanka, ta fito tai salla ta bata Abinci, ba wani ci tai ba, Anty Uwani tai mata sallama tace zata gida ta dawo. Fitar Anty Uwani ba daɗewa, kawai sega Sunusi ya shigo ɗakin da Farhan take shi da Huzaifa, Huzaifa se tuttura baki yake. Nan da nan Ta haɗe rai kamar ba ta dariya, taƙi ko kallon in da yake, yana shigowa ya turare ɗakin da warin hannatarsa me maƙaƙi a wuya. Huzaifa kuwa juyawa yai ya bar ɗakin, dan ya tsani Sunusi shima. Ya ƙarewa ɗakin kallo Sannan yace "Ya jikin naki?" "Da ssauƙi" ta amsa a ciki. "Ki dena Wannan cunkusa fuskar, dan ba abunda ze sauya, a satin nan za'a kawo kuɗin Aurenmu" Ko kallonsa ba tai ba ta ɗauke kanta daga kallonsa. "Hmm yarinya kenan, ai ranar a idona aka ɗakkoki daga gida, wani shinƙimemen ƙato ya ɗakkoki kamar inje in bazar da shi, ai an san ina unguwar saboda tsabar wulaƙanci ni ba a aika an kirani na ɗakkokin ba, se wani zindiƙin ƙato za a kira ya ɗauke ki ina mijinki, wannan ai ba yi bane" "Karka ƙara kiranka da mijina, na gayamaka" "Wallahi ko kinƙi ko kin so, nine nan mijinki ke mallakina ce" "Ke tawace Farhan, babu wanda ze mallakeki seni, duk wanda yai gangancin yin hakan, zan nuna masa abunda zan iya yi akanki" Maganar Sadik ce ta dawo mata, gaba ɗaya taji jikinta yai sanyi. A hankali ta furta "come back to me Prince" "Me kike cewa ne?" Sunusi yai maganar yana zuri kansa daf da ita. "Dalla meye hakane, karka sake ka sa jikinka a nawa" Buɗe ƙofar akayi, wanda yasa Sunusi daidiata nustuwar sa. "Farhan did they serve your medications?" Abbas ya shigo yana magana. Ta girgiza kai alamar a'a, sam be lura da wani Sunusi a gurin ba. Sunusi kuwa ya gane shi, dan ya kan ganshi a layinsu, yazo gidan Hajiya, sedai yaga Abbas ɗin yai masa kwarjini sosai. Farhan tace "A'a, amma a bari se anjima" ta faɗa a Sanyaye. "Ni, yanzu ne lokacin yi, nasan allura ce ba kya so, sedai kiyi haƙuri, ba kiga because you are so special yasa nake miki allura da baki magani da kaina ba, bana son Nurses suyi miki me zafi" Tai murmushi ba tace komai ba, yayin da Sunusi ya cika yai fam. Abbas ya haɗa allura, ya kamo hannun Farhan, ya buɗe canula yana mata, yanayi yana shafa kan jijiyar da canulan take, saboda kar tai mata zafi, amma shi Sunusi se yaga kamar da Iskanci Abbas yake hakan, kuma tai fusuƙi da kai tana kallonsa. Ya kalli Fuskar Farhan yace "Ai ba zafi ko?" Tai murmushi tace "eh" Yace "Yawwa, ai dama na gaya miki ba zafi, saura ta baya se kuma in sa miki drip zan tafi gida". A ɗan shagwaɓe tace "wayyo Allah" Abbas yace "to yi kuka kawai mana, kin samu lafiya ne shiyasa kike kuka" Sunusi ji yake, kamar ya dunƙule hannu yai ta kirɓar Abbas. Abbas ya kalli in da Sunusi yake, wanda se da ga baya ya lura da shi a ɗakin yace "ɗan bamu guri zamuyi allura ko?" "Ba inda zani, nace ba in da zani, tunda nine mijinta ayi a gabana mana in ba munafunci ba se lailaye mata jiki kake, Wato in baku guri kaji daɗin yi, to ba zan fita ba" Abbas ya zare gilashin idonsa yace "Kaine mijin nata ko wa?" "Eh nine nan, kallon ku ai kawai nake" "I don't fucking care who so ever you are, kaje waje zan mata Allura, kuma ni babu wanda yacemin matar wani ce, tunda aka kawota mahaifinta nake gani a kanta, dan haka ka bamu guri" Abbas ya kalli Farhan yace "wai ma waye wannan?" Kuka Farhan ta saka ta kasa magana. Be kuma cewa komai ba, yai waya gate sega security da bindiga yazo ya fitar da Sunusi. Har gari ya waye tsakanin Mother da Abba, ba wanda ya kula wani kowa sabgar gabansa yake da saƙa abunda yake ganin shine daidai a gareshi. Da safen Abba harya shirya ze fita, yaje ɗakin da Nana take dan ganin halin da take ciki, ya tarar da ita a kwance a ƙasa. Abba ya ƙarasa da sauri, yace "Nana, kwanciyar me kike a ƙasa haka?" Nana ta tashi zaune tace "Abba ina kwana" "Lafiya ƙalau, meyasa kika kwanta a ƙasa?" "Zazzaɓi nake ji shiyasa" "Meysa baki faɗa ba to, ai da ko maman naki kin gayawa, wannan kukan da ki kai ai dole kiyi zazzaɓi" Tace "Ai ban ganta bane, shiyasa ban gayamata ba" Ya kalli idon Nana, ya ga yadda tai wuri wuri kusan kamar ma a galabaice take, yace "kinci Abinci kuwa?" Ta girgiza kai alamar a'a. "Jiya fa an baki Abinci?" Tace "eh" "Gayamin gaskiya, an baki ko ba a baki ba?" Yai maganar cikin razanarwa. Tai sauri tace "A'a" Abba ya jinjina kai yace "dole in nunawa yaron nan da uwarsa a ƙarƙashina suke, zasuga matakin da zan ɗauka. Littafin nan ₦300 ne kacal. 0009450228 Aisha Adam Jaiz Bank 07063065680 KO kuje manhajar AREWA BOOKS ku siya. domin kuwa ya fi sauƙi ta can. Littafin nan ₦300 ne kacal. 0009450228 Aisha Adam Jaiz Bank 07063065680 KO kuje manhajar AREWA BOOKS ku siya. domin kuwa ya fi sauƙi ta can. Abba ya tashi Fuuuu ya fice daga ɗakin da Nana take, an ɗan jima kaɗan sega Talatu ɗaya daga cikin masu aikin gidan ta kawo wa Nana Abinci. Tace "Nana, ya akai ki ka zo ban sani ba, baki nemi kowa a gidan nan ba?" Murmushin ƙarfin hali kawai Nanan tayi, idanunta sunyi jawurr sun kumbura. Tace "Yallaɓai ne yace a kawo miki Abinci, Ya kike ya Hajiyar?" Nana tace "tana nan lafiya" "Madalla, ashe ba da ita kuka zo ba" Nana ta fara ƙosawa da hirar Talatun, dan haka tai shiru, ta haɗa tea ta fara sha saboda yadda cikinta yake a ƙulle. Sosai take cin Abincin ba dan tana so ba, sedan azabar ƙullewar da cikinta yai. Daga Inna har Hakimi babu wanda yai baccin kirki, mussaman Inna da ta dinga kuka cikin dare, akwai shaƙuwa me ƙarfin gaske tsakanin ta da Nana, lokaci ɗaya ba tare da ta shirya ba, an raba su. Abba kuwa yana zuwa gate, ya kira security. Cikin hanzari yazo cikin girmamawa yace "gani ranka ya daɗe" Abna yace "Dan Allah, daga yanzu zuwa lokacin da Sadik ze bar Gidan nan karka kuskura ka barshi ya fita, idan kuwa har yai maka gardama ka harbe shi a ƙafa" Buɗe baki security yai da mamaki, ɗan Auta kuma shalelen ake cewa a harbe, Abba yace "Umarni nake ba, idan ba kai abunda nace ba ka bari ya fita, to kai zan harbeka" Jiki na tsuma yace "shikenan, insha Allah baza'a bari ya fita ba" Daga haka Abba ya fice daga gidan. Sadik kuwa tun daga ƙwarin gwiwar da ya samu daga gurin Mother yaji zuciyarsa ta ɗanyi masa sanyi. Wayoyinsa ya ɗakko ze saka a caji, dan yau da Yamma yana son fita ya sha iska, sedai ya tuna ya baro simcards ɗin sa duka a can ƙauye, a ƙulle a ƙasan kilisai. Wani dogon tsaki ya ja, ya jona wayoyin, sannan ya fita BQ. Yana zuwa ya tarar da Faruk yana karyawa, Faruk yai masa murmushi yace "Ango Ango, Ango ka sha ƙamshi Allah ya karɓi Addu'ar ka kayi Aure ka barni" Tsaki Sadik yai yace "Wannan har wani Aure ne? Da shi da babu duk ɗaya dan babu abinda na tsana sama da Yarinyar nan" Faruk ya Ajiye kofin hannunsa yace "A'a Sadik, koma menene babu laifinta a ciki, ba ita tace tana sinkaiba, yadda a kai maka ba zata ita ma haka a kaimata, dan haka karka cutar da Ita Sadik" "Ba abunda yai min zafi, yadda kakaninta suka dinga azabtar dani akanta zan rama, kuma da ƙafafuwanta zata koma in da ta fito, zata gane kurenta" A ɗan hasale Faruk yace "Sadik, ka manta abunda Hakimi yace maka, amana ce a gurinka" "Mother tace ai ba Ubana bane, dan haka ba abinda ze faru dan ban bi son zuciyarsu ba" "Sadik! Are You mad? Babu biyayya ga abokin halitta gurin saɓawa mahalicci, a nan gurin be kamata kaiwa Mother biyayya ba, kakanmu mahaifinmu ne tunda yai silar kawo mahaifinmu duniya, a tunaninka da baffansu Mother yana raye shi ya ɗau wannan hukuncin zata gaya maka haka ne? Mahaifiyarmu ce amma Yakamata mu dimga tunani akan wasu abubuwan" Sadik yace "Stop it please, babu wani abu da zaka gayamin da ze sa in sauka daga kan bakana, bana ƙaunarta kuma ba zan zauna da ita ba, se ta koma ƙauyensu, dan yadda suka azabtar dani sena rama a kanta" Be kuma sauraron Faruk ba yai waje, ya bar shi da buɗaɗɗen baki. A harabar sukai karo da Khairat, cikin fara'a da murna Khairat ta nufi in da Sadik yake, sedai ko kallo ba ta isheshi ba, saboda yadda ransa yake a ɓace. In da masu aikin Gidan ke hutawa ya nufa, yana zuwa ya kallesu yace "Ina Bala?" Security yace "ya fita da Alhaji" Sadik ya kalli security yace "buɗemin ƙofa zan fita" "Zuwa inam" ya tambayi Sadik. "Ban gane zuwa ina ba, ka aikeni ne?" Ya faɗa a hasale. "Am sorry, megida yace kar in yadda in bari ka fita, in kai gaddama a harbeka a ƙafa" Saroro Sadik yai yana kallon security, tabbas baya wasa da su, balle ace tsokanar sa suke, wannan maganar Abba ya faɗe ta. Da sauri ya koma cikin gida, ya iske Mother a kitchen cikin ɓacin rai. "Lafiya kuwa?" Mother tai Maganar tana ƙare masa kallo. "Mother, wai Abba yace kar a kusakura a bari na fita, wai idan nace sena fita a harbeni, abun har ya kai haka?" Mother tace "Ai babu uwar da ta tsuguna ta haifi baturen da ya sarrafa bindigar harbinka, duk wanda ya harbeka sena sa an ɓatarmin da shi, rabu da shi duk dan ya muzguna mana ne ni da kai, kuma ba gudu ba ja da baya sena kashe Auren nan murus, ƙyaleshi kar ka sake attempting zaka fita ma, ka nuna masa baka damu da hakan ba" Sadik ya sauke ajiyar zuciya, cike da takaici ya juya ya bar Kitchen ɗin. Abba da kansa ya kawowa Nana magani, ya bata ta sha, sannan ya fita. Gaba ɗaya ya tattara Mother da Sadik yai watsi da su, ya dena shiga sabgar kowa a cikin su, ya cigaba da harkokin sa. A masallaci ya sanar da ɗaurin Auren Sadik, kuma ya shirya ƙwarya ƙwaryar walima shi da abokansa, suka taya shi murnar Auren Sadik. Yayin da a ɓangaren Mother abun kunya ne a ce anyi auren ɗanta a haka, Auren mara galihu. Sunusi kuwa tunda ya bar Asibitin ya dinga mita yana masifa akan abunda Abbas yayi masa, tare da cin alwashin akan Farhan ze rama abunda a kai masa. Tun da Sadik ya dawo, Khairat take son yi masa Magana, amma babu fuska dan ko falo baya fitowa a ɗaki yake wuni, ko BQ baya zuwa saboda yadda Faruk yake sa shi gaba yana masa Nasiha. Ɓangaren Nana ma ko da wasa bata fitowa ko falo, saboda tasan aranagamarta da Mother abun baze mata kyau ba, kullum tana ɗaki Talatu ke kawo mata Abinci, kasancewar akwai banɗaki a ɗakin, a ciki take wanka ta wanke kayan da ta cire, ta shanya a ciki. Talatu na ta son dukan cikin Nana, dan ta fuskanci abunda yake faruwa, amma Nana taƙi Magana. Wata irin kewar gida take sosai da sosai, tana kewar Inna da makarantar ta da ƙawayenta. Kullum se Abba ya zo ya dubata, sun gaisa da kansa yake tambayar ta idan tana buƙatar wani abu, se tace masa ba ta buƙatar komai. Ƙarfe takwas na dare Dr. Ya zo gidan, ɓangaren Mother ya nufa kai tsaye, tana ganinsa tace "kai kaɗai, ina Jiddan?" Yace "Ba ta jin daɗi ne, shiyasa na taho kawai" Mother tace "too, ko ciki ne?" Dr. Ya ɗan ɗage kafaɗa yace "i dont know" "Kamar ya You don't know? Baku je Asibiti an dubata bane?" "Bata son Zuwa Asibiti, wai tana tsoron Allura, she prepare to take drugs, ni ba zan takurata ba" "But atleast, yakamata kuje Asibiti a tabattar da me ke damunta, zuwa yanzu ai ba abun mamaki bane ta samu ciki, ai kun huta dan nasan wataƙila wani abun ku kayi, shiyasa ba ta haihu ba" Murmushi kawai Dr. Yai, bece Komai ba. Mother ta sa aka kawo masa fruit, dan be fiye cin Abincin dare ba. Yana cikin ci Mother ta kalleshi tace "hmmm ka san abinda Babanku kuwa yayi?" Dr. Cikin ko in kula Yace "me yayi?" "Sadik ya dawo ai shekaranjiya" Yace "Wow, that's good se hankalinki ya kwanta ai" "Hmmm, ka san wai Anyiwa Sadik Aure?" "Aure Kamar yaya?" "Hmm, ai ni nama rasa ta in da zan fara maka bayani, baƙin ciki ya hanani in kiraka in sanar da kai" Dr. Yai murmushi yace "that's good" "Kamar ya that's good?" "Ahh abunda yake so ne ai ya samu?" "Kai Maganar Sadik wata maganar kirki ce? Me Sadik ya sani banda salon lalata shi da za'ai masa wani Aure? Me Sadik ya sani guda nawa yake? Ko degree be haɗa ba yaron da Just recently ya kammala secondary, shima dan an masa jumping, wai shi a kaiwa Aure, kuma a rasa wadda za'a aura masa se wannan 'yar ƙauyen jikar ta su" Usman yai murmushi yace "Children of now adays are beyond your expectations, karki zafafa ki zo ya baki Kunya" "Ai bazan ɗau wannan abun da a kaimin ba, dole in kashe Auren nan" Usman a ransa Yace 'haifar Sadik ki kai, amma baki san waye ba, baze iya haƙurin da nai ba, ya fito gatse gatse ya gayamiki Aure yake so, amma kina cewa be san komai ba, be san komai ba ya akai yasan yana son Aure?" Wani murmushi ya sake yi a fili yace "bari inje mu gaisa da Abban" Mother ta ɗan taɓe baki tace "seka dawo" Ya miƙe ya bar part ɗin Mother, yana mamakin yadda ta rintse idonta taƙi kallon gaskiya. A falon sashin Abba ya tarar da shi yana kallon CNN. Dr. Yace "barka da hutawa Abba, ai ban san ka dawo ba" Abba yace "na shigo tun ɗazu ai, naga motarka na san kana gurin mahaifiyarka, kaima tana maka famfo akan yadda zaku haɗu ku juyan baya ko?" "Haba dai Abba wane ni? Ba haka bane ba" "Amma dai ta gaya maka abunda ke faruwa, ina ga tun a shakranjiya ta kiraka ta sanar da kai abun da ya faru?" Usman ya gyara zama yace "No, ban san meke faruwa ba gaskiya se yanzu da na zo take gaya min" Abba ya numfasa yace "Usman, ni kaina banji daɗin matakin da Hakimi ya ɗauka akan Sadik ba, Sadik yayi ƙanƙanta da Riƙe Aure baze iya ba, amma ba zan iya bijirewa umarnin mahaifina ba, saboda dani da ku duk mallakinsa ne, amma abun mamaki se ga mahaifiyarku tana nema ta ɗagan hankali ta sa in bijirewa umarnin su dan in faranta mata". "A'a ba haka bane Abba, ka san tana kallon Sadik ɗin ne yaro har yanzu, kuma ya nuna mata baya son Auren, kasan yadda take son sa" Yace "duk da haka dr. Ba yau mahaifiyarku ta fara nuna min iyakata ba akan dangina na ƙauye, tana nuna min abubuwa da dama amma ina kawar mata da kai ta kasa ganewa, yanzu kalli yarinyar nan matar Sadik ɗin, tare muka zo gidan nan da ita, tare zasu tafi London, amma Yarinyar nan ta wuni ta wayi gari ba a bata Abinci ba, ta kwana da zazzaɓi ba wanda yabi ta kanta seni, ai yau ku 'yar tsintuwa na kawo nace Hauwa ta riƙe min,be kamata tai min haka ba" "Hakane Abba, amma kayi haƙuri dan Allah" "Haƙuri ai sedai in ɗora akan na baya, sedai zan nuna mata ku da ita a ƙarƙashin ikona kuke, idan ita ban isa da ita ba, ku na isa da ku ai, dama dalilin da ya sa na kiraka shine, in ban takura maka ba, sonake ka tafi da Nana gidanka, zuwa lokacin da zasu tafi, dan tata visa haryanzu bata fito ba, amma in kana ganin ba matsala ban takura muku ba" "Haba Abba, babu wata matsala ko takura, zan tafi da ita Insha Allah, ko cewa kai in riƙeta a gidana zan riƙe ta" Abba yai murmushi yace "Allah sarki, haihuwa me rana, nasan da kai akaiwa Auren nan ko Faruk ba wanda ze ɗagan hankali, ta ɓangaren ka ba zan gane kai murna ko akasin haka ba, Faruku kuwa baze taɓa nunamin ɓacin ransa ba, se Sadik amma shima zanyi maganinsa, zuwa da safe in Allah ya kaimu se kazo ka ɗauketa koma in kawo ta da kaina" "A'a Abba, a taso ta mu tafi yanzu kawai" "Kana ganin ba matsala?" "Abba babu wata matsala sam" Abba yace "to shikenan, Allah yayi albarka ya a baka masu jin ƙan ka" ya amsa da Ameen Abba. Abba da kansa yaje ya ƙwanƙwasa ƙofar ɗakin da Nana take, ta taso ta buɗe yace "maza ɗakko akwatinki" Seda ta ɗan tsure, dan ba ta san dalilin hakan ba. Ta ɗakko Akwatin ta, ta fito falo karon farko tun randa suka zo bata fito ba. A falo taga Usman, ta gaishe shi ya amsa tare da cigaba da abunda yake. Jin hayaniya a falo yasa Mother ta fito, ta tarar da Nana da Akwatinta, ga Dr. Yace "Mother seda safe, dare ya fara yu" Mother za tai magana amma Abba na tsaye a gun, ya kasa ya tsare ya raka su har bakin mota, se da suka tafi sannan ya dawo, da ya dawo ɗin ma be kula Mother ba, ya wuce sashinsa. Nan Mother ta tsaya tana tunani, meyasa Dr. Ya tafi da Yarinyar nan. Ɗakin Sadik ta nufa amma taga ya kashe fitila, dan haka tai tunanin ko bacci yake, Sadik kuwa idonsa biyu kallo yake a system ɗin sa, wanda ya haddasa masa damuwa, ya dafe kansa yana ƙoƙarin yin tunanin wani abu me mahimmanci a tare da shi amma ya kasa, gefe guda kuma ga wata irin fitina da take damunsa, a hankali ya fesar da iskar bakinsa ya kashingiɗa ya lumshe idonsa. Tunda suka fara tafiya da Nana, ba wanda ya cewa wani komai daga dr. Har Nana, dama dr. Ba me magana bane dama Faruk ne. Suna tafiya Mother ta kira dr. A waya, ba tunanin komai ya ɗaga ya sata a hansfree. "Dan ubanka me kuke shiryawa kai da ubanka, ina zaka kai Yarinyar nan?" "Gidana zata koma" ya bata amsa kai tsaye. "Akan wani dalilin? Meyasa zata koma gidan naka?" "Eh Abba ne yace ta koma can, shiyasa na zo na tafi da ita" "Amma kuma shine baka gayamin ba? Za kai gaban kanka" Usman yace "to Mother ai banga wani abu a ciki ba" "Ai baka da hankali dama, kai da Faruk wasu lokutan baku san abunda yakamata ba dama, ka kyauta" Usman kawai ya Ajiye wayar tare da girgiza kai. Suka ƙarasa gidan dr., Ya buɗe bayan motar ya ɗakko Akwatin Nana yai cikin gida, ba ta da zaɓin da ya wuce tabi bayansa. Cikin sauri tabi bayan nasa, sedai da yake cikin sauri yake tafiyar ya rigata shiga falon. Tana zuwa ta tarar da shi a tsugune a gaban 3seater, Jidda na kwance da wasu irin fitinannun sleeping wears, yana magana ƙasa ƙasa "ko dai zamu tafi Asibiti, har yanzu jikin ki da zafi fa" "A'a Baby na sha magani fa" Kallo ɗaya Nana taiwa Jidda taji wata kunya ta kamata, yadda take zaune ƙanin tsirara ga dr. Yana kallonta (lolz🤭😂) Yace "Munyi baƙuwa fa" "Baƙuwa kuma?" Tai maganar tana ƙoƙarin tashi zaune, idonta ta sauke akan Nana, take Jidda tai murmushi tace "Ƙawata, yaushe suka zo?" "Eh tun shekaranjiya tana gida, yau Abba yace inje in ɗakko ta" "Kai amma naji daɗi, Nana ya kike ya Inna?" Nana tace "lafiya ƙalau, tana sunkuyar da kai" Usman yace "ga ɗakin dake kallon dining nan, ki shiga ki ajiye Akwatin naki, kije Kitchen ki ɗebi Abinci ki ci" Nana ba tace komai ba ta ja Akwatinta, ta shiga ɗakin da akai mata umarni, tana jinjina fitsara irin ta Jidda. Usman ya maida kallonsa kan Jidda yace "muje daga ciki, ki wanka da ruwan ɗumi seki kwanta zaki ji daɗin jikinki" Ta kwanta a jikin dr. Tace "Nikam naji daɗin zuwan Nana, amma naji kunya baka taɓa kaini naje na gaida Inna ba, ga Hakimi yai rashin lafiya shima banje ba, gobe in Allah ya kaimu ka kaini gida mu gaisa da Innan" "Ke in da ita aka zo zata bari a ɗakkota a taho da ita nan ne? Matar Sadik ce fa" yai maganar yana wata shu'umar dariya. Jidda tace "kace 'yar gida za'ai idan ya kammala Makaranta, to Allah ya nuna mana kuma sunyi matching Sosai" "Ai an riga anyi ma" "Akayi me?" Tai tambayar cikin mamaki. "Akai Auren, jiya ma Abba yai walima da abokansa" "Dan Allah Baby be serious, wane irin Aure kuma ana zaune ƙalau" Usman yace "na saba yi miki ƙarya ne? Am serious Hakimi ya masa Aure, tare ma zasu tafi London, maganinsa kenan dama ba shi mara kunya ba, a gaban uban kowa ma faɗa yake Aure yake so, yanzu kuma an masa wai baya so" Kawai Jidda ta kwashe da dariya, Usman ma ya tayata. Nana fitowa tai dan ta nemi ruwan da zata sha, dan tana jin ƙishirwa. Ta tarar da su a manne da juna suna dariya, Nana a ranta tace "Wannan wace irin watsewa ce?" Tace "zan sha ruwa" Dr. Ne ya ɗago ya kalleta yace ta shiga Kitchen ta duba fridge. Jidda kuwa na kallon Nana se dariya ta kuma kamata, tace "but seriously dr., She's still young an katse mata hanzari, bana tunanin zata iya ɗaukar ɗawainiyar Aure, yarinya ce Sosai daga ita har Sadik ɗin sunyi ƙanƙanta sosai" "Su sukace miki sunyi ƙanƙanta?" Jidda ta toshe baki tana cigaba da dariya, Usman ya miƙe ya ɗagata suka nufi ɗaki suna cigaba da dariya. Nana kam daskarewa tai a gurin, wannan wace irin taɓara ce da watsewa haka? Kamar ba Musulmai ba. Dama haka Usman ɗin nan yake tana kallonsa wani shiru shiru da shi, wannan ai ba yi bane. Jiki a sanyaye cike da kunya, Nana ta koma in da aka bata ta zauna, tana mamakin abunda su Jidda su kai. Kwana biyu 'yan ajinsu Farhan ba sa ganinta, Lilly ce kawai ta damu da tambayar wai Ina Farhan ta shiga kwana biyu ba ta zuwa. Rashin samun amsar ta ne yasa ta tafi Ofishin Sir Nazir, cike da ɗokin sanar da shi mahaifinta ya amince ya fito. Ta tarar da shi da su Taslim a Office ɗin nasa yana koya musu karatu, kasancewar yanzu sune zasui jarrabawar ƙarshe. Yana ganin Lilly, ya sallame su yace sa cigaba an jima, bayan sun fita ta maida idonta kansa tace "me suke a gurinka?" 'karatu muke, baki gani ba gimbiyata?" Ta ɗan tura baki, sannan tace "Albishirinka" "Goro fari tas" Lilly tace "Daddy yace ka zo ya ganka" Cikin Sir Nazir ne ya bada wata irin ƙara ƙuuuu, wani gumi ya shiga tsatsafowa daga goshin sa. Tace "ya naga kayi wani iri? Meyafaru" "Hakanan naji ina fargaba Lilly" "Fargaba kamar yaya?" Yace "fuskantar babban mutum kamar mahaifinki ba abune me sauƙi ga talaka kamata ba" "Kaga kar ka damu, ni dai karka watsan ƙasa a ido na samu ya amince, kar yace ƙarya nake masa ma" Nazir ya jinjina kai yace "shikenan, zuwa yaushe kike ganin yakamata in je?" "Ko a Weekends ɗin nan ne, next week ze koma aiki fa" "Shikenan Allah ya tabbatar mana da Alkhairi, Allah yasa ya Amince ya bani ke" "Ameen ze ma baka" Nan suka zauna suka cigaba da hira ita da shi, sedai bayan fitarta yai shiru wani tunani ya ziyarce shi, yanzu Allah ne kaɗai ya san bayan shi bata mu'amala da wani ko tana yi? Anya ya dace ya zaɓi yarinyar nan a matsayin matar Aure, kuma uwar 'ya'yansa? Idan kuma da Auren nasa ta cigaba da bibiyar wasu mazan fa? Dan ku san ita ta fara nuna masa alamomin buƙatar ta a gare shi. Nan fa ya shiga tunane tunane daban daban, yana ƙoƙarin tsayar da mafita guda ɗaya, amma ya rasa meyakamata ya zaɓa a matsayin mafitar, daga ƙarshe dai ya tsaya akan zashi yaga mahaifin nata, ya gani in abunda ze yuwu ne, yace musu in ta gama Sakandire ze Aureta, kafin lokacin ya bar Kano ba tare da sanin kowa ba, dan ya fara kokwanto akan Auren Lilly. Da safe ma a gurin karyawa, Nana duk a ɗarare take, se soyayyarsu kawai suke a gaban Nana hankalinsu a kwance, dan dr. Ne ma ya ke bawa Jidda Abinci a baki, har aka gama karyawar, yayin da Nana take ta sunkuyar da kai da ganin rashin dacewar abunda suke. Seda dr. Ze fita Jidda ta tafi rakashi, sanna Nana ta samu damar cin Abincin nata Sosai, tana jin mace kamar Jidda goɗai goɗai take narkewa tana zubawa dr. Shagwaɓa abun ko tsari babu a gurin Nana. Bayan ya fita Jidda ta wuce ta shiga wanka, Nana ta tattara kwanukan da aka karya, ta shiga Kitchen ta wanke su tsaf, ta gyara Kitchen ɗin ta share ko ina, ita ma taje tai wanka ta canza kaya, ta ɗora hijjabi akan kayan, sannan ta fito falon, da niyyar ta zo ta kalli cartoon, amma ta tarar da Jidda tana kallon wani shiri. Murmushi Jidda tai tace "Amaryarmu" Sunkuyar da kai Nana tai, tare da ɗan tura baki ta nemi guri ta zauna. "To ki cire hijjabin mana, ba kya jin zafi ne?" Nana tace "bana jin zafi, ni ko a gida da shi nake yawo" Jidda ta jinjina kai sannan tace "Amaryar Sadik, dr. Yace min next week zaku tafi ai" Nana tace "hmmm, ai kafin nan ma ya sakeni, na koma ƙauyenmu shi kuma ya tafi" "Wane irin saki kuma ana zaune ƙalau?" Cike da Yarinta Nana tace "Ba fa sona yake ba, kuma nima bana son shi" Jidda tace "Subhanallah, haba Nana me Sadik ɗin yai da ba kya so?" "Wannan ɗan yaron, kawai se ince mijina ne, nan gaba  fa sena kamo shi a tsawo, dan nima doguwa ce, gashi masifaffafe ga takurar tsiya, ni bana son shi" Wata irin dariya ce ta zowa Jidda, Lallai Nana Yarinya ce sosai da sosai. Tace "Haba Nana, saki ai ba abun so bane, babu macen da za ta so tai Aure a saketa, Sadik yana da sauƙin kai sosai da sosai zaku zauna lafiya" "Lallai Anty baki san halin Yaron nan ba, a ƙauye daga ni se zani har ɗakin kakata ya biyo ni ya kwasheni da maruka, se a nan in da ba Kowane ze ƙyaleni?" Nana tai Maganar jiki a sanyaye. Jidda tace "Nana, karki kuma cewa Sadik yaro, koma menene yanzu mijinki ne, akwai dalilin da ya sa aka haɗa Aurenku, kiyi haƙuri kinji ki dena masa tsiwa kina da kirki kema zaku zauna lafiya" Nana tai shiru tana share hawaye, ita ba ta taɓa ganin wani abun kirki da Sadik ya taɓa aikatawa ba. Jidda ta so ta ɗan yiwa Nana lectures akan Aure da yadda zata tafiyar da Sadik, amma ita kanta kunya take ji, ba ta san da wane yaren za tai mata amfani ba yadda zata gane, dan akwai zunzurutun yarinta akan Nanan, dan ma kuma Nana a hakan 'yar gayu ce ba ta fiye nuna ƙauyanci ba. Ɗan zaman da su kai da Jidda, Jidda ta lura Nana akwai tsafta sosai da sosai, nan Jidda ta bata turaruka da kayan kwalliya, duk da iya kwalliyar Nana kwalli ne se man leɓe hoda ma bata dameta ba, saboda ba baƙace sosai ba tana da haske. Zaman Nana a gidan dr. Ya sa ta ma manta da wani batun Aure da a kai mata, sedai kewar gida da ke matuƙar damunta, gefe guda kuma taɓarar Jidda da mijinta, wasu lokutan in dai dr. Na nan ko falo ba ta fitowa, saboda idonta baya hanasu abunda Allah ya nufe su da yi, duk shakkar dr. Da take ji, se da taga mutuncinsa ya ragu a idonta saboda watsewar da suke a gabanta, gashi a lokuta kaɗan ne Jidda ke shigar kirki ta atamfa ko kayan mu na Hausawa, kullum cikin tsukewa take kamar inyamura. Kwanan Nana tara a gidan dr., Sannan Abba ya zo da daddare, Nana ta dinga murnar ganin Abban. Har Abban yai ƙoƙarin kira mata su Hakimi su gaisa amma wayar ta ƙi shiga, nan da nan kuma se kuka. Abba yace "meye na kukan kuma Nana? Jiya naje ƙauye duk suna gaisheki, Hakimi ya bada kilishi Inna ta bada turaruka tace a kawo miki, ki shirya gobe in Allah ya kaimu zaku tafi, da kaina zan raka ku can" Aikuwa Nana ta sake fashewa da kuka, kamar Abba yace ze kaita in da za'a kashe ta, Jidda ce ta janye ta ɗaki tai ta rarrashin ta, dan ita tasan dama gobe zasu tafi, Dr. Ya gaya mata, bata gaya mata bane dan kar ta ɗaga hankalin ta. Wasa wasa Abbas yaƙi sallamar Farhan, ya barta a Asibitin sedai kullum se yana duba BP ɗinta safe da Yamma. Gaba ɗaya zaman Asibitin ya gundure ta, se dai ta kasa dena tunanin abun ƙaunarta wato Sadik, ga damuwar Sunusi hakan ya sa jininta ya ƙi sauka, dan in dai Sadik be dawo ba Aurenta da Sunusi babu fashi. Yanzu ma Dr. Abbas ne ya shigo da abun awon BP. Yana ƙoƙarin ɗaura mata tace "Doctor" Ba tare da ya kalleta ba yace "Na'am Babyna" Wani Yarrr ta ji, tare da binsa da kallo. Yai murmushi yace "it sounds like na raina miki hankali ko? I don't mean I love you, i mean you are my daughter" Ba abunda ya faɗo zuciyar Farhan se Sadik, bakinsa yafi kowane baki iya furta kalmar Baby, ba zata manta lokacin da ya rungumeta yana maimaita Babyna a kunneta ba. Ba ta dawo daga hayyacinta ba, taji Abbas ya zauna a kusa da ita. Da sauri ta ja baya daga kusa da shi. Yai murmushi yace "ba taɓaki zan ba Farhan, zan sallameki ne a yau, naji daɗin yabon da Hajiyata ta dinga miki na tabattar ke me tarbiyya ce sosai, Amma Sadik ɗin nan da yake zuciyar ki, dan Allah ki aje shi aside ki kula da karatun ki da lafiyarki, duk da baki gayan ba nasan alaƙace ta soyaya tsakanin ku, amma kinyi Yarinta da love Crises, ki cire Sadik daga ranki maybe baze dawo gareki ba, tunda har ki kai rashin lafiya be zo ba, Yanzu dai tashi muje, Zan maida ke gida, in Antynki ta zo zata ɗaukar muku kayan" Jiki a Sanyaye Farhan ta sakko daga kan gadon, tabi bayansa. Tana ta ƙoƙarin gazgata abun da Abbas ya faɗaa, amma zuciyarsa ta kasa amincewa da Sadik ɗinta baze dawo ba, haryanzu tana nan akan cewa be dawo daga ƙauye bane. Har gida ya kai Farhan, ya kalleta yace "nan da sati ɗaya zanje Zariya yin clearance, zan tafi ƙasashen waje ƙaro karatu, ina fatan idan na dawo in tarar kin manta da komai, karatunki yayi nisa, murmushi kawai tayi ta buɗe ƙofar ta fita. tana zuwa gida ƙannaneta suka dinga murna, nan da nan maƙota wanda sukaje Asibiti dubiya da wanda ba su zo ba sukai ta shigowa dubata. Sedai abun mamaki, ko sau ɗaya Umma ba ta kalleta ba balle tai mata sannu, abun ya dinga damunta tana  cigaba da jinjina ƙiyayyar da mahaifiyarta ke mata. Seda daddare kowa ya tafi, ƙannaneta har sun kwanta sannan Umma ta shigo ɗakin Farhan, ta cillo mata wayarta tace "Wayar waye wannan?" Gaban Farhan yai mummunar faɗuwa, dan ta manta da wayar a ƙasan pillowan ta kwana ranar da abun ya sameta. "Wato kin fara biyewa yaran banza da zasu lalata miki rayuwa ko? Na bawa Huzaifa ya karanta min saƙonnin da ke cikin wayar, duk da shima ɗin ba komai ya karanta min ba dan ya kareki. Kin bani mamaki, dama tuntuni na fara ganin take takenki, ashe yaron nan dagaske yake wani ne a gefe yana hure miki kunne, har kin san ki dinga gayawa Namiji irin wannan maganganun, ban nunawa mahaifinki wayar ba, amma Ranar Asabar iyayen Sunusi za su zo, watanni uku rak za'a sa Aurenku, a yanzu ma bani da tabbacin in haryanzu ke budurwa ce kar a cuci ɗan mutane, kin bani kunya wallahi kin ɓata wayon ki! Tirƙashi, WACE RAYUWA NANA DA SADIK ZA SUYI A ƘASAR WAJE? MOTHER ME ZATA SHIRYA DAN RABA AUREN SADIK DA NANA? A WANI BABI FARHAN ZATA KASANCE, ME KUKE TUNANIN ZE FARU NAZIR ZE AURI LILLY KO AKWAI MATSALA? INA JIRAN RA'AYOYIN KU, BELIEVE ME YOU WON'T REGERET BUYING THIS BOKK 😍😍😍😍 Littafin nan ₦300 ne kacal. 0009450228 Aisha Adam Jaiz Bank 07063065680 KO kuje manhajar AREWA BOOKS ku siya. domin kuwa ya fi sauƙi ta can. . Littafin nan ₦300 ne kacal. 0009450228 Aisha Adam Jaiz Bank 07063065680 KO kuje manhajar AREWA BOOKS ku siya. domin kuwa ya fi sauƙi ta can. Gigicewa Farhan tayi, cikin tsananin tashin hankali ta fara tattaro kalaman kare kanta, duk da ba ta da tabbacin kalaman nata za suyi tasiri a gurin Umman na ta. "Umma, dan girman Allah, Umma ki saurareni dan Allah" "Rufemin baki, ƙanƙanuwar ki dake, amma kin san munafunci, kin san ki yiwa namiji wannan kalaman, kin cuci rayuwarki, kuma kanki ki kaiwa ba ki min ba, dama dan babanki ya takura se kinyi bokon nan ne, amma dan tani gara ai miki aure" Ta ƙarasa maganar tare da ɗauke wayar daga jikin Farhan, ta fice daga ɗkin. "Innalillahi wa innalillahi raji'un, ya rabbi Allah ka shiga lamarina, Allah ka kawon mafita" Take taji ƙirjinta saitin zuciyarta yai mata wani irin nauyi, ta dafe gurin hawaye na fita daga idonta. "Dagaske Sadik ka barni? Shikenan haka alƙawarin ze tafi a banza, za'a Auramin wani bayan ka koyar dani abu me wahalar sha'ani, ka da sa shukar da ba zaka iya bata ruwa ba? Sadik zuciya ta ba zata iya jure tarayya da wani a matsayin miji ba kai ba, Please come back" ta ƙarasa maganar tana rushewa da kuka. Sadik kuwa sam ya kasa murna da wannan tafiyar, an sai masa sabuwar waya da Komai da Komai, Mother ta shirya masa kayansa da ze tafiya da su. A ɗaki ta tarar da Sadik, yana shirin kwanciya ta nemi guri ta zauna a bakin gadon ta kalleshi tace "Sadik ina son ka buɗe kunnenka da kyau ka saurareni, ba kai ba Yarinyar nan, ba kai ba shiga sabgarta, tai rayuwarta kai taka ina nan zanyi duk me yuwuwa in ga nai Dalilin da zan kawo ƙarshen Auren nan" Sadik yace "dama ni me ze haɗani da ita, boarding fa za ai kata ni kuma ina hostel" Mother tace "Yawwa, ai ni ban san da Wannan Maganar ba ma, shikenan ta kwana gidan sauƙi, babu wani dalili da ze dinga haɗaku ma, ka maida hankali kayi karatunka kaji Auta, na san you are gifted, amma kayi karatu da kyau, idan ka kammal karatu da kaina zan maka Aure irin na 'ya'yan gata, in aura maka wadda kake so, dan wannan yarinyar ba ajinka bace, ba tsarar ka ba ce son zuciya ne kawai na kakannin ka yasa su ka aura maka ita" SADIK yai murmushi yace "shikenan Mother, Allah ya kaimu in gama makarantar Nagode sosai da kulawar ki My mum" "Mentioned not dirling, am gonna Miss you so much" "Me too mom" yai Maganar yana rungume Mother da tuni ta fara hawaye, ƙarshe Sadik ne yai ta rarrashin ta, tai masa sallama ta kashe masa fitila. Har Sadik ya kwanta, yaji wani abu me nauyi ya tokare masa zuciya, wani abu me mahimmanci ya shiga cin zuciyarsa, wata irin damuwa ta baibaye shi, da farko ya danganta hakan da tafiyar da ze da kuma Auren da a kai masa, sedai damuwar da yake ji ko lokacin da aka ɗaura Auren be ji ta ba, ji yake kamar zuciyarsa za ta tsaga ƙirjinsa ta fito, amma ya kasa tuna me ya jefa shi cikin wannan mawuyacin halin haka. Ya tashi zaune ya dafe kansa, yana jujjuya kan ya na son ya tuna menene wannan abu a zuciyar sa da ƙwaƙwalwarsa ta kasa tuna masa? Amma kansa ya shiga sara masa, the more yake pressing ƙwaƙwalwarsa the more yake jin wani irin ciwon kai. Ya runtse idanunsa, yana sauraron yadda zuciyarsa ke wani bugu kamar zata fasa ƙirjinsa. Haka ya lumshe idanunsa, da ƙyar bacci ya ɗauke shi. Farhan kuwa, jiki a sanyaye taje ta ɗauro Alwala ta tada salla, sedai ta kasa sallar da ta fara karatun sallar se ta rikice, zubewa tai akan daddumar tana kuka, tana faɗin "Ya rabbi, Ya rabbi" a hankali bacci kuwa dama ba ta yi shi ba sam. Washegari tun da sassafe, Jidda ta sa Nana tai wanka, ta shiryata amma Nana taƙi karyawa se kuka da take. Se da Usman ya zazzare mata ido, ya sata a gaba sannan ta ci Abincin. Bayan ta karya suka ɗau hanya zuwa gidan Abba. Suna zuwa gaban Nana ya shiga faɗuwa, dan a falo suka tarar da Mother ta hakimce tana kallon TV. Tana ganinsu tai murmushi tana musu sannu da zuwa, amma ta na ganin Nana ta haɗe rai, Nana har ƙasa ta durƙusa ta gaida Mother, amma Mother tai mata banza ta na yiwa Jidda Magana. Usman kansa be ji daɗin yadda Mother taiwa Nana ba sam, Jidda tace "Mother ashe abun Alkhairin da ya faru kenan, Allah ya sanya Alkhairi ya basu zaman lafiya, Amma Mother ai ko walima Yakamata a shirya mana kafin su tafi" Tsaki Mother tai tace "ke rabani da wannan shiriritar, dan ban ɗau wannan auren wani Auren kirki ba, ya jikin naki ance min baki da lafiya, hankalina ne ba a kwance ba shiyasa ban zo dubaki ba" Jiki a sanyaye Jidda tace "Jiki da sauƙi Alhamdilillah" Suna cikin hirar sega Faruk ya shigo shi da Sadik, Nana ta na ganin Sadik gabanta yai mummunar faɗuwa sakamakon kallon da yai mata. Faruk yace "our runaway bride, shine kuka haɗa baki da Abba ki ka koma gidan Dr. Ko ai shikenan ya kike?" "Lafiya ƙalau" Nana ta faɗa a Sanyaye. Faruk yace "Sadik ga amaryar fa, ai kwa gaisa ko" Wani uban tsaki Sadik yai, ze wuce ɗakinsa. Dr. Ne ya daka masa wata irin tsawa yace "zo nan, ana maka Magana waka kewa tsaki?" Mother tace "ya za kai masa tsawa haka, ba dole yai tsaki ba, an samun yaro a damuwa, dole yai tsaki" Dr. Yace "Mother please, abu Kafin ya faru ake nuna masa ƙiyayya, ko ɗaukar matakin hana faruwarsa, amma wannan ya riga ya faru, karki tsananta ƙiyayya akan lamarin nan daga baya ki zo kiji kunya, ki fita sabgar yaran nan please" "Ni kake gayawa haka Usman?" "Mother, I don't mean to say anything bad to you, but Maganar gaskiya ce tunda lamarin nan ya faru kiyi haƙuri dan Allah, ki musu Addu'a" "Rufemin baki!" Mother taiwa dr. Tsawa. "Dan ba kai a kaiwa haka ba shine kake wannan maganar ko? Dan kai ka kammala karatu ka samu aiki ka zaɓo matar da kake so ka samu ka Aura, shine shi zaka dinga zare masa ido, dan ba kai aka aurawa 'yar ƙauye ba ko? Aka ɓata career ɗinka da burin ka na karatu ba?". Jidda ba ta ga abun tada jijiyar wuya da Mother ke yi ba, sema tausayin da Nana ta bata, dan se kuka take, abun da tausayi a dinga nuna maka ƙiyayya a gabanka, ana goyon bayan a wulaƙanta ka. Jidda tace "Nana, ta shi ki shiga ɗaki kafin Abba ya dawo" sannan ta maida hankalinta kan Mother tace "Dan Allah Mother kiyi haƙuri, gaskiya ba a kyauta muku ba, amma dan Allah kiyi haƙuri" "Ƙyaleni Jidda, wannan mijin naki be san yakamata ba, ban san me Sadik yai masa ba da yake takura masa haka" Dr. Ze magana, Jidda ta girgiza masa kai alamar yayi shiru, yayin da Sadik se cin magani yake yana hura hanci. Shi Faruk dama takaici ne ya hana shi Magana gaba ɗaya. Nana kam a ɗakin ma takurewa tai, ta dinga kuka tana tunanin tun a nan kenan, ina ga in sunje can in da ba kowa, Allah kaɗai ya san irin zaman da za suyi. Khairat ce ta leƙo ɗakin da Nana take, ta kalleta tace "kwaɗayayyiya kawai 'yar ƙauye, hadda kukan munafunci nan kuwa ƙasan zuciyarki murna kike" Nana ba tace mata komai ba, se kuk kawai da take, dan ba ta da lokacin Khairat a yanzu. Kusan awa ɗaya da zaman Nana a ɗaki, Jidda ta shigo tace "Nana ta so mu raka ku airport Abban ya dawo" Jiki ba ƙwari Nana ta taso, tana ta goge hawaye, Jidda ta rungumota Zuwa falo, Sadik ya rungume Mother yana kuka tana kuka, Allah sarki Nana ita babu me rarrashin ta, Jidda ce take ta bata haƙuri ta na mata Nasiha. "Zaka zo ka wuce ne, ko kuwa in ƙyaleka ka fasa karatun, in ya so uwarka tai romonka ta cinye?" Abba yai maganar a fusace Mother tace "Amma dai ai ka bari in sallama da ɗa na" "Ba abunda ya dameni bane, ya zo ya wuce in ba haka na tafi, wallahi se dai ki nemi kuɗinki ki biya masa" Mother har mamakin yadda Abba ya koyi masifa take, Sadik suka fito harabar gidan, suka shiga mota ɗaya shi da dr. Da Faruk, Abba kuma suka shiga ɗaya shi da Jidda da Nana da Khairat. Suna tafe Dr. Yace "kai Sadik, dan kut..... Bar ganin a gaban Mother muke ɗazu na ƙyaleka, wallahi ka kula da kanka, idan ka sake ka cuci Yarinyar nan Magana ta dawo kunnen Abba ka san matakin da ze ɗauka ba ze maka daɗi ba, kuma in da zakaje ba idon kowa a kanka, dan haka kaji tsoron Allah ka kula da addinin ka" Shiru Sadik yai Kamar ruwa ya cinye shi, yana ta kallon gari, yau kusan wata biyar kenan rabon da yabi wasu guraren, kuma gashi daga yau ze tafi wata Duniyar se dai in ya zo hutu kuma. Khairat da ma gulmace ta sa ta biyo su Nana rakiya, Jidda ta rungume Nana a jikinta, kamar ƙanwarta tana mata faɗa ƙasa ƙasa yadda ba me ji se Nanan. "Yanzu idan Sadik ya dawo yana sonki, ai kema zaki so shi ko?" Jidda tai maganar a kunnen Nana. Nana ta girgiza kai alamar a'a. "Yarinya zaman Aure ya wuce tunaninki, amma idan kina son ya dena miki masifa ku zauna lafiya, kinga yadda nake wa dr. A gida? Kema haka zaki dinga yi masa" Nana a ranta tace "taɓɗijan, wallahi ba zan zama 'yar iska ba, bayan Inna ta hana maza su taɓa ko hannu na, in na dawo taga na zama 'yar iska ai seta koreni' "Ya naji kinyi shiru, ko ba zaki iya ba?" Nan ma shirun Nana tayi, Jidda tai dariya kawai tana ɗan dukan bayan Nana alamar rarrashi. Ƙarfe ɗaya suka isa Airport, kasancewar jirgin ƙarfe biyu zasu hau, ya sa suka tsaya su kai salla, suka ci Abinci banda Nana da tabi ta takura kanta. Ƙarfe biyu jirgin su ya ɗaga, sedai Sadik yana ji a jikinsa ya bar wani abu me matuƙar kusanci da shi a Nigeria, amma ya kasa tuna ko menene. Nana na kusa da kujerar Abba, Sadik kuma na ta bayansu, sam Abba yaƙi kula Sadik a Abunda Abban be taɓa yi ba, ya share Sadik tsawon kwanaki ba tare da ya kulashi ba, komai girman laifin da yai kuwa. Abun duniya ya addabi Farhan, Rana zafi inuwa ƙuna, Umma ta ƙara watsi da lamuran Farhan fiye da da. Hajiya ta shigo sake duba Farhan a gida, tana ta tsokanar ta wai babanta yace ta duba masa idan ta fara ƙiba. Hajiya tace "Umman Farhan, wai ni ko dai haryanzu jikin ne na Farhan, naga duk ta ƙara zubewa bayan fitowar ta daga Asibiti, ta rame sosai tayi duhu" Umma tace "A'a ai taji sauƙi sosai" "Ai ni na ga ramar tayi yawa ne, yarinya me garin jiki tubarakallah amma duk tabi ta rame, ni gani nai kusan har gara tana Asibiti, amma yanzu ta rame sosai" Umma tace "kuma kimga ta na shan magungunan ta" "Hakane, to Allah ya ƙara Afuwa" Nan Umma ta ku ma yiwa Hajiya godiya sosai, sannan Hajiya ta tafi. Farhan kam ta yanke shawarar komawa Makaranta ko ba ta gama jin sauƙi ba, dan da ta cigaba da zama tana ganin ɓacin rai a fuskar Umman nata, gara ta koma Makaranta ta dinga tafiyar da mafi yawan lokacimta a can, ta samu ta dinga rage zafi. Su Nana an sauka lafiya, sedai tun daga airport ta ga akwai banbanci tsakanin gida Nigeria da ƙasashen ƙetare, ba karonta na farko kenan ba da hawa jirgi, an taɓa zuwa da ita umara tana yarinya sosai, tana da burin sake hawan jirgi, amma da yake ba daɗi ne ya hau da ita jirgin ba, ko murna ba tayi da hakam. Ko ina fitule ne a birnin kamar rana, saɓanin gida Nigeria, wani gurin da haske wani kuma babu. Wani baƙin Bature ne ya zo da mota, ya ɗauke su daga airport ɗin. Da alama sun san juna da Abba, dan suna haɗuwa suka gaisa, suka fara hira, Sadik ya gaishe shi, Nana kuwa tai shiru tana kallonsu, dan yadda Abban ya jiya harshe yana turanci shima Kamar Bature. Wani gida mutumin ya kaisu, sedai gidan girmansa yayi yawa, ga mutane burjik a gidan suna shiga suna fita, wannan motar ta shiga wannan ta fita, a taƙaice dai Hotel ne, da yake Nana ba ta san ya abun yake ba ta ɗauka gida ne. Wani ɗaki suka shiga, falo da bedroom biyu, Abba yaiwa Nana umarni da ta shiga ɗaya daga ɗakunan, shi da Sadik kuma suka shiga ɗaya, Mutumin nan yai musu Sallama ya tafi, har Abinci duk an samar a ɗakin. Suka fara rama salloli ta hanyar yin ƙasaru, Abba ya sa Nana a gaba taci Abinci sosai, ko ta kan Sadik ba ya bi da Nana yafi damuwa. Bayan ta gama ci ya kalleta yace "to Nana, gobe in Allah ya kaimu da safe, zanje in kai ki Makarantar ku, a in da zaki zauna, ina me miki Nasiha da kiji tsoron Allah, na san ke me Addini ce ki kula da kanki, kiyi karatun ki, karki wasa da Addini ko kuma al'adar ki, sannan kiyi taka tsantsan kibi dokokin su, kin san nan ba Nigeria ba ce. Ki nutus kiyi karatu da kyau kinji 'yar gidan Inna, duk abunda kike buƙata akwai in da zakije ki faɗa a makarantar za'a kirani a waya muyi magana, in munje duk za'a nuna miki Insha Allah, ni dai fatana kiyi karatu da kyau kinji?" Nana tace "to zanyi in Allah ya yadda" "Yawwa Allah yai miki Albarka, maza tashi kije ki kwanta" Nana ta tashi jiki ba ƙwari ta shiga ɗakin, sedai ita gaba ɗaya ɗakin tsoro yake bata, ba ta tunanin zata iya kwana a ɗakin ita kaɗai. Sadik yai shiru yana kallon Abba, yana tunanin wane irin zafi Abban ya ɗauka haka? "Lafiya kake kallona?" Abba ya tambayi Sadik. "Abba, dan Allah ka dena fushin nan da ni, ba na jin daɗi wallahi, baka taɓa yi min haka ba" Abba yai murmushi yace "kai harka damu da fushi na Sadik? Ni da ko gaisheni ka dena saboda uwarka ta na ziga ka, Ni Sadik ku ka sa yi min alfarma in bi nawa iyayen sannan kuce kuna son cigaba da Ganin walwala ta, duk abunda kuke shiryawa da ita na sani ƙyale ku kawai nake. Idan ka wulaƙanta Yarinyar nan ni ka wulaƙanta ka nunawa Duniya ban isa da kai ba, amma ka sani yadda wannan Auren igiyarsa take a hannunka yin wasa da shi, tamkar wasa da igiyar Auren mahaifiyar ka ne da ke hannuna, dan da iyaye na kuka sameni ba zan zaɓe ku a kansu ba!" Gaban Sadik yai mummuna faɗuwa, be taɓa zaton haka daga Abbansa ba, Lallai Abba da gaske yake, amma ya san Abba faɗa yake ba ze taɓa iya sakin Mother ba, Komai ze biyo baya za suyi settling daga baya, Amma ba ze taɓa zama da Nana a matsayin matarsa ba dole kowa ya kama gabansa. Nana ido biyu ta kwana, saboda tsananin tsoro da fargaba, gaba ɗaya ɗakin tsoro yake bata, ƙarshe ta fito falon kan kujera ta kwanta, shima bacci se ɓarawo ne ya ɗauke ta. Da safe suka shirya suka bar Hotel ɗin, mutumin jiya ya kaisu gidansa, matarsa baturiya ce fara sol, se yaransu uku, biyu farare ɗaya baƙi. A nan su kai breakfast, sam Nana ba ta gane turancin da suke, da ƙyar take picking wasu kalmomin, a nan suka karya, Abincin na su duk gashi nan ta kasa gane kansa, tea ta iya sha se chips, shima ba sabawa tai da cin irin sa ba. Suna gama karyawa, Abba yace su tashi su tafi, a zaton Nana Hotel za su koma. Ashe Makaranta za'a kaita, an gama mata Komai, hatta kayan da zata buƙata an tanadar mada su, aji da ɗaki kawai za'a bata, se 'yan kayan da Abba ya sa ta ɗakko a akwati. Nan Nana ta tubure ta sa kuka, Mutanen da ko yarensu ba ta ji, ta ina zata iya rayuwa da su, Abba yai ta rarrashin ta yana nata Nasiha, aka bata Uniform da ɗan ƙaramin veil ta saka, saɓanin sauran ɗaliban ma da basa saka hijjabi gaba ɗaya jikinsu a buɗe yake, Nana ta gansu duk farare kamar zabiyai saboda fari. Kuka sosai Nana ta dinga yi, aka wuce aka kaita aji, ajin akwai farare da baƙaƙe dan akwai wanda suka fi Nanan ma baƙi a ajin, dan tana da hasken fata. Se da Abba ya tabbatar komai yayi normal, sannan ya tafi shi da Steve, wannan Black ɗin. Dama Sadik be bisu ba. Farhan ta gama shirin Makaranta, ta fito yiwa Abba Sallama, yai mata addu'a ya bata kuɗin Makaranta, tana fitowa tsakar gida Umma ta kaalleta tace "Ina zaki haka?" "Makaranta zani Umma" "Ai wannan makarantar ma haƙura zaki da ita, tunda Aure zaki ai ba ta da wani Amfani ma a gareki" Abba yana daga ɗaki yace "A'a, karatu akwai amfani, duk da Aure za tai, ai na gaya masa zata cigaba da Makaranta, ki ƙyaleta ta tafi" Umma ji tai kamar ta gaya masa abunda ta kama Farhan da shi, Amma tai shiru ta fasa. Farhan ta na tafe a hanya ta na kuka, kamar wata mara galihu, rana zafi inuwa ƙuna, zuciyarta a cunkushe haka taje makaranta. Lilly na ganinta tace "Farhan lafiya kuwa kika dena zuwa makaranta?, Da fa yau zanje har gidan ku in ga ko lafiya?" Farhan tai murmushin yaƙe tace "bani da lafiya ne" "Eyya, shiyasa duk kin rame sosai wallahi, Allah ya sawwaƙe sannu" Ta amsa da Ameen. Kusan duk Malamin da ya shiga ajin in yaga Farhan se ya tambayi ya akai kwana biyu ba ta zuwa, Lilly tace ba ta da lafiya, sukaita mata sannu, dan kallo ɗaya za kai mata ka tabattar hakan. Bayan an fita break ne, taji su Lilly suna hira, wai an kama Mubarak Babba, saboda ta'amalli da kayan maye, anje kame aka kama da shi. Duk da hakan yayiwa Farhan daɗi, ko banza yanzu ba ta da fargaba, amma ita babban abunda ya dameta be wuce son sanin halin da Sadik ke ciki ba. Ba ta gana yanke shawara ba, ta tashi ta nufi ajin su Sadik, tana jin kamar zata ganshi idan taje. Sedai ta na zuwa ajin, ta tsaya ta window tana leƙawa, zubawa gurin zamansa ido, in da suke zama yaita damunta yana tsokanar ta, ko ya kwanta ya ɗora ƙafafunsa akan benci yana danna waya. Wasu irin hawaye ne suka shiga zubowa daga idon ta, tana jin wata wutar ƙaunarsa na sake Ratsa ta. "Zan wuce" taji an mata Magana. Da sauri ta waiwayawa, taga Amin ne abokin Sadik. Ya kalli Farhan yace "Lafiya? Kukan me kike haka?" Tai saurin share hawayen ta tace "ba kuka nake ba" "Ba kuka kike ba, wannan hawayen fa?" Farhan tace "ba kuka nake bax Yace "shikenan, amma tsayuwar me kike a nan?" Cikin in da in da tace "da..daa..dama zuwa nayi" se kuma tai shiru. "Ko akan Sadik kika zo?". Ko Sannu ba ta haɗata da abikan Sadik, mussaman da ba jituwa suke ba, suna jin haushin ta, amma Da sauri ta ɗaga masa kai alamar eh. Yace "kaddai kice kema ba ya nemanki?" Ta ɗaga masa kai alamar eh. Yace "Subhanallah, ni dai na san munyi waya, one month back, yace min yana ƙauye kuma in da yake ba service, tun daga nan ban sake jinsa a waya ba" Farhan tace "Ni yafi wata ɗaya ma ban same shi a waya ba" Amin yace "ki kwantar da hankalinki, insha Allah zan bincika miki, zanje har gidan su inji in da yake, zan zo in gayamiki insha Allah" Farhan tai murmushi tace "to nagode" Yace "bakomai jeki aji, ki dena kuka" Jiki a sanyaye, ta bar ƙofar ajin nasu. Amin na shiga class ɗin Nas ya fara murmushi yace "kai baba yane? Ko kai zaka maye gurbin Prince ne?" Amin yace "kai bari Nas, Yarinyar nan tausayi take bani, ba ƙaramin so take wa Sadik ba, wai ashe more than a month, ba suyi ko waya ba shine ta zo tana leƙo ajin nan" Nas yace "to shine me?, Dama wannan har wata Soyayya ce, ɓata lokaci ne kawai, soyayyar Makaranta ai shirme ce" Amin yace "ba kowace Soyayya ce shirme ba, har kuka take wallahi, ta bani tausayi sosai" "To kai meye naka a ciki, ya manta da ita, maybe yayi wata ne, mu da ya sanmu kafin ta, muma ai ba nemanmu yake ba, tun da mukaje gidan su akace baya nan" "Ai ni ka san munyi waya, yace min yana ƙauye, gurin kakanninsa, amma insha Allah zanje gidansu in ji abunda ake ciki, ko dan Yarinyar nan" Nas yace "ai se kayi" Kamar an jefota haka Nazir ya ga Lilly a office ɗin sa, yace "lafiya?" "Dole ka tambaye ni lafiya mana, haba Nazir ya kake so in yi ne? Ka ƙi zuwa gurin mahaifina so kake yai fushi da ni ne?" "Lilly ba haka bane, wallahi tsoro nake ji" "Au tsoro kake ji ko?" "Wallahi abunda ya hanani zuwa kenan, ban san ya ze krɓe ni ba" "Nazir in kaga dama, yau da daddare kaje, dan na ce masa yau zaka zo, idan kuma ba haka ba shikenan shi ze zo ya sameka" A gigice yace "ai ba za'ai haka ba ma, zan zo insha Allah yau ɗin nan ba se gobe ba" Tai ajiyar zuciya tace "da ka temaki kan ka" ta jiya ta fice. Dafe kansa yai yace "wannan wane irin bala'i ne? Wace irin masifa na jefa kaina a ciki haka?" Farhan har ba ta son a tashi daga Makaranta ta koma gida, saboda ba ta san abunda zata tarar a gidan ba, gaba ɗaya ta kuma susucewa ta zama wata iri kamar mara jini a jika. A daren Nazir ya shirya ya tafi gidansu Lilly, cike da Zullumi da tsoron abunda ze tarar, dan tun a gate aka tare shi, aka kira baban Lilly, yace a kai masa shi guest room ɗin sa. Yana nan a zaune yana tsuma, yana rarraba ido, Daddyn Farhan ya shigo ɗakin, seda kayan cikin sir Nazir  suka juya. Ganin baban Farhan, babban mutum me cike da siffar ƙarfi da kwarjini, dan da hannu ɗaya ze iya sama da sir Nazir. Ya nemi guri ya zauna ya kalli Nazir, sir Nazir cikin rawar jiki yace "barka da yamma ranka ya daɗe" "Kai ne corper ɗin da kake son Lilly?" "Eh nine" "Meye sana'arka, sannan kuma ɗan waye kai?" "Sunana Nazir, ni ɗan Jigawa ne, na kammala degree na ne nai service a Kano, yanzu ina aiki da wata private school ne, kafiiin samu aiki" "Kaine kake hure mata kunne kenan, kar tai karatu tace aure take so ko?" "A'a ranka y... "Shut up! Ƙarya tani za kai kenan? Kana hure mata kunne, yarinyar guda nawa take, me ta sani a Auren da zata ce ba ta son karatu se Aure? Ba dan na ganka a kamile da siffar mutunci ba, da sena sojoji sun ragaragaza min kai, an casa min kai aje a watsar da banza, kai kalli rigar jikinka ma kawai, har kana da ƙwarin gwiwar da zaka tunkari 'ya ta kace ka na so? Ba ma wannan ba da ma ta kai munzalin auren ne, na nema maka abunyi in aura maka ita, amma 'yar mitsitsiyar yarinya kamar wannan har ta samu ƙwarin gwiwar cewa Aure take so, ai daga jin wannan batu ka san zigata ake" Ya kalli wani Soja yace "kiramin Lillyn dan ubanta" Cikin ƙanƙanin lokaci, se ga Lilly, dan ba ta ma son Nazir ɗin ya zo ba. "Daddy gani" "Ke yanzu dama wannan ne ke hure miki kunne, kike cewa ba zaki karatu ba aure kike so? To ki buɗe kunnenki da kyau ki saurareni, ba ke ba wannan mutumin, ke da Aure sekin kammala degree, dama na kirashi ne dan in ga ko mutumin banza ne, in sa a koya masa hankali, amma se na ganshi a kamile dan haka bake ba shi kaima ba kai ba 'ya ta, idan ba haka ba i will show you what am capable of doing, tashi ka ban guri mutumin banza kawai" Jiki a sanyaye sir Nazir ya miƙe ya nufi hanyar fita, yaji zafin abunda baban Lillyn yai masa, kuma se yaji ba daɗi hana shi Lillyn da babanta yayi. "Ke kuma wuce ki koma ciki, sakarya kin bi ƙyal ƙyal banza kin bi kyau, kalli sosasshen yadin jikinsa, har kina gayamin Aure kike so, get inside before I slap you, hopeless kid" Da gudu Lilly ta shige tana kuka, bata taɓa zaton Daddyn ta ze disappointing ɗinta ba, ta ɗauka dagaske ze mata Aure kamar yadda ta buƙata, amma yaci zarafin Nazir haka. Nana kam ta kasa dena kuka, har a kai lesson ɗin ranar ba ta fahimci komai ba, ɗakin da aka kaita ita da wata yarinya ne, su biyu ne a ɗakin, komai akwai a cikin ɗakin nan na buƙata, Nana ba ta komai se dai tai wanka tai salla, idan tana salla se Yarinyar tai ta kallonta. Idan yarinyar taiwa Nana Magana, sedai tabi Yarinyar da ido, dan ba ta fahimtar abunda Yarinyar ke cewa, gashi tana son tayiwa Nanan Magana, amma Nana ba ta kulata, wani abun tana jin abunda yarinyar ke faɗa kaɗan kaɗan amma ba zata iya mayarwa ba, se in ta gaji ta ƙarewa Yarinyar zagi da hausa 😂. Washegari Abba ya koma Nigeria, Sadik ma ya tafi tasa makarantar, sedai a hostel yake shi, Sadik be sha wata wahala ba, dan ya saba zuwa ƙasashen waje, kuma ya iya turanci sosai, nan da nan ya fara mantawa da halin damuwa da yake ciki da haushin Auren da a kai masa, sedai in sunyi waya da Mother ne yake tuna yana da Aure, dan kullum sun kai waya cikin kashedi take masa akan Nana. Farhan taji sauƙi, sedai jiki kam babu ƙwari, se idanuwa a cikin fuskarta, duk tayi fayau, saboda kuka da damuwa, bacci dama sedai in ɓarawo ya ɗauketa, Amma kullum cikin tunani take. Farhan na kwance a ɗaki, tana matsar ƙwalla, tana tunanin anya zancen Abbas ba gaskiya bane da yace ta manta da Sadik ba, ya barta. Abba ta jiyo a tsakar gida yana gayawa Umma, wai sun haɗu a gidan su Huzaifa an karɓi kuɗin Aurenta daga gurin iyayen Sunusi Naira dubu Ashirin da biyar, sunce sun saka watanni biyar! Littafin nan ₦300 ne kacal. 0009450228 Aisha Adam Jaiz Bank 07063065680 KO kuje manhajar AREWA BOOKS ku siya. domin kuwa ya fi sauƙi ta can. Littafin nan ₦300 ne kacal. 0009450228 Aisha Adam Jaiz Bank 07063065680 KO kuje manhajar AREWA BOOKS ku siya. domin kuwa ya fi sauƙi ta can. Wani makirin kallo Sunusi ya bi Farhan da shi, amma tai kamar ba ta ganshi ba, ta miƙe ta fara tafiyarta. "Ke, saboda tsabar baki da mutunci, ba ki da ta ido wato har yanzu baki fasa bin maza a mota ba ko? Kuma dan wulaƙanci in ganki amma ki nuna ko a jikinki, kamar baki ganni ba?" "Idan har zan bi maza ban ji kunyar Ubangiji ba, kai waye da dan na ganka zanji tsoro? So kai in zura da gudu ko kuma in yi yaya?" A fusace Sunusi yace "wallahi tirr da halinki, kuma sena gayawa mahaifinki yawon fasiƙanci kike, ko da yake na sha gaya masa amma banga wani mataki da yake ɗauka akan ki ba, idan tsoron ki suke ji ba zasu iya tsawatar miki ba, ni dai dai nake da ke, kwaɗayayyiya kawai" Kalmar fasiƙa da ya gaya mata ta doki ranta fiye da kima, take taji jikinta har wani rawa yake ta kalli Sunusi tace "Allah ya karɓa min hakkina na sharri da kai min" nan da nan se hawaye. Abbas ya fito daga mota, ya nufo in da suke da sauri yana faɗin "lafiya kuwa, meke faruwa ne?" Sunusi na ganinsa ya gane shi yce "to munafukin Allah, dama ba tun yau naga alamun watsewa ku ke ba, shine da iskanci ka ɗakko ta a mota, tana matsayin matar Aure" Se yanzu Abbas ya gane shi, ya kalli in da Farhan ke tsaye tana kuka yace "Farhan waye kuma wannan?" "Shine zaɓin iyayena, wai shi suke da burin su aura min, yana nuna musu shi na Allah ne amma kullum yana jifana da miyagun furuci, na barka da Allah" Ta juya da sauri ta nufi ta nufi hanyar gidansu. Ƙarewa Sunusi kallo Abbas yayi, tun da ga sama har zuwa ƙasa, ya kalli kayan jikin Sunusi kamar ɗan gudun hijira, be ga in da Sunusi ya dace da Farhan ba. Sunusi yace "ƙaremin kallo da kyau, nine zan Aureta mata ta ce" Baƙin ciki ya hana Abbas magana, se shiga cikin gidan Hajiya da yai a fusace. Hajiya tana zaune tana kallon Sunna TV, taga Abbas ya faɗo ba ko sallama. "Kai ya haka kai da wa kake wannan hucin?" Be iya magana ba se cigaba da gwagwagwama numfashi da yake, se da ya sakko dan kan sa sannan yace "wai dama dagaske kike Aure za'aiwa Farhan?" "Dan ƙaniyarka na saba yi maka ƙarya ne? Meyafaru to?" "Na zaci wani mutumin kirki za a aura, ashe wani sakaran yaro ne da nake gani a layin nan, kwanaki yaje Asibiti duba ta, yau a wajen makarantar su na ganota, muka taho tare Shine ya tare ta yana mata masifa" Hajiya ta zare glashin fuskarta tace "Ya salam, gaskiya nima nayi mitar haɗa Aurenta da wannan yaron, Yarinyar ba ajinsa bace sam, duk da shi mutum ba abun ƙyama bane, kuma arziki na Allah ne, amma kyakykyawar yarinya me nutsuwa kamarta, wallahi da gidan hutu ta dace" Tsaki Abbas yai yace "Ni wallahi ji nake kamar in kai iyayenta ƙara human rights" Buɗe baki Hajiya tai tace "kai ka kiyayeni, akan me zaka kai su ƙara su da 'yar su, su suka san me suka gani suke yanke mata wannan hukuncin" "Yarinyar nan ba ta son mutumin nan, sun san negative impact ɗin abunda suke shirin yi ka iya haifarwa? Yarinyar da ta farfaɗo da kyar kamar zata mutu saboda damuwa, ni da ita ta gayamin ba ta son sa, akwai wanda take so fa, tayi ƙanƙanta da irin wannan stress ɗin, what If she commit suicide? Ko ta faɗa wani hali da ba'a so?" Hajiya tace "to rufeni da duka Abbas, tunda nice zan mata Auren, ko dai kishi ka ke ne, wannan zaƙalƙalewa haka?" Abbas ya sassauta muryarsa yace "Hajiya, am a doctor, ina hangewa iyayenta abunda ze iya faruwa akan Yarinyar nan, mutane masu irin ɗabi'arta na zurfin ciki damuwa na iya kashe su lokaci ɗaya, ko kuma su sami taɓin hankali, da alama ba ta da wani wanda zata raɓa taji daɗi, sedai ba abunda take yawan nanata wa kamar Sadik, that means he means a lot to her, se su bincika waye Sadik? Kuma su ƙyaleta da Auren nan tunda ba ta so, tana nunawa iyayen duk hukuncin da su kai akanta dai-dai ne, su kuma zasu kashe ta indirectly, nace zan Magana da babanta amma taƙi yadda, wace irin rayuwa ce haka za'a kashe ƙaramar yarinya, waya san baiwar da Allah ya ajiye a tare da ita?" "To, ni dai bani da ta cewa, tun da ba 'ya ta bace, abunda yafi kawai mu tayata da Addu'a, tunda 'yar su ce bamu da iko da ita" Abbas yace "Allah dai kawai ya kyauta, Allah ya basu 'ya ta gari, amma za suyi dalilin shigarta wani yanayi a banza" Ƙarshe Hajiya se bin Abbas tai da ido, saboda yadda ya zage yana ta surfa bala'i akan Farhan. Farhan kuwa da Sauri ta wuce gida, tai sa'a ba kowa a tsakar gida, tana zuwa tai cilli da jakarta, ta faɗa kan katifa ta rintse idanunta, tana jin yadda zuciyar ta ke bugawa, da tsananin ƙiyayyar Sunusi, so take ko bacci ta samu tayi, amma abu ya gagare ta gaba ɗaya, 'yan kwanakin nan sam ba ta bacci, se dai tai ta juyi  in ta gaji ta tashi tayi Alwala tai salla, tai ta gayawa Allah damuwarta. "Yanzu dan Allah kaima Yaya Faruk tafiya za kai?" Khairat da ke zaune a kusa da Faruk yana shan tea tai maganar a shagwaɓe. "Eh mana, me zan zauna in muku?" Khairat tace "wallahi i will Miss you, the house will be so boring, ba kai ba Auta" Dariya Faruk yai yace "ai sekin fi missing Sadik, shine abokin shirirtarki" "Ai na saba da rashinsa a gidan nan yanzu, amma gaskiya sena fi missing ɗin ka" Faruk yace "ba wani, faɗi gaskiya ni a wa zaki missing ɗi na?" "Kai a big Lovely brother na" Murmushi ya kuma yi me ƙayatarwa yace "wannan yabo haka? Ko dai wani abun kike buƙata ne?" "Shikenan ba zan yabe ka se ina buƙatar wani abu?" "Hmm, to ai shikenan godiya nake Lil Sisy" "Kai ba za kai missing ɗina ba?" "Mmm to, gani nan dai ban sani ba ko zanyi ko ba zan ba" Ɗan shiru tai ta zuba masa ido tana kallonsa. Miƙewa yai ya na murmushi yace "don't mind dear, i will so much Miss you" Yai Maganar tare da ficewa daga falon yana murmushi, tabi bayansa da kallo. Ji take tamkar ta sanar da Faruk cewa son shi take, amma ba ta san ta in da Yakamata ta fara ba, gashi yana ta shirin tafiya, ta rasa yadda zata ɓullowa lamarin. Kusan duk bayan sati biyu Steve yake zuwar wa Nana visiting, ya kawo mata provision saboda Ba Komai na Abinci ake bata ba, ba a bata abunda ya wuce tea, fruit ko chips se bredi, saboda suna amfani da Naman alade, ita Nana ba ta san dalili ba, ba ta damuwa da yadda ake bambanta su gurin Abinci, da safe ta sha tea da ƙwai ko dankali, ga kayan siyayyar tarkacen madara da kayan ciye ciye da Steve yake kawo mata yace inji Abba. Nana tana karatu sosai, duk da idan rigimar ta ta motsa zata zauna tai ta kuka, babu wanda yake takura mata komai gashi nan a wadace ba takura, amma ita hankalinta ya na kan gida Nigeria, dan tafi sakewa a nan. Tayi ƙalau da ita kamar ba ita ba, fatarta tayi fresh saboda zama guri ɗaya, shi kansa Steve yai mamakin ganin yadda Nana ta ƙara kyau a cikin ƙanƙanin lokaci, gashi har harshen ta ya fara sauyawa, babban abunda yai masa daɗi yadda malaman suka yabeta academically and morally. Ya kira Abba ya gaya masa cigaban da aka samu game da karatun Nana, Sannan ya bata Wayar. "Abba ina wuni" Abba yace "A'a turancin dai za'ai min, ya Makaranta Nana" "Lafiya ƙalau Abba, ya su Faruk da Mother da su Anty Jidda" "Duk suna nan lafiya, ai last week naje gidan, Inna na ta gaishe ki" Nan da nan ƙwalla ta taru a idon Nana tace "ya jikin Alhaji?" "Ahh jikinsa yai kyau sosai Alhamdilillah, kun kusa hutun session ko?" "Eh mun kusa, ai zan dawo ko?" "No, kuyi zamanku ku cigaba da karatu, zamu zo ai, zamu shigo muku visting insha Allah, ga kilishinki kayan guda Hakimi ya bani, zan zo miki da shi" Nana tace "to Abba nagode, in kunyi waya kace ina gaishe su, nayi missing ɗin su sosai" "Bakomai kiyi haƙuri, ki kwantar da hankalinki kinji, kiyi karatunki da kyau, Steve ai yana kawo miki kayan buƙatunki ko?" "Eh yana kawo min, duk sati biyu se ya zo" "To Alhamdilillah, ya ɓangaren addinin ki, ba wata matsala da kike fuskanta ko?" "Ba wata matsala, ina addini na ba ruwansu da ni" "To Alhamdilillah, ki kwantar da hankalinki kiyi karatunki, wataran se labari" "To Abba, Nagode sosai a gaida su Mother" "Zata ji insha Allah, Faruk ma ya kusa tafiya matsers ɗin sa, gidan ze zama se mu kaɗai" "Allah sarki Yaya Faruk, ace ina gaishe shi Allah ya bada sa'a" "Ameen ya hayyu ya ƙayyum, se anjima" Sukayi Sallama, Mother da ta shigo tun ɗazu ta kalleshi tace "wao da wa kake waya haka ne? Se murmushi ka ke?" "Ni da Nana ne, naji daɗin yadda ake yabonta tana ƙoƙari Sosai a makarantar, na jinjinawa ƙoƙarin ta sosai da sosai, a 'yan watannin nan ace tana capturing abunda suke gaskiya tayi ƙoƙari" Taɓa baki Mother tai, tai masa shiru ta cigaba da abunds take, dan ko sunan Nana ba ta son ji. Sadik ya zama famous a Makarantar su, yana da abokai da ƙawaye kala kala, gashi yai suna a team ɗin su na ƙwallon ƙafa na makaranta, ga competition da suke na gyming, gaba ɗaya ya canza kamar baƙin bature, ya tara uban gashi kullum cikin kashewa gashin nan kuɗi yake. Amin har baya son ya haɗu da Farhan, dan da sun haɗu take expecting samun wani information daga gare shi akan Sadik, yaje gidan su Sadik sau biyu amma tun a gate ake sanar da shi baya nan, kuma baam wanda ya taɓa gaya masa ga in da ya tafi. Duk da Farhan ɗin ba tambayar sa take in da Sadik yake ba, amma ya san yai mata alƙawarin ze bincika mata in da Sadik ɗin yake. Yau ma a Library suka haɗu, duk da ba karatu ne ya kaita Library ɗin ba, taje ne dan ta keɓe kanta daga mutane, ta zauna a in da suka saba zama ita da Sadik tayi tunaninsa sosai ba tare da wani ya takura mata ba. Amin ya zauna a kujerar gaban Farhan yace "sannu ina fatan ban takura miki ba" Tace "A'a bakomai" Yace "Na san na miki alƙawari, akan bincika miki in da Sadik yake, wallahi zuwa na biyu gidan su, amma tun a gate ake cemin baya nan, naga an canza musu megadi da wancan ne mun saba sosai ze bari in shiga ciki ko lambarsa in samo, amma wannan bama ya bari a shiga gidan nasu, amma dai ba zan gaji ba zan cigaba da bincikawar" Farhan tace "bakomai kar ka damu, hakan ma Nagode sosai Allah ya saka da Alkhairi" Yace "bakomai karki damu, ki kwantar da hankalinki nasan duk in da yake shima kina nan a ransa, kuma ze dawo gare ki" "To shikenan, Allah ya sa" Yace "insha Allah" Tana Library, har aka tashi daga Makaranta ta tashi ta tafi gida, taje ta tarar Umma ta dawo daga kasuwa, ta yo siyayyar kayan Kitchen, ga Adda Maryam ta zo suna ta dudduba kayan da Umma ta siyo. Adda Maryam na ganin Farhan ta fara rangaɗa guɗa, wai ga Amaryar su. Murmushin yaƙen ma kasa ƙaƙalo shi tai balle taiwa Adda Maryam, kawai ta shige ɗakinta ba tare da ko gaishe ta tayi ba. Shirye shiryen su kawai suke na biki, yayin da hakan ke baƙantawa Farhan ɗin rai, babu wani karsashi ko ɗoki na amare a tare da ita. Duk da adda Maryam ta san Farhan ba ta da magana, amma tayi mamakin yadda Farhan taƙi kulata sam, duk rashin son maganar Farhan tana hira da Adda Maryam, ko ita ko Adda Hafsatu, amma wannan karon Farhan taƙi kulata. Farhan haushin Adda Maryam take ji, dan tana ɗaya daga cikin wanda suka taka muhimmiyar rawa, akan lallai se an aurar da ita, suka dinga bugo waya suna cewa lallai ai mata Aure, sekace ance musu lalacewa tayi. Bayan magariba Farhan na kwance a ɗakinta, yau ba Islamiyya, sedai wata irin kewar Sadik tana damunta, ga wani irin feelings from no where da ya dameta, wanda hakan kan faru a duk lokacin da ta kusa yin period.   Juyi kawai take akan katifar ta, wasu hawaye masu ɗumi suna bin gefen idonta, Babu abunda take buri banda ta ji ta a jikin Sadik, haka kurum take jin kamar ƙamshin turarensa take ji. "Yasalam kar in haukace" ta furta lokacin da wasu hawayen ke zuba daga idonta Kamar an kunna famfo, ko ba komai zubar hawayen ma samun sassauci ne a gareta. Adda Maryam ta ɗaga labulen ɗakin Farhan tace "ke 'yar Fulani ban san me nai miki ba kin ƙi kulani, ko duk kunyar ce? Kije ana Magana da ke a waje, ina ga ko angon namu ne?" Farhan tace "to zanje" "Naji Muryar ki a shaƙe, ko baki da lafiya ne?" "A'a" ta bata amsa a taƙaice. Bayan fitar Adda Maryam, Farhan ta zura hijjabin ta da niyyar tana zuwa, ta huce abunda ke damunta akan Sunusi, sedai tun daga soro ta fara jin ƙamshin turare, tana zuwa ta ga Abbas maimakon Sunusi. Ya kalleta yai murmushi yace "muje Hajiya ke neman ki dama" Tace "to bari in faɗa a gida" Ta koma gida ta sanar da Umma, sannan ta fito suka jera da Abbas zuwa gidan Hajiya, ba tare da wani ya furta komai ba. A kai sa'a akan idon Sunusi suka nufi Gidan Hajiyar sa. Farhan ta zauna a falon Hajiya, Abbas ma ya nemi guri ya zauna ya kalli Farhan yace "ba Hajiya ce ke kiranki ba, dama ni nake neman ki" Ta ɗago ta kalleshi ta sunkuyar da kanta. "Bana son mu tsaya a ƙofar Gidan ku ne, wannan shashashan, sorry in dena zaginsa shi zaki aura, bana son yazo ya samu gaba da masifa shiyasa na janyo ki nan" "Amma ina Hajiyar?" Yai murmushi yace "Hajiya tana nan, tana ɗakinta tana salla, na gaya mata zanje in taho da ke muyi Sallama, je ki duba ɗakinta in baki yadda tana nan ba" Ta girgiza kai tace "na yadda" Ya gyara zama yace "gobe in Allah ya kaimu zan tafi, tafiyar tawa ce nayi ba nayi ba, se yau Allah ya nufa gobe in Allah ya kaimu zan tafi, na zo in sake ganinki ne, sedai haryanzu ba wani cigaba se ramewa kike kuma yi" Farhan tai shiru ba tace komai ba. "Farhan, kowane bawa da kika gani a rayuwarsa, da irin ta sa ƙaddarar kiyi haƙuri ki karɓi taki, tun ranar da na fara ganinki zuwa haɗuwar mu ta ƙarshe, da naga wanda zaki aura, naji ina matuƙar tausayinki, kina cikin hatsari Sosai da sosai sedai dan Allah duk abunda ze faru, You have to maintain your diginity, kar kije garin nemawa kanki mafita ki faɗa wata hanyar daban kiyi haƙuri" Farhan bata gama gane inda maganganun Abbas suka nufa ba, ita dai tana jinsa ne kawai. Tana cikin nazarin maganganun sa taji ya riƙo hannunta cikin hanzari ta kalleshi, a hankali tai ƙoƙarin zame hannunta amma taji ya riƙe gam. Wata irin fargaba ta shige ta, ya kai hannunsa ze cire zoben hannunta, wanda Sadik ne ya bata a lokacin birthday ɗin ta. Da hanzari ta miƙe tace "ka sakarmin hannu tafiya zanyi" "Nima ba wani abun zan miki ba, ba mutumin banza bane ni, mahaifiyata tana nan, ya za'ai in yi wani mummunan kuskure, nima ina da 'ya'ya, na san irreplaceable Sadik ne ya baki wannan zoben, so I want substitute him from your life". "Dan Allah ka bari" ta faɗa a raunane. "Ba kya son ki manta da shi ko? Bayan shi ya manta da ke?" "Be manta dani ba" "Meyasa zuciyar ki ba ta son Gaskiya ne? Farhan?" Shiru tai tana goge hawaye da hannu ɗaya. "Shikenan muje in rakaki gida, nasan kan in dawo daga karatu kinyi Aure, ina fatan Allah ya baku zaman lafiya, ina kuma yi miki nasiha akan kiyi haƙuri na bawa Hajiya gift ɗina na Aurenki ta baki, kiyi haƙuri kinji?" Ta jinjina kai alamar to. Seda suka fito tsakar gida, sega Hajiya ta fito daga ɗakin ta tace "Farhan, seda yaje ya tattago ki ko? Wa shi me 'ya, salla nake ne, nace in so yake sedai ya haƙura kin zama rabon wani, amma na kasa gane inda ya dosa, wai ai ke 'yarsa ce" Abbas yace "Hajiya kenan, bari in rakata gida" "To shikenan, ki gaida Ummanki" Farhan tace "to zan gayamata insha Allah seda safe" Suna fitowa daga gate ɗin gidan su Abbas, suka ga Sunusi da wasu abokansa a ƙofar Gidan yace "kun gani ko? Yanzu kun yadda da abunda na gaya maku? Sun kusa awa guda cikin gidan nan, daga ita se shi ba kowa a gidan, yanzu da nai magana ace sharri nake mata. Haladu ne yace "haba Sunusi, ya za ka dinga zargin matar da zaka aura? Baka da tabbas fa akan maganar da kake" "Kamar ya bani da tabbas? A gaban idona fa ta fito daga gida, suka shiga gidan nan tare, saboda sheda shiyasa na kiraku" Abbas ya kalli Farhan yace "muje" Hawaye wani na bin wani ta cewa Abbas "kalli irin mutumin da zan aura? Kullum ƙoƙari yake yabi diddigi na ya wulaƙanta ni, Hajiya fa tana cikin gidan nan amma kalli abunda ya tara mutane yake faɗa" Abbas ne kaɗai yake iya jin me take faɗa. Yace "bakomai, ki barwa Allah, muje kawai" Har ƙofar gida ya raka Farhan, yayin da Sunusi ke ta zazzaga bala'i. Farhan na shiga gida, gurin Abba ta shiga tana kuka, hankali a tashe yace "Lafiya kukan me kike haka?" "Abba Sunusi ne" "Me Sunusin yai miki?" Nan ta kwashe Abinda ya faru ta gaya masa, Abune mawuyaci Farhan ta kai ƙara tace gashi an mata laifi, ko lokacin yarinta sosai, ba ta zuwa ta kawo ƙara duk girman laifin da akai mata ko cutarwa kuwa. Shi kansa Abba yaji babu daɗi abun da Sunusin yai, dan haka yace "ki dena kuka, tashi ki tafi ɗakinki zan masa Magana" Farhan ta tashi ta fita tana kuka. Aikuwa tana shiga ɗaki aka turo ana sallama da Abba, Abba ya miƙe ya fita yana zuwa ya tarar da Malam Labaran da kuma Sunusi. Abba suka gaisa da su, Sannan Malam Labaran yace "to ina zaune Sunusi ya zo min da wata Magana akan matarsa, to nace ban sani ba ko kana da masaniya a kai" Abba yace "Malam Labaran, girma da mutuncinka na gani ya sa zan bawa Sunusi yarinyar nan, da kuma nustuwar sa da addininsa da yadda yake girmama mutane, daga fara neman Auren nan zuwa yanzu ba zan iya faɗar adadin sau nawa ya kawo min ƙarar ta ba, shi fa lamarin Aure ɗan haƙuri ne, yarinyar nan baka Aureta ba tukuna dole wataran samari zasu biyo ta tun da yanzu take kan ganiyar ƙuruciya yanzu take girma, idan ka kawo min ƙararta ina ɗaukar mataki bata taɓa nuna damuwarta akan haka ba, ba fa dan bana sonta nake mata haka ba, yau da bakinta ta kawomin ƙarar ka akan abinda kai mata, ka tara mutane a waje kace wai ta keɓe da namiji a cikin gida, ƙaddara ma hakane ai kai me rufa mata Asiri ne,balle seda ta shigo ta faɗa a cikin gida, Hajiya ta turo ɗanta wane tace taje tana nemanta, ba'a Aure da zargi fa in ka san kana zarginta to a haƙura da lamarin nan kawai" Da sauri Malam Labaran yace "A'a ba za ai haka ba, dan Allah ayi haƙuri insha Allah hakan ba zata sake faruwa ba, kai kuma Sunusi kar ka sake haka, zaka ɓata mata suna a unguwa, ba a haka baka kyauta ba" Cikin ikon Allah suna cikin maganar sega Hajiya da Abbas, ta ƙara so suka gaisa da su Abba Sannan ta kalli Abba tace "Malam Ali banji daɗin abunda ya faru yanzu ba, Ina cikin gidan da izini na Abbas ya kira Farhan, ba zan taɓa bari ayi ɓarna a gaban idona ba, saboda nima ina da baya, Abbas shine likitan da ya duba Farhan, ze tafiya ƙaro karatu, yace min yana son suyi sallama, ya kuma bata abunda ze bata ance za tai Aure, amma an tara min jama'a a ƙofar gida wai ɗana ya keɓe da 'yar wajenka a cikin gida ne, wanda maganar ba haka take ba" Abba yace "dan Allah kiyi haƙuri, kinga yanzu haka zancen da muke kenan" Nan suka taru suka ƙarewa Sunusi ta tas, suka nuna masa ba a haka. Abbas yace "wallahi ba dan Hajiya ta sa baki ba, se nayi karar Yaron nan hukuma tabi min haƙƙina na yunƙurin ɓatamin suna da yai" Sukai ta bawa Abbas haƙuri sanann suka bar gurin. Sunusi be taɓa zaton Abba ze iya iƙrarin hana shi Farhan ba, yaji Abba ya fara cewa ai yanzu take girma dole samari su biyota, dan haka ya fara tunanin abunda ze yi wanda ze hana faruwar hakan. Maganar Kamar wutar daji, a daren Magana ta fara bazuwa wai an kama Farhan da Abbas a gidan su, alhalin da kuɗin Auren wani a kanta. Baiwar Allah sam Farhan ba ta san meke faruwa ba, ita abunda ya dameta kadai take tunanin mafita a kai. Amin yana kwance yana duba waya, ya shiga IG yai posting hotunan sa na friday, daga nan ya cigaba da kallon hotuna. Yana shirin ya rufe datar yai karatu, kasancewar jarrabawar WAEC na ƙaratowa, kawai yaci karo da hoton Sadik a gym tare da turawa wata baturiya ta ɗora tare da caption of "ma hottest mate dude" Da sauri ya tashi zaune, ya cigaba da duba hotunan tabbas Sadik ne, kuma wannan hotunan na kwanan nan ne, kenan Sadik ya tafi karatu ba tare da yayi wa kowa sallama ba, kuma ya kashe wayoyin sa gaba ɗaya, to meyasa yai haka sekace wanda ba shi da gaskiya. Da sauri yai screenshots ɗin hotunan, ya tura group ɗin su na whats app na 'yan ajin su, nan da nan suka fara Sharhi wasu suka ce suka sun gani. Sunyi mamakin yadda Sadik yai tafiya haka ba labari. Washegari a school, su Nas da sauran 'yan ajinsu ma, haka suka ci-gaba da tattauna batun tafiyar Sadik ba labari. Har ajinsu Farhan Amin yaje, ya tarar da ita tai shiru ta zubawa 'yan ajinsu ido, suna ta hirarsu, suna sha'aninsu banda ita da se kallonsu kawai da take. "Sannu dai" Amin ya faɗa yana zama. Farhan ta kalleshi tace "yawa sannu" Amin yace "na zo da labari ne, wanda ban san ya zaki ɗauki abun ba, amma koma dai ya ne ki ɗauki lamarin da sauƙi. Jiya na ci karo da hotunan Sadik a Instagram, da alama ya tafi karatu ne, dan a cikin turawa naga hotunan nasa, hakan na nufin ya tafi karatu ne" Farhan tai murmushi tace "shikenan, tunda yana lafiya Alhamdilillah, Nagode sosai" Amin ya dinga binta da ido, dan ganin reaction ɗin ta amma ya kasa gano halin da take ciki. Gaba ɗaya zuciyar Farhan ta bushe, meyasa Sadik ze tafi ba tare da ya sanar da ita ba?. Ta rasa tunanin meyakamata tayi, kuka ko farinciki? Sadik yana nan lafiya, amma har ya tafi karatu ƙasar waje be nemeta ba, what does that mean? The relationship is over, he don't want her anymore, he dumps her aside? So Abbas gaskiya yake gayamata kenan, Sadik ya barta kenan?! Ya ilahi. Idanunta su kai jawur, does she deserves this from him? Tana zamanta lafiya, ya koyar da ita son shi, kuma ya tafi ya barta ba tare da tunanin wani hali zata shiga ba. 'No, he can't do this to me? Sadik yana sona, akwai dalilin da yasa ya tafi be neme ni ba, shikenan Aurena da Sunusi ze tabatta, Ashe doctor gaskiya yake gaya min? Gaba ɗaya ta rasa tunanin meya kamata tayi. Seda ta ɗaga kai taga ba kowa a ajin, sanann ta gane an tashi kowa ya tafi. Haka ta ɗau jakarta ta bi hanya itama, ba tare da ta ɗau ko babban hijjabin ta da ta saba sawa ba. Ji take kamar ta samu wani gurin da babu kowa ta ƙwala ihu da ƙarfi ko ta samu sassauci Amma babu halin hakan. (This is how depression starts, and later on you will see what it leads to) Yauma akan idon Sunusi Farhan ta dawo, da skirt iya ƙwaurinta, ya matse ta rigar Makaranta duk a ɗame, ga wani ɗan mitsitsin hijjabi, kasa Magana yai sema buɗe baki da yayi yana kallonta dan be taɓa sanin haka Uniform ɗinta na Makaranta suke ba, ga wani irin kyau da sukai mata, dirarriyar budurwa me kyakykyawar ƙira komai nata daidai da jikinta. Se ya rasa kishi zeyi, ko kuma farincikin ganin abunda ze aura?. Haka ta shiga gida babu ko sallama, Umma ta bita da kallo, tana zuwa tai jifa da jakar Makarantar ta, ta faɗa kan katifarta. Adda Maryam tace "yarinyar nan kuwa Lafiya take?" Umma tace "oho mata" Adda Maryam ta shiga ɗakin Farhan tana mata Magana, amma Farhan ta ƙi kulata. "Anya Innar Farhan ba aljanu ne suka kada ita ba, Sannan kalli kayan jikinta wannan ai dole Aljanu ma su shafeta dama wannan watsewar ake makarantar? Wannan ne kayan makarantar ta ta?" Umma tace "to ni me zance, bani da yadda zanyi babanta ne ya dage se tayi, kuma ni bata taɓa aljanu ba, amma bari Amira ya shigo ya kira Malamin su Sunusi ko Sunusin su zo suyi mata addu'a" Farhan na jinsu tai musu shiru, amma yadda take ji a ranta idan aka kusakura Sunusi ya zo in da take a halin yanzu, seta masa Illa!. Abba da su Mother suna kan dining suna cin abincin rana, suna ta hira Faruk se dannan waya yake. Mother tace "wai ba zaka ajiye Wayar nan kaci Abinci ba, ka ƙi maida hankali, idonka akan waya" Yai murmushi yace "Am sorry maam, ina ganin wani abune a IG yanzu zan ajiye" Abba yace "ai matasan mu se fatan Allah ya shirya, amma sun maida waya kamar wani nau'i na ibada, in basu Danna waya ba ba sa jin daɗi" Faruk yai murmushi yace "Abba kenan, kasan yanzu Komai ya koma kan waya shiya........ Kai!" Abba yace "ya dai?" Faruk ya ƙurawa wayarsa ido. Abba yace "wai menene?" Faruk ya miƙawa Abba wayar, Abba ya karɓa yana dubawa. Ɗiffff Abba yai, yan nazarin abunda ya gani a wayar. Ba tare da yace uffan ba, ya ajiye wayar ya tashi fuuuuuu! (Me Abba ya gani 🥺🙄🙄) Littafin nan ₦300 ne kacal. 0009450228 Aisha Adam Jaiz Bank 07063065680 KO kuje manhajar AREWA BOOKS ku siya. domin kuwa ya fi sauƙi ta can. Littafin nan ₦300 ne kacal. 0009450228 Aisha Adam Jaiz Bank 07063065680 KO kuje manhajar AREWA BOOKS ku siya. domin kuwa ya fi sauƙi ta can. Take tsigar jikin Farhan ta tashi, taji kanta yai wata irin sarawa, wani irin sanyi ya shiga Ratsa ta, taji tamkar an ɗora mata dutse a ƙirjinta, zuciyarta ta bushe hawayen ma suka gagara zubowa balle ta ji sauƙi a ranta. Umma da ke tsakar gida tace "dubu Ashirin da biyar kuma?" "Eh, sun ta bada haƙuri kin san ba masu ƙarfi bane, sedai yaron akwai zuciyar nema" "Hakane, Allah ya sa albarka ya kaimu lokacin ya sa ayi damu" Ya amsa mata da "Ameen" "Allahumma ajirni fi museebati, wa akhlifni khairan min ha" shi Farhan ta dinga maimaitawa, dan wata irin muguwar tsanar Sunusi take ji tana ƙara ratsata, ji take kamar ta kwashi kayanta ta gudu, da tai ido huɗu da wannan mummunar rana da za  ace Sunusi shine mijin da zata aura. "Why Sadik? Meyasa kai nisa da ni ka bari nake shan wahala haka, come back to me please" tai Maganar tana ƙanƙame pillow a ƙirjinta, tana tura hancinta jikin pillown, tamkar zata ji ƙamshin turaren Sadik a jikin pillown, gashi tai tai tayi kuka, amma kukan ya gagara zuwa sam, se wata irin Azabar raɗaɗi da zuciyar ta ta take mata. Tana jiyo Ummanta tana ta kiran danginta tana gaya Musu, ai an kawo kuɗin Auren Farhan, suna ta murna suna yaren fullanci suna mata barka da arziki. Huzaifa ne yai sallama ya shigo gidan, dan tun da Umma ta ritsa shi ta sa ya karanta mat saƙonnin cikin wayar Farhan, yake jin kunyar zuwa gidan su haɗu da Farhan, dan lokacin da Umman ta bashi wayar ya duba mata, be san wayar waye ba, dan a saninsa Farhan ba ta da waya, sedai yai nisa a karanta saƙonnin sannan ya fuskanci wayar Farhan ce. Ɗakin Farhan ya leƙa, ya hangota tayi ruf da ciki akan katifar ta, kanta ko ɗan kwali babu, dogon gashin ta ya hargitse, ta dunƙule guri ɗaya da Sauri ya saki labulen yana ambaton Allah, dan be san a haka ze ganta ba, amma kana ganin yadda take zaka gane tana cikin damuwa da tashin hankali, ko ba a faɗa ba yanayin ta ze nuna tana cikin damuwa sosai. "Ahh Huzaifa har ka zo?" Yaji Maganar Umma, ya waigo da sauri yace "eh Umma, wai ki bani kayan in tafi da su" "To Huzaifa, kai ko Allah sanya Alkhairi ma baka mana ba, bayan a gidan ku aka karɓi kuɗin Auren ta" Huzaifa kawai ya sunkuyar da kai yana murmushin yaƙe, dan kwata kwata ya rasa meya rufewa su Umma ido, suka ga dacewar haɗa Auren Farhan da wannan ƙazamin mutumin me masifar tsiya. Yana karɓar saƙon da ze karɓa ya tafi, dan ji yake kamar yaiwa Farhan kuka, messages ɗin wayar nan ya tabattar masa akwai wanda take so, ba wannan Sunusin ba, zuciyarta na tare da wani daban, gashi an gaza ba ta damar zaɓen abokin rayuwa, ga katse mata karatu da akayi. Sadik kuwa tuni yai sabbin abokai, dama shi ba ruwansa ba shi da wuyar sabo idan ya ga dama. Dan ba ko yaushe yake miskilancin ba. har wani group ne da su shi da abokansa, ba ya taɓa ɗaukar littafi yai karatu, abune me wahala yai wannan, sedai abubuwa sun fara caza masa kai daga lokacin da ya fara bin abokai zuwa club, wanda Addinin su da al'adar su ba ɗaya bane, hugging, shaking hands and Even hugging is not something big a gurinsu. Mussaman da Sadik yake burge 'yan mata, he is young but looking sexy and hot (ba inji ni ba, kun san dai su ba ruwansu faɗa za suyi 🙄🙄🙄) yana da suffa me kyan gaske, mussaman idan ya cire rigarsa ya shiga ninƙaya a ruwa, yana samun masu zuwa su ɗauki hoto da shi. Mata suje hostel ɗin maza, ko maza suje hostel ɗin mata wannan duk ba wani abu bane normal ne, suna iya haɗuwa su yi wa junansu bitar karatun da a kayi a aji. Sadik yana iya ƙoƙarin sa, gurin kula da addinin sa, da kiyaye abunda ze kaucewa hanya, amma abubuwa na nema sufi ƙarfinsa. Hajiya Nana kuwa, ta ɗan fara sakin jiki da Linda, wato room mate ɗinta, idan ta saurara da kyau, tana iya gane abunda Lindar take faɗa, tana yawan tambayar Nana kukan me take yi, idan ta ga ta zauna tana kuka, ko in taga Nana tana salla ta tambaye ta menene wannan take yi haka? Linda akwai shegiyar tambayar tsiya, yayinda Nana wasu tambayoyin suke bata haushi, dan ba ta san ta ya zata fara gaya mata ba, lokuta da dama se tai mata mixing our Nigerian English da hausa ta bata amsa (lolz 🤭😂). Linda ta kan gayyaci Nana ta zo suje gurin motsa jiki, ko wasannin Nana tace ba zata ba, saboda ba zata iya shiga ba hijjabi ba, kuma ta lura in dai zata fito da hijjabin nan se ta zama abun kallo a gurin su. Ƙawayen Linda kan kawo mata ziyara ɗakin su, suyi ta kallon Nana, suna mata magana amma tai banza da su sema tace "in ku mayu ne Yakamata ku ƙyaleni haka, se wani kallona kuke kamar an kawo muku buranya, dama ance haka kuke ce mana bururruka, banzaye zabiyai kawai, kuma ai munanan ne daga me ƙaton leɓe se me zanzana da cin zuma a haƙori, masu kyan kawai ake nunawa a TV" Da yake basu sa me Nana take cewa ba, sedai su bita da ido, ta ƙare musu zagi tsaf ba su san me take cewa ba. A hankali kuma Nanan ta fara gane turancin, dan har tana iya mayarwa, yadda Lindar zata gane. Har su kanyi hira koma Linda ta gayyace ta suje suyi karatu a Library. Sam Linda ba ta nunawa Nana ƙyama, mussaman da taji ance 'yar Afrika ce Nigeria ta na son Sanin abubuwa da yawa a game da Afrika especially Nigeria, shiyasa take yawan yiwa Nana tambayoyi, duk da Nanan ba bata amsa take ba. Abubuwa da dama na bawa mamaki game da rayuwar yaran turawa, ko laifi su kayi ba a fiye tsawatar musu ba. Watarana anyi karatu a aji, Malamarsu Nana tai mata tambaya, gashi ta san amsar tambayar amma ta kasa bayarwa, saboda tunanin yadda zata haɗo turancin tayi, kawai se 'yan ajin suka kama yi mata dariya ganin yadda tai wiƙi wiƙi da ido, tana tura baki, wani irin takaici ya kama Nana, kawai ta fashe da kuka, ga mamakinta se taga hankalin malamar ya tashi tana ta bata haƙuri tana rarrashin ta. Nana ta fuskanci ana bawa ra'ayin ɗalibai mahimmanci sosai da sosai, ga ba duka ba zagi a harkar koyarwar ta su. A hankali Nana ta fara sabawa da su, ta dage sosai tana ƙoƙarin mayarwa idan a kai mata turanci. Yanzu tana hira da Linda sosai, dan bayan Lindar ma har wasu ƙawayen tayi, amma ɗabi'arta ta yawo da hijjabi na nan ba ta dena ba. Mutane na ta shigowa yiwa Umma Allah Sanya Alkhairi yayin da a unguwa ake tayi da su, wai wannan 'yar yarinyar za'a aurawa Sunusi, wasu sukace Asiri yaiwa iyayenta, wasu suce ita yarinyar ce yaiwa Asiri take son shi, kowa da abunda ze faɗa. Hajiya ma ba a barta a baya ba, Wajen zuwa yiwa Umman Allah Sanya Alkhairi,  sedai se da tai ƙorafi tace "Umman Farhan, meyasa za'a aurar min da Farhan yanzu, tayi ƙanƙanta kuma karatun ta fa?" "A'a ba haka bane, kin san sha'anin rayuwa da kuma yanayin yaran namu na zamani, kamata yai da sun kawo ƙarfi a kauda su" "Hakane Maganar ki, amma ai ki godewa Allah, kinga Farhan nustsatsiyar yarinya ce, ba ruwanta da hayaniya irin ta yaran zamani, wallahi ki gode Allah amma yaran zamani suna kangarewa son ran su, amma kinga ke taki a nutse take kamar ke kika zaɓowa kanki" Umma a ranta tace 'wannan ɗin ma dan ba ki san halinta bane' A fili kuma tace "hakane, amma lokaci ne, idan yazo se anyi" "Haka yake, amma ze bar mana ita ta ƙarasa karatun ko? Dan ba wanda yasan abunda Allah ze sa ta zama nan gaba" "Eh yace ze barta, ai ba wani ne a nesa ba fa, Sunusi ne" Hajiya tace "wane Sunusin?" "Yaron nam dai Sunusi, Almajirin Malam Labaran" Hajiya tai galala tana kallon Umma tace "Wannan baƙin yaron me doguwar ƙeya?" Umma se taji ba daɗi abunda Hajiyar ta faɗa, amma ta maze tace "ba ruwana sirikinki me dai" Hajiya tace "Ni ko me Farhan ta gani a jikin wannan tsotsatstsen mutumin? Haba Umman Farhan dan Allah, kyakyawar bafullatanar Yarinya me tarbiyya kuma a rasa wa za'a bawa se wannan" Umma tace "kayya, banda abunki Hajiya, ai albarka ake nema a aure, su kyawawan, ko masu arzikin nawa aka aura amma Auren beje ko ina ba? Kuma naga ai shima mutum ne yaron, kuma gashi nutsatse ne" "Eh albarka ake nema a aure tabbas, amma gaskiya wannan haɗin be ba, kowace ƙwarya akwai abokiyar burminta, amma shikenan Allah ya Sanya Alkhairi ya sa ayi da mu". "Ameen ya Allah, dama addu'a dai ita ce" Hajiya na shirin tafiya, Farhan ta shigo daga Islamiyya, tana tafe sannu a hankali kamar ba ta taka ba. Tana ganin Hajiya tai murmushi tare da gaida Hajiyan. Seda Hajiyan ta ƙare mata kallo cike da tausyawa, sannan ta amsa tace "Ashe kuma abun Alkhairi ya samu, to ubangiji Allah ya sanya Alkhairi ya kaimu lokacin" Farhan tai murmushin yaƙe, tare da ƙoƙarin danne wani irin ɗaci da ya taso daga ƙasan zuciyarta, yake ƙoƙarin fallasar da zunzurutun damuwar da ke cikin ƙirjinta, ta hanyar kwaranyowar hawaye, ta nufi ɗakinta. Kasancewar ba ta salla, har a kai sallar magariba ba ta fito daga ɗakin ba, se da akai sallar isha'i sannan ta fito ta tafi makarantar dare, sedai ta layin da Sadik yake ajiye mota tabi, ji take kamar za ta ganshi, sedai gurin wayam, ba motarsa da yake tursasata ta shiga ko yace ze ɗagata ya sata motar, mussaman idan su kai faɗa. Duk da wasu abubuwan da suke a cikin motar ya saɓawa ƙa'ida, amma makauniyar soyayyar da ke cin ranta da kuma RUƊIN ƘURUCIYA ya sa take mantawa da hakan ta biyewa Sadik. Barandar wani gida ta samu ta zauna, ta haɗa kai da gwiwa ta na wata irin sheshsheƙa, ga hawayen kirki yaƙi ya fito se ajiyar zuciya da take ta jerawa. "Dan Allah Sadik ka dawo, zuwa yanzu zuciyata tayi rauni, ba zan iya jurewa ba Komai ze iya faruwa da ni, ina kewar ka Sadik" Makarantar da ba ta je ba kenan, se da tai kuka me isarta, lokacin tashi yayi Sannan ta taho gida. Tana cikin wannan yanayin, ta shiga ɗaki ta kwanta, akai sallama wai Sunusi yana nemanta, kuma Umma ta bada amsar tana zuwa. Tai shiru a ɗaki, seda Umma tai mata Magana Sannan ta tashi ta fita. Kamar yadda ta saba, tana zuwa ta ja guri ta tsaya, ta ɗauke kanta. Yai murmushi yace "Amarya ba kya laifi, yanzu kin yadda kin zama tawo ko?" "Allah ya kiyaye, idan wannan tunanin kake tun wuri ka dena, har Gaban Abada ba zan taɓa zama taka ba" "Zancen banza kenan, ai tunda mahaifin ki ya riga ya karɓi kuɗin Aurena da ke, ai aikin gama ya gama, fatiha kawai tai mana saura, baɗi i yanzu in da rai da lafiya kina nan kin haihu ko kin kusa" Wani irin kallon banza taiwa Sunusi, muddin ta aureshi ba abunda ze hanata shan guba ta mutu, tai saurin kauda wannan tunanin daga ranta, dan sheɗan kar yai tasiri a zuciyar ta. "Dan Allah ki kwantar da hankalinki, wannan ɗan yaron da kike biyewa ba Aurenki ze ba, dan ba sonki yake ba, Yaushe rabon da ya zo in da kike, ni ɗin ne dai nine me sonki" yai maganar yana dariyar mugunta. "Ko Sadik ya zo in da nake, ko be zo in da nake ba, zuciyata da tasa abu guda ne, da zasu kasance da juna har ƙarshen rayuwa, kuma babu wani namiji da ze taka matsayin da Sadik ya taka a zuciyata" Nan da nan Sunusi ya fusata, yace "Ni kike gayawa haka? A gabana kike zancen wani sakarai?" "Kai ne sakarai ba shi ba, ni mallakin Sadik ce, ba zaka taɓa samu na ba, kuma yadda ka dage kake ƙoƙarin Mallaka ta ta ƙarfin tsiya bayan ka san bana sonka, kaima Allah ba ze ji tausayin ka ba, Allah ya saka min, ba zan taɓa bijirewa zaɓin iyayena ba, amma zan dawwama ina maka Addu'a Allah yai maka abunda kai min" tana gama maganar cikin huci fuu tai gida. Be taɓa zaton Farhan na da baki haka ba, ba ta taɓa masa rashin kunya Kamar haka ba, maganar ma ba son yi take ba, amma yau ta wanke shi tsaf ta nanata masa ba ta son shi. A hankali ya fara jan silifas ɗinsa, ji kake sharaf, sharaf, sharaf ya nufi makwancinsu. "Baban Soyayya, anje gurin amaryar ne?" Haladu yai maganar yana dafa kafaɗar Sunusi. "Bari Haladu ina cikin damuwa wallahi" "Damuwar me kuma, kai daka kusa zama Ango?" "Bana tunanin Aikin da nai akan Yarinyar nan ya kamata, yauma ta sake jaddada min ba ta sona, wancan yaron take so" "Too, ikon Allah abun be kamata ba kenan?" "Alamu sun nuna hakan" Sunusi yai maganar cikin damuwa. "Aikuwa ina tunanin ita ma ba haka take zaune ba, dan haka seka sake sabon shiri". "Hakan za'ayi Haladu, zan sake shiri dole kan bikin nan, dole ta fara sona" "Gaskiya ne, se ka bada himma" Ɓangaren Lilly ma, abun duniya ya isheta sosai, yadda babanta yaci mutuncin Nazir ba ta ji daɗi ba sam, ta ƙallafa rai akan ze mata aure kamar yadda ta buƙata, amma ya watsa mata ƙasa a ido, gashi a yadda take ji gaskiya ba zata iya rabuwa da sir Nazir ba. Gaba daya kunyar yadda zata tunkare shi ma take ji. Ta kirashi ba adadi, amma yaƙi ɗagawa ta tura masa tarin saƙonni, nan ma ba wanda yai mata reply, ta whats app ma duk be duba messages ɗin ba balle yai mata reply. A ɓangaren sa kuwa, yaji zafin abunda mahaifin Lillyn yai masa sosai da sosai, ta wani ɓangaren kuma yaji gara ma da akai haka, shikenan ya huta ba shi ba Auren Lillyn, kowa se ya kama gabansa. Amma da yake Allah ba Azzalumin sarki bane, se wata irin soyayya da ƙaunar Yarinyar suka sake shigarsa, kwana biyu da ba ya amsa wayarta ma, jinsa ya dinga yi kamar a prison, Tabbas shigowar Lilly ratuwarsa ƙaddara ce. Tabbas rabuwa da ita ba abu ne me sauƙi ba, dan sunyi sabo ba ƙarami ba, ga kusanci da suke da shi da juna. Se da ya jera kwanaki biyu, ba ya zuwa makarantar, abun ya ƙara damun Lilly Sosai da sosai, se a rana ta uku sannan ya zo, ranar shi ze shiga ajinsu first period, kallo ɗaya tai masa ta san ba ya cikin walwala, dan ransa a haɗe yai lesson ya fice ko in da take be kalla ba. Yana fita da 'yan mintuna, ta bi bayansa ta tarar da shi yana marking papers, yana ganinta ya haɗe rai sosai ya cigaba da abunda yake, ta ja kujera ta zauna. Ba tare da ya kallet ba yace "can You Please excuse me, i have something to do now" "Korata ka ke?" "Me ze sa ba zan koreki ba, haka shine masalaha ai" "Amma ai ba ni nai maka laifi ba, babana ne" Ya ɗago ya kalleta yace "amma ta sanadin wa akai min, ok dama kin gayyace ni gidanku ne dan a ci min mutunci, a ci zarafina? Kin san mahaifinki ba ze amince ba kika sa naje ya min wulaƙanci?" "Dan Allah ka fahimceni, wallahi be nuna min ze maka haka ba, kawai yace min yana son ku gana ne, wallahi ban san haka ze ma ba, ni kaina banji daɗin abunda yai maka ba dan Allah kayi haƙuri" "Naji na haƙura, amma daga yau kawai mu haƙura mu yanke duk wata alaƙa da ke tsakanin mu, tun da mahaifinki ba ya so, kar inje ya sa a kassarani, ni kaɗai ne namiji a gurin mahaifiyata" Tashi tai daga in da take zaune, ta zagaya in da yake ta hau kan teburin, ta ɗan ƙura masa ido sannan tace "ba zan iya rabuwa da kai ba" "Saboda me?" "Saboda dalili me ƙarfin gaske, kayi haƙuri da abunda mahaifina yai maka, ka bari ya wuce" "Lilly ba zan iya mantawa da abunda mahaifinki yai min ba, dan ba wanda ya taɓa yi min abunda yai min a rayuwa ta" Ta kai hannu kan sajensa da ke ta ƙyalli ta shafa, sannan ta ɗan lumshe idanunta ta buɗe akansa tace "na sani, amma na ari bakinsa na ci masa albasa, kayi haƙuri Please i miss You so Much, ba zan iya rabuwa da kai ba" "Am missing you too, but is better to be apart, da Matsala ta afku" "Meyasa kake kira mana matsala ne? Ba matsalar da zata faru Insha Allah" Duk da ƙarancin shekaru irin na Lilly, se da tai abunda ta sa ya manta da matsalar da mu'amalarsu za ta iya haifarwa a gaba, sosai sheɗan yake ingiza su, suke ƙoƙarin sake biyewa son zuciyar su. Takun da sukaji ne da surutu, alamar ana hawowa step ɗin benen da Office ɗin yake, ya sa Lilly saurin tashi daga jikinsa, ta daidaita nutsuwarta, ba tare da ta iya furta komai ba, tai masa alamar za su waya, ta fice daga Office ɗin, yayin da shi kuma ya lumshe ido, yana maida numfashi a hankali. Su Taslim ne suke hawowa benen, dan zuwa ya koya musu wani aiki. Taslim ta kalli Meena tace " ke tayani gani mana, wai meke going ne tsakanin yarinyar nan da mutumin nan?, ku san kullm fa se mun ganta a nan" Meena tace "ba ance budurwar sa bace, ai ba abun mamaki bane" "Duk da haka, me suke a Office su ka ɗai a saman nan, kullum fa semun ganta anya ustazancin nasa na gaske ne?" Meena tai dariya tace "a'a sedai ki bari in mun shiga ki tambaye shi" su kai dariya gaba ɗaya suka shiga Office ɗin. Nana ce zaune akan gadonta, ta lumshe ido tana karatun Alkur'ani a hankali, cikin sauti me daɗin sauraro, kasancewar ita kaɗai ce a ɗakin Linda ba ta nan. Seda ta kai aya ta buɗe ido, taga Linda da wata ƙawarta sun zubo mata ido, kamar sunga wani abu daban. Cikin harshen turanci tace "Lafiya, meyasa kuke kallona?" Linda tace "wai dan Allah me kike karantawa haka?" "Is my holy book qur'an" Linda tace "wow, kuma kin san abunda kike karantawa, na ga ba kowane musulmi ne yake jin larabci ba" Nana tai murmushi tace "Yanzu balaraben da yake Kirista, idan ya karanta bible ya san abunda yake karantawa?" "A'a, amma ai akwai bible na larabci" Nana tace "to Kasancewar Alqur'ani da larabci, hikima ce ta Ubangiji, karanta shi kuma ko baka san ma'anarsa ba yana samar da nustuwa a zuciyar me sauraronsa, wani abun nasan fassarar abunda nake karantawa. "Hakane, yana da daɗin sauraro kam, amma zan so wata ran ki karanta bible, shima zaki ji daɗinsa" Nana da hausa tace "kaji 'yar baƙin hali, ni zaki canzawa addini, amma da turanci tace "to shikenan babu damuwa" Ƙawar Linda tace "amma meyasa kike saka hijjabi, da dogayen rigunan larabawa, ku Mutanen Africa kuna koyi da larabawa ne?" "Ba da larabawa muke koyi ba, dokokin addinin mu muke kiyayewa, shi yai mana umarni da sanya hijjabi da suturta jikinmu" "Amma da gaske Africa babu Abinci, duk matalauta ne?" Cewar ƙawar Linda. "Ji shegiya da fuska kamar alade, Abincin gidan ubanki muke ci muka girma, ji 'yar banza me koɗaɗɗiyar fuska" Linda tace "ba mu gane me kike cewa ba" Nana tace "Addu'a nake da hausa, bacci nake ji yanzu, ma cigaba wataran" Ta juya ta kwanta ta na cigaba da ƙunƙuni da mita. Mother gani tai lamarin Abba dagaske yake, ya watsar da ita ya fita harkarta gaba ɗaya, sabgar gabansa kawai yake, haka ta dinga lallaɓashi, kamar ta zubar da makamanta, har ta samu ta shawo kansa da ƙyar, ya ɗan sakko ya rage fushin da yake, har suka koma cin Abinci tare da kwana guri ɗaya. Faruk ma yana ta shirye shiryen komawa South Africa, in da zeyi master's ɗin sa, yayin da Khairat ta kamu da tsananin ƙaunarsa, tana ta nan nan da shi tana ba shi kulawa ta mussaman, sam shi be taɓa kawo wani abu ne a ranta na Soyayya ba, ga shi Haseena na ta takura mata, akan dan Allah wai ta haɗa da Faruk tana sonsa. Kwanci tashi asarar rai, tamkar ana jan kwanakin, haka suka dinga gudu, awanni, da ranaku suna shuɗewa, zuciyar Farhan cike da burin sake tozali da masoyinta ta kasa fidda ran Sadik ɗin ta ze dawo gareta, ko ta samu ta rabu da Sunusi, dan yau kusan wata guda kenan da sa ranar Aurenta da Sunusi. Ko a makaranta yanzu ba ta ƙoƙari, bata iya fahimtar karatu sam, in akai test ko jarrabawa ma faɗuwa take a wasu, grade ɗinta yai ƙasa sosai, kullum tana zaune shiru ba sawa ba fitarwa. Kamar kullum, tana wannan tafiyar tata kamar wadda a kaiwa dole, fitowarta daga Makaranta kenan, ta miƙo hanya za ta fito titi ta samu abun hawa, taji ana mata horn, cikin hanzari ta waiga, zaton ta za taga Sadik. "Sena buge ki ki lanjare ko? Kina tafiya kamar ba kya so, ko haryanzu jikin ne?" Murmushin ƙarfin hali tai tace "ina wuni" "Lafiya ƙalau, dama makarantar nan kike zuwa?" Ta jinjina masa kai alamar eh. Yace "Masha Allah, shigo mu tafi' Ta girgiza kai alamar a'a. "Wasa nake da ke, shigo mu tafi nace"  yai maganar yana haɗe rai sosai. Tana matuƙar jin nauyin Abbas sosai, ta buɗe baya zata shiga ya kalleta yace "waye direbanki, gaba zaki shigo" Jin ta take kamar zata aikata zunubi, ba wanda ta taɓa shiga gaban motar sa banda Sadik, wata zuciyar tace idan Sadik ya ganki fa? Ze iya jin ba da daɗi. Haka ta shiga tana wasi wasi, ya ja Motar suka fara tafiya. Abbas yace "Lalallai Baba yayi ƙoƙari, wannan makarantar kike zuwa?" "Scholarship ne na samu" Yace "Masha Allah, you deserves it, dama nasan kina da ƙoƙari ai" Tai murmushi tare da sunkuyar da kai tana wasa da yatsun hannunta, kawai Sadik take tunawa, ta kalli hannun Abbas da yake tuƙi, taji ina ma zata ga hannun Sadik me ɗauke da agogo da zoben azurfa, ta ɗaga kai ta kalleshi ya waigo ya kashe mata ido ɗaya Allah sarki Sadik. Wata irin nannauyar ajiyar zuciya ta sauke, wadda se da Abbas ya waigo ya kalleta yace "Lafiya kuwa?" "Lafiya ƙalau" ta bashi amsa a hankali. "Baki tambaye ni ya akai kika ganni ba, bayan nace miki zanje ƙaro karatu" "Mantawa nayi" Murmushi yai yace "kinji ki, wai mantawa ki kai, ba ki niyya ba dai,na gama clearance next week zan tafi insha Allah" "Allah sarki, Allah ya bada sa'a" "Ameen, Farhan, idan kika kammala secondary School, insha Allah zan karɓi takaddun ki, school of Nursing zaki tafi, zaki dace da aikin jinya, duk da ban san meye ambition ɗin ki ba" Ai kamar ya taɓo mata wani abu da yake damunta ta fashe da kuka. "Subhanallah, meya saki kuka kuma?" Cikin kuka Farhan tace "burina ba ze cika ba doctor, Babana Aure ze min" "Aure kuma? Na zaci da wasa Hajiya take min da tace min an kawo kuɗin Auren ki" Wani irin tausayin Farhan ya mamaye shi, yace "calm down please, yi haƙuri ki share hawayen ki, ai darajar 'ya mace in ba Gidan iyayen ta ba dama to ɗakin mijinta, in dai ze barki ki cigaba Alhamdilillah" Duk da rashin son Magana, da tsananin zurfin ciki irin na Farhan, amma ta tsinci kanta da cewa "bana son sa, ba na ƙaunarsa, ban taɓa son sa ba" Jiki a sanyaye ya kalli Farhan yace "kina nufin ba ke kika kaishi kika ce kina so ba?" "Bana son shi, maganar Soyayya ba ta taɓa haɗani da shi ba, ya tura aka nema masa aurena a gurin Abba, Abba kuma ya amince, Amma bana son shi" "Ya Salam, yanzu na ƙara gano dalilin rashin lafiya da ki kai, amma kin gayawa Abban cewar ba kya son sa?" "Ai ba su taɓa tambayata ko ina son sa ko bana so ba, koma sun tambaya ba zan iya bijire musu ba, saboda sun min komai a rayuwa, ba zan iya bijirewa ba" tai maganar tana wata irin sheshsheƙa. Ya ɗan zuba mata ido, yarinya ce Sosai, sedai ba kowa Allah ke bawa yaro me nustuwa da biyayya a wannan zamanin ba, ba kowace Yarinya ce zata iya hangen nesa da kuma iya Magana kamar Farhan ba. Yai ƙasa da murya yace "ni kin bani dama in tari baban in gaya masa ba kya son Auren?" Tai saurin girgiza kai tace "wannan sirri ne na gaya maka, dan Allah kar ka gaya musu, nasan ba wani dalili da zesa a fasa Auren nan, dangin mahaifiyata ba zasu yadda ba, dan sune suka asassasa lallai a bar karatuna ai min Aure" Abbas ya shiga mamakin wannan wace irin rayuwa ce, akwai banbancim zamani tsakanin rayuwar da su kai a baya da wadda ake a yanzu, amma an takura Yarinyar nan da yawa, gaba ɗaya jikinsa yai sanyi wani irin tausayin ta ya mamaye shi gaba ɗaya. Ya kuma kallonta yace "to ya batun Sadik fa?" Ta share hawayen ta tace "na fara yadda da maganar ka, na Sadik ya barni amma zuciyata ta kasa gazgata hakan, Sadik ba ze taɓa barina ba" "How sure are you,ba ze taɓa barinki ba?" Shiru tai ta kasa Magana. "Ki bawa wanda zaki Aura ɗin dama mana, he might be more than Sadik" A hankali ta girgiza kai tace "Never, he is irreplaceable! Ba Wanda ze iya maye gurbin sa" Tana gama maganar ta fita daga cikin Motar Abbas, sedai tana fita ɗin Sunusi na jikin pole a tsaye, yana binta da ido!. Littafin nan ₦300 ne kacal. 0009450228 Aisha Adam Jaiz Bank 07063065680 KO kuje manhajar AREWA BOOKS ku siya. domin kuwa ya fi sauƙi ta can. Littafin nan ₦300 ne kacal. 0009450228 Aisha Adam Jaiz Bank 07063065680 KO kuje manhajar AREWA BOOKS ku siya. domin kuwa ya fi sauƙi ta can. Mother ta kalli Faruk tace "ni miƙomin wayar in ga meka nuna masa haka?" Faruk ya miƙa mata wayar, hoton Sadik ne a beach, daga shi se gajeren wando, ya tara uwar suma kaya guda a kansa, ya yiwa gefenta ado da pink color, ga matan turawa da bikini, irin watsatsun kayan nan da suke sawa, halittu a waje, duk halittu da tsiraicin su a waje. Ya ɗaura wani ƙaramin abu a wuyansa, fuskarsa ɗauke da baƙin glass, matan nan duk suna kusa da shi su kusan huɗu a kai hoton. Mother tai scrolling, hotuna kala kala, na Sadik da wannan mata, wasu da abokansa, wasu a club babu guda ɗaya da yayi ma a cikin ajin. Mother tace "Innalillahi wa innalillahi raji'un, Faruk meyasa ka nuna masa?" Faruk yace "wallahi rikicewa nayi, kuma ko ban Gaya masa ba ze iya samun labarin hakan" Mother tace "kaiii, Sadik sam baya gudun matsala, kullum cikin jawa kansa magana yake, Allah kaɗai yasan hukuncin da ze yanke a kansa. Ta tashi da sauri tabi Abba ɗakinsa, ta tarar da shi a zaune a gefen gado ya dafe kansa, yai shiruuu yana tunani. "Abba dan Allah kar wannan abun ya ɗaga maka hankali, abi komai a sannu" Abba ya kalleta yace "karya ɗagamin hankali kika ce? Meyasa ke kullum ƙoƙarin ki ki kare yaran nan in sunyi laifi, ba tunanin yadda za'a maganace matsalar da suka ɗakko ba?. Ba zan ɗauki wannan sakarcin ba sam. Se yanzu na sake gane hikimar Hakimi, da yace kar a turashi ƙasar waje karatu, kin sa ina ganin kamar takurawa yaran nan ake, amma Sadik kam fitinar sa ta shallake tunani na, duk 'yan uwansa da sukaje su kai karatu ba wanda yai haka se shi, gaba ɗaya ya fita zakka a cikin yaran nan, babu wanda yai fitinar sa, dole ya dawo gida, yazo yai karatun a nan, nan da shekara goma ƙila ya gama degree, iya azabar strike da strees na karatun Nigeria ma ya ishe shi" Mother tace "dan Allah Abba, kar kace ya dawo yayi karatu a nan, dan Allah kayi haƙuri" Abba ya miƙe yace "se kuma kiyi" daga nan ya fice ya bar mata ɗakin. Wayarta ta ɗakko, ta kira wayar Sadik, ta kirashi ya kai sau huɗu sannan ya ɗaga, yana ɗagawa yace "what's up Mum, am sorry bana kusa da wayar ne" "What's up ɗin ubanka? Sadik meka aikata haka?" A ɗan shagwaɓe yace "me nayi?" "Kamar ya me kayi, dama abunda aka turaka ƙasar waje yi kenan? Hotuna da 'yan mata tsirara" Yace 'Mother, ba fa wani abun nai ba, naje beach ni da friend's ɗina ne, suka ganni sukace suna son muyi hoto tare, so ni kuma naga ba wani abun bane dan dai hoto kawai shine mukayi" "Zakaga ba wani abun bane, aikuwa gashi nan ya fusata ya fara iƙirarin seka dawo Nigeria" "In dawo Nigeria kuma? Ya akai yaga hoton ne?" "Muna zaune muna cin abinci, Faruk ya gano hotunan a social media, ni dai ba ruwana" Sadik ya marairaice yace "haba Mother, ba fa wani abun bane, dan Allah ki ganar da shi, ya za'ai ace in dawo Nigeria, ai se ai min dariya ma, dan Allah ki bashi haƙuri" Mother tace "Ni kai na ba zan so ka dawo Nigeria ba, amma dai zan an yadda zan da shi, amma ka kiyaye na gaya maka, idan ka kuma ɗebo wata rigimar zan sa muku ido" "Ok, Mum thank you very much I miss you so much" "I miss you too, ya school ɗin?" "Alhamdilillah, mun kusa fara exams ma" "To masha Allah, Allah ya bada sa'a" "Ameen, ashe Broz shima ya kusa tafiya ya barku ku kaɗai?" "Eh a wannan watan ze tafi matsers Insha Allah, Allah ya bada sa'a" Ya amsa da Ameen sannan ya kashe wayar. Ana ta hayaniya gidan su Farhan, Abba ya dawo ya tarar da su cireki cirko, yace "lafiya meke faruwa ne?" Umma tace "yarinyar nan ce, muke tunanin ko iska ta tayar" Cikin rashin fahimta Abba yace "Iska kamar yaya?" Adda Maryam tace "yo tun da ta shigo, ta wuce ɗaka ta faɗa kan katifa ba ta kula kowa ba, shiyasa nace wannan hadda lamarin iskokai" Sunusi ne yai sallama a gidan ya risina ya gaida su Umma. Abba ya kalli Sunusi yace "ya akayi ne?" Umma tace "na aika a kirashi ne, ko karatu za'ai mata" Abba yace A'a ba ta kai ga haka ba, bari inga Farhan ɗin. Abba ya shiga ɗakinta, ya tarar da ita a kwance ta lumshe idanunta, kanta ko ɗankwali babu, gashin ta duk ya cukurkuɗe, da alama ko tazar Kirki baya gani, gata masha Allah tana da gashi Sosai. Abba ya ɗakko bedsheet ɗin dake kan katifarta a ninke, ya lulluɓa mata, sannan ya sa mata hula a kanta. Adda Maryam ta buɗe baki tana kallon ikon Allah, yadda yake taɓa 'yar sa ta fari ba kunya. A hankali ya kira sunan Farhan. Da ƙyar ta buɗe idanunta da su kai mata nauyin gaske, ta kalli cikin idon Abba. Seda ya tsorata ganin yadda idanunta su kai jawur, tamkar an zuba mata barkono a idon. Yace "meya sameki haka?" Ji tai kamar tace masa Auren nan ne ba ta so. Amma ta lumshe Idonta. Ya kuma cewa "ki gayamin meke damunki?" A hankali ta nuna masa kanta da ƙirjinta. Abba yace "ciwo suke miki?" Ta jinjina masa kai, "Sannu Allah ya baki lafiya, bari muzo mu tafi Asibiti" Tai saurin girgizawa Abban kai. Abba ya kalli Umma yace 'ko tana da sauran magungunan ta, a bata ta sha?" Ita Umma ko kalar magungunan Farhan ɗin ma ba ta sani ba, balle ta san ko akwai ko babu. Tace "ni ban san in da ta Ajiye magungunan ba" Abba yace "shikenan, bari inwa Ko Isa me chemist ne magana ya zo ya duba, yaga maganin da za'a bata, in kuma Asibiti zamu tafi shikenan" Abba ya fito tsakar gida, ya tarar da Sunusi a tsaye, ya kalleshi yace "karka damu, ba wasu iskokai da suke damunta, Kamar wannan ciwon da tai ne, tace kanta da ƙirjinta ke ciwo, bari inje gun yaron nan me chemist ya zo ya ga abunda ya dace ayi" Sunusi yace "Abba ai duk ba se anyi wannan ba, bari inje in mata rubutu yanzu zata warware, ba se an kira wani ya dubata ba" Abba yace "ban ƙi ta taka ba, amma a dubatan ma yana da kyau, saboda a san daga ina matsalar take, karka damu" Abba yaja Sunusi suka fita. Farhan kuwa ita kaɗai ta san abunda take ji a ranta, kwata kwata ko surutun mutane ba ta son ji, ji take ina ma zata samu wani guri in da zata kasance ita kaɗai ba tare da wani ya takurawa Rayuwar ta ba. Ba a jima ba se ga Abba da me chemist, tana nan kwance ya auna BP ɗinta ya ga ya hau, ga zazzaɓi da ya rufeta. Ya kalli Abba yace "gaskiya jininta ne ya hau, kuma naji ga jikinta da zafi sosai, bari in bata taimakon da zan iya, da yamma abunda hali yai in ta warware shikenan, in bata warware ba se a tafi Asibiti". Abba yace "ba damuwa, amma ina mamakin abunda yake sa Yarinyar nan hawan jini haka, 'yar mitsitsiyar yarinya kamarta" Ya saka mata ruwa da allurai, nan da nan wani wahallalen bacci yai awon gab da Farhan, wanda rabon da tai baccin awa biyar cikakke har ta manta. Sunusi Kuwa cika yai tayi yana batsewa, yana hura hanci. Haladu yace "wai yau kuma kai da wa kake ta wannan buɗe ƙofar hanci haka?" "Wannan mutanen mana, kawai idan yarinya ba ta da lafiya se kira wani, kwazgwamemen ƙato ya rufu a kanta,nace in mata rubutu ya isa amma babanta yaƙi" "Kaga Sunusi, har yanzu fa baka Aureta ba, suna da cikakken iko akan 'yar su, kai ka fiye Matsala wallahi" "Wace irin matsala? Ya ni da matata ba zan kishi a kanta ba, ni bama wannan ba, ina ga nayi nasara akan wannan yaron da take kulawa Sadik, naga bam sake ganinsa ba, yanzu ɗan gidan waccan matar ne naga yana rawar kai da shishshsige mata, wallahi idan be wasa ba idan nai masa wani zazzafan aikin, se ya kusa haukacewa" Haladu yace "Subhanallah, Sunusi wannan kuma ai kazo da son zuciya, ya zaka haukata mutum akan abunda be kai ya kawo ba" "Agurinka ne be kai ya kawo ba, ni agurina lamari ne me girman gaske, kana ganinsa da kyau da Mota, ni ina yawo a ƙasa haka kurum inje ta koma son sa, ni nayi nayi ta soni Yarinyar nan taƙi, kwata kwata aiki baya tasiri a kanta sam, yi nake amma Kamar bana yi" Haladu yace "to ai kaine baka mata yadda suke mata, shiyasa taƙi sonka, ka dena mata hargowa da nuna isa, kalli Ranar da suka fito da ɗan gidan Hajiyar nan, kamar ze shige cikin ta, babba da shi amma yayi ƙasa da muryar sa, se Magana yake mata cikin nutsuwa, kai kuma komai naka cikin hargowa kake yi mata, kalli yadda ka tara mu a ƙofar Gidan nan dan Allah, ka gayamata miyagun maganganu a gaban mu, ta yaya zata soka?" "To nima ɗin ce maka a nai bana mata, wallahi ina lallaɓa Yarinyar nan shegen taurin kai ne da ita da kuma kwaɗayi, su suke ɗawainiya da ita kawai" Haladu yace "to Allah ya kyauta, kamata yai dai ka gano in da matsalar take ka gayara, ni zanje aiken da malam da yai min" Sunusi yace "seka dawo" Farhan ba ta sake sanin in da kanta yake ba, se bayan sallar magariba, ba ƙaramin jin daɗin baccin nan tai ba, dan rabonta da bacci haka har ta manta. Adda Maryam ta haɗa mata ruwa tai wanka, amma Abinci ya gagara ciwuwa, da ƙyar ta sha tea, tace ta ƙoshi. Abba ya ƙi gayawa Mother matakin da ze ɗauka akan Sadik, tunda yace se Sadik ya dawo gida be kuma ce mata komai ba. Ta sameshi a ɗaki yana danna waya, ta zauna kusa da shi ta kalleshi tace "Abba nifa haryanzu baka gayamin wani mataki zaka ɗauka akan Auta ba" "Ai na gama magana, me kike so ince miki kuma? Gida ze dawo ya haƙura da karatun kawai, da ya lalace gara ya dawo ya zauna, in ya ga dama yayi karatun a nan" Mother tace "dan Allah kar kayi haka, ka dai ja masa kunne, kuma nima na kirashi, nai masa faɗa dan Allah ka ƙyaleshi" Abba ya girgiza kai yace "is too late" "Is not late, kaga yaro ne shirirtar Ƙuruciya ce ke damunsa, amma baze ƙara ba" "Ya a kai kika san ba ze ƙara ba?" Mother ta gyara zama tace "Munyi waya da shi ai, yace baze sake ba" Abba ya sake girgiza kai yace "na gama yanke hukunci kuma ba zan canza ba" "Dan Allah kar kayi haka,kas... "Kinga, ya isa haka na gama magana" Abba ya fututtuke yaƙi saurarar Mother, haka ta tashi jiki ba ƙwari ta bar ɗakin ta koma sashinta. Dr. ta kira a waya, ta sanar masa abunda Sadik yai, da hukuncin da Abba ya yanke. Usman yace "Wallahi Mother Sadik is  so much spoiled, mu meyasa ba muyi haka ba da mukai karatun a waje, se shi?" A fusace Mother tace "ba kiranka nai kai min faɗa ba, na ga mahaifinka yana shawara da kai, shiyasa na kiraka ka taushe shi kaima, dan ni yaƙi saurarata sam" Usman yace "to Allah yasa ni ɗin ya saurare ni, dan abunda kika kasa yi ba lallai mu mu iya ba". "Ai kwanan nan duk ya canza wallahi, ka dai tuntuɓe shin, ko Allah ze sa ya yadda" Usman yace "shikenan, zan shigo gidan zuwa gobe insha Allah" Mother tace "Allah ya kaimu, ka gaida Jiddan" Ya amsa da "za taji insha Allah". Lokacin Auren Farhan na ta ƙaratowa, ba tare da samun wata fahimtar juna tsakanin ta da Sunusi ba, kullum cikin faɗa suke da tashin hankali, Gashi ta kasa fidda ran Sadik ze dawo rayuwarta, wasu lokutan ta kan tuna da Doctor Abbas, dan ba zata taɓa manta Alkhairinsa ba, dan set ɗin tukwane non stick ya sai mata, da gas cooker, da kuɗi har dubu hamsin, haka Hajiya ta kai gidansu Farhan tace inji Abbas. Idan Farhan ta ga kayan da ake siya da sunan Aurenta, se taji ina ma gidan Sadik za'a kaita da kayan nan ba gidan Sunusi ba. Tayi duk yadda za tai ta cire Sadik daga ranta, amma abu ya gagara, gashi kamar wadda akaiwa Asirin farinjini, duk da ƙanƙantar shekarunta, kusan kullum idan ta fita se tai saurayi, suyi ta binta, abunda yake ƙara caza mata kai kenan, shikuma Sunusi da ya ganta da wani se ya hau bala'i yana surfa mata jaraba. Gashi ya ɓata mata suna a unguwa, tun lokacin da ya tara mata Mutane a ƙofar Gidan su Abbas. Abubuwa suka sake damalmalewa Farhan, ta rasa in da zata saka ranta taji sanyi. Lilly kuwa abu kamar wasa, suka koma ruwa ita da Nazir, dan tamkar matar da ya sa sadaki ya auro haka ya maida ita, duk lokacin da ya buƙace ta, za taje ba musu ba komai. Mussaman yake mata allurar family planing, saboda gudun sake samun matsala, makarantar kanta wasu lokutan ba ta zuwa, se tai tafiyar ta gidan sa, fafur taƙi yadda direba ya cigaba da kaita yana ɗakkota, a cewar ta ai yanzu tai girman da ta wuce wannan level ɗin. Abba yai banza da batun Sadik, be kuma yin Maganar ba, har Mother tai zaton ya haƙura da batun ne, ta cigaba da sabgogin ta. Rana tsaka yace mata zeje London. Ta tashi hankalinta "dan Allah idan akan maganar yaron nan zakaje kayi haƙuri, na gaya naka baze sake ba" Abba yace "Ai ba Sadik kawai na ajiye a London ba, ina da 'yar da zanje in ga halin da take ciki, dan haka ni yanzu babu ruwana da lamarin ɗanki, 'ya ta zanje in gano" Maganar Abba taiwa Mother ciwo nesa ba kusa ba, ta so ta mayar masa, amma ta ƙyaleshi, dan yanzu se su kuma haurawa da shi, dan haka ta ƙyaleshi. Nana farinciki take yau kamar me, tana murna yau za'ai musu hutun session, watanninta huɗu kenan tunda aka kawota ba ta sake ganin wani yazo mata daga Nigeria ba, kuma ba ta fita daga makarantar ba. Ta sa ran ganin Abba, Amma ga mamakinta se taga Steve, duk da ba haka ta so ba, amma hakan be hanata nuna farinciki da ganin sa ba. Shine ya ɗauke ta, ya tafi da ita gidansa in da suka taɓa zuwa farkon zuwan su garin. Matarsa da yaransa na da kirki matuƙa, suka karɓeta cikin mutunci. Tana son ta tambayi ina Abba, amma se taga zasuga kamar abunda suke mata suna ta tarairayarta, kamar ba tai appreciating ba, dan haka tai shiru. Se yamma liƙis, ba tsammani taji muryar Abba, kamar an mata kyakyawan Albishir haka ta tashi cikin murna da fara'a. Abba yaga Nana tai fresh da ita kamar ba ita ba, yai murna ƙwarai da gaske da ganin Nana. Yaci Abinci yai salla, ta dinga ba shi labarin Makaranta da kuma ƙawayen da tayi a makaranta. Wannan karon a gidan Steve Abba ya kwana shima, da safe taga an fito da Akwatin ta, da kuma Akwatin kayanta na farko da ta zo da su, duk an saka a Mota. Tai ta murna tana tunanin Nigeria za su dawo, sedai ta ga sunyi doguwar tafiya, sannan suka shiga wata unguwa, me ƙarancin gidaje, kusan gidajen da suke unguwar iya wani ɗan rukuni ne kawai. Wani matsakaicin gida akai parking, taga su Abba sun buɗe motar sun fita, Abba ya leƙa yace "Nana fito" Ba musu ta fito, taga Steve ya sauke Akwati nan ta daga Motar. Kai tsaye Abba ya nufi Gidan, yasa hannu ya buɗe ƙofar Gidan, suka bi bayan Abba. A falo Nana tai tozali da Sadik, ba ƙarya yayi kyau fatarsa tai fresh, sumarsa se ƙyalli take ya ƙara wani kyau na musamman. Seda gabanta ya faɗi, dan rabon da ta ganshi tun Ranar da suka bar gidan Steve aka kaita Makaranta. Kallo ɗaya yai mata ya ɗauke kansa, suka nemi guri suka zauna, Steve ya fita waje ya basu guri. Abba ya nemi guri ya zauna, sannan yai wa Nana umarnin ta zauna, ba musu ta nemi guri ta zauna tana rarraba ido, tare da satar kallon Sadik da yake ta haɗe rai. Abba ya kalli Sadik yace "Wannan shine hukuncin da na yanke a kanka, wallahi da niyyata hatta makarantar, se ka barta ka koma Nigeria, amma 'yan uwanka su kai ta bani haƙuri, da ne nake maka kallon yaro ƙarami, amma tunda abunda ka zaɓawa kan ka kenan, ga matarka na kawo maka, idan ka ga dama ka kwaɗata ka cinye, sedai ba zan cigaba da maimaita maka ba, duk abunda ka ga dama kai mata, daidai nake da kai, dan ba zan sa ido ka lalace a banza ba, ka ɓatamin suna". Ya maida idonsa kan Nana yace "Nana, Steve ya karɓo miki takardar transfer, in aka koma Makaranta ze kaiki sabuwar makarantar da zaki koma, daga nan gidan zuwa makarantar ba nisa, day ce Makarantar, Steve ze dinga zuwa yana duba ku, duk lokacin da yai miki wani abu, na rashin jin daɗi, ki karɓi wayar Steve ki kirani ki gayamin. ki kwantar da hankalinki, ki masa biyayya tunda Allah ya ƙaddara mijinki ne, kai kuma in kaga dama, kai mata riƙon da ka ga dama, zaka ga yadda zan da kai, miƙomin wayarka" Sadik ya ciro wayar ya miƙawa Abba, Abba ya zare layukan wayar, da wayar ya sa a aljihunsa, ya miƙe ya nufi hanyar fita. Nana tabi Abba da kallo, kamar ta tashi ta bi Abban da gudu, dan ta san kashinta ya bushe tun da aka ce ta zauna  ita da shi a gida ɗaya, ba ta san laifin da yayi Abba yake masa faɗa haka ba, amma da alama laifin da yayi babba ne. Ba ta ƙara tsurewa ba, se da taga irin ɗan banzan kallon da yake binta da shi, nan da nan ta sake jin jikinta yai sanyi. Daga Nana har Sadik aka rasa wanda ze raka Abba, saboda kowa da abunda yake saƙawa a zuciyar sa. Suna jiyo ƙarar motar Steve, Sun tafi. Nana ta ɗaga kai ta kalli Sadik, suna haɗa ido ya ja wani uban tsaki ya tashi ya fice ya bar gidan gaba ɗaya. Nana ta zauna tsuruu ita kaɗai a zaune, ba tai zaton za'a mata transfer ba, se yanzu take jin ta shaƙu da su Linda Sosai. Farhan dai gata nan gata nan, wasu lokutan kamar mara hankali, gaba ɗaya gudun mutane take yanzu sosai da sosai, kullum se dai ta ƙule a ɗaki, tai kuka tai tunani rashin son maganarta ya ƙaru fiye da da, babban abunda yake damunta shine rashin bacci da matsanancin feelings da take fama da shi, wanda Duk silar Sadik ne ta shiga wannan halin da take ciki. Ta dawo daga makarantar dare, ta biya ta gurin me chemist ɗin nan da ya zo ya dubata. Suka gaisa Sannan tace masa "dan Allah maganin bacci nake so ka bani, da rage damuwa" Ya kalleta yace "wane irin maganin bacci kuma da rage damuwa?" Tace "wallahi nafi wata uku bana bacci duka dare, se ciwon kai bana iya bacci" "To ai kinga jininki ne yake hawa yana sauka, haƙuri zaki ki cire duk wata damuwa da take ranki" Farhan tace "dan Allah ka temaka min, ko baccin ne in samu in dinga yi, kaga allurar da kai min kwanaki naji daɗin ta, ka temaka min kar kaina ya tarwatse" Ya ɗanyi shiru Sannan yace "shikenan ba damuwa, bari in baki amma kaɗan kije ki gwada, duk in da kika sha na kwana uku zuwa huɗu, se ki dena sha" Farhan tace "to, nawa ne?" Yace "karki damu, ki bar kuɗin kawai, kije ki jarraba Allah yasa a dace" Ta karɓa tai masa godiya ta tafi gida. Nana gajiya tai da zama, dan babu alamar Sadik ze dawo Gidan nan, ta tashi ta shiga lelleƙa ɗakunan, haka kurum gidan yake mata kama da wani gida, a wani film na horo da ta taɓa kalla a gidan Dr. A tsorace ta samu banɗaki tai alwala tai salla ta dawo falon ta zauna, se zazzare ido take kamar korarriya. Wata irin yunwa se sakatar ta take, ta rasa in da zata sa kanta, wasa wasa har duhun magariba ya fara yi, babu Sadik babu alamarsa, hankalin Nana ya tashi, tsoro take ji sosai ta koma wajen ƙofa ta zauna, tana ɗaɗɗaga kai tana kallon gidan. Ba zato ba tsammani taji an buɗe ƙofa, a gigice ta tashi zata zura da gud, amma taga Sadik ne, kallo ɗaya yai mata ya tsaki ya wuce ya nufi wani ɗaki, yasa mukulli ya buɗe ɗakin ya shiga. Miƙewa Nana tayi ta koma kan kujera ta zauna, tana jiran Sadik ya nuna mata in da zata ajiye Akwatunan ta. Sedai ko motsinsa ba ta kuma ji ba, tashi tai ta nufi in da ya shiga, ta tura ƙofar da sallama. Yana zaune a gefen gado, hannunsa ɗauke da sabuwar waya yana dudduba ta, ya ɗaga kai ya kalleta yace "uban me kika biyo ni ki min?" Ta cuna baki tace "ni yunwa nake ji, kuma baka nunan in da zan ajiye kayana ba" "Meya hana ki tambayi wanda ya kawo ki abun da zaki ci?" Mamaki ya kama Nana, meyasa Sadik sam ba shi da ta ido ba shi kunya? "In da zaki kwana kuma, in kin ga dama ki kwana a waje, matsalar ki ce, ki ɓace min daga gani na kan in zo in saɓa miki" mamaki ya hana Nana motsawa daga in da take, Sadik ya taso ya turata waje, ya rufe ƙofar ɗakinsa. Jiki a sanyaye, ta koma kan kujera ta kwanta, zuciyarta na wani irin tafasa, nan da nan ta fara kuka, dama ba ai mata wannan transfer ɗin ba, an barta a boarding ɗin ta, dan babu alamar imani a tare da Sadik sam. Garin akwai sanyi sosai, ta buɗe kayanta ta ɗakko bargo ta lulluɓa, ta dinga kuka a cikin bargon, ta san kashinta ya bushe a wannan zama da za suyi. Da Abba ya koma gida ba yadda Mother ba tai ba, akan se taji matakin da Abba ya ɗauka akan Sadik, amma fafur yaƙi gaya mata, ta kira wayar Sadik amma wayar ba ta shiga. "Dan Allah ka gayamin matakin da ka ɗauka akan Yaron nan" Abba yace "Ai na gaya miki ni ba gurinsa naje ba, gurin 'yata naje" "Amma na kira layinsa baya shiga fa" Abba yace "wannan kuma ban san dalili ba" Cikin damuwa Mother tace "Yanzu kaje har ƙasar ka dawo, ba ka je ka ganshi ba?" Abba yace "to menene a ciki, tunda ya nuna ban isa da shi ba" Kan Mother ta kuma magana, yai tafiyarsa ya barta a gurin. In da a kai sa'a, in da su Nana suke akwai wani ɗan ƙaramin masallaci, kasancewar akwai musulmi a unguwar. Kan Sadik ya tashi Nana ta tashi, dan sanyi ya dameta sosai da sosai, tai alwala ta tada salla, Sadik ya wuce ta ya fice ya tafi masallaci. Bacci ne ya kuma kwashe Nana, motsin Sadik ne ya tashe ta, ta buɗe ido taga ya shirya ya ɗau jaka, alamar fita zeyi. Nana ta kwaɓe fuska tace "wai yanzu ma fita za kai? Ni wallahi tsoro nake ji" Wani Mugun kallo yai mata, yace "uwar tsoro kike ji ba tsoro ba" "Dan Allah to ka bani abunda zan ci, kar yunwa tai min illa" Ko saurarar Nana be ba, ya fice yace "zaki gane baki da wayo, izayar da kakanninki su kai min akan ki zan rama". Haka Nana ta kuma wuni da yunwa, banda kuka ba abun da ta ke yi, se wajen ƙarfe tara na dare sannan Sadik ya koma gida, ya tarar da ita ta ci kuka, idanunta sunyi wuri wuri, ya wuce ɗaki abunsa, wajen mintuna goma da wucewar sa Nana ta tashi ta bi shi ɗakin. Yana zaune yana cin Abinci, wanda Nana sam ba ta san me yake ci ɗin ba, kawai se ganinta yai a gabansa, ta sa hannu ta fara cin Abunda yake cin. Ba shiri ta furzar da abunda ta sa a bakin nata saboda azabar yaji, kawai ta kuma fashewa da kuka. Sadik ya bita da ido, yace "ubanwa yace ki zo min ɗaki?" "Yunwa nake ji wallahi, gaba ɗaya cikina ciwo yake" "To ni na ajiye ki da zan nemo abun baki?" "Dan Allah ka temaka min, kar in mutu" Kawai Sadik ya tuna yadda ta dinga sintirin ba shi Abinci a ɓoye, idan aka bashi abunda ba ya so a ƙauye. Tashi yai ya barta a ɗakin, mintuna kaɗan se ga shi ya dawo, ya ajiye mata madara da fruit a gabanta. Ta kalleshi tace "nifa Abinci nake son naci, yunwa nake ji, ta yaya wannan zam ci in ƙoshi?" Tana faɗar haka ya durƙusa ya ɗau plate ɗin ya koma gefe, ya fara yankawa ya na ci. Haushi ya kama Nana, hankalinsa kwance yake cin abunsa, wato ta mutu da yunwa. Tashi tai ta ɗauke plate ɗin daga gaban Sadik, tai waje tana kuka, dan ba yadda za'ai ta ƙoshi yadda ta kwana biyu ba ta ci ba. Farhan taji daɗin maganin nan da ta karɓa a chemist, tayi bacci Sosai da sosai, wanda rabon da Farhan tayi shi tun suna tare da Sadik, taji ta samu sassaucin baƙin cikin da take ciki. Kamar yadda me Chemist ya gaya mata, kwana uku ta ajiye ta dena sha, amma fa damuwa ta kuma dawowa, mussaman yanzu da saura wata ɗaya ya rage Aurenta da Sunusi!!! Littafin nan ₦300 ne kacal. 0009450228 Aisha Adam Jaiz Bank 07063065680 KO kuje manhajar AREWA BOOKS ku siya. domin kuwa ya fi sauƙi ta can. Littafin nan ₦300 ne kacal. 0009450228 Aisha Adam Jaiz Bank 07063065680 KO kuje manhajar AREWA BOOKS ku siya. domin kuwa ya fi sauƙi ta can. Haka Farhan ta cigaba da gudanar da rayuwarta, kamar mara cikakkiyar lafiya. Babu wanda ta gayawa batun za tai Aure a cikin 'yan makarantar su, dama ba harkar mutane take shiga ba, dan ba ta da wasu ƙawaye, rayuwarta kawai take yi. Tana zaune a ajinsu, tai zurfi a cikin tunani, taji an dafa ta, a hankali ta waiga taga waye ya dafata. Tai tozali da Lilly, Lilly ta zauna a kusa da ita tace "Farhan, wai dan Allah meyake damunki haka?" Fahan tace "me kika gani?" "Kin ga yadda ki kai wata irin rama kuwa? Kullum cikin tunani kike, ga malamai suna ta complain akan kin dena karatu yanzu haba Farhan" Shiru Farhan tai ta sunkuyar da kai ƙasa. "Farhan" Lilly ta kira sunanta. Ta ɗago ta kalli Lilly. "Ko dai dan Sadik ba ya makarantar nan ne yasa duk kika zama wani iri?" Jurewa Farhan take ƙoƙarin yi, ta girgizawa Lilly kai, amma cikin rashin sa'a ƙwalla ta taru a idon Farhan, dan tun bayan Doctor Abbas babu wanda ya kuma taɓo mata abun da yake damunta. "Yasalam, yi haƙuri idan na faɗi wani abu da be miki daɗi ba, amma ki yi haƙuri, naji ance babu wanda ya san ze yi tafiyar nan, ciki kuwa har da ke, sam be kyauta ba, amma kiyi haƙuri ki kwantar da hankalinki, wallahi duk kin rame Farhan" Farhan a ranta tace 'da za a ƙyaleni da Auren Sunusi, a barni da tunanin Sadik kawai, da na samu sassauci a raina' Amma a fili ta kasa Magana sam, se ƙoƙarin mai da hawaye kawai da take yi. Lilly tace "Farhan, ke naki me sauƙi ne, Soyayya shu'umar a bace, mussaman idan ta kama ka a lokacin da baka shirya mata ba, Sadik be kyauta ba, dan babu wanda be san Soyayyar ku ba, amma ni dai roƙona a gareki kiyi haƙuri ki manta da shi" Se da ƙirjin Farhan ya buga, kowa seyace ta manta da Sadik, how could this be possible, ya tabatta Soyayyar su RUƊIN ƘURUCIYA ce kenan?. A zahiri ta jinjinawa Lilly kai, dan zuwa yanzu surutan Lillyn sun cika mata kunne, sam ba ta son hayaniya ko yaya take yanzu. Sam Nana ba ta ji ta ƙoshi ba, saboda yunwa take ji sosai da sosai, amma Sadik ya haɗata da fruit, har gara madarar ta temaka mata, saboda maiƙon da ke jikin madarar. Yau ma a falon ta kwana, kwanciyar ƙasa da ta kan kujera ta sa, haƙarƙarinta da wuyanta se ciwo suke mata. Yau bayan tai sallar Asuba, taƙi komawa bacci ta nemi guri ta zauna, Har ƙarfe bakwai, Sadik ya shirya ze tafi makaranta, miƙewa tai tsaye ya zo ze wuce ta kalleshi tace "Nifa yunwa bake ji wallahi" "Se ki cinye ni ai, bani hanya ni zan wuce" "Dan Allah ka bani abun da zan sawa cikina, wallahi yunwa za ta kashe ni" "In da zata kashe kin ai da na huta" Hawaye ya taru a idon Nana, dan karma tai kuka yaji tausayinta, ya raɓata ya fice. Nana ta zauna ta ci uban kuka, har wajen ƙarfe tara, sannan ta gaji ta tashi, ga wanka ta na son yi, ga yunwa ta addabeta. Ta tashi ta dinga leƙe leƙe, har ta gano Kitchen, ta shiga tana duba Kitchen ɗin, kayan da ke Kitchen ɗin, sun sha banban da irin namu na Nigeria, wasu abun akwai a Nigeria wasu babu ba ta sansu ba, mussaman ita da take ƙauye. Ta buɗe fridge ɗin da ke Kitchen ɗin, amma bakomai a ciki se wani sauran yoghurt. A kitchen ɗin ta zauna ta shanye shi tsaf, ta ajiye kwalbar amma ba ta ji alamar ƙoshi ba. Ga shi wanka take son yi, amma babu sabulu a banɗakin da take Alwala. Daga baya ta yanke shawarar shiga ɗakin da Sadik yake, aikuwa ta samu kayan wanka a ciki, ta samu tai wanka, ta canza kaya ta shafa creams ɗin sa, ta haye gadonsa tai kwanciyarta. Se bayan azahar Sannan ta tashi, tai salla ta ɗakko Akwatinan ta ta ajiye su a cikin ɗakinsa. Yau a kai sa'a da la'asar ya dawo, amma ya tarar da ita a falo, duk tai wuri wuri saboda yunwa. Ta na kallonsa ta shareshi ba ta kula shi ba, shima kuma be kulata ba, ya shiga ɗakinsa yai wanka ya canza kaya, Sannan ya dawo falon ya sameta ya ajiye mata wani ƙaramin pack a gabanta. Cikin sauri ta buɗe park ɗin, farfesun wata ƙatuwar kaza ce a ciki, se ƙamshi take. Ba ta san lokacin da tai murmushi ba, taje ta wanke hannunta, ta sa kazar na a gaba ta dinga ci saboda ba ƙaramar yunwa take ji. "Ke! Ke! Kina ina?!"ta jiyo Sadik yana ƙwala mata kira. "Kut, nice ma ke ɗin, wallahi ba zan amsa ba" ta cigaba da cin kazarta. A fusace Sadik ya fito yace "kina ji ina miki Magana kika shareni, uban waye yace ki ajiyemin Akwatin ki a ɗakina?" "To ni a ina zan ajiye?" "A kaina zaki ajiye" ya bata amsa yana huci. Ko kallonsa ba tai ba ta cigaba da cin abunda ke gabanta. Sadik ya kai matuƙar ƙulewa da haushi, se jinsa tai yana janyo Akwatinan yana shiga wani lungu a falon. Tashi tai da sauri ta bi shi, dan ganin ina ze kai mata kaya. Ɗakina babba, da gado da mudubi kamar na Sadik, har da kayan wasa su teddy da komai da komai, ga zane zane masu kyau, da a kai framing ɗin su, aka saka a jikin bango. Ya waigo ya kalleta, jin takunta a bayansa yace "Nan shine ɗakinki, karki kuskura ki kuma shigarmin ɗaki, na gaya miki" Nama tace "Amma ka san da nan ɗin, dan mugunta ka barni nake kwana a cikin sanyi, wuyana se ciwo yake" Tsaki yai ya juya ze fita tace "Amma, naga ɗakin a ƙarshen gida, in abu tsoro ya zo fa, ko kuma gobara ta kama ai har abun ya cinye ni kan in fito" Sadik ya kalleta da mamaki, wannan yarinyar wasu lokutan Mahaukaciya ce, wai batun gobara take da abun tsoro. Tsaki ya ja, ya fice daga ɗakin ya barta ta na cigaba da kallon ɗakin. Ta gama mamakinta ta fito, ta kasa cinye kazar da Sadik ya kawo, ta tashi zata kai sauran Kitchen, ta tarar da Sadik a Kitchen ɗin yana ta shirya kaya a cikin fridge, wanda ba ta san da su ba ma. Ya ɗakko kwalbar da ta shanye madarar ciki yace "ke kika taɓa wannan kwalbar ko?" Ta tura baki tace "to ai yunwa nake ji, shiyasa na ɗauka na sha" Sadik yace "Yawwa, kin kyautawa kanki, a garin tsinannen kwaɗayi kin sha wa kanki" "Me na sha?" Ta tambaye shi tana zare ido. "Madarar karnuka ce, Nonon karya ne  a ciki" Take ta dafe ƙirji tace "la'ila ha illa anta subhanaka inni kuntu mina zalumin, dan Allah meya kawo Nonon karya cikin fridge?" "Ban sani ba, daga yanzu kya dinga kiyaye abunda zaki ci, in ba haka ba wataran naman karen zaki ci" Ya fice ya barta dafe da ƙirji tan zare ido, take taji cikin ta na juyawa, naman da taci ma yana taso mata. Sadik ya koma falo kan kujera yai zamansa, ya kunna tv, wanda tun da suka tare a gidan ba'a kunna ba. Yana kallonta ta fito daga Kitchen ɗin jikinta a sanyaye, da alama ma kuka tayi, Ba wani Nonon karya da ta sha, Sadik yana sane ya gaya nata haka duk cikin salon yadda ze ƙuntatawa Nana. Ta koma ɗakin da yace shine nata, ta shirya kayanta a wardrobe, ta shiga banɗaki tai ta kakarin amai ko zata amayar da madarar nan, amma abu ya gagara abu da ta ri ga ta sha tun safe. Ko da ta dawo Falo, Sadik ya fice ba kowa a gidan se ita kaɗai. Ta koma tana ta ɗaɗɗaga teddies ɗin dake ɗakin, tana jujjuya su sedai abu guda, wata zundumemeiyar 'yar tsana ce take ba ta tsoro. 'yar tsanar tamkar ɗan shekaru shida, se taga Kamar 'yar tsanar zata fara motsi. Ƙarshe ta kuma komawa falo ta zauna, shima ta na yi tana waige waige, wai kar 'yar tsanar ta biyo ta falon. Haka tai ta wannan zaman ɗarɗar ɗin, har ƙarfe goma na dare sannan Sadik ya shigo, sallama yai ta amsa ya zo da kaya niƙi niƙi ya wuce Kitchen, se dai tai ta hamdala da ya dawo ɗin, dan a tsorace take sosai. Ya fito daga Kitchen har ze gota ta, ya jefo mata abu jikinta, wata roba ce a cikin 'yar ƙaramar jaka, ta zaro robar dabino ne a ciki da yawa, irin lubiyar nan. Ta bi bayansa da kallo dan wulaƙanci maimakon ya bata, shine ya jefata da shi. Ta girgiza kai ta ɗan ɗaga murya tace "Nagode" Yana jinta yai banza da ita ya wuce ɗaki. Nana ba ta yadda za'ai ta iya kwana da wannan 'yar tsanar a ɗaki ɗaya, dan haka a falon yau ma ta kwana. Washegari da safe ba Makaranta, Sadik da wuri ya shirya cikin wando 3quater, da 'yar shimi ya wuce Nana a falo tana bacci, ya  fita jogging. Se da gari yai haske sannan ya dawo, tuni Nana tai wanka ta canza kaya. Sadik na shigowa kallo ɗaya tai masa ta ɗauke kanta, duk da ba wani datti a gidan, amma ta gyara ko ina fes, ta ɗau ragowar kazarta ta ci. Haka su kai sati a gidan nan, in ba da wani ƙwaƙwaran dalili ba Sadik ba ya kula Nana, duk da Nana akwai rawar kai, ita dan be kulata ba, ba ya hanata yi masa Magana in tana buƙatar wani abu. Kullum ze zo da Abinci, ya Ajiye Mata. Ɗakinta kuwa ta samu bargo ta rufe wannan 'yar tsana da ke bata tsoro, amma duk da haka a tsorace take kwana a ɗakin. Zaune yake a bakin wani ƙaton ruwa, akan fararen kujeru yai shiruuu yana tunani, teburin gabansa ɗauke da tarin littattafai, amma hankalinsa yana gurin. Ji yai an taɓa shi, hakan ya dawo da shi da ga dogon tunanin da ya tafi. "Abbas, ka kammala nazarin litattafan ne ka zauna tunani?" Abbas ya ja wata irin ajiyar zuciya, tare da lumshe idonsa. "Wai meyake damunka ne? Tunda mu ka zo garin nan naga kamar ba ka sukuni, ko akwai matsala ne?" Abbas ya ɗanyi miƙa sannan ya gyara zamansa, ya kalli me masa maganar yace "Ahmad, wallahi hankalina yana Nigeria" "Me kake tunani a Nigeria? In Madam kake tunani, ta biyoka nan ɗin mana" Abbas yace "Mmm, ita ma ina tunanin nata, se dai gaskiya abunda ya dameni daban ne, wallahi wata yarinya ce ta tsaye min a rai, ina tunanin halin da Yarinyar take ciki yanzu haka" Ahmad yace "budurwa kai kenan?" "A'a, ba budurwa ta bace, she's my client amma ina tunanin halin da take ciki". Nan Abbas ya kwashe labarin Farhan ya gayawa Ahmad. Ahmad yai murmushi yace "Lallai Yarinyar ta cancanci a tausaya mata, amma sonta kake" "Kai, rufamin Asiri kar kasa Matata ta sakeni mana, yarinya ce Sosai not more than 14years, but she's deeply in love with someone, ga kuma a halin da iyayenta ke shirin sa ta". Ahmad yace "Ni ban da lalacewar zamani, ina 'yar shekara huɗu ina wata Soyayya?" Abbas yace "Ahmad kenan, Soyaya ai gaskiya ce ba ƙarya ba, kuma ka duba yanayin lokacin da muke ciki, akwai banbancin zamani, yanzu yaran yanzu idansu  a buɗe yake, ga kallace kallacen fina finai, dan haka tunaninsu ba iri ɗaya ba ne da yaran da. Ni babban abunda yake damuna, bagidajen da iyayenta zasu aura mata, wani wawa mara hankali, ga ta she's very calm, ko Magana ba tayi sosai, wallahi tausayinta duk ya cikan zuciya, idan lissafin da nake daidai ne, saura wata guda ya rage a ɗaura mata Aure, ina tsoron kar deprssion ya kama Yarinyar nan, ko ta faɗa mummunan hali" Ahmad yace "ka gama kewaye kewayenka ka dawo in da Magana take, You love her" Abbas yai murmushi yace "ka ga, mu fara abunda ya kawo mu, a bar wannan zancen" Haka kuwa akayi, nan su ka shiga nazarin litattafan da suke gaban Abbas. Faruk ya samu delay a tafiyarsa, se yanzu Allah yai tafiyar, ya shirya komai tsaf, washegari da sassafe ze tafi. Khairat ta kasa zaune ta kasa tsaye, duk ta shiga cikin damuwa. Ƙarfe tara da na dare, har Faruk ya fara shirin kwanciya se ga Khairat. Da mamaki ya kalleta yace "Khairat, ya dai? Meyafaru na ganki yanzu, bayan yanzu na baro cikin gidan?" "Magana nake so muyi" Yace "ok, ina jinki" Nan ta shiga in da in da, ta rasa ta ina zata fara masa bayani. "Calm down, nag duk kin ruɗe Kamar wadda taje screening da fake result, Faruk ne fa feel free to tell me" "Wata Magana nake so in gaya maka, amma ban san yadda zaka ɗauke ta ba" "Ina jinki Khairat" Ta ɗan kalleshi sannan tace "Yaya Faruk" "Na'am sister Khairat" "I...mm...dama" "Dama me?" "Ina son in gaya maka, Yaya ina sonka ne" Murmushi Faruk yai yace "Nima ina sonki ai Khairat" "I serious mean it, please keep joke aside, I want you to marry me" Ɗan Jimm Faruk yai yana kallon Khairat, yai murmushi yace "Khairat, Nifa yayanki ne, ki bar wannan maganar kinji ko, kar ma ki bari wani yaji ta, babu wannan a tsakanin mu, zumunci da 'yan uwanta ka ne a tsakanin mu, you are still young Khairat, kar ki biyewa RUƊIN ƘURUCIYA kin ji, maza je ki ki kwanta kimga dare ya fara yi" Jiki a sanyaye Khairat ta baro BQ, tana matuƙar son Faruk, ba ta taɓa zaton haka daga gareshi ba, gashi dai be mata wulaƙanci ba, amma dai be karɓi Soyayyar ta bs, wanda hakan ya tssye mata a rai. Yanzu Nana idan Sadik baya nan, zama take ta kunna Tv dake falo tai kallo, hakan yana ɗebe mata kewa Sosai, duk da akwai tv a ɗakinta amma ba ta san yadda za tai operating ɗin ta ba, dan babu remote ta falon ce dai akwai remote, dan haka kullum cikin kallon cartoon take. Yau ma ya dawo ya tarar da ita tana kallon cartoon ɗin ta, kamar kullum ba wanda ya kula wani a cikin su. Da alama a gajiye yake, ya ɗan jima a ɗakinsa sannan ya dawo falo ya zauna, ya kalli Nana yace "kawon ruwa a fridge" Kamar ba zata tashi ba, se kuma ta tashi tana tafiya a hankali, kamar mara lafiya, ta kawo masa ruwa da kofi. Sedai tana kawowa ta tarar ya ɗauke remote, ya canzs channel. Ta dire masa a gabansa, ta koma gefe tana kumbure kumbure, be ko kulata ba ya ɗau ruwansa yana sha. Kallonsa take, saboda Ruwan da sanyi sosai, ga yanayin garin da sanyi Sosai, Amma yake shan ruwa me sanyi. "In kin ga dama, kije ɗaki na kan gafo, ki ɗau Abinci" Ba musu ta miƙe, taje ta ɗakko wata jaka, wadda ita kaɗai ta gani a ksn gadon ta dawo falo. Ta zauna ta buɗe, amma gugguru ne a ciki. Ta kalleshi tace "wannan ne Abinci?" Be ko kulata ba ya maida hankalinsa kan TV. "Wannan ai ba Abinci bane, ni wallahi na gaji da cin wannan abubuwan, wannan ai ba Abinci bane, ya mutum ze ƙoshi da wannan, ni Wallahi Abinci nake so na fi ƙoshi, ko wannan bredin da kake siyo min, amma wannan ai dan nishaɗi ake ci ba yunwa ba" Kamar be existing a ɗakin ba, haka ta fara ci tana mita. Can ta maida hankali kan abunda Sadik yake kallo, wani horror Film ne me matuƙar razanarwa yake kallo (the conjuring), nan da nan mood ɗin ta ya canza, ta shiga tsoro Sosai, ba ta taɓa ganin bala'i a film kamar wannan ba. Wani razanannen ihu da Nana tai, seda shi kansa Sadik ɗin ya razana. "Meye haka, baki da hankali zaki wa mutane irin wannan ihun?" Kamar za tai kuka tace "tsoro naji fa" "Kuma se kiwa mutane wannan ihun, saboda hauka da ƙauyanci? Tashi ki bar falon nan kije ki kwanta, dama ai dare yayi" Ta noƙe kafaɗa tace "bana jin bacci ai" "Zaki tashi ko sena make ki?" Ba shiri ta tashi tana tura baki, duk ta ɓata gurin da gugguru, tai tafiyarta ɗakinta tana ƙunƙuni. Tai wanka, ta sa kayanta na bacci ta ɗora da kayan sanyi, Sannan ta saka hijjabi ta kwanta, se dai tana kashe fitila ta kwanta, se ta ga kamar teddies ɗin ɗakinta na motsi. A razane ta tashi zaune, ta kunna fitila tana waige waige. Sedai ta ga komai normal, har wani gumin wahala ta fara, ta kasa bacci se zazzare ido, sedai da yake bacci ɓarawo ne, ya kwashi Nana tana daga zaune ba tare da ta shirya ba. "Innalillahi wa innalillahi raji'un!" shine abunda ta furta lokacin da ta diro da kan gadonta, tai waje da gudu ta nufi ɗakin Sadik, saboda mummunan mafarkin da tai akan film ɗin. Ya cire kaya, daga shi se gajeren wando ya saka rigar wanka, ze wanka dan ya kwanta se gata kamar an jefota tana haki. "Ke meye haka?" Kamar za tai kuka tace "tsoro nake ji" "Tsoron me?" "Wani abu ne a ɗakina yake tsorata ni" "Kuma ni seki zo min nan, fitar min daga ɗaki" Hawaye ya cika idonta tace "dan Allah kayi haƙuri, wallahi tsoro nake ji" Tsaki yai ya gyara rigar wankansa ya nufi hanyar banɗaki ai kuwa ta bishi. Ya tura ƙofar banɗakin ze shiga, nan ma ta biyo shi. "Au banɗakin zaki biyo ni? Dama so kike ki ganni tsirara kenan, to bismillah shigo" A dirirce tace "yi haƙuri, ni ba biyoka zan ba, akan me zan ganka tsirara? Ni tsoro nake ji ne" Ta nemi guri ta tsaya a waje, se haki take. tsaki Sadik yai, ya shige banɗakin. A ƙofar banɗakin ta tsuguna, tana ta haki jikinta yana rawa. Ya gama wankansa ya fito sanye da rigar wanka, ya ga yadda take jujjuya idanu. Shi dariya ma ta so ta bashi, horror film ne ya sa ta zama haka, ga iya rashin kunya ga uban tsoro. Ya sa kayan baccin sa, ya nufi kan gado ze kwanta, nan ma ta bishi. "Ke wai uban me zan miki ne? Ki fita ki koma ɗakinki ba zan kwana ɗaki ɗaya da ke ba" Har da hawaye tace "dan Allah kayi haƙuri, wallahi ina ga wannan yarinyar ce a ɗakina, ta film ɗin ɗazu" Sadik yace "Wai wa ya gaya miki film gaske ne?" "Wallahi motsi naji a ɗakin" Sadik ya ɗan taɓe baki yace "seki kwanta a ƙasa, dan ba zan baki pillow ba, da pillow biyu nake amfani" "To ka bani bargonka, se in shimfiɗa a ƙasan" "Baki da hankali" shine amsar da ya bata ya kwanta. Haka ta duƙunƙune a cikin hijjabinta, tana karanto duk Addu'ar da ta zo bakinta. Cikin dare Sadik ya farka ya ganshi ba a cikin bargo ba, yana kunna fitila ya ga ta ɗauke bargon da filillukan ta barshi a haka, yana can yana bacci. Seda ya kusa zagi, ya sa hannu ze fincike bargonsa daga jikinta, amma hakan ya sa ta farka a matuƙar razane, kamar numfashinta ze ɗauke. Tunda Sadik yake be taɓa ganin mutum me tsoron tsiya irin Nana ba. "Dan kin raina min hankali, shine kika janye min bargo da fililluka?" Se ya lura kamar a gigice take gaba ɗaya, se maida numfashi take, sam ba ta jin me yake cewa, yaga idan ya matsa kar ta zo ta haukace masa, ƙarshe se ƙyaleta yai. Faruk ana idar da sallar Asuba, yaje ya samu Mother yai mata sallama, sedai a wannan karon ma se da tai kuka, Faruk akwai biyayya tai masa Addu'a ta fatan Alkhairi, Abba ds Usman ne zasu kai Faruk airport, suna shirin tafiya Khairat ta fito, idonta jawur alamar tayi kuka. Faruk ya sakar mata murmushi yace "Khairat, ko zaki bini ne?" Ta girgiza masa kai tace "Allah ya tsare" Yace "Ameen Bloody na, am gonna Miss you my chef, zan missing girkin ki wataran me daɗi wataran jagwalgwalo" Su Abba su kai dariya, daga nan suka shuka shiga mota suka tafi. Ta daɗe a gurin a tsaye, tana tunani kan ta koma cikin gida. Zuciyar Farhan ta kasa gazagata cewar Sadik ya barta, tana ji a jikinta a kowane lokaci ze iya dawowa gareta, ko ta yi niyyar cire shi daga zuriyar ta, ko ta ji haushinsa se ta ji ta ka sa, se taji yakamata tai masa uzuri kan ta yanke masa hukunci, kullum Addu'ar ta Allah ya dawo da Sadik cikin Rayuwar ta. Iyayen Sunusi sun aiko wai Ranar juma'a zasu kawo kayan lefe, duk unguwa ta ɗauka Sunusi ze auri Farhan. Wasu suna ganin an ƙwareta, wasu kuma suna ganin ze temaka mata ne, tunda ba wanda a unguwar ba shi da labarin an kamata ita da Abbas a gidan Hajiyar sa, Kamar yadda akai ta yaya tawa a unguwar. "Ke! Ke! Wai ba zaki tashi bane?" A hankali Nana ta motsa tai miƙa, tare da buɗe idonta tana ɗan tura baki. "Dalla ta shi" Sadik yai maganar yana kallon ta. Ta tashi zaune sannan tace "dan Allah ka dena ce min ke, ni bana so" "Zaki tashi ki barmin ɗaki, ko sena ɓaɓɓala ki na bawa karnuka". Ta tura baki tace "wallahi na fi ƙarfin karnuka su cinye ni. Yawwa nace me zanci da safen nan ne, wallahi jiya da yunwa na kwana" "Se ki ci kan ki ai, ba uwar da ki ka iya dafawa, sedai nike nan cikin yawon nemo miki abunda zaki ci, har ki na gayan magana" Nana tace "To akan me zan kuma garajen shiga wannan Kitchen ɗin in ci wani abu, bayan ranar ka ce min nonon karya na sha, har yanzu istigfari nake Allah ya yafe min. kuma ni ban iya amfani da wannan kayan da suke a Kitchen ɗin ba" Sadik yace "tashi muje Kitchen ɗin" Nana ta miƙe ta bi shi, suka shiga nan ya dinga nuna mata komai da amfanin sa, ya nuna mata in da kayan Abinci suke. Nana tace "ikon Allah shinkafa a kwali, ni na saba ganinta a buhu, ban taɓa zaton zan ganta a kwali ba, har su wake duk a kwali Lallai cigaba" Sadik dai be kulata ba ya nuna mata yadda za tai amfani da gas cooker. Nana tace ita Allah karta tsoron wannan abun take ji, kar yai bindiga da ita, sedai a san yadda za'ai a samo mata murhu, ko risho. Sadik Kamar ya ɗora hannu a ka yai ihu, idan yai gabas se tai yamma, duk da ta ɗan waye amma haryanzu da ƙauyanci a kanta, wanda Sadik ya fi dangant hakan da hauka. Ƙarshe Sadik ne ya kunna gas ɗin, Suka dafa tea, suka fere dankali su ka soya, kai kaca kaca da Kitchen ɗin, suna yi suna faɗa, Nana rashin kunya shi kuma masifa. Suka gama, suka dawo falo su karya, Sadik ya ɗakko ketchop ze ci dankali da shi, Nana tace ita ma ya samata ta ci da shi, yace mata jinin alade ne, in zata iya ci kuma shikenan. Lilly ta ɗan ƙurawa Farhan ido, kullum jiya i yau, kullum rama take da tunani. Lilly ta kalli Haseena tace "Hassyy, dan Allah ki bani lambar Khairat ɗin nan mana, sister ɗin Sadik" "Me zaki da ita?" "Se kin tambayeni, abu ne me mahimmancin gaske" Haseena tace "gaskiya ba zan bayar ba, se kin gayamin me zaki da ita" "Ke riƙe ki cinye in Abinci ce" Lilly ta faɗa a fusace. Haseena tace "sorry masoyiya, ai bama haka bari in baki lambar" Ta bawa Lilly lambar Khairat. Dama Lilly so take ta kira Khairat, a gaban Farhan in da hali ta taimaka ta basu lambar Sadik ta ƙasar waje, sedai Farhan ba ta gurin zamanta. Library ta tafi, dan mafi akasari yanzu nan ne gurin zaman Farhan. Aikuwa tai sa'a ta tarar da Farhan a Library, sedai idanunta sunyi wani irin ja, kamar wuta ta ƙurawa guri ɗaya ido. Lilly tace "Farhan, ga lambar ƙanwar Sadik Khairat, na karɓo se mu kirata" "No need" Farhan ta faɗa a hankali. "Meyasa zaki ce haka? Ai yakamata kiji a wani babin ya ajiyeki, dakon soyayya wahala ce Farhan" "No need! Soyayya ta da Sadik RUƊIN ƘURUCIYA ce kawai, an sha gayamin ban yadda ba, duk Makaranta ta ɗauka he got married to his cousin" "Waye ya gaya miki wannan maganar, ta yaya Sadik ze yi Aure a wannan ƙananan shekarun?" "Is possible, har nan Abokinsa ya zo ya gayamin, ya haɗu da yayansa yau a airport, yaje raka babansa, Yayan Sadik ne ya tabbatar da hakan, am fool da na tsaya na yadda da maganganun Sadik da ya dinga furta su, ni kuma RUƊIN ƘURUCIYA ya ɗebe ni na amince da shi, am Stupid, am more than fool, am idiot!" Cikin ɗaga murya take Maganar, dan ma Library ɗin ba kowa, jikinta na tsuma ta fice daga Library ɗin. Ba a tashi ba, amma Farhan ta tafi gida, idonta ya bushe babu hawaye, ƙoƙari take ta ga ko zata iya samawa Sunusi matsuguni a zuciyar ta, dan ta cire Sadik amma ina, Sadik ya mamaye ko ina, ya mu'amalance ta da kyakykyawar mu'amala a lokacin da ta rasa wanda zata raɓa. Gidansu babu kowa, Umma ba ta nan suna ta shirye-shirye, ta tafi kasuwa, kuma a yau ne za'a saka ranar Aurenta, wanda baze fi sati biyu ba. Wata irin wuta ce ta ke cin zuciyarta, ta rasa me za tai taji daɗi, ta buɗe jakarta ta ɗakko sauran maganin baccin nan da aka bata, uku kawai ta sha a jiki Kamar yadda me chemist ya gaya Mata. A take ta ɓalle uku ta watsa ta kora da ruwa, ta runtse idonta ta na jiran ta ji bacci ya ɗauketa amma abu ya gagara. Ta dinga watsi da kayan da ke ɗakinta Kamar Mahaukaciya, ta watsar da komai tana zazzare ido, amma ba taji sauƙin abunda ke ranta ba, ta toshe kunnenta ta ƙwala ƙara, gaba ɗaya ta firgice ta fita hayyacinta, tamkar Mahaukaciya. Cikin azama ta fito daga ɗakin ta, ta shiga Kitchen ta hau sauke kwanuka ta na dube dube, ta zaro wata sharɓeɓiyar wuƙa jikinta na ta karkarwa!!! (This is deprssion!) (ME KUKE TUNANIN FARHAN ZA TAI? YA KUKE TUNANIN ZAMAN NANA DA SADIK? WACE IRIN RAYUWA FARHAN KE SHIRIN FAƊAWA? KUNA TUNANIN AUREN FARHAN DA SUNUSI ZE YUWU? WANE IRIN ZAMA ZA SUYI? 💃💃💃💃💃💃💃💃HAR KULLUM COOL TAKU CE, INA FATAN ANA ƊAUKAR DARUSSAN DA KE CIKIN LITTAFIN). Littafin nan ₦300 ne kacal. 0009450228 Aisha Adam Jaiz Bank 07063065680 KO kuje manhajar AREWA BOOKS ku siya. domin kuwa ya fi sauƙi ta can. "Farhan!" Huzaifa ya kira sunanta da ƙarfi, ya saki kayan hannunsa ya ƙaraso in da take da gudu, ya fizge wuƙar da ke hannunta, idanunta gaba ɗaya sun juye, sunyi jawur gashin kanta a hargitse kamar Mahaukaciya. "Farhan, meyafaru haka? Meyasa zaki yunƙurin kashe kanki?" Hannayenta ta saka ta rufe fuskar ta, ta fashe da kuka, jikinta har rawa yake, cikin hanzari Huzaifa ya tattare kayan da ta sauke ƙasa ya kalleta yace "zo muje ɗaki ki sa ka hijjabi ki kintsa jikinki, an jima mutane zasu kawo lefenki da ga gidanmu" Ko motsi ba tai ba se kuka da take, jijiyoyin kanta duk sun ɗaga sun kumbura, se sheshsheƙa take. Huzaifa ba shi da zaɓi illa ya kamo hannunta, ya kaita ɗakinta ya tarar nan ma ta watsar da komai, ya shiga kwashe kayan yana mayar mata drower ɗin ta. Ya ɗakko hijjabi ya miƙa mata ta ƙi karɓa, nan ma se shi ya samata, ya kalleta yace "Yaya, meke damunki haka? Koma meke damunki ina tauhidin ki? Wane irin hali zaki shiga ki manta da Ubangiji ki zaɓi nema ki kashe kanki? Kin san wuta ce makomar duk wanda ya kashe kansa, amma ki kai yunƙurin halaka kanki, haba Yaya meyasa?" Maimakon tai Magana, sema ta nemi guri ta kwanta, saboda ji da tai kanta yana wata irin juyawa, tana ganin duhu a idonta. Huzaifa ya ƙura mata ido,yana jin wani irin matsanancin tausayinta ya na ratsa shi. Ya fuskanci kamar bacci ne ya ɗauketa, harya yunƙura ze tashi ya fita, yaji ta fara surutai. "Meyasa! Meyasa zaka min haka? I still love you, but why? Why me?!" Huzaifa ya san Farhan ba ta son Auren nan, akwai wanda take so, amma ba bu wanda ya taɓa tunanin zama da ita ya ji damuwarta. Ya girgiza kai ya koma tsakar gida, dan kar ta farka ta kuma yunƙurin aikata wani abu. Yau a falo Nana ta tarar da Sadik, ta ga kamar fuskaarsa a ɗan kumbure take, yana kwance akan kujera ya ɗage ƙafafunsa tare da lumshe idanunsa. "Nace ba, yau me zamu ci?" Tai maganar tana hamma. A ransa yace 'ji jarababbiya, ba ta da zance se na Abinci' Banza yai mata yaƙi buɗe idonsa. "Magana fa nake" ta maimaita cikin tsiwa. Sadik be kulata ba se ma tari da ya fara yi, da alama mura ta kama shi sosai, se tari yake. Nana tace "lokacin da kake shan ruwan sanyi, da nayi magana se kace bani da kunya, amma da nai maka shiru gashi nan jikinka ya na gaya maka" Buɗe idonsa yai yana bin Nana da kallo, yadda take masa faɗa Kamar wata uwarsa. Ya maida idanunsa ya lumshe, yana jin yadda kansa ke masa ciwo. Ta wuce shi ta barshi a falo, can mintuna goma se gata ta dawo da tea a cup, ta ajiye masa tace "ga shayi ka sha, se ka je Asibiti a duba ka" Be kulata ba yai banza da ita, hakan ba ƙaramin bawa Nana haushi yai ba, tace "wai ba zaka sha ba ne?" "Ke! Dalla ki ƙyaleni, ina ruwanki da ni ne, dole ne se kin shiga sabgata?" Seda ta razana saboda tsawar da yai mata, tace "Allah ya baka haƙuri" Ta koma gefe ta tsura masa ido, se atishawa yake yana tari, da alama ba ƙaramin kamu murar nan tai masaba. Ya bi ya dunƙule guri ɗaya, da alama har da sanyi yake ji. "Ko in ɗakko maka bargo, na ga kamar ka na jin sanyi?" Se da ya harareta ta tuna yace karta kuma shiga harkarsa. Suna nan zaune kamar kurame, taji ana kaɗa bell ɗin ƙofar gida. Tun da suka zo gidan nan, da wasa ba ta taɓa leƙawa ko ƙofar gida ba, ta tashi da nufin ta je ta buɗe ƙofar amma ta kasa, tana ta kokawa da ƙofar, se ji tai an tureta gefe, ta ɗaga kai ta ga Sadik ne. Ya buɗe ƙofar, wasu yaran turawa ne sa'anin Sadik uku maza, biyu mata. Sadik yana ganinsu ya fara murmushi,yai musu iso zuwa cikin falo, ya bar Nana a bakin ƙofa. Ta biyo bayansu, ɗaya daga cikin matan, ta zauna a kusa da Sadik ta dafa goshin sa, cikin kulawa take masa sannu da harshen turanci. Nana kam se bin su take da ido, ɗaya daga cikin su ya kalli Nana, ya tambayi Sadik wannan fa. Sadik ya kalli Nana yace "she's my made" "Wow she's beautiful" cewar ɗaya daga cikin 'yan matan. Ɗayar tacewa Nana "ya kike?" Wata uwar harara Nana tai watsawa Yarinyar, Sadik yace "karki damu, ba ta jin turanci ai" Wani abu ya tokarewa Nana a zuciya, ita Sadik ya kira da 'yar aiki, lallai wannan ƙarshen cin mutumci ne a gareta, seda ta ji wata ƙwallar baƙin ciki ta taru a idonta, ta wuce ɗakinta. Nan suka baje kayan ciye ciye, suna ci su da Sadik, Kamar gidansu haka suka dinga shagalinsu a gidan. Nana ba ta sake fitowa ba, har Azahar suna gidan, se bayan azahar Sannan ta dena jiyo motsinsu, ko da ta fito falon ta tarar ba sa nan har Sadik ɗin. Sunyi kaca kaca da Gidan, kuma sunyi tafiyar su sun bar gidan a haka, haka Nana ta zage ta na gyarawa, tare da tunanin in da Sadik ya tafi alhalin ba shi da lafiya. Yau abun na Sadik ya zarce tunani, dan har fiye da ƙarfe goma na dare ba ta ji dawowarsa ba. Tsoro ya gama cika zuciyar Nana, ta dawo jikin ƙofar gida ta zauna ta takure jikinta Sosai, a haka wani wahallalen bacci ya kwashe ta. Se sha biyun dare sannan Sadik ya dawo, dan yawo suka tafi da abokansa, suka sai ticket suka tafi kallon ball, be sake tunawa da Nana ba seda ya dawo ya tarar da ita a takure a bayan ƙofa tana bacci. Har yai gaba abunsa ze barta a gurin, se yag rashin dacewar hakan, ya dawo da baya yasa ƙafarsa yana taɓata. A razane ta buɗe ido, ga miƙe tsaye tana waige waige, ta kalli Sadik ta kalli agogon da ke falon, ba tace masa uffan ba ta wuce ta kama hanyar ɗakinta ta na tangaɗi saboda baccin da take ji. Jin hayaniyar da tai ne ya sa ta buɗe idonta a hankali, ta farka da wani irin matsanancin ciwon kai, se hayaniya take jiyowa sama sama. "Ke Farhana, wai wannan wane irin bacci ne haka, ki tashi ki alwala ki sallar isha'i, tun da muka dawo Gidan nan kike bacci, ba yadda ba muyi ba ki tashi amma kin ƙi, wane irin bacci ne haka?" Seda tai shiru na wasu lokuta, sa'annan ta gane muryar Maman Huzaifa ce. A hankali ta gyara kwanciyarta, ta tashi zaune, sedai kanta juyawa kawai yake, ta yunƙura ta miƙe tsaye amma ta tafi luuuu za ta faɗi. Maman Huzaifa ta riƙeta tace "ko baki da lafiya ne?" Farhan ba tace mata komai ba, ta fara takawa, amma se ta dinga ganin Kamar ginin Gidan ze ruso a kanta, da kyar ta kai kanta banɗaki, tai alwala ta na jan ƙafa ta koma ɗaki. Gidan Mutane se shiga suke suna fita, ana ganin kayan lefenta, sedai har ta fito tai alwala ba wanda ya kula da ita. Ta jero sallolin da ba tai ba, ta idar ta dinga yiwa Allah godiya da be sa ta aikata abunda tai niyya ba, na kashe kanta. Sedai jikinta sam ba ƙwari, tana kwance aka kawo mata Abincin dare, amma sam, ba ta jin za ta iya cin Abincin. Sama sama take jin ana cewa "Masha Allah, kaya sunyi kyau, an saka sati huɗu biki, Akwatinan ta guda biyu, ƙatuwa da 'yar ƙarama se jakar bagco" Ana haka kunnuwanta suka jiyo ana cewa, wai ana Sallama da ita inji Sunusi, Adda tace ba ta da lafiya yayi haƙuri ba zata iya fita ba. Da haka wani baccin ya kuma awon gaba da ita. Farhan ba ta gane a zahiri take ko a mafarki, Sadik take gani kwance a kusa da ita yana mata murmushi yace "Princess, kin rame Sosai meyasa?" "Ba tafiya kai ka bar ni ba, bayan kace ba zaka bari a Auramin Sunusi ba, meyasa ka tafi ba ka dawo ba?" "Ai na dawo ba gani ba" Ta matsa ku sa da shi, ta rungume shi,  tana shaƙar ƙamshin turarensa, yayin da a zahiri kuwa pillow ne take gani kamar Sadik yana mata Magana, ta ƙanƙame pillown ta na cigaba da surutai, ta na jin Tamkar Sadik ta rungume. Ba Adda Maryam ba, hatta Umma abun ya bata mamaki, yadda Farhan ke wani irin bacci na rashin kan gado, har sha biyun rana bacci take taƙi tashi, ko sallar Asuba ba tai ba, anyi anyi ta tashi amma Abu ya gagara. Da ƙyar ta iya tashi, ta haɗa sallar Asuba da ta Azahar, sedai gaba ɗaya jikinta a mace yake, ko Abinci ba ta ci. Seda Adda Maryam tai ta mata masifa, sannan ta sata gab ta sha kunun tsamiya daga haka ta ƙi cin komai. Adda Maryam zaton ta kawai miskilancin Farhan ne, da kuma rashin lafiya dan haka ta ƙyale Farhan ɗin. Tana nan kwance akan katifar ta, ta ƙurawa fankar sama dake ɗakinta ido, tamkar za taga Sadik a jiki, tana tuna irin rayuwar da sukai, me cike da kulawa da Soyayya, ko da wasa ba ta taɓa kawo Sadik ze iya Auren wata ya barta ba. "Assalamu alaikum" taji anyi sallama a ɗakin. A hankali ta juya ƙwayar idonta, dan ganin me yin sallamar, Hajiyar Abbas ta gani, nan da nan ta yunƙura ta tashi zaune, kanta kuwa ya sara seda ta ɗan rintse ido. "Hajiya ina wuni" ta faɗa a hankali. Hajiya ta ɗan tsura mata ido tace "Lafiya ƙalau Farhan, ohh ni Maimuna, Amare na ƙyalli ke kina baƙi, fatar duk tai duhu kin rame se idanuwa haka, anya Farhan, wace irin rashin lafiya ke damunki haka?" Farhan tace "bakomai Hajiya" "A'a fa, ban yadda bakomai ba, kimga daga ni seke a ɗakin nan, gayamin menene?" "Dagaske nake Hajiya bakomai" "Hmm, ko dai Auren ne ba kya so?" Farhan ta girgiza kai tace "A'a" Ba ta san Abbas ya riga ya gayawa Hajiya, ba ta so Auren ba, nan Hajiyar ta sake jinjina zurfin ciki irin na Farhan. "Farhan, shi lamarin rayuwa haƙuri ake da shi, ƙaddara duk a yadda ta zowa bawa haƙuri yake ya karɓeta, dama nace nasan iyayenki ba lallai su damu da yi miki wani abu ba, ga Aure zaki yi, kuma shi Aure mace duk in da take se da gyara, ana zaunar da ke ai miki faɗa akan yadda zaman Aure yake?" Farhan ta girgiza kai alamar a'a. Hajiya a ranta tace 'se aukin siyan kwanuka kawai suka sani, ba a san a gayawa yaro wace irin rayuwa ze fuskanta ba' Hajiya ta kalli Farhan tace "idan kinje kama ruwa, kina ganin farin Ruwa, ko ƙaiƙayi a al'aurar ki alamu na sanyi?" Farhan ta ɗanyi jimm, ta ƙi Magana. Hajiya tace "ke kalle ni nan, ni ba wadda zaki ji kunya bace, na haifa nima 'ya ki ke agurina, ki gayamin" Nan ma Farhan ta girgizawa Hajiya kai, alamar a'a. Tace "to shikenan, duk da haka dai na sa a haɗamin magungunan sanyi, akwai saiwar zogale da jar kanwa, zan dafa in aiko miki da shi, maganin sanyi ne sosai, in ma akwai a jikinki ze temaka miki". Farhan dai tai shiru ba tace komai ba. Hajiya ta numfasa tace "Abbas ya takuramin akan lallai yana son Magana da ke, bari in kirashi in haɗaki da shi" Tai maganar tana danna wayar hannunta. Tai ringing na seconds, sannaan ya ɗaga Tare da yin Sallama. Hajiya ta amsa sannan tace "Ga Farhan ɗin" ta miƙawa Farhan wayar tace "in kin gama, ki bawa ko su Amir ne su kai min Wayar" Farhan ta jinjina kai sannan ta karɓi wayar ta saka a kunnenta. "Assalam Alaikum" yai mata sallama. A hankali ta amsa sa da "wa'alaikum salam" "Daughter, jikin ne dai kokuwa, naji muryarki a ƙasa ƙasa?" "A'a, lafiyata ƙalau" Yai ajiyar zuciya yace "jikina ya bani ba lafiya ƙalau kike ba, duk da muryarki a haka take, Amma tana ɗauke da damuwa meyafaru ne?" Kamar ya na ganinta ta girgiza kai tace "bakomai" Yace "Shikenan, Hajiya tace min an kawo lefenki an saka wata ɗaya ko?" "Mmmm" shine abun da ta iya cewa. "Farhan" ya kira sunanta. "Na'am" "Kiyi haƙuri, ki kwantar da hankalinki irin taki jarrabawar kenan, Allah ya baku zaman lafiya, Allah ze baki ladan biyayyar da ki kaiwa iyaye" Se da ya kai aya, sannan yaji ta sauke wata irin nannauyar ajiyar zuciya, Kamar duk surutun da yai hankalinta ba ya kansa. "Me kike tunani ne?" "He's gone" ta faɗa a Sanyaye. "Who?" "Sadik, he replaced me with another girl" Abbas yace "subhanallah, and how do you know that?" "Gayamin a kai, na yadda da maganar ka, Sadik baze dawo ba, Dole se na Auri Sunusi, amma ka gayamin ta ya zan dena tunaninsa?" Tai maganar tana hawaye. "You still love him?" "Yes i do" "Ki sawa zuciyarki ke Yanzu mallakin wani ce, ki nesanta kanki da duk wani abu da ze sa ki dinga tuna shi, Sannan kiyi haƙuri, ki miƙa lamarinki ga Allah" Ta ɗan ja numfashi tace "shikenan, Nagode sosai doctor nagode" "Karki kuma yi min godiya, Allah ya sanya Alkhairi" Ba ta amsa ba ta cire wayar da ga kunnenta. Haka kurum se ta tsinci kanta da saka lambar Sadik da ta haddace, a cikin wayar ta gwada kira amma wayar a kashe. "Meyasa ba ki da zuciya ne Farhan?" Wata zuciyar ta tunasar da ita. Ta ajiye wayar a gefe, ta kuma bin guri ta kwanta. Yau unexpected, Steve ya kawowa su Nana ziyara, Nana tai murna sosai suka karɓe shi cikin girmamawa, Weekends ne dan haka Sadik ma ya na gida. Nan yake sanar da Nana cewa, Ranar Litinin ze zo ya kaita sabuwar makarantar da zata cigaba da zuwa, Nana tai murna sosai dan dama zaman gidan duk ya isheta, ga wanda take zaune da shi ba shiga sabgarta yake ba. Steve ya ɗakko wayarsa yace, bari in kira babanki yace in haɗaki da shi idan na zo" Ta kalli Sadik da yake zaune yana kallo, ko uffan be ce musu ba. Tace "kuma wallahi se na gayawa Abba duk abunda kakeyi, da yawon dare da kake da tara abokai da taɓa mata duk se na gaya masa". Sadik a ransa yace 'wannan mahaukaciyar Yarinyar tsaf za ta kuma jamin wata damuwar fa' amma a fili kallo ɗaya yai mata ya maida idonsa kan tv ya cigaba da kallonsa. Steve ya miƙawa Nana waya, se da wani murmushi ya kufce mata tace "Abba ina wuni" "Lafiya ƙalau daughter na, ya kike ya gidan?" "Lafiya ƙalau Alhamdilillah, ya su Yaya Faruk da Mother?" "Suna lafiya, Faruk ya tafi karatu shime" Nana tace "Allah sarki, Allah ya bads sa'a" "Ameen ya Allah, Steve ya gaya miki ranar monday in Allah ya kaimu ze kaiki Makaranta da zaki cigaba da zuwa ko?" "Eh ya gayamin Abba, ita ma boarding ce?" "A'a ga mijinki Yaushe za'a kuma kaiki boarding, day ce, ko kin fi son boarding ɗin?" "Eh Abba na fi son boarding" Abba yace "Yana miki wani abun da ba kya so ko?" "A'a ba ya min Komai" "Ki gayamin gaskiya Nana, me yake miki na rashin kyautawa?" "Allah Abba dagaske nake, ba abunda yake min na rashin kyautawa" Sadik ya ɗago yana kallonta, ya san koma mene akansa ake Magana. Abba yace"in dai yai miki wani abu na rashin daidai, ko kika ga yana aikata wani abu na rashin kyautawa ki bugo ki gayamin" Tace "to Abba" "Yawwa, Allah yai miki Albarka, kina da buƙatar wani abu ne?" "Eh Abba, ammm. Ina son siyan mayukan shafawa, wanda na zo da su daga school sun ƙare, kuma garin akwai sanyi sosai" Abba yace "Ai Sadik zaki gayawa, na saka masa kuɗi a account ɗin sa, duk abunda kike buƙata ki gaya masa, in yaƙi yi kuma shima ki sanar da ni, bari in haɗaki da Hajiya, gani na zo garin" Miƙewa tsaye Nana tayi, cike da murna. "Salamu Alaikum" "Inna ta ke ce?" Inna tace "ji wani shirme, to da wace in ba ni ba" "Wayyo Allah, Yaushe rabon da inji muryarki Innata? Dan Allah ba ki kewata ba?" "Kice haryanzu dai Nutsuwar da sauƙi ba ta ratsa ki ba" Nana ta ɗan tura baki tace "haba Inna, in ban kewarku ba kewar wa zanyi, ina Kakana? Ya jikinsa?" "Jiki da sauƙi sosai Alhamdilillah, sunje gangare ɗaurin Aure, ai yanzun nan baban naki ya zo, yace takanas ya zo dan ya haɗamu a waya" "Allah sarki, wallahi Inna ina kewar gida sosai" Inna tace "kin dena koke koken kenan? Ina mijin naki?" Nana ta kalli inda Sadik yake, ta harare shi tace "Allah ya kiyaye ni ba mijina bane" Inna tace "Meki ka ce?" "Ni Inna dan Allah a dena wani ce masa mijina, haba dan Allah wannan ɗan yaron ai abun kunya ne ace mijina ne, nan gaba idan na ƙara tsawo fa sena kamo shi a tsawo, Ni babba zan aura me hankali, kawai ku dinga min Addu'a Allah ya bani miji nagari, se ki ga ma na kawo miki bature a matsayin sirikinki" Inna tace "Innalillahi wa innalillahi raji'un, ke baki da hankali ko, dan ubanki Aure abun wasa ne? Wato nan ɗin ma zuwa ku kai kuka cigaba da raba abun faɗa ko Nana, duk nasihar da nai miki ba ki ji ba kenan?" "Ni wallahi Inna ba na son shi, Auren dole fa akai min, wannan yaron ban da hantara da masifa meya iya, a gabanki fa har dukana ya dinga yi, ni dai kawai ki min fatan Allah ya bani miji nagari" Inna tace "na shige su, a nan ɗin ma dukanki yake?" "A'a ni be dakeni ba, amma dai wallahi ba na son shi, shima kuma ba ya sona, dan Allah ba se ya sakeni ba, in Auri wanda nake so". Inna tace "Allah ya sa uban Yaron nan ya fita salla, da a gabansa zaki dinga wannan sakin bakin, dan ubanki a ba kya son nasa kike satar jiki, ki ɗau Abinci ki kai masa a ɓoye ko? Lokacin da yake garin nan" Nana tai mamakin yadda akai Inna ta gane, amma ta maze tace "To ai wannan tausayinsa nake ji" "To yanzu ma ki cigaba da jin tausayin nasa, Nana Aure ba abun wasa ba ne fa, karki kuma cewa ba kya son sa, ko kina son sa ko ba kya son sa mijinki ne, dole ki masa biyayya kiyi haƙuri, zama yau da gobe zaki ji kina son nasa, karki kuskura yaji ko ki bari mahaifinsa yaji kins cewa ba kya son sa" Nana tace "Na nawa kuma? To yana zaune ya na jin wayar da nake" "Inna tace Eh na ƙara tabattar da Baki da hankali Nana, doguwar banza da ta wofi se tsawo ba hankali, Nana miji yafi gaban wasa, Allah ƙara nunamin kinyi wannan furicin se naci ubanki, mara hankali kawai" Nana dai tai shiru tana tura baki, Sadik kuwa yana jin duk abunda Nana take faɗa, babu babban abunda ya fi tsaye masa irin kalmar yaro da ta dinga ce masa, kawai yai ƙwafa ya ƙyaleta. Ta gama wayarta, ta bawa Steve wayar tana tai masa godiya. Ya tashi ze tafi, Abba ya kuma kiran Steve, ya nemi ya haɗashi da Sadik, aikuwa ya bawa Sadik wayar, sedai Sadik be zauna a falon ba ya fita. Ya kai mintuna goma Se gashi ya dawo jikinsa a sanyaye, Ya raka Steve ya tafi, be kuma tankawa Nana ba ya cigaba da sabgogin sa. Kamar yadda Steve ya gaya mata, Ranar Litinin ya kaita sabuwar makarantar da zata cigaba da zuwa, Farhan tai murna sosai ko ba Komai yanzu ta dena zaman gadi, ta huta da zaman kaɗaici. Wannan makarantar ta lura akwai yaran Musulmai sosai a ciki, dan akwai masu saka hijjabi bayan ita. Tun da ta fara zuwa Makaranta ba ta haɗuwa da Sadik se dare, idan ta fita tun safe se la'asar take dawowa gida, School bus ce ke zuwa ta ɗauketa ta dawo da ita. Sadik kam ba ta ganinsa se dare, yau kamar an sata ta shiga ɗakinsa, ya hargitsa komai hatta wardrobe ɗin sa, yai kaca kaca da ita Sadik ba ya son ƙazanta amma be iya gyara ba. Tana mita haka ta zage, ta gyara masa ɗakinsa tsaf, saboda Nana ta gaji tsafta a gurin Hajiya Inna. Ba ƙaramin daɗi Sadik yaji ba, da ya dawo ya tarar ta gyara masa ɗakinsa, sedai ko nuna mata ya gani beba balle yai mata godiya. A Kitchen ya tarar da Nanan, tana wanke fruits, ya kalleta yace "wai uban wa yace miki ana shiga Kitchen da hijjabi, ke kenan kullum cikin hijjabi?" "Ina ruwanka da hijjabina ne, kayi rayuwar ka mana" Se da Sadik ya ji haushin kansa na tanka mata ma da yayi. Farhan maganinta da take sha na bacci ya ƙare, ta koma 'yar gidan jiya babu bacci, ta dinga jin kanta Kamar ze rabe biyu ga wani irin nauyi da yai mata. A haka ta daure take zuwa Makaranta, saboda zamanta a gidan ba abunda yake ƙara mata se matsananciyar damuwa. Ta ɗauki takaddar maganin da me Chemist ya bata ranar, ta tafi da shi wani Chemis ɗin,  dan ta siya amma me Chemist ɗin yace ba ze siyar ba se da katin Asibiti. Gaba ɗaya makarantar su ta ɗauka, Sadik ya yaudareta yayi Aure, wasu suna tausaya mata wasu na mata dariya suna cewa dama ai kyan ƙwarya ta bi ƙwarya, Ita ba sa'ar Aurensa bace ta na 'yar talakawa. Ba a tashi tayar da zancen ma se an ganta, se a hau hirar Sadik, hakan ba ƙaramin sake jefa Farhan cikin mummunar damuwa yayi ba, ta ƙara tsangwamar kanta, daga baya makarantar ma ta ajiye ta dena zuwa gaba ɗaya. Ba ta cin Abincin kirki, ba walwala kamar me takaba haka take rayuwa, Umma ta bar hakan a mazaunin alhinin Aure ne da za tai yake damunta. Ta cigaba da bincika yadda za tai ta samu maganin nan amma abu ya gagara, ba ta samu maganin ba. Ɗan kuɗin gyaran jikin nan, dana walima da ango ke bawa Amarya ba wanda Sunusi ya bawa Farahan, hasali ma duk majalissar da ya zauna se yace ai temakawa ze ya aureta, dan binnmaza take, ƙarshe ya shirya ya tafi ƙauyansu dan cigaba da shirye-shiryen biki. "Gaskiya na gaji da wannan abun da kake Min, kullum ba zaka dawo ba se cikin dare, in ta faman jin tsoro yanzu idan wani abu ya sameni fa? Ba kowa a gida se ni kaɗai?" Shigowar Sadik kenan take ta wannan mitar. Ko kulata be ba, ya nemi Guri ya zauna, ya ɗakko wayarsa yana waya. Da mace yake wayar, dan a hankali yake Magana, cikin harshen turanci, haryanzu bakomai Nana ke iya fuskanta a Turancin ba, amma dai ta gane da mace yake waya. Wato ya maida ita kamar wata Mahaukaciya, ta na ta banbami amma yai mata banza Yana waya. Bata san lokacin da ta ja wani uban tsaki ba tace "Aikin banza" Ta wuce ta nufi hanyar ɗakinta. Bayanta yabi da kallo tare da yin ƙwafa. Ita kaɗai a ɗaki, amma ta cigaba da yin mita, ta shiga tai wanka ta fito, ta saka kayan baccin ta, vest da wani guntun wando, sedai babu man da zata shafa ya ƙare tas. Tsaki tai ta jefar da doguwar robar cream ɗin, ta saka hijjabi ta nufi ɗakin Sadik. Yauma sanye yake cikin Rigar wanka, ze shiga banɗaki, se gata ba sallama bakomai. Ya ɗago ya kalleta, cikin tsiwa tace "Nifa man shafawata ya ƙare, Abba yace duk abunda nake buƙata in gaya maka, amma kaƙi saurarata, ina buƙatar abubuwa da yawa, amma kullum ba zaka dawo ba se dare balle in gayamaka" Kallo ɗaya yai mata ya shiga banɗaki, ya barta a tsaye a ɗakin. Guri ta nema ta zauna, tace "Ai duk abu ba zaka kwana a banɗakin ba, dole zaka fito ina nan ina jiran ka" Se huci take, dan gaba ɗaya haushin Sadik take ji. Jin ƙarar buɗe ƙofar banɗakin ne ya sata ɗaga idonta ta kalli ƙofar. Sadik ne ya fito daga shi se towel a ƙugunsa, ya yafa wani a kafaɗarsa, jikinsa jiƙe da ruwa. A razane tace "Subhanallah" ba ƙaramin shiga kiɗima tayi ba, ba ta taɓa ganin namiji tsirara ba se yau, dan Sadik ba shi da maraba da tsirara, to ina ma zata ga namijin balle ta ganshi haka. Tashi tai cikin azama za ta fice ta bar masa ɗakin, amma ya riƙeta ya ajiye towel ɗin dake kafaɗarsa, ya rage saura na ƙugunsa. Nan da ta shiga razana, jikinta ya hau rawa, ta haɗiye wani irin yawu da ƙyar. Sadik yai wani shakiyyin murmushi, ya ƙara mata manyan idanunsa, yace "uwar marasa kunya, kin ɗauka na canza da ga yadda kika sanni, dan kinga ina kawar miki da kai shine kike zaƙewa haka? A gabana kinyi waya kin gama ƙaren rashin mutunci kina cemin yaro, ke ba kya so na, yau kuma ina waya kin yi tsaki kince min Aikin banza, kina kishi na kenan?" Kasa Magana tai se zare ido, baki ya mutu. "Ke kina Tunanin Ni Sadik zan so ki ne? Ai nima ba son naki nake ba, Sadakar kifa aka bani kalleki fa wata ƙwaila da ke, ba gaba ba baya, kedai gaki nan ba wani alamar girma a tare da ke, balle a sa ran zaki zama cikakkiyar mace nan kusa, da har zan sa ran in kalleki ki burgeni, ke nan kawai a matsayin 'yar aikina kike, zaman da kike kenan, kuma yau sena cire wannan hijjabin in ga abunda kika taka kike min wannan fitsarar kike kirana da yaro!!!. "Innalillahi wa innalillahi raji'un, dan Allah karka ciren hijjabi na, dan girman Allah" Kan ta rufe baki, Sadik yai sama da hijjabin nata, hakan ya sa ta ƙwala ihu da ƙarfi..... (Malam Sadik ya haka ne?🙄) Littafin nan ₦300 ne kacal. 0009450228 Aisha Adam Jaiz Bank 07063065680 KO kuje manhajar AREWA BOOKS ku siya. domin kuwa ya fi sauƙi ta can. AYI HAƘURI BA EDITING.... Gaba ɗaya Nana ta razane, ta sa hannu ya kare ƙirjinta, se zare ido da take, ko Inna ba ta yadda ta ganta ba hijjabi, Se Sadik da ya taɓa ganin ta sau ɗaya ba hijjabi, shima kuma be kalleta Sosai ba. Sadik kam yayi mamakin ganin Nana, saboda Yadda take zunduma hijjabai ba za kai zaton ma ta na da wani fasali ba. Yayi mamakin yadda jikinta ya bayyanar da alamun girma haka, sedai ba hankali a tare da ita sam. Ya sa hannu ya riƙe vest ɗin, ita ma ze cire mata. Cikin magiya tace "dan girman Allah kayi haƙuri, ba zan sake ba kar kai min tsirara, ni marainiya ce dan Allah kark min haka" "Ai ba kya tsoro, ni da nake Yaro,gara ai mu kece raini tsakanin ni da ke" Tana jin yadda fatarsa me ɗauke da ruwan wanka, ke ƙara mannuwa a jikin ta ta fatar. Kawai ta fashe masa da kuka, saboda tun da take ba ta taɓa shiga fargaba kamar yau ba, wai ita ce a hannun namiji yana mata wannan tijara, wanda ko hannun wani namiji ba ta taɓa riƙewa ba. Sadik ya kama vest ɗin ta, da gaske ze cireta, ta sa hannu ɗaya ta riƙe rigar, ɗaya kuma ta rufe ƙirjinta ta na kuka. Janyota yai zuwa gaban gado, tana turjewa ta na masa magiya, ga hawaye ya kalli Fuskar ta, yadda tai shaɓe shaɓe da hawaye, yace "kneeldown" "To ka cika min rigar se inyi" Ya cikata, aikuwa tai kneeldown, har da ɗaga hannu ta rufe ido. Ji yai kamar yai dariya, amma ya dake yace buɗe idon ki ki sauke hannunki". Ta buɗe ido, ta sauke hannayentA, ta kuma rufe ƙijinta. "Wai uban me kike ɓoyewa, sauke hannayenki" yai maganar cikin tsawa. Haka ta sauke hannun, tana cigaba da kuka. Ya kalleta yace "ke mara kunya ko? Ni kike wa tsiwa ki na gayawa Magana ko?" Ta girgiza kai. Yace "to bari in tuɓeki, in ga abunda kika taka da zaki kalli kamarni kice min yaro" "Nace dan Allah kayi haƙuri fa" "Naji zan haƙura amma bisa wasu sharuɗɗai" Tace "to" "Na farko, daga yau karki ƙara zuwa kaina kina magana ba girmamawa, ba ma kya faɗar suna na, sedai kawai ki fara Magana da ni kai tsaye, to da ga yau am your boss, na gaya miki ke 'yar aikina ce, Boss Sadik zaki dinga kirana. Abu na gaba, zaki dinga gyaran ɗaki da wanken toilet kullum sau biyu a rana. Kuma zan downloading different receipe, da za'a iya sarrafawa a nan ƙasar, zaki dinga mana girki dan na gaji da yawon siyan Abinci, kuma ki kai jagwalgwalo se na miki abunda ba ki zata ba. Always talk to me with respect and manners, am not your mate, idan ba haka ba se na tuɓeki na turaki ƙofar gida ki kwana a haka" Cikin kuka tace "to zan dinga yi, amma dan Allah ka ƙyaleni in saka hijjabi na" "Ba zaki saka ɗin ba, abu na gaba kince ai ba kya sona ko?" Ta jinjina masa kai alamar eh. Yace "good, dama nima ba son ki nake ba, dan ban yi kalar Auren 'yar ƙauye ba, Naji kina gaywa kakarki zaki samo mata siriki Bature Allah ya temaka, Amma ki faɗa da bakinki" Ta ɗan tura baki tace "Ni ko ma dai saki nawa ne, amma kawai ka sakeni" "Shikenan, zan sake ki, amma nan da lokacin da zamu kammala karatu, yanzu dai ki kiyaye dokokin da na shimfiɗa miki, idan kuwa ba haka ba sena aikata abinda nai niyya" Da sauri ta jinjina kai tace "to" "Tashi ki ban guri" Da sauri ta tashi ta na cigaba da rufe jikinta, ta fice da sauri Daga ɗakin. Bayanta Sadik ya bi da kallo, yai murmushi da be san ya kufce masa ba ya tafi kan mudubi dan shafa maia. Nana kuwa haki ta dinga yi da taje ɗaki, tace "yau na ga masifa, da ma tun ba yau ba na fuskanci ɗan iska ne Sadik ɗin nan, ya saba taɓa mata amma ban ta ɓa zaton ze yunƙurin yi min tsirara ba, Allah ka kiyayeni da Sharrin sa". Da safe Nana har fargabar fitowa take, saboda ko haɗuwa da Sadik ba ta ƙaunar yi. Amma ta tuna da kashedinsa, da sassafe ta tafi ɗakinsa ta shiga da sallama, dan gyara masa Sannan ta shirya ta tafi makaranta. Sedai Ko tashi be ba daga baccin safe, haka ta shiga a gaggauce ta gyara masa toilet, ta tattare iya tsakar ɗakin, ta wuce ɗakinta dan ta shirya zuwa Makaranta. A falo ta tarar da Sadik, ya fito jikinsa sanye da dogon wando da vest, ya kalleta ya yatsuna fuska, yayin da ita kuma se sunkuyar da kai take ko haɗa ido ba sa son yi. "Kwomin coffee" ya faɗa cikin isa. "Zan makara fa" ta faɗa a raunane. "I don't care" ya faɗa yana ɗaukar remote. Haka ta koma Kitchen cikin sauri, ta na kumbura baki ta dafa, ta zo ta aje masa tai waje ranta a ɓace. Umman Farhan ta ɗaga labulen ɗakin Farhan tace "ki je babanki na kiranki a ɗakinsa" Ta ɗan lumshe ido Sannan ta tashi, ta nufi ɗakin Abban. Abba ya kalleta yace "Ya akai kika dena zuwa Makaranta ne?" Tace "bakomai" "A'a da komai, Gayamin meyasa?" "Gani nai lokaci yana ƙaratowa, ba amfani cigaba da zuwana Makaranta" Abba ya girgiza kai yace "A'a, Aure da zaki ba ya na nufin shikenan karatunki ba, karatunki na da matuƙar mahimmanci, dan mun riga munyi magana da mijin naki, ze barki ki cigaba dan haka se Allah ya kaimu satin bikin zaki dena zuwa, gobe in Allah ya kaimu ki shirya ki tafi makaranta" Abba da ya san halin da zuwa Makaranta ke sawa ta shiga, da be ce ta koma ba, amma ba yadda ta iya, haka ta amsa masa cewar za ta koma ɗin. Daga nan Abba yace "Yawwa Allah yai miki Albarka, aita haƙuri da rayuwa, shi Aure ɗan haƙuri ne, ba ni da shakka akan kibda tarbiyyar da muka baki, na san ke Yarinya ce ne ladabi, amma a ƙara ai ta haƙuri, ki bi mijinki sau da ƙafa, ki yi biyayyar Aure, ki nemi aljannar ki, insha Allah ba zaki dana sanin wannan Auren ba, ina sa ran ze kula dake, kar ki kalli duk wani ƙyale ƙyale na rayuwa kwanciyar hankali a zaman Aure, ita ake nema" "To Abba insha Allah" "Yawwa ta shi kije, Allah yai miki Albarka" Ta amsa da Ameen Abba. Magungunan da Hajiya take bata ne, suka ƙara jefata cikin mawuyacin hali, da ma can ya lafiyar kura, balle yanzu da Hajiya ke aiko mata da kayan shirya amare. Wani irin feelings ne ke sake takura mata, sedai tai ta juyi akan katifa kamar macijiya. Ta kan tuno yadda akan Sadik ne ta san wani abu makamancin haka, a hankali take sauke ajiyar zuciya ta na lumshe ido. A hankali ta fara tunani, ta taɓa jin yadda Taslim da Meena suke hirar, Mubarak Babba ya na ba su abunda yake sa mutum ya mata damuwarsa. Take ta ji tana son sanin meyake ba su, idan da dama ita ma ya bata ko Allah ze sa ta manta da Sadik, taji sauƙin raɗaɗin da ke cikin zuciyarta. Se kuma ta tuna ai Ance an kama Mubarak ɗin, dan haka ba ta san in da zata ganshi ba. Dafe goshinta tayi, tana sake rintse idonta, saboda yadda kan nata ke wata irin sarawa kamar ana dukanta da guduma a kanta. Nazir ne rungume da Lilly a Office ɗin sa, yana kwantar da kansa a jikinta yana lumshe ido. "Please ka ƙyaleni, in tafi bana son wani ya zo ya ganni a Office ɗin nan, zargi ya fara shiga" Muryarsa ƙasa ƙasa yace "wane irin zargi kuma, ba wanda ze ganmu ai duk ana Class, bari in saka key please karki tafi" Tace "gaskiya am not in mood, ka ƙyaleni" Yai ajiyar zuciya yace "to, naji amma yaushe zaki zo gidan, nai missing girkinki" Lilly tace "Daddy fa ya na gari, ba yadda za ai in zo, ni ka ƙyaleni in huta mana haba" Murmushi yai yace "duk wannan hutun da ki kai, yaushe rabonmu da juna? Ke ko missing ɗi na ba kya yi?" "Hmmm, ai ni kwana biyun nan hutu na ne" "Ko dai kin samu wani ne? Shine kike ƙoƙarin juyan baya?" Dariya tai tace "kai ka sani a layi, kuma ba wanda nake mu'amala da shi se kai, Karma ka sake kawo wannan tunanin a ranka, and lokacin sake ɗaukar allura ta yayi, shiyasa ka ga naƙi sakin jiki, ba na son a samu matsala" "No karki damu, babu wata matsala da za a samu Insha Allah, allurar za ta iya ɗaukar dogon zango a jiknki, but allow me to enjoy please" Haka suka saka key a Office ɗin, suka sheƙe ayarsu, tsakanin Malami da ɗalibarsa (waiyazubillah, Allah ya shirya mana zuriya). Khairat ta tattare kayanta ta bar gidan Mother, tana cikin damuwa sosai, saboda tun daga lokacin da Faruk ya ƙi amincewa da soyayyar ta, ta ji zaman Gidan ya isheta, ta tattara ta koma na su gidan, ta na cigaba da jin yadda ta ke matuƙar jin kewarsa. Kwana biyu Nana ta ɗan nutsu, ta rage yiwa Sadik tsiwa da rashin kunya, dan da gaske ta yadda ze mata tsirara, ita kuwa da yai mata tsirara ga ra ta bi shi a sannu. Sadik kuwa ya samu dama, ya ke juyata yadda yake so, saboda ya gano lagonta, dan har gugar kaya yake sata, yai ta sata aiki kamar baiwa. Yau da daddare Sadik ya samu Nana a falo, tana duba litattafanta. "Jeki shirya zamu fita" ya faɗa a taƙsice. "Ina zamu?" "Ban sani ba" ya bata amsa. Seda ta ɗan tura baki, sannan ta miƙe. "Idan kika sako wannan uban hijjabin, sukace kin ɓoye bom ba abunda yai min zafi kamaki za suyi su kaiki prison" "Kai wannan masifa da me tai kama?" Tai maganar tana jan ƙaramin tsaki. Doguwar rigar abaya ta saka, da mayafinta sannan ta fito. Seda ta ɗan jira Sannan Sadik ya fito, haka ta biyo bayansa tana mamakin in da za su a daren nan. Taxi suka hau, suka tafi ba tare da ta san in da za su ba. Wani katafaren mall suka je, Tun da Nana ta zo London ba ta taɓa yawo aka garin ba, nan ta saki baki ta na kallon ƙayatuwar garin. Cikin mall ɗin suka shiga, Nan Nana ta zama cikakkiyar 'yar ƙauye saboda kallo. Ya kalleta yace "ki shiga ki ɗau abunda kike buƙata" "To ina zan je?" "Bakiga in da mutane suke bi ba?" "Dan Allah ka zo muje, ni wallahi ba zan iya zuwa nikaɗai ba". "Tun da cinye ki za suyi ko?" "A'a dan Allah ba danni ba" tai maganar tana langaɓe kai. Guntun tsaki ya ja, yai gaba ta bi bayansa. Nan ta dinga ɗibar abunda ta ke so, abunda Sadik ya siya babu yawa, yace ta zo su tafi. Ta kalleshi tace "to kayan fa?" Be kulata ba ya kuma yin gaba, tana binsa kamar jela. Farfajiyar mall ɗin suka koma, ya sa aka kawo musu coffee, be ce ta sha ba, be ce kar ta sha ba, shi dai ya ɗau na sa yana sha. Wayarsa ya ɗakko ya daddana, ya saka a kunnensa. Nana ta ɗau coffee ɗin ta tana sha, tana lumshe ido da alama yanayin yana mata daɗi. "Hello Mother" Se da cikin Nana ya kaɗa jin ya kira sunan Mother. "Sadik, kai kuwa meyasamu wayarka? Duk na bi na ɗaga hankalina, har na fara shirye-shiryen sawa a duba min kai, fiye da wata guda wayarka ba ta shiga" Sadik ya ɗan gyara zama yace "Abba ne da ya zo, yai seizing ɗin wayata, ban san dalili ba, se da na sai wata na canza sim, so ban samu liscesne ɗin amfani da layin bane, se jiya shiyasa kika jini shiru" "Kai, amma hankalina ba ƙaramin tashi yayi ba, wallahi na shiga damuwa sosai, amma ni sam be nuna min cewar ya zo in da kake ba, cemin yai gurin 'yarsa zeje" "A'a ya zo" "Shikenan, ina fatan ba wata matsala dai?" "Ba wata matsala, am just missing You mum" Mother tace "Allah sarki Autana, ya makarantar?" "Makaranta Lafiya ƙalau, komai normal" "To Masha Allah, Allah ya bada sa'a, ka kula da kanka sosai da sosai, ina kuma jadadda maka ba kai ba yarinyar nan, karka kuskura kaje in da take, ina nan ina wani shiri yadda zan raba Auren nan kan ku dawo, ba tare da mahaifinka ya ji haushin mu ba" Kallon Nana Sadik yai, ya ga She's busy siffin her Coffee, tana yi ta na kalle kalle. Ranar da Steve ya zo gidansu, ya haɗa shi da Abba a waya, Abba ya ja kunnensa sosai sannan yai masa Nasiha yace "Yanzu Sadik, idan ni ko mahaifiyarka ya mutu, ya zakaji?" Sadik yace "haba Abba, dan Allah ka dena irin wannan maganar" Abba yace "ina son ka bani amsa ne" Sadik yace "zan shiga damuwa, ban san yadda zan misalta halin da zan shiga ba" Abba yace "idan kuma ka rasa mu duka fa?" "Abba, dan Allah ka dena wannan maganar, kar ka sa zuciyata ta karye" "To ina son ka misalta kanka a matsayin Nana, haka fa ta tashi ba uwa ba uba, ba ta san daɗinsu ba sam, ta dai tashi tsakanin kakaninta, ka sanya kanka a matsayin da Nana take na maraici, duk gatan da za'a maka ba kamar gatan iyaye ba ne, ni ba zan takura maka se ka sota ba, amma dan Allah ina roƙonka, kar ka cutar da ita, ka yi haƙuri da ita ka dubi maraicinta, akwai falala me girma a cikin riƙon maraya, ba ita tai maka laifi ba, kar ka huce a kanta, kayi haƙuri, ina lallaɓaka a yanzu, amma idan kaje ka aikata son zuciyar ka, to duk hukuncin da Ubangiji yai maka sedai in kalleka" Wannan maganganu na Abba ne ya sa jikinsa Sadik yin sanyi sosai, ya zamana da ya kalli Nana, se yaji tausayinta haka ta tashi ba ta san mamanta ba, ba ta san babanta ba ta rasa wannan Soyayyar ta su har abada, wannan dalilin ne ya sa ya ɗan sassauto da ga wannan ƙiyayyar da yake mata. "Kai wai ba ka jina ne?" Se yanzu Sadik ya tuna waya yake da Mother, yace "Ina jinki, dan Allah ki turomin lambar bro, da yake amfani da ita yanzu" Mother tace "shikenan, zan turo maka" A hankali ya sauke wayar daga kunnnsa yana kallon Nana, da take ta lunshe ido alamar bacci take ji. Ya miƙe tsaye ya kalleta yace "mu tafi" Ya samo taxi suka ɗauki siyayyar da sukai, suka tafi gida, sedai kan suje tun ta ɓingire ta na bacci a Mota. Kallonta yake, yana tunanin yadda ze tashe ta ba tare da ta masa ihu ba, dan ya san kaɗan da aikinta. Ya fita daga Motar, ya sassauke kayan, ya buɗe gida sannan ya dawo ya ɗauketa, zuwa cikin gida. A kan gadonta ya ajiyeta, Sannan ya shigo da kayan da suka siyo. Duk wannan budurin da Sadik yake ba ta san yanayi ba, saboda baccin nata yai nisa sosai. Bisa ga umarnin Abba, Farhan ta komaa Makaranta, ta cigaba da zuwa, sedai ba ta gane Komai, kuma ba ta son mutane gaba ɗaya. Yau an fita break, Lilly ta shigo da ledar takeaway a hannunta, Farhan ta kalli Lilly tace "dan Allah Fatima, ina Mubarak Babba?" Da mamaki Lilly tace "meyasa kike nemansa? Ina bakwa shiri da shi?" "Eh na tambaya ne kawai, naji kamar rannan kince an kama shi ko?" Lilly tace "eh hakane, ai dama shi wannan kusan kullum cikin kama shi ake, Amma karki mamakin yanzu haka ya fito, saboda babansa ya tsaya masa" Farhan ta jinjina kai tace "shikenan Nagode" "Ko dai ya cigaba da bibiyar ki ne?" Farhan tace "A'a na tambaya ne kawai" Amma a ƙasan zuciyar ta, so ta ke ta haɗu da Babba dan ta samu abun rage damuwa, hatsarin da ke cikin hakan be dameta ba, ita mafita kawai take nema. Nana taji daɗin siyayyar da sukai, sedai Assignment ne da ita na Maths, na ta rasa yadda za tai solving ɗin sa, ga shi yanzu tsoron Sadik take ji. Ba ta da zaɓi illa zuwa ta sameshi, yana aikin na sa na video game tace "Amm.. dan Allah Assignment zaka koya min" Ya ɗan ɗago ya kalleta ya cigaba da game ɗin sa. "Dan Allah ka koyamin in ka iya" "Ban hanaki ki zo kaina ki tsaya ba, kina min magana a haka ba, me nace ki dinga kirana da shi" "Yi hakuri, na manta ne" Ya miƙa mata hannu, alamar ta bashi littafin. Ba musu ta miƙa masa, ya ɗan kalli Assignment ɗin sannan ya kalleta yace "ke wannan ne se an koya miki? Meye abun wahalar a nan?" "To ba nayi na kasa ba" tai maganar tana cuna baki. Tsaki yai ya karɓi biron hannunta, ba tare da yace mata komai na, ko yayi using calculator b, ya fara solving. Abun ya bata mamaki sosai, ba ta taɓa ganin Sadik na karatu ba, sedai video game ko litattafan turanci, se kuma yawonsa. Amma cikin nutsuwa yake solving ɗin, a mintuna ƙalilan ya kammala ya miƙo mata, ya karɓa ta kalla tace "to ai ban san yadda kai ba, idan kuma aka tambaye ni ya akai nayi fa?" "Se kice, yi miki a kai ke ba ki iya ba" "Hmm Allah sa ma daida kai min, kar in kai inci zero, kawai ka karɓi biro ka min rubutu a cikin littafi" Kallonta yake da mamakin tsiwa irin ta Nana, sedai yaji gabansa ya faɗi, gani yake kamar abu makamancin wannan ya taɓa faruwa da shi a gaske, kamar wannan abun ya taɓa faruwa. Take kansa ya fara juyawa, ya fara kokawa da memory ɗin sa, akan ya tuna meyafaru, wani abu me mahimmanci yana cin sa a zuciya, amma ya kasa tuna ko meye. Jifa yai da remote ɗin hannunsa yana dafe kansa, a gigice Nana ta kalleshi tace "Subhanallah, meke faruwa ne meya same ka?" Cigaba da rintse ido yai Sosai, yana jujjuya kansa akan ya tuna wannan abun, amma se yaji kamar kansa ze rave biyu. Ta jefar da littafin hannunta, ta yo kan Sadik da sauri tace "baka da lafiya ne?" Ya girgiza mata kai alamar a'a, da sauri taje fridge ta ɗakko ruwa ta kawo masa tace "karɓi ka sha ruwa" Ba musu ya karɓa, ya ɗaga kai ya sha sosai, Sannan ya ajiye. A sanyaye tace "ko Steve za ka kira, a kaika Asibiti?" Ua girgiza mata kai, ya nemi guri ya kwanta yana ajiyar zuciya. Nana ta zauna tai tagumi tana kallon sa. Ya kai awa guda a wannan yanayin sannan ya watstsake, ya tashi ya fita. Yau saura sati biyu, Auren Farhan ta sake susucewa, gaba ɗaya ta koma wata wujiga wujiga, kamar korarriya, banda azabar ƙiyayyar Sunusi da kuma son Sadik ba abunda yake ɗawainiya da ita. Yau bisa ga jagorancin makauniyar zuciyar Farhan, me cike da neman mafita ta tafi ajinsu Sadik, gurin Tasleem. Tasleem tayi mamaki da Farhan tace wai gurinta ta zo. Farhan tace "dan Allah temaka min nake son kiyi" Tasleem tace "wane irin taimako kenan?" Farhan tace "da daɗewa naji kuna cewa, akwai maganin rage damuwa da sa bacci, shine nake son dan Allah zan siya ba na iya bacci sam" Tasleem tai murmushi tace "duk tunanin Sadik ɗin ne?" Farhan tai shiru ba tace komai ba, Tasleem tace "welcome to the jungle Yarinya, Allah ya baki kyau da ƙira, ki mori ƙuruciyar ki, amma kika tsaya biyewa Soyayyar RUƊIN ƘURUCIYA, a wannan surara ta ki, ba iya kayan caji Yakamata ki tsaya ba, Yakamata ace kina ehhhh" Tasleem tai maganar tana shafa bayan Farhan........... ME KUKE TUNANIN ZE FARU? FARHAN BA IYA DAMUWA KE DAMUNTA BA, HAR DA MATSANANCIN FEELINGS, ZATA SHIGA GANG ƊIN SU TASLEEM, LET'S DISCUSSED THIS BEFORE ALLAH YA KAIMU BAYAN SALLA) (Amin afuwa, typing ba yawa, saboda yanayi na Salla, in Allah ya kaimu gobe ranar Arfa, zanje hutu se Allah ya kaimu bayan salla insha Allah zamu ɗora, dan Allah kar ku manta da ni a cikin Addu'oin ku a ranar Arfa.) AYI HAƘURI BA EDITING.... Gaba ɗaya Nana ta razane, ta sa hannu ya kare ƙirjinta, se zare ido da take, ko Inna ba ta yadda ta ganta ba hijjabi, Se Sadik da ya taɓa ganin ta sau ɗaya ba hijjabi, shima kuma be kalleta Sosai ba. Sadik kam yayi mamakin ganin Nana, saboda Yadda take zunduma hijjabai ba za kai zaton ma ta na da wani fasali ba. Yayi mamakin yadda jikinta ya bayyanar da alamun girma haka, sedai ba hankali a tare da ita sam. Ya sa hannu ya riƙe vest ɗin, ita ma ze cire mata. Cikin magiya tace "dan girman Allah kayi haƙuri, ba zan sake ba kar kai min tsirara, ni marainiya ce dan Allah kark min haka" "Ai ba kya tsoro, ni da nake Yaro,gara ai mu kece raini tsakanin ni da ke" Tana jin yadda fatarsa me ɗauke da ruwan wanka, ke ƙara mannuwa a jikin ta ta fatar. Kawai ta fashe masa da kuka, saboda tun da take ba ta taɓa shiga fargaba kamar yau ba, wai ita ce a hannun namiji yana mata wannan tijara, wanda ko hannun wani namiji ba ta taɓa riƙewa ba. Sadik ya kama vest ɗin ta, da gaske ze cireta, ta sa hannu ɗaya ta riƙe rigar, ɗaya kuma ta rufe ƙirjinta ta na kuka. Janyota yai zuwa gaban gado, tana turjewa ta na masa magiya, ga hawaye ya kalli Fuskar ta, yadda tai shaɓe shaɓe da hawaye, yace "kneeldown" "To ka cika min rigar se inyi" Ya cikata, aikuwa tai kneeldown, har da ɗaga hannu ta rufe ido. Ji yai kamar yai dariya, amma ya dake yace buɗe idon ki ki sauke hannunki". Ta buɗe ido, ta sauke hannayentA, ta kuma rufe ƙijinta. "Wai uban me kike ɓoyewa, sauke hannayenki" yai maganar cikin tsawa. Haka ta sauke hannun, tana cigaba da kuka. Ya kalleta yace "ke mara kunya ko? Ni kike wa tsiwa ki na gayawa Magana ko?" Ta girgiza kai. Yace "to bari in tuɓeki, in ga abunda kika taka da zaki kalli kamarni kice min yaro" "Nace dan Allah kayi haƙuri fa" "Naji zan haƙura amma bisa wasu sharuɗɗai" Tace "to" "Na farko, daga yau karki ƙara zuwa kaina kina magana ba girmamawa, ba ma kya faɗar suna na, sedai kawai ki fara Magana da ni kai tsaye, to da ga yau am your boss, na gaya miki ke 'yar aikina ce, Boss Sadik zaki dinga kirana. Abu na gaba, zaki dinga gyaran ɗaki da wanken toilet kullum sau biyu a rana. Kuma zan downloading different receipe, da za'a iya sarrafawa a nan ƙasar, zaki dinga mana girki dan na gaji da yawon siyan Abinci, kuma ki kai jagwalgwalo se na miki abunda ba ki zata ba. Always talk to me with respect and manners, am not your mate, idan ba haka ba se na tuɓeki na turaki ƙofar gida ki kwana a haka" Cikin kuka tace "to zan dinga yi, amma dan Allah ka ƙyaleni in saka hijjabi na" "Ba zaki saka ɗin ba, abu na gaba kince ai ba kya sona ko?" Ta jinjina masa kai alamar eh. Yace "good, dama nima ba son ki nake ba, dan ban yi kalar Auren 'yar ƙauye ba, Naji kina gaywa kakarki zaki samo mata siriki Bature Allah ya temaka, Amma ki faɗa da bakinki" Ta ɗan tura baki tace "Ni ko ma dai saki nawa ne, amma kawai ka sakeni" "Shikenan, zan sake ki, amma nan da lokacin da zamu kammala karatu, yanzu dai ki kiyaye dokokin da na shimfiɗa miki, idan kuwa ba haka ba sena aikata abinda nai niyya" Da sauri ta jinjina kai tace "to" "Tashi ki ban guri" Da sauri ta tashi ta na cigaba da rufe jikinta, ta fice da sauri Daga ɗakin. Bayanta Sadik ya bi da kallo, yai murmushi da be san ya kufce masa ba ya tafi kan mudubi dan shafa maia. Nana kuwa haki ta dinga yi da taje ɗaki, tace "yau na ga masifa, da ma tun ba yau ba na fuskanci ɗan iska ne Sadik ɗin nan, ya saba taɓa mata amma ban ta ɓa zaton ze yunƙurin yi min tsirara ba, Allah ka kiyayeni da Sharrin sa". Da safe Nana har fargabar fitowa take, saboda ko haɗuwa da Sadik ba ta ƙaunar yi. Amma ta tuna da kashedinsa, da sassafe ta tafi ɗakinsa ta shiga da sallama, dan gyara masa Sannan ta shirya ta tafi makaranta. Sedai Ko tashi be ba daga baccin safe, haka ta shiga a gaggauce ta gyara masa toilet, ta tattare iya tsakar ɗakin, ta wuce ɗakinta dan ta shirya zuwa Makaranta. A falo ta tarar da Sadik, ya fito jikinsa sanye da dogon wando da vest, ya kalleta ya yatsuna fuska, yayin da ita kuma se sunkuyar da kai take ko haɗa ido ba sa son yi. "Kwomin coffee" ya faɗa cikin isa. "Zan makara fa" ta faɗa a raunane. "I don't care" ya faɗa yana ɗaukar remote. Haka ta koma Kitchen cikin sauri, ta na kumbura baki ta dafa, ta zo ta aje masa tai waje ranta a ɓace. Umman Farhan ta ɗaga labulen ɗakin Farhan tace "ki je babanki na kiranki a ɗakinsa" Ta ɗan lumshe ido Sannan ta tashi, ta nufi ɗakin Abban. Abba ya kalleta yace "Ya akai kika dena zuwa Makaranta ne?" Tace "bakomai" "A'a da komai, Gayamin meyasa?" "Gani nai lokaci yana ƙaratowa, ba amfani cigaba da zuwana Makaranta" Abba ya girgiza kai yace "A'a, Aure da zaki ba ya na nufin shikenan karatunki ba, karatunki na da matuƙar mahimmanci, dan mun riga munyi magana da mijin naki, ze barki ki cigaba dan haka se Allah ya kaimu satin bikin zaki dena zuwa, gobe in Allah ya kaimu ki shirya ki tafi makaranta" Abba da ya san halin da zuwa Makaranta ke sawa ta shiga, da be ce ta koma ba, amma ba yadda ta iya, haka ta amsa masa cewar za ta koma ɗin. Daga nan Abba yace "Yawwa Allah yai miki Albarka, aita haƙuri da rayuwa, shi Aure ɗan haƙuri ne, ba ni da shakka akan kibda tarbiyyar da muka baki, na san ke Yarinya ce ne ladabi, amma a ƙara ai ta haƙuri, ki bi mijinki sau da ƙafa, ki yi biyayyar Aure, ki nemi aljannar ki, insha Allah ba zaki dana sanin wannan Auren ba, ina sa ran ze kula dake, kar ki kalli duk wani ƙyale ƙyale na rayuwa kwanciyar hankali a zaman Aure, ita ake nema" "To Abba insha Allah" "Yawwa ta shi kije, Allah yai miki Albarka" Ta amsa da Ameen Abba. Magungunan da Hajiya take bata ne, suka ƙara jefata cikin mawuyacin hali, da ma can ya lafiyar kura, balle yanzu da Hajiya ke aiko mata da kayan shirya amare. Wani irin feelings ne ke sake takura mata, sedai tai ta juyi akan katifa kamar macijiya. Ta kan tuno yadda akan Sadik ne ta san wani abu makamancin haka, a hankali take sauke ajiyar zuciya ta na lumshe ido. A hankali ta fara tunani, ta taɓa jin yadda Taslim da Meena suke hirar, Mubarak Babba ya na ba su abunda yake sa mutum ya mata damuwarsa. Take ta ji tana son sanin meyake ba su, idan da dama ita ma ya bata ko Allah ze sa ta manta da Sadik, taji sauƙin raɗaɗin da ke cikin zuciyarta. Se kuma ta tuna ai Ance an kama Mubarak ɗin, dan haka ba ta san in da zata ganshi ba. Dafe goshinta tayi, tana sake rintse idonta, saboda yadda kan nata ke wata irin sarawa kamar ana dukanta da guduma a kanta. Nazir ne rungume da Lilly a Office ɗin sa, yana kwantar da kansa a jikinta yana lumshe ido. "Please ka ƙyaleni, in tafi bana son wani ya zo ya ganni a Office ɗin nan, zargi ya fara shiga" Muryarsa ƙasa ƙasa yace "wane irin zargi kuma, ba wanda ze ganmu ai duk ana Class, bari in saka key please karki tafi" Tace "gaskiya am not in mood, ka ƙyaleni" Yai ajiyar zuciya yace "to, naji amma yaushe zaki zo gidan, nai missing girkinki" Lilly tace "Daddy fa ya na gari, ba yadda za ai in zo, ni ka ƙyaleni in huta mana haba" Murmushi yai yace "duk wannan hutun da ki kai, yaushe rabonmu da juna? Ke ko missing ɗi na ba kya yi?" "Hmmm, ai ni kwana biyun nan hutu na ne" "Ko dai kin samu wani ne? Shine kike ƙoƙarin juyan baya?" Dariya tai tace "kai ka sani a layi, kuma ba wanda nake mu'amala da shi se kai, Karma ka sake kawo wannan tunanin a ranka, and lokacin sake ɗaukar allura ta yayi, shiyasa ka ga naƙi sakin jiki, ba na son a samu matsala" "No karki damu, babu wata matsala da za a samu Insha Allah, allurar za ta iya ɗaukar dogon zango a jiknki, but allow me to enjoy please" Haka suka saka key a Office ɗin, suka sheƙe ayarsu, tsakanin Malami da ɗalibarsa (waiyazubillah, Allah ya shirya mana zuriya). Khairat ta tattare kayanta ta bar gidan Mother, tana cikin damuwa sosai, saboda tun daga lokacin da Faruk ya ƙi amincewa da soyayyar ta, ta ji zaman Gidan ya isheta, ta tattara ta koma na su gidan, ta na cigaba da jin yadda ta ke matuƙar jin kewarsa. Kwana biyu Nana ta ɗan nutsu, ta rage yiwa Sadik tsiwa da rashin kunya, dan da gaske ta yadda ze mata tsirara, ita kuwa da yai mata tsirara ga ra ta bi shi a sannu. Sadik kuwa ya samu dama, ya ke juyata yadda yake so, saboda ya gano lagonta, dan har gugar kaya yake sata, yai ta sata aiki kamar baiwa. Yau da daddare Sadik ya samu Nana a falo, tana duba litattafanta. "Jeki shirya zamu fita" ya faɗa a taƙsice. "Ina zamu?" "Ban sani ba" ya bata amsa. Seda ta ɗan tura baki, sannan ta miƙe. "Idan kika sako wannan uban hijjabin, sukace kin ɓoye bom ba abunda yai min zafi kamaki za suyi su kaiki prison" "Kai wannan masifa da me tai kama?" Tai maganar tana jan ƙaramin tsaki. Doguwar rigar abaya ta saka, da mayafinta sannan ta fito. Seda ta ɗan jira Sannan Sadik ya fito, haka ta biyo bayansa tana mamakin in da za su a daren nan. Taxi suka hau, suka tafi ba tare da ta san in da za su ba. Wani katafaren mall suka je, Tun da Nana ta zo London ba ta taɓa yawo aka garin ba, nan ta saki baki ta na kallon ƙayatuwar garin. Cikin mall ɗin suka shiga, Nan Nana ta zama cikakkiyar 'yar ƙauye saboda kallo. Ya kalleta yace "ki shiga ki ɗau abunda kike buƙata" "To ina zan je?" "Bakiga in da mutane suke bi ba?" "Dan Allah ka zo muje, ni wallahi ba zan iya zuwa nikaɗai ba". "Tun da cinye ki za suyi ko?" "A'a dan Allah ba danni ba" tai maganar tana langaɓe kai. Guntun tsaki ya ja, yai gaba ta bi bayansa. Nan ta dinga ɗibar abunda ta ke so, abunda Sadik ya siya babu yawa, yace ta zo su tafi. Ta kalleshi tace "to kayan fa?" Be kulata ba ya kuma yin gaba, tana binsa kamar jela. Farfajiyar mall ɗin suka koma, ya sa aka kawo musu coffee, be ce ta sha ba, be ce kar ta sha ba, shi dai ya ɗau na sa yana sha. Wayarsa ya ɗakko ya daddana, ya saka a kunnensa. Nana ta ɗau coffee ɗin ta tana sha, tana lumshe ido da alama yanayin yana mata daɗi. "Hello Mother" Se da cikin Nana ya kaɗa jin ya kira sunan Mother. "Sadik, kai kuwa meyasamu wayarka? Duk na bi na ɗaga hankalina, har na fara shirye-shiryen sawa a duba min kai, fiye da wata guda wayarka ba ta shiga" Sadik ya ɗan gyara zama yace "Abba ne da ya zo, yai seizing ɗin wayata, ban san dalili ba, se da na sai wata na canza sim, so ban samu liscesne ɗin amfani da layin bane, se jiya shiyasa kika jini shiru" "Kai, amma hankalina ba ƙaramin tashi yayi ba, wallahi na shiga damuwa sosai, amma ni sam be nuna min cewar ya zo in da kake ba, cemin yai gurin 'yarsa zeje" "A'a ya zo" "Shikenan, ina fatan ba wata matsala dai?" "Ba wata matsala, am just missing You mum" Mother tace "Allah sarki Autana, ya makarantar?" "Makaranta Lafiya ƙalau, komai normal" "To Masha Allah, Allah ya bada sa'a, ka kula da kanka sosai da sosai, ina kuma jadadda maka ba kai ba yarinyar nan, karka kuskura kaje in da take, ina nan ina wani shiri yadda zan raba Auren nan kan ku dawo, ba tare da mahaifinka ya ji haushin mu ba" Kallon Nana Sadik yai, ya ga She's busy siffin her Coffee, tana yi ta na kalle kalle. Ranar da Steve ya zo gidansu, ya haɗa shi da Abba a waya, Abba ya ja kunnensa sosai sannan yai masa Nasiha yace "Yanzu Sadik, idan ni ko mahaifiyarka ya mutu, ya zakaji?" Sadik yace "haba Abba, dan Allah ka dena irin wannan maganar" Abba yace "ina son ka bani amsa ne" Sadik yace "zan shiga damuwa, ban san yadda zan misalta halin da zan shiga ba" Abba yace "idan kuma ka rasa mu duka fa?" "Abba, dan Allah ka dena wannan maganar, kar ka sa zuciyata ta karye" "To ina son ka misalta kanka a matsayin Nana, haka fa ta tashi ba uwa ba uba, ba ta san daɗinsu ba sam, ta dai tashi tsakanin kakaninta, ka sanya kanka a matsayin da Nana take na maraici, duk gatan da za'a maka ba kamar gatan iyaye ba ne, ni ba zan takura maka se ka sota ba, amma dan Allah ina roƙonka, kar ka cutar da ita, ka yi haƙuri da ita ka dubi maraicinta, akwai falala me girma a cikin riƙon maraya, ba ita tai maka laifi ba, kar ka huce a kanta, kayi haƙuri, ina lallaɓaka a yanzu, amma idan kaje ka aikata son zuciyar ka, to duk hukuncin da Ubangiji yai maka sedai in kalleka" Wannan maganganu na Abba ne ya sa jikinsa Sadik yin sanyi sosai, ya zamana da ya kalli Nana, se yaji tausayinta haka ta tashi ba ta san mamanta ba, ba ta san babanta ba ta rasa wannan Soyayyar ta su har abada, wannan dalilin ne ya sa ya ɗan sassauto da ga wannan ƙiyayyar da yake mata. "Kai wai ba ka jina ne?" Se yanzu Sadik ya tuna waya yake da Mother, yace "Ina jinki, dan Allah ki turomin lambar bro, da yake amfani da ita yanzu" Mother tace "shikenan, zan turo maka" A hankali ya sauke wayar daga kunnnsa yana kallon Nana, da take ta lunshe ido alamar bacci take ji. Ya miƙe tsaye ya kalleta yace "mu tafi" Ya samo taxi suka ɗauki siyayyar da sukai, suka tafi gida, sedai kan suje tun ta ɓingire ta na bacci a Mota. Kallonta yake, yana tunanin yadda ze tashe ta ba tare da ta masa ihu ba, dan ya san kaɗan da aikinta. Ya fita daga Motar, ya sassauke kayan, ya buɗe gida sannan ya dawo ya ɗauketa, zuwa cikin gida. A kan gadonta ya ajiyeta, Sannan ya shigo da kayan da suka siyo. Duk wannan budurin da Sadik yake ba ta san yanayi ba, saboda baccin nata yai nisa sosai. Bisa ga umarnin Abba, Farhan ta komaa Makaranta, ta cigaba da zuwa, sedai ba ta gane Komai, kuma ba ta son mutane gaba ɗaya. Yau an fita break, Lilly ta shigo da ledar takeaway a hannunta, Farhan ta kalli Lilly tace "dan Allah Fatima, ina Mubarak Babba?" Da mamaki Lilly tace "meyasa kike nemansa? Ina bakwa shiri da shi?" "Eh na tambaya ne kawai, naji kamar rannan kince an kama shi ko?" Lilly tace "eh hakane, ai dama shi wannan kusan kullum cikin kama shi ake, Amma karki mamakin yanzu haka ya fito, saboda babansa ya tsaya masa" Farhan ta jinjina kai tace "shikenan Nagode" "Ko dai ya cigaba da bibiyar ki ne?" Farhan tace "A'a na tambaya ne kawai" Amma a ƙasan zuciyar ta, so ta ke ta haɗu da Babba dan ta samu abun rage damuwa, hatsarin da ke cikin hakan be dameta ba, ita mafita kawai take nema. Nana taji daɗin siyayyar da sukai, sedai Assignment ne da ita na Maths, na ta rasa yadda za tai solving ɗin sa, ga shi yanzu tsoron Sadik take ji. Ba ta da zaɓi illa zuwa ta sameshi, yana aikin na sa na video game tace "Amm.. dan Allah Assignment zaka koya min" Ya ɗan ɗago ya kalleta ya cigaba da game ɗin sa. "Dan Allah ka koyamin in ka iya" "Ban hanaki ki zo kaina ki tsaya ba, kina min magana a haka ba, me nace ki dinga kirana da shi" "Yi hakuri, na manta ne" Ya miƙa mata hannu, alamar ta bashi littafin. Ba musu ta miƙa masa, ya ɗan kalli Assignment ɗin sannan ya kalleta yace "ke wannan ne se an koya miki? Meye abun wahalar a nan?" "To ba nayi na kasa ba" tai maganar tana cuna baki. Tsaki yai ya karɓi biron hannunta, ba tare da yace mata komai na, ko yayi using calculator b, ya fara solving. Abun ya bata mamaki sosai, ba ta taɓa ganin Sadik na karatu ba, sedai video game ko litattafan turanci, se kuma yawonsa. Amma cikin nutsuwa yake solving ɗin, a mintuna ƙalilan ya kammala ya miƙo mata, ya karɓa ta kalla tace "to ai ban san yadda kai ba, idan kuma aka tambaye ni ya akai nayi fa?" "Se kice, yi miki a kai ke ba ki iya ba" "Hmm Allah sa ma daida kai min, kar in kai inci zero, kawai ka karɓi biro ka min rubutu a cikin littafi" Kallonta yake da mamakin tsiwa irin ta Nana, sedai yaji gabansa ya faɗi, gani yake kamar abu makamancin wannan ya taɓa faruwa da shi a gaske, kamar wannan abun ya taɓa faruwa. Take kansa ya fara juyawa, ya fara kokawa da memory ɗin sa, akan ya tuna meyafaru, wani abu me mahimmanci yana cin sa a zuciya, amma ya kasa tuna ko meye. Jifa yai da remote ɗin hannunsa yana dafe kansa, a gigice Nana ta kalleshi tace "Subhanallah, meke faruwa ne meya same ka?" Cigaba da rintse ido yai Sosai, yana jujjuya kansa akan ya tuna wannan abun, amma se yaji kamar kansa ze rave biyu. Ta jefar da littafin hannunta, ta yo kan Sadik da sauri tace "baka da lafiya ne?" Ya girgiza mata kai alamar a'a, da sauri taje fridge ta ɗakko ruwa ta kawo masa tace "karɓi ka sha ruwa" Ba musu ya karɓa, ya ɗaga kai ya sha sosai, Sannan ya ajiye. A sanyaye tace "ko Steve za ka kira, a kaika Asibiti?" Ua girgiza mata kai, ya nemi guri ya kwanta yana ajiyar zuciya. Nana ta zauna tai tagumi tana kallon sa. Ya kai awa guda a wannan yanayin sannan ya watstsake, ya tashi ya fita. Yau saura sati biyu, Auren Farhan ta sake susucewa, gaba ɗaya ta koma wata wujiga wujiga, kamar korarriya, banda azabar ƙiyayyar Sunusi da kuma son Sadik ba abunda yake ɗawainiya da ita. Yau bisa ga jagorancin makauniyar zuciyar Farhan, me cike da neman mafita ta tafi ajinsu Sadik, gurin Tasleem. Tasleem tayi mamaki da Farhan tace wai gurinta ta zo. Farhan tace "dan Allah temaka min nake son kiyi" Tasleem tace "wane irin taimako kenan?" Farhan tace "da daɗewa naji kuna cewa, akwai maganin rage damuwa da sa bacci, shine nake son dan Allah zan siya ba na iya bacci sam" Tasleem tai murmushi tace "duk tunanin Sadik ɗin ne?" Farhan tai shiru ba tace komai ba, Tasleem tace "welcome to the jungle Yarinya, Allah ya baki kyau da ƙira, ki mori ƙuruciyar ki, amma kika tsaya biyewa Soyayyar RUƊIN ƘURUCIYA, a wannan surara ta ki, ba iya kayan caji Yakamata ki tsaya ba, Yakamata ace kina ehhhh" Tasleem tai maganar tana shafa bayan Farhan........... ME KUKE TUNANIN ZE FARU? FARHAN BA IYA DAMUWA KE DAMUNTA BA, HAR DA MATSANANCIN FEELINGS, ZATA SHIGA GANG ƊIN SU TASLEEM, LET'S DISCUSSED THIS BEFORE ALLAH YA KAIMU BAYAN SALLA) (Amin afuwa, typing ba yawa, saboda yanayi na Salla, in Allah ya kaimu gobe ranar Arfa, zanje hutu se Allah ya kaimu bayan salla insha Allah zamu ɗora, dan Allah kar ku manta da ni a cikin Addu'oin ku a ranar Arfa.) Littafin nan ₦300 ne kacal. 0009450228 Aisha Adam Jaiz Bank 07063065680 KO kuje manhajar AREWA BOOKS ku siya. domin kuwa ya fi sauƙi ta can. Kasa ɗaga ƙafarta tai da ga in da take tsaye, tai shiru ta shiga tunani "yanzu idan ki ka fita ina zaki a Wannan dare? Wa kike da shi da zaki gurinsa? Idan ki kai haka kin wa kanki adalci kenan? Mutuncinki da kimar ki za su zube a idon duniya, kuma ki bawa iyayenki kunya, ace kin gudu ranar ɗaurin Auren ki. To amma ai auren dole za'aimin, yanzu shikenan nai bankwana da farinciki? Shikenan haka rayuwata za ta ƙare, in rayu da mutumin da babu alamar Soyayyar sa a raina? Ta ya zan iya Rayuwar Aure da Soyayyar wani a raina? Abba meyasa kuka kasa fahimtar kawaici nai muku? Bana son wanda zaku Auramin?" A hankali wasu siraran hawaye suka fara zirarowa daga Idonta. A hankali ta ja ƙafarta ta koma cikin ɗakinta, ta ɗakko maganin da Babba ya ba ta, ta ɓallo ɗaya ta ɗau ruwa ta shanye, a tunanin ta ko tai bacci ta samu sassauci. Ta nemi guri ta kwanta ta ƙurawa guri ɗaya ido, tana tunani daban daban a zuciyar ta. Befi mintuna goma da shan maganin nan ba, ta ji kanta yana mata wani irin abu, Kamar duniyar na jujjuyawa, ta rintse idonta ta buɗe amma ta ga komai yana juya mata, gani tamkar ginin ɗakin da take ciki ze ruso kanta. Hannu ta sa ta danne kanta, ta rintse ido, wani irin gumi ya shiga kwaranyo mata, ta rasa gane a wace duniyar take, a zahiri abunda take gani ne, ko kuma ita kaɗai take ganin abunda take gani. Haka ta wanzu a wannan hali, ba tare da sanin in da kanta yake ba. Sadik yayi bajinta sosai a wasan ƙwallon da akai a makarantar su, duk da kasancewar sa baƙar fata, amma yana da magoya baya sosai da sosai, club ɗin sa ne suka ci 4 abokan karawar su kuma suka ci 2, Sadik ne ya saka ƙwallaye uku a raga. Bayan an tashi daga wasan, aka dinga hotuna da Sadik, Nana tana gefe tana kallonsa tana murmushi. Tana nan zaune tana kallon yadda ake ɗaga shi sama ana hotuna da shi, sedai abun takaicin bayan ya je ya canza kaya, sun shiga cikin makarantar, nan 'yan matan turawan nan ma suka dinga rungumarsa, suna ɗaukar hotuna har da masu masa kiss a goshinsa. Hakan ba ƙaramin ɓatawa Nana rai yai ba, dan haka Sadik ya nemata ya rasa a gurin ko sama ko ƙasa. Hankalinsa ya tashi sosai ya shiga nemanta a gurin, sedai be ganta ba sam, ga guri ba ƙaramin guri ba balle yace bari ya zaga ko ze ganta, idan ma zagawar ze ta ina ze fara. Nan da nan ransa ya fara ɓaci, wannan wace irin kudahumar Yarinya ce da ba aiwa abun arziki, daga zuwa da ita guri ta kama Gabanta.   Tun Sadik yana ɗaukar abun wasa, ya ga Dagaske ba ta gurin,ba ita ba alamunta, nan hankalinsa ya ƙara tashi, gashi babu waya a hannunta a balle yai mata waya yaji ina ta shiga. Ga duhun magariba ya fara yi, ga London ba Nigeria bace, kowa sabgar gabansa yake, balle ya bi mutane ya fara tambayar su, to wa ma ze tambaya, kuma ma me ze ce?. Ya kuma komawa im da take zaune da farko, amma be ganta ba, nan ya fara tunanin ko report ze kai, Gurin jami'an tsaro? Yarinyar nan idan ɓata ta yi me zance wa Abba?" Ya tambayi kansa yana cigaba da rarraba ido. Abu kamar wasa har isha'i, Sadik yana neman Nana amma be ganta ba, ya yanke shawarar bari yaje gida, daga nan ya ga me ya dace yayi. Haka ya kama hanyar tafiya gida, ya manta da batun ɗakko kayan da suka siya a shagon siyayya gaba ɗaya hankalinsa na kan, ina ze ga Nana. Se da yana zuwa gida, ya tarar da ita a gida tana kwance abunta tana kallon cartoon, tana ciye ciye. "Ke, dama gida kika taho, ki barni ina ta bulayin nemanki tun ɗazu?" "Eh, gida na taho, na biyo wasu 'yan makarantar mu da na gani, suka kawo ni gida suka tafi,  na barka, kaji daɗin rungume mata son ranka, dan ni ba zan iya kallon zunubi ba, tun da kai in baka taɓa mata ba baka jin daɗin rayuwa" tai maganar cikin tsiwa da tsantsar kishi. Wani irin marurun baƙin ciki ne ya turnuƙe Sadik, ji yake tamkar ya rufeta da duka, saboda ba ƙaramin tashi hankalinsa yai ba, yai zaton ɓata  yi. Bece mata uffan ba ya wuce ɗakinsa ya barta, tun da ya shiga ɗakinsa be kuma fitowa ba, har gari ya waye. Da sassafe Nana ta shiga ɗakinsa, dan tai dutyn ta da ta saba, ta tarar Sadik yana toilet yana wanka, ta fara gyara masa gafoy, tana cikin gyarawa ya fito. "Me kike min a ɗaki?" Ya faɗa a kausashe. "A'a, me kuwa nake yi, gyara maka mana kar in makara" "Get out from my room" ya faɗa cikin tsawa. Nana tace "to me nai maka?" "I said get out" ya maimaita. A razane ta juya ta fita, dan ya koma Sadik ɗin sa na ainihi. Se kuma ta tuna abunda tai masa jiya, tai shiru tace "haushi yaji kenan? To amma ai gaskiya na faɗa ba ƙarya nai ba. Sedai kuma a wani ɓangare na zuciyarta, sam ba ta ji daɗin yadda Sadik yai watsi da ita ba, dan a 'yan kwanakin nan tafi sakewa, da suke shiri da shi. Haka nan ta tafi Makarantar sukuku. Farhan maye sosai take a ɗakinta, dan bata san in da kanta yake ba, ba ta gane mafarki take ko zahiri ne abunda ke faruwa.   An girke tukwanen biki, ana ƙoƙarin aza wutar tuwon 'yan ɗaurin Aure. Malam Zakari ya tashi ɗan aike, yace ace a gayawa malam Labaran da magabatan Sunusi cewar, muddin be nuna musu in da ze Ajiye musu 'ya ba baza'a ɗaura Auren nan ba, kuma ya tabattar Ya zo da takaddar gwajin Asibiti, na lafiyarsa, idan ba haka ba ba za su ba su 'yar su ba. Shi ko Sunusi na can garinsu, ana ta shiri daga can zasu ta ho gaba ɗaya gurin ɗaurin Aure. Adda Hafsatu ta shiga ɗakin Farhan tana mita "wai wannan wace irin Amarya ce haka? Ana ta faman shiri amma kin ƙule a ɗaka ko wanka ba ki ba, balle a sa ran ki kintsa kafin dangin mijinki su zo, ba zaki ta shi ba ina miki Magana?" Shiru Farhan ba ta amsa ba se ma sake juyi da tayi akan katifar ta. Zuwa tai ta daki ƙafafuwan Farhan, "ke dan ƙaniyar ki magana nake miki fa, ba zaki ta shi ba" Cikin maye Farhan ta fara magana "Wai..wai..... Meeee zan miki ne?kiiiiiii ƙyaleni ba na son in buɗe ido na...hmmmmmm... wai ba kya ganin gini ne ze faɗo a kaina?" Buɗe baki Adda Hafsatu tai tace "Na shiga uku ni Hafsatu, Farhan me ya sameki haka? Me kike yi haka Farhan?" "Ni,ni,niiii dalla ki rabu da ni, ba na son kowa ya zo gurina dan Allah" Cikin azama Adda ta fita waje, ta janyo Umman Farhan gefe tace "kin san halin da 'yar ki kuwa take ciki?" "Kamar yaya?" "Wallahi gani nai kamar tana maye, amma zo muje ki gani" A tare suka shiga ɗakin Farhan, suka tarar da ita kamar Mahaukaciya, duk ta ware gyaran gashin nan, gashin na ta ya hargitse gaba ɗaya. Ta na zaune ya jingina jikinta a bango, ta lumshe idanunta. Umma tace "Ke! Menene haka?" Farhan tai shiru ba ta motsa ba. Umma ta zo, ta kai hannu ta taɓa Farhan. Farhan ta bige hannun Umma tace "Ni,niiiii..... Kar ki sake taɓa ni......tun da kin tsane ni.. ba na son ganinki, ki tafi ki bar nii" "Innalillahi wa innalillahi raji'un, ke me kika sha haka? Me zan gani, maue fa take Hafsatu" "Nima abunda na gani kenan, da ma ta na shaye shaye ne?'" Umma cikin tashin hankali tace "Ni ina na sani? Idan ma yin take saboda tsabar wulaƙanci ta rasa lokacin da za ta sha abun maye, se lokacin aurenta, mutsne sun cika gida, dan ta kunyata ni, tana mace za tai shaye shaye, wannan wace irin yarinya ce, da ma fa nema take ta lalace, Yaron nan ya sha kawo ƙarar ya ganta cikin mota ana kawota, mahaifinta ya ƙi yadda, ji wannan abun kunya ina zan sa kaina, mace da shaye shaye?" Umma tai maganar cikin rauni. Adda Hafsatu tace "da ma abunda ake jiye muku kenan, shiyasa muka damu a aurar da ita, ka aura da 'yar tun tana ƙarama ba ta san komai ba, shine rufin Asiri da kwanciyar hankali, amma kuka ƙi, wai ku se tai boko, ga sakamakon bokon nan ai" "Innalillahi wa innalillahi raji'un, yanzu meye abun yi?" Farhan ta kalli Ummanta, idanunta jawur, cikin maye amma ta tsurawa Umma ido Sannan ta fara Magana "Meyasa......ki ka tsane ni? Meee nai miki...... Ni bana son Auren nan, ba na son ammma kika dage, ni ki tashi ki tafi, ko in kashe kaina, zuciyata zata buga......damuwa tai min yawa ku ƙyaleniii......" Farhan ta ƙarasa maganar cikin ƙaraji, tare da ƙwala ihu, tana mimmiƙewa. Har se da hankalin mutane ya so ya kai gurin. Cikin azama Umma ta miƙe jikinta na tsuma, cike da tsoro da fargaba. Ita dai a iya saninta Farhan ko ytsa ka sa mata a baki, ba lallai ta iya taunawa, amma ita ce ke wannan ƙarajin take mata tsawa. Adda Hafsatu tace "Maryamu, wannan ba maye bane, Farhana Aljanu ne da ita wallahi, kinga muje waje maza, a samo mukulli a rufeta a ɗaki, wallahi iskokai ne, zata iya mana duka a ɗakin nan, rufe ta a ɗakin a jira zuwa lokacin da iyayenta zasu dawo daga gurin ɗaurin Aure, a ji me za su ce" Cikin damuwa Umma tace "abun ya bani mamaki, ni na kasa gane kan wannan lamari, kuma aljanun ne se Ranar ɗaurin Aure?" "Kin ga ni ban hanya in wuce, ba ki ji suna cewa ba sa son Auren ba, shiyasa sam ba ya walwala tun da aka fara shirin bikin nan, ashe ba ita kaɗai ba ce, ni ban hanya kan ta haɗa min jikina a safiyar nan, dama ni ba ƙwari na cika ba" Haka suka fito suka kulle Farhan a ɗakin, ita kuwa Farhan sam ba ta san a zahiri tai wa Ummanta tsawa ba, zaton ta a mafarki komai ke faruwa! Mutaina ta shigowa suna tambayar ina Amarya, se ace musu ai bata da lafiya, da yake a can Babban masallacin juma'a da ke unguwar su Farhan za a ɗaura aure, duk danginsu maza, sun tafi can. Sadik kam yau, ba da iya takaicin Abun da Nana tai masa ya tashi ba, har da wata irin damuwa, da tsananin fargaba da ya ta shi da ita, wadda be san dalilin hakan ba. Wata irin faɗuwar gaba yake ta fama da ita, haɗi da Zullumi, yai iya ƙoƙarin sa dan ya gano, meke sa shi wannan fargabar da zullumin amma ya ka sa tuna Komai. Yana jin Nana ta fita ta tafi makaranta, amma ya na ɗakinsa be fito ba, dan ko makaranta ma ƙin zuwa yai, yai kwanciyar sa a ɗaki, yana jin yadda zuciyar sa ke ta bugawa da ƙarfin gaske. Tunani yai kowane abune yake faruwa a gida, ya miƙa hannu ya ɗakko wayarsa, ya kira layin Mother. Se da ta kusa tsinkewa sannan ta ɗaga tace "Sadik lafiya kake kirana a wannan safiyar haka?" Yace "kune a nan safiya, amma mu a nan ai rana ta yi, barka da safiya" "Yawwa, kana lafiya?" "Eh, lafiya ƙalau Alhamdilillah" Mother tace "be lectures ne, ka kirani yanzu?" "Banje makaranta ba yau" "Saboda me?" Ta tambaya cike da kulawa. Yace "bana jin daɗin jikina ne gaba ɗaya" Mother tace "Yasalam, ina fatan dai ka je Asibiti, dan na san halinka, ba ka son magani" Yai ajiyar zuciya yace "ai ba wani abun damuwa bane zan ware Insha Allah" Mother tace "A'a, babban ciwo da ƙarami yake faraws, kaje ka ga likita yafi" Yace "to shikenan, insha Allah zan je ina Abba?" '"Abbanku yana gurin aiki, ba ya gari" "Ok, hakane na manta ne, ina Dr. Da Matarsa?" "Duk suna nan lafiya ƙalau Alhamdilillah" "Ba bu dai wata matsala ko?" Mother tace "kai Sadik, ba wata matsala fa" Yace "to shikenan, amma naji kimce Abba ya koma aiki, ya jikin Hakimin, za'a kai shi jamus ɗin kuwa?" Mother tace "eh to, ka san halinsa, ya ɗan samu sauƙi gaskiya, yace ba in da za shi, yaje a sake wahala da shi, a barshi ya mutu a ƙasarsa a binne shi cikin salama, ba se an kai shi ya mutu a can, a wahalar da gawarsa ba" Sadik yace "Allah sarki, cuta ai ba mutuwa bace, Allah ya ƙara sauƙi" Ta amsa masa da Ameen, da ga nan suka ɗan taɓa hira, sannan su kai sallama. Still dai ya ji be samu nutsuwa ba, se da ya kira Abba a waya, nan ma ya dinga tambayar Abba Komai lafiya? Abba ya tabattar masa da komai lafiya, sedai su cigaba da yiwa Hakimi Addu'ar samun lafiya a gurin Allah. Haka Sadik ya dinga bi yana kiran waya, yana jin lafiyar 'yan uwansa, da kowa da kowa, amma be ji ance masa ga wata matsala, haka ya haƙura ya ajiye Wayar, ya cigaba da zancen zuci shikaɗai. Tun kan mutane su gama taruwa a wajen ɗaurin Aure, Malam Zakari ya hallara, yana jiran zuwan Magabatan Sunusi, dan ya fuskanci alamu sun nuna kamar ba su da dattako ko kaɗan. Da suka iso gari ma, ba su wuce ko ina ba, se gurin ɗaurin Aure matan ne suka tafi gidan malam Labaran, aka sauke su a can, mazan kuma suka hallara a masallaci. Sanin sanyin hali irin na Abban Farhan, ya sa Malam Zakari tsayawa bil haƙƙi, dan ganin ba a ƙwari Farhan ba. Bayan an gama gaisawa, ana jira mutane su ƙarasa zuwa, lokaci ya cika afara ɗaurin Aure, a gaban Liman Malam Zakari ya kalli Sunusi da ahalinsa yace "Bayin Allah, ina alƙawarin da mu kai da ku?" Wani kawun Sunusi yace "Wane alƙawarin kuma?" "Eh, ai shi malamin da yaron sun sani, na farko ba ku gaya mana in da za'a ajiye mana Yarinya ba, sannan abu na gaba kamar yadda na gaya muku, mu a nan ba a ɗaura Aure, se an kawo sakamakon gwaji Sannan ake ɗaura Aure". Ƙanin baban Sunusi yace "Ikon Allah, to ai batun in ds Yarinya zata zauna, anyi wannan maganar in da za ta zauna, ai can garin su yaron ne wato Sunusi, sannan ni ban san wani batun gwajin Asibiti ba, tun da mu a ƙauye ba a yi, amma kai Sunusi ya abun yake ne?" Malam Zakari yace "eh ai shi ya san yadda mu kai da shi, be muku bayani ba dama?" Sunusi yace "Nifa gaskiya ba ni da halin da zan wani kama mata gida a garin nan, dama a garin mu za ta zauna, nikuma ina nan ina ɗan buge buge na ina aikata mata, amma ai an san bani da ƙarfi, tunda ba kaina zan siyar in kama nata gida ba" A nan 'yan uwan Farhan suka fara jinjina Wannan lamari, sam Sunusi ba shi da ɗa'a, se wani Magana yake cikin gadara ba wani girmamawa. Shi kansa Abban Farhan, be taɓa zaton haka Sunusi yake ba. Liman ya kalli Sunusi da magabantasa yace "bayin Allah, ai ko a karkara ilimi ya wadata, ana gwaji kan Aure, dan haka mu a nan ba ma ɗaura Aure se an kawo mana sakamakon gwaji, idan ba bu kuma zakuje se an kawo sannan zan ɗaura Aure" Malam Zakari yace "kuma, ba zamu bada 'yar mu a kai mana karkara ba, muna nan akan bakanmu, aka ma wa yarinya gida a birni, saboda karatun ta" Liman yace "Malam Zakari, ai batun zama a ƙauye ko a birni, ba shi a cikin sharaɗin Aure". Malam Zakari yace "duk da haka Allah gafarta malam, mu bamu gamsu da in da za'a kai mana Yarinya a ajiye ba, kuma shi angon ya san akan wannan sharaɗin muke" Mutane sun gama taruwa, dan har sun fara ƙosawa, a ɗaura aure abu ya gagara, ga rana ta ɗaga Sosai. Liman yace "to ku, kunji abunda iyayen wannan amarya suka ce me zaku ce, Sannan ya batun gwajin? A ɗaga ɗaurin Auren kuje ku yo gwajin ku dawo ne, ko zuwa in Allah ya kaimu la'asar se a ɗaura?" Malam Labaran yace "to, ni Allah gafarta malam, wai me ye amfanin gwajin nan ne? Me za'a gani a gwajin?" Liman yace "Yawwa, abunda ya kamata dama ku tambaya a wayar muku da kai kenan, idan ba ku sani ba. Shi wannan gwajin yana da mahimmanci ƙwarai da gaske, duba da yanayin cututtukan ƙarshen Zamanin nan da su kai yawa, akwai nau'in cututtukan da idan ɗaya daga cikin ma'aurata yana da shi ɗaya ba shi da shi, to ɗaya ze shafawa ɗaya. Ko kuma, akwai kuma wanda idan suna ɗauke da wani nau'in jini, ba ze yuwu suyi Aure ba, saboda za su iya samun yara marasa lafiya, masu ɗauke da ciwon sickler wato Amosanin jini. Idan aka kawo mana gwajin muna Duba, rukunin jinin ze yuwu ma'auratan suyi Aure, ba tare da sun haifi yaro me larurar sickler ba. Muna duba ciwon hanta, tun da shima likitoci ance ciwo ne da ake ɗauka, amma shi ba a fiye damuwa da duba shi ba kamar yadda muke duba ciwon ƙanjamau, wannan shine mafi hatsari ma, tun da shi ciwon hanta ana warkewa, ƙanjamau kuwa ba a warkewa, ka ga kuwa gwaje gwajen duk suna da mahimmanci, dan tabattar da babu wanda aka cuta a lamarin". Sunusi yace "ni lafiyata ƙalau, babu wani gwajin da zan yi, kawai an shigo da yahudanci cikin lamarin Aure, duk dan salon barin abunda addini ya ɗora mu a kai, ai idan ma cuta ce sedai a samu a jikinta ba ni ba, dama ai jihadi zan in Aureta, babu wanda be san yawo take ba. Maza ne ka ɗaukarta suna yawo da ita a mota, saboda shegen son abun duniya. Ranar a gabana suka shiga gida ita da wani, sunfi mintuna arba'in sannan suka fito, kuma a gaban mutane suka fito, dan se da na kira shedu suka gani, ita ba a samu ciwon a jikinta ba se ni za a samu a jikina, na ga ai temaka mata zanyi, da an san ba za a bani yarinyar nan ba se an gama wulaƙanta ni, meyasa aka ce za a bani, ko da ma can ƙaƙaba min za ai an san ba ta da lafiya, ta gama yawon banzanta, shine za a zo ana min burga, kamar tainaka min za ai" Da ƙarfi Sunusi yake magana ba a hankali ba a hankali ba, hakan ya janyo hankalin mutane da suke gurin,  kai tsit ana sauraren sa, Abba yai shiru ya rasa abunda yake masa daɗi. Malam Zakari yace "sadaƙallahul azeem, dama in da muke jira a zo kenan, mu ga gwajin 'yar mu a hannun mu, ba ta da ciwon Komai, lafiyarta ƙalau, kai kuma kaje sharrin da kaiwa 'yar mu mun barka da Allah, duk unguwar nan ba wanda be san tarbiyyar da yaranmu ke da ita ba, wanda har ake son haɗa zuriya da mu" Malam Labaran yace "A'a Malam Zakari, ai ba a shedar ɗan yau, ta idonka daban, ta bayan idonka daban, amma duk da haka, nasan Sunusi be kyauta ba, haka yake da zafin zuciya idan ransa ya ɓaci, amma mutumin kirki ne, ina nan ina masa rubutun samun sanyin zuciya. Ayi haƙuri dan Allah, yanzu dai zamu je ayo gwajin a kawo, se a ɗaura Auren" Sunusi yace "gaskiya ni Malam, ba in da za ni, ba wani gwaji da zan, in sunga za su bani a haka su bani" "Wai Sunus ba ka da hankali ne? Ya ana ƙoƙarin saita lamura, kai kuma ka na sake ɓata lamarin" Malam Zakari yace "ba zamu bawa mara mutunci, wanda be san darajar kansa 'ya ba, Allah ya ha ɗa kowa da rabonsa" Abba yace "A'a, ɗan uwa babu yadda za'ai a gyara lamarin nan? Ka ga fa mun tara jama'a" "Dan dai jama'a, bakoma sa watse Allah ya haɗa kowa da rabonsa, dama yarinyar ba wani girma ne da ita ba, a kunnen ka ya gama ci mana mutunci, da aibata mana 'ya yaiwa kansa, tun da be san abun arziki ba" Sunusi ya sake tinzira, ya dinga bala'i yana cigaba da aibata Farhan, a gaban al'ummar da suka zo dan halartar ɗaurin Auren. Umma ta na cikin matuƙar zullumin halin da Farhan ke ciki, gashi tun sha ɗaya aka  ce za'a ɗaura Aure, amma har ɗaya saura shiru ba su dawo ba, ga mutane sun cika gida, babu Amarya babu dalilin ta ta na can ta na fama, ba ta san in da knata yake ba, gashi angwaye shiru suma babu su ba bu dalilin su. Huzaifa ne yai sallama ya shigo, cikin faran shadda, Babbar rigarsa riƙe a hannunsa. Umma na ganinsa tace "Huzaifa yaya, ina su baban naku an ɗaur ne?" Hauzaifa yai dariya yace "aka ɗaura me? Ai an fasa Aure" Tace "kamar yaya, kai bana son shashanci fa" Yace "wallahi dagaske nake an fasa ɗaura Auren" Umma ta janyo Huzaifa gefe tace "ka gayamin tsakani da Allah, ka san ba na wasa da kai ko?" Yace "wallahi Umma ba ƙarya na ke gaya miki ba, an fasa ɗaurin Auren nan" "Huzaifa ko dai za'a ɗaura an jima?" "Wallahi Umma fasawa a kai" "Amma saboda me?" Huzaifa yace "Nima ban sani ba, se dai in su Abban sun dawo" Please manage, bana jin daɗi ne. Littafin nan ₦300 ne kacal. 0009450228 Aisha Adam Jaiz Bank 07063065680 KO kuje manhajar AREWA BOOKS ku siya. domin kuwa ya fi sauƙi ta can. Not Edited! Sam Huzaifa ya ƙi gayawa Umma dalilin da ya sa aka fasa auren Farhan, gaba ɗaya hankalinta ya tashi, ga gida a cike da mutane. Ana haka se ga su Abba sun dawo, Abba ji yake tamkar ƙasa ta tsage ya shige saboda kunya, ya rasa da wani ido ze dubi wannan al'ummar da su ka tara, ga mutane har an fara ƙananun surutai, saboda yadda Sunusi ya dinga miyagun maganganu akan Farhan, wajen ɗaurin Aure. Wasu daga mutane suka goyi bayansa, cewar suma sun sha gani ana sauketa a mota, kuma falla fallan motoci na alfarma. Ya yin da wasu suke ƙaryata abun da Sunusin ya faɗa, suna yabon halayen Farhan, ɗin na tarbiyya da girmama mutane. Su Abba na dawowa, Abba ya wuce ɗakinsa, dan baze iya haɗa ido da mutane ba. Ba kunya Malam Zakari yai musu bayanin cewar an samu mishkila, da haka an fasa wannan biki, abinci da aka dafa, kowa yaci sadaka, Allah ya zaɓawa yarinya Mafi Alkhairi. Nan aka shiga salati da salallami, gashi Malam Zakari mutum ne me kwarjini, dan haka aka rasa wanda ze tunkare shi ya tambaye shi dalilin hakan. Dangin Umman Farhan, sukai kanta da tambayoyi "Maryamu dan me za'a fasa Auren nan? A tara wannan jama'a haka kuma ace an fasa, lallai ku mutan birni ba kwa gudun abun Kunya, mu dai kin san da a garinmu ne, ba za'ai haka ba, mu zuriyar mu ba a taɓa wannan abun kunya ba , se akanki da 'yar ki. Yo koma mene ya faru ai ba a fasa biki ba, a rufa a ɗaura Aure haka nan, amma kawai ace an fasa" Sosai Umma take kuka, dan ba ta da amsar da zata kare kanta da shi a gurin 'yan uwanta. Malam Zakari ya shigo yana ƙwalawa Umma kira, Umma ta fito ido duk hawaye. Yace "ai ba kuka yakamata ki ba, ki gode Allah da Allah be sa an bawa wannan shashashan auren 'ya ba, ina ita Farhan ɗin take? Ta zo muna son ganinta ni da babanta" Umma ta goge hawaye tace "ta na can a ɗaki, ni ban san abinda ya sameta ba, amma malam meyasa aka fasa auren nan mun tara mutane?" "Kinga kar ki damu, da wata wahalar gara wata, yaron nan mutumin banza ne mara ɗa'a, muje ina yarinyar take" Umma na sheshsheƙar kuka, ta wuce gaba ta buɗe masa in da Farhan take. Ana buɗe ɗakin, ta zabura ta shige cancikin saƙo, ta takure kanta sosai. Malam Zakari ya ƙarasa shiga ɗakin yana faɗin "Subhanallah, Farhan lafiya kuwa?" Farhan ta ɗago jajayen idanunta, ta sauke akan Malam Zakari, wanda tuni idanun na ta suka juye, kamar harare garke. "Meke damunki?" "Ni..Ni ku ƙyaleni dan Allah, du...duuuk ku fita ku barni, ba na son ginin nan ya faɗo mana a ka..... Allah ya sa ma dai, ya faɗo mana a ka, kowa ya huta" Malam Zakari yace "Innalillahi wa innalillahi raji'un, me Yarinyar nan take haka kamar maye?" Umma cikin kuka tace "Nima ban sani ba, na kasa gane kan wannan lamari" Gida kam tuni labari ya ba zu, ya cika unguwa cewar an fasa wannan biki. Sunusi kuwa se da ya ga da gaske, an fasa wannan Aure sannan ya shiga hankalinsa. Yace wa malaminsu "Malam dan Allah aje a basu haƙuri, ina son Yarinyar nan Sosai wallahi" Malam Labaran yace "wallahi ba zani ba , lokacin da nake kwaɓarka akan maganganun da kake ai ba ka saurareni ba, kai ga ka kuturu Sarkin zuciya, ba irin halaccin da iyayen yarinya nan ba su maka ba, amma ka rufe ido ka dinga rashin mutunci kana ciwa 'yar su mutunci, ba dani ba ba in da zanje" Haladu yace "Sunusi ba tun tau ba, na sha ba ka shawarar ka rage wannan saurin fushin, amma ka ƙi gashi nan a banza ka janyo kan ka,da tuni Allah ya rufa maka asiri,kai wuf da zuƙieƙiyar Yarinyar nan, amma baƙar zuciya da taurin kai ya janyo maka.meye a ciki dan ace ka je kai gwaji, in da kasan ka na da gaskiya ai ba abun damuwa ba ne, kuma kamar yadda suka faɗa, 'yar su ba kalar ƙauye bace, ba zata iya wannan wahalar ta ƙauye ba, ka na da kuɗi ka kama mata gida ka ƙi, gashi nan kaiwa kan ka, sedai nan gaba ka ga wani yana morarta, dan kai dai ta maka nisa wallahi" Sunusi yace "inji uban wa, wallahi yadda ban Aura na mora ba, ba bu me mora, sedai kowa ya rasa, za su gani ai" "Za su ga me? Ka ga Sunusi ka ƙyale mu su 'ya ta huta" "Wallahi Haladu ba me hutawa, yadda aka hana ni Aurenta haka za su zauna da ita, dan ba zan bari kowa ya aureta ba, na dinga ɓata lamura kenan, har se sun gaji sun bani mata ta" "Amma kuwa ba ka da imani, ba ka da mutunci duk halaccin da su kai maka?" Tsaki Sunusi yai yace zuba ido ka ga. Nana ta dawo daga makaranta, ta tarar da Sadik a gida, sedai a fuskar sa kawai ta lura kamar wani abu na damunsa, ko dai duk saboda laifin da nai masa ne? Ta tambayi kanta. Sallama tai, ya amsa ba tare da ya kalleta ba. Tace "Friend na dawo" ba kulata ba balle yai mata sannu da zuwa,haka ta wuce ɗakinta. A ɗakin ta tarar da kayan siyayyar da sukai jiya a kanti, ba ta bi ta kan kayan ba, ta cire kayan jikin ta tai wanka tai sallar azahar, Sannan ta fito falo. Sadik yana nan a in da ta bar shi, take Kitchen ta ɗakko bredi, ta dafo tea ta dawo ta zauna. "Friend ka ci Abinci kuwa?" A wannan karon ma be tanka mata ba. A karo na biyu cikin damuwa tace "Dan Allah kayi haƙuri, na ga fushi kake da ni, dan Allah kayi haƙuri ba zan kuma ba" Miƙewa yai ya nufi ɗakinsa, ya bar mata falon, dan ya gaji da jin surutun  ta. Nana ta shiga damuwa sosai, saboda yadda ta ga gaba ɗaya ya canza, duk saboda abun da tai masa, ba ta zaci abunda tai ɗin ze sa Shi fushi haka ba. Har dare ba ya shiga harkarta, a ɗaki ya gama wuninsa ko fita be ba, kuma ba ta ga alamar ya ci Abinci ba, shi ko Sadii Bayan haushin Nana da yake ji, harda matsananciyar damuwa da be san dalilin ta ba. Nana harta fara shirin kwanciya, tai tunani a ranta tace "Ni, Nana idan ya kwana da yunwa duk laifi na ne, saboda ni na ɓata masa rai, amma ai nace yai haƙuri" sakkowa tai daga kan gadonta, ta saka hijjabi ta tafi ɗakin Sadik. Yana zaune akan gadonsa, yai tagumi da hannu ɗaya ya zubawa guri ɗaya ido ko ƙiftawa ba ya yi. Tai Sallama amma be amsa ba, kai tsaye ta tafi gabansa, ta durƙusa akan gwiwowinta tace "dan Allah dan Annabi Yaya Sadik kayi haƙuri, ba zan kuma ba, dan Allah ka dena jin haushi na" Shi mamaki ma ta ba shi, bil haƙƙi har ranta haƙuri take ba shi. Ya fuske yace "karki sake zuwa in da nake, ki rayuwar ki inyi tawa, haka kurum kika ɗagamin hankali na dinga nemanki, kuma dan baki da Kunya, kika dinga gayan magana, wai kin barni da mata inje in ta taɓa su ko?" Ta ɗan tura baki tace "kayi haƙuri, amma ai gaskiya na faɗa maka, se ka je kai ta taɓa mata, alhalin kuma ka san ba kyau, kuma ni haushi nake ji" Be san lokacin da yai murmushi ba yace "to meyasa kike jin haushin?" "Bana son a rubuta maka zunubi, Allah ya kamaka" "Hakane, kina sona kenan?" Da Sauri ta ɗago kai tace "taɓ a'a wlh" "To ai kishi na kike" "Meye kishin?" Ta tambaye shi ta na tsare shi da ido" Sadik yace "shikenan, tun da ba ki san meye ba, yanzu ke dai burinki in dena taɓa mata ko?" Ta jinjina masa kai da confidence ɗin ta. Yace "shikenan, ɗakkon wayata akan mirror" Ba tunanin komai, ta ɗakko ta kawo masa, tana miƙo masa ya sa hannu ya riƙota, ya Ajiye wayar a gefe, cikin zafin nama ya cire hijjabin jikinta,ya kwantar da ita akan pillow, ya ɗora kansa akan ƙirjinta. Tsoro ya baibaye Nana, tace "Sadik meye haka? Dan Allah ka bari" Hankali kwance Sadik yace "ai kince in dena taɓa mata ba kya so, ni kuma ba zan iya rayuwa ba tare da nayi hakan ba, kinga se ki maye min gurbinsu" Cikin rawar murya, da janyo numfashi Nana tace "Wallahi babu kyau, Inna ta hana ni, wallahi tace idan na bari namiji yana taɓani zan lalace, dan Allah ka ɗagani, naji ka cigaba da taɓa matan" Yai murmushi, tare da saka hannunsa akan cikinta yace "so kike a rubutan zunubin taɓa mata?" Tana kuka tace "Au so kake a rubuta mana tare ni da kai shiyasa kake taɓa ni, wallahi idan Inna ta san abunda nake kenan, za tai fushi da ni Sosai" Hawaye take Sosai, Kamar wadda za'a yanka, Sadik yai banza da ita, ya sake kwanciya sosai a jikinta, a hankali yaji yana samun sauƙin wannan damuwar da ke ta ɗawainiya da shi tun safe. Se da jikin Nana yai laƙwas, bakinta ya mutu, ajiyar zuciya take tana jujjuya ido. A hankali ya ɗaga ta, ya nufi banɗaki, tana ganin ya shige toilet, ta miƙe ta sakko daga kan gadon tai waje, sedai taji gaba ɗaya jikinta ya mutu, se mita take da ƙananan maganganu ƙasa ƙasa. A can gidan su Farhan kuwa, Farhan ce zaune tai shiruu, duk da haryanzu a cikin maye take, amma ta na iya fuskantar abubuwan da ke faruwa, sedai ta kasa gane hakane a zahiri, an fasa Aurenta da Sunusi ko kuma mafarki take. Gefe ga Umma na ta uban kuka, kamar ance mata Farhan ce ta mutu, a ganinta dalilin da ya sa aka fasa Auren, ba wani dalili ne da ya taka kara ya karya ba. Abba kam ya rasa abunda yake masa daɗi, dan tabbas Farhan maye take a wannan lokacin. Malam Zakari yace "Umman Farhan, haƙuri za kiyi, duk abunda kika ga ya samu bawa to yana rubuce a cikin kundin ƙaddararsa ne, ki sa a ranki, da ma Allah be ƙaddara mijinta bane" Cikin kuka Umma tace "Baban Huzaifa, kamar ni ka ɗai na taɓa haihuwar 'ya a rayuwa ta, daga wannan se wannan, yarinyar nan duk wani salo da za ta janyo min abun kunya, da abun faɗa ta sanshi, kuma za ta aikata. Kalli fa maye take Ranar ɗaurin Aurenta, kuma Sunusi ba ƙarya yai ba, na kamata da wayar da saurayi ya bata, zamanta a gidan miji ba shi yafi Alkhairi ba, yanzu ta samu lasisin aikata abun da ta ga dama, na rasa wannan wace irin kangararriyar yarinya ce!" Kalmar kangararriyar yarinya ta daki zuciyar Farhan, fiye da kima, ta ɗaga jajayen idanunta ta kalli Ummanta, yau ita Umman take dangantawa da kangararriyar yarinya, tabbas ko da ace mafarki take abubuwan nan da suke faruwa, har ta koma ga Allah ba zata manta wannan kalma ba. "Ashsha, ya kike kamanta 'yar da kika haifa da kangarewa, duk biyayyar da Yarinyar nan take da shi, dan an samu wannan akasin se ki danganta ta da kangara? Kin san meye kangarewa kuwa? Kar ki sake wannan kuskuren, da kika ganta da wayar saurayi wane mataki kika ɗauka? Dan Allah kar wannan abun ya sa ku yiwa Yarinyar nan baki, dan yarinya ce me biyayya a baya, kamata yayi aji meyasa tai shaye shaye, garin yaya a kai ta rasa lokacin da zata sha wani abu se ranar ɗaurin Aurenta, ni anya ma kuwa tana son Yaron nan?" Daga Abba har Umma ba wanda yave uffan, se ma Umma da tace "shikenan, tun da haka ta zaɓawa kanta, taje ta ƙarata, ga gidan nan ta zo tai ta zama muna jerawa, tana kallona ina kallonta, ai duniya makaranta ce" Umma ta tashi fuuu ta bar ɗakin, Abba ma bece komai ba ya tashi ya bar ɗakin, haka kowa ya fice aka bar Farhan. 'yan biki duk aka watse, ana ta gulmar ashe ma Yarinyar lalatacciya ce, bin maza take ga shaye shaye tana yi. Lamarin ba ƙaramin dukan Hajiyar Abbas yai ba, ta yi mamakin yadda aka ce wai Farhan tana shaye shaye, da yake ran ɗaurin Auren ba ta gari, se da yamma ta dawo, kan ta shirya ta shiga gidan su Farhan, har gida aka sameta aka bata labarin abunda ya faru, da yadda aka fasa Auren Farhan ɗin. Ita kanta Hajiya, ta lura da yadda Farhan ke cikin damuwa, amma iyayenta ba su maida kai, dan gano meye damuwar ta ta ba, su dai kawai su mata Aure, dan haka dama dole ta nemawa kanta mafita, wannan abun dama Abbas yake ta ji, masu irin halin Farhan in damuwa tai musu yawa, a ƙarshe dole su nemawa kan su mafita. Baƙinciki ya hana Hajiya ko zuwa gidan su Farhan, ta sha takaicin yadda sunan Farhan ya ɓaci, gaba ɗaya unguwa ta ɗauka, an innocent kid like this, gashi mutane ba sa wa kansu adalci, suna hukunci ne da iya abinda idonsu ya gane musu. Tabbas, ba dan abun ya zo a ƙurarraen lokaci ba, kuma ba tattauna da dangin baban su Abbas ba, da ba abunda ze hana tace a ɗaura da Abbas, dan ba ta yanke hukunci akansu se da sanin dangin mahaifinsu, saboda a tsaye suke a kansu. Nana ko haɗuwa taƙi yadda suyi da Sadik, suka koma wasan 'yar ɓuya, da ta ji motsinsa a falo, ba zata fito ba. Jin shiru ya sa ta ɗauka ya fita, yana kallonta ta window ɗakinsa, tan sanɗa, ta shiga Kitchen. Se da ya bari an ɗau lokaci da shigarta, ta sakankance, sannan ya fito ya risketa a Kitchen ɗin. Tana ganinsa ta hau ƙwalala ido, ya shiga takowa a hankali, tana ja da baya har suka ƙure bango, ya kalleta yace "Yau ni zan gyara ɗakin nawa?" Ta tura baki tace "zan gyara, amma se anjima" "Wace anjima kuma? Azahar ce fa Yanzu, tun safe yakamata ki gyaramin ai. Amm an gayyacemu cin Abinci da yamma" Nana ta kalleshi tace "Ni gaskiya ba zani ba" Yai ƙasa da murya yace "idan naje ni kaɗai gaskiya zan taɓa mata" Tace "Allah yana kallonka" Yai murmushi ya sunkuyo daidai da tsawonta, ya sa hancinsa a wuyanta, seda ta saki ludayin da ke hannunta, ta ƙanƙame jikinta, tana jin wani abu da ba ta san menene ba. Sadik yana kallon reaction ɗin ta, yace "Mijinki yaro da shi, amma se....." Se kuma yai shiru yana wani miskilin murmushi. "Abincin ze ƙone fa" ta faɗa a daƙile. Shiru yai bece komai ba, ji tai abun nasa yana zarce hankalinta, ta dage iya ƙarfinta ta kurma ihu, a gigice ya cikata yace "meye haka?" "Wallahi ni ba 'yar iska ba ce, da zaka dinga min irin wannan abubuwan' Tsaki yai a ransa yace "wannan kwantacciyar Yarinyar ba ta san abunda ya halatta a aure ba ne?" A fili yace "karki wuce ƙarfe huɗu ba ki shirya ba, idan ba haka na tafi ba zan dawo ba se gobe in Allah ya kaimu" Ita Nana dan ya tafi ya kwana ba damuwar ta bace, dan yanzu ta saba da zaman kaɗaici, jin yace idan yaje ze taɓa mata ne ya sa ta ƙuduri se ta bishi. Ƙarfe huɗu ta shirya suka fita, wani katafaren gurin cin Abinci sukaje, gurin ya haɗu Sosai da sosai. Wani ɗaki ya ja Nana suka nufa, a nan ta tarar da Abokansa da suka taɓa zuwa gidan su, nan suka shiga gaisawa, abun takaici har da Matam duk se da Sadik ya bi ya gaisa da su. Nana se hararsa take, amma yaƙi ko kallonta. Nan wasu suke tambayar sa, wannan me aikin ta sa ce, yace tsokanar ta yake Ranar, amma ƙanwarsa ce, suka miƙawa Nana hannu dan su yi musabuha, aikuwa ta miƙa wa wanda ya miƙo mata hannu suka gaisa, na biyun ma har ta kai hannu za su gaisa, Sadik ya sa nasa hannun ya kalleta cikin masifa yace "ba ki da hankali ne? Da auren naki kike gaisawa da maza?" "Kai ma da Aurenka kake gaisawa da mata?" Tai maganar tana murguɗa baki. "To ni da ke ɗaya ne?" "Eh mana, da biyu ne, kai kake cemin 'yar ƙauye ai, gara in abunda zan waye" Sadik ba ya son su raba abun faɗa a cikin jama'a, dan haka ya ƙyaleta, ya ƙwafeta  a ransa. Suka dinga yaba kyan Nana, suna cewa tana da kyau, har wani abokin Sadik yana cewa, akwai yiwuwar in ya tashi Aure, ya zo Nigeria ya samu mata, dan ace suna da Black beauties kamar Nana. Sadik kasa cin Abincin yai saboda takaici, Itama Nana ba ta saba da cin abinci a gaban mutane ba, dan haka ta kasa sakewa ta ci. "Ke tashi mu tafi" y faɗa a kausashe. "Ni gaskiya ba zan tafi yanzu ba, daga zuwanmu se tafiya" "Wallahi se kin tashi, tun da baki da man kai, tsabar rashin mutunci kike gaisawa da mazs, a gabana shashasha kawai" "Ikon Allah, na ga kai ka fara yi ai, kuma gaisawa ce fa kawai, ai kai na gani kina yi" "Za ki min shiri, ko se na ɓarar da kanki a nan gurin?" Wata yarinya ce a cikin su ta ke tambayar su lafiya kuwa?. Sadik yace lafiya ƙalau, tafiya za suyu. Nan suka shiga tambayar meyasa za su tafi yanzu. Sadik yace wani uzuri ne da shi a gida, dan haka za su tafi. Mussaman saboda nasarar da Sadik ya samu suka shirya wannan cin abinci, amma Sadik yace tafiya ze yi. Suna tafe a hanya yana wa Nana masifa kamar ze maketa, ita kuma se ƙunƙuni take, ta na harare harare. Abubuwa fa sun ƙara damalmalewa Farhan, dan ba cinya ba ƙafar baya, dan a maimakon fasa Aurenta da Sunusi ya sata a farinciki, sema sake shiga cikin wata damuwar da tai. Dan bayan ƙwayar ta saketa, ta gane duk abubuwan da suka faru gaske ne, Abba ya dena shiga harkarta gaba ɗaya, yai watsi da ita, dama Umma ba a magana, ta tattara Farhan ta watsar ko kallon in da take Umma ba ta yi. Ga mutane da suke ta shigowa, wai yiwa Umma jaje da yawa ba jajen ne ke kawo su ba, zunzurutun gulma ce ke kawo su. Haka a waje ma, Abba tararsa ake da maganganu daban daban, wasu na masa jaje wasu kuma na gulma, nan fa abun duniya ya kuma tsayewa Farhan, kullum cikin wunin ɗaki take, in ta fito banɗaki za taje. Abun duniya ya sake sakota a gaba, ta rasa abunda yake mata daɗi, har ɗaki taje ta samu Abba ta durƙusa akan gwiwowinta tace "Abba, dan Allah dan Annabi kayi haƙuri, nasan nayi kuskure amma ku yafemin dan Allah" "A'a Farhan, karki sake cewa kuskure, ganganci dai da son zuciya, Farhan 'ya'ya na maza ba suyi shaye shaye ba, ki barni inji da alhinin abunda ya sameki, na fasa Aurenki, amma dan ki kunya tani a idon duniya, Ranar ɗaurin Auren ki ita ce zaki sha abun maye?" "Abba, maganin ciwon kai na siyo, ban san abun maye bane wallahi, na zaci maganin ciwon ka ne kawai, dan Allah Abba ka yafe min" Abba yace "Ai dama bance miki komai ba, tashi kije" Jiki a sanyaye Farhan ta bar ɗakin Abba, tana zubda hawaye, tana kallon yadda Umma ke wurga mata wani irin mugun kallo, amma Farhan ta sunkuyar da kanta ƙasa, ta wuce ɗakinta. Sedai fa maganin nan da ta sha, ta ji sauƙin nauyin da kanta ke mata, ta ɗorawa kanta laifi ne saboda rabi aka ce ta sha, amma ta sha fiye da haka, sedai tunda maganin ya saketa, take jin kanta ya cigaba da nauyi, zuciyarta na mata wani irin zafi. Washegari da safe, Umma ta ga Farhan ta shiryo cikin Uniform, ta kalli Farhan tace "ina zaki?" "Umma makaranta zan koma" "Wallahi baki isa ba, bayan abun kunyar da kika janyo mana, ki wanke ƙafa kice zaki wata makaranta, me karatun naki ya amfana mana, kik biyewa saurayi ya hure miki kunne, kinyi kutungwilar da aka fasa Aurenki" Mamaki ya cika Farhan, meye laifinta a cikin fasa Aurenta da a kai, ita wace gudunmuwar ta bayar na fasa Auren. "Umma dan Allah ki barni in cigaba da zuwa makaranta" "Ba in da zaki, wuce ɗaki ki zauna, ke da ba ki ɗau abun kunya wani abu ba, ke da boko har gaban abada, wuce ɗaki, yadda kika samu a wannan halin na damuwa ke ma ba zaki ga da kyau ba, tun da kangarewa ki ka zaɓa ga ki ga duniyar nan" Da ƙyar Farhan ta cira ƙafa ta koma ɗaki, zuciyarta kamar tai bindiga, ita ka a rayuwar ta wane irin laifi taiwa Umma da ta tsane ta haka? Take jifanta da mummunar kalmar kangarewa. Nan zuciyarta ta shiga kai komo, da tsananin buƙatar nemawa kanta mafita. Nana kam bayan sun dawo ma faɗa suka cigaba ita da Sadik, ya dinga mata masifa akan cewar dan me za ta gaisa da maza. Tace "Ashe kai ma ka fara kishin nawa?" "Ubanwaye ze yi kishin na ki?" Tace "to in ba kishin ka ke ba, ina ruwanka da ni?" "Ni kike wa haka?" Yai maganar yana nuna kansa. Ta tura baki tace "to yadda ka ji ɗin nan, haka na ke ji idan na ga kana taɓa mata" Ƙwafa yai ya raɓata ze wuce, se kuma ta bishi da Sauri tana faɗin "Abokina dan Allah kayi haƙuri, wallahi nima ban ji daɗi abinda nai ba, se Astagfirullah nake, wallahi nayi ne dan ka ji abunda nake ji, amma ka yai haƙuri ba zan sake ba" "Kije ki cigaba, tunda abunda kike yi kenan a makaranta" Ta ƙwalalo ido tace "wallahi bana taɓa maza, ka ji na rantse maka, dan Allah kayi haƙuri" tai maganar a marairaice. Yace "Naji, jeki ki bani guri" ta ɗan zumɓura baki ta fita. Amma a ƙasan zuciyar sa sosai, yaji pain na gaisawar da Nana tai da abokinsa, amma ya danne dan ya san shima ba shi da gaskiya. Farhan ta na son Zuwa Makaranta sosai, dan zaman Gidan ba abunda yake sa mata se tsananin damuwa, da tsangwama da ga mahaifiyarta. Abba ta je ta kuma samu, akan Umma ta hanata zuwa Makaranta, yace bakomai ta shirya ta koma makaranta, Umma taji hasuhin hakan, amma ba yadda ta iya da su. Se dai yau ma da kanta taje neman maganin da Mubarak ya bata, Tasleem ta ce mata ita ma babu maganin agunta, kuma Mubarak yau be shigo makarantar ba, amma idan za ta iya, yau za'ai birthday ɗin Meena, a wani Hotel ta san babba ze je, taje se ta karɓa. Farhan kam, ba taji za ta iya zuwa Hotel ba, dan ba ta taɓa zuwa ba, sedai da aka tashi daga Makaranta, tana dosar gidansu, ta fara jin fargaba, saboda ta san ta dawo kurkuku, yanzu za ta cigaba da jin baƙaƙen maganganun Umma, damuwa kuma za ta sake baibaye ta! Gashi abun takaici, Ranar da ta fara fita, aka fara zunɗemta ana nuna ta da baki, akan abunda ya faru da ita. Nan fa ta shiga tunanin meyakamata tayi ne, shan maganin nan kawai shine mafita ga damuwar ta. Ta faki idon Umma tana banɗaki, ta ɗau hijjabin ta ta fice daga gidan. Littafin nan ₦300 ne kacal. 0009450228 Aisha Adam Jaiz Bank 07063065680 KO kuje manhajar AREWA BOOKS ku siya. domin kuwa ya fi sauƙi ta can. But Farhan ta fice daga gidan, se sauri take ta bar layinsu. "Hajiya Farhan ina za ki ne kike sauri?" Muryar da tafi tsana a rayuwarta taji ta daki dodon kunnenta, ta waiga ta kalli in da Sunusi ke tsaye yana ƙare mata kallo. Ƙwafa tai kawai tai gaba, dan ko ganinsa ba ta son yi, balle tuna wani abu ya taɓa haɗa ta da shi. Ta tari abun hawa, ta gaya masa in da ze kai ta. Suna tafe ta zubawa sabuwar dubu ɗayan da ke hannunta ido, Sadik ne ya bata ita, a ƙalla akwai kuɗi sun kai 20k a hannunta, wanda Sadik ya kan bata, kuma ya fututtuke yace se ta karɓa. A hankali ta ji hawaye masu ɗumi na bin idonta, har yanzu zuciyarta na begen Sadik, sedai ta dage da Addu'a Allah ya sa ta manta da shi a rayuwarta. Har gaban Hotel ɗin me abun hawan ya kai Farhan, ta sakko ta ba shi kuɗin sa, nan ta shiga rarraba ido, dan sam ba ta san in da za ta dosa ba. Tana nan tsaye jikin wata mota, tana waige waige "What are you looking for?" Taji wata murya ta daki dodon kunnenta, a hankali ta ɗaga idanunta ta ga me maganar. Matashi ne a ƙalla ze shekaru talatin da takwas, ya kuma cewa "wa kike nema ne?" Janye idonta tai da ga kansa, ta cigaba da jujjuya ƙwayar idonta, ko za ta hango su Tasleem. Yace "Ikon Allah, shikenan tun da ba za'a kulani ba, nace zan iya ɗaukar mota ta?" Yai maganar da sigar ladabi, ɗan kallon motar Farhan tai, Sannan ta ɗan yi jimmm, a hankali kuma ta janye jikinta daga jikin Motar, ta koma gefe. Matashin yai murmushi yace "Miskili kafi mahaukaci ban haushi, dan Allah ki min magana mana" yai maganar yana kallon Farhan da ga sama zuwa ƙasa. Ba tare da ta san in da zata nufa ba, tai gaba abunta ta bar shi a gurin, babban burinta be wuce ta ga su Babba, ta karɓi maganin nan ta koma gida ba, in ya so se taiwa Umma ƙaryar siyan magani ta fita. Wata zuƙeƙiyar mota ce ta shigo cikin hotel ɗin, Farhan ta ɗan tsaya motar ta wuce, amma taga Motar ta tsaya a Gabanta, sauke glass ɗin motar akai, ta hango Tasleem a ciki. "Laa Farhan, da ma zaki zo? Ya na ganki a nan?" Farhan tace "ban san in da ake taron bane, ban ga Mubarak ɗin ba" Tasleem tace "bari in sakko mu shiga tare. Farhan ta kalli mutumin da suke tare da Tasleem, har ga Allah Farhan ta ɗauka baban Tasleem ne, ta durƙusa tana gaishe shi. Amsa mata yai yana murmushi, yana binta da kallo kamar maye, ya gyara parking ya kalli Tasleem yace "Wannan sweet sixteen ɗin fa? Ya za'ayi?" Tasleem tace "Ai fa, ido a mata, to wannan dai ba ta san wannan harkar ba, kuma ta na da taurin kai, a hankali nake son na hilato ta" Yace "Subhanallah, Tasleem dan Allah ina son a riƙe mata wuta, ko nawa kike buƙata zan ba ki, wallahi tayi min ɗari bi sa ɗari gata 'yar Yarinya amma ƙirarta ta min wallahi" Tasleem tace "kaga, sallameni zan tafi kuma ka dawo ka ɗauke ni" Yace "ko nawa kike so zan baki, amma ina buƙatar Yarinyar nan, ke daga Naira ɗaya zuwa millions, zan bayar in sameta, in ajiyeta mussaman in dinga hutawa" Tasleem tace "ba ka da case, but for now, sallameni" "Karki ji komai, zaki ga alert irin wanda ba'a taɓa miki ba" Tace "kaji ka, kasan nawane a account ɗina kake cewa ba a taɓai min irin alert ɗin ba? Kawai dai ina jira" daga haka ta fito daga motar. Farhan tai mamakin shigar da ke jikin Tasleem, wando ne jeans ya matse ta sosai kamar tai juyi ya tsage, ga wata matatsiyar riga a jikinta, attachment ɗin ta har ɗuwawu, kuma kanta ba ko ɗan kwali se uban glass baƙi ƙirin a Fuskarta. Tace "Farhan muje ko" ba musu Farhan ta bi Tasleem, Kamar raƙumi da akala, se kallon Tasleem take sake yi. Wani ƙaramin hall ne a wani ɓangare na Hotel ɗin, kallo ɗaya za kaiwa wanda suke gurin, kasan ba Mutanen kirki bane, gaba ɗaya Farhan ta sha jinin jikinta, take ta tuna lokacin da a kai na ta birthday ɗin, abunda ya gudana a gurin tsakanin ta da Sadik. Take ta ji hawaye ya ƙwace mata, Babba ne ya hango su ya ƙaraso in da suke ya kalli Tasleem yace "ya kuma take kuka?" Tasleem tace "Nima ban sani ba" Yace "Common beb, whats wrong?" Yai Maganar yana ƙoƙarin janyota jikinsa. Haɗe rai tai ta matsa tace "don't try it, ka bani zan tafi" Yai murmushi yace "shikenan, zan baki, bari Nas ya ƙaraso suna hannunsa" Suka bawa Farhan guri ta zauna, sam ta dena fargabar za'ai mata faɗa a gida, babban burinta be wuce ta ga maganin nan ya zo hannunta ba, dan tai imanin idan ba shi ta sha ba, shikenan sun ƙulla da damuwa kenan. Tana nan zaune Tasleem ta kawo mata ruwa tace "Farhan ga ruwa, kan su kawo miki" "Ni ba na sha, so nake a bani in tafi, kar a neme ni a gida" Tasleem tace "ba komai, karki damu, yanzu za su kawo dan Allah ki sha ruwa mana" Ba tai tunanin komai ba, ta karɓi ruwan nan ta sha sosai, ta ajiye sauran. Ko mintuna goma ba'ai ba, Farhan ta ɓingire a gurin ta na bacci. Sadik ji yake kamar an kunna wuta a cikin zuciyarsa, ya miƙe ya kai ya kawo a ɗakinsa, ya kaiwa iska naushi yana wani irin huci, ba tare da ya san meya haddasa masa hakan ba. Ya zauna a gefen gado, ya dafe kansa yana jujjuya kai, yana son gano matsalar sa amma ya kasa. Kawai ya fashe da kuka, hawaye wani na bin wani. Nana ce tai sallama ɗakin na sa ta na faɗin "Aboki, dan Allah ka koyamin wannan Assignment ɗin, koyamin za kai, ba yi min za kai ba, sabo....... Se kuma tai turus, ganin Sadik na kuka, a kiɗime ta ƙarasa in da yake, ta jefar da littafin hannunta ta zaune, tana janye hannunsa daga dafe kan da yai "Sadik meye ya faru? Me a kai maka?" Ta jero masa tambayoyin. Maimakon ya amsa mata se ma cigaba da kukan da yai. Itama ta fashe da kuka tana faɗin "Dan Allah Sadik menene? Ka gayamin" "I don't know, something is killing me inside, and i dont know what is it, ina cikin damuwa amma ban san menene ke damuna ba, zuciya ta kamar za tai bindiga" Matsawa tai kusa da shi tana share masa hawayen, tace "dan Allah to ka dena kuka, Allah ze yaye maka damuwar ka, ka dena kaji" Tai maganar tana zubar da hawaye, maimakon ya dena se ya kwanta a jikinta, yana jin kamar zuciyarsa za ta kama da wuta. Sumar kansa ta shiga shafawa, tana cewa "Allah Ubangiji ya yaye maka damuwar ka, Allah Munyi tawassalli da sunayenka Allah ka yayewa yayana damuwar sa, ka iya 40 rabbana?" Ta tambaye shi tana kallonsa. Girgiza mata kai yai alamar a'a. Tace "Inna ce ta koyamin su, ta sa na haddace su, tace in dinga yawan yi, idan aka ɓatamin rai na karanta ina jin daɗin su sosai, bari in karanta maka kaji" Ya jinjina mata kai, jikinsa ya ɗau zafi , idanunsa sunyi wani irin ja kamar wuta, se jan numfashi yake. Ta ɗora hannunta, akn ƙirjin Sadik saitin zuciyarsa, se da ta ɗan tsorata ko dai zuciyar Sadik ke ciwo, wani irin harbawa ta ji zuciyar ta sa nayi, da sauri sauri. A hankali ta fara karanto Addu'oin rabbana rabbana da suke cikin Alqur'ani. Hannayensa ya sa ya danna hannun Nana sosai a saitin zuciyarta sa yace "Nana ciwo take min, wani abu na barazana ga rayuwata da farincikina, ina jin kamar wani abu nawa me mahimmanci da yake neman rabuwa da ni" Yai maganar yana kuka sosai kamar ɗan ƙaramin yaro, sosai ita ma Nana take kuka tace "duk abunda yake naka ne, in dai rabonka ne se ka same shi, insha Allah ba abunda ze same ka, yi shiru in karanto maka Addu'oin" Yai shiru tare da rungume hannayenta sosai a ƙirjin na sa, har ba ya son ta motsa hannun na ta. Nan ta shiga karanto masa Addu'oin, ya lumshe idanunsa ya na sauraren ta. Wani irin releif ne ya shiga ratsa Sadik, a hankali ya fara jin sassauci daga tsananin bugun da zuciyar ta sa take yi. Jin Nana tai Shiru ne ya sa yace "Nana" Tace "Na'am, ya kake ji yanzu?" "Alhamdilillah, Nagode sosai naji yana min sauƙi, ki sake karanta min" "To Alhamdilillah, amma ka san wani abu?" Yace "A'a" "Na san za ka ji haushi, amma gara in gaya maka, Aboki Inna ta na gayamin, a duk lokacin da mutum yai nesa da Allah, abubuwan damuwa suna zuwa su dami rayuwarsa, amma idan mutum yana tare da Allah a ko yaushe, to abubuwa na zuwar masa da sauƙi. Ka ga ba kullum kake salla a jam'i ba, kuma alhalin ba mu da nisa da masallaci sosai, kuma idan ka salla ko tasbihi ba ka yi, shafawa kawai kake ka tashi, balle Azkar ɗin safe da yamma. Alqur'ani ko ba ka karanta ba, ka kunna a wayarka ka saurara, insha Allah zaka dinga samun mafita a cikin Al'amura. Sannan wannan yawon kallon ball ɗin da kake ba yau ba gobe, da yawon darw duk ka dena su, ni Allah ya sa ma ba aljanu ne suka kama ka ba*. Duk maganganun ta da take, idanunsa a rufe suke, se da tai maganar aljanu Sannan ya buɗe idonsa ya kalleta yace "ubanwa Aljanun suka kama??" Tace "Ni bance sun kama ka ba, cewa nai Allah yasa ba su bane" "Nafi ƙarfin aljanu su kamani" Nana tace "da kana Azkar ne se kai wannan cika bakin" "Dan kin ganni akan cinyar ki kike gayan magana ko?" Tace "haba Aboki, ni na isa in gaya maka Magana, Allah ya baka haƙuri gaskiya nake gaya maka ne, zamu dinga karanta rabbana nan tare, har Allah yasa kaima ka haddace ka dinga karantawa" "Naji, amma dai yanzu cigaba da karanta min" Murmushi tai tana jinjina rigima irin ta Sadik, shi da ta samu a galabaice amma harya samu kansa ze fara masifa. Tana cikin karanta masa karo na biyu, bacci yai awon gaba da shi. A hankali ta zame kan Sadik daga cinyarta, ta sa masa pillow, ta tashi ta ja masa ƙofar ɗakin nasa, ta koma na ta, tana masa Addu'a Allah ya ba shi mafita akan abunda yake damunsa. A hankali ta motsa, ta buɗe idanunta da suke mata wani irin yaji, ga kanta da take jin tamkar ba na ta ba, tun tana gani dishi dishi, har Idonta ya fara washewa, se dai ba ta gani clearly. Kwance take a wani ɗaki, da ba ta san ina ne ba, ta tashi zaune akan gadon da take kwance, ta ƙarewa ɗakin kallo. Hijjabin ta ta gani a gefe a yashe, ga kamta babu ɗan kwali, ta janyo hijjabin ta ta saka, ta yunƙura ta miƙe tsaye, sedai tsaiwar ta gagare ta saboda yadda take tangaɗi. Ƙofar fita daga ɗakin ta nufa, ta buɗe ta fito, duk wata gaɓa ta jikinta ciwo take mata, tana tafe tana nema tai karo da bango, a haka ta fito harabar Hotel ɗin. Safiya ce wajen ƙarfe Goma na tara, haka ta dinga tangaɗi, ta na ƙoƙarin fita daga cikin Hotel ɗin. Wata mota ce ta dinga mata horn, amma ta rasa daga ina motar take mata horn ɗin. "Ohh Allah yayi yau ma mun kuma haɗuwa" Duk da maye take, amma ta gane shi, mutumin jiya ne, da yaita mata magana ta ƙi kula shi" Yace "ina zaki ne?" Ta ɗan yatsina fuska tace "gida zani" ta ƙarasa maganar tana dafe kanta. "Ina ne gidan?" Ba musu ta kwatanta masa. Yace "to muje in sauke ki, be kamata ki fita kina maye ba" Ba musu ta bi shi Mota, ta shiga gaban mota, tun da ta shiga ta kifa kanta, yaita mata magana amma ba ta kulashi ba. Tiryan tiryan da ya bi kwatancen nata, se ga su a ƙofar Gidan su Farhan, layinsu shiru babu kowa. Ta fara ƙoƙarin buɗe motar ta sauka yace "gashi mun zo amma ba ki gayan ko sunan ki ba" "Dan Allah ka ƙyaleni" tai maganar tare da buɗe motar ta fita, ta nufi gidan su. Yace "Ikon Allah, wannan 'ya akwai mulki" Da ta shiga gidan shiru, babu kowa ko sallama ba tai ba, ta wuce ɗakinta, ta zube akan katifarta ta cigaba da bacci. Kusan mintuna ashirin, Farhan taji muryar ƙaninta Ameer yace "Laaa Umma kinga Yayan a ɗakinta tana bacci" Umma a gigice tace "dagaske?" Tai maganar tana ƙoƙarin leƙa ɗakin Farhan, aikuwa ita ɗin ce. Tace "kira babanku kace masa ga ta ta dawo" Tun da suka farga ba ta gida, ake nemanta tun jiya, har gurin 'yan sanda aka shigar da report, ana ta cigiya ana nemanta, lokacin da ta dawo ma, Abba ya tafi gurin 'yan sanda, Umma kuma ta na bin gidajen 'yan uwa ko za'a sameta. Ba a jima ba sega Abba yace "Ina Farhan ɗin take?" Ya leƙa ɗakinta ya ganta a sharɓe tana bacci, take jikinsa yai sanyi yace "Innalillahi wa innalillahi raji'un, Allah na san wannan jarabtace ka jarrabe ni, Allah ka shirya min 'ya ta" yai maganar idonsa fal ƙwalla, ko ba a gaya masa ba ya san a cikin maye Farhan take saboda surutan da take. Ya koma ɗakinsa, wata irin ƙwallar baƙin ciki ta taru a idon sa, Umma ta biyo shi tana Malam meye abun yi akan Yarinyar nan, ni kam na gaji da wannan lamarin, ba yau ba gibe ta dinga janyo mana abun Magana". Abba ya girgiza kai yace "kiyi haƙuri, muyi shiru da bakinmu mu dinga mata addu'a, takura ko tsauri ba za suyi aiki ba" Cikin kuka Umma tace "kaga irin abunda nake ji ko? Da an haƙura anyi Auren nan da shikenan, koba Komai tana can Asirin mu a rufe, amma yanzu watan tonon Asirin mu ya tsaya, Malam kwana fa tai a waje, a ina ta kwana?" Abba yace "kar ma ki kuskura ki tambaye ta a in da ta kwana, ba abunda hakan ze haifar banda ɓacin rai, muyi mata Addu'a Allah ne ya jarrabe mu, na san jarabta ce, yarinya ta me hankali ce da tarbiyya, Allah ya shirya ta" "Shikenan, babu wani mataki da zaka ɗauka akan ta?" Abba yace "to in ba addu'a ba, so kike in tsine mata? Ko kuma in koreta ta bar min gida? Addu'ar dai ita ce mafita" Umma ta dinga kuka, Abba na mata nasiha, saboda hawayenta masifa ne a Rayuwar Farhan. Se bayan la'asar Farhan ta gama dawowa hayyacinta, taje tai wanka ta jera sallolin da ake binta, ba tare da shakkar laifin da ta aikata ba, ita babbar damuwarta haɗa salloli da tai. Shiru tai tana ƙoƙarin tuna abunda yafaru da ita, Gabanta ne yai mummunar faɗuwa da ta tuna, taje tana jiran Babba ya bata magani ne, aka ba ta ruwa ta sha, daga nan ta farka ta ganta a ɗakin Hotel. "Innalillahi wa innalillahi raji'un, meyafaru da ni to? Meya sameni, me sukayi min? Innalillahi wa innalillahi raji'un, Allah yasa ba keta min mutunci su kai ba, naiwa Sadik Alƙawarin komai daren daɗewa ba wanda ze mallake ni se shi"   'ji banza, yana can yai Aure, maimakon ki ta kanki, amma ke ta wani Sadik kike, bayan shi yana can yana shagalinsa' wata zuciyar ta tunatar da ita. Wani irin gumi ne ya shiga keto mata, jikinta ya hau rawa, kenan bugar da ita sukai, su kai mata fyaɗe? Shikenan mutuncinta da kimarta, Mubarak ya yaudareta kenan, sun haɗa kai da 'yan ajinsu sun cutar da ita, shiru tai ta shiga tunanin yadda ake labarin taƙadirancin Mubarak. "Innalillahi wa innalillahi raji'un" shine abunda Farhan ta faɗa tare da dafe kanta, ta fashe da wani irin gigitaccen kuka, tabbas ta ta ta zo ƙarshe rayuwarta ta ɓaci. "Wace irin masiface haka take bibiyata, da ga wannan se wannan, shikenan ba ni sa sa'a  rayuwa ta? Astagfirullah wa atubu ilaih"  ta shiga jujjuya kanta da ya riga yai mata Wani irin nauyi. Da safe har Nana ta tafi Makaranta, Sadik baccin sa yake, tun da yai sallar Asuba ya koma gado ya naɗe ya cigaba da baccin sa. Ba ta tashe shi ba, saboda yadda ya sha wahala jiya kan yai bacci, dan haka kawai ta tafi makaranta. Ko da ta dawo gida, Sadik ba ya nan, nan ta tabbatar da lallai ya samu lafiya, tun da harya samu ƙafar yawo. Nana na tsakar ɗakinta tana karatun exams, ta jiyo muryar Sadik a falo yana ƙwala mata kira "Friendy where are you?" Daga ɗaki ta amsa masa "gani a nan, Lafiya Kuwa?" Buɗe ƙofar ɗakin yai yace "Ashe kin dawo?" "Na dawo tun ɗazu, naga ka ware harka fita" SADIK yace "Yeah, come and see something" Tace "something like what?" "Zo ki gani mana" Ta ɗan lanƙwasa wuya tace "karatun exams fa nake" Yace "dan Allah ta so ki gani" Ta miƙe ta biyo bayan Sadik, ƙofar gida ya jata ya nuna mata sabon babur dal. Ta kalleshi tace "Friend wannan kuma na waye?" Yace "Namu ne? Har lasisin tuƙi na yi" Tace "wai siya kayi?" "Eh mana, be kyau bane?" Ta naɗe hannayenta a ƙirjinta tace "yayi kyau sosai, amma ba ka ganin muna yiwa Abba ɓarnar kuɗi da yawa" "Ke wai fina son Abban nan ki kai ne? Allowance ɗina ne, na ƙwallo da shi na siyo mana" Tace "Au har biyanka suke?" Yai murmushi yace "au ke da duk wannan facakar da muke da kuɗi kin zata duk kuɗin Abba ne? Ina samun kuɗi da ball ɗin nan, ba dan karatu ba ma da babban club ne za su siyeni, business zan fara fa" "A siyeka kuma, se kace Zamanin bayi?" "Ke fa Matsala ta da ke kenan, wauta ke ba ki taɓa jin ance an sai ɗan ball ba?" Nana tace "yo ina gida, a ƙuryar turakar Inna ta ina zan sani. yanzu masha Allah, Congratulations to us, ubangiji Allah ya tsare mana, saura kuma ka dinga tafiya kana barina" "Ɗakko ɗan kwalinki, ki zo muje ɗani" Nana ta ɗan ɓata fuska tace "karatun exams fa?" "Ke dalla, shikenan rayuwa bawa ba ze huta ba, ki dinga hutawa kan ki da bokon nan, maza jeki shirya mu ware kawai, yau ba zama munyi ƙafa" Nana tai murmushi ta koma gida, ta ɗakko mayafi, tai rolling akan abayarta, ta hau sabon babur ɗin Sadik suka shiga zaga gari. Sun sha yawo sosai, sun zaga gari Sosai, sannan Sadik ya maida Nana gida ya sake fita gararambarsa. Se taran dare ya dawo, ya wuce ɗakin Nana, ze sa ta girki, dan yawon da yai, yunwa yake ji sosai. Yana shiga ya tarar tana banɗaki tana wanka, ya kalli yadda ta ɗame gadonta, ɗakin se ƙamshi yake, aikuwa dan ya tsokane ta yaje ya haye gadon, ya kwanta. Ya kai mintuna goma a kwance akan gadon, yana game a wayarsa, Nana ta buɗe toilet daga ita se towel ta fito. Se da ta razana ganin Sadik a kwance a kan gadonta tace "meya haka dan Allah zaka shigo min ɗaki ba sallama?" Ya ɗan kalleta yace "yunwa nake ji wallahi, sonake ki ɗan dafamin wani abun" Ta riƙe ƙugu tace "taɓ, ni baiwarka ce? Ina shirin kwanciyar zan maka girki, ai yaseen ba zan ba" tana cikin yi masa tsiwa, ta ga ashe har da takalmi ya hau mata kan gado. A fusace ta nufo kan gadon tace "dan Allah meye haka, na gyara gadon ka hau min kan gado da takalmi, wannan ai wulaƙanci ne, dan Allah ka saukar min daga kan gado" Shareta yai ya ci-gaba da game ɗin sa, a fusace taje ta sa hannu ta cire takalaman da ke ƙafar Sadik, ta ajiye su a ƙasa tana cigaba da masifa. Ganin ba shi da niyyar kulata ne, ya sa ta ɗau kayan baccinta, ta shiga banɗaki ta saka, ta fito ta shafe jikinta da mai, ta shafa turaruka, ta ɗako turare ta ɗau lallausan duvet daga wardrobe, ta feffesa masa turare, ta zo kan gadon ta ɗau fululluka ma, ta shafa musu turare. Sadik yana kallonta ta wutsiyar idonsa, a ransa yace 'wannan Yarinyar akwai ɓarna' Sedai ƙamshin da ya gauraye ɗakin, ya saukar masa da kasala, se wani lumshe ido yake yana shaƙar ƙamshin turarukan da suka gauraye ɗakin. Kan sa ta zo ta tsaya, hannunta rungume da bargonta, ta kalli Sadik tace "Ni ka tashi, zan kwanta" "Ai ban hanaki ba" yai maganar ba tare da ya kalleta ba. "To ka saukar min daga kan gado, kasan dai na zan kwanta tare da kai akan gado ba" "Ashe kuwa zaki kwana a ƙasa, dan ba zan tashi ba" Haushi ne ya kama Nana, ta san Sadik da taurin kai, ta ɗakko pillow, za ta kwanta a ƙasa ta tsaya tace "kaiii, ni da ɗakina kuma gadona in kwana a ƙasa, rannan da nake jin tsoro naje ɗakinka ai a ƙasa na kwana, yau kuma se ka kwana a gadona ni kuma ina ƙasa, to wallahi ba ze yuwu ba" ta ƙarasa maganar tana hayewa kan gadon. Fulo ta sa a tsakanin su, ta nemi guri ta kwanta. Take Sadik ya ji shi a wata duniya ta daban, kasancewar Nana a kusa da shi, tana wannan ƙamshi me daɗi. Lumshe ido tai tana Addu'oin ta na kwanciya bacci. Ɗiff taga Sadik ya kashe lantarkin ɗakin. Tace "A'a ya naga haka, ya zaka kashe fitila, ga ka ɗare ɗare akan gado, wannan ai ba ɗabi'ar arziki bace" Ji yai kamar ya kwashe da dariya, yace "ni ba na iya bacci fitila a kunne. "Gaskiya idan muka kwana gado ɗaya baka kyauta min ba wallahi, gaskiya ka shiga hakkina" Shareta yai, yana cigaba da tattaɓa wayarsa. Har bacci na ƙoƙarin kwashe Nana, ta ji Sadik a jikinta, muryarsa ƙasa ƙasa yace "Husna, haka zaki barni in kwana, yunwa nake ji wallahi" "Ni na aike ka yawo? Wai ma wa ya gaya maka sunana na gaskiya? Ba wanda ya san sunan nan se wanda suka raɗamin" Kamar ze mata kuka ya zagayeta da hannayensa yana sa hancimsa a wuyanta yace "So kike Ulcer ta kamani ko? Husna" ya kuma faɗa a hankali. "A gaskiya bana son irin wannan abun da kake min, ni wallahi jikina wani iri nake ji in ka taɓa ni, gaskiya ka dena, kaga ni cikani in koma falo, naji zan bar maka ɗakin" Cikata yai yace "Sorry, na ƙyaleki ba se kin fita falo ba, yanzu zan tafi, have a nice dreams" Murguɗa baki tai kamar yana kallonta a ranta tace "Mutum shi dai in be naniƙi mace ba ba yajin daɗi, shiyasa rayuwa cikin turawa be ba, mutum yai ta kwafar banzayen ɗabi'u' Ta koma can ƙarshen gado, ta takure, a haka har bacci ya kuma kwasheta. Sadik kam ya rasa meye ma abun yi, yayi dana sanin zuwa ɗakin Nana, ya rintse idanunsa, yana ajiyar zuciya. So yake ya tashi ya bar ɗakin, amma ya kasa motsawa, yana nan a kwance, dare ya cigaba da tsalawa ba tare da ya samo mafita ba. Nana akwai make-make in ta na bacci, yo ta saba da kwana ita kaɗai, ta buga masa hannu a ƙirji, in aka jima ta maka masa ƙafa, ƙarshe gaba ɗaya ta dawo kansa tana baccinta. A gigice Nana ta farka daga baccin da take, jin wani baƙon al'amari da ba ta taɓa zata ba. Sedai Sadik ba wani tausayi ko makamancin haka, yai abunda zuciyar sa ke raya masa, se dai bayan ya nutsu ya dinga jin kamar ya aikata ba daidai ba, tamkar ya aikata wani gagarumin laifi, duk da yasan Nana matarsa ce, amma ya kasa gane dalilin da yasa yake jin hakan Se dai ya bar abun a Nana tai ƙanƙanta da abunda yai mata, shi kansa be san yadda akai al'amuran suka kasance ba, jinsa yake kamar ba shi ba, kamar wani sabon mutum daban haka yake jin kansa. Nana kam baki ya mutu ƙus, se kuka da take ko Magana ta kasa, se Allah ya isa da take masa a zuciyar ta. A hankali ya janyo Nana jikinsa yace "Am sorry Husna Please..... Ai be ƙarasa ba, ta ƙwace daga jikinsa tana kuka, sedai ta kasa Magana sam. Ya lumshe ido, yana son rarrabe wane irin yanayi yake ciki a halin yanzu. Ya ɗau dogon lokaci a haka, Sannan ya miƙe ya shiga toilet ɗin dake ɗakin Nana. Ya ɗan jima Sannan ya fito daga toilet ɗin, ya samu guri ya zauna a gefen gado, ya zubawa Nana ido, dan be san meya kamata yai mata ba. Wayarsa ya ɗakko, yana ɗan daddanawa, daga ba ya koma banɗakin, sannan ya dawo a hankali yace "ki tashi ki shiga toilet ki gyara jikinki" Banza tai masa ta sake shigewa cikin bargo. Cikin tsawa yace "ba kiji me mace bane?" Ai a razane ta diro daga kan gadon, ta Sanya doguwar Rigar baccin ta, ta nufi banɗaki tana kuka me sauti. Yace "kuma ba wankan soso da sabulu za ki ba" "To wann zan yi?" Ta faɗa tana share hawaye. "Ba'a koya miki wankan tsarki a Islamiyya ba, shi za kiyi" Wani kukan kura ne ya ƙara ƙwacewa Nana, Sadik ya gama raina mata hankali. Ƙasan zuciyarsa kuwa, wani irin tausayin Nana ne ya mamaye shi, amma ya san halinta, yana lallaɓata zata lanƙwashe tai ta Iskanci. Bayan tai wankan ta fito, ta ga Sadik ya kuma kwanciya akan gadon nata, har da lulluɓa da bargo. Ta canza kayan baccin ta, ta ɗau pillow ta koma ƙasa ta kwanta, tana ta sheshsheƙar kuka. Sadik yana jinta, yai mata shiru. Se da yaji alamun tai bacci, sannan ya sakko daga kan gadon, kansa yana wata irin sarawa, ya ƙaraso in da Nana ke kwance, ya kwanta a kusa da ita, ya lulluɓe su da bargo, ya rungumeta tsam a jikinsa, yana faɗin "Am sorry Friend, na miki laifi but am so sorry" yai maganar yana sake ƙanƙameta, yana jin yadda jikinta yai zafi, se ajiyar zuciya take a bacci. Ras!Ras!!Ras!!! Gaban Farhan yai wata irin mummunar faɗuwa, ƙirjinta ya buga da ƙarfi a jere, wanda se da numfashinta yai barazanar ɗaukewa. Littafin nan ₦300 ne kacal. 0009450228 Aisha Adam Jaiz Bank 07063065680 KO kuje manhajar AREWA BOOKS ku siya. domin kuwa ya fi sauƙi ta can. Littafin nan ₦300 ne kacal. 0009450228 Aisha Adam Jaiz Bank 07063065680 KO kuje manhajar AREWA BOOKS ku siya. domin kuwa ya fi sauƙi ta can. Miƙewa tsaye Farhan tai, taje gaban Window ta tsaya, ba tare da ta san dalilin hakan da tai ba. Har gari ya waye idon Farhan biyu, ba ta rintsa ba, zuciyarta se suya take, mussaman idan ta tuna abunda su Mubarak Babba su kai mata. Da safe Umma na can na fafutukar shirya yara su tafi makaranta, Farhan ta ɗakko wayar Umma, ta ɗakko lambar Mubarak Babba, da ya bata Ranar da ya kawota gida. Bugu biyu ya ɗauka yace "hello waye?" "Farhan ce" ta bashi amsa. Yace "Ohh beb ya kike?" Farhan tace "ina zamu haɗu? Ina son ka bani abun nan" Mamakine ya kama Mubarak, yadda be ji ta tambaye shi, abunda ya faru da ita ba. Yace "mu haɗu a Hotel ɗin nan" Farhan tace "ka jirani ƙarfe huɗu na yamma" Ta kashe wayar, taje ta ajiyewa Umma, tana ƙoƙarin Fitowa daga ɗakin, su kai karo da Umma, ta kalli Farhan tace "me kike min a ɗaki?" Farhan ba tace mata uffan ba, ta raɓata ta fice daga ɗakin. Tana jin yadda Umma ta rakata da zagi, da ƙanan maganganu amma tai shiru ba tace komai ba. Da Asubar fari Sadik ya tashi yai alwalwa, ya dawo ya tashi Nana dan tai salla. Daga haka ya fice ya bar mata ɗakin, Nana tana alwala tana kuka, har ta zo tai salla ta idar, koke koken ta take yi. Har wajen ƙarfe tara na safe, se da Nana taji yunwa za ta mata illa, sannan ta lallaɓa ta fito falo. Sadik na kwance akan doguwar kujera, hannunsa riƙe da remote, Kallo ɗaya tai masa, ta ɗauke kanta daga kallonsa ta wuce Kitchen. Binta yai da kallo, yana gano zunzurutun fushi a fuskar ta, ga tausayin ta da ya ke ratsa zuciyarsa. Kitchen ta shiga ta haɗo tea, ta soya ƙwai ta ɗakko bredi ta fito, har zata wuce ɗakinta Sadik yace "ke, ni kenan da yunwa zan zauna?" Ranta a haɗe ta koma Kitchen, ta haɗo masa kayan Abinci, ta kawo ta ajiye masa, zata koma ɗakinta yace "nemi guri ki zauna" Ba dan ta so ba, ta samu guri ta zauna tana hura hanci, saboda yadda take jin haushin Sadik. Sadik ya ci Abincin sa ya ƙoshi, ya ƙare mata kallo yace "wai ke uban me akai miki, se wani huran hanci kike?" Ai kuwa dama ƙiris take jira, ta fashe da kuka tace "bayan ka lalata min rayuwata, kuma kake tambayata me kai min, a kafi kowa sanin abunda kai min. Duk yadda Inna ke ƙoƙari a kaina kar in lalace, ta ke tai min nasiha akan in kiyayi maza, shine ka lalata min rayuwata, yanzu da wani idon zan kalli Inna? Sun turoni inyi karatu, ka lalata ni, me zance musu?" Ta ƙarasa maganar tana rushewa da kuka. A ransa yace 'anya wannan 'yar ta na da kai kuwa?' A fili yace 'ni kike tambaya me zaki gayawa Inna? Ki gaya mata Sadik ya ɓata miki rayuwa, ga amsa a bayyane" "Au haka ma zakace, ka cuceni kuma kana gayan baƙar magana? Wallahi ba zan taɓa yafe maka ba, shikenan mutuncina ya zube" Sadik yace "ai seki bi shi ki kwaso shi, sokuwa kawai" Baƙin cikin duniya ya ishi Nana, Sadik ya mata wannan abu kuma ya koma yana raina mata hankali, kamar be yi komai ba. Kamar yadda Farhan su kai da Mubarak, ba tare da neman izinin kowa ba, ta shirya ta fita daga gida, se dai babu wayar da zata kira shi tace masa gata ta zo. Tana nan tsaye ta hango shi yana fitowa daga reception, yana ganinta ya hau murmushi irin na 'yan Duniya yace "My baby, ashe kin ƙaraso?" Farhan ta kalleshi cikin tsana, dan ko fuskarsa ba ta son gani. Yace "muje daga ciki ko?" Ba musu ta bi bayansa, wani ɗaki ya kai ta a cikin Hotel ɗin, ta tsaya tana ƙare wa ɗakin kallo. Yace "zauna mana, bari in kawo miki abun taɓawa ko" Farhan ta kalleshi tace "ba shi na zo yi ba, Mubarak me ku kai min ranar da na zo Hotel ɗin nan?" Yace"Normal ne, ki basar kawai beb" Cikin ɓacin rai tace "Kar ka kuma cemin wata beb, Mubarak me ku kai min? Ka gayamin?" Ta faɗa cikin kuka. Yai ajiyar zuciya yace "Am sorry, kawai ki ɗau haƙuri, ba shi da amfani sanin abunda ya faru" "Kamar yaya me kake nufi?" tai maganar hawaye wani na bin wani. Mubarak yace "Farhan, ai bana alƙawari in saɓa, tun da na ƙyalla ido na ga Sadik ya mutu akan sonki, nai alƙawarin se na miki illa na ɗanɗana masa baƙin ciki me raɗaɗin gaske" Kamar Mahaukaciya Farhan tace "Meye nawa a ciki? Ni laifin me nai maka? Ina ruwana da abunda ya haɗa ku?" Mubarak yace "ok har kin manta lokacin da kika mareni kenan, kin ɗauka kin ci bulus?, na samu abunda nake so, kuma ba ni kaɗai ba ne nai, ko ba Komai na barwa Sadik ajiya me muni. Mu huɗu mu kai amfani da ke, kuma ki sani ko kin kai gaba ba abunda aka isa ai min, saboda ke ba 'yar uban kowa bace, face 'yar talakawa mara amfani, ba ki da kuɗin da zaki ja da ni, ai Tasleem ta ga ma min komai" Farhan ta haɗiyi wata irin muguwar ƙwallar baƙin ciki ta kalli Mubarak tace "ni 'yar talakawa ce, amma ba mara amfani ba, tabbas ka zalunce ni saboda abunda ya haɗo ku da Sadik daban, ni kuma alaƙata da shi daban. Kayi naka ɓangaren, saura nawa zakaga abunda zan iya yi" Ta juya ta fice daga ɗakin cikin sassarfa, wani duhu da ƙunci ya mamaye zuciyarta. Mutum huɗu su kai mata fyaɗe tana maye, wannan wane irin bala'i ne, gurin wa za ta kai ƙara bayan ita ta kai kanta?. "Duk kai ka janyo min Sadik, tarayya ta da kai ba ta amfana min Komai ba se zunzurutun bala'i, ka sanya ciwo a zuciyata, da fari nayi zaton Alkhairi ne shigowar ka rayuwata, amma yanzu na tabattar da kai ƙaddara ne, insha Allah daga rana me kamar irin ta yau zan shafe ka a tarihin rayuwata, ko a lahira bana fatan sake yin ido biyu da kai, na tsaneka Sadik, na tsane ka Tsana me tsananin gaske. Zan shiga bariki in tara kuɗin da zan kawo ƙarshen Iskanci da tsageranci na Mubarak babba da tawagar sa. Ba ni ba Aure, sedai se na rama yaudarar da Sadik da yai min akan sauran maza!. Da irin wannan maganganun ta nufi hanyar fita daga Hotel ɗin, zuciyarta kamar ta tarwatse. Nana ta gama fushin ta ta sakko, dan ba za ta iya dogon fushi da Sadik ba, dan ta fuskanci idan ta biye masa, haukata ta zeyi, dan ba shi da aiki se tsokanar ta, da takura mata be kuma gigin cewa ze mata wani abu ba, hakan ya sa ta ɗan sakko daga fushin da take, amma haryanzu idan ya so ganin ɓacin ranta, se ya kwanta a jikinta, nan za tai ta mita tana cewa wallahi ba ze sake lalata ba. Yau sun gama cin Abincin dare, Nana tace "Friend nifa gaskiya Islamiyya nake son shiga, dan Allah ka sani a Islamiyya mana" Sadik yace "ke kinga wata Islamiyya a nan ne, to ni makarantar addinin Musulunci ɗaya na sani a garin nan, kuma tana da nisa sosai daga nan gidan, sedai in biya miki ta online ki dinga yi a system ɗina" Tace "yawwa, amma fa nagode Sosai, Allah ya saka da Alkhairi Autan Mother" yai murmushi kawai ba tare da yace mata Komai ba. Tana nam zaune ya ɗakko System ɗin sa, yai mata registration na Online islamic classes, hatta kuɗin da ake buƙata ya biya mata, nan Nana ta dinga murna tana masa godiya, tare da yi masa Addu'oi kala kala. ********** "Khairat, wai meke damunki ne? Kullum kina ɗaki kamar me jego" Khairat ta ɗan ɓata fuska tace "ba Komai fa" "A'a ban yadda bakomai ba, ke kenan kullum a ɗaki, Mother ta kirani a waya ba a dadi, akan kije amma kin ƙi, kwata kwata kin ɗauke ƙafarki daga gidansu" Ta tura baki gaba tace "to ni Mummy me zanje Gidan in yi?" "Kamar ya me zaki je ki yi, da me ki ke zuwa yi?" "Mummy gidan fa ba kowa, daga ni se ita da 'yan aiki, gidan is boring wallahi" "To amma duk da haka, zaman ki a gidan ma ɗebe mata kewa, kinga ita kaɗai ce a gidan" Khairat tace "hmm Allah sarki, gidan b kowa yanzu, Sadik yana can, ni shi nake son in ga yadda ya zam, gashi tun da ya tafi ko a waya, be taɓa kirana ba, Mother tace min ya canza layin da yake amfani da shi a can, na karɓi sabuwar lambar ta sa amma ba ta shiga, tace min lokuta da dama idan ba shi ya kiraka ba, wayarsa ba ta shiga" Mummy tace "hakane, amma mahaifinsa ne ya sama sa takunkumi, ya ƙayyade masa iya wanda ze dinga kira da layin, an saita layin na sa da iya lambobin da ake so ya dinga ta'amalli da su, haka HAUWA tace min" "Taɓ, gaskiya an matsan ta masa da yawa, gashi an haɗa shi da 'yar ƙaiye haka ze ta fama" Mummy tace "yawwa, ni se da ki kai wannan maganar ma, sannan na tuna da batun Yaron nan Abdul, ɗan Gidan Hajiya Azumi, dan ubanki Khairat meye aibun yaron nan da yace yana sonki? Kike wa ɗan mutane wulaƙanci lafiyar ki ƙalau kuwa?" "Haba Mummy ni fa Yarinya ce, kalleni 'yar Yarinya da ni kawai kuma se in fara wata Soyayya?" "To meye a ciki, so kike se kin tsofe tukuna, abunda wasu ke rububin nema ido rufe, shi fa Dagaske yake Aurenki yake son yi" Khairat tace "Wallahi Mummy baƙi ne" "To baƙin a wuyanki zaki rataya shi? Ina ruwanki da baƙinsa, dan kina fara akace dole se kin Auri fari?" "Mummy wallhi shi na sa baƙin yai yawa, bana son shi ne ma wallahi" "Haba Khairat, ina wani baƙi a nan gurin, yaro da sana'arsa da rufin Asirinsa da komai, ai ba kala ake dubawa ba, in da za'a samu kwanciyar hankali" Ji tai kamar ta gaywa Mummy, ita fa Faruk take so, amma se ta kasa, tai shiru tana sauraran Mummy da ke tai mata nasiha akan Abdul, nasihar da ke shiga ta hagu ta fita ta dama, dan sam ba taji wata alama na za ta iya son Abdul ba, dan ita Faruk kawai take so. Nana ƙarfe takwas na dare, ake fara musu karatun Islamiyya na online, mutum ze iya ajiyewa ya saurari lecture idan an gama in ba shi da lokaci, amma ita Nana tafi son ƙarfe takwas ɗin nan ya zamana anyi karatu da ita. Idan Sadik yana nan, yana kusa da ita yana kallon yadda take tattara nutsuwarta akan abunda ake koyawa, da littafin ta da bironta, amma shi ba ruwansa, yana gefen ta yana aikin game a waya, ko a talabijin. Sam harkar Addini ba ta wani damu Sadik ba, iya wuya da shagala ba ya wasa da salla, wannan ze yi ta akan lokaci amma ba lallai yaje masallaci, se dai yayi a gida, dama batun wani tasbihi da Addu'a ba yi yake ba, da ya idar da salla yake shafawa ya tashi. Nana tana lura da shi, sedai ba ta son tayi Magana, yai fushi su hau faɗa, dan haka bayan ta kammala karatun Ranar ta kalleshi tace "Friend, kayi sallar isha'i ne?" Yace "No, yanzu dai zan yi" Tace "ok, to bari im yi Alwala seka jamu sallar, yau a nasihar ƙarshe da Sheikh yake mana kullum, yai jan hankali akan sallar jam'i, ka ga gara mu dinga yi tare muna samun lada da yawa ko?" Yai murmushi yace hakane. Taje tai alwala, ta saka hijjabi ta bi bayan Sadik. Normal ya ja su salla, suka idar ta ga ya yunƙura ze miƙe tace "A'a, Friend na ga ba kai tasbihi ba" "Wane tasbihin?" Ya tambaye ta. Tace "Subhanallah, Alhamdilillah, Allahu Akbar, da akeyi ƙafa talatin da uku, da sauran Addu'a" Sadik yace "Ai ba farilla ba ne" "Amma ai Sunna ce me ƙarfi, ya zaka ji idan na baka dafaffiyar shinkafa ziryan babu mahaɗi, Astagfirullah kar in yi saɓo, baka san ladanka yai yawa sosai? Idan fa mutum yai ibada ba shi da tabbacin an karɓa, dole se mutum yana haɗawa da Addu'oi. Gashi kai da kake shirin zama salamburuti, na 'yan ƙwallo ai dole mu dinga Addu'a Allah ya ɗaukaka ka, da kuma Allah ya tsare ka" Komawa yai ya zauna, ya shiga yin tasbihi, wanda rabonsa da yayi bar ya manta. Duk da ƙuruciya da shirirta irin ta Nana, amma a haka ta hilaci Sadik, yai tasbihin sa gaba ɗaya, da Addu'oin da ake bayan idar da salla, da azkar ɗin maraice" Tace "yau za kai bacci me daɗin gaske, saboda kai Addu'oin nan, zakaji kamar ba ka da damuwa, ba ka ji ana Addu'a takobin mumuni ba?" "Hakane, Thank you for the reminder" Tai masa murmushi daga nan, sukai sallama kowa ya nufi makwancin sa. Farhan kam, shaye shaye da ta fara ya sa ta dena jin shakkar kowa, sedai ba ruwanta da mutane, duk wani wanda ta saba gaisawa ta dena, kullum tana ɗaki. Ita kanta ba ta jin daɗin shaye shaye da take yi, ko tayi yunƙurin denawa ta taji Soyayyar Sadik na ƙoƙarin dawo mata, se ta nemi abun da za ta sha ta manta Komai. Abba ya zubawa sarautar Allah ido, banda Addu'a ba abunda yake yi, yayin da abun duniya ya ishi Umma, ta rasa in da za ta saka kanta, duk da halin da Farhan ke ciki, ko da wasa Umma ba tai tunanin jan ta a jiki ba, sema ƙyama da ta shiga nunawa Farhan ɗin, ta hana ƙannen Farhan ma shiga sabgar Farhan ɗin. Yau juma'a, bayan an sakko daga Masallaci, Huzaifa ya zarce gidan su Farhan dan kai musu ziyara, ya kwana biyu be je gidan ba, saboda yanayin makaranta da yake zuwa. Ya tarar da Umma, ya zauna suka dinga hira, can yace "Umma wai ina Yaya ne?" Umma ta kwaɓe baki tace "ba ka san sabuwar rayuwar da ta zaɓawa kanta ba, rayuwar bin duniya, tana ɗaki tana aikin shaye shaye" "Innalillahi wa innalillahi raji'un, Umma wane irin shaye shaye kuma?" "Shaye shaye dai da ka sani, ai rabonka da Gidan nan ka daɗe, tun ranar ɗaurin Aurenta ba ka sake zuwa ba, a ranar ma shaye shaye tai, tayi mankasa abunta, yanzu kwana a gida ma se ta ga dama, nayi nayi Abbanku ya ɗau mataki a kanta, amma ya ƙi ya zuba mata ido, wai muyi mata Addu'a, addu'a ba tare da ɗaukar mataki ba" Jikin Huzaifa yai sanyi ƙalau, ko da wasa idan aka ce Farhan za tai shaye shaye ze ƙaryata, yanzu ma ba dan Umma ce ta gaya masa da bakinta ba, cewa ze ƙarya ne. Mahaddaciyar Alƙur'ani, m Yarinya me tsananin riƙo da Addinin ta, amma ace wai ta na shaye shaye, to me ya janyo hakan? Jiki a sanyaye ya nufi ƙofar ɗakin Farhan, ya bubbuga. Cikin sassanyar muryarta tace "shigo" Huzaifa ya shiga ya tarar da ita a zaune, duk ta rame tai wani iri. Yace "Yaya, dagaske abunda Umma ta gayamin hakane? Wai kina shaye shaye?" Ta jinjinawa Huzaifa kai alamar eh. "Kenan yanzu da gaske ne?" Farahan tace "hakane Huzaifa" Huzaifa yace "innalillahi wa innalillahi raji'un, Yaya  me yai zafi haka? Meyasa kika zaɓi ɓata Rayuwar ki?" "Huzaifa, idan nai shaye shaye ne kawai nake samun mafita, ina da damuwa Huzaifa, damuwa ce ke barazana ga rayuwata, Huzaifa se in kwana uku a jere ban rintsa ba ko na awa guda, ƙwaƙwalwa ta zata iya bindiga" "Amma Yaya ina Alqur'ani? Kika ajiye shi kika kama wannan mummunar rayuwa?" Cikin hawaye Farhan tace "bana iya karantawa yanzu, ko na buɗe kasawa nake,idan nace zan biya haddata nan ma bana iyawa, hadda ta duk ta zube, ji nake kamar zan mutu" Huzaifa cike da tausaywa yace "Yaya, meye damuwar ta ki? Me kike buƙata ina Auren Sunusi ne kuma gashi an fasa?" Girgiza masa kai tayi tace "faɗa maka damuwa ta ba shi da wani amfani, amma daga cikin sashin abunda yake haifar min da damuwa, shine ɓata min suna da Sunusi yai, wanda hakan yake bibiyar rayuwa ta" ta dafe kai tace "subhanallah, Huzaifa ba na son tuna Komai dan Allah ka tafi in samu in huta" "Amma Far.... "Dan Allah ka tashi ka tafi, ba na son ganin kowa a kusa da ni" Jiki a sanyaye Huzaifa ya tashi, ya bar ɗakin ya fito ya tarar da Umman Farhan na wanke wanke a tsakar gida, ya kalli Umma yace "Umma, Amma babu wani mataki da za'a ɗauka akan wannan lamarin?" "Wane mataki, babanta yace a ƙyaleta ai mata Addu'a" "Amma Umma, kamar za'a iya shawo kan matsalar, akwai abunda yake damunta in aka zauna da ita aka ji matsalar ta wataƙila a shawo kanta ta dena" Umma tace "koma meyake damunta Allah yai mata magani, ni ba zan iya ba taje tai abunda ta ga ya dace da ita" Shikansa Huzaifa yana mamakin hali irin na Umman Farhan, kawaicinta akan Farhan yai yawa. Tabbas da Malam Zakari, wato mahaifinsa yana gari, da yaje ya sameshi yai masa magana, wataƙila shi ya iya shawo kan matsalar Farhan. Ɓangaren Lilly kuwa, se abunda yai gaba, Nazir ya maida ita tamkar matar da ya ba da sadaki ya aura, wasu lokutan taje har gida ta same shi, su sheƙe ayarsu, ba tare da iyayen ta sun san me take aikatawa ba. Sannu a hankali Nana ke ribatar Sadik, ta ke sanya shi kula da addini, mussaman Addu'oi, dan sam ba su dame shi ba ba yinsu yake ba. Wataran idan ya na jin mutunci, se aita abun arziki, idan kuma akasin hakane se su yita faɗa ba ze yi ba.   Zuwa yanzu Sadik ya zama popular Sosai a cikin makaranta ba bu wanda be san shi ba, saboda harkar ƙwallon ƙafan da yake yi. 4months later. ******************* Tsaye yake a jikin mota, ya zuba mata ido, ko ƙiftawa ba ya yi. "Dan Allah ka dena kallona" tai maganar tana haɗe rai. "Dole in kalleki Farhan, na rasa yadda zan yi da ke, kin ƙi yadda da wancan lamarin, nace miki muyi Aure amma shima kin ƙi yadda, na rasa in da kika sa gaba, ki tausayamin haka mana" Ta ɗago idanunta da su kai mata nauyi, ta zuba masa Sannan tai wani irin ƙasaitaccen murmushi, tare da ɗan tura baki tace "ka bani dariya, wai ka rasa gane in da na sa gaba, ni nace maka zan aure ne? Ai ban isa Aure ba ni" "Haba Farhan, ya zaki ce haka? Wannan wace irin Magana ce, ba ki isa Aure ba amma kike yawo?" Ta ɗan tsuke fuska tace "Wannan kuma wani dalili ne na daban, da na barwa kai na sani, ka ga If you are tired, juts leave me ni ba zanyi Aure ba, dan babu shi  a tsari na" Yai ajiyar zuciya yace "shikenan, amma ba zan iya rabuwa da ke ba, bari in tura miki kuɗi kya sa kati" Ba tace Komai ba ta ɗauke kanta zuwa kallon wajen motar da suke ciki. Wayar hannunta tai vibrating, alamar saƙo ya shigo, ta duba taga kuɗi ya turo mata, dubu hamsin wai ta sa kati. Murmushin ƙarfin hali tai, ta buɗe motar ta fita ta nufi cikin gidan su. A ƙofar gida ta tarar da Abba, shi da baƙo, ta gaida baƙon nasa sannan ta wuce cikin gidan. Ta na kallon Umma a tsakar gida, ko uffan ba tace mata ba ta wuce ɗakinta, ta zauna tana jujjuya kuɗin da Wannan saurayin na ta me suna Nura ya sa mata, ta duba account balance ɗin ta, kuɗi fal a cikin account ɗin, amma ita kanta ƙyamar kuɗin take, ga kuɗi a account ɗin ta amma sun kasa ba ta farinciki. Babban abunda ke rage mata damuwa shine shaye shaye, yanzu zuwa anjima wani hamshaƙin attajirin ɗan siyasa ne ze zo su fita, shine yake ɓata ta da kuɗi, tun da ta faɗa wannan mummunar harkar take haɗuwa da Samari kala kala, duk da tarin ƙuruciya da ƙarancin shekarunta, amma a haka maza ke binta.   Sallamar Abba da ta ji a ƙofar ɗakinta, ya sa ta dawo hayyacinta, ta amsa masa tare da gyara zamanta. Abba ya shiga ɗakin, ba tare da ya kalleta ba yace "nace a cikin manemanki wa kika turo gurina?" Farhan ta kalli Abba tace "Abba ni ban turo maka kowa ba" Yace "wani mutum yazo gurina, neman Aurenki, kuma da alamu mutumin kirki ne da gaske yake" Farhan tace "Abba ban turo kowa ba gaskiya, kuma ni gaskiya Abba bana buƙatar yin Aure a yanzu" Abba ya dubi Farhan yace "se zuwa Yaushe? Haka zaki cigaba da zama kina zubar min da mutunci a unguwa? Wannan yazo gurinki anjima wancan yazo, in ta raya miki ki bar gida ki kwanaki a waje, kina min adalci kenan?" Farhan ta miƙe, ta dawo gaban Abba tace "Abbana, da zan tona maka zuciyata na san zaka tausaya min, kai kaɗai kake jin tausayi na, tunda Allah ya saukar min da ƙaddarar nan, ba ka taɓa buɗe baki ka aibata ni ba, saɓanin uwar da ta kawo ni duniya. Abba ka sani, babu mutumin kirkin da ze bari ɗansa ya Aure ni, na sauka daga turbar da ka ɗorani, na kama wani layi na daban, amma Abba kasani Addu'ar ka tana tasiri a kaina. Bayan suna na da ya ɓaci a unguwar nan, duk wani mutumin kirki da ya zo neman Aurena, se an hana shi, kuma ba kowa ke min haka ba se Sunusi, ya hana kowa zuwa gurina. Duk wanda suke zuwa gurina ba Mutanen kirki bane ba". Ta kamo hannnun Abba cikin na ta tace "dan girman Allah Abba kar kai min baki, kar kai min mummunar Addu'a, na sani zuciyarka na cike da takaicin lalacewa ta, Amma dan Allah Abba kar kai min baki, ka cigaba da yi min Addu'a, dan Allah kar ka tsaneni Abba, na rasa soyayyar uwa tun da ƙuruciya, dan Allah kaima kar in rasa taka. Nasan ina ɓata maka rai, amma kar in mutu kana fushi da ni, Abba dan Allah kayi Magana". Ta ƙarasa maganar tana wani irin kuka me ban tausayi. Abba kasa Magana yai, se hawaye da ke bin fuskarsa, ya ɗora hannunsa akan Farahan yace "Allah yai miki Albarka, Allah ya shirye min ke, da dukkan 'ya'yan musulmi, na ɗau wannan abu a matsayin ƙaddara, dan haka zan cigaba da yi miki Addu'a insha Allah" Yana gama Maganar, ya fice daga ɗakin nata, yana share hawayen dake bin fuskarsa. Nana ce kwance a ƙasa, se juyu kawai take yi, ta rasa abunda yake mata daɗi, ita ba zafi take ji ba ita ba sanyi ba, ita dai gata nan gaba ɗaya zaman ƙasar nan ya isheta, shekara ɗaya da wani abu kenan, tana zaune a London, ba tare da taje gida ba, dan haka komai ma ya isheta. A haka Sadik ya dawo daga Makaranta ya tarar da ita, se cika take tana batsewa. Ya kalleta yace "Ikon Allah, yau kuma lafiya kike fushi ke kaɗai?" Ai yana rufe bakinsa se hawaye "Ni wallahi na gaji da zaman garin nan, haba dan Allah ai ko sau ɗaya Yakamata in je in ga gida, amma in ayi hutu ma sedai in zauna a nan gaskiya ni na gaji" "To yanzu ya kike so ayi?" Tace "Ni ka gayawa in Abba in anyi hutu dan Allah ya bani dama in koma Nigeria in huta, wallahi na gaji" Ya kalleta yace "in kunyi hutu, ni kuma ai lokacin ba muyi ba" Ta kalleshi tace "to kai ba se ka zauna ba, ni wallahi na gaji, idan hutun ya ƙare na dawo, kai ba se ka zauna a nan ɗin ba" Sadik yai murmushi, ya zauna a kusa da ita, ya rungumeta a jikinsa, yana kwantar da kansa a wuyanta, yai ƙasa da muryar sa yace "an kawoki ƙasar nan ki karatu ne, saboda kar in lalace kuma seki tafi ki barni, ba kya tsoron in lalace ko?" Nana ta tura baki tace "Lalacewa ta nawa kuma? Tun da nima ban sha ba, ni kawai gida zan koma" Sadik yace "to ba zaki koma ba, wa ze dinga kula da ni da min sauran ayyukan gida?" "Kayi da kanka mana" Sadik yace "Shikenan, tun da hakane, ki koma in ya so se a kawomin Khairat ta dinga kula da ni" "Abunda yafi Khairat za'a kawo maka, ɗagani" "To meye kuma na fushi, bayan ke kika ce zaki tafi" "To na fasa" ta faɗa tana murguɗa baki. Yace "Aikuwa se kin tafi, dama duk kin isheni, rigimammiya Kawai" "Ba zan tafi ɗin ba" tai maganar tana share hawayen fuskarta. Yai murmushi Sannan Yace  "Stop crying, zamu je hutu insha Allah, ni kaina ina son zuwa Nigeria, ji nake akwai wani mahimmin abu da Yakamata in yi, amma na manta menene, amma zamuje tun da haka kike so" Nana tai murmushi, tare da kwantar da kanta a na, Sadik da ke kafaɗarta. Shiru ya ɗan gudana a tsakanin su, sannan Sadik yace "ke ya naji Kamar jikin ki na ɗaukar zafi ne?" Nana tace "Wallahi nima ban sani ba, haka nan se in dinga jin sanyi sosai, se kuma zazzaɓi, se kuma anjima ya sauka" "Kuma ba ki gayamin ba, se ya kwantar da ke tukuna?" Nana tace "ai ba wani sosai yake kamani ba, shiyasa" Yace "duk da haka yakamata muje Asibiti a duba ki" Tace "to Besty, yadda kace, amma wallahi ba za'aimin allura ba" "Koma dai meya ya kama yi miki za'ai, insha Allah kuma Allura ce". "To ɗagani, tun da Mugun fata kake min" Sadik ya ƙi ɗaga ta se murmushi da yake faman yi. "Na shiga uku Mummy, cikina ciwo yake zan mutu, dan Allah ki taimaka min!" Mummy tace "Innalillahi wa innalillahi raji'un, na rasa wannan ciwon ciki da kike fama haka Lilly, bari in wa Peter magana, ya zo ya kaimu Asibiti. Sosai Lilly take kuka, tare da riƙe cikin ta tana wani irin murƙususu, idanunta duk suka yo warwaje! Littafin nan ₦300 ne kacal. 0009450228 Aisha Adam Jaiz Bank 07063065680 KO kuje manhajar AREWA BOOKS ku siya. domin kuwa ya fi sauƙi a can. Sosai Farhan ta zage, ta zazzage abunda ya daɗe yana ci mata tuwo a ƙwarya tsawon tasowarta, wanda ita kanta Umman ba ta san hakan cutarwa ne ga Farhan ɗin ba, ciki har da yadda ta ke nuna banbanci tsakanin ta da ƙannenta. Fuskar Farhan duk hawaye tace "Umma na azabtu da wannan al'ada da bata da tushe a addini, Rayuwata ta shiga cikin garari, da kina jana a jiki ƙila da kin nusar dani illar soyayyar RUƊIN ƘURUCIYA, amma baki haka ba se da bakin alƙalami ya riga ya bushe, kuma still kina sake ɗoramin laifi, ina roƙonki idan wani laifin nai miki, da ya sa kike min haka, Allah ya baki haƙuri, ki yafemin" Tana gama maganar ta tashi Fuuuuu za tai waje. Baban Huzaifa yace "dawo ki zauna ba mu gama maganar ba ai" Farhan ta dawo ta zauna tana sheshsheƙar kuka Baban Huzaifa ya ja ajiyar zuciya yace "gaskiya ɗan uwa kunyi kuskure, yanzu dama irin wannan rayuwar Yarinyar nan take haka? Na san muna karantawa yaranmu na fari, kamar yadda muma a kai a kanmu a zamanin mu, amma wannan zamanin idan kai haka akan yara dole su lalace" Cikin damuwa Abba yace "wallahi ɗan uwa, ba yadda ban ba akan ta dinga sassautawa yarinyar nan, amma ta ƙi gane hakan, bayan haka muna da matuƙar tsanani akan tarbiyyar yaranmu, mussaman ita da ita kaɗaice mace a cikin yaran, Allah ya nuna mana dabarar ka ba ita ke shirya maka ɗa ba, amma Alhamdilillah daidai gwargwado mun lura da tarbiyyar Farhan, se dai kam ta rasa soyayyar uwa da ja a jiki" Umma ta share hawaye tace "duk da haka wannan ba hujja ba ce, yaran da iyayen su suka mutu suka bar su fa?" Malam Zakari yace "wannan daban, wannan mutuwa su kai, amma ke kina raye tana kallonki kina kallonta, amma ba zata iya zuwa ta sameki ta gaya miki damuwar ta taji daɗi ba, gaskiya akwai matsala, kuma yanzu fisabilillahi kun san ba ta son wannan yaron amma kuka dage se kun aura mata shi?" Abba yace "wallahi ni ban san ba ta son shi ba, kuma ni ban niyyar yi mata aure yanzu ba ma, mahaifiyarta ce ta damu, ga surutu da aka fara wai ana gani ana kawota gida a Mota, amma ban taɓa sanin ba ta ƙaunar Yaron ba, kuma ni ban san tana son wani ba" Malam Zakari yace "Farhana kin ɓata rawar ki da tsalle, kin tashi yarinya me ilimi da addini, amma kalli yadda ki ka maida kan ki 'yar shaye shaye me zaman kanta, kinwa kan ki adalci kenan?" Farhan ta girgiza kai tace "Baba ƙaddara ce" Yace "ba ƙaddara ba ce Farhan, ganganci ne ke ki ka kai kanki, kar ki sake ɗorawa ƙaddara" "Baba, ni kaina ban san shaye shaye na fara ba, na fara ne da rashin iya bacci, ga damuwa na cin raina ji nake kamar kaina ze tarwatse, na fara neman maganin rage damuwa da saka bacci, har yunƙurin kashe kaina nai, Huzaifa ya hana ni, a hankali ya zamana idan ban sha abun maye ba, bana bacci, saitin zuciyata yai ta min zafi, nai haka ne duk dan in manta damuwa ta" "To yanzu ina shi Yaron da kike so ɗin?" Malam Zakari ya tambayi Farhan yana tsareta da ido. Tai murmushi me ciwo tace "ba Soyayya ba ce, RUƊIN ƘURUCIYA ne, hadda Soyayyar sa a cikin abunda ya jefani a damuwa, mutane sun sha gayamin Soyayyar mu RUƊIN ƘURUCIYA ce, amma na kasa yadda, ya jani a jiki, yana son farinciki na yana gudun damuwata, yana bani kulawa, na saki jiki da shi na sakankance, se ji nai yayi Aure ya tafi karatu ƙasar waje, ga shi ni kuma za'a Auran wanda ban taɓa ƙaunarsa ba a raina ba" Abba yace "a ina shi Yaron yake ɗan waye?" Farhan tace "Abba dan Allah a bar maganar nan, wallahi ba na son tunowa da shi, ni dai ku cigaba da yi min Addu'a Allah ya shirya ni ya sa in dena abunda nake" Abba ze kuma magana Malam Zakari ya girgiza masa kai alamar yai Shiru ya kalli Farhan yace "munji duk bayanan ki, an miki ba daidai ba ta wani fannin amma ta wani fannin ke ma me laifi ce, yanzu kiyi ƙoƙari ki tuba ga Allah, ki dena wannan yawace  yawacen da kike, bin maza baze haifar miki da ɗa me ido ba" Yaita yiwa Farhan Nasiha, ta sunkuyar da kai tana sauraren sa, yai ya ƙare Sannan ta miƙe, ta fita waje, kayan Abinci yara suka dinga shigowa da su, suka tsaya suka bi kayan da ido, Farhan ta dawo cikin gidan, Abba yace "wannan na menene?" Farhan tace "kayan Abinci ne Abba na kawo muku" Umma tace "ba zamu ci kayan haram ba, ki kwashe kayanki" Farhan tace "Umma ta ya kika san kayan haram ne? Kyautar su aka bani nima, amma bana haram bane dama kayan al'umma ne nima aka bani, Allah ya nunan lokacin da Umma zaki bani kariya ko inga soyayya ta a cikin idanun ki, ko naji abunda 'ya'ya suke ji" tana gama faɗin haka tai waje,se ƙarar kunna mota suka ji, ko a ina ta samo mota har ta iya tuƙawa da wannan ƙananun shekarun naat oho mata. Malam Zakari yai taiwa Umma Nasiha akan tai haƙuri da halin da Farhan ta shiga, ta janyota a jiki, ko Allah ze sa a samu ta dawo hanya. Ita Umma har ga Allah lokacin da ta haifi Farhan, tana ƙaunar 'yar ta sosai da sosai, sedai a garinsu ta haifeta, kuma seda Farhan tai wata uku Sannan ta dawo, tun a can garin dama sun saba, ɗan fari ba a jansa a jiki sam. Kuma ga ƙarancin shekaru lokacin, da tai wani yunƙuri na bawa Farhan kulawa se ayo caaa a kanta ana cewa ba ta da Kunya, ko Shayar da Farhan ba ta iya sakin jiki tayi, a garin gudun kar tai wani abu da zesa ace tai rashin kunya, ta fara watsi da lamarin Farhan, se ta ke ganin ai Kamar ba'a san ɗan fari ne, dan haka har suka dawo gida sam ba ta wani kula da Farhan. Watan Farhan biyar ta samu wani cikin, dan haka tai ta fama da laulayi, daga can garinsu aka zo aka tafi da Farhan, aka yayeta tana da wata takwas, wataran Abba yaje duba Farhan a garin, ya tarar ba ta da lafiya kuma anƙi kai ta Asibiti se jiƙe jiƙe ake mata a gida, aiko yace da ita ze tafi, an kai ruwa rana  sosai da Abba, tare da ƙananun maganganu akan rashin ta ido da ya nuna, dan seda Auren ya so ya samu matsala. Umma taji haushin Abunda Abba yai Sosai, a cewarta ya zubar mata da mutunci a rigarsu. Hakan ya sa ba ta wani bi ta kan Farhan, tana fama da laulayinta kusan Abba ne yakewa Farhan Komai, a haka har Umma ta haihu, ta haifi Amir aka sa masa sunan mahaifinta, nan ta ɗau ƙaunar duniya ta ɗora akan Amir, amma ba ta damu da Farhan ba, a haka Farhan ta tashi. Wani uban gumi ne yake ketowa Sadik, tun bayan da sakamakon gwajin da akai wa Nana ya tabattar da tana da juna biyu har na watanni uku da sati biyu, idan lissafin sa daidai ne, to a karon farko da ya kasance da ita ta samu cikin turƙashi!. Ya san akwai daru na gaske, idan har Nana ta san tana ɗauke da juna biyu, shi kansa wata irin kunya ce ta kama shi, da wani ido ze kalli iyayensa musamman Mother, da ta ke ta kumfar bakin ita ɗanta be isa Aure ba, ga kashedin ta a gareshi na babu ruwansa da Nana. Da wani idon ze kalli Inna, da ya gama ce musu baya son jikarsu, katsam se su koma a ganta da ciki, ya fito da niyyar tafiya pharmacy ya karɓo magunan da likita ya tura musu, yaje ya karɓa, ya hangi Nana tana ta ciye ciyenta hankalinta a kwance tana kalle kalle, gaba ɗaya ƙuruciyarta ta sake fitowa Yarinya ce sharaf, chocolate ɗin da take sha, duk ta ɓata gefen bakinta da ita, kuma hankali kwance take sha, tan kaɗa ƙafafuwan ta. Sadik ya kalli kamsa a madubi, shi kamsa kunyar kansa ce ta kama shi, as he is, he impregnent this little girl Subhanallah, abun kunya ya afku. Yaje ya karɓo mata maganin, ya zo in da take zaune ya kalleta yace "taso mu tafi gida" Ta ɗan ɓata fuska tace "ɗan yi haƙuri in ƙara hutawa, ƙamshin Asibitin ne yai min daɗi" "Meye abun so a nan, ban da warin magani ba abunda Asibitin yake fa" Nana tace "Wallahi ni dai ya min daɗi" "Kimga ta so mu tafi, ko in barki a nan ina son zan shiga school ne, muna da training yau" Nana ta tashi ta bi bayan Sadik, suna tafe a hanya tana ta sashi kashe kuɗi, tace zata ci wannan tace za ta ci wancan, shikam abun duniya ya ishe shi. Tunani yake ta yaya ciki ze rayu a jikin Nana, da wani idon za su kalli iyayensu idan sun koma gida?" Suna zuwa gida, Nana tun a falo ta cire kayan jikinta, ta bi lafiyar kujera ta kwanta, dan abu kaɗan yanzu se ta ji ta gaji, Sadik ya ɗan ƙurawa cikin ta ido, tabbas cikin ta ya ɗan ɗaga. "Wai ya na ga kana ta kallona ne, Lafiya kuwa?" Yace "Lafiya ƙalau" Tace "yawwa, ni ba ka gayamin me ma sukace ba fa" Ya ɗan yi ajiyar zuciya yace "ba su ce komai ba, magunguna ne ga su nan in kin tashi shiga ɗaki seki tafi da su" Nana tace "to, amma meye yake damun?" "Malarai ce kawai" "Malarai kuma? A ina sauro ya ganni ya ciza, ai nan ƙasar babu sauro, ta yaya na samu malarai?" Nana kenan, akwai shegiyar tambaya da kaifin basira. Sadik yace "ke bana son yawan surutu, da wannan tambayoyin naki, typhoid ne kawai, da Ulcer kuma sunce idan ba kya cin Abinci mutuwa zaki, hanjinki ya tsitsinke" Zare ido Nana tai tace "Na shiga uku, wani irin hanjina ya tsitsinke kamar taliya, wannan ai ba maganar da ya dace a gayawa mara lafiya bane" "Ai in dai ba zaki kula da kan ki ba, ki maida kai ki dinga cin abinci ba, abunda ze faru da ke kenan" "To ni ba amai nake ba idan naci, ba abunda ze sameni Insha Allah, ji min mutane da kalen tsiya" tai ta mitarta, Yayin da Sadik gaba ɗaya jikinsa a sanyaye yake. "Lilly ki gayamin Wanda yai miki cikin nan tun kan mahaifinki ya dawo, wallahi idan kika bari ya dawo daga ni har ke mun shiga uku, ki gayamin waye?" Sosai Lilly take kuka tare da girgiza kai, amma ta kasa furta komai, se hawaye da ke zuba daga idanunta, ga wani uban gumi da ta haɗa, kamar me naƙuda. Cikin zafin zuciya Mummy tace "zaki gayamin ne ko sena danne ki na shaƙeki, kan shi ya dawo ya kashe ki?" "Mummy ban sani ba wallahi" Lilly tai Maganar da ƙyar kamar numfashinta ze ɗauke. "Ƙarya kike munafuka, shegiya maƙaryaciya, ni zaki rainawa hankali, likita ya tabbatar min da ba wannan ne karonki na farko ba, wai Lilly har kin san ki ɗau ciki ki zubar, a wannan ƙananan shekarun naki Lilly, zaki gayamin waye ko sena yanka ki" "Wallahi Mummy ban sani ba" tai maganar tana ja da baya. "Kika kuma cemin ba ki sani ba, sena gwara kanki na fasa miki kai, ni zaki wa ƙarya? A ruwa kika sha dan ubanki? Ko a iska kika shaƙa, wane tsinanan ne yai miki ciki, zan farke wannan ɗinkin da ke jikinki idan baki gayamin gaskiya ba" Mummy tai maganar tana shaƙo wuyan Lilly. Jikin Lilly na wata irin rawa, laɓɓanta se kakkarwa suke, ga gumi da yake ɗiga daga jikinta tamkar ana narka mai, ta janyo numfashinta da ke barazanar barin huhunta tace "zan faɗa miki Mummy, zan faɗa amma dan Allah kar ki kashe ni, ki cikani ba na iya shaƙar numfashi" Tai jifa da Lilly a gurin, take Lilly ta fasa wata uwar ƙara, ta dafe cikin ta in daa a kai mata aiki, abunka da uwa, nan da nan kuma hankalin Mummy ya tashi, ta yo kan Lilly da gudu tana taɓata. Tana duba gurin da a kai mata ɗinkin, taga yana tsatsafar da jini, alamar fama gurin tai, da fari ji tai kamar tai banza da ita ta ƙyaleta, amma taji ba zata iya ba, haka ta ɗau mayafi suka koma Asibiti. Se da aka sake dressing ɗin gurin, likita yai ta mita yace "Hajiya, ki kwantar da hankalinki wannan abun ba akan ku aka fara ba, sakaci ne dai an riga anyi shi, aikin gama ya gama, duk wata tuhuma da za kuyi mata, ku bari ta warke ta samu Lafiya tukuna, idan ba haka ba, zaku mayar mana da aiki baya ne, idan tana famawa gurin baze warke da wuri ba" haka yaita faɗa sannan ya sallame su suka koma gida. Lilly ta rasa in da za ta saka ranta, dan gaba ɗaya Mummy tai watsi da ita ba ta shiga harkarta, gashi ta kashe wayarta, duk wanda yaji labarina ba ta da lafiya ya zo dubiya, se ace ai appendicities ne yake damunta a kai mata aiki. Faruk ne ke kwance yana video Call da Sadik, "Autan Mother, wai dan Allah me kake ci ne haka, ka wani zama ƙato Kamar ba kai ba" Sadik yace "hutu da kwanciyar hankali mana" "Lallai kam, kai karatu yana sa mutane su rame, amma kai ka zama ƙato, ni ba ka ga yadda duk na rame ba?" Sadik yai murmushi yace "ni da kai ɗaya ne? Ko ka manta ina da Aure ai akwai banbanci" Faruk ya kwashe da dariya yace "kaga ɗan banza, ni zaka gayawa Magana, wai kana da Aure, kamar ba kuka ka dinga yi kana cewa kai ba ka so ba" Sadik yai dariya yace "to yanzu ina so, ya ranka?" Faruk yace "rai na fes, ina Nanan?" "Wai ina ruwanka da mata ta ne?" "Allah ya shirye ka Sadik, na san wataƙila Mother ta kusa ɗaukan jika ko?" Gaban Sadik ya faɗi, amma ya maze yace "Ni yaro ne gaskiya, akace Mother za ta ɗau jika daga gurinmu ai kashin mu ya bushe" "Ba wani kashinku ya bushe, Kamar ba nan ka ke zuwa ka sameni kake gayamin wai kai Aure kake so ba, kai akwai wadda ka ke so something like that" Sadik yai shiru ya fara tunani, wace ce yake so to? Kamar wani abu ya taɓa faruwa, amma ya kasa tunawa. "Friend, wai me kake a ɗaki ne, ka zo ka taya ni kwalemar falon nan" Sadik ya kalli Nana yace, zo ku gaisa da Faruk. Murmushi Nana tai ta ƙaraso ta kwanta a jikin Sadik tace "Yaya Faruk ya kake?" Faruk yace "Lafiya ƙalau Nana, ya karatu?" "Alhamdilillah, Yaushe zaka zo ka ganmu"? Faruk yace "Nana ina Makaranta nima, tunda na tafi bana samun lokaci isashe, amma na so zuwa nima in ganku" Nana tace "Allah ya temaka, ai mun kusa zuwa Nigeria hutu, ko Friend?" Tai maganar tana kallon Sadik. Sadik yace "yaushe mu kai haka dake?" "Kai ne fa kace zamu je Nigeria in kunyi hutu" "To mun fasa" Hararar Sadik tai tare da tura baki, Faruk ba ƙaramin farin ciki yai ba, ganin Sadik da Nana suna cikin kwanciyar hankali, da alama babu wata damuwa a tare da su. Faruk yace "mhmm, nikam se anjiman ku, naga abun naku bana ƙare bane" Sadik yace "Allah sarki Gwauro, ka huta lafiya muma bari muje muyi feeding ɗin juna" "Kaci ubanka ne, nine gwauro ko? Zan kama ka ne" Sadik ya ajiye system ɗin tare da ɗan lumshe ido. Nana ta kalli Fuskar Sadik, zuwa ƙirjinsa, wani kwantaccen gashi ya fito a ƙirjinsa, gashi gemu ya fara fitowa a haɓarsa. Murmushi tai, ta kai hannu gemunsa ta shafa Sannan tace "su friend an girma, mun fara gemu irin na Yaya Faruk" Buɗe idonsa yai ya kalleta yace "Au ke haryanzu a gurinki ban girma ba?" "To ai se mutum yai gemu, Sannan ya zama babba, Allah yasa kai ma naka yai yawa kamar irin na Yaya Faruk" "Hmmm, kina son gemu ne?" Ta jinjina masa kai alamar eh. "To daga yau ba zaki sake gaisawa da Faruk ba, tun da gemunsa burge ki yake" Ta ɗan ɓata fuska sannan tace "daga na ce Allah ya sa gemunka ya zama irin nasa shine kuma abun Magana?" "Eh ɗin, ɗagani ma" Ƙara narke masa tai a jiki tana kukan shagwaɓa tace "ni fa bance yana burgeni ba, kawai cewa nai Allah yasa gemunka yai irin nasa" "To naji, amma daga yau kar wanda ya ƙara burgeki in bani ba, kin ji ko?" Tace "to naji" "Good girl" yai maganar yana murmushi. Tsaye yake a bakin gate ɗin gidan, yana ƙarewa layin kallo, yana tuna Yaushe rabonsa da layin, komai yana nan yadda yake, a guje yaga an fafaro wata farar mota vibe, wata uwar ƙura ta tashi a layin, mamaki ne ya kama shi, yabi motar da kallo yana tunanin waye wannan yake gudu irin haka, a wannan ɗan ƙaramin layin?. Mamkine ya kama shi ganin wadda ta fito daga motar, se dai yana tantama anya wadda yake tunanin ce?. Sunusi ne ya sha gaban Farhan, ta fito daga cikin mota, sanye da riga da skirt mayafinta a hannu, da jakarta. "Yanzu Farhan wai ba kya jin kunyar yawon da kike a gari haka?  Haba Farhan kiyi haƙuri ki zo mu sasanta in rufa miki Asiri, muyi Aurenmu ni haryanzu ina sonki wallafa" "Lallai, ya tabatta ka haukace Sosai da sosai, kalleni ka sake kallona, ko a lokacin da aka amsa za'a baka Aurena kai ka san ni ba sa'ar Aurnka ba ce, yau Da ace kai mutumin kirki ne zan iya haƙuri in Aureka, amma mutumin banza irinka, mutum na farko da ya fara haɗani da iyayena, da in Aureka gara in ƙare rayuwata a titi ba Aure" "Ke har ni zaki gayawa Magana, kina karuwa wulaƙantacciya, dama niyyar caka min ke a kai, Allah ya rufan Asiri" "To tun da Allah ya rufa maka Asiri ba a caka makan ba, wani munafuncin ne ya sa ka zo kake cewa in Aureka?" Ta daki jikin motar da ƙarfi sannan ta nuna Sunusi tace "wallahi idan ba ka fita daga sabgata ba, sena sa an casa min kai wallahi, sakarai ƙazami kawai" galala Sunusi ya bi Farhan da kallo tare da mamakin maganganun ta. Cikin Azama Abbas ya shiga cikin gidan Hajiya, yana ƙwala mata kira. Hajiya tace "Subhanallahi, wane irin kira ne haka Abbas? Daga dawowar ka ka zo mu gaisa, seka dinga min wannan kiran?" Ajiyar zuciya Abbas yai yace "yi haƙuri Hajiya, wallahi wani abu ne ya ɗan rikita ni, barka da gida" "Yawwa barka, shigo" Abbas ya shiga falon Hajiya, ya tarar da manya manyan kuloli da ta shirya masa Abinci, kwanansa biyu da dawowa, yau ya shigo gurin Hajiya. Suka zauna su ka gaisa, tana masa ya hanya ya karatu?. Ya nisa yace "Hajiya, wata na gani kamar Farhan, amma ina tantama, a mota na ganta da shigar da ban taɓa ganinta ba ba hijjabi a jikinta" Hajiya tace "kai dai bari Abbas, zancen ne ba daɗi" "Hajiya, ba daɗi kamar yaya? Meke faruwa ne?" Hajiya tace"zancen babu daɗi Abbas, abunda a kaita gufunyne dai, yanzu Farhan ta canza daga yadda ka santa, ba a samu ɗaura Aurenta da wannan yaron ba, kamar dai yadda kai ta gargaɗi da gudun karta shiga wani hali, amma dai Allah be ba abun da ake gudun ya faru" Abbas yace "Innalillahi wa innalillahi raji'un, Hajiya meyasa baki gayamin ba, amma tukuna wai ma meya faru da ita ne?" "Yawon banza Abbas, ga kuma shaye shaye, dan tun a ranar ɗaurin Aurenta tayi mankas, ba ta san me take ba" Hannu bibbiyu Abbas ya saka ya dafe kansa, yana sauke numfashi. Ya ɗago yace "Hajiya, iyayen Yarinyar nan ba su yiwa kansu adalci ba, Allah ya basu nutsatsiyya yarinya, amma sakaci ya sa sun bar rayuwarta ta gurɓace" "To kowa da irinsa ne, aikin gama ya riga ya gama sedai a tayata da Addu'a, Allah ya shirya" Abbas kasa cewa komai yai, ya shiga cikin damuwa sosai, gaba ɗaya hirar ma sama sama su kai da Hajiya, Abincin ma kaɗan yaci, yaiwa Hajiya Sallama yace tafiya zeyi. Haryai niyyar hawa motarsa ya tafi, amma ya hangi motar Da ya hangi Farhan ta zo da ita ɗazu. Ƙofar gidan su Farhan ɗin ya nufa, yana nan tsaye yana kallon Motar, sega wani Almajiri ze wuce, yace ya shiga gidan yace ana sallama da Farhan. Tace Ba za ta zo ba, shine amsar da yaron ya bawa Abbas, yace inji Farhan. Guri ya nema ya zauna akan wata baranda, yana ta juya tare da mamakin yadda Farhan wai ta koma yawon banza. Yana nan zaune sega Farhan ta fito cikin wata haɗaɗiyar purple ɗin abaya, ta sha duwatsu Fuskarta tai fresh, tare da bayyanar da tsantsar yarintar ta. "Assalamu alaikum" shine abunda kunnuwan Farhan suka jiyo, fasa buɗe motar tai, ta waiwayo ga mamakinta se ta ga Abbas a tsaye. Faɗaɗa murmushin ta tai tace "Saukar Yaushe ba labari?" Murmushin ƙarfin hali yai yace "kinyi mamakin ganina ko? Tun shekaranjiya na sauka amma se yau na shigo unguwar ta ku" "Masha Allah, ka kammala course ɗin kenan?" "Eh na kammala Alhamdilillah, dan se da na ƙara watanni ma na huta sosai" "To Allah ya Sanya albarka a abunda ka karanta, yasa al'umma su amfana" Abbas yace "Ameen ya hayyu ya ƙayyum, nace in ba damuwa ko in zo in rakaki in da zaki?" Ta girgiza kai tace "a'a Nagode" "Meyasa ba kya son rakiyar tawa?" "Haka kawai" ta bashi amsa. "Ban taɓa tunanin zan dawo in ganki a wannan yanayin ba Farhan, why? Garin yaya haka ta faru?" Farhan ji tai kamar ya soso mata in da yake mata ƙaiƙayi se hawaye. Ya ɗan matsa gabanta yace "Farhan why? Kalli yadda kika maida rayuwar ki, kina ɗaya daga cikin wanda ake kwatancen nagartattun yara ne masu tarbiyya a unguwar nan, meyasa kika zaɓi canza akalar waccan rayuwar zuwa wannan me munin?" Ba ta ce masa uffan ba, tana kuka ta buɗe motar, ta shiga ta tafi. Abbas ya daɗe a tsaye yana jinjina lamarin, Farhan Just needs guidance and counseling to save her, and he promised to do so for her, saboda yana matuƙar jin tausayin ta. "Sadik dan Allah kai min magana, a tsorace nake amma na gaya maka abunda ke damuna ka ƙi kulani" Sadik yace "to me zance miki?" "Kalleni fa, kalli yadda na koma, na zama wata ƙatuwa, wallahi wani abu ne yake min yawo a ciki na, kuma kalli cikin ƙara girma yake dan Allah ka mai da ni Asibiti" tai maganar cikin kuka. 'malama karki ɗaga min hankali, Abincin da kike ci ne yai yawa, shiyasa cikin yake girma" "Ni yaushe nake cin abinci balle cikina yai girma, shikenan wata Cutar ce ta kamani, dan Allah ka maida ni Asibiti" "Ke, ciki ne ba wani abu ba" ya bata amsa kai tsaye. Saroro tai tana kallon Sadik, se taji kamar ba ta ji daidai ba, tace "me kace?" "You Are pregnant, abunda likitoci suka gayamin kenan wancan lokacin da muka je Asibiti, You Are four months pregnant" "Innalillahi wa innalillahi raji'un, Ciki ne dani? Na shiga uku na lalace" "Ke meye haka? Wace irin magana ce haka kin shiga uku kin lalace" "Ban sani ba, shikenan ka gama da rayuwa ta, ya zanyi da ciki Sadik? Kawai se in koma gida a ganni da ciki na shiga uku, wallahi se an zubar da shi lalacewar tai min yawa" Wani Mugun kallo Sadik yaiwa Nana yace "mutuwa zaki a banza, ƙarafa za su sa miki a jiki, in aka zubar da cikin ki mutu a banza, wani Auren zanyi ni ba ruwana" Nana ta sake ɓare baki tana hawaye, har da majina tace "shikenan ka gama da Rayuwata, 'yar yarinyata da ni ace ina da ciki, shikenan na dena zuwa Makaranta, Inna kasheni za tai ta koreni daga ƙauye, ina zan sa kaina? Wallahi seka sakeni, ba zan cigaba da zama ba kana cuta ta" Sadik ya shafi sumarsa yace "Aikin gama ya gama Yarinya, ko na sakeki kin zama bazawara ba zaki taɓa komawa yadda kike ba, kuma ma abun tausayin da kike bani, 'ya'ya biyar ne a cikin na ki, Allah sarki shikenan zaki zama Mama, ga 'ya'ya na binki ba karatu ba gayu, inje a kuma Auramin wata gallaliyar Yarinyar. Kuma wallahi ki kai wani ganganci akan cikin nan sena ɓata miki rai" "Na shiga uku ni Asma'u, wallahi ka gama dani, Allah seya saka min wallahi, kuma nasan mutuwa zan yi, ta ina 'ya'ya biyar za su zauna a cikina, shikenan ratuwata ta zo ƙarshe" Sadik ya rungumota jikinsa yace "Allah sarki, nima kin bani tausayi wallahi, ɗan yaron mijinki ya jefaki a wani hali sorry baby" yai maganar yana mata dariyar mugunta. Yayin da gefe guda kuma zuciyarsa cike take da zullumin yadda ze fuskanci wannan ƙalubalen da ke gabansa, na bayyanar ciki a jikin Nana. COOL CE Contact me at 07063065680 to subscribe, at affordable price or visit Arewabooks to purchase. Kafin Lilly da mamanta su ƙaraso tuni major yai umarni aka ja motar, aka barsu a nan, ƙarshe se daidaita sahu suka hau zuwa gida. Suna tafe Lilly na kuka, a fusace Mummy tace "ki rufen baki ko in jefaki kan kwalta dan uwarki, kalli halin da kika jefamu a ciki, ƙanƙanuwarki da ke wai kin san ki bi namiji har yai miki ciki ki zubar, turr da halinki" haka Mummy tai ta mata masifa har sukaje gida. Suna zuwa gida suka shiga falo, suka tarar da Major yana muzurai, a fusace yace "ban ce karki dawo min da Yarinyar nan gida ba? Tun wuri ki san in da zaki kaita ta barmin gida" "Wasa ma kenan, ai kaima kasan wannan Magana faɗa kawai kake, ina ka ke so in kaita?" "Duk in da ki ka ga ya dace, tun da a garin sokoncin ki da hauka, kika bari harta ke yawo baki sani ba, kina uwa 'yar ki na bin maza amma kika gaza ganewa" A ƙufule Mummy tace "haramun ne kai a matsayinka na ubanta idan ka gano hakan? Ina ni da ita duk a ƙarƙashin ka muke, alhakin kula da mu a wuyan ka yake, ko kuma ni kaɗai Allah ya ɗorawa Alhakin kula tarbiyyar yaran?, su sauran da nai tarbiyyar su har su kai Aure, ka taɓa zaunar da ni kace ka gode naiwa yaranka tarbiyya ba su lalace ba, se yanzu dan wannan ta lalace zakace inje in san yadda zan da ita, 'yar ka ce kaima zaka iya ɗaukarta ka kaita duk in da ka ga dama" "Ni kike gayawa haka?" "Na gaya maka ɗin, akan me zaka ɗaga min hankali? Bari in tuna maka wani abu da kake ƙoƙarin mantawa, barewa ba ta gudu ɗanta yai rarrafe, a yawace yawacen aikinka kai meye ba kai ba, ko ka ɗauka ka ci bulus ne? Better get back to your sense, ka ɗau mataki a cikin hankalinka, kar ka yanke hukunci cikin fushi abunda ba kai zato ba ya biyo baya" Sororo Major yai yana kallon Mummy, tai wucewarta ɗaki ta bar su a tsaye shi da Lilly. Wata uwar ƙwafa yayi, sannan shima ya bara falon, Lilly ta durƙushe a gurin tana kuka, tabbas koma meyafaru ita ta janyo shi, ta ɗora laifin kacokan akanta, take taji nadamar abubuwan da ta aikata suka baibaye ta, shikenan yanzu ba ta da sauran wata kima da mutunci, ta zubar da su a dalilin banza da na wofi, yanzu Allah ne kaɗai yasan matakin da mahaifinta ze ɗauka a kanta. Abbas mussaman yaje har gida yai sallama da baban Farhan, Abba baze manta da Abbas ba, duba da irin taimakon da yai lokacin rashin lafiya Farhan. Abba cikin fara'a ya saki fuska suka gaisa da Abbas, yake ce masa "Nikam yaushe rabon da in ganka, harna manta" Abbas yai murmushi yace "da yake watana kusan goma bana gari, naje ƙaro karatu ne" Abba yace "Allah sarki, Allah ya yi jagora ya dafa" Ya amsa da Ameen Sannan ya ɗora da cewa "dama Abba na zo muyi magana ne akan lamarin Farhan" Jiki a sanyaye Abba yace "wani abun tai maka ne?" "A'a ko ɗaya, se dai in baka manta ba tun bayan rashin lafiyar ta, na baku shawarar sa ido akanta da kula da ita, sedai bayan dawowata banji daɗin yadda na tarar da ita ba, tun kan in tafi na lura akwai damuwa me yawa a tare da ita, tana cikin yanayi na son wani, ku kuma kuna yunƙurin aura mata wani, kuma ba zata iya yi muku musu ba. To a yanzu ma nai interview da ita, na gano meye damuwar ta, sedai ina son ku bani haɗin kai gurin ceto rayuwar ta" Abba yace "tayaya kenan?" Abbas yace "Masha Allah, dan Allah Abba duk da halin da take ciki a yanzu, na san baya muku daɗi, amma dan Allah banda tsangwama, kar a tsangwameta, ayi haƙuri a ja ta a jiki, yana daga cikin abunda ta rasa harta faɗa soyayya me zurfin gaske, rashin ja a jiki, da ba ta samu a gida ba shine taje ta samu a waje, wanda ya jefa ta cikin soyaya RUƊIN ƘURUCIYA" Abba ya nunfasa yace "hakane, dama ni ban tsangwameta ba, ina mata Addu'a ne Allah ya shirya ta, dama matsalar daga mahaifiyarta ne, kuma ita ma tayi nadama yanzu" Abbas yace "Masha Allah, sannaan abu na gaba shine, Abba nace idan ba damuwa ina Neman wata alfarma guda ɗaya a gurinka" Abba yace "wace alfarmar ce haka?" "Ina son ka bani Auren Farhan" Abba ya kalli Abbas yace "Malam Abbas ka san me kake faɗa kuwa? Ba ka ga yadda ta koma bane, ba Farhan ɗin da ka sani a baya bace ba fa" "Eh Abba na sani, ina son in temakawa rayuwarta ne, dan Allah ka duba lamarin" Abba yai shiru Sannan yace "komai nufi ne ne Allah, bana son sake maimaita kuskuren da nai a baya, amma ka nemi yardarta in dai daga gareka ba wata matsala kuma ta amince shikenan" Abbas yai murmushi yace "nagode Sosai Abba" Abba yace "bakomai, ka gaida gida" Su kai sallama da Abba, sannan ya nufi gidan Hajiya, se a lokacin wata fargaba ta zo masa, dan be san ya abun ze kasance ba, Hajiya za tai murna da hakan ko kuma zata ce ba ta yadda ba. Abba ya je wa da Umman Farhan abunda suka tattauna da Abbas Umma tace "Anya kana ganin wannan lamarin ze yuwu, Yarinyar nan ta riga ta ɓata rawarta da tsalle, ba na jin mahaifiyarsa ma za ta yadda" Abba yace "to, ni dai ba ni da ta cewa, na bar komai a hannun Allah, Allah ya iya mana" Umma tace "Ameen". Ranar gardaution ɗin su Tasleem, ana party a makaranta, ana ta kaiwa ana komowa, yara cikin shiga kala kala, ta arziki da ta banza, se cahsewa ake, ana ciye ciye da shaye shaye, labari ya karaɗa makaranta an kama sir Nazir, amma babu wanda ya san dalilin kamun nasa. Ba zato babu tsammani 'yan sanda sukai dirar mikiya a makarantar, aka kama Director makarantar, da principal, aka kama 'yan ajinsu Lilly, a nan 'yan Sanda su kai katarin kama su Nas da ƙwayoyi a jkinsu ranar graduation ɗin, dan haka aka tattarasu duk zuwa police station. Aka kori kowa gida, aka garƙame makarantar. A station director se masifa yake, wai anci zarafinsa ana neman a ɓata masa sunan makaranta, an kama shi da ɗalibansa anci zarafinsa. Aka shiga da shi wani Office, da sauran malamai aka zo da Lilly da malam Nazir, aka warware abunda yake faruwa a tsakanin su, ga kuma su Nas da aka kama da ƙwayoyi a wannan shekarun nasu. Nan aka shiga kiran iyayen yara suka cika police station, yadda aka faɗi da yadda Lilly ta lalace, ya bawa iyaye da yawa tsoro da Mamaki. Su kansu su Haseena da Yasmin akace ba'a yadda da su ba, se anje anyi musu screening tun da tare suke karance karancen, a nan allura ta dinga tono garma, dan a ɗaliban har da masu Implant a jikinsu, banda wanda aka samu da ciki, banda masu ɗabi'ar neman jinsin su (Subhanallah). Baban Lilly yace "baze bar wannan rashin Albarka ba, se an bi masa haƙƙin 'yar sa. Labari ya karaɗa gari, akan irin ta'asar da aka bankaɗo a wannan makarantar, wadda tai ƙauran suna akan makaranta ce ta yaran masu hannu da shuni. Abbas ne a gaban Farhan, ya zuba mata idanunsa, ita kuwa ta ɗauke kai gefe se tura baki take. Fitilar wayarsa ya sa ya haskata, ta sa hannu ta rufe fuskar ta ta saboda hasken fitilar. "Farhan" ya kira sunanta. Ƙin kallonsa tai gaba ɗaya. "Farhan, meyasa ba kya so na?" "Ni na ce maka ba zan yi Aure ba" "Meyasa? Kin fi so ki cigaba da rayuwa a haka?" Farhan tace "meyasa zaka auri ragowar wasu, ba ka cancanci Auren yarinya iri na ba" Abbas ya nisa yace "ke kika cemin ba kya zina ai, kuma ma ni ba wannan nake dubawa ba, makomar rayuwar ki nake dubawa" "Kai in ba abunda nake kenan ba, a ina kake tunanin nake samun maƙudan kuɗaɗe? A banza maza za su dinga bani kuɗi ne ba wani dalili, ai maza ba kwa abu dan Allah se da dalili" Abbas yai murmushi yace "kar ki mana kuɗin goro mana, ke dai kawai ki ce min har yanzu Sadik kike so" Take ta haɗe rai ta kalleshi tace "bana buƙatar ko sake jin sunan sa a ratuwata, dan Allah kar ka kuma sako min zancensa" "To in ba Sadik kike so har yanzu ba, meyasa ba kya so na? Na miki tsufa ko?" Murmushi tai tace "kai nagartaccen mutum ne, me tausayi da sanin yakamata, ni kuma 'yar shaye shaye ce kuma..... "Shhhhhh, ki dena wannan maganar dan Allah, keep it aside, ina sonki Farhan dan Allah ki bani dama na Aureki" Noƙe kafaɗa tai irin na yara tana sake tura bakinta gaba. "Ikon Allah, is all this for me? Ni in ki na hakan nan burgeni kike" Take jikinta yai sanyi, haka Sadik ma yake mata, yai ta cewa tana shagwaɓa, wadda ba ta san ta na yi ba. "To munafukin Allah ta'ala, ka zo duhu zaka cigaba da lalube min mata, wanda kai a baya be isheka ba, to wallahi babu me mallakarta tunda ban mallaketa ba" Sunusi ne tsaye akan su Farhan yana Wannan banbamin. Wani irin ɓacin rai ne ya baibaye Farhan, ta rasa yadda za tai tai maganin wannan katsalan dan da yake mata a cikin rayuwarta, ya hanata sakat duk wani motsinta akan idonsa, kuma se ya san yadda yai ya ci mutuncin ta. Abbas yace "dan Allah, kai kuwa me mu kai maka haka? Allah be yi ka Aureta ba, kuma seka dinga masifa wani baze Aureta ba?" Sunusi yace "ai wallahi yadda ban Aureta ba babu me Aurenta, in kaga wani ya Aureta se dai in bana raye, sedai ta ƙare rayuwarta a karuwanci amma ba dai tai Aure ba" "To Sunusi dan ban Aure ba se me, da dai in Auri sakarai irinka gara ban Auren ba, ka cigaba da min shishshsigi a cikin lamurana, zan sa ai min maganinka banza kawai" Sunusi ya gama banbamin masifarsa yai gaba. Abbas ya girgiza kai yace "dan Allah Farhan, duk sanda ya zo yana wannan abun ki dena kula shi, kuma kiyi ta addu'a, kar bakin nan da yake miki tai taisiri a kanki" Cikin rawar murya Farhan tace "tasiri kuma na nawa? Bayan yadda ya dinga aibata ni da bakinsa tun  a baya yana ɓatamin suna, na bar shi da Allah kawai, ka gaida gida se da safe" daga haka ta juya gida tana zubar da hawaye. Ba zato ba tsammani taji Umma ta shigo ɗakinta, ta zauna a gefen katifar Farhan tace "har ya tafi ne?" Idon Farhan duka hawaye ta kalli Farhan tace "lafiya kuwa?" Farhan tace "lafiya ƙalau" "Amma kike kuka?" "Umma bakomai fa" "Shikenan, nace to ya batun Abbas ɗin, shi kina son nasa?" "Umma nifa ba zan yi Aure ba" "Saboda me?" "Na ɗau darasi a Soyayyar RUƊIN ƘURUCIYA, sannan ga abunda ya faru da rayuwata Yanzu, gara in rayuwata kawai nika ɗai" "Yanzu kin zaɓi ki cigaba da yawo, Shekarunki ba sj kai sun kawo ba, amma kalli yadda kika maida kanki, Auren shine rufin Asirinki ai" Tsurawa Umma ido Farhan tai, a hankali ta matsa kusa da Umma, ta kwanta a jikin Umman, ta maƙalƙaleta kamar wani ze ƙwaceta sanann cikin hawaye tace "wannan nake buƙata Umma, idan da wannan ba na buƙatar wani namiji ya kuma shigowa rayuwata, kulawarki da addu'arki, dan Allah Umma ki dinga sona kamar yadda ake son kowane ɗa, ki dena tsanata dan Allah ina sonki sosai Ummana amma kin ƙi bani damar more Soyayyar uwata" tausayin Farhan ya mamaye zuciyar Umman, a hankali ta rungume Farhan ɗin, tai shiru tana jin yadda Farhan ɗin ke kuka cike da ajiyar zuciya. Ya zubawa Nana ido da cikinta da ya fito sosai, ta ƙara ƙiba ga wani shape da tai, wani ɗan gajeren wando ne a jikinta da half vest, hakan ya sake bawa cikin nata damar fitowa ras. Se shirya musu kaya take a cikin akwati, cike da farinciki, se ta ɗago riga tace "Friend kalli, ni ina ga base mun tafi da wannan ba, ta dena shiga ta, kalli wannan wandon ma, duk son da nake masa, amma sedai kawai in ajiye ba ze shigeni ba" Ta kalli Sadik taga yadda yai zuruuu da ido yana kallonta. "Tunanin me kake ne?" "Mhmm, bakomai naga bakinki yaƙi rufuwa ne" Nana ta ɗan yi fari da ido tace "ta yaya bakina ma ze rufu, zan koma in ga Innata da Hakimina tsoho me ran ƙarfe, idan muka koma Nigeria ni da ƙasar nan se da ziyara" Ya kalleta yace "saboda me?" Ta ɗan yatsuna fuska tace "to idan na haihu da ɗan zan taho?" "Eh, da shi zamu taho" "Kuma se in dinga zuwa da shi Makaranta? Gaskiya ni ba zan dawo ba" Yace "ashe kuwa zaki zauna, ba tare da kin koma gida ba" ɗan haɗe rai tai ba tare da ta kuma cewa komai ba. Murna a gurin Nana kamar ta zuba ruwa a ƙasa ta sha dan murna da farinciki, yau ita ce za ta koma gida Nigeria, bayan shafe shekara guda da watanni ba tare da taje ƙasar tata ta haihuwa ba, seda sukaje gidan Steve su kai masa sallama, shine ya kaisu har airport, suka hau jirgi. Nana kam murna take tana lissafa kala kalar Abincin da za ta ci wanda tai missing, Sadik jinta kawai yake, amma tunanin artabun da za suyi da Mother kawai yake. Gefe guda kuma yana jin, wannan abun da yake damun zuciyarsa, wanda ya rasa ko menene, se Alla Alla yake su sauka ko Allah ze temake shi ya tuna wannan abu da yake damun zuciyarsa. Abba da Dr. Tuni suna airport, suna jiran saukar su Sadik, tun daga nesa Sadik ya taka da gudu yaje ya runume Abba yana Abbana i miss You. "I miss You too my lovely Auta" Usman yace "ji sha sha sha, se kuma ka bar mata dakon Akwatunan" Nana ta ƙaraso tace "gaskiya Akwatunan nan sun min nauyi, da wanne zan ji" Ta kalli Abba ta durƙusa har ƙasa tana gaishe shi. 'Abba yace Masha Allah, Mamana kinga yadda kika koma kuwa, Alhamdilillah ya karatu?" "Lafy ƙalau Abba, Uncle Usman ina wuni" "Lafy ƙalau ya school" Tace "School Alhamdilillah" Sadik yace "Abba ina Mother?" Abba yace "tana can tana ta shirin tarbar ku" haka suka rankaya zuwa gida baki ɗaya. Mother na jin ƙarar mota ta fito harabar gidan cikin hanzari, Khairat ta biyo bayanta tare da Jidda matar dr. Sadik da Mother suka rungume juna, cike kewar juna tana cewa "I miss You Autana" Nana kuwa se bin su take da kallo gwanin sha'awa tana murmushi. Cikin rawar jiki Nana take gaida Mother, amma Mother ta amsa a wulaƙance, Sadik ne kawa ya lura da abunda Mother yai, ya basar bece komai ba. Jidda ta rungume Nana tana faɗin "Masha Allah, Nana kinga yadda kika ƙara girma kuwa, lallai Sadik ya iya kiwo" Nana ba abunda take se yaƙe, dan ta san ba zasu samu jituwa da Mother ba, ta dinga fatan Allah ya sa a yau ba se gobe ba a maida ita ƙauye gurin Inna. Ma'aikatan gidan kansu se barka da dawowa sukewa Sadik. Suka rankaya zuwa cikin gida gaba ɗaya, Mother kamar ta maida Sadik cikinta saboda murna, Khairat ma se wani shishshsigi ta kewa Sadik, sedai ta lura Sadik ɗin yanzu ba irin na da bane, se wani basarwa yake yana kamewa. Suka gabatar da sallar la'asar, jikin Nana duk yai mata tsami, gashi ta kasa sakewa, ƙafafunta duk sun kukkumbura se sake duƙunƙunewa take ciki doguwar rigarta me haɗe da hijjabi, saboda kar a ga cikin nan. Aka baje kayan Abinci, fried rice ya sha kayan lambu se ƙamshi take, ga nama nan ya sha kayan ƙamshi da lemuka, duk saboda Dawowar Sadik, sedai fuskar Nana kawai Sadik ya kalla ya san ba tai na'am da wannan Abincin ba ba lallai ta ci. Ta dinga zuba zoɓo tana sha, amma ta ƙi cin Abinci. Sadik se kallonta yake gashi ba ya son yai wani abu da ze sa Mother, ta fuskanci wani abu a tsakanin su. Jidda tace 'Nana ki ci Abincin mana, naga se juya spoon kike" Sadik ya wani maze, Nana tace "ina ci fa Anty Jidda" Jidda tace "kunya dai kike ji, ko a kai miki ɗaki ki ci?" Abba yace "waye baƙonta a nan dan ƙaniyarta, ki zage ki ci Abinci Mamana" Nana kawai tai murmushi tana sunkuyar da kai. Yayin da Mother se wurga mata uwar harara, Sadik ya faki idon Mother yaiwa Nana alamar ta ci Abincin. Amma ta tura baki tana yatsuna fuska. Ta ɗau spoon ɗin ta fara cin abincin, se dai sam ba ta ji dadin Abincin ba, ji tai ma yana taso mata. Nana ta miƙe tace "bari inje ɗaki" Duk da rashin magana na Usman amma seds ya magantu yace "kamar a takure take ne, anya Sadik ba wani abun kake mata a can ba naga kamar duk a takure take" Sadik ya ɗan ɗage kafaɗa cike da basarwa, ya cigaba da cin Abincin sa ƙasan zuciyarsa kuwa so yake ya bita, yasan tana jin yunwa Sosai, kuma tunda ta ƙi cin Abincin be mata ba, da suna can ma haka take yi, in Abinci be mata ba ba zata ci ba. Nana kuwa se da ta amayar da Abincin da ta taci tas, sannan ta samu katifa tai kwanciyarta. Aka gama cin Abinci aka zauna hira, Mother tana gayawa Sadik yadda tai missing ɗin sa, har kusan sallar magariba ana zaune ana hira, yayin da hankalinsa yana kan Nana. Se da aka tashi, za'ai salla sannan Abba yace "wai ina uwata ne?" Jidda tace "tun ɗazu ta tafi ɗaki, wataƙila gajiya ce tai mata yawa" Sadik se wani basarwa yake irin be damu ba ɗin nan, amma a ransa kamar yai layar zana ya tafi gurin matarsa. Bayan sallar magariba, Jidda da mijinta suka shirya tafiya gida, Jidda ta leƙa ɗakin da Nana take, ta hango ta sanye da Hijjabi, alamar Salla ta idar. Tace "Amarya, mu mun tafi Allah huta gajiya" Nana tace "Anty Jidda tun Yanzu zaku tafi?" "Eh mana, naga kin zo kin ƙule a ɗaki ke kaɗai" Nana ta ɗan ɓata fuska tace "wallahi duk na gaji ne Anty Jidda" "Eyya sannu, gara da kika huta ai, seda safe" Nana tace "to Allah ya tashe mu lafy, ku gaida gida" Sadik ya faki idon Mother ta shiga sashin Abba, ya nufi ɗakin da Nana suka saba zama, in sun zo gidan. Ya tarar da ita kwance akan sallaya, ya ƙarasa ds sauri yace "lafiyar ki kuwa?" Ta kwaɓe fuska tace "yunwa nake ji, kuma wallahi se juyawa cikin yake ya hanani sakat" Yai ajiyar zuciya yace "to ai ina kallonki baki ci Abincin ba" "Ni ba irin wannan nake so ba, da naci ma se da nai amai" Yace "subhanallah, Allah ya sa ba aman nan ze dawo miki ba, amma me kike so to" "Tuwo, ko awara, ko wainar fualawa" "A gidan ubanwa zan samo wannan abunda kika lissafa?" Yai maganar yana hararata. "To ba yunwa nake ji ba, kuma naga ai ba yin kaina bane, ni in baza'a samu ba na haƙura in zauna da yunwa" Seda Sadik ya ja gajeren tsaki, dan be san ya ze wa Nana ba. Miƙewa yai ya bar ɗakin, ya wuce Kitchen ya tarar da Talatu me aiki tana wanke wanke. Ya kalleta yace "dan Allah baba Talatu, wainar fualawa nake son ki ɗan soyamin ko kaɗan ce" Ta kalli Sadik da mamaki, ta san sam wannan ba cimar Sadik bace, ba ya cin wainar fulawa, amma me ze sa yace ta soya masa wainar fulawa, amma a zahiri tace "yadda kace haka za'ai ɗan auta" ya ɗanyi murmushin gefen baki ya fice. Ya shiga ɗakinsa na nan falo an gyara shi tsaf, Abba ya fito falo shi da Mother yace "Auta wai lafiya naga gaba ɗaya uwata ta koma ɗaki ta takure?" Sadik ya ɗan ɗage kafaɗa yace "i dont know what's wrong with her" Abba yace "kirawota inji daga bakinta" Sadik ya nufi ɗakin Nana, ya tarar tana zaune tana game a wayarta, yace "ki fito falo inji Abba, amma dan Allah karki abunda zamu raba hali, bana son mother ta fuskanci wani abu, balle a zo ga maganar cikin nan" Maimakon tai magana sema sa hannu sa tai a baki tana bin Sadik da kallo. "Husna magana fa nake miki" "Ni wallahi yunwa nake ji, jiri ne yake kamani" "Dan girman Allah kiyi haƙuri, ki lallaɓa ki fito kar Asirin mu ya tonu a gano cikin nan" "Kaifa kace min ba wanda zece komai akan cikin, kuma yanzu kana faɗar wsni abu daban" Sadik yace "hakane, amma ai da kunya ace an ganshi yi haƙuri ki tashi muje" Da ƙyar ya lallaɓota suka fito falon. Abba yace "Nana, ko akwai matsala ne naga kin koma ɗaki ke kaɗai?" Nana tai murmushi tace "ba wata matsala Abba" "To Alhamdilillah, ya zamanku a London ya kasance ya kuma makarantar". Nana ta dinga amsawa Abba tanbayoyinsa, yana murmushi yayin da Mother ta haɗe rai tai kicin kicin. Daga baya aka kawo Abincin dare, jalop sphagetti, nan ma Nana ba ta ci ba, aka gama kowa ya watse, Sadik yana son ya kaiwa Nana wainar nan, amma Khairat na falo. Yana nan a ɗakinsa yana tunanin da suna can, da yanzu yana sa ta aiki tai ta masa hidima kan ta kwanta. Mother ce ta shigo da sallama, ya amsa tare da faɗaɗa murmushin fuskarsa, ta ƙarasa ta zauna a gefen gadon Sadik, tace "Auta yaya, ina fatan ba wata matsala?" Yace "matsalar me fa Mother na?" Tace "game da Auren nan naka?" Ya ɗan taɓe baki yace "ba wata matsala, me kika gani?" Ta ɗan yi shiru sannan tace "ban so Auren nan naka ya kai i Wannan lokacin ba, na so tuni kan ku dawo na lalata Auren nan, amma mahaifinka ya kasa ya tsare a kan lamarin Auren nan, amma duk da haka ba zan karaya ba, zan ga abunda yakamata ayi a kai, dan bana ƙaunar Auren nan" Sadik a ransa yace 'wannan shi ake kira da ihu bayan hari' Sadik be cewa Mother komai ba, har ta gama surutanta ta tafi. Tana fita ya leƙa ya ga ba kowa a falon, ya ɗau kwanon nan yaje ɗakin Nana, ya tarar da ita a zaune ta riƙe ciki tana kuka. "Menene kuma?" Ya tambaya yana leƙa fuskarta. "Yunwa nake ji" "To kuma se ki ta kuka, ga shi nan" ya dungurar mata da flask ɗin waina. Ta ja abunta ta fara ci, ji take nan duniya wannan wainar fulawa ta fiye mata Komai daɗi. Sadik ya zuba nata ido yana kallonta yadda take aika wainar nan ba ƙaƙƙautawa. "Ki ci a hankali kar ki ƙware malama" "Wai kai ina ruwanka da ni ne dan Allah? Ka ƙyaleni mana in ci cikin kwanciyar hankali" "To seki yi ai" Se da ta ci ta ƙoshi sosai, sannan hankalinta ya kwanta, ta kalleshi tace "Nagode sosai, Allah yai maka albarka kaji Abokina" "Kawai kin sani wahala" "Allah ya baka haƙuri, amma ai wannan ne ya sani" tai maganar tana nuna masa cikin ta. Sadik yai murmushi tare da shafar cikin nata yace "Husna ina son abunda ke cikin nan naki, fiye da yadda kike tunani" Murmushi tai masa tace "ka tashi ka tafi, kar a ganka a ɗakin nan" Yai ajiyar zuciya yace "Nana, zan missing ɗin ki yau wallahi" Tace "to naji, amma dai ka tafi kaji Abokina" Da ƙyar Sadik ya tashi ya bar ɗakin nan. Khairat tayi mamakin yadda Sadik gaba ɗaya ya canza, ba ya shiga harkar ta sam kamar da, yadda suke ɗasawa amma sam tunda ya dawo ba wannan. Gashi kamar an masa Asiri, sam ba ya fita waje ba in da yake zuwa, kullum cikin zaman gida yake, sedai a takure yake sosai saboda rashin sakewarsa da matarsa, Nana kuma kullum cikin zaman ɗaki take saboda kar wani ya ga cikin nan. Cikin bacci da daddare Nana taji mutum a jikinta, ta tashi cikin hanzari amma Sadik yace "Shhhhhh nine" "Friend meye haka, ka kusa danne min ciki fa" "Am sorry ai ban danne ɗin ba" "To me kake yi a nan?" "Ke nifa na gaji ne, haba yau kwananmu tara a gidan nan na gaji da wannan wasan kwaikwayon" "Ni dai yanzu, dan Allah ka rufa mana Asiri, ka tashi ka tafi tun wani be ganka ba" "Wallahi ba zan bar ɗakin nan ba se Allah ya kaimu Asuba, na yi magana da Abba, na shirya mana tafiya ƙauye gobe in Allah ya kaimu, zamu gidan dr. Daga nan mu wuce" Cikin farinciki Nana tace "dan Allah dagaske?" "Ina miki ƙarya ne?" "A'a ba kamin sedai tsoratani da sani tashin hankali wasu lokutan" murmushi su kai tare yana sake rungumeta. (Asuba tagari, in da rabon Mother ta kama Sadik kuma ba ruwana lolz😂😂) Littafin nan ₦300 ne kacal. 0009450228 Aisha Adam Jaiz Bank 07063065680 KO kuje manhajar AREWA BOOKS ku siya. domin kuwa ya fi sauƙi ta can. Bin su sa ido Mother ta cigaba da yi, gaba ɗaya Nana ta ƙanƙame jikinta, saboda tsabar kunya. Tabbas wannan cikin na Nana ko yanzu ta haife shi ba abun mamaki bane ba, amma tana me ba ta san da cikin ba duk wannan kwanakin da su kai a gidan?. Babban abunda ya ƙara ƙular da Mother be wuce yadda take ta banbami tana masifar Sadik ya rabu da Yarinyar ba, yayi ƙanƙanta da Aure, ashe kallon biri take masa yana mata na ayaba. Jiki a sanyaye Mother ta janye jikinta, ta bar ɗakin jikinta ba ƙwari dan ta rasa wane tunani Yakamata tayi, ta nufi sashinta. Nana kam gaba ɗaya a rikice take, ta rasa abunyi gaba ɗaya se kuka take, Sadik yace "to kukan me kike kuma? Ai gara ma da Allah ya sa taga cikin hankalinmu ya kwanta da fargaba" Nana ta gaza cewa komai yace "ko in kamaki in maida ke kan katifar?" Nana ta girgiza masa kai alamar a'a. Ya rungumota yana ƙoƙarin share mata hawayen dake bin fuskarta amma ta ƙwace tace "kai ba ka gudun abun magana, idan Mother ta kuma dawowa fa?" "Karki damu ba zata kuma dawowa ba" Mother ɗakinta ta koma tana safa da marwa, tama rasa wanda zata gayawa maganar, wayarta ta ɗakko da hanzari ta kira Mummyn Khairat, tai sa'a kuwa ta shiga. "Har kin isa gida ne? Naga kiranki" cewar Mummy bayan ta ɗaga wayar. Mother tace "hmmm na isa, na tarar da abunda ya bani mamaki na marasa abun Magana" "Me kenan?" "Hmm kin san matar Sadik ciki ne da ita haihuwa ko yau ko gobe?" Mummy tace "wane Sadik ɗin wai?" "Sadik dai nawa, ina ta fafutukar yadda zan kashe Aure ashe kallona kawai yake, naje na tarar da su tare, da uban ciki a jikin wannan Yarinyar" Mummy tace "iko se Allah, kinga dr. Da suke ta nema Allah be basu ba, se wannan da ba'a bawa Auren nasu mahimmanci ba, ohh Sadik da ɗa" Mother tace "Abun ya ɗauren kai, Sadik haryanzu gani nake kamar jiya na haife shi, guda nawa yake?" "Hmm ke dai ki gode Allah da yasa Auren a kai masa, in ba haka ba da wani zancen ake ba wannan ba, ki shirya karɓar jika kawai" Mother tai ajiyar zuciya tace "mhmm, se anjima kawai" ta kashe wayarta, ta riƙe ƙugu tana sake juya lamarin, Sadik ɗinta za'a haifawa ɗa Allah me iko. Haka ta wanzu tana wannan salallamin, har bayan isha'i Abba ya dawo, ta gabatar masa da Abinci, ta koma gefe tai zuguum. "Madam ya dai? Meke faruwa ne?" "Yallaɓai meye ma be faru ba?" "Ok, to in da hali a gayamin wanda ya farun na ganki wani iri kamar a cikin damuwa" "Abba, do you know you are welcoming your grandchild very soon?" Abba yai murmushi yace "Alhamdilillah, Masha Allah" "You don't even ask from who?" Abba yace "ok, i ask?" "Matar Sadik fa, ciki ne da ita a kowane lokaci zata iya haihuwa" Abba yace "Ikon Allah, Lallai Autana an girma" Mother tace "Are you not even suprised? Sadik guda nawa yake?" "Ba abun mamaki bane ba ai, duba da iyaye da kakanni da ƙananan shekaru suma suke Aure" "Yallaɓai, Sadik fa ba Faruk ba, so Sadik can impregnent this little girl? Abun ya ɗauren kai yara ƙanana, Sadik guda nawa yake?" Abba yace "yanzu kin gane dalilin da yasa kakkaninsa su kai masa Aure? Da fari irin tunaninki ne da ni, ni kaina naga baiken Auren da akai masa yayi wuri da yawa, amma tunda naga hotonsa da 'yan matan turawa rabin tsirara, nasan ze aikata hakan, na yanke shawarar haɗe su guri ɗaya da matarsa" Mother ta dafe kai tace "ya ilahil alamin Sadik fa, and how can that girl endure the hardship of labor?" Abba yace "da ta fara se a kaita Asibiti, su sun san abunda ya dace suyi, yanzu seki tuntuɓe su, kiji cikin watanni nawa ne, sannan aje ai siyayyar da ya dace na haihuwa" "Abba ni ta yaya zan fara wannan tambayar, ni na rasa kunya zanji ko me zanyi," tai maganar tana dafe kanta. Murmushi kawai Abba yai ya cigaba da abunda yake. Daga bisani yace "kinga yanzu kince wataƙila ta kusa haihuwa, ki tambayesu kiji, kuma ta dawo ɗakinsa su dinga kwana tare, dan na sh ganinsa yana sanɗa daga ɗakinta, ki ɗauke kanki akan su, da da hali gida zan ba su su koma su zauna, amma ban san yadda cigaba da karatunsu ze yuwu ba, kuma ba abun ince su koma BQ ba, ban san yadda haihuwar zata zo mata ba, kinga daga shi har ita ba me wani hankalin kirki. Ajiyar zuciya kawai Mother Tai, amma bakinta ya gaza furta komai. A waya ta kira Sadik tace ya sameta a ɗakinta, be daɗe ba se gashi yaje, sedai shi kansa Kunyar Mother yake ji. Tun da ya shigo take binsa da kallo tana ƙare masa kallo Daga sama har ƙasa, ya nemi guri ya zauna. "Sannu ko" Mother ta faɗa tana kallonsa, yai shiru tare da sunkuyar da kai. "Ka bani mamaki Sadik, ina ta ɓaɓatu akan an maka auren wuri, Auren dole se gashi ka kunyata ni, so as you are you can impregnent a lady?" Tsuke Fuskar sa yai a ransa yana faɗin 'wannnan wace irin magana ce Mother' "Wai ni garin yaya ma a kai haka ta faru Sadik? Gaba ɗaya ka shammaceni" "Mother dan Allah, ni Wallahi gaba ɗaya kin sani a kwana in ba so kike in gaya miki komai ba, dan Allah ni dai kiyi haƙuri ki manta da zancen nan" "A'a nina isa in tambayeka yadda abu ya faru, Allah ya kyauta amma ka kunyatani, haryanzu ƙanƙantar ka nake gani Sadik" Sadik ya sunkuyar da kai ya ƙi Magana. "Hmm, cikin nata wata nawa ne?" "Tara" ya bata amsa. "Kuma shine da kuka dawo baku faɗa ba, balle a sa ran kaita Asibiti" Yace "munje ɗazu da ba kya nan, an mata scanning da booking na komai da komai na masu ciki, sunce da ta fara naƙuda aje Asibiti" "Ikon Allah, ashe har Asibiti kuka je, hmm aishi kenan, se batun siyayyar haihuwa, ko baka san anayi ba, cikin kawai ka iya" Sadik yace "Innalillahi wa innalillahi raji'un" "Ni kake jawa wannan innalillahi dan ubanka" Cikin shagwaɓa yace "Mother ni wallahi na rasa me ma zance, dan Allah ki dena wannan maganar, munyi siyayyar mu tun a can" "Ina abunda kuka siyo ɗin?" Sadik yace "Suna ɗakinta" Mother ta sa shi a gaba zuwa ɗakin Nana, Nana duk tai wuri wuri da ido. Sadik ya kalli Nana yace "Ina Akwatunan nan, da mu ka sai kayan babies?" Nana ta nuna masa in da Akwatunan suke, Sadik ya ɗakko ya ajiyewa Mother a gabanta, ta bubbuɗe sun sai komai, hatta net ɗin jariri sun siya, abun shanya da kayan robobi ne kawai babu. Mother tace "kai waya nuna muku duk wannan kayan ake siya?" Nana ta kalli Sadik, dan ko da sukaje siyayyar ku san shi ya sai komai. Yace "a waya nai browsing" Mother ta sasu a gaba tana ƙare musu kallo, ta rasa murnar samun jika za tai a'a ko kuwa, idan ta kalli Fuskar Nana gaba ɗaya tausayi take bata, tana tausaya mata idan labor ya zo, kuma se Yanzu ta lura Ashe tun da suka dawo a hankali take tafiya, bata abubuwa da kuzari sam hankalin Mother be kai kansu ba. Mother tace "to seka tattara mata kayanta, ku koma ɗakinka saboda ko da wani abu ze taso cikin dare, kar a barta ita kaɗai, sannan ka bani result ɗin teses ɗin da a kai mata, zan haɗa Akwati a shirya mata kayan haihuwa, dan zata iya haihuwa a Kowane lokaci. Sadik yaji daɗin yadda Mother ta nuna kulawarta akan Nana. Haka kuwa akayi, Sadik cikin ɗoki da murna ya kwashe kayan Nana zuwa ɗakinsa da ke cikin falon. Abbas yai ƙuri da ido yana kallon Farhan da ke cikin motarsa, tana ta dannan wayarta. "Waya ta fini mahimmanci ko Farhan" Ta ajiye wayar tace "Ni na isa ince haka, Tuba nake ranka ya daɗe" Yai murmushi tare da shafar ƙasumbarsa yace "Farhan, ashe an rufe Makarantar ku?" Tace "Eh, na gani a news, dama ai ta cancanci a rufeta, da za'a bi shawarata ma ƙoneta yakamata ayi" "Meyasa?" "Saboda makarantar nan tayi silar rusa rayuwar matasan yara da yawa irina, koma me ya faru da ni makarantar nan ce sila, malamin da abun ya faru akansa, yayi iya yin sa ya rabani da Sadik, yana akrar dani RUƊIN ƘURUCIYA ne yasa muke soyayya amma na ƙi yadda, laifinsa ɗaya ya dinga aibata mu da miyagun maganganu ni da Sadik, se shi kuma Allah ya sa ya faɗa tarkon RUƊIN ƘURUCIYA" Abbas yace "Yasalam, abu be daɗi ba, Allah ya tsare ya kiyaye, yanzu in Allah ya kaimu ranar Monday, zan zo in ɗauke ki muje makarantar da zan sa ki, ina son su kai ki ss2 ne, da kin fara se azo ai maganar Aurenmu ko beuty na?" Haɗe rai tai ta tura baki, yace "laifin me kuma nayi?" Tace "ni gaskiya na gama boko a rayuwata, ba zan sake ba" "Yanzu wannan dalilin ze sa ki zaɓi dena makaranta, ki hana al'umma amfanuwa da baiwar da Allah yai miki?" "Ni gaskiya ba zani ba" tai maganar a hankali tare da jingina da seat ɗin Motar. "Dan Allah ayi haƙuri a temakawa marayan Allah a koma makaranta, ko dan saboda feature kids ɗin da zamu haifa" Shiru tai masa taƙi magana, ya kira sunanta amma tai shiru, kamo hannunta yai cikin nasa yana murzawa a hankali, yana cigaba da kiran sunanta. "Sadik dan Allah ka bar.... Se kuma tai shiru. "Sadik kuma? Believe me haryanzu kina son Sadik, ina kishin ki fa ki dena kiran sunansa a gabana" "Dan Allah kayi haƙuri, wallahi bana son Sadik yanzu, haka kurum se jikina ya dinga bani yana daf dani, ko kuna kamar muna tare, amma na san sharrin ƙwayoyin da nake sha ne, amma ba zan kuna ba insha Allah kar kai fushi kaji Doctor, ba ka fushi fa" Tai maganar tana leƙa fuskar sa. "Ina fushi mana, in dai za'a taɓaki Dole in yi fushi, kuma ni na mayi fushin am jealous" Ta marairaice murya tace "Ohh God am sorry please, na dena ba zan kuma ba ka dena fushi kaji Doctor" "To shikenan na dena, dan Allah ki kwana a gida yau kinji" "Insha Allah a gida zan kwana, na maka alƙawarin yau ba in da zani" "Shikenan, good night za muyi waya kan in shiga gida" Dariya Farhan tai tace "Mijin tace, in ba tsoro ba mutum ya bari se ya shiga gida muyi wayar mana" Dariya yai yana sosa kai, Farhan ta fice daga motar. Yai reverse ya koma ƙofar gidan Hajiyarsa yai parking ɗin motarsa, ya sakko ya shiga gidan. Ya tarar da Hajiya na kallon Sunna TV, yai sallama ta ɗago ta amsa masa, ya nemi guri ya zauna yace "Barka da Yamma Hajiya" "Yawwa barka, daga ina kake haka?" Ya ɗan sosa kai yace "daga Asibiti" "Ni na kasa gane wannan sintirin da kake min a gida, tun da ka dawo kusan kullum kana layin nan, ka gayamin gaskiya me kake zuwa yi ne?" "Hajiya bakomai fa, ba abunda nake zuwa yi" "To ya akai se yanzu ka shigo, bayan tun ɗazu naji ƙarar motarka ka wuce" Ƙuuu cikinsa yai ƙara, yai wuri wuri da ido. Hajiya tace "daa gurin Farhan kake ko?" Yai Shiru ya sunkuyar da kai. "Abbas, tun kan ka tafi na gane son Yarinyar nan kake, ni kaina na maka sha'awar Aurenta a da, amma yanzu ba ka ga yadda ta koma ba?" Ya ɗan marairaice yace "Hajiya, a ganina Farhan za'a iya taimaka mata ta gyara Rayuwar ta, saboda na san bakin zaren matsalar ta, kuma Insha Allah ina tunanin zan iya taimaka mata, idan aka ƙyaleta Rayuwar ta zata cigaba da lalacewa, dan Allah ki bari in Aureta" Hajiya ta numfasa tace "tun kan ka fara tausayinta nake jin tausayin ta, se dai ni ba irin iyayen nan ce masu kafiya ba, dan ban san yadda Allah ze da tawa zuriyar ba, ba ka da matsala daga gareni, amma ka san dangin mahaifinka ba za su amince ba, dan dole se sunyi bincike akanta kan su yadda su nema maka Aurenta" Abbas ya sharce gumi, dan ya san dangin mahaifinsu ba ƙanan masifaffu bane ga su da kafiyar tsiya, ko da mahaifinsu ba ya raye, a tsaye suke a kansu, ya san ba zasu amince ba, dan za'a kai ruwa rana sosai, mussaman da matar da yake Aure, daga ɓangaren su aka haɗa su. Hajiya tace "kaje kai ta Addu'a, Allah ya zaɓa abunda yafi Alkhairi" Ya amsa da Ameen Sannan yai shiru ya cigaba tunani. Haladu ne ya shigo ya tarar da Sunusi yana ta zazzage wata 'yar ƙaramar jaka, Haladu yace "ya dai me kake nema ne?" Sunusi yace "wani aiki zazzafan aiki zanyi ne" "Allah mutumina, wane irin aiki kenan kuma wa za kaiwa aikin? Nasan an shaƙa maka kuɗi" Sunusi yace "ba wani zanwa ba se Yarinyar nan Farhan da wannan shegen me motar" Haladu yace "wannan karon me kuma tai maka?" Sunusi yace "ni zata kalla tana gayawa baƙaƙen maganganu, kuma naga wannan ɗan Gidan matar can ya dage, dan haka dole inyi wani abu a kai" "Haba Sunusi, wallahi yakamata ka bar Yarinyar nan ta huta haka, wallahi ka cutar da ita da yawa, ka rabata da masoyinta duk ta zama wata iri" "Kaga ba ruwanka, yadda suka min wulaƙanci suka hanani ita Ranar ɗaurin Aure, se baƙincikinta ya kashe su, babu me Aurenta, dani suke zancen" "Amma Sunusi yakamata....." "Kaga Haladu ka samun ido kawai, ka ƙyaleni" Haladu yace "shikenan, daɗinta dai shi Allah ba Azzalumin sarki bane" Sunusi yai masa Shiru, ya tattara jakarsa ya fice. Haladu yai shiru yana nazari, gaba ɗaya tausayin Farhan yake, Sunusi ya cutar da ita sosai da sosai. Khairat ta shigo falo ta tarar da Mother zaune, da uban kaya a gabanta, Khairat tace "Mother me zaki da kayan jego?" "Hmm jika zan ɗauka" "Jika kamar yaya?" "Matar Sadik ce ta kusa haihuwa" Zaro ido Khairat tai tace "wai wannan Yarinyar?" "Ita fa tsohon ciki ne da ita" Khairat tace "turƙashi, ke kina nan kina fafutukar raba Aure ashe kallonki kawai suke?" "Kema dai kya faɗa, ni duk kaina ya kwance" haka suka gaba da jajanta lamarin. Mother tayo siyayya abunda ya rage ba su siya ba, tana yi tana sake cika da Mamaki, wai Sadik za'aiwa haihuwa. Duk da halin da Nana ke ciki na wannan tsohon ciki, Sadik yaji daɗin dawowar ta ɗakinsa, ɓangaren Nana kuwa ba ta so wannan haɗen ba, dan Sadik akwai takura, seda ta samu yai bacci, ita kuma ta kasa baccin gaba ɗaya ta tashi ta koma falo. Cikin dare Mother ta fito ɗaukar ruwa, ta tarar da Nana a zaune a babban falo se juyi take akan kujera. "Ke lafiya kuwa?" Mother tai maganar tana ƙarasowa cikin falon. Nana ta miƙe zaune a hankali tace "bakomai" "To me kike a zaune a falo haka?" "Na kasa bacci ne" "Ko kina jin wani ciwo ne?" Nana ta girgiza kai alamar a'a. "Ina Sadik ɗin?" "Yayi bacci" Mother ta wuce ɗakin na su, ta tarar da Sadik ya baje yana ta bacci. Ɗala masa duka tai ya tashi a gigice yana mutsutsuke ido tace "ka bar 'yar mutane na fama, kai kana nan kana bacci, se ka tashi kaje kaji me take buƙata" Sadik yai miƙa ya sakko daga kan gadon, ya fito falo, ya tarar da Nana a zaune akan kujera, Kamar za tai kuka. "Friend lafiya kike kuwa?" "Lafiya ƙalau" ta bashi amsa. Mother kuwa wucewa tai part ɗinta ta barsu. Sadik yace "ko Asibiti zamu tafi?" Tace "A'a" "To menene?" Ya faɗa cikin kulawa. "Na kasa bacci, duk na gaji, ko ina na jikina ciwo yake cikin nan ya min nauyi, na rasa ta yadda zan kwanta inji daɗi, gashi abincin da na ci ya tsaya a ƙirjina yaƙi wucewa kuma na kasa amayar da shi" tai maganar hawaye na zubo mata. Sadik yace "shikenan na gane, zo muje ɗaki nai miki tausa ko zaki iya baccin" Tai saurin girgiza kai tace 'kaje ka kwanta ka barni a nan" "A'a ba za'ai haka ba" ya zauna yana mammatsa mata ƙafafunta, se hamma yake yi kamar ze ci babu. Nana tace "zo ka kwanta, naga kana jin bacci" ba musu yai kwanciyarsa a kan cinyarta yana baccin sa. Ita kuwa Nana, naƙuda ta fara ba ta sani ba, dan a hankali yake tsira mata, se taji mararta ta ɗaure amma ta daure. Se gefin Asuba ciwon ya lafa mata, bacci ya kwashe ta, Abba ya ci karo da su Nana a falo, Sadik ya kwanta a cinyar ta yana baccinsa, ita kuma ta jingina da kujera tana baccinta. Abba ya koma ya kira Mother, yace "kizo ki tashi ɗanki" Mother da ta fito ta gansu tace "yanzu da haka za'a raini ɗan idan an haife shi, kai Sadik, Sadik" a firgice suka farka gaba ɗaya, Kunya ta lulluɓe Nana, Abba ya fice kamar be ga Komai ba. Gaba ɗaya wunin ranar Nana haka tayi shi babu daɗi sam, daurewa kawai take, amma tana jin ciwo kaɗan kaɗan, Mother kuwa ita yanzu Nana ce take bata tausayi, saboda abunda take tunkara, wato naƙuda ga nauyin ciki duk se haƙuri. Seda Nana ta jera kwana tana ciwo a tsaye, Mother tace Nana ta koma ɓangarenta ta dinga kwana, Nana tai matuƙar mamaki dan rabonta da shiga sashin Mother, tun bikin dr. Da ta shiga aka korota. Tace su kwana tare da Khairat a ɗakinta da ke cikin sashen Mother, Nana tace ita a ƙasa zata kwanta ba ta jin daɗin kwanciyar Kan gado. Khairat ko kallon kirki ba taiwa Nana ba, dan haushin Nanan take ji. Cikin dare Khairat ta dinga jin nishi, ta farka ta kunna wayarta, taga Nana ta haɗa gumi se salati take tana kiran sunan Inna. Da sauri Khairat ta kira Mother, ta sanar mata da halin da Nana ke ciki, aikuwa Mother ta taso cikin magagin bacci. A daren suka sa Nana a mota zuwa Asibiti, sedai aka duba akace haihuwa ce Amma da saura. Sadik yana can yana bacci be san budurin da ake ba, se da Safe ya samu labari, ya shirya ya tafi Asibitin. Sadik duk a zatonsa haihuwar ba wahala, yaje ya tarar da Nana a zaune, fuskarta duk tai wani iri, gumi kawai take. Yace "wai haryanzu baki haihun ba?" Ji tai kamar ta kife Sadik da mari, dan a yanzu hausinsa take ji, dan duk shi ya sata a wannan bala'in. Yace bari yaje gida ya ɗakko ruwan tofin da suka zo da shi daga ƙauye. Harya koma gida ya dawo Nana na cikin jazabar labor, kuma ance haihuwa da saura, Mother ce a gurinta se sannu take mata. Ko da Sadik ya kawo tofin nan Nana ta sha, tamkar an tunkuɗo ciwon, ta gigice gaba ɗaya, aka shiga da ita labor room, Sadik ya zata ana shiga da ita za'ace ta haihu, amma abu shiru. Abba ma da kansa ya zo Asibitin, amma Nana babu labari, nan Sadik jikinsa ya fara sanyi, dan be zaci abun ya ka haka ba. Gashi an hana kowa shiga gurin Nana, suna nan tsaye Nurses suka kira likitar da take duta akan tazo ta duba Nana, dan sun kasa gane kan labor ɗin na ta, kamar ba ya progressing, Sadik ya faki idon Mother ya shige ciki shima. Yaje ya tarar da Nana ta fita hayyacinta, ga fanka amma kamar an jiƙata da ruwa, ga wata a gefe tana danna cikin Nana, wata na ƙoƙarin yadda za'ai kan ɗan ya fito, ga Nurse ɗin riƙe da forcep zata bata tear. Ai gigice ya ƙarasa ya ture Nurse ɗin, idanunsa su kai ja yace "wace irin mara imani ce ke? Ya zaki sa mata wannan ƙarafan a jiki" ya ɗago Nana da zuwa yanzu ta fara galabaita, idanunta sunyi ƙanana saboda Azabar ciwo. "Nana, buɗe idonki kina ganina?" Yai maganar yana girgiza ta. "Sadik mutuwa zanyi, ba zan iya haihuwa ba, na gaji ba zan iya ba, ka yafemin" "No, ba zaki mutu ba Nana, zaki haihu lafiya Insha Allah" Likitar ta fita tana faɗa akan dan me Sadik ze shiga ɗakin haihuwa ze han su aikinsu, shi kuwa ya rirriƙeta se hawaye, saboda ya tausaya mata, be taɓa tunanin Azabar labor ta kai haka ba. Usman ne yace "Doctor dan Allah kiyi haƙuri, mijinta ne bakiga duk yara ne ba, ba hankali kiyi haƙuri" Ta zaro ido tace "mijinta? Amma gashi na ganku manyan mutane wayayyu, akaiwa yara Auren wuri haka mussaman ita" Mother tace "doctor, yanzu ba lokaci ne na tattauna wannan magana ba, ya ake ciki?" "Eh to, ta samu prolonged labor, aiki za'ayi a cire babyn, kuje a biya kuɗin nan da ƙarfe goma insha Allah surgical team ɗin za su iso, ayi mata aiki" Da ƙyar aka ɓanɓaro Sadik aka fito da shi daga ɗakin, sedai yana fitowa yaji ance aiki za'ai ya kuma gigicewa, ya dinga kuka kamar ƙaramin yaro. Usman yace "wai kai wannan wane irin shirme kake, kai da zaka bata ƙwarin gwiwa" Abba yace "de na yi masa faɗa, ka kwantar da hankalinka auta na, insha Allah Lafiya ƙalau za'ai mata aikin a fito da ita" Se da Sadik ya bawa Mother haushi, yadda yake kuka Kamar wani yaro, rabon da ta ga yai kuka har ta manta, amma shine yake kuka haka, Hakan ya tabattar mata da cewa yana son Nana kenan. Jidda kanta da ba ita ke naƙudar ba, ta shiga tashin hankali nesa ba kusa ba. Ana ta shirin shigar da Nana tiyata, tana ta ambaton Allah, dan sam ta dena jin nishin ma gaba ɗaya, ƙarfinta ya gama ƙarewa, cikin ikon Allah tai wani yunƙuri sega sankacecen jariri ƙato ya fito gaba ɗaya tare da mabiyiya. Nurse ɗin tace "Alhamdilillah ala kulli halin, sannu kinji" Nana ta lumshe ido kawai, saboda wani sanyi da ya dinga ratsata, ta ƙudurce a ranta ita da haihuwa har abada, Auren ma ta haƙura dan wannan Azabar da ta sha yau, ba ta san ya zata kamanta ta ba, tun da ta ɗau cikin nan take wahala har zuwa haihuwa, Nurse ɗin ta yanke cibiya, ta ɗagowa Nana jaririn tace "kalli me kika haifa?" Nana tace "ke dan Allah ƙyaleni, haba wannan wahala haka, Allah ka jiƙan Mamana, Allah duk wata uwa ka sata a Aljanna, wanda ba su haifa ba Allah ka basu, ka shirya al'ummar Musulmi" Ta ƙarasa Addu'ar tana hawayen wahala. Sosai ta bawa Nurse ɗin dariya, aka gama gyara jaririn aka zo ɗinki, Nana tace Allah kar ta baza'a kuma gana mata wata Azabar ba. Sadik kuwa tuni aka sanar musu ta haihu, Sadik ya dinga murna, dan dama Addu'a yake tayi kar ai mata aikin, ba ya son a yanka mata jiki. Nurse ɗin ta kalli Nana tace "kinga in baki tsaya anyi ba, nan gaba da kansa ze sako ki gaba ya zo a ɗin ke ki, ki nutsu ayi" Nana tace "taɓ waya gaya miki zan koma, ai bani ba Aure na gama dama ban isa Auren ba" Tai dariya tace "Yarinya man kaza, ƙil nan da wata taran zaki dawo mana haihuwa ta biyu" "Wallahi Allah ya kiyaye, ba dai ni ba" Da ƙyar ta tsaya akai ɗinkin, ta gyara jikinta, akace ta bawa yaron Nono ama tace me za ta bashi, ba su kai girman yadda ake shayarwa ba, sedai in magani za'a bata su ƙara girma" haka Nana tai ta shirme suna mata dariya. Kan ace su shigo tuni Oga Sadik ya zura kai ɗakin, ya ƙarasa gaban gadonta da Sauri ya rungumota yana "Sannu Besty na, sannu My Asma" Tura baki tai taƙi kallonsa, "Sannu kin sha wahala na tausaya miki Sosai" Tace "Ashe dai ba ka son in mutu, harda kuka" tai maganar tana masa dariya. Yace "Kuka nake karki mutu, alhalin ki na wa miji rashin Kunya, wallahi ban san haka haihuwa take ba Nana" "Hmm ai ba zan ƙara ba, daga wannan ɗan ba zan kuma haihuwa ba" Murmushi yai ya miƙe, ya nufi in da aka kwantar da jaririn ya ɗakko shi yana cewa "Alhamdilillah, yanzu wannan namu ne Husna" Nana tace "gashi nan da ƙaton kai kamar na babansa ba, ya ban wahala" Sadik yace "wallahi bani da ƙaton kai, se kuma bakinsa irin na babarsa na tsiwa ba" Nurse ta shigo tace "Ikon Allah, waye yace ka shigo ne?" "Se ance in shigo ni da ɗa na da matata" Tace "lallai kam" Su Abba suka shigo tare da Mother, Sadik ya miƙe yana murmushi, ya danƙawa Abba jaririn, yana faɗin "Abba kalleshi, kamar mu ɗaya da shi ko?" Abba yace "sosai makuwa" Usman yace "Wai kai ba ka da kunya ne?" Sadik yace "wace kunya, tunda Allah yayi ya zo duniya" Nan da nan aka shiga buge bugen waya, Inna ta rasa in da zata sa kanta dan murna, a ranar tace a aika mota a ɗakkota. Asibiti ya cika da jama'a, se zolayar su Sadik ake, wai yaran Iyaye. Awan Nana shida a Asibiti bayan ta haihu aka sallame ta, sedai mursisi ta ƙi shayar da yaron, wai me ze sha. Da labari ya samu Faruk ma, a ranar ya fara shirye-shiryen yadda ze dawo Nigeria, sun samu jariri a familyn, bayan shafe tsawon lokaci ba ai haihuwa ba, kasamcewar danginsu ba masu yawan haihuwa ba. Mother ta riƙe jariri gam, Kamar ta haɗiye shi, saboda tana matuƙar ƙaunar yara. Inna ta taho da kayayyakin ta da akewa mai jego, se da Inna ta zo ta sa Nana a gaba, sannan tai ƙoƙarin shayar da shi, shime da ya fara sha se ta sa kuka tace ita zafi. Shi kuma Sadik da ya ɗan fita aka jima se ya dawo, ya shiga cikin 'yan barka ya karɓe ɗansa ya zauna yana kallonsa. Inna tace "Yau naga abunda ya isheni, za'aga shiririta agun wannan sakarkarun iyayen". Idan Sunusi baya nan, Haladu se yai ta bincike masa kaya, ko Allah ze sa ya gano wane irin Asiri yaiwa Farhan, Sunusi ya na ɗan taɓa harkar tsubbu, ya sa a ransa cewa duk yadda ze zeyi dan ya taimaki rayuwar Farhan da Sunusi ya tarwatsa. Tana zaune a gurin cin Abinci ita da Alhajinta, da yake kashe mata kuɗi, yana ɗan duba wayarsa yace "Farhan, kalli wasu young couples, kina cewa wai ke baki isa Aure ba, kin ƙi yadda muyi Aure, ko ki bani haɗin kai mu huta, kalli wannan young couples ɗin, sun haihu" Ta sa hannu ta karɓi wayar tana kallon screen ɗin wayar, a Instagram ne, hoton Nana da Sadik sun haɗa kai suna murmushi, gefe an saka hoton jaririn. Take Jikin Farhan ya kama rawa, yawun da take ƙoƙarin haɗiya ya kasa wucewa, take ta saki wayar ta fara tari!. Littafin nan ₦300 ne kacal. 0009450228 Aisha Adam Jaiz Bank KO kuje manhajar AREWA BOOKS ku siya.  Tari ne ya sarƙe Farhan, ya shiga jera mata sannu, sedai a sannun nasa ko ɗaya ba ta amsa ba, ta miƙe ta ɗau jakarta tai hanyar fita, ko gabanta ba ta gani sosai tafiya kawai take. Bayanta ya biyo yana kiran sunanta, amma ba ta saurare shi ba, ta tari abun hawa ta shige, suna tafe tana kuka, kuka me tsuma zuciya, me Napep ɗin yana ta cewa Baiwar Allah kiyi haƙuri, ki sassauta kukan nan dan Allah. Ko saurarensa ba tai ba ta cigaba da rera kukanta. Suna zuwa gida ƙofar gidansu, ta cillawa me Napep ɗin dubu ɗaya ta shige gida, a ɗakinta ta tsaya ta rufe ƙofa ta sa sakata, ta zube a gurin ta dinga kuka, kamar zuciyarta zata tsaga ƙirjinta ta fito. Allah ya temake ta gidan ba kowa balle a rarrashe ta, ta rasa wace irin Soyayya da shaƙuwsce haka tsakanin ta da Sadik, ta kasa mantawa da shi, ta kasa rufe babinsa daga rayuwar ta, yayi Aurensa har an haifa masa ɗa, ita kuwa tana nan tana gararamba a titi, ba Auren ba karatu sema lalacewa. Ta sake fashewa da kuka, ga Wani irin kishinsa da ya dinga taso mata, ya haɗa jikinsa da wata, bayan ta riga ta yadda da shi, shine namiji na farko da ta amince ta haɗa jikinta na sa. Ji tai wani irin abu yana taso mata daga zuciyarta, ga wani irin ciwon kai da ya addabe ta, ta watso kayan drower ɗinta, ta ɗau wata kwalba, ta shanye abunda ke ciki tas, ta jefar da kwalbar ta kife kan katifarta tana cigaba da zubda hawaye. "Sadik ka Cutar dani, cutarwa mafi muni, ka rusa rayuwata da ban sanka ba da ba lallai wannan abubuwan su faru da ni ba, nayi dana sanin saninka, ba zan maka Allah ya isa ba, ba zan iya ba, Allah ya dawwamar da kai a cikin farinciki ni kuma ya bani mafita" ta ƙarasa maganar cike da rauni. Tana jin yadda zuciyar ta keta tafasa, ga wayarta se ringing take, amma ta kasa ko da motsa yatsanta ne, saboda maganin da ta sha ya fara aiki a jikinta, wani irin bacci ya fara fizgarta. Da yawa mutane ba su san Sadik yai Aure ba, se labarin haihuwa suka ji, ga yaron Kamar Sadik yai kaki ya ajiye, kamarsa ɗaya da Sadik sosai da sosai. Kwanansu uku da haihuwa, Faruk ya iso Nigeria, cike da ɗokin ganin ɗan Sadik, Sadik kamar su cinye juna shi da Faruk, gidan aka rasa wanda yafi wani ƙaunar jaririn nan, hatta Khairat rawar kai take akan jairin nan. Se jaririn nan yaita kuka, Nana tai mursisi kamar bata san yanayi ba. Sadik ya shigo ya tarar da Mummyn Khairat taiwa jaririn wanka, se rarrashin sa take amma se tsala kuka yake. Sadik yace "Mummy ba yunwa yake ji ba kuwa?" Mummy tace "to ai uwar ta sa ce se a hankali, ina ga Madara yakamata a nemowa yaron nan a dinga haɗa masa da ita" Sadik yace "kawo shi" ya karɓe ɗansa ya saɓa shi a kafaɗa, yana shafa bayansa ya nufi ɗakin sa Nana take. Ta harɗe ƙafa tana shan shayi da farfesun kaza. Sadik yace "Friend meyasa kike haka ne? Yaro se kuka yake amma ke kina nan kina cin Abincin ki, shi kuma ko oho?" "To ni ya zan masa, shikenan ni ba zanci Abinci ba?" "A'a waye yace karki ci Abinci? Amma shima seki ba shi nasa" "Dan ba ka san zafin da nake ji ba ko? To ka ba shi naka ya sha, shikenan da na motsa ko a cikin mutane ne sai ya ta kuka" Sadik yace "to yanzu ai ba a cikin mutane bane, dan Allah ki karɓe shi  ki bashi" Ta ƙara tura baki tana tauna bredinta. "So kike ya mutu da yunwa?" Ta zazzare ido tace "ya mutu kuma?" "Eh mana, kalli yadda yake kuka fa, anya kina son sa?" Nana tace "wallahi ina son shi sosai, zafi nake ji sosai in zan Shayar da shi, tun daga ciki har raino duk ba sauƙi friend" Sadik ya gyara zamansa yace "ai duk aikin lada babu sauƙi, a cikin sa yanzu dai daure ki karɓe shi," Ta sa hannu ta karɓe shi, ta fara ƙoƙarin Shayar da shi, sedai yadda take rintse idonta, zaka gane tabbas da gaske take zafi take ji. Sadik ya zuba mata ido cike da tausaywa, gaba ɗaya lamarin babu me sauƙi, yace "Sannu" tace "yawwa" Yana tsaka da sha, Nana ta tsige shi ta miƙawa Sadik shi tace "karɓe shi na gaji wallahi" "Haba Nana, be ƙoshi ba fa" "Kar ka kuma cemin Nana" tai maganar tana zumɓura baki. "To naji, amma kinga fa kuka yake, Allah Sarki babyna, yi haƙuri ita ma maman naka ba'a daɗe da yayeta ba, shiyasa take baka wahala" Inna ce ta shigo tana ƙwalawa Nana kira "ke ki taso ga ruwa can an kai banɗaki" Nana ta ɗora hannu a ka tace "Na shiga uku, daga wannan se wancan, wallahi wankan nan da zafi dan Allah ku min rai" Inna tace "yau naga shashasha, in ba'ai wankan ba so kike ki lalaltaccen jego? Kaikuma kasa ta a gaba, da ɗa hannu yana faman kuka, ka bata shi mana" Sadik yace "Ai yanzu ta bani shi, bari in kaiwa Mother shi ta goya shi ko ze bacci" Inna tace "A'a wataƙila yunwa yake ji, ki karɓe shi" Sadik yace "A'a Inna, ƙyaleshi Kawai, amma dan Allah wankan a bari ruwan ya huce, naji tana cewa yai mata zafi da yawa" Inna tace "jimin ɗa da feleƙe, ni tafi ka bani guri, ke kuma zaki ta so ko sena zo na janyo ki?" Haka Nana ta taso, tana ta zubar da hawaye, ta wuce akai wankan nan. Sosai Mother ke shiri akan taron Suna da za'ai abun har mamaki yake bawa Inna, ba Inna ba hatta Nana abun mamaki yake bata. Katin gayyata na Online da na bugawa, anyi Nana ba ta san adadin su ba. Daga haihuwar zuwa yanzu kuwa, 'yan barka kawai sun tarawa Nana sha tara ta arziki, dan ma wani abun Mother ake bawa, kowa yai sallama da abunda ze kawo. Kayan fitar Suna kuwa, lefe da ba'aiwa Nana ba, shi Abba ya saka ai mata, kaya na gani na faɗa. Gefe guda Jairi na ta shan wuya a gurin yarinyar uwarsa, tana son yaron amma idan ya isheta da kuka, zama take ta taya shi kukan, idan yaa isheta da tsotso ma haka take dire shi, ta cigaba da sabgogin ta, ai tai mata faɗa amma ko a jikinta, ba abunda yake bata haushi irin cikin dare yaita tsala kuka, Kamar ana cire masa ido, ta juya ta shige bargo ta bar mutan gidan da rarrashin sa. Har magariba sannan Farhan ta farka daga mayen da take, tai alwala ta rama sallolin da ba tai ba, tana kwance a ɗakinta Amir yai sallama yace "Yaya, Doctor yana sallama da ke" "Kaje ka ce masa ba zan zo ba" Mamaki ya kama Amir, ze yi Magana amma tai masa tsawa tace "kace ba zan zo ba" Yaron yaji maganar tai nauyi yaje ya gayawa Doctor, dan haka ya wuce yaje ya gayawa Abba abunda Farhan tace. Abba ya tashi da kansa ya je har ƙofar ɗakin Farhan ya ƙwanƙwasa, amma tai shiru. Ya ɗaga labulen, amma kasancewar da wuta ya ga fuskarta a kumbure, ta dunƙule guri ɗaya. "Meya sameki ne haka? Kukan me kike? Har kika ce acewa yaron nan ba zaki zo ba?" Aikuwa ta kuma fashewa da kuka tace "Abba, da yawa maza ba sa tsoron Allah, Ba zan Auri Doctor ba dan Allah ni a ƙyaleni, wallahi Abba na gaji da Komai gani nake kamar a duniya ni ka ɗai aka tsana" Abba ya ƙarasa cikin ɗakin ya zauna a kusa da ita yace 'ki dena irin wannan maganar, Allah ya jarrabi dubunki da abunda ya ninninka naki, ki godewa Allah ya baki rai ya baki lafiya, ki dena wannan maganar" Gaba ɗaya ta manta tare da Abba take magana, neman in da zata amayar da abunda ke ranta kawai take, cikin kuka tace "Yayi Aure fa Abba, har an masa haihuwa" "Shi wa?" Abba ya tambaya cike da rashin fahimta. "Abba Sadik mana, Sadik Abdullahi Rano, na so shi na so shi, ya kyautata min ya sa na fara son shi, amma ya yaudare ni Abba, kuma na kasa mantawa da shi" tai maganar tana wata irin whalalliyar ajiyar zuciya. Abba ya jinjina sunan nasa, wato matashin nan da ya taɓa kawo mata invitation na bikin yayansa, tabbas ba ze manta yaron ba. Wato shine silar duk wannan wahalar da Yarinyar tasa take sha, shine Yaron da take faɗa dama? Wanda ya dinga hure mata kunne? Abba ya haɗiye wani abu me ɗaci a maƙogwaronsa sannan yace "banda abunki dama Farhan, ina ke ina wannan yaron, ai kyan ƙwarya tabi ƙwarya dama, idan ta bi Akushi fashewa za tai, wannan yaron ba sa'an Aurenki bane, yaro ne ƙarami kuma ɗan masu kuɗi ina ke ina shi?" "Abba, da Umma ta ja ni a jiki kamar sauran 'ya'ya da Sadik beyi galaba a kaina na fara son shi ba, Astagfirullah, Astagfirullah Abba da Sadik da Sunusi, zan iya yafewa Sadik amma ba zan iya yafewa Sunusi ba, shine mutum na farko da ya fara ɓatani a gurin iyayena, da kuma mutanen unguwa, Abba ta yaya zan kuma yadda da wata Soyayya a gurin maza, Sunusi ba da'awar yana sona yake ba? Amma hakan be hana shi yi min wannan sakayya ba". Shi kansa Abba daga baya yake godewa Allah, da yasa aka fasa Auren nan, dan yanzu idan Sunusi ya ganshi ɗauke kai ya ke, koma ya fara yada masa maganganu da habaici. "Na sani Farhan, Amma cikar kimarki, da abunda ze goge miki wannan tabon shine Aure, ba duka maza ne suke haka ba, Kamar yadda kuma wasu matan ba ku da kirki, kar laifin wasu ya shafi Abbas. Na so ki koma Makaranta, amma a yanayin da kike ɗin nan ba zan so ki cigaba da zuwa Makaranta ba, kiyi haƙuri kinji Farhan" A sanyaye tace "to Abba" ya dinga rarrashin ta yana mata Nasiha, har hankalinta ya ɗan kwanta. Abba da kansa yaje ya samu Abbas yace masa yayi haƙuri yau bata jin daɗi, sedai ya dawo ko zuwa gobe ne in Allah ya kai rai. Abbas yace ai mata sannu daga nan ya tafi. Tun da Faruk ya zo Nigeria, Khairat take ta ƙoƙarin yin shishshsigi a wajensa, amma ya basar da ita, sedai ya ɗan tsokane ta, ya ƙyaleta sam yaƙi yarda ta shiga jikinsa, tun da ya tafi ko ta waya ba shiga sabgarta yake ba, dan shi sam Faruk be damu da harkar mata ba balle wata Soyayya. Tun ana i gobe suna aka kawo manyan raguna guda biyu na suna se saniya wadda za'ai hada hadar Abincin suna, Nana ta sha gyaran kai da lallae kamar Amarya. Ranar suna yaron yaci sunan Abba, wato Abdallah, akai masa inkiya da Sahal. Anci an sha a gurin taron sunan nan kamar ba gobe, Sadik ya sha shadda Nana kuma wani danƙareren leshi ta saka, sun samu kyaututtuka Sosai, mutane da yawa ba su san anwa Sadik Aure ba, se da a kai wannan haihuwar. Wuni guda a kai ana cin Abinci daban daban a gurin nan, aka sha hotuna da raye raye, se bayan magariba sannan aka watse daga gurin sunan. Tunda Abbas yaje gidansu Farhan akace ba ta jin daɗi, ya buga wayarta ya kai sau goma amma ko ɗaya ba ta ɗaga ba, a wannan karon ma ne gaji ba, ya kuma kiran wayar ta ta yai sa'a ta ɗaga tai Sallama cikin sassanyar muryarta. Yai ajiyar zuciya a sanyaye yace "ranki ya daɗe, yau Allah yayi an ɗaga wayata?" Tausayin Abbas ne yakamata, babban mutum kamar wannan yai ta wahala akanta, a hankali tace "Doctor kana lafiya?" "Eh Alhamdilillah, sedai gaba ɗaya bana jin daɗi kwana biyu da banji muryar ki ba kuma bamu haɗu ba" Farhan tace "Ina cikin damuwa ne, amma yanzu Alhamdilillah" Abbas yace "damuwa damuwa, Allah ya kawo mana ƙarshen wannan damuwowin naki" Tace "Ameen, ka san meya sani a damuwa da kuma kokwanto" Yace "A'a se kin faɗa" Tace "Hoton Sadik na gani, matarsa ta haihu, se nai tunanin irin soyayyar da mu kai ya juyan baya, Sunusi yai iƙirarin yana sona, amma shima ya tozarta ni, shiyasa nake jin tsoron in saki jiki da kai Doctor, amma nasan kana haƙuri da ni" "Farhan, duk abunda ya samu bawa a rubuce yake a cikin littafinsa na ƙaddara, haƙiƙa ya cancanci ki guji maza da halayenmu, saboda an ɗanɗan miki maɗaciya a silar Soyayya, amma hakak ba ya nufin duka maza haka muke, ki bani dama Farhan kar ki hukunta ni da laifin da ba nawa ba" Ta gyara kwanciyarta tace "to Doctor, ya kake ya aikin?" Yace "Aiki Alhamdilillah, gobe in Allah ya kaimu zan kai ki makaranta fa, fatan baki manta ba?" "Bance maka ni bana son makarantar nan ba?" "Dan Allah Farhan, kar Muyi haka da ke, kinga na biya komai dan Allah ki amince ki koma Makaranta, alfarmar da nake nema  a gurinki kenan, dan gara kice ba kya sona da ki ƙi cigaba da karatu" Ta ɗan ja numfashi Sannan tace "shikenan, se ka Zo" "Kin amince im zo in kai ki?" Tai murmushi tace "Na amince doctor" Sukai Sallama sannan ya kashe wayar. Inna ce zaune akan kujera Abba na ƙasa tana sanar masa da cewar za ta tafi da Nana can ƙauye, dan kula da ita zuwa Arba'in, da Nana taiwa Sadik zancen cewa yai wallahi ba in da zata, Inna dama ba ta bi ta kan wani Sadik ba, Abba takewa bayani. Abba yace "to Inna, ban ƙi ta taki ba, amma abubuwa za suyi miki yawa sosai, ga jinyar Hakimi, ga mejego da jariri gashi ke ka ɗai ce, ga babu wanda ze dinga taya ki, kinga abun ze miki wahala sosai, amma kinga nan ga Hauwa'u, ga sauran mutane zasu tsaya su kula da ita sosai, ga kai yaro riga-kafi da cigaba da kula da ita Nanan, tunda kinga doguwar naƙuda tai ga ƙanƙantar shekarunta se ana zuwa ana cigaba da kula da lafiyar ta". "Na san da haka, amma ni nafi ganewa inje in kula da ita a can, a nan ba ta da mataimaki se Allah, matarka ba wani ƙaunar Yarinyar nan take ba, wannan abubuwan da take ma, saboda jikanta takeyi, gara ka bani 'yata inje in kula da ita sosai" Abba yace "dan Allah Inna, kiyi haƙuri ki barta a nan, na miki alƙawarin za'a kula miki da ita, ko ki zauna a nan se ki kula da ita" "Shi kuma baban naku waze kulamin da shi?" Abba yace "ga hadimansa nan da suke hidima da shi, shi kansa Sadik rigima ze sa akan a raba shi da yaron nan, kina ganin fitsarar da yake akan yaron, ba ya kara ko jin kunya sam, in yaso idan tai Arba'in se kuje ƙauye ko sati ɗaya tayi, kuma Hakimi ya ga ɗan jikansa". Inna tace "ni ba zan zauna a garin nan har kwana Arba'in ba, tana yin sati uku zan tafi" Da ƙyar Abba ya lallaɓa Inna ta Amince da shi. "Baban Lilly kana ganin matakin da kale shirin ɗauka akan Yarinyar nan shine daidai? Kayi haƙuri a sasanta ai musu Aure da yaron nan kawai kowa ya huta" Ya ɗan ɓata fuska yace "hmmm, Amina kenan, haryanzu maza sunan mu kike ji ba ki san suwaye mu ba, kina tunanin za tai daraja ko wani mutunci a idon yaron nan ne? Bayan abunda duk za'aiwa ɗokin ta gama ba shi, har da ciki ana zubarwa kashi kashi, wahala kawai za ta sha, matakin da na yanke akanta shine daidai" "To shikuma malamin na su ya za kai da shi?" "Se yai prison wallahi, Allah ma ya rufa masa Asiri, da wallahi duka na so in sa kurata suyi masa, dukan da se sun karya kowace gaɓa ta jikinsa, sannan aje a watsar da shi, zan saki kuɗi se an ɗaure min shi, ɗaurin wulaƙanci aita jan shari'ar se an manta da shi a prison". "Amma yakamata shima ai masa adalci, yanzu ka gama cewa haryanzu ban san maza ba, duk da yawon da kai a duniya banjin haryanzu ka san menene kaidin mace, Lilly itace musababbin faɗawar yaron nan halaka, dan da bakinta tace da ba ruwansa, yanzu ka sassauta masa, Sannan ka sa a ranka kaima laifukan da ka aikata ne a baya suke bibiyar ka, ko ka manta irin gwagwarmayar da akai a baya?". Yai ajiyar zuciya Tare da girgiza kai yace "Allah ya yafe mana kawai, amna jibi insha Allah zan wuce da ita can" "Banji daɗin rabani da Lilly da za kai ba, amma ina fatan hakan ya zama silar shiriyarta". Baban Lilly ya yanke shawarar kai Lilly gidan wani babban amininsa da ke aiki a Benue shima babban soja ne, ze kaita can ta cigaba da makaranta a can, ƙarƙashin kulawa da tsaro me ƙarfin gaske. Abokin baban Lilly ya santa farin sani, kuma shi ya bawa Baban Lilly shawarar ya kai masa ita can, ta ƙarasa makarantar a can, in ya so ko a cikin sojojin da ke Barrack ɗin ne a samu a aura mata wani, wanda be san Meta aikata ba. Da safe Abbas yaje har gida yai sallama da Abba, suka gaisa yai masa bayanin mai da Farhan Makaranta da yayi, Abba ya nuna farincikinsa amma yace "ka dena zura jiki gurin ɗawainiya da Yarinyar nan, kasan haryanzu tana ƙasa tana dabo ne, ba ta amsa cewar za ta Aureka ba, kuma kaga haryanzu ba ta dena yawace yawacen da take ba, ka dena ɓarmar kuɗinka akanta" Abbas yace "bakomai Abba, ko ban Auri Farhan ba, idan Allah yasa ta dena shaye shaye, ta cigaba da karatunta, anci riba sosai, a cigaba da yi mata Addu'a , Allah ya sa ta tsaya tai karatun" Abba yace "Ameen ya hayyu ya ƙayyum, Allah yai maka albarka" Abba yana shiga gida ya tarar Farhan, ta shirya cikin dogon hijjabi, yai mata nasiha da Addu'oi Sannan ta fita. Har makarantar Abbas ya kaita, ya danƙata a hannun shugabar makarantar, wadda kusan 'yar uwace gareshi, dan haka tun kan ya kai Farhan yai mata bayanin Komai. Ta karɓi Farhan hannu bibbiyu, a kai mata interview ta jinjina kaifin ƙwaƙwalwa irin na Farhan tace za ta kaita ss2 kawai. Abbas ya ja mata kunne akan in an tashi ta jira ze zo ya ɗauketa ta amsa masa da to, sedai tun bayan kaita aji an mata jumping ɗin Class ɗaya, ta tuna romon bakan da Sadik ya dinga yi mata, yai jumping ɗin Class ɗaya shima, saboda ya gama Makaranta ya Aureta, aikuwa maimakon ta maida hankali akan karatu, se kuka haka taita kuka har aka tashi. Sadik yaji daɗi da ya zamana Nana ba zata tafi ƙauye tai Arba'in ba, ko ba komai jaririnsa ba ze yi nisa da shi ba, dan da sedai ya bisu ayi Arba'in ɗin tare da shi, ko Mother ba ya yiwa kara akan Sahal, wanda yake kira da Junior papa, ko yace masa J papa, kowa so yake ya ɗauke shi, tun yana koke koke har ya saba da jagwalgwalon hannun mutane. Sadik suka haɗu da Abba a masallaci gurin sallar isha'i, akan hanyar su ta dawowa Abba yake cewa Sadik "yaushe zaka koma Makaranta ne? Na san kun kusa cigaba da lectures" Sadik yace "Abba ni dai a nemo min transfer, in cigaba da karatuna a Nigeria" "Saboda me?" Sadik yace "Abba ka ga baze yuwu in tafi da su Nana ba, a ina zamu dinga barin Sahal in zamu tafi school? Kuma ba na son ya tashi a tsakanin masu raino ne" Abba yace "hakane, shikenan zan duba in ga me yakamata ayi, amma dai gara ka koma ɗin" haka suka cigaba da hira har zuwa gida. Suka haɗu da Faruk, Faruk ya dinga yiwa Sadik mitar yayi ɗa ya dena kwanan quarters wai shi me mata, Sadik yai ta murmushi yace "yes call me abu Sahal, wo ni Daddy da ya fara magana zaka ji yana cewa Daddy ina yes my boy" Faruk yace "eh kuma kai ma a gabansa za'a dinga kiranka boy ba, ana ce mak Autax Sadik yace "naji bakomai" haka suka cigaba da zolayar juna. Sadik ya wuce ɗakinsa, yai wanka ya canza kaya, yana son ya fita ya ci Abinci ya je ya ga Nana, ya janyo wata drower, se ga System ɗin sa da yake amfani da ita a Nijeriya, dama be tafi da ita ba a nan ya barta. Ya sa hannu ya ɗakkota, sedai yana ɗakkota kansa ya sara, gabansa ya faɗi take bugun zuciyarsa ya ƙaru. Maida system ɗin yai ya ajiye, ya tashi yana layi, ya nufi sashin da Nana take, yai sa'a ba kowa tana zaune tan kallo a ɗakinta. Zuwa yai ya zube akan cinyarta yana kokawa da numfashi. A rikice tace "Subhanallah besty menene?" Ya kamo hannunta ya ɗora akan ƙirjinsa saitin zuciyarsa. Tai ajiyar zuciya tace "Anya kuwa kana Azkar, bana saka a gaba muyi tare ka dena ko?" Shiru yai bece komai ba, a hankali ta fara karanto masa duk Addu'ar da ta zo bakinta, sun kai mintun ashirin a haka, ta tsinkaye shi yana ajiyar zuciya alamar yayi bacci. Inna ce ta shigo ta samesu, Inna tace "Au har ya fara lallaɓowa yana zagayowa, har kin mata wahalar naƙudar kenan, kin shirya yin wata?" Nana tai mata alamar tai shiru bacci yake, nan ta kwashe komai ta gayawa Inna, yadda yake shiga wannan yanayin tun suna London. Inna tace "iyayensa ne 'yan boko, yanzu da kace wani abu se su ce su ba haka ba, ba se a zuba musu ido ba" Nana ta marairaice tace "Inna, kar abi ta tasu, dan Allah ai waya ƙauye, ko in kin koma a dinga yi masa saukar Alqur'ani, da ya fara idan nai masa Addu'a se yai bacci" Inna tace "to Allah ya kyauta, ba shi kaɗai ba ma, dukkanin ku yakamata ai muku dan neman tsari da kariya daga miyagu, kana da ido bana ganin gari ba". Kwanci tashi asarar rai, Nana ta kwan Arba'in cif da haihuwa, Sadik kam kwana Arba'in ɗin nan kuwa a takure yayi ta, dan Inna ta kasa ta tsare, ko ɗan shishshsigi ta ga yana yiwa Nana, se ta fara yi masa kwakwazo a cikin mutane, ta kunyata shi. Anyi shirin tafiyar su Nana ƙauye, se murna take zata yawon Arba'in, dan a ƙalla za tai sati biyu a ƙauye ta ɗan sake ta huta sosai. Sega Mother da yin rakiya har bakin mota, kamar tace su tafi su a bar mata Sahal, Inna kallon Mother kawai take tana girgiza kai, hadda Sadik za'aje kai su Nana ƙauye, ji yake kamar yace a bar masa ɗan sa a gida. Se da su ka kai su Nana har can, Hakimi kamar ya maida Sahal cikinsa dan murna, yai ta masa Addu'a da shi da iyayensa. Hakimiya kalli Abba yace "yanzu ka gane dalilin da yasa mu kaiwa ɗanka Aure? Ba muyi dan muna ƙin sa ba, amma ka sani da ba'ai masa Airen nan ba idan lokacin zuwan ɗan nan duniya yai, ko kuna so ko ba kwa so ta halak ko ta haram, se ya zo duniya, zaman Sadik a gidan kawai na ga abubuwa da dama da ku da kuka daɗe da shi ba ku lura ba, ina fatan Allah ya dawwamar da farinciki a rayuwarsu baki ɗaya" Abba ya amsa da Ameen. Sadik kuwa yana can yana sallama da Nana yana mita "ina Alla Alla ki Arba'in ɗin nan, mu koma ruwa, kuma kinyi Arba'in an wani ce se kin zo nan kin yi sati biyu haka akeyi?" Nana tace "kai da wa zaku koma ruwan? Ai ni kuwa da ɗin hakan naji yaseen" Harararta yai yace "zaki bayani idan nace a nan zan zauna, Allah sarki J papa na ze missing ɗina na san" Nan tace "To ka tafi da shi mana na huta nima" "Dan dai babu abun ba shi ne, da da shi zan tafi, ko ki tara masa bokiti bokiti in yai kuka a dinga ba shi" Nana tace "eh tun da ga Nonon saniya ko?" Dariya ya dinga yi yace "ba ruwana bani na faɗa ba, ke kika faɗa da bakinki" Tace "Ali shike nan, dan Allah ka kular min da kanka kaji Besty, ka dinga Azkar yadda yakamata, Tun kan mu taho Inna ta sa ana mana saukar Alqur'ani, Allah ya ye maka damuwar ka, kuma ina ta maka Addu'a" Yai murmushi yace "Allah yai miki Albarka, insha Allah zan kula Sosai, let me kiss you am missing you" Murmushi Nana tai, jin takun Inna da maganarta ne ya sa shi cika Nana, ya fita daga ɗakin da sauri, yana jin yadda yake kewar ta Sosai. Su kai musu sallama suka juya, wanda ba su samu damar zuwa can yi musu barka ba, suka dinga zuwa suna ganin Jaririn Nana, fari sol da shi gashi da cikar suma gwanin sha'awa. Kwanan su Nana uku da tafiya, Ama Sadik ji yake kamar sun shekara, duk yai kewarsu mussaman ɗan jaririnsa, Mother kanta kullum se tai zancen Sahal. Faruk ma tuni yai shirinsa ya koma in da yake karatu. Sadik na kwance akan gadonsa, yana kallon musabaƙar Alqur'ani, shi duk irin wannan ba su dame shi ba, a dalilin Nana yake jin wani wa'azi da sauran su. Ɗauke wuta a kai, Solar ta kama ya miƙa hannu ya kashe socket ɗin TV, ji yai kamar an yaye masa wani bargo daga kansa. Kamar an tsikare shi, ya miƙe ya kuma zuwa gaban drower nan, ya ɗakko system ɗin nan ya goge ta, ya jona ta a caji, yana son ya gwada ya ga ko haryanzu tana yi, ya tashi dan ya ɗakko memoryn hotunan sunan Sahal, dan tunda a kai masa copying ɗin sa a jikin memoryn be dub ba, yana cikin dubawa se ga sim cards ɗin sa nan da ya ɗakko a ƙauye. Ji yai kansa yana sarawa, cikin hanzari ya buɗe wayarsa ya zare layukan cikin wayar, ya saka wannan layukan, ya buɗe system ɗin ya kunnata, kamar me jiran wani abu ya faru haka zuciyarsa tai ta azalzalarsa. Hoton Farhan ne ya Bayyana a jikin screen ɗin wayar, wanda tun Asali dama hotonta ne a jiki, turus yai yana bin hoton da kallo, wayarsa kuwa wani irin vibrating ta dinga yi, tamkar zatai tsalle sama, saboda Azabar saƙonni da suke shigowa. Jikinsa ne ya ɗau rawa, ya zubawa screen ɗin ido yana kokawa da zuciyarsa zuwa ƙwaƙwalwarsa akan ya tuna sunanta. A hankali ya janyo wayarsa dake ta vibrating, ya shiga duba tulin saƙonnin da ke ciki. "Dan Allah Sadik kai responding in kaga message ɗina, zuciyata tana kewarka, za'a Auramin Sunusi idan ba ka dawo rayuwata ba" Wani irin jifa yai da wayar, ya ambaci "Farhaaaaaaaaaannn!" Ji yai kamar ya farka daga wani irin nannauyan bacci da ya jima yana yi. Tashi yai a zabure jikinsa na wata irin tsuma, yai waje ba tare da yasan ina za shi ba! Kamar wanda ya ga wani abun tsoro, haka Sadik ya fito falo ya nufi hanyar fita, be san ma ina Yakamata yaje ba, kawai tafiya yake, hakan yai daidai da shigowar Usman, ya tunkari Sadik yan faɗin "kai lafiya kake kuwa? Meye haka kake yi ne?" Idanun Sadik sunyi jawur, be saurari dr. Ba ya fara ƙoƙarin fita, riƙo shi Abbas yai yana faɗin ina zaka haka? Meke damunka?" "Dan Allah ka cika ni, zuciyata zata tarwatse, ka cikani" Sadik yai maganar a hasale. Dr. Ya kuma riƙe Sadik yace "meye hakane Sadik" gaba ɗaya ya lura Sadik baya hayyacinsa. Da ƙarfin tsaya Usman ya janyo Sadik zuwa cikin falo, se fizge fizge yake akan Usman ya ƙyaleshi ya fita. "Buɗe idonka ka kalleni, meke damunka?" Dr. Yai maganar yana kallon Sadik. Sadik yace "bakomai, nima na kasa gane meke faruwa dani, Kamar mafarki nake yi, amma shikenan" Ya juya ya nufi ɗakinsa, ya zube a ƙasa, ya zubawa hoton Farhan ido, yai yai ya tuna dalilin ya sa ya manta da Farhan a duniyarsa. Ya zubawa hoton ido cikin rauni yace "how comes? How? Farhan ya akai haka ta faru da ni, meya sameni ne? Ko na haukace ne, ya salama anya kuwa nine? Meke damuna ne haka? Ya Allah" Yai maganar yana dafe kansa, wani irin zafi kansa ya ɗauka jikinsa ya dinga wata irin tsuma. Littafin nan ₦300 ne kacal. 0009450228 Aisha Adam Jaiz Bank KO kuje manhajar AREWA BOOKS ku siya.  Kamar wanda ya ga wani abun tsoro, haka Sadik ya fito falo ya nufi hanyar fita, be san ma ina Yakamata yaje ba, kawai tafiya yake, hakan yai daidai da shigowar Usman, ya tunkari Sadik yan faɗin "kai lafiya kake kuwa? Meye haka kake yi ne?" Idanun Sadik sunyi jawur, be saurari dr. Ba ya fara ƙoƙarin fita, riƙo shi Usman yai yana faɗin ina zaka haka? Meke damunka?" "Dan Allah ka cika ni, zuciyata zata tarwatse, ka cikani" Sadik yai maganar a hasale. Dr. Ya kuma riƙe Sadik yace "meye hakane Sadik" gaba ɗaya ya lura Sadik baya hayyacinsa. Da ƙarfin tsiya Usman ya janyo Sadik zuwa cikin falo, se fizge fizge yake akan Usman ya ƙyaleshi ya fita. "Buɗe idonka ka kalleni, meke damunka?" Dr. Yai maganar yana kallon Sadik. Sadik yace "bakomai, nima na kasa gane meke faruwa dani, Kamar mafarki nake yi, amma shikenan" Ya juya ya nufi ɗakinsa, yana zuwa zube a ƙasa, ya zubawa hoton Farhan ido, yai yai ya tuna dalilin ya sa ya manta da Farhan a duniyarsa amma ya kasa. Ya zubawa hoton ido cikin rauni yace "how comes? How? Farhan ya akai haka ta faru da ni, meya sameni ne? Ko na haukace ne, ya salam anya kuwa nine? Meke damuna ne haka? Ya Allah" Yai maganar yana dafe kansa, wani irin zafi kansa ya ɗauka jikinsa ya dinga wata irin tsuma. Ya koma gefe ya kwanta, ya zubawa laptop ɗin ido, har ta ɗauke gaba ɗaya Sadik ya kasa gane a wace duniyar yake, so yake ya tabattar da gaske Farhan ɗinsa yake gani, ko dai wata duniyar ce take masa gizo. Ko da akai sallar isha'i a ƙila wa ƙala, yai salla yana tunanin ko dai haukacewa yai, ya kwanta a ƙasa kan tiles yai shiru a haka har bacci ya kwashe shi. Cikin baccin ba abunda ya dinga mafarki se Farhan tana kuka, da ya tunkari in da take ze rarrasheta se ta fara jifansa da duwatsu. Haka ya farka firgigit daga baccin da yake, ana ta sallar Asuba ya tashi jiki ba ƙwari, ya shiga yai Alwala yai sallar raka'atanul fajir, sannan yai sallar Asuba wanda duk sanadin Nana yake yin su, ita ta koya masa. Ya fara karanto azakar, ya idar ya karanta fourty Rabbana da sauran Addu'oin da ya saba yi, wanda duk Nana ce ta koya masa su. Yai shiru ya tuna rayuwar da yai a ƙauye, da yadda suka dinga communicating, da irin rayuwar da su kai da Farhan, tsananin Soyayya da shaƙuwa da yadda ya cire Sim cards ɗinsa ya bar su a ƙauye, zuwa yadda ya manta da ita da rayuwar da su kai a London da Nana zuwa yanzu, komai ya dawo masa tsaf a kansa. Zumbur ya miƙe yana faɗin, "Allah yasa ba haukacewa nai ba, meya sameni haka ne?" Ya koma kan System ɗin da sauri, ya sake buɗe ta hoton Farhan ya sake bayyana a kai. Ya zuba mata ido yace "Farhan, meyasa kika barni tsawon wannan lokaci kika bar cikin duniyata, na rayu tsawon wannan lokaci ba kya tare da ni, ba ki neme ni baki nemi in da nake ba" Yana wannan surutan, haka ya shiga cikin gallery ɗin sa, ya duba in da ya tara hotunan ta kala kala, har da na gurin brithday ɗin ta. Ya sa hannu bibbiyu ya dafe kansa, ya rasa abunda yake masa daɗi ga wata irin sabuwar soyaya da ke cin zuciyarsa game sa Farhan. Ƙarfe bakwai na safe dai-dai, Sadik ya je ɗakin Mother ya ɗau key, yaje ya ɗau mota ze fita, megadi zeyi Magana amma wata gigitacciyar tsawa da Sadik  yai masa take jiki na rawa ya buɗe masa gate ɗin, ya fafari motar kamar ze tashi sama yai waje. Tiryan tiryan ya kama hanyar zuwa gidansu Farhan, gari shiru babu kowa se jefi jefi mutane ke gilmawa, yai parking in da yake tsayawa da motar su sha Soyaya, ya ƙare wa gurin kallo, ya fito jiki a sanyaye yana waige waige ya. Ƙofar gidan su Farhan yaje, ya samu wani dakali ya zauna ya zubawa gidan ido, ji yake tamkar ya tashi ya shiga cikin gidan, saboda wata irin azaba da azalzala da zuciyarsa take masa. Seda yai kusan awa guda a zaune a gurin, se ga Amir ya fito da shirin sa na zuwa makaranta. Sadik cikin azama ya tashi yace "Amir, Yaya tana nan kuwa?" Yaron tsayawa yai yana kallonsa jin ya ambaci sunansa. Sadik ya sake maimaita masa tambayar, Amir yace "bata nan" "Ina ta tafi?" Amir yace "nima ban sani ba" Sadik ya kalli Amir yace "dan Allah ka gayamin in da take kaji, akwai wani abu me mahimmanci da zan karɓa a gurinta" Amir yace "gaskiya na gaya maka, ba ta kwana a gida ba" "To a ina ta kwana?" "Ban sani ba, bari in sauri in tafi zan makara" Sadik ya sauke wata irin ajiyar zuciya, yana mamakin amsar da Amir ɗin ya ba shi, a yanayin da shi kansa ba ze iya tantancewa ba, ya bar ƙofar gidan ya nufi in da motarsa take, ya hau ya kunna ya fizgeta a guje, ya nufi titii,  hakan yai daidai da kunnowar motar Abbas, saura ƙirisa suyi taho mu gama, saboda irin yadda Sadik yake tuƙin a haukace. Abbas ya waiga yace "ji wani mara hankali kuma, ga abunda yai amma ko a jikinsa" ya ƙarasa maganar tare da jan tsaki ya cigaba da tafiya. Yai parking a ƙofar Gidan su Farhan, ya kirata a waya, dan ta fito ya kaita Makaranta, sedai abun haushin tana ɗagawa muryarta kawai zaka gane mankas take, dan se surutai take, kuma galibi a surutun na ta Sadik take ambata. Jiki a sanyaye Abbas ya kashe wayar, tare da mamakin wannan wane irin so takewa Sadik, Babu damar zuwa makaranta, kasancewar a buge take, haka nan jiki babu ƙwari ya ja motarsa ya bar ƙofar gidan. Sadik kam abokansa me suka faɗo masa na makaranta, wanda su kansu ya manta da su gaba ɗaya, Allah ne kawai ya tsare Sadik a irin tuƙin da yake na ganganci, kowa ya gani se yai Magana. Be tsaya ko ina ba se ƙofar makarantar su, wadda itace tushe, ko ince kanwa uwar gamin kowacce ƙaddara da ta afakawa galibin jaruman. Sedai tun daga farkon layin makarantar, Sadik be ga ana shiga ana fita da motoci ba na masu kai 'yan Makaranta ba kamar yadda yake a da ba. Abun ba ƙaramin mamaki ya bashi ba, haka ya ƙarasa ƙofar gate ɗin, amma yana zuwa ya ga uban kwaɗo a tangamemen gate ɗin harabar makarantar. "Maraba maraba, Prince yau kai ne sa kanka bayan dogon zamani ba ka waiwayo mu ba" Sadik ya waiga yaga ɗaya daga security ɗin makarantar ne, wanda suke yawan faɗa da Sadik akan fita daga makaranta ba akan ƙa'ida ba. Sadik kamar ze rushe da kuka yace "Ɗan Ala, ya naga kwaɗo a ƙofar makarantar?" Ɗan ala yace "kai yanzu baka san abunda ya faru ba, ko a jarida ba ka gani ba, ko dayke ance ba ka ƙasar, abokan naka ba su gaya maka ba?" Sadik yace "meyafaru ban sani ba" Nan ɗan Ala ya kwashe komai ya gayawa Sadik. Jikin Sadik ya hau wata irin tsuma, bayan tuna irin miyagun maganganu da sir Nazir ya dinga gaya masa shi da Farhan, a kiɗime yace "ɗan Ala Farhan fa, Farhan ɗina fa meyafaru da ita?" Ɗan Ala yace "Allah sarki Baiwar Allah, tun daka bar makarantar nan duk ta ƙara zama wata iri, kamar wadda ƙwaƙwalwaeta ta samu matsala haka ta koma, a kai tayi da ita ɗalibai suka takura mata, duk ta damu kanta, tun wani zuwa da tai da kayan gida a jikinta na ganta a gurin parking ɗin motoci, da ita da Aminun ajinku da Mubarak Babba ban kuma ganinta ba, ta dena zuwa makaranta baki ɗaya" "Kace Mubarak Babba?" "Eh shi" Sadik be ƙara cewa uffan ba, ya doshi motarsa zuciyarsa na wani irin tsalle kamar ta fasa ƙirjinsa. Ɗan ala yace "Prince da gaske wai kayi Aure?" Ai Sadik ya kurumce, be ma ji me ɗan Ala yace ba, saboda ba ya gane komai gaba ɗaya. Cikin wani irin zafin Nama, ya ja mota ya bar layin, ya dinga mamakin yadda akai ƙanin Farhan yace be san in da take ba, gaba ɗaya yaji abubuwa sun dabaibaye shi ya ma rasa wani tunani yakamata yayi, meye haɗin Farhan da Mubarak Babba. Dukan sitiyari yai, yaja wani wawan burkin da yai wannan tunanin, nan da nan zuciyarsa ta ƙara shiga taradaddi, meye haɗin Mubarak da Farhan? Babban abunda ya sake jefa shi a ruɗani be wuce yadda har abokansa ya manta da su ba. Ya kuma fizgar motar ya cigaba da tafiya, lokacin kusan goma da rabi na safe, unguwar su Amin ya wuce, dan ɗan Ala yace masa da Amin da Mubarak da Farhan ya gani ranar ƙarshe da ta zo makaranta. Idan yaje guri ya tarar da cunkoso a hanya, ji yake kamar yaiwa motar fuka fukai ya je in da za shi, saboda Azabar ruɗani da hanzarin son ya ga Farhan. A ƙofar Gidan su Amin yai parking, gashi ko waya be ɗakko ba, idan ma ya ɗakko wayar ina yaga lambobin 'yan ajin na su yanzu. Wani irin mahaukacin horn ya dinga yi, wanda se da layin gaba ɗaya ya ɗauka, a gigice megadin gidan ya fito yana wane mara tunanin wannan? Sadik ya sauke Glass yana kallonsa, megadin yace "Ahh Yau kaine da kanka, Yaushe rabon duniya da ayyaraye, munyi cigiyarka har mun gaji" Sadik ransa a haɗe yace "yi min magana da Ameen" "Aminu yana makaranta ai" "Wace makarantar?" "Yana Makarantar nan, ta Nijar amma nasan yau zuwa gobe in Allah ya kai rai, ze shigo ko dai a satin nan" Dukan sitiyari Sadik yai, yana wani irin huci, a hankali ya furta "Why Farhan, meya haɗaki da Mubarak, tabbas idan na kama Mubarak da aikata wani abu akan ki da hannun na zan kashe shi" Ya kuma jan motar nan ya bar unguwar su Amin, kusan duk abokan nasa na ajinsu ya zaga, amma ba wanda ya samu balle ya samu wani information, ya koma unguwar su Farhan, ya aika yaro a kirata amma aka kuma ce masa ba ta nan. Har ƙarfe biyar na yamma Sadik yana gararamba a gari akan yadda ze samu Farhan, amma abu ya ci tura. Haka ya koma gida, Mother na ganinsa ta fara faɗa "daga ina kake haka? Jiya Usman yace min ya zo ya tarar da kai wani iri, na duba naga kana bacci, yau wayewar gari kan in tashi wai har ka fice daga gidan nan, kalli se yanzu biyar da rabi ka dawo, daga ina kake haka?" Sadik yace "ba ko ina?" "Kamar ya ba ko ina?" "Mother bani da lafiya ne, naje Asibiti ne aka samun ruwa" "Kuma shine ka kasa kiran kowa a waya ka sanar masa? Ya jikin naka?" Yace "naji sauƙi Alhamdilillah" "Sun baka magani ne?" Sadik ya gaji da tambayoyin Mother ya jinjina mata kai kawai ya shige ɗakinsa. Tea ta sa aka dafa masa, ta kai masa ɗaki ta takurashi akan ya sha. Sam Sadik ya manta da wata yunwa, dan ba ya jinta sam. Mother ta kalleshi tace "Sadik, ko dai duk akan Yarinyar nan ne kabi ka da mu ka ɗaga hankalinka?" Da sauri Sadik yace "Mother wace Yarinyar?" "A'a wace Yarinyar ban da matarka? Ko dan sun tafi ƙauye ne kake wannan abun harda rashin lafiya?" Sadik ya girgiza kai yace"A'a" Mother tace "ka dai shiga hankalinka ka dena wannan zaƙewar, su mata ba a musu haka, idan ta fuskanci irin wannan son kake mata, wahalar da kai za tai, idan kuma saboda ɗanka ne ai za su dawo, ka sha tea ɗin nan ga doya nan ka ci kan ai sallar magariba, da anyi isha'i se ka kwanta" Da ƙyar Sadik ya cakali Abincin yaci ya bar shi, dan a ganinsa Mother ba zata gane halin da yake ciki ba. Sunusi ne keta binciken kayansa, yayin da Haladu ke gefe yana rubutu a jikin allo. Aƙalla Sunusi ya shafe da mintuna talatin yana zazzage kaya yana mayarwa, amma Haladu be ce masa uffan ba. Sunusi ya ɗago ya kalli Haladu a fusace yace "Haladu" Haladu ya ɗago ya kalleshi yace "ya akayi?" "Ka taɓa min kaya da bana nan" "Ban fahimci me kake faɗa ba, Kamar ya ina taɓa maka kaya, ƙaddara ma ina taɓa maka yau na fara taɓa kayanka ko kai ka taɓa nawa, ka taɓa ganin na maka sata ne, ko ba ka nan na ɗau abu ka dawo ina gaya maka" Sunusi yace "kar ka rainamin hankali mana, ba yau ka saba ta;a kayana ba amma tun ɗazu nake neman abu ko ka tambayi me nake nema?" "Meyasa zan tambaye ka bayan nasan ban ɗaukar maka komai ba" Sunusi yai shiru can yace "kai wallahi Haladu kai ne, in ba kai ba ba wanda ze ɗau abunda nake nema" "To wai me kake nema ne?" Sunusi yace "jakar da nake ajiye ajiyen aikin da nakewa mutune aka taɓa min, na nemi wasu laƙanai da nayi ban gani ba, kuma ni gani nake kamar an sauya min layoyin nan da wasu" "Kuma shikenan sekace nine na ɗauka, meye haɗina da aikin da kakewa mutane da ze sa in ɗaukar maka, na taɓa yi maka hakane?" Sunusi ya dawo gaban Haladu ya tsuguna yace "Haladu, naga take takenka ne a 'yan kwanakin nan, ka damu da lamarin Yarinyar nan, matar da zan Aura, wallahi ka sake ka shiga hurumin da ba naka ba, ko kuma na gano kai ka ɗau abinda nake nema, zaka ga abunda ze biyo biya" Seda cikin Haladu yai wata irin ƙara saboda yasan Sunusi ze iya, amma ya dake yace "ba ka isa kai min abunda Allah be min ba, kuma Yarinyar da kake iƙrarin zaka Aura, ba sonta kake ba wallahi, kuma ba zaka taɓa mallakar ta ba tunda Allah ba ya barin zalunci sam" Malam Labaran ne yai gyaran murya yace "wai meke faruwa ne, hatsaniyar me kuke ne?x Sunusi yai saurin cewa "bakomai Malam, saɓanin fahimta ne kuma Komai ya wuce" "Ku dinga ƙoƙarin kai zuciyarku nesa, ku dena irin wannan hatsaniyar yaran nan da ku suke koyi, ku dena aikata rashin ɗa'a suna jinku" Sunusi yace "to malam, insha Allah" Malam na barin gurin, Sunusi yaiwa Haladu wani Mugun kallo irin na zan haɗu da kai ne, sannan ya fice. Haladu kuwa ajiyar zuciya yai yana fatan Allah ya tsare shi daga Sharrin Sunusi, dan Sunusi ba shi da imani sam. Kwana uku kenan, Sadik yana sintiri a tsakanin gidan su Farhan da na su Amin, har gidan su Nas yaje, amma akace shima baya nan yana dutse, baya so ya tunkari in da Mubarak babba yake ba tare da ya san in da Farhan take ba. Abun duniya ya damu Sadik, ya rasa in da ze sa ransa, gaba ɗaya Mother ta kasa gane kan Sadik gaba ɗaya, baya wuni a gida baya cin abinci, tun tana mitar har ta gaji ta ƙyaleshi, ta zata kawai kewar matarsa yake da ɗan sa, dama kuma tun da suka dawo Nigeria ba wani fita yake ba, dan haka kawai ta zaci se yanzu yake zaga abokansa. Wanka ma se yayi dagaske yake iyayi, salla kawai yake cikin kwanciyar hankali, raba dare yake ido biyu, haryanzu ya kasa gane dalilin da yasa ya manta da Farhan a duniyarsa, babban abunda yake ɗaga masa hankali be wuce batun Ganin Farhan da Mubarak da akace anyi ba, ya rasa in da ze sa kansa ya ji daɗi ba shi da wani burin da ya wuce ya saka Farhan a idonsa. "Nana ba zaki sha kunun nan ba se ya huce, se fama kike da waya a hannu tun ɗazu" Nana ta ɗan ɓata fuska tace "Inna, Besty yau kusan kwana Biyar be kira mu ba, kuma ni na kira wayarsa amma ba ta shiga" Inna tace "waye kuma haka?" Nana ce "baban Sahal mana, kullum fa se ya kirani a waya, yace in kara wayar a jikin Sahal yaji numfashinsa amma kwana biyar be neme mu ba" Inna tace "to jiki da jink, ai dole wataran ze gaji ko?" "Inna yau fa kwana biyar, Allah ya sa Lafiya yake hankalina ya fara tashi" "Ban da abunki ai Lafiya ita ke ɓuya, yana nan lafiya insha Allah" "To Inna Allah yasa, amma yana da kula sosai in lafiya baze kasa kiranmu tsawon wannan lokacin ba" Inna tace "to ai se kiyi, tun da akan ku ze ƙare" Nana ta ja bakinta tai shiru, amma dai jikinta na bata akwai wani abu a ƙasa. Yauma da safiyar Allah Sadik yana hanya gari ya ƙarasa wayewa, hanyar makarantar su Amir ƙanin Farhan yaje ya tsaya, da Amir yaga Sadik se da abun ya bashi mamaki ba ze iya faɗin sau nawa yaga Sadik ba, ba yau ba gobe cikin sintiri yake, gashi kamar Farhan ta san da zuwansa taƙi zaman gida sam. Sadik ya nufo Amir, Amira ya gaisheshi ya amsa sannan yace "Ameer dan Allah ko lambar Farhan ka bani mana" Ameer yace "dan Allah kayi haƙuri, wallahi ba ta nan, dan Allah in wani abun tai maka kayi haƙuri, ka barta ta ji da halin da take ciki" Sadik yace "a wani halin take dan Allah, ka gayamin" Shiru Amir yai, se ga ƙwalla ta taru a idonsa zeyi kuka. Sadik ya dafa kafaɗun Amir yace "dan Allah ka gayamin halin da take ciki, da kuma in da zan sameta" 'gaskiya ko ɗaya ba zan iya gaya maka ba, amma kaje gobe in Allah ya kaimu zan nemo lambar ta ka zo in baka" Daga haka Amira ya zame kafaɗarsa yai gaba abunsa. Sadik ya koma cikin mota ya kifa kansa a kan sitiyari, yana sauke numfashi da kyar, ga cikinsa har wani ciwo yake, saboda Azabar yunwa har wata ramar dole yayi. Wasa wasa Har ta gaji da kiran layin Sadik amma kullum a kashe, dan harta fara kuka a ɓoye dan kar Inna ta gane tai ta mata faɗa. Amir har mamakin nacin Sadik yake, dan a ƙofar Gidan ya tarar da Sadik da uwar sassafiya. Ya koma gida ya ɗakkowa Sadik lambar Farhan a jikin takadda. Wata irin ajiyar zuciya Sadik yai, ji yake tamkar yaga Farhan, dubu biyar ya bawa Amir, amma fafur yaƙi karɓa. Se dai Sadik be fito da waya ba, dan haka ya nufi gida, kawai ya ratse hanya ya koma gidansu Amin. Megadin su Amin na ganinsa yai murmushi yace "a wannan karon kayi sa'a, ya shigo jiya da daddare, bari in masa Magana. Kusan mintuna biyar da shigar megadin, se gasu tare da Amin, shima ya ƙara girma yai fresh, ya fito fuskar sa cike da fara'a yana "Takawarka lafiya Prince namu, ba amana wallahi" A Wani irin fusace Sadik ya buɗe murfin motar ya fito, fuskar sa babu walwala ya ƙure Amin da ido, cikin huci yace "Aminu ina Farhan take?" Amin yace "wacw irin tambaya ce wannan? Ai kai zan wa wannan tambayar" "Kayi haukane Amin? Ina tambayar ka kana nema ka raina min hankali?" "Kai zan tambaya ko kayi hauka ne? Ni ka barwa ajiyarta ne? Ka tafi ka manta da batun Yarinyar mutane tsawon lokaci, kaje kai Aurenka kuma ka zo nan kana min hauka, kaje gidansu mana ka tambaya" A fusace Sadik ya fizgo Amin, ya haɗa shi da jikin mota ya zuba masa ido jikinsa na rawa yace "Al'ameen kai na barwa Amanar Farhan kan in tafi, ko ka manta Sadik baya mantuwa? Amina meye haɗin Farhan da Mubarak, Ɗan Ala ya gayamin ranar ƙarshe da ta zo makaranta tare ya ganku kai da ita da shi" Sadik ya haɗa hannayensa kamar me neman gafara 🙏 cikin rauni yace "Amin, kar ka gayamin kun ɓata min Farhan, ka buɗe baki kaimin bayani, ka tsaya kana kallona" ya ƙarasa maganar cikin tsawa idonsa yai wani irin ja. Amin yace "Am sorry Sadik" "Sorry for what? Kai min bayani" "Sadik, ba laifina bane, nayi iya yina gurin bata kariya, but i fails you, I don't know how to explain amma koma mene da sa hannun Babba da Taslim da kuma Nas" Sadik ya danƙi sumar kansa yana jin yadda kalaman Amin ke sukar zuciyarsa ɗaya bayan ɗaya. "Just cut the story Amin, nagode Sosai da sosai, ka gayawa Mubarak Babba da Nas, idona idon ɗaya daga cikin su sena kashesu, mussaman Mubarak" Amin yace "Sadik kabi komai a hankali, kar kai kisan kai, kuma koma menene laifinka ne daka tsallake ka tafi ka barta kaje kai Auren ka, ka sa...... "Shut up kan in fara ta kanka" yai maganar yana shaƙe Amina. A guje megadin ya zo ya raba su yana mamakin meya haɗasu haka? Yasan abokaine sosai da sosai amma ya haka ta faru a tsakanin su bayan shafe dogon lokaci basu haɗu ba. Sadik be jira komai ba ya hau mota, da fari farautar Mubarak ya so yayi, amma se yaga ɓata lokaci ne, sanin in da Farhan take shi yafi mahimmanci, dan haka ya nufi gida, jikinsa na wata irin tsuma kamar wanda ake bugawa gangi. Yana zuwa gida beyi wata wata ba, ya ɗau wayarsa ya kunna, ya saka lambar Farhan a ciki, ya shiga kiran layin. Sedai ko da yaji wayar ta shiga, se ƙirjinsa ya tsananta bugawa, har ya fara jin Kamar zuciyarsa na barazanar tsaga ƙirjinsa, amma haka ya dake cike da ƙwarin gwiwa yana sauraron amon shigar wayar. Farhan kuwa tana cikin maye, dan haka ko yatsanta kasa ɗagawa tayi, tana kwance tana jin wayar na ringing ta miƙa hannunta ta ɗau wayar abu ya gagara, idanunta suka cigaba da lumshewa ta cigaba da baccinta. Sadik ya kirata ya kai sau talatin, amma ba wanda ta ɗaga, be san lokacin da zuciya ta ɗebe shi, yai jifa da wayar ba, Ta faɗi ta tarwatse a gurin, ya koma gefe yana huci, ya kai idonsa kan hoton Farhan a jikin laptop ɗin sa, yace "Why Princess, why don't you pick my calls? Kina son in mutu ne?" Ya ƙarasa maganar yana dafe goshinsa. A ranar Sadik ya fita ya siyo wata wayar, Mother se masifa take akan ta gaji da wannan jigilar da yake, na tare da tasan in da yake zuwa ba, ai be kula Mother ba ya shige ɗakinsa ya rufe ƙofa. Haka ya wanzu har cikin dare yana kiran layin Farhan, amma ba bu amsa. Wata shawara ya yanke a ransa, kasamcewar ya san kan computer sosai da sosai, nan ya shiga ƙoƙarin bin diddigin layin Farhan, amma Network ya hanashi samun abinda yake so. Yadda yaga rana haka yaga dare, ko kaɗan be rintsa ba, sam baya jin baccin ma. Wayewar garin Allah, haka ya koma ka computer yana cigaba da ƙoƙarin locating in da Farhan take ta hanyar lambar wayarta. Se yamma sannan Sadik ya iya gano in da Farhan take, Cikin azama ya kuma fafarar mota, ya bar gidan sannu a hankali ya shiga rukunin gidaje na Nassarawa GRA da ke garin Kano, yana yi yana duba wayarsa, a haka ya ƙaraso wani katafaren Hotel. Saboda sauri a waje yai parking ɗin motar, ya shiga cikin Hotel ɗin, tuni zuciyar Sadik ta karaya ganin Farhan na cikin Hotel. Sannu a hankali se gashi a ƙofar ɗaki me lamba ta goma sha ɗaya, wanda ya kasance VIP, hamshaƙan manyan mutane ne ke kama irin wannan ɗakin. Sadik ya sa hannunsa a jikin handle ɗin ƙofar ɗakin, zuciyrsa na wani irin harbawa, cike da Zullumi da fargaba ya buɗe ƙofar yaji a buɗe take, ya shiga ɗakin, ba ya fargabar koma ba ɗakin ya shigo ba, babban burinsa kawai ya sa Farhan a idonsa. Ɗakin ba kowa, ya ƙarewa ɗakin kallo, ya kuma kiran lambar Farhan, ai kuwa yaji ringing ɗin wayar a ɗakin, yana ɗaga kai ya kalli in da sautin ke tashi, idonsa ya sauka akan wayar da ke kan side bed, ga manyan kwalaben magani da wasu tablets a akai. Jikinsa ya ɗau rawa ya ƙarasa gaban side bed ɗin, Sadik ya shiga jujjuya magunan zuciyarsa na wani irin zafi, irin ƙwayoyin da Mubarak ke ta'amalli da su ne, na saka maye. Ƙofar banɗaki yaji an buɗe, ya ɗaga idonsa ya zubawa ƙofar. Sanye take da wata matatsiyar riga doguwa iya gwiwar ta, sosai rigar ta fitar da shape ɗin jikinta, kanta ba ɗan kwali, tana ɗan dafa kanta alamar ko yana mata ciwo, ko haryanzu tana maye. Ƙamshin turaren da ya daki hancinta ne yasa kanta ya sara, ta san babu wanda take irin wannan ƙamshin se Sadik, tun da ya bar duniyarta ba ta sake jin sa ba, ta ɗago manya manyan idanunta da suka ɗan yi ja. Wani irin ƙuuuu cikinta ya bayar, ta shiga ƙifta idanuwa, dan ta tabattar da ƙwayar da ta sha ta saketa, ko kuma gizo ne abunda take gani. Sadik ya zuba mata ido, ko ƙiftawa ba yayi, ta tabbata Farhan ɗin sa ta sauka daga turbar da ya santa  a kai. Jiki a sanyaye Ya fara tunkararata, wata irin ƙaunarta na fizagarsa. "Stop their!" Ta daka masa tsawa. Ƙoƙarin tunkararta yake amma ta kuma cewa "kar ka zo in da nake, i said you should Stop their". "Farhan, nine fa Sadik ɗinki ne" "Shut up, bad lier ko suna in dai da kai ake ba na ƙaunar jinsa, azzalumi mayaudari leave my room now, get out from sight". Kamar Sadik ze kuka yace "Farhan dan Allah ki saurareni" "Wallahi ka zo in da nake se na caka maka abu, bana sonka bana son ganinka na tsaneka, na tsani me sonka ka fita ka bani guri" ta ƙarasa maganar kanta na juyawa, da son tabattar da mafarki take ba, dan yana yawan yi mata gizo a cikin mayenta. Ya ƙaraso in da take, amma ta ja da baya ta ɗago fuskarta da tai jawur, kamar mayunwaciyar kura ta cigaba da Magana "nace maka ka fita ka barmin ɗaki na, nan gurin sana'ata ne, bana buƙatar mutum irinka a nan" Sadik yace "Farhan ko sau ɗaya ki saurareni" "Ba zan taɓa saurarar ƙarya da yaudar ba, daga bakin maƙaryaci, kalli halin da nake ciki duk sanadiyyar ka, ka fita nace maka kan in maka illa da kwalba yanzun nan" Daskarewa Sadik yai yana kallon Farhan ɗin sa, me tsananin kunya da bin unarninsa yau ita ke masa tsawa haka. Ai be Aune ba ta dinga hankaɗashi, gudun kar taiwa kanta illa yasa ya ƙyaleta ta hankaɗashi har waje, ta rufe ƙofarta ta zauna a bayan ƙofar tana rera kuka. Sadik ya jingina da jikin ƙofar, yana sauraron sautin kukanta, dake ƙona zuciyar sa. Wani baƙin ciki ne ya tasowa Farhan, jin yadda ƙasan zuciyarta ya ƙawata mata girma da kyan da Sadik ya ƙara yi, ta tabattar wa da kanta zahiri ne abunda ya faru ba Sharrin ƙwaya ba. Sautin fasa kwalba Sadik yaji, daga nan yaji ta ƙwala ƙara, a gigice ya jinjina ƙofar amma yaji ta rufeta gam. AYI HAƘURI A LALLAƁA BA EDITING, WAYAR TA SAMU MATSALA. A gigice Sadik ya shiga jijjiga ƙofar yana kiran Sunan Farhan, Amma ta ƙi buɗe ƙofar, ya nufi reception cikin hanzari ya sanar musu da abunda ke faruwa, aka zo da spare key, aka buɗe ƙofar, tana zaune tana kuka, ta yanka hannunta yana ta zubar da jini. Sadik ya shiga cikin ɗakin da Sauri ya tunkareta, amma ta miƙe ta ɗau sauran kwalbar, ta saita shi tace "wallahi ka zo in da nake se na caka maka ita" So makaho ya cigab da nufarta, yana faɗin "ki tsaya Farhan, ba ki ga yadda hannunki ke zubda jini bane? Ki tsaya ki ji" Ganin ba shi da niyyar dena kusanto in da take, ya sa ta saita cikin ta da tsinin kwalbar, tace "Wallahi ka zo in da nake se na sokawa kaina kowa ya huta". Receptionist ɗin da suka zo tare da Sadik tace "kaga malam, dan Allah tunda kaine ba ta son gani ka ƙyaleta, kar ta kashe kanta ku janyo mana bala'i" Jiki a sanyaye Sadik ya juyo ya baro ɗakin, ya fito waje ya zauna, ya dafe kansa yana jin yadda kan ke sara masa, wai yau shi Farhan ke gudu haka, take jifa da miyagun maganganu. Farhan ba ta damu da yadda jini ke zuba a hannunta ba, sedai yadda take jin haushin zuciyarta da ƙasan zuciyar ke ƙoƙarin shiga cikin farincikin ganin masoyinta. Ta yanke shawarar barin Hotel ɗin ta canza wani, dan idan ta koma gida ma ze iya binta can, dan haka ta zura doguwar rigar ta, ta zauna a gefen gado ta ɗau wayarta missed calls rututu ta gani, abun ya bata mamaki wannan lambar waye haka?. Sadik na nan zaune ya ga wani hamshaƙin mutum ya taho, tinkis tinkis ya nufi ƙofar ɗakin da Farhan take, ai a zuciye Sadik ya miƙe, ya rufa masa baya, cikin azama ya sha gabansa ya tare ƙofar ɗakin. Mutumin ya kalli Sadik yace "kai Samari lafiya kuwa?" Sadik yace "kai zan tambaya ko lafiya" "A'a kaga matsa ka bani hanya" "Wallahi in dai ina motsi a gurin nan ba ka isa ka shiga ɗakin nan ba" Mutumin yai saroro yana kallon Sadik yace "kai wai meye matsalar ka ne?" "Matsalata shine ka koma, ba zaka shiga ɗakin nan ba" "A saboda me?" Mutumin ya tambayi Sadik cikin mamaki. "A saboda mata ta ce a ciki" "Ikon Allah, wato Farhan ta fara mu'amala da mahaukata kenan" Cikin ɗaga murya Sadik yace "kaine mahaukaci, tsohon banza da na wofi, ka zo kana haikewa ƙanƙanuwar yarinya 'yar cikinka dan Allah dube ka mutumin banza da na wofi" Galala ya buɗe baki yana kallon Sadik, ba'a taɓa baƙanta masa rai aka ci mutuncin sa kamar yadda Sadik yai masa yau ba. Ya nuna kansa da yatsansa yace "ka san ko ni waye kuwa?" "Mutumin Banza mana, wanda be san ciwon kansa ba" "Yayi kyau, dole in sa akawomin ƙarshen rashin kunyarka a yau ba se gobe ba" Sadik yace "ba irina akewa barazana ba kaji ko" Jin hayaniya yasa Farhan Fitowa daga ɗakin, sedai ga mamakin ta taga Sadik a tsaye a gurin. Ta kalli Alhajin tace "ashe ka zo amma ba ka min magana ba" "Eh na zo, wannan sakaran yaron ne yai min rashin kunya ya hanani shigowa, waya zan azo a tafarmin da shi a koya masa hankali" Sadik ya tunkaro Farhan yana cewa "dan Allah Farhan ki saurareni, yanzu ki bari ina kai ki a duba hannunki, se muyi Magana" "Wallahi ka kuma doso in da nake, sena baka mamaki" ta maida Idonta ga mutumin nan tace  "Ya ci arzikina, ka ƙyaleshi ba ruwanka da shi, muje kawai" Cikin hanzari Farhan tai gaba, Sadik ya bita yana cigaba da kiran sunanta. Ba ta tsaya ko ina ba se jikin motar mutumin nan, cikin takaici mutumin yace "wai ke ina kika samo wannan mayen yaron ne mara hankali"? Abun takaici se taji Maganar da Alhajin yai ta ɓata mata rai, amma ta basar tace "buɗe min ni in shiga mu tafi" A zafafe Sadik ya ƙaraso gurin, dai dai lokacin ya buɗe mata motar za ta shiga, amma Sadik ya ture shi ya sa ƙafa ya daki murfin motar, ya juya kan Farhan yana huci, amma ya gaza furta komai. Tuni hankalin mutane ya fara dawowa kansu, Sadik ya kalli mutumin nan yace "wallahi idan ba ka fasa bibiyarta ba, se na tona maka Asiri a garin nan, se nayi maganinka kan ka kayi maganina tsohon banza da na wofi" Kan Sadik ya waiga tuni Farhan ta kak gate ɗin Hotel ɗin, ya zura da gudu ya bita sedai kan ya cin mata ta haye Napep tai gaba, ya juya kamar mahaukaci ya hau motarsa ya bisu, sedai ɓat suka ɓace masa. Duk da haka be karaya ba haka ya cigaba da bulayi a tsakanin unguwar nan, amma be ga Farhan ba balle alamarta. Be koma gida ba se bayan ƙarfe tara na dare, haka ya koma wujiga wujiga kamar wanda ya dawo daga filin yaƙi. Already yayi Sallah isha'i a waje, bq ya wuce dan kar ma Mother ta ganshi ta sa shi a gaba da tambayoyi. Ya ɗau wayarsa ya fara kiran wayar Farhan, sedai ya jita a kashe. Inna ce ta shigo ɗakin da Nana, take tana ta jijjiga Sahal da hannu ɗaya, yana ta uban kuka, hannu ɗaya kuma tana riƙe da wayarta tana dannawa, hasken wayar ya haska fuskar Nana tana zubar da hawaye. "Ke lafiyar ki kuwa?" Firgigit Nana ta shiga goge hawayenta, tace "bakomai" "Kamar ya bakomai kina kuka?" Aikuwa ta sake fashewa da kuka tace "Inna yau fa kwana takwas Besty be kirani ba, kuma ni na kira tasa wayar ba ta shiga" "Ikon Allah, saboda mijin naki kika zauna kina kuka haka? Ke da kika ce ba kya son sa da" Nana ta tura baki tana ci-gaba da share hawaye. "To ki kula da yaron hannunki, ki rarrashe shi, seki kira uwarsa kiji ko yana lafiya" "Inna Kunya nake ji, ba zan iya kiranta ba" "To ni ki kira, se ki bani in mata Magana" Cikin Sauri Nana ta nemo lambar Mother, ta kira ta miƙawa Inna. Mother taga baƙuwar lamba, dan ba ta da lambar Nana, amma jin muryar Inna ta ɗan sake suka gaisa. Inna tace "dama matar Sadik ce tace ko lafiya, yau kusa kwana takwas be kira su ba, duk tabi ta ɗaga hankalinta, kuma shi tasa wayar ba ta shiga" Mother tace "ai Sadik ɗin ne gaba ɗaya na kasa gane kansa kwanan nan, ban san meke damunsa ba amma bari in bashi wayar" Mother ta katse kiran, ta wuce BQ ta tarar da shi a kwance akan kujera, yai shiru ya dulmiya cikin tunani. Mother tace "Allah yai maka maganin ko ma mene yake damunka, na rasa gane kanka gaba ɗaya kwanan nan, kuma kaƙi gayamin meke damunka" Sadik yai shiru bece komai ba, se gyara kwanciyarsa da yai. Mother ta kira layin Nana, Nana ta gaisheta, ta amsa mata tace ya suke ya Sahal, Nana tace suna lafiya, daga haka ta miƙawa Sadik wayar. "Assalamu alaikum" Sadik ya faɗa a Sanyaye. "Besty, laifin me mu kai maka haka, ka manta damu gaba ɗaya, na kiraka wayarka a kashe me mu kai maka ne?" Jikin Sadik yau sanyi ƙalau, cikin rashin ƙwarin jiki yace "Am sorry Nana, bana jin daɗi ne" "Shine kake faɗan sunana ko? Me nai maka dan Allah" ta ƙarasa maganar tana kuka sosai. "Subhanallah, ya da kuka kuma ke baki san kin zama Mum ba ne, ke ki kuka Daddyna ma yayi" "To ba kai ne ba, ka manta da mu gaba ɗaya, hankalina duk ya tashi na rasa meke faruwa" "Tabbas nayi muku laifi, amma kiyi haƙuri bana jin daɗi ne" Cikin kulawa Nana tace "eyya, meke damunka?" "Ciwon kai nake fama ne" "Sannu, ko dai in dawo ne? Nasan ba ka wani kula da kanka, kai in baka da lafiya gaba ɗaya wani iri kake komawa" Yai murmushi na ƙarfin hali yace "No,  kar ki damu ina kula da kaina Sosai, ki zamanki idan kin huta se in zo in ɗakko ku" "To kaje Asibiti ne?" "Eh naje, har an bani magani ma" "Nifa duk hankalina ya tashi, muryarka fa duk tayi wani iri Allah" tai maganar cikin shagwaɓa. Ya lumshe ido yace "Besty" "Na'am Besty na" ta amsa masa. "Dan Allah ki rarrasan min ɗa, ina jin kukan sa fa" "Bayan ma ka dena kiransa a waya kaji ya yake" "Kiyi haƙuri, insha Allah hakan ba zata sake faruwa ba, ki tai min Addu'a" Tace "to shikenan, Allah ya baka lafiya nan ma ana tai mana saukar Alqur'ani Allah ya ƙara mana zaman lafiya ya baka lafiya, kuma kullum a idan nai salla ina maka Addu'a Allah ya yaye maka damuwar ka ya biya maka dukkan buƙatunka na Alkhairi" Tabbas yasan Nana tana yawan yi masa addu'a, ko ya sani ko be sani ba, wani irin tausayin ta ya mamaye zuciyar Sadik, tabbas yana son Nana, amma baze iya haƙura da Farhan ba, ko me ze faru ze yi duk me yuwuwa ya mallaki Farhan. "Besty ya kai shiru?" "Bakomai, anything special for me? Am missing you fa" yai maganar yana son basar da abunda ke ransa. "We are missing you too, in gaya maka Sahal ya fara dariya" "Dagaske, Allah ya sa be riga yi miki dariya kafin ni ba" "Ai se yana bacci yake yi, amma Inna tace ya fara ƙyuya, kallon mutane yake Sosai" "Ahh gaskiya gara in zo in taho da ku, tun kan ya fara yi min ƙyuya" Tai murmushi tace "Naji daɗi da naji muryarka, ka kula da kanka sosai kaji Besty na" Sadik yace "to my Asma, Ummu Sahal, Yarinya ta zama Mummy" "Hmm ai zama Mummyn nan ma ba sauƙi, daga Sahal na gama" "Baki isa ba, next year by now insha Allah kin kuma haihuwa" Nana tace "ba ka san ya ake ji in za'a haihu ba ko?" "Na sani mana, tunda tare mu kai naƙuda" Dariya tai tace "besty me, se da na zo ƙauye naji muna missing ɗin ka wallahi" Ya shafi sumar kansa yace "karki damu, insha Allah zuwa next week zan shigo in ɗakko ku, nima na fi son in jiku a kusa dani" "To shikenan, have a nice day, Allah ya baka lafiya ingantacciya abu Sahal" Sadik yace "thank you wifey, ki kulamin da kanki da babyna, a gaida Hakimi da Inna" "Zasuji insha Allah" "Kiss me before you quit the call" Nana tai murmushi tace "i will kiss you when we meet" "Da kiss da me?" Yai maganar yana murmushi. "Da kiss da ba ruwana, Inna tana jinka" Da sauri Sadik ya kashe wayar, ya lumshe ido tare da ajiyar zuciya, yana jin tausayin Nana sosai da sosai, saboda sosai alamu sun nuna ta na son Sa sosai da sosai. Inna ta shigo ɗakin tace 'ikon Allah, har kin watstsake kin dena kukan?" Tai murmushi tana sunkuyar da kai cike da jin kunya. "Hankalinki ya kwanta dai ko? Maman soyayya" Nana ta rufe fuska tana dariya. Sadik ya miƙe ya shiga gida, kaiwa Mother wayarta, ya shiga sashinta da Sallama ta amsa masa, ya ƙarasa ya miƙa mata wayar yace "Mother ga shi" Mother 5a kalleshi tace "zauna za muyi magana ne" Sadik ya nemi guri ya zauna, Mother ta ɗan ƙare masa kallo sannan tace "Sadik, ka gayamin gaskiya tsakanin ka da Allah, menene yake damunka" Sadik yace "Mother me kika gani?" "Kamar ya me na gani, kai baka ga yadda gaba ɗaya ka koma bane? Ba ka walwala kamar mara lafiya duk ka canza, wanda da ba haka kake ba, ka gayamin ko dai har yanzu Auren ne ba ka so?" Yace "A'a Ina so" "Ko dai akwai wata matsala ne?" Yace "Mother wallahia bakomai fa" Mother tai shiru sannan tace "kaga kuwa yadda ka koma? Da Abba na  gari da shi zan haɗaka ban sani ba ko shi ka gaya masa". "Allah Mother bakomai dagaske nake" Mother tai ajiyar zuciya tace "shikenan tashi ka je, Allah ya kyauta koma mene yake damunka Allah ya yaye maka" Jiki a sanyaye ya amsa da Ameen, ya tashi ya fita Mother ta bi bayansa da kallo. Komawa yai ya cigaba da lissafin ta in da ze ɓullowa Farhan, ko sau ɗaya ta yadda ta saurare shi, taji uzurinsa, yayi mamakin yadda ta rufe ido ta nuna ba ta ko ƙaunar ganinsa, tabbas be kyauta mata ba, amma har ga Allah idan Farhan ta guje shi be san yadda ze yi ba, saboda yana matuƙar ƙaunar ta. Farhan kuwa suna tafe a hanya tana rera kuka, ga hannunta na ta zubda jini, Asibitin su Abbas ta sa me Napep ya kaita. Ta sauka ta biya shi kuɗinsa, ta shiga sedai Abbas ɗin baya nan, wata Nurse tace bari suyi attending ɗin ta ai dressing ɗin hannun, amma tace ita Abbas take nema, ga wayarta ta ɗauke ba caji, da wayar Asibiti ta kira shi, ta sanar da shi cewar ga ta a Asibitin su tana jiransa. Ai cikin hanzari ya kamo hanyar zuwa Asibitin, saboda yadda yai kwanaki yana zuwa gidansu bata nan, kuma taƙi yadda ta gaya masa in da take. Yana zuwa ya tarar da ita a reception, ta naɗe hannunta da mayafinta. Da hanzari ya ƙarasa in da take yace "Farhan, ya akayi ne lafiya kuwa?" Idon ta fal ƙwalla tace "ciwo naji" Yace "subhanallah, garin yaya? Meyasa baki bari an duba ciwon kan in zo ba?" Ta share hawayen fuskarata tace "saboda so nake ai min a hankali, kuma na san kai a hankali za kai min" Yace "ok to shikenan, mu shiga emergency in duba" Ta miƙe, yana tafe tana binsa a baya, har suka shiga, ta kwance mayafin, ya fara duba ciwon, ya kalleta yace "dame kika ji wannan ciwon?" "Kwalba" ta ba shi amsa kai tsaye. "Garin yaya?" Shiru tai ba tace komai ba, duk yadda yai ta gaya masa amma ta ƙi, ya ƙyaleta yai mata dressing, ya ɗakko mata magani, da jakar kayanta da ta zo da ita, ya kai motarsa tana biye da shi zuwa motar. Sam Abbas be mata maganar a ina take kwana ba, da rashin ɗaga wayarsa se ma sannu da yake ta jera mata. Suna tafe amma tai shiru, tana ta saƙawa tana Warwarewa, gani take kamar har yanzu abubuwan da suke faruwa sharrin ƙwayoyin da take sha ne, amma ba Sadik ta gani a zahiri ba. Har sukaje gida ba ta ce masa uffan ba, ta sauka ta ɗau jakarta ta ta kalleshi tace "Nagode sosai doctor, Allah ya saka da alkhairi" be amsa ba se ɗan tsura mata ido da yayi, sannan yace "ki kula da kanki sosai, ki kula da shan magani" Ta jinjina masa kai ta wuce, Umma na tsakar gida tana aiki Farhan ta zo tai salama ta wuce, ta amsa mata ba tare da ta kuma ce mata koma ba, ita ma Farhan ba tace koman ba ta wuce ɗakinta, ta samu guri ta zauna a gefen katifarta, ta dafe kanta tai shiruu tana sake tunani tabbas Sadik ɗin ne dai ya ke ƙoƙarin dawowa duniyarta. Tabbas dawowar Sadik duniyar ta barazana ne a gareta da ka iya jefata cikin wani mawuyacin hali wanda yafi wanda take ciki a yanzu. Ta miƙa hannu ta janyo pillow, ta kwanta a kai tai shiru, wasu irin hawaye da bata san dalilin zubarsu ba suka shiga zarya da rigr rigen fitowa daga idonta, ko a mafarki ba ta taɓa tunanin za ta sake sanya Sadik a idonta ba. Gaba ɗaya Lilly a takure take da zaman cikin barrack ɗin nan, makaranta kawai take zuwa, shima a kaita a ɗakkota, gashi ba ta saba da mutan gidan ba sam, ga wata irin kewar gida take yi, gani take kamar sun manta da ita gaba daya, a sati sau ɗaya tak Major ya bada umarnin ai waya da ita daga can gida. Babban abunda ya tayar mata da hankali be wuce wani babban soja da kusan sa'an su Daddynta ne ba, da ya nuna yana sonta, tun da ya ganta a barrack ɗin, yake sintiri a nan gidan da take, kuma Abokin Daddynta yace ya saurare shi zeyi magana da Daddynta, abunda yace shikenan. Hankalinta a matuƙar tashe yake, ta san yadda Daddy yake a ƙulen nan da ita, amsa wa wannan sojan shi yafi komai sauƙi a gurinsa. Sir Nazir kam shekaru uku aka yanke masa a gidan yari, da biyan tarar naira dubu ɗari da Ashirin na abunda ya aikata, in da Allah ya rufa masa asiri a case ɗin ba fyaɗe akace ba, lalata ne da ƙaramar yarinya da kuma zubar da juna biyu. Shi kansa me makarantar ya rabauta da watanni takwas a gidan gyaran hali, ba tare da zaɓin tara ba, kuma aka kulle makarantar sa kullewa ta har abada. Ko da garin Allah ya waye, Farhan ta farka da ga Bacci, ta duba hannunta tagan shi da ciwo, hakan ya sake tabbatar mata ba sharrin ƙwaya bane, Sadik ne dai ta gani ya dawo gareta. 'kinyi haukane, mutumin da ya gujeki yaje yai Aure har da ɗa, shine zaki murnar dawowarsa rayuwar ki, shine dalilin shigar ki wannan halin fa, me ze dawo yai miki?' wata zuciyar ta tunatar da ita. Seda tai kuka me isarta Sannan ta miƙe ta nufi banɗaki. Sadik ya cigaba da zaryar gidansu Farhan, sedai tun ganin da yai mata a Hotel ba su sake haɗuwa ba, duk zuwan da ze se ace bata nan. Gefe guda baya son saka Nana a cikin damuwa, haka nan yake kiranta a waya suyi hira, amma hakan be hana ta gane yana cikin damuwa ba, ganin yadda ta damu sosai yasa yace ze je ya taho da su Ranar Asabar, dan yana kewarsu sosai. Ko da ya sanar da Mother zeje ɗakko su Nana tai murna, dan ko ba komai ta ga jikanta dan tayi kewarsa. Sedai tace "yanzu kai kaɗai zakaje ɗakko su, zaka iya driving har garin nan?" Sadik yai murmushi yace "Haba Mother, nifa yanzu magidanci ne" Mother tace "sannu sarkin fitsararru" Sadik yai murmushi ya fice. Inna kuwa se gyara Nana take, ita kuwa Nana bata san me ake ba, tai ta mita ita ta gaji da wannan abubuwan da Inna take bata, masu ɓata mata ciki da sata zawo. Inna tace "shashasha, ke kam Allah ya nunan lokacin da zaki hankali, nan gaba in kika gane amfanin abunda nake miki, kya dawo da kanki ki nema" Nana ta yamutsa fuska tace "wannan ɗin? Ni cikina yai ta ciwo idan kika bani, ni ba rashin lafiya ba amma ki ta bani wannan abubuwan, da masu da ɗi da marasa daɗi" Inna tace "dan ubanki duk wannan rawar kan da kike zaki koma gidan miji, haka zaki koma masa ba wani shiri, to karki abunda na saki, ke kin haihu ma amma har yanzu banga hankali ya fara shigarki ba" Tace "Nifa ba rawar kai nake ba Inna" Inna tace "kya dai ji da shi". Farhan kusan kwanaki biyar da haɗuwarsu da Sadik, ta kulle duk wata hanyar da zasu sake haɗuwa ta toshe ta, sedai hakan ya kasa yi mata daɗi, tana son ko sau ɗaya ta sake sa shi a idonta ko taji daɗi. Idan ta tuna abunda yai mata, se taji wani irin mugun haushin kanta Ya kamata. Da Sadik ya je ɗakko su Nana, Nana tai mamakin yadda ta rame sosai da sosai, Hakiki yai musu nasiha sosai da fatan samun zaman lafiya da zuriya ɗayyiba, Sadik ya ƙanƙame Sahal yana shafa shi, yana jin kamar ya Shekara be ganshi ba, wata irin ƙaunar yaron na sake kama zuciyar sa. Bayan sallar azahar suka kamo hanyar dawowa Kano, Nana ta haɗe rai tana tura baki. Sadik yace "Madam ya dai?" "Besty ni kamar ba kai murnar gani na ba, ta Sahal kawai kake" Ya gyara zamansa yace "Ai ke no matter how zan nuna miki yadda nai missing ɗinki, ba zaki gane ba se mun fi haka yawa" Tsit tai ba ta kuma magana ba, yace "ya ki kai shiru kuma?" Tace "bakomai" yai murmushi ya cigaba da tuƙinsa, sedai tana kallon yadda fuskarsa babu walwala, damuwa kwance a fuskarsa. Abun Allah Mother, har da sawa ayiwa su Nana girki, aka gyara musu BQ, a cewarta ba zata iya da fitsarar Sadik ba, su koma can su zauna, kan Abba ya dawo a ga yiwuwar komawarsu London, dan har yanzu ba a yanke yanayin komawarsu ba, saboda Sahal. Nana tai mamakin yadda Mother ta karɓeta, suna zuwa ta karɓi Sahal, sati ukun da tai ba ta ganshi ba, ta ga ya ƙara girma da wayo, sedai ta bakin inna Sahal ya fara gane uwassa, dan Kuka ya dinga tsalawa Mother, seda Sadik ya karɓe shi Sannan yai shiru. Mother tace "yau naga fitsararen ɗa, har ka san iyayenka? Aikuwa ƙyuya ba'a nan gidan ba". Tun da Sadik ya kawo Su Nana ya fice cigaba da farautar neman Farhan. Nana kuwa turaren wuta ta kukkuna a BQ ɗin, irin wanda Inna ta sa aka haɗa mata da na barka da ta samu. Sahal kuwa dama yana gurin Mother, duk da kukan da yake yi, ta goye shi har yai shiru. Nana Ba ta sake saka Sadi a idonta ba, se bayan sallar isha'i. Ya dawo ya tarar ta sha kwalliya cikin ƙananan kaya, Ta gyara Sahal cikin kayan baccinsa se se bacci yake. Nana ta gabatar masa da Abincin da Mother ta aiko musu, sedai taga se cakala yake yi, ta sashi a gaba da mita da tambayar meke damunsa, ba shi da amsar ba ta, dan haka ya dinga tura Abincin nan, ba dan yana jin daɗinsa ba, sedai bayan yaci Abincin yaji daɗi dan rabonsa da abinci ya ci ya ƙoshi har ya manta. Sedai duk yadda yake iƙrarin yai missing ɗinta, da yadda tai masa kyau amma ya kasa komai saboda damuwar da ke sasaƙar zuciyar sa. Nana ba ta damu ba, ita rungumetan da yai ma a jikinsa ya ishe ta nishaɗi. Abu kamar wasa Damuwar Sadik ta shafi Nana, duk baya walwala, sedai in ya ɗan ɗau Sahal, ga tunani da rashin cin abinci da yake, tayi tayi amma ya ƙi gayamata damuwarsa. Yanzu ma bacci take, amma ta buɗe ido taga Sadik a zaune, ya zubawa window ido. Kawai ta fashe da kuka, gigice ya juyo yana faɗin "lafiya kuwa?" "Ban sani ba, ya kake so in yi da raina Sadik? Damuwaka fa ba kai kaɗai ta dama ba, farincikina da ɗanmu yana da alaƙa da farincikin ka na rasa laifin da nai maka, kace ban maka laifi ba amma kuma duk ka canza min, ba ka walwala ba ka isashen bacci, ni ya kake so inyi ne?" Tai maganar tana fashewa da kuka. Sosai tausayinta ya mamaye zuciyar Sadik, idan da alƙawari be kamata ace ya bar hawayen Nana na zuba ba. Ya janyo ta jikinsa, ya shiga shafa bayanta yace "Besty na, bana son ganin hawayen ki, dan Allah ki yafe min, ki cigaba da yi min Addu'a, Allah ya yaye min dmuwata" "To Meye damuwar taka to?" Kwanciya yai tare da kwantar da ita a jikinsa yace "Nana, kina sona ne?" Jin tambayar tai banbarakwai, amma tai shiru. "Ni ina sonki Nana" yarrr ta ji a jikinta. "Ina sonki Nana, so da gaske ba wasa ba, amma....., Amma.... Asma" "Na'am Besty" "Dan Allah duk abunda ze taso, ki zama me min adalci, kema idan kika barni zan shiga damuwa, dan Allah Husna" "Nifa ban gane duk wannan maganar taka ba" Yai ajiyar zuciya yace "don't mind me, just believe that I love you" Kwantar da kanta ta sake yi a jikinsa, yace "to ni ba kya sona?" "Mmmm, ina sonka sosai da sosai baban Sahal, Allah yaye maka damuwar ka ya baka abinda kake so duniya da lahira" "Ameen my Love" Daga nan kuma suka shiga fagen soyayya. Wayewar gari Sadik Nana na bacci, Sadik ya fita, unguwar su Farhan kai tsaye ya wuce, yai parking a bakin hanya, ya shiga cikin layinsu, ya samu guri ya zauna ya zubawa ƙofar gidansu ido, yana nan zaune se ga Motar Abbas tai parking, Sadik yana zaune yana kallon ƙofar gidan sega Farhan ta fito cikin uniform, Sadik ya miƙw cikin azama amma tuni ta shige Motar Abbas tace su tafi. Kamar taɓaɓe haka ya koma tasa motar, ya dinga bin su a baya, Farhan ta ga Sadik, amma Abbas be lura da su yake bi ba. Har ƙofar makarantar Sadik ya bisu, Abbas ya sauke Farhan, ta shiga makarantar, haka Sadik ya samu guri ya zauna, yana jiran har a tashi su Farhan daga makarantar. Sadik ya daɗe a gurin, har ƙarfe biyu tun safe yana can, ɗalibai na ta fitowa Farhan ta fito itama, ta samu guri ta tsaya tana dannan wayar hannunta da alama kiran waya za tai. Ƙamshin nan dai da ya saba kashe mata jiki, tare da narka mata zuciya shi taji. Ta ɗag idanunta ta saka a na Sadik, ja da baya tai zata raɓa shi ta wuce, amma ya sha gabanta ya tsaya yana ƙare mata kallo. "Bani hanya zan wuce ko" "Farhan, yanzu ni kike gudu haka? Na san ni mai laifi ne, amma ki bani dama ko sau ɗaya kiji ta bakina" Tsaki tai ta juya zata bar gurin, amma ya riƙo dantsenta na dama, aikuwa ta sa na hagun ta bashi lafiyayyaen mari. A fusace tace "kana da abunda zaka gayamin ne? Meyw baka gayamin a baya ba, tarin ƙarairayi da daɗin baki, idan ka kuma nuna ka sanni, se na maka tijarar da baka taɓa tunani ba, ba Farhan ɗin da ka sani bace a baya, wannan tantiriyar 'yar maye ce, da ta goge a hannun 'yan iskan abokanka" Ya dafe kuncinsa yai murmushi yace "ni haryanzu Farhan ɗina nake gani, sam masifar taƙi hawa dake, soyayyata da kewata kawai nake gani a idonki! AM SORRY NOT EDITED! Tuni idon mutane ya dawo kansu Sadik, amma ko a jikinsa ya cigaba da yiwa Farhan magana, "Farhan ba haka kike ba, kuma wannan yanayin da kike ciki ma yaƙi karɓar zubin halayyar da Allah yai miki, dan Allah ki bani dama Farhan, kiji ta bakina" Ko kallonsa ba ta kuma yi ba, kawai ta sa kai ta cigaba da tafiyarta, Yayin da wani irin tausayin sa ya fara mamaye ilahirin zuciyar ta. Sadik ba ya son cigaba da takura mata, saboda haka ya hau motarsa ya koma gidansu Amin. Ko da Amin ya ga Sadik, a nesa da shi ya tsaya yana kallonsa. Sadik yace "magana na zo muyi Amin" Amina yace "mu yi ta daga nan ba zan zo ka sake shaƙe ni a banza ba" Sadik yace "am sorry, Wallahi ba abunda zan maka, Magana kawai nake son muyi" Da ƙyar Amin ya amince, Sadik ya ƙarasa in da yake, ya miƙa masa hannu suka gaisa, Sannan Sadik yace "Amin, dan Allah ina son ka gayamin tsakani da Allah, abunda ka sani tsakanin Farhan da Mubarak" Amin yai ajiyar zuciya sannan yace "tun bayan barinka makarantar, Farhan ta cigaba da zaryar neman ka, har ajinmu take zuwa, nine nake kwantar mata da hankali, ta ƙara nesanta kanta da mutane sosai fiye da da, se ta fara zuwa ajinmu tana neman a bata maganin hana damuwa, dan ta taɓa jin su Tasleem na maganar suka shan maganin rage damuwa. A nan Mubarak da Nas suka fara ƙoƙarin bata kayan maye, Wallahi Sadik nayi iya yina akan kar Farhan ta fara shan kayan maye, amma ta sanar da ni ba zan gane irin halin da take ciki ba, dan haka in ƙyaleta, da haka suka fara bata kayan maye. Am sorry da abunda zan gaya maka, wataran sun gayyaceta Hotel, da zuwan idan taje za su bata magani, ban sam meyafru ba, sedai a yadda suke hira kamar, kamar they rape her their" Daram ƙirjin Sadik ya buga da ƙarfin gaske, ya dafe kansa yana sauke wani irin wahalallen numfashi, ya ɗago idanunsa da su kai ja yace "idan Mubarak yai min haka ba abun mamaki bane, amma Nas ban taɓa zaton ze min haka ba, kaimin alfarma ɗaya Amin" Amin yace "wace Alfarma kenan?" "Ka kaini in da zan samu su Mubarak" Amin yace "nasan halinka Sadik, ina jin tsoron abunda ze biyo baya" "Ba abunda ze biyo baya insha Allah, ka min wannan alfarmar dan Allah" Amin yace "shikenan, amma kaima Sadik kome yarinyar nan tayi, da sa hannunka a ciki, kawai se nemarka mu kai muka rasa, mu kanmu abokanka ba bu wanda ya san in da kake, a airport fa naje raka babanmu na haɗu da Faruk ya gayamin kayi Aure, mu kanmu Banu sani ba, how comes Sadik?" Sadik ya girgiza kai yace "ba zan iya yi maka bayani ba yanzu Amin, ni dai muje ka rakani" Gaba ɗaya Sadik tausayi ya bawa Faruk, dan haka bece komai ba ya shiga gayawa Sadik in da za su su samu su babba. Farhan kuwa gida ta tafi, tana tuhumar kanta akan marin da taiwa Sadik a cikin mutane haka, gaba ɗaya se taji ba taji daɗi ba sam. Gefe guda Alhajin nan ya takura mata akan lallai se ta gaya masa waye Sadik, dan ba ya jin ze iya ƙyale shi akan abunda yai masa. Wata mashaya Amin ya kai Sadik, ƙeyar mubarak kawai ya hango ya ganeshi, ya bawa in da suka shio baya yana ta sakin hayaƙi. Sadik ji yake tamkar ya ƙarasa yaje ya shaƙe shi ya kashe shi kowama ya huta, saboda ba ƙaramin hatsari bane ga al'umma. Sam Mubarak be lura da Sadik ba, harya ja kujerar gabansa ya zauna, ya busa hayaƙin wiwi, ze kuma zuƙa kawai ya saka idanunsa a na Sadik, seda yai wata irin zabura ya saki wiwin hannunsa, Sadik manakin yadda babba ya sake lalacewa yai, idanunsa duk sun fito waje, sunyi jawur saboda azabar shaye shaye. Mubarak ya wani basar yace "Man yane, saukar yaushe?" "Saukar uwarka da ubanka" Sadik ya bashi amsa a harzuƙe. "Mubarak, me kaiwa Farhan meye alƙarka da ita?" Wani irin murmushin rainin hankali Mubarak yai yace "kamar yaya, ai sanin wannan amsar ba shi da amfani a gareka, tunda ka tafi ka barta ba ka so, anyi mata abunda ya dace ne kawai" Wata irin shaƙa Sadik yaiwa Mubarak, ya ɗagoshi tsaye yace "me kai mata? Why do you rape her? Me tai maka?" Mubarak yace "haba Sadik, a tunaninka abunda kai min ka ci bulus ne? Se da na tabbatar da idan na taɓa ta zan maka illa, sannan nai mata abunda ba zaka manta ba, we rape her, four of us, a Hotel and we shoot a video mu saka a yanar Gizo ya kawo mana kuɗi, mun sata a layi yanzu haka kasuwancin da take kenan". Sadik ji yai kamar zuciyar sa na ci da wuta, ya wujujjiga babba ya jefa shi ƙasa, ya dinga dukansa. Cikin azama Amin ya riƙe Sadik yana faɗin "Sadik za kai kisa fa" Nan mutanen da ke gurin su kayo kansu, ana bin ba'asin abunda ke faruwa. Sadik ya ɗau wata kwalba a gefe ya fasata ya tunkari Babba jikinsa na rawa, aka rirriƙe Sadik, yayin da Mubarak ya dinga ƙyaƙyata masa dariya har da tuntsurawa. Gashi ya kasa tashi saboda yadda ƙwaya tai masa laga laga. Da Sadik yai wata girgiza, gaba ɗaya ya watsar da su, yai kan Mubarak cikin hanzari, kai tsaye cikin Mubarak ya nufa da kwalbar, amma Mubarak yai saurin juyawa Sadik ya caka masa ita a cinyarsa, take jini ya ɓalle, ya kuma soka masa a hannunsa, aikuwa ya kurma uban ihu cike ɗimuwa da azabar zafi, beyi zaton Sadik ze niyyar kashe shi ba. Wasu suka riƙe Sadik, sukace a kira 'yan sanda, duk da Mubarak na cikin azabar raɗaɗi amma yace "kar su kuskura su kira jami'an tsaro, idan suka kira su kashinsa ya bushe ba na Sadik ba, saboda Sadik yana da legal backing akwai abunda ze kare shi. Da ƙyar Amin ya janyo Sadik da ke ta zuba huci waje, yace "ka gani ko, saboda haka fa nace ba zan rako ka ba" Sadik kamar ze kuka yace "could you imagine Amin, saboda ni ya lalata rayuwar yarinya, me tai masa meye laifinta dan kawai ina soyayya da ita?" Amin yace "nikam dan Allah wai meke tsakanin ka da Mubarak ne haka, da har ze iya yi maka wannan abun?" Cikin ƙunar rai Sadik ya girgiza Kai yace "bakomai, nagode sosai da gudunmuwar da ka bani, saura Nasir har gidan ubansa zanje in nuna masa waye ni, a rayuwata ban taɓa jin zanyi amfani da dukiyar da muke da ita in wulaƙanta wani ba, amma a wannan na sauya tunani, se na tabbatar da Mubarak da tawagarsa sun wulaƙanta, kuma abunda yai ba ze hanani Auren Farhan ba, sonta nake da gaske ba dan wani dalili ba" ya ƙarasa maganar cikin rauni. Amin yaita rarrashinsa yana ba shi baki, daga baya ya karɓi tuƙin, dan Sadik ba lallai ya iya tuƙin. Nana kam ta gaji ta zubawa sarautar Allah ido game da al'amarin Sadik, gaba ɗaya ta kasa gane kansa ta koma yi masa Addu'a kawai, Allah ya yaye masa abunda ke damunsa. Wasu lokutan kamar zeyi kuka haka ze ta bata haƙuri, yace ya san tana haƙuri ba ta jin daɗin yanayinsa a kwanakin nan, amma tayi haƙuri ta cigaba da yi masa Addu'a, komai ze wuce. Farhan ta kasa gayawa Abbas Sadik ya dawo cikin rayuwarta, tana matuƙar jin nauyinsa da kunyarsa, kuma idan har tana son ta nesanta kanta da  Sadik to ya zama dole ta amince da Abbas a matsayin miji, ko ba komai ta gujewa rigimar Sadik. Suna motar Abbas suna hira, yana duba mata hannunta, ciwon ya ɗakko warkewa yana mata sannu, ta ɗan ƙur masa ido sannan tace "doctor" Ya amsa da "Na'am ranki ya daɗe" "Kana son ka Aureni a yadda nake?* Cikin hanzari yace "sosai makuwa" "To ka turo iyayenka gurin Abba, ina son muyi Aure a ƙasa da wata ɗaya, duk a in da ka ajiye ni zan zauna" Abbas yace "Amma meyasa kika yanke wannan hukuncin haka? Makarantar ki fa?" "Doctor ina da dalili, makaranta kuma na cigaba a gida ka sedai in ka dena sona" "Ya ma za'ai in dena sonki, insha Allah zan yadda kika ce, zan turo magabatana insha Allah zanyi Magana da su" "Angon Farhan" tai maganar da sigar tsokana. "Na'am Amarayar Abbas" su kai murmushi, suka cigaba da taɗinsu yayin da ƙasan zuciyar ta cike yake da tausayin Sadik. Abbas kam ya shiga taradaddin yadda ze sanar da Auren da yake son yi ga dangin mahaifinsa, dan ya san dole za suyi bincike akan Farhan, yana tunanin yadda wannan abu ze kasance. Yaiwa Hajia magana, amma tace ba ruwanta ya tuntuɓi dangin mahaifinsa in sun nema masa shikenan. Sadik ya kasa gajiyawa da zaryar gidansu Farhan zuwa makarantar su, amma ko sau ɗaya ta kasa ba shi damar yi mata Magana ko kare kansa. Yau ma yana nan zaune a ƙofar gidan su Farhan, Abbas ya kawo Farhan a motarsa, kasancewar magariba ce ba ta ga Sadik ba, Abbas yai reverse ya koma ƙofar gidan Hajiyarsa, tana shirin shiga cikin gida, taji an janyo ta da ƙarfin gaske. Turaren Sadik kawai ta shaƙa ta gane shine, wani irin huci yake kamar wani kumurci. "Dalla meye haka?" Tai maganar a hasale. "Farhan wai me kike son ki maida ni ne? Mahaukaci? Kullum cikin zaryar gidanku nake ki bani lokacinki kin ƙi, kullum sedai wannan ya ɗauke ki a mota wannan ya sauke?" "Au ai idan hauka ne, kai baka daɗe a cikin sa ba, kwanan nan ka fara ni shekaru biyu na shafe a cikinsa, kuma ba zan taɓa saurararka ba Sadik, dan Allah ka rabu da ni" "Ba zan rabu da ke ba, Wallahi kika kuma shiga motar wani duk abunda nai miki ke kika siya" Tace "ikon Allah, saboda ubana ne kai?" "Saboda ke mallakina ce, Wallahi na kuma ganinki da wani se na illata shi, kar wannan wawan ya kuma zuwa yace ze ɗauke ki a motarsa na gaya miki" Fizge hannunta ta tai tace "ba ma ka da kunya Wallahi, kaifa Aure kaje kayi, se ka zo ka takurawa rayuwata, ka fita sabgata dan saura wata ɗaya a ɗauran Aure" "A ɗaura miki Aure da Sadik ba" "Allah ya kiyaye, ko hauka nake aka ɗauramin kai se na kwance na yar, mayaudari kawai" yana kallonta haka ta wuce cikin gida. Sadik be taɓa zaton Farhan tana da irin wannan zuciyar ta kafiya da taurin kai ba, saboda shi sanyin ta kawai ya sani. Haka nan ya wuce ya tafi gida, da yaje ya tarar tuni Nana tayi baccinta, yai wanka ya nemi guri ya kwanta ya rungume su ita da Sahal a jikinsa, wani irin tausayin su yana ratsa shi, da da ne se ta jira ya dawo ta bashi Abinci sannan su kwanta, amma yanzu har ta gaji da abunda yake yi. Abbas yaje ya samu wan mahaifinsa da suke cewa Alhaji, ya sanar da shi yana son ƙara Aure, se da yai mita sosai da sosai, akan ƙare ƙaren Auren nan in ba dace a kai ba baya haifara da ɗa me ido. Abbas yaita lallaɓa shi, da ƙyar ya amince sannan ya tambaye shi 'yar waye kuma a ina take?. Abbas ya gaya masa, Alhaji yace "na gane mahaifin yarinyar, na san shi farin sani mutumin kirki ne, wata mu'amala ta taɓa haɗani da shi, zamuje insha Allah daga nan ai binciken da duk Yakamata" Abbas yace "Alhaji ai ba se anyi wani bincike ba tun da kasan mahaifin ta, kuna kace mutumin kirki ne, itama ta na da kirki" Alhaji yace "in baka da hankali mu muna da shi, ɗan yau ka haife shi ne baka haifi halinsa ba, dan haka zamuyi bincike tashi kaje" jikin Abbas yai sanyi ƙalau, haka ya baro gidan Alhaji, dan yasan muddin binciken su ya gano halin da Farhan ke ciki, bayan hana shi Aurenta se sun ci masa mutunci tsaf. Abun mamaki Farhan ta ɗan saki ranta a kwanakin nan, bata yawan ƙunci da damuwa kamar baya da Sadik ya ɓacewa duniyar ta. Sedai duk da haka yanzu ta ƙauracewa zaman gida, dan sosai take son t nesanta kanta da Sadik, in dai zata cigaba da ganinsa, to tabbas zata iya kasa Auren Abbas, kuma hakan tamkar ta saka alkhairi ne da sharri. A samarinta ta saka Alhajin nan ya kuma kama mata ɗaki, a wani hotel ɗin, ta koma can abunta, Abbas ya kaɗa ya raya akan ta koma gida, fafur taƙi kuna taƙi gaya masa dalili, abun ya dame shi matuƙa, in dai zeje ze tarar da ita ita kaɗai, be taɓa kamata da wani a hotel ba, amma dai zaman hotel be dace da ɗiyar kirki ba, amma Farhan tai burus da shi, tai zamanta. Amir ƙanin Farhan har mamakin wannan uban naci na Sadik yake yi, yana ganin kwata kwata ba shi da zuciya, musamman duba da yadda Farhan ɗin ke masa wulaƙanci. Kamar yadda Alhaji ya alƙawartawa Abbas, sunje neman Auren Farhan, kuma har sun saka ranar da zasu kawo kuɗin Auren, sun nemawa Abbas izini, kuma an bashi. Watanni uku Alhaji ya saka, dan a cewarsa baze biyewa Abbas ba, dan be ga abun gaggawa a lamarin ba. Abba ya dinga murna tare da Addu'ar Allah ya tabbatar da wannan lamarin, kar ya watse kamar yadda aka dinga zuwa neman Aurenta abun na watsewa, saboda yanayin rayuwar da take yi. Sam Farhan ta kasa murna da batun kawo kuɗin Auren, ba ta zumuɗi sam, ta rasa dalili, ƙasan zuciyar ta na ƙoƙarin gaya mata har yanzu tana son Sadik, amma ta dage ta cire wannan tunanin a ranta. Yanzu ma ta fito daga wanka, ta na sanye da doguwar riga a jikinta, tana zaune tana duba litattafnata, dan haryanzu akwai son karatu a tare da ita, makaranta ce kawai ta fita daga ranta gaba ɗaya. Turo ƙofar ɗakin a kai, ta zuba ido, dan ganin waye haka ya zo mata ba izini ba komai. Seda ta buɗe baki dan mamaki, ya akai Sadik ya gano in da take. Ya ɗan tsura mata ido sannan yace "kina mamakin yadda a kai nasan in da kike ko?" Haɗe rai tai tace "kaga kar ka zo ka samun ciwon kai, ka tafi ka bani guri" Bece mata komai ba, ya nufi kan dressing mirror ɗin da ke ɗakin, ya kwaso magungunan da ke kai ya zuba a aljihunsa, ai da sauri ta miƙe ta nufo shi, cikin haɗe rai tace "ka ajiyemin kayana malam" "Na ƙarfi ne ki ƙwata" yai maganar shima ransa a haɗe. Shiru tai tana huci tana kallonsa. Cikin tausasa lafazi Sadik yace "Farhan meyasa baki da tausayi ne? Ko iya sintirin da nake miki, ya isa ki sassauta min ki kwantar da hankalinki ki saurareni, nasan na miki laifi amma ki sani da bana sonki, ds Wallahi ba zan dawo gareki ba, haryanzu ina sonki Farhan, dan Allah ki saurareni" "Kana sona da kenan, amma banda yanzu" Ya ƙarasa gabanta, ya kamo hannayenta yana kallonta yace "Farhan dan Allah ki sassauta min idan ba so kike in rasa raina ba" Kawai ta fashe da kuka tace "wai ya kake son in yi ne? Me kake nema a gurina, na ɗora rai a kanka amma ka yaudareni, a haukana na sakankance zaka dawo ka Aureni, a lokacin da nake tsaka da neman ɗauki, soyayarka na barazana ga rayuwata, amma ka yanke alƙa dani ba tare da ka sanar dani dalili ba, haka na haƙura da son yiwa iyayena biyayya in auri wanda ba na so, soyayyarka ta hanani sukuni da nustuwa, na fara neman maganin da ze mantar da ni kai, wanda iyayena suka zaɓamin ya bi ya ɓatamin suna yana cewa ni mutuniyar banza ce, ko da yake hakane,. Lokacin soyayyarka ta rufemin ido, ina iya sakin jiki kai min koma menene saboda son da nake maka, aka zo aka fasa Aurena ranar ɗaurin Aure, ya cigaba da bina da sharri kala kala a gari. Katsam na tsinci labarin kayi Aure Sadik, bayan duk alƙawarurrukan da kai min, kai Aure ka barni, ba amo ba labarinka, ta yaya ba zan shaye shaye ba, ka koyamin abubuwa masu wuyar mancewa da ƙuruciyata, ba abunda nake kewa, banda tausayawarka da daɗaɗan kalamanka na yaudara, na saba da kwanciya a jikinka, ƙamshinka da barkwancinka lokaci ɗaya ka yanke wannan alaƙa da ka gina, sannan duk a garin in samu mafita miyagun abokanka suka min fyade suka lalata min rayuwa ta. Duk wanda ya zo neman Aurena, se Sunusi ya ɓata, Mubarak babba bayan cin zarafina ya kirani da ƙasƙantacciya mara amfani saboda bamu da kuɗi, shiyasa na yadda in nemi kuɗi in rama abunda yai min. Sadik me yai saura da kake da shi wanda zaka gayamin menene?" Tai maganar cikin ƙaraji. Lumshe ido yai, yana jin yadda magananunta suke tasiri a cikin zuciyar sa. A hankali yace "ban san da wani suna ya dace in kira kaina ba, amma duk sunan da kika kirani, mayaudari maƙaryaci duk na cancanci hakan. Farhan na so ki tun ban san menene son ba ma, kuma na shirya yadda zan rayu da ke, amma har kullum shi bawa ba shi yake da kansa ba, Allah ke tsara masa komai nasa. Farhan kakanni na ne suka Auramin ƙanwata Nana a cewarsu zuwana ƙasar waje karatu nikaɗai hatsari ne, na sha gayawa iyayena ina son Aure, amma suka dinga dankwafeni, suna min kallon yaro, hakan ya bawa kakannina damar Auramin Nana, ba tare da sun tuntuɓi ko ina da wadda nake so ba. Ban sani ba ko hakacewa nai Farhan, amma lokaci ɗaya da ke, da makarantar mu, da abokaina Wallahi kamar an min formatting na manta komai, haryanzu na kasa gano dalilin yadda a kai haka ta faru da ni, na manta da komai a shekarun nan ko da wasa, ban iya tuna kowa da ya shafi makaranta da rayuwar da nai a cikin ta ba". Ture shi tai tace "ai dole ka manta mana, tunda kai Aure, ka barni a wahala" Matsawa ya sake yi daf da ita yace "idan ma hakane, mahimmancinki da soyayyar ki a gurina yasa na sake dawowa rayuwar ki a karo na biyu, in nemi afuwarki kuma in sake neman soyayarki, duk da nasan soyayyata haryanzu tana nan a tare da ke" "Kar ka yaudari kan ka malam" tai maganar ranta a haɗe. "Hmm, ba yaudarar kai bane ba Farhan, sannan zan nunawa Babba ke mace ce me tsabar daraja da kima, duk wanda suka ci zarafinki sena ɗau mataki a kansa, kuma ni a haka nake sonki Farhan, zan Aureki ina sonki Wallahi" "Se kuma kayi, dan an sa min ranar Aure, saura watanni uku, kuma ko ba'a sa ba ba zan Aureka ba". Be damu ba yace "zan zo neman Aurenki, ba ki da mijin da ya wuce Sadik, ki rubuta ki ajiye wannan, and magana ta gaba, ba zaki min asara ba, shaye shaye yana kawo illa ga ƙwayoyin haihuwa, ban sani ba ko da yarana a cikin ki, dan haka na hana shan wani abu daga yanzu, dama saboda ni kike sha, to gani na dawo. Na dena lallaɓa ki ko kina so, ko ba kya so zan Aureki Farhan dan tabbatar wa da Duniya soyayyar mu ba RUƊIN ƘURUCIYA bace, saboda so ba ruwansa da ƙuruciya". Mamakin ƙarfin hali irin na Sadik take yi, harya juya ze fita ya dawo ya kalleta yace "kar kuma in sake ganinki tare da wannan farin mutumin, da koma waye suke zuwa gurinki, ki gaya musu ke matar Aure ce, matar Sadik ce idan suka cigaba da bibiyarki kuma, Wallahi se na yiwa mutum illa, kuma ki tattaro kayanki ki bar Hotel ɗin nan ba zan miki dole ki bar nan yanzu ba, amma Wallahi na kuma ganinki a hotel, kafin in gaya miki matakin da zan ɗauka bari in tuna baya, let's remember our first kiss". Kan tai Magana ya rungumota jikinsa, ya fara kissing ɗinta so deeply. Lumshe ido tai, tabbas ta tuna first kiss ɗinsu, a gurin birthday ɗinta, she so much Miss him, ji take tamkar ta rungume shi, itama ta mayar masa, amma tuna yadda ya gujeta yai Aure har da ɗa, ya sa ta fara mutsu mutsu za ta ƙwace, ba ta tsinke da lamarin Sadik ba se da taji ya zuge rigarta, kokawa suka shiga yi, ta saka kuka tana girgiza masa kai tace "ba ka da hankali ne me kake yi haka?" Ya cire rigar da ga ita se underwears, ta rurrufe jikinta, take hawaye ya wanke mata fuska, be damu da abunda yai ba, ya sa hannun sa ya fizge nata daga kare jikinta da tai Sannan ya kalleta yace "ko da tsiya, ko da tsiya tsiya in dai ina numfashi ke tawa ce, ba zan cigaba da lallaɓaki kina wahal da ruhi na da gangar jikina ba, ke har ma da matata da ɗana ba, ba jikinki nake so ba, zuciyar ki nake so, da jikinki nake so ba zan Aureki ba bayan wasu sun riga sun..... Se kuma ya datse zancen ya ɗora da "Wallahi, Wallahi idan na kuma ganinki a hotel, i will sleep with you there, tunda abunda kike so kenan, ki ke zaman banza a hotel kina tara ƙarti" Sosai Sadik ya bata tsoro, jikinta se rawa yake yi, a ranta tace 'wai ba jikina kake so ba, Sadik na sanka kamar yunwar cikina" amma a zahiri ko motsi ta kasa se hawaye. Se kuma ya lumshe ido yace "kin ƙara girma da kyau sosai princess, am sorry na saki kuka, ban sanki da gardama ba, amma ƙwaya duk ta canza min ke, amma daga yau insha Allah se kin dena sha, tunda gani na dawo, sa rigarki muje ki ci Abinci in kai ki gida". Ta ɓoye tsoronta ta dake tace "ka fita ka barmin ɗaki, kace ba jikina kake so ba amma kai min tsirara, ka fita ka bani guri" Murmushi yai be kuma cewa komai ba ya fice. Yau wani irin nishaɗi Sadik yake yi, sedai yana tunkarar gida gabansa ya shiga faɗuwa, saboda be san ta ina ze ɓullowa lamarin a gida ba. Tunanin yadda Sadik ze sake tunkarar iyayensa da batun yana son sake ƙara Aure kuma ya baibaiye shi, dan ya san abune me wahalar gaske su amince, na farin ma da ya akayi balle ya sake zo musu da wannan sabuwar maganar. Nan fa tunani ya sake komawa Sadik sabo. Yau Abba ya zo hutun ƙarshen wata da yake zuwa, sedai shima ya lura da canjin yanayin Sadik, sedai be ɗau abun da mahimmanci ba, saboda yasan halin Sadik ɗin wasu lokutan ba gane kansa ake yi ba. Sedai abun ya ɗan dameshi, ganin ita kanta Nana duk tana cikin damuwa, wadda ita kanta ba ta san tana da damuwar ba. Abba ne ya kalli Nana, da ke zaune a babban falo, gefenta Sahal yana bacci, ya zauna a ɗaya daga kujerun falon ya kalleta yace "Nana, meke faruwa ne daga ke har Sadik gaba ɗaya na kasa gane muku, duk kunyi wani iri ko akwai matsala ne?" Nana ta girgiza kai tace "A'a" Abba yace "A'a, kar ki ɓoyemin komai, baki san fuskar ki ta nuna bane?" Kawai ta fashe da kuka, Abba ya barta tayi tayi, sannan yace "ina jinki" Mother da tazo wucewa tace "lafiya take kuka?" Abba yace "Abunda nake son ji kenan" Nana ta share hawayen fuskarta tace "Abba, ni na kasa gane kansa gaba ɗaya, na tambaye shi idan wani laifin nayi masa yace A'a, gaba ɗaya ya dena kula da mu kamar da, har gara Sahal yana ɗaukar sa, amma ba ya wuni a gida, wataran se dare munyi bacci yake dawowa, na tambaye shi menene yaƙi gayamin, ko Abinci ba kullum yake ci ba" Mother tace "Aikam nima nayi iya yina, akan ya gayamin meke damunsa amma fafur yace bakomai, ni kaina na lura da hakan a tare da shi, duk ya canza" Abba yace "ki dena kuka, zan zauna da shi inji ta bakinsa, ki dena kuka kinji yarinyar kirki, dama haka auren yake ai" Yaita rarrashinta yana kwantar mata da hankali. Se da aka kwana biyu da maganar da su kai da Nana, Sadik yaje gaida Abba a sashinsa, Abba ya dinga jansa da hira, daga baya yace "kai ya akayi ne gaba ɗaya ka canza fa, gayamin meke damunka ne?" Sadik ya ɗan sosa kai yace "bakomai Abba". "A'a da komai mana, yanayinka ya nuna, don't forget that we are friends, so you can share your problems with me, to see if I can help" Sadik ya ɗanyi shiru yana nazari, tabbas wannan shine right time, da Yakamata yaiwa Abba Magana. Ya kalli Abba sannan ya ɗan gyara zama yace "Abba, ina son in ƙara Aure ne!!!. Littafin kuɗi ne, ku tuntuɓi wannan lambar dan samun naku akan kuɗi ₦300 kacal 07063065680 Abba ba tare da ya kalli Sadik ba yace "You must be crazy" Sadik ya gyara zamansa yace "Abba am serious, wallahi da gaske nake dan Allah ka bani goyon baya, ina son ƙara Auren nan" "Shut up!" Abba yai masa tsawa. "Kwata kwata yaushe kai Auren, ko ka manta da ya kai Auren fari, kawai seka zo kace zaka ƙara Aure, saboda baka da hankali" Sadik ya marairaice yace "dan Allah Abba ka fahimce ni" "Ba zan taɓa fahimtar ka ba, wai tsaya ita wadda kake tare da itan, me ka rasa a gurinta ta ina ta gaza gayamin ina jinka" "Abba Wallahi ba abunda Nana tai min, tayi iya ƙoƙarinta a kaina, idan nace zan butulce mata ko in cutar da ita Allah baze barni ba, amma Abba akwai dalilin da yasa nak...... "Kai dalla rufen baki, tashi ka bani guri" Kamar Sadik ze kuka yace "Abba dan Allah ka saurareni" "Ka fita ka ban guri nace" Abba yai maganar cikin tsawa, haka Sadik ya tashi ya fita gwiwa a sanyaye. Nan abubuwa suka sake sha masa kai, ya rasa mema Yakamata yayi. Haka nan Farhan ta tsinci kanta da tattara kayanta, domin barin Hotel ɗin nan, dan tana shakkar Sadinya aikata abunda yace, tunda har yai rantsuwa, to ze iya aikatawa. Ta tsinci kanta cikin wani nishaɗi tun bayan sumbatar da Sadik yai mata. Mother ce ta shigo kawowa Abba Abinci, tana mitar yadda ta sa aka kira me gyaran solar amma be zo ba, se inji aka kunna, sam taga hankalin Abba ba ya kanta. "Yallaɓai lafiya kuwa?" Abba ya girgiza kai yace "kin san me ɗanki ya zo min da shi?" Mother tace "wanne daga cikin 'ya 'yan?" "Ɗan Autan ki" "A'a seka faɗa" Abba yace "wai Aure ze ƙara" "What?" Mother tai Maganar cikin ɗaga murya. "Wallahi abunda yace min kenan" "Amma ka tsinka masa mari ko, dan ya dawo hayyaccinsa" Abba yace "ba wani marinsa da nai ni, sedai kawai na koreshi ne" Mother tace "lallai yaron nan ba shi da hankali, gaba ɗaya yaushe yai Auren farin, da har ze ɗakko wannan maganar, da ya a kai masa Auren farkon ma?" "Rigima mana, irin tasa ai Sadik halinsa se Addu'a, ya zo ya tattara ya koma makaranta, Ya bar su a nan ita na nema mata wata makarantar ta cigaba da zuwa, in ya so ko me raino se a samo mata, wadda zata dinga riƙe mata takwarana" Mother tace "base an wani samo me raino ba, ta dinga bar min shi zan riƙe" Abba yace "to shikenan, Allah yayi jagora, amma dan ubansa makaranta ze zo ya koma bana son rigima". A falon BQ ya tarar da Nana, ta saka Abinci a gaba tana son ta ci, amma Sahal se rigima yake ya hanata cin abinci, kuma da alama tana jin yunwa sosai, se haɗe rai take gashi baya gajiya da tsotso. Sadik ya ƙarasa ya karɓi Sahal, yana rarrashinsa, ita kuna ta fara cin abincin, ya ɗan zuba mata ido sannan yace "wato yanzu kin dena damuwa da ni ko? Ko ki min tayin Abincin?" Cikin ko in kula tace "am tired ne, dole in zubawa sarautar Allah ido" Jikinsa ya ɗanyi sanyi, tabbas Nana duk da tarin shiriritar ta, tayi iya yinta taga Ya dawo da walwalarsa, amma abu yaƙi yiwuwa. "Husna" ya kira sunanta, ta ɗago ido tana kallonsa. Yace "am so sorry, na san gaba ɗaya ba kya jin daɗin yanayin zaman mu a yanzu, amma kiyi haƙuri komai ze wuce insha Allah". Shiru tai ba tace komai ba ta cigaba da cin abincin dake gabanta, se ganin hawaye yai yana ɗiga akan hannunta daga idonta. Ya ɗan lumshe idanunsa ya kwantar da Sahal da yai shiru, yana cin hannunsa, ya zauna a kusa da ita sannan yace "tuba nake my wife, kiyi haƙuri dan Allah, zan canza insha Allah, zamu koma normal yadda muke, ki dena kuka bana son hawayenki Besty" yai maganar cike da kulawa yana share mata hawaye, ita dai ba tace masa komai ba, ya cigaba da rarrashinta. Bayan sallar isha'i Sadik yai kwalliya cikin manyan kaya, ya tafi gidansu Farhan, amma ya tarar da ita tana zance acikin motar Abbas, ransa ya ɓaci sosai amma be ce komai ba, ya fito daga motar yaje ƙofar gidansu ya samu guri yai zamansa. Farhan ta ƙi fitowa daga motar Abbas, ta dinga jansa da hira daban daban, har mamaki abun ya bawa Abbas, yace "ya dai na fuskanci hira kike ji sosai, Allah ya kaimu bikin nan a raƙashe babyna" Farhan tace "hmm ba wani raƙashewa, ai ɗaurin Aure da wuni rana ɗaya kawai" Abbas yace "A'a, dole ki shirya wani ɗan reception ke da ƙawayenki" "Ai ni bani da ƙawaye" "Ahha haba dai, to suwaye zasu raka ki gidana?" "Dagaske bani da ƙawaye, 'yan uwanmu ne zasu kai ni" Yai murmushi yace "ke dai abun mamakin ki baya ƙarewa Farhan" haka suka cigaba da hira, daga bisani su kai sallama Ta fito daga motar, ya ja ya tafi. Ta zo zata shiga gida, ta share Sadik kamar ba ta ganshi ba, ya miƙe ya tare mata hanyar shiga ta dube shi tace "meye haka kuma? Bani hanya zan wuce" Sadik yace "ba zan matsa ɗin ba, me nace miki akan shiga motar mutumin nan?" "Ban gane ba, wai kai meye haɗina da kai ne, dan Allah ka ƙyale rayuwata ta huta" "Ba ke ba hutu, idan har ba ni kika Aura ba, tunda kika zauna tsawon wannan lokacin har na dawo baki Aure ba, to ki sani ke rabona ce Farhan, dan Allah ki zama me yafiya" "Kaga dan Allah ka bani hanya zan wuce gida" "Yadda kika bashi lokacin ki, nima dole ki bani lokaci, sannan let me warn you for the last time, kar in sake ganinki a motarsa, kuma kar ya sake zuwa gidan nan gurinki" "Saboda ubana ne kai? Mutumin da zan Aurane nan da ƙanƙanin lokaci, kai na bawa dama a farko ba kai amfani da ita ba, dan haka yanzu damar wani ce" "Farhan ba ki yadda da duk abunda na gaya miki bane?" "Na yadda mana, ka manta dani a rayuwarka saboda rashin mahimmanci na, kai Auren ka har da ɗa, ka ƙyaleni nima in Auri wanda nake so ka dena shiga rayuwa ta" Sadik yai wani murmushin rainin hankali sannan yace "da alama kina kishi da matata sosai, hakan ya sake tabbatar min da kina sona haryanzu, karki kishi da matata ba ruwanki da ita, ko ki tambayi ya sunan ɗana ko?" Wani takaici ne ya ƙule zuciyar Farhan, zata bangaje Sadik ta wuce, amma ya riƙeta kasancewar gurin ba haske. A fusace tace "meye haka, ka dena taɓani" "Meye na pretending kuma in dena taɓa ki, meye ba muyi ba a baya, duk ki ka lalata ni, na dinga cewa Aure nake so, se da a kaimin Aure na nutsu duk ke kika koyamin, kika saba mun da..... Se kuma yai shiru yana wata shu'umar dariya. Wani takaici ya cika zuciyar Farhan, tare da dana sanin kuskuren da tai a baya, ta biyewa Soyayar RUƊIN ƘURUCIYA. Kawai ta fashe da kuka. "To me nai miki kuma zaki min kuka, daga tuna baya se kuka, mara kunya kalli da ɗan mayafin da kike shiga motar wani, Allah sarki i miss my old Farhan so much". Kuka take sosai har da sheshsheƙa, yai mata banza kuma yaƙi bata hanya ta wuce, se da tai me isarta Sannan yai ƙasa da murya ya kai bakinsa kunnenta yace "munyi kuskure a baya, wanda nine dalilin hakan, son da kike min da ƙuruciyar da ke kanmu ya sa soyayyar mu da shaƙuwarmu ta kai mataki me wuyar mantawa, Farhan ke yarinya ce me nutsuwa da tarbiyya, a dalilin soyayyata duk kika canza, idan na gujeki Allah baze barni ba, duk wanda zaki Aure nan gaba ze iya yai miki gori, ni kuwa fa nine silar komai, kuma yanzu ba ki ga na ƙara girma ba, har ɗa ne fa dani, kyakykyawa kamar mamansa". Tsaki Farhan tai, zata raɓashi ta wuce ya sake riƙota yace "to meye na fushin kuma? Matata Tana da kyau sosai kamar ke ɗin nan, ki rage kishi kuma ki yarda haryanzu kina son Sadik ɗinki, ki kulamin da kanki, I love You" ya ƙarasa tare da sumbatar kumatunta. Ya cikata, ya juya cikin takunsa a nutse ya nufi motarsa, yayinda galala tabi bayansa da kallo. Seda motarsa ta bar layin, Sannan jiki a sanyaye ta shige gida. Da safe Sadik yana bacci, wayarsa ta fara ringing, ganin Abba ne ya sa Nana ta ɗaga kiran, suka gaisa ya tambayeta ina Sadik, ta sanar masa bacci yake, yace idan ya tashi su zo duka yana son ganinsu. Se wajen goma sannan Sadik ya tashi, bayan ya karya Nana ta sanar masa da kiran Abba, suka shirya zuwa cikin gida, kai tsaye part ɗin Abba suka wuce, suka tarar da shi ds Mother a can. Suna zuwa Mother ta karɓi Sahal a hannun Sadik tana masa rawa. Suka gaida su Abba, Abba ya kalli Sadik yace "kai me ka shirya ne akan komawarka makaranta?" Sadik yace "Makaranta kuma Abba?" "Eh mana Yakamata ka koma" Sadik yace "dan Allah Abba ka ƙyaleni ba se na koma bs, ai min transfer in dawo Nigeria" "Saboda ba ka da hankali? Ka koma makaranta ita ma na fara tuntuba in da za'ai mata registration ta koma makaranta a nan, takwarana kuma Kakarsa tace zata dinga riƙe abunta taje makarantar ta dawo" "Abba dan Allah ka barni a nan, ba zan iya komawa makaranta in bar su ba" Mother tace "zama ka faɗi gaskiya ne" Abba yai mata alama da ido, akan karta tonawa Sadik asiri a gaban Nana. Abba yace "yanzu ka gwammance in asarar kuɗina kenan?" Sadik yai shiru ya sunkuyar da kai ƙasa, Abba yace "tashi kaje zan nemeka" Suka fito shi da Nana, cikin damuwa Nana tace "besty, da Sahal ya isa ysye da na yaye shi na bika, naga Abba ya fi son ka koma" Sadik yai ajiyar zuciya yace "zaman baze min daɗi ba, ba zan iya zuwa in zauna nikaɗai ba, ke kin san meyasa, Abba ba za su fahimce ni ba" Ƙunshe baki tai tana masa dariya, yace "au dariya ma kike min ko?" "To Besty kai ɗin ne ai se a hankali, ai gara ma ka tafi ko nayi ƙiba" "Wallahi duk na damu, kin rame sosai Besty, kin fi ƙiba da muna London" Nana tace "to ya zanyi? Shayarwa Sahal ba shi da haƙuri gurin ci, gashi kai kuma duk ka canza abun yana damuna sosai" Sadik yai ajiyar zuciya yace "dan Allah ki dena damuwa masoyiya, Wallahi kin rame dan ki kwantar da hankalinki" Nana tace "ai kwanciyar hankalinka its ce tawa, hankalina baze kwanta ba idan kana cikin damuwa" Sosai take bashi tausayi, ta damu da shi sosai be san yadda zataji ba a lokacin da taji batun ze ƙara Aure. Sadik yace "kije ki shirya, zan zo muje yawo Yanzu, ni zanyi magana da Mother" Nana tace "to Besty, kuma ga Sahal na gurin Mother" Yace "bakomai, zamu bar mata shi a gida ne" "Ok, bari inje in shirya". Sadik ya samu guri ya zauna, har Mother ta fito daga gurn Abba ta koma sashinta, Sadik yabi bayan Mother, ta waiwayo ta ganshi a bayanta tace "ya dai kake bina?" Sadik yace "magana nake so muyi Mother" "To ina jinka" Sadik yace "Mother, na san Abba ya gaya miki maganar da mu kai da shi, na batun ina son ƙara Aure, kuma kinga dama ke kika ce zaki sake min wani Auren, dan Allah Mother ka bani goyon baya in ƙara Aure" Mother tace "rufen baki, lokacin da na so ka bani haɗin kai har a kai ga yi maka wani Auren, ba ƙasa ka watsamin a ido ba? Ka bani kunya sega yarinya da ciki, ni yanzu na dena jin haushinta tausayin ta nake ji, yarinya ƙarama ga ɗawainiyar ka ga ta ɗanka kuma dai-dai gwargwado tana kula da kai sosai, kuma kawai yanzu se ka zo da wata maganar banza, dudu guda nawa kake zaka riƙe mata biyu, dama ba kwa tare ne da sauƙi, amma guda nawa kake da za kai batun ƙara Aure?" Sadik yace "dan Allah Mother ki fahimce ni, na aikata wani kuskure ne a baya, na fara ajiye 'ya'ya, ba zan so hakan ta faru a kansu ba, dan Allah Mother ki bani goyon baya" "Wallahi ba zan baka ba, tunda ba ka da hankali, fita ka barmin ɗaki" "Dan Allah Mother" A fusace tace "zaka fita ko sena zageka, na ɗuɗɗura maka Ashar". Jiki a saɓule Sadik ya fice daga ɗakin Mother yana tunanin mafita. Daga ƙauye aka kira Abba, wai Hakimi yana son ganinsa, abun ya ba shi mamaki sosai da sosai, da fari yayi tunanin ma ko jikin Hakimin ne ya tashi, seda yaje ya tarar da shi jikinsa da sauƙi sannan hankalinsa ya kwanta. Hakimi yace da Abba "Na san zaka yi mamakin kiranka da nai, ba wani dalili ne ya sa na kiraka ba, shekaranjiya Sadik ya zo garin nan, Masha Allah ya kawo mana abun arzikinsa fal, Allah yayi albarka" Abba yace 'ikon Allah, ai bamu san ya zo bama" Hakimi yace "hakane, ya kawomin ƙara ne, ko ince ya zo neman alfarma ne" Abba yace "wace Alfarma kenan ranka ya daɗe?" Hakimi ya ɗanyi tari sannan yace "kan in tafi kai tsaye ga abunda ya sa na kiraka, lokacin da Sadik ya zauna a garin nan, na sha kama shi yana waya da Mace, yana iƙrarin idan har ta Auri wani ba shi ba ze iya hallaka shi, da kunne na naji wannan cikin dare, na fuskanci yana soyayya da wata yarinyar a wannan shekarun nasa, kuma da alama yarinyar Aure za'ai mata, to da ai haka yaje yai mana wannan gangancin da yanayin ɗabi'un sa, da abunda kakarsa ta gayamin ta gani a game da shi, hakan yasa na ɗau Nana na ba shi, a gefe guda na Aura masa Nana dan sanin Nana marainiya ce ina sa ran in suka zauna guri ɗaya, su sassautawa juna wannan ƙiyayyar da suke wa juna, kuma tunda 'yar uwassa ce ina sa ran ya riƙet da amana ko ba ranmu, banji ta bakin kowannensu ba na yanke wannan hukuncin. Sadik ya zo min da cewar yana son ya ƙara Aure, kuma dama na bashi wannan damar a lokacin da na Aura masa Nana, nace idan yana da buƙata a nan gaba ze iya ƙara Aure, dan haka kar ku kalli yarintarsa tun da yana so, ba ku san dalilinsa na cewa yana son ya ƙara ba, ya min bayanin komai na fuskance shi, kuma na bashi goyon baya ɗari bisa ɗari, ya gayamin yana ƙaunar Nana yai min alƙawarin baze wulaƙanta ta ba, dan haka dan Allah ku bashi dama, kuyi haƙuri da yadda Allah yayi shi, ku bashi dama yayi, kuma zan bada kuɗi a sai masa isashen gida da ze ishe su, Allah yai musu albarka gaba ɗaya" Abba be ji daɗin yadda Sadik ya kawo ƙararsa ba, kuma har Hakimi ya bada goyon baya, Abba bece komai ba, Hakimi yai tai masa nasiha, se Yamma sannan ya tafi Kano. Sam be yiwa Sadik zancen ba, sedai ya fita daga harkarsa gaba ɗaya. Nana tana shirya Sahal tana masa wasa tace "bari in shiryaka in kaiwa Abba kai, yaga wankan juma'arka, ko ɗan kyakykyawan Babansa" Se shiriritar ta keyi, dama Talatu ce take zuwa taiwa Sahal wanka, Nana kuma ta shirya abunta tana shirya shi, tana masa hira kamar yasan me take faɗa. Sadik ya samu Abba a falonsa ya gaishe shi, da ƙyar Abba ya amsa masa, jiki a sanyaye Sadik yace "Abba dan Allah laifin me nai maka?" Abba yace "tambayata ma kake ko Sadik? Bayan kaje ka kaiwa Hakimi ƙarata na hanaka Aure ko? To shikenan kaje kai abunda ka ga dama" Sadik yace "dan Allah Abba ka fahimce ni, Wallahi ba dan na ɓata muku rai nayi ba, Abba ina da dalilin da yasa nake son ƙara Auren nan, Farhan na fara so a rayuwata, saboda ita nai jumping na gama secondary School, dan Allah Abba ku amince in Auri Farhan, wallahi muna son juna sosai, Kasan lokacin da na Auri Nana ba sonta nake ba, Farhan na fara so". Gani yai Abba ya ƙurawa ƙofa ido, Sadik na ɗaga kai yaga Nana a tsaye da Sahal a hannunta, hawaye harya cika mata ido, alamar taji duk abunda ya faɗa, juyawa tai cikin hanzari har tana tuntuɓe, hawaye na zuba daga idonta. A falo ta haɗu da Mother, Mother tace "ke kula mana zaki yar da yaron hannunki" Jiki na rawa ta miƙawa Mother Sahal, tai waje da gudu. Sadik kuwa dafe kansa yai yace "ya salam, Wallahi ina son Nana ma, ina ƙaunarta sosai amma..... Abba yace "oho maka dai, ya rage naka" Mother ta shiga falon Abba tana faɗin "me a kaiwa yarinyar nan ne? Naga ta fito hankali a tashe tana neman ta yar da yaron hannunta?" Abba yace "tambaye shi, bayan ƙarata da ya kaiwa Hakimi, akan in bar shi yai Aure, shine ya samu ƙwarin gwiwar tsayawa a gabana yana cemin dama wata yake so aka aura masa Nana, shi yana da wadda yake so, ita kuma ta ji, ina sane na ƙyaleka ka cigaba da zuba, kaga gara ka dena munafutarta, duk ta ɗaga hankalinta akan kana cikin damuwa baka walwala, kai kuma ba ta tata kake ba, wata kake so". Gaba ɗaya Sadik ya rasa in da ze sa kansa, Nana ba taji maganar har ƙarshe ba, ya san da iya abunda taji za tai masa hukunci. Jiki a sanyaye ya baro part ɗin Abba, ya tafi BQ, sedai ya daɗe a tsaye a bakin ƙofar shiga, be so labarin ƙara Aurensa ya zo wa Nana a haka ba, tabbas ya san za ta ji babu daɗi, jiki babu ƙwari Sadik ya shiga, ya tarar da ita a ɗaki, tana ta aikin kuka. Jin motsinsa ya sa ta ɗago ido ta kalleshi, abunka da me manyan idanuwa, tuni idonta yai jawurr saboda kuka fuskarta duk ta kumbura. Sadik ya ƙarasa ya zauna a kusa da ita, yace "dan Allah Nana ki fahimce ni, ki tsaya in miki bayani" Ɗaga masa hannu tai tace "har akwai wani bayani da za kai min bayan wanda naji? Sadik ba sona kake ba ka dinga gayamin kana sona, har na yadda da kalamanka, ka yaudareni da kyautatawa da tausayawarka, ina tunanin nayi kuskuren ƙoƙarin bijirewa zama da kai a matsayin miji da nai da farko, na ɗauka na Auri mijin marainiya, ka san ba ka sona meyasa ka ɓoyemin kake nuna min soyayya, an tauyeni na Aureka maimakon a shekaruna ace ina makaranta, ka ɗau damuwa ka ɗorawa ranka, nima ka sani a damuwa, ashe duk dan kana son ka ƙara Aure ne, duk da ƙanƙantar shekaruna, da ka min bayani zan fuskance ka, ba ka se shiga damuwa dan kana son ka ƙara Aure ba, Sadik ko matan duniya duka zaka dinga aurar huɗu kana saki kaje ka Aura, amma ka tabbatar ka sakeni, se ka Auro duk wadda ka ke so, dan ba zan zauna da wanda ba ya  so na ba" Sadik kamar ze kuka yace "Wallahi Nana ina sonki, baki ji ƙarshen zancen bane, meyasa zance ina sonki bayan ƙarya nake" "Wai meyasa kake son rainamin hankali ne? Sadik da kunne na fa naji abunda kake faɗa, ka nemi wadda zaka rainawa hankali ba ni ba" ta sauka daga kan gadon ta koma ɗaya ɗakin. Sadik ya dafe kai, ya rasa wani tunanin Yakamata yayi, ai kome za'ai sedai ayi, amma ba ze yadda ya rabu da Nana ba, duk da son da yakewa Farhan, Nana ba abar wulaƙantawa bace, kuma ya cancanci ta nuna fushinta akan abunda taji yana faɗa, ya san zata ji babu daɗi, amma Baze iya haƙura da Farhan ba ma. Wunin ranar sam Nana bata shiga harkarsa ba, se kuka da take, ba abunda yake dukan zuciyar ta irin yadda da kunnenta taji yana cewa ba sonta yake ba, ko Abinci ba wanda ya iya ci a cikinsu. Ɗaki ma daban daban kowa ya kwanta, ta bar shi da Sahal, cikin dare ya dinga tsala masa kuka, haka yaita faman rarrashinsa, bacci kam duk ba su rintsa ba. Da safe ma Nana ba ta saurari Sadik ba, sedai yadda rana ɗaya duk tai wani iri ba ƙaramin tausayi ta ba shi ba, ya sake tabbatar da kishi bala'i ne, sedai hanyar da ze bi ya wanke kansa a gurin Nana yake. A falo ya fito ya sami Nana ta na shayar da Sahal, ya samu guri ya zauna a kusa da ita ya kira sunanta "Husna" banza tai masa Kamar ba da ita yake ba. "Magana fa nake miki, dan Allah ki tsaya in miki bayani" "Ba ka da wani bayani da za kai min, ai bayani na gama jinsa kawai ka ƙyaleni, ka rubutan takarda sakina, ka Auri matar so wadda kake so, idan na yaye Sahal ma zan kawo maka ka bata, in ya so se in koma makaranta wataƙila a gaba, in samu wanda ze so ni saboda Allah" "Dan Allah Besty ki saurareni" Cikin kuka tace "ba wata Besty, dama ka sha gayamin ni ba komai bace face me aikin ka, ka cutar da ni baka sona ka bari na haihu da kai, ka kashemin rayuwa, Allah ya bani ladan biyayya amma na gama zama da kai, ƙauye zan koma na gama Auren" Be taɓa zaton Nana mafaɗaciya ce haka ba, ya dai santa da tsiwar tsiya amma tana da matuƙar sauƙin kai sosai da sosai, amma a wannan karon kam ba ya tunanin za ta fahimce shi. Ta shirya tai tafiyarta cikin gida, ɗakin da tai jego taje tai kwanciyar ta. Haka Sadik ya wanzu cikin tsananin damuwa, Besty ta caza masa kai, ga ɓangaren guda na zuciyar sa na son ganin Princess. Da azahar ya shirya ya tafi gidansu Farhan, sedai zuciyarsa ba daɗi, abun ya zame masa biyu, da idan Farhan ta caza masa kai, rarrashinsa da Nana ke yi, ba ƙaramin nutsuwa yake samu ba, to gashi Yanzu ma Nana ta juya masa baya. Tun da Motar Sadik ta shigo layin Farhan ta sha jinin jikinta, dan tana tare da Abbas, ya dawo da ita daga makaranta. Abbas ya kalli Farhan yace "ya dai na ga kin canza?" Sadik yai parking ya fito babu walwala, kai tsaye ya tunkaro in da su Farhan ke tsaye, ko kallon in da Abbas yake be ba, ya kalli Farhan yace "Farhan me nace miki ne wai? Bance ki sallami mutumin nan ba?" Abbas ya kalleshi yace "bawan Allah ya dai?" Sadik yace "ba da kai nake ba, da matata nake" "Ya akai ta zama matarka? Nine nake shirin Aurenta ai" "Ni kuma nine mijinta, ka tambayeta kaji" Sadik yai maganar yana maida idonsa kan Farhan. "Sadik meye haka kake min ne? Meyasa kake min haka? Na gaya maka wannan shine wanda zan Aura, meyasa kake son ta ƙarfin tsiya se ka dawo rayuwata, nace maka bana buƙatar ka, bana sonka Sadik ka fita daga rayuwata, ka jefa rayuwata cikin bala'i kuma kana cigaba da bibiyata meya haka Sadik?" Sadik ya kalleta ya jinjina kai yace "Nagode Farhan, amma ba gudu ba ja da baya, nine mijinki ki rubuta ki ajiye, idan ba ni ba Wallahi ko wa kika aura tare muka aureki" yana gama maganar ya nufi motarsa cikin hanzari. Abbas yace "wannan ne Sadik ɗin naki dama?" Farhan kamar za tai kuka tace "Shine amma..... Abbas yace "Shhhhh, no need to hear anything from you, se anjima" shima ya nufi tasa motar. Farhan ba ta gane wani hali Abbas ya shiga ba, fushi ko akasin haka?. Sadik kuwa ikon Allah ne kawai ya kai shi gida, dan ba a hayyacinsa yake tuƙin nam ba saboda damuwa. Yana zuwa gida BQ ya wuce sedai ya tarar Nana ba ta nan, ga wardrobe ɗin Sahal duk an watso kayansa ƙasa. Cikin hanzari ya fito har da haɗawa da gudu, ya shiga cikin gida yana ƙwalawa Mother kira. "Kiran me kake min haka?" Sadik yace "Mother ina Besty? Naga bata BQ" Mother tace "ta je gidan dr." Sadik yace "Ya salam, Mother meyasa kika barta, Wallahi ƙauye zata tafi" Mother tace "yo ni na sani ne? Na zaci ta da saninka, kuma koma mene banga laifinta ba, tunda kai ne baka da hankali, ba zaka kashe 'yar mutane da ƙuruciyarta ba" "Mother yanzu kin goyi bayan ta tafi ta barni, Wallahi ina sonta Mother" "Na goyi bayanta ɗin, ko ni kaiwa abunda kai mata na gama zama da kai, mara hankali kawai!!! Littafin kuɗi ne, ku tuntuɓi wannan lambar dan samun naku akan kuɗi ₦300 kacal 07063065680 Sadik ya zauna akan kujera jiki babu ƙwari, yana murza goshinsa saboda wani irin zafi da kansa yake masa, gaba ɗaya ya rasa ina ma ze dafa yaji daɗi, Mother kuwa tai tafiyarta ta bar shi a gurin a zaune. Ya tashi ya shiga ɗakinsa na nan falon ya nemi guri ya kwanta, yanzu azahar ta wuce, idan yaje ƙauye yanzu ba ze samu damar dawowa akan lokaci ba. Nana kuwa tana ɗakin Inna, se uban kuka take kamar wadda aka tsinewa, idanunta duk sun kumbure, fuskarta tai jawur. Inna ta kalleta tace "to yanzu Nana ke yaji kika yo ko me?" Nana tace '"Ni ba zan cigaba da zama da shi ba, kawai ya sakeni ya zauna da wadda yake so" Inna tace "ba shakka sarauniyar marasa hankali, shi kuma ɗan naki ya zaki da shi?". "Ba shi abunsa zanyi, ba ze ƙara shan Nono a jikina ba, yaje ya san yadda ze yi da shi" Inna tai murmushi irin nasu na manya tace "Yarinya ƙuruciya na ɗawainiya da ke, kin ban kunya Nana, kin ganni ban taɓa yaji ba duk zamana a gidan kakanki tsawon wannan shekaru ba dan kuma ba ma samun saɓani bax Ba kunya Nana tace "kema dan bece ze miki kishiya bane, kuma ai ke sonki yake ya Aureki ni kuwa fa, aka cusa masa ni ya Aureni, dama ya sha yi min gorin sadakata aka ba shi bana damuwa, ashe da gaske yake, dan kunnena naji yana faɗar ba sona yake ba" ta ƙarasa maganar tana kuka. Inna tace "sannu mara kunya, ni kike cewa dan ba ai min kishiya bane ba ko?" "Inna kiyi haƙuri raina ne a ɓace wallahi" Inna tace "kin kyauta, ki dena wannan kukan ki ɗau ɗanki ki shayar da shi yanzun nan kan in ɓata miki rai" Haka nan Nana tana kuka, ta ɗau Sahal tana rarrashinsa, ta fara shayar da shi. Inna tace "ki kwana da shirin gobe in Allah ya kaimu da safe zaki wanke ƙafarki ki koma ɗakinki" Nana ta sake fashewa da kuka, gaba ɗaya Inna kamar ma ta tsanete ne duk wannan abun ko guri ɗaya ba ta ga alamar za su bawa Sadik laifi ba. Taƙi cin abinci se aikin kuka, daga salla se kuka, har ta fara ji a ranta da iyayenta na da rai ba za'a nuna ba ta da amfani ba s gurin Sadik, sunfi son Sadik Yanzu a kanta. "Ki ta so kakanki na kiranki" taji muryar Inna, kamar ba zata motasa ba se kuma ta tashi, ta nufi turakar Hakimi, ta tarar yana kashingiɗe gefensa ga Sahal a kwance yana shan hannunsa. Nana ta shiga ta zauna ba tace komai ba, tana ta goge hawaye. Hakimi yace "matso kusa dani abar sona" Nana ta girgiza kai tace "Allah Alhaji ka dena sona, Sadik kuke so tun da kuka fifita farincikinsa kun dena sona" Hakimi yai murmushi yace "haba Nana, ya kike tunani irin haka? Tun daga tasowarki muke riƙe da ke, ba mu taɓa zaɓa miki abunda ze cutar da ke ba, dan haka yanzu ma ba zamu zaɓa miki abunda ze cutar da ke ɗin ba, ki kwantar da hankalinki ki zauna a gudanki, ki rungumi mijinki da yaronki, dama shi namiji mijin mace huɗu ne, kiyi haƙuri na san an miki laifi amma kiyi haƙuri" "Cewa fa yai ba ya sona, da kunne na naji, zaman me zanyi kenan?" "A'a ba kiji dai dai bane, Ya tabbatar min da yana sonki sosai, kar ki bari sheɗan yai tasiri a rayuwar Aurenki, kiyi haƙuri, na san kinyi biyayya amma kiyi haƙuri ki ƙara kinji yarinyar kirki" Nana a ranta tace dama idan akace kayi haƙuri an so cutarka ne, ba ta sake cewa uffan ba ta koma ɗakin Inna, ita kaɗai ta san zafin da zuciyarta take mata. Washegari tun da wuri Inna ta saka Nana ta fara kintsawa wai ta koma, abun kunya ta fito be sani ba kuma a ga ta koma da ƙafafuwan ta, ta rasa abunda yake mata daɗi gaba ɗaya. Tunds Abbasa ya tafi Farhan take kiran wayarsa, amma a kashe har wayewar gari, wayarsa ba ta shiga sam, kasa daurewa tai, ta tabbatar da tabbas Abbas yayi fushi ne, abunda tun haɗuwarsu be taɓa yi ba, duk irin girman laifin da zatai masa ba ya taɓs kai ya duba balle ya nuna yayi fushi, shiryawa tai ta bishi Asibiti. Sedai da taje baya cikin office ɗinsa, wata Staff ta tambaya, ta sanar mata baya jin daɗi yana office ɗin sa na saman bene ya kwanta. Da hanzari Farhan ta bi matattakalar bene zuwa office ɗin saman, ta tura ƙofar tare da yin sallama. Yana kwance akan aboservation bed ɗin da ke office ɗin, yana ganinta ya tashi zaune tare da ƙaƙalo fara'a yace "Madam yau da kanki?" Da sauri ta ƙarasa gaban gadon tana faɗin "doctor, na ganka a kwance ba ka da lafiya ne?" Abbas yace "A'a hutawa nake yi kawai" Farhan tace "Amma na ganka duk wani iri?" Yace "bakomai fa, kar ki damu" Farhan tace "dole in damu doctor, tun abunda ya faru jiya wayarka a kashe, doctor dan Allah ka fahimceni, Wallahi bakomai a tsakanina da Sadik a yanzu" Ya ɗanyi murmushi sannan yace "meyasa kika ɓoyemin dawowarsa gareki?" Tace "saboda ba abune me muhimmanci da zan sa a gaba har ya zama topic ɗin tattanawa ba, babu amfani dawowarsa ratuwar tawa, dan haka babu dalilin da ze sa in gayamaka, hakan ka iya ɓata maka rai" "To ai ni rashin gayamin ɗin yafi ɓatamin rai Farhan, amma bakomai dai ya kike?" Kamar za tai kuka tace "doctor bana son zama, butulu dan girman Allah kayi hsƙuri, nayi laifi amma kayi haƙuri Please" "No,ba kya laifi Farhan naji daɗin dawowarsa rayuwar ki" Farhan ta kalleshi da mamaki tace "saboda me?" "Saboda shine jigon matsalar ki, dawowarsa tamkar yaye fiye da rabin damuwarki ne" "Doctor dan Allah ka dena wannan maganar, me zanyi da Sadik for God sake? Kalli irin rayuwar da na faɗa saboda soyayyarsa, me dawowarsa ze amfana min? Ni dai ba kuma gangancin komawa soyayyarsa zan ba, dan haka dawowarsa rayuwat ba amfani" "Idan ke kin dena son shi ai shi haryanzu yana sonki, kuma yana kishinki" "Dan Allah doctor ka bar Wannan maganar ka ji, kayi haƙuri Please" "Ai ba ki min laifi ba" "No, na maka laifi mana, gashi har ka faɗa min. ina neman afuwarka Please" "Farhan kenan, to naji shikenan ya wuce, yanzu me kike so ayi?" "Ina son kaje ka karya, ka zauna a office ka duba marasa lafiya" Abbas yai murmushi yace "ya akai kika san ban karya ba?" "Doctor saboda na san damuwa farin sani, na san wahalarta da ƙalubalenta" Murmushi kawai yai ya sakko daga kan gadon, ya biyo Farhan suka fito. A ƙasan zuciyar Inna tana jin tausayin Nana, amma ta danne dan da Nana ta gano hakan za ta cigaba da taɓara, da iya shege kala kala, dan haka ta danne ta ƙi nunawa Nana tana tausayinta. Tana zaune tana ta uban kuka, Sahal ma kukan yake ta tsalawa, Inna tai faɗan tai faɗan amma Nana tai burus tana ta kukanta. Sallamar Sadik da ta ji se da ta tsagaita, dan tabbatar da in Sadik ɗin ne da gaske. Sallama ya sake yi, Inna ta amsa masa, Sadik ya shiga cikin ɗakin, yana shiga su kai ido huɗu da Nana, da idanunta su ka kumbure saboda azabar kuka da kishi. Ya gaida Inna ta amsa masa cike da kulawa, ta tashi ta ba shi guri, ya nufi in da Sahal yake tsala kuka, ya ɗauke shi jikinsa duk a sanyaye, ya rungume Sahal a jikinsa yana rarrashinsa, Nana ko kallon in da yake ba tai ba, ta ɗauke kanta. Sadik ya ƙarasa ya zauna a kusa da ita, ya zauna amma ta ɗauke kanta. "Besty" ya kira sunanta. Wata uwar harara ta wurga masa, cike da tsiwa tace "Nana dai kamar yadda kowa ke kirana, ba wata Besty ba sunan yaudara" "Nana nine nake yaudarar ta ki?" "Au to da me kake? Tun da nake da kai ka taɓa gayamin kai ka na da wadda kake so? Ka dinga cewa kana sona ashe kai da wadda kake so rainamin hankali kawai kake" Sadik yai ajiyar zuciya yace "Husna, meyasa kika taho ba izini na?" "Saboda ba zan koma in cigaba da zama da kai ba, daga nan sakina za kai ka ɗau ɗanka ka kaiwa wadda kake so ta riƙe maka" "Nine zan sake kin?" "Eh ka sakeni" "Haba Nana, ina ilimin naki na addini, Wallahi baki ƙarasa jin abunda zan faɗa bane ranar, ina sonki Nana, ƙara Auren da nake son yi, ba dan in cuzguna miki bane dalili ya kawo hakan, kar ki manta gidan Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam mata goma sha ɗaya ne". "Eh mana, tunda nake da kai ba ka taɓa cemin Annabi yace ba, se yanzu da yake Aure zaka ƙara, zaka wani fara cemin meye meye, waima ta yaya zaka iya riƙe mu mu biyu? Gaba ɗaya shekarunmu nawa ne, ni Wallahi ka gama dani ka gama raina min hankali, kawai kaje ka bawa Hakimi takarda ta" Sadik yace "haka kike so?" Tace "eh, haka nake so" "Shikenan, tashi muje gurin Hakimin ki gaya masa, abunda yace shikenan" "Ni ba zan wani je gurin Hakimi in gaya masa ba, kai ne zakaje ka gaya masa" "Malama, ba sakin kike so ba tashi mu tafi gida" "Wallahi ba zan tafi ba, ai ba asararriya ce ni ba, da zaka ce ba ka sona ba, kuma in koma in cigaba da zama da kai ba" "Nana, da ba na sonki ba zan biyo ki nan ba, dan Allah kizo mu koma gidanmu, Please". Se kuma kayi, tai maganar tana juya masa ƙeya. "Ke Nana ku hanzarta, ku zo kuyi sallama da kakanku kuzo ku wuce ku tafi" cewar Inna da ke tsakar gida. Ai take Nana ta sake fashewa da kuka, Inna taga abun Nana nayi ne, dan haka ta dinga zaginta ta sa ta a gaba, ta shirya suka shiga gurin Hakimi, ya daɗe yana musu nasiha, Sannan suka nufi tafiya. Ta ajiyewa Sadik Sahal a gaban mota, ta koma bayan mota, tai zamanta. Sadik ya fara jinjina yadda ze fara zama da Nana da Farhan, kowacce be san halinta ba se yanzu da wannan Magana ta taso. Har suka je gida Nana ba ta kula Sadik ba, yai surutun harya gaji tai masa banza, ta ma yi kwanciyarta a bayan mota ta bar shi da ɗansa. Mother tayi mamakin yadda Nana ta dawo, amma ba abun mamaki bane dama ta san Inna ba zata barta ba, tun da Nana ta dawo, ta bawa banza ajiyar Sadik, dama ba girki take ba, daga cikin gida ake kawo musu, sedai idan tana son ta girka masa wani abu, ko kuma yace yana son ta dafa masa wani abu, idan tai wankanta ta gyara ɗanta se tai tafiyarta ɗakin da ke sashin Mother tai zamanta. Sadik be taɓa zaton son da yake wa Nana ya kai haka ba, se da ta dena shiga sabgarsa gaba ɗaya, lokacin da suke normal in dai yana nan tana jikinsa, tana zuba masa shirirta suyi ta ƙuruciyarsu tare, ga uwa uba ba shi girmasa da take yi, duk da Nana akwai lafiyar tsiwa amma ba ta raina Sadik ba, ba shi girma da take yasa take ƙara burge shi, sam ta manta da miyagun maganganu da yake mata a baya, saboda ba sa jituwa in sun tuna ma sedai kawai tayi dariya. Amma yanzu gaba ɗaya ta buntsure ya kasa gane kanta, yai missing ɗinta over, ko gurin kwana ba ta haɗawa da shi. Yanzu ma ya dawo daga gidansu Farhan, amma be samu ganin Farhan ɗin ba, ga wata irin yunwa da take addabar cikinsa, ya tarar ta tsuke a cikin wando da vest, sabgar gabanta kawai take kamar ba ta ganshi ba, ga gashin kanta da tai parking ya sha gyara, da da ne idan be yaba ba da ya sha mita da haɗe rai, ta dinga binsa kenan tana wai ba ka ganni bane? Amma yau ko kallo be ishe ta ba. Kamar me jin tsoronta yace "Husna dan Allah zan sha tea" Ba ta amsa masa ba, ta shiga kitchen ta dafa ta kawo masa, daga nan ta wuce ɗaki tai kwanciyar ta. Har bacci ya fara ɗaukarta, taji yana shafa gashin kanta, da yake ta ƙamshin man gashi. "Meye haka wai?" Tai maganar tana ture hannun Sadik. "Nana, nine fa" "Kai ɗin fa lafiya?" "Tambayata kike lafiya dan na zo in da kike? Kina ganin abunda ki kai na watsar da ni kin kyauta dan kawai nace zan ƙara Aure, gaba ɗaya kin ƙaurace min?" "Kai da za kai sabon Aure a kawo maka amaraya, me kuma za kai da ni? Dama amfanina gurinka kenan, ka biya buƙatar ka in samu ciki in haihu, matar so tana nan tafe za'a kawo maka" "Yasalam, Wallahi Nana ba dan wani abu nake son yin Auren nan ba, kuma ni ba don abunda nake sonki kenan ba, ina sonki ne saboda Allah, amma kiyi haƙuri". Daga haka ya juya mata baya, yai shiru yana tunanin meye mafita a gare shi, dan ya rasa mema Yakamata yayi akan wannan al'amarin. Can dare Nana tai juyi, ta zata bacci yake, gari yayi sanyi sosai sedai Sadik be rufa ba, saboda a yanzu ko sanyin ba ya ji, ta janyo bargo ta lulluɓe shi, ta dafa goshinsa taji ya ɗau zafi, ba ta sauke hannunta ba ta shiga karanto masa adduoin bacci, da sauran adduoin da suka sawwaƙa a bakinta, dan ita ce take sa shi a gaba yayi dama kan su kwanta, se suyi tare dan haka yanzu ta san ba lallai yayi Adduoin bacci ya ɗauke shi. Ta idar ta tofa masa, ta sake rufeshi sanann ta kuma juya masa baya. Sadik ya sauke ajiyar zuciya a ransa yace "You love me too Husna, kishi ke damunki, amma ta ya zan wulaƙantaki, zan yi haƙuri da duk abunda zakiyi, Allah ya kawomin mafita" Saukar numfashinta ya fara ji, alamar bacci ya kwasheta, ya matsa kusa da ita, ya rungumota jikinsa yana shaƙar sassanyan ƙamshin da take, yana jin yadda yai kewarta, amma Yanzu da yai yunƙurin wani abu, ko za ta yadda se sunyi faɗa, shi kuma baya son ya takurata sam. Usman takanas ya zo gidan, da Mother ta ba shi labarin abunda Sadik ya ɗakko, kuma kakansa ya bashi goyon baya, har gida ya zo, ya samu Sadik ta in da ya shiga ba ta nan yake fita ba, yai masa tatas ya zage shi. "Guda nawa kake dudu, shekarunka nawa saboda hauka da rashin hankali, kace wai zaka ƙara Aure, dan ubanka dukiyar da kake taƙama da ita, ai ubanmu ne ya tara sanannan muka samu, kuma kasuwanci yi maka ake, ba kai kake yi ba, ba ka san wahalar komai ba, makaranta ma kaƙi komawa, sedai ka ci ka tara mata, kai ga wanda ya kawo jarabar bin mata duniya, to Wallahi ka shiga hankalinka idan ka sake ɗaga wannan maganar se nai maganinka Wallahi" Sadik ya fusata ainun, su ba su san ɓarnar da ya tafka a bayan ƙasa ba, su ƙyleshi tun da yana da halin riƙewa yayi, amma anyi caa a kansa, iya haihuwar da Nana tai, ya isa su ɗau darasi amma an kasa fahimtar sa, shi ba dan Nana ta gaza ze Auri Farhan ba, sedai Auren Farhan shine mafita ɗaya da ze cetota kuma ya wanke lafimsa na baya, ya nawa Farhan son da baya tunanin ko Aure tai ze iya rabuwa da ita, a irin son da yake mata, kowane hali take ze iya haƙuri ya aureta, amma kowa yaƙi fahimtar sa, yaji haushin maganganun da dr. Yai masa, amma be ce uffan ba ya bar masa falon shi da Mother, kuma be ji alamar ze janye abunda yai ƙuuduri ba. Da azahar rana tsaka Sadik yaje gidansu Farhan, se ya haɗu da Huzaifa ze shiga gidan ya tsaya suka gaisa da Huzaifa sannan yace masa 'dan Allah cikin gidan nan zaka shiga?" Huzaifa yace "eh ciki zan shiga" Yace "dan Allah in ka shiga ka cewa Farhan tana da baƙo a waje" Huzaifa yace "to zan gaya mata insha Allah" Shigarsa babu daɗewa se ga Farhan ta fito, tana waige waige dan ta ga wake nemanta da tsakar ranar nan?. Tana ganin Sadik ta haɗe fuska tace "lafiya?" "Ba Lafiya ba, meyasa kike guduna kike wulaƙanta ni haka? Kulluma na zo seki ƙi fitowa" Cikin ko in kula tace "idan na zo me zan maka? Sadik na gaya maka kar ka sake zuwa ƙofar gidan mu, na gaya maka, idan kuma ka cigaba da zuwa ka dinga ganin wulaƙanci da rashin mutunci da ga gurina kenan" "Yanzu kina ganin wulaƙanta nin shine mafita?" "Shine babbar mafita a gurina, a gurinka kuma dena zuwanka shine mafita, kowa yayi rayuwarsa". "Kamar Sadik naji kina cewa?" Cewar Abba da yake ƙoƙarin fitowa daga cikin gida. Gaba ɗaya suka sha jinin jikinsu, Sadik ya rusuna yana gaida Abba, Abba ya ƙare masa kallo tabbas ba ze ta ɓa mantawa da Sadik ba, ya sha ganinsa dan baze manta zuwan da yai kawowa Farhan kati ba. "Kai ne Sadik ɗin dama?" Sadik yace "Eh nine Abba" Abba yace "kaine dam silar duk wannan wahalar da ɓacin rai da na shiga akan Farhan? Kai ne ka dinga hure mata kunne da soyayya, ka tafi ka barta ta shiga mummunar rayuwa irin wannan, ni na ɗauka wani babban mutum ne ma ashe kaine, kaje ba zance maka komai ba, amma idan abunda kai dai dai ne, zaka gani a ƙwaryar shanka, ka tafi ka barmin ƙofar gida kar in sake ganinka, na samu wani ze Aureta ba ze yuwu ka zo ka cigaba da hure mata kunne bax Sadik kamar ze yi kuka yace "Abba dan Allah". Abba ya ɗaga masa hannun yace "ka ɓace min daga ƙofar gida kar in sake ganinka". Abba ya ƙarasa maganar yana nuna masa hanya. Gaba ɗaya se jikin Farhan yai sanyi, Abba ya kalleta yace "ke kuma wuce gida, idan na kuma ganin ya zo kin fita sena ɓata miki rai, mara zuciya kawai" Farhan jiki ba ƙwari ta koma cikin gida. Sadik kuwa kifa kansa yai a saman motarsa, ya rasa abunda yake masa daɗi, a hankali ya buɗe ƙofar motar, yana ƙoƙarin shiga, a dai dai lokacin kuma Sunusi ya kawo kai, ƙiƙifta ido Sunusi ya shiga yi dan tabbatar da dagaske Sadik yake gani ko gizo ne, sedai kan ya gama murje idon, Sadik ya bawa motar wuta ya bule Sunusi da ƙura. Kusan a guje Sunusi ya ƙarasa makarantar su, yana son tabattar da in abunda ya ganewa idonsa gaske ne. Mahaifin Lilly yaje har can in da ya kai ajiyar ta, saboda rashin lafiyar da akace masa tana yi, an kaita Asibiti amma ba wani cigaba. Ya tsorata sosai da ganin yadda ta rame, tai duhu tana ganinsa se kuka, tana "dan Allah Daddy ka yafemin ka maida ni gida, na tuba ba zan sake ba Daddy" abunka da ɗa da mahaifi, se tausayinta ya kama Major, dan haka yace da ita ze taho Kano. Ita kanta Mummy ta tsorata da ganin yadda Lilly ta koma, fara ce jawur Lilly amma ta koma duk tai wani iri. Ƙanwar mahaifin Lilly Anty Sa'a, tana gidan Major ya dawo da Lilly, tayi mamakin ganin yadda Lilly ta koma, nan ta tambayi ba'asin abunda ya sa aka kai Lillyn can kudancin Nigeria gidan abokin Major aka barta. Mummy ba ta ɓoyewa Anty Sa'a komai ba, ta gayamata abubuwan da suka faru. "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, innalillahi wa inna ilaihi raji'un, na shiga uku kaico na". Mummy tace "Anty Sa'a, lafiya kike wannan salatin haka?" Anty Sa'a ba ta amsa ba ta kalli Lilly tace "Lilly, waye ya kawo muku irin wannan litattafan kuka karanta?" Lilly bata ɓoye mata ba, ta gayamata yadda ƙawarsu Yasmeen ke tura a wayar yayarta ta turo musu su karanta, ko ta kawo musu su karanta a aji. Anty Sa'a ta kalli Mummy tace. "Yanzu kuna me kuka bar yarinya ƙarama kamar Lilly da wayar hannu ba tare da kuna bibiyarta ba" Mummy tace "wallahi saboda Assigment, kusan kullum cikin ɗaukar tawa wayar take, wai tana Assigment shiyasa ya siya ya bata dan ta bar min tawa". Anty sa'a tace 'ban taɓa dana sani a rayuwata ba kamar na yau, ina da sa hannu a lalacewar Lilly, kuma ba ita kaɗai ba yaran mutane da yawa, nayi nadama a lokacin da bani da halin gyarawa, mugun abun da na aikata ya riga ya cika duniya". Mummy tace "to ai ni ban fuskanci abunda kike nufi ba". Anty Sa'a ta share hawaye tace "irin litattafan da su Lilly ke karantawa, irinsa nake rubutawa, na fara wannan salon rubutu ne saboda ina burin in suna a harkar rubutuna, na fara irin wannan rubuce rubucen, ba irin nasihar da ba aimin ba, amma na ƙi na kasa denawa, katsam Allah yaiwa ɗaya daga cikin wadda muke irin wannan rubutun rasuwa, kuma rubutun be dena yawo a duniya mutane na la'antar rubutun ba, a gaɓar da jikina yai sanyi na dena, se gashi ashe 'yar ɗan uwana ta lalace ta sanadiyyar irin wannan rubutu, kaico na ba zan taɓa yafewa kaina ba wannan abu da na aikata, dan Allah ku yafemin, nayi ƙoƙarin sauke duk irin rubutun a kafafen da na san na ɗora, amma wasu site ɗin ba ni da bani na ɗora ba bani da ikon saukewa, dan Allah ku yafemin". Mummy tai shiru ta rasa abunda yake mata daɗi, ta rasa abunda za tace, sam ba taji a zuciyarta zata iya yafewa Anty Sa'a ba, duk da kasancewar ta ƙanwar mijinta. Sadik kam ya koma salihin ƙarfi da yaji, ya zamana rana zafi inuwa ƙuna, Amma duk da hakan sam baya jin ze iya janye ƙudurinsa na Auren Farhan, kuma mahaifinta ma ze cigaba da bibiyarsa yana sa ran ze haƙura ya ba shi ita. Da wannan ƙwarin gwiwar ya kuma tunkarar Abbansa yana masa magiya "Abba dan girman Allah ka fahimceni, kar ka duba ƙanƙantar shekaruna, tun da ka ga na dage akan lallai ina son yin Auren nan, Akwai dalilin hakan" Abba yace "to meye dalilin naka?" Sadik yace "Abba, a bar batun tona dalilin ni dai dan Allah ka amince min, Wallahi ba zan wulaƙanta Nana ba, ina sonta, Amma Farhan na fara so a rayuwata, ban san yadda a kai al'amura suka juye min ba" "Yanzu kai Sadik ban da haɗama ya za kai da mata har biyu, kai kanka haryanzu da saura ba ka gama hankali ba, ya za kai da mace har biyu saboda rashin hankali" "Au Sadik haryanzu ba ka janye maganar Auren nan ba ko? Duk faɗa da cin mutuncin da nai maka a kai, kaje kai abunda ka ga ya dace da kai, tun da kai dai ba ɗan Arziki bane, ban isa ince bana son abu ka bar shi ba, Allah sarki Faruk Wallahi da shi ne da tuni ya bar maganar nan, amma banda kai, nayi dana sanin sangarta ka da nai, to the extent da baka jin maganata". Sadik kamar ze fashe da kuka yace "haba Mother, Dan Allah..... "Rufemin baki, Aure ko kaje kayi amma ba da yawu na ba, kuma ka nemi wata uwar bani ba, wadda ta isa da kai" Dummmmm haka Sadik ya ji kansa yayi, cikin jiri ya fara tafiya a hankali, ya bar sashin yana lumshe idonsa, da ya fara ganin duhu. Nana na zaune a falo, tana yiwa Sahal wasa, tana babana ya fi na kowa, se ɓaɓɓaka dariya yake, yana kallonta tare da miƙa hannu ze kamo fuskarta. Ba ta ji Sallamar Sadik ba, se ganinsa tai ya shigo yana dafa bango, ɗan binsa da kallo tai dan ta gano ma'anar hakan da yake yi, a hankali ya fara kiran sunanta yana miƙo mata hannunsa. Tai sauri ta tashi ta ƙarasa in da yake tace "ya dai meke faruwa?" "Jiri nake ji, kuma duhu nake gani a idona" Nana tace "Yasalam, ta ya haka?" Ta riƙo hannunsa za tai masa jagora zuwa kujera, kawai ta ga ya faɗi ƙasa! Littafin kuɗi ne, ku tuntuɓi wannan lambar dan samun naku akan kuɗi ₦300 kacal 07063065680 A gigice Nana ta durƙusa akan Sadik, tana jijjiga shi, se dai ko motsi ba ya yi, kuma idanunsa sun rufe, gaba ɗaya jikinsa yai sanyi. A guje Nana ta ruga cikin gida, ta nufi shashin Abba, se dai da ta je ɗin kasa magana tayi, se nuna masa hanyar waje take, ganin ta kasa magana ya sa da Abban da Mother suka biyo bayanta dan ganin meke faruwa, suna zuwa suka tarar da Sadik a ƙasa cikin fita hayyaci. Nan suka shiga rafka salati, Abba yace wa Nana ta bashi ruwa me sanyi a fridge, ta je ta ɗakko ta kawo, aka shashshafa masa a fuska, amma be ko motsa ba. Abba yace wa Nana, maza je ki cewa Sabo ya fito da mota mu tafi da shi Asibiti. Haka Nana ta kuma kwasa tai waje, taje ta gayawa Sabo saƙon Abba, bayan fito da motar, Sabo da kansa ya ƙarasa BQ suka ɗakko Sadik shi da Abba, suka kai shi mota, ita kanta Mother hankainta a tashe yake. Abba ya kalli Nana yace "Nana, koma maza gurin Sahal, ki zauna duk abunda ake ciki ma kira ki a waya" Nana da tuni hawaye ya wanke mata fuska tace "Abba dan Allah ku bari in biku" Abba yace "A'a maza koma cikin gida". Daga haka ya shiga motar ya rungume Sadik a jikinsa, Mother ta zauna a ɗaya gefen suka nufi Asibiti. Kai tsaye Asibitin da suke da file suka tafi, A emergency aka karɓi Sadik, aka  shiga da shi likitoci suka rufu a kansa, dan ƙoƙarin ceto rayuwar sa. Kusan awa guda su Mother na waje, sedai likitocin da Nurses su zo su wuce su, ba wanda yace musu komai, Mother ta kira dr. A waya ta sanar masa halin da ake ciki, ba daɗewa se gashi da Jidda sun zo Asibitin. Se bayan kusan awa ɗaya da mintuna sha biyar sannan babban likitan ya fito yana cire safar hannunsa ya cewa Abba suje Office ɗinsa. Bayan sunje suka sake gaisawa, doctor ya kalli Abba yace "Yallaɓai, ya akai aka bar abokina ya shiga wannan yanayin haka a wannan ƙananan shekarun nasa?" Da yake likitan da Familyn Abba sun daɗe tare suna zuwa Asibiti sosai, dan haka ya san Sadik sosai mutuminsa ne. Abba yace "meya same shi ne haka?" Likitan ya ɗanyi ajiyar zuciya yace "well, jininsa ya hau ranka ya daɗe, hawa ba na wasa ba kam, da shekarunsa sun ja sosai fiye da haka, yadda jinin nan nasa ya hau, kuma ya faɗi da ya kamu da paralyse" Abba ya zaro ido yana kallon doctor. Doctor ya cigaba da cewa "na sa an ɗebi jininsa an kai lap, dan yin wasu gwaje-gwaje, yanzu kuma zan rubuta hoton ƙwaƙwalwa da na zuciya idan ruwan da aka saka masa ya ƙare, se kuje ayo a waje, dan nan bama yi" Abba ya jinjina kai yace "Ikon Allah, to Allah ya bashi lafiya". Doctor yace "Ameen, se ai ta kula ana kwantar masa da hankali, amma a shekarunsa ace jininsa yana irin wannan hawan gaskiya akwai matsala" Haka Abba ya fito jiki a sanyaye, yaiwa su Mother bayani, Usman ya hau faɗa "yanzu akan an ce baze Auren ba shine yake nema ya kashe kansa? Aikuwa sedai ya mutu dan ubansa a wannan karon ba ze samu yadda yake so ba". Jidda tace "haba dr., Dan Allah ka tausayawa halin da yake ciki ka bar wannan Maganar dan Allah, a bari ya samu lafiya". Mother na shirin yin Magana, wayarta ta fara ringing kan ta cirota ta katse, missed calls ɗin Nana kusan guda Ashirin, Mother ba ta sani ba, ta bi lambar Nanan, tana ɗagawa kukanta ta fara jiyowa, Nana tace "Mother ya jikin nasa? Ya tashi kuwa?" Mother tace "ki kwantar da hankalinki, yaji sauƙi an masa allura ne yana bacci". Tace "to Mother in biyoku?" Tace "A'a, ki zamanki likita yace a barshi yai baccinsa karki damu, tare zamu dawo gida insha Allah". Nana tace "to, dan Allah a masa sannu, amma ba abunda ya same shi ko?x Mother tace "eh, malaria ce, kuma an ba shi magani". "To Allah ya ba shi Lafiya". Mother ta amsa mata da Ameen. Zuwa jimawa se ga Mummyn Khairat ma, tare da Khairat sun zo duba Sadik, nan suka dinga jajanta lamarin wai Sadik da hawan jini. Har akaje gurin hoton ƙwaƙwalwar da zuciya Sadik be san anyi ba, saboda ƙarfin Allurar da a kai masa. Abu Kamar wasa Sadik se bayan sallar isha'i sannan ya farka da ga nannauyan baccin da ya wuce da shi bayan suman da yai, likita ya zo kansa ya dudduba hoton ƙwaƙwalwa da akai masa, da na zuciya duk lafiya ƙalau ba matsala. Likita yace "Alhamdilillah, zuciyarsa lafiya ƙalau haka ƙwaƙwalwarsa, amm he is at risk of stroke, saboda jininsa yadda ya hau, yanzu dai muna ta ƙoƙarin jinin ya sauka zuwa normal, gashi can ya farka a samu a bashi Abinci, yai salla zamu kuma yi masa Allurar bacci, amma kar a matsanta masa se yai Magana, sannan kar a ɗaga murya a ɗakin nasa, komai ai masa a hankali". Mother ta amsa da "to". Usman ne ya kai Sadik ya kama ruwa, ya zo yai salla ba wanda yace wa Uffan, aka kawo masa Abinci ba wani ci yai ba, ya ɗauke kai, ya gyara kwanciyar sa ya lumshe idanunsa. Se jera masa sannu suke, amma babu wanda ya amsa. Usman yace Su Mother su tafi gida, shi ze zauna a gurin Sadik, musamman saboda Nana da ta na can cikin damuwa. Jin an ambaci Nana Sadik ya buɗe ido yace "Nana tana ina?" Mother tace "tana gida, ita da Sahal" "Ace mata tayi haƙuri dan Allah, Mother ku bata haƙuri dan Allah". Sadik kamar yana cikin magagi ne, be san meyake faɗa ba, surutai kawai yake yi. Mother da Abba su kai sallama da dr., Suka tafi gida, dama Jidda tuni ta koma gida tai musu girki ta aiko musu da shi. A falo Mother suka tarar da Nana, tai shiru kana ganinta ka san a cikin tashin hankali take, tana ganin su Abba ta miƙe tana faɗin "Abba, ina yake? Ina baban Sahal ɗin?" Abba yace "kwantar da hankalinki, se Allah ya kaimu da safe, Sannan za'a sallame shi". Nana tace "to waze kwana da shi a can?" Mother tace "Usman yana can, tare da shi zasu kwana" "Mother da ma ni aka bari na kwana da shi" Abba yace "ba damuwa, ki kwantar da hankalinki, ya warke ai, ai gobe in Allah y kaimu za ki je ki duba shi" Da kyar suka kwantar wa da Nana da hankali, sedai se aikin kuka take tana Allah ya ba shi Lafiya. Ba Mummyn Lillyn ba, shi kansa Major ya ji baƙi ciki da takaicin abunda 'yar uwassa ta aikata, dan da fari cewa yai ya barta da Allah, dan ba ya jin ze iya yafe mata abunda ta aikata, taje ta yi abu ya dawo kan 'yar sa. Mummy ce tace "kaga Major kayi haƙuri ka yafe mata dan Allah, ka san kaima Akwai naka laifukan da ka aikata, mu bar hakan a mazaunin ƙaddara kawai, Allah ya ƙara shirya mana zuri'a". Major yace "wannan abu da me yai kama? Ina amfanin irin wannan rubutu da tai, Yanzu idan ta mutu yaran mutne suka cigaba da karantawa suna lalacewa fa? Allah kaɗai ya san adadin yaran da suka gurɓace a sanadin abunda ta rubuta, Wallahi ji nake kamar in mata Allah ya isa" "A'a Major, kayi haƙuri tun da har tai nadama, Aikin gama ya gama, se fatan Allah ya kiyaye gaba" Haka Mummy tai ta bashi baki, tana kwantar masa da hankali. Bayan fitar Major, Lilly ta shigo ɗakin Mummy, gaba ɗaya tai wani iri ta zama saliha sosai da sosai. Mummy ta kalleta tace "ya dai?" Jiki a sanyaye tace "Mummy alfarma na zo nema a gurinki". "Wace irin Alfarma kenan?" "Mummy, dan Allah karki bari Daddy ya auran wannan sojan bana son sa, ya min girma sosai, dan Allah kuyi haƙuri ku yafemin ba zan sake ba, kuma bana son a maida ni garin nan, dan Allah kumin rai". Mummy tace "A'a, ba dai ba kya jin magana ba, ba ruwans duk hukuncin da ya yanke a kanki daidia ne, tun da ubanki ne". "Mummy dan Allah, ku min rai Wallahi bana son sa". Mummy tace "ba kya son sa to wa kike so?" "Mummy, dan Allah ki saka Daddy ya sa a saki sir Nazir, idan aka sake shi se muyi Aure, tun da shine.... Se kuma tai shiru. Mummy tace "ƙarasa mana, sarauniyar marasa kunya, ashe ma haryanzu ba ki nadama ba Lilly ta girgiza Kai cikin hawaye tace "Mummy nayi nadama, ina neman afuwarku, amma haryanzu ba zan dena zargin kaina, da ni nai silar komai ba, Sir Nazir Mutumin kirki ne, RUƊIN ƘURUCIYA da tashen balaga ya kai ni ga yi masa tarko, kuma ya kasa tsallake tarkon nawa, muka afka ga wannan ramin da muke nadama a yanzu haka, dan Allah Mummy ku bari in Auri Nazir" Mummy ta kalli Lilly tace "ba ki da hankali, ke kina tunanin idan ya Aureki zaki daraja a idonsa, duk abunda ze wa ɗokin kin riga kin miƙa masa a waje, har kin yiyyi ciki kin zubar dan haka babu abinda zaki burge shi da shi, kuma baze taɓa yadda da ke ba, ke a wannan rayuwar ka kaiwa ɗa namiji mutuncinka gidansa ma, cin ubanka yake balle ke da kuka gama watsewa a waje, kullum a cikin zarginki ze kasance kuma kaf danginsa ba wanda be san meyafaru ba yanzu, ba zasu dinga ganin laifinsa ba, se naki laifin, dan haka ki maida hankalinki tun wuri, tun da Allah ya sa shi wannan be san ta'asar da kika aikata ba, kuma ya ɗan kwan biyu, ze kula da ke kuma ba lallai ya damu ba, tun wuri ki manta da wannan yaron" Lilly ta share hawayenta tace "to Mummy, nagode" Mummy tace "kije ki nemi guri ki huta" Lilly tace "to Mummy, da tun da farko Daddy ya Auramin Nazeer, wataƙila da wannan abun be faru ba, amma dan Allah ku yafemin" Mummy tace "daga ni har mahaifinki, munyi kuskure, Allah ya yafe mana baki ɗaya". Ƙarfe takwas da rabi na safe, Nana tana cikin Asibitin da aka kwantar da Sadik, Nana kasa haƙuri tai, Mother ta sa direba ya kawota kafin su zo, Nana a rikice ta shiga ɗakin da akace Sadik yana ciki, ta ƙarasa gaban gadonsa, ta zuba masa ido, rana ɗaya amma har ya rame, ga ruwa yana shiga jikinsa a hankali. Ta ja kujera ta zauna ta zuba masa ido, a hankali ta kwantawa da kanta a ƙirjinsa, ta fara kuka. Ji tai ya sa hannu ya riƙo nata hannun, be mata Magana ba se hawaye dake bin gefen idonsa, ta ɗan ɗago ta kalle shi tace "Sannu" Be amsa ba se ƙara matse hannunta da yai a nasa. Dr. Ne yai sallama shi da Khairat da Jidda, Dr. Ya ƙarasa gaban gadon yace "meye haka zaka saka yarinya a gaba kana kuka, kamar wani ƙaramin yaro salon ka sake ɗaga mata hankali?". Jidda tace "Baby ka ƙyalesu dan Allah, kana gani tun jiya be wani yi ƙwaƙwƙwaran mosti ba, alama ce ta ya fara samun sauƙi". Dr. Yace "duk da haka ai se ita ma ya ɗaga mata hankali". Nana kasa ɗaga Sadik tai, shima kuma ya kasa sakin hannunta, "Allah ya baka lafiya, in dai nice kayi Aurenka in dai hakan zesa hankalinka ya kwanta" Usman yace "ke tashi in maida ke gida, ba ze Auren ba". Nana ta girgiza Kai tace "dan Allah Yaya Usman ku bar shi yayi, kar ya rasa ransa". Usman ya ƙaraso ya ɓanɓare Nana daga jikin Sadik yace "wuce muje, baze sa miki hawan jinin ba kema, kun zo kunawa mutane kuka, haryanzu ba ku san kun girma ba, kun haifi ɗa amma kunawa mutane koke koke". Nana tana kuka haka Dr. Ya sata a gaba ya maida ita gida. "Farhan, ranar Asabar insha Allah, nake sa ran in ji feedback ɗin yayyan babana, zasu kawo kuɗin Auren mu, amma dan Allah zan miki wata tambaya, ki gayamin tsakanin ki da Allah" Farhan tace "to doctor, Allah yasa na sani" Abbas ya gyara zamansa yace "do you still love him?" "Who?" "Sadik". Gaban Farhan ne yai wata mummunar faɗuwa, ta ja wata ajiyar zuciya tace "meyasa ka tambaye ni?" "Saboda sonki nake tsakani da Allah, ba na son in cutar da ke, ko in miki dole idan haryanzu kina son Sadik ni me fahimtar ki ne, farincikin ki nake so Farhan". Zuciyar Farhan ce ta tsananta bugawa, amma tai jarumta tace "yanzu doctor idan ka ga zan komawa Sadik seka barni? Guda nawa yake ta yaya ze iya riƙe mata biyu?" "Farhan, yana daga cikin matsalolin mu a yanzu, haramtawa kanmu abunda Addini ya halarta mana, Dan haka ki dena duba wannan". Farhan tace "Doctor, ba na buƙatar Sadik a rayuwata, lokaci yayi da zan fuskanci rayuwata, dan ka dena kawo zancensa, Soyayar mu Ruɗin ƙuriciya ce kawai, dan haka a manta da wannan maganar". Abbas ya kalleta yana wani iri murmushi da shi kaɗai ya san ma'anarsa. Farhan tace "dariyar me kake yi kuma?" Yace "bakomai". Nana tun da doctor ya dawo da ita gida, ta kasa nutsuwa ta kasa zaune ta kasa tsaye, ta rasa in da zata saka ranta saboda tsananin damuwa da tashin hankali, ko Abinci ta kasa ci haka ta wuni gaba ɗaya babu daɗi. Se bayan ƙarfe goma na dare, sanann ta ji tsayuwar motar Abba, alamar sun dawo daga Asibiti. Ta ɗan jira zuwa ƙarfe goma da rabi, sha ɗaya saura sannan ta shiga cikin gida. Abba yace "Daughter ba ki bacci ba?" Nana tace "eh, Abba ya jikin baban Sahal ɗin?" Mother tace "ni idan kika ce baban Sahal ɗin nan, dariya kike bani da kunya". Sukayi dariya banda Nana da fuskarta ke bayyanar da damuwa. Abba yace "jikinsa yayi sauƙi sosai, dan ina ga gobe in Allah ya kaimu za'a sallame shi, ya tashi har yace a gaishe ku". "Abba yayi Magana kenan?" "Sosai makuwa, munyi hira da shi sosai". Jiki a sanyaye Nana ta durƙusa akan gwiwowinta tace "Abba, Mother a madadin Sadik, dan Allah dan Annabi ina roƙa masa alfarma ba danmu ba, dan Allah ku ba shi dama yai Auren nan, in dai hakan ze sa ya samu farinciki". Saroro suka bi Nana da kallo, Mother tace "ke anya kina da hankali kuwa? A biye muku kuyi ta shirme, ta yaya Sadik ze iya riƙe mata har biyu?" Nana tace "tun da ya iya riƙeni mu biyun ma ze iya insha Allah, bana son Sahal ya zama Maraya, duk da rayuwa a hannun Allah take, Hakimi yai min Nasiha, na rungumi ƙaddara ta, zan cigaba da zama in kula da yarona, amma shi dai a ƙyaleshi ya Auri wadda yake so, tun da yace ita yake so, ita ya fara so dama". Abba yace "Nana, tashi kije ki kwanta dare yayi". "Abba, in kana son ka shiga cikin ceton Annabin rahama, dan Allah ku bari yayi, ka nema masa Auren nan, Mother dan Allah ki sa baki, ku bar shi yayi, in dai hakan ze sama masa kwanciyar hankali". Abba yace "Naji, jeki za muyi shawara". "Abba dan Allah ka yanke wannan shawarar yanzu, bana son Sahal ya rasa mahaifinsa akan abunda za'a iya magance shi, kaga yayi ƙarami ace yana da hawan jini, hawan jini se mutum ya fara tsufa, ko gane muta8fa ba yayi sosai, in dai ze iya faɗuwa jininsa ya hau saboda soyayya, to abun a duba lamarin ne, ni dan ta tawa me sauƙi ce, na yadda da ƙaddara, ƙaddarar Haihuwar Sahal ce ya sa na aure shi, amma dan Allah ku bari ya auri wadda yake so". Wani irin tausayin Nana ne ya kama Mother, jiki a sanyaye Mother tace "Nana, shikenan kije ki samu ki kwanta". Nana tace "to yaushe za'aje a tambayo masa Auren, bana son ya mutu" Nana tai maganar tana kuka sosai, kamar zata shiɗe. Abba yace "Ai na riga na amince, kije Allah yai miki albarka, kin cika 'yar halak Nana, bari ya samu sauƙi zamu ga abunda zamuyi a kai". Nana tace 'to kun yadda zaku yi masa Auren?" Abba yace "za'ai masa, tashi kije ki dena kukan haka". Nana tace "to Abba nagode sosai, Allah ya saka muku da Alkhairi ya sa ku gama da duniya da lafiya, Allah ya baku abunda kuke nema". Abba yace "Ameen, Allah yai miki albarka". Nana ta tashi da goyon Sahal a bayansa, ta bar falon. Mother tace "Allah sarki, so bala'i ne, banda haka me zesa yarinyar nan ta damu aiwa Sadik abunda yake so? Waye yake son ai masa kishiya, ji nake kamar in mata kuka, ga kishi a tare da ita kuma ga mafita take nema masa, Sadik bewa kansa adalci ba" Abba yai shiru, dan shi kansa tausayin Nana ne ya cika zuciyar sa. Duk da wannan jihadin da Nana tai, kwana tai tana kuka, saboda tausayin kanta da kuma tsananin kishin Sadik da ya addabi zuciyarta. Farhan kwana biyu taji wani iri, saboda sam ta dena ganin gilmawar Sadik, gashi haka kurum idan ta tuna wai kuɗin Aurenta Abbas ze kawo, se gabanta ya tsananta bugawa. Seda Sadik ya kwa huɗu a Asibiti sannan aka sallamo shi, bayan hawan jini har da ulcer da typhoid suka kama shi, likita ya kakkafa wa Sadik dokoki, sannan aka sallami Sadik. Mutane suka dinga zuwa duba Sadik, tsawon kwanakin nan sau biyu aka bari Nna taje ta ga Sadik, saboda koke koke take idan ta ganshi, yau tun da ya dawo ta shigo tai masa sannu ta koma gefe, Sadik se binta yake da ido, yana son yai mata magana, amma baya son yin Magana saboda hakin da yake yi. Nana ta tausayawa Sadik yadda ya kamu da wannan ciwon, da ƙanan shekaru haka, sedai ƙasan zuciyarta ta kan ji haushin sa idan ta tuna, Aure zeyi tai sharing ɗin sa da Wata, wani irin kishi ya dinga taso mata. Da dare yai BQ tai tafiyarta ta bar shi a nan ɗakinsa na cikin gida, yana son ta zauna a kusa da shi, amma sam taƙi kula shi, ko Sahal ta hana shi, duk da yadda yaron yake ta koke koken yana son yaje gurin Sadik, amma ta hana shi ta wayance da ai Sadik ba shi da lafiya. Abun mamaki har su Abba sun kwanta, se ga waya daga ƙauye, hankalin Abba ya tashi sosai da sosai, ya ɗaga wayar jikinsa na rawa Mother kuma tai masa ƙuri da ido, tana jiran jin dalilin kiran. Muryar Hakimi yaji yai masa sallama, Abba yai ajiyar zuciya yace "Alhaji da kan ka?". Hakimi yace "eh da kai na bawan Allah, nace ya batun maganar da mu ka ne? An tambayowa Yaron nan Auren?" Abba yace "Alhaji ai Sadik ɗin ma ba lafiya, yau muka dawo daga Asibiti". Hakimi yace "Subhanallah, kuma ba ku faɗa ba? Ya jikin nasa?". "Jiki yayi sauƙi, an sallamo shi ma". "To Allah ya bashi lafiya, dan Allah Abdullahi ba na son in mutu ban cikawa Yaron nan alƙawarin sa ba, yai min halacci yana riƙe da abar ƙaunata, ba cin mutunci ba wulaƙanci, nima dan Allah ina roƙon ku bari ya auri wadda yake so, kar in zama tsohon banza, kar ku duba ƙanƙantarsa, Addini be hana masa ba, kuma kai Allah yai maka arzikin da zaka tallafa masa ya riƙe su". Abba yace "to shikenan Alhaji, za'ai yadda kace insha Allah". Alhaji yace "to madalla, ai masa sannu a gaidamin Nana da abokina, ace ina son su sosai, A cewa Sadik ga amanar abar ƙaunata nan, a kulamin da marainiyar Allah" "To ranka ya daɗe insha Allah zan gaya musu". Su kai sallama Abba yai shiru yana sake jinjina lamarin. Sadik ya warke ras, sedai jikinsa babu wani ƙwarin kirki, hankalinsa yana kan Nana sosai, da yadda ze yaje ya ga Farhan. Yau a bedroom ɗinsu ya tarar da Nana, ya zauna a kusa da ita, kallo ɗaya tai masa ta cigaba da danna wayarta. Karɓe wayar yai, ya ɗan tsura mata ido sannan yace "haryanzu fushi kike da ni ko Nana?" "Akan me zan fushi da kai kuma?" "Ba gashi ba, tun da na dawo bata sauya zani ba, sam bana gabanki" Nana tace "A'a, meye nawa na cigaba da shishshigi kuma, ai na sadsƙar, ni yanzu zaman ɗana zan yi kawai". "Nana me zan gaya miki wanda ze sa ki yarda da ni?". "Ka ga Please, haryanzu ba ka da lafiya, kar kaje ka kuma sumewa, in dai nice kaje kai Aurenka ka dena faɗuwa kana suma saboda soyayya". Shiru yai yana cigaba da binta da ido, se ƙoƙarin mai da hawaye take kar su zubo, kishinta ƙarara ya kasa ɓoyuwa. "Ni me laifi ne a gareki, ba zan fasa baki haƙuri ba, amma ina sonki Nana ba zan taɓa wulaƙanta ki ba". "Dan girman Allah ka dena gayamin kalmar nan, ƙona min zuciya kake, ka dena yaudarata da kana sona, bana son ji dan Allah" ta ƙarasa maganar hawayen da take riƙewa suna zubowa. Jiki a sanyaye ya tashi ya bar mata ɗakin, ya fita ya ɗau mota ya bar gidan. A ƙofar gidansu Farhan ya ja ya tsaya, yana ta waige waige, yana son ya samu wanda ze aika ya kira masa ita. Kawai ya hango ta tana ƙoƙarin shiga gida, hannunta riƙe da leda "'yan mata daga ina"? Yai maganar cikin sanyin murya. Se da gaban Farhan ya faɗi, yadda Sadik yai duhu ga rama, alamu suka Bayyana ba shi da lafiya. Hararsa tai zata wuce, amma ƙasan zuciyarta ji taka tamkar cikin shagwaɓa ta tambayi meya same shi haka. Ledar hannunta ya ƙurwa ido, tana ƙoƙarin wuce shi ya fizge ledar hannunta, ya buɗe maganin tari ne da wasu ƙwayoyi a ciki, se da kan Sadik ya sara yace "Farhan, yanzu kuma meye damuwarki da zaki sha wani abu?" "Ka aikeni ne? Bani ledata in wuce". "Ba zan bayar ba, Wallahi ka fita daga sabgata na gaya maka". "Ba zan fita ba, ki kiyayeni Farhan ki bar ganin ina lallaɓa ki, Farhan meye daɗi a cikin wannan shaye shayen da kike?" Farhan na ɗaga kai ta ga motar Abbas na shigowa, ta ɗaya ɓangaren kuma Abba ne ke tunkaro gida shima. Kasa motsawa Farhan tai daga in da take, se tsananin bugawa da ƙirjinta yake. "Ke Farhan, ban hanaki tsayuwa da wannan yaron ba?" Abba ya fara magana tun kan ya ƙarasa. Kasa Magana tai, Abba ya ƙaraso ya dinga faɗa ta in da ya shiga ba ta nan yake fita ba, kamar ze ari baki, daga Sadik har Farhan aka rasa me motsawa. Abbas kam zama yai yaƙi fitowa daga cikin motar. Abba ya cigaba da sababi, "ke banda shashanci me zaki da wannan yaron? Ina Hankali ya gama ratsa shi? Wuce ki bar nan kan in saɓa miki, kai kuma zan maka kashedi na ƙarshe, kar in sake ganinka a ƙofar gidana, ko ta rasa mijin Aure ba zan taɓa aura mata mutumin kawai irinka ba, dan haka ka ƙyalemin yarinya tai Aure na karɓi kuɗin Aurenta bana son shirirta da RUƊIN ƘURUCIYA". Huzaifa yana tsaye a soron gidan su Farhan yana jin komai, ya jinjina kai a ransa  yace "wannan ne Sadik ɗin kenan? Idan kuwa hakane Abba yana shirin sake tafka kuskure dan haryanzu Farhan tana son Sadik'. Farhan ko lura da Huzaifa ba tai ba, ta wuce cikin gida ranta a ɓace ba tare da ta san dalilin ɓacin ran ba. Se da Abba ya gama faɗansa, Sannan Sadik ya juya, yana jin wani irin jiri ya nufi motarsa, kasa buɗewa yai ya jingina da jikin motar tare da dafe kansa. Dafa shi yaji anyi ance "ɗan uwa ya dai?" Sadik ya ɗago ya kalli Huzaifa yace "bakomai". "Naga ka dafe kanka" Sadik yace "No bani da lafiya ne, kaina yana min ciwo, amma magunguna na suna mota zan sha insha Allah, nagode sosai". Yace "idan ba zaka iya tuƙin ba, ka jira ka samu sauƙi" Sadik yace "No, zan iya nagode sosai". Haka Huzaifa ya koma cikin gidan su Farhan, sedai abun mamaki ya tarar Abba ya cigaba da sababi a tsakar gida, da ya leƙa ɗakin Farhan kuwa, hangota yai ta dunƙule guri ɗaya tana kuka. Huzaifa a ransa yace "Akwai damuwa, na rasa dalilin da yasa iyayenmu ke yanke hukunci da zuciyar su, maimakon ƙwaƙwalwa. Duk abun nan da ya faru, akan idon Abbas ya faru, a hankali ya ja motarsa yai baya, kan Sadik ya rarako tasa motar ya zo ya buga masa, dan ya lura yaron RUƊIN ƘURUCIYA na damunsa. Abba me ya tsare Sadik a bakin ƙofar shiga falo yace "daga ina kake?". Sadik yace "Naje shan iska ne?" Abba ya girgiza kai yace "Kafin ka mace mana saboda soyayya, ka gayawa yarinyar zamu zo nema maka izinin Aurenta. Murmushi ne ya bayyana a fuskar Sadik, sedai lokaci ɗaya murmushin ya ɗauke, bayan tuna furucin Abban Farhan, da kuma Nana da ke bayan Abba, tana son su gama Magana ta wuce, da alama Abba be san tana tsaye a gurin ba, aikuwa maganar Abba ta soki zuciyar ta, take idanunta su kai ja, ta juya cikin hanzari ba tare da Abban ya ganta ba. "Magana nake maka, amma ka tsaya kana kallona". Sadik yace "to Abba, nagode sosai Allah ya ƙara girma". Abba bece komai ba yai gaba abunsa. Sedai Sadik ya rasa ƙwarin gwiwar da ze tunkari Nana, Wannan shine ga ƙoshi ga kwanan yunwa. Nana yadda ta ga rana haka ta ga dare, saboda yadda zuciyar ta ke mata wani irin zafi, ta rasa in ds zata saka ranta taji daɗi, haka ta kwana sirr ba bacci, se nafilfili da adduoin da dinga yi, Akan Allah ya yaye mata son Sadik, da wannan kishin nasa da ke damunta. Washegari da Sassafe Mother ta ƙwanƙwasawa Nana ƙofar ɗaki, da yake a cikin gida ta kwana yau, tace wa Nana ta shirya zasu tafi ƙauye. Abun ya bawa Nana mamaki ƙwarai, ta tambayi Mother dalili amma Mother tace mata, Hakimi ne yake son ganinsu. Abun mamaki daga Mother se Nana, se Jidda, har da Mummyn Khairat suka tafi a mota ɗaya, Su Abba wai tun Asuba suka tafi. Nana tai jigumm ba tare da sanin meke damunta ba, Sahal ma kasa riƙe shi tai, se Mummyn Khairat ce ta karɓe shi, haka suka tafi ba wanda yakewa wani magana. Sam Nana ta dena ji ta dena gani na wucin gadi, ta dena gane komai se tsintar kanta tai a cikin turakar Hakimi bisa jagorancin Mother, tana zuwa ta tarar da gawa, ga Inna da Abba, ga Sadik har da Faruk, sun kewaye gawar idanunsu sunyi jawurr. Jiki na rawa ta ƙarasa, ba tare da wani ya dakatar da ita ba, ta ɗaga bargon da aka lulluɓe Hakimi, tai tozali da kyakywar fuskar Hakimi, cike da haiba da kamala kamar tace 'tashi Kyakywan kakana, kamar yadda ta kanyi, in ta so tsokanar sa❗❗❗ Littafin kuɗi ne, ku tuntuɓi wannan lambar dan samun naku akan kuɗi ₦300 kacal 07063065680 AFUWAN BA EDITING. Jikin Nana ne ya ɗau rawa kamar zata fita daga hayyacinta, ta nemi guri ta zauna daɓas, idanunta sukai jawur. Can cikin ƙaraji Nana tace "Inna, dan girman Allah ki tasheni daga baccin nan da nakeyi, ki cemin mafarki nake ba Alhaji ne ya mutu ba, dan Allah ki tasheni dan girman Allah". Usman yace "Nana se haƙuri,ki sassauta muryarki, dama duk me rai mamaci ne, kiyi haƙuri ki yi masa Addu'a". "Ba zan ba ni ku ƙyaleni, dan Allah Inna ki tashi Alhaji, ki ce masa ya tashi kar ya tafi ya barni mana". Inna da take zubda hawaye, ta janyo Nana jikinta tana duddukan bayanta a hankali alamar rarrashi. Tabbas duk wanda ze ji rasuwar Hakimi barin Nana ne, tun da Allah yasa su Inna suka rasa iyayen Nana suka ɗau son duniya suka ɗora mata. Banda Inna a tsaye take akan tarbiyyar Nana, ds a sangarce za ta tashi, dan ta Hakimi shi be ya takurawa Nana, duk abunda take so shi yake mata, kasancewar yaransu duk sun rasu se Abba, ita kaɗaice jikarsu da ke gabansu, Nana ko dangin mahaifiyarta ba ta wani sansu ba, saboda ba zuwa take ba, iyakaci sedai su su zo, sam Hakimi baya son tai nesa da shi. Ko zaman fada da ƙyar Inna ta hana shi yi da Nana, lokacin ta fara girma, akwai matsananciyar shaƙuwa ds soyayya a tsakanin Nana da Hakimi, shaƙuwa ta gaske kuwa. Wani dogarin Hakimi ne yai sallama a ƙofar turakar yace "A fito da shi, mutane sun idar da alwala za'a shigo da makara a ɗauke shi". (Innalillahi wa Innalillahi raji'un, ya Ubangijin talikai kasa ranar da zamu dawo gareka ta zama ranar farinciki a gare mu, Allah kar ka sa mu mutu ɓatattu kasa mu mutu a tafarkin ka da na manzonka". Abba jikinsa na rawa ya miƙe, hawaye na zuba a idonsa, Faruk ma kukan yake sosai suka miƙe, dan a ɗau gawar Hakimi, amma Nana ta gigice, ta miƙe jikinta na wata irin rawa, ta riƙe gawar Hakimi tana girgiza kai tace "Inna idan kika bari suka tafi da shi, ba zan sake ganinsa ba fa, Inna kakana a duniya waze mayen gurbinsa, dan Allah kar ku tafi da shi". Gaba ɗaya ta gigice bata hayyacinta sam, surutai kawai takeyi, duk da jikin Sadik babu ƙwari haka ya miƙe, ya janye Nana daga jikin gawar Hakimi, ta shiga ture Sadik, amma ya riƙeta sosai a jikinsa se miƙa hannu take tana kuka, yai waje da ita. Gidan ya cika da mutane sosai da sosai, Sadik ya wuce da ita wani ɗaki, ya zauna da ita a ƙirjinsa tana ta fizge fizge se ta ƙwace. Sadik ya rungumeta tsam a jikinsa, ya shiga faɗin "Innalillahi wa Innalillahi raji'un" a kunnenta. A hankali ta lumshe ido tana wani irin sauke nannauyan numfashi, a hankali ya kwantar da ita, sedai babu tabbacin tana hayyacinta. Ko da Sadik ya fito har an fita da Hakimi, Sadik ya leƙa yace "Mother, maman Sahal tana can ɗakin ko zaki zauna da ita?". Mother tace "to shikenan". Ta tashi ta tafi ɗakin da Nana ke kwance, wadda a kwance kawai take ba tare da sanin a wani yanayi take ba, suma ko ido biyu. A kaiwa Hakimi salla, aka kai shi makwancinsa. Hakimi kam yai jama'a sosai da sosai da sosai, bayan an masa jana'iza ma haka mutane suka cigaba da zuwa gaisuwa. Bayan an dawo daga kai shi, su Abba suka zauna a waje suna cigaba da karɓar gaisuwa, su Inna kuma na cikin gida, Inna ko iya amsa gaisuwar ba tayi, se jinjina kai kawai, lokaci lokaci ta share hawaye. Mother se goya Sahal tai, se uban kuka yake yi, saboda yana jin yunwa, Mummyn Khairat ke taiwa Nana fifita. Sadik yai sallama ya shiga ɗakin yace "Mummy ba ta tashi ba ko?". Mummy tace "kaga dai na kasa ganewa, a sume take ko idonta biyu?". Sadik ya ƙarasa in da Nana ke kwance, ya ɗagota a hankali ya kira sunanta Husna. Ta buɗe idanunta da sukai ƙanana ta kalleshi, sedai ba tace komai ba. "Kina gani na?" Ya tambaye ta, ba amsa se binsa da take da ido. "Meye yake miki ciwo?" Nan ma ba amsa se ido kawai. Khairat ta zubawa Sarautar Allah ido, yarinyar da suke kafsa uban faɗa da Sadik, itace Yanzu yake ririta ta a matsayin matarsa. "Tabbas munyi babban rashi, mun rasa Hakimi, amma kowa na hakane duk zaman jiranta muke yi, dan Allah ki kwantar da hankalinki, muyiwa kakanmu Addu'a Allah ya sada shi da rahamar sa, halinsa na gari ya bishi, dan Allah Husna kiyi Magana bana son wani abu ya sameki". Yai maganar hawayensa na ɗiga a kan kuncinta. Nana ko motsi ba ta iya yi, se bin idon Sadik da kallo, ita ma hawaye na zuba daga nata idon. Mummy tace "Sadik meye haka? Kai da zaka kwantar mata da hankali, se ka sakata a gaba kana kuka kuma?". Sadik be saurari Mummy ba, ya cigaba da zubda hawaye. Mother ta shigo, hannunta riƙe da kofi da ta sa aka samo mata madarar shanu ta bawa Sahal, dan yunwa yake ji, yana ta kuka. "Sadik meye haka kake yi ne?" itama Mother be tanka mata ba. "Kai wannan ai shirme ne, tana buƙatar kalma me daɗi da zata kwantar mata da hankali, kai kuma kazo ka sakata gaba kana kuka, wannan ai shirme ne" Ganin Sadik ba shi da niyyar cika Nana, balle su dena kukan yasa Mother, ta sa aka kira mata dr. Usman ya kallesu, Sadik ya fiye abun haushi wasu lokutan, wai nan magidanci ne har da ɗa, amma yakasa rarrashin Matarsa, ya zauna tayata kuka. "Wai dan Allah Sadii se a yaushe zaka girma ne? Kai da zaka rarrasheta, amma kun haɗa kai kuna aikin kuka, meye haka?" Yai maganar tare da ƙaraswa ze janye Sadik. Mummy ce tace "Usman, ƙyale su kowanne dole zeji mutuwar nan, shi da alama bayan mutuwar har da tausayinta da yake ji, ka ƙyale su kawai. Mother tace 'yo banda abun kunya, gidan surukai azo a tarar ka ƙanƙame mata kana tayata kuka, wannan ai ragwanci ne" Mummy tace "suwaye sirikan, ba duk abu ɗaya bane? Ku ƙyaleshi kawai". Sadik se da yai me isarsa, Sannan ya gyarawa Nana kwamciya, ya samu abun fifita ya dinga fifita ta, sedai gata nan ne dai kawai, ba ta gane komai. "Farhan, yaushe rabon da Sadik ya sake zuwa gurinki?" Abbas yaiwa Farhan tambayar. A bazata taji maganar ta sa, ta kalleshi da mamaki tace "wace irin tambaya ce wannan?" Abbas yace "kawai dai na tambaya ne". "Banji daɗin wannan tambayar ba, kana gani ina fama ya rabu da ni ya den bina, kai kuma kana tambayata shi". Abbas yace "baki tunanin meyasa kwana biyu ya dena zuwa ba?". "Abba ne yace kar ya sake zuwa, Aure zanyi". "Hmmm, hakane amma a yadda yake nace miki kina ganin kashedin Abba kawai ze hana shi ya cigaba da biniyarki?" Ɗan shiru Farhan tai, dan wancan karon ma Abban ya masa kashedi amma ya kuma dawowa. "Kin san wani abu, ranar nazo na daɗe a tsaye ina kallonku ke da shi, har Abba ya zo ya sameku, dui da ba na jin abunda kuke cewa, amma nasan Abba kashedi yake masa, haka nan naji ya bani tausayi yaron". Farhan tace "to me kake nufi?" "Ba abunda nake nufi, amma ba shi da lafiya" "Haba dai? Meyasame shi?" Reaction ɗinta kawai Abbas yabi da kallo, wata zabura tai lokacin da zata tambayeshi, wanda ita ba ta san tayi ba. Abbas yace "nima ban sani ba, yanayin sa na kalla tun a lokacin, naga akwai banbanci da ranar da na fara ganinsa da kuma ganin ƙarshe da nai masa, duk yayi wani iri, akwai alamun rashin lafiya a tare da shi, da kuma damuwa" Shiru tai ta tafi tunani. "You still love him Farhan". Farhan tace "A'a ni bana son Sadik, wai se yaushe zaka yadda da hakan?" "Kinga yadda yanayinki ya canza kuwa? Ina ta baki dama ne kar in tauyeki, idan haryanzu kina son sa, ni me iya jagora ne in samu Abba in masa bayani yadda ze fahimta". "Doctor, dan Allah ka fahimceni, a baya na so Sadik, so ba na wasa ba, ya bani kulawa da soyayya a lokacin da na rasa hakan daga in da Yakamata, ya soni ya kula da ni, amma ƙaddara ta gifta, ba zan iya Auren Sadik ba, faɗan da Abba ma yake yi wai me zan da wannan Yaron, kuma idan na ce ina son Sadik ban maka adalci ba doctor" "Saboda ki min adalci ke se in kasa yi muku adalci? Ai soyayyar gaskiya shine sadaukarwa dan samawa wanda kake so farinciki, abunda iyayenmu basu gane ba, ita soyayya ba yin mutum bace, sirrin Allah ce a zukatan bayinsa, ba kowa ke iya sarrafa soyayya ba, idan kika tabattar min da kina son Sadik, ni kuma zan wuce gaba in wa Abba bayani, kuma batun yarintar sa iyayenmu da kakanni shekaru nawa suke Aure?". Cikin kuka tace "Ni bana son sa, bana son Sadik doctor, ni dan Allah ka hanzarta a kawo kuɗin nan in huta da nacinsa, dan Allah" Abbas yace "to naji, ya isa dena kukan haka, amma kiyi addu'a Allah ya sa yana lafiya, ranar da ya bar nan da ƙyar ya iya shiga motarsa". Shiru Farhan tai tana goge hawaye, yayin da ƙasan zuciyarta tsananin tausayin Sadik ya cikata. Sunusi ne yake huci Kamar kumurci yace "Wallahi Haladu zan maka abunda ba zaka taɓa mantawa ba, kai ne ka sace min kayana". Haladu yace "in sace su in uwar me da su wai, wai meke damunka ne haka?" "Dole ka faɗi haka mana, ka ɓatamin aikina naga wannan ɗan iskan yaron ya dawo rayuwata" Haladu yace "ita wa kenan?" "Farhan matata mana, wannan yaron ya dawo rayuwarta na ganshi a ƙofar gidansu" Haladu yace "Masha Allah, Alhamdilillah ai dama irin wannan Asirin ba ya daɗewa yake karyewa". "Kenan ya tabatta kai ne ka sacemin kaya ka ɓata min aiki?" "Na san yadda kai aikin ne balle in ɓata maka?" Sunusi yace "ƙarya kake Haladu, Wallahi sena sake sabon aiki a kansu, ba su kɗai  ba har kai, za ka ga abunda zan maka, kowa yaci tuwo da ni miya ya sha, zaka san ka shiga aikina ka min shishshigi" "Wallahi Sunusi idan ba ka ji tsoron Allah ba, se ka wulaƙanta, iliminka be maka amfani ba, yanzu na sake fuskantar dalilin da ya sa wasu ke ƙalubalantar ilimin soro, Alƙur'ani kawai muka sani, bamu san tauhidi da sauran litattafai na addini ba, Alqur'ani kawai muka sani, kuma wasunmu irinka muna amfani da shi ta hanyar da ba ta dace ba, irinka suke surkulle da shi saboda rashin tsoron Allah, Wallahi Sunusi kaji tsoron Allah kafin hakkin mutane, musamman na yarinyar nan ya kama ka". "Dalla rufemin baki, ka zuba ido zaka gani, daga kai har ita da wannan sakaran a wannan karon zasuga abunda zan musu" daga haka ya fice yana kumbura wuya. Har bayan la'asar Nana ba ta magana sam, kuma ba ta ci komai ba, gashi rabonta da Abinci tun jiya da rana, se bayan la'asar sanann Inna ta zo kan Nana, ta tashe ta ta tashi zaune amma ba Magana. Inna ta rungumeta, ta shiga karanto mata adduoi, kusan mintuna Ashirin sannan Nana ta fara ajiyar zuciya, sautin sheshsheƙa kukanta ya fara fita  tace "Inna" Inna tace "ya isa haka kukan Nana, Innalillahi wa Innalillahi raji'un, shi zaki ta maimaitawa" Zata kuma magana Inna ta girgiza mata tace "yi ta maimaitawa Innalillahi wa Innalillahi raji'un". Nana tace "Inna dan Allah shikenan ba zan sake ganin Alhaji ba?" Inna tace "mun rasa shi Nana, Allah ya buƙaci abunsa, Innalillahi wa Innalillahi raji'un, ki ta maimaitawa ki tashi kije, ki alwala ki salla". Inna ce ta kamota zuwa tsakar gida, mutane na tai mata sannu suna mata gaisuwa, amma ba ta iya amsawa, sedai Inna ta amsa. Ta rama duk sallolin da ake binta, gurin cin abinci shima haka a kai ta fama da ita da ƙyar Sadik ya sata a gaba sannan ta sha kunu kaɗan, har Sahal ya samu ya ɗan sha Nono. Bayan azahar Mummy da Khairat suka tafi gida, karon farko a rayuwa Mother ta kwana a ƙauye, tun bayan Aurenta da Alhaji Abdullahi. Washegari mutane suka dinga ɓarkowa, ciki harda maƙota da 'yan uwan Mother suka dinga zuwa yin gaisuwa, abunka da rasuwar an maida makokin na zamani, aka dinga shiga ana fita a gidan makokin nan, sedai wanda a kaiwa rasuwar zakaga sune cikin matsananciyar damuwa a fuskokinsu. Abu Kamar wasa, Farhan taga Sadik ya dena zuwa, ta fara tunani kala kala a ranta, anya ba da gaske ba shi da lafiya ba kamar yadda doctor ya faɗa ba? Ko dai korar da Abba yai masa ne ya sa ya dena zuwa?. Shiru tai ta rasa abunda za tai, a hankali ta tashi zaune, ta ɗau wayarta ta shiga yanar gizo dan rage zafi. Sedai labarin farko da tai karo da shi ne ya girgiza ta, mutuwar kakansu Sadik. Jikinta yai sanyi matuƙa, taji rasuwar ƙwarai da gaske, a nan taiwa Hakimi addu'a sosai. Tana nam zaune tana tunanin yadda mutuwar kakan Sadik ta daketa sosai, Huzaifa yai sallama a ɗakin nata. Ta amsa masa tare da faɗaɗa murmushin fuskarta. "Hajiya Yaya ana nan ana hutawa?" "Wallahi kuwa, daga ina haka?". Huzaifa yace "naje wani guri ne, nace ai naga Sadik, ashe ya dawo garemu amma ba labari?" Farhan ta haɗe rai tace "A ina ka ganshi?" "A ƙofar gidan nan mana, sedai ban ji daɗin abunda Abba yai masa ba, yakamata a fahimci juna, yazo asha biki kawai tunda Allah ya dawo da shi" "Huzaifa ka san me kake faɗa kuwa? Abbas ya kusa kawo kuɗin Aurena kuma kana maganar wani Sadik, dan ka bar wannan maganar, ni ba abunda zanyi da Sadik" Huzaifa yai murmushi yace "ji kamar gaske, a tunaninki abu ne me sauƙi kice kin dena son Sadik a yarda? Ya kamata Abba yai tunani akan lamarin nan kan ya yanke hukunci, ni dai na tafi se anjima" ya ƙarasa maganar yana miƙewa tsaye, Farhan ta bi bayansa da kallo. Kwanaki bakwai da rasuwar Hakimi, Abba yace za su tafi da Inna can Kano, su cigaba da zama amma Inna fafur tace a'a ita su barta a ɗakinta taiwa Hakimi takaba, ta duba a dangi ta samo wadda zasu dinga zama tare, amma ba zata bar gidanta ba, ba yadda Abba be da ita ba, amma taƙi yadda se haƙura yai ya ƙyaleta.   Nana kam haka tai kwanakin nan sam ba walwala, abinci dama ba ciwuwa yake a gurinta ba, daga salla se kwanciya, duk ta rame. Ranar kwana bakwan Abba yace tare da ita zasu koma gida, jikinta babu ƙwarin da za tai jayayya, dan haka ta bi su suka taho, tana ta kuka tana sake jin yadda mutuwar ke sake dukan ta kamar lokacin akayi ta. Huzaifa ne zaune tare da Malam Zakari, wato mahaifinsa suna hira, Huzaifa yace "Baba ka san wani abu?" Yace "A'a seka faɗa Huzaifa" "Wannan yaron da Farhan take so fa ya dawo" "Ya dawo ina?" Cewar malam Zakari. "Ya dawo, yace aurenta zeyi yana sonta, amma Abba ya koreshi yace karya sake zuwa" Malam Zakari yace "Subhanallaahi, garin yaya ai ni be gayamin ba, idan da yadda za'ai kawai gara a bashi kar wata matsalar ta kunno kai". Huzaifa yace "Baba, ka manta da anzo an tambayi Aurenta za'a kawo kuɗi" "To ai Huzaifa, komai masalaha ake dubawa, shi wannan tunda su kai magana, shiru ba su turo ba, zanje in samu baban naku, a wannan karon ba zan so a kuma ganganci da rayuwar yarinyar nan ba, hakan akai a wancan karon aka jefa rayuwarta cikin matsala". "Husna, duk me rai mamaci ne, dan Allah ki kwantar da hankalinki, ki dena wannan kukan mu cigaba da yi masa Addu'a, Allah ya sa ya dace, ki ɗau Abincinki kici kinji" "Ka ƙyaleni, ni bana son komai bana jin daɗin komai, ka rabu da ni da wani Abinci" "Dan Allah Nana, kici ko ba yawa Please" "Ni ba zan ci ba, ka rabu da ni". "Sadik, Sadik" ya jiyo muryar Abba yana kiransa a falo. Cikin sauri Sadik ya tashi, ya fito yace "Abba gani". Abba yace "Yawwa, ina son cika wasiyyar Hakimi da ya bari, ka gayawa iyayen yarinyar nan ranar Asabar in Allah ya kaimu, zamu kai maka kuɗin Aure, amma a cikin kuɗin ka za'a ɗauka a kai" Sadik yace "Abba, amma me ze hana a bar kai kuɗin Hakimi yai Arba'in, kuma ga Nana haryanzu tana cikin alhini" Abba yace "kaga, bana son wani kame kame kaji ko? Ai ka san da haka kaje gurinsa ka dage akan se an nema maka aure, abunda yafi kyautuwa a cika masa wasiyyar sa, dan haka kaje ka sanar da su" Abba be saurari abunda Sadik zece ba yai waje. Jiki a sanyaye Sadik ya koma in da ya bar Nana, yadda ta kalleshi ne kawai ya tabbatar masa taji duk yadda su kai da Abba, gaba ɗaya ya rasa murna ze ko takaici, yana matuƙar jin tausayin Nana, ba ta shirya jin komai daga Sadik ba, dan haka ta kwanta ta juya masa baya. Mother ta cewa Sadik ya ƙyale Nana a nan ɓangaren cikin gida, saboda yanayin da take ciki. kullum Sadik se ya zo gurin Nana, sedai haka nan take ba walwala, cin abincin ma ba yi take ba, ba dan Sadik ya tsaya ba, da Sahal se ya yaye kansa, saboda sam ba ta damuwa da shi balle ta shayar da shi, ga shi da kukan banza.   Nana ta rasa meyakamata tayi, ga alhinin rashin Hakimi, ga kuma tsabar kishi da ke damunta, ta rasa in da zata saka kanta ta ji daɗi. Yau a cikin tsananin sa'a, Sadik ya je gidansu Farhan dan yana zuwa ya tarar da Huzaifa na shirin shiga gidansu Farhan. Huzaifa ya tsaya cikin sakin fuska suka gaisa da Sadik. Huzaifa yace "Farhan ɗin zan kira maka ne?" Sadik yai murmushi yace "eh, Allah ya sa tana nan, dan naga gudu na take" Huzaifa yace "ka barta kawai, ka san taji zafin abunda ya faru a tsakanin ku, haryanzu akwai wannan pain ɗin a tare da ita, gaskiya ta soka so na gaske, ta sha wahala ta azabtu a sanadin barinta da kai, ta afka mummunar hanyar shaye shaye, ga binta da sharri daban daban da wanda da za'a aura mata yai, duk wanda ya zo gurinta ko akai niyyar Aurenta, se ya bi ya hana, yaita ɓata a gurin mutane, haka ya sa ta shiga shaye shaye, da yawon kwana a hotel, ta dinga rashin lafiya ga gida babu daɗi, ta sha wahala dole ta gujeka ɗan uwa". Sadik kamar ya fashe da kuka yace "Wallahi ba laifi na bane, Wallahi ka ji na rantse maka, yadda ka san anyi formatting memory na, haka na manta da komai, ba Farhan ba hatta makarantar da nai da abokaina da duk wata rayuwata makamanciyar wannan haka na manta da ita, ban yi dan in zalunci Farhan ba, Aure kuma da nai, na gaya mata kakana ne ya Auramin ita muka tafi karatu tare, ƙanwata ce, amma dan Allah ka tayani bata haƙuri Wallahi ina sonta da gaske, ni ba ruwana da wace rayuwa tayi, komenene nasan nine sila, amma dan Allah ta yafemin, ka ga ni yanzu haka, nai magana da babana, za'a zo tambayar min Aurenta, ina da halin da zan riƙesu gaba ɗaya". Huzaifa ya ɗanyi shiru sannan yace "to ai anyi Magana da wani, ze kawo nasa kuɗin" Sadik yace "ina jin tsoron ta auri wanda ze wulaƙanta ta a gaba, saboda tambarin da taiwa kanta, ni ɗin dai tunda nine silar komai ban isa in mata gori ko wulaƙanci ba, saboda nine sila, yanzu idan ka ban Alqur'ani zan dafa in rantse maka Farhan duk yawon Hotel ɗin da take ba ta bin maza, saboda Soyayar kanta nine na koya mata, nasan halinta kamar yunwar cikina, shikuwa wancan ba si da wannan tabbacin, kai nifa ko mazan take bi, naji na gani ina so zan aureta in zauna da ita ina sonta, ita na fara so, dan Allah ka tayani rarrashinta, da kuma bawa Abba haƙuri akan ya amince dan Allah" Gaba ɗaya tausayin Sadik da na Farhan ya kama shi, yai ajiyar zuciya yace "bakomai, Allah ya wuce mana gaba, bari inje in mata magana" Sadik yace "to shikenan nagode sosai" Sadik be wani sa ran fitowar Farhan ba, kuma sam ba ya jin fargabar Abba ya sake ganinsa, ko da kuwa ze kuma yi masa faɗa idan ya ganshi. Yana nan tsaye yana tunani, ya ɗaga kai ya hango Farhan, cikin dogon hijjabi, a hankali ta ƙaraso in da yake tsaye ta kalleshi, ya ƙara rama se tsawo, yana cikin farar jallabiya, sedai ya ƙara kwarjini sosai, a ɗan tsiwace tace "Sannu ko" Ɗan tsura mata ido yai sannan yace "Yawwa ya kike?" "Lafiya ƙalau, ashe Allah yaiwa kakanku rasuwa" Sadik yace "Wallahi kuwa, Hakimi sa'i yayi, ashe kin samu labari?" Tace "eh na gani a social media, ina Addu'a Allah yai masa rahama, yasa aljanna ce makomarsa, ku kuma Allah ya baku haƙurin jure rashin sa" Sadik yace "Ameen ya hayyu ya ƙayyum, nagode sosai da sosai Princess" juyawa tai za ta koma yace "A'a Farhan ya haka, ina zaki kuma?" "Au har ka manta kashedin da Abba yai maka ne? In ka manta ni ba manta ba" "Nasan da kashedin Abba, kuma ba dan in fatali da kashedin na sa na zo ba, Abba ne za su zo nema min Aurenki ranar Asabar insha Allah". "Wai kai Sadik ba ka ganewa ne? Sau nawa zan gaya maka wani ya riga ka, Aure zanyi dan Allah ka ƙyalemin rayuwata ta huta" "Ke zaki bada damar rayuwata da taki su huta" "Aikuwa sedai kar su huta, dan ranar Asbar Abbas ze kawon kuɗin Aure, kuma sati biyu za'a saka" "Hakan ba damuwa ta bace, kaina na sani" daga haka ya juya ya barta a tsaye tana jinjinawa ƙarfin halin Sadik. Ganin damuwar ta Nana tayi yawa, ya sa Abba ya nema mata makaranta, a satin ya sa direba ya fara kaita, ya ɗakkota Sahal kuma yana gida, sedai babu wanda za'a cewa Nana matar Aurece ya yadda. Abba yai mata nasiha sosai akan ta saki ranta ta maida hankalinta tai karatu, sannan ta kula sosai tunda ta san cewar ita matar Aurece. Nana ta koma ɓangaren su na BQ, sedai tsakaninta da Sadik sedai ido, gaba ɗaya ta dena walwala ta zama kamar wata me jinya, daga salla se kwanciya, se taji yunwa zata kassarata Sannan ta nemi Abinci ta ci. Umman Farhan na ta murna Farhan ta dena yawo, gashi za'a kawo kuɗin Aurenta, se murna take yi, akan za ta samu ta aurar da ita, ta huta da wannan zullumi da tashin hankali, se Addu'a take Allah ya tabattar da lamarin nan. Farhan kuwa na ɗakinta, tana kwance tana karatun Alkur'ani a hankali, tana tunanin yadda ta bar makaranta ta ada karatunta na Addini, gaba ɗaya taji wata Nadama na zuwar mata. "Farhan! Farhan kina ina?" Ta jiyo muryar Abba a tsakar gida. Da sauri ta tashi ta fita, tana tunanin kiran Me Abba yake mata haka?. "Burinki ya cika, a karo na barkatai kin kuma maida ni mutumin banza, shine kika zagaya ki ka samu ɗan uwa kika ce masa wannan yaron kike so, kwana biyar ashe iyayensa sun kai kuɗi, ina nan na saki baki likitan nan iyayensa su kai kuɗi, ashe ni kika mayar mutumin banza, Yaron da yai silar ɓata rayuwar ki, nai miki iyaka da shi amma kika zaɓe shi a kaina, to kije gaki gashi nan, tunda kin fifita shi a kaina kije ki ƙarata, ba dai ke kwaɗayi ba zai Auri yaro ƙarami kamar wannan kije, gaki nan gashi ina ga yaron nan shine ajalinki" ƙura masa ido Farhan tai, ba tare da ta iya firta wani abu ba, saboda tsananin mamaki ta ma rasa wane irin tunani za tai, waye ya kai Sadik gurin Malam Zakari? Ya akai ba wanda ya gayamata an kai kuɗin? Kuma shi kansa Sadik ɗin ba ta sake ganinsa ba? Tambayoyi barkatai suka cika mata kai, ta ina zata fara yiwa Abba bayanin bata san maganar da yake ba se yanzu? Lokacin da take yawonta ma be mata Wannan alkaba'in ba se yanzu akan Sadik, aiko me za'ai ba ita ba Auren Sadik musamman da Abba yai mata wannan maganganun, kuma ba zata zama me cin Amana ba, idan akai haka ba'aiwa Abbas adalci ba" Tun da Nana ta samu labarin kai kuɗin nan, ta ƙara takure kanta, ta shiga wata damuwar saboda ba abunda take hangowa se bankwana da ɗan ragowar farinciki da ya rage mata. Abba ya tura Sadik ya duba gidan da yake so, a gidajen Abban, wanda Hakimi kan ya rasu, seda ya bada kuɗin da za'a saiwa Sadik gida a matsayin gudunmawarsa. Sadik ya dawo daga sallar isha'i, ya shiga suyi magana da Abba, ya tarar da Usman, da Abba a zaune da alama Magana suke me mahimmanci. Abba yace "madalla dama kai muke jira" Sadik ya ƙarasa ya zauna yana jiran yaji jiran me ake masa? Abba ya miƙa masa wata takarda yace "duba Wannan" Sadik ya karɓa ya buɗe ya fara karantar, sedai tun ba aje ko ina ba, jikinsa ya hau rawa, gumi ya wanke masa goshi ya shiga tashin hankali. Littafin kuɗi ne, ku tuntuɓi wannan lambar dan samun naku akan kuɗi ₦300 kacal 07063065680 AFUWAN BA EDITING. Bakomai ne a cikin takardar ba face, bayani ne akayi shi dogo akan Farhan, na miyagun halayenta na shaye shaye, da bin maza da takeyi, da gantalin kwana a hotel. Sadik yayi mamakin wani ƙasaitaccen munafukin ne ya zauna ya shirya wannan kitumurmurar. Abba yace "ina fatan ka karanta abunda ke ciki?". Sadik ya jinjina kai jiki a sanyaye, yace "Abba sharri.... "Dakata Sadik, kan in kiraka in nuna maka takardar nan, yau kwananta uku a gidan nan, na saka Usman yaje ya bincika min gaskiyar maganar ne, amma maganganun da ke fitowa, akan yarinyar suna cin karo da juna. Wasu na sheda mutuniyar kirki ce, wasu na sheda akasin haka, amma batu mafi rinjaye, banji daɗin bayanan da aka samo min akan yarinyar ba, kai ka san a haka take amma kaje zaka jajubo ta ka sakamana ita a cikin zuriyar mu? To da sake ba zan lamunci hakan ba, kaje zan cigaba da bincike hukunci kuma zaga abunda ya dace". "Abba, dan Allah idan ka tashi yanke hukuncin, ka yanke wanda zan iya ɗauka dan Allah kar ka yanke wanda ze rabani da Farhan" Usman yace "wai anya Sadik ba ka fara shaye shaye ba kuwa? Ko ba da hausa aka rubuta takardar da ka karanta ba" Sadik yace "Na sani, na karanta amma dan Allah ku fahimce ni, ni dai dan Allah karku rabani da Farhan" Usman yace "Anya Abba ba asiri a kaiwa Yaron nan ba?" Abba yace "ba wani Asiri da akai masa, shashanci ne kawai, tashi ka bawa mutane guri" Sadik a ransa yace 'Abba ba zaku gane dalilin da ya sa na dage ba, duk da kun nuna ba kwa so' haka nan jiki a sanyaye ya bar sashin, yana tunanin waye da wannan kuturun baƙin munafunci da ya kawo Wannan takardar?. Jiki ba daɗi ya isa nasu part ɗin, Nana tana nan zaune tana aikin nata na tunani, duk ta rame tai wani iri, Sahal na bacci ita kuma ta zubawa guri ɗaya ido, da alama tai zurfin gaske a tunanin. A hankali Sadik ya ɗanyi gyaran murya, ta ɗago ta kalleshi, amma ta kasa dena kallonsa kuma ta gaza furta komai. Ya kalli in da aka kawo kwanukan Abinci da alama ba taci ba, ya ƙarasa ya buɗe babban food flask ɗin, tuwon shinkafa ne da miyar taushe ta sha nama, ya zubo kaɗan ya zo gaban Nana ya zauna ya ajiye mata, yana tausayinta sosai ba ya son ya shiga hakkinta da yawa, gaba ɗaya ta dena walwala ta takure kanta fiye da kima, ba'a ta ɓa yiwa Nana rasuwa ba, dan haka dole wannan ta shigeta sosai. "Bismillah, ci Abinci" ya faɗa cikin bada umarni. "Na ƙoshi" ta bashi amsa. "Kika ƙoshi da kika ci me?" "Na sha shayi" ta bashi amsa. "Abinci zaki ci, Nana meyasa kike son sekin illata kanki ne? Kin saka damuwa a ranki, ga yaron nam shi ba saurarar miki yake ba idan ya na jin yunwa, haba ki zama me karɓar ƙaddara mana, kiyi haƙuri ki ci-gaba da yiwa Hakimi addu'a, in kuma kema so kike ki rasa ranki kuma se inji" "Saboda iyayenka suna raye, uwa da uba, kuma yanzu Magana ake ta zaka Auri wadda kake so, ni ban san uwar ba ban san uban ba, babban bango a rayuwata ya faɗi, ban taɓa ɗanɗanan ɗacin rashi ba se a wannan karon. Nima fa ba jin daɗin yanayin da nake ciki na nake, nayi iya ƙoƙarina amma na kasa daurewa, komai ya fita daga raina, dan Allah ka ƙyaleni idan da rabon in koma yadda nake shikenan, in kuma nima a zan mutu shikenan Ka bawa Mother Sahal, ko Su Anty Jidda" "Meyasa zan ƙyaleki? Yadda kike cewa farincikin Sahal da naki ya na tattarr da farincikina, haka nima farimcikina da na Sahal suna tattare da naki ne, insha Allah da kanmu zamu raini Sahal muyi tarbiyyar sa, ki dena irin wannan tunanin, komai ze wuce Insha Allah, kan ki rasa Hakimi mahaifinki suka rasa, kuma suka cigaba da rayuwa, har kika girma, kowa yana jin haka idan yai rashin wani abu da yake so, dan Allah ki kwantar da hankalinki ki dena koke koken nan". "He is very kind and generous, wannan halin nasa na tausayi da kulawa ne yasa na fara son shi, ashe shi da wadda yake so, kar ya cigaba da yaudarata da wannan halin nasa, yasa in cigaba da son sa, amma hanklinsa ya koma kan wata gaba ɗaya" a zuciyarta tai ta wannan tunanin, a zahiri kuma take kallonsa yadda yake ta rarashinta cikin kulawa da tausayawa. "Doctor magana nake amma kai banza dani, meyasa zaka min haka? Akan me meyasa? Ka dena ɗaga wayata ka dena zuwa gidanmu, kuma kana jina ina ta magana kai banza da ni" Farhan tai Maganar cikin ɓacin rai. Abbas ya tashi yaje ya kulle ƙofar Office ɗinsa, Sannan ya jingina da ƙofar ya kalli Farhan yace 'gayamin, me kike so ayi, ko kuma meye baki gane ba?" "Au kana nufin duk wannan ɓaɓatun da nake yi ba ka ma san me nake cewa ba? Ina can ina jiran ka ka kai kuɗin Aurena, kawai se inji Sadik ya kaimin kuɗin Aure how? Meyasa haka zata faru? Meyasa za kai min haka?" "Au haba, dagaske Sadik ne ya kai kuɗin Auren, Masha Allah, Allah ya Sanya alkhairi yasa ayi damu" Kawai Farhan ta fashe da kuka, kuka sosai har da sheshsheƙa. Ɗan murmushin ƙarfin hali yai yace "Am sorry, ba ina nufin in saki kuka bane my dear, Farhan ni babba ne bana son in zama babban banza, ina tausaya muku da ke da Yaron ne, shiyasa na sadaukar masa da ke, a dalilinsa kika faɗa wannan mummunan halin, kuma a hakan ya dawo yace yaji ya gani, dagske yake sonki, mahaifin Huzaifa ne ya nemeni, kuma naje muka tattauna a matsayina na likita, dan shawo kan matsalar ki, muka tsaya a wannan matsaya, ina tayaki murna tare da yi miki fatan Alkhairi" Cikin kuka tace "dama na sona kake ba? Na ɓata lokacina gurin sonka da tunanin Allah ya musanya min Sadik da kai, ashe kaima yaudarata za kai, yanzu duk azabar da naci saboda Sadik ruhina be cancanci ya huta ba zan koma gareshi, me soyayya RUƊIN ƘURUCIYA ta amfana min? Nagode da wannan sakamako da kai min, na soyayyarka da tunanin zaka tsamo ni daga tsaka me wuyar da nake ciki, Nagode da abinda kai min, kuma ka sani zanje in warware wannan maganar dan ba zan taɓa Auren Sadik ba, gara in cigaba da yawo". Abbas yace "Subhanallah, haba Farhan ki fuskanci dalilina manax "Ba wani dalilinka da zan fuskanta, duk mazs kun taru kun maida ni karkatacciyar bishiyarku me daɗin hawa, tamkar wata ƙwallo wannan ya jefawa wannan, in kuka haukatani kun huta ai" ta ƙarasa maganar tare da murza key ɗin ƙofar tai waje. Abbas ya dafe kai, tare da neman guri ya zauna, ya zaci Farhan za tai murna da wannan abu da yayi, be taɓa tunanin za tai bore ba, shi kansa ba ƙaramin jihadi yai ba gurin haƙura da Aurenta, sedai ko ne haƙura da Auren nata ba, dangin mahaifinsa sunce ba shi ba Auren Farhan, saboda mugun fentin da suka ci karo da shi wajen bincike akan Farhan ɗin. "Malam, dan Allah ka bi koma a hankali, kar a kuma haihuwa a ragaya a game da yarinyar nan, kaje ka samu Malam Zakarin ku tattauna, kaji ya akai ya karɓi kuɗin wancan yaron maimakon kuɗin gurin likitan". Abba yace "ba in da zani, ba zasu maida ni mutumin banza ba daga shi har ita, suje suyi yadda suke so, na gaji da halin yarinyar nan da maganar da take janyo mana". Umma tace "dan Allah kayi haƙuri, in dai wannan ɗin shi tak so, zata zauna da shi ze Aureta a haka ai shikenan, ni babban fatana shine tai Auren nan mu huta gaba ɗaya". "To shi yanzu likitan idan ya kai nasa kuɗin ya zasu yi kenan? Bayan sun tambaya ance an basu?" Umma tace "to kaji ance sun kai ɗin ne? Tun yaushe suke cewa zasu kai? Kayi haƙuri kaje ku tattauna" "Kin san Allah, ba in da zani suje su ƙarata can, ai shima ubanta me ya isa da ita, dan haka ba hannuna". Sadik yai sallma a ɗakin Nana, ya tarar tana ta shirin makaranta, ga ƙoƙarin shirya Sahal da ya hanat sakat, gaba ɗaya tausayi take ba shi,shi kansa rainon na ƙaramin ƙoƙari take yi ba. "Makarantar zaki tafi ne?" Yai tambayar yana kallonta. Tace "eh". Yace "Ajiye Sahal ɗin, tashi kije Sabo ya kai ki, bari in ƙrasa shirya shi in kaiwa Mother, in an tashi zan zo in ɗakko ki" Nana tace "to" ta ƙarasa shiryawa ta fita, shikuma Sadik ya ɗau Sahal zuwa gurin Mother. Ya tarar da ita a falo, tana bawa Talatu umarnin, gyaran kitchen da take so ai mata yau. Yace "Mother ina kwana" kallo ɗaya taiwa Sadik ta ɗauke kai, ba tare da ta amsa gaisuwar tasa ba ta karɓe Sahal daga hannunsa. "Mother gaisheki fa nai". Mother tace "Ai zuwa yanzu Sadik kafi ƙarfin ka gaisheni, ai na tashi daga matsayina na uwarka zuwa wani abu daban, tun da har zaka iya dagewa akan abunda ba na so, Yanzu Sadik ashe yarinyar da ka dage seka Aura ɗin makaranta ɗaya ku kai, bana wannan ba, an tabattar da yarinyar mutuniyar banza ce, har gida aka kawo wa ubanka takadda, kuma ya tura a kai masa bincike aka kuka tabattar masa da hakane, anya Sadik kanawa kanka adalci? Ita wadda kake tare da ita meye ta gaza da har hange hangenka ya hango maka waccan ɗin?" Sadik yai shiru ya kasa furta komai. Mother tace "Ai shikenan kaje kayi, amma ni dai kama ba da yawuna ba".daga haka ta gyarawa Sahal kwanciyar sa a kafaɗarta da yake bacci yake, ta wuce sashinta da shi. Sadik ya rasa abunda yake masa daɗi ga ƙoshi ga kwanan yunwa, ko ina babu daɗi, amma yasan wannan Auren da ze yana kan ƙa'idar shari'a sedai ze cigaba da Addu'a Allah ya kawo masa mafita. Ƙarfe biyar na Yamma Sadik yana ƙofar gidansu Farhan, tun da aka kai kuɗin nan be sake zuwa ba se yau, ya tura Amir yace yai masa sallama da Farhan. Da Amir ya samu Farhan a tsakar gida ya sanar mata, se cewa tai yaje yace masa ba zata zo ba. Abba da yake aswaki yace "baki isa ba, tashi ki fita, tashi kan in saɓa miki" Haka nan ta shiga ta ɗakko hijjabinta, ta saka ta fita ranta a matuƙar ɓace. Ko da taje zuwa tai ta tsaya ko kallon in da yake taƙi yi. "Barka da yamma 'yan mata" "Meye kawoka gurina? Sadik meyasa zakamin haka, da izinin wa kaje kai kuɗin Aurena gurin ƙanin mahaifina?" "Au sena nemi iznin ki? Ai tun farko na gaya miki" "Akan me zakamin haka? Ni nace maka na dena sonka ya za'ai mutumin da ya sha wuya gurin ganin dawowar farinciki na, a lokacin da ka gujeni lokaci ɗaya ai masa haka? Na zama butulu irinka kenan?". Sadik yace "Nine farincikin dama, da na tafi kuma gashi na dawo, dan haka kawai ki dena wannan goce gocen" "Ba zan dena ba, ba zan dena ba ɗin, bana sonka Sadik bana son ganinka, kuma ba zan Aureka, idan kuma kai gangancin Aurena ka shirya karɓar abunda ba kai zato ba, ni ba butulu bace irinka, Abbas zan Aura, mayaudari kawai" har ta gama masifar kallonta kawai yake yi, tai masifarta ta. Sadik yace "in kin gama masifar, ina son inji meye tsare-tsaren ki na bikin, kuɗi zan baki ko kayan lefe kike so?" "Bana so, ka riƙe abunka dan ba zan taɓa Aurenka ba" tai wucewarta cikin gida ta barshi a tsaye yana binta da kallo. Nana ta dawo a gajiye sosai, ta wuce ta ɗakko Sahal sannan ta koma BQ, dan ta san maybe yana nan yanawa Mother kuka. Ta tarar ana ta shirye-shirye, Nana tace "Mother, baƙi za'ayi ne?" Mother tace "A'a Faruk ne ze dawo, ya kammala master's ɗinsa, se abunda ba'a rasa ba" Nana ta ɗanyi shiru Sannan tace "Mother, ki yiwa Baban Sahal Magana ya koma makaranta shima" Mother tace "ni ƙyaleni da batun mijin nan naki, daɗi Aure ya zauna yai tayi, kar Allah ya sa ya koma makarantar, ni na zuba masa ido yaje yai abunda yaga dama" "Dan Allah Mother karki ce haka, Yakamata ya cigaba da makarantar ss" Mother tace "kunfi kusa, kema zaki iya gaya masa ai, Khairat kawo mata abinci ta ci" Gaba ɗaya Khairat haushin Nana take ji, yanzu haka ji tai kamar ta cewa Mother ba zata zubo mata Abincin ba. "Mother, Sahal yau yai kukan kuwa?" Mother tace "ɗan ƙaniya, yayi amma ba sosai ba, Dr. ne ya tafi da shi, be daɗe da dawo da shi yai bacci ba" Nana tace "to shikenan, tun da bacci yake, nima naje in ɗan kwanta". "Ɗan uwa, wai tunda aka kawo kuɗin yarinyar nan na zata zaka zo, a tattauana yadda al'amarin ze gudana amma na jika shiru" Abba yace "dan me ba zaka jini shiru ba, ni ka nemeni ne? Ko da kuka tashi yanke hukuncin ku ni nemana kukayi, kawai inji labarin wai kuɗin wannan yaron ka karɓar mata" Malam Zakari yace "A'a, shi Abbas ɗin be zo ya sameka bane?" "Ni ba wanda ya zo ya sameni" Malam Zakari yace "to ai Abbas ɗin har gidan nan ya zo, yace min ya janyewa shi wancan yaro, kuma yai min bayani na gamsu" Abba yace "kamsr yaya, kaga yaron kuwa? Yaro ne fa ƙarami sosai" "To Addini ya hana ne? Na ga yaron har gidan da nake yaje, na ganshi, Abbas ya tabattar min da tana son yaron nan, kuma shima yaron yana sonta. Ɗan uwa a karon farko kasan laifinka ne da na matarka ya ingiza yarinyar nan shiga wannan halin, a dalilin Yaron nan ta faɗa mawuyacin hali kuma ya dawo yace yana sonta a haka, addini be haramta auren nan ba, meyasa kake son kai ka haramta, mahaifinsa sanannane ne mutumin kirki, kuma duk da mutum ne me kuɗi, cikin girmamawa da mutunci suka kawo kuɗin nan, ita kanta Farhan ban tsaya bi takanta ba na karɓi kuɗin, shi wannan likita yace idan aka tsaya biye ta tata za tsce ba ta so ne, amma kuma ƙasan ta shi take so. Zamanin iyayenmu har a shekara sha bakwai anwa ɗa Aure kuma ya zauna, addinin mu be haramta ba, dan haka ai musu addu'a kawai, kayi haƙuri ta ta ƙaddarar kenan". Abba yai ajiyar zuciya yace "shikenan ɗan uwa, Allah ya basu zaman lafiya" Malam Zakari ya amsa da Ameen. Sadik yaji daɗin dawowar Faruk sosai da sosai, a wannan karon ma Khairat se ƙoƙarin yiwa Faruk ɗin bajinta take, amma shi sam be ɗau hakan a matsayin wani abu na musamman ba. Dama da yazo jana'izar Hakimi, kwanan sa uku a ƙauye, ya koma in da yake karatu kasancewar exams zasu fara, dan haka Wannan karon da ya dawo, ɗakin Sadik Na cikin gida ya koma, kasancewar su Nana suna BQ. Sadik yana tare da Faruk suna hira, Faruk yace "Man, gaskiya kayi ganganci Sadik, ka duba yadda ake ji da kai a gidan nan, amma kowa ya watsar da kai saboda abunda ka ɗakko, guda nawa kake da har zaka ɗorwa kanka wani ƙarin Aure, Auren ma na yarinya mara ɗa'a, dan Allah me Maman Sahal ta rage ka da shi?" Sadik ya nisa sannan yace "Bro, kowa yaƙi fahimta ta amma ina sa ran, kai ka fahimceni" ya ɗakko wayarsa ya nunawa Faruk hoton Farhan yace "ka gane wannan yarinyar?" Faruk ya ɗanyi shiru sannan yace "nasan fuskar nan amma na manta in da na santa" Sadik yace "2yrs back, ita ce yarinyar da na ɗorawa raina cewar Lallai sena Aureta, na dinga cewa Aure nake so kana cemin RUƊIN ƘURUCIYA ne, itace yarinya ta farko da na fara so a rayuwata, ka san meya ja hankali na ta burgeni na fara sonta? Tsananin kamun kai da tarbiyyar ta, da karatun addini. Tun yarinyar nan tana guduna, se da ta fara yadda da ni, soyayya me ƙarfin gaske ta shiga tsakaninmu, zanniya cewa ƙaddarar haihuwar Sahal ce ta gifta Hakimi ya Auramin Nana, a lokacin da gaba ɗaya aka shafe tunanin Farhan a zuciyata na manta da ita, cikin ikon Allah Maman Sahal ta zo da gagarumin sauyi a rayuwata, kuma ta zame min wani kyakkyawan bago da na jingina a jiki. Duk abunda Farhan tai na lalacewa, nine sila Faruk, Yarinya ce me tarbiyya duk a sanadina komai ya sameta, yanzu idan na gujeta na ƙi Aurenta naiwa kaina adalci? Nima fa yanzu na zama uba, na fara tara iyali, ba zan so aiwa ɗana abunda naiwa Farhan ba, duk da shi Allah ba'a masa wayo. Amma su Mother sunƙi su saurareni balle su ji uzurina, a tunaninsu son zuciya ne kawai yasa nake son ƙara Auren nan, amma hatta jumping class da nai, duk cikin planing ɗina ne na in auri Farhan, ina matuƙar sonta she's my first Love, gashi Husna kanta yanzu haushina take ji, ta dena shiga sabgata wanda hakan shima ba ƙaramin damuna yake ba, duk da nasan kishi ke damunta, amma ba zan hanata kishi a kaina ba, saboda koma mene laifina ne na shammaceta ban taɓa nuna mata nai soyayya da wata ba, wanda nima ba laifina bane, yadda nake ɗin nan fa nake Magana ina kan maganin hawan jini ne fa haryanzu, na rasa in da zan saka kaina" Faruk yai ajiyar zuciya yace "ni na fuskance ka Sadik, zan cigaba da tayaka da addu'a Allah ya kawo komai cikin sauƙi" Sadik ya amsa da Ameen. Unguwar su Farhan ta ɗauka, an kai mata kuɗin Aure, dubu ɗari amma an rasa waye mijin, an bi diddigi an tarar ba Abbas bane, lallai tayi goshi saɓanin lokacin da Sunusi ya kai mata dubu Ashirin da biyar, sam Abbas ya ɗauke ƙafarsa, dan baya son ya cigaba da zuwa, su samu Matsala da Sadik, dan haka daga gefe ya cigaba da yi mata fatan alkhairi, tare da rarrashinta ta waya, wanda shima daurewa kawai yake yi, amma har ga Allah yana ƙaunar Farhan dagaske ba wasa ba. Sadik kuwa in dai yazo wataran taƙi fitowa, ko ta fito suyi faɗa ya tafi, wanda hakan shima ya sa ya dena zuwa, hakan yasa 'yan unguwar ba su san waye ya kaiwa Farhan kuɗin ba, dan an dena ganin kowa yana zuwa in da take. Da Sunusi ya samu labari kuwa ji yake kamar yai hauka, dan be taɓa tunanin wani ze fito haka ya iya yunƙurin Auren Farhan ba, yai iya yinsa amma be gano waye ba, dan sam be kawo Sadik ba, saboda a ganinsa yarone waze bashi Auren 'ya?. Sosai aka gyara gidan da Sadik ze zauna, wanda ba shi da wani nisa sosai daga gidan su Sadik, gidan yayi kyau sosai da sosai, Sadik shikaɗai yake fafutukar shirin Aurensa, se Anty Jidda da ya kan tambaya wasu abubuwan se ɗan uwa Faruk, duk da har ga Allah daga Faruk har Anty Jidda Nana suke yi suma, amma Sadik abun a tausaya masa ne shima. A gidan dr. Ya haɗa lefensa cif, Abba yai Maganar ze saiwa Nana furnitures, Sadik yace Abba ya bari shi ya sai mata, tunda kayan lefenta suna nan ba abunda ta taɓa, base yai mata kayan faɗar kishiya ba se yai mata furnitures, amma Abba yace basa buƙatar kayansa. Abubuwa har mamaki suke bawa Nana yadda Mother ta sauya, dan ita ta sai mata komai na kayan kitchen, duk abunda uwa za taiwa 'ya, Mother ta saiwa Nana shi, dan dama bata da 'ya mace, bata taɓa Auren 'ya ba, dan haka ta kashewa Nana kuɗi sosai, aka zuba a sashin Nana da ke sabon gidan da zasu zauna. Gashi musamman Mother ta biya kuɗi aka ɗakko me gyaran jiki, take gyara Nana, wanda ko da aurenta ba wanda yai mata wannan haka nan zallarta aka bawa Sadik (lolz🤣). Gidansu Farhan na ta shiri, ita kuwa sam ta rasa farinciki take ji ko haushin wannan Auren take, dan sam ba ta farinciki ji take tayi butulci na gaske na ƙin Auren Abbas, musamman idan ta tuna irin ɗawainiyar da shi da mahaifiyarsa suka dinga yi da ita. "Amm dama nace, dan Allah ina son zuwa ƙauye, ko sati ɗaya muyi". "Se yanzu da buƙatar kanki ta taso kika tuna dani Husna?" Banza Nana tai masa tana tura baki. "Gaba ɗaya kin mai da ni hoto ba ruwanki dani, anya rayuwa za ta tafi a haka? Dan kawai nace zan aure shikenan kika watsar da ni" "Dan Allah ni a bar wannan zancen, bana so" Sadik yace "wane zancen?" "Zancen Aurenka ni bana so". "To na dena" ya bata amsa. "To ka barni?" Tai maganar idonta fal hawaye. Wata irin kewarta ce ke fuzgarshi, shi kansa ya san yayi dauriya, dan rabonsa da ita har ya manta. "Uhmm kayi magana mana" tai maganar a shagwaɓe. Rungumota yai cikin bazata yana kissing ɗin ta. "Wayyo Allah na, Mother" da sauri Sadik ya cikata yace "Besty meye haka kamar wata ƙaramar yarinya?" Yadda take tura baki tana hararsa ne, ya ga ta koma yarinyarta sosai, ya ɗan lumshe idonsa yace "kinyi kyau sosai, nai missing ɗinki zo kiji" Noƙe kafaɗa tai tana share hawaye, yace "Shikenan, dan Allah goge hawayen, idan Mutan gidan nan sukaga kina hawaye se su rufeni da duka yadda suke jin haushin nan nawa, jeki Allah ya kaiku lafiya". A ciki ta amsa Ameen ɗin, tai waje ita kanta tai missing ɗin Sadik, amma tsabar yarinta, taurin rai da baƙin kishi yasa Nana ba ta jin hakan da take a matsayin wani laifi. Tun da Hakimi ya rasu Nana ba ta sake zuwa ƙauye ba yau, tai murna sosai da ganin Inna, amma tana kallon turakar Hakimi se kuka, Inna tai ta mata nasiha akan ta de na yi masa kuka Addu'a za tai masa. A yanayin bugun cikin Nana da Inna tai, ta fuskanci sam Nana bata shiga shirgin Sadik, haryanzu Nana tana fama da tarin ƙuruciya da wauta. Inna ta zauna ta dinga yi mata nasiha da hatsarin de na shiga sabgar Sadik da tai har take bata misali da "da uwar mijinki ai bata ƙaunarki, amma sannu a hankali da ki kai haƙuri ba gashi komai ya wuce ba, har siyayya tai miki kamar 'ya da uwa ba? To komai na rayuwa haƙuri ake me wucewa ne. Kuma tun da sabon Aure yai zakiga abunda ba kya so, amma ni daure ki ɗauke kai ki kwantar da hankalinki, komai ze wuce bance ki saki jiki a wulaƙanta ki ba, ki kama mutuncinki amma karki wulaƙanta mijinki, yana ƙaunarki sosai". Nana dai tai shiru tana sauraren Inna, amma tana jinjina lamarin dan babu sauƙi sam. Yau da Sadik yaje gidansu Farhan, Abba na nan dan haka dolenta ta fito, suna tsaye yana ta Magana tai banza da shi, sega wata danƙareriyar mota, Wannan mutumin da suka taɓa Faɗa da Sadik akan Farhan ne ya fito, a fusace ya tunkaro su yana zuwa ya kalli Farhan yace "mayaudariya munafuka, nai nai ki Aureni kika ƙi, amma naji labarin wai zaki Aure, bayan kin gama sawa na kashe miki kuɗi, to ki tattaro duk abunda kika san na baki, na kashe miki ki dawon da abina". Sadik yai caraf yace "An cinye ƙarfi ya ƙwata, kaje ka kai duk in da zaka kai, lokacin da kake bata kunyi a rubuce cewar zata Aureka dan haka zaka kashe mata kuɗi? Ko kuma ita ta roƙe ka? Dan haka ka saurara, kaje ka kai in da kaga za'a ƙwatar maka" A fusace yace "kai ka kiyayeni,kar ka min rashin kunya" "Anyi maka rashin Kunyar, kaje ka kai in da duk zaka kai" Haka Mutumin nan ya ƙaraci borin kunyarsa ya tafi, Sadik ya sanarwa da Farhan cewar saura kwana uku su kawo lefe. Ko da aka kai kayan lefen nan duk da gidansu Huzaifa aka kai kayan, unguwar su Farhan ta ɗauka, aka dinga zuwa kallo, Akwatuna Bakwai ne na gaske masu kyan gaske, kayanta 'yan cif se tsada, har da gwal biyu a ciki, kayanta manyan kaya sosai da sosai, da babban buhun shinkafa. Akace se yanzu a kaiwa Farhan lefe, ba kayan Sunusi ba Akwati biyu har da hodar nan irinsu Aisha tsamiya a ciki. Nana bata dawo ba se satin biki, shima Mother ce tai waya tace Lallai ta dawo. Mutane nata surutun Faruk ko Auren fari be ba, amma an bar Sadik se Aure aure yake. Nana kawai yaƙe take, amma ƙasan zuciyarta daurewa kawai take, ana gobe za'a fara biki Sadik ya tarar da Nana a ɗakin Mother, fatar jikinta har wani sheƙi take, gashin kanta an gyara shi an masa ƙananan kitso, ta sha lalle ja da baƙi, tai shar Kamar ba ita ba se ƙamshi take. "Madam ina Mother?" Ba tare da ta kalleshi ba tace "tana gurin Abba" "Sahal fa?" "Yana gurin babansa" Sadik yace "wane baban nasa?" "To shi da yake da iyaye da yawa, yana gurin Uncle Faruk" Sadik ya ƙara so kusa da ita ya zauna yace "You look young and beautiful, kamar in sace ki in gudu, dan Allah Nana ki dawo part ɗinmu mu kwana tare" "Kana ganin gidan cike da mutane, Mother faɗa za tai min" "Allah ba abunda za tace miki, Please Besty" Kasa jurewa tai ta fara kuka, kuka sosai da hawaye saboda abun ya motsa. "Besty kuka kuma? Na miki laifi amma kamar yadda na gaya miki Ina sonki Husna, ba zan taɓa wulaƙanta ki dan na Auri Farhan ba, dan Allah ki dena kukan nan se in zaci wani abun daban" ya rungumeta yana share mata hawaye tare da kwantar mata da hankali. "Kina buƙatar wani abu ne?" Nana ta girgiza masa kai. "Dan Allah ki min alfarma ki dena wannan kukan" "In ban kukan ba wani abu ne yake tsayamin a wuyana yaƙi tafiya" Sadik yace "Yasalam, na san ba daɗi amma ki dena dan Allah". "To zan dena insha Allah" Ya ɗanyi ƙasa da murya yace "to yaya, zaki rakani BQ ɗin?" "Mother za tai min faɗa Wallahi" "To shikenan, kayan da Abba ya sai miki sunyi kyau sosai, bari in nuna miki" "A'a ka bari in muka tare na gani" "To shikenan, dan Allah Besty ki tayani basu haƙuri nasan suna fushi da ni, naga yanzu kece 'yar gaban goshi" Nana tace "to ai Inna tace ze wuce, na gayamata ta yiwa Abba Magana ma" "Akan suna fushi da ni ko?" Ta jinjina masa kai. Yace "Allah Sarki Besty na, You will remain my Besty forever inshallah, i will not fail you" yai maganar yana shafa hannunta. Maganar Mother ya jiyo, hakan yasa Sadik cikin azama ya tashi, Mother ta shigo tana masa kallon tuhuma. "Dan ubanka me kai mata?" Sadik yace "Wallahi Mother ban mata komai ba". "Ƙarya kake yi, me yai miki?" Nana tace "bakomai" "To fita ka bar min ɗaki" Bayan fitar Sadik Mother tace "idan kika kuskura kika yadda da shi, kan ku tare a gidanku ni da kene, ba ya zo yana kashe miki murya ba" Nana tai shiru cike da jin nauyin Mother.   Littafin kuɗi ne, ku tuntuɓi wannan lambar dan samun naku akan kuɗi ₦300 kacal 07063065680 Farhan jin abubuwan take tamkar a mafarki, wai ita ke shirin Auren Sadik abun Kamar almara. Dangin Babar Umma se cewa suke Allah ya musanya mata me arziki, akan kayan tsiyar da Sunusi ya kawo mata. A wannan karon Umma anyi abun arziki, dan cikin tsananin kunya, ta sa aka samo mata wata da take gyarawa Farhan jiki, a wannan karon ma ɗaya gyaran Hajiya ce ta ɗauki ragamar gyara Farhan ɗin, tai shar da ita kamar ba ita ba. Ta sha gyaran gashi da ƙunshi, sedai haryanzu Farhan gani take kamar a mafarki, wai zata auri Sadik, sedai ta kasa farinciki, musamman idan ta tuna irin ɗawainiyar da Abbas yai da ita, kuma ga mahaifiyarsa tana ta cigaba da yi mata ƙoƙari. Sadik na zaune ya shiga social media, ya ga hotunansa nata trending, wai ɗan Auta  gidan Alhaji Abdullahi Rano, ze auri mata ta biyu yana da shekaru Ashirin a duniya, nan ya dinga ganin Comments kala kala, wasu suna cewa iyayen da suke ba shi yaran ne mahaukata, wasu suce tunda iyayensu ɓarayin ƙasa ne, dole suyi abund suka ga dama, nan ba da daɗewa ba ze sake su a aura masa wasu, haka dai kowa da kalar abunda yake faɗa, wani na alkhairi wani na sharri, Sadik ya rufe datarsa yace "Insha Allah, Allah baze bamu kunya ba". A wannan karon ma Abbas da kansa ya kaiwa Farhan dubu hamsin, ta kasa masa godiya se kuka, kamar wadda a kaiwa mutuwa, yai ta bata haƙuri yana kwantar mata da hankali tare da yi mata Nasiha. Babban abunda yake sake faɗarwa da Farhan gaba be wuce yadda ba zata kai mutuncinta gidan Sadik ba, ta san abu ne mawuyaci duk da son da Sadik hake mata tai mutunci a idonsa, saboda budurcin mace shine 'yan cinta a gidan miji, ga shi tana da abokiyar zama, tabbas ta san akwai damuwa a wannan lamari, gaba ɗaya jikinta ya ƙara sanyi sosai da sosai. Sadik ba yadda be da Farhan ba akan ya kama mata guri, tai walima tace ba ta so, a layinsu a ka kafa runfuna aka kira malamai mata sukai lecture, akai mata kamu aka ci Abinci aka sha daidai gwargwado. Duk yadda Nana ta so dakewa kasawa take yi, dauriya kawai take tana sabgoginta, amma abun yana dukanta sosai da sosai, gashi Sadik se kujiba kujibarsa yake yi, ko ganinsa ba ta samun yi sosai, sedai ta hange shi. Faruk na zaune a falo yanawaa Sahal wasa, Khairat ta zo tana yauƙi ta ɗan kashe murya tace "Man a kawo coffee ne?" Faruk yace "No thank you" Nana da ke gefe tace "gaskiya Uncle ka yunƙura, zan tsaya maka bana son ganinka a haka ba Aure, karka fara tsufa fa" Faruk yai murmushi yace "kedai bari kawai, ni da ban wani damu in Auren nan ba, amma tun da Allah ya sa aka haifi Sahal, na samu abun wasa, naji nima ina son in auren, a haifamin abun wasa ko Abbana" yai maganar yana ɗaga Sahal sama. Nana tace "gaskiya uncle ka motsa". "To maman Sahal, amma kin san matan ne se a hankali, samun tagarin ne se a slow". Su Nana ba rufi se cewa tai, "Ba wani se a slow, ga mata a gida se ka tafi dawa, naga ga Khairat nan tana ƙwanƙwasa, dan Allah ka bada dama a wuce gurin". Shi kansa Faruk se yaji kunya, balle Khairat da Nana ta farkewa laya haka ba rufi, Khairat taji kamar ƙasa ta tsage ta nutse. Nana tace "ya naji kun wani yi shiru ne? Ko na faɗi ba daidai bane?" Faruk yace "da dai a bar wannan maganar?" Nana tace "ba za'a barta ba, ai Magana ce ta gaskiya, a gaskiya a gida a na so ba zamu bari kaje waje ka auro ba, muna da wannan zuƙeƙen saurayi haka, ace a kai waje, gaskiya a'a tunda ana so a gida, shikenan mun maka mata, zan shigar da maganar ku da zarar an gama bikin Besty" Sumsum Khairat ta miƙe, dan ba ta zata shishshigin da takewa Faruk ana ganewa ba, da sauri ta bar falon, Nana a ranta tace ina sane na faɗi haka, gurin mijina dai ba space wannan ma dan ya ƙallafa ransa ne, ni ba kishiyarki ba amma kin sani a gaba" a zahiri kuma tace. "dan Allah uncle a duba lamarin nan, save the innocent soul of your sister" Faruk yace "Maman Sahal, gaskiya a tsarina bana son Auren Yarinya, nafi son me ɗan hankali, Khairat tai min yarinta da yawa, kuma ƙanwa kawai na ɗauketa" Nana tace "haba Uncle, meye aibun Khairat ne?" Faruk yace "ba ta da kunya, ga shigar banza, ga ta da abokai maza da yawa, kowa friend ɗinta ne, yarinya ƙarama da hak ai be dace ba, and at least yakamata ace ko level 2 ta shiga kan tai Aure" Nana tace "Yanzu ni ban isheka misali ba? Ni ma lokacin da Besty ya Aureni bani da Kunya Wallahi, ka tambaye shi kaji, ni ga rashin Kunya ga ƙauyanci, duk da dai ƙauyancin nawa ba wani na azo a gani bane, amma gara Khairat tana da tsoro yin rashin Kunyar wasu lokutan, ni a lokacin bana son sa, kasan dai irin takun saƙar da muke yi da shi, amma a hankali da na fara sonsa duk na dena. Ita mace in dai tana sonka, za tai duk wani abu dan ta burgeka, kuma zaka iya saita ta yadda kake so. Auren Khairat da zakai ze iya cetota, idan ta shiga Jami'a ma ze zama tana da katangar Aure a Tare Da ita, hakan baze bari ta cigaba da kule kulen mazan da baka so ba" Faruk yai shiru, yana mamakin yadda Nanan ke tsara magana cikin hikima. Faruk kawai yai murmushi yace "Hajiya Nana kenan" Nana tace "Uncle, ka taɓa soyayya kuwa?" Murmushi yai yace "eh to, bana ce a'a ba na taɓa" "No gaskiya ba ka taɓa ba, da ka taɓa ba zaka ƙi karɓar tayin Khairat ba, baka da nauyin Soyayar kowa a kanka, zaka iya farawa da soyayyarta, dan Allah kar ka bari ta shiga hatsarin soyayya, soyayya akwai wahala musamman idan kana son maso wani" ta ƙarasa maganar tana ƙoƙarin goge hawayenta. Faruk yace "Subhanallaahi, dan Allah Nana ki dena, ko Sadik ɗin ne yake miki wani abu?" Tace "A'a, sedai na fara son Sadik a lokacin da be kamata ba, lokacin da ban san akwai wadda take ransa ba, yana da kyakywar mu'amala, kan ka zauna da shi zakaga ya fiye izza, da raina mutane, amma ba haka yake ba a zahiri, hasali kyawawan ɗabi'unsa suka sa na fara son shi, sedai na makara, ina ta ƙoƙarin danne komai ya koma bakomai ba, amma na kasa bana jin daɗin yadda nake masa, amma ba yadda zanyi ne. Ni babban damuwata shine su Mother su dena jin hausinsa, su yi masa uzuri dan so ba shi da linzami. Dan haka uncle dan Allah kar ka bari Khairat ta cutu, idan har ba wata a ranka ka amince da ita dan Allah, tana sonka sosai za tai maka biyayya insha Allah, amma ni zan haɗa lefe kuma haihuwar fari sunana za'a saka, ko na Besty" ta ƙarasa maganar tana ƙoƙarin ƙaƙalo murmushi duk da hawaye ne a fuskar ta. Wani irin tausayinta ya kama Faruk, tabbas Nana 'yar halak ce, yayi mamamki da Mother tace masa Nana ce ta saka baki, da kuma maganar Hakimi sannan suka amince, yarinyar tana da sadaukarwa, kuma dagaske take son Sadik ba wasa ba, tabbas idan Sadik ya cutar da ita dan yana son wata Allah ze saka mata. "Maman Sahal, naji dukkan maganganun ki, kuma insha Allah zan san abunda zanyi akan Khairat, and akan mijinki ki dena cewa kina son maso wani, Wallahi Nana Sadik yana sonki, so na gaske kuwa, ai kin riga kin gama da shi tunda har kika nema masa alfarmar a bashi dama yai Auren, wani babban abun burgewa da halayensa shine baya butulci Sadik, ba wai dan ɗan uwama bane no, ba goya masa baya nake ba, amma idan ki kawai Sadik alkhairi bayan shekaru yana sane a ransa, mutum ne me halacci sosai, dan haka ki sawa ranki ƙaddarar junanku ce a tare duk ku ukun, ki duba wani abu na ikon Allah, dokar gidan nan seka haɗa master's za kai Auren fari ma, amma shekarun sa sha bakwai zuwa sha takwas aka aura masa ke, kuka haifi Sahal, yanzu haka se nan da wata uku in Allah ya kaimu ze cika shekaru Ashirin dai-dai, amma kalli mata ta biyu za'a aura masa duk da tsananin zafi da Aƙida ta iyayenmu, amma wani ikon Allah, dr. Da ake cewa ya isa Aure yau kusan shekaru huɗu zuwa biyar da Aurensu ko ɓari matarsa ba ta taɓa yi ba, ni gani kalleni nima haryanzu ban Auren ba, nima idan nayi babu tabbacin in samu ƙaruwa, shine ƙaramin mu Amma Allah ku ya fara bawa ɗa, haka ya isa ya tabbatar miki da cewa rayuwa Allah shike tsarawa bawansa komai, kalli irin ƙiyayyar da Mother ta nuna miki a baya, fafur cewa tai se ta kashe Aurenku kin sani, duk da yadda yake akwai matukar shaƙuwa tsakanin Sadik da Mother, saboda yana sonki yai burus da umarnin ta be sake ki ba, saboda yana sonki, kuma da yake Allah baya ɗorawa bawansa abunda ba ze iya ba, cikin ƙanƙanin lokaci Allah ya juya komai, Yanzu Mother jinki take kamar ita ta haifeki, kalli yadda yanzu take ta nan nan da ke, dan haka ki kwantar da hankalinki, Allah yana tare da ke a Kowane hali, kuma albarkacin kin saka baki, ƙanwata ce ke da kika isa da yayanki, za duba maganganun ki akan Khairat" Nana ta ɗago tana murmushi tana share hawaye tace "Nagode uncle, naji daɗin maganganun ka, sun bani ƙarfin gwiwa, insha Allah komai ya wuce, zan daure zuciyata in dubi Ni'imomin da Allah yai min, in yaƙi sheɗan da kishi". A daidai nan Sadik ya shigo, ya tarar da Faruk da Nana a zaune, ga Nanan tana share hawaye, wani abune ya soki zuciyar sa ya tsuke fuska yace "ina son magana da ke" Faruk yace "meye haka zaka shigo ba sallama?" Nana tace "to ka gayamin a nan mana, naga Ai Yaya Faruk ne kawai a gurin". "Cewa nai ina som magana da ke" ya faɗa a kausashe. Tashi tai tabi bayan Sadik, suka shiga wani ɗaki ya kalleta yace "Me yake ce miki?" Nana tace "shi wa?" "Faruk" "Me kuwa yake cemin, hira muke yi" "Hira kukeyi shine har kike masa kuka yana rarrashinki?" Nana tace "Haba to meye a ciki, Yayans fa nima" "Yayanki me amma yana da iyaka, ni kaɗai na cancanci kiyi kuka in rarrasheki ba hurimin Faruk bane" Nana cikin mamaki tace "Abun harya kaimu ga haka? Yau na fara hira da Faruk? Kasan ma akan me muke magana? Kawai zaka fara yi min faɗa?" "Bana buƙatar jin koma menene, amma ki sani akwai iyaka tsakanin ki da shi" mamaki ne ya kama Nana, bayan ficewar Sadik, tun kan yai Auren kenan, idan yai Auren kuma wataƙila dukanta ze farayi, amma ai ba yau ta fara hira da Faruk ba, gaba ɗaya se jikinta ya sake yin sanyi sosai. Shikuwa Sadik kishi ne ya kama shi, dan Nanan ba ƙaramin kyau tai ba, gashi duk in da ta shiga ƙamshin turare take, hakan ne yasa yaji wani haushi ya tokare masa wuya da ya ganta da Faruk. Sadik ya cigaba da hada hadarsa, groups na 'yan makarantarsu ya ɗauka akan cewa Prince ze angwance da Farhan, kowa da abunda yake faɗa akan Auren nasu, wasu na son barka wasu na tofa abunda ba'a so, wasu suna ba su taɓa ganin Soyayar gaskiya ba irin wadda Sadik yakewa Farhan. Sadik reception kawai ya shirya zeyi da abokansa, idan aka dawo daga ɗaurin Aure. Sadik jinsa yake Tamkar ze sauke wani gagarumin nauyi da yake kansa, yakama gobe in Allah y kaimu ne ɗaurin Aure, se wani nishaɗi yake yi, har ze kwanta kawai ya tuna da wani hali Nana zata shiga, shifa ganinta yai kawai da Faruk suna hira yaji haushi, ita kuma ya zata ji, shi da ze tare da wata ya take ji a ranta, nan take nadamar abunda yai mata ya baibaiye shi, tashi yai ya zura rigarsa ya koma cikin gida, yana mitar da suna tare a BQ da ba wanda ya sani ze bata haƙuri, amma yanzu Mother ta hanata zuwa in da yake, wai se sun tare, haka ya tafi yana mita. Dubawa ɗakin da take kwana yai amma bata nan, ya nufi sashin Mother, da Mother ya fara haɗuwa yace "Mother dan Allah ina Besty?" Mother tace "ban sani ba" Sadik yace "Mother Magana kawai zan mata dan Allah" "Nace maka ban sani ba, ka ɓacemin daga ganina" tunani ya shiga yi ko dai ta gayawa Mother abunda yai mata ne. A lokacin ya sake jinjinawa ƙoƙarin ta, tabbas kishi babu daɗi sam, ya koma BQ ya kira layinta amma a kashe, daga ƙarshe se haƙura yai. Yau haka Sunusi ya wayi gari sukuku, kamar wanda aka yashe, ga wani irin ciwon kai da ya tashi da shi, ko sallar juma'a be samu ya halarta ba, unguwar su Farhan shiru, Kamar ba sauran mutane a unguwar, can ya fara jin hayaniya, alamar an dawo. Haladu ne ya shigo ɗakinsu yana faɗin kai Abu na Allah, Allah me ƙudira sassauya lamuransa yadda ya so. Sunusi yace "wai meyafaru ne?" Haladu yace "kan in gaya maka, duk da bani da murya bari in rera waƙar mawaƙin nan Wayeka oho dai da yake cewa "duk yawan rabo, in ba kai kar ka ɗau salon jahili, in rabo ya tsago da kai, kuma abun ya tabbata da kai, Rabbu ne yace se da kai, in seda kai kawai se da kai. in abun ya zo babu kai, Rabbu ne yace babu kai, in babu kai kawai babu duk duniya ba me sa da kai, Rayuwa wucewa take kawai, Rayuwa mubi a hankali kawai" "Wai dan Allah ka gayamin meyafaru ka tsaya a kaina, ka saki murya kamar fitar tusa kana waƙa, kamar wani maroƙi" Haladu yace "koma kamar zubar zawo ce, in dai saƙona ya fita ai shikenan, Allah ne ya nuna ƙudurarsa, yaron da kaiwa Farraƙu da Farhan, ashe shi zata Aura, an ɗaura musu Aure da sadakinsa dubu ɗari Wallahi". A zabure Sunusi ya tashi zaune yace "wannan ɗan yaron?" Haladu yace "shi fa, Allah ya nuna maka shike da komai, kai kaga tarin motoci na alfarma a unguwar nan, Allah ne yai yarinyar nan ba ta da rabon shan wahala dan dama sam baku dace ba, shiyasa tsabar taurin kanka da ƙauyanci yasa baka sameta ba. Kai kaga yadda yaron ya ɗau wanka tubarkallah, se haskawa yake kai turaren da yake tashi a jikinsa shi da 'yan uwansa yadda kasan a kamfani, kai abun arziki na masu arziki ne, na matsiyata se Innalillahi wa Innalillahi raji'un". "Dalla rufemin baki, waye matsiyacin ka bar wannan cika bakin, ka bari ka gani idan zasuyi zaman Auren cikin daɗin rai, har yau har gobe matata ce" "Matarka ta ina, ba dai jahilci ya ja maka ba? Meye aibu dan ance kai gwaji, kuma ba kama mata gida a birni, ka tsaya kana cin zarafinta, Allah ya ƙara yanzu sedai kaga wani ya mora ba dai kai, ba ɗan cicif daidai ita ga gayu kamar ita ba kai ba , da seka kwana uku baka wake baki ba" Haladu yasa Sunusi a gaba da cin mutumci, ƙarshe seda su kai faɗa baran baran uwaki ubaki, ga ciwon kai da ya addabi Sunusi. Gidansu Farhan ya kaure da hayaniya, tare da shewa ana ta rangaɗa kuɗin Sadakin Farhan, ita Farhan duk jin abun take kamar a mafarki, wai ita aka ɗaurawa Aure da Sadik, ikon Allah. Su Sadik suka shigo domin ɗaukar hotuna, Farhan ta saka farin lace me golden color, shikuma Sadii ya sanya fararen kaya, ya ɗora farar alkyabba me adon golden yayi kyau matuƙa. Fuskar Farhan ba yabo ba fallasa, kallon Sadik kawai take ji take kamar almara, amma da ta tuna Abbas gaba ɗaya se taji Auren Sadik ya fita a kanta. "You look so much beautiful, Alhamdilillah yau kin yadda son da nake miki ba RUƊIN ƘURUCIYA bane?" Wata uwar harara ta galla masa, Murmushi kawai yai be kuma cewa komai ba. Duk da Sadik yana da girman jiki, dan idan aka faɗi shekarunsa wasu har mamaki suke, amma a haka Wasu suka dinga surutun Angon Farhan ɗin yaro ne, kuma a haka yana da mata kuɗi iyayenta suka bi suka ba shi 'yar su, 'yan baƙin ciki kuma na kwanan nan ze sakota dan duk abunda a kai ba dan Allah ba baya lasting. Mother ta shiga bedroom ɗinta tarar da Nana a kwance ta zubawa guri ɗaya ido, gaba daya Mother tausayin Nana take, ta ƙarasa gaban gadon tace "ya baki tashi kinyi wanka ba? Yanzu 'yan ɗaurin Auren nan zasu dawo, su cika gidan nan ki maza ki shirya, kar a zo a ganki a yanayi na ba daɗi, ki daure bari in sa a kawo miki Abinci. Nana gaba ɗaya tun da ta fuskanci an ɗaura Auren jikinta yai sanyi ƙalau, dan tun abunda Sadik yai mata akan Faruk gaba ɗaya ta sare da lamarin. Jiki a sanyaye tai wanka, ta fito tana shafa abubuwan gyaran jikinta, me kwalliya ta shigo tai mata light makeup, ta saka wani danƙareren leshi da Mother ta sai mata, ta fito ras da ita tai kyau. Mother ta shigo tana faɗin "Masha Allah, kinyi kyau sosai, yanzu abunda nake so da ke, zamu fita falo wasu basu sanki ba, yau zasu ganki, dan Allah ki daure ranki karki bayyanar da damuwarki, ki nuna komai normal kinji ko?" Nana ta jinjina kai, Sannan tai gaba Nana na binta a baya, da yawa wasu se ranar sukaga uwar gidan Sadik, musamman matan abokan Abba, nan suka dinga yabata suna gata yarinya ƙarama kyakykyawa, lallai Sadik ya more. Nana kam a nutse take komai, bayan sun gama gaisawa ta samu guri ta kame ta cigaba da sabgoginta. 'yan ajiksu Sadik sunje reception Sosai, suna cewa sun zata gagarumin party ze shirya musu, Sadik yace "da kenan, yanzu an girma, har da ɗa, ai dole a nutsu" har da wasu daga cikin malaman makarantar sunje bikin na Sadik. Ƙarfe huɗu Mother tace azo wasu su raka Nana kan a kai amarya, Sadik ya shiga cikin hada hada sosai, ƙarfe biyar ya sauya wasu haɗaɗɗun kayan, ya shigo cikin gidan, ana ta tsokanar sa, ya wuce ɗakin Mother in da aka gama shirya Nana, yanzu wani material ne a jikinta, me wasu duwatsu kallo ɗaya Sadik yai mata yasan dauriya kawai take, tayi kyau matuƙa. Ya shiga bedroom ɗin ya kalli wasu cousins ɗinsa yace "A bamu guri zan ga matata" "Ikon Allah, lallai Sadik yanzu mu kake kora, wai kai magidanci?" "Eh ya ranku?" Suka fita suka basu guri. Se uban ƙamshi yake, ita ma Nanan haka se zuba ƙamshi take yace "Ina ɗa na?" Nana jiki a sanyaye tace "ina ga yana gurin dr. Ko Anty Jidda". "Idan ya ɓata a taro kya samo mana wani, tunda zuwa yanzu kin manta labor room" Sunkuyar da kai tai tana wasa da dogayen yatsunta. "Besty, shekaranjiya na miki laifi, Mother kuma ta hanani shigowa, kawai kishi ne ya kamani ranar a kanki, amma kiyi haƙuri dan Allah" Nana tace "ya wuce". Ya ɗago haɓarta tana kallonsa, ya haɗe bakinsa da nata, seda ya shanye jambakin bakinta tsaf, sannan ya cikata, ya saka hannu a aljihunsa ya ɗakko wata leda, ya cire mata yari da sarƙar kunnenta, ya ciro na zinare ya sakamata, saboda tunda ya fara hidimar bikin nan, ba abunda ya ɗauka ya bata. Ya kamo hannunta ya ɗaura mata abun hannu, Sannan ya saka mata zobe yace "ba zan gaji da baki haƙuri ba, Nasan ni me laifi ne a gurinki, amma dan Allah ki yi haƙuri Nana, Kamar yadda nai miki alƙawari, insha Allah zanyi iya yina gurin kamanta muku adalci, Sannan ki tayani da addu'a in cika alƙawarin da nai wa Hakimi, Besty kina da wata kima a idona da duk juyin zamani ba zan zama butulu a gareki ba, ina sonki Husna, ki sa a ranki ƙaddarar mu ce a haka" A hankali ta murza zoben hannunta tace "Nagode sosai Allah ya saka da alkhairi, Allah ya sanya alkhairi ya baku zaman lafiya" ta ƙarasa maganar hawayen da take maƙalewa suka fallasa zuciyarta. Ta kai hannu zata goge hawayen, amma Sadik ya riƙe hannun yace "Cry besty, you deserve to do so, i know is painful cry Besty, amma ki tausayamin kar hawayenki su zame min fitina a rayuwa, Allah baya son hawayen Maraya" ta ɗaga ido tana kallon Sadik da shima idanunsa suka cika da hawayen. Ta sa hannu ta goge nata hawayen tace "mayar min da jambakina da ka goge min" tai maganar cike da son basar da yanayin da suke ciki, ta ƙara da tabattar da Sadik baya son damuwarta musamman ta zubda hawaye. Yai murmushi ya ɗakko jambakin yace "wanko fuskar, sena sa miki" taje ta wanke fuskar ta dawo, ta shafa hoda ya saka mata jambakin, ya buɗe ledar da ya shigo da ita, ya ɗakko alkyabbar mata, me matuƙar kyan gaske ya saka mata, ya ɗakko mata takalminta ta saka, Sannan ya riƙo hannunta suka fito shima sanye da tasa. Suna fitowa matan ɗakin suka dinga rafsa musu guɗa, wasu na musu video ya dinga ratsawa da ita zuwa ɗakin Abba, Abba yana tare da wasu abokan nasa, Abba yai musu Nasiha da fatan alkhairi, akai ta musu Addu'a sannan suka fito. Mummyn Khairat tace "Kai Sadik kufa muke jira, zamu rakata". Sadik yace "Mummy kuje, ni zan taho da ita" Mummy tace "yau kuma Soyayar uwargida ce ta motsa" "Ai kullum soyayarta a motse take a raina" A harabar gidan se da a kaita musu hotuna, sannan ya saka Nana a mota, Faruk yace su tafi ze kawo Sahal, Sadik ya ja motar ya bar gidan. Ita kanta Nana ta yaba tsarin gidan, yayi kyau sosai da sosai, gashi ɓangaren ta ya sha furnitures Abba ya kashe mata kuɗi sosai da sosai. Ƙarfe takwas na dare sannan aka kawo Farhan, Sadik kuwa be shigo gidan ba se ƙarfe sha ɗaya na dare, kowa ya watse. Farhan jin abun take banbarakwai, wai yau itace matar Sadik, abun abun mamaki sosai. Nana kuwa tuni ta canza kaya zuwa na bacci, Sahal yayi bacci tuni, ta nemi guri ta zauna akan gadonta, ta dinga maimaita Innalillahi wa Innalillahi raji'un a cikin ranta, saboda wani abu da ya tsaya a maƙogwaronta ya ƙi wucewa. Sadik yai sallama a bedroom ɗinta, ds ƙyar ta iya amsa masa, ya zauna tare da ajiye mata leda manya guda biyu. Zeyi magana ta ɗora hannunta akan laɓaɓanta tace "Shhh, seda safe Allah ya bamu alkhairi" fafur ta hana shi Magana, haka ya tashi ya ƙyaleta. Sashin Farhan ya nufa da sauran ledojin, yana yiwa Allah godiya yau Allah ya tabattar masa da mafarkinsa na mallakar Farhan, lallai soyayyar su bata tsaya a iya RUƊIN ƘURUCIYA ba, yana fatan Allah yasa Auren Farhan da yai ya zama kankarar laifin da ya aikata a baya. Da sallama ya shiga bedroom ɗin Farhan, ta takure guri ɗaya da alama sanyin AC yai mata yawa. Ya rage AC Sannan yaje kusa da ita ya zauna, amma Farhan ta matsa. Sadik yace "Ikon Allah, yau kuma ni kike gudu?" Shiru tai ba tace komai ba. Ya cire rigar jikinsa ya bar shirt da wandon yadinsa, yace "yo alwala ki zo muyi salla" "Bana salla?" Ta gaya masa kanta tsaye, cikin ko in kula yace "ok fine" dan ya lura haryanzu Farhan a ƙule take da shi. Yaje yai alwalarsa yazo ya gabatar da nafila raka'a biyu, ya ɗakko plate ya juye kazar a kai, ya zauna a kusa da ita tare da yaye mayafin lafayar jikinta amma ta ƙanƙame jikinta. Shi Sadik dariya ma ta bashi, yace "Bismillah, muci Abinci" "Naci tuwo a gida, na ƙoshi". "Tuwo daban kaza daban, kici" "Ni na ƙoshi" tai maganar tana zumɓura baki. Be kuma ce mata komai ba, yaci nasa ya rufe sauran, se ƙare mata kallo yake kasancewar ta sha ado da gyara, kuma ta Sunkuyar da kanta. Da Sadik ya matsa in da take, se ta matsa yai murmushi yace "wani darene jemage be gani ba amaryar? Dama kin dena wannan abun, Sadik ɗin ne dai ba wani ba, kuma Farhan ɗince dai ba wata ba, ki bari mu ɗora a in da muka tsaya mana" yai maganar yana kashe mata ido. Wata nadama ce ta sake kama Farhan, duk da Sadik ya Aureta amma ta tafka kuskuren biye masa da ta dinga yi a baya. Be kuma kulata ba yaje ya kashe fitilar ɗakin,yana ta hamdala a zuciyarsa, ganin yai kwanciyar sa yasa ita ma ta ɗosana ta kwanta, dan a gajiye take matuƙa, ta shiga tunane tunane daban daban a cikin zuciyarta har bacci yai awon gaba da ita. Seda ya tabbatar tayi bacci, sannan ya tashi zaune, ya kwance lafayar jikinta tsaf, skirt ne a jikinta da shirt, ya kunna fitilar wayarsa, ya haskata wata irin soyayyarta da ƙaunarta suna fuzgarshi, ji yake kamar ya maida ita cikinsa saboda so da ƙauna, bacci take sosai har da ajiyar zuciya saboda gajiya. Ya kashe fitilar, ya matsa kusa da ita ya rungumota jikinsa, yana shaƙar ƙamshin turaren da ke ta shi a jikinta, fatarta tayi wani irin santsi da laushi. Murmushi yai ta ƙara girma sosai, saɓanin lokacin da ya tafi ya barta. Sosai Sadik yake jin yadda yai missing ɗinta, farkawa tai daga nannauyan baccin da ya ɗauke ta, ture Sadik ta fara ƙoƙarin yi. Murya can ƙasa yace "meyasa ki kai min ƙarya?" "Ƙaryar me nai maka?" Tai maganar kamar za tai kuka. "Au baki san ƙaryar da ki kai bama ko? To bari in gama fanshe soyayyata da wahal da ni da kika dinga yi, se ki gane ƙaryar da ki kai min" "Dan Allah Sadik ka rabu dani, ni gaba ɗaya haushinka nake ji, dan Allah ka ƙyaleni". "Umm, Umm I don't care Baby". Littafin kuɗi ne, ku tuntuɓi wannan lambar dan samun naku akan kuɗi ₦300 kacal 07063065680 Sosai take ture Sadik da iya ƙarfinta, tana kai masa duka, cikata yai tare da ɗagota tana kallonta, se sauke numfashi take kamar tayi gudu me nisa. "Farhan me kike nufi ne?" "Nace maka ka ƙyaleni". "Saboda me zan ƙyaleki?" "Ni bana sonka, bana ƙaunarka yaudarata kake yi ka ƙyaleni". Tai maganar gabanta na tsananta faɗuwa. Sadik yai ajiyar zuciya yace "Me zanyi wanda ze sa ki yarda dani ne Farhan? Sadik ne fa" "Ni ka ƙyaleni dan Allah" "Why?" Yai maganar yana cigaba da abunda yake. "Stop it please, am not in mood". Wata miskilar dariya yai iya maƙogwaronsa yace "I know how to turn you on, ko kin manta Prince ne?" "Sadik am on my period, i told you earlier" "Meyasa ba kya jin kunyata yanzu ne? Kike min ƙarya yadda kike so". "Ni ba ƙarya nake ba, ka ƙyaleni nace" Tana ji tana gani, Sadik yai burus da ita, dama ba wani fashin salla da take, ta gaya masa ne da biyu, na farko tana cikin fargabar abunda ka iya komowa saboda rashin kai budurcinta, abu na biyu kuma haryanzu tana jin haushin Sadik, ga wani irin tsoro da ya baibayeta. Hankali kwance Sadik yai abunda Allah ya nufe shi da yi, musamman da burinsa ya daɗe yana fata ya cika, mafarkinsa ya zama gaskiya yau ya kasance da yarinyar da ya fara so a rayuwarsa. Farhan kuwa ta gigita da lamarin, dan ta Sha jini jikinta, ba ta zaci lamarin ya kai haka ba, kukan ma Muryar ta ƙasa ƙasa ta dinga fita, dan Sadik ya bata mamaki ƙwarai. Fuskarsa ya ɗora akan tata, yana son yai mata Magana, amma ya kasa se sauke mata numfashi da yake a fuska. Janye ta ta fuskar take ƙoƙarin yi, a hankali yace "Indeed, you are good girl, a promise keeper, Princess your crown will never fall, you will forever remain in the throne, you will remain the queen of my Emirate, inshallah i love You fisabilillah Farhan" Ita Farhan gaba ɗaya ta kanta take, dan haka ba gane kan wannan surutun nasa take ba. Sadik ne ya fara tashi, yaje yai wanka ya dawo ya taimaka mata, duk yadda ya so tai magana ba ta kula shi ba, tai masa shiru ta ƙi Magana, sedai babban abunda take tunanin shine, Babba yace sun mata fyaɗe su huɗu, amma ta ji ta garau Ranar, to ya akai taji banbanci sosai haka yau? Ba tace komai ba dai amma se tunanin abun take. Sadik ya ƙanƙame Farhan, kamar yau ya fara sonta, duk wani shakku da yake ya kau, jinta yake wata ta musamman a zuciyarsa. First night ɗinsa ya tuna da Besty, cike da shiririta da daru a gurin Nana, murmushi ya saki, dan Nana rigimamiya ce lambar farko. Da Asuba seda Suka makara, dan haka a gida yai salla ya koma bacci, Farhan kam sanyi take ji sosai, jikinta ya ɗau zafi Sadik ya dinga jera mata sannu, daga nan suka koma bacci. Se bayan tara Sannan Sadik ya tashi, Farhan kam ko ƙwaƙwƙwaran mosti ba ta yi, baccinta kawai take yi. Be tashe ta ba yai wanka, ya kintsa cikin ƙananan kaya, ya kalli wayoyinsa dake kashe, ya ɗauka ya zuba a aljihunsa, sannan ya fita kai tsaye part ɗin Nana ya shiga. Ba ta bedroom ɗin, ya zauna yana jiranta, wani dadaɗan ƙamshin humra ne ya daki hancinsa, Nana ce sanye da wasu English wears masu matuƙar kyau da duka amshi jikinta sosai, ta shigo hannunta riƙe da kofi, sedai kallo ɗaya za kai mata ka san ba tai bacci ba, idanunta duk sunyi wani iri. Zuba mata idanunsa yai, har ta ƙaraso ta zauna tace "Ina kwana?" Be amsa ba se kallonta kawai da yake, yai ajiyar zuciya yace "kin tashi lafiya?" Tace "Lafiya ƙalau" "Kin karya ne?" Nana tace "Eh" "Me kika ci" Tace "Abinci mana" "A ina kika samu Abincin?" "Na sha cornflakes, ga Abinci can an kawo daga gida" "Besty meyasa ba kya tausayin kanki ne? Shayarwa fa kike ya za'ai wani cornflakes ya riƙe ki? " "To ai ya fara cin abinci, ni Abincin ne baya kaina" Be ce mata komai ba yaje kitchen, ya tarar da Manyan warmers, kunun gyaɗa a teaflask, se soyayyan dankali da ƙwai a flask ɗaya. Ya zubo dai-dai cikin Nana, ya koma ɗakinta, ya sata a gaba ya takura mata, ya dinga bata a baki da kansa, cikin kulawa Kamar ba wanda yake da sabuwar Amarya ba, se da ya tabattar ta ƙoshi sannan yace "Yawwa yanzu Sahal ze samu Abinci sosai shima, ki dena min wasa da cikinku in ba baka ba za muyi faɗa, wai ina Sahal ɗin ma yake?" "Da aka kawo Abinci, Mother ta saka aka tafi da shi" "Kai Mother dai na fuskanci so take mu bar mata ɗan nan, kuma ba wanda zan iya bawa, bari ajima inje in ɗakko shi" Nana tace "to in dai kaje ni dai ba ruwana, bance a ɗakko shi ba" Bece komai ba ya miƙe ya fita, sashin Farhan ya koma, ya tarar ta tashi har tai wanka ta canza bedsheet, ta zauna tana shafa mai a jikinta, sam ba ta san yana nan be fita ba, da Abincin da aka kawo ya shigo, yace "Princess, barka da safiya" Kamar ba ta ji ba tai masa shiru, ya ƙara so gaban mirror yace "kina jina fa, amma ki kai min shiru, kawo in tayaki shafa man" "A'a Nagode, tai maganar tana karɓe robar man, ta gama shafa manta ta ɗau kayan sawarta ta shige toilet, shi dariya ma ta ba shi. Ta fito cikin riga da skirt na atamfa, se kare jikinta take saboda yadda kayan suka matsteta, aikuwa ya zuba mata kyawawan idanunsa, se wani haɗe rai take wai ita a dole dole a kai mata ta Aureshi ta dena son sa. "In kin gama ɓoye ɓoyen, seki zo mu karya" "Ka ci naka, in ka fita naci nawa" ta bashi amsa. Sadik yace "Ina zan fita in je, ina da zankaɗeɗiyar Amarya a ɗaki, ba in da zani muna tare tip da tire, soyayya zamu sha". "Se dai ka sha da matarka ba ni ba, ita ke sonka se kuyi ba dani ba" "To ke yanzu ina ruwanki da mata ta? Kuma kema ai mata ta ce" neman guri tai ta kwanta, ta share Sadik. Tana kwanciya Sadik be jira komai ba, shima ya bi bayanta kan gadon yace "Ai ta kwana gidan Sauƙi Beb, na gane abunda kike nufi" Wani uban tsalle tai ta sakko tana haki, yai dariya yace "kin raina ni Farhan, hmm to ko ki zauna ko kuma ni in zo in sameki" Haka Farhan ta zauna, Sadik ya dinga bata Abincin nan da kansa, tana karɓa idonta har da guntun hawaye. Sha biyun rana ƙannnen babar su Farhan da wasu 'yan uwansu suka zo gidan, bayan sun gaisa da Sadik ya fita ya bar gidan. Suka kawowa Farhan miya da akai mata, ta sha nama, ga Nono kaya guda da suka kawo mata, da su kayan daddawa da kaɗin miya, Adda Hafsa tace "Ina abokiyar zaman naki ne mu gaisa, mu yau zamu koma" Farhan tace "nima ban san in da take ba" "Kamar yaya baki san in da take ba?" Farhan tace "to ai ni tunda na zo ban ganta ba" "To shi mijin naki be haɗaku ya muku nasiha ba" Farhan ta jinjina kai, Adda Hafsa tace "dama abunka ds harkar yara, gayyar shirirta wataƙila ma be san anayi ba" Bayan azahar sukace zasu tafi, sukaiwa Farhan sallama tare da yi mata nasiha sosai, sukai mata sallama suka tafi. Daga Nana har Farhan ba wadda ta kuma fitowa, balle wata taga wata. Se magariba Sadik ya dawo, a zatonsa suna ta yin baƙi ne, part ɗin Nana ya fara zuwa, hannunsa ɗauke da Sahal, ya ajiye Sahal sannan yace "Besty, zamuyi dinner a falo tare gaba ɗayanmu, zan gabatar muku da juna". Idan Sadik ya gani daidai wani mugun kallo Nana ta watsa masa, ji tai kamar tace ba zata fito ba, amma tai shiru bata faɗa ba. Itama Farhan da ya je gurinta, haka su kaita artabu da ita, tsiwa kala kala, wadda be taɓa saninta da ita ba. Bayan sallar isha'i yace mata "muje falo, zaki gaida uwargida na" Yamutse fuska tai, ba tare da tace komai ba, ji yai kamar yai dariya, amma ya haɗiye, suka fito ƙaton falon tare, Sadik ya nufi sashin Nana, yana Addu'a, dan mutuniyar ba sauƙi hukuma ce se da rarrashi. "Sarautar mata, ke muke jira fa" Tace "Me za'ayi?" "Kin manta maganar da mukai ne?" "Dan Allah ni ka ƙyaleni, ba se naje ba" Sadik yace "karki ɓatamin rai Please, tashi muje" ya ƙarasa maganar yana saɓa Sahal a kafaɗarsa yai waje. Nana ta wani sake karkace ɗaurin kallabinta, sannan ta biyo bayan Sadik. Farhan na ganin Sahal ta fara murmushi, yaro tubarkallah lafiyayye, kai da ganinsa ka san akwai kulawa, ƙato da shi, fari tas me yawan suma a ka baƙi ƙirin, ko ya ya yamutsa fuskarsa se dimples ɗinsa sun lotsa, Sahal kyakykyawa ne yaron sosai. Sadik na ƙarasowa Farhan ta miƙe tana murmushi, tana son ta karɓi Sahal, Sadik yace "mara kunya, kince ba kya so na, amma kina wa ɗana dariya zaki ɗauke shi, to ba zan bayar ba nima" Saroro tai tana kallon Sadik, tace "dan Allah ka bani shi" "Ba zan bayar ba, ba kya sona kike son ɗana?" Nana ce ta fito ta same su, sedai tana fitowa suka haɗa ido da Farhan, sunawa juna kallon sani, a take gabansu ya faɗi, kowacce tana ganin anya 'yar uwatta ba ta fita komai ba. Nana ta fara janye idonta, ta samu guri ta zauna, ta maida idonta kallon wani gurin, tana kaɗa ƙafafunta. Sadik yace "bari mu fara da Addu'a, Besty yi mana addu'a" Nana tace "ai kai yakamata kayi" Be kuma tanka mata ba kar suyi faɗa, yai addu'a sannan ya fara bayani. "To Dukkan yabo da godiya sun tabatta ga ubangijin talikai, buwayi gagara misali, wanda ya haɗa dukkanin mu ƙarƙashin inuwa ɗaya ta Aure. Dukkanin ku ina alfahari da kasancewar ku a ƙarƙashina matsayin matana, wadda kowacce dan ina sonta ne nake tare da ita, babban fatana da roƙona a gareku be wuce dan Allah ku haɗa kanku ba, kar a samu wata ɓaraka da wani daga waje ze shigo ciki ba. Ku haɗa kanku ku bani damar in muku adalci, Nana ke ce Uwargida amma Farhan gaba take da ke, amma matsayinki na uwargida yana nan baze canza ba, Farhan kece ƙarama amma gaba kike da Nana, a bata girmanta a matsayin ta na uwargida na Please, Besty ga amanar Princess ɗina, Princess ga amanar Besty na nan, dan Allah ku haɗa kai ku zauna lafiya" har ya gama ɓaɓatunsa ba wadda ta tanka masa, dan Nana ma kashingiɗa tai akan kujerar tana shilla ƙafarta a hankali, rabin hankalinta akansa rabi akan tunani. "Bestyna, ko kina da abinda zaki tofa?" Ta girgiza masa kai alamar a'a. "Magana fa nake, nace ko kina da Magana?" "Babu"ta faɗa a taƙaice. Ya kalli Farhan yace "Princess ke fa, do you have anything to say?" "Babu" itama ta bashi amsa. Sadik yace "Madalla, ga Abinci nan ku sakko muci Abinci". Nana tace "Nikam na ƙoshi, a ci lafiya" Sadik yace "meyasa?" "Ka san bana cin abincin dare, saboda ban son in ƙiba". Farhan wani dumm taji, tana tunanin ko dai magana Nana ta faɗa mata, dan ita 'yar duma duma ce. Sadik be sam wani Nana ba ta cin abincin dare ba, tsabar kishi ne da iskanci kawai. Be kulata ba, yace Farhan ta zo taci, ba ta wani ci ba, ta koma gefe tana kallon Sahal da Sadik ya kwantar da shi yana bacci. Seda suka gama, Sadik yace "bari in kai mata Sahal, ina dawowa. Yaje ya iske Nana har tai shirin bacci, ya ƙare mata kallo, Sannan yace "Haba Nana, Yakamata fa ki kula, kar kishi ya sa ki abunda zaki zubar da kimarki a gurin ta da wuri, she's very kind and simple, meye abun cewa wai ba zaki ci Abincin dare ba dan kar ki ƙiba?" Saboda cusa haushi, setai kamar ma ba ta san da ita yake ba Fizgota yai tana fuskantar sa yace 'ba da ke nake magana bane? Wai yaushe kika zama haka ne? Shikenan ban isa in magana ba se ki rainamin hankali, kina ji ina miki Magana, se lalaɓaki nake amma kina buntsurewa ya kike so in yi da raina Nana? Da me zanji? Fushin su Mother ko kuma abunda kike min?" Kuka ta fara yi masa, abunda Sadik ya tsana, kuma sanin baya son kukan yasa daga taji ya matsata se ta fara kuka. "Me nai miki kuma kike min kuka?" Yai maganar a sanyaye. "Ba kaine kake min faɗa ba" "Haba Besty idan banyi faɗa ba ya zan miki? Duk kin bi kin ɗagan hankali na kasa samun nutsuwa saboda halinki" "To ni me nayi?" Tai maganar cikin sigar shagwaɓa, jikin Sadik yai sanyi ya fara bin bakinta da kallo, se tura shi take tana kuka. "Allah ya shiryeki, da rikicin gangan" "Ni ka cikani bacci nake ji" "To Allah ya bamu alkhairi, kwanta in lulluɓeku" Ta kwanta ya ja musu bargo, sannan ya kashe musu fitila ya tafi sashin Farhan. Farhan har ta ƙule, daga zuwa kai Sahal, yaje yai zamansa aikuwa taji haushi, ta nemi guri ta kwanta. Yana zuwa ɗakinta ya ga ranta a haɗe har ta kwanta, bece mata komai ba kuma be ƙudurci yai mata wani abu ba ya ƙyaleta, saboda ya ga yadda ta haɗe rai. Khairat ta fito daga ita se rigar bacci, kanta ko ɗan kwali babu, zata fita babban falo neman aunda zata ci, tai kiciɓis da Faruk yana shigowa, wata kunyarsa cea kamata, dan tun lokacin da Nana tai wanan Maganar take jin kunyarsa. "Ina zuwa?" Ya tambayeta yana kallonta. "Kitchen zani, ina jin yunwa ne" Yai gaba yace "follow me" ba musu tabi bayansa, be tsaya da ita a ko ina ba, se a gaban mudubi, yace "look at you, kalli rigar jikink kaki babu ɗan kwali, kuma kin san haryanzu da sauran mutane a gidan nan, amma zaki fita a haka, am very jealous, idan har kina sona dagaske kina son mu shirya, to gaskiya ki dena yawo a haka" Kunya ce ta kamata kamar ta nutse ta sunkuyar da kai, tun da Nana tai masa magana akan Khairat, ya fara jinta a ransa, kuma yana tausayin yadda take son sa. "Oya, aje a canza kayan nan maza". Tace "to". Sunusi yana kwace yana fama da kansa, Wani irin matsanancin ciwon ka ne yake damunsa, ya sha magani amma abu kamar turi, baya jin magani, yana kwance a ɗaki ya ga wata inuwa tana shawagi a kansa, ya waiwaya amma be ga komai ba, ya yunƙura ya tashi yana waige waige amma ba kowa, ya koma ya kwanta, amma ya kuma ganin inuwar yana ɗaga kai, yaga Farhan a kansa hannunta riƙe da wata bulala, jikinta duk a ƙoƙƙone. "Ke Farhan meye haka? Meye ya ƙonaki haka?" Ba tai Magana ba ta shiga zuba masa bulalar hannunta, nan ya dinga kurma ihu kamar wanda ake cirewa ido. Haladu ne ya shigo a gigice yana faɗin "lafiya, menene ya faru?" Sunusi yace "ita ce, dukana take" "Ita wa?x "Farhan ce take dukana da bulala" Haladu yace "wace irin Farhan kuma?" Sunusi yace "Wallahi yanzun nan ta bar ɗakin nan" yai maganar cikin ƙaraji. Da ƙyar Haladu yai tai masa Addu'a, da tunanin ko gamo Sunusi yai. Duk yadda Sadik yake tunanin lamrin ya wuce tunainsa, dan sosai Farhan ke gudunsa, take nuna masa ba ta sonsa, ita Abbas take so amma ya Aureta, se fama yake da ita, amma babu alamar zata sassauta masa, abun ya bawa Sadik mamaki sosai, Nana kuma tai watsi da su, kamar ba suyi existing ba, idan ya zo in da take shikenan, in be zo ba ba ta damu ba, makarantar ta take tafiya, in aka taso ta tafi gidan Mother ba zata dawo ba se dare. Ranar da Sadik ze bar ɗakin Farhan, ya ɗaukesu zuwa gidansu, dan su gaida Mother, Nana tana zuwa ta shige bayan mota, ba tare da ta saurare su ba, Farhan ta miƙ hannu ta ɗau Sahal, amma ya dinga ihu ya ƙi yarda, Saboda akwai shi da ƙyuya. Farhan tai mamakin ganin Nana ta kame a bayan mota, ta basar da su, dan ta Farhan ba ta son Irin wannan zaman da suke da Nana, duk da ita ma Farhan ba me son mutane bace, amma yadda suk zaman kowa da halinsa, ba ta jin daɗin hakan sam. Ko da suka je gida, suna zuwa sabo direba yai murmushi yana kallon Farhan yace "Allah yayi, Amaryar Sadik Allah ya amsa wannan soyayya" Farhan ta sunkuyar da kai cikin jin kunya, tana gaida Sabo. A falo suka haɗu da Abba yana shirin fita, Nana ce ta fara gaisheshi ya amsa cike da kulawa yana cewa ina abokin nasa wato Sahal. Sega Sadik sun shigo tare da Farhan da Sahal, suka gaida Abba ya amsa ba yabo ba fallasa, yai musu sallama saboda yana sauri ze shiga taro, sedai Abba ya dinga tantamar abunda aka faɗa akan Farhan, saboda a nutse take sosai ba alamar rashin ji a tare da ita. Mother ce ta fito, ba tare da tasan su Sadik sun zo ba, Nana ta fara gani tsce "ke kuma daga ina haka?" Tana rufe baki ta ga Sadik tare da Farhan. Turus tai tana bin Farhan da kallo, cikin ladabi Farhan ta gaida Mother, guntun tsaki Mother tai ta cigaba da maganarta. Se Nana taji ba taji daɗi ba, saboda ta san raɗaɗin irin wannan abun, Sadik yace "Mother ga Farhan na kawo miki" Mother tace "naganta ai, se a kai yaya?" "Ai naga ta gaisheki ba ki amsa ba". "To in amsa ince mata me? Ba dai Aurene ka dage ka je ka Aureta ba, to ga ka nan gata ai, dama na gaya maka ba ruwana da Aurenka ba hannuna a cikin wannan Auren, dan haka kar ka ƙara kawomin ita wai ka kawota gurina bana buƙata" Dam dam! Gaban Farhan ya faɗi, kenan iyayen Sadik ba sa so amma ya Aureta. Nana tace "Mother, ai aikin gama ya gama, abu ka ya faru ake ƙinsa, amma ya riga ya faru dan Allah kiyi haƙuri komai ya wu.... "Dalla rufemin baki mara zuciya kawai, ke har abada Mijinki baya laifi komai yai daidai ne, amma hakan be hana yai miki kishiya ba ai, sakarya" Nana ta ja bakinta ta tsuke, Farhan kuwa se murza yatsunta take, amma hawaye ne ya cika mata ido fal, Yanzu da Abbas ta Aura da shikenan ba ruwanta da wannan tashin hankali. Haka suka wuni a gidan nan, babu daɗi sam dan Farhan tai dana sanin zuwa gidan nan, dan ta sha miyagun maganganu a gurin Mother, maganganu na muzantawa, ba tare da la'akari da koma menene ɗanta ne sila ba. Se bayan sallar isha'i sannan suka koma gida, ko Abincin gidan Mother Farhan ba ta ci ba, ita kanta Nana sam ba ta ji daɗin abunda Mother taiwa Farhan ba sam, duk da ba shiga shirgin Farhan take ba, amma Koba komai Allah ya riga ya ƙaddara Auren be kamata tai haka ba. Suna zuwa gidan Farhan ta wuce ɗakinta, ta dinga kuka kamar ranta ze fita, saboda wani irin ɗaci da zuciyarta ke mata. Sadik ya durƙusa a gabanta cikin sigar rarrashi yace "Farhan, nasan abunda mahaiiyata tai miki ba daɗi, amma dan Allah kiyi haƙuri komai ze wuce, watarana se labari". "Yanzu dan Allah kasan mahaifiyarka ba ta sona amma ka Aureni? Ba ka kyauta min ba ba kai min adalci ba, da ka barni na Auri wani daban da shikenan da duk ba haka ba, amma kana tunanin akwai lokacin da ze zo Mahaifiyarka ta canza ra'ayinta a kaina? Baka kyauta min ba tunda ka shigo rayuwata nake haɗuwa da ƙaddara kala kala, ni haɗuwata da kai ba ta haifarmin komai ba se tsananin nadama da gurɓacewar rayuwa, ina dana sanin haɗuwa da kai, bana son ko ganinka Sadik". "Farhan, kar ɓacin rai ya sa kiyi kuskure, ina son in gyara laifukana a gareki" "Ba wani abu da ze gyaru, ka tafi ka bai guri kawai, ni ko san ganinka bana yi, ka cutar dani Sadik da ba saka ba da duk wannan abubuwan ba su faru da ni ba" a sanyaye jiki ba ƙwari, Sadik ya bar ɗakin gaba ɗaya ya rasa abunyi. Ya daidaita nutsuwarsa Sannan ya nufi ɗakin Nana. Ya tarar tai shirin bacci, tana shan madara a kofi, ta kalleshi tace "ya dai ya na ganka?" Hararta yai yace "saboda kin sallamani har kin manta yau zan dawo gurinki" "Aini ban zaci zaka dawo ba, ka koma na ƙara maka wata ɗaya kyauta" Banza yaiwa Nana,yaje gaban mirror ya cire agogon hannunsa ya wuce toilet, ko da ya fito Nana har ta kwanta, bayanta shima yabi ya kwanta, ya rungumeta ta baya, gaba ɗaya ransa a cunkushe. Nana tai ajiyar zuciya tace "kamar wani abu na damunka?" "To Besty ya zanyi? Kowa ya ƙi fuskanta ta, duk yadda nake da Mother ta juyamin baya, kun ƙi yadda Auren nan nawa ƙaddara ce, rabona da ke a shimfiɗa ta watanni uku da wani abu, amma yau in dawo gareki kice wai kin ban wata ɗaya, ya kuke so inyi ne? Da wace kalma zan miki amfani wadda zata tabattar miki da ina sonki?" Ya ƙarasa Maganar cikin tsantsar damuwa. Nana ta juyo tare da fuskantar Sadik sosai tace "Besty ya zanyi, ka auri wadda kake so dole in ja jikina, kar in fiye maka shishshigi, amma ni kaina bana son abunda Mother tai, amma nasan lokaci ne, tunda Mother ta ƙaunace ni, to tabbas ita ma watarana zata so ta". "To amma meyasa kuke zama kamar na gaba, ina kallo fa wataran se tai miki Magana ki shareta, bana jin daɗi, kin san in ita ce ba zan taɓa bari ta wulaƙanta ki ba, ke meyasa kike mata haka?" "Saboda ina so da kishin mijina, ins ganin ta rage min wani jin daɗi na rayuwata, amma ina tausar zuciyata za dena insha Allah, ba zan sake ba hakan yai maka?" Sadik ya janye jikinsa daga nata yace "Ni rabu dani, idan na mutu ai duk kun huta" Ta rungumo shi tace "haba Besty, am sorry ba zamu so ka mutu ka barmu ba, dan Allah kayi haƙuri Bestyna, i miss You sosai" Yace "serious?" Ta jinjina masa kai alamar eh, murmushi yai ya sake rungumeta a jikinsa, daga nan suka sha soyayyarsu, hakan ya ragewa Sadik damuwar da yake ciki, dan da gaske yai kewarta. Farhan kuwa seda ta tabattar yau ba tare zasu kwana da Sadik ba, sannan ta shiga hankalinta, wani irin kishi ya dinga damunta, tare da kewar Sadik ɗin. Da safe yau Nana tai girki, Sadik ya ƙi zuwa su gaisa da Farhan, ya shareta ya cigaba al'amuransa. Gaba ɗaya se abun ya dameta, ranar da ze dawo gurinta da safe, ya shigo ɗakinta amma ta ganshi da travelling bag, kallonsa tai saroro tace "ya naga haka?" "Zan tafi Zariya ne" "Zariya kuma, me za kai a Zariya?" Sadik yace "makaranta zan koma, tun kan ai bikinmu nake ƙoƙarin komawa can, Alhamdilillah na samu zan tafi" Kamar za tai kuka tace "amma meyasa ba ka gayamin ba?" "Ni da ba kya so, idan na tafi kika dena ganina maybe ki dena jin haushina" be jira me za tace ba, yai waje abunsa, binsa tai da kallo ta kasa furta komai. Can kuma seta bi bayansa da sauri, amma tana leƙawa har ya kunna mota, Nana tana tsaye da Sahal tana ɗaga masa hannu. Jiki a sanyaye ta koma ɗakinta, gaba ɗaya taji abubuwan da tai ba ta kyautawa Sadik ba sam, shiru tai ta rasa abunda yake mata daɗi, gashi sam ba ta ƙawaye ko wata wadda zasu tattauna akan matsalar tare. Nana na falo tana son ta ci Abinci, amma Sahal ya hanata, se ƙoƙarin zubar da Abincin yake, yana kai hannu cikin kwanon, Farhan ta fito daga ɗakinta, ta kalli Nana tace "barka da rana" Nana tace "yawwa barka" daga haka ta cigaba da kokawa da Sahal. Can Nana tace "Ya salam da wannan Yaron, kai ga babarka can tafi ka bani guri" tai maganar tana nuna masa Farhan, murmushi Farhan tai tana miƙawa Sahal hannu. Nana tace "maza jeka, ta kai ka gurin Besty, ko gurin Mother maza tafi,yaron tun da ya fara rarrafe ya hana mutane sukuni". Farhan ta ƙaraso ta ɗauki Sahal, sedai a wannan karon be mata kuka ba, se leƙa fuskarta da yake yi, a taƙaice dai a ranar saboda Sahal su Nana suka ɗanyi magana ranar. Ranar da Nana zata Makaranta, Farhan tace ta bar mata Sahal. Nana tace "a'a fa, ze wahalar da ke baya zama guri ɗaya, ga kukan banza da ci, Mother ce take iya masa" Farhan tace "bakomai zan iya kula da shi" Nana ta tafi makaranta ta bar mata Sahal. Nana taje ta dawo, ta tarar da Sahal tsaf da shi. Farhan duk kiran da za taiwa Sadik baya ɗauka, Haka zalika in tai masa message baya replying, gaba ɗaya abun duniya ya dameta. Ranar da ta cika wata ɗaya cif,ta shirya taje gida, ta turawa Sadik saƙon zata gida, wuni tai a gida, Umma taji daɗin ganin Farhan, tai kyau tai ƙalau da ita, abun mamaki Umman Farhan har da sakin jiki suyi hira sosai. Se da Farhan tai sallar magariba Sannan ta shirya tafiya gida, ta kusa ƙarshen layinsu ta haɗu da Haladu, Kamar ta wuce amma Haladu yai mata magana, ta tsaya suka gaisa da Haladu, Haladu yace "Farhan, ina miki murnar Aure da ki kai, naji daɗi da Allah yasa shi Sadik dai shi ya Aureki, amma bari in gaya miki wani abu da baki sani ba, Sunusi shine yai miki Asiri da shi Sadik ɗin, ya manta da ke a rayuwarsa gaba ɗaya da duk wani abu da ya shafeki, kuma ya haɗaku da wata aljana wadda ta dinga ingizaki kina abunda kike, So yai ki zama mutuniyar banza abar ƙyama a cikin mutane, amma Aljanar ta gaza tasiri sosai a tare da ke, se akan Sadik shima daga baya da ya ke addu'a, matarsa ta sa yana Addu'a shine Aljanar ta dinga ƙonewa, wannan aljana ce ta dinga assasa miki ɓacin rai,ke kuma seki kasa jurewa se kinyi shaye shaye, yanzu haka duk ta ƙoƙƙone, ta fara zuwar wa Sunusi a siffarki tana nema ta haukata shi, duk da nima na bada gudummawar ɓata Asirin da yai miki, dan Allah Farhan ki yafe masa, ya cutar da ke iya cutarwa, musamman mijinki da be ji ba be gani ba, Amma dan Allah kiyi haƙuri ki yafe masa" Kan ya gama gayamata, jikin Farhan tuni ya hau rawa cikin kuka tace "in yafe masa kace? Bakomai ni ba zan masa Allah ya isa ba, na bar shi da Allah" Jikinta na tsuma tai gaba, tana tunanin yadda ta dinga yiwa Sadik wulaƙanci, duk son da ɗokinta da yake, se da ta tunzura shi ya watsar da ita. Ta koma gida kamar korarriya, ta dinga kuka, kamar zararriya tana Allah sarki Prince ɗina. Ko Abinci ba ta iya ci ba ranar, sallar isha'i kawai tai, ta saka kayan bacci tana shirin kwanciya, taji kamar motsi a ɗaya ɗakin nata, fita tai ta leƙa taga meye yake motsi. Sadik ta hango kwance, sanye da kayan baccinsa yana waya, ya dawo a ɗakinta ya sauka amma be nemeta ba. Da sauri ta shiga ɗakin, tana zuwa ta maƙalƙale shi ta fashe da kuka, mamakine ya kama Sadik, ya ajiye wayar yace "ya dai?" Ƙanƙame shi ta sake yi tana kuka tace "Am sorry my Prince, dan Allah ka yafemin, kayi haƙuri Please" "Me ki kai min kike bani haƙuri" "Komai ma na maka, dan Allah kayi haƙuri ka yafemin, ina sonka Prince, i still love you, am just pretending to revenge what you did to me, but am sorry I love you" Sadik yai murmushi yace "yau kuma soyayyar Sadik aka tuna? An dena fushin da ni ai kince ba kya son ganina" cikin hanzari ta haɗe bakinsa da nata ta zubar da hawaye, ƙanƙameta shima yai, wasu hawaye na zuba daga idonsa ba tare da ya san dalilin yin su ba. (🫣🫣🫣 Naga abun ya motsa, yau RUƊIN ƘURUCIYA suke ji, dan haka se anjima 🚶🚶) NA kuɗi ne ₦300 kacal. Sadik ya zame bakinsa, ya kalli Farhan yace "My love wai ya akayi ne? Duk kamar a birkice kike" "Da Allah ni dai kayi haƙuri, Wallahi haryanzu ina sonka, ɓacin rai ne duk ya sa na maka abunda nai maka" tai maganar tana hawaye tana sharewa Sadik hawayen fuskarsa. "Do you mean, you still love me?" "Yes i do My Prince" Murmushi yai yana sauke ajiyar zuciya yace "Alhamdilillah, ban taɓa zaton abubuwa za su da sauƙi haka ba, duk da ƙalubalen da muka fuskanta a rayuwa, so ya tabbatar wa da Duniya cewar,ba ruwansa da tsoho ko yaro, kowama kamawa yake yi" Tace "meyasa ka dawo baka gayamin ba?" Yace "ai kince ba kya son ganina, shiyasa bana son in kuma Abunda zan ɓata miki rai" "To kaci Abinci?" "Naci, Besty ta bani Abinci ya kika baro su Umma" "Duk suna Lafiya ƙalau, nai missing ɗinka tun da ka tafi nake tunaninka" Murmushi yai yace "Anya kinyi missing ɗina Kamar yadda nai missing ɗinki?" "Nayi mana" tai maganar cikin sigar shagwaɓa. Da haka dai yau an sha Soyayya me tsayawa a zuciya, soyayya wadda aka sha gwagwarmaya kafin a cinma nasara a cikinta. Washegari Nana har ta gama shirin ta ba su fito ba, dan haka ta shirya Sahal, ta kaiwa Mother shi daga nan ta tafi makaranta. Se wajen sha ɗaya na safe, sannan Farhan ta tashi ta sama musu abunda za su karya, bayan sun karya ɗinma tana maƙale a jikin Sadik, duk da haryanzu tana jin nauyinsa, wannan kunyar ta ta tana nan. Sadik ya shafa bayanta yace "Wai ni meye sirrin wannan soyayya da tattalin da ake tai min ne? Gaskiya naji daɗi sosai, kuma ina sae baki haƙuri akan abubuwan da suka faru". Farhan tace "ni yakamata in baka haƙuri, saboda baka da laifi, nima ɗin dan nai fushi ne cikin rashin sani, amma na sha wahala sosai da sosai, na rasaka a lokacin da nake tsananin buƙatar ka, ka ɓacewa duniyata se jin labari nai a gari wai kayi Aure, ga Auren dole da akai shirin yi min a gida, Auren ya zo be yuwu ba, ya dinga bi yana ɓatamin suna a unguwa, ga damuwa da tsananin soyayyar ka suka ƙi barina, hakan yasa na kasa jurewa, sheɗan yai tasiri a kaina, na kasa tawakalli na fara shaye shaye, katsam abokanka kuma sukai min fyaɗe, gaba ɗaya duniyar tai min zafi, na dinga attempting in kashe kaina in huta". Sadik ya nisa yace "Farhan, ban san ya akai kika bar tunanin tsawon lokaci ba, ko da wasa ban taɓa zaton zaki iya barin raina ba, ko da na minti ɗaya bane, haryanzu na kasa gano ya akai abubuwa suka faru da ni a haka?" "Prince ba laifinka bane" Nan ta bayyna masa abubuwan da Haldu ya gaya mata jiya. Jikin Sadik ya ɗau rawa, idanunsa su kai ja yace "Me mu kai masa ze mana haka? Akan wani dalilin? Kalli yadda yai silar tagayyara rayuwaki ya sa ki wahala, to Wallahi ba zan bar shi ba, sena ɗau mataki" Farhan tace "saboda me? Bayan Allah yai mana komai, duk da sharrinsa da yadda mutane suka dinga cewa Ruɗin ƙuriciya ce, yanzu dai na ga shi Allah ya ƙaddara munyi Aure ba, ka manta da shi kawai dan Allah, mu fuskanci rayuwar mu, Se dai abunda ya faru baze gogu daga rayuwata ba, haryanzu ina jin kamar ban wa Abbas adalci ba, a lokacin da kowa yake ƙyamata, a lokacin ya dinga bina yana lallaɓani yaga ya rabani da shaye shaye da bin Hotel, haryanzu ina baƙin cikin baƙin fentin da naiwa kaina, sedai a shekaruna ba kowa ze iya ɗaukar ƙaddarar da ta riskeni ba, ga fyaɗe da Babbab yai min shi da abokansa" Sadik yace "Ƙarya yake,ya faɗa ne da ya cuzguna min, ba abunda sukai miki". Tace "ya akai ka sani, bayan se da suka bani ƙwaya, suka bugar da ni ban tashi farkawa ba, se washegari". Sadik yace "baki ji banbanci ba, da waccan Ranar da Ranar da aka kawoki gidana ba, ke a tunaninki da sun miki fyaɗe su huɗu zaki iya tashi ma? Ko kin manta yadda kika dinga... Be ƙarasa ba ta toshe masa baki, hawaye na bin fuskarta a lokaci guda ga murmushi tace "tabbas, ranar ni banji komai ba, akwai banbanci amma dan Allah da gaske kake, ba suyi min komai ba?" Sadik yace "ba abunda su kai miki, ai naje na samu Mubarak ɗin, har mashayar su, nai masa duka, sedai hakan be min ba, na koma na saka 'yan sanda suka kama shi, kuma aka ritsashi aka sameshi da hodar iblis shi da Nas, na saka aka matsamin shi, dan inji da gaske ne sun miki fyaɗe a bi mana hakkinmu, amma ya tabattar da ba abunda yai miki, sun bugar da ke dan suyi miki fyaɗe, amma hijjabinki kawai ya iya cirewa, da ya tunkareki se ya ji wani irin hucin zafi yana fitowa daga jikinki, kamar ze ƙona shi, haka suka ƙyaleki a gurin ba abinda su kai miki. Kuma nima na tabattar da hakan, tsaf na sameki da mutuncinki, Allah be ɗora miki wahala ba Farhan, da har mu mutu ban san me zanwa Babba in huce ba" Ta kwantar da kanta a ƙirjin Sadik tana cigaba da hawaye, Shi kansa Sadik wani irin tausayinta ne ke ratsa shi, tabbas Farhan ta fuskanci ƙalubalen rayuwa daban daban, wanda kusan shine sila. Sadik yace "amma meyasa kike yawon Hotel?" Tace "Saboda iyayena, da 'yan uwana na shiga damuwa idan na bugu, shiyasa na zaɓi inje Hotel, in da ba wanda ze ganni in yi shaye shaye na in bugu ba wanda ya ji balle ya gani, amma nai dama sanin yadda na gurɓuta rayuwata, saboda shaye shaye sam ba mafita bane, musamman ga ni mace, duk mazan nan da suke bina, suka kashen kuɗi ne, saboda suna sa ran zan amince da su wataran, amma Wallahi ban taɓa zina ba" Sadik yace "Shhhh, ni zan bada wannan shedar, ni na fara karatun, kuma na dawo na tisa shi na wanke allon" ya ƙarasa maganar yana kashe mata ido. Wani irin sanyi ya dinga ratsa zuciyarsu lokaci ɗaya. Can ta nisa tace "Prince, wai dan Allah meye a tsakaninka da Mubarak, da yake ta ƙoƙarin ganin se yai abunda ze ɓata maka, har ya sakoni a ciki?" Sadik ya ɗanyi shiru sannan yace "Lokacin da aka kawo Mubarak Babba, yana Ss1 ina Jss3, ya zo da zafinsa makarantar, sedai ya tarar gani ƙarami sosai, amma shahararrene ni ana ji da ni, ina da ƙoƙari ina son gayu, kuma ina da sakin hannu sosai. Se ya fara cewa ina burgeshi yana son yai abota da ni, kasancewar kowa nawane ya sa ban damu ba, muka fara abota da shi, abokina ne shi sosai, sena fuskanci yana shaye shaye, nai ta masa nasiha akan ya dena yana ɓata rayuwarsa ne kawai. Kwatsam wataran ya zo min da wata mummunar magana, da ba zan taɓa mantawa ba, lokacin daga ni se shi a ajinsu, muna wata game a waya, ba kunya ba tsoron Allah ya gayamin wai sha'wata yake. Da farko ban kawo komai a raina ba, nake masa dariya se daga baya muraran ya nunan buƙatar sa, ashe riƙaƙƙen ɗan Neman maza ne, duk yana da ƙanan shekaru a lokacin, ya sanar min ba wanda ya san sirrinsa se ni, shima wani abokin babansa ne ya koya masa, kuma yake biyansa kuɗaɗe akan hakan, saboda ƙuruciya har sunan mutumin ya gayamin. Hankalina ya tashi ƙwarai da gaske, saboda mutumin babban mutum ne, ganin ba zan yadda ba yasa Mubarak Babba ya so yai amfani da ƙarfin tsiya, kasancewar ya na da girman jiki sosai, a lokacin muna amfani da ƙararrawa ne ba jiniya ba, dan haka Allah ya temake ni, na ɗau ƙararrawa na buga masa a mararsa, na bar shi a gurin. Ba wanda na gayawa, amma abun ya tsaye min, na dinga mamaki saboda ni ban taɓa sanin, namiji na ɗan uwansa namji ba, se a wannan ranar. Mubarak se da yai wata biyu baya zuwa Makaranta, wai ba shi da lafiya, ranar da ya dawo, muka haɗu ya dinga min wani irin kallo da ban gane kansa ba, kawai naji zuciyata ta kasa nustuwa ina komawa gida na gayawa Abba komai. Aikuwa daga Abba har Mother hankalinsu ya tashi sosai da sosai, Abba yace ba ze yuwu ba, ya shigar da ƙorafi gurin 'yan sanda. Babba be san waye mahaifina ba, dan haka aka kamo shi, da shi da uban gidan nasa gaba da Mahaifinsa. Seda suka kwan uku a gurin 'yan sanda Sannan Abba ya ɗauke ni muka je, aka sa na maimaita abunda ya faru, se da aka gayyato har shugaban Makarantar, Abba yace seya rufe makarantar, a kai ta bawa Abba haƙuri, da ƙyar ya haƙura a nan aka sanarwa da Abba cewa, ai dukan da nai masa a mara, baze taɓa haihuwa a rayuwarsa ba, dama duk ya gama lalata kansa, gurin aikata wannan mummunan aiki, yaro ƙarami da shi, amma yana wannan mummunan aiki, babban abunda ya ban mamaki be wuce yadda daga abokin mahaifin har mahaifin ba su damu da abunda Mubarak ɗin yai ba. Abna yace se ya ɗaure Mubarak, a kaita bawa Abba haƙuri, shine a kai min iyaka da shi, kuma aka nemi in rufa masa asiri, aka kuma ce muddin aka kuma kamashi da irin wannan laifin se an hukunta shi, akai rufa rufa aka binne case ɗin. Kinji in da gabar mu ta samo asali, yai alwashin yadda nai masa illa, shima se yai wani abu da ze min illa, ban taɓa gayawa kowa ba se ke, kuma a binciken da nai da babansa talaka ne, sanadiyyar ba da Mubarak ɗin da yai ne, ake wannan harkar da shi yai wannan arzikin. Jikin Farhan yai sanyi ƙalau, tace "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, Allah yai mana tsari da mugayen mutane, thank God da Allah ya tsaremin mijina" Sadik yace "godiya ta tabatta ga Ubangijin da ya tsaremin mata ta, ba tare da wani abu ya sameta ba" Su kai murmushi a tare, se wajen azahar sannan suka sake wanka, suka sha kwalliya, suka shiga kitchen tare, Farhan ta kalleshi tace "Prince, dan Allah ka ɗakko min Sahal mana" Sadik yace "kai gaskiya bana son motsawa daga nan zuwa can in barki" "Dan Allah ka ɗakko min shi, baka san yadda nake son yaron nan ba ne" Sadik yace "to kamar yaya kike son babansa?" Yai maganar yana saka fuskarsa a wuyanta. "Ina son babansa sosai, kuma ina son ɗana ma sosai" "Ni zakiwa wayo?" Farhan tace "dan Allah kaje ka ɗakko min shi, Kafin ka dawo na gama girkin" da ƙyar ya iya ƙyale Farhan ya tafi ɗakko Sahal. Sadik ya tarar Mother ta fita, Faruk ne yake rainon, Sadik yace "kai aka bari da rainon?" Faruk yace "to rainon Sahal ɗin har wani aikin wahala ne?" Sadik yace "lallai kam, lallai kuna son Abban nan sosai, gaskiya kaima ka yunƙura mana, mu tarawa Mother yara da yawa" Faruk yai murmushi yace "kan inyi Aure, na san amaryarka ma ta juye ita ma, ƙarami da kai se kasada". Kwashewa da dariya Sadik yai yace "kaga ni fa Sahal na zo ɗauka, Farhan ta dameni in zo in ɗakko mata shi". "To a dinga yi ana tausayawa marainiyar ƙanwarmu, naga akan wannan kake ta rawar kai". Sadik yace "wai dan Allah waye ya gaya muku bana son Nana? Wallahi ina son ta sosai, kowacce akwai mazaunin da ana ajiye ta, kowacce tana da matsayi na musamman a zuciyata" Faruk yace "hmmm Allah ya sa, ka san ni tunda Nana ta ɗarsa min son Khairat naji kamar ina sonta, na fara jinta a raina sosai" Sadik yai murmushi yace "kai amma na tayaka murna, Soyayya ai duniya ce, wanda baya Soyaya da me yake more rayuwa, inji wani mawaƙi" Haka suka taɓa hira, sannan ya ɗau Sahal ya tafi gida. A falo suka baje sukai salla suka ci Abinci, suna hira Farhan ta haɗawa Sahal madara ta na ba shi, Nana ce tai sallama a falon, Nana na shigowa Farhan tai saurin tashi daga jikin Sadik. Nana ba ta nuna taga wani abu ba, ta zauna tana cire safarta, Sadik yace "Sannu da zuwa besty, ya school ɗin?" "Alhamdilillah" shine kawai ta faɗa, ta cigaba da abunda take. Farhan tace "Sannu da zuwa" "Yawwa Sannu da gida, ɗakko Sahal ku kai kenan, Allah ya sa be takura miki ba" Farhan tace "A'a ai uwa ba ta gajiya da ɗanta". Nana tai murmushi tace "lallai kam" Sahal kuwa ƙoƙarin rarrafawa yake ya tafi gurin Nana. Nana ta miƙe tsaye tace "kai daga daowowata zaka fara wani kuka a ina ka sanni". Kuka Sahal yake, a lallai se yaje in da Nana take. "Kai lallai ma yaron nan, ga madara nan an baka ka sha ka ƙoshi, amma se ka zo ka addabamin, aikuwa ba ka isa ba" tai maganar kamar ta na yi da sa'anta. Sadik yai murmushi yace "Allah ya shiryeki Besty, ya nunan lokacin da zaki girma" Sahal ya biyota da rarafe, ta ɗau jakar makarantar ta da gudu, tai part ɗinta. Ba Sadik ba Farhan kanta abun dariya ya bata, ta tashi ta ɗakko Sahal tana rarrashinsa. Abunda yake bawa Farhan mamaki, Sahal ma Besty yake ƙoƙarin kiran Sadik da Nana, a gwarancimsa na yara. Farhan tace "wannan sunan shi Daddy kaji ko" tai maganar tana nuna masa Sadik. Sadik yace "ai yaron nan ba yadda ban ba yace Daddy ya ƙi se besty yake so shima ya dinga cemin". Farhan tai dariya tace "to ai ku ɗin ne kamar yayyansa ba iyayensa ba" Sadik yace "Lallai kin ci mu wasa". Rayuwar gidan Sadik ta cigaba da tafiya, yana iya ƙoƙarin sa gurin ganin kowacce ya kula da ita daidai da buƙatar ta, Farhan ma ta koma Makaranta, dan ita har taje Ss3, Nana kuma na Ss1, shi kuma yana zuwa ABU zariya, duk ƙarshen wata yake zuwar musu, sedai sam haryanzu Mother ba ta maraba da Farhan. Soyayyar da Farhan ke nunawa Sahal, da kuma zuwan da Inna tai, tai musu nasiha sosai yasa Nana fara sakkowa daga kishin da take, Inna ta nuna musu su haɗa kansu su zama kamar 'yan uwa, se rayuwa ta fi yi musu daɗi ganin hakan ya sa ita ma Farhan ta sassauta na ta kishin. Sadik baya nan yana makaranta, Farhan ta na ta rashin lafiya, Nana ce ta lura da hakan tace "Nikam Mummyn Sahal lafiyarki kuwa, duk kin rame haka". Farhan tace "Wallahi besty zazzaɓin dare nake, ga ciwon ciki na rasa abunda yake min daɗi". Nana tace "Ai ba kya zauna da ciwo ba, bari in wa Sabo direba waya, ya zo muje in rakaki Asibiti" Farhan ba tai musu ba, sedai suna zuwa Asibiti, gwajin farko aka ce ciki ne da ita, har watanni biyu. Ita Farhan ma kunya ce ta kamata, Nana kuwa tausayi Farhan ɗin ta bata, Saboda ta san ɗawainiyar ciki akwai wahal, tun da suka dawo gida kuma laulayi ya saka ta a gaba, koma a ci se amai, Nana ce keta ɗawainiyar kula da Farhan, har mamaki abun ya dinga bawa Farhan, Nana ba dai tausayi ba. Nana ca ta sanarwa Sadik halin da ake ciki, murna Kamar ya zuba ruwa a ƙasa ya sha. Ranar da ze dawo, Nana tace "Princess be kamata ya dawo ya ganki a haka ba, duk kinyi wani iri, ki wanke gashin ki, se in miki stretching. Haka kuwa aka yi, ta gyarawa Farhan kai, ta sakata a gaba akan Lallai ta ci Abinci, ba ta son a haifo musu yaro ramamme. Suna cin abinci Nana na bata labarin zaman London da sukai, da irin wautar da ta dinga yi, musamman lokacin yace ta sha Nonon karya. Sosai suke dariya, ta dinga bawa Farhan labarin yadda Inna take sata a gaba, akan kula da kanta da yanayin rayuwar da tai tare da kakanninta. Se taga jikin Farhan yai sanyi, Nana tace "meyafaru, ko na faɗi abunda ba kiji daɗinsa ba?" Farhan tace "A'a, kawai dai kin tunan wani abu ne, ke gashi ba ki rayu da iyaye ba, amma kin samu kyakkyawar kulawa, Besty har ga Allah ni na ajiye batun wani kishi, ban ɗauke ki kishiya ba, se 'yar uwa shiyasa zan gaya miki wani abu da ya shafi rayuwata, kinga ni ga uwata ga ubana, amma mahaifiya ta sam bata damu dani ba, har gara ma yanzu akan da, kinga Inna itama ba fulatana ce, amma kimga halayarta ta sha bamban da ta Ummana, abubuwa da dama ban san su ba, har sonake in ga mutum da mamansa kamar ƙawaye, kinga Inna ta tsufa, Allah ya maye miki da Mother, rashin kulawar uwa ba daɗi" Nan ta ɗan ɓincinawa Nana wani abu na daga Rayuwar ta. Nana arhar hawaye, kawai ta kama kuka, ita ma Farhan ba ta da zaɓin da ya wuce tai kukan, Sahal ya tsaya yana binsu da ido. Sadik ne yai sallama ya dawo daga makaranta, amma ya tarar da su a zaune suna kuka, se yai turus, ya ƙaraso yana tambayar su ko Lafiya. Nana tace "bakomai hira muke" "To kuma hira se ku hau kuka, wace irin hira ce haka?" Farhan tace "Sirrinmu ne ai, ba se kaji ba" Sadik yace "iyeee, to Allah yasa ba laifi nai muku ba, kalli kun sa ɗanku a tsakiya kuna kuka, wannan abun kunya da yawa yake. Yai maganar yana ɗaukar Sahal da jin daɗin yadda ya gansu. Babban abunda ya ƙara burgeshi shine yadda Nana ke kiran Farhan Princess ita kuma take kiranta Besty, hakan yai masa daɗi ƙwarai da gaske. Lilly kuwa a ss2, tai graduating, Kamar yadda Mummynta ta bata shawara, haka ta amince dan ba ta son sake aikata abunda za tai dana sani kamar yadda take yi a yanzu, dan haka ta bi shawarar Mummynta don Auren wancan soja shine rufin Asirinta. Gashi ya manyanta, amma sonta yake kamar ze haɗiyeta dan so da ƙauna, dan haka ta amince ya kawo kuɗi aka tsayar da Ranar Aurensu, yayin da Sir Nazir yake can gidan yari. Khairat ma Faruk ya kai kuɗin Aure, an saka rana tana yin Candy za'ai biki, tare da walimar graduation ɗin ta. Ya haɗa lefensa na gani na faɗa, Sadik yace su shirya suje su gani. Farhan se fartabar zuwa gidan su Sadik take, saboda Mother har kashedi tai mata, akan kar ta ƙara zuwar mata gida. Se dai yau ma bata canza zani ba, dan tunda sukaje Mother tai mata wani irin mugun kallo, musamman da ta ga alamar ciki a jikin Farhan, ta dinga zazzaga mata masifa da baƙaƙen maganganu, Nana da Faruk na niyyar su dakatar da ita, amma suma ta ƙare musu, ba shiri Farhan ta miƙe ta nufi hanyar fita, Sahal ya bita yana kuka, ta sa hannu ta ɗauke shi tana share hawaye ta tafi. Nana ma kuwa ta saka kuka, har da sheshsheƙa, Mother ta buɗe baki tana kallon ikon Allah, da mamakin sakarci irin na Nana. Nana tace "dan Allah Mother ki dena zaginta, Wallahi tausayi take bani, bana jin daɗin hakan, tana da kirki sosai". "Rufen baki, ko in zo in mangareki shashasha, wannan ɗaukar ɗan naki da take ne yasa kike wannan rawar kan" Sadik da ke zaune Mother tai faɗanta ta gama, har Farhan ta tashi ta tafi bai motsa ba, shi kansa Faruk be ji daɗin abunda Mother tai. "Kai kuma dama baka kake so, ga mata nan ka tara, yau Wannan da ciki gobe waccan da ciki shine babban burinka, kaje kai tayi". Abba da ya shigo Yanzu ya shiga tambayar Lafiya kuwa, ya gansu jingum jingum ga Nana na ta uban kuka. Sadik ya tafi gaban Mother ya durƙusa yace "Mother, idan rabuwata da Farhan, ze sa ki samu kwanciyar hankali, insha Allah daga nan idan na bar nan, zan sawwaƙe mata, dan ba ta cancanci a cigaba da maita haka ba saboda ni, amma kan nan bari in faɗa muku dalilin da ya sa na dage, na Auri Farhan duk da ba kwa so, ban sani ba ko zaku fahimce ni, Mother Farhan Yarinya ce ta gari me tarbiyya wadda kowa ze so haɗa zuriya da ita, sedai ni da tarbiyya tai min ƙaranci na kutsa rayuwarta, na liƙe mata se da ta fara sona, Mother zina ce kawai ban aikata a rayuwata ba, na tafka ta'asa iri iri...... Nan ya fayyace labarin soyayyar su da Farhan, ba ɓoye komai ba, har rayuwar da tai bayan rabuwarsu, zuwa Aurensu a yanzu, ya ɗora da cewa "a yanzu haka Mother na fara tara zuriya,kuma nasan duk abunda ana aikata akan ɗan wani se anwa nawa, na auri Farhan saboda ina sonta, kuma saboda ina fatan Aurenta ya zama silar Allah ya yafe min kuskuren da na tafka, idan baki ysdd6ba kuma ku tambayi Sabo direba ya san wasu abubuwan, amma tun da ba kya so, zan rabu da Farhan, in dai hakan ze zama masalaha" ya ƙarasa Maganar hawaye na zuba daga idonsa. Gaba ɗaya ɗakin yai tsit, saboda abun ya bawa kowa mamaki da tausayi, asje Sadik ne ƙwallon se a hankali, shine silar komai. Nana ta taso ita ma ta zo gaban Mother ta durƙusa tace "Mother na, ke uwace, kuma ciwon 'ya mace na 'ya mace ne, be kamata mata 'yan uwanmu su dinga shiga matsala saboda mu ba, bayan muna iƙrarin ciwon 'ya mace na 'ya mace ne ba, dan Allah a karo na biyu, ina nemawa Abban Sahal alfarma, dan Allah kiyi 6ya rayu da Mummyn Sahal, tabbas gaskiyar ki me ɗa wawa, son da takewa ɗa na da kyawawan halayenta ya sa nake sonta nima. A wannan gaɓar nice ƙaddararsu da na raba wannan Soyayya, dan haka be kamata kowa ya goyan baya ba, ina son Sadik, amma ina kwatanta kaina idan ni na tsinci kaina a matsayin da Farhan take, dan Allah Mother karki bari Auren nan ya mutu, dan girman Allah" Kuka Nana take sosai tana riƙe ƙafar Mother. Abba ya nisa yace "Allah sarki Nana, halinki irin na marigayi Hakimi, ya yadda ya rasa na sa farincikin saboda wani ya samu, shiyasa ya samu soyayyar mutane. A karo na biyu kenan tana nema maka alfarma, lokacin da kake neman Auren nan, haka ta saka gwiwowinta a ƙasa akan mu bari kai Auren nan, a karo na biyu tana nema maka wata alfarmar, tabbas idan ka wulaƙanta Nana, kanka ka wulaƙanta. Abba "ya za'ai in wulaƙanta ta, wallahi Abba ina son Nana, so na gaske" Abba yace "kaje kar ka rabu da matarka, Allah ya kyauta ya tsare gaba, ya ƙara haɗa kanku" Mother kiyi magana, Sadik yai maganar yana kallon Mother. Mother tace "Ai kuma ba ni da ta cewa, ai ban san haka abubuwan suka gudana ba, Allah ya kyauta" Abba yace "ɗau matarka ku tafi gida" Sadik ya sa Nana a gaba suka bar falon, suna tafe a mota, ya kasa magana, se riƙe hannunt da yai cikin nasa, yana jin wani irin sonta a ransa, ga wat kima da ta ƙara yi a idonsa. Sukaje gida suka tarar Farhan, ta hsɗa Akwatinta, abun tausayi ta goya Sahal a bayanta, zata tafi. Da sauri Nana ta karɓe Akwatin, Sadik yace "Ina zaki?" Cikin kuka tace "gida zani, gara in haƙura da Auren tun da Mother ba ta so" Nana tace "Haba Princess, in kika tafi bamu da Princess ɗin da zata maye mana gurbinki, dan Allah a madadin Mother ina baki haƙuri, dan Allah karki tafi, Farhan nice ƙaddarar da ta ratsa tsakanin soyayyarku, ban san haka abubuwan suke ba, dan Allah kiyi haƙuri ki zauna" Rungume Nana Farhan tai tana kuka tace "Besty Mother ba ta sona" "A'a tana sonki" Nana tai maganar cike da tausayin Farhan, tana ji a jikinta idan har ciwon 'ya mace na 'ya mace ne, to be kamata ta ga Farhan na zub da hawaye ba, saboda ta sha wahala. Sadik ya ƙaraso ya rungumesu gaba ɗaya, yana faɗin 'kukan ya isa haka, ke kuma da kika goya Sahal ina zaki da shi?" Ta share hawaye tace "da shi zan tafi" Sadik ji yai kamar yai dariya, saboda wauta da yarinta, za tai yaji amma za ta tafi da ɗan da ba nata ba. Yayin da yake sake mamakin Nana, saboda ita a rayuwarta ba ta son ta ga wani yana kuka, sosai kimarta ta ƙaru a idon Sadik. Mother da kanta taje gidan Sadik, cike da borin kunya, ta nunawa Farhan komai ya wuce. Sunusi kuwa ciwo yake tuburan, da fari abun kamar aljanu, daga baya kuma likitoci sukace ya samu brain tumor, ya dinga wani irin ciwon kai, da fizge fizge irin na mahakata, ana neman wasu uban miliyoyi ai masa aiki, wanda ba wanda yake da wannan uban kuɗi. Wata irin kulawa Sadik yake bawa iyalan nasa, cikin taka tsantsan ba tare da ya shiga haƙƙin wani ba, da tsohon ciki Farhan ta gama sakandare, idan kai baƙo ne ka zo gidan ba zaka ce kishiyoyi bane, balle ka gane wacece ta haifi Sahal, dan tunda Nana ta yaye shi, Farhan ta karɓe shi. Watan cikin Farhan tara, ta haifi sankaceciyar jaririya, ta haihu daf da bikin Faruk da Khairat, Nana ta dinga murna kamar ita ta haihu, dan ba ƙaramin son 'ya mace take ba. S kace za'a haɗe bikin Khairat da sunan Farhan, idan Sahal ya ga Farhan ta rungume jaririya tana shayarwa, se yai ta tureta, wai dole se an saketa daga kan cinyarsa. Nana tace "ban taɓa ganin garujen yaya ba, irin Sahal. Haihuwar Farhan ma ta cika ko ina, aka haɗe suna da bikin Faruk, akai gagarumin shagali. Farhan tace sunan mahaifiyar Nana take so a sawa jaririyar, Sadik kam be musu ba ya amince, Nana taji daɗin karar da Sadik sukai mata, hakan ya sa ta ƙara ƙaunar jaririyar da mahaifiyarta, aka sa mata suna Khadijah sunan mahaifiyar Nana, suke ce mata Neehal. Umman Farhan kuwa dai-dai gwargwado tai playing role ɗinta na uwa da Farhan ta haihu, saboda tai dana sanin irin riƙon da taiwa Farhan a baya. Sir Nazir ya gama shekaru biyunsa, ya koma garinsu, sedai zaman garin ya gagare shi, saboda da ya fita ake nuna shi ana zunɗensa. Ya tattara kansa ya koma Lagos neman kuɗi, a can ya haɗu da wata ya aura, sedai shima ya tarar da ragowar wani ya aura, sedai ba shi da cewa saboda Abunda ya aikata shima. Sadik ya kammala karatun sa, be dogara da aikin gwamnati ba, ya cigaba da harkar kasuwancinsa, gidansa ya tsaya tsayin daka gidansa babu ɓaraka, kansu Nana a haɗe yake, Sosai Nana ta ke riƙon Neehal, da soyayya da ƙauna kamar yadda Inna ta riƙeta, Sahal kuma ya zama ɗan gidan Farhan, ya cewa Farhan Mummy, ya cewa Nana Besty. Allah sarki Jidda, seda ta shekara bakwai da Aure, sannan Allah ya bata haihuwar tagwaye, Allah me kyauta da ƙari, ba wanda be musu murna ba, mahaƙurci mawadaci. Tasleem ta haɗu da Cancer bakin mahaifa saboda azabar zubar da ciki, Meenal kuwa hauka tuburan saboda shaye shaye, Mubarak Babba da Nas ma haka aka yanke musu shekaru masu yawa a prison, saboda laifukan da aka kama su da su. 25years later. Sanye yake cikin gajeren wando da 'yar shirt, tafiya yake cikin ƙasaita yana taje sumarsa da comb, ya shigo cikin falon da 'yan matan suka cika da surutu. Suna ganinsa suka nutsu sukai tsit, ya ja tsaki yace "sekace gyare, muryaoyin caicaicai, ko gajiya ba kwa yi, ku ɓace min daga falon nan". "Ba zasu tafi ba, uban masifa ba yadda yara za su sake seka zo kana muzurai" cewar wata 'yar gayun mace, da ke zaune akan dining, se da na ƙura ido naga ashe Nana ce. Farhan tai murmushi tana fitowa daga kitchen tace "like father like son, baya son hayaniya ne, ta ho nan sweetheart, zo muje falona kaci Abinci mu bar musu nan". Nana tace "eh naji, a ƙyalemin yara su huta, kuje can ke da ɗan naki". Gidan Sadik kenan bayan shekaru Ashirin da biyar, Farhan na da yara uku, mata biyu, ɗaya namiji, Nana na da huɗu, biyu mata biyu maza. In ka gansu a cikin yaran kamar yayye da ƙanne, Abba ya tara jikoki, dan Faruk kawai yaransa shida Khairat ta haifa, Dr. Kuma na da Biyar. Jikoki duk syka baibaiye Mother, tuni ta mnata da ƙiyayya ta kama sirikanta da jikokin ta, saboda ta ɗau darrusa a rayuwar Sadik da yaransa. Farhan tai karatunta na Nursing, Nana kuma 'yar Jarida, kansu a haɗe dan hatta harkar business tare suke yi, suka riƙe mijinsu cike tsantsar soyayya da kulawa, Inna kuwa ta rasu shekaru uku bayan rasuwar Hakimi. TAMMAT BI HAMDILLAH, ALHAMDILILLAH ALA KULLI HALIN, DUKKAN YABO DA JININA DA KIRARI SUN TABATTA GA UBANGIJIN TALIKAI, NA FARA WANNAN LITTAFI LAFIYA NA KAMMALA LAFIYA. GODIYA TA MUSAMMAN GA MASOYA DA KU KAI HAƘURI, TARE DA JIMIRIN BIBIYAR WANNAN LITTAFI HAR NA KAMMALA. BA ZAN SAUKE ALƘALIMINA BA HAR SE NA MIƘA JINJINA GAREKU AUTAR MANYA, SARAUNIYAR MASOYAN LITTAFIN RUƊIN ƘURUCIYA 😂, IDAN NAGA KIRANTA TO JIRAN POSTING TAKE. ZEE KUMURYA MUM AMNASH INA MATUƘAR GODIYA A GAREKU, ALLAH YA BAR ZUMUNCI. COMMENTS SECTION KUMA BA ZAN MANTA DA KU BA, YADDA KUKA DINGA NISHAƊANTAR DANI DA SHARHINKU, ALLAH YA BAR ZUMUNCI DA ƘAUNA. DAN ALLAH INA JIRAN JIN RA'AYOYINKU AKAN LITTAFIN, KO TA GROUP KO TA PRIVATE. GYARA KO SHARHI, KO SHAWARA, INA JIRAN RA'AYOYIN KU. NACE BA, DUK DA ALHAMDILILLAH A WANNAN KARON BANGA ANA GANTALAMIN BOOK ƊIN BA, AMMA DUK WADDA AKA TURAWA BA TA BIYA BA, DAN ALLAH TA BANI ƊARI UKU NA, ƊARI UKU BA ZATA SAKI TALAUCI BA, KEMA DA KIKA TURA BA DA IZINI NA BA, ALLAH YANA KALLONMU GABA ƊAYA TABBAS, DAN ƊARI UKUN KI BAKI BIYANI ZAFIN DA IDONA YAKE BA, DA KUMA DARUSSAN DA KE BOOK ƊIN BA, DA ZAKI TURAWA WATA🙄🙄🙄 BANYI ALLAH YA ISA BA AMMA A BIYANI 300 NA, KO IN YI😬😬😬 AYSHERCOOL 07063065680