AJEEMAL🌬 STORY AND WRITING By Oum amreesh? DAGA ALKALAMIN Khaleeseart Raeeys💦💦 ........... .... .........Free book😍 ............ Page 4?8?.............................. 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 ....... .. G'yara tsa yuwa heelah tayi baki bude heelah kebin Ajmal da Nisha da kallo yayin da Nisha ke serving dinshi ta shaka abinci a plate ta tura masa plate din gabanshi, jikake dadda d'an kamshin abincin gabaya daya ya gauraye tsakar parlourn duk wani abunda nisha tasan ajmal zai bukata seda ta tanadar masa, heelah takaici yacikata kamar ta hadiye ranta jitayi tamkar ta isa garesu tarufesu da duka tadauki plate din abincin tajuyewa nisha atsakiyar kanta , da kar fi Raheelah ta ciza lips dinta daga bi sani cikin sauri ta haura upstairs tabar arean parlour , tsit kakeji parlourn kamar bakowa , Nisha tunda ta gama serving din Ajmal taja baya ta tsaya tana bin Aheel da kallo gwanin ban tausayi ya shige jikin papansa tamkar mai shirin ko mawa ciki, se ajiyar zuciya yake saboda tsawar dayasha gurin mommynsa dazu , itade kullum tausayin Aheel da kaunarsa sake karuwa yake kullum sake tasiri yake cikin zuciyarta , jitake inama ace Aheel daga cikinta yafito da ya sha ta rai raya kulawa tareda shagwabashi , wacce baisamu daga mom dinsa , Ajmal kuwa hankali kwance yakecin abincin yana latsa phone dinsa, yau wajan cin abincin nasa harwani lumlumshe ido yake da alama yana amsar sakon girkin yanda yakamata , kamar wanda akace yadago kai , karaf idonsa yasauka akan nisha wacce ta zura masa ido yuwa zata lasheshi seai zuba murmushi take , ganin yanda taga ajmal keta lumlumshi ido kamar maijin bacci , har kullum face dinsa kara kyau da kwarjini yake ga kyakykyawan dimple dinsa dake lo tsawa yayin da yake cin abincin , duk wanda yasanya ido kansa bazaiso yajanye idonsa daga kansaba" He! are you okay ajmal yatambaya yana hade gira , " I'm okay nisha tafadi adan razane because yakamata tana masa kallon kwaf, jin haka yasa yacigaba da cin abincin , yana kammalawa , yajuya gefe yakalli kyakykyawan dan nashi aheel wanda tuni yasuma gyangyadawa jikin papanshi , ajmal hanu yasa yasun kuci aheel yadaura saman cinyarshi aheel tar idonsa akan papanshi yashiga zuba murmushi, ajmal shima kallon dan nasa yake tareda fadin," My little boss aje ayiwasu hajia gaisuwan safe ajmal yafadi yana masa alamar yabi nisha sutafi aheel kamar jira yake dama cikin hanzari yazame daga cinyar papansa ya isa gun nisha yana washe mata baki, itama se murmushi take zubawa, nan tamatsa tashiga tattare saman table din tareda daukan tray din tana shirin barin parlour, "As from now bana bukatan breakfast lunch ko dinner daga side din su daddy , duk wani abun bukata na tanadesu cikin store dina , kululu yan hanjin nisha yakada meyake nufi ?kitchen dinsu zata shiga tanamasa girki ? " Bakiji bane? " ajmal yatambaya jin shiru bata amsashiba, nisha murya asanyaye tace " To naji " daga haka tadauki hanyar fita tareda aheel dake biye da ita , ajmal tunda tajuya yakurawa bayanta ido hartafice ,karun farko daya tsaya yasanya ido akan yarinyar yau shigar da nisha tayi skirt and blouses yayi matukar yimata kyau gashi yafitar mata da shape sosai ajmal baisamu daman kallonta da kyauba har seda tajuya baya sannan yasamu daman yimata kallon tsaf yanda take tafiya slowly kamar wata macijiya gwanin daukan hankalin mai kallonta ba laifi yarinyar akwai tsari da yanayi maikyau duk da ba tsayawa wani kallonta yake da kyauba, balle yasan sauran baiwar da Allah yamata wani gauron numfashi yasauke daga bisani yamike yanufi upstairs yashiga bedroom dinshi tunda yashigo dakin yafahimci kamar ankimtsa bedroom din ba kamar yanda yafita yabariba , koda yashiga toilet ma haka angyarashi an wanke duk dadai gyaran bawai dari bisa dari bane yasan bazai wuce aikin heelah ba. tadaiyi kokari because bawani iya aiki tayiba just kinibibine irin nata, koda yashiga toilet din bakinsa ya wanke tareda face dinshi sannan yafito yanemi sofa yazauna , laptop dinshi yashiga dannawa yafada wani aikin jim kadan heelah taturo kafa tashigo kallo daya ajmal yamata yakai dakai yacigaba da abunda yake, tana karisowa tanemiguri kusa dashi tazauna ," "sannu da hutawa honey " Heelah tafad'i tana dan murmusawa, batareda yakalletaba yagyada mata kai batareda yace komai ba, dan silent Heelah tayi daga bisani tadaura head dinta a shoulder dinsa tashiga raira masa kuka, mamakine yakama Ajmal jin sautin kukan Heelah ya doki kunnuwansa , rantsa ido yayi tareda zame shoulder dinsa yajuyo suna fiskantan juna , "what are you cry" yatambaya yana kallon Heelah dake matsar kwalla, head dinta tamayar saman cinyarshi cikin kuka take fadin, "Pls honey meyasa duk abunda zanyi naburgeka bakaso ? why? inwani laifi nayi aiseka sanar dani nabaka hakuri pls !" Heelah tafad'i gamida tasowa tarike hand din Ajmal, " niba abunda kikamin, kuma niban hana kiyi abunda zaiburgeniba duk da burgeni abune mai walaha kema kin sani yafad'i yana dan zame hand dinshi, "But meyasa kazabi waccan yarinyar amatsayin mai hidama dakai bayan gani amatsayin matarka, "I'm not choosing her abunda yakamata kiyine tanuna miki amatsayinki nayadda kikafada koba komai tafara maido dake cikin sense dinki" Ajmal yabata amsa tareda mikewa yadauki phone dinshi yana kokarin barin dakin, takaici duk yacika Heelah jin abunda Ajmal yafad'i mai yake nufi da ita tadawo da ita hankalinta, dasauri Heelah tawuce gabanshi tana fadi'n, " to daga yau banason sake ganin kafarta cikin side dinnan idan ba hakaba sena karyata gida uku.., ihu heelah tasake sakamakon damko gashin head dinta da Ajmal yayi , rai amatukar bace yake magana," baki fiska danayi bashi yake nufin kimin rashin kunya ba , sake murda gashin nata yayi yanacigaba da fadin " yarinyar dakike magana akanta kuma she is my staff nitakeyiwa aiki bakeba barunki da ita , yana gama fadin haka yasaketa yajuya yafita abunsa , daganan Heelah tafad'i kan gwiwowinta tasaki sabon kuka tamkar wacce tayi sabon hauka ,.... dariya suke sunashewa gwani sha'awa ana breakfast anatafa hira kamar yanda aka saba , su Hajia Goggo rabi ammi ga daddy wanda Aheel kecinyarsa yanashan fruit salad , gefe su yan matan ammi Reeda da a Fadeelah sekuma Nisha dake gefen hajiarta "Niko nace ya maganar komawar takine , ko kincanza shawara ba yanzu ba" Daddy ke tambayan Goggo rabi , tambayetade ya kama tasamu takoma tabar bar gidanta tamakale anan, Hajia takarb'i zancen tana kallon Goggo rabi, dan zumbura baki Goggo rabi tayi kamar wata karamar yarinyar tana fadi'n," ba fasawa nayiba jira nake atsai da bikin yaranan nan saboda nasamu daman dawowa bikinsu nan kusa , " Hhh wasu yaran wai? Daddy yatambaya yana yar dariya , " gasu agefenka kana kallonsu Goggo rabi tanuna su reeda dasuke zazzare ido , " yo banda abunki yaranda suke karatu basu tsaida samariba balle asa ranar auraddasu gwarama ita fareeda yar gd za ayi ba matsala but ita hajia karama ( fadeelah ) babu saurayin ma balle ayi tunanin hadasu Daddy yafadi yana dan kurban ruwan tea dariya duka suka bushe dashi suna kallon fadeelah wacce taturabaki tashagwabe fiska," To albishirunku , itama fadeela anyi mata miji lokaci kawai mukejira, gabaki daya hankalinsu suka mayar kan ammi wacce takemagana, " ina mijin yake akawo manashi mugansa Goggo rabi tafadi suna koma dariya, ," seriously last week MODIBBO yasameni da maganar cewa yayiwa Fadeelah miji nasanarwa Daddynsu atsaida ranar bikinsu, " Amma ai ba asanar da nidinba , amma waye yayi babban sa'a haka Daddy ya tambaya gaba daya suka koma maida kallonsu ga ammi suna jiran amsa harda Fadeelah dayi tsuri tsuri da ita tana jiran tajiwaye akayiwa sadakanta haka , murmushi ammi tayi tana dan juya ido takalli Fadeelah miji nagari zabi mai kyau aboki ga yayansu kuma Doctor gida da waje doctor fu' ad Allah yasa zamin yayi miki ammi tafad'i tana kallon Fadeelah data zaro ido waje , tsan tsan farin ciki batasan sanda tafurta," Alhamdulillah abaiyane wanda yasa tayi hanzarin mikewa dasauri tabar gurin tanufi bedroom da gudu , nan fa su Nisha da Reeda suka rufa mata baya , daga nan fa dukansu suka shigayin hamdallah lallai yayansu yayiwa k'anwarsu zabi nagari sede fatan dacewa , " Masha allah komai yayi kyau yanda akeso , duk da tafiya tasameni cikin week dinan ammade zanje muzauna da dan uwana (abu)muga abunda yadace se musamu mutsaida bikin ko nan da 1 month tunda bawani abunda zamu tsaya jiraba, sede muyi fatan Allah ya aramana tsawon rai da lokaci, nan su ammi suka shiga amsawa da "Ameen , yau kowa farinciki fal zuciyarshi , Fadeelah kamar tazuba ruwa akasa tasha saboda tsan tsan murna da farinciki , haka suka wuni suka kwana cikin nishadi , washe gari da safe karfe 8 Nisha tayi wanka tafito takimtsa jikinta tashirya tsaf cikin duguwar gown tareda yafa mayafi bisa kanta tanufi fita side din Ajmal , kamar yanda ya fada baya bukatan wani abu daga bangaransu , tana isa part dinshi kamar kullum seda suka gaisa da securityn dake wajan sanan tasamu daman shigewa ciki, koda Nisha tashiga ciki hamdallah tayi ganin bakowa cikin parlourn sidi sidi , tashiga kitchen, seda tafara g'yara kitchen din takimtsa komai daga bisani tashiga duba kayayyakin da zatayi amfani dasu bada wani bata lokaciba tashiga hada masa dadda dan delicious data saba , cikin dan kankanin lokaci ta kammala komai tafito tajerashi komai slowly takenyinshi gudun kar wanan masifaffiyar matar tajiyuta, nan tasuma kokarin komawa kitchen din but kankace kwabo heelah tabaiyana a parlourn kaikace kamar jiratake, " Mayya dama nasan kece mai mini buruntu a kitchen, tundaga sama nakejin motsi akasa mai kikazo dauka? heelah ta tambaya yayinda take kokarin karisawa ga nisha wacce tayi tsayowar soja batare da tawaiwayoba , " tambayarki nake kibani amsa kinyi ajiya a kitchen dinne da kikazo dauka , Heelah takuma tambaya tareda juyo da nisha suna fuskantar juna, " Uhm breakfast nazo na hadawa papan aheel, Nisha tace tana zare ido," Uhm yayi kyau dakinbar wannan muzuran dakikeyi ba koranki zanyiba , because ke yar aikin mijinane Mai mana hidima , Bakomai kicigaba da aikinki , sede warning dina dake shine banason wadanan kazamun kafafuwan naki yasake taka bedroom din mijina da sunan g'yara , wannan nikeda hurumi da hakki akanshi inafatan kin gane,? but babu laifi kig'yaramin nawa bedroom din , dan matsawa Heelah tayi dining table area tashiga duba girkin da Nisha tashiryawa ajmal, dan tabe baki tayi sannan tace," Inada bukatan abinda zanci yanzu wadannan abubuwan DA kika shirya banida ra ayinsu, ko zaki iya shiga kitchen kigirkamin abinda nakeda bukata ," kiyi hakuri aunty niba yar aiki bane bazan iya sake girkawani abin yanzuba because inada abunyi yanzu, nisha tafadi tana mai kokarin barin parlourn ," ke tsaya Heelah tafad'i gami da janyota baya, mekike nufi dake ba yarki bane bayan aikatau kekawoki side dina kuma akarkashin mijina kike , dole kikasance akarkashin matar shi, dan haka kiwuce kije kiyi abunda nasaki , cike da takaici Nisha tadubi Heelah tana fadin" Eh akarkashin mijinki nake but kekuma ban kasance akarkashinki kiba because ni yar hidiman mijinkinkine bakeba , dan uwa kuma yayana nadauki mijinki ba uban gida ba,, incede kima macece kamarni , zaifi kyau kishiga kitchen kiyiwa kanki abunda zakici , ni inada abunyi nisha tana fadin haka tajuya zatafice , aiko cikin takaici da bakin ciki heelah batayi wata wataba tasha gaban nisha tadauketa dawani gigitaccen mari wanda yasa nisha zubewa kasa ta tallafe gefen face dinta tasaki kuka wuiwui kamar karamar baby , " tas Nisha taji andauke heelah damari itama wanda yasa nisha mikewa daga durkuson datayi tana kallonsu, Ajmal ne tsaye jikinsa sanye da white jallabiya wanda yake tsaya tundazo daga sama yana hango rikicinda Heelah keyi, ganin marinda Heelah tayiwa Nisha yasa yayi saurin sakkowa cikin bacin rai yadauki Heelah DA mari seda taga wasu taurari, " nikamara? heelah ta tambaya tana kallon ajmal wanda shima Itan yake kallo cikeda takaici," saboda namari wannan mara kunyar yarinyar shine kasa ahanu afiskana da sunan mari , abunda bantaba fiskanta daga garekaba wlh azim yau kajawo mata kwanan kabari Heelah tafadi akidime tayi wajan dining tazari wata yar karamar wuka zatayi kan Nisha dashi, Nisha kamar wacce aka dasa agurin gaba daya tatsorata takasa yin gaba ko baya , ganin abunda Heelah ke kokarin aikatawa yasa Ajmal yashiga gaban Nisha yatare Heelah daga abunda takeson aiwatarwa rike hand din Heelah yayi tareda fisge dan karamin wukar dake hanunta yacillashi gefe , daganan yasa hanu ya sunkuci Heelah saman shoulder dinsa ya haura da ita sama, direct bedroom dinta ya nufa da ita , seda yakata harsaman bed ya wullar da ita daga bisani cikin hanzari yabar dakin tareda baida kofar yarufeta tabaya da key, Heelah kamar wanda hauka yasuma taba kwakwalwarta haka take dukan kofar da karfi tana fadin Ajmal yazu ya bude yau seta kashe nisha, ajmal ko ajikinsa haka yanufi downstairs cikin sauri , amma kafin isowarshi , Nisha najin motsin sakkowanshi ahanzarce tasamu daman watsawa dagu tayi waje, Ajmal naganin fitarta yasa yakoma yazauna kan sofa , yadau mintuna yana zaune agurin daga bisani yamike yahaura sama yanufi bedroom din Aheel, koda yashiga yasamu dan nasa se bacci yake tasha hankali kwance , hakan yasa Ajmal ya fice daga bedroom din Aheel yanufi nashi dakin , yana shigowa yadauki phone dinsa domin duba time karfe 9 dawasu yan mintuna gakuma miss call dayasamu cikin wayarsa jikin screen din wayar anrubuta " My blood , phone din ya ajiye yanufi toilet yayi wanka yafito yashirya cikin shiri maikyau daga bisani yanufi kasa, kotakan breakfast din biyeba yawuce yafita abunsa , Aban garan Nisha kuwa tana barin side din Ajmal tanufi part dinsu direct bedroom dinsu tawuce tasamu su reeda se bacci suke basuda niyan farkawa yanzu, itama kwanciyar tayi tana share hawayenta tareda maida ajitar zuciya , bakaramin takaici tajiba da marin da Heelah tayimata, amma ko bakomai taji radadin da takeji yarago tunda agabanta Ajmal yasa hanu yawanke matansa da mari saboda ita , bakaramin jindadin hakan tayiba , ko bakomai da lamamun tana da dan mutunci aidonsa tunda ya iya marin matarsa akanta abunda baitabayiba kuma yanuna baccin ransa sosai afili, to kuwa itama yanzu takejin takudiri damaran farantawa mijinta tareda yimasa hidima yanda yakamata tunda ita tagaza daha bacci mai nauyi yadauketa because dama tagaji gashi jiya batayiwani bacci sosaiba saboda kwana tayi tana karantu exam dazatayi na jam gobe gashi dasafe ta tashi dawani aikin kuma, Misalin karfe 11pm nisha bacci mai nauyi take , cikin baccin taji anataba mata tafin yan kafafuwanta, but takasa bude idanunta because baccine sosai acikinsu haka cikin muryan bacci Nisha kefadin ," Uhm uhm Banaso! cankuma sejitayi ankoma anakokarin jan pillown data kwanta Kai ahankali, jin head dinta nakokarin barin saman pillow yasa tabude ido ahankali , tar tabude idonta gamida tashitsaye tsakiyar gadon tana zazzare idanu , farkon bude idonta ganitayi kamar Ajmal tagani yana tsaye kanta, daga bisani kuma data murza idon dakyau Kamal tagani tsaye yana washe mata baki yana fadin," Surprise! da mamaki take binshi da kallo sekuma tamaida kallonta ga dakin ita kadai su fadeelah basanan sekuma takalli kamal wanda keta zubamata murmushi kamar gonar auduga, " Ya kamal! Kaine? nisha tafad'i ahankali, dariya yakwashe dashi kafin yace," Year I'm nacanza mikine? yafadi yana mata kayataccen murmushi, sakkowa nisha tayi daga bedroom din tana fadin, " saukan yaushe? Ina aunty nabilah? dan matsowa yayi kusa da ita yana fad'in " Nayi surprising din kune because duk gidan nan bawanda yasan da zan dawo ya ajmal ne kaide yasani in fact ma shiya daukomu daga airport, kallonshi kawai Nisha keyi tana murmushi," Ina Aunty Nabilah Nisha tasake tambaya karo nabiyu, kamar bazaiyi magana ba sekuma taji yace," tana sashin Hajia a can muka sauka duk family anacan kekuma kinanan kina bacci, cikin hanzari nisha tashiga fadi'n, " Muje can musameso to tafad'i tana kokarin yin gaba , ga mamakinta setaga Kamal yanuke, bakin bed yanema yazauna tareda hade raii, " Zomuje mana! Nisha tafadi gamida jiyowa tana kallonshi, amma kamal senukewa yakumayi yaki tashi, dariya nisha tasaki ganin yanda kamal yayi tamkar wani baby harda wani nuke shoulder, " Please meyasa? Nisha tafadi tana d'an shagwab'e fiska " Naki d'in da murna da d'auki nataho gareki but ko tambayan yanake bakiyiba balle. adanyi hugging dina amatsayina na brother dinki, dariya nisha takumayi tana fad'in, " I'm sorry bro ya kake let me shaking hands nisha tafadi gamida mika masa hanu , haka kamal yadauki hanu yamika mata amma ga mamakinta setaga kamal gam yarike mata hanu tareda janyo hanunta tafado jikinsa tsam yarungumeta akirjinsa kamar wata baby, cikin hanzari nisha tajanye jikinta akunyace tafice da gudu tana murmushi, shima mikewa yayi cike da farin ciki da nishade yana murmusawa yabi bayanta, Nisha bata tsaya da gudunba harseda ta iso door din Hajia taja tatsaya ganin Ajmal dake kokarin fitowa wanda harsuna kokarin karo da juna , kallonta Ajmal ya tsayayi da mamakin hanzarin metake gashi harwani haki take kamar wacce tayi tsere , daga kanda zaiyine ya hange Kamal dake biye da ita wanda ganin yayansu yasa yarage saurin yashiga tafiya slowly yana sosa keya irinta marasa gaskiya " wato shiyasa akane meshi cikin family aka rasa ashe gun wannan yarinyar yaje yatare Ajmal yashiga maganar zuci , baitsaya jiran isowar Kamal ba yasamu daman barin wajan yanufi side dinshi, wanda hakan yabawa Nisha daman shigewa part din Hajia cikin hanzari kamal shima yasamu daman biye mata baya, Ajmal yana isa cikin parlour ya hangi Aheel da mom dinsa wacce tayi amfani da extra key wajan bude kanta tazuba musu abincin da Nisha ta girka sunaci , Aheel naganin papanshi yashiga washe baki yataso da gudu ya rungumeshi , cidak ajmal yadaga Aheel suka karisa dining table suka zauna, " Your welcome dear Heelah tafad'i kamar ba ita tagama daru dazuba, shiru yayi baice mata kala ba sema kallonta dayake idonta sunyi subul subul dasu saboda kukan datasha dazu , mikewa tsaye tayi tashiga yin serving din Ajmal ba tareda yanemi taimakon taba , shikuwa baiyi kokarin dakatar da itaba hartagama tatura masa plate din abincin gabanshi tareda duk wani abun bukatu , bamusu yasuma cin abincin , yana tsaka da cin abincin kamar wanda aka tsikareshi idanunshi suka shiga hasko masa nisha dake tafe cikin hanzari kamal nabiye da ita, Nan kuma ya kauda wannan tunanin daga ransa, lokaci d'aya kuma yaji abincin yafita daga ransa ma' ana yakoshi , haka yasoma kokarin mikewa , " Papa ina zakaje ? Aheel ke tambayan papanshi ganin yamike" I'm going to the rest kazauna kusa da mom dinka ,gyada kai aheel yayi tareda cigaba dashan cornflakes dake gabanshi , heelah bayan ajmal tabi da kallo tana tab'e baki harya kurewa ganinta ,.. , Ab'an garansu nisha kuwa tunda suka shiga sashin Hajia , a parlour suka tararda sauran familyn anatashan fira cikin raha Daddy Ammi Hajia da Goggo rabi sesu fadeelah da reeda wanda suka sanya Nabilah a tsakiya sunata zuba mata surutu da tambayoyi, itakuwa Nabilah duk hankalinta nakan Kamal da nisha wanda sukashigo yanzu atare , duk yanda Nabilah tayi iya kokarinta wajan mantarda Kamal soyayyan nisha amma abun yaci tura , yanzu gashi daga saukanso zuwa gida ita yafara cigiya , koyanzuma da ake tsaka da hira tafahimci yanda suke jefawa junansu wani kallo suna murmushi, shiyasa koda sukashigo cikin parlour Nisha data dagawa Nabilah gaisuwa ba harzuci ta amsa mataba saboda yanda kishi ke d'awai niya da ita, itakuwa Nisha kallon Nabilah take ganin yanda takara canzawa tayi kyau taciko kuma takara haske ,da alama hutu yakarbeta Masha allah wasa yayi kyau kamal kundawo cikin SAA sai dai kuma kasam mashemu because bawanda kafadawa , yanzu yakamata mubarku kuje kuhuta kaida matarka dan nasan baza arasa gajiya atareda kuba, Daddy yafadi yana kallon kamal daga bisani kuma yamaida kallonsa ga Ammi yacigaba da fadin," yakamata kiyiwa Barka magana ta tanadar musu da abuntabawa , daga bisani kuma munada bukatar ahadamana kayataccen dinner in the night saboda farinciki wannan ranar , " Insha allah yanzu kuwa Ammi tafadi cikin farinciki tareda mikewa tafice , sundan taba hira sosai yayinda Kamal yaciga ba dabasu labarin yanda wasansu ta kwallon kafa takasance, seguraran azahar tagabato kai suka suma watsewa domin gabatar da bautan ubangiji, koda suka fadeelah suka shigo bedroom dinsu Reeda ne kadai tashiga toilet tagabato alwalanta sukuwa Nisha da Fadeelah suna fashin sallah ya bakon nasu kusan atare yaziyarcesu, cikin Nisha da yamurda matane nayunwa yasa tatuna tunsafe ba abunda tasawa cikinta , hakan yasa tamike tafice tabar fadeelah dake kwance saman bed tana latsa wayarta , Nisha direct kitchen tanufa ta tadda barka tana tsaka da aikin da ammi tasata , barka naganin nisha tasaki murmushi, "yar nan yau koma ina kika shiga kolekoni ba kiba inata cikiyarki "murmushi nisha itama tayi tana fadin "kinsan yanzu papan Aheel yace nadaina kawo masa breakfast daga nan sede naje can part dinsa nayimasa girki dana dawo kuma bacci nakomayi shiyasa yau bakijiniba ai " . " Kai amma yayankun nan yana wahalar mana dake amma ko bakomai zaki samu lada ai, amma koya kikeji da wannan masifaffiyan matar tashi mai bala'in kishin tsaya duk ita take kore masu mata aiki saboda rashin hankali irin nata , Barka tafad'i gamida jimami" "Uhm baba barka taimakeni da a binda zansawa acikina because yunwa nakeji sosai tunsafe namance banci komai ba Nisha tafad'i gamida kaiwar da zancen barka," "laa ai ammi tafadamin bake a breakfast din dazu sabida bacci kike baki tashiba shiyasama nakillace miki naki breakfast din amma inda wani abunda kikeso kifadi yanzu sena miki shi," "aa basekin wahalar da kankiba iya wannan dinma yayi ," "To shikenan kede jekizauna a dining table yanzunan zanfito" Barka tafad'i, bamusu Nisha tayi abunda Barka tace ba dadewa Barka tafito daga kitchen tajerawa Nisha plate agabanta plate din Irish and chicken dawani hadin salad agefe se dan madaidaicin kyakykyawan bowl mai daukeda fruit salad wanda yaji madara Yakuma sha sanyi ,bawani tsayawa jira Nisha tasoma ci seda taci takoshi takauda yunwar dake tareda ita daga nan tadauki plates din tanufi kitchen, tana shiga ta ajiyesu daga bisani tashiga taya Barka da aikace aikacen da take ,sannu ahankali sunayi suna fira hatsuka kammala daga nan suka shiga jera kayan lunch bisa dining table daga nan Barka takoma kitchen tadauko try din abincin data tanadarwa kamal da matarsa masu lunch din tasuma kokarin ficewa, "Baba Barka ina kuma zaki bayan gani ? nasan lunch din su ya kamal ne da Aunty Nabilah please bani nakaimusu na hutar dake ," "Aa yar nan baza ayi hakaba, tunsafe kika gama bautan yayansu yanzu kuma nabarki kikare Dana kaninsa gaskiya baza ayi haka daniba kibarshi kawai yanzu zanje nadawo " "Please baba Barka kibari nakai mana " nanfa Nisha taita mata magiya tareda dagewa Barka wanda yasa dole Barka tahakura tabata try din abincin nisha ta amsa tareda sa kai tafice , Nisha nakarisowa door din Kamal tashiyin knocking bugu daya zuwa biyu aka bude, koda budewa kuwa Nabilah takagani tsaye cikin shirin kananun kaya t shirt da wando skintight wanda yawuce gwiwar kafarta kadan tasakalo sumarta har baya yakwanta lub tayi kyau da ita, murmushi Nabilah tasakarwa Nisha cikin sanyin murya tace , " Please come in! ahankali nisha tasakalo kafarta takariso cikin parlour yayinda Nabilah tamaida door tarufe ta dawo kusa da Neesha ta tsaya tana cigaba da murmushi, itama nisha murmushi take daga bisani tashiga fadin, " " Am..dam.ma lunch dinku nakawo muku ," "Ayya thanks you so much" Nabilah tafad'i gamida karban try din abincin takarisa dashi saman table ta ajiye ganin haka yasa cikin hanzari nisha tace," " se anjima daga haka tajuya tafice tabar nabilah tsaye tana binta daga kallo hartafice , Neesha nafita tundaga nisa ta hangi ajmal hanunsa dauke da na Aheel se kamal da Daddy wanda yanzu dawowarsu daga masallaci sunjero suna tafiya gwanin sha'awa da burgewa Kamal daga nesa ya hangi nisha tafito daga part dinshi amma kafin su iso harta shige bangaransu cikin sauri, direct Ajmal yanufi side dinshi shida dansa hakama Daddy yanufi nashi sashin , daga nan Kamal shima yakarisa nashi part din, Da dare guraren karfe 9:pm gabaki daya ahalin abubakar modibbo bature sun hade guri guda suna gudanar da kayataccen dinner, dining table medauke da gurin zaman mutum 12 kowanne acikinsu yakasance daga daya daga ciki wasu suna facing din wasu gwanin burgewa da ban sha'awa harda Heelah wacce Ajmal ya gayyatota badan komai because Daddy yace yana bukatan kowa yakasance gurin dinner, Heelah batasan da dawowarsu kamal ba kwata kwata seyanzu da tashigo ta ganewa idonta wanda hakan ba karamin mamaki tayiba , Nisha kuwa tayi tsayuwar daka wajan taya Barka kawo abinci anajerewa wanda komai tare suka gudanar dashi seda suka kammala jera komai Barka tajuya takoma ciki nisha kuma tasamu daman zama kamar yadda kowa yazauna ,daga nanfa kowannensu yashiga serving din kanshi da abunda yakeso yana zubawa a plate, banda ajmal dako motsi baiyiba bayida kuma niyar motsawaa "yade kowa yadibi abunda yakeso yana ci kaikuwa kasa phone agaba kana dannawa?" Daddy ke tambayan ajmal dayayi sunkuye da kayi yana latsa phone dinsa, dan dago kai yayi ba tareda yace komai ba ya ajiye phone din gefe daga bisani yagyara zama ya kallo nisha wacce idonta ke kanshi because kujerunsu yana facing najuna, yanda yakora mata ido tasan serving dinshi yakeso tayi amma ita kuma nisha setashiga kallon heelah wacce takecin abinci tana yamutsa fiska kamar wacce akasa dole ko kallon inda sukema batayi, nan kuma taimada kallonta ga ajmal wanda ya hade rai yabata fiska wani kallon da yakuma watsa matane yasa nisha mikewa tsulum wanda hakan yayi sanadin dawowada hankalim ahalin guresu, daga Hajia Daddy suwa Ammi suka shiga murmusawa ganin yanda Nisha ke serving din ajmal gwanin shaawa da burgewa duk da dama sunsan ajmal inde tawannan fanninne to komai se amsa abincin ma inda zaisamu adinga bashi abaki ajiye spoon zaiyi , Goggo rabi bakinta kamar zai taba kumatu tsabar murmushin jin dadi, kamal kuwa da mamaki yake kallon nisha ganin bani na iya irin na yarinyar dayin abunda ba asataba gaba daya yarinyar tanasun bawa kanta wahala , taban garan heelah nunawa tayi ko ajikinta amma cikin zuciya allah kadai tasan kunar zunda take gaba daya nisha Rana shigar mata hanci amma ba dadewa zata facuta, Nisha harta gama serving din ajmal takoma tazauna kamal kebinta da kallo , nabilah kuwa duk motsin mijinta idonta nakansa , abincin dake gabanta bawani ci sosai takeba kawai tsakura take tana juya spoon ajmal kuwa nisha nagama serving dinshi yashiga gunar da nashi cin abincin, Jim kadan ta bangaran nabilah tafarajin kanta na bala'in sarawa, jitayi duniyar najuya mata ahankali ta ajiye spoon din hanunta adan dafe tamike daniyar tashi , "Bade harkin kammalaba" Ammi ta tsareta da tambaya , nabilah bude baki tayi daniyar magana sekuma takasa because wani yunkurin amai dayataso mata aiko cikin hanzari ta toshe bakinta tawatsa aguje tafice daga parlourn, gabaki dayansu se bin bayanta da kallo suka shigayi harta fice banda kamal dayayi yunkurin tashi yabita, "mekatsaya jira da ka kasa bin bayan matarka kamata yayi kabita idan da wani abunda yaci karfinku sekazo kayi magana" Hajia tafad'i tana kallon Kamal wanda keta zare ido shibai zaunaba baikuma tsayaba but jin abunda hajia tafad'i yasashi jin karfin gwaiwar bin bayan matarshi dan haka cikin hanzari yabi bayanta, " " Masha allah , ikon allah kai allah abin godiya, tsarabar Canada har gida kai alhamdulillahi" Goggo rabi tafadi tana daga hannuwa sama, hajia da Ammi farinciki harsun kasa cewa komai , Daddy kuwa kai kasa se murmushi yake heelah se hararo Goggo rabi take wacce keta kwararo godiya ga ubangiji", " dama kinbar wannan godiyar dakike dan abunda kuke tunani insha allahu zubewa zaiyi bade tahaifeshi cikin gidan nanba heelah ke maganar zuci , gefe kuwasu reeda ne ke magana kasa kasa tsakaninsu, "Awwwn nabilah fa kamar cikine gareta ko" fadeelah tafad'i ahankali, " bakamar bane cikinema" reeda tabata amsa yayinda sukacigaba da cin abincinsu kamar basu suka gama kuskus yanzuba, duk abunda suka gama tattaunawa tsakaninsu nisha najinsu se murmushi take gefe gefe aheel zaisamu kani zasu samu little baby, shikuwa gogan ko ajikinshi tamkar baisan me akecikiba abincinsa yakeci cikin kwanciyar hankali, Kamal nakarisawa part dinsu koda yashigo parlour ba nabilah aciki hakan yabashi daman karisawa cikin bedroom nan yaci karo da sautin nabilah cikin toilet tanata faman zabga amai cikin hanzari yakarisa baking toilet din ya tsaya harseda ta gamayin aman tawanke bakinta tafito ta tararda kamal bakin door yana jiranta, "sannu! meyake damunkine" Kamal ya tambaya gamida tallafota suka karisa bakin bed suka zauna, " "Please tell me what's wrong ? "Kamal yakuma tambaya, " " bakomai nabilah tafadi gamida sunnar dakai kasa ,cikin hanzari kamal yadauki phone dinshi yasuma lalubar wata number, "Wait! what are you doing?" Nabilah ta tambaya gamida rike hanunshi, " doctor fu'ad zankira yanzo ya dubaki yafadamin meke damunki" Kamal yabata amsa cikin damuwa Nabilah karban wayar tayi ta ajiye gefe daga bisani takalleshi yana fad'in, " bakasan me yake damunaba? gyada mata kai kawai kamal yayi daga nan nabilah tadauki hand din shi tadaura saman cikinta tacigaba da fad'in, "You are doing to be father soon insha allah" Cikin murna da farinciki gamida d'auki kamal ke kallon nabilah, "Oh god waiyanzu ciki gareki ? "d'an g'yad'a kai nabilah tayi tasunnar dakai tana murmushi, "Oh Allah nagode maka zanzama Daddy yanzu nakara girma nima " kamal yafad'i tareda rungumo nabilah yana cigaba da fad'in, "Nagode Allah yamiki albarka ya kareki keda babyna " , daga nan nabilah tarungumishi cikin tsatsan so da kauna tana fad'in " Ameen sannu ahankali suka suma lulawa duniyar maaurata cikin shauki da begen juna , .... Abangaransu Daddy koda sukajira suga dowowar kamal sukaji shiru hakan ya tabbar musu lapiar kenan da haka suka cigaba da gudanar da dinner d insu , koda suka kammala daga nan kowa yashiga watsewa don yau ba tsayawa dugun hira kasancewa dare yayi sosai , dama ajmal baitsaya wani dugun cin abinciba yatashi yafice, matarshima tarufa masa baya tareda aheel daketa rigima shi bazai mom dinsaba gurin auntynsa zai kasance , daker heelah tasamu tayakiceshi daga jikin nisha suka fice , sude hajia har kullum suna mamakin sabonda aheel yayi da nisha , dan haka suma suna gama kammala cin abincin suka suma watsewa kowa yanufi turakarsa , zuciyoyinsu cike da farin ciki da nishad'i, washe gari guraren karfe 8:am bayan ammi tayi breakfast di'nta yanda tasaba tayi shirinta nazuwa office, nan tafito daga part dinsu direct tanufi part din kamal , seda tazo daidai door d'in tashigayin knocking, bugu daya zuwa biyu aka bude kamal ne yafad'e door d'in yanda sanye cikin black jallabiya ganin ammi tsaye bakin door yasan yashiga sakin murmushi yana fad'in, "Please Ammi yakika tsaya shigo mana" ,murmushi itama ammi keyi batareda wani musuba takarisa shiga cikin parlourn, can doguwar sofa ta hangi nabilah takishingida wanda ganin ammi yasa tamike zaune tana yar murmushi gamida sun kuyar dakai "Ai dama kinyi kwanciyarki karna takuraki , ammi tafad'i gamida karisawa kusa da nabilah tazauna," Ammi ina kwana antashi lapia, "Lapia qlu yajikin nakikuma dafatan ba abunda yake damunki yanzu, d'an gy'ada kai nabilah tayi tana fad'in "Bakomai !" ", that's good dama yanzu nake shirin tafiya office shine nace bari nazo naga jikin naki , kuma natambaya Inda akwai wani abunda kikeda shaawa nasa akawo miki because karkicigaba da wahalar da kanki, " "Yauwa Ammi tambayeta de yanzunan nakita tambayanta tafad'i min metakesu taci naje nayi mata order but taki wai bata shaawar komai, kinga wadannan kayan fruit din sune kadai tasamu tadan tabasu Kamal yatare maganar yana nunawa Ammi plate d'in kayan fruit dake ajiye saman table, Yana kuma kallon Nabilah dayi sunkuye da kai , "sudinma babu laifi suna da amfani amma fruit kad'ai bazai wadaceki keda bari naje zansa barka takawomiki abun tabawa wanda zaki'iyaci , karkidinga barin cikin ki dayunwa, d'an g'yad'a kai nabilah tayi taga haka ammi tamike tana kallon kamal tana fad'in" Nizan wuce kakula da kyau , " To ammi kamal yace daga haka yarako ammi harbakin door daga bisani sukayi sallama kamal ya maida door yarufe tareda komawa kosa da nabilah yazauna yamata matashi da cinyarsa kamar yanda suke dazu kafin shigowar ammi , ahankali yakeshafa sumar kanta yana fad'in, " allah yasa kihaifamin baby mai kama dake kamal yafadi yana kallon nabilah da face dinsu ke fiskantar najuna, dan wani cool smile nabilah tasake tana fad'in, " Nikuma nafison nahaifi baby sak irinka , because of what? Kamal ya tambaya " Because kafini kyau da komai nabilah tafad'i cike da murmushi, shima murmushin yake yaname jan dugun hancinta yana fad'in, " And you ba fatanmu de allah yasauke ki lpy " Ameen nabilah ta amsa cikin sanyin murya ,Jim kadan suna tsaka da yar firan tasu sukajiyo knocking din door, " come in! kamal yafadi ba tareda ya motsa daga inda yakeba gaba kidayansu suka tsirawa kofar ido dan ganin maishigowa ganin Barka dauke da try din abinci yasa kamal yasake jingina da jikin sofa yana murmushi, ita kuwa Nabilah kokarin tashi daga cinyarshi tashigayi amma kamal ya hanata dan haka yasa tahakura da tashin , " Megida Barka da safiya fatan antashi lpy baba bakar tafadi tana yar dariya because kamal mutumintane sosai , tasu tazo daya kasancewanshi mai barkwanci da sun wasa wani lokacin bakamar yayansuba shikadai yafita zaka cikin gidan bayida wasa kuma bayidason magana sosai wani lokacin kuma inyajuye kamar bashiba," Yauwa barkade uwar daki ya aikin kamal yabata amsa yana yar murmushi, dama Ammi tace nakawowa madam wannan Barka tafadi gamida ajiye try din abincin saman table dinda ke gabansu tashiga kallon nabilah dake kwance saman cinyarshi tayi lamo takamar mai bacci wanda ganin shigowar barka yasa takulle ido because yanzu gaba daya kunyar kowa take ko hada ido dakowa batasonyi, amma daga kaga yanda eye lashes dinta kerawa zaka fahimci ba baccin takeba rufe ido kawai tayi dan murmushi Barka tasaki gamida kada kai tana fad'in, " Megida bari naje nakarisa aiyukana se anjima allah ya inganta , kamal cikin farinciki ya amsa da " amin mungode daga haka Barka takama hanyar fita still de murmushi bai gushe daga face dintaba harta karisa ficewa tajanyu musu door din tarufe, kamal kallonsa yamayar kan nabilah yayinda yakuma jan dugun hancinta yanda fad'in, " To yanzu kam semi samudaman bude idon iyayen kunya , waima kunyar mekikejine haka shigowar ammi dazu kigabi kika takura kanki sewani nuke nuke kikefa , bude ido tayi tana kallonshi daga bisani tatura baki tana fad'in" Ni wallahi kunyar kowa nakeji yanzu ko hada ido dakowa banasonyi ," meye dalili ko saboda kintaho musu da tsaraban Canada kamal yafadi yana yar dariya, dan bugu takaiwa shouldern kamal tana fad'in, " Kaikam bakajin komai ko ? " To maizanji kuwa bayan nasan kokarin danayi tashi muyi breakfast dan yunwan nakeji kamal yafadi gamida tada nabilah zauna yashiga bude food flats din abincin, pepper soup din kifine da soyayyiyar irish tareda wani hadin salad nakayan itatuwa masu kara lafiya da kuzari se wani dan madaidaicin bowl wanda ke rufe da Yugo fruit salad ancika madara acikinsa, bawani tsayawa bata time kamal yashiga serving din su , yana gama zuba abincin a plate yashiga bawa nabilah abaki kamar karaman baby shima yanaci ba laifi komai tadan tabashi taji kuma jidadin abinci sosai especially hadin salad din tafi bashi ma himmanci dadin dadawa yanda kamal yayi tsayuwar kaida fata wajan ganin taci takoshi bakaramin dadi hakan tajiba koba komai yana kula da ita sosai but hankalita yaki kwanci ganin kamal da nisha Inuwa daya suke zaune suna haduwa dajuna wanda hakan baya mata dadi kokadan , *_IG AJEEMAL*_ Story and writing by Oum amreesh Nisha hanunta har rawa yake gurin kunna light din bedroom din aiko tana kunnawa haske maikyau da inganci yabaiyana cikin dakin , ahanzarce tajiyu tamaida hankalinta ga saman carpet , kwance yake ya dunk'ule guri guda kamar mejin sanyi still yana rungume da pillow tsam a chest dinshi yana sanye cikin kyakykyawan milk jallabiya gashin kansa duk sun hargitso face dinsa sun manne saboda zufanda suka tsatstsafo masa , idonsa arufe jin motsin mutum da kuma kuna light da akayi yasashi kokarin bude ido ahankali yasaukesu kan Nisha dake kokarin karisowa inda yake lips dinta se bari yake, idonsa yamayar yarintse wanda sukayi jawur dasu because haske yayiwa idonsa karfe " Ya ilahi Nisha tafurta ahankali yayinda tagama karisawa gareshi gefe ta sunkuya kasa tana kallonshi" meyasa sameka? are you okay? Nisha tashiga jera masa tambayoyi cikin rawar murya, jin shiru bai amsa mataba yasa takuma tambayan shi still shirun yakumayi ba amsa hakan yasa tayi tunanin tashi tabashiguri domin atunaninta maybe hanlin nasane na miskilanci yamotsa , amma ayanda taganshi yanzu kamar Wanda bashida cikakkiyar lapia saboda yanayinsa gaba kidaya yanuna hakan gashi yayi shiru baya magana balle tasan abinda ke damunshi, can gefe takalla inda wayansa keta faman ruri saman bed sekuma ta maida kallonta gareshi shiru bai motsa ba baikuma sake bude idoba se ajiyar zuciya dataji yana saukewa , gaba kidaya tagama tsorita anya papan aheel kalau yake kuwa ? gashi haryanzu kiran phone dinshi aketayi ba adenaba da alamar mekiran ya k'agu , Ahankali Nisha ta isa ga bed din tasa hanu ta dauki wayar daga fiskar wayan taga maikiran sunan doctor fu'ad ya baiyana jikin screen phone din , nan Nisha ta fahimci yau ana duba file din ajmal that means bashida lapia kenan Nisha karisawa tayi tareda wayar inda ajmal take kwance taduka kusa dashi tana fadi'n," ga phone dinka anata kira , halwayude bai kumace mata kalaba idonsa arintse se red lip dinsa daketa faman bari yana motsi, " Allah sarki maybe yanajin jiki sosaine da hartayi tunanin daga masa wayar tafadawa doctor fu'ad halinda ta iske ajmal aciki to amma wayakaita wannan karan banin dan haka seta ajiye wayar agefensa tana fadi'n," sannu bari naje nafadawa su hajia azo akaika asibiti Nisha na gama fadi'n haka tamike cikin hanzari, charab taji yariko kasan riganta cikin sauri Nisha tajuyo takalleshi still idonsa a rufe se bakinsa dayaketa kokarin motsawa yanaso yace wani abin , Nisha dawowa tayi kusa dashi tasunkuyu tana kallonshi,tana kuma kallon lips dinsa meyakeson fadi" Help me! abunda taji yace kenan slowly araunace Nisha tashiga tambayanshi," wani abun kakesone kafin takomacewa wani abu sejitayi yace ," d'agani ! dan tsaro ido Nisha tayi tana kallonshi kafintace ," indagaka zuwa ina ? " Bed kawai taji yakuma fadi yana mai sake rungume pillow jikinsa da alamar sanyi yakeji sosai , kallonshi Nisha tashigayi sama da kasa yanzu inba neman magana irin na papan aheel ba ina ita ina iya dagashi , gaba kidayanta in aka hadata guri guda bata wuce lumansa dayaba ga tsayi gajiki tasan ba karamin nauyi zaiyiba to amma yazatayi tunda ya nemi taimakonta dole ta taimaka mishi yaka karfinta , dab dashi taje takuma tsugunawa ta dan janye pillow dinda yarungume ita kanta pillow seda tayi dumi saboda zafin jikin ajmal, dan koda ta matso dab dashi numfashinda yake fitarwa shima dumine jikinsa yayi zafi sosai, da ganan Nisha shiga taimaka mishi wajan tashin takamo hand dinshi tadaura saman shoulder dinta dakyar da sidin goshi tareda taimakonsa cikin karfin hali suka samu daman mikewa , sede koda suka tashi taku daya zuwa biyu suka shigayin tangal tangal da juna ajmal karfenshi ya gaza because jikinsa ba kwari sosai bayajin karfi ajikinsa jikinsa duk amace yake haka Nisha taji yasake mata ragaman jikinsa gaba daya duk yanda Nisha tayi kokarin tallafoshi amma se jikake luuu ajmal na kokarin faduwa aiko cikin sauri da fargaban faduwar tasa Nisha taja hanusa da karfi suka fada saman bed tare kamar kifan mazar k'waila haka suka kife ruf ajmal yarufe Nisha da faffadan k'irjinsa ko burbud'inta ba agani, wani dugun numfashi ajmal yashiga saukewa jinshi saman lallausan bed din shi zamu iyacewa gaba daya ajmal baya cikin sense dinshi Sam yamance yana kwance kan halittan da adam , itakuwa Nisha tunda suka kife takasa motsi se zazzare ido tashigayi face dintama ba agani balle hancinta yashaki numfashi taririn zafin jikin ajmal sebugunta yake gashi bayida niyar dagata hala ko suma yayi taji shiru bai dagataba bugun heart dinshi da yanayin yanda yake sauke ajiyar zuciya duk tana iyaji , shikuwa mutumin jin dumin jikin Nisha yabashi wani yanayi mai dadi da kozari ajikinsa yasa yashiga sake tattarota jikinsa yarungume kamar yanda yasaba rungume pillownsa jinwani wawan runguma da ajmal yamatane yasa idanunta suka fito waje tsabar tsoro dakidima Nisha tasaki wani kara tana fadi'n," Wayyo Allah wayyo ummana zaikashenii.., tar ajmal yabude ido jin muryan Nisha datake sumbatu, cikin zafin nama dakarfin hali ajmal ya kauce gefe cikin sauri yasa hand yadafe goshinsa face dinsa yana kallon sama yarintsa idonshi, Nisha najin kaucewan ajmal tayi hanzarin zamowa daga bed din tana sauke ajiyar zuciya tareda tattaro numfashin ta dake kokarin tsayawa hanu takai tadauki mayafinta dake saman bed din Wanda yafice daga kanta tamaidashi mazauninsa , sidi sidi tasuma kokarin barin bedroom din kanta asunkuye hartazo bakin door tajiyu takai kallonta gareshi, lokacin harya yasan gyara kwanciyarshi yakai hannu yaja blanket yarufo jikinshi , Nisha juyawa tayi tafice daga bedroom din ajmal yabi bayanta da kallo akunyace yarasa wani irin zazzabine yarufeshi haka da har yakasa control kanshi har seda yanemi taimako, rintse ido yakumayi gashide yarufe jikinsa da blanket but baisamu irin relief dinda yasamu dazu da yarungume Nisha ba amatsayin pillow shine mai wannan dumi me dadinba dan mintunan daya samu yayi ajikinta har yafara jin saukin abunda ke damunshi, gaba daya ji yayi ransa yadagule masa yarasa meke masa dadi , Nisha kuwa tana fitowa daga bedroom din tanufo downstairs gudu gudu sauri sauri haka take sakkowa idonta duk sun fito waje tsabar o, tana gama sakkowa taja ta tsaya ganin doctor fu'ad zaune bisa kujeran parlourn yanata faman Kiran line din ajmal, ganin sakkowan Nisha arikece yasa hankalin doctor fu'ad dawowaa gareta wanda yasashi mikewa yashiga yimata murmushi, itama murmushin tashiga kirkirowa tana shafa gefen wuyanta daga nan tashiga dagawa doctor fu'ad gaisuwa, cikin fara'a ya amsa da mamakin yanda yariyar ta canza kyanta yagara baiyana dan da ace baisan tabama ba lallai yace yataba ganin taba ," mutuminfa nakirashi bai daukaba doctor fu'ad ya tambaya," yana bedroom din shi Nisha ta bashi amsa asanyaye," Alright barinaje naduashi doctor fu'ad na gama fadi'n haka yanufi upstairs tareda akwatin agajinsa yana kuma waiwayen kallon Nisha yarinyar akwai kyau da kwarjini ba amagana gurin yarinyar ga hankalin da nitsuwa ga kuma shiga zuci, yana isa bakin door din yatura door din yakarisa shiga bakinsa dauke da sallama yanda Nisha tafita tabarshi haka doctor fu'ad yazo ya taddashi idonsa arintse kamar mai bacci, ajmal jin bude door anshigo yasashi bude ido ahankali ganin doctor fu'ad tsaye kansa yasashi kara bude idon dakyau yana kokarin gyara zama doctor fu'ad dakanshi ya taimaka masa wajan gyara masa zamar ganin cewa yau abokin nashi jikin ba kwari sosai, " sannu boss yajikin ?doctor fu'ad yafad'i tareda duba yanayin zafin jikinshi , " tunyaushe kake fama da zazzabin maizafi haka? doctor fu'ad yakuma tambaya, Dan numfasawa ajmal yayi cikin cool voice yake fadi'n " Problem din da kasanine ya tasomin after that bayan sallahn asuba zazzabi yabiyo baya , " meye amfanin pills in problem din yatasu meyasa kakeson wasa da lapian kane ? " I'm tired ajmal yafad'i yana Dan ya mutsa face, Dan murmushi doctor fu'ad yasaki yana kallon abokin nasa wanda ya hade gira yabata fiska " Hmm naji tunda ka gaji dashan pills se ka sauke miskilanci dake kanka kafahimci rayuwar aure kadinga sauke hakkin dake kanka kabar cutar da kanka da bokiyar zamarka duk da nasan matsalar ka da ita amma hakan bazai hana katauyewa kanka hakkiba, so gaskiya inde zaka cigaba da cutar dakanka haka zanyiwa Daddy da ammi bayani Dan bazan tsaya insa maka ido kana kokarin cutar da lapiyar kaba , kana daya daga cikin maza masu bukata over so kama tayi katafiyar da lapiyar ka yanda yakama karka tsaya cutar da kanka because wannan problem din bakaramin effect garetaba lokaci daya zaiyi affecting naka ba tareda ka ankara ko kashirya masaba so you have to be very careful with that issue ajmal shiru yayi yana sauraron zantukan doctor fu'ad duk da ba yau yasaba jinsuba yasaba tunatar dashi duk lokacin da suka kasance tare shima duk yarasa meke damunshi , idan yace baya bukatan mace yayi karya to amma feelings akan matarshine Sam bayida ita kwata kwata bayajinta aransa balle yaji shaawar neman wani abu daga gareta , some times itake bibiyanshi tana shishshige masa wani lokacin yabiye mata wani time dinkuma inta dameshi haka zaizame yafice yabata guri , duk da wani lokacin yakanso yiwa kansa fada Dan yasan ba karamin cutar da ita yakeba baya bata kulawar da tadace , to amma ya zaiyi rayuwarsace tazu da haka amma yana fatan canzawa , sauke ajiyar zuciya yayi yana kallon doctor fu'ad wanda ya mike tsaye yabude akwatin agajinsa ya zaro allura seda yayi arranging din alluran kafin ya kalli abokin nasa yana fadi'n," Allura zan maka wanda zazzabin zai sauka daga haka yanufoshi ba musu ya gara yamasa alluran daga bisani yakuma dauko daya alluran yakalli ajmal yace wannan kuma alluran baccine zan maka because kanada bukatan kahuta sosai nasan jiya baka iya bacciba , shide ajmal binsa yake da ido bayacewa komai harya gama alluransa ya kuma ya tsaya yana fadi'n," Zuwa anjima bacci zai iya daukanka kafin doctor fu'ad yagama ida zancensa seji sukayi anturo door anshigo Nisha ne tafe bakinta dauke da sallama tashigo hanunta dauke da try din abinci tanufi table din tsakiyar dakin ta ajiye daga bisani takai hanu tadauki cup din dake bisa saman try din Wanda ta hadowa ajmal hot coffee din daya saba sha yakeso especially yau datake tunanin baisa komai acikinsaba saboda rashin lapiyan da yatashi, dashi , gabaki daya zuba mata ido sukayi barinma ace doctor fu'ad yakalleta yakalli ajmal wanda ya zuba mata namujiya yana kallonta gaba daya itama Nisha setaji wani irin nauyin ganin irin kallon da suke mata , " am dama coffee na hadu maka kokanada bukata Nisha tafadi muryarta harsakewa yake harta suma kokarin kasa kasa da hannuta ganin bai karba cikin sauri doctor fu'ad ya amsa yana fadi'n," sannu da kokari sister kamar kinda abunda yake da bukata kenan doctor fu'ad yafad'i yana mata kataccen murmushi, itama dan murmushin tayi jiki asanyaye takalli ajmal wanda yasuma lumlumshi ido allura yasuma ratsashi daga bisani tamaida kallonta ga doctor fu'ad wanda keta zuba murmushi kamar gonar auduga kafin tajuya tafice tabasu gari , doctor fu'ad naganin fitanta yajiyu yakalli ajmal wanda ya lumshe ido bacci ya fara cinye idonshi doctor fu'ad cup din coffee ya mayar ya ajiye bisa table ya kai hanu yadauki akwatin agajinsa daga nan yasuma kokarin ficewa ganin mutumin nasa yasamu bacci seda yarage masa hasken dakin kafin doctor fu'ad yasamu daman ficewa daga bedroom din yajanyo masa door din yarufe , yana fitowa daga side ajmal yashiga motarshi mai gadi yabude masa geat yafice yaso yashiga sugaisa dasu hajia but saurin dayake bazai bari yakarisa cikin gidan ba yabari sewani lokacin da ya ware na musamman, yaumade kamar kullum bayan sun kammala dinner dinsu suka koma parlour akashiga taba hira kamar yanda kasaba gabaki daya family da kakalli fiskokinso zaka fahimci suna cikin nishadi da jin dadi , daya yasanar dasu gobe Daddy zaiyi tafiya kamar yanda yafad'i musu abaya , kuma sanar dasu cewa sun zauna da dan uwansa sun tattauna tsakaninsu yakuma sheda musu yanda sukayi sun tsayar da bikinsu fareeda da fadeelah zuwa 2 month masu zuwa inshallah, su hajia ba karamin dadi sukajiba da wannan kyakykyawan labarin ," Masha Allah to allah de yakaimu yasa albarka cikin lamarin , hajia tafadi cikin murna da farin ciki goggo rabi Daddy da ammi sukashiga fadi'n," Amin Banda su reeda da suka shiga kallon junasu suna muzurai farin ciki ba amma magana Nanda dan wasu lokaci suma zasu zama matan aure gurin mazajensu , sede ita hajia karama( fadeelah) ta dan damu because gashide ana maganan tsaida ranar bikinsu but ko saudaya basu zauna da mutumin nata sun tattauna tsakaninsu balle kowannensu yabada labarin yanda yake feeling dan uwansa to amma de tazubawa sarauta Allah ido taga yanda lamarin zai kasance, " Alakullihalin tunda alamaru suntafi yanda yakamata nimade zuwa jibi jirgina zai daga zan koma gida nima, " Au wai tafiyar zakiyi baza kitsaya ayi bikin da keba seki koma gaba daya naga month din bayawa Daddy yafad'i cikin zolaya yana kallon goggo rabi wacce tafiddo ido waje ," wani ! rufamin asiri gida yayi kewata nafa jima anan tun bikin kamal yau kusan wata daya kenan gashi har ansamu rabo inanan ina zaune ai gwara natafi daga baya nakuma dawowa ga baki daya family dariya sukashigayi jin batun goggo rabi sunsa ba karamin miss dinta zasuyiba zayi miss barkwancinta , sun raba dare suna hira har guraren 10 daga bisani sukashiga yiwa juna sallama kowa yanufi makwancinsa , gari yayi shiru gida yayi tsit su nisha duk sunyi shirin bacci sun kwanta , reedane kawai take zaune bisa sofa tana waya da habibinta Wanda take sanar da ita zaizo seda suka kammala wayan tadawo bed takwanta zuciyar ta fari tas farin ciki da annashiwa ba a magana , aka har bacci ya dauketa , Nisha kuwa lumshe ido kawai tayi but bacci yakasa daukanta ta juyanan ta juya can bacci yaki , nan tunanin ta yashiga tuna mata yanayin da suka kasance dazu da ajmal, yanda tayiyo zafin jikin ajmal bisa jikinta time din dasuka fad'i bed dakuma time dinda yarungumota Wanda yasanya tsikar jikinta tashi , mikewa tayi zaune tazauna ," oh Allah koya jikin nasa yanzu ? Phone din ta tadauka ta sakko daga bed din tanufi parlour shiru parlourn ba kowa harta doshi hanyar fita se kuma taja ta tsaya ganin dare yayi sosai gashi tasan wannan uwar tsiwar Heelah tanan batasan ya zasu kareba but tamatsu taga ya yanayin jikin nasa yanzu, haka tanemi guri tazauna tana ta sakawa da kuncewa mafita dayane yazo mata Kiran line din Ajmal kamar yanda yace zata iya kiranshi taji koyanada wani bukatan duk da ba kowani lokaci yake daga kiranba balle yanzu dayake cikin halin rashin lapia, ba wani tsayawa bata time tashiga kiranshi kamar yanda tunanin ta ya bata, Ajmal wanda tashinsa kenan tun bayan da Doctor fu'ad ya masa allura bai farkaba se yanzu 11 cikin yanayin kasala da rashin karfin jiki Ajmal ya yaye blanket din jikinsa saboda zufanda yasuma tsatstsafo masa alamar cewa zazzabin ya sauka adafe yanufi toilet wanka yayi sosai tareda alwala ya fito, sam bai lura da Heelah wacce take kwance saman sofa tamike bacci yayi awungaba da ita se yanzu daya fito idonsa yasauka kanta, kauda kanshi yayi yashiga zaro wata jallabiyar yasanya sannan yashin fida sallayan yashiga jera sallolinda suka biyoshi, seda yamika sallonshi duka sannan ya sallame ya ninke sallayan yadawo saman sofa ya zauna abincin da Nisha takawo masa dazu yashiga budewa because yunwa ya tashi dashi acikinsa, Heelah jin buruntun bude food flakes yasata motsawa tabude ido tana kallonshi," Dear wani irin bacci kayine yau din nan? Heelah tashiga tambayan Ajmal cikin muryan bacci shiru yayi mata yana kallon try din abincin da Heelah tajera a table din Heelah mikewa tayi ta taso tamatsu gareshi tana fadi'n," bari nayi serving dinka nan tashiga kokarin serving dinshi ya tsaya kawai baice mata komaiba gaba daya jiyayi ransa yadagule masa ganin ba abincin da Nisha tashigo masa dashi dazubane wani sabon girkin heelah tayi daban, kallon abincin yashigayi time din da take serving dinshi pepper soup din kazace da soyayyiyar doya da kwai girkin ko kamshi mai dadi baya bayarwa balle kasa ran zaimaka dadi abaki komawa yayi yajin gina da jikin sofa haryaji yunwar da yakejima tatafi, sam bai ji dadin canza masa girki data yiba kusa dashi Heelah tasamu tazauna tadaura hand dinta saman cinyarshi tasuma fadi'n," kayi shiru Dear meya samekane yau? tun bayanda muka dawo nadauko Aheel daga school mukazu muka taddaka kana bacci still har dare yayi sosai haka Aheel da mararin son farkawanka yayi bacci baka bude idoba nima naita yawo akanka shiru baka bude idoba ni harna tsoritama nace ko mutuwa kayi amma sena fahimci kana numfashi meyasameka kaketa wannan baccin haka kalau kake kuwa?" I'm fine yabata amsa a takaice, Alright kasamu kaci abincin ga gashashshiyar cheese burger with sausage pizza danayi mana order time din da muke dawowa nasan kanaso Heelah tafadi tana mai kai hanu tadauki plate din burger da pizza tamika masa ba musu ya gyara yamasa jin order tayi dan haka seya Kai hanu yadauki lallausan cheese burger yakai baki yasuma ci, barina hadu maka coffee daga haka Heelah tamike tafice bajimawa ta dawo dauke da cup din coffee tamika masa ya amsa ba tareda da wani jinkiriba , ataikace burger da pizza kadai ajmal ya iya ci papper soup din baiwuce tabi daya yayiba ya kauda plate din gefe ya Kai hanu yadauki phone din shi, 4 miss call yagani ankirashi koda yaduba yaga 2 miss call from staff and another miss call from Doctor fu'ad phone din nashi a silent take shiyasa ko karanta baijiba idonsa yarintsa ya kuma budewa time yakai idonsa ya duba 12 dan haka seya ajiye wayar baikira kodaya daga cikin suba because dare yayi sosai, mikewa yayi yanufi bed dinshi ya kwanta ya rintsa ido Heelah naganin haka itama tabishi tahaye saman bed din nashi takwanta ajmal yanajin motsinta agefenshi amma yaki bude idon shi harseda yaji takai hanu saman k'irjinsa ta rungimushi tashige jikinsa kamar mai komawa ciki yasa yabude manya manyan idonsa yana kallonta wacce itama shidin take kallo tana masa murmushi, ahankali yadan zame jikinsa ya mirgina yajuya mata baya because kwata kwata baya son farkawanka ita kuma heelah takasa ganewa itade heelah har kullum mamaki ajmal kebata seyaita zille mata yana gudunta se yanzu take kokarin yarda da kalamun faruk nacewa mijinta bayida maraba da mace da yar uwarta mace take rayuwa gashide aido namiji har namiji but abu yake sekace mace anya kalau yake kuwa? ita tarasa gane wannan lamarin ace kullum ita ke nanike dashi yana zille mata se yaga dama tukun yake iya amincewa da ita gaskiya tagaji da abunda Ajmal yake mata na guje mata da yake itade tasan ba kazama bace tana tsafta daide gwargwado to meye matsalar ne? wani kuka takawo tasake harda shashsheka cikin hanzari tamike daga bed din tafice daga bedroom din da gudu tana kuka, Ajmal najin fitan Heelah cikin yanayi kuka yasa ya mike daga kwanciyar da yayi yakoma ya jingina da jikiin bed , shiru yadanyi nawani lokaci yadau tsawan mintuna ahaka kafin yamike yasakko daga bed din yafito daga bedroom din shima , bedroom din aheel yanufa yana zuwa yatura door din yashiga, kwance yasamu Dan nasa yarungume wata big teddy bear yana ta baccinsa cikin kwanciyar hankali karisawa yayi yazauna gefen gadon yashafo gefen fiskan dan nasa yanajin sonsa da kwanarsa yana kara shiganshi, daga nan kuma yamike ya gyara masa rufowan blanket din daga bisani yarage masa hasken light din bedroom din yarufo masa door ɗin , bedroom din heelah ajmal ya nufa yana shiga yasameta tagama kukanta tahakura har bacci barawo yasaceta gaba daya jiyayi ba dadi tabashi tausayi , duk da bayajin karfi ajikinsa daniyar rarrashinta yazo ya kuma bata abunda tanema to ganin cewa tayi bacci yasa ya gyaleta yakashe musu light din dakin ya haye saman bed dinta ya kwanta tabayanta ya janyu musu blanket yarufe su daga haka yarintsa ido, bajimawa shima bacci yayi awungaba da shi, tun bayanda Nisha tayi kiran ajmal a phone kusan sau 2 baiyi picking ba yasa ta hakura dasake kira takuma bedroom din su takwanta cikin yanayi na sanyin jiki da rashin jin dadi, dakuma kulla aniyar gobe da safe zataje taga yanayin jikin nasa __________________________________ washe gari da safe 8:00 Nisha tayi wankanta tashirya cikin shirinta me kyau kananun kaya riga t shirt mai dogon hanu pink color mai laushi tana dauke da adon me alamar heart agaban rigar , se dogon skirt black se hulan dake kanta shima black tayi matukar kyau da ita fitowa tayi daga bedroom din tabarsu fadeelah da reeda da suketa baccinsu kamar yanda suka saba because dama su basu cika tashin safe dawuriba inba school suke dashiba suna sallahn asuba suke komawa sukwanta bacci, direct side din shi tanufa seda suka gaisa da securityn dake tsaye wajan kamar yanda suka saba gaisuwa yabude mata door din tashiga, koda tashigo parlourn azaune ta iske heelah bisa sofa da bowl din cornflakes tana sha gefe kuwa saman table plate ne dauke da kayan snacks tana ci tadaura daya kan daya tana kallon tv jin motsin shigowar Nisha yasa tamaida hankalinta gareta , gamida hararota yayinda take karisowa cikin parlourn," barka da safiya abunda Nisha tafad'i kenan kanta kasa tana kokarin karisawa da nufin tafiya kitchen," Hee uwar iyayi dakata! Heelah tafad'i tana wurgawa Nisha harara, Nisha tsayawa tayi tana kallonta ba tareda tace komai ba, mikewa heelah tayi tana kallon Nisha sama da kasa kafin ta tabe baki tana fadi'n," yau uban gidan naki baya bukatan komai already yayi breakfast dinshi yayi fitarsa but zaki iya shiga kitchen akwai wasu wanke wanken da ban iyayiba kihada da wadannan plate da bowl din kitafi dasu daga haka Heelah takuma watsawa Nisha wani hararan kafin tamatsa daga wajan tanufi upstairs tabar Nisha tsaye awajan tana binta da kallo tareda takaici umarni da take bata hala yar aikinta takeson maida ita , Nisha hartayi niyar barin parlourn sekuma tafasa takai hanu tadauki kayan tarkacen da Heelah tayi amfani dasu tanufi kitchen, tunda tashiga kitchen din take karewa gurin kallon ganin yanda akayi kaca kace dashi ga tarkacen wanke wanke da heelah ta tarashi agurin bata iya wankesuba har kullum Nisha mamakin Heelah take da irin lalacin da takedashi amatsayin ta na mace kwata kwata ba tsabtace muhalli ba karamin fama papan Aheel yake da Heelah, bawani bata time Nisha tashiga kimtsa kitchen duk wani abunda kitchen din dake bukata Nisha seda ta mishi ta gyara ta tsaftace, tana kammalawa Nisha tafito daga kitchen din tana yarfe zufar face dinta because ba karamin gajiya tayiba , daidai time din da aka turo door din a parlourn, Ajmal ne yashigo tareda kamal Wanda suka dawo daga raka Daddy airport, suna tafe cike da nishadi kamal ganin Nisha cikin parlourn Ajmal se raba ido take ga zufa duk ya wanke mata face se yashiga mamakin ganinta ita nan suka karisa shigowa cikikn parlourn suka zauna bisa kujera still kamal se kallon Nisha take shikuwa Ajmal kamar baima san da tsayuwarta jikin parlourn ba Nisha matsowa tayi tashiga daga musu gaisuwa kamal yane ya amsa da ganan Nisha tashiga tambayan Ajmal ya jikinsa kansa sunkuye hankalinsa yana kan phone dinsa ya amsa mata da fadi'n," Alhamdulillaha! ba tareda ya kalli inda takeba dan tabe baki Nisha da mamakin kamar ba ita yanemi taimako gurin taba har numfashi fashinta yaso tsayawa sobada shi amma yanzu tana tab bayarshi yajiki kamar bazai amsaba balle ya dago ya kalli inda tak yanzu da lapia tasamu za acigaba da halin Nisha sid'i sid'i Nisha tasamu tafice daga parlourn kamal se waiwayanta yake harta fice, " Bro meyasameka? Kamal ya tambayi y'ay'an nasu cikin nuna kulawa da damuwa, dagowa ajmal yayi ya kalli kanin nasa tareda sakar masa murmushi yana fadi'n, "Nothing wani dan zazzabi nayi but now I'm okay, cikin sanyin murya tareda sauke ajiyar zuciya Kamal yace ," Masha Allah , Allah yakara lpy bro " Amin! Ajmal ya amsa fiskarsa dauke da murmushi ," yaushe zaka koma office kaci gaba da aiki ko baka gama hutawaba ? Ajmal ya tambaya yana kallon Kamal, dan shafo gefen wuyansa Kamal yayi yana yar murmushi yace ," am da yau nakeda niyar komawa but nabari se zuwa gobe because akwai dan Shirin da nake kamal yabashi amsa cikin girmamawa ," That's good daga haka Ajmal yamaida hankalinsa ga phone din shi but ya lura da yanda kamal yaketa muzurai kamar bakinsa yana bukatan cewa wani abun se wani nuke nuke yake ," Eheem ina jinka kace kanaso muyi wata magana but kayi shiru kuma what happened? Ajmal ya kuma tambayan Kamal yayinda ya ajiye phone din shi saman table din parlourn yana kallon Kamal tareda sauraron shi, Kamal bude baki yayi daniyar magana but jin rurin karan wayan Ajmal yasashi dakatawa daga abunda yakeson fadi'n, Ajmal hanu yakai yadauki wayan nashi ba tareda ya daga Kiran ba ya kalli Kamal yana fadi'n," I'm very sorry zan fita office yanzu but zan nemeka any time , " Okay bro kamal yafad'i because dama maganar dayazo dashi nauyin fadawa yayan nasa yake dan haka Kamal yayiwa Ajmal sallama yafice daga parlourn, Ajmal yana ganin fitar Kamal shima ya mike yanufi upstairs bedroom din shi yashiga daga nan yashiga cire kayan jikinsa yanemi towel yadaura a waist dinshi yanufi toilet wanka yayi yafito yasuma shiryawa cikin shiga maikyau black suit yayi kyau matuka yasanya black glass da takalmi se wani agogon gold ta hanu daya sanya kyau kan kyau abun ba amagana, fitowa yayi daga bedroom din shi yanufi downstairs daga bisani yafice izuwa haraban gidan parking space yanufa yashiga daya daga cikin motocinsa white color tsadaddiyar hadaddiya abun kallo da ban sha'awa me gadi yana ganin fitowan Ajmal cikin barin jiki ya bude masa geat Ajmal yayiwa motarsa key yasa kai yafiice, Karfe 11:30 Hajia da Goggo rabi dasu Reeda suna zaune parlour wanda tun bayan kammala breakfast dinsu suka yada zango gurin suna dan taba hirarsu da suka saba ," yaude yakamata naje saloon din nan da shopping kafin tafiyata gobe Hajia karama (Fadeelah) fatan zakimin rakiya , Goggo rabi ta tambaya tana kallon Fadeelah dake washe baki gami da faɗi'n," Eh Goggo rabi zan miki rakiya Fadeelah tafad'i tana kallon Reeda gamida yimata g'walo Banda Nisha datayi sunkui da kai tana murmushi , Fadeelah da Reeda suna kaunar fita yawo because basu cika fitaba daga gida se makarnta barin ma yanzu dasuke hutu ba zuwa school duk se zaman gidan ya ishe " Goggo rabi dukansu uku taso suyi fitan tare zaifi armashi but ganin cewa Nisha da igiya uku akanta baikamata sufitaba ba tareda sanin mijin taba , to gwara sutafi da Fadeelah Reeda ta Taya Nisha debe kewa kar abarta shiru ita kadai, itama taban garan Nisha da Goggo rabi cewa tayi tare zasuje amma ganin cewa tacanza zabi se bata damuba , Hajia itama tasan dalilin dayasa Goggo rabi tayi hakan amma da tare duk yakamata sufita tunda dukansu suna shaawar fitan, " Allah sarki yarinyar batasan nauyin da ya rataya wuyan taba wannan duk ninayi sanadin hakan amma nan ba da jimawaba zata San nauyin dake kanta duk da batasan ya Nisha zata kalli lamarin takuma karbeshi batareda wani damuwaba duk da tasan hankali da nitsuwa irin na yarinyar, Hajia ke maganan zuci yayinda take kallon Nisha cikin tausayawa da hukuncin da tayanke ba tareda tayi la akari da wani abunda zaije ya dawoba , tana matukar kaunar yarinyar tana kuma jinta sosai cikin zuciyar ta bazataso tayi wani abunda zaicutar da itaba, sunyi firansu sosai gabatuwan sallahn azahar ne yasa duk suka Mike suka nufi muhalinsu domin gabatar da sallah , Goggo rabi da Hajia suka nufi sashinsu sukuma yan matan suka nufi bedroom dinsu' bayan sun idar da sallansu suka daura aniyar zuwa side din Kamal gurin Auntyn su Nabilah yar uwa kuma kawarsu suna jin dadin kasan cewa da ita ba kaman Heelah ba da ko kallon side din ta basayi balle suji sha' awan zuwa duk da ita din yar uwarsuce tajini but halinta yasha ban ban da nasu because Heelah akwai bakin hali da rashin kunya shiyasa basa shiri balle suje inda take " Ke bazaki biyomu muje firan bane gurin Aunty Nabilah, su Reeda ke tambayan Nisha wacce take zaune bisa bakin bed tana kallonsu," A'a ni bacci nakeji kuje kawai, Nisha ta basu amsa , basu takura mataba because sunsan kwanan zancen dan haka suka fice daga bedroom din cikin rawar jiki sukabar Nisha wacce ta gyara kwanciyar ta bisa saman bed din , nanfa tafara g'yan'gya dawa bacci yanason cinye idonta Karan shigowar message ne yasa tabude ido da kamar bazata duba wayarba sekuma ta janyota tashiga dubawa , tsulum tamike tazauna ganin message din Ajmal ne Wanda yake bata umarni tashirya masa lunch hulan kanta tazara da sauri Wanda yafice daga saman kanta tamai dashi mazauninsa, dan turo baki tayi ita batasun komawa side din shi ta tarar da wacce masi faffiyar matar tashi tunda matarshi tana nan mai zai hana ta mishi lunch din kamar yanda tamasa breakfast , mikewa tasomayi daniyar tafita daga bedroom din ganin shigowar Kamal yasa taja ta tsaya tana kallonshi da mamakin me yakawoshi ," yade wannan kallonfa? Kamal ya tambaya yayinda yake karisowa yanemi sofa ya zauna , still de Nisha kallonshi take ba tareda ta motsaba kotace wani abinba ," sisy kizauna mana wata magana nazo muyi Kamal yafad'i yana kallon Nisha wacce tadaga kafa ahankali takoma tazauna bakin bed tana kallonshi, murmushi Kamal ya sake yana kuma fadi'n," Ko kina wani uzurinne nazo nakatseki , murmushin itama ta kwakwalo tana faɗi'n," A'a bakomai, " Alright barinaje kan batun da yakawone ba tareda bata lokaciba, " yarda da amincewarki nakeda bukata, dan zaro ido waje Nisha tayi tana faɗi'n," Amincewata akan me ya Kamal,? dan gyara zama Kamal yayi hankali kwance yana mata murmushin kashe zuci yace," tunbayan da nabada labari abaya gaban Nabilah friends da sisters dina yanda sonki da kaunar ki yadinga d'a wainiya dani har kawo yanzu damuke gida daya dake but ta ban garanki bansan ya kika dauki soyayya taba inaso naji daga gareki ya matsayin kaunata agareki ? yakike feeling soyayya ta cikin heart dinki? shin kina sona kamar yada nabai yana miki ko aa? inason sani wannan shine tambayoyin da Kamal yajerowa Nisha Wanda yasatayin shiru tana kallon kasa kamar mai nazarin wani abu, " sisy what are you silent kamata yayi ki amsamin tambayoyina ," Ya Kamal tambayarka bata da amsa Nisha tafad'i ba tareda tadago sun hada idoba, "means bak'ya sona? nikaɗai nake ta dakon soyayya? shiru Nisha tayi batace kalaba bata kuma ɗago kai takalleshi ba , shima Kamal shirun yayi tareda sunnar da Kai kasa tsawon wasu mintuna kafin ya ɗago kai yakuma kallonta idonsa duk yayi jawar kamar mai Shirin yin kuka , mikewa yayi jiki ba kwari yasuma tafiya asukwane kamar wanda aka zarewa lakan jiki, wani dariya da Nisha tafashe dashine yasa Kamal dakatawa daga tafiyar dayake yajuyo ahankali yana kallonta, ganin yanda Kamal yajiyo yana kallontane yasa ta kai hanu takulle bakinta tana me cigaba da dariyan kasa kasa tareda mikewa daga zaunen da take tashiga karisowa inda yake tsaye seda tawurga masa wani murmushi kafin tace, "tafiya zakayi ba tareda kaji mai zan faɗi' ba" "mekikeson na tsaya naji bayan kince ba k'yasona , still kin ɓige dayimin dariya like kinga wani mahaukacin" Kamal yabata amsa tareda hararota yana mai kauda kai gefe, murmushi Nisha takuma yi tana fadi'n "ya Kamal yaushe kaji nace bana sonka?" Nisha takuma tambaya still ta tsareshi da ido , rintsa ido Kamal yayi ya bude tareda sauke ajiyar zuciya ahankali kafin ya jiyo da face dinsa suna facing juna yace "I'm hearing you talk me kinasona kamar yanda nakesonki ko a'a ?" Kamal yakuma tambayan Nisha yaname tsareta da ido , dan juya mishi baya Nisha tayi kafin tashiga fadi'n, " Ya Kamal wata macece zaka mata tayin soyayya taki amsa , tun ranar da muka soma haduwa nayabawa hankalinka duba da yanda ka durkusa kana bamu hakuri bisa rashin hankali da dan uwanka yamana duk da ba laifin ka bane haka kuma baka sareba kabimu har lnda muke kaci gaba da bamu hakuri, juyowa tayi takalli Kamal wanda ya tsura mata ido yana kallonta yayinda take maganar kafin taci gaba da faɗin " Ya Kamal baka da girman Kai zuciyar ka kyakykyawa ce kuma kana da tausayi duk da ilartar da kai danayi cikin rashin sani sana diyar zalunci irin na dan uwanka hakan bai hana nazo da damuwata gareka ka kasa kashare min hawayeba a lokacin da narasa me taimakona ,amm tunani na....... "shiiiii Kamal ya katsare ta daga surutan da take tafaman kwararo masa " har yanzu banji amsar da nakeson jiba daga gareki do you love me or not" Kamal yasake jefo mata tambaya, dukar dakai kasa Nisha tayi kafin tace "Ina sonka ya Kamal but Aunty Nabilah.., cikin hanzari Kamal ya dakatar da ita daga maganar da takeson yi yashiga fadi'n, "karkisa wani tunani game da ita kibar komai hanuna , kwai abunda zan gaya miki shine bana tsayawa buye abunda nakeso dan haka zan sanar dasu Ammi cewa muna soyayya kuma aure zamuyi banason bata time, dan zaro ido Nisha tayi tana faɗin, " da sauri haka ? Ya Kamal yaushe ma akayi auren naku gaskiya idan akayiwa Aunty Nabilah haka ba amata adalciba maganar aure tsakanina dakai yayi sauri gaskiya please ajin kirta, " I'm sorry bazan bari ina kallon muna rayuwa gida daya ace nakasa mallakankiba , bazan iya jiran dugun time ba , karki mantafa nina mijine , mijin mata 4 kuma Allah ne ya bani wannan daman to me Zan tsaya jira nifa ko daga yau zuwa gobe nace ina bukatan Karin aure ba mecemin a'a ko ayi kokarin dakatar dani because sunnace nakeson rayawa kinga kuma bamaija da sunnar annabi (s .a .w ), da ace tun farko kowa yasan tsakaninmu kuma nasan matsayin soyayyata a gareki dayanzu matsayin matata kike, dan haka banaso kisawa kanki wani damuwa kibarni zanji da komai , shiru Nisha tayi jikinta duk ya mutu sam bataji dadin hakan ba 'yanzu yanda Aunty Nabilah take cikin halin laulayin nan taya zaifara tinkaransu da wani zancen aure' jin shafo gefen face dinta da Kamal yayine yasa ta dawo daga duniyar tunanin da ta tafi ɗago kai tayi tana kallonshi yayinda yake tazuba mata murmushi, "Am dama akwai wani tambaya da nakeson nami, but inkin bani dama kuma ban takurakiba, kan Neeshi kasa taɗan girgiza masa kai alamar bai takurataba , bude bakin Kamal keda wuya wajan kwararowa Neesha tambaya phone dishi datashiga yin rori yasa ya dakata da maganar yashiga zaro wayar cikin pocket din wandonsa ganin mekiran da kuma mahimmancin shi yasa yadauki kiran ya kara akunne , Nisha bataji mai ake faɗa daga cikin wayarba seji tayi Kamal yace "I'm coming" daga haka yakatse wayar yakalli nisha daketa faman kallonshi yayinda yake wayar "Excuse me bari naje nadawo so zamuyi magana back" daga haka Kamal yafice ahanzarce ya bar nisha tsaye tsakiyar dakin , daker ta tattaro nitsuwarta tasamu daman daga kafarta tabi bayanshi, Nisha naganin time din da Kamal yashiga motarshi ya mata key mai gadi yabude masa geat yafice, daga itama tasamu daman karisawa side din Ajmal, bata kaiga karisa shiga tsakiyar parlourn ba taci karo da Heelah dake sakkowa daga upstairs taci uwar ado tarayo mayafi gefe guda tareda back dinta se hararo Nisha take yayin da take sakkowan , kan Nisha kasa bata kuma dagowa takalli Heelah ba , itakuwa Heelah still harran Nisha take bata daina ba seda takariso gefe da ita tazuba uban tsaki tareda wani dugun kwafa takalli Nisha tana fadi'n "mayya" kafin takuma hararnta tashige tayi ficewarta tabar Nisha agurin kai sunkuye , girgiza Kai Nisha tashiga yi ita tarasa wani kaddarace takawota gidan nan har takasan ce ak'ark'ashin bayan Allah nan gaskiya takaji da wannan wula kancin dan haka tana dab dayiwa tufkar hanci, kitchen din Nisha takarisa shiga tashiga hadawa Ajmal dinner kamar yanda ya bukata , tadau lokaci tana aikin kafin daga bisani tasamu daman kammalawa but har tagama bata ji motsin dawowar shiba gashi haryamma tayi amma shiru kakeji nan tasuma kokarin jira masa abincin bisa dining table kamar yanda tasaba tanemigu tazauna tana jiran shiguwarshi, hankalinta ta mayar kan TV dayake kunne yana channel din boolywood ana gabatar dawani drama na larabci duk da bajin labcin takeba haka tazubawa TV ido tana kallon yanda aketa zuba soyayya ciki gwani burgewa da ban sha'awa Nisha tayi nisa cikin kallon soyayya , jidatayi anfadu saman cinyartane yasa cikin yanayin tsoro da firgici tashiga fida ido tana kallonshi cikin kayan uniform yanata washe mata bakin nan nashi daya yasaba , "Sorry Aunty nabaki tsoro ko ?" murmushi Nisha tayi tana sauke ajiyar zuciya tace, "Aa akomai" daga ido tayi takalli bayanshi but bata ga kowaba jin motsin mutum tabayanta yasa tajuya bayan Ajmal ta kallah wanda tuni ya haura upstairs yana shirin nufa bedroom din shi, kallonta tamayar kan Aheel Wanda haryanzu washe mata baki yake cike da murna da farin ciki, kaje sauya kayanka kadawo kaci abinci , Nisha tafad'i gamida Kai hanu tana kokarin karban lunchbox din shi takarisa dashi kitchen, but sai taga Aheel yanuke shoulder ashagwabe yake fadi'n, "Aunty muje kitayani , like father like son shima komai se ammsa , dan karya wuya Nisha tayi tana fadi'n Oya muje to nan takama hanun Aheel suka haura sama suka nufi bedroom din Aheel, sam Neesha bata gajiya da kallon gwanin sha'awa ga kyalekyale da akayiwa dakin Wanda zai nishaadan tar da yara ga teddy iri da kala kyan wasa bedroom din Aheel ba a magana Nisha seda tasa Aheel yayi wanka duk da bawai ya iya wankan sosai bane yadai dauraye jikin sane kwai yafito, Nisha tashiga kimtsa shi, ta tayashi ya sanya kyawawan kayanshi marasa nauyi Wanda bazai takuraba, daga nan ta janyo hanun shi suka nufo downstairs, koda suka kariso Nisha bataga Ajmal cikin parlourn ba alamar cewa haryanzu bai fitoba kenan, dining table din takarsa da Aheel tazaunar dashi tashiga serving dinshi da daddadan delicious food dinta, vegetables cuscus with liver soup and macaroni salad shine abinda Nisha tayiwa Aheel serving sedan wani madaidaicin bowl wanda ta zuba masa pepper soup chicken curry mai dadin gaske, duk da tasan Aheel bawai wani cin abinci yake sosaiba amma tanaso kowanne yazamu yasa masa albarka, gefe kuma tashiga tsiyaya masa sassanyan mango smoothie juice, ganin yanda Aheel yake bin abincin da kallo yasa Nisha tasake murmushi gamida shafo gefen face din shi tana fadi'n "naba abakine, aikuwa kamar jira yake Aheel yashiga daga mata Kai alamar " eh" Nisha kujera taja tazauna tana facing dinshi tashiga dibo abincin cikin spoon tana kaiwa bakin Aheel yana ci, cikin matsuwa take bashi abincin yanaci yana mata surutan nan nashi daya yasaba, "Aunty abincin nan akwai dadi sosai kece kika dafa? " Eh mana saboda kaima nayi Nisha tabashi amsa tana murmushi, dan tabe baki Nisha taga Aheel yayi yana fadi'n "Mommy na bata iya irin wannan abincin mai dadin ba but zaki koya mata? Aheel ya tambaya yana kallon Nisha, " shiii !be quiet kaci abincin ka " Nisha tafad'i gamida shafa bayansa, daga bisani Aheel yashiga kaɗa kai rin nayarinta yakai hanu ya dauki cinyar kaza yakai baki ya suma cin yana Santi, har wayaude zuwa yanzu shiru kakeji ba motsin Ajmal ba kuma alamar zai sakko har Aheel ya kammala nashi cin abincin papanshi bai sakkoba gashi har magarib ya gabato kai dan haka yasa Nisha taja hanun Aheel suka fice daga parlourn, Nisha tana isa bedroom dinsu Reeda kaiɗai tagani cikin bedroom din alamar daya batacewa Fadeelah suntafi saloon din da Goggo rabi Reeda jin motsin shigowar su yasa tadago kai tana kallonsu gamida sakar musu murmushi yayinda suke karisowa ciki, da sauri Aheel yasake hanun Nisha yanufi sofa inda Reeda take zaune tana danna waya cikin hanzari Aheel yafada cinyar Reeda tareda fashe mata da kyakykyawan da riyanshi irinta yara " My little yaron k'irk'i antaso daga school anzu acikamu dasu rutu koh? Reeda ta tambayi Aheel yayinda take sakar masa murmushi tana jan dan kyakykyawan dugon hancinsa, k'yelk'yale mata da dariya yayi gamida gyada mata Kai yana kallonta, "Oh no ba dani ba wannan surutan naka sede Aunty Nisha kaga tafiyata ni alwalama zanje nayi oya ga phone dina kayiwa Angela wanka kayi feeding nata kafin nadawo Reeda tafad'i gamida zame jikinta daga na Aheel tamike masa phone dinta because tasan shi masoyin game ne especially game din Angela hanun Aheel har rawa yake wajan amsan wayar yana washe baki, Nisha de kallonsu take tana murmushi har fareeda tashige toilet danyin alwala itakuwa Nisha tamike tadawo kusa da Aheel tazaunar tana kallon yanda yake gudanar da wasan angelan nashi,,.. karfe 9 na dare familyn an hadu cikin kata faren parlourn bayan kammala dinner suka shiga gudanar da fira a tsakaninsu gwanin sha'awa, Ammi Hajia Goggo rabi, tareda yan matan Ammi, gefe ga Kamal tareda muhaiseen Wanda Kamal ya daukoshi daga airport dazu ba Wanda yasan da zuwanshi hatta mom dinsa Goggo rabi batasan da zuwansa ba se ganin shi tayi shima Kamal din muhaiseen kirashin kawai yayi yace gashi ya sauka Kamal yaje ya daukoshi , Aheel dake zaune cinyar Ammi ya nata zuba hamma da alamar bacci cikin idanunsa because duk ya gama yin laushi, " da alamufa yaron nan bacci yakeji naga se g'yan'gya dawa yake gaba kidaya bacci ya kama idonsa" Goggo rabi tafad'i tana kallon Aheel da idonsa sukayi ciki sun kankance, Ammi s hafo gefen face din Aheel tayi tana kallon shi daga bisani takalli Nisha wacce itama hankalinta yake kan Aheel " ya kamata akai little ya kwanta because dare yayi sosai " aiko kafin Ammi tarufe baki Aheel yatashi sukuf dashi yanufi Nisha yasuma kokarin kama hanuta sutafi, bamusu Nisha tabishi suka fice daga parlourn su hajia se murmushi suke tareda cigaba da hiransu , Jim kadan Kamal da muhaiseen suka tashi sukafice daga parlourn suna dan k'usk'us atsakanin su "kije ki gyara bedroom din da yayanku yasauka a shimfuda bedsheets , komai yazama clean" Ammi tafad'i cikin yayi na bada umurni tana kallon Reeda, ba bata lokaci Reeda tashiga fadi'n "to" daga haka tamike tafice , bajimawa suma suka shiga watsewa because sundau tsawon lokaci suna firan, koda Reeda ta isa bedroom din da ya muhaiseen yasauka baya ciki da alamar bai kariso bedroom din ba suna tareda Kamal, bedroom din a tsaftace yake komai fine because dama ba abarin ko ina da datti agidan ko dayaushe anasharewa a tsabtace shi agoge ko ina bedsheet dine kadai ba ashin fidawa se time din da bako ya ziyarci dakin , karisawa Reeda tayi ta bude wardrobe tadauko wani kyakykyawan bedsheet mai taushi tareda blanket tashiga shinfida bedsheet din saman bed daga bisani tadaura blanket saman bedsheet din , tana tsaka da gyaran muhaiseen ya turo door yashigo idonsa yasauka kan Reeda dake kimtsa masa bed nan yashiga sakar mata murmushi tareda karisowa ciki, itama Reeda murmushi tamayar masa tareda maida hankalinta ga abinda take but bata ankaraba seji tayi muhaiseen bisa bayanta yarungumu waist dinta gafi da sakalo face dinsa ta gefen wuyarta yana fadi'n," I miss you very much my pretty gaskiya nayi kewarki dayawa na kagu adaura auramu na daukeki natafi dake , nifa banki gobe ashafa mana fatiha nawuce dakeba , but Daddy yakaimu har 2 month wanda hakqn yamin nisa gaskiya ya muhaiseen yafad'i yayinda yake sake rungumar Reeda a jikinsa yanajin yanda sonta da kaunarta yake sake zama sabo fil cikin zuciyar shi, jin yanda ya muhaiseen ya rungumuta tamakar zai maidata jikinsa yasa gaba daya setaji wani irin yanayin da tunda take arayuwa bata taba jinsaba ga kamshin turarensa mai masifar dadi dayasa takasa janye jikinsa daga nata bata ki sutabbata hakaba har tsawon rayuwa , ba karamin kewarsa takeba itama ganinsa yayiwa idonta tsada se adau tsawon lokaci basuga junaba sede suyiwaya ko video call nan ma se inyana free because kullum cikin busy yake bugu dakari gari ba daya kuma baicika zama kasarba, jin shiru batayi maganaba ta tsaya kamar sak'aguwa yasa yajanye jikinsa tareda juyo da ita but seyaga ta lumshe ido murmushi ya muhaiseen yayi yana fadi'n "Yadai " tareda shafo gefen face dinta, bude ido Reeda tayi dasaure gaba daya tafada duniyar tunani ta mance ida take nan tasuma yar kame kame "Uhm am ba abunda kakeda bukata? Zan iya tafiya ?" " That's means ke bakiyi missing dina ba" muhaiseen ya fadi'n tareda yin baya ya zauna bisa sofa dakin yana kallonta, girgiza Kai Reeda tayi tana fadin "Aa ya muhaiseen meyasa zakace haka?" "gashi kuwa kina fadi'n zaki tafi kibarni cikin kewarki maimakon kizauna kitayani fira har wayewar gari , fito da ido waje Reeda tayi tana fadi'n," " wayewar gari fa kace ? "Eh mana bawani matsala ai Dan munraya dare kina min firan soyayya mai dadi" muhaiseen ya amsa yana mata k'ayataccen murmushi, dariya kawai Reeda tayi gamida tabe baki tana fadi'n " Muk'wana lapia " tana fadi'n haka tajuya zata fice , "ba ki jiba " jin muryan muhaiseen na magana yasa Reeda dakatawa daga fitan da take kokarin yi tajiyo tana kallon shi Wanda ya mike yanufi inda take , kallon kallo sukashiga yiwa juna kafin muhaiseen yadan numfasa ya Kai hanu ya janyo hand din reeda sannan ya sanya dayan hand dinshi bisa pocket dinshi ya zaro wani box dan karami gwani sha'awa wanda ke dauke da kyakykyawan rings na gold mai haske da kyalkyali zoben ya zaro daga box din yasaita yatsar Reeda natsakiya ya sanya mata akwai ya zauna mata damas gwani kyau rings din ba karamin sake fito da kyakykyawan hand dinta tayiba, "I'm sorry pretty wannan karamin kyautace daga gareni but zoben nan yayiwa hand dinki kyau ko mace hand din ki yayiwa rings din kyau, muhaiseen yafad'i gamida murmushi yana kallon Reeda wacce tasake baki ta zaro ido waje yayinda take kallon hand dinta tana juyashi gamida karewa zoben kallon, " wow ! wow!! Ya mu muhaiseen gaskiya rings din nan ya yayi kyau sosai ya burgeni matuka thanks you so much gami da sunbatan zuben tana murmushi farin ciki, " but wannan kyakykyawan sumbatar niyakama ta ayiwa ba zoben ba , dagowa Reeda tayi takalli muhaiseen wanda ya miko mata face dinsa gamida rintsa ido yana mata alamar nuni da yatsansa ta sunbaci kumatunsa aikuwa ba tsammani yaji saukan k'ayataccen kiss bisa kuncinsa saide kafin yabude ido tuni tajuya baya tabude door tafice da saurin, lumshe ido yayi tareda shafa kumatunsa inda ta sumbace shi sauke ajiyar zuciya yayi kafin ya tattaro nitsuwarsa ya shiga cire kayan jikinsa ya sanya towel yanufi toilet wanka yayi sosai daga bisani ya fito ya sanya white jallabiyar sa yanemi saman bed ya kwanata yadau lokaci yana dan tunane tunane face dinsa yana kallon sama sannu ahankali bacci b'arawo ya saceshi, itama Reeda koda takarisa bedroom dinsu tasamu Fadeelah tayi d'aid'ai tana bacci da alamar baccin ta yayi nisa sosai ga wayarta dake gefe saman bedside table yanata kawo hasske alamar Kira but phone din ta sanyashi silent shiyasa baza aji karantaba dan leka phone din reeda tayi domin ganin mai uzurawa da wannan Kiran ganin boyayyiyar number ne wato ( private number) yasa ta share tashiga neman Nisha cikin bedroom din but ba ita ba alamarta ,. 'bade tunda takai Aheel side din su bata dawo ba' Reeda ta tambayi kanta ganin cewa bata da amsa tambayar ta yasa ta d'an tabe baki daga bisani tashiga yin Shirin bacci kafin ta kwanta tareda rungumu hand dinta tana kallon d'an ya tsanta wanda ke sanye da kyakykyawan zoben gold da hubbynta ya yasanya mata yaude da mutukar murna gamida annashuwa cike da tunanin gwarzon masoyin nata bacci yayi awungaba da ita,.......... 'haba Nisha ashe duniya zata iya rudanki ki mance da mahaifinki ? asha akwai rayuwa cikin daula da jin dadi zai iya mantar dake tushenki , Nisha Ina alkhari da kikayimin akan kasance wa da mahaifinki atare dake? ashe zakiya mancewa da abbanki cikin sauki haka? shin kinsan wani irin hali yake ayanzu ? "wakeup! wakeup !!mana yanzu dan fitowar nan da mukayi daga gida harkin kiyi bacci, Fadeelah ke magana yayinda take tashin Nisha daga d'an gajeren baccin da tayi, nan Nisha tashiga zazzare idanu tana kallonsu se zuba ke tsatstsafo mata idonta yayi jawur dashi yayinda zuciyar ta kuma keta maimaita sunan umma because mafarkin datayi da ita yanzu bisa tuhumar da take mata akan abbanta na nauyin da ta daura mata , " Lapia kike kuwa? yanaga kamar arazane kike ko mafarki kikayine? girgiza Kai Nisha tayi tana fadi'n "Aa" "kode bakijin dadine because tunsafe nake ganinki so silent " Reeda tajefo mata tambaya, gyada Kai Nisha tayi tana fadi'n "kaima ked'an ciyo" Nisha ta bawa fareeda amsa cikin kosawa da magana, "Sorry kijira mu a motar bari muje muyi shopping din mudawo but bari na sauke miki glass din motar saboda iska yadinga shigo miki" gyada Kai Nisha takuma yimusu daga nan Reeda ta sauke mata glass din motar because dama itace ke driving dinsu daga suka fice daga motar suka nufi cikin babban plazan suka bar Nisha cikin morta wacce take ta faman sauke ajiyar zuciya idanunta suncika tab da k'walla karo na farko da tayi mafarkin umma wanda ya bata tsoro yakuma farkar da ita daga shagalan da tayi dan haka takudiri aniyar fita daga motar tagudu tashiga duniya neman mahaifinta, fitowa tayi daga motar tareda handbag dinta da phone din ta tasuma tafiya, harta danyi nesa da plaza sekuma taja ta tsaya ganin wani mutum dake tin karota yana gudu yana haki, yana sanye cikin manyan kaya riga da wando but sede kayan sunci ubansu da dotti shikanshi mutumin yayi kura yayi futu futu dashi fiskarshi tayi baki sosai gashin kanshima tayi kura gakuma tacika akansa cunkus ga gemanya gaba daya de kallon daya zaka masa yuwa kaga tsohon mahaukaci , nanfa Nisha cikin tsoro tafarayin baya jikinta har rawa take nan tashaga waige waige da neman inda zatayi tunda da alamar gurin wannan mahaukacin yake yiyuwa, harta juya da gudu zata koma gun motarsu saitaji sautin wannan mutumin yana ihun neman agaji "taimako! taimako jama'!! dan Allah a taimakamu suna bina zasu kamani sucutar dani dan Allah a taimakeni, cak Nisha tatsaya daga kokarin guduwan da take tamaida hankalinta ga mutum dan ganin ina yanufa still gurinta yanufu gadan gadan hakan yasa tarintsa ido gam jiki se bari yake, jin shiru yasa tabude ido bata ganshiba nan tashiga waige waige seda tajuyo bayanta tanganshi ya dukunkune face kanshi da hand dinshi jikinsa se kyarma yake nan tamaida kallonta daga hanyar dataga yafito nan made bakowa bakuma wanda yake binnashi 'to taimakon mai yake nema' jiyuwa tayi takalleshi tashiga tambayan shi," " malam suwaye ke binka bacin banga kowa dake biye dakai ba "? "gasu can suna kuma biyoni" mutumin yabata amsa ba tareda ya dago face dinshiba sake duba hanyar tayi da kyau still de ba k'yallin kowa dan haka Nisha tasauke ajiyar zuciya takalli mutumin ciki da murmushi tace, dago fiskarka ka kalli bakowa dake binka duba kagani, jin abunda tafad'i yasa mutumin cire hand din shiga face dinshi yashiga kyalla ido yana dube dube kafin ya sauke ajiyar zuciya yana dariya yana fadi'n," " Alhamdulillah wallahi natsira sundaina biyoni kasan cewan yanayin gari da hadari sosai nan take ruwa mai karfi ya sakko ganin haka yasa gaba kidayansu suka shiga neman mafaka nan taga mutumin ya watsa da gudu yanufi wata runfa ya shige domin fakewa Nisha itama cikin sauri tabi bayanshi tashige tana rawan sanyi tsayawa tayi tana kallon mutumin yasanya hanu yana taran ruwan yana kaiea baki da alamar yaji k'ishin ruwa seda yasha yakoshi sannan yashiga wanke fiskarshi datayi baki abar tsoro seda ya wanke face dinsa sannan yajiyu yakalli Nisha wacce ke gefe ta zuba masa na mujiya tana kallonshi, kauda kaiyayi yacigaba da wanke gabban jikinshi but jin motsin mutum kusa dashi yasa ya dakata ya kallo inda take idonta cika tab da kallo amma bakinta se murmushi yake yana barin cewa wani abin daker bakinta ya iya furta "Abba?abbana kaine haka" Allah nagode maka Nisha tafad'i yayinda take matsowa gareshi da sauri yaja baya yana kallonta cike da mamaki amma bai iya cewa kalaba ganin haka yasa Nisha sake fadi'n," "Abba baka ganeni bane yarkacefa Nisha"tafad'i tana kuma tinkaroshi da kokarin fadawa jikinsa cikin murna but seyaga yasake ja dabaya 'to ko ta canzane bai iya ganetaba' tashiga tambayan kanta " " Abba fa nice Nisha dinka ka kalleni da kyau nice , gamamakinta setaga ya watsa aguje yashigayin gudu itama cikin sauri tashiga bin bayanshi duk da ruwandq ake gudu yake sosai tamakar yaga wani abin tsoron itama Nishi se karayin saurin take but yamata nisa sosai , wata tsadaddiyar motane taga yaz o yasha gaban Abba aka bude murfin kofar motar aka kutsa abbanta ciki bataga ko suwayeba suka jashi csuka maidakofar suka rufe sukaja motar sukatafi dashi, "Innalilahi wa'ina ilaihi rajuun" Firgit Nisha ta tashi daga mafarkan da tashigayi tana kuma maimaita" inna lillahi wa'ina ilaihi rajuun abbanaaaaaaa!" bedroom din tashiga bi da kallo nan ta ganta wance kan gadon Aheel wanda tun kawoshi yakwanta yashiga rigimar sede su kwanta tare dalilin dayasa ta kwanata a domin ta samu yayi bacci seta sulale ta tafi but se bacci mai nauyi ya dauketa hardasu markin umma da Abba gaskiya mafarkin da tayi da Abbanata da irin halinda takaganshi ba karamin daga mata hankali yayiba, duk da sassanyan AC dake aiko cikin bedroom din but zuba take sosai kallon Aheel tayi wanda ya yabaje yanata sharan baccinsa wayarta tazaro tashiga duba time 4 na asuba zaro ido tayi tasakko daga bed din tanufi downstairs cikin sauri ahanzarce take sakkowa daga benen koda ta karisa sakkowa se tsayawa tayi jinin jikinta yatsaya cak yabar aiki ganin Ajmal kwance saman duguwar sofa yana sanye cikin kyakykyawan jallabiyar shi yana karatun Qur'an tacikin phone dinshi , saka makon jiya da takawo Aheel basu ganshi a parlourn ba shima kuma Aheel bai nemi papan nashiba ya nace mata sede sukwana tare harda yar kukanshi karta tafi tabarshi atsorace tajuya cikin sauri zata koma atunaninta bai lura da itaba but setaji yace "You! come back here, "nan Nisha tashiga mis mis da ido tana Shirin kuka ita tarasa wani tsautsayim bacci mai dugun zango ya kamata cikin side din Ajmal ahankali tashiga takowa, jikinta sai rawa yake gaba kidaya bata hayyacinta saboda mafarkin da tayi gaba daya hankalinta atashe take kuma tana cikin tsoro sosai hankalin takarisa inda yake tadurkusa saman carpet kanta na kasa gaba daya zufa yagama wanketa tas gashin kanta duk ya manne jikin face dinta yayinda da idonta kuwa hawayene fal ciki suna kokarin gangaruwa kumatunta sosai take sunkuyar dakai saboda hawayen dake kokarin zubu mata, kallo Ajmal ya tsareta dashi sosai yake bin sumar kanta da kallo baki wuluk dashi se wani shainin take jin shiru baice komai ya tusata agaba yasa ta dago kai ahankali ta kai kallon ta gareshi daidai time din da sirarun hawaye suka sauka kuncinta ganin kallon da ya kafeta dashi kamar mai Shirin ganu wani abu a face dinta yasa tamaida kanta kasa tarasa shirun me Ajmal yayi yana kallonta ko wani irin kallone yake mata haka takasa ganewa kode kallon tuhuma yake mata na kasan cewa da tayi a side din shi, "Aheel ne ya bukaci na tayashi kwana bayaso natafi nabarshi shine..,,, dakatar da ita yayi da ga surutan da kefaman jero masa because ba a bunda yakeda bukatan tambayar taba kenan dama yasan Aheel da fitina ayanda ya kwallafa rai da Auntynsa dayake fad'i wataran cewa zai ta dawo side din ma gabaki daya yasan halin d'ansa Ajmal yanason d'ansa sosai yanda Aheel keson Nisha yake kaunar kasancewa da ita da kuma kulawar da Nisha take bawa Aheel yasa Nisha tasamu sassauci daga tsana dakuma ki dayake mata abaya , shiyasama yanzu bai cika fargaban halinda Aheel yake ciki ba because yasan akoda yaushe tana kasancewa da shi kulawar da take bashi ko uwar data haifaishi Heelah bata bashi , Aheel raunin mahaifinshine baiso alakar Aheel da Nisha tayi nisa haka bas because Ajmal hankalisa Sam yakasa kwanciya da yarinyar yakasa karbarta kamar yanda agdn suka karbeta hanu biyu wani tunani yake da ban akanta da kuma shakku , wani lokacin kuma tausayi take bashi yanda take wasu abubuwan cikin tsoro da rawar jiki kamar mara gaskiya wannan yana daya daga cikin abunda yasa yakeda alamar tambaya akanta, "you can go" abunda Ajmal yace kenan , kamar jira take because tagaji daga dukawan da tayi dan haka cikin sauri tamike tafice taname goge hawayen face dinta , lumshe ido yayi tareda tunanin cikin zuyarshi yarasa meyasa yarinyar sometimes cikin fiskar damu take yanzuma harda hawaye yagani saman kuncinta Wanda yasa yakasa tambayar takamar yanda yayi niya lallai akwai bukatan sanin wacce ita da kuma labarin ta, mikewa yayi danufin haurawa upstairs kamar ance ya daga kai sukayi ido biyu da Heelah wacce take tsaye tundazu daga saman bene tana kallonsu kauda kai yayi irin na ko inkula tareda haurawa upstairs yana kokarin nufan bedroom din Aheel Heelah kamar jira take yagama karisowa tayi sauri shan gabanshi tana fad'in "ahala wannan stupid girl din harcikin dare kanada bukatar ta , wai nikam me kuke nufine because nakasa ganewa lamarinku , Heelah ta tsareshi da tambaya cikin yanayin tuhuma but bai kulataba yaka kauce mata danufin ci gaba da tafiya amma se ta sake shan gabanshi tana cigaba da fad'in "ina magana kashareni to mezai hana ka aureta da irin wannan maden da kukewa juna... damko gashinta dayayi da karfine yasa tahadiye sauran maganar da take kokarin yi tashiga kiciniyar kwace kanta " a kullum ina fada miki kidinga nan na de harshenki daga warwareshi da kike kina furta abunda kikaga dama ni ba d'anki bane kuma niba sa'anki bane so be careful with me yana fadi'n haka ya kuma jijjiga gashin kanta da karfi kafin yayi wurgi da ita gefe yawuce yanufi bedroom din Aheel domin tabbatar da lapian shi, koda yashiga yasameshi cikin aminci yana tashan baccinsa harda minshari dan matsawa yayi kusa da bed din nan yaci karo da hulan Nisha da ta mance saman bed din Aheel wanda bata lura da shiba a takaicema batasan baya kantaba tsoro da far gaban mafarkin da tayi da kuma baccin da yasaceta a bedroom din Aheel side din Ajmal besa ta lura da shiba , hanu yasa yadauki hular yana jujjuyata daga bisani ya ajiye ya gyarawa Aheel blanket yarufishi dakyau kafin yanufi hana hanyar fita, koda yadawo parlourn ba takoma bedroom din ta cikin kuka , bedroom din shi yashiga daga bisani ya ajiye phone dinsa kafin ya nufi toilet danyin alwala domin time din sallah ya kawo kai yana idar da alwalan yafito da nufin shiga masallaci koda yafito suka hadu da Kamal wanda yafito shima danufin tafiya dan haka suka hade hanya suka tafi a tare duk da kasancewa masallacin a gidan yake but se kafita geat kafin ka iya shiga masallacin because kofar tawaje take ba ta cikiba, Nisha kowa cikin hanzari tashige bedroom dinsu tasamu duk suna bacci Fadeelah nabisa gado Reeda yayinda Reeda kuma tamike saman sofa tana bacci slowly kamar mara gaskiya tadauki towel direct toilet suma kokarin shiga sekuma ta tsinkayi muryan Reeda wacce tayi likimo ta kira sunanta , Nisha tsayawa tayi jikinta duk asanyaye , karisowa Reeda tayi tana mai karewa Nisha kallo wacce ta jingina kanta da jikin bangon dakin cikin damuwa "yadai Nisha Ina kuma kikaje bade a side din ya Ajmal kika kwanaba because bamu iya ishashshen bacci ba tareda keba, Nisha fada mata yanda sukayi da Aheel tayi irin rigimar da ya shiga mata sede sukwana tare bacci ya dauketa garin rarrashinsa but bata san time yaja hakaba, " Alright no problem sede kuma kamar yanayin ki nagani cikin damuwa what's wrong? girgiza Kai Nisha tayi tana fadi'n " Bakomai" "okay" Reeda tafad'i tareda ja baya domin bata damar shiga toilet da takeda niyar yi , Reeda komawa tayi tazauna bakin bed da tunanin keyasamu yar uwan tasu taganta haka bade yayan nasu bane yamata wani abin haka Reeda tazauna tana ta sake sake har Nisha tafito daga wanka hade da alwalan because ta kammala period dinta dan dama tarega Fadeelah farawa wardrobe tanufa ta zaro riga da hijab ta sanya daga nan tashin fida sallayan ta tada sallah ganin haka yasa Reeda Jan wani goron numfashi sannan itama tamike daga zamar da tayi tanufi toilet tayiyu alwala tanemi hijab ta sanya ta jera da Nisha itama ta tada sallahr daidai shigowar Amma domin tayar dasu sallah kamar yanda ta saba but setaga yau yaran nata sunyi hankali yau suntashi da kansu sun hutar da ita Fadeelah kawai ta hango saman bed ta baje se bacci take wacce tasan matsalar ta murmushi kawai Ammi tayi tafice da ga bedroom din tanufi nata dakin, kamar yanda kowa yasani yau jirgin Goggo rabi zai daga zata koma karfe 10 na safe bayan kammala breakfast gaba daya family suka kasance compound din gidan domin sallama da Goggo rabi because yau zatatafi Hajia Ammi Nabilah gefe su Reeda banda agogo sarkin aiki Heelah tun farar safiya tafice daga gdn, su Fadeelah sunyi jigun jigun dasu lamari babu dadi zasuyi miss din Goggo rabi comedy bazasu sake ganintaba kuma se biki dama bawani zuwa takeba sosai se sa'i da lokaci, sekuma wani taro mai mahimmanci biki ko suna, Nisha da bata santaba abaya yanzu setaji yanzu tafi kowa shakuwa da ita , an kammala sanya kaya a mota komai ya zama ready, " To saduwan alkhari se biki kuma in Allah yanuna mana muna cikin rayayyu " Ammi da Hajia suka shiga fad'in "Amin " daga nan Goggo rabi tashiga daga musu hanu suma suka shiga daga mata hanun daga bisani tashiga rantsatstsiya motar Ajmal wanda dashi acikin rakiyar kuma a motarshi shiyake but Kamal ke driving dinsu se Ajmal ke gefensa muhaiseen da Goggo rabi suna daga gidan baya nan Kamal yayiwa motar key mai gadi yabude musu geat Kamal yaja motar suka fice, harsuka fice Fadeelah da Reeda basu daina bye bye ba sun sake baki se daga hannu suke "To malamai sun bacewa ganinku daga hanun ya isa haka" Ammi tafad'i tana hararosu yayinda tajuya tanufi cikin gida,su Reeda sauke hannun sukayi jiki asanyaye ko wannensu ya nufi muhallin shi , ,...... rayuwa yanzu yayiwa Nisha kullin huhun goro kullum cikin tunani da far gaba take tunanin mahaifinta da sanin wani hali yake ciki kullum shine aikinta hatta kyakykyawan cin abinci ta dainayi alwalantama ba kamar da ba wanda yasa hankalin su Hajia ya dawo kanta ganin canjij da sukayi atareda ita, but sun tambayi mai yakawo sauyi a tareda ita mai yake damunta setace "babu" dan haka sesuka daina tambayan suka cigaba da janta ajiki cikin kulawa tareda wasa da dariya domin a tunanin su kewar mahaifiyar tane ya dawo mata sabo, wanda kuwa ba haka bane yanzu ba abunda take ga umma da yawoce addu'a gareta da fatan dacewa ga mahaliccinta tunanin ta daya shine tasamu hanyar fita daga gidan nan because taji gidan ya ishe tunaninta ya koma kan abbanta tun mafarkin da tayi da ashi da kuma halinda ta ganshi yana bukatan tai mako sede duk hanyar da tabi na kokarin barin gidan abu yaci tira because ko barawone yasamu nasaran shigowa gidan nan tofa fita zaiwuya agareshi matukar da kafarshi zaifita , sede in ba cewa zaiyi domin security ne abaje ko ta ina gashi ko kyakykyawan bacci basayi balle kasamu daman silalewa , gashi su gdn bawani fita akeba kullum ana jikin gida duk wani shopping din gidan barkace kezuwa tareda wasu securities din, but tabarwa kanta sanin cewa ta tsaida lokacin tafiya tabar gidan nan ko ta halin yayane domin taje gurin tushenta wannan karon tashiryawa Mami koda tsiya tsiya setaga mahaifinta sai tafad'i inda ta kai Abba because taga alamun ba gaskiya alamarinta, ranar wani lahadi da Nisha takasa mancewa dashi cikin rayuwarta tana kwance tana kwance bisa sofa cikin bedroom dinsu Fadeelah da Reeda sun kaiwa Aunty Nabilah ziyara kamar yanda suka saba sunacan sunata zuba mata surutu wanda hakan bakaramin dadi yakewa Nabilah hakan yana mata dadi sosai kasan cewar su kawaye yan uwa uwa uba kuma tana auran yayansu , but rashin jin dadinta daya takasa gane meyasa Nisha ke gudunta bata zuwa tareda su Reeda suna hira kodai ta dauka haryanzu tana fushi ko kishi da itane ita sam duk ta yada wannan mukaman zuciya daya tariketa yanzu , koda ace ya Kamal auranta zaiyi yanzu bazata wani damuba because yanzu yarinyar tausayi take tun wancen lokacin but itade tadaina kishi da ita musamman yanda Kamal yake kulawa da ita sosai ko bacin rainta bayason ganin yanzu duk wani abunda yakeso ko zaisashi farin to itama tana son shi saboda tsantsan so da kaunar da take mishi zataso duk abunda yakeso koda ita bai mataba, ta rintsa ido tana ta faman tunanin da tasaba koda yaushe tadaurawa kanta tunani da damuwa bude ido tayi tazauna tareda dafe goshinta cikin tafin hannunta , nan ta sakalo kafarta kasa ta sakko daga sofan tanufi window, daga labulen window tayi tana ta kallon geat inama ace ana bacewa da tabace yanzun nan because duk tunanin ta ya ta al laka ga barin gidan motsin shigowar da tajine yasa tamaida da hankalinta ga door din ganin Kamal tsaye bakin door din face dinsa yayi jawar idonsa duk yacika da kwallah yasa tajiyo gabaki daya tana kallonshi tareda karisawa inda yake tsaye, kallonshi take sosai cike da mamaki mutumin da kullum yake cikin raha da dariya but yau face dinsa ya canza "ya Kamal what's happened naganka cikin wannan yanayin? " Nisha ta tambaye shi ciki kaduwa Amma setaga ya juya baya yadafe hanunshi jikin bangon dakin ya sunkuyar dakai kasa " Ya Kamal kasani cikin damuwa naganka cikin yanayin da ban saba ganin ka ahakaba, please kasanar dani damuwarka" "Nisha dama ke ba tawa bace " ras gaban Nisha yafad'i jin abunda Kamal ke fad'in " but meyasa zakace haka ni takace mana Nisha tabashi amsa cikin damuwa narashin sanin dalilin dayasa yazo mata cikin wannan yanayin yana irin wannan maganan, "Ke batawa bace Nisha because da aure akanki kika boyemin kuma nazo miki da soyayyata kika amsa ba tareda sanin igiyar aure ne akanki ba , why kika boyemin baki sanar da niba why Nisha? Kamal ya fad'in cikin daga murya gamida damuwa da baccin rai yana tambayan ta, Nisha turos tayi tana kallon shi da mamakin maganganun da yake fitowa daga bakinsa, 'anya ya Kamal yana cikin hankalinsa kuwa Ammi tagani tazo da sauri kusa dashi ta dafa shoulder dinsa tana fadi'n "Kamal mekakeyi haka ne? kamata yayi ka tsaya kaji abunda zan fad'i ba kafito ka kyaleniba yayinda nake magana kasaita natsuwarka mana haba Ammi tafad'i cikin sigan fad'a "Ammi idan kowa zai boyemin ita bai kamata ta boyemin ba because tasan inasonta kuma na baiyana mata soyayya na agareta ta amsa batare da ta fad'amin matsayin taba, am,. "Ya isa haka Kamal itama ba tasan komai gameda auran nan ba haka zalika shima Ajmal baisan da auranta akanshi ba iya tsakanimu magnar ta tsaya sai kai yanzu da kabijiromin da batun soyayyarku da na nemi na fahimtar da kai kaki saurarata". Ammi tafad'i cikin sigan shiga damuwa sam bataso abun ya kasance ta hakaba taso abi abun asannu ahankali but taurin kai irin na Kamal yakasa fahimtarta balle ya saurareta gashi yanzu yasa tayi subul da baka sirrin ciki yafito fili, "Innalilahi wa'ina ilaihi rajuun" abunda Nisha take furtawa kenan ahankali yayinda ta dafe goshinta wanda takejin yamata nauyi saitaji mak'ok'oronta ya bushe yawun bakinta ya kafe dib ' Aure! Aure dai ' Nisha keta maimaita wa cikin zuciyarta ba jimawa idonta tasuma ganin walkiya walkiya haske haske hazo hazo kankance mai dakin yafara jiyuwa mata kafin su ankara tafad'i kasa sumammiya, sallallami sukashiga yi harsuna gwaral wajan karisawa wajanta tso da fargaba duk ya dabai bayesu "Kaga irinta ko Kamal ga irinta nan da ka saurareni munyi maganan cikin nitsuwa da duk haka bata faruba da batajiba bare hankalinta ya tashi yanzu ga abunda taurin kanka ya haifar", Ammi tafad'i cikin rudu da tashin hankali "Please Ammi kibar wannan maganan yanzu bashine solution ba mudagata mukaita asibiti don aceci lapiyar ta because karwani abin ya sameta" Kamal yafad'i cikin rikicewa da tunanin mezaije ya dawo "Kamal kira doctor kira doctor fu'ad please kirashi da sauri" "Why not bazamu kaita asibiti ba?" "Zaka sake taurin kainne ko zakayi abunda nace " Ammi tafad'i a tsawace , cikin hanzari Kamal yamike yazaro phone dinsa cikin pocket dinsa marmaza yashiga dealing number doctor fu'ad yana dagawa Kamal yasanar dashi ana bukatarsa agida yana gama sanar dashi ya katse wayar ya kalli Ammi yana fadi'n "Ammi taimaka min mudagata izuwa bed kafin doctor fu'ad din yakariso ba musu Ammi tasa hanu suka sunkuci Nisha wacce ke maga shiyar kamar macecciya suka daurata saman bed Ammi tazauna kusa da ita ta janyo hanun Nisha ta daura bisa nata tana murzawa idon ammi duk ya ciko gaba daya tausayin yarinyar ya kamata ita dama kwata kwata bataso al amarin nan ya kasance ba Hajia ce tayanke hukunci ba tareda tayi la akarin abunda zaije ya dawo ba da ace tasan kaunar da Kamal yakewa Nisha tabbas bazata taba bari wannan lamarin yafaruba gashi yazo mata time din da yariga ya makara wanda hakan yajawo tonu abunda aka rufe wanda dama duk daren dadewa zaibud'u,. duk da sunso abi abun daki daki Amma zuwan Kamal duk ya cakuda abubuwa saboda shegen zuciya irin tashi Ammi hararo Kamal tayi wanda keta safa da marwa cikin dakin cike da damuwa, ba ji mawa Kamal yaji ki ciniyar bude geat aiko cikin sauri yafice ya taroshi cikin hanzari suka kariso shigo cikin bedroom din, ganin Nisha kwance idanuwanta arufe Ammi na gefen ta cikin damuwa yasa doctor fu'ad saurin karisawa kusa da bed din yana tambayan ba'asin meyafaru da ita, saidai ba amsa saima Ammi da ta kai kallon ta ga Kamal wanda shima itan yake kallo ta kuma cilla masa harara wanda ya sa shi sunnar da kai kasa cikin na dama jin shiru ba wanda ya samu daman ba shi amsa yasa yace su ba shi guri ya dubata ba musu Ammi tamike tafice Kamal ma ya rufa mata baya haka suka fito sumu sumu da su. Gefe Ammi tazauna bisa sofa ta raf ka uban tagumi shi kuwa Kamal bai samu daman zama ba sai kaiwa da kawo yake tsakiyar parlourn, jim kadan doctor fu'ad ya fito wanda suna ganin fitowar shi yasa suka nufoshi suna tambayan shi ya jiki Nisha ya amsa musu da "Shi is fine but baku bani amsa ba maiyayi causing dinta shiga wannan ya nayin doctor fu'ad ya kuma tambaya yana kallonsu Kamal dai har yanzu bai iya cewa komai Ammi ce ta saukar da ajiyar zuciya jin kyakykyawan labari Nisha na cikin koshin lapia, takalli doctor fu'ad ko ma wa tayi ta zauna kafin tayiwa doctor fu'ad nuni da ya zauna dan yi masa ba ya ni. Dan muskutawa Ammi tayi tagayara zama kafin takalli doctor fu'ad wanda ya mata zoro yana sauraron abinda zata fad'i, doctor fu'ad kai ba mutumin da za abuyewa komai bane, kamar yanda kasani shekarun baya da suka wuce Hajj mama itace silan hada auran Ajmal da Heelah , to halinda ake ciki yanzu wasu kwanaki dasuka wuce Hajia tasake hada auran Nisha da Ajmal but tayanke hukunci ne cikin bacin rai bisa rashin kunya da rashin girmamawa da Heelah da mahaifiyarta suka zo suka gabatar kwanakin baya akan wata yar hatsaniya da ya faru tsakanin Raheelah da Nisha nan Ammi tashiga korawa doctor fu'ad yanda lamarin yakasance da kuma dalilin da yasa Hajia ta zarta da wannan hukunci ba tareda tayi la akari da afkuwan wani matsalaba dan kauda kai Ammi tayi tana murza hannayenta irin na shiga damuwa tace," "Duk tsawon kwanakin nan inata kokarin na fahimtar da ita cikin natsuwa bisa auran Ajmal da ke kanta amma senaji nakasa maganar tayimin nauyi because bansan da wani ido zan kalletaba kuma bansan wani irin kallo zata mana ba bisa amanarta da mukaci nadaura mata aure da da' nmu ba tareda yarda ko amikamatrta ba , sam bamu san Kamal yana da ra ayi akantaba se yanzu yasameni da batun soyayyarsu wanda yanzu shiyayi causing wannan problem din banso ta tsinci lamarin ta wannan sigarba, Ammi tafad'i tana sunnar da Kai kasa , wani goron numfashi doctor fu'ad ya sauke tareda jinjina kai yana mai mamakin lamarin, yama rasa tacewa but tawata fiskar yaji dadin kasan cewar hakan because tun randa yafara ganin yarinyar ya yabawa hankali da nisuwarta koma ba komai yasan zata kula dashi sosai fiye da tuna ninsa to amma yanda zai karbeta amatsayin mata yake tunanin because koda yakarbeta amatsayin mata yasan Nisha bazataji dadin zama dashi especially yanda bai gama gamsuwa da itaba, dan gyaran murya Doctor fu'ad yayi kalli Ammi yana fadi'n "Amma senake ganin kamar bai kamata acigaba da boye batun aure tsakaninsu ba duk da ita Nisha tasani yanzu shima Ajmal yana da hakkin yasan nauyin da aka daura masa or yayi accepted or rejected dan haka boyewa bashi dawani fa'ida kamata yayi yayi azauna dasu ko duk susan matsayinsu wannan shine shawaran da zan iya bayarwa doctor fu'ad ya fad'i yana kallonsu Ammi da kamal wanda yayi zoro daga gefe yana jimami, dan gyada kai Ammi tayi alamar gamsuwa da maganar tashi batare da ta iya sake cewa komai ba, "so nizan wuce zuwa gobe zandawo naga yanayin jikin nata duk da ba wana matsala bane kawai tsoro da firgici ne yayi causing," doctor fu'ad ya fad'i tareda mikewa nan idonsa yasauka kan su Fadeelah da Reeda wanda suke tsaye bakin door Wanda basu ankara da suba balle susan da tsayuwarsu sungama jin komai jikinsu duk asanyaye cikin sauri suka kariso ciki suna kokarin nufa bedroom din dan ganin halinda Nisha ke ciki cikin hanzari doctor fu'ad ya dakatar da su gamida fad'in," "Please karku dameta yanzu because tana bukatan hutu, so kudan kara hakuri" jiki ba kwari suka nemiguri kusa da Ammi suka zauna suka sanyata tsakiya kowaccensu tajin gina head dinta jikin shouldern Ammi cikin damuwa, doctor fu'ad binsu kawai yayi ganin yanda sun wani lagwabe jikinsu duk yayi sanyi dan girgiza kai yayi daga bisani yayi sallama da Ammi yafice Kamal ya rufa masa baya jiki amace, seda Kamal yaraka doctor fu'ad harbakin motar sa kafin sukayi shaking hand doctor fu'ad ya shige motarsa yamata key mai gadi yabude masa geat yafice daga bisani Kamal shima ya juya cikin gidan direct part dinsa ya nufa inda ya iske Nabilah bisa sofa tana danna wayarta jin motsin shigowar Kamal yasa tamike cike da murmushi but lokaci daya kuma murmushin ya kawar kan face dinta ganin Kamal cikin wani yanayin wanda bata saba ganisa cikiba, Direct bedroom taga yajufa ko inda take bai kallaba aikuwa cikin sauri itama ta tashi tabi bayanshi, koda tashiga bedroom din bakin bed taga ya yazauna yayi juguk dashi hakan yasa Nabilah karisowa inda yake tadurkusa saman carpet tadaura hand dinta saman cinyarsa tashiga tambayansa meke damunsa amma se shiru yayi bai kulataba, " Please ya Kamal kafada min meke da munka ni matace agareka bai kamata kaboyemin matsalar data damekaba" "ko nice nayi wani laifin ban saniba kasanar dan" ganin yanda take masa magiya duk tashiga damuwa ganinsa haka yasa yace "Please Nabilah banason yawan tambaya ni ba abunda yake damuna so kidena damun kanki" yana fadi'n haka yamike yanufi toilet jiki ba gwari Nabilah tamike tafito daga bedroom din takoma parlour tanemigu tazauna tana tunanin meyeke damun Kamal taganshi cikin wannan halin, jim kadan taga ya fito cikin wani shirin ya fice ba tareda ya kalletaba balle yace mata wani abin, komawa tayi ta kwanta kankance me hawaye suka shiga zarya cikin idanunta sam bataji dadin kasan cewar sa cikin wannan yanayin ba to kowani laifin tayi masa bata saniba kamata yayi yasanar da ita ba yadau zafi hakaba,. Guraren karfe 9 na dare Nisha tasaki wani dugun nufashi kafin tashiga kiciniyar bude ido seda takarewa bedroom din kallo sannan tasauke ajiyar zuciya tadauka zata bude ido ta ganta agushewarta because yanda zuciyarta wani buguwa da karfi time daya sam ba tayi tsammanin bude ido ta ganta araye ba dakin shiru yake ba kowa sai ita kadai dake kwance anrufeta da blanket, yaye blanket din tayi ta mike zaune ta najin yanda kanta yai mata nauyi tamkar an aza mata kaya maganganun Ammi ne ya shigadawo mata cikin kai yana mata yawo cikin kwakwalwarta, cusa kanta tayi tsa kan kanun kafafuwanta tashiga rera kuka har da shashsheka. Ringin din k'aran wayarta ne yasa ta tsagaita da kukan ta shiga leka phone dinta daketa faman ruri saman bedside table but kafin ta dauki phone din I kiran ya katse jawo wayar tayi tashiga duba mai kiran 5 miss call tagani daga kawarta salma wasu sabbin hawayene suka sake kwaranyo mata ganin k'iran salma wacce ta turo mata da IV dinta tun last week auranta cikin wannan week din Nisha ba k'aramin buri ta ci ba na auran kawarta salma sai dai kafin auran salma ita andaura nata auran wani sabon k'iranne ya kuma shigowa Nisha kamar baza ta daga k'iran ba saboda yanayin da ta ke ciki bazata iya magana ba harya kusa katsewa sannan ta dauka tare da kara wa akunne ba tareda ta ce komai ba, "Haba Nisha tun yaushe naketa kiran wayanke ba kya picking kuma baki biyoniba ni ba wannan ba yaushe za ki zo ne because ya kamata a fara komai dakefa" " Hello wai ko ba kya ji nane kam "salma ta tambaya jin shiru ba magana sai shashshekar kuka da ta ke ji kasa kasa "Wai mai yake faruwane Nisha naji kinyi shiru inata magana kinyi shiru qalau kike kuwa, ?" dib Nisha ta katse wayar ta sake phone d'in saman bed tashiga rera wani sabon kuka ta na cikin wannan ya nayin sai ji tayi anturo door ana kokarin shigowa wanda yayi saurin mayar da ita sense d'inta cikin hanzari tashiga goge hawayen face d'in ta ta koma ta kwanta ta rintsa ido kamar mai bacci, cikin natsuwa HAJIA ta turo door ta shigo hade tura kofar ta rufe, girgiza kai Hajj mama tayi ganin Nisha kwance yanda suka barta kamar mai bacci saka makon zuwan ta bakin door din ta jiyo sautin shashshekar kuka wanda kuma Nisha ce keyi karisowa tayi kusa da bakin bed d'in ta zauna tare da shafo kan Nisha tashiga fadi'n "Ki ga far ceni y'ar nan na yanke hukunci ba tareda izini yarda ko amincewarki ba nayi hakanne ba dan na cutar da ke ko saki cikin damuwa ba " tar Nisha ta bude ido jin Hajj mama ke magana ta na kokarin matsar kwalah Manyan idanuwanta wayanda suka kumbura ta sauke akan Hajia wacce tayi sunkuye cikin kunya da na dama tana ta faman sharce , hawaye da gefen zaninta hankali Nisha tasuma kokarin gyara zama wanda yayi sana diyan dago da kan Hajj mama cikin sauri tashiga taimakawa Nisha wajan gyara mata zaman tana fadi'n "Sannu 'yar nan ya jikin naki dan allah ki gafarce ni ba na son ki shiga da muwa sabida ni hak'ik'a nayi babban kuskure wajan yanke hukunci ba tare da sani ko yardarki ba amma dan allah,.. cikin hanzari Nisha tariko hanun Hajj mama wacce duk ta da burce ta shiga da muwa cikin sanyin murya Nisha tasuma fadi'n "Please Hajia kidaina neman afuwa agareni aganina kun isa da ni shiyasa kuka zabamin miji kuma nasan ba dan kucutar da ni bane yasa kukayi hakan, inde nakasance daya daga cikin y'ay'an gidan nan to kunada kowacce irin dama akaina ba zabin da zakuce kunyi nace AA ko nayi musu please Hajia kidaina damun kan ki zabin da kukayi agareni shiya dace dani because ni yar kuce, Nisha ta karishe zancen da rintsa ido saboda hawayen da yacika idanuwanta, "Aa Nisha kema kina da naki ra'ayin kuma kina da zabi, hakika naji komai daga bakin Ammi soyayyarku da Kamal wanda kuwa da nasan hakane kokusa ko alama da bazan fara wannan katubaran ba nide burina kikasance daya daga cikin sirikar gidan nan alakarmu dake takara kusanci sosai , hakika nice sila aurarraki dayawa daga cikin family nan saboda dauren family na , kama daga auran habu d'ana(Daddy) nina hada auran sa da yar wajan k'anwata hafsa wacce Allah ya azurta ta da yammata biyu Bilkilsu da Maryam, wanda daga baya Allah yamata rasuwa nina cigaba da rikeso lokacin Ina tareda mijina Alh Muhammad bature wanda shi balaraben saudia ne a saudia muke da zama acan na haifi y'ay'ana maza guda biyu Abubakar wanda muke kiransa da habu(Daddy) da Muhammad wanda muke cemasa modi(Abu) sai Rabi'atu itace karama, Bayan rasuwar k'anwata hafsa can natafi dasu kasan cewar ita a Nigeria tayi aure kuma tana kusa da baffa Sani wanda yakasane wan mahaifinmune shiyarikemu yarenemu saboda mu marayune duk mahaifanmu sun rasu shiya cigaba da rikemu bisa amana kulawa da kuma nuna mana gata because iyayenmu sunada wadata sosai bamusan meye wahala ko taluciba alhamdulillah muna cikin rufin asiri bayan rasuwar baffana da kuma k'anwata ba karamin shiga damuwa nayiba because narasa dangina yanzu banida wasu family da wuce y'ay'ana 5 da mijina dan haka sena rungumesu muka cigaba da rayuwar farin ciki dajin dadi yayinda kowannesu yake karatu gurare daban shi Abubakar a Paris yake ban garan kasu wanci yayinda shikuma modi yazabi Landon ban garan likitanci sukuma y'ay'a matan agabana suke karatu because ni ban yarda da karutun y'ay'a mata awani gurin da ban ba shiyasama kikaga Fadeelah da Reeda suke karatunsu a maryam abacha komai zasuyi ido nakansu, Bayan kammala karatun kowannesu yacika burinsa yayinda modi ya zama babban doctor nan kasar Landon din yake aiki yayinda yabude hakararren hasibiti nashi nakanshi dake gida Nigeria da sunana HAJIA MADINA hospital inda yarsa Heelah take ai kenan kuma ita take jagorantar asibitin ,shikuwa habu yazama babban dan kasu but shi rayuwarsa harta ban garan siyasa ya taba yayinda yashahara wajan kasu wancin gwala gwale anan kasar England yayinda ta ban garan siyasa yake na hanun daman shugaban kasa, ganin kowannesu yacimma matsayan dayakeso tsayawa yasa nabijiro musu da batun aure cewa kowannesu ya gabatar min da macen da yakeso kuma yakeda burin aure ban garan habu yanuna min shide tukunna bashida wanda yake so yanzu baisaniba ko nan gaba but azahiri yanda naga sunfi shakuwa da Balkisu kullum suna tare suna fira nayi tunanin soyayyace a tsakanin su but saiya tabbatar minda ba abunda nake tunanibane to amma banida zabi wannan alkawarine da nayiwa zuciyata hada auran su dukansu 4 saboda sake dankun zumunci because a ganina nagida bai koshiba ba abawa na wajeba, Kasancewar modi shine babba senayi tunanin hadashi daHafsa because yarinyar akwai nitsuwa sosai ga hakuri but shi modi akwai taurin kai gaskiya wani lokacin baya jin magana ga fada ba kamar habu ba dan shi yanada saukin kai ga raha but shima wani time inya juye baka gane masa shiyasa nayi tunanin shikuma na hadashi da Balkisu (Ammi) Balkisu yarinyar tana da raha ga suruta kamar aku saide kuma akwai tsiwa wani lokacin shiyasa nake ga zasufi dacewa da habu tasu zaifi zuwa daya saboda ita Hafsa tanada shiru shiru sosai batafiye maganaba kuma itace karama akan Balkisu, koda nakawo shawaran hada junansu aure bawanda yakawomin cikas se modi dama nayi tunanin hakan domin kuwa yaki amsan tayin da namasa na auran Hafsatu yakawomin azurin yanada wacce suka d'aid'ai ta a Nigeria take da zama azirga zirgan dayake tsakanin Nigeria da london suka hadu, har ya gabatar min da hoton ta sunanta Jumanah azahirin gaskiya yarinyar bataminba Hafsatu naso na hadasu amma sam yadage se waccer yarinyar mai ido atsakarka ganin banasu natakura masa yasa nazuba masa ido yayi yanda yakeso yayinda shikuma habu ya amince da zabin da nayi masa, haka itama Rabi ta gabatar min da wanda take so saide shima asalinsa dan Nigeria ne shima babban dan kasuwane yau yanaca gobe yana nan but yafi zama Nigeria, dan haka aka daura aure kowannesu, Koda aka daura aure modi cewa yayi a Nigerian zasu tareda domin acewarsa amaryarsa tace bazata zauna inda yakeba because bazatabar dangintaba saide shiyabiyota suzauna acan domin bazata zauna inda ba kowa nataba modi duk abunda tace masa kamar yanka wuka haka zaidau lamarin a tak'aice dai yabita can Nigeria acan suka tare , itama Rabi tana can tareda mijinta a Nigerian karatunta da komai ya koma can, nida maihaifinsu wanda yake kwance jinya da habu da amaryasa mukadai muka kasance anan duk da shima habun bai wani cika zama sosai ganin yanda Balkisu take zama cikin kadaici yasa nace yadinga tafiya da ita matsawar bazata takurawa aikinsaba dan haka seyabi maganata yakan tafi da ita sa'i da lokaci kasan cewa itama karatu take bawai ta kammala bane inda take bangaran alkalanci, Hafsatu ita kadai takasan agabana da batayi aureba tacigaba da karatunta inda take da burin zama shahararriyar barrister saide kafin kammala warta tasamu miji inda wani malaminsu yanuna ra'ayinsa akanta ma'ana yanason ya aureta aikuwa ba bata lokaci akayi auran, saide kafin agama warware gajiyan bikin rai yayi halinsa watansu 3 yayi hatsarin mota Allah ya dauki rayuwarsa tadawo gida muka zamana yayinda ta cigaba da karatunta alokacinda Balkisu take dauke da tsohon cikin Ajmal a wannan yanayin mijina Alh Muhammad bature Allah yamasa rasuwa bayanda Balkisu tahaihu ta santalo santalelen jarumi d'an wanda yaci suna Muhammad anakirasa da AJEEMAL idan kinji ance Ajmal ananufin abu mafi kyau, mai kya , kyakykyawa, tunda suka haifi Ajmal sama da shekara 8 sannan ta sake samun cikin Kamal wanda kusan tare suka haihu da Rabi tsakanin muhaiseen da Kamal bai wuce sati 2 ba Saida aka hafi muhaiseen bayan sati 2 aka haifi Kamal shiyasa tsakaninsu ba yawa wanda tunda taga haihuwan muhaiseen Rabi bata sake samun wani cikin ba shiyasa ta dauki son dunya ta dau rawa muhaiseen because shi kadai Allah yabata, Kamal nada shaira 6 Ammi ta sake samun cikin yan biyun ta Fadeelah da fareeda ita fareeda sunan k'anwata taci yayinda ita kuma Fadeelah ni a kayiwa mai suna, ina matukar alfahari da family na mun zama tsintsiya madaurinki daya saidai gaba daya hankalina ya koma kan Rabi da Modi da suke Nigeria especially Modi da hankalinta ya kasa kwanciya da shi g'wara ita Rabi hanun namiji take but shi Modi ahanun mace yake saboda ita ta jashi sai yanda tayi da shi wannan abu yana d'agan hankali., Bayan da su Reeda da Fadeelah suka kammala primary School nayanke shawaran komawa Nigeria tushe na domin hankalina ya kasa kwanciya da rarrabuwan kan ahalina saidai Kamal da babban yayansu karatunsu yayi nisa shi Kamal yana Americans shikuma Ajmal yana Dubai kowannesu da inda yake karatu dan haka koda Habu ya dawo nake sanar da shi hukunci da nayanke na komawa Nigeria tun da dalilin wanda nake aure anan din Allah ya masa rasuwa dan haka zan koma mahaifata Habu baimusa mi ni ba saidai yace mu d'an basa lokaci domin duba mana gidan da zamu zauna, aikuwa cikin satin yazo ya nuna mana amincecen gidan da ya siya mana a gida Nigeria cikin babban birnin kano gidan yayi kyau fiye da tunanin mai tunanin dan haka sai muka soma shirin komawa Nigeria , . Koda muka dawo Nigeria muka sauka agidan da Daddy ya siya mana gidane mai kyau na alfarma babu abunda babu acikinsa komai na bukata an ta na daishi acikin gidan sai dan abunda da ba arasa ba bayan kwana biyu da zuwan mu na bukaci Daddy da ya kira Modi ya sanar dashi zuwan mu saboda ni inna kirashi baya shiga saidai shi ya kirani wani sa'i bayan lokacin watakil shi akwai yanda suke sadarwa kwana biyu da yin hakan aikuwa Modi ya turo da wata kyakykyawan mota acewarshi ad'ibomu akawomu inda suke aikuwa hakan akayi duk mukayi shiri muka shiga motar da ya aiko domin mu shi kuwa Habu motarsa na bayan mu yanabin duk inda yaga munyi har Allah yasa muka isa gidan Masha Allah gidan da modi yake rayuwa aciki yanada kyau matuka Saida kyansa zai biyo bayan wanda Daddy ya siya mana Wanda muke kokarin fara gina sabon rayuwa a ciki, balaifi anyi mana kyakykyawan tarba an gabar mana da abubuwa kala kala kama daga a bubuwan ciye ciye da na lashe lashe. Alhamdulillah naga d'ana cikin aminci da kwanciyar hankalin da alamu shima yaji dadin ganin mu tare da jin kyakykyawan labari dawowar mu Nigeria Saida abun lura dashi tun shigowar mu Modi ke tabin Hafsatu da kallon bakinsa keson cewa wani abin ita kuwa Hafsatu ba ta shima take ba hankalinta gaba daya yana kan yarinyar da ta ke ta shiga tana fice wajan d'a wainiya da mu duk wani abunda ake da bukata ita ke samarwa cikin hanzari kaida ka ga yarinyar baka kalar y'ar aikatau ko wahala ba kyakykyawan yarinyace kuma ga hankali yarinyace karama da bata wuce sa'arsu Fadeelah 13 year's sai girman jiki da suke da shi kai ka ce yan 20 year's. Gaba daya nima hankalina sai ya karkata yakoma kan ta nan nefa nake tambayan Modi tunda nazo banga giftawar jininsa ko guda daya ba nan yake sanar dani duk suna can ture suna karatu but nan da karshen shaikara zasuyi hutu zasu dawo insha allah daga nan zai gabatar dasu gareni amma ga k'anwarsu Nabilah Abu yafad'i yana nuna min Nabilah wacce tasunnar da kai kasa tana jiran abata umarni tayi nace dashi yanzu wannan din yar kace na tambaya da mamaki dan k'wata k'wata ba zakayi tunanin yar gidan bace duba da yanda taga Jumanah tana ta tsawata mata d'an kuskure kalilan zata hantare ta gaba daya dai yanda take mata zakayi zammani aikatau take wanda kuwa ba haka bane, nan ya fara neman da nayafe masa ataikace dai yayi aure shaikarun baya da suka wuce auran bai jimaba matar tarasu saka makon jinya da taita fama dashi wanda aka kasa gane kan lamarin har Allah ya karbi rayuwarta. Tabbas Modi ya shayar dani ruwan mamaki ban dauka zai iya mai dani ba a bakin komai na keba a garesa da har zai iya kula wani al amarin ba tari da nasa ni ko naji labari ba ban bi takanshiba ballai nasan sauran zancen da yake natashi na nufi gurin jikata tare da janyo ta jikina wanda ya sanya yarinyar sakin wani kuka mai tsuma zuciyan mai saurare gwanin ban tausayi take parlourn ya dau shiru bawanda yake magana daddy tunda muka shigo parlourn bayan gaisawa bai iya sake cewa kala ba ya zubawa sarautar Allah ido yana ganin yanda dan uwan nasa gaba daya ya koma sususu, fareeda da Fadeelah kawai na kallah na basu umarni dasu je ciki su ta ya Nabilah hada kayanta domin kuwa tare zamu tafi zama yakare mata agidan nan, amma Jumanah ba kunya babu tsoron Allah tashiga mita mai ya sa za adauke Nabilah daga gidan bayan ansan ita ta ke mata hidman cikin gida saboda Jumanah tamkar y'ar aikin ta haka ta dauki Nabilah duk wani ayuka na gidan ita takeyi amma ban bi takan ta kan surutan ta ba su Fadeelah suka hada kayan Nabilah suka fito muka wuce har muka fice daga parlourn HAJIA Jumanah mita ta ke wa Modi mai ya sa bazai dakatar damu daga kokarin tafiya da Nabilah da mukeson yi ba shikuwa Modi ya kasa tsaida mu kuma ya ka sa jure mitar da matarsa keyi haka muka tafi muka barso,,. Turo door din da a kayine ya sa HAJIA da ka ta wa daga labarin da take bawa Nisha suka shiga zurawa door din ido don ganin mai shigowa, ganin Ammi ne tashigo bakinta dauke da sallama yayin da hannayenta ke dauke da trary din abincin tashigo ta tsaya daga gefe tana aikawa Nisha da kallon tausayawa kafin ta ce " Hajia ya ka mata ki je ki ki kwanta kihuta ni because kin ga ke ma ba k'oshin lapia ga re ki ba d'an numfasa wa Hajj mama tayi kafin ta gyada kai takByalli Nisha tare da shafo gefen face d'in ta tana fadi'n "Zan tafi saida safe ki kula da kan ki" gyad'a kai Nisha tayi daga haka Hajj mama ta mike ta fi ce daga bedroom fadi'n "To yanzu bari natafi na baki guri ki kwanta ki huta good night" Ammi tafad'i tana yi wa Nisha kyakykyawan murmushi itama Nisha murmushin yak'e ta shigayi tana g'yad'a kai daga haka Ammi tafice daga bedroom din cike da jin dadin yanda Nisha ta sake jiki, nan Nisha ta koma ta kwanta because jikin ba k'wari kuma amace duk wannan sa kewar da Nisha tayi taci abinci cikin raha da rashin damuwa kawai ta danne zuciyarta ta ne because bata son su dinga shiga damuwa ta dalilin ta but Allah kadai yasan kukan zucin da ta ke. Washe gari da asuba Nisha yanda taga dari haka wa ye wan gari because bacci ya kasa daukar ta gefe Fadeelah da Reeda sai bacci suke cikin kwanciyar hankalin amma ita bacci ya kasa ziyartarta sam tunani duk yabi ya adda bi k'wanyarta ta kasa gaskata wannan lamarin wai ita aka daura wa aure da Ajmal papan Aheel mutum da Sam baya kaunar kasan cewar ta atare da shi in ba ya ka sance dole ba taya ma zata iya kasan cewa da shi tare da wannan ma sifaffiyan matar tashi Heelah mai bala'in kishin tsaya duk time din da taji wannan al'amarin tasan saita konata da ranta, haka Nisha ta dinga juyi saman bed ta juya nan ta juya can daga karshe taga kwanciyar ya gagara haka yasa ta sab'ulu daga saman bed tanufi bathroom because asuba tayi anata kiraye kirayen sallah ga mai niya . Wanka tayi sosai daga bisani ta fito ta naimi duguwar gown sannan ta sanya hijab tare da shinfida sallah tashiga jera salloli, karan ringin din wayar Fadeelah wata sai ta arlam na asuba shine ya tashesu daga nan nauyan baccin da suke, koda suka tashi idanuwan su ne ya sauka kan Nisha wacce ke zaune bisa sallaya bayan idar da sallolin ta tashiga yin lazumi ko waccen su mikewa tayi tasakko daga bed daya bayan daya sukayi alwala suka fito suma suka ta da sallah gefen Nisha, koda suka idar da sallah sukayi addu'a daga bisani suka mike Fadeelah tanufi bakin bed ta zauna yayin da Reeda ta ne mi saman sofa ta zauna gaba daya suka tusa Nisha a gaba suna kallo wacce kanta ke sun ku ye gaba daya yinin jiya bai musu dadi ba du ba da ya nayin da y'ar uwarsu ta kasance a ciki na rashin jin dadi ta wani ban ga re kuma ba karamin farin ciki suke da kasan cewar wannan lamari ba ko ba komai alak'a ya kara karfi tsakaninsu. Jin shirun ko wannen su ya sa Nisha juyawo suka hada ido da su Fadeelah wanda ya sa su ka yi saurin sakar mata murmushi, itama Nisha murmushin ta mayar musu hade da jawo alqur'ani mai girma ta shiga karanta ko damuwar da ke zuciyarta zai kawo , tayi nisa cikin karatun yayinda kakejin yar siriruwar muryanta wanda ka ke ji kamar ana busa sarewa tsabar zakin muryar ahankali ta ke karatun saboda gudun shiga hakki, sai guraren 7:30 kafin ta samu daman tsagai tawa time din har su Reeda bacci ya sake kwashesu daga inda suka k'ishin gid'a ita Fadeelah ta G'yara kwanciyar saman bed itakuwa Reeda ta mike saman sofa sunata baccin su, ajiye alqur'ani Nisha tayi tare da ninke sallayan ta ya ye hijab din da tarufu ta nemi ma ya fi ta sanya bisa kanta tanufi hanyar fita daga bedroom din direct kitchen ta nufa ko zata tarar da barka cikin kitchen din but sai ta tarar ba ta ciki kamar bata fito ba kenan sometimes zaka iya tarar da ita guraren 6: ta na aikace aikace Harta wu ce za ta koma sai kuma taji kamar shashshekar kuka ana jan akanci da surutai kasa kasa da ya ke kofar Barka yana gefe da kitchen shi ya sa Nisha ta jiyo sautin, ba da wani jin kiri ba Nisha ta matsa jikin door din Barka tare da murda handle din kofar ahankali bakin ta dauke da sallama ta tura kofar ta shiga, ko da Nisha ta shiga bedroom Barka a zaune ta sa me ta bisa sallaya tana addu'a yayin da ta daga hannuwa sama tana rokon Allah jin motsin shigowar mutum ya sa Barka saurin shafa addu'a tare da mutstsike hawayen face d'in ta tashiga k'irk'iro murmushi tana kallon Nisha yayin da ta kariso gefenta ta t'suguna "Baba barka lapia kuwa mai yafaru?" Nisha ta tambaya tana kallon Barka wacce ta ke mammatse ido cikin damuwa, "Bakomai y'ar nan lapia qalau na ke ya yau baki koma baccin ba kenan ya jikin naki ashe bakiji dadi ba Barka tashiga jero mata tambaya ta na murmushi da nuna ba wani da muwa da ke damun ta, "I'm okay but sai na ke ga kamar kinada damuwa because ga face din ki ya nuna hakan" "Lah ke kuwa y'ar nan mai zai da me ni a duniyar nan da ya wuce tsofa da tunanin mutuwa yau ko gobai" girgiza Kai kawai no Nisha tayi dan ba wai ta gamsu bane dan yanayin da taga Barka ciki ba ta saba ganin ta haka ba infact ma bata taba ganinta cikin damuwa ba balle harta kaiga zubar hawaye kullum cikin walwala da raha tareda wasa da dariya ta ke, d'a n numfasa wa Nisha tayi tana fadi'n "Shikenan daman naje kitchen ne ban sa me ki ba shine nace bari na duba ki a bedroom din ki muje na ta ya ki aikin kafin Ammi ta fito idan kuma bakijin dadine sai na karba miki aikin "Tab rufamin asiri y'ar nan kin gani qalau na ke yanda baki da koshin lapia ko aikin ban isa ki ta yani ba kije kiyi kwanciyar ki kihuta" tura baki Nisha tayi tare da b'ata fiska tana fad'in "Nifa lapia ta kalau muje kawai Nisha tafad'i tare da juyawa tayi gaba Barka nabin bayanta tana murmushi hade da girgiza kai tana tunanin halin kirki irin na Nisha, karfe 8:30 Ammi tazo kitchen d'in ta tadadda Barka tare da Nisha sunyi nisa cikin aiki daga bakin door din kitchen din ta tsaya tana kallonsu ba k'aramin jin dadi ta yi ba kuma hankalinta ya k'ara kwanciyar ganin yanda Nisha ta sa ke sosai kai ka ce ba abunda ya faru hankali kwance su ke hiransu da Barka suna raha, "Sannun ku da aiki" Ammi tafad'i time din da ta karisa shiga kitchen din duk juyo sukayi suna kallon Ammi wacce ta ke ta zuba murmushi kamar gonar auduga, cikin nishadi Barka tashiga dagawa Ammi gaisuwa sai da suka gaisa kafin Nisha tashiga mika nata gaisuwan "Ina kwana antashi lapia" "lapia qalau kyakykyawan y'ata ya kwarin jikin? ashe har kinfito kuma kika shiga wahalar da kanki" "Wallahi kinga nima sai da na ce ta bari taje tayi kwanciyar ta ta huta amma taki kinsan mutumiyar ta ki akwai son aiki" Barka ta karbi maganar murmushi Ammi tayi gamida shafo gefen face d'in Nisha tana fadi'n "Allah dai yamiki albarka but tafi wayance shashashon da basu da aiki sai bacci da danna phone zanga ya zasu kare da mazajen nasu idan basa bukatan y'an aiki kamar yayansu" dariya Barka tayi tana fad'in "Aiko dai" Nisha dai shiru tayi tana murmushi wanda bai kai zuwaci ba because yanzu bata da aikin da ya wuce murmushi yak'e ko dariyan dole saboda k'wata k'wata hankalinta ba akwance ya ke ba kwai dai danne zuciyarta ne karta nuna damuwarta afili tasasu cikin damuwar su ma, Ammi kallon Barka tayi tana fadi'n "So fatan breakfast ya zama ready? but zanje nayi wanka na shirya asamar min da breakfast please" "To ba damuwa yanzu kuwa" Barka ta amsa cikin b'arin jiki irina karb'an umar nin nan, daga haka Ammi ta juya ta fice daga kitchen d'in, ba bata lokaci Nisha da Barka suka shiga gabatar wa da Ammi breakfast d'in ta bisa dining table guraren 9 Nisha ta zame daga kitchen d'in ta fito tanufi hanyar fita daga parlourn. Side din Ajmal ta nufa security da ke can gefe ganin Nisha na karisowa yasa ya mike da sauri ya shiga kiciniyar bude mata door din parlourn sai da tayi masa sannu kafin ta sa kafa tashige, shi kuwa security sai zuba murmushi yake harda na sayarwa kafin ya maida kofar ya rufe, bakowa cikin parlourn shiru kakeji kamar ba masu rayuwa ciki, direct kitchen ta nufa yau ta ci sa'a bubu uban tarkacen wanke wanke da Heelah ta saba tarawa cikin kitchen d'in da alamar jiya bata musu mahaukacin girkin da ta sa ba ba da yanzu kaga kitchen kaca kaca da tarin wanke wanke, ba tare da bata lokaci ba tashiga gyara kitchen d'in ta tsaftace shi daga bisani tashiga daurawa Ajmal breakfast mai dan sauki because ta gaji sosai, Daga ban fitowa tayi ta dauki vaccum cleaner ta shiga tsaftace parlourn k'wata k'wata parlourn bai cika dutti ba kamar ba a zama cikin sa, tana ga mawa da parlourn sai kuma ta shiga haurawa upstairs, Bedroom din Aheel ta nufa tabude ta shiga wani murmushi ta sake har kullum dakin Aheel ya masifar burgeta especially kyawawan Teddy's d'insa masu kya da ban sha'awa duk ya watsasu ko ina har saman bed, karisawa tayi ta zauna bisa gefen bed din lokaci diya tasaki wani murmushi mai sauti big teddy bear d'in da Aheel ya yake kwanciya da shi lokacin shitaga ya sanyawa Teddy bear d'in shi dariya ne ya kufcewa Nisha tare da daukan teddyn tana kallo, daga bisani ta rungume Teddyn kafin ta maida shi ta ajiye nan tashiga g'yarawa Aheel shin fidarsa tareda tattare masa kayan wasa da Teddy's d'insa guri guda kafin ta fito ko door d'in Ajmal ba ta kalla ba balle tayi tunanin ta shiga ta g'yara du ba da gargad'in da Heelah tayi mata akan shiga bedroom d'in mijin ta so duk randa tayi katari ta shiga tofa sai d'an buzun ta shiyasa ma ta dawo downstairs ta koma kitchen domin ci gaba da aikinta , Guraren 9:35, motar Ajmal ya sako kai cikin gidan time din da mai gadi yabude masa geat sai yayi parking kafin ya fito ya nausa kai cikin side din shi har security ya taho da niyar bude masa door Ajmal ya dakatar dashi sau da dama yakan hanasu yi masa duk abunda yasan zai iya wa kansa tofa yafi gane yayi da kanshi shiyasa bude masa door mota ko door din parlourn ko wani rakiya private bai cika son amasa hatta door din office d'insa da hannunsa yake budewa baya bukatar taimakon kowa sai dai irin wani taron biki ko taron siyasa ko wani taro na musamman da zai kasan ce awajan to nanne yake bukatan girmamawa kasan cewar shi shugaba koma shararren dan kwangila,. Yana shiga parlourn saman table d'in parlourn ya ajiye key d'in motarsa tare da phone d'insa daga bisani shi kuma ya zauna bisa duguwar sofa ya mike yana sauke ajiyar zuciya remote ya dauka ya kunna television, dai dai time d'in da Nisha ta fito daga kitchen hanunta dauke da tray d'in abincin ganin Ajmal da tayi zaune bisa kujera ya kurawa TV ido yana kallon News channel, shi kuwa jin motsin mutum ta ba yanshi ya sa shi ju ya wa suka hada ido . Kallon kallo suka shiga yiwa juna daga bisani Ajmal ya dauke kai ya maida shi kan TV yayin da ita kuma Nisha tashiga ta kowa ahankali ta kariso tsakiyar parlourn tare da ajiye tray d'in abincin bisa table kafin ta dago kai ta kallai shi. "Ina kwana antashi lapia?" Kamar bazai amsa ba amma kamar wanda akasa dole daker ya motsa baki ya amsa mata da "Fine" Mikewa tayi da nufin tashi ta fita but sai ta ji ya ce "Zo nan" Jiki asanyaye Nisha ta dawo ta t'suguna ta sauraron mai zaice, "Mai yasa kika daina g'yara bedroom d'ina" Ajmal ya tambaya yana tsareta da ido daker ta iya motsa labenta wajan fad'in "Am., damman Aunty Heelah ce ta ce karna sake shiga inba haka ba zata karya kafata" Nisha tafad'i kanta sun kuye, saura "Nina saki aikin ko ita ?" Ajmal ya tambaya yana b'ata fiska tare da hade gira, cikin rawar murya Nisha ta amsa da "Kai.,kkaine" "So kar nasake miki tambaya akan hakan " "To" Nisha ta amsa tana g'yada kai nan yayi shiru na dan wani lokaci bai sake magana ba ita kuma Nisha kanta na sun kuye jin shiru ya sa tayi tunanin ya gama korafin nashi hakan yasa cikin hanzari Nisha ta sake mikewa da shirin barin parlourn still sai ji tayi ya sa ke fad'in "Come back ban ce kitafi ba" Ajmal ya fad'i yana hararota , cike da k'osawa Nisha ta dawo ta kuma duk'awa ba karamin ga jiya tayi ba tana bukatan ta huta but ya tsaida ita yana mata surutai gaba dayaa sai taji haushinsa ya kamata duk abubuwan da take masa ba gani yake ba, jin knocking anturo door yasa Ajmal da katawa daga maganar da yake kokarin yi ya kurawa door din ido don ganin wa ke shigowa haka babu excuse. Doctor fu'ad ne ya turo door ya shigo bakinsa d'auke da sallama ganin haka yasa Ajmal g'yara zama time d'in da doctor fu'ad ya karisa shigowa ya nemi guri ya zauna face d'insa cike da fara'a yana kallon Ajmal da Nisha wacce tayi sunkuye da kai tana d'urk'ushe saman carpet tayi ladab " Yallabo'i amin afuwa nashigo babu karban izini Doctor fu'ad yafad'i yana kallon Ajmal wanda shi d'in ma shi yake kallo, Ajmal bai ce masa k'ala ba dan yasan halin doctor fu'ad ko yaushe cikin tsokana da wasa yake " Ina kwana?" Doctor fu'ad ya tsinci y'ar siriruwa muryan Nisha tana mai d'aga masa gaisuwa cikin kankan da kai . " Lapiya qalau ya jiki naki " Doctor fu'ad ya amsa yana mai tambayar ta dagowa tayi ahankali kafi ta amsa masa da cewa "Da sauki" " but now naje duba ki aka shaida min kina nan shine nabiyo naga yanayin jikin naki but alhamdulillah naganki garau dake masha Allah" murmushi kawai Nisha tayi masa tana g'yada kai becauseause ta kosa ta tafi shikuwa Ajmal mamaki maganganun doctor fu'ad yayi because dama tambayar da zai mata last kenan, Ajmal komawa yayi ya kuma manne wa bayan shi da jikin sofa yana kallon Nisha karfin yayi gyaran murya hade da fad'in " Sai nace ki zuba abincin" mamaki Doctor fu'ad ya shigayi ganin mulkin mallaka da Ajmal ke yiwa marainiyar Allah sid'i sid'i Doctor fu'ad ya ga Nisha tamike a sanyaye ta nufi kitchen wasu plates da spoons Nisha ta kuma dau kowa ta dawo ta bude foodflast tashiga serving dinsu wani daddadan kamshin na musamman ya shiga gauraye parlourn fried chips with plantain and vegetables soup with roasted chicken ga sandwich with pancake gefe kuma ga lemon iced tea Nisha sai da ta gama serving din ogan nata kafin ta janyo wani plate din tasoma kokarin serving din doctor fu'ad "No karki wahalar da kanki kibarshi kawai zanyi serving da kaina tunda kin sallami mai gidan naki ya wadatar" wani kallo Ajmal ya dago yabi doctor fu'ad dashi kafin ya maida hankali kan abincin sa ya suma ci , "Za,.zan iya tafiyaiki " Nisha ta tambaya tana kallon Ajmal yayinda ya kai yayinda ya kai lallausan pancake bakinsa g'yada mata kai kawai yayi ba tare da yayi magana ba cikin hanzari Nisha tamike ta fice daga parlourn sai turo baki ta ke shi kuwa Doctor fu'ad an barshi da mamakin abokinsa ganin yanda ya tusa yar mutane gaba yana bata umarni cikin isa da gadara wai dan ma bai san matsayinta gareshi ba ,yarinyar akwai hankali da nitsuwa kuma ba maisun ha ya niya bace balle yawan magana ,. sam baya so Ajmal ya dauki halhakinta da yawa because yasan halin Ajmal na ko in kula especially yanda yaga yamai da yarinyar tamkar mai masa hidamane y'ar aiki kawai yana fatan akan yarinyar nan Ajmal ya fahimci maiye soyayya kauna da kuma yadda akejin shaukin wadda akeso ya fahimci rayuwar aure da kuma ma'anarta, a iya sanshi da Ajmal duk bai fahimci wadannan a baben ba kuma ya kasa tsayawa ya fahimta , haka ma ta ban garan aurataiyya bai daukeshi da wani mahimmanci balle ya tsaya ya fahimci yanda alamuran suke tafiya but ya tsaya ya na ta wahalar da kanshi "What are you thinking?" Wani dugun numfashi doctor fu'ad yaja yana mai kallon Ajmal wanda ya tsare shi da tambaya kafin ya saki wata murmushi yana fadi'n "Nothing" daga nan ya kai hanu shima ya dauki lallausan sandwich wanda ya ke hango shi tamkar zane "Tun shigowa na hancina ya cikaro da kyakykyawan kamshin abincin nan nasan cewa ba gama garin delicious ake gabatar waba ashai amaryar muce ta karbi office " Doctor fu'ad ya fad'i yana kallon Ajmal ta gefen ido kafin ya danna daddad'an sandwich cikin bakinsa. shi dai Ajmal har wa yau bai kullashi ba dan yasan Doctor fu'ad inya fara zuba kamar fanfon kasuwa yake bakin ba burki kuma cikin maganarsa ya dinga sa wasa da tsokana aciki. "Bana manta wani delicious da naci time da Raheelah ke amarya only one spoon but ranan kwana nayi ina zaryan toilet I hope HAJIA karama ta iya kayatattun delicious irin haka like Nisha ba girman parlour ta ke kamar Heelah ba " Doctor fu'ad ya sauka layi sai barin magana yake maybe dad'in girkin Nisha ke sa shi wannan zuban, Ajmal bai san sannan da ya saki wani murmushi mai sautin ya na kallon doctor fu'ad da ke ta kada kai ya na ta faman surutu shi dai a iya sanin shi k'anwartashi ba ta da mara ba da Heelah duk ba abunda suka iya sai dai ta iya zuban surutu kamar shi "Please kaci abincin kadaina surutun nan haka" murmushi doctor fu'ad yayi gamida da dan buga head d'insa kadan yana fad'in Sorry fa dad'in girkin ne yasa nake ta surutu ban sani ba , honestly mutumi na yarinyar nan ta tsa moka daga k'angi ta taimake ka yanzu kayi bye bye da ordern restaurant, cikin ta kaici da maganganun Doctor fu'ad yasa Ajmal da katawa da cikin roasted chicken din da yake ya ya b'alli tissue paper ya shiga goge hannayenshi kafin ya koma ya jingina Jikinsa da kujeran yana hararo Doctor fu'ad ' wai ta tsamoshi daga k'angi ta na taimakesa, shi inbama na sihar da Ammi ta yi masa akan yarinyar da kuma nuna tana bukatan mu amalarsu tare ba da mai zaisa ma kafarta ya fara tako side din shi tun kafin zuwanta yana rayuwarsa ba cikin k'angi ko taimakon wani ba zuwanta ba zai canza komai ba kuma k'angi da taimako da yake fadi'n duk wani bauta ko hidama da take da shi biyanta zaiyi dan baya bukatar hidimar da ta ke masa a kalle shi a fiskar taimako ko fita daga k'angi,' Doctor fu'ad ganin kallon da Ajmal ke yi masa yasa shi ya saki sakin murmushin kasa kasa "Naji kana tambayar ta ya jiki mai ya sa me ta" Ajmal ke tambayar doctor fu'ad because kasan cewarta a k'ark'ashisa zaiso sanin damuwa ko matsalarta, zame hanu Doctor fu'ad yayi shima ya shiga goge hannayenshi kafin ya gyara zama yana fad'i "Eh to da farko dai a sumammiya naje na sa me ta Ammi da kammala suna ne suke kaiwa da kawo bisa kanta but da na duba ta bakomai bane fa ce tsorita ne da firgici duba da yanda zuciyarta ta ke bugu yana kaiwa da kawowa shiyasa mu likitoci muke da d'a wayar da kai ba kowace irin magana akeso adinga fad'awa mutum kai tsaye ba ko ya tsinci magana kamar daga sama ma'ana baiyi zato ko tsammanin jin maganar ba especially mutum mai saurin razana tsoro ko firgici ba kasan halinda zai fada ba like ita Nisha ,. " Ammi Kamal? su sukayi coursing matsalar kakeso kace" Ajmal ya tambaya yana mai tsare doctor fu'ad da manyan idanuwansa "Kusan haka but Ammi ta fada min dalilin faruwan hakan wanda lamarine da ya shafi tsakanin ka kai da Nisha , is very confident Ajmal ya gyara zama yana fad'in "Ina jinka banaso kana tsayawa yayin maganar ka dunkule min zance cikin kalama daya," murmushi Doctor fu'ad yayi gamida fadi'n "Bana tunanin zai dunkulu ta kalma daya shi yasama banso na sanar dakai yanzuba because banzo da Shirin yi maka bayani yanzu ba nayi tunanin wa re wani time da ban dan tattauna maganganun because tattaunawar is very important cikin rayuwarku kai da ita but why not na sanar dakai yanzu nasan zaka saurareni kuma zaka fahimce batuna kuma ka dau shawaran da zan baka, ". Ajmal ya k'osa ya ji kan zance but shi kuma doctor fu'ad sai dugun ba yani yake da ma fa matsalar su kenan likitoci nan ba zasu tsaya su maka zance kai tsaye ba sundinga kwane kwane kkenan harsai mutum ya hasala "Look idan zancen ba fa'idar na sani kabarshi kawai ina da abubuwan yii" Ajmal ya fad'i ciki takaici da bacin rai ya mike yana kokarin tafiya cikin hanzari doctor fu'ad ya kamo hanun Ajmal yana fadi'n "I'm sorry mutumina zauna na maka bayani" because yasan halin mutumin da saurin hasala komawa Ajmal yayi ya zauna cikin hade gira ya ce "I'm hearing you talk " cikin na tsuwa tare da kawar da wasa alamarin doctor fu'ad ya shiga zaiyyanu zantuka da labarain da ya samu da Ammi game da batun auransa da Nisha,.. ______Tun bayan da Nisha ta fito da ga side din Ajmal ta nufi sashinsu a kokarin ta na shiga parlourn time d'in kamal shima ya sako kai da nufin fitowa nan suka game da juna gefensa dauke da Nabilah wacce ke biye da shi , ganin su da tayi sai da kirjinta ya d'an buga. ja ba ya Nisha ta yi ta matsa gefe kad'an tana kallonsu, Kamal fiska dauke da murmushi ya suma tambayar ta "My sister! Ke muka shiga dubawa yanzu but ba mu tadda ke ba. " Ya jikin naki" Kamal ya ya tambaya yana duban Nisha cike da murmushin nasa da baya yanke sai wani ikon Allah "Da sauki Nisha ta masa cikin sanyin murya, jinjina kai kawai Kamal yayi yana fadi'n "Masha Allah haka akeso" kafin ya juya ya kai kallonsa ga na Nabilah gamida fad'in "Ni zan wuce sai na dawo take care of yourself" g'yada masa kai Nabilah tayi tana fadi'n "Allah ya tsare" Daga haka Kamal ya wuce ya nufi compound d'in gidan daidai parking space ya shiga motarsa tare da yi mata key mai gadi yabude masa geat yafice. har yabar ha raban gidan Nisha binshi da kallon ta fad'a tunani ba k'aramin mamaki Kamal ya ba ta ba kwata kwata ba wata damuwa kan face d'insa gani tayi duk tafishi shiga da muwa da kad'uwa, but shi hankalinsa akwance yake kamar ma ba shi da wani damuwa. 'kodai kwai da ma wasa yake da hankali da tunaninta ba wani sonta ya ke ba but ya cusa mata soyayyarsa da ra'ayinsa da sha'awar fara sabowar rayuwa tare da shi ' jin anruko hannayenta yasa ta dawo cikin hankalinta da tunanin da ta ta fi time din idonuwanta har sun ciko da k'walla tab. Nisha kallon Nabilah tayi wacce ke rike da hannayenta duka biyu tana kallonta cike da murmushi tana fadi'n "Idan ban ta kura kiba inaso mu dan tattauna wasu maganganun da ke amma fa in ban shiga time d'in ki ba, girgiza kai Nisha tayi tana fadi'n bakomai" still Nabilah ba ta da ke hannun Nisha ba fiiiii Nabilah ta ja hanun Nisha suka nufi sashinta. Ko bayan da suka karisa shiga parlourn Nabilah ta zaunar da Nisha bisa kujera kafin Nabilah ta koma dining area ta hadu musu coffee ta dawo ta mikewa Nisha cup d'in zazzafan coffee shekeke Nisha ke bin Nabilah da kal kafin ta karbi cup ta rike still idanuwanta ba su dainabin Nabilah da kallon mamaki ba ita kuwa Nabilah sai murmushi ta ke ta zubawa Nisha kafin itama ta nemi guri kusa da ita ta zauna tare da kai coffee d'in cup bakinta. Sai da ta kurb'a zazzafan coffee d'in kafin ta kalli Nisha wacce ta sa ke baki ta na kallonta kamar hoto ta kasa shan coffee d'in da Nabilah ta ba ta "Ki sha mana kin tsaya kina ta kallona kamar ba ki sanni ba "Nabilah ta fad'i gamida murmushi ta cigaba da shan coffee d'inta kafin itama Nisha ta kai bakinta jikin cup ta suma sha. dan kadan Nisha ta shaa ta sauke cup d'in ta sa ke Kai kallonta ga Nabilah ta na son jin dalilin da yasa ta jawo ta nan da kuma maganan da ta ce zasu tattauna, Nisha muryan Nabilah taji ta suma magana da cewa " Tun bayan da naji tsakaniku da da ya Kamal na ji duk ki yai yan da na ke miki ya kau infact ma ko auranki ya bijiro da shi bazan wani damu sosai ba duk da kasan cewa ta macece mai kishi sosai especially akan abunda nakeso kuma nake matukar kauna ranar. farko da na fara ganinku tare a guest house d'in Daddy naji kishi sosai raina kuma ya baci harma nayi tsammanin wani abu tsakanin ku wanda kuma bai kamata nayi wani zargiba but time din idona yarufe naita fadan maganganun da bai da ce na fa de su ba akan zargin da ban da hujja ko tabbaci, Sam awance lokacin banason ya Kamal fada cikin yanayinda ya Kb yayi nisa aciki duk da abaya ya dauki wani ban gare irin na rayuwar Kb,. Juyowa Nabilah tayi tana fiskanta Nisha ta cigaba da fadi'n Kasan cewa na taba rayuwa cikin gida nan wanda shine sana diyar haduwata da Kamal time din da ya dawo daga American HAJIA ta sa aka shirya kayataccen waliman taron dawowar jikokinta dakuma murnar haduwar ahalinta, Kamal da KB makaranta daya suke karatu but ba wanda ya San Dan uwansa ko ya taba ganin hoton dan uwansa balle su shaida junansu.sai bayan haduwarsu aliyafar ne sannan ne suka shai da juna nima sannan ne na ga ya Kamal mukayi amanna da juna kasan cewa ina rayuwa cikin gidan su shiyasa muka shaku alakarmu ta kara karfi sosai wanda kowa ya fahimci hakan. Kamal mutum ne mai fara'a sosai da sun wasa tsokana da ban nishadi wanda shiyasa na kara sa ke sosai na fara mance duk wata damuwa na Kamal ba kamar babban yayansu Wanda ke da fiskar fusatattu sam bayi da fara'a sai mutum ya ci sa'a yake iya tuzali da murmushi ko da dariyansa ballai ma ba na zaton yana murmushi balle wani dariya shiru yake maganan bata da mai Shi ba infact ma duk inda yake da hayaniya ko ake surutu wajan tofa baya zama yafi kadai tuwa shi ka dai Sam ba yi da son ha yaniya ni tsoronsa na ke ji sosai ko ido ba na yarda muhada da shi time d'in da nake rayuwa gidan nan but karfin hali irin na Aunty Heelah haka ta dinga cusa kanta cikin rayuwarsa da nuna sha'awar soyayyarta gare shi amma shi sam baya bata fiska ita kuwa Aunty Heelah sam babu kunya cikin idonuwanta zaman turai ya ba ta ta duk wata kunya da akasan ya mace na dashi to ga Aunty Heelah kam babu infact ma ba ta sanshiba. Dabi'un da Aunty Heelah ke yi cusa kai ba kwarjini kiri kiri ba kunya haka take binshi wani sa'in abun har kunya ya ke bani ,ba ni kadai ba ma kusan kowa yana hankalce da tarkon da ta fad'a duk da sunsan wannan cusa kai da shige masa da ta ke baya waiwayarta ballai yasan halin da ta ke ciki because ba yida lokacinta harkan gabanshi kawai yake kamar baisan da lamarin ta ba amma Hajj mama duk ba ta yi la"akari da ta ban garansa ba yana da ra'ayinta ko aa hajia ta sa aka shirya bai konsu duba da yanda Aunty Heelah ta k'walla fa rai da shi ta nuna sha'awar so da kaunarta gareshi,. Ya Ajmal duk da bai nuna interested akan Aunty Heelah ba but bai nuna ya na da ja ko musu a kan abunda HAJIA ke kokarin yi ba time d'in da Aunty Heelah ta kammala karatunta a kasar England aka tsaida ranar auransu already ya Ajmal ya Kammala masters d'in shi dan haka aka tsaida ranar auran tare da na Aunty Hafsatu kanwar ammi acewar hajia tunda har mahaifina zai iya cin amanarta yayi wani auran har asamu karuwa amma ace bai iya fada ma ta ba kuma bataji labari ba to yanzu bashida ikon da zai da katar da ita daga hukunci da tayanke na auran Aunty Hafsatu koya amince ko bai amince ba yana so ko baya so duk da abaya ya bijirewa hakan ba da son rantaba, bayanda da Aunty Hafsatu ta kuma gidanmu da zama amatsayin matar Abu to bayan wasu lokaci jima na koma gida na cigaba da da Auntynsa hafsatu. Aunty Hafsatu tana da dadin zama sosai ta rike ni bisa amana tana kula Dani sosai tamkar wacce na fito daga cikinta kulawar da take ba ni ko mahaifiyata tana raye iya kulawar da zata ban kenan, ba kamar sanda na ke hanun mommy ba time d'in jinke gidan kamar ba na mahaifina ba kamar ba cikin gidan na girma ba gidan ya zam ta tamkar akan k'aya na ke saboda ita time din ko yan aiki hana mahifina tayi ya kawosu ninake komai a gidan ga tsan g'wama da kyara na zama tamkar bora acikin gidan, wanda kuwa ba haka ta kewa su Aunty Heelah da yaya KB ba duk da nayi farin ciki da ban kasance ta bani irin tarbiyan da ta taso da yayanta ciki ba gaba daya ta ga ma sangartasu ba ta k'wab'ansu duk abunda suke so shi sukeyi walau mai kyau ko mara kyau . Sun kuyar da kai Nabilah tayi saboda wani hawayen da ke kokarin zubu mata na tuna wahalar da ta sha ahanun mommy gaba daya Nisha jikinta sai ya kara yin sanyi gaba daya tausayin Nabilah ya kamata wato kowa da yanda ake jarabashi arayuwa, parlourn ne ya dau shiru ba wanda ya yi magana cikin su jim kadan Nabilah takuma dagowa ta kalli Nisha tana fadi'n Kiyi hakuri bana kiraki Dan na baki labari ko surutu abunda ya shafi rayuwa ta bane sai d'an kinzama daya daga cikin family gidan nan kina da right din kisan wani ban garai da yashafi ahalin nan da kuma yanda rayuwar familyn ke gudana, because Kamal ya bani labarin komai daran jiya ganin yanda hankalinsa ya tashi sosai ya kasa nitsuwa wanda nima yasa nakasa nitsuwar hankalina ya kasa kwanciya har sai da ya labar ta min abunda ke faruwa matsayinsa na mijina kwantar masa da hankali tare da bashi shawarwarin da zai Kara matar dashi damuwarsa ya manta da ya cireki daga zuciyarsa ya manta ya ta bata jin wani abunda ya Dan ganci soyayya da ke because ke ba rabunsa bace ke matar yayansa ne yanzu alkar ku zaima yanzu yan uwan ta ka ne kawai ba batun so ko wani kauna ba. Sannan ke ma ina mai baki shawara ki mance da Kamal ki fiskanci rayuwa auran da zaki fara da wanda zai zama shine jigo yanzu cikin rayuwarki duk da kin tsinci rayuwar auranki ta wani siga da ban kuma ina tayiki alhinin hakan ina kuma taya ki bankincikin kasan cewar Aunty Heelah amatsayin wacce zaki zauna da mijin ta ku zama kishiyoyin juna., _______Nasan halin yar uwata sosai tamakar yanda nasan yunwa cikina ina mai baki shawara ki dage da addu'a sosai har lokacin da Allah yasa ta fahimci ma tsayinki awajan mijinta , ina fatan Allah ya yayyafawa lamarin ruwan sanye komai ya tafi daidai cikin kwanciyar hankali because nasan Aunty Heelah da kuma hali irin na ta, akarshe nima zan sanyaki cikin addu'ata kuma ina rokonki da kidaina guduna haka nan nima ki dauke tamkar yanda kika dauki su Reeda nima ki daukine daya daga cikinsu because muriga munzama daya yanzu Nabilah ta fad'i ta na riko hannayen Nisha,. jiki a sanyaye Nisha g'yada kai tare da sunnar da kai kasa maganganun Nabilah duk ya sa ke kashe mata jiki tsoron ta ya k'araru matuk'a bata san ya zata fara fiskantar wannan k'addaran auran ba sam ji ta ke ina ma duk wanda nan abubuwan da ke faruwa da ita ya kasan ce mafarkine ba gaskiya ba da kuwa inta farka bazata sake komawa wannan baccin ba girjinta sai bugun goma goma yake da ga Heelah har mijin nata tsoron su ta ke ballai kuma yanzu da ta ke kokarin fara rayuwa cikinsu wani irin yanayin zata tsinci kanta a tare da su a tuna ninta dukansu babu mai rang'wamen fiskar da zataji saukin mu'amala dashi. rintsa ido idanu Nisha tayi tana furzar da wani irin zazzafan ajiyar zuciya ta shiga karanto wasu addu'oi a hankali tana jin zuciyarta dan sanyi kadan kad'an kamar ana yayyafa mata ruwan sanyi, ganin halinda da ta shiga yasa Nisha ta bawa Nabilah tausayi nan ta cigaba da tausan ta tare da bata shawarwari masu kyau wadan da zasu amfane ta, haka wunin yau Nisha ta yi shi cikin sanyin jiki har wani zazzabi zazzabi ta ke ji ya dawo mata, da dare bayan sun kammala dinner sun zauna bisa parlour suna fira kamar yanda suka saba, wanda nan Ammi ke shaida wa su fareeda ce wa Saturday and Sunday suna da private class na koyan girke-girken zamani kasancewar bikinsu yana ta karatuwa kuma ba abunda suka iya na ciman zamani ballai na gargajiya wacce zasu nishadantar da mazajensu Dan haka ta yanke shawaran kaisu akoya musu delicious kala kala saboda afita kunya shi ya sa ta ware wadan nan kuwanakin because sauran lokutan basu da lokaci saboda karatunsu, ranar murana gurin su Fadeelah ba a cewa komai. Suna tsaka da firanne wayar Nisha ta shi ga k'ara alamar kira nan Nisha ta kalli screen d'in wayar salma ce ke kira duk duk da kasan cewar tun safiyar ranar ta ke ganin k'iran ta but takasa dagawa because bazata iya magana dan ta San da ta fara magana zata fashe da kuka shi ya sa ta ke gudun ta d'aga mata hankali ana tsaka da shirin bikinta dan ta san duk wani damuwarta damuwar salma ne haka duk damuwar salma da muwarta ne sun d'auki juna tamkar jini d'aya sam basu yi tsammanin rabuwa haka lokaci daya ba, abaya da suke rayuwa tare basa kwana d'aya ba su ga junansu ba ba tare da dalili mai karfi ba amma gashi yanzu sun rabu sai ayi wata basu ga junaba sai awaya kawai suke haduwa , yan zunma kifa wayar ta yi gefenta kanta kasa ta ci gaba da murza Dan ya tsanta tana ta karatun zuci "Ba kiran ki ake awayar bane?" Hajia ta tambaya tana kallon Nisha, Nisha dagowa tayi ahankali ta kalli Hajia gamida g'yada mata kai tana fadi'n "Eh kirane " "Waye ya ke kira ki ? d'auka ki je bedroom ki amsa kiran mana kar mu da meki da ha yaniyar mu" ba musu Nisha ta dauki phone d'inta ta nufi bedroom tareda neman guri ta zauna ta shiga kiran salma time d'in idanunta haar sun kawo ruwa, ba wani dugun rigin carab salma ta dauki wayar ta suma magana. "Haba Nisha why ba kya picking call d'in sai kinga dama duk kinsa hankalina ya tashi wai mai take faruwane "salma ta shiga jerowa da Nisha tambayoyi dan ko sallama ba tayi ba. "Bakomai" Nisha ta amsa mata can kasan ma koshinta, "Ko bazaki samu zuwa bikin nawa bane kika kasa fad'a min" "Eh " Nisha ta ce time d'in da ta ke dab da fashewa da kuka shiru salma tayi na Dan wani lokaci ba wanda yace kala acikinsu. "Nisha kodai dunyar tayi miki dad'in da zaki iya watsi danine haka daga jiya zuwa yau na kiraki ya fi akirga but ba kya picking yanzu koma naji yanzu kuma da muke magana sai na fahimci kamar baki son magana na da meki , ko dai wani laifin na miki duk da nasan yanzu munyi nisa da juna bana tunanin hakan, dan wani abune ya ke faruwa da ke ya kamata ki fad'a min because ni abokiyar fad'a wa matsalar ki da damuwarki ne ko abunda ya shafeki please ki fad'a min in wani abunne ke da munki" nan fa taji Nisha saki wani kuka waiwai kamar karamar yarinya, ba k'aramin ta shin hankali salma ta shiga ba jin yanda Nisha komai ta ke kuka kamar wata k'araman baby nan Salma ta rude ta shiga tambayarta ba sanin kukan but ba amsa, tambayar duniyar nan salma tayiwa Nisha amma ta ki kulata, nan Salma ta ka tse wayar daga haka Nisha ta kwanta saman bed d'in ta ci gaba da koke koken nata a hankali ba tare da sautin ya fito anlura da halinda ta ke ciki ba. Sai da ta yi kukan ya isheta kafin ta g'yara kwanciya dan ko kayan jikinta ba tasamu daman canzawa ba taja blanket ta rintsa ido tana sauke ajiyar zuciya kanta harya suma ciyo saboda kukan da ta sha yau ko tunanin kiran Ajmal taji ko yana da bukatan wani abin duk da tasan bai cika bukatan wani abin da dare ba infact ma bai cika dawowa da wuri ba koma ba dan hakan ba bazata bi ta kanshi ba, ta masa na Allah duk da ba wani koshin lapia garai ta ba, da safen nan ba k'abisa da aramin gajiya tayi ba ga kuma haushinda ya kuma bata tana cikin wannan yanayin har bacci b'arawo ya sace ta, washe gari karfe gusan 10 Nisha ta kammala ta shiga jerawa dining table kamar yanda ta sa ba parlourn shiru sai karan TV da ya ke ta aiki sai kuma ita da ta ke ta faman Kai kawo tsakanin kitchen da dining area tana shirya breakfast ,. Nisha harta gama komai ta kimtsa ko ina ba kwalkiyan ko mutum daya da taji duk da tayi tsammanin tun shigowa ta zata ci karo da Heelah ko ta ji motsin ta but sai ta ga sabanin haka wanda hakanne ya bata daman yin aikinta cikin na tsuwa, ta nufi upstairs direct bedroom d'in Ajmal ta nufa ta g'yara masa kamar yanda yayi korafi, tana zuwa bakin door d'in ta shiga yin nocking a hankali bugu daya zuwa biyu ba ayi magana ba hakan yasa ta murda handle door d'in ta ku tsa kai bakinta dauke da sallama ta karisa shiga, . bedroom din ba kowa ciki duk da anrage light d'in dakin ba komai ta ke iya gani ba d'an haka ta karisa cikin tsakiyar dakin ta nufi switch light d'in ta kunna nan haske mai kyau ya gauraye bedroom d'in nan fa idonta ya hango mata Aheel da ke kwance yana sharan bacci yana rugume da pillow kamar kamar zai shige ciki ya rungume shi tsam ajikinshi Nisha ba ta san sanda ta saki murmushi ba tana mai kallon kyakykyawan face d'in Aheel mai kaman antsaga kara da papanshi, karisawa tayi ta zauna bisa bakin lallausan bed d'in sai da ta lumshe ido tsabar taushi da laushin bed din, cike da murmushi Nisha ta kai hannu ta shafo gefen face d'in Aheel, kamar wanda ya yake jira a taba shi aiko tar ya bude idonsa bisa face d'in Nisha Aheel na ganij Nisha zaune gefen shi tana ta zuba masa murmushi, shima washe mata baki ya shigayi cike da farin ciki ganinta ya fad'a jikinta tare da rungume ta, cikin farin ciki da kyawan yaron Nisha ta dinga shafa bayanshi a hankali kafin ta dan zame jikinta daga nasa ta shiga tambayarshi "My little yau ba school ne naga Kanata bacci har wannan time d'in, "washe baki ya kuma yi yana fadi'n "Laaa Aunty jiya fa mukayi hutu, kuma hutu mai yawa aka bamu har 3 weeks Aheel ya fad'i ya na nuna da yan tsun hanunsa uku murmushi Nisha ta tayi gami da fadi'n "Good tasu muje to baccin ya isa haka" , nan ta juya masa baya alamar ya hau bayanta shikuwa cikin zumudi ya dale bayan Aunty Nishansa tare da sakalo face d'insa gafen wuyarta yana ta dariyan jin dadi daga haka suka fice daga parlourn bedroom din Aheel suka nufa ta sa ya cire wannan tausasun kayan baccin da ke jikinsa ta bashi dan k'aramin towel ya daura yashiga bathroom domin ya wanke jikinshi yayinda ita kuma ta nufi wardrobe ta dauko masa kyawawan kaya t shirt and jeans rigar white color sai black jeans tana jin yanda Aheel ke ta wasa cikin toilet Dd'in yana tsalle tsalle yana wasa da ruwa ganin bayida niyar fitowa yanzu yasa no Nisha mikewa tashiga toilet d'in ta taimaka masa yayi wankan kafin suka fito ta kimtsashi tare da sanya masa kaya kafin ta jawo hanun shi suka nufo downstairs. Dining table ta nufa dashi ta zaunar da shi ta dauki plate ta sanya masa breakfast duk abunda ya nuna ya naso shi ta sanya masa ta tura masa gabansa ya suma ci, daga haka ta zame jiki ta koma bedroom din.dining zuciyarta daya tunfi toilet domin fara wanke shi murda handle d'in tayi ta shiga , zaune yake cikin bathtub yayi tsam da ranshi idanuwansa a lumshemaganganun Doctor fu'ad sai d'a masa yawo cikin kunnuwa su ke sam ya kasa gas gata maganganun sa because yasan doctor fu'ad dasa zulaya cikin lamauransa in ba daga wajan su Daddy ko wajansu hajia ya ji bataun kai tsaye daga gare suba bazai taba gas gata hakan ba, idan kuma harta tabbata hakan lamarin bazai taba daina bashi mamakiba. ko Time d'in da aka aura masa Heelah ba waii dan ba yi da ikon hanasu ko da dakatar da su bane kawai ya kyalesune ya zuba musu ido ba wai dan ya rasa yanda zaiyi bane but hakan ba shi zai basu daman jogana masa wannan wata mace ba especially wacce baisan wacece ita ba bai kuma san daga ina ta ke ba ballai asan asalin wacce ita, turo door din toilet d'in da akayine yasashi bude ido da sauri don ganin wake kokarin shigo masa bathroom ba neman izini, Nisha ya gani ta shigo kai tsaye wacce itama da alamar ba ta lura da shi ba because toilet d'in yana da girma sosai tamakar parlourn wani gidan fiskarta dauke da fara'a takarisa gaban katafaran mirror da ke cikin toilet d'in da ya ke fara kallon mutum yayinda ya shigo tsayawa ta yi tana hango kanta ciki rabunta da ta tsaya ta kalli kanta madubi harta mance time d'in kallon kanta ta ke sosai tana karawa tare da shafo face d'inta ta jikin mirror ganin tayi har wani kumatu tayi kuma ta kara haske sosai. tabbas itama yau tayi mamakin yanda taga yanayinta ya canza gaba daya hutu ya zauna mata haka ta dinta juya lallausan hannayenta tana kallo kamar ataba jini ya fito time daya kuma fara'a ta ta dauke face d'inta ya koma face d'in jimami saka makon tunawa da maganar salma na cewa 'duniya yayi mata dad'in da zata iya mancewa da ita' duk da ba ta yi tsammanin wannan furcin daga gare ta ba because ita dai a iya saninta bawani jin dad'in da zata tsinci kanta aciki ta kasa tunawa da aminiyar ta kawar yarinta abokiyar cin mushe su kashe su bunne tare wasu zaffan hawayene suka gangaro mata kafin cikin hanzari ta shiga goge hawayen ta suma waige waige don fara aikin da ya kawota kar ogan nata ya zu ya taddata anan tana ta karanta wasikar jaki, wani ihu Nisha ta kawo sake tana sallati gamida rintsa idanunta because ganin Ajmal time d'in da ya mike ya na kokarin daura towel bisa waist d'insa tana kuma yin baya ganin Ajmal tsaye cikin bathtub yana kokarin daura towel bisa waist d'insa, baya Nisha ta kuma yi da sauri idanuwanta a rintsai jikinta sai k'yarma ya ke a aikuwa sai timmm kakeji ta zame santsin tailed ya zamar da ita a zafafe ta ta kuma mikewa tanufi door sai da ta bude ido kafin ta murda handle d'in tafito ta watsa aguje ta fice. Aheel na zaune bisa dinning table yana breakfast kamar yanda Nisha ta barshi sai ganin Auntynsa yayi tafito fuuu kamar wata mota ta wuce ta fi ce da gudu daga parlourn ko waiwaye ba ta yi Aheel bin ba yanta yayi da kallo tare da kai kallonsa upstairs dan ganin mai ta ke wa gudun dan ba k'aramin tsoro ta ba shi ba sai zare ido ya ke amma ba kowa da ke biye da ita nan ya shi ga zamowa daga kujeran da nufin bin bayanta but sai ya ji muryan mom d'insa ta kira sunansa wanda ya sa ya mai da hankalinsa garaita ya shiga washe mata baki tare da kokarin karisawa gareta yayinda ta ke sakkowa ta na sanyi cikin kananun kaya wata half vest sai d'an wani gajeren wando iya gwiwa ta tufke gashinta a tsakiyar kanta sai lilo ya ke bayanta ta yi kyau da ita, Cike da murmushi ta kariso ga Aheel ta re da sa hanu ta sun kuci d'an nata tana fadi'n "Good morning in this morning my love" Morning Mommy Aheel ya fad'i gamida kwantar da kai jikin mommynsa " What are you doing here" Heelah ta tambaya tana mai kallon Aheel ta na kuma kallon dining table d'in da kawata shi da kyawawan girke-girke kala-kala ta shaida wannan aikin Nisha ne nan ta shiga hararo abubuwan da ke jere bisa dining tana tabe baki nan Aheel ya shiga zamowa daga jikin mom d'insa kafin Heelah ta direshi akasa ta na kallonshi. "Mom taho ki zauna kiye breakfast Aunty Nisha na ne ta yi mana delicious mai dadi " ta ho ki zauna ke ma " Aheel ya fad'i cike da murna yana washe baki gamida jawo mata kujera alamar ta zauna but Heelah sai Jan wani banzan tsaki tayi tana tabe baki tana kallon Aheel da ke ta rawar Kai wai Aunty Nishansa tabdi. "Come and seat Mom" Aheel ya kuma fad'i yana kallon mom d'in nasa wacce ke ta faman hararo shi da shi da table d'in gaba daya tana fadi'n "Kai da Allah rabu da ni mai zan zauna na ci a wannan tsiyar Allah kaidai yasan hade haden da ta ke cikin girke-girken nan da ta ke tana jan hankulanku da tunanin ku ku ke ta wani ribibi a kanta ta ga ma siye zuciyoyinku da yin nasara a kanku to nikam na fi karfinta ta Allah ba ta mutum ba muna fukar banza kawai Heelah ta karisa fad'i hadai da jan wani dugun k'wafa zuciyarta ta sai zafi ta ke ita ta rasa ya zatayi da wannan yarinyar gaba daya ta shige mata hanci da k'udunduni juya baya tayi yayinda ta hade hannayenta a k'irji ta na kada kai ta na tunano irin hanyar da zatabi da Nisha, shikuwa Aheel shiru yayi jikinsa duk yayi sanyi ganin yanda mom d'insa ke ta surfa masifa akan Auntynsa duk da baisan inda zantukan na ta suka do sa ba baikoma fahimce ta ba. Shiru yayi ya na ta kallon mom d'insa da ke tsaye ta na ta kaiwa da kawowa ta kasa zama gefe guda kuma ya hangi papansa wanda ya ke sakkowa daga upstairs yana sanye cikin kyakykyawan black suit and black shoes sai bakin glass da ya sanya ya tushe idanuwansa, da gudu Aheel ya taho ya d'ale jikinsa time d'in da ya gama karisowa, cike da murmushin nan na shi Ajmal ya dago Aheel ya sunbaci kumatunsa kafin ya sauke shi kasa karfin Aheel ya ja hanun papansa suka zauna bisa dining table Ajmal ko kallon inda Heelah ta ke baiyi ba ballai ya San da tsayuwarta ya nemiguri ya ya zauna, Heelah tunda ya sakko ta ke binshi da kallo harya karisa dining ya zauna kafin ta tabe baki gamida matsawa kusa da shi ta ja kujera ta zauna ta na fad'in "good morning dear" "Morning" Ajmal ya amsa cikin cool voice na shi ya na mai kokarin kai hanu dan serving din kanshi cikin hanzari Heelah ta a ga je shi ta shiga serving d'insa shikuwa bai dakatar da ita ba because ya na bukan hakan , tana gama serving d'insa itama tayi serving kanta ta zauna ta tusa plate agaba tana ya mutsa fiska sai ka ce wanda aka ce ta ci dole gefe kuma Ajmal breakfast ya ke cikin kwanciyar hankali yayinda Aheel ke gefe shima sai kada kai ya ke time din da ya ke shan daddad'an yoghur fruit ya na santi wayar Ajmal ne ya shiga ruri alamar Kira wanda ya sa shi dakatawa daga breakfast din ya kai kallonsa ga phone din ya kalli screen din wayar dan ganin mai kira, sharewa yayi ya ci gaba da cin abincin sa Heelah sai mika wuya ta ke tana kokarin hango sunan da ke makale jikin screen din wayar dan ganin wanda ya uzura da kira haka shikuwa Ajmal ya ki kula wayar tana a jiye saman table daga karshe ma silent ya sanya wayar ganin an matsa da k'iran, Ajmal mikewa yayi gamida goge hannayenshi ya kamu kan Aheel ya sunbaci goshinsa yana fadi'n " take care of yourself bye yana fadi'n haka ya dauki phone d'insa tare da key din motarsa cikin hanzari ya fi ce daga parlourn Heelah har ya gama ficewa daga parlourn ya kurewa ganita binshi ta ke da kallo tana tab baki , shi kuwa Ajmal yana fitowa direct parking space ya nufa ya shiga mai gadi ya na ganin fitowar da rawar jiki ya tashi yabude masa gate haka Ajmal ya zo ya sa kai ya fice mai gadi sai daga masa gaisuwa take Guraren4 yamma wasu kyawawan mota guda biyar duka danno kai cikin gidan time din da mai gadi ya bude gate motar ga ba Daddy ne aciki sai kammala da ke driving dinsu sai yan rufa masu baya mota guda 3 suka karisa shigowa su kayi parking daidai parking space daga nan Daddy da Kamal suka fito daga bisani sauran security gidan suka shiga yayiwa Daddy sannu da isowa daga haka Kamal ya karbi dan madai daicin troler ya karisa shiga masa da shi, yau gurinsu fareeda murna ba a magana Daddy ya dawo duk ida yau anacikin murna duk da tafiyar tashi ba wani jimawa yayi ba but kowa yayi kewarsa sosai kasan cewar Daddy mai yawan wasa da dariya wanted sa'in harda tsokana, awanan rana ammi ta kasa tsugul sai da ta zaiyyane masa duk wani abunda ya faru bayan ta fiyarshi wanda abun ba k'aramin mamaki ya ji ba jin har suma Nisha ta yi ta kwanta rashin lapia ga kuma soyayyarsu da Kamal wanda basu san da shiba nan ya yanke