✧✦ 𝐓𝐀 Ƙ𝐈 𝐙𝐀𝐌𝐀𝐍 𝐀𝐔𝐑𝐄 ✦✧ 𝐁𝐲 𝐊𝐡𝐚𝐝𝐞𝐞𝐣𝐚 𝐂𝐚𝐧𝐝𝐲 *©️®️Hakkin mallaka nawa ne ni Khadeeja Candy, ban yarda a sarrafamin labari ta kowace siga ba balle har a dorashi a Website ko YouTube ba tare da izinina ba, yin hakan kuskure ne babba domin zai iya janyowa mutum matsala saboda haka a kiyaye ⚠* SHIMFIDA... “Ni ma ina da buri, ina da mafarkai irin na kowace mace, sai dai kuma kaddara ta shata min liyi, yadda alƙalamin ya zana dole haka zanbi... Daga lokacin da na fahimci haka, sai tsoro da fargabar me zai faru a gaba ya fice a zuciyarta. Tafiyar da babu dawowa ta zama dakuna...” TA ƘI ZAMAN AURE... Share fagen wata tafiya ce mai sarkakiya da daure kai. Wata kalar kaddara ce mai rikitarwa, shimfida ce dake lalaye tafiyar wasu daidaikun mata.... Tafiya ce ta irin matan da duniya ta canja musu zane, suke da wani rufaffen sirri a zuciya! Sai dai kadan daga masu ilmi ke fahimta. A cikin rayuwa akwai mutuwa haka ma a cikin mutuwa akwai rayuwa shim kun ankara da haka? Mabudin kowace kofa makulli ne sai dai wannan kofar a balleta ne ta kasa, sai shigar cikinta ta kasa yi ma mai dakin dadi. Al'umma sun kasa yi mata uzuri iyayenta  sun kasa fahimta, mazajen kuma sun kasa riko...! Uba na gari jigo, sai dai ita bata dace ba, miji na gari gimshiki a nan din ma dai bata dace ba, kuma duka laifin yana komawa zuwa gareta ne.... Duniya ta yi mata juyin masa, ta yadda ta kasa banbance fari da baki, ji da gani sun mata nisa,  albishin daya take jira... mutuwa...! Masoyana Assalamu Alaikum Khadeeja Candy ke muku sallama tare da fatan na same ku cikin aminci da kwanciyar hankali.          Gani dauke da wani sabon labari kuma ina fatan zai kayatar da ku fiye da sauran. Labari ne akan NOOR da rayuwarta da iyalan gidanta. Labarin nan kirkiren labari ne idan yayi daidai da rayuwar wasu ko wata to arashi aka samu. Za ku fi samunsa a AREWABOOKS @KhadeejaCandy Ranakun posting. Monday - Friday Chapter 1 بِسْمِ اللّٰهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ Tasss muka ji sautin saukar mari, irin marin da zai iya kurmantar da mutum a take. Na kai hannuna da sauri na dafe kuncina hawaye na sauko min. Hana ta rufe fuskarta ta fashe da kuka, kamar yadda Mama ma take kukan marin da Abbah yayi mata. “Abun da na ga damar badawa kenan idan kin ga dama ki zubar daman baki taba godewa ba ai baki taba godewa ba idan na yi miki abu, kullum cikin kuka kike kuma a cikinsa zaki kare Hajara...” Ba a iya fatar baki yake mata fadan ba, sai da ya hada mata da duka yana harbin kafafuwanta har sai da ta fadi. Da gudu na nufi gurin da take ina kuka, sai dai kamin na tabata sai ya fisge ni ya jefar a kasa. “Abbah dan Allah ka yi hakuri” Na fada ina kokarin tashi na sake nufa gurin da mahaifiyata take. A madadin yayi hakuri sai ya kara rufeta da dukan kamar ana kara masa karfi, ya saba idan ya fara dukanta sai ya canja mata kamannin sannan yake barinta, dukan mahaifiyarmu a gaban idonmu wani abu ne da Abbah ya saba yi, tun muna kanana har girmanmu, agaban kowa zai iya fada mata magana marar dadi, idan kuma ta yi masa ba daidai ba baya duban mu ko a tsakar gida zai iya rufe ta da duka, mu kuma muka kasa sabawa da halinsa. A kullum idan yana dukanta na kam ji kamar ni yake duka zubar hawayena suka fi nata yawa domin ko bayan abun ya laba na kam kebe na yi kukan abun da Abba yake mata. “Dan Allah Abbah ka yi hakuri...” Na sake fada ina kwantawa ta inda yake shurinta domin na tare mata, sai ya hada har da ni yana shurin har sai da yayi mai isarsa sannan ya kyale mu ya fice daga gidan. A nan na samu damar tashi na rika Mama ita ma ta tashi, da taimakon Hana  muka kaita daki, karfi hali irin na Mama muna shiga dakin sai ta yanke kuka da take ta share hawayena ta dubu mu ni da kanwata Hana ta ce. “Kar na ji wani ya fadawa Yayanku abun da ya faru, musamman ma ke Noor kin fi uban kowa baki” Ta nuna ni saboda ni suke cewa na fi rawar kai da surutu. “Wallahi Mama ba zan fada masa ba” Hana ta fada, ni dai na yi shiru domin Allah ne kadai ya sani ko zan iya rike kaina ban fada ko kuma na fada, ya danganta da yadda abun ya tsikare ni. Waje mu ka fito ni da Hana mu ka cigaba da aikin gidan, ita take wanke wanke ni kuma ina shara sai da muka gyara gidan tsab sannan Hana ta fara shiga ta yi wanka bayan ta fito ni ma na shiga na yi wanka na fito mai kawai na shafa ma zauna a kan katifarmu har sai da ta gama shiryawa ta fita sannan na bude durowarta na dauko doguwar rigarta na saka na dauki bakin dankwali na daura, na san zata yi masifa dan haka na shiryawa komai ma. Ina fitowa waje ta hau da masifa na saka mata gown na je na cire. “Wallahi ba zan cire ba, tufafina duk sun yi datti haka kike son na zauna sirara a gida ko kuma so kike na saka mai datti ko kuma na Mama zan saka, duk masifar da zaki yi sai dai ki yi amman ba zan cire ba” “Noor ki cire min tufafi kin ga kullum kin fi son mu yi masifa har ana jin mu makota ko? Mama ta miki magana ki daina taba min kaya ba zaki daina ba ko?” Na marairaice mata fuska. “Ki yi hakuri daga wannan ba zan sake ba” “Kullum ai haka kike cewa daga wannan ba zaki sake ba kuma ba zai hana gobe ki sake din ba” Ban san lokacin da na watsa mata wani kallon banza ba. “Wai ke Hannatu baki gajiya da masifa ne kamar tsohuwa kullum cikin bala'i” “Allah ya raba ni da bala'i ai ke kika ja, kullum sai kin yi abun da za ayi magana” A raina na yi tsaki na nufi karkashin inuwar mangoro na zauna ina ta hararata, bata dai kula ni ta cigaba da karatun, ni kuwa sai aikin gyara rigar dake zubo min nake daman jikin ba daya ba kayanta sun min yawa ta fini kiba da tsayi idan muka jera wani sa'in ma sai ace ita ce  yaya ni ce kanwa, daman kuma tsakanina da ita wata goma sha uku ne. “Mtscheeeeeeee bakar masifa tufafi ya mata yawa amman sai ta saka, ko kunya bata ji a ganta da kayan kanwarta” Daga inda nake zaune nake jiyo ihunta duk da ba ni take kallo ba na san da ni take. “Ai bala'in neman zuwanki duniya ne ya hana ni kiba, gashi nan Mama tana fadar yadda na sha wahala kamar ba zan rayu ba saboda ke, ko gama shan no-no ban yi ba kika karbe azzaluma” Kyalkyalewa ta yi da dariya ta kalleni domin ta fahimci a bakin gaskiyata nake maganar. “Mahaukaciya, daman can ba jikin kibar ne dake ba, ke da aka haifa da wata bakwai ma Allah ne ya so ki Wallahi da yanzu baki duniyar ma” “Yen yen yen yen... Fuska kamar agwaluma sai baki kamar zunubi” Na fada ina yamutsa mata fuska, a madadin ta ji haushi sai ta sake kyalkyalwa da dariya tana girgiza kai. A karo na biyu na sake watsa mata harara na dauke kai ina kallo kofa domin na san lokacin dawowar Yaya Nabil ya kusa ko ma nace yayi. Ashe kuwa na canka daidai kamar jiran ake na maida ido a gurin sai gashi ya shigo rike da yar ledarsa kamar na tashi da sauri na tarbo shi, ni ce mai binsa kuma ni ce mai karba duk abin da zai shigo da shi gidan a kullum saboda na san kayan dadi yake kawowa daga restaurant din da yake aiki. “Sannu da zuwa Yaya Nabil...” “Yauwa ina Mama?” Ya nufo gurin da na tashi ya zauna sai na zauna kusa da shi ina fadin. “Tana daki tana bachi” “Bachi lafiya?” “Tun dazun ma take bachin fadan da suka yi da Abbah ne sai ta yi bachi” Hana ta bude yana kallona. “Ahhh ke kam kin ji haushin rayuwa Noor kin ji haushi kin shiga uku” “Toh ai dai ba fada masa na yi nace ya doketa ba, ko kin ji na yi maganar dukan da yayi mata ne? Munafuka me zuwa lahira da kokon dambu” Ta ja tsaki ta tashi ta nufi dakin Mama, yaya kuma ya jefar da hular ya mike tsaye zuciyarsa na cika. “Wai Abba yaushe zai daina wannan halin ne? Wai yaushe zai fahimci Mama ta kai matsayin da ya kamata ya daina dukanta, ba zan iya jurar wannan abun ba, gaskiya na gaji, Wallahi ba dan yana ubana ba ba zai saka hannu da doki Mama na bar shi da rai ba, wannan wane irin rayuwa ne...” Fada yake sosai kana kallonsa zaka san ransa ya bace, daman haka yake hawa idan ya ji abun da ya faru, idan kuma yana gidan tarewa yake baya taba yarda hannun Abba ya kai hannun Mama. Yana cira kafa ya nufi dakin Mama ta fito Hana na bayanta kana gani kasan ta kitsa mata munafurcin abun da na yi, ni kuma ba wai na yi ne dan bana jin maganar Mama kawai dai na fada masa ne saboda mu taru mu yi bakincikin a tare, ai shi ma yana daga cikin iyalan gidan ya kamata komai ya faru ya sani. “Noor wai ke wane irin kunne ne da ke, me ke motsi a kanki?” Na sauke kaina kasa domin ban san kalar amsar da zan bawa Mama ba, daman can ko ban yi laifi ba ganin laifina take balle kuma Hana ta kitsa mata munafurci. “Me na fada miki?” “Cewa kika yi kar na faada masa” “To yanzu me kike yi?” “Fada masa na yi” “Wane gargadi na yi miki?” Na dan turo baki gaba na mike tsaye na tsaya bayan Yaya Nabil, domin karamin aikin Mama ne ta riko ni ta fara duka a gurin. “Cewa kika yi kar na fada, sai kuma na fada” “Toh ya miki kyau, yau sai kin ci ubanki a gidan nan” Na yi saurin ba bayan yaya ba tare da na dandana abinci da ya dawo da shi ba, na fito kofar fita gidan na tsaya a nan rai a bace san tun da Mama tace sai na ci ubana sai na ci duka ko wani hukuncin mai tsanani kuwa. “Ka dawo ya aikin?” Magana take da Yaya Nabil tana kokarin zauna a gurin da na tashi. Daker ya amsa mata da Alhamdullahi ya nufi dakinsa ni dai ina tsaye a bakin kofar jiran kawai nake na ga ta taso na auna a waje. Ina kallo suka cinye jollof din da Yaya ya zo da ita har da nama Mama bata ba ni ba saboda kawai na fada masa abun daya faru. “Mama yanzu kuwa cinyewa kuka yi? Ina kallo ku hana min?” Ina maganar hawaye na silalon min a ido domin abun yayi min bakinciki. A take Mama ta kara min da kalamai masu zafi. “Ba kin zabi munafurcin, zaki ci ubanki ai kuma karki fasa ki cigaba ko zaman aure sai ya miki wuya Noor saboda wannan halin naki” Ni dai ban sake cewa komai ba na nufi gurin da Hijab dina yake rataye na dauka na saka talkamina na fice daga gidan. Gida uku na wuce sannan na shiga na hudu da ya kasance gidansu kawata Zee. Sallama na yi aka amsa min na gaishe da Mamanta cikin mutunci sannan na tambayi kawata. “Umma Zainab na nan?” “Zainab bata dawo ba, ta tafi gurin bikinsu Salwa na dauka ke ma kina can?” “Aa ni bana da kudin abun hawa kuma nesa za'ayi event din shi yasa na ce sai dai gobe idan za'ayi kamu sai na tafi” “Gaskiya ai ya kamata ki tafi kam, Salwa ai kuna mutuncin sosai idan baki je ba ba zata ji dadi ba” Na zauna a gurin na karbi kayan miyar da take gyara na cigaba da gyara mata ina mata hira. Daman mun saba na kan zauna na yi hira da ita fiye da yadda nake yi da Zainab ma, sai dai duk yawan surutun da suke cewa ina da shi ban taba fada mata labarin gidanmu ba domin na san a inda surutun nawa yake. Sai da gama na nika mata a blender ta sannan na ari wayarta, na shige dakinsu Zee na kira rabin rayuwata Zafeer. “Hello babyna” Na yi dariya mai cike da shuki da jindadin yadda ya gane ni dince tun kamin ma na yi magana. “Ya aka yi ka gane?” “Da zarar na ga bakuwar number ko an yi min fulashin ko an kira na san Matata ce” “Toh ka kira kar mu cinye katin wayar Maman Zainab ce” “Baby Noor me kai ki ga wayar Maman Zainab kuma?” Na bata fuska kamar yana gaba jin yana kokarin kara min bacin rai bayan wanda aka saka min a gidanmu. “Zainab bata nan kuma ina son jin muryar ka what do you expect then? Kasan Yaya Nabil ba zai ba ni wayarsa sai idan na sata” “Calm down Baby is okay bari na kira yanzu” Na yi murmushi na kashe wayar, haka yake rikicewa idan ya ji raina ya bace ko kadan baya son damuwata. Few seconds da yanke kiran ya kira ni na amsa na kara a kunne na kwanta a kujera ina murmushi. “Zafeer ka dawo school?” “Na dawo ina gurin aiki ma” “Zafeer na so?” “Me zaki yi a nan” “Na gan ka kawai” “Aa nan gurin aikina ne Babe Noor be kamata kina zuwa ba sai da dalili, anjima ai zan shigo sai mu ga juna ni ma na yi missing dinki” “Okay” Na amsa shi sai ya dauko wata hirar ta soyayya mun kusa minti talatin muna wayar sannan ya muka yi sallama yana ta tsokana ta da ce min amaryarsa. Bayan mun gama wayar na fito waje na yi alwala na shiga dakin da na fito na yi sallah ban daga daga kan sallayar ba Umma ta kawo min shimkafa da miya a plate har da spoon da ruwa. Aiko na gyara zama ina godiya da Allah yayi min sakamakon da abincin da Mama da hana min gashi na samu shimkafa da miya my favorite. Rabi na ci na sha ruwa na dauko plate din na fito waje na samu murfi na rufe. “Gida zaki je da shi?” Sai na juyo na kalleta a kunyace domin ban yi tsammanin tana daga bakin kofarta zaune ba. “Zauna ki ci, idan zaki tafi sai na zuba miki a cooler ki kai musu” “Aa daman rufewa zan yi kar na bar abincin a bude saboda na koshi...” Ta yi dan murmushi domin tasan karya nake, plate biyu ma zan iya zama na cinye balle plate daya, kibar ce kawai babu amman cin abinci nake sosai kamar yar yunwa. “Ke Nooriya zauna ki cinye abincin, nan ba gidan bakuncinki ba ne, Idan zaki tafi zan zuba miki wani nace, ni kike kunya ko kuma su Zainab da basa gidan?” A kunyace na zauna waje na cinye abinci tass sannan na aje plate dinta. Sai ta tashi ta shiga kitchen dinta ta zubo min wani abincin a madaidaiciyar cooler ta rufe ta miko min na karba ina godiya kunya na lullube ni, da ma Zainab dince ba zan ji kunya ba amman mahaifiyarta ai da nauyi. “Na gode Umma” “Babu komai, ina wayata kin gama da ita?” “Eh tana dakin su Zainab a can na aje” “To zan dauka idan kin je ki gaishe da Mamanki” “Zata ji” Na juyo na nufi kofar fita har lokacin kunya nake ji, ina fitowa gidan na lullube abincin da Hijab, ko kofar gidanmu ban kalla ba na wuce na mike hanyar har na fita kwararon gidanmu na kama hanyar titi, daga unguwarmu zuwa unguwar da Zafeer yake aiki babu wani tazara mai yawa, dan haka da kafa na taka har gurin aikinsa yana hango ni ya aje karfen dake hannunsa ya taso ya nufo inda nake da mamakinsa a fuska. “Baby i thought mu yi magana ba zaki zo ba” Na dan yi fuskar shagwaba kamar zan yi masa kuka. “Abinci na kawo maka fa...” Na bude hijab din sai kular da na boye ta bayyana. Ya saka hannu biyu ya karba da sauri yana kallon fuskata da manyan idanuwansa masu tsananin fari da kyau. “Ban sani ba I'm sorry... Na kusa tashi ma wacan motar kawai zan yi ma faci sai na tafi, zo ki zauna ina gamawa sai mu tafi gida” Shi ya fara wucewa gaba ni kuma na bi bayansa har muka isa gurin motar ya bani cooler na rike shi kuma ya shiga yi ma motar faci. Ta gilashin motar da ya kasance baki nake kallon kai na ina gyara girata da ta yamutse, ba zato ba tsammani aka fara zuke gilashin motar har aka saukeshi kasa, ban taba zaton akwai mutun a cikin ba har sai da na yi arba da wata kyakkyawar matar da nake kyautata zatin budurwa ce amman ta girme ni nesa ba kusa ba, irin yan matan nan yayan masu kudi masu ji da kamsu. Murmushi ta yi tana gyara zaman katon gilashin dake idonta. “Wannan kanwarka ce?” Matar da tambaya kamshin turarenta na fitowa dake cikin motar da kida yake tashi a hankali. Zafeer ya dago ya kalleni yana mikewa tsaye. “Aa....” Ni kuwa na yi karaf na tare numfashinsa na ce. “Eh ni kanwarsa ce” Zafeer ya kalleni da sauri sai daga masa gira. “Yaya zan aje abincin a can” Shi dai mamaki ya hana shi ce min komai har na juya na nufi gurin da yake zama na aje abincin, juyowar da zan yi sai ganinsa na yi a bayana. “Me yasa kika ce haka Baby Noor” “To ka sani ko sonka take yi, baka ga mai kudi ba ce” “Idan tana so, me hakan zai kare ni da shi” “Sai ta rika baka kudi” “And...?” He asked still confuse. “Sai ka aure ni..” Murmushi ne abun da ya biyo bayan mamakinsa sai ya girgiza kai ya juya ya koma gurin motar, ni ma na bi bayansa ina murmushi ina tsaye gefensa yayi mata facin ya gama, sai ta cire gilashin idonta ta miko masa 5k. Tana masa wani kallo kamar wata rikakkiyar karuwa. “Gashi you can keep the change” A take na ji ana kirkira wani abu mai kamar wuta kamar garwashi a zuciyata. “Na gode” Ya furta sannan ya juyo ya kalleni. “And wannan matar da zan aura ce In Shaa Allah, so ba kanwata ba ce I'm her fiance an mana engage da ita shekara uku da suka wuce” “Wow Maa shaa Allah Allah ya sa alheri” Ta fada sannan ta rufe gilashin motarta ta yi mata key ta kama hanya. Na dube shi “Me yasa ka fada haka? Gashi har ta baka kudi mai yawa ma tun yanzu” “Ta saba ai duk lokacin da ta zo kudi mai yawa take badawa, and ni bana jiran kudin wani na kusa kare karatu kuma ina wannan aikin waya san me zan zama nan gaba? Ban ga amfanin yin karya ba saboda na ci kudin wani, and be kamata na boyewa kowa a alakarmu ba i love you so much ban ga dalilin da zai saka na boye alakarmu a guron wani ba, you're my life Noor ke tawa ce har abada” Cikin tsakiyar idanuwana yake kallo yana kitsa min maganar da ta dade da zaunawa a zuciyata. Na yi murmushi wutar sonsa na kara huruwa a zuciyata. “Mu tafi gida Zafeer” “Jira ni a nan zan bawa oga kudinsa sai mu tafi, i love you” Ya kashe min ido daya tare da yi min blow kiss. A gurin ya bar ni sai da ya bawa ogansa kudinsa ya dauko kayan aikinsa da cooler da na kawo masa abinci muka kamo hanyar gida muna tafe muna hira. Har muka shigo unguwar mu dabam tsakanin gidanmu da gidansu gida biyar ne a tsakani sai dai be shiga gidan na su ba duk da Kasancewar ya fi kusa har sai da ya rakani har kofar na mu gidan sai da na shiga sannan ya juya. #KhadeejaCandy https://chat.whatsapp.com/ExyBEuiZZ0J1ivlVK5lIOx Assalamu Alaikum... Ina talata muku KHADEEJA CANDY STORE 🥰🙌 Muna siyar da Atamfa, Laces, Mayafai, Talkami da Jaka, Akwaituna, Kayan Kitchen, Zanen Gado, da kuma kayan kawata gida ko falo. ✧✦ 𝗧𝗔 Ƙ𝗜 𝗭𝗔𝗠𝗔𝗡 𝗔𝗨𝗥𝗘 ✦✧ 𝗕𝘆 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆 𝐂𝐡𝐚𝐩𝐭𝐞𝐫 -2 Daga bakin zaure na tsaya ina leka ciki sai na hango Hana tana daka a turmi Mama kuma tana zaune gaban murhu tana aikin hura wuta. Yaya Nabil kuma yana daga gafe yana wanke wandonsa da talkami. “Ina kika je?” Na kalli Yaya sai na jingina da kofar bana son amsa masa tambayar domin na san fada zai min ni kuma ban iya karya ba komai za ayi min sai na fadi gaskiya. “Ba magana nake miki ba” Ya daka min tsawa, na dan matsa baya na saka hannu a baki ina cin akaifata. “Yaya Mama fa ta cinye abincin da ka kawo kuma tace zata min duka shi ne na bar gidan na tafi gidansu Zee mamanta ta ba ni abinci bayan na ci ta zuba min wani a kula na kaiwa Zafeer” Yaya ya girgiza kai yana murmushi. “Yanzu ke gidan ku ana kokuwar yadda za a cefane a girka masara amman kin samu abinci sai ki kaiwa saurayinki? Noor Allah ya shirya ki” Mama ta tabe baki “Ai wannan yarinyar abu ne mai wahala ta yi jinkaina, duk abun da ta samu a duniyar nan sai dai ta kai ma saurayi babu ruwanta da ni” “Toh ni Mama me nake samu? Kullum fa babu ne a gidan, kuma ai kece kika ce dukana zaki yi shiyasa na kai masa” “Kya ji da shi dai, wuce ki daki kasan gadona ki dauki kudin adashe ki kai ma Assabe ki ce ga zubi na biyar nan” “Mama yanzu kina da kudin adashe kika hana ni na babur din da zan tafi bikinsu Salwa?” “Kudin adashen zan baki ki tafi biki? Wa nake ma dashen ba ku ba? Kudin kayan aure nake tara muku ai” Ina jin haka na san Mama ta sauko kenan dan haka na wuce cikin gidan na shiga dakinta na dauko kudin a gurin da ta saba ajewa na fito ina kallon Yaya Nabil da zai zubar da ruwan kumfa. “Yaya na kawo kala ɗaya ka wanke min dan Allah?” Wata uwar harara ya watso min sai na yi saurin barin jikin kofar dakin na nufi hanyar waje. “Kawo kala daya amman” Ban yi mamakin jin haka daga gareshi ba, daman Yaya Nabil mutum ne mai sauki kai a gareni. Na juyo cike da kuzari da jindadi na nufi dakinmu na dauko tufafina na sallah babba da mayafin sai kuma na tuna ba lallai ne Hana ta yarda ta min kwaliya ba dan haka na dauko abayata na mika masa ta. “Gashi Yayana na gode” Na mika masa cike da ladabi. “Kuma na fada miki ki daina zuwa gurin aikin Zafeer ko? Ba yau na sha miki magana amman baki ji” “Abinci kawai na kai mishi idan ba yace na kai mishi abinci ba ko kuma na zo na karbi abu Wallahi bana zuwa, Yaya ni ma fa ina da hankalina” Be sake ce min komai ba ya jefa abayar a ruwa ya fara wankewa ni kuma na nufi kofar fita ina yi ma Hana gwalo. Domin na san idan ita ce ba zata wanke min ba ko da kuwa zan yi hauka. “Dan Allah can mai kayan aro” “Na ji dai na ji dai ba zan cire ba” Na fice abuna ina tafiya a natse, daman can bana kama da marasa tarbiya ko natsuwa zakewar da nake abu ma idan na san mutum ne ne nake yi, idan ban sake jiki a guri ba ko uffan bana cewa. Cikin natsuwa na isa gidansu Talatu mai adashe na bata kudin kuma na fada mata zubi na shida ne kamar yadda Mama tace ma fada, sannan na juyo na fito, a kokarina na takaitawa kaina wahala na biyo ta kwararo kwararo domin ya fi sauki sama da mike hanya sambal. Wani abun da ban saka rai da tsammani ba ashe rabon ganin wani abun ne ya biyo da ni ta hanyar, Abbah na gani tsaye kofar gidansu Gambo mai furar yan gayu rike da yar ledarsa baka sai gyaran riga yake. Ban yo mamaki ba domin akwai zaurawa a gidan har biyu da kuma yan matan da ba a taba yi ma aure ba. Rage tafiya na yi saboda na samu damar ganin wadda Abbanmu yake so cikin ƴaƴan gidan, amman hakata bata cin ma ruwa ba, domin har na kawo kusa da Abbah yarinyar bata fito ba. “Abbah ina wuni” Na gaishe shi, sai yayi saurin dauke kai kamar be gan ni ya hade rai. “Abbah gidan dawo (Fura) za a siyo maka kawo na karbo maka” Na fada cikin ladabi sai dai hikimar ba dan na siyo masa ba ne kawai sai dan na dalilinsa na zuwa gurin. “Me kike yi a nan?” Ya daka min tsawa dai da na zabura zuciyata ta buga kamar zata fado. “Mama ce ta aike ni na siyo mata fura” Na fada ina kokarin kare kaina, rufe bakina ke da wuya sai ga Bilki ta fito daya daga cikin yan matan da suke gidan ta chaba ado kamar wanda zata je gurin biki. Ganina tsaye ina kallonta ya saka ta juya da sauri ta koma cikin gidan ba tare da ta fito ba. “Zaki wuce ko sai na ci ubanki?” Kalamin da Abbah yayi ya dawo da dubana gurinsa sai na matsa baya da sauri na kama hanyar gida ina tafe ina waigensa shi kuma be fasa cika yana min dakuwa ba (Zagin hannu kun san hausar mu da ta ku ba daya ba😁) har sai da na karya kwana a nan na boya cikin wani kwararo ina lekonsa, wayarsa na ga ya ciro yana dannawa sai dai kamin ya kai wayar a kunne wani kamin yaro ya fito yayi magana da shi, sai na ga Abbah ya mika masa ledar hannunsa sannan ya juya ta hanyar da na biyo ya wuce. ‘Wato Balki da Abbah na take soyayya kenan hmmm’ Na fada a raina a zahiri kuma sai na juya na nufi hanyar gida, kamin na isa zuciyata ta cika har ta kusa fashewa tsabar takaici da baki ciki. Ban tsaya sallama ba haka na shiga gidan na zauna kusa da Mama dake tuka tuwon masara na jera mata abun da ya faru sai hakki nake saboda bacin rai. “Wata kila dai fura zai siya” Yaya Nabil ya fada kamar wanda be yarda da maganar ta ba. “Wallahi ba wata fura, ai ba leda aka kawo masa ba shi ya bada ledar aka shiga da ita gidan, kuma har ce masa na yi ya kawo kudi na karbo masa sai ma zagina da yayi” Ina maganar ina yamutsa fuska. “Wallahi sai na mata mugun duka” Mama ta nuna ni da muciyar da take tuka tuwo da alamar dake nuna babu wasa maganarta. “Wallahi ko yatsa na ji ance kin nunawa Balki sai na ci ubanki sai na miki dukan da zai daukeki lokaci kina jinya, kuma kin san halin Abbanku ko? Bara saboda Amaryarss ya karya miki hannu, idan baki cire idonki akan Balki ba sai zai iya kashe ki ma” “Amman abun da yake be dace ba, irin wannan ke janyo raini s unguwa, kuma ko aure zai yi me zai yi da Balki Fisabilillahi” Cewar Yaya Nabil cikin da bakinciki. Mama tace “To ya zaku yi Mahaifinku ne sai Hakuri, idan ya tashi aikata abu kun san babu wanda ya isa ya hana hakan faruwa, saboda haka bana son na ji bakin kowa a cikinku, musamman ma ke Noor ke ce marar jin magana, duk dukan da za'a miki ba ki ji” Na turo baki gaba, domin Allah kadai ya san irin rashin mutum da zan yi ma Balki idan ta yarda da auri ubanmu. “Har da leda baka ya bata” Na sake fada ina tuna dukan da yayi ma Mama dazun saboda tace ya bada garin masara babu kudin cefane. “Daman ke kin iya karawa miya gishi ai, idan baki fadi komai ba to ba ke ba ce” Na juya ba kalli Hana na watsa mata harara. Yaya Nabil ya shafa kansa damuws na bayyana a fuskarsa. “Wani lokacin sai na ji kamar na tafi na bar garin nan Wallahi, abubuwan da Abbah yake sun yi yawa, muna neman abun da za mu ci amman shi ta aure yake, yaushe ya auro Baaba Maryam yanzu kuma ace har ya fara tunanin auro wata, watan ma karamar yarinya sa'ar yarsa” “Kuma dazun saboda kudin cefa ne ya doke ki Mama wai bata godewa komai ya kawo Allah kadai ya san meye a ledar nan da zai bawa Balki” Mama ta rufe tuwon tana fadar. “Cigaba karki fasa, tun da kin zama yar iska gararariyar gidan nan, ke idan aka ce kar ayi abu sai kin yi, ki cigaba” Ina jin haka na yi shiru da bakina ban sake cewa komai ba, daga haka maganar ta mutu sai dai kowa da abun da yake sakawa a ransa. Ana hada hadar kiran sallah magariba Abbah ya shigo gidan a lokacin duka hannayenmu suna cikin tuwon masarar da Mama ta girka. Ni da Yaya muna ci a kwano daya daman idan yana gida hade mana abinci nake saboda na bawa Hana haushi. “Wa'alaikumussalam” Mama ta amsa mu kuma muka masa sannu da zuwa, sama sama yake kallo kamar wanda yayi arba da abun kyama, more especially ma ni. “A kawo abincin ko sai ka yi Sallah” Abbah yayi kamar be ji abun da Mama take fada ba ya nufi wani dutse da ya saba zama yayi alwala ya zauna, ina ganin haka na cire hannuna a abinci na nufi butarsa na dauka na zubo ruwa kamin na karasa gurin da yake zaune sai fada ya biyo baya. “Wai kamar ni a cikin gidan za a wurgar min da buta a waje, aje ta babu ruwa har sai na taba, saboda an rai min wayo kuma duk laifinki ne Hajara” Ban yarda na karasa gurin da yake zaune ba, na aje butar daga nesa domin yanayinsa yana nuna alamar ransa a bace yake kuma zai iya kai min duka. A madadin ya dora laifin a gareni sai ya juya ya kalli Mama yana nuna ni da hannu. “Kin gani ko? Raina nin da kike min yara sun dauka, gashi ta kawo ruwa ta aje nesa da ni wato na taso na dauka” Mama ta kalleni kamar zata ce wani abu sai kuma ta yi shiru, domin yanayin tsayin da na yi ya nuna alamar tsoron karasa nake kusa da shi. Ko da kuwa ban aikata komai ba Abbah zai iya min duka balle kuma na gan shi a gidansu Balki kuma ya san sai na fada. “Ba zaki dauki ruwan ki bashi ba sai na ci ubanki” Yaya Nabil ya daka min tsawa kamar ba shi ba, wata kila laifin da Abbah ya dorawa Mama ne ya fusata shi. Na duka na dauki ruwa, ban kai ga mika ma Abbah ba ya juyo ya kalli Yaya Nabil. “Tooooo ka ci ubanta, ni kake zagi ba ita ba, daman ai ni na san ba kaunata kake a gidan nan ba, to sai ka ta so gani zaune a nan ki cinye ni, zan baka mai da yaji, daman ai yanzu abun da yara suke yayi kenan su kashe iyayensu, sai a fara saka ka a gidan redio ana hira da kai ka ga ka ci riba...” “Subhanallahi kar Allah ya kaddara mana wannan ranar ko bana raye, kar Allah ya nuna mana wannan ranar, bana fatan hakan” Mama ta fada tana cire hannunta a kwanon tuwon da take ci. “Kina fata kan ai duk tarbiyar da kika koya musu ita suke yi, daga matan har mazan ita dai wannan babu albarka a tare da ita tun da aka haife ta komai ya lalace, gashi nan kuma yanzu tana daukar tarbiyar da kike koya Musu” Ya karasa yana nuna ni haka yake yawan fada, wai tun da aka haife ni komai ya lalace masa har yau be zama kowa ba. “Dukan abun da zai samu bawa daga Allah ne Malam ka daina maida laifin a gurin Noor, kuma ni bana koya musu tarbiyar da zai saka su raina ka Allah yana gani ai” Mama ta fada cikin yanayin dake nuna kukan na son fitowa a idanuwanta da bakinta. Sannan ta kalli Hana ta ce. “Karbi ruwa ki ba shi wata kila tsoro take ji kar ka doketa kasan halin Noor Malam ba sai an fada maka ba” Kana ta kalli Nabil “Tashi ka tafi gurin Sallah” Ya cire hannunsa a tuwon da tuni ya dakatar da cinsa ya mike tsaye ba tare da ya wanke hannun ba ya fice a haka kamar wanda baya son kara minti daya a gidan. Hana ta karbi ruwan hannuna ta karasa kusa da Abbah ta aje masa, sannan ta Abbah ya kalleni. “Kuma bari na fada miki Noor, idan na ji yarinyar da fadi wani abu akanki sai na lahira ya fi ki jindadi, kin san sau uku ina neman aure kina lalatawa ko? Allah yasa ki aikata wani na ji” Na yi shiru ina tsaye a gurin kamar hoto har sai da Mama ta yi min alama da na bar gurin da kai. Sannan na kauce na koma na dauke kayan da muka ci abinci na kai gurin da muka saba ajewa, juyowar da zan yi sai hawaye ya sauko a ido. A cikin kalaman da Abbah yake yawan yi min babu mai bata min rai kamar cewar ni din ba alheri ba ce a tare da shi, kusan ya fi tsanata fiye da Hana da Ya Nabil. Hannuna na saka na share hawayena na nufi wata butar na dauka na zuba ruwa na nufi bandaki, ina fitsari ina hawaye, ban yarda na fito ba har sai da Abbah ya fice daga gidan, ba zan iya fadar cewar ni ce kadai ban san dadin mahaifi ba, kusan dukanmu haka muke tun da muka bude ido mun samu mahaifinmu mutum mai wuyar sha'ani da baya sakewa da iyalansa duka kuma babu kalar wanda be mana, musamman ma ni da na kasance marar jin magana. Abu ne mai wahala wani kalami mai dadi ya fito daga bakin mahaifinmu izuwa garemu, idan ma mun dada masa to zai bar abun a ransa ne ba zai yi magana ba, idan kuma muka bata masa a take zamu gani. Mahaifina wani kalar mutum ne mai wuyar sha'ani mai wuyar mu'alama ga Iyalinsa, kuma mai son zuciya da zafin hannu abu kadan zai doke mu ko mahaifiyarmu a gaban idonmu. Rayuwar da muke yi a cikin gidan mu izuwa yanxu ya ci ace mun saba da ita amman ni na kasa sabawa da hakan, kullum ganin abun nake kamar sabo. “Noor ba dai kuka kike ba?” Na daga kai na kalli Hana dake rike da karamar buta tana dafe da kafadata. “Hana Abbah yana yawan fadar bani da albarka ko ba ni da sa'a, yana yawan cewa sanadina ya rasa aikinsa sanadina ya fara talauci, idan mutum ya ce miki haka sai kin ji kamar ki kashe kanki, balle kuma mahaifi, kullum kalma sabuwa take zame min” “Haba Noor ke da kike haske? Hake gidan nan hasken zuciyarmu, idan baki nan babu mai sakewa maganar Abbah ta daina damunki, Abbah ba shi da dadi a gurin kowa ke kin sani Mama ma be raga mata ba balle kuma mu, dan Allah karki bata ranki” “Toh” Na amsa ina share hawayena, sannan na cigaba da alwalar. Yaya Nabil be dawo gidan ba sai bayan Sallah Isha'i yana shigowa Mama ta hada mu gaba daya ta yi mana nasiha shi kuma ta ja masa kunne akan zagin da yayi min dazun a gaban Abbah. “Raina ne ya bace Mama Noor ce ta yi laifin Amman gurinki yake maida laifi, kuma ita ja hakan ya faru, ba wai na zage ta dan yana tsaye a gurin ba ne, Wallahi zuciyata ce ta rufe na yi mata zagin” “Toh ka rika danne zuciyarka dan Allah ka rika kawar da ido akan komai, ka samu ku rabu lafiya da mahaifinku” Yaya amsa da In Shaa Allahu sannan ya tashi ya dauko kayan da ya wanke ya shimfida tabarma a waje ya fara gogewa da dutsen karfe na wuta. Sai da ya gama goge na shi sannan na dauko Abayata ya goge min ya nade min ya kawo min har inda nake zaune ya mika min. “Na gode Yayana” Murmushi kawai yayi min ya juya ya shige dakinsa na kalli Hana dake sauraren littafi a wayar Mama na ce. “Kin gani ba irinki ba, ke baki da nasiha ko tufafinki aka taba sai kin fara fada” Uffan bata ce min ba gaba daya hankalinta ya tattara ya koma gurin wayar dake makale a kunnenta. Sai dai sallamar da Abbah yayi ya saka ta yi saurin cire wayar ta tashi zaune ni kuma na amsa sallamar na masa sannu da zuwa na shige dakinmu, shigata da mintuna kadan Hana ta shigo. Daga ni har ita babu wanda ya sake fita dakin gar garin Allah ya waye. Kamar yadda muka saba Hana ce take hada mana abun karyawa saboda ita ce mai zuwa makaranta, saboda haka da wuri take tashi ta dumama mana idan an raga abinci idan kuma koko za a siyo ko a dama duk ita ce take yi. Sai dai yau ni dai bana sha'awar cin dumame dan haka ban fito na karbi nawa ba sai da na ji motsin Yaya Nabil yana magana da Mama a tsakar gida. Fitowa na yi na zauna bakin kofar dakinmu a lokacin Hana ta dade da wuce makarantar boko. “Yaya ina kwana” “Lafiya Kalau sai yanzu kika tashi” “Tun dazun ta tashi, wai ita yau bata son dumame shi ne taki fitowa ta karba” Mama ta fada tana juyowa ta kalleni. Yaya Yayi murmushi ya girgiza kai. “Ni dai yau ba ni da ko sisi idan zaki ci dumame ki ci, idan ba zaki ci ba cikinki ne” “Yaya dan Allah ka siya min indomie Wallahi bana son dumeme kullum shi muke ci” Mama ta saka dariya. “Wuya bata ci ba yarinya, idan kika ji yunwa da kanki zaki nemi tuwon ma” Mama ta tashi ta shige dakinta, Yaya kuma yayi fitarsa aka bar ni a gurin zaune, sai da na ga babu sarki sai Allah na dauki kwano na gutsira tuwon kadan na ci na aje sauran, tsintsiya na dauka na share ko'ina na gyara daman wanki da wanke wanke ko girki ba nawa ba ne, a cikin aikin gidan babu abun da na tsana kamar wanke wanke da wanki, girki kuma Mama ta fi sha'awa ta girka da kanta, ba kasafai take bari muna mata girki ba. Misalin karfe biyu da mintun Hana ta dawo daga makaranta, ita kam bata tsaya neman wani abincin ba ta saka dumamen da na ce ba zan ci ba ta cinye abunta ta bar ni da yunwa a ciki. Ina tsaka da miyar ta cinye min tuwo kawata Zee ta shigo gidan cikin shirinta na ankon kamu, ba karamin burge ni ta yi ba domin ta yi kyau sosai ankon ya karbe ta gashi ni ban yi ba, sai yabon kyauta nake. “Mama kin gani sai da na ce Yaya yayi min ankon nan ya ki” “Komai dai Yayanki, ki rika tausaya masa mana Noor abun ai sai ya masa yawa, komai dai shi ne, me yasa baki ce Zafeer yayi miki ba?” Na kalli Mama dake kare danta. “Shi ai be da kudi” “Shi kuma yayanki banki ne ko?” Na turo baki gabana ina son yi mata kukan shagwaba. “Yanzu kuma ko sisi ba ni da na tafiya bikin nan fa” “Daina kallona Wallahi ni ma ba ni da ko naira” Zee ta saka mana dariya. “Ashe kuwa ba za aje da ke ba, ni ma ba ni da kudin tafiya, na san dawowa ba zai yi wahala ba saboda samari” “Bari na tafi gurin Yaya ina binsa kudi 700 ya bani ko 200 na samu na napep” Na tashi na zuba ruwa a bokita na shiga bandaki na yi wanka na fito na shafa mai na dauki hodar Hana na shafa da jan bakinta na yi kwalliya na yi kyau sosai sannan na saka abayata na dora mayafin, na fito daga dakin na bar Zee tana kara gyara fuskarta sa kayan kwalliyar Hana dake ta yi mana masifa wai sai mun biyata ai kwaliyar kudi take ba kyauta ba. “Daga nan zaki iya tafiya a kafa har gurin aikinsa? Kuma kika sani ko yana da kudin ko babu, wannan tafiyar kamar ta dole Noor?” Mama ta fara kokarin hana ni, aiko take na bata fuska. “Mama komai fa ban tafi ba na Salwa kuma wannan ne event na karshe ni dai ina son zuwa, kuma Yaya ba zai rasa kudin da zai ba ni” “Allah ya kiyaye ga ki ga hanya, idan be ga dama ba ai ba zai baki ba, ko ma ya hana ki tafiya bikin” Na saka talkamina na high hill na fice daga gidan, ba a kafa na taka ba titi na isa na tari mai adaidaita sahu na fada masa inda zai kai ni yace na bada 200 naira kasancewar babu wani tazara sosai. “Kadai san Kareem Restaurant ko?” “Hajiya tun da ke kin san guri ai babu wata matsala” Na shiga Napep din ya ina ta rabon ido har muka isa Fancy Restaurant din na fito na shiga ciki domin ba wannan ne zuwana na farko ba, can ciki na wuce na yi magana da wani na fada masa ya kira min Yayana. “Yana can ciki aiki suke lafiya?” “Lafiya kalau mai Napep zan sallama kuma zan yi magana da shi” “Bari na kira shi a waya amman idan suna girki ba a bari su fita” Ina tsaye a gurin abokinsa yana ta kiransa a waya be amsa ba, hakan ya saka hankali ya dan tashi domin na san halin wasu masu Napep ba su da mutunci. Komawa na yi na leka waje na sake dawowa ganin hankalina ya tashi ya saka Yusuf tambayar nawa ne kudin napep din na fada masa sai ya saka hannunsa aljihu ya ciro 200 ya ba ni na fita da saurina na kaiwa mai Napep din. Sannan na dawo na tsaya reception din, ina ta kallon mutane da yadda ake ta sake sabunta gurin, a kullum idan ka zo sai ka ga ya sake zama sabo. “Noor yayi picking yace ki zauna ki jira shi sai sun gama girkin zai fito” Abokinsa ya fada, na kalli katon agogon dake gurin na ga uku da yan mintuna, na san ya kusan tashi aikin ma gaba daya, saboda haka na nemi guri a teburin da mutane suke zama na zauna ni kadai ina ta jin rashin sakewa saboda akwai mutane da yawa a gurin, duk kuwa da kasancewar kowa sha'anin gabansa yake. Ta dayan bangaren kuma ina jin dadin yadda sanyin Ac ke ratsa jikina, rabon da na ji sanyi ac har na manta. https://chat.whatsapp.com/ExyBEuiZZ0J1ivlVK5lIOx Assalamu Alaikum... Ina talata muku KHADEEJA CANDY STORE 🥰🙌 Muna siyar da Atamfa, Laces, Mayafai, Talkami da Jaka, Akwaituna, Kayan Kitchen, Zanen Gado, da kuma kayan kawata gida ko falo. ✧✦ 𝗧𝗔 Ƙ𝗜 𝗭𝗔𝗠𝗔𝗡 𝗔𝗨𝗥𝗘 ✦✧ 𝗕𝘆 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆 𝐂𝐡𝐚𝐩𝐭𝐞𝐫 -3 Ina zaune a gurin wasu iyalai suka shigo, ba zan iya fadar cewar masu kudi ne sosai ko akasin haka ba. Sai dai alama ta nuna suna da rufin asiri. Teburin sake gabana suka kama yan mata hudu ne sai maza uku da kuma magidancin da zan iya shaidar cewar mahaifinsu saboda kama da tsufan da yayi. Wadda ta zauna a gefensa kuma bana bukatar a fada min cewar ita din uwace domin alamu ya nuna haka. Hannu biyu na saka na yi tagumi ina kallon yadda uban yake handling yayansa mazan suka koma a dayan teburin suka zauna matan kuma suka zauna tare shi. Sai da suka fara daukar littafin dake teburin suka duba kalar abincin da suke so, tukuna daya daga cikin ma'aikatan gurin ya zo yayi taking orders. Ni kam sai kallonsu nake cike da burge, ba kudin ne abun burgewa ba, ba zuwa restaurants ko order abinci, soyayyar ce ta shiga zuciyata yadda uba yake nunawa yayansa soyayya da kauna yana ta hira da matan suna dariya mazan kuma suna jefo na su hirar daga can inda suke zaune. Wani abu ne da ni na rasa tun tashina, ban tana zama da mahaifina ya tambaye damuwata ko dadi ba, wata hirar farincikin bata taba hada ni da shi ba, ban taba aikata wani abu ya nuna jindadinsa. “Noor....” Na juyo dama da ni sai na yi arba da Yayana, hannayensa na ji a fuskata yana share min hawayen da ban san sun zubo ba. “Kuka kike yi? Saboda na dade?” Ya tambaya saboda ya san ni da kukan shagwaba kamar wata wadda ta tashi cikin gata. Sai na girgiza masa kai na juya na kalli mutanen “Wani abu da na rasa nake kallon wasu da suke da shi, kalli yadda suke cin abinci tare da Babansu be burge ka ba Yaya?” Ya daga kai ya kalli gurin kamin ya dube yana sauke ajiyar zuciya. “Wata rana ina jin kamar hakan zai faru amman na san ba zai taba faruwa ba” “Kin cika tunani da yawa, a kawo miki wani abu zaki ci?” Na saka hannuna da kaina na share hawayen da suka sake zubo min na dubi Yaya dake sanye da uniform din gurin sai tausayinsa ya kama ni, na san yayana ba mutum ne mai son zaman banza ba, yana da kokarin nema, saboda dukanmu mun taso a rayuwar talauci mun san babu kuma mun saba da hakan. A aljihunsa ake samun kudin chefane gidanmu a kullum kuma da kudinshi Mama take zuba adashe tana mana tanadin kayan aure. “Wa zai biya? Ni ba ruwana bana da ko shishi...” Yayi dariya domin ya san kadan daga halina ne zan iya komai ko bana da ko sisi sai dai duk abun da zai faru ya faru. “Za a cire salary” “Toh a kawo, daman Yaya ban ci komai ba tun safe, kuma ban taba cin abinci a Restaurant ba” “Me kika so?” “Akawo naman kaza da na kayan ciki da shawarma da pizza da...” Ban gama zanawa ba ya katsene. “Ke fa baki da hankali, duk plate daya a nan 5k plate nawa zaki ci?” Na bude baki na kalli mutanen gabana na kirga si na kirga kudin da za su kashe. “Tab toh Yaya a kawo kaza” “Kaza 10k ne ke kuma abun da zaki ci ba zai wuce 2k” “Toh ai ka ce 5k ne plate” “Rabi zan kawo miki” Be jira abun da zan ce ba ya juya ya bar ni a gurin zaune. Babu jimawa ya dawo rike da plate wata yar shimkafa ce kamar na roka sai wani kofin lemu da gorar ruwa mai yawa. “Yaya wannan ba zai ce min komai ba, iya halshe zai tsaya” “Masu kudi kadan suke ci ki yi cin masu kudi, ko baki ga yadda Restaurant din yake ba?” Ya zare min ido sannan ya tafi ya bar ni a gurin. Ba dan kar nutane su kalle ni da ba zan ci wannan abinci ba, wannan ai rowa Yaya yake min a gurin aikinsa. Na daure na kai zuciyata nesa na cinye abincin nan tass ko shimkafa daya ban bari a gurin ba, lemun ma duka na shanye sannan na dauki ruwan na sha. Kamin na mike tsaye sai ga Yaya ya zo yana kokarin dauke kayan har da ruwan aiko na saka hannu na dauke ruwana, gudun siyar da hali yasa be ce min komai ba ya shiga ciki da kayan, babu jimawa ya fito sanye da kayansa na gida ya rika hannuna muka kama hanyar fita. “Mi zaki yi da gorar ruwa wane irin kauyanci ne wannan Noor dan Allah ki aje” “Wallahi ba zan jefar ba, ai ba kyau wulakanta ruwa, kuma ai siya muka yi ba sata ba” Ina jinsa yana jan tsaki amman ban jefar da ruwana ba, ko ba komai kowa ya gani zai san na ci abinci a gurin, masu kudi ma haka nake ganin suna yi ai, suna rike gorar ruwa a hannu idan suna yawa. Sai da muka fita gate din gurin gaba daya sannan yake tambaya me ya kawo ni ma. “Yaya kudina zaka ba ni, bikin salwa zan je, dari bakwai daka ara zaka ba ni abuna” Ya daka min tsawa. “Ba salwa ba kwai, yanxu saboda bikin wata Salwa kika kwaso kafa kika zo har gurin da nake aiki har da aron na Napep, kuma sau nawa zan biyaki bashinki ne Noor shekarab jiya kin karbi dari biyu last week na baki dari uku dari biyu kawai kika biyo ni, kuma yanzu kin hau Napep da ita, gashi nan kin saka ni siyen plate daya 5k sakaryar yarinya kawai” Ban san lokacin da na tsayar da tafiyar da nake na dube shi. “Yaya wannan abincin da naman kahirar ne 5k? Kam bala'i Wallahi a ana zalimci duniya, kuma ni kudina 700 ne” “Da yardar Allah ba zan sake rantar kudinki ba, ke idan an ari kudinki babu zaman lafiya, kuma sai ki rika kari saboda baki tsoron Allah” Yana masifar yana tare mai adaidaita, yadda fuskarsa ta hade sai ka rantse da Allah ba shi ne yake tarairayata a cikin restaurant din ba. “Kuma wannan abincin da kika ci bashi ne sai kin biya. Malam Wurno Road” Ya karasa yana magana da mai adaidaita sahun. “Yaya ba gida zamu je ba?” “Ban sani ba, kuma Allah yasa mu je kin zubar min da mutunci mu koma gida ki ga yadda zan miki wulakanci” “Toh wai ni nace ka kawo min abinci? Ba kai ka ba ni ba dan kanka to miye na masifa kuma” “Saboda dari bakwai kika zo har gurin aikina, kuma idan ban kawo miki wani abu abokan aikina ai za su min gulma, kuma kin ba ni tausayi da farko” Ban yarda na sake cewa komai ba, domin abu ne mai sauke ya sauke ni a hanyar ya tafi ya bar ni, na lura ba karamin hawa yayi wannan masifar da yake ta min kamar na ce ya ba ni abinci a dole. Tun da muka shigo unguwar mai adaidaita be tsaya ko'ina ba har sai da Yaya ya bukaci haka. Gaban wani katon gida ya faka Yaya ya fito ya saka hannunsa aljihu ya ciro kudi ya bawa mai adaidainta. “Zai wuce da ke gida” Ina jin haka na yi saurin fita cikin Napep din na fara yi masa magiya ina kuka. Har ga Allah ba zan yarda ya shiga wannan katon gidan ba tare da ni ba, ko ba komai ai zan bawa idanuwana abinci. “Yaya ka yi hakuri dan Allah karka ce ya wuce da ni gida, tare da kai zan tafi dan Allah Yaya ka yi hakuri, na yafe maka 700 din ka yi hakuri Yaya dan Allah” “Ba biki zaki ba?” “Na fasa” Ya tsaya yana kallona kamar wadda ya rasa ya zai yi da ni. Ni ko sai rokonsa nake ina magiya kamar wadda za a saka a cikin wata ni'ima. Ganin haka ya saka ya sallami mai Napep din ya nufi gate din gidan dake rufe. Kwankwasa yayi aka bude masa farin gate din muka shiga ciki yana gaisawa da masu tsaron kofar. Galala na yi ina tafiya ina kallon yadda gidan ya tsaru da abubuwa gidan sama har hawa biyu, gashi komai na gidan fari ne tun daga motoci har fentin gidan, wata babbar kofar ya nufa ya danna door bell sannan yaja ya tsaya, kallo daya yayi min na natsu sa kyau na sauke kaina kasa, ba sai ya tuna min ba, ni ma ai ina ganin yadda komai yake tsare na san gidan masu alfarma ne. Wata yar lukutar yarinya ce ta bude mana kofar, fara ce sosai babu alamar kashi a jikinta tsokoki ne suke ta rawa kamar wata tufa. “Tine babanki na nan?” “Eh ku shigo” Yaya ne ya fara wuce sannan na shiga ina maimaita sunan nata da yayi min kama da ba kafirai. Suuuuuu na fara jin sanyin ac na ratsani irin tsarin nan na musamman, wannan sanyin ya ci uban na wanda na ji a Restaurant. Da katon Tv na fara arba indiawa dake ciki suna magana kai kace fasa tv za su yi su fito, ga wani kamshin turare da ke tashi kamar dakin Amarya. Ban raina kaina ba sai da na zauna a kujerar da Yaya ya zauna, wani kalar laushi na ji da ban taba jin na zauna a makamancin abu na ji haka ba. Idanuwa suka ce me muka zo yi ba kallo ba, a nan na fara tantance komai na katon falon da ya kasance fari kamar yadda curtains din da labulaye suke, wata kalar wuta ce a rufin mai blue sai haskowa take. A hankali na sauke idona gurin stairs da aka kawata kamar ba za a mutu ba, a nan na lura da kasan ba tile ba ne, ba kuma suminti ba, wani abu ne mai tsantsi da daukar ido aka malaya a gaba daya falon har zuwa inda muke zaune, ga wani zare zare da aka saka a ciki kamar maciji. “Yaya Yaya Yaya” Na kira sunansa na taba shi ya nuna masa wutar sama dake blinking na nuna masa tv na nuna masa tile din sannan na matse hannuna ina masa rada. “Ac ac ac, sanyi dadi, kujera laushi, kamshi ko'ina ko Yaya?” Da sauri ya kawar da fuskarsa yayi kamar be gan ni, can kuma ban san abun da zuciyarsa ta raya masa ba, sai ganin na yi ya mike tsaye ya kama hannuna na Mike tsaye muka nufi kofa ya bude kofar ya tura ni waje ya rufe. Ba dan ina da zuciya mai kyau ba Wallahi da na nuna masa tijara na koma ciki da karfi, daga zuwa gidan masu arziki sai wulakanci ta biyo baya, miye laifina dan na ga wani abu ya burge ni, ina ce ban taba gani ba sai yau. Kuma gidanmu ai ba ac nake ba fankar dakinmu ma ta lalace kullum a zafi muke bachi. A raina na yi guntun tsaki, ina jin haushin yadda be bari na ga mutanen gidan ba, wata kila ma su kawo masa wani abu mai dadi ya ci shi kadai ko ma me ya zo yi a gidan oho, ta dayan bangaren kuma ina mamakin Ina Yaya ya san masu arziki haka. Entrance na nufa na tsaya a gurin na rumgume hannayena tare da gorar ruwan sa na yi guzuri, ina kallon kofar falon ko za a bude. “Who's this?” Wani mutun ne tsaye a gefena rike da laptop a hannuna yana kallona. “Noor...” Na amsa masa ina dauke kai irin dauke kan dake nuna fushi nake. “Me kike yi a nan? Can i help you?” “No ina tare da wani ne” “Wani?” “Nabil” “Okay” Har ya wuce sai kuma ya dawo baya kadan ya kalleni. “Me sa kika tsaya a waje? Ke budurwarsa ce?” Kallonsa nake jin yake yake kokarin kure hakurina da tambayoyi kamar wani dan jarida. “Me yasa kake ta tambaya haka? Kai ne mai gidan nan ne ko kuma me?” Ya daga kasansa ya Kalli gidan, da alama dai shi ma bako ne domin yanayin kallon da yake ya nuna haka. “Aa ni yaron mai gidan nan” “Daman ai baka yi kama da mai gidan ba” Ya dan bude ido ya daga gira kadan yana kallona. “Haka ne, ke budurwar Nabil ce?” “Ni kanwarsa ce, mun fito daga wata Stupid Restaurant ne yace na rakoshi nan” “Stupid Restaurant?” Tambayata yake kamar mai mamaki shi ma dai da alama bakauye ne kamar ni. “Eh mana idan ba Stupid Restaurant ba, ina za a siyar da abinci haka haka ba wai 5k” Na nuna masa kam akaifata, sai yayi murmushi ya kara juyowa da kyau kamar mai jindadin zancen. “Abinci akwai tsada ne?” “Sosai ni zan iya cinye plate goma ma ban koshi ba, sai wani munafukin lemu da ake zubawa a cup, da ruwa ka ga ragowar ruwan nan na zo da shi, wai Yaya na jefar na Jefar ni kuwa na ki, har da wani cewa wai masu kudi ai kadan suke ci su koshi, masu kudi dan ba su san darajar naira ba za su je wannan gurin su ci abinci har na 5k wai kazar ma 10k ji fa? Saboda yan raina yan Nigeria, Mtseee” Na ja guntun tsaki. “Amman da gaske ke za ki iya cinye abincin plate goma?” “Tsab kuwa” Ya kalleni daga kasa zuwa sama kamar mai auna idan zan iya ko ba zan iya ba. “Haka nake ba kiba sai ci, hahaha” Na yi dariyar kunya kamin ya fara kokarin kare kaina. “Wasa nake na koshi” Yayi murmushi mai sauti. Sannan ya miko min hannunsa daya. “Nice to meet you....” “Noor...” Na fada masa, sannan na duba ko'ina na ga babu mai ganina na mika masa hannuna, daman can gaisawa da maza na daga cikin abun da yake matukar burgeni. “Kai me ye sunanka?” “Kareem, you can call me Kareem” “Nice, nan gidan kake zama?” “Ba sosai ba, mai gidan be cika son ina zama ba” Ya amsa ni, ni kam ban yi mamakin amsar ba. “Ai dole yayi wulakanci wadanda ba su kai shi kudi ba ma suna wulakanci balle mai wannan gidan, kana gani ka san mai kudi ne sosai” Na fada, sai ya sake daga kamshi yana kallon gidan. “Not really yana da rufin asiri dai” “Ba wani rufin asiri yana da kudi sosai Wallahi, kai dan Allah wannan gidan be burge ka ba?” Yayi murmushi, a madadin ya amsa ni sai ya jefo min wata tambayar. “Me yasa kika tsaya a waje? Da kin shiga ciki kin ga yadda cikin yake ai” “Na shiga fa, amman Yaya ya fito da ni kar na masa kauyanci” Be sake ce min komai ba ya nufi kofar ya bude, sai ya juyo ya kalleni yayi alama da na zo na shiga da kai. Abun nema ya samu haka na taka na nufi kofar na shige cikin falon, sai dai wani abun da ya daure min kai kuma ya ba ni mamaki shi ne mikewar da Yaya Nabil na yi zaton ko zai sake korani waje ne sai na ga ya risina yana mikawa mutumen dake baya gaisuwa. “Ranka ya dade barka da yamma” “Nabil ya gida?” “Lafiya Kalau Oga, ban samu zuwa tare da Coworkers dina na duba ka dazun saboda ina can ciki gurin girki, shi ne na yanke shawara sai na tashi aiki sai na zo na gaishe ka” “Ka kyauta have a seat please” Ya nuna masa kujera sannan shi ma ya zauna, ni dai tsabar mamaki sai na tafi zan zauna a kasa saboda kunya da daurewar kai. “Karki zauna a kasa mana, ga kujera” Ya nuna min kujerar da Yaya yake zaune. Sai Yaya ya bugu kafadata. “Ki gaishe shi mana, oganmu ne, shi ne mai Restaurant din da muke aiki” Kulololo na ji cikina yayi wani kuka kamar na yunwa, har sai da ya kalleni hakan kuma be hana ni zubewa kasa na sabunta gaisuwata ba. “Ina wuni” “Mun gaisa a waje ai, kin tuna? Tashi ki zauna” Na mike tsaye ina juyawa na kalli Yaya Nabil sai ya watsa min wani mugun kallo. Na yi saurin sauke idona kasa ina jin kamar na tsargi kaina. “Toh ai Yaya baka fada min oganka ba ne, ao ya za'ayi na sani...” Na yi zaton a zuciyata nake maganar ashe ta fito ban sani ba, har sai da ogan da ban gama yarda shi ne mai gidan ba ya amsa ni. “Toh me kika yi? You're just friendly that's” Da sauri na rufe bakina, wata sabuwar kunya na kara rufeni, kamin na daga kai ina kallon wata mata dake saukowa a stairs, babu wani walwala a tare da ita, shi ma kuma mai gidan na lura da yadda fuskarsa ya sauya daga murmushin da yake min zuwa hade fuska irin na mazan da basa son wasa. “Nabil” “Hajiya ina wuni?” “Lafiya Kalau ya aiki?” “Alhamdullahi” Ni ma na gaishe ta sai ta amsa min fuska a sake, sai dai bata yarda ko gefen da mijinta yake ta kalla ba, shi ma kuma sai yayi kamar be san da wanzuwarta a cikin falon ba. Har ta nufi wata hanyar da nake kyautata zaton kitchen ne. Yaya Nabil ya mike tsaye ya kalleni ni ma sai na mike tsaye. “Zamu wuce oga Allah kara lafiya yasa kaffara ne” “Ameen na gode” Ni dai ban ce komai ba, na bi bayan Yaya ina kallon kofar da matar ta shiga. “Nabil” Yaya ya juyo da sauri yana kallon ogan nasa da ya kirashi. “Ranka ya dade” “Ka koma da ita Restaurant ta zabi duk abun da take so, Noor sai an jima ko?” Ya karasa yana kallona da Murmushi a fuskarsa kamar ba shi ba, wani kyakkyawan murmushi na aika masa mai kayatarwa sa jan hankali saboda jindadin yace a ba ni duk abun da nake so. “Amman... Okay Sir mun gode sosai Allah ya kara rufa asiri” “Thank You” Na fada in a low voice gudun kar matarsa ta ji ta fito tace zata min duka, domin na lura matan auren yanzu ba su da hankali akan mazanjesu sai su yi ma mace duka. Hannu ya dago min alamar bye bye sannan na juya muka cire tare da Yaya. Rufe kofar falon ke da wuya Yaya ya fara tambayata me na yi. “Ban yi komai ba, amman Yaya baka lura ba? Kamar baya zaman lafiya da matarsa ko?” Yaya janyo hannuna da sauri muka sauko daga gurin. “Wallahi ba dan wani abu ba, da sai na ce masa ina gyaran aure saboda na ci kudi, na ce masa ni mai bada shawarware ni akan aure.... Kuma yana da kyau ko Yaya? Wannan lukutar yarinyar yarsa ce? Matarsa ma kyakkyawa ce ko Yaya?” Muna tafiya ina fadar abun da ke zuciyata a iyakar gaskiyata. “Ban sani ba, Noor Ban taba sanin baki da hankali ba, sai yau gidansa fa ko'ina camara ne har da wani fadar kina gyaran auren saboda baki da hankali, shiyasa kika nace sai kin biyo saboda ki zubar min da mutunci” Be sake hannuna ba sai da muka fito daga cikin gidan gaba daya. A raina ina ta ayyana irin takeaway da zan yi ma rabin raina Zafeer idan mun koma restaurant din... https://chat.whatsapp.com/ExyBEuiZZ0J1ivlVK5lIOx ✧✦ 𝗧𝗔 Ƙ𝗜 𝗭𝗔𝗠𝗔𝗡 𝗔𝗨𝗥𝗘 ✦✧ 𝗕𝘆 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆 𝐂𝐡𝐚𝐩𝐭𝐞𝐫 -4 KAREEM POV. After fitarsu, Yusura ta fito daga kitchen rike da cup din ruwa. “Me za a girka anjima?” Daf da zata wuce shi tambaya. Ba tare da ya kalleta ba ya amsa. “Ba a gida zan ci abincin dare ba” Ta daga kadunta alamar ko a jikinta sannan ya wuce ta haye sama. Mike tsaye ya saka hannunsa daya a aljihu dayan kuma rike da wayarsa a hannu ya sake cewa daga falon ya nufi gurin da ya saba zama. Sai da ya isa gurin sannan ya amsa kira na biyu dake shigowa wayarsa. “Hello” “Darling na yi missing dinka badly” “Toh ya muka iya, tun da mijinki ya ki barin gari? Sai hakuri” “Zamu iya haduwa ko yana gari...” Yayi murmushi ya shafa sajensa. “aa kar dai mu shiga hakkinsa da yawa, kar zunubin ya mana yawa, kara idan baya gari wannan kina da Hujja” “Wata kila baka yi marmarina yadda na yi marmarinka ba ko?” “Na yi mana, amman dai kar mu wuce gona da iri, kin san ai yadda nake kaunarki” “Ko kirana baka yi Kareem” “Be kamata na kira ki idan mijinki yana gari ba, akwai abubuwan da na iyakancewa kaina aikatasu, Safeena dole muna hakuri da wani abun fa” “Kawai dai baka so na kamar yadda nake son ka shiyasa” Ya shafa kansa yayi murmushi. “You're the love of my life, ke kadai kika na aikata wani aiki da zai ba ni zunubi mai yawa Safeena, ke kin sani idan bana sonki ba zan yarda wata mu'alama ta hada mu ba haka ne?” “Eh amman...” Sai kuma ta yi shiru kamar wadda ta rasa abin cewa. “Yau na ga wata yarinya mai yanayi da ke, har ta fiki wauta da sakarci ma” Yana maganar yana murmushi. “A ina ka ganta?” Ta tambaya daga dayan bangaren. “Wani yarona na gurin aiki ne ya zo duba ni sai ta biyo shi, ina kallonta ke nake ta tunawa” Shiru ne ya biyo baya har na tsawon lokaci. “Safeena...” Ya kira sunanta sai ta amsa masa da muryar dake nuna ta damu. “No wait ba abun da kike tunani ba ne, ke kin cika kishi fa, ba yadda kike zato ba ne, babu wannan a zuciyata har abada ke kadai ce kwallin kwal...” Ta sauke ajiyar zuciyata. “Duk ranar da ka so wata Kareem zan iya mutuwa” “Ba zaki mutu ba, saboda ba zan so ba, na san yadda kike da tsananin kishi ai, zan kiyaye” “Ina fatan haka” “Ina mijikinki yake?” “Yana daki, ni kuma ina harabar gida ne” “Ni ma ina harabar gidan, amman yanxu zan fita, je ki samu mijinki zamu yi magana anjima” “Okay i love you” “I love you too” Ya sauke wayar yana murmushi. Kana ya busar da iskar bakinsa ya sake shafa kansa ya sauko zuwa sajensa. Sannan ya juyo ya fito daga garden din ya nufo cikin gidan. Ganin kofar falon bude ya fahimtar da shi bako ya shigo gidan, domin daga shi har matarshi da yaransa biyu basa barin kofa a bude. Be karasa ba ya ji sautin kuka da kara mai razanarwa da muryar da be tantance ba. Hakan ya kasa shi cira kafa ya shiga falon da sauri. Yarinyar da ta fita dazun ya gani tsaye kusa da kofar rike da kai tana ihu, Yusura na tsaye gabanta rike da glass cup. “Me ke faruwa a nan?” Yarinyar ta juyo ta kalleshi da sauri sai ta kara rushewa da kuka. “Wai daga na shigo ina nemanka sai ta buga min cup din ruwa akai kalla har yayi jini” Ta nuna masa jinin hannunsa. Sai ya juya ya kalli Yusura. “Why?” “Rashin kunya ta yi min” Ta ba shi amsa babu alamar wasa a fuskarka. Yarinyar ta girgiza kai da sauri. “Wallahi karya take komai ban ce mata ba, kawai na shigo nace dan Allah ina mai gidan nan, mijinta shi ne kawai ta buga min cup a kai” Kareem ya juya ya kalli Yusura dake tsaye rike da cup din. “Kishi kike?” “Kishi?” Ta maimaita tana ja baya tare da yin dariyar rainin wayo. “Kishi dai kishi? Na rasa waye zan yi kishi sai kai? Allah ya tsare gatarina da saran shuka mtscheeeeeeee” Taja dogon tsaki ta juya ya bar musu gurin. Kareem ya kalli yarinyar da jini ke fita a goshinta yace “Me yasa kika dawo?” “Yaya ya tafi abun shi, wai ba zai koma restaurant din ba, kuma zai buga waya ya fada musu karya nake kar a bani, yana ta min fada a hanya, kuma yace ba zan bishi gida ba sai dai kowa yayi tafiyarsa, shi ne ya saka a Napep yace ya kai ni gida, ni kuma sai da muka yi nisa sai na cewa mai napep din ya dawo da ni nan gidan amman ya biyo wata hanya da Yaya ba zai gani ba, kuma yana waje ban bashi kudi ba” “All this long story ban gane me kike nufi ba” “Ina nufin Yaya so yake na tafi gida ba tare da na karba kyautar da ka ba ni ba, kuma yace ba zai tafi da ni can din ba” Ya rike kunkurunsa yana murmushin da ya kusa zame masa dariya. “Ammm ya ma sunanki?” “Noor sau uku kenan ina fada maka” “Yanzu ba zan sake mantawa ba, I'm sorry yanzu muje a duba kanki...” Ta juya tana rike da goshin ta fita daga falon, sai ya bi bayanta har sun saka entrance din sun isa gurin motarsa ya tuna keys dinsa basa aljihunsa. “Noor jira ni a nan zan dauko keys dina” “Toh amman ka yi sauri kar ta fito” Yayi murmushi. “Ba zata sake fitowa ba” Ya juya ya koma cikin falon, kai tsaye sama ya nufa ya shiga dakinsa ya dauko keys din, ya nufo curtains dinsa dake dage zai sauke kasa sai ya hango Noor tsaye a inda ya barta sai daga hannu take bakinta na motsi da alama masifa take, hakan ya saka shi saurin saukowa domin yayi tunanin ko Yusura ce tsaye jikin kofar falon, saboda ya hango kofar take kallo. Ga mamakin sai ga ita kadai ce take fadan tana kallon kofar falon. Sai da yaja kofar sannan ya nufi Motar ya bude sai da ya fara shiga sannan Noor ta shiga, yayi reverse ya fice gidan, tuki yake a hankali yana kallon yadda Noor ta natsu sam ba zaka ce tana da yawan magana ko kiriniya ba, babu wannan alamar a fuskarta da jikinta natsassiya ce sosai idan bata bude baki ba. NOOR POV. Shiga motar alfarma irin wadda ban taba shiga ba, ga wani sanyi ac mai dadi da laushi yana ratsa fatata ya saka natsu sosai ina jin yadda duniyar masu arziki take da dadi, sam na manta da ciwon da mahaukaciyar matar ogan su Yaya ta ji min a goshi har sai da muka isa wata babbar Asibiti, ni da nake zaton chemist zai kai ni domin ciwon ba wani babba ne ba. Fakawa yayi a gaban kofar emergency baya tsoron ma su masa fada. “Za su maka fada basa bari a faka a nan ” Daf da zai fita na fada masa haka sai ya juyo ya kalleni yayi min murmushi, da alama dai murmushi al'adarsa ce, ko ba komai ai yana masa kyau. Wani abun da ya ba ni mamaki shi ne har muka shiga cikin asibitin gaishe shi ake kuma babu wanda yace masa komai a yanayin yadda ya faka motarsa. Wani karamin daki da zan iya kira da office ya shiga da ni, yaja min kujera. “Zauna” Ya fada, sai na zauna kamar yadda ya bukata ina rabbata masa yadda komai ya faru. “Ina yin sallama fa na ga ta sauko sai na ce mata ina wuni tace lafiya kalau, sai na ce dan Allah mai gidanki yana nan, sai tace me kike nemansa, na ce mata ni ce yarinyar da yace na je restaurant na karbi abu ina son magana da shi, kawai sai ta matso kusa da ni ta buga min cup, bata ma tsaya ta ji ko miye ba, ni ai ba soyayya muke ba balle ta yi kishi ko?” Ya dauke idonsa daga kallon waya da yake ya kalleni. “Ba kishi take ba, kawai dai kaddara ta hau kanki ne, wata kila ranta ne a bace, kin san daman irinku kaddara ta fi hawa kanku” “Kishi take mana, ta ga budurwar kyakkyawa ta yi tunanin na zo gurin mijinta ne, ni kam lalacewa ai bata kai na bi saurayana har gidansu ba” Wannan karon murmushin da ke bayyana hakoransa yayi. “Ba kishi take ba, bata taba kishina ba, kuma ba zata fara yanzu ba?” “Ba matarka ba ce?” “Matata ce” “Dole ai zata yi kishinka, iskanci kawai yayi mata yawa, ni daman tun zuwana na fahimci baku zaman lafiya, Wallahi da zaka bi shawara kawai ka yi mata kishiya” Kamin na fadi kalmar karshe sai da na rage muryata gudun kar wani ya ji, ganin nake kamar tana kusa zata iya sake rusa min wani abun akai ne. Gira biyu ya daga yana kallona kamar mai mamaki. “Wallahi ka kara aure, duk zata daina wannan halin” “Wani be taba ba ni shawarar nan ba, amman kin kawo shawara mai kyau, sai dai ni bana sha'awar auren mace sama da daya, saboda haka na zabi na mutu a haka” Na yatsina fuska zan yi magana aka turo kofar office din, wata likita ce ta shigo tana sanye da atamfa ta dora rigar likitoci a sama. “Doctor gashi, ni kam na ce lafiya ka shigo yanzu” Murmushi yayi mata ya karbi keken da ta turo masa. “kin kare kenan thank you” “Ur Welcome” Sai da ta fice sannan na kalleshi jin an kira shi da Doctor. “Kai likita ne ko?” Ya daga min kai yana saka safar hannu sannan ya rika goshina ya fara gyara min gurin, sai da ya saka min wasu ruwan azaba na gane ashe na ji ciwo sosai kawai dauriya ce da jarumta irin tawa ta saka ban yi hawaye ba sai ihu. Idona ya kai gurin katon hotonsa dake office din yana sanye da suit a kasan hoton an rubuta masa Dr Kareem. Mamaki ya cika ni sai a lokacin hankali ya karkata akan abun da ya kamata na gane tuntuni. “Kai ne Dr Kareem? Ana yawan fadarka har a redio ana hira da kai laaa ashe kai ne” “Kina jin labarina kenan?” Ya saki kaina bayan ya gama rufe min raunin. “Sosai... Laaa amman Yaya be taba fada min kai ne Dr Kareem ba, kuma be taba fada min kai ne mai Kareem Restaurant ba...” “Toh ai baki san ni ba, shiyasa be fada miki ba” “Haka ne” Na fada ina kallonsa cike da burgewa domin likita ne da yayi kaurin suna a garin nan, sai dai ban taba zaton zan ganshi bagas a arha haka ba. “Wai mutane suke cewa wai idan mace ta yi cikin shege ko kuna unwanted ciki domin da ta zo gurin Dr Kareem zai zubar mata, haka suke fada wai gaskiya ne?” Ba da wata manufa na yi tambayar ba, tambayar abun da nake son sani ne akansa a iyakar gaskiyata domin haka mutane suke yawan fada akansa shiyasa ake cewa yana da kudi sosai. Sai dai yanayin yadda na ga ya dago ya kalleni ya razanar da ni, ni ko a ganina tambaya ce kawai na yi domin hausawa sun ce waka a bakin mai ita tafi dadi. Matsowa yayi kusa da ni ya raba hannayensa biyu ya daga kujera da nake zaune yana kallon cikin idona. “Noor shekararki nawa?” Na yi saurin sauke idona kasa na kama jikina sosai zuciyata na bugawa. “Ka ba ni tsoro” Sai yayi murmushi ya dauke hannayensa ya matsa baya. “Aa sheri suke min kin san mutane akwai hassada, hassada ce kawai” Ni dai na yi shiru domin jikina na bani da farko kamar tambayar ta wa bata masa dadi ba, ko kuma ya fahimta a baibaiye ne. “Kin san me yasa na tambaya shekarun ki?” Yana tambayar yana kallona, na girgiza kai ina jin kamar duka na zai yi duk kuwa da kasancewar murmushi ne a fuskarsa. “Saboda my ex kamar ke take, zata yi tambaya any how, zata fadi duk abun da ya zo mata a bakinta, bata tunani irin na mutane ita a komai nata tunanin dabam yake, yanayin surutunki mu'alamarki sakin jiki da kowa duk haka take, ina son ki zama kawata shiyasa na tambaya shekarunki” Sai a lokacin hankalina ya kwanta, sai na yi dariya na mike tsaye. “Idan na zama kawarka hakan yana nufin idan na zo asibitin nan, kyauta za a duba ni, kuma a duk lokacin da ba ga dama zan tafi restaurant dinka na ci abin da nake so ko na karba ba zaka ce komai ba” “Huh?” Ya furta yana kallona cike da burgewa, sai na daga masa kai. “Eh shi ne abotai ai” “Shikenan na yarda” Ya furta cikin sanyi murya, yana kada kai a hankali. Farinciki ya cika ni har na kasa ce masa komai sai murmushin dake tattare da dariya nake. “Mu tafi ko?” “Toh” Na bi bayansa domin tuni yayi gaba ya bude min kofar. “Ni daman na san sheri suke maka ai da kana zubar da ciki ba zaka haifi wannan yarinyar ba, matarka zaka fara zubarwa...” Ban karasa ba na ji hannunsa ya rufe min baki, dayan hannunsa kuma a wuyana ya saka ni gaba yana turani kamar wata akuya, aiko sai na duke na subuce na juyo na kalleshi rai a bace. “Ya kana min haka sai aje ce an ga Noor wani Kato na taba ta” Ya nuna kansa. “Ni ne Katon? Beside neman mata ba halina ba ne, kowa zai iya shaidata da wannan bana neman mata, kuma na rufe bakinki ne saboda karki fadi wata maganar wasu su ji” “Na gane” Na amsa a hankali sannan na jera tare da shi muna tafiya, kana gani kasan ni kanwarsa domin ya fi ni tsayi sosai. Da kaina na Bude Motar na shiga shi ma ya shiga bangarensa a yanzu kam na gane dalilin da ya saka ba ayi masa fada ba a lokacin da ya faka mota a kofar emergency. Ban sake cewa komai ba domin na lura kamar surutuna ya fara effecting dinsa. “Noor ya na ji ki shiru, ko maganar ta kare” A lokacin da na juyo na kalleshi sai na ga kallona yake da da abun da ya zame masa wajibun wato murmushi a fuska. “Na ga ai baka son surutu ne?” “Inji waye? Ni ina son surutu sosai, shiyasa na sake da ke ba, ni mutum mai mai son wasa da dariya mai son nishadi, shiyasa kika burge yau din nan domin ina son mace da ko iska ya wuce sai ta bani labari yadda ya wuce, shiyasa nake son Ex dita amman na lura ke kamar ma kin fita” “Ex din mutuwa ta yi?” Ya girgiza kai ba tare da ya kalleni ba. “Tana nan” “To ka auro ta mana, ka aje ta a gidan ka, ka ga matarka ma ba zata sake fasawa baki kai ba saboda kishi” “Ta yi aure ai, ina miki zancen baya ne” Na yi kwafa. “Wallahi ba dan haka ba da zai na zugaka ka kara aure, ni Wallahi da ni ce kai aure zan kara matar nan ta bata min rai daga tambaya? Kamar ta ji kowa kishi” Wannan karon dariya yake min. “Matata bata kishi, babu wani abu mai alaka da kishi a tsakanina da Matata, kawai dai kin zo a rashin sa'a ne, ko dai kin mata rashin kunyar kamar yadda ta fada, kawai an rubuto jininki zai zuba a yau ne” Takaici ya hana ni cewa komai, wato bangaren matarsa zai dauka har yana yarda da zancenta ya watsar da nawa. Har muka isa restaurant din ban sake ce masa komai ba. “Me za a kawo miki?” Na dan kalleshi ina turo baki gaba. “Ai da kunya ba komai zan iya fada a nan ba, ni dai zan shiga na karba ka fada musu” Yayi shiru yana kallona kamar ba zai ce komai ba, sai kuma yayi murmushi ya daga min kai, sannan ya ciro wayarsa ya kira wadda ban san waye ba, ya fada masa wata zata shigo yanzu ya bata duk abun da take so. “Zaki iya tafiya, amman ba sai kin fadawa kowa tare muke ba, ba a taba ganina da mace ba” “Zaka iya tafiyarka ai, ni ma ba a ganina da maza, ni ma ba yar iska ba ce ba wai kai ne kadai na kwarai ba” Ina fada ina yatsina fuska domin na lura so yake ya nuna shi na kwarai ne, ni ce yar iska. “Ban ce ke yar iska ba ce, kawai ina son na kai ki gida ne cikin mutunci saboda na yi ma iyayenki bayanin yadda kika ji rauni, waya sani idan ban tafi ba za su iya dukanki” Na kalleshi da sauri na tuni ma na manta da rauni. “Eh Wallahi musamman ma Baba, bari na je na dawo to” Na bude motar na fita ina jin kaina kamar wata yar shugaban kasa, ahh a rayuwata fa ban taba shiga mota mai kyau mai tsada irin wannan ba, kuma ina fitowa motar na shiga restaurant na karbo kayan dadi, wayyo Allah ina ma yan unguwar mu za su gan ni a yau. Sai da na kusa shiga reception din sai kuma na tuna da wani abu na dawo baya da sauri na kwankwasa gilashin motarsa sai ya sauke bakin gilashin yana kallona. “Dan Allah ko zaka min alfarma idan na fito daga sai ka rufe idonka ko kuma ka fita motar har sai na saka abun da na karbo tukuna” A bakin gaskiyata nake fada masa, domin kar na kwaso kaya da yawa ya ji babu dadi ai da kunya ko, daga kyauta na wuce gona da iri kuma yana gani. “Ki ce karya min jari zaki yi ko?” Yanayin yadda yayi maganar da kamar tsoro sai ya saka dariya ta subuce min, na yi bayabaya ina tafiya da baya baya ina dariya, shi ma murmushi yake yana kallona har na juya. Ni dai iyakar abun da na sani ba zan bar wannan banzar ta wuce ni ba, ba zan yarda na fito ba tare da na dauko abun da nake so ba, waya sani ma ko ba zan sake zuwa ba, ai Yaya ba zai bari na sake zuwa ba, kuma hausawa sun ce waman taraka bati sidda fa huwa wawa au sakare, wai duk wadda ya ga bati ya bar shi shi wawa ne ko sakare. Ina shiga gurin na fada musu abubuwan da nake so, snack kala kala da naman kaza da farfesun kifi da na kayan ciki, har da wata yar tsutsa da na taba ganin turawa suna ci a tv sai da na saka aka hado min da ita yau dai ni ma zan dandana kayan masu kudi na ji me ake ji. Haka na riko leda biyar na fito ina boye ledodin a bayana dan kar ya gani, yace ba ni da hankali na kwashe masa kayan shago. A lokacin da na iso gurin motar sai ya bude min bayan motar na saka komai a ciki na rufe sannan na bude gidan gaba na shiga. Cingan na tarar yana ci yana kokarin juya motar “Ka ga me na zo da shi?” “Ba kin ce kar na kalla ba? I respect that” Ya amsa ba tare da ya kalleni ba. Hakan ba karamin dadi yayi min ba. Sai na saki jiki ina fada masa inda zai bi har muka isa unguwarmu. “Kwanar gidan mu mota bata shiga, ka aje motarka a nan ka raka ni a kafa” “Ko dai na kira Yayanki ya zo ya tafi da kai?” “Aa ko da shi ya yarda Babanmu ba zai yarda ba, kara dai kaje idan aka kira Babana ka masa bayani shi ne zan tsira, dan Allah ka min wannan alfarmar ba zan sake damunka ba daga yau na maka alkawari ba zaka sake ganina ba” Ya daga min kai, sannan ya kashe motar. Har na bude na fita sai kuma na dawo ya leka shi. “Amman ka zauna a motar sai na yi nisa sai ka biyo ni” “Saboda me?” “Saboda Saurayina idan ya gani zai ji haushi ransa zai bace yana da kishi sosai zai iya maka duka ma” Yayi murmushin kasaita. “Ni mai dukana ai sai ya shirya, zai dai yi kishi amman ba zai ina nuna min yatsa ba ma” “Yana da karfi” Na fada masa dan ya san Zafeer dina ba rago ba ne. “Yana da kudi?” “Aa” “Toh ba shi da karfi” “Ba zaka gane ba ai” “Ke ce dai ba zaki gane ba, saboda ke yarinyar ce baki san yanayin kasar nan ba” “What ever ni dai karka jera da ni, kuma zan bar maka ledodin a mota sai ka dauko min idan mun isa ka bawa Yayana ya shiga da su?” “Na dauko kuma?” “Eh ai ni mutanen unguwa za su iya fadawa Zafeer sun gan ni da ledodi manya, amman kai babu wadda ya san ka ai, ko kuma idan mun tafi ka kira Yaya ka ce ya zo ya dauki ledodin” “Toh sai dai haka” “Da nine kai ma cewa Yaya zan yi ya tafi gida yayi kwana biyu” Ya kalleni. “Saboda ya wulakanta kanwarsa, ai idan ni yarka ce ba zaka so ayi min haka ba right? Kuma ya bijirewa umarninka be kamata yayi haka ba” “Haka ne” Na fita na rufe motar na kama hanya ina fakar idon mutane, sai da na yi nisa sannan na juyo na kalleshi, bawan Allah ashe yana bayana daga can nesa yana bin sawuna. Sai da na isa bakin kofar gidanmu sannan na ja na tsaya har ya iso. “Ka aika yaro kace kana Sallama da Babanmu” “Okay” Tsakanin amsawarsa da okay da yayi da kuma fitowar Baba da ban yi zaton yana gidan a wannan lokacin ba ban san wadda ya riga wani ba. Na ja baya da sauri na koma kusa da ogan kamar zan shige jikinsa. “Toh Yar iska marar mutunci ina kika dauko wannan kuma?” Kamar yadda nayi tsammani kalma marar dadi ce ta fito daga bakin mahaifina a izuwa gareni a gaban mutumen da mahaifina be san waye ba. “Ayi hakuri ranka ya dade, dan akasi aka samu ta bugu a kai shi ne na ce bari na zo na yi muku bayani” “Ai dama mutuwa ta yi, wannan yarinyar bata da amfani a garemu, wawuyar banza yar iska, ta maka hauka ko?” Ogan Yaya ya juyo ya kalleni kamar mai mamakin jin furucin mahaifina akaina, ni kuma kunya da bakincikin suka saka na sauke kaina kasa ina taba yatsuna. “Aa kareta ta na yi ba da gangan ba, ina tare da mota ne bata lura ba ni kuma burkin be tsaya ba sai na ji mata rauni a kai kadan, shiyasa na ce zan so na yi bayani a gidansu kuma na bada kudin magani, amman ayi hakuri dan Allah ba laifinta ba ne” Baba na jin zancen mota da kudin magani sai fuskarsa ta sauya ya dan saki fuskar kadan. “Babu komai, ita ce ai bata jin magana” “Sunana Kareem Ibrahim Kalil, ni ne mai gurin da yaronka Nabil yake aiki” “Maa Shaa Allahu, ashe ma abun duk gida ne, sannu da zuwa, bari na kira shi shi ma be dade da shigowa gida ba ai” Kamin mutumen ya sake cewa komai Baba ya juya ya shiga gida. A lokaci ne ya juyo ya kalleni. “Ki yi hakuri da abun da mahaifinki ya fada, wata kila ransa ne ya bace” Na kalleshi ina murmushi. “Na saba ai, Babana yana yawan cewa ba ni da sa'a babu alheri a tare da ni” Da dare na karasa maganar irin dariyar dake tattare da bakinciki, shi kam kallona kawai yake kamin ya juya daga ni har shi mu kalli Yaya da ya fito daga cikin gidan. Cikin rawar jiki da girmamawa Yaya ya gaishe shi sannan ya kalleni. “Noor ina kika je? Na iso gida Mama tace baki zo ba, dole na koma nemanki” Na yi shiru ina turo baki, babu zato balle tsammani na tsinkayi muryar Ogan nasa yana karanta masa cewar ya zauna gida yayi kwana biyu. “Ranka ya dade laifi na yi? Ko... Ko.. Noor ta yi wani abu ne” Yana tambaya jikinsa na rawa. “Kai ne dai ka yi laifi a wane dalili zaka tafi kai dabam ita dabam? Yanzu idan wani abun ya same ta fa? Kuma na baka umarni cewar ka tafi da ita ta dauki abun da kake so baka yi haka ba? Ban isa da kai ba kenan?” “Dan girman Allah ka yi hakuri oga... Dan Allah ka yi hakuri” “Ba korarka na yi ba, amman dai ka zauna sai Monday zaka koma aiki” Wallahi ji na yi kamar na daka tsalle na dire saboda muryar lallai wannan mutumen mai saukin kaine sosai mai jin maganar mata. “Mu je mota ka karbo mata sako, Noor Allah ya tsare gaba” Ya karasa yana kallona. “Ameen” Na amsa sannan na shige cikin gida ina jin kaina kamar wata sarauniya a yau. https://chat.whatsapp.com/ExyBEuiZZ0J1ivlVK5lIOx Assalamu Alaikum... Ina talata muku KHADEEJA CANDY STORE 🥰🙌 Muna siyar da Atamfa, Laces, Mayafai, Talkami da Jaka, Akwaituna, Kayan Kitchen, Zanen Gado, da kuma kayan kawata gida ko falo. ✧✦ 𝗧𝗔 Ƙ𝗜 𝗭𝗔𝗠𝗔𝗡 𝗔𝗨𝗥𝗘 ✦✧ 𝗕𝘆 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆 𝐂𝐡𝐚𝐩𝐭𝐞𝐫 -5 KAREEM POV. After ya mika masa tsarabar Noor ya bude motar ya shiga sai Nabil ya rage tsawonsa yana bashi hakuri. “Ranka ya dade dan Allah ka yi hakuri, Wallahi ba zan sake bijirewa umarninka ba, kuma idan wani abun marar dadi Noor ta yi maka da ya saka ya kanye wannan hukuncin dan Allah ka yi hakuri” Kareem ya kirga 10k ya mike masa. “Noor bata min komai ba, kuma a yanzu ina jin hakan da na yi yayi daidai domin be kamata na baka umarni ka saba ba, ba wai na koreka ba ne noo zaka zauna ne a gida har Monday” “Toh ranka ya dade” Har Kareem yaja gambo zai rufe motar sai kuma ya kalli Nabil “Shekarar kanwarka nawa?” “Wannan watan zata yi 15” ‘Fresh one, shiyasa kanta be tsaya ba, tashen balaga take’ Ya fada a ransa a zahiri kuma sai ya sake tambayar Nabil. “Kai kuma fa?” “19 ranka ya dade” “Okay, amman tana karatu?” “Bata karatu gaskiya, bata son makaranta” “Why?” “Haka nan kawai bata son karatun, kanwarta da kusan suke tawaye tana karatu sosai amman ita bata son makaranta” “Kuma aka zuba mata ido? Baku tsoron future dinta ya lalace?” “Toh ya za'ayi ranka ya dade ai ka ga yadda take, Baba ne kawai zai iya da ita shi kuma karatun ba damuwarsa yayi ba” “Allah ya kyauta” “Ameen mun gode” Ya rufe motar ya juya, ya fice daga unguwar. Ba gida ya nufa kai tsaye ba restaurant dinsa ya sake komawa a gurin yayi sallah La'asar yana fitowa Masallacin abokinsa Hafiz na fakawa kusa da motarsa, Kareem ya karasa gurinsa ya mika masa hannu suka gaisa. “Dazun na ga motarka, na so mu yi magana amman ban san fitarka ba” Kareem yayi murmushi tunawa da Noor. “Wata bakuwa na yi mai kiriniya ita ta saka ni zuwa nan kuma na kaita gida” “Bakuwa?” Hafiz ya tambaya domin be taba jin abokinsa yayi zancen wata mace ba bayan Safeena da matarsa, ko siblings dinsa iyakarsa da su gaisuwa, sai kuma fada idan sun yi ba daidai ba. “Yeah wani yaro na ne, da yake aiki nan ya zo duba ni sai ya zo da kanwarsa to kanwarsa ce rikitacciya” Yana maganar yana murmushi maganarsa da ita yake tunawa a lokacin da take fada masa abincin restaurant dinsa yayi tsada. “Kuma ka kawo ta nan ka kaita gida? Ko dai...” Kareem yayi hanzarin katse shi yana girgiza kai “Noo kai yarinya ce irin fresh yaran nan yanzu take girma, kuma ni bayan Safeena babu kowa a raina” Hafiz yaja tsaki jin ya ambaci sunan matar da ya fi tsana a duniya fiye da kowa, matar da ta sauya dabi'u da mu'amalar amininsa zuwa wani dabam da ba shi ba. “Ya jikinka?” “Alhamdullahi na ji sauki sosai” “Amman baka shiga aiki ba yau, domin na shiga ban same ka ba, na tambaya aka ce baka shigo ba” “Na shiga da yamman nan na kai Noor na mata treatment” “Wace Noor me ya faru?” “Yarinyar da nake baka labari yanzu ita ce Noor, Yusura ce ta buga mata abu akai kan ya fashe jini ya zuba shi ne a kaita asibiti” Da mamaki Hafiz yake kallon abokin nasa. “Yusura ta fasa mata kai kace fa? How?” Kareem ya dan tabe baki yana jingina da motar Hafiz. “Yusura tace wai ta fada mata magana ne, amman ita yarinyar tace Yusura kishinta take saboda ta ga kyakkyawar budurwa” Yana maganar yana dariya, Hafiz ma yayi dariya. “And she got lucky ka kaita asibiti” “Daman wa zai kaita asibiti ba ni ba, matata fa ta fasa mata kai, a asibitin ma tambayoyi take min har da na banza wai ance ina zubar da ciki” Hafiz ya tintsire da dariya. “Kirikiri?” “Wallahi a gida ma haka ta gama ba ni labari wai restaurant dina yana da tsadar abinci, amman bata san ni ne mai restaurant din ba sai daga baya” “Zan so ganin yarinyar nan” “You better not babu ruwanta take zata fara maka maganar da ta zo bakinta, kuma ka san kai ba irina ba ne zaka iya fusata, amman labarin cikin nan ya ba ni mamaki” “Kareem kenan, ka yi kaurin suna kowa ya san kwarewarka akan iya aiki da daukar komai babu wasa, so dole makiya za su nemi hanyar da za su yada wani abun kyama game da kai” “Toh ai ni taimako kawai nake, bana cirewa sai wanda na san akwai matsala, amman masu cikin shige ni bana zubarwa” “Duk yadda zaka yi ba zaka gujewa mutane ba, wata ma cikin banza zata dauko ta zo tace maka mai matsala ne ka burke mata ta zubar” “Aa sai na yi bincike nake yi ai, ni ba shashasha ba ne irin Noor” Hafiz da sai a lokacin ya rufe motarsa ya kalli Kareem. “Muje ka bani labarin yarinyar nan there is something special about her...” Kareem ya jera da abokinsa suna tafiya ya zuba hannayensa duka biyu aljihu. Har suka isa office labarin abun da Noor ta yi masa yake ma Hafiz, and Hafiz was so excited domin ya dade yana jiran irin wannan labarin daga gurin abokinsa. “Amman be dace mahaifi ya furtawa yarsa haka ba, ko da daga ita sai shi ne balle kuma har a gaban wani” Hafiz ya fada bayan ya zauna. Kareem ya daga kafadunsa. “Ni ma shi na gani, irin haka ke sa yaro ya lalace, ni ma ban jidadi ba balle kuma ita, amman tace min ita ai ta saba, duk sai ta ba ni tausayi Wallahi, gata karamar yarinya she's just 14 no 15 this month” “Kasan fa wasu iyayen idan talauci ya halbo su ido rufewa yake” “Baka da kirki Barrister amman fa akwai alamar haka, domin daga ganin gidan nan da unguwar ma ka san suna fama da talauci ko'ina kwata” Ya fada yana ciro wayarsa dake ringing ya duba, ganin sunan Safeena ya saka shi dan shakkun dagawa a gaban Hafiz domin ya san ba karamin abu ba ne su yi fada saboda kiran, but babu yadda zai yi dole ya daga domin ba zai tana iya rejecting kiran Safeena ba kuma ba zai ga kiranta ya kasa dagawa ba. “Hello...” “Kareem guess what?” Safeena ta fada daga dayan bangaren. “Ina guest's House dinka” “Safeena i thought mun yi magana idan mijinki yana nan ba zamu ga juna ba? Dazun nan ma ba mun yi maganar nan ba?” “Na kasa rike kaina ne, kuma i have surprised for you shiyasa na zo, kawai magana za mu yi” “Shi ke nan gani nan zuwa” Ya amsa da kamar yanayin damuwa, sannan ya sauke wayar. “Yanzu baka ko jin kunya barina zaka yi a nan ka tafi ka gurinta” Cewar Hafiz cike da takaici. Kareem yayi murmushi. “Kamar baka san tsakanina da Safeena ba? Tana son ganina and i can't say No” “Ka ji tsoron Allah Kareem, kana mu'alama da matar aure macen har da yayanta hakkin ai sai ya maka yawa” “Shiyasa na ce idan mijinta yana gari ba zamu rika ganin juna ba” “Yanzu idan wani ya kwanta da matarka ya zaka ji? Amman kai kana yi ma matar wani?” “If wani ya aikata matata haka, kashe shi zan yi, ba zan iya jurar komai ba, ko da kuwa Yusura ce da bana so balle ace wadda nake so” “Amman kake aikatawa matar wani? Idan kuka mutum a wannan halin kace me? Waya sani ma ko ita ma tana tare da Ex dinta” “Ex dinta yana can kasar waje, ba dan an cilasta mata aurena ba, da yanzu tana can tare da shi suna rayuwa ni ma da yanzu da Safeena nake rayuwa, amman ya zamu yi kaddarar mu ta zo a haka” “Ka yi sabon Allah kace kaddararka ce a haka? Kareem ka raina wayon mutane Wallahi” Kareem ya busar da iskar bakinsa. “Wai da duk wannan abun why not ta kashe auren ka aureta?” Kareem ya girgiza kai da sauri saying no to Hafiz question. “Har abada, ba zan iya aurenta ba, idan ta fito gidan mijinta wa zai rike mata yayanta? Ni dai yadda nake da kishin nan kasan ba zan iya rike yayan wani ba, kuma...” Yayi shiru. “Kuma me? Ba zaka aureta ba saboda kana jin ba da kai kadai take tare ba?” “Da ni kadai take tare a yanzu na sani, amman daga lokacin da zan aureta ba ni da wannan tabbacin, what after na aureta ta koma tana mu'amala da tsohon mijinta kuma? Ko wani? Daga lokacin da na fara kaiwa jikin Safeena sai aka tsinke igiyar aminci a tsakanina da ita, for now na san ni kadai ne, amman idan na aureta ba zan samu aminci ba” “Kenan haka zamu yi ta zama har bada?” “Not har a bada, ina fatar canjin” “A hakan?” Hafiz ya tambaya yana masa wani kallo. Kareem yayi dariya grabbing his phone ya mike tsaye ya fice daga office din. “Allah ka tsare mana imaninmu ka tsare mu da auren mata irin Safeena” Ya fada yana juyawa ya bi kofar office din da kallo. Kareem na shiga motarsa ya dauki hanyar gidansa da ya gina da kansa saboda Safeena da kuma irin tsarin da take so, sai dai kaddarar rayuwa bata ba su damar zama ma'aurata ba, sai suka zama ma'aikatan aikata zunubi. Yana yin horn mai gadi ya bude masa gate sai ya shiga ya faka motarsa, yana ganin motarta ya tabbatar tana gidan kamar yadda ta fada masa. Ya bude motar ya fito ya nufi kofar falon ya saka key ya murda ta bude ya shiga. Yanayin arba da ita sai murmushi ya baibaiye fuskarsa ta taso da sauri tana kamshi turare mai karfi ta rumgume shi. “I miss you so much” Ta fada tana shafa fuskarsa, bakinta ya sumbanta ya rike bayanta. “I miss you too, kwana biyun nan da baki kusa kamar na yi hauka” Ta yi dariyar jindadi. “Ba ga matarka ba?” “Matata ai kin san once in a month ne, amman ke kullum ne, kin san yadda nake sonki ai” Ta sake yin murmushi ya kai bakinsa cikin nata, sun dauki lokaci a haka kamin ya cire bakinsa. “Yau kam ba zamu wuce nan ba, Safeena ina son ki rika jin maganata, na fada miki idan mijinki yana nan ba zamu rika haduwa ba” “Na sani, yanzu kawai na zo maka da abun mamaki ne kuma abun Farinciki” “Surprised din me ne?” Ya tambaya yana kokarin raba jikinsa da nata, sai ta yi baya ta nufi jakarta ta bude ta dauko abu sannan ta boye a bayanta. “Rufe idonka” Ya rufe idon yana murmushi har sai da ya ji matsowarta kusa da shi ta ce ya bude sannan ya bude. Yana yin arba da surprised din sai murmushin dake fuskarsa ya gushe, mamaki ya koma masa tashin hankali. “Innalilillahi Wa'inna Ilaihirraji'un” Ya furta har sau biyu sannan ya karbi PT scrip din yana dubawa. “Me hakan yake nufi?” “Ciki mana Kareem, kai fa likita ne” Ta fada cikin tsananin farinciki, da tsammanin shi ma farincikin zai yi. A take ya ji gaba daya tsigar jikinsa tana tashi. “Cikin waye Safeena?” “Cikin Kareem, mijina shekaranjiya ya dawo ai ba za ace na yi cikin tsakanin jiya zuwa yau ba, kuma tun da liyin ya nuna sosai that's mean cikin ya dade, kasan for the whole 3 months muna tare, I'm happy Kareem zan haifi ďanka...” Ta kai hannunsa ta taba fuskarsa tana murmushin jindadi sai ya buge mata hannaye ya fadi zaune ya shafa kansa ya mike tsaye ya sake komawa ya zauna. “Me ya faru? Wannan abun Farinciki ne a tsakaninmu Kareem” Ta nufeshi ta rika shi sai ya kauce daga rikon. “Baki da hankali Safeena baki da hankali, miye abun farinciki a nan? Kina da aure ki yi ciki da wani a waje kuma ki ce abun farinciki?” “Saboda naka ne Kareem, duka yara uku da na haifa na Abdull be, ina son na haihu da kai, ka san yadda nake sonka...” Ya aje PT din trying to calm himself down. “Na sani, amman ban da ciki, wannan kuma mun wuce gona da iri ba zamu iya rumgumar abun da ya biyo baya ba” Ta kalli cikin idonsa hawaye na cika idonta. “Me kake nufi?” “Zamu zubar Safeena ba zamu taba haihuwa a tsakaninmu ba har abada, babu wannan” Ya matsa zai taba ta sai ta matsa baya tana kallonsa. “Me kake nufi kenan?” “Zubar zamu yi, ba zam iya wannan ba Safeena ba mu wuce gona da iri ba” “Na yi mamakin jin wannan kalamar daga bakinka, ban yi zaton haka ba, ni ina son cikin idan kai baka so ni ban daina kaunarka” “Ni ma ban daina kaunarki ba, amman ba zamu yi cikin banza ba, kuma da igiyar aure akanki” “Ba zan iya zubarwa ba Kareem, ba zan iya ba” “Safeena na san muna son juna amman...” “Ba zan zubar ba Kareem ka daina magiya...” Ya tsaya yana kallonta da mamaki. “Shi ke nan ki aje cikin, ni kuma zan tsinke duk wata alaka tsakanina da ke” Yana furta haka ya nufi kofar fita falon ransa a bace. “Kana wasa da mace Kareem” Ta fada masa cikin fushi sai ya juyo ya kalleta. “Ke kuma kina wasa da rayuwarki...” Ya juya Fuuu ya fice daga falon ya barta tsaye cike da mamaki. NOOR POV. Sai da Yaya ya fara aje ledodi sannan ya ciro dubu goma cif ya mikawa Baba. “Gashi yace a siya mata magana” Baba ya karbi kudin da sauri ya kirga sannan ya saka aljihu ya mike tsaye be kula abun da ke cikin ledodin ba yayi ficewarsa ba tare da ya ba ni ko sisi ba, balle kuma Mama. Da kadan yake jira tace yayi rufeta da masifa, ni kam ban yi hanzarin tana komai ba har sai da na dan jira na ji ko Yaya zai yi fada amman ga dukan alamu damuwa ta hana shi cewa komai. Hana ta janyo ledodin da fara budewa daman tuni kamshi ya kara cika mana hanci. “Nidai bari na bude idan ba za ku bude ba” Na kai hannu na taba leda daya sai Mama ta buge min hannu, ina kokarin juyowa na kalleta ta dauke ni da mari har sai da yatsanta ya fada min ido, zan yi ihu ta rufe ni da duka iyakar karfinta. “Shiyasa ubanki kullum yake kuka dake, halinki ya fara isata, na gaji da ke Noor na gaji da halinki sakaryar yarinya dakikiya marar hankali da bata san ciwon kanta ba, yar iska gantalalliya, kullum haka kike ke babu ranar da za ki gayu” Daker Yaya ya kawace a hannun Mama ina kuka sosai. Ba zan iya fadar dalilinta na duka ba, iyakar abun da zan iya shaida shi ne ranta a bace yake tun shigowata har zamana, wata kila Baba ne yayi mata ba daidai ba, dalilina ko kuma wani abun ne ya faru kamin dawowata. “Babu abun da zaki ci a cikin nan, wannan Mugun kwadayin da rawar kai sai ya zama ajalinki matukar baki daina ba, yar iskar yarinya da bata gudun abun magana” Na mike tsaye ina kuka har bada iya gani saboda hawayen da suka min zuba. Ji nayi an kwashe min kafafuwa na fadi kasa ribbbb gurin da na ji rauni a dazun ya sake buguwa har na yanzu ya fi na dazun radadi da zurfi. “Mama dan Allah ki yi hakuri, ki yi hakuri Mama dan Allah ki yafe mata” Shi ne abun da na ji Hana na fada Yaya kuma yana rikon Mama. Follow the KHADEEJA CANDY channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaNTEQTFXUuaypyV5O01 *Duk mai son ya rika samun Littafin TA KI ZAMAN AURE yayi following wannan Channel din mai suna KHADEEJA CANDY a nan zaku rika samu duka littafaina in Sha Allah* ✧✦ 𝗧𝗔 Ƙ𝗜 𝗭𝗔𝗠𝗔𝗡 𝗔𝗨𝗥𝗘 ✦✧ 𝗕𝘆 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆 𝐂𝐡𝐚𝐩𝐭𝐞𝐫 -6 Duka sosai Mama tayi min tun tana dukana tana zagina har ta kai tana dukana tana kuka kamar yadda nake kuka. Hana ma kuka take saboda ta ga ina kuka daman haka take duk fitinarmu da ita idan wani abu ya bata min rai ko ya saka ni kuka ita tana shiga damuwa sosai, wani lokacin har ta kan fi ni ma saboda Mama tana cewa ni ban san ciwon kaina ba, sai dai wani ya sanin min. Na rarrafa na tashi zaune ina jin tsiyayar ruwan da na tabbatar na jini ne a kaina. “Mama yanzu me ye amfanin haka? Gashi yanzu kin ji mata rauni a raunin da ta ji, yanzu kuma a koma jinya ana neman na magani Baba kuma ba badawa zai yi ba kin san tun da kudin nan suka kai hannunsa ba zai bada su ba, kuma halin nan ba dainawa zata yi miye amfanin dukan?” Bana ganin fuskar kowa saboda kuka, sai dai zan iya shaidar muryar Yaya Nabil ne mai maganar cikin yanayin damuwa. “Innalillahi Wa'Inna Ilaihirraji'un” Shi ne abun da nake ta jin Mama na maimaita cikin kuka, na dai na samu na isa bakin kofar dakinmu da rarrafe, na shige ciki na kwanta. Daga lokacin da na kwanta sai kukan ya tsaya min daman can Allah be yi da son kuka ba, ba komai ke saka ni kuka na dade ba, sai dai na bar abu a cikin zuciyata idan na tuna ya kuna min rai, shi ma kuma da zarar na samu wani abu da zai dauke min hankali a take zan manta sai idan an bude sabon shafi kuma. “Jinin ya tsaya?” Na ji muryar Yaya Nabil sai na tashi zaune na kai hannu na taba gurin har lokacin zafi yake min sosai, kuma jinin yana zuba sai dai ba kamar dazun ba. “Rashin jin magana ke ja miki shiga matsala Noor, ke babu ranar da zaki yi hankali? Kuma kin san idan kika aikata wani abu laifin a gurin Mama yake komawa, fitar nan da kika yi babu kalar fadan da Baba be yi ma Mama ba saboda ta barki kin fita, na dawo gida na tarar baki gidan sai wani sabon fada ya tashi” “Ka ce Mama ta yi hakuri ba zan sake ba” Shi ne akwai abun da na ji zan iya fada, domin ni na janyowa kaina matsala da kaina, kuma Mama ta yi gaskiya kwadayina ne sila. Yaya Nabil ya fita daga dakin be jimawa ya dawo rike da maganin ciwon kai ya mika min. “Ki Sha biyu idan jinin be tsaya ba anjima sai mu tafi gurin Saminu ya sake gyara miki gurin, ni ma gashi kina son ki zama silar korata daga aiki, Allah kadai ya san me kika masa da yace na zauna gida na kwana biyu” Na san fadar gaskiyar zai sake jefani a matsala ne, dan haka na zabi shiru daman hausawa sun ce shiru ya fi yawan magana alheri. Ina cikin dakin ban fito ba sai da aka yi sallah magariba, a lokacin jinin ya daina min zuba, dan haka na nemi tsumma na gyara gaban kaina na goge jinin na saka wani kyalle na daure gurin sannan na fito na nufi gurin da buta take na dauka na zuba ruwa na yi alwala. Ina ganin ledodin Kareem Restaurant a tsakar gidan na san Mama sun cinye komai, hakan kuma ba karamin koma min rai yayi ba, ashe wahalar banza na sha ba zan ci komai a ciki ba. Da hawaye na gama alwala na mike tsaye kenan Hana ta fito daga bandaki rike da buta, Mama kuma tana dakinta tana sallah. “Mama ta rantse ba zaki ci ba, shiyasa ban shiga da shi dakinmu na ci a dakin Mama” Na kalleta cikin yanayi na rashin jindadi dake bayyana har a muryata na ce. “Kun cinye duka kuma?” Ta daga min kai. “Mama ta miki haka ne saboda karki sake aikatawa gobe, dan Allah ki daina abun da kike Noor, dan Allah ki daina” “Ba roka na yi ba, shi ya ba ni ku tambayi Yaya idan ba ku yarda ba, Hana har da yar tsutsar kun cinye?” “Aa zubarwa aka yi, waye zai ci tsutsa idan ba ke da abinki ba Noor, abun kyama” Ban sake ce mata komai ba na nufi dakinmu na shimfida dankwalina na saka hijab na fara sallah idan na yi sujuda sai na kai gefen goshina a kasa saboda rabin ciwon yake min. Ina gama sallah yaro ya shigo yana sallama, ina jin Mama ta amsa masa. “Wai Zafeer yana sallama da Noor” “Ka ce gata nan zuwa” Yaron ya juya ya fita, shiru ban ji Mama tace na tashi na tafi ba, na san kuma Zafeer ba tafiya zai yi ba sai ya gan ni, ko kuma idan an fada masa ba zan samu fitowa ba. Dan haka na mike tsaye na fice daga dakin na isa bakin kofar dakin Mama na tsaya daga bakin kofa na fara da bata hakuri. “Mama ki yi hakuri, ba zan sake ba” Ta yi kamar bata ji ba. “Na tafi gurin kiran da Zafeer yake min?” Na tambaya a kokarin na zama yarinyar kirki. “Idan kika tashin fitsararki umarnina kike nema? Yar iskar yarinya marar mutunci” Daga jin wannan kalama na san Mama bata gama sauka daga fushin nan ba. Sululu na fice daga gidan kamar macijiya, ina fita waje na samu Zafeer tsaye yana danna wayarsa, kamin na karasa gurin da yake tsaye na fashe masa da kuka a take ya dago kai da sauri ya kalleni hankalinsa a tashe. “Me ya faru Baby Noor waya taba ki?” Ya kunna fitilar wayarsa ya haska fuskata. “Subhanallahi me ya same ki waya fasa miki kai? Me kika yi Noor who did this to you? Who touch my Babeee” Tambayata yake hankalinsa a tashe zuciyarsa na cika, ban yi mamaki ba domin ya saba fusata a duk lokacin da aka taba ni. “Waya miki wannan duka Noor fada min mana...” Cikin kuka na fada masa abun da ya faru tun daga irin karyar da Kareem yayi ma su Mama cewar mota ce ta buge ni, har zuwa dukan da Mama ta yi min. “Kuma sun cinye duka naman ba su ba ni komai ba, ko yar tsutsar nan da na so na ci ba su ba ni sun zubar” Juya baya yayi yanayin fuskarsa ya sauya kamar zai fashe da kuka, ya jingina da ginin gidanmu ya kife kansa. Kamin ya dago ya kalleni. “Iyeyenki kadai suka kai su yi miki haka Noor, su kadai ne suka da ikon dukanki su fitar miki da jini haka kuma na kyale su, Allah ya daran talauci Noor, ba dan shi ba da yanzu na aureki da yanzu karkashina kike rayuwa, wani abu duk ba zai faru ba” “Sun cinye komai har tsutsar nan irin wadda masu kudi suke ci, na so na ci na ji me ake ji” “Ana zancen rauninki kina zancen tsutsa, idan kin ci me zaki ji?” “Na ji abun da suke ci mana, har kai na dauko maka naka fa, ai kasan komai na samu sai na kawo maka” Na fada cikin kuka. “Ni dai dan Allah ki daina daukar komai kike gani ki saka a bakin nan Noor, wani abun da kike ganin masu kudi suna ci, masu kudin nan ba dukansu ne suka da hankali ba, komai kika samu ki ta kaiwa bakin nan na ki kuma idan mun yi aure....” Na share hawayena na kalleshi. “Me? Kawai ba ina son na ji yadda ake ji ba ne, yanzu ai ba zan sake samu ba” “Yanzu dai shiga cikin gida ki fadawa Mama zan kaiki a duba raunin nan” Na juya sai ya kira ni na dawo. Ya haska fuskata ya saka rigarsa ya goge min hawayen da kyau. “Kar ki shiga kuma tace kin min kuka ta miki fada” Na dauke kai na koma cikin gidan na tsaya daga jikin kofar dakinta na sanar mata. “A dawo lafiya” Ita ce amsar da ta ba ni, sai na juyo ya dawo na fada masa muka kama hanyar titi ni da shi. Muna tafiya yana kallona har muka isa na zauna a kujera mai shagon ya bude ciwon ya sake wanke min ya sake rufewa ina kuka saboda zafi, Zafeer kuma yana rarrashina kamar wata jaririya. “Ya isa ya isa shikenan an gama daga wannan, ka yi mata a hankali, da zafi fa” Bayan ya gama ya bani maganin ciwon kai da na rage radadi. Sannan Zafeer ya biya shi muka taso muka kamo hanyar gida. “Me kike son na siya miki?” “Kana da kudi?” “Ina da dubu uku fada min abun da kike so na siya miki, kin ce Mama bata baki komai ba ko?” Na daga kai. “Eh amman ka aje kudin ba kudin aure muke tarawa ba?” “Idan ana tara kudin aure sai aki cin dadi? Jira ni a nan zan je na dawo” “Toh” Duk maganar da nake masa cikin shagwaba nake masa, daman can haka al'adarta take magana cikin shagwaba kamar wata wadda ta tashi a cikin gata, balle kuma na kai ga wadda ke shagwaba ni. Ta inda ya bar ni akwai hudu kasancewar unguwar babu wuta yau, babu wadda zai shaidi ni ce har ya je yayi siyayyar da zai yi ya dawo. Nama ya siyo min saboda ya san halina da son nama kamar kura, sai kayan marmari a dayar ledar dayar wadanda suka hada da Apple biyu sai ayaba da lemu da kankana, dayar ledar kuma cake ne irin kananan da ake saidawa 150 guda daya, ya siyo min guda hudu da kunun aya. “Na gode sosai Zafeer” Na fada ina jindadi sosai gaba daya ya wanke min kwadayi da bacin ran dake tare da ni. “Anything for my Baby Noor, idan Mama tace fada min kika yi abun da ya faru, ki ce aa daman na zo da siyayyar tun kamin mu tafi” “Toh” Na amsa sannan na jera da shi muka kama hanya, muna tafe muna hira har muka iso gida. “Ni zan tafi, yau babu hira saboda baki da lafiya, sai dai gobe idan na dawo, amman Noor ki daina bijirewa maganar iyayenki, duk abin da kika san zai saka Mama ta dukeki ko Baba ki daina kin ci? Kuma ki yi ta mana Addu'A Allah ya bude mana kofofi na samu karasa gidan da nake na hada komai a bani ke ki huta nima na huta” “Okay, toh... Zafeer ina sonka sosai sosai sosai” Yayi murmushi yana kallona cikin hasken farin wata. “Ina sonki ninki yadda kike so na Noor, ke tawa ce har abada, we mean to be akwai wani bend a tsakaninmu da babu wadda zai iya karya shi i love you so much” Magana yake min a hankali cikin sanyin murya da kwantar da kai kamar mai son na fahimta ko na haddace. Kamin ya juya ya duba ya ga babu mai ganinmu ya sumbanci goshina sannan yayi baya da sauri ya daga min hannu yana min bye bye. Ni ma na mayar masa sannan na shiga gida raina fess har na manta da komai, dakin Mama na fara shiga da murna ta sai kuwa na yi sa'a ina taka kafata wutar nepa na kawowa. Ba zube ledodin a gabanta da far'ata. “Mama gashi Zafeer ya siyo min” Wani banzan kallo da Mama ta watsa min ya saka annurin dake fuskata gushewa. “Fada masa kike yi abun da ya faru yaje yayi miki siyayya?” “Aa ban fada masa ba, na fada masa dai na ji ciwo ne saboda mota ta buge ni, daman ya zo da siyayyar kamin mu tafi na aje a zaure ne” “Je ki ci ni wadda na ci dazun ya wadatar da ni” Ta fada tana cigaba da jan carbinta, fadar hakan kuma sai ya saka na ji wani iri na ji komai ya fita a raina. “Mama dan Allah ki ci” Ta juyo ta kalleni sannan ta kai hannu ta bude ledodin ta bude ayaba ta dauki daya ta bude ta ci. “Allah ya shirya ki, Allah ya yaye min wannan bakinciki na ki” Ta fada idonta na cika da hawaye, ban san me zance dan haka na dauke ledodin na fice daga dakin. Hana ma kadan ta dauka saboda ta ci na dazu, na cire leda daya na ajewa Yaya nashi, daman shi Baba be cika maida hankali a irin wannan ba ko ba shi aka yi zai iya cewa baya ci ma. Na ci komai sannan na dauki na yaya na kai masa dakinsa na dawo na yi sallah Isha'i na kwanta. Ban farka ba sai washe gari ana kiran sallah Asuba. Kamar kullum Hana ta hada abun karyawa sannan ta wuce makaranta, ni kuma na fita na fara dibar ruwa daga fanfo ina kawowa cikin gida, Yaya ne yake yi sai dai a duk ranar da yake da makaranta baya diban ruwan ni nake yi saboda ni ce mai zaman banza. Bayan na gama na dauki tsintsiya na share ko'ina na shiga na yi wanka na dauki tufafin Hana na saka, ina fitowa Mama ta rufe ni da fada. “A haka zaki kare saboda baki san ciwon kanki ba, wuce ki cire mata kaya” “Nawa sun yi datti Mama” “Ki saka haka, ko kuma ki daura zane ki dauko tufafin ki wanke, har na islamiyarku ki wanke dan yau sai kin je makaranta” Na juya na koma cikin rashin jindadi na cire tufafi na dauki zane na daura na ciro uniform din da kala biyu na fito waje na wanke na shanya. Na koma daki na zauna, ina jin lokacin da yaro ya shigo yace Zafeer yana sallama da ni. Katon Hijab na nema na saka saboda zane ne a jikina nan ma ban tsira ba ina fitowa Mama ta fara halbina da kalamai marasa dadi. “Ai dole ki zuba katon hijab saboda baki da tufafi, ke kan kin ji haushin rayuwa, wannan Zafeer din zai daukarwa kansa aiki, Allah yasa ma zai iya zama da ke, domin dai babu namijin da zai iya zama da mace irinki, matukar baki sauya hali ba zaman aure sai ya miki wuya Nooriyya” Ni dai ban ce komai ba na fice daga gidan, sai na same shi a waje tsaye yana jiran fitowa. “Baby Noor ya jikin?” Na masa dariya a yayinda yake min murmushi. “Na ji sauki, har na yi wanki na yi diban ruwa” Ya kalleni kamar zai ce wani abu sai kuma yayi shiru. “Mama ta miki fada jiya?” “Aa ban fada mata gaskiya ba, yadda ka fada haka na ce mata” “Shikenan ki shiga ciki ni zan wuce makaranta yanzu, yau zamu zana jarabarmu ta karshe ki min addu'a Allah ya ba ni sa'a” “Allah ya baka sa'a Allah yasa ka fito da results mai kyau” “Ameen i love you” “I love you too” Yayi min bye bye Ni ma na masa sannan ya wuce, ni kuma na koma cikin gidan. Kamar yadda Mama ta fada sai na tafi makaranta lokaci na yi na shirya cikin uniform dina kuka ne kawai ban yi ba amman bana son zuwa makaranta ko kadan, ina saka uniform Hana na tsokanata wai yau ni nice zan tafi makaranta za'ayi ruwa bla bla ne dai ban kulata ba, Mama ta zuba mana kwadon kanzo muka ci, Hana ya raga na hade da nata na cinye sannan na sha ruwa muka kama hanya. “Ni da zaki taimaka min ma ba zan tafi ba, sai na tafi bikin Salwa yau ne za'ayi na karshe fa, kuma jiya ban tafi ba, na san idan na yi ma mama magana zata min fada shiyasa ban yi ba” “Da rauni a kai zaki tafi biki kamar Bikin dole? Yanzu duk fadan da aka miki jiya be shige ki ba, sai wani zancen bikin kike Noor kin shiga uku” “Ni ban shiga uku ba, ke kika shiga uku” Na rama, sannan muka cigaba da tafiyar, cikin rashin jidadi na isa Islamiyar, kowa mamakin ganina yake kusan tun da na yi sauka sai dai na leko makarantar na koma bana wani zuwa. Har Malaminsu sai da tsokani ne wai ya ga ana hada hadari a gari ashe ni ce zan shigo makarantar. Ni dai ban kula su ba, na bude littafaina aka fara zuba min karatu kamar ba gobe, shiyasa malamaina suke yawan yabani suna cewa da zan natsu na yi karatu ba karamin amfanina za aci ba, kuma ni ma zan ci amfamin ilimina domin ina da fahimta sosai ina da basirar haddace abu, kuma komai aka fada min bana mantawa, natsuwa ce kawai da jin magana suke ganin kamar bani da ita, nikam ina ganin natsuwata suke dai suke ganin haka. Kowa ya tambaya me ya same ni a kai cewa nake mota ta kade ni. Misalin karfe biyar aka fara haramar tafiya duba Malam Sule mai bin babban malaminsu kusan komai da ya shafi makaranta shi yake yi, ashe ba shi da lafiya wai kariya ya samu sati biyu, ni ban sani ba sai yanzu, saboda bana zuwa karanta duk wani abu da ya shafi makaranta bani da labarinsa. Malam Babba ne ya dauki nauyin duka Napep din da muka hau, mu biyar muka matse a Napep daya zuwa unguwar da Malamin yake, muna isa muka shiga cikin gidan muka gaishe shi, muna waje wata Hajiya ta shigo da manyan ledodi Kareem Restaurant ta aje sannan ta rage tsawo ta gaisa da Malamin. Ni kuma na kira Hana dake can gefe na nuna mata Ledodin. Ta kalla sai ta yi dariya ni ma na yi dariya, sai dai kamar hakan be yi ma Matar dadi ba, ko kuma dai tana cikin fushi ne take son hausakewa a kanmu oho a take ta hau fada. “Ledodin Kareem kun san abun da ke ciki? Ko kuma kun raina abun da na kawo ne? Wane irin abu ne wannan?” Malam Babba ya kalleta. “Hajiya Lafiya?” “Ga yarinyar da ta kira dayar can ta nuna mata ledodin da ba kawo, ban san manufarta na yin haka ba” Malam Babba ya juyo ya kalleni. “Nooriyya me ya faru” “Jiya ne mai Restaurant din ya zo da kanshi ba aike ba, har gida ya kawo mana kayan dadi, shi ne na kira Hana na nuna mata ledar ina nufin ta kalli wannan daga can ya fito shi ne wai ta fara bala'i ita masifaffiya, Wallahi na fiki bala'i ni har na siyarwa ina da, daga magana zaki fara fada kamar an miki wani laifi” Na mayar amsa ina murguda mata baki, kuma na fada mata shi ya zo da kansa saboda ta san muna da matsayi muma. “Oh ai ban dauka haka ne ba, na dauka wata maganar ce ya dabam, yi hakuri” Na yi zaton haushi zata ji sai na ga ta maida abun na dariya ta saki fuska ta sauko wata ta fahimci ni ma muna da matsayi, ba dan ma muna cikin yan makarantar mu kuma kowa ya san Zafeer zan aura da sai na yi mata karya na ce saurayina ne. Sai dai wani abun da ban gane kansa ba shi ne kallona take har ta gama gaisawa da Malam Sule ta mike tsaye idonta a kaina yake. Gabatar da ita da Malam Sule yayi a gurin Malam Babba ne muka ji cewar ita ce silar ciwonsa saboda kade shi da ta yi da mota. “Malam dan Allah ba ni aron dalibar ka zan yi magana da ita” Ta nuna ni, ni kam abun nema ya samu daman so nake na nuna mata karyar arziki take da kurin banza na ga mai arzikin da be dauki kansa wata tsiya ba, ba kamar ita ba daga magana ta fara ruwan masifa. Malam ya juyo ya kalleni. “Allah yasa dai ba wata matsala ba ce?” “Babu wata matsala Wallahi tambayarta kawai zan yi” Ta amsa fuska a sake. Malam yayi min izini da na tafi sai na mike tsaye na isa gurinta, sai ji na yi ta dafa kafadata muka fita tare bata min magana ba sai da muka isa waje, gaban motar da nake kyautata zaton ta, ta ce muka tsaya tana murmushi ta ce “Ya sunanki?” “Noor” Na amsa a takaice. “Shi Kareem din mai Kareem Restaurant Saurayinki ne? Ko dan'uwanki” Jimmmm na dan yi ina tunanin na zaba sakanin saurayi da dan'uwa, idan na ce mata dan'uwa zata san ina da muhimmanci amman Saurayi zai fi karamin kwarjini a idonta dan haka na amsa da. “Saurayina ne, me yasa kika tambaya?” Ya sauke ajiyar zuciya da alama jin haka be mata dadi ba. “Kawai na tambaya ne, saboda ina yawam siyen abinci a restaurant din, kuma a yadda na ji shi Kareem din kwararen likita ne mai duba mutane, na so na samu maganinshi tun da dadewa amman ban samu haka ba, saboda masu aikinsa basa bari na ganshi kuma asibitin idan naje bana samun na duba ni, shiyasa yanzu da na ji kin ce kin san shi na ji dadi kuma har na nemi magana dake private” “To me zan yi miki?” Gabana ya fara faduwa karta roki na yi mata alfarmar da ba ni da halin yinta. “So nake ki hada ni da shi dan Allah” “Aa gaskiya shi baya son haka” “Taimaka min zaki yi ina cikin matsala ne, ina fama da wani ciwo ne na kansa a ciki, kuma ance idan har na samu ganinsa ya rubuta min magani zan samu lafiya, dan Allah ki taimaka min kinji kanwata, ni zan ma iya biyanki” “Aa gaskiya, ni yanzu ganin Malaminmu muka zo, gidanmu idan aka ji za'ayi min fada” “To karya kike yi ba saurayinki ba ne kenan?” Na fara saurin kare kaina. “Aa da gaske ne mana” “To ki nuna min, indai har da gaske ne, ki kai ni gurinsa” “Toh ai yanzu baya gida” “Eh yana restaurant dinsa, daman ance idan Yamma ta yi restaurant dinsa yake zama, idan kin yarda ga mota nan mu tafi yanzu, ga mota nan sai mu shiga, ni zan ma biyaki zan baki ko nawa kike so, ni dai ke hada ni da shi kawai na yi magana ne burina” Na yi shiru ina nazari na bita ko kuma dai na ki tafiyar, idan kuma na ki tafiyar zata karyata ni, idan kuma na tafi ba lallai ne nima su bar ni na ganshi ba. “Mu tafi? Dan Allah ki taimaka min, sai magiya nake miki kamar ba musulma ba? Ke baki da tausayi ne a zuciyarki?” Na kalleta, bata yi kama da mayaudara ba balle na ce karya take, kuma yadda ta marairaice murya nan sai na dan ji tausayinta. “Ba zamu dade ba?” “Ba zamu dade ba, kina hada mu zan baki kudin Napep ki dawo sai ki bar mu a can” “Toh” Ta bude min mota na shiga sannan ta shiga, ni dai zan taimaka mata ne saboda ta nuna tana cikin damuwa, ba wai dan kar na karyata kaina kawai ba. Har muka isa Restaurant din wata kalma bata shiga tsakanina da ita ba. Na bude motar na fita ita ma ta fito bayan ta saka mask kuma ta maida mayafin dake wuyanta zuwa saman kanta. Gabana na faduwa muka doshi reception din ina ta sake saken kar na ga Yaya duk da na san by this time ya wuce gida domin karfe shida ta yi. Me zan fadawa ma'aikatan su bar ni na shiga ciki shi ne abun da ya tsaya min a rai, idan ma sun bar ni ban san a ina Office dinsa yake ba. Ta inda na yi sa'a na samu abokin Yaya da duty a gurin kuma ya san ni farin sani, hakan ya taimaka min gurin fada masa ya shiga ciki ya fadawa Dr Kareem Noor ce take son magana da shi.. Babu jimawa ya dawo sai ya ce Dr Kareem din ya ce a shigo da ni ciki, dadin dake cikin raina baya misaltuwa haka na wuce gaba matar da ban san sunanta ba tana bayana abokin Yaya kuma yana gaba har muka isa office din sannan ya nuna min kofar ya juya ya koma. Na juyo na kalli matar dake jan numfashi da karfi tana fitarta wata kila saboda ciwo ne oho dai, na yi murmushi na juya na kai hannu na murda kofar na bude na shiga ciki. “Noor... Lafi...” Be karasa ba yayi shiru yana kallon gefena, matar dake bayana tana shigowa wani mutum dake zaune tare da Kareem din da ban san waye ba ya kalleni yana murmushi ya ce. “Noor Amaryarmu!!!” Na kalleshi da sauri ina mamakin jin furucinsa kamar wadda ya san karyar da na shiryo. Kareem din ma kallonsa yayi tare dake bayana kuma na ji ta sauke numfashi da karfi ta juya. Ni kuwa na kai hannu na taba ta wai na fada mata ga Dr Kareem din nan, sai jin na yi ta kama hannun ta murde tana kokarin karyawa. “Safeena...” Na ji Dr Kareem ya kira sunan da karfi sannan ya nufo inda muke yana kokarin kwace ni a hannunta... __________________________ Domin samun littafaina akan kari, ku yi following din Channel dina mai suna KHADEEJA CANDY za su samu TA KI ZAMAN AURE daga farko har zuwa inda ake, kuma a can zan rika posting duka littafaina In Sha Allah. Amman kamin nan ku fada min wane Team kuke. Team Kareem Ko Team Zafeer Anya kuna ganin Kareem yayi ma kansa adalci kuwa? Mu'alama da matar aure mai yaya har uku? Shin kuna ganin akwai Uba irin Baba kuwa? Babu dadi gurin matar gidan haka kuma babu gurin yayan gida? Anya abun da Mama take yi ma Noor tana kyautawa kuwa? Ku aje min ra'ayinku ni kuma na aje muku dogon shafi gobe idan Allah ya amince. #KhadeejaCandy Follow the KHADEEJA CANDY channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaNTEQTFXUuaypyV5O01 *Duk mai son ya rika samun Littafin TA KI ZAMAN AURE yayi following wannan Channel din mai suna KHADEEJA CANDY a nan zaku rika samu duka littafaina in Sha Allah* ✧✦ 𝗧𝗔 Ƙ𝗜 𝗭𝗔𝗠𝗔𝗡 𝗔𝗨𝗥𝗘 ✦✧ 𝗕𝘆 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆 𝐂𝐡𝐚𝐩𝐭𝐞𝐫 -7 KAREEM POV. Kareem yayi kanta da sauri ya rike Safeena yana kokarin kwatar hannun Noor da ihunta ya cika dakinta tana fadin hannunta. “Safeena karki karya mata hannu” Daker ya kwaci hannun Noor a hannunta ta murgude hannun har yayi yaushi, gaba daya Noor ta rude kamar wadda ta fita hayyacinta ta fadi kasa ido a zare tana haki. “Kin fita daga hayyacinki ne? Me ke damunki?” Kareem ya tambaya cikin tsawa kamin ya juya ya rika ya kai hannu zai taba hannun Noor sai ta juyar da shi dayan gefe. “Ya karye Azzaluma yar masan wuta ta karyashi” Noor ta fada cikin kuka. Kareem ya shiga mata magana a hankali cikin rarrashi yana kokarin rika hannun ya duba. “Be karye ba, kawo na gani” Wani hawaye mai zafi ya saukowa Safeena, zafin da take ji a zuciyarta ya fi wadda Noor take ji a hannunta. Duk abun da ake Hafiz na zaune yana kallo be ce kuma be yi yunkurin yin wani abu ba, sai a lokacin da ya ga hawaye ya sauko a idon Safeena. “Tirr da ke, tirr da uwa irinki... Tir da mata irinki... Tir da haihuwar ya irinki, tir da auren mace irinki, indai har sabon Allah ya kai ya rufe miki ido ki kama hannun wata ki murde saboda kishi, A gaban idona to kin yi hasara kuma kin cika tantiriyar yar iska, kuma haka da kika yi ba zai hana Kareem auren yarinyar nan, albashi sai ki hade zuciya ki mutu” Ta dauke idonta daga barin kallon Noor ta kalli Hafiz, kamin ta kai hannu ta taba hawayen da bata san da saukarsu ba sai a lokacin, ta yi murmushi ta dubi Kareem dake fadin. “Babu komai tsakanina da Noor, wace magana kake haka? And ka cire bakinka daga magana da ita, babu ruwanka idan zaka yi magana ka yi da ni ba da ita ba, ba ka da wannan hurumin” Dauke kai Safeena ta yi ta juya ta fice daga office din. Kareem ya kalleshi cikin damuwa ya ce. “Akan me zaka fadi wannan maganar? Zata dauka da gaske ne, Safeena tana da mugu mugun kishi, baka san abun da zai je ya dawo ba” Hafiz ya wulga masa wani wulakantaccen kallo. Har zai yi magana sai kuma ya juya ya kalli Noor da ta cire hijabi saboda wani azabar zafi da take jin ya game jikinta gaba daya sai kuka, Kareem ya ci albakarcin Noor tana gurin ba dan haka ba, Hafiz zai fada masa magana ne marar dadi, sai dai baya son Noor ta san komai dan haka yayi shiru. Kareem ya juya ya kalli Noor sannan ya nufi gurin da keys dinsa suke ya dauka, ya nufi inda take. “Taso mu tafi asibiti zan duba miki a can” Noor ta girgiza kai tana jin wani irin azaba a hannu. “Aa a barshi haka, gyaran akwai zafi ni taimakonta kawai na yi, me yasa zata min haka? Miye laifina ni?” Kareem din take tambaya tana kuka sai gumi take. Kareem yayi shiru yana kallonta cike da tausayawa ya rasa me zai ce. “Mamana bata san na zo nan ba, jiya sai da ta yi min duka sai da kaina ya fashe saboda kai, bata bar ni na ci komai da na tafi da shi ba, yau kuma wata ta karya min hannu saboda kai, kuma na san Mama sai ta min duka ko Baba, na san haka zata min ba zan biyota na zo ba” Tausayinta ya kama shi. Ya sake mika hannu ya rika hannun ta kauce tana kokarin mikewa tsaye. “Be karye ba Noor, duba kawai zan yi sai na baki magani, idan akwai zafi ba zan taba ba na miki alkwari” Ta kalleshi. “Rantse” Ya daga hannunsa. “Na rantse” “Ce ka rantse ba zaka taba min ba idan akwai zafi” “Na rantse ba zan taba miki ba idan akwai zafi” “Ce Wallahi Wallahi ba zaka taba ba idan akwai zafi” “Wallahi Wallahi ba zan taba ba idan akwai zafi” Ya rantse kamar yadda ta bukata sannan ta yarda, ya dauki Hijabinta zai saka, sannan ya nufi kofa ya bude mata, ta fita tana kuka, a yar fahimtar da yayi mata daga jiya zuwa yau ya san ba lallai ne yace ta yi shiru ta yarda ta yi shirun ba, balle yace ta hakura da kuka saboda hankalin mutane dake karkatowa izuwa garesu a duk inda suka wuce. Ya riga isa gurin motar ya bude motar ta shiga ya rufe sannan ya zagaya ya shiga bangarensa ya tashi motar. Har suka isa asibitin kuka Noor take domin a tunaninta hannunta ya samu kariya ne. Wannan karon be shiga da ita office dinsa ba ya tsaya da ita a gurin da ake duba marasa lafiya kamar kowa. Ya nade hijabin ya kalli hannu yana son ya taba yana tsoron tsare da ido da ta yi. “Har yanzu akwai zafi?” “Eh mana, kana ganin hannun ya karkace ba” “Kashin ne ya bar gurinsa, amman ba kariya ba ce” “Wallahi Wallahi da ace ni mai gata ce sai na yi shari'a da matar nan, amman na barta da Allah Allah ya isar min, Allah yasa ciwon jikinta kar ya warke har abada” Kareem dai be ce mata komai ba sai kallonta yake kamin ya mike tsaye ya bar gurin. Be yi minti goma da tafi ba wata likitar ta zo ta duka tana duba hannun Noor. “Ta so muje” Noor ta mike tsaye ta bi bayanta suka shiga bani dakin jinya, a nan suka samu Dr Kareem ya sanya safar hannu yana aje wasu kwalabe a saman karamin teburi. Da kai Dr Kareem yayi ma likitar da ta shigo da ita magana da ma wadda ta shigo bayanta. Sai da ta bari Noor ta zauna sannan dayar ta kama hannun ta rike gam, Noor ta kalli Kareem da sauri. “Kace ba zaka taba ba” Ya daga hannunsa sama ya cire safar ya juya yayi ficewarsa daga dakin. Be dawo ba sai da aka gama komai, Noor ta yi kuka har ta galabaita. “Sannu...” Ta kalleshi kurun tana hawaye, shi kuma ya kalli bandajen dake kanta sai a lokacin ya lura da ba wadda ya saka mata ba ne a jiya. “Waya canja miki wannan?” Ta yi shiru tana haye yawu kamin ta fara kokarin sauka kam gadon. “Ina saki je?” “Gida” Ta amsa tare da fara takawa tana rike da hannun da aka daure mata. “Okay zan kaiki gida, amman me zamu je ce? Ko dai mu kira Yayanki ya zo asibitin nan?” Ta girgiza kai da sauri. “To me zan fadawa Iyayenki?” Ta girgiza kai. “Kira min Zafeer” “Waye Zafeer?” “Shi ne wadda zan aura” “To zo ki zauna” “Bana son asibitin nan bana sonta” Ta fashe da kuka. “Shi kenan, muje na kira shi a mota sai ya same mu a restaurant haka ya miki?” Ta daga kai, sai ya nufi kofar ya bude mata ta fita sannan ya fita. Har suka isa gurin motar tana rike da hannunta kamar wadda ke dauke da jariri. Sai da ya fara tukin sannan ya kalleta a hankali cike da tausayawa ya ce. “Noor ina kika hadu da wannan matar?” Ta bashi labari cikin kuka. Sai yayi mata wata tambaya da ya saka ta watsa masa harara. “So na kike yi?” Ta hada masa da kwafa. “Toh why do you lie me yasa kika mata karya?” “Kaddara da rabon sha wahala, ashe ma ta sanka ita din budurwar ka ce?” Yayi shiru be amsa mata ba ya dauke kai ya cigaba da tukinsa. “Ina ta sanka?” “Ba kin ba ni shawara kara aure ba?” Ya fada yana kokarin kawar da maganarta. “Wallahi karka aureta, zata hadu da wacan matar ta ka su yi ta maka hauka” Yayi murmushi sannan ya dauki wayarsa ya mika mata. “Saka number saurayin” Ta karba tana kallon yadda wayar ta cika mata ido. “Me yasa Mama ta dake ki? Gaskiya kika fada mata?” “Aa bata fada min laifina ba, wata kila ta dauka ko na roke ka ne” Ya kalleta. “Duk abun da kika zaba jiya baki ci komai ba?” Ta daga masa kai tana kokarin kai wayar a kunnenta. “Ni zan yi magana da shi” Ya karba ya kara wayar a kunnesa. “Wa'alaikusalam ina magana da Zafeer ne” “Eh wake magana?” “Sunana Kareem, kuma ina tare da Noor yanzu haka, sai dai ba wata matsala ba ce ta ji ciwo ne a hannu shi ma ba sosai ba, tace a kiraka ka zo ka tafi da ita gida” A take hankalin Zafeer ya tashi. “Subhanallahi garin yaya? Ina take tana lafita me ya same ta?” “Ka kwantar da hankalinka da sauki ba sosai ba ne, gata ka yi magana da ita” Ya mika mata wayar sai ta karba ta fara zuba masa shagwaba. “Wata ce fa daga na taimake ta sai ya rike min hannu ta murde, sai da aka daure min aka gyara” “Kina ina?” “Ina cikin motar Kareem din, shi ne wadda ya kade ni jiya, gamu mun iso Restaurant dinsa ka zo ka tafi da ni gida, bana son ya kai ni kar Mama ta sake yin fada” “Noor me ya kai ki gurinsa? Me yasa baki jin magana ke? Taya ma kika tafi gurin? Why Noor why?” Ta yi shiru bata ce masa komai ba. Kareem na ganin yanayin fuskarta ya sauya ya mika hannu ya karbi wayar ba dan ya san me Zafeer din ya tambaye ta ba. “Ka zo Kareem Restaurant ka dauke ta, idan ka zo kace a kawo ka office dina kai tsaye” Ya kashe wayar. “Jiya na so na kira Yayanki na ce ya jikinki, amman wata damuwa ta saka ni a gaba, na manta da komai” Bayan ya karbe wayar yake fadar haka a daidai lokacin da ya faka a harabar. “Kasan wannan matar ko?” Ta aiko masa da tambayar da be san yadda zai sarrafa halshe ya amsa mata ita ba. “Na ji ka fadi sunanta, ni ban ma san sunanta ba, budurwarka ce?” Yayi shiru na tsawon lokaci yana kallon waje ta cikin gilashin motar. “Aa” “Tace min tana son ta ganka, mesa ta yi karya?” “Ke me yasa kika yi karya? Already kina da wadda zaki aura akan wace hujja zaki yi karya?” Ta yi shiru, sai ya bude motar ya fita ya rufe ya bar Noor a ciki, ya busar da iskar bakinsa ya rufe ido ya bude ya girgiza kai. Sai kuma ya bude motar ya dauko wayarsa ya rufe. Number Safeena yayi dialing ya kai a kunnensa. Wayar ta yi ringing har ta gaji bata daga ba. Ya sake cika bakinsa da iska ya koma cikin motar ya zauna. “Noor karki sake yi ma wani karyar kin san ni, kuma ki daina bin motane any how ko kin san su ko baki san su ba” Ta daga mishi kai a hankali cike da natsuwa. “Kuma ki rika jin maganar iyayenki kin ji?” Nan ma ta daga mishi kai. “Ka yi hakuri, ba zan sake ba daga yau ba zaka sake ganina ba” Ta fada tana hawaye sai kuma ya ji babu dadi. “No ba wai bana son zuwanki ba ne, kawai bana son ki saka kanki a matsala ne, kin ga iyayenki suna miki duka da fada, kuma kin ga yanzu kin samu rauni saboda haka” “Na fahimta...” Ta amsa masa murya a sanyaye hakan sai ya kara masa raunin tausayinta dake zuciyarsa. “Me kike son ki ci?” Ta girgiza kai, ta bude motar ta fita. Sai shi ma ya bude ya fita ya wuce gaba ta bi bayansa. NOOR POV. Babu kowa a office din, mutunen dazun da ban san waye ba yayi tafiyarsa. Kareem da kansa yaja min kujera na zauna sannan ya zauna a kujerar dake facing din tawa. “Baki sha'awar cin komai? Ko kuma na miki takeaway” Na girgiza masa kai, ji nake bana sha'awar komai nasa a yanzu. “Noor” Ya kira sunana a hankali a lokacin da na dago kai sai na tarar ni yake kallo. “Kin sa na ji babu dadi, maganar da na yi ce ta bata miki rai?” Nan ma na amsa masa da kai. Yanzu kam gaba daya hankalina ya koma gida gurin mahaifiya hukuncin da zan karba idan na koma shi ya tsaya min a rai. “Ina tunanin gida ne, yau Mama sai ya sake karya min hannun babu wadda zai cece ni” Na fada hawaye na sauko min, domin a lokacin ne na gane kuskuren da na aikata na biyo matar har nan. “Ko zamu tafi tare da Saurayin na ki sai mu bata hakuri mu yi mata bayani? Bana son ta dake ki?” Magana yake min kamar wadda ya damu da ni da gaske. Na girgiza masa kai ina kallon hannuna da aka daure. “I'm sorry haka kaddara take wani lokaci, ba ma iya kauce mata” “Ni kaddara ce marar kyau a gidanmu, shiyasa ni ce mai laifi kullum, shiyasa Babana...” Na samu kaina da fadar haka, sai kuma na yi shiru domin be kamata na fadi ciwona a inda babu magani ba. Wani abun da ban yi zato ba, shi ne tashin hankalin da na gani a fuskar Kareem a lokacin da yake kallona, damuwa da tausayi sun bayyana karara a fuskarsa. Na sauke kaina kasa tare da saukowar ruwan hawaye. “A duk lokacin da kika ji kina bukatar wani abu ki zo gurina kofata a bude take, ko gobe idan wani ya tambaye ki miye alakarmu ki fada masa abun da yayi daidai da ra'ayinki, karki ji haufi” Ban ce masa komai ba, kuma ban dago ba hawaye kuma ba su fasa min zuba ba. Ta gilashin dake window na lura da Magariba ta yi saboda duhun da ya fara shigowa. Yunkuri yayi sai mike tsaye sai aka turo kofar office din aka shigo bayan ya kwankwasa. “Ranka ya dade wai wani ne yake nemanka, sunanshi Zafeer” “Shigo da shi” Sai ya koma ya zauna da kyau bayan ya amsa, sannan ya kalleni. “Share hawayenki kar ya ga kina kuka” Na share hawayen na maida hankalina da dubana gurin kofar shigowa. Babu jimawa Zafeer ya shigo dakin yana kallon hannuna hankalinsa ya kara tashi. “Innalillahi Wa'inna Ilaihirraji'un Baby Noor me ya same ki?” Na yi shiru wani sabon hawaye ya cika min ido ni da ban saba hawaye sosai ba. Kareem yana masa bayani amman Zafeer ko kallon inda yake be yi ba, da alama daga bakina yake son jin karin bayanin. “Wata mata ce tace na kawo ta nan...” Na fada masa gaskiyar yadda komai ya faru. Sai dai a yadda na lura gaskiyar tawa ta masa ɗaci domin kuwa rufe ni yayi da fada abun da be saba ba. “Me yasa zaki yi haka? Wa kike son ki burge? Me kike nema a gurina da baki samu ba har zaki kwadayin wani ya zama saurayinki? Ita din me kika mata da zata ji Miki ciwo a hannu haka? Saboda me? Daga makaranta sai ki tsallake ki zo nan yanzu matar nan idan cin mutane take sai ta cinye ki” Wani irin fada yake min da tsawa kamar ba Zafeer dina ba. Lallai na yarda ni sokuwa ce kuma an aikata babban laifi. Ta cikin ruwan hawaye na ke ganin Kareem ya mike tsaye yana fada. “Haba Malam daga zuwanka sai ka rufe ta da fada, ta ki yarda na kaita gida saboda tana tsoron fada, tace a kiraka saboda tana tunanin zata samu sauki a gurinka sai kuma ka rufe da fada babu sauraren Uzuri, yarinya ce fa bata kai matsayin da kuke tunanin ta banbance daidai da akasin haka ba kuma babu wadda baya kuskure” Zafeer ya kalleshi. “Ai kai ka banbance daidai, tun da kana tsaye aka ji mata a hannun, sai yanzu zaka ce bana sauraren uzuri, uzurin me zaka ba ni?” Kareem ya nuna shi da tsaya. “Tsaya matsayinka ka kula da kalamanka, wata kila ba dan yarinyar nan ba, da baka da alfarmar shigowa office din nan, so respect yourself” “Gaskiya ne, kai ya kamata ka fara respecting kanka ai, kamin ka ni, babu ruwanka da yarinyar nan babu ruwanka da ni, baka san abun da ke tsakaninmu ba” Zafeer ya fada. Kareem ya kalleni ya kalleshi sai kuma ya dauke kai. sannan sannan ya kalleni a fusace. “Mu tafi” Na wuce da sauri ya biyo bayana, haka ya saka ni a gaba har muka isa titi. Ya tari Napep ya shiga sannan ni ma na shiga, gaba daya a rikice nake, yadda na ga ran Zafeer ya bace ya saka hankali kara tashi, shi kenan da yake goyon baya baya son bacin raina balle kuma Baba ko Mama ya ransu yake a yanzu. “Noor” Na kalleshi. “Me yasa kika ce mutumen nan Saurayinki ne?” Na yi shiru domin ba ni da wata hujja da zata gamsar da shi, indai har Hujjar dazun da na bashi labarin komai be gamsar da shi ba ban san me zai kare kaina sa shi ba. “Saboda yana da kudi?” Zuciyata ta buga da karfi, Zafeer ya fara lissafin da ban taba yi ba, ya zarge ni da abun da ban yi tunani ba. Sauke murya yayi kasa sosai kamar marar lafiya. “Zan yi kudin In Shaa Allah Noor zan gina miki irin gidan da kike so, da irin tsarin da kike so, zan wadata ki da komai, zan maida ke sarauniya na maida ke abar kwatance, ki kara hakuri ki kara min lokaci kin ji?” “Ba saboda haka ba ne, ni dai kawai na yi ne saboda na firgita matar” Ina jin lokacin da ya sauke ajiyar zuciya ya kalleni a raunace. “Dan Allah karki sake, rai na ya bace yau saboda abun da kika yi, ban jidadi ba kin saka na raina kaina, kuma kin saka na miki wani kallo da be kamata ba, Baby Noor ki zama mai sauraren maganar iyayenki kin ji? Ki zama mai bari idan aka hana ki, mai yi idan aka ce ki yi kin ji Baby na” Na daga mishi kai har lokacin jin nake kamar ba Zafeer dina ba ne, Mai Napep din ya juyo ya kalleni. “Lafiya?” Zafeer ya tambaya be ce komai ba ya juya ya cigaba da tukinsa. “Kin san inda matar nan take?” “Ban santa ba” Na amsa ina share hawayena. Zafeer yayi kwafa. “Zafeer ka yi hakuri ba zan sake ba” Na fada murya na rawa, sai yayi min ya girgiza min kai. Be sake ce min komai ba har sai da muka fita Napep din ya sallami mai Napep din a lokacin duhu ya fara sosai sai dak hasken wutar nepa da ya haska unguwar ya taimaka mana. “Ina sonki Noor Allah ya saka min sonki fiye da yadda kike tunani, kuma na san kina so na kema, dan Allah karki bari shedan yayi nasara akanki, karki biyewa kyale kyalen zamani, with time ni ma zan yi miki komai” Muna tafe yana fada min haka, ban iya furta komai ba har muka doshi gida, zuciyata kuma ta doshi bugawa kamar wadda azali ke kiranta. Daga nesa muka hango mota fake a kofar gidanmu, ni dai daga inda nake Ina iya shaidar Kareem ne tsaye a tare da Baba, domin akwai wutar nepa a unguwar, kuma na gane tufafin jikinsa na yau da motarsa sai dai abun da suke tattauna ne ban sani ba. Na kalli Zafeer sai na ga yanayinsa ya sauya kamar be ji dadin haka ba, ni dai da mamaki na karasa gurin faduwar gabana yana karuwa, hakan ya saka ni rage tafiyar da nake Zafeer ya kalleni. “Muje zan masa bayani zai fahimta ba zai miki komai ba” Kamar Kareem ya san abun da Zafeer yake fada sai na ji ya ce. “Noor karaso nan, na yi magana da Baba na masa bayanin komai, kuma ya fahimta daman shi ne makasudin da ya saka na yi rigaku zuwa” Na kalli Zafeer har sai da yayi min alama da na tafi sannan na tafi ina rike da hannuna. “Allah dai ya tsare babu karaya ai” Cewar Baba da far'arsa kamar ba shi ba. Zafeer ya gaishe shi, Baba ya amsa. “Ashe kai ta kira...” Zafeer ya risina. “Eh ayi Hakuri dan Allah Baba” “Babu komai, Allah kyau gaba Ai shi Alhaji yayi min bayanin komai” Zafeer ya kalleshi ya kalleni. “Shiga gida Noor” Na nufi kofar gidan kamar yadda ya bukata na shige cikin gidan. Sai dai ban isa a inda Mama take zaune ba kamar tana jirana, Yaya Nabill ma dake kusa da ita ina iya karantar yadda yake cika yana batsewa. ‘Idan na tsira daga dukan Baba Mama fa?’ Na tambayi Kaina... Follow the KHADEEJA CANDY channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaNTEQTFXUuaypyV5O01 *Duk mai son ya rika samun Littafin TA KI ZAMAN AURE yayi following wannan Channel din mai suna KHADEEJA CANDY a nan zaku rika samu duka littafaina in Sha Allah* ✧✦ 𝗧𝗔 Ƙ𝗜 𝗭𝗔𝗠𝗔𝗡 𝗔𝗨𝗥𝗘 ✦✧ 𝗕𝘆 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆 𝐂𝐡𝐚𝐩𝐭𝐞𝐫 -8 Daga Yaya har Mama babu wanda ya ce da ni shigo ki zauna ko kuma juya ki koma. Ina tsaye a gurin na kasa kuka na kasa magana har Baba ya shigo. “Shiga ciki ki zauna mana, ai duk abun da kike ba laifin ki ba ne uwarki ce ta ke goya miki baya, baki da matsala ke” Cewar Baba sannan ya wuce ni ya shiga cikin gidan. Mama kamar tana jiransa ta ce. “Daman ai kullum ni ce ice mai dadin hawa, nan gana Noor ko kisan kai ta yi ni zaka dorawa laifi, duk abun da kowa zai aikata kaina zai dawo, shin ni kadai nake da hakkin tarbiyantar da ita? Kai ba Uba ba ne?” “Saboda ina uba sai aka ce na zauna gida na kula da yara? Tarbiya ai ta uwace no Cewa aka yi na fita na nemo, ke zaki kula da gida dan haka dole duk abun da yara suka yi na ce laifin ki ne” Mama ta yi shiru na san kuma ba dan ta rasa abun cewa ba sai dan tana gudun fadan yayi nisa. “Ni na gaji da halin yarinyar nan, tun da aka haife ta cikin wahala nake, kar taje nan gaba ta dauko min abun magana tun da har ta gane bibiyar maza a inda suke, daga bige hannu da kai ban san inda za'a tsaya ba, ko yanzu Allah kadai ya san gaskiyar abun da ya faru, kar taje ta dauko min abun kunya na kasa fita cikin jama'a, zan fadawa yaron idan ya shirya fito ayi auren daman ni dai ba wani abu na aje ba, balle na ce zan dauka na kai masa, ko zane daya Allah ya hore masa ya kawo a hada ya da tabarma ayi musu aure su je can su karata, ke dai ba iya tarbiyarta kike ba tun rana karama balle kuma yanzu da take kara girma” A fusace Mama ta mike tsaye sai ganin na yi bulalar wayar wuta ta fado a jikinta. “Wai Malam tunanin kake abun da Noor take dadi yake min? Ko kuma ganin kake ni nake zaunawa na tsara mata shirirtar da zata je ta yi a waje? Daga Islamiya fa ta bar yar'uwarta ta tafi gurin yawon shiririta, a can idan kasheta za'ayi an dade ba'ayi ba, kuma kamar Noor ace ta san ta tsame kafa ta bi wata su tafi restaurant, kanen ubanta ne a can ko na uwarta, babu sanarwa babu neman izinin kowa” Baba ya rike gemu. “Toh.... Ai ga irinta nan a gabansu kike fada min magana son ranki kina min tsawa saboda kin isa, ai tarbiyarce suke kallo suna dauka” “Tarbiyar ce, idan baka Gamsu da ita ba Malam ka auro wata uwar ta zo ta ba su wata tarbiyar, daman ai ka saba aure aure” Yau kai na ga dabam, Baba ce take fadawa Baba magana cikin bacin rai abun da bata taba ba a gaban idona. Baba kamar yana jira sai ya nufe ta yana nuna kansa. “Ni kike cewa na saba aure aure...?” Ya Nabil dake zaune yayi hanzarin mikewa tsaye ya tare Mama ya shiga tsakiyarmu. “Toh ko dukana zaka yi? Nace dukana zaka yi?” “Ba dukanka zan yi ba Baba amman ba zan zuba ido ina kallo ka daki Mama ba a gaban idonmu, Baba abun da kake babu dadi wani abun ba laifinta ba ne amman sai ka dora mata laifi komai aka yi a gidan nan cewa kake laifinta ne, ta ina yanzu laifin Noor ya shafe ta? Baba be kamata ace a gaban idonmu ka doke Mama ba wani abun ai ka daga mata kafa ko dan mu” “Ayyy haka ne, lallai Nabil wuyanka yayi kwari, yanzu ni zaka zauna ka tsarawa magana haka son ranka? Ashe kai ma baka da mutunci toh sai ka doke ni na san ka girma marar mutunci, saboda ina talaka kake raina ni?” Mama ta ja Nabil gefe ta tura shi. “Fita can waje idan ya fita sai ka dawo...” Tana rufe baki Baba ya dauke ta da mari. “Ya fita sai na fita ya dawo wato ga mahaukaci ko? Ga mahaukaci na hauka” “Baba...” Ya Nabil ya zaburo da karfi yana hakki har sai da Mama ta rike shi. “Kul kul kul ko yanka ni ubanka yayi ka kai hannu ka dake shi ban yafe maka ba Nabil, karka kuskura zuciya ta debeka ka aikata abu makamancin wannan” Sai kuma ya fashe da kuka Mama ma ta saka kuka. “Fice ka bar min gida, karka sake kwana min a gida daga yau, kuma kar a sake ba shi abincin gidana” Baba ya fada yana nuna masa kofar waje. Ni kam na yi tsaye kamar hoto ina kallon drama da ake a cikin gidanmu, na san halin Baba na dukan Mama ko fada mata magana marar dadi, domin mahaifina irin mazajen nan ne da ba su girmama matansu sun maida matansu kamar ba yi, shiyasa duk auren da yayi babu mai dadewa suke fita su bar Mama. Sai dai abun da ban saba gani ba shi ne mayar da martani na magana da Mama ta yi a yau, da kuma yunkurin da Ya Nabil yayi, duk kuma saboda ni ne. Baba ne ya fara ficewa daga gidan sannan Yaya ya nufo kofar fita sai na jinin jikina na matsa jikin gini sosai gabana na faduwa hawaye na ta zirya a fuskata. Ashe dai ban tsira ba domin yana kawowa kusa da ni ya dauke ni da mari mai bala'in zafi da radadi har sai da na taune halshena. Kuma yaja ya tsaya a gabana, jira yake na yi kuka ko na kalleshi ko kuma na furta wani abun yayi min duka. Ban yarda na daga ido ba balle na kalleshi ban bar wata kalma ta fito daga bakina ba, kuma kuma ban yunkurin yin motsi ba har ya gaji da tsayin yayi ficewarsa. Sannan na dago kai na kalli na kalli cikin gidanmu, Mama na jiyo tana fadin. “Kin yi nasara an kuri dan'uwanki ga dakinsa can sai ki share ki zauna, ba ke kadai na haifa ba amman ke kika saka ni ciwon kai da ciwon zuciya kullum, girmanki ya kai ace kina da wayo da hankali amman yayi miki nisa, baki bar ni da bakincikin ubanki ba, ba ki bar ni da bakincikin neman abun da zan aurar dake da abun da zamu ci ba, wani kike lalabowa kina yafa min, kullum nuna miki ake amman sai ki rufe ido bako duban daidai na gaji da halinki Noor” Na durkusa daga inda nake tsaye ina son na bata hakuri na kasa magana. Gurin da muke aje kayan wanke wanke ta nufa tana juyowa na ga wuka a hannunta, domin tabbatarwa sai ta nufi suminti ta koda wuyar sannan ta juyo ta kalleni. “Kin ga wuka nan na koda, yau sai na kwantar da ke na yanka, na gaji da halinki yau din ba zaki kwana da rai ba...!” Yanayin da na samu kaina a lokacin da Mama da nuna ni da wukar tana furucin da ya dursaso da tashin hankalina a kusa ya wuce misali. Ashe har na gundurar da Mama haka, rashin jin magana ta ya kai Mama tace zata yanka ni? Ashe uwa zata iya kashe yarta? Na mike tsaye ina jin kamar wata murya na fada min na juya na fice daga gidan, sai dai idan na fita ina zan je? Wa zan je na roka ya bawa Mama hakuri? Yau ta yi fushin da bata taba yi ba, yau ta furta min kalmar gajiya, ta furta sao ta yanka ni, na tabbatar babu wadda zai ceto ni a yau na kwana da rai. Na fito na tsaya daga bakin kofar gidan na raba jikin ginin na rumgume hannuna ina tunanin inda zan je. Kamar ance dago kai ina dagowa na yi arba da Hana tana kuka ashe tana cikin gidan amman ban ganta ba duk abun nan da ake. “Ki tafi gidansu Maman Zainab ki kwana, dan Allah karki gudu ki karawa kanki laifi, Baba yayi min duka saboda na ki fadar inda kika je lokacin da na dawo daga makaranta har sai da na fada sannan ya kyale ni, Noor miye amfanin abun da kike yi? Dubi yadda kika sakawa kowa bakinciki yau” Ita ma dai bani da amsar da zan bata dan haka na duka na duka a gurin ina jin halshena yana zogi saboda marin da Yaya Nabil yayi min. “Hannatu...” Mama ta kira da karfi, sai ta juya da sauri ta koma cikin gidan ta bar ni a gurin duke ina tunanin makoma. Can kuma na mike tsaye na nufi gidansu Zafeer domin ban san wani abun da zan yi ba, sai dai tunawa da ba lallai ne Mama ta hakura ba ko da ya mata magana ya katse hanzarina, a madadin shiga cikin gidan sai na mike na kama hanyar gidansu Kareem. Tafiyar da zan biya 200 a kai ni gidan ita nake yi a kafa ba tare da gajiya ko kasawa ba. Zan iya shaidar kaina ina ba basira da gane abu ko da kuwa sau daya na gani, hakan ya saka na yi saurin gane gidan sai dai na shiga unguwar a lokacin da sawu ya fara daukewa ne, bana da agogo balle na iya fadar karfe nawa, amman tabbas dare yayi domin mai gadin gidan ma hanani shiga yayi bayan na kwankwasa. “Toh dan Allah ka fada masa Noor ce tana waje” Na bashi sako sannan na ja na tsaya ina jin tsoron wajen saboda babu kowa. “Ki jira a nan ina zuwa” Ya rufe gate din ya bar ni a gurin tsaye, bayan dan lokaci na sake jin an bude kofar. “Shigo” Na shiga cikin gidan, na doshi main door kamin na karasa Kareem ya fito sanye da pajamas ya nufo inda nake sai muka ci karo a tsakiyar gida. “Noor lafiya?” “Mama tace sai ya yanka ni, tace yau ba zan kwana da rai ba, ta nuna min wuka kashe ni zata yi, Yaya yayi fada da Baba har ya koreshi saboda ni, kanwata ma an mata duka saboda ni” Ina maganar hawaye suna fadar yau ce ranar mu, jikina na karkarwa kamar mai jin sanyi. Shiru yayi yana kallona kamar mai tunani me zai fada ko ya aiwatar. “Babana yana jin maganarka, Mama kuma tana jin maganar Baba, so nake ka tafi ka bawa Baba hakuri shi kuma ya bawa Mama hakuri ta yafe min, ka fada ma Baba ya fada mata daga yau ba zan sake ba, ka ce ina rokonta ta yafe min” Na fada masa bukatata. “Waya kawo ki nan?” “A kafa na zo, ka yi hakuri ba zan sake takura maka ba daga yau ba zan sake batawa kowa rai ba” Ni dai ban san ya aka yi ba na jini na jikinsa ya rumgume yana rarrashina. “Ya isa haka Noor I'm sorry” Ji na yi kamar na samu wata mafaka sai na fashe da kuka mai mugun karfi. “Ya isa ya isa haka kar yarana su ji” Ya sake ni da sauri. “Shigo ciki na canja kaya sai mu tafi gurin mahaifin naki” Na bi bayansa muka shiga cikin falon sai na tsaya daga bakin kofa ina kallon matarsa dake zaune tana cin abinci. Sama ya nufa be jima ba ya sauko sanye da jallabiya da hula hannunsa rike da keys. “Wani taimako take son na yi mata, zan je na dawo yanzu” Ya fadawa matarsa, sai ta dubeshi ta dauke kai. “Kai ka ta shafa, idan ka aikata abun kunya yayanka ne a kunya ba ni ba, ni matsalarka bata gabana” Amsar ta bata ba ni mamaki ba kamar yadda shi din ya ba ni mamaki ta hanyar dauke kai ba tare da ya ce mata komai ba ya kalleni ya ce “Mu tafi” Na juya na fara fita sannan ya fito, sai da ya janyo mota sannan na bude da hannun hagu na shiga domin na dama a daure yake. Tun da muka shiga motar be ce min komai ba, ni ma ban ce masa ba muka isa unguwar yanayin yadda na ga mutane sun rage ya tabbatar da dare yayi sosai. “Ina zamu samu ganin Babanki a yanzu?” “Yana zama a majalisa kamin ya shiga gida” “Ina majalisar take?” Na fada masa sai ya bude motar ya fita yana kara tambayar kwatancen domin be san kan unguwar ba. “To jira ni a nan” Na daga masa kai na bishi da kallo har na daina hangoshi. A kiyasina za'ayi minti talatin da fitarsa sannan na hango bullowarsa tare da Baba dake rike da fitila duk da kasancewar akwai wutar nepa. Na bude motar na fito ina kallon Baba. “Ah ah Noor to ai da sauki ma tun da gurinka ta tafi, da ta fi duniya ai shikenan to zo mu tafi gida” Na nufeshi ina jin tsoro, Kareem kuma ya koma cikin motar ya zauna har sai da muka yi nisa sannan ya biyo bayanmu. Baba ne ya fara sallama ya shiga cikin gidan sannan na bi bayansa. “Ke Hajara fito ga Noor din gata nan ki yanka ta” Da gudu na ga Mama ta fito har sai da na tsorata naja baya. “Noor ina kika je?” Ta tambaye ni tana kuka “Ina kika tafi na aika nemanki ko'ina baki nan” Ban samu amsa mata ba Kareem yayi sallama ya shigo sai Baba ya amsa masa sallamar. Kareem ya kalli Mama ya gaisheta “Dan Allah ayi hakuri, abun da kika furta kin tsoratata ma bar gida ta tafi a kafa ta same ni har gida tace na zo na baki bakuri tare da Babanta, kuma tace na fada miki ba zata sake ba, dan Allah ki yi hakuri” “Babu komai na yafe mata, ni ma na gane kuskuren fadar hakan da na yi bayan ta bar gidan, domin bayan gidan nan bata da wani masauki, kuma mace ce hankalin ya tashi sosai a lokacin da aka duba ko'ina ba ganta ba, wani lokacin rai ne yake baci ka aikata abun cikin bacin rai, Zafeer ma be dade da aikowa kiranta ba nace a fada masa bachi take, na mata haka ne saboda ta tsorata ta daina abun da take, ba dan ina da niyar aikatawa ba” “Alhamdullahi, daman na san uwa dole zata nemi yarta duk runtsi, addu'a ya kamata ana yi ba sai tsoratarwa ba” Kareem ya fada sai Mama ta mika hannu ta janyo ni ta rike. “Ai Alhaji Noor din ce sai hamdala, ni ina ganin aurar da ita kawai zan yi na huta, shi yaron nan idan ya shirya ya fito idan kuma be shirya ba ko a Masallaci ne zan yi cigiya na bada ita sadaka, ita ta huta mu ma mu huta” Baba ya fada, sai Kareem ya kalleshi ya ce. “Noor din nawa take da za'ayi mata haka? A dai yi hakuri, ni zan koma ga dubu ashirin a siya wani abu” Baba ya saki fitar hannunsa ya mika hannu ya karba. “Ahhh Allah da iko yake, kai yaron nan gajiya da kyauta, dazun ma fa sai da ka ba ni wasu kudin, Allah dai ya saka da alheri ya rabaka da iyayenka lafiya Allah ya kara budi” “Ameen Ameen” Har ya juya sai kuma ya juyo ya kalli Baba dake kokarin yi masa rakiya. “Am Baba dan Allah ina son na bada hakuri akan Nabil ka yafe masa shi ma dai ya dawo gida ya zauna, ku daina daukar zafi akan yaranku ayi hakuri dan Allah” Baba ya amsa da sauri. “In Shaa Allah, babu komai na yafe masa ya ci albakarcin ka ba komai” “To na gode” Ya juya ya fice Baba ya bishi yana addu'a, ni kuma na kalli Mama. “Mama ki yo hakuri daga yau ba zan sake ba” Sai ta kwantar da ni jikinta tana kuka. “Na yafe miki Noor, bakincikin ne yana min yawa, amman dai idan bana duniya babu wadda zai fada miki gaskiya, Allah ya sauya miki rayuwa ya canja wannan hali na ki” Ta nufi dakinta da ni tana rumgume da ni, wani dadi da natsuwa na ji marar misaltuwa saboda yafe min da Mama ta yi har ta rumgume ni. KAREEM POV. Ajiyar zuciya ya sauke bayan ya faka motarsa a harabar gidan, sannan ya ciro wayarsa ya shiga WhatsApp dinsa da datarsa take always on ya shiga chatting dinsa da Safeena ya rubuta mata sako. “Safeena wannan ya zama karo na karshe da zaki sake kai hannunki jikin yarinyar nan, babu wani abu tsakanina da ita, duk abun da ta fada ko Hafiz ya fada sun fada ne kawai saboda su fusata ki, ina sonki kin sani, kuma na san kina so na, amman hakan ba zai baki damar ki aikata sakarci a gaban kowa ba, ko kuma ki yi yunkurin cutar da wani ba zan lamunce miki wannan ba, kuma babu ruwanki da yarinyar nan daga yau” Yana aje mata sakon ya bude motarsa ya fita ya rufe sannan ya kama hanyar falon gidan. Shiga falon ke da wuya sakonta ya shigo wayarsa sai ya bude arba yayi da hoton bari da kuma rubutun sakon dake bin bayan hoton. “I lost my baby today saboda bakincikin jin cewar kana son wata Kareem, mijina ya kasa gane kaina yau saboda kai, na fitunu da kaunarka da Kareem, amman kokarin cire ni kake a rayuwarka bayan duk budulcin da ka yi min na kin aurena” Ya karanta sakon kusan sau uku sannan ya sake duba hoton barin da ta turo masa, a madadin ya ji dadi abun da yake nema ya samu wato cikin ya zube, sai abun ya tsorata shi, har ya fadi zaune a kujera yana mamakin kansa. ‘Ta ya yayi zurfi a zuciyar matar wani haka? Har bakincikin jin cewar yana son wata zai saka cikinta ya zube, me yake aikatawa haka? Wane irin mutum ya zama? Wane kalar uba ya zama? Wane kalar miji? Wane kalar ďa? Ashe tasirin sabon da zuciya take kwadaituwa da aikawa ya kai haka?’ Ya mike tsaye zuciyarsa na bugawa da karfi, idan ya mutu a cikin daren nan yana da wata hujja da zai fada ya fanshi kansa a gurin Allah? Me ya aikata haka? Zina ba halinsa ba ne me yasa zuciya ta kai shi? Ta ya yake kokarin lalata rayuwarsa? Su ne tambayoyin da suke masa yawo a kai idonsa suka cika da hawaye. Ya nufi sama da sauri ya tura kofar dakin yaransa ya tsaya daga bakin kofar yana kallon Tine dake bachi ya karasa ya zauna kusa da ita ya kai hannu ya shafa kanta yana tuna maganar matarsa. “Kai ka ta shafa, idan ka aikata abun kunya yayanka ne a kunya ba ni ba, ni matsalarka bata gabana” Ya hade yawu ya mike tsaye ya gyara mata bargonta sannan ya fice dakin a hankali ya ja kofar. Dakin matarsa ya nufa nan ma a hankali ya tura kofar ya shiga sai same ta kwance tana bachi Areef na gafenta shi ma yana bachi. Karasa yayi ya kalli dansa ya kalleta ya mika hannu ya shafa dansa sannan ya juya ya fice. Follow the KHADEEJA CANDY channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaNTEQTFXUuaypyV5O01 *Duk mai son ya rika samun Littafin TA KI ZAMAN AURE yayi following wannan Channel din mai suna KHADEEJA CANDY a nan zaku rika samu duka littafaina in Sha Allah* ✧✦ 𝗧𝗔 Ƙ𝗜 𝗭𝗔𝗠𝗔𝗡 𝗔𝗨𝗥𝗘 ✦✧ 𝗕𝘆 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆 *Talla👇👇👇* KINADA DAYA DAGA CIKIN WADANNAN MATSALOLIN ❓👇👇👇 To kiyi saving numba ta ki danna wannan link👇 https://wa.me/message/N2S6DQEPETKQO1 Idan kinyi saving ki fadamun zanyi SAVING TAKI😍ko Baki Siya yanzu ba WATARANA zatayi maki AMFANI👇👇 1.INFECTION CIWON SANYI 👉LALACEWAR BREAST👉RASHIN HIPS & BUTT👉KIBA TAYI MAKI YAWA KINASO KIYI SLIMMING👉TUMBI YAYI MIKI YAWA KINASO KI RAGE ?👉 AKWAI KUMA INGANTATTUN KAYAN MATA APHRODISIACS MASU KYAU DA INGANCI GA kUMA SABAYA ASALIN MAI KYAU 3500 only 👌 KIZO KI GWADA KAYAN AMNOOR INA TABBATAR MAKI BAZAKIYI NADAMA BA 👉 KIYI SAVING NUMBER TA DM ME https://wa.me/message/N2S6DQEPETKQO1 Chapter - 9 KAREEM POV. 8:19am ya nade sallayar da yayi sallah ya aje, sannan ya dauki wayarsa dake ringing ya duba. Ganin number mahaifiyarsa ya saka shi farinciki. “Hello Momy” “Ashe zaka dauka, ai na dauka idan an kira ka ma ba zaka dauka ba” “Haba Hajiya me ya kawo wannan maganar kuma?” “Yaushe rabon da ka kira ni?” Ya sauke ajiyar zuciya ya zauna gefen gadonsa. “Na kira sai Baba Karami ya dauka ya ce min kina bachi kuma likitocin sun ce a barki ki huta na kwana biyu kar a takura miki, ana son ki samu bachi” “Wannan ba hujja bace, hakan ai be hana matarka kirana safe da rana da dare ba, kullum sai ta kira ni sau uku ko da ban amsa wayar ba zata ce idan na farka a sanar min ta kira waya, haka ma mahaifinku kullum sai ya kira ta gaishe shi” Yayi shiru for few seconds sannan ya ce. “Yi hakuri Momy, Wallahi saboda likita yace a barki ki huta ne yasa ban takura da kira ba, Daddy kuma ina son na shiga this Saturday na gaishe shi” “To ya dai kamata dai, ina yaran?” “Suna lafiya Momy, ya karfin jiki” “Alhamdullahi ina samun sauki, yanzu dai suna gasa min kafafuwan ne, sun ce jinin ya sauka” “Maa Shaa Allah haka nake son ji, Allah kara sauki ya dawo mana dake lafiya” “Ameen, Allah ya muku albarka kai da yaranka, Yusura ma Allah ya mata albarka mace ce mai mutumci samun mace irinta akwai wahala yanzu, yarinya ce mai kirki da biyayya duk da kasancewar ta yar'uwa ta kara karfafa zumuncin, bata taba nuna min cewar ba ni na haifeta ba, shiyasa ko da yaushe nake jan kunnenka akan riketa amana, duk da na san kai ma yaro ne mai biyayya da kulawa, Allah dai ya muku albarka” Sai da Kareem ya hade wani abu da ya tsaya masa a wuya sannan ya amsa da Ameen yayi mata sallama ya sauke wayar. Sannan ya mike tsaye ya aje wayar ya nufi kofar dakin ya bude ya fita, sai da ya fara leka dakin Tine ya duba bata cikin sannan ya rufe kofar ya sauko kasa. “Ina kwana?q” Ya gaishe da Yusura dake jera kuloli a dinning. A madadin ta amsa sai ta tambaye shi domin shi da ita ba al'adarsu ba ce gaisawa da juna da safe, kara ma shi ya kan fada mata wani sa'in idan zai fita, ko kuma gaisheta musamman idan yaransa suna nan. “Wani abu kake bukata ne” Ya kalli tv domin shi ma ba son kallonta yake ba, yana daga cikin dalilin da ya saka duk yadda yake son tsara gidansa ko tsara zama fa matarsa wannan rashin son, da kuma rashin ba shi hadin kai sai ya wargaza tsarinsa. Ya dauke ba tare da ya kalleta ba ya ce. “Momy ta fada min kina kiranta kullum ki ji ya jikinta” “Ba saboda kai nake yi ba, bana bukatar godiyarka, ina yi ne saboda kulawa da ita da girmamata wani abu ne da na saba da shi tun kamin na aureta, aurenka ba shi da tasiri a gurina baka da kimar da zan maka alfarma” Ya zuba hannayensa a jallabiyarsa ya daga kai ya kalli yadda Allah ya wadata da mazaunai da shape kamar wadda ta yi surgery. “Me yasa tun farko baki fada mata baki son danta ba, wannan soyayyar karya kike nuna mata” Ya juyo ta kalleshi. “Danta ya kasa fuskarta ya fada mata be son matar da ta zaba masa sai ni? Dukan abun da na ke yi ma Momy ina yi saboda Allah kuma saboda ita din uwace a gareni, ta rike ni a lokacin da uwata ta tafi ta bar ni, ta rike ni a lokacin da yan'uwan mahaifina suna wofintar da ni, ta rike ni a lokacin da ban san komai ba, tun bana iya cin komai sai madara har na mallaki hankalin kaina, a hannunta na yi ilmi a hannunta na girma ita nake kallo a matsayin uwa, da Momy zata ce Yusura dauki wuka ki dabawa kanki Wallahi zan daba. Na fada maka duk wannan ne saboda ka san ba saboda kai nake yi ba” “Ni ma bana fatan shiga alfarma, bana fatan kasancewa a karkashin inuwar alfarmarki, ina jin fiye da abun da kike ji game da auren nan” Ta tintsire da dariya. “Na nawa kuma? Ai na gama yi maka alfarma Kareem tun da har ka kasa rike kanka ka keta rigar mutuncina, kuma ka yi nasara har na haifa maka yaya biyu, ka gama cin alfarmata, sai kuma me?” Ta daga masa gira tana jiran amsarsa. Baya jin zai biye mata su fara abun da suka dauki lokaci ba su yi ba, ta saba fada masa magana marar dadi amman a haka yake hadewa ya danne saboda yana jin shi namiji ne ya fita hankali da tunani, and wani lokacin yana jin kamar ta ci albarka cin yaransa. Yayi murmushi ya sake kallonta ya dauke kai ya juya ba tare da yace komai ba ya nufi stairs. “Ga breakfast dinka nan” “Ba a gida zan ci abincin safe ba” Ta tabe baki ta ja kujera ta zauna tana magana a hankali da muryar da ba zai ji ba. “Ni dai kawai ina ibada, kuma ina jiran ranar takaba” Kareem ya shiga dakinsa ya cire tufafin jikinsa ya shiga bandaki ya fara murza jikinsa har yayi wankan ya gama maganar da Yusura ta jefeshi da ita cewar ta gama yi masa alfarma tun da har ya kasa rike kansa har sai da ya kai ga jikinta tana cin ransa. The part that ita bata san duk kokarin kai kansa da yake gurinta yana yi saboda ya bata hakkinta ba is more painful sama da aurenta. Yana fitowa ya shirya cikin farar shadda ya saka hula ya fesa turare ya dauki abubuwan bukatarsa ya saka talkaminsa ya fice daga gidan. Ko da ya sauko tana zaune a dinning din tana cin abinci. Be kulata ba ya fice daga falon motarsa ya shiga ya murza key mai gadin ya bude masa yana mika masa gaisuwar barka da safiya. Hannu kawai Kareem ya daga masa sannan ya kama hanyar da zata kai shi gidan abokinsa. Yana kan hanya kiran Safeena ya shigo wayarsa, duba wayar kawai yayi ya aje be sake daukarta ba sai da ya isa gidan Hafiz sannan ya kira ya sanar masa yana waje. “Shigo ciki mana” Kareem ya bude motar ya fito ya rike da wayarsa da Safeena ke kara kira. Iskar bakinsa ya busar sannan ya amsa wayar. “Hello” “Baka kira ka ce ya jikina ba? Baka yi tunanin ko bana jindadi ba? Miscarriage na yi ba jiya, yanzu baka ma damu da lafiyata ba Kareem?” “Safeena ina son za mu yi magana da ke face to face amman bana son mu yi magana yanzu sai idan mijinki baya gari” “Na ji muryarka wani iri, matarka ce ta bata maka rai?” “Me zai saka matata ta bata min rai?” “Ban sani ba, amman dai na san nice mai faranta maka a kodayaushe ba tare da gajiyawa ba” “Ya jikinki.?” Ya tambaya domin ko da yace be damu da Safeena ba ko lafiyatarta ko kuma yace baya sonta yayi karya. “Da sauki, ina asibiti yanzu haka” “Idan kin dawo zamu yi magana” “Okay i love you” Ba tare da ya amsa mata da i love you too ba ya kashe kiran ya saka wayar aljihu sannan ya doshi kofar shiga yayi knocking. Hafiz ya bude masa kofar. “Shigo mana” Ya shiga falon kamar marar lafiya. “Bismillah ga breakfast na san baka karya ba” Hafiz ya fada yana nuna masa dinning, Kareem ya karasa daman gidan ba bakonsa ba ne. Ya zauna a kujera Hafiz ma yaja kujera ya zauna. “Yanzu nan ni ma na dawo gida, na sauke madan a gurin aiki” Kareem ya sauke ajiyar zuciyar dakw bayyana damuwarsa sannan ya ce. “Hafiz ina cikin matsala, ina jin kamar ina daure da sarka, ina jina kamar ina a tsakiyar hanya da ta kasu na rasa wacce zan bi?” “Me ya faru bayan abun da na sani?” Tambayar da Hafiz yayi masa kenan yana zuba madara a cikin tea da already ya saka sugar. Kareem ya fara masa samun cikin Safeena da kuma zubewar wadda shi ya fi damunsa a yanzu. Hafiz ya aje tea cup din dake hannunsa yana kallon abokinsa da mamaki. “Yanzu abun ya kai jar ciki ya shiga tsakaninku Kareem kuma har ta yi alfahari da haka? Subhanallahi abun ya munana ya kazanta” Kareem ya dauke idonsa daga barin kallon abokinsa saboda kunyarsa da yake ji. “Baka ji tsoro ba ace cikin ya zube saboda kishina?” “Hakan ya ba ni tsoro sosai kuwa, kuma hakan yana nufin idan baka shata line tun da yanzu ba, Safeena zata wuce gona da iri, kuma zata jan yo maka matsaloli da yawa, a cikin idon yarinyar nan na hango rashin kunya da rashin imani, matukar baka takawa lamarinta burki ba zata janyo maka matsalar da baka isa ka fitar da kanka ba, kuma zata jefa duk wadda yake tare da kai a matsala” Kareem ya sauke ajiyar zuciya. “Zuciyata na raya min wani abu akan son haihuwa da take da ni, na san tana sona, amman na tsorata da wannan son, idonta yana kokarin rufewa akaina ina jin kamar tana son ta haihu da ni ne a yanzu, saboda a gaba mu kasance tare, ni kuma babu wannan a tsarina ba zan iya auren Safeena ba” “Idan kuma ta gane haka ba karamar illa zata maka ba, shiyasa nake son ka rabu da ita tun yanzu ka tuba ya canja Kareem, karshen cin amanar da zaka yi shi ne ka bari matar nan ta dauki cikin da bana mijinta ba kuma ta haifa masa yaron yayi hidima da shi, kuma da zarar ta haihuwa zata bukaci ka aureta ne ko kuma wani abun dabam, a yadda na lura bata da kunya zata iya lalata rayuwarka saboda idonta a rufe suke, zata iya maka illar da zaka rasa aikinka ka rasa matarka ka rasa girmamawa daga yayanka kuma ka rasa kima a idon mahaifiyarka da yan'uwanka, duk wata kima da martaba da ake ganinka da ita zata iya zubar da ita” Kareem ya dauki tea ya sha yana nazarin kalaman Hafiz. Sai da Hafiz ya motsa tea ya sha ta gutsira biredi sannan ya ce. “Ina yarinyar nan? Ya hannunta Noor ko?” A take murmushi ya cika fuskar Kareem kamar ba shi ba. “Ka ma tuna min ya kamata na kira na ji ya jikinta, jiya ta dawo bayan na kaita gida...” Hafiz ya girgiza kai bayan ya gama sauraren labarin da Kareem ya ba shi na abun da ya faru tsakaninsa da Noor da iyayenta a jiya. “Mahaifinta yana son abun duniya sosai kuma baya tunanin abun da ya dace, miye abun sadaka a nan?” Kareem ya tabe baki. “Ba dan na bashi kudi ba babu abun da zai hana shi dukanta, yarinyar tana ba ni tausayi ga mahaifiyarta ta kai ga nuna mata wuka” “Kawai tana nuna musu real her ne, su kuma sun ki fahimta” “Shi kansa saurayin da wahala ya iya handling dinta, yana zuwa ya rufe ta ta fada duk sai na ji babu dadi, shiyasa ma na riga su isa na yi magana da Babanta, sun kasa fahimtarta but with time zata daina, yanayin rayuwa ne kowa da yadda yake tashi” Hafiz ya kalleshi yana murmushi. “She's sweet” “Yeah she's so friendly tana da shiga rai” “More especially when she meet someone like you, kana son wasa da kiriniya a yadda na sanka Kareem kai mutum ne mai son rayuwar aure da nishadi, kai mutum ne mai son shakuwa da mace, kana yawan ba ni labarin yadda kake son ka yi rayuwar aure da matarka irin na soyayya da kaunar juna da taimakona, idan ban manta ba yana daga cikin dalilin da ya saka kake son Safeena sosai” Kareem yayi murmushi ya girgiza kai. “Wannan duk da ne Hafiz, ban da yanzu” Hafiz ya sake yin murmushi ya cigaba da karyawarsa har sai da Kareem ya ciro wayarsa yana fadin “Ka tuna min ma, bari na kira Yayanta na ce ya bata na yi mata ya jiki ba mamaki kuma ban siya mata magani ba na manta sam” “Karka kira, tashi muje mu duba ta kawai zai fi mutunci, kuma sai ka rubuta mata maganin nan daga nan ko ba siya ba sai ka bada kudin maganin” Kareem ya kalleshi ba dan yana jin son tafiyar ba. “Why?” “Zata ta maka complain ne idan baka je ba ai, na lura ita ma tana son kasancewa da kai if not ba zata yi karya tace kai saurayinta ba ne” Kareem yayi dariya. “Wato wannan yarinyar ko? Idan baka fahimce ba zaka hau sama ka fado ne ka ji rauni, babu wani son kasancewa kawai tsabar iskanci ne da son nuna ita wata ce ai ta fada min gaskiya” Hafiz ya aje cup din ya Mike tsaye. “Ba mamaki abun da muke fata ya kasance ai, shiyasa na kirata da Amaryarmu a gaban Safeena, kuma na san ba zaka kunyata ni ba, ba za ka zabi bangaren Safeena ka bar bangarena ba, ko ba Noor ba dole zaka yi aure Kareem, saboda ka samu gurin da zaka rika jin sanyi, kuma karin sauren zai nesanta ka da wannan zunubin da kake diba, ina fatar dai Momy ba zata ba mu matsala ba” “Momy bata da matsala da karin aurena, ni din ne dai bana ra'ayin mace fiye da daya” “Ai shi ya cutar da kai har kuka fada tarko kai da Safeena, auren fari baka auri wadda kake so take sonka ba, yanzu zamu nemi mai sonka mu aura maka” “Indai dan haka ne, kar muje gidansu Noor yarinyar nan tana da wadda take so, ba kuma zan sake kuskuren auren macen dake son wani ba, na yi na farko saboda biyayya ba zan yi na biyu ba” “Take so ko dai yake sonta, ai ita bata san so ba a yanzu, kai ka fada min shekarunta fa, kuma kaga yadda rayuwarta take, shi kuma ba lallai yana sonta ba ko kuma zai iya zama da ita, and ba dan wannan zamu je ba, zamu je ne saboda mahaifinta ya maka alfarma idan muka yi haka next time idan ta sake laifi ta gudo gurinka zamu iya ba shi hakuri kuma ya hakura” Kareem ya bishi fa kallo, ya fi gamsuwa da reasons dinsa na karshe dan haka ya mike tsaye ya bi bayansa. A motar Kareem suka dauki hanya, kamin su isa Kareem ya bi ta wani pharmacy ya siya mata magani ciki har da na zafin kafa saboda tafiyar da tace masa ta yi a jiya. NOOR POV. Ban kwanta ba sai da na rama sallah magariba da ban samu yi ba saboda tafiyar da na yi a kafa zuwa gidan Kareem sannan na kwanta a dakinmu tare da Hana, washe gari na farka da asuba, da kaina na warware hannuna saboda alwalar da zan yi na ji azaba sosai amman a haka na daure daman karfin hali rayuwata ce, Hana ce dai da bata saba da wahala ba ta tashi da zazzabi saboda dukan da Baba yayi mata. Mama ita ta yi shararta da safe bayan ta gama hada mana abun karyawa. Ina zaune dakinmu ina ji sallamar yaro Mama ta amsa Baba dake daki kwance yana sauraren redio kuma ya kashe radio yana sauraren abun da yaron yana fada. “Wai Zafeer ya ce a ga sako a abawa Noor kuma yace yana waje yana sallama da ita” “Toh shiga ga dakinta can ka kai mata” Na ji Mama ta fada, sai yaron ya iso bakin kofar dakinmu yayi sallama, na mike tsaye na amsa sai ya shigo rike da katon kwando ya aje min. “Gashi Wai Zafeer yace a kawo Miki kuma yace yana waje yana sallama” “Toh” Yaron ya juya ya fita ni kuma na dauki hijab dina na saka sannan ya bude kular dake cikin kwandon na duba kwai ne soyayye da plantain sai kamshi suke. Na rufe na fita ina jindadi na nufi waje cikin natsuwa, tsaye na same shi rike da wata ledar da ban san meye a ciki ba. “Baby Noor ya jikin?” “Alhamdullahi, kai ka aiko min da sako?” “Eh na yi tunanin ko ba zaki iya cin abun da aka girka ba a gidan na saka aka shirya miki wannan” “Na gade” “Never mind, jiya na kwana da tunaninki a raina, na zo Mama tace kin kwanta, jiya ya bani kamar wani abu ya faru dake, sai na kasa natsuwa” “Lafiya Kalau” “Kin ji sauki? Ya hannu mu gani” Na bude masa ya duba cike da tausayawa. “Noor dan Allah ki daina wannan rashin jin nan bana jindadi yadda abubuwa suke faruwa dake, kuma bana son yadda Mama ko Baba suke miki hukunci, kuma Noor please bana son na sake ganinki da mutumen nan, bana son na sake jin wata alaka tsakaninki da shi” “Bafa komai tsakanina da shi, kawai shi yace abokina ne wai, na fada masa ina da saurayi ina da wadda zan aura” Ya daka min tsawa. “Wane irin aboki? Abota ake mace da namiji ne? Kar na sake jin sunansa ma na fada miki ko?” “Eh na daina” “Good karbi wannan magani ne na siyo miki na sha da shafa” “Toh na gode Sosai Zafeer ina sonka sosai” “Ina sonki Noor, ina sonki irin son da baki taba tunani ba, irin son da idan na rasa ban san wane hali zan shiga ba” “Ni ma idan ba kai ba ba zan auri kowa ba” “Ko ma kin yi auren ba zaki zauna ba, babu wadda zai iya dawainiya dake Noor sai ni kadai, da zaki auri maza dari Noor ba za su iya dake ba sai Zafeer ke tawa ce har abada!!!” Na yi murmushi ina jindadi shi kuma ya mika min ledar na karba yayi min murmushi sannan yace. “Allah ya baki lafiya, shiga ciki kar ace kin jima a waje” “Toh” Na masa waving na dawo cikin gidan, a tsawon shekara uku da muka yi tare da Zafeer ba zan iya fadar ranar da kaunarsa bata karuwa a zuciyata ba, kamar yadda ba zan iya bayyana yadda yake kaunata ba. Soyayyarmu da shi wani abu mai rikitarwa, duk yadda iyaye suke gajiya da ni shi be taba gajiya da ni ba. Ko da na shiga dakin na samu Hana ya bude wasu abubuwa tana ci, ban ce mata komai ba na dauka ka kasa na cirewa Mama da Baba na su sannan na zubawa Hana na ta na fara cin biredin kamin na fita waje na dauko kofi na zuba tea dake cikin karamin flask na fara tsomawa kamar mai cin tuwo da miya. Ina gama cinyewa wani yaron ya shigo yana sallama da Baba, ina jin lokacin da ya fita be dade ba na ji ya shigo da baki yana kiran a dauko tabarma. Tashi na yi na fara lekawa waje a hankali ashe sara na yi kan gaba, idona ya sauka akan na Kareem dake kallon kofar dakinmu kamar ya san a nan nake rayuwa. Murmushi ya sako min sai na yi saurin komawa na zauna gudun kar Mama ko Baba su ce na yi laifi. “Noor... Fito ga Alhaji ya zo ganinki” Na dauki Hijab dina na saka na fito waje n zauna. Na gaishe su cikin natsuwa suka amsa mutumen da ya kira ni da Amarya a office din Kareem ya amsa yana murmushi kamar ya san ni. “Lafiya Kalau Noor ya jikin?” “Lfy kalau” “Waya ce ki warware?” Kareem ya tambaya cike da kulawa yana kallon hannun nawa kamin ya koma kallon fuskata. “Idan zan yi sallah ruwa be tabawa” “Noor..” Sai yayi shiru wata kila yana gudun Baba yayi min fada ne. Murmushi yayi min sai na sauke kaina kasa ina murmushi. “Noor me kika ci haka bakinki duk maiko” Abokinsa ya tambaya sai na kai hannu na taba bakin cike da kunya domin ban san maikon ya bata min baki ba. “Ai kazamar Budurwa ce nan” Cewar Baba yana kokarin kunyata ni. Abokin da ban san sunansa ba yayi dariya ya ce. “Aa Baba mantawa ta yi dai da alama, gashi nan ta gyara muku gida ko'ina an share fes” A nan kam na yi sa'a Baba be tona min asiri ba, yayi dariya kawai yayi shiru. “Ni sai nake ganin kamar na sanka, amman dai ba zan iya tunawa ba ashe nan ne gidanka” “Ikon Allah zai iya yiyuwa ka san ni Wallahi, ai da yake ku masu arziki ba tuna talaka kuke ba, amman na yi mamaki” Mutumen yayi murmushi yana cigaba da fadar. “Haba Baba wadda ke da irin wannan gidan za a cewa talaka sai dai mai rufin asiri” “Yaro ai haya nake a nan ba gidana ba ne, tukuna na dai” Mamaki ya saka na kalli Baba da sauri jin yana fadar gidan da muke ciki ba gidansa ba ne. “Allah yayi budi, yanzu kuna biyan nawa a wata kamar wannan?” “Toh da dai talatin ne, amman wannan shekarar na ji yana fadar zai maida shi dubun hansi, saboda halin rayuwa” “Allah ya bada yadda za'ayi” Baba ya amsa da Ameen, duk abub da ake idon Kareem yana kaina, idan muka hada ido sai ya sakar min murmushi. Sai daf da za su tafi sannan ya ba ni ledar magani ya bude ya nuna min yadda komai yake. “Baba ka bincika, mu ji gidan idan be fi karfinmu ba sai mu siya zai fi biyan haya” Cewar Abokin yayin da ya kai tsaye, Kareem ya kalleshi da sauri ni ma na kalleshi baki sake ina mamaki Baba kuma ya mike tsaye. Follow the KHADEEJA CANDY channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaNTEQTFXUuaypyV5O01 *Duk mai son ya rika samun Littafin TA KI ZAMAN AURE yayi following wannan Channel din mai suna KHADEEJA CANDY a nan zaku rika samu duka littafaina in Sha Allah* ✧✦ 𝗧𝗔 Ƙ𝗜 𝗭𝗔𝗠𝗔𝗡 𝗔𝗨𝗥𝗘 ✦✧ 𝗕𝘆 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆 *Talla👇👇👇* KINADA DAYA DAGA CIKIN WADANNAN MATSALOLIN ❓👇👇👇 To kiyi saving numba ta ki danna wannan link👇 https://wa.me/message/N2S6DQEPETKQO1 Idan kinyi saving ki fadamun zanyi SAVING TAKI😍ko Baki Siya yanzu ba WATARANA zatayi maki AMFANI👇👇 1.INFECTION CIWON SANYI 👉LALACEWAR BREAST👉RASHIN HIPS & BUTT👉KIBA TAYI MAKI YAWA KINASO KIYI SLIMMING👉TUMBI YAYI MIKI YAWA KINASO KI RAGE ?👉 AKWAI KUMA INGANTATTUN KAYAN MATA APHRODISIACS MASU KYAU DA INGANCI GA kUMA SABAYA ASALIN MAI KYAU 3500 only 👌 KIZO KI GWADA KAYAN AMNOOR INA TABBATAR MAKI BAZAKIYI NADAMA BA 👉 KIYI SAVING NUMBER TA DM ME https://wa.me/message/N2S6DQEPETKQO1 *Chapter - 10* “Dan nan? Kai kam uwar da ta haifo ka ta iya haihuwa, Allah mai iko na gode na gode Allah ya saka da alheri” Baba ya kai kasa yana masa godiya har da kuka, ni kam mamaki ya hana ni rufe bakin sai kallon ikon Allah nake. Muna hada ido da Kareem na sauke kai kasa na bata fuska, domin abun da Baba yayi be min dadi ba, ina jin yin haka ba daidai ba ne. Sai dai ba babu bakin yin magana baba ya dafa ni danya ya cinye. Kareem ya sauke hannunsa a hankali kasa yayi yana motsa agogonsa har sai da na dago na kalleshi sai ya daga min gira daya irin na wadda ke tambaya a boye. Ban ce komai ba daman ni me zance a gaban Baba ko ba a gabansa ba ne na riga na daina duk wani abu da be shafe ni ba. “Baba anjima Nabill zai kawo Noor asibiti a sake daure hannu saboda ba son a kwance har sai ta ji sauki, kuma kar ayi wasa da maganin da na kawo” Na ji Kareem yana fada, sai na lake kafada daya bacin ran nawa ya kara bayyana na saka kuka a take. “Aa Wallahi ni bana so, akwai zafi sosai” “Aa ba sake taba hannun za'ayi ba, daurewa kawai za'ayi” Ya amsa min hakan be canja kudurina ba na girgiza masa kai. “Ni dai bana so a bar shi a haka” Baba ya juyo kaina kamar mai jirana. “Aiko sai kin so, ka ga sakaryar yarinya ko? Haka ta da sakarci, ba da zafi ake cire zafi ba, shashashar yarinya kawai” Kareem ya kira sunan Baba a hankali sannan ya ce. “Baba dan Allah ku daina kiranta da sunaye marasa kyau, kamar yanzu kace mata sakarya, su iyeye kamar wani bakin tabo ne a jikin farin tufafi duk yadda ya diga sai ya bayyana, shiyasa ake son a rika taka tsantsan da kalami, yara basa jin magana mun sani dukanmu muna da su, amman a haka muke kai zuciya nesa idan ba haka ba, sai mu yi barna kuma a karshe dai mu din ne za mu wahala, misali yanxu kana kiranta mahaukaciya to ba zata taba yin hankali ba, ko da kai mutanen unguwa ne suke mata wannan ikirarin balle mahaifi. Amman fa ka yi hakuri na shiga tsabgar da ba tawa ba” “Aa ai gaskiya ka fada, haka ne Wallahi ai bakin ne ya saba kuma ita wannan Noor din idan ka zauna da ita na wuni daya, In Shaa Allahu sai ka ji ta gundureka saboda bata jin magana sam, shiyasa ma nake so na aurar da ita na huta” Na kalli Kareem sai na rufe idona ina jin kunya ta rufe ni, ta dayan bangaren kuma ina jindadi, ni kaina ai na fi son ayi min auren ma na huta domin na san Zafeer ba zai min abun da ake min a gida ba, shi ba zai taba gajiya da ni ba. “Baba yanzu, Noor tana da wadda zata aura kenan?” Abokinsa ya tambaya. Sai Baba ya ce. “Shekara uku da yin baikonsu kuwa, amman har yanzu be shirya ba, ni ai idan be gama shiri a cikin lokacin nan ba to sai dai ya hakura da ita domin so nake na aurar da ita In Shaa Allah, Yaya yayyuna da suke kauye sa'aninta duk an musu aure” Na bude ido ina kallon abokin da ya kalleni yayi murmushi sannan ya juya yana fadin. “Gaskiya kam idan ka aurar da ita hankalinka zai fi kwanciya, ita daman ya mace gidan aure aka santa” “Shiyasa ai nake son ayi komai na huta ta huta” Allah ya gani ni dai sai na ji na tsani abokin Kareem din nan ko ma dan'uwansa ne oho domin ya bawa Baba shawarar da ba zata taimaka wajen gyara soyayyata da Zafeer ba sai dai ma ta bata abun. Suna daf da ficewa Kareem ya juyo ya dago min hannu kasa kasa. Ni dai kallonsa kawai na yi ban yi wani Yunkuri ba har ya fice. Fitar ke da wuya Mama ta fito daga dakinta da ta boya ta zauna a inda suka tashi tana fadin. “Malam an samu hanyar kudi ina jin suna magana, baya ko tunanin gaskiya ta bayyana ya ji kunya” Hana ta fito daga dakinta ita ta zauna kusa da ni tana fadin. “Mama ai kara da yayi haka wa zai bari wannan damar ta wuce shi haka” Mama ta tabe baki. “Kudin me za su amfana mana Hannatu? Ai ba za su wuce ya bamu na cefane, sauran kuma idan be kara aure ba, su kare a gurin zaurawansa tun da Allah be raba shi da ganin mace ya ce yana so ba, ko ba shi ko sisi kuwa balle wata hanyar ta bude” “Shi ne kawai abun da yake bata min rai da Baba, wasu iyayen idan suka samu sai ka ga iyali sun wadata amman shi babu ruwansa da mu” Ni dai ban ce komai ba gudun kar na saka baki na fadi wata maganar ace na bata ran Mama ko Hana. Can na ji Mama ta ce. “Ni ko wannan mutunen sai na ke jin kamar da biyu suke mana wannan dawaniyar” Na kalli Hana dake tambayar Mama “Kamar Yaya Mama?” “Ta ya mutum zai shigo cikin gidanku haka nan kawai yace zai siye muku gida? Ko dai yana son ya bukaci auren Noor ne ko kuma wani abun dabam haka siddan kace zaka siyawa mutum gida daga zuwa? Kalli yadda yake kyautar kudi kamar tsintarsu yake” Na kalli Mama. “Ya san ina da Miji na fada masa ina da Miji, kuma ya san Zafeer har ya kira min a waya lokacin da wannan abun ya faru” Mama ta bude baki ta sake magana sai ga Baba ya shigo baki har kunne. “Kai kai kai Noor yau dai rashim jin maganar nan naki ya janyo mana alheri, gidan nan zai siya min, Allahu Akbar masu arziki na inda suke, ina ma ace ďana ne wannan yaro” Mama ta ce “Shi ma danka ba mu cire rai ba, wata rana inda rai da rabo zai maka komai Malam” “wannan Nabil din ko ya samu ai sai dai ya bawa uwarsa, ai baya kaunata sam bana saka rai ma” Ban yi furucin Baba ba, daman shi be yarda yayansa za su iya kawo masa abun arziki ba musamman ma ni. “Yanzu Malam yarda ka yi ka karbi kudin gidan da yake naka? Wannan abun da ka yi zubar da girma ne be dace ba” “To... Wato na bari rabo na ya wuce ni kenan? Amman dai Hajara ba ki da hankali garabasa ce fa wannan sai kuma na bari ta wuce ni?” Mama ta sauke ajiyar zuciya. “Indai domin Noor yake yi Noor tana da miji, ba za mu watsar da zancen shekara uku mu zama kananan mutane ba, be kamata ba Wallahi, yaron nan yana sonta kuma yana iya kokarinsa akanta” “Kokarin me yake da ita? Tun da nake da shi ya taba daukar dubu goma yace Baba gashi ka siya wani abu? Shi dai yana sonta kawai amman babu wani hidima da yake, kuma na zancen aurenta da yaron nan kika ji na yi ba har kike wannan maganar ke dai kam Hajara ba dan ina mijinki ba sai na ce hassada kike min, ke dai baki farinciki da samu na, ba ki son jin alherina, ina zaton ganin farinciki a fuskarka sai ki tare ni da wani zancen banza karuwa da zane! Ai da har ina cewa ko zane daya ne ya kawo ayi musu aure to yanzu na fasa yayi mata komai kamar yadda ake yi ma kowa, yau din nan zan kira shi na fada masa na shirya aurar da Noor, kudin gidan nan da za a bani ai sai na tsakuri wani abu a ciki na yi mata hidima sauran kuma na yi lalurar dake gabana, ba a bori da sanyin jiki kuma ice tum yana danye ake tankwara shi idan ya shirya ya fito kawai kamin kudin su kare” “Malam ina fada maka gaskiya ne kawai bana adawa da samunka, duk mace ta gari tana burin samun Mijinta musamman idam yana kyautatawa a gidansa” “To ni bana yi, Wallahi ba dan yau ina cikin alheri ba babu abun da zai yana na bata miki rai yanzu nan, shashashar mata kawai” Ya ciro wayarsa yana fadin “Bari na kira dan iskan yaron nan ko yanzu sai da Alhaji yayi min maganarsa, kuma duk laifinki ne ke kike goyo masa bayan yi min rashin kunya” Ni dai ba zan iya cigaba da sauraren jin tsabani da sa'insa tsakanin uwa da uban da suka kawo ni duniya ba, dan haka na tashi na shige dakinmu na kwanta ina kallon ceiling, wata zuciyar na fada min idan ma taimako Kareem yake son yin to ba Baba ya dace yayi ma. KAREEM POV. Sai da suka shiga mota sannan Kareem ya kalli Hafiz ya ce “Miye dalilinka na yin haka?” Hafiz ya kalleshi kamar be san abun da yayi ba. “Me ba?” “Siya masa gida mana” “Oh taimako ne, after ma na siye zan gyara masa shi, ina da halin yin haka ya kamata na yi” “Me yasa baka yi ba tuntuni sai yanzu” “Saboda Noor ne” Hafiz ya kure tambayarsa dan haka yayi shiru ba dan ya gamsu ba. “Wai ni kam ya aka yi kace a kawo maka Noor?” Hafiz ya tambaya yana taba agogonsa. “Na ga alamar kamar tana son magana ne, kuma tana tsoro, and gaskiya ne ai dole za a sake daure gurin saboda kai ya ki warkewa” Hafiz yayi murmushi. Sai Kareem ya ce. “Ba abun da kake tunani ba ne Hafiz, ba zan iya neman aure a cikin aure ba, Annabi ya hana, na san yadda ake ji idan ka rasa wadda kake so, ba zan yi kuskuren aikatawa wani ba, na auri wadda bana so ban ci da dadi ba, na bar wadda ke so na hakan ya jefa ni a matsala ba zan so hakan ya faru da kowa ba, indai saboda ni kake yi dan Allah ka daina Hafiz” Hafiz yayi kamar ba da shi Kareem yake magana ba ya kawar da kai dayan gefen yana jin haushin yadda abokinsa yake fadar Amnabi ya hana amman shi yake aikata abun da kisan kai da shirka sai yi da wani ne ya fi shi zubuni. A gida ya sauke Barrister sannan ya kama hanyar zuwa gurin aikinsa. Be fito asibitin ba sai karfe biyu, gidansa ya nufa kamar yadda ya saba yana shiga ya samu matarsa zaune a tsakiyar falon tare da yaransa, suna ganinsa suka taso da gudu suka tarbe shi dai ya daga su sama ya subance su sannan ya rika hannayensu. “Baku tafi Islamiya ba?” “Yanzu za mu je, idan mun gama cin abinci direba zai kai mu” Tine ta fada tana tsalle ya fadada murmushinsa. “Yayi kyau, Allah ya muku albarka ya tsareku ya shirya min ku” “Amin Daddy, anni Daddy” Tine ta amsa sannan Areef ma ya amsa, sai ya mike tsaye ya nufi inda suke cin abincin ya zaunar da su ba tare da ya kalli Yusura ba ya ce. “Madam sannu da gida” Ta yi murmushin dole saboda yaranta suna kallonta amman amsa masa ne take jin be zama dole ba. Shi ma dai yana yi duk abun da yake ne saboda yaransa kuma saboda ya bata hakkinta. Sama ya nufa ya shiga dakinsa rigar jikinsa ya fara cirewa sannan ya nufi bandakin ya cire wandon yayi wanka ya fito ya sake shiryawa ya saka wasu tufafin sannan yayi sallah. Yana kokarin mikewa tsaye Noor ta fado masa a rai, sai yayi murmushi yana mamakin yadda bata yi surutu ba a yau, wata kila saboda tana tsoron Babanta ne ko kuma dai ta shiryu din ne kamar yadda ta yi ikirari, amman yadda ta natsu nan babu surutu sai ya ji duk ta ba shi tausayi kuma sai ya ga kamar ba ita ba. Kwantawa yayi saman gadonsa ya dan taba chat for like 30min yana ganin Safeena ta hau online sai yayi saurin kashe data ya sauka ba tare da ya bude sakonta ba, ba kuma dan be bukatar hakan ba, domin be saka nuna mata rashin kulawa ba, amman a yanzu yana kokarin ganin ya gujewa wasu abubuwan ne kamin ya san matakin da zai dauka a gaba, so yake ya saba mata da wasu hayyarsa da bata san da su ba, shakuwar dake tsakaninsu ta ragu. Saukowa yayi ya dauki abubuwan bukatarsa ya fice daga dakin cikinsa na kukan yunwa, domin ya san ko yunwar zata kashe shi a gidan nan Yusura ba zata shigo dakinsa ta kawo masa abinci ba sai dai ta aje masa a dinning, shi tun da suka yi aure yau shekara bakwai be san wata rana da Yusura ta taba shigowa dakinsa yana ciki ba, ko gyara dakin da take takan gyara ne kawai idan baya ciki sai dai idan ya dawo ya tarar an share ko'ina an gyara. Sai dai shi yana leka nata dakin sau daya a wata idan zai sauke mata hakkinta, ya sauko downstairs da kuzarinsa ya nufi kofar fita falon. “Ga abincinka a dinning” “Yarana sun ci ya wadatar, ni zan ci a waje” Ta tabe baki ta dauke kai ta cigaba da kallon da take daman yaran suna gama cin abinci suka wuce Islamiya. Cikin motarsa ya shiga ya zauna yayi shiruuuuuu yana nazarin rayuwa, kamin kira waya ya katse masa hanzari. Ganin number Nabil ya saka shi murmushi domin baya kiransa sai da wani babban dalili, a yanzu kuma ya san dalilin ba zai wuce Noor ba kawar nishadinsa. “Hello” ‘“Ranka ya dade barka da wuni” “Bakar Nabil ya kake?” “Lafiya Kalau ranka ya dade” “Ina fatar kun samu fahimtar juna tare da mahaifinka” “Komai ya wuce ina godiya Oga” “Toh Alhamdullahi ina Noor” “Eh daman saboda ita na kira, dubata da kace zaka yi nace kana asibitin yanzu mu tafi” “Ba sai kun je asibiti ba ka kawo ta, restaurant zan zo da abun daurin a nan idan na daure mata sai ku tafi” “Toh Oga” Ya kashe wayar sannan yayi ma motarsa key, Asibitin ya fara zuwa ya dauko abun bukata sannan ya nufi restaurant dinsa. A reception ya same Noor zaune a kujera zaune tana raba ido da alama shi take jiran bullowarsa. Suna hada ido ta sakar masa murmushi shi ma yayi mata murmushin yayi tsammanin zata taso ta tare shi ne ko kuma ta bi bayansa sai be ga ta yi ko daya ba sai binsa da ta yi da kallo har sai da ya kirata. “Noor” “Na'am” Ta amsa sannan ta mike tsaye ana ta kallonta ta nufi inda yake tsaye yana jiransa har sai da ta iso sannan suka jera suna tafiya. “Ya aka yi na ganki yau kamar ba ke ba?” Ta kalleshi murmushi har zuci. “Ka karramani...” “Da na yi me?” Ya tambaya da kamar mamaki sai ya washe masa hakora. “Ka ce Noor a gaban mutane, kai ne fa mai gurin nan kuma ka kira ni a gaban mutane kuma ka tsaya ka jira ni har sai da na zo, ba ka ga kowa kallona yake ba sun dauka ni ma wata ce” Ta yi tsalle kadan ta dire tana jindadin da ya haifarwa da Kareem jindadi. “Oh just? Abu kadan ke faranta ranki baki da matsala yarinya i like your style” Ya fada sannan ya saka key ya bude office din ya bude mata ta fara shiga sannan shi ma ya shiga. NOOR POV. tsayawa na yi har sai da yayi min izinin zama sannan na zauna, ina kallon yadda kananan kayan jikinsa suka karbe shi yayi kyau da har na kasa boyewa sai da na fada. “Ka yi kyau, kayan ya maka kyau” “Thank you” Ya fada yana murmushi tare da aje ledar dake hannunsa sannan ya janyo kujera ya zauna, a yadda na lura yanayinsa kamar ba a yadda ya saba ba, na lura akwai damuwa a tare da shi, sai dai ban ce komai ba domin damuwarsa ba tawa ba ce. “Zaki ci wani abu a kawo miki? Yunwa nake ji zan ci abinci sai na daure miki hannu” Har zance aa sai kuma na tuna wannan abincin fa Free ne idan ma ban ci ba ni nayi ma kaina. “Eh amman ba zan ci gabanka ba” Yayi murmushi. “Me za'a kawo?” “Zan iya fada da kaina?” Ya daga min kai sai na ce. “To ka kirata na fada mata da kaina ba zan iya fada maka ba, kuma idan ta shigo ka rufe kunnenka karka ji dan Allah” Cikin saukin kai yayi min yadda nake so ya kira matar a lokacin da ta zo sai yaja kujerarsa baya ya ce. “Face her” Matar ta fuskance ni shi kuma ya saka yatsa ya rufe kunnensa. Dadin da na ji a lokacin da yayi abun da ya bukata ya fi dadin da na ji a lokacin da ya yi min tayin abincin. Sai da na gama fada mata sannan ya dauke hannunsa ya fada mata abun da zata kawo masa, bayan ta fice na kalleshi na ce. “Ka ji me na fada mata?” “No kin ce ai kar na ji” “Ce Wallahi baka ji ba” “Wallahi ban ji ba, ai kin ce kar na ji i respect that” “Ya aka yi ka gane na gama fada to?” “Ina karanta bakinki ne” Na yi murmushi ina kallonsa. “Kana da sauki babu ruwanka kamar ba kai ne mai gurin nan ba” “I wish people knew” Ya furta ya kalli agogonsa. “Kareem daman ina son zuwa saboda ina son magana da kai, na jidadi da ka ce a kawo ni” “Daman na lura akwai magana a bakinki ai, fada min Minene?” Na dan yi shiru na sosai kaina da dayan hannuna ina dan jin nauyin maganar. “Daman akan gidan da zaka siyama Baba ne...” Sai a lokacin ya dago ya dube ni. “Uhmm hmmm” “Cewa na yi me zai hana kudin ka bawa Zafeer idan dai taimakon dan Allah ne zaka yi? Zai jidadi kuma zai siye gida, amman Baba shi yana da gurin zama ai” Murmushi yayi. “Shi kuma Baban fa?” “Shi shi fa yana da gida, kuma idan ka ba shi kudin aure zai yi, amman Zafeer zai aure ni ne da kudin ya siye gida ko ya kama haya” “Sai a bar Babanki yayi ta haya kenan? Kuma fa ba ni ne zan siye gidan ba” “Ni dai daman ina son na fadi gaskiya ne, kuma ina son na roke ka dan Allah ka taimaka masa, Wallahi Babana ya boye muku ne amman gidansa ba haya yake ba, ban fada gabansa ba ne saboda kar ya yi fushi ya ce zai koreni ko ya dake ni” Dariya ya fara yi kadan kadan kamin ta fara yin yawa ni dai na san a cikin labarina babu abun dariya amman sai kyalkyalar dariya yake har sai da na dan ji tsoro. “Sorry” Ya daga min hannu sai kuma ya sake tintsirewa da dariya ya mike tsaye ya nufi teburinsa sai da ya fara aje wayarsa dake hannunsa sannan ya dafa teburin yana girgiza kai. “Wallahi ban taba haduwa da yarinya kamar ki ba, ke duk yadda nake misaltaki da ex dita kin fita, amman da babanki ya san kin zo nan kin fadi haka sai ya yanka ki ko Noor” Na yi dariya na sauke kai kasa kamar wata wadda ta yi abun arziki. “Amman kar kace ka ji na fada kace mutanen unguwa ne suka fada, ko kace Malam Sani ne ya fada maka, abokin Baba ne na san Baba ba zai rasa fada masa ba” Ya sake yin dariya har da saka hannu ya tare kwalla da suka cika masa ido. “Ya Allah Wallahi na dade ban yi dariya haka ba, ina cikin damuwa amman kin mantar da ni komai ina son mutane masu gaskiya sai na ji kin kara burge ni” Mamakin jin cewar yana da damuwa ya saka na manta da banbarar da na yi. “Yanzu kai har kana da damuwa? Kana da kudi fa, kana da mata da yara kana da aiki kuma zaka shiga mota mai kyau ka saka tufafi mai kyau kuma ka shigo nan ka ci abincin da kake so a haka kuma kana da damuwa? Daman masu kudi suna da damuwa sukan? Ai damuwa sai talaka ko?” “Ke dai babu ruwanki, yadda rayuwa ta nuna miki haka kike tafi da ita i wish i was just like you” Ya fada har lokacin dariya yake. Matar da ta karbi order ta kwankwasa kofar office din yayi mata izinin shigowa sai ta shigo. Sai da ta fara aje min plate uku sannan ta aje manya ledado biyu a gabana. “Gashi, zan dauko lemu yanzu” “No need akwai lemu a nan” Ya fada sai ta amsa masa da Okay Sir sannan ta fice daga office din. “Karka ji babu dadi daman ina son na kai ma Zafeer ne, shi ma idan ya ci abu yana kawo min” Yayi murmushi kawai ya nufi kofar office din ya bude. “Zan je na ci abinci ke ma ki ci na ki” Ya fice, aiko a nan na samu damar saka hannun hagu na sauka kasa na zauna na ci yadda raina yake so da hagu sai da na koshi sannan na nufi fridge na dauko kalar lemun da nake so na sha. Na dawo da ragowar zan zauna kenan wayarsa da ya fita ya bari ta yi ringing ban kula wayar ba, sai dai da alama mai kiram be san rashin samu ba, sai ya kara kira. Na nufi wayar na dauka babu suna babu number a jiki sai wasu dot dot dot da aka jera kusan guda hudu. Na amsa wayar na kai kunnenta. “Kareem” Na ji muryar ta fada. “Baya kusa ya aje wayar ne ya fita” “Wacece ke?” Na yi shiru domin na ji mai tambayar ta tambaya ne da tsauri gashi kuma ni din ban san me zan ce ba. “Ke ce yar iskar yarinyar nan ko? Wato ba zaki cire kanki a lamarin Kareem ba, karya miki hannu da na yi be zame miki darasi ba ko?” A take na gane ko wacece. “Eh ni ce, kuma yanzu ma na zo ne ya daure min hannu bayan wadda yayi min, kuma ya kawo min abinci mai kyau na ci, kuma ina cikin office dinsa ni kadai saboda na isa, kuma hannu na ni be karye ba Wallahi arziki kika ce saboda Kareem ya fada min ke daman haka kike baki da hankali ba dan haka ba da dai Babana ya kulleki gidan yari, dan Babana ya fi ki bala'i, ke din banza Kareem dai ni zai aura na fada miki kuma ki cire da shi, ballagaza kawai mai karyar ciwo, ai ciwon zuciya sai ya kashe ki, azzalumar banza da wofi” Na yi hanzari sauke wayar na aje a inda na ganta ina jin tana magana amman ban saurara ba, ina ta kallo har sai da gaji da haushinta ta kashe wayar. Na koma na zauna na natsu sosai dan kar ya gane na yi wani abu, amman hakan be hana shi fahimtar na taba wayarsa ba, domin wayarsa ce farko abun da ya fara dauka a lokacin da ya dawo dakin. “Ya aka yi wayata ta samu maiko?” “Fadowa ta yi na dauke maka” Ya kalleni kamar be yarda. “Noor fada min gaskiya dai kirana aka yi kika daga kuma baki son na san kin daga haka ne?” Mamaki ya kama ni jin yadda yayi saurin gano gaskiyata. “Halam kana da aljannu” Yayi murmushi kawai ya zari tissue ya goge wayar. “Na manta da ita sai da na fita na tuna, kuma na yi tunanin kar na dawo na samu kina cin abinci ki ji babu dadi” “Na gama zaka daure min yanzu zan tafi” Ya saka wayar aljihunsa sannan ya janyo kujera ya zauna ya dauko ledar daya shigo da ita ya bude ya dauko abun daurewar ya daure min a hankali ba tare da ya matse na ji zafi sosai ba. “Kareem me ye tsakaninka da matar da ta karye min hannu” Ya daga kai ya kalleni. “Me ya kawo wannan maganar?” “Har yanzu ina mamaki me yasa ta yi min haka ne, amman dai ko miye na barta da Allah ba zata ga alheri ba” Be sake ce min komai ba har ya gama sannan ya kalli plate din da na ci tsutsusar nan da nake ta kwadayi. “Ke kika ci? Daman zaki iya cin wannan?” “Tana da dadi, baka taba ci ba?” Ya girgiza kai. “Bana cin sea food, bana cin English breakfast” “Ni kam na ci, akwai dadi ai” “Idan ba ki ci ba ai ba ke ba ce” Ya nuna ni yana murmushi. “Wannan ce Noor din da na sani daman wacan da gani a gidanku shiru na san ba ke ba ce, this is the real you” “Na gode Kareem, dan Allah ka fadawa abokinka gaskiya idan yana son taimako to ya taimaki Zafeer” Ya amsa min da kai yana lumshe ido ya bude. “Zan fada masa” Na mike tsaye na dauki ledodin da hannun hagu. Sai ya mike tsaye shi ma ya karbi ledodin ya aje ya matsa da ni kusa da teburinsa ya zari tissue ya goge min yatsuna dake da maikon naman da na ci, domin abinci dai da spoon na ci. “Haka nan kake yi ma matar ka ko Kareem? Ni ma Zafeer zai iya min haka yana ririta ni kamar sarauniya” Yayi murmushi ya kalleni. “Irinku haka ake tafiyar da ku sai a samu yadda ake so, ita mace awaza ce idan kace zaka lankwasa sai ta karye sai dai a lallaba, duk yadda mace yake ni ina iya zama da ita da zarar na karance ta, rayuwar duniya sauki ne da ita sai wadda ya so wahalar da kansa” Na mayar masa da murmushin sannan ya ce. “Zauna bari na kira Nabil ya zo ya kai ki gida” “Bana son ya kai ni gida da kaina zan tafi” Na fada masa saboda na san fada Ya Nabil zai min akan ka karbi takeaway. “Ai be san kin shigo nan ba, ya kamata ya sani” Ya dauki wayarsa ya taba sai na ga ya dago ya kalleni da fuskar mamaki amman be ce min komai ba ya maida idonsa kan wayar ya kira Yaya. Babu bata lokaci Yaya Nabil ya iso suka gaisa sannan ya fada masa ya kai ni gida. “Toh ranka ya dade an gode Allah ya saka da alheri, ban ma san ka shigo ba sai da na neme ta aka ce kai ka kirata” Ya daga masa kai, ni kuma na mike tsaye “Ko ka saka ta Napep tun da aiki kake” “Okay Oga” Ya amsa sannan ya daukar min ledodin ni dai ban yarda na kalleshi ba har na fice office din. Na yi zaton ko Yaya zai yi magana yace ka karbi takeaway amman be ce min komai ba har muka isa titi ya tari Napep ya saka ni ya fada masa inda zai kai ni. Mai napep yaja mota ina jindadin yadda be tsangwame ni ba, na kalli ledodin na yi murmushi daman leda daya ta Zafeer ce daya kuma ta Baba saboda plan din da nake da shi. A bakin hanya ya sauke ni, ban shiga gida ba sai da na fara biyawa gidan da Mama take zubin adashe na yi mata karya cewar Mama tace a bata dubu goma a ciki tana da wata lalura zata maido zuwa gobe, na yi sa'a Talatu ta ba ni dubu goma bayab ta gama karanta min na fadawa Mamarmu kar ya wuce gobe. Na karba na fito gidan na nufo gidanmu cikin natsuwa ni kaina na san na samu canjin rayuwa daga jiyan nan zuwa yau na natsu sosai. ____________________ Gashi nan na yi long page na biya bashin na jiya 😆 Follow the KHADEEJA CANDY channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaNTEQTFXUuaypyV5O01 *Duk mai son ya rika samun Littafin TA KI ZAMAN AURE yayi following wannan Channel din mai suna KHADEEJA CANDY a nan zaku rika samu duka littafaina in Sha Allah* ✧✦ 𝗧𝗔 Ƙ𝗜 𝗭𝗔𝗠𝗔𝗡 𝗔𝗨𝗥𝗘 ✦✧ 𝗕𝘆 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆 *Talla👇👇👇* https://chat.whatsapp.com/GY1W0qJiFbJD5A5J6F0fqA *INA MATAN DA SUKASAN DARAJAR GYARA❓DAKU NAKE MACE MAI GYARAN BATA ZAMA BORA❌* *KUZO GA INGANTATTUN KAYAN MATA MASU KYAU DA INGANCI💪BA MUNA KAYABA❌ HAJIYA KIZO KISAI KAYAN MATA WURIN DA BAZAKIYI ASARAR KUDIN KI BA* *INA MASU CEWA NI KO NASHA KAYAN MATA BASAMIN AIKI HMMM HAJIYA BAKIDAI SIYA KAYA MASU INGANCI BANE, KAYANMU SUNA KARA NI'IMA, TAYARDA SHA'AWA, DADI, TIGHTENING (MATSI), CIKO DA GABAN MACE (DUK BUDEWAR SA), DUMIN GABA GA, KAMSHIN GABA GA KUMA NA KARA DANDANO OVER 💃💃💃💃💃👉 GA KUMA INGANTACCEN MAGANIN SANYI MAI DAGARGAZA SANYI KODA YA SHEKARA 10 A JIKINKI* 09038090328 *A DAYA BANGAREN KUMA MUNADA SABAYA MAI GYARAN NONO DUK LALACEWAR SA KO KIN HAIHU GOMA SABAYAR MU ZATA CIKO MAKI DA BREAST SUYI GIRMA SOSAI MADAME* *GA KUMA TA HIPS (MAZAUNAI)SU CIKO SUYI BULBUL NONO YA CIKO SOSAI HJY KIYI KIBA YAR DAIDAI SKIN DINKI YAYI KYAU KI KOMA TAMKAR TARWADA* AKWAI KUMA NA GYARAN NONO WANDA BAYA SAKA KIBA💃💃💃 GASKIYA NA YARDA DA INGANCIN KAYANTA👆👆👆 *Chapter - 11* Ban bude ledar da na isa da ita gida ba, kudin ma sai na boye ban bari Mama ko Hana sun gani ba. Bayan na yi sallah La'asar Mama ta kira ni na fito ta ba ni danta malelen da aka girka, ko karba ban yi ba na ce na koshi daman wadda ya ci kayan dadi me zai yi da wani malele. “Me kika ci?” “Na ci abinci a can” “Yanzu gaban maza kika zauna kika ci abinci saboda ki nuna ba ki da tarbiya? Kuma rokonsa kika yi? Ai na ga kin dawo da ledodi kin boye baki nunawa kowa ba. Yanzu duk abubuwan nan da suka faru kwana biyu ba su isa su zame miki darasi ba? Wai Noor idan baki yi hankali yanzu ba yaushe zaki yi hankali? Matukar baki canja rayuwa ba zaki sha wahala nan gaba, ki ce yayar Hannatu amman ke ce shashasha” Na sauke kaina kasa ina jin kalamin na Mama yana min yawo a zuciya ta bangaren rashin dadi. “Ba a gaban maza na ci ba, ni kadai ce lokacin da na ci, ya bar ni a dakin ne sai da na koshi sannan ya dawo” Bata sake ce min komai ba, kuma daman bana wani abun fada dan haka na juya na koma dakin. Ban sake fitowa ba sai da aka yi sallah magariba ina gama sallah na kwanta ina jiran Yaya ya shigo na ari wayarsa na kira Zafeer domin na san Mama ba zata bar ni na fita na je gidansu Zainab na ari wayar Mamanta. Bayan Sallah Isha'i Baba ya shigo gidan, ina jinsa na yi saurin dauko leda daya da na shigo da ita na dauko kudin da na boye na fito na tare shi. “Baba sannu da zuwa” “Yauwa” Ya amsa min kamar yadda ya saba da daure fuska, na dan tsawon wuya na leka dakin Mama na ga bana hangota sannan na mika masa ledar hannuna. “Gashi Zafeer yace a baka” Na hada masa da kudin da na karbo gurin adashen Mama. Baba ya karba yana dubawa. “Me ye ne” “Ban sani ba ni ma cewa dai yayi a kawo maka” Ya bude abincin da ya fara expire saboda yana cikin leda kuma gashi na masa mugun boyo. Sannan ya kirga kudin na yi zaton dadi Baba zai ji saboda ya min gori jiya cewar Zafeer be taba ba shi ko dubu goma ba, a tunanina hakan da na yi zai haifar da faeinciki da jindadi a zuciyar Baba sai na yi arba da tsabanin haka. “Fada masa kika yi? Ni fa bance ya kwashe kudin aikinsa ya kawo min ba, kar ya zo yana kuka da ni, kuma ban ce yayi sata ya ba ni ba, duk abun da zai biyo baya kar ya saka sunana a ciki” Na yi shiru na rasa me zan ce, ban san taya zan kare Zafeer ba, haka kuma ban zan iya fitowa na fadi gasjiyar cewar kudin adashen Mama ne ba, kamar yadda kalaman Baba basa min dadi a yanzu. “Wai ance ana kiran in ji Zafeerrr” Almajirin da aka aiko ya fada bayan yayi sallama. Na kalli kofar Baba ma ya kalli kofar a daidai lokacin da Mama ta fito daga dakinta tana kallon ledar dake gaban Baba “Je ka ce tana zuwa” Mama ta fada, sai Baba ya mike tsaye. “Bari na fara magana da shi daman ina nemansa” Kan kace kwabo Baba ya mike tsaye ya fice daga gidan, ban ji komai a raina ba domin na san duk tsanani Zafeer ba zai tona min asiri ba ko da kuwa be san me na shirya ba ba zai taba fadar abun da zai haifar min da matsala ba. Bayan fitar Baba Mama ta dube ni ta ce. “Fada masa kika yi Baban ki yace be bashi komai ba?” Na sauke kaina kasa kamar ba ni ba, cikin na tsananin ladabi da ban san ta ina yake fito min ba na ce. “Aa Wallahi ban fada masa ba, kawai dai kila anyi dace da yayi niyar aikata hakan ne” “Amman wannan ledar tun dazun kika shigo da ita” “Eh shi ya bani, acan ya siya komai sai ya ba ni tare da kudin” “Allah yasa gaskiya kika fada, domin idan na gano rokon bawan Allah nan kika yi kudi saboda ki bawa Babanki sai na miki mugun duka a gidan nan” A take cikina yayi kuka ba irin kukan yunwa ko wahala ba, kukan tsoron shan duka da na san idan Mama ta gane a gurin adashenta na karbo kudin nan sai ta fi cin ubana ma fiye da roko” Ta dauke ledodin ta shige ciki ni kuma na juya na koma dakinmu ina ta tunanin matafitar da ban yi tunaninta ba tun farko. Bayan kamar minti talatin Baba ya dawo cikin gidan ya yana kwala min kira. “Noor” “Na'am” Na amsa da sauri sannan na mike tsaye na fito. “Tafi yana jiranki” Na juya na koma cikin gidan ina jin faduwar gaban da ban saba ji ba, kuma ban san na Miye ba. Hijab dina na dauko na saka zuciyata bata raya min ransa zai bace idan na ba shi abun da na zo masa da shi daga gurin Kareem ba, kwalkwalwa ta mantar da ni gargadi da yayi min har sai da na fita rike da leda na tsaya a gabansa ina kallon yadda yanayinsa ya canja ba kamar yadda na saba ganinsa ba. “Zafeer” Ya sauke ajiyar zuciya sannan ya kalleni. “Noor Baby Noor” Yanayin yadda ya kira ni ma muryarsa ta sauya, ina karantar damuwar dake tattare da shi tun kamin ya fada min. “Baba ya maka wata magana marar dadi?” “Mai dadi ce amman dacin mai daci ne a gareni yanzu” “Me yace maka?” Ya kalleni. “Baku yi magana da shi ba?” “Magana daya ce kawai? Ni dai ka fada min” Na masa magana a shagwabe kamar zan masa kuka. “Baba ya min godiya, me kika bashi?” “Kyauta da kudi dubu goma na ce masa kai ne ka ce bashi” Ya sake dubana da mamaki. “Kyautar me? Ina kika samu kudin?” A nan fa ido ya raina fata domin ba zan iya fadar yadda na samu kudin ba, kara ma kyautar zan iya fada tun da gashi har na riko masa wata. “Gashi dai yanzu ni dai na riko maka kayan dadi” Na mika masa, sai ya kai hannu ya karba ya duba a take ya hade rai. “Ban miki magana akan mutumen nan ba?” “Shi ne yace a kawo ni zai duba min hannu ba ni ce na je ba” “A gurinsa kika karbo kudi kika bawa Baba? Noor me ke damunki...!” Ya daka min tsawa sai da na zabura, ba zan iya cewa ba a gurinsa na karbo ba saboda ba zan iya fada masa gaskiyar inda kudin ya samo asali ba. “Mutumen nan kokarin juyar da hankalinki yake, yana son ya siya Baba, yanzu Baba ya gama fada min yana son ya aurar da ke karshen shekarar nan idan na shirya na fito, karshen shekara nan sauran wata uku, ba ni da gurin aje ki Noor, ba ni da wata kafkarfar sana'a da zan iya rike ki, a yanzu ne zan tafi service, ba ni da wasu kudi da na aje domin yin hidima, ina ganin kamar mutumen yana kokarin rabamu ne, kuma ya fara yin nasara tun da gashi har na miki magana amman baki ji ba” Fada yake min sosai har jikina yana rawa domin be saba min fada ba, ban saba ganin bacin rai a fuskarsa irin haka ba. Na kai hannu na karbi ledar na aje a kasa jikina yayi sanyi, sam bana son na ji wani abu mai alaka da rabuwa tsakanin ni da Zafeer. “Ba zan sake ba, daga yau ba zan sake rashin ji ba, ba zan sake kin jin maganarka ba, ko ya zo ba zan sake kula shi ba, kuma zan yi magana da Baba zan fada masa ya bari har sai ka shirya tukuna” Ya matso kusa da ni yana kallona. “Ba ke zaki yi magana da shi ba, zan turo iyayena su roka min Baba ya daga har zuwa next year ko ma shekara biyu, inda muka fito be kai inda zamu nisa ba, kuma ba ki yi girman da Baba zai matsu ya aurar da ke ba, sai dai wata kila saboda wannan rashin jin maganar da kike ne, dan Allah ki natsu Noor, ni dai har ga Allah ina sonki a haka, kuma na so ki tun kamin natsuwarki ta kawo haka, kuma ina fata ina tunani nan gaba zaki daina, idan ma baki daina ba ni dai Allah ya saka min sonki a haka ina matukar kaunarki” “Ni ma idan ba kai ba zan ma auri kowa ba” Na samu kaina da fadar haka, sai na ji murmushinsa. “Bana fatan ki auri kowa sai ni, domin ni kadai zan iya dake, babu namijin da zai iya zama dake Noor ya rike ki sai ni, duk wani mai ganin yana iya zama dake gani kawai yake, amman babu wadda zai iya zaman aure da ke, sai ni ke tawa ce har abada” “Ba sai ka yi wata hidima mai yawa ba Zafeer, ni na ma yafe maka sadakin, kuma ba sai ka yi min tufafi ba, can gaba idan ka samu sai ka yi min” Na fada a iyakar gaskiyata domin bana son masoyin nawa ya wahala. Sai na ji hannayensa a kumatuna ya kama fuskata ya rike yana kallon cikin idona ba tare da tunanin wani zai fito ya ganmu ko ya wuce ba. “Dan Allah ki natsu Noor, ki daina kula wannan mutumen bana son wata alaka ta sake hada ku, da ace ina da hali maganar da Baba yayi min sai na fito kai tsaye ayi auren nan, amman bana son na yi aure ni a wahale ke a wahale rayuwa nake son mu yi ta jindadi bance sai na zama mai kudi ba, amman zan wadata ki da kwanciyar hankali da tufafi da abinci mai kyau daidai gwargwadon halina” Kamar an kwance wasu notuka a cikin kaina an daure wasu, an sabunta shafin tunanina, an wanke kwakwalwata an haska basira, haka na ji a lokacin da Zafeer ya zuba kalamansa a cikin kaina. Sai aka sakaukar min da natsuwa da wani rauni a zuciya, aka share duk datti yake a cikin tunani na, aka daure wasu karafuna da suke rawa a kaina. Daga ranar ne Zafeer yayi nasarar sauyani daga wata yarinya da ake cewa bata jin magana zuwa mai tsananin ji, daga marar hankali da shashanci zuwa mai natsuwa da hankali da tunani. Daga ranar aka dauke nishadi na, aka nesantar da rashin tunanina, aka bude min wani sabon littafi mai sabon shafi da sabuwar rayuwa. Tambaya ta yake wane kalar gida nafi sha'awa a rayuwata, ina fada masa yadda nake son tsarin gidanmu ya kasance a ban gaba idan zai gina mana gida. Sai goma na dare muka yi sallama ya tafi ba tare da ya karbi ledar ba, ni ma kuma ban sake kallon inda take ba tun bayan da na karba daga hannunsa na aje ta a kasa. A daren ranar ban yi bachi ba, ina ta jina kamar bani ba, abun da ban taba yi ba a rayuwa shi na raya daren da shi a ranar wato sallah dare, sai a lokacin da na daga hannu da niyar addu'a sai na rasa wacce zan yi, Allah ka bawa Zafeer abun aurena ko kuma Allah ya sa Baba ya daga masa kafa har zuwa lokacin da zai samu komai? Na kasa rokon ko daga sai kawai na roki Allah ya lullube mu da alheri ni da Zafeer da Iyayena. Sai da na yi sallah Asuba sannan bachi ya buge ni, na fara bachi kamar ba gobe. Ko da na farka Rana ta yi sosai abincin karyawar da aka aje min har ya sha iska, a haka na dauki kokon na sha, na balle magani ba dan rai yana so ba na sha sannan na fito waje ina kallo ashe Mama har ta gama gyara gidan. Abakin balcony na zauna ina tunanin kudin da na karbo jiya, gashi tace a dawo mata da shi yau, kuma ban isa na tinkari Baba nace ya bada kudin ba, a take wata zuciyar ta raya min cewar na fadawa Mama gaskiya idan ma kashe ni zata yi to ta kashe ni na huta. Cikin karfi hali na tashi na nufi dakin shi kam tsoro daman na dade ina samun nasararsa domin ko ina jin tsoro ina aikata abu balle kuma yanzu da gaskiyarce nake nufi bayyanawa, a tare da canjin da yake jikina yanzu. Sallama na yi na shiga dakin na zauna kasa ina rike da hannuna na ce “Mama daman wata magana ce ma zo mu yi gaskiya ce na zo na fada miki” Tana jin haka ta kashe redio dake kunne ta kalleni. “Gaskiyar me?” Ban boye mata komai ba, na fada mata dalili na yin haka saboda Baba yayi gori ne, sannan na fada mata inda na karbo kudi. Wani irin wawan duka ta kai min a fuska “Wannan yarinya baki da mutunci, yanzu kudin da nake tarawa na aure kika je kika karBo kika ba ubakii da baya tsinana muku komai? Ashe dai ke har abada ba zaki yi hankali ba? Har dubu goma Noor?” Ta mike tsaye ta fice daga dakin a take hankalina ya tashi gabana ya tsananta faduwa, sai gata ta shigo dakin rike da katon kudi. “Ce min karya kike ba gaskiya ba ne” Cikin kuka na ce “Da gaske ne Mama, amman na miki alkawari daga wannan ba zaki sake dukana akan rashin jin magana ba, Wallahi na daina Mama” Ina maganar ina yin baya ina tara hannun nawa mai ciwo ina kare fuskata. Wata kila tausayi na bata sai ta jefar da itacen kasa ta fashe da kuka. “Ai har abada ba zaki daina ba, ba zaki daina saka min bakinciki ba, ba zaki daina wannan haukar ba, ni dai ban yi ma iyayena haka ba, uwata bata zubar da hawaye akaina ba, amman ke ina ji miki tsoron gaba Noor bakinciki uwa bashi da kyau, ni ban san wace irin ya Allah ya ba ni ba, kara ma ayi miki auren na huta ni, yaje can shi idan zai iya ya rike ki, idan ba haka ba nan gaba gawata za'a gani, bakinciki yana cikin zuciyata yayi min yawa” Ta zauna bakin gadonta ta rike kai tana kuka, ni ma kukan nake amman hakan be hana ni bata hakuri ba. “Yi hakuri Mama, Wallahi ba zan sake ba daga yau, dan Allah ki yi hakuri” “Tashi ki fita ki bar min daki” Ya fada cikin kuka, sai na tashi na nufi kofar dakin na fita, hakan kuma yayi daidai da shigowar Ya Nabil yana rike da bakar leda, na nufi dakinmu na zauna ina sauraren zuwan Yaya domin na san zai zo matukar yayi arba da hawayen Mama, sai gashi kuwa ya shigo dakin ya doso inda nake zaune, wani mugun shuri ya kai min a ciki har sai da jini ya fito min ta baki kokon da na sha kuma ya fito min ta hanci, ya fisgeni ya jefar a dayan gefen ya saka kafarsa ya bugar min kai. “Wai ke miye a cikin kwakwalwarki ne Baba ya saka ta kuka ke ki saka ta kuka? Me yake damunki?” Kamar zai ruguza dakin haka yake tambaya yana shurina kamin ya cire talkamin kafarsa ya fara dukana da shi, can kuma ya fita sai gashi ya dawo rike da wayar wuta ya fara dukana da ita ta ko'ina har sai da ya fasa min jiki, ba kafai yake dukana ba, amman idan ya fara be iya ba sai ka rantse baya so na ko babu imani a tare da shi idan yana dukan. Sai yayi min zina zina ya hada min jini da majina sannan ya fita ya bar ni ina kwara amai, ko'ina an jikina yana zugi kamar an zuba min wuta. KAREEM POV. Noor na ficewa da yan mintuna Hafiz ya shigo office din daman nan suke zama idan yamma ta yi kowa ba shi da aiki sai su tare a nan suna tattauna ko warware wata matsalar, Kareem dake kallonsa yana Murmushi ya ce. “Yanzu nan Noor ta fita” Kamar wadda aka yi ma albishir haka Hafiz yayi murmushi. “Me ta zo yi?” “Hannu ta zo na duba mata, kuma ta ba ni sako na baka” Kareem ya fada masa, Hafiz yayi fuskar mamaki. “Sako? Ni?” Kareem ya zayyana masa yadda suka yi da Noor yana kwasar dariya kamar wadda yayi a dazun bata wadace shi ba. Hafiz ma dariyar yake sosai “Tun a nan zaka fahimci yarinyar nan she's very silly girl, idan ba ita ba wa zai tonawa Babansa asiri? Kuma tace wai a bawa saurayinta kudin? Da Baban ya san ta zo nan maybe sai ya yanke mata kafafuwa” “I'm telling you, tace kar na fada masa ai nace amininsa ne ya fada min” Kareem ya saka yatsansa ya cire kwalla data cika masa ido saboda dariyar da yayi, ya busar da iskar bakinsa. “Na manta rabon da na yi dariya irin yau Wallahi” Hafiz yayi murmushi yana kallonsa. “Ka ga idan ka aje ta a gidanka ka huta bakinciki” Kareem ya kai hannu ya dauki tissue ya goge hannunsa da idonsa. “Kai ma dai ka kusan zama kamar ita, ni dai na fada maka sakonta next time kar ta zo tana min masifa” Hafiz ya kwantar da kansa jikin kujerar. “Ba zamu fasa ba, zan iya ma Babanta gidan, kuma zan nemi saurayin na ba shi jari, ko na taimaka masa ta wani bangare” Da mamaki Kareem yake kallon abokinsa. “Wasa kake?” “Wallahi da gaske nake, za mu fada masa ai ta nemi a taimaka masa ne, kuma taimako ba laifi ba ne” Kareem ya jidadin jin haka daga amininsa hakan na nufi ya janye kudinsa na son sai ya lalata alakar Noor da wadda take so. “Da ka kyauta kuwa, dan dai tana son gayen nan, duk da yake ba lallai ne ya iya rike ta ba ma idan ya aureta domin na ga yana da zafin rai, ita kuma sai mai hakuri zai iya zama da ita” “Ita ai bata san wa take so ba, har yanzu akwai kurciya a tare da ita, kuma yanayin girma kowa da yadda yake yinsa, wani sai yayi shekaru yake hankali ya natsu wata macen ma zaka ga sai ta haihu, da zaka gwada mata soyayya tsab zaka siye zuciyarta balle ma har ta saki jiki da kai nan da nan ne zaka shawo kanta” “No ni ba zan iya ruguza soyayyar wani ba, kuma ba zan so kowa ya samu kansa a yadda na samu kaina ba, ba zan so ta auri wadda bata so ba” “Amman kai kana sonta ai” “Wannan yar mitsitsiyar yarinyar? Ni fa ba sonta nake yi ba, kawai dai tana burge ni ne” “Rainonta zaka yi irinsu sun fi dadin aure, yadda duk ka bi da ita haka zata tafi, ni dai burina ka rabo da Safeena kuma ka samu farinciki ne ne manufata” Hausawa suka ce dan halak kaki ambato, wai da an ambace shi sai ya bayyana haka kuwa ne ya faruwa a daidai lokacin da Hafiz ya ambaci sunan Safeena sai ga kiranta ya shigo wayar Kareem. Abokinsa ba zai iya rejecting ba, ba kuma zai iya kin picking ba saboda Safeena ce, tsohuwar masoyiyarsa dan haka ya tashi a hikimance ya fice daga office din ya nufi wani bangare dabam ya hade rai sannan ya amsa wayar. __________________ Hmmmmm yanzu ne zamu tsuduma a cikin labarin, ina fatan kun shirya. Kun ji dai Kareem yace shi ba sonta yake ba. To Team Kareem sai ku tattara kayanku a gurin Noor ku ware 😆 Team Zafeer kun ji na ku yana cikin damuwa, sai ku fara tara masa kudin aure ko kuma ku roki Baba ya daga masa 😁 Noor dai tace ta daina anya zata iya? Ga mu dai gani gurguwa da aure nesa 🤔 Follow the KHADEEJA CANDY channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaNTEQTFXUuaypyV5O01 *Duk mai son ya rika samun Littafin TA KI ZAMAN AURE yayi following wannan Channel din mai suna KHADEEJA CANDY a nan zaku rika samu duka littafaina in Sha Allah* ✧✦ 𝗧𝗔 Ƙ𝗜 𝗭𝗔𝗠𝗔𝗡 𝗔𝗨𝗥𝗘 ✦✧ 𝗕𝘆 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆 *Talla👇👇👇* https://chat.whatsapp.com/GY1W0qJiFbJD5A5J6F0fqA *INA MATAN DA SUKASAN DARAJAR GYARA❓DAKU NAKE MACE MAI GYARAN BATA ZAMA BORA❌* *KUZO GA INGANTATTUN KAYAN MATA MASU KYAU DA INGANCI💪BA MUNA KAYABA❌ HAJIYA KIZO KISAI KAYAN MATA WURIN DA BAZAKIYI ASARAR KUDIN KI BA* *INA MASU CEWA NI KO NASHA KAYAN MATA BASAMIN AIKI HMMM HAJIYA BAKIDAI SIYA KAYA MASU INGANCI BANE, KAYANMU SUNA KARA NI'IMA, TAYARDA SHA'AWA, DADI, TIGHTENING (MATSI), CIKO DA GABAN MACE (DUK BUDEWAR SA), DUMIN GABA GA, KAMSHIN GABA GA KUMA NA KARA DANDANO OVER 💃💃💃💃💃👉 GA KUMA INGANTACCEN MAGANIN SANYI MAI DAGARGAZA SANYI KODA YA SHEKARA 10 A JIKINKI* 09038090328 *A DAYA BANGAREN KUMA MUNADA SABAYA MAI GYARAN NONO DUK LALACEWAR SA KO KIN HAIHU GOMA SABAYAR MU ZATA CIKO MAKI DA BREAST SUYI GIRMA SOSAI MADAME* *GA KUMA TA HIPS (MAZAUNAI)SU CIKO SUYI BULBUL NONO YA CIKO SOSAI HJY KIYI KIBA YAR DAIDAI SKIN DINKI YAYI KYAU KI KOMA TAMKAR TARWADA* AKWAI KUMA NA GYARAN NONO WANDA BAYA SAKA KIBA💃💃💃 GASKIYA NA YARDA DA INGANCIN KAYANTA👆👆👆 *Chapter - 12* Kun ji ni shiru kwana biyu sakamakon rashin da muka yi. Amman Alhamdulillahi ala kulli halin. ______________________ Ta dade shiru bata ce komai ba kamar bata jikin wayar har sai da ya dauke wayar daga kunnesa ya duba ya sake mayarwa. “Safaeena ina tunanin saboda kina da magana da ni ne kika kira ni” Cikin muryar kuka ta soma magana. “Ka canja min Kareem, daga lokacin da ka hadu da mahaukaciyar yarinyar nan gaba daya hankalinka ya tashi daga gareni ya koma gareta, yau har ta kai ta daga wayarka ka fada min magana son ranta, Wallahi da ban yi kokarin rike kaina ba da Allah kadao ya san abun da zan aikata a yau din nan kuma Allah ya san halin da zan shiga” Ya sauko daga matakalal dake gurin yana rike da wayar a kunnensa. “Ina kokarin shata liyi ne a tsakaninmu, akwai abubuwan da idan suka yi yawa, rashin tunani yana shiga ciki ya zauna, kamar yadda yake kike tunanin son haihuwa da ni yayinda kike da aure da wani, abun da kika yi niyar aikatawa ya tsorata ni, kuma ya bani mamaki, sannan ya farkar da ni daga dogon bachin da nake” “Baka ji tsoro ba? Lokacin da na ce maka cikina ya zube saboda kishinka? Baka yi tunanin zan iya shiga damuwa idan ka guje min ba, Kareem a can baya ma da muka yi soyayya kawai da na rasa ka sai da na rasa mijin aure saboda na kusa haukacewa, aka rasa namijin da zai aureni sai Abdull, balle kuma yanzu da na riga na san ka farin sani ka tsara jikina ta yadda bana jindadin mu'alama da miji sai da kai, ka san duk yadda zaka yi ka kawar min da kishina ka faranta zuciyata, Kareem saboda ina sonka ne ya saka nake son na haihu da kai, saboda ina da mafarkin da nake son ya tabbata a nan gaba, Wallahi ina sonka Kareem na sabu da kai, idan ka sake guje min a karo na biyu ba zan hakura ba...” Wani dogon numfashi ya sauke ya juya ya kalli kofar da ya fito sannan ya ce. “Safeena na san kina so na, ni ma ina sonki amman Allah be kaddara mu zama ma'aurata ba, be kamata mu yi ma yaran mu haka ba, be kamata ke ma ci amanar mijinki ba, ya kamata mu karbi kaddarar mana ko dan karin imaninmu da yafiya daga zunubanmu” Yana jin lokacin da taja majina tukuna ta amsa. “Mun karba, shiyasa kake auren wata macen ni kuma nake auren wani namijin da ba kai ba Kareem” “Idan har zamu cigaba da aikata abun da muke aikatawa kazantar ta yi yawa abun yayi muni, kuma hakan yana nufin ba mu karbi kaddarar ba Safeena” Ta yi dariya da zai iya ji. “Ba akan mu farau ba Kareem, kuma shi Allah mai yafiya ne a koda yaushe, ba haka za mu dauwama ba, wasu ma suna matsayin budurwa da saurayi suke yi balle mu da muke da aure, wannan abun duk kauna ce ta kawo, karka bari yarinyar nan ta canja min kai” “Babu ruwan Noor a alakata da ke, ni ba soyayya nake da ita ba, kawai dai an yi sara ne akan gaba ne, amman ba aurenta zan yi ba” Fashe masa ta yi da kuka. “Kana cewa mu rabu kamar abu ne mai sauki Kareem, kana kokarin juya min baya bayan kuma na saba da komai na ka, taya kake son na jidadin rayuwa babu kai a kusa da ni? Wallahi saboda kai bana sha'awar Mijinta yayi sati daya a garin nan, saboda kai bana jindadin duk wata mu'alama da mijina, kullum mafarkina da burina akanka ne Kareem, ka juya min baya a lokacin da na fi bukatarka, yanzu kuma mun sabu da juna kake kokarin guje min a karo na biyu? Ko ka manta wacece Safeena a gurinka Kareem....?” Tif... Ya kashe wayar ya sauke ajiyar zuciya, jin kamar kalamta na kokarin saukar masa da tausayinta kuma suna kokarin kusanto da rauninsa. “Me na jefa kaina a ciki? Me yasa na bari zuciyata ta yi nesa? Ba zan sake aikatawa ba, ba zan sake ba, ba zan sake cutar da wani ba, ba zan sake bari zuciyata da yaudari da jindadin da ba zai tabbata ba a gareni” Ya saka wayar aljihu sannan ya sake sauke ajiyar zuciya a karo na Biyu ya juya ya koma ciki. A bude ya samu office din babu kowa a ciki ma'ana dai Hafiz ya fita daga office din. Wayarsa ya fara cirewa daga aljihu ya dora a saman teburinsa sannan ya zauna ya dafe kansa. Abu da yake a bayyane gurin kowa kuma sirri dake aje a zuciyarsa yana son Safeena irin son da yake jin ba sai taba samun mai maye masa gurbinta ba, irin son da ya tabbatar sai dai ya mutu da shi domin ba zai iya aurenta ba a yanzu kuma baya jin zai iya cigaba da mu'alama da ita ta kazamtacciyar hanyar da ya sabawar kansa.  Sai bayan sallah Isha'i Kareem ya koma gidansa, yana shiga falonsa ya samu Yusura zaune tana duba waya, laramin danta dake cinyarta ya zo da gudu ya tare shi. “Daddy Oyoyo” Kareem ya cillashi sama ya cafke sannan ya sauke shi ya shafa kansa yana murmushi. “Areef ya kake?” “Lafeeya lau, amman Momy bata da lafiya” Kareem ya daga kai ya kalleta sai ya ga har lokacin idonta yana kan wayar dake hannunta kamar ma bata san da shigowarsa ba. Ya maida dubanshi gurin Areef “Me ya same ta?” “Jikinta da zafi ta yi amai kuma ta yi kuka...” “To yayi kyau je dakinka ka kwanta gobe akwai makaranta, ina Tine” “She's sleeping” “Okay kai ma je ka kwanta” Ya sumbance shi yaron ma ya mayar masa sannan ya sake shi ya nufi sama da gudu yana waigensa. Sai da ya haye sannan Kareem ya karasa gurin da Yusura take zaune yana daga tsaye zai yi magana ta riga shi ba tare da ta kalleshi ba. “Ga abincinka a dinning room” Ya kalli dinning area din sannan ya sake dubanta. “Ai da baki girka ba, tun da baki da lafiya kuma abinci ba wani damuna yayi ba...” Ta tsayar da taba wayar da take ta dago ta kalleshi. “Idan har ban girka abinci a gidan nan ba, wata kila ina ciwo ne mai tsanani da ba zai bar ni na iya tsayuwa da kafafuwana ba, amman girka abinci, gyara gida, kula da yaranka da kuma tsare mutuncina, wani abu ne da addinin da al'ada suka taru suka samar mana, ina yi ne saboda sauki nauyi na matar aure a gidan Kareem, ba wai ina yi ne saboda Kareem ba, ina jin tsoron tsayawa a gaban mahaliccina ya tambaye ni wani hakki na bawansa na kasa amsa masa, ko Kareem ya ci abinci ko kar ya ci Yusura zata girka, ko ka tsare mutuncinka ko kar ka yi Yusura zata tsare nata, ko ka kula yaranka ko karka kula Yusura zata ba su tarbiya gwargwadon halinta...” Ya hade wani abu da ya ji yana masa yawo na rashin dadi ya danne zuciyarsa ya sake yin furuci a gareta. “Ya jikin na ki? Me yake damunki?” Ta sake daga kai ta dubeshi. “Kana da bukatar wani abu?” Ya saka hannunsa aljihu ya ciro wallet dinsa ya cire ATM dinsa ya aje mata a hannun kujerar da take zaune. “Gashi idan kina bukatar wani abu ki siya, idan kuma kina bukatar ganin Likita ki je ki ganshi, 5885 is the pin” Yana dauke hannunsa daga aje ATM din ta mike tsaye. “Bana bukatar komai daga gareka, ina da rufin asirin da zai wadace na yi ma kaina komai, sai da safe” Ta bar a gurin tsaye ta nufi stairs. Binta yayi da kallo har sai da ta haye sama sannan ya zauna a inda ta tashi ya ja hular kansa baya ya kai hannunsa yana murza gaban goshinsa dake masa ciwo ya rufe ido. YUSURA POV. Tana shiga dakinta ta maida kofar dakin ta rufe ta zauna bakin gadonta hawaye suka sauko mata. Ba burinta ba ne fadawa mijinta bakar magana ba burinta ba ne yin zaman auren da babu farinciki a cikinsa, amman tsananin kiyayyar da take yi ma Kareem ya hana ta mallaka masa ruhinta, daman ita zuciyata ta san ba zai taba samunta ba, domin bata taba jin wani abu akansa ba duk tsawon lokacin da suka dauka a tare, tana kone zuciyarta ne kawai tana azabtar da kanta. Kareem yana da kyau da cikar kamala irin wadda yana da kudi ya shahara a cikin sa'aninsa masu irin aikinsa, amman babu dalili daya da kai ya saka ta so Kareem domin ba shi take so ba tun farko, aure da matar da ta rike ta a matsayin uwa ta hada, a lokacin da ba zata iya ce mata a a ba. “Har zuwa yaushe zan yi ta zama a cikin wannan yanayin? Sai yaushe zaki tafi Momy? Mutuwarki kadai nake jira, ko kuma ta Kareem na yi takaba na wanke wannan bakincikin, bana fatan mutuwa da aurensa, saboda bana son na tashi tare da shi gobe alkiyama, wata kila dai ba zan iya cin wannan jarabawar ba, kiyayyar da kike ganin kamar zata iya zama soyayya ba zama ba Momy, ta ma kara rura wutar kiyayyar da zata iya hada kasashen dake cikin zuciyoyi yaki da ta yi” Magana take da kanta zuciyarta na mata zafi, abu ne da ta riga ta sani har abada ba zata taba son Kareem ba, ba kuma dan be kai a so shi ba, ba dan yana mata wani abun ba, sai dan bata taba jin tana kaunarsa ba tun farko, shiyasa kullum take jin kamar a kurkuku take ba a gidan aure ba. A hankali ta kwanta gadon tana kallon gefen dakinta tana ta nazarin rayuwa. NOOR POV. A wahale na wuni a ranar, daga mama har Ya Nabil babu wadda ya sake bin ta kaina. Hana ce kawai ta taimaka min ta kwashe aman da na yi bayan ta dawo daga makaranta. Ina jin lokacin da Mama take mata fada wai ai da ta bari na kwashe taya zata kwashe min amai ai shagwaba ni da ake ne yasa nake son lalacewa. Wani abun da Mama bata saba min da shi ba shi ta yi min a yau, wato horo da yunwa ta hana ni abinci rana da hana ni na dare ko da wata safiyar ta waye jikina har rawa yake domin na saba ci ba kadan ba gashi kuma na wuni na kwana ban ci ba. Bayan Hana ta wuce makaranta na fito waje ina jin jikina kamar ba nawa ba, na nufi tukunyar dumame na bude na duba babu komai a ciki, sai na lashe tukunyar na dawo dakinmu na zauna ina jin rashin kyauta abun da na aikata tun farko... Da sannu na sabarwa kaina da zaman daki bana sha'awar fita ko'ina tun a wacan ranar da Zafeer yayi min huduba. Kwana hudu na shafe ko kofar gidanmu ban leka ba, kullum kuma ina sauraren yaron da zai shigo yace Zafeer yana sallama da Noor amman shiru. A ranar da aka cika kwana biyar ne mutumen da yayi ma Baba alkawarin siye masa gida ya zo aka yi maganar gidan da wani abokin Baba amatsayin shi ne mai gidan aka yi ma gidan kudin miliyan uku da yan kai a take ya biya kudin, duk abun da suke ina jin domin ina cikin dakinmu kwance. Ban motsa ba har sai da abokin Baba ya fita tare da shaidun da suka yi shaidar gidan da aka siyarwa Baba. Kareem din da abokinsa suka bukaci ganina. Sannan na saka hijabina na fito daga dakin ban kalli kowa ba har na zauna na natsu sosai kamar ba ni ba, domin ni kaina na san na canja. “Noor” Kareem ya kira sunana sai na daga kai na kalleshi. Shi ma yayi rama kamar dai ni, Murmushi ya sakar min yana tambayar ya jikina, a madadin na mayar masa da murmushin sai hawaye suka cika ido na ba tare da dalili ba, na yi ta yunkuri kirkiro murmushin na kasa. “Waya cire miki bandajen?” “Ni na cire” Na amsa ina maida kaina kasa. “Kina shan maganinki dai ko?” Na daga masa kai, domin bana son dogon zancen ni yanzu babu wadda nafi bukatar gani kamar Zafeer. Ban san me ya hana shi zuwa ba kusan sati daya yau, gashi Yaya Baya shiri da ni balle na ari wayarsa na kira shi na ji ko lafiya. “Ko dai wani abu aka mata Baba? Na ga ta canja? Kamar ba ita ba kuma ta yi rama” Baba ya juyo ya kalleni yayi dariya. “Ba abun da aka yi mata, mu kan mu muna mamakin yadda ta zama haka” Abokin Kareem din da ya siyawa Baba gida ya dube ni. “Duk lokacin da na fada maka wani abu akan yarinyar nan baka yarda ai, she's very simple and easy going cikin kankanen lokaci zata iya canjawa daman” Kareem din yayi kamar be ji shi ba, ya cigaba da magana da Baba ta zuba godiya kamin ya miko min wayarsa “Duba ki gani irin wannan maganin ne da na rubuta miki kike sha?” Na karbi wayar, a madadin hoton magani ko sunansa wani rubutun ne na gani zube a screen din wayar da Kareem ya miko min. “Me ya faru Noor? Why the sad face? I Miss the old you, indai damuwarki akan Zafeer zamu taimaka masa, idan kuma akwai wata matsalar bayan ita rubuta min yanzu” Na dago na dube shi sai na ga daga shi har abokinsa idonsa suna kaina, na girgiza masa kai. “Ba shi ba ne” “Amman dai babu wata matsala ko?” Na daga mishi kai. “Babu...” Na yi murmushin domin furuncin na cewar zai taimakawa Zafeer ya faranta min rai siye da siyen gidan Baba da suka yi a bisa karya. Ya miko hannu ya karbi wayar ya saka aljihu ni kuma na juya na kalli Mama da ta fito tana musu godiyar siya mana gida da suka yi. “Ba komai Mama ayi dai cigaba da hakuri da Noor da halinta, wata rana sai labari gashi dai yanzu ta janyo muku alheri” Cewar Hafiz abokin Kareem, sai Baba ya fashe da kuka kamar gaske. “Haka ne haka ne, Allah dai ya saka muku da alheri, ita kuma Allah ya kara mata hankali, ya kawo mata miji na gari...” “Ameen” Suka amsa ni da Kareem muna kallon juna kasa kasa kamar wadanda suka kula wani munafurci. Wata kila Baba ji yake kamar ba su fahimci zaren addu'ar ba, wata kila kuma sanadi ne da ni ma zan ji halin da ake ciki game da Zafeer domin tsinkayo Baba muka yi yana fadar abun da ban san an yi ba kuma wani be fada min halin da ake ciki ba. “Shi wannan yace be shirya ba, wai ba shi da hali yanzu, ya turo yan'uwansa sun zo nan kwana uku da suka wuce da dare yana neman a daga har nan da shekara biyu ko daya da rabi, shi ma kuma ya zo da kansa amman ni na fada musu ba zan iya ba, domin so nake na aurar da Noor na huta, ba karatu take ba, kuma ba wani aiki take tare mana ba balle ace za a daga har lokacin Ƴa mace da ta tasa kyauta dakin miji, balle kuma irin Noor kara na aurar da ita tun ina da rai” Na kalli Baba da sauri hawayen da ban san yaushe suka taru a ido ba suka zubo min. Sai dai wani kyauta da dadi sai na kasa cewa Uffan ba kamar da ba, wata kila da zan iya daka tsalle na rantsewa Baba na kunyata shi ko a gaban waye nace Zafeer nake so domin shi ne zabin raina... Amman a yau sai na kasa furta ko da kalma daya ne. “Baba Noor tana son saurayin nan nata, kuma shi ma yana sonta, be kamata ka shiga tsakaninsu ba, da dai zaka duba ka ba su damar zai fi, inda aka fito be kai inda za'aje ba” Kareem ya fada sai na juyo ina kallonsa da kamar damuwa a fuskarsa. “Ba wai bana son ta aure shi ba ne, samarin ne na yanzu sai a hankali ni har na fi sha'awar Noor ta auri mai mata sun fi rikon aure, kuma ita Noor ai ba wani so ta sani ba, ita dai barta ga shirmenta mu lokacin da muna yara ai ba wani soyayya muka sani ba, sai dai kawai ace an maka mata kuma sai ku yi zaman aurenku lafiya lau, zamani ne ya lalace har aka san wani lobe lobe, kuma ita Noor ai kawai dai ayi sha'ani...” Baba ne yake maganar ya karasa da dariya irin wadda ke nufin Noor bata san abun da take ba. Abokin Kareem ya ce. “Gaskiya, kuma ance abun da Babba ya hango yaro ko hau tsauni ba zai hango shi ba, to Allah yasa hakan ne mafi alheri, kuma kana da gaskiya ba Baba idan yarinya bata karatu babu inda ya fi dacewa da ita irin gidan aure, ko da ma tana karatun balle kuma irin Noor cikin kankanen lokaci zata fara son wani ma” Shi ma dai kallonsa na yi wata kila ya manta da ina zaune a gurin yake wannan zancen, kamar Kareem ya san abun da yake zuciyata sai ya dubi abokin nasa ya ce. “Hafiz dan Allah karka zuga Baba ya aurawa Noor wadda a shi take so ba, baka san komai game da auren wadda baka so ko baya sonka ba, idan ba zaka lurar ba, to karka lalata” Mama ta tashi ta shige dakinta, ni kuma na mike tsaye ina jin Baba na fadar. “Ai gaskiya ya fada babu wata zuga, Noor ai tana da saukin kai sosai kowa ya same ta ya zamu mata ba dan tana ƴata ba, sai dai ace bata jin magana amman tana da saurin sabo sosai” Daga haka ban sake juyo me suke tattaunawa ba, har suka ci suka shude suka fita ban san anyi ba, domin hankali ya karkarta a gurin Zafeer ina ta hararon dalilinsa na rashin zuwa, Allah kadai ya san me Baba yace masa ko yan'uwansa, amman me yasa Mama bata fada min hali da ake ciki ba? Shim ba ni da hakkin sani ne? Ko kuma ita ma din bata sani ba? Ko kuma saboda sun mayar da ni wawuya marar hankali da tunani ne? Tun da na yi alwala azahar ban sake fita ba dakin ba har aka yi Isha'i da ita na yi sallah, abinci ma da Mama ta kira tace na zo na dauka na dare sai na kasa fita na ji kamar bana bukatar abincin. Misalin karfe tara da yan mintuna yaro yayi sallama ya ce Zafeer yana sallama da Noor, kamar ina jira ba tashi da sauri daman akwai hijab a jikina na fito waje na saka talkamina zan nufi kofar sai Baba dake kishingide yana sauraren redio ya ce. “Ina zaki?” Na yi shiru na rasa me zance, domin na san ya san dalilina na fita a yanzu. “Na fa fada masa zan miki miji tun da shi be shirya ba, na san halin wasu yaran yan iskan unguwa sai su nemi lalata yarinya ma idan suka ga ba su samu damar aurenta ba, gashi ke ba wayo ba balle na ce” Mama dake zaune gafensa ta ce. “Haba Malam.. Ai ko da ka fada masa haka be kamata ka hana ta fita ba, baka san me ya zo da shi ba, kuma ba san abun da Allah zai yi a gaba ba, ko rabuwar za'ayi ai ta mutunci tafi, Wallahi Allah kadai yasan zagi da za'ayi maka a unguwar nan saboda kin dagawa yaron nan kafa da ka yi” Baba ya juya ya kalleta a fusace. “An dade ba a zage ni ba, a cikin masu zagin akwai mai wani mudu daya na shimkafa? Ko akwai mai ba ni dari biyar na kara na yi chefane? Ni fa ban hana shi aurenta ba, amman na fada masa muddi be shirya ba to kar ya batawa yarinya lokaci kuma ni na gaji da halayarta ina son na aurar da yata, ai Annabi S. A. W ma cewa yayi idan wadda kuka yarda da addininsa da mu'alamarsa ya zo son yarku to ku aura masa, addinin musulunci ya bawa iyaye damar zabar wa ƴaƴansu mazajen aure, daman can ni ban wani yarda da tarbiyar yaron nan ba, waya sani ma ko zuwa yayi ya hure mata kunne ta bishi su gudu?” “Zafeer din Baba?” Na furta da kaina kuka yana cin karfina. Sai ya zabura ya tashi zaune. “Zafeer din fa, ko ubanki ne shi ko kanen uwarki ne? Dan'adam babu abun da ba zai iya aikatawa ba ai, ke kuma kwakwalwar kifi ce dake gaki sokuwa sai ya tsara miki ki yarda ki hau ki bi, to daga yau sai yau kar ya sake sallamawa ki fita, ke ban ma yafe miki ba ki kula shi ko a hanya, ban yafe miki ba wata magana ta sake shiga tsakaninki da shi” Mama ta tashi tsaye dukan kirji. “Malam kana lafiya kuwa? Wane irin abu ne wannan? Saboda wani ya bullo ya nuna yana son Noor cikin kankanen lokaci ya siye bakinka da zuciyarka da dukiyar da baka san hallaci ko haramcinta ba zaka yarda ka rusa soyayya da baiko shekara uku dake tsakanin yaran nan? Duk irin iya shegen da Noor take haka Zafeer ya ganta yace yana so sai kuma ka shiga tsakani yanzu da yake hararo gaba? Haba Malam kar ka yi abun kunya mana kar kasa hakki ya bibiyemu” Baba ya mike tsaye ya dauke Mama da mari. “Duk wata doka da zan saka a cikin gidana ke kike rusa ta kuma ke kike ba su damar rusawa, ko a addinance ba ni da laifi tun da shi yace be shirya aurenta ba a yanzu, kuma wannan yaro da kike zargi Allah ya isansa domin har yau be fito yace min yana son Noor ba, dan haka ya barki da Allah da zargin lalata alaka da kika masa, kuma bari ki ji na fada miki idan yaron nan ya sake yin sallama kika bar Noor ta fita abakin aurenki....! Wato yan unguwa su yi da ni, na shigo cikin gida ki dora min tukunyar masifa, to ba zai yiyu ba, daman can Allah yayi ba matarsa ba ce” Ya saka talkaminsa ya dauki radio ya fice babu ko hula akansa. Mama ta dube ni ta kara min da wani bakincikin. “Allah ya kara, duk abun da ya faru ke kika ja, shegen shishigin tsiya da iyayi da yawo da shashanci shi ya ja miki, kuma ni ba zan bari aurena ya mutu ba saboda ke, domin ba zan koma neman gurin zama ko rabawa ba kuma zan yarda rayuwar Hannatu da Nabil ta shiga wani hali ba saboda ke, kadan ma kika fara gani, hawayen da kika yi ta saka ni ina fada miki gaskiya kina bijirewa yau ga sakamakon kin fara gani, kuma wannan so min tabi ne baki san me zai biyo baya ba, sai ki zuba ruwa kasa ki sha...” Tana maganar tana nuna ni ta muryarta nake karantar kukanta domin nawa hawayen sun hana ni ganin fuskarta. A kananen shekaruna na fara dandana zafi da bakincikin rabuwa, Baba ya sauya tunanina ya rusa burukana, ya wargaza shirina, ya saka ni a wani gidan kurkuru da ban isa na fitar da kaina ba, ban san ma ya kofar fitar take ba.... Follow the KHADEEJA CANDY channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaNTEQTFXUuaypyV5O01 *Duk mai son ya rika samun Littafin TA KI ZAMAN AURE yayi following wannan Channel din mai suna KHADEEJA CANDY a nan zaku rika samu duka littafaina in Sha Allah* ✧✦ 𝗧𝗔 Ƙ𝗜 𝗭𝗔𝗠𝗔𝗡 𝗔𝗨𝗥𝗘 ✦✧ 𝗕𝘆 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆 *Talla👇👇👇* https://chat.whatsapp.com/GY1W0qJiFbJD5A5J6F0fqA *INA MATAN DA SUKASAN DARAJAR GYARA❓DAKU NAKE MACE MAI GYARAN BATA ZAMA BORA❌* *KUZO GA INGANTATTUN KAYAN MATA MASU KYAU DA INGANCI💪BA MUNA KAYABA❌ HAJIYA KIZO KISAI KAYAN MATA WURIN DA BAZAKIYI ASARAR KUDIN KI BA* *INA MASU CEWA NI KO NASHA KAYAN MATA BASAMIN AIKI HMMM HAJIYA BAKIDAI SIYA KAYA MASU INGANCI BANE, KAYANMU SUNA KARA NI'IMA, TAYARDA SHA'AWA, DADI, TIGHTENING (MATSI), CIKO DA GABAN MACE (DUK BUDEWAR SA), DUMIN GABA GA, KAMSHIN GABA GA KUMA NA KARA DANDANO OVER 💃💃💃💃💃👉 GA KUMA INGANTACCEN MAGANIN SANYI MAI DAGARGAZA SANYI KODA YA SHEKARA 10 A JIKINKI* 09038090328 *A DAYA BANGAREN KUMA MUNADA SABAYA MAI GYARAN NONO DUK LALACEWAR SA KO KIN HAIHU GOMA SABAYAR MU ZATA CIKO MAKI DA BREAST SUYI GIRMA SOSAI MADAME* *GA KUMA TA HIPS (MAZAUNAI)SU CIKO SUYI BULBUL NONO YA CIKO SOSAI HJY KIYI KIBA YAR DAIDAI SKIN DINKI YAYI KYAU KI KOMA TAMKAR TARWADA* AKWAI KUMA NA GYARAN NONO WANDA BAYA SAKA KIBA💃💃💃 GASKIYA NA YARDA DA INGANCIN KAYANTA👆👆👆 *Chapter - 13* Babu kowa a tsakar gidan balle na ce wani ne ya rika ni ya isa da ni kofar dakinmu, haka kuma ba zan iya fadar cewar kafafuwana sun kawo ni ba, domin samun kaina na yi tsaye a tsakiyar dakinmu ina kallon hudun daren da ya cika daki. Can ka na ji an dafa ni muryar Hana ta fara isa kunnena. “Da ni ce ke, zan auri mutumen nan ko dan na samu rabuwa da Baba lafiya, kuma zaki huta da duk wata masifa tashi da tashin hankali ko fada, idan kika yi aure zaki huta Noor” Na juyo na kalli ta saitin inda take tsaye. Amman na kasa ce mata komai sai hawaye ne suke min zuba, a rayuwa ban tana jin wani abu tashin hankali ba irin wadda na ji a yau din nan. Sai na ke jin kamar sanarwar mutuwa aka min cewar Zafeer ya mutu ya bar ni a raye. “Noor ki yi addu'a kawai, kuma karki bari so ko shashancin da ake ganinki da shi ya zama silar lalacewarki saboda bakin da Baba yayi cewar be yafe ba idan kika kula Zafeer” Na sulale kasa a hankali na zauna a gurin, na rasa me zan yi ko na ce, kalamaina kamar sun kare, duk wani kuzari a yau ba ni da shi. Me yasa Baba zai min haka? Anya ya san yadda nake son Zafeer kuwa ko kuma yadda shi Zafeer din yake so na? Mama ta yi gaskiya tace ni ce na janyowa kaina kuma haka din ne, domin ni na yi silar zuwan Kareem da abokinsa a gidanmu gashi sun lalata baiko ba tare da na san waye mai so na a cikinsu ba, ba ma nuna suna so na ba, kuma ba su furta ba ban taba ganin wata alama dake nuna soyayyata a garesu ba.  Gaba daya sai na ji kamar mafarki nake wunin ranar sai ya zame min kamar ba gaske ba, ni dai na san ina matukar kaunar Zafeer irin kaunar da nake jin idan ba shi ba ba zan iya zaman aure ba. A inda na zauna ban tashi ba har garin Allah ya waye kuma bachi be kusanci idona ba, haka kuma ban bude baki na ce da kowa komai ba ban kuma ihu ko kururuwa ba, saboda ina jina a wani yanayi na dabam da ban saba jina ba. Bayan na yi sallah asuba na nemi gurin kwanciyata na kwanta sai idona suka ce firr ba dai bachi ba Nooriyya, karyarki ba a wannan wunin ba, haka na tashi zaune na kurawa kofar wajen ido, na dade a zaune kamin na iya bude baki na fara ambaton Allah, Ban yi wani kwakwaran motsi ba har Hana ta gama shirinta na makaranta ta fita ta zuba kunu sannan ta kawo min nawa har inda nake kallo daya ta yi min ta fahimci a tsorace nake ga idona yayi wani Ja kamar wadda ta shekara bata yi bachi ba. “Ga kununki in ji Mama...” Na kalli kunun na dauke kai ina jin ba zan iya kai komai a cikina ba yanzu. Ni dai ba wani sanin damuwa na yi ba amman ina jin dakinta na daf da ni domin kokarin rabani da Zafeer da Baba yake ko ma yayi wani abu da ban taba mafarkin faruwarsa ba. “Wa'alaikusalam” Muka ji Mama ta amsa sallamar Zainab dake sanye da uniform din makaranta, Hana ta jiya ta fice daga dakin kamar dai babu wadda ya damu da halin da nake ciki, wata kila ba su yi zaton soyayya ta ta kai haka ba, ko kuma ganin suke wani abu ne da zan iya mantawa a take. Ko kuma dai saboda ni na janyowa kaina ne shiyasa lamarin ya zo min ta haka. “Noor... Lafiya kike kuwa?” Kamar an bude min kofar sassauci tana tambayar haka sai na fashe da kuka na kwanta jikinta amman na kasa fada mata damuwata har ta gaji da tambayata ta koma rarrashina. “Allah dai yasa lafiya, Zafeer ya je gidanmu shi ma cikin damuwa yace na fada miki ya zo jiya amman be samu ganinki wai yana son ku hadu a gurin aikinsa ko kuma kwanar dan musa mai itace anjima da karfe goma” A sirrance take fada min sakon na Zafeer, abun da hausawa ke cewa ga bikin zuwa babu zanen daurawa, domin ban isa na tsallake umarni da furucin mahaifina na je na ganshi ba, kuma a yau bana jin zan iya budewa kawata cikina balle na fada mata damuwata da babu mai min maganinta sai Allah. “Noor akwai wata matsala ne? Fada min ko minene dan Allah” Na girgiza mata kai na matsa baya na kwanta ina maida numfashi daker. “Wai fada kuka yi da shi ne ko kuma me?” Nan ma dai ban ce mata komai ba. Har ta gaji ta tashi ta fita ta barni rumgume da bakincikina. Ban iya fitowa na yi komai ba har Mama ta gama aikinta na gida, Yaya ya dauko ruwa sannan yayi wanka ya fita, a nan na samu mikewa tsaye ina jin kaina na masifar ciwo ga wani jiri jiri da nake ji yana dibata yana yawo da ni. Ruwa na zuba na shiga bandaki wai saboda na samu na yi wanka amman sai na saka yin wanka na zauna a bandakin ina ta kuka. Hankali be kara tashi ba sai da wani almajiri ya shigo ya ce Zafeer na sallama da Noor Mama tace masa yaje yace bana gidan. Rumgume kaina na yi ina ta kukana babu mai rarrashina har sai da na gaji na tashi na daura zanena na fito ba tare da na yi wanka ba na aje ruwan a waje sannan na nufi dakin Mama na zauna daga bakin kofar dakin ina kuka na ce. “Mama Wallahi duk na daina abun da nake, ba zan sake kin jin maganar kowa ba, Mama ki yafe min kuskurena, kuma dan Allah ki roka min Baba yace ya yafe min yayi hakuri ya bar ni na auri Zafeer dan Allah Mama” Kaya take ninka amman haka be hana ta kalleni ba ta ce. “Kin fi kowa sanin halin Babanki ai, yanzu ya ga mai kudi ba zai yarda da soyayyarki da yaron nan ba, kuma ni ban ga laifin ubanki ba, daman tsuntsu da ya ja ruwa ai shi ruwa kan doka, tun abun nan be yi nisa ba ya kamata ki gane gadar zare kike yi ma kanki amman ina, hankali yayi yamma ke kin yi gabas, idan kika ga Babanki be hada aurenki da wannan mutumen ba to sai idan shi din ne yace baya sonki ko kuma wani ya gani wadda ya fishi” “Ba so na yake ba Mama Wallahi wata kalmar soyayya bata taba shiga tsakanina da shi ba” Na fada da muryar kuka wani kukan na cin karfina. “Wannan kuma ke kika jiyo, ga dubu biyu nan tashi ki kai gidan mai adashe, bashin da kika ci ne ban gama biya ba” Ta jego min kudin ni kuma sai na kai hannu na dauka, na kalleta sannan na tashi na fice daga dakin ina hawaye. Dakinmu na koma na zauna gaba daya sai na rasa abun da ke mini dadi. Na kusan minti talatin a dakin ina kuka har sai da Mama ta yi magana sannan na yunkura na tashi idona a kumbure na saka rigata da hijab na riko kudin na fito na saka talkamina na fice daga gidan. Kamar wata marar lafiya haka nake tafiya har na isa gidan mai adashen na bata kudin na juyo na fito ta babu wani kuzari a tare da ni. Daf da zan isa gida na ji muryar Zafeer yana kiran sunana amman na kasa waigawa saboda bana son na yi arba da fuskarsa kar rauni ya saka ni karya doka da mahaifina ya saka min, amman hakan be hana shi shan gabana ba. “Noor magana fa nake miki kina tafiya kamar baki gan ni ba, me ke faruwa ne?” Na dauke kai na kauce daga gabansa na cigaba da tafiyata. “Noor... Noor.. Ni ne fa, Noor” Na kasa juyawa kuma na kasa amsa masa sai hawaye suka zubo min. Ya sake shan gabana. “Jiya na tafi gidanku ban samu ganinki ba, idan har Baba zai juya min baya ya ki sauraren uzurina ban yi zaton haka daga gareki ba Noor, kin san ina sonki sosai zan iya jure komai ban da rashinki Noor, na roki Baba jiya na ce ya yi hakuri ya ba ni wata biyu zuwa uku zan yi na yi duk yadda zan iya, zan aureki Noor ko haya ce zan kama mu zauna kamin na samu aiki, amman me yasa kike kokarin canja min? Ko wani abu aka ce na miki? Ko kuma an fada miki wani aibuna ne...?” “Babu wani aibunka da za a fada min da zai saka na tsane ka Zafeer, babu wadda zai iya shiga tsakanina da kai, babu wani laifi da zaka aikata a duniyar da zai saka na juya maka baya” Magana nake masa a zuciyata amman a zahiri na kasa furta komai sai kallonsa nake. “Noor...” Ya sake kiran sunana muryarsa a sanyaye, nan din ma ban amsa ba sai ma kauce da nake kokarin yi daga gabansa na cigaba da tafiyata. “Baby Noor Noor yau ni nake miki magana kina tafiya? Ina kiranki kin ki amsa min? Me yake faruwa? Fushi kika yi? Saboda na ce ba ni halin aurenki a yanzu? Zan aureki Noor ko ta halin Yaya na miki alkawari hakan yayi miki?” Nan ma ban juyo ba shi kuma be fasa bin bayana yana bayyana min kalaman da suke kara tsuma zuciyata ba. “Noor please, ina binki a baya kina tafiya kamar wani bakonki miye haka?.... Nooorr!” Daga karshe ya kira sunana a tsawace har sai da na tsaya cak daga tafiyar da nake. “Ko dai mutumen nan ne ya fada miki wani abu a kaina? Ko kuma Baba ya fada miki wani abun ne dabam da ba shi na fada ba, me yasa kike min haka? Why?” Na hade yawu na cigaba da tafiya da sauri na barshi a gurin tsaye, ina shiga gidan na samu Mama sanye da hijab ta nufo kofar fita. “Alhamdullahi, daman bayanki zan bi saboda na san halinki zaki iya satar kafa ki tafi gurin Zafeer din nan” Ni dai ban ce komai na nufi dakinmu na kwanta ina ta gurzar kuka kamar babu gobe. A haka Hana ta dawo daga makaranta ta same ni har na yi rama tsabar kuka da tashin hankalin da na samu kaina a ciki. “Noor dan Allah ki ba kanki lafiya, ki yi ta addu'a idan Zafeer mijinki ne zai aureki babu wadda ya isa ya hana” A nan na samu damar amsa mata da toh sannan na tashi zaune ina kallon kunun da ya aje min tun safe. “Baki sha kunun ba?” “Ba zan iya cin komai ba, Hana” Na kira sunanta sai ta amsa min ta duko. “Dan Allah ki roka min Baba yayi hakuri Zafeer yace zai nemo kudi nan da wata uku zai aureni, ki ce yayi hakuri ya bar ni na yi magana da shi, hukuncin yayi min tsauri...” “A ina kika ga Zafeer din?” “Dazun da Mama tace na kai kudin adashe...” “Amman dai ke kam Noor baki jin magan yanzu duk bayan gargadin da Baba yayi miki yace miki be yafe ba idan kika sake magana da Zafeer sai da kika yi? Kin san abun da tsinuwar iyaye take nufi kuwa...” Na girgiza mata kai da sauri. “Ban yi magana da shi ba, shi ne yake bibiyata yana fada min haka, ransa ya bace da ban yi magana da shi ba, ni ma na ji kamar na mutu saboda yayi min magana ban amsa masa ba, Hana babu dadi dan Allah ku yi magana da Baba ko zai ji, ni na san haushina yake ji amman ke zai iya saurarenki saboda ya san kina da hankali” “Aa Mama ma bana jin zata iya tunkararsa da wannan maganar balle kuma ni, indai ba son kike ya tsine min albarka ba ni ma, ki dai ta addu'a ni ma zan taya ki” “Na gode” Na fada mata sannan na tashi kamar yakusasshen lawashi na fita daga dakin, alwala na yi na dawo dakin na yi sallah azahar na yi ta addu'a. Misalin karfe hudu na yamma Yaya Nabil ya shigo gidan da ledarsa kamar yadda ya saba, ko da an yi girki balle yau da ba a girka komai a gidan ba. Awaje ya zauna gurin da Mama take zaune domin kusa da kofar dakinmu ne, ina jinsa yana ta fada da alama ransa a bace yake ban fuskanci me yake magana akai ba, amman na ji sunan Zafeer da Oga Kareem kuma na ji zancen yan sanda. Hakan ya saka na mike tsaye ina jin jiri na taka na isa kofar na rike kofar na tsaya ina kallonsa. “Innalillahi Wa'Inna Ilaihirraji'un abu be yi dadi ba, yaushe wai?” Na ji mama ta fada sai Yaya yace. “Yanzu nan ba a dade ba Wallahi, kuma duk Baba ne sila, shi ai yana da gaskiya ko nine zan aikata fiye da haka, me yasa Baba zai yi halin karanta miye amfanin haka? Fisabillilahi haka ake yi, ni gaba daya bana jindadin yadda Baba yake tafiyar da rayuwar gidan nan, ban taba ganin uba irin na mu ba” Mama ta juyo ta kalleni sai ta miko min hannu. “Zo nan ki zauna” Na isa kusa da ita na zauna sai ta saka ni a jikinta ta rumgume ni. “Wai an kama Zafeer” Na daga kai da sauri na kalleta. “Me yayi?” “Wai ya tafi gurin aikin Ogansu Yayanki yayi masa cin mutunci a cikin mutane shi ne shi kuma ya saka aka kama shi yana can rufe” Na fashe da kuka ina jin kamar na tashi na tafi amman babu dama. Yaya ya kalleni a tausaye ya ce. “Ni na rasa gane wane irin kalar uba Allah ya ba mu, gaba daya babu ruwansa da damuwarmu, yanzu mutumen ko auri Noor Wallahi ba zai ga mutuncinta ba saboda ya san yadda aka yi ya aureta...” “Jarabawa ce ta rayuwa, sai hakuri Nabil duk yadda zaku ji be kai yadda ni nake ji ba, ku ai ubanku ne ni ko mijina ne, duk jarabawar da za'ayi mace ko yaya ko wace iri ce mai sauki ce idan ba a gidan aurenta ba ne, idan mace tana shan wahalar rayuwa akan ce idan kika yi aure kin huta, amman idan ta tararda kaddarar a gidan aure, to wannan ita ce jarabawa mai girma, domin shi aure yana nufin rayuwa ne ko mutuwa, babu yadda zaka yi, duk yadda kuke jin bakincikin ubanku be kai yadda ni nake ji ba, yara biyu na rasa kamin na haife ku, shekara shirin da uku da aure babu ranar da bana kwana da bakincikin ubanku” Ta karashe zancen cikin kuka Ya Nabil ya sauke kansa kasa rai a bace nikam kuka kawai nake ina jin bana da makiyi a duniyar kamar Kareem, sai kuma mahaifina da nake jin na tsane shi a yanzu. Na dago daga jikin Mama na kalli Ya Nabil “Yaya dan Allah ko zaka kira min Kareem a wayarka na yi magana da shi please? Dan Allah?” “Me zaki ce masa?” “Magana kawai zan yi da shi dan Allah Yaya, kar yaje yayi ma Zafeer wani abu dan Allah Yaya” Rokonsa nake da muryar kuka hawaye na min zuba, sai ya saka hannunsa aljihu ya ciro wayarsa ya kama number sai da ya kira sannan ya mika min. Ni kuma na karba na mike tsaye na shiga dakinmu. “Assalamu Alaikum” Ban amsa sallamar ba na yi shiru kamar wadda ta rasa abun cewa. Hakan sai ya fahimtar da shi ni ce a waya ba Yayana ba. “Noor me ya faru...?” “Komai ma ya faru Kareem, na yi dana sanin saninka a rayuwata, sanadinka Baba ya raba ni da Zafeer ni shi kadai nake so ba zan taba son kowa ba, saboda me zaka kama shi?” “Ba a fada miki abun da yayi ba? Planning ma fa nake na yadda zan taimaka masa ya aureki, tun jiya da na fahimci abun da Babanki yake kokarin aikatawa, amman sai gashi yau a restaurant a gaban jama'a yana ci min mutunci yana kira da sunaye kala kala, shiyasa ai na rufe shi sai yayi hankali tukuna” “Kana takama da kudi ne kawai Kareem, shiyasa ka siye Babana kuma yanzu ka kulle saurayina, to ni ba zan siyu ba, ba zan taba sonka ba, kuma na tsane ka da na san bakincikin da zaka haifar min kenan ba zan yarda ko magana ta shiga tsakanina da kai ba...Ka sake shi Wallahi saboda ka ga shi ba shi da kudi ka yi masa haka...” Ban gama fadar Abun da nake son fada ba Yaya ya fisge wayar ya kashe. “Shi ke nan na rasa aikina...” KAREEM POV. Sai da kiran ya katse sannan ya kalli Hafiz dake zaune a gabansa. “Ka ji da kunnenka ko? Shiyasa na saka hands-free ai saboda ka ji” Hafiz ya dauke idonsa daga wayar ta Kareem dake aje a kan teburin ya kalli Kareem. “Kurciya ce fa kawai take damun yarinyar nan, ai kai baka fito ka fada mata cewar kana sonta ba ko? In ba shi ba miye na wani kiranka ta fada maka magana haka? Wallahi bata da wayo” “Ko ma dai minene yanzu ta fadi mind dinta, tun farko na fada maka yaron nan take so, ko na rasa matar aure a duniya ba zan taba auren matar da bata so na ba, kuma ba zan yarda na shiga tsakanin masoya ba, so ka sake tunani Hafiz ka je ka gyara lamarin yarinyar da saurayinta kuma ka nunawa mahaifinta gaskiya, karka cutar da ita ka cutar da saurayinta” “Amman baka ga abun da ya zo mana ba dazun nan” “Abun da yayi be kyauta ba, abu ne da kowa ya sani, shiyasa har na saka aka kama shi, kuma yanzu za a sake shi, amman kokarin ganin ka shiga tsakaninsa da Noor daukar alhaki ne, indai saboda ni kake yi ka daina ni dai ba zan auri yarinyar nan” “Ni fa alheri kawai nake kokarin kullawa, kuma ni ban cewa mahaifinta ya rabata da saurayinta ba, kuma ban cewa saurayinta ko ita su rabu da juna ba, ni dai ina kokarin sama maka mafita ne Allah ya san manufata shiyasa nake ganin zaka iya koya mata sonka cikin kankanen lokaci, amman zan gyara komai kuma na maka alkawari daga yau ba zan sake rokon ka auri Noor ba, kuma zan je na samu mahaifinta zan gyara duk inda kake tunanin na lalata, daga nan har zuwa nadewar duniya Kareem ka cigaba da zama a haka ba zan sake maka magana ba” “Hakan ya fi ba, na san yadda kiyayya take ba zan yarda na sake aikata kuskure a karo na biyu ba, kuma ba zan yarda na shiga tsakanin soyayyar kowa ba, yadda rayuwar Noor take ba zan yi mata sha'awar ta zauna da wadda bata so ba” Ya dauki wayarsa ya mike tsaye ya fice a office din a fusace. Hafiz ya bishi da kallo yana murmushin takaici. “Ba laifinka ba ne laifina ne, kuma zaka gane ka yi da ďan halak...” Ya fada sannan ya cize bakinsa ya hade rai. Follow the KHADEEJA CANDY channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaNTEQTFXUuaypyV5O01 *Duk mai son ya rika samun Littafin TA KI ZAMAN AURE yayi following wannan Channel din mai suna KHADEEJA CANDY a nan zaku rika samu duka littafaina in Sha Allah* ✧✦ 𝗧𝗔 Ƙ𝗜 𝗭𝗔𝗠𝗔𝗡 𝗔𝗨𝗥𝗘 ✦✧ 𝗕𝘆 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆 *Chapter 14* “Kasan halinta ai da shirme da ma dai baka bata wayar ba” Mama ta fada sai ya juya ya kalleta. “Na dauka magana zata yi masa ta hankali amman meye na fada masa magana haka gatsai, babban mutum ne fa Mama kawai yana da saukin kai ne shiyasa Noor ta same a ruwan sanyi” “Yanzu aikin gama ai ya gama, sai a tari gaba, ka je ka bashi hakuri kace baka sani ba ta dauki wayarka ta kira shi” “Haka zan yi” Ya juya ya fita Mama ta bi bayansa ni kuma na zauna ina ta aikin kuka. Yadda na kwana banci ba haka na wuni haka wani daren ya sake tararda ni na kasa cin komai sai ruwa kawai nake iya sha... A daren ma sai na kasa bachi saboda tunanin Zafeer ko ya dawo ko kuma yana can, a wane hali yake a can? Wace kalar azaba suke gana masa? Me zai saka ma su kama shi? Na ji yayi abun da be dace ba amman ai taba shi aka yi domin be taba zuwa haka nan kawai ya ci mutuncin Kareem ko ya masa wani abun ba sai yanzu. Mama ce ta shigo har cikin damunmu a lokacin da Hana take shirin makarantar Islamiya kasancewar yau assabar ba kamar sauran ranakun da take zuwa makarantar boko ba. Ta zauna kusa da ni ta aje min kunun. “Noor daure ki sha idan kika ce zaki saka damuwa a ranki zata wahalar da ke, kuma ita kaddara ba a kauce mata komai wayon mutum, idan Allah ya kaddara Zafeer mijinki ne zai aureki babu wadda ya isaya hana, idan kuma Allah yayi shi ne mijin ba ko an taru an hadu za a daura muku aure ba zai dauru ba, kalli yadda kika rame cikin kwana daya da rabi, kin koma kamar ba ke ba, ki yi hakuri kinji ƴata” Ta kwanto da ni jikinta sai na ji sanyi a raina na lallabar da ta yi min da kuma kokarin kwantar min da hankali. Na bude bakin a hankali ta fara ba ni kunun ina sha har na sha rabin kofin sannan na ji na koshi. “Na koshi Mama” Hana ta kalli kunun ta kalleni. “Lallai na yarda kina son Zafeer kalli yadda kika natsu kika koma kamar ba ke ba, kuma yadda kike fushi ko kuka baki rabuwa da abinci amman yau dubi yadda kika ki cin abinci” Na kalleta kawai na dauke kai domin ni kadai na san yadda nake ji a raina ni kadai na san halin rayuwar da bake ciki “Ni ma dai na yi mamakin yadda noor ta natsu kamar ba ita ba” Mama ta fada kamin ta yunkura ta tashi tsaye ta dauke kunun ta fice daga dakin. Hana kuma ta gama shirinta ta kama hanyar makaranta, aka bar ni a dakin ni kadai ina jin jikina babu karfi tunani ne ko kuma dai yunwar da bana ji ce take karya garkuwar jikina. Ina daga kwance na ji sallamar kawata Zainab, na tabbatar a lokacin Mama bachi take domin ban ji ta amsa mata ba, wata kila kuma tana bandakin ne ko kuma ta fita ba tare da na sani ba. Cikin dakinmu ta shigo ganinta ya saka na tashi zaune domin na san ba zan rasa labarin Zafeer a bakinta ba. “Noor amman dai baki da lafiya ko?” Na daga mata kai. “Me yake damunki?” “Ni ma ban sani ba” Ta yi shiru tana kallona kamin ta kawar da kai ta ce. “Wata magana na ji ana ta yi Noor, ko da yake dai ba zan boye miki komai ba gaskiya Zafeer ma ya fada min kuma ya aiko ni gurinki na kawo miki wannan takardar, amman ina son na san me ya hada ku Noor?” “Ba abin da ya hada mu, me kika ji?” “Baki ji an kama Zafeer ba? Jiya misalin sha daya na dare ya dawo gida, kuma kamin a kama shi ina ta jin magana sama sama cewar ke da mahaifinki kun bi kudi wai ana son a aura miki wani ba Zafeer ba, ance har da gida ya siyawa Babanki kuma yana kawo muku kayan dadi a gida” Mamankin jin cewar ya siyawa Babana gida ba abu ne na mamaki ba, wata kila Baba ne ya fada wata kila kuma abokansa. Amman zancen yana kawo mana kayan dadi wani zance ne da ban san da zamansa ba. Kuma ban san wata rana da Kareem ya kawo mana kayan dadi haka nan siddan ba, har sai idan ni na shigo da su, jin cewar mahaifina da ni kaina mun karkarta ga mai arziki wani abu ne da ya fi ko wane yi min daci, domin idan har abun da Baba yake kudiri ya tabbata mutane za su yi mana kallon maciya amana ne. Musamma ni babu ta inda zan iya wanke kaina. Ta damka min takardar dake hannunta. “Gashi Zafeer yace na kawo miki, kuma Noor da gaske ne Babanki yace kar Zafeer ya sake zuwa kofar gidanku?” Hawaye na amsar tambayarta domin su suka fara fita madadin kalma a bakina. “Ina ganin kamar da akwai matsala a kasa Noor baki son fada ne kawai, ko dai dole ake son yi miki?” Nan ma bance mata komai ba, zata sake yin wata maganar ta ji muryar Mama da ta fito daga bandaki. “Zainab ce” Sai ta tashi da sauri ta fita daga dakin tana gaisawa da Mama. Ban bude takardar ba sai da ta fice gaba daya daga cikin gidan, ina warwarewa gabana yana faduwa kamar ance zan karanta sakon mutuwarsa ne a ciki. “Noor... Me yake faruwa? Nace ki zo ki same ina son magana da ke kin ki, na hadu dake na miki magana kin ki ki amsa ni, an kama ni jiya na yi tunanin zaki zo ko da gidanmu ne ki tambaya ko ki kira wayata, amman na tambaya baki yi ko daya ba, why? Da farko na dauka ko Baba ne kawai aka yi nasarar sauya masa ra'ayi kaina, amman jikina yayi sanyi a lokacin da na ji baki neme ni ba, ko dai ke ma ya sauya miki ra'ayi akaina ne Noor? Shekara uku da muka yi a tare kike son batawa saboda kudi? Kina son ki manta da ni ki rayuwa da wani saboda kudi? Haba Noor kin san fa ina sonki, jiya da na dawo gida ke na fara tambayar kin zo, Inna ta yi kamar zata kashe ni saboda haushi, amman hakan be hana ni rubuto miki wannan wasikar ba a yau kuma zan sake rokokin ki a karo na karshe... Ina son ki fito mu hadu a bayan islamiyarku, zan jira ki a gurin daga yanzu har zuwa azahar, ina son mu yi magana ne Noor bana nufin cutar dake, kuma hakan zai karyata abun da zuciyata take hararon game dake, na san ke karamar yarinya ce kuma kina son rayuwar jindadi, amman hakan be isa ya saka ki yi watsi da ni ba ki kama wani da baki da tabbacin ko zai iya rike ki... Noor in har baki fito ba to ni ma zan hakura dake har abada kuma hakan yana nufin ya sauya miki ra'ayi akaina kenan!” Ina karatun hawayena na jika takardar, Zafeer ya zo min da wani abu mai nauyi da ba zan aikatawa a yanzu ba, domin ba zan tsallake maganar mahaifina kuma na yi silar mutuwar auren mahaifiyata a yanzu ba. Ina sonsa amman Baba ya shata liyi a tsakaninmu. A nan wata zuciyar ke ce min na fita naje na dawo ai Baba baya gidan kuma be san an yi ba, wata kuma na ce min na lallaba Mama na ce ta roki Baba naje an ga Zafeer ko da na iya yau ne kawai. A cikin duka shawarwarin ban dauki ko daya ba, A kowane sakon da minti idan na tuna Zafeer yana can yana jirana sai na ji hankalina ya tashi, a haka na wuni a dakin ina kuka har na ji kiran sallah Azahar. Shinkafa da miya na daga cikin favorite food dina amman ranar sai na kasa cin wadda Mama ta girka. Da dare ina jin lokacin da take labartawa Mama cewar tun ranar ban sake cin komai ba har yanzu, a madadin Baba ya ji tausayina sai ya rufe ta fada wai ita take goya min baya nake wannan iskanci. Tashi na yi zan fita sai Hana ta fara kokarin hana ni. “Noor karki fita” “Magana kawai zan yi da Baba” Na amsa ta sannan na fita na isa har gurin da Baba yake na risina kasa ina kuka. “Baba dan Allah dan Allah Baba ka yi hakuri karka aura min wani idan ba Zafeer ba, Wallahi Zafeer nake so Baba shi kadai nake so, idan na auri wani ba shi ba mutuwa zan yi Wallahi” Ya haska ni da fitilarsa mai haske... “Eyyyyyyeeee lallai duniya ta miki dadi, tabbas kin samu yadda kike so Noor, yanzu har abun ya kai ki dubi idona ki fada min ga wadda kike so ki aura? Duka nawa kike? Ke har wata soyayya kika sani ma? Dan uwarki can da da ake aure wata soyayya aka sani amman yanzu saboda zamani ya lalace duniya ta bude muku ido kuma uwarki ta saka kin raina ni shiyasa kika zo kika zame ni kina fadar zaki mutu idan ba Zafeer ba?” Ya juya gurin Mama ya rufe da fada tana amsa masa sai ya rufe ta da duka ni kuma na yi hanzari tashi cikin karfi hali da rashin karfin jiki na tare Mama sai ya hada ni da ita yayi mana duka kamar be san inda muka fito ba. Dukan Mama a gaban idonmu wani abu ne da yake saka mana tsanar mahaifinmu kullum kuma wani abu ne da Baba yake jin dadi aikatashi, wata kila yana tunanin hakan zai saka mu kara tsoronsa ne abun da be sani ba hakan yana saka sanar kiyayyarsa a zuciyarmu ne kawai kuma ya kan saka mu yi masa kallon wani azzalumin mutun tsabanin Uba da kowa wane yaya suke yi ma iyayensu. “Dacan ina cewa Haihuwar Noor ce ta kawo min kariyar arziki, ashe ke ma baki so na da arziki duba abun da yaron nan yayi mana daga zuwansa, kuma inda zata huta ne ba gidan wahala ba amman kin bi rana da safiya idan na fita kina hore mata kunne kar ta saurare shi idan ya zo ko? To ni zan kira shi zan bashi ita sadaka na ga uban da zai hana auren idan akwai wadda ya haifa min Noor din, gaba daya baki iya ba su tarbiya ta kwarai saboda baki san zafin haihuwa ba” Haka Mama ta mike tsaye tana kuka tana fadin. “Malam idan har ka aikata hakan ni kuwa zamana a gidanka ya kare, ba ta yadda zan zauna ka wulakanta ni kuma ka aurar da yata a inda za a wulakanta, babu yadda za'ayi wadda ka aura mata ya ga dararja ko taka, babu ta inda zata yi kima a gurinsa, mutumen da be bude baki yace yana sonta ba saboda ya siya maka gida zaka ce ka dauki Noor ka bashi sadaka bayan kuma yarinyar nan ba shi take so? Wannan abun kunyar har ina?” Baba ya dan matsa baya ya ce. “Ni kike fadawa Haka Hajara?” “Na fada maka Malam Naziru, ka yanka ni yau ka ci, na gaji da kai na gaji da halinka...” Baba ya nufi i da fitilarsa take ya duka ya dauka ya haska fuskar Mama da kyau. “Hajara yau ni kike fadawa haka? Idan kika sake fadar wata kalamar a gareni marar dadi to a bakin aurenki...” Wani irin karfi da kuzari da ban san Mama da shi ba, ta yi sufa ta isa gurin da Baba yake tsaye ta saka hannayenta biyu ta tureshi da karfi sai da ya fadi kasa. “Na aikata wanda ya fi wannan ka kashe ni yau karka bar ni na kwana da rai... Tun da na aureka ban huta, yara har sun girma su ba su huta ba ni ban huta ba, cin mutunci babu kalar wadda baka min ba, to na gaji aure kuma na hakura da shi na fi sha'awar na mutu a haka” Ni da Hana muka nufi Mama muka rike ta da karfi muka kuka domin ba halinta ba ne, macen dake tsoron daga kai ma ta kalli Baba yau ita ce ta saka hannu ta ture shi a kasa. “Kalu Innalillahi.... Wa'Inna..... Ilaihirraji'un.... Hajara... Ba ke bace, Wallahi ba ke bace..” Yana fada yana girgiza kai, sai kuma aka yi sa'a nepa ta dawo a lokacin, daga ni har Hana muna kallon yadda yake yunkurin tashi ya kasa domin ba karamar faduwa yayi ba. Na saki Mama na nufi inda Baba yake na rika shi ya mike tsaye sai dai be tsaya daidai ba hannunsa daya yana rike da kunkurunsa, na nufi inda fitilarsa take na dauko na kawo masa sai ya karba ya nufi kofar gidan ya fIce ba tare da ya sake cewa komai ba. Ni kuma na gurin ina jin kamar an dora wano nauyi a kai saboda na zama silar fadan iyayena a yau ma, gashi an doki Mama kuma Baba yayi rauni. Na dade a haka ina hawaye sannan na nufi kofar dakin Mama na zauna na fara rusa kuka kamar ba ni ba, Mama da kanwata Hana kuma suna cikin daki suna na su. Shigowar Baba ne ya saka na tashi tsaye da sauri kuma na yi hanzarin yanke kukan da nake ina kallonsa tare da wasu abokansa biyu. “Ina take?” Suka tambaya bayan sun yi sallamar da ban samu amsa musu ba saboda kuka da nake ta kokarin ganin na ci karfinsa. “Tana can ciki ko ta fita Noor?” Baba ya fada yana tsaya daga can baya su kuma suka shigo cikin gidan suka isa gurin kofar Musamman ma Malam Isuhu da ya kasance Malamin Addini. “To wai magana suka yi ne ko me? Ke Noor Mamanku tana ina ne?” Na nuna masa kofar daki. Baba kuma ya ce. “Ai na san ba ita bace yadda ta tureni din nan ba karfinta ba ne, kuma duk zamana da ita bata taba nuna min yatsa ba, amman yau tureni ta yi a gaban yara, yanzu haka bana iya tsayawa daidai, ai ba ita ba ce shiyasa ban sake ce mata komai ba, na fita na kira ku ayi abun da ya dace idan karatu za a mata ko addu'a sai ayi” Baba na rufe baki Mama ta taso ta fito daga dakin a fusace. “Babu wasu aljannu Malam Isuhu kar ya wahalar da ku, azaba ce da zaman auren na ukuba na ganshi a gidan har na gaji, yace idan na sake yi masa masifa a bakin aurena to na yi aure ya kare, ka aurawa Noor wadda duk ranka yake so amma zamana a gidanka ya kare, yara ba kanana ba ne da wayonsu ranar da duk suka so ganina sai su tararda ni inda nake” Malam Umar da Malam Isuhu suka juya suna kallon Baba cike da takaici da mamaki. “To wai miye silar wannan abun ne?” Baba ya nuno ni da fitila ya karaso cikin gidan yana kashe min ido. “Ka ga yar iskar yarinyar da ta assasa komai nan, ita ce silar komai ita ta lalata lamarin nan” Mama ta shiga tsakani ta tare ni. “Babu ruwan Noor a ciki, ni ka saba yi da ni ka yi da ni, yarinyar da abinci ma ya gagareta ci saboda mugun bakin halinka ita kake dorawa laifi, daman kullum cewa kake saboda na haifo maka ita rayuwarka take cikin matsala, saboda baka yarda da kaddara ba” A take masifar ta koma gurin Mama ya koma yana haskata da fitila yana tafiya a karkace ka ganinsa ka san kunkurunsa ya bugu. “Toh... Wai da kike wannan hakilon kina hauka kin isa ki hana ni aikata abun da na yi niya ne? Ai daman na fada miki idan kika sake magana a bakin aurenki to ki je na sake ki saki uku Hajara na gaji da ke na gaji da halinki, kije kya gani Noor kuma sai na aura mata yaron nan mai mutunci mai karamci sai dai ki hadi zuciya ki mutu, ita kuma idan ta haihu ta bijire min na gani...” Ban san lokacin da na dora hannu a kai na kwala ihu ba, domin na san miye saki na kuma san abun da saki uku yake nufi babu sauran zama a tsakanin iyayena kenan. Kuma duk ni ce sila. Malam isuhu ya rufe Baba da fada ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba, Malam Umar ma fadan yake yana Allah wadai da abun da Baba ya aikata a gabansu. Hana kuma ta shiga zubewa kasa tana tashi tana ihu. “Mun shiga uku mun lalace, Mama idan kika tafi mun shiga uku Innalillahi...” Na yi zaton Mama zata tausaya mana ko ta tausaya ma kanta amman ban ga alamar hakan a tare da ita ba, domin babu hawaye ko daya a idonta. Sai ma juyawa da ta yi ta shiga dakin ta fara hada kayanta. Malam Umar yana bata hakuri sai abokinsa da suka zo tare wato Malam Isuhu ya ce. “Hakuri me zata yi lamari ya lalace ya sake ta har saki uku? ABu dai kamar wadda aka jefa, baka dubi yaranka ba baka kalli kai kanka ba ka saki mace da girma ya fara kama ku a tare, har ina aka taba haka?” Baba ya fara kokarin kare kansa. “Baka san halin matar nan ba, Wallahi hakuri kawai nake da ita, yanzu ai sai ta koma can ta zauna cikin dangi ta ji idan akwai mai iya daukar abun da nake dauka, wulakanci take min kala kala duk ita ce silar lalacewar yarinyar nan Noor, ga bakinciki kamar ba mijinta ba, bata kaunar wani abun farinciki ya same ni, na gaji....” Takaici ya saka Malam Isuhu ficewa daga gidan, Mal Umar ne kadai ya tsaya ya fitar da Baba yana masa fada abun da yake be kamata ba. Na taka na isa cikin dakin na tsaya ina kallonta. “Mama tafiya zaki yi?” “To zama zan yi? Auren ubanku har aure ne? Ku dai da yake ubanku dole ku yi hakuri ku zauna a haka amman ni yanzu kam Allah ya sama min yanci, kuma kin fi kowa zama sakarya wawuya a gidan nan, idan zaki canja hali ki canja idan kuma ba zaki canja ba, to zaki sha wahala rayuwa ba yanzu ba har nan gaba” Na matsa baya na jingina jikin kofa ina kallon Mama har ta gama hada kayanta. “Kar wadda ya bini yana min ihu kuma kar wadda ya sake min kuka, kukan be hana ni tafiya, kuma ni da mahaifinku zama ya kare har a bada....!” Haka ta saka kai ta fice a fusace ko kadan kuka be ziyarci idon Mama ba, ni yau sai ta canja min ma kamar ba ita ba. A dakin muka zauna na tsawon lokaci muna kuka ni da Hana dake ta dora min laifi. “Sai da na ce kar ki fita amman baki ji ba, gashi nan kin yi sanadin da Mama ta tafi, jindadi da sanyi da muke ji ta bangarenta kin yi sanadin da muka rasa shi, kuma duk saboda Zafeer din nan ne, kamar kanki farau soyayya, yanzu kuma sauran ki yi sanadin da Baba zai tsine miki sai kiji sanyi, kullum ke kike janyo mana matsala a gidan nan kullum da ke ake kuka...” “Babu wadda zai sake kuka da ni Hana ba zan sake aikata abun da wani zai yi kuka da ni ba” Na tashi ina jin jikin babu karfi, gurin da Yaya yayi min wacan dukan yana taso min da ciwo. Na koma dakinmu na kwanta hankali be kara tashi ba sai da na ji shigowar Yaya Nabil domin na san ba zai min da sauki ba, a take na tashi zaune na zubawa kofar dakin ido ina jiran shigowarsa. Shiru shiru ban ji ya shigo ba, hakan ya saka na tashi tsaye na isa gurin kofar sai na hango shi zaune bakin kofar Mama rike da yar leda ya kifa kai da guiwa a kasa... *** **** *** GAM..... ya rufe motar ya saka key din a aljihunsa sannan ya fara waigewaige inda zai samu yaron da zai aika. Daga karshe sai ya nufi kofar gidan ya kwankwasa yaja baya ya tsaya yana kallon agogon hannunsa da ya nuna karfe goma sha daya da rabi. Nabil ya fito yana murza ido da alama a lokacin ne ya farka daga bachi. “Nabil kana ciki...” Sanin cewar abokin ogansa ya saka Nabil ya mika masa hannu da sauri suka gaisa. “Ina Baba fa yana ciki?” “Aa magana zaka yi da shi? Allah yasa ba wata matsalar bace?” “Aa babu wata matsala na zo ne kawai na yi magana da mahaifinka?” “A game da ni ne? Ko oga ya kore ni ne? Saboda Noor ta ari wayata ta yi masa maganganu marasa dadi” Hafiz ya girgiza kai. “Aa ba haka ba ne, wannan abun ai be kai a koreka ba, ni kaina na san halin Noor a yanzu balle kuma shi Kareem da ya fi kowa fahimtar ta, ba mamaki ace baka sani ba ta ari wayarka ta kira ko?” Ya daga kansa da sauri. “Eh ba da sanina ba ne” “Ba matsalar ce ta kawo ni ba, wata maganar ce dai mai muhimmanci, kuma bana tunanin Kareem zai koreka gaskiya saboda ya san hanyar cin abinci ka a nan take, Kareem yana da kirki sosai fiye da yadda kake tunani, kuma yana da saukin kai amman be san ma na zo nan ba ” Nabil ya ji hankalinsa ya dan kwanta kadan, sai dai tashin hankali rashin mahaifiyarsu yana nan a cikin ransa. Ya juya zai koma cikin gidan. “Bari na sallamo maka shi” Hafiz yaja ya matsa baya ya jingina da motarsa yana kallon yanayin unguwar, ta dayan bangaren kuma yana jin bakinciki yadda Kareem ya watsa masa kasa a ido. Babu bata lokaci Baba ya fito yana gyara hula, ganin Hafiz ya saka shi murmushi ya karasa da kansa ya mikawa Hafiz hannu suka gaisa cikin girmamawa. “Yanzu ake tafe?” “Eh Wallahi wani abun ne ya kawo ni, na yi tunanin za a fi samunka da safe ne shiyasa na zo kamar yanzu...” “Maa Shaa Allah aiko na jidadin zuwanka, daman ina nemamka har ina shirin fadawa Nabil ya kira min kai” Hafiz yayi fuskar mamaki tare da murmushi a fuskarsa. “Ikon Allah toh Allah yasa lafiya dai?” Baba yayi dariya. “Lafiya kalau, sai alheri a game da Noor ne amman dai bari na fara jin abun da ke tafe da kai tukuna” “Aa Baba a sawun giwa ya take na rakumi, fada min na ji dalilin neman tukuna” Baba ya gyara tsayuwarsa ya jingina da motar Hafiz tare da sauke ajiyar zuciya. “Watooo ka san lamarin mace, ko da babba ce balle karama kamar Nooriyya, ni abun ma sai yayi min wani iri Wallahi, ina ce yaron nan yaje yayi muku tashin hankali jiya?” Hafiz ya daga kai sama. “Eh haka ne, shi ne ma dalilin zuwa na bada hakuri kuma na bada shawara....” “Toh ai saboda kai ne yaje yayi wannan tashin hankalin” “Saboda ni kuma Baba?” “Kwarai kuwa, ai yarinya buga kafa ta yi a kasa tace kai take so, saboda na yi masa maganar idan be shirya ba to fa ya kauce saboda ina son na aurar da ita, shi ne ya zo yana rokonta yana rokona sai na sake zaunar da su na fada musu dalilina na son aurar da ita, sai ya tashi yana zage zage kasan abun ka da marar tarbiya, ita kuma ta fusata tace ba zata ma sake kula shi ba, to in takaice maka da magana uwar ta saka ta a gaba da masifa tace to idan ta juya masa baya sai ta fitar da wadda take so, ita kuma tace kai take so...!” Da mugun mamaki Hafiz ya nuna kansa. “Ni kuma Baba? Ni ko dai abokina Kareem?” Baba yayi dariya kamar gaske. “Kai din dai, sanadin haka uwarta ta yi fushi yanzu haka bata cikin gidan ma, amman waka a bakin mai ita tafi dadi bari na kira maka ita Nooriya sai ka yi magana da ita ka ji” Kamin Hafiz yayi wani yunkuri Baba ya nufi cikin gidan ya shiga. Hafiz ya nuna kansa har lokacin mamaki yake. “Ni...? Baba dai ba fahimta da kyau ba” Ya furta yana kallon kofar gidan zuciyarsa na bugawa da karfi... ____________ Toh fa ana zaton wuta a makera.... Anya ana samun uba irin Baba Naziru kuwa? Auren Mama dai ya kare amman an bar baya da kura. Nikam na tambaye ku mana, Zafeer be baku tausayi ba? Hafiz na kokarin kulla alheri reshe na shirin juyewa da mujiya yaya kenan? Follow the KHADEEJA CANDY channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaNTEQTFXUuaypyV5O01 *Duk mai son ya rika samun Littafin TA KI ZAMAN AURE yayi following wannan Channel din mai suna KHADEEJA CANDY a nan zaku rika samu duka littafaina in Sha Allah* ✧✦ 𝗧𝗔 Ƙ𝗜 𝗭𝗔𝗠𝗔𝗡 𝗔𝗨𝗥𝗘 ✦✧ 𝗕𝘆 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆 TALLA 👇👇👇 https://chat.whatsapp.com/DUwtFhhxfsS4zLHhxb28Wo About us *Legit contacts *Verified address including shop address and social media handles *Wholesale price *Group support *Group buying if you can't afford moq *Connect with supplies from Yaba, trade fair, Lagos island, balugon, e t c just for 2k👌 *Chapter 15* Ni da Hana kuka muka sha har muka gode Allah, ni dai sai tunanin ya zame min biyu tafiyar Mama da kuma Zafeer, tsammanin da nake Yaya Nabil yayi min fada ko duka ko ya min wata maganar babu ko daya, haka muka kwana cikin bakinciki da kuka. Baba be shigo ba sai da safe, a lokacin ragowar karfin jikin ma ya tafi ya bar ni, zazzabi kuma ya rufe ni har bana iya daga ido da kyau, ina jin lokacin da Baba ya shigo ya bawa Hana kudi wai ta siyo kunu, ta tashi ya fita bata jima ba ta dawo da kofin kokon ta aje a nan dakin ta nemi guri ta zauna ta yi tagumi, duk irin yadda take kaunar makaranta da rashin son wasa da karatun da take a yau ban ga tana shirin tafiya makarantar ba. Ina jin motsin fitowar Ya Nabil amman be cewa Baba uffan ba ya koma ciki, ba kamar yadda yake gaishe shi da safe idan ya ganshi ba, ni ma da na saba lekawa na gaishe shi a yau sai na ji bana bukatar ganin fuskarsa ko yi masa magana. Muna zaune dakin kamar wadanda aka yi ma mutuwa har wajen karfe goma sha daya, sannan Yaya ya sake fitowa yana wanke baki wato brush muka ji an buga kofar gidan, gabana ya fadi wata zuciyar na raya min cewar Zafeer ne ko wasani nasa. Sai da Yaya ya gama wanke bakin sannan leka waje, ya dan dauki lokaci sai dai ba sosai ba ya dawo cikin gidan ina hange lokacin da ya shiga dakin da Baba yake wato dakin Mama, sai na ga hango Baba ya fito da sauri ya fita. Wata zuciyar sai ta raya min cewar wani ne daga familyn Mama wata kila ya biyo sawu ya ji abun da ya faru. Sai dai yadda Baba ya dawo ya shigo dakinmu da kuzarinsa ya katse hanzarina. “Ina... Nooriyya...” Na tashi zaune jiki babu karfi. “Taso ga Alhaji nan ya zo” Na tashi tsaye ina jin kamar ba zan iya tsayi ba, ba kuma dan na san wane alhajin yake magana a kai ba. “Saka Hijabinki mana” Na juya na dauko hijabin na saka na bi bayansa, sai da muka fita waje sannan Baba ya tsayar da ni ya ce. “Ke saurara kar kije ki yi hauka, kin ga dai mutumen nan mai mutumci ne, kuma yayi mana karamci yadda ya dace, zuwan da yayi yanzu yace min ya zo da magana ne, kuma na fahimci maganarsa ta neman aurenki ne, ban riga na bashi ba, amman dai na fada masa ke ma kina maraba da hakan, karki kunyata ni Noor, Allah ya ba mu wannan damar ya ba mu wannan ikon na zabawa yarinyar mijin da zai dace da ita, kuma ni ubanki ne ba zan zaba miki abin da zai cutar da ke ba, dan haka nake son na baki umarni ba shawara ba, duk abun da ya tambaye ki ki amsa da eh karki karyata mahaifinki karki saka kimata ta zube a idonsa, ki tafi a natse ku yi magana ta hankali idan kika dawo zamu yi magana ta fahimtar juna kin ji ko?” Na daga masa kai ba dan na fahimci duka yaren da yake karanta min ba, ina mamakin yadda ya kwantar da murya yana min magana kamar ba shi ba, abun da tun da na zo duniya be taba min ba, na bude ido ne da tsawarsa da duka ta tsana da fargabar fadan yau dabam gobe dabam. Na fara takawa ina ganin hanyar tana rabe min na isa gurin kofar na fita daga kan da zan yi na kalli dama da ni sai na hango Zafeer a tsaye nesa da kofar gidanmu ya rumgume hannayensa yana kallona. Na dauke kaina na nufi gurin da Abokin Kareem yake a zatona Kareem din yana cikin motar ne. Na karasa gurin na tsaya na rumgume hannuna ina jin hawaye na bin fuskata. “Noor..” Na ji ya kira sunana, na kasa amsawa kuma na kasa daga kai na kalleshi. “Noor magana ce na zo da ita kuma na ga baki cikin yanayin da zamu yi maganar, amman zaki iya komawa ciki zan dawo anjima” Na girgiza masa kai domin na san komawa ta ciki zai iya zama laifi. “Noor akwai wata matsala ne?” Na yi shiru, sai ya gyara tsayuwarsa. “Please ki shiga ciki zan dawo anjima” Kamar ina jira sai na juya da sauri na dawo cikin gidan ina jin kamar ana turani. Ban karasa dakinmu ba juri ya dibeni na fadi a tsakar gidan sai ga Baba da gudu ya zo ya kamani. “Baki ji ciwo ba dai ko?” Na dubeshi ina mamakin haka ko wane uba yake ko kuma dai nawa ne a haka? Na daga mishi kai sannan na mike tsaye shi ya rika ni ya saka ni a dakinmu sannan ya kalli Hama dake zaune ido a kumbure ya ce. “Ke yau baki zuwa makaranta ne?” “Ina zuwa” Ta amsa sannan ya fice ita kuma ta tashi ta fara shirin tafiya makaranta a lokacin da na san kamin ta isa ta yi latti sosai. A tare suka fice da Yaya aka bar ni kadai a gidan sai damuwata da kunci. Baba ne ya sake dawowa dakin ya same ni a kwance. “Noor Allah yasa ba wata maganar kika fadawa Alhajin nan ba, na ga yayi saurin tafiya kuma kin dawo cikin gida” Na daga kai na kalleshi. “Ba mu yi magana ba Baba, yace zai dawo anjima ne” “Tom tom tom shikenan” Ya juya ya fita daga dakin be fita gidan ba sai bayan sallah azahar, a haukace na dauki Koko da Hana ta siyo na sha saboda wani yunkuri na amai da nake saboda yunwa har ina jin numfashina kamar zai dauke. Daker na iya tattalawa na fita na yi alwala na dawo na yi sallar a zaune saboda ciwon da cikina yake yi. A gurin na zube ban sake motsawa ba sai da aka yi sallah la'asar, ita ma dai haka na yi ta cikin karfin hali, ina jin kadaici da kewa domin ni kadai ce gidan, ba mamaki Hana ta wuce gurin Mama domin ya isa ace ta dawo daga makaranta tun karfe 2pm, Yaya ma be dawo ba balle kuma Baba da be fita ba sai azahar. Yammancin La'asar na ji an buga kofar gidan har sau biyu, ban fita ba ban kuma tambaye waye ba domin babu kuzari ko muryar aikata hakan a gareni yanzu. Har sai da yaron makota ya shigo ya ce wai ana sallama da Noor inji Kareem da abokinsa, shi ma dai ban amsa masa ba amman na tashi sanye da Hijabin dake jikina ina dukuduku na fita dakin na saka talkamina na isa zaune gidan, sai na tsaya daga cikin zauren har sai da na dan huta sannan na rike gambun karfen na leka waje. Kareem da ya bawa kofar gidanmu baya ya juyo ya kalleni. Abokinsa kuma dake zaune a motar da gambunta yake bude ya fito daga motar, sai na ja baya na koma cikin zaune na duka kana kallona ka san a wahale na ke. “Noor...” Cewar Kareem da ya fara shigowa zaure yana kallona, shi ma sai na duka daidai tsayina damuwar da tabbatar ta munafurci ce tana shimfide a fuskarsa. “Noor...” Ya sake kirana, muna hada ido sai na ji wani kuka mai karfi ya zo min a take na fasa kuka har ina sarkewa. “Subhanallahi me ya faru Noor? Kin rame kuma kuka kike yi akwai wata matsala ne?” Ni dai ban san ya aka yi mutumen da nake fushi da shi ya samu sa'ata ba har na bude baki ina fada masa damuwata. “Baba ya saki Mama jiya, Hana tun da ta tafi makaranta bata dawo ba, Yaya be dawo ba, ni kadai aka bari a gidan, bana ina cin abinci jikina babu karfi kuma ina ganin jiri, Baba kuma yace ba zai aura min Zafeer ba, kuma Zafeer na san ba zai yafe min ba...” Haka na jera masa komai tsab ina kuka sai ya matso kamar zai taba ni kuma ba taba din ba, sai ajiyar zuciya da ya sauke ya daga kai ya kalli abokinsa dake tsaye kamin ya sake dubana. “Saboda ke ne Baba ya samu matsala da Mama? Yanzu ina Mama take?” Na watsa masa wani mugun kallo ina jin kamar na shake wuyansa. “Ban san a ina Mama ta tafi ba, kila gidansu gurin Yayarta saboda saki uku Baba yayi mata, amman duk saboda kai ne komai ya faru, kai ka lalata komai Kareem, kai ne kasa Baba ya juya ma Zafeer baya, kuma saboda kai aka saki Mama jiya, kuma ka saka aka kama Zafeer...” Ya matsa baya da sauri ya mike tsaye ya juya zai fice daga zaure. “Kareem...” Na kira sunansa cikin kuka sai juyo ya kalleni. “Na tsane ka...! Da na san haduwa ta da kai haka zai zame min matsala da ban yarda na hadu da kai ba, kai ba mutumen kirki ba ne, yanzu na gane me yasa matarka bata sonka, kai mai son kai ne i hate you...” Murmushi na gani a fuskarsa a madadin bacin rai, yana kallona yace. “Kin jahilci waye ni Noor, na zo miki a baibai ne, kuma ni ban shiga tsakaninki da masoyinki ba, ni bana shiga tsakanin masoya na san yadda abun yake, a gurin ma ni da nake babba balle kuma ke, da wannan nake miki addu'a ina rokon Allah idan aurenki da Zafeer din alheri ne, Allah ya tabbatar kuma ki fada masa ya zo ya same ni zan masa duk wani taimako da ya dace har ya aureki kuma saboda ke zan yi, domin rayuwarki abar tausayi ce...” Ya juya ya fice ya daga zauren sai ya rage daga ni sai abokinsa, sai da na ji karar rufe mota sannan abokinsa ya kalleni ya ce. “Noor be kamata ki yi haka ba, kin ga na daya dai Kareem ya girme ki, ba tsararki ba ne, na biyu kuma shi babban mutum ne fiye da yadda kike tsammani, be kamata ki rika fada masa magana anyhow ba, kuma abokina mutumen kirki ne, shiyasa be so zuwa nan ba saboda kina dora masa laifi ni na takura masa da zuwa nan din kuma kin ga ya fita ba cikin dadin rai ba” “Ba ruwana na da mukaminsa ba ruwana da shekarunsa kawai dai bana sonsa karka sake zuwa da shi” “Tom” Ya amsa sannan shi ma ya fice sai kuma na fashe da sabon kuka. KAREEM POV. Ya ciro wayarsa ya lalabo Number Nabil ya kirashi. “Hello ranka ya dade” “Kana lafiya?” “Lafiya kalau oga” “Naje aiki yau?” Ya dan yi shiru for seconds sannan ya ce. “Aa ranka ya dade shekaranjiya nan Noor ta dauki wayata ta kiraka ta yi maka rashin mutunci ban sani ba, sai da na dawo Mama take fada min abun da ya faru, na yi tunanin ko akwai wata matsala ne ko ka yi fushi” Kareem ya shafa fuskarsa. “Ina tunanin ko ku da kuke yan'uwanta ba ku fini sanin halin Noor ba a yanzu, ita ma ai ba laifi ta yi ba balle har ya shafe ka, ka cigaba da zuwa aiki, yanzu kana ina?” “Ina gurin abokaina” “Noor din tana lafiya?” “Ban sani ba na fito tun safe ban koma ba” “Toh ka koma ka dubata sai ka dawo gurin aiki” “Toh ranka ya dade Allah ya saka da alheri” “Ka rika mata wani abu kamin ka shiga gidan, ba mamaki ma kila bata ci komai ba” “Toh ranka ya dade Allah ya kara sutura” Kareem ya sauke wayar ba tare da ya amsa ba, kuma ba tare da ya kalli Hafiz ba ya ce. “Yaron nan ma yana karatu wai? Ni na manta kamar ya taba fada min yana yi ne ko be yi na manta dai, amman ya kamata ace yana yi saboda rayuwar gidansu abar tausayi ce musamman mahaifiyar da kuma kanensa” Hafiz ya rage gudun motar ya faka gefe ya kalli Kareem. “Me yasa ka kira shi?” Da mamaki Kareem din ma ya kalleshi. “Baka ga halin da muka baro yar ficikar yarinyar nan ba kuma ita kadai cikin gida? Idan tana bukatar wani abu ai zata fada masa kuma zai dubata ko?” Hafiz yayi murmushi. “Ko yargwangwani ce ka damu da yarinyar nan Kareem, da na same ka a office na fada maka Noor tana cikin damuwa kuma tana bukatar ganinka office din ka bari ka shigo motata ka biyo ka dubata a yanzu, kuma Wallahi dazun na tambayi yarinyar akwai wani matsala ne bata min magana ba amman kai tana ganinka sai ta fashe da kuka ta bude maka cikinta” Kareem yaja tsaki. “Kai dai baka da zuciya Wallahi, ni ban yi zaton zaka sake min maganar yarinyar nan ba, yanzu gashi kasa na zo na ji bakar magana kawai kuma a gabanka ta nanata wadda take so” Hafiz ya sauke numfashi. “Ni ma kaina ban yi zaton zan sake maka maganar ba, amman zuwana dazun da niyar na fadawa mahaifinta gaskiyar cewar ba sonta kake ba sai ya tare ni da wani labari na dabam wai Noor ta fada masa tana so na” Kareem ya kalleshi ya sake kallonsa ya kasa cewa komai. “Abun da ban gama gamsuwa a yanzu shi ne, ita Noor din da gaske ta fadi hakan ko kuma dai mahaifinta ne ya fada saboda wani tunani nasa na dabam?” Kareem ya dantse hakwaransa yana magana da karfi “Ko dai minene kai ka janyo Hafiz... Mahaifinta be yi tunanin rabata da wadda take so sai da ka shiga rayuwar yarinyar nan, kuma yanzu kana jin yadda iyayenta suka rabo duk saboda kai ne” “You're just blaming me Kareem, ni fa duk abun da nake yi saboda kai nake yi, bana jindadin yadda kake mu'alama da Safeena, kuma bana jindadin irin zamantakewar auren da kake yi, ina kokarin ganin ka samu farinciki ne ka koma kamar yadda kake a da, ina hango maka farinciki a auren yarinyar nan ita ma kuma ina hango nata farincikin a tare da kai, ubanta be tantance waye mai sonta ba kawai ya fada min tana so na kuma ni na san abu ne mai wahala Noor ta amsa haka, idan mu mutanen banza ne haka zai dauki yarinyar ya ba mu fa, baka kula da yanayinsa ba? Yarinyar nan abar tausayi ce matuka” “Ni rayuwata ba abar tausayi ba ce? Na auri wadda bata so na yanzu kuma na sake auren wadda bata so na? Mahaukacin ina ne kai?” “Akwai banbanci, Yusura baka sonta bata sonka, amman ita Noor kana sonta kuma ita zaka iya koya mata sonka cikin sauki, shi wadda take ikirarin tana sonsa hauka kawai take, wannan yaron ba zai iya rike ta ba, baka ga yadda yake mana hauka ba? Sabo ne kawai yake wahalar da ita kai ma tana sabowa da kai zata manta da shi, kuma ni a abun na lura halin da ake ciki a yanzu idan baka aureta ba mahaifinta ba zai bari ta auri yaron ba, kuma ba zai barta ta samu salama ba, saboda kwadayaye ne” Kareem ya daga masa hannu. “Hafiz ba zan auri yarinyar nan ba, idan kana tausayinta ko kana tunanin rayuwarta kai ka aureta mana sai ka koya mata sonka ba kace abu ne mai sauki ba, to ka gwada mana, kai ma ai kana bukatar kara aure matarka daya kuma kullum aiki take zuwa bata zama gida, kana bukatar mai kula maka da yara” Hafiz ya nuna kansa. “Ni kake fadawa haka Kareem?” “Akwai illa a fada maka haka ne?” Hafiz yayi murmushi. “Tunanin kake kamar cutar da zan yi saboda ina kokarin ganin abubuwanka sun saitu? Zan baka mamaki kuma sai ka yi nadamar wannan maganar da ka fada min, and I'm sure you Wallahi Tsumma Tallahi sai na AURI NOOR, daman ka ce ni na bata komai to zan gyara” Hafiz ya danna burgi ya ja motar da karfi ya fara tuki, Kareem be sake ce masa komai ba shi ma kuma be sake cewa Kareem din komai ba har ya isa gidansa ya faka a harabar gidan, Kareem ya bude motar ya fita Hafiz kuma yayi reverse ya juya ya fice daga gidan. Kareem be samu Yusura a gidan ba amman ya samu note a center table rubuce cewar ta tafi dubiya tare da yara. A gurin ya zauna ya rike kansa yana jin kamar kan yana ciwo kuma kamar ba ciwon ba, ya rasa me ke masa dadi. Kamin ya mike tsaye ya nufi upstairs. Yana shiga dakinsa ya ciro wayarsa ya kira mahaifiyarsa da liyinta na waje, ya kuma yi sa'a wayar tana hannunta domin ba ko da yaushe take daukar waya ba. “Sallamu Alaikum” “Wa'alaikusalam Momma na kina lafiya?” “Alhamdullahi ya gidan ya yaran?” “Kowa lafiya kalau Momy ban da danki” “Subhanallahi me ya samu ďana nawa?” “Momy baki kusa kuma kin san babu mai yi ma Kareem gata sai ke, na yi marmarinki Momy” “Babban mai maka gata shi ne Allah wadda ko bana raye zai kula da kai, kuma yana nan kusa da kai, ni na zo a ta biyu ne idan kuma bana kusa matarka Yusura tana nan dan haka kana da gata ta ko'ina” Ya sauke ajiyar zuciya. “Momy yaushe zaki dawo? Ina tunanin daukar hutu na zo na dubaki ko na sati ne” “Aa cikin satin nan zamu dawo da yardar Allah, jiki yayi sauki sosai matarka ma ta matsa na dawo zamu dawo babu jimawa” Yayi shiru kamar ba zai ce komai ba. “Amman jikin yayi sauki ko?” “Sosai sai ka yi mamaki idan ka gani” “Alhamdullahi haka nake so, zan kira ki video call anjima” “Na turawa matarka video ai tana ta murna ta ga jikina yayi kyau, ta ji dadi bata nuna maka ba” Samun kasa yayi da kasa amsawa har na dakika biyar. “Ta fada min, amman ta manta bata nuna min video ba” “Ta manta kam, Yusura yarinya ce mai kirki Kareem, ka rike ta amana dan Allah yarinyar nan bata da uwa bata da uba sai ni, sai kuma kai da kake matsayin mijinta a yanzu, tana so na tana girmamani kuma tana da hankali da natsuwa, abu ne mai wahala a samu mace kamarta a wannan zamani, ba zaka gane hakan sai ranar da ka kara aure ko ka rabu da ita bana fatan hakan amman duk ranar da ka rasa Yusura ka rasa mata ta gari” “Haka ne, ai na fi kowa sanin halinta Momy” “Na san kai ma kana da hakuri amman dai ta fika gashi tun da aka yi aurenku ba a taba jin kanku ba, hakan yana saka ni farinciki kuma yana kwantar min da hankali” “Hankalinki zai cigaba da kwanciya har abada Momy indai aurena da Yusura ne ba zaki taba jin wata matsala ba har abada” “Allah ya muku albarka ya raya abun da kuka samu” “Ameen Momy Allah ya kara miki lafiya kuma ya dawo da ke lafiya” “Ameen Ameen” Yayi mata sallama ya sauke wayar, ya dade zaune a dakin sannan ya fito ya sauko kasa dinning ya nufa ya bude abincin dake gurin kamshin ya daki hancinsa sai dai hakan be be saka shi sha'awar ci ba domin ba kasafai yake son cin abun da Yusura ta girka ba, ba dan bata iya girkin ba sai dan babu shaukin yin duk wani abu da ya shafe ta. Kitchen ya nufa kamin ya shiga yaransa suka turo kofar falon suka shigo da gudunsu, ya juyo yana kallonsu da murmushi a fuskarsa. “Kun dawo?” “Yes Daddy yanzu ka dawo?” Babbar ta tambaya sai ya daga mata kai ta cire hijab dinta ta aje ta nufi gun da yake tsaye. “Zan sha ruwa Daddy yau na gaji da yawa na yi gudu a Islamiya” Ya shiga kitchen din ya debo ruwan ya mika mata. Bayan ta sha ta kalleshi. “Ina Momy?” “ina momyn kuma? ba tare kuka je duniya ba?” “Aa mu muna islamiya ai nan muka barta gida” Yayi fuskar mamaki yana jin gabansa na faduwa. “Ba tare kuka fita ba?” “Aa” Ta mika masa kofin sai ya karba ya aje ya fice kitchen din da sauri, gurin da ta aje masa takardar ya nufa ya dauka ya sake karanta abun da ya rubuta. “Na tafi duniya tare da yara” Ya nufi sama rike da takardar ya shiga dakinsa ya dauki wayarsa, sai da yayi ba searching sannan ya iya kama sunanta domin rabon da ya kirata a waya ma har ta manta, kiranta yayi tana dagawa ya ce “Kina?” “Wane irin tambaya ne hak...” “Kina ina...?” Ya daka mata tsawa. “Ina gurin duniya” “Umarni ne ko kuma?” “Umarni ni” Ya kashe wayar, ya sauka falon yana tunani kala kala gaba daya sai ya ji ya kasa natsuwa har sai da ta turo kofar falon ta shigo a lokacin yaransa suna bayan gidan gurin da lilinsu yake suna wasa. “Ina kika je?” Ta cire mayafinta ba tare da ta kalleshi ba ta amsa. “Duniya” “Kin ce kin tafi da yara ga yara sun dawo ba tare da ke ba, waye ba lafiya? Duniyar wa kika je?” “Kawata ce Zeenatu” Ya mike tsaye ya fuska a daure. “Karki sake fita ba tare da yaran nan ba, kuma karki sake fita ba tare da na baki izini ba” Ya wuce zai haura stairs sai ta bishi da kallo. “Na saba idan zan fita rubutu nake na aje maka, idan zaka fita kai ma haka kake min? Me yasa aka samu canji yau? Zargina kake yi?” Ya tsaya cak sai dai be juyo ba. “Wani abun kake aikatawa da kake ganin kai ma za'a iya aikatawa matarka? Duk yadda duniya ta lalace har gobe akwai na kwarai Wallahi, ni ba zan iya zina ba ko babu aure balle da aure da Yaya, idan ma kana tarayya da matar aure, budurwa ko bazawara wannan kai ya shafa, ni dai ba za'ayi da ni ba, ubana be yi da yar wani ba ba zan aikata ba Wallahi, amman kai ka kuka da yarka kuma Allah ya isa zargin da kake min...” Ta wuce shi ta haura stairs din ta shige dakinta ta rufe kofar da karfi. Shi kuma ya juyo ya sauko yana jin babu dadi wani abu ne ya same shi a yau da be saba samunsa ba, be taba zargin matarsa ba ko sau daya amman yau ya ji rashin natsuwar a fitarta gashi har ta ja masa Allah ya isa. Falon ya koma ya zauna ya rufe ido, yana tunanin wata kila da ba baya aikatawa da duk hakan be faru ba. Wayarsa ya ciro ya kama number Safeena ya saka a blacklist sannan ya goge number yana kallon hoton yarsa dake lake a falon. NOOR POV. A zauren da suka tafi suka bar ni a nan Yaya ya shigo ya same ni, ina kuka sai ya rika ni ya shiga da ni cikin gidan ya tambaye ni lafiya. “Ba komai” “Ko dan an barki ke kadai?” Na daga mishi kai, sai ya tashi ya fita be dade ba ya dawo da fura irin wadda ake siyarwa a titi damammiya ya zuba min a kofi na sha ya debo min ruwa na sha. “Ina Hannatu?” “Bata dawo ba” Na amsa da muryar kuka. “Kila ta wuce gurin Mama, Baba kuma be dawo ba?” “Eh ni kadai aka bari” “Shi ne kika yi ta kuka ko? Ni ma oga ne ya kira ni yace na zo aiki kuma na dubaki” “Ina ka ganshi?” Na yi shiru bance komai ba, mintuna da ya kara be wuce talatin ba ya ce min zai tafi aiki ya fita ya bar ni. Ama daf da kiran Sallah magariba Zainab ta shigo gidanmu sanye da uniform dinta na islamiya, kamar da tsoro ta shigo dakinmu tana tambayar ina mama. “Bata nan” Ta saka Hannu a jakarta ta dauko takardar da miko min sannan ta tashi da sauri. “Bari na tafi kamin ta dawo kar tace ni nake kawo miki sako” Ni dai binta kawai na yi da ido har ta fice sannan na maida dubana gurin takardar gabana yana faduwa, na san mai aiken sakon ciki ne dai ban san me ya kunsa ba. Na dade ina kallon takardar cike da fargaba sannan na bude. “Abu dai kamar wasa Noor ina shirin rasa ki, Wallahi ina sonki Allah ya sani, duk wadda yake son ki be kai ni ba, kuma zasu bata miki lokaci ne kawai su ci amanarki su gudu su barki, za su lalata rayuwarki ne kawai Noor karki aminta da su, babu wadda zan iya dake ya jure sai ni, ni kadai ne mutumen da zai iya zama da ke a kowane hali na rayuwa, amman duk wadda zaki aura Noor sai dai ki je ki yi ki dawo ba zaki taba zaman aure ba matukar ba ni kika aura ba, babu wadda zai iya zama da ke sai ni, kuma ke din tawa ce har abada ba zan daina kaunarki ba Noor har abada, kin manta yadda muka tsara rayuwa? Zaman tare duk kin manta Noor, Amana ta ba zata barki ba, ba zaki taba zaman aure ba, ke je ki yi auren zan jira ki saki dawo, zaki gane kuskurenki Noor a lokacin da zaman auren zai gagareki, ba fata nake miki ba amman ni na san ba zaki taba iya zaman aure ba har abada...! Saboda na san wacece ke Noor, ba zan daina sonki ba, zan mutu da kaunarki Noor Ba zan taba son wata mace kamar ke ba, talauci yayi min illa, ke kuma zaman aure zai zame miki kaya kun ci amanata kuma amana ba zata barku ba, ban yi tunani zan baki umarni ki kauce ba, ban yi zaton zan miki magana ki juya min baya ba... Kin ba ni mamaki Noor... ” Na dunkule takardar a hannuna ina jin tausayin kaina da, gashi ba ni da wata hanya ta wanke kaina daga zargin da Zafeer yake min. Na kwanta a gurin ina kuka. Ban sake ganin kowa ba sai bayan sallah Isha'i da Baba ya dawo da ledar nama. Duk yadda bakina ya saba da kwadayi sai na kasa cin wani abun kirki sai kadan ka ci na bar sauran na shige dakinmu cikin hudu na kwanta har lokacin Yaya da Hana ba su dawo ba, daman Yaya ya saba yin dare a waje shi da Baba Hana ce dai rashin dawowarta ya dame ni domin na koma ni kadai a gidan. “Wato Hannatu ta zabi uwarta ko? Shi ne daga makarantar ta wuce gurin Hajara ko? To sai ta yi ta zama a can kar ma ta dawo gidan nan” Fada Baba yake sosai inda yake shiga ba nan yake fita ba, tafiyar Hana gurin Mama ta yi masa ciwo sosai. Ni dai ban ce uffan ba sai da yaro ya shigo yace wai ana sallama da Noor inji Hafiz. Sanin Hafiz din yana tare da Kareem ne ya saka na ji bana bukatar zuwa amman ban isa na yi hakan ba saboda Baba yana cikin gidan. “Je kace tana zuwa” Baba ya amsa masa ni kuma na tashi na dauki hijabina na saka na fito daga dakin Baba na haska min talkamina na saka na fita waje. Nesa kadan da kofar gidan na hango shi ganina ya saka shi fitowa daga motar da already tana bude ya rufe yana kallona. Ni kuma na karasa ina jiran na ga fitowar Kareem. “Sannu Noor” Ya fada sai na daga mishi kai ina kallon kasa cike da natsuwa. “Ba tare da Kareem na zo ba, kuma ba matsalar Kareem ce ta kawo ni ba, na zo ne mu yi wata maganar dake mai muhimmanci” “Ina jinka” Na fada a sanyaye. Sai da ya sauke ajiyar zuciya ya gyara tsayuwarsa sannan ya ce. “Dazun na so mu yi magana amman na lura kamar baki cikin yanayin da ya kamata na yi maganar” Sai kuma na ji shiru jikina ya bani kallona yake, ina daga kai sai na yi arba da idonsa a kaina. “Noor Baba ya fada min wata magana a dazun, ba zan ce ba haka ba ne amman abun ya ba ni mamaki” Gabana ya fadi. “Me ya ce maka?” Ya matsa kusa da ni kadan ya rage muryarsa. “Ya fada min wai ya tambaye ki fitar da miji sai kika ce ni kike so haka ne? Ko kuma dai Baba be fahimce ki ba ne? Ko kuma dai Kareem kike nufi Baba be fahimta ba yace ni” Kallonsa nake ina ta kokarin hada kalmonin da ban fahimci manufarsu ba, ta dayan bangaren kuma gargadin da Baba yayi min dazun da safe yana dawo min. “Noor ko ba haka ba ne?” Kiran sunana yake tare da tambayar da bam san taya zan amsa masa ita ba. Ba zan iya karyata Babana ba, bayan duk gargadin da yayi min, idan har na yi haka ban zan me zai biyo baya ni ma zai koreni kamar Mama ne ko kuma zai yi ta dukane ne yace babu ruwansa da ni. “Ban sani ba tukuna” Na fada da muryar kuka ina kai hannu na na taba zuciyata. “Hakan yana nufin ba gaskiya ba ne kenan?” Ya sake tambaya ta sai na amsa masa ina fashewa da kuka. “Gaskiya ne....” Na juyo na shigo cikin gidan da wani irin kuka mai karfi, a tsakar gidan na zube na rushe da kuka ina jin tsanar mahaifina fiye da kowa a duniyar nan. Taya zai yi min haka ta ina zan iya Zaman Aure da Hafiz wane irin abun kunya ne wannan? Baba babu ruwansa da damuwata babu ruwansa da wadda nake so, daman can Hafiz ne yake so na ba Kareem ba ko kuma dai dukansu wasa suke da hankalina ne? Ni kadai ce mai uba irin Baba ko ina da ta biyu..! “Lafiya wani abu ya faru?” Na daga kai na kalli Baba ina kuka. “Baba bana son Hafiz kai kace masa ina son shi? Ni Zafeer kawai nake so, ni idan ba Zafeer ba ko an min auren ba zan zauna ba, Baba bana son kowa sai Zafeer” Tsawa ya daka min sai da na zabura. “Rufe min baki, Wallahi sai kin auri wadda na zaba miki sai idan shi yace ya fasa, kuma idan kika yi sanadin da ya fasa aurenki sai na lahira ya fi jindadi” Yana rufe baki ya hau dukana. “Karki yi zaman auren idan an kaiki ki fito ki dawo gida ki zauna, daman ai haka uwarki take so haka kike so, ke kin fi son ki yi ta gantali a gari kin zama wawuya to mu zuba ni da ke, Wallahi ko zaki mutu sai kin auri Mutumen nan idan ba ki aure shi sai na tsine miki Noor, ki bi duniya ki lalace daman kin fi son lalatar kin sha'awar ki zama watsatsiya kowa yana miki kallon mahaukaci, ko da yake ba laifinki ba ne, laifin ne da ban zabo uwar da zata koyawa Yayana tarbiya ba, gashi ita Hannatu ta bar gidan ke kuma kina son saka min hawan jini ko? To ba ku isa ba, ai yara da dawo ana musu aure ko basa so amman basa musawa sai ke da babu albarka a tare ke...” Azabar dukan da yake min da hannu bata saka na gane kuskuren yi masa musu ba har sai da ua dauko maburkin Mama na ice yana duka na da shi, a take fara rokon gafararsa ina sosa jikina ta ko'ina ina jin kamar wuta yake watsa min a jiki. “Na bari Baba na bari, zan aure shi Wallahi zan aure shi Ina son shi ina kaunarsa Baba zan zauna dan Allah ka yi hakuri Baba na bari ba zan sake ba” Rawa jikina yake kamar mazari majina da hawaye sun hade min guri daya, numfashina na fita da karfi... __________________ A nan muka kawo karshen Book One na litfafin TA KI ZAMAN AURE, sai bayan Sallah idan mai kowa mai komai ya amince mana zamu dora a book two... A inda littafin zai amsa cikaken sunansa. Akwai tambayoyi da yawa da kuke bukatar amsoshinsun a tare da Noor da kuma Zafeer da Kareem da ma wasu a gaba. Anya fitar Mama a gidan Baba zai haifa da da mai ido kuwa? Wai ina labarin Safeena ne? Ta hakura ko tana kan bakarta? Kuna Ganin Yusura zata iya juyowa ta kalli Kareem da idon rahama? Shin Kareem zai iya jurewa Abokinsa ya auri Noor kuwa? Me. Zafeer yake nufi da cewar ba zata ta Zaman aure ba? Me yake Hana Noor zaman auren ne? Rashin dace da miji ne ko bakin iyeye ko kuma rashin Hali na gari? Ko kuma daga mahaifin ne? Akwai wani dunkullen sako a cikin Littafin da nake son isarwa idan Allah ya ara min lokaci kuma ya amince min. Allah yasa mu amfana. #KhadeejaCandy +2348036126660 Follow the KHADEEJA CANDY channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaNTEQTFXUuaypyV5O01 *Duk mai son ya rika samun Littafin TA KI ZAMAN AURE yayi following wannan Channel din mai suna KHADEEJA CANDY a nan zaku rika samu duka littafaina in Sha Allah* ✧✦ 𝗧𝗔 Ƙ𝗜 𝗭𝗔𝗠𝗔𝗡 𝗔𝗨𝗥𝗘 ✦✧ 𝗕𝘆 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆 WELCOME BACK... Fatan mun yi Sallah lafiya, Allah ya karbi ibadunmu. AMEEN. *Book 2 - Chapter 1* 6 -Month Later... @8:11am Yana tsaye rike da mug yana kallon harabar gidan aka wuce da motar yaransa zuwa makaranta. Sai da aka rufe gate din sannan ya juyo zai dawo wayarsa ta yi kara alamar shigowar sako. Hannunsa na hagu ya saka ya ciro wayar ya duba, sako ne aka turo da bakuwar number. “I Love You I love You Kareem Ina sonka sosai” Haka ya bi sakon yana karanta kalma bayan kalma sai kuma yayi saurin kiran number da sakon ya shigo masa ya kara a kunnensa ya juyo ya sauko daga entrance din... “Hello... Kareem...” Dakika biyu ce tsakanin amsawa da Hello da kuma kiran sunansa, sai ya lumshe ido ya matse bakinsa domin be ji muryar da yake zaton sakon ya zo daga gurinta ba. “Safeena What Now?” “Na yi marmarinka Kareem, na san idan na kira da line na zaka iya kin dagawa, ina cikin damuwa rashin saka a ido da na yi, ina sonka Kareem ka sani ina sonka sosai” Ya katse Kiran ya sauke wayar tare da ajiyar zuciya, sannan ya busar da iskar bakinsa. What he got himself into? Matar aure matar sunna ta tsaya tana fada masa yadda take kaunarsa, ya san ya cutar da Safeena na bin umarnin Momy ya auri Macen da ba ita zuciyarsa take ba, ya cutar da kansa kuma ya cutar da Safeena, gashi yanzu shi da ita sun fada cikin halaka. Ya shafa kansa sannan ya juyo ya nufo kofar falon ya tura ya shiga arba da yayi da Yusura tana mopping ya dada bacin ransa, domin ita ce macen da ta ruguza masa komai a rayuwarsa. Me yasa bata amsawa Mahaifiyarsa cewar ba zata iya zama da shi ba tana da wanda take so? Shi ba zai iya musawa Momy ba, amman ita zata iya fada mata bata sonsa da yanzu duk haka be faru ba, gashi suna da yara har biyu amman wani abu mai suna so be fara shiga tsakaninsu ba. “Breakfast dinka is ready” Ta fada masa ganin yadda ya tsaya a gurin yana kallonta fuska babu Annuri, ita kanta ba son take ya kalleta ba, yadda yake jin tsanarta haka take jin tsanarsa a zuciyarsa har ma ta fi shi. Ya dauke kai ya bar kofar a bude ya nufi stairs. Yana shiga dakinsa ya aje mug din ya aje wayarsa a saman gado ya cire tufafin jikinsa ya dauki bathrobe ya saka ya nufi bathroom kamin ya shiga wayarsa ta yi ringing. Juyowa yayi ya dawo ya dauki wayar ganin number mahaifin Hafiz ya saka shi zaunawa sannan ya amsa wayar cike da ladabi. “Hello Abbah” “Naam Kareem kana lafiya?” “Lafiya Kalau Abbah ya gida?” “Lafiya Kalau” Daga haka Abbah yayi shiru be sake cewa komai ba har sai da Kareem ya tambaya. “Abbah lafiya?” “Lafiya Amman ni ma ita na kira na ji, na ga duk hidimar auren nan da ake ba ka zo ba Kareem ko last week da aka kai lefen abokinka na yi zaton zan ga domin maza suka kai lefe amman ban ganka ba, ko da yake dai ya ba da izuri cewar aiki ya maka yawa amman ina fatan dai ba matsala kuka samu ba” Kareem yayi murmushi. “Haba dai Abbah ni da Hafiz ai mun zama yan'uwa dangantakarmu ta wuce abota ina kallon Hafiz a matsayin dan'uwa ne na jini ba aboki ba, babu wani abun da ya shiga tsakaninmu kuma babu abun da zai taba shiga tsakaninmu har abada” “Toh haka nake fatan ji, shi ma kuma haka ya fada min amman zuciya bata natsu ba sai shiyasa na kira da kaina” “Abbah kullum muna tare da Hafiz ma, kasan gurin zamanmu daya, indai ba ina aiki ba kullum muna tare da juna, babu wani abu da ikon Allah” “Tohm Allah ya muku albarka” “Ameen Abbah Sai anjima” Ya aje wayar sannan ya mike tsaye ya shiga bandakin. Ya dauke shi awa daya daga fitowa wanka zuwa shiryawa cikin manyan kaya kasancewar yau Jumma'a. Sai da ya dauki abubuwan bukatarsa sannan ya fito daga dakin ya sauko kasa ya fice daga falon yana zuba kamshi kamar shi ne angon. Motarsa ya nufa ya bude ya shiga ya murza key yayi warming din motar sannan ya kwanta ciki yayi relaxing yana murmushin da shi kadai ya san ko na minene. Can kuma ya dago ya ja motar yana danna horn Mai gadin ya bude masa Gate. A minti goma shabiyar ya isa kofar gidan mahaifinsa ya faka a harabar gidan da karin minti uku, ba yabo ba fallasa ya fito motar ya nufi kofar falon da zata sada shi da bangaren mahaifiyarsa. Gidanta gidane dake cike da jikokinta da na dangi domin kuwa ita mace ce mai tsananin son yara da yan'uwa, sai dai kasancewar safiya ce babu ko daya duk sun tafi makaranta. A falo ya sameta tana zaune ta dora kafafuwanta a karamin Center Table hannunta kuma rike da plate din dafaffen nama tana ci. Kusa da ita ya zauna yana fadin. “Momy ba zaki daina cinye cinye nan ba, mai surga fa baya wannan cinye cinye” Ta kalleshi tana murmushi. “Yanzu ma Khadija ta yi ta gaji ta tafi ta bar ni, so kuke na mutu da rama ai sai a zagi mahaifinku ma” Ya shafa kansa ya kai hannunsa ya dauki tissue ya dauki nama ya fara ci. “Momy saboda lafiyarki ake fa, kina fama da BP ga Suga mu lafiyarki muke so ba ciwo ba” “Ai ku likitocin nan haka kuke, idan mutum be cin dadi ku ce ya rika cin kaza da nama da kayan dadi, idan kuma yana ci ku ce za su saka masa ciwo ya daina, ni ba zan bi ba, ku bar ni na ci dadi mutuwa da wahala ba a musu wayo ai” Wannan karon dariya Kareem yayi yana dariya. “So yanzu laifi muke idan muna bawa mutum shawara akan lafiyarsa da irin abincin da ya kamata ace ya ci ko?” “Eh mana abun ai kamar da gayya kuke yi, ni ba wanda zai hana ni cin kayan dadi wani wai ina da suga” Ta sauke daukar wani naman ta kai bakinta, sai Kareem ya mika hannu kamar zai sake dauka ya ci ya fisge plate din ya mike tsaye ya koma nesa da ita ya zauna ya cigaba da cin naman da spoon din dake kai. Kallon mamaki take masa kamin ta hade rai daman ya saba yi mata haka idan ya tarar tana cin wani abun da yake da illa ga lafiyarta. “Kareem rainin nan fa ya fara yawa! Dawo min da plate dina” “Momy ba zan yarda cuta ta yi miki yawa ba, yanzu idan kika fara ciwo waye a wahala? Mu ne a tashin hankali mahaifina da kashe kudi” “Okay... Wato tashin hankalin da kashe kudin kake mahaifinka kake ji ba ciwon da nake ji ba ko?” Ya saka dariya yana auna naman a bakinsa daman be karya ba ya fito. “Toh Momy ban da neman rigima Fisabillilahi miye na saka kayan dadi a gaba kina ci, kuma idan kika yi rashin lafiya a dora mana laifi?” “Amman kai naman kake ci yanzu ai? Ka bar ni na ci kamin na tafi na bar muku duniyar” “Ba zaki tafi ba, zaki zauna tare da mu har sai mun riga ki tafiya, me aka girka miki da safen nan First Love?” “Ban sani ba, can gidanka baka ci abinci ba ka fito?” “Wallahi ban ci ba” “Saboda me?” Ya kalleta kamar mai tunani. “Saboda Me? Ra'ayi Momy sau nawa nake zuwa nan ina cin abinci” “Amman ba haka ake so ba kanen miji ya fi Miji kyau” “Toh ai Aryam be fi ni kyau ba balle Yusura ta fi sonsa da ni” Ya fada yayinda yake mikewa tsaye Momy ta girgiza kai tana murmushi. “Allah ya shirye kai kam” Dinning din falon ya nufa ya hada tea ya dauko biredin da kanwarsa Khadija ta gasa ya dawo ya zauna. “Ya shirye shirye?” Ya kalleta cikin rashin fahimta yana zauna bread din. “Na Hafiz mana” “Oh yana nan muna yi” “Toh Allah ya taimaka, yanzu ya bude maka Kofa ko?” “Kofar me?” “Kofar aure mana, ai daman Abokai ne suke budewa aboki kofa, mahaifinka ma Abokinsa ne sila” Yayi murmushi “Momy Tsoron kike yi ma yarki kishiya?” “Toh ya muka iya Allah yace ayi, ko bama so dole mu hakura ai, ni ma hakurin na yi da aka min ita gashi yanzu an zama daya, kuma Allah yasa dai macen kirki ce, dawowar nan ma da na yi Khadija bata son zama bangaren nan sai can” “Momy ba wani kwana kwana kawai Daddy na ya iya kwatanta adalci ne shiyasa” “Ba laifi ya rike amana gaskiya, kuma ita ma Husaina tana da hankali tana kokarin nuna masa idan ya kwance, shi ma kuma ya san duk yadda aka yi ba a kaiwa gun uwargida har abada, da ya rike wannan sai muka zauna lafiya. kai ma dai ba dan halin maza ba wanda ke da mace kamar Diyata ai wata ba zata burge shi ba, mace ga kyau ga kyau hali” Kareem ya aje cup din dake hannunsa yana tabe baki. “Yusura dai ta samu sa'a bana sha'awar tara mata ne kawai, amman kyauta be taba burgeni ba balle ya hana ni ganin kyau wasu matan, kyau hali kuma ita zai amfana ba ni ba” Momy ta karkato tana kallonsa. “Kyauta be taba burge ka ba? Amman tana da kyau ko?” Kamar mai nazari haka yayi sannan yayi murmushi ya amsawa Momy. “Kin san ni kyau mace be cika daukar hankalina ba, na fi son na ga mace tana amsa sunanta na mace da rauni irin na mata da wasu abubuwa da suka shafi mata” “Karya kake yi Kareem kana son kyau, me yasa ka nacewa yarinyar nan marar tarbiya” Yayi murmushi domin ba wannan ne karon farko da mahaifiyarsa take kiran tsohuwar budurwarsa da marar tarbiya ba. “Ba dan kyau ba ne, kawai dai ina sonta ne” Ya duba agogon hannunsa ya mike tsaye. “Kar na yi latti bari na wuce gurin aiki” Ya fara takawa ya isa kofa yana kai hannunsa ya bude kofar Momy ta ce. “Kareem...” Ya juyo ya kalleta “Allah ya maka albarka” Yayi fuskar mamaki yana dan murmushin da ya zame masa ado. “Na minene?” “Ina jindadin yadda kake zuwa kullum ka gaishe ni sannan ka tafi aiki, ka yaro ne mai tsananin biyayya da son farincikin iyaye, idan na ce kar ka aikata kana gudu kake kaucewa hanina idan kuma na ce ka aikata a take kake aikatawa ka banbanta da yaran zamanin nan kana da biyayya da gudun bacin ran iyaye fiye da yan'uwanka, wasu iyayen basa samun haka” Fasa bude kofar yayi ya dawo gurin mahaifiyarsa da kusan zai iya kiranta da kawarsa saboda yadda yake mu'amala da ita. “Na gode Momy, Allah kara miki lafiya” Yayi mata side hug ita kuma ta amsa da Ameen sannan ya fice daga gidan... Daga gidan kai tsaye asibiti ya wuce gurin aikinsa, he spend 6 hours a gurin sai da yayi Sallah La'asar sannan ya koma gidansa kai tsaye ya wuce dakinsa yayi wanka ya canja wasu tufafin sannan ya fito ya sauko kasa ya fice daga falon ba tare da ya kalli kofar kitchen din da yake jin motsi ba. Restaurant dinsa ya wuce ya shiga office dinsa, da telephone yayi using ya fadi abun da yake bukata for lunch aka kawo masa. Daf da zai gama cin abincin Hafiz ya turo kofar Office din ya shigo. Kareem na ganinsa ya aje abincin ya zari tissue ya goge bakinsa ya dauki ruwa ya sha, sannan ya kalli Abokinsa da murmushi a fuskarsa. “Ango, da gaske dai auren yarinyar nan zaka yi” Hafiz ya zauna yana fadin. “Idan har wani sai ce zai yi abu kuma ya fasa, to wani dabam ba Hafiz ba, ka fi kowa sanin idan na yi magana daya bana canjawa” “Amman me yasa ake ta boye min? Kai sadakinka ma a gurin wani na ji, dazun kuma Abbah ya kira yana tambayar ko lafiya baya ganina a cikin abubuwan ka wai an kai lefe be gan ni ba” “Wadanan abubuwa ne da suka shafi mata, ba dole sai na fada maka ba, bana son na fada maka wani abu da zai saka ka ji babu dadi shiyasa duk wani jan ragamar auren ma Madam na barwa ita ta yi” Kareem yayi murmushi kamar babu komai bayan kuma ya san can a kasan zuciyarsa yana jin babu dadi. “Na yi mamakin da Aisha take ta baka goyon baya, ban zata za ta karbi abun salin salin ba babu fada babu daga hankali” Hafiz ya cire hular kansa. “Ni kaina na yi mamaki, gaskiya Matata yar Aljanna ce Kareem matar nan ta ba ni goyon bayan da duk ake bukata, ita ta saka na ja maganar auren nan ta dauki lokaci haka saboda ta samu damar yin shirye shirye, lefen nan ma ita ta hada ban yi tunanin zan samu haka daga gareta ba, da na fada mata silar auren ma karka so ganin yadda take tausayawa Noor” Kareem yayi jimmmm na dan lokaci jikinsa yayi sanyi, kamar Hafiz ya san abun da yake sakawa a zuciyarsa sai ya ce. “Ban fada mata alakarka da Safeena ba, ba abu ne mai kyau ba balle na tallata, kuma wannan sirrinka ne da be kamata kowa ya sani ba, Noor din ma da ta zama sila ba zata taba sanin alakarku da Safeena ba, domin ban san me Allah zai yi ba a gaba, idan har zan iya daukar wuka na daba maka na kashe ka Kareem toh Tabbas zan iya fadawa wani sirrin dake tsakaninka da Safeena, ni dai duk abun da na yi kuduri na neman janye ka daga aikata alfasha ne da kuma nema maka farinciki, Ban san ya abun yake ba, domin ni abun da nake so shi na samu mun yi soyayya da Aisha kuma mun auri juna, muna zamantakewar aurenmu cikin amincin da kaunar juna” A sirrance Kareem ya sauke ajiyar zuciya a sirrance domin shi be san wannan dadin ba. Na auren macen da kake so, da kuma be san dadin zaman auren ba, domin be san wani rana daya da suka rayu da Yusura ba cikin soyayya da shaukin juna. Dago kai yayi yana kallon Hafiz dake amayar masa da abun da ke ciki a game da rayuwar Kareem din. “Indai har yadda soyayya take da tsananin karfi, haka kiyayya take da shi, toh kai abun tausayi ne Kareem, Sabuwar da wadda kake so, ka auri wadda zaku yi zaman aure har ku haihu biyu baka ji kana sonta ba, ita ma bata ji tana sonka ba, lamarinku yana ba ni mamaki Kareem ban tana ganin ma'aurata masu tsananin kiyayyar junansu irinku ba” Kareem ya kwanta jikin kujera yana maida numfashi. “Daman can kasan ni Yusura bata burge ni, ban taba jin ina son yarinyar nan ba Wallahi tun tana gidanmu, ita ma bata da abokin gaba Irina tana matukar jin haushin tsarin rayuwata, kuma tana da wadda take so amman kaddara ta riga fata, Momy ta ji bata gamsu da tarbiyar Safeena ba bata karbeta a matsayin in-law ba, shiyasa ta musanya min da Yusura ni kuma ba zan iya musa mata ba, Ina son farincikin Mahaifiyata Hafiz, Yusura ma ba zata iya ce mata Aa ba saboda ta bude ido a hannun Momy Momy ta zame mata uwa ta zame mata uba ta mata gatan da yan'uwan mahaifinta suka kasa yi mata, sai take ganin idan ta musawa Momy za a ce saboda ba ita ta haife ta ba ne, kuma Yusura tana da tsakanin Biyayya Ga Momy fiye da Khadija da Momy ta haife da cikinta” “Kun kasa karbar kaddarar ne Kareem kun kasa bude zuciyoyinku kun kasa kallon junanki da Rahama shiyasa har yanzu kuka kasa zaman jindadi” Kareem ya busar da iskar bakinsa. “Wata kaddarar bata nufin zama har abada Hafiz, idan kiyayya ta yi yawa daya ke tafiya ya bar daya, ko dai na mutu na bar Yusura ta huta ko kuma ita ta rasu ta bar ni na samu salama, domin ba zan taba aikata abun da zai daga hankalin Momy ba, ba zata taba sanin irin zamantakewar da muke ba” “Wata kila tana son sulhu kai ne dai ka ki ka bada kai, domin idan ka hau saukowar abu ne mai wahala Kareem” “Hafiz Yusura bata so na, ta barar da 3rd cikin da ta samu” Hafiz ya kwalo ido yana sakin baki. “Garin Ya?” “Ra'ayi, watanin baya na ga wasu hallaya da dabi'u a tattare da ita da take idan tana da ciki, kuma ta fada min zata je asibiti, but after that babu cikin nan” “Wata kila dai ba cikin ba ne Kareem ko kuma ya zube a karan kasan ne” Kareem yayi murmushi mai sauti, ya kada kai ya hade hannaye yana kokarin kawar da maganar. “So yanzu me ya rage a shirye shiryen da kake?” Hafiz ya mike tsaye ya isa gurin da Abokinsa yake zaune ya dafa kafadarsa. “Kareem ka min alkawari dan Allah ko da ba yanzu ba, nan gaba zaka aure macen da take sonka kake sonta zaka yi aure na farinciki da soyayya ko da bana raye, mu'amala da Safeena ba kaddara bace ganganci ne, kuma ba dalili ba ne” Kareem ya dafa hannun Hafiz dake kan kafadarsa. “Na maka alkawari, amman Safeena muna wata na bakwai wani abu be shiga tsakanina da ita ba, na aje Safeena a gafe Hafiz” “Ina fatan hakan” Hafiz ya karasa yana bubbuga kafadarsa sannan ya koma gurinsa ya zauna. NOOR POV. Duk yadda ake yaba uban lefen da Hafiz ya dankaro min ni babu abun da ya burge ni a ciki. Fargabata da tsoro sun ninku fiye da baya saboda gabatowar auren mutum da babu shi a lissafin masoya na, kuma babu shi a cikin mafarkina. Ko sau daya hannuna be kai cikin kayan na duba ko daya ba balle na jidadi, ko da yake ina jindadin a kyauta ko kyautata ga mutumen da baka so? Ban ji ina son Hafiz ba ko na wuni daya, zan yi biyayya wadda ta zame min dole ba dan zuciya na so ba, ta dayan babin kuma tausayin halin da Zafeer yake ciki ya hana ni tausayawa kaina ya hana ni jindadin abinci ya hana ni sha'awar komai a rayuwata, kusantar kwanakin auren da zan iya kira na kaddara ina jinsa kamar gabatarwar mutuwata. “Wallahi kin yi dace Noor gaba daya unguwar nan labarin lefenki nan ake” Na dago na kalli Zainab cike da takaici da bakinciki. “Yabon kawai kika ji ba ki ji ana zagi ba?” Cikin sanyin muryar da raunin fuska ta amsa da cewar. “Na ji, amman kowa ya san kina son Zafeer shi ma kuma yana sonki, wasu dai suna dora laifin a gurin mahaifinku ne, har ana cewa saboda haka mahaifiyarku ta fita” “Bana son mutumen nan da zan aura, Baba ya dage sai shi, ban san ya zan yi zaman auren ba, ban san ya zan kalli fuskar mutumen da bana kauna na rayu da shi na tsawon lokaci ba, ji nake kamar na gudu” Ina maganar hawaye ya wanke min ido zuciyata ta kara karaya. “Dan Allah karki yi ki jefa mahaifiyarki a matsala dan dai kin san ta Baba ba ruwansa, da ma dai zai miki lamani ki koma gurin Mama ki zauna kamin auren zaki fi jin sanyi” “Ba zai bari ba, ita kuma ta yi rantsuwa ko mutuwa aka yi ba zata zo daga gidan nan ba, balle kuma aurena, lefen nan ma tace ta yafe ganin ba zai ya zo ba kuma ba sai an kawo mata ba, kuma Baba ya hana mu zuwa gurinta yanzu” “Ki yi hakuri Noor, ni dai zan tafi kar Baba ya dawo ya tararda da ni yayi zaton wani munafurci nake zuwa yi” Ta mike tsaye tana saka Hijab dinta na bita da kallo ina hawaye. “Amman Zafeer din ya ji sauki?” “Har yanzu dai yana asibiti, idan ma an sallame shi garin zai bari haka na ji Mamansa tana fadawa Ummanmu tace zai koma gurin Yayan mahaifinshi Abuja” Na saka hannuna na share hawayena na mike tsaye na biyo bayanta, har kofar gida na rakata na tsaya ina kallon tafiyar har sai da na daina hangota sannan ya juyo na dawo wasu hawayen suna bin fuskata... “Ba zan yafe maka ba Kareem, kai ne silar wannan masifar da ta same ni” Na karasa cikin kuka mai karfi har sai da Hana ta fito daga dakin Mama da gudunta. “Noor Lafiya” Na rike hannayenta ina kuka. “Hana bana son mutumen nan Wallahi bana sonsa bana son shi ko kadan, Zafeer kawai nake so, yanzu yana asibiti duk saboda ni, tun yana ciwo a gida abun ya kai shi asibiti kuma saboda ni ne, ba zai yafe min ba, Allah ba zai bar ni ba” “Babu wanda ya isa ya hana Baba abun da yayi niya Noor kin sani, kuma aure yanzu sauran sati biyu hakuri kawai zaki yi, Allah ya riga ya kaddara wannan ne mijinki ba Zafeer ba, ba kuma Kareem din ba ma, kuma kin ga ya sama Baba sauki ya ce baya bukatar akai ki da komai, ta ya Baba zai yarda a fasa aurensa ki auri Zafeer” “Amman ni Zafeer nake so” “Baba be san soyayya ba Kudi kawai ya sani, kowa da jarabawarsa mu kuma irin ta mu kenan” Ta rike ni ta mikar da ni tsaye ina kuka. Wata zuciyar na raya min ko dai na gudu kamin aure ko kuma bayan domin ina jin soyayyar Zafeer ba zata bar ni na yi zaman aure ba. I have few pages for book 2 ragowar Pages din na wadanda suka biya ne. If you want to subscribe Pay 500 to Zenith Bank Hadiza Abubakar 2451879008 Or 6484787074 Khadeeja Candy Moneypoint And send the evidence of payment to 08036126660 See you🥰✌🏻 #KhadeejaCandy Follow the KHADEEJA CANDY channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaNTEQTFXUuaypyV5O01 *Duk mai son ya rika samun Littafin TA KI ZAMAN AURE yayi following wannan Channel din mai suna KHADEEJA CANDY a nan zaku rika samu duka littafaina in Sha Allah* ✧✦ 𝗧𝗔 Ƙ𝗜 𝗭𝗔𝗠𝗔𝗡 𝗔𝗨𝗥𝗘 ✦✧ 𝗕𝘆 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆 *Book 2 - Chapter 2* Kusan zan iya cewa na saba da kuka a duk lokacin da rai ya bace, balle kuma yanzu da kaddara ta sauya min mu'amala da dabi'u. Kuma ta rufe ni a cikin wani dakin da ban isa na fitar da kaina ba. Idanuwa na saka ina ta kallon yadda ake ta kai da kawo na sha'anin bikin aureni a yayinda bani da wani kuzari na magana ma balle na motsa, kamu, walima da wani event da ake yi na aure ban shirya ko daya ba, Hana ce mai kokarin ganin na yi wasu abubuwa amman ban saurareta ba domin ni kadai ya san yadda nake ji a rayuwata na auren mutumen da ba shi a lissafina. Ana sauran kwana biyar adaura auren Hafiz ya saka a sallamomi, a lokacin na ci kuka har na sauya kalar idanuwana, sai na fito ina tafiya kamar bana son isa inda yake tsaye. Daga jikin kofar gidanmu na tsaya na rumgume hannyena kaina na kasa domin bana son kallon fuskarsa ma. Daga inda yake jingine jikin mota sanye da kananan kaya ya dago ya karaso kusa da ni kamshin turarensa na kara kusantar hancina. Wayarsa ya ciro daga aljihu ya kunna haske fitilar ya haska fuskata. “Noor Lafiya kike kuwa?” “Ni ban taba lafiya ba tun da kuka shigo rayuwata” Na amsa masa ba tare da na kalleshi ba. Wayar na ga ya kashe ya saka aljihunsa. “Daman na zo ne na tambaya me zaki yi a cikin shirye shiryen da yan mata suke yi?” “Ba zan yi komai ba” Na amsa a takaice. “Okay, daman dai na zo na ji saboda na bada kudin shirye shirye idan har zaki yi, kuma Balkisu wato uwargidana kenan ta shirya Walima da Kamu, saboda na fada mata daman abu ne mai wahala ki iya shirya wani event, wannan ina fatan zaki je?” “Ba zan je ba” Ya tsaya kallona kamin na ji saukar ajiyar zuciyarsa. Ya gyara tsayuwarsa ya fuskance ni da kyau sannan ya kira sunana kai tsaye da siffar da be taba yi ba. “Khadija...” Na daga kai na kalleshi duk da kasancewar bana ganin fuskarsa da kyau saboda duhun dare. “Ina son na yi wata magana dake, na san kina da kiriniya kina da kurciya amman duk da haka kina da hankali kuma kina da tunani irin na mutane domin ke mutum ce. Kin ga tun farko ni da ke ba mu san juna ba, ban san ki ba baki san ni ba, amman da Allah yayi nufin hada wani abu a tsakaninmu sai ya kawo dan'uwanki a gurin kasuwancin abokina, duk da haka kuma be hada ni da ke kai tsaye ba sai ya hada ki da abokina wanda shi ne silar faruwar komai a yanzu” Yayi shiru na wasu dakiku sannan ya shiga. “Wallahi Noor ban saka ran aure nan kusa ba, kuma ban yi tsammanin zan aureki ba, ina wani tunani da tsari ne na dabam a rayuwata game da ke ashe abun da Allah yake tsara mana dabam, kuma dai kamar wasa na amsa abun nan gashi ya zame min gaske, ban san zafin rabuwa da masoyi ba, amman na san dadin auren wanda kake so domin matata ta farko auren soyayya muka yi, sai dai ke ina hango miki wani abu a yanzu wadda na kasa gani a baya, kuma ina hangen wani rame da yake shirin fadawa da ni” Ya gyara tsayuwarsa. “Shiyasa yau nake son mu kai karshe da ke, Noor ko dai mu karbi kaddarar nan ko kuma mu hakura da juna, saboda ina jin tsoron abun da zai je ya dawo, ance idan gemun dan'uwanka ya kama da wuta to ka shafawa naka ruwa, Zan iya samun Mahaifinki na fada masa cewar na sanyi zancen auren nan, domin na lura san baki ra'ayi na, yadda nake tunanin zan iya juya ki kamar hakan sai gagara a gareni” Na kalleshi da sauri ina girgiza kai hawaye na sauko min. “Fasa aurena ba zai saka Baba ya amince na auri Zafeer ba a yanzu, kawai zai janyo min matsala ne tsakanina da shi, zai tsine zai yi fushi da ni, Kareem ya riga ya kawo ka a rayuwata kun ruguza min komai” “Babu ruwan Kareem a cikin matsalar nan, da kin san yadda yake son farincikinki da baki furta haka ba, abu ne da aka riga da aka tsara tun farko, shiyasa nake son ni da ke mu karbi wannan kaddarar...” Ya jinjina kai alamar gamsuwa ina share hawayen da suke sauka a lebena. “Na karba Hafiz, na karba...” Na amsa masa sannan na juya ina kuka na shige cikin gidan. Rasa na yi gurin da zan raba na yi kuka dan haka na dauki buta na shige bandaki na rufe baki na dinga kuka kamar raina zai fita. Daga ranar sai kukan ya rubbanya, domin ina jin a zuciyata na rabu da mutumen da shi ne farincikina. Hankali be kara tashi ba har sai da yan'uwan Baba suka fara sauka gidan wasu daga dangin mahaifiyata dake zuwa kullum suna kawo min maganin mata da ya zame min cilas Ina sha ba dan zuciya na so ba. Ranar Alhamis aka yi kamu a gurin da uwargidan Hafiz din ta kama, sai dai ban samu zuwa ba saboda zazzabin da ya rufe ni ya hana ni ko da bude ido. Mafi akasarin dangin mahaifina suna dorawa Mama laifin damuwa na ne, sai na kasa sakewa ne saboda bata kusa da ni, ta ki ta leko bikin aure, wata kanwar Baba ma cewa take Baba ya fada mata ita ta hure min kunne nake son bijire masa a auren mutumen da ya saya masa gida kuma ya dauke masa komai na aure. “Ke ni fa ba dan Hajara ita ta haifi yarinyar nan ba, Wallahi sai na ce bakinciki, domin yau mijin da Noor zata aura Miji ne da ko wace uwa take son a aurawa yarta, mutum mai alheri mai son yarka” Cewar Gwaggo Saude, Gwaggo Hasana ta amsa mata da cewar. “Tohm ke ma dai kya fada, tun ba yau ba fa Yaya yana kuka da Hajara, wasu abubuwan da Noor take ma ni sai nake ganin kamar har da goyon bayanta, domin dai Yaya yana tsaye akan yaransa suna tsoronsa amman ita kam aa sam so take ma su raina shi, yanzu ba gashi ta yi ma kanta ba ina dadi ayi auren yarka kai kuma naka auren ya mutu? Ka koma gida da tsufanka da komai kana zawarci, yaran matasa ma yanzu ya suka kare balle kai da ke da manyan yaya” Gwaggo Saude ta yi kwafa. “Ai muje dai zuwa nan gaba kadan sai ta yi nadama, gashi babu gyara balle ace za a gyara, kuma Yaya dai aurensa zai yi domin yace ana yin auren Noor shi ma zai yi nasa” “Ai ni Wallahi ban dauka zai kai yanzu ma be yi auren ba” Anty Larai ce ta katse hirarsu tana kanrar da su abun da suka manta. “Yaran nan fa suna jinku kuna zagin uwarsu babu dadi” “Gaskiya muke fada Anty Larai, da a fada bayan idonsu ai kara a fada gaban idonsu, su ji komai saboda tuwon gobe ake wanke tukunya, ai da gulmarta zamu yi ba zamu yi a inda zasu ji ba” “Toh ban da abinki Saude su kansu yaran ai ba tsoronsu muke ba balle mu kasa fadar abun da yake ranmu, ita gaskiya ai dole a fade ta” Anty Larai ta ce “Hassana dan Allah a bar zancen nan ai ana barin halak dan kunya, kuma babu kyau cin gira kusa da ido, yara kuma duk da wayonsu kawai suna son dasa ma kanku kiyayyar ku a zuciyar yaran ne idan kuna cin fuskar uwarsu suna saurare, dan Allah kar wanda ya sake tada zancen nan” Daga haka ban sake jin wata maganar nan. Daga ni har kanwata Hana ba mu motsa ba, ba wannan ne karon farko da suke yawan bawa Mama laifi idan wani abun ya faru ba, domin Baba yana zaunawa da yan'uwansa ya zageta ya nuna bata da gaskiya ko da kuwa ita ce mai gaskiya. A duk lokacin da suka zo ko ta hadu da su suna yawan fada mata maganar da duk ta so bakinsu marar dadi kamar da gatse, ma'ana dai Mama da yan'uwan Baba suna irin zaman nan ne na doya da manya, sai dai ba duka ba. A yanzu na kara tabbatar da hakan domin daga Baban da ya kasance Miji a gareta da yan'uwansa babu wanda yayi marmarin dawowa ta a gidan ko da a munafurce ne. Ina cikin dakin kwance Baba ya shigo gidan da dan saurinsa. Yan'uwansa suka amsa sallamar sai ya tambaya ina nake, tun kamin na ji dalilin neman gabana ya fadi. “Ina tunanin tana daki kasan ba fitowa take son yi ba kamar mai tsoron mutane” Gwaggo Saude ta fada. “Wai yaron nan ne ya matsa yana son magana da ita, yaje ya same ni cikin mutane sai rokona yake jama'a duk sun saka baki mi Wallahi har kunyata ni yayi a cikin mutane” “Wane yaro kuma Yaya?” “Zafeer mana” Na tashi zaune da sauri kirjina na bugawa da karfi jin Baba ya amsawa Gwaggo Hassana da sunan masoyina. “Toh Lafiya? Me yake nema” Natsuwa na yi sosai ina saurarem irin amsar da zata fito daga bakin Baba tare da fatan zai amsa mata da cewar ya fasa aurar da ni g Hafix zai aura min Zafeer din da nake so. “Wallahi gaba ya saka ni da roko da komai yana son zai yi bankwana da Noor” Na tashi da sauri na isa bakin kofar dakin na tsaya ina kallon Anty Larai dake fadin. “Bankwana kuma? Ikon Allah ban taba ji haka ba...” Gwaggo Saude ta tabe baki. “Waya sani ko wani sherin ya dauko yake son ya shafa mata? Albashi idan taje ta kasa zaman aure ko kuma ta miJin ya juya mata baya, kai wannan yaro da naci yake” “Gaskiya Yaya karka barshi, tana ina zaka yarda taje su yi bankwana waya sani ma ko sace ta zai yi su gudu” Na kalli Gwaggo Hassana kamar na yi magana amman na kasa domin ban isa ba na yi wata maganar ace wani abun muke shiryawa. Anty Larai ta juyo ta kalleni sannan ta juya ta kalli Baba. “Me yasa yake son magana da ita?” “Wai bankwana zai mata” “Bankwana ma auren da zata yi ko kuma na me? Bankwana kamar ya?” Gwaggo Hassana tace. “Waya sani Anty Larai ko wani abun ya dauko ace da sun hada ido zata ce bata son wacan shi take so, kuma yarinyar da ya rage kwana biyu a daura mata aure ai matar wani ce ta ina za a bar wani da ba mijinta ba ba muharraminta ba ya ganta... Ni dai zuciyata ba ta natsu da wannan ba” Ajiyar zuciya Anty Larai ta sauke sannan ta ce. “In har ya zama dole to ya shigo nan a gabanmu idan wata maganar ce ya fada mata, amman ba za a fitar da ita waje ba, kuma ba zai kebe da ita ba” “Ni dai kam da za a dauki shawarata ba zai ga ganta ba, ba mu san sherin da ya dauko ba, duk abun da yake son fada mata ya rubuto mata a takardar a kawo mata” “Eh to kuma kin kawo shawara Saude bari ayi haka din a huta kawai zai fi” Baba ya amsa sannan ya juya ya fita, kusan ni da hoto banbancinmu kadan ne a lokacin domin bana iya motsi kuma na kasa cewa komai hawaye ne kawai abun da ke fitowa a idanuwana. Anty Larai ta taso ta dafata ta shigar da ni daki sannan ta fito tana fadin. “Ni dai kam da dai Yaya be yi wannan abu ba, ina ganin kamar Hajara ta fishi gaskiya a nan domin yaran nan suna son junansu” “Haba Yaya Larai yaron nan fa be tashi aure ba irin masu batawa yan mata lokaci ne kawai ga wanda ya shirya sai kuma ace ba za'ayi da shi ba, kuma kowa yana son ya kai yarsa inda zata huta Yaya yana da gaskiya Wallahi” Haka suka yi ta juya maganar tsakaninsu, ni kuwa na kashe kunne ina ta sauraren dawowar Baba, amman be dawo ba har dare ya fara yi sosai, wasu ma tuni sun fara bachi. “Yaya sannu da zuwa” “Yauwa Larai baki kwanta ba” Na ji Baba ya amsa yana sauke gajiya. “Shiru kuma dazun baka dawo ba ka bar mu da tsammani da jira” “Ai ina fada masa cewar ya hakura ba zai samu ganinta ba Gwaggwaninta sun hana sai ya fara gajiya, ni kuma bukaci ya rubuto ko ma minene, da na fada mata sai na wuce tare da Malam Usman daman tare muke, to bayan na koma can majalisa bayan sallah Isha'i ya same ni ya ba ni takardar” A zatona Gwaggo Saude ta yi bacci domin ban ji motsinta ba tun bayan da suka gama tsinewa Zafeer a dazun, ashe ban canka daidai ba sai jin muryarta na yi tana fadin. “A bude A duba idan ba wani maganin ya saka a ciki ba” “Ni zan karbe ta ma sai da na yi addu'a na yi bismillah sannan na karba kuma na bude tun a can na duba ban ga komai ba, ban san dai abin da ya rubuta ba saboda ba gane karatun zamani nake ba da ma ace ajami ne zan gane” “To a karanta gaban kowa kowa kuma ya ji” Gwaggo Saude ta fada sai Anty Larai ta tari numfashinta. “Aa wannan kuma be dace ba, sirrinsu ne a bata ita ta duba abunta.. Noor” Ta karasa da kiran sunana sai na tashi jiki na rawa na fita daga dakin na isa inda take na duka, sai ta karbi takardar daga hannun Baba ta mika min. “Ga sako inji Zafeer yace a baki” Hannu biyu na saka na karba sannan na mike tsaye na koma cikin dakinmu, babu wutar nepa da hasken fitilar da aka kunna mana na yi amfani na bude takardar ina hade yawu zuciya cike da fargaba. “Wannan kam ta karshe ce, bankwana ne da ban yi tsammanin zuwansa ba, ban taba mafarkin ko tunanin zan rayuwa da wata macen da ba ke ba Noor i love and i will love you unconditionally, wannan wani abu ne da yake tabbatacce a rayuwata. Sai dai kuma ba zai hana na manta da wannan cin amanar ba, ba kuma zai saka na fasa fada miki hakkina zai bibiye ki ba. Noor ana halittar ko wace mace da rib din mijinta ne, kuma ke ce rib dina and I'm yours, zaki gane hakan nan gaba, zaki neme ni a lokacin da nema ba shi da amfani a gareki, zaki yi nadama bayan kurewar lokaci, Noor ba zaki sake ji daga gareni ba, It time to say good bye Ba zan iya zama na ji ko na ga daurin aurenki da wani da ba ni ba, Noor idan kika ce na fasa tafiya zan tsaya, idan kika amsa cewar zaki aureni kin wanke ni daga damuwa, ina kaunarki Noor ba zan daina kaunarki ba har abada... Tafiya ce da ba ta waiwaye ba... but this is not the end...! Wannan be kare ba, Zan jiraki Noor zan jira...” Na karanta na sake karantawa hawaye na sauko. Na rumgume takardar a kirjina ina kuka marar sauti. Da wane zan ji? Bakincikin auren wanda bana so ko kuma na rabuwa da wanda shi ne sadaukin rayuwata? Ko kuma na dora min laifi da Zafeer yake? Me yasa ya kasa bude ido ya kalli irin kunnar da nake ciki? Shin labari be je masa cewar dole aka min ba? Ko kuma zuciyarsa tana da nauyin karbar gaskiya ne? Yadda na ga rana haka na ga daren babu wani banbanci, saboda kuka da bakinciki mai hana bachi kusantar idanuwa. Washe garin ranar, rana ce mai tsananin daraja da martaba ga duk musulmi, sai dai ni na ji ta a dabam, saboda kusancewar abun da nake aunawa da mutuwa. Bana iya komai sai ance tashi ki yi duk wadda ya kalleni ya san bana farincikin da auren da zan iya cewa Baba siyar da ni yayi aka ba shi kudi. Ko kuma na ce rawar kai ya janyo min na dauko ajalina har gida na kawo. Misalin karfe uku aka zo da motA daga gidan ango aka dauke ni tare da kawata Zainab, zuwa wani shagon kwalliya, ana fente fuskar ina hawaye hakan ya hana kwalliyar. Daya daga cikin matan da aka je dauko ni tare da ita ce ta kama hannuna ta jani zuwa wani guri na dabam da muka kebe daga ni sai ita. Ta zauna kusa da ni sosai ta kai hannunta ta dago kaina muka fuskanci juna. “yarinya aure sirri ne, kukan ba shi da amfani a gareki mijina mutum ne mai tsananin tsoron Allah mai kawaici mai adalci, miji ne da ko wace mace mai hankali zata so kasancewa d shi, da ace kin san halinsa na gari da kuma yadda yake taka tsantsan da duniya da baki zubar da wannan hawayen ba, tun da muka yi aure da miji be taba wulakanta ni ba, haihuwata uku da shi ga ciki na hudu, ba zan miki karya ba mu kan samu tsabanin amman babu wanda yake sani, saboda baya bari a san sirrin gidansa” Kallonta nake irin kallon da na gagara yarda da gaske Matarsa ce. “Wacece ke?” Ta lumshe ido ta bude “Abokiyar Zamaninki yar'uwarki kuma yayarki...matar mijinki” Na hade yawu mamaki ya saka hawaye yanke min a take, a wacan karon da ya fada min ta shirya Kamu da Walima ban dauka da gaske ba, domin ban yi tunanin akwai wata mace da zata yarda ta shirya wannan wa kishiyarta ba, a yanzu kuma taje ta mota suka dauko ni zuwa gurin kwalliya, hakan duk be wadatar ba har sai ta fada min kyawawan halayyar mijinta anya Hafix mutumen kwarai ne kuwa. Ta dafa hannuna tana murmushi. “Na san zaki yi mamaki jin furucina, zuciyarki zata raya miki cewar ko dai mutumen da za a daura min aure da shi ba mutumin kirki ba ne? Ko?” Na daga mata kai domin abun da yake shimfide a zuciyata kenan. “Ko kadan, Wallahi Barrister mutumen kirki ne, kawai ina fada miki gaskiya ne saboda hankalinki ya kwanta, karki ce bana kishi ina yi, amman na yi Kokarin fin karfin zuciyata ne, saboda ina son farinciki Mijina, kuma idan har yana neman goyon baya akan wani abu ina tunanin ni ce ta farko da zan fara bashi wannan goyon bayan, Barrister ya so ni, ya kaunace ni ya nuna min gata, ya sauya lissafina ya banbanta ni a cikin dangina, kuma ya tsaya tsayin daka ganin yan'uwansa sun nuna min girmamawa da kauna, ni kuma ba zan yarda na bata wannan alakar ba, ba zan saka masa da mummunan sakamako ba” Na sake dubanta irin duba na kokarin tantance gaskiyar mutum da akasinta. “Baki kishi ne?” Kamar jira take na yi mata tambayar sai hawayen da ke makalle a idonta suka zubo mata. “Ina yi mana, musamman da na san ke din budurwa ce yanzu ne MiJina zai yi auren budurwar da saurayi, domin ni a bazawara ya aureni, Wallahi Noor Barrister mutumen kirki ne idan kika yi rasa shi kin yi babbar hasara...” Ta share hawayenta, ta dafa kafaduna duka biyu. “Dan Allah ki kwantar da hankalinki ki daina damuwa, damuwarki tana saka shi a cikin damuwa shiyasa ana dag da auren nan yake ta nanata min yana son ya janye, babu amfani kuka a public place kamar wannan, idan ma zaki yi ki bari sai kin kebanta kinji” Na daga mata kai daman tuni hawayen suka tsaya min saboda mamakinta. Kalamanta kuma sun karfafa min guiwa duk kuwa da kasancewar zuciyata bata yarda 100% mijinta mutumen kirki ba ne. Wata kila dai zagon kasa take min. Anyi kwalliya cikin nasara saboda na bada hadin kai, bayan an gama ta dauko min wani farin lace na saka rigar ta yi min yawa sosai saboda jikin nawa ba na irin sauran yan mata bana daman ni duk abun da na saka sai ya min yawa, ta saka na cire tufafin aka fita da su aka rage sannan aka dawo min da su na saka suka min cif. Kowa yabon kyau na yake a falon na kwalliya saboda yadda na yi kyau daurin dankwalin ma kansa abun kallo ne saboda yadda ya tsaru akaina. Gurin da muka boya dazun ta sake boya da ni ta kira mijinta facetime. “Madam...” “Barrister ka iya zabi” “Da na zabo ki ko?” Ta kauce fuskarta ta kara masa tawa fuskarka. Natsuwa yayi na wasu dakiku ya dauke wuta yana kallon fuskata kamin yayi murmushi. “Noor...” Na kalleta sai ta yi min alama da na amsa. Sai dai ban amsa din ba kuma ban mayar masa da murmushin ba. “Please Smile” Ya fada yana cigaba da kallona, sai na lake masa kafada alamar ba zan yi ba. Sai na ga murmushin dake fuskarsa ya kara fadada. “Noor kin yi kyau Maa Shaa Allah, Allah ya muku albarka ke da ita” Ban ce masa komai ba, amman a raina na amsa da ba Ameen ba domin bana bukatar addu'arsa. “Madam...” Ya kira sunanta sai ta amsa ta yi facing dinsa. “Ke ba a miki kwalliyar ba?” “Yanzu za a min an fara kwalliya wa a amaryar ka ne, na ce bari na nuna maka kamin masu hoto su daukar maka” “Kin kyauta Allah ya miki albarka” “Ameen sai ka dawo” Ta kashe wayar sannan ta kama hannuna muka fito. Sai da aka mata kwalliyar sannan muka wuce a tare zuwa gurin walimar da sun riga da sun shirya komai. Na yi mamakin da na samu dangin mahaifina da wasu daga dangin mahaifiyata har an dauko su an kawo su gurin. A guri na musamman aka zaunar da ni masu manyan wayoyi suka fara wani flash na wayarsu musamman dangin da nake kyautata zaton na Hafis ne ba kuma dan na san su ba sai dan ankon da na ga sun yi kala daya wasu kuma suna kama da shi sosai. Na ga kauna na ga soyayya na ga haba haba na ga marhabun daga dangin Hafix da kuma matarsa na yi mamakin yadda suke ririta ni kamar nice matarsa ta farko, kuma na yi mamakin yadda matarsa ta aje kishi a gefe ta mu'amalanceni kamar kanwarta ba kishiyarta ba. Jikina yayi sanyi sosai na tsorota da yadda na same su. Sai bayan sallah Isha'i suka dawo da ni gida domin daga gurin Walimar gidan wata kanwarsa aka wuce da ni na huta na yi wanka aka min gyaran kai sannan suka dawo da ni gida. A gidan na tarar kowa sai yabon halin matar yake da yan'uwan Hafiz har wasu na cewa na dace, indai abun ya bi haka. I have few pages for book 2 ragowar Pages din na wadanda suka biya ne. If you want to subscribe Pay 500 to Zenith Bank Hadiza Abubakar 2451879008 Or 6484787074 Khadeeja Candy Moneypoint And send the evidence of payment to 08036126660 See you🥰✌🏻 #KhadeejaCandy Follow the KHADEEJA CANDY channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaNTEQTFXUuaypyV5O01 *Duk mai son ya rika samun Littafin TA KI ZAMAN AURE yayi following wannan Channel din mai suna KHADEEJA CANDY a nan zaku rika samu duka littafaina in Sha Allah* ✧✦ 𝗧𝗔 Ƙ𝗜 𝗭𝗔𝗠𝗔𝗡 𝗔𝗨𝗥𝗘 ✦✧ 𝗕𝘆 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆 *Book 2 - Chapter 3* Ni dai tsoro ya kamani zuciyata na raya min ko dai cewa aka yi a samo mai irin soffofina. Sam zuciyata bata natsu da wannan ba. Saboda haka na yi amfani da Hana na saka ta ari wayar Ya Nabil da sunan wata yi ma kawarta flashing ta kawo min. “Noor Allah yasa ba wani abun zaki yi ba” Na karbi wayar ina dan turo baki. “Ni me zan yi ba Hafix ne yace na ari wayar na kira shi ba, kuma kin san idan ni ce ba zai bani ba” “To kina da numbershi a kai ne” “Ina da shi a littafi dai” “Kin san halin Yaya dai dan ana bikinki ba zai hana yayi miki dukan tsiya ba, kuma dan Allah karki kira Zafeer” Na mata banza na tashi na dauko littafin na zauna a gafe daya kamar ina saka number alhalin number Kareem dake cikin wayar Yaya nake dauka. Sai da na gama na mika mata wayar “Gashi na ma fasa kiran” Ta karba ta duba sashen kiran ta ga ban kira ba ta sake miko min. “Ni ban hana ko kira ba amman karki kira Zafeer da wayar Yaya kin san abu mai sauki ya hada mu yayi mana duka, kuma kowa ya ji ya san baki yi daidai ba” “Ni fa ba Zafeer zan kira ba, ai Baba yace be yafe min ba idan na yi magana da shi Wallahi ba shi zan kira ba, kuma ki bar shi zan ari wayar Gwaggo na kira da ita” Duk yadda ta so na karbi wayar sai na ki saboda sanin halin Yaya da na yi kamar yadda ta fada. Sai da ta fita azuwan mayar masa da wayar sannan na fito na tsaya daga jikin kofa na ari wayar Anty Larai domin ita ce mai lafiya a cikin yan'uwan mahaifina. Har ta ba ni na juya sai kuma ta kira na juyo bata ce min komai ba sai da na matsa kusa da ita. “Noor Allah yasa dai ba tsohon saurayinki zaki kira ba?” “Wallahi ba shi zan kira ba Anty Larai ai Baba yace be yafe min ba idan na sake magana da shi” “Toh, na san ai kina da hankali ba kamar yadda suke fada ba tafi ciki ki yi wayar” Na shiga dakin na nufi littafin da na rubuta number Kareem jiki na kwashi number na saka a wayar Anty Larai sannan na fito daga dakin na faki idon mutane na shige bandaki na rufe sannan na aika masa da kira. KAREEM POV. Jikin Momy ne babu dadi kwana biyu, ciwon da take yawan fadar rayuwarta yake nema ya sake sallamo mata sai dai wannan zuwan be tsanannta kamar yadda yake tsanani idan aka bude file dinta ba. Tun daga ranar da take jin fever din yana zagoyo mata Yusura take ta zirga-zirga na zuwa dubata, idan ta gama abun da take Kareem zai wuce da ita ya sauke ta gidan Momy sai dare zai dauko ta. Kasancewar yau Jumma'a babu makarantar Allo da Yamma washe gari kuma Weekend ne babu boko sai ya kwasa har da yaransa suka tafi duba Momy, ba sabon abu ne ba a gurin yaran kusan ko wane yana kai su su wuni sai dare ya dawo da su domin Momy mace ce mai son yara kuma gidansa ma yana cike da yara a duk ranaku hutu na yayan da ta raina ta aurar ko na Abokiyar zamanta ko kuma na yan'uwana. Kamar kullum yau ma sun tarar da jikokin dangi da kuma na kanwar Kareem dake aure a garin. Hakan kuma ba karamin dadi yayi ma yaransa ba domin suna fama da kadaici a gidansu da babu kowa sai kayan kallo. Yusura ta shiga dakin Momy da lullubinta da far'a tana yi mata ya jiki. Kareem ya zauna kusa da mahaifiyarsa yana sauraren yadda take amsawa Yusura tana shi mata albarka. Yusura ta kalli Mijinta fuska a sake kamar ba ita ba, ta ce. “Abban Tine ba zaka matsa Momy ta koma asibitin nan ba? Yau kwana biyu jiki ya ki dadi fa” “Akwai wasu magani da muka dora ta akai, kin san ciwon ya kan taso wani lokacin kwana biyu sai ya tafi, to daga yau zuwa gobe dai idan ba a samu sauyi ba dole asibiti zamu koma” Ya fada ba tare da ya kalleta ba. Momy ta tashi zaune tana mika hannu ta dauko plate din zogalen da Khadija ta gyara mata. “Ko zan koma asibiti ba ta garin nan zan zauna, ba zan sake fita wajen nan ba, na gaji da yawo nan na gaji da shan maganin nan, ko mutuwa ce dai kara na mutu cikin iyalina” Zancen mutu ya daga hankalin Yusura sosai a take idanuwanta da fuskarta suka sauya. “Momy kullum baki da magana sai ta mutuwa, mu kike karyawa guiwa musamman da ba ni da gata sai ke a duniyar nan, cuta ai ba mutuwa ba ce” “Masu lafiyar ma tafiya suke balle kuma mu, kuma idan ka ga ciwo yaki ci ya ki cinye ko yana tafiya yana dawowa rayuwa yake nema, kuma karki sake fadin baki da gata a duniyar nan kina da gatan da ya wuce na mijinki? Ko bana raye Kareem ba sai bari ki yi kuka ba ina da wannan tabbacin” Yusura ta daga ta kalleshi shi ma ya kalleta kamin ta yi saurin kawar da kanta. “Haka ne, Allah ya ba ni ikon cigaba da yi masa biyayya” “Ameen Allah ya miki albarka” Kareem ya sauke ajiyar zuciya sannan shi ma ya amsa da Ameen a addu'ar da Momy ta yi musu. Sannan ya kai hannunsa fuskar Momy yana fadin. “Ba za ki tafi yanzu ba, sai nan da shekaru dari da hansin Momy na farincikina” Sanin hancinta zai taba ya saka ta buge hannun “Wai Kareem ka mayar da ni abokiyar wasar ka, gaba daya ka mayar da ni wata kakarka” “Toh ya za'ayi babu kakar Momy ke ce makwafinsu, idan ban yi wasa da ke ba da waye zan yi a gurinki kadai nake samun farinciki” Yusura ta kalleshi tana Fake dariya kamar yadda ta saba idan suka shiga mutane musamman ace gidan Momy ne. “Abban Tine ka ji tsoron Allah, idan kana fadin haka ai Hajiya sai ta dauka ko wahalar da kai ba ne bana baka kulawa” Kareem ya kalleta irin kallon da su kadai suka san manufarsa and then he smile. “Duk farin da zaki ba ni ai be kai wanda Mahaifiya zata bawa danta ba” Momy ta aje plate din zogalen da spoon biyu kawai ta yi ta kama kunnen Kareem ta ja da karfi. “Kai ne babba amman kullum idan ka gan ni sai ka maida kanka wani karamin yaro, ka maida ni kakarka Shiyasa Hajiya Na'eema take cewa ita kullum ganin take kamar ba ni na haife ka ba, gaba daya ka maida ni abokiyar wasar ka sai idan bana kusa” Yusura ta yi murmushi. “Wannan kuma Momy wani abu ne da kuka saba yi tun kurciya, ko dai ko da na bude ido a gidan nan na yi wayo na san baki da abokin shawara abokin wasa kamar Kareem, Kareem kuma ba shi da abokiyar wasa irinki, yadda kuke mu'alama babu wanda zai zaci ke da shi uwa da ďa ne, kum fi kama da Yaya da kanwa ko Kaka da jikanta, kin fi shakuwa da Kareem fiye da sauran Yayanki, shi ma ya fi shakuwa da ke fiye da Daddy” Momy ta saki kunnensa tana murmushi. “Ni kaina na kan yi mamaki yadda kunyar nan ma ta uwa da da Allah be dora min ba tsakanina da Kareem tun ana gulma har an gaji an saka mana ido, kuma kin ga yadda nake wasa da Kareem bana iya sake jiki na yi da Aryam haka shi ma da yake na biyu bana fari ba, wata kila hakan yana da nasaba da yadda yake da tsakanin tausayina da so na tun yana karami” Kareem ya mike tsaye yana murmushi. “Haka Barrister Hafiz yake ce min wani lokacin, wai Momy ko dai tsinto ka ta yi, ki ji dan iska...” Duk suka yi dariya har Yusura. “Allah ya tsare a dawo lafiya” Daf da zai fice Yusura ta yi masa addu'ar da bata saba yi masa ba idan suna gida, juyowa yayi ya kalleta ya san tana yin duk abun da take ne saboda suna a gaban Momy ne. “Ameen” Ya juya ya fice. Be dawo gidan ba sai bayan Sallah Isha'i exact time din da ya zaba zuwa daukar Yusura. Babu fadan da be yi ba a lokacin da shiga falon ya samu Aryam da Khadija ga Yusura suna kallon Momy na cin gassashiyar kaza. “Miye amfanin zamanku a nan toh? Kun san matsalar da take ciki ba, shiyasa ciwon ko ya tafi yake dawowa” “Doctor kamar baka san halin Momy ba, karamin abu ne ta fara fada idan muka hana ta cin abun da yake so” Cewar Aryam, Kareem ya tashi daga inda yake zaune ya karasa ya dauke plate din ya koma ya zauna. “Wallahi ku bar ni na ci dadi na tun ina da rayuwa, kar sai na tafi ku yi ta nadama, musamman kai Kareem kana bakinciki ka ga ina cin nama ko wani abun dadi” Kareem yayi dariya ya tashi ya shiga kitchen ya wanke hannunsa ya fito ya dauki naman ya fara ci, taunawa yake a hankali zuciyarsa na wani gurin hana tuna masa da wani abun da ya wanzar da murmushi da nishadi a fuskarsa. “Momy halinku yayi kama da Noor, da ace ban san iyeyenta ba sai na ce ke kika haife ta, yarinyar nan Allah yayi mata rigima” “Wace Noor?” Momy ta tambaya yana murmushi. Sai ya kalleni Momy kamar dai ya manta da Momy ce kadai a falon ba. Sai dai hakan kuma ba zai hana shi karasa mata labarin da shaukin Zuciya ya debe shi ya fara furtawa ba. “Yarinyar da Hafix zai aura yanzu...” “Au Noor ne sunanta?” “Eh... Noor” Kusan sautin muryarsa da sautin shigowar kira a wayarsa a tare suka fita. Yarsa Tine ta zo da sauri ta ciro masa wayar daga aljihunsa ya amsa kiran ba tare da ya saka ta ba kuma ta saka hands-free saboda yayi masa sauki ganin ya bata hannayensa da maikon ferfesun kazar Momy da ya karbe. Ta matsa masa da wayar kusa da fuskarsa yana kallon bakuwar number ya furta. “Hello” “Kareem... Noor ce....” Ta fashe masa da kuka, sai ya dago da sauri ya kalli Momy dake kallonsa ya kalli Aryam ya kalli Khadija ya Yusura ce ta karshe da ya kai dubansa a gareta kamar wani marar gaskiya gabansa sai bugawa yake da karfi. “Kareem ni dai Wallahi bana son Hafiz din nan ko kadan ni dai ban taba jin ina son shi ba...” Yayi saurin aje naman dake hannunsa ya taba wayar da maikom ya cire hands-free din ya mike tsaye ya fice daga falon da sauri kamar zai hada da gudu. Harabar gidan ya fita sai ga ya juya ko'ina ya ga babu mai ganinsa sannan ya kara wayar a kunnensa. “Noor me yasa kika kirani? Ina kika samu Number? Wayar waye?” Ta yi shiru. “Wane zan fara amsawa?” Ya juya ya kalli kofar falon Momy dake bude sannan ya juyo ya kalli gate din ya sauke ajiyar zuciya. “Me kike yi ma kuka?” Ta sake fashewa da kukan. “Wallahi ni dai Allah ya gani bana son Hafiz din nan, kuma waya sani ko wani manufa yake da ita akaina ma? Duk kaine sila kuma” “Me ya faru me Hafiz din yayi?” “Matarshi ta yi min kirki da yawa ni abun ya ba ni tsoro shiyasa na kira na tambaya tsakani da Allah Hafiz mutumen kirki ne?” Ya kai hannunsa ya rike goshinsa. “Noor idan Hafiz ba mutumen kirki ba ne, ai ba zai aure ki ba, ya fi ni zama mutumen kirki, matarsa kuma halinta ne ni ma tana kyautata idan na je gidan” “Na ji tsoro waya sani ko cewa aka a samo wata yarinya mai wadda ta rabu da saurayinta marar jiki fara mai saurin kuka ayi wani tsafin da ita? Taya za'ace mace bata kishin mijinta? Sai idan hada kai suka yi waya sani ko kudin da yake ta kashewa ni aka siye” Murmushi yayi ya lumshe ido. “Babu wani hadin kai, Wallahi Hafiz mutunen Kirki ne mai nagarta ba shi da matsala, wayar waye wannan?” “Ta Gwaggo na ce” “Ina kika samu number na?” “Na sata a wayar Yaya Nabil” Ya bude idonsa ya daure fuska kamar ance masa tana gabansa. “Okay daga yau sai yau karki sake kira number na, karki sake tambaya wani abu game d Hafiz ko wani dabam duk abun da kike son sani ki bincike shi, gargadi ne wannan na karshe, kuma zan fadawa Nabik kin kira ni shi ma kuma zan gargade shi” “Ai dole na kiraka kai ne ka yi ruwa ka yi tsaki ka kawo min abokinka ka raba ni da Zafeer, kuma yanzu kace na daina damuwa dole ne mu yi damuwa tare” Ya yanke kiran ya saka number a blacklist. “Da gaske fa yarinyar nan bata da hankali...!!!” Yana rufe baki wani kiran ya shigo da wata number dabam ba wacan ba. Mamaki ya kara kama shi har zai yi rejecting sai kuma ya amsa da zimmar yi mata fada. “Noor What?” “Noor....” Safeena ta furta sunan daga dayan bangaren sannan ta cigaba da magana da murya mai ban tausayi da lafazi mai karya zuciya. “Yarinyar nan ta yi nasarar shiga tsakanina da kai Kareem, ina ji ina gani ka juya min baya hankalinka ya koma gurin wata karamar yarinya, ka mata soyayya da ke tsakaninmu, fada min ba zaka cutar da ni ba ashe karya ne? Cewa auren dole aka maka ma karya ne, domin gashi yanzu zuciyarka ta bude har ka fara son ta, ni kuma ka raya ni da soyayyarka irin rayuwar da yau zan iya aikata komai saboda kai, ka saba min da rabar jikinka, na saba da mu'amala da kai ina gamsuwa fiye da mijina, rashinka ya saka na auri Abdull amman son ka be bar ni na ga laifinka ba, kaunarka bata bari na samu salama ba har sai da na rabeka, yanzu kuma ka juya min baya a karo na biyu, tsawon wata bakwai ban samu kebancewa da kai ba Kareem gaba daya ka sauya min, baka daga kirana baka maida amsar sakona, idan ina son ganinka sai dai na kama hotonka ko kuma na shigo motata na zo na faka a restaurant dinka ina shiga ko fitarka, shin baka tunanin ka azabtar da Ni? Kana ganin hakkina ba zai bibiye ka ba? You don't care how bad it hurts, kanka kawai ka sani Kareem? Ka yi hakuri mana son ka ba zai bari na yi rayuwa mai tsawo a duniya ba zan tafi sai ka so wata sai ka auri wata amman ina raye? Abdull gangar jikina kawai yake aure amman ruhina yana tare da kai.. Kareem ina zaka kai hakkina? You broke me first...” Gaba daya sai jikinsa ya mutu iska ya busar daga bakinsa zuwa sarari. “Noor... Sorry Safeena abun ne yayi yawa, kina da yaya ni ma ina da su, kina da miji amman mun biyewa shedan muna jefa kanmu a halaka, tun da Momy ta kawo ni a duniya ban tana aikata zina ba, kawai na biye miki ne saboda na faranta miki rai, na san na cutar da ke da farko amman ba kudirina kenan ba, kaddara ce ta zo mana a haka kuma ba zan iya cewa Momy aa ba, kuma da ace na san tun farko Momy ba zata yarda na aure ki ba ba zan zurfafa a soyayyarki ba, balle har mu wahala da yanzu ba mu kawo a wannan matsayin ba, da za ki fara tunanin haihuwa da ni alhalin kina da aure...” “Shi ne kawai matsalar? Ba zan sake yi ba, i need to see you now i miss you so much, zan zo gidanka yanzu” Yayi saurin tariyar numfashinta. “No karki fara ba mu taba haka dake ba, and ba mu gida ina gurin Momy” “Zan zo gurin Momy din ko kuma ka zo k same ni a inda muka saba haduwa, ba zan iya bachi ba a yau sai na ganka Kareem...” “Zan yi tunanin” “Zan zo yanzu Wallahi ba zan bari wata macen ta karbe min kai ba...” Ta yanke kiran, ya duba wayar ya sake kiran layi bata daga ba ya sake kira bata daga ba. Juyawa yayi ya koma cikin falon, be kalli kowa ya wuce kitchen ya wanke hannunsa ya zari tissue ya goge wayarsa ya goge hannunsa sannan ya fito, ba tare da ya zauna ba ya kalli Yusura ya ce. “Tashi mu tafi gida” “Lafiya?” Ta bukaci sani. Ya daga mata kafadunsa. “Lafiya mana, by this time muke tafiya gida i think?” “Noor din ce ta kira?” Momy ta tambaya, sai ya kalleta. “Eh tsabani suka samu da Hafiz, ina son na sauke Yusura gida sai na je na yi magana da shi” “Ya kamata kam, ana shirin daura aure gobe ne ko jibi kuma ace an fara samun tsabani, ai ba dadi” “Allah ya kara sauki Momy sai na shigo gobe da safe” Yana fada yana aikawa Safeena sakon cewar zai zo ya same ta a inda suka saba haduwa. Shi ya fara fitowa ya shiga motarsa yayi mata key sannan Yusura ta karaso yaranta na yi mata sai da safe ya shiga motar yaja yana daga musu hannu. Tun da suka shiga motar bata ce masa uffan ba shi ma kuma be kalli gafen da take zaune ba har suka isa gidan. A haraba ya faka ta bude ta fita yayi reverse ya sake ficewa daga gidan. Ya hau titi da zai kai shi guest house dinsa bangaren da ya fi kyau na zuciyarsa na nuna masa illar hakan yana sanyaya masa jiki. Sashen da ya fi muni na nuna masa halin da Safeena zata shiga idan be tafi ba, domin ta siye kwarin guiwarsa da kalamanta na dazun. Ya kasa zaba tsakanin daidai ta akasin haka shedan ya shiga ciki har dayan bangaren ya rinjaye dan'uwa ya faka a harabar gidan bayan mai gadi ya bude masa gate. Motarta ya fara kallo ya sauke ajiyar zuciya kana ya bude tasa motar ya fito ya rufe cikin rashin kuzari ya doshi kofar. Kamar an masa dole haka ya kai hannu ya murda kofar ya bude ya shiga, da wani irin fitinannen kamshi ta tarbe shi wani kalar sexy perfume ne mai daga hankalin namijin da ya amsa sunan Namiji. Kofin ruwan dake hannunta ta aje ta mike tsaye ta nufo inda yake cike da zumudi jikinta har rawa yake idanuwanta suna auna marmarin Kareem da ta yi. Kamin ta karasa ya zuba hannanyensa duka biyu aljihu a kokarinsa na hana kansa taba abun da ba halalinsa ba. Bata tsaya komai ba ta rumgume shi, daman ya san ba zai iya hana ta aikata hakan ba amman zai iya hana kansa taba jikin matar da ba tasa ba. “Na yi marmarinka...” Ta sumbance bayan ta dago daga jikinsa sannan ya sake rumgume shi wuyanta a kafarsa, har sai da ya runtse ido saboda fitinar da turarenta yake kaiwa hancinsa, ta san weakness dinsa turare da Physical touch, hakan ya saka ta sumbantar wuyansa har sai da tsigar jikinsa ta tashi. A karo na biyu da ta dago daga jikinsa sai ta zuba masa ido har sai da ya bude nasa idon ya kalleta. Sai ta cire dankwalin dake kanta kananan kitson dake kanta suka bayyana, numfashi ya sauke a hankali ya hade yawu slowly, yana marmarin abun da ya kwashe wata 8 be hada numfashi da Yusura da nufin shi ba. Bakinta ta kai saitin sansa ta san ba zai hana ta ba kuma ba zai iya gujewa haka ba, in less than second he lost control again. Hannayensa ya cire daga aljihun ya rumgumeta ya fara mayar mata da martani tun suna tsaye har tsayin ya gagara suka zauna daga bisani suka canja musalli daga Sitting room to Bedroom... NOOR POV. Ban kwanta da nufin farkawa ba, fata na yi idan na kwanta kamin safiya Allah ya karbi rayuwa. Sanin yau ce ranar daurin aurena sai nake ji kamar ranar mutuwa zata fi min farinciki fiye da wannan ranar da za'a daure da igiyyoyin aure. Misalin karfe bakwai na safe Anty Larai ta kawo min wani kaza mai tsananin daci wai na cinye ni kadai kuma kar na rage ko kadan. Tana fita na na saka yara suka debo min ruwa a bota na na nade kazar a dankwali na shiga bandaki na jefa a shadda sannan na dawo dakin na zauna kamar na ci. Ba a jima ba aka sake zuwa da mota aka dauke ni zuwa gidan wata mai lallen. Ban dawo ba sai Azahar bata min da yawa ba amman yayi matukar kyau domin kwarariya ce mai yi ma mare kunshi. A lokacin da na dawo gidan na tarar da yan'uwan mahaifiyata suka fara shigowa sai kewarta ta kama ni, na ji ina ma ace tana kusa da ni wata kila zan ji sanyi fiye da kuncin da nake ji a yanzu, a jikin Mama Shafa na kwanta kaina na ciwo sosai kamar zai rabe gida biyu, hakan kuma ba zai rasa nabasa da rashin samun bachi da kuma tunanin da ke kokarin fi karfin kwakwalwata. Ban damu da sanin yaushe daurin auren ba abun da kawai na sani shi ne yau za a daura auren ko ma aka daura. Domin ban dade da shigowa ba ina daga kwancen a cinyar Mama Shafa na hango shigowar Yaya da Baba da kuma wasu daga cikin iyayena maza cikin shiga ta manya kaya sai gabana ya fadi, kuka ya rufe ni na kasa rike kaina ina ta kuka sosai jikina ya fara rawa numfashi yana fita da karfi. Wai yau da wani aka daura aurena ba da Zafeer ba Wallahi ban taba tsammanin haka ba. Yan'uwan Mama suka yi ta rarrashina suna kwantar min da hankali har suka samu na yi shiru sai dai na ci kuka kuma kuka ya ci ni har idanuwa sun sauya kala. Har aka ci aka cinye ni dai bana wani kwarran motsi kuma bana da walwala balle sakewa ga wani irin tsoro da fargaba da ya rufe ni. Ba yi wani wuni da na ga saurin karewarta irin ranar yau Assabar, kan kace kwabo har hudu ya fara shigowa ana maganar a tafi da ni na yi wanka na shirya kamin masu daukar amarya su ta iso. Wani gidan na makota aka tafi da ni, amman na kasa wanka haka na zauna a bandakin ina ta rusar kuka har aka gaji da jira aka shigo aka fita da ni. Haka na sake saka wasu tufafin ba tare da na yi wanka ba domin bana iya komai babu kuzari a tare ba. Na samu kaina cikin wani irin rashin hankali da bakinciki na rabuwa da wanda nake so da kuma auren wanda bana so! Ashe haka abun yake ashe haka ake ji, wata sabuwar rayuwa zan shiga wani matsayi zan taka amman ba da wanda nake mafarki ba. Wani ya zo ya mana shigar rago ya shafe tarihin da muka so kafawa, ya rusa gina da muka fara, ya dauki ajiyar da ba ta shi ba. Bakinciki be kara rufe ni ba, sai da Baba ya tsaya kai da fata akan cewar ba za tafi dani gurin Mama da sunan ta yi min huduwar aure ba, idan ba zata tako ta zo ba to be yarda akai ni, duk yadda dangin mahaifiyata da wasu daga danginsa suka so ya bari na tafi hakan ya ci tura, domin Baba murdadden mutum ne idan y tsaya kan abu baya sauya. Ina ji ina gani aka hana ni ganin uwata har yan'uwan Mama suka fusata suka yi fada da Baba kacha kacha babu dadi. Bayan sun tafi na koma jikin Hana ta rumgume ni ita kuka ni kuka. Yaya ya shigo dakin ya mika min wayar “Ga Mama zata yi magana da ke” Na karbi wayar na kara a kunne na saka hannu biyu na dafeta a kunnena na kwanta a kasa ina jin kamar ina kwance a jikinta ne... “Mama... Mamma... Mma... Mmama... Ma” Na fada cikin wani irin kuka mai sarke numfashi. “Noor ki yi hakuri haka Allah ya kaddara, kuma ki yi biyayya ga mijinki ni na yafe miki duk abun da kika min, Allah ya miki albarka... Ki roki kowa yafiya haka ake idan za'ayi aure” Daga karshe sai ta fashe da kuka ni ma na fashe da kuka ina kiran sunanta. Bayan ta kashe ya dago na mikawa Yaya wayarsa. “Yaya dan Allah kai ma ka yafe min” Ya rage tsawonsa ya rumgume ni. “Na yafe miki Noor, na fi kowa son farincikinki, Allah ya auren wannan shi ne mafi alheri fiye da Zafeer shi kuma ya ba shi wata wadda ta fiki zama alheri a gareshi, ki yi hakuri Noor kin ji ki yi hakuri” Na sha kuka a jikinsa sosai sannan ya sake ni ya fita, Hana kam kasa ce mata komai na yi ni da ita muka rika kuka kamar an mana mutuwa muna rumgume da juna. Har sai da Baba ya shigo ya fara min huduba tare da yan'uwansa shi ma na roke shi yafiya ya yafe ya saka min albarka da addu'ar Allah yasa gurin zamana ne. Manya motoci na alfarma aka jera daga kofar gidanmu zuwa gidansu Zainab, gurin fitowa da ni ne ya zama aiki na kama Hana na rike gam ita ma ta rike ni daker aka banbare ni a jikinta aka saka ni motar, kuka be barta ta bi ni ba sai Gwaggwani da suka shiga motar tare da ni suna min fada wai sai kace kaina farau aure ina wannan kukan na tashin hankali. Daga gidanmu aka dauke ni zuwa gidan da za a rusa farincikin. I have few pages for book 2 ragowar Pages din na wadanda suka biya ne. If you want to subscribe Pay 500 to Zenith Bank Hadiza Abubakar 2451879008 Or 6484787074 Khadeeja Candy Moneypoint And send the evidence of payment to 08036126660 See you🥰✌🏻 #KhadeejaCandy PAID PAGE 4️⃣ ©KhadeejaCandy ©®Copyright 2024 Littafin nan na kudi ne, don't read if you didn't pay... One word kika karanta baki biya ni ba, ban yafe hakkina ba. To be part of the journey pay 500 to 2451879008 ZenithBank Hadiza Abubakar And send the evidence of payment to my WhatsApp number 08036126660.... You can read my latest update on arewabooks a handle dina @KhadeejaCandy https://www.arewabooks.com/book?id=659a94c8be87d7a51f831153 _______•••_______ Zaunawa yayi bakin gadon yana kallona. “Noor dan Allah ki kwantar da hankalinki, abun nan be kai yadda kike tunani ba, kuma ke ba fa jaririya ba ce da za ace idan zan matsa kusa da ki ri rika ihu kina daga hankalinki kamar yar shekara shida, haba Noor tun yaushe muke abu daya gashi har yau nake shirin barin dakinki? Hmmm i promise you i won't hurt you” Ya miko hannunsa gaba daya sai na ji hankalina ya kara tashi, ko da ace ina son shi yadda Aisha ta fada min halinshi yake da yadda zafin abun yake dole na tsorata balle kuma bana son shi. “Zo mana Noor...” Na matsa can nesa ganin ya mike tsaye, ina ganin ya doso inda nake ya rikona na fara masa ihu iyakar karfina irin da na tsira yi masa a duk lokacin da ya nuna zai yi forcing kansa a gareni, sai dai a duk lokacin da na fara ihun yana saurin saki na ya kyale ni ba kamar wannan karon ba, da ya rike sai ya rikide min kamar ba shi ba ya sakar min karfinsa na kasa motsa hannuna ma ihun kawai nake iya yi, kamin mu ji ana dukan kofa da karfi kamar za a ballata, can kuma aka dawo gurin windows din ana bugawa da karfi. Sakina yayi dan dole ba dan ya samu abun da yake so ba, ya sauka daga kan gadon ya dauki rigarsa ya saka ya bude kofar dakin ya fita, ni kuma na tashi zaune na gyara rigata na ina jan numfashi da karfi. Aisha ce ta shigo dakin da gudunta “Noor Lafiya?” Na rumgume jikina ina hawaye sai ta juya ta kalleshi. “Barristers miye haka? Da yamma haka? Wane irin rashin hakuri ne? Sati daya da aka yi a bangarenta be wadatar da kai ba sai ka nuna mata fin karfi da ido na ganin ido? Kowa ya san halin da kuke ciki? Mai gadi ne fa ya fada min ihun da yake ji a nan yayi yawa naje na duba? Yanzu wannan ba abun kunya ba ne? Kuma duk zaman da ka yi be wadatar ba sai ka shiga hakkina? Yau fa zaka bar nan, daga yin auren kuma sai ka fara abu kamar karamin yaro ko wanda ya fita hayyacinsa? Me kake haka Barristers kanka farau auren budurwa?” Ta fashe da kuka ta fice daga dakin, sai ya juyo ya watso min wani mugun kallo. “Kin ga abun da kika ja ko?” Na sauke kaina kasa. “Ke wai wace irin yarinya ce? Wawuya kawai sakarya, marar hankali marar tarbiya” Uffan ban ce masa ba, ba dan kuma bana jin zafin kalaman nasa ba, sai dan na san nice marar gaskiya a nan, be kamata na yi ihu ba amman kuma kiyayyarsa da tsoron da matarsa ta ba ni ba zai bari na zame masa yadda yake so ba. A fusace ya fice daga dakin, ni kuma na kwanta a gurin ban tashi ba sai da aka yi kiran sallah Magariba bayan na yi sallah na fito daga dakin na sai na samu plate din abincin da ya zuba a dazun aje a gurin, kadan na ci na ji gishiri kamar zai yanka halshena da sauri na zubar kasa na kasa hadewa na nufi kitchen da sauri ina taba kofar na ji ta a rufe da makulli a dole na dawo dakina na shiga bandaki na wanke bakina ina mamakin yadda gishiri yayi yawa haka domin na dandana abinci a lokacin da na gama girkin ban ji gishiri haka ba. Dawowa na yi na zauna a dakina domin zuciyata bata raya min cewar Aisha zata iya kara min gishiri a abinci ba balle na zarge ta, da ma dai ace bama zaman lafiya ne, wata kila kuma jika yayi a yanzu shiyasa yayi yawa. Bayan sallah Isha'i na sake fita na taba kofar kitchen din sai na same ta a rufe da alama da Hafiz ya rufe kitchen yayi tafiyarsa ya bar ni da yunwar cikina. Ni nake kamar zan iya jurewa na dan lokaci ne zai hakura ya dawo min da keys din ko kuma ya shigo ya bude min idan ya gaji. Saboda haka na shiga dakina na kwanta cikin tsoro domin wannan ne karo na biyu da na kwanta ni kadai a bangaren bayan kwanan da na yi na daren farko a gidan. Washe Gari na farka da tunanin yadda za'ayi ni ma kanwata Hana ta zo ta rika taya ni bachi idan baya bangarena saboda na rage kadaici kamar yadda ita ma kanwarta Ni'ima take tayata kwana, na yi ta jiran tsammanin ko ko Hafiz zai leko bangare ya duba lafiya kamar yadda yake duba lafiyar Aisha kullum amman shiru ko da yake ni idan yana nawa bangaren yaransa ne suke tashinmu daga bachin safe da muke komawa, yau kuma yana bangaresu wata kila shiyasa be leko nan ba, ko kuma dai fushi yake ne har yanzu be sauko ba? Domin jiyan nan na bata masa rai sosai, to me ya kamata na yi na bashi hakuri? Ko kuma na share shi idan ya gaji ya zo? Ni kadai nake ta sake sake na na rasa makama. Shiru shiru be shigo ba matarsa ma bata leko ni har azahar gashi yunwa sai cini take daman na kwana da ita. Sai kusan uku na rana sannan ya fita ina ganin haka na jikina ya mutu kuma na gane kuskuren abun da na aikata. Falon na dawo na zauna ina jin wata azzababiyar yunwa gashi babu kudi hannuna balle na siya wani abu kuma kitchen da rufe balle na saffara wani abu. A wani taimako na Allah sai ga matarsa ta shigo da sauri bangarena da far'ata kamar kullum ni kuma na dube irin duba na yar'uwa. “Kanwata ya kike?” “Lafiya kalau” Ta yi fuskar tausayi. “Wallahi ina can amman zuciyata na tare da ke ina tausayinki sosai, na san kin sha yunwa yau ko?” Na daga mata kai. “Ya ji haushina jiya ko? Ina son na bashi hakuri amman ban san ya zan yi ba, na ga har ya rufe kitchen din ya tafi da key din haka na kwana da yunwa” “Allah sarki, gashi ya rantse kar na baki abincin da na dafa, saboda na fada masa da ke zan dafa” Na ji babu dadi kamar na yi kuka kuma dai na daure kar na zubar da hawaye a gabanta. “Aisha ki ce yayi hakuri” “Zan fada masa amman ke karki yi saurin ba shi hakuri ki zubar da ajinki, yanzu kin san yadda zamu yi ga kudi 5k ki tafi ki siyo abinci a waje ki dawo ki ci” Na zaro ido da sauri gabana na faduwa. “Aa ba zan iya ba, jiya fa a gabanki na ce zan fita kin ga yadda yake fada shi ne sanadin ma duk wannan abun balle kuma ace na fita be sani ba” “To zaunawa zaki yi yunwa ta kashe ki Noor? Ya tafi da keys din kuma ya rantse kar na baki abincinsa kuma ya fita ya fada min sai bayan Isha'i zai dawo saboda gurin Hajiyarsa zai tafi na bashi abinci ya tafi mata da shi” Na kalli kudin sannan na girgiza mata kai. “Ba zan iya ba, be kamata na fita be sani ba balle kuma ace siyen abinci zai yi fada idan ya ji” “Taya zai ji? Ba zan fada masa ba” Na girgiza kai na lake kafada. “Ni dai ba zan je ba” “Shikenan ni daman saboda ina tausayinki ne, bari na aje kudin” “Sai idan ba a bawa mai gadi ya siyo min” “Maigadin kuma? Ai ba zai yiyu ki aike shi ba, ba zai ma tafi ba saboda gadi yake yi kuma zai iya fadawa Barrister” “Ni dai ba zan iya tafiya ba, sai dai ko ke idan zaki siyo min” “Ni kuma? Da ciki dako dako na tafi siyo miki abinci.? Ina laifina na tausaya miki Allah ya baki hakuri” Ta mayarda kudinta ya fice daga falon, ni kuma na koma na kwanta ina jin yunwar na min yawo a cikin, haka na kwana da wahala da kuka da bakinciki wata zuciyar na cewa na tafi na karbi kudin na siyo abinci domin ba ni da wata mafita bayan wannan, wata zuciyar kuma na fada min na tafi kawai na bashi hakuri kuma na fada masa ina jin yunwa ya ba ni key na dafa abinci domin alama ta nuna ba zai shigo bangaren nawa ba ya duba ni tun da gashi har dare yayi be shigo ba kuma ya dawo. Na tashi ina jin jiri na fita daga bangaren nawa ina sanye da atamfa riga da zane na shiga bangaren Aisha na samu yaranta suna ta wasa a falon ita kuma tana bare giďa. Da far'a ta tarbe ni ta dakawa yaranta tsawa wai su gaishe ni haka suka gaishe ni jikinsu na rawa na amsa ina zaunawa, kana ganina ka san yunwa ta ci ni har ta gaji. “Lafiya Amarya?” “Hafiz yana nan?” Yaransa duk suka kalleni jin na fadi sunan mahaifinsu kai tsaye. “Eh yana nan? A kira Miki shi?” “Eh ina son na yi magana da shi” “Toh” Ta aje plate din giďar ta tashi ta shiga dakinta, bata wani jima ba ta fito ta ce min. “Yace ki jira shi zai yi wanka” “Tohm” Na amsa idanuwana kamar za su yi magana tsabar yunwa dake matsa min lamba. Haka suka bar ni a gurin tun ina jiran fitowarsa har na fara bachi.... Ko da na farka babu kowa a falon sai ni kadai, tashi na yi na kamar zan fadi na fice daga falon na dawo bangarena ina kuka. Indai har horo ne Hafiz ne Wallahi na horu daga jiya zuwa yau kawai... **** **** **** Yusura na kokarin aje remote din hannunta akan Center table ta dago tana amsa sallamar da Safeena take yi. “Wa'alaikusalam” “Sannu da gida” “Yauwa sannu dai” Safeena ta maida kofar falon ta rufe ta shigo cikin falon ba tare da an yi mata izini ba ta zauna a kujera. “Kin gane ni kuwa?” Yusura ta yi murmushi yake. “Ta ina fuskarki zata bace min? Safeena Right” Safeena ta yi murmushi. “Haka ne, na ga kamar ba jiya ba ne abun, ya gida ya karin hakuri? Na zo gaisuwar Momy ne” “Gaisuwa...? Ko dai murna?” Cewar Yusura babu alamar wasa a maganarta. “Ah haba Subhanallahi ana murnar mutuwa ne? Hana dai Yusura sai kace wata kafura” “Na ga abubuwa sun yi ta faruwa ba ki taba zuwa ba, kamar haihuwata sau biyu ina haihuwa da Kareem amman baki zo mana barka ba, sai yanzu?” “Ban ji ba ne, amman ita mutuwa kin san ba a sanarwarta ni fa gaisuwa kawai na zo, ba fada ba ina tunanin yanzu duk mun girma mun zama manya har da yara” Yusura ta yi murmushi. “Haka ne, baya gida amman ki jira shi ba jimawa zai shigo sai ku gaisa” Ta mike tsaye ta haye dama Safeena ta bita da harara tana jin wani masifaffin kishi na cinta. Yusura na shiga dakinta ta fara safa da marwa tana cizon bakinta gaba daya ta ma rasa gane hikimar zuwan Safeena gidan, ko bata rantse ba ta san Safeena ta yi farinciki da mutuwar Momy domin tana cikin manyan makiyanta da suka hana Kareem aurenta. Kasa zama ta yi har sai da ta hango tsayawar motar Kareem a gurin da ya saba tsayuwa sannan ta nufi kofar dakin ta fita, ta san be kamata ta nuna kishi ba domin ba son Kareem take ba, but abun da Safeena ta yi a yanzu kamar cin fuska ne da mutuncinta, kuma idan har Momy zata tsani Safeena ita kuwa bata san dalilinta na kaunarta ba, zuwanta kuma ya nuna ta jidadin mutuwar Momy if not ai tana da number wayarsa sai ta kira shi ta yi masa gaisuwa ko kuma ta same shi a wani gurin. KAREEM POV. A lokacin da ya faka motarsa ya lura da wata bakuwar mota fake a kusa da Entrance din shiga falonsu. Be raba dayan biyu ba ko dai yar'uwarsa ko kuma yan'uwan Yusura ta bangaren uba ne suka zo gaisuwa ko ziyara, ba tare da fargabar komai ba ya shiga falon. Yana rufe kofar Falon Yusura na saukowa ta karaso gurinsa ta karbi Keys din hannunsa da ledar hannunsa tana murmushi kamar ba ita ba, sai kuma ta sumbanci bakinsa. “Sannu da zuwa...” Safeena na kallonsu ta ji kamar ta kama da wuta, Kareem kam be lura da Safeena sai kallon matarsa yake yana mamakin inda wannan ya samo asali. “Ga Safeena ta zo gaisuwa” Ya juya ya kalli saitin da Safeena take zaune tana ci da wuta. Ya tako ya karaso gurin da take zaune da mamaki a fuskarsa. “Safeena? Me kika zo yi nan?” “Gaisuwa...” Ta amsa daker numfashinta na gargada. Ya kalli Yusura sannan ya sake kallon Safeena “Ashe Momy lokaci yayi” “Haka Allah ya so” “Allah ya mata rahama, ya bada hakuri zan tafi” Ta dauki jakarta ta mike tsaye ta fara tafiya kamar wadda ta rikice. “Ka rakata mata, amman karka dade ka ji Babyna... Bari na hada maka ruwan wanka” Kareem ya kalleta sai ta sakar masa murmushi tana masa alama da ya amsa da gira. “Okay...” Ya amsa With so many questions da yake bukatar amsarsu. Sannan ya juya ya bi bayan Safeena da ke tsaye jikin kofar tana jin komai. Rufe kofar falon yayi suka sauka kasa. “Wannan ya zama na farko kuma na karshe da zaki sake tako kafarki a gidana, ba zan daukar miki wannan ba” “Me yasa ka yi min karya? Kace kai da Yusura baku zaman lafiya, kalli yadda ta tarbeka a gaban idona? Da far'a da soyayya, shiyasa gaba daya ka canja min, tun kamin Momy ta rasu daker na samu kanka yanzu kuma baka amsa kirana baka mayar min da amsar sakona” “Safeena ina cikin jimami na rashin Momy a yanzu, bana bukatar wata maganar, abu na biyu kuma ki natsu ki fara tunanin yayanki da mijinki ki cire ni a rayuwarki... Na gane baki da hankali shiyasa har kika tunanin kashe aurenki ki bar yaranki ki dawo gareni, yanzu kuma abun ya wuce da har kin kai ki tako kafarki a gida? Ba zan daukar miki wannan ba, ban hada iyalina da kowa ba” “Idan na ce zan aikata wani abu akanka Kareem baka ganewa, baka amsa kirana kana ta kokarin kauce min a lokacin da nake da tsananin bukatar saka ka farinciki, da kana kula ni da ban zo gidan nan ba, na riga na sabu da kai, na cutu da soyayyarka ba zan oya warkewa ba amman a haka a mahaukaciya kake kallona?” “Taya mahaifiyata zata hane ni da abu na aikata? Taya tana raye zata hana ni aurenki yanzu kuma bayan ta mutu kike tunanin zan iya cigaba da wani mu'amala da ke? Safeena wake-up ki cireni a rayuwarki and i mean it....” Ya bar ta tsaye a gurin ya rufe kofar falon ya shige ciki. “Aurenta ya mutu ne?” Ita ce tambayar da Yusura ta fara yi masa a lokacin da ya shigo falon. Be tunanin ta yi labe ta saurari abun da suke tattaunawa sai idan zuwanta a gidan ne ya bata mamaki. “Me ye ma'anar abun da kika yi?” Ta mike tsaye tana kallonsa. “Irin abun da muka saba yi ne, a duk lokacin da baki suka zo, nuna cewar muna cikin soyayya da kaunar juna. Aurenta ya mutu ne ko kuma kashewa zata yi ta aureka saboda macen da ta yi mata karan tsaye ta bar mata duniyar?” “Miye matsalarki da hakan?” “Kana tunanin zan so abun da Momy ta ki? Har abada...! Ka fada mata kar ta sake zuwa gidan nan ba saboda ni ba saboda yaranka” Ta aje masa keys dinsa da ledar dake hannunta a kujera ta nufi stairs, binta yayi da kallo har ta haye sannan ya zauna yana kai hannunsa ya taba hancinsa. “Kai Mata kuna da wuyar sha'ani” Ya sauke ajiyar zuciya ya mike tsaye ya dauki ledarsa da keys din ya haura sama ya shiga dakinsa... #KhadeejaCandy https://chat.whatsapp.com/Jd2OwsAcXE7EjI7NHeFQV0 Assalamu Alaikum... Ina talata muku KHADEEJA CANDY STORE 🥰🙌 Muna siyar da Atamfa, Laces, Mayafai, Talkami da Jaka, Akwaituna, Kayan Kitchen, Zanen Gado, da kuma kayan kawata gida ko falo. ✧✦ 𝗧𝗔 Ƙ𝗜 𝗭𝗔𝗠𝗔𝗡 𝗔𝗨𝗥𝗘 ✦✧ 𝗕𝘆 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆 *Book 2 - Last free Chapter* KAREEM POV. Misalin karfe goma sha daya na dare ya sauko da kafafuwansa daga kan gadon yana kallon dakin kamar bakonsa. Kamin ya juya ya kalli Safeena da ta fara bachi, ya samu gamsuwa sosai sai dai kuma jindadin ya wuce zunubin yana nan, ya sake komawa ruwa, daman abu ne mai wahala idan namiji ya fara aron hannu ya daina, ko da kuwa yana samun kulawa a gurin matarsa balle kuma shi. Mikewa yayi tsaye ya nufi bandaki, sai da yayi wanka sannan ya fito ya mayarda tufafin da ya cire ya dauki wayarsa dake ta ringing a dazun amman shaidanci ya dauke masa hankali ya kasa duba wayar ma balle ya amsa. Ganin Miss calls daga Daddy da Khadija da kuma Aryam ya daga masa hankali sosai. “Lafiya?” Ya tambaye kanshi, Safeena ta dago ta kalleshi. “Me ya faru?” Kamin ya amsa mata kiran Hafix ya shigo wayarsa, ya amsa da sauri ya kara a kunne. “Hello...” “Kareem na dauka ba zaka sake komawa ruwa ba?” “Kamar ya?” “Saboda me zaka yi karya da ni ka je ka aikata alfasha? Kai da bakinka ka fada min yanzu babu ruwanka da Safeena saboda me zaka koma?” “Ka yi hasashenka akan kuskure bana tare da Safeena yanzu” “Ita kadai ce ta kai ka kebe da ita a irin wannan lokacin Kareem na san waye kai” “Shi kenan kuma idan na kebe da ita sai zuciya ta raya maka wani abun muke aikatawa?” “Muryarta ma haramun ne a gareka, idan kuma lada zaka samu sai ka fada min” Kareem yayi shiru yana kallon Safeena wadda ta tashi zaune tana kallonsa ba tare da ta rufe jikinta ba. “Momy bata da lafiya kuma jikin yayi tsanani tana asibiti, an kira wayarka baka daga ba sun kira suka tambaye kana ina nace ina tare da kai, ka zo ka dauke ni mu je” Jikin Kareem yayi sanyi gabansa ya hau duka tashin hankali kuma ya baibaye shi jin cewar jikin Momy yayi tsanani. “Okay” Ya furta da sauri sannan ya saka wayar aljihu ya nufi Wallet dinsa da keys din mota ya dauka ya dauko agogonsa be tsaya sakawa ba ya rike a hannu. “Lafiya? Na ga hankalinka kamar ya tashi...” Ya juyo ya kalleta a wani yanayi da ya fi kama da bacin rai ko damuwa. Sai kuma ya hade yawu ya juya zai tafi. “Hankalinka fa a tashe yake Kareem” Ta sake fada sai ya juyo ya fuskance ta. “Kullum hankalina a tashe yake Safeena, tun daga lokacin da muka fada a ramen wuta ni da ke, nake tsoro da fargabar kar na mutu a haka, kullum burin Hafiz na kauce daga wannan hanyar da na dora kaina kuma he's right, ba abu ne mai kyau ba, yanzu gashi saboda ke an kai Momy Asibiti ba tare da ni ba, ina kokarin ganin na kauce daga sabo amman yau kin rusa wannan kudin na wa, kina amfani da weakness dina kina jefa kanki da kai a halaka, baki tunanin future dinki da yaranki da makomarki?” “My future is You...” Ta amsa da karfi sannan ta sauko daga kan gadon ta dauki tawul ta daura. “Yarana mijina ba su ne a gabana ba, burina nake son samu muradina nake ta hasashe, kuma kai ne, Idan ma ka gaji da wannan rayuwar da muke yi toh mu yi aure mana, daman ai ba son Yusura kake ba, toh mu yi aure ni da kai muna son junanmu” Da mamaki yake kallonta. “Auren da yake kanki fa?” “Zan cire na aje, na auri Abdull ne saboda rashinka, auren farko ka bi umarnin Momy ka yi yadda take so ita ma yanzu ai ya kamata ta so abun da kake so” Ya matsa kusa da ita. “Saboda ita ta haifeni ba ni na haife ta, Karki sake fadin sunan Momy da wani abun a bakinki” Yana kaiwa nan ya fice daga dakin ya fito da gaggawa ya shiga motarsa maigadinsa har ya fara bachi ya tashi ya bude masa gate. Kareem ya fice da sauri gidan Hafiz ya nufo a bakin gate ya tsaya ya kira shi a waya ya sanar masa yana waje. Babu bata lokaci Hafiz ya fito daga gidansa take ta kamshin sabon fentin da aka yi yau ya bude motar Kareem ya shiga. “Muna daf da samun matsala da kai Kareem, matukar baka rabu da Safeena ba, ba zan iya cigaba da zama da abokin da zai kansa wuta ba” “Barrister...” Hafix ya daga masa hannu yana rufe da fada rai a bace. “Babu wani reason da zaka fada min, duk abun da kake ta son zuciya kake aikata shi, babu yadda ban yi ba saboda ka auri Noor, abun da nake maka hange rabuwa da Safeena da samu salama ta bangaren Yusura, amman ka watsa min kasa a ido, ka daure ni ka daure yarinyar nan a gurin ubanta, gobe za a daura auren nan amman idan na tuna da yarinyar nan bata so na hakan yana daga min hankali” Kareem be sake yunkurin sake furta komai ba, yana da tabbacin Hafiz ba zai fahimce shi ba nacewar baya son auren macen da bata sonshi kuma ba zai fahimci irin halin da yake ciki ba da har saka shi komawa ruwa tare da Safeena. “Idan kuma ita Safeena kake so ta kashe aurenta ka aureta ya fi ku yi ta aikata alfasha haka nan” Wannan karon Kareem ya amsa with full confidence. “Ba zan iya auren macen da ba zata iya tsare kanta da mutuncinta ba, ba zan auri macen da yarana za su zama b damuwarta ba, bana son mace mai irin tunani da zuciyar Safeena yanzu, ta riga ta zubar da kamarta a idona” Hafiz ya kalleshi “Amman kana son jikinta?” “Wannan jikinta ne ita ta bani a kyauta, da farko ina tausayin yarinyar nan amman yau ta ba ni mamaki, ba Allah a zuciyar Safeena” Hafiz yayi wata yar siririyar dariya. “I'm glad ka fara ganewa next time sai ka kiyayeta” Daga haka ba Kareem be sake cewa komai ba har suka isa Asibiti. Ya san gurin da ake yawan aje ta sai dai ba shi da tabbacin dakin da aka aje ta har sai da ya bincika. Waje ya tarar da Aryam da Khadija da Abokiyar Zamanta wacce ta kasance tamkar yar'uwa a gareta, Yusura kuma tana tsaye jikin kofar saboda an hana kowa shiga dakin, idonta har ya kumbura kuma still hawaye take kana kallonta ka san a firgice take irin firgita nan na mai tsoron mummunan labari. Kareem ya rage tafiyar da yake yana kallon yanayinsu gabansa yana dukan uku uku, Hafiz ya karasa gurin Aryam. “Wani abun ne ya faru?” “Aa jikin ne dai yayi tsananin, sosai ko da muka kawo ta nan bata san inda take ba” Sai a lokacin Kareem ya samu kuzarin karasowa gurin ya tambaya dalilin tashin ciwon. “Fitarka babu jimawa ta ce tana jin jiri jikin ya kara zafi sosai, 2 hours later ta fara Innalillahi Wa'inna Ilaihirraji'un in less than 5 minutes ta rikice mana, amman yanzu likitocin sun saka mata oxygen sun mata allura amman dai sun hana mu shiga mu dubata” Kareem na jin haka ya nufi dakin da Momy take ya tura ya shiga. Hankalinsa ya tashi sosai fiye da yadda ya saba ganinta a halin ciwon, ba wannan ne karon farko da aka saka mata oxygen ba kuma ba wannan ne karon farko da take shiga matsananin hali irin wannan ba. Amman wannan ne karon farko da ya kasa ganin bakin idonta sai zallar farin kawai, jikinta yayi fari ba irin farin fata nutural ba, irin farin nan mai ban tsoro, and kokarin da likiton suke na gano jijiyarda za a saka mata drip ya gagara. Juyowa yayi ya fito jiki a mace kamar ba likita ba, ya saba ganin irin wannan amman ya kasa dauka na mahaifiyarsa ya kasa jure kallon yadda ake ta neman jijiyar. “Da Sauki?” Yusura ta tambaya hawaye na sauko mata. Kallonta kawai yayi ya dauke kai be ce mata komai ba. “Ka fada min mana Kareem” Wannan karon jikinta har rawa yake kamar zata fadi. Kareem ya karasa kusa da matarsa ya rikata sai ta kwanto jikinsa tana numfashi da karfi, ji take ba zata iya daukar rashin macen da ta zame mata uwa da uba a lokaci daya, even though tana ganin kamar mutuwar Momy mafita a gareta but da abun ya zo mata a gaske yau din sai ta ji shi a dabam. “Da sauki, likitocin suna bata taimako da ya dace” Ta sassauta numfashi yana sauke ajiyar zuciya. Mayar da numfashi da zata yi sai ta maida tare da wani kamshin turaren da tabbatar ba na shi ba ne, ko da bata shiga jikinsa kullum ta san kalar kamshin da mijinta yake yi, domin turarensa irin mai sanar da isowarsa ne tun kam ya karaso a guri idan kuma ya bar guri zai bar kamshin ne for the whole day, and the most curious thing is turaren ya fi yi mata kama da na mata. In a curious manner ta dago daga jikinsa ta kalli fuskarsa sai ta tarar ita yake kallo. In a low voice ya ce. “Why are you faked it?” “Why do you hug me then?” Ya dauke hannayensa daga jikinta ya kauce daga inda take tsaye ya nufi gurin da Hafiz yake ya zauna. “Na dauka ciki zaka koma ko zaka iya bata wani taimako?” “Ba zan iya ba Hafiz I'm scared” “Scared...?” Hafiz ya maimaita cike da fahimtar inda Kareem ya nufa. Hafiz ya daga hannunsa ya dafa abokinsa. “Zata samu sauki da yardar Allah” Kareem ya daga kai cike da karfin hali. Kusan gaba daya dayansu a asibitin suka kwana daga Aryam har Khadija da Yusura da Hafiz da ya kasa tafiya ya bar abokinsa a halin da ya fi bukatarsa. Har garin Allah ya waye babu wanda ya samu shiga dakin sai Kareem shi ma dan yana likita ne. Shi ya kwana da ita bayan an yi nasarar samun jijiyar hannunta an saka mata drip. Sai bayan da suka yi sallah asuba suka ka jikinta d sauki sannan Hafix na koma gida Aryam ya tafi Yusura ma aka aka bar Hajiya da Kareem a gurinta da kuma autarta Khadija. Dalilin ciwon Momy ya hana Kareem halarta daurin auren abokinsa da aka gabatar a washe garin Ranar ta assabar, be je daukar amarya ba ba da shi aka kai ango ba. Daman kuma be jin zai iya yin haka ba ko da babu dalilin ciwon Momy. Around 5pm Kareem na zaune kusa da Momy yana bata ruwan zamzam a baki a hankali Aryam Khadija ta mike tsaye ta dauki kulolin abincin da aka kawo da safe ta fara sakawa a basket. “Gida zaki tafi Khadija?” Hajiya ta tambaya tana rike da karbinta, Hajj Farisa ma dake zaune kusa da Hajiyar ta kalleta. “Eh kayan abincin zan tafi da su” Kareem ya mike tsaye ya cire Lapcoat dinsa ya mika mata. “Wuce da ita gida, ki dauko wata” “Daman ba a nan kuke bari kayan ba?” Hajj Farisa ta tambaya. “Ana bari amman na fi sha'awar na tafi da tawa gida, akwai ta office tana cikin office ai” Ya amsa cikin yanayi na rashin son magana. Momy ta juya ta kalli aurarta wadda ta kasance budurwa yar 200L a jami'a kamar zata yi magana amman babu hali domin tun da ta farka bata cewa kowa komai ba, an karya halshen bakin idon ya bata ya bar fari, jikin yayi sanyi ya saki da idanuwa kawai take iya bin mutane da kallo, tun daga yan'uwanta dake ta shigowa da safe har zuwa yanzu idan an mata sannu bata amsawa sai dai ta daga kai, kuma komai aka saka mata bata iya hadewa dawo mata yake. “Kai ba zaka tafi gida ka huta ba Kareem tun jiya kake a nan fa” Hajiya ta fada cike da tausayinsa domin shi ne mai damuwa sosai fiye da yan'uwansa. Hajj Farisa ta sauke ajiyar ta ce. “Ya kamata kam ka tafi ka huta Kareem” “Hajiya ku bar ni nan, hankalina zai fi kwanciya idan ina kusa da ita fiye da gidan, idan ma na koma ba wani abu zan yi ba” Momy ta kalleshi ta yi murmushi, shi ma murmushin ya mayar mata sai ta kai hannu ta taba fuskarsa. “Allah ya maka albarka... Ya hada kanku” Ta fada cikin wani irin furuci mai daga hankali da tsoratarwa, domin maganar nata be fita sosai. Hajj Farisa da Hajiya suka taso da sauri suna kallonta. Momy ta juyar da kanta ta kalli abokiyar zamanta wadda ta zame mata kamar yar'uwa. “Ga amana nan mai nauyi na baki, na san kin riga a ido balle kuma bayan idon zaki kyautata, Musamman Khadija yarinya ce karama bata gama mallakar hankalin kanta ba” Khadija ta saki kayan dake hannunta ta fashe da kuka. “Haba Yaya ki daina wannan Maganar dan Allah zaki tashi da yardar Allah zaki yi ma yarki aure da kanki har jikokinki za ki gani” Hajiya Hassana ta fada tana kuka. Hajj Farisa ma ta saka kuka. Kareem ya aje ruwan zamzam din dake hannunsa ya rike hannunta. “Momy akwai mai binki bashi ko kike bi?” Ta kalleshi na tsawon dakiku sannan ta ce. “Eh Akwai Murja mai mana wanki, akwai kudinta na wata biyu a hannuna, kuma na arawa Hajiya Kudirat kudi Hassana ta san komai a gabanta aka yi” Kareem ya daga kai cike da gamsuwa zuciya kuma cike da nauyi. “Bayan wannan ba wani abu?” “Akwai filina na gado da gada gurin mahaifina, na bawa Yusura kyautar filin nan na fadawa mahaifinka kuma na rubuta Hassana kuma ta sani” “Bayan shi babu wani abu? Ko kasuwanci tsakaninki da wani ko wata?” Ta girgiza masa kai. Sai ya hade yawu mai daci ya danne zuciyarsa ya ce. “Momy ki yafe duk abun da na yi miki” “Kareem Allah ya maka albarka, ya baka yaran da za su maka biyayya fiye da yadda ka yi min, na hana ka auren wadda kake so kuma ka ha nu... ” Ta tsaya ta kalli Khadija dake kuka. “Ka auri wadda nake so, ban taba jin wani abu marar dadi a tsakaninku ba, hakan na saka na jidadi na ranta min rai” Ta juyo ta kalleshi idomsa na cika da hawaye. “Ko da zaka kara aure a gaba, karka wulakanta Yusura, Allah ya baka mai kaunarka macen kirki wadda ta dace da kai kuma wadda kake so, Allah ya muku albarka gaba dayanku, na yafe muku dukanku, Allah ya hada kanku mahaifinku ma idan akwai wani abu a tsakaninmu na yafe masa, Na yafewa Hassana na yafewa kowa ma... Ina fatar Allah ya yafe min” Bata sake cewa komai ba sai hawaye ya sauko mata. Khadija ta fada jikinta tana kuka. “Mama dan Allah ki daina wannan maganar zaki tashi da yardar Allah, karki tafi ki bar ni ina da bukatarki” Kareem ya daga ta daga jikin Momy ya rike hannunta ya fice da ita daga cikin dakin. Sai da ya rufe kofar dakin sannan ya fara yi mata magana cikin natsuwa. “Khadija, kukanki nan zai daga hankalin Momy sosai, kuma shi marar lafiya natsuwa da kwanciyar hankali yake so” “Ya Kareem baka ji abun da take fada ba?” Yayi kokarin hana hawayen idonsa fita. “Marar yana zama kamar tsoho ko yaro ne, wasu komai sai an musu, wasu kuma suka samu gushewar tunani na dan lokaci, amman ni ban ga wata alama na mutuwa a jikin Momy ba, tambayar da kika ji ina mata ina yi ne saboda na ji idan tana a cikin hayyacinta” “Da gaske Yaya?” “Likita ne ni na san irin abubuwan nan, kuma na sha haduwa da cases irin wannan” Kalamansa sun karfafa mata guiwa har ta share hawayenta. “Yanzu daga nan ki wuce gida ba zai kin koma dakin ba” “Tohm” Ta yi yadda ya bukata bata koma dakin ba ta kama hanya. Rakata yayi har sai da ta shiga adaidaita sannan ya dawo cikin asibitin, Office dinsa ya shiga ya jingina kansa a one of the visitors chair ya rufe ido. Can kuma ya kira mahaifinsa ya sannan ya nufi kujerar ya zauna.... NOOR POV. Sai da aka fara shiga da ni bangaren uwargidan aka yi mana huduba, yan'uwan mahaifina suka jadda mata amanar da suka bata, ta ba ni atamfa Julius Holland exclusive da turare, suka karba min suna godiya sannan aka shiga daki bangarene sai kamshin turare yake irin na amare. Can tsakar gadona aka zaunar da ni kaina a lullube har lokacin hawaye nake. Gwaggwanina suka sake yi min huduwa tare da kashe na kar su ji wani abu kar su gani na san waye mahaifina. Bayan sun tafi aka bar ni daga ni sai kawaye na, Zainab ce zaune a kusa da ni ta kama hannuna ta rike sai magana take ba ni tana kwantar min da hankali. “Dan Allah Noor ki bawa mara da kunya, kin ga yanzu ido yana kanki, idan baki zauna ba za a ce amanar Zafeer ce, kuma kin ga Baba ba zai miki da kyau ba, haka kuma hankalin Mama zai tashi, mutanen unguwa ma idonsu duk kanki yake dan Allah karki aikata abun da zai raba ku Noor mutumen ya nuna miki kauna kalli irin hidimar da yayi miki yayi ma mahaifinki kuma duba irin gidan da ya kawo ki” “In Shaa Allahu ba za aji wata matsala daga gareni ba, zan bawa mutane mamaki” “Allah ya ba ku zaman lafiya” Na kasa amsawa da Ameen kuma na kasa daina kukan da nake wadda ya zame min al'ada. Mun kwashe awa daya a dakin sannan aka shigo da ango, wani abun da ya ba ni mamaki shi ne, ban ga Kareem a tare da shi ba babban abokinsa, a madadin haka uwargidansa ce ta yi masa rakiya ta chaba ido na irin wanda na ga a dazun da muka shiga bangarenta ba. Kaina ya daure sosai me yasa Kareem be zo ba? Na tsammaci ganinsa har a gurin dauka balle kuma zuwa raka ango. Ta dayan bangaren kuma ina mamakin kalar zuciyar da take a kirjin matar Hafiz daman aka samu mata irinta masu yi ma miji komai babu nuna kishi ko kadan, har ma su raka ango dakin amaryarsa. Abokansa sai saka mata albarka suke suna yaba halinta, ni kuma suka ja min kunne akan na rike ta tamkar Yayata ita ma zata rike ni a matsayin kanwa. Anyi siyen baki cikin mutunci da karamci, suka bada kudi da kyautar da kawaye na ba su yi tsammani ba, abokansa suka maida kawayena gida, aka bar mu daga ni sai Hafiz sai kuma matarsa da har yanzu ban san sunanta ba bayan Madam da yake kiranta da shi. Hada mu yayi yayi mana nasiha da jan hankali akan yadda zamu mu'amalanci junanmu da kuma dora shi a hanya idan ya kauce. Ni dai har lokacin ban iya hada ido da daya daga cikinsu ita har shi. Sai dai zan iya shaidar muryarta dake fita tana jaddada akidarta ta yin adalci da rike tamkar yar'uwa. “Ni yar'uwa aka kawo min ba kishiya ba, yarinya ce karama idan ma ban rike ta amana ba ai Allah sai ya tambaye ni, kuma duk abun da zai kwantar maka da hankali kai ka sani ina son shi ko da ba zai min dadi ba, idan na ga ta yi ba daidai ba zan gyara mata ni ma idan na yi kuskure ko mantuwa sai ki tunatar da ni saboda na ankara, kuma karki biye zugar kawaye zai lalata miki zaman aurenki ne, ni ma kuma zan yi kokarin ganin ban yi haka ba. Allah ya baka ikon yi mana adalci...” Ta fashe da kuka ta tashi ta fice daga dakin da saurinta tana kuka sosai. Hannayensa na ji a jikin mayafina yana kokarin daga mayafin nawa har yayi nasarar yin haka ya kalli fuskata yana murmushi. “Amarya ayi min uzuri a gafarce ni zan tafi na lallaba yayarki, na dawo yanzu nan kin san zuciya bata da kashi...” Na daga mishi kai sai ya mike tsaye ya cire babbar rigarsa ya aje a gurin ya fice daga dakin, fitar da be dawo ba kenan har garin Allah ya waye.... __________________ Alhamdullahi a nan na kawo karshen free pages na TA KI ZAMAN AURE labari mai cike da darasi da kalubale da kuma soyayya da kunci. Me ke hana ta zaman auren ne? Hakkin Zafeer ne ko rashin dace, ko halinta ne ko kuma bakin iyayene ko dai duka hudun ne? Kun san dai ban saba ba ku kunya ba ina kokarin ganin na isar da sakon ta inda ya dace kuma ta yadda kuke so. Wannan ma dabam yake da sauran wata kila ma ya fi sauran, zabi yana gareku sai kun karanta za ku yi judging. Mai son cigaba zai biya 500 to Zenith Bank Hadiza Abubakar 2451879008 Or 6484787074 Khadeeja Candy Moneypoint And send the evidence of payment to 08036126660 za mu fara Paid Pages on Monday In shaa Allah. And za ku iya samunsa a AREWABOOKS @KhadeejaCandy karku manta ku yi following dina domin samun notifications da zarar na Update. See you🥰✌🏻 #KhadeejaCandy 08036126660 PAID PAGE 4️⃣ ©KhadeejaCandy ©®Copyright 2024 Littafin nan na kudi ne, don't read if you didn't pay... One word kika karanta baki biya ni ba, ban yafe hakkina ba. To be part of the journey pay 500 to 2451879008 ZenithBank Hadiza Abubakar And send the evidence of payment to my WhatsApp number 08036126660.... You can read my latest update on arewabooks a handle dina @KhadeejaCandy https://www.arewabooks.com/book?id=659a94c8be87d7a51f831153 _______•••_______ Zaunawa yayi bakin gadon yana kallona. “Noor dan Allah ki kwantar da hankalinki, abun nan be kai yadda kike tunani ba, kuma ke ba fa jaririya ba ce da za ace idan zan matsa kusa da ki ri rika ihu kina daga hankalinki kamar yar shekara shida, haba Noor tun yaushe muke abu daya gashi har yau nake shirin barin dakinki? Hmmm i promise you i won't hurt you” Ya miko hannunsa gaba daya sai na ji hankalina ya kara tashi, ko da ace ina son shi yadda Aisha ta fada min halinshi yake da yadda zafin abun yake dole na tsorata balle kuma bana son shi. “Zo mana Noor...” Na matsa can nesa ganin ya mike tsaye, ina ganin ya doso inda nake ya rikona na fara masa ihu iyakar karfina irin da na tsira yi masa a duk lokacin da ya nuna zai yi forcing kansa a gareni, sai dai a duk lokacin da na fara ihun yana saurin saki na ya kyale ni ba kamar wannan karon ba, da ya rike sai ya rikide min kamar ba shi ba ya sakar min karfinsa na kasa motsa hannuna ma ihun kawai nake iya yi, kamin mu ji ana dukan kofa da karfi kamar za a ballata, can kuma aka dawo gurin windows din ana bugawa da karfi. Sakina yayi dan dole ba dan ya samu abun da yake so ba, ya sauka daga kan gadon ya dauki rigarsa ya saka ya bude kofar dakin ya fita, ni kuma na tashi zaune na gyara rigata na ina jan numfashi da karfi. Aisha ce ta shigo dakin da gudunta “Noor Lafiya?” Na rumgume jikina ina hawaye sai ta juya ta kalleshi. “Barristers miye haka? Da yamma haka? Wane irin rashin hakuri ne? Sati daya da aka yi a bangarenta be wadatar da kai ba sai ka nuna mata fin karfi da ido na ganin ido? Kowa ya san halin da kuke ciki? Mai gadi ne fa ya fada min ihun da yake ji a nan yayi yawa naje na duba? Yanzu wannan ba abun kunya ba ne? Kuma duk zaman da ka yi be wadatar ba sai ka shiga hakkina? Yau fa zaka bar nan, daga yin auren kuma sai ka fara abu kamar karamin yaro ko wanda ya fita hayyacinsa? Me kake haka Barristers kanka farau auren budurwa?” Ta fashe da kuka ta fice daga dakin, sai ya juyo ya watso min wani mugun kallo. “Kin ga abun da kika ja ko?” Na sauke kaina kasa. “Ke wai wace irin yarinya ce? Wawuya kawai sakarya, marar hankali marar tarbiya” Uffan ban ce masa ba, ba dan kuma bana jin zafin kalaman nasa ba, sai dan na san nice marar gaskiya a nan, be kamata na yi ihu ba amman kuma kiyayyarsa da tsoron da matarsa ta ba ni ba zai bari na zame masa yadda yake so ba. A fusace ya fice daga dakin, ni kuma na kwanta a gurin ban tashi ba sai da aka yi kiran sallah Magariba bayan na yi sallah na fito daga dakin na sai na samu plate din abincin da ya zuba a dazun aje a gurin, kadan na ci na ji gishiri kamar zai yanka halshena da sauri na zubar kasa na kasa hadewa na nufi kitchen da sauri ina taba kofar na ji ta a rufe da makulli a dole na dawo dakina na shiga bandaki na wanke bakina ina mamakin yadda gishiri yayi yawa haka domin na dandana abinci a lokacin da na gama girkin ban ji gishiri haka ba. Dawowa na yi na zauna a dakina domin zuciyata bata raya min cewar Aisha zata iya kara min gishiri a abinci ba balle na zarge ta, da ma dai ace bama zaman lafiya ne, wata kila kuma jika yayi a yanzu shiyasa yayi yawa. Bayan sallah Isha'i na sake fita na taba kofar kitchen din sai na same ta a rufe da alama da Hafiz ya rufe kitchen yayi tafiyarsa ya bar ni da yunwar cikina. Ni nake kamar zan iya jurewa na dan lokaci ne zai hakura ya dawo min da keys din ko kuma ya shigo ya bude min idan ya gaji. Saboda haka na shiga dakina na kwanta cikin tsoro domin wannan ne karo na biyu da na kwanta ni kadai a bangaren bayan kwanan da na yi na daren farko a gidan. Washe Gari na farka da tunanin yadda za'ayi ni ma kanwata Hana ta zo ta rika taya ni bachi idan baya bangarena saboda na rage kadaici kamar yadda ita ma kanwarta Ni'ima take tayata kwana, na yi ta jiran tsammanin ko ko Hafiz zai leko bangare ya duba lafiya kamar yadda yake duba lafiyar Aisha kullum amman shiru ko da yake ni idan yana nawa bangaren yaransa ne suke tashinmu daga bachin safe da muke komawa, yau kuma yana bangaresu wata kila shiyasa be leko nan ba, ko kuma dai fushi yake ne har yanzu be sauko ba? Domin jiyan nan na bata masa rai sosai, to me ya kamata na yi na bashi hakuri? Ko kuma na share shi idan ya gaji ya zo? Ni kadai nake ta sake sake na na rasa makama. Shiru shiru be shigo ba matarsa ma bata leko ni har azahar gashi yunwa sai cini take daman na kwana da ita. Sai kusan uku na rana sannan ya fita ina ganin haka na jikina ya mutu kuma na gane kuskuren abun da na aikata. Falon na dawo na zauna ina jin wata azzababiyar yunwa gashi babu kudi hannuna balle na siya wani abu kuma kitchen da rufe balle na saffara wani abu. A wani taimako na Allah sai ga matarsa ta shigo da sauri bangarena da far'ata kamar kullum ni kuma na dube irin duba na yar'uwa. “Kanwata ya kike?” “Lafiya kalau” Ta yi fuskar tausayi. “Wallahi ina can amman zuciyata na tare da ke ina tausayinki sosai, na san kin sha yunwa yau ko?” Na daga mata kai. “Ya ji haushina jiya ko? Ina son na bashi hakuri amman ban san ya zan yi ba, na ga har ya rufe kitchen din ya tafi da key din haka na kwana da yunwa” “Allah sarki, gashi ya rantse kar na baki abincin da na dafa, saboda na fada masa da ke zan dafa” Na ji babu dadi kamar na yi kuka kuma dai na daure kar na zubar da hawaye a gabanta. “Aisha ki ce yayi hakuri” “Zan fada masa amman ke karki yi saurin ba shi hakuri ki zubar da ajinki, yanzu kin san yadda zamu yi ga kudi 5k ki tafi ki siyo abinci a waje ki dawo ki ci” Na zaro ido da sauri gabana na faduwa. “Aa ba zan iya ba, jiya fa a gabanki na ce zan fita kin ga yadda yake fada shi ne sanadin ma duk wannan abun balle kuma ace na fita be sani ba” “To zaunawa zaki yi yunwa ta kashe ki Noor? Ya tafi da keys din kuma ya rantse kar na baki abincinsa kuma ya fita ya fada min sai bayan Isha'i zai dawo saboda gurin Hajiyarsa zai tafi na bashi abinci ya tafi mata da shi” Na kalli kudin sannan na girgiza mata kai. “Ba zan iya ba, be kamata na fita be sani ba balle kuma ace siyen abinci zai yi fada idan ya ji” “Taya zai ji? Ba zan fada masa ba” Na girgiza kai na lake kafada. “Ni dai ba zan je ba” “Shikenan ni daman saboda ina tausayinki ne, bari na aje kudin” “Sai idan ba a bawa mai gadi ya siyo min” “Maigadin kuma? Ai ba zai yiyu ki aike shi ba, ba zai ma tafi ba saboda gadi yake yi kuma zai iya fadawa Barrister” “Ni dai ba zan iya tafiya ba, sai dai ko ke idan zaki siyo min” “Ni kuma? Da ciki dako dako na tafi siyo miki abinci.? Ina laifina na tausaya miki Allah ya baki hakuri” Ta mayarda kudinta ya fice daga falon, ni kuma na koma na kwanta ina jin yunwar na min yawo a cikin, haka na kwana da wahala da kuka da bakinciki wata zuciyar na cewa na tafi na karbi kudin na siyo abinci domin ba ni da wata mafita bayan wannan, wata zuciyar kuma na fada min na tafi kawai na bashi hakuri kuma na fada masa ina jin yunwa ya ba ni key na dafa abinci domin alama ta nuna ba zai shigo bangaren nawa ba ya duba ni tun da gashi har dare yayi be shigo ba kuma ya dawo. Na tashi ina jin jiri na fita daga bangaren nawa ina sanye da atamfa riga da zane na shiga bangaren Aisha na samu yaranta suna ta wasa a falon ita kuma tana bare giďa. Da far'a ta tarbe ni ta dakawa yaranta tsawa wai su gaishe ni haka suka gaishe ni jikinsu na rawa na amsa ina zaunawa, kana ganina ka san yunwa ta ci ni har ta gaji. “Lafiya Amarya?” “Hafiz yana nan?” Yaransa duk suka kalleni jin na fadi sunan mahaifinsu kai tsaye. “Eh yana nan? A kira Miki shi?” “Eh ina son na yi magana da shi” “Toh” Ta aje plate din giďar ta tashi ta shiga dakinta, bata wani jima ba ta fito ta ce min. “Yace ki jira shi zai yi wanka” “Tohm” Na amsa idanuwana kamar za su yi magana tsabar yunwa dake matsa min lamba. Haka suka bar ni a gurin tun ina jiran fitowarsa har na fara bachi.... Ko da na farka babu kowa a falon sai ni kadai, tashi na yi na kamar zan fadi na fice daga falon na dawo bangarena ina kuka. Indai har horo ne Hafiz ne Wallahi na horu daga jiya zuwa yau kawai... **** **** **** Yusura na kokarin aje remote din hannunta akan Center table ta dago tana amsa sallamar da Safeena take yi. “Wa'alaikusalam” “Sannu da gida” “Yauwa sannu dai” Safeena ta maida kofar falon ta rufe ta shigo cikin falon ba tare da an yi mata izini ba ta zauna a kujera. “Kin gane ni kuwa?” Yusura ta yi murmushi yake. “Ta ina fuskarki zata bace min? Safeena Right” Safeena ta yi murmushi. “Haka ne, na ga kamar ba jiya ba ne abun, ya gida ya karin hakuri? Na zo gaisuwar Momy ne” “Gaisuwa...? Ko dai murna?” Cewar Yusura babu alamar wasa a maganarta. “Ah haba Subhanallahi ana murnar mutuwa ne? Hana dai Yusura sai kace wata kafura” “Na ga abubuwa sun yi ta faruwa ba ki taba zuwa ba, kamar haihuwata sau biyu ina haihuwa da Kareem amman baki zo mana barka ba, sai yanzu?” “Ban ji ba ne, amman ita mutuwa kin san ba a sanarwarta ni fa gaisuwa kawai na zo, ba fada ba ina tunanin yanzu duk mun girma mun zama manya har da yara” Yusura ta yi murmushi. “Haka ne, baya gida amman ki jira shi ba jimawa zai shigo sai ku gaisa” Ta mike tsaye ta haye dama Safeena ta bita da harara tana jin wani masifaffin kishi na cinta. Yusura na shiga dakinta ta fara safa da marwa tana cizon bakinta gaba daya ta ma rasa gane hikimar zuwan Safeena gidan, ko bata rantse ba ta san Safeena ta yi farinciki da mutuwar Momy domin tana cikin manyan makiyanta da suka hana Kareem aurenta. Kasa zama ta yi har sai da ta hango tsayawar motar Kareem a gurin da ya saba tsayuwa sannan ta nufi kofar dakin ta fita, ta san be kamata ta nuna kishi ba domin ba son Kareem take ba, but abun da Safeena ta yi a yanzu kamar cin fuska ne da mutuncinta, kuma idan har Momy zata tsani Safeena ita kuwa bata san dalilinta na kaunarta ba, zuwanta kuma ya nuna ta jidadin mutuwar Momy if not ai tana da number wayarsa sai ta kira shi ta yi masa gaisuwa ko kuma ta same shi a wani gurin. KAREEM POV. A lokacin da ya faka motarsa ya lura da wata bakuwar mota fake a kusa da Entrance din shiga falonsu. Be raba dayan biyu ba ko dai yar'uwarsa ko kuma yan'uwan Yusura ta bangaren uba ne suka zo gaisuwa ko ziyara, ba tare da fargabar komai ba ya shiga falon. Yana rufe kofar Falon Yusura na saukowa ta karaso gurinsa ta karbi Keys din hannunsa da ledar hannunsa tana murmushi kamar ba ita ba, sai kuma ta sumbanci bakinsa. “Sannu da zuwa...” Safeena na kallonsu ta ji kamar ta kama da wuta, Kareem kam be lura da Safeena sai kallon matarsa yake yana mamakin inda wannan ya samo asali. “Ga Safeena ta zo gaisuwa” Ya juya ya kalli saitin da Safeena take zaune tana ci da wuta. Ya tako ya karaso gurin da take zaune da mamaki a fuskarsa. “Safeena? Me kika zo yi nan?” “Gaisuwa...” Ta amsa daker numfashinta na gargada. Ya kalli Yusura sannan ya sake kallon Safeena “Ashe Momy lokaci yayi” “Haka Allah ya so” “Allah ya mata rahama, ya bada hakuri zan tafi” Ta dauki jakarta ta mike tsaye ta fara tafiya kamar wadda ta rikice. “Ka rakata mata, amman karka dade ka ji Babyna... Bari na hada maka ruwan wanka” Kareem ya kalleta sai ta sakar masa murmushi tana masa alama da ya amsa da gira. “Okay...” Ya amsa With so many questions da yake bukatar amsarsu. Sannan ya juya ya bi bayan Safeena da ke tsaye jikin kofar tana jin komai. Rufe kofar falon yayi suka sauka kasa. “Wannan ya zama na farko kuma na karshe da zaki sake tako kafarki a gidana, ba zan daukar miki wannan ba” “Me yasa ka yi min karya? Kace kai da Yusura baku zaman lafiya, kalli yadda ta tarbeka a gaban idona? Da far'a da soyayya, shiyasa gaba daya ka canja min, tun kamin Momy ta rasu daker na samu kanka yanzu kuma baka amsa kirana baka mayar min da amsar sakona” “Safeena ina cikin jimami na rashin Momy a yanzu, bana bukatar wata maganar, abu na biyu kuma ki natsu ki fara tunanin yayanki da mijinki ki cire ni a rayuwarki... Na gane baki da hankali shiyasa har kika tunanin kashe aurenki ki bar yaranki ki dawo gareni, yanzu kuma abun ya wuce da har kin kai ki tako kafarki a gida? Ba zan daukar miki wannan ba, ban hada iyalina da kowa ba” “Idan na ce zan aikata wani abu akanka Kareem baka ganewa, baka amsa kirana kana ta kokarin kauce min a lokacin da nake da tsananin bukatar saka ka farinciki, da kana kula ni da ban zo gidan nan ba, na riga na sabu da kai, na cutu da soyayyarka ba zan oya warkewa ba amman a haka a mahaukaciya kake kallona?” “Taya mahaifiyata zata hane ni da abu na aikata? Taya tana raye zata hana ni aurenki yanzu kuma bayan ta mutu kike tunanin zan iya cigaba da wani mu'amala da ke? Safeena wake-up ki cireni a rayuwarki and i mean it....” Ya bar ta tsaye a gurin ya rufe kofar falon ya shige ciki. “Aurenta ya mutu ne?” Ita ce tambayar da Yusura ta fara yi masa a lokacin da ya shigo falon. Be tunanin ta yi labe ta saurari abun da suke tattaunawa sai idan zuwanta a gidan ne ya bata mamaki. “Me ye ma'anar abun da kika yi?” Ta mike tsaye tana kallonsa. “Irin abun da muka saba yi ne, a duk lokacin da baki suka zo, nuna cewar muna cikin soyayya da kaunar juna. Aurenta ya mutu ne ko kuma kashewa zata yi ta aureka saboda macen da ta yi mata karan tsaye ta bar mata duniyar?” “Miye matsalarki da hakan?” “Kana tunanin zan so abun da Momy ta ki? Har abada...! Ka fada mata kar ta sake zuwa gidan nan ba saboda ni ba saboda yaranka” Ta aje masa keys dinsa da ledar dake hannunta a kujera ta nufi stairs, binta yayi da kallo har ta haye sannan ya zauna yana kai hannunsa ya taba hancinsa. “Kai Mata kuna da wuyar sha'ani” Ya sauke ajiyar zuciya ya mike tsaye ya dauki ledarsa da keys din ya haura sama ya shiga dakinsa... #KhadeejaCandy PAID PAGE 5️⃣ ©KhadeejaCandy ©®Copyright 2024 Littafin nan na kudi ne, don't read if you didn't pay... One word kika karanta baki biya ni ba, ban yafe hakkina ba. To be part of the journey pay 500 to 2451879008 ZenithBank Hadiza Abubakar And send the evidence of payment to my WhatsApp number 08036126660.... You can read my latest update on arewabooks a handle dina @KhadeejaCandy https://www.arewabooks.com/book?id=659a94c8be87d7a51f831153 _______•••_______ Tsananin yunwar da nake ji bata bar ni na yi bachi ba, haka na zauna a falon ina kuka jikina na rawa ga kuma tsoro da ya baibaye ni. Misalin shabiyu na dare na ji an murda kofar dakin an shigo, na zabura na tashi da sauri ina kallon kofar sai na yi arba da Hafiz sanye da kayan bachi fuska ba yabo ba fallasa ya shigo. “Baki yi bachi ba?” Madadin na amsa sai na duka a kasa ina kuka. “Ka yo hakuri dan Allah, na daina ba zan sake ba, karka min horo da yunwa ina wahala sosai kuma ina jin tsoro” Be ce min komai ba ya nufi kitchen din ya bude, ni kuma na zauna a gurin ji nake ko kallonsa ba zan iya sake yi ba idan be min izini ba, domin na lura babu imani a tare da shi. Shayi ya hada min ya kawo min, sannan ya sake komawa ciki ina jin kamshi yana tashi, ni dai ban yi komai ba ina zaune a gurin da ya bar ni har sai da ya gama abun da yake ya fito da plate din indomie ya aje min. “Taso ki ci” Na taso na dawo kusa da shi na zauna na fara cin indomie yana kallona har na gama ya kawo min ruwa na sha. “Na gode” “Zaki iya kwana ke kadai?” Na girgiza kai. “Ina jin tsoro” “Zan kawo Ikram da Yayarta ta kwana tare da ke, amman Noor ki zama mai tsananin biyayya da gudun bacin rai please, ina da tsananin fushi da fada, amman idan ka iya zama da ni, ba wahala mun saba, kamar yadda yayarki take yi yanzu” Na daga mishi kai. Sai ya kai hannunsa ya shafa fuska yana murmushi. “Ki yi hakuri, be kamata na yi haka ba, amman na yi ne saboda ki gane kuskuren abun da kika aikata” Ya sumbanci kumatuna sannan ya mike tsaye. “Muje ki saka kayan bachinki” “Nan zaka kwana?” Na tambaya ina kallonsa. “Aa yau ai ba girkin ba ba ne dakin Yayarki zan kwana sai nan da kwana biyu zan dawo” Gaba ya saka ni na har cikin dakin na dauko kayan bachina yana kallona na canja arzikina daya ina da zanen dake daure tare da tare da shi na samu na yi dabara har na canja na saka riga da wando na bachi. Cak na ji an dauke ni daman ba wani jiki da ni ba kuma ya fi ni girma nesa ba kusa ba, saman gadon ya aje ni kwance ya kwanta da jikinsa ban gama fahimta ba na ji bakinsa cikin nawa. Na daure ne kawai saboda babu yadda zan yi ba dan ina so ba, ya dauki dakiku a haka sannan ya cire bakinsa ya daga ni ya sauka daga kan gadon. “Ko ke fa amman da ba ni da ikon taba ki sai ihu, kamar budurwar kauye” Na yi shiru ina kallonsa zuciyata na bugawa da karfi kamar zata cire, murmushi yayi min ya juya ya fice. Da gudu na tashi na shiga bandaki na fara korawa bakina ruwa na wanke shi tasss sannan na saka mai goge baki da buroshi na fara goge bakin ina jin kyankyami. Kamar daga sama na ga an turo kofar dakin ta jikin madubi nake kallonsa har ya fito murmushi yake kamin ya kai hannunsa ya cire brush din ya debo ruwa ya wanke min bakin sannan ya sake hade bakinsa da nawa wannan karon da ya cire sai da ya cilasta min hade yawun bakina. “Na hade” “Toh muje ki kwata, kar na sake kissing dinki ki wanke baki daga yau” Na kalleshi kamar na ce wani abu sai kuma na kyale na bi umarninsa. Saman gadon na hau na kwanta ya lullube ni sannan ya fita be jima ba Ikram da Walida suka shigo suka hauro gadon suka kwanta tare da ni. Bachin yayi min dadi sosai domin ban kwanta tare da shi ba, babu fargaba ko tsoro a kusa da ni. Washe gari bayan na yi sallah ban koma bachi ba na fita falon na gyara kitchen na gyara falon na wanke na wanke na goge na goge sannan na dawo na zauna. Zamana babu wuya Aisha ta shigo falon kiran yaranta da sai a lokacin suka tashi bachi. “Amarya ya kwanan kadaici?” Na yi murmushi. “Yara na zo kira, ko sun tashi” “Eh sun tashi bari na kira su” Haka ta bini da kallo har na shiga dakina na taso yaran suka fito, ta kama hannunsu suka fice tare. Dakin na gyara sannan na shiga na yi wanka na fito jikina na ciwo domin ban saba aikin wahala haka ba, mai na shafa na dauki riga da skirt material na saka sannan na shiga kitchen din na dafa shayi da gass na soya kwai biyar na soya dankali na fito na zauna. Ina tsaka da ci Hafiz ya shigo falon rike da biredi ya aje min. “Good Morning” Na amsa da murmushi sai ya gutsuri kwain dake gabana ya ci. “Ashe kin iya soya kwai” Na yi murmushi, ya mayar min da murmushin sannan ya tashi ya fice. Ina gama karyawa na hau bachin wahala idona cike da kwalla indai haka auren yake ba shi da dadi ni dai a gurin, ba zan fita ba ga aiki kullum ga wahalar kyautatawa miji ko baka so... Na yi wannan tunanin na yi wacan har bachi yayi gaba da ni ban farka sai azahar shi ma saboda Aisha ta shigo har dakina ne ta tashe ni daga bachin. “Ke bachin rana kin yi sallah ma tashi mu yi hira” Na tashi ina murza ido, bayan na yi sallah na dawo muka zauna da ita falo tana min hira mafi yawan hallayar Hafiz take fada min marar kyau, tana kara tsorata ni akan mijinta, sai dai abun da ya bani mamaki kuma ya daure min kai shi ne yadda take zaune da shi lafiya babu wani tashin hankali sai soyyayah da kaunar juna. Ba ita ta bar bangaren ba sai biyar na yamma a lokacin ne na shiga kitchen na sarrafa shimkafa da miya da naman kaza na ci, na bar ragowar kamar yadda na kasa cinye kwan da na soya a dazun. Da dare Hafiz ya shigo ya duba ni sannan Yaransa suka shigo muka kwana tare, washe gari ma haka ya na gyara komai na yi wanka na girka shimkafa da wuri, kamin na kwanta bachin kanwarta ta shigo kirana wai yau tana son na shigo bangarenta mu yi hira. Kwasar fafauwana na yi na shiga bangarenta tana ta bani labarin irin soyayyar da suka yi, ashe aure ta yi bata dace ba ta fito shi kuma ya ganta ya nuna yana sonta iyayensa suka amince kasancewar ba masu matsala ba ne, shi yayi mata komai kamar yadda yayi min a aurena, a lokacin ne take fada min shi ya saka ta makaranta ta yi karatu har take aiki. “Amman ban taba ganin kin tafi aikin ba?” Ta yi murmushi. “Yanzu kin ga ina da ciki wata 6 kuma gaskiya bana sha'awar aiki, na fi sha'awar zama a gida yanzu na kula da mijina da aurena, daman dai babu abun da na rasa kawai ra'ayi ne, yanzu kuma na gane hakan ina son zama a gidana ko ba komai hankalinsa zai fi kwanciya za mu kula da shi tun da ba ni kadai ba ce a yanzu” “Haka ne, amman aiki yana da sha'awa ina son aiki sosai” “Amman ke baki gama karatu ba aka miki aure ko? Na ga ke din yarinya ce sosai har yanxu baki gama wayo ba” Na sauke kaina kasa. “Haka ma a gidanmu ake cewa wai bana da hankali ba na da wayo, wai kanwata ta fi ni wayo, amman ni bana ganin haka” Ni da ita muka juya muka kalli kofar falon da aka bude Hafiz ne ya shigo ba a irin lokacin da ya saba dawowa ba, har da yar tsabararsa. “Welcome Barrister” “Yan mata na har biyu, me ake tattaunawa?” “Hira ce kawai ta karatu take fada min tana sha'awar aiki, ni kuma yanzu ya gumshe ni har na aje sai nan gaba kuma idan komai ya daidaita” Yayi murmushi ya miko min ledar hannunsa sai na saka hannu biyu na karba, sai dai na lura kamar hakan be mata dadi ba domin a take fuskarta ta canja. “Aiki kike sha'awa Noor, ni yanzu bana sha'awar mace ta yi aiki, ita ma saboda ta dage sai ta yi ne, zan saka ki makaranta ki yi karatu mai zurfi saboda gaba, amman zancen aiki ba yanzu ba” Na wara ido baki sake kai kace son karatun nake. “Da gaske zaka bar ni na yi karatu?” “Me zai hana ni fa dan boko ne, karatu sai kin ture yarinya” Zan yi magana ta cafke ta nuna masa murnarta a fili na jindadin yadda yace zan yi karatu tana ta yabonsa har da masa godiya. “Ke gani ko ai na fada miki ki kwantar da hankalinki Barr be da matsala ko kadan, shi mai son kyautata ma iyalinsa ba” Annashuwa ta suka fuskarsa. “Wato gulmana kika yi ko? Na kama ki” Sai ta yi dariya tana kallonsa. Shi kuma ya kalleni. “Ba zaki bude ledar ki ga miye a ciki ba Noor” Na bude ledar na ciro gasashiyar kaza da kayan ciki mai Onion and vegetable sai kamshi suke. Leda ta uku kuma faranti ne dauke da yar tsutsar nan da na yi sha'awar ci tun ina zuwa restaurants din Kareem. “Waya fada maka ina son wannan?” “Na taba ji gurin Kareem” “Na gode” Ina fada ina kallonsa gaba daya ya gana faranta min zuciya a yau. “Me aka dafa?” “Ghanian jollof na yi” “Ku kunci kenan?” “Har kunci kenan?” Ta amsa. “Eh mun ci” Na mike tsaye rike da leadar. “Zan tafi bangarena na ci wannan sai na sha tare da tea” “Okay Amarya aci dadi lafiya” Ta fada na fice daga bangaren na dawo bangare na, wanke hannuna ne kawai ya same ni dole na wanke hannun na zauna na fara ci ina jin wani shauki saboda mai da take da shi gashi ta yi laka laka kamar kitsen kilishi. Bayan na gama na wanke hannun na yi alwala na yi sallah ina nade carpet ya shigo rike da plate dake dauke da kayan ciki da kazar da ya siyo dazun. “Kin manta wannan Noor ko ba ki ci.” “Na ci wannan abun na koshi” “Ki aje wannan anjima sai ki ci” Na karba na juya zan fice sai na ji ya rikoni yana kokarin rumgume. “Kin yi min kyau yau fiye da kullum, ko dan kin dan sake jiki kin sake fuskar nan ne” Na yi murmushin yake Ina sauraren yadda yake yawo da hancinsa a wuyana. Sallamar Na'ima ce ta katse hanzarinsa a dole ya sake ni da sauri yana amsawa. Ya fice daga dakin da sauri “Wai Anty tana kiranka” “Okay” Na bi bayansa na shiga kitchen na aje naman sannan na fito na dawo falo na zauna ina kallo. Da zai shigo yi min sai da safe ne yake sanar da ni wai an yi gobara a gidan Baba, hankalina ya tashi sosai jin cewar gidan ya kore gaba daya. “Amman ba a rasa kowa ba?” “Da an rasa rai da Baba ya fada min, kin san baya boyo, amman dai gobe zamu je mu duba” “Da dare nan aka yi wutar?” “Da yamma” “Dan Allah ko zaka kira min Baba na ji shi?” Na tambaya tare da fatar zai karba bukata sai dai hakan be samu ba. “Ki yi hakuri gobe zamu je mu duba” “Tohm” Kusan sai da na yi mafarkin wutar saboda na kwanta a abun a zuciyata, washe gari na gyara komai na shirya da wuri ina gama karyawa ya shigo bangarena da shirinsa muka fita, a nan ma na ga rashin jindadin fitar ta mu a tare a fuskar Aisha domin ta kasa saki fuska kamar yadda ta saba sai ce masa take ya dawo ya ci abincin rana. “Wata kila ba zan samu dawowa ba, ita ma ai zata dawo ta yi girki ko?” Ya kalleni ina zaune a gidan gaba. “Eh” Ta yi mana Allah ya tsare na rufe motar yaja muka kama hanya. Ba mu yi nisa da fara tafiyar ba ya kama hannuna ya rike yana murzawa a hankali. “A kwana biyun nan fa ina ta jin sonki yana kama ni, kin san ni ban san dadin auren budurwa ba sai yanzu, Allah yasa na same ki fiye da yadda bake tsammani” Na yi shiru ba dan ba gama fahimtar inda zancensa ya dosa ba. Shi kuma be sake ce min komai ba har muka isa unguwar, ina kallon gidansu Zafeer dai da idona ya cika da kwalla, a nesa da kofar gidanmu ya faka ba tare da ya kashe motar ba ya ce. “Ki fadawa Baba idan zan zo daukarki xan shigo mu gaisa ina masa jaje” Na kalleshi kadan na dauke kai, wata kila ya fara gajiya da halin Baba ne, ko kuma dai yana jin abun da yake nema a yanzu ya samu shiyasa yake son kaucewa daga jikin Baba. Ko da yake Baba din ne iya masa sai Allah ba kowa ne zai jure ba. Bude motar na yi na fita sai da na isa kofar gidanmu sannan yayi reverse ni kuma na shiga cikin gidan namu da ya kone tun daga waje har cikin gidan. Da gudu na karasa gurin Hana dake kwance tsakar gidan da konuwa a fuskarta zuwa cinyar hannunta. “Innalillahi Hana” Ta fara yunkurin tashi zaune. A lokacin da Baba ya fito bandakin da sauri yaka aje butar ya kalleni yayi murmushi. “Aha ahhh wa nakd jin muryarta a gidan kamar Nooriyya yar albarka” Na juya na kalleshi ina hawaye. “Baba ashe gobara aka yi?” “Kin gani dai haka Allah ya kawo mana, wutar da dare, ina mijin naki? Baki ce ya shigo ba? Kika bar shi a waje? Ba kara ya shigo ya ga yadda gidan yayi ba” Ya fara tafiya sai na dakatar da shi. “Baba ya tafi yace yana maka jaje za ku gaisa idan zai zo daukata” “Au be tsaya ba? Tohmmm... Toh toh ba matsala ai duk daya ne, kuna dai zaune lafiya ko?” “lafiya Kalau Baba, Baba me yasa ba a kai Hannatu asibiti ba? Kuna ce fa” Na fada ina kallon maganin gargajiya da aka shafa mata. “Ina kudin yake Noor? Kin san yanzu abun duniya ba zama yake ba, ban da rayuwa ba ni da komai a yanzu, sai kuma wanda ya ga Allah ya ga Annabi ya kyautata mana, kina kallon yadda gida ya zama kamar kango, abun bakin cikin ma sai da na sake masa sabon fenti” Ya fada kamar zai fasa kuka, na daga kai ina kallon bakin wutar da ya rufe ginin ya hana a gani fentin. “Ai na so Hafiz din ya shigo ya ga yadda gidan ya koma” Na kalli Baba bance komai ba. Kamin ya shiga tambayata ya kishiyata ya zaman gidan Baba wata matsala, na amsa masa da komai lafiya. Ina nan wasu makotan suka shigo jaje suna ta maraba da ganina har suna fadin wai na fara natsuwa saboda na kasa hada ido da su. “Aure na natsar da mutun, wai Noor ce a haka, Allah ya bada zaman lafiya” A fuskar Baba nake ganin yadda kalamansu suka masa dadi, bayan sun fita shi ma ya fita a nan na samu damar hira da Hana tana fada min yadda wutar ta fara. “Daga dakin Mama ta fito, kuma bachin ya mana nauyi duk ba mu san ta kama ba sai da hayaki ta cika gidan, Yaya yana dakinsa na zaure Baba kuma a waje ya kwana ni kadai ce a daki” “Ya aka yi ta kai ga jikinki?” “A lokacin da na farka na ga wutar tana ci sosai har kusan kofa ba damar na wuce ta saman kuma ta sauka kan katifa sai ta kama tufafinmu ceiling saman kuma yana ta narkewa yana fado min a jiki kin san na roba ne idan ya digo kamar fatar zata cire nake ji, sai da Alhaji Bashiru ya shigo ya fitar da ni” “Ni ma ban sani ba sai jiya da dare Hafiz yake fada min, amman Hana baki ma Yaya magana ba ya kai asibiti?” “Ba shi da kudi ai kin ga da ya kai ni, Baba kuma ba zai iya kashe kudinsa ba ji yake hasara yayi, ban dan ma gobarar nan ba jibi za a kawo amaryarsa shiyasa kika ji yana fadar yayi fenti” Na gyara zama ina mamaki. “Auren dai yana nan da gaske?” “Noor to me zai hana? Mama ma aure zata yi?” “Ita ma? Yaushe? A ina?” “Garin nan, wani mai rufin asiri ma kuwa motarsa ma abar kallo ce” Dadi na saka ni murmushi. “A ina Mama ta hadu da shi?” “A cikin unguwa ya zo gidan wani abikinsa” “Amman shi ne ba a fada min ba? Bani da labarin kowa babu mai zuwa gurina kun bar ni can ni kadai” “Noor ba a kusa kike ba balle nace zan taka da kafa na tafi, ba ni da kudin abun hawa kuma mijinki ma zai gaji idan aka ce kullum zai na je” “Ba zai gaji ba ita ma kanwarta tana yawan zuwa ai, ko jiya ma taje kuma baya cewa komai” “Sai na samu lafiya zan zo” Da kanwata da kusan zan iya cewa tawainiyata ma muka sha hira muka koshi, ina ta sake saken yadda zan saci kafa na tafi na ga Mama babu hali, domin na san Baba zai yi fada idan ya dawo be tarar da ni ba, dole a wayar Yaya na gaisa da ita har nake tambayarta ance zata yi aure. “Da yardar Allah kuwa Noor, idan lokaci yayi ai dole za a fada muku” “Mama yaushe zaki zo?” “Yaushe aka yi auren ma balle na kwashi kafafuwa na tafi Noor? Ni fa uwace ba zai yiyu na tafi gidanki ba sai da dalili” “Amman Mama kin ji Baba yayi wuta?” “Uhmmm Allah ya kyauta gaba, Noor ki rike aurenki da mutuncinki, idon mutane yana kanki kowa jiran yake wani abu ya faru da ke, kuma kin ga zaman gidanku nan ba shi da dadi, da alama kuma mijinki mai hankali ne da tunani, kishiyarki kuma ki rike ta da mutuncin kuma ki yi taka tsantsan da ita, ki rika kula da rayuwa na san halinki da sakarci, balle kuma an dauke ki an kai ki gurin babbar mace ina yarinya karama, ta fiki wayo ta fiki hankali kuma ta fiki sanin kan mijinku, ki bi a hankali kuma ki rike addu'a kar na ji kar na gaji wani abu ya faru, kuman ko da wasa bana son na ji kin bibiye Zafeer aure ya rabaki da kowa yanzu” “Toh Mama, zan kiyaye, Zafeer ni ba zan taba yin magana da shi ba, ai Baba yace be yafe min ba idan na yi masa magana” “Toh sai ki kiyaye, ki zauna lafiya a gidanki kin ji?” “Toh Mama” Sallama muka yi sannan ta kashe wayar na mikawa Yaya. “Mahaifiyar Kareem ta rasu ko Yaya?” “Eh kwana uku aka yi ai ba a bude restaurant din ba, sai da aka yi sadakan uku duk mun je masa gaisuwa” “Yayi kuka?” “A gabanmu zai yi kuka? Sai dai a boye ko? Kin masa gaisuwa” “Hafiz be bari na tafi ba matarsa kawai ta tafi, wata kila sai nan gaba idan na fara fita” “Kila” Saman sama muke taba hirar Yaya na fada min Kareem din ya rame sosai abun ya taba shi. Na yi zaton Hafiz zai dawo da rana ya dauke ni saboda yayi min zancen girki amnan shiru be zo ba sai bayan Isha'i a lokacin Baba har ya gaji da jiransa. Yana yin sallama Baba ya tarbeshi jiki na rawa suka gaisa sannan ya shiga nuna masa gidan yana fada masa yadda gobarar ta fara. “In shaa Allah zan kira ka Baba sai mu yi magana na ga abun da ya dace ayi” “Na gode Allah ya saka da alheri ya kara rufa asiri...” Baki har kunne baba yake Fadar haka, sai dai ko kadan ban ga alamar sake fuska a gurin Hafiz ba, yadda yake rawar jiki da Baba ma wannan karon ban ga yayi haka ba. Ba Baba kadai ba ni kadai na yi tsammanin zai bawa Baba kudi ko kuma ya ce akai Hana asibiti amman ba ko daya har muka fito gidan. Na shiga motarsa shi ma ya zagaya ya shiga sai da yayi min wani kallo da ban fahimci ma'anarsa ba sannan ya tashi motar muka fara tafiya. Ban kalleshi ba, sai dai na ji a jikina yana yawan kallon gefe da nake zaune. “Noor na ga kin bata rai, ko kin yi marmarin gida ne?” Na yi shiru bance komai ba, hannu na ga ya mika bayan motar ya dauko kwali ya dora min a cinya. “Ya kamata ke ma ace kina da waya ko?” Na kalli kwalin wayar na kalleshi ina zaro ido. “Tawa ce?” Ya daga min kai, sai na rasa ina zan saka kaina tsabar farinciki domin taba rike wayar kaina ba. Yana faka mota harabar gidan na fita da sauri na shiga bangaren Aisha ina nuna mata wayar, sai ta fini farinciki da jindadi ma ita ta taimaka min na saka sim din ta nuna min yadda ake operating wayarsa. #KhadeejaCandy PAID PAGE 6️⃣ ©KhadeejaCandy ©®Copyright 2024 Littafin nan na kudi ne, don't read if you didn't pay... One word kika karanta baki biya ni ba, ban yafe hakkina ba. To be part of the journey pay 500 to 2451879008 ZenithBank Hadiza Abubakar And send the evidence of payment to my WhatsApp number 08036126660.... You can read my latest update on arewabooks a handle dina @KhadeejaCandy https://www.arewabooks.com/book?id=659a94c8be87d7a51f831153 _______•••_______ “Allah ya tsare ya sa albarka” Ta yi min addu'a sai na amsa da amin sannan na karbi wayar bayan ya saka min number shi da number Baba da kuma na Aisha. “Amman fa karki je ki kira Saurayinki da wayar nan na sa halinki” Ta fada tana min wani kallo kamar na zolaya, ni kuwa na kalli Mijina na kalleta da mamaki. “Ya za'ayi na kira sho kuma? Na fa yi aure yanzu na sani” Ta sake fuskar zolaya tana min wani kallo na rashin yarda. “Ke dai kin san yadda muke sirrinmu ko? Kawai dai ki kiyaye, ke matar aure ce a yanzu kin ji kanwata” Na amsa mata da tohm domin kawai na takaita zancen sannan na mike tsaye rike da wayar da kuma jata na fice daga bangaren. Ina shiga bangarena na tare a kujera ina ta kallon wayar bude nan taba nan hotunan da na yi kuma sun fi a shirin a zama daya. Ima tsaya da daukar wani hoton sai hango Hafiz na yi ta cikin hoton ya leko kansa. Na juya na kalleshi ina dariya shi ma dariyar yayi ya matso kusa da ni ya zauna. “Daukin wayar ne har yanzu” “Eh na gode Hafiz” “Ki daina cewa Hafiz Noor” “Tohm Yallabai” A bakin gaskiya ta na fada sai dai na lura kuma hakan dariya ya saka shi domin dariyar yake kamar na fadi wani joke. “Ur Welcome..” Ya kama hannuna na rike ya juyo da kafadata daya na fuskance shi da kyau. “Noor, please karki ba ni kunya i trust you, kar na ji ko na ga abun da zai bata min rai wayar nan, ba ma waya kadai ba a komai ma, kin ga Aisha ta fada min abubuwa da kika fara fada mata akan zamantakewar duka duka kuma yaushe muka fara zaman auren? Sirrin dake tsakanina da ke na mu ne mu kadai kawaye iyeye ko abokiyar zama babu wanda zai sani, wanda ke tsakanina da ita kuma ita ma zata rike babu wanda zai sani, kin ga da farko na ji haushi amman daga baya na yi tunani hankalinki da tunaninki ba irin nata ba shi, saboda shekarun ba daya ba, amman ina son na ja kunnenki karki fadawa kowa sirrinmu kin ji? Kuma zancen baki so na kika aure ni na san wannan ita ma ta san wannan ba sai kin yi ta nanata mata ba kina fada mata yadda na raba ki da saurayinki, yan'uwana ba su san irin auren da muka yi ba, so bana bukatar su san cewar wai baki so na kika aureni kinji” Na daga mishi kai. “Me tace na ce” Na tambaya ina mamaki, domin ban san na taba fada mata wani abu a game da Hafiz ba, yo ni da har yanzu ba mu taba hada shimfida ba ta ina zan fada sirrinsa? Kuma yaushe nake fada mata yadda ya raba ni da Zafeer. “Cewa ta yi kin kura min ido kamar zaki cinye ni” Ya ja hancina hana kallon cikin idona. Na sauke kai kasa. “Baki jin yunwa ne? Ko kin ci abinci a gida?” “Aa ban ci ba, kai baka ci ba?” “Ban ci na so ki dawo ki girka, ni ma ban samu dawowa ba sai daren nan” “Girki cikin dare akwai wahala kamin ka fada na yi bachi” “Wa zai dafa?” Na dan saci kallonsa na sauke ido, ba dai yana nufin ni na girka ba? Ganin na yi ya mike tsaye. “Taso muje mu siyo wani abu a waje” Na mike tsaye ina rike da wayata, a nan na bar jakar da na dawo da ita daga gida. Hannuna ya kama muka fita daga falon be sake ba har gurin motarsa ya bude min na shiga sannan ya zagaya ya shigo ya kunna motar sai kuma ya  kalleni. “Bari na tambaya Madam ko za a siyo mata wani abu” “Tohm” Yana fita na fara daukar kaina hoto a motar, be jima ba ya dawo ya ja motar muka kama hanya. Na yi zaton zamu tafi Kareem Restaurant ne sai na ga ya faka a wani restaurant da ban sani ba, ko'ina na gurin wuta ce mai calar blue da ja daga waje. Ciki kuma farin haske ne irin wanda ko allurarka ta fadi zaka iya gani. Sai da ya fara fita sannan ni ma na fito muka jera a tare muka shiga. “Me kike son ki ci?” “Ice Cream” “Ice Cream ai ba abinci ba ne” “Ni idan na ci shi ya ishe ni, sai kuma nama” Muna tafiya ina fada ina rabon ido, katon guri ne aka yi kowa bangare abu dabam ne, idan zaba sai ka tafi gurin biya ka biya sannan ka fice. Gurin masu pizza ya fara zuwa ya daukar mana daya, ya nufi shawarma ya dauki biyu, sannan muka nufi gurin masu kaza dake cikin gilashin tana juyawa kawar wata karuwa. “Ba mu daya” Ya fada sannan ya kalleni ya ciro wayarsa aljihu da hannu daya ya matsa can gefe yana amsawa. Mutumem ya gama yanka kazar ya saka a leda sai ya miko min, na waiga na kalli saitin da yake tsaye yana wayar da murmushi a fuskarsa da alama da Madam yake waya domin ita ce kadai zata iya saka shi irin wannan murmushi kuma ta dauke masa hankali. Ban bi ta kansa ba na nufi gurin masu ice cream ina duba wanda ya fi girma a jikin hoton dake gaban box din, domin sai ka zaba sannan za a dauko maka. “Wane ya fi dadi?” “Kowane ne yana da dadi yan mata, amman dai ki dauki vanilla ice cream mata sun fi son shi” Na ji an fada daga gefena, na juyo na kalleshi sai ya sakar min murmushi. “Can i pay” Na girgiza masa kai alamar no, sai ya bata fuska kamar mai magana da yarinya. “Why? Baki son na samu lada?” “Kai Malam Lafiya” Hafiz ya fada tun kamin ya karaso ni da shi muka juya kallon Hafiz din da ya daso gurin da saurinsa. “Waye wannan? Yayanki ne?” “Mijina ne” Ya matsa nesa da ni ya kalli daga sama zuwa kasa. “Duk kyaun nan naki, wannan ne mijinki” Ban ce masa komai ba, shi ma kuma be sake cewa komai ba ya nufi gurin biya ya bar shi a gurin tsaye. “Waye wannan?” “Ban san shi ba, yau na fara ganinshi ni ma” “Amman ai magana na ga kina yi da shi” “Tambaya yayi zai iya biya na ce aa ni matar aure ce” Hafiz ya kalli gurin da mutumen nan yake tsaye, shi ma kallonmu yake kamin ya karbi katinsa a fara saka masa kayan a babbar leda. “Mu tafi...” Na wuce gaba yana bayana muna isa gurin Mutumen ya karbi kayansa ya fara tafiya. “Oga Abdull ga canjinka” Daya daga cikin masu karbar kudi a gurin ya fada yana mika masa canjin 750. “Keep the change” Ya fada ba tare da ya juyo ba. Hafiz ya ciri Atm dinsa ya biya kudin aka fara saka mana a babbar leda, a nan na samu damar satar kallon mijin na wa, ni ban taba lura da yanayinsa kyau ko muni ba dress ko yanayinsa, gaba daya babu ko daya a gabana sai yau da mutumen nan yake mamakin ni din matarsa ce. Kuma gaskiya ya fada Hafiz ba shi da wani kyau na azo a gani, ba laifi dress dinsa na zamani riga da wando, kuma yana ta kamshi ba laifi ba zaka kira shi baki ba haka kuma ba fari bane. “Muje” Ya rika duka ledodin gaba ya saka ni sai da na fara fita sannan ya fito. Kamin mu isa motar na hango yarinyar nan da Zafeer yake yi ma gyaran mota tana doso gurin, ita ma kallona take kamar yadda nake kallonsa da alama ita ma dai ta gane ni kamar yadda na wayance ta. “Noor ko?” Ta fada yana nuna ni a lokacin da ta karaso kusa da ni. Na daga mata kai ina murmushi Hafiz ya kalleta. “Wacece wannan?” “Waye wannan Yayanki ne?” Ita da shi kusan a lokaci daya suka yi tambayar kowanensu yana kokarin sanin abun da ke tsakanina da daya. “Mijina ne” Na fara amsa mata jiki a sanyeye ina jin babu dadi domin ta san alakata da Zafeer. A take na ga yanayinta ya sauya kamar mai mamaki kamar kuma bata jidadin amsar tawa ba. “Zafeer...” Sai kuma ta yi shiru... “Allah be yi da shi ba, Noor shiga mota mu tafi” Hafiz ya fada rai a bace yana ba ni umarni. Na nufi motar ina jin wani abu marar dadi ya tokare min zuciya. Kamin na isa gurin motar hawaye ya cika idona har ya fara zubo domin ta tuna da abun da nake kokarin mantawa da shi a kankanen lokaci, mutumen da ba ya kunyar nuna soyayyata a gaban kowa. Tsaye ta yi tana kallonmu har sai da muka bace mata. Kaina a kasa yake har muka isa gida na ki yarda na dago dan kar Hafiz ya ga hawayen dake min zuba, sai dai hakan be hana shi fahimtar kuncin dake zuciyata ba, domin yanayina ya sauka ba kamar yadda muka fita ba. “Mutumen nan kamata yayi ki fada masa kina da miji tun farkon da yayi miki magana, kin san kina burge maza for no reason me ya ba zaki kama kanki ba? Ke komai sai an fada miki sannan zaki yi? Aisha tana da gaskiya be kamata na baki wayar nan a yanzu” Ban ce masa komai fadansa sai kara min zafin hawaye yake. “Ba ni wayar...” Ya miko min hannunsa yana kashe motar. Sai da na hade yawu sannan na mika masa wayar. “Zan baki amman sai nan gaba idan kin yi hankali, yanzu ko na barki da ita hankali ba zai kwanta ba, ai na ga darasi gurin abokina mata ba ku da amana if not taya kina tare da ni zaki zubar da hawaye saboda da wani da ba zai iya zaman aure da ke ba, ba zai iya miki rabin abun da na yi miki ba” Na kalleshi. “Amman zai ba ni farinciki, irin wanda ba zan taba samu a gidanka ba, da baka bar ni tsaye ba ka je kana waya da munafukar matarka ta ya wani zai min magana? Ko kuma an rubuta a goshina na ne cewar ni matar aure ce? Wayarka kuma ka aje bana so ko da nan da tsufa ne, idan ba ka yarda da ni a yanzu ba ba zaka taba yarda da ni ba har abada” Na bude motar na fita a fusace na bar masa kofar a bude ba tare da na rufe ba. Falon na shiga na zauna kan kujera gaba daya na rasa me ke min dadi. A kan kujerar da nake zaune ya watsar siyayyar da muka yi. “Noor For the very last time karki sake kiran Aisha munafuka, ko ba komai ta girme ki, ta cancanci girmama daga gurinki, balle kuma tana matata, ba zan yarda ki shigo gidana ki rainata ba, babu kalar soyayyar da bata nuna miki ba, idan baki gode ba karki zage ta ba zan yarda a raina min uwargidana ba uwar yayana, ki tsaya matsayinki...” Uffan ban ce masa ba na tashi na shiga daki na kwanta kan gadona ina kallon OPO dake dakin hawaye na zubo, haduwata da matar a nan ya tuna min da waye Zafeer a gurina, abu da duk wanda ya san alakarmu zai yi mamakin ace ba shi na aura ba. “Miye wannan?” Ya tambaya a tsawace dagowar da zan yi ya watso min wani abu mai kamar magani a fuska da wata roba. Na tashi zaune na dauki maganin mai kananan yaya na duba, sai wata roba da ban gama sanin ta miye ba guda biyu, roba na fi duba domin ta yi min kama da balloon sai dai ta banbanta da ballon sosai, ba kuma zan iya fadar ko ta miye ba domin ban san amfaninta ba. Na sake duba maganin shi ma wani kalar magani ne mai 2 colors da ban taba ganin irinsa ba. “Miye wannan.?” Ya daka min tsawa har sai da hankalina ya tashi, gaba daya fuskarsa da hallitarsa sun canja jikinsa har rawa yake kamar zai doke ni. “Ban san ko miye ba...” “Karya kike munafuka, a jakarki na ganshi yanzu waya baki ina kika siya?” Na girgiza kai amman na kasa magana domin tsoron fushinsa da nakr gani a yanzu ya cika zuciyata. Furta cewar a jakata ya gani ya saka na sauka da sauri da zimmar na tafi na duba jakar tawa da na bari a falon sai na ji ya fisgoni iyakar karfinsa na wulgar da ni kan gadon. “Ina zaki je? Ba zaki fada min ba? Uban waye ya baki wannan maganin? Ina kika siya? Mi ya kawo condoms a jakarki?” “Wallahi ban sani ba... Ba.. Ba.. Ban saka.. Magani ba... Ni ban...” Na kasa magana tsoro da kuka suka ci karfina, ban san me yake fada ba maganin ne condoms ko kuma robar, ko ma duka? To miye illarsu? Miye kawo su a jakata? Taya? Ya hauro saman gadon da talkaminsa ya riko ni da duka karfinsa. “Ina kika siye Noor? Saboda me kika siya?” “Ban saya ba, ban san amfaninsa ba, ni ban saka komai a jaka na ba, ban san maganin miye ba, ban san robar ta miye ba, ba nawa ba ne Wallahi” “To ina aka samu ya aka yi na ganshi a jakarki?” Na rike hannunsa daya jikina na rawa. “Wallahi Wallahi ba nawa ba ne, ban san miye ba” “Da na aje ki gidanku ina kika je?” “Ban tafi ko'ina ba Wallahi” “Amman kin yi magana da Zafeer?” “Ban yi ba, Wallahi ban ga Zafeer ba” “To wannan abun su suka kawo kansu a jakarki kenan?” “Wallahi ban san na miye ba, Hafiz sai idan saka min shi aka yi a jaka..” Fwauuu ya buge min baki. “Ban ce ki daina fadar sunana ba? Ke gaba daya kanki babu tunani babu tarbiya babu hankali? Gaba daya baki da lissafi? Waya saka miki maganin to? Waye? Ko ki fada min ko na ci ubanki da duka Wallahi” “daga gida ban je ko'ina ba, kanwata kuma ba zata saka min wannan abun ba, ni da ita duk ba mu taba ganin wannan abun ba” “To waya saka miki? Ina kika samu? Ni zan dauko na saka miki a jaka?” “Sai idan Aisha ce ta saka min saboda ta yi min sheri, Wallahi ban san na miye ba” Ina fadar hakan sai ya sake ni, ya sauka daga kan gadon ya fita daga dakin. A nan an samu damar daukar maganin na duba na sake duba balloon din har biyu sannan na nufo falo na duba jakata da ke kasa sarka da yan kunne da na cire na saka a ciki tun a gida suna watse a kasa. Naira biyar ma ba ni da ita a jakar to a ina zan siye magani? Kuma maganin miye zan siya, wane chemist bayan cikin gidan mu ban san na taka ko'ina ba. Ban gama shiga tashin hankali ba har sai da Aisha ta shigo falon tare da Hafiz. “Noor ni na saka miki magani da condom a jaka? Ta ina? Da zaki fita na karbi jakarki ne? Kuma ai tare kuka dawo da Barrister idan na saka miki wani abu a ciki zai gani, Kuma na rantse da Allah bayan fitarku ban shigo dakin nan ba, me zai saka ma na yi haka?” Ta juya gurinsa da sauri ta zube kasa. “Na shiga uku kar ta kashe min aure, daman burin yan matan yanzu kenan, Wallahi ba ni na saka, idan ni na saka mata shi a jakarta kada Allah ya ba ni abun da nake so Wallahi ba ni ba ce Barrister Innalillahi Na shiga uku...” Ya rika ta ya mikar da ita tsaye, gaba daya sai suka daure ni na rasa ya zan zarga ita ko kanwata? Ko kuma shi da ya saka min jakar a lefe? Yanzu ta ya zan wanke kaina. “Tafi bangarenki” Ta kalleni tana kuka. “Allah ya saka min gareki, na barki da Allah saboda kar a zarge ki shi ne zaki maida laifin a kaina? Ba ni ba ke Noor daga yau kowa ya tsaya bangarensa....” Na kasa cewa komai sai kallonta nake hawaye suna sauko min kamar ba gobe. Ta rufe fuska tana kuka sosai ta fice daga falon, kamar fitarta yake jira ya juyo kaina. “Ta rantse ba ita ta saka miki ba, daman makasudin kiran kenan, fada min ina kika samu wannan? Yanxu kika samu ko kin dade?” Na yi shiru kamar wadda kalamai suka karewa. “Ba magana nake miki ba?” Ya sake daka min tsawa. Still ban iya ce masa komai ba, domin babu wasu kalmomi da zan hada na wanke kaina. “Shiyasa auren mace mai mutunci mai tarbiya da natsuwa yana da dadi, ka aureki saboda na rufa miki asiri amman kullum matsala kike ba ni, ni ban taba samun matsala da matata irin wannan!” Yana matsowa ina matsawa baya jira kawai nake ya kai min duka a jiki domin alamar hakannta bayyana a jikinsa da fuskarsa. Kwafa yayi ya nufi ledodin da muka shigo da su ya kwashe gaba daya ya fice daga falon. Ranar kwana ne amman be kwana a dakina ba sai ya kwana a dakin Aisha, ni kuma na kwana a falon cikin kunci da rudani mai tsananin daure kai. A haka muka kwashe sati biyu be shigo bangare na ba, da girkina da ba nawa ba duk baya zuwa gurina, sai dai na hango shi ta window idan zai fita ko ya dawo. A lokacin damuwa ya fara shiga raina, na tabbatar Zafeer ba zai iya min haka ba, gashi Baba ya aurar da ni ga wanda bana so kuma be iya zama da ni ba. Kukan safe dabam na rana dabam da dare ma idan zan kwanta dabam ga abinci amman bana iya sarrafawa na ci saboda damuwa sai ruwan sha yi babu bread domin ya daina kawo min komai, wani lokacin kuma na dafa taliyar yara kadan na ci. Idan na zauna da tunani sai na rasa wa zan kaiwa kukana, Baba zan je na fadawa ko kuma Mama ko kuma dai Kareem zan fadawa shi da yake abokinsa? Ko kuma gidan iyayensa zan bincika na fada musu ko kuma na zauna a haka? Na zuba masa ido? Gashi babu wani dan'uwa da ya sake zuwa gurina na balle na bude masa ciki na fada masa damuwata. Amman har zuwa yaushe zai yi ta fushin da Ni? Zuwa yaushe zai sauko? Agogon dakin na duba karfe biyu da mintuna na rana, tashi na yi na dauki green hijab dina na saka na dauki jakar nan da na yi fitar farko da ita na sake dauka na bude marfin madubina na dauko balloon din nan da maganin na saka a jakata na saka talkamina na fito falon na leka windows din waje ban motarsa ba hakan na tabbatar min da baya cikin gidan kenan. Bude kofar falon na yi na fita sannan na janyo kofar ba gabana na faduwa na sauka entrance din na nufi gate. Kamin na fice har wani gumi ke karyo min domin idan ya tare ni a kofar gate din ko hanya ban san me zan fada masa ba. Mai gadin ne ya bude min na fita dama ko hagu sai na rasa ina zan dosa can wata zuciyar ta raya min dama domin ta nan muka bi lokacin da zamu tafi gida tare da shi. #KhadeejaCandy PAID PAGE 7️⃣ ©KhadeejaCandy ©®Copyright 2024 Littafin nan na kudi ne, don't read if you didn't pay... One word kika karanta baki biya ni ba, ban yafe hakkina ba. To be part of the journey pay 500 to 2451879008 ZenithBank Hadiza Abubakar And send the evidence of payment to my WhatsApp number 08036126660.... You can read my latest update on arewabooks a handle dina @KhadeejaCandy https://www.arewabooks.com/book?id=659a94c8be87d7a51f831153 _______•••_______ Na yi tafiya mai nisa kamin na samu Napep na tara ya fada masa inda zai kai ni na shiga. Sai da ya fara tafiya sannan na fara sake saken idan na tafi gida me zan fada? Na nuna musu abun da ya gani a jakar tawa ko kuma dai na fada ma Baba cewar ya daina shigowa bangarena? Gidanmu zan tafi ko kuma na su gidan? Idan ma na ce zan tafi gidansu ina zan bi domin ban taba tafiya ba be kai ni kamin auren ba, bayan aure kuma ba mu samu kwanciyar hankalin da zai kai ni gidan ba. Wata zuciyar kuma na raya min na tafi gurin Mama kai tsaye sai dai kuma ita ma zan iya shafa mata laifi. Ya mace bata da gidan da ya fi na mahaifinta saboda haka na fada masa unguwarmu kai tsaye. Har kofar gidanmu ya faka Napep din na fita na shiga gidan da sallama. Yaya na fara cin karo da shi yana wanki sai kuma Hana dake gaban murhu tana girki har yanzu da sauran kuna a jikinta domin na same ta babu riga a jiki. “Yaya dan Allah dari biyar zaka ba ni zan sallami mai napep” “Lafiya?” Ya tambaya yana kallon yanayi na, domin na shigo gidan ne cike da damuwar da ta kasa boyuwa a fuskata. Na yo shiru be sake ce min komai ba ya tashi ya shiga dakinsa ya dauko dari biyu da naira dari ya miko min. “Su kenan suka rage min, nawa ya kawo ki?” “Ban yi ciniki da shi ba, bari na tambaya” Na juya na fita, ta inda na yi sa'a ina tambayar mai Napep din nawa ya ce min dari uku sai na mika masa na dawo cikin gidan na nufi kofar dakin Mama na zauna. “Noor kin rame? Ko baki da lafiya?” Hana ta fada satar kallon Yaya na yi dake kallona sannan na ce. “Har yanzu konan be warke ba?” “Eh da saura, kin san wuta bata warkewa da wuri, kowa ma cewa yake na yi sa'a jikina yana da kyau ne” “Ina Baba?” “Dazun ya kawo cefa ne ya fita, anjima na san zai dawo cin abinci ai tun da yace ya gama da wuri” Na sake kallon Yaya sannan na kalli rufin kwanon da aka yi da tsohon kwano a dakunan da suke kone, shi ma kuma daga dakinmu sai na Mama da take ciki na Yaya har lokacin a bude yake. “Ashe an rufe” “Eh Ya Nabil ne suka rufe shi da abokinsa, tsofin kwanon da suka kone ne suka rufe da su” Duk maganar da nake Hana ce take amsa min shi dai be sake cewa komai ba sai dai ya kalleni. Ina zaune a gurin har ya gama wankin ya shiga yayi wanka ya fito Hana ta gama girkin ta zuba mana, na samu cin abincin da yawa kasancewar a tare muka ci da ita kuma muna ci muna hira. Bayan mun gama na yi alwala La'asar na yi sallah na zauna akan tabarma ina jiran shigowa Baba har lokacin na gagara fadawa Hana ko Yaya dalilin zuwan nawa. Yaya Nabil yana yi alwalar La'asar ya fice daga gidan, sai ya rage daga ni sai Hana ita din ma na kasa ce mata komai, gani nake kamar yayi wuri na fara fadar matsala wata kila ba za su yarda da ni ba. Shigowar Baba ta saka hantar cikina kadawa na kasa samun sukunin zama sai motsi na ke irin na marasa gaskiya. “Ahh Yau Norriya ce a gidan na mu? Maraba maraba da zuwa Nooriyya an tuna da gida kuma?” Na yi murmushin karfin hali na yi masa sannu da zuwa ya amsa Hana ta dauko masa kujera ya zauna kusa da ni yana kallona far'a kamar na zo masa da albishir. “Ya gidan lafiya? Ina mijinki yana lafiya ko?” “Lafiya Kalau Baba” “Tun dazun kika zo?” “Eh da rana na zo” “Madallah kin ci abinci?” “Eh na ci Baba” “Haka ake so, Mijin na ki dai yana lafiya ko?” “Eh Baba” Na amsa cikin rashin sakewa, tsoron duka ko zagin da zan sha a gurin Baba ya hana ni fada masa damuwar da na zo da ita, haka na hade hannu ina kallon Baba yana cin abinci yana fada min wai kwanan baya ya kira Hafiz a waya be daga ba. “Ina ta saurarensa yace zai kira ni kuma be kira ni, kuma na kira shi be daga ba” “Wata kila baya kusa da wayar ne” “Ni ma na yi tunanin haka, amman ai ya kamata ya kira idan ya ga kiran nawa, amman dai ba komai ai zai zo daukarki ko?” “Eh zai zo, yace ma na tafi gurin Mama na dawo da wuri kamin ya zo” Na yi karya ina jin kamar a gurin mahaifiyata zan fi samun sakewa na fada mata damuwa fiye da shi, da zai iya rufe ni da fada ko duka. “Ah aha shi ne kuma kika zauna har yanzu? Tashi ki tafi mana ga yamma na yi sai ki dawo da wuri karki tafi ki zauna fa, ki dawo da wuri kar zo be same ki ba” “Tohm Baba, amman ba ni da kudin abun hawa” Ya saka hannu aljihu ya ciro tari bakwai ya ba ni. “Tashi ki tafi, karki jima” Na karba da hannu biyu na dauki jakata na mike tsaye ina kallon kanwata. “Tafiya zaki yi” “Eh ba zaki raka ni ba Hana?” Jin haka ya saka ta shiga daki ta dauko hijab ta dora a saman zanen da take daure da shi, na yi ma Baba sallama da zimmar dawowa idan na tafi na fito Hana ta rako ni muka fito. Ko kadan ban yarda na daga kai na kalli kofar gidansu Zafeer ba, saboda ji nake kamar zan ganshi ne ko ya ganni hakan kuma ba zai mana dadi ba dukanmu. Har bakin Titi Hana ta rakoni na tari Napep ina tsaka da ciniki da shi na ji ta dafa ni. “Noor Wallahi yanayinki kamar akwai matsala!” “Akwai, ki min addu'a kawai Hana Allah ya min mafita” “Ameen, je ki dawo sai mu yi magana” Na daga mata kai na shiga Napep din. Yana tafiya ina hawaye har muka isa gidansu kakaninna. Farincikin ganin mahaifiyata da yan'uwanta da kuma su kansu yan'uwan mahaifiyata da suka yi farinciki ganina ya mantar da ni yar damuwar da na zo dauke da ita. Suka kawo min abinci har kusan hudu kasancewar gidan family house ne mai bangare dabam dabam irin na mutanen da da ake zama tare da jikoki da yaya da yan'uwa. Sai da na kebe da mahaifiyata sannan damuwa ta dawo min a take yanayi na ya canja. “Ba zaki ci abincin ba?” Mama ta tambaya, sai na kalleta ta yi jikinta ta yi haske kamar ba ita ba da alama hankalinta yanxu ya fi kwanciya fiye da lokacin da take gidan baba. “Na ci abinci a gida kamin na zo” “A gidan Baban na ki ko mijin? Ance ubanku ma aure zai yi? Kuma mai kudi wai Mama?” Ta yi dariya. “Eh ke ma ai Hana tace min aure zaki yi Mama” “Eh In shaa Allahu jumma'ar nan ta sama za a daura auren, ina son daman sai an kusa na shirya na tafi na ga dakinki, yan'uwa sai yabawa suke, na san dai baki son auren amman ya miki komai Noor domin ubanki ba zai iya zuba miki wannan kayan ba, duk da dai ban gani ba amman ina jin ana ta yabawa” Na yi shiru na sauke kaina kasa. “ina abokiyar zaman naki kuna lafiya ko?” Na dago na kalleta. “Lafiya Mama sai dai...” Sai kuma na yi shiru, ita ma shirun ta yi tana kallona. “sai dai me? Noor karki fara dan Allah, yaushe aka miki auren balle har ace matsala ta fara shiga, shi zaman aure dan hakuri, kina kallon yadda na sha wahala gidan ubanki balle wannan dake kaunarki kamar ya hade, na san halinki Noor shiyasa tun farko na gargade ki, wauta da sakarci sun miki yawa, abun kadan zaki iya ganinsa ba daidai” “Wata kila kuma ni nake da gaskiya Mama” Na fada murya kamar zan fasa kuka, idona na tara ruwan hawaye. Sai ta hade min rai ta dauke kai. “Bana son na ji, indai shi ya kawo ki gidan nan, to tashi ki tafi ba ki zo ganina cikin dadin rai ba sai zaki kawo min wani korafi? Je ki samu Babanki shi da ya daura miki auren ki fada masa, sai ni da kika raina, salon ace ni yanxu zan yi aure ke kuma na kashe miki aure? Noor kin san iya idon da yake kanki kuwa? Ana kalle da ke ana jiran wani abu ya faru, aure kasa da wata daya ki fara zuwa zaki fada min an miki ba daidai, daman miki daidai sai Allah Noor ki rufa ma kanki asiri ki zauna dakin mijinki, in har kika ce haka zaki fara da shi, to ko ba zaki taba zaman auren ba, ni bana son na ji komai tashi ki koma dakinki” Kamin ta gama bayanin kuka ya gama cin karfi, haka na tashi ina share hawaye na saka hijabina na dauki jakata na fito gidan ana sallah magariba. Hanya na kama na rasa ina zanje, yanzu kuma waye zan fadawa kukana? Ko dai na tafi gidansu? Kuma da wane idon zan kalli iyayensa? Me zan fada musu cewar ya ga wani abu a jakata yayi fushi da ni? Wata kila ya ji haushin haka ko kuma su ma su kasa fahimta kamar yadda shi ma be min uzuri ba, gashi ban san gidan na su ba. Ko dai na koma gida? Kuma idan na koma haka zai cigaba da yi min na san zuwa yanzu kuma ya dawo be same ni a gidan ba. A take zuciya ta raya min na tafi gidan Kareem na fada masa halin da nake ciki na fada masa abun da abokinsa yake min wata kila zan samu mafita, domin ina jin babu dadi yadda ya wofintar da ni babu ruwanshi da ni akan laifin da ban aikata ba. Mai napep din da na shiga be sauke ni ko'ina ba sai kofar gidan Kareem. Na bashi kudin Napep 400 sannan na doshi kofar na buga mai gadin ya bude min. “Dan Allah Kareem yana ciki?” “Gaskiya yana ciki be dawo ba, amman dai iyalinsa tana nan” Sanin halin matarsa na rashin maraba da mutane, da kuma kokarin fasa min kai da ta yi a wacan karon ya saka ban yi sha'awar shiga ciki na zauna a gefen gate din cikin flowers din da suka yi ma gidan ado. Ina zaune a gurin har aka kira sallah Isha'i aka sauko daga sallah sannan motar Kareem ya tsaya a gaban gate din yana horn. Na mike tsaye da sauri na nufi gilashin motar na kwankwasa sai ya sauke farin gilashin yana kallona. “Noor...” “Na'am” Na amsa ina hade hannayena waje daya yanayina na karantar da duk wanda ke kallona damuwata. “Ke da wa kika zo nan? And lafiya?” Hawaye ya fara sauko min. “Kareem ina cikin matsala, kuma ina jin kai kadai zaka iya taimaka min, dan Allah karka ce ba zaka saurereni ba, ina jin tsoron Baba na kasa fada masa kar ya kure ni ko ya min duka, Mama kuma ta ki ta saurare ni” Ya dan tsaya kallona kamin ya ce. “Shiga cikin gida” Na wuce sai da na fara shiga sannan na shigo da motarsa ya faka kusa da ni, ya bude ya fito ya kalleni. “Hafiz ya san kin zo nan?” “Aa be sani ba” “Me ya faru?” Na hade yawu. “Baya shiga bangarena yau kusan sati biyu, baya min magana matarsa ma fushi take da ni, ba ni da walwala Kareem gaba daya na ji na tsani gidan na tsani kaina” Ya ciro wayarsa ya fara tabawa. “Wani abun kika masa ko?” “Ban masa komai ba, kawai dai wani abu ya gani a jakata ya fara fada....” Na fada masa komai cikin kuka. “Minene to?” Na Cire jakar daga kafata na bude na dauko maganin da balloon din na mikawa Kareem.  Sai yaja baya da sauri kamar ya ga abun kyama. “What the F**uk, miye hadin ki da wannan Noor” Na kalli maganin na kalleshi. “Na minene? Ban san maganin miye ba Wallahi, wannan ballom din ma ban taba ganin irinta ba, Wallahi Wallahi ban san ko abun miye ba Kareem” “To ya aka yi kika samu?” “Ban san ya aka yi ba kawai shi ya ganshi a jaka” “Wannan maganin hana daukar ciki ne, wannan kuma Condom ne” “To me zai hada ni da maganin hana daukar ciki? Wallahi ban san shi ba ban taba ganinshi ba ma, ban san inda aka siyarwa ba, shi condom din me ake yi da shi?” Yayi shiru yana kallona. “Bayan aurenki baki hadu da Zafeer ba?” “Aa Wallahi ban sake ganinshi, kuma Baba yace idan na sake magana da shi be yafe min ba, ance ma ya tafi baya garin nan” “Akwai mai shiga dakinki ko ya taba jakarki?” Na girgiza kai alamar aa. “Dole akwai yadda aka yi Noor magani ba zai kawo kanshi ba, dole akwai yadda aka yi” “Ni dai na yi zargin Aisha amman tace ita bata saka ba, ban san ya zan wanke kaina ba Kareem, yanzu baya min magana kuma baya shigowa gurina fushi yake da ni” “Me yasa kika zargeta?” “Saboda tace wai na fada mata sirrinsa kuma ban taba fada mata ba, kuma a gabansa tace na ce zan kira saurayina a waya kuma Wallahi ban taba ce mata ba” “To kin taba barin jakarki a bangarenta?” “Aa, amman Wallahi ban san a ina aka samu maganin ba, ni ban taba ganin wannan ballom din ba ban san me ake yi da shi ba” Yayi shiru alamar tunani ni ma shirun nake ina hawaye. “Kawo?” Ya miko min hannunsa na bashi maganin da  balloon din ya saka aljihu, sannan ya dago ya kalleni ido cikin ido ya sauke ajiyar zuciya. “Noor ba zan iya miki komai ba, sai dai na baki hakuri, akwai dalilin da ya san ba zan shiga maganar ba” “Wallahi ban san wanda ya saka ba Kareem ba nawa ba ne” “Na yarda da ke Wallahi Noor i trust you, ko ma waye yana son yayi amfani da innocent you ya cutar da ke, Hafiz ya san abun da baki sani ba a game da ni, ba zan iya shiga maganar nan ba, wata kila shiga ciki zai iya janyo miki matsalar da ta fi wannan ba, iyaye ya kamata ki samu da wannan maganar iyayenki ko nasa” “Baba ba zai yarda ba, Mama kuma bata ma saurare ni, ban san gidansu ba, kuma idan naje wata kila ba za su yarda ba” Ya busar da iskar bakinsa damuwa ta bayyana a fuskarsa. “Kawai ki yi hakuro Noor ki tafi gida kar ma ki fada masa kin zo nan” “Tohm” Na share hawayena wasu na sauko min na juya na fara tafiya, sai ya kira ni. “Noor” Na juyo. “Kina da kudin Napep?” Na girgiza kai, sai ya saka hannunsa aljihu ya ciro kudi 2k ya ba ni, na karba ina kallon matarsa take tsaye jikin windows din sama tana kallonmu, shi ma daga kai yayi ya kalleta. Na juya sai kuma na sake juyowa a karo na biyu na kalleshi. “Kareem ya keke?” Yayi min kallon rashin fahimta. “Rasuwar Mahaifiyarka ban samu yi maka gaisuwa ba, amman abun yana raina, na san kai ma kana cikin wata matsala kuma na zo maka da wata am sorry...” Yayi min murmushi kawai. Ban sake cewa komai ba na kama hanya ina tafiya hawaye na sauko min har na fita cikin gidan. Ashe haka auren yake, ashe haka rayuwar auren take? Idan mutum yana cikin matsala babu wanda zai saurare shi, babu mai kawo masa dauki, shiyasa Baba yayi ta ganawa Mahaifiyarmu Azaba kala kala kuma ake ta ba shi gaskiya a duk lokacin da za a fadi matsalar. A lokacin da na tari Napep na hau sai fargaba ta ta koma gurin hukuncin da zarar tarar a gida, domin be min izini ba na fita gashi kuma dare yayi ban dawoda wuri ba, kuma abun da naje nema ban same shi ba. Dubu daya na mikawa mai napep din da ya kawo ni gida, ban tsaya karbar canjin ba na shiga ciki, ina hango motar Hafiz wani irin faduwar gaba da tsoro suka mamayeni, a haka dai na daure na karasa bangare na taba kofar falon na murda sai na ji ta a rufe na sake murdawa na tura na jita a rufe gam da alama an saka mata key an rufe ne. A gurin na sulale kasa na zauna gaba daya na rasa me ke min dadi. Ina zaune a gurin na hango Aisha ta fito da saurinta ta nufo inda nake babu jimawa Barrister ya biyo bayanta, ina ganin haka na mike tsaye ina kallonsa fargaba ta saka ni gaba kamar ance ga mutuwarki nan zuwa. “Ba magana make miki ba?” “Wallahi Barrister ba zan yarda ba, ko dai ka bude mata ta shiga ko kuma na kaita bangarena ta kwana ko kuma ni ma na bar maka gidan, cikin uku dole ayi daya, yanzu duk abun da ya faru mutane ni za su dorawa laifi, ace na hana muku zama lafiya, babu wanda zai iya wanke ni, Wallahi sai na yi ma Walida tsinanen duka a gidan nan, sai da na gargade ta karta fada maka amman saboda kunnen kashe ne da ita sai da ta fada” “Karki kuskura ki taba min yarinya, kuma ki cire bakinki ki cire idonki akan zamantakewarmu, ba ke kike aurenta ba ni nake aurenta” Yana fada ya jefo min keys din, sannan ya nuna mata bangarenta. “Wuce mu je” Ta share hawayenta, ta dora hannunta a cikinta da be gama girma ba. “Dan Allah Noor ki natsu, ko da baka son auren mutum ba haka ake rayuwar aure ba, be kamata ki fita baki fada masa ba, ki sani yanzu baki da ikon kanki ikonki yana gurin mijinkin ne, kuma idan ba ki yi dan Allah ba baki yi dan shi ba ki yi dan ni mana, Wallahi idan wani abu ya faru tsakaninku ni za a zaga, kuma a zarge ni” Cikin kuka take maganar sannan ya juya ta nufi bangarenta. Tsaye yayi yana kallona irin kallon na tsana da jin haushin mutum, sannan ya juya ya shige bangaren nata. Ni kuma na sunkuya jiki babu karfi na dauki keys din na saka na bude kofar na shiga, na rufe na jingina da kofar falon suuuu na tafi kasa na zauna ina kuka... KAREEM POV. Tsaye yayi yana kallonta har ta fice sannan ya juya ya nufi hanyar shiga cikin gidan. Murda kofar ya shiga. “Sannu da zuwa...” Yusura ta fada masa, sai ya kalleta fuska ya yabo ba fallasa ya amsa. “Yauwa” Ta sabuntawa kanta wasu dabi'u da hallaya da bata masa a baya, kamar kaima masa abinci a dakinsa yi masa sannu da zuwa ko a dawo lafiya idan zai fita. Tun a wacan ranar da Safeena ta leko gidan duk wasu hallaya da dabi'u nata sai suka sauya. Ya wuceta zai haura sama sai ta juyo tana kallonsa. “Ina tunanin a matsayina na matarka ina da hakkin tsare mutunci da martaba ta” Ya juyo. “Akwai wani furuci ko wani aiki da nake yi da ke zubar da kimarki?” “Kamar zuwan yan matanka, ya kamata ka san ina da girma a matsayina na matarka” “Noor Matar Hafiz ce, amaryarsa Safeena matar aure ce miye baki sani ba a ciki?” Ta masa wani kallo sannan ta ce. “Ga abinci can a dakinka” Ba tare da ya sake cewa komai ba ya haura saman ya shiga dakinsa. ko'ina kamshin sinasir yake da miyar da ta ji nama da manshanu. Amman ko kadan be kula abincin ba ya cire tufafinsa ya shiga yayi wanka kmar yadda ya saba ya fito ya saka kayan bachi, daman baya dawowa gidan sai ya cika cikinsa. (Idan kika karanta min littafi baki biya ban yafe ba.) A daren ya kwanta da tausayin Noor da kuma tunanin yadda zai bullowa lamarin, ta ko wane bangare idan ya hango sai ya ga kamar shiga maganar zai iya zama matsala. Sai dai ya yarda da wani abu daya, Noor bata aje maganin a jakarta domin idan har ajewa ta yi ba zata bari ya gani ba, wata kila dai tsakanin Aisha da Zafeer akwai mai shirya mata wani abun bata fahimta ba. Washe gari misalin 7am ya bar gidan saboda operation da za su a 8am a asibiti. Be wuce 10 -15 Min da fita ba Yusura ta shigo dakin kamar yadda ta saba ta fara bude kayan abincin da ta kawo ta ga be ci, daman kuma ta san ba zai ci ba domin yar kullum ce be cin abincinta ita ma kuma bata fasa girkawa. Sai da ta fitar da kayan sannan ta dawo dakin ta nufi gurin da yake aje kayan dauda ta bude ta dauko green shaddarsa ta jiya ta zauna gefen gadon tana lalaben aljihun kowane bangaren. Domin zuciyarta bata natsu da abun da ta hango Kareem ya karba a hannun yarinyar da ta taba fasawa goshi ba jiya... #KhadeejaCandy PAID PAGE 8️⃣ ©️KhadeejaCandy ©️®️Copyright 2024 Littafin nan na kudi ne, don't read if you didn't pay... One word kika karanta baki biya ni ba, ban yafe hakkina ba. To be part of the journey pay 500 to 2451879008 ZenithBank Hadiza Abubakar And send the evidence of payment to my WhatsApp number 08036126660.... You can read my latest update on arewabooks a handle dina @KhadeejaCandy https://www.arewabooks.com/book?id=659a94c8be87d7a51f831153 _______•••_______ Wani irin faduwa gabanta yayi a lokacin da ta yi arba da abun da ke cikin rigar aljihun Kareem. Me hakan yake nufi Kareem yana tare da yarinyar nan kenan? Ba ita kadai ba wata kila har da Safeena, matan aure yake bi kenan? Shiyasa yake takura mata a lokacin da take fita gani yake kamar ita ma gurin wani zata tafi? Anya ma wannan Amaryar Hafiz ce? Idan har gaskiya ne me zai saka yayi tarayya da ita? Ta mike tsaye da sauri ta fice daga dakin rike da maganin da robar ta shiga dakinta sai da ta dauki wayarta sannan ta tuna bata da number matar Hafiz domin ba kowa take hulda da shi ba a cikin matan abokan Kareem, iyakar ta da wasu gaisuwa. Number wayar Samira ta nema ta kirata suka gaisa cikin mutunci sannan ta bukaci Samira ta turo mata da number Aisha matar Hafiz. “Wai daman baki da number ta” “Ban taba karba ba” “Kai kawata baki da kirki, bari na turo miki yanzu” “Yauwa na gode, Ai na san kuma good time da ita ba zaki rasa number ta” “Okay” Ta sauke wayar kamin Samira da ta kasance cousin dinta ta turo mata mumber Aisha har ta matsu. Sakon mumber na shigowa ta bude da sauri ta taba Number ta kira sai daf da zata yanke Aisha ta daga. “Assalamu Alaikum” “Wa'alaikusalam Aisha ya gida?” “Lafiya kalau ya yaran?” “Alhamdullahi kin gane mai magana?” “Na so dai na gane, amman ban gane ba” Yusura ta yi murmushin karfin hali. “Yusura ce Maman Tine” “Kawai ki ce min Mrs Kareem zan fi ganewa, uwargida ran gida” “Oh oh toh ke ma ai uwargidance, ko da yake yanzu nake jin cewar Hafiz ya kara aure” “Wallahi haka ne, kika ji ko dai Kareem ya fada miki, ai ke ma auna arziki kika yi da yanzu ke za a kawowa ita” “Ban gane ba” Yusura ta fada daman abun da take nema kenan. Aisha ta sauke numfashi. “Hmmm ai mijinki ya so aurenta shi yayi sonta sosai, sai dai ban san miya hana shi aurenta ba, kwatsam Hafiz ya zo min da zancen auren, wai zai rufa mata asiri ya aureta saboda wanda zata aura an fasa auren sanadin Kareem shi kuma Kareem din yace ba zai aure ta ba, kin san mazajen na mu da hadin kai ko ma dai miye Allah kadai ya sani” “Amman kika yarda Aisha?” “au hanawa zan yi? Kin ji Yusura da wata magana, namiji da zai yi aure zaka iya hana shi ne? Ai idan namiji zai kara aure baya ji baya gani, shiyasa na nuna masa na fi shi tausayinta, na san waye Hafiz na gama karantar mijina daman kuma idan ka fahimci waye mijinki zaman aure ba zai yi ma mace wahala ba, shiyasa na goya masa baya dari bisa dubu aka yi komai aka gama cikin mutunci lefen ma ni na hadawa kaina na hada mata, yadda na san Hafiz ina daga hankalin na daga na shi zuciya zata iya dibarsa ya sallame ni gidanmu, amman hakan da na yi sai na siye zuciyarsa da ta yan'uwansa gashi muna zaune lafiya ni gani nake kamar ma ya fi so na yanzu sama da lokacin da be auri yarinyar ba, domin na kara value a idonsa” “Toh Allah yasa yar gidan mutunci aka dauko miki kin san yan matan yanzu” “Waya sani ance dai ubanta dai shegen kwadayi ne da shi ko kashe rai zai iya yi akan kudi, ita kuma gaskiya ance bata tsayawa kanta ba, kawai dai maza ne mace daya bata isarsu sun maida karin aure rayuwa, kuma basa tsayawa su duba yar gidan mutunci daukowa kawai suke, saboda tana da kyau” “Oh Allah ya kyauta, matan zamanin nan sai a hankali” “Ameen kedai ina nan ina lallabawa karta kashe min aure, ga yara ga ciki na tafi ina? Samun miji irin Hafiz a wannan mazanin ai sai an tona is rare gaskiya” “Allah ya tsare miki aurenki, ni ai be fada min ba sai yanzu, na ce dole na kira na miki jaje” “Hmmm na gode, zan yi saving number ki ai a rika gaisawa” “Toh sai anjima” Yusura ta kashe wayar gabanta na bugawa da karfi. What her husband got into? Ko shiyasa ta zo nemansa har cikin gidan kamar yadda Safeena ta zo? Me yake kokarin zama ne? Matan aure yake nema? Ta mike tsaye ta fara tafiya tana daga kanta. Amman ita miye nata a ciki idan ma neman matan yake yi? Kabarinsa dabam nata dabam, kuma bata fatan zama da shi har abada. “Saboda yaranki...” Wata zuciyar ta fada mata. domin saboda su ta dawo tana kokarin kyautata masa tun daga lokacin da Safeena ta leko gidan. Ji take indai tana raye ba zata iya bari Kareem ya auri Safeena ba ko da kuwa bata da aure domin Momy bata son Safeena ko kadan, mutuwarta kuma zai iya saka Safeena ta yi tunanin sake kulla alaka da Kareem. Gashi yanzu babu Momy babu mai masa fada idan yayi ba daidai ba. “Innalillahi Wa'Inna Ilaihirraji'un” Gaba daya ta rasa me ke mata dadi, ta rasa ina zata kama abun ya daure mata kai, wai saboda be sonta yake bin mata ko kuma dai wani sabon hali ne ya kirkirarwa kansa? Tunaninta ya kasa tsayawa guri daya. KAREEM POV. @4:11pm suka fito daga massalacin dake cikin restaurant din, Kareem na gyara hannun rigarsa ya ce. “Ni dai da zaka dauki shawarata Barrister karka karbi case din nan, case ne mai matukar hadari kasan yadda yan siyasa suke” “Amman za a samu kudi mai kyau fa Doctor” “Rayuwa ta fi kudi muhimmanci, duk kudin da zaka samu idan ba zaka samu rayuwa ba ba su da amfani” “Kusan kowane aiki akwai risk ciki, kawai dai ka taya ni da addu'a” “Allah ya tsare, amman ni ban yarda ka karba ba gaskiya” Hafiz ya tura kofar office din ya fara shiga yana fadin. “Su suka neme ni fa, kuma saboda cancanta suka neme ni, ba zan oya watsa musu kasa a ido ba, abu na biyu ba a nan za'ayi ba a Kaduna ne” Kareem ya daga kafadunsa. “Indai ka nace sai ka yi ai babu mai hanaka, haka shi ne kawai matsalata da kai” Yayi murmushi yana gyara zamansa a kujerar da ya zauna. Kareem yayi shiru na yan mintuna sannan ya kalli Hafiz cikin karfin hali ya ce. “Hafiz ya iyalinka?” Wani kallo Hafiz yayi masa a cikin kallon da yake masa idan yana tuhumarsa da wani abun. “Lafiya?” “Ka tabbata?” Hafiz ya gyara zamansa. “Akwai abun da kake son mu tattauna?” Kareem yayi murmushi domin shi da abokinsa kowa ya san halin kowa, da zarar dayan ya fuskaci wani canja ko da na magana ne zai fahimci akwai manufar aikata hakan. “Amm... Ban san ya zaka dauki abun ba, na so na bar maganar sai kuma nake ganin kamar zaka kone kanka ka cutar da iyalinka, be kamata na shiga cikin maganar ba amman dole ce ta saka” Hafiz ya mika masa duka hankalinsa yana kallonsa. “Lokuta da yawa idan ka ga In aikata wani abu da be dace ba kana yawan jan hankali kuma ka lurar da ni gurin da illar abun take” “Ka wuce duk wannan Kareem fada min kawai” Kareem ya zauna da kyau. “Hafiz akwai wata matsala tsakaninka da Noor ne?” Hafiz ya kalli wani gafen alamar tunani sannan ya kalli Kareem. “Ta zo nan ne?” A madadin Kareem ya amsa masa sai ya dora da abun da yake jin kamar shi ne matsalar. “Hafiz ka rika bincike kamin ka yi fushi ko yanke hukunci” “Kareem ta fada maka abun da ta yi?” “I don't think Noor zata yi abun da kake tunani, she's very innocent, Hafiz bata ma san amfanin abun da ka gani a jakarta ba bata san me ake yi da shi ba, kuma abun mamaki ne ace ta san wannan a yanda take da kananan shekaru, she's too young for that ita ba karuwa ba ba matar da ta shekara hudu gidan miji ba” Hafiz ya nade hannayensa. “Idan bata sani ba taya suka zo a jakarta? Kasan dai ba za su kawo kansu ba ko? Idan ba ta siya ba maybe wani ya bata wani like Zafeer amman ta ki yarda ta fada wanda ya bata, ko kuma ya fada mata ta siya, ranar da na kaita gidansu ta wuni a ranar da ta dawo ne na karbi wayar da na bata kawai wata zuciyar ta raya min na bude jakarta and i did na ga abun a ciki” “Taya zata amsa laifin da ba nata ba, bata san ya aka yi ya zo jakanta ba” “Kai kuma ka yarda da ita?” Kareem ya kasa cewa komai wannan babin saboda baya son ya janyo mata laifi gurin Hafiz. “Ya kamata dai ka yi bincike, ta rantse bayan aurenta bata hadu da Zafeer ba ko ta yi magana da shi” Hafiz ya kwanta jikin kujerar. “Wa kake zargi? Aisha saboda ta fada maka Aisha, shiyasa na kirata ai lokacin da ta zarge ta kuma ta rantse a gaban Noor ba ta saka ba, sai me?” “Maybe the way you confront her zai iya sakawa ta rantse ko da akan karya ne saboda ta wanke kanta” “Me yasa ka yarda zata aikata amman baka yarda Noor zata aikata ba?” “Saboda Noor bata waye duniya, da zaka ce min ta shiga gidan mutane ta yi arba da nama ta sata ko ta dauki wani abun dadi ta boye a jakarta zan fi yarda, amman ko kudi bana saka ran Noor zata dauka a dan fahimtar da na yi mata na kankanen lokaci Noor ba zata san miye abun da ke jakarta ba, kuma mace makira ce Hafiz na ga hakan a zaman da na yi da Safeena da Yusura, baka iya ganewa kansu, yanzu idan ka ga yadda Yusura take min a gaban mutane ba zaka tana tunanin akwai wani abu na rashin so ko zaman lafiya a tsakaninmu ba, yanzu kuma har wani hali ta kirkira saboda Safeena ta zo gidan har dakina take kawo min abinci idan zan fita tace Allah ya tsare idan na dawo tace min sannu da zuwa, na fara tsorata da lamarin matar nan” Hafiz yayi murmushi. “Safeena ta zo gidan fa ka ce Kareem? Amman ban taba ganin mutumen da ya raina matarsa ba irinka” “Ba zuwa na yi da ita ba, kuma na gayyato ta na yi ba saboda na daina daukar wayarta ne ya saka ta zo da sunan ta zo min gaisuwa, amman dai na taka mata burki. So ni ina ganin ya kamata ka yi bincike ko kuma ka yafe mata ka rufe maganar kawai ba wai ka dauke mata kafa ba, kuma ka daina magana da ita a halin da take karkashin kulawarka. Ka ga duk yadda nake da Yusura bata so na bana sonta ba ma zaman dadi amman a haka idan na ga ta wuni bata fito shiryawa yara abu ba, ko kuma ban ji motsinta ba na kan leka na duba lafiyarta domin hakkinta ne da ya rataya a wuyana, please ka gyara” “Zan gyara, amman kamar yadda baka yarda Noor bata san komai akan samun maganin a jakarta ba ni ma ban yarda Aisha ta saka mata ba, na san wacece Aisha shekara nawa muna tare da ita, mace ce mai kirki mai mutunci” Kareem be sake cewa komai ba, domin baya son ya zafafa kasancewar ba shi da hujja kuma baya son Hafiz ya dauki abun ta wata sigar. Sai dai abun da be sani ba Hafiz ya gama fahimtar har yanzu akwai Soyayyar Noor a zuciyarsa hakan kuma ya saka shi jin kamar aurenta ba shi da amfani a gareshi. Sai bayan Sallah Magariba suka rabu da juna Hafiz ya nufi gidan Kareem kuma ya fito ya zauna a harabar kamar yadda ya saba domin baya shiga gida sai bayan Isha'i lokacin da yake tare da Safeena gidansa da suke badala yake tafiya sai kusan 11 ko 10pm suke rabuwa... A hanya yayi sallah Isha'i sannan ya shiga gidansa, yana faka mota yaransa suka fito da gudu suka tarbe shi sai ya daga su sama yana ajewa yana dariya. “Baku yi bachi ba” “Eh Daddy me ka siyo mana” “Ban siyo komai ba amman dai akwai chocolate a daki muje na baku” Ya kama hannunsu suka shiga ciki babbar ta rufe kofar falon, Yusura ta mike tsaye daga zaune da take. “Sannu da zuwa” “Yauwa Sannu” Yana rike da hannun yaransa ya haura sama suka shiga dakin, gaban maduni ya tsaya ya fara cire agogonsa akan Areef ya hau gado yayi tsalle ya haye masa baya yana dariya, shi ko yana juyowa ya fara masa chakulkuli sai dariya suke har shi gogan. Gurin da yake aje kayan dadin ya bude ya dauko ya mika musu. Yusura ce ta shigo dakin hannayenta a baya tana kallonsu. “Tine ku je falo zan yi magana da Daddy” Ya juyo ya kalleta, su suka sauka daga kan gadon suka fice daga dakin. Karasa ta yi kusa da shi ta dora masa abun da ta samu a aljihunsa kan gado. Ya kalli maganin da sabuwar robar ya kalleta irin kallon nan na me aka yi? Ita ma ta yi masa irin kallon ya aka yi suka zo aljihunka. Ya dan tabe baki “Ba nawa ba ne” “Su suka kawo kansu?” “Ni ban taba amfani da condom ba a rayuwata, da maganin da cdm din ba nawa ba ne, dalili ya kawo su” “Dalilin nake son ji” “Miye matsalarki da shiga hurumi har kina bincikar kayana? Ki tsaya matsayinki kar ki sake yi min haka” “Okay so kake na zuba maka ido ka lalace? Matan auren har gida suke zuwa nemanka? Ka ba su fuska na nuna musu ba ni da muhimmanci a gurinka?” “Babu wata alaka tsakanina da su, can you excuse me please...” “No idan wani abu ya faru yanzu ai ni za a zaga saboda Momy bata raye ni za a dorawa laifi” Da mamaki yake kallonta wato gata uwarsa. “Me ya same ki ne? Why are you behaving like this? Ba ma shiga hurumin juna, me ya canja yanzu” “Babu abun da ya canja, kawai duk abun da nake ina yi ne saboda yarana, kuma ba zan sake daukar wata karuwa ta shigo cikin gidan nan nemanka, ka tsaya can waje ka yi tun da ka lalata rayuwarka, ka dauki hakkina ga hakkin yara ga hakkin Momy ga hakkin Daddy ga hakkin Allah ga hakkin matan da kake lalatawa ga hakkin mazansu da yayansu kana zuwa lahira wuta a a saka ka kai tsaye...” Shi dai kallonta kawai yake har ta gama balbalin bala'in ta fice daga dakin. Because he's not a fan of argue. Juyawa yayi yana kallon kofar be taba aikata wani abu da ya shafi rayuwarsa ya ga Yusura ta fusata haka ba irin wannan, kuma ta nuna a fili sai wannan karon, and the most funniest part is yadda ta jero masa hakkin kowa a kai kamar ita zata kai shi wutar. Kai ya girgiza sannan ya shiga bandaki yayi wanka ya fito ya shirya cikin Pajamas. NOOR POV. Yadda nake kwana sati biyu da suka wuce haka na kwana a yau ma. Wato kwanan bakinciki da damuwa da kuka da kuma kadaici. Da safe na fito na gyara falon da be yi dattin komai ba na shiga kitchen na hada tea na fito falon na zauna ina sha. Muryar Aisha na ji tana yi ma Hafiz Allah ya tsare. Hakan ya saka ni mikewa tsaye na isa gurin windows din na bude sai na hango shi zai shiga mota ita kuma tana tsaye da murmushi a fuskarta sai hannu take daga masa. Har ga Allah bana son Hafiz kuma bana jin zan iya son sa ba shi kadai ba har zuciyata ba zata taba kaunar wani namijin ba bayan Zafeer amman tabbas ina jin zafi sosai yadda ya aje ni a karkashinsa amman ya kasa yi min inuwa kuma yana min ba ni muhimmanci a gurinsa. Ina kallonsa ya tuka mota ya fice daga gidan ba tare da ya shigo bangarena ba, na yi tunanin zai shigo ko da fada ne yayi min ya tambayi ina na tafi ba tare da izininsa ba. Kuka na yi har sai da numfashina ya fara sakerwa na kasa cin komai a wunin sai kuka. Sallah ma daker na yi saboda jikin babu karfi, I'm so hopeless babu mai taimakona, ko da zan mutu a wannan halin na kunci da nake ciki babu wanda zai kawo min dauki. A falo na yi sallah magariba ina sanye da hijab dina milk color na ji tsayawar motar Hafiz, sanin ba zai leko bangarena ba ya saka ban leka waje ba, kar na yi arba da bakinciki. Sai dai abun da ban yi zato ba ne ya faru, ganinsa na yi a falon kamar an jefoshi gabana ya shiga bugawa da mugun karfi ganin yayi tsaye a kaina yana kallona ni kuma na gagara cewa komai. “Ina kika je jiya?” Gabana ya fadi na gagara cewa komai sai hade yawu nake. “Gurin Kareem? Office kika same shi ko gida.?” Na sauke kaina kasa nan ma bana iya fadar komai. “Ke wai sai yaushe zaki yi hankali?” Na ji sanyi hawaye ya jika fuskata. “Ta so muje” Na dube shi da sauri. Kamin na yi wani yunkuri har ya mike tsaye, a dole ni ma na yi tsayen na bi bayansa sai ya juyo ya kalleni. “Je ki saka talkaminki” Na nufi gurin da talkamin suke na saka shi kam tuni ya fice daga falon ma. Ko da na fito ya tashi motarsa da kansa ya bude min front na shiga na zauna ya rufe sannan yaja motar muka fara tafiya, be kalli inda nake ba ni ma ban kalleshi ba sai sake saken nake a zuciyata ina zai kai ni? Me Kareem ya fada masa? Ina son na tambaya amman na kasa saboda bakinnya rufe min gam. Unguwarmu ya nufa yana ratsa gidajen dake ciki har ya isa kofar gidanmu, a nan na fahimci so yake ya hada ni da iyayena. Na kalleshi hawaye na min zuba. “Fita ki shiga gida, ki zauna sai na neme ki...” Ya fada ba tare da ya kalleni ba, na juyar da kaina dake rawa na bude motar na fita sai na yi tsaye na kasa daina kallonsa na kasa juyawa na shiga cikin gidan. Mun dauki mintuna a haka sannan ya miko hannu yaja gambun motar ya rufe yayi mata key ya bar ni a gurin tsaye cikin ruwan hawaye. Me kuma aka ce na ce? Yanzu kuma wane kalar laifin na aikata? Na zauna sai ya neme ni ya sake ni kenan ko kuma yaya? #KhadeejaCandy PAID PAGE 9️⃣ ©️KhadeejaCandy ©️®️Copyright 2024 Littafin nan na kudi ne, don't read if you didn't pay... One word kika karanta baki biya ni ba, ban yafe hakkina ba. To be part of the journey pay 500 to 2451879008 ZenithBank Hadiza Abubakar And send the evidence of payment to my WhatsApp number 08036126660.... You can read my latest update on arewabooks a handle dina @KhadeejaCandy https://www.arewabooks.com/book?id=659a94c8be87d7a51f831153 _______•••_______ Na kusan minti talati tsaye kofar gidanmu kamar wanda aka cewa shiga ki tararda hisabinki haka tsoron shiga gidan ya kamani, domin na san waye mahaifina. Amman ba ni da wani gurin da ya fi gidan ina zan je? Ai ba ni na kawo kaina ba shi ya kawo ni. Cikin kasala da fargaba irin na wanda ya rasa makoma na saka kafata a gidan, duk yadda nake son hana hawayena zuba kasawa na yi. Sai kuma na yi rashin sa'a Baba na tsakar gidan yana alwala, ban yi sallama ba domin bakin har lokacin a rufe yake. Baba ya hasko ni da fitilarsa mai haske. “Wa nake gani kamar Norriya?” Tafiya kawai nake cikin gidan na kasa Cewa komai. “Lafiya?” Na durkusa a gabansa. “Wani abu ne ya samu Hafizun?” Na girgiza kai. “Toh me ya faru?” Hana ta fito daga daki tana kallona cikin tashin hankali. “Cewa na zauna sai ya neme ni” Fitilar dake hannun Baba ta subuce ta fadi kasa. “Innalillahi Wa'Inna Ilaihirraji'un, daman ai sai ba ke ba Noor, yanzu duk irin abubuwan da mutunen nan yayi min yayi miki sai da kika kai shi makura? Tafiya kika yi kina masa shashanci da sakarcin na ki ko? Har ya gaji yanzu ya koroki gida” Na matsa baya da sauri jikina na rawa domin fadan da Baba yake min irin na son duka ne. “Yaushe aka yi auren da zaki biyo dare yanzu ki ce wai yace ki zo gida?” Na bude baki zan yi magana ya daka min tsawa ya cire talkaminsa ya jefani da shi. “Ban son jin komai daga bakinki, marar mutunci daman ai na san sai kin masa shashanci, kina kallon yadda rayuwa take a gidan nan kin samu mai rufa miki asiri ne shi ne kika fara masa rashin kunya ko? Saboda ya sake ki ki auri Zafeer ke ga ki shim mai ruwa uku shashasha, sakinki yayi?” Na girgiza kai. “To tashi maza ki koma dakinki, ina nan ina jindadi na samu suruki mai dauke mana komai shi ne zaki fara watsa mana kasa a ido? Ni daman sai da zuciyata ta raya min anya ba kina masa rashin mutunci ba ne, in ba haka ba da yanzu ya gyara mana gidan nan amman shiru, ashe kina can kina nuna masa rashin tarbiya, mai kashin tsiya so kike mu koma rayuwarmu ta baya ko? Ke yar zamani, minti biyar ban yarda ki kara yi a gidan nan ba, koma dakinki gobe zan zo na ji me ke faruwa amman Wallahi ba zaki kwana gidan nan ba, wato halin uwarki zaki dauka na rashin hakuri ko? Ko kuma so kike ya sake ki ki dawo ki sake zaunawa ke da kanwarki a daki daya? Wawuya marar hankali, wato ki zaki nunawa wai ba zaki yi zaman aure ba ko? To na fiki zama dan tasha... ” Ya karasa yana daukar butar da yake alwalar da ita ya jefa min. Na tashi da sauri na fice daga gidan ina kuka, Baba be saurari izurina ba ya koroni daman na san hakan zai faru, da na fito sai tashin hankalin yayi min yawa na rasa ina zan je, na koma gidan Hafiz din da ya kawo ni gida yace na zauna sai na neme ni ko kuma na tafi gidan Mama? Ita ma koroni zata yi. Haka na bi hanya ina tafe ina hawaye har na isa titi, wata zuciyar na ce min na tafi gidansu kawata Zainab na kwana, domin ba ni da kudin abun hawa ma balle na koma gidan na san kuma ba zai ba ni ba, wata kila ma na samu ya fadawa mai gadinsa cewar kar a bar ni na shiga cikin gidan. Juyowa na yi na dawo cikin unguwarmu na shiga gidansu Zainab, Umma na ganina ta san ba lafiya ba, kamin Zainab tace min komai Umma ta fara tambayata lafiya. “Umma Hafiz ne yace na zauna a gida sai ya neme ni, na zo kuma Baba ya kore ni, na san idan na tafi ma Mama ba zata saurare ni ba, ban san inda zan je ba” “Wani abun kika masa?” “Ban masa komai ba Wallahi ban masa komai ba” “Aa Noor ba zai yiyu haka nan kawai yace ki tafi ki zauna a gidanku ba, sai kin masa laifi, Allah yasa dai ba Zafeer kika saka a zuciyarki ba, kar soyayyarshi ta hana ki zaman aure, ki kama kanki Noor ki natsu, yaushe aka miki auren da har za ace an fara samun matsala irin wannan?” Na yi shiru domin ba kowa zai yarda da ni ba. “Kin ga ni ba zan baki mafaka ba, mahaifinki ya koreki wace ni na baki gurin zama? Ai zai ma iya ci min mutunci ko kuma a ce saboda ni ba uwarki bace yasa na yi haka, ki yi hakuri ki koma dakinki ki bawa mijinki hakuri ku zauna, shiyasa ma na hana Zainab tafiya gidanki kar wani abu ya faru ace ita take hure miki kunne, ki yi hakuri ki koma dakinki Noor” “Tohm...” Na amsa kana na juya domin bata bar ni na zauna ba ma, haka na fito daga gidan ina hanya Zainab ta tarar da ni ta ba ni 500. “Mama tace ki hau Napep, kuma Noor idan ba zaki iya komawa gidan kai tsaye ba, ki tafi gidan iyayensa ko kuma wani dan'uwansa wanda kika san yana jin maganarsa, sai a kira shi a yi masa magana kinji” “Ban san gidansu ba, be taba kai ni ba” “Ko gidan wani abokinsa ba kisa ni ba?” “Na sani amman hakan zai iya bata masa rai, jiya naje can na fada masa amman be yi komai ba, wata kila shiya saka yau na ce na dawo gida na zauna” “Idan kin tafi kice ya fada miki gidan iyayensa ki tafi, ba wai dole shi zai masa magana ba, kuma Noor na san halinki da rashin jin magana dan Allah ki zauna lafiya” Na yi murmushi ina jin ina ma ace ni ce a matsayinta. “Na gode Zainab” Ta tsaya a gurin har sai da na samu Napep na hau sannan ta juya. Kuka ne abun da nake yi har mai napep din ya isa kofar gidan Kareem. “Allah yasa lafiya kike wannan kuka ko mutuwa aka yi?” Ban ce masa komai ba na mika masa dari biyar din na fita Napep din ina kallon gate din gidan ban san me zan sake ce masa ba. Ina ta zuwa masa da matsalata, waya sani ma ko hakan ya zama sanadin mutuwar auren nawa gaba daya. Sai dai ba ni da wata mafitar bayan wannan, a gaban gate din na duka ina kuka sosai. Da rarrafe na isa gate din na kwankwasa, babu jimawa mai gadin ya bude ya leko. “Waye?” Na share hawayena na mike tsaye. “Ni ce wadda na zo jiya, Kareem yana nan?” “Eh yana ciki” Ya bude na shiga ido a kumbure hancina n yaji saboda majina da gugar da ya sha, fuskata ta yi ja sosai. Kai tsaye na nufi cikin gidan cikin rashin sakewa da tunani kala kala a raina, damuwa ta saka na manta waye matar Kareem, na manta cewar huruminta na shigo domin mijinta. Na kwankwasa kofar falon ta bude min ni da ita muka tsaya kallon juna. “Ke ce?” Na daga mata kai. “Kareem yana nan?” “Eh yana nan shigo” Na goge gudun hawayena na shiga falon na tsaya daga gurin kofar ina kallonta. “Ina son magana da shi ne dan Allah” “Okay ina zuwa bari na kira shi” Ta juya ta nufi wani gurin da nake kyautata zaton kitchen ne. Bata ji ba ta fito nufo gurin da nake tsaye. “Ki shigo ki zauna mana bari na kira shi” Ba tare da tunanin komai ba na shigo kamin na zauna ta ware hannunta ta buga wani abu mai mugun karfi a kai, ban gama tantance miye ba na sake jin saukarsa a wuyana, wani irin jiri ya dauke ni na soma ganin ta zame min biyu kamin idon ya rufe... *** *** *** Babu ihu babu kokarin kare kai Noor ta yi kasa idon suka rufe, gefen da ta buga mata mociyar kuma jini ya fara jika hijabin har ya zubo kasa. Da sauri Yusura ta saki muciyar ta matsa baya jikinta ya fara rawa, me ya kaita? Me yasa ta aikata? Ina tunaninta ya tafi haka? Sai kuma ta matsa ta taba Noor ta ji bata motsi ta sake matsawa baya ta zauna kan kujera hankalinta a tashe jikinta na rawa. Kaminnta tashi da sauri ta haura sama. Dakin Kareem ta shiga yana sanye da multicolours din Pajamas dinsa hannunsa rike da books din Rules of the Journey. Daga kishingiden da yake ya dago kai ya kalleta ko'ina na jikknta rawa yake tashin hankali a fuskarta karara. “Ya.. Yarinyar da ta zo jiya ce ta dawo yau” Kareem ya rufe littafin yana kallonta hankalinsa kwance. “An samu akasi na buga mata abu ta fadi” Wani irin tsalle ya daka ya sauko daga kan gadon. “What.... Me yake damunki? Why?” Ya fice daga dakin da sauri sai ta bi bayansa kamar zata yi kuka. Kareem ya sauka kasa ya karasa gurin da Noor take kwance cikin jini. “Innalillahi Wa'Inna Ilaihirraji'un, Me kika aikata haka Yusura? Baki san me ya kawo yarinyar nan gidan nan ba, ban san halin da take ciki ba kawai ki kara mata da wannan?” “Ta mutu ne?” Yusura da ta kasa karasa saukowa ta tambaya cikin kuka. Kareem ya saka hannunsa ya cire Hijab din Noor ya taba wuyanta ya cire dankwalin kanta ya daure mata kan dake zubar da jini sannan ya tashi ta sauri ya haura sama ya dauko keys dinsa ya fita ya janyo motarsa ya kawo kusa da entrance din ya shiga falon ya dauko Noor da bata san inda take ba ya saka ta bayan motar ya shiga driver side ya ja motar sai asibiti. Gado aka bata shi yayi mata duk wani treatment da ya kamata, ya saka mata drip sannan ya lalaba aljihunsa ya sai a lokacin ya tuna be zo da wayarsa ba. “Oh nikan matan nan son hada min wuta...” Ya fada yana kallonta. “Me ma ya sake fito da ke Noor?” Tambayarta yake kamar ance masa zata iya amsawa. Dakin ya fita be bar asibitin ba sai da ya tsabtace kansa sannan ya shiga motarsa ya koma gida. Yana shiga falon Yusura ta mike tsaye tana kallonsa. “Tana raye?” Wani mugun kallo ya watsa mata. “Kusan wannan ne karo na biyu da kike kokarin illata yarinyar nan, wannan ya zama na karshe, wacan karon kamin ta yi aure ne har ina fada mata kawai dai an samu akasi ne, ba wai dan kishi ba, yanzu kuma ban san me ya zo kanki ba...” Ta matsa kusa da shi. “Yanzu din ma akasi ne, gobe da jibi din ma akasi ne matukar bata dauke kafarta daga gidan nan ba, kusancinta da kai yana kusanto maka da mutuwa ne kai da ita” “Idan kika kasheta zai ba ni mamaki, domin baki da wani dalili na aikata hakan. Kashe ni ba zai bada mamaki ba, tun da na san ba ki so na, ko akwai abun da ya canja?” “Babu Kareem babu, babu abun da zai canja har gaban abada...!!! Ko a mafarki bana fatan ko a lokacin da kake da natsuwa balle yanzu da kake bibiyar matan aure ciki har da matar amininka...” Ta fada da karfi sannan ta juya, fisgota yayi ya dawo da ita. “Babu wata alaka tsakanina da Noor, idan har zan kulla wata alaka makamanciyar wadda kike zargina da ita, to da zan aureta ne na aje ta a gidan nan under the same roof mu rayu har abada ni da ita, sai dai kuma babu irin wannan sha'awar tsakanina da ita” “An fada min ai, kun yi soyayya sai kuma ka saka abokinka ya aureta deal ne?” Sakinta yayi yana murmushi. “Haba ke kuwa taya Kareem zai yi soyayya da wata yarinya, yana da damar aurenta kuma sai ya ki aurenta ya saka abokinsa ya aure ta? Daga baya kuma ya zo yana bibiyarta? Wane irin ƙidahumi ne ni? Ai da abun da aka fada miki ne ya faru to sai dai na aurota na kawo nan mu sha soyayya” Abu ta hade da karfi ta juya ta haura sama ta barshi a gurin tsaye. Ta wani bangaren baya ganin laifin abun ta aikata domin gidanta suka shigo kuma neman mijinta, ta gurin da abun zai daure masa kai ace tana kishinsa domin abun da ake so ake kishi, shi kuma be saka ran samun haka daga gurin Yusura. Isakar bakinsa ya busar ya nufi dakinsa ya wayarsa ya dauka ya kira Hafiz. “Hello...” “Barrister kana gida?” “Ina gida lafiya?” “Zaka iya fita waje mu yi magana” “Okay....” Shiru na 2 minutes ne ya shiga tsakani kamin Hafiz ya amsa daga dayan bangaren. “Ina jinka” “Kun sake yin fada da Noor ne?” “Daman ba fada muke ba, kawai dai na turata gidansu ne yau?” “Saboda me?” “Tana bukatar a koyar da ita zamantakewar aure Kareem, ba zan Boye maka ba na fara nadamar auren yarinyar nan!” “Subhanallahi, to maybe wani abun ya faru a gidansu ko kuma bata tafi gidan ba, ta zo gidana by mistake Yusura ta fasa mata kai yanzu haka dai tana asibiti” Hafiz yayi shiru kamar ba zai ce komai ba. “Dan Allah kaje ka sameta kuma ko miye a tsakaninku ka yi hakuri mana Hafiz, hankalin Namiji baya zama daya da mace, kuma san halin mahaifin yarinyar yana daga cikin dalilin da ya saka ka aureta saboda ka tsamota daga kunci, to miyasa ba zaka jure ba kana lurar da ita har ta fahimta, ba mamaki mahaifinta korarta yayi ta rasa gurin zuwa ta zo nan, ni kuma ban ma sani ba sai fitowa na yi na samu Yusura ta yi mata aika aika, kuma kai ya kamata na kira domin responsibility dinta yana kanka as her husband don't misunderstand the issue please” “Tana ina yanzu?” “Tana asibitinmu, emergency room 44, please ka sassautawa yarinyar nan Hafiz duk yadda kake tunanin hankalinta be kai can ba, a yanayin yadda na fahimta ta tashi a wani yanayi ne na rashin dace da iyaye shi ne musabbabin komai, idan ka hada mata zafi iyayenta suka hada ma za ku iya sakawa ta kamu da depression domin bata da mai rarrashinta bata san gurin da zata tafi ta ji sanyi ba, ta yi kankanta ace ta fara samun matsalar aure tun a yanzu, and idan bata samu kwanciyar hankali a gidan ka ina zata samu? Already ta rabu da wanda take so, idan ta rabu da kai iyayenta za su iya juya mata baya, idan a gidanka bata jin sanyi kashe kanta kuke son ta yi? Kai da kanka ka ce za a iya koya mata son wani, to ka koya mata mana, ka nuna nata gurin da illar abu yake da sannu zata gyara” Hafiz ya ki ce komai ba, sai wani cika zuciyarsa take duk abun da Kareem yake fada shi wani abun yake hangowa can dabam. “Good Night” Kareem ya kashe wayar ya jefar kan gado ya sauke dogon numfashi. “Poor girl” Ya furta, ya zauna bakin gadon yana jinjina kai. NOOR POV. “Good Morning...” Na ji wata matar da ban taba arba da kalar fuskarta ba ta fada tana yi min murmushi. Yunkurin tashi na yi zaune sai ta rika ni na zauna na sake dubanta da idanuwa da ba su gama budewa ba. “How are you feeling now?” Na daga mata kai ina jin kamar an dora min wani dutse a gefen kaina saboda nauyin da yayi min. Hannu na kai na taba sai na ji an daure gurin, gefen wuyana ma an saka min wani abu a gurin sai ciwo yake min. “Ya jikin na ki?” “Da sauki” Na amsa ina kallon dakin da ban san lokacin da aka kawo ni ba. Gashi babu kowa a kusa da ni sai wannan nurse din da ba musulma ba domin sakar cross ce a wuyanta sai gashin doki da ta dora. Ta taba jikina ya cire robar ruwan da be kare ba sannan ta yi rubutu akan files din dake hannunta tana min tambayoyi, sunana umguwata ina da aure ko babu sai kuma number wayar Mijina ko ta mahaifina, da alama dai sabon file take bude min a yanzu. Sai da ta gama sannan ta saka hannunta aljihu ta ciro wata takarda ta miko min. “Ga wannan mijinki yace idan kika tashi a baki” Na mika hannu na karba, a gabanta na fara warware takardar har na bude. “A yau 2 ga watan 6 ni Hafiz Abdullahi na saki Matata Noor saki daya” Shi ne a rubuce, gashi sunana da nasa ne a rubuce balle na ce kuskuren fahimta aka yi aka ba ni abin da ba nawa ba. “Wayyo Allah.. Na shiga uku na lalace, wayyo ni Allah me yasa Hafiz zai sake ni yanzu na shiga uku, yanzu ina zan je? Wayyo Allah... Baba kashe ni zai yi, yanzu korata za su yi, na shiga uku” Na kalli matar ina kuka mai taba zuciya. “Dan Allah ki kira min shi” “Ya riga ya tafi, but bari na kira Doc abokinsa ne ai sosai” Ta fita dakin, sai na sauko daga kan gadon i don't even care about the pain haka na zube kasa kaina ya sake buga da gadon asibitin ina wani irin kuka, domin na san karshena ya zo, matar bata dade ba ta dawo ta miko min waya. “Ga Doctor zai yi magana da ke” Na karbi wayar da sauri na kara a kunne na saka hannu na dafe. “Noor sakinki yayi?” “Ya sake ni Kareem, rayuwata ta kare Baba zai iya tsine min ma, ba za su fahimta ba, dan Allah ka taimaka min ka ba shi hakuri, ka ce yayi hakuri ya maida ni gidansa ya yafe min, ka ce masa zan zauna a haka ba zan sake kai kararsa wani gurin ba, Kareem ka ba shi hakuri dan Allah ya hakura ya maida ni...” Ina maganar ina kara matse wayar a kunnena ji nake kamar yana tsaye a gabana ne na kama kafafuwansa na bashi hakuri, domin ni kadai na san halin da zan shiga a sakin nan da yayi min. “Ba zan ba shi hakurin ba” Ta cikin wayar Kareem ya daka min tsawa ya kashe wayar. Na kalli matar da bana iya ganin fuskarta a yanzu saboda hawaye ya tare ko'ina na idona. “Ya kashe... Ya kashe... Sun ruguza min rayuwa, sun raba ni da mai so na tsakani da Allah mai kaunata mai fahimtata mai tausayina, yanzu kuma sun hada ni da mahaifina shikenan rayuwata ta kare wayyo Allah na ni Khadija, Allah ba ni da gata sai na ka...” Nurse din ta dafa ni. “I'm sorry... Please take heart” Na kwanta jikinta ina kuka sosai kamar zan mutu, ni kadai na san waye mahaifina ni kadai na san halin da zan shiga. Da sauri na dago daga jikin matar mai sanyin hali na fara share hawaye, so nake na tafi na samu Hafiz a duk inda yake na ba shi hakuri ya maida ni gidansa... #KhadeejaCandy PAID PAGE 1️⃣1️⃣ ©KhadeejaCandy ©®Copyright 2024 Littafin nan na kudi ne, don't read if you didn't pay... One word kika karanta baki biya ni ba, ban yafe hakkina ba. To be part of the journey pay 500 to 2451879008 ZenithBank Hadiza Abubakar And send the evidence of payment to my WhatsApp number 08036126660.... You can read my latest update on arewabooks a handle dina @KhadeejaCandy https://www.arewabooks.com/book?id=659a94c8be87d7a51f831153 _______•••_______ KAREEM POV Fuskarsa a hade yana tsaye gaban madubi yana kokarin saka agogonsa Yusura ta turo kofar dakin ta shigo. Be dago ya kalli kofar ba amman hakan be hana shi fahimtar ita dince ta shigo dakin ba. Tsayawa ta yi nesa da shi ita dai fuska babu annuri ta ce. “Ina kwana?” “Lafiya Kalau” Ya amsa a taikaice sannan ya fuskanci madubin da kyau ya dauki turare ya fara fesawa. “Ka ce zaka yi shawara, zaka duba lokacin da ya dace ka aiwatar da abun da zai bawa kowa yanci a tsakaninmu, har zuwa yaushe ne Kareem” “Abokiyar shawarata wadda ta bani shawarar aurenki ko na ce umarni bata duniya, amman zan yi shawara da Daddy tukuna” Ya danna abun da ta ji yana taso mata a zuciya. “Har zuwa yaushe kenan? Tsawon shekarun da muka yi da kai ina numfashi ne cikin matsuwa, ina ta jiran ranar samun yanci” Kwalbar turaren ya aje ya juyo ya kalleta. “Na fiki shiga kangin na takura da kunci, da kin san matsalolin da aurenki ya janyo min wata kila, kin shiga daki kin rufe kanki kin yi kuka, Yusura na rasa natsuwata, na rasa farinciki, rayuwar da nake buri ko mafarkin yi aurenki ya ruguza ta, ba ke kadai ba ce a dakin damuwa, ni ma yancin nake nema, i deserved happiness too ba kullum bakin ciki ba, so please karki matsa komai a sannu yake zuwa, kuma zan fi jindadi idan kika daina shigowa dakina kamar yadda kike yi tun farkon zamanmu, bincikar kayana ko bibiyar rayuwata ba na ki ba ne. And ki daina biyo ni har daki da abinci, a dinning ma ya isa idan ina ra'ayi zan ci a can... Please excuse me... ” Ya zagayeta ya fice daga dakin, binsa ta yi da kallon ita kadai ta san yadda take danne zuciyarta take rayuwa da a gidan, amman yau ya kalli idonta ya fada mata magana son ransa. “You got to be kidding me... I'm doing all this saboda na sauke hakkina da Allah ya dora min, waya fada maka a cikin dadin rai ko neman kauna nake? I need space...” Ita kadai take magana da kanta a lokacin da ya dade da fice daga dakin, so take ta kyautata masa kamin ta bar gidan, tun a wacan daren da Safeena ta zo gidan, wani bangare na zuciyarta ke raya mata wata kila saboda rashin samuwa kulawar da ya dace ne ya saka shi tunanin aron hannu ko kuma ma aron gaba daya, tana jin kamar idan ta mutu Allah zai tambaye ta ko da kuwa bayan ta bar gidan ne. But what happened yesterday ya canja tunaninta idan rashin samun kulawa ne ya kai shi ga kula Safeena a yadda take zargi, to ita wannan Noor din fa? Bayan abun da ta kama a aljihunsa wadda ta hango Noor din tana hannanta masa ga kuma abun da Aisha ta fada mata. Now ta ji kamar ba zata iya tarar yakin ba, ba zata iya rumgumar wani dacin ba bayan wanda take ciki. Takowa ta yi ta fito daga dakin ta shiga nata dakin, arba da ta yi da hoton yaranta biyu like a bango ya tsumata. “Rabuwar ita kadaice mafita, ita kadai ce maslaha a gurina, nesanta da Kareem shi ne burin da na dade ina binnewa a zuciyata, dakun mutuwar Momy da nake a baya duk saboda samun yanci ne...” Ya zauna kan gadonta tana kallon hoton hawaye na sauko mata. “Yanci irin na ya mace mai burin auren wanda take so, yanci na rayuwa a karkashin inuwar wani namijin dabam da zuciyata zata yi na'am da shi ba Kareem ba, Wallahi kullum da wannan bakinciki nake kwana da shi nake tashi. Momy ta hada wuta da ruwa ne ba tare da tunani ba, bama haduwa da juna, ba mu dace da juna ba, dan Allah ku yafe mini” Ta kwanta saman gadon tana hawaye, tana jin kaunar yayanta domin babu ruwansu a cikin matsalarsu, sai dai kuma Kiyayyar Kareem ta fi soyayyar yaransa karfi a zuciyarta. *** ***  *** Tuki yake da hannu daya a lokacin da wayarsa ta yi ringing. Sai da ya kalli mai kiran sannan ya daga ya sakata a speaker. “Hello” “Doctor Ka fito gida?” “Eh ya aka yi?” “Wani dan abu na aikata” “Na me?” Barrister ya sauke ajiyar zuciya ta ciki wayar sannan ya ce. “Na saki Noor..!! Na san ba abu ne mai dadi ba, but ina ganin kamar hakan zai fi zame mana mafita, saboda akwai abubuwanta da ban gamsu da su ba, kuma ina ganin kamar ba zata iya canjawa ba” Doctor ya tabe baki ya kalli ne mirror sannan yayi overtake yana tabe baki. “Okay.. Daman aure rai ne da shi, na wasu ya kan dade na wasu kuma be dade ba, Allah yasa hakan shi ne mafita alheri, ya baka zaman lafiya da matarka, ita kuma Allah ya bata wanda ya fika ya dace da ita..” Hafiz yayi shiru ya kasa amsa da Ameen kuma ya kasa sake wani furucin, all what he expected Kareem ya fada hakan da ka yi ka yi daidai or no baka yi daidai ba. Sai dai kam be ji haka daga gurin abokin shawararsa ba. Kareem ya kashe wayar jin Hafiz be ce komai ba kuma be yanke kiran ba. Tuki yake cikin natsuwa har ya ratso cikin unguwarsu Noor, a gaban gidansu ya faka ya bude motar ya fito rike da wayarsa. Nabil ya kira yana dagawa ya ce. “Ranka ya dade” “Kana gida?” “Eh ina gida ranka ya dade” “Fito ina waje” Before Kareem yayi blink Nabil ya fito ya fito da saurinsa. At that time ne Kareem ya daga kai yana kallon kofar gidanta data kone kana ganin gidan zaka san an yi gobara. “Oga Allah yasa ba wani laifi na yi ba” Kareem ya mika masa hannu da suna gaisawa amman Nabil ya ki ya karba saboda yana jin kamar kuskuren gaisawa da mai gidansa a lokacin da yake karkashinsa, shi kuma yake samansa sosai. “Ka yi laifi zan biyo ka har gida? Me yasa kullum tunaninka ka yi laifi ne ko dai akwai laifin da kake min ne a restaurant ban sani ba?” Nabil ya shafa kansa yana dariya. “Aa Wallahi oga, na ga yanzu Noor bata nan balle ace ita ta janyo min wani abun a gurinka” Kareem be biye mishi da maganar ba sai ya tambaye shi yaushe aka yi gobara a gidan. “An yi sati uku yanzu” “Subhanallahi, Allah maida alheri na zo gurin mahaifinku ne yana ciki?” “Eh yana ciki kasan safiya ce yanzu, be isa fita ba” “Good ka yi masa sallama, amman kamin nan me yasa kullum nake samunka a gida baka karatu ne?” “Na fara kuma abun ya zo da dan nauyi sai na aje sai nan gaba kuma” Nabil ya fada yana sosa kansa cike da kunya. “Allah ya taimaka, sallamo shi” “Ameen ranka ya dade” Nabil ya juya ya shiga cikin gidan, nan ma babu jimawa Baba ya fito yana gyaran hula ganin Kareem ya saka shi washe hakora ya mika masa hannu biyu suka gaisa. “Baraba da zuwa, baka shigo ba kake zaune a waje” “Ba sai na shiga ba, magana ce kawai na zo da ita zamu iya yi a waje ma Baba” “Toh Allah yasa dai lafiya” “Lafiya Kalau, Irin na amsu lafiya ba irin na masu matsala ba, Baba na zo da magana ne mai nauyi kuma daci sai ka jure” “Kar ka ji komai fada min ko minene kai tsaye” Kareem ya sauke ajiyar zuciya. “Baba jiya, ko kuma ma na ce kamin jiyan Noor ta samu matsala da mijinta wanda amini ne a gurina, kusan ma ni ne dalilin auren domin sanadina ya san ta ni kuma na san ta sanadin danka Nabil” “Haka ne, ai ta zo nan na korata bana son sauraren komai daga gareta, domin na fahimce take takenta so take ta kashe auren, yaushe aka yi auren ma? Fisabillilahi, a yau ma nake da niyar tafiyar gidan shi Hafizun na ji rashin mutuncin da take masa, domin komai aka ce Noor ta yi bana musu yarinya ce da bata da jin magana sam” “Amman ka bincike me yasa ta zo gida?” “Bana bukatar ji, ai ita mace baiwa ce namiji ko dukanta yake be kamata ta yi yaji ba ko ta zo gida kawo shedu idan na bata wannan kofar kamin ka ankara kashe auren zata yi” “Zaman lafiya be tsawaita aure, tashin hankali be gajarta aure, ko ya kashe rai ne da shi ko ana zaune lafiya mutuwa yake, idan lokaci yayi, wani kuma ga tashin hankali amman auren ya ki mutuwa saboda lokacin rabuwar be yi ba, da dadi da ba dadi as long as auren yana raye za a zauna” “Haka ne, amman Noor ba a nuna mata wannan, yarinya da bata da tunani babu natsuwa a tare da ita” “Amman ko minene ya kamata ka saurari damuwarta, ka aura mata wanda bata so at her young age kuma ta yarda ta aureshi, yanxu kuma ta zo da matsala ya kamata ka aurareta, mace bata da gidan da ya wuce na uba a duniya idan aka cire gidan mijin, wani bangaren ma gidan uban ya kan fi na mijin, domin yanzu da ya korota gidan ubanta ta doso, da namiji ne shi zai yi korar ko kuma ya nemi wani gurin ya fake, irin haka yana saka rayuwar mace ta lalace” “Wato duk abun da za a fada maka ba zaka gane ba, ita Noor dabam take ta sauran yaya, kuma ka duba yadda abokin ka yayi hidima da mu, ace wai Noor ta kwaso jiki ta zo gida ai be kamata ma na saurareta ba” “Ina ganin ku kuka haifi Noor a hannunku ta girma ta yi wayo, amman ko ku din ba ku fi ni fahimtarta ba, ban sani ba ko dan ina kallonta a wani yanayi ne da ku ba a baka kuke kallonta ba” “Ni fa na haifi noor na san halinta gaba da baya” Kareem ya aje numfashi da karfi. “Ko ma dai minene yanzu, Baba ina son ka karbi wannan kaddarar, dan Allah ka yi hakuri ya karbi Noor, ni kuma zan shiga na fita na ga na yi abun da ya dace” “To wai sakinta yayi ne ko kuma me?” “Sakinta yayi, ni kaina ban san abun da ya hada su ba, amman dai yanzu haka Noor din tana asibiti saboda buga mata abu da aka yi a kai ta ji ciwo sosai” “Yayi daidai ai kara da yayi mata duka, daman Noor bata san arziki ba, wato ni zata watsawa kasa a ido ko? Aure ko wata daya be yi ba ta an sakota ta dawo? Oh Allah na gode maka da ka yi min wannan kyautar, yarinyar nan ban da bakinciki babu abun da take saka min tun da aka haife ta, yanzu ina murna na aurar da ita na huta ita ma ta huta, sai kuma yanzu na ji wani labarin na dabam? So take fita sallah cikin jaama'a ma ya gagareni?” Kareem yayi shiru ba tare da fada masa dalilin dukan ba, ko fayyace masa cewar ba Hafiz ne yayi ba matarsa ce ta yi mata duka a rashin fahimta. Sai kawai ya dora da “Hakuri zaka yi Baba, komai zai wuce” Baba yayi baya baya ya jingina da ginin gidansa, gaba daya furucin saki da Kareem ya furta ya fi jefa Baba cikin damuwa, duk wani buri da hangen dafgen da Baba yake a auren Hafiz da Noor ta yi ya sha ruwa. “To wai saki har nawa yayi mata ne?” “Daya ne ina zaton ba zai wuce haka ba, ni dai abun da nake so daga gurinku shi ne hakuri ku karbeta, zan binka komai kuma da yardar Allah zata koma dakinta amman dole sai ka yi hakuri Baba” Kareem ya fada ne kawai saboda ya samawa Noor matsuguni a gidansu ba wai dan yana da niyar yin wani abun akan auren ba. Be ji zai iya sake tuntubar Hafiz ma da maganar ba balle har yayi ruwa da tsaki Noor ta koma gurinsa. “Innalillahi Wa'Inna Ilaihirraji'un, wannan yarinya ba zata tana canja hali ba, to sai ta zo ta zauna ai ta ji idan zaman gidan dadi ne da shi, sakarya kawai marar hankali” Kareem be ce komai ba ya bude motarsa ya dauko 50k ya mikawa Baba. “Baba ga wannan ayi chefa ne, ina mai kara baka hakuri akan abubuwan da suka faru, kowa baya wuce kaddararsa. Ka yi hakuri dan Allah yanzu haka Noor tana asibiti, ita kanta tana cikin tashin hankali na abun da ya faru” Baba ya saka hannu biyu ya karbe kudin ya jefa alJihu sai dai har lokacin damuwar bata bar fuskarsa ba. “Toh dole ai zai hakuri, yaran zamani ne duk yadda zaka fada musu abu ta bayan kunnensu yake bi” “Allah ya kyauta, zan tafi zan samu abokin nawa sai mu tattauna” “Toh an gode, ka ba shi hakuri dan Allah, na san halin Noor zata iya komai, ka ba shi hakuri ita kuma In Shaa Allahu za mu gargadeta” “Tohm” Kareem ya shiga motarsa yayi mata key ya juya ya fice daga unguwar. NOOR POV. Duk yadda na yi kokarin tafiya sai matar ta sha gabana da kalamai ta hana ni fita. Ina zaune har kusan sha daya na rana ina ta tunanin mafita, na sake kiran Kareem na masa magana ne ko kuma dai idan na samu damar fita na tafi kai tsaye gurin Hafiz na ba shi hakuri. Karar turo kofar dakin ne ya saka na daga kai na kalli kofar arba da na yi da fuskar Aisha ya saka ni jin kamar an kara min ciwon dake jiki even though ba ni da tabbacin tana tare da Hafiz ne ko akasin haka. Cooler abinci ce a hannunta Ina zaune ta karaso ta aje kayan abinci cikin tausayin da yanzu na tabbatar na makirci ne Aisha ta zauna a kujera tana kallona kamar zata fasa kuka. “Noor ya jikin na ki?” Na dauke kai na kawarta da fuska ba tare da na amsa ba. “Noor rai ne ya bace haka? Ki yi hakuri da abin da ya faru, ni kaina ban jidadi ba, Wallahi be fada min ba sai yanzu da zai fita, shiyasa na yo rushing na zo dubaki ya jikin” “Bana bukatar dubiyarki, dan Allah ki tashi ki tafi” “Ikon Allah ni miye nawa a ciki Noor? Dalilin zuwana fa so nake a gyara abun nan kamin ma familynsa su sani” Na juyo na kalleta. “Duk halin da na shiga a yau ke ce sila, gaba daya kin rikita min tunani kin dasa min abubuwan da babu a zuciyata, daga baya kuma kike daure ni da su kina cutar da ni, bana son ganinki Aisha” “Hmmm Allah sarki, an hure miki kunne ko? Ke yarinya ce baki san miye duniya ba, amman ni kauna nake nuna miki saboda na rike ki ne tsakani da Allah” “Karya kike yi, kina munafurci ne kawai kina ke din ta kwarai ce alhalin ba haka ba ne, to yanzu ya sake ni hakan be wadatar dake ba sai kin biyo ni har nan?” “Alheri ne ya kawo ni ba sheri ba, ban jidadin yadda kike jefata da zargina da abun da ba hali na ba, wata rana zaki gane gaskiya” Ta mike tsayeta fice daga dakin. Wasu hawaye masu zafi ne suka sauko min, na sani ko da zan fadi kasa na yi birgima na roki ta ce Hafiz ya maida aurensa da ni ba zata yi hakan ba, domin ita ce silar lalacewarsa, aikata hakan kuma raina kai ne a gurinta da janyowa kai gori. Ban saka tsamanin zuwa kowa ba domin ba zan iya tunkarar mahaifina da takardar Saki ba, kamar yadda na san Mama ba zata saurare ni ba, babu wanda zai duba ni, babu wanda zai yarda da ni ko da kuwa ina da gaskiya. Sai dai abun da ya fi komai yi min ciwo shi ne, me yasa Hafiz zai aureni alhalin ya san yana son matarsa kuma ya san ba zai iya adalci a tsakanina da shi ba, ba zai iya tausaya min ba. Misalin karfe daya ina zaune a dakin shiru Gwaggo Saude tare da kanwarta suna shigowa bata duba halin da nake ciki ba ta rufe ni da fada kamar wadda bata da gata, sai kanwarta ce take dan tare min tana cewa ba a bincika ba wata kila ni ce mai gaskiya. Ban san waya fada musu ba ban san ta ina suka ji ba maganar sakin ba domin ban yi maganar da kowa ba bayan Kareem. Haka na yi kwana biyu a asibitin a duk tsawon zaman da na yi Hafiz be leko ba, daman me zai saka ya leko ni bayan ya datse igiyar data hada, mahaifiyata kam ina jin bata da labarin komai sai dai abun da ya daure min kai shi ne rashin zuwa Ya Nabil da Hana duba ni, haka ma Baba be zo ba, Kareem din ma da matarsa ta yi min illa be leko ba ko sau daya be taba shigowa ya duba ni ba. A zaton su raunin da na samu Hafiz ne yayi min duka ni kuma ban damu na fada ba domin ni na kai kaina fadar zai kara janyo min karin wani tsanar ne ko fadan. Idan suka tambaye me ya faru tsakaninmu sai na ce babu komai ban masa komai ba, na samu kaina da nauyin fadar dalilin asalin fada na samun robar c**mdom da maganin planning a jakata, a lura da na yi ne da hakan babban abu ne da zai iya sakawa wasu ma su zarge ni kamar yadda Hafiz ma ya kasa yarda da ni shi da yake mijina. Ranar da aka sallamoni daga asibitin tare da Gwaggo na dawo gida, gaba daya tsoron irin tarbon da Baba zai yi min ya gama firgita ni ya saka na fita hayyacina a take, tsoronsa da nake ji a yanzu ya ninka wanda nake ji a lokacin da ban yi aurenba. Ban gane dawowa gidan na zauna kuskure ba ne har sai da gari ya waye, na leka daki na gaishe da Baba ya ki ya amsa min, daman tun da muka shigo be sake min fuska ba. Haka Ya Nabil ma be ce min komai ba, hana ma ta kasa sake min kamar ba ita ba. Within a week na lalace kamar ba ni ba, labarin sakin da aka yi ma ya cika unguwa wasu na tambayar yaushe ma aka yi auren har na dawo gidan, daman sun san ba zan yi zaman aure ba, haka Zainab take fada min yadda ake yawo da ni a unguwa. Ga shi cikin zaman babu dadi domin sun hade min kai, Yaya baya min magana, Hana bata hira da ni iyakacinta idan ta girka abinci ta zuba min ta koma gefe ta zauna, Baba kuma idan ya shigo ba yi masa sannu baya amsa min, idan zai fita ko da safe idan na gaishe shi baya amsa kuma be taba tambayata me ya faru ba!! Haka Mama bata kira ta tambaye ni me ya faru ba, na san kuma ba zata rasa sani ba, domin Ya Nabil yana yawan waya da ita, Hana kuma ta tafi gurinta sau biyu a zuwan da ta yi na karshe take fadawa Yaya jumma'ar ne aka daura mata aure. A tunanina suna min horo ne da wannan saboda a gaba idan na koma kar na sake marmarin dawowa gidan, Sai dai abun da suka kasa fahimta shi ne mace bata sakin kanta, ni kaina na zan iya cewa ga abun da na yi masa ba da har ya saka ya sake ni, saboda suna ganin bana jin magana tun asali ne shiyasa babu wanda zai yarda da ni. Hakan kuma ya saka na ji kamar a gidan yari nake rayuwa saboda kunci da takura, a kowace Sallah sai na roki Allah ya daidaita ni da mijina, sannan na daukarwa kaina alkawari ko da Hafiz sai yanka ni ya ci ko kuma yayi min horo da wuta ba zan taba daga ido na kalleshi ba balle har na yi wani kuskuren da sai saka ya sake sakina. Tsegumin mutane kadai ya ashe ni, wasu har fadar suke wai amanar Zafeer, ba mamaki kuma ta kan iya zaman amanarsa ce ta hana ni zama cikin amincin a gidan Hafiz, domin na cutar da Zafeer na raba kaina da shi da na yi, sanadin Baba wata ila da gaske amanarsa ce Allah kadai ya san halin da ya shiga a sanadin haka. #KhadeejaCandy PAID PAGE 1️⃣2️⃣ ©KhadeejaCandy ©®Copyright 2024 Littafin nan na kudi ne, don't read if you didn't pay... One word kika karanta baki biya ni ba, ban yafe hakkina ba. To be part of the journey pay 500 to 2451879008 ZenithBank Hadiza Abubakar And send the evidence of payment to my WhatsApp number 08036126660.... You can read my latest update on arewabooks a handle dina @KhadeejaCandy https://www.arewabooks.com/book?id=659a94c8be87d7a51f831153 _______•••_______ Ina ta tsammanin zuwan Hafiz ko Kareem da sunan gyara amman ban ga ko dayansu, hakan kuma ba karamin Mamaki ya ba ni ba, sai na ke ganin kamar daman can Hafiz ba sona yake ba, ya aure ni ne kawai saboda yana son raba ni da wanda ke tsananin kaunata. Sai dai Kareem ya fi ba ni mamaki domin sanadinsa na san Hafiz ko kuma nace Hafiz ya san ni, kuma na kai masa kukana ba sau daya ba amman har yanzu be yi komai ba. Idan na zauna ina tunani sai na ji zuciyata kamar zata fashe, gaba daya na rasa tudun dafawa na rasa ina zan saka kaina na ji sanyi, Mijin da ya dauke ni ya saki ni be waiwayo ba, abokinsa da shi ne sanadin auren be yi wani yunkuri ba, a gidanmu kuma Baba baya min magana saboda yana ganin laifina, Kanwata bata hira da ni, yayana baya kulani na rasa, hakan ya saka na dauki laifin na dorawa kaina. Kullum burina taya zan bullowa lamarin na samu komawa dakin mijina. Da yammancin wata labara na saka hijabina na saka talkamina na fito tsakar gidan. A lokacin Hana ce kadai zaune tana karatun biology, sau daya ta kalleni ta maida kanta bata ce min uffan ba duk kuwa da ta san fita nake da niyar ni. “Hana” Ta juyo ta kalleni ba tare da ta amsa ba. “Abun da kuke min ya dace kenan? Kun maida ni bare a gidan nan?” “Toh ya kike son ayi miki Noor, idan fa ba ki canja hali ba, zaman rayuwar duniya zai miki wuya” “Amman babu wanda ya tambaye waye mai gaskiya me ya faru?” “Baba be son jin uzurinki, saboda ya ci buri a aurenki, na san Baba be kyauta miki ba aura miki wanda baki so, amman be kamata ki ce ba zaki zauna ba, da zarra an daura aure kin tashi daga budurwa Noor, Mama farko bata farinciki da auren amman bayan aurenki nan tana ta jindadin yadda mutane suke yaba gidanki, kuma idan ta duba yadda zaman gidan yake babu dadi sai ta ce kara ma da aka miki auren yanzu ta huta sauran ni, to miye kuma na zuwa ki fito Noor auren da ba a dade da yi ba?” Na share hawayen da suka zubo min. “Ganin kike laifina ne?” “Tohm laifin waye? Mutumen dai yana sonki, ke ce baki son shi, kuma Noor kowa ya san halinki na rashin jin magana sanadin haka kika je kika hadu da wannan mutumen sai kuma yanzu ki dawo kina kame kamen ba zaki zauna ba” “Hannatu ke ma fa mace ce, baki san ya rayuwa zata kasance miki ba, na tabbatar da kin san yadda zafi da bakincikin auren wanda baka so yake da baki fadi haka ba” “Na sani ni mace ce, amman tun yanzu ai ba irin rayuwarki nake ba, kuma bana fatan na yi kalar rayuwarki Noor, ke ce kin son makaranta ke ce jawo ki ce rashin jin magana ke ce saka Mama kuka bakinciki komai dai ke yanzu kuma ana murna an miki aure sai kuma ki kashe auren ki dawo? Yanzu ai sai ki ji idan zaman gidan dadi ne da shi” Bana jin akwai sauran abun da zan fada da zai gamsar da yar'uwata a yanzu, ko kuma ya wanke ni daga mummunan kallon da suke min, gaskiya ta fada da ace ni din kamar ita nake mai jin magana wata kila da yanzu ban samu matsala kamar haka ba. Fita na yi daga gidan ina tafiya jikin ba dadi as well as zuciyata bana iya daga kai na kalli ko'ina har na isa titi, Napep din da ta faka kusa da ni na nufa. Ban tana sanin ina tsananin kaunar Zafeer sai a yau da na yi arba da shi ya fito daga Napep din da nufa zan shiga, ya rame kamar dai he is the only person da na kalla daga fitowa ta gida zuwa nan, shi ma kallona yake kamin ya dauke idonsa ya saka hannunsa aljihu ya dubu daya ya mikawa mai napep din. “Canjin ka kai wannan inda zata je” Wannan karon muna hada ido hawaye suka zubo min. Ya dauke kai ya matsa baya ni kuma na shiga na zauna ina kallonsa har mai napep din ya fara tafiya... “Ina zamu je Hajiya?” A take hankalina ya dawo jikina, kunya da damuwa da bakinciki nadama da kuma dana sani suka rufe ni. Yaushe Zafeer ya dawo garin? Ko dai be tafi ba? Har yanzu yana so na? Ko ya daina? Ya yake kallona? Wata kila ya ji labarin mutuwar aurena amanarshi ta kamani. Ina Son ka Zafeer ina sonka sosai ina son Zafeer Allah ka sani, shi ne abun da nake ta fada a zuciyata, ban hakaro da inda nake ba har sai da Mai napep din ya sake tambayar ina zai kaini. Toh ina zan je kuwa bayan restaurant din Kareem by this time na san Hafiz yana gurinsa, zan fi jindadin tunkararsa a can na bashi hakuri kuma na fada masa ba zan sake aikata kuskure ba, duk kuwa da na san ni din ba ma'asumiya ba ce. Rokonsa a can zai fi min rufin asiri fiye da rokonsa a gidansa kuma a gaban muguwar matarsa wadda ita ce silar faruwar komai. A gaban restaurant din ya sauke ni, ina jin zuciyata kamar ba tawa ba tsananin kunnar da take min, na fito na doshi gate din sai masu gadin suka tare ni. Suna tambayar ina zan tafi, ban yi mamakin jin sabuwar dokarsu ba ta sanin wanda zai fita ko ya shiga, domin aikinsu ne bada tsaro a matsayinsu na masu kula da gate din. Sai dai abun da ya ba ni mamaki shi ne fadar sunana da suka yi, sannan suka tabbatar min da Kareem baya gurin. “Ba gurin Kareem na zo ba, gurin Hafiz na zo” “Shi ma Hafiz din baya nan” “Zan iya shiga na jira?” “Aa gaskiya Oga yace kar abarki ki shiga” Na yi murmushi na juya na kama hanya, yanzu kuma ban san ina zan je ba, ashe abun har ya kai haka? Na zo ace is kar na shiga ciki. Dama na kama na fara tafiya a kafa domin ba ni da kudin abun hawa, idan ma na hau yanzu ban san inda zan je ba. Motar da ke fuskanto ni har ta wuce ni Sai kuma ta dawo ta faka gabana, ban san hawaye nake ba har sai da Kareem ya fito motar ya kalleni ya ce. “Dole ne sai kin fadawa kowa kina cikin damuwa?” Na kai hannu na share hawaye ina kallonsa. “Na zo sun ce kace kar a bar ni na shiga ciki” Ya dan dauke kansa. “Wannan zuwan ba saboda kai ba ne, na zo gurin Hafiz ne, saboda bana son na tafi gurin matarsa kai tsaye, na san a irin wannan lokacin yana gurinka ne, na san na takura maka da yawa Kareem, ba zan sake ba na sani ai na ishe kuwa a yanzu” Ajiyar zuciya na ji ya sauke. “Me Hafiz zai miki?” “Hakuri zan ba shi, zan roki ya maida ni gidansa...” Gambun motar da yake rike da shi ya sake yana kallona kamar mai mamaki. “Noor ba ayi ma namiji haka, shi ya sake ki ai let him come to his senses idan maida ke zai yi sai ya maida ke, amman be kamata ki roke shi ba” “To ya kuke son na yi? Kun raba ni da wanda nake kauna yake so na tsakani da Allah, yanzu kuma abokinka ya sake ni na dawo gida, Baba baya min magana be amsa gaisuwa ta, Hana bata hira da ni, Yaya ko kallona baya yi, a unguwa ana ta yi da ni, Mama tana fushi da ni? So kuke na kashe kaina?” Na karasa maganar ina fasa wani irin ihu kamar wadda ya fita daga hankalinta. Da sauri Kareem ya matso kamar zai rika ni. “Noor... Lafiya” “I'm alright...” Na amsa ina kaucewa daga gabansa na cigaba da tafiya. “Zuwan da kike gurina yana daga cikin abun da yake haddasa fitina tsakaninki da Hafiz, shiyasa na ce kar abarki ki shigo, domin na san zaki sake zuwa ne, a yadda na lura Hafiz yana kishi da hakan, saboda akwai abun da baki sani ba a tsakanina da shi” “Ba zan sake takura muku ba Kareem, ba zan sake zuwa ba” Na fada ba tare da na juyo ba. Sai ya kira ni “Noor...” Na juyo ina wani irin kuka har naman fuskata na rawa. “Hafiz baya garin nan, ya tafi Kaduna gurin wani case tun jiya, amman yau zai dawo. Shim kina son komawa gidansa?” Na daga mishi kai. “Shi kenan, Hafiz zai maida ke na miki alkawari” “Na gode” Na furta daker sannan na juya na cigaba da tafiyar, daga restaurant din zuwa unguwarmu tafiya ce mai nisa amman haka na tako da kafa har gidanmu saboda ba ni da kudin abun hawa kuma na san babu mai ba ni a wannan karon, tufafi ma tun wanda na zo da su daga asibitin ban ni da na canjawa sai dai idan suka yi datti na wanke da ruwa na shaya idan suka bushe na saka, haka nake kamar wata matar gata... Ina shiga gidan, Yaya Nabil ya rufe ni da kuka saboda Baba yayi masa izinin haka, wai na ki zaman aure ina son na fara yawa ina na fito? Gurin uban waye na tafi? Na kasa magana sai kuka nake, duka sosai Yaya yayi min har sai da ya sauya min kamanin fuskata. Baba kuma ya kara min da zagi yana fadin ai ya ji labarin Zafeer ya zo garin nan gurin iyayensa ba mamaki gurinsa na tafi mika hadu. Da rarrafe na shiga dakin na kwamta a kasa a lokacin da ake kiran sallah Magariba a kowane Masallaci, a gurin na kwanta ban iya tashi ba har safe... KAREEM POV. Tsaye yayi a gurin yana ta kallonta tsawon lokacin da ta dauka tana tafiya a kafa har ta karya kwana. Babu abun da yake bata masa rai a rayuwar Noor da Hafiz kamar kasancewa a tsakani, ya zama tsakanin ma'auratan guda biyu, duk ta inda zai motsa kura zai tayar, and the most sadness thing is sanadinsa ne auren ya kullu, ta wani bangaren yana ganin kamar har da rashin so ke wahalar da su, domin ya san yadda zafi da wahalar abun yake, da ace yana sonta da zai iya hakuri da ita a yadda ya same ta ko da kuwa na dan lokaci ne. Shiyasa Noor din ta fi ba shi tausayi domin abokinsa yana da future, yana da matar da yake so take sonsa ya aureta har suka yi zuri'a yanzu. Ita kuma ya rabata da wanda take so kuma yanzu yana wahalar da ita, at her early age lokacin da ya kamata ace tana jindadi. Cikin motar ya koma ya dauki wayarsa sai ya tararda miss calls din Hafiz har biyu, ya dade yana kallon wayar kamar mai tunanin abin yi, har ga Allah be so ya sake yi masa magana akan aurensu ba, domin sakin da Hafiz yayi mata ya bata masa rai, saboda me zai saketa a lokacin da ya same shi ya ba shi shawarar yadda zai zauna da matarsa. Be gama yanke shawarar ba kiran abokinsa ya sake shigowa a karo na uku he pick the call ya kara a kunnensa yayi shiru har sai da Hafiz din ya fara magana cikin farinciki da murna kana jinsa zaka san yana cikin jindadi, daman kuma idan dayansu ya samu wani abun jindadi ko farinciki kamin kowa ya sani sai sun fara labartawa junansu. “I win the case Doctor, we won it...” Kareem yayi murmushi jindadi ya rufe even though dai baya cikin farinciki a yanzu. “Congratulations to us, daman na san zaka yi winning ai, bana da shakkun akanka congrats” “Thank you, ba karamin dadi na ji ba nasarar nan da na samu, domin babban case ne wannan zai kara min martaba sosai zai daga darajar aikina” “Haka ne, ko da yaushe kana nasara Hafiz, kai mutumen mai tsananin jajirce da hikima da wayo tun muna yara, sai dai abun da yake ba ni mamaki shi ne yadda ka gagara fahimtar matanka ka gagara saita gidanka, kuma ka gagara fahimtar wacece ne? Wane irin zama ya dace ka yi da ita, kuma ya kamata ka tafiyar da rayuwarta” “Na fahimci gidana Kareem, na san waye Noor, akwai abun da na fahimta a game ita da zai hanata kuma ni ma ya hana ni jindadin zaman aure da junanmu” “Ka jefa yarinyar a cikin matsala Hafiz, ka rabata da masoyinta mutumen da she can dia for him, ka siye mahaifinta ka aureta yanzu kuma ka sake ta a wace hujja?” Yayi shiru be ce komai ba sai tukin motar yake. “Hafiz, zan roke wannan alfarmar a gareka, zan saka ka aikata saboda ina jin na isa da kai, bayan wannan ba zan sake rokon komai ba, ina son ka maida aurenka da Noor yau... Yarinyar tana wahala ka jefa rayuwarta a masifa, wani abun bakinciki kuma duk saboda ni ne, ka san baka sonta you don't have to married her What kind of wickedness is this? Na taina wayonka Hafiz” “Wait... What....” “Ka mai da aurenka da ita a yau Hafiz...” “Amman kansan bana gari ina hanyar dawowa, na maka alkawari Kareem ina dawowa gidansu zan sauka zan daukota mu tafi gida tare, hakan ya maka..?” “Yayi, thank you my friend” “Ka fi karfin haka, amman ban taba jin ranka ya bace irin haka ba, baka taba bani umarni ko rokona wata alfarma irin wannan ba” Kareem ya sauke ajiyar zuciya shi kanshi ya san he's too harsh for his friend, abun da be saba ba. “ABun ne naka ya daure min kai Hafiz, na rasa gane ma kake nufi fa yarinyar nan, kuma a rasa wanda zai fada maka abun da ka aikata ba daidai ba ne ko Mama ko Baba” “Babu wanda ya san ya sake ta sai Aisha ita kuma na gargadeta kar ta fadawa kowa, Mahaifinta kuma na fada masa zan waiwaye shi, tun daga lokacin ban sake amsa wayarsa ba” “Ka bar abun da ya wuce ya wuce, a fuskanci gaba ita kanta a yanzu na san ta yi sanyi ba zata yi maka laifi ba, sai dai hakan ba zai saka na kasa fada maka ka yi hakuri da Noor ba, ba zan ce ka daina bawa matarka yarda 100% ba, na san maya suna sa wuyar fahimta wuyar sha'ani, but still ka rika bincike kamin ka aiwatar da abu, ka daina compare Noor da AISHA Noor yarinyar kuma bata san komai ba akan aure, Aisha kuma ta waye ta san komai ka tuna ba kai ne first husband dinta ba, kuma Aisha ta yi karatu har degree ba zaka hada ta da Noor da bata ma son zuwa makaranta ba, bawa ta irin wannan wayewar da duniyancin da yan matan yanzu suke da shi, and kishiyace ta koro Aisha daga gidan mijinta na farko, abu ne da ka san shi na san shi, har abada na zata taba son kishiya ba, babu ma macen da zata so kishiya you should think about it Hafiz” “Hmmm...” Kawai Hafiz yace, hango soyayyar Noor da yake a zuciyar abokinsa ne ya hana shi walwala da bude mata nata shafin soyayyar a zuciyarsa, yana rayuwa da matar da ba shi ya kamata ya aureta ba, kuma matar da abokinsa amininsa wanda ya zama dan'uwansa yake sonta, kuma a haka ita kuma a zuciyarta tana son wani dabam ba shi ba. “Sai na dawo...” Ya fada sannan ya kashe wayar. Kareem ya sauke ajiyar zuciya ya yi ma motarsa key ya karasa restaurant. Yana shiga office dinsa Cashier ya shigo suka fara lissafin abubuwa da suka kamata. Be fita ba sai 6pm Kareem ya saka aka kawo masa coffee ya sha saboda ya samu sauki stressed, domin jin yake jikinsa ya mutu gaba daya har wani abu yake ji kamar bachi kamar ba bachi ba. Be bar office din ba sai da aka fara kiran sallah magariba. Yana fitowa sallah kira ya shigo wayarsa, yana ciro wayar ya duba. Number Hafiz ce ba tare da wani dalili ba gabansa ya fadi, babu tsoro ko fargaba amman haka zuciyarsa ta rika bugawa da mugun karfi yana ta kallon wayar tana ringing har ta katse ya kasa amsawa. A karo na biyu da aka sake kiran sai hannunsa da zuciyarsa suka hau rawa. “Innalillahi Wa'Inna Ilaihirraji'un” Ya furta domin be taba jin yanayi irin wannan ba, haka kuma Hafiz be taba kiransa ya gagara amsa wayar ba a yayinda take rike a hannunsa sai yau. Sai da aka sake kira a karo na uku sannan ya iya amsa wayar. “Hello” “Assalamu Alaikum... Barka dai” “Barka ina mai wayar?” Ya tambaya yana jin kirjinsa na masa wani irin nauyi. “Wayar ya samu hatsari a hanyarsa ta shigowa garin Kano, mun samu wayarsa a motarsa sai muka bude da fingerprint dinsa, da muka shiga log calls na sa sai muka samu number ka ne da yayi waya da ita last” “Innalillahi Wa'Inna Ilaihirraji'un... Yana ina?” “Mu sami'an kula da hadarukka ne, yanzu haka muna hanyar asibitin Malam Aminu Kano ne tare da shi” Kareem ya yanke wayar da sauri ya nufi motarsa da gudu ya hau motar ya taka titi kamar wanda baya son rayuwarsa. Kamin su isa asibitin har ya rigasu ya fitowa motarsa ana fitowa da shi daga motar Road safety. Da gudu ya nufi abokinsa dake numfashi daker jini na fita ta cikin kansa. “Hafiz... Hafiz...” Haka ya bi gadonsa da aka dora shi akai aka wuce da shi ICU, Kareem ya dora hannu saman kai kamin ya sauke ya nufi motarsa, wayarsa ya dauko ya kira mahaifin Hafiz, yana dagawa ya ce. “Hafiz din ya rasu ne?” “Aa yanzu suka shigo da shi, Baba kar a fadawa Mama dan Allah” “Tohm ni ma ai sun kira ni, gani nan hanyar asibitin” Ya sauke wayar ya kira mahaifinsa ya fada masa. Yana sauke wayar wani likitan da ya san shi ya fito ya dafa Kareem. “Doctor Kareem, Mutumen yana son magana da kai, ka shiga ka ganshi ka yi abun da ya dace...” Kareem na jin haka gabansa ya tsinke ya fadi, domin shi ma likita ne ya gama fahimtar yaren na su. Cikin rashin kwarin guiwa ya shiga sai ya samu likita uku da Nurses suna kokarin tsayar da jini dake ta zuba amman sun kasa, not because of ba su iya ba, sai dan lokacin tafiya yayi mai ajiya zai karbi abarsa, dabara bata tare damuwa. “Kareem... Allah yayi ba zan samu cika maka burinka ba, ba zan samu dawowa na tafi da Noor ba, ka gyara inda kake ganin na bata, ka san son yarinyar nan Kareem na ga haka a idonta da aikinka, na so ka da farinciki ne shiyasa na so ka aureta, ko yanzu lokaci be kure ba, dan Allah ka auri Noor Kareem ka samawa kanka farinciki, ga Iyeyena nan na bar mana amanarsu, ga Yayana ka ce a kula min da su, na yafewa kowa ka ce kowa ya yafe min, ba zan tashi ba, na san me nake ji na san me nake gani lokacin yayi babu tsayawa...” Magana kawai yake ba dan yana ganin kowa ba domin an yanke ganin, ana saka masa oxygen yana cirewa yana magana daker. Kareem ya rike hannunsa yana kuka. “Yaushe Momy ta tafi, ban gama warkewa daga ciwonta ba zaka tafi ka bar ni Hafiz?” Hafiz ya cire Oxygen din zai yi magana bakinsa ya cika da jini. Sai ya fara kalmar shahada yana tari jinin yana koma masa yana sake fitowa. Mahaifinsa na shigowa wa'adin yana cika rai yayi halinsa Hafiz ya amsa kira... PAID PAGE 1️⃣3️⃣ ©KhadeejaCandy ©®Copyright 2024 Littafin nan na kudi ne, don't read if you didn't pay... One word kika karanta baki biya ni ba, ban yafe hakkina ba. To be part of the journey pay 500 to 2451879008 ZenithBank Hadiza Abubakar And send the evidence of payment to my WhatsApp number 08036126660.... You can read my latest update on arewabooks a handle dina @KhadeejaCandy https://www.arewabooks.com/book?id=659a94c8be87d7a51f831153 _______•••_______ Wani abun da Kareem be sake yi ba shi ne hawaye. A gaban idonsa ran abokinsa amininsa abokin shawararsa ya fita. Ya saba ganin mutuwa ya saba sanar da ita ya saba jinta but this one is different mutuwar Hafiz ta yi hitting dinsa in a different way, na farko a lokacin da be yi tsammani ba, kuma a gurin wanda be sakawa ba, mutuwar Momy ta zo masa da sauki domin ta yi ciwo kamin ta rasu, and ko da yaushe tana yawan fadar zata mutu zata mutu tana kan tunatar da su idan sun manta. Amman abokinsa da yake lafiya kalau suka yi waya a hanyarsa ta dawowa har yayi masa alkawarin dawowa da Noor, ta yi hitting dinsa so so so bad. A hanyar da be yi tsammani ba, what a lost, this is a great lost to him ya rasa RAI BIYU within a year... Ya rasa uwa ya rasa babban amininsa. Har kara ma mutuwar Momy ya samu zubar da hawaye yayi kuka a lokacin da ya kebe kansa amman mutuwar Hafiz ta yi hitting dinsa in a way da ta tare hawayensa ta tare zuciyarsa daga kuka tun daga asibitin da mahaifinsa yake kuka har aka dauko gawarsa aka dawo da ita gida gurin iyayensa yan'uwa da matarsa suka rufe gawar da kuka shi kam ko kadan hawaye be kusanci idonsa ba. Kuma ta hana idanuwansa runtsawa a lokacin da ya kwana tare da gawar abokinsa domin yin masa sallama ta karshe.. Da kansa ya wanke abokinsa yayi masa sutura sannan aka jira wayewar gari domin kai shi gidansa na gaskiya. Suna fitowa daga sallah azuba ya shiga cikin gidan ya tambayi mahaifiyar Hafiz ko an sanar da Noor. “Aa ba a fada mata ba, jiya na tambayi Aisha ya ba su zo tare ba sai tace wai tana gidansu ta tafi kusan sati uku bata gidan” “Ya kamata a sanar da ita, hakki ne a fitar mata da shi...” “Aisha tace sakinta yayi, amman be fada mana ba, ko ka sani” “Haka ne, amman tana da hakkin a sanar mata... Mama ki aika a daukota” “Toh ko zaka tafi tare da Raliya sai ku taho da ita, tun da kai ka san gidan” Yayi shiru kamar yace a a sai kuma ya amsa mata da kai ya ce Raliya ta tashi su tafi. Karfe 6am daidai suka faka a kofar gidan. “Shiga ki musu magana” “Tohm...” Ta amsa tana kuka sannan ta bude motar ta fita. NOOR POV. Muna tsaka da tafiya sai na ga sun yi nisa sun bar ni, yana rike da hannun uwargidansa Aisha ita kuma tana rike da hannun yaranta. Gajiya ta saka na zauna a gurin da suka bar ni mai tsananin turbaya da jar kasa, sai dariya nake sun yi nisa sosai kamin Hafiz ya juyo ya kalleni a lokacin ne ya hankara bana tare da su sai ya rugo a ruje ya nufo inda nake yana rike da hannun Aisha ya karaso kusa da ni yana numfashi daker. “Noor taso mu tafi...” Ya miko min hannunsa sai na daga kai na kalleshi sannan na mika masa nawa hannun zai kama kenan kasar da yake tsaye akanta ta bude ta rusga da shi ya fada, sai ya bar mu a gurin ni da Aisha muna kallon ramen da ya fada, ita tana rike da yaransa ni kuma ina daga zaune a gurin domin be kai ga riko ni ba ya fada. Dariyar Aisha ce ta dawo da hankalina zuwa gareta kamin ni ma na fara dariyar sai na mike tsaye. Ban lura ba ashe saman wani tsaye nake tsaye mai tsananin tsawo da saka jiri. Tangal tangal na fara kamar zan fadi sai na ji wani ya rike ni ta dama, yana sakina ya fara tangal tangal wani ya rike ni daga hagu, yana sakina na sake komawa yar gidan jiya, sai kuma na ji an rike ni ta baya, kamin na ji wani dabam kuma ya rumgume ni a kirjinsa, a chest with full of hairy chest har yana shiga min baki. .....Firrrrrrr gigit na farko daga bachin wahala da kuma mafarkin da na tabbatar ba na kwarai ne, domin mafarkin dariya yana nufin bakinciki ga mai yinsa sai dai ta inda ban fahimta me yasa ni da Aisha muke dariyar? Kuma su waye suke rike ni? Waye wanda na kwanta a kirjinsa. Tashi na yi na alwala na rama sallah sannan na gabatar da sallah asuba ina jin fuskata na min yaji saboda dukan da Yaya yayi min ya ji min ciwo a kumatu da gafen ido har ma da saman bakina. Na jingina kadan ina lazimi da hannuna na ji an buga gidanmu, Yaya ne ya bude bana jin me ake cewa amman tabbas na ji yana fadin. “Eh tana nan” Sannan ya kwala min kira na tashi da sauri da kuzari na fita gudun kar na yi laifi. A tsakar gidan na yi arba da kanwar Hafiz, domin Aisha ta gabatar min da su a lokacin da suka zo ina amarya haka ma a burin Walima mun hadu da juna. Hawayen da na gani a idonta ne suke min magana ba bakinta. “Yaya Kareem yana waje ya ce ki zo mu tafi” Na nufi kofar babu talkami a kafata na fice daga gidan zuwa kofar waje. Kareem ya na samu jingine jikin wata bakuwar mota ya rumgume hannayena yana kofar gidanmu. “Hafiz ya rasu...!” Na fada domin a yanzu na gama fahimtar mafarkina. “Ban fada mata ba” Na ji kanwarsa ta fada daga bayana. Juyowa na yi na kalleta. “Na sani, na gani a mafarkina na gani jiya ya saki hannuna ya zo zai kama ni sai wani rame ya bude ya fada da shi, ya saki hannuna da na Aisha, ya tafi ya bar ni ina tangal tangal, wayyo Allah na, na shiga uku wayyo Hafiz...” Na ruka zan kai kasa sai kanwarsa ta rike ni ni da ita muka fashe da kuka mai karfi. “Karfe 8am za ayi masa sallah, you need to be there kamin a tafi da gawarsa” Kareem ya fada ganin kukan na mu ba mai karewa ba ne. Yaya ya leko yana ganin Kareem ya gaishe shi, sai Kareem ya ce. “Ka fadawa Baba Allah yayi ma Hafiz rasuwa jiya da dare, sakamakon hatsarin da yayi a hanyarsa ta dawowa daga Kano” “Innalillahi Wa'Inna Ilaihirraji'un” Yaya ya fada ya juya ya koma cikin gidan, Kareem kuma ya bude mana mota ni da ita muka shiga baya. Yanzu ta ina zan roki gafararsa ya tafi be fahimce ni ba, ina jiran tsammanin zuwa ko aikowa a dauke ni sai labarin mutuwarsa ya riske ni a yanzu. “Ni ma tawa rayuwar ta kare...!” Wannan kawai na iya furtawa ina kuka bayan haka ban sake fadar komai ba har muka isa gidan. Gidan ya cika tam da mutane amman ba cikar farinciki ba domin kowa kuka yake da jimami. Haka na fito motar babu talkami a kafata kanwarsa ta ja ni ta shiga da ni har gurin da gawar take. Sai ta ja ta tsaya daga bakin kofa ta ni kuma na kwance, yana kwance cikin kagara an masa sutura amman likkafaninsa yana jike da jini. Ban taba arba da gawa ba sai a ranar domin ban taba rasa kowa ba, ban rasa uwa ba ban rasa uba na ban rasa yaya ko kanwa ba. Ban san ya zafin abun yake ba, ban taba zauna a daki daga ni sai gawa ba sai yau. Ashe mijina ne farkon abun da zan fara rasawa a kananan shekaruna... Ban taba sanin idan mutum ya mutu abubuwan da kake masa marar dadi ne suke zuwa su tsaya maka a rai ba sai yau. Yadda yayi ta kokarin kaiwa ga jikina ina hana shi da ihu da kokawa ne ya tsaya min a rai, ya saka ni fasa ihu ya saka ni rawar jiki, me yasa ban bari ya kai ga abun da yake halalinsa ba? Me yasa na biyewa Aisha da tsoro har abubuwa suka zo mana a haka? Ashe zaman ba mai tsawo ba ne ko da na zauna a gidansa ne. Wasu matane ne suka shigo suka fitar da ni, ina wani irin kuka da ban san ina yi ba, sai hakuri suke ba ni suna rarrashina amman ji nake kamar suna cewa bude baki ki yi kuka sosai Noor yau ranar kukanki ce. Ni dai na san bana son Hafiz amman kuma ba kinsa nake ba, amman a ranar na ji tausayinsa kuma na ji tausayin kaina, ban gane haka ba sai da aka fito da gawarsa za a fita da ita domin yi masa sallah. Ban san ya aka yi ba na isa gurin na ratsa cikin maza na rike makara, ina kiran sunansa kamar ance zai iya amsa min. Daker aka banbare hannuna daga jikin makarar su kuka ni kuka ana rike ni aka fita da gawar mijina wanda shi ne duniyata a yanzu. Ban kara raina kaina ba sai da aka kai shi gidansa na gaskiya aka dawo, maza suka shigo cikin gidan domin yi mana gaisuwa, ashe wata kalar azaba ake ji idan aka yi maka gaisuwar wanda ya rasu. Allah ya jikansa yayi masa rahama ya raya abun da ya bari haka kowa yake ta fada. Cikin taron masu yi mana gaisuwa Mama ta kutso ta shigo ta iso inda nake ta zauna sai ta saka hannunta biyu ta rika fuska. “Yi hakuri Noor yi hakuri” Ta fara karanta ayatul kursiyu ta tofa min a kai ta busa ido. Ban sani ba ashe ba daidai nake kallon mutane ba, idanuwan nawa juyewa suka yi ina kallon mutane a baibai. Ta rumgume ni tana kuka, sannan yan'uwanta da na Baba suka shigo suka zauna suna gaisuwar kamar yadda yan'uwan Aisha ma suke cike a gidan, ita ma kuka take tana gurnani ko'ina ana jinta sai hakuri ake bata wasu na addu'ar Allah ya sauke ta lafiya. Ni kuwa a zuciyata ba ni da makiyiya irin Aisha domin ita ce silar duk wata fitina a gidan Hafiz, ashe ma ba dadewa zai yi tare da ni ba, me yasa ta zuge min kunne bata bar ni na yi zaman aure kamar ita ba? Amman laifin ba nata ba ne nawa ne miyasa na dauki zugarta? Why? Har aka yi addu'a uku ban daina ganin laifin kaina ba, kuma ban daina fargabar yadda rayuwa zame min ba bayan tafiyar Hafiz, na san kowa zai dora min laifi ne a gidanmu, kuma na cancanci haka ya kamata ayi min kowane kalar hukunci a yanzu. Na gane ba laifin kowa ba ne nawa, ni ce wawuyar da ban fahimci duniya ba. Wani irin nauyi na ji an dora min ashe haka ko wace mace take ji idan ta rasa abokin rayuwa, ni kenan da ban dade da shi ba kuma ban haihu da shi ba ina ga wandanda suke da yaya kuma suka dade a tare? Wani abun da zan iya cewa tsana ce ko tashin jindadi na ga ganina fuskar iyayen Hafiz bayan sadakan ukun ita ce ta mutuwar auren. Ina da tabbacin a cikinsu babu mai iya bada shaidar abun da ya faru indai ba Aisha ta fada ba, domin sun ce ba su san da sakin ba har sai da ta fada, amman sai na ga nuna min wani kallo, mahaifiyarsa na tambayar me ya hada mu har tana fadan danta mutumen kwarai ne mai mutunci mai rike amana, domin tun da ya auri Aisha ba su taba jin wani abu ba, yana zaune lafiya da matarsa. “Waya sani ma ko bakincikinki ne ya saka shi sakin motar har yaje yayi hatsarin, kin saka na rasa mijina uban Yayana mai so na tsakani da Allah” Na kalli Aisha dake maganar ina hawaye. “Allah ya isa tsakanina dake, ke ce silar da Hafiz ya sake ni, Allah ya isa ban yafe miki ba” “Mijina be san tashin hankali ba sai da ya aureki, daga sunan taimako, Wallahi Hafiz baya sonki shi be taba sonki ba daga ya taimaka ya auroki sai kika zo cikin gidan suna son cin amanarsa” Mahaifinsa ya daka mata tsawa. “Aisha ya isa haka, ko dai minene ya riga ya faru, Allah ya masa rahama, babu amfanin maido baya” “Ai amana bata barin kowa, Allah ya masa rahama, ni dai ina son na tafi da Noor can gidana idan kun yi min izini, yarinya ce ba zata iya wanka ita kadai a gidan ba” “Ai wanka be hau kanta ba domin ya sake ta tun kamin ya rasu, da wanka da gado duk basa kanta” Mahaifinsa ya fada. Sai Aisha ta karba. “Balle ma bata taba yarda da shi ba, kullum addabarsa take da fitina bata taba yarda ya taba ta har ya rasu” Na kalleta ban ce komai ba na dauke kai. Yayan mahaifin Hafiz ne ya ce. “Ko ma dai minene ba mu yanke hukunci ba, sai mun bincike malamai mun ji me ake ciki tukuna, ki tafi da ita din idan mun bincika duk abun da yake nan za mu sanar miki” Yana maganar yana kallon Mama sai ta amsa da tohm. A bisa wannan muka fito daga gidan, wani abun da ban yi tsammani ba shi ne direba ne da mota ya daukemu daga gidansu Iyayen Hafiz zuwa family house din su Mama. Muna shiga kowa sai tausaya min yake suna ta shawarar inda zan zauna a gidan, domin sun ce zaman wanka wai sai da mai kulawa da mace, domin gidan Baba babu mata Hana kuma karamar yarinya ce bata san komai ba. “Ki barta gurin Kawu Garba, matarsa bata da matsala zata kula mata” “Na fa yi magana da Alhaji, shi da kansa ya ce ta zo ta zauna ba wani matsala” Yayanta ya girgiza kai. “Amman Hajara baki yi tunani ba, saure sati daya ki yi masa maganar kawo yarki a gida? Haba dan Allah” “Wallahi Yaya ba ni na yi masa magana ba, tun da aka yi rasuwar na fada masa yace na shirya na zo matarsa ma sau biyu tana zuwa, to kuma jiya da aka yi sadakan uku yake min maganar cewa na maidota a gidan ta zauna tare da ni zata fi sanyi, saman da zaman gidan ubanta domin babu mai kula mata a can din, babu yadda ban yi amman yace na kawota ai kowa ya san lalura ce bata wuce kowa ba, kuma gidan gida ne babba mai yalwa zata iya yin sha'aninta har ya shigo ya fita bata sani ba, domin bangarena dabam bangaren matarsa dabam kuma bangaren nawa ma babba ne sosai” “Aa ni dai ban aminta da hakan ba, kawai dai ya fada ne saboda kawaici, da dai kin hakura ki barta a nan din ta zauna idan ta gama wanka idan ya sake magana sai ta koma amman a yanzu ki barta a nan” Cewar wata yayarta. Sai Mama ta ce “Toh ai na ji suna fadar wai ba zata yi wanka ba, saboda ya sake ta” Yayanta ya kalleni. “Sakinta yayi? Yaushe?” Mama ta fada musu komai sai dai ita ma ba zata iya fadar dalilin sakin ba. Ni kuma na gagara fadar abun da ya gani a jakata har ya zama silar lalacewarki komai. “Ni fa yadda ba lura wannan matar tasa kamar ba ta Allah ba ce, duba yadda yake son kunyata Noor cikin danginsa” “Na lura Wallahi Yaya, ai gata ga su idan wani za su kara aura mata sai mu gani, na san Noor bata jin magana amman a yanzu na lura wannan matar ta fi ta wayo, wata kila da zaman ya dade Allah kadai ya san me zai kasance” Mama ta fada. “Aa laifin duk na wannan yarinyar ne, ba mamaki taje tana masa hauka da nuna masa ita wacan take ba kin san halinta da shirme da shashanci to ya bar miki duniyar kin huta” Cewar Yayanta, haka dai suka ci suka cinye ni dai bana iya cewa komai idona sai ciwo suke saboda kuka da na sha. Daman na san laifin a kaina zai dawo duk juyin da za'ayi ba zan taba wankuwa a idonsu ba. Daga karshe dai aka yanke shawarar bari a gidan Baba domin ya tsaya kai da fata ba zan zauna ko'ina ba sai a gidan, bayan har Kawu Garba ya ce zan zauna a gidansa. A dole na dawo gidan da zama sai wani sabon kunci ya bude min kofa. Hana ta min magana ta kan ja ni da hira Yaya ya kan min magana amman Baba har lokacin fushi yake da ni, yar karamar rayuwar da na yi a gidan Hafiz ta dawo min sabuwa, ina tuna lokacin da ya siya min waya ko kuma yake rarrashina idan kuma na tuna abun da na yi masa na bacin rai sai na ji kamar zan runtse ido na mutu na huta, ina ma ace zai dawo na kyautata masa? Ina ma ace zai dawo ya fahimci ba ni na saka robar nan da magani a jakana ba. But the part da na tuna Aisha tace shi ma haya so na ya kan saka na ji wani iri, be so kuma ya aure ne? Saboda me? Ya san be so ya raba ni da mai so na kuma ya aure ni.... KAREEM POV. Yana zaune a kan tool holding his best friend picture yana kallo, har lokacin baya iya kukan rashin abokinsa zuciyarsa tana nan da nauyinsa pain din ya fi karfin kuka, har gobe he can't believe abokinsa ya tafi ya barshi. “Sun ce mutanen kirki ne suke tafiya da wuri, ka fini kirki har a gurin Allah domin baka aikata abun da nake aikatawa ba, kana kokarin tsare dokokin Allah, kullum burinka na daina abun da nake marar kyau, a lokacin da ka fahimci bana cikin farinciki sai ka fara gina tubalin matso min da shi kusa, maganar mu ta karshe ma umanine kake kokarin cikawa saboda ka faranta min, ba zan taba barin iyalinka su shiga kuncin rashinka ba Hafiz” Yana maganar idonsa suka fara tara hawaye, at the same time Yusura ta turo kofar dakin ta shigo. Kusa da shi ta karaso ta tsaya sai da ta kalli hoton dake hannunsa sannan ta kalli Kareem ta ce “Kyautatawa abokin zama, makoci ko aboki wajibi ne gudun kar ya tafi a dawo nadamar da bata da amfani” Ya aje hoton ya rufe drawer madubin. “A iya sanina Noor bata son Hafiz ko kadan, saboda ya raba ta da wanda take so kuma ya aurenta alhalin shi ma kansa ya san baya sonta kamar dai ke, banbancin mu da su, ba iyaye ne suka cilasta ba, duk wani yunkuri da yake saboda ni ne, daga karshe kuma sai abun ya fada kansa, ashe saboda ya tafi ya bar ni da bakinciki kasa cika masa burinsa ne da ban yi ba...” Ya dago ya kalleta yana murmushi. “Kin san banbancinki da Noor? Ta fi ki wayo ta fi ki imani da yardar da kaddara, ta fi ki tsoron duniya, yarinyar nan bata iya munafurci da pretending ba, tsabar saka shi da ta yi a zuciya na nesan da ta yi na kwana biyu sai da ta yi mafarkin mutuwarsa tun kamin a fada mata ya rasu, a ranar da za a binne Hafiz na ga wani abun da ban yi zato ba gurin yarinyar nan, ta rike karagarsa tana kuka, na tabbatar da ni aka sanar miki na mutu murna zaki yi...” Ta yi murmushi. “Kasan da hakan kuma kake zaune da ni har yanzu? Idan zaka kwatanta Noor da misalta ta da Safeena mana, ka ce ta fi Safeena wayo, amman ba ni ba, ni din na san abun da nake so da wanda bana so. Ko da yake dole ka yaba Noor ai, saboda kana sonta shiyasa ka cilastawa abokinka aurenta, yanzu kuma ya tafi ya barku sai ku cigaba daga inda kuka tsay....” Tana kai aya yana wanke mata fuska da wani zazzafan mari, har sai da ta ja baya “Ka mare ni Kareem? How dare you...!!” “Saki kike so? Tafi na sake ki Yusura” A take ta daina jin zafin marin, farinciki furucinsa ya wanke mata damuwarta. Idan ta tace bata ji tausayin Kareem na mutuwar amininsa ba ta yi karfa haka ma idan tace bata yi farinciki da sakin da Kareem yayi mata a yau ba, ta yi babbar karya. A gurin ta yi sujudar godiya sannan ta mike tsaye ta fice daga dakin. Slowly ya zauna bakin gadonsa be taba tsammanin kiyayyar da Yusura take masa ta kai haka ba. Be yi tunanin akwai kiyayyar da zata kai irin ta Yusura ba a zaman aure, ba zai yana sonta ba, amman baya ganin rabuwa da ita a yanzu mafita ne saboda yaransu. Baba yana kallona ne kamar ni na kashe Hafiz saboda, Hafiz ya tafi be samu kyautatawa Baba kamar gyara masa gida ko kuma yi masa wata babbar kyauta da yake tsammani ba tun a bayan aurena. Ni ma ban fahimci hakan ba sai a ranar da Hafiz ya cika sati daya da barin duniya, Mama ta kira waya tana kara kwantar min da hankali, bayan mun gama wayar ne Baba ya rufe ni da fada wai na ci amanarsa wata kila da na kyautata masa da yanzu Allah kadai ya san yadda rayuwa zata zame mana. “Daman sai da zuciyata ta raya min ba zaman lafiya kike da yaron nan ba, saboda juya min baya da yayi ko lokacin da gobarar nan ta tashi be zo yayi min jaje ba, be ba ni komai ba, ashe ma ba zai dade duniyar ba, kina ta shuka masa rashin mutunci, in ba shi ba taya za su ce wai ba za ki masa wanka ba? Ta ina aka taba haka so suke su hana miki gadonsa kenan” Ni dai bance komai ba, gaba daya duniyar bata min dadi, ni kaina ina dorawa kaina nauyin da ba zai gogu ba saboda hana mijina hakkinsa da na yi, ya tafi da abun a ransa kuma na daukarwa kaina zunubi. “Wallahi zan iya kararsu akan haka, domin babu hujjar da tace ba za a baki gado ba, na bincike limin yace kina da hakkin wanka domin an riga da an daura muku aure, kuma sakin da yayi miki ai ba ki cika idda ba” Sai a lokacin na kalleshi cikin wani irin rauni da damuwa na ce. “Baba dan Allah ko da sun ce ba za su ba ni hakkin wanka ba, dan girman Allah dan Isar Annabi, Baba kar kace zaka yi kara ko fada ko kuma daukar wani mataki, dan Allah ka kyale su, idan ma ina da hakki Allah ya sani zai saka min” “Toh haka za a zuba musu ido su ci su cinye hakkinki Noor? Idan aka karba ai ko wani abun a rage da shi, dubi yadda gidan nan yake fa, ko gyara aka yi ba a rage ba? Allah kadai ya san abun da bawan Allah nan ya bari” “Ko ma dai miye bari Baba mai karewa ne, rayuwar ma ta kare balle kuma abun da rayuwarta ta aje, ni dai da zaka yarda da magana ta Baba da ka yi hakuri ka kyale komai dan Allah” “Ai daman ke sakarya ce baki san komai ba, sai shashanshanci, ba dan kin nuna masa rashin tarbiya da rashin hankali ba yaushe zai sake ki? Allah ya wadarranki Noor, duk yadda nake ganin kamar zaki natsu ko ki yi hankali ba zaki taba yi ba, duk yadda bake ganin kamar sanadinki wata kila zan warke sai kin kunyartar da ni, ke dai har abada va yar arziki ba ce” Ya rufe da fada ta inda yake shiga ba nan yake fita ba. Ni dai kam na san ban yi dacen abubuwa da yawa ba a rayuwa ciki har da uba. Domin ko a labari ban taba jin uba makamancin nawa ba, mai tsananin kwadayi da son abun duniya. Na sani sarai idan na kara wata maganar zai iya rufe ni da duka, a dole na yi shiru na ina ta sauraren masifarsa har yayi ya gama ya fice daga gidan. Haka na gagara tashi a gurin har Hana ta dawo daga makaranta ta same ni zaune a kofar dakin, ni ba kuka nake ba damuwa karara a fuskata, tunanin yadda rayuwa zata zame min nake, hankali ko tunanin da suke ganin kamar ba ni da shi ina da shi, ni na san ina da shi, idan ma babu a da to yanzu yana tare da ni. Rayuwar gidance nake jin kamar ba zata min dadin zama ba, gashi kuma ba ni da wani gurin rabawa da zan zauna na ji sanyi. Yunkurawa na yi na tashi na nufi gurin da kayan wanke wankemu suke na wanke komai tass Hana kuma ta dora girki ta girka mana shimkafa da miya, duk da kasancewa white rice and stew are my favorite amman ban iya cin wani abun kirki ba, daman abinci ya daina burge ni. Kamar wani zanenen al'amari a daren da muka yi haka da Baba sai ga kanen margayi ya zo gidanmu, ban san ya aka yi ya gane gidan ba, kusan ni dai zan iya cewa ban taba ganinsa ba, idan ma na ganshi ba zan iya shaidar fuskarsa ba, domin ban jima a gidan ba balle na san duka yan'uwansa balle kuma mazan da be gabatar min da su ba. A zauren gidanmu ya shigo bayan yayi sallama Hana ta yi masa izinin shigowa. Dogon hijab ne a jikina har kasa kaina kuma a kasa na kasa kallonsa ganin nake kowa kallona yake a wani muhalli da Aisha ta saka ni a idonsu. Bayan mun gaisa ya gyara tsayuwarsa ya ce. “Ya Hakuri Noor?” “Alhamdullahi” “Haka Allah ya so sai hakuri, shi kuma Allah yayi masa rahama” “Ameen” Na amsa ina jin idanuwa suna cika da kwalla. “Na san babu dadi, musamman ma ke da kike farkon shiga gidansa ba ki jima ba mutuwa ta yi muku gaggawa, amman duk da haka ki yi hakuri yana cikin jarabawa ne” “Haka ne, na gode” “Na san ba ki san ni sosai ba, ni kane ne a gurin Margayi uwa daya uba daya, ni ne kanensa na biyu, makasodin zuwa na a nan shi ne... Abubuwa marasa dadi sun shiga kuma za su biyo baya na sani, amman dan Allah ina son ku kawar da kanku musamman ma ke, ki yi hakuri da abubuwan da zaki ji ko ki gani” Na yi shiru ina ta sauraren bayaninsa da ban fahimci inda ya dosa ba. “Na ji wasu abubuwan ne da ba su min dadi a gidanmu, na iya yadda zan iya na taushe abun amman ya gagara saboda haihuwarmu aka yi ba mu muka haife su ba, dole sai hakuri, amman na san ke zan iya neman alfarma a gurinki kuma na roke ki duk kuwa da ba ki san ni ba, amman ina rokon alfarmar dan Allah karki ce zaki yi jayayya da iyayen margayi akan gadonki, ke ba da kike da shi ba balle ace saboda da gaba, kina gama wanka na san In Shaa Allahu zaki yi aurenki, bana son na ji wata matsala ta taso daga gurinki, ni dai ina kyautata miki zato sosai” “Ni ba zan iya jayaya akan abun da rai ya tara kuma ya tafi ya bari ba, wanda ya tara abun ma ina yake? Toh me zai saka ni yin jayayya? Idan ma ina da hakki abun da za su ba ni ba zai taka kara ya karya ba, ba shi ne gabana ba, kuma na maka alkawari ba zaka taba jin wani abu makamancin wannan daga bangarena ba” Ya sauke ajiyar zuciya yana kallona. “Na yi farinciki da jin haka, na jidadi sosai Allah ya saka miki da alheri, ya baki wanda zai maye miki gurbin Ya Hafiz har ma ya fi shi” Na yi shiru ban iya amsawa da Ameen ba. Daga haka yayi min sallama ya tafi, ni kuma na dawo cikin gidan ina ta mamaki mi ya ji danginsa ana fada har dauko kafafuwansa ya zo ya tari nawa fadan, ni kan idan gado ne ko nawa ne ba zai daga min hankali ba balle ya saka ni yin magana ko daukar wata dokar tsorona duk na Baba ne. Ban fadawa Baba wani ya zo ba, sai dai na lura hakan be yanke komai daga hanzarinsa na niyar saka iyayen Hafiz a kotu ba, idan har ba su ba da hakkina na wanka ba, na fahinci hakan ne ta dalilin wayar da na ji yana yi da yayansa wai ya bincika ko'ina ance ina da gado, dan haka ba zai saka musu ido su cinye min hakkin ba. Ban ce komai ba daman kuma ban isa na ce ya rufe da fada ba mamaki ma ya kara min duka. Zaman gidan sam baya min dadi kamar ina zaune a kaya haka nake ji. Ba ka kamar lokacin da sabuwar matar da Baba ya aura ta tare a gidan. Gaba daya sai gidan ya kara fice min a rai, domin na lura ta shigo da wani salo na hana mu walwala ni da Hana da kuma Yaya, gara ma yaya ba a gidan yake wuni ba, sai dare yake dawowa ni da Hana ne muke ganin rayuwa a gidan. Babu kuma wanda ya isa yayi magana domin mun san halin Baba ba zai taba yarda da mu ba. Umma bata wuce wata biyu ba a gidan ta cigaba da sana'o'inta da take, daman na ji Hana na fadar wai ance tana siyar da kunun waken soya kuma tana wara tana kosai, domin ba yar garin Kano ba ce asalinta yar riɓa ce dake can kusa da zuru ta birnin kebbi amman take zaune a nan Kano gurin Yayarta bayan rasuwar mijinta na farko, tana sana'a har Allah ya kawo mata Baba ya aureta a yanzu. Bata taba haihuwa ba a wacan auren nata kamar yadda take labarta masa wani lokaci ni da hana, ba wata babbar mace ce be domin Mama ta yi kanwa da ita ta biyu, sai dai tana da irin jikin nan sosai da zata iya daukar Mama da irinta uku ta goya ta gudu, domin ni da Mama jikinmu daya, ita ba kiba ni ma babu kibar, ba mamaki ma kibar ce ta burge Baba ya aurota. Wani sabon salo da ta kirkira shi ne na dorawa Hana tallar awarar a titi tana siyar mata kullum zata bata 500 naira, ita kuma tana yin kunun waken soyar a gida, ana shigowa ana siya sai dai ba sosai kamar yadda take fada mana ba. Dole ce ta saka Hana yarda tana soya mana awara a waje ba dan tana so ba, domin ko a lokacin da Mama take gidan kuma muke cikin tsananin shan wahala bata taba gwada dora mana talla ba, amman ita wannan da ba uwarmu ba ta fara dora ma Hana talla daga zuwanta. Ko da yake ba laifinta babne laifin Baba domin shi ya bata dama Hana kuma bata isa tace ba zata yi ba, duk kuwa da kasancewar bata so ko kadan. Domin fita tallar ya kashe mata tafiya makarantar yamma, ya zama boko kawai take iya tafiya da safe. Ni kuma aka bar ni da wahalar aikin gidan, shara wanke wanke da hura wuta tun ban iya ba har na iya, girkin ne kawai bata bari na yi domin na gwada girkanwa ta ji be yi mata yadda take ba. Idan zata hada kunun wanken soyan ni nake wanke goruna ni nake mata komai har tacewa, awara kuma ni zan gyara wake da dare da safe taje ta kanta ta kai nika, idan ta dafa a tare zamu natse ni zan yanka idan aka soya be wuce a ba ni da hansin ba ko saba'in. Wani sabon shafin wahalar rayuwa Umma ta bude mana a idan, ni da Hana saboda sana'ar da take wai ai ba ita zata fita ta yi ba a dole hana zata soya mana wara a waje ni kuma na yi aikin cikin gida. Ta inda nake samun sauki shi ne takaba da nake bana fita, saboda haka duk wani aiki na fita ita zata fita ta yi, da safe kuma Yaya sai ya cika gidan da ruwa sannan yake fita. Ta inda gurin da ta samu banbancin da Mama a zamanta gidan ita kam Baba yana bata abinci da cefane mai kyau, ba kamar Mama ba da wani lokacin zai ce be da shi ko kuma ya bada abinci ya hana cefane ko ma ya hana gaba daya. Wata kila saboda ita din tana da dan da sauran kurciya ba kamar Mama ba, wata kila kuma dokin amarci ne yake Allah masani. Idan kuma aka yi girki ba a ba mu wani abun arziki Allah ma ya sa yanzu damuwa bata barina na ci na koshi kamar da, wani lokacin har ragewa nake na bawa Hana a da kam na fi kowa cin abinci a gidan, ranar da Hana ta tafi family house din Mama ta fada musu halin da ake ciki na dora mata talla, washe gari Kawu Garba ya samu Baba yana nuna masa hakan be dace ba, sai Baba yace kar wanda ya sake saka masa baki akan lamarin yaransa shi ya ga damar su yi, kuma babu mai ciyar masa da yara sai su. A nan yake fadar ai tun kamin auren ya fada mata yaransa za su rika mata wani abun saboda ta fada masa ita fa tana sana'a kuma aure ba zai hana ta yi ba, shi kuma ba zai iya ganin matarsa da aure ta fita waje ta yi sana'ar wara ba, domin haka yarsa zata maye masa gurbi. Ni kam gaba daya na zama kamar ba ni ba duk abun da ake bana iya cewa komai sai ido, wani kalar canji ne ya same ni irin wanda ban yi zato ba. KAREEM POV. Da kansa ya shiryawa yaransa abun karyawa ya dauko lunch box dinsu ya raka su har gurin School bus suka shiga sannan ya juyo ya dawo, dakinsa ya shiga yayi wanka ya shirya ya fito ya shiga motarsa. Family house dinsu ya wuce domin fara gaisawa da iyayensa kamin ya wuce aiki kasancewar yau Monday. Wani abun da ya sabawa kansa da shi ne, na kin kallon mahaifiyarsa a duk lokacin da ya shiga gidan. Kai tsaye ya wuce bangaren Hajiya Hassana wadda take step mom dinsa. Karyawa ya same ta tana yi tare da Khadija da Aaryam da sauran yaransa Aneesa da Kamla. Kanensa duk suka gaishe shi ya amsa, Yusura dake zaune gefe daya ta mike tsaye ta shige dakin Hajiya Hassana sai a lokacin ma Kareem ya lura da ita. Khadija ta kwashi kayan abincin ta bi bayan Yusura Kamla da Anessa ma haka, sai ya rage daga Step Mom dinsa sai kanensa Aaryam. “Zaka ci abincin a zuba maka?” Hajiya ta tambaya. “Aa” “Baka cin abinci yanzu, tun da Momynka bata nan, shigowa nan ma sai monday Monday kake yi ka duba mu, idan Momynka bata nan ni da mahaifinka ai muna nan kuma Kanenka suna nan be kamata kana haka ba” A hankali ya sauke ajiyar zuciya. “Hajiya Bana jindadin shigowa ne yana yawan tuna min da Momy kuma ina jin babu dadi” “Tohm ya za'ayi haka tsarin Allah yake, kai kanka mutuwa zaka yi balle kuma wasu, sai hakuri rayuwa ta gaji haka, ni kaina yanzu gidan ba dadi yake min ba Wallahi, amman a haka nake daurewa saboda Khadija da Aaryam da kuma Aneesah, dole na yi walwala idan ba haka ba dukanmu sai mu taru mu takura mu yi ta bakinciki da kuka” Yayi shiru be ce komai ba. Hajiya ta dauki tissue ta goge hannunta. “Likita..” Ta kira shi sai ya kalleta daman haka take kiransa tun Momy na gidan. “Ni fa ba zan boye maka ba, ban gane manufar abun da ka yi ba, kuma ban gane inda kuka dosa ba” “Na miye ba Hajiya?” “Kai da Yusura mana, ta dawo gida kawai tace mana ka sake ta, saki daya biyu ko uku ba mu sani ba, Daddy ka ma fushi yake da kai shiyasa be maka maganar ba har yau, Khadija da Aaryam ma gashi a zaune kullum haushinka suke ji saboda haka” Kareem ya juya ya kalli Aaryam kyakkyawan saurayi mai jini a jika, sai yayi murmushi. “Saboda Yusura?” “Eh mana, Daddynka cewa yayi ba zai maka magana ba, kuma kar wanda yayi maka a saka maka ido kawai, ita kuma ta so barin gidan ni na hana, saboda na san idan Momynku tana raye Yusura bata da gurin zama sai gidan nan, a nan ta girma nan ta saba yanzu kuma dan Momy bata nan babu wanda zan bari ya dauketa ko kuma ita ta tafi ta bar mu, sai idan na mutu, kai ma dan kana ganin Momy bata nan ya saka kake son ka wulakanta amanar da ta baka, to ka sani Yusura ta fika gata a gidan nan, kuma matukar ina raye ni ce gatanta ba kuma zata wulakanta ba” Kareem yayi gutun murmushi ya girgiza kai, kana ya sake juyawa ya kalli Saurayin Kanensa ya ce. “Fushi kuke ta yi da ni akan abun da Baku san komai a kai ba” Aaryam ya ce. “Haba Big Bro ko dai minene ai be kamata ace ta kai ga haka ba, kai fa Namiji ne, kuma ga yara tsakaninku, kawai dai ban maka magana ba ne saboda Daddy yace kowa ya saka maka ido, kuma ina kasa da kai be kamata na tsuma baki a irin wannan ba sai idan ka bukata” “Gaskiya ne” Kareem ya fada tare da aje numfashi sannan ya mike tsaye ya nufi bangaren mahaifinsu, sai a yanzu ya fahimci dalilin da ya saka har yau da suke wata biyu da sati biyu da rabuwa Daddy be taba kiransa ya tambaye shi miye ya faru ba, kuma be taba yi masa maganar ba a duk shigowar da yake gaishe shi a gidan. A natse ya shiga bangaren kamar yadda ya saba sai bayan da ya zauna sannan ya gaishe da Daddy dake sanye da gilashi yana duba newspaper. “Lafiya Kalau, Kareem ya gidan ya yaran?” “Lafiya kalau Daddy” “Maa Shaa Allah, yau Monday ko akwai aiki” “Haka ne Daddy” “Allah ya taimaka ya bada nasara” “Ameen” Kareem ya mike tsaye har ya fara tafiya sai kuma ya dawo ya zauna yana kallon Daddy. Daddyn ma ya kalleshi “Allah yasa lafiya, akwai wata matsala ne?” Kareem ya hade wani abun da ya tsaya masa a makoshi sannan ya ce. “Daddy, ban ji kace komai akan dawowa Yusura gidan nan ba” Daddy ya aje newspaper dake hannunsa. “Oh wai Yusura, Mijinta ne ya sake ta kasan kuma bata da wani gidan da ya wuce nan, bata da gata a duniyar nan sai mu, zamanta a nan ya takura maka ne? So kake a koreta?” Kareem yayi murmushi jin yadda Daddy yake fadar mijinta ne ya saketa kamar be san Kareem din ne mijinta ba. “Aa Daddy ai ban isa na ce a koreta ba” “Good kara dai da kasan haka” Ya sake yin murmushi, a yanzu ne ya kara tabbatar Daddy fushi yake da shi. “Kawai dai na yi zaton ko zaka bincike abun da ya faru ne” “Abun da ya faru, tsohuwar budurwarka tana zuwan nemanka, amaryar abokinka tana zuwan nemanka ta yi magana sai ka mareta ka ce ka saketa” Dif Kareem ya dauke wuta kamin ya kalli Daddy ya ce. “Haka ta fada maka?” “Ba gaskiya ba ne Daddy, Safeena ta zo gaisuwar Momy ne, kuma na gargade kar ta sake zuwa domin babu wata alaka tsakanina da ita, Noor kuma tana zuwa ne saboda tsabanin da suke samu da Hafiz a lokacin” “Zan yarda da wannan, domin ban san ka da wani aiki na assha ba, shi ma wannan saboda Hassana ta matsa ne ya saka ta fadi wannan dalilin, amman bayan haka bata fada mana komai ba, ni kuma na auna abun a ma'aunin kishi ne, sai dai kai kuma ka yi kuskure na aikata saki a take” Kareem yayi shiru kamar ba zai ce komai ba. Daddy ya cigaba. “Shiyasa na yi shiru na zuba maka ido na gani shin kana da hankali kansan ya kamata ko baka sani ba” Kareem ya sauke numfashi mai nauyi. “Daddy, akwai abubuwan da ni da ita muka boye ba mu bar kowa ya sani ba, ban san ya zaka fahimta ba gaskiya ce mai matukar nauyi da daure kai, Daddy ni da Yusura ba mu taba son junanmu ba, ban taba jin ina sonta ba ita ma bata taba jin tana so na, wannan sakin ma ta dade tana bukatar na yi mata shi, saboda da nisanta da ni” Daddy yayi murmushi mai sauki ya cire gilashin idonsa. “Kareem karka maida karamin yaro mana, baka sonta bata sonka aka yi muku aure kuka zauna lafiya har kuka haihu ba a taba jin kanku ba sai yanzu da Mahaifiyarka bata raye zaka ce wai baka sonta? Wannan ba hujja ba ce” Cikin tsananin damuwa Kareem ya ce. “Wallahi Daddy bana son Yusura ita ma bata so na, kawai dai mun amsawa Momy ne kuma mun zauna saboda ita, ni da ita ba za mu iya bijirewa umarninta ba” “Okay yanzu da bata raye mu ne abokan wasarka? Kai da ita? Ni ba zan ma yarda ba ku son junanku ba. Kareem zan baka shawara karka yarda ka rasa Yusura, na yi aure tun kurciya har yanzu na zauna da mata biyu a lokacin da mahaifiyarka take raye, mu kan samu tsabani mu yi dadi, wani lokacin har iyaye su sani, amman ban taba ganin matar aure da bata taba kuka da mijinta ba sai Yusura, bata fadin sherinka, bata kawo kararka, kai a gurinka ba abun kunya ba ne aji ka saki matarka? Kuna da yara biyu me kake fada musu? Idan aure kake son karawa you're free to do so ba sai ka saki matarka ko ka wulakanta ta ba, idan har kana fadar saboda Mahaifiyarka ka aureta to miye amfanin sakin a lokacin da mahaifiyarka bata raye? Ke nan ganin idonta kake yi ma biyayya ba saboda Allah ba? Yanzu da ban yi magana ba haka zaka zuba ido ta cika idda? Ko saki uku ka yi mata? Domin bata fada mana ko saki nawa ka yi mata ba, kuma ita bata zauna kamar kai ta kalli kwayar idonmu ta fada mana bata son dan mu ba, Kareem idan ka sake ka rasa Yusura ka rasa matar kirki kenan har abada” Kareem yayi shiru be ce komai ba, domin ya fahimci Daddy ba zai yarda da duk wani zancensa ba. “Saki nawa ka yi mata?” “Daya” Sai a lokacin Daddy ya sassauta muryarsa ya daina yi ma Kareem fada. “Ka yi hakuri, shi zaman aure dan hakuri ne, duk can talkaminmu suka tsinke, dole sai an kai zuciya nesa, bana son na sake jin wata matsala a tsakaninku, ka maida matarka dakinta ku zauna lafiya dan Allah” Kareem kamar zai fasa kuka ya ce. “Daddy mai daki shi ya san inda yake masa yoyo...” Be rufe baki ba Daddy ya rufe shi da fada yana masa tsawa. “Get out Kareem, tashi ka dauki matarka ka aje ta gida sannan ka wuce aiki, wato Momy kake tsoro kana gudun zuciyarta mu kuma ka raina mu ko? Toh ka bari har bayan raina sannan ka saketa idan ka ga dama ka hada har da yayanka ka koresu gaba daya” Da sauri Kareem ya sauko daga kan kujera yana bawa Daddynsa hakuri, domin idan akwai abun da yake gudu da tsoro a rayuwarsa to fushin iyayensa ne. “Ka yi hakuri Daddy, na maida aurena saboda kai, kuma zan dauke ta mu tafi gida yanzu kamar yadda ka ce ka yafe min dan Allah” Daddy ya dauke kai ya kai hannu ya dauki gilshinsa ya mike tsaye ya shige bedroom dinsa. Kareem ya dafe kansa ya rumtse ido, ya fi karfin minti talatin a haka sannan ya dago ya fito daga bangaren ya dawo bangaren Hajiya Hassana ya zauna a falon ya kasa yin komai har sai da Step mother dinsa ta fito sannan ya gabatar mata da abun da ya maido da shi bangaren nata. “Na maida aurena Hajiya, a fada mata ta fito mu tafi” Hajiya Hassana ta yi murmushin jindadi. “Haba yanzu na ji magana, ko kai ba haka ake so, kuma dan Allah ayi ta hakuri karka ce zaka biyewa mace ita mai rauni ce, kuma duk matsala da za a samu a daina saurin saki, muna raye idan ya kamata mu ji sai ka sanar mana mu tsawatar mata yafi ayi ta saki ga yara” “Tohm Hajiya” Ya amsa irin amsawar nan na wanda ya rasa interes da mafaka da kuma gata a lokaci daya, daman tun farko yayi tsammanin haka shi ya hana shi sakinta a lokacin da Momy bata dade da barin duniya ba, da ace kuma ya sake a lokacin da take raye Allah kadai ya san irin fushin da Momy zata yi da shi. Ya mike tsaye yana jin wani fever na rufe shi ya nufi motarsa ya bude ya shiga ciki ya zauna yana jiranta bakinciki cike fal a zuciyarsa. Ya bata awa daya a haka sannan Aneesah ta fito ta bude motar ta ce masa. “Big Bro wai Hajiya tace ka tafi zata kawo ta da kanta” “Toh ki fadawa Daddy haka idan na wuce” Cikin tsananin damuwa Kareem yake maganar sannan ya ja motarsa ya fice daga gidan. Wunin ranar aiki kawai yayi dan ya zame masa dole ba dan jikinsa da zuciyarsa suna cikin dadi ba. Bayan ya gama yana kokarin hada kayansa ya wuce wata mate room ta shigo ta kawo masa takardar envelope. “Maman Khalid miye wannan” “Wallahi ban sani ba, wata ce ta zo dazun bata same ka tace bari ta ba ni na aje maka dan Allah kar na bawa kowa sai kai hand to hand” Ta fada cikin hausarta da bata gama kwarewa ba, kasancewarta bayarabiya. Ya karba fuska ba yabo ba fallasa yayi mata godiya ya hada kayan saukinsa ya fice daga office din. Sai da ya shiga motarsa sannan ya bude envelope din wani kamshi mai dadi ya bugi hancinsa, flower ce farkon abun da ya fara cirewa daga takardar sannan wani sexy chocolate da kuma farar takardar mai rubutu red. Be yi tsammanin ganin romantic abu irin wannan ba sai a Safeena kuma ya canka daidai a lokacin da ya fara karanta sakon na karin shekararsa a yau. “Happy birthday Love, barka da zagayowar ranar haihuwar mutumen da bana son zama da kowa sai shi, barka da zagayowar ranar haihuwar mai bani farinciki a zuciya da jiki, mai kwantar da min da hankali, mutumen da ke nisantarsa ke haukata ni ta hana ni sukuni, barka da karin shekara My future husband, my partner in crime, the father of my future kids, father to be... I know its your birthday today.. I am sure u will give me treat in a big house like we use to be.. so I shall talk to you in person there, because I don't know to express my feelings in paper, i love you duk yadda kake tsammanin za mu iya rabuwa da junanmu ba zamu iya ba Kareem saboda muna son junanmu, ba zan iya kyaleka a irin wannan yanayin da kake da bukatar wani a kusa da kai ba, i know how painful it's to lost a best friend and Mother. Please take good care of yourself for me...” Ya girgiza after ya gama karantawa, so today is his birthday gaba daya ma ya manta, daman tun kamin su rabu tun tana girlfriend dinsa ita take tunawa da birthday sai kuma Momy, and even after break up bata daina wishing dinsa ba a duk lokacin da ranar zata zo. Wani gurin ya bude a motarsa ya saka takardar ya rufe ya yi ma motarsa key. Kusan wannan ne karo na farko da yake jin kamar baya sha'awar komawa gidan all his thoughts is Yusura ta koma gidan by that time, hakan ne ya rike shi daga komawa da wuri domin samawa yaransa abun da za su ci da rana wani lokacin daga restaurant yake karbowa ya je musu da shi, wani sa'in kuma da kansa yake girkawa tare da su ko kuma kamin su dawo. He park his car near the entrance ya bude motar ya fito ya shiga falon. To his greatest surprised yaransa suke tarbe shi da wani irin farinciki da murna da ba su taba tarbonsa da shi ba. “Dady welcome home, Dady Mamy ta dawo” Ya rage tsawonsa yana kallonsa da murmushin da ya ara ya yaba a fuska saboda yaransa. “Kun jidadi?” “Eh sosai” Babbar ta fada sai ya shafa kanta, ba su taba tambayarsa ina Mamy su tafi ba, yaushe zata dawo me yasa bata gidan, tun da suka dawo daga school ba su same ta ba ba su sake walwala ba, kuma ba su tambaya ina take ba, kai ka ce sun fahimci sakinta aka yi, tun daga lokacin Kareem be sake kai su family house dinsa ba saboda gudun su ganta ko kuma su yi kuka idan zai dawo da su. “I'm happy too” Ya fada yana kallonsu cike da alfahari, and he's not lie farincikin yaransa farincikinsa ne, hakan kuma ba yana nufin ya jidadin dawowar Yusura ba, idan har akwai abun da yake nadama a yanzu be wuce aurenta ba, me yasa be fadawa Momynsa gaskiya from first place ko da ba zata jidadin haka ba? Yanzu a wa gari ya waya, waye a matsala sama da shi? “Kun ci abinci?” “Eh munci Mamy ta dafa mun ci, naka yana dinning Dady” “Okay bari na je na yi wanka na shirya sannan na zo na ci, ku je ku yi shirin islamiya” “Okay Dady” Karamin ya amsa, babbar kuma sai da ta sumbance shi sannan ta nufi sama da gudu tana murna. Tsaye yayi yana kallonsu har suka haye suka shige dakin Yusura sannan ya sauke ajiyar zuciya ya haura stairs din ya shiga dakinsa. Bayan yayi wanka ya kwanta a dakin yayi bachi awa daya ya farka, bandakin ya shiga yayi alwala ya fito ya saka ya sauya tufafin jikinsa daga kanana zuwa shadda sannan nufi madubi ya dauki dan'uwansa turare ta feshe jikinsa sannan ya dauki wayarsa ya wallet dinsa then car keys ya fice daga gidan gaba daya. A hanya ya tsaya yayu sallah la'asar sannan ya karasa restaurant dinsa. Yana shigowa reception din Nabil da ya gama dutysa zai fita ya gaishe shi cike da girmamawa. Kareem ya mika masa hannu suka gaisa. “Ka gama naka eh?” “Eh na gama ranka ya dade, daman duty safe nake yau, ko akwai abun da zan yi?” “No aa, ka ce ka daina karatu?” Ya gosa kansa cikin jin kunya ya amsa domin abun kunya ne wannan zamanin a kalli matashi kamar shi ace baya karatu a . “Eh Wallahi, amman dai zan koma nan gaba idan Allah ya yarda” “Me ka taba karanta? Wane course?” “Mass Com na fara, amman dai ina son nan gaba idan zan koma na canja course” Kareem ya cigaba da tafiya yana fadin. “Why baka son aikin jarida ne?” “Ina son, amman dai yanzu na fi sha'awar Public health” “Karatun health yanzu yayi yawa, why not ka yi political science? Karatun yana da kyau, kuma idan ka dace da gurin aiki kamin an ankaro ka dauke nauyin gidanku” “To da har ka kawo wannan shawarar da yardar Allah shi zan yi ranka ya dade” Kareem yayi murmushi yana jindadin yadda Nabill yake girmamashi. “Na jidadin haka, ni kuma zan yi kokarin sama maka scholarship, a private ko kuma gov school, ban sani ba ko a samu a nan gida nigeria ko kuma a waje, fatan dai ba zaka ba ni kunya ba” Nabil ya rasa me zai ce ya rika hannun Kareem yana son masa godiya ya kasa domin be taba kawo wani zai dauki nauyin karatunsa ba, wanin ma kuma Kareem. “Ranka ya dade, na rasa me zan ce ma” “Toh ka aje kalamanka sai idan an samu tukuna, sai ka yi godiya” Cewar Kareem yana dafa kafadarsa sannan ya wuce yana murmushi ya bar Nabil tsaye da mamaki. Be yi taku goma ba ya juyo ya kalli Nabil. “Nabil ya Noor take?” Nabil ya hade yawun bakinsa da sauri ya matsa yana amsawa. “Ta.. Tana lafiya ranka ya dade” “Ba wata damuwa babu wata matsala?” “Eh to tana dai cikin damuwa, mutuwarta nan ta dan taba ta gaskiya, domin ta canja gaba daya kamar ba ita ba” Kareem be ce komai ba, ya juya ya cigaba da tafiyarsa. Office dinsa ya shiga sai da ya zauna sai kuma ya tashi yake yi yanzu a duk lokacin da ya shigo, da zarar ya kalli kujerar da Hafiz yake zama idan ya shigo office din da yamma sai ya ji babu dadi. Har yanzu ya gagara sabawa da rashin abokinsa wannan kawa zucin yana nan tare da shi, shi ke hana shi walwala a duk lokacin da ya shigo office din. Be wuce minti ashirin a ciki ba, ya mike tsaye ya dauki keys dinsa ya fice da kansa ya shiga ya saka aka zuba masa abincin da yake sha'awar ci yaron gurin ya rika masa har gurin motarsa. Front seat ya bude aka zuba abinci sannan ya rufe ya shiga bangaren tuki yaja motar ya fice daga restaurant din gaba daya. Tuki yake not knowing what to do or to go, shi dai gashi nan duniyar gaba daya ta ki ta yi masa dadi. Be faka ba sai da ya samu wasu itatuwa dake gefen hanya, ta cikin itatuwan ya ratsa ya faka motarsa sannan ya bude ya dauki abinci yana ci, gurin is so fresh ga wani iska mai dadi babu damuwa ko hayaniyar kowa it's just him and himself. NOOR POV A kwana a tashi babu wuya ga Allah, kamar jiya na fara wanka duk dai wasu sukance wankan be wajaba a kaina ba, saboda ya sake ni, sai dai zancen da ya fi karfi shi ne na yin zaman takaba domin akwai gyara a auren kuma ban kai ga cika idda ba ne ya rasu. A ranar da na yi wata hudu da kwana goma Mama ta aiko da waina da fanke aka raba sadaka yan'uwanta suka zo tare da yan'uwan Baba aka saka ni na yi wanka na saka sabuwar atamfar, a ranar kuma mutuwar Hafiz ta dawo min sabuwa kai kace mun yi shekara aru aru da shi ba yan watanni ba, sai dai abun da ya daure min kai shi ne na rashin zuwan dangi ko yan'uwansa a gurin tun a ranar da na dawo gida har zuwa yau babu wanda ya leko ni ko ya bincika lafiyata, abincin da ake cewa dangin miji ma suna kawowa matarsa idan tana takama basu kawo min ba. Wata kila Aisha ta shafa min bakin fenti a idonsu domin na lura har bayan mutuwar Hafiz kishi take da ni. Bayan sallah Isha'i, a lokacin da kowa ya watse, ina zaune ina gyara wake soya Yaya ya shigo cikin gidan da kuzarinsa ya ce. “Noor oga Kareem ne a waje yace na kira ki” Na yi shiru na wasu dakiku sannan na mike tsaye kamin na cira kafa na ji Umma ta tabe baki tana fadin. “Wannan ai ba mutunci ba ne, ace ana maka sallama ka mike kai tsaye ka fice ba tare da tunanin fadawa mahaifi ba, kai ma ai ba ita ya kamata ka samu kai tsaye ka fada mata ba mahaifinku ya kamata ka fadawa” “Ba kisan waye oga Kareem ba Umma, oganmu ne na gurin aiki kuma abokin mijinta nw Hafiz ya saba zuwa nan akai akai” Ya Nabil ya bata amsa. “Tohm Allah ya kyauta, tashi ki tafi, amman gaskiya idan haka mahaifiyarku ta koya muku ba abun kirki ba ne, ai sai uba ya aminta ake fita domin shi yake aurar da yarinya” A kam ban iya rike kaina ba sai da na mayar mata da martani. “Baki san komai akan uwarmu ba, karki sake fadin wata mummunar kalma akanta” Kallona ta yi ta dauke kai bata ce komai ba, ta cigaba da dakan yajin da take. Ni kuma na shiga ciki na dauko hijab dina na saka na fito kofar gidanmu. Sai na same shi a gurin da suka saba tsayuwa shi da Hafiz idan sun zo, ko kuma idan ya zo shi kadai. Ganinsa ya tuna min da Hafiz sosai sai zuciyata ta yi min babu dadi, shi kuma na lura baya cikin walwala da farinciki, gashi ya rame kamar ni yayi hudu haskensa ya rage. Gambun motar dake bude ya rufe sannan ya jingina da motar yana kallona kamar wanda be taba gani na ba. “Noor how are you now?” Tambayar yake ya nake, amman sai na ji kamar yace na fada masa damuwata ta hanyar kukana. Kawai sai na fara hawaye ina kallonsa, i miss him i miss his friend i miss my previous life. “Kina cikin damuwa ko?” Na daga mishi kai, sai na ji ya sauke ajiyar zuciya. “Duk yadda kike tsammanin abun ya wuce nan Noor, na fi ki shiga damuwa yanzu, i loss hope, kawai ina rayuwa da kokarin tsayawa saboda Yayana, a yanzu babu wani daki da zan iya rufe kaina na ji sanyi, duka dakunan zafi ne da su kamar wuta” Na share hawayena. “Da zan iya komawa na gyara rayuwata ta a baya...” Na ji ya fada sai kuma yayi shiru be cigaba ba. Ni kuma na kalleshi na ce. “Da ka goge shafina a rayuwarka” Ya girgiza min kai. “Ba zan iya goge ki a rayuwata ba Noor ko da kuwa ace ina da wannan damar, ba ki min komai ba, babu dalilin da zai saka na natsane ki, you're just innocent, precious soul, and Hafiz was right akan abubuwa da yawa akanki” “toh me zaka gyara?” Yayi murmushi ya gyara tsayuwarsa. “Ba wannan ya kawo ni, na zo nan ne saboda na yi magana da ke da kuma Baba, amman kamin nan fada min ya kike?” “Ina lafiya, amman mutuwa bata da dadi Kareem, shiyasa lokacin da Hafiz ya fada min mahaifiyarka ta rasu, na yi kuka sosai na tausaya maka yanzu kuma na ji yadda ake ji” Murmushi yayi ya daga kansa sama sai kuma ya sake kallona. “Noor... Kamin na manta, na zo nan ne saboda maganar gadonki da kuma kayan dakinki” Na cigaba da kallonsa ina sauraren abun da yake fada. “Noor dan Allah karki ce zaki yi jayayya da iyayen Hafiz akan gado ko wani abu, sun ce baki da gado kanensa ya kira ya fada min kuma na je na same su na yi musu magana na fahimtar da su, amman ba su yarda ba, iyakar hujjarsu wai Hafiz ya sake ki kamin ya rasu, kuma kamin ya sake ki wai be taba tarayya dake ba haka ne?” A nan na sauke kaina kasa na dan bata rai. “Aisha ta bata ni a gurin kowa, kuma ita ce silar duk faruwar haka” “Babu wanda zai iya bata ki a gurina, kuma mutuwar aure abu ne da Allah ya kaddara, kuma ba dan Allah ya rubuta haka ba, na yi magana da Hafiz kuma yayi alkawarin yana dawowa zai zo ya dauke ki ku tafi gidan tare, sai dai kamin ya iso Allah yayi ikonsa” “Da gaske?” Ya daga min kai. “Yes Noor na lura kina cikin damuwa a lokacin kuma kin fada min kina son komawa ai, babu wani abun da zaki roka ban miki shi ba Noor sai idan ba zan iya ba” “Na dauka ina takura maka ne, na ga har baka son zuwana gurinka, na san ni ina da takura ai” Yayi murmushi. “To ki yi hakuri, idan Baba yana ciki shiga ki masa magana” “Baya nan yana majalisa” “Shiga ciki zan je can na same shi, ki kwantar da hankalinki Allah zai baki abun da ba su ba ki ba, kayan dakin ma sun ce ba za su baki ba ai saboda shi yayi komai” “Ni fa ba abun da ya dame ni da wani gado, su je su yi ta riko, amman ka yi magana da Baba shi ne dai na ji yana zancen zai yi kara idan ba a bada ba” “Okay” Kallona yake har na shige cikin gidan, ina shigowa Ya Nabil ya fita waje. Duk wata maganar da zai yi da Baba na san ba zai saurare shi, amman kudi za su iya sakawa ya fahimci komai kuma ya sassauto. Da alaka kuma Kareem yayi amfani da su ne domin babu ya shigo da far'a har da tsarabar nama yayi ma Umma. Cewa yake a yanzu ya hakura zai kyalesu amman saboda Kareem be kawai ba dan haka ba da babu abun da zai hana shi jan min hakkina. Yanka biyu aka ba mu, sai da muka cinye sannan yayi mana albishir wai Kareem ya fada masa ya nemawa Ya Nabil karanta a Sudan. Farinciki ya cika ni a lokacin da Baba yake fada min Kareem yana neman izininsa idan ya aminta sai ya fadawa Ya Nabil din ya kai masa takardunsa na SSCE. Sanin da na yi ba karamin dadi Ya Nabil zai ji ba, ya saka ni farincikin da na kwana biyu ban yi ba. Hakan kuma ya karantar da ni cewar Kareem yana da kirki ta wani bangaren, domin gashi ya danne kudirin mahaifina kuma yana kokarin nemawa dan'uwana karatu alhalin be hada komai da mu ba. Farinciki a gurin Yaya Nabil ba a magana kamar zai zuba ruwa kasa ya sha domin murna, daman abun da yake nema ne yana son karatu shi da Hana ba kamar ni ba. Washe gari da safe Kanen Hafiz ya sake kawo min ziyara sai dai wannan karon ba, maganar gado ce ta kawo shi ba, ya zo min ne da tsaraba ta atamfa biyu da kuma turare sai sabulu da talkami da kudi 10k wai yana taya ni murna fita waka, kuma na yi hakuri da yadda yan'uwansa suka nuna min halin ko'ina kula. Na karba na yi masa godiya muka yi sallama na shiga ciki, bana tunanin ina da wata bukata ta kudi a yanzu wannan ya saka na dauki kudin na bawa Hana na ce ta kaiwa Mama idan ta tafi gidan, domin ita ce mai yawan zuwa ni ban taba zuwa ba domin an yi auren ne a lokacin da ba ni da halin yawo. Abu kamar wasa, shiryen shiryen tafiyar Yaya Nabil Sudan ya fara, duk wani abu da za'ayi Kareem ne yake ba shi kudi yayi, har aka kammala komai within three months. Ranar da zai je yi ma Mama bankwana na bi shi muka tafi tare, ni da shi sai a ranar muka fara zuwa gidan. Babba gida ne mai bangare kusan hudu, gida ne mai kyau da tsari Mama da kanta na san ba ta taba mafarkin aure irin wannan gidan ba. Da muka shiga ciki sai ta zame mana kamar wata bakuwarmu saboda yadda rayuwa ta canja mata, ta yi kiba ta kara haske ga tufafi masu tsada kayan kallo kai har da dinning da ac kamar daman can Mama bata taba auren talaka ba, duk inda ta wulga kallonta nake kamar wata bakauya. “Noor na zame miki sabuwa yanzu ko?” Na yi dariya ina kallon plate din taliyar da ta aje min nama batsa batsa kamar wanke. “Mama ina ta mamaki ne, ina kika hadu da wannan mutumen ne?” Ta dan hade rai. “Mutume? Toh idan ba zaki iya kiransa da Baba ba, ki kirashi da suna Alhaji kamar yadda kowa yake kiransa a gidan nan, wato ke dai sakarcin ki ba zai canja ba ko?” Na yi shiru ina kallon Yaya dake cin taliyar, sannan na soma cin tawa. Rabin abincin kawai Yaya ya ci ya sha ruwa yace zai tafi. “Da wuri Nabil na yi zaton sai dare, saboda Alhaji ya dawo ku gaisa, yana ta fadar ban taba gabatar masa da sauran yarana ba, be san kowa a cikinku ba sai Hana da ke yawana zuwa” “Bana son na kai dare Mama, akwai guraren da ya kamata na tafi kamin ba bar garin nan, kuma kin ga kwana biyu ya rage min” “To sai dai kai ka tafi Noor kuma zata tsaya sai ya dawo kun gaisa tukuna ta wuce” Mama ta shiga dakinta ta dauko masa babbar leda cike da kaya sannan ta danka masa 20k tana ta sakawa Kareem albarka wai daman a yanzu tana ta tunanin wace makaranta zata nemawa tarin kudin da take shi take yi ma, amman gashi ya dauke mata nauyi. Bayan Ya Nabil ya wuce muka zauna da Mama muna hira take tambaya ko Zafeer ya ji rayuwar Mijina. “Zai iya ji tun da iyayensa suna cikin unguwar, ko basa nan ma ai yan gulma suna nan, fitowar nan ma cewa suke ta yi hakkinsa ne” “Zafeer yana sonki sosai, zai iya dawowa yanzu ma, wata kila kuma iyayensa su hana shi, ko da yake a can baya ma sun yi ta kokarin hana amman ya nace sai ke, gashi kuma an watsa masa a ido, Wallahi mahaifinku be kyauta ba” “Baba ma da yace be yafe ba idan na sake masa magana, shi ne abun da ya fi damuna” “Wai har yanzu? Toh ai Hafiz din baya raye kuma, yanzu idan Zafeer ya dawo ba zai bari ya aureki ba?” “Ban sani ba, amman da kamar wahala saboda yana ganin Zafeer talaka ne” “Haka ne, ubanki be ji wani yare sai na kudi, gashi babu mai iya ja masa liyi a dangi komai yayi daidai ne a idonsu” Na daga kai ina kallon POP din falon. “Taso mu tafi ki gaisa da mutanen gidan, suna ta tambayar, da kika fita wanka ma sai da matarsa tace zata tafi ta duba ki kuma Allah be yi ba” “Ita bata kishi ne Mama?” “Ana tabawa mana ayi mace babu kishi, amman boyewa ake na ciki na ciki, ita dai tana da kirki ba kamar wasu ba” “Ko dai irin na Aisha take miki ba, haka take nuna min ba komai ashe wayo take min” “Ke dai da halinki Noor, na san ki ba, kuma zamanmu a nan Alhaji ya fada mace kamar riga take a wuyansa duk wanda ta daga masa hankali cire ta kawai zai yi ya aje, duk tarin yaransa babu wanda uwarsu take cikin gidan nan, sai wannan matar da yaranta uku, sauran duk iyayensu sun fita, ni ma sai bayan auren nake ji, wata kila shiyasa ta kama kanta” Ina jin haka na san an gudu ba a tsira ba ne, kenan ita ma idan ta yi masa ba daidai ba zai iya sakinta. Daga bangaren Mama muka fito muka shiga bangaren matar da take gidan a yanzu. A cike muka samu falon da mata da maza, Mama ta yi sallama suka amsa suna gaisheta da mutunci. “Noor Ya hakuri?” Wata budurwar da ban waye ta ba ta fada sai na amsa da Alhamdullahi na gaishe da Hajiyar. “Lafiya Kalau Noor, an fita wanka ko? Tohm Allah ya bada hakuri ya kawo na gari” Mama ta amsa da Ameen. “Alhaji ne be santa ba sai mita yake ina boye masa yara, tare da yayanta take jibi zai wuce Sudan gurin karatu, ya zo bankwana amman be tsaya ba, ita kuma ba ce ya tsaya ta gaisa da yan gida” “Ta kyauta gaskiya, da ma dai kin maido nan kila zata fi jin sanyi kin san gidan na mu cike yake da mutane” “Mahaifinta ne ai be yarda ba, ko takaba a nan ya so ta yi amman uban yace ba zata yi ba” “Kin san wasu mazan akwai kishi” Haka dai suke ta hirarsu ni dai kaina na kasa ban dago har sai da na ji an bude kofar falo alamar mutum ya shigo. Dagowar da na yi sai muka yi ido hudu da Safeena tana dauke da cikinta da be gama girma ba. Bata kallon kowa sai ni ni ma kuma bana kallon kowa sai ita muka rika kallon kallo wata kila ita ma tana mamakin ganina ne kamar yadda nake mamakin ganinta. Gidansu ne? Ko kuma zuwa ta yi? Ko kuma dai tana da wata alaka ce da mutanen gidan? “Kin dawo Safeena?” Hajiyar ta fada sai Safeena ta amsa mata ba tare da ta kalleni ba, har lokacin ni take kallo. “Na dawo Hajiya, na karbo files din gobe zan tafi asibitin na kai” “Toh Allah ya taimaka ya raba lafiya” “Ameen” Ta amsa sannan ta dauke idonta ta zauna a kujerar dake facing dina, sai kuma ta sake dasawa daga inda ta tsaya. “Anty Safeena kin santa ne?” Na kalli mai tambayar wata kila su ma sun lura da kallon da take min yayi yawa. Ga mamakina sai ta amsa da cewar “Aa ban san ta ba, wacece hala? Ta yi min kama da wata kawata ce ta yarinya” “Noor ce yar wajen Anty Amarya, wanda mijinta ya rasu” “Allah sarki Allah ya masa rahama” Ya juya tana kallon Mama dake amsawa da Ameen sannan ta sake kallona. Har muka baro bangaren babu abun da take sai kallona kamar wata bakuwarta. Ban kuma san dalilinta na boye cewar ta san ni ba. A bangaren Mama na koma na zauna har dare ina jiran dawowar mijinta saboda mu gaisa, be shigo ba sai bayan Magariba a lokacin da ake hada hadar Sallah Isha'i. Na yi mamakin yadda yayi murna da farinciki ganina babu wata kyama, har na na yi sha'awar ina ma ace shi ne mahaifina ba Baba ba, zaunawa yayi a falon yana ta min nasiha akan hakuri da rayuwa na halin da na samu kaina da kananan shekaru, na yi masa godiya ya saka hannunsa aljihu ya ciro 10k ya ba ni. “Aa na gode” A bakin gaskiya ta ba zan karba ba, domin ko na karba ban san miye zan yi da su ba a yanzu. Sai dai na lura hakan be masa dadi ba domin rufe ni yayi da fada a dole na karba na yi masa godiya. “Tafi bangaren Hajiya ki ce na ce cikin yaran nan duk wanda yake nan ya sauke ki gida” “Tohm” Na mike tsaye na yi ma Mama sallama sannan na fice daga falon yana ta kallona. Bangaren Hajiyar na dawo na sanar mata abun da Alhaji ya fada sai mutumen dake tsaye a gabanta yayinda take zaune ya juyo ya kalleni. A nan ma wani mamakin ya kara kama ni, mutumen nan da ya taba yunkurin biya min kudin siyayyar da na yi a wani dare da muka fita tare da Hafiz. “Kamar na sanki?” Na bude baki kamar zan yi magana sai kuma na yi shiru, ban san me zan ce ba, ni dai ina da saurin gane mutane shiyasa na gane shi. “Noor ce Yar wajen Anty Amarya ce, ita ce wadda mijinta ya rasu” “Ai ban sani ba, Allah ya jikanshi da Rahama” “Ameen, ku tafi tare sai ka sauke ta ka wuce, Noor bari ga Abdull zai fita yanzu sai sai ya wuce da ke, ki jira shi a waje” “Okay” Na juya na fito daga ciki, ban san wacece motarsa a cikin motocin gidan ba dan haka zauna a balcony har ya fito. “Kika zauna a kasa?” Bance komai na na mike tsaye na bi bayansa muka isa gurin wata sabuwar mota, sai da ya fara shiga sannan na bude na shiga front seat. Ba tare da yace min komai ba yayi reverse ya fice daga gidan. “Ina ne unguwarku?” A lokacin da na dago sai na ga idonsa akaina suke. Na fada masa na sake maida kaina kasa kamar ba ni ba. Na ji lokacin da wayarsa ta yi kara ya amsa. “Hello Safeena...” Sai kuma yayi shiru, yana sauraren abun da ake fada masa. “Yanzu na fito gida, amman zan biya ta can, sai na zo miki da shi, shi kadai kike so ko da wani abun?” Na yi shiru ina saurarensa kamar wata Munafuka kamin na ji ya ce. “Okay sai na dawo” Ya aje wayar ya dago zan kalleshi idona suka fada cikin nasa da sauri na dauke kaina ina jin sautin murmushinsa. Ban sake kallon gefen da yake ba har muka isa unguwar. “Ka sauke ni a nan unguwar bata da kyau can ciki” Na fada. “Karki damu, amanarki aka ba ni sai na kai ki har gida” Yadda ya fada haka ya aiwatar har kofar gidanmu ya isa da motarsa ya faka, ni kuma na bude na fito zan rufe kofar ya ce. “Ba godiya” Ban ce masa komai ba na rufe motar, na gode masa sai ka ce rokonsa na yi ya kawo ni. Sai da na shiga gida sannan na ji motarsa ta bar kofar gidan. KAREEM POV. Yana gama sallah asuba ya shiga kitchen hadawa yaransa breakfast. Domin Yusura bata musu komai tun da ta dawo gidan, Kullum shi zai hada musu breakfast ko kuma ya saka aika musu daga restaurant dinsa kamin su tashi break. And now cooking is one of his favorite things, yana samun nishadi a girkin, musamman idan yaran suka farka suka same shi a kitchen suna hayani yana aikinsa har ya gama, ya karya tare da su wani sa'in kuma ya zuba musu na su, ya tafi da nasa a office ko kuma su su tafi da na su school shi kuma ya ci a gida. Idan ya fita sannan Yusura take saukowa ta gyara ko'ina ta dora na rana. Tun da ta dawo gidan be taba leka dakinta ba, be taba ce mata uffan ba, ita ma kuma bata bari sun hadu ba, da zarar ta ji motarsa ko ta san lokacin dawowarsa sai ta shige dakinta. Yau ma sai da ya raka su har gurin bus sannan ya dawo ya zauna ya ci nasa breakfast. Bayan ya gama ya mike tsaye ya shiga dakinsa yayi wanka ya shirya cikin kananan kaya ya fito yana rike da lab coat dinsa da wayarsa sai kamshi yake zuba. Yayi kyau sosai ramar da yayi ta kara masa kwarjini da haifa. Sai da ya fice daga falon sannan Yusura ta sauko a zatonta ya fice gaba daya, dinning ta nufa ta tsaya tana kallon kayan karyawar da ya shirya, biredin da ya gasa ta dauka taba tabe baki ta shinshina ta aje. Sannan ta ja kujera ta zauna ta bude flask din ruwa zafi, a daidai lokacin Kareem ya turo kofar falon ya shigo domin daukar wallet dinsa da ya manta a dakinsa. Kallo daya yayi ma gurin da take zaune ya dauke kai ya haura sama ya dauko wallet dinsa ya sake fice. Yusura bata taba jin kunya irin ranar ba, bayan amincewa da aurensa da ta yi wannan ne abu da na biyu da take bakinciki a rayuwarta, ji ta yi kamar ta fasa komai na gidan dan bakinciki. Tuki yake a hankali har ya isa asibitin, ya faka motarsa a gurin da aka rubuta Dr Kareem sannan ya fito ya dauki kayansa ya rufe motar ya shiga cikin Babbar asibiti ana miko masa gaisuwa yana amsawa. Office dinsa ya shiga ya fara duba takardun dake gurin sannan ya fita ya fara duba marar lafiyar da aka aje da ya kamata ya duba su. After ya gama ya dawo ya zauna a office dinsa patient din dake shigowa suka fara shigowa yana dubata. Third person da ta shigo ita ce Safeena, tana sanye da dogon Hijabinta har kasa sai dai hakan be boye cikin dake jikinta, har ta zauna ita yake kallo. Sai da ta aje jakar dake hannunta sannan ya jingina baya ya kwanta jikin kujerar yana kallonta. “Wai ke wace irin yarinya ce Safeena?” “Ni din wata yarinya ce, mai wuyar warke ciwo, wata yarinya ce da ka koyawa soyayyarka kuma kake kokarin guduwa bayan ka yaudareta da farko” “Gargadin da na yi miki, da kuma tazarar da na baki daga lokacin da muka yi haduwar karshe zuwa yau bata fahimtar dake, na rumgumi kaddarata, ke ma ki rumgumi taki?” “Ka rumgume kaddara saboda Yusura tana sonka tana kyautata maka a yanzu? Ko kuma daman can karya ka yi min kace bata kula saboda kullum ka rika samun biyan bukatarka da ni? Ka yi breaking heart dina da farko yanzu kuma bayan na saba mu'alama da kai na saba da kwanciya a kirjinka na saba da soyayyar kake tunanin sake guduwa ka bar ni?” Ya mike tsaye daga zaunen da yake ya nufi windows dinsa ya bata baya. “Kana da kyau, Kareem kana da kudi amman duk wannan be tabbatar min da ina sonka ba sai da mu'amala ta hada mu, all this while na kyale ka ne saboda ina dauke da cikin nan” “Me kika zo yi yanzu? Tashi ki fice daga office din nan” “Baka da wannan damar ba saboda da kai na zo ba, saboda cikin nan ne, na dawo da awon cikin nan a nan ne, a nan zan yi ta zuwa har zuwa lokacin da zan haihu” Ya dafa Window ya rike kansa. “Namiji zan haifa suka ce, kuma ina alfahari da haka” Kareem ya dauki lokaci a haka kamin wani tunanin ya zo masa sai ya juyo da sauri ya kalli cikin na ta sannan ya kalli fuskarta, sai ta yi masa murmushi. “Fita ki bar office din nan” Ya nuna mata kofar, zata sake magana da daka mata tsawa har sai da ta zabura. “Fita ki bar office din nan na ce” Ta mike tsaye da sauri ta dauki jakarta tana kallon yadda ya hade fuska kamar be taba ganinta ba, ta fice daga Office din. Dawowar yayi ya zauna kan kujerar ya dafe kansa ya runtse ido yana numfashi da karfi, ya girgiza kai kamin ya daga hannunsa ya buga a tebur din yana jin wani irin bakinciki marar misaltuwa... It could be a joke maybe tana gwada shi ne, if not ai tana da hankali matukar ba wata manufa take da ita akansa ba ba zata taba sha'awar haihuwa da shi alhalin tana da aure ba, ta dauki dawainiyar cikin da ba na mijinta ba ta kai masa yayi komai, ba zata fara ba. Abun da zuciyarsa ta raya masa kenan har ya ji ya samu saussaucin cigaba da aikin da yake. Sai da lokacin tashi aikinsa yayi ya tuna da ba shi da abokin hira ko shawara a yanzu domin Hafiz is no more balle ya fada masa hasashensa ko damuwarsa. Tafiyar Ya Nabil karatu ta zame ta bude min wani gurbi a gidan. Domin ruwan da yake debo mana da safe yanzu nauyin ya koma kaina, ni nake cika gidan da ruwa ga jikin nawa ba mai son wahala ba ne amman haka nake daurewa ina yi saboda gujewa hayaniyar Baba bana son ya jefe ni da wata kalmar marar dadi a yanzu. Haka ma ba fita nake son yi ba, saboda idanuwan mutane yana kaina, idan na hadu da kanen Zafeer har jefa min magana suke kamar ni na so mutuwar auren ko kuma zaman gidan. A haka dai na daure na danne zuciyata ina cigaba da rayuwa a gidan ubana. Ranar wata labara Anty Larai ta kawo mana ziyara har da tsarabarta domin ta dade rabonta da gidan. Rabon da na saka a ido kuma tun a gurin gaisuwar Hafiz. Na yi murna sosai da ganin tana cikin Gwagganina masu hankali da kamanta adalci daidai gwargwado. Ina zaune kusa da ita nabban danta Ridwan Wanda ya kasance cousin ne a gareni sai tsokana ta yake, ni kam baki ya mutu bana cewa komai, Hana ce take ramawa sai Umma dake dan jefo magana sama sama. Gwaggo ta shafa kaina zuwa bayana tana murmushi ta ce. “Ka bi ka saka min yarinya a gaba, saboda yanzu ka samu ta yi lafiya ko? Da ada ne ai ba zaka iya da ita ba” “In ji waye ko a da ne zan iya, kawai ina daga mata kafa ne” Anty Larai ta bude jakarta ta dauko goro ta gutsira tana fadin. “Nabil an tafi ko? Ya zo min bankwana ai, Allah yasa ayi karatu cikin nasara” “Ameen” Na amsa ina daga kai na kalli Ridwan dake shirin tafiya. “Zaki dare nan?” “Aa idan dai ka yawato ka samu abun da zaka samu sai ka dawo ka dauke ni mu tafi gida” “Yaya Ridwan har yanzu Napep din kake ja?” “Toh ya za'ayi abincin a nan yake” Ya amsawa Hana dake tambayarsa domin tun tashinmun, Yaya Ridwan ba shi da wata sana'a da ta wuce jan Napep, da ita ya rike gidansa ya yaransa da matansa biyu har ma da mahaifiyarsa. “Allah ya taimaka” Cewar Umma, dukanmu muka amsa da Ameen sannan ya fice. Shimkafa da miya Umma ta girka saboda zuwan Anty Larai, bayan mun ci mun yi sallah Hana ta dauki awara ta fice gurin sana'ar da ta zame mata dole, ni kuma na zauna da Anty Larai muna ta hira, a cikin hirar nake gutsura mata irin zaman da muka yi da Aisha da yadda yan'uwansa suka jajirce ba za su ba nu gado ba. “Daman can Allah ya gani, zuciyarta bata natsu fa yarinyar nan dari bisa dari ba, mata makircinsu yana da yawa, ke kuma ba wayo ne da ke ba kuma babu mai tsawata a tare da ku, dama ace irin gidanmu ne da muke hade kin ga wani abun ko dan ganin idon uwar miji dole a bar shi” “Ni kadai nake zaune kuma kowa da bangarensa, amman hakan be hana ta cutar da ni, gashi ya yarda da ita, komai aka fada masa akanta baya yarda” “Ki barta da Allah, yanzu ai mai rabawa ta raba, Allah ya ba ki na gari ita kuma sai ta je can ta karata” Na yi shiru ina zane a hannuna da karen tsintsiya, kamin na kira sunan Gwaggo. “Anty Larai” “Na'am Khadijatu” “Anty Larai, alfarma nake nema a gurinki, na san Baba yana jin maganarki, dan Allah ki roka min shi yayi hakuri yace ya yafe min na yi magana da Zafeer” Na kora bukatar tawa ne ba tare da na kalleta ba, domin ina jin nauyin kallon idonta a yanzu. “Zafeer din ya dawo ne? Aiko ya kai masoyi kuma lallai yana sonki da gaskiya bawan Allah nan” “Be dawo ba, yana da zuciya sosai wata kila ba zai sake sona ba har abada, amman ni ina son a duk lokacin da na ganshi ko kuma na samu dama na masa bayanin da zai gamsar da shi cewar ba wai na ki aurensa saboda ba shi da kudi ba ne, na lura yan'uwansa har yanzu ganin suke kudi na bi na bar Zafeer” “Idan har yana sonki da gaske zai dawo, ai mai sonka be ganin ramar ka, be ganin tsufanka, kuma shi ma mahaifinku ai be dace ya shata muku layi mai kauri irin wannan ba, saboda zuciya bata da kashi” “Dan Allah ki masa magana, yace ya yafe min” “Zan mishi magana idan ya shigo, noor har yanzu kina son yaron nan ko?” Na daga mata kai ba tare da boye ko jin kunya ba, zan iya fadar ina son Zafeer a gaban, duk kuwa da na san a yanzu yayi min nisa. Sai na ji ta yi dariya tana buga bayana. “Aiko da har ina cewa Ridwanu ya shigo ko Allah zai ba shi sa'arki, sai ayi tuwona maina tankaden bakin gado?” Murmushi ne kadai abun da zan iya yi na kwanci kaina a wannan lokacin kuma shi na yi, sai dai ko kadan manufar da take son isarwa a gareni ba mai yiyuwa ba, sai idan cilasta Baba zata yi yayi min auren dole. Baba be shigo gidan ba, sai da yamma liss ya dawo a gajiya. Na debi ruwan wanka na kai masa yayi wanka ya fito ya zauna kusa da yar'uwansa yana cin abinci suna gaisawa. Ina alwalar magariba na ji tana yi nasa maganar Zafeer. “Ai wannan duk da ne, yanzu kam komai ya wuce, ko lokacin da na yi mata wannan furucin ta fusata ni ne shiyasa kuma na lura a wacan lokacin tana son ta biyewa zugarsa ne ta bijirewa umarnina, amman yanzu komai ya wuce” “Duk da haka dai ka ce ka yafe ka san bakin iyaye lalle ne” “Haka ne, toh na yafe Yaya Larai kina shagwaba Noor” Ta yi murmushi ni ma murmushin na yi ina jindadin janye takukun da Baba yayi tsakanina da Zafeer. Daki na shiga na yi sallah bayan na gama na fito na yi ma Anty Larai godiya a lokacin Baba yana masallaci. Shigowar Ridwan da mintuna kadan Baba ya dawo daga masallaci suka gaisa Ridwan yayi masa alheri sannan ya fita waje jiranta. Ni kuma na yi mata bankwana Baba ya rakata har waje suna tafe suna hira har suka fice daga gidan. Hana na shigowa na labarta mata cewar Baba ya daga min kafa a yanzu, yace ya yafe min na yi magana da Zafeer, na yi zaton zata taya ni farinciki ne kawai sai na ji ta fashe da kuka marar sauti. Hankali ya tashi da sauri na dafata na dago kanta. “Hana lafiya?” “Na gaji da rayuwar gidan nan Noor tun da Mama ta tafi ba mu da jindadi babu walwala, zuwan Umma ya kara mana matsuwa kuma ban mu isa mu yi magana ba, ni ban taba talla ba, sai wannan karon idan na fita da la'asar ba zan dawo ba sai bayan Isha'i dole sai na siyar da komai idan ba haka ba idan na dawo sai ta fara fada tace keta nake son mata. Baba kuma ba zai shigar mana ba sai ita, kawayena a yanzu babu mai talla sai ni, maganar nan har ya kai makarantar mu na boko, gashi yanzu mun fara jawaba, muna karewa zata oya kirkiro wani abun da zai hana ni zaman gida da safe, yanzu kina gani yadda karatun addini na bar shi saboda tallar nan, gaba daya rayuwar gidan nan ta isheni Noor ji nake kamar na gudu” Tausayinta da kuma na kaina ya kamani, idan har ita zata fadi haka to ni nace me, kashi uku na ukuncin rayuwarta data gidan Hana bata shiga daya ba, domin ita har yanzu bata kula kowa ba balle a rabata da wanda take so kamar yadda Baba yayi min. Bata yi aure ba balle ta hadu da kishiya irin Aisha wani abun na rayuwar har yanzu bata san ya zafinsa yake ba. “Ya muka iya? Tun Mama tana gidan nan muna cikin takurawar Baba balle kuma yanzu da bata nan, ni ina ganin idan kin kare karatunki kawai ki koma gurin Mama ki zauna, za ki jidadi kuma mijinta da take aure a yanzu yana son mutane ba kamar Baba ba” Ta kalleni hawaye na mata zuba. “Amman kina ganin Baba zai yarda? Ba zai yarda?” “Me zai hana idan ma be yarda ba ki yi ma Anty Larai magana zata saka baki, kin san kuma Baba yana jin maganarta” Ta fara share hawayenta. “Allah yasa” Ta mike tsaye ta cire hijabinta ni kuma na tashi na fita waje gurin aikin gyaran wake da nake kullum da dare. Tiya uku na zuba a tray na shimfida matacciyar tabarmarmu na zauna kamin na saka hannuna a waken wani yaron unguwarmu ya shigo wai ana sallama da Noor. “Je ka ce waye?” Umma ta ba shi umarni yaron ya juya ya fita. “Gashi Malam baya nan balle na ce a nemi izini gurinsa, yaran yanzu kuma ba natsuwa ce da su ba, musamman zaurawa” Tana maganar tana kallo, wata kila so take na yi mata ba daidai ba ta fada min ba dadi ko kuma ta hada ni da Baba, idan ba haka me miye na cin fuskar, ita ba zarwacin ta yi ba kamin ta auri Baba, su zaurawan dabam suke da sauran mata.? “Sallamu Alaikum, ya ce wai wanda ya saba zuwa” Ina jin amsar yaron zuciyata ta raya min Kareem ne, wata kila ita ma ta fahimci hakan shiyasa ta ce na tashi na tafi bayan ta gindaya min sharadin kar na jima saboda gyaran wankenta. To me ya zo yi kuma wannan karon? Biyo yayi ya duba ni ko kuma dai wata matsalar ce ta taso daga bangaren iyayen Hafiz da na tattara lamarinsu a gefe na aje. Bakuwa mota ce da ban taba gani ba mai bakin gilashi baka ganin wanda ke ciki duk da kasancewar akwai hasken lantarki a lokacin. Tsaye na yi ina jiran Kareem ya bude motar ya fito, sai akasinsa ya fito, mutumen nan da na taba haduwa da shi a mall kuma shi ne dai wanda ya dauko ni daga gidan Mama ya kawo ni gida. “Hajiya Nooriya kin yi mamakin ganina ko?” Toh ko dai yayi arba da mamakin a fuskata ne shiyasa ya ke tambaya. “Eh gaskiya na yi mamaki, ban yi tsammanin kai zan gani ba” Na fada ina rumgume hannayena. “Akwai wanda kike tsamanin zuwansa kenan, kar fa bazawarin ya tarar da mu ya dauka soyayya muke yi, yayi fushi” Na yi murmushi feeling Speechless daman mi zan ce bayan shi ya zo shi ya kamata yayi magana ai. “Well kawai hanya ce ta biyo da ni, sai na tuna i have a friend here na ce bari na biyo just to say, hope ban yi laifi ba?” “Are we friends daman?” Tambaya nake a bakin gaskiya ta domin ban san wata rana da muka zama kawaye ko abokai ni da shi ba. Da alama kuma tambayar tawa ta ba shi dariya har sai da ya bayyana hakoransa. “Uhm ba ma bukatar request ai, idan ba mu zama abokai ba mun zama yan'uwa saboda Mama ko?” “Maybe” Na fada ina dan wara ido. “Not maybe, pretty gal ban da jan aji, ko da yake kamata yayi na gabatar da kai ne, taya za ayi abota ba a san juna ba” Ya miko min hannunsa. “I'm Abdull by name, engineer ne ina zama a Lagos for now, ko da yake ni dan garin Kano ne haifaffen garin kano aiki ne ya kai ni Lagos kuma idan na tafi na kan yi wata biyar hudu uku har fi a can, am ina da mata da yara uku a yanzu” Kallon hannuna nake wata kila dai ya manta da cewar ni da shi hausawa ne kuma musulmai, idan ba haka ba miye na miko min hannu mu gaisa. Kareem ne kadai ya taba yi min haka bayan shi kuma bana jin akwai wanda zai sake miko min hannu na karba. “Nice to meet you Abdull” Na amsa ba tare da na ba shi hannun nawa ba. “Ba zaki gaisa da ni ba?” “Ba ayi min wannan hallacin ba tukuna” Yayi murmushi tare da maida hannun nasa. “Daman dai na zo na gaishe ki ne, hallaci kuma za'ayi miki nan gaba kadan, abu na karshe bana bukatar ki fada min komai a kanki na tambayi Mama wacece ke ta fada min yadda kike da kafiya da rashin magana, ban yi mamaki ba kuma saboda kina da kyau kin san mata masu kyau suna da rashin magana sosai” Na yi murmushi kadan, sai ya bude motarsa ya dauko leda ya mika min. “Ga tsaraba ki shiga da shi gida” “Aa na gode” “Mu ai ba ma yin kyauta a mayar mana, ko dai ki karba ko na aje miki na tafi” Jin haka ya saka na kai hannu na karba, na yi masa godiya na juya sai na ji ya kira sunana. “Noo oor” Na juyo. “Yaushe zaki je ganin Mama?” Sai da na yi nazari kamin na amsa masa. “Friday” “Okay see yeh✌” Ya sara min da yatsu biyu sannan na yi masa murmushi as responsed sannan na juya na shiga gida. Gudun laifi ya saka na aje ma Umma ledar da ya ba ni ba tare da na bude ba. “Shi ne abokin mijinki?” Bana son dogon zance dan haka na amsa mata da eh ina kallon turaran da take fitarwa da man shafi masu kyau. “Ko dai son ki yake?” “Aa daman tun kamin na san Hafiz din na san Kareem” “Toh bari a aje idan mahaifinki ya dawo sai a nuna masa” Akan haka muka rabu, ban sake ganin ledar kayan ba sai washe gari bayan Baba ya fita ta miko min ledar wai ita ta dauki turare daya Baba ya dauki biyu sun dauki man shafi biyu suka bar min daya. Ban ce komai ba na karba na shiga da shi dakinmu na aje ma Hana man shafin da turare daya na dauki dayan da ya rage. Sai da na dan kimtsa sannan na fito sanye da hijabina, kamshi kam kai kace gidanmu ake kamfanin turare na fesa wanda Abdull ya kawo min sosai saboda yana da dadi da saka sanyi zuciya. Tsakar gidan na fito na dauki bokiti uku da nake deban ruwa da su na fice daga gidan domin yin abun da ya zame min wajibi. Fanfon da muke dibar ruwa irin wannan ne mai tuka tuka sai ka yi ta bugawa kamin ya cika, haka na yi ta wahala ni kadai ina jan karfen yana jana har na cika. Da kuduri biyu na fito daga gida, kudirin debo ruwa da kuma ziyarar gurin da na san Zafeer yana aiki, domin ban isa na tunkari gidansu da bukatar ganinsa ba. Idanuwa kaikaiyin ganinsa suke, zuciyata tana ta muradin mai sakata farinciki, na san ba zai kalleni ba idan ma yana gurin ba lallai ya sake kaunata ba, amman ni zan ji sanyi idan na yi magana da shi ko da kuwa zagina yake. Tafiya ce mai dan nisa haka na kama hanya ina tafe ina ta sake saken yadda zan fara masa magana idan ma na sameshi a gurin. Na tarar da Ogansa a gurin muka gaisa yayi min gaisuwar Hafiz, kana kuma ya sokeni da wata kalma mai daci. “Noor kin guje mana ko? Duk soyayyar nan da muka nuna miki sai da kika butulci mana, gaskiya ban jidadi ba kuma na yi mamaki sosai, Wallahi ba karamin damuwa kika jefa Zafeer ba” Na aje numfashi a muhallinsa ina jin yadda bakinciki ya fara yawo a zuciyata. “Gurinsa na zo ko yana nan?” “Kai ai Zafeer ya bar nan, tun a lokacin da kika yi aure yace ba zai iya zama garin nan ba, kwanan baya dai ya zo, amman ya koma gaba daya ya kwashe komai nasa a nan, shi ma kuma Allah yayi masa sakamako na alheri yar wani babban mutum zai aura karshen watan nan In Allah ya yarda” Indai abun da nake ji a yanxu, irinsa Zafeer ya ji a lokacin da na yi aure na bar shi, tabbas ya shiga tashin hankali, kasa rike kaina na yi har sai da na fasa kuka sai kuma na yi hanzarin rufe bakina, hawaye suke Noor yau ma muna sha'awar yin ado a fuskarki. “Haka daman abun Allah yake, lokacin da wani ya ƙi ka da wuni, wani zai ya so ka da kwana, yadda kika guje masa kika auri mai kudi, shi ma Allah ya ba shi yar masu hannu da shune, yar babban mutu kuma babbar ma'aikaciyar banki, an yi lokacin da take kawo gyara a nan, bata duba talaucinsa ko kaskancinsa ba ta aure shi” “Baka san komai akaina ba oga Lawal dan Allah karka yanke min hukunci” Na fada ina hawaye, na cira kafa daker ina tafiya kamar wata tsohuwa. Har na iso gurin bohol din hawaye nake, zuciyata zafi take wasu abubuwa nake ji a cikin kaina suna min yawo. Ban tarar da ruwan da bokitan da na kawo ba, daga ruwan har bokitin wanda ya fi ni so yayi awon gaba da su, wani mai dan hali mai son biya lahira. Bana cikin yanayin da zan iya shiga gidajen da suke kusa da Bohol din balle na tambaya ko sun ga wanda ya dauka ko kuma sun dauko. Sai kawai na nufo gida ina tafe ina hawaye har na iso. “Ina ruwan?” Umma ta tambaya tana daura dankwalinta. “An dauke kayan” “Garin ya? Taya kika yi sake har aka dauke kayan? Sai kuma ki dawo min gida kina kuka, Wallahi ko kije ki nemo min kayana ko kuma na fadawa mahaifinki idan ya dawo wannan ai keta ce da sheri, kamar ya an dauke kayan kina aikin me aka dauke? Kukanki ba zai kwace ki ba” A zatonta ina kuka ne saboda an dauke kayan, bata kukan bakinciki nake ba wanda ya fi na sata ciwo. Dakinmu na shiga na dauko dubu goma da Alhaji ya ba ni a lokacin da na tafi gurin Mama na cire 1k na mika mata saura. “Ga kudi ki siya wasu” Sai da ta gama kallon kudin baki sake sannan ta karba bata ce min komai ba ta shige dakin Mama wanda ya zama dakinta a yanzu. Ni kuma na sa kai na fice daga gidan, bana iya daga kai saboda bana son kowa ya ga idanuwa. Ina isa titi na tari Napep na hau na fada masa inda zai kai ni, domin ba ni da gurin zuwa yanzu da ya wuce can. Ko da yake idan ma na tafi ban san me zan fada mata ba, ba lallai ne ta ji yadda nake ji ba, ni kadai nake iya fahimtar kaina. Bayan na sauka na ba shi dubu daya ya ba ni canji na nufi gate din dake bude na shiga, a lokacin ne wata motar ta iso kusa da gate din zata fice. Daidai saitin da nake tafiya mai motar ya tsayar ya sauke gilashin kasa. “Noor kika ce min sai friday?” Na kalleshi Abdull ne a cikin motar yana sanye da facing cap. Ban ce masa komai ba na nufi bangaren da Mama take. Ina tana kofar na jita a rufe na fara kwankwasawa. “Bata nan fa ta fita” Na juyo na kalleshi sai ya saka hannayensa aljihu ya cire hular kansa yana kallona. “Sai dai ki shiga bangaren Hajiya” “Aa ba sai na shiga ba, zan koma gida kawai” Na fada ina mamakin Hajiyar mahaifiyarsa ce ta Safeena tsakanin shi da Safeena gidansu waye ne? Ko kuma shi da ita Yaya da kanwa ne oho. “Okay Let me drop you off Girly” Ban masa musu ba ya wuce gaba na bi bayansa har muka isa gurin motar na bude na shiga, shi ma ya shiga yaja motar muka fice daga gidan. Tafiyar kamar ta kurame haka ta zama bana cewa komai sai tunanin Zafeer nake da irin rayuwar da yake ta fada min zamu yi. Ban ankaro ba na ji hannunsa a cinyata yana shafa ni. “Kin yi shiru baki cewa komai Noor” Na yi saurin buge masa hannu. “Miye haka?” Sai yayi murmushi. “I'm sorry daman ina gwadaki ne kawai” “Gwada ni kamar yaya to see what?” Asking with little bit of confuse. “To see if you're wife material...” “Sauke ni a nan” Ya dube ni da sauri. “A nan?” “Eh a nan zan sauka” “Ba gidanku ba ne ai” “Na ce ka sauke ni a nan zan sauka” Wata kila bakin hadarin da na hada a fuskata ya firgita, domin na daure fuskar sosai babu alamar wasa. A dole ya faka gefen titi ni kuma na bude na fita na bar masa motar a bude. “Kin ga ni fa gwadaki ne kawai nake ba wani abu ba...” Ban kula shi ba na cigaba da tafiya a kafa, ya so gwada bina a motar yana min magana da ya lura ba zan saurare shi ba kuma ba ni da niyar shiga motar sai ya motarsa yayi gaba. Tsaye nake ina jin kamar na fasa ihu na fadi na yi birgima a guri. Kusa da ni wata motar ta tsaya wannan karon ina ganin wanda ya fito motar sai na ji sabon kuka ya taso ni gaba, wani irin shagwaba da narkewa na fara yi kamar wata yar baby. “Me ya faru? Me kike yi a nan?” Ya tambaya tun kamin ya karasa fitowa daga motar, matsawa na yi kusa da inda ya faka motar ina kuka har da shessheka. “Kareem...” Ya kalleni hankali a tashe. “Me ya kawo ki nan Noor waya taba ki?” “Kowa ma taba ni yake...” Ya kama hannuna ya ratsa da ni ta cikin wasu itatuwa da ke gurin muka shiga ta can ciki gurin da ke da sanyi da iska mai dadi, sakin hannuna yayi. “Fada min me ya faru?” Na daga kai na kalleshi kawai hawaye na sauko min. Cikin kwantar da murya da lallabawa ya ce “Can i be your best friend?” Na daga mishi kai. “Okay daga yanzu na zama best friend dinki, yanzu fada min damuwarki” I don't know why, how and when, i just find myself laying on his chest idanuwa na zubar da kwalla. “Zafeer zai yi aure Kareem...” Mun dauki 12-seconds a haka, ni da shi babu mai motsi kamar mun mutu, but zuciyata na bugawa da wani irin karfi kamar yadda nake jin tasa ma tana bugawa, sannan ya matsa baya hakan ya saka dole na dago daga jikinsa, he look straight into my eye ball ya ce. “Noor ki daina saka turare mai yawa haka idan zaki fita, Haramun ne” “Kai turaren ne damuwarka?” “Saboda yana dagawa mutane irina hankali turare is my weakness, my weak point” Ban gama fahimtar abun da yake fada ba, na ganshi slowly yayi kasa ya zauna akan turbaya ya nade kafafuwansa ya dago yana kallona. “Zauna karanta min damuwarki, maybe zamu iya solving matsalar...” Na zauna a gurin ina fuskantarsa da irin zaman da yayi..... Na maida idanuwana kasa ina jin wani sabon kuka na tunkaro ni, ban sani ba raini ne ko kuma yarda ce ta saka nafi sakewa a kusa da Kareem ne kamar yadda nake sakewa da Zafeer sosai ko ma fiye da haka. Ina jin son fada masa damuwata ko da kuwa ba zai saurare ni ba, na kan ji kuka sosai idan ina kusa da shi musamman idan damuwa ta yi min yawa, tsabanin sauran mutane. “Noor...” Wata kila yanayin yadda ya kira sunana ne ya kara masa kwarjini a idona lokacin da na kalleshi. “Ka rame, Kareem” “Ke ma kin rame, ni da ke duk muna cikin damuwa mabanbanta, fada min taki” “Ya aka yi kasan ina nan?” Ya kalli gurin ya sake kallon ya sauke ajiyar zuciya. “Na kan gwada zuwa nan yanzu, saboda ina jindadin gurin, bana son zaman office a yanzu saboda zaman yana tuna min da Hafiz, na kan zauna a nan na yi tunanin rayuwa, mafita, da kuma nazarin rayuwa” Na sauke kaina kasa ina wasa da yatsun hannuna. “Ke waya kawo ki nan?” “Wan...” Sai kuma na kalleshi da saurin ina jin kamar na yi barin zance. “Wani...? Wani? Har kin fara samari?” “Ba saurayina ba ne...” Na fada masa yadda alakar take. “To me ya sa ya sauke ki a nan?” “Taba ni yayi sai na ce ya sauke ni a nan” “Taba ki?” Na daga mishi kai. “Ki yi taka tsantsan da zaman yanzu, okay” Na daga mishi kai sannan na fara karanta masa damuwata. Na yi tsammanin zai taya ni bakinciki ne amman sai na ga mamaki karara a fuskarki. “Amman Noor ke kika fara gudunsa, yanzu kuma ya samu mai son shi, so kishi kike ko kuma kina ganin kamar ya ci amanarki ba” “Ban sani ba ina dai jin babu dadi, kuma hakan yana nuna kamar ya daina so na, zai yi rayuwa da wata ba ni ba” “Sai hakuri, wata soyayyar bata nufin daurewa har abada, wata alakar kuma mai daurewa ce, ke dai ki yi addu'a duk abun da yake na kwarai mai alheri a gareki Allah ya tabbatar miki” “Tohm” Idona ya cika da hawaye, sai ya leko fuskata. “Bayan wannan akwai wata damuwar?” Na daga mishi kai, na fara fada masa yadda zaman gidamu ya dawo yanzu ni da Hana duk ba ma jindadinsa. “So yanzu so kike na yi ma mahaifinku magana ko kuma Yaya?” “Aa kawai dai na fada maka ne” Yayi min murmushi yana kallona. “Kin san na zama best friend dinki a yanzu zski fada min damuwar da bukatunki a duk lokacin da hakan ya taso, hakan ya miki?” Na rausayar da kai Ina zane a kasa. “Toh kai fada min damuwar kai ma a kana cikin matsaloli” A take na ga murmushin dake fuskarsa ya gushe damuwata ta bayyana karara. “I don't want to talk about this da ke? Ba zaki fahimta ba Noor” “Zan fahimta mana, gashi kai ma ka fahimce ni kuma ina ganewa idan kana cikin damuwa” Wannan karon dariya yayi. “Tun mutuwar abokina ban yi hirar damuwata da kowa ba, kuma ban nemi shawarar kowa ba hakan kuma yana kara jefani a matsala” “Toh fada min damuwarka a yanzu” Na fada ina kallonsa da idanuwa kamar na yan fari. Sai da ya sauke ajiyar zuciya sannan ya ce. “Wasu abubuwa na aikata da nake tsananin nadamarsu a yanzu, sai dai kuma na fi nadamar babban wanda shi ne silar dukan ukun” “Fara fada min babban” “Amincewa na auri macen da bana so bata so na, shi ne babban domin shi ya janyo kananan matsalolin” Na kalleshi da duba mai kyau. “Kana nufin ko da ka auri Yusura baka sonta bata sonka?” Da mamaki yake kallona. “Why Yusura kika sani ko na taba aure kamin ita?” “Ban sani ba, amman ai ita ce na lura ba ku zaman lafiya, bata son ka, ko shiyasa kake cewa bata kishinka a baya?” “Ashe kina da hankali Noor har kanki ya kawo wuta haka?” Na yi murmushi. “To miyasa ka aminta” “Saboda Momy na ne, akwai wata budurwa da na yi a lokacin baya, mun so juna amman Momy ta ce ba zan aureta ba, saboda bata yarda da tarbiyarta ba, ita kuma a lokacin akwai wanda take so, amman a haka Momy ta gabatar mana da matsayarta, ni kuma ina tunanin babu hanyar sakawa iyaye sai biyayya a garesu, na amsa mata da na amince, ita kuma ta amsa da hakan saboda tana tsoron kar ace ta yi butulci bayan irin rikon da Momy ta yi mata tun tana karama har girma” Ya dan yi shiru yana kallon wani gefe. “A haka muke ta rayuwa a haka muka haihuwa haka muke har yau, kuma a haka zamu rayu a nan gaba, amman a yanzu abun yana ci na sosai” “Ka fada min daya sauran uku..” Ya dube ni with seriousness ya ce. “Na aikata wani abun da yake hana ni sukuni a yanzu, zunubi ne mai girma” Jin haka ya saka ni mamaki. “Shirka kai yi?” Ya girgiza kai alamar AA. “Wani ka kashe?” Ya girgiza min kai. “Ko dan kana zubar da ciki?” Nan ma kan ya sake girgizawa. “Zina ka yi?” Ya kalleni. “Me yasa Zina ta zo miki a kai?” “Saboda tana cikin manyan zunubai” “Haka ne, gashi dafinta yana ta bibiyata” “Ita ma Allah yana yafe ta, zunubi ne mai girma, amman malamai sun ce Allah yana yafewa idan an tuba da gaske” “Na tuba da gaskiya, amman ina jin kamar akwai wani illa da na yi ma kaina akanta” “Illar me?” Yayi shiru tare da sauke kansa kasa. “We shouldn't talk about this...” “Safeena ce matar?” Ya kalleni da sauri. “Me yasa ita ta zo miki a rai?” “Saboda na lura da tana kishina lokacin da take zaton ko akwai soyayyar a tsakaninmu, kuma ta zo gurinka ka tuna? Amman tana da aure ko?” Yayi shiru kamar ba zai ce komai ba, sai kuma ya daga min kai. “Tana da aure kake tare da ita?” “A da ba, amman yanzu na riga na daina, macen da mahaifiyata bata so, kuma abokina ya tsana yake ta kokarin ganin na guje mata amman hakan be samu ba sai bayan rayuwarsu it pain me, and tana da iyali ina da iyali be kamata muna haka ba, abaya duk ban gane haka ba sai bayan na rasa mutane masu muhimmanci” “Da gaske ka daina?” “Na daina saboda ba abu ne mai kyau ba, Na rantse da qur'ane da wanda ya aiko da shi da gaskiya na daina kuma ba zan sake ba, daman tun farko bana so kawai dai na biye sherin zuciya ne kuma bana son ta ga kamar da gaske na yaudareta ne na ki aurenta shiyasa na biye mata, amman yanzu Wallahi bata burge ni gaba daya” “Indai da gaske ka yi nadama, Allah mai yafiya ne zai yafe maka, kuma ni ma zan yi ta rokon Allah ya yafe maka” “Na gode” Ya fada da murmushi a fuskarsa irin na wanda ke kokarin kore damuwa. “Sai kuma nadamar me kake yi?” “Na rashin amincewa da kudurin abokina kuma abun da zuciyata take ta muradi a yanzu” “Akwai abun da Hafiz ya bukata baka masa ba?” “Yeah, and yanzu ina bakincikin haka” “Minene?” “Ba zan iya fada miki ba” Ya amsa min da sauri. “Amman I'm your best friend” “Na sani, amman ba zan iya maganar nan da ke ba” “To fada min muradin zuciyarka” Yayi murmushi ya mike tsaye. “Noor kina ta min tambaya kamar wani karamin yaro” Ya kalleni da sani irin duba, yayinda yake tsaye ni kuma nake zaune a gurin. “Kin samu kaina sosai” “Zauna Kareem” Na bukata sai ya duba agogon hannunsa. “Akwai inda ya kamata na tafi” “Gurin budurwarka? Ita ce muradin zuciyar?” Ya dawo ya zauna with shock. “Ganinki ake kamar baki da wayo, amman kina da shi Noor yanzu na gani” Na yi murmushi ina boye fuskata, shi ma murmushin yayi yana kallona. “Ni dai fada min toh wata kake so?” “Me yasa kike son ki sani?” Na bude idon kuma na yi shiru. “Akwai, akwai wacce nake jin tsananin sonta a yanzu, amman ina ajin kamar ita din mai tsabta ce ni kazami ne, saboda na aikata sabo a baya, da ban dauka ina sonta ba sai yanxu na san ina sonta, ina jin farinciki da farincikinta, ina damuwa da damuwarta, ina son kusanci da ita, amman ina tsoron yadda za'a kalli lamarin, domin na yi ma kaina illa tun farko na gujewa shawarar makusanci na, but i feel guilty, I'm hopeless” “Kana sonta sosai?” Ya rutse idonsa da wani farin ruwa ya fara taruwa a ciki. “Kamar yadda kake son Safeena?” “Fiye, kaunarta rayuwata ce, ina sonta irin son da nake jin ita kadai ce bukatar da ta rage min a duniya yanzu, ina sonta irin son da nake jin da za'a raba ni da komai a yanzu a bar ni da ita ba zan ji komai ba, she's my last hope ina jin kamar aurenta ne zai yaye min damuwata kuma zai saka na fahimci waye ni” Tausayinsa ya kama ni, as well as nake jin wani abu marar dadi yana zagaye kirjina. “Kareem” Na kai hannu na gafen fuskarsa zan yi masa magana irin wadda ban taba zama da wani na bashi irinta ba. “Lokacin da nake tafiya makaranta, Malamin ya taba fada mana cewa Allah yafe yafe ko wane laifi amman ban da shirka, kai kuma ba shirka ka aikata ba, Allah zai yafe maka, kai mutumen kirki ne mai taimako mai juriya, saboda Yusura bata son ka kar ya karya maka guiwa ka ji cewar kamar wata ba zata so ka ba, kana da kyau kana da kudi kana da hankali, kuma dan ka aikata sabo kar ya hana ka ganin kamar ba zaka dace da rahamar Allah ba, ance babu mai yanke kauna daga rahamar Allah sai batattu, Kareem indai ka tuba da gaske zaka dace there's no need to feel guilty about it, kawai ka aureta” Ina masa maganar yana juya fuskarsa a hankali a tafin hannuna da yake kuncinsa na dama, sai da ya shinshina hannuna sannan ya bude idonsa ya mike tsaye. “Kin karfafa min guiwa, thank you” “Yanzu ka yi min alkawari ba zaka bari yarinya ka guje maka ba? Zaka aureta?” Ya tsaya kallona har na mike tsaye na sake fada. “Ka yi min alkawarin Kareem, ina sonka da farinciki, bana son na ji kana damuwa kuma indai har ka samu wanda kake so a yanzu be kamata ka bari ta maka nisa ba ko be kamata ka yi ta zama a haka da bakinciki ba, ina son ka yi aure ko dan matarka muguwa, kuma zaka samu farinciki idan ka auri wanda kake so” Ya miko min karamin yatsansa yana kallon kwayar idona. “I pinky promise you zan aureta” Na ji dadi domin har ga Allah ina son Kareem da farinciki. Ina jin damuwa da matsalar ko da kuwa be fada min ba. Na lakam yatsan ina dariya sannan na yi gaba ina tsalle da dariya har da daga hannuna sama ina jin wani irin farinciki. Kallona kawai yake yana murmushi har muka fito daga gurin. “Noor ga wannan ki hau Napep, I'm sorry ba zan iya kai ki gida ba yanzu, dole sai kin yi taka tsantsan da rayuwa, saboda mutane za su saka miki ido kuma kin san waye mahaifinki” Ya miko min 5k. Na karba na cire 1k na mayar masa da sauran. “Yayi yawa wannan ya isa” Ya karba ya rike yana kallona. Har na fara tafiya sai kuma na juyo ina murmushi jindadi da farinciki a fuska fal. “Thank you so much Kareem you make me feel so special, wani be taba zama da ni ya fada min damuwarsa ba, ban taba bawa wani shawara ya dauka ba, ba a taba tsayawa an saurare ni kamar yadda kaka yi ba, ba a taba daukar kalamaina da muhimmanci ba sai kai, ban taba bawa wani shawara ya yarda ya dauka ba sai kai, ka saka na ji kaina a dabam, am felling so proud so good so happy” Ina maganar ina shisshekar farinciki. Murmushi yayi min yana yawo da idonsaa fuskarsa. “Your Welcome, My Best sweet friend, daman you're special mutane ne ba su gane ba” Na yi dariya mai sauti ina tafiya baya baya kamar ba ni ba, gaba daya na manta da wata damuwar da bakinciki a lokacin har sai da na isa unguwarmu, sannan komai ya dawo min. Na yi mamakin ganin Abdull zaune a kofar gidanmu, ganina ya saka shi mikewa tsaye yana kallona har na karasa. Hade rai na yi na bata fuska sosai domin ban jidadin abun da yayi min a dazun ba. Ina kokarin wuce na shiga gida ya sha gabana. “Haba kyakkyawa wannan fushin na minene? Tun da na sauke ki a can na zo nan gidanku jiranki aka ce baki dawo ba” “Me zan maka?” Na tambaya fuska babu annuri. “Hakuri zan baki na abun da nake miki, kuma na fada miki gaskiyar abun da yake raina” Na gyara tsayuwata. “Uhmm” “Zaki taimaka mu tafi gurin motata mu tsaya? Please” Na kalli gurin da ya faka motar nesa da gidanmu. Na fara tafiya sai ya jera da ni yana tafiya har muka isa gurin motar ya fi ni tsaye sosai domin ya dara Kareem tsayi. “Da farko dai zan fara da baki hakurin abub da ya faru, ba wai na yi da wata manufa ba, kawai gwadaki zan yi” “Miye hujjarka na gwada ni toh?” Ya sauke ajiyar zuciya ya cire facing cap din dake kansa. “Noor gaskiya tun a lokacin da na fara ganinki a shopping mall, kin burge ni, natsuwarki kyaunki, farinki da kuma yadda kike da rashin jiki komai na ki yayi min, sai dai an samu akasi a lokacin kina tare da mijinki, sai dai damuwar da na sake yi dake bayan mutuwar mijinki a gidanmu, ya sake motso min da burina akanki, kin ga sanadi sai Allah yasa Alhaji ya auro mahaifiyarku gashi yanzu har ina magana dake, wata kila da ba zan ma san mijinki ya mutu ba” Na kalleshi kawai domin ban gama fahimtarsa ba. “Noor ba zan boye miki ba, ina son ki kuma ina son na aureki idan har Allah ya kaddara, kuma ni ba da wasa na zo ba, bana ma son a bata lokaci, har ga Allah ni dai kin yi min, ina son mace irinki kuma daman ina da burin kara aure saboda inda nake aiki ni kadai nake zaune a can matata kuma tana nan tare da yara, na kan dauki wata hudu uku ban zo ba, mahaifiyata ma tana son na kara aure amman dai ban ga wanda ta yi Sai a yanzu da na hadu da ke, babu wanda ta sace min zuciya ba sai ke” Na nuna kaina. “So na?” “Eh, kuma idan kika bani dama zan tabbatar miki da gaske nake iyaye za su shiga maganar da yardar Allah, already ma na yi maganar ki da Mama, amman dai ban fada mata kudirina akanki ba tukuna” “Ni ba aure zan yi ba yanxu, yaushe ma mijina ya rasu da zan sake yin aure?” “Ke yarinya ce, karki cutar da kanki kuma ki cutar da masu kaunarki ki ce ba zaki yi aure ba sai nan gaba, wata kila nan gaba babu wanda zai kalle ki ya yi sha'awar aurenki komai yana da limit Noor, zai fi kyau dai ki yi shawara” “Toh zan yi shawara” Ita ce kawai amsar da na bashi na juyo ina tafiya, har na shiga gida ban juya na kalli inda yake ba. Ina shiga gidan na samu Baba a gida sai ya rufe ni da fadan batar da bokitan da na yi, Allah ya shiga lamarin dai be doke ni ba. “Kuma gidan uban waye kika fito yanzu?” “Gurin neman kayan na fito, kuma ban gansu ba” Na fake da hakan domin ba ni da wata hanyar wanke kaina. “To su kuma kudin da kika bata a ina kika samu?” “Alhaji ne ya ba ni ranar da muka je gidan ni da Yaya gurin bankwana” “Wane Alhaji” “Mijin Mama” Baba ya bude baki “Har dubu goma?” “Eh yace na hau Napep” “Yanka kai yake ne ko kuma minene? Allah yasa ba jininki zai sha ba, dubu goma a take?” “Mai kudi ne sosai Baba, gidan ma kowa da bangarensa” Mtscheeeeeeee yaja dogon tsaki ya nufi gurin da buta take ya dauka ya shiga bandaki. Ni kuma na nufi dakinmu na shiga na zauna, ina tunawa da Mama ba san zaman gidan Baba be da dadi a gareta da mu, amman duk da haka ina jin kewarta kuma ina jin babu dadi idan na tuna a gidan wani take rayuwa a yanzu ba gidan mahaifinmu ba. Kamar an kare ni haka hankali ya tattara ya koma gurin zancen da na ji na auren da Zafeer zai yi, ko yana sonta kamar ni ko kuma dai shi ma zai aureta ne kamar yadda na auri Hafiz ba dan ina son shi ba. Ya yake a yanzu? Ya sauya rayuwa ya cireni a zuciyarsa ko kuma ina ciki? Tunaninsa ne ya karkato da ni na tuna da wunin yau dan karamin lokacin da Kareem ya ba ni kuma ya saurare ni ya yarda da zance. “Allah ka yafe masa ka yaye masa damuwarsa kuma ka bashi abun da yake nema, macen da yake so Allah kasa ta so shi, yana da kirki sosai” Har cikin zuciyata nake da masa addu'ar da kuma fatan dacewa da rayuwar da yake ta mafarki. Tun daga lokacin ban sake saka Kareem idona ba, shi ma be sake ganina ba, daman baya zuwa nemana sai da dalili yanzu kuma babu wannan dalilin, amman addu'ata tana tare da shi a kullum. Zuciyata kuma ta ki bari na huta da tunanin Zafeer da rayuwarsa, sai na yi ta hasashen irin zaman auren da zai yi da Amaryarsa she turn to be my enemy a yanzu. Duk bayan kwana daya biyu sai Abdull ya zo gidanmu ya saka sallamo ni, a duk lokacin da yayi min sallama sai na fito mu gaisa ya ba ni tsaba ya tafi, tun ina kin karba har na saba idan ya ba ni dole na karba na shiga da shi gida. Kuma sai na lura Umma har farinciki take da zuwansa saboda baya zuwa hannu sake, yana yawan fada min labari akan rayuwarsa tsarinsa irin zamantakewar da yake da iyalinsa da kuma wanda zai yi idan ya aure. Ni dai saurarensa kawai nake idan ya tambaye ni sai na ce masa har yanzu ina tunani ne ban gama yanke shawara ba. Ni da shi kuma muka taki sa'a duk zuwan da yake ba taba haduwa da Baba ba, ni kuma be taba zuwa ko aikowa kirana na Baba yana nan ballle ya tambaye ni alakata da shi. It's Friday again ina zaune ina wanke wanke Baba ya fito da shirin na masallaci, farar shadda ce jikinsa da babbar riga sai hula da yake gyara tsayuwarta a kansa, kusa da ni ya karaso ya tsaya ina ganin haka na san akwai abun da zai fada, ko dai na yi wani abun ba daidai ba ya rufe da fada da zagi ko kuma umarni ne ga yin wani abun ko hani. “Nooriya” “Na'am Baba” Na amsa ina jefa kwano a ruwan kumfa, sannan na juyo na kalleshi. “Ko kina da wanda kike so?” Na yi shiru na sauke kai kasa ina jin abun wani kala, domin be taba min irin wannan tambayar ba. Na dauki lokaci a haka ina ta sake saken me zan fada, na yi karya na amsa ina da shi alhalin babu shi a yanzu? Ko kuma na fadi gaskiya na ce babu din? “Toh na dai baki lokaci ki yi shawara nan da kwana biyu, idan akwai wanda kike so, to sai ki gabatar kar na gabatar miki ace na sake yin karan tsaye, idan kuma babu to ina son na hadaki da ďan yar'uwata Ridwan mahaifiyarsa ta yi min magana, kuma shi ma yayi min magana da kansa, amman Anty Larai tace sai idan babu kowa, zan tafi masallaci sai na dawo” Na hade yawu da karfi na daga kai ina kallonsa har ya fice na kasa ce masa Allah ya tsare ko a dawo lafiya, Ridwan kuma? Wane irin Ridwan mutum mai mata biyu da yara tara ga kuma suruka duk a gida daya, gidan da ba wadatacce ba? A ciki zai aje ni ko kuma dabam? Ina ma zan iya zama da Ridwan. Gaba daya sai kasala ta kama ni tunanin ma na rasa wane zan yi. Haka dai na yi aikin na gama, ina ta tunanin mafita, ba ni da wani da zuciyata take so a yanzu duk wanda zan tsayar sai dai na tsayar kawai amman ba dan ina kaunarsa ba. Ban yi shawara da kowa ba, ban nemi jin bakin wani ba na yanke shawarar da ban sani ba, ashe na yi ma kaina da yar'uwata babbar illa ne. A daren ranar da Abdull ya zo yayi min hira sosai, yawancin zuwan da yake shi yake min hira ina saurarensa gurin dariya na yi ko murmushi. Daf zai tafi ya kalle ni ya ce. “Har yanzu dai hakona be cin na ruwa ba? Har yanzu sarauniyar bata samu amsa bukatata ba? Gashi ina ta shirye shiryen komawa dan hutun da suke ba ni na wata biyu ya kare, gashi babu waya a hannu kuma ina tsoron siya miki ki ce ba zaki karba ba” Na dube shi cikin duba na rashin aminta da abun da baki yake furtawa a gareshi. “Hakanka ya cin ma ruwa Abdull ka yi yaki kuma ka yi nasara, zan sanar da mahaifina sai ka gana da shi idan ka shirya” “Yes Yes yes...” Ya fada yana daga hannunsa sama cikin farinciki da murna, wanda ya saka samu ni, na sani ni kam dai na rasa so tun a lokacin da na rasa Zafeer, bana jin kaunar kowa ko sha'awar zama da kowa a yanzu. Shi ma dai saboda ba ni da wata mafitar ne da ba zan aminta da bukatarsa, kamar zai dauke ni ya goya a baya haka ya rika murna yana farinciki da jindadi. Washe garin ranar na sanar da mahaifina cewar akwai wanda nake kauna kuma nake da burin aure, sai kuma na samu nasara Umma ta saka min baki tana taya ni siyasar gurin Baba ta yardar yaba Abdull duk da kasancewar bata wani san shi ba, ita dai ta dogara ga alheri da yake min ne kawai. Na lura da wani abu sabo a gurin Baba da ban saba gani ba, gabatar masa da Abdull be masa dadi ba. Wata kila saboda be san mahaifin Abdull mai kudi ne ba kuma shi ma kansa mai rufin asibiti ne, sai ya nuna min ya fi kaunar ďan yar'uwarsa wacce take Gwaggo a gurina wato Ridwan. “Shikenan tun da kin nuna kin fi son bari da dan'uwanki, duk abun da zai faru babu ruwana, ba zan miki dole ba amman ni dai ba zan so bare sama da jinina ba, ki fada masa ya same ni mu kare magana idan da gaske yake, sai mu gani kuma ni ba dade nake son ayi ba, sannan kuma ki sani ni ba ni da wasu kudin yi miki hidima shi ma margayi saboda ya dauke komai ne ya saukaka min, wannan kuma ba mu san ya yake ba” Yana gama fadar hakan ya mike tsaye ya fice daga dakin fuska a daure. A takaice dai jari mahaifina yake son yi da ni, in ba haka ba ta ina za ace ko da yaushe mijin da zai aureka ne zai maka kayan daki? “Umma dan Allah ki fada masa, ina son na tafi na duba Mama yau, na dade ban je ba” “Toh bari na fada masa” Ta amsa da far'a ta fice daga dakin, wata kila tana murna zan yi aure na bar mata gidan ko kuma dai da gaske farinciki take zan yi aure! A waje ta sami Baba dake ta fada masa bukata ta sai yace “Allah ya kiyaye” Ina jin haka na tashu daga dakin na fito waje na shiga dakinmu sai na samu Hana tana hawaye. “Idan kika yi aure kika tafi kika bar ni, ni za su kashe da aiki a gidan nan, na gaji Wallahi” “Baba ya shirya aurar da ni, idan har ban fitar da wani ba, zai aura min Ridwan ne ni kuma ina ganin kamar zaman gidansa ba zai min dadi ba” “Allah yasa alheri ya sa gurin zamanki ne, kin huta Wallahi” Na amsa da Ameen, na fita na yi wanka na shirya na dauki ragowar canjin da Kareem ya ba ni na hau Napep da su na tafi gidan Mama. Na wuni a can na fada mata kudurin da na yake sai ta nuna min farincikinta fiye da yadda na zata, hakan kuma ya karfafa min guiwa na ji cewar kamar amincewa da Abdull a matsayin miji da na yi, na yi abu mai kyau, a gidan na wuni sai dare na dawo gidan mahaifina tare da yi ma Hana albishirin Mama ta ce da zarar na yi aure zata dauke ta daga gidan ta maida ita gidanta ta saka ta makaranta a can. A daren da na dawo a daren Abdull ya gana da Baba ya gabatar masa da kansa Baba yayi masa tambayoyi ya amsa gamsasshen amsoshim da yake so, sai kuma ba lura yayi na'am da shi saboda ya fahimci mai rufin asiri ne irin yadda yake so. Na je masa rakiya ne nake bayyana masa mamaki ne zuwa da wuri gurin baba. “Ai ba a bori da sanyi jiki, kuma ance a bari ya huce shi ke kawo rabon wani, zumudi ba zai bar ni na dade ban zo gurin mahaifinki ba, turawa sun ce dama tana zuwa sau daya a rayuwa” Na dan yi murmushi. “Yanzu ina son iyaye su shiga maganar ne, idan komai ya kam na tabbatar da an ba ni ke sannan na sanar da matarta cewar zan kara aure, gashi na yi sa'a ta sauka yanzu ta haihu balle ace zan kunsa mata bakinciki” “Wacece matarka?” Na tambaya da mamaki a fuskata, sai ya ciro wayarsa ya kamo hotonta ya nuna min. “Safeena, kin ganta, ita ma kyakkyawa ce kamar ke, amman ita tana da dan jiki kadan ba kamar ke ba” Na kalli hoton na sake duba na sake kallo... KAREEM POV. It's a faithful Monday for him today. Tun daga wacan ranar da ya zauna da Noor ya barke mata cikinsa ta ba shi shawara kuma ta karfafa masa guiwa sai ya ji damuwarsa ta yi kasa. And when ever ya tuna da yadda take dariya ta ba shi shawara sai ya samu kansa da murmushi. A zatonsa idan ya fada mata laifin da ya aikata da Safeena zata tsorata kuma ta guje masa a take ko ma nuna masa bacin ranta. But ta masa abun da matarsa bata yi masa ba, wata kila saboda ita din bata sa munin abun ba ne, wata kila kuma saboda tana da sauran kurciya ne har lokacin bata gama fahimtar duniya ba, amman ko ma dai yaya ne, ta fada masa kalamai masu dadi da kwantar da hankali, hakan kuma ya rura wutar alakar zuciyarsa da ganinta. Amman haka yake daurewa zuciyarsa gudun abun da mutane za su fada ko kuma ita kanta kallon da zata masa idan ya matsa da zuwa gurinta. To me zai rika a matsayin Hujjar tafiya a gurinta, babu dan haka ya shafawa kansa lafiya. After ya gama saka key din a mota ya bude ya shiga yayi warming dinta sannan ya fara tukawa, as usual every Monday yanzu yana fara zuwa family house dinsu ne gaishe da iyayensa sannan ya wuce aiki. A harabar gidan ya faka Aaryam dake tsaye jikin tasa motar ya dago yana gaishe shi. “Ranka ya dade” “Aaryam ya kake?” “Lafiya kalau, ya aiki” “Gashi mun yi shirin tafiya” “Daddy ya fita da safen nan kuwa” “Lafiya?” “Lafiya kalau, wai akwai abun da za su yi” “Okay” Ya amsa sannan ya shiga ciki ya gaisa da Hajiya Hassana da kanensa ya fito, har ya bude motarsa zai shiga sai kuma ya rufe ya nufi inda kanensa yake zaune a balcony ya zauna. Aaryam ya kalleshi cike da damuwa irin na dan'uwa mai damuwa da dan'uwansa ya ce. “Lafiya big Bro?” Kareem ya sauke ajiyar zuciya. “Lafiya, i just need some advice” Aaryam ya aje wayarsa a gefe ya fuskanci jininsa. “Ina jinka” Kareem ya kasa cewa komai, har Aaryam ya fara guessing. “Ko matsala kuka samu da Yusura again?” “No ba ma fada juna ai, it's just that dai ba ma zama kamar sauran ma'aurata, saboda tana jin na takura mata, ni ma haka” “Kamar ya?” “Aaryam ba zaka fahimta ba ko na fada maka” “Ban kai na fahimta ba ne?” “Ka kai amman ba zaka kalli abu ta sigar da nake kallonsa ba” “Fada min dai minene?” “Ni da Yusura ba mu taba son juna ba fa...” “Na san wannan abaya, duk wanda ya tashi gidan nan ya san kai da ita abokan gaba ne, amman bayan aure kake nufi ko kamin aure” “Har yanzu, har gobe har jini and abun yana damuna sosai” “Subhanallahi, taya kake iya zama da ita kuma baka sonta? Indai har da gaske ne to tsanarku mai girma ce” Kareem ya dan daga girarsa ya rage idonsa yana kallon harabar gidan. “Idan baka son mutum baka son shi ne Aaryam, haka dai nake ta zama saboda kaddararmu ce a haka” Cike da tausayi Aaryam yake kallon yayan nasa ya ce. “Ita ma har yanzu bata sonka?” “Da zaka mata albishir da na mutu yanzu, zata baka goro” “Innalillahi,,, to miyasa za ku cigaba da zama?” Kareem ya kalleshi. “Shiyasa muka rabu, amman Daddy ya kasa fahimta ya cilasta mana sake zama, kuma halayen da take min a yanzu sun fi muni fiye da na baya” “Ku sauwakewa junanku kawai zai fi, zan yi magana da Daddy zan fahimtar da shi...” “A yanzu ba rabuwar ce damuwata ba, Aaryam aure nake son na kara, maybe haka zai saukaka min wasu abubuwa kamar yadda Hafiz yake ta hararo min” “Kana da wanda kake so ne?” “Eh akwai ta, amman ban san ya ku da sauran mutane za su kalli abun ba, gashi abokin shawata ya tafi ya bar ni, shiyasa nake neman shawararka” Slowly Aaryam ya kalleshi. “Hope dai ba Safeena ba” “Har bada, ba zan taba auren Safeena ba ko da mata sun kare a duniya, wata yarinya ce mai tsananin bukata ta, ina jin kamar zan iya zama da ita zan iya kyautata mata, zan maye mata gurbin abubuwa da yawa da ta rasa, ko zata rasa a nan gaba” “Indai yarinyar kirki ce, babu wata matsala ka yi aurenka Bro, ka yi kokarin ni ba zan iya irin jihadinka ba, ba zan iya auren macen da bana so ba, ka kyauta ka saka Momy farinciki kai ma naka farinciki yana tafe, sannan ina mai baka shawara karka bari wannan yarinyar ta suBuce maka, Daddy ba zai hana ka kara aure ba, mu kuma kanenka ne ba mu zamu zauna da ita ba” Kareem ya aje numfashi ya shafa kansa sannan ya fadawa Aaeyam yarinyar da yake so, da kuma alakarsa da ita da kuma mijin da ta aura. “Ba haramun ba ne, kuma ba abu ne sabo ba, indai kana sonta tana sonka ba wani abun tsoro a ciki, karka duba abun da mutane za su fada zaka saka kanka ne a damuwa kawai, kuma gashi Hafiz din ya fada maka kamin ya bar zuciya, ka amsa masa kawai kuma ka yi addu'a, kuma karka manta tun farko kai aka tashi aurawa ita Allah be yi ba har haka ta faru, dan Allah ka aureta, idan ka aureta ka samu abun da kake so kuma ka cika burin abokinka, ita ma kuma ka taimaka mata, wata kila ma hakan ya zama silar rabuwarku da Yusura cikin sauki, ita ma ta samu wanda take so ta aura shikenan” Shirruuuu Kareem yayi yana ta saurare ni dan'uwansa. “Duniyar nan bata da tsawo ga wasu, kara ka bawa kanka abun da kake so karka yi sanya, ka same ta kawai ku tattauna idan kun kai karshe sai ka fadawa Daddy, wata kila ma a hade tare da nawa auren” Kallonsa Kareem yayi yana murmushi. “Shikenan sai ka taya ni da addu'a, thank you” “Allah ya bada sa'a” “Ameen” Ya mike tsaye ya nufi motarsa Aaryam ya bishi da kallo yana mai tausaya masa da mamakin karfin hali da kuma tsananin biyayya irin ta dan'uwansa wadda yake jin shi kam ba zai iya yi ba. Ya wuni a office da nazarin kalaman Aaryam yana amsawa zuciyarsa muradinta, a yanzu ma kanansa ya kafafa masa guiwa abu daya ya rage masa ya gabatar ma da Noor bukatarsa ya ji ya zata karbi abun. After work ya koma gida ya shirya cikin kananan kaya ya sake fita zuwa gurin da yake zama a yanzu, ya saka an yi masa gurin zama na kujerar sumitin a gurin amman ranar be yi sha'awar zama a can ba, sai ya zauna daidai gurin da yayi wacan zaman a wacan ranar da suka yi hira da Noor ta fada masa damuwarta ya fada mata ta shi. Sai da yamma ta fara yi sannan ya nufo motarsa yana shan ruwan gora ya bude motar ya shiga ya sake kama hanyar gida. A hanya yayi sallah Magariba sannan ya karasa gidan ya sake sabon wanka ya saka sabuwar shadda sai kamshi take tun kamin ya saka mata turaren. Ya hada kamshi kusan kala biyar sannan ya fito fuskarsa da haiba, feeling some how for the second time zai sake fita neman aure, so yake ya kwankwasa ya ji idan Noor zata iya daukuwa. Har ya sauko be kalli gefen da Yusura take zaune ba, ita bata yarda ta kalleshi ba sa ta gafen ido. Yanayin yadda yayi dress din da kamshi dake take masa bayan, zuciyarta ta raya mata neman aure zai je. Mikewa ta yi tsaye ta isa gurin window ta daga curtain din tana kallon motarsa har ya bar gidan mai tsananin haske kamar ba dare ba. Ya isa kofar gidan su Noor a lokacin da ake ta kiran sallah Isha'i, a kokarinsa na samu Jam'in sallah ya rufe Motar ya nufi masallacin dake kusa yayi alwala a gurin ya shiga aka sauke farali tare da shi, sannan ya fito ya dawo gurin motarsa. Yayi knocking kofar gidan saboda babu yaron da zai aika a lokacin, babu bata lokaci Hana ta leko suka gaisa. “Noor na ciki?” “Eh tana ciki, bari na kira ta” Ta juya ta koma cikin gidan, babu jimawa Noor ta fito sanye da atamfa da karamin mayafi a kanta zuwa kafadarta. Suna hada ido ta sakar masa murmushi shi ma ya mayar mata. “Ka yi kyau, kana ta kamshi kamar ango” Farinciki furucinta ya saka jin kamar an yaye masa rabin damuwarta, when last yayi kwalliya ace masa yayi kyau, yana kamshi ya manta. Lumshe ido yayi ya tsotsa bakinsa ya bude. “Besty ta yaba kwaliyata hakan ma yayi” Ta yi murmushi kamar ba ita ba. “Mun kwana biyu ba mu ga juna ba, i miss this face so much, tare da murmushin nan mai tsada” She then looks at him jin wani sabon salon furuci wai murmushi mai tsada. “Shiyasa ka zo ko wani abun ne ya ta so” “Eh to wani abun ne ya taso, da ina jin tsoro ina sanya yanzu kuma na shirya fuskanta ko miye ma a wuce gurin” “You want us to talk about something?” “Yeah Besty” “Kamar ka san ina nemanka, ni ma akwai abun da nake son fada maka” Ya jingina da motarsa. “To bari na fara jin na ki, ladies first fara fada min na ki” Shiru ta yi na dan lokaci sannan ya dago ta kalleshi. “Kareem idan...” Ya dakatar da ita. “Besty, I'm your bestfriend remember?” He said try to correct her, sai ta yi murmushi ta daga mishi kai. “Yeah” “Okay carry on” Yayi mata alama da hannu. Rumgume hannayenta ta yi. “Besty idan mutum ya taba son wani, yana jin zuciyarsa ta rufe kamar ba zai sake son wani ba again?” Kallonta yake kamar his life depends on her. “Haka kike ji?” “Eh shiyasa nake son na tambaye ka, ai kai ka taba son wata baka samu ba how do you feeling tun da gashi har kace ka samu wata dabam da kake so?” Ya daga kansa sama. “Wow... Abun is not easy, amman Hafiz yana yawan fadar wani abu cewar wani lokacin mutum be san abun da yake so ba, ko ya dace da shi sai a gaba. Noor lokuta da yawa mu kan kasance da wani abu ko kuma ma mu so kasancewa da shi alhalin ba son shi muke ba, shakuwa ce kawai da shalholiyar zuciya, daga baya zaka fahimci abun da kake so kuma ya dace da kai. Wani sa'ilin idan Allah ya hana ka abu shi ne mafi alheri a gareka, na fahimci hakan ta dalilin rashin auren Safeena da ban yi ba a yanzu” “Amman ya aka yi ka fara jin kana son wata a yanzu?” Ya maida idonsa akanta “Wallahi ban sani ba, mun hadu a kan kuskure i think i like so many things about her and her life, i like her laugh, her smile, her jokes, her sincerely, most of all i love her heart and her happiness... Shi ne kawai abun da zan iya fada amman ban san ya aka yi na fara sonta ba, kuma ban fahimci ina sonta ba sai yanzu” “Wata kila saboda kai din na dabam ne, amman ni har yanzu ban ji ina kaunar kowa ba” Tana maganar kamar da shagwaba, furucinta kuma ya dan tsare masa guiwa. “Zaki ji nan gaba, babu abun da yake zuwa da sauki Besty” “Me kake son mu tattauna?” “Ina son mu tattauna ne akanki da kuma kaina, yarinyar dana fada miki ina kauna akanta nake son mu tattauna” Ta yi murmushi na taya shi farincikin yarinyar da yake so. “What a lucky girl, but ni ma ina son na fada maka wani abu” Na maida hankalinsa gurinta sosai. “Fada min, komai na ki ne first na wa zai zo daga baya” Ta taka ta isa gurin motarsa ta jingina damuwa ta bayyana a fuskarta. “Kareem daman ina son na fada maka na tsayar da wanda nake son na aura...” Sai kuma ta dube shi kamar yadda yake kallonta with heartbreak. “Amman dai har yanzu ban ji wani abu akansa ba, kawai na amince ne saboda bana son Baba ya sake yi min auren dole...” As how? Is she for real? Ya tambayi kansa feeling so downfall, fell in the hot fire and drowned... NOOR POV. ya dauke idonsa daga kallona ya juya ya jingina da motarsa ya kifa kai, sai kuma ya dago ya bude motar ya shiga ba tare da yace min komai ba yayi motarsa key ganin hakan na saka na dago daga jinginawar da na yi jikin motar ina mamakin me na fada ba daidai ba. Da reverse yaja motar har yayi nisa ina kallonsa, sai kuma na ga ya tuko ya sake zuwa inda nake tsaye ya faka, ina hango yadda ya kifa kansa jikin sitiyarin motar kamin ya dago ya kalleni. Karasa na yi na bude murfin motar ina kallonsa. “I'm sorry” Ya juyo ya kalleni. “Sorry for what?” “Ban sani ba ko na fadi wani abun ba daidai ba ko be maka dadi ba, bana son ka ji haushina” Na fada a shagwabe ina jin kamar na fasa masa kuka. Yayi min murmushi yana kiran sunana. “Noor...” Na matsa baya ganin yana kokarin fitowa, sake rufe motar yayi ya jingina jikin motar ya sauke ajiyar zuciya yana kallon kofar gidanmu. “Waye wannan mutumen?” “Wane ne, sunanki Abdull a Lagos yake aiki, yana da mata da yara” “Ina kika hadu da shi?” “Mun taba haduwa tun Hafiz yana raye a Mall yayi min magana be san ina da aure ba, sai na fada masa ina da aure, sai kuma na sake haduwa da shi a gidan da Mama take aure a yanzu, kuma Mama ta yaba da halinsa” Ya dan bata fuska kadan wata kila ya tuna da abokinsa ne, ko kuma taya shi kishi yake. “Amman an yi bincike ba shi da wata matsala?” “Na dai sanar da Baba kuma ya zo ya ga Baba an yi magana da shi, yanzu ya rage Baba ya bincika” “Okay, Allah ya tabbatar da alheri Noor, ina miki fatan jindadi da samun rayuwa mai kyau a duk inda zaki kasance” “Na gode” Na fada ina kallonsa shi kuma yaki yarda ya sake kallona a yanzu. “Fada min abun da kace zamu tattauna!” “Nace za mu tattaunawa wani abu ne?” “Eh akan yarinyar ka” Yayi dariya mai sauti. “Ni nawa labarin ba mai dadi ba ne...” Na yi hanzarin dakatar da shi domin bana son jin wani abu marar dadi daga gareshi, abun zai tsaya min a rai na yi ta tunani ina damuwa. “Ba sai ka fada min ba” “Why? Baki son jin yadda na rasa yarinyar da nake so?” “Abun zai tsaya min a rai ne na yi ta tunawa ina jin babu dadi, bana son na ji wani abu marar dadi ya same ka, abun zai yi ta damuna ne yana hana ni sukuni da zarar na tuna, ban san miya ba ina damuwa da kai sosai Kareem” Ya kalleni yana murmushi mai laushi. “Amman kin san idan kin yi aure zamu yanke alaka ne? Babu waya ko ziyara saboda ni ba muharraminki ba ne, ba ni kadai ba har ma duk wanda kika san ba Nabil ba ne, ki kula da aurenki kuma ki tsare hakokin Allah Besty, kin ga kin yi aure ba ki dade ba aka fara samun matsala, ki kula ki yi taka tsantsan da rayuwar aurenki” Na daga mishi kai hawaye na sauko min. “Zan kiyaye Kareem, na gode” “Your Welcome, and maybe wannan ne zuwa na karshe da zan yi a gurinki, saboda kar ya zo ya tarar da ni na hada fitina a tsakaninku, kuma mahaifinku ba ba zai yarda an tsayar miki da wani ba ki kula wani” Na ji babu dadi a kalamansa sai dai hakan da zai yi shi ne daidai kuma shi ne gaskiya. “Wish you all the besty” Ya bude motarsa ya shiga, zuciyata na ayyana min na fada masa Abdull mijin Safeena, sai kuma na fi karfinta na aje wannan sirrin a zuciyata ina kallonsa har ya tafi. Sannan ya shiga gida ina jin babu dadi a rai saboda bankwana da na yi da Kareem. Zuwan da Abdull yayi a wannan karon ya zo min da babbar waya da sabon liyi, na yi murna sosai domin bayan Hafiz wani be taba min kyautar waya ba, ya saka min line ya saka min numbersa da sunan da yake son na rika kiransa. “Soul” Yayi saving ya hannanta min wayar, na yi masa godiya sosai na shiga gida na nunawa Umma wayar na nunawa Hana Baba ma da ya dawo na karba na nuna masa, na dauki Number Ya Nabil ta sudan da ta nigeria sannan na dauki Number wasu yan'uwan Baba, na saka number Mama da na haddace na yi saving na kirata muka gaisa na fada mata Abdull ya kawo min wayar, ta taya ni murna sosai ta yi addu'ar Allah yasa alheri. Da ya sake zuwa sai ya bude min WhatsApp wai saboda ya fi saukin chat, hakan kuma na kara min jindadi domin ta nan nake magana da Yaya Nabil ya turo mana hotuna da video sa, ni ma idan na dauka sai na aika masa, idan yayi status na kalla. Yawancin chat din da yake da ni yana gargadin idan na yi wannan auren na zauna ne. Na kuma yi masa alkawarin zan zauna domin na lura kamar Abdull ba shi da matsala, ko da yake ba a goshi ake likawa ba sai idan an zauna. Zancen auren da zan yi, ya karade ko'ina cikin unguwarmu, wasu da gangan suke dukan cikina domin jin wanda zan aura. Mamaki be kashe su sai da Abdull ya zuba min lefe kamar budurwa, ya saka min kaya masu matukar tsada ni kaina na yi mamaki domin ban dauka arzikinsa ya kai can ba. Sadakin ma 100k Baba ya yanka masa sai gashi ya kawo 150k. A lokacin ne Baba ya fara saka min albarka yana fadin idan na yi auren nan bayan son ya ji wata matsala. Sai dai iyayensa ne suka yi komai, domin shi baya garin ma a halin yanzu, ya koma Lagos gurin aikinsa, sai dai mu yi waya ko chatting idan hira ta yi dadi ya kan dauko zancen gidansu familynsa da abokai ya fada min. Ta haka ne nake jin cewar Safeena cousin dinsa ce, a gidansu take zama sai dai ba a gidan ta tashi ba, bayan gama SSCE ne ta dawo garin Kano daga Jigawa mahaifarta saboda admission da ta samu a BUK bayan kallama karatun kuma ta cigaba da zama a gidan, har Allah ya kulla alakar aure a tsakaninsa da ita. Mahaifiyarsa ita ce mace ta biyu da Alhaji ya fara aure kamin ya auri wasu matan, ita ma bata gidan a yanzu tana can gidanta dabam tana zama tare da wasu iyalin a aurenta na biyu da ta yi. Hakan ya kara fito da maganar Mama cewar Alhaji kamar riga ya dauki mace, ko da yake Abdull be fada min cewar Babansa yayi aure aure ba, amman dai ya fada min mahaifiyarsa bata gidan kuma yaran da suke gidan uku ne kawai suke da uwa ana, na kuma gane karatun tass duk kuwa da kasancewar be fito min a fili ba. Ina kyautata zaton sai bayan da ya biya sadaki an kawo lefe ne ya sanar da matarsa, wata kila kuma bata dauka da gaske ne ba har sai da ta ga haka. Sai gashi ta aiko min da zagi na cin mutunci da kaskanci a WhatsApp, har na yi kamar na rama sai kuma wata zuciyar ya hana ni. Kai tsaye na yi forwarding zagin gurin mijinta kuma na yi sa'a yana online. “Subhanallahi waya miki wannan zagin haka?” Ban bashi amsa ba na tafi gurin chat din na yi screen shot din number ta da hotonta dake dp na tura masa. “Safeena... Dan Allah ki yi hakuri zan dauki mataki, kin san mata idan za a kara aure sai an yi hakuri da su, ni kaina duk ta bi ta daga min hankali” Nan ma ban ce masa komai ba. Na kashe data na tashi na fara gyara dakinmu, ina tsaka da shara kira ya shigo wayata da bakuwar number. Na duba wayar da kyau ina mamakin waye mai number domin ban san na bawa wani number na ba, dan haka ban amsa kiran ba har sai da aka sake kira sannan na amsa ina sallama. “Assalamu Alaikum” “Yar iska marar mutunci karuwa mai bibiyar mazan mutane, to kira na yi na miki gargadi, Wallahi Wallahi karki yarda ki ce zaki auri, domin zaki auri mutuwarki ne, akan mijina zan iya komai Wallahi, Idan ma burinki shigowa gidana to gidana kabari ne mai cike da azaba” Na sauke wayar daga kunnena na duba number sannan ya sake maida wayar kunena. “Gidana zan zauna ba naki ba, kuma ni a Lagos zamu zauna da shi gurin da yake aiki ko be fada miki ba? Ke be isheki hankali ba yadda na bar ba banza ajiyarki na sauka daga WhatsApp din ba tare dana baki amsa ba? Hakan yana nufin ba a fada da mahaukaci” “Uwarki ce mahaukaciya, Noor baki san waye ni ba, na fi guba hadari kuma bana yafiya Wallahi, idan kuma na sakawa raina burin wani abu bana wasa sai na cin masa, tun wuri ki shafa kanki lafiya, wato za'a zo a ji dadi ko? An ga mai kudi? Daga auren uwarki ke kuma kin ga shiga gurin dan masu gida, kin manta karya miki hannuna da na yi ko? Wannan karon rayuwarki zan karya, wato baki samu shiga gurin Kareem ba shi ne kika dawo gurin mijina ko? Ke baki da aiki sai bibiyar mazan mutane, kin shigar min hanci da yawa Noor sai na fyato ki” “Ashe dai kin gane ni, Amman kika nuna baki san ni ba, a gidan da aka rika ki har kika auri dansu” “Okay wato shi dan dadi aure ko? Ya kwashe labarina na fada miki? To zan ci uwarku ne daga ke har shi” “Ashe dai baki da tarbiya, gaskiya akwai bukatar na shigo gidan ko dan gyara miki tarbiya, har yaushe zaki raina mijinki ki ce zaki ci uwarsa?” “Uwarki ce marar tarbiya jaka karuwa...” Na mike tsaye a fusace na ce. “Safeena ina son ki saurare ni da kyau, kin san na san abun da mijinki be sani ba ko? Kina da aure kike nuna kishi da hauka akan wani? Ko kina tunanin na manta alakarki da Kareem? Ni Wallahi ban yi tunanin kina da aure ba ma, wai ashe kishinsa kike, to yanzu kuma kina kishin mijinki wace irin mace ce ke?” Ta yi shiru irin na wanda jikinta yayi sanyi. “Me Kareem ya fada miki?” “Na fahimci komai Safeena, idan babu so miya kawo kishi? A yanzu kuma kina kishin mijinki har kina zagina akansa? Toh bari na fada miki wani abu, idan har ban auri Abdull ba ke kuma ba zaki taba cigaba da zama da shi ba Wallahi, sai na fadawa kowa abun da kika yi min saboda Kareem, kuma na fada musu har office dinsa kike zuwa, kin ga ni da ke duk muna ruwa kusa da kada, ko dai ya cinye mu duka ko kuma mu nutse a ruwan a ruwan mu mutu dukanmu” “Karya kike yar talakawa, babu wata alaka tsakanina da Kareem, ke kamarar yarinya ce da baki gama fahimtar komai akan rayuwar duniya ba, na fiki zama tantiyar yar iska, sai na koya miki darasi Noor” “Ni dince dai zan koya miki darasi kuma na gargade ki, karki sake daga ma mijina hankali, karki sake kirana ko aiko min da wani zagi ta WhatsApp, idan ba haka ba zan fadawa mijinki da iyayensa alakar dake tsakaninki da Kareem, daman ai kowa ya san tsohon saurayinki ne ko? Har gurin da kuke boya ku aikata alfaha da aurenki na sani, na san yadda kika yi yaki kamin ki samu kansa, na kuma san yadda abokinsa yayi fama raba tsakaninku, kuma abun takaicin idan mijinki ya sake ki Kareem ba zai taba iya aurenki ba, shiyasa ya janye jikinsa daga na ki, ke din kazantace a yanzu, to yanzu fada min tsakanin gasawa da suya wanne ya fi jin wuta?” Dip na ji ta katse wayar, sai na daka tsalle na dike, ashe dai ni ma mace zan iya yaki zan iya kwantarwa kaina yanci, a yanzu na samu baki ba irin wacan karon ba. Daman ance auren fari makaranta ce aiko na koyi darasi mai girma. Na nufi gurin da kayan kwalliyarmu suke na dauki madubi na duba bakina da fuskata. Ashe dai tsiwata tana nan, ni da kaina nake yi ma wata gargadi haka akan mijinta. Da mamaki na wuni a ranar da na tuna sai na ji raina yayo fari tass. KAREEM POV Da ciwon zuciya Kareem ya koma gida, abun da be saba ba ko a lokacin da ya rabu da Safeena be taba jin ciwon zuciya ba, ya ji babu dadi sosai kuma ya shiga damuwa amman be taba jin zuciyarsa na masa zafi da kuna irin wannan karon ba. Rasa Noor da yayi a yanzu na dago masa da damuwa ba suke zuciyarsa. Yana shiga falon be ma kula yaransa da suka bar wasar da suke ba suka yi masa welcome, kansu kawai ya shafa ya haura sama ya kwanta ruf da ciki ya rufe ido. Yaran suka bishi suka shiga dakinsa domin ba su saba ganin mahaifinsu a haka ba, duk maganar da suke masa da tambayar da suke masa ko be da lafiya ne be iya amsa musu ba sai dai ya daga kai ko ya girgiza ba. Har suka gaji suka fito daga dakin suka shiga dakin mahaifiyarsu. "Mamy Dady ya dawo yana yin damuwa kuma baya magana ya kwanta a haka” Areef ne mai maganar yana nuna yadda ya kwanta. Yusura dake shace kanta ta kallesu ta tabe baki. “Wata kila kasa shi aka yi” Ta fadi hakan ne domin ta window ta hango yadda ya dade zaune a mota kamin ya shigo cikin gidan. “Mamy kasha shi kamar yaya?” Tine ta tambaya, kamin Yusura ta bata amsa Areef ya ce. “Mamy a tray aka kasa shi? Ko yaya?” Ta yi murmushi mai sauti ta saki gashin nata mai tsayi ta jasu a jikinta ta rumgume. “Ku kadai ne nake gani na ji sanyi yanzu” “We love you Mamy” Cewar Tine Areef kuma ya cigaba da tambayar yadda aka kasa Dadynsa domin be fahimci zancen mahaifiyarsa ba. Tun daga ranar sai Kareem ya tattara komai ya aje gefe, ya karbi kaddararsa ta rasa Noor ya maida hankalinsa gurin aikinsa da yaransa, hakan kuma baya nufin ya manta da ita ya cireta a rayuwarsa, da zarar ya zauna baya komai ita ce take fado masa a rai kuma yawan tunata da yake yana saka shi damuwa sosai. Ganin yake kamar nasa zanen kaddarar be zano masa da farinciki ba, domin ya rasa Safeena da farko a lokacin da yake jin ita ce farincikinsa aka musanya masa da Yusura a yanzu kuma da yake jin ya sake samun farinciki, sai gashi ya sake rasawa, ya kuma tabbatar rashi ne na har abada domin baya fatan ta Noor ta samu wata matsala a gidan aurenta balle har auren ya mutum. Shi ma yana da ya mace ba zai yi mata fatan abun da ba zai so ya faru da yarsa ba. *** *** *** Hannu ya kai ya rage sautin dake tashi a motarsa sannan ya faka a inda ya saba fakawa ya bude motar ya fito ya rufe. Cikin natsuwa yake tafiya har ya shiga restaurant din ya amsa gaisuwarsu as usual sannan ya wuce office dinsa yana kokarin budewa ya ji kamshin turare a bayansa juyawa yayi ya duba. Safeena ce tsaye fuska babu annuri be ce mata komai ba ya sake juyawa ya bude kofar ya shiga sai ta take masa baya. Sai da ta rufe kofar sannan ta dora jakarta akan teburinsa tana kallonsa kamar ba ita ba. “Hausawa sun yi gaskiya da suka ce duk macen da ta rike namiji uba zata mutu marainiya” Kareem ya kalleta yana daga zaune fuska ba yabo ba fallasa. “Ka fada min bayan ni ba zaka so wata ba, ban yi zaton bayan ni zaka iya kulla wata alaka makamanciyar tawa da wata ba, sai gashi ka ba ni mamaki” Be ce mata komai ba sai kallonta yake domin be fahimci da me ta zo ba wannan karon. Ganin hakan ya saka ta zaunawa, ba dan ta zo da niyar zaman ba. “A baya ka yi min karya ka ce kai da Safeena ba ku zaman lafiya, sai gashi na je gidanmu na sameku cikin so da kauna, sannan kuma ka juya min baya ka kulla alaka da Noor, Kareem wai ba baka ji kunya ba? Yanzu na gama fahimtar gaskiyar da kake boyewa, na gama fahimtar yaudarata kake yi, tun asali ba wai kaki ka aure ni ba ne saboda Hajiyarka, kaki ka aure ni ne saboda zuciyarka tana son Yusura, lokacin da na ce zan kashe aurena mu yi aure kin amincewa ka yi, ashe saboda kana jin kamar yanzu na gama yi maka amfani ne ko? Bayan ka gama lalata min rayuwa” Ya kwanto jikin teburin dake tsakaninsa da ita yana kallonta. “Kamin na aureki wata alaka makamanciyar wadda muka yi a baya ta taba hada ni dake? Na taba bukarta ki ba ni kanki? Ke kika kawo kanki bayan aurenki, babu yadda ban nuna miki hakan kuskure ba ne amman kika rufe ido har sai da muka aikata ya zame mana jiki, to yanzu kuma miye laifi idan na gane kuskuren hakan na tuba?” “Ba tuba ka yi ba, wata sabuwar ka samu, ni kuma ba zan taba manta cin amanar ka yi min ba, kuma ba zan yafe ba, dadin zama ne ya saka ka manta da komai ka fadawa Noor sirrina da kai? Har take min barazanar idan ban bari ta auri mijina ba, ni ma zan rasa aurena? Shikenan mu zuba zuwa ni da ita ga fili ga mai doki, daman ina da cikinta na bakinciki sai na haife shi...” Tana kaiwa nan ta mike tsaye ta fice daga office din. Kareem ya mike tsaye yana mamakin abun da ta fada cewar Noor ta yi, sai a yanzu ya gane mijin Safeena Noor zata aura, sunansa da ta fada masa Abdull da kuma inda yake aiki da kuma fada masa yana da aure. But abun da be fahimta me yasa Noor zata yi risking fadawa Safeena haka? Me yasa zata fara fallasa sirrinsa? He thought he save da ya fada mata damuwarsa, amman gashi a yanzu zata yi ma kanta da shi da kuma Safeena illa, why ya fada mata from first place? Ya dafe kansa ya zauna yana jin tashin hankali yana tunkaro shi, ko kadan baya son abun da zai bata matsa suna ya bata sunan Yayansa da iyayensa, can kuma ya dago ya mike tsaye ya fice daga office din. NOOR POV. Washe garin ranar da muka yi fadan da Safeena, Mama ta aiko kanwarta Mama Jamila ta kawo min kayan kitchen daidai gwargwadon hali, ni ban yi tunanin zan samu ko kyale daga gareta ashe tana nan tana min tanadi ba wasu masu yawa ba be sosai ko masu tsada, sai dai za su wadace ni na yi duk abun da mace zata iya dafawa ko aikatawa da pot da plates jug da abubuwan bukata. Na jidadin haka wata kika Alhajin ne ya bata kudi ta siya min ko kuma kudin da take samu ne a gidan Allah masani, ko ma dai minene mahaifiyata ta fitar da ni daga kunyar kayan kitchen sauran na daki da ban saka ran Baba zai yi min ba. Ni da Umma muna duka kayan domin a lokacin Hana bata gidan tana gurin talla, sai da na gama duba komai sannan ta rika min na kai su dakinmu, ita kuma ta saka hijab dinta ta yi shirin tafiya ba tare da ta sha ruwa ba balle har ta tsaya cin abincin da yanzu ake girkawa, babu wani far'a a fuskarta na san kuma hakan baya rasa nasaba da yadda suke kallon Baba a matsayin ma ci amana kuma marar mutunci a yanzu, daman Mama Jamila ta fi kowa daukar zafi ko a lokacin da Mama take aure Baba balle kuma yanzu da babu alaka sai ta yaya. Bakin titi na rakata tana ta yi min gargadi na zauna lafiya gidan mijina na san waye mahaifina kuma na san yadda zaman gidan yake a yanzu, har tana addu'ar ita ma Hana Allah ya kawo mata na gari ta yi aurenta ta guta wannan wahala da takaici na gidan uba. Sai da ta shiga Napep din sannan na juyo na nufo gida, ina tafiya na ji karar mota bayana matsawa na yi gefe domin ba mai motar hanya. Kamar haka yake nema sai ya wuce ni ya isa kofar gidamu ya faka, tun kamin ya fito motar zuciyata ya raya min Kareem ne domin motarsa ce gashi kuma ya faka a kofar gidanmu. Me ya kawo shi? Wanda ya ce mun yi bankwana tun a kwanan baya? Ko dai ya ji ba zai iya jurewa ba ne sai ya gan ni shiyasa ya dawo ko kuma wata matsalar ce? Ta a yanzu da ya rage sauran sati daya a daura mana aure da Abdull. Na fi kyautata zaton matsalar domin ba kasafai Kareem yake zuwa gidanmu da rana ba, kuma bana tunanin marmarin ganina kawai zai kawo shi a gidan ana sauran kwana bakwai na zama matar wani. Wani tunanin aka jefo min na Safeena da alakarsu da kuma fadan da muka yi jiya da ita. Na karasa gurin na tsaya ina kallonsa ba tare da tsoro ko fargabar wani ya gan ni tare da shi ba a yanxu da zan yi aure na biyu, domin ba alakar soyayya ce tsakaninmu ba balle ace na kula wani, haka kuma Abdull baya garin nan a yanzu ya kuma tabbatar min ba zai dawo ba sai ana gobe daurin aurenmu. Matsalata daya ce kar Baba ya ce zai yi masa fada ko yayi min idan ya tararda mu a tare. Ko da yake Kareem din mai gidan ďansa ne kuma mai yawan yi masa kyautar kudi mai kyautata masa, wata kila hakan ya saka ya daga masa kafa ya ji kunyar yi masa wani abun na cin mutunci ko cin fuska. Sai a lokacin ya rufe motar Motarsa da yake rike da gambun yana kallona har na iso. https://chat.whatsapp.com/Jd2OwsAcXE7EjI7NHeFQV0 PAID PAGE 2️⃣0️⃣ ©️KhadeejaCandy ©️®️Copyright 2024 Littafin nan na kudi ne, don't read if you didn't pay... One word kika karanta baki biya ni ba, ban yafe hakkina ba. To be part of the journey pay 500 to 2451879008 ZenithBank Hadiza Abubakar And send the evidence of payment to my WhatsApp number 08036126660.... You can read my latest update on arewabooks a handle dina @KhadeejaCandy https://www.arewabooks.com/book?id=659a94c8be87d7a51f831153 _______•••_______ Rumgume hannayena na yi ina kallonsa with my innocent face. “Besty how are you?” Ya tambaya yana daga kai ya kalli harabar unguwar. “I'm good and you?” Ya daga gira not happy not sad. “I'm not fine” Na dan matsa kusa da shi. “Me ya same ka?” Sauke kai yayi kasa sannan ya ce. “Bestyna kamar kin taba fada min sunan wanda zaki aura ko?” “Eh Abdull” Ya dago ya kalleni. “Yana da mata kika ce idan ban mata ba” “Eh da yara uku matarsa ya haihu na hudu” Ina jin sautin hade yawunsa. “Amman kin taba ganin matarsa?” Na dan kawar da ido daga kallonsa sannan na amsa. “Eh na taba ganinta ya nuna min hotonta” Ya langwashe halshensa. “Kin san sunanta?” “Safeena your ex-” Murmushi yayi ya jinjina kai yana juya idanuwansa like na bashi mamaki sosai, kamin ya kalleni. “Kin san duk wannan kuma kika yarda zaki auri Abdull?” “Ba mutumen kirki ba ne?” “Ban san komai a kansa ba, amman na san komai akan Safeena, ba zaki iya kishi da yarinyar nan ba, she's criminal” Na dan tabe baki. “Bana jin zata yi kishina, ai kai take so kuma kai take kishi, me zai saka ta yi kishin mutumen da bata so indai har da gaske bata son shi” “Mijinta ne uban yayanta taya ba zata ji kishi ba, kuma ni ban taba fada miki cewar bata son shi ba, taya zata ki mutumen da shi ya tsamota daga ruwa a lokacin da na jefata?” Na daga kafaduna not knowing what to say yanzu kuma. Ajiyar zuciya ya sauke ya kwantar da murya ya ce. “Noor me kika fadawa Safeena?” Na kalleshi da sauri daman na san za a zo gurin. “Me tace na fada mata?” “Sirrin da na yi dake ta zo ta fada min duk abun da kuka yi, saboda me zaki nuna mata cewar kin san abun da yake tsakaninmu” Na ciro wayata daga aljihun rigata na nuna masa sakon da ta turo min, kamin wani abu ya tsikare ni kamar zan yi fada na fara magana. “Ganin na yi tana neman daga min hankali tun kamin na shiga, ni kuma ba na yi aure ne saboda na je na fito ba, bana son aurena ya sake rabuwa sai idan mutuwa ta raba” “Amman sai ki yi amfani da wata hanyar ba wannan ba, ke yarinya ce, baki gama fahimtar duniya ta mutanen cikinta ba, ba ki san illar abun da kika ba sai bayan ki aikata” “Ba ni da wani weapon na yakarta sai wannan” “Amman wannan sirrina ne, na fada miki ne saboda na yarda dake and i need someone to talk to, taya zaki aikata abun da zai iya janyo matsala ya janyo miki?” Zan yi magana ya daga min hannu ya nuna min yatsa. “Look Noor ina da yara, mahaifina yana raye ina da yan'uwa da abokaina, ko kadan bana son abun da zai zubar min da mutunci, na fada miki damuwata ne saboda na yarda dake, kuma ina jin kusanci da zuciyata, ba dan ki bayyana ma duniya ba, na san na aikata abun a lokacin da idanuwa suka rufe shekaru suka tsirewa tunani, and now i realize na yi wa kaina babbar barna and i regret it, you shouldn't discuss this with anyone!!” Ya bude motarsa ya shiga ya bar ni a tsaye ina kallonsa hawaye na sauko min, domin be taba rufe da fada irin na yau ba. Har yayi baya sai kuma yayi gaba ya faka a inda ya faka dazun ya sake bude motar ya fito ya tsaya kusa da ni. “I'm sorry, Na san na kaurara amman Noor ban ji dadin abun da kika yi ba, wannan sirrina ne, be kamata kowa ya ji ba ” “Bana hira da kowa, ban taba fadawa kowa ba, kuma ita wanda ta ji daman ai ita abun ya shafa” Na bashi amsa cikin sautin kuka. Idonsa ya sauke kasa yana sake fuskarsa. “Bana nufin sakaki kuka ko kara miki damuwa akan wanda kike ciki, amman ni abun da kika aikata yanzu zai daga min hankali ya saka ni a damuwa, waya sani ko zaki sake fadawa wani? Kuma Safeena ba zata zura miki ido hakan nan kawai ki cigaba da rayuwa a free ba, bayan kin san sirrinta, ni da ita duk muna da iyali, ki rika duba wannan kamin ki aikatawa wani abun Noor” Na share hawayena. “Ta je ta bata ni gurinka ko?” Ya rufe ido yana murmushi sai dai hakan be hana ni fahimtar damuwar dake shimfide a fuskarsa ba. Bude ido yayi yana min magana a hankali. “Bata iya wannan, babu wanda zai iya wannan ma, just be careful yanzu Safaeena tana kiyayya dake ta kofa uku ne, Allah ya tsareki kuma ya baki zaman lafiya, amman Bestyna Noor ina son ki sani ko mutuwa na yi bana son na tafi na barwa ƴaƴana abun kunya” “Ni ma ba zan so haka ba, kuma na maka alkawari daga wannan ba zan kara ba, kuma babu wanda zai ji” Yayi tattausan murmushi da ya kara masa kyau. “Thank You, Allah ya tabbatar miki da alheri” “Ameen” Ya sake Bude motarsa zai shiga. “Shikenan tafiya zaka yi?” Ya juyo “Ko kina da bukatar wani abun ne?” Na girgiza kai. “I will miss you alot” Yayi murmushi ya sauka kansa. “Akwai abun da kike bukata na auren Noor? Akwai abun da Baba be miki ba?” Na girgiza masa kai alamar aa. A ganina kamar be kamata na dora masa nauyin komai ba, kuma ai da kunya na bukaci kayan daki a gurinsa, domin su ne kawai nake saka ran Baba ba zai yi min ba, shi ma kuma ba ni da tabbaci. “An yi komai” Yayi murmushin dake nuna kamar be aminta da ni ba. “Sai wata rana” Wannan karon be sake kallona ba ya shiga motarsa yayi mata key ina tsaye ina kallonsa har na daina hango shi. Wata kila shi kam ba zai yi marmarina ba kamar yadda anke jin kewarsa tun a yanzu, ba mu wani dade a tare ba amman shakuwa mai karfi ta shiga tsakanina da shi. Bayan tafiyarsa ne fahimci na yi katobara na bayyana ma Safeena na san komai a tsakaninsu ba dan ita ba, sai dan shi wata kila hakan zai iya haifar masa da matsala, sai dai iya abun da na sani shi ne, Safeena ba zata yarda asirinta ya tonu ba, domin tana da aure da yara kamar yadda ya fada, ni kuma ba zan sake tattaunawa da kowa akan matsalar ba. Hakan da na yi ya saka na samu yanci gurin Safeena, mijinta ma ya samu kwanciyar hankali domin ana sauran kwana biyu a daura aure nake tambayarsa ya Safeena sai yake cin yanzu ai ta fahimci, tashin hankalinta ba zai hana aurenmu ba ta shafa masa lafiya. A raina na ce ko dai ta fahimci Ni din ba kanwar lasa ba ce ta bawa kanta lafiya da ni. A daren ne yayi ta damuna da maganganu da be sana yi min ba, hakan kuma ya raunata yarda ta ya haifar min da tsoro akansa, sai dai na lura shi kam sam baya kunyar fadar haka, wata kila saboda ya taba auren ne, ko kuma yayi zaton a aurena na farko na san komai kamar shi. A yadda na lura Abdull irin mutanen nan masu masara kunyar ido da furta komai a take. Ni dai bana iya cewa komai idan ya jefeni da wani kalamin, na kan ji kaina yayi girma kunya ta rufe ni. Washe gari gidanmu ya cika da yan'uwa mahaifina wadanda suka zo shirye shiryen abubuwan da za'ayi, ta hirar da Baba yake da su ne na ji yana fadar mai gidan Nabil wato Kareem yana da kirki da mutumci sosai. “Yanzu bayan daukar nauyin karatun yaron nan da yayi, auren nan da za'ayi sai da ya same ni a majalisa ya damka min kudi mai yawa wai na kara na yi hidima, Allah dai yayi masa albarka ya yara masa yaransa, wutar nan ma da ta taso tsakanina da yan'uwan Hafizu shi ya kashe ta” “Ai wasu masu gida haka suke da taimako da kirki, musamman idan sun san baka da shi, wasu kuma suna bakincikin abun da zaka samu ma” Cewar Baba Garba. “Haka ne, ni farko ma na dauka shi zai ce yana son Noor ne, kuma na ga kamar ba haka ba ne, ai ba dan kar ta ba ni kunya irin na wacan karon ba, Wallahi da sai na aura masa ita saboda kunyar abun da yake min, ya rike amanar abota” Jin hakan a gurin Baba ya saka na ji Kareem ya kara kima a idona, tabbas shi din mutumen kirki mai son taimako, babu ruwansa da duba matsayi ko girma. Haka dai na yi ta jin suna ta hirarsu ta yan'uwa yana fadin mutanen da suka taimaka masa a yanzu da kuma aurena na farko. A lokacin da suka dauko zancen abubuwan da zai kai na ji Baba Garba yana tambayar Baba. “Toh yanzu kai Magaji ka siyo mata kayan dakin ne?” “Ni babu abun da na siya kuma babu abun da zan siya, ai ya fada mana da zarar an daura aure za su wuce can Lagos din da ita, to taya za a tsaya wani siyen kaya nan tun da nan za su zauna ba? Dubu hansin zan bashi a cikin kudin sadakinta idan sun je can ya siya mata abun da ya kamata” Anty Larai ta ce “Aa gaskiya be dace ka yi haka ba, ai ana son ka siyama yarka girma, ko dai ba mai tsada ba kowa ya san karfi ba daya ba, sai ka mata na iya karfinka saboda Allah magaji” “To wai me za'a siya ma? Uwarta ta aiko mata da kaya, kuma ba a nan za su zauna ba, ai kayan sun isheta komai” “Kayan da ta aiko mata kayan kitchen ne, kai kuma naka kayan daki ne da dan wani abu da za aka bawa ango” “Aa aa aa karya haram ba zan iya kashe kaina ba, yarinya suka ce suna so ita za a ba su, ita da Allah yayi jininta jinin masu kudi me zai kai ni wahalar da kai na siye wasu kayan daki? Hafizu ma Allah ya masa rahama da kansa yace ba zai na yi komai ba ya dauke min komai” “Toh shi wannan ai be ce ba, gaskiy...” Bata karasa ba Baba ta tari numfashinta. “Ni fa dan abun da na samu, gyaran gidana zan yi na kuna kallon yadda gidan nan gaba daya ya canja babu wani taimako da na samu, sauran kuma sai na bude shago na zuba kayan masarufi” Jin cewar Baba ba zai yi min furniture ba ya disashe farinciki dake zuciyata, wata kila shi din ba kamar Hafiz ba ne da zai ce ya yafe komai, hakan kuma wani abun gori ne a gurina da danginsa da ma kishiyata. A ranar aka yi min kunshi mai kyau mai ja sosai, da dare kuma Hana da kawata Zainab suka raka ni na tafi gurin gyaran gashi domin ni ba mace ce ma'abociyar son kitso ba. A nan na samu damar fada musu damuwata, Hana ta nuna damuwata da jin cewar Baba ba zai siya min komai ba har ma take cewa. “Yanzu da ace Mama bata aiko da wannan ba haka za'a kai ki ko spoon din aiki ba ki da shi?” Na sake jin babu dadi domin Baba baya kyautata min a rayuwa, wasu hakokan da ya kamata uba ya saukewa yarsa shi baya sauke min su. “Noor kar hakan ya daga miki hankali, Baba ya fadi gaskiya idan ba nan za su zauna ba, babu amfanin siyen kaya, daukar kaya daga Kano zuwa Lagos wani aiki ne babba, kuma kin ga yace ba a nan za su tare ba” Zainab ta shiga kwantar min da hankali, na dube ta na ce. “Amman wasu ko ba a garin za su zauna ba, ana yi komai Zainab a garin da miji yake, saboda can aiki yake yi ai, wata rana zai iya dawowa mahaifarsa” “Ki gode Allah Noor, idan mijinki mai sonki ne duk ba zai ga wannan ba, kuma zai rike ki amana, idan ma Baba bai miki ba ke zaki iya yi ma kanki ko kuma shi mijinki yayi miki, dan Allah ki kwantar da hankalinki Noor” Duk yadda zata karfafa min guiwa sai da ta yi har ta yi nasarar kwantar min da hankali na dan sake raina. A napep muke ta labarin Zafeer da sabon auren da aka ce yayi a gurinta nake jin labarin irin hidimar da aka yi na bikin auren domin Zainab tana abota da kanwar Zafeer sosai, shi ma kuma yana good time da ita ko a lokacin da muka samu matsala ita yake aikowa gurina. “Amman kin ga yana dariya?” Na tambaya ina jin bakinciki marar misaltuwa kamar ba ni na fara guje masa. “To zai ki dariya ne Noor? Ai dole yayi farinciki ko yaya ne, wata kila ma yanzu ya manta da soyayyarki, domin yar masu kudi ya aura ance mahaifinsa ma shi zai sama masa aiki, daman ita yarinyar tana aikinta, ance ta girme shi da shekara uku” “Allah ya saka masa tun ba ayi nisa ba, ya samu wadda ta fi ni komai” Na fada hawaye na sauko min, Zainab ta dube ni. “Noor har yanzu kina son Zafeer wai?” “Unconditionally, har abada zuciyata ba zata daina son Zafeer ba, ba zan taba son kowa kamar yadda na so shi ba” Shiru ne ya biyo baya babu wanda ya sake cewa Uffan daga ni har su. Har muka isa gida hawaye nake, haka na shiga gida rai babu dadi zuciya na kuna, kiran da Abdull yayi ta min ma kasa dagwa na yi saboda damuwar data haifar min da ciwon kai. Washe gari ya Friday gidanmu ya cika da makota da yan'uwa na kusa da nesa maza da mata, kusan wannan bikin ma kamar ya fi wacan yawan jama'a. Bayan saukowa daga Massallaci na fita waje na yi alwala na shigo dakinmu kenan wayata ta yi kara, dubarwa da zan yi sai na yi arba da number Abdull, a take na amsa kiran na kara wayar a kunnena. “Hello...” “Congratulations an daura aurenmu, Alhamdullahi” Gabana ya fadi har sai da kaina ya sara, kai kace ban tsammaci zuwan wannan ranar ba. “Allah ya ba mu zama lafiya” “Ameen” Ya amsa sannan ya kashe wayar, shi ne mutum na farko da ya fara min albishir, kamin gidan mu ya dauki guda har Hana ta shigo dakin tana rangwada guda tana farinciki, sabanin wacan auren na farko da bata yi farinciki ba. Madadin na yi murna sai na fashe da kuka na zube a gurin an rufe idona ina ta rutsar kuka kamar wanda aka sake yi ma auren dole. Haka na wuni ban iya cin komai ba, sai da Anty Larai ta siyo fura ta dama min ta saka kankara sannan na iya sha shi ma ba da yawa ba, yan'uwan Abdull sun leko mana wuni, daga bangaren mahaifiyarsa da kuma na mahaifina. Angon kuma be duro gidan ba sai isalin karfe takwas na dare. A lokacin da na kira a waya ya sanar min yana waje, sai na jin kunyar fita a dole na yi masa karyar Gwaggonta tace ba zan fito ba. Ban san da wa yayi magana ba, sai ga Baba ya shigo yana fadin na tashi na leka waje mijina ya zo tare da abokinsa yana son magana da ni. Jin cewar yana tare da wani ya karfafa min guiwa kuma ya rage min kunyar da nake ji ta mutane. Hana ta dauko turare ta kara fesa min, Anty Larai kuma ta saka na cire lace din dake jikina na saka farar lafaya sannan na fita gashin kaina na yawo domin ban saka ribbon ba. Nesa da gidanmu ya faka ta inda mutane ba za su ganshi ba, ni ma ba dan na kira shi a waya ba ba zan iya gane shi ba. Kamar ana daure min kafafuwa haka na karasa gurin motar sai ya sauke gilashin ya kunna hasken wayarsa ya haska fuskata. “Amarya ba kya laifi, kyakkyawar amarya mai tsaye siririya duk ni kadai” Kunya ta saka ni sauke kai kasa ina murmushi. “Shigo motar mana, kar na gajiyar da matata” “zan iya tsayuwa a nan” Bude motar yayi ya fito ina kallonsa ya kama hannuna ya zagaya da ni ta baya ya saka ni a back seat sannan shi ma ya shiga. Rabon nake ko zan ga abokinsa amman ban ga kowa ba. “Ka ce kana tare da abokinka...” “Na fadi haka ne saboda na rage miki kunyar dake kanki” Ya yana maganar kallon bakina zuwa kirjina. “Ko ban kyauta ba?” Kamin na amsa na ji na kara matsowa kusa da ni sosai har ina jin numfashinsa, ta dama da ni ya lakamo hannunsa yana lasa cikina a hankali. “Ya gajiyar biki?” “Alhamdullahi” Ina kokarin cire hannunsa sai ya juyo da fuskata zai sumbance ni, na dauke kai na dauke numfashi ina jin wani iri. Murmushi yayi ya saka dayan hannunsa ya juyo da kaina. “Da alama dai kunyar nan zata cutar da ni” Ya sumbanci goshina ya shinshina hancina kamar mai kokarin tantance wani abu. Rufe ido na yi jikina ya hau bari ina jin wani bakon al'amari. Hakan kuma be hana shi kai bakinsa cikin nawa, sai da na ji yana kokarin wuce gona da iri tukuna an matsa baya na rike hannunsa. “Abdull za a iya ganinmu fa” “Babu wanda zai gani bakin gilashi ne” Ya sake kai hannunsa a jikina sai na tare. “Baba zai ga na dade” “Me yasa kike ta guje min ne Noor? Kin san how long nake ta jiran wannan ranar? Ni fa yanxu halalinki ne” “Na sani amman ban tare ba, kuma na fito gida ne da sunan zaka yi magana da ni” “An riga an daura ko da sadakin da na biya kin zama mallakina balle kuma an daura, sadaki shi ne aure ai wasu da zarar an biya sadaki ma suke sakewa juna balle mu da har an daura mana aure” “Auren dai shi ne gaskiya, amman biyan sadaki ba aure ba ne, tun da har ana daura mana ai ya kamata mu yi hakuri har zuwa lokacin da za mu tare babu dadewa” “Allah yasa zan iya jira, sai monday zamu bar garin nan Noor, kuma ba wani abu zan aikata da ke ba a yanzu, it's just a kiss, ina kokarin wayar da ke kamin mu tare domin na lura kamar baki gama fahimtar rayuwa ba” Na yi murmushi karfin ina mamakin yadda yake da rawar jiki haka, kuma ina yaba kokarin Hafiz na jurewa da yayi ashe shi din jarumi ne sosai. Na matsa ta gefen da kofar take na bude na fita. “Sai da safe” “Sai da safe my shy Bride, an hana ni kiss ko? Zan rama” Murmushi na kawai abun da na yi na fara takawa ina tafiya har na isa cikin gidanmu. A dare wata kanwar Mama ta cika min ciki da wasu kayan mata har sai da kaina ya fara ciwo. Haka na kwashe kwana biyu ana ba ni abubuwan nan da bana bukata, ban kuma isa na ce aa sai a rufe ni fada. A cikin kwanakin da na yi a gida bayan daura auren, babu ranar da Abdull baya zuwa da dare a kowa dare kuma sai yayi kokarin taba ni har ya wuce gona da iri. Baba yayi min nasiha da kuma jan kunne, ranar Lahadi Mama ta aiko da mota aka dauki zuwa gidanta ta yi nata nasihar, acan na kwana sai washe gari na dawo. Na dawo gidan na tarar Hana ta gyara min kayana ta kintsa komai, a take na fara jin kewar gidanmu duk kuwa da kasancewar ba wani dadin zaman gidan nake ji na. Ranar Monday da misalin karfe 2pm Abdull ya iso gidanmu tare da wani abokinsa da kanensa mata biyu da sunan za su dauke ni. Sai Baba ya tsayar da shi jege suka tattauna, ban san me suka tattauna a kai ba, bayan sun gama na fito ina sanye da green abaya da mayafinta sai mask da na saka na rufe fuskata. Handbag dina tana hannuna tare da wayata da karamin akwaitin da yace da shi kadai zamu tafi a yanzu saboda jirgi zamu shiga. Yace daga baya zai aiko da mota a dauki saura kayan nawa da kuma yan'uwana domin su ga gurin da muke rayuwa. Da ace ina da iko da tun a yanzu zan tafi da Hana domin ta rage min kewar gida da kuma bakuntar gurin da ban sani ba. Na yi kuka sosai ina jin kamar wata kasar zan tafi ba iya Lagos ba. Har gurin mota Baba ya rako mu tare da Hana da Umma, na shiga gidan baya tare da kanensa shi kuma yayi ma Baba sallama ya shiga front seat kanensa kuma yaja motar sai airport.... Ban taba ganin airport a fili ba sai a ranar da muka isa gurin, ashe babban guri ne mai hada hadar jama'a mun zauna a wani guri jiran jirgin bayan an gama yi mana check-in. Id card din dake hannuna nake ta kallo, sai dai zuciyar da tunanin yana can wani guri. Hannun Abdull na ji cikin nawa yana kokarin saka yatsunsa cikin nawa. “Amarya are you Okay” Na kalleshi sai na ji hannunsa a fuskata yana share min hawayen da ban san taya suka zubo ba. “Har kin fara missing din gida ne?” Ban yi magana ba na kalli kanensa dake can gefe zaune suna ta hirarsu, jira suke har sai jirginmu ya tashi sannan su koma gida. “Ka yi min wani alkawari” “Cewar ba zaka taba cutar da ni ba” “Me yasa kika fadi haka Noor” “Ba komai ni dai ka yi min alkwarin rike ni amana, ina fatan wannan auren da muka yi mutuwa ce kadai zata raba” “In Shaa Allahu, na miki alkawari ba zan taba cutar da ke ba Noor” Ya ba ni tabbacin da nake bukata sannan ya amsa kiran dake shigowa wayarsa ban san da wa yake magana amman na ji yana fada masa lokacin da zamu sauka. Ni kuma na juyar da kaina ina kallon wani gafen. Kalamansa sun saka na ji hankalina ya kwanta, na samu natsuwar da na rasa. Na sani mutum ba zai taba samun abun da yake so dari kan dari ba, shiyasa na yarda da wannan kaddarar kuma na shiryawa wannan zaman aure da dadi babu dadi zan zauna, ko da Abdul zai rika yanka naman jikina ya siyarwa ne. Zan jure ko wace kalar azaba da ukuba ko da kuwa ita ce zata yi silar ajalina... An samu delaying gurin tashin jirgin, karfe biyu da mintuna goma sha biyar ya kamata mu tashi amman ba mu tashi ba sai misalin Karfe uku daidai muka tashi daga filin jirkin saman Aminu Kano, bayan mun yi bankwana da yan'uwan Abdull, har na ji ina ma ace ni ma nawa yan'uwan sun rakoni kamar yadda na shi suka yi. Abdull ne ya saka min belt ya sakawa kasa ya rike hannuna ganin yadda nake jin tsoro sosai lokacin da na yi arba da jirgin for the first time. Sai da muka yi nisa da kasa sosai jirgin ya fara tafiya sannan ya cire min belt din shi ma y https://chat.whatsapp.com/Jd2OwsAcXE7EjI7NHeFQV0 Can cikin bachi na ji ya taba an taba ni, hakan ya saka ni bude ido sai na ga wutar dakin a kunne. “Taso mu yi magana” Ya riko ni na tashi zaune ina sanye da kayan bachi wando ne da ya tsaya oya cinyata dai karamar riga marar hannu. Shi kuma yana sanye da pajamas dark green. “Me ya faru?” Na murza ido. Ajiyar zuciya ya sauke ya kama hannuna ya rike. “Noor ina son ki fahimce ni please, ba wai bana son haihuwa ba ne kawa...” “Indai maganar zubar da ciki ne, zai fi maka kyau ka tafi ka kwanta, ba zan zubar ba Abdull” Ya kara sassauta muryarsa alamar rarrashi. “Baki gane ba, ni gani nake ma kamar ba zaki iya haihuwa ba, kalli kunkurunki ma fa, karami ne sosai kuma be kamata ki fara haihuwa da kurciyarki kamar haka ba, Safeena ma sai da muka yi shekara biyu tukuna ta fara haihuwa...” “Babu wasu kalamai da zaka iya daure ni da su Abdull, ni dai kawai abun da zan roke ka ka aje sirrin nan a tsakaninmu, bana son yar'uwata ta san mijina ya juya min baya, kuma bana son ta san baka son abun da zan haifa, mu kwana lafiya” Na juya na kwanta na ja bargo na lulluba har kaina. Kwafa na ji yayi ya tashi ya fice ba tare da ya kashe min wutar dakin da ya tarar a kashe ba. Tashi na yi zaune na ina hawaye. Daren be mini dadi ba saboda haka ban runsa ba. Sai bayan na gama sallah na kishingida jikin gadon dake dakin sannan bachi ya dauke ni kadan, domin ban dade ba na farka saboda kiran da yake ta kwala min kamar zai tashi gidan. Na zabura na fito falon ina kallonsa. “Karfe Nawa ace baki hada abun karyawa ba? Ko salon na yi magana ki ce layi kike ke ga mai ciki” “Zan shiga na hada yanzu” Ita ce amsar da na bashi sannan na cire hijabina na aje akan kujera na shiga kitchen na fara dora ruwan zafi, ina tsaka da soya kwai amai ya taso min domin bana son karnin kwai a yanzu. Da gudu na fito na shiga bandaki na yi amai na wanke bakina da hannuna da fuska sannan na fito na shiga ba da aikina. Sai da na gama hada masa komai na kawo a dinning na aje sannan na koma kitchen din na gyara shi. Na fito cike da gajiya sai na ganshi da shirinsa na fita. Kallon mamaki na yi masa kamin na yi magana ya ce. “Ba zan iya cin wannan breakfast din na kazanta ba, sai ki zauna ki ci” Wani bakincikin ne na ji ya ratsani, yanzu ya san ba zai ci ba kuma ya saka na girka? Ai ya sani dole zan yi amai me yasa be girka da kansa ba? Da kallo na bishi har sai da ya kai kofa sannan ya juyo ya kalleni ya ga har lokacin kallonsa nake na ma kasa motsawa daga inda nake tsaye. “Barakallah Maa Shaa Allah, babu abun da zaki iya yi da ni, idonki ko mugun nufinki a zuciya ba zai min komai ba, na sha tabara na sha yasin nan gani nan bari Abdullahi kam, duk wani nufin da kike da shi akaina sai dai ya koma kanki lafiya zan tafi lafiya zan dawo kuma lafiya zan cigaba da rayuwata” Ban san lokacin da hawaye ya zubo daga idona ba. Shi kuma ya bude kofar ya fita ya bar ni rumgume da bakinciki. A gurin na zauna ina tambayar rayuwa me yasa take min haka? Ina tunanin kamar na dace sai kuma wannan ya bullo min? Kamar an karfafa min guiwa haka na ji sai na mike ina fadawa kaina cewar zan iya jure wannan ma kara bakincikin gidan miji da wanda zan fuskanta a gidanmu ko unguwarmu. Dakina na shiga ina gyarawa ina mamakin wai haka Safeena take rayuwa da shi idan yana kusa da ita ko kuma dai ni yake yi ma haka saboda baya son haihuwa? Wata kila shiyasa take son Kareem sosai take ta rufe ido tana aikata abun da zuciyarta take so. Waya sani ko ita ma bata jindadin zama da shi. Na yi zaton shi zai aika mata da kudin mota ko ya siya mata ticket din jirgi ta zo ta jirgi amman be yi ko daya ba. Dan kudin da nake samun gunsa ne lokacin da yake so na na hada na bawa Mai gadi ya saka mata a pos ta account din mai pos din unguwarmu. Sannan na fada mata ta rubuta number wayata a takardar saboda idan ta iso ta ari wayar wani ta kira sai a na fada mata inda za a kawo ta. Sanin dakuna biyu ne a gidan ya saka na kwshe kayan Abdull da suke dayan dakin na dawo da su dakina kamar yadda suke a da, domin ba zan kwana da ita a dakina ba shi kuma ya kwana a daki daya dabam, hakan ma be dace ba, kuma zata iya fahimtar kamar ba ma zaman lafiya tsakaninmu. Ana gobe zata taso sai gashi ta kira ni da bakuwar number ta fada min karamar waya ce Mama ta bata tare da layi a ciki, kuma ta kara mata wani kudin da zata rike saboda expensive na hanya. Na jidadi sosai hakan zai taimaka mu rika communication kamin ta iso. Washe gari misalin 6am na kirata domin ta fada min tun asuba zata tafi ta sha. Duk bayan awa daya sai na kira ta fada min yanzu suna guri kaza da haka dai har suka sauka Lagos. Na fada mata sunan unguwarmu ta tari okada ta hau, a nan sai da aka kara bata lokaci saboda yamma ta yi, akwai cinkoson mutane sosai. Ina jin an taba gate na fito daga falon da sauri na, a lokacin da muka hango juna ni da ita sai murna ta bare na je gurinta a guje ita ma ta yo kaina a guje ta bar jakar kayanta a gurin tana murna. Tsalle nake ina direwa tsabar murna da jindadi na ga yar'uwata, domin na san abubuwa za su zo min da sauki. Mai gadinmu ne ya riko jakarta ya shigo da ita cikin falo, sannan mu ma muka shiga ina tambayarta ina Mama ina Baba. Sai da ta huta na kawo mata indomie da na dafa ta ci sannan take ba ni labarin yadda aka yi ta rigima kamin Umma ta amince mata ta zo saboda ganin take idan Hana ta zo sana'ar da take zata gurgunta babu mai fitar mata da awara. Abdull be dawo gidan ba sai misalin 10 na dare, ina zaune falo ina kallo ya shigo fuska babu annuri, a lokacin Hana ta yi bachi a dakin da na nuna mata zata rika kwana. “Sannu da zuwa” Yayi kamar be ji ba ya nufi dakin. “Hana tana ciki na maida kayanka a dakina tare zamu rika kwana har sai ta tafi” Ya juyo ya kalleni. “Saboda kin raina ni ko saboda me? Vabu sanarwa babu komai zaki kwashe kayana ki kai can, kuma ki aje ta nan?” “Amman dai ai ba falo zata kwana ba? Kuma zai yiyu na kwana da ita daki daya ba alhalin kana mijina, na fada maka bana son kowa ya san zaman da muke yi, amman idan haka ya bata maka rai ka yi hakuri” Guntun tsaki yaja ya wuce dakina ba dan ransa ya so ba. “Allah ka ga halin da nake ciki, Allah ka shirya min mijina ka karkato da shi ya fuskance ni” Na yi addu'a na shafa sannan na mike tsaye na bi bayansa. Washe gari ma be ci abun da na girka na breakfast ba saboda ni na girka, Hana tana daki tana ta bachin gajiya bata farka ba sai 11am a lokacin Abdull ya dade da barin gidan. Tsintsiyar dake hannuna ta karba. “Kawo na share miki ba dan halinki ba” Na kai mata dudu a baya daman ta fini naman jiki, ni babu komai a jikina sai kashi ba kamar ita ba da take da cikar gaba da jiki, wasu har cewa suke ma ni ce kanwa ita ce Yaya. Ta share gidan tass ta gyara ko'ina sannan ta dora mana girkin rana bayan ta gama cin nata breakfast din. A nan ma mun sha hira har Mama ta kira a waya muka gaisa, na kira Baba muka gaisa sannan ya fada min Hana ba zata dade a gidanmu ba, da zarar na fara jin sauki zata dawo, a haka din ma na yi masa godiya domin yayi kokari da ya barta ta zo ma. A ranar ma Hana bata ga Abdull ba, washe gari ma ko da ta tashi ya tafi aiki, har take tambayar su basa samun sukuni ne tun safe suke fita kuma basa dawowa sai dare yayi sosai, na yi mata karya da cewar yanayin aikin ne yanxu a haka. Sai da ta kwashe kwana biyu a gidan sai a rana ta uku suka hadu kasancewar weekend ne, babu aiki kuma ita take girma mana abun karyawa a yanzu, na jidadin ganinta da yayi burina ya fahimci ba ni nake girkin ba a yanzu ya rika ci saboda kar yar'uwata ta zargi wani abu. Sun gaisa cikin mutunci yayi mata ya gida ya mutanen gidan duk ta amsa da lafiyarsu kalau. A ranar ni da ita da shi duk a dinning muka yi breakfast ina ta Jefa masa hira sai ya ga dama yake amsawa, arziki na daya be fadi wata maganar marar dadi ba, har muka gama. Sai da zai tashi yake tambayar wa zai girka abinci a yau. “Hana zata girka ai ita take girkawa a kullum yanzu” “Me za a girka?” “Me kake so?” Na tambaye shi sai ya kalleta. “Kin iya dambu?” “Babu abincin da Hana bata iya ba, ta fi ni kokari ita bata jin wahalar aiki da girki ma” “Sai na ci na ji zan tabbatar” Ya amsa ba yabo ba fallasa, kamar dai bakar magana kuma kamar a bakin gaskiyarsa kenan. Na yi murmushi “Shikenan sai ta baka mamaki kuwa” Ya kalleta kadan ya dauke kai. “Za mu gani” Na yi dariya ita kuma ta yi murmushi. Sai da ya bar dinning sannan take fada min next time zata zuba nata abincin ta ci a dakinta. “Why?” “Ni dai kawai na fi jin sakewa, ki bar ni na ci a dakina ku kuma ku ci a falo” “Shikenan ba dole ai sai rai na so” Na fada mata ina dariya. Ya ci abun da ya girka da rana saboda a gida ya wuni, be yaba ba amman kuma be isa yace be yi dadi ba domin kowa ya ci dambu a ranar ya san yayi dadi. Da haka dai har ya gaji ya fara yabawa idan ta yi girki, wani lokacin har cewa yake a sake yin jiyar jiya. Sannu a hankali ya fara sakewa da ita ita ta dan sake da shi har sukan zauna su yi hira a falo. A gaba ranar yake tambayar makaranta ta fada masa ta kare amman bata cigaba gaba ba saboda tana jin Baba ba zai aminta ba. “Indai haka ne sai mu rike ki a nan a saka ki a makaranta, ga makarantu masu kyau a nan, kuma da ganinki zaki yi kokari ba kamar Noor ba” Na kalleshi da sauri ina hade rai irin na wasa, jin yana shigar mata a yau, domin idan yana wasa da ita nuna yake na fita iya komai alhalin ya san kuma ta fi ni. “Yau kuma?” Yayi saurin kai hannu ya taba ni. “Ke wasa nake, ta ina zata fi Mamata kokari, kawai ina dan zuga ta ne kar ta ji babu dadi” Muka yi dariya dukanmu. After magariba ya fita titi zagayawa, ni kuma na yi dawo falon na zauna inda Hana take cin abinci. “Noor gaskiya yanzu kam kin dace, yadda kuke rayuwa da Abdull abun ya burgeni Allah yasa hakan ya dore” “Ameen” Na amsa ina hamma, domin tun da na shiga wata na hudu nake ta yawan bachin dare, da zarar an yi magariba zan fara jin bachi sosai. Sai bayan sallah isha'i ya dawo tare da tsarabar suya. Hana ta dauko katon plate aka zube kamin kowa ya kai hannu ni har na kai baki tare da albasa da tumatir. Sai da ya ci yanka biyu sannan ya kalli Hana ya ce. “Ci mana” Sai ta mike tsaye. “Bari na dauko plate a saka min” “Kamar ya? Ki saka hannu mu ci a tare, hana karki zama bakauya yar zaria mana” Muka kwashe da dariya daman kowa ya san yan zaria bayin kanawa ne. “Ni dai zan fi jindadi na ci ni kadai” “Wallahi ba zan zuba ba, idan ba zaki zo ki saka hannu mu ci tare ba sai dai ki hakura ci” Jin yayi rantsuwa cikin zafin rai ya saka ni ma na yi mata magana sai ta dawo fa zauna ta saka hannu muka fara ci a tare dukanmu, har hira ta biyo baya yana fada min gurin wani basakkwacce mutumen yabo ya siyo suyar nan. A take kuwa Hana ta saka santi. “Har na tuna da wani kilishi da Mama ta ba ni da naje mata bankwana tace daga Sokoto aka zo da shi a local government Dange, Dangin kilishi” Muka saka dariya har sai da na sarke, ita kanta sai daga baya ta gane santi ta yi. Na jidadin yadda Abdull yake kula Hana, da farko na yi zaton wulakanci ne zai biyo bayan zuwanta gidan, sai gashi har da ni ya canja min na samu sassauci, na yadda yake mu'amala da ni daga samun cikin. Sai dai kuma a duk tsawon lokacin Abdull baya kai hannunsa balle jikinsa a nawa, zamu kwana a gado daya mu tashi amman ba zai ma bari ko a kafadarsa na kwanta ba. Na yi masa uzurin wannan saboda na san baya son cikin, wata kila yana hora ni ne har yanzu. Ta dayan bangaren kuma bana mamakin kaurace min da yayi, musamman a yan kwanakin nan da nake yawan farkawa tsakar dare na ga baya nan amman ina jin motsin ruwa a bandaki, wata kila yana biyawa kansa b*ka*ta ne saboda ya kaurace min gaba daya. Ranar da Hana da cika wata biyu da sati biyu a gidan ta fara min zancen komawarta gida, saboda Baba ya matsa ta dawo, kullum ya kira waya fada yake mata, bata dawo ba. Sai tace masa ban ji sauki ba, da muka kai shi makura sai ya rufe mu da masifa daga ni da har ita yana ta zaginmu a waya. Washe gari friday kamar kowace jumma'a ya shirya cikin manya kaya na malam bahaushe yana ta kamshi, yana tsaka da saka agogo na ce. “My Soul jiya Hana ta yi min zacen tafiya gida” Ya juyo ya kalleni. “Tafiya gida kamar ya?” “Gida dai wai tana son ta koma saboda na fara jin sauki, kuma Baba ma ya matsa gaskiya Saboda Umma take yi ma sana'a” “Aa ba yanzu ba, ta bari sai kin haihu tukuna, idan zaki koma gida sai ku koma tare, ko ma ku yi zamanku a nan gaba daya” “Baba ba zai yarda ba, yayi ta mana fada jiya fa sosai saboda dawowarta, wai taje ta zauna” “Toh wai idan ta koma me zata masa ne?” “Babu fa kawai tana yi ma Umma talla ne ina tunanin Umma ke zugawa ta dawo, saboda sana'arta” “Ki yi magana da ita ta yi hakuri ta zauna a har sai kin isa haihuwa mana” Zan yi magana ya riga “Bari na yi mata magana” Ya juya ya fita, sai na sauka daga kan gadon na bi bayansa. A falo muka same ta zaune tana rike da remote. Abdull ya fara mata magana sai ta nuna masa ita bata da matsalar zama, matsalar ta Baba ce sai ya aminta. “Fada min gaskiya ko dai saurayinki ne ya matsa ki dawo” “Hana bata da saurayi for now” Na amsa sai ya wara ido yana tsokanarta. “Taya tsaleliyar budurwa irinki, ace bata da saurayi duk kyaun nan na ki” Ta rufe ido tana jin kunya. Sai yayi murmushi ya ce. “Zan kira shi na yi magana da shi, wata kila yana jin nauyi na ne shiyasa be taba kirana yayi min magana ba, idan ma ta kama na rika saka masa wani abu a account da za a rika bawa Umma madadin kudin tallarki zan yi haka, daga nan ma sai ya aiko mana da takardunki a sama miki makaranta ki samu ko nce ko diploma” Ni da ita muka kwalo ido waje ta taso da gudu ta rumgume tana tsalle tana murna, ta duka kasa tana masa godiya. Ni ma na masa godiyar ina jin kamar Allah ya amsa addu'a ta ne ya sauya masa yar rayuwar da ya fara na wulakanta. Domin kyautatawa yar'uwa ta jini kamar kyautata min ne. Be ce komai ba sai kallonta yake yana murmushi har ta dauki karamar wayarta ta kira Mama ta shiga dakinta tana fada mata. “Kanwarki ta fi ki kyau Noor, ko wani friend dina da ya zo ranar ya ganta sai da yace yana da kyau” Ya fada min kai tsaye, ba tare da fargabar komai ba na yi murmushi, ai jindadi ne a yabawa dan'uwanka a gabanka. “Tana da kyau, kuma ita tana da jiki ba kamar ba” Ya mike tsaye yana lalaba aljihunsa. “Ba wani jiki da ita sosai ba, ta dai fiki cika ne kawai. Zan tafi sai na dawo” “Allah ya tsare, ka siyo min rake idan zaka dawo” “Toh” Na raka shi har waje sannan na dawo cikin gidan. Ina jin hana tana ihu da murna kamar zata fasa gidan dan murna, na zauna kan kujera ina murmushi yau kuma ta zama kamar ni da hauka. Kamar jira ake na zauna sai na dan abun da ke cikina yayi motsi, ban taba ji ba sai ranar na bude rigar da sauri na kalli cikin, sai ya sake yin motsi da sauri. Hawayen farinciki ya cika idona na kai hannu na shafa cikin ina jin sanyi a cikin raina. It's 500 Zenith Bank Hadiza Abubakar 2451879008 And send the evidence of payment to my WhatsApp number 08036126660 https://chat.whatsapp.com/Jd2OwsAcXE7EjI7NHeFQV0 KAREEM POV. Dagowa yayi daga rubutun da yake a diary ya kalli Safeena dake zaune gabansa fuska a murtuke kamar an mata mutuwa. “I thought na fada maki bana bukatar sake ganinki?” A take ta yi murmushi. “Ta ina zaka so ganina ka samu sabuwar mace? Ka ba ni mamaki Kareem, ashe zaka iya bude zuciyarka wata ta shiga not just zuciyarka jikinka ma zaka iya hadawa da ita?” “For the very last time ko ki fita ko na saka security su fitar da ke” Wannan karon dariya ta yi. “Ashe zaka iya wulakanta ni saboda wata banzar bazara, me ta fi kwarewa akai? Karamar yarinyar kamar Noor zata dauke maka hankali” “Karki sake zaginta, tana gidan mijinki tana zaman aure noor ba karuwa ba ce, ta san mutumcin aurenta” Ta runtse ido kadan ta tauna halshenta. “Ni da kai ne ba mu san darajar aure ba kenan? Da rarrashi na zo gurin amman na lura gaba daya ta canja maka tunani akaina ta canja maka kwakwalwa, shikenan” Ta mike tsaye. “Daman na zo nan ne na ji, cikin dake jikinta na mijina ne ko naka?” Kareem ya watsa mata wani mugun kallo. “Ita fa ba fasika ba ce” “Kawai dai na tambaya ne, saboda na sani kamar yadda ita ma ta san cewa dan da na haifa yanzu naka ne” Ya kalleta without blinking try to connect his heart with his brain. “You're stupid...” Ta yi murmushi “Yau har na kai haka? Lallai Kareem kai ba dan goyo ba ne, cikin kanen lokaci ka canja min, gaba daya yarinyar nan ta dauke maka hankali, haka mijina yanzu ba shi da lokaci na” “Daman mijinki be taba lokacinki ba, dan haka karki zargi Noor, idan ya koma garin da yake manta ki yake yana can yana sha'aninsa kina na ki” “Muna na mu dai” Ta gyara masa tana kallon idonsa cikin bakin rai. “Me yarinyar nan ta tare miki ne wai? Baki da magana sai na ta” Ta zagayo Inda yake yana ganin hakan ya mike tsaye. “saboda ita ta kwace min kai, a rayuwa kai ne kadai mutumen da zaka nesanta da ni, azabar son ka ta azabtar da ni na kasa hakuri da kai, da ba haka kake ba, amman zuwan yarinyar gaba daya ka sauya min kuma ka kwashe sirrinmu gaba daya ka fada mata, har tana yakata da shi, baka jin kunyar mu'alama da mata har biyu? Bayan karyar da ka yi min akan Yusura?” “Ban taba hada shimfida da Noor ba, kuma ba zan taba ba har abada, indai har sai ta kazantacciyar hanya zan samu Noor, to ina rokon Allah ya hana min ita har abada, kuma aure take a yanzu bana fatan ya mutu, fatana ta samu kwanciyar hankali a ko'ina zata kasancewa?” Ta dan matsa baya. “Baka taba kaiwa jikinta ba? To me ya dauke hankalinka ka fada mata sirrinmu? Ba na mu'alama kadai ba wai har na haihuwar da muka yi?” “What? You're not serious? Taya za fada mata abun da ba ayi ba?” Ta matso kusa da shi tana kallon wayar idonsa. “Miye ba a ayi ba a ciki? Haihuwa ko alaka?” “Na ji na fada mata alaka, amman yaushe muka haihuwa balle na fada mata?” “Yanzu kuma kokarin wasa kake da hankalina?” “Wane irin wasa da hankali? Karya kika mata cewar mun haihu ne? Idan ma kin yi haka to kin yi akan aurenki ne kina kashe kanki ne, domin Noor baki ba linzami ce” Ta kalli gefe sannan ta sake kallonsa. “Taya zan fada mata sirrina? Kai ka fada mata, shiyasa da ta zo gidana ta fada min magana son ranta” Ya fisgota ya rike cinyar hannunta. “Stop talking about Noor, yaushe muk haihu? Are you out of your mind?” Ta fisge hannunta. “Ai na fada maka tun ina da ciki ko? A asibitin nan aka karbi haihuwa danka, kuma Wallahi jininka ne! Au kenan baka yarda ba da na fada maka? Ka dauka karya nake?” Kareem ya daka mata tsawa. “Yaushe rabon da na yi wani abu da ke? Akwai dai abun da kike kokarin yi Safeena” “Babu abun da nake kokarin yi, ni ba zan iya cutar da kai ba, amman ďan da na haifa yanzu Wallahi naka ne, last haduwar da muka yi na samu cikin, sati biyu na kara akan lokacin da nake period a satin Abdull ya dawo, yana barin garin nan naje aka min test aka ce ina da ciki dan sati uku, yaron da na haifa yanzu idan aka kalleshi kallon kurilla za a san cewar danka ne, idan baka yarda zan kawo shi ka gwada jininsa” He lost his temper when he was saying. “Baki da hankali Safeena? Taya zaki aje ciki i mean taya zaki haihu? Dan Haram ne Safeena kuma ki dauka ki kawai mijinki? Ina da aure da yaya safeena kina da aure da yaya taya zaki yi haka?” Ya fadi zaune yana rufe bakinsa. “I don't believe you?” “Na kawo maka yaron ka auna?” Ya kalleta. “Idan gaskiya me ye hujjarki na aikata haka?” Ta risina a gabansa. “So so ne, Kareem ina kaunarka ba zan iya zubarwa ba, ko da ba zan same ka ba zan so aje jininka, kuma waya sani ko nan gaba mu kasance ma'aurata” “Ina zamu kai zunubin Safeena? Ga na zina ga na daukar alhaki? Mu dauki alhakin yaron mu dauki na mijinki? Why how? Why why why Safeena why?” “Ni ma bayan na haihu na yi tunanin be kamata mu yi haka ba, amman komai ai ya riga da ya faru, kuma ba a kanmu farau ba, suna nan da yawa yaran da ba na iyayensu ba” Ya kalleta babu alamar wasa ya ce. “Je ki dauko yaron” Ta mike tsaye ta dauki jakarta ta fice daga office din. Fuskarsa ya shafa yana jin gumi na karyo masa, daman da ta fada masa tana dauke da cikinsa gaskiya ta fada? Ya dauka tana masa wasa ne ko barazana shiyasa ta dawo asibitin. Kuma tun bayan rabuwa da ita be sake bincikarta komai ba saboda yana tunanin ya yanke alaka da ita. Ya mike tsaye yana jin kamar baya iya numfashi. “I can't believe this ba gaskiya ba ne, Kareem” Ya fadawa kansa yana nufar windows din ya rika gaba daya ya rasa me ke masa dadi. Juyowa yayi da karfi ya dauki keys dinsa ya fice daga restaurant din gaba daya. Gurin aikinsa ya koma, ya kira waya ya sanar mata inda yake, a can Safeena ta kai masa yaron mai cike da koshin lafiya mai jiki da haske gwanin sha'awa. Tun da Safeena ta aje yaron yana kallonsa gabansa na faduwa domin ya ga kamaninsa a fuskar yaron, ta dayan gefen kuma yana kama da Safeena. Be ce mata komai ya fita office din, babu jiwa ya dawo sanye da safar hannu ya debi jinin yaron a syringe. “Idan har abun da kika fada ya tabbata Safeena kin cutar da ni, kin cutar da kanki kuma kin cutar da yaron nan” Ta kalli yadda yake kuka bayan Kareem ya dauki jininsa ta ce. “Abu ne da zamu iya ajewa, mijina be sani ba, matarka bata sani ba, to mu bar shi a boye mana, sirrinmu ne ai” Be sake ce mata komai ba ya fice daga office din. Tun tana jiran dawowarsa har ta gaji ta tashi ta fita. Be bar asibitin ba sai da ya debi nashi ya hada ya kai laboratory suka auna masa. He wait they sai da aka hada results aka ba shi. Tsoron abun da zai gani ya saka shi kasa duba takardar har ya shiga motarsa. Ta zauna a motar na tsawon awa daya yana tunanin yadda rayuwa zata kasance masa a yanzu, idan har ta tabbata dansa ne, idan a gurin wasu ba abun kunya ba ne shi a gurinsa abun kunya ne. Daker ya ja motar ya fice daga asibitin, be yi nisa ba ya faka gefe titi ya kai hannu ya dauki result din ya duba. Booom..... Zuciyarsa ta buga da karfi, gaskiya Safeena ta fada, dansa ne jininsa ne. “Why Safeena Why?” Na hade takardar da karfi ya yaga ya jefar ya bugu sitiyarin motar da karfi, ya bude motar ya fita ya fara tafiya sai kuma ya juyo ya dawo ya halbi motar da kafarsa. Ya jingina ya rufe ido ya zai yi? Me yasa ya aikata tun farko? Yaya kenan yanzu? Ya bude motar ya shiga ya kwantar da kujerar motar ya kwanta ya rufe ido. Be daga ba sai da lokacin sallah magariba yayi, a wani masallaci dake kusa da gurin yayi sallah Magariba ya kasa fitowa masallacin har aka yi sallah Isha'i. Sai kusan Tara da rabi ya doshi gidansa. Yana driving yana jin kamar kar ya tafi, kunya hada ido da iyalinsa yake duk kuwa da kasancewar ba su san komai akai ba. Harabar gidan ya faka ya kwanta a motar ba bachi yake ba tunanin yadda zai tafi da wasu abubuwa yake. Yana tuna shawarwarin da abokinsa ya ba shi lokacin da yake raye. Da kuma yadda zuciya ta debi shi ta saka idonsa ya rufe a lokacin ya kasa fahimtar illar da Zina zata yi a rayuwarsa. Ya sani duk wani abu da Allah yace kar a kusance shi, ba abu ne mai kyau ba. Ba ma karku aikata ba kar ma kusanci inda take balle har ku aikata haka Allah ya fada, amman ya take sanin ya murje ido ya aikata, yanzu wa gari ya waya? Kamar zai fadi haka ya bude motar ya fito jikinsa babu kuzari. Sai da ya daga kansa sama ya kalli gidan gabas da yamma sannan ya taka ya isa bakin kofar falon ya shiga. A hankali yake takawa har ya haura sama, dakin yaransa ya fara turawa sai ya samu suna bachi an kashe wutar dakin an kunna musu ocean, sakin kofar yayi ya shiga cikin dakin dakin ya zauna kusa akan gadon Tine yana kallonta kamin ya juya ya kalli Areef. “Maybe nan gaba ku ji kun tsane ni, idan ina raye ko a mace, ku yi bakinciki da na kasance ubanku, kuna da yancin yin haka, domin na bar muku abun kunya, bayan ni kuma nawa iyayen ba su bar min abun kunya ba, sun yi kokarin tsare mutuncinsu da na mu” Ya hade yawu. “Ni dai na san ba zan kashe yaron nan ba, duk wani abun da zan biyo baya dole na karbe shi domin ni na aikata, but no matter what ku sani ina matukar kaunarku kuma ina kokarin na tsare mutuncinku, saboda kar na lalata Future dinku” Ya shafa kan Tine ya sumbance ta, sannan ya tashi ya nufi dayan ma ya shafa kansa ya sumbance shi, ya kallesu cike da bakinciki sannan ya fice daga dakin ya ja musu kofa. Dakinsa ya shiga, yadda ya shigo sanye da talkami da kananan kaya haka ya fada saman gadonsa ya rufe ido, ko agogonsa be iya cirewa ba. Haka ya kwanta har safe ko kadan be yi bachi ba, sai juyi yake idan ya gaji da kwanciyar sai ya sauko kasa ya zauna. Sai da asuba ya siya motsawa ya cire tufafin jikinsa da talkamin ya shiga bandaki yayi wanka tare da alwala ya shimfida carpet, nafila ya fara yi sannan ya gabatar da farilla. A lokacin da ya daga hannunsa zai roki Allah sai kunya ta kama shi, ba zai iya komai ba sai kuka, to me zai ce Allah yayi masa bayan ya bijirewa umarninsa ya bi son zuciyarsa? Allah ya hana shi kuma ya aikata, yanzu kuma ya roki me? Mafita? Ko yafiya? Shafa hannayensa yayi a fuskarsa ya kwanta a gurin feeling so hopeless. Kansa har wani nauyi yayi tsabar damuwa da fargaba da suka same shi lokaci daya, ga kuma rashin bachin da be yi ba gaba daya daren jiya. Usually yaransa suna tafiya makaranta ne ba tare da jiran su ganshi ba, wani lokacin ko da za su tafi yana bachi, Yusura kuma ta koya musu idan yana bachi basa tashinsa. But yau sai ya sha banban da sauran ranakun, Areef ya fara shigowa rike da jakar abincinsa Tine na bayansa, Kareem na jin motsinsu sai ya rufe idonsa not like he don't want to see their faces but kunyar kallonsu yake kuma bakinciki zai taso masa ne. “Bachi yake Areef mu tafi” Areef be ji maganar yayarsa ba sai da ya leka fuskar mahaifinsa ya ga da gaske bachin yake sannan ya juya suka yafi. Suna fita Kareem ya bude idonsa yana kallon ceiling da raunannin idanuwansa. Ya tashi zaune, ya dafe kansa, gaba daya ganin yake kamar ranar jiya ba gaskiya bace mafarki ne. Misalin tara ya shirya cikin kananan kayan babu zancen saka agogo ko shafa mai turare da ya zame masa dole kawai ya tsaya domin baya iya rayuwa babu kamshi. Gefen gadonsa ya zauna ya bude drawersa ya dauko diary da pen yayi rubutu a kai ya nade ya aje pen din ya mike tsaye ya dauki wayarsa ya fice daga dakin. Da dai daya ya rika taka stairs din yana saukowa yana kallon Yusura dake goge dinning kanta babu dankwali. Damuwa ta bayyana karara a fuskarsa kyawawan idanuwansa sun fada sun yi ja sosai irin na wanda be ga bachi ba bachi be ganshi ba. Kusa da ita ya karasa ya aje mata takardar a dinning. For the first time ever ta ji gabanta ya fadi irin faduwar da be taba ba. Ta kalli takardar ta kalleshi. “Miye a ciki?” Ya kalleta. “Yancinki ne, yancin da kika dade kina nema” Ta hade abu da karfi. “Babu amfani Daddy zai sake sakawa ka maida ni” “Wannan yanci ne na har abada, it mean forever...” Ta sake dubansa kamar yadda yake kallonta. “Ina mai baki hakuri akan duk wani abu da na yi miki, wanda kika sani da wanda baki sani ba Yusura, bankwana ne na har abada” Her heart and body star shaking idanuwanta suka tara hawaye. “Na gode da kika taya ni aje farinciki mahaifiyata har sai da ta bar duniya. Yanzu kam kina da yancin ki auri wanda kike so ki yi rayuwar da kike so” Ya juya ya fara tafiya, ta juya tana kallonsa? Me yasa yau ta ji dabam? Ta dade tana jiran zuwan ranar amman ta kasa farinciki, wacam karon ta jidadi da ya sake ta amman ta kasa farinciki. “Yaran fa?” Ya juyo ya kalleta hawaye ya gani suna fitowa daga idonta suna zuba a fuskarta. “Zan kula da su” “Za su fi jindadin zama a gurina” Ya taka zuwa inda take tsaye. “Idan haka kike so, zan minta, but only on one condition, no matter how happen a raye ko a mace zaki fadawa yaran nan cewar mahaifinsu yana kaunarsu, duk wani abun bacin rai ko bakinciki da zai biyo baya ko ya biyo i still love them, ki fada musu mahaifinsu yayi kokari ganin ya tsare duka hakkinsu sai abun da ya fi karfinsu” Ya juya ya nufi kofa sai ta risina kasa ta kira sunansa. “Ka yafe min Kareem, na cutar da kai na sani, kiyayya bata bari na yi biyayya ba” “Komai ya kare yanzu Yusura it over now” Ya amsa mata ba tare fa ya juyo ba ya fice daga falon. Yana shiga motarsa ya murza key mai gadi ya bude masa gate ya dauki hanyar da zata sadashi da gurin aikinsa. Be yi nisa da gida ba hudu ya rufe masa ido kansa ya fara juyawa yana ta kokarin controlling motar amman ya kasa. NOOR POV. “Innalillahi Wa'Inna Ilaihirraji'un” Abun da na fada kenan a lokacin da na farka da karfi, sakamakon mummunan mafarkin da na yi. Wai muna tafiya a jirgi sai ya muka fado kasa ni har da ni ciki, na bugi icce har sai da hankalina ya gushe. Addu'a na yi na neman tsari daga mummunan mafarki. Na yi a'uzubillahi har karshe na tofar dama na sake yi na tofar hagu, sai haki nake kamar wanda ta yi yaki, hannu na kai na lalaba ban ji Abdull ba, sai na sauka daga kan gadon na kunna wuta na nufi bathroom din da nake jin motsin ruwa na tsaya jiran ya fito na shiga. Da na lura ba shi da niyar fitowa sai na tura kofar na fara lekawa babu kowa a ciki, shiga na yi ciki da mamaki, tab din ne a kunne ruwa na zuba kadan kadan amman babu kowa a ciki. Kashewa na yi na bayan na gama fitsari wata kila ya manta ya bar shi a kunne ne. Sai da na nufo gado na zauna sai kuma wata zuciyar ta tambaye ni ina ya tafi? Bargon na sake yayewa na sauko da kafafuwana ina mikewa tsaye sai gashi ya shigo dakin. “Ina ka tafi?” “Ruwan na ji na hada tea, ina zaki ke?” “Ai dai ba zan bata ba a gidana ko? Idan bana dakin nan ina falo ko kitchen” Ya hauro saman gadon ya kwanata rai a bace kamar an masa wani abun, har ya manta be kashe wutar ba, wata kila tambaya ta ce ta bata masa rai. Sauka na yi na kashe wutar na dawo na kwanta. It's not Free pay 500 to Zenith Bank Hadiza Abubakar 2451879008 And send the evidence of payment to my WhatsApp number 08036126660. https://chat.whatsapp.com/Jd2OwsAcXE7EjI7NHeFQV0 PAID PAGE 2️⃣0️⃣ ©️KhadeejaCandy ©️®️Copyright 2024 Littafin nan na kudi ne, don't read if you didn't pay... One word kika karanta baki biya ni ba, ban yafe hakkina ba. To be part of the journey pay 500 to 2451879008 ZenithBank Hadiza Abubakar And send the evidence of payment to my WhatsApp number 08036126660.... You can read my latest update on arewabooks a handle dina @KhadeejaCandy https://www.arewabooks.com/book?id=659a94c8be87d7a51f831153 _______•••_______ Rumgume hannayena na yi ina kallonsa with my innocent face. “Besty how are you?” Ya tambaya yana daga kai ya kalli harabar unguwar. “I'm good and you?” Ya daga gira not happy not sad. “I'm not fine” Na dan matsa kusa da shi. “Me ya same ka?” Sauke kai yayi kasa sannan ya ce. “Bestyna kamar kin taba fada min sunan wanda zaki aura ko?” “Eh Abdull” Ya dago ya kalleni. “Yana da mata kika ce idan ban mata ba” “Eh da yara uku matarsa ya haihu na hudu” Ina jin sautin hade yawunsa. “Amman kin taba ganin matarsa?” Na dan kawar da ido daga kallonsa sannan na amsa. “Eh na taba ganinta ya nuna min hotonta” Ya langwashe halshensa. “Kin san sunanta?” “Safeena your ex-” Murmushi yayi ya jinjina kai yana juya idanuwansa like na bashi mamaki sosai, kamin ya kalleni. “Kin san duk wannan kuma kika yarda zaki auri Abdull?” “Ba mutumen kirki ba ne?” “Ban san komai a kansa ba, amman na san komai akan Safeena, ba zaki iya kishi da yarinyar nan ba, she's criminal” Na dan tabe baki. “Bana jin zata yi kishina, ai kai take so kuma kai take kishi, me zai saka ta yi kishin mutumen da bata so indai har da gaske bata son shi” “Mijinta ne uban yayanta taya ba zata ji kishi ba, kuma ni ban taba fada miki cewar bata son shi ba, taya zata ki mutumen da shi ya tsamota daga ruwa a lokacin da na jefata?” Na daga kafaduna not knowing what to say yanzu kuma. Ajiyar zuciya ya sauke ya kwantar da murya ya ce. “Noor me kika fadawa Safeena?” Na kalleshi da sauri daman na san za a zo gurin. “Me tace na fada mata?” “Sirrin da na yi dake ta zo ta fada min duk abun da kuka yi, saboda me zaki nuna mata cewar kin san abun da yake tsakaninmu” Na ciro wayata daga aljihun rigata na nuna masa sakon da ta turo min, kamin wani abu ya tsikare ni kamar zan yi fada na fara magana. “Ganin na yi tana neman daga min hankali tun kamin na shiga, ni kuma ba na yi aure ne saboda na je na fito ba, bana son aurena ya sake rabuwa sai idan mutuwa ta raba” “Amman sai ki yi amfani da wata hanyar ba wannan ba, ke yarinya ce, baki gama fahimtar duniya ta mutanen cikinta ba, ba ki san illar abun da kika ba sai bayan ki aikata” “Ba ni da wani weapon na yakarta sai wannan” “Amman wannan sirrina ne, na fada miki ne saboda na yarda dake and i need someone to talk to, taya zaki aikata abun da zai iya janyo matsala ya janyo miki?” Zan yi magana ya daga min hannu ya nuna min yatsa. “Look Noor ina da yara, mahaifina yana raye ina da yan'uwa da abokaina, ko kadan bana son abun da zai zubar min da mutunci, na fada miki damuwata ne saboda na yarda dake, kuma ina jin kusanci da zuciyata, ba dan ki bayyana ma duniya ba, na san na aikata abun a lokacin da idanuwa suka rufe shekaru suka tsirewa tunani, and now i realize na yi wa kaina babbar barna and i regret it, you shouldn't discuss this with anyone!!” Ya bude motarsa ya shiga ya bar ni a tsaye ina kallonsa hawaye na sauko min, domin be taba rufe da fada irin na yau ba. Har yayi baya sai kuma yayi gaba ya faka a inda ya faka dazun ya sake bude motar ya fito ya tsaya kusa da ni. “I'm sorry, Na san na kaurara amman Noor ban ji dadin abun da kika yi ba, wannan sirrina ne, be kamata kowa ya ji ba ” “Bana hira da kowa, ban taba fadawa kowa ba, kuma ita wanda ta ji daman ai ita abun ya shafa” Na bashi amsa cikin sautin kuka. Idonsa ya sauke kasa yana sake fuskarsa. “Bana nufin sakaki kuka ko kara miki damuwa akan wanda kike ciki, amman ni abun da kika aikata yanzu zai daga min hankali ya saka ni a damuwa, waya sani ko zaki sake fadawa wani? Kuma Safeena ba zata zura miki ido hakan nan kawai ki cigaba da rayuwa a free ba, bayan kin san sirrinta, ni da ita duk muna da iyali, ki rika duba wannan kamin ki aikatawa wani abun Noor” Na share hawayena. “Ta je ta bata ni gurinka ko?” Ya rufe ido yana murmushi sai dai hakan be hana ni fahimtar damuwar dake shimfide a fuskarsa ba. Bude ido yayi yana min magana a hankali. “Bata iya wannan, babu wanda zai iya wannan ma, just be careful yanzu Safaeena tana kiyayya dake ta kofa uku ne, Allah ya tsareki kuma ya baki zaman lafiya, amman Bestyna Noor ina son ki sani ko mutuwa na yi bana son na tafi na barwa ƴaƴana abun kunya” “Ni ma ba zan so haka ba, kuma na maka alkawari daga wannan ba zan kara ba, kuma babu wanda zai ji” Yayi tattausan murmushi da ya kara masa kyau. “Thank You, Allah ya tabbatar miki da alheri” “Ameen” Ya sake Bude motarsa zai shiga. “Shikenan tafiya zaka yi?” Ya juyo “Ko kina da bukatar wani abun ne?” Na girgiza kai. “I will miss you alot” Yayi murmushi ya sauka kansa. “Akwai abun da kike bukata na auren Noor? Akwai abun da Baba be miki ba?” Na girgiza masa kai alamar aa. A ganina kamar be kamata na dora masa nauyin komai ba, kuma ai da kunya na bukaci kayan daki a gurinsa, domin su ne kawai nake saka ran Baba ba zai yi min ba, shi ma kuma ba ni da tabbaci. “An yi komai” Yayi murmushin dake nuna kamar be aminta da ni ba. “Sai wata rana” Wannan karon be sake kallona ba ya shiga motarsa yayi mata key ina tsaye ina kallonsa har na daina hango shi. Wata kila shi kam ba zai yi marmarina ba kamar yadda anke jin kewarsa tun a yanzu, ba mu wani dade a tare ba amman shakuwa mai karfi ta shiga tsakanina da shi. Bayan tafiyarsa ne fahimci na yi katobara na bayyana ma Safeena na san komai a tsakaninsu ba dan ita ba, sai dan shi wata kila hakan zai iya haifar masa da matsala, sai dai iya abun da na sani shi ne, Safeena ba zata yarda asirinta ya tonu ba, domin tana da aure da yara kamar yadda ya fada, ni kuma ba zan sake tattaunawa da kowa akan matsalar ba. Hakan da na yi ya saka na samu yanci gurin Safeena, mijinta ma ya samu kwanciyar hankali domin ana sauran kwana biyu a daura aure nake tambayarsa ya Safeena sai yake cin yanzu ai ta fahimci, tashin hankalinta ba zai hana aurenmu ba ta shafa masa lafiya. A raina na ce ko dai ta fahimci Ni din ba kanwar lasa ba ce ta bawa kanta lafiya da ni. A daren ne yayi ta damuna da maganganu da be sana yi min ba, hakan kuma ya raunata yarda ta ya haifar min da tsoro akansa, sai dai na lura shi kam sam baya kunyar fadar haka, wata kila saboda ya taba auren ne, ko kuma yayi zaton a aurena na farko na san komai kamar shi. A yadda na lura Abdull irin mutanen nan masu masara kunyar ido da furta komai a take. Ni dai bana iya cewa komai idan ya jefeni da wani kalamin, na kan ji kaina yayi girma kunya ta rufe ni. Washe gari gidanmu ya cika da yan'uwa mahaifina wadanda suka zo shirye shiryen abubuwan da za'ayi, ta hirar da Baba yake da su ne na ji yana fadar mai gidan Nabil wato Kareem yana da kirki da mutumci sosai. “Yanzu bayan daukar nauyin karatun yaron nan da yayi, auren nan da za'ayi sai da ya same ni a majalisa ya damka min kudi mai yawa wai na kara na yi hidima, Allah dai yayi masa albarka ya yara masa yaransa, wutar nan ma da ta taso tsakanina da yan'uwan Hafizu shi ya kashe ta” “Ai wasu masu gida haka suke da taimako da kirki, musamman idan sun san baka da shi, wasu kuma suna bakincikin abun da zaka samu ma” Cewar Baba Garba. “Haka ne, ni farko ma na dauka shi zai ce yana son Noor ne, kuma na ga kamar ba haka ba ne, ai ba dan kar ta ba ni kunya irin na wacan karon ba, Wallahi da sai na aura masa ita saboda kunyar abun da yake min, ya rike amanar abota” Jin hakan a gurin Baba ya saka na ji Kareem ya kara kima a idona, tabbas shi din mutumen kirki mai son taimako, babu ruwansa da duba matsayi ko girma. Haka dai na yi ta jin suna ta hirarsu ta yan'uwa yana fadin mutanen da suka taimaka masa a yanzu da kuma aurena na farko. A lokacin da suka dauko zancen abubuwan da zai kai na ji Baba Garba yana tambayar Baba. “Toh yanzu kai Magaji ka siyo mata kayan dakin ne?” “Ni babu abun da na siya kuma babu abun da zan siya, ai ya fada mana da zarar an daura aure za su wuce can Lagos din da ita, to taya za a tsaya wani siyen kaya nan tun da nan za su zauna ba? Dubu hansin zan bashi a cikin kudin sadakinta idan sun je can ya siya mata abun da ya kamata” Anty Larai ta ce “Aa gaskiya be dace ka yi haka ba, ai ana son ka siyama yarka girma, ko dai ba mai tsada ba kowa ya san karfi ba daya ba, sai ka mata na iya karfinka saboda Allah magaji” “To wai me za'a siya ma? Uwarta ta aiko mata da kaya, kuma ba a nan za su zauna ba, ai kayan sun isheta komai” “Kayan da ta aiko mata kayan kitchen ne, kai kuma naka kayan daki ne da dan wani abu da za aka bawa ango” “Aa aa aa karya haram ba zan iya kashe kaina ba, yarinya suka ce suna so ita za a ba su, ita da Allah yayi jininta jinin masu kudi me zai kai ni wahalar da kai na siye wasu kayan daki? Hafizu ma Allah ya masa rahama da kansa yace ba zai na yi komai ba ya dauke min komai” “Toh shi wannan ai be ce ba, gaskiy...” Bata karasa ba Baba ta tari numfashinta. “Ni fa dan abun da na samu, gyaran gidana zan yi na kuna kallon yadda gidan nan gaba daya ya canja babu wani taimako da na samu, sauran kuma sai na bude shago na zuba kayan masarufi” Jin cewar Baba ba zai yi min furniture ba ya disashe farinciki dake zuciyata, wata kila shi din ba kamar Hafiz ba ne da zai ce ya yafe komai, hakan kuma wani abun gori ne a gurina da danginsa da ma kishiyata. A ranar aka yi min kunshi mai kyau mai ja sosai, da dare kuma Hana da kawata Zainab suka raka ni na tafi gurin gyaran gashi domin ni ba mace ce ma'abociyar son kitso ba. A nan na samu damar fada musu damuwata, Hana ta nuna damuwata da jin cewar Baba ba zai siya min komai ba har ma take cewa. “Yanzu da ace Mama bata aiko da wannan ba haka za'a kai ki ko spoon din aiki ba ki da shi?” Na sake jin babu dadi domin Baba baya kyautata min a rayuwa, wasu hakokan da ya kamata uba ya saukewa yarsa shi baya sauke min su. “Noor kar hakan ya daga miki hankali, Baba ya fadi gaskiya idan ba nan za su zauna ba, babu amfanin siyen kaya, daukar kaya daga Kano zuwa Lagos wani aiki ne babba, kuma kin ga yace ba a nan za su tare ba” Zainab ta shiga kwantar min da hankali, na dube ta na ce. “Amman wasu ko ba a garin za su zauna ba, ana yi komai Zainab a garin da miji yake, saboda can aiki yake yi ai, wata rana zai iya dawowa mahaifarsa” “Ki gode Allah Noor, idan mijinki mai sonki ne duk ba zai ga wannan ba, kuma zai rike ki amana, idan ma Baba bai miki ba ke zaki iya yi ma kanki ko kuma shi mijinki yayi miki, dan Allah ki kwantar da hankalinki Noor” Duk yadda zata karfafa min guiwa sai da ta yi har ta yi nasarar kwantar min da hankali na dan sake raina. A napep muke ta labarin Zafeer da sabon auren da aka ce yayi a gurinta nake jin labarin irin hidimar da aka yi na bikin auren domin Zainab tana abota da kanwar Zafeer sosai, shi ma kuma yana good time da ita ko a lokacin da muka samu matsala ita yake aikowa gurina. “Amman kin ga yana dariya?” Na tambaya ina jin bakinciki marar misaltuwa kamar ba ni na fara guje masa. “To zai ki dariya ne Noor? Ai dole yayi farinciki ko yaya ne, wata kila ma yanzu ya manta da soyayyarki, domin yar masu kudi ya aura ance mahaifinsa ma shi zai sama masa aiki, daman ita yarinyar tana aikinta, ance ta girme shi da shekara uku” “Allah ya saka masa tun ba ayi nisa ba, ya samu wadda ta fi ni komai” Na fada hawaye na sauko min, Zainab ta dube ni. “Noor har yanzu kina son Zafeer wai?” “Unconditionally, har abada zuciyata ba zata daina son Zafeer ba, ba zan taba son kowa kamar yadda na so shi ba” Shiru ne ya biyo baya babu wanda ya sake cewa Uffan daga ni har su. Har muka isa gida hawaye nake, haka na shiga gida rai babu dadi zuciya na kuna, kiran da Abdull yayi ta min ma kasa dagwa na yi saboda damuwar data haifar min da ciwon kai. Washe gari ya Friday gidanmu ya cika da makota da yan'uwa na kusa da nesa maza da mata, kusan wannan bikin ma kamar ya fi wacan yawan jama'a. Bayan saukowa daga Massallaci na fita waje na yi alwala na shigo dakinmu kenan wayata ta yi kara, dubarwa da zan yi sai na yi arba da number Abdull, a take na amsa kiran na kara wayar a kunnena. “Hello...” “Congratulations an daura aurenmu, Alhamdullahi” Gabana ya fadi har sai da kaina ya sara, kai kace ban tsammaci zuwan wannan ranar ba. “Allah ya ba mu zama lafiya” “Ameen” Ya amsa sannan ya kashe wayar, shi ne mutum na farko da ya fara min albishir, kamin gidan mu ya dauki guda har Hana ta shigo dakin tana rangwada guda tana farinciki, sabanin wacan auren na farko da bata yi farinciki ba. Madadin na yi murna sai na fashe da kuka na zube a gurin an rufe idona ina ta rutsar kuka kamar wanda aka sake yi ma auren dole. Haka na wuni ban iya cin komai ba, sai da Anty Larai ta siyo fura ta dama min ta saka kankara sannan na iya sha shi ma ba da yawa ba, yan'uwan Abdull sun leko mana wuni, daga bangaren mahaifiyarsa da kuma na mahaifina. Angon kuma be duro gidan ba sai isalin karfe takwas na dare. A lokacin da na kira a waya ya sanar min yana waje, sai na jin kunyar fita a dole na yi masa karyar Gwaggonta tace ba zan fito ba. Ban san da wa yayi magana ba, sai ga Baba ya shigo yana fadin na tashi na leka waje mijina ya zo tare da abokinsa yana son magana da ni. Jin cewar yana tare da wani ya karfafa min guiwa kuma ya rage min kunyar da nake ji ta mutane. Hana ta dauko turare ta kara fesa min, Anty Larai kuma ta saka na cire lace din dake jikina na saka farar lafaya sannan na fita gashin kaina na yawo domin ban saka ribbon ba. Nesa da gidanmu ya faka ta inda mutane ba za su ganshi ba, ni ma ba dan na kira shi a waya ba ba zan iya gane shi ba. Kamar ana daure min kafafuwa haka na karasa gurin motar sai ya sauke gilashin ya kunna hasken wayarsa ya haska fuskata. “Amarya ba kya laifi, kyakkyawar amarya mai tsaye siririya duk ni kadai” Kunya ta saka ni sauke kai kasa ina murmushi. “Shigo motar mana, kar na gajiyar da matata” “zan iya tsayuwa a nan” Bude motar yayi ya fito ina kallonsa ya kama hannuna ya zagaya da ni ta baya ya saka ni a back seat sannan shi ma ya shiga. Rabon nake ko zan ga abokinsa amman ban ga kowa ba. “Ka ce kana tare da abokinka...” “Na fadi haka ne saboda na rage miki kunyar dake kanki” Ya yana maganar kallon bakina zuwa kirjina. “Ko ban kyauta ba?” Kamin na amsa na ji na kara matsowa kusa da ni sosai har ina jin numfashinsa, ta dama da ni ya lakamo hannunsa yana lasa cikina a hankali. “Ya gajiyar biki?” “Alhamdullahi” Ina kokarin cire hannunsa sai ya juyo da fuskata zai sumbance ni, na dauke kai na dauke numfashi ina jin wani iri. Murmushi yayi ya saka dayan hannunsa ya juyo da kaina. “Da alama dai kunyar nan zata cutar da ni” Ya sumbanci goshina ya shinshina hancina kamar mai kokarin tantance wani abu. Rufe ido na yi jikina ya hau bari ina jin wani bakon al'amari. Hakan kuma be hana shi kai bakinsa cikin nawa, sai da na ji yana kokarin wuce gona da iri tukuna an matsa baya na rike hannunsa. “Abdull za a iya ganinmu fa” “Babu wanda zai gani bakin gilashi ne” Ya sake kai hannunsa a jikina sai na tare. “Baba zai ga na dade” “Me yasa kike ta guje min ne Noor? Kin san how long nake ta jiran wannan ranar? Ni fa yanxu halalinki ne” “Na sani amman ban tare ba, kuma na fito gida ne da sunan zaka yi magana da ni” “An riga an daura ko da sadakin da na biya kin zama mallakina balle kuma an daura, sadaki shi ne aure ai wasu da zarar an biya sadaki ma suke sakewa juna balle mu da har an daura mana aure” “Auren dai shi ne gaskiya, amman biyan sadaki ba aure ba ne, tun da har ana daura mana ai ya kamata mu yi hakuri har zuwa lokacin da za mu tare babu dadewa” “Allah yasa zan iya jira, sai monday zamu bar garin nan Noor, kuma ba wani abu zan aikata da ke ba a yanzu, it's just a kiss, ina kokarin wayar da ke kamin mu tare domin na lura kamar baki gama fahimtar rayuwa ba” Na yi murmushi karfin ina mamakin yadda yake da rawar jiki haka, kuma ina yaba kokarin Hafiz na jurewa da yayi ashe shi din jarumi ne sosai. Na matsa ta gefen da kofar take na bude na fita. “Sai da safe” “Sai da safe my shy Bride, an hana ni kiss ko? Zan rama” Murmushi na kawai abun da na yi na fara takawa ina tafiya har na isa cikin gidanmu. A dare wata kanwar Mama ta cika min ciki da wasu kayan mata har sai da kaina ya fara ciwo. Haka na kwashe kwana biyu ana ba ni abubuwan nan da bana bukata, ban kuma isa na ce aa sai a rufe ni fada. A cikin kwanakin da na yi a gida bayan daura auren, babu ranar da Abdull baya zuwa da dare a kowa dare kuma sai yayi kokarin taba ni har ya wuce gona da iri. Baba yayi min nasiha da kuma jan kunne, ranar Lahadi Mama ta aiko da mota aka dauki zuwa gidanta ta yi nata nasihar, acan na kwana sai washe gari na dawo. Na dawo gidan na tarar Hana ta gyara min kayana ta kintsa komai, a take na fara jin kewar gidanmu duk kuwa da kasancewar ba wani dadin zaman gidan nake ji na. Ranar Monday da misalin karfe 2pm Abdull ya iso gidanmu tare da wani abokinsa da kanensa mata biyu da sunan za su dauke ni. Sai Baba ya tsayar da shi jege suka tattauna, ban san me suka tattauna a kai ba, bayan sun gama na fito ina sanye da green abaya da mayafinta sai mask da na saka na rufe fuskata. Handbag dina tana hannuna tare da wayata da karamin akwaitin da yace da shi kadai zamu tafi a yanzu saboda jirgi zamu shiga. Yace daga baya zai aiko da mota a dauki saura kayan nawa da kuma yan'uwana domin su ga gurin da muke rayuwa. Da ace ina da iko da tun a yanzu zan tafi da Hana domin ta rage min kewar gida da kuma bakuntar gurin da ban sani ba. Na yi kuka sosai ina jin kamar wata kasar zan tafi ba iya Lagos ba. Har gurin mota Baba ya rako mu tare da Hana da Umma, na shiga gidan baya tare da kanensa shi kuma yayi ma Baba sallama ya shiga front seat kanensa kuma yaja motar sai airport.... Ban taba ganin airport a fili ba sai a ranar da muka isa gurin, ashe babban guri ne mai hada hadar jama'a mun zauna a wani guri jiran jirgin bayan an gama yi mana check-in. Id card din dake hannuna nake ta kallo, sai dai zuciyar da tunanin yana can wani guri. Hannun Abdull na ji cikin nawa yana kokarin saka yatsunsa cikin nawa. “Amarya are you Okay” Na kalleshi sai na ji hannunsa a fuskata yana share min hawayen da ban san taya suka zubo ba. “Har kin fara missing din gida ne?” Ban yi magana ba na kalli kanensa dake can gefe zaune suna ta hirarsu, jira suke har sai jirginmu ya tashi sannan su koma gida. “Ka yi min wani alkawari” “Cewar ba zaka taba cutar da ni ba” “Me yasa kika fadi haka Noor” “Ba komai ni dai ka yi min alkwarin rike ni amana, ina fatan wannan auren da muka yi mutuwa ce kadai zata raba” “In Shaa Allahu, na miki alkawari ba zan taba cutar da ke ba Noor” Ya ba ni tabbacin da nake bukata sannan ya amsa kiran dake shigowa wayarsa ban san da wa yake magana amman na ji yana fada masa lokacin da zamu sauka. Ni kuma na juyar da kaina ina kallon wani gafen. Kalamansa sun saka na ji hankalina ya kwanta, na samu natsuwar da na rasa. Na sani mutum ba zai taba samun abun da yake so dari kan dari ba, shiyasa na yarda da wannan kaddarar kuma na shiryawa wannan zaman aure da dadi babu dadi zan zauna, ko da Abdul zai rika yanka naman jikina ya siyarwa ne. Zan jure ko wace kalar azaba da ukuba ko da kuwa ita ce zata yi silar ajalina... An samu delaying gurin tashin jirgin, karfe biyu da mintuna goma sha biyar ya kamata mu tashi amman ba mu tashi ba sai misalin Karfe uku daidai muka tashi daga filin jirkin saman Aminu Kano, bayan mun yi bankwana da yan'uwan Abdull, har na ji ina ma ace ni ma nawa yan'uwan sun rakoni kamar yadda na shi suka yi. Abdull ne ya saka min belt ya sakawa kasa ya rike hannuna ganin yadda nake jin tsoro sosai lokacin da na yi arba da jirgin for the first time. Sai da muka yi nisa da kasa sosai jirgin ya fara tafiya sannan ya cire min belt din shi ma y https://chat.whatsapp.com/Jd2OwsAcXE7EjI7NHeFQV0 Washe Gari na tashi da wuri saboda zan tafi asibiti, dan haka na gyara da wuri na fito falo, ina jin motsin Hana na nufi kitchen din na dan rikawa mata aiki. Ina tsaka da kashe socket ta yi min wata magana da ta saka na kalleta. “Noor ina son na tafi gida” “Me yasa Baba ya sake magana ne?” “Aa kawai dai ina son gida yanzu, na fi jindadin zama gida sama da nan” Na juyo da kyau na fuskance. “Hana wani abu na yi miki ba daidai ba ko Abdull yayi miki?” “Aa ba ko daya, kawai dai na fi sha'awar tafiya gida ne” Na dan jimm ina mamakin dalilinta na fadar haka a yanzu, daman na lura yanayinta gaba daya ya canja. “Hana mafarki kika yi marar kyau ko me?” “Ba komai ni dai kawai ina son na tafi gida” “To kije ki dawo ko kuma ki koma gidan gaba daya?” “Gaba daya dai nake son na koma” “Karatunkin fa?” “Zan hakura na san idan naje can Mama zata iya sakani idan Baba ya yarda” Na matsa kusa da ita domin babu ta yadda lafiya zata saka ya yanke karatunta ta koma gida haka nan kawai sai da dalili. “Hana na san muma yawan samun tsabani da ke a gida, amman nan gidan aurena ne, idan kina ganin akwai abun da nake miki da baya miki dadi zaki iya fada min sai na gyara, idan kuma aiki ne kike ganin na sakar miki ragamarsa zan rika yin rabi, amman dan Allah ki zauna ina jindadin zamanki ina son yar'uwa a kusa da ni, ba ni da kowa nan zamanki a gidan nan yana rage min kewa” “Babu wani tsabani da zamu samu har ya saka na ji bana bukarki a kusa da ni, mu na samu tsabani a gida a nan ma zamu iya samu, saboda zama tare dole wata rana zaka ji an maka ba daidai ba, amman Noor ni ba zan iya cin amanarki ba” Ta rumgume ni tana kuka, jikina yayi sanyi sosai kalaminta na karshe ya saka min shakku a zuciya. “Akwai abun da yake faruwa tsakaninki da Abdull ne?” Ta dago da sauri. “Aa Wallahi Babu, dan Allah karki zarge shi ki lalata aurenki, Wallahi Wallahi na rantse miki da Allah babu wani abu tsakanina da Abdull” Hankali ya dan kwanta da ta yi min rantsuwa cewar ba tsakaninta da Abdull ba ne. “To ya kawo zancen cin amana Hana?” Ta share hawayenta. “Ina nufin kamar na guje ki saboda kin min wani laifi, ai kamar na ci amanarki ne a matsayinki na yar'uwata” “To me yasa kike son tafiya gida? Kina karatunki a nan, Abdull ma idan ya ji ai zai yi fada, Mama ma sai ta miki fada tace kin san ba zaki karatu ba kika saka bata kudi aka biya miki har na shekara uku” “Kawai ina yawan mafarkin marar kyau ne, kuma ana baki tsoro a gidan nan ina tunanin akwai aljannu a gidan” “To ki rika addu'a mana Hana, ke da kike fada min yadda zan bi da rayuwa na jidadi yau kuma ke kika rasa ya zaki yi?” Ta yi murmushi “Gaba daya na rikice mugun mafarkin da na yi ya daga min hankali” Zan sake yin magana Abdull ya kirani. “Noor kin fasa zuwa awon ne? Karki makara fa” Na dauki ruwan zafi na fice daga kitchen, sai da ta jera mana komai a dinning sannan ta zuba nata ta dauka. “Lafiya na ga kamar yanayinta ya canja” Abdull ya tambaya she dai shi ma ya lura da yadda take ta hade rai bata son kallon kowa. “Lafiya kalau” Ta wuce dakinta bayan ta amsa mishi, da kallo na bita sai da ta shige sannan na juyo na kalleshi, kamar na fada masa kudurinta sai kuma wata zuciyar ta hana ni, na san ba abu ne da zai masa dadi ba, saboda kudin makaranta da ya biya mata ga yawan hidima da yake mata, tafiya makaranta ma kullum sai ya bata kudin bus kuma ya rage mata hanya saboda akwai tazara daga unguwarmu zuwa makaranta kuma babu abun hawa sosai ta gurarenmu sai idan sun kawo Passenger. “Ina jin bata da lafiya ne” “Me yake damunta? Ko kuma dai mood swings ne” “Yeah” Ko da muka gama karyawa ta yi shirin makaranta da uniform dinta da suke sakawa kullum. Tare muka fita sai da ya fara sauketa sannan ya sauke ni a asibitin ya wuce gurin aikinsa. Tun daga ranar Hana bata sake yi min maganar komawa gida ba, sai dai na lura da yanayinta gaba daya ya canja kamar zaman gidan ya daina mata dadi a yanzu, domin ko hirar da take zama muna yi tare da Abdull a da yanzu duk ta daina, ko da yake yanzu ba kamar da ba ne, da take gida kullum yanzu kuma idan ta tafi bata dawowa sai yamma idan ta dawo wani sa'in ta hau aikin gida ko da ta gama kuma sai bachi. Sai can ba a rasa ba muke zama muna hira a falo da zarar Abdull ya shigo zata masa sannu da zuwa ta shige dakinta ba zata sake fitowa sai gobe. Ko wani abun ya siyo sai dai na kai mata nata dakinta, ko kuma shi ya kwankwasa kofar dakin ya aje mata daga bakin kofa, wani sa'in idan ina jin wahalar tashi. Wata kila ta fara haduwa da abokan banza masu hore mata kunne ne, ko kuma dai ta gaji da yin aikin gida ne, ko kuma nata gidan mijin take son tafiya ita ma. Ko ma dai yaya ne na daure ma zuciyata na zauna da ita a haka, saboda bana son ta lakata karatunta a lokacin da take tsananin bukatarsa, kuma ana yi da kai ya fi ba'ayi, zamanta yana taimaka min ko yaya ne tun da ita take min komai a gidan kuma ina ganinta na san ina da yar'uwa a kusa ina jin sanyi a haka din ma. KAREEM POV. Da sauri ya maida idon ya rufe ya kai hannunsa dake sanye da drip ya murza idon sannan ya sake budewa. Hannun ya kai ya cire robar dake bakinsa yana kokarin daga hannunsa daya sai ya ji yayi masa nauyi dubawar da zai yi sai yayi arba kan dansa Areef a hannun. Yunkurawa yayi a haka ya tashi zaune ya saka dayan hannun a hankali ya cire hannunsa. Haka ya cire duk wani abu da aka laka masa sannan ya sauko da kafafuwansa yana tuna abun da ya faru. Ya san dai yana tsaka da tuki hudu ya sauko masa daga lokacin kuma be sake sanin inda yake ba, maybe ya hadari yayi, ba ma wata kila idan be yi hadarin ba ai ba za a kawo shi nan a aje ba. But why ICU shi da be ji ciwo ko daya a jikinsa ba, domin be ga wani guri da ya ji ciwo bako ya bugu. Hannu ya mika ya janyo files dinsa ya bude ya duba. Daman ya sani zama unconscious or in a critical condition ke saka a aje mutum a gurin. Ya duba ya gani kwanansa biyu a dakin amman be sani ba sai yau da ya farka, babu wata rauni a jikinsa but hankalinsa da numfashi sun yi nisan da an dauka barin duniyar zai yi. Ko me ua buga oho, ya san dai hakan baya rasa nasara da damuwar da yake ciki, kusan ita ce silar faruwa komai. Ya aje files din ya shafa kan dansa dake sanye da uniform din makaranta yana murmushi ko dan yaran nan yana bukatar rayuwa. Areef ya bude ido sakamakon shafa kansa da Dadynsa yayi. “Hey young Man” Yaron ya tashi zaune ya matsa ya rumgume mahaifinsa yana murna. “Dady ka farka” Kareem ya saka hannu ya shafa bayansa yana murmushi kamin wani azababben ciwo ya ratsa zuciyarsa har sai da ya ji ta motsa kamar ta bar muhallinta. “Oh...” Ya furta Areef ya dago ya kalleshi. “Dady minene?” Kareem ya murmushi. “Ba komai ina Tine” “Suna waje bari na kira ta har da Mama ma tana nan, kullum zai mun zo kana bachi, Hajiya tana nan ita da Uncle Aaryan nan yake kwana” Har ya isa kofa sai kuma ya juyo ya kalleshi. “Daddy ma kullum yana zuwa, yana yin addu'a yana tofa maka, Dady kuma Momy ta kwashe kayanta gaba daya ta koma gurin Hajiya an bata bangare daya tace tare zata zauna da mu” Kareem ya daga mishi kai. Areef ya fita da gudunsa, Kareem kuma ya mike tsaye ya fito daga dakin da kafafuwa normal yake jin kansa kamar be yi hadari ba. Ya san yadda asibitin take fa kuma dokokinta sai ya canja ma kansa daki bayan ya gaisa da ma'aikatan dake ta masa sannu Doctor dake duty yana da tsokarsa yana fadin ya bari yayi aikinsa yanzu shi majinyaci ne ba likita ba Files din dake dayan dakin likita ya dauko ya dawo da su sabon dakin da Kareem yake, sannan aka bawa visitors damar shiga, yan'uwa na ta shigowa suna masa sannu na nesa kuma suna kira a waya. Duk wani motsi nasa yana kan idon Yusura kallonsa take sosai kamar bata taba ganinsa ba, sau daya ta yi masa ya jiki bata sake ba sai dai duk dagowar da zai yi sai ya ga tana kallonsa. Tun daga ranar kuma bata sake zuwa ba duba shi har aka sallame shi after four day's da yayi a asibitin. Ranar da zai bar asibitin babu yadda Hajiya bata yi ba akan ya dawo family house ya zauna har sai jikin ya kara warwarewa da kyau saboda a can gidan babu kowa a yanzu amman ya ki, domin baya son zama gidan zai fi sakewa a gida ko da kuwa ba shi da lafiyar balle baya jin ciwon komai a jikinsa. Taya zai saki matarsa ta tare a family house dinsu shi ma ya koma can ya tare kamar mace. Ba karamin godiya yayi ma Allah ba lokacin da Aaryam ya kai shi gidan ya ga yadda gaban motarsa ya lalace, bayan ma ya bugu ba karamin accident yayi ba amman Allah ya kawo masa sauki tun da be ji rauni a ko'ina ba. Aaryam ya fada masa yadda hadarin ya afko sai da ya cika da tsananin mamaki. “Babu wanda ya dauka zaka rayu fa, Wallahi duk mun tsorata, babba mota ka buga irin mai zube yashin tefa. Mai motar yace yana ta maka horn domin ya ga yadda ka zo da gudu amman baka tsaya ba sai da ka bugu shi, gashi ita kuma wata motar ta bugi taka a baya, daker aka fito da kai motar babu rauni amman baka numfashi hankali ya bace gaba daya, asibitin ma sai da aka yi da gaske sannan numfashinka ya dawo” Yayi murmushi. “Kwana ne ba su kare ba, da lokacin yayi da ba zan farka ba, Alhamdullahi” “Gaskiya mun auna arziki, da mun rasa ka rayuwa ba zata yi dadi ba” Kareem ya kalli falon ya mike tsaye. “Wata rana dole za ku rasa ni Aaryan dole kuma ayi hakuri da rayuwar” “Haka ne, amman ba ma fatan zuwanta yanzu, Allah dai ya kara maka lafiya” “Ameen” Aayam ya sauke ajiyar zuciya. “Yusura da Khadija sun sha kuka, Hajiya har sai da aka zuba mata ruwa, ban taba ganinta cikin tashin hankali irin na ranar ba, babu wanda be yi kuka ba sai ni” Kareem ya juyo ya kalleshi. “Eh kai mai zuciyar fir'auna ko?” Aaryam yayi dariya. “Ai duk abun da zai saka namiji kuka ba karamin abu ba ne, Allah dai ya tsare faruwar hakan” Dinning Kareem ya dafa. “Yusura bata fada muku abun da ya faru ba?” “Ta fada mana, har ta kwashe kayanta ai Hajiya ta bata bangare daya ta zauna saboda ta samu sakewa ita da yaranta, Khadija da Nana sun koma bangarenta, na yi mamakin kukanta wata kila ita ma ta dauka mutuwa zaka yi” “Daddy be ce komai ba a game da rabuwarmu?” “Ba ka da matsala da shi, tun a lokacin da aka fada min halin da kake ciki sai na same shi na yi masa bayanin komai, saboda mu samu goyon bayansa idan zaka kara aure, ashe Allah da kai ba, amman dai ya sani kuma ya daga maka kafa. Kawai addu'a yayi Allah yasa hakan shi ne mafi alheri” Dogon numfashi Kareem yaja ya sauke ya daga kansa sama. “Ameen” A gidan Aaryam ya wuni saboda ya ragewa dan'uwansa Zango har sai da yamma ta yi sannan ya tafi bayan sun sha hira sosai. Kareem ya juyo kenan daga rakiyar da yayi ma Aaryan bakin kofar falon sako ya shigo wayarsa. “Wata kila ni ce silar hadarinka? Shin ka aikata hakan ne da nufin kashe kanka? Ka ji zafin gaskiyar da ka sani ne Kareem? Ni ma daga baya na gane ban kyauta ba na yi kuskure, amman na maka alkwari babu wanda zai ji wannan, ina zuwa dubaka asibiti a kullum amman bana samun damar shiga na ganka saboda yan'uwanka da matarka suna gurin. Yau kuma na tafi aka ce an sallame ka na jidadin haka kuma na ji tausayinka na yi bakinciki abun da ua faru da kai, ina kaunarka Kareem Wallahi ina kaunarka” Ya goge sakon bayan ya gama karantawa, ko ya fada mata yayi hadarin ma oho, falon ya shiga ya kwanta akan kujera ya rufe ido yana maida numfashi a hankali. NOOR POV. A lokacin da cikina ya shiga wata bakwai na samu sauki abubuwa da yawa na daina amai da kwadayin sosai, ko zabar abinci. Har ta kai ni nake shirya abun karyawa da safe da kaina. Domin yanzu Hana ce mai tsananin bachin safe idan ta gama sallah ta koma ta kwana sai kace ba yar makaranta ba. Kullum sai ta buga latti saboda bachi, har tausayi take ba ni domin na san wahala ce ta yi mata yawa, na aikin gida da take ga kuma karatu da basa daga kafa. Abun sai ya zame mana kamar duty ni ce mai saurin bachin dare ita kuma ta yi rankon na safe. Domin da zarar na gama sallah Isha'i Abdull ya kawo lemun juice da yake hada min a kullum, domin likita yace na rika cin yayan itatuwa sosai a yanzu fiye da kayan zafi ko kwadayi irin su madara da danginsu. Saboda kina yana ta girma ne a yanzu, ban yi kasa a guiwa ba na rumgumi kayan marmari, kullum sai na ci da dare kuma sai Abdull ya hada min lemun juice da juicer da ya siya gurin Khadeeja Candy Store, zallar ruwan fruit take matsewa sai dan sukari kadan da yake kasa min ko kuma abar da bana so wato zuma, wani lokacin saboda bakin nawa ya saba da zaki idan babu ba zan sha ba. Da zarar ya hada min na sha sai bachi yayi gaba da ni, ko motsi ba zan yi ba sai safe. Ina tsaka da shafa face cream ya shigo dakin ya aje min cup din natural orange juice. Sannan ya nufi wardrobe ya bude ya dauko kayan bachinsa ya saka. “Kina bukatar wani abu?” Na kalleshi kamar na ce ina da bukatar ka, yau wata shida kenan ban hada shimfida da mijina ba, tun cikina na wata daya da yan kwanaki ya nade sha'awata ya jefar saboda kawai na ki yarda a zubar da cikin. Sai kuma wata zuciyar tace na daure mana na zuba masa ido tun da haka ya zaba. “Aa” “Okay to zaki yi kallo?” “Aa bachi zan yi” “Yanzu ai kin lalace da bachin dare, da dare yayi sai bachi kamin tara na dare ta yi har kin kai Morocco, Allah yasa ba raguwa ko rago zaki haifa ba, wannan lalaci yayi yawa” Na yi dariya mai sauti ina masa gwalo. “Bachin yana min dadi, da na kwanta bana sanin me duniya take ciki sai na farka” “Asha bachi lafiya Mom Unborn” Ya fice ya bar ni na cigaba da shafa face cream din, sai da na gama sannan na dauki lemun juice din na sha kadan sai na ji zakin zumar yayi min yawa gashi ba son zuma nake sosai ba, haka na saka dole na tashi na shiga bathroom na kunna tap na tara lemun na kara ruwa kadan, na kashe juyowar da zan yi santsin tile ya kwashe ni, aiko ba shiri na saki kofin na rike tab din sai kofin ya fadi kasa lemun ya zube. “Allah ya tsare na auna arziki yau kai...” Na fada ina hakki, da na fadi gurin ba karamin ciwo zan ji ba, waya sani ma ko na karye tun da jikin babu karfi. Ruwa na saka na wanke lemun da ya zube na dauke kofin da ya tsaga na fito na aje shi a inda na saba ajewa na hau gadon na yi addu'a na kwanta, nan da nan kuwa bachi yace wa yake jira ba ni ba, kamar na mutu haka na fara bachin ban san shigowar Abdull dakin ba, kashe wuta da yayi ma duk ban sani ba. Daman bana sanin komai sai safe. Ina tunanin shan lemun yana taimaka min sosai gurin samun bachi mai dadi kuma mai nauyi da tsayi, domin yau da ban shanye shi gaba daya ba na farka sai dai ban kai ga motsawa ba na ji saukar Abdull daga kan gadon ya nufi bathroom, yana shiga na ji kararar ruwa be jima ba ya fito ina kallonsa ya rufe kofar a hankali ba tare da ya kashe ruwan ba. Mamaki ya cika kwakwalwata ashe har yanzu be daina wannan abun ba, domin tun a wacan lokacin zuciyata take raya min yana biyawa kansa bukata ne a bandakin. Ina ganin ya dauki wayarsa sai na rufe idona, na yi zaton bandakin zai koma sai gashi ya kunna fitilar wayar ya haska fuskata. Ni kuma na yi kamar bachin nake da gaske har sai da ya kauce sannan na bude ido. Ga mamaki na sai na ga ya nufi kofar fita ya bude a hankali ya fice. Zumut na tashi zaune kamar ledar da iska ya dauka. Na zauna gurin da tsawon minti biyar ban ji ya dawo ba, sai na sauko daga kan gadon na bude bandakin na kunna guluf na duba sannan na kashe na janyo kofar na rufe a yadda take. Takawa na yi na fita dakin, a tunanin yana falo ne, sai dai kuma ban same shi a falon ba, domin wutar falon ma a kashe take ban ga hasken wayarsa ba kuma ban ga alamar mutum ba ta dan hasken waje da yake shigowa. Na nufi ma kunnun wutar kamar zan kunna sai kuma na fasa na nufi kitchen na leka nan ma baya nan. Na juyowa na nufo dakina da mamaki domin ko kadan zuciyata ba ta raya min abun da kunnuwa za su ji ba. Daf da zan shiga dakina ne na ji karar rufe kofar dakin Hana wata kila kuma na bandakinta ne yayi kara har na ji saboda dare ne, hakan ya saka hankalina ya karkata can, to daman idan baya falo baya kitchen baya dakina ina zai je? Waje? A tsakar daren nan ba zai fita waje ba sai idan da wani babban dalili. Na taka cikin faduwar gaba na doshi kofar dakin, na kai hannu zan murda da nufin na bude na shiga sai kuma dauke hannuna na matsa kusa na dora kunne na a kofar dakin. Shiruuuu ban ji wani motsi ba, na sauke ajiyar zuciya ina jin kamar hankali ya kwanta, ashe dan'uwansa ne ke tafe da gumurzunsa irin tafiyar da ban yi tsammani ba. “Sai yaushe za a zubar to?” Na ji muryarta, hakan ya sakan ni kwantar da kunne a jikin kofar sosai na natsu numfashi ma daker nake fitarwa saboda na ji me take fada. “Kina da matsala ne ke Wallahi, na fada miki ni ai na san lokacin da ya kamata a zubar ko?” “Tsoro nake kar ya girma, kuma ina tsoron na sha wahala” Ta fada cikin muryar kuka. “Ai na sani idan ban ja lokaci haka ba, ba zan samu hadin kanki ba, yanzu ana zubarwa kuma ba zaki sake yarda da ni ba” Rarararararsssssssaaaa. Gabana ya bugawar da mai sauraren tsawa dake tafe da ruwa. “Zan yarda, ni dai dan Allah a zubar” “Kin yi alkawari?” “Eh, dan Allah a zubar” “Ki kwantar da hankalinki mana, na san abun da zan yi, kin san ina sonki sosai ai, ina son ki Hana, amman ki yi ta wahalar da ni, Wallahi da ace ke na fara gani ba zan auri yayarki ba...” Ban sake jin komai ba sai shesshekar kukanta kadan kadan. Tashin hankali ne be bari na sake jin komai ba ko kuma dai ba su sake cewa ba din. Na dauke kunne na shafa wuyana ina lalaben sarkar da babu ita a wuyana. Jikina ya fara rawa hawaye suka yi ambaliya a idona. Na shiga na same su a ciki na nuna musu na sa komai, ko dai wai ban ji daidai ba, ko dai gizo kunnuwa suke min. Na bar kofar na fara takawa na nufi dakina na shiga na hau gadona na kwanta na rufe ido na tsawon min biyu sannan na bude. Wai ko zan ji cewar mafarki, amman ban ga alamar haka ba. Na mari kaina sai na ji zafin na tsara kunci na, tabbas gaske ne ba mafarki nake ba. Amman taya? Kanwata ce fa uwa daya uba daya, kanwata da mijina? Kanwata ta jini mai bina, kanwata da muka kwanta a mahaifa daya ciki daya uwa daya ta kawo mu duniya? Kuma mijina mijin da nake aure auren sunna! Mijin da nake dauke da cikin dansa ko diyarsa. Tun yaushe haka take faruwa? Na mike tsaye na nufi madubi na sai kuma na zauna a kasa. Me na yi da na cancanci haka? Why me? Why? Kanwata? Jinina? “Wayyo Allah na” Na dafa zuciyata sai wani irin kuka mai ban tausayi da taba zuciya ya zo min. Wannan abun yayi min muni ina ji a wasu gurare amman ban dauka abun zai zo kusa ni ba. Na tashi daker na koma saman gadon na kwanta jikina na rawa na takure guri daya na rumgume fillo, a wannan daren bachi be samu damar ziyarta idona ba, kunci be bar ni, kamin safe zazzabi ya rufe ni, filon da na rumgume kuma ya jike da hawaye na. Abdull be dawo dakin ba sai asuba, ina jin shigowarsa da lokacin da ya kwanta saman gadon ya lulluba... Littafin nan ba kyauta ba ne. Biya ki karanta cikin aminci. Pay 500 to Zenith Bank Hadiza Abubakar 2451879008 And send the evidence of payment to my WhatsApp number 08036126660. Be dade da kwanciya ba na ji nishanrinsa alamar bachi mai nauyi ya dauke shi. Juyowa na yi na kalli kwanciyarsa, ina mamakin karfin hali irin na ďa namiji a haka kuma yake kallo muna ta rayuwa a gidan kamar babu komai a tsakaninsa da Hana. Sallah bata wani dame shi ba daman ni ce mai tashi da wuri na yi, dan haka na sauko da kafafuwana kasa na nufi bandaki, wanka na fara yi sannan na yi alwala na fito sanyin ruwan da kuma ac dakin yana ratsani sai ya saka na dan ji sassauci a jikina. Na zuciya kan na san har abada ba zan samu ba. Ni da farinciki mun yi bankwana. Doguwar riga na zuba na shimfida sallaya na sauke farali sannan na fara tasbihi. Ban daga sallayar ba har sai da na ji farkawarsa misalin bakwai na safe. “Miyasa ba ki tashe ni ba gashi rana ta yi” “Ni ma ban farka da wuri ba” Shi kawai na iya amsawa na koma saman gadon na kwanta na lafe kamar mai bachi, domin har lokacin ban san me zan yi ba. Na nuna musu an san komai na rufe su da fada ko kuma na danna na barwa zuciyata komai na bar su da Allah? Amman zan yi? Ina jin abun kamar ba shi da sauki, ina jin zaba da radadin cin amanar da yar'uwata ta yi min fiye da kunar garwashin wuta. Ina jin da ya taba ni yana fadin. “My soul ta so muje mu yo breakfast” “Sai anjima bana son komai yanzu” Na amsa hawaye na min zuba yayin da fuskata take lullube a cikin bargo. “Okay, ba ki da lafiya ne?” “Lafiya kalau bana son damuwa dan Allah ka tafi” “Okay.. I'm sorry dear...” Ya fice daga dakin sai after like 40m ya dawo yayi shirin office. “Bachin be ishe ki ba kenan? Ni zan wuce aiki sai na dawo” Bance masa komai har ya fita. Sannan na tashi zaune gaba daya na rasa me zan yi kaina ya daure abun yayi min muni. Sauka na yi saman gadon na fito falo na nufi windows ya na daga curtain ina kallon motar da Abdull ya shiga Hana kuma ta bude front seat ta shiga ta zauna. Hawaye ya sauko min a haka suke kallona? Yar'uwata ta zama kishiyata ta san sirrina ta san komai akan mijina. Kusan a falon na wuni ina ta yawo ya kasa sukuni na rasa kalar tunanin da zan yi, kamin na samu natsuwar yankewa kaina shawarar da nake ganin ta dace da ni. Bayan ruwa ban iya sha ko cin komai ba har karfe biyu ta yi na rana na je na yi sallah na fito falo na zauna ina jiran dawowar Hana, domin ita ce mai dawowa da wuri Abdull sai biyar ko shida yake dawowa gidan. Na bata awa daya a zaune sannan ta turo kofar falon ta shigo da sallama na amsa mata ba tare da na bari ta kalli ido na. Domin na yi kuka har idon ya kumbura, kai tsaye ta wuce dakinta, kaya kawai ta canja ta fito ta nufi kitchen kamar yadda ta saba sai na bi da kallo wai yanzu ita ma tana dauke da ciki kamar yadda nake dauke da shi kuma cikin mutum daya. Sai da ta shiga ta kunna gas ta dora ruwan zafi sannan ta tambaye daga can kitchen din. “Noor me za a dora” Na mike tsaye na nufi kitchen din na shiga, sai na zame ta tana yanka lemu zata sha sai dai gani na ya saka ta tsayar da yankan da take. “Lafiya? Me ya samu idonki?” “Kuka na yi” Ta aje lemun da wukar ta matso kusa da ni. “Kuka dai? Fada kuka yi da Ya Abdull ne ko baki da Lafiya?” Na kalleta ina mamakin yadda take nuna min kulawa kamar ba zata ci amanata a bayan idona ba. “Na san muna samun tsabani Hana, amman ina sonki ina sonki sosai, zuciyata bata taba raya min na cutar da ke ba, ni ba zan iya?” “Me ya kawo wannan maganar Noor?” “Ina tunanar da ke ne idan kin manta, Wallahi Hana ko rayuwata kika ce kina so zan iya baki, balle mijina zan iya mallaka miki Abdull mallakawa ta har abada Hana, Wallahi zan iya yin duk yadda zan yi na ga ya sake ni in ya so sai ki aureshi” Ta matsa baya tana kallona cikin tashin hankalin da ya bayyana a fuskarta. “Me Abdull ya fada miki? Wallahi sheri yayi min” “Babu wanda ya fada min komai, ni na ji da kunena, na kuma gani da idona, kika hada kai da mijina yana ba ni maganin bachi saboda yayi tarayya dake” Ta daga hannu biyu tana yi min rantsuwa. “Wallahi Wallahi Wallahi Noor ban hada kai da shi ba?” Na daka mata tsawa. “To me yake zuwa yi dakinki? Kullum sai ya ba ni maganin bachi na sha sannan ya tafi dakinki kishiyata ce ke?” Ta girgiza kai tana kuka. “Aa amman ba yadda kika tunani ba ne, Wallahi ni ban ci amanarki ba, Wallahi Noor ba son raina ba ne” “Haka ne, shiyasa ai yake tafiya dakinki har kuna hira kina tambayarsa yaushe za a zubar da ciki, ina dauke da cikinsa kina dauke da cikinsa wane irin wulakanci da kaskaanci ne wannan?” Ta zube kasan guiwoyinta tana kuka. “Na shiga uku dan Allah Noor ki yi hakuri ki fahimce ni” “Wace fahimta zan miki wanda ta wuce wannan? Ko karya nake baki dauke da cikin Abdull ba ki tarayya da shi?” “Gaskiya ne ina dauke da cikin ina tarayya da shi, amman ba ta yadda kike tunani ba ne, ina son dan Allah ki fahimce ni” “Toh ina jinki fahimtar da ni” Ta kasa magana sai kuka take daman ai ba zata iya magana ba, tun da bata da kalaman da zata wanke kanta da su a gurina. “Tun yaushe kuke cin amanata?” Nan ma ta kasa magana, sai na matsa kusa da ita na tabbatar mata da abun da shi ne tabbbatacce a zuciyata. “Na bar miki Abdull har abada, na bar miki Hana, yau ba zan kwana da aurensa ba” Na wuce na shige dakina na fada kan gadona ina kuka mai karfi. Abincin da bata girka ba kenan ni kuma ban sake fita dakin ba sai da na ji motar Abdull. Tsanar hada ido da shi ne ta saka na fice daga dakin na nufi kitchen na tsaya a cikin har ya shigo. “Bacchi kuke ne?” Na ji ya fada domin yayi sallama be ji kowa ya amsa masa ba. Sai da na tabbatar ya shiga dakin, sannan na fito kitchen din. Dakin da Hana take na shiga na nufi gurin da takardunta suke na bude jakarta na dauko littafi na cire paper na dauki pen, sannan na kalli kofar bandakinta da nake jiyo kukanta na munafurci daman na san haka zata yi ai, karshen munafuki jin kunya. Na shiga da kuzarina, domin na gama yanke shawara Wallahi ko auren Abdull ne rayuwata yau kam na shiryawa mutuwa domin ba zan iya kara awa daya da aurensa ba. Zaune na same shi sanye da suit dinsa na aiki da be cire ba yana duba wayarsa da alama wani abun yake kallo. A lokacin da na kalli fuskarsa sai na ji ban taba tsanar kowa a duniya kamar yadda nake jin tsanarsa ba. Kusa da shi na karasa na aje masa takardar da biron. Ya kalli takardar da biron da na aje masa. “Miye wannan?” “Me ka gani?” Na tambaya ina kallonsa cike da tsana da kyama. “Takardar da biro” “So na nake ka rubuta min saki” Ya kalleni. “Are you okay?” “Ka ji ni ai i mean it ka rubuta min saki na ce!!!” Na karashe zance a tsawace. Ya aje wayar hannunsa ya mike tsaye. “Saki? My soul kin san me kike fada kuwa? Ba a wasa da wannan kalmar fa” Ya dafa ni sai na buge hannunsa ina tauna hakora ta cikin bakina. “Wani abu kika sha yau?” “Eh... Na sha bala'i da masifa da wutar da zan amayar maka a yanzu nan idan baka sake ni ba” “Na sake ki kamar yaya me yake damunki?” “Kai ne kai kake damuna Abdullahi, na tsane ka, damba marar tunani dan duniya wulakantacce, barikin ta wuce waje har sai ta shigo cikin gidana? Sai ka hurumina da yar'uwata?” “Kina da hankali kuwa? Ni kike kira damba...” Ya daga hannu zai mare ni, a nan Allah ya ba ni iko da karfin iya rike hannun da dukanin karfina. “Maci amana, karka sake tsinanen hannunka ya kai ga halattaciyar fuskata ma ci amana ka bi yaya ka bi kanwarta, haihuwar hasara” “Okay ta kwashe karya da gaskiya ta fada miki kin zo kina zargina da abun da ban aikata ba ko? Saboda tsaurin ido har ki kalleni kina kirana da suna kala kala ko? Ni fa mijinki Noor” Na tofa masa yawu a fuska. “Allah ya kiyaye Allah ya kiyaye yanzu kam, da can amman ban da yanzu” “Okay rashin kunya zaki nuna min ko? To sai na ga idan akwai uban da ya isa ya saka na sake ki, kuma kika sake fada min wata maganar banza sai na ci ubanki yanzu nan” “Ubana yayi maka yawa, kuma babu wanda zai saka kaka kai zaka sake ni dan kanka, wato kai da yake namiji mai karfin hali dan duniya har kana da bakin yakata ko? Taya zaka ba ni maganin bachi ka tafi ko wane dare ka kwanta da yar'uwata sai asuba ka dawo ku ci amanata a tare kuma ka ce ba zaka sake ni ba? Wallahi karya kake Abdullahi” Ya nuna kansa yana murje ido kamar da gaske be aikata ba. “Ni nake saka miki maganin bachi?” “Aa ni nake sakawa kaina, wanda ka ba ni jiya ya zube ban sha ba, ina kallon lokacin da ka tashi daga dakin nan ka tafi dakin Hana, na labe na ji abun da kuke magana a kai, har ciki za ku zubar” Na fashe da kuka domin ba ni da wani abun yi a yanzu kamar shi. “Ba laifinka ba ne, laifin yar'uwata ne ita da ta ci amanata, dama kum jira wata kila gurin haihu zan mutu ai sai ka aureta ku zauna” “Innalillahi Wa'Inna Ilaihirraji'un” Ya sassauta muryarsa. “Noor Wallahi aikin sheidan ne, kuskure ne aka samu, me Hana ta fada miki?” “Ban saurareta ba, kamar yadda ba zan saurareka ba, saki kawai nake so ka sake ni” “Ni ba zan sake ki ba Ina son ki Noor shedan ne Wallahi” Kalmar ina son ki ta saka na ji kamar da wuka a kusa na daka masa a sautin zuciya. Ya matso kusa da ni “Abu ne da zamu tsaya mu rufawa juna asiri, ita yar'uwarki ce ni kuma mijinki ne, kuma ga cikina a jikinki Noor, Wallahi na miki alkawari ba zan sake ba” “Gobe zan tafi na bar muku gidan, ku cigaba da aikata abun da kuke har mahadi ya bayyana, ni dai ka sake ni” “Ba zan sake ki ba Noor ni ba zan sake ki ba, ni ban taba aikata komai ba sai a wannan karon da Allah ya kawo tsautsayi” “Karya kake, ba wannan ne karon farko ba Wallahi kawai dai ban gane ba sai yanzu, shiyasa tun kamin ka aure ni kake ta taba ni, da na yi magana ka ce gwada ni kake yi, ashe gwadawa kake ka gani idan ni yar iska ce na amince maka a waje, ka gama da ni ka tafi, da hakan be samu sai ka bijiro da maganar aure, da na samu ciki kuma sai na daina burge ka saboda ba auren Allah ba ne, auren sha'awa ka yi min. Sai kuma sha'awarka ta koma gurin kanwata jinina, ita kuma bata duba alaka ba ta yarda kuka taru kuka ci amanata” Na dafe zuciyata ina bakincin da ban fahimci wannan red flag din ba tun farko, ga kuma Safeena ma ai izina ce. Ya dafe kansa ya juya ya juyo ya fara safa da marwa kamin ya samu tsayawa gabana a rikece har da fashe min da kuka. “Dan Allah ki kwantar da hankalinki mu yi magana ta fahimta, sakinki zai bata abubuwa ne kawai, ina zaki je da ciki? Abun nan aikin shaidan ne Noor zai iya fadawa kan kowa, zan tafi na bar miki gidan har hankalinki ya kwanta amman ni ba zan sake ki ba” A take kukan ya yanke min. “Ba zaka sake ni ba saboda kana tsoron kar a tambayi dalilin mutuwar na fadi cewar kai da yar'uwata kuka ci amanata?” Yayi kamar be ji ba dauki wayarsa yana kuka zai fice dakin. “Ba zaka sake ni ba, sai na hada maka cewar dan da Safeena ta haifa maka yanzu ba jininka ba ne, ďan falkanta ne, ex-boyfriend dinta? Sai na fada maka dalilin da ya saka Safeena ta daina daga maka hankali akan aurena? Sai na fada maka na san Safeena irin wanin da baka yi mata ba? Sai na fada maka a duk lokacin da ka bar Kano tana tarayya da Ex dinta ne har sai ka dawo? Sai na fada maka Safeena ta taba ji min ciwo a hannu saboda ta yi tunanin Ex dinta kuma falkamta so na yake, saboda kishinsa?” Ya juyo ya kalleni kukan da yake ya tsaya. “Kina cikin bachin rai ne, zaki iya fadar komai Noor na sani” “Ina cikin bacin rai, amman ba cikin gushewar hankali ba, idan baka yarda ba ka dauki yaron ka gwada jininsa da naka mana, ka cancanci haka ai, daman shege sai dan iska, a da har mamakin dalilin Safeena nake na aikata haka, ashe ta yi daidaita kai din tsohon shege ne” Ya daka min tsawa. “Ya ishe ki haka yanzu kam ya ishe ki haka? Mace nawa take kama mijinta yana abun da be dace ba amman ta rufa masa asiri a zaune, balle ni da kaddara ce kuma ba ni kadai ba har da yar'uwarki, kusan ma ita ta ja ra'ayi a komai” “Wallahi ko kai ne dan autan maza na gama zaman aure da kai Abdull, ko ka sake ni ko na daga na kira uwarka a yanzu na fada mata abun da ka aikata da kanwata kuma na tabbatar mata cewar ďan da Safeena take shayarwa a yanzu ba jikanta ba ne? Domin ba jininka ba ne, na yarda idan aka bincika aka tararda tsabanin haka a kai ni kotu, ko dai so kake na kira kanenka da mahaifiyata ma fada musu? Kwanciyar hankalinka ka sake ni, Ba zan fadawa kowa abun da kuka aikata ba ni na bar ku da Allah” A fusace ya nufi takardar ya dauka yayi rubutu a kai ya jefa min a fuska. “Ke ce da bakinciki ba ni ba...” Ya nufi kofa. “Allah ya raba ni da bakinciki tun da ya raba ni da kai” Na fashe da kuka mai karfi. Na yi kuka kuka sosai kuka irin na macen da rauni ya mamayeta ta rasa makoma, saki nake so kuma na samu yanzu idan na koma gida me zan fadawa iyayenmu? Na fada cikina ina bakinciki da ban zaba masa uba na gari ba. A dakin na kwana, sai dai bachi be dauke ni ba, bayan ruwa bana shan komai ba, shi kuma tun da ya fita be dawo ba, har garin Allah ya waye. Cikin kuka da bakinciki na yi sallah Asuba, na roki Allah ya sanyaya min zuciyata ya sanya min saka min kana'a domin har lokacin ban ji zan iya yi ma yar'uwata wata bakar addu'a ba, har gobe ita din jini na ce idan wani abun ya faru da ita kamar ya faru da ni ne. Ni dai na san na barta da Allah shi ya san abun da ya dace da ita kuma shi ya san sakamakon da zai yi min akanta. Misalin shida da rabi na fara hada kayana cikin akwaiti sai da na yi nisa da hadawa sai kuma, sai kuma na ji bana bukatar kala ko daya domin Abdull ne ya siya, a yanzu kuma bana sha'awar duk wani abu mai alaka da shi. Cikinsa ma da yake jikina da ace zan iya da cire shi zan yi na aje masa a gidansa na yi tafiyata. Jaka kawai na nufa na dauka na hada yan kudadena na dauki wayata ita ma dan ta zame min dole a yanzu. Hijabi na saka sannan na dauki takardar sakin da ban iya karantawa ba na saka a jaka na nufi kofar dakin na bude, sai na yi arba da doguwar takardar aje a kofar daki. Na duka na saka hannu na dauka a tunani Abdull ne ya aje min amman da na fara karantawa sai na tararda sabanin haka.. _Yar uwata noor, ban ci amanarki, ba zan taba iya cin amanarki ba, ba ki saurare ni ba, bakinciki be bari kin tuna da halina ba! Yadda kika dauki abun ba haka yake ba, Wallahi mijinki ya nuna min fin karfi ne, ya fara tallata min bukatarsa tun a lokacin da na bukaci tafiya gida kika hanani ne. A lokacin bana son fada miki ne saboda kar na zama silar lalacewar aurenki..._ Na hade yawu na nufi kujera na zauna. _Da ya fahimci ba zan aminta ba, sai ya shirya min tarko, ranar Monday da muka fita da sunan zai sauke ni a hanya, sai ya biya da ni a wata tsohuwar ma'aikatarsu, yace min zai tafi ya duba wani abun ne, ban yi tunanin zai nuna min karfi ba ne, shiyasa ta yace na shiga wani office na dan jira shi, na jira har na gaji da zama be dawo ba da na fito sai na lura gurin babu mutane sosai, na tsorata da farko na dauka siyar da ni zai yi, ashe kudirinsa dabam ne. Na koma ciki na zauna jiransa har ya dawo, sai ya fara lallaba ni yana min kamfe da abubuwan da yake min na kyautatawa ashe ba dan Allah yayi min ba, da na nuna masa ba haka ya fara kokawa da ni, Wallahi na yi ina yadda zan iya na kare kaina Noor amman hakan be samu ba sai da ya biya bukatarsa, a ranar ban samu tafiya makaranta ba a gurin na wuni, sai da ya dawo aiki ya biyo ya dauke ni aje ni nesa da gidan na tako na iso da kafa sannan ya shigo_ Hawayena sun zuba jikin takardar na juya dayan shafin ina karantawa. _Daga ranar ne ciki ya shige ni, tun daga lokacin yake bibiyata yana ba ni hakuri kuma yana lallaba ni ko zan amince amman ban amince masa ba, ba zan iya fada miki ba ne, saboda kar na zama silar lalacewar aurenki da na Mama na rumgumi a abun a matsayin kaddara. Shi da kansa ya ba ni abun auna ciki ya ce na auna idan babu ciki saboda kar mu ya bayyana mu ji kunya, kuma da na auna sai na samu akwai ciki amman ban san ko wata nawa ba ne, da na fada masa sai yace za a zubar amman sai na amince masa ya ci gaba da mu'alama da ni, da hakan ya ribance ni na amince saboda ina son a cire cikin kar ki gane, domin ya fada min ya san duk yadda zai yi ya wanke kansa ni ya bar ni a ruwa idan ban aminta ba, kuma gaskiya ya fada ni mace ce bayyanar cikin zai rusa rayuwata, shi kuma namiji ne, wanda ya riga ya gina rayuwarsa kaddarata bata isa ruguza komai ba_ Ya share hawayena ina kuka. _Ki yi tunani mana Noor yadda dangi da iyaye suke murna da dan halak, haka suke bakinciki da na haram, na san Baba kashe ni zai yi idan ya sani, buri na yadda za a zubar da ciki ne ba tare da kowa ya ji ba. Kullum maganar da nake masa kenan kuma saboda haka nake amincewa da shi, shi kuma yana ga jan lokaci saboda biyan bukatarsa. Amman ni ba zan iya cin amanarki ba Noor zuciyata ba haka take ba, ba a mana wannan tarbiyarba, tsorona na lalacewar aurenki ne da na Mama, ba ki tsaya kin saurare ni ba, ban san ya zan miki bayani ba_ Na mike tsaye da sauri a lokacin da nake karanta sakonta na karshe. _A lokacin da zaki samu sakon nan ki karanta bana gidanki, na bar gidanki Noor, kuma ba gida zan tafi ba, ba zan kaiwa Mama abun kunya ba, ba zan tafi da cikin shege gidan Baba ba, na san zaki fada musu dukan abun da ya faru a lokacin da zaki koma gida ko kuma aka neme ni aka rasa. Dan Allah ki fada musu gaskiya Wallahi ba da son na aikata ba, kaddara ce ta riga fata, zan tafi inda ban san kowa ba kuma kowa be san ni ba, na bar ku Noor ku yafe ni, musamman ke...!_ Na jefar da takardar na nufi dakinta da sauri ina kiranta. “Hana Hana Hana...” Na tura sai na samu dakin babu kowa, na fada bandaki nan ma bata nan, na fito da gudu na nufo gate ina tambayar mai gadi ko ya ga fitarta. “Hana ai tun jiya da dare ta fita, misalin sha daya na dare” Na fashe da kuka na bude gate din na fita da gudu kamar ance zan ganta. Na yi dama na kalli karshen Titi da babu mutane na juyo na yi hagu nan ma babu alamar sawunta. A gurin na zube na kwarara wani irin ihu da dukan karfina ina kuka har sai da abun da ke cikina na motsa.... Duk wanda ta karanta min littafi bata biya ba na barta da ALLAH. duk wanda ta yi min sharing paid pages na barta da ALLAH. It's 500 Zenith Bank Hadiza Abubakar 2451879008 And send the evidence of payment to my WhatsApp number 08036126660 “Lafiya Hajiya Lafiya?” Ban kula mai gadin ba na dago da guduna na dawo cikin gidan na nufi jakata na bude na kira number wayarta. Na yi sa'a ta shiga kamin ta amsa har wani jiri nake ganin tsabar bugun da zuciyata yake yi. Ringing tayi ta katse bata daga ba, ina sake kira sai na ji wayar a kashe. Faduwa na yi zaune kan kujerar, ban san abun da zan yi ba, ban san ta ina zan fara nemanta ba. Ban san kowa cikin kawayenta ba. Hana bata da kawaye a garin nan sai yan makaranta kuma ban san waye zan fara bincika ba, ni ban ma san ina makarantarsu yake ba. Takardar na dauka na saka a jakata na koma dakin na dauko babban akwatina na zuba iya kayan da nake iya gani na rufe na janyo akwati na fito ina kuka. Bana son na kira Mama na fada mata domin bana son su san abun da yake faruwa da Hana, musamman Baba da ba fahimta zai yi ba. Idan kuma na koma me zan fada musu? Miye silar mutuwar aurena? Kuma ina zan ce na bar Hana. Ban amsa tambaya ko daya da mai gadin date din yake min ba. Na mike hanya na fara tafiya ina hawaye har na isa babban titi na tari okada na fada masa tashar da zan hau motar Kano zai kai ni. Ya charje ni dubu biyu daga unguwar da nake zuwa unguwar da ya kai na hau mota. Na taki sa'a na isar tashar a lokacin da ake neman mutum daya motar Kano ta tashi na mika duka kudin da nake da su na shiga motar na zauna bayan sun karbi information dina. Tafiyar ta min nisa sosai wata kila saboda mota na hau, domin ban tana zuwa ko dawowa a mota ba sai wannan karon, wata kila kuma saboda abubuwan da suka saka ni gaba ne. Dan carjin da ya rage min na siye ruwa da shi su nayi ta sha, har muka isa Kano. Karfe shida muka sauka garin Kano, domin Tafiyar awa tara ne daga Kano to Lagos a babbar mota. Na fito motar aka cire min akwatina na karba na fara ja zuwa gate din tashar. Napep na shiga na fada masa kasuwar da zai ni, wato kasuwar yan waya. “Dan Allah ka dan jira ni sako kawai zai karbo” “Okay amman Karki dade” “Ba zan dade ba” Na bar akwatina a ciki na shiga cikin kasuwar a lokacin da wasu suke ta hada hadar tashi saboda yamma ta yi. Wani shagon na nufa na nuna masa wayar hannuna. “Malam kuna siyen irin wannan wayar?” Ya kalleni irin duban nan na rashin yarda. Sannan ya karbi wayar ya duba waje da ciki. “Wayar waye?” “Tawa ce siyarwa zan yi” “Saboda me zaki siyar?” “Ina cikin matsalane ina bukatar kudi” “Ina receipt da kwalin wayar” “Suna gida” “To kije ki dauko waya a hannuna haka ai ta sata ce” “Wallahi tawa ce, ka duba ciki akwai hotuna na a ciki, kawai ina cikin matsala ne ina bukatar kudi” Na fada hawaye na jika fuskata. Dayan dake gefensa ya taso ya karbi wayar ya duba. “Nawa zaki siyar” “Ni ban san kudinta ba ku siya kawai” “Iphone 14pro max mu baki 305k kin ga ta dan ji jiki” Na zaro ido ashe babbar waya nake riko ban sani ba. A zatona wayar ba zata wuce 50k ba idan ma ta yi tsada. “Ka dai kara, dan Allah matsala ce ta saka zan siyar Wallahi” Sai ya miko min wayar. “Ba zan iya siyenta fiye da haka ba, siyen waya haka ma ai it's risk kawai dan na ga kina cikin damuwa ne zan siya, kin ga ma yanzu tashi zamu yi” “To kawo kudi” Ya cire min layina ya miko min sannan ya kirgo kudin ya miko min ba tare da na kirga ba na karba ina masa godiya. Na fito da sauri na samu mai napep din nan a inda na bar shi ina shiga ciki ya rufe ni da fada wai na bar shi yana ta jira. “Yi hakuri” “Ina zan kaiki?” “Hotel” Na fada kai tsaye domin kudirin da ya saka na siyar da wayar kenan domin babu sauran kudi a hannuna. “Wace hotel” “Ko wace ma wacce dai mutane ba su cika yawan cikawa ba” Ya fara lissafa min sunayen hotel yana tambayar wacce za zai kai ni. Zuciyata kuma taya raya me kamata na tafi can ba, gida ya kamata na tafi, amman idan na tafi gida me zan fada. “Kai ni ko wace ma” “Okay” Na share hawaye ina jin bakinciki a zuciyata, yau ga ni a garin Kano amman ba damar tafiya gidanmu. Ina yar'uwata take a wane hali take yanzu? Me ye makomar cikin dake jikinta? Me yasa ban saurareta ba wata kila da bata gudu ba. Ya sauke ni a gaban wata katafariyar hotel mai girma da haske ko'ina. “Mu shiga ciki ko na sauke ki a nan?” “Nan ma ya isa” Na fito na dauko akwaiti na bude jakata na dauko 3k cikin kudin wayar na mika masa, sai ya karba yana min godiya. Na juya na hotel din sai kuma na ji bana ra'ayin shiga ciki. Dan haka na tari wata Napep din na shiga domin aiwatar da kudirina. A kofar gidan Kareem mai napep din ya sauke ni, na sallame shi na nufi flowers din da suke gefen gidan na daga akwaitina na jefa a ciki sannan na nufi gate din. Na kwankwasa na san by that time yana gida ko hanyar gida, domin muna hanya aka yi sallah Magariba. Mai gadin ya bude ya leko. “Mai gidan yana nan?” Ina magana numfashi daker domin karfina ya gama karewa ga bakina ya bushe, har lokacin kuma ban ji ina sha'awar komai ba duk da kasancewar ina jin yunwa. “Eh yana nan” “Dan Allah ka ce mishi yana da bako a waje dan Allah ya fito abu ne mai muhimmanci” “Wa zan ce masa?” “Kawai ka fadi haka dai” “Tohm” Ya juya ya koma ya rufe gate din. Ni kuma na kai hannuna na dafa ginin ina jin zuciyata kamar zata fashe. Tun a lagos na kudurtawa zuciyata zuwa na fada masa damuwa ba, da na yi nufin na fara sauka hotel ne washe gari na je na same shi a restaurant ko asibitinsa na fada masa, amman burin ceton yar'uwata ya saka na ji kamar idan ta kai gobe zan iya rasa rayuwarta. Na kwashe minti talatin tsaye a gurin sannan ya sake bude gate din. “Yace a shigo da bakon” Na cira kafa na shiga cikin gidan na fara takawa sai na hango shi tsaye a entrance yana kallona har na karaso. Ya kalli daga kasa har zuwa sama. “Noor” Na kalleshi ba tare da na amsa ba. “Minene kuma wannan karon?” “Kareem na san ina damunka ina shiga rayuwarka da yawa, amman dan Allah karka ce min aa na maka alkawari daga wannan ba za sake ba, dan Allah ka taimaka min dan girman Allah” Na kai kasa ina rokonsa sai kallona yake ya kasa cewa komai. Na nufo shi ne saboda ina jin yana karfi na dukiya wata kila har da hanyar da zai taimaka min. “Shigo ciki” Ya juya. “Matarka za....” “Bata nan” Na mike tsaye na bi bayansa na shiga cikin falon sai na zauna a kujera shi ma ya zauna nesa da ni yana kallona. “Me ya faru?” Na bude jakata na dauko takardar sakin zan tashi na kai masa sai ya taso ya karba ya zauna a dayar kujerar dake kusa da tawa. Yana gama karanta takardar ya kalleni “Innalillahi Wa'inna Illaihirraji'un, Saki Noor mi ya faru?” Na ciro dayar takardar da Hana ta aje min na mika masa ina hawaye. Ya karba ya fara karantawa mikewa yayi tsaye ya girgiza kai ya runtse ido, can kuma ya bude idon ya kalleni. “Da gaske?” Na daga mishi kai har sau uku, ya koma ya zauna na dafe kansa. “Ko da yaushe idan ina cikin damuwa, na kan zo gareka saboda ina samun mafita kuma kana taimaka min, dan Allah ka taimaka min ta dawo, bana son Mama ta sani ko Baba domin idan Baba ya ji zai Fadawa Umma ita kuma zata yada a cikin unguwa, Mama kuma idan ta ji wata kila ba zata iya hakuri zata janyo mutuwar aurenta, bana son daya daga ciki ya faru?” “Na ji zan taimaka miki amman dole ne iyayenki su sani Noor, me zaki fada musu a mutuwar aurenki? Kuma yanzu kamin a gano yar'uwarki me zaki fada? And idan ma an ganta amman ba a cikin hali mai kyau ba dole za su ji ba zaki iya boye wannan ba, yanzu idan kin tafi gida me zaki fada?” “Ba gida zan tafi ba Hotel zan zauna, har sai an gane Hana sai mu tafi gida tare, na Fadawa Baba kawai mun yi fada ne ya sake ni” “Noor yanzu kurciyata tana damunki, matsala irin wannan iyaye kadai suke iya tsayawa mutum, dole ne ki fada musu gaskiya, gidan ba zaki iya Fadawa Baba ba, to ki fadawa Mahaifiyarki, kaddara ce babu wanda ya wuce kaddara” “Kaddarar ita ce kullum a biye da ni, aure na biyu kenan ina yi babu dadi, gashi yanzu har na janyo Hana ta gudu ta shiga duniya” Na fada ina kuka. Mikewa yayi tsaye ya haura sama ya bar ni a falon ina ta kuka ni kadai gaba daya ma duniyar ta isheni. Be dade ba ya sauko da waya a kunnensa. “Yeah let me ask her” Ya kalleni. “Ina kika saka ran zata tafi?” “Ni da ita ba mu san kowa a Lagos ba, ban san inda zata tafi ba, bata da kawaye sai yan karantarsu ban san gurin waye zata tafi ba” “Wai bata san kowa a lagos ba” Can kuma na ji ya amsa da “Okay Thank you” Ya zauna sannan ya amsa kiran da ya shigo. “Aaryam na kira baka daga ba” Ya kalli agogo. “Okay, daman wani taimako nake so dan Allah, wata yarinya ce ta gudu a Lagos nale son a nemo ta, na san kana da friends yan Lagos sosai maybe you can help” Ya mike tsaye ya nufi kitchen ya turo kofar, bana jin komai da yake fada har sai da ya gama wayar ya dawo ya zauna. “Ina wayarki dole sai an tura hotonta” “Na siyar na siyar da ita yanzu, suka ba ni 305” “Wayar?” “Eh” “Saboda me?” “Ba ni da kudi ne, kudin sun kare a hawan mota, shi ne na siyar da wayar saboda na yi amfani da kudin, irin wayarka ne” Ya kalli wayar ya kalleni. “15 pro max suka baki 305k?” “Aa taka ta tsufe tawa da shekara daya, tawa 14pro max ce” Na ciro kudin na zube duka a gurin. “Wane barayo ya siye wayar?” “Ba barawo ba ne shago ne” “Saboda kawai sun ga baki san kan waya ba sai su siye a 305k? Dole sai an nemo hotonta da Yanzu ina layinki yake? Dole sai an nemo hotonta da sunan makaranta su” Na yi shiru ina tunanin gurin da zamu hotonta domin ban zan tafi gida babu ita ba. “A dp dinta na whatsapp akwai hotonta kuma sunan makarantar su Victory College Of Health” “Yanzu ina line ki?” Na saka hannu jaka na dauko layi na mika masa, sai ya karba ya haura sama sai gashi ya sauko rike da wata wayar touching amman ba iPhone ba. Ya saka line da na bashi ya dade yana taba wayar ban sa me yake dubawa ba kamin ya miko min wayar. “Saka number ta” Na karba sakon karta kwane ya rubuta a messager wayar. “Dan Allah Hana ki dawo, tafiyarki ta haifar min da matsaloli da yawa, na bar Lagos na dawo Kano, amman na kasa tafiya gidanmu saboda ban san me zan fada musu ba, bana son na fadawa kowa matsalarki, na miki alkawari babu wanda zai ji, dan Allah ki dawo na yafe miki kuma na fahimce a yanzu, Abdull ya sake ni, Hana kuma kin sani ina da ciki zan iya rayuwa zan iya mutuwa, idan baki dawo gida ba, ni ma zan koma ba, zan tafi na bar garin Kano ne, domin rashin izurin da na yi miki ya hana ni sukuni, ina kaunarki yar'uwata dan Allaj ki dawo, na miki alkawarin babu wanda zai ji” Na saka number ya na dago na mika masa wayar ina kallonsa. Kwarjinsa da kirmarsa sun cika min ido, Kareem mutum har da rabin mutum, shi din mai tsayawa ne akan damuwata mai kokarin ganin bayan abun da ya hana ni farinciki. “Na gode...” Na furta ina hawaye. “kwashe kudin ki tafi gida” “Toh” Na kwashe kudin na saka a jaka sai ya miko min wayar. “Indai yar'uwarki tana sonki da gaske zata dawo ko ta kira ki tsakanin yau zuwa gobe, idan kuma bata kira ba, zamu yi amfani da line mu gano inda take, amman dai zata dawo na miki wannan alkawari ki kwantar da hankalinki” Na daga mishi kai sannan ya karbi wayar na mike tsaye da cikina. “Noor Zauna" Na koma na zauna sai ya tashi ya nufi kitchen be dade ba ya fito rike sandwich da lemu ya janyo karamin lebur ya dora min a kai. “Zaki iya cin wannan? Ko wani abun kike so a kawo miki? Jikina na rawa akwai yunwa a tare da ke” Ban tsaya ba shi amsar zan iya ci ko aa ba na dauka na fara ci. “Kar matarka ta dawo ta same mu a nan” “Ba zata dawo ba. Yaushe rabonki da abinci?” “Rabona da abinci tun jiya bana iya cin komai sai ruwa, gaba daya maza ba su da kirki, Zafeer be fahimce ni yanzu yana can yana cewa na ci amanarsa, na auri Hafiz ban jidadi ba, yanzu kuma wannan” Ajiyar zuciya ya sauke ya bata rai sosai yana kallona. “Wannan duk ya fi su zama dan iska, ni mana ban so aurenki da shi ba, kawai babu yadda zaka hana abun da Allah ya tsara faruwarsa ne, taya zai aikata duk wannan kuma ya sake ki? Ga cikin shi a jikinki” “Ni na ce ya sake ni, ba zan iya zama da shi ba, ba zan iya zama da mazinaci ba” Ina maganar ina kuka har na cinye duka sandwich din na shanye lemu na aje kofi, na mike tsaye Kareem be sake cewa komai ba. Ya dauki cups din ya kai kitchen ya kawo min tissue ma karba ina tsaka da goge hannuna ya jefa min tambaya. “Noor ko da ya tuba?” “Eh, ba zan taba iya zama da namiji mai neman mata ba” “Kina da gaskiya, abu mai kyau na mai kyau ne, go ahead and live your life” Na aje masa tissue a gurin na nufi kofar fita. “Noor, kin san bana baki shawarar da zata cutar da ke ko?” Na juyo na kalleshi. “Daga gidan nan ki tafi gurin Mahaifiyarki kuma ki fada mata komai karki boye mata, ba zaki iya handle wannan ke kadai ba, you're too young for this” Ban ji ina iya musa masa ba, saboda haka na amsa masa da kai sannan na juya na fice daga falon. Mai gadin ne ya bude min gate sai na nuna masa akwatina ya dauko ya ba ni na fara ja har na isa babbar titi na tari Napep na hau na fada masa umguwar da zai kai ni. A daidai gate din gidan Mama ya aje ni na ciro kudinsa na bashi ina jin marata na ciwo sosai. Na fita ina jan akwatin na shiga cikin gidan, hankali be tashi ba sai da na shiga falonta, Mama tana cikin jindadi da kwanciyar hankali, rayuwar da bata samu ba a gidan mahaifinmu gashi a nan ta same ta, anya zan iya zuwa mata da wannan tsarabar? Kaddara ta shafi Hana, yanzu kuma ta shafi Mama...!! Na juya na fara tafiya bana son na zama silar mutuwar auren Mama, ta fada min jikinta be dauki mace a baki komai ba, face rigar da zai iya sakawa ko ya cire. “Subhanallahi” Na juyo jiki babu karfi na kalleta da kumburarrin idanuwana, wani tsadadden green lace ne a jikinta har kyalli yake. “Noor...” Ta fada cike da mamakin ganina. “Lafiya me ya same ki? Jini kike zubarwa” Na sauke kaina kasa na kalli kafata zuwa tile din da jini ya bata gurin da na taka na juyo. Kamar jira ake na kalla sai jiri ya kwashe ni a gurin hudu ya rufe idona marata ta hau murdawa da wani irin radadi da ban taba jin irinsa ba, zafin har cikin bayana yake kai min. Bana iya ganin komai sai muryar Mama da nake ji tana rikona tana kiran sunan wata da ban san wacece ba, a gefe daya kuma ina jin wayar da Kareem ya saka min layi ya ba ni tana ringing... KAREEM POV. Sai da ta fice sannan ya nufi tissue da ta aje ya dauka ya kai hancinsa ya shinshina, yayi baya baya ya zauna ya jinke tissue din. “I deserve this, i lost everything, babu wani abun da ya rage” Ya aje tissue din, be yi addu'a ko fatan Noor ta fito ko wani abun ya sameta a aurenta ba. Shiyasa a lokacin da ta yi auren ya ayyana a ran cewar ya rasata, na tattara lamarinta gaba daya ya aje a gafe, not because of baya sonta but because of yana mata fatan samun farinciki da zaman lafiya, duk kuwa da ya san ba lallai ta samu hakan ba. Saboda Safeena da kuma mijinta. But fada mishi cewar ba zata iya mazinaci ba ko da ya tuba it break him into piece, ya san ya rata ta kenan har bada. Bayan ita kuma babu wata, bayan farincikita babu wani, bayan sonta babu wata, bayan burinta babu wani. “That's okay, it alright Kareem...” Ya furta yana encouraging kansa, ya mike tsaye kenan wayarsa ta yi ringing. Daukar wayar yayi ya duba wata bakuwar number ce da be santa. “Hello..” “Wallahi... Wallahi... Wallahi... Idan Noor ta kashe min aure, kuma ta zama silar tonuwar asirina sai na sai na shuka muku biyar bakinciki kai da ita, domin ba laifinta ba ne ita kadai, har da kai kai da ka fada mata sirrina saboda kana sonta, bata isa ta lalata min rayuwa kuma ita tace zata yi rayuwar jindadi ba” “Excuse me” Ya fada jin muryar Safeena da kuma kalamanta cikin kuka da bacin rai. “Yes ,ina tabbatar maka wannan, domin idan bata fada masa wani abu ba babu yadda zai shigo, haka kurum ya kwashi yara da sunan yawo sai da suka dawo suke fada min asibiti ya kai su aka debi jininsu, kuma duk kai ne sila ai Kareem” Ta kashe wayar tana kuka. Faduwa Kareem yayi zaune saman kujera hannuna rike da wayar ya rufe ido ya dafe kansa. “Noorrrr...! Kai...! Meyasa na aikata ma to? Ita lu'u lu'u ce da na tsallake hanin da Allah yayi na aikata? Why from first plate?” Ya rumtse ido sosai yana jin kamar ya hade zuciya ya mutu, ya san abun da zai biyo baya ba zai musu dadi ba. Na dauki awa hudu ina nakudar da ban san da zuwanta sai da muka tafi asibiti, na wahala iya wahala har na yi zaton rai zai yi bankwana da duniya ne. Suka can na yi nishi na yunkura ina ta kokarina, amman kamar bana yi, ban yi zaton haka haihuwa take da da wahala da ciwon fa azaba ba sai da na kai matakin. A lokacin da likitoci suka bada shawarar a shiga ni tiyata domin ceto rayuwata da rayuwar abun da yake ciki ganin na kasa haihuwar, na katse sosai na yi zaton idan ana shiga da ni ba zan fito da rai ba. Sun fada idan ba ayi haka ba zan iya samun matsala ko abun da ke ciki ya samu, domin haihuwar ce ta zo min babu abun da ya isa ya tare, ma'ana dai zan yi haihuwar bakwaini kamar yadda aka haife ni. Cikin ikon Allah da rahamarsa kamin asuba wani karfin ya zo min, yunkuri daya biyu a uku kan yarinya ya fara fitowa, da na sake yunkurin ta kara fitowa, likitan da ya karbi haihuwata ya yanka gurin ya janyo babyn, azabar sai ta zame min kala biyu, ba ma kamar lokacin da ake dinkewa. Ko ba a fada min na sani yata bata so da rai ba, domin ban ji kukanta a lokacin da ta fado duniya ba. Sai dai ban tabbatar da sai bayan da aka min wanka aka gyara min jikina aka canja tufafina. Sannan Mama ta sake shigowa domin da taimakonta aka yi min komai. Ta shigo dakin da fuska a kumbure da alama ita ma ta yi kuka kamar ni. “Sannu ya karfin jikin na ki?” “Alhamdullahi” Na amsa ina jin maganar ma kamar ba zan iya ba. Domin babu ragowar karfi a jikina kamar ba na da kashi haka nake ji. “Mace kika haifa, amman bata zo da rai ba, na bada ita can gurin dangin mahaifinta, saboda Mahaifiyarki Abdull ta karba” Abu ne da na riga na sani kuma na fahimtar da kaina. Amman da Mama ta fada min sai na ji wani irin babu dadi. Duk wahalar da na sha babyn bata zo da rai ba. Tea mai kauri Mama ta miko min na karba na sha rabin kofin sannan na aje sai ta miko min wayarta. “Kin ganta nan” Na karbi wayar na kalli hoton yarinyar mai kyau da jiki kamar ba yar wata bakwai ba, fara kyakkyawa kamar na kirata ta amsa amman babu rai, an lullube ta da zane gwanin sha'awa. “Yi hakuri, Allah ya baki wata mai albarka, ita kuma Allah yasa mai ceto ce, na tsorata da nakudarki kin wahala har hankalina ya tashi” Na share hawaye na mika mata wayarta. “Mama baki ga waya a jakata ba?” “Na gani, kuma na ga kira na amsa sai na ji muryar abokiyar zamanki wai zaki kashe mata aure Wallahi sai ta ga bayanki, da ta ji muryarta ina mayar mata da martani sai ta kashe bata sake cewa komai ba, fada kuka yi?” Ta banbare magani ta miko min na karba na sha. “Aa ba ni wayar na duba abu” Ta bude jakarta ta dauko wayar ta miko min, sannan ta dauko ragowar tea da na aje ta ba ni. “Daure ki shanye Noor kamin anjima sai ki ji jikinki ya sake, wata kila zuwa gobe su sallame ma idan ba wata matsalar ta biyo ba, yau dai sun ce zaki wuni a nan ki samu bachi” Ba tare da na musa ba na karba na shanye na aje cup din sannan na duba wayata ko zan ga sakon Hana amman shiru. “Ina kika bar Hana ya aka yi kika zo a tare da ita ba? Na kira wayarta kashe mijinki kuma na yi ta kira be daga ba, shiyasa na kira kanwarsa da uwargidanmu na fada musu, su suka kira mahaifiyarsa suka fada mata, kanensa ma jiya duk suna nan mahaifiyarsa kuma a nan ta kwana, ita ta tafi da jaririyar ma, shi din ne dai be kira ba” Wata zuciyar tace na yi mata karyar cewar Hana tana makaranta shiyasa ban zo tare da ita ba. Sai dai tunawa da shawarar da Kareem ya ba ni ya saka na yanke shawarar fada mata gaskiya. “Daman kin ji alamar haihuwar ne kika dawo? Ai kara da kika yi haka a can babu kida kowa sai Hana ita kuma yarinya ce ba sani komai kuka yi ba, ko da yake likitoci ne suke yin komai, amman dai hankali ba zai kwanta ba kara da kika haihu a gida” Na daga kai a hankali na kalli fuskarta, wani tea take kokarin hada min. “Mama” “Na'am” Ta kalleni. “Hana bata tare da ni” Ta kalleni da sauri. “Kamar ya?” “Wani abu ne ya faru, shiyasa na dawo gida ba haihuwa na dawo ba, kuma na dawo ne da takardar saki, Abdull ya sake ni” Ta dauke hannayenta daga tea da take hadawa na biyu tana kallona. “Ya sake ki? Me ya faru? Me kika masa?” “Ban masa komai ba...” Bata bari na karasa ba ta fara min fada. “Karya ne, ba zai sake ki ki dawo gida da ciki wata bakwai haka kawai domin jindadi ba, akwai abun da kika yi?” Na kalleta idanuwana na cika da kwalla. “Me yasa kullum ni ce mai laifi Mama?” “Saboda baki jin magana, ba ki tunani kamin ki aikata abu, gaba daya ke ba rayuwar aure ce a gabanki ba, shiririta kawai kika saka a gaba, wacan auren na farko ma be dade ba ya sake ki, yanzu kuma wannan da ciki ki dawo ki haihu ina murna ki ce min wai ya sake ki? Kin san farincikin da uwa take ji idan ta aurar da yarta Noor? Zaman aure nake son ki ji ba jeka ka dawo ba, yanzu mutane za su fara magana, ba ki gudun abun fada, daman an raya cewar ba zaman aure zaki yi ba, ke dai kin ki zaman aure Noor kin ki zauna” Ta karasa tana kuka, ni ma kukan nake marar sauti. “Ni ma ina da buri, ina da mafarkai irin na kowace mace, sai dai kuma kaddara ta shata min liyi, yadda alƙalamin ya zana dole haka zan bi...” Na lumshe idanuwa. “Daga lokacin da na fahimci haka, sai tsoro da fargabar me zai faru a gaba ya fice a zuciyarta. Tafiyar da babu dawowa ta zama dakuna a yanzu, gashi har kaddarata ta shafi yar'uwata” A take ta daina kukan da take. “Me ya faru me ya samu Hana?” “Abdull ya keta mutuncinta, har ciki ya shiga....” Faduwa Mama ta yi kasa zaune a lokacin da na labarta mata abun da ya faru, ba kuka take ba tagumi ta yi tana kallon kasa. “Yanzu tana ina?” “Ban sani ba” Ya cije baki ta rumtse ido sosai tana girgiza kai. Tashi ta yi ta fice daga dakin ban sake ganin kowa ba sai misalin bakwai wata nurse ta shigo ta yi min allura ta ba ni magani na sha, sannan ta ce anjima likita zai zo ya duba ni, wata kila a sallame ni yau. Haka kuwa aka yi likitan ya zo ya duba na fada masa bana jin komai a yanzu sai rashin karfi sai kuma gurin da aka min dinki ne kawai ke zafi. Magani ya rubuta da allurai masu yawa sannan ya bani takardar sallama misalin karfe biyu na rana. A lokacin Gwaggo Saude da Anty Larai suna asibitin sai kuma kanen Mama biyu. Kai tsaye gidan Baba aka wuce da ni a can ko da muka je mun samu Umma ta dora ruwan zafi, babu bata lokaci ta zuba min a zuba na shiga bandaki na xauna a cikin ruwan da ta zuba shirina na zauna, ga azabar dinki ga na zuwan dake taba gurin ga kuma na zuciya da tunanin yar'uwata. Kowa tambayar yake ina Hana take, sai karya na yi nace jarabawa suke shiyasa ba zai yiyu ta zo ba, kuma na fada musu a hostel take zama ba a gidan ba gudun zargi. Makota suka fara shigowa suna duba ni tare da addu'ar Allah ya ba ni wani mai albarka. Bakinciki be kara min yawa ba sai da dare yayi na gwada number Hana har lokacin a rufe ga kuma bakinciki na haihu amman abun da na haifa babu rai. Kofin ruwan zafin dake hannuna na je na lalabo wayar da Kareem ya ba ni na kira Mama. “Mama” “Noor kina lafiya?” “Ba lafiya ba Mama, na san ke ma kina cikin damuwa” “Ina ciki Noor Kaddara ta riga fata, ni daman ban so tafiyarta, kawai saboda kun matsa ne ke da shi, kuma da san hakan zai kasance da ban bari an yi auren nan ba, ina masa kallon mutumen kirki ne mai sanin ya kamata, jindadi nake hango miki shiyasa na goya masa aka yi auren ina farinciki” Hawaye na zubo ido. “Hana ta kira ki?” “Aa, tashin hankalin kenan, ban san wane hali take ciki ba” “Kareem yace min zai iya kokarinsa ta dawo, amman har yanzu shiru” “Alhaji ma yace zai yi iya kokarinsa za a samota” “Kin fada masa ne?” “Na fada masa cewar daga tafiya makaranta ta bata, ban fada masa abun da dansa ya aikata ba, idan maganar nan ta fita Noor Hana ba zata taba aure ba, babu wanda zai aureta abun yayi muni, fyade kuma har ta yi ciki? Babu wanda zai karbi wannan kadarar, kuma zata kunyata a unguwa zata zama abar kwatance” “Shiyasa ni ma ban fadawa Baba ba, na masa karyar cewar tana hostel din makaranta, saboda bana son Umma ta ji ta yada, amman kuma Mama haka zamu bar Abdull ya tafi a free?” “To ya zamu yi? Sai hakuri, ni dai Allah ya kawo min Yata” “Ameen” Kiran Mama na fita wayata kiran Hana ya shigo, jiki na rawa na daga. “Hana” “Noor” Na daga sai na ji muryar Kareem, fashewa na yi da kuka. “Dan Allah karka ce wani abu ya same ta, dan Allah karka ce ta mutu ka, na haihuwa yata bata zo da rai ba, i lost my baby, bana son sake jin bad news, ya isa haka yanzu” Ina maganar ina kuka sosai sai ya kashe wayar hakan ya tashi hankalina sosai, domin na fahimce ba ya tafe da labari mai dadi, idan ba haka ba me ya kai wayar Hana hannunsa? Me yasa ita ba zata min magana ba? Na dafe zuciyata ina numfashi daker. “Ke Lafiya me ya faru?” Na kasa magana sai kuka nake... KAREEM POV. Yayi ending call din ya nufi wani motarsa ya dafa kamar wanda ya rasa abun yi. Kamin ya dago ya kalli gate din da aka bude motar Safeena ta doso harabar gidan, yana tsaye yana kallonta har ta karaso ta faka motar ta fito sanye da atamfa sai mayafin da be gama rufe jikinta. “I thought i warning you karki sake na yanke duk wata alaka da ke” “Alakata da kai ba zata taba yankewa ba, do you want us to talk about it a nan ko mu shiga ciki?” Ya kalli Mai gadinsa da ya gama rufe gate ya kira shi, ya zo da sauri yana sassarfa. “Ga ni ranka ya dade” “Kalli wannan matar da kyau” Mai gadin ya kalleta da kyau kamar yadda mai gidansa ya ba shi umarni. “Na ganta ranka ya dade” “Daga yau karka bari ta sake shigowa cikin gidan nan, idan ka bari ta sake shigowa a bakin aikinka” “Toh Wallahi ba zata sake ba, ko da kuwa ita din aljanna ce, wuce Hajiya dan Allah ki wuce” Safeena ya rausayar da kai tana kallon Kareem domin ba da wasa ta zo ba. “Really?” Kareem ya daga mishi hannu. “Ban da yau, bar ni zan yi magana da ita” “Toh ranka ya dade” Mai gadin ya juya ya koma, sannan Kareem ya dauke kai ya nufi falon. “Baki da hurumin shigowa gidana, na baki 2 min to talk your rubbish and go” Cewar Kareem bayan ya shigo, sannan ya nufi Center table ya dora wayoyin dake hannunsa ya juyo yana kallonta fuska babu annuri. Safeena ta tabe baki. “Gaskiya ne, hausawa suka ce namiji ba dan goyo ba ne, kuma na gani na tabbatar a yau, har ka manta wacece ni kake fadawa mai gadi kar ya bari na sake shigowa gidanka? Kuma ka ce bana da hurumin shigowa gidan? Saboda me? Ai Yusura bata gidan yanzu, balle ka ce kar ta gani, kuma kana ganin yanke alaka da ni zai sama kama yanci da zaman lafiya ne?” Ya aika mata da wani kallon kaskanci da tsana. “i don't want to see your face, kin cutar da ni iyakar cutarwa, sai yanzu nake hango abun da Momy take guje min, na gode Allah da ban aure ki ba” “Kai ka fara cutar da ni, kai ka fara yaudara da sunan zaka aure ni alhalin kansan mahaifiyarka ba zata bari ba, ina ji ina gani ka aje ni ka auri wata, na yi duk yadda zan iya saboda na cire a zuciya na amman na kasa, bayan na samu mai aurena na yi aure kuma ka sake sabunta min kaunarka har ta kai bana iya gane komai sai naka, na yi sha'awar haihuwa da kai ne saboda ina sonka, amman yanzu na gane na yi babban kuskure domin yaudarata kake a kullum, gashi yanzu na haifi jininka kuma aurena zai lalace bata sigar da nake so ba” Hawaye na mata zuba ta matsa kusa da shi. “All my plan was wata rana zaka aureni, saboda ka saba min da kanka, bana da buri sai na zama da kai, bana jin dadin mu'amala da mijina sai kai, a hakan ka budewa wata zuciyarka ta shiga, kuma ka kwashe sirrina duka ka fada mata, gashi yanzu ta yake ni da shi, igiyar aurena haka ya rage ta katse” Ta muna mishi tazarar dake tsakanin babban yatsanta da mai binsa a yayin da ta kusa hade su. Ta goge hancinta “Ya dauki yaran duka ya auna jininsu kuma na san ya gani, amman be ce min komai ba ya koma Lagos, the next thing da zai biyo na sani saki ne da tozarci a cikin dangi” Ta share hawayenta. “Kanwarsa ta fada min ya fada musu ya Saki Noor amman be fada musu dalilin rabuwar ba, ta dawo gida ta haifi bakwaini, kuma be zo da rai ba, are you planning all this? It's because you love her more then me?” “I didn't plan this, but yes i love her more then you, i love her so much” “And think zan tsaya ina kallonku ku auri junanku ne, bayan kun gama lalata tawa rayuwar? Taya? Ka ci amanata Kareem” Ya daka mata tsawa. “Babu wanda ya lalata rayuwarki, ke kika lalata rayuwarki da kanki, kuma karki zargi kowa a nan” “Anyway na zo na na gargade ka, kuma na fada maka, idan har Abdull ya sake ni to ni ce zan maye gurbin Yusura, na san kai ma ba zaka so mutuncinka ya zube ba, ba zaka so a san ka haihu da matar aure ba, kuma na zo na gargade ka ne, ka fadawa Noor ta fita daga rayuwarka, kuma ta yi taka tsantsan da nata rayuwar domin Wallahi ba zan bar wannan ba” Tsakanin rufe bakinta da kai hannunsa a wuyanta ba za a oya fadar wanda ya riga wani ba, shaketa yayi sosai har sai da idanuwanta suka fito. “You're hurting me Kareem you're hurting me” Baya baya take yana binta. “Karki, taba yarinyar da bata miki komai ba saboda ni, kin cutar da ni that's enough, you have no idea what she's going though, because of your stupid husband, and yanzu kuma ke ki ce zaki saka ta gaba, kuma duk a kaina, ya ishe ki haka” Ta fara bugun hannunsa da karfinta jin da gaske kokarin kasheta yake, she's fighting for her life. Sai da wayarsa ta fara ringing sannan ya sake ta fuska a hade, ita kanta bata taba ganinsa cikin bacin rai irin na yau ba. Tari ta fara tana hakki kamin ta juya da sauri ta fice daga falon. Wayarsa dake ringing ya nufa ya dauka number Yusura ce, for the first time take kiransa bayan rabuwarsu, be haddace number duka ba but ya rike karshen numberta tun a lokacin da take gidan. “Hello” “Sallamu Alaikum” “Wa'alaikumussalam, Lafiya?” “Tine ce bata da lafiya, tun shekaran jiya, an bata magani amman abun be yi ba, jikinta ya tsanani yanzu” “Ganin nan zuwa” Ya sauke wayar ya dauki wayoyin duka biyu ya nufi stairs keys dinsa ya dauko ya sauko ya fita daga falon. 30m ya isa family house dinsu be faka ko'ina ba sai a bangaren da Yusura take tare da kanensa da yaransa. A falo ya same su daga Yusura har Tine din da aka yi ma shimfida a falon. Tun da ya shigo Yusura take kallonsa har ya karaso falon da babu kowa sai yarsa da tsohuwar matarsa dake sanye da katon Hijab domin a yanzu shi din ba muharraminta ba ne. Ya kai hannu ya taba jikin Tine sai ya ji shi da zafi sai dai ba sosai ba, domin bachi ma take. “Me yake damunta?” “Zazzabi ne kawai sai ciwon kai da take cewa ta yawan tari da ciwon ciki” Ya saka hannayensa ya tallafota ya maidata jikinsa yana taba cikin nata, a nan ta bude ido ta kalleshi. “Dady ka zo?” “Eh baki da lafiya” “Eh amman da sauki” “Fada min abun da kike ji” Ta nuna masa gun da ke mata ciwo ta fada masa. “Okay zan siyo miki magani yanzu, idan baki ji sauki ba daga nan zuwa gobe sai mu auna ki mu gani kin ji?” Ta daga mishi kai tana kwantar da kanta jikinsa. “Dady i miss you i miss our home, yaushe zamu koma?” Ya kama hannunta ya rike yana wasa da shi. “Tine akwai abun da ya kamata ku sani, the thing is...” “Yara ne ba za su fahimta ba” Yusura ta tari numfashinsa sai ya daka mata tsawa. “We have to make them understand...” “Are you Okay?” “I'm Not...” Nan ma ya amsa mata a tsawace, Tine ta dago daga jikinsa ta kalleshi “Dady why are you shouting?” “Am... Uhm..” Ya rasa me zai ce, sai ya maida ita kirjinsa ya rumgume. Kamin ya kwantar da ita ya mike tsaye ya fice daga falon. **** **** **** Ta faka a harabar gidanta misalin karfe goma daidai na dare. Kanta ta jinginar a kujerar dake bayanta tana kuka. “So cuta ne Allah ka cire min son bawan Allah nan, shi baya ganina ba ni ce a gabansa ba, ina kaunarsa amman baya gani” Ta fada tana kuka sosai, ta bugi gambun motar. “Ba zan kyale mutanen ba, taya za su lalata rayuwata su kuma su zauna a free? Ni na rayuwa a bakinciki shi kuma ya auri wacce yake so ya rayuwa cikin farinciki? Na san duk shi ya shirya wannan ai daman yana cire ciki, ta kashe aurenta ta fito yanzu ya aureta ko? Tun fa ya rabu da matarsa, bayan ni tawa rayuwar ta gama lalacewa, shiyasa ya fada mata sirrina, to ba ni kadai zai shafa ba har da kai Kareem, ganin yake idan yayi haka zai wanke kansa zai tsira ko? Okay zamu ga ni ai” Ta bude motar ta fita sannan ta share hawayenta ta nufi cikin gidan cikin zafin zuciya tana taba wuyanta da dayan hannunta, dayan kuma yana rike da key din mota. Cikin motar ya shiga ya zauna ya lumshe idonta yana maida numfashi a hankali. Be dago ba sai da ya ji ana buga gilashin motar, juyawa yayi a hankali ya duba sai ya ga Areef tsaye rike da ipad. Ya sauke gilashin kasa yana murmushi “Areef my love” “Dady na hango ka ta window Hajiya” Ya bude motar gaba daya ya dauko dansa ya zauna a saman jikinsa ya kwantar da shi jikinsa. “Ka iya gulma ko Areef?” Yayi dariya yana boye fuskarsa, Kareem ma murmushin yayi ya shafa bayan dansa. Yaransa na cikin farinciki da Allah ya ba shi domin yana son yara ko ba nasa ba balle kuma jininsa. Slowly ya sauke ajiyar zuciya tunawa da yayi da Noor ta raya abun da ta haifa, shi da yake namiji yake son yara balle kuma ita da haifa da kanta kuma ta yi nagudar abunta, ya lalabo wayarsa ya sake kiran line Noor da wayar yar'uwarta. Ta amsa kiran tana kuka sai har yana jinta. “What now ta mutu ko?” “I'm sorry for your lost, Allah ya baki wani mai albarka, and your sister...” Yayi shiru for a while sannan ya furta. “She's safe, but tana asibiti saboda ta dan bugu da mota, ba mu san yaushe ba amman haka aka zo mana da ita, amman tana raye” “Ka rantse ka ce wallahi tana raye tana duniya” “Me zai saka na yi miki karya?” “Saboda na jidadi na kwantar da hankalina” Murmushi mai kyau ya fadada fuskarsa. “Kin sa ina son kwanciyar hankalinki kenan?” “Eh na sani fada min gaskiya” “Wallahi tana da rai tana asibiti” “Me yasa ba zata yi magana ba? Me yasa kai kake rike da wayarta?” “Saboda tana bachi, kuma na kira na fara tambayarki ko kin fadawa iyayenki gaskiyar abun da ya faru so that na san ya zan musu bayani” “Na fadawa Mama ba ka ce na fada ba, amman Baba be sani ba, mama tace kar a fada masa tace ace bata ta yi kawai” “Okay zan fada musu yanzu an gano ta” “Zaka kira Mama yanzu?” “Yeah” “Zan aje wayar ka kirata sai na tabbatar da gaske kake tana raye” Yayi murmushi. That's why i love you, ya fada a ransa a zahiri kuma sai ya amsa mata da “Okay” Ta katse kiran sai ya aje wayar ya murza key din motar ya fara tukawa tare da dansa ya tafi ya siyo maganin ya rubuta yadda zata sha sannan yayi mata tsarabar gasasshiyar kaza da snack domin ya san tana sonsu sosai, sannan ya dawo gidan Areef ya rika masa leda daya ya shiga ciki wannan karon ya same ta tana kallon tv ne ta lulluba da bargo. “Tine ya jikin?” “Na ji sauki” Ya aje mata tsarabar ya bude maganin da kansa ya bata sannan yayi mata sallama tare da Areef ya fice, Uffan be cewa Yusura ba dake zaune a gafe daya tana kallonsu. Bangaren Hajiya ya shiga ya gaisa da ita da kannensa sannan ya fito ya nufi asibitin... NOOR POV. Hankali be kwanta ba har sai da kiran Mama ya shigo wayata ta fada min Kareem ya kira da wayar Hana ya fada mata tana asibiti, rumgume wayar na yi ina jin wani irin kima da mutuncin Kareem a ido na, na yarda wani lokacin Allah ya kan kawawa bawa abun da be yi zato ba, ina jin Allah ya hada ni da Kareem ne domin ya share min hawayen abububuwa da yawa. Umma na kwalawa kira domin tun dazun take tambaya me ua faru na gagara fada mata saboda kuka, tana shigowa na fada mata cewar kukan da nake Hana ce ta bata daga sunan tafiya makaranta amman an ganta tana asibiti yanzu haka. Tun daga ranar kusan rabi damuwata sai na ji ya gushe, domin yar'uwata yana raye, rabuwa da miji abu ne mai sauki, kamar yadda samun wani dan ko yar yake da sauki a gurin Allah. Duk yadda na so na tafi ganinta ban samu dama ba, sai waya na yi da ita, shi ma kuma sai washe gari bayan ta farka. Sai da na yi kwana uku sannan Baba ya yarda na tafi na ganta tare da kawata Zainab, da ake ta shirye shiryen aurenta a watan nan. Da dare muka fita saboda gujewa idanuwan mutane, Napep muka hau yana fara tafiya na kira Kareem na fada masa cewar zan zo na duba Hana. “Bana asibitin yanzu, ba ki san gurin ba?” Ban san gurin ba, amman Zainab ta sani domin ta je duba ta kamar yadda mutane unguwa da yawa suka je dubata, but i just neet to see him so nake na masa godiya i just miss him. “Ni ban san gurin ba” “Okay a me kika zo?” “Napep” “Ina family house yanzu nan na shigo, amman zan saka Aaryam ya zo ya tare ki? Ya nuna miki gurin. Kuma ina tunanin akwai wata kanwar mamanku a can ko ki kirata” Na kashe wayar ba tare da nace masa komai ba. Sai dai ga mamaki ina mai napep na sauke mu a bakin asibitin sai hangon shi na yi ya taho da kafa zuwa inda muke tsaye. “Ashe ku biyu kuke?” Ina kallonsa murmushi ya zo min for no reason na sauke kaina kasa kamar mai jin kunya, murmushi ya mayar min ya kalli Zainab. “Kawarmu ce wannan?” “Eh sunanta Zainab” Zainab ta gaishe shi ya amsa, sannan ya juya yana kallon wani mai kama da shi da ya doso inda muke yana fadin. “Ga key dinka ka shiga da motar ka ciki, sai mu taka na nuna mata gurin” Kareem ya ce. “Malam kai zaka ja motar ka shiga da ita ciki” “Aa Wallahi, ai ba motata ba ce kuma ba asibitina ba ce” “Amman kai ka nace sai ka biyo ni” “Da na ji ita ce ba, saboda na ganta mana, malama bismillah ga hanyar nan” Ya nuna min titi da zamu mike da hannunsa, ni kuma na kalli Kareem irin kallon nan na jiran umarni. “Karki damu, ni kanensa ne uwa daya uba daya, muje ke kuma kawarta ku je ya sauke ki inda zai faka motar” Kareem ya karbi keys din hannunsa ya juya ya nufi gurin da motar take fake tare da Zainab. Ni da kanensa kuma muka fara takawa a kafa zuwa cikin asibiti dauriya kawai nake domin ina jin zafin dinkin da aka min har yanzu. “Sunana Aaryam” “Nice” Na fada feeling so nervous. “Ke fa ya sunanki?” “Noor” “Haka ne na tuna, na san baki san ni ba ko?” “Eh” “Haka ne, ni ma ina dan jin sunanki gurin big bro ne can sama haka” Now kuma I'm feeling awkward like Kareem yana hirata ne da mutane? Domin Hafiz ma haka ya taba fada min farkon haduwarmu. “Ni nake bin Kareem, shi ne babba a dakinmu, muna da kanen mata akwai daya da Momy ta bari sai kuma yaran Hajiya su uku, sai kuma Yusura” Na kalleshi kamar na yi maganan sai kuma na fasa. Ashe ya lura “Na san zaki ce Yusura ba matar Kareem ba ce?” Na daga mishi kai. “Haka ne, amman a gidanmu take zama a nan ta girma” Ya ba ni labarin zamanta a gidan yadda aka yi aurenta da Kareem da kuma rashin son junansu da suke. “Amman a haka Kareem yayi kokari ya bata duka hakokinta, har sai da ta nemi saki so yanzu sakin da yayi mata babu gyara a tsakaninsu” Mamaki ya kama ni, Kareem be fada min ya saki matarsa, wata kila shiyasa yake cewa ba zata zo ta tararda da mu ba, jin cewar bata sonsa kuma ba sabu abu ba ne na fahimta tun a zuwana na farko gidan, kamin shi kansa Kareem din ya fada min yadda aka yi auren a wacan ranar da ya fada min sirrinsa. “To yanzu yaran fa?” “Suna hannunta, idan Kareem yana son ganinsu zai zo ya gansu ne sai ya koma, shi kadai yake rayuwa a gidan yanzu, yana cikin kadaici da ban tausayi sosai, gashi ya rasa yarinyar da ya so ya aura, abun ba dadi, ni ba zan iya biyayyar da Kareem yayi ba, ba zan iya auren macen da bana so ba, auren kiyayya ba shi da dadi shiyasa Yayana yake matukar ba ni tausayi, yana da zuciya da hallaya masu kyau, amman har yanzu be samu farinciki ba” Tausayinsa ya kama ni sosai domin na san yadda rayuwa da wanda baka so take, na gwada na san yadda ake ji. “Kin san me yasa nake baki labarin nan?” Na amsa masa da alamar ban sani ba. “I want you to be his best friend, domin yanzu ba shi da abokin shawara ya rasa Hafiz, ya rasa mahaifiya ni kuma tawa safgar nake dabam, na lura da wani abu yayana yana samun farinciki idan kuna tare ko yana zancenki, please idan kin ganshi a cikin damuwa ki yi kokarin cire shi, kuma ki yi iya yadda zaki iya ki ga ya auri wacce yake so take ba shi farinciki yana cikin damuwa sosai...” Aaryam yana maganar ina kallon Kareem dake tsaye hannayensa zube a aljihu yana jiran karasowarmu. “Kin min alkawari zaki saka shi ya auri wacce yake so? Shi ma ya samu farinciki kamar kowa? Farincikinsa shi ne na mu, and don't tell anyone mun yi maganar nan” Ban iya amsa masa da eh ko aa ba har muka isa gurin da Kareem yake shi kadai yana kallonmu. Da dan zargi yake kallon kanensa sai Aaryam ya daga masa hannu ba tare da ya ce komai ba ya wuce cikin asibiti. Sai da na daina hango shi sannan na juyo na kalli Kareem. “Me ya fada miki?” “Yadda akan samu Hana” Na amsa kai tsaye. “Come on karki wasa da ni mana, na san ki fa” Na yi murmushi. “Ba ka ce ba zaka zo ba?” “Na ji kamar hakan da na fada be miki dadi ba, shiyasa kika yanke wayar maybe you want to see me huh?” Ya daga min gira sai na yi murmushi “I miss you, i just wanna say thank you, ban taba haduwa da wani mutum mai karamci da sanin ya kamata da kawaici da son farinciki ba sai Kareem, ba alakar uwa ba ta uba amman komai nake so kana yi min, people like you a rare, kai mutumen kirki ne, kai mutum ne mai damuwa da damuwar wani, Allah ya faranta maka ya baka abun da kake nema Kareem” Yayi murmushi mai kyau ya daga kansa yana kallon saman kaina domin yana tsaye ne a matakar dake bawa mutum damar hawa ward din dake cike da mutane, ni kuma ina kasa daman ya fi ni tsayi balle ya hau akan abu. “Kalamanki sun lashi zuciyata, a duk lokacin da kike bukatar wani abu, ko wani ya taba ki just come to me zan miki duk abin da kike so, if you ever need safe just come to me” “Da me zan saka maka Kareem?” Yayi dariya mai dadin sauraro. “Thank you, just let me be right beside you in anything you do” Ya fada yana lumshe ido. Na yi murmushi ina kallon mutane fake ta kai da kawo. “Mu je ciki ki ganta” Muka jera muna tafiya sai kamshi yake mai kwantar da hankali. “Kareem” “Uhm mmn” “Ina Yusura?” Ya tsaya cak ya daina tafiyar da yake ya kalleni. Zai yi magana wani mutum ya ba shi hannu suka gaisa, after ya gaisa da shi ya juyo ya kalleni. “Ina wannan ya fito kuma?” “Kawai ka amsa min mana” “Tana gida family house dinmu, ba ma tare yanzu” “I'm happy for both of you, rayuwa da wanda baka so ba shi da dadi” Ya sauke gutun numfashi. “Haka ne, rayuwa mutum shi kadai ma bata da dadi, amman dai da sannu zan saba” “Ai ba haka zaka zauna ba, zaka yi aure kai ma ka auri wanda kake so take sonka” “Ba zan taba wani auren ba Noor, yarinya daya nake so kuma na rasa ta, shi ke nan, ba zan sake son wata ba” “Maybe zaka iya son wata, ita ma ai baka san zaka sota ba sai daga baya ko?” “No tun farko haduwa da wannan yarinyar na ji wani akanta, amman ban fahimta sai daga baya, kuma yanzu na yi latti I'm not the one she mean to find, every thing keep us apart, amman ni na san ina kaunarta sosai, i love her so much” Ban san miyasa ba, na dan ji babu dadi da yace yana kaunarta sosai. “Amman ka yi sanyi ne da baka same ta ba? Kai din nan babu wanda zata ce bata sonka” “Na je ne a makare, wani ya riga ni shiga zuciyarta, kuma ita dai tana jin ban mata ba zata iya aurena ba, har yanzu bata da wayo bata gama fahimtar duniya ba, amman dai zan jira har lokacin da zata yi hankali ta natsu ta fahimce ni, maybe we can rewrite the start...” Na masa duba mai cike da tambayoyi, na ji wani bangare na zuciyata na raya min ko dai da ni yake.? “Ya sunanta ma?” “Sunanta Hafsat” “Ta yi aure ai ka ce ko?” “Eh” “To tace maka zata fito ne da ka ce zaka jira ta?” “No, tana gidan mijinta har yanzu” Ya bude min kofar dakin yana kallon cikin idanuwa. “Noor” Kiran da Hana ta yi min ya saka na dauke idona daga kallon Kareem na kalleta, na shiga dakin da farinciki da murna da jindadi sosai ta ji rauni a kai da kai da kuma hannu har an saka mata bandeje an daure. Na rumgume sai ta fashe da kuka sosai. “Inna a ba su guri su tattauna mana, Aaryam mu tafi ko?” Ina jin lokacin da Kareem yake fadar haka, ban dago ba sai da suka fice gaba daya daga dakin har kanwar Mama. “Dan Allah ki yi hakuri, da na sani ba zan je na zauna a gidanki ba Wallahi” “Ba laifinki ba ne, halinsa ne daman da ace ba halinsa ba ne ba zai fara ba, ke ya kamata na bawa hakuri na janyo ki a jiki gashi sanadina kin cutu, kuma ban fahimce ki ba sai da kika tafi” “Haka Allah ya tsara min, ban isa na wuce wannan ba, arziki na ma daya an cire cikin” Na dafata. “An cire? Waya cire? Yaushe?” “Tun a ranar da na dawo yayi min allurar amman sai jiya ya dauke ni ya kai ni wani gida wata nurse ta wanke min marata yace an cire komai?” Farinciki ya lullube ni. “Amman ta sani amman?” “Eh ta sani, tare muka je da ita yace a bar maganar ne ba sai an fadawa kowa ba, kanensa ma be sani ba” Na sake rumgume ta ina jin kamar Kareem na rumgume tsabar farinciki. “Amman Kareem din nan son ki yake yi ko Noor?” Na dago daga jikinta “Aa be taba nuna min ba, be taba fada min ba” “Kyautatawar da yake miki ta wuce misali” “Wata kila saboda ina matar abokinsa ne, kuma yana da tausayi ke ma kin ba shi tausayi shiyasa ya saka aka cire cikin” Na sauke kanta kasa hawaye suka sake idonta. “Na yi nufin kashe kaina, lokacin da na bar gidanki, ba ni da gurin tafiya, kuma ba zan iya koma gida ba, da kaina na tara kaina a titi mota ta bugu ni, amman ban mutu ba sai na ji ciwo a hannu da kafa da kai, mutumen be tsaya kai ni asibiti ba ya gudu, sai mutane ne suka taimaka min suka kai ni, su ma suna kai ni suka gudu, asibitin kuma suka ce ba za su taba ni ba, sai da dansa kuma sai an siye kati, a gurin aka bar ni wulakance, sai da wahala ta yi min yawa na kunna wayar na ga sakonki, da kuma wani sakon ta wata number yace min shi Aaryam ne idan ina bukatar taimako na fada masa, a madadin na kira ki sai na kira shi, da muka yi magana sai yace kar na kira ki, shi yasa aka dauko ni daga can aka kawo ni Kano. Abdull ba zai gama lafiya ba, kuma na jidadi da baki samu ďa da shi ba Noor, ni kadai na san me nake ji a raina, kuma shi kenan ya sha a free babu abun da za a masa” “Saboda gudun abun da zai biyo ba ne, Mama ta ce idan wani ya ji ba za a aure ki ba, kuma zai zama abun magana a cikin unguwarmu, amman ki kaiwa Allah kararsa zai saka miki” “Kullum sai na fadawa Allah, ina masa Allaj ya isa, amman wannan abun ba zai taba gogewa ba” Turo kofar dakin da aka yi ne ya saka ta yi saurin share hawayenta ni ma na share nawa. Zainab ce take fadar na tashi mu tafi dare yayi, Mama Talatu ma ta dawo dakin sai na yi mata sallama sannan muka tafi. A napep ma Zainab ta tambaye ni kwatankwacen abun da Hana ta tambaye ni cewa wai Kareem so na yake. “Be taba fada min ba” “Amman ke baki lura ba, ji yadda yake kallonki fa, kuma yana ta yi min tambayoyi a kanki” “Amman ni be taba cewa yana so na ba, kuma yana ma da wacce yake so sunanta Hafsatu” “Ikon Allah, toh amman dai abun da mamaki wata kila jini ne ya hadu ko kuma ya riga ya fara sonta ne ba yadda zai yi da ke” “Tun kamin ya hadu da ita fa, muke tare ai da ya fada min, kuma ni bana ma son shi” Na yamutsa fuska tunawa da na yi da wani abu. Zainab ta gwalo ido. “Saboda me?” “Haka nan dai” “Tab Wallahi baki san abun da kike so ba, kamar wannan zaki ce baki son shi? Mutum mai kyau mai kudi mai komai, ko ni za'ayi aurena a watan nan Wallahi yace yana so na zan iya balle auren na aure shi” Na kalleta da mamaki sai kuma na ji haushinta na fadar hakan fa ta yi ban sake cewa komai ba har muka sauka Napep din. Komai ya zamar mana kamar labari, ni na danne ciwon zuciyata Hana ma ta danne nata mun barwa Allah komai muka koma cigaba da rayuwa kamar yadda muka saba, a bayan. Sai wani shakuwa da kaunarnan junanmu da tausayi ya kara shigarmu, Mama kuma tana ta rayuwa a gidan aurenta ba tare da wani tashin hankali ba. Abun da ya faru da Hana muka haka kasa muka rufe ba tare da kowa ya sani ba, daga ni sai ita sai kuma Mama da Kareem da kuma uban gayyar da yayi aikin. Ranar da Baba ya saka ni gaba da tambayar dalilin da ya saka Abdull ya daina zuwa gidan na fada masa ya sake ni ne, Baba tsine min ne kawai be yi ba, amman duk wani kalar zagi na duniyar nan sai da yayi min shi. Musamman da na yi masa karyar cewar kawai bana son sa ne ni na bukaci ya sake ni, kuma da ya bincika sai Abdull ya tabbatar masa da cewar ba fada ba zagi kawai na bukaci sakin ne shi kuma ya aiwatar. Har kusan korata Baba yayi sai da yan'uwansa suka saka baki, Umma ma sai ta koma tana jin haushina domin tallafin da yake bata na sana'ar da Hana bata mata a yanzu ya janye ya daina yi. Sai tace wai bakinciki nake mata saboda ita din ba uwata ba ce, kuma hassada ta bata tsaya kaina ba har da yar'uwata nake yi ma. Ni da Hana ba ma ce mata komai domin mun san abun da bata sani ba. Hana ta samu sallama a yanzu da bata fita siyar da awara domin Mama tana ta shirye shiryen sakata wata makarantar ne a nan garin Kano, hakan ya saka hankalinta ya dan kwanta, kuma wani abun Allah samari da masu mata sai kawo mata hari suke a yanzu. Sai dai ni ban tsira daga maganar mutane unguwa ba, ganin na yi arba'in amman ban koma gidan mijina ba, ba mutanen unguwar kawai ba har cikin family na samu masu jefa min magana wai na ki zaman aure, Mama ta fada cewar wasu daga familyta sun ce haka za a zuba min ida ina aure ina fitowa na ki zaman aure. Na kan yi murmushi kawai na bar maganar a bayan kunnena, domin mai daki shi ya san inda yake masa yoyi, dadi dai ba zai saka mace ta kashe aurenta ta fito domin ta zauna a gidansu ba, ko kuma ta raba a wani guri, ba ni kadai ba mata da yawa al'umma basa musu uzuri, macen bata sakin kanta bata rike kanta amman ba a fahimtar haka, a koda yaushe mutuwar aure yana komawa a bangaren mace idan afku. Ba zan ina cikin jindadi ba, domin zaman gidan ba shi da dadi agaremu. Amman jiki ya dan bude haihuwa ta kara min kyau ta cike min gurbin kasusuwan da na nake da su a wuya, ba wani jiki na yi can sosai ba amman dai jikin ya bude na cika na zama mace. Bayan bikin Zainab na je gidanta na wuni a can muka sha hira sosai na ji abubuwa da yawa da mutanen unguwa suke fada, wasu su ce hakkin Zafeer ne, wannan kam ba zan yi mamaki ba idan aka ce hakkinsa ne, domin ya cutu, wasu kuma suka ce TA KI ZAMAN AURE, har da masu cewa wai Zafeer asiri yayi min ba zan taba iya zaman aure ba, wasu kuma su ce ina da aljannu ne kawai da basa son aure. Na yi dariya sosai na danne ciwon dake zuciyata na bar sirrina a cikin raina. Ta rakoni bakin kofar gidanta ta koma ni kuma na haka hanya gyale na a kafada, kaina ya sha dauri fuska kuma ta dauki ido kamar wata budurwar kai wata budurwar ma albarka domin gyaran da nake yi a yanzu bana yinsa a lokacin da nake budurwa. Ina kokarin tare mai Napep wani dattijo ya faka gabana, ya sauke gilashin motar yana kallona fuskarsa da murmushi. “Ina zuwa?” Na waiga na kalli bayana na kalleshi na yi zaton ko da wata yake magana ba ni ba domin ba yaro ba ne zai haifi kamata da wanda ta fi ni sau goma ma. “Baba ni?” Na nuna kaina, yayi dariya. “Yan mata kenan, shigo na rage miki hanya” “Aa na gode” “Ba zaki shigo ba? To saka min number ki a nan” Ya miko min wayarsa. “Amman lafiya” “Lafiya Kalau Wallahi, kawai na ga ruwan dake min wanka ne, saka min number ki yarinya” Na karbi wayar na saka masa number na, sai ya miko min kudi. “Rike wannan ki hau napep” Na karba na masa godiya, sai ya wuce na bi matarsa da kallo ina dariya, to ko dai ya ga na yi masa kama da tsofi ne ya tare ni haka har da wani ruwan dake masa wanka, tsab kuwa zan masa wankan kwashe kudi na kara gaba domin ba zan iya da kayan majina ba. Allah ya tsare ni. Na tofar da yawu. Ina yin gaba kadan wata motar ta faka shi ma dai sauke gilashin yayi yana min magana. “Hajiya ina zuwa haka?” Na dan taba fuska, yau dai wata kila aljannu sun shafa min maganin farinjini a fuska ko kuma kwaliyar da na yi ce ta dauki hankalin mazan oho. “Gida” Na amsa sai kawai na ga ya bude motarsa ya zagayo ya bude min front seat. “Ki min alfarma motana ta samu lada, na sauke ki gida Hajiya, karki ce aa” Ta ina zan ce aa bayan yace kar na musu, shi din ma be yi kama da wanda za a musa masa ba. Na samu kaina da bin umarninsa duk kuwa da na san ba mutuncina ba ne, na zauna a motar ya rufe ya zagaya ya shiga ya tashi motar. “Sunana Salees” “Noor” “Thank you” Ya fada ba tare da ya kalleni ba, ni kuwa sai satar kallonsa nake baki ne mai dogon hanci ga yalwataccen gashin gemu da zaje gwanin sha'awa. “A ina unguwar take?” Na fada masa, har lokacin be kalleni ba sai da muka shiga cikin unguwar, nesa da gidanmu na ce ya sauke ni. “Baki son na ga gidanku ne?” “Ba kasafai ake kawo ni da mota ba, mutane za su iya wani zaton, kuma Baba baya son haka” Ya juya ya kalleni first eye contact da muka yi gabana ya buga da karfi. “Hakan yana da kyau, tarbiya ce amman da kika san Babanki baya so sai ki kiyaye, abu na biyu ki daina saka veil idan zaki fita, hijab ya fi mutunci, idan kina sha'awar veil ki saka babba wanda zai suturta ki, kina da kyau na zan maza da yawa sun fada miki haka, so ki suturta kyaunki ga wanda yake halalinki haka Allah ya fada” “Na gode zan kiyaye” “Idan kin min izini zan tsaya daga nan har na ga shigarki, saboda zan dawo ko kuma ki saka min number wayarki” Ya miko min wayarsa na karba na saka masa numberta sai ya kira ni. “Ki yi saving number zan kira ki anjima, na gode da kika shiga motata” Na bude na fita ba tare da na ce masa komai ba. Shi kuma yayi reverse ya juya, na ciro wayar a jakata na yi saving number, ashe Kareem ya ga fitowa motar domin motarsa tana fake a gefen gidan makotanmu ne, ban lura ba sai da na karasa, gaba daya sai farinciki ya baibaye ni, ganinsa da na yi. “Laa Kareem baka fada min zaka zo?” “Laa Kareem baka fada min zaka zo?” Ya kwaikwaye ni da wata murya kamar ba shi ba yana mocking dina fuska a hade. “Ba ki da aiki sai raba Number, ki so wannan ki so wannan, ke baki ma san abun da kike so ba, baki san mai son ki ba, ke baki ma gajiya da halin maza ne?” “Haka zan yi ta yi har na dace Kareem” Na fada a shagwabe murya kamar zan yi kuka. “Ba ni wayata” Yana fada be jira na ba shi ya fisge wayarsa dake hannuna ya bude motarsa ya shiga. “To ai line na yana ciki ka ba ni layina” Banza yayi min ya ja motarsa baya ya bar ni tsaye na fara dora hannu a fuska zan yi kuka, ganin hakan ya saka tsaya da motar be tafi ba kuma be yi gaba zuwa inda yake dazun ba, ya dade a ciki sannan ya fito motar ya tako da kafa ya zo ya mika min wayar. “Kalli wani mayafi da kika saka kika fita, haba Noor, kin saka duk raina ya bace Wallahi, idan kika sake shiga motar wani ko kika saka mayafi irin wannan kika fita, ban yafe miki ba, kuma mun bata ba zan sake kula ki ba” Na karbi wayar ina kara bata fuska alamar zan yi masa kuka, i feel so childish when ever I'm near him, da wani ne ya fada min haka ba zan damu ba amman shi na ji babu dadi, kuma abu kadan idan yayi min sai na masa kuka nake jindadi. Motarsa ya koma rai a hade ya bar ni a gurin, sai da ya wuce na duba sai na ga babu liyi a wayar, ashe sim din ne ya cire a motar ya kawo min wayar kawai. Kamar na kwala ihu haka na ji a wane dalili zai karbe min layi ya tafi da shi. Hayaniyar da na ji a zaure ne ya saka ni karasawa cikin gidan da sauri, Hana na zube a kasa tana rusar kuka Baba kuma yana ta zazzaga masifa. “Shiyasa aka boye min, saboda tana auren ubansa, wato kar aka taba mutumcin aurenta ko? Bayan ni kuma ya taba mutuncin aurena” “Me ya faru Hana?” Hana nake tambaya sai Baba ya amsa min. “Munafukar yarinya, daman ai uwarki ta koya miki kiyayya da ni, shiyasa ni baki son farinciki ba ruwanki da damuwa da uwarki kawai kika damu, ashe abun da ya kashe miki aure kenan amman kika boye” “Baba me kake fada?” “Ashe mijinki mutumen banza ne, fyade yayi ma Hana shiyasa kuka rabu, kuma aka boye min? Magana mai girma haka? To ba zan bar wannan ba, Wallahi sai na ja hakkin yata ba zan bari a tafi a banza ba, sai na yi karar ubansa” Na saki wayar hannuna da jakata da mayafin duka suka zube a kasa. “Baba a ina ka ji wannan? Ba gaskiya ba ne sheri ne...” “Sheri? Ai abun duniya baya boya ina zamana wata mata ta zo ta fada min” Na dafe kaina. “Innalillahi Wa'inna Illaihirraji'un, Baba ba gaskiya ba ne, kawai na gaji da zama da shi ne muka rabu” “Kika sake magana sai na tsine miki albarka ma, har matar da ta cirewa Hana ciki na ganta da idona na yi magana da ita, kuma ba zan bar maganar nan ba” Hana ta girgiza min kai tana kuka ni ma kukan na fara Umma kuma ta saka salati yana tabi da rike baki... Pay 500 to 2451879008 Zenith Bank Hadiza Abubakar And send the evidence of payment to my WhatsApp number 08036126660. Da zullumi da tunani kala kala na kwana a raina kamin safiya ta waye har na matsu, haske na fara fitowa na safa hijab dina na sa ci kafa na fice daga gidan ba tare da kowa ya sani ba. Na isa titi ina kama jiki domin hadari ya hadu a garin iska mai sanyi na kadawa sosai, na wahala sosai kamin na samu napep din da ta dauke ni, tun a cikin Napep din na ba shi kudinsa. Ina sauka na kwankwasa kofar gate din gidan Kareem, babu jimawa mai gadin ya bude, na yi zaton zai kauce ya ba ni hanya na shiga ne sai ya tare ni, ya hana ni shiga. Wai ya masa warning cewar idan ya bar wata ta shiga a bakin aikinsa. “Abu ne mai muhimmanci, dan Allah ka shiga ka fada masa Noor ce” “Ko fa haske ce yace kar na sake bari mace ta shiga, ba zan yarda na rasa aikina saboda ke ba” “Fada masa kawai zaka yi, ba shiga zan yi ciki ba” Kusan ni zan iya cewa ban taba haduwa da mutum mai tsananin kafiya da kin yin alfarma ba irin mai gadin Kareem, babu irin magiyar da ban masa ba amman sam yaki bari na shiga kuma ya ki tafiya ya fadawa Kareem din ina waje. Na bata awa 2 a gurin domin na iso ne karfe 7 na safe kareem kuma be fito gidan ba sai tara da wani abu. Ana bude gate din na auna da gudu cikin gidan, mai gadin ya biyo ni yana fadin na fita ban kula shi ba na nufi Kareem. Fitowa mota yayi ya daga mai gadin hannu alamar ya kyale ni, sannan ya rufe motar yana kallona. “Sim kika zo karba?” “Me yasa ka ce mai gadinka kar ya bar ni na shigo? Ko ka gaji da ni ba zan daina kawo maka bukata na ba mun riga mun zama Family” “Ba ke na ce kar ya bari ki shigo ba, amman ko ba a fada ba ke ma kin san be dace ba, ba mutuncinki ba ne, zaki iya kirana na zo na same ki mu yi magana idan kina da bukata” “Da me zan kira? Ba ni da number ka, kuma ka karbe sim din, mai gadinka ya aje ni a waje har na awa biyu na wahala sosai” “Kin yi samari ba zaki iya zama ba sai kin yi waya da su ko? Tun jiya da dare suke kirana har yau da safe, har da wani mijin kawarki wai ya kira ya ji kin isa Lafiya, me yasa zaki yi ta raba numbobinki ga maza Noor?” Da fada yake min maganar ransa a bace har fuskarsa ta nuna. “Mijin kawata ba ni na bashi number na ba, ban san ina ya samu ba, kuma ni ban taba waya da shi ba, tun zuwan da na yi ma na yi muka gaisa ya tafi ban sake magana da shi ba” “Su kuma mazan biyu da suka kira fa? Sannan wani ya sauke ki mota a gaban idona ai waye shi” Na turo baki gaba ina wasa da yatsuna. “Shi.. Shi..shi... Ai rage min hanya yayi sai kuma ya karbi number na, ka ganshi yana da kyau ko?” Na wara masa ido ina murmushi sai ya kara hade rai. “Ni ba ni da kyau ne da wani zai burgeki? Me yasa ni baki taba ganin kyauna ba? Noor ki tsayar da hankalinki ki fahimci rayuwa please” “Are you jealous?” “Yes...” Ya amsa min kai tsaye yana kallon cikin idona kamin ya dauke idonsa ya lumshe ido, sasauta fushinsa yayi sannan ya kalleni. “Shi kuma Baban Aisha fa miye hadinki da shi?” “Baban Aisha? Wace Aisha?” “Matar Hafiz” Baki sake nake kallonsa da mamaki. “Ya fadi cewar ya san ni ne?” “Duk wanda ya kira yana introducing kansa, sannan yace da ke yake son magana, kuma na saka Sim dinki a wayata truecaller yana nuna sunan kowa” “Amman ba ni da number Babanta ni ban ma taba ganin mahaifinta ba, sai idan wani abun kuma ta hada min har mahaifinta zai kira ya min magana to ma ina ya samu number na?” Ina karashe maganar wani tunanin ya fado min, wata kila tsohon da na fara haduwa da shi har ya ba ni kudin Napep mahaifinta ne. “Na tuna jiya na hadu da wani tsoho mahaifinta ne kenan?” “Ban sani ba, tare muka tafi? Taya zaki tambaye ni” Ya amsa min kamar da fada, gaba daya na lura daga jiya zuwa yau kamar dai haushina yake ji ko kuma baya son mu yi zaman lafiya. Ya bude motarsa zai shiga. “Ni fa ba sim din na zo karba ba, wata matsala ce ta faru jiya bayan ka wuce shiyasa na zo nan, babu wanda ya san na fito ma” Ya kalli ruwan da suka fara dauka ya kalleni. “Shigo ciki” Ya rufe motar ya koma cikin gidan ni kuma na bi bayansa muka shiga falon, ac ya fara kashewa sannan ya zauna a hannu kujera ya duba agogon hannunsa sannnan ya kalleni kallona. “Zauna fada min minene?” “Baba ne, wai zai yi karar mahaifin Abdull saboda abun da ya faru da Hana” Mikewa yayi tsaye yana mamaki. “Ta ina ya ji wannan maganar?” “Ban sani ba, amman yace wata mace ce ta fada masa kuma har matar da ta zubar mata da cikin ya gani da idonsa, kuma idan maganar nan ta fita, rayuwarta zata lalace ni ma ba zan sake samun wanda zai aure ni ba” Ya kalleni with so much effection. “Duk yadda zaki zama Noor akwai wani yana nan yana jiranki, idan duniya da mutanen cikinta suka juya miki ba, shi yana nan tare da ke, babu wani abu da zaki aikata ko waninki ya aikata da zai saka shi gudunki, idan kika ga ba ki da kowa a duniyar nan hakan yana nufin ba shi a raye” “Waye?” A madadin ya amsa min sai ya sauke kai ya jefo min wata tambayar. “Kin fadawa Safeena abun da ya faru da Hana ne?” “Ban fada mata ba, ni ban ma yi magana da ita bayan faruwar hakan ba, sai dai idan shi ya fada mata, ko kuma kai!” Ya girgiza min kai “No ba ni da wata alaka da Safeena yanzu, babu yadda za'ayi wata maganar ta shiga tsakanina da ita, balle wannan sirrinku ne, ba zan iya cutar da ke ko wani na ki ba Noor” “Me yasa ka ambaci sunanta? Kana ganin zata iya wani abu?” “Saboda zata iya yin haka, zata iya tona wannan asirin ta hada wannan makircin saboda bakinciki rasa ni, saboda na fada mata ba zan sake dubanta ba, na san na yi kuskure a baya, amman yanzu na gyara komai ya wuce, ta fada min aurenta yana gad da lalacewa saboda kin fadawa mijinta cewar danta data haifa ba na shi ba ne, kuma ya dauki yaran yaje gwada jininsu, ta fada min idan aurenta ya mutu ba zata kyale ki ba, kuma dole sai na aureta ni kuma ba zan taba aurenta ba” “Me yasa ba zaka aureta ba? Ya zaku yi da dan kenan?” “Me zan yi da ita? Ko ba ita ba ba zan sake yin aure ba a rayuwata” “Saboda me?” “Ba zan auri macen da bana so ko bata so na ba, mace daya nake so a duniyar nan, idan har ba zan same ta ba, to zan hakura da aure ne har abada” “Wacece? Hafsat” “Noor... Noor ce...” Ya amsa min tare da sautin fitar iska, fuskarsa kuma cike da rauni. Na mike tsaye ina kallonsa, sai ya tako ya matso kusa da ni, ya zuba min kalaman da na gagara mantawa. “Babu wata Hafsat Noor ke ce, i love you so much, tun a farkon haduwata da ke na ka mu da sonki Noor, amman a lokacin baki ganin kowa a gabanki sai Zafeer, bana son na lalata alakarku saboda bana son ki samu rauni a zuciyarki, ni ne dalilin da ya saka Hafiz ya aureki, saboda ya fahimci ina sonki, amman ina tsoron na yi rayuwar aure da babu dadi a tsakanina dake, a kokarinsa na gyara tsakanin ginin da ya rusa na Zafeer da ke, mahaifinki ya Kyautar masa da ke” Kallon juna muke daga ni har shi falon yayi tsif kamar babu kowa a ciki. “Kamin ya rasu ya fada min na samawa zuciyata abun da take so, kuma ke zuciyata take so Noor, yarinyar da na baki labarin wani ya riga ni ke ce Noor, ke ce karshen bukatuna, ina son ki Noor” Na sauke idona kasa hawaye suka sauko min. “Ina jin zan iya kyautata miki Noor, na baki rayuwa mai kyau, gatan da kika rasa, zan sama miki, burina kullum na ganki a farinciki, but i know I'm not perfect, ban cancance ki ba, you deserve someone better da me, akwai wata kofa da ba zata bude ba a tsakanina da ke, na bata rayuwata na sani, kin fada min ba zaki iya zama da mazinaci ba, ko da ya tuba, kina da gaskiya Noor na girmama ra'ayinki” Hannu ya saka ya cire hawayen da ya taru a idonsa. “Ina son murmushinki, ina son dariyarki, ina damuwa idan kin damu, ina jin farinciki da farincikinki, idan na tunaki ina jin nishadi, ina son rautarki i love every about you Noor but I'm weak, ban cancance ki ba, ni ba mutumen kirki ba ne, taya nagartacciyar yarinya irinki zata auri namiji kamar ni wanda ya aje ďa ba tare da aure ba? Kuma da matar wani matar sunna?” Yayi murmushi “I'm so lonely, ina fatar kalamaina ba za su bata miki rai ba, i hope ba zaki yanke alaka da ni ba, ganinki ma yana saka ni jindadi, ina son na roki abu daya” He take one step forward i take one step backward. “Kawai ki bar ni na rayu da kaunarki, if you ever need someone you know I'm here, daga yanzu har zuwa karshen rayuwa, ina fatan duk wanda zaki aura nan gaba, zai rike ki amana ya baki kulawa irin wacce na so baki, ban miki fatan rashin dacewa duk da yake kaddara tana rabaki da su, tana kara kusancinmu, amman bayan nufin zan aure ki Noor, amman ina sonki Noor na mutu a kaunarki, i was waiting for so long ma fada miki yadda nake ji akanki, ba ni da sauran farinciki a yanzu sai ke sai yarana” Ya saka hannunsa aljihu ya ciro sim din ya miko min, na daga kai ina kallonsa. “Ba ni da wata dama na hana kowa rabarki, ina jin kishi saboda ina sonki, amman ba ni da wata hujja ta alakantuwa da ke, amman ko na mutu noor ina son ki sani KAREEM YANA KAUNARKI i wanna tell what i feel in million meaning...” Juyowa na yi ya nufo kofar fita daga falon da nake jin yayi min kada a yau duk kuwa da irin girmansa. “Ruwa ake Noor ki bari a dauke ruwan” Ban juyo ba balle na amsa shi haka na fita cikin ruwan ina hawaye da ban san na miye ba, me yasa bake kuka? Me yasa Kareem ya fada min haka yanzu? Da gaske so na yake ko dai yana son yayi min irin na Safeena ne? Kalamansa sun yi min nauyi sun mantar da ni dalilina na tafiya gidan. Ashe Zainab ta fadi gaskiya Hana ma ta fada cewar Kareem yana so na. Tafiya kawai nake irin na wanda ya rasa gurin zuwa, ruwan saman da ake kama da bakin kwarya yana dukana, da na fara gajiya da tafiyar sai na samu wani guri a gafen wani babban gida dake unguwar na tsaya, ina matukar tsoron ruwa da tsawa ko walkiya amman a ranar gaba daya tsoron komai ya fice min a kai. Motar Kareem nake facing dake fake a daidai inda nake tsaye, abun da ban sani ba ina tafiya yana bina a baya har na samu gurin tsayuwa. Front seat ya bude yana kallona, takawa na yi cikin ruwan na nufi motar na shiga na zauna, a bude na bar kofar har sai ya kwanto ya miko hannunsa ya rufe gambun motar. Wani yanayi nake ji na dabam shi ba tsoro ba, ba jindadi ko akasinsa ba, a yanzu na kasa sakewa da shi, kamar bako haka nake jinsa. A tsawon awannin da muka yi a motar ko kadan ban yarda na kalli hafen da yake zaune. Amman shi nasa idon suna kaina har aka dauke ruwan. Sannan ya tashi motar yana tuki yana kallona har muka isa. A gaban gidanmu ya faka sai a lokacin na juyo kadan na kalleshi idanuwana suka sauka cikin nasa. “I'm sorry i hurt your feelings, wata kila kin fi son abota da ni, wata kin fi sakewa idan ba soyayya ba ce, bana nufin bata ranki Noor kawai dai na fada miki ne saboda na samu sassaucin abun da yake zuciyata, dan Allah kar hakan ya saka ki canja min ina jindadin kasantuwata da ke” Na juya na bude motar na fita, shi ma sai ya bude ya fito. “Ki sanar da Baba ina waje” Ban juyo ba kuma ban amsa bana shiga ciki, a zaurenmu na tsaya na rumgume kaina ina wani irin kuka mai karfi amman bana iya barin sautin ya fita, da za a tambaye dalilin kukan ni kaina ban sani ba, zuciyata ta yi min nauyi da bata taba min ba kamar ba zan iya daukarta a kirjina ba haka nake ji. Gefen hijabina na saka na share hawayena sannan na shiga cikin gidan da idanuwa da suka yi ja. Dakinmu na shiga na samu yar'uwata ita ma tana nata kukan. “Hana me ya faru ina Baba?” “Ya tafi yanko sammaci ya ce ba zai kyale maganar nan ba, shikenan rayuwata ta lalace” Na tashi da sauri na fice daga dakin waje na fito na samu Kareem tsaye yana kallon kofar gidanmu. “Baba ya tafi kotu zai saka karar” Motar ya bude ya dauko wayarsa ya zagayo ya mika min wayar. “Saka min number Baba” Na karba na saka masa jiki na rawa na mika masa kasa ya sunkuya ya aje min sim dina ya juya ya wuce, ina tsaye a gurin ina kallon motarsa har ya bace min. KAREEM POV. Be yi nisa da unguwar ba ya faka motarsa ya jingina kansa yana ya runtse ido, wani azabben ciwo yake ji a kirjinsa da ya wuce misali, ya kusa minti talatin tsaye a gurin sannan ya dago ya kira number mahaifin Noor. Da farko be daga ba har sai da ya sake kira. Cikin mutumci Kareem ya gaisa da shi sannan ya gabatar masa da kanshi, sannan ya kora da dalilin kiransa. “Baba na wani labari na ji marar dadi, cewar an yi ma Hana fyade abun ba dadin fada ma, ban jidadi ba gaskiya sai dai abun da ya fi daga min hankali shi ne cewar da aka yi zaka yi karar wanda ya aikata abun ko haka ne?” “Haka ne mana, ta ya zan bar wanda ya keta haddin yata ya tafi a banza, dole na kai shi kotu hukuma ta hukunta shi, suna aikata hakan ne saboda suna ganin ba a musu hukuncin komai” “Haka ne, kaiwa kotu yana da amfani musamman idan har za a musu hukunci, sai dai Baba ina son ka sani kotun yanzu ba irin ta baya ba ce, kuma mutumen nan yana da rufin asirin da zai iya komai dan ganin asirinsa ya rufu, mahaifinsa ma babban mutum mahaifiyarsa ma haka kuma ita ma babban mutum take aure, baka tunanin aikata hakan zai janyo ka jefa rayuwarka cikin hatsari?” “Bana tsoron komai ni, Allah yana tare da mai gaskiya, tarin kudinsu ko ikon da suke da shi ba zai hana na kaisu kotu ba, shiyasa ma zan yi karar uban ai, domin shi yake gari ba dan ba, kuma ya san dansa ba ban kirki ba ne ya zo nema masa aure? Ko da lamarin nan ya faru ai ya kamata ya zo ya same ni ya ba ni hakuri kuma ya samu dan wani abu ya ba ni ko? Duk be yi ba sai ya zuba min ido yarinya ace har ciki aka zubar mata kamar wata karuwa, ai an fada min kai ka zubar da cikin, ashe kai ma zaka iya cutata Alhaji na yi zaton ai an zama daya yanzu” Kareem ya shafa goshinsa ya sauke ajiyar zuciya. “Duka mun yi wannan abun saboda kar kowa ya ji, idan maganar nan ta fita Hana zata rasa abubuwa da yawa, zata takura cikin mutane kuma abun zai zama abun magana ba lallai ta samu mai aurenta a haka ba, dan Allah Baba ka bar maganar nan ko dan mutuncin yaranka, kuma karar mahaifinsa be dace domin ba mahaifin ne ya aikata ba, hakan zai iya janyo alakar dake tsakanin Mama da mahaifinta ta samu rauni” “Idan ta samu rauni ni miye nawa a ciki Alhaji? Daman ai an fada min Hajara ta boye wannan ne saboda uban wai kar aurenta ya mutu saboda yana da kudi ko, wato ta fi son rayuwarta akan rayuwar yaranta saboda kwadayi da son abun duniya” “Ina da tabbacin ba dan haka ba ne Baba, saboda kar rayuwar Hana ta lalace ne kawai ba dan wani abu ba, dan Allah Baba karka shigar da karar nan ka tsaya ka yi nazari” “Na yi iya nazarin da zan yi daga jiya zuwa yau, kuma na duba na ga abun da ya dace na aikata kenan, yanzu haka na biya kudi an yanka sammaci an aika wa ubansa zamu hadu kotu litanin mai zuwa rana irin ta yau” “Baba zan biya duk wani kudi da ka kashe na kai sammaci kuma zan samu wani abu na baka, zan yi duk abun da ya dace zan dauki abubuwa dan Allah Baba ka bar maganar nan” “Ka gani Alhaji Kareemu ina ganin mutuncinka sosai ina mutumta ka, dan Allah mu tsaya a matsayinmu kar abun ya wuce nan, ni ba makwadaici ba ne, ba irin uban nan ba ne da zaka ce ka dauki kudi ka ba ni ka rufe baki, wato saboda ka raina kuma ka maida wannan matsalar ba komai ba ko? Shiyasa kake son ka rufe bakina, ba dan na san ka da dadewa ba ai sai na ce Abdullahin ne ya aiko ka, ni ba zan bar maganar ba sai na kwaci hakkin yata” “Ayi hakuri Baba” Kareem ya sauke wayar tare da sauke ajiyar zuciya, wannan karon ya kasa shawo kan Baba yana mamakin me aka nuna masa haka da har ya dage dole sai yayi wannan karar, shi dai kam zai iya fada be taba ganin mutum mai zuciyar Baba ba, baya tsayawa tunani idan zai aikata abu. Nurse da ya saka ta yi ma Hana wankin ciki ce second person da Kareem ya kira after Baban Noor. “Hello” “Juwairiyya ya kike ya gida?” “Lafiya kalau Alhamdullahi ranka ya dade ya aiki?” “Kwanan baya akwai wata yarinya da na kira kika mata wankin ciki zaki iya tunawa?” “Eh ba a dade sosai ba ai ko?” “Haka ne, kuma ina tunanin lokacin da na kiraki na fada miki cewar yarinyar kaddarace ta hau kanta, kuma tana da matukar muhimmanci a gurina shiyasa na kasa yi mata da kaina na saka ki yi, domin zan iya cire ciki ko ya kai wata takwas kuma mace ta rayu, abu da kika san na kwarai a kansa, amman na kira ki na bukaci ki mata ne saboda bana son na ga yarinyar a wani yanayi da be dace ba, abu na biyu duk mai aikin lafiya ya san aikin lafiya sirri ne cin amana ne ka dauko sirrin wani ka yada kin san da wannan?” “Na sani, me ya faru?” “Da wa kika yi hirar yarinyar nan? Saboda abun ya zagayo yana bibiyar yarinyar nan” “Ban yi maganar da kowa ba gaskiya” “Don't lie to me please, mahaifinta da bakinsa ya fada cewar har wadda ta cire mata cikin ya gani da idonsa” “Ni Wallahi ban san na samu wani na yi wannan maganar da shi ba, me zai saka na yi haka? Gaskiya akwai dai yadda aka yi amman Wallahi ni ban yi magana da mahaifinta ba ban san ma mahaifinta ba ban san kowa nata ba, wata kila dai ita can ta fada har maganar ta juyo amman ni ban fadawa mahaifinta ba” “Ba ki yi maganar da kowa ba?” “Gaskiya ban yi maganar da kowa ba” “Lokacin da na kiraki na fada miki ciki ne nake son ki wanke waye a kusa da ke?” “Akwai kawayena guda biyu lokacin mun je barka kawata yar makarantarmu da ta haihu, amman ko su ban yi maganar da su ba?” “Zan iya sanin sunansu?” “Yeah Safeena Jafar Ishaq da Amina Alhassan” Sunan farko da ta ambata ya sanyaya guiwar Kareem a nan ya gane gurin da maganar ta fita, wata kila bata son fada masa cewar ta sanar da Safeena ne, wata kila kuma gaskiyar take fada masa idan har zata boye wani abu ba zata ambaci sunan Safeena ba. “Mi ya faru?” Ta tambaya jin yayi shiru. “Kawai ina tunani ne, wata kila ita ta fada ko yayarta zan bincika ta can na ji a ina maganar ta fita” “Sai dai idan can domin ni ban yi maganar da kowa ba” “Okay” Ya sauke wayar ya bugi sitiyarin motar da karfi. “Safeena...!!!” Ya lalobo number Safeena yayi mata kira ya fi a kirga bata daga ba har sai da ya aika mata da sako. “I need to talk to you abu ne mai muhimmanci” Few seconds da delivery sms din kiranta ya shigo wayarsa. “Magana nake son mu yi mai matukar muhimmanci, ki same ni a guest house, yanzu” Yana fadar hakan ya kashe wayar ya hau titi ya dauki hanyar gidansa da suka saba haduwa. Ya rigata isa domin shi yake son magana da ita a yanzu, a yanzu ikon a gurinta yake hakan ya saka ta bata masa lokaci na tsawon mintuna arba'in sannan ta shigo gidan. Yana tsaye ta window falon yana kallonta har ta fito motarsa ta turo kofar falon ta shigo. “Lafiya kake son ganina?” “Me kike so Safeena” Kamar jira take sai ta sauke gyalenta ta aje jakar a kujera ta nufo shi tana nuna shi. “Kai Kareem kai nake so!” “To miye matsalarki da Noor? Miyasa kike cusata a cikin matsalarmu?” Ya tambaya ba tare da ua juyo ba hannayensa duka biyu suna zube a aljihunsa. “Saboda Noor ce ta raba ni da kai, Noor ce macen da ta cike gurbina da ita, kuma ita ce ta kashe min auren da takardar kawai ya rage Abdull ya ba ni” “Ban cike gurbinki da na noor ba, wani gurbi na gina mata mai kyau mai tsabta, mai cike da kauna da soyayya, dan Allah ki cireta a cikin matsalarki” Har lokacin da yake maganar be juyo ya kalleta ba. “Ita ce babbar matsalata a rayuwar nan Kareem, ta lalata min aure tun da mijina ya dauki yaran nan ya tafi da su ya auna jininsu be sake dawowa gidan nan ba, last week ya aiko kanensa ya dauki yaransa biyu aka bar karamin da na haifa da kai, yanzu haka mijina yana garin nan amman be tako kafarsa gidana ba, ya daina min aike ya daina kulani baya amsa wayata baya ba ni amsar sakona, na sani saki na zai yi bayaj ya gama kwance min zane a kasuwa, zai saka kowa ya tsane ni a danginmu saboda abun da na aikata Mijina cousin dina ne, kuma duk sanadin Noor ce ne domin ita kadai ta san sirrina ita kadai zata iya fallasa wannan” Ya juyo ya kalleta. “Ta aikata kuskure na fahimta, mu ma mun aikata dukanmu mutane ne, amman saboda me zaki lalata rayuwar kanwata me ya shigo da kanwarta ciki? Kina da tabbacin Abdull din ne ya aikata?” Ta matsa kusa da shi tana masa wani kallo na tsana for the first time. “To waya aikata kai? Ko kuma dai ita ta aikatawa kanta?” “Baki da tabbacin Safeena karki jefa rayuwarki a matsala” Ta yi wani shu'imin murmushi. “Na san komai Kareem kai ka san wacece ni, ina da tabbaci mana, a gabana ka kira kawata ina jin muryarka lokacin da kake fada mata cewar wata yarinya kake son ta yi ma wankin ciki ka mata allura amman dai ka fi son a wanke saboda ka samu tabbacin komai ya zube, ka fada mata kaddara ce ta hau kan yarinyar fyade aka yi mata ko ba haka ba?” “Ita Juwairiyya ce ta fada miki haka?” “No Wallahi bata fada min komai ba, amman na ari wayarta na duba bangaren kira sai na ga number ka, daman kuma na ji muryarka domin wayarta ana ji duk abun da mutum ke fada sound din kiranta a karshe yake, lokacin da na duba zuciyata ta fada min Hana ce, there is no way da zai saki Noor da ciki ba tare da wani abu ba, kuma ya fadawa yan'uwansa wai ta tayar masa da fitina ne sai ya sake ta shi kuma ya sake ta saboda TA KI ZAMAN AURE, kana ganin hankalina zai dauka? Idan babu wani abu me zai saka Noor ta fada masa cewar dan da na haifa ba na shi ba ne? Mw zai saka yar'uwarta ya yanke karatunta da duk wani gata da yake musu ta dawo ita da kanwarta su zauna a gida? Daman ni ban yarda ba na san akwai wani abu a kasa, domin na san waye mijina ba kasafai yake iya rike kansa ba, a tsawon watanin da yake a Lagos da sunan aiki na san me yake aikatawa, kawai na zuba masa ido ne saboda babu yadda zan yi, kana tunanin namiji zai saka al'adar neman mata a gaba kamar yadda Abdull yake kuma ace matarsa bata sani ba?” Ta share hawayen da suka zubo mata cikin daga murya ta cigaba da fadar. “Neman matansa ya taimaka min gurin bibiyarka da kokarin kulla alaka da kai Kareem, na san yana neman mata tun kamin na aure shi, na aure shi ne saboda an matsa min a gidanmu na yi aure, kai kumaka guje ni, duniya ta min zafi, shi kadai ne mutumen da ya zo zai share min hawaye a lokacin, bayan mun yi aure ya zama bana burge shi saboda ya saba da matan waje, mijina ba shi da lokacina, baya ganin kyauna, ba ya ganin ado na, kullum idonsa akan matan waje ne, mijina baya iya gamsar da ni yadda kake min Kareem, gaba daya ban yi dacen rayuwa ba, amman a haka nake zaune kullum burina idan har na bar Abdull kai ne” Wannan karon da cinyar hannu ta goge hawaye idonta na dama. “Na san na yi kuskure na haihuwar ba ta sunna ba, dukanmu yin yi kuskure amman sai mu rumgumi wannan kaddarar, nan gaba kadan Abdull sakina zai yi, to sai ka aure ni mana Kareem” Ya juyo da kyau ya fuskance ta. “Ba zan taba aurenki ba, amman zan tabbatar maki da abu daya, Noor ba zata aure ni ba, saboda bana cikin mazan da take so, please ki cireta a cikin matsalarki” “I don't care ka auri Noor ko karka aureta ba matsalata ba ce, abun da kawai na damu da shi, shi ne idan Abdull ya sake ni zaka aure ni” “Har abada ba zan taba aurenki ba, aure ya haramta a tsakaninmu” Ta rausayar da kai tana murmushi. “Na fahimci hakan ai, shiyasa na bullowa ubanta ta wannan sigar na fada masa gaskiya kuma na kwadaita masa dukiyar da zai samu idan ya Abdull ko mahaifinsa suka bukaci a sirrinta abun, na samu wata kawata muka je a zuwan ita ce nurse din da ta cire ciki, kuma na samu kudi mai kauri na ba shi. Ka ga yanzu hankalin Abdull zai koma gurin abun da ya aikata ne ba wanda zai aikata a gareni ba, kuma idan ya fallasa sirrina duniya zata zage mu a gaba dayanmu mu uku, kai ni da kuma shi” Kareem ya sasauta fuskarsa ba dan tsoron furucinta ba sai dan yana son ta fahimcin illar fa hakan zai mata ba mijinta kadai ba. Ya busar da iskar bakinsa ya jin kirjinsa na ciwo sosai. “Ki rika yin tunani kamin ki aikata abu, kina da yaya Safeena, tun farko baki rike aurenki kika biyewa shaidan muka aikata alfasha, hakan be wadatar da ke ba sai da kika ga mun haihuwa, yanzu gashi abun ya dawo yana bibiyarmu, kuma duk yadda wannan abun zai taba ni be kai yadda ke zai miki illa ba Safeena, saboda ke mace ce ni kuma namiji ne, shiyasa da Allah zai ambacin mazinata a kur'ane sai ya fara da mace, domin ita ce mai rauni kuma ita ce mai shiga kaso 90 na matsala sama da namiji” “Zaka aure ni Kareem? Ka min alkawari kawai zaka aure ni Wallahi zan yi duk yadda zan iya mahaifinta ya janye shari'ar nan” Ya cire hannunsa daya a aljihu yana nuna mata. “Let me make this clear to you, idan har zan sake wani aure a rayuwata, to mace daya ce zan aura Noor, idan har ba zan auri ba ba zan sake aure ba, so ki saka a ranki ni da ke ba mu taba sanin juna ba, ba zan taba aurenki ba Safeena!!” Wani mugun kallo take masa zuciyarta na bugawa da karfi. Cikin ihu da takiya ta ce “Ba zan saka ya janye shari'a ba Kareem kuma zan daukar masa lauya, domin ina bukatar abun da zai daga hankalin Noor ya zubar da mutuncinta da na iyayenta ya kashe auren uwarta ya jafata a matsala, ba ni da makiyaya a duniya irin Noor yarinyar da saboda ita igiyar aurena take rawa? Saboda ita juya min baya, yar sikar yarinya shashasha mahaukaciya, yarinya da bata kai ta goge talkamin kafata ba, yarinyar da bata kai ka rika hannunta ba, amman ita kake so? Yarinyar da ubanta baya jin wani yare sai na kudi? Yarinyar da ubanta be san wani mutuncin ba sai na kudi? Yarinyar da babu komai akanta sai hauka da gidadanci, fasika da bata iya komai ba sai bibiyar mazan mutane yarinyar da...” Tassssss ta ji saukar lafiyayyen mari a fuskarta daga hannun masoyinta Kareem, Wani irin numfashi taja da karfi ta kai hannu ta dafe kuncin hawaye masu zafi na sauko mata. Cikin wani irin bacin rai da Kareem be san yana da shi ba ya nuna ta da yatsa ya ce. “Kul bakinki ya sake kiran Noor dita da wata kalma marar kyau, iyakar kiyayar da kike mata saboda tana da alaka da ni ne, ni kuma ba aurena zata yi ba, ki fadawa mahaifinta karya kike ya janye shari'ar nan idan ba haka ba...” Wayarsa ta yi ringing ya ciro wayar ya duba farincikinsa ce take kira wato Noor, ya amsa wayar ya kara a kunne shi ma dai sound din kiransa a karshe yake kamar yadda na mutane da yawa yake a manyan wayoyin yanzu. “Kareem ka yi magana da Baba? Me ya fada maka?” Sai da yayi iya yadda zai ya danne yakin dake zuciyarsa ya amsawa Noor da murya mai sanyi. “Na yi magana da shi be yarda ba, amman zan sake samun shi gida mu yi magana karki daga hankalinki” “Ki kwantar da hankalinki ko?... To yaudararki yake yi yarinya, ke ma amfana zai yi da jikinki ya jefar da ke kamar yadda ya jefar da ni ki bi sannu...” Safeena ta fada da karfi, Kareem yayi hanzarin kashe wayar, fuska a hade ya jefawa Safeena mugun kallo da idanuwansa da suka gama canjawa. Wani marin ya sake kai wata, ya saka kafarsa ya kwashe nata kafafuwan sai da ta fadi kasa, ya daga kafarsa ya daki bayanta sai da ya amsa, sannan ya cire belt din jikinsa ya fara zuba mata ba ji ba gani... Duka yayi mata sosai kamar wani ubanta sannan ya fice ya barta a gurin tana ihu tana kuka. Motarsa ya shiga ya kama hanyar tafiya ganin yarsa domin ya san a yanzu su kadai suke rage masa, aikin ma baya jin zai iya tafiya a yau tun tashinsa baya jin lafiya balle kuma yanzu da abubuwa suke juye masa. Sai da ya shiga unguwa ya ji ba zai iya karasa family house dinsu ba, nesa da gidan ya faka mota ya kwantar da kujerarsa ya jinke hannunsa ya rufe ido yana nadamar dukan da yayi ma Safeena, domin be tana kai hannunsa yayi ma mace duka irin wanda yayi mata a yau. Yana cikin motar ya aka kira sallah azahar sannan yaja motar daker yana jin kansa na ciwo kamar zai tsage gida biyu ya isa masallacin unguwar yayi sallah ya sake komawa motarsa, sannan ya karasa gidansu. A harabar gidan ya faka motar ya kashe yana kallon flowers din da suke gabansa amman zuciyarsa tana can wata duniyar. Wayarsa ya ciro ya duba number Noor ya sauke ajiya zuciya ya kai sau takwas sannan ya danna na aika mata kira cikin tsoro jikinsa har rawa yake. Shiru yayi bayan ta daga kiran, sai kuma ya rasa me zai fada mata, ya zai fara mata bayanin komai ya zai wanke kansa, ta ina zai fara fahimtar da ita, be ma yi tsammanin zata amsa kiran ba. “Karka sake kirana Kareem, karka sake zuwa kofar gidanmu, na zan sake karba ko neman wani taimako a gurinka ba, matsalata da ta yan'uwana tawa ce zan ji da kaina, na yanke alaka da kai har abada...!” “Noor” Zai yi magana ta yanke kiran, runtse ido yayi sosai, ne bude ba sai da ya ji an bude gate din gidan, direban dake dauko yaransa daga makaranta ne ya dauko su ya faka a inda ya saba faka motar. A yake Kareem ya nemo kwarin guiwa da juriya ya sakawa zuciyarsa ya bude motar ya fito cikin karfi hali yake takawa yana murmushi ya nufi yaransa da suka nufo shi suna. “Oyoyo Dady Dady Dady” Kamin ya karasa gurinsu su ma su karaso gurinsa ya yanke jiki ya fadi kasa ribbbb. “Dady.....!” Tine ta saka ihu ta saki bag dinta da lunch box din dake hannunta ta kama mahaifinta tana kiran. “Momy Hajiya... Anty Khadija... Yaya Aaryam... Dady na ya fadi... Dady...” NOOR POV. Sai da na zabura a lokacin da yayi hanzarin yanke wayar, kenan yana tare da Safeena har yanzu? Kuma yake fadar yana so na? Yake fadar ya tuba? Yake fadar yayi nadama? Me ya kai shi gurinta? Me yasa ma zai amsa wayata a gabanta. “Ki kwantar da hankalinki ko?... To yaudararki yake yi yarinya, ke ma amfana zai yi da jikinki ya jefar da ke kamar yadda ya jefar da ni ki bi sannu...” Maganar Safeena ta sake nanata kanta a kunnena, zai iya zama gaskiya shiyasa dazun ya daure ni da kalamansa, namiji zai iya aikata komai domin ya samu biyan bukatar kansa. Na mike tsaye zuciyata na raya min Safeena ce matar da Baba yace ta same shi da maganar, ita kuma ta ji ne ta gurin Kareem. Ya fada mata sirrina kamar yadda ya fada min nata, me yasa yake haka? So yake ta jefa ni a matsala ta yadda zan rasa kowa sai shi kadai shiyasa yake taimako na a ko da yaushe? So yake na rasa kowa na zama tare da shi shi kadai, shi kuma sai ya juya ni a yadda yake so? Yanzu na gane dalilin duka taimakonsa na gane manufarsa, na gane buri da bukatunsa. Sai bayan Sallah azahar sannan kiran Kareem ya shigo wayata, na sani daman zai kira ko ya zo domin kare kansa, kuma na shiryawa duk wata karyarsa sai na ga iya gudun ruwansa. Na amsa kira sai yayi shiru ba tare da ya ce komai ba. “Karka sake kirana Kareem, karka sake zuwa kofar gidanmu, na zan sake karba ko neman wani taimako a gurinka ba, matsalata da ta yan'uwana tawa ce zan ji da kaina, na yanke alaka da kai har abada...!” Na fada masa kai tsaye hawaye na zubo min zuciyata na zafi because this is the most hardest words i had ever said to someone, who's there for me in every Situations, rabuwa ce irin wanda rai be so ba amman dole na yi. “Noor...” Zai yi magana na yanke kiran ba tare da na tsaya na saurari abun da zai fada ba. Na dafe zuciyata ina kuka he's someone who's  always been a good friend to me, but the fact that i know yana da manufa na yin haka ya yanke duk wani hanzari, ya ture duk wani uzuri nasa, ba zan iya yarda na lalata rayuwa saboda namiji ba. Karfin hali na yi na fita na siyowa Hana maganin zazzabi domin jikinta yayi zafi sosai fever ya rufe ta. Ana gama sallah la'asar ban tsaya cin abincin rana da Umma ta sauke ba na yi mata karya cewar Zainab ta kira waya na kaiwa mahaifiyarta su yi magana saboda wayar mahaifiyarta ta lalace. “Ki dawo da wuri, domin Babanki tun da ya fita be dawo ba har yanzu kin san kuwa yana hanya a yanzu, idan ya dawo be same ki ba, ke ce a ruwa” “Ba zan dade ba In Shaa Allahu” Na saka talkamina ina kara sirranta jakata dake boye a hijab dina na fice daga gidan, kai tsaye titi na nufa daman manufar ta samu dalilin fitar ne. Ina kokarin taron Napep na muka yi ido hudu da Zafeer zai karya kwanar gidanmu da wata kafirar mota mai kyau da kyalli. Wuce ni yayi ya shiga kwanar ni kuma na shiga Napep din na fada masa inda zai kai ni, yana tafe ina mamakin mi ya kawo Zafeer a nan ya domin tuni ya dauke iyayensa daga unguwar saboda likkafa ta yi gaba a wata unguwa mai kyau suke zaune a yanzu. A kofar gidan Abdull kuma gidan Safeena mai napep din ya sauke ni na bashi kudinsa na shiga gidan bayan mun gaisa da mai gadin, har yake fada min bata dade da shigowa gidan ba. Da manifa biyu na zo gidan an roketa alfarma ta saka mahaifina ya janye ko kuma na yi mata ta karfi. A bakin kofar falon na tsaya na bude jakata na dauko wayata na sakata a airplane mode sannan na kunna recording na shiga falon ina sallama, wayar na rike a hannuna. “Wa'alaikumussalam, bakar macijiya me kuma ya kawo ki?” Ta amsa min tana tsaye rike da maganin da ban san na miye ba a hannunta, fuskarta ta kumbura daga bakin inda yake ina kallo a jikin, fuskarta da kafadarta zuwa kafafuwanta da hannunta sun yi ja, alamar an mata duka. “Magana na zo mu yi dan Allah ki saurare ni Safeena” “Ina jinki” Na matsa kusa da ita na fara mata magiya da raunaniyar murya. “Idan kina tunanin wani abu ne a tsakanina da Kareem, Wallahi babu dan Allah dan girman Allah ki yi hakuri da abun da na yi miki, ina rokonki alfarma ki saka Baba ya janye shari'ar nan” “Ashe kin san kin cutar da ni, wato yanzu kina son mu sasanta dan kar auren uwarki ya mutu kuma asirin kawarki ya tonu ku kunyata ko? Amman ke kika son kunyata ni, ki bara ni da abun da nake so, kin yi iya yadda kika iya har sai da kika fitar da ni a zuciyar Kareem, hakan be miki ba sai da kika auri mijina, hankalinki be kwanta ba sai da kika fada masa cewar dan da na haifa ba jininsa ba ne” “Cikin fushi na fada masa hakan, kuma ba dan ya sake ko ya juya miki baya ba, kawai na fada ne saboda a lokacin raina yana bace ne, na bakinciki abun da yayi ma kanwata” “Ai kin ci riba idan bibiyar mazan mutane yana da kyau kin gani ai, kin gaji kwadayi gurin ubanki, gaba daya kin firgita min tunani, kin saka Kareem ya tsane ni mijina ya tsane ni, mijina yana garin nan amman ya ki ya zo gidana, yau kuma Kareem yayi min abun da be taba ba, kin saka masa wani banzan hali da ba na shi ba, na tsane ki Noor” Na risina kasa ina rokonta. “Dan Allah ki taimaka min Safeena, Wallahi ba zan fadawa kowa cewar kin haihu a waje ba, dan Allah ki fadawa Baba karya kike ya janye shari'ar nan” “Fadi na nawa kuma, ai kin gama fada tun da kika fadawa mai gayya mai aiki, kin fadawa Abdull ya sani to miya rage? Wato Kareem fada miki ni na fadawa mahaifinki haka ko? To be yi karya ba ni na fada, ni kuma shi ya fada min, ki daina biye masa kina yaudarar kanki ni dai na riga na harbo jirginsa, kuma babu abun da za a fasa idan kina son ubanki ya fasa shari'a to ki fadawa Kareem ya aure ni, ya kyale ki shikenan nake bukata sai ki samu salama idan ba haka ba kin fara ganin matsala kenan a rayuwarki tafi ki bar min gidana” Ta fara turani, sai na tashi na share hawaye na fice daga falon, ban yi nisa da gidan ba na shiga contact list din na whatsapp na tura mata recording din da na yi saving sannan na buga mata warning. “Ko dai ki fadawa Baba karya kike ki karyata kanki, ko kuma na tura audio nan a gurin surukarki da mahaifin mijinki da kanensa kuma da gaske nake na baki daga yau zuwa gobe” Ina fitowa na cire airplane mode din na kunna data da domin sakon ya samu isa, sannan na tari Napep na shiga, gidan Mama na nufa domin labarta mata halin da ake ciki na tabbatar bata san wainar da ake soyawa ba, idan har ta sani zata kira ta fada min ko ta tambayi wani abu, wata kila ita ma idan ta saka baki Baba zai aminta ya sauko. Sai dai na yi rashin sa'a ban same ta a gidan ba, sai mai aikinta na samu tana kallo a falo. Ruwa kawai na sha na kira wayar Mama, ta amsa ni ta fada min bata gidan tana gurin gaisuwa wata kanwar mijinta mahaifin Abdull ce ta rasu. “Mama idan kin dawo ki kira ni akwai maganar da zamu” “Ki jira na dawo, lafiya na ji yanayinki haka?” “Mama bari sai kin dawo” Kiran Mama na yankewa, sai ga kiran Baba ya shigo wayata ina dauka ya fara zagina yana tambayar ina na tafi. “Ina gidan Mama” “Maza maza ki dawo gida yanzu nan” Na mike tsaye babu shiri na yi ma mai aikin sallama na fice. Tare muka fito gidan da Abdull yana cikin motarsa ni kuma ina tafiya a kafa, ban yi mamakin ganinsa ba domin gidan ubansa ne, kuma Safeena ta fada cewar yana gari. Sai dai abun da ya ba ni mamaki kuma ya tsorata ni a lokaci daya tsayar da ni da yayi yana son magana da ni, ashe karfin halin maza har ya kai haka. “Magana ce kawai zamu yi Noor dan Allah ki shigo” Na yi kamar ban san da wanzuwarsa a duniya ba domin babu wanda na tsana irinsa kallonsa ma idan na yi bakinciki nake ji. “Zamu yi magana ne akan karar da mahaifinki ya shigar, ina nan ya kawo sammaci, magana ce da zata sama mana masalaha gaba dayanmu” Na tsaya wata idea na zo min, sai na saka wayata a recording kamar yadda na yi dazun idan na samu yadda nake so, zan iya mixing abubuwa su tafi yadda nake so. A gurin da na tsaya ya faka motar ya bude min front seat. “I know you hate me but please ki shigo mu yi magana magana ce ta sirri” Na kalli gurin sannan na shiga na zauna. “Na ga shigowarki, na so na miki magana amman na san ba zaki saurare ni a lokacin ba, shiyasa na jira har kika fito” “Ka ce zamu yi magana akan abun da ya shafi Shari'a ne ba wani abu ba, idan baka ka abun fada zan fita” Na fada a tsawace jikina har bari yake ji nake kamar ace akwai wuka kusa da ni na caka masa. “Akan shari'ar da mahaifin ya shigar ne, baki tunanin hakan zai iya shafar ki ya shafi kanwarki? Ni fa ban aikata komai ba? Wane tabbaci kike da shi cewar ni na yi mata fyade?” Na dube shi. “Baka aikata ba karya ake maka?” Sai yayi saurin dauke idonsa. “Na ji na aikata, amman ai kaddara ce da bata wuce kowa ba, kuma ke kin san ba zan amsa wannan a kotu ba, kuma baku da wata shaida, na san ubanki ya shirya haka ne saboda kwadayi irin nasa, zan bashi kudi enough, ya janye karar nan karya bata min suna ni da mahaifina, abun da zai biyo baya ba zai muku dadi ba” Kalaman da suke fitowa bakinsa sun karfafa min guiwar aje wayata a cinyata fa yadda sautin zai samu daukuwa da kyau. “Sannu namiji wato har kana da baki da karfin halin da zaka min bazarana kuma ka cilasta ni ko mahaifina, bayan duk abun da ka yi? Ka keta haddin kanwata har ka yi mata ciki sannan ka kalli kwayar idona ka yi min barazana Abdull...!” “Baku da wata hujja akan hakan, kuma fitar wannan zancen zai zubar mata da mutunci ne kawai, dan haka ki natsu ki tattauna da mahaifinki mu taru mu rufawa juna asiri, idan wani abu yake so zan ba shi” Kiran mahaifina da kwadayayyen da suke ya fi komai kona min rai sai dai babu yadda zan yi domin Baba ne ya budewa kowa kofa. Sam na manta da ban saka wayata a airplane mode ba, sai da kira ya shigo wayar. Wayar ta kawo haske kiran yayi appearing saman screen recording din kuma daga tsayaki daman wayar ba a key take ba, tun da Kareem ya ba ni ita ban saka mata password ba. Na yi hanzarin daukar wayar amman hakan be hana shi gani ba, daga Safeena da take kira har zuwa Recording din da nake. “Recording kike? Ina kika dosa Noor” Na bude motar na fita da sauri sai ya bude ya zagayo kamin na yi wani yunkuri ya kamani da kokawa ya murde min hannu ya karbe wayar. “Ka ba ni wayata Abdull” Be kula ni ya rufe gefen da nake tsaye ya zagaya zai shiga motarsa na bishi ina fadin ya ba ni wayar. “Ka goge recording din ka ba ni wayata” Be kula ni ba ya rufe motar yayi mata key ya bar ni a gurin tsaye cikin bakinciki da nadama. Why I'm such a fool and idiot me yasa ma na yarda na yi magana da shi, no wait me yasa ban saka wayar a airplane mode ba kamar yadda na yi dazun. Da kafa na taka na isa Family house din su Mama, a gidan na kwana gaba daya na rasa ya zan yi kuma na san idan na koma gida Baba zai rufe ni da fada ne wata kila har da duka. Abun da ban sani ba, ashe bachin da na yi a gidansu Mama na tsira ne, bachin na chanji ne daga wata kaddarar zuwa wata, ashe na bude wani sabon babin ne na kaddara, domin na wayi gari da mummunan labari... “Innalillahi Wa'inna Illaihirraji'un...” Haka kowa ke fada sai kallona suke na rasa wanda zai amsa min tambayar da nake, sai rufe rufe suke min. “Hana ce ta rasu na san jiya na barta bata da lafiya” “Ke Noor shiga daki ki zauna” “Ba zan iya ba Kawu, gida ya rikice haka kowa yana uhu amman na kasa fada min komai, ni dai ina son na tafi gidan na ji” Na mike tsaye na fara takawa domin a bakin gaskiyata gidan zan tafi na ga abun da yake faruwa. Sai wata matar Yayan Mama ta rikoni. “Dawo Noor zuwanki ba shi da amfani” “Ku fada mata gaskiya mana dole ai zata ji ba a boye mutuwa” Na juyo na kalli kanwar mahaifiyata wato Mama Aisha dake maganar. “Wa na rasa? Mama ko Baba ko Hana ko duka?” Wani irin numfashi ya fara zuwa min da karfi yana shiga haka ma idan zai fita sai ya fisga da karfi. “Gobara ta tashi jiya, gidan ya kone gaba daya babu abun da ya fita” Na rufe ido da sauri ina jin kamar mafarki nake. “Sai hakuri Noor sai hakuri” Haka na ji kowa na fada, sai kuma na jini a jikin mutane ashe faduwa na yi ban sani ba. “Ki yi hakuri Noor haka Allah ya so” Bana gana mai magana sai kallon gurin da sautin yake fitowa nake amman bana iya ganin komai sai duhu. “Baba ya rasu kenan? Hana ma? Biyu na rasa ko daya?” “Biyu kika rasa Noor kin rasa uba kin rasa yar'uwa, sai hakuri” “Innalillahi Wa'inna Illaihirraji'un, Allah ka wakwantar min da hankalina Allah ka ba ni natsuwa Allah ka kara min karfin imani, ka ba ni ikon jure wannan jarabarwar” Shi ne abun da nake ta fada ina dafe da zuciyata, hawaye kam daman ai ranar yau ta su ce, idanuwan ma sun rufe ruf bana ganin komai sai duhu hayaniyar mutane kawai nake iya ji hankalin ma yana kokarin gushewa. “Noor noor noor” Ta rumgume ni, wannan muryar da sanyin da na ji a yayinda ta rumgume ni na ji shi a dabam, dumin jikin na uwa ne data kawo wa yarta dauki a lokacin da ta fi bukatarta. Kuka take ni kuma hawaye nake gidan kuma ihu ake, mutuwa kadai ta kai haka, ba mai iya rarrashin wani. Wasu ruwa mai sanyi na ji an zuba min daga saman kai har jikina aka wanke min fuska da ruwan kankarar sannan aka cire min hijab dina Mama kankam tana kuka. “Karki tafi bar ni ke kuma dan Allah” Na daga ido na kalli saitin da kanta yake a yanzu duhun ya yaye amman hawaye sun hana ni ganin fuskarta. “Da gaske... Da gaske... Baba ya rasu Mama da gaske Hana ta rasu?” Rufe baki ta yi yana danne kukanta, a lokacin ne na kwala wani uban ihu na fashe da kuka na fara shurin kafafuwana ina buri kamar wata mai aljannuna. “Ki yi hakuri Noor ki yi hakuri, kowa aka cewa yayi hakuri ya rasa ki yi hakuri Noor Allah yana son bayinsa masu hakuri” Babu irin kalmar da ba a fada min ba, babu irin rarrashin da ba ayi min ba, amman na kasa rike kaina har ji na yi ina ma ace da ni a cikin gobarar na mutu na huta. Babu irin bala'in da ban kira ba, babu kalar kukan da ban yi ba, da zuciya ta ayyana min sun tafi kenan sai na ji ba zan iya jurewa ba, musamman yar'uwata da take da kurciya da burika masu yawa a gabanta, wayar da muka yi ta karshe da Baba har yayi min fada ta fi tsaya min a rai, sai kuma Hana da na bari a gida cikin rashin na fito. Ni sha kuka ni da Mama tun ina yi ina jin muryata na fita har ta daina fita. Hankalina be kara tashi ba sai na muka isa family house din su Baba muka tarar da gawar mutum uku ana yi mata sallah, Babana, kanwata da kuma matar ubana... Mutuwa bata da kyau mutuwa bata da tausayi, bata da sabo, bata da dadi, na fara dandanarta ne tun a mutuwar mijina na farko. Amman bata min ďaci kamar yau ba. Na yi kamar zan yi hauka, na ji kamar na bisu na ji kamar ace min komai ba gaske ba ne. Daga wajen da aka yi musu sallah aka wuce da su gidansu na gaskiya, ashe tun a jiya na yi bankwana da kanwata ban sani ba, na yi bankwana da ubana ban roki gafara ba, na san ya tafi da bakincikina da fushina a zuciyarsa. Gaisuwar ma idan aka yi min ciwo take min, Allah ya baki hakuri Allah ya jikansu da Rahama ki yi ta musu addu'a haka kowa yake fada, wasu na fadar na gode Allah bana cikin gidan ni ma da yanzu gawace, sai dai Allah yayi ba zan mutu a gobarar ba, babu rabon shan wahala shiyasa ban kwana a gidan ba. Alhamdullahi nake ta maimaitawa a zuciyata, ba dan ina jindadi ni na rayu su sun mutu ba, sai dan ya wajaba na godewa Allah kuma na bukaci daukinsa a cikin tsanani da walwala a cikin kunci da bakinciki, a cikin farinciki ko kishiyarsa. Bana iya cin komai bana iya amsa gaisuwar kowa idan aka yi min, sai dai na bi kowa da ido. Masu fadar kyawawan hallayar Baba suna ta fada, masu fadar ta Hana ma suna ta fada. Babu zancen da ya dauki hankali kamar wanda Anty Larai take fadar Baba Kabiru yace a daki daya aka same su, kuma hannayensu a daure dukansu. “Wannan abu yana da daure kai, Allah kadai ya san yadda wannan abun yake” “Ni ma abun ya ba ni mamaki matuka kam, wata kila gorar ce ta saka suka boya a daki daya, to amman kuma waya daure musu hannayen?” “Shi ne fa abun mamaki, Allah kadai ya san yadda wannan abun yake” Haka suke ta juya zancen, Wallahi ban san lokacin da na kwarara ihu ba na fashe da kuka mai karfi, domin na san ni na janyo komai, wata kila sai da aka kashe su sannan aka saka wutar saboda a batar da sawun, wata kila kuma dauresu aka yi aka bar su a gurin har wutar da cinye da su. Ga dukan alamu saka wuyar aka yi ba tashi tayi ba da kanta ba, domin na ji sun fada ko da aka yi abun babu wutar nepa a unguwar balle ace ita ce sanadi. Na san iya juyawar da za'ayi a juyo ba zai wuce Abdull ba, shi ya aika a yi komai saboda asirin abun da ya aikata ya rufe, wata kila recording din da na yi ne ya daga masa hankali yana gudun tonuwar asirinsa. Daman Baba yana fadar cewar ni ba alheri ba ce a gareshi ashe ma ni zan zama sanadin mutuwarsa da ta kanwata, bayan na zama sanadin lalacewar rayuwarta. Baba yayi gaskiya babu alheri a tare da ni, wannan ya fi komai saka ni a kunci da damuwa. A lokacin da Safeena ta zo mana gaisuwa tare da yan'uwan mijinta wadanda suka kasance step daughters ga Mama da Hajiyarsu wato abokiyar zaman Mama sai na ji kiyayyar mijinta ya kara fadada a kirjina, gashi na rasa wayar balle na kwatarwa kanwata yancinta ko da kuwa bata numfashi. Duk wani motsi da zan yi yana idon Safeena a yadda take kallona sai na lura kamar akwai magana a bakinta, daman ai ba zata rasa abun fada ba, domin tana cikin tashin hankalin barazanar da na yi mata. “Sannu Noor Allah ya musu rahama, ya kyautata na mu zuwan” Ban amsa mata ba sai kanen mama ne suka amsa mata saboda bata da kunya har tambayar take wai ance ba a fita da komai ba “Komai fa ba a fita da shi ba, ita dai Noor Allah be yi kwananta zai kare ba, shiyasa ta kwana gidanmu, ita bata kwana a can ba” “Allah sarki Allah ya bada hakuri” Daga haka bata sake cewa komai ba kuma bata fasa kallona har suka tafi. Da dare yayi Mama na shirin tafiya ta shiga daki sai na bi bayanta na fara fada mata abun da ke raina. “Mama ganin nake kamar Abdull ne ya saka aka kashe su Baba kuma aka saka wutar saboda ace gobara ce” Mama ta yi shiru na dakiku kamin ta ce. “Ni ma jikina ya ba ni haka, ashe mahaifinku ya ji zancen fyaden nan? Har ya saka maganar a kotun” “Shi na je na fada miki ban same ki ba, kuma Baba ya kira yayi min fada yace na dawo gida” “Na samu labarin bayan kin tafi, kuma na kira wayarki baki daga ba, daga baya kuma sai na ji wayar a kashe, ashe gida kika tafi” “Eh, saboda na ji raina ya bace ne sakamakin karbe wayar da Abdull yayi, na ji tsoron fadan da Baba zai yi min shiyasa ban koma gidan ba” Mama ta zauna gefen gadon dake dakin. “Ta ya Abdull ya karbe wayar? Ina kika ganshi?” Ni ma na zauna sannan na labarta mata abun da ya faru tare da kudirina. Dauke ni ta yi da mari ta rufe ni da duka. “Sakaryar yarinya shashasha, mahaukaciya, dabam da bata san ta tsaya ta yi tunani ba kamin ta aikata abu, ta ina zaki je ki yi recording din matarsa saboda kina mahaukaciya kuma ki yi nasa? Ke lauya ce da zaki yi amfani da wannan a matsayin shaida ko kuma yar daba ce ke da zaki riki hakan a matsayin garkuwa? Me yasa baki tunani kamin ki aikata abu? Mutumen da ya ci zarafin yar'uwarki ya keta haddinta shi zaki shiga motarsa har ki saurare shi? Har abada ba zaki gyaru ba Noor ke dai kam har abada ba zaki taba hankali ba, mahaukaciya sha sha sha...” Ta karasa fadan da kuka Mama Aisha na rike da hannayenta tana tare dukan da take min, a lokacin da na yi zurfi a cikin nawa kukan, na zube kasa na rarrafa na boya a bayan kofar dakin na takure guri daya, ina jin kaina cikin kuncin marar misaltuwa. Mama ta yi gaskiya ni shashasha ce, kuma bana da tunani wannan ma gaskiya ne domin gashi na janyo mutuwar mahaifina da kanwata da Umma da bata ji ba ba ta gani ba. Duk yadda aka so na fito daga bayan kofar sai na ji, domin na fi jin sanyi a gurin, a bayan kofar na kwana har safe kamar wata marar gata, hakan ya ba ni damar tausayawa kaina. Washe gari Sallah asuba ce kadai ta fitar da ni daga gurin, shi ma ina gamawa na dawo na zauna a gurin na takure ina jin tsanar kaina, meyasa na aikata haka? Me yasa ban yi tunani ba? Me yasa ma na roko Hana ta zo gurina from first plate? Wata kila da yanzu tana raye bata mutu ba. Ranar wuni na uku na zama kamar mahaukaciya ina ta tsoron mutane, gashi sai dorawa kaina laifi nake. Bayan an yi musu addu'a ne mijin Mama ya saka aka kira ni, domin yace ni ce kadai be gani ba gurin gaisuwar, na fito ina rike da hannun Mama Aisha sai kallon mutane nake ina jin tsoro, gani nake kamar wani zai ce saboda ni Baba da Hana suka rasu. A wajen motarsa muka same shi yana zaune daga baya ya bude kofar motar yana jiran fitowata. Na risina a gurin jikina na bari gaba daya a tsorace nake. “Noor” Na kalleshi da sauri ba tare da na amsa ba, daman kuma ba zan iya amsawar ba. “Ya hakuri...” Na daga mishi kai hawaye shar kamar saukar ruwan sama. “Ki yi hakuri kin ji, duk mai rai mamaci ne, kuma kowa baya wuce lokacinsa” Nan ma dai kai kawai na iya daga masa. “Kuma na ji abun da ya faru, ma samu labarin a daren da Allah ya karbi rayuwar mahaifinki, domin na dawo gida sai na tararda sammaci daga gareshi, wai yana karata saboda ďana ya keta haddin yarsa, ba zan boye miki ba na ji haushi sosai na yi mamaki kuma na yi bakinciki, ashe Allah yayi ba za a tsaya shari'ar ba, ba ni da tabbacin abun da yake zargin Abdullahi da shi...” Yayi shiru na dan dakiku sannan ya cigaba. “Zan cika zan iya iya kokarina na gane gaskiya, idan har ta tabbatar Abdullahi ya aikata abun da ake zarginsa, to ina baki tabbacin zan hukunta shi, domin ya zalince ki ya zalinci yar'uwarki, zan zame miki uba Noor zaki same ni mai kaunarki kamar mahaifinki, sai dai ina son na fada miki ki aje sirrin nan a cikinki domin bayyanarsa zai rusa abubuwa da yawa ciki, hakan kuma ba yana nufin zan bar maganar ba zan yi abun da ya dace In shaa Allahu” “Shi ya kashe min Babana Abdull ne silar mutuwarsu, shi ya saka a kona gidan saboda na yi recording muryarsa yana fadar abun da ya aikata, kuma yayi hakan saboda kar kowa ya san abun da ya aikata” Ina maganar ina hakki sai ya kura min ido yana kallona kamar mai nazari. “Ki shiga ciki, ki samu natsuwa” Na mike tsaye na nufi gurin da Mama Aisha take tsaye tana jirana, domin na fahimci ba da gaske yake ba daman ta ya zai hukunta dansa. I'm such a fool again. Na kama hannunta na rike muka shiga cikin gidan, wannan karon na samu zama akam tabarmar da aka shimfida ina kallon Mama dake rusar kuka, ni da ita duk mun fahimci Hana da Baba sun yi tafiyar da Baba dawowa. “Na yafe ma yata duk abun da yake tsakanina da ita, Allah ka yafe mata, ka isar mata, mahaifinku ma na yafe masa duk wani abun da yayi min, Allah ya jikansa da rahama” Wani kukan be tashi ba sai da Yaya Nabil yayi mana saukar bazata, rirrike shi na yi ina karkarwa saboda kuka, shi ma kukan yake Mama haka, kusan sai da muka saka kowa kuka a gidan. Duk wanda zai ji mutuwar Hana be kai ni ba, domin muna tare da juna ni da ita a koda yaushe she's been with me for my life. A tare muka tafi da Mama a family house dinsu, duk yadda Anty Larai ta so a bar mata da ni Mama bata yarda ba. Domin yanzu mu biyu kawai muka rage mata, daga ni sai Yaya. A dakin empty room din Yayanta muka tare har ita, ita da Yaya suka raya dare da hirar Hana da Baba ni kuma na raya shi da kuka da nadama. Washe gari na yi yaki sosai kamin na samu kai abu a cikina. Ina shan furar ina jin Yaya yana hirar Kareem ne ya siya masa masa ticket din jirgi saboda ya zo ya yi gaisuwa. Mama na ta saka masa albarka. Dakin yayi kamar zai kama a lokacin da Yaya ya samu labarin abun da ya faru, har fadar yake Wallahi da zai ga Abdull sai ya kashe shi sai dai shi ma a kai shi gidan yari. “Haka Allah ya kaddara, ni yanzu ko sunan yaron bana son ji, shiyasa na ce ba zan koma gidan Ubansa ba, babu wanda ya fi mu ku yanzu” Duk hirar da suke bakina a rufe yake gum bana furta komai sai kallonsu nake idan hawaye suka zubo min sai na share. Da yamma Zafeer ya zo min gaisuwa ina cikin dakin ya shigo yayi ma Mama gaisuwa sannan ya dube ni ya ce. “Noor ya hakuri?” Kallonsa kawai nake kai kace bana jin yaren da yake magana da ni. “Ai ita bata uhm bata uhm uhm, tun da aka yi rasuwar nan bata iya amsa gaisuwar kowa” “Ki yi hakuri kowa yana da tabon mutuwa, kuma idan lokaci yayi ba a tsayawa Allah ya musu rahama ki yi ta musu addu'a kin ji?” Na daga mishi kai sai ya mike tsaye yana kallona cike da tausayi da damuwa ya fice, Yaya Nabil ya tashi ya bi bayansa, Yaya Nabil ya dawo mana da tsaraba mai yawa buhun shimkafa uku da cefa ne da kudi 100k daga Zafeer, Mama ta karba tana ta yaba masa da yana hallayensa... Daidaikum mutane suna ta zuwa mana gaisuwa bayan an watse sadakan uku ciki har da manema auren Hana. Sai dai duk wannan ban ji daga Kareem ba har na tsawon kwana biyar, wata kila ya hakura da ni ne kamar yadda na fada masa, but no matter what ai mutuwa ta fi gaban wasa ya kamata yayi min gaisuwa ko fa yake na ji Yaya dake shirye shirye komawa a yau yana zancen Kareem ba shi da Lafiya har yana fadar Mama ta je ta duba shi. Ranar da Ya Nabil zai bar garin mun kashe adashen kukan da muka zuba, ni da shi da Mama muka yi ta tunanin Hana musamman wacan bankwana da ta yi masa lokacin da zai tafi ashe na karshe ne ko gawarta ba zai sake gani ba. Haka ma Baba ashe ba zai ga karshen karatun dansa ba, kudin da yake kwadayi ashe ba zai ga dansa ya fara rikawa ba. “Amman wai Mama haka za a bar maganar nan shikenan ya tafi a Free?” Ya tambayi abun da yayi fi masa ciwo a yanzu fiye da komai. Ni kaina ba ni da wata damuwa a yanzu kamar Abdull. “To ya za'ayi, babu wata shaida ai, kuma ita wanda za ayi domin ita bata duniyar, wutar ma sai dai mu ce zargi muke domin ba mu da tabbacin komai” Yaya yayi kwafa ya girgiza kai ya cije baki. Kwana biyu da tafiyarsa Mama ta tafi asibiti duba Kareem, bayan ta dawo take ta bada labarin yadda ya rame ciwon ya taba shi sosai. Ni dai ban ce komai ba, domin damuwata yanzu ta ishe ni riga da wando bana bukatar damuwa ko tunanin kowa a yanzu. The following day kanensa Aaryam ya zo family house dinmu, ban san wanda ya kwakwanta masa ba domin be san gurin ba. Sai da yayi min gaisuwa sannan ya isar min da gaisuwar Kareem kuma ya fada min ba shi da lafiya sosai jibi za a fitar da shi waje domin yi masa aiki. Ban san miyasa ba, na ji ina bukatar ganinsa duk kuwa da ina jin kamar be cancanci haka ba. “A wane daki yake?” Na samu kaina da tambaya, wata kila na je duba shi domin ina gudun kar shi sai ya mutu na dawo nadamar rashin duba shi kamar yadda nake nadamar abubuwa da yawa a yanzu. Sai da Aaryam ya tafi sannan na koma cikin gidan na fadawa Mama ina son zan tafi na duba Kareem ance jikinsa da tsanani sosai. “Karki ce ke kadai, ku tafi tare da Asma'u” “Toh” Na fita na nufi bangaren su Asma'u wacce ta kasance Cousin dita, sai dai ban same ta bangarensu mahaifinyarta ta fada min bata gidan ta fita, ban damuwa da na koma na nemi wani dan rakiyar ba na kama hanya ni kadai. Ba asibitin na nufa kai tsaye ba, zango na yada a unguwarmu ma shiga gidan da ya zama kofai, domin komai ya kone kurmus. Bakin kofar dakinmu na zauna ina kallon cikin dakin, Hana kawai nake tunawa yadda muke rayuwa a ciki, da kuma ganina da ita na karshe na fita na barta tana rashin lafiya. Umman su Zainab ce ta shigo gidan ta fitar da ni tana ta ba ni hakuri har da addu'a take min tana tofa min a kai. A gidanta na zauna har sai da na samu sakewar zuciya sannan na fita daga unguwar na nufi asibitin da Kareem yake aiki kuma yake ciki. KAREEM POV. Yana ganinta sai ya ji kamar an zare masa ciwon dake kirjinsa, kusan daman ita ce energy sa a yanzu, da kuzari ya yunkura ya tashi daga kwance da yake yana kallonta, be tsammaci zuwanta ba ko da kuwa ace yana gangar mutuwa ne. “Noor shigo mana” Ta kalli Kareem sannan ta kalli Hajiya Hassana dake tsaye tana kankare masa kwai, ta maida kanta kasa ba tare da ta shigo cikin ba kamar yadda ya bukata. “Wannan Hajiyar mu ce, mahaifiyarmu karki ji komai shigo” Hajiya Hassana ta juya ta kalleta ganin ta tsane kanta gurin kofar kamar mai tsoron mutane. “Shigo yarinya ni fita zan yi yanzu nan” Ta aje kwan da bata gama barewa ba ta nufi kofa, sai a lokacin Noor ta kauce daga jikin kofar kuma ta gaisheta. “Lafiya Kalau, sannu” Hajiya Hassana ta fice daga dakin ta ja musu kofa duk kuwa da bata san wacece ba a gunsa. Noor ta tsaya a jikin kofar yatsun hannunta sarke da juna, fatar idonta da fuskarta kawai ya kalla ya fahimci irin kukan da ta sha, ta rame kamar ba ita ba ta zama so innocent. Ji yayi kamar ace yana da iko da damar da zai sakata a kirjinsa ya rarrasheta da kalamai masu dadi, ina ma ace idan yayi mata alkawarin farinciki zata yarda da shi, ta ina zai fara rarrashin rabin rayuwarsa macen da ta hana shi ganin kyaun sauran matan duniya. “Shigo ki zauna ko na taso ne Noor?” Ta dago ta kalleshi da raunannin idanuwanta a take ya ji kamar ba shi da wani gata a duniya sama da ita. “Daman na zo dubaka ne” Tana maganar tana hawaye “Baki son mu tattauna akan rayuwa? Wata kila idan aka tafi da ni aikin nan ba zaki sake ganina ba, shigo ki zauna Noor” Ta fara takowa ta isa gurin kujerar dake facing din gadonsa ta zauna. “Ya kike?” Ta share hawayenta. “Lafiya kalau” “No ya kike?” Ta dago ta kalleshi sai kawai ta fashe da kuka, rumtse ido yayi yana yawo da kansa a lokacin da sautin kukanta ke sauka kunnuwansa, be taba jin tausayinta a irin wannan karon ba, be taba kewa da kaunarta irin na yau ba, kamar ana cire kunnuwansa da zuciyarsa haka yake jin kukanta na kona masa rai. “Na ji fiye da yadda ka ji a lokacin da ka rasa mahaifiyarka Kareem, na rasa miji na rasa uba na rasa kanwata saboda sakarcina da sha sha shanci” Ya bude idon ya kalleta “Babu laifinki a mutuwar kowa cikinsu” “Akwai ni na aikata abun da ya zama silar mutuwarsu” “Me ya faru Noor dita fada min me kika yi” Ya cika da mamaki a lokacin da ta fada masa abun da ta aikata tana kuka. “Me yasa haka Noor?” “Because i was so stupid, ni sakarya ce ai daman bana tunani irin na mutane, bana ganin dacewa da rashin dacewar komai sai bayan na aikata, bana da tunani irin na mutane ni mahaukaciya ce kawai mai tarin shashanci” Ya kara jin tausayinta ya rufe shi, zaunawa yayi da kyau yana kallonta, kaunarta ma figarsa. “Kina da hankali da tunani irin na mutane Noor, zuciyarki da kwakwalwarki masu kyau ne, ke kawai mafita kike nema kokarin kare kanki da iyalanki kike, irinki kadan ne a duniyar nan, idan har abun da kike zargi ya tabbata to akasi ne aka samu a lokacin da kike kokarin neman mafita” Ya sauke numfashi a hankali yana kallon yadda hawaye sauko mata ta daga kanta tana kallonsa irin kallon nan mai cike da tsoro da fargaba. “Rayuwa bata da sauki Kareem, abubuwa da yawa basa nufin samuwa, burika da yawa basa cika, kaddara ta zama babi babi, idan wata ta rufe kofa sai wata sabuwar ta bude, farinciki ya zame min kamar lu'u lu'u mai wuyar samu” Ta yi murmushi mai kone zuciya. “Me yasa duk nake fada maka wannan? Kai ma kana cikin mutane da suka jefa ni a matsala, wata kila da Safeena bata samu labarin cire cikin ba, da duk haka be faru ba, da bata zuga Baba ya kai maganar kotu ba, da yanzu Hana tana raye” “Ban fada mata komai ba Noor, Safeena shu'umar mace ce da zan iya kira da mummunar kaddara, Wallahi ban fada mata komai ba, idan har zan fadi sirrin wani, to sirrin wani zan fada ba na ki ba Noor, ta hanyar Nurse din da ta yi mata wanki ciki ta samu labari, a ranar da kika ji muryarta a wayata na je na same ta mun yi magana kuma ta fada min yadda ta tsara komai, amman baki saurare ni ba Noor shiyasa baki fahimce ni ba, bana da wata alaka da Safeena, zuwan da na yi ma domin ke ne” Ya hade wani abu da ya tsaya masa a wuya. “Na yi nufin baki farinciki Noor, na yi nufin maye miki gurbin abubuwa da yawa da kika rasa you're my only hope, ke ce cutata kuma ke ce magani, amman ba zan samu damar haka ba, domin na yi making mistake da zai yi ta hurting dina for the rest of my life, shiyasa duk abun da Allah yace kar a aikata a cikin hanin akwai alheri da nasara” Ya lumshe ido. “Ko yaushe zan huta ni? Ko yaushe zan samu salama na samu kwanciyar hankali? Yaushe damuwa zata bar ni? Ina jin tsoron duniyar nan mai fadi Kareem” Ya kalleta idanuwansa cike da kaunarta. “Nan gaba kadan Noor idan kin kwantar da hankali kin fahimce ni, kuma idan Allah ya ba ni aron domin ina tsakanin mutuwa da rayuwa ne a yanzu” Me yake damunka Kareem?” Ta tambaya tana share hawayenta. “Tun a lokacin da na yi hadarin a baya, kirjina ya bugu amman ban dauka zai zo da matsala ba, shiyasa ban zafafa a gurin bincikar gurin ba, sai kawai na cigaba da harkokina, na kan ji yana min ciwo wani lokacin amman ba kamar yanzu ba, idan zan tashi sai na yi daker, ranar da muka yi waya dake na karshe a ranar na fadi, aka kawo ni asibitin nan ban san an zo ba, zuciyata ta yi kasa ta bar muhallinta dole sai an yi min aiki, aiki ne mai matukar hatsari wata kila na rayu wata kila kuma ba zan rayu ba” Ta sauko daga kan kujerar ta zube kasan guiwoyinta ta kama gadon ta rike tana kallon fuskarsa, duk yadda take tausayin kanta take cikin damuwa sai ta ji kamar ta Kareem ta dara tata. Shi ma kallonta yake yana jin tausayinta fiye da kullum ta shiga taskon rayuwa ta fuskanci kalubale tun tana karama har yanzu, a zuciyarsa yake ayyana yadda take ji a nata zuciyar, a yanzu bata da kowa sai Mamanta sai Nabil su kuma ba za su iya samar mata gatan da yake jin zai iya samar mata ba. “Zaka rayu Kareem, zaka rayu ko dan ni da yaranka we need you” Ta kwantar da kanta saman gadon hawaye na sauko mata, Kareem ya kai hannu kamar ya shafa fuskarta sai kuma ita din ba halalinsa ba ce a yanzu. Jimke hannun yayi ya kwanto da kansa saman fuskarta tazara kadan ya bari a tsakanin fuskarsa da nata, lumshe ido yayi yana maida numfashi a hankali kamar yadda take yi, hawayenta na sauka a jikin gadon na idonsa kuma suna sauka a fuskarta. Dif dif dif ta ji wasu ruwa masu dumi suna jika gefen fuskarta, har suka gangaro suka hade da nata hawayen suka sauka a kan gadon. Bude ido ta yi ta dago kadan ta kalleshi sai ga ta fuskarsa so cool very calm and innocent kamar ba daga idonsa hawayen suke fita ba. “Kuka Kareem...” “Ina sonki Noor, ina son rayuwa da ke, ina kewar mahaifiyata ina son na rayu da Yayana, ina kewar abokina ina jin rashin abubuwa da yawa I'm hopeless now... Every one is lonely sometime” Ya furta ba tare da ya bude idon, kamin ya kai hannunsa ya share hawaye da be isa ya hana su zuba ba. Ba shi kadai ba kusan duk namiji da zai zubar da hawaye kuma ya bari a ga hawayensa tabbas yana cikin tsanani damuwa ko bukatar da abun da zuciyarsa take so. Ya bude idon ya kalleta yana maida numfashi a tare da ita zuciyarsa da nata suna bugawa at the same time something very deep inside their heart ya saka zuciyoyinsu nauyi. “Idan wani ya sake nuna miki yatsa, Noor ki kaddara bana raye, idan wani ko wata ya saka ki zubar da hawaye i will show him the other side of me, as long as you're with me you're not alone and you will never be, you're not alone we're family. Ki fadawa Mama da duk wanda ya kamata ya sani, anjima Babana zai zo tare da Aaryam za ku tafi gurin DSS za'ayi yarjeje ni tsakanin ke fa Safeena da kuma ke da Abdull cewar idan wani abu ya same ki su ne” “Why?” “Duk wanda zai kona gidanku gaba daya, to rayuwarki yake nema ba ta iyayenki ba, an kashe su ko kuma an kone saboda tunanin ke ma kina ciki, kuma bana raba dayan biyu Abdull ko matarsa” “Na fi zargin Abdull saboda case din gaba daya akansa ne, kuma shi ya karbe min wayar ai” “Safeena ma zata iya, zuciyarta bata da kyau kuma ta san yadda nake sonki, a fada mata idan har zan sake yin aure a rayuwata to mace daya zan aura kuma ke ce Noor, idan har ban same ki ba, ba zan sake aure a rayuwata na hakura, idan ma na rayu hakan kuma ba zai hana na yi miki fatan auren wanda kike so ba kuma zai rike ki amana Noor ina son farincikinki a duk halin da zaki samu kanki i love you unconditionally, i never knew it could be so much, ina rokon Allah ya ba ni aron rayuwa i will spend every hour of every day keeping you safe, you're my favorite girl, na san wata rana zaki tuna da ni zaki so ni, sai dai babu tabbacin ina raye, but i will wait to capture your love, i will not give up” Ta baki yake furta kalaman amman ta ido yake zuba mata su, ta kasa dauke idonta akan nashi, zuciyarsa ba isarwa na ta zuciyar da sakonsa, sanyin jikin daga numfashinsa ya fito ya shiga nasa sai ya saukar mata da natsuwa da take jin da kamar ta rasa. Kalamansa sun yi nasara gaskiyarsa ta yi tasirin sanyaya zuciyarta a yanzu kwakwalwar ta bude zuciyarta ta karbi sakonsa. “Zan aure ka Kareem!! Ka tafi jinyar zaka same ni a yadda kake son na kasance, zan aure ka kuma na maka alkawari zan rike ďan da ka haifa da Safeena i will save you, i will make your life complete 100%, dan Allah Kareem na roke ka cutar da ni please don't let me down...” Mafarki yake? Gaskiya ne? Ko dai suma yayi? Kuma tsananin kaunar Noor ta fara saka masa abubuwa ne? Ko dai yayi losing mind dinsa ne? Zan aure ka Kareem!! Zan aure ka Kareem!! Zan aure ka Kareem!! Haka yake ta jin sautin muryata mai dadin sauraro da taushi a kunnesa. Kallonta yake kamar be fahimci yarenta. Mikewa ta yi tsaye sakamakom shigowar da kanwarsa Khadija ta yi ba tare da sake furta masa komai ba ta fice daga dakin. Ya kasa motsi ya kasa numfashi ya kasa yarda idonsa na ne kawai suke kanta har ta fice, Khadija ta juyo ta kalli kofar da Noor ta rufe ta kalli Yayanta dake kallon kofar ta sake duban kofar ta dube shi har lokacin kofar yake kallo. “Big Bro...” Ta tara masa hannunta tana motsa domin gani idan ya san abun da yake. Sai ya lumshe ido ya koma ya kwanta a hankali numfashi ya dawo da karfi kamar zai fasa huhunsa zuciyarsa ta buga da karfi ya jimke hannunsa yana sauraren sauti daya na Noor Zan aure ka Kareem!! A yau kalaminta ya fi na kullum dadi, muryarta da fi ta kullum zaki. NOOR POV. Na aminta har a zuciyata na ji cewar zan iya auren Kareem a yanzu, i was afraid to lose him, a broken heart ce ta rage min yanzu, and i need someone who can fix it ba wanda zai saka broken heart dina into piece ba. And if Safeena zata min duk wannan saboda Kareem to akwai bukatar na aure shi saboda ta fahimci ni na ci gasan. If Kareem zai bata lokaci kudinsa wajen ba ni kariya ko farinciki, to ya kamata na ba shi abun da yake so a gareni in har zan iya kuma ba tsabawa addini ba. I saw my future in his eyes. Mun fara da kamar abota ne when we fell in love not knowing what it was. A yanzu dai yana fahimtata ina ji kamar zai iya rike ni. Ina tafe ina tunani kala kala har na iso gida, na ga bakuwar mota a kofar gidanmu ban kawo tunanin kowa ba, na shiga dakin Mama sai na samu mijinta a ciki tare da Yayanta suna magana. Waje na fito na zauna ina ji zazzabi zai rufe ni jikina yayi zafi ga ciwon kai da ya rufe idona, zuciyata na daukar abubuwan da suka fi karfinta. Wani karamin cousin dina ya ce ana kirana a waje. “Waye?” “Ban sani ba, da mota ya zo yana waje dai” “To je ka ce ina zuwa” Na fada masa ma my mind was telling me Aaryam ne ya zo daukata kamar yadda Kareem ya fada, wata kila kuma ya turo shi ne ya fada ma Mama da kansa, ko kuma ya zo daukar mu ne gashi kuma ban fadawa Mama ba domin na same ta da baki, haka dai nake ta sake sake, gudun barinsa a waje ya saka na fita domin sanar masa cewar ban riga na fadawa Mama ba ya dan jira su kare magana tukuna. Zatona ya sha banban da abun da na gani, idanuwa suka yi arba da abun da zuciyata ta dade tana kauna, rashin tsammanin dawowarsa ya haddasa min faduwar gaba. Na taka na isa gurin da yake tsaye na rumgume hannayena kaina a kasa. “Baby Noor” Sai da ya rufe ido na bude a lokacin da ya furta min sunan da yake kira na da shi a lokacin da muke abokan rayuwa. Ya matso kusa da ni, matsawowarsa ya masar d bugun zuciyata towards him. “Ya kike ya hakuri ya gida ya Mama ya kowa?” “Kowa lafiya kalau” Na kasa daga ido na dube shi, kunya da nauyinsa sun baibaiye ni. Ya saka hannunaa daya a aljihu yana kallon unguwarmu. “Kawai dai na zo na duba ki ne, ina fatar babu wata matsala” Na girgiza kai na amsa murya can kasa. “Babu” Mun dauki tsawon lokaci a haka be sake magana ba ni ma ban sake cewa komai ba. Can kuma sai na ji ya kira sunana. “Noor” “Na'am” Na amsa jikina na karkarwa. “Daga ki kalleni mana, ko dai har yanzu tsanata kike?” Na girgiza kai alamar Aa sannan na dago a hankali na kalleshi, shi din dai Zafeer mutumen da Baba ya cilasta min juya masa baya a lokacin da yake tsananin kaunata, ashe har yanzu ina da kimar da zai biyo ni ya tambayi lafiyata, hawaye suka sauko min, shi ma kallona yake idanuwansa da rauni kamar yadda fuskarsa ma ta nuna. “Na zo ne na dubaki, no matter what happen kina cikin raina ina tausayinki” “Na gode, na ba ni abun da ban cancanta ba” “Mu bar abaya ta wuce baby Noor abun da ya wuce ya wuce, mu fuskanci gaba” Na daga mishi kai sai ya sauke ajiyar zuciya. “Zan tafi akwai abun da kike bukata?” “Aa bana bukatar komai” “Take care of your safe, sai na sake zagayowa” Na yi baya baya sai ya bude motarsa ya shiga ni kuma na juya na shiga cikin gidan. A zauren gidan na jingina na lumshe ido ina maida numfashi a hankali, na sani Zafeer ya zo duba ni saboda karfin zuciya irin nasa, ba dan yana nufin dawowa ba, domin ban cancanci haka ba. Kuma na yarda wata soyayyar bata nufin aure, wani auren kuma baya nufin zama. Na dade a gurin dafe da kirjina har sai da na ji na samu salama sannan na share hawayena domin yanzu kuka ya zama abinci na, na shiga cikin gidan, ban shiga bangaren da Mama take ba sai na zauna a dayan bangare da kanenta da yake da Amarya na shiga falonta na kwanta jikin kujera na rufe ido kamar mai bachi. Ban san me suka tattauna ba, Mama ce dai ta shigo ta kawo min wayata da Abdull ya karba tare da sim din da komai a ciki amman babu recording din an goge shi har ma da wanda na yi ma Safeena. Kiran da na ga ya fi yawa a wayata har an hada da sako na mayar domin jin dalilin kiran da kuma sakon da aka turo min _ki kira ni_ Ina kira sai ya daga muka gaisa ya gabatar min da kansa. “Sunana Alhaji Sule unguwa Uku” Har lokacin ban fahimci waye ba har sai da ya fada min shi ne wanda ya karbi number kwanan baya ina hanya. “Na kira sai wani ya daga, yace kar na sake kira wai ke matar aure ce” Na dan yi murmushi na san Kareem zai aikata abun da ya fi wannan ma. “Amman zuciyata bata aminta ba, domin matar aure ba zata yi irin shigar da kika yi ba, wata kila dai shi ma yana cikin masu neman auren ne kamar yadda ni ma zan shigo yanzu, shiyasa ban yi kasa a guiwa ba na sake kira tana ringing ba a dagawa daga baya wani lokacin kuma sai na jita a kashe” “Eh wayar tana hannun Yayana ne” “Yayanki ko saurayinki? Ko dai karbe abarsa yayi saboda shi ya siya?” “Aa yanzu ta dawo hannuna ai” “Hakan yayi kyau, ya kamata na shigo mu gaisa ko ba haka ba? Mu fahimci juna kuma tattauna abun da ya kamata, ba mu san abun da Allah zai yi ba, ni dai na ga abun da ke min” Na cire wayar a kunne na kalli screen na sake mayarwa, ashe dai uban Aisha nan haka yake da son zuciya shiyasa ita ma take da son zuciyar ta hana ni zaman lafiya a gidan Hafiz. Idan ba son zuciyata ba ta ina zai kalli mace kamar ni yace wai na masa, yarsa Aisha ma yayata ce ta uku balle kuma ni. “Ba yanzu ba gaskiya sai nan gaba” “Saboda me baki son na san gidanku ne? Ni fa da gaske nake babu alamar wasa” “Yanzu ba gida nake ba, yanzu ina family house din mahaifiyata ne saboda Babana ya rasu tare da kanwata” Ya tausaya min sosai yayi min gaisuwa sannan ya fada min zai zo yayi gaisuwa gurin Mama da ni. Na amsa masa da okay ne kawai dan babu yadda na iya, amman na kudiri aniyar idan ya zo zan fada masa gaskiya cewar ni ina da wanda zan aura wato Kareem... Minti goma da kare waya da shi airtime na 10k ya shigo wayata... Alhamdullahi Allah ya maimaita mana. 🤲     ***     ***     ***    ***    ***   ***   ***    *** Sauka na yi daga kan kujerar na zauna kasa ina kallon Kareem dake shigowa bayan na Alhaji Sule unguwa uku ya sauka. Tun kamin na amsa wayar na samu kaina da murmushi. “Hello” “My heart beat, my life, my happiness...” Ya fada murya can kasa kamar mai gudun wani ya ji. -Uhm hmm- “Kawai na kira ne na fada miki ina kaunarki” Na yi murmushi ina shafa fuskata. “I love you so much, my Beb my one and only” “Hey... Ya isa haka” “Be isa ba, i love you i love you i love you i miss you i need you, Noor jin nake kamar ba ke ba ce a yau, gani nake kamar ranar yau mafarki ce, after this fever i will survive komai zai zama kalau” “Haha” Na yi dariya. “Amsa min mana ki ce min ke ce Noor maybe zan yarda” “Ni ce Noor noor ta Kareem” Na fada ne da zolaya sai na ji ya sauke ajiyar zuciya yayi shiru na wasu dakiku sannan ya ce. “Noor da kin san yadda nake son ki a zuciyata wata kila da kin tsorata, ina masifar sonki Noor, irin son da ban taba mafarki ba” Na yi shiru kamar wadda ta rasa abun fada, ajiyar zuciya na ji ya sake saukewa. “Ta ya wayarki ta dawo hannunki? Kawai na rike number ki ne ina kallo sai kuma na gwada kira ashe zai shiga” “Mama ta shigo ta kawo min, na dawo na tarar da mahaifin dare da Kawuna da Mama ban san me suke magana ba, kawai Mama ta shigo ta ba ni wayar” “Okay, zan aiko a karbe ta a canja miki wata, ina son zuciyata ta natsu kina cikin aminci Noor” “Okay” “I love you” Ya furta sannan ya kashe wayar, na mike tsaye na fice daga falon na shiga bangaren da Mama take, kamin na shiga dakinta Kareem ya sake kiran wayar. “Hello” “Noor, na ce tun da kin amince da ni me zai hana a daura mana aure kamin na tafi?” Na yi baya baya na fasa shiga dakin Mama juyo ina rufe baki. “Kareem yayi wuri ai, kwana biyu ya rage ka tafi fa, ni kuma ban fadawa kowa ba, babu wanda ya san da alakarmu” “Zan aiko neman aurenki ne, albashin idan suka zo sai su sanar cewar sun zo ba tare da izininki ba” “Aa ka bari sai ka dawo Kareem” “Noor what if ban dawo ba fa? Ina tsoron kar ki canja shawara kamin na dawo, ina tsoron rasaki Noor” “If we mean to be zaka samu sauki zaka dawo Kareem, kaddara ce ta hada mu ai ka fada” “Noor ina tsoron rasa ki” “Ta ya? Babu kowa a gabana yanzu sai kai Kareem” “Na gode da kika sanar min wannan, thank you anjima Aaryam zai zo ya dauke ki, ki sanar da Mama” “Okay” Sai da ya sake fada min yana kaunata sannan ya kashe wayar, ni kuma na juya na sake komawa bangaren na shiga dakin Mama, babu kalar tambayar da ban yi mata ba akan zuwan mahaifin Abdull da kuma yadda aka yi ya ba ni wayata amman Mama bata amsa min tambaya ko daya ba. Daga karshe sai na sanar mata Kareem yace zai aiko kanensa ya dauke mu domin yin sharadi a gurin DSS. Jimm Mama ta yi da alama hakan kamar be mata dadi ba, sai dai bata ce min komai ba, cewar na tafi ko kar na tafi, kuma bata amsa da cewar zata tafi tare da ni ko akasin haka ba. “Mama baki ce komai ba” “Noor ki yi taka tsantsan da yaron nan, ba zan yanke alakarku kai tsaye ba, amman dai ki yi taka tsantsan da shi, izuwa yanzu ya kamata ace kin dauki darasin rayuwa, auren biyu kenan kika yi da kurciyarki da kananen shekarunki, duk yadda zai zubar da mutuncinki ko nawa to ki yi kokarin tsare shi, kin ga a yanzu hannuna kike mahaifinki baya raya dawainiyarki da tarbiyarki a kaina take, bana fatan ki aikata wani abun ko wani abun ya same ki da za a furt cewar ke yar mace ce” “In Shaa Allahu Mama zan kiyaye” Jikina yayi sanyi zuciyata na raya min akwai wani abu da Mama ta sani amman bata son fada min. “Mama ko dai na fada masa ba zamu samu damar tafiya ba?” “Aa abun da yake bukatar a aikata abu ne mai kyau, ko da be kawo shawarar ba, ni zan kawo aikawatar da haka saboda tsaron lafiyarki domin gujewa gaba, za mu tafi” Na yi shiru na wani lokaci sannan na daga kai na kalleta. “Mama ko wani abu kika ji akan Kareem ne? Domin mutumen kirki ne” “Ba a gane mutumen kirki a fuska ko a furuci, ba a fuska ake zanawa ba Noor, Abdull ma ba mu yi zaton zai aikata ba sai da muka gani” “Haka ne” Daga wannan ban sake furta komai ba. Da yamma Kareem ya aiko da mota kamar yadda ya fada aka dauke mu ni da Mama da Babban yayanta da kanen mahaifi da mama ta aika masa ya zo jar gida aka tafi tare da shi. Office din DSS aka kai mu kai tsaye, ko da muka isa mun tararda Safeena da mijinta a can a ranar na fara arba da mahaifin Kareem suna kama da Aaryam sosai fiye da Kareem wata kila Kareem din ya fi kama da Mamansu ne. Ban ga alamar maraba a fuskar mahaifinsa ba, zuwansa sai yayi min kama da wanda aka tirsasa ya aikata abun da ba shi da ra'ayin akai, hakan kuma ya saka ni jin wani iri. “To ni me ya shigar da ni cikin lamarinta? Ina ce Abdull ta aura ni miye nawa a ciki da za a zo nan da ni?” Aaryam ya dan tabe baki kadan irin na mai mamaki “Ni ma na yi tunanin haka, but Kareem ya ce da ita za a zo” Abdull ya kalleshi. “Wait Waye ya taramu a nan to? Ni fa d aka aika min da takardar gayyata cewa aka yi mahaifiyar Noor take nema” “An fada maka haka ne kawai, Yayana ne ya taraku a nan saboda a dauki matakin da ya dace” Abdull ya sake daga ido ya kalli Aaryam sannan ya sauke kansa ba tare da ya sake cewa komai. Har aka yi komai aka gama Mama ce take magana da yawuna, wani abun kuma Kawu ya saka baki ko Baba Kamilu. Motar da ta kawo mu ita ta dawo da mu gida. Bayan na shiga gidan Kareem ya kira wayata ya ce na fito waje Aaryam yana tsaye yana jirana. Ban bata lokaci ba na fito sai na same shi a gurin da na bar shi, sabuwar waya ya bude a gaban idona ya karbi ta hannu ya cire sim din ya saka min a sabuwar wayar sannan ya mika min ya tafi da tsohuwar. Rayuwa ta cigaba da tafi min a yadda ubangiji ya tsara min ba a yadda ni na tsara ba, Alhaji Sule unguwa uku ya zo gidanmu yayi min gaisuwa kuma yayi ma Mama da yan gidan ya kawo mana alheri na abinci da kudi, wata matar Kawuna har tsokana ta take wai Noor mai kwashe kwashe, iyakaci murmushi bana cewa komai amman ni na san ba aurensa zan yi ba. Wannan ya saka ban yi kasa a guiwa ba zuwansa na biyu na fada masa cewar akwai wanda yake neman kuma nake saka ran aurensa nan kusa idan Allah ya amince. “Ai ba a san maci tuwo ba sai miya ta kare, ita mace allura ce cikin ruwa mai rabo ka dauka” “Haka ne” Na furta ina gyara mayafina. “Dan haka karki yi saurin yanke hanzarina, ni ma zan gwada sa'ata kuma ko da ban aureki ba ni na ci riba domin na tsaya da ke kuma kin min tarba ta mutumci na jidadin haka” Na yi murmushi na sauke kaina kasa. “Kuma kar haka ya saka ki ji nauyin tambayar wani abu a gurina ko bukatar wani abu, ni ina taimako ma ko a banza balle kuma akwai dalili, daga naira miliyan daya har miliyan dari zan iya kashe miki Khadija kashewa mace kudi ba asara ba ne, musamman macen da kake fatan ta zama Matarka kuma uwar yayanka” Mamaki ya kamani ashe dai su ma tsofi sun iya kalaman soyayya, bawan Allah nan sai kokarin daure ni yake da kalamansa. Sama sama muka yi hira sannan ya dauko leda motar ya aje min a gabana. “Ban gama sanin komai akan sarauniyar ba, amman dai ina fatan abubuwan da na zabo za su burge ki” “Na gode, amman ba zai ka yi min dawainiya ba, bana bukatar komai a yanzu” “Sakamakon rashin bukatar da kike da shi ne ai, bukatar take nemanki ke dai ki bar ni na gina miki sabuwar rayuwa kawai” Na yi murmushi na sunkuya na dauki ledar. “Na gode” “Toh sai mun yi waya, bye bye” Ya dago min hannu ni ma na daga masa. Ina shiga dakin na samu Mama bata ciki sai dariyar da na riko a waje ta subuce min, shi fa dattijon ya dage a bakin gaskiyarsa yaki yake yi ma soyayyarsa a gurin. Kayan tande tande ne da lashe lashe a ledar sai turaruka da bandir din 200 sabi. Na bude ice cream din na fara sha ina lumshe ido sanyi yana kai min har cikin zuciya. Kiran Kareem ne ya shigo wayata sai da na daga na gane ashe video call ne. Na fara isar masa da murmushi sai dai shi tasa fuskar kamar yana cikin damuwa. “Ya kike?” “Lafiya kalau, sad face?” “Me kike sha?” Na daga na nuna masa robar. “Waya kawo?” Na yi shiru ina kallonsa i kNow if i lie zai gane domin ya san ba zan fita na siyawa kaina ice cream ba but me zan ce? Ban gama tunanin amsar da zan ba shi ba na ji ya ce. “Wannan baban Aisha Alhaji Sule unguwa uku nan ba aurenki zai yi ba Noor, matansa hudu kuma yayansa duka manya ne, kuma yadda kike fresh and young me zaki yi d tsoho?” Na yi dariya. “Ni ma na aurensa zan yi ba kuma na fada masa ina da wand nake so fa, shi ne kawai ya nace sai ya ce wai zai gwada sa'arsa” “Bana son na ji ya kara zuwa kofar gidanku nemanki, please ki fada masa kina da wanda zaki aura kuma baya son kina kula kowa” “Okay zan fada masa, amman ka sake fuskarka Kareem ka bata rai” Na fada a shagwabe kamar zan masa kuka. “Any thing for my heart beat” Ya sake fuskar yayi murmushi tare da sumbantar screen din wayar ya shafa shi yana kallona. Mun sha hira sosai irin ta masoya haka muke a kullum baya gajiya da kira bana gajiya da amsawa kamar kar ya bar kasar nan wani irin shakuwa ya shiga tsakaninmu idan ya kir har bana son ya yanke kiran shi ma kamar zai dauke ni ya cinye haka yake min. Daf da zamu yi sallama ya fada min gobe za a shiga da shi aiki, na ji hankalina ya tashi sosai domin ya damu da ciwo wata kila ya wuce yadda nake gani ko tsammanin ma. “Na so na ganki Noor kika ki zuwa mu yi bankwana tun ranar ban sake sakaki ido ba and you know how much i love you” “A matsayina na wa zan tafi? Iyayenka ba su san alakarmu ba, ko da ma sun sani ai da kunya ace ina tafiya ganinka” “Sun sani mana, baki ga mahaifina ba? Kanena ma sun sani duk wanda ke gidanmu yanzu ya sani” “Yanzu dai Allah ya baka Lafiya ya dawo da kai lafiya kuma ya sa ayi aikin cikin nasara” “Ameen ki kula min da kanki please, bana son mazan nan dake kawo miki hari, kin ga ko Ustan din nan ya sake zuwa bayan ganin da na masa ya sauke ki a mota, Noor bana son kina kula kowa, ki rika daukarkanki kamar an daura mana aure” “I will” Ya sakar min ido sosai yana kallona. “Aaryam zai zo ya kawo miki atm ko da zaki bukaci wani abu, bana son ki ji cewar kin rasa wani abu a lokacin da kike tare da ni” “Bana fa bukatar komai Kareem ba sai ya kawo min ba” “Ba ki bukata Alhaji Sule yake kawo miki leda kina karba?” Na zaro ido na juya na kalli gurin d ledar take baya ganinta amman ta ina ga ya ledar har yake fadar haka? Ko dai ya chanka ne kawai, amman fa dazun ya furta cewar Ustas din nan ya zo ta ina ya sani domin ban fada masa ba, amman na san Kareem da wayo wata kila yana son kure ni ne. “Ni baya kawo min leda” “Hmmm na dai fada min kar na sake ganinsa a gurinki” “Gashin shi kake yi daman?” “Makaho ne ni? Ina nan amman duk wani motsinki idona yana kanki, idan kuma ke kika makantar da ni sai na ji” Na kyakkyale da dariya sosai har da tintsirawa. A lokacin da na dago sai na ga kallona yake da murmushinsa mai kyau. “That's my girl, that's the real Noor i know i love you Babe” Na rufe idona ina jin kunya. Shigowar Mama ne ya saka na yi masa sallama na aje wayar. “Wannan kuma minene?” “Wa.. Wannan ne Alhaji nan da yayi muku gaisuwa ya kawo min yau” Mama ta duka ta dauki kudin ta duba. “Noor ina ta jan kunnenki, ki dai ba zaki taba hankali ba? Ga mugun kwadayi ki yi ta zubar da kanki mutunci a gurin maza? A tunanin tara maza wannan ya so gobe wani ya so shi ne soyayya?” “Aa” Na amsa a sanyaye sai ta nufi gurin ajiyarta ta aje kudin kayan zakin kam ko kallonsu bata yi ba ta sake ficewa. Bayan sallah la'asar Alhaji Sule ya sake kiran wayata yana karyar da murya da marairaice gwanin shaushi. “Uhm uhm ni baki kira ni kin ji ko na sauka Lafiya ba, ni na yi fushi zan yi kuka...” Na yatsina fuska ina jin kamar na buga masa robar ice cream din da ya kawo min dan haushi. “Me yasa kake magana haka kamar yaro?” Yayi dariya. “Soyayya ai bata san yaro ba bata san tsoho ba, soyyayya ce kawai domin na lura har yanzu akwai sauran kurciya a tare da ke Babe na” Wani amai na zo ya min da ya kirani da Babe. “Wane irin Baby kuma dan Allah ka daina ni fa na san ba aurena zaka yi ba, kana yara kamar ni da wadanda suka girme ni ma to ta ina zaka aure ni, kuma matanka hudu fa haba” Shiru yayi na lokaci jin na harbo jirginsa, can kuma ya dan yi murmushi kadan. “A ina wannan maganar ta fito Khadija?” “Kasan abun duniya baya boyuwa” “Haka ne, amman dole akwai wanda ya fada miki haka, ko kuma dai gidanku an yi bincike akaina ne?” “Aa ai maganar bata kai gurin iyaye ba balle su yi bincike, ina gida aka fada min yanzu ina son ka amsa min maganar haka ne ko ba haka ba?” “Ba gaskiya ba ne, matana uku ke nake fatan ki zama ta hudu” “Gaskiya ta gun da na ji ba zan za a maka karya ba, domin wanda ya fada min ya Sanka sosai” “Ko dai wani ne yake son shiga tsakaninmu? Fada min mana yan mata na waya fada miki wannan maganar? Wa yake min wannan sheri haka da tsakar rana?” “Aisha...” Na fada kai tsaye ba tare da tunanin komai ba, kuma na yi hakan ne da nufin ya san ta majiya mai karfi na ji kuma ya san alakata da yarsa. “Wace Aisha?” “Aisha yarka matar Magaryi Hafiz” “Ina kika san Aisha?” “Saboda mun auri miji daya ni da ita, ni ce amaryar da Hafiz ya aura kamin ya rasu” “Ahhhhhh.... Ikon Allah da gaske” “Ka tambaye ta ka ji ta san Noor zata fada maka?” “Amman ke kin san ni mahaifin Aisha ne daman?” “Na sani yanzu saboda ta fada min, har abun da ban sani ba” “Khadija kar dai ace yarinyar ta zo ta miki cin mutunci ne” “Hmmmm sai anjima, ni dai na fada maka daman ina da wanda zan aura, Allah ya baka wata” Na kashe wayar ba tare da na saurari abun da zai sake fada ba, kamar zai haukace haka ya fara kiran wayata na ki na daga daga karshe ma sai na saka shi a blacklist. Bayan saukowa daga salla magariba yaro ya shigo kirana, a lokacin ina daga kwance ina chatting da Kareem domin babu damar yin video Mama tana dakin. “Je ka ce waye” “Mama ki ce kawai bana nan ba zai wuce Ustazun nan ba ya zo yayi ta takura min, kuma ai kin ce na daina tsayuwa da maza barkatai, ni da na sani ma ba zan fada masa kofar gidan nan ba” “Ai kya bari mu ji ko waye ko? Ke kin fi son maza yan duniya ko? Su sauran da suke kiranki a waya suna zuwa fada min kike ne?” Na yi shiru na cigaba da chatting din da nake ina murmushi, fada min yake irin rayuwar da zamu idan muka yi aure. “Wai ya ce Zafeer ne...” Na dauke kaina daga screen din wayar na kalli Mama dake kallona. “Zafeer kuma? Tohm...” Mama ta fada ni kuma sai na ce. “Me zan masa?” “Ai sai ki je ki ko? Ki san dai Zafeer ya wuce wulakanci a gurinki, duk mutumen da zai so ka farko kuma ya sake dawowa ba karamin masoyinka ba ne” “Ba fa so nake ba Mama! Abu ne mai wahala Zafeer ya so ni yanzu, bayan duk abun da ya faru” “Ba sonki yake ba zai yi ta zuwa kofar gidanku ne? Ke ni bana son shashanci tashi ko tafi” Na aje wayar na dauki hijab dina na saka na fita da tunanin kalaman Mama, ni kam a nawa haukar da tunanin Zafeer ba zai sake kula mai irin sunana ba balle kuma ni fin kaina. Ashe na yi kuskure fahimta domin shi yana nufin maida hannu a miya ba. Ban tabbatar da sai bayan na gama kwance masa ciki na labarta masa halin da na tsinci kaina a duka auren da na yi, yayi min tambayoyi da dama kuma na amsa masa da gaskiya babu boye komai. “Mutum kamar Abdull be kamata ace yana aiki a kamfanin nan ba ” “Ba lallai ne su sani ba ai, ni ma da be aikata hakan ba ba zan sani ba” “Haka ne, amman za su sani yanzu kamfanin na mahaifin Matata ne, ni da na taba aiki da shi a Lagos din na ga halinsa, yana shigewa mata sosai shiyasa na raya cewar ba zaki iya zama da shi ba, ko ba shi ba ma Noor babu wanda zai iya rike ki sai ni” Na daga ido na kalleshi sai kuma na sauke kai a sanyeyye. Ya gyara tsayuwarsa yana sauke numfashi. “Noor na zo nan ne, saboda wani abu mai muhimmanci” “Wani abun ne ya faru?” “Babu abun da ya faru, a yanzu dai nake fatan faruwarsa tsakanina da ke, hausawa suka ce fa tsohuwar zuma ake magani kuma na yarda, domin na yi yadda zan yi na ga baki fili ki yi iya wasanki, amman na kasa saboda akwai wani abun da Allah yake nufin shiryawa a tsakaninmu, na so ki da farko na yi iya yadda zan iya na ganin na aureki amman ya gagara, amman har yau har gobe bana son kowa yadda nake son ki Noor, na ce zan jira kuma na jira, ina tunanin lokaci yayi da ya kamata ace mun zama ma'aurata ni da ke, burin da muka kasa cin ma a baya wata kila zamu iya cin masa a yanzu, a tsawon lokacin nan ina ta kallon tafiyar rayuwarki ne Noor babu wanda zai fahimce ki ko ya zauna da ke a yadda zan iya, daga Kareem din da yayi kokarin raba ni da ke, har zuwa wanda duk zai ganki ya aureki babu mai iya zama da ke sai ni Noor” Yana maganar jikina ya fara shocking hawaye suka cika idona, ashe ina da kima da daraja a gurin Zafeer har haka? Ashe soyayyata ta kai ya sake dawowa neman aurena duk bayan abun da ya faru? “Baby Noor...” Na daga na kalleshi ta cikin hasken farin wata. “Shim zaki iya aurena a yanzu? A yanzu na shirya ko gobe za a iya daura mana aure, zaki aure ni?” Kallonsa nake hawaye na sauko min. “Ko kuma dai har yanzu wani ya rigani? A yanzu din ma wani zai min kutse kamar yadda aka min a baya? bayan na gina soyayyata? Har yanzu kina jin ba zan iya kula da ke ba Noor? Ina da kudi enough zan baki duk wani jindadi da kuma rayuwar da kike mafarki. Shin zaki aure ni?” Na girgiza masa kai na yi baya baya. “Aa aa ba zan iya ba...” Na juya na shige gida ina hawaye a kofar dakin Mama na tsaya na dafe zuciyata har sai da na samu sa'ida sannan na shiga dakin ba tare da na share hawayen ba. Kan karamar kujerar da nake kwance a dazun na zauna. “Lafiya?” Ta dauki fitilarta ta haska fuskata. “Ba komai kike kuka?” Ban ce mata uffan ba na sakw fita dakin na yi alwala na dawo na gabatar da sallah Isha'i da aka gama tun 8:10pm, sannan na janyo wayata, ashe ban fita daga chatting din da nake da Kareem ba, hoton tsayuwata da Zafeer na gani fitar da na yi dazun nan da magariba. “Zan sake rasaki a karo na uku Noor, na sani indai Zafeer zai dawo ba zaki yarda ki aure ni ba” Shi ne sakon dake biye da hoton. “Ba zan aure shi ba Kareem ba zan iya aurenshi ba” Na rubuta masa a matsayin amsa ashe har a fili na fada, ban hakara ba sai da Mama ta taba ni. “Ke mi ya faru?” Na aje wayar na fuskanceta. “Mama Zafeer sake dawowa wai yana son ya aure ni” Fuskar mamaki Mama ta yi ta zauna kan kujerar dake kusa da ni tana kallona ba tare da tace komai ba. “Me yasa kika ce ba zaki iya aurensa ba? Saboda Kareem?” Na kalleta na yi zaton zata fahimci abun da na fahimta ne kamar ni, ashe fahimtarmu ta sha banban. “Mama idan na yarda na aure shi a yanzu, zaman ba zai mana dadi ba, saboda zai rika kallona a matsayin macen da ta guje shi a lokacin da yake cikin talauci yanzu kuma na aure shi saboda yayi kudi, wannan uzurin Zafeer ya kasa yi min shi ko a can dama, ganin yake saboda ba shi da kudi na guje masa” “Toh ai ba karya ba ne, na sani da yana da kudi mahaifinki ba zai zabi Hafiz ya bar shi ba, bayan tsawon shekarun da kuka yi a tare” “Amman shi be fahimta ba, saboda Baba ya hana na yi masa magana ban fahimtar da shi” “Sai ki fahimtar da shi yanzu mana, Noor karki zama shashasha mana, yaron ya so ki kuma na san kina son shi, saboda rashin aurensa mahaifinki ya sake ni, babu irin yakin da ba mu yi ba ni da ke na ganin auren ya tabbata amman hakan be samu ba, yanzu kuma bayan aure biyu ya dawo yana son ya aure ki ki amsa da cewar ba zaki iya aurensa ba, anya ba ki ji kunya ba?” “Ji nake kamar...” “Kamar me? Ki rika yi ma kanki fatan alheri, ni dai na san kina son Zafeer kuma ina da tabbacin zai rike ki amana sosai, domin yaro ne mai kirki kuma mai tsananin sonki, kuma mun san iyayensa tarbiyarsa da komai ba mu da haufi a kai, ba ina son ki aure shi saboda yana da kudi ba, aa sai dan ina hango miki jindadi irin na mai hankali d sanin ya kamata” Na sauke idona kasa hawaye nake for no reason. “Ni dai idan har zaki yarda da ni da kuma abun da nake so, to ki auri Zafeer” “Mama Kareem...” “Kina son Zafeer yadda kike son k Kareem?” Na girgiza kai ko kadan ba za a hada soyayyar da nake yi ma Zafeer da wadda nake yi ma Kareem ba. “Ko kuma kina da tabbacin Kareem din zai rike ki amana? Bana fatan ki sake aure ki fito Noor, shi ma Kareem din ba natsentse ba ne, kina masa kallon mutumen kirki ne kawai amman ba haka yake a zuciyarsa ba, domin mutumen kirki ba zai yi tarayya da matar aure ba har ta kai ga haihuwa, shiyasa kullum yana shiga cikin lamarin gidanmu yana kyautata mana, na yi zaton sonki yake da farko, amman bayan aurenki na farko da na biyu na gane so yake ya bata miki lokaci ko rayuwa” Na kalli Mama da sauri ina mamakin a gurin da ta ji wannan maganar. “Mama a ina kika ji wannan? Kazafi ake masa Kareem mutumen kirki ne” Na yi hanzarin dora ginin da zai tare zubewar mutuncin Kareem a idon Mama, na san duk abun da ta ji ko aka fada masa a kansa gaskiya, but i know yana da kirki kuma ya fahimci kuskurensa, ba zan taba iya tona masa asiri ba, ba zan iya kara masa bakinciki bayan wanda yake ciki ba, mutumcinsa yana da muhimmanci a gurin Iyayensa kanensa da Yayansa. “Ke yarinya ce Noor baki san komai akan rayuwar duniya da mutanen cikinta ba, har yanzu baki gama wayewa ba, baki da zurfin tunani da fahimtar rayuwa” “Waya fada miki wannan Mama?” “Safeena, kishiyarki kuma abokiyar shedancinsa, har hotunansu ta nuna min wani gurin tana kwance a jikinsa, ita ma yaudararta yayi kamar yadda yake son ya yaudareki, abu ne da kika sani, domin ta fada min kin fadawa mijinta ďan da ta haifa yanzu ba jininsa ba ne kuma mijinta yayi bincike ya gane gaskiyar hakan har ya dauke kafarsa daga gidan yanzu hana tace kayanta a hade suke domin ta san zai iya bata takardar saki a duk lokacin da ya tashi” Na hade yawu da karfi na sauke kaina kasa a yanzu kam ba ni da wani kuzarin furta wani abu, amman yaushe Safeena ta zo nan? Yaushe ta fadawa Mama haka.? Kamar Mama ta san abun da nake tunani sai na ji ta ce “Ranar da kika tafi ganinsa Asibiti ita ma ta fito asibitin daga ganinsa ba, ta fada min ta ganki, saboda haka ki kwantar da hankalinki ki daina biyewa Kareem ko da ba aure ba ni bana son alakarku, idan har Zafeer da gaske yake ko kuma mutanen da suke zuwa zance gurinki da gaske suke kawai su fito ayi auren a huta, ki samu gurin da kika zauna kowa ya samu kwanciyar hankali” “Tohm Mama” Babu wani abun da zan iya fada, kalamaina ba su isa su kare aikin da Kareem ya aikata ba, da ace be kusanci Zina ba tun farko da abubuwa ba zu masa a haka ba. Na sani idan Mama ta san na amsa masa cewar zan rike yaron da suka haifa ma zai kara sakawa ta tsani Kareem din ko ta rufe ni da duka ma. But deep down i feel something about ina jin tausayinsa fiye da yadda na ji tausayin kaina a lokacin da aka raba ni da Zafeer. Tun a wannan daren na san ba zan auri Kareem ba domin Mama bata yi maraba da shi ba, kuma tana da gaskiya kowa yana son suruki na gari, kowa yana fatan yarsa ta yi aure a inda za'aji dadi babu fargaba. Na raye daren da sallah da kuma rokon Allah ya bawa Kareem lafiya, ina jin kamar ba zan iya rama masa abun da yayi min ba a ko'ina sai ta nan. Washe gari misalin karfe takwas Aisha ta fado family house din su Mama da zan iya kira da gidanmu a yanzu, ita da kanenta biyu da wata macen da ban san ta ba. Bangaren mu aka kawota har kofar dakinmu domin ta fada musu ni take nema, ko ya aka yi ta gane gidanmu ma oho, ni dai na sha mamakin ganinta har na rasa taya zan tarbiya, duk kuwa da na san ba lallai ne alheri ya kawo ta ba, bayan abun da na fadawa mahaifinta ta aikata akan karya. Dan haka ban yi gaggawar yi mata maraba ba na daga kai kawai ina kallonta kamar wadda bata wayeta ba. Mama dake hada tea ta mike tsaye ta fito daga dakin tana kallonsu. “Toh Allah yasa Lafiya” “Lafiya amman ba kalau ba” Kanwar ta amsa, Aisha kuma ta juyo ta kalli Saitin da nake zaune tana cin magani ta ce “Noor ashe wuyanki yayi kauri, ashe kin zama tantiyar yar bariki Kareem ya lakawa Hafiz kin kashe shi da bakinciki, domin na san tunanin abun da kika masa ne ya saka shi hatsari, kika maida ni bazawar karfi da yaji kika maida yarana marayu duk hakan be miki ba sai kin kulla soyayya da ubana? So kike yi ki karashe shi ma? Kuma ki shirya masa karya” Na mike tsaye ina murmushi. “Na yi kishi da ya na ji yadda ake ji, shiyasa yanzu nake son na yi kishi da uwarta, kuma dole ace da mijin Iya Baba” “Karya kike Wallahi, kin yi kadan ke a su wa? Har abada ba zaki taba wannan matsayin ba Wallahi, kuma ubana matansa hudu cif ba shi da gurin saka ki” “Zaki gani idan zan yi matsayin ko akasin haka, mata hudu kuma ba matsala ta ba ne, uwargidan zai fitar ya saka ni, kuma da kike zance na saka ki a zawarci ai kin saba zawarci domin Hafiz ba budurwar ya aureki ba, shiyasa kika yi duk yadda zaki yi dan ki hana mu zaman lafiya saboda kar ya san banbancin dake tsakanin auren budurwar da kuma bazawara, ni ba ni na ga mahaifinki na ce ina so ba, ubanki ne ya ga abun da yayi masa ya biyo sawu kamar yadda mijinki ya biyo” Farat kanwar ta yi ta fado dakin ta rufe ni da duka sai Aisha da dayar kanwarta da matar da suke tare suka fado suma suka fara min duka sai ihu nake ina maida martani a duk inda na samu, abun da ban sani ba ashe Mama ma tana nan tana min yaki a waje dukansu take ta ko'ina, wata cousin dita yar sister Mama ma ta shiga aka yi ta fafatawa da ita, sai da manyan gida suka ankara aka kawo mana dauki aka raba fadan. Kawu ya rufe Mama da fada wai madadin ta raba sai ta shiga ana yi da ita. “Yaya ta ina zan tsaya su kashe min ita? Daga ita sai Nabil suke rage min, ina zan yarda su yi mata illa su bar ni da jinya da hannu a kai, kana ganinsu manyan mata da su sun fi karfinta ta ina zan tsaya raba su?” Mama na fadan tana rika ni da duba hannuna da suka kusa karyawa. “Wai ke ina kika janyo wadannan mutanen? Ke dai Noor Allah yayi ki da rashin jin magana Wallahi, ya aka yi suka san gidan nan kuma su waye su?” Kawu ya rufe ni fada shi ma kamar zai min duka. Mama ta ce “Aisha ce fa da kanenta Aisha matar margayi Hafiz” Kawu ya rike baki, Mama Asiya ma mamaki ya shaki wuyanta. “Ai ni ban gane ta ba, ya aka yi ta san gidan nan kuma me ya kawo ta? Ina ce mai rabawa ta raba? To miye na duka kuma?” Mama ta fada musu komai kamar yadda na fada matan tun farkon fara zuwan Alhaji Sule unguwa uku a gidan. Kawu ya nuna ni da tsaya hannunsa na rawa kamar zai dakeni “Ke yanzu ina ke ina tsoho? Ina ke ina kishi da uwarta? Ashe ke ce marar gaskiyar ma, kina girma hauka na shiga kanki? Ai duk abun da suka miki ke kika ja” “Kawu ba fa ni na janyo shi ba, shi ya tare ni a hanya ya karbi number wayata kuma ban san mahaifinta ba ne sai daga baya, kuma Wallahi na yi blocking number shi ma” Na fada cikin kuka Mama na ja min hannun. Sai bayan da komai ya laba sannan na dauki wayata na cire number shi daga blacklist na fita daga gidan gaba daya na shiga makota na kira wayarsa, ringing daya ya daga sai na fashe masa da kuka sosai. “Ni ban ce ka je ka fadawa uwargidanka abun da yarka ta fada min ba, shiyasa na ce ba zan aureka ba saboda gidanka ya fi karfinka” Yayi shiru irin na manya masu nazari, ina jin haka sai na kashe wayar. Ga ayi second biyu ba kiransa ya shigo na ki na daga, sai da ya sake kira sannan na daga na kara fashewa da kuka. “Me ya faru Khadija?” “Matakar ta aiko yarka Aisha da kanenta biyu sun zo har gida sun min duka, ni Mamana har Aisha na fadar wai ba Mamansu ta ce a fada min ba zaka taba aurena ba matanka hudu baka da gurin jefani, wai kuma so nake na koya maka zaman banza domin ba ta inda zaka aure ni daman na san ba aurena zaka yi, gashi ma ashe gidanka sun fi karfinka akan me uwargidanka zata aiko ayi min duka? Mi miye nawa a ciki? Ai kai ka gan ni kace kana so na ko?” “Khadija” Ya kira sunana a natse sai na kara narke masa da kuka. “Ki yi hakuri, kuma ina son na fada miki ni Alhaji Sule gidana be fi karfina ba, kuma ban zo gurinki domin shashanci ba, aure nake sonki kuma shi ya kawo ni, abu daya zaki min a yanzu ki burge ni, ki amsa cewar zaki aure ni!” “Na aureka taya? Mata hudu fa haka uwargidanka ta aiko a fada min, kuma idan ma na aureka na je matanka su rika min duka” “Wallahi Wallahi babu wanda ta isa ta saka miki hannu Khadija, kuma zan tabbatar miki da haka, ki bawa Mama hakuri zan zo yanzu da kaina na ba su hakuri, kuma ki jira matakin da zan dauka” “Amman da gaske zaka aure ni? Ni tsoro nake karka cutar da ni ba ni da kowa sai Allah sai Mamana da suka yi ma duka dazu, har kusan karya min hannu suka yi” “Wallahi Wallahi zan aureki Khadija, idan ma kin amince cikin satin nan sai a daura mana, ni bana bukatar komai daga gareku, zan zo yanzu nan na bawa Mama hakuri” “Toh sai ka zo” Na kashe wayar ina murguda baki, daman bahaushe yace idan ka san me zaka fada baka san me zai dawo maka ba. Ba a jima ba Alhaji Sule ya zo gidanmu tare da abokinsa ya bawa Mama da yan gidanmu hakuri ya aje mana kudi mai kauri sannan ya tafi, ko be bani labari ba na san ba za'ayi mai kyau ba. A daren ne Zafeer ya sake sallamawa a gidanmu sai dai wannan karon ba da ni yai magana ba sai da ya shiga ciki yayi magana da Mama ban san me suka tattauna domin fita na yi na bar musu dakin. A dakin Anty Amarya ina amsa facetime with Kareem. Fada yake few hours suka rage ya shiga da shi tiyata. “Da dare za'ayi maka?” “Mu nan safiya ce, akwai banbanci lokaci” “Na maka addu'a sosai da dare, a kowace sallah ma ina maka, Allah ya baka lafiya Kareem” “Amman baki min addu'a ki ce Allah ya ba ni ke, idan ni din alheri ne a gareki?” Na dan yi shiru ina jin wani iri domin kudirinsa akaina ba zai ga ci ba, kuma ban san taya zan buda masa littafin ya karanta har ya fahimta ba. “Babyna” Kallonsa nake ba tare da na amsa ba. “Zafeer ya sake dawowa ko? Kuma Baban Aisha ya zo?” “Taya kake sanin duk wannan Kareem” Yayi murmushi daya kara bayyana ramarsa. “Karki da wannan, i just hope idan an yi min tiyata na tashi zaki min albishir mai dadi” A kokarina na karfafa masa guiwa domin samun yin aiki a cikin nasara na daga masa kai na jadda masa zan tarbe shi da labari mai dadi. “Ina fatar hakan, zan huta na tsawon kwana hudu, ba lalle na sake facetime dake ba sai na ji an samu results din da ake bukata, but what so ever dai i love you i want you to know that i know you” Na yi murmushi ina jindadin furucinsa har cikin raina, for the first time na ji ina sha'awar kwantawa a jikinsa na rumgume shi mu yi bankwana amman babu dama, na shafa screen din wayar. “Hey... No more tears, bana son na ga idonki da kuka, i love you so much” Na share hawayen wasu na zubo min. “Allah yasa ayi aikin cikin nasara Kareem get well soon please” “I will” Ya laka yatsunsa biyu a screen din wayar, ni ma na lika nawa a saitin nasa, ni da shi aka rasa wanda zai dauke ido daga barin kallon dan'uwansa, tausayin halin da yake ciki a yanzu da kuma wanda zai shiga idan ya tasa ni, ya saka ni zubar da hawaye kamar babu gobe. Ya maida hannunsa gurin bakinsa ya sunbanci yatsun ya sake lakawa saitin da nawa suke. “Idan har na rayu na aure ki Noor, sai na mantar da ke duk wani daci da bakinciki da yake cikin duniyar nan, sai na saka kin gamsu cewar wata mace bata fiki gata da samun soyayya ba a gurin miji, zan so ki har abada Noor” Na lumshe ido na maida lips dina na kaaa tsakanin hakorana ina tauna zafin rabuwar da ba mu riga mun yi ba. “Noor ta so ana kiranki” Na kalli Anty Amarya sannan na kalli wayar dake aje gabana. “Zan tafi Kareem ana kirana” “Okay Love... Fada min wani abu mai dadi kamin ki tafi” “I love you” Na fada with no hesitation, murmushi yayi ya shafa fuska ta jikin wayar sannan ya daga min hannu. “Bye” “Bye” Mun dade muna kallon juna ni da shi, kewaraa ta hana ni kashewa shi ma kuma baya son ya daina ganin fuskata. Sai da na yi da gaske sannan na iya aje wayar na share hawayena na fita daga dakin Anty Amarya. Bangaren da Mama take na koma na shiga a wani yanayi kamar ba ni ba, gaba daya Mood dina ya canja. “Ki tafi Zafeer yana waje yana jiranki” Na cire hijab dina da ya jike da hawaye na dauki wani na saka, sannan na fita na tsaye a kusa da motarsa har muka gama gaisawa ban kalli fuskarsa ba. “Noor na yi magana da Mama na tambaye ta ko akwai wanda kike so da har ya hana ki amsa aure na a karo na biyu bayan duk wulakancin da kika min? Ta fada min babu ta tabbatar min har yanzu kina kaunata kawai dai kina wasu hange hange ne da ba su da amfani” Ya gyara tsayuwarsa. “Ni kuma na san akwai mai wasa da hankalinki har yanzu, wannan Kareem din ko? Ba aurenki zai yi ba Noor kawai yana wasa da hankalinki, ya raba ni da kw farko Noor ban yi tunanin zaki sake kula shi ba, balle har ya zama dalilin da zai saka ki amsa cewar zaki aure ni” “Ba shi ne dalilin ba, kai da Mama kun yi kuskure fahimta ne kawai” Na fada domin a zatona Mama ta yi masa maganar Kareem ne. Sai ya tari numfashina “Mama bata min maganar Kareem ba, kuma bata fada min komai akansa ba Wallahi, amman kin san ba zan rasa sanin halin da makiyina yake ciki ba ko?” Na yi shiru ina jin babu dadi, na kasa sakewa zuciyata na raya min zan ci amanar Kareem ne, amman kuma. Zafeer ya cancanci komai a gurina, ba ni da masoyi irinsa, ya nuna min so iyakar so. “Ina hango yadda kake kallona a idonka nw Zafeer” Ya sassauta muryasa. “Ki bar wannan maganar, ni dai babu abun da na iya kuma na sani sai kaunarki, zan iya yin komai saboda na aureki, na so ki Noor kin sani, na kusan mutuwa a lokacin da na rasa ki, ba ni fa wani buri a yanzu da ya wuce na aureki, rayuwar da muka sha alwashin ginawa a baya ba mu samu dama ba nake son mu gina a yanzu, shin kina so na har yanzu?” A nan kam na daga kai na kalleshi da idanuwa dake hasko min irin rayuwar d muka yi a baya. “Ina sonka har gobe har jibi har gata Zafeer” Yayi min murmushin da na manta rabon da na ganina fuskarsa, ya matso kusa da ni cikin wata siga da ta fi kama da rada ya furta min. “Zaki aure ni Noor?” Na daga mishi kai. “Zan aureka Zafeer” Wani kuka mai karfi ya zo min. Tun daga ranar sai soyayya tsakanina da Zafeer ta dawo sabuwa ya karbe liyi na ya siya min wata wayar da sabon layi, kowa a gidanmu sai da ya san Zafeer ya dawo gareni, domin ya hanani kula kuwa ciki har da mahaifin Aisha da ya saki uwargidansa saboda ya aureni, kamar yadda ta sake zuwa har gida ta yi min cin mutunci ta fada min na kashe auren uwarta ni kuma na jira nawa sakamakon. Duk wani shirye shiryen aurar da ni Mama ta fara domin Zafeer ya fada min ba zai bata lokaci kamar yadda yayi a wacan karon har ya rasa ni ba. Dawowar Zafeer ta min dadi, musamman da ya sanar min an kori Abdull a kamfanin da yake aiki, sai dai bana jinsa a yadda nake jinsa da farko, idan kuma na tuna Kareem ba da masaniyar komai akaina babu ta inda zai same ni sai hankalina ya tashi, lokuta da dama na kan so gwada kiransa a sabuwar wayar da Zafeer ya siya da sabon layi domin na haddace number sa, sai kuma na tambayi kaina me zan fada masa idan ya amsa kiran nawa. Na san an yi nasarar aikin a satin da aka amsa aikin na ji a gurin Yaya Nabil an masa aiki kuma anyi a nasara, amman na kasa kira na tambayi jikinsa ko na yi magana da shi. Ya miko min zobe daya ya saka daya. “Wannan na ki ne” Na karba ina murmushi na yi saka a yatsana, soyayya sabuwa ni da Zafeer kamar ba mu taba shiga damuwa a baya ba. “Dukanmu mun taba yin aure, ni na yi aure na farko ke ma kin yi har biyu, so ni a yanzu bana son ayi wani biki ko taro, ba zan yanke hanzarinki ba, na san mata kuna da son biki wata kila zaki yi walima ko?” Na dan yi shiru ina nazarin abun da zan yi, domin Mama ce take ta shirye shiryen auren, har yanzu ban yi wani yunkuri ba. “Bani ba ko Mama zata yi, amman dan ta ni bana sha'awar wani shirye shirye” “Good, zan fi jindadin haka, ba sai an wahalar da ke ko Mama ba” “Babu wahalarwar a ciki, ba za mu bukaci komai ba” “No ba ina nufin kudin da zan bada ba no zan baki kudi enough ki yi hidimarki, kawai dai dauaniniyar ce wahala ai, kuma ina son na fada miki na kama gida a bypass ba laifi gida ne mai kyau sosai kuma yana da tsari mai kyau sai dai ba ma kusa da mutane” Na dan kalleshi da mamakin jin furucinsa domin a tunanina yana gidan kasansa ko da yake gidan ba zai amfana min komai ba. Yayi murmushi yana kallona. “Ya na san zaki yi mamakin na fadi haka ko? Gidana da nake zaune wanda nake tare da Fanna ne, kin ga yadda muka sha soyayya ni da ke kamata yayi ace mun tare a gidanmu mu kadai babu sa ido babu ganin laifi ko?” Abun da ya fada haka ne, za mu fi sakewa idan muka tare mu kadai. “Wai ni kam taya ka lallabata ta amince ka kara aure?” “Ban gane ta amince ba, ni ne fa mijin ba ita ba! Tun kamin na aureta ai ta san ina sonki kuma at any chance zan iya aurenki, abu na biyu Fanna ba mace ce mai matsala ba, kuma bata cika zama ba, saboda ita ce tabbar yar mahaifinta yawancin abubuwan da suka shafi kasuwancin mahaifinta ko kamfaninsa ita take tafiyarwa, yanzu haka bata kasar ma” “Amman me yasa baka bita ba?” Ya daga fadunsa. “Ra'ayi, tana son muna tafiya a tare sosai saboda tana son na zama ďa namiji da mahaifinta ya rasa, na maye gurbin ďa namiji da ba shi da, so nan din ma akwai abubuwa da nake kula masa da su” “Amman ance ta tsofe ka wai haka ne?” “Ko ma dai minene ai ta taimaka ta aure ni a lokacin da kika zubar da ni a kasa ko? Ita ta rarrashi zuciyata na samu sukuni har na rayu” Na ji wani abu ya soki zuciyata. “Daman tun a farkon zuwan da take na lura da sonka take yi, shiyasa take baka kudi mai yawa har ta taba tambayata wai kai saurayina ka tuna?” Yayi murmushi ya shafa kansa. “Manta da duk wannan, yanzu dai ya maganar tufafinki? Ina tunanin kudi zan baki ki siya duk abun da kike so” “Me yasa ba zaka hada min da kanka ba?” “Kawowar ne nake tunani kamar zai fi dai ki hada da kanki” Bana masa jayyaya akan abubuwa daman can ni ba mace ce mai son ja'in ja ba, balle kuma shi da bana son ya ga laifina a yanzu ko da kuwa kan akaifa ne. A yadda ya tsara a hakan na bi sai ya kawo min kudi mai yawa da sunan siyen kayan lefe, Mama ta siya min kadan sauran kudi kuma ta kara gurin siyen kayan daki da na kitchen domin komai sabo ta yi min kamar auren fari. Yan'uwan Mahaifina sun yi kokari matuka, sun hada kudi mai yawa suka kawo gun Mama a matsayin gudunmawarsu. Mama ta hada da wanda ta samu a danginta da kuma kudin da Zafeer ya ba ni na lafe ta siya min kayan daki fa kayan Kitchen masu kyau irin na mai rufin asiri. Ba ayi walimar ba kamar yadda Zafeer ya bukata, saboda Mama tace ta fara gajiya da shidawa mutane aurena a yanzu, gwara kawai mutane su ji an daura. A iya cikin gida muka yi bikinmu ba tare da tara makota ko kawaye ba. Iyana yan'uwan mahaifina sai na Mama da suke gidan kawai suka san da daurin auren da aka daura a ranar Jumma'a. Jikina ya sha gyara ta ko'ina ba a taba yi min gyaran jiki ciki da waje mai kyau irin wannan ba, Mama ta kashe kudi sosai gurin gyara yarta mace da ta rage mata daya tilo wato ni kenan. Ni kaina na san na gyaru domin fatar jikina har wani tsantsi take kamar auduga. Ranar assabar aka yi wunin biki bayan an yi jere ranar alhamis, na yi zaton ganin yan'uwa da dangin Zafeer amman ban ga ko daya ba, daman tun da aka fara neman auren bayan iyayensa maza da suka kawo sadaki, wani daga familynsa be sake leko mu ba. Wata kila har yanzu mahaifiyarsa da kannesa ba su gama da hukuncin Allah ba, domin komai kaddarrawar Allah ne, ya rubuta ba zan auri Zafeer a wacan karon ba sai a yanzu. Na sha huduba na sha nasiha na sha gargadi tun daga kan Mama har zuwa kanenta da yayye fa kuma yan'uwan mahaifina, ba laifi kawata Zainab na ta yi ta min nasiha akan aure da zaman aure ta nan na fahimci har yanzu wasu ganin suke kamar ni nake kashe aurena dan ra'ayin kaina, ko da yake dole ne na musu uzuri domin ba kowa ya san dalilin mutuwar auren ba, ba kowa ya san abubuwan dake faruwa ba. Tsofi biyu ne suka zo daukar amary sai kanwarsa daya da wasu yan mata da ban waye su waye ba. Mun yi tafiya sosai kamar zamu bar gari kamin mu isa gidan da ya kama haya, kaina a lullube aka shiga da ni gidan amman hakan be hana ni ganin kyau da gidan yake da shi ba. Sai karnuka biyu dake ta haushi ganin Shigowarmu. Anty Larai na rike da ni har cikin dakin Farincikina. A gafe gadon ta zauna da ni ta sake yi min nasiha yan'uwanta ma suka min sannan suka tafi aka bar ni da cousins dina sai Zainab da wasu kawaye biyu, domin ban gayyaci kowa ba sai wanda ya ga dama ya zo dan kansa. Bayan iyaye sun tafi na daga mayafina na kalli dakina idanuwa dauke da abun da ya zame musu ibada wato hawaye. Akwai farinciki akwai jindadi akwai kwanciyar hankali da sakewa a auren wanda kake kauna, masoya ne kadai za su iya labarta haka. Ban taba samun kaina a yanayi da na samu kaina a yanzu ba, farincikina na ninku, samun cikar buri ba abu ne mai sauki ba. Take a gurin na sauka kan gadon na yi sujadar godiya ga Allah. “Awwww finally yau dai buri ya cika Noor ta zama matar Noor halak malak” Cewar Zainab tana tsokanata. Sai na yi murmushi na shafa fuskata, for the first yau na yi aure na shigo gidan mijina ina mai farinciki da jindadi, kuma ina mai fata aure ne sai idan na mutu na bar shi domin bana fatanya mutu ya bar ni, bana sha'awar rayuwar zawarci bana burin aurena ya sakw mutuwa a yanzu. Mun kusa awa biyu a gidan sannan ango ya shigo tare da rakiyar abokansa biyu Mansur da Yusuf daman na san su tun muna tare da Zafeer. Kusa da ni ya zauna ya kama hannuna ya rike yana dariya, Mansur na tsokanarsa wau tsohuwar soyayya yau ta tabbata daman hausawa sun ce da tsohuwar zuma ake magani. “Noor muna muku addu'a Allah ya ba ku zaman lafiya da zuri'a dayyiba, kuma Allah ya hada kanku da abokiyar zamanki, dan Allah ku yi zaman lafiya ta yadda hankalinsa zai kwanta, kin san dai irin gwagwarmayar da aka sha kamin buri ya samu cika, to ki yi ma mijinki biyayya dan Allah” Na ji dadin Shawarar Yusuf, Mansur ma ya kara da nasa yana tsokanar Zainab wai ba A su siya baki ba domin ba ba su ni lokacin da suka bukata ba, kuma ni din a yanzu ba budurwa ba ce ba sai an yi sayin baki ba. Wannan kuma haka yake a iya sanina budurwa ake yi ma siyen baki ba bazawara ba. “Aa za a siya bakin Matata mai tsada ne ko aure dari ta yi sai an siya” Zafeer ya amsa da kansa yana murza hannuna a hankali. Sai duk suka saka dariya, abokansa suka ciro kudin da zai kai 100k suka mikawa Zainab, ba sai sun fada ba na san Zafeer ne ya bada kudin domin cikinsu babu mai arzikin da zai iya kyautar 50k ma balle 100k. Zainab ta karba tana ta ihu da murna kamar ba matar aure ba, gaba daya ta cire auren ta aje a gefe sai sha'aninta take saboda bikina ne, abu ne da ta so ta yi tun auren farko amman be samu ba sai yanzu. Sallama suka min suka Zainab na rada min lalata a kunne tana dariya sannan suka tafi tare da abokansa da za su sauke su gida, bayan sun yi mana addu'a tare da fatan alheri. Zafeer ya saka hannu ya yaye mayafina gaba daya ya kalleni, ni ma kallonsa na yi cike da farinciki duka auren da na yi ko wane ina tafiya da soyayyarsa da tunaninsa ne a gidan wasu, amman yau a gidansa na tare, tare da soyayyarsa to mi yafi wannan, ni ma dai na ji farincikin da masoya suke ji. “Alhamdullahi, shekara da shekaru sai yanzu Allah ya cika mana burinmu, ko ma nace burina domin ni cutar ta fi kamawa” Ya shafa fuskata da hawaye ke zuba. “Ranar da aka daura aurenki da Abokin Kareem Hafiz ko? Na yi kamar na mutu na ji kamar ban taba samun farinciki a rayuwata ba, na wahala sosai domin ban yi zaton soyayya zata kai mu ga haka ba, ban yi zaton rashin imanin mutanen ya kai haka ba, musamman ma Kareem ya raba ni da ke ne kawai saboda yana jin cewar ya isa kuma yana da kudi, ba dan zai aureki ba, aurenki na biyu ma ba zan iya misalta bakinciki ba, har sai da na tambayi kaina miyasa kaddara take hada ni da ke bayan ko wane aure na ki, ashe akwai abun da kaddara take saka mana da ba mu sani ba” “Wani abun a nesa yake, kamin a samu cikar buri akan wahala wani lokacin” “Haka ne, domin na wahala kamin na same ki Noor, talauci ya cutar da ni ya nesanta ni da ke, amman Alhamdullahi gashi a yanzu arziki ya sadamu” “Kaddara ce ta raba kuma ita ta sake hadawa yanzu, ba talauci ba, ba Kareem ba, kuma ba arziki ba” Yayi murmushi mai sauti, da alama amsata bata gamsar da shi ba, tun a daren na san zama ba zai mana dadi a gidan ba, domin yana kallon na guje shi ne saboda talauci yanzu kuma na aure shi saboda arziki. Shi kadai yayi alwala domin ni na yi tawa tun a gida, raka'a biyu muka yi muka gode Allah muka yi addu'a sannan ya juyo ya rike goshina yayi min addu'a. Sai da na cire tufafin jikina an saka na bachi kamar yadda ya bukata kuma ya saka sannan ya dauko mana abun tabawa. He feed me, i feed him cikin soyayya da kauna, sannan kwashe kayan ya rufe kofofin gidan ya rage hasken dakin ya kwanta bayana. A wannan daren na tsammaci abubuwa da yawa daga gurin Zafeer, kamar hugging, kissing romanced, da ma uban gayyar, ba dan ina da bukata a sai dan sani ba, kowane masoya suna raya darensu da soyayya ne. Wata kila akwai gajiya a tare da shi, domin be dade da kwanciyar ba na ji bachi ya dauke shi sai ninshari yake irin na wanda bachi yayi masa dadi. A haka muka kwana ni a karshen gado shi kuma a farkon gado fili mai yawa a tsakaninmu. A tare muka yi sallah asuba, bayan mun gama na gaishe shi na kwantar da kaina a cinyarsa, sai ya dora hannunsa a fuskata yana shafa fuskar a hankali. “My beautiful Wife Good Morning, how was your night” “Alhamdullahi ya naka daren” “Alhamdullahi ni ma na kwana cikin farinciki, wannan ne karo na uku da abun farinciki mai girma ya same ni” Na juyo kaina da kyau saitin fuskarsa na kalleshi. “Fada min biyu, na san na uku” Yayi murmushi ya lakaci hancina. “Na farko, Auren Fanna, yarinyar nan ta yi kokarin ganin ta dawo da ni hayyacina a lokacin da kika guje ni, ta nuna min kauna ita da iyayenta, na jidadin da Allah ya hada ni da ita, a daren da aka daura aurenmu ta mantar da ni dukan wata damuwa” “Ta ya aka yi ta san mun raba?” Na tambaya ina jin kishi a raina, domin a yanzu na sani ba ni kadai ba ce a zuciyar Zafeer. “Waye ma be sani ba, gaba daya fa rayuwara ta canja Noor da na rasa ki, na kusan na yi hauka, Allah ya sani na kaunace ki sosai a lokacin, kin san tana kawo gyara ta zo ta same ni wani iri ta tambaye ni me ya same ni na sauya haka, ban fada mata ba amman oga ya fada mata, a lokacin da ta sake zuwa na bar garin nan ne saboda ina jin ba zan iya zama idan ba same ki ba, a lokacin ina jin kamar ba zan iya rayuwa idan babu ke ba Noor” Ya sauke ajiyar zuciya. “Ta samu number wayata ta gurin oga, ta kira ni ta min nasiha sosai kuma tunatar da ni abun da na manta iyeyena da karatu wanda su suka fi muhimmanci sama da soyayyata da bata samu cikar buri ba, na fada mata ba zan iya zama a garin ba saboda makiya za su min dariya kin yi aure kin bar ni, sai ta bukaci na tafi Sokoto gurin wani dan'uwan mahaifinta na zauna a can, na zauna a can har sai da na samu sukuni na dawo hayyacina ni da mazan gidan muka zama kamar abokai, a lokacin da na dawo sai ta yi min ta yin kaunarta bayan ta ba ni gata na kwantar min da hankali da yin magana da iyeyena, kuma ta gabatar da ni a gurin iyayenta suka min nasiha. Na amsa soyayyarta amman bata bar ni na kashe naira ba, bayan sadakinta da na biya ban san wani abun wahala da na yi ba su ma kuma kudin sadakin ta gurinta na same su, bayan aure kuma takarduna suka fito na yi service sai mahaifinta ya ba ni babban gurbi a ma'aikatarsa” Na tabe baki ina jin zafi a zuciyata. “Mai arhace ma, ashe ita ta yi maka tayin kanta, kuma ta yi maka komai, wata kila dan bata da masoyi ne” Da gatse na yi maganar domin na lura bara mana soyayya yake, a cikin labarinta da yake ba ni akwai kauna da soyayyarta a zuciyarsa, sai dai ina da tabbacin be kai nawa ba, wata kila ma dai kimarta ne kawai yake gani domin ta cancanci a yaba mata. “Noor duk zaman da zamu yi dake karki yarda ki fadi wata magana marar dadi akan Fanna, ban ji babu dadi kuma bana son abun da zai kawo tsabani a tsakaninmu, idan Allah ya hada ku ina son ki yi mata biyayya fiye da yadda zaki yi min” “Zan dai maka biyayya kai da kake mijina domin kai na aura kuma kai nake aure ba ita ba, ita dai matsayinta ba zai canja a matsayin matar ka ba, kuma abokiyar zamana” Yayi murmushi ya dauke idonsa akaina. “Na ji farko fada na biyu” “Na biyun aikin da mahaifinta ya ba ni, already na fada a cikin na dayan ai, daren fa ban iya bachi ba, saboda farinciki, gashi ya sake ma iyayena muhalli kuma bana da su za ayi hajji da yardar Allah, na ukun dai nw baki sani ba” “Na sani mana aurena ko?” Yayi shiru for seconds tare da kai hannunsa a kunnena. “Eh haka ne, aurenki ne farinciki na uku amman makasudin jiyar da wanda ya jiyar da ni bakinciki ne” Kamar ya san zan tambaya waye sai ya ba ni amsa tun kamin na bukata. “Na ji farinciki jiya na kwana a farinciki, yau kuma na farka a farinciki wanda ya raba ni da ke kuma na san jiya ya kwana da bakinciki ya farka da shi, zai ji kwatankwacin abun da na ji a lokacin da ya raba ni da ke saboda kawai yana jin yana takama da kudi, kuma ba ma aurenki zai yi ba ya aurawa abokinsa, manufarsa ta yin hakan ne ban gane ba har yau” Gaba daya sai jikina yayi sanyi, zuciyata ta karaya saboda me Zafeer zai aikata abun da zai hana Kareem farinciki? A da can ni ma ban fahimce shi ba, amman a yanzu na sani ba shi da burin da ya wuce ganin farincikina. Na tashi zaune daga kan cinyar Zafeer na kalleshi. “Bana jin ya raba mu ne saboda isa ta kudi, kuma abokinsa shi ya amsa cewar yana sona a lokacin da alakarmu ta lalace, Baba ne silar komai na sani Allah ka yafe masa” “Me yasa shi be aure ki ba idan har sonki yake?” “Saboda na fada masa na sake nanata masa cewar kai nake so, shi kuma yana tsoron ya auri macen da bata son shi” “A yanzu ya fahimci kina son shi ne shiyasa yake ta shirye shiryen aurenki ko kuma dai yana son ya aureki a haka ne ko da baki son shi, ko kuma dai yana son ya maida ki kamar tsohuwar budurwarsa ne saboda yana ganin kamar baki da wayo...!!” Na kasa sake furta komai na kasa fahimtar gurin da kalaman Zafeer suka dosa, maganar sai ta juye min upside down. Daga haka kuma wata maganar bata sake fitowa daga bakina ba. Shi ma kuma tashi yayi ya fita waje yana amsa wayar matarsa ko ma na ce uwar dakinsa. Tea ya hada mana daman tun da dare ya siyo kayan tea da komai, ni dai ban ma iya cin biredi ba sai tea kawai na sha, duk inda ya juya kallonsa nake kalamansa nake tunani, na kasa hadewa har sai da na tambaye shi. “Zafeer idan na canka daidai kamar ka aure ni ne saboda Kareem ya ji babu dadi ba dan kana so na ba?” Ya kalleni. “Idan na ce bana sonki zaki yarda? Ina sonki mana Noor har gobe, amman dai makasudin na dandana masa abun da ya dandana min ne” Tun a kalamin na yi kuskure, ban kuma sake sakin jikina ba, farinciki da ya kamata na samu a gidansa sai na gagara samunsa. Wata kila ni dai kam ba ni da rabon dacewa a cikin aure wata kila tawa kaddarar a cikin aure take. Har na gama cin amarci yan'uwan Zafeer ba su taba takowa gidana ba, duk wanda zai zo ko ya zo to daga dangin mahaifiyata ne ko mahaifina ko yan unguwa. A tsawon sati biyu da na kwashe a gidan Zafeer be taba kissing dina ba, be taba kai hannunsa a jikina da nufin jiyar da ni jindadi ba, idan har jikina ya hadu da nashi, to ni na kwnatar da kaina ko jikina a nasa, ko kuma na shiga jikinsa da dare idan zamu kwanta sai ya rumgume ni mu yi bachi, hana rantsuwa idan ya dawo daga aiki yana taba fuskata ko hannuna ya tambayi ya nake. Tun ina hakuri har zuciyata ta fara raya min ba daidai ba, ko dai Zafeer yana kyamata ne ko kuma yana ganin kamar na yi tarayya da Kareem ne, ta ina ma ya san Kareem yana da tsohuwar budurwa? Ta ina ya san Kareem yana shirye shiryen aurena? A duk lokacin da zai amsa wayar matarsa sai ya tashi ya fita a falon ko dakin, idan kuma yana jin kuiyar fita ya kan umarce ni da na yi shiru ne ko kwararan motsi baya son na yi. Yau ma kamar jiya tana kira yayi min alama da na yi shiru sai na tashi na fice daga dakin na shiga kitchen dina domin duba girkina. Shimkafa da miya na girka domin ita na fi kwarewa kuma ita ce favorite dina. A plate daya na zuba mana na kawo na aje a gabansa sannan koma na dauko mana lemu da ruwa da spoon na dawo na zauna ina facing dinsa, a rayuwata ban taba tunanin zan auri Zafeer na yi irin wannan zaman auren da babu soyayya a ciki ba. “Ruwan miyar nan be tsane ba Noor kuma gishiri yayi yawa a miyar nan” “Hannuna ne ya subuce” Na amsa cikin rashin jindadi daman na san ban iya ba, kuma abu ne da na cutar da kaina da shi tun a kurciya hauka da rashin natsuwa ba su bar ni na tsaya na koyi girki kamar kanwata Hana ba. “Ki maida hankali mana, babu abun da namiji yake so irin mace da ta iya girki, haka jiya kika girka tuwo be tuku ba shimkafa a tsaye a ganinta. Kin ga Fanna Wallahi duk gatan ubanta ta iya girki, ban tana siyen abinci ba tun da na aure ta, komai fa maida hankali ne aurenki biyu kina nufin kullum siyen abinci suke ba zaki girka ba? Idan baki iya ba sai yaushe zaki iya Noor?” Ba da fada yayi min maganar ba, amman ambatar Fanna ta fini iya girki ya saka na ji raina ya bace. “To ka kirata ta zo ta girka maka mana, ai ni ka san ni tun kamin ka aure ni, kuma a haka ka ji zaka iya zama da ni, ba kai kace babu wanda zai iya da ni sai kai ba? Me yasa tun yanzu ka kasa?” Kallona kawai yake har na ci na tsude be ce uffan ba. Sai ma tashi da yayi ya dauki wayaarsa da makullin motarsa ya fice daga gidan. Ni kuma na kwanta a gurin ina hawaye, a yanzu kam na yarda 100% rayuwa bata nufin jindadi a gareni, indai har Zafeer zai aureni na kasa samun farinciki to ba zan same shi ba har abada. A dole kuma haka zan yi hakuri domin ba ni na tsarawa kaina komai ba. Ni ma ban iya cin abinci ba saboda kuka da bakinciki, bayan fitarsa sai fargaba da tsoro suka kama ni, idan na cigaba da fusata akan wata zan yi ta samun matsala da mijina ne, wata kila har hakan ya zama silar mutuwar aurena wanda bana fata, domin mutane sun min shaidan bana zaman aure, alhalin mai daki shi ya san inda yake masa yoyo. Be dawo ba sai dare a lokacin kuka har ya sauya kamanin fuskata, abu ne da ya kamata ace idan da sabo na saba da shi kukan amman na kasa a lokacin da ya kwankwasa kofa sao na bude. “Sannu da zuwa” “Sannu amayar ya kike fatan an gama fushin yanzu” Yana cire rigarsa yana amsa min, sai na shiga gabansa na durkusa har kasa na bashi hakurin abun da na yi masa a dazun kuma na roki yafiyarsa. Da sauri ya rika ni ya mikar da ni tsaye “Haba Haba Baby Noor, ki daina wannan dan za ki ba ni hakuri har sai kin kai kasa? Nooo na yafe miki, amman duk abun da nake miki magana akai ina miki ne saboda ki gyara” For the first time ya kai bakinsa ya sumbanci goshina ya sumbanci wuyana, ina jin lokacin da ya fara wasa da gabobin jikina har ta kai mu ga kwanciya saman gadon, sai kuma yayi zumut ya zare hannunsa da jikin da sauri ya sauka bakin gadon ya sauke kai kasa yana sauke ajiyar zuciya. Kwakkwaran motsi ban yi ba har safe tunani ya rufe ni, kyamata Zafeer yake ko kuma dai akwai abun da baya son fada min. A tare muka shirya abun karyawa, a duk lokacin da na kalleshi sai na yi ta tuna kalamansa na baya, idan na tuna yadda ya fada min zamu shimfida soyayya sai na tambayi kaina to yanzu me yake jira? Zuciyata ta kan tunatar da ni cewar a yanzu ba ni kadai ba ce a zuciyar Zafeer, kuma na san baya kallona a wacan matsayin na da, a dole na shafa kaina lafiya. Wata rana da muka fita tare da shi muna zaga gari yana ta nuna min gurare ciki har da gidan da yake zaune da matarsa gidan sama ne mai hawa biyu ba ko daya ba, wajen gidan kadai ya wadatar da mai kallo, dan haka bana bukatar aban labarin cikinsa. Ya kai ni gidansu gurin iyayensa su ma gidan mai kyau suke zaune ba laifi Mahaifin Fanna yayi kokari gurin sama masa ingantacciya rayuwa shi da iyayensa. Tun da muka gaisa da mahaifiyarsa ta fice ta bar ni a dakin, kanensa ma kamar an musu dole haka suka gaishe ni, suka fice daga dakin kai kace wani na kashe musu, ko da yake suna da hujja na guji dansu a da can sai a yanzu na aureshi. Sai da za mu fita na sake yi mata sallama a tsakar gida na wuce ko Allah ya kiyaye hanya bata ce ba, balle ta yi godiyar abinci da na kawo musu. Daga gidansu ya sauke ni gurin Mama ta yi farincikin ganina tun da yake zuwana na biyu ne bayan auren, ni ma jidadi ganinta na same ta tana ta shawarar maka Alhaji a kotu wai so take ya sake ta ta huta shi kuma yace ba zai sake ta ba. “Amman Mama ba ke kika ce mace kamar riga take a wuyansa ba? Me yasa ba zai sake ki ba?” “Shi da kansa haka ya fada min kuma haka mutane suka shaida amman na yi kida na yi rawa na yi yakin duniyar bawan Allah nan ya ki yarda ya ba ni takardar sakina, shi kokarin ma yake ya ga na koma” Ba zan bata shawarar komawa ba, domin duk wani abu da ya shafi Abdull bana kaunarsa a yanzu, kuma ba zan karfafa mata guiwar kashe auren ba domin ban san abun da Allah zai shirya a gaba ba. Mun yi hira ta saka min albarka domin ita ma na kai mata abinci da dan alheri da zan iya. A lokacin da Zafeer ya dawo daukata ya shigo suka gaisa sannan ya fito tana saka min albarka muka dawo gida tare. A daren na kwana da ciwon mara sosai washe gari na tashi da period. Kwana uku na yi sannan yi tsarki, kamar yadda na tsammata Zafeer ba neme ni ba, sai ma ya zo min da albishir wai Fanna zata dawo wannan weekend din, na taya shi farinciki domin na ga farincikin ne a ransa, na yi ma kaina alkawari zan yi hakuri da duk halin da zan samu kaina, zan jure kuma zan yi masa biyayya na yi mata kamar yadda ya fada min a washe garin aurena idan har hakan ne zai dauwamar da ni a gidan aurena to zan aikata ko da kuwa ba zan samu farinciki ba. “Akwai abun da za a shirya mata?” “Aa a gidansu aka aiko mata da abinci idan ta dawo” “Hakan yayi kyau, Allah ya dawo da ita lafiya” “Ameen” Ya sumbanci hannuna daga haka zancen ya sauya salo, sai dai hakar bata kai ga cin ma ruwa ba yayi saurin janye jikinsa ya tashi ya saka tufafin bachi ya kwanta, ni ma na saka nawa na kwanta. A weekend din da ya fada a weekend din ta dawo domin ya zo yayi min sallama ranar assabar ya fada min ta dawo zai kwana a gurinta. Na masa addu'a kuma na mika gaisuwa ta a gurinta, na raka shi har gurin mota ya shiga ya fice ya bar ni tsaye ina kallon gate din gidan. Idan har abun da nake ji a yanzu haka Aisha da Safeena suka ji lokacin da aka auro ni, gaskiya sun yi juriya domin na ji kamar na samu wuka na dabawa kaina da shi mu mutu gaba daya, kallon wanda kake kauna a tare da wata abu mai matukar ciwo da zafi. Falo na shigo na zauna, ina ayyanawa kaina cewar ba zan yi kuka ba, ni ma ya kamata na zama mai juriya mana na zama kamar sauran mata. Na karafafa kaina guiwa kuma na yi nasara domin ban bari hawayen bakinciki sun sauka idona ba. Sai na cigaba da rayuwata irin yadda na saba kamar yana cikin gidan, sai a dare ne kawai tsoro ke kama ni shi ma idan na yi addu'a na kwanta sai na kwana cikin sallama. Ranar da yayi kwana biyu a can na girka taliya domin ina tsammanin dawowar a gurin, be fada mana ko kwana nawa zai yi ba amman a ka'ida kwana biyu ake yi ko daya ba kasafai ake uku ba balle kuma sati. A ranar kuma na yi babban bako dan'uwana ya ziyarce ni, daman tun a tafiyan da na yi gida Mama ta fada min Ya Nabill ya fada mata a satin zai dawo. Last chat din da muka yi da shi ma yana tambayar me zai siyo min ne. Na yi murmushi na yi farinciki kamar zan cinye shi sai daka tsalle nake ina rumgume shi. “Wai ke ba zaki girma ba? Miye haka?” “Yaya na jidadin ganinka ne” Mun sha hira yana ta ba ni labarin karatunsa da rayuwar mutanen Sudan abincinsu da tufafinsu ya kuma nuna min hotunan da suka dauka da yan karantarsu wani kuma da mutanen kasar. “Na ji dadin tafiya kasar nan, shiyasa babu ni ba ni da kamar Oga Kareem a rayuwar nan, ina son mutumen nan ya tallafi rayuwata Allah ya saka masa da alheri” “Kareem yana da kirki sosai” Na fada kasa kasa. “Wai ashe sonki yake Noor?” Na kalleshi. “Ta ina ka sani?” “Ranar da aka daura aurenki da Zafeer na saka hotonki ina miki addu'a, sai ya min reply wai Nabil ka hana ni kanwarka ko? Na ce masa oga ai baka yi magana ba ne, Wallahi da ka fada ko bata sonka sai ta aureka, sai yace Uhmm Allah dai ya sa hakan shi ya fi alheri” “Ya ji sauki?” “Ya ji sauki sosai ya dawo da dadewa fa yana garin nan” Ban sake cewa komai ba na tashi na zubo masa taliyar da na dafa, ya ci sosai kuma ya yaba min har mamaki yake wai na yi girki yayi dadi, sai da yamma ya bar gidan na raka shi har gate ban dawo ba sai da na daina hangoshi domin a kafa yayi tafiya sai fa ya kai karshen layin sannu ya samu abun hawa kasancewar unguwar sabuwar unguwa ce ba kasafai kake ganin masu ababen hawa ba. Zafeer be shigo ba sai da Magariba, ya shigo da far'asarsa kamar kullum na tarbe shi na yi masa sannu da zuwa ya amsa min sai na fara cire masa talkamin kafarsa. “No ba sai kin cire ba, ko komawa zan yi, kawai na zo ne na duba ki na tafi” Na kalleshi da mamaki. “Komawa kuma? Kwana nawa ka raba mana? Na yi zaton yau girkina ne” “Noor kin ga ita ba zata take a gari ba, kw kuma kullum a nan kike, shiyasa na yanke shawarar idan tana gari zan rika zama a gidanta sai ta tafi sai na dawo nan daman kwanakin da nake a nan sun fi wanda zan rika yi a can” “Ban taba jin hakan ba, wannan ba adalci ba ne Zafeer, raba kwana ake yi idan biyu ko uku ko sati ko kwana daya, abun da yayi min yayi mata ake yi ba abun da yayi maka ba, kuma tafiyar da take ai tana tafiya ne akan aikinta ba kai ka dauke mata kafa ba” “Na sani, amman ni hakan nake ganin zai fi” “Aa be fi ba kam, shi kenan za a ce idan tana gari ba zan samu mijina ba sai ta tafi? Ka zama mijin Hajiya kenan, wannan ai milkin mallaka ne, ta ina aka taba haka? Ba adalci ba ne gaskiya ni ba zan yarda fa hakan ba” “Ke kin san adalcin ne? Kin san shi kika zabi kudi kika bar ni? Ina ce a karkashina kike yanzu, kuma duk umarnin da na bada shi zaki bi, kuma ke da mai tunani ce yadda yarinyar nan ta zama silar gyaruwar rayuwata har kika gan ni kika aure ni ai ke da kanki zaki bada shawarar yafe mata kwananki har sai ta bar garin nan” Na mike tsaye a fusace na ce. “Ni ban bi kudi na barka ba, kuma ban dawo gareka saboda kudi ba, idan har zan bi kudi to Kareem zan aura ba kai ba, domin ya fika arziki na ninka abun da kake ganin ka tara, kuma shi din arzikinsa ne ba na matarsa ko uban matarsa ba, kuma ban yarda ba ba zan yafe kwana na ba, dan bata fi ni gata ba” “Ta fi ki gata, ta fi ki ilmi ta fiki tarbiya domin bata taba daga min murya ba, bata taba sa'insa da ni ba, ban taba cewa A tace aa ba, kuma bata taba ambatar sunan wani namijin a gaban idona ba, ke kuma muradin kenan Kareem shiyasa kika bishi tun farko kika bar ni, yanzu kuma da kike ganin kamar zaki iya jindadi a gidan sai kika yarda kika aure ni, amman har kina da bakin da zaki ce ina takama da kudin wasu, ke ba kudin kika bi ba? Wane irin roko ne ban miki ba? Wace kalar soyayya ce ban nuna miki ba? Amman haka kika watsar da ita kika auri wanda kika ganin zaki huta a gidansa” Hawaye ya sauke min ina kallonsa. “Wannan ba Zafeer din da na sani ba ne, ba ainahin masoyina ba ne, Zafeer din da yake jin ya fi kowa fahimtata, yake jin ya fi kowa kaunata ta, yake jin shi kadai zai iya zama da ni? Shi a yau yake fada min haka? Yake kyamata?” “Ada kenan kike da wannan kimar a idona Noor, amman daga baya na fahimci waye ke, kuma su waye iyayenki” “Ka sauya Zafeer...” Na fada cikin kuka sai ya mike tsaye yana daka min tsawa. “Ke baki sauya ba? Rayuwarki dabi'unki jikinki komai ya sauya, i know who you're now” “Ka yi gaskiya jikina ya sauya amman zuciyata tana nan a yadda take, shiyasa ka kasa kusantata ji kake wani a jikina ya ragu?” “Wani abun be ragu ba? Yadda kike a da haka kike? Ba ni ne farkon ba ina kishin hakan” Na yi murmushi mai sauti kamin na fada wani irin ihu. “Kasan da duk wannan me yasa ka aure ni?” Ya dauke ni mari sai na kawar da fuska gafe. “Saboda ina sonki Noor, na yi tunanin zan jure bayan auren kuma sai na ji ina kyamar haka, na shirya yin rayuwa mai kyau da ke amman kika watsar da ni, tun a lokacin kimarki da ta iyayenta ta fita idona, daga baya kuma aka ba ni shawarar gwadaki, da na gwada kuma sai na fahimci gaskiya Safeena ta fada kudi kike bi, domin gashi kin amince da ni, saboda na raba ki da Kareem ya karfafa min guiwar aurenki, yanzu kuma burina ya cika fada min me kike saki? Daman ni na san ba za ki taba iya zaman aure da kowa ba, babu wanda zai iya da halinki sai ni, ni kuma kin riga kin zubar da kimarki a gurina, fada min saki kike so?” Na girgiza masa kai alamar aa, ya sake ni na tafi ina? Mutane su min shaidar abun da suka saba? ace TA KI ZAMAN AURE sai dandane take, na jefa Mama a cikin bakinciki? Hudubar da yan'uwan Baba da Mama suka min na watsar da ita na bi son zuciya? Wayarsa ta yi ringing ya ciro wayar ya amsa kiran da yanayin da ya fahimtar da ni Fanna ce. “Hello Babe” “Eh amman gani nan dawowa na je gurin wani abokina ne” Ya yi murmushi sannan ya kashe wayar ya fice ba tare da yace da ni komai ba. Binsa na yi da kallo kamar wata tababbiya kamin na cira kafa na bishi har bakin kofa ina kallonsa ya shiga motarsa yayi mata key ya fice daga gidan. Da gaske tafiya yayi da gaske Zafeer ya sauya da gaske kyamata yake da gaske ya fifita wata akaina yanzu. Na sulale na zauna kasa a cikin kofar hawaye na bin kumatuna majina na fita daga hancina. Ashe ma babu komai a cikin aure sai wahala da bakinciki, ashe ma babu komai a aure sai hakuri da ciwon zuciya, ashe duk masu nuna soyayya suke karya suke. Bana fata amman ko da Allah ya kaddara min fita a gidan Zafeer ni kam na gama aure ba zan sake auren kowa ba, domin na ga aure aure kuma ya gan ni, na dandana shi ya dandana ni na san me ake ji a ciki duk pretending ne. Idan har Zafeer zai iya juya min baya yayi min haka to waye ma ba zai iya ba? Na dora hannaye biyu a fuskata, wai yau ni ce Zafeer ya mara, lallai kaddara ce tabam take ba ni da rabon dacewa a cikin aure, shiyasa a kowane aure mummunan abu yake bina, wannan ma idan ma har auren ya mutu jama'a za su zage ni za su kirga min aure, Mama ma ba zata min uzuri ba, gara kawai na hakura idan ma bakincikin zai yi ajalina na huta. Na gane ni kam ba a raba farinciki da ni ba, kuka na fara yi a gurin tun ina kuka da kuzari har karfi ya kare na fara amai a gurin kamar raina zai fita... Tun da ya saka kafarsa ya fita be sake dawowa gidan ba, haka ya kara kwana uku bayan kwana biyu da yayi a gurinta. Tsoron saki da irin rayuwar da zan fuskarta bayan sakin ya haddasa min tashin hankali da tashin lafiya. Yaushe aka yi auren ma da za ace na fara samun matsala da mijina, koma minene ya kamata na jure na daure na rumgumi kaddarar aure uku ko yanka naman jikina ake ya kamata na hakuri na zauna. Na gwada kiransa a waya amman idan na kira baya dagawa na aika masa sako na bada hakuri nan ma shiru, daga baya idan na kira sai na ji line busy da alama yayi blocking dina ne, hakan kuma ba karamar damuwa ya haifar min ba, kusan rabin rayuwar da na yi a gidan Hafiz ita nake fuskanta a yanzu, domin Zafeer yayi fushi da ni irin yadda Hafiz yayi, banbancinsa da Hafiz ya dawo min bayan kwana ki kadan amman shi sati muka dauka a haka babu aike babu waya babu zuwa dubana. A duk lokacin da tuna Zafeer nake aure kuma yayi min haka, sai na ke ganin kamar waninsa ne aka kawo min aka dauke asalin Zafeer din da na sani. I spend hours ina kuka gaba daya na zama hopeless, tunanin ma sai na rasa ta ina zan fara, ya zaman kama zaren lamarin. Misalin karfe La'asar wani tunanin ya zo min, why not na shirya na tafi gidan uwargidansa matar da yake so a yanzu, na bashi hakuri, domin ban isa na fuskaci iyayensa da zancen ba kasancewar basa ganina da gashi. Ban kuma isa na tafi gidanmu na daga hankalin Mama kuma na janyowa kaina fadanta da zaginta, na san laifina zata gani ba nasa ba. Tashi na yi na alwala na yi sallah La'asar sannan na dauki abaya na saka a saman atamfar dake jikina na bude zip din dake jiki ya sauka har kasa. Sannan na dauki jakata da wayata na fito rike da makullin gidan, a kofar falo na saka talkamina na rufe kofar falon na fita. Karnunan dake tsakar gidan suna ganin fitowa na suka fara haushi, domin har yau har gobe zan saba da su ba, su ma ba su saba da ni ba, a duk lokacin da na fito sai sun yi haushi. Na fadawa mai gadin kar ya bar kowa ya shiga gidan domin zan fita, addu'a yayi tare da fatan dawowa lafiya. Na fita ina tafiya a hankali a hanya na rufe kaina ruf da babban mayafin abayata, tafiya sosai na yi kamin na samu Napep hakan ya saka ban tsaya tayawa ba na hau na fada masa unguwar da zai kai ni. Wani bangarena na zuciyata na fada min tafiyata zata iya kara laifi, dayar kuma tana karfafa min guiwar idan na tafi na ba shi hakuri wata kila zai dube ni ya yafe min. A kofar gidan aka saukewa na sallami mai Napep na kwankwasa gate din, abun da Zafeer be fada min a lokacin da yake nuna min gida shi ne, sai an bincike waye zai shiga kamin a bar mutum ya shiga. Mutanen da suke gadin gidan sun fi kama da jami'an tsaro, sai dai kuma babu uniform a tare da su sai bakin wando da riga. Sai da dayan ya fara lekowa ta wata karamar huduwa dake jikin gate din sannan ya bude. “Lafiya?” “Na zo gurin Zafeer ne ko yana ciki?” “Wacece ke?” Cikin tsoro da faduwar gaba na ce “Noor ka fada masa Noor ce zai gane ni din matarsa ce” Mutumen mai kirar manyan duwatsu ya kalli daga sama har kasa sannan ya ce. “Baya gidan ya fita” Na ji babu dadi tafiyata ta zama aikin banza kenan. “Amman matarsa tana nan?” “Eh tana nan” “Dan Allah ka fada mata zan shigo na jira shi ya dawo?” “Ta san da zuwanki?” Toh ashe tana da matsayin ne har haka ko da yake ance mahaifinta babban mutum ne kuma ita ce babbar yarsa mai tafiyar da kasuwancinsa dole a bata tsoro da gata sosai har haka. Na fada a raina a zahiri kuma sai na ce “Eh ka fada mata Noor ce matar Zafeer” “Okay ina zuwa” Ya koma ciki na wasu mintuna sannan ya bude ya fito ya miko min wayar hannunsa. “Noor wace Noor” “Noor dai da kika sani, tsohuwar budurwar Zafeer kuma matarsa a yanzu” “Me kike nema?” “Ina son na yi magana da shi ne so badly kuma baya nan ina son na jira shi ne” “Ba shi wayar” Na mika masa, ban san me ta fada masa ba kawai na ga ya bude min kofar gate din yace na wuce. Shi yayi guiding din na har kofar falon, a ranar na raina duk wani kalar kawa da arziki da na taba gani a duniya, harabar gidan ta yi kamar a wata kasar turawa kake ciki ba nigeria ko Kano ba. Ba a wani cika falon da kwalliya ba amman an masa ido irin an burgewa da wayewa kana ganin kasan an kashe nairori ko dollars a kawata falon kadai. Tun kamin ayi min izini na zauna kan sofa laushin kujerar ya wuce yadda nake tsammani. Abu na biyu da idanuwa suka akai shi ne hoton Zafeer da Fanna na aure wani gurin tana sanye da wedding gown wani kuma pre-wedding picture ne. Sun yi kyau ta ko'ina daman Zafeer a kyau ba baya ba, ita ma kuma kyakkyawa ce mai jiki ba kamar ni ba. “Noor Noor Noor haka sunan yake ko?” Na juya na kalli stairs din da take saukowa wando da riga ne a jikinta irin ready-made din nan masu kyau na waje. Ban amsa ba domin na ji a kiran sunan kamar da rainin hankali. Ta zauna nesa da ni tana kallona kamar bata gane ni ba. “Ban fa waye ki ba can you introduce yourself” Is like kamar tana son ta wulakanci a gidanta taya zata ce bata gane ni ba bayan gabatar da kaina da na yi a kofar gidanta. “Karki damu ba gurinki na zo ba, ba dole sai kin gane ni ne” Ta yi murmushin shakiyanci. “Yarinya a falona kike zaune, ki iya kalaminki” “Karki sake kirana da yarinya ni da ke matsayi daya muke” “Karya kike Wallahi har abada ba zaki taka matsayin da na taka ba, ko auren Zafeer kawai da ni ke kin san na ci ki da yaki, kwadayayyiya mai gudun dangi, butulu marar kunya, ashe har kina iya daga kafa ki tako a gidan da Zafeer yake rayuwa da iyalinsa? Bayan kin gushe shi saboda kina ganin ba shi da arziki, to wai me ya dawo da ke yanzu? Har kike ikirarin matarsa saboda baki da kunya?” “Idan na guji Zafeer saboda talauci, ke miyasa kike aure shi? Saboda kin yi alo babu Mijin aure ko? Domin na san mai arziki baya son talaka, shiyasa aka fada mana ai kin ba shi shekara biyu, that's mean kin matso ki yi auren kenan sai kika same shi a arha” “How dare you talk me like that in my own house?” “Saboda kin bukaci haka, na fada miki ba gurinki na zo ba gurin Zafeer na zo” “Ya miki me? Zafeer ai ya gama dake yarinya talkaminsa ma baki isa ki wanke ba a yanzu get out of my house” “Aurensa nake ko be fada miki ba?” Ta mike tsaye tana kallona. “Kam bantan uban nan...!!!” Da alama dai kamar bata da labarin aurena da Zafeer wata kila a boye yayi aure shiyasa ya dauke min kafa gaba daya, kuma ya kasa fada mata a inda yake ranar da ta kira shi ina gidan. A yanzu na gane dalilinsa na cewar na yi shiru idan yana waya da ita ko ma ya fita daga gidan gaba daya dan kar ta ji hayaniyata. Upstairs ta nufa ta haura sama da gudunta, ni kuma tsoron lalata rayuwar Zafeer da aurensa ya kama ni, na tsaya a gidan jiransa ko dai na kama gabana na yi tafiyata? Na kasa tashi tsoro da fargabar abun da zai faru ya hana ni sukunin zama cikin natsuwa a katon falon, mai kama da daular larabawa. Ban tabbatar da gaske boye mata aurena yayi ba har sai da ya turo kofar falon ya shigo hankali a tashe. Kamar be gan ni ba haka ya zo zai wuce ni ya haura sama har sai da na kira shi. “Zafeer...” Ya juyo ya kalleni. “Na'am ya kike wacece ke?” Kokarin yake ya nuna kamar be waye ni ba na lura da yanayinsa da kuma yadda yayi min tambayar. “Kamar ya? Ni ce fa Noor” “Na sanki ne?” Mamaki ya hana ni furta komai. Dawowa yayi saitin da nake zaune ya tsaya “Yanzu na gane ki! Me kike yi a nan?” Na mike tsaye da sauri jikina na kyarma domin tsawa ya daka min har na rasa ta ina zan fara. “I thought tun rabuwar da muka yi a can baya na yanke alaka da ke? Waya nuna miki gidan nan me yasa kike bibiyar rayuwarta a yanzu, and ya aka yi kika shigo cikin falon nan?” Gaba daya ma sai na rikice, shim shirin film ne ake shiryawa da ni ko kuma dai littafi nake karantawa, wata kila kuma mafarki nake domin wannan be yi kama da zahiri ba. “Tambaye ta domin tun da ta shigo gidan nan take fadar ita matarka ce, gaskiyar nake son na sani a yanzu, shiyasa na kira ka” Na juya na kalli Fanna dake saukowa daga stairs. “Me kike yi a nan? Me kike so? Kin guje ni yanzu kuma kin ga na samu kwanciyar hankali kike kokarin ganin kin ruguza rayuwata? A mafarki muka yi aure ko kuma wani sabon makarcin ne kika shiryo” Na nuna kaina wasu hawaye masu zafi na sauko min. “Ni ce baka sani ba? Ni ce baka aura ba?” Murya na rawa nake masa tambayarsa sai ya murje ido ya kara tabbatar da zancensa. “Yaushe na aureki? Ko kin fara shaye shaye ne?” “Aa ban yi shaye shaye ba, ban taba shaye shaye ba, kuma bana fatan yi, amman zaka maimaita hakan a ranar lahira, na yi nadamar saninka a rayuwata, na yi nadamar soyayya da kai, na yi nadamar aurenka Zafeer...” Na juya gurin Fanna na kalleta idon cikin hawaye. “Zafeer shi ya nuna min gidan nan, ni da Zafeer ma'aurata ne a yanzu weather you believe it or not, ya dauke min kafa saboda kin dawo, yace ba zai koma bangarena ba sai kin tafi, ya kama min hayar gida a bypass, ranar da....” Ban iya karasa furucin da na dauko ba saboda marin Zafeer da na ji a fuskata, kamin na maida numfashi ya rufe ni da duka, kamar be san inda na fito ba. Dukan namiji ba daya da mace ba, a take kamanina ya sauya, idona na hagu ya kumbura, bakina yayi kamar an kunsa min dutse a ciki. “Ni ban ce ka kashe yar mutane ba, kawai ka amsa min abun da take fada gaskiya ne ko karya...?” Ban san irin amsar da ya bata ba, domin ban tsaya ya kashe ni ba, da rarafe na fito daga falon mayafin abayata a hannuna, ban tsaya daukar jakata ba, talkami ma ban saka ba na nufi gate, suka bude min na fice ban san ina zan je ba, ba kuka nake ba mayafin a hannu haka na kama hanya ina tafiya ina jin jiri na kama hanya ba talkami ba jakar kudi ba wayar da zan kira na bar komai a gida, mayafin abayar kuma na gagara yafawa na rike a hannu kaina a bude tafiya kawai nake. Gaba daya na rikice mutane sai kallona suke na san suna min daukar mahaukaciya ne, ni ma dai ba zan iya shaida ba a yanzu ko ina da hankalin ko babu, kafa nake ta tafiya bana ma jin gajiya ko zafin hanya, har na iso a gurin mayan itattuwan nan da Kareem ya taba zuwa da ni, a gurin da ya labarta min labarin rayuwarsa kuskurensa da nadamarsa. Kusawa na yi ciki na shiga na isa har gurin da muka saba zama na zauna akan wasu abun zama na sumitin da aka yi a gurin. Sai a lokacin wani irin kuka mai tafiya da numfashi ya zo min. Na kwanta a gurin an takure guri daya daman gurin zama ne ba kwanciya ba, ina kwance hawaye na zuba. “Har abada ba zan taba jindadi ba, yanzu ina zan je? Gida zan koma? Ko na tafi na fadawa Mama? Me yasa Zafeer zai min haka? Ni haka zan yi ta aure ba dacewa...” Magana nake da kaina, ina karkartawa kadan sai idanuwana suka fara min gizo, Kareem nake gani tsaye a kaina yana kallona sanye da facing cap. Tashi na yi sannan na mike tsaye ina kallonsa a yanzu kam na tabbatar rayuwar yau gaba daya mafarkice. Na lumshe ido kamshin turaren mai dadi da ya gauraya da iska bin numfashina. Fuskarsa nake tabawa har lokacin hawaye nake even though idona yana rufe. Ji na yi an rika hannun nawa an sauke daga imaginary fece din da nake tabawa, na bude ido na bi hannun da kallo har aka sauke shi kasa sannan na kalli fuskar Kareem, facing cap dinsa ya cire yana kallona. “Waya taba miki jiki haka Noor?” Lallai mafarkin yau mai nauyi ne, slowly na zube kan simitin na zauna ina lumshe ido kamar mai jin bachi. “Noor...” Na zabura na zabura na bude idon da sauri ina kallonsa. “Subhanallahi, I'm sorry” Na ji ya fada. “Mafarki ne wannan?” “Zahiri ne? Waya taba ki haka? Ina mayafinki ina talkaminki idonki jini ya kwanta, me ya faru da ke?” “Ban dace ba Kareem, Zafeer is the worse, ba zan taba dacewa a rayuwata ba? Ji yadda ya dake ni ya fadawa matarsa shi be sanni ba” Na fada ina kuka sai kuma na yi kauce shi na yi gaba zan kama hanya. “Noor...” Ya sha gabana, iska mai karfi ya hura min a ido har sai da na rufe idon, ruwa mai sanyi na ji ya sauko daga saman kaina zuwa jikina, kamin ya karbi mayafin dake hannuna na karba ya rufe min kaina, a lokacin ne a gane ba mafarki nake ba zahiri ne. Sanyin ruwan ya dawo min da hankalina, bude idon na yi na kalleshi sai na yi sauri dauke kaina na bar shi a gurin tsaye na yi tafiyata. Ina fita gurin na tari Napep na hau, tun da na shiga nake kuka har muka isa gidan, gurin mai gadi na karbi kudi na ba mai Napep din sannan na wuce cikin gidan. Ko da na shiga na samu Jakata da talkamina da wayana akan kujerar falona, da alama Zafeer ya riga ni isowa gidan sai dai ban same shi ciki ba. Na zauna a gurin ina ta rusar kuka har aka sauko daga sallah magariba. Bayan na yi sallah na kwanta a gurin ban daga ba sai da aka yi isha'i. Misalin goma na dare Zafeer ya shigo dakina saman gado ya hau ya kwanta ba tare da yace min komai ba. Da na dago na kalleshi sai na ga hararata yake da alama idan na sake kallonsa zai iya kara min wani dukan. “Gani na dawo sai ki dafa ni ki ci” Tashi na yi na koma falo na zauna har dare ya raba ban iya runtse ido ba. Haushin karnuka na ji yayi yawa sai kuma karar bude gate hakan ya tsorata ni, na kalli agogon falon sai na ga karfe biyu ne da rabi. Da sauri na kashe wutar falon sai na ji ihun mai gadinmu, baya baya yi a lokacin da na ji ana kokarin balle kofar falon. Da gudu na shiga dakina sai na samu Zafeer a tsaye ya shiga bandaki ya rufe. Saman gado na hau ina kallon kofar dakin cikin tsoro da tashin hankali marar misaltuwa. Kamar daga sama maza hudu suka fado dakin dukansu fuskarsu rufe da kyale wasu kuma sun kara da facing. Wutar dakin suka kunna dukansu suna rike da kami irin na jagaliya. “Ke ina mijinki? Idan kuma baya nan ki fada inda za mu same shi” Na nuna kofar bandaki jikina na kyarma. “Kwantar da hankalinki ba gurinki muka zo ba” Ina ji ina gani suka balle kofar bandaki suka shiga ciki, babu abun da kake ji sai ihun Zafeer, duka suka masa abun da yake duka duka na rashin imani, duka na rashin na rashin tausayi, duka na fitar hankali, sai da suka masa jina jina sannan suka fice ba tare da sun harare ni ba balle su taba ni. Sai da suka fice sannan na sauka daga kan gadon jikina na rawa zuciya kamar zata fado domin tsoro, na nufi bandaki na leka sai na same shi kwance jina jina sai numfashi yake, gafen kansa sai jini yake sun yanki hannunsa bakinsa sai jini yake. Hannu na dora a kai na kwala wani irin ihu https://chat.whatsapp.com/Hg8DYsNGb6R8F294cRUu3j *Ina matan da suke son fara siyar da kaya masu sauki kudi, ina masu neman kayan Lagos kaya masu kyau da inganci Ummu Ahmad got you covered tana da kaya masu kyau da inganki order Lagos cikin sauki da rahursa. Ku yi join grp dinta domin siyen daya daya ko sari.* *Ko kuma ku tuntube ta ta wannan line +234 803 235 0261* *** *** *** Gaba daya na rikice babu abun da nake sai ihu kai kace ba dare ba ne, na manta a halin yanzu babu wanda zai iya fitowa ya kawo maka dauki, balle kuma irin unguwar da muke zaune gidanje suna nesa da juna wasu ma ba a gama ba wasu kuma babu kowa a a cikin. Faduwa na yi ita ta haki jikina na rawa sosai gani nake kamar dawowa za su yi. Daker na iya nufar gurin da wayata take na dauka sai kuma na rasa wa zan kira da tsohon daren nan. Can dai dabara ta fada domin na kira Mama two miss calls bata daga ba, na kira line Yaya Nabil na Nigeria shi ma be daga ba. Bayansu ban san waye zan kira ya kawo mana dauki da wuri ba. Na gwada kiran line Anty Larai ita kuma sai na ji wayarta a kashe, ban san kowa cikin abokan Zafeer ba, ba ni da number kowa balle na ce zan kira. A familynsa ma babu wanda nake waya ko chat dashi balle na kira, wayarsa na nufa na dauka sai na samu tana da key, bandakin na nufa cikin tsoro da tashin hankalin da ban saba gani ba na karasa kusa da shi na daga hannunsa na taba thumb print na cire key din, na duba wayarsa na dauki number wayar mahaifiyarta na kira ita bata daga ba. Na kira duka kanensa nan ma babu wanda ya daga. Fashewa na kara yi da kuka domin babu abun da Zafeer yake sai nishi irin na marar lafiyar da yayi nisa, ga jini na fita bakinsa da kansa, ga kuma yankuwa a hannunsa, har number da aka rubutawa Babyna da nake kyautata zaton number Fanna ce sai da na kira ita ma ba a daga ba. Na kira number wasu mutum biyu da nake zaton abokansa su na kamar hadin baki babu wanda ya amsa. “Innalillahi Wa'inna Illaihirraji'un” Shi nake ta maimaitawa gaba daya na rasa me zan yi, zaunawa na yi abakin kofar bandakin ina kallonsa, sakarci da shashanci irin nawa zuciyata sai raya min take Zafeer mutuwa zai yi. Sy waye ma mutanen nan ma? Me yayi musu? Ko dai Fanna ce ta turo ayi masa duka? Wata kila kuma mahaifinta ne, saboda ya boye musu cewar yayi aure da ni. Shi ne abin da zuciyata ta fi raya min, sai idan kuma fada yayi da wani kamin ya iso gidan ya turo a masa duka ko kuma suka yi masa. Da ace wani abu suka zo nema za su bukaci kudi ko abun kudi amman ba su tsaya daukar komai ba suka masa duka suka tafi, kuma ni ba su taba ni ba, gaskiya da alama akwai abun da ya aikatawa wani ko kuma mahaifin Fanna ne, domin bana jin ita din kanta zata iya aikowa ayi ma mijinta wannan mummunan raunin da ya sauya kamaninsa. Dankwalin atamfa ta na saka na daure masa kai, na saka tissue na tare jinin dake fita bakinsa, na zauna a gurin ina ta Kallonsa tsorona daya kar ya mutu, gaba daya ma na manta da nawa dukan zugin jikin da nake ji da komai ya bace min. Sai asuba aka fara maido mana da kira, daga kan Mama har Ya Nabil, ta wayarsa ma ana ta kira idan na daga na fada musu abun da ya faru da kuma halin da yake ciki sai hankalinsu ya tashi, domin a lokacin ya daina nishin da yake, sai na taba hancinsa kawai nake iya jin numfashinsa. Mahaifiyarsa ce mutum na farko da ya fara dira gidanmu tare da wasu maza biyu da ban san su waye ba suka dauke shi suka saka a Napep tana ta kuka, bayanta na bi sai na fita sai na ga irin barnar da aka yi na lalata gate din gidan, Mai gadin ma ban san a ina ya gudu ba domin babu shi babu labarinsa. Aa tare muka isa babban titi amman babu abun hawa domin yanzu ake saukowa daga sallah azuba. Umarni ta yi min da na koma ita kuma ta kama hanyar tana ta tafiya tana kiran wani a waya. Ban yarda na koma ba domin ganin nake kamar dawowa zasu yi su min duka. Ina gurin Yaya ya kira ni na fada masa gurin da nake ashe yana gidan ma sai ganinsa na yi da police tare da Mama, da sauri na rumgume Mama ina kuka. Ya Nabil ya shiga haske jikina da wayarsa police din ma suka haska ni. “Ke ma sun miki duka ko?” “Aa ba su min duka ba Wallahi ba su taba ni ba” “Ga fuskarki ya kumbura idonki ma haka” “Wallahi ba su taba ni ba” “To miye a fuskarki?” Mama ta tambaya na kasa amsawa. “Akwai abun da kike boyewa ne Noor?” “Zafeer ne yayi min duka jiya” Na fada cikin kuka. Mama ta saka salati “Shi Zafeer din ne yayi miki duka?” “Eh” “Me kika masa?” “Saboda na tafi gidan matarsa, ya ji haushin haka saboda be fada mata yayi aure ba” “What?” Cewar Yaya Nabil, police din da suke tare da shi suka ce. “Ku yi hakuri dan Allah sawun giwa ya take ba rakumi, bari mu karasa gurin na duba kuma a tabbatar yana raye duk abun da zai biyo baya sai ya biyo” Su suka kawar da komai, muka dunguma gaba daya muka isa gidah. “Ni ba su min komai ba, cewa suka yi ba gurina suka zo ba?” Na bawa police din amsa bayan sun gama duba gidan. Har haske ya fara fitowa tambayoyi suke min yadda mutane suka shigo da kuma irin kamamin da suke dauke da shi, har tambayar suke ko zan iya gane fuskarsu, na amsa da aa ko da na ga fuskar ba zan fada ba su ce ni na fada balle ma ba zan iya shaidar fuskar kowa a cikinsu ba domin sun rufe fuskokinsu gaba daya. Ni da Mama da Yaya a gidan muka yi sallah asuba, Mama sai kallon fuskata take da hannayena da suke da jan duka har lokacin. “Wai yanzu duk wannan raunin dake jikinki Zafeer ya ji miki shi?” Na sauke kaina kasa. “Me kika masa? Tun yaushe ya fara dukanki?” “Jiya ne kawai...” Na labarta musu abun da ya faru ban boye komai ba. “Meyasa baki fada min ba? Shegiya ce ke da zai boye aurenki? Ko kuma ita wanda yake aure ta fiki ne? Ko kuma ke ya maida yar talakawa marar gata? Miyasa baki fada min ba tuna ranar farko da ya mareki?” “Na san ko na fada ba zaki yarda da ni ba, zaki ce laifi na ne” “Dole a inda kike da laifi a baki laifi, amman gurin da kike da gaskiya dole a fada, babu kalar dukan da ubanku be yi min ba, amman ni ba zan yarda ayi ta azabarta da ke da duka ba, zan baki shawarar yin hakuri ko wane kala ban ce da duka ba, mu da muka haife ki kadai muka isa miki wannan” Police din da suke falo dayan ya leko yana bawa Mama hakuri wai ta sassauta muryata daga fadan da take saboda lamarin da ya faru. A madadin yin shiru sai Yaya ya fara nasa fadan. “Abun haushi yanzu Zafeer din ne zai daga hannu da kansa ya dake ki? Saboda yana jin ya kai? Ai kara da aka masa wannan daukan ma ko waye yayi masa dukan nan Allah ya saka musu da alheri, amanarki ce ta fita” “Ina zaton mahaifin Fanna ne suka aiko ayi masa duka saboda ya boye musu aure” “Idan tsoron matarsa yake tun farko saboda me zai aureki?” Mama ta fada a fusace, yau kam na ga fushin da ban saba gani a fuskarta ba. Police din sun yi dan rubuce rubuce suka sake min tambayoyi sannan suka tafi bayan sun fada mana wai za su sake daukar statement idan ya farfado, wayar Zafeer dake hannuna Mama ta karba ta mikawa Police din ta ce idan sun tafi su bashi, tun a lokacin na san Mama ba zata je asibitin ba kuma ba zata bar ni na tafi ba, haka kuwa aka yi daga gidan kai tsaye gida ta wuce da ni aka bar police biyu tare da Yaya saboda gudun barayin unguwa kar su shigo su kwashe kayan dake gidan, domin gate din a balle yake kamar dai kofar falona. KAREEM POV. Ya rufe motar ya matsa remote din dake hannunsa ya tabbatar motar ta rufe sannan ya nufi gurin da ya zame masa kamar dole sai yaje, baya son zaman restaurant dinsa a yanzu shiyasa ya saka wani a matsayin manajan gurin ya rika kula da komai a matsayinsa. Zama a restaurant yana tuna masa da abubuwa da yawa na rayuwa da baya son tunawa, and he has nowhere to go now daman can shi ba ma'aboci yawo ba ne haka ma ba shi da kwashe kwashen abokai, iyakanci ayi zumunci sai kuma idan wani abu ya taso. Yana rike da gorar ruwansa ya ratsa ya shiga gurin, kusan tun da ya dawo ba daga jinya ba ya da wani gurin zama sai nan, yanayin gurin yana masa dadi, kuma yana tuna masa da abar kaunarsa. Yayi mamakin hango mutum kwance a gurin timinti da ya saka aka gina a gurin saboda da zama, karasa yayi gurin sanye da facing Cap dinsa ya leka fuskar wadda take kwance ga mamaki sai ya ga Noor.... Yanayinta furucinta da kuma acting dinta ya karantar da shi bata san me take ba, ko me ya faru da ita abu ne da ya taba ta sosai ga jikinta na nuna duka, ga shi kuma ta furta da bakinta, yayi duk abun da zai iya na dawo da ita hayyacinta na zuba mata ruwa a kai da hura mata iska kuma yayi nasara ta dawo hayyacin nata. Binta yayi da kallo har ta fice gurin, sai da ya tabbatar ta yi nisa, sannan ya bi bayanta da motar, a lokacin hankali ya rika bin Napep din har zuwa gurin da aka sauketa. a zauna a motarsa ya jira har ta shiga Napep. Nesa sosai da gate din gidan ya faka amman haka be hana shi hango lokacin da ta fito ta bawa mai napep din kudinshi ta koma ciki, kwafa yayi, sannan yayi reverse ya juya da motarsa ya dauki hanyar family house dinsu, dagawa yayi kadan ya ciro wayarsa dake aljihun wandonsa ya duba time sannan ya aje wayar ya cigaba da tukinsa har ya isa umguwarsu, ba kofar gidansu ya faka ba sai ya faka kofar wani matsakacin gida, dauki mask dinsa dake motar ya saka ya daidaita zaman facing cap dinsa sannan ya dauki wayarsa ya bude motar ya fita. Bakin kofar gidan ya karasa ya kwankwansa yaran da ke guje guje suka fito da gudu sai ya rike daya. “Kai Yellow yana nan?” “Aa baya nan ya fita tun dazun” “Kasan inda yake yanzu?” “Aa” “Akwai number wayarsa?” “Ba shi da waya amman dai yana da number” “Ai ka ji matsalar” Ya juya ya nufi motarsa kamin ya bude ya ji ana aika masa da gaisuwar manyan arna. Har hada hannu da hannu yake yana masa gaisuwar yan sara suka. “Sai oga, kowa ya taba ka mu ci bantan ubansa, hayya hayya oga” Kareem ya juyo cire janye mask dinsa yana kallonsa yayi murmushi. “Kanena ya kake?” “Hayya Babban Yaya lafiya ne, babban yayan lafiya kalau ne sai yunwa” “Karka zan faka motata a farkon layi ka same ni a can zamu yi magana yanzu nan” “Angama Babban Yaya” Kareem ya shiga motarsa yayi reverse sannan ya juya motarsa can ya koma karshen layin ya faka motarsa gefen titi. Be dade da fakin din ba Yellow ya iso da gudunsa domin ya san waye Kareem yana kyautata masa iya gwargwadon hali a duk lokacin da ya shigo unguwar ko kuma suka hadu. Kareem ya bude masa mota ya shiga, sai kawai ya kyalkyale da dariya jin sanyin ac ya ratsa shi. “Ya aka yi ka gane ni?” “Haba Babban Yaya ai mutuwa ma ta san mai rai, kowa ya san mai bashi, ina farkon layi na hango motarka shiyasa na biyo da gudu ashe ma gidanmu zaka je?” Kareem yayi murmushi sannan ya gabatar masa da bukatarsa. “To yanzu so kake ayi masa duka, ko ma aika shi barzahu” “Aa duka dai nake son yi masa, ban ce a kashe shi ba ban ce a karya shi ba, just duk kawai kamar yadda yayi mata, so nake ya ji a jikinsa idan akwai dadi, saboda kawai ya mayar da ita marar gata zai mata duka har ya bayyana a jikinta, shi ma ku masa dukan da zai ji a jikinsa, amman ba ban ce ku kashe shi ba, kuma ban ce ku bar wata shaida da za a gane ku ko wanda ya aiko ku ba, abu na biyu kuma karku kuskura ko harar matarsa ku yi, domin kanwata ce, idan kuma baya gidan ku nemi ta fada muku inda yake ku far masa” Kareem na kaiwa karshe ya bude gurin da yake ajiyar kudi ya dauko 200k ya dora masa a cinya, a take yellow ya saka ihu. “Kai Wallahi sai mun ci uwarta, yanzu nan ma zan far masa” “Aa aa sai dare, kuma ba kai kadai zaka tafi ba, ka nemi yan'uwa mana, kamar dai kai ma ba dan gari ba” “An gama Yaya, yanzu ina zan same shi?” “Muje na nuna maka gidan, kuma idan kun yi aiki yadda nace zan kara muku wani abu” “Ayya Sa Ayya sa Babban Yaya godiya nake, nuna min gurin naje an dauko abokan aiki mu duba ta inda zamu shiga gidan” Sai da Kareem ya sake komawa unguwar tare da Yellow ya nuna masa gidan sannan ya dawo da shi. A nan suka rabu Yellow ya wuce gurin neman abokan aikinsa shi kuma ya nufo family house dinsu. Ana bude masa gate gidan ya hango Yusura tsaye sanye da hijab tana dariya, Ex Boyfriend dinta yana tsaye suna facing din juna shi ma murmushi yake. Kallo daya Kareem yayi musu ya dauke kai ya faka kusa da su ya bude motarsa ya fita ya shiga cikin gidan. Ya gaisa da Hajiya Hassana only domin ita ce kadai a gidan yaransa suna islamiya, kannensa ma haka Aaryam ma baya gidan Balle kuma Daddy da ba kasafai yake zama gidan da yamma ba. Be wuce 30min ba ya fito a lokacin Yusura ta sallami masoyin nata ta shiga bangarenta. Motarsa ya shiga ya dauki hanyar gidansa, tukin yake yana ta ganin dukan da Zafeer yayi ma Noor, har yake jin idan be saka an masa duka ba, ba zai samu peace of mind ba. Taya kato kamar Zafeer zai rufe yarinyar da yake ikirarin yana kauna da duka? Bayan dukan ma Allah kadai ya san me yake mata a gidan na bakinciki. Yana son a koya masa darasi ne not because of yana son Noor sai dan yana jin a yanzu ya zame mata dan'uwa, ta shiga damuwa kala kala maza biyu bata dace ba shi da ake kyautata ma zato sai kuma ya zo da haka? Or maybe saboda yana jin yanzu yana da kudi ne he don't know. “Wasu daman talauchi ne ke boye halinsu, maybe kuma he marry her saboda ya dauki fansa, sakarai kawai wawa” Ji yake kamar ya shiga gidan da kansa ma yayi masa dukan. Yayi fakin a bakin gate din gidansa a gefe saboda Safeena ta faka a inda zai fi ya shiga da motarsa cikin gidan. Sauke gilashin motar yayi yana kallonta kamar yadda take kallonsa, ta rame sosai kana kallonta ka san tana cikin damuwa domin babu kuzari a tare da ita. Ta bude matarta ta fito ta iso inda yake. “Na je restaurant dinka ban same ka ba, na zo nan kuma Mai gadi ya hana ni shiga, kuma ka yi blocking dina ta ko'ina idan kuma na kira da wani layin baka dagawa shi ma sai ka yi blocking” “Neman na minene?” “Ina son na yi magana mai muhimmanci da kai Kareem” “Ina jinki” “Maganar ba zata yi a tsaye ba, dan Allah ka saurare ni Kareem, ka ba ni lokaci ka saurari abun da zan fada maka” “Ba ni da wannan lokacin, ki dauke motarki zan shiga gidana, kuma mutanen unguwar nan sun san bana da mata a yanzu ki daina zuwa nemana please, karki zubar min da mutunci” “Kana tsoron kar mutuncinka ya zube ne? To ka aure ni...” Kallonta yake a tsanake sannan yayi murmushi ya kwanta a jikin kujerar motar. “Aure kike son mu yi?” Ta daga mishi kai. “Zan aure ki only on one condition” “Minene?” Ta tambaya da sauri zuciyarta na raya mata abubuwa da yawa. Kareem ya danna horn mai gadinsa ya fito. “Bude mata ta shiga” Mai gadin ya koma ciki da sauri domin duka umarnin da aka ba shi ya bude gate din, ita kuma ta koma motarta ta shiga ta tuka har cikin gidan, sannan Kareem ma ya shiga... Ya zauna a kujerar dake nesa da ita domin ta riga shi shiga falon. Ta daga kai tana kallon falon. “Mafarkina a kullum na yarda zan gina rayuwa da kai a karkashin inuwa daya, na ci buri na aurenka Kareem saboda ban saba da soyayya kowa ba sai taka, ba a taba dandana min zaki soyayya kamar yadda ka dandana min ba, abubuwa da yawa sun faru amman yanzu komai ya kau meyasa ba za mu cika burinmu ba? Baka da aure yanzu Kareem balle kace Yusura kake tsoro, ni kuma na san Abdull sakina zai yi soon” “Be sake ki ba kike fadar mu yi aure?” “Zai sake ni, a saboda ya san gaskiyar komai, ya dauke kafarsa a gidan da dadewa, ya daina kula ni, ya dauke yaransa ya bar ni da ďanka ya koma a dayan gidan da ya bada haya a can yake rayuwa yanzu, saboda an koreshi daga aiki, baya bani komai ni nake yi ma kaina komai, ban san a ina zan kai kukana ba, ba zan iya tunkarar iyayensa ba, ban san ko ya fada musu ba” Hawaye ya zubo mata. “Kareem ka sha fada min cewar kana kaunata, amman wannan furuci ne, yanzu ne lokacin da zaka nuna min gaskiyar kaunar da kake min, ka aure ni sai mu rumgumi dan da muka haifa” Kareem ya daga kai ya kalli falon nasa sannan ya sake sauke idonsa a kanta. “Daya daga cikin illar da kika min kika yi ma kanki kuma kika yi ma yaron nan shi ne haihuwarsa, wannan abun kuma zai bibiye rayuwarki fiye da tawa” “Son da nake maka ya fi wanda kake min, shiyasa idona ya rufe burina na aurenka ne kawai da gina tayuwa ta har abada tare da kai” Yayi murmushi kadan “Hafiz ya taba fada min haka, yace kina son ki haihu da ni ne saboda a gaba ki yi amfani fa hakan ki yake ni, kuma ki aure ni, gashi baya raye amman haka ta tabbata” Ta share hawayenta tana masa wani kallo mai cike da kauna. “Minene sharadin? Zan iya komai saboda na aureka Kareem, a yanzu kai kadai ne last hope nawa” Ya cire facing cap dinsa ya fuskance da kyau. “Zaki iya shafe kazantacciyar rayuwar da muka yi a baya? Zaki iya maida yaron nan a cikinki ya zama labarinsa be wanzu ba? Zaki iya zama a gidan mijinki kina masa biyayya da ladabi? Zaki iya kula da yaranki ki ba su lokacinki ki kula da tatbiyarsu? Ki zauna a gidan mijinki har sai wata kaddarar da ba wannan ba ta raba?” “Kana maganar baya ne fa!” Ya amsa mata a tsawace. “Yes!! Saboda kin bata tarihinki a shinfidar farko, da farko mahaifiyata ta hana na aureki saboda tana ganin wayewarki ta yi yawa Safeena, yadda ya kamata ace ya mace mai tarbiya ta zama baki zama haka ba, amman bayan mun rabu na san idan har wata kaddarar ta fito ke, wata kila zamu iya auren juna, i was stupid as you da farko saboda ina ganin wayewa irin ta wannan zamanin da ta kazanta ita ce soyayya, but then i realize ba son ki nake ba my Heart was young when i fell in love with you, and now kin bata komai” Bata taba zubar da hawaye irin na yau ba, kallonsa take irin kallon da mai yinsa ya rasa ta ina zai aje idonsa. “Ba a taba fada min wani abu mai daci irin na yau ba, duk wani abun da aka taba fada min a duniyar ko na ji ko ya bata min rai, be kai na yau ba? Kuma duk haukankan da kake akan Noor ne, yarinyar da ta riga ta yi aure ta barka, tun da ta shigo rayuwarka ka sauka min, da bata shigo ba da ka aureni da baka shigo rayuwarka ba da ba zaka guje min ba” “Saboda Shigowarta rayuwata ya farkar da ni daga dagon suman da na yi na son zuciya da shashanci” Ta dafa zuciyarta tana kuka. “Ta saka ka ka ci amana kai da ita ba zaku ga daidai ba, ta raba ni da kai kuma ra rusa aurena, ta lalata rayuwata, ba zata karewa lafiya ba, sai na lalata rayuwarta” “Me yasa ni ba zaki lalata tawa rayuwar ba? Meyasa kike bibiyar macen da bata damu da ke ba? Ku mata kullum tunaninku na cutar da yan'uwanku mata ne? Idan har ba zan bar mijinta da yake aurenta a yanzu ya duke ta ya kwana lafiya ba, to ba zan kowa ya taba ta ya kwana lafiya ba, ba kisan wahalarda yarinyar nan ta sha ba, domin ina daukar Noor a yanzu kamar yar'uwata ta jini, daga tashinta zuwa yanzu bata san wani abu jindadi ba, wani namiji be taba tsayawa tsayin daka ya nuna mata gata ba, daga uba har zuwa mazan da take aure, ke fa kin samu gata gurin iyayenki da yan'uwansa, a gidan yan'uwan mahaifinki kika hadu da Abdull su ma sun sonki kamar ba gobe, wace kalar soyayya ce ban nuna miki ba? Wane kalar gata da jindadi ne mijinki be baki ba? Ta ina yanzu Noor zata zama silar bakincikinki?” “Har bada ba zata samu farinciki ba, kuma har abada ba zaka aureta ba, kuma ba zata taba zaman aure ba, TA KI ZAMAN AURE sai ta amsa sunan nan da bakinta har karshen rayuwarta, haka zata yi aure tana fitowa shi ma wannan Zafeer din sai ya sake ta, daman be aureta dan yana sonta ba, sai dan ya gwada shaidar da na yi mata, ba dan taimakona ba da yanzu ma be aureta, ya kuma gwada kuma ta tabbata, ba zata taba samu farinciki a gidan ba, domin yar talakawa mai kwacen maza mai kwadayi irin Noor ba zata iya takara da yar mai arziki ba” Kareem ya hade rai ya ci magani kamar be taba dariya ba a rahirin rayuwarsa. “Tell me you plan all this without telling, you're the reasons behind auren Zafeer da Noor why? Me yarinyar nan ta yi miki? Baki tausayinta da halin da take ciki ne? Karamar yarinya ce da alkamin kaddara yayi mata zane ta kasa tsallakewa” Ta nuna kanta tana hawaye. “Ni baka ganin tausayina? Har yanzu sonta kake yi Kareem? Ai ta wulakanta ta dauki tsohon saurayinta saboda yayi kudi, kuma na san sai ya nuna mata azaba har wadda bata yi mafarki ba, kuma zai sake saboda aure da saki kaddararta ce, har abada ba zata yi zaman aure ba” “Karya kike baki san komai akan kaddara ba, kuma bari na tabbatar min da wani abu, idan Zafeer yayi wawancin sakin yarinyar nan Wallahi! Wallahi!! Wallahi!!! Sai na aureta, ko ana ha maza ha mata, sai na bata gata da kyakkyawar rayuwar da ta rasa, sai na maida ita sarauniyar mata, kuma Wallahi ba zan sake ta ba ko da kuwa zata gasa ni a wuta kullum, idan ba mutuwa ba babu abun da zai raba ni da ita, sai na zame mata gwarzon jarumin da babu irin shi a tarihin rayuwarta, sai na mantar da ita duk wani bakinciki, no one will break her heart again, make my words” Mikewa ta yi tsaye tana haki kamar zata shide. “Hahh hahh ha ha ha ha ha ha ha haha ha ha ha ha ha” Ta dafe zuciyarta ta koma ta zauna, ta kasa yarda Kareem da take kallo a matsayin farinciki kuma fatanta na karshe ne a yau yake fada mata baya kaunarta kuma ya fi kaunar wata akanta. “You re dealing with the wrong person, sai na ga bayan yarinyar nan sai na saka kunci da bakinciki fiye da wanda na saka ta, sai na raba ta da duk wani mai kaunarta yadda ta raba ni da farinciki sai na rabata da farinciki, sai dai ta ga murmushi a fuskar wasu, sai na rabata da duk mai kaunarta” “So tell ke kika saka ma gidan iyayenta wuta saboda ki rabata da rayuwarta da duk masoyanta ko kuma saboda ta yi recording dinki?” Ta yi murmushin takaici ta girgiza kai. “Indai ina raye Kareem sai kun rasa farinciki kai da ita, ka gama da jikina yanzu ka daina sha'awata ko? Ita wane tabbaci kakw da shi cewar tana da tarbiyar? Ita ka san da waye da yi tarayy...” Bata karasa ba ya zabura ya mike tsaye sai ita ma ta yi tsaye tana kallonsa har ya karaso kusa da ita ya nunata da yatsa. “One bad word for Noor... Zan dauke rayuwarki gaba daya...!!” Babu annuri yake kallonta har wani kashe ido yake yana kankance su tsabar tsana da jin haushinta da yake, ita ma kallonsa take tana hawaye masu kumshe da nadama... Kamin ta kauce ta fice daga falon da gudunta. Dinning ya nufa ya ya dora hannayensa ya hura iska, sai da ya burzar da iskar bakinsa sau bakwai sannan ya samu sukunin maida numfashi, kansa ya daga sama ya sauke. Ya fada Safeena tsantsan gaskiyar abun da ke ransa ne a yau saboda ta san bata da matsayi a gurinsa kuma ta san baya kallonta ta kauna ko na kwayar zarra ya sani yanzu ko babu masu gadi ba zata sake sha'awar kusantar gurin da yake ba. Ya raya daren yana tunanin abokinsa da shawarar da yake yawan ba shi a lokacin da yake raye, ya taba fada masa Safeena bata da zuciya mai kyau kuma a yanzu ya yarda domin ga zahirin ya gani, ta dayan bangaren kuma yana murnar hana shi auren Safeena da Momy ta yi a yanzu ya gane ba karamin gata ta yi masa ba. A lokacin da dare ya raba sai ya tashi yayi alwala yayi sallah ya rokawa mahaifiyarsa da abokinsa gafara kuma ya rokawa kansa da yayansa shirya, sannan ya rokawa Noor mafita. Da ya koma kan gado kuma sai tunanin yadda zai karbi yaron dake hannun Safeena ya saka shi gaba, hakkin yaron a kansa da kuma yadda zai bullowa yaransa da yan'uwansa su fahimce shi. Misalin tara da mimtuna Yellow ya shigo gidan bayan Kareem ya bawa mai gadi umarnin barinsa ya shigo. Kareem be shiga da shi falonsa ko wani bangare na gidan ba suka tsaya a waje Yellow na labarta masa yadda suka yi ma Zafeer kacha kacha a daren jiya “Hope dai baku taba matarsa ba?” “Ko hararar ta idan na yi Allah ya tsinen, kallonta ma dan ya zama dole ne, da ba zan kalleta ba” “Kuma baku dauki komai a gidan ba, baku bar wata shaida da za a gane ku ne ba?” “Ni fa sai dai ace dan iska ne amman bana tsaba alkawari kuma na san aikina balle kuma aikin ka babban yaya” Kareem yayi murmushi, ya tashi ya shiga ciki ya fito ya mikawa yellow 300k “Ga sauran biyanku, ko da an kama ku karka kuskura sunana ya fito” Yellow ya kai kasa yana godiya sannan ya karba, yana rantsuwar ko da an kama su ba zai fadi sunan Kareem ba kuma ba zai labarta ma kowa ba. Kareem yayi tsaye yana kallonsa har ya fice sannan yayi murmushi gefen baki wannan ne karo na farko da ya saka aka zalinci wani kuma yake jin kamar yayi daidai har ma yake jin dadi a ransa. *** *** *** Da wani irin karfi ta fisgi motarta ta fice daga gidan, yadda take gudu da mota kai ka dauka bata son ranta, ko kuma she's ready to kill someone domin bata damu da rayuwarta a halin yanzu balle ta wasu. “Ni Kareem zai fadawa haka yau ni k. Kareem zai juyawa Baya? Ni zai wulakanta saboda wata yar iska da bata shirya zaman aure ba kuma ba zata shirya shi har bada” Tana ta magana da kanta tana kuka har ta isa gidanta a harabar gidan ta faka tana ta kuka na rashin arziki kuka sosai kamar wadda ta rasa uwa ko uba. Gaba daya bata lura da motar Abdull dake gidan ba sai da kwantar da kujerar motarta da nufin zata kwanta sannan idonta ya sauka a motarsa dake kusa da entrance. Veil dinta ta saka ta share hawayen ta goge fuskarta tashin hankalin da take ciki fa kuma wanda take tsoron fuskanta a gurin Abdull a yanxu ya mantar da ita tissue dake cikin motar. Bude motar ta yi ta fito kamar wadda ta yi shaye shaye tsabar mayen damuwa da ta yi mata yawa, ta kusan minti uku tana kallon motarsa sannan ta nufi kofar falon ta kai hannu tana hade yawu ta murda ta shiga. A falo ta zame shi zaune da alama yana jiranta ne. Cikin yanayi na rashin gaskiya ta karasa falon ta zauna tana kallonsa sai tauna cingan yake fuska kamar bakin maciji. “Ina kika fito?” “Wata kawata ce Maryam Mamanta ta rasu shi ne na je gaisuwa” “Kuma da gyale? Taya ta kukan kika yi a can?” Ta yi shiru tana hade abu da karfi. “Na baki dama da yawa Safeena, sai kuma kika yi wasa da ita har ta bude miki kofar tafiya ki yi lalata da wani” “Sheri Noor take min” Ya zaburar mata irin na mai shirin kai duka. “Rufe min baki, idan sheri take miki jinin da aka auna ma karya yake ko? Ko kuma kin maida ni mahaukaci?” “Ni da kai duk jirgi daya ya kwaso mu, na san na yi kuskure yanzu ina neman yafiyarka, hakan ba zai sake faruwa ba, kai ma ka aikata laifi ai, na san na fika laifi but I'm sorry” “Sorry banza, ni ban wadace ki? Miye bana miki?” “Kana ba ni kudi da abinci amman baka ba ni kulawa da nake so, baka dubana yadda kake duban matan waje, baka bani cikankiyar kulawa irin ta asalin masu aure, amman duk da hakan na san ni mai laifi ce I'm sorry” “Kin san zafin dake cikin abun da kika aikata? Tun da kika samu cikin yaron nan da awa daya abinci na kike ci, da ruwan gidana kike wanka, karkashin kulawata kike har kika haife shi, na yi masa suna na yi masa hidima kamar ubansa, ba zan iya zsma dake ba Safeena” Ta yi saurin sauka daga kan kujerar tana girgiza masa kai ta rike kafufuwansa. “Aa dan Allah Aa ka hukunta ni da ko wane kalar hukunci amman ban da Saki Abdull, mu rufawa junanmu asiri mu zauna dukanmu masu laifi ne na sani dan Allah ka yi hakuri” Kamar jira yake sai kuwa ya furta mata sakin da kakkauran halshe. “Na sake ki ki bar min gidana in less then 48 hours, na tsane ki na tsani ne ki” Ya fisge kafarsa ya fice ya barta da kallonsa baki sake. Marin kanta ta yi har sau biyu kamin ta rushe da kuka, ta fara yamutsa duk wani abu dake falo, abun da ke fashewa na ta jefar da shi, ta fisgo curtains din dake falon ta zubar kasa kamar mahaukaciya. Kwance ta yi a gurin tana kuka sosai har yarinyar makota dake rika mata yaronta ta shigo kawo mata yaron da ya fara kuka. Cikin kuka ta tashi ta karbe shi ta rufe kofar sai ta rumgume shi tana kuka. Wayarta ta nufa ta dauka ta kira mahaifiyarta, ta labarta mata sakin da Abdull yayi mata. “Me kika masa? Ina Mahaifinsa be sani ba?” “Mun dade a cikin rashin jituwa Ammy, kuma sun sani ba su shiga tsakani ba, yanzu ya sake ni, rayuwata ta kare Ammy” “Rayuwarki bata kare ba Safeena saboda namiji? Karki sake fadin haka” Ta kashe wayar tana kuka gaba daya ta rasa wa zata sake kira again. Rayuwa ta juya mata a yadda bata zata and she's still blaming Noor domin ita ce silar komai. Ji ta yi bata bukatar zama a garin Kano gaba daya, hakan ya saka ta shiga daki ta hada kayanta a akwaiti ta fito falo ta dauki wasu abubuwan da ta san yaronta zai bukata, ta zauna a kujera tana dubawa ko zata samu flight from Kano to Dutse da yammancin nan ba. Sai kuma ta yi rashin sa'a bata samu haka ba, saboda haka ta yanke shawarar driving kanta, domin ta san ko take tasha ba lallai ta samu motar garinsu a yanzu ba, ita kuma ta shirya ko ta halin yaya ba zata kwana a kano ba yau ta riga ta sakawa ranta wannan, and one of her mugun halinta akwai nace akan kudinta. Tana saka akwatinta a mota mahaifiyarta ta kira wayarta ta kwantar mata da hankali kuma ta fada mata mahaifinta yayi waya da dan'uwansa, kuma gobe zai taso daga Dutse zuwa Kano ya ji abun da ke faruwa, after Ammy ta kashe mahaifinta Pro Dahiru ya kira waya ya tambayeta me ya faru. “Ban sani ba, ban masa komai ba” “Ko ma dai minene gobe zan zo, kuma Alhaji yace idan ya dawo gida zai saka a dauko ki ya ji dalilin haka, domin ba shi da labarin komai” “Tohm” Ta kashe wayar, saurin saka kayan ta yi ta shiga motar ta saka danta a front seat ta ja motarta ta fice daga gidan, kunyar hada ido take da Alhaji wanda ya kasance uba a gareta kuma a gurin mijinta, gani take kamar Abdull ya labarta musu komai, but iyayenta fa? Zata iya daukar musu abun kunya ta kai musu? Neman amsar wannan tambayar ne ya saka ta fakawa gefen hanya ta kalli danta sai ta fashe da kuka. Sanin bata da wani gata da mafita da ta wuce ta mahaifinyarta ya saka ta sake hawan titin ta cigaba da tukin, daman ta kware tun kamin aure take tuka kanta sai dai bata gangancin tafiya wani gari ba, ko da rana balle yanzu da ake ta kiran sallah magariba a ko'ina. Ta sani mahaifiyarta zata fahimce kuma zata karbe ta no matter what ta aikata, and tana bukatar komawa gida ko dan ta dauki matakin abun da Noor ta janyo mata, da kuma wulakancin da Kareem yayi mata...! NOOR POV. Kin san halin Noor ba zaman aure take so ba, kin san halin Noor da rashin jin magana ba mamaki wani abun ta aikata kuma ba zata fada ba. Haka kowa yake ta dora min laifi a lokacin da muka isa gida tare da Mama duk yadda ta so ba ni goyon baya sai suka nuna mata ba haka ba, wannan ya saka ta sauko daga fushin da ta yi na daukar zafin boye auren da kuma dukan da yayi min. Aka aje maganar akan cewar idan ya ji sauki za a zauna aji ba asin komai. Mama ta saka na shirya na tafi asibitin duba shi ni ma a lokacin bana jindadin nawa jikin saboda dukan da yayi min, amman a haka na daure, a gurin mahaifiyarsa da yan'uwanta kam ban ishe su kallo ba. Kwana biyu yayi be san inda yake ba sai a rana ta uku ya dawo hayyacinsa a duka ranaku babu ranar da bana tafiya yan'uwana Mama da Baba ma duk sun tafi duba shi har Mama amman ban da Yaya Nabil Mama ta yi juyin duniyar nan yace ba zai je ganinshi ba. A duk zuwan da bake ina samun yan'uwan matarsa ko surukansa sun zo duba shi amman ban ga Fanna ba. Ban shiga duba shi ba sai da kowa ya gama shiga ya rage daga mahaifiyarsa sai shi, ita kanta tsoron kallon da take min nake bana da sakewa a gurin yan'uwansa ko kadan. Daga bakin kofa na fara tsayawa a lokacin da na shiga dakin, ina jin wani abu yana taso min, wulakancin da yayi min a gidan Fanna yana dawo min sabo. Mahaifiyarsa na ganina ta fice daga dakin, Zafeer ya dauke kai yana juya idonsa kamar baya son kallona “Iyaye ne suka ci karfina shiyasa na zo dubaka, ba dan haka ba ba zan zo ba saboda ka ce baka san ni ba” “Ji kamar mai jin maganar iyayenta, na san ai kin yi fatan na mutu ko?” Ban sake ce masa komai ba na fice daga dakin. Ban sake dawowa asibitin ba sai da ya kwana biyar har ana maganar za a sallame shi kamar yadda na ji Kawu ya fada, wannan karon Kawu ne ya rakani da kansa asibitin saboda yana son naje na duba Zafeer, so suke ko ma minene na hakura na zauna saboda an riga an daura kuma mai faruwa ta faru. Na ci kuka sosai kamin na fito muje duba shi saboda bakincikin wulakancin da Zafeer yayi min, kuma na san ba ni da wata mafita a yanzu sai ta zama da shi ko da kuwa zai kashe ni. Har bakin kofar dakin da Zafeer yake Kawu ya rakoni sai da na shiga sannan ya juya. Zafeer yana zaune akan gadonsa jiki yayi sauki amman har yanzu akwai tabo a tare da shi, kuma ba a cire bandejin da aka saka masa ba waya a kunnensa yana amsawa. “Wallahi har yanzu ba a gano ba, amman dai za a gano ko suwa ye da yardar Allah, kuma sai sun fuskanci hukunci” Na dan tabe baki na juya zan zan bude kofar dakin. Sai yayi saurin sauke wayar kunnensa ya ce “Tsaya ina da magana da ke” Na juyo na tsaya har sai da ya gama wayar, sannan ya kalleni. “Cilasta miki ake yi kina zuwa duba ni ko?” Na yi shiru. “To daga yau ba za a sake forcing dinki ba, ba zan bari ki sake zama silar lalacewar rayuwata ba, you broke me first, kin bi kudi kin yi aure, kin bar ni kin manta duk soyayya da wahalar da na yi akanki, you don't care how bad it hurt, gashi amanata ta hana ki zaman aure, daman na gwada aurenki ne dan na gwadaki, na yi nufin sakinki tun a ranar da na aureki but this stupid innocent face dinki ta saka ni daga miki kafa, kin yarda kin aure ni saboda kina ganin na yi kudi ko? Yes na yi kudi ne Noor, amman Zafeer din da kika sani a da ba shi ba ne a yanzu, ba zan iya zama da mace mai irin zuciyarki ba, ba ki kuma kai matsayin da zan zabe ki na bar Fanna ba, saboda haka ki tafi na sauwake miki, daman mutane sun fada ba zaman aure kike so ba, saboda kwadayi da dogon buri karamar yarinya da ke kin lalata rayuwarki, na yi nadamar aurenki Noor! Kuma Allah ya isa amanata da kika ci, har abada ba zaki ga da kyau ba, ba zaki taba zaman aure ba... Kuma Wallahi idan bincika ya tabbatar da da sa hannunki ko wani dan'uwanki aka min wannan dukan na mutuwa sai kin sha mamaki...” Kafe shi na yi da ido ina kallonsa hawaye na sauko min, ashe haka butulci yake da zafi...?Shi ma da nake tsammanin zai rike ni ya sake ni yanzu kuma me ya rage? Me zan fuskanta? Ni haka kaddarata take kenan, mutane sun chanfa ni kuma na chanfu. Kowa na raba sai wani kaddara ta raba mu, wata kila aure baya nufin na rayu da shi.... Na juya na bude kofar dakin na fice ina tafiya kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki, kullum haka nake da tsoron da fargabar abun da zai faru da ni. Nufin nake na samu kulawa da kwanciyar hankali kawai a gidan miji, ko da ban samu soyayya ba zan zauna. Amman na kasa samu ko daya, to ni din me na yi? Aure ya kake min haka? Farinciki me yasa kake guje min? Wane laifi na aikata na cancanci tukuicin bakinciki da kunci da damuwa? Peeee3eeeeeee karar motar dake kokarin kade ni ta dawo da ni hayyacina “Ke baki da hankali ne zaki tsallaka titi babu dubawa” Na kauce na ba shi hanya, na raba gefen hanya ina tafiya, har na isa gindin wata bishiya na zauna a karkashinta na nade kafafuwana na noce kaina kasa ina kokarin hana kaina kuka. Kuka na yi sosai sai da na koshi sannan na cire kaina na saka gefen hijab dina na share hawayena. Number wayar Yaya na kira yana jin yadda na amsa sallamarsa ya san ba lafiya ba, domin muryata ta shake sosai gashi sai shakkuwa nake saboda kukan da na yi. “Noor lafiya?” “Yana nan gafen hanya Yaya Zafeer ya sake ni, bana son na yafi gida, Mama zata min fada ta ji haushina” “Kina ina?” “Ban sani ba a hanya ne na fito daga asibitin ne” “Ki zo gida yanzu nan gani nan zan dawo daga restaurant” “Tohm” Na amsa sannan na kashe wayar na mike tsaye, napep na tsayar na shiga muna tafiya ina hawaye har muka isa. Makota na shiga na karbo kudin na bashi sannan na shiga gidan na zauna jiran Yaya ya kira. Fargabana yadda Mama da yan'uwanta za su kalli abun ne, na san duk yadda zan juya zance na je na dawo laifina kaina zai fada. “Kina ina?” “Ina makota gidansa Maman sani” Na bashi amsa bayan na amsa wayar. “Fito ina waje” Na tashi na fita maman sani na nanata min na karbo mata kudinta da na ara na bawa mai napep. Da ace damuwa mutum ce na tabbatar da zarar mutane sun yi arba da ni za su san sun hadu da damuwa. Na kalli Yaya hawaye na saukowa min, sai ya umarce ni da ni da na shiga cikin gidan, amman na kasa har sai da ya wuce gaba na bi bayansa. Kusan ko wace ya idan tana cikin damuwa mahaifiya ce farkon mutumen dake kawo mata dauki kuma take ganin zata fahimce ta, amman ni tsoro fuskantar tawa nake saboda kaddarar dake faruwa da ni. Na shiga dakin Mama ina labe a bayan yaya kamar waya yar yarinya. “Lafiya?” Ta aje plate din abincin dake hannunta. Yaya ya juyo ya kalleni. “Wuce mana” Ganin bana da wata mafita data wuce shiga dakin na zauna, ya karfafa min guiwa fitowa daga bayansa na nufi gurin da Mama take zaune na zube a kasa na rike kafarta. “Babu abun da nake yi saboda na bata ranku, hankalina da kaddararta ba kamar ta sauran ba ce shiyasa kuke ganina dabam, Mama Wallahi ban fadawa Zafeer wata maganar marar dadi ba, ban ce ya sake ni ba, shi ma dai kawai ban dace ba, dan Allah ki fahimce ni Mama karki dora min laifi, babu mai share min hawaye sai ke, Mama ki yi hakuri da yadda Allah ya tsara min” Tun kamin na farasa zangon da zaren lamarin sakin yake, na ji Mama ta rumgume ni ta fashe da kuka. “Shi ma ya sake ki ko?” Yaya ya amsa mata. “Haka ta fada min, kuma tana tsoron abun da zaki ce” “Me zan ce? Idan na dora miki laifi a auren baya, ba zan dora miki laifi a yanzu ba domin na san yadda kike son Zafeer, kuma idan har zai iya boye aurenki, be cancanci zama da ke ba” Ta dago ni daga jikinta ta share min hawayen idona. “Indai addu'ar uwa tana aiki, Noor sai kin dace na gane kaddarar kenan, amman bakinciki baya dawwama, a kurciyarki kin yi ta shirme, ki yi ta bata min rai mahaifinki ma haka, wata kila a cikin bacin rai na yi wani furuci a gareki ban sani ba, idan har shi ne yake bibiyar rayuwarki ina rokon Allah ya yafe miki ya yafe min, kuma na yafe miki duk wani abu da kika taba min, na janye duk wani kalami da na taba miki marar dadi Noor, albarkar Allah, amincinsa da rahamarsa su zama a tare da ke, Allah ya kwantar miki da hankali ya yaye miki damuwa Noor, Allah ya baki wani gurin da zaki ji sanyi ki manta da dukan damuwa ni ma hankalina ya kwanta.. Allah ya miki albarka Allah ya miki albarka Allah ya miki albarka... ” Ta furta min har sau uku, lallai uwa rahama ce, uwa farinciki ce, uwa maganin dukan damuwa ce, uwa waraka ce uwa mai dadi, take yanke kun fa ya kun in ji Allah sai damuwar sakin da Zafeer yayi min tsoron abun da Mama zata fada ya yaye min lokaci daya. Na kwantar da kaina a cinyarta na rufe ido zuciya fess har ina jin kamar babu wanda ya fi dace da farinciki a yanzu. “Alhamdullahi Allah ya kara miki tsawon rayuwa Mama” Yaya ya fada cikin shauki da jindadi, ina jin lokacin da Mama ta kai hannu ta shafa fuskata da hannunta mai sanyi. “Allah ya hada kanku, ya yaye damuwa ko wace kala ce, duk abun da nake yi ina yi saboda ku gyaru ba dan bana kaunarku ba” Ina daga kwance a cinyarta na cika mata cinya da ruwan hawaye na farinciki. Ashe dai ni ma wata rana zan rabi mahaifiyata ta karfafa min guiwa na ji sanyi. “Duk wanda ya cutar da ke, sai yayi nadama sai rayuwarsa ta fi taki shiga damuwa, bakin uwa lalle ko? To na daura miki shi daga yau Noor, Wallahi ba zaki sake bakinciki ba, indai addu'ar uwa tana aiki to Allah ba zai kunyata ni ba, Wallahi sai farincikinki ya mantar da ke damuwa Noor, Allah ya kwantar miki da hankali, na fara miki addu'a kenan daga yau har karshen rayuwata” A hankali na motsa kaina ina murmushi, ji nake kamar na tsaga cikinta na shiga tsabar farinciki da jindadi. Bayan komai ya laba ne Mama take tambayar saki nawa yayi min na amsa mata da cewar ban sani ba, domin be fada ba yace dai na tafi ya sauwake min dai kawai. Fita ta yi ta fadawa yan'uwan saboda su san halin da ake ciki, a take Yayanta ya fara dora min laifi wai Allah kadai ya san me na fada saboda ban so tafiya ganinsa ba. Abun Mamaki sai gashi Mama ta yi ruwa ta yi tsaki gurin tare min laifina, da alama boye aurena da zafeer yayi ya fi komai yi mata zafi, domin fadar take tun da ta ji cewar ya boye auren yayi a boye ta san da manufa yayi. Har tana fadar ko da na zauna zan yi zaman kunci ne domin alamu sun nuna tsoron matarsa yake kuma ba dan Allah ya aure ni ba. Duk yadda Kawu ya so ya tafi a shirya auren Mama sai ta hana har tana ikirarin ko da ya maida auren ba zata bari na zauna ba. Ta bangaren Baba ne dai ba su saurara ba sai da suka tafi suka samu Zafeer da zancen bayan an sallame shi daga asibitin. Sai yayi ta hada karya da gaskiyar abun da ban yi ba ya fada musu kuma yace shi dai ba zai iya zama da ni ba. Da suka dawo sai suka rufe ni da fada, duk yadda na karyata basa yarda da ni sun fi yarda da zancensa saboda ni noor ce mai tambo kowa a zuci da ido. Na sha mamaki a ranar na fada musu ni da laifi wai har na tafi na ci mutuncin matarsa, kusan duk mazan da na aura babu wanda ya taba juyar da gaskiyar zance ya dora min laifi sai Zafeer. Kuma a cikinsu babu mai kyamata sai shi babu wanda ya aure ni domin daukar fansa sai shi. Daga ranar na maida kur'ane abokina sallar dare ta zama majinginata, sai kuma hakan ya saukar min da natsuwa da kwanciyar hankali fiye da gidan auren ma. Wani abun da na sakawa zuciyata kuma ya zauna min shi ne ba zan sake yin aure ba, domin na gane idan wani yayi rawa aka ba shi kudi ni idan na yi duka zan sha. KAREEM POV. Ya dade yana kallon hoton yaron kama yake da shi sosai fari ne kyakkyawa kamar dai mahaifinsa. “Innalillahi Wa'inna Illaihirraji'un” Ya furta yana jin sauyin yaron da bar duniya tun a satin da ya wuce amman ba shi da labari sai yau. Idonsa ya cika da hawaye hakkin yaron yake tunani idan sun hadu a gaban Allah ya zai yi da hakkin yaron nan me wace kalar amsa zai bada. Yara ma suna da hakki akan iyayensu kamar yadda iyaye suke da hakki akan yara sai dai na iyaye ya fi yawa. “Ka samu abun da kake so Kareem, sai ka je ka kashe auren Noor ka aureta” Shi ne sakon da ta rubuto masa, domin a lokacin bata da labarin auren ya mutu ko yana nan. “Miye hadin mutuwar yaron nan da auren Noor? Ashe har yanzu baki yi hankali ba?” “Ban yi ba, kai ka haukata ni, saboda kai komai na rayuwata ya lalace saboda kai nake kwance a asibiti yau, saboda da bakincikin na butulcin da ka yi min na kama hanya a dare, gashi na halaka kaina na kashe ďana, saboda bakincikinka na dauki tsawon lokaci ban farfado ba, har mutane suna zaton na mutu, ka cutar da ni Kareem kuma hakki na ba zai barka ba? Rayuwata shiga matsala, zaka taba ganin farincikin ba zan tana yafe muku ba, kai da Noor kun ruguza rayuwata” Ta fashe da kuka Kareem na gama sauraren voice note din da ya biyo bayan sakon da ta aiko masa da bakuwar number ya rubuta mata amsa jikinsa a sanyeye mutuwar yaron ta taba shi sosai duk kuwa da kasancewar be yi rayuwa da shi kamar sauran yayansa ba. “Allah yasa hakan ya zame mana darasi, ba ni da sauran wata alaka dake Safeena daga yau” Yana bata amsar yayi blocking din sabon layin nata. Ya aje wayar cikin rashin jindadi. “Na yi kuskure, Allah ka hana na aikata yanzu na gane illar hakan na tuba Allah ka yafe ni, Allah ka so ni, karka duba tarin zunubaina na sani ni mai yawan tsabo ne mai yawan aikata ba daidai ba, na gane kuskurena na tuba ka yafe min Allah” Ya busar da iskar bakinsa be sani ba, da ba zai bari Safeena ta aje cikin nan ba, ba zai bari su kawo ďa ta mummunar hanya ba. Harabar gidan ya fito ya tsaya yana ta kallon gurin tsantsar nadama da damuwa suka yi masa kawaya. *** *** *** Wani kalar numfashi ta aje da karfi ta aje wayar dake hannunta a gefe tana kuka. Ji take ta rasa komai a yanzu saboda ta rasa Kareem, ta rasa aurenta kuma ta rasa ďanta ta kuma rasa lafiyarta tun da likotocin sun tabbatar mata da spinal cord dinta ya samu matsala, tun a wacan daren da zuciya ta debeta ta kasa hakurin zaman garin Kano ta kama hanyar Dutse da kanta bayan kuma bata taba tuka mota da nufin barin gari ba. Idan ta tuna yadda mota ta kwace mata motar sakamakon overtake din da motar bayanta take kokarin yi har ya zama silar da ta bugu babbar motar dake dakon kayan masarufi sai ta ji abun ya dawo mata sabo. Wani karin bakincikin shi ne, sati daya tayi a asibitin Kano amman mutumen da a sanadinsa ta rasa lafiyarta, ba shi da labarinta, a yanzu kuma da ta yanke shawarar aika masa da sakon mutuwar danta da abun da ya faru da ita, madadin ya tausaya mata sai yayi blocking dinta. Hannu ta kai ta shafa gefen kanta kanta da babu gashi ko daya saboda askin da aka yi mata bayan an mahaifinta ya saka an yi mata transfer daga Kano zuwa Dutse domin kula da lafiyarta. Gurin da ba a kwance dinkin da aka mata a kai ba ne take lalabe daga kwancen da take tana kuka. Nadamar soyayyar Kareem take domin ita ce silar faruwar komai, butulcin da yayi mata yafi komai kona mata rai fiye da rasa lafiyarta da ta yi a yanzu. Har ga Allah bata yi tsammani Kareem zai gujeta ba, to a yanzu waye zai rabe ta? Mutumen da ya kamata ya hakura ya zauna da ita a kowane kalar hali domin ya fi kowa amfana da rayuwarta ya juya mata baya. Wata kila da zai dawo a yanzu zata aurareshi ta ba shi lokacinta, domin tana masa wani irin so nw da zata iya mutuwa domin shi ya rayu. “Allah ka isar min a gurin Noor, da tuntuni kashe ki da na huta, Allah ka hana yarinyar nan farinciki” Addu'a take tana jin za a amsa mata, ta manta duk abun da ta yi, zina da aure, hakkin mijinta da na yayanta da na ubangiji, har tana sha'awar haihuwar shege, ta manta daukar hakkin rayuwa uku da ba su mata komai ba saboda selfishness irin nata a kokarinta na boye laifinta. Yan jagaliyar da ta dauka a daren ranar da Noor ta bar gidanta da recording din voice dinta ta biya su suka kona gidan mahaifin Noor a tunaninta Noor tana ciki har ita ta mutu. Har gobe mutanen ba su daina zuwa mata a mafarki ba. Tun a ranar da ta aikata take cikin kunci da azaba na hakkin rai har yau da take kwance akan gado da bata da ikon juyawa, sai an juyar da ita. NOOR POV. Ranar jumma da nake cika wata daya da saki Kawu ya samu Mama da zancen komawarta gidan Alhaji wato mahaifin Abdull, a yadda na lura gaba daya rayuwar Mama bata yi dadi da zancen ba. Ba ita kadai ba ni kaina bana mata sha'awar komawa gidan saboda abun da Abdull ya aikata. Haka ta fada cewar tana ganin mahaifinsa yana tuna mata da Abdul ne tunawa da shi kuma tunawa da yarta ne. “Amman ba shi ya aikata ba Hajara, kuma shariyar nan da kike ganin zaki iya da shi, wahala kawai zaki sha, domin yana da arziki zai iya wasa da shariyar yadda ya ga dama tun da ya san manya, ba ma abun alfaharinsa ba ne ace shi yana shari'a dake yadda yake babban mutum, kuma tun da kika ga ya nace ya ki ya sake ki to yana son ya wahalar da ke ne kawai” “Yaya ba zan iya zama da mutumen nan ba” “Ni kuma a ganina be kyauta ace ke kina gida yarki ma tana gida ba, kamata yayi ace daya daga cikinku tana dakinta, da zaki bi shawarata da kin hakura kin koma dakin mijinki, ita Noor ki barta nan ta zauna har Allah ya kawo mata wani mijin aure” “Zan duba yaya, ba akin ta mutane wai ance da barawo ya gudu, amman dai abu ne mai wahala” “Ki dai yi tunani ko dan mutuncin yarki da ke kanki” Da wannan ya fita a barta. Ni dai bana cewa kuma daman kuma idan iyaye suna magana ban isa na furta wani abun ba a yanzu. Na san matsayi na san limit dina. Na yi idda na wata uku like every Muslim girl. daga lokacin sai na fara tunanin abun da zai dauke min hankali kamar karatu, abu makarantar islamiya wannan dole ce na sani dan haka dole na saka ta a lissafi. Boko ne kawai nake da tantama kamar ba zan iya ba kai nake jin abubuwa sun masa yawa, kuma ban maida hankali na yi karatun da farko da kyau ba kamar Hana gani nake a yanzu kamar zai yi min wahala. Sai dai karfafa min guiwa da Yaya Nabil yayi ya saka na ji sha'awar karatun sosai kuma na ji kamar zan iya, idan ma na zauna ba wani abu zan yi ba sai zaman gida amman idan na hada da karatun both boko and islamiya zan kara ilmi kuma zan samu experience na rayuwa, kuma hakan zai rage min damuwa. “Kuma karatun zai rage miki damuwa sosai, indai zaki iya to sai a nema miki, gashi Yayanki ma ya kusa gamawa, ke ma sai ki samu ko diploma ce ko nce ake cewa ko?” Mama ta fada sai muka yi dariya ni da Yaya “Bari na bincika idan sun fara siyar da form idan kuma ba su fara ba” “Kai da zaka wuce jibi Yaya?” “Ko da na tafi ne zan saka abokina ya siya miki” “Okay wace makaranta?” “Wace kike so? Kuma wane course ma kike so tukuna” Na yi shiru alamar nazari. “Ina son irin aikin da zan rika zaunawa kujera ina juyawa, kuma ina son aikin jarida” “Ai sai aikin jarida kam wannan baki naki” Mama ta fada sai muka saka dariya ni da Yaya. Haka muka yi hira har aka kira sallah magriba. After two days Yaya ya koma makaranta aka bar ni da Mama daman ya dade be samu hutu mai yawa irin wannan ba. Tafiyarsa da sati daya na cika wata uku da sakin da Zafeer yayi min, domin na cika idda ne da period ba da kirgar kwanakin saki ba. Ina kwance misali karfe biyar na yamma wani yaro ya shigo kirana wai wani abokin Yaya Nabill ya aikoshi na zo na karbi sako, ba tare da tunanin komai ba na tashi na saka hijab dina na fito ina rike da wayata, sai da na shiga bangaren Kawu na sanar da Mama dake can tana hira sannan na fita, a tunani abokin Yaya Nabill ne ya zo da zancen karatu na domin ya fada min idan an fara siyar da form abokin sa zai siyo ya kawo min na cika. Abun da zuciyata take raya min dabam abun da idanuwana suka gani dabam. Ban cancanci na juya na koma a ciki na ce ba zan yi magana da shi ba, domin be yi min laifin komai ba a yanzu, sai dai a yanzu ina kallonsa ne da irin idanuwan da nake kallon sauran mazajen duniya, domin na gane ba a gane rashin mutunci ko butulci a idon maza ko goshinsu, sai an zauna. Kallona yake da dan murmushinsa na kwarin guiwa har na karasa na tsaya gefensa. “Barka da yamma” Ya leko fuskata domin na furta hakan ne a lokacin da na dauke ido daga barin kallonsa, na kasa sake masa fuska duk wani shauki da farinciki da nake ji idan na ganshi yau babu shi a tare da ni, saboda maza sun fita raina a yanzu babu wanda ke burge ni kuma babu wanda zai burge ni. “Na bata miki rai ne? Ko kuma baki jidadin zuwana ba ne?” “Ba ko daya?” “Toh meyasa baki far'a? Ba haka na saba ganinki ba Noor, ko wani abun ya faru?” “Babu komai fa Kareem” A take yanayinsa ya sauya ya sauke ajiyar zuciya. “Wata kila ni na bata miki rai ko kuma kin tuna da wani abu ne, ko a gida aka bata miki rai, ko ma minene I'm sorry amman bana son ganin bacin ranki” Na dan daga ido kadan na kalleshi, maza kenan idan ana waje a nuna maka soyayya kamar da gaske, shi ma yanzu da zan aure Allah kadai ya san kalar ayar da zai gasa min a hannu. “If I'm not mistaking yau kike cika wata uku da sakin da Zafeer yayi miki? I count every second, every minute, every hour, every day, every month, a lissafina yau ne kwana casa'in da awa bakwai da minti arba'in da da hudu, da second bakwai takwas tara goma...” Haka yayi ta kirga dakikun yana kallon agogon hannunsa. I was surprised sanin aurena ya mutu ba abu ne da za a boye ba, but counting minutes, hours and day ya ba ni mamaki. “Ta ina ka ji aurena ya mutu har kake kirgawa?” “Lokacin da kika kira Nabil yana tare da ni, tun daga lokacin na fara kirga har yanzu” “Meyasa kake kirgawa?” “Saboda na san lokacin da ya dace na yi magana da ke, gudun kar na taka dokar Allah a karo na biyu, bana son ki haramta a gareni” Ya fada ba tare da ya kalleni ba sai kofar tsohon gate din gidansu Mama yake kallo. “So fada min kin cika idda ko da saura?” “Na cika” Na amsa bayan shiru ya dade da shiga tsakaninmu. Ajiyar zuciya ya sauke ya kalleni yana murmushi mai taushi. “I miss you so much, irin yadda ba zan iya fassarawa ba, shiyasa ban kira ki ba i just need to see your innocent face” Na yi murmushi kadan domin ban san me zan fada ba, i miss him too but not like i use to do. “Noor” Ya kira sunana na dago na kalleshi cikin ido. “How are you Noor?” The way da yayi min tambaya muryarsa so low, kuma ina kallon tsakiyar idonsa ne, sai kawai na ji hawaye ya taru a idona, abubuwan da na manta suka dawo min. “You're not alright i know, kina jin kin tsani rayuwarki kin tsani maza? Kina ji kina ganin kowa azzalumi” Na daga mishi kai. “Yes ana samun haka a mata da maza ko da yaushe akwai bata gari, kuma dace ana yinsa ne idan an dage da addu'a mutanen da baka saka ran za su gujeka ko su cutar da kai ba su suke yi, baki da tabbacin kirkin kowa ni ma karki sheda ni” “Indai har Zafeer zai iya kyamata ya kushe ni, ya wulakanta ni kuma ya sake ni, to kowa zai iya” “Yeah, da zan baki shawara ki yarda da kin koma makaranta islamiya da boko cigaba da karatu you can meet new friends damuwa zata rage miki, ki aje soyayya a gafe auren ma ki dan daga masa kafa” Na share hawayena ina mamakin yadda yake cankar duk abun da yake raina da kuma kudina. “Wannan shi ne plan dinta, ni ban shiryawa aure ko soyayya ba” “Haka ya kamata, karki sake bari wani yayi breaking heart dinki, and ke ma karki sake breaking heart din kowa” “Ni ban taba breaking heart din kowa ba, Zafeer ne, shi ma kuma yanzu na gane hi deserve it” Yayi murmushi mai sauti. “You have no idea i feel lokacin da kika auri Zafeer baki fada min ba, you break my heart into piece, don't try that again” Na dube shi. “Kareem are you hare because you love me?” “No, I'm here because you need me, I'm your best friend remember? Kuma ba miki alkwari zan kasance da ke a kowane kalar hali?” Na daga mishi kai. “Good please smile my princess kin hade rai” Yayi min alamar murmushin da hannunsa, sai gani ina murmushi kamar ba ni ba. Daga nan hira ta canja salo ya dauko min labarin tiyatar da aka yi masa, kamin ya tambaye ni wace makaranta nake son shiga. “Sa'adatu Rimi akwai yan unguwar nan da suke can” “No karki duba yan unguwarku da suke can, wani lokacin makarantar da kawayenka suka yi yawa zai iya sakawa ki kasa maida hankali, zan duba miki wata makaranta mai kyau private school kin ji?” “Amman...” “No amman ki bar komai a hannuna, as your best zan duba miki komai zan kula da komai” “Kareem wayo” Na lankwafe kai a shagwabe na ce. “Wayo kake min Kareem kana min duk wannan saboda kana so na!” “Idan ina kin ki ai ba zan tsaya a nan ba ko? Ke ce dai kike min wayo ki cinye min kudi idan buduwarta ta ji ki sai ta yake ki” “Wacece ka yi budurwa ne?” Ya gyara rayuwarsa with seriousness ya amsa min da amsar da bata min dadi ba kuma ban tsammata ba. “Ina da wanda nake so a yanzu Noor, she's my new girlfriend” “Da gaske?” “Nawa zaki ba ni idan na miki karya? Lokacin da kika yi breaking heart dina lokacin ne Allah ya ba ni wata” “Wasa dai kake Kareem, to a ina take?” “Zaki ganta soon” Kamar hadin baki aka kira wayarsa yana dagawa na ji yace “Baby... Okay na sani kawai ina jin zolaya ne yau, ya aka yi?” Na ji wani abu na rashin dadi ya ziyarce ni, okay na ji ya amsa da shi sannan ya sauke wayar ya kalleni. “Zan tafi akwai abun da kike so?” “Cewa ta yi ka zo tana son ganinka?” Na tambaya abun da be kamata na tambaya ba domin be shafe ni, murmushi yayi ba tare da ya amsa min ya sake tambayar abun da nake so. “Ni bana son komai, amman dai mata ba su da tabbaci ka yi taka tsantsan kai ma” “Zan yi Bestyna” Ya amsa ni, ko ina ruwana a cikin lamarinsa oho shi ma fa da gani zai iya cin amana domin gashi nan daga rabuwarmu har yayi sabuwar budurwa. “Ko Safeena ce?” Na tambaye shi yayinda ya bude motarsa zai shiga, domin maganar ci na take na kasa hadewa kai kace bana da damuwar da ya kamata na damu da ita. Ya rufe motar ya juyo ya kalleni. “In har mata za su kare a duniyar nan, ya rage sauran Safeena kadai to zan yafe aure ne ba zan taba aurenta ba, yana daga cikin godiyar da nake yi ma Allah kuma nake tuna Momyna ina jindadi, na hana ni auren Safeena da ta yi, na ga alfanun hakan yanzu, kuma na gane ba dukan abun da kake so alheri a gareka ba” “Amman ita new girlfriend dinka ta san kana da Safeena? Kuma zata rika maka shi? Ko zaka bar shi gurin Safeena?” Na fada ina yatsina fuska. “Safeena ta yi accident Noor, mijinta ya sake ta ta tuka kanta sai dai kamin ta bar garin Kano ma ta yi hadari, kuma yaron ya rasu, ita kuma har yanzu tana asibiti kuma kashin bayanta ya samu matsala, bata iya tashi” Na rufe baki da sauri tsoron Allah na kara kamani. “Innalillahi Wa'inna Illaihirraji'un, ita kuma haka rayuwa ta yi da ita?” “Ta cancanci fiye da haka karki ji tausayinta, matar nan tana daga cikin mutanen da suka nesanta ki da farinciki, na tabbatar halin da take ciki yanzu somin tabu ne mai wuyar yana nan zuwa, kowa yayi da kyau zai ga da kyau, masu mummunar karshe su ne ba su tsaya sun kyautata rayuwarsu ba” “Amman shi Abdull din yana ina? Meyasa ya sake ta? Da ya hakura ya zauna da ita ai halinsu daya” “Ba ni da labarinsa” Ya amaa yana sauke ajiyar zuciya sannan ya sake bude motar ya shiga, ya dauko katinsa ya ba ni. “Ki kira ni, a tunani yanzu kamar ina da hurumin kiran wayarki ko?” “Ina da number a kaina” Ya kalleni yayi murmushi ni ma na mayar masa, sannan na daga masa hannu na yi masa bye bye as my best friend, domin ni ban shiryawa saurara kowa ba a yanzu, ko da ace ma na shirya shi ai ya riga da ya samu wanda yake kauna a yanzu, oh maza masu abun mamaki kamar ba shi na fada min bayan ni ba zai sake son wata ba, yau shi ne yake ffada min ya samu wacce yake so. “Daman da gani shi ma ba son kwarai yake min ba azzalumi, haka yayi breaking heart din Safeena shiysa yake bibiyar rayuwarsa, shi ma da yanzu ya sake ni” Na fashe da kuka. “Gaba daya maza babu na kirki, shiyasa ma na daina soyayyar na huta” Na share hawayena domin babu dalilin kukan, kokarin goge numbersa nake dake cikin kaina kawai haushinsa nake ji ba zan iya kira ko yin chat da shi ba, ba shi kadai ba mazan duniyar ma gaba daya haushi suke ba ni. Sai da dare nake labartawa Mama yadda muka yi da Kareem na neman a bar masa ragamar komai na karatuna. “Ni wannan abu na ku yana daure min kai, Kareem din nan idan har son ki yake ai ya ci ace ya nuna, tun kamin aurenki na farko yake bibiyar rayuwarki, kika yi aure ya kika fito ya dawo kike sake kika fito ya dawo, yanzu kuma ya sake dawowa, na rasa gane inda ya dosa, ki yi taka tsantsan da shi, kuma ki fada masa na ce aa domin ba aurenki yake ba balle yace hakkinki yana kansa, kuma ba ba haihuwarki yayi ba balle na ce ubanki ne. Na san yayi iya kokarinsa hidima da Nabil kadai abun a yaba masa ne, Allah ya saka masa da alheri amman ke na dauke masa” Abun da Mama ta fada ni ma shi nake ganin ya dace, ni dai a yanzu bana bukatar wani abu nasa ya tafi can su karasa ta new girlfriend dinsa, kuma mama tana da gaskiya meyasa yake min duk wannan bayan ya san yana da wacce yake so. “Wa'alaikumussalam” Na ji Mama ta amsa waya, har tana fadar “Toh Allah yasa lafiya dai” A take na tattara hankalina na maida gurinta. “Toh gobe zam shigo In sha Allahu” Ta sauke wayar. “Mama waye?” “Daga kotu ne aka kira ni wai na zo gobe Kotu tana son ganina” “Amman lafiya” “Taya zan sani? Wata kila wani abun ne ya taso, ta bangaren Alhaji, domin tun da aka shiga kotun nan be taba zuwa ba, kuma ba a taba zama ba, kullum da kalar uzurin da lauyansa yake bayarwa” “Sai idan na je sai mu ji” “Allah yasa mu ji alheri to” “Ameen” “Sun ce na zo da wani nawa” “To ki je da ni kawai Mama” “A cikin manya na suke nufi ba ke ba” “Ni dai gaskiya Mama sai na biki hankalina ba zai kwanta ba idan ba mu je tare ba, a yanzu ke ce kawata ni ce kawarki ni gaskiya sai na biki na san me zai faru?” Mama ta tabe baki tana kallon yadda nake zuba mata shagwaba. “Kyaji da shi, kawunki ba zai bari ba” “Tun yanzu idan zaki fada masa Mama ki ce masa sun ce azo da ni” “Ban iya karya ba” Na bata fuska haka na yi ta maga magiya har ta gaji ta tashi ta bar min dakin. Washe gari da wuri Mama ta shirya shirin tafiya kotu, kamar na san zata je da ni ni ma na tashi na shirya na shafa mai da powder na zauna ina ta kallonta. Ban san me ta fadawa Kawu ba, ya aminta a tafi da ni ji na yi tace na tashi mu tafi, a take na fito da hijab dina dake boye a bayana na saka ina ta zumudi muka kama hanya. Kusan wannan ne karon farko da kafata ta taka kotu, gabana sai faduwa yake ashe ko da baka da laifi tsoro kake ji. A bangaren rigistira muka shiga muka zauna domin mun iso ne tun kamin alkalin ya shigo, wai ance kotu bata jira sai dai a jirata. Da na gaji da zaman ne na fito waje domin zama a gurin da na hango wasu suna zama wasu kuma suna cikin kotun suna jiran isowar alkali. Kamar daga sama na ji an kira sunana. “Noor...” Na kalli saitin da sunan yake fitowa sai na yi arba da ustazun nan da Kareem ya hana ni tsayuwa da shi yana sanye, nuna shi na yi ina kokarin tuna sunansa. KAREEM POV. Driving yake yana murmushi sauyin yanayi da ya gani a fuskar masoyiyarsa Noor a lokacin da ya fada matana yana da wanda yake so, bata iya rike kanta ba kuma ya ji dadin haka. Ya gama karantarta ya san tsare tsarenta shiyasa be fada mata ko nuna mata soyayya ta kawo shi ba, kuma ya goya mata baya akan kudurinta duk kuwa da yana jin kamar ba zai iya jurewa ba. Sai dai a yanzu bakin zaren lamarin yake nema dole, ya tafi mata a yadda take so. Harabar gidansu ya faka ya bude motar ya fito yana murmushi, ya nufi main door ya murda ya bude ya shiga, kanwarsa Khadija dake rike da plate din kankana ta amsa masa sallamar da yayi. “Wa'alaikumussalam Big Bro” “Little Sis ya kike?” “Lafiya kalau, Big Bro yau nishadi kake ji da adama” Ta fada tana kallonsa, ya fadada murmushinsa. “Me kika gani?” “Da na kira ka ka ce min Baby” “To me ai, you're baby, kuma ina kusa da girlfriend dita ne kawai ina son na saka ta kishi ne, shiyasa na fadi haka” Ta wara ido. “Big Bro da gaske? Ina take ina kuka hadu? Wacece ita?” “Zaki santa soon” “Yaushe, da wuri za ayi auren?” “Haka nake fata, kawai ta cika kafiya ne, amman dai na fita wayo ai” Ta yi dariya. “Hajiya na ciki ita tace a kira ka” “Okay” Ya saka fork ya dauki yankan kankana daya da take sha ya kai bakinsa sannan ya nufi dakin Step mother dinsa yana tauna kankanar. “Kin manta ni ko? Sunana Salees. Me kike yi a nan?” “Na zo kotu ne” Na fada da dan kunya. “Gurin me? Kashe aure? Sharia kike da wani?” “Aa ni aurena ya mutu ai, ba aurena ba” “Auren da kika yi har ya mutu kuma?” Kunya ta kama ni na masa alama da ya rage murya. “Ashe ka san na yi aure” “Na sani mana, last zuwan da na yi an fada min kin yi aure” Na yi shiru mutane sai kallonmu suke even though basa jin abun da muke tattauna. “Me kike yi a nan?” “Ba komai” Ai da kunya na fadi cewar Mama ne take son kashe aure bayan kuma ni nawa auren ya mutu. “Kai me ya kawo ka kotun?” Yayi murmushi kawai ya wuce ciki da kallona na bi shi na yi zaton cikin kotun zai shiga sai na ga ya zagaya ta wani gafen ya bi ta wata hanya. Ni kuma na juya na koma gurin da su Mama suke na zauna, babu jimawa aka shigo kiran Mama tare da kawu sai muka dunguma har ni muka bi dan aiken har chamber Alkali ashe daki ne a gefen kotun har da ac da carpet. Mama ta fara shiga sannan Kawu ni ce ta uku, wa zan gani a kujerar dake dakin mai dauke da tebur da takardu ba Salees ba? “Ranka ya dade ga mu” Mama ta fada ni kam na sakar masa ido kamar tv daman Alkali ne, shi kam be yarda ya kalleni ba. Sai magana yake da Mama cikin girmamawa. “Mama abokin shari'ar wanda zan iya kira da mijinki ya aiko da sako ta hannuna yana son na hannata miki” Ya dauko wata takardar ya mikawa Mama ta karba ta bude. Alhamdullahi na ji ta fada tana sauke ajiyar zuciya, ashe saki ne a ciki ban fahimta ba sai da Kawu ya karba ya karanta. “Miye abun godiya a saki?” “Yace ba zai iya ja dake akan abun da yake fa ikon aikawa a take ba, domin shi sanannen mutum ne baya son abun da zai janyo ka ce na ce” “Da haka ya aikata tun farko ai da ba mu kai ga zuwa nan ba, mun gode ranka ya dade” Kunya ta kara rufe ni a lokacin da ya kalleni zai ce ni da Mama ba ma zaman aure kenan domin shi be san other side of the Story ba. “Sannu Noor” Yanayin yadda yayi min maganar sai ka dauka lokacin ne farkon haduwarmu a kotun. “Ina kwana” “Lafiya kalau” Mama ta kalleni. “Kun san juna ne?” Kamin na yi magana yayi murmushi ya ce. “Zan shiga kotu Mama a sauka lafiya” Muka mike tsaye a tare shi ya kwankwasa kofar kotun ma'aikatan suka zo da gudu ni kuma na bi bayan su Mama muka fice. A napep Kawu sai fada yake yi ma Mama akan abun da ya faru ita ce bata ce uffan ba balle kuma da zai iya daukewa da mari. Sai da muka isa gida sannan Mama take tambayar ina na san Alkalin na labarta, yayi so na amman be taba fada min shi Alkali ba ne kawai yace min aikin gobnati yake yi, kuma ban samu damar tsayawa na yi zance da shi yadda ya dace ba balle ya fayyace min komai, ko a lokacin bana son zuwa saboda tsananinsa na son sai na saka Hijab ga wa'azi sama da kasa, gashi idan ya zo be wani dadewa sosai, kamar mai tsoron mutane haka yake amman yanzu na gane dalilin. Da yamma liss aka aiko kirana zuciyata ta raya min ko dai Kareem ko abokin Yaya ko kuma Salees, na fito sanye da hijab sai na samu Salees din a mota zauna ganina ya saka shi fitowa ya jingina da motar yana murmushi fararen tufafin dake jikinsa sun kara masa kyau. Yadda yake da kurciya ba kace Alkali ba ne ashe akwai yara alkalai. “Hajiya Noor” “Ranka ya dade” Na fada ina murmushi. “Ya kike ya gida” “Lafiya Kalau, ya Kotu ashe kai Alkali ne ko?” Yayi murmushi, ni ma murmushin na yi a karo na biyu na kalli gurin da na ji karar rufe mota. Kareem na gani fuska a hade kamar be taba murmushi ba har tsoro ya ba ni. A take nawa murmushin ya gushe, da kai yayi min alama da na wuce cikin gida. Ba ko musu kamar yayi magani sai kuwa na juya da sauri na shige cikin gidan na bar Salees a tsaye. Ina shiga dakin Mama na zube mata a kasa na fashe da kukan shagwaba. “Me ya faru?” “Kareem ya ce na wuce gida, kuma na dawo din na bar Salees a waje” “Waye kuma Salees ke dai har yanzu ba ki bar janyo mana maza kala kala ba ko?” “Wannan Alkalin ne fa shi ne Salees” Mama ta rufe baki. “Kika bar shi a waje kika shigo Noor” “To ba Kareem ba ne wai yace na shiga gida da kai, kuma na shiga” “Ina kika ga Kareem din?” “Yana waje” “Oh Allah ya kyauta, amman haka au wulakanta mutum ne ba kyau, be kamata yayi haka” Na turo baki gaba, ina jin lokacin da aka sake aiko yaro kirana ban fita ba, sai bayan da yaron ya juya ya koma sannnan na tashi na bi bayansa na fita. Kareem kawai na samu tsaye a bakin kofar motarsa na nesa da gidan ta inda ya fakata. “Ina wuni?” Be amsa min ba ha jefo min tambaya. “Ba na ce ki kira ni ba?” “Mantawa na yi” “Amman shi wannan da ya sallamo miki ai baki manta ba ko?” “Ban san ko waye ba kawai dai ance ana min sallama da na fito kuma sai na ga shi ne” “Ke da kika ce ba zaki yi soyayya a yanzu ba, miye na kula shi? Ai da sai ki fada masa” “Ba mu gama gaisawa ba ka ce na wuce cikin gida kuma na tafi” Ya gyara rayuwarsa fuskarsa babu alamar wasa ya ce. “Noor bana son ganinki da kowa, zuciyata kamar zata fashe take ina kishinki” “Kareem kana so na har yanzu?” Ya kalleni irin duban nan dake saukar da rashin natsuwa ga wanda ake yi ma shi har sai da sigar jikina ya tashi. “To ai na ga kana da wadda zaka aura kuma kake so ka fada min you're my best friend kawai” “Kin san me yasa na zo nan?” Na girgiza kai. “Saboda wata magana mai muhimmanci da Hajiya ta yi min a Jiya bayan na bar nan, kuma ganin wannan Ustazun da na yi ya karfafa guiwar abun da nake tafe da shi” Natsuwa na yi sosai ina kallon fuskarsa mai cike da kwarjini da haiba. “Na ce ki kira a jiya me yasa baki kira ni?” Na yi shiru na maida kaina kasa ina wasa da yatsun hannuna. “Saboda baki bukata ne Noor? Kina jin kamar na takura miki ne?” Na girgiza kai da sauri. “Aa” “To miyasa?” “Na ji haushi ka ce ka yi budurwa shi ne na yaga katin” Ido ya kura min yana kallona sai kuma yayi murmushi. “Jiya bayan na bar nan, na tafi gida gurin Hajiya wadda ita ce uwa a agaremu yanzu, ta yi min maganar aure sai na fada mata akwai wanda nake so sai dai ina ganin kamar da dan sauran lokaci be kamata na kusanto da bukata ta aure a gareta yanzu, sai ta tambaye ni wadda nake so yarinya ce ko babba budurwa ce ko bazawara, na fada mata ko wacece ke, sai ta tunatar da ni abun da na manta, cewar aure na biyu zan yi na yi kokari na auri wadda nake so, kuma take fahimtata, kar na cilasta, and i have no time to wast, kuma tana da gaskiya be kamata na daukarwa zuciyyata abun da ba zata iya ba, ba zan miki karya ko na karya zuciyarko ba. Macen da kika ji ta kira ni jiya, kanwata ce na kira ta da Baby ne saboda na auna reaction dinki” “Kenan babu wata sabuwar budurwa da ka yi?” “Babu, ai na fada miki idan har ba zan sake miki ba, to wata ba zata same ni ba, i know baki gama hucewa daga tabon da Zafeer yayi miki a zuciya ba, but noor ina son ki sani ina kaunarki kuma ina rokon alfarma ki ba ni dama ta aurenki a yanzu idan zaki iya, Noor ba zan iya bari ki yi aiki ba ko da kin yi Karatu you need yo know this, Yusura ma ta yi karatu kamin na aureta amman bayan na aureta na hana ta aikin saboda bana ra'ayin haka” Yayi shiru na wani lokaci kamin ya cigaba. “Bana son na karya zuciyarki da wani abun da za ki tararda ba hakan ba ne, burina na mantar da ke duk wani kunci na maida ke yar gata, amman hakan ba zai samu ba sai da amincewarki, Noor shiga karanta a yanzu zai janyo miki idon maza kala kala kuma ina da kishi, bana ra'ayin karatunki kawai na goya miki baya ne saboda abun da kike ra'ayi ne” Jiki ya fara sanyi kalamansa sun sanyaya min guiwa kuma sun saka ni tunani da jin wani iri. “Noor I'm here to beg for your love, kin tambaye ni dazun, zan amsa miki yanzu ina sonki Noor irin da babu wanda ya taba miki irinsa a duniyar nan, idan aka cire iyayenki babu wanda ya kai ni sonki a duniyar nan” Na dan matsa baya idanuwa na cika da hawaye. “Kareem ban shiryawa wannan ba, ni soyayya bata burge ni a yanzu, babu wasu kalamai da namiji zai fada ya siye zuciyata, ma dandana ba daya ba biyu ba na san yadda abun yake, ni bana sha'awar aure a yanzu” Ina maganar hawaye na sauko min. “Yanzu ne lokacin da ya kamata ki yi sha'awar aure saboda ki dandani dadin dake cikinsa, shim ba kin taba fada min ba haka zaki yi ta yin aure har ki dace? Taya kika canja sha'awa? Idan kika ce ba zaki yi aure a yanzu ba, to baki yarda wannan jarabawa ba ce” Ya matsa kusa da ni calmly ya ce. “Please stop crying bana son zubar hawaywnki, i can't force you idan baki shirya ba, zan jira sai kin shirya kin natsu da hakan Noor” Na share hawayen kamar yadda ya bukata sai dai kuma tambayar da ta fito daga bakinsa ta saka wasu hawayen sauko min. “Noor kina so na? Zaki iya aurena?” “Zuciyata babu komai a cikint yanzu sai tsoro da fargabar abun da zai faru da ni, na rufe babin aure ko soyayya Kareem, ina jin tsoro duniyar nan, da zaka hakura da ni da zan fi kwanciyar hankali” “Zan iya hakura da rayuwa Noor, na zabi mutuwa saboda na san idan na mutu zan manta da komai, amman ba zan iya hakura da ke ba son wani abu ne da ba zai taba mutuwa ba, na so ki Noor tun kamin na san ina sonki, na so ki bayan na san ina sonki, and now kaunarki kara tasiri take a zuciyata, i don't want to losing you” Kalamansa suna tsara zuciyata kalmar ina sonki a zahiri aikinta ya riga furucinta isowa a gareni, na sani Kareem yana so na, and na san a yanzu ya shirya aurena kamar yadda ya fada kuma ya kudurta kamin na bar shi ya auri Zafeer. Amman tsoro nake kar shi ma bayan auren wani abu ya faru, kar sai ya aure ni ya fada min ba dan Allah ya aure ni ba, kar sai ya aure ni wata fitinar ta taso. “Tsoro kike ji?” Na daga kai har sau uku ina kuka sosai, ya daure ni da kalamai bana son na amsa da aa, sai dai kuma ina tsoron abun da zan je na tarar. “Ki yarda da Allah, na baki dama ki bawa Allah zabin, ki kai kuka ga ubangiji ki roka ya zaba miki tsakanin aurena da fasawa, ni ma zan yi zan daga miki kafa na zuwan lokacin da zaki gamsu da zabin Allah, amman idan na dawo amsa daya nake son ji Eh ko Aa, abun da duk kika ji zuciyarki ta natsu da shi to shi ne abun da Allah ya zaba miki. Na barki lafiya” Ya bar ni tsaye a gurin ya nufi motarsa ba tare da ya juyo ya ba. A zauren gidan na tsuguna na rufe fuskata da tafin hannayena, irin zuwan da Kareem yayi shi duka mazajen nan suka yi, banbancinsa da sauran shi yace na bawa Allah zabi kuma zan yi hakan. Amman bayan shi babu wanda yake zuwa min da sunan yaudara ko cutarwa, nuna min suke su mutanen kirki ne, kuma zan samu rayuwa mai kyau idan an yi aure, idan kuma aka yi sai labarin ya canja abun da nake kyautata zaton zanje na tarar sai na riske shi a baibai. Ina shiga na samu Mama na fada mata abun da Kareem ya zo min da shi. Sannan na bayyana mata tsorona, na abun da zai je ya dawo. “Akwai tsoro ba ke kadai ba, ni kaina ina tsoron abun da zai faru, amman ina ta yi miki addu'a kuma na san Allah zai karba, ko ma ya karba, ga dukan alama idan kika aure shi zaki jidadi, amman halin nan da Safeena...” “Wallahi Mama Safeena ta zo nan ta fada miki duk abun da ta fada saboda kawai ta bata shi a gurinki domin burinta ta aure shi...” Na fada mata abubuwan da Safeena ta yi da kuma halin da take ciki yanzu, kana na jaddada mata cewar Kareem ya canja yayi kuskure amman a yanzu ya tuba, kuma Allah ma yana son bayinsa masu tuba balle kuma mu da muke yan'adam, kuskuren da Kareem ya aikata ba zai zama hujja ta hana ni aurensa ba. Kaddarata kawai nake tsoro kar ta juya bayan auren. Kamar yadda ya fada haka na dukufa da aikatawa, na kan tashi a tsakiyar dare na yi sallah nafila raka biyu, idan na gama na yi salati ga Annabi Muhammad S A W, na yi daga hannu na yi kirari ga ubangiji sannan na roko zabinsa a cikin auren Kareem ko hakura, ban maida sati ba Allah ya saukar min da natsuwa da aminci akan Kareem tare da hope na jin cewar kamar zan dace. KAREEM POV. “Ya Allah ka sani ina son Noor, ina kaunarta, amman Allah ka fimu sanin abun da ya dace da mu, ka fi mu sanin daidai a cikin zabinmu ko akasin haka, Ya Ubangijina ina rokonka idan aurena da Noor akwai Alheri, ya Allah ka saukar mata da natsuwa da gamsuwa akaina, kuma ka hada kan mu cikin sauki, Ya Allah ina rokonka idan ni din ba alheri ba ne a gareta ka sanya min hakuri a zuciyata, kuma ka sassauta min kaunar da nake mata Ya Rahamanin Raheem, Allah idan ni da ita alheri ne ga juna Allah ka ba ni ita, idan kuma ka ba ni Allah ka hana ni cutar da ita, duk wani abun da zai yi sanadin zubar hawaye a idonta ka hana ni aikata shi ya Allah” Ita ce addu'ar da yake a kowane dare, ya san yana tsakanin kaunar Noor kuma baya jin zai iya cutar da ita ko da kan akaifa ne, sai dai be san gaibu ba, domin matsalolin da suka biyo baya har suka shafeta ta bangarensa be yi tsammanin zuwansu ba. Wannan ya saka yake neman zabin Allah kuma yake addu'ar nema tsare daga cutar da ita. Baya dagawa sai an yi sallah asuba, idan ya gama yake rama bachin da be samu yi ba na yan sa'o'i kadan sannan ya tafi gurin aikinsa. Each and every day kaunar Noor karuwa take a ransa, he miss her so much be dauka zai iya hakuri kamar yadda ya fada mata cewar zai daga mata kafa ba. A yau ma sai da yayi mafarkinta yayi mafarkin rayuwar aurensu irin yadda yake a kowane dare tsabar saka ta da yayi a ransa. Mika yayi hana hamma sannan ya sauke kafafuwansa ya duba wayarsa Miss call ya gani guda daya da bakuwa Number. Be damu ba ya aje wayar ya shiha bandaki yayi wanka ya wanke bakinsa sannan ya fito ya shirya kansa, daman shi gwanin kamshi ne tutare sai da ya kusa karar da kwalba. Yana tsaka da murza wani oil perfume a wuyansa wayarsa dake aje ta yi vibrating ya kalli wayar kamar ba zai dauka ba domin baya son picking bakuwar number, ba dan ma gudun uzuri ba zai iya saka wayarsa a bangaren da idan ba shi da number ka ba zaka iya kiransa ba. “Hello” Ya saka wayar a speaker ya aje ta akana madubin yana cigaba da shirya kansa. Shiru ba a ce komai ba kuma ba a kashe wayar ba. Kallon wayar yayi da dan mamakinsa sai kuma yayi murmushi tunawa da yayi da mutum daya ke iya masa haka ko ma take yi. “Noor My Love besty, my Beb” “Na'am” Ta amsa a shagwabe da sauri ya aje agogon da yake shirin sakawa ya dauki wayar ya cireta a speaker ya kara a kunnensa. “Hey Beautiful, how are you?” “Ina tafiya, i just miss you” Ya lumshe ido zuciyarsa ta yalwanta da farincikin da be taba ziyarta sa ba, yayi murmushi mai matukar kayatarwa. “I miss you more, do you want to see me?” “Uhmm Umm” Ya shafa kansa ya kwanta saman gadon, this is not the first time da Noor tace tana missing dinsa but one hit different. “Okay your prince will arrived soon” Ya mike tsaye da sauri ya aje wayar ya kalli kansa a madubi, sai ya ji kamar dress din be masa ba. “Noo nooo nooooo” Ya cire tufafin da sauri ya saka wasu ya dauko wani turaren ya fesa sannan ya dauki keys dinsa da waya ya fice da sauri. Tafiyar minti 35 ya nade hanya yayi ta a minti goma sha biyar. Daf da kofar gidan ya faka ya dauki wayarsa ya kira line da ta kira shi. “Hey Beautiful na iso” “Okay” Ya sauke wayar yana kallon screen din tsabar kauna heart wallpaper ne a jiki amman fuskar Noor yake gani tana masa murmushi, saboda kaguwa. Bude motar yayi ya fito ya tsaya saitin kofar gate din yana kallon kofar. Cikin natsuwa ta fito gidan tana tafiya a hankali, he count every step nata har ta iso gurin da yake tsaye. Kyakkyawan murmushin dake a kyakkyawar fuskarta ya sautar da shi kamar be taba ganin mace mai murmushi ba haka yake kallon Noor, ina ma ace zai iya bude cikinsa ya sakata ciki ya rufe. “Ina kwana...” Sai da ta fada har sau uku sannan ya dawo daga hayyacinsa a rikice ya ce. “I'm... I'm.. Sorry, Hey Beautiful, Good morning” Sai kuma ta yi shiru kamar wadda ta rasa abun fada. Shi kam kallonta kawai yake kamar ya cinyeta zuciyarta har zalzalza take, be taba jin Noor a yadda take jinta a yau ba, gaba daya ta cika idanuwansa ta cika zuciyarsa da kauna. A hankali ya sauke idonsa kasa yana murmushi he then realize hannayenta duka biyu suna a bayanta a boye. “Why are you hiding your hands? Me ya faru?” “Lalle aka min bana son kowa ya fara gani sai kai” Ya daga kirjinsa. “Of course my Queen, i will glad na zama na farkon fara ganin lallenki my Lord” Ta yi murmushin da ya kara mata kyau musamman da ya bayyana fararen hakoranta, and her giggle laugh is something else da ya ba shi pleasure. Ta cire hannun a bayanta ta daga sama saitin fuskarta ta rufe fuskarta da su ta yadda zai iya ganin tafin hannun da kyau.. _Yes i will marry you❤_ Shi ne rubuce a tafin hannunta da jan lalle with symbol of heart. Karantawa yake yana kara karantawa yake ta karantawa yana hada kalmomin a zuciyarsa kai ka ce ya manta yadda ake karatu gaba daya. Hannayensa ya saka ya rufe idonsa ya girgiza kai sannan ya bude ya sake kallonta ya shafa kansa ya juya ya kwanta jikin motaraa how he wish yana da damar da zai rumgume ya daga ta sama ya juyata just to show her how happy he's. “Alhamdullahi Alhamdullahi Alhamdullahi” Ya furta har sau uku yana jin farincikin da be taba jin irinsa ba, domin be aure matar da ya zaba da farko ba, auren hadi aka yi masa da Yusura, wannan joy and happiness din be san shi ba sai yau. A yanzu take jin zai yi aure abun da ake kira da aure aure that Worth it. Ya taka ya isa gabanta ya tsaya sai ta sauke hannayen a hankali fuskarta da murmushi mai sanyaya zuciya, bata taba masa kyau irin yau ba, be taba jin yana kaunarta irin yau ba. Be taba jin yayi sa'a da dacen rayuwa irin yau ba, ashe haka ake ji idan ka samu wanda kake so? Haka felling din yake? Yau Noor ta amince masa Noor ta yarda ta zama matarsa gonarsa mallakinsa. Har ya bude baki zai yi magana sai kuma ya sauke numfashi ya daga kanshi sama ya sake gode ma Allah, bayan kyautar Yaya da Allah yayi masa idan aka cire lafiya da musulunci be taba samun kyauta mai nauyi mai girma mai faranta rai irin ta yau ba. “Noor...” Ya furta sai kuma ya jimke hannunsa kalmominsa sun kare, yau Noor ta gama masa komai, godiya zai mata ko kuma zai lissafata mata yadda yake kaunarta ne, domin abun da yake ji a yanzu ya wuce so, kauna ce, hawayen da ya gani yana zuba a idonta yayinda fuskarta take dauke da murmushi ne ya saka jin kamar duniyar ma ta rikice. “Come on girl, no more tears ever” Ta dafa saitin zuciyarta tana magana cikin kuka mai dauke da farinciki. “Ban taba amincewa zancen aurena yayi murna ya nuna min jindadinsa kamar yadda ka yi min a yanzu ba, you make me feel special... Allah yasa ka rike ni amana” “But you're special, idan har zan ci amanarki a yanzu ko nan gaba kada Allah ya ba ni ke Noor” Ta share hawayena tana murmushi, mota ya nufa ya bude ya dauko tissue ya bude wani gurin ajiyarsa ya dauko wani tissue da aka yi amfani da shi ya boye a hannunsa sannan ya fito ya mika mata ta karba ta share hawayenta, sai ya mika mata hannu ta bashi ya ciro hannunsa dake baya tsoho tissue da ta taba goge hawaye da shi a gidansa ya dauka ya aje. Ya hada da wanda ta bashi a yanzu ya kai hancinsa ya shamki kamshinta ya lumshe ido ya bude. “I love you so much girl, you're my dream my life, i will be your prince charming” Ya bude idon ya kalleta with so much love, respect and lonely. “Can you say i love you back?” “I love you Kareem...” Ta furta slowly cikin kunya da murya mai dadi har wani lumshe ido take ga murmushi mai rikita hankali Jarumin namiji. “Ooooooooooooooooo...” Ya ji wani abu ya fada a zuciyarsa mai sanyi, ears dinsa suka sosu da dadi mai mantar da bakinciki, is like be taba jin wata kalma mai dadin wanda ta fito yanzu a bakin Saraniyarsa ba. Feeling like ya daga ta sama ya jujuyata ya rumgumeta ya nuna mata yadda yake kaunarta sai dai babu dama domin ba halalinsa ba ce a yanzu. “Ba zan iya jira ba, yau za'ayi mana Baiko” Ya juya da sauri ya nufi motarsa mamaki ya saka Noor binsa da ido baki bude. “Kareem...” Ya girgiza mata kai ba tare da ya kalleta ba. “Please don't, a bari ya huce shi ke kawo rabon wani, irinki ce zan tsaya bata lokaci Noor? Nooooooo ba da ni ba gada a makabarta, just make sure idan suka tambaye ki ki amsa musu da yes” NOOR POV. kallonsa kawai nake har ya tashi motar ya juya da ita ya fice, na taba fuskata na shafa jikinta ina mamakin ko dai na kara kyau ne? Ko kuma wani abu ya ga ni a fuskata da ya saka shi kaunata da jindadin amincewarta har haka? Wani be taba min haka ba, wani be taba sakawa na ji cewar ni din ta musamman ce ba irin yau. Da sauri na dawo cikin gida na dauki madubin Mama dake aje tun bayan da aka kwaso kayan dakinta a gidan Mahaifin Abdull bata taba shi ba. Na duba fuskata ba ga wani abu ya sauya daga kyakkyawar hallitar da Allah yayi min ba, but why Kareem ya bude har haka? Haka yake so na daman? Allah yasa zai rike ni amana dai kar yayi min irin na sauran. Na yi murmushi na aje madubin na kwanta a katifar Mama ina jin kaunarsa na tsara birnin zuciyar zuwa ruhina. Na rufe ido ina jin wani yanayi mai dadi, daman ni a rayuwata ba mai kudi ko mai mukami nake nema ba, ni dai ina neman wanda zai mutunta ni ne zai kwantar min da hankali ya ba ni kulawa da so ni ko da kadan ne. Ban dauka da gaske Kareem yake ba har sai da iyayensa maza suka zo tambayar aurena bayan Sallah La'asar. Kawu ya shigo ya tambaya ko na san da zuwansu, sai na fada masa na san shi kuma mun yi magana da shi amman ban san da zuwansu ba. Na yi wannan karyar ne gudun yayi min fada yace na san da zuwan kuma ban fada musu ba, kuma yace yaushe auren nawa ya mutu amman har nake karkarin yin wani. Bayan fitar Kawu Mama ta shigo ta zauna kusa da ni ta kira sunana cikin natsuwa na amsa. “Na'am Mama” “Ke kika ba shi izinin tambayar aurenki?” “Mun yi magana da shi dazun na fada masa na amince zan aure shi, amman ban dauka zai aiko yanzu ba, ban san da labarin aikowar ba” “Yanzu abun da ya fi muhimmanci nake son na sani shim kina son shi?” Na dago na kalleta Mama bata taba yi min irin wannan tambayar ba, balle kuma Baba. Na daga mata kai. “Kin tabbatar kina son shi? Babu cilastawa ko takurawa ko kawauci? Bude baki yi min magana” “Ina son shi Mama” “Toh Alhamdullahi Allah ya tabbatar da alheri, yasa mijinki ne har aljanna kuma ya sanya alheri ya sa mu ci dadin wannan auren, yasa kuma an tafi kenan Babu dawowa” “Ameen” Ta tashi ta fita. Kawu ne yayi musu jagoranci har Family house din Baba, a can din ba waya suka kira suka aka ba ni Yayan Mahaifina ya tambaya ko ina son Kareem na amsa musu kamar yadda na amsawa Mama. A daren aka yi Baiko duk wani abun da ake kawowa budurwa na baiko sai da Kareem ya kawo min, a daren Farinciki be bar shi yayi bachi ba. Waya muka fara yi yana fada min yadda take ganin ranar yau da daren kamar mafarki daga baya kuma ya kira ni video call na fita daga dakin na dayan bangaren muka yi video call din, bayan da dare ya raba muka yi bankwana na dawo dakinmu na kwanta a lokacin Mama ta yi nisa da nata bachin ma. Na rufe kofar na kwanta sai ya sake kirana video call na yi sa'a wayata tana a silent ne if not Mama zata ji kuma zata min fada. Akan doguwar kujera na koma na kwanta na rike wayar muka cigaba da call din ina magana murya kasa dan kar Mama ta ji, ban san ta ya wayar ta subuce a hannuna ta fadi ba, bachin ma ban san lokacin da ya dauke ni ba. Sai farkowa na yi na ji ana jiran Sallah na tashi na kunna wutar dakin na nufi wayata na dauka. “Good morning” Ya fada yana kallona babu alamar bachi a idonsa tana daga zaune kamar yadda yake a jiya da muka fara wayar. “Je ki yi sallah ni ma zan yi sallah yanzu” “Okay” Na amsa ina murza ido sannan ya kashe wayar, ni kuma na nufi Mama na tashe ta. Be sake kirana ba sai da gari ya waye yayi haske na amsa video call dinsa na samu yana saka button din hannun rigarsa. “My Beb My One and Only, the only girl da ta hana ni zaman lafiya, ta fitini zuciyata ta hana ni zaman lafiya, ta kore kowa ta zauna ita kadai” A laugh laugh out loud saboda ni kadai ce a dakin lokacin, kirarin ya ratsa ni shi kuma sai ya tsaya yana kallona yana murmushi. “Wannan ce Noor dita, wannan yarinyar zan aura mai yawan dariya mai yawan shagwaba mai yawan kiriniya mai yawan rauta mai bakin cin dadi ba wacan mai kuka da kunci da bakinciki ba. Haka na san ki kuma haka nake son ki tabbata har abada” Kusan wunin ranar a tare muka yi aikin asibitin domin ya aje ta inda zan rika ganinsa, ni kuma data da ya saka min tana bude ni ma yana kallon duk wani motsina. Sai idan zan yi sallah ko Mama ta shigo kawai yake kashewa, kamin na sake amsa kira kuma sai ya kira wayata sau goma wai ji yake kamar guduwa zan yi ko wani ya kawace min shi. Da daren ranar da ya zo yayi min tsarabar kayan dadin restaurant dinsa, a nan ma mun sha hira kusan duk dagowar da zan yi idonsa yana kaina. Tun ina jin rashin sakewa har na sake jiki. “Ji nake kamar na cinye ki, kai Noor ina sonki kamar na yi haka ban taba jin haka ba, ban taba jin ina son wata mace yadda bake sonki ba, i want you i can't hide this” Na yi murmushi ina sauke kaina kasa. “Love...” Na kalleshi sai ta taba kirjinsa. “You're, sha zamanki ki huta, daga ke babu kari, Kareem na ki ne har abada, ke din tawa ce har Aljanna, Noor ta Kareem, Kareem na Noor for every, duniyar nan ta mu ce mu kadai” Kauna da shauki sun rufe ni, muka yi hara cikin kauna da son juna, lokacin da zan fita motar sai ya zagaya ya Bude min na fito ya raka ni har kofar gida. “I just want to make sure kin shiga gida Safe, kar sai bayan na wuce wani ya sace min ke” Na yi siririyar dariya a shagwabe na rausayar da kai na ce “Kareem...” “Uhmm Babena” “Good Night” Na juya sai kuma ya kira ni. “My diamond Girl” Na juyo sai yayi blowing kiss gareni. “You hold my love, you're my beath, karki manta da wannan” Na yi murmushi na shiga cikin gidan kamin na kai bakin kofar dakin da Mama take na tsaya na jingina jikin ginin na lumshe ido, kalaman Kareem sun fi tsarabarsa dadi, kamar ya san tunaninsa nake sai ya aiko min da sakon karta kwana. “My Golden Girl, I love you” I reply to him. “I love you too” He then reply back again “I love you more” Na yi dariya sannan na shiga dakin, ni da Mama muka ci muka koshi. The following day Baba Ibrahim wanda yake Yaya a gurin Mahaifina yana fadawa Mama wai Zafeer ya zo yana ta ba su hakuri yana rokon afuwar abubuwan da suka faru. Bayan Mama ta gama wayar takr fada, ni kam na cika da mamakin rashin kunya da karfin hali irin na Zafeer yanzu duk bayan abun da ya faru yana jin idan na yafe masa zan iya komawa na zauna da shi? Ya shirya wata sabuwar azabar ne da zai min ko kuma dai yayi nadamar da bata da amfani ne. “Wata kila dai ya samu labarin baikonki ne yake kokarin ganin ya lalata, domin Yaya Ibrahim ya fada sai da ya fara cewa wai yana son ya maida aurensa ne, suka ce ai kin cika idda har an miki baiko shi ne fa ya fara bada hakuri, sun ce zai zo ya baki hakuri ai” “Kamar ya zai ba ni hakuri? Ni fa hurumin Kareem ce a yanxu, be kamata ya zo ba” “To sun ce zai zo na isa na hana ne Noor? Yan'uwan ubanki ne yadda suka juyaki dole haka zaki tafi, kawai dai yadda za'ayi idan ya zo za'ace baki nan, idan kuma ya bukaci ganina ba zata masa dadi ba, domin sai na dauke shi da mari” Abu kamar wasa, sai ga Zafeer a gidan ya zo ba ni hakuri yana aikowa aka ce bana gidan sai ya tafi haka ya kwashe kwana uku yana zuwa da sunan ba ni hakuri be samu gani ba. Ban yarda na fadawa Kareem ba na san yadda yake ji na a yanxu zai iya sakawa a rufe Zafeer ma, kuma hankalinsa zai iya tashi yayi tunanin ko zan iya barinsa ne na zabi wanda a yanzu bake jin be kai kafarsa ba ma. It take us 2 good months kamin Kareem ya gama shirye shiryensa, sabun lefe aka yi min lefen da ko budurwa sai yar wane da wane ake yi ma, lefe ne mai dauke da komai a ciki idan na ce komai ina nufi tufafi masu tsada da aka siya gurin Khadeeja Candy Store, tun daga kan akwatuna har lace da atamfa da materials, kudin ya bata ta hada min lefe complete kamar yadda ya fada min. Akwane set din akwati an saka min dan kunne zinari da sarka kai kace auren fari ne. Ba a unguwarmu kadai ba har makotan unguwarmu sai da aka yi ta zuwa kallon lefen da ni kaina ban taba mafarkin irinsa ba, ba budurwa ba ce ni, amman haka ya kawo kayan al'adar na auren budurwa kuma ya biya sadaki ya siye ni da kudi har naira miliyan shiri. Da kudin sadakina Mama ta yi hidimar komai tun daga kan siyen furniture da sabin kayan kitchen gurin Khadeeja Candy. Na gayyato mutane da yawa a bikin irin gayyatar da ban samu yi a duka auren da nake musamman na fari kasancewar bana son auren, Mai dilke kullum sai na tafi ta gyara min jiki ta turare ni da turaren kamshi mai kyau mai dadi, wanda zata ba ni na yi tsuguno dabam na jiki ma dabam bayan humurar da take ba ni ina shafawa kullum a jiki da kuma turaren da nake sakawa a ruwan wanka kullum idan zan shiga wanka. Har ta kai ko zama na yi na tashi kamshi ke fita a gurin da na zauna. Na yi Walima a wani babban gida da yake unguwarmu, Kareem kuma ya shirya mana dinner a Charming Hotel dake Garin Kano kusan babu wanda Hotel da ta kai ta kyau da tsari da kashe kudi. Ni da shi muka yi ankon Marron color ni na saka dubai bridel material shi kuma ya saka Gizna mai kyau maroon color. Babu wanda zai kushe hallitar da Allah yayi mana a ranar sai makiyi, domin na yi kyau mijina ma yayi kyau ko da yake ban samu damar kallonsa yadda nake so ba, domin ya tsare ni da ido. Kusan sai da kowa ya shaida yana kaunata a ranar. The following Day aka daure aurenmu a babban masallacin Juma'ah, a ranar Mama ta yi taron biki, and all abun da aka ci ko aka sha a gurin daga Kareem restaurant aka kawo shi, ma'aikatansa ta turo gava dayansu suka tare a gidanmu idan bako ya shigo sai sun tambaye shi me yake so kamin su kawo masa. Bayan Sallah Isha'i manyan motoci na alfarma suka yi layi a kofar gidanmu har sai da suka yi yawa. Ni dai a sabuwar mota aka dauke ni motar da ba a ko cire mata leda ba, na yi zaton tsohon gidansa za a kai ni, gidan da yayi rayuwa a baya gidan da ya zauna da Yusura, amman sai aka kaini wani gida dabam wanda ya fi wacan kyau da fasali, shi ma dai gidan sama ne mai hawa daya sai dai ya fi wancan tsari nesa ba kusa ba. Sai kamshi turaren wutar da Mama ta saka ka yi ke tashi. Na shiga falona da kafar dama tare da bismillah kamar yadda Mama ta fada min na yi idan zan shiga, a lokacin da aka shiga da ni falona sai da na yi kamar na saka karamar ihu saboda murna, i can't believe falona ne, balle kuma dakin da kalamai suka kare akansa, ta cikin farin mayafina nake ganin komai kasancewar mai shara shara ne zaka iya ganin komai. A kan gadona suka zaunar dai suka min nasiha irin ta gwaggwanin, kanen mahaifita ma suka min sannan suka kora kowa suka tafi, ganin cewa ni ba budurwa ba ce a yanzu balle ace sai an tsaya siyen baki. Shi ma dai yan'uwa da abokan arziki sun rako shi suka mana nasiha sannan suka tafi. Mayafina ya fara cirewa ya dago kaina na kalleshi sai ya saka hanayensa duka biyun ya rike fuskata yana yawo da idanuwanshi a fuskata kamin ta samu saka idanuwanshi cikin nawa. Sai kuma ya lumshe ido ya hade goshinsa da nawa, hancinsa ma yana taba nawa ni ma lumshe idon na yi ina jin lips dinsa saman nawa yana motsa su yayin da yake magana. “Na mutu a kaunarki mabanbanta lokuta mabanbanta ranaku, kin zo min a lokacin da ban yi zato ba kika dauke min zuciya kika guda and heart Speak to me, son ki ya fara kamar tsiro, da ya girma sai ya hana ni zaman lafiya, tun ina iya boyewa har hakan ya gagara, Noor har a mafarki zuwa min kike, ada ina jin bancancanta ba amman yanzu Allah ya saka min natsuwar hakan... Ina sonki irin son da kalmomin duniya za su kare gurin bayyana sona a gareki” Na sauke numfashi a hankali mai gauraye da nasa, jin ya daga daga fuskata hawayen da na ke kyautata zaton na farinciki ne a fuskata Kareem ya saka halshensa ya lashe har saman idona da suke rufe. “No more tear my golden Girl” Na ji bakinsa a hancina, a hankali kuma sai na ji lips dina sun jika da yawun bakinsa, he then kiss my front head. Ya mike tsaye ya cire babbar rigarsa ya fita be dade ba ya dawo muka shiga muka yi alwala muka yi sallah, bayan mun gama yayi addu'a ni ma na yi. Ya dauko mana abun tabawa madarar kawai na sha ban iya cin komai ba, shi ma be ci ma, da adama farincikin aurena sa kallona ya kosar da shi. Bandaki na shiga na canja kayan jikina zuwa na bachi, na fito sanye da riga da wando matching color da na shi. Madubi na nufa ina cire agogo da dan hannun dake hannuna. A hankali na ji yana cire min sarkar wuyana ya aje a gaban madubi yana kallon idona ina kallon na sa ta cikin madubi. Hannunsa ya kai ya bude saman rigata kadan ya sumbanci kafadata, ya dora hancinsa a wuyana yana shakar fitinannen kamshin dake tashi a jikina, har wani lumshe ido yake. Juyowa yayi da ni ashe ya bude maballan rigarsa ban sani ba, kunya ta saka ni rufe ido kwarjininsa ya kama ni fiye da kullum. Nawa maballan ya fara budewa ina jin kamar na hana shi domin daren yayi min kamar darena farko a gidan miji. Ban yanke shawarar hanawa ko bari ba, har yayi nasarar bude min rigar bachi, na rufe idona da sauri jin skin dina yana taba na shi, and i feel something so soft, so scent, so fresh, so cool, so hairy har yana shigar min baki. Na ji wani abu so special wani abu mai dadi mai kwantar da hankali mai saukar da natsuwa mai faranta zuciya. Kirjinsa faffada ne sosai ya yawalwace ni na yi lamo a kirjin mai cike da sanyi da yalwar gashi. “I just want to feel the connecting... I love you unconditionally, you're forever mine, at long last we are together...” Ya furta min saitin kunnena har bakinsa yana taba kunena, yana kara rumgume ni, ni na na daga hannayena na rumgume bayansa ina jin gamsuwa da natsuwa, feeling so comfortable, wani spark nake ji daya hada skin to skin heart to heart wani be taba rumgume ni na ji abun da nake ji a yanzu ba. Ɗin din din bugun zuciyata ke tafiya tare da na shi. Mun dade a haka kamin ya dauke ni cak kamar jaririya ya dora akan gado, sannan ya nufi wutar dakin ya kashe, then ya sake dawowa jikina ya rumgume ni ta yadda zan kwanta a kirjinsa. Littafin nan ba free ba ne, biya ki fita hakkin karatu pay 500 to 8036126660 Hadiza Abubakar Opay And send the evidence of Payment to 08036126660 Kirjinsa dake cike da yalwar gashi nake kallo har ya karaso kusa da ni ban sani ba. “Hey Beautiful” Na daga ido na kalleshi sai ya daga min gira ya kashe min ido, murmushi ne ya subuce min na rufe idona da sauri, sai na ji ni a kirjinsa ya rumgume ni ya karbi towel din dake hannuna ya cigaba da goge min gashin nawa dake jike da ruwa. Sai ya goge min gashina sannan ya aje tawul din ya rumgume ni da kyau. “I love you” Na yi lamo kamar babu ni a dakin sanyin dake kirjinsa da ni'imar gashin da Allah ya wadata shi da shi ya saka ni jindadin kwantawa a kirjinsa yatsuna a cikin nasa, ya dora gemunsa a saman kaina yana shafa bayana da hannunsa daya. “Mutanen da suke aurenki suna rabuwa da ke Noor ba su san So ba, ba su san me ya dace da su ba, ba san fahimci rayuwar aure da zamantakewa ba, basa jin abun da nake ji akanki, suna da kuskuren fahimta irin tawa ne” Na dago daga kirjinsa na kalli fuskarsa sai ya sakar min murmushi ya hura min iska a ido ya sake maida ni kirjinsa ya rumgume ni sosai kamar za a kwace masa ni. Sai da muka ji kiran sallah asuba sannan ya dago ni daga jikinsa ya dauke kafafuwana na dora ni akan gadon ya mike tsaye ya isa gurin da tufafinsa suke ya bude ya dauko jallabiya ya saka sannan ya ciro min jallabiyarsa daya ya kawo min. “Zan shiga bandaki na canja” “No a nan zaki canja” Ya fara kokarin cire min tawul din dake jikina. Kunya da mamaki suka rufe ni. “Kareem ba zan iya canja kaya a gabanka please” Ya girgiza min kai. “No please pleasure, ina son na yi rayuwa ne irin ta masoya rayuwar irin wadda na tsara zan yi ban samu dama ba sai yanzu” “Okay Okay zan saka da kaina” Na yi saurin fada sai ya sakar min riga na sauka daga kan gado ina kallon kofar bandaki, ina cira kafa da zimmar zubawa da gudu sai yayi charaf ya cafke ni, ya daga sama ni da shi muka fada kan gado muna dariya. “I knew it, couse i know you” “Kareem dan Allah ka bar ni na canja ba zan iya canjawa a gabanka ba” “Ba dole sai kin bude jikinki ba, amman ina son ki sake jikinki ne da ni from day one saboda ni mijinki ne ABOKIN RAYUWARKI har bada” “Na sani amman ba zan iya canjawa ba” Na fada a shagwabe ina dan turo baki sai ya kama lips din nawa ya rike yana matsawa a hankali. “Dole zaki iya Matar Kareem” Ya kwanta lips din nawa kadan, na yi kamar zan masa kuka domin na ji zafi kadan. “Akwai zafi fa” Ya cire hannunsa ya mike tsaye ya riko ni ya sauko da ni daga kan gadon, sannan ya dauki rigar ya saka min ta sama ba tare da ya cire min tawul din ba, har sai da rigarsa ta sauka kasa sannan ya saka hannunsa ya zare min tawul din ya aje. “Hey Beautiful look at you in my jallabiya” Ya rika fuskata yana juya kaina yana dariya kamin ya daga ni sama yana juyawa kamar wata yar yarinya sai yawo nake a jallabiyar daga hannunta har tsayinta sun min yawa. Sai da ya chakwalkwala ni sannan ya sauke na dauki mayafina na rufe kaina ya shimfida carpet ya jagorance mu Sallar. Bayan mun gama na yi addu'a shi ma yayi sannan ya juyo ya miko min hannunsa na kama, sai ya janyo na dawo kusa da shi ya kwantar da ni a cinyarsa ya tofa min addu'a a kai zuwa fuskata ya shafe min. Ya sumbanci bakina ya sunbanci goshina yana shafa hancina. “Hey Beautiful, Good Morning” “Ina kwana” “Kin kwana lafiya yar kyakkyawata?” Ba daga mishi kai sai ya sake sumbantar saman ido daya ya sunbanci dayan ma. “Zo mu kwanta kamin anjima” Kamin na mike tsaye ya riga ni, ya cire min mayafin ya aje gefe ya kai hancinsa a cikin gashina yana shakar kamshin dake tashi a cikin kaina. “That's my wife” Ya fara daga rigar jikina. Na yi saurin hana shi domin ban gama jiyar daren jiya ba. “Aa aa aa bachi kace zamu yi?” “Yes bachi zamu yi” “Then ba sai na cire rigata ba” Yayi murmushi. “Ba abun da kike tunani ba ne, Wallahi bachi zamu yi normal bachi, but ni bana bachi da matar da nake so da tufafi a jikinta that's my number one rules, because ma'aurata need to cuddle, and duk lokacin za mu kwanta bana son naji wani abu yana taba skin di na, i just want to feel your skin touching my skin, and that doesn't mean zamu aikata wani abu, no ni haka kawai nake so kuma haka nake” “Ni... Ni bana so.. Ni bana bachi babu tufafi” “Beautiful baki da ikon kanki, kina da yancin ki yi yadda kike so a gidanki ko a kaina but ban da wannan bangaren ba zan baki wannan ikon ba, besides ina ce rigar nan tawa ne? So ba ni abuta” Na girgiza masa kai. “Wasa dai kake” “Okay let me show my strong Babe” Ya rage wutar dakin ya fara kokawa da ni har sai da yayi nasarar raba ni da rigarsa, kunya ta saka ni yi masa yadda yake so wato na rumgume shi ina boye fuskata a kirjinsa. Sai ya ja blanket din da aka siya min mai kyau gurin Khadeeja Candy ya lullube mu. Bachi muka yi mai dadi ina rungume a jikin mijina, kamshin dake fita a jikinsa ya dada Mafarkina. Sanyi da na ji a babban yatsan kafata ne ya saka na motsa ina mika, sai kuma na ji kamar an cikari yatsan hakan ya saka ni saurin bude ido, Kareem ne sanye da kananan kaya yatsan kafata a bakinsa yana cizawa. “Da zafi ba” “Uhmm, these are mine” Ya dawo gurin kaina ya daga ni zaune ni kuma na riko bargon ina rufe jikina. “Tashi bachin haka, kar mutane su fara shigowa su same ki kina bachi” Ya sumbance ni, na kalleshi sai na yi arba da nashi idon da suka tsufa a kaina. “What kin yi mafarkina ne?” Na yi shiru domin ya canka daidai. “Ai na sani zan yi ta fitinarki ne har cikin mafarki, haka zan rika binki har Aljanna” Na fara kokarin sauka daga kan gadon ina murmushi sai ya rumgume ni. “Na kasa yarda yanzu kin zama tawa Noor i love you so much...” Lumshe ido na yi ina sauraren numfashinsa dake sauka a wuyana. Mun dade a haka sannan ya sake ni na sauka na nufi gurin da lace din na jiya yake na dauka ina jan bargon dake rufe a jikina. “If you don't want me to see my halal then, zan bar miki dakin sai ki canja” Ya fada ganin na nufi kofar toilet. Na daga mishi kai sai ya mike tsaye ya nufo gurin da nake tsaye ya sunbance ni. “I love you” Ya fice ina kallonsa fuskata da murmushi. Lace din na saka na shiga bandaki na yi fitsari na sake gasa kaina sannan na fito. “Is my beautiful already?” Na kalli kofar ina girgiza kai, sometime Kareem yana abu kamar yaro. “Can i come in Babe?” “Yes” “Thank you” Ya turo kofar dakin na shigo, ya zauna kusa da ni ya saka hannunsa ya kwanto da ni a jikinsa. “Me kike son mu karya da shi?” “Tea?” “And” Na yi shiru ina tunani, shi kuma sai kallona yake yana mursa yatsun hannuna. “Come here” Ya daga ni ya zaunar da ni a saman cinyarsa ya sumbance ni. “Bari na nuna miki yadda ake order abinci a restaurant din mijin Noor a Online” Na yi dariya mai sauti, yadda ya fadi Mijin Noor in just one day da daura aure abun dariya. “Oh i need more” Ya fara min cakulkuli ina dariya har sai da ya shi ma yayi dariyar sannan ya sake maida ni jikinsa ya min rumfa da kirjinsa ya saka hananyensa biyu yana nuna min gurin da zan taba, a duk lokacin da nake bukatar wani abu. “Kin gane?” “Eh” Ya juyo da fuskata yayi min wani French kiss with his soft sweet lips, har sai da hankalina ya kusa gushewa. At that time na gane wa na aura and i what i have been missing for my whole damn life. “My direction” Ya fara min idonsa cikin nawa, kamin ya kwantar da ni a kirjinsa ya rumgume.. “My innocent girl” On that day na gane i found my missing rib, because when ever he hug me i feel something that i have never felt before. He feed me ya kuma gyara ko'ina da muka bata ya gyara gadon, sannan ya riko hannuna muka fito yana nuna min ko'ina na gidan, sannan ya fita shi ma saboda yan uwa sun fara kawo min ziyara ne. Idan na cire kamshi, kissing, cuddle, saying i love you, hugging na cikin abubuwan da na fahimci mijina yana so a zamantakewar aurenmu, domin a tsawon kwana uku da na yi a gidan ba ma rabuwa da dayan abubuwan nan sai idan ya fita. For now zan iya cewa Kareem yana gudun bacin raina kuma yana kokarin ganin ban samu damuwa a kamai ba. Na kara fahimtar hakan ne a ranar da yaransa suka zo tare da kanwarsa, ina ta jin tsoro haduwa da su musamnan yaransa gani nake kamar ba za su taba so na ba. Amman Kareem ya kwatar min da hankali ya fada min ba zai yarda su tsane ni ba, ba kuma zai bude min kofar da ni ma zan tsane su ba. Suna zaune falo na fito da dan tsoro na zauna kusa da shi ina kallon babbar domin ita ce mai wayo. “Hey Beautiful....” Ta fada tana dariya na kalli Kareem da sauri sai ya girgiza kai ya dafe kansa yana dariya. “Two days before a daura aurenmu kika kira ni a gabanta sai na manta na ce Hey Beautiful shi ne fa ashe ta rike” Na yi murmushi na mika mata hannu sai ta taso ta dawo tsakiyarmu ta zauna. “My mommy said ke ce New Momy mu a yanzu, kullum idan muka zo mu rika yi miki biyayya mu rika natsuwa” Na rumgume ina jindadi har cikin raina. Areef ma ya taso ya dawo saman jikin Babansa ya zauna, mun wuni da su babu wani tashin hankali karamin mai kiriniya a yadda na fahimta, Tine din ce mai hankali. And na yi mamakin da na ji cewar mahaifiyarta tace su yi min biyayya, ko dan ta san aurenta da Kareem ya kare ne ko kuma dai ita ma irin Aysha ce. Sai dare suka tafi gida na yi zaton bayan sati da amarcina a gidan zai dawo da su amman ban ga alamun haka ba, domin be yi min zancen ba, ni ma ban masa ba. Satina biyu a gidan ya dauke ni muka tafi gidan iyayensa na gaisa da Hajiyarsu wato Hajiya Hassana wacce ita ce tamkar uwa a garesu yanzu, ita ma ta tarbe ni da girmamawa kanensa ma haka. Ba kamar Aryam da yake fadar wai na kusa haukata masa dan'uwa, bayan sallah Isha'i Mahaifinsa ya dawo kanwarsa Khadija ta shiga da ni bangarensa muka gaisa yayi min nasiha, kuma ya ce idan Kareem yayi min abun da be yi min ba na yi gaggawar kawo masa kara kar na tafi gidanmu domin a yanzu su ne family na. Sun yi min alheri sosai na kuma jidadin haka. The following day ya kai ni idanmu na wuni gurin Mama, muka sha hira ta tsefe min kai aka min kitso, sai dare ya dawo ya dauke ni yayi mata alheri sosai, ta yi mana addu'a muka dawo gida. Yana fakawa harabar gidan yayi saurin fitowa ya bude min kamar yadda ya saba na fito, sai na rumgume shi hawaye na taruwa a idona. “Allah yasa hakan ya daure Kareem” “Babu abun da zai canja, an hallicce ni ne domin ke, aka hallicce ki domin ni, i love you” He hold me har sai da na samu natsuwa sosai sannan ya sake ni ya rufe motar ya riko hannuna muka shiga falon. “Yunwa nake ji sosai” “Bari na saka order” “No need bana son abincin waje” Na dan ji wani iri domin tun zuwana gidan ban taba gwada girki ba, sai dai mu yi order abinci a kawo mana. “Amman ka san ban iya girki mai kyau ba” Ya jefar da keys dinsa a kujera ya kama duka hannayen nawa ya sumbanta. “Babu abun da zaki girka da wannan blesse hands din be yi dadi ba, put that in your head” “But i don't know how to cook” “Baki taba mamakin miyasa mijinki ya bude restaurant ba?” Na wara ido. “Saboda ya samu kudi” “Ba kudin ne kawai bukata ba, saboda mijin kwararen mai girki ne, so i got you covered” Ya kashe min ido daya kissing my cheek both side. Bedroom muka shiga na canja atamfar jikina zuwa short jean dake bayyana fararen cinyoyina da wata yar karamar vest da bata rufe cibiyata ba na saka hula, yana ganin haka sai ya cire hujar ya aje ya sunsuna kaina. “Ina bukatar ganin sabon kitson nan” Shi ma short ne a jikinsa sai vest ya riko hannuna muka shiga kitchen, duk wani abu da na yi ina cikin kirjinsa ne ina fuskantar girkin shi ma yana fuskantarsa sai dai na jingina da kirjinsa ne. Zuba wannan kara wannan yanka wannan be saka min hannu ba sai dai ya fada min har mu ka gama with the support of kissing and cakulkuli from him har muka gama fried rice. Falo ya dawo ya zauna. “Now i want you to serve me” “Okay” Na samu karamin plate na zuba masa na dauko cikin fargaba na kawo masa domin kamshim abinci ba shi ne dadinsa ba. Na aje masa na tsaya a gabansa ina kallonsa, ya dauki spoon din ya debi abinci ya kai bakinsa ya tauna ya hade, sai ya lumshe ido. “Hmmmm...” “Abincin nan yayi dadi Babena” “Da gaske rate me” Ya bude ido. “I can't rate you, you taste like heaven i can only rate the food” Na rufe ido da hannayena ina jin kunya, na buga kafa a kasa kamar zan yi kukan shagwaba. “Hey Beautiful bude idonki, abincinki yayi dadi na baki 8” Baki sake nake kallonsa ina jindadi sai ya debi abinci ya kai min spoon din a baki. Lokacin da na ci abinci sai na ji yayi dadi sosai kamar ba ni na girka ba. Na gudu na je na haye kujerar dake kusa da wanda yake zaune ina tsalle na bude hannayena ina rawa da su. “Okay hug hug hug” KAREEM POV. Kallonta yake da murmushi a fuskarsa farinciki da yake gani a tattare da ita ya saka shi jindadi, dukawa yayi ya aje Spoon din ya nufi gurin da take, madadin ya rumgume ta sai da riko cinyoyinta ya daya ta sama. “Here I am beautiful” Ya sumbanci cibiyarta sai ta kyalkyale da dariya mai burgewa. Ya sauke ta sai ta rumgume shi. “Thank you for Kareem” “Uhmm.. This is just the beginning” Shi ya shiga kitchen din ya zuba musu abinci ya dauko ruwa da lemu ya aje, sannan ta zauna suna fuskartar juna ita da shi suka ci abinci. Da suka gama ya kwashe kayan suka wanke komai a tare suka gyara kitchen din a tare. Then suka yi wanka ta shafe jikinta da turare shi ma haka, da suka je kwanciya bata jira ya jaddda mata number one rules dinsa ba. He hug her yana ta bata labarin abubuwan da bata sani ba a rayuwarsa, yadda ya koyi girki yadda aka fara kafa restaurant din har ya kawo yanzu and so on... Da safe ma tare suka shirya abun karyawa sannan yayi wanka ya fita gurin aikinsa. Misalin karfe daya na rana kiran Yusura ya shigo wayarsa, yayi mamakin ganin kira kusan tun da suka rabu idan ba rashin lafiytar yara ba shi ma sai yayi tsanani take kira, wannan karon ma sai yayi zaton ko wani ne babu lafiya. “Hello...” Ta amsa kuma ta gaishe shi with respect. Sai kuma ta yi shiru. “Yara ba su da lafiya ne?” “No Kareem ka san zan yi aure” “Yeah congratulations, akwai abun da kike bukata ne?” “Thank you, but ba na kira dan ka taya ni murna ko bukatar wani abu ba, kawai na kira ne saboda maganar yara ina za su zauna yanzu, because ba kasar nan zamu zauna da wanda zan aura ba for now saboda yana aiki a New York ne” “Yara za su zauna gurin Hajiya, zan dauki Nanny da zata kula da su kuma kanena suna nan Hajiya ma tana nan, babu abun da za su rasa, already sun saba da gidan yanzu, zan dawo da su gurina but sai Noor ta haihuwa tukuna” “Okay ba matsala” “By the way na gode da kika bar su suka so Matata, hakan shi ne tarbiya” “I'm just doing my job as a good mom, and thank you for giving me the opportunity to find my love, wish you happy married life” “Wish you the same Yusura, enjoy your life” Ya sauke wayar, sai kuma ya ji babu wanda yake bukatar gani ko ji sai Noor dinsa. A take ya aika mata kira tana picking ya ce. “Hey Beautiful” “Hey handsome” Ta amsa mishi with awesomeness, ya kwanta jikin kujerar yana shafa kansa da murmushi a fuskarsa feeling so heart warming. “I miss your hairy chest, i need cuddle” Ta fada a shagwabe. Gaba daya sai ya ji ya rikice. “I will be there right away my beautiful” Ya sauke wayar ya dauki abubuwan bukatarsa daman lokacin tashinsa yayi sai ya fice daga Asibitin da sauri. Tun kamin ya fara harabar gidan ta fito sanye da hijab yana ganin haka ya san kananan kaya ne a jikinta domin ya fada mata idan zata fito harabar gidan ta rika rufe jikinta saboda mai gadi. Waving dinsa ta rika yi daga bakin kofar falon da take tsaye har ta karaso ya sauke gilashin motarta. “Hey Beautiful” “Hey Handsome” A kokarinsu na rigen rigen futarwa juna suka fada a tare, sai duk suka saka dariya. Yana fitowa motar sai ta zo a guje ta daka tsalle ta fada jikinsa ya cafketa ya daga sama ta lake kafafuwanta a kunkurunsa. “I miss this face, i miss this girl” Ya fada yana jan kumatunta, ita ma sai ta ja nashi tana fadin. “I miss this hug, i miss this guy” Yayi dariya ya nufi entrance din da ita. Suna shiga falon ya fara kissing dinta, sannan ya sauke ta kasa. “What's up Beauty” Ta yi dage ta lakaci hancinsa. “I cook something delicious...” “Let me smell it then” Ya fara kokarin cireta mata hijab yana shinshinar kamshin dake tashi a jikinta. “I said i cooked not in my body” “Ouoooo, my bad, i have dirty mind” Ya daga ta yana dariya... Bayan Shakara Daya... NOOR POV. Na bullo da kaina gurin wuyan rigarsa na tura hannuna da gun da hannunsa yake, sai ya zama na ni ma na shiga cikin T-shirt din dake jikinsa, shi yana daga kwance rairai ni kuma ina samansa na lafe a jikinsa skin dina yana taba nashi. “Baki karasa min ba, sai aka yi yaya?” Na dan yi shiru ina tunanin a ina na tsaya da labarin da nake ba shi na sabon littafin Khadeeja Candy mai suna ABOKIN RAYUWA. “Yauwa sai be aureta ba, ita fa yarinyar christen ce, bayan ya musuluntar da ita sai kuma yan'uwan shi suka rika cewa ba bahaushiya bace saboda ita din igbo ce amman tana da kyau, sunanta Emily” “Ta yi kyaunki?” Na daga na kai masa cizo a gemu har sai da yayi kara. “Ita fa kyakkyawa aka ce” “To ni yanzu akwai mace mai kyau da ke burge ni irinki, kin mamaye zuciyar kin hana ni ganin kyaun kowa ai, da zarar na motsa nan sai na ji ana Noor idan na juya can na ji ana Noor, to ya zan yi? Kin saka kwado kin kulle idon da zuciyar gam” Na yi dariya mai sauti. “Kuma na jefar da makullin ya bata” “What ever ni dai abun da nake so na samu, Noor kin cika rigima na fada miki ki daina shigowa rigata ta front ki rika juyawa so that idan ina son na yi hugging dinki sai na yi, yanzu ya zan yi hugging dinki a haka?” Na turo masa baki a shagwabe na ce. “To ni haka nake so” Yayi kasa da kansa ya goge min hancinsa. “Rigimammiya duk kin bare min riguna” “Skin to skin, ruhi to ruhi, love to love” Na daga mishi gira na kashe mishi ido irin yadda yake min. Sai ya saka dariya sosai yana girgiza kai. “Funny girl, Allah ya shirya min ke” Na kwantar da kaina a kirjinsa. “Ameen” Na yi lamo ina jin bugun zuciyarsa. “My king” “Yes my Queen” “Satin nan ya Nabill zai tafi kauye gurin yan'uwan Babanmu da suke can, zaka bar ni na je” “No...” Ya amsa min kai tsaye, fita na yi a rigarsa na matsa gefe na rufe jikina da blanket na hade rai na ci magani. Sai ya sauka daga kan gado ya shiga yayi wanka ya fito na dauke fuska na juya dayan gefen, sai ya zo ya kama fuskata. “Hey Angry Girl bring back my Beautiful Girl” Na kara hade rai, sai yayi dariya ya sake ni ya shirya kansa. Sannan ya dawo inda nake ya rika fuskata ya goge min hancin. “Hey Beautiful saki fuskarki mana, za ki tafi amman ba yanzu ba, sai kin haihuwa” “To ai yanzu babu cikin ka bari idan....” Be bari na karasa ba ya rada min. “We ganna make one tonight” Yayi kissing front head dina ya nufi kofa. “Off to work, i love you” Na nade hannayena na turo baki na ki nace masa i love you too kamar yadda muka saba, sai ya juyo yana rike da kofar dakin. “Can i hear i love you back” “No” “Come on Beauty” Ya dawo ya fara min cakulkuli har sai da na fada. “I love you back” “Nope ina son na ji i love you too” “I love you too” “Good girl” Ya sake ni sannan ya fice. Hausawa suka ce fadi gareka cikawa ga Allah it take us another year kamin na samu ciki, ba dan kuma ina da matsalar komai ba sai dan lokacin hakan ne be yi ba. Na fara ne da rashin lafiya, sai kuma na fara jin sauki but jiki ya zama so weak, sai dai gane cewar ciki ba ne till one day na dauki wani karfe da Kareem yake workout da shi sai yayi saurin hanawa ya rike ni. “Mace mai karamin ciki bata daukar abu mai nauyi careful don't hurt yourself” “Ai ba ni da ciki” “Says who?” “Says me” “Are you a doctor?” “Amman ai ni matar likita ce?” Yayi murmushi ta lankamo wuyana. “Kina matar likita baki san kina da ciki ba?” Na yi shiru ina nazari, sai ya dauke ni ya bude kofar baya ta falon ya shigo da ni falo ya aje kan kujera ya zauna kusa da ni. “Ina mutuwar Sonki Noor balle kuma abun da zaki haifa, dole sai kin yi taka tsantsa kar wani abu ya samu cikin nan dan Allah, kwanta ki huta zan motsa jini waje” Ya mike tsaye sai kuma ya dawo ya rumgume ni ya sumbance ni. “Thank you, my happiness, my love” Na yi murmushi na lafe a jikinsa. “Baby be son ka yi workout he need a cuddle” Ya daga kafafuwana ya matsar da ni jikin kujerar sannan ya kwanta a gurin ya rungume ni. “I will do what ever pleased you and my baby” Na saka hannuna ina jan gashin dake kirjinshi kamshin turarensa na kwantar min da hankali. “Da gaske ina da ciki?” “Uhmm. Why would i lie?” Na jidadi ya rufe ni. “Kuma kana son Babyn?” Ya saka hannunsa ya dago kai. “Har tufafinki ina so balle babyn da zaki haifa, ba ki san irin dadin da na ji ba lokacin da na gane kina da cikin nan” Na saka hannu biyu ina jan gashin chest dinsa. “Shiyasa ka ce na daina zuwa da gudu ina rumgume ka idan ka dawo?” “Yap” “Me yasa baka fada min ina da ciki ba?” “Saboda fitina ta zaki yi, yanzu da kin tashi fita ki ce Baby yana son yawo, and kin san yadda nake kishinki bana son kina fita ko kadan” Na yi dariya, domin ya canka a daidai yadda yayi zato haka nake aiwatarwa, a duk lokacin da aljannun yawon suka motsa kuka kawai nake kasa masa na ce baby yana son yawo, idan har yana kaunar zaman lafiya a ranar dole ya kai ni yawo ko kuma ya bar ni na tafi gidanmu. Haka muka yi ta fama abinci ma sai an jera min shida bakwai sannan na samu wanda zuciyata take so, abu kadan ya bata min rai, ni kaina taka tsantsan nake da kaina balle kuma Kareem da har tsoron kallona yake domin zan iya cewa kallon be yi min ba haka dai har na shiga wata na takwas. KAREEM POV. Sautin kukanta ne ya tashe shi daga bachin da yake, ya mika hannu ya kunna bedside lamp sai ya ganta zaune tana kuka. Ya tashi zaune da sauri ya rikota. “Hey Beautiful me ya faru?” Ta ki ta yi magana sai kuka take, sauka yayi daga kan gadon ya dauki jallabiyarsa ya saka ya fita dakin be dade ba ya dawo dauke da ruwa ya rika kanta ya kai mata ruwan a baki ta sha, har tana sauke ajiyar zuciya sannan ya aje kofin ya zauna gefen gadon ya bude kafafufuwanta yana matsawa. “Me ya faru? Mafarki kika yi marar kyau?” “Aa” “Me kike yi ma kuka? Baki da lafiya” “Lafiyata kalau, na tuna da lokacin da ka zo gidanmu ka ce wai wata yarinya kake so, kuma tana sonka sunanta Hafsa, kuma ka san ni ce miyasa baka fada min gaskiya cewa ni ce wannan yarinyar ba sai da na ji babu dadi” Kallonta kawai yake ya rasa ma me zai furta mata. “Yanzu wannan abun shekara biyu da wani abu ba ki tono shi ba sai yanzu? Kuma miye abun kuka a ciki ai ke ce yarinyar” “Miyasa baka fada ba tun farko? Ka yi breaking heart dina” “Okay I'm sorry ba zan sake ba, Allah ya baki hakuri, yar kyakkyawata” “Dauko min riga na saka” Ta fada a shagwabe kamar mai shirin fashewa da wani sabon kukan. Ya sauka ya nufi wardrobe dinta ya dauko mata rigar da gown irin ta masu ciki mai free size. “Bana son rigata” “Tawa kike so?” Ta daga mishi kai, sai ya juya ya aje nata rigan ya bude side dinsa ta dauko mata T-shirt dinsa ya saka mata daman ko ba ciki tana saka kayansa balle kuma tun da cikin ya fara girma kayansa take sakawa. “Da short” Ya bude wardrobe dinta ya dauko mata karamin short ya saka mata. “Shikenan? Ko kina bukatar wani abu?” “Ni ka daina tambayata idan ina bukatar wani abu ba ina magana ba” “Allah ya baki hakuri, na daina” Ya kwantar da ita a hankali sannan ya kashe wutar ya kwanta bayanta ya rumgumeta. Washe gari ma haka ta tashi da rigima there is one food she hate the most tun da ta samu cikin nan bata son jollop rice, as early morning take fadawa Kareem wai su daina girka abinci a restaurant din Yana tsaye gaban madubi ya juyo ya kalleta. “Saboda me?” “Ba ke ake girkawa ba?” “To bana dai sonta” Da ya karanci matarsa rigima take ji sai ya amsa mata da “Okay zan fada musu su daina girkawa, shi kadai ko da wani?” “Shi kadai, amman Hubby ina son idan ka dawo da dare mu tafi shopping na siya turare” Ya juya ya kalli mirror dake cike da turaruka kala kala. “Okay za mu je In Shaa Allahu” Ya sumbanci bakinta ya sunbanci cikinta sannan ya sake kissing front head nata ya ja hancinta. “Take care of yourself sai na dawo” Ya fice yana dariya shi kadai, domin be tana samun kansa a cikin wannan yanayin ba sai yanzu, yara biyu da suka haifa da Yusura bata taba masa haka ba. Sai gwanarsa Noor. Yadda yayi mata alkawari haka ya aiwatar misalin tara na dare ya dauketa suka tafi shopping mall gurin siyen turaren da be san ya zata yi da shi ba. Sai da ya fara fita ya zagaya ya bude mata ta fito tana sanye da hijab har kasa. NOOR POV. Ina tura cikina muka shiga ciki turare biyu kwai kamshinsu yayi min dadi na zaba sai wasu shoes da abaya, idan na zaba shi nake bawa har na gama muka nufi gurin biyan kudi muna tafe muna hira. Gafen da nake tsaye Abdull yake tsaye amman ni ban kula ba domin hankalina yana gurin kayan wata mata da ake dubawa. Kareem ya bar gefensa ya dawo nawa gefen ya tsaya ya shiga tsakanina da Abdull. Kamin ya aje kayan hannunsa a gurin ya riko hannuna, sai a lokacin na lura da Abdull din da shi ma jiran yake a duba nasa kayan ya biya kudi. Kallona yyai sai yai saurin dauke ido kamar wanda ya rikice ya bar gurin ta koma cikin mall din. Kareem be sake ni ba sai da muka iso gurin motarsa ya bude min na shiga. “Abdull ne ko?” Kamar yana jira sai ya rufe ni da fada. “Dole sai kin fadi sunansa? Kina da alaka da shi?” “Aa” “Na yi nufin na zo na saka ki a mota ki kira ne sai na gama biya mu tafi, amman yanzu na fasa ba za'a siye kayan ba” Ya rufe min gambun ya zagaya side dinsa ya shiga yayi ma motar key. “To ni miye laifina dan kawai na ce Abdull ne” “Kara fada kike yi?” Na yi shiru kamar zan yi kuka. “Ka san ai ba kaunarshi ne ke ba, domin ba zan taba manta abun da yayi min ba da Hana, rayuwarsa ba zata kare da kyau ba” “Kadan ya rage masa ai, ko a yanzu ya halaka tun da ya rasa aikinsa da yake ya koma karantarwa a secondary school, kuma ya kwashi ciwo” Na zaro ido. “Da gaske? Taya ka sani?” “Wani likita naje gani asibitin da naje awo, na ganshi layin yan HIV ko dai ya kamu ko kuma yana tunanin ya kamu ne, in ba haka ba babu abun da zai saka shi tafiya awo” “Amman tabbas shi ne?” “Shi ne mana Beb saboda na tabbatar sai da na duba files din ma na ga sunansa, saboda ya saka mask da facing cap ya rufe fuskarsa” Na yamutsa fuska. “Daman karshen alewa kasa, Allah ya kara masa ya isar mana, da ma ya rufawa kansa asiri ya maida maitarsa sun zauna, ko da yake ita ma ba zata yarda ba saboda yana da ciwo yanzu ko?” Be amsa ni ba ya faka gaban wani mai tsire. “Zaki ci na siya?” “Eh” “Okay” Ya siya mana na 5k sannan yaja motar muka yi gaba. “Ai Safeena ma bata garin nan ko Hubby?” “Tana nan” “Ba kace ta koma garinsu ba? Kuma kace ta yi hadari?” “Eh amman bayan ta koma gida daga asibiti, last year suka yi gobara a gidan iyayenta suka rasu ita kuma ta yi kuna a jiki, sai mahaifin Abdull ya daukota ya dawo da ita garin nan daman shi ya rika ta ko lokacin da iyayen suke da rai” “Innalillahi Wa'inna Illaihirraji'un, bayan watan nin da ta yi asibiti kuma da ta koma gida sai iyayen suka rasu? Wayyo Allah bata da yan'uwa kuma?” “Tana da su mana, amman shi baban Abdull din yayan mahaifinta ne ya rigata shiyasa ya sake dawowa da ita yanzu” “Ta ba ni tausayi” Na fada har a raina domin rayuwarta abar tausayi ce a yanzu. Kareem ya kai hannu ya rika hannuna ya cigaba da tukin da hannu daya. “Be kamata ma ki ji tausayinta ba, kin san wutar da ta tashi a gidanku? She's the reasons” Na rufe baki da hannu daya. “Taya ka sani?” “Zuciyata ta raya min haka daman, kuma na karanci hakan cikin kalamanta lokacin da muka yi fada, ta aiko kawarta ta fada min kuma yana neman magana da ke” “So har yanzu....” Na tambaya cikin kuka, domin na tuna da mahaifina da yar'uwata. “Nononononononononononono Wallahi tun da muka rabu ban sake sakata a idona ba, ban san labarinta sai da kawarta ta same ni a office, kuma kawarta nurse ce muna mutunci a tsakaninmu if not ba zan ma tsaya na saurareta ba” Ya faka motar ya fita ya zagayo ya bude min na fito, ya dauki tsiren ya riko hannuna muka shiga ciki ina kuka, kan tebur ya aje ledar ya zauna kusa da ni ya rungume ni. “Idan ni na mata laifi me Baba da Hana suka mata?e yasa zata kashe min mahaifi da yar'uwa?” “Ke ta yi nufin kashewa sai kuma baki kwana a gidan ba, kukan ya isa haka Beb, i already told you no more tears” Ya rumgume ni tsantsam a kirjinsa yana shafa bayana alamar rarrashi... Na dago daga jikinsa na kalleshi. “Ina son na ganta” Ya kama fuskata da hannu biyu ya rike. “Baki bukatar ganinta Love” “Ina son na ganta, ina son na yi magana da ita” Yatsunsa ya saka yana share min hawayen da saukowa. “Saboda me amman?” “Ni dai kawai ina son na ganta” “Zan yi tunani akai, yanzu manta da ita bari na bude miki namanki ki ci huh” Ya sumbanci bakina. “Ka dafa min indomie sai ka saka naman cikin ka saka kwai” “Okay” Ya sake ni ya mike tsaye sai na riga hijab dina sai ya rika min na cire na koma daga ni sai skirt da T-shirt dinsa dake jikina. Ya aje min hijab din da dayan bangaren sannan ya nufi kitchen ni kuma na mike kafa ina kallon tv amman hawaye nake kewar mahaifina da yar'uwata. Tun da ya shiga kitchen din be fito ba sai da ya gama, a lokacin da ya hango hawaye a idona sai ya zo da sauri yana kallon fuskata. “Na dade gurin dafawa ne?” Na girgiza kai alamar aa. “Minene?” “I miss my Dad i miss my sister” “Wannan dalilin ne ya saka bana fada miki wani abu Beb, bana son hawayen nan na ki da tashin hankali” Ya rumgume ni a tsayen da yake yana shafa kaina. “Addu'a suke da bukata a yanzu, ba kukanki ba, kuma yanzu komai ya wuce I'm right here My Love” Na lumshe ido ina sauke ajiyar zuciya. Sai ya duko yana taba fuskata. “Haba yan matana, haba uwargidan Kareem kuma amarya, daga ke babu kari, haba yar tilon Mama, kanwar Nabil, duk ke kadai ehen ga ki kuma yar gatan mijinta, mai son ganin bacin ran Kareem ya taba Noor, haba ta Kareem bada kanki a asare ki je ki cewa Mama ya fadi, haba autar mata....” Na kalleshi ina murmushi, duk wani abun da Kareem zai yi ya kwatar min da hankali ya san shi kuma yayi kuma yayi nasara domin mun ci abincin da ya girka min cikin farinciki da kaunar juna. Ya wancin aikin gidan shi yake yi ya dauke min nauyi abubuwa da yawa tun da muka yi auren balle kuma a yanzu da nake dauke da babynsa. Wannan cikin ya zo a dabam ba kamar cikina na farko ba ina fama da yawan rigima abun da be kamata na damu da shi na kan damu, abun da babu ruwana ma sai na shiga, na tabbatar da a gidan haya muke wata kila da yanzu an koramu ni da mijina. Cikina na wata tara mun fito daga family house dinsu Kareem na rika masa magiyar ya bar ni na ga Safeena idan dai tana garin nan. Ba dan ya so ba ya tafi da ni gidansu Abdull kuma gidansu Safeena a yanzu, kamin a bude masa gate yake fadar ba lallai a bar mu mu ganta ba, ba lallai idan ta san mu ne ta yarda ta fito ba. Ni mna na raya wannan a zuciyata sai dai ta inda muka taki sa'a muna shiga bangaren uwargidan wanda a nan ne ake rikon Safeena sai muka same ta harabar gidan zaune a well-chair tana kallon motarmu. Gabana ya fadi na ji kamar bana bukatar ganinta kamar yadda Kareem ya fada da farko, sai dai kuma mun riga da mun zo, har Kareem ya bude min mota. “Zan tsaya a nan, karki dade” Ya jingina da motar fuskarsa na kallon gate din gidan. Ni kuma na taka ta tulelen cikina na karasa kusa da ita na tsaya ina kallonta tana kallona, can kuma sai ta yi murmushi. “Na san kin yi nasara Noor baki bukatar nuna min, kin raba ni da wanda nake kauna, kin raba ni da aurena, kin juyar da mutumen da yake tsananin kaunata zuwa makiyi na, yanzu miye dalilin zuwanki? Rayuwata kike nema ko me? Ko kin zo nan ne, saboda ki fada min kin yi nasara a rayuwa? Kin zo ne saboda ki fada min kin auri Kareem har kin samu ciki da shi?” Na girgiza mata kai ina kallonta ita din abar tausayi ce a yanzu me yasa bata tausayin kanta? Kusan rabin fuskarta zuwa habarta na bangaren hagu ya bar mata tabon wuta alamar kone da aka yi aka warke. “Ban zo nan saboda na nuna miki na yi nasara ba, zan fada miki na yi nasara ne idan muka shiga aljanna ni da Kareem. Na zo nan ne saboda na tunatar da ke abun da kika manta, mutum baya iya canja abun da Allah ya kaddara zai faru ga bawansa, dabara da wayo basa sauya kaddara, kuma ba zaka saka wani a bakinciki kai kuma ka yi tsammanin zaka dauwama a farinciki ba, ta kika kone nawa iyayen ke ina naki iyayen suke a yanzu? Da kika so raba ni da rayuwa ke ya taki rayuwar take a yanzu? Annabi Muhammad S A W ya fada, imanin dayanku ba zai cika ba har sai ya sowa dan'uwansa abun da ya so ga kansa, ina imaninki ya tafi Safeena? Abun da kika yi nufi da ni, za ki so ya faru da ke?” Ta dauke kai tana hawaye. “Ni na yi nufin bawa zuciyata abun da take so ne kawai, kamar yadda kika yi jarabawa ta ce son Kareem, amman kin raba ni da shi, go home and celebrate” Na juya na kalli Kareem dake tsaye fuskarsa tana wani gafen baya kallon gurin da muke tsaye, sannan na juyo na kalleta. “Kamin mu yi aure, ba zan iya cewa ina son Kareem ba, ko da ina son shi to ni ban sani ba, amman da kaddara ta yi nufin hadamu sai abubuwa suka faru, daga karshe kuma sai ya zama abokin rayuwata. Amman Safeena namiji be yi tsadar da za a kashe rai saboda shi ba, namiji be yi tsadar da za a haihu ba tare da aure da shi ba. Kin yi sikar mutuwar mahaifin da be miki komai ba, da yar'uwar dake cike da buruka, Allah ya isa ban yafe miki ba...” Na juya na nufi motar Kareem ina kuka, sai na ji ta kira sunana. “Noor... Ki yi hakuri dan Allah” Na juyo na kalleta sai ta fashe da kuka ta rufe fuskarta da tafukan hannayenta. Na juya na cigaba da tafiya ba tare da na ce mata komai ba. Ina isa Kareem ya rumgume ni. “Na fada miki baki bukatar zuwa, ba ki ji ba” Ya bude min mota na shiga ya rufe sannan ya zagaya ya shiga, ya juya motar muka fice daga gidan. Hannuna daya ya rike yana tukin yana kallona har muka isa gida “Wani abu ta fada miki ne?” Na girgiza masa kai, ya fita motar ya bude min na fito ya rikani muka shiga falon ya zaunar da ni a kujera, sannan ya shiga kitchen ya dauko min ruwa kaina ya rika sai ba ni ruwan a baki sai na saka hannu na karba na aje na mike tsaye na bude masa hannayena. “Ina son ka Kareem” Ya rumgume yana shafa bayana. “Ni na dade da mutuwa a sonki Beb Allah ya sauke ki lafiya” “Ameen” Addu'ar da yake min kenan a kullum, ni ma nake yi ma kaina mahaifita ma take min. Hakan kuma ya taimaka min sosai haihuwar ta zo min da sauki, na haihu ba tare da na sha wahala sosai kamar haihuwa ta farko na haihu daga ni sai likitana a gida. Shi ya wanke ni ya gyara min jiki ya wanke jariri ya kwantar da ni sannan ya kira iyaye ya sanar da su. Jaririn ya dauko yayi masa huduba ya rada masa sunan mahaifina sannan ya saka min shi a hannuna na fara ba shi nono da be da ruwa a lokacin domin ruwan Nono be kawo da wuri ba. Ina rumgume da ďana mijina yana rumgume yana min sannu da kissing. Na kalleshi hawaye fal a ido na ce. “Wannan yana da rai” Ya sunbance ni. “Haka zaki yi ta haifo mana masu rai da yardar Allah har sai kin gaji” Ya sumbanci yaron ya karbe shi daga hannuna yana kallona cike da kauna, bakinsa ya miko min muka sunbanci juna be cire ba har sai da ya ji alamar shigowar mutane a gidan. Kan kace kwabo yan'uwansa da nawa sun suka gidan kowa sai murna yake. Yaransa da sai daukin babyn suke kamar za su cinye shi. Duk yadda Mama ta so a bar ni na koma gida ganin kamar haihuwar fari ce Kareem be yarda ba, yace kamin yanzu na taba haihu Mama ta bar masa matarsa kawai shi dai zai fi kwanciyar hankali idan ina gidan. A yanzu ne na san yadda uwa take ji idan mace ta haihuwa hidimar jego da jariri sai yanzu nake samu domin wacan haihuwa ta zo ne ba a yadda aka yi zato ba. Wannan kuma ta zo a lokacin da ya dace cikin so da kaunar miji ga yan'uwa miji da yaya masu son new babyna da muka yi masa alkunya da RAYID. An ci an sha an wadata da komai a ranar sunan RAYID, kawayena har na nesa sai da suka zo, a ranar sunan ne kawata Zainab dake da yara biyu a yanzu take fada min Zafeer ya rabu da matarsa, shekara daya bayan mun rabu, na sha mamaki domin ban dauka zai iya sakinta ba. “Amman ya saketa Zainab?” Na tambaya ina juyar da fuskata mai min kwalliya tana shafa min jan baki. “Hmmm ta dai sake shi, ke kina ganin zai iya sakinta ne? Ance fa tun da kika fita babu zaman lafiya baya jindadinta abububuwa take masa na rashin jindadi, kuma kamfanin mahaifinta ma da aka saka shi suka cire shi, daman ni na san za a cire shi ai, saboda za su yi tunanin be da amana, indai har zai iya cin amanarta ya aureki ba tare da ta sani ba, to zai iya yin komai ma” “Hmm ai maza haka suke da cin amana” Mai mini kwalliya ta fada ni kam sai na yi karaf na ce. “Wasu dai ban da nawa” Sai duk suka saka dariya Zainab ta kai min dudu a baya. “Wato Noor ban da Kareem” “Aa ban da shi gaskiya, Kareem dan albarka ne rabin rayuwata, bawan Allah mai son farincikin matarsa” Mun yi wunin sunan cikin farinciki an yi hotuna a gurin da Kareem ya saka ayi decoration da sunan RAYID, na yi ta zuba zinarina ana min hotuna cikin shiga kala kala. Wani kuma aka yi mana tare da Kareem wani tare da yaransa as family picture. Sati daya da yin taron sunan ina zaune falo dattijiwar dake yi ma baby wanka ta kawo min kunun ganye bayan ta gama gyara min yarona, na karba cup din ina kallon Kareem dake rumgume da ďansa yana daukata hoto a waya. “Ya aka yi? Tun dazun kike kallona karki cinye ni” Na yi murmushi da ya bayyana hakora na, tsohuwar ma ta yi dariya, na shanye kunun na mika mata kofi ta nufi kitchen sai na amsa masa murya kasa kasa. “Cinye ka zan yi” Be ce min komai ba sai ta da aje cup din ta fito ta yi mana sallama ta fice, sannan ya taso daga inda yake zaune ya dawo kusa da ni yana saka min fuskarsa a cikina yana cizon cikin. “Aya gani cinye” Na buge masa kai na ja masa kunne ina dariya. “Idan na fara rama cizo da kwantar da kake min a gidan nan Hubby ba zaka iya da ni ba” Ya aje babyn ya fara kokawar cire min riga. “Bari na cije ki inda zaki fi jindadin ramawa” “Dan Allah ka bari Haba Kareem Haba Kareem” Ya zare ido. “Haba Kareem? Wato Kareem ko?” “Mantawa na yi Wallahi haba Hubby haba haba.... Hahahahahahah” Dariya ta ci karfina saboda cakulkulin da yake min, ya riko ni muka fada kan carpet din dake kasa, ni da shi muna dariya. *** *** *** Married is sweet when you meet the right person, sai ya mantar da kai damuwa da duk wani hali da ka taba kasancewar a rayuwa. Na yarda da wani abu a rayuwa, ba zaka cutar da wani ba, kuma ka yi tsammanin rayuwa zata tafi maka daidai, ba zaka zalinci wani kuma ka ce zaka ga daidai ba a rayuwarka. Kuma na yarda dukan tsanani yana tare da sauki, na yarda riba mai hakuri tana da yawa, na yarda addu'a maganin dukan wata musiba ce ta rayuwa, haka ma na yarda dukan wanda Allah ke yi ma fada baya fada. Idan kuma Allah yace kai ne to kai be babu makawa babu wanda ya isa ya sauya wannan? Hausawa suka ce matar mutum kabarinsa, shi ma yarda, domin duk mazajen da nake aure ban zauna ba sai a gurin Kareem, ba su iya rikon ba, sai shi, zuciya bata natsu ba sai da ta kai ga wanda aka hallicceta domin shi. Aure yayi albarka domin shuka ta yi yabanya, kan na maida shekara bakwai a gidan mijina na sauke masa yara biyu mata bayan RAYID, sai na hada su da nasa yaran na rike kamar yayana. Ni ma dai ashe zan girma, zan yi hankali zan zama abar misali a gurin wasu, ashe dai ni ma zan yi hankali na zama uwa, sai dai na kasa girma a gurin mijina a kullum yarinya yake ganina, ni kuwa na yi ta yarintata musamman akan shimfidarsa. Na tashi daga TA KI ZAMAN AURE zuwa tana dakin mijinta yaranta, daman mutane ne ba su fahimci kaddara ba, idan mace ta fito sai ayi gulma suna manta su ma iyayen matan ne, wasu kuma iyayen basa fahimta kamar Mama kamin ta sauya, wani kyaun kuma an baro shi ne tun gurin haihuwa, kamar dai yadda iyeye suka ta yi min baki da farko, ko da yake kaddarar kowa dabam, saboda wata ta dace a farin farko ko na biyu, ba shi yake nufi wata zata dace ba, kuma saboda wata bata dace ba ba shi yake nufin ke ba zaki dace ba. Rayuwar aure akwai dadi, akwai daci, akwai farinciki wani lokacin kuma akan samu tsabani da bakinciki, manufar abun dai aure ibada ce, ribar tana a gurin Allah ne. Babu macen da zata kashe aurenta saboda tana jindadin zaman gidansu, babu kuma macen da zata ki zaman auren saboda dadin zaman gidansu, mace bata sakin kanta mace yar sunna bata gudun sunna. Kar wahalar gidan auren wata ya saka ki cire rai daga samun mijin na gari, kar rayuwar auren wata ta burgeki ta saka ki dogon buri, just pray and hope for the best. Kaddara mai sauya labari, a yanzu an bude min wani sabon shafi na farinciki ni da mahaifiyata a gidan nata sabon mijina. Dan'uwana ma a yanzu baya kasar a makarantar da yayi karatu suka dauke shi karantarwa bayan yayi masters, suka ba shi muhalli sai ya dauki amaryarsa Mariya da dansa ďaya suka koma can sai idan sun kawo mana ziyara ko kuma mu din mun tafi. KAREEM POV. “Okay Daddy, daman dai saboda na ga yara ne, amman tun da ka saka baki zan barta ta tafi” “Hakan ya fi” Ya sauke wayar sannan ya bude motar ya fita, ya shiga cikin gidan da babu kowa a yau sai matarsa yaran duka suna family house gurin Hajiya Hassana. Kamshi turare ne ya fara yi masa lale marhabun a lokacin da ya saka kafarsa a falon. Noor dake saukowa ta zo da gudu ta tarbe shi sai ya rumgume ta ya cije hancinta. “Saboda na ce ba zaki je ba kika hada ni da Daddy ko?” Ta sake shi ta fara rawa tana rauyasa. “Idan ba haka na yi maka ba ba zaka bar ni na tafi ba” Murmushi yayi ya rikota ta dawo jikinsa cike da so da kauna yake kallonta. “Bana son ki yi nisa da ni ne ko kadan, kin riga kin shanye min zuciya ko aiki naje Allah Allah nake na dawo na ga fuskar yar budurwar nan tawa” Ta yi murmushi, shi ma murmushin yake yana kallonta kamar zai cinyeta, yana son ta wannan abu ne da kowa ya sani, yana son farincikinta wannan kuma wani aiki ne da ya rataya a wuyansa. A cikin abubuwan da yayi mata alkawari akwai mutuntawa, akwai farinciki, akwai riritawa, akwai gata, akwai soyayya? Kusan ya cika kowane amman har yanzu zuciyarsa bata gamsar da shi Noor ta wadatu da farincikinsa ba. A kullum yana neman hanyar da zai faranta mata yake. Domin shi na shi farincikin ya cika ya samu matar da yake so yake kaunar matar dake mantar da shi damuwa matar idan ya kalleta sai farinciki da nishadi su kama shi, matar da kamshinta ke fitinarshi, matar da zuciyarsa ke marari, gashi ta haifa masa kyawawan yara, kuma ta hada da na shi ta rike kamar nata, shi kam yanzu me ya rage masa? Sai yi ma Allah godiya. “Mu je ki raka ni” Ya fada yana jan lebenta. “Ina?” Ta tambaya a shagwabe, domin mace shagwababbiya ce a gurin mijinta no matter how old she's balle kuma ita da take matashiyarta. “Gurin yaran Hafiz zan kai musu na su kayan ne” Ta sunbance shi sannan ta sake shi ta shiga ciki ta dauko mayafinta suka fita tare. Har gobe har jibi idan za su fita ko suka dawo shi yake bude mata mota ta fita ko ta shiga, yaransa har sun koya idan za a fita da ita su yi ta rigen rigen bude mata front seat. Suna tafe suna hira har suka isa gidansu Aisha sai da yayi sallama aka sanar mata sannan ya shiga ciki ya gaisa da ita Noor ma gaisa da ita Aisha na amsa mata sama sama, Kareem ya saka aka shigar musu da abinci da kayan tea da kayan kwadayi irin na yara, ya bawa yaran kudi suna ta murna daman ya bawa kansa a duk lokacin da yayi siyayar gidansa zai yi na yaran abokinsa Hafiz. Daga gidan suka wuce gurin Iyayen Hafiz su ma yayi musu alheri ya ba su na su siyayyar suna ta saka masa albarka da Noor har ya fito. A mota take masa ta yin tafiya kauyen tare da shi. “Aa ki tafi yanzu ke kadai ni ki bar ni da yarana idan mun dawo Ummara sai mu tafi da su can” “Ni na tafi kauye ku, ku tafi ummara kenan?” “Eh mana ba kin nace sai kin tafi kauye ba?” “Amman ni ma ai ina son na tafi” “Last year baki tafi ba?” “Ina son na sake zuwa” Ta turo baki gaba, hannunsa ya kai ya ja bakin. “Ba za a da ke ba, ni dai zan tafi da yarana mu yi addu'a sabon restaurants din da zamu bude a Kaduna da Abuja da Sokoto da Lagos ya zama babban kuma ya karbu kamar na Kano” “Idan babu ni addu'ar ba zata karbu ba” Ya saka dariya. “Tashi zaki yi ki rike ta?” “Tsab kuwa yadda na rike maka zuciya ba” Yayi dariya sosai ya riko hannunta. “Ke da nake shirye shiryen canja miki mota kike min zancen tafiya kauna” “Tun wacan zuwa fa ban sake zuwa ba, amman da gaske zaka sauya min mota?” “Eh mana taki zai a barwa Mama” Ta rumgume shi tana murna ya rage gudun yake da sauri. “Kai kai kai karki samu tafiya lahira ba mu shirya ba” “Muna tafiya ai sai mu shige aljanna kawai” Dariya kawai take tana murna shi kuma yayi murmushi ya girgiza kai. “Alhamdullahi Allah na gode da ka ba ni Kareem a matsayin miji” “Ni ma na gode Allah da ya ba ni Noor a matsayin Mata, my match” Ta sumbanci fuskatarsa, ya sumbanci hannunta. *** *** *** Tammat Bi Hamdillahi Ni Khadeeja Candy ina addu'a ga duk wata budurwa ko bazawara dake karanta littafin nan Allah ya hada ku da maza na gari Ameen. Masu aure kuma Allah ya dauwamar da farinciki a gidanjenku, ya raya zuri'arku ya shirya mazajenku tare da mu gaba daya. Alhamdullahi na gode Allah da ya nuna min farko da karshen wannan labari mai suna TA KI ZAMAN AURE, Allah yasa mu amfana da darasin ciki, ya ba mu ikon kiyaye kuskure kuma ya yafe mana. Ku yi hakuri da typing errors da ake samu a pages ko rashin cika kalma ko yankewa rashin samun isashen lokacin editing ne ke kawo haka, fatar za ayi ma yar marainiyar Allah afuwa 🥺🤲 Kamar yadda nake fada littafin nan ba kyauta ba ne, na kudi ne marasa tsoron hakki suke fitarwa, idan kun shirya sauke nauyin hakkina sai ku biya 500 to 8036126660 Opay Hadiza Abubakar. Godiya ga duk wanda ya siya littafin nan, na gode sosai Allah ya bar kauna son so Fisabilillahi 🥰❤ Ta ku har Kullum Khadeeja Candy ke muku fatan alheri. 😍 karku manta ina siyar da kayan kitchen da boxes, akwai tufafi kala kala da abaya. Please patronized me. +2348036126660