Ummi Tandama😇: 📚4️⃣ RANA DAYA BOOK 4 Page 1 Cikin zafin rai Shatima ya isa gurin da Salma da ke tsaye tana cika tana batsewa. Ya zabga mata mari, ya sake zabga mata a dayan gofen. Salma ta gigice, ta ce,In ba ka sona iyayena suna sona ba sai ka kashe ni ba. ka sake.Ya sake kai wa bakinta kwabda, ta fadi Kasa bakin ya fashe jini ya soma tsiyaya. Shatima ya ce, "Kin dade ba ki tafi ba, kin ji ko? In ki ka sake magana sai na sumar da ke Ya fice bai bi ta kan kayan da ya zube a kofar daki ba, ya nufi dakin Aliya yana huci cikin tsananin bacin rai. Aliya ta tare shi da sannu, amma ganin ya kasa amsawa sai ta fahimci yana cikin bacin rai, don haka sa ta aje ruwa a gabansa ita ma ta samu guri ta zauna. Salma kuwa tana tashi ta shiga bandaki ta sa ruwan dumi ta wanke jinin da ke zuba. Lebenta ya kumbura suntum, jini kuma bai tsaya ba, ta ce,Ai yau komai dare sai na tafi" Ta dauki jaka da akwatinta daidai an tada sallar magriba ta san Baba maigadi yanzu ya tada sallah, ta yi ficewarta. Ba ta yi nisa a layin ba ta samu dan acaba ta tare ta nufi titi. Ta dan jima kafin ta samu motar zuwa Zaria. Da ta sauka ta sake daukar dan acaba zuwa gidansu.Maman Nana makociyar Nafisa ta shigo gidan da sallama, Nafisa ta amsa tare da fadin,Har kin dawo?"Maman Nana ta ce, "Ai kin san asibitinbabu layi, kana zuwa za ka ga likita, ina su Nana suna ta yi miki rashin ji ko?" Nafisa ta ce,Suna can falo suna kallon carton da su Ashraf"Ta ce, "To bari tunda ba su ji zuwana ba in je in gama aikina"Nafisa ta ce, "To ga makullin can" Ta nuna mata shi a windon kicin, har ta juya sai kuma ta dawo tana cewa, "'Au! Maman Ashraf ina ta zuci-zuci in fada miki wata magana, amma ban san yanda za ki dauki abin ba Nafisa ta ce, "Haba Maman Nana, inda zaki fada min ko mene ne kawai ki fada min" Ta ce,Ban fada miki da wata manufa bá, sai don ki yi saurin daukar mataki, amma cikin nutsuwa da hikima ba wai tashin hankali ba" Nafisa ta zaro ido,Mene ne don Allah? Ki fada min". Maman Nana ta ce, "A'a kar ki daga hankalinki, shekaran jiya waccan na dawo gidan Maman Sabir naga mijinki ya sauke wannan yarinyar Zinatu shine nike son ki fada masa ba yarinyar arziki ba ce. Duk namijin da ta dafe masa sai ya yi kamar ya zauce don sonta. Ta yi aure sau biyar duk wanda ta aura sai ta sa ya rabu da iyalinsa sannan ta ki zama, sai ya sake ta. Yanda ki ka san annoba haka ta zama a layin nan" -' Nafisa ta ce, "Na shiga uku, to ni Baban Ashraf in ya ce zai so ta ai mun bani, mu hudu ne fa, wa zai saki?"Maman Nana ta ce, "To nan bala' in yake,ko mutum ba ya neman mata in har ya hadu da Zinatu zai fara. Tana da kyau kamar aljana, ga ta fara tas, ga diri ta iya gayu sosai. Sai dai fa akwai shiga malamai" Nafisa jikinta har rawa yake, ta ce, "Ya je Kaduna zan ma jira ya dawo kuwa? Ina jin a waya zan kira shi"'.Maman Nana ta ce, "A' a ki dai bari har ya dawo din sai ki nutsu ki yi masa magana cikin lumana" Nafisa ta ce, "To shi kenan, na gode Maman Nana" [8/23, 15:33] Ummi Tandama😇: 📚4️⃣ Page 2 Nafisa ta samu guri ta zauna cikin damuwa, in Shatima neman mata zai fara lallai za a samu katuwar matsala. Ta tashi ta dauko waya da nufin kiranshi, amma sai ta tuna fa tana cikin damuwa da zakuwar ya dawo. Badi'atu tana kwance a kan gadonta,zazza6i ne a jikinta rijib, mijin ya shigo ya dube tà,badi'atu wai har yanzu jikin?"Ta ce, "Eh don Allah a kai ni asibiti Bari Maman Kausar ta gama ku je Badi'atu ta ce, "Haka jiya ka ce za mu je tare da ita, ta ce ta yi baki sai haka na kwana da ciwo. To ni kawai in ba za ka kai ni ba, ka min kwatance Ya ce,Yau za ku je insha Allahu, jiya ma don tayi baki ne"Badi'atu ta koma ta kwanta,Ya ce, "To ni zan fita, sai na dawo" Don haushi ba ta tanka ba. Maman Kausar ita ce kishiyar Badi'atu, kuma ita ce za ta raka ta zuwa asibiti Badi'atu ta sauko da kyar ta yi wanka ta canza kaya, ta kwanta a kan kujera a falonta tana jira. Sai sha biyu da kwata mai aikinta Sahura ta shigo, "Amarya wai ki fito in ji Maman Kausar Badi'atu ta tshi tana ganin jiri, a haka ta nufi gurin mota. Bayan motar ta samu a bude,nan ta shiga ta kwanta. Maman Kausar ta waiwayo, "A' a tashi zaune, bana son langwai Badi'atu ta ce, "Gaskya jiri nike gani ba zan iya zama ba Ta ce, "To ki sani ko mun je ba zan iya kama ki ba, gara ma kin karfafa jikinki" Ta dubi mai aikin,Sahura shigo sai’In sauke ki bakin kasuwa ki sai min nama, ki wuce gidan Anty Baby zan biyo in dauke ki Da yake asibiti ne mai zaman kansa suna zuwa suka ga likitan, anyi gwajin jini nan take dana fitsari. Ciki ne babu tantama, likitan ya bara shawarwari da kuma magungunan da ya rubuta.Suka fito a zaton Badi' atu a bi a sai magani tunda ya ce ya ba ta kudin, sai ta ga tunda suka fito Maman Kausar ta hau yin sabgarta. Sun je gidan Anty Baby sun shantake, ita ga zazzabi ga yunwa ba ta ci komai ba, don ba ta karya ba, gashi ba a sai mata magani ba, sannan suka wofintar da ita a falo tana jin irin zagin da suke yi mata, wai don tana da ciki ta lankwashe sai shagwaba take yi.Na ce, to da 'ya ya gidan ba haihuwar fari ba ce bare a ce za a yi na marmari. Shima ya shigo da rawar kai tun jiya, wai a kai ta asibiti, nace bai dai wuce ciki ba, don haka ba kanta farau ba, na yi bala"in taka masa birki" Tana jin Anty Baby din tana fadin, "Kin kyauta, gara dai ki rike ajinki, kuma ba a raina kishiya komai kankantarta, bugu da Kari kina da daurin gindi a gurin uwar mijinki" Suka kuma sa dariya, maman Kausar din ta ce, Tabdi! To ba ita ba ko shi sai Hajiya ta Saba mishi a kaina bare wata ita Sun jima dai suna zantukansu kafun ta ji tace. "Ga cikon kudin kayan nan Ta kawo wasu, "Wannan ma da cewa ya yi mu sai magani amma ba 'zan siya ba, takardar zan kai mishi" Badi'atu ta ce, "Lallai na shigo matsala".Ta mike ta je kofar, Tace Maman Kausar don Allah kizo mu tafi, yunwa nike ji kuma kin dai ji likita ya ce in sha magani Ta fito fuska a daure, "Ki je ki tari abin hawa in kin matsu, ni sai sun gama girkinsu naCi Zan tafi Badi"atu ta mike ta dauki jakarta a tsakar gida ta tambayi Sahura mai aikin Maman Kausar, sunan inda za ta ce a sauke ta. Ta fada mata don haka ta wuce abinta. Ba ta sha wahala ba ta je gida, tana shiga wayarta tana ringin ta ciro, mijin nasu ne ta yi zaton zai ji ya jikin ko sun dawo, ko dai wani abu makamancin haka,amma sai ta ji ya rufe ta da fada, wai kan me za ta taho don sun biya gidan yayarta? Badi'atu ta rasa me za ta ce; sai kawai ta saki kuka. Ya ce,To mene ne na kuka daga magana?" Badi'atu cikin kuka ta ce,Gaskiya ni ban san ya ku ke so da ni ba, Ta kai ni ta aje ga ciwo likita ya ce in ci abinci in sha magani, sai kuma mu je mu zauna kuma bayan ina jinsu suna ta yi da ni Ya Ce, "To yanzun-kin ci abincin?"Ta Ce, "Tea na sha kuma fa ba a sai maganin ba".Yace,Ta fada min kudin sun kare, inna dawo zan sai maganin, don Allah ki ke karfafa jikinki ciki ba ke ce farau ba"Cikin jin haushi tace,Ai ko a gurina sabon abu ne tunda ban.taba yinshi, ba?"Ta kashe wayar ta kwanta tana ci gaba da kuka. Wani sashe na zuciyarta tana fadin, tun yanzu zan soma ganin sakamakon kin bin shawarar iyayena? Na shiga uku ni Badi'atu!" Sai ko da ya dawo da yamma sannan ya amshi takardar maganin ya je ya siyo, lokacin tana kwance kan abin sallah tunda ta rarrafa ta yi sallar la 'asar ba ta iya tashi ba. Ya ce, "Sannu, ya jiki?" Ba tare da ta dago ba ta ce,Umhum" Ya ce,Bari in siyo miki maganin Ta dago kai, 'Don Allah ka zo min da abin da zan ci, yunwa nike ji"• Ya ce, "A'a ga abinci ba za ki girka ba?"Ta ce,Dubi mana yanda jikina ya yi laushi, ba zan iya aikin komai ba"Ya ce, "To ni zan yi miki girkin kenan? Kin san dai ba zan sa Maman Kausar ba, tunda kowa da gurinsa Badi'atu ta ce,Ni ban ce ka sa ta ko kamin girki ba, in ba zaka samo min ba ka barshi"Ta soma kuka,Ni kawai ma ka kai ni gidanmu" Jin haka sai ya ce,To kiyi shiru, ina zuwa Ya fice da sauri. ya kawo mata sakwara da nama da kuma magani, ta ci ta koshi ta sha magani. Ya [8/23, 15:41] Ummi Tandama😇: 📚4️⃣ Page 3 Ya dauki take away din ya fita da shi kar maman Kausar ta gani. Badi'atu ranar ba ta yi bacci ba tana tunanin lallai ta fado cikin matsala. Ba dai har za ta soma karbar hukuncin kin yarda ba abin da iyayenta suka so ba, domin ita ta soma yin da ta sani tun yanzun,. Wa za ta tunkara da matsalarta? Salma ta sauka a kofar gidansu ta ciro dari biyu ta ba dan acaba ya ba ta canji, jan akwatin tayi ta nufì cikin gida. Lokacin karfe tara sauran yan mintuna, Inna ta shiga bandaki ta ji karar jan akwatin. Da sauri ta fito don ta ji ko karar menene. daidai lokacin Salma ta saki akwatin a tsakar gidan ta nufì daki da son kuka. Cikin sauri da faduwar gaba Inna ta aje buta ta bi Salma daki tana fadin, "Lafiya! Bikin ne ki ka zo tun yau? Ta saki zancen ganin Salma tana kuka. Ta kunna makunnar wutar dakin haske ya gauraye dakin. Inna ta kalli fuskar Salma a razane ta ce, "Hatsarin mota ku ka yi?"Salma cikin kuka ta ce,Shatima ne ya doke ni" maganar yasa Jikin Inna ya dauki rawa,Duka kuma wane iri? Me ki ka yi masa haka?" Salma ta ce,Wai kawai don nace sai ya sake ni, shine ya yi min duka" Inna ta fusata cikin bacin rai ta ce,Tashi ki koma dakinki ba ni da masaukinki. Tuntuni baki san ba ya sonki ba sai yau?"Salma ta ce,Inna..Ta katse ta, "Tashi da Allah ki fice min a nan, in ma ba za ki koma dakinki ba, to ki nemi gidan wata uwar duk irin karamcin da wannan yaron yake mana ba don son naki yake mana ba? Shekaran jiyan nan ya turo wa Yayanku Auwal kudin sadaki na auran nan nashi. Hayarmu kwanan nan ya biya da guntu-guntu saboda hidima da ta masa yawa, amma wai ki bude baki ki ce ya sake ki saboda gata da ya miki yawa? Ai dukan da ya miki ya yi kadan tunda ya bari ki ka iya fitowa da Kafarki, da karya ki ya yi sai ya fi burgeni Haushi ya sa Inna ta kai ma Salma dundu Itare da fadin,Fice min Salma ta tashi ta dauki jakar tana sabon kuka, har ta gota akwatinta Inna ta ce, "Dawo ki dauki kayanki, wane shegen ne za ki bar maWa?"Salma ta jakar tana rusa kuka kamar wadda aka yi wa mutuwa. Inna tana biye da ita tana fadin,Je ki duk inda za ki?' Don ta ji Salma na fadin, "Ni ba zan koma can gidan ba" . Tana fita Inna ta sa sakata. Salma ta fi minti bakwai tana kuka a kofar gidansu, har sai da ta ji idanunta suna radadi,sannan ta fara tunanin zuwa gidan Yaya Hadiza.Ta tare mashin ya dauki kayan ta hau. Har ya yi kwanar gidan yaya Hadiza sai kuma ta kalli layin su Hajiya Kaka, ta ce da mai mashin ya juya ya shiga layinsu Hajiya Kaka. Har sun kulle gidan ta yi ta bugawa, Salihu matashin da ke gidan dan dan uwan Hajiya kaka ne, tuni yake gidan zaune yana karatu. Shine ya fito ya bude kofar. Ganin Salma ya cika da mamaki, yana fadin, "Anty lafiya na ganki haka?" Ta ce,' "Salihu dauki mu je ciki. Kaka ta yi bacci ne?"Ya ce,Ba ta yi ba, don yanzun na kai mata manzafi da ta sa na siyo mata Ya dauki akwatin yana fadin, "Anty kunyi hadari ne?"Salma ta ce,Humm" Maryama tana shafa ma kaka man zafi suka ji sallamar Salihu, tare suka amsa, ya shigo da akwatin hannunsa. Kafin su ce ta wane ne, Salma ta shigo. Duk da kallo suka bi ta, ta zauna a bakin gado. Hajiya Kaka ta ce, "Kamar Salamatu nike gani fuska kumbure, ko dai idona ne Maryama ta ce, Ita ce, ko hatsari ku kayi?»Salma ta soma kuka tare da fadin, "Ba hatsari. ba ne, Shatima ne yayi min haka". "Shatima?" Kaka ta nanata cikin mamaki. Salma ta ce,Dukana ya yi, kuma na je gida Innarmu ta koro ni".Hajiya Kaka tace, "Maryama tashi ki debo mata ruwan dumi ta shiga bandaki ta dan gasa fuskar tata. Salihu kai kuma zo ga dari biyu canjin da ka kawo min yanzun ka siyo mata maganin ciwon jiki"Ya ce,TO" . Ya fita yana tambayar kansa dalilin da Shatima ya yi wanna danyen aikin. Bayan ta dan dumama fuska, Maryama ta hado mata shayi ta sha, sannan ta sha magani.Kaka ta ce, "Kwanta, za mu yi magana da safe"Shatima ranshi ya baci karshe, ya shiga dakin Aliya ta ganshi tamkar an jeho shi. Ta dube shi,Yanzun ka shigo?" Ya ce,Je ki kwaso min jakata a kofar yarinyar can Salma yake nufi ta sani, kuma tunda ta ganshi rai bace, to lallai wani abu ya afku. Ta kwaso kayan idanunta na kan falon Salma wanda yake a hargitse. Ta dawo dakin ta ci gaba da ririta shi, aka kai ruwan wanka, aka hada abinci, har ta samu ya sauko amma har yanzu bai ce mata komai game da Salma ba. Ga shi tana son jin abin da ya faru. Ya dauki Abulkhairi ya fita ya nufi grin Amna, ya je ya duba su sannan ya dawo.Ta ce,Na ga falon Salma a hargitse,lafiya dai ko?"Ya ce, "Kila tana kwalema ne". Sha dayan dare da mintuna Shatima harya yi shirin kwanciya duk iyaka kokarinshi na son share Salma ya kasa, domin ya ga jinin bakinta a hanninshi. Ya aje turaren da yake fesawa na bacci, ya nufi fita. Aliya dake kwance a kan gado ta dago ta dube shi. Fita za ka yi baban Abulkhair?Ya ce, "Yanzun zan dawo" Tana jin fitarshi ta taho sadaf! Sadaf!! Taleka ta windo, sashen Salma ya nufa. Kamar ta fita ta bi shi, amma tana tsoron kada ta fita shi kuma ya juyo. Dole ta daure ta ci gaba da tsayuwa a gurin. Yana shiga ba ta falon, ya shiga [8/23, 15:57] Ummi Tandama😇: 📚4️⃣ Page 4 Tana jin Titarshi ta taho sadaf! Sadaf!! Ta leka ta windo, sashen Salma ya nufa. Tamkar ta fita ta bi shi, amma tana tsoron kada ta fita shi kuma ya juyo. Dole ta daure taci gaba da tsayuwa a gurin. Yana shiga ba ta falon, ya shiga dakin ta bata,nan karshe dai ya duba ko'ina amma ba ta babu dalilinta, cikin sauri ya fito ya nufi gurin maigadi. Ya ce, "Baba, Salma ta fita ne?"Ya ce, "Gaskiya ban ga fitar kowa ba Shatima cikin mamaki ya sake shiga ya duba ko'ina, sai lokacin ya lura babu akwatin daya ga ta dauko, kuma babu jakar hannunta. Ya fito ya nufi dakin Aliya, cikin sauri ta juya da gudu ta koma gurin danta da yake ta kuka, amma saboda leken gulma ta kasa zuwa gurinsa. Ya dauki wayarsa a caji ya zauna a falo layin yayan Salma Auwal ya kira, suka gaisa, yaCE, "Ka yi hakuri na kira ka da daddare Auwal ya ce,Ai daren ma bai yi ba". Shatima ya ce,Salma ta zo?" Auwal ya ce, Yanzun nan na zo na samu gida a rufe, na zo Inna ke fada min zuwanta tun dazu, amma dai ta kore ta. Ina zaton tana hanyar dawowa Shatima ya ce,ya yi mata kyau" Auwal ya ce, "Ai na so in same ta, da sai na mata dukan tsiya, don Allah ka yi hakuri" Shatima ya ce, Sai da safe ka ce, ina gaida Inna Aliya ta yi murmushi, "An kai ga yaji kenan, bari ya zo mu ji, ai sai naji kan zancen Shatima ya kasa shiga daki, ya zauna zaman jiran dawowar Salma. Har ya soma gyangyada karfe dayan dare ta buga, Shatima ya tsorata kar dai yarinyar nan ta fada mugun hannu garin rashin jinta. Aliya ta fito ta same shi yana kai-kawo. Tace Wai lafiya?"Ya ce, "Salma ce wallahi, ta kama ta tafi Zaria da daren nan". Aliya ta ce, "To ba sai ka yi kwanciyarka ba? Ai na san tuni ta je"Ya ce, "Na kira an ce ta taho"Aliya ta zaro ido, "To ita me ya kai ta Zaria da daren nan? Yarinyar nan kuwa ba ta da aljanu?"Shatima ya ce, "Nima na soma tunanin haka, tunda na zo na ga ta shirge kaya guri guda a falo. Yanzu ko ina kuma ta yi? Oho!"Aliya ta ce, "Allah ya sa ba aljanun ba ne suka yi wani gurin da ita. Sai dai kuma in dai sune ba za su bari wani ya cutar da ita ba" Shatima ya kalli Aliya da son jin karin bayani . Aliya ta ce,Za su tsare ta, ai suna haka" Shatima ya ce, In ko haka ne na cutar da ita, don na dake ta Dariya ta so kwace wa Aliya, ta yi saurin maida dariyar hamma, sannan ta ce,« Amma ba ka kyauta ba Ta kama shi, "Mu je ciki ka dan kwanta, insha Allah tana cikin kulawa. Kuma Allah ya bata lafiya'Dalilin jimawar da ya yi a daren ya sa yana yin sallar asubahi bacci mai nauyi ya yi awon gaba da shi.Karfe shida daidai Hajiya Kaka ta ce da Maryama ta kira mata Hajiyan Shatima a waya.Hajiyar tana lazimi kiran ya shigo, cikin sauri ta dauka tana fadin, "Ba dai ba ce da jikin?" Sai ko ga Hajiya Kaka, da sauri ta daga "'a Maryama ta gaida ta, sannan ta mika ma Hajiya Abu Kaka. Suka gaisa, sannan ta ce, "Ina son ku zo ke da mijinki da safen nan" Hajiya ta ce,Lafiya, ba dai jikin ba?" Kaka tace, Ba jiki ba ne, in kun zo za kuji' Bakwai da mintuna Alhaji suka shigo. Sun samu su Hajiyan a falo tana sauraron radiyo. Sun zauna duk sun gaida ta cikin girmamawa, sannan ta ce, "Maryama turo min Salamatu' Ta ce, "To"Su dai sun yi shiru suna son su ji me yake faruwa? Salma ta fito ta zo ta durkusa gabansu sannan ta gaida su. Suka amsa duk da Hajiyan Shatima can Kasan makoshi ta amsa. Hajiya ta ce,Salma, dago kanki" Ta dago, Kaka ta ce, Ku kalli fuskar yarinyar nan'A lhaji cikin sauri ya ce, "Subhanallah! Me ya same ta haka?"Kaka ta ce,Shatima ne wai ya ware Karfi babu ko kunya ya daki 'yar wannan yarinyar, har ya kai ga mata wannan raunin. Su kuma iyayenta da yake mutanen da ne sai suka kora ta wai ta koma gidansa da dare fa jiya ta zo nan kusan goma. Ai ni na ga shirmensu, ai ba a haka sam. Mazan yanzun ne za su koro min *ya sannan nima in kora ta, bare ta zo da wannan fuska suntum"Alhaji cikin takaici yace, "To shi Shatima shaye-shaye ya fara da zai mata wannan duka babu wani dalili?" Kaka ta ce,Ai ko da dalili dukan mace, ba tsarin tarbiyyar gidan nan ba ce. Amma bansan bangaren Hajiyarsa ba Hajiya ta ce, "A'a, mu ma dai kaf din mazan gidanmu ba dai a ce wani ya daki matarsa ba. Amma an binciki dalili kuwa?"Kaka ta ce,Ban bincika ba, yanzu dai sai ku bincika ku tunda iyayensa ne Alhaji ya dubi Salma,Me ya hada ku?"Salma cikin zubar hawaye, ta ce,Shi ne yake ta fada wa mutane wai ba ya sona. Ni kuma na ce kawai ya sake ni tunda ba ya sona, shi ne ya kama ni da duka, ya mare ni har a baki"Alhaji yace,Wannan zance haka ne babu karya a cikinsa Hajiya ta ce, "Ni kuma zan so a ji ta bakinsa tukunna, domin ko don haka aka yi alkali' Alhaji ya ce, "Ai in ba ki manta ba ya taba fadi a gabanmu cewa taimakon yarinyar nan yayi, ba sonta yake ba. Ni ma ban ga laifinta ba don ta ce ya sake ta"Hajiya ta ce, **Aikin asiri ne, kuma in ya karye dole a ga ba daidai ba. Ai gara ma ya saketa, ni na fi son hakan ma'Kaka ta ce, Da kanki Hajiya Amina ki ke wannan maganar? Da kanki?" Hajiya ta ce,To gani na yi ita ma ta nemi sakin ko?" Kaka ta ce,Amma dai kin san wannan maganar bata dace ga maida ita a wani guri ba ko? Ina miki kashedi ku ne dai iyayensu mu namu shawara ce, amma game da zancen wannan yarinya ina son kai Alhaji ka kira Shatima yazo,dalilin wannan duka nike son sani. Daga baya ayi sauran zance, kuma sai ka dauke ta ku kai ta asibiti" Nan fa fuskar ta sace a bisa jiya da tazo suntum har da busasshen jini. Alhaji yace, "Insha Allahu zan kira shi, ke kuma tashi mu je a duba ki Hajiya tace,Kaka, Allah ya huci zuciyarki, nima zan masa fada Kaka ta ce, "Ya dai kamata"A cikin mota, Salma tana baya zaune, Hajiya tana gaba tana ta surutu, ita gara Shatima ya saki Salma, ban da ma Salmar butulu ce duk hidimar da yake musu don ya dake ta har ta wani zo kawo Kara? Alhaji ya katse ta da cewa,Hajiya Amina in ba ki yi min shiru ba gaskiya zan tsaya a nan ki sauka" Dolenta ta yi shiru don ta san Karamin aikinsane.An duba Salma, an ba ta magunguna,sannan suka maida ta gida. Har ciki Alhaji ya kai ta, ya kuma yi wa Hajiya alkawarin kiran Shatima. Ya fito wanka daidai lokacin sha daya da wani abu kiran Alhajinsa ya shigo. Ya gaida su cikin girmamawa, sannan Alhaji ya ce, "Lallai yana son ganinshi da azahar. Shatima ya ce,Dama yanzun nike shirin zuwa Zaria din Suka yi sallama akan cewa sai ya zo.Shatima ya kalli Aliya wadda ta gama shirin tafiya gurin aiki, tana jiran ya sauke ta. Ya ce,Ko dai Salma ta je gurin su Alhaji ne? ya ce wai yana nemana yanzun nan" Aliya ta ce,Ko kuma aljanun sun ingizata can ba"Ya ce,To bari in je dai in ji". Ta Ce,Kyau kafin ka kai can ka samu mai rukiyya Shatima ya ce,Ina zan samu wani mai rukiyya kuma?"Ta ce, "Munnir za kai ma bayani kan kazo zai sama maka, idan an yi mata karatu sai su fita in Allah ya taimake ta Shatima bai Ki ba, ya kira Munnir suka gaisa. Ya ce, "Abokina an samu matsala ne, jiya Salma ta taho gida. Ashe kuma aljanu ne daga baya muka gane hakan, shine zan shigo Zari' yanzun na ce ko za ka binkita mana wanda zai mata karatu kafin na shigo?"Munir yace, "Subhanallahi, Allah ya kyauta. Zan yi wa Fatima magana kaninsu yana yi domin har shagon islami yana da shi" Shatima ya ce,Yauwa, to sai na iso". Bayan tafiyar Shatima Aliya ta yi ta kwasan dariya, wai ta jona ma Salma hauka. Shatima ya samu Alhajinsu gida, bayan sun gaisa ne kafin Alhajin ya soma maganar Hajiya ta tashi ta yi dakinta. Alhaji ya dubi Shatima ya ce, "Yanzun saboda Allah abin da kayi daidai ka yi kenan? Ka ware karfi ka jibgi yarinya karama, duk ka ji mata ciwo haka sai kace hatsarin mota? Ni da naganta na yi tsammanin mota ce ta fadi da ita. Gaskiya Babana ka bani kunya, ko da wasa ban zaci haka daga gare ka ba"Shatima ya ce,Alhaji, yanda ta yi min ne ban san lokacin da na kai mata mari ba. Sai daga baya ma Aliya ta ke fada min cewa, aljanu ne suke damunta. Munnir zai zo da wanda zai mata karatu"Alhaji ya ce, "Ban gane aljanu ba?" Shatima ya ce, "Zage-zage ta ke yi tun kwanaki uku da suka wuce, kuma ta hada duk kayan dakinta a falo. Alamu dai ga su nan". Alhaji ya ce,tana can gidan Kaka". Shatima ya ce, to bari su je su tafi da mai karatun. Alhaji ya yi masa fada sosai tare da gargadin kar ya kuma jin haka.Hajiya tana jiran ya same ta a nata dakin ne ta bayyanar masa da nata ra'ayin, sai kawai ta ji tashin motarsa, Yana daukan su Munnir din ya ji wayarsa na ruri, Hajiya ce take kira. Ya daga, Tace, "Waton ban isa ka shigo gurina mu gaisa ba ko? Yace Ba haka ba ne, yanzun zan dawo, Munnir suna jirana ne"Salma tana bacci lokacin da suka shiga, Hajiya Kaka ta yi gum da fuska tamkar ba ta taba dariya ba. Hakan ya tabbatar ma Shatima lallai tayi matukar fushi. A ciki ta amsa gaisuwar tasu,Shatima ya soma yi mata bayani,ya nuna Khamis mai rukiya, Malami ne zai yi wa Salma karatu" Kaka ta dube shi, "Karatu? Aljani ne a kanta?"Shatima ya ce, "E Kaka, aljanu ne". Ta ce, "Lallai kuwa, ka kai karshe a rashin son yarinyar nan tunda har hauka kake son dora mata Malamin yace,Hajiya, aljanu ai ba hauka bane, cire.Ta daga mishi hannu, "Dakata kai yaro,kai ne mai karatun?" Ya ce, "Ni ne".Hajiya ta ce, "Tashi ka je abinka, ba ta da koma• Ta kalli Shatima,Ka ba ta takardarta Shatima ya dubi Hajiya,Ban gane in bata takardarta ba?"Hajiya ta ce, "To, tashi ka je ubanka zai maka bayani yanda za ka gane".Munnir ya ce, "Hajiya, a yi haQuri da kin bari an fara yi mata karatun tukunna" Hajiya ta ce Muniru ya fada maka abin da ya faru?"Munnir ya ce, "Ba mu yi cikakken bayaniba" Ta Ce, «To shi kenan ku je ya yi maka bayani kawai"Munnir ya ce,Ina Salmar ta ke?"'Hajiya ta ce, "Alhaji nasa ya zo ya kai ta asibiti sun mata allura tana bacci. Dukan daya [8/23, 16:06] Ummi Tandama😇: 📚4️⃣ Page 5 Mata na zalunci tunda iyayenta sun kasa daukar mataki, ni zan dauka Munnir zai sake magana, Kaka ta ce, "KuJe kawal Shatima ya ce, "Hajiya amma ta fada miki gà abin da ta yi?Hajiya Kaka ta ce, "Na ce dai ku wuce, bana bukatar sake ganinka in har ba takardar sakin Salma ka kawo min ba Cikin fushi Shatima ya ce,Ku tashi muJe Kiran da Hajiyanshi ke masa ya sa suka yi sallama da su Munnir, ya dauki dubu daya ya ba mai rukiyya. Yana shiga falo ya samu Hajiya tana zaune ta sake kiranshi. Ya shiga wayarshi tana ringin, ya ce,Hajiya ga ni na shigo Ranta a bace, ta ce,In nice uwar da ta haife ka ban yarda ka maida Salma ba Ya kasa zama yayi tsaye yana kallonta Ta ce,Ka tsare ni da ido, da ma ni na gaji da zamanta da kai tunda kai ma ba wai kana sonta ba ne, ka sake ta mana. Ni na taba jin wannan masifar?Zai yi magana ta ce,Yimin shiru,umarni na ba ka Ya lumshe ido, a zuciyarshi yana nanata innalillahi, sai da ya kai aya sannan ya ce,To zan iya tafiya?"Tace "'In ka so, amma ka tabbatar ka cika umarnina Bai amsa ba ya wuce Hadiza ta shiga gidan Inna don amsa kiran Inna. Suna gaisawa Innar ta sanar da ita a kan zuwan Salma a daren jiya. Hadiza ta ce, "Kash Inna, da ba ki kore ta ba kin ji dalilin zuwan nata Inna ta ce,Ai ta ce sakinta ta ce ya yi Hadiza ta ce,Duk da haka Inna, in babu dalili ta ce a sake ta? inna ta Ce,Ina tsoron kada a ce yar mace Hadiza ta ce, "To kin ce jiya sha biyu saura mijin ya kira Auwal?" Inna ta Ce, yana nan muna maganar ya kira shi. Shine yanzun nike son ki kira min shi Auwal din Hadiza ta ce, "Bari dai in kira ita Salma Kira ya fi goma ba ta daga ba tana bacci. Hadiza ta ce,Inna ba fa ta daga ba. Allah dai yasa lafiya inna ta Ce,To amin dai. Ki Kira shi yayan naku Hadiza ta kira shi ta sanar da shi sakon Inna. Ya kira Shatima suka gaisa, ya tambaya ko Salma ta dawo? Shatima ya ce, "Tana can gidan kakarmu a nan unguwar taku, Ni ma yanzun nike shirin dawowa daga Zaria zuwa Kaduna Auwal ya ce, "To a yi dai hakuri Bayan sun yi sallama Auwal ya kira Hadiza ya fada mata, Hadiza ta fada ma Inna yanda suka yi Inna ta ce, "'To Hadiza zuwa za kiyi ki je Kiji a can gidan Hajiya Kakar Hadiza ta Ce. "A a Inna, sai yamma ZanJe insha Allahu Biyar saura Hadiza ta isa gidan Hajiya Kaka, ta samu Salma tana zaune tana cin tuwon shinkata, suka gaisa da Kaka. Kaka ta rufe Hadiza da fada sai ka ce ita ce ta koro Salma, ta ce,Don hauka sai yarinyar ta zo da kukanta, amma a kore ta? To yanzun Ita ce ta aiko ki duba ta?"Hadiza ta ce, "Ita ta turo ni, ko bacci ta Kasayi Hajiya Kaka ta ce, "Da gangan ta kasa baccin al, tunda ta kore ta da ta fada hannun Mugu da ta kasa baccin da nujja Hadiza dai ta yi ta ba wa Kaka hakuri, sannan suka dore da hirarsu, inda Kaka ke ba Hadiza labarin abin da ya faru, da kuma matakin da ta dauka. Hadiza ta ce, "Amma da ba a yi haka ba Kaka, ai gara dai a sasanta" Kaka ta ce,To ke ma bana son zuwanki in dai ba za a zuba min ido ba" Hadiza ta yi ta ba Kaka hakuri. Salma kuwa ta kasa gane yanayin da ta ke ciki game da matakin da Kaka take shirin dauka. Amma ta san dari bisa dari tana bayanta, domin zama da wanda ba ya sonka bai ma taso ba. Shatima dai abubuwa sun dame masa, har ma ya rasa matakin da ya kamata ya dauka. Kaduna ta ishe shi, ta fita ransa, don haka a daddafe ya sake kwana dakin Amna ya kwana dama ita ba ta ma san ana wani bidirin tafiyar Salma ba, ita dai ta tashi da fushin ambatonta da Nafisa da ya yi a daren jiya da zai ce ta kawo masa caja ya jona waya. Tun daren yake lallashinta da cewa mantuwa ce,da kuma kasantuwar zamansa da Nafisar a Abuja, duk da haka bata yarda da zancen nashi ba, don haka da safe shine ya yi wa kansa komai har ya hada kayansa tana kwance. Ya ce, To ni na yi shiri zan tafi"Ta ce,Don ka kosa ka tafi gurin wadda ka ke so shi ya sa, amma ai ba da safe ka ke tafiya ba Ya ce, "To ina da uzuri a can Ta ce, "Ni dai na kusan gajiya Shatima ya ce,To in kin gaji din sai ki fada min, na daina damun kaina a kan kowace yarinya a gidan nan, duk wadda ba za ta zauna da ni ba, ga hanya nan Shatima ya sauka Abuja cike da damuwa. Bai samu Nafisa a gida ba, hakan ya ba shi haushi kasancewar ba ta fada masa za ta fita ba,- ta san kuma ba ya son hakan. Nan zuciyarsa ta fada masa cewa, Nafisa na fita ba tare da izininshi ba. Ya yi kamar ya kira wayarta, amma sai ya fasa, yana son ya ga tsawon lokacin da zata dauka. Dakinshi ya shiga ya kwanta yana nazarin rayuwar shi yana son sanin ainahin abin da ya yima Salma, Gaskiya tun farko ya yi kuskure da bai saurari dalilin da Salma ta nemi saki ba,amma kuma ai ita ce ta zo da raini. Wata zuciya ta fada mishi haka. A fili ya ce, kuma na [8/23, 19:32] Ummi Tandama😇: 📚4️⃣ Page 6 Biye mata. Ta je ta yi ta zama, amma fa ba zan sake ta ba, lokaci bai yi ba"Ya kai awa biyu kafin ya ji shigowar Nafisa, don hauka gidan a bude ta barshi, karar talabijin da ta ji daga dakinshi shine ya sa ta nufi dakin cikin sauri. Gabanta ya fadi da ganinshi kwance, duk da tana cikin damuwa kuma ta kosa ya dawo don a yi wadda za a yi,amma sai da ta tsorata da ganinshi. Ta ce, "Au ka iso kenan?"Ya ce, "Ina ki ka je?"Gabanta ya fadi ganin yanda ya murtuke fuska, amma da ta tuna inda ta je cikin gadara da son ya san tasan yana neman wata ta ce, "Gidan su Zinatu na je"Ya dube ta da sauri,Wace ce kuma Zinatu? Mene ne alakarku da har za ki je gurinta ki kwashe sama da awa biyu ba tare da izinina ba? Kuma ki bar min gida a bude?" Nafisa ta ce, "Ai gani na yi don na je gurin Zinatu ai kara na maka, kodayake na fada mata cewa, mu hudu ne duk da ta ce ka mata alkawarin sakin daya daga cikinmu don ka maye gurbi da ita. Sai dai ina neman alfarma a sake ni, don bana son a jona ni da cutar zamani Kan Shatima ya kulle, sam bai fahimci me Nafisa ke son fada mishi ba, illa dai ya fi tunanin borin kunya take son yi "Zan fi son ki fada min gaskiya fiye da wannan borin kunyar. Abin da kawai nike son sani, inda ki ka je"Murmushi tayi Ta ce,Baban Ashraf kenan, ban ce kana borin kunya ba sai ni? To bari dai in fito maka baro-baro gurin karuwarka na je Zinatu!" Shatima ya daga hannu zai tsinke Nafisa da mari, sai muryar Hajiya Kaka ta zo masa," Wannan ba dabi,ar gidanmu ba ce! ba a dukan mace!'Ya kankame hannunshi tam jikinshi har Bari yake yi, ya sa kai zai fita yana jin tana fadin,"'Da ka da ke ni, Allah da ka daki auranka"Shatima ya fada mota a fusace, ya fige ta tamkar zai tashi sama, amma sai motar ta mutu kafin ya kai bakin get, ya san cewa batir din yayi-sanyi tunda ba da ita ya je Kaduna ba, kuma ga -shi yanayin sanyi ake ciki. Ya fito ya bar motar nan ya fita ba tare da ya san ina za shi ba.Yayi tafia mai nisa kafin ya zauna bakin wani masallaci; munane suna ta alwala. Shi ma ya yi, sannan ya bi sahun sallar. Yana zaune bayan an idar, tunani yake yi, wai su mata har abada suna da lissafi kuwa? Ko dai sun hada baki ne don su tozarta shi su uku? Shi ya sa yana son Aliya, yana kuma girmama lamarinta, ita ce har zuwa yau daga auransu ba za ya tuna wani abu da ta yi masa wanda zai Bata masa rai Abin da zai fi kawai gara ya hada su su ukun ya sake su, inyaso ya yi zamansa da Aliya. Wace ce Zinatu? Wai kuma karuwarsa? Nafisa tana hauka ne ta ke danganta shi da wannan laifin? Yana da mata har hudu me zai burge shi da wata matar waje? To ko Salma ita ma ta ji wannan zancen ne? Haka ya yi ta tufka da warwara har aka kira la 'asar ya yi. Ya jima yana addu'o'insa, sannan ya ji zuciyarshi ta dan yi sanyi. Lallai lamarin mata sai addu'a, amma ya daina saka kanshi cikin damuwa, duk wadda ta gaji to zata iya tafiya gidansu. Abin da ya faru, Nafisa tunda ta ji labarin Zinatu shi ke nan ta shiga bin diddigi har sai data gano gidan su Zinatu, wanda yake a cikin layin. Zinatu da yayarta duk suna zaman kansu ne, Nafisa ta kama hanya ta nufi gidan nasu wai za ta yi wa Zinatu kashedi duk kuwa da shawarar da Maman Nana ta bata na cewa, kar ta je. Ta samu Zinatu tana cin taliyar indomi, Nafisa tana ganinta ta gane cewa ita ce Zinatu, saboda surarta da ake bada labari. Nafisa ta ce,Ke ce Zinatu ko?"Zinatu ta ce, "Nice,ke ce Maman Ashraf?"- Nafiza ta zaro ido, Zinatu ta ce,Kina mamakin yanda aka yi na sanki ne?"Ta nuna mata kujera, "Zauna mu yi magana, kin san an ce shirin zaune ya fi na tsaye Nafisa ta ce, "Ban zo zama ba, zuwa na yi in ja kunnenki ki fita hanyar mijina" Zinatu ta Ce,Tofa! Ki ce da babbar magana ki ka zo. To amma kin makara tunda har ki ka bari na soma sonsa, sannan shi ne yafi dacewa da ki ja masa kunne, don shine ya gani ya taya".Ta mike tsaye tana juyi gaban Nafisar,Kalle ni sosai, ba ni da makusa. Ki bari in auri kyakkyawan mijinki, ina sonsa da yawa".Nafisa ta ce,Ki aure shi ta ina? Ai mu hudu ne a gurinsa, kin ga kenan ba ki da sauran gurin shiga tunda mu din musulmi ne" Zinatu ta boye mamakinta, wai su hudu ne, ko dai ta ce haka ne don ta sa ta rabu da shi?Ta dubi Natsa,Ya yi min alkawarin sakin daya don ya maye gurbi da ni. Zai fi kyau ki rage kishi don kishi da ni babu dadì. Duk gidan da na shiga nice mandiya, kin san Mandiya?" Bata jira amsa ba, ta ce, "Ina nufin isasshiya"Nafisa ta ce,Insha Allah ba za ki shigo cikinmu ba, ki je can ki nemi watsattsu irinki"Zinatu ta yi dariya In kin je ki tambayi mijinki sau nawa muka watse da shi? Sannan ki fita, ina da 'yan daba, waya kawai zan musu sai sun yaga ki"Nafisa ta ce, "Insha Allahu mijina ya fi karfinki". Ta fice da sauri ganin Zinatu tana danna waya.Tana jiyo dariyar Zinatun tana fadin,Karamar kwaruwa".*Shine tana zuwa ta amu Shatiman ya zo. Bayan sun yi wannan sa'insar ya fita, ta ce, "Aiko na rantse ba zan ji wannan bakin cikin ni daya ba, dole sai na fada ma sauran matanshi nima, kowacce ta dandana Ta soma laluben layin Aliya tana fadin, "Kila ma don ita ne ya dawo da safen nan, harni zai wa alaye wai bai sonta?"Aliya ta daga cikin sauri da mamakin kiran Nafisa gare ta, domin ba ta kiranta a waya, ba ta yi zaton Nafisar tana da lambarta ba. Suka gaisa à takaice, Nafisa ta ce, "Maman Abulkhairi [8/23, 19:43] Ummi Tandama😇: 📚4️⃣ Page 7 Dama kiranki na yi in fada miki cewa Baban Ashraf yana neman, wata yarinya a nan kuma na rasa ko neman me yake mata tunda mu hudu gare shi, kuma da na taka na je gidan su yarinyar har tana min ikirarin suna lalata da shi, yanzun ma zai saki wata cikinmu ya aure ta"Duk zantukan da Nafisa ke yi ban da innalillahi babu abin da Aliya ke fadi. Duk ta rikice kafafunta sun hau rawa, Nafisa dai ta kashe wayarta tana fadin, "Ai gara kowa ta ji abin da na ji"Ta kira layin Amna. Ita ce ma sai a kira na uku sannan ta daga, Nafisa ta ce, "Maman Jafar nice maman Ashraf"* Amna ta ce, "Ok, a dayan wayana ne nike da laynki, ya ku ke?"Nafisa ta ce, "To lafiya, amma ba lau ba. Mijinmu dai ya kama neman mata, dazu don in tabbatar na tafi gidan su yarinyar muka yi zage-zage, kuma ya mata alkawarin sakin dayanmu ya aure ta. Ban da haka ma ta tabbatar min suna fita. Don haka na ce bari in sanar da ku don kowa ya sani, na kuma fada masa ni zai saki in ya tashi,domin ba zan zauna ya zo ya sa min ciwo ba" Amna ta yi shiru cikin mamaki, sai dai tana ganin kamar a dai kara bincike. A gaskiya 'za ta iya yarda da wani abin, amma ban da neman mata domin sun zauna da Shatima a wata duniya in da ba su da mai kwa6a musu da sunan karatu, amma Shatima bai taba ko da rike hannunta ba sai da ta zama matarsa. Kuma lokacin ta lura sosai bai nemi wasu ba ma. Nafisa ta katse mata tunani da cewa, "Kinyi shiru Maman Jafar" Amna ta Ce, "Ina shakka ne, amma mutum yana iya canzawa daga yanda ka san shi" Nafisa ta ce, Ai ki cire shakka Amna ta ce, "'To yanzu mene ne abin yi?" Nafisa ta ce, "Kowa ta nema wa kanta mafita, ni dai ba zan zauna ba Amna ta ce,Ke ta gaban goshi kin fadi haka bare mu? Allah ya kyauta Nafisa taCe,Kaji dai Maman Jafar, ni ce ta gaban goshi ko Aliya? Ni dai sai anjima" Har lokacin Amna ba ta gaskata Nafisa ba. Sai dai tana fita don tafiya shagonta Aliya ta tsaida motarta a kusa da gate, take tambayar ko Nafisa ta fada mata zancen mijinsu? Amna ta ce, ta ji, Aliya ta ce,Me ki ka ga za mu yi?" Amna ta ce,To ni yanzun ba zan ce komai ba tunda ba ni da wata shaida da zan riqe"Haushi ya kama Aliya, ta ce,To bari kiji, ni na yarda domin yanzun ya yi wa Salma duka jiya, kuma ya kore ta. Kin ga kenan zai auri karuwar Amna ta kasa dauke ido daga kan fuskar Aliya kamar a nan ne za ta gano gaskiya, Aliya ta ce,Da za ki sauko a motar nan ki leka falon Salma na san za ki gaskata zancena, har kayanta ta hada" Amna ta sauka ta je ta leka falon Salma, mamakinta ya tsananta, Amna ba ta ce komai ba ta zo ta shiga motarta ta fice. Cike da murna Aliya ta shige daki tare da fadin, "Ai gara ku tarwatse, Salma tana can, ke ma ki tafi, Nafisa ta dawo Zaria. Wai ai tuni zan watsar da aikin nan in koma Abujan in ma da karuwar ne mu fafata, ita ma aijeho ta daga gare shi mu sha zamanmu" Ta yi rawa da juyi cikin murna. Shatima ya zo daidai layinsu sai ya tuna da motarsa da ya barta a kusa da gate, don haka ya juya neman masu batir. Abuja ba gari ne da zaka samu abin da ka ke so a ko'ina ba, don haka ya nufi inda ya san zai samu. Sai da ya hau tasi sannan ya dauko mai batir. Ya shiga falon ba kowa sai dai ya jiyo maganar yaranshi a dakin Mamansu. Ya nufi dakinsa ya dauko kudi ya sallami mai batir, ya mika ma mai tasi nashi kudin, ya ce ya maida mai batir sannan ya amshi lambar mai batir saboda in yana bukata. Ya maida motar gurin zamanta, a ranshi yana raya tuni ya kamata ya canza mota, hidimar yau da gobe sun hana. Kai tsaye ya nufi dakinshi yana kwala ma Ashraf kira. Yaran suka fito da gudu a tare, suka nufe shi. Ya daga su duka yana cewa, "Babana da babana". Su kuma suna fadin, "Oyoyo Daddy Shatima ya zuba su a tsakiyar gadonshi shima ya hau. Take ya ji duk wani kunci ya yaye daga zuciyarsa, ya yi rigingine suka haye ruwan cikinsa, ya ce, "Ban ganku ba da na dawo. Jafar da Abulkhairi sun ce in gaishe ku Ashraf ya ce,Yau ba su bada sweet a kawo mana ba?"Shatima ya ce, "Sun ba ni mana, su ma na ba su wannan biskit din da ku ka ce in kai musu"Ashraf ya ce,To Daddy dauko mana" Ya ce,Sai za ku je islamiyya zan ba ku" Wannan wata dubara ce da Shatima yake yi don cusa kaunar juna a tsakanin yaransa, yana daukar abu ya ba kowa ya ce in ji dan uwansa na wancan dakin, sannan ya yi musu hirar juna. Ashraf ya ce, "Daddy muna gidan Mama Nana muna wasa ne fa, shi ne da ka zo ba ka ganmu ba" Ya ce,Amma dai ba kwa fada ko?" Ya ce,Ba ma yin fada. Ita ko Momi tana ta kuka a gidan Mama Nana, wai za ta je gidan wata, Maman Nana tana cewa kar ki je, kar ki je Shatima ya ce, Gidan wata mata?" Ya ce;Eh, wai ko ina ne ai mu ba mu je ba ko Shahid?"Ya dubi Kaninsa, wanda ke tawasa da wayar Baban. Shahid ya ce cikin maganarshi da ba ta gama gogewa ba, "Momy ta she za mu she gidan Mama Ashraf ya amshe da cewa, "Kai ne za ka kai mu a motanka ko Dady? Ai tana hada mana kayanmu yanzun" Shatima kanshi ya sake kullewa, wai me ke faruwa ne? ya ce,Ku tashi mu kalli talabijin"Ya kuna ya kamo musu cartoon. Yana ganin sun tare hankalinsu, ya kwaso musu sweet ya ce,Ga shi in ji Jafar da Abulkhairi ina zuwa -_Ya fita bayan ya kauda wayoyinsa da laptop don kada su yi masa barna. Ya nufi dakin Nafisa. [8/23, 20:48] Ummi Tandama😇: 4️⃣📚 Page 9 Haka ta yi ta bai wa Nafisa shawarwari, har dai Nafisar ta sauko, amma duk da haka dole ta dauki mataki. Shatima kuwa yawo ya yi ta yi da yaranshi, su shiga nan su fita can. Guraren shakatawa. Lokacin sallah suka je masallaci, sannan suka je gidan cin abinci suka ci suka yi dam! Bai nufo gida ba sai sha daya lokacin yaran sun yi barci. A dakinshi ya kwantar da yaran suka kwana. Da safe ya shiga shirin tafiya aiki, ta zo ta kwashi yaran don shirya su zuwa makaranta, kamar yanda suka saba tare suka karya amma ita ba ta zauna ba. Ya fita da yaran don kai su makaranta, sannan ya wuce nashi gurin aikin. Salma ta warke sarai, sai dai tana ji tana gani aka yi bikin Auwal Inna ta ce karta ganta matsawar ba ta koma gidanta ba. Hadiza ta aiko lokacin da Hadizar ta zo karbar kudin hannun Salma da ta ce ta zo ta amsa don hidimomin na bikin. Ta ci gaba da zuwa makarantarta daga gidan Kaka, a ranar da ta cika kwana biyar da zuwa gidan. Kaka ta ce, kar ta damu, ta kwantar da hankalinta ta ga yanda za su kwashe da Shatiman. Ranar asabar ya iso Kaduna, kwana daya zai yi don ba ya son matsala. Ya ji dadin tarbar da ya samu daga Aliya tare da kwantar masa da hankali, gami kuma da lallashinsa kan kar ya damu da tuhumar da matansa suke masa. Ya shiga gurin Amna da safe, bai zaci zai samu kallon mutunci ba, amma sai ya ga sun gaisa cikin mutunci kamar yanda suka saba. Tare da shi suka fita kai Jaffar hadda. Sun dawo ta ce,Baban Jafar ina son ka fada min gaskiya, ba ka taba yi min zancen da ba gaskiya ba ne, kuma zan yarda da duk abin da ka fda min. haka kuma in ma ka aikata laifin zan iyayi maka uzuri sakamakon gaskiyarka da kuma kasancewarka sabo a cikin laifin Shatima ya kama hannun Amna ya matse cikin nashi tafin hannun, Na yi miki alkawarin cewa, zan fada miki gaskya a kan abin da na Sani Amna ta tsura mishi ido kamar mai son ta gane gaskiyarsa a cikin idanunsa, ta ce, Menene gaskiya game da yarinyar da Nafisa ta kira ni ta ce min kana nema da lalata, kuma wai ka yi alkawarin sakin daya daga cikinmu don ka maye gurbnta? Shatima ya yi rantsuwa da girman Allah, har sau uku sannan ya ce bai san komai game da maganar ba. Bai san ina maganar ta fito ba. Amna ta ce,To ni dai Nafisa ta kira ni, Aliya kuma ta sake tabbatar min da maganar har ta fada min cewa, Salma ka ke son ka saki don ka dake ta, kuma ka kore ta Shatima ya zaro ido,Aliya kuma? Ai ita da tace ba ta san wannan maganar ba Amna ta ce, "Gaskiya ta sani, don mun yi maganar da ita"Ran shatima ya baci amma zai mata magana, ya ce, "To gaskiya matsala ta da Salma daban ce, ita tuhumar da take min daban ce, bata, shafi wata ba. Rashin kunya kuma ta min na dake ta Amna taCe, To ita Nafisa ina ta ji wannan maganar? Ya kamata ku zauna ta fada maka inda ta ji don ka gano bakin zaren" Shatima ya ce; Gano bakin zaren kuwa shine zai warware wannan kullin? Amna ta ce, "Haka ne Shatima mamaki yake wai Aliya ta san da zancen nan? Me ya sa ta nuna ba ta sani ba? Me ya sa ta kafa ma Amna hujja da Salma? Gaskiya yana son ya san dalilinta. Ya samu Aliyar har kicin dinta tana shirya "abincin rana, ya ce, Aliya ashe kin san maganar nan ki ka nuna min ba ki sani ba sam-sam?"In ji wa?" Aliyar ta tabamya cikin tsananin faduwar gaba." ya ce,Amna ta fada min kin sani, harma ta fada min kin nuna mata dakin Salma tare da ba ta labarin matsalarmu, sai dai kin danganta matsalarmu da Salma a cikin wannan matsalar a kokarin gamsar da ita cewa na aikata"Aliya ta sóma kuka, "Yanzun ka yarda da abin da aka ce maka a kaina? Ina ce tsakaninmu akwai amincin da in ka ji abu za ka yarda kuma ka tantance na yi ko ban yi ba?Ta nufi falo,Yasha gabanta Ya riko ta zuwa jikinshi, *A a maganar bata kai haka ba. Ina mamaki ne musamman da yake na san Amna ba ta iya' karya ba. Ba ta da rufa-rufa sak! Take Aliye ta ce,kenan ka yarda na fada?" Ta kama kici-kici, "Mu je kawai? na tambayeta a inda na fada mata Ya ce, "*Amma dai na ce abar maganar ko?" Ya sake ta, «Tunda ke ma taurin kan za ki koya, je ki same ta" Aliya ta dawo ta ci gaba da aiki tana sharar kwalla. Shi ko Shatima wata alama ya dora yana ta auna zancen Amna da Aliya. Sam bai yi niyyar zuwa Zaria ba, haka nan ya kira Alhajinsa sun gaisa ya bada uzurin ba zai zuwa Zaria ba. Alhajin ya ce,Babu komai, ya ya batun matarka?" -Shatima ya ce,Wai Salma?"Alhaji ya ce, "Ita"Shatima ya ce,Na bari ne Hajiya Kaka ta huce sannan inje mu yi magana Alhaji ya ce, "'Shikenan"Yana hanyar komawa Abuja Hajiyarsa ta kira shi, cikin faduwar gaba Shatima ya daga. Ta Ce,Tunda ka guje ni don nace ka saki wannan annobar yarinyar shine ka dauki gaba dani?'Ya ce, "Hajiya, don Allah ki yi hakuri zan kira ki, kwana biyu aiki sun min yawa ne Ta ce,Aiki sun maka yawa ko kuwa sharrin matanka? Ina son ka sani kuma matan naka su sani zan sa kafar wando da kowaccensu.Ina sane da duk abin da ke faruwa a gidanka daga can Abujar har Kadunar, kuma ina son ka zama namiji tsayayye kamar yanda na sanka ba soko ba [8/23, 20:53] Ummi Tandama😇: 📚4️⃣ Page 8 Yana shiga ya samu ta gama shirya kaya a cikin akwatuna, ya zauna a kan kujera daidai lokacin da sako ya shigo cikin wayar da ya saka a cikin aljihunsa. Ya ciro wayar tare da fadin,Nafisa ina son ki sanar da ni ainihin abin da ke faruwa" Idanunshi suna kan fuskar wayarshi don duba kowane sako ne ya shigo cikin wayarsa. Amna ce cikin sauri ya bude yana karantawa.Baban Jafar ina son mu yi magana da kai, amma ba ta waya ba. In abin da na ji da kuma hujjar da aka kafa min da Salma haka ne, to gaskiya ka ba ni mamaki sosai. Kafin in tafi gida ina son sai mun zauna na ji wasu abubuwa daga bakinka. Har yanzun ni na yarda da kai, kuma na sani gaskiya ka ke fada min a kowane lokaci. Abu daya nike son ka tuna, iyayena mutane ne da ba su son in takura ko in shiga wani hali. Ko babu komai na je na ce musu na gaji da aurenka ka san za su tsaya min a haka. Na tuna maka ne don kasan cewa, in na saka kafa na bar gidanka da sunan na tafi, to ka sani fa na tafin kenan Shatima ya runtse ido yana fadin," Allahumma ajirni fi musibati'. Ya fita waje ya nufi harabar gidan. Nafisa ta bi shi da kallo, tare da son sanin sakon da ya samu a cikin wayarsa.Munnir ya kira, ko gaisawa bai bari sun yi ba ya shiga fadin,Ina cikin musiba Munnir. Wacce qaddara ce take bina?" Munnir yace,Me kuma ya sake faruwa?" Shatima ya ce,Ban san komai ba, bansan abin da ke faruwa ba, gabadaya matana sunA min bore, kuma ban san komai game da tuhumar da suke min ba" Munnir ya ce,To ka zauna da su ka ji kan zancen mana Shatima ya ce,Ina Abuja yanzun haka". Ya ba shi labarin komai a takaice, ya ce, "Ka taimaka min dan basiran tawa ta toshe ban san me zan yi ba. Ban fahici me kowaccensu take nufi ba Munnir ya ce, '"Kira Aliya ka ji, na san ita za ta fada maka komai" Ya ce,Kuma haka ne, don ita ba ta ce wani abu ba Yana kiran Aliya ta daga kamar dama jiransa take yi, ya ce,Aliya me ki ka sani game da abin da ake yadawa a tsakaninku?" Ta ce, Me ake yadawa?" Ya ce,Nafisa da Amna suna tuhuma ta da wani laifi ko iri daya, ko kuma kowa da nata. Haka kuma Salma ma tana tuhumata kina nufin ke ma ba ki san komai ba?" Aliya ta ce,Ni dai ban ji komai ba gaskiya"Ya ce,To ki tayani da addu'a" Tace, "Insha Allahu Suna gamawa Aliya ta sa dariya, "Ai nunawa zan yi ban san komai ba, kuma ba zan canza masa ba ko da kallon banza Shatima ya nufi ciki gurin Nafisa, da ya shiga dakin nata sai ya kulle da makulli saboda kada yaransu su fito su shigo su same su a dakin. Tana shirya wandunan yaran da singiletinsu a Karamar akwatinsu, ya je har inda take ya ce,Ke madam, bar wannan aikin ki zauna ki ba ni aron hankalinki a nan" Kamar ta share, amma sai ta cije ta ce, "Ina jinka" Ya ce,Ina son ki nutsu ki fada min duk abin da ke faruwa, don ban san komai a kai ba" Ta ce,Tunda ba ka sani ba a bar maganar Ya ce, "Haba Nafisa?" Ya sake tausasa harshensa, "Kin san dai ta hanyar tattaunawa ake warware matsala ko?" Kallonshi kawai take yi tana takaicin raina mata hankalin da yake yi. Tsaki ta ja sannan ta ce,In har kana nuna ba ka san komai ba, wannan yana nufin ba za ka amsa laifinka ba, wanda kuma amsa laifi malamai sun amince alamu ne na rabin tuba Shatima ya tsura ma Nafisa ido cikin bacin rai, ya ce,Amma sai a fada min laifin nawa in sanshi ko?"Ita ma ta dube shi a hasale,To tunda so ka ke ka maida ni jahila da ana magana ne a kan Zinatu karuwarka,wadda ku ke watsewarku da ita har ma ka yi mata alkawarin sakin dayarmu ka aure ta. Marin da ya sakar mata ne ya tilasta mata sakin wancan zancen tare da fadin,Wayyo Allah"Jikinshi har tsuma yake yi, ya ce, "Sharrin da za ki min kenan? To in don wannan zantukan da ki ka kaga min ne zaisa ki tafi ki je. Amma in kin tafi kin tafi kenan, kuma ki bar min yarana a nan babu inda za ki da su" Ya bude kofar ya fita, kaya ya canza sannan ya kwashi yaransa ya zuba a mota suka fice.Sai da Nafisa ta ci kukanta ya ishe ta,sannan ta kira Anty Maimuna tana fada mata. Anty Maimna ta ce,To yanzun ke tahowar za kiyi?"Nafisa ta ce, "Gobe zan taho gaskiya" Anty Maimuna ta ce, "*Ba ki da hankali, inkin tafi ai kin ba karuwar dama ta zo gidan ta baje kolinta, kuma ita za ta rike "ya°yanki ko da aure ko babu. Abin da nike so da ke shine, ko yaranki kada ki bari su san kuna da matsala.Haka nan fushinki ba zai kawo maslaha ba. Da ya ce ma ku zauna ku tattauna ban da yarinta da wauta irin taki ai ba za ki kwashi hayagaga ba sai ki yi masa zance cikin hikima da nuna masa illar abin da zai saka kansa kuma ya jefa ku. Ban dake ai wannan kin da ya yi ma alama ce ta ba ya son bacin ranki, mazan yanzun da suke neman mata ina ruwansu da wani boye ma iyalinsu? Kizo barikinmu ki yi kallo, wani sai ya zo da mace ya koro- matarsa waje, shi ya shiga ciki da karuwa [8/23, 20:59] Ummi Tandama😇: 📚4️⃣ Page 10 Shatima ya ce, "Hajiya zan kira ki in na sauka, ba a mota ta nike ba, haya na hau. Zamu yi maganar Tagumi Shatima ya yi yana ta mamakin wa yake kai ma Hajiyan sirrin gidanshi? Wata zuciyar ta ce, Lallai dole ya tsanana bincike, ko dai Nafisa ce tunda ga shi ita ta fada ma Amna? Ba shi da hujja don haka ya tsaya a kan zai yi bincike. A Abuja Nafisa ta ki ba shi hadin kai su fahimci juna, don haka shi ma kyale ta suka koma zama na rashin dadi, sai dai sukan yi kokarin kauce wa abin da zai sa yaransu su fahimta. Salma sun gama jarabawa kuma sun yi hutu, duk da hutun nasu na sati biyu ne, amma tana sa ran kafin karewar hutun Shatima kila yazo su warware, ko dai ta koma gidanshi, ko kuma ya kawo mata takarda.Tana kwance a falon Kaka suna ta chatting da Salma Sadik Dankasa, kullum Salma tana mita da mamakin ashe Shatima mijin Salma ne, amma shekara nawa suna tare shine ta boye mata? Salma ta ce,Zuwa yanzun ki hakura da mitar nan haka" Ta ce, ita ma yanzun an kawo gaisuwarta, Salma cikin murna ta ce, "Wa za ki aura?" Salma Dankasa ta ce, "Lawal din nan dai na gidanmu da nike ba ki labari yana sona"› Salma ta yi murna, suka ci gaba da zantukansu. Sako ya shigo wayar Salma, sai taga daga bankinta ne, don haka ta sauka daga online ta duba. Dubu dari biyar ce in dai ba kuskuren idanunta ba ne. Ta tashi zaune cikin sauri, Safwan El-Nasir ne ya turo mata. Cikin mamaki ta ce, ina ya samu account dinta, kuma kudin mene ne? sako ta rubuta ta tura mishi cewa. 'Lokaci baiyi ba da za mu ji daga juna.Har yanzun ni matar Shatima ce, don haka zan maido maka da kudinka. Ko minti uku ba ta karasa cika da tura sakon ba, sai ga amsa.Ban ba ki da wata manufa ba, ki dauka ko kina gidan Shatima zan iya zuwa har gabanshi in miki kyauta. Sai abu na gaba, banso yanda kika zafafa abin har ki ka bar gidansa ba. Da fatan za ki koma ki jira har shi da kansa ya yi yanda yace tun farko. Salma ta tura masa cewa. 'Ina ganin wannan ba huruminka ba ne, ka jira tukunna. Sai dai zan maido maka kudinka.Ya turo mata cewa. NO Ni dai baki na yi, amma ki shawarci wadanda ki ke zaune da su, in sun ga lallai ki dawo min da shi, ba sai kin sanar da ni ba, kawai ki maido min. shi ya sa na ba ki kadan don gudun kar ki zarge ni Salma ba ta Kara tura sakon ba, kuma ba ta da niyyar fada ma kowa, za dai ta bar kudin a cikin asusun nata tukunna. Badi'atu cikinta ya soma kwari zuwa yanzun ta murmure tana dan aikinta. Amma fa ta gama gano cewa, mijin nasu mijin tace ne Domin Maman kausar ta kan zo har sashenta ta fada mishi duk abin da ta ga dama cikin gadara da isa, kuma ba ya taba gani ko fadin laifinta. Sannan a tuni ta gano uwar mijinsu ba ta sonta domin tasha fada mata cewa, lallai in tana son zama a, wannan gidan sai dai ta bi Maman Kausar, don gidan natane, mahaifinta ya sai musu shi su zauna. Sannan Yarta ce ta zumunci, don mahaifinta wane na Hajiyar cikinsu guda. " Badi'atu ta gama yin nadama da aurensa, kuma ta danganta halin da take ciki da rashin daukar shawarar iyayenta, don haka ma ko da Anty Momiyo suka zo duba jikinta ba ta yarda ta sanar da su halin da ta ke ciki ba, kuma ko da suka ga irin gadarar da Maman Kausar din take mata, sai ta dinga karewa. Sai dai ta ci kukanta wanda ya ishe ta, ta koma ta zauna. Hakan yasa ta rame kuma ta yi baki. Sannu-sannu lokaci yana Kara ja, Salma sun koma makaranta. Dubu ashirin Shatima ya turo mata a asusunta. Ta sanar da Hajiya Kaka, ta ce,Ciro ki yi bukatunki, muna nan zai samemu" Duk da Kaka tana a'a'aa sai da Salma ta ba ta dubu biyu don ta ki karbar biyar. Ta je gida ta ba Innarsu dubu uku. Koyaushe ta je sai Innar ta nuna takaicinta ga zaman Salman a Zaria, wanda ba ta san asalinshi ba. Salma ta kan ce mata.Inna ba na ki komawa ba ne, Kaka ta ce sai ya zo, kuma shi ya ki zuwa. Har Alhajinshi sun zo sau biyu wai za su maida ni, Kakar ta ce sai ya zo. Shi kuma ko waya ya Ki yi, shi ya sa ni ma ban damu ba" Inna ta ce; "Makota har sun soma tambaya ta". Salma ta ce,Mutane da gulma, ina ruwansu da ni? Kuma ba fa a gidanmu nike ba,gidan danginsa nike Inna ta ce,To, ni dai ina ta addu°a, Allah ya sa a sasanta"Tuni Shatima ya fada kasuwanci, duk da Hajiya ba ta ba shi kudin gurinta ba sai da ya yi mata alkawarin ba zai dawo da Salma ba. Dukda ya san ba har zuciyarsa ya yi maganar ba,kasuwancin ya soma burinkasa a cikin *yan watanni kalilan. Haka kuma sun sake shakuwa tsakanin Safwan da Shatima, Safwan din ya yi ta bai wa Shatima shawarar zuwa ya bada hakuri ya dawo da matarsa, a duk lokacin da Shatima ya yi masa zancen Salman. Kakar su Salma Dankasa ta rasu, ranar uku ta kama juma' a, don haka Salma ta sanar da Kaka. Kaka ta ce, ta je ta kwana daya. Can ko ta kwana, ranar asabar Salma suka rako ta titi don ta hau mota. Ta sha mamaki da taji zuciyarta tana ta ayyana mata Shatima zaizo,kuma tamkar an ce ta dago ta ga motarshi. Ta fito daga yuton. Kai tsaye gabansu ya tsaya,Aliya da danta suna zaune a gefensa. Salma ta kure shi da ido duk da faduwar da gabanta ke yi, kamar ta taka da gudu. Shi ma itan yake kallo [8/23, 21:24] Ummi Tandama😇: 📚4️⃣ Page 11 Fuskarshi daure, su Salma suka soma gaida shi"Sannunku"Kadai ya ce ya kauda kanshi. Salma ta dubi Salma,Mu dan matsa can ko?"Shatima ya katse mata maganar da cewa, "Shiga mota mu je"Ta dauke kai gefe. Ga mamakinta sai ta ga ya fito ya nufo ta, ta lumshe ido ta saka ran cewa zai tsinka mata mari ne, sai kawai ta ji ya kama hannunta. Ya bude motar ya tura ta ciki, ya dubi su Dankasa ya ce,Ku je gida abinku" Ya figi mota, Salma tana zaune tana tura baki Sai da ya figi motar sannan ya ce, «Ina miki magana kin banza, daga ina ki ke?" Ta ce,Ni gaisuwa na je"Ya Ce,Da izinin wa?" Ta kauda kai zuwa titi. "Kaka mana"Ya ce, "Kaka take aurenki?" Ta yi shiru. Ya ce, "Kina ganin zaman da ki ke yi gidan Kaka shine ya fi miki ko?" Ta ce, "Eh" Bai zaci amsar ba, har ya taka burki babu shiri. Sai da suka yi gaba dukkansu, Aliya tace, '"Mu dai kada ka zubar da mu". Bai bi ta kanta ba, ya ce,Salma kina nufin kin fi zon zama da Kaka a kan zama dani?" Aliya ta sake fadin, "Don Allah ka kai mu gida" Ya dube ta, "Don Allah ki tsaya min, ina zuwa Ya dubi Salma. Ta ce,Dole zan fi son zama da kaka,domin ita tana sona'Ya ce,Ni kuma bana sonki ne?. Salma ta ce,Ai na san ba ka sona tuntuni Ya tausasa murya,Salma, ina sonki. Waya fada miki bana sonki?"Salma ta dago ta dube shi, ta ji kalmar har tsakiyar kanta. Ta lumshe ido,Yanzu ka fara sauke ni in shiga mota, za muyi, maganar nan gaba kadan- Ya ce, "Mu tafi gida, sai mu je da ke mu ba Kaka hakuri"A ranta ta ce, "Tab! In ko na yi hakan na bada Kaka" Ta dube shi,Ka bari mu bi a hankali" Ya tada mota ya nufi garejin Kawo da ita. Shi da kanshi ya sauka ya je ya samar mata mota, saura mutum biyu ake jira ya biya kudin duka, ya ce ta fito. Kafin ya dawo daga gurin masu mota Aliya wadda takaici ya isa, sai tsaki take yi. Salma ta ce, Gara ma da ya fada a gaban masu min gorin. Ni ko ba sonshi nike ba, ya gama rawar kan ya ba ni takarda ta' Aliya tace,Kar dai ki min rashin kunya". Salma ta yi yar dariya ta maimaita abin da ya fada ma Aliya,Don Allah ki tsaya min ina zuwa" Aliya za ta yi magana ta ga Shatima ya nufo su, Salma ta dube shi, in har ya sa kananan kaya suna matukar yi mishi kyau. Ta ce,In ka iso ka bude min kofa Tamkar ya ji yana zuwa ya bude mata, "Fito ku taff?"Ta dubi wurin Aliya,Sai anjima Aliya ta yi mata banza, Shatima ya dubi Aliya,Tana miki sallama Aliya ta ce, "Uhum sai anjima, ban ji bane Ya sake raka ta har gurin motar. Sai da ta shiga ya ce, "Za mu yi waya anjima?" Ta dubi cikin idanunshi,Za mu yi" Ya yi murmushi ya juya. Ta bi shi da kallo har ya shiga motar, ya tada ya dube ta, tare da daga mata hannu, ita ma ta daga mishi don turawa Aliya haushi. Suna tafiya a titi tana ta murmushi ita kadai, ba ta san dalilin ba yau ta ji zuciyarta fes, ko don Shatima ya furta mata kalmar so? Kuma a gaban Aliya? Gaskiya yau Shatima ya burge ta. Aliya kuwa da suka isa gida kosawa ta yi Shatima ya fita, don ta kira Hajiya. Tana kiran Hajiyar ta daga, suka gaisa, ta ce,Dama kiranki na yi kawai mu gaisa "Shatima ya zo wannan satin?" Hajiya ta tambaya. Aliya ta ce, Ya ZO, yanzun nan ma muka dawo daga kai Salma gareji tare da shi" Hajiya ta ce,Salma kuma, gidan ta koma?" Aliya ta ce,A'a mun fa dawo duba abokin aikinshi ne daga asibiti, sai kawai muka tsince ta ita da wasu kawayenta. Shi kenan ya hau rawar jiki yana ta lallashinta wai ta dawo. Da yake ta samu dama har ni ta dankara ma magana, saboda ta ga ya yi min tsawa Hajiya ta ce,Lallai! Ki ce ni aikin banza ma nike yi. Kenan zirma ni yake yi da ya ce zai sake ta?" Aliya ta ce,Addu'a kawai yake bukata. Don na jima ban ganshi cikin irin wannan walwalar ta yau ba" Hajiya tace "Na gode, zan kira shi yanzun Aliya ta ce, "Hajiya, kar ki kira shi. Ki dai masa addu'a, zai ce ni na fada miki, dama rannan yake ce min bai san wane ne ya ke kai sirrinshi gurin Hajiya ba Hajiya ta ce, "Sai na masa magana tunda ba ubana ba ne shi Kafun Aliya ta yi magana har Hajiya ta katse wayar. Aliya ta tsure kar dai Hajiya ta fada masa. Salma kuwa sai ta kasance cikin jiran kiran Shatima, har ta yi kamar kada ta kira shi, sai kuma ta fasa. Ta yi shirin kwanciya, zuwa lokacin ta cire rai da cewa zai kira ta. Idanunta suna lumshe tamkar mai bacci, Maryama da ke kwance kusa da ita tuni ta yi bacci. Gunjin wayarta ta ji don ta cire mata Kara tuntuni saboda in Kaka ta ji karar waya sai ta tambaya waye ke kira? Wani lokacin ma har sai ta nemi jin dalili. [8/23, 21:30] Ummi Tandama😇: 📚4️⃣ Page 12 Ta dauki wayar ta sauka zuwa falo bayan ta bi Kaka da kallo wadda ke lullube a kan katifa. Sai da ta kwanta kan kujera, sannan ta daga.Ya ce,Na yi tunanin ma ba za a daga ba?" Tace, Saboda me?"Ya ce,Ana fushi dani"Ta ce,Humm. Ina yini?" Ya ce,Lafiya ba lau ba'Ta ce,Me ya faru?"Ya ce,Rashinki mana' Ta ce, "Yaya kenan. Rashina me zai hana? Ni da dama ba wai ana sona ba ne?"Yace, "Salma ki daina wnanan maganar"Ta ce, "Ai ko ba zan iya daina ta ba, ko, ince ba za ta gogu a raina ba, domin ban san iyakacin mutanen da ka ce ma ba ka sona ba". Ya ce,Wai yaushe na fada ne? Ta ce, «Ka tuna ka fada gaban su Hajiya da kishiyoyina, sannan kuma ka fada ma Aliya,sannan akwai wasu yan uwanka da kayi maganar da su".Ya ce,Ban yi maganar da Aliya ba. Na san na fada gaban su Alhaji gaskiya lokacin ban fahimci cewa ina sonki ba. To amma ke ki fada min inda ki ka ji bana sonki, har ki ka fusata kike son in rabu da ke" Ta ce,Ba zan taba fadin inda na ji dayan ba. Amma ko a ranar Anty Aliya ta goranta min zancen so da haihuwa, ba ta san ni ba su ba ne a gabana ba'Shatima ya yi shiru, Aliya ta canza hali yanzun kenan. Jin ya yi shiru ta ce, "Na san ba za ka yarda da abin da na fada ba, sai dai lokaci na zuwa za ka sha mamaki" Ya ce,Mu bar zancen kawai, ni dai nasan na fada a gaban su Hajiya din nan to sai dai Safwan wata rana da muka yi maganar da shi Salma ta ce,Au? Har shi ka fada masa baka sona kenan?"Ya ce,Yanzun fa zan iya fada ma duk wanda na fada ma bana sonki da cewa, ina sonki". Salma ta dan yi dim, "Na kasa yarda" Ya ce,Kin kasa yarda cewa ina sonki?" Salma ta ce,Eh" Ya ce,To me ki ke son in yi da zai sa ki yarda cewa ina sonki?" Salma ta ce,Abu uku za kayi Ya ce,Fada min su". Ta ce,Da daidai da daidai za ka yi. Yanzu dai ka fara sanar da duk wanda ka san kace ma ba ka sona, cewa kana sona. Shine mataki na farko" Ya ce,Hajiya tana son ganina gobe. Zanzo Zaria ki fito mu hadu Salma ta Ce,Hajiya Kaka ba za ta bari ba. Ince mata naje gurin wa?"Ya ce,Gurin Inna Ta ce, "Kada ka koya min haka, in na iya kuma kai ma watarana in maka? Ka zo dai in ka matsu"Ya ce,Za mu yi waya"Ta ce, "Shi kenan, sai da safe kenan?"Ya ce, "Za ki yi mafarkina?"- Salma ta yi murmushi, "Ban sani ba ko zan yi?"Sai dai ta ji ya sumbaci wayar kai tsaye, cikin kunnenta. Tsigar jikinta ta tashi har ta dauke wuta, ba ta san ya kashe wayar ba. Hajiya ba ta zauna ba saboda ganin Alhaji yana gidan. Ta yi ta aiki a kicin don son Alhajin ya fita, sai aka yi rashin sa'a Alhajin ya ki fita, kuma da ya tashi fita sai ya ce, Shatima ya kai shi gidan Alhaji Nadabo ya samu Hajiya a kicin, "Zan tafi ne daga can in na sauke Alhaji, ga shiba ki ce komai ba' Ta ce, "Ma yi waya, ko ka zo sati mai zuwa don maganar bana son yinta a gabanshi". Shatima ya ce,Wai mene ne Hajiya don Allah?"Ta ce, "Tunda yau zaka koma Abuja in ka isa ma yi waya da dare Ya ce, "Allah ya kai mu daren. Ina son inbi in gaida Hajiya Kaka' Ta ce, "Na haramta maka zuwa har sai Salma ta bar gidan, saboda ita na kunshi bakin ciki kala-kala" Shatima ya ce, *Bakin cikin me Hajiya?" Ta ce, 'Ban ta6a fada maka ba ka ji ba,sai a dalilinta. Ko, wannan kadai kalubale ne ina tsoron nan gaba ma sai ka guje ni a kanta" Shatima ya ce,Hajiya, ki kwantar da hankalinki, Ki yi addu'a kawai Ta ce Ina alkawarin da ka yi min na sakinta? Alhaji ya kwala masa kira,Babana, fito mu je mana, kace yau za ka Abuja kuma ba a jirgi ba"Ya ce,Hajiya za mu yi wayar". . Ya fice cikin sauri. Alhaji ya ce, "Ungo mika mata wannan kudin da ka bamu tayi cefane"Hajiya ta ce, ya barshi. Alhaji yace,Kuna fada ne da uban nawa ne?" Bata tanka ba, Alhaji ya ce, "Mu je". Suna fita, Alhaji ya ce, "Ka yi hakuri fa Babana, na rasa abin da ke damun Mamanku Ta damu a kan maganar yarinyar nan. Yanzun ina maganar ta tsaya tunda Kaka ta ce lallai in cire bakina a maganar?" Shatima babu dama ya ce Hajiya ta gindaya mishi kalma a kan zuwa gidan, sai ya ce,Kaka ta dage sai na sake ta, kuma ni ina son matata Alhaji ya yi "yar dariya,Ka fara sonta kenan? To kaka ta yi namijin kokari da ta sa muka san haka, da ba ta rike ta ba kila da kai ma ba ka san ko kana sonta ba ko?" sai' Shatima ya shafa kansa, ya san Alhaji yana tsokanarshi ne, ya ce, "Ni dai da za ku sa baki matata ta koma gida Alhaji yace,Babu ruwana. Amma zan ba ka shawara, ka je ka ce mata kana son matarka, iyaka ta maka fada ta ba ka matarka. Amma kaki zuwa" [8/23, 21:37] Ummi Tandama😇: 📚4️⃣ Page 13 Shatima dai ya yi shiru, don rigima zai hada iyayenshi in har ya ji cewa Hajiya ta hana. Salma ta kasance cikin tunanin hirarsu da Shatima, haka kuma ta samu kanta cikin yawan murmushi. Maryama har sai da ta tambaye ta.Anty Salma kina ta murmushi yau?" Salma ta ce,Ina tunawa ne za mu je Katsina an ce Anty Badi'atu tana da ciki" • Ta fadi hakan ne don ta ga Kaka tana kallonsu. Maryama ta yi dariya, tun kafin ta haihu za ku je?" Salma ta ce,Ai don makaranta ne da na tambayi Kaka na je Kaka ta ce, "Allah dai ya raba ta lafiya. Cikin yana ba ta wahala, ai ke ina ga har maganin haihuwa za a nema miki, shekaru nawa shiru? Innarki ma ta iya shiririta, shi ko namiji ne ina ruwansa bare ya ga ya samu *ya ya daga sauran matanshi? Ai ko haka ma ya yi miki wulakanci kin san wasu mazan sai su ga kamar in mace ba ta haihu dasu ba zama da ita ma ba dole ba ne"Salma dai ta yi shiru, Kaka ta ce,Lallai in kin fita kibi ki ce ina neman Innarki" Shatima ya shiga super market don siyayyar kayan masarufi. gurin biyan kudi yarinyar ta ce,Sannu Baban Ashraf"Ya dube ta,Yauwa sannunki" Ya cigaba da bada kudin da ya kirga. Yana saka kayan a kujerar baya, yana bude mazaninshi yana shiga, ita ma ta bude dayan bangaren. Yana zama ita ma ta zauna, ya dube ta, "Ya ya, lafiya, daga ina?"Ta kafe shi da idanunta,Taimakona za kayi. Layinmu daya, sai ka barni ina jiran abin hawa?"Yace,Me zai hana tunda ba ni na kawo ki ba, ko na ce ki zo?"Ta gyara zama tare da kau da kai,Masu kamun kai irinka suna burge ni sosai. Taimaka ka kaini" Ya figi mota ba tare da tsayawa ba ta amsa taba. Duk da ta yi ta dan jeho maganganu, sam bai tanka ba domin yana tuno zantukan Nafisa na zarginshi da take yi. Matsawar taganshi za ta ce lallai halinsa ne, shi ya sa kafin ya shiga kwanar layinsu ya ce,To sauka nan Tace Haba ina laifin inda muka karasa?" Kiran Salma ya shigo wayarsa, kafin ya yi magana sai ya kalli fuskar wayar. Ganin kiran Salma ya dauka cikin sauri,tare da fadin,Masoyiyata"Salma ta dan yi tsam don tana cikin makaranta ne ta ji tana son jin muryarsa, ta ce,Yaya dama na ce ne ina son zuwa Katsina, zan duba jikin Anty Badi'atu".Ya ce,A'a ki bari sai innazo juma' a sai muje asabar mu kwana a can"Ta ce, "A gidanta za mu kwana da kai?"Ta tambaya cikin mamaki.Yace,A'a, hotel za mu je mana" Ta ce,Tab! Ina tsoron Kaka. Sannan kuma har yanzun ba ni da tabbas a kan cewa kana sona ko a'a"Ya ce,Ya kike maganar nan? Allah ina sonki Salma, kullum cikin tunaninki nike".Ta ce,Ni nace sai in ka fata ma wadanda ka fada ma cewa ba ka sona" Ya ce,Ai na fara don wallahi na fada ma Alhaji"Salma ta saki 'yar dariya, sannan ta ce,Yanda ka fada a cikin mutane haka nike son ka sake tara su ka fada musu" Yace Salmata gamida kwantar da murya,Haba taya zan tara wadannan mutanen?" Cikin shagwaba ta ce, "Ni ban sani ba. Amma in bakayi haka ba, ba zan bi ka zuwa Katsina ba" • Ya ce,Amma za ki yarda da son da nike miki?" Ta ce,A'a ba zan yarda ba Ya ce,Shi kenan, zan ga yanda zan yi hakan. Kuma za mu yi magana da dare" Ta ce,A'a, sai anjima"Ya ce,Jira ki ji Salma" Ta ce, Katina zai kare, kuma bana cikin wadanda ka ke saka ma kati duk sati" Ya ce,Na gode Allah da gori ni Jafar. Zan sa miki anjima"Zinatu wadda ke zaune tana sauraronshi tace,Baban Ashraf ka manta da nine wai?"Cikin sauri ya dube ta, har ga Allah ya manta da wata a kusa da shi, ya ce, "Ke fita mana, zaman me ki ke yi a nan?" Cikin sauri ta ce,Au haka ma za ka ce?" Ta yi maganar cikin daga murya ko don Salma taji. Fahimtar hakan ya sa yayi saurin katse layin na Salma. Ya bude kofar, "Fita na ce da Allah". Zinatu ta fita tana fadin, " Amma ba a taba yi min abin da ka yi min ba" Ya fisgi motarsa ya yi cikin layinsu. Salma bata zargi komai ba game da muryar da ta ji da suna wayar. Zatonta Nafisa ce don haka ta tabe baki tare da fadin, "Kamar mai tsoronta?"Wasa-wasa haka lokaci ya yi ta tafiya, lamura suna canzawa har cikin Badi'atu ya kai wata bakwai. Tun daga lokacin Badi' atu ta soma nacin za ta koma gida ta haihu a can. Abin da ke ba ta haushi, sai ya dinga nuna mata za su yi shawara da matarsa. Ta kuma sha tambayar akan cewa, matar ce take auranka ko shi? A duk lokacin da ta yi wannan tambayar sai sun yi rigima. Sam auren ya fice a zuciyarta, wannan yasa kullum ta ke cikin kuka da bakin ciki. Salma kadai ta san cewa tana cikin matsala, don suna chatting. In ta fada ma Salma ne take jin dadi, sannan Salmar tana lallashinta da cewa, ibada ce take yi ta yi ta hakuri. Amma ta ba ta shawara da cewa, in ta haihu ta zo wanka ta sanar da halin da take ciki don a nema mata 'yanci. Sai dai shi Shatima in ya kira Salma za suyi magana, amma ya yi ya yi ta fito su hadu taki, domin shi ma yaqi zuwa ya samu Kaka. [8/23, 21:42] Ummi Tandama😇: 📚4️⃣ Page 14 Kaka ta fusata matuka don tana ganin raini mai tsanani ya shiga tsakaninta da Shatima, kuma tana ganin laifin uwarsa ne, domin ita ma ta dauke Kafarta daga gidan, amma tana nan tana zaman jiransu. Nafisa tana shirya su Ashrafzuwa islamiyya, sai ta ji sako ya shigo wayarta. Tana dubawa ta ga Maman Nana, gabanta ya fadì ta sani in ta ga sakon Maman Nana, to zancen mijinta ne. da sauri ta karanta gajeran sakon. "Yanzun na ga mijinki ya sauke Zinatu a bakin layi, da alama siyayya suka yo, don na ganta da ledoji, kuma shi ma yanzun zai shigo'. Nafisa ta mike cikin tashin hankali, sai taji shigowar Shatima. Tabbas babu karya, domin da leda ya shigo.-Daga irin kallon da ta yi masa ya san akwai sabuwar matsala, domin ko da suke takun saka tana yi masa sannu da zuwa, kuma tana gaida shi. Ya mika mata ledar hannunsa taki amsa ta juya ciki. Shatima ya dauki yaran yakai su islamiyya, yana dawowa inda ya bar kayan a nan ya same su. Ya dauka cikin bacin rai ya shiga. '"'Kin ce kina bukatar abubuwa na siyo na kawo sai ki watsar min a nan gurin?" Ta ce, "Ka kai ma wadda ku ka je tare ta hada tunda kai ka yarda ka zubar min da mutunci Ya yi shiru yana nazari, sannan ya ce, "Sai yanzun na fahimta da ma a kan wannan yarinyar kike ta wannan haukan?"' Ta ce, "Au hauka ne ma? Ai dama nasan ka santa kake yi min alaye, duk motsinku ina sani kuma na gaji zan fada ma Hajiya kila inta maka fada za ka ji Ya sani Nafisa za ta aikata, in ko ta fada bai san ya zai yi don wanke kanshi ba, don haka ya shiga raba idon inda zai ga wayarta. Saman kujera ya hango ta sannan yaje ya dauka da sauri ya nufi fita. Ta ce, "Ni ka ba ni wayata".Bai ko kula ta ba, ya yi tafiyarshi.Da mota ya fita ya shiga layin yana dubawa ko zai ga Zinatun, layin ba kowa sai wasu matasa biyu zaune a kofar gidansu. Ya san yan layin ne, don suna sallah a masallacin nan layin. Ya same su suka gaisa, yace,Ina ne gidan su wata yarinya fara haka, mara kamun kai?"Kafin Shatima ya rufe baki dayan ya ce,Zinatu". Shatima cikin gamsuwa ya ce, "Ita ce, don Allah inane gidansu?"Daga nan suka kwatanto masa gidan, ya kama hanya. Babu maigadi, don haka ya yi ta buga gidan, cikin sa°a ita ce ta nufo kofa tana fadin,Wane ne don Allah kar a karya mana gateTana budewa ta ga Shatima, ba za ta iya fassara abin da ke tattare da zuwansa ba, don fuskarsa kamar yanda ta saba ganinsa. Ta turo dankwalin kanta gaba tare da fadin, "Na sani sai ka zo har gida Ya ce,Bismilillah zo mu Ta kalli jikinta"Ban minti daya da rabi in dauko mayafina"Bai ce komai ba ya juya mota. Har da turare ta Kara, ya dauke ta a mota tana ta kaudi.Cikin mamaki taga ya karya kwanar shiga gidansa. Har za ta yi magana, sai kuma ta yi tunanin ko matarsa ce ta fita shine ya dauko ta. Ya aje motar ya fito, sannan ya ce mata, "Fito"Ta bi shi suka nufi falon, ta shiga ta samu guri ta zauna ta dora kafarta daya kan daya. Shatima ya nufi ciki, Nafisa tana zaune bakin gado ta zabga tagumi duk abin duniya ya ishe ta.Ya shigo ya dube ta, Taso mu je" Ta mike ta bi shi babu musu. Tana ganin Zinatu ta zaro ido cikin tashin hankali,Me wannan ta zo yi gidana? Me ya kawo ta?"Shatima ya ce,Ke kina da damuwa, ki tsaya ki ji abin da ya sa na kawo ta Ya ja kofar falon ya kulle, ya zare makullin ya dawo ya dubi Zinatu, "Ki fada mata alakar da ke tsakanina da ke" Shatima ya yi maganar cikin daga murya. Zinatu ta tsorata ta dubi Nafisa, sai kuma ta dake ta ce,Soyayya Ya nufi kanta tamkar zai rufe ta da duka, ya ce,Da wa ki ke soyayya? Na taba cewa ina sonki?" Ta kankame guri daya tare da fadin, "Nike sonka Ya ce, To wallahi ko ki fadi yanda aka yi ki ka shiga motata, ko kuma in sa a Batar da ke. Daga, nan in na yi waya aka z0 aka dauke ki kin tafi ke nan!"Nan take Zinatu ta soma rawar jiki tare da rokon Shatima kan ya yi hakuri, sannan ya ce, ai sai ta fadì gaskiya. Nan ta shiga rero zantuka tana maida yanda aka yi, har zuwan Nafisa gidansu. Shatima cikin mamaki da takaici ya dubi Nafisa ya ce,Ai kin ba ni mamaki da har ki ka kasa shaidar halina, zuciyarki ta yarda zan iya neman kamar mace irin wanna da kowane Kazami ke zuwa gurinta"Ya jefi Nafisa da makullin,Bude mata kofar ta fita". Ya nufì ciki rai a bace. Zinatu ta mike cikin sauri tana share zufa, Nafisa ta bude kofar tana fadin, "Fita nan banza masharranciya*Sai da ta tabbatar ta fita sannan ta ce,Oho dai ko ba komai na gwara kanku, kuma kinci sa'a da in nayi muku wani kullin Karyar ne ki kwance shi"Nafisa ta samu Shatima tana ba shi hakuri,ya ce Na san ajin da na aje ki daga yau kawai, tunda ba ki bincike kike yanke hukunci" Ya ciro wayarta ya mika mata tare da fadin,Kina iya kiran Hajiyar yanzun ki sanar da ita sannan na gode ma Allah da ya haska min wasu abubuwa sakamakon wanna kazafin Nafisa ta yi ta kokarin fassara zancen nashi, amma sai ta kasa.Amna ta kalli Maman Afra, sannan ta kalli kofin hannunta, "Me ki ke nufi da wannan?"Ta ce, "Ki amsa ki sha domin na gaji da korafin da ki ke kawo min, ba ni da isassun kalaman da zan ba ki shawara akan matsalolinki". [8/23, 21:48] Ummi Tandama😇: 📚4️⃣ Page 15 Ta kalla ta Bata rai, "Gaskiya Maman Afra ba zan iya shan wannan ba, zan yi amai" Ta ce,In kin sa a ranki cewa za kiyi ba" Ta kama hannunta ta dora mata kofin, tare da fadin,Zan Kara hada miki wani kala yanzun, sannan ki sha da niyyar biyan bukata" Amna tana bata rai tana komai ta shanye garin dakan, sannan ta kuma shanye gumbar data ba ta. Ta sha zuma, ta sha tsimi, har sai da taga ta kusa aman da gaske sanan ta barta. Ta ba ta wasu na matsi, ta ce, "Kayan nan ba su da wata illa, masu kyau ne, kuma za ki dawo ina nan. Yaushe mijinku zai dawo?" Ta ce,Yau ne, amma dakin Aliya yake sauka, sai ya tafì dakina" Ta ce, "Wai har yanzun yarinyar nan ba ta dawo ba?"Amna tace, Ba ta dawo ba, kuma wani abin al'ajabi Baban Jafar yaqi fada min dalili. Ko da sau biyu na taba tambayarsa, sai ya ba nì amsa iri daya wai ba matsalata ba ce" Maman Afra ta sa dariya tare da fadìn,Ni kuma ya burge ni, domin ke ma ba zai fada ma wata sirrinki ba Amna ta ce,*Ai kuma hakan yake, Baban Jafar ba zai taba yin zancen wata ba ko da sunan wasa, kuma yana son hada kan yaranshi in dai yana dakina ba ya karanta ma Jafar kananan labaran da nike karanta masa, sai dai ya ba shi labarin yan uwansa su Ashraf, ya kawo abubuwan da ya san Jafar na so ya ce in ji su. Kullum yana damun Baban wai ya kai shi gurinsu, kayan wasanshi haka zai ba da wai a kai ma kannenshi" Maman Afra ta ce,Gaskiya salonshi yayi sosai, ki ke ki taimaka a kan haka, in yara suka samu kyakkyawar tarbiyya tunda farko suna tashi da hadin kai. Amma wani lokacin iyaye mata ke kashe wannan dangantaka, wata sai ta ja ya' yanta daki ta yi ta cusa musu mummunar akida tana rushe ginin da uban yake yi" Amna ta ce,Haka ne, amma ni ba ni da wannan ra'ayin, ina son yara su tashi da hadin kai* Mamaki Amna ta yi a ranar da Shatima ya kwana a dakinta. Ta kira Maman Afra ta kasa magana, sai dariya. Maman Afra ta ce, Adana sirrinki, na san da ma za a yi haka, wancan na baki dandane,- yanzun in kina so sai ki shirya kudinki in sa ki a kan layi" Amna ta ce,Zan shigo" Yau da gobe asarar mai rai, cikin Badi'atu wata tara, da kuka ta kira Hajiya wai a z0 a dauke ta in ba haka ba za ta mutu. Hajiya ta tsorata sosai don ba ta san cewa Badi'atu tana cikin matsala ba. Anty Momiyo ce suka je sun samu Badi atu ta rame, ta yi baki. Nan ta soma karanto matsalolin da ta ke fuskanta. Ta ce,Har zuwa yanzun ba a sai ko wando na jariri ba, wai matarshi ta ce ba yanzunba, kuma kowane lokaci za ta iya haihuwa. Abinda ya ba su mamaki ko da mijin ya dawo suka yi masa zancen tafiya, wai sai sun yi shawara. Washegari da kanta Maman Kausar ta shigo har gurinsu suka gaisa, tace musu,Gaskiya babu maganar tafiyar Badi'atu, domin mu ba ma wannan al'adar' Anty Momiyo ta ce,Tofa! Ai mu shi muka yi wa magana ba ke ba Ta ce, "To ai shawara muka yi da shi da mahaifiyarsa. Amma tunda kun ce hakan bari kwa ji daga bakinsa, ko na mahaifiyar tasa" Baba Ladi yar uwarsu da suka zo tare, tace, '"'Ai mu ba ruwanmu da wata mahaifiyarsa" Maman Kausar ta fita, Anty Momiyo tace, "Ai kawai Baba Ladi mu tashi mu hada kayan yarinyar nan mu nuna musu babu fashi. Kalli don Allah yanda Badi' atu ta koma" Baba Ladi ta ce,Kafin haka, jira mijin ya zo mu ji ta bakinshi" Shatima yana tsugune yana gaida Hajiya, nufinshi da sun gaisa ya wuce dakin Alhajinsa don duba jikin Alhajin, ya zo bai ji dadì ba. Haka kuma ba ya son jin komai daga bakin Hajiyar don kullum zancen daya ne, ya saki Salma. Shi kuma wata irin kauna da son Salma yake ji wanda ba zai iya fassarata ba, amma sai Hajiyar ta ce, *"Zauna ina da magana da kai ka sani" Ya ce,Hajiya ai kin fada min maganar Salma ce"Hajiya ta ce, "Ni fa babu daga Kafa sam-sam ba za ka bar garin nan ba, sai ka sake ta Shatima ya ce,Hajiya kin san ban isa in kai takardar gaban Hajiya Kaka ba' Ta ce, "Shi ya sa kwanan baya ka dauki Salmar a mota har da wulakanta Aliya a gabanta?" Shatima ya ce,In ji wa?"Ta ce, "Bari ka ji, duk abin da ke faruwa a gidanka na sani. Wato ga *yar iska ina nan ina hakilon ka sake ta, ashe kai kana can kana lallaba ta kana kiranta a waya, sannan har ka ganta babu izininka ta tafi yawonta, amma ka dauke ta har kanama matarka mai haihuwa tsawa? To ka dawo min da kudadena don na san ita za ka sakar ma ta cinye su. Bari ma ka ji..Kiran wayar da aka yi ta Hajiya ita ce ta sa ta fadin,Je ka dubo shi kazo yau sai an yi an gama, in ma Kakar za ta rike ta ne bayan ka sake ta, sai ta ci gaba da rike ta. Ai daman kai tuni ka fada ba ka sonta, wannan faman ma da nike yi da kai duk aikin asiri ne, na sani". Shi dai ya fice cikin sauri ya shiga gurin Alhajinsa. Alhaji yana kishingide yana duba jarida, Shatima ya ce, "Alhaji ba ance ka samu hutu bane?"Ya ce, "Ubana ai gani a kwance ban fita ba"Ya ce, "Amma ka dauki jarida kana dubawa?" Ya ce,To in ban fita ba kuma ban duba halin da duniya take ciki ba Babana nan ma sai zuciyar mutum ta buga Shatima ya yi dariya, sannan ya zauna tare da fadin, "Ai kwakwalwarka ake bukatar ta huta" [8/23, 21:56] Ummi Tandama😇: 📚4️⃣ Page 16 Alhaji ya'ce, "Barsu duk wannan ba za ta hana mai rai mutuwa ba, sai dai in lokacinsa baiyi ba Shatima ya ce,Haka ne, Allah ya ba mu sa'a Ya rusuna yana gaida Alhajin, bayan ya amsa ya ce,Ni fa sai na ji kamar muryarka,amma da na ga tun jiya zuciyata ta ke min gizo ina jin muryarka, sai na tsammaci yau ma haka ne" Shatima ya ce,Ai haka kawai na aje gidana na nufo in ga jikin". Hajiya ta shigo hankali tashe, tana fadin, «Wallahi su taho min da 'yata gida, ai ko ba zata sabu ba" Alhaji da Shatima suka dubi Hajiya duk cikin son Karin bayani. Hajiya ta ce, "Ku ji abin tsiya, wai Badi'atu ba za ta dawo gida ba in ji uwar mijinta da kishiya. Su suke aurenta da zasu hana?"Alhaji ya ce, "'Saurara Hajiya Amina, inhar mijinta bai yarda ba gara ta zauna. Ai na zaci ya barta ne" Hajjya ta ce,Ba fa miji aka ce ba, uwar mijin fa Alhaji! Ita kuma a wa?" Shatima ya ce, "Hajiya uwarshi ta isa ta hana shi, ki ka sani ko lokacin da suka fada mishi da ya je gurin uwarshi sai ta ce kar ya bari? Kuma kin ga bazai iya zuwa ya ce musu ba za ta ba, da yake ita uwar a tsaye take shi ne ta same su Hajjya tamkar ba ta gane karatun da Shatima ya yi ba, sai ta sake fadin, "Shi ke auranta ko ita?"Shatima ya ce, "Hajiya ki kwantar da hankalinki, duk da na gari dole ya bi zancen iyayensa. Kar ki gurgude ma Badi'atu aure" Hajiya ta ce, "Ka rufe min baki da Allah,ya dade bai mutu ba, auran banza ance min duk ta lalace, wai komai sai abin da iyayensa da matarsa suka ce" Alhaji ya ce,Ki bi sannu, yanzun dai kice su dawo za a san yanda za a yi a samu maslaha"Hajiyar ta fita da sauri tana fadin, "Tab! Ai ni dai su taho min da yata" . Ko da ta je ta dauki wayarta abin da kawai ta ce shi ne,Ku tattaro ta ku taho da ita. Shatima ya ce,Allah kenan, Hajiya taja ma Badi'atu matsala"Alhaji ya ce, "Kamar ya ya?" Shatima ya dafe baki, domin zatonshi zancen zuciya yake yi. Alhaji ya tashi zaune,Me ya' sa ka ke ganin Hajiya ce taja ma Badi'atu?"Shatima ya ce,To ni ai dole in fadi haka. Hajiya ta manta ita ce ta hana ni maido Salma,sannan ta ce uwarsa ba ta isa ba"Alhaji ya ce,Tuni na zargi Hajiya a cikin matsalar nan shi ya sa aka ce ko ba ka da ya'ya kar ka sake ka takura dan wani. Domin kana da na yan uwa. Amma kai duk wannan tsawon lokacin me ya hana ka fada min?" Shatima ya ce,Na san ranka zai baci, kuma bana son ku samu matsala a kaina Alhaji ya ce,To ka barta cikin ruwan sanyi za ta saitu. Ka kara hakuri ka san an ce mata komai shekarunsu tamkar yara suke" Shatima ya ji dadì sosai, da zai tafi ya je gurin Hajiya ya samu ta zabga tagumi, ya ce, "Hajiya ina son mu karashe magana, zan tafi Ba tare da ta dube shi ba, ta ce,Je ka Ya ce,Hajiya kar kisa damuwa a zuciyarki fa" Ta dubi Shatima cikin sanyin murya ta ce, '"Dole in damu, yarinya karama ta fada cikin kaddarar aure Shatima ya ce, "Allah zai warware Tayi dan tsaki Shi ya sa duk wanda yaQiji bayaqi gani ba. Ina laifin Safwan ta Fututtuke taqi shi? Shatima yace "Allah dai ya sa ba shi ne mijin ba. Ki yi bakuri" Ta ce,Ai su ne da hakuri don na ce su Momiyo su yo min gaba da yata ba zan dauki wulakanci ba Shatima ya ce,A bi sannu Hajiya, babu kyau fa mutum ya shiga hurumin aure, kin san komai Hajiya"Ta dube shi,Je ka abinka kawai".Shatima ya fita, shi ma ranshi ya shiga damuwa da lamarin Badi'atu, kowa ya san yanda yaya yake son Kanwa. Shatima ya shiga gidan Inna da nufin gaida ta kamkar yanda ya saba, suka gaisa ta tambaye shi mai jiki, ya ce da sauki sosai. Ta ce,Salma ke sanar da ni jiya da ta biyo daga makaranta"Ya ce, Ya samu sauqi"". Inna ta Ce,Yanzun Alhaji ba ka je gurin Kaka ba ko ma me za ta yi maka?" Ya ce, "Zan je insha Allahu Inna kwanan nan, Kakar ce ta fiye rigima tunda ta ga ana lallaba ta"Ta ce,Zaman nan ya yi yawa, ga shi ana neman kusan wata sama da bakwai. Ka kokarta ta koma ga azumi ya kusanto Ya ce, "In Allah ya yarda zan yi kokari" Shatima suna waya da Safwan, batu ne na harkokin kasuwancinsu. Gidan mai aka bude na Shatima ne, amma an biyo shi bashin miliyan ashirin, ya ce zai ba da domin ya san ya yi wa Alhajinsu karkaf kafin gidan man ya samu. Safwan ya ce,Insha Allah za ka bada kwana kusa, domin kai ma kana da albakar kasuwanci".Ya ce, "Wai amaryarka ta dawo kuwa?"Shatima ya ce, "Kai dai bari, Kaka fa taki sam-sam" Safwan ya ce, "To kai in har ka tabbatar ba ka sonta ai gara ka sahale mata, domin akwai daukan alhaki" Shatima ya ce,Da ma kai ma na fada maka bana sonta ko? Safwan ya ce,Eh mana, ni fa kwanan baya har sako na bada a bata na wasu yan kudì domin da ka ce min ba ka sonta, duk tunanina bama za ka ba ta abin kashewa ba" [8/24, 21:11] Ummi Tandama😇: 📚4️⃣ Page 17 Domin da kace mani baka sonta duk a tunani na ba zama da ita zakayi ba, Shatima ya danyi tsam amma sai yace" Safwan dama wowta nayi a lokacin domin sai daga baya na gane Ina tsananin sonta, gaban Safwan ya fadi yace "kuma". Shatima yace " kayi mamaki ko? Ni kaina nayi matukar mamaki." Safwan ya daure sosai yace "to shikenan kayi gaggawar maida ita dakin ta" "Insha Allah dama Hajiya ne ta rike wuta to gashi kuma an kunnowa Badi'atu wuta itama a gidan ta," wacce irin wuta kuma? Safwan ya tari numfashin Shatima. Shatima ya bashi labarin irin matsalar da Badi'atu ke ciki, Safwan yace "kuma shine sai a barta ta mutu a can? Yace jiya dai Alhaji yake fadaman tun ranar su Aunty mamiyo suka maidata gida amma surukar tace bazai yiwu ba,kuma ko wandon jariri basu siya ba,." Safwan yace"subuhanallah gaskiya dole sai nasa an daure mijin nan,ai Badi'atu tafi karfin cin mutumci yasan wacece Badi'atu kuwa? Shatima yace "ka barsu dai da halinsu yanzu dai bari muyi ta lafiyar ta da Babyn tukunna." Safwan yace" yanzu Zan bar Lagos zan zo Kano zan kwana amma na fasa dole Zaria zanje naga halin da take ciki tukunna" Shatima yace" Allah dai ya kawoka lafiya. Kamar yadda Safwan ya fada kusan tarema suka sauka a Zaria da daddare ya sauka kai tsaye yasa direba ya wuce dashi gidan Hajiya. Badi'atu na kwance kan doguwar kujera ta gama cin abinci tasha magani tana kallon talabijin, Safwan ya yi sallama ya shigo, Badi'atu ta tashi zaune cike da mamakin jin muryarsa. Ya tsaya gabanta ya rike kugu yana kallon ta cikin mamaki,bai lura da Hajiya da Alhaji da ke zaune suna kallon talabijin ba,Saida Alhaji yace " Safwan ne a daren nan,"da mamaki ya kalli Alhaji. "Garin ya ya Yarinyar nan ta dawo haka Alhaji?" Hajiya ne ta mike tare da fadin "nan ma aitayi kyan gani" meka gani anan? Aida lokacin da aka dawo da ita daga asibiti ka ganta kam abin sai a hankali" Safwan yace "ko yanzu ma kamata ya yi ace a kwance take a karkashi kulawar likitoci," Alhaji yace "ai ta kwana daya a asibitin shine suka sallame ta." Safwan yace "Hajiya ku shirya yanzun nan mu koma asibiti" take ya ciro wayarshi ya soma kiran layin likitanshi yace "Victor kana gari kuwa? Yace "eh Ina nan" Safwan yace "to don Allah ga kanwata za a kawota yanzun nan zama muzo tare kawai. Alhaji yace"kana ganin a kara kaita asibitin? Tanada maganin ta da wancan asibitin suka bata" Safwan yace" Alhaji kwararrun likitoci ne waɗannan. Badi'atu ta kasa tashi kuma ta kasa magana saboda kunya kanta a kasa, Hajiya ta mike tasa hijabi da takalmi. Nan da nan aka kaita likita ya duba ta ya bata gado domin yace akwai alamun nakuda tare da ita,dama tun safe take ciwon mara tana daurewa ne dan kawai taga yadda iyayen ta suketa kaiwa da kawowa akanta, Safwan ya dubi likita yace"likita me za a bukata? Yace "kayan haihuwa,a daren suka fita neman kayan,dare ya yi duk an tashi sai dai abinda ba a rasa ba. Badi'atu tasha wahala sosai har garin Allah ya waye bata haihu ba, kwana Safwan ya yi yana kiran waya amma babu wani zance bare wani labari, Hajiya harda kuka domin ta cire rai da Badi'atu abin haushi ma ta kira mijin ta sanar dashi sai yace "Allah ya sauketa lafiya,be kara da wani abuba ya kashe wayar. Daga lokacin kuma be kira yaji ya ake ciki ba,har garin Allah ya waye. Likita yace "mijin ta yazo yasa hannu dole sai anyi aiki, Hajiya batayi fushi ba ta sake kira ta sanar dashi yace "shifa bazai zo Zaria ba dan yanada abin yi gurin aiki zai tafi," Safwan da yaje yaji yayi fada akan me Hajiya zata kirashi,ya tafi gurin likita da kanshi yasa hannu aka shigar da ita dakin aiki. Anyi nasarar aiki an ciro yaro saidai babu rai yasha ruwan nakuda ita kuma tasha wahala,suka daukeshi aka tafi dashi gida,ita kuma aka cigaba da kula da ita. Ranar da Shatima ya diro yaji bakin ciki sosai game da abinda mijin Badi'atu ya yi don haka ya kirashi ya fada mashi dan shi yazo babu rai kuma lallai sai yazo suna son sanin abinda yake nufi da ita,yace "shifa ba abinda zaizo ya yi tunda yazo babu rai an huta,kuma gaskiya sai ya samu lokaci in zai iya zuwa ma." Hajiya da sauran mutanen dake dakin sukayi salati don a handfree yasaka wayat, Shatima ya kashe wayar yana fadin "ai dole ma ai zauna da wannan mutumin" kowa ya amsa da hakan ya yi amma a bari tasamu lafiya,haka dai aka rufe yaron, Badi'atu ta warke kwananta goma aka sallame ta,ranar kuwa Kaka sukaje suka duba Badi'atu tunda ta dawo gida Salma dama taje asibitin. Suna shiga suka samu Shatima da matansa,tunda Salma da Maryama suka shigo falon suna tura keken Kaka, Shatima yake kallon Salma duk da hijabi ne a jikinta hakan be hanashi gane yadda kirjinta da jikinta ya ginu ba. Kaka bata amsa sannun da Hajiya takeyi mata ba,ta amsa gaisuwar Amna ne da Nafisa kadai,ta kama hannun Abulkhairi tana fadin " kai sannu kaine Aminu ? Uwarka bata taba kawo ka ba ko? Aliya tadanyi murmushin yake tare da fadin zai zo ai Kaka" a'ah barshi nima bana neman sa ai ita duniya wanda yakeyi dakai dashi zakayi. "Salamatu turani wajen maijegon nan muje muyi mata sannu,muzo mu wuce," Salma ta gaidasu Hajiya da sauran mutanen falon,tayi mamakin yadda Hajiya ta amsa mata gaisuwa da sauri,tayi zaton kodan ganin Kaka ne. Hajiya Kaka ta yiwa Badi'atu sannu tare da bata hakuri abisa abubuwan da suka faru da ita a gidan auren ta na rashin dadi,ta kuma bata shawarwarin addu'a Allah ya zaba mata abinda yafi zama alkhairi,tare da mata addu'ar Allah ya jikan jaririnta. Da suka zo falo kuwa Shatima yace Kaka inata gaisuwa kinki amsawa," tayi banza dashi tare da fadin Maryama tashi muje ko kinji,dan ita bata bisu ciki ba,sai kuma taga ya kamata tayi masa gori a dai dai lokacin da yace " Kaka nasan nifa mai laifine" Kaka tace" kai,,karkaga nazo gidan ku ka zata bikonka nazo,Ni awa nakai kai gaisheni? Wulakanci a duniya dan kayi saime? Yanda ka daki wata ka korota gashi nan kaima an kusan kashe maka kanwarka,in kaji zafin abinda aka yiwa Badi'atu to kasani haka dan'uwan Salma ma yaji zafin abinda kayi mata,idan uwarka da ubanka sun haifo kuma sunji zafi to suma iyayen Salma ma sunji zafin abinda akayi mata,kuma inason kasani gata nan zata soma zaman gida kamar yadda Salma take zaune ita ba bazawara ba ita kuma ba matar aure ba,ai be saketa ba ko? To mu gani don girman Allah,ko yaushe dai muna nan muna kallo sai muga yadda film din zai kare." Zancan Kaka ya daki Hajiya da Shatima ba kadan ba da sauri yasha gaban keken Hajiya Kaka ya durkusa tare da fadin "Hajiya wallahi,wallahi inason Salma ya kalli duk yan dakin yace don Allah kujuyo ku zama sheda wallahi inason matata Salma so mai tsanani kuma matatace." Salma ta kalleshi tasan wani sharadine yakeson cikawa nata,ta dubeshi tare da girgiza kai alamun beyi ba,Ina sonki Salma, Kaka tace" muje Salamatu kinji saida yaga an wulakanta kanwarshi sannan zai san da darajar ki,wai yana sonki. Ta karkata kujerar ta suka wuce ta gefenshi yana tsugunne,ya mike ya bisu da kallo matanshi gaba daya sun saki baki daga mai tsaki sai mai kwafa sai mai kauda kai,Amna dai waya taketa daddan nawa,tamkar bata sanma da abinda ke faruwa ba. Suna isa gurin mota Kaka ta rufe Salma da fada,ke kuma dana kyale ki,Ina jinku fa abinda kukeyi ke dashi na kyale kune dan naga baki badaman kasa a ido ba,saura kuma idan yazo babu wani kamun kai babu martaba ki kwashi jiki kice zaki koma ya sake koroki. Salma tayi kus saboda kunya da taji ashe Kaka tana lura da ita tasan tana waya da Shatima kenan. A daren ranar bata daga wayar shi ba dan haka ya turo mata sakon cewa "ya cika alkawari ya bayyana yana sonta a gaban kowa kamar yadda ya yi a farkon lokacin dayace baya sonta kuma a gaban waɗanda ya baiyana masu cewar yana kinta" tace " baiyiba domin babu kusan mutum uku a gurin kuma yayi hakuri ya dena kiran layin ta,ya yi lissafi suwaye,suwaye a wancan lokacin kuma suwaye a yau?. .... [8/24, 22:56] Ummi Tandama😇: 📚4️⃣ Page 18 Hajiya ta zabga tagumi ko ba a fada mata ba dole zata yarda cewa duk abinda kayiwa dan wani sai anyiwa naka, hakan yasa cikin ta ya yi mugun duran ruwa kuma ta dauki aniyar cire bakin ta daga harkokin cikin gidan Shatima. Dan haka ta samu Alhaji da kanta tace masa tanason ya shiga gaba don Allah ya taimaka Salma ta koma dakin ta,yace " yanzu da kikaga kema anyiwa yarki haka shine kikeso kiyiko? To badani za'ayi zan cen nan ba kuma badan Allah ba za'ayi shi,tun a baya dana shiga Kaka tace babu ruwana kinga dolene inyiwa uwata biyayya bazan yadda in saba mata ba,tunda dai wasu ma daban sunyi mata biyayya to inaga ni data haifa,don haka ke da kika hana danki zuwa saiki tashi kuje ke dashi,Kakarshi ce,karki manta fa mahaifiya tace. Kikayi amfani da damarki ta uwarshi har kika gindaya mashi doka cewa in yaje baki yafe ba,kin kyauta,Babu abinda zaisa inje. Hajiya Amina tace" ni bazan iya zuwa ba ina matukar jin kunyar gidan Kaka rabona da gidan tun yaushe amma yanzu sai in tashi inje, "Wannan kuma ruwan ki." Salma taki daga wayar Shatima duk irin sakonnin magiya da yake tura mata tare da son jin muryar ta. A ranar juma'a da karfe biyar na yamma Salma taci adon ta,tanayi masu faten doya kamshin sane ya cika gidan. Shatima ya yi sallama tare da shiga falo, Kaka da take zaune kan kujera ta amsa ciki ciki tana ganin Shatima sai gimtse fuska kawai takeyi,zama ya yi jikinshi a sanyaye ya sunkuyar da kai yana gaisheta. Tunda tace "lafiya" to daga nan bata sake magana ba bare kallon shi, Maryama dake shafa mata man zafi a kafarta ta gaishe shi ya amsa yanason yace ina Salma yana tsoron Kaka, domin be taba ganin ta a Bacin rai irin haka ba,tun daga ranar da Salma tazo ya dake ta tun wannan da yaga fushin ta be kara gani ba sai yau, Salma ta fito daga kitchen tana sanye da riga da siket na atamfa zaman ta gidan Kaka ne ta koyi abubuwa da dama masu yawa,ciki harda girki kowanne kala dayake yan aikin Hajiya Kaka kwararriya ce agun girki sannan ta koya mata tsafta duk da dama ita din ba kazama bace. Hajiya Kaka takance da kwalliya akasan mace bawai kawai mace ta zauna dan tayi wanka ta zauna babu kwalliya ba,kuma kisa sababbin kayanki bawai sai zaki fita anguwa ba, sannan ta koyi lalle da sauran su tace mace ta zauna hannun ta fari tas gaba haka beyi ba, menene zai banbanta ki da namiji indai bazakiyi irin wannan adon ba. Wannan ne yasa Salma ta kulla abota da lalle da kitso haka zalika ta koyi zama da lalle. Kafin ta shigo falon taga takalmin Shatima kofar dakin haka kuma kamshin turaren shi ya daki hancinta,ta dubi jikinta ko Ina babu makusa,data tabbatar babu makusa ta shige falon,kofar daya fuskantane ya yi kyau cikin farin boyel tamkar matashin saurayi,babu wanda zai kalleshi yace ya ajiye mata har hudu bare ya'ya. Salma tayi saurin dauke kai ta dubi Hajiya Kaka wacce ta tsareta da idanunta duk da dai suna cikin gilashi mai karawa ido gani, Salma Yarinya ce mai hattara zamanta a gidan Kaka ta gama sanin wacece Kaka domin ko kallon ta Kaka ta yi tana iya tantace mai kallon yake nufi da haka kai tsaye ta wuce cikin daki domin ta fahimci kallon da take mata kenan,tana gani ne taga ina zataje kuma wacce karba zatayi wa Shatima? Ganin ta shiga dakine Kaka ta maida kai gurin Maryama "bani ruwa nasha," Shatima wanda yabi Salma da kallo har sai da ta shige daki sannan ya kalli Kaka dan girman Allah kiyi hakuri gani nazo da kaina na kawo kaina da kafufuna" tace Ni awa? Na isa mutum ne ai dana isa mutum da kazo har kiranka fa nayi amma tunda hakan ya yi ai babu laifi,sau nawa ne ban kiraka ba, yanzu da kaga ishara ta sauka a cikin gidan ku shine zakazo? Banida tacewa ai katashi kaje idan matar taka taga zata iya to shikenan." Shatima yace "wallahi ba kin zuwa nayi ba, Hajiya ce tace lallai kada nazo, shiru ya yi kamar yana dana sanin abinda ya fada. Ta kalli Maryama "tashi kije ciki," Maryama ta fita Kaka ta kalli Shatima "Amina ta hanaka zuwa?" Babu laifi ban tsammaci haka ba, amma banyi mamaki ba dan itama ta dauke kafar ta a gidan nan,tun daga lokacin da nayi magana babu laifi, yanzu ka tashi ka tafi,sai ranar da tazo da kanta kuma ta hakura saina maida ita. "Kaka nasan yanzu ko naje nace mata tazo ba zatazo ba, inason matata wallahi" Kaka tace" kaga karka bata mani rai idan ni bazakaji maganata ba ubanka zaiji magana ta, abinda nace maka kenan ka tashi ka bar mana gida. Shatima ya mike " kiyi hakuri hajiya Kaka zanje insame ta kuma zan dawo. Yana tafiya Kaka ta kira Salma tace " wallahi kuma sauran idan ya dawo idan yace kiyi hakuri ke kuma kice kin hakura babu wani kamewa balle aji zakiga me zan miki, Salma tace "to shikenan shiyasama daya shigo ko Zama a falon banyi ba. Kaka tace" ya rage naki, amma ai kin kafeshi da ido ko? Salma tayi dariya ai ban masan ina kallon shi ba Kaka. Madallah shiyasa nace yana zuwa kada ki mashi abu kamar sakarya. Bayan magriba Salma tanata juya hannun ta cikin tuwon dake gabanta ta kasa ci duk da dai rabonta da abinci tun karin safe da tayi,yau tuwo miyar kuka sukayi ga manshanu ankawo masu kuma ga yajin jego na Badi'atu nan da ta haihu ankawo, amma dai ga tuwon a gabanta ta kasa ci. Kaka ta dubeta a karo na uku sannan tace kinga idan kin koshi dauke tuwon nan daga nan ki maidashi,da rana ma ina kallon ki kin kasa cin abinci,mijinki yazo kinganshi shikenan kin rasa natsuwar ki, "tace haba dai Kaka cikina ne babu dadi amma ba danshi bane" Kaka tace" matsalar kice kuma wannan" ko komawa kikayi idan jikinki babu Kumari shikenan bazaki burgeshi ba,danshi namiji da kike ganinsa in mace ba lafiya amfanin ta kadanne a gurinsa." Salma ta soma tura tuwon badan tanajin dadin shi ba. Ga mamakin su sai sukaji sallamar shatima,da sauri ta tashi tabar tuwon tayi daki a ranta kuma tace yau lahadi gobe kuma litinin ko da safe zai wuce Abujan ne?. Shatima ya zauna inda Salma ta tashi ya kalli Kaka "don Allah Kaka kiyi hakuri kiman duk hukuncin daya dace dani amma ki bari intafi da matata." Ban hanaka tafiya da matarka ba ai gata can,cewa fa kayi uwarka bata sani ba dan haka sai ta sani" yace "ai ta sani yanzu gurinta na dawo duk tayi ladama." Hajiya Kaka ta yi dariya tare da cewa "lallai kam ai batayi ladama ba kuma bata gane gaskiya ba data gane annabi ya faku daba haka ba data tako tazo da kafar ta nan gidan". Shatima ya tashi ya koma gurin tuwon Salma "Kaka inje inyi magana da ita? Kaka tace "banason insake jin wani magana daga bakin ka akan tsakanin ka da matar ka.bana bukatar inkaraji,in kuma ba haka ba ranka zai baci idan har uwarka tazo naji dalilin ta to shikenan,idan kuma batazo ba banji hujja ko dalilin ta ba,billahil azim saidai ka bama Yarinyar nan takardar dan ba rasa masoya tayi ba,kaji bayanina wannan shine hujja kuma magana ta ta karshe da zanyi maka." Ya mike "bari inyi magana da ita kafin Kaka ta bashi amsa ya shige dakin hannun shi dauke da kwanon tuwon ta. Kaka ta bishi da kallo tana fadin " daka dauki tuwon ka bita dashi dura mata zakayi? Be tankaba ya shige dakin, Salma tana ganinshi ta fada bandaki ta kulle,ya ajiye tuwon yaje bakin kofar yana fadin "don Allah ki bude muyi magana wallahi inason ki Salma ke kadaice matsala ta a yanzu bana iyayin bacci,bata tanka masa ba kuma bata bude ba. Kaka kuwa tana nan ta cika tayi dam tana jiran Shatima ya wuce su kwasheta da Salma,don a zaton ta Salma ta shantake suna hirane da Shatima shiyasa ma dataji shiru tace "Maryama zo ki kamani muje dakin nan. Suna shiga kawai ta ganshi tsaye kofar bandaki,yace "don Allah Kaka kiyi hakuri kisa baki ta bude,duk tsawon lokacin nan tana bandaki taki fitowa." Kaka tace" Maryama kai tuwon nan kitchen ta dube shi "da Allah malam ka fitar man a daki kwanciya zamuyi lokaci na tafiya" "Indai bata fito ba wallahi nima sai dai in kwana a nan,da taga da gaske yakeyi tace "ka fitarman kaje falo ka kwanta amma badai a dakina ba" "Kaka don Allah ki taimaka ko magana tai mani" Malam bakaji nace maka dare yayi bane,kar in sake juyowa nan insame ka". Daya tabbatar abin ba zaiyi masu da kyau bane ya tashi ya tafi. .......... [8/25, 09:01] Ummi Tandama😇: 📚4️⃣ Page 19 Salma ta fito taci kuka idanunta sunyi jawur Kaka tace"kukan na menene? Wato sonshi kikeyi kenan? Saboda na hana ki kibishi kike kuka" Salma tace" Ni ya rabu danine kawai matsala ta" Kaka tace "babu batun rabuwa a auren nan,nafison ki tabbatar da yana sonki tukunna,ta share hawaye" niban ya so yake ba" Kaka tace "zauna nan kiban aron hankali ki,nan ta zauna ta lankwashe kafafunta kamar me zaman cin tuwo tace "Salamatu kefa macece kuma yar zamani taya za ayi nida nike tsohuwace ni zan koya maki yadda zaki fahimci mijinki yana sonki ko baya sonki," Salma tace"Kaka ba gashi ba duk da ina yar zamani ke kika koyaman zama da miji da kuma zama da kunshi da kamshi,girki na musamman da komai,ada kam idan nayi kitso yana jimawa kin koyaman girkin gargajiya da sauran abubuwa nawa kika koyaman" Kaka tace"mu duk juma'a zamuyi lalle da kitso abinci na musamman,turaruka kala-kala kuma muda muke ya da,ne yadda zaki gane mijin ki yana sonki ta hanyar kula dake da damuwa da damuwar ki,inkunada yara ya kula dasu,kuma idan yanada hali ya sauke duk nauyinki dake kanshi,kinsan wani abu? Mazanmu na hausawa suna fadin "inasonki"Ina sonki" a fatar bakine kawai kafin ki shiga gidan sa,kina shiga ya dena wannan kalamai na soyayya da yake maki a waje, lokacin da kauna zatayi aiki sai kuma hakuri ya biyo baya,daga nan zai wofintar dake kamar yadda Shatima ya wofintar dake na tsawon lokaci, wannan ne yasa nayi tunanin ba sonki yake ba kamar yadda ya fada a baya. Shatima bai cika karya ba,don haka na yarda da maganar daya fada na cewa yana sonki, Hajiyarsa ce kawai tayi haka amma na yarda mijinki yana sonki sai dai kuma inason mahaifiyar shi tazo da kantane domin inji dadin jan kunnenta kuma kema kina soshi na sani tun ba yau ba,tun lokacin da kuke yawan waya dashi nasan da haka. Salma tace "Kaka ni banida tabbacin ina sonshi ko kuma son da yake yiman gaskiya ne". Kaka tace" abinda kikayi yau shine ya tabbatar da cewa kina sonshi,yini guda kinkasa cin abinci tunda ya shigo, sannan inason daga yau ki dena kwanciya bayan kin kaini nayi alwallah saboda sallar dare yanada matukar amfani kema ki rinka yi,Kiyita addu'a Allah zai daidai ta tsakanin ku dashi, Salma tace "insha Allahu Kaka daga yau zan kula. Washegari litinin Salma sun tashi karfe uku daga makaranta,ita da abokanen karatun ta su uku daya namiji daya mace duk yan unguwar su ne tare suke dawowa,suna cikin tafiya suka Salma ta tsaya cak Hauwa'u tace "muje mana Salma" ga mamakin ta sai taga Salma tana kallon wata mota. Shatima ne ya fito da kananun kaya juns da rigane mai ruwan kasa wandon baki,ya yi kata kwarjini sosai,ya nufo Salma,ta kauda kai gefe yace "muje zanyi magana dakene" tace "babu inda zanje" Wanda suke tare dashine yace "malam lafiya?" Shatima ya mika masa hannu tare da yi masa sallama suka gaisa, sannan yace "matatace" Hauwa'u da haruna suka kalli juna, sannan suka kalli Salma da sauri ta daga masu kai da alamun hakane,to shikenan sai anjima. Suna tafiya Shatima yace "shiga inkuma kinki zama zan daukeki da kaina wallahi," ta danja da baya sannan ta soma tafiya cikin sauri yabi bayan ta, "wai me kike nufi ne?" Tace "don Allah ka Bari inyi tafiyata". Yasha gaban ta tare da rike mata hannu "Salma a gaskiya bari kiji tukunna, zuciya ta bazata dauki wannan wulakancin ba,kuma inason ki sani bazan taba sakinki ba haka zalika kuma hakkina bazai barki ba,na kasa komawa Abuja gurin aikina saboda ke,na yarda na rasa aikina saboda samun farin ciki na,ba komai bane farin cikin ba kuma sai ke,kada kibi zan cen Kaka batasan yanda nikeji a zuciya ta game dake ba. Salma tace"don Allah kaga humm,ko sallar azahar banyi ba" Muje na kaiki gidan to,babu yadda zatayi dole taje suka shiga motar bata ankara ba sai taji ya rungume ta tsam a kirjinsa,mutsu mutsun da takeyine alamun ya barta,amma be kyaleta ba,ta kasa furtawa,ya dago fuskar ta, "Ina sonki Salma" "Ina sonki Salma kinji na rantse maki da girman Allah mahaliccina ban tabajin so me kona zuciya ba sai lokacin da kikabar gidana" da alamun na jima da sonki batare da nasani ba" Ta sabule daga jikinshi"naji ka kaini hanyar gida na tafi" Yace "har gida zan kaiki," ta soma masa magiya don Allah ka saukeni kafin gida, Kaka zatayi zaton ko nicema nace maka kazo" "Zan saukeki har kofar gida,sai dai bazan shiga ba" kina jin yunwa muje gidan cin abinci tukun. "Banyi sallah ba ka bari zanje gida naci" Kaka tasan lokacin da nike dawowa idan najima zansha tambayoyi" Shikenan wannan dalilin yasa bandamu ba dakike gurin ta nasan zata kular man dake,ya tada motar suka soma tafiya,kadan-kadan yakan kallo ta, kallon shi itama take dadi kawai yakeji kasancewar su a tare yace "Salma kin canza baki daya kamar ba Salma tah dana sani ba mai girmama ni take kuma shakkata" tace "ai yanzu kuma komai ya ruga ya yi maka nisa,na koyi rashin kunya ba kadan ba". Tunda kika zama yar jami'a nasan kin kara wayewa da gogewa kin kara kyau ba kadan ba gaki da kamshi na musamman gashi kin iya gayu inajin kishin lallen nan ba kadan ba haka kike tafiya mutane sunata kallon ki,ta kalli lallen ta dubeshi, "yayi murmushi ina kallon sona fa a kwayar idanunki Salma kina sona" Ta maida kallon ta kan titi "ni bansan wani so ba iya gaskiya ta kenan" Yakai Hannun shi ya damki hannun ta "ki bani dama na koya maki yadda akeyin son" ta sabule hannun ta daga nashi Yaya ka lura kada ka wuce gidan. Ya rage tafiya tare da fadin kai harmun zo ne? Nayi mamakin saurin mu, ta kama kofar zata bude yace Salma "don Allah kiman wani abu dazan rinka tunowa dake idan na tafi matata" lumshe ido tayi sannan ta bude cikin shagwaba tace "nagaji fa gashi na gaya maka banyi sallah ba" hakan ma ya yi nagode shagwabar ma inaso,bude motar tayi ta fita ya bita da kallo wani kara sonta da yaji kamar kada ya tafi,saida ta shige sannan ya tafi. Shatima ya samu Alhaji ya fada mashi yadda sukayi da Kaka yace Alhaji yasa Hajiya taje gidan Kaka dan Kaka tace sai Hajiya taje da kanta tukunna. Alhaji yace to zasuyi magana daga baya, yanzu da akan maganar Badi'atu ne mijin be zo ba bare ta koma tunda dai taji sauki gwara kawai asan me ake ciki, Shatima yace "Alhaji kada dai asake a maida ita kabari sai sunzo da kansu . Alhaji yace"munyi magana da Babanka Musa zai kira waliyyin yaron aji manufar su" Shatima yace "to ayi hakan don inson samu ne gwara ya bata takardar ta, Alhaji yace "aishi aure raine dashi babu kyau mutum ya yi sanadiyar kasheshi inhar Allah ya kawo karshenshi shikenan," Shatima yace"to shi bari ya tafi,yana shiga gurin Hajiya tace "mai yasa yau be tafi Abuja ba tunda yau litinin ne? Yace shifa a gaskiya so yake matarshi ta dawo. Hajiya tace"to kaje mana aini tuntuni nabar wannan zancen, Shatima yace "amma dai kinsan Hajiya Kaka bazata yarda ba sai kunsa baki dan sam taki yadda, Hajiya tace"shikenan zamuyi magana da Alhaji. Ya shirya yana isa kaduna ya tadda Aliya ta cika tam,yace "lafiya" tace babu komai sanin cewa Shatima kan shiga damuwane lokacin daya ganta cikin damuwa,yasa tayi hakan, amma ga mamakin ta sai taga kawai ya shashantar da ita ya cigaba da harkokinsa ko kula beyiba. Ta lura ya shiga bandakinta sai ta dauki waya tanayin wayar karya zuwa a matsayin Madina kawarta,Madina dazun muna magana dake katin ya kare,inason fada maki Salma ta kirani tana zagina harma da boye number wai mijin da muke takama dashi gashi nan yana binta kuma bazata dawo ba saiya........ Tayi saurin sauke wayarne domin taga Shatima wai a dole bataso yaji,ya dubeta wacce Salma ce ta zageki? Ta sunkuyar dakai banso kaji wannan zancen ba. Ina sauraren ki fada mani? Ta soma zubda hawaye "Salma ce ta kirani tana zagina tare da fadaman maganganu akanka" yaushe ta kira ki? "Dazun da misalin karfe uku" Shatima ya tsurawa Aliya ido cikin mamaki yace "muga lambar data kirakin?" Ta tashi da sauri ta dauko wayar ta nuna mashi wani kiran da akayi babu suna ya duba lokacin uku saura minti biyar ya gani,tabbas kirane babu lamba to amma bazai yarda Salma ce tayi ba don ya duba tsawon maganar da Aliya tayi kusan awa daya ,inhar ya yarda Salma ce ta kira uku sauran minti biya sun kusan dauki awa daya suna magana kenan,har lokacin daya dauki Salma karfe uku da minti na kenan har lokacin suna wayane har zuwa lokacin dayaje ya ajiye ta hudu saura ya tafi masallaci kafin yaje gurin Hajiyarsa,yasake duban Aliya wacce ta tsareshi da ido tana kallon irin nazarin da yakeyi kuma tanason jin yadda zai dauki abun. Ba Salma ce ta kiraki ba kidai tuno da kyau, Aliya tace haba Baban Abulkhairi Salma ce ta kirani nafasan Salma yau muke tare ne? Kuma ga ma abinda ta fada,yace ai lokacin da nagani din domin a wannan lokacin muna tare da Salma kuma babu wanda ta kira haka zalika babu wanda ya kirata. Tayi shiru cikin mutuwar jiki "Salma ce nidai abinda naji kenan,na rasa gane kanka duk ka canza kana zaton zan maka karyane ko zanyiwa Salma sharrine ko kuma me kake nufi? Ta soma kuka na rasa wadda keson shiga tsakanin yarda da amanar dake tsakani na da kai. Shatima cikin takaici ya saki murmushi sannan yace "banason na nuna maki na gane duk makirce makircen da kike hada mini saboda banason na kunyata mutum,naso mu tafi a haka amma nasan matsayin dana ajiyeki to kisani na lura cewa shi makaho idan ba ka zungureshi ba bazai San ana kallon shi ba,Dan haka ayau zan faiyace maki komai ko Allah zaisa ki dena ki gyara halinki,Aliya naji kunya sosai lokacin dana fahimci kece kike rura wutar tsana tsakanin Salma da Hajiya a lokacin da naji haka raina ya baci sosai sannan duk sirrin gidana yana kunnen Hajiya ta a cikin salonki nason ki hadani da ita haka zalika kina rura wuta tsakani na da matana ta irin sigar da bazan iya fahimta ba,sai dai kuma kin manta cewa Allah baya zalinci kuma duk daren dadewa zalinci baya dorewa kinyi matukar bani kunya kin zubar da girman ki da kimar ki wadda kullum nike kallon ki da ita,amma inaso ki sani ina fada maki wannan abu guda dayane na karshe tsakani na da matana babu saki babu wani abu har abada,hardake da kike wannan aikin saidai kowacce daga cikin ku da matsayin da zan dorata akai ke a halin yanza kin riga kin sauko daga matsayin dana baki saboda kin zubar da kaso tamanin da biyar cikin kima da mutumcin ki a gurina,saura dame ki tarairayi na gurin abokan zaman ki suma kin Bari ya zube dama shi mutumci madara ne,idan ya zube baya dibuwa, sannan ban karbi wannan sharrin da kikayiwa Salma ba abu na karshe kuma dazan fada maki shawara ce dazan baki ki dakatar da abubuwan nan da kikeyi domin bazasu kaiki ga nasara ba,in kuma kin cigaba to ke zaki barbadar da ragowar kimar taki. Aliya cikin kuka ta durkusa tare da cewa don Allah ka yafeman" don Allah kayi hakuri ka yafeman ka cigaba da kallo na da mutumci na ka maidani matsayi na,na tuba bazan kara ba. Shatima yace"bazan maki alkawari ba idan dai kinyi niyya kin taimaki kanki to shikenan" ta fashe da kuka duk tsananin son da nike makane ya kawo man haka,ya yi murmushi yace so bazai sa a cutar da masoyi ba Aliya,ya lumshe ido ya tuno lokacin daya ke ganin sonshi tsantsa a kwayar idon Salma, ajiyar zuciya ya yi zan tashi zuwa Abuja komai daren dadewa Amna bata dawo ba ina bukatar ki hadaman kayana yanzu,yasa kai ya fita ya barta cikin nadama da bakin cikin abinda ta aikata. Duk kwanakin nan Shatima jinshi kawai yake kamar wani sabon matashin yaro shekarar shi ta farko na shiga soyayya na kuma balaga,ko yaushe ya zamana cikin tunanin Salma yake,domin ko yaushe hirarta yakeyi bashida wanda zaiyi hirar nan dashi sai munnir amma kuma Munnir din yana nuna zancen Salma ya isheshi,domin ko karatu ne yaci ace ya haddaceshi,tunda dai kullum abu daya ake nanatawa ya zanyi ya zanyi indawo da Salma? Munnir Salma ta waye intana magana sai naga kamar wata sarauniya. .. [8/25, 09:04] Ummi Tandama😇: 📚4️⃣ Page 20 _____Munnir Salma ta waye intana magana sai kaga kamar wata sarauniya,saita zabi kalmomin da zatai man magana dasu,a halin Yanzu haka shatima yafi ganin kusancin Abuja zuwa Zaria fiye da kaduna zuwa Zaria,dan haka inda mota yazo yakan wuce riga cikun ya isa Zaria yaje gidan Kaka kodama ace Salma bazatace mishi kalaba hakan ya fiye mashi sauki. A bangaren salma ma itama haka abin yake bata dare takeyi wajen tunanin Shatima ta gama yarda cewa tana son shi sosai,a kowanne lokaci tana sauraren kiranshi ko zuwanshi ko da bazasuyi magana ba,bugu da kari ga tausayin shi da yake ziyartarta tana tausaya mashi akan zaryar da yakeyi wadda har yasa ta soma ganin zafin Kaka ya yi yawa da taki sauka daga kan kujerar nakin data hau saidai babu halin ta nuna haka domin itace dama ta sama mata yancinta,wanda ada ta kasa samu,shawara daya kawai data bawa kanta shine mikewa da addu'ar ta don Allah ya yayyafawa abin nan ruwan sanyi,dan tayi azumi a dakin ta. Kaka ta kalli Hajiya da Alhaji da suka iso, sannan ta cigaba da kontale-kontalen bakin dake jikin goron ta Wanda ta dauka zataci, Hajiya ta sake cewa,"Kaka dan girman Allah kiyi hakuri wallahi Kaka kunya ce ta hanani zuwa inda kike,nasan nayi laifi megirma mai yawa amma ni matarsa Aliya ce taketa izani itace take duk abubuwan nan,itace take kirana tana fadaman abubuwa game da Yarinyar nan, amma tun tuni na watsar da batun iyalanshi." Kaka bata tankaba, Hajiya ta dubi Alhaji,tace "Alhaji don Allah kace wani abu mana,kasa baki don Allah ta yafe mani". Alhaji ya saci kallon Kaka sannan yace "Ni kuma me zance,nifa rakiya kika rokeni kuma na rakoki alfarmar dai da kika roka kena na rakoki saboda kinajin kunya,nifa tuntuni Kaka tayiman gargadi akan cewa incire bakina a wannan maganar." Kaka ta danyi murmushi irin nasu na manya domin jin dadin wannan dubara da Alhaji yayi, sannan tace " uhum,,,to yanzu dai maganar dake tafe daku kai tsaye zakiyi mani. Hajiya tace " hakuri za ayi Kaka dan Allah Salma ta koma dakinta,Kaka tace "to ai bani bace Salma ko baki ganine, itace da magana in ta hakura zata koma shikenan" Hajiya tace"don Allah Kaka ki taimaka ayi hakurin in kikace ta koma bazatayi musu ba a kirata inyaso sai nima na kara bata hakuri saboda ance durkusawa wada ba gajiyawa bane dan ka durkusa ba zaisa ka tashi ba tsawo ba zaka tashi da tsawon ka." Kaka tace "yau ne kikasan da haka kenan Hajiya Amina,ta cigaba da cewa gaskiya Hajiya Amina kin bani mamaki matuka a rayuwa,na zaci zaki rike surukanki kamar yadda na rikeku a iya zaman da mukayi dake na taba cutar dakene?." Hajiya Amina tace " wallahi ba ko daya" "To ke meyasa zaki cuci Yar mutane? Me yasa zaki nace sai ansaketa? Shiyasa gashi kema kinaji kina gani aka gasa maki Yar taki gatanan har yanzu ke da kanki bakisan matsayin taba,matar aure ko bazawara,ga kuma abinda mijin yake maku na wulakanci". Hajiya Amina tace hakan dana gani kuwa naga ishara ganin idona,jiya Safwan ne ya turo lawyen shi suka kai maganar kotu,shine da akayi masu sammaci,tare da takardar saki suka hado, Safwan yazo yace sai anje a kamomin mijin,nida Alhaji muka hanashi,tunda ya saketa shikenan,ni yanzu banason wani tashe-tashen hankula aje a debo mata kayanta kawai." Kaka tace"Allah ya kyauta,ta daga murya tace ke Salamatu!! Salma kuwa data kasa kunne domin taji me ake fada,amma bataji ba saboda tazarar dake tsakanin falo da daki,ta amsa tare da tahowa sanye da hijabinta,ta durkusa cikin jin kunya tana gaida surukan nata duka, Hajiya tace matso kusa dani yata zonan. Saida ta kalli Kaka tukunnah,Kaka tayi mata alama akan taje don haka ta matso, Hajiya ta janyota jikin ta ta rungume tace "Salma kiyi hakuri ki yafeman,kiyi hakuri kinji kiman uzuri hakan bazai sake faruwa ba." Salma cike da jin kunya tace Hajiya ai uwa bata laifi a gurin ya'yanta bantaba kallonki a matsayin me laifi ba," Hajiya tace" duk da haka ki yafeman,ki furtaman kin yafeman kinji? Salma tace " na yafa maki Hajiya nima ki yafeman?." Alhaji yayi caraf yace " haba Yarinya aike bakiyi laifiba sam-sam. Kaka ta sake yi masu doguwar nasiha game da cusa kai a lamarin surukai da akeyi Wanda a cikin lamarin ya'yansu insuna haka beba. Harma tai masu bayani da irin aurer raki da ake rasawa akan wannan kutse da uwar miji takeyi Wanda bazasu lissafu ba aurar rakin da suka mutu akan hakan, sannan tace suje gida su turo mata Shatima domin biyan diyar jinin daya zubar na Salma. Hajiya da Alhaji saida suka dara cikin raha sannan suka kara bawa Kaka hakuri,sun bata hakuri sosai Hajiya ta bude pose din ta ta ciro kudi ta sama Salma a hannu ta damka mata sababbin kudi. Salma tace "ki barsu Hajiya," Hajiya tace Ina bazai yiwu ba ki karba kawai, Salma ta amsa tare da godiya,suna tafiya Salma ta mikawa Kaka kudin, Kaka tace " kudin nan nakinefah bazan amshesu ba" Salma tace "nifa inada kudi wanda Safwan ya turoman a account dina, Kaka tace "banace ki ciro kudin ko dubu dari biyune ki siyawa iyayen ki fili,ko da baki samu damar yi masu gini ba,nasan Yayanki zai zaigina masu, mahaifiyar ki ta wuce ta zauna a gidan haya yanzu." Salma tace to Kaka mai zai hana ayi amfani da kudin har wajen tada masu da gini koda ciki daya ne," Kaka tace shikenan,sauran saiki gyara dakinki tunda kema kinjima bakyanan a dakin,kin dai sa bazaki ganshi da kan gado ba" Salma tace to shikenan,nidai ki rike wannan," To bazaiyiwu na rike ba ranashi biyu kiban rabi," dubu biyar ne kudin don haka ta dauki dubu biyu ta bawa Kaka sauran. Kaka tace Salma yau dai ankasa bacci dan murna. Maimakon ki bata dare cikin damuwa mezai hana kita sallah kina kai kukanki wajen Allah ya maido maki da mijinki,yau kuma sai kiyi godiya ga Allah tunda gashi ya dawo maki dashi" Salma ta sinne kai cikin cinya tana dariya,itama Kaka dariya tayi tana fadin "ja'ira ina hankalce da cewa ai kema kin kosa ki koma gidan mijinki duk da haka shawara daya dazan baki kada ki nuna masa dakinki ki bisa a sannu,kuma ki sani yanzu tamkar sabuwar rayuwa zaki fara ki canza daga wancan zaman da kikai dashi kinsan kowacce mace da irin nata salon,kije da sabon salo kema macece da baki bukatar saina kara maki wasu bayanai na yadda zakiyi. Salma tace"Kaka insha Allah zan kokarta akan hakan,kiran Shatima ne ya katse hiran nasu, Salma ta dubi Kaka kingan shiko har yaji yazo kenan. Kaka tace "amsa mana" Salma cikin salo da karya harshen da batasan ta iyaba a duk lokacin da zatayi waya da Shatima dagawa tayi tare da sallama,ya amsa tare da fadin Salmatah bawa Kaka tukunna nayi godiya" Gata nan ma a kusa ai ta mikawa Kaka,ta amsa suka gaisa yanata zuba godiya Kaka tace " ka dena godiya har yanzu da sauran matsala domin zuwa zakayi sai ka biya diyar jinin daka zubar mata kafin nan inba haka ba kuma matsala ta dawo sabuwa,yace aiko Zan biya Kaka,Zan biya bandama aiki yayiman yawa da gobe zanzo, amma juma'a ina tafe" To Allah ya kawoka lafiya ta mikawa Salma wayar, Salma ta tashi ta shige cikin daki a dai-dai lokacin da yake fadin" ki tashi kusa da Kaka" tace na riga na shige daki,yace "Yauwa Salma ina cikin farin ciki nasan yau bazan iya bacci ba,ki shirya Ina zuwa zamu dawo," Salma tace "mu dawo ina!?" "Gidana mana" "Humm tace ina saina gyara dakina zan koma" "Salma gidan nan baki daya fah zan saka a sauyashi ayimasa fenti za a gyara miki tun kafin ki dawo" Tace "na sani,to zan sayi sabon gado tukunna da sauran abinda banidashi da kudin nan,ta fada mashi yadda sukayi da Kaka" Yace "hakan ma yayi,sun jima suna hira Shatima yana nuna zakuwa tare da kosawa akan kasancewar su tare. Duk matan Shatima sun sha mamaki da sukaga rana tsaka antashi ana gyaran gida tare da gyaran duk wani abinda ya lalace. Ranar alhamis Salma sukazo kaduna itada Yaya Hadiza da Maryama inda suka samu wata Yaya Salma tayi masu jagora,sai da tasai gadonta na dubu dari da hamsin da talabijin da karamin firij da sauran tarkace irin na mata Wanda baza'a rasa ba,sukaje suka gyara dakuna tsaf na Shatima ma tasa masa sabon gado ta dora katifarshi akai daya dakin kafet,bayan sun gama suka maida komai suka rufe sannan suka fito suka fice har Salma. Washe gari juma'a Salma gidan kitso da lalle ta wuni,annashuwar da takeji tamkar yaune ranar auren ta ga wani son Shatima da take karajinsa a zuciyar ta,bayan juma'a ta dawo gida,tana fitowa daga wanka Kaka ta miko mata wata kwalba tare da fadin gashi nan kiyi wannan kisa gawayi a kasko ki hura kiyi turaren nan inason ki tsugunna akanshine a kalla dai yadan kai koda second gomane ko fiye da haka,sai ya kare ki tashi. Salma tayi yadda Kaka tace kamshin turaren duk ya shige ta ta ko'ina. Da magriba tana shafa mai kawai sai ga sallamar shatima,ya zauna a wajen Kaka suna hira,dan tace Salma na wanka, Salma ta fito cikin bakar doguwar riga da mayafin ta,tun kafin ta karaso Shatima kejin kamshi wanda a hankali yake ratsashi, cikin girmamawa ta gaidashi. Kaka tace "Kawo masa abinci mana" "Kaka na koshi nazone kawai mu tafi," Kaka tace" ku tafi ina? Bata sallami innarta ba,kaje saidai gobe kazo ku tafi. Yace" Kaka na kwana dai zakice inyaso gobe mu tafi shikenan" Tace "Ina" banason musu dakai ka koma cikin iyalanka ka kwana inma a kaduna inma a zariya matsalar ka amma bazata tafi yau ba. Dole Shatima ya yi hakuri domin ya fahimci cewa in yace zaiyi gardama matsala zata tashi,yana kallon Salma be samu damar kebewa da itaba. Bayan tafiyar shine Kaka tace ai baki gama turaren ba tukunna kuma ka'idarshi sai kin gama ba ason ko hannun ki miji ya rike. Washegari tun asuba Salma ta soma turaren ta sha biyu ta gama, Kaka tace "to ko yanzu yazo zaki iya tafiya,kudi na kashe a ka kawo turaren nan, Salma ta idarda sallar azahar taci abinci ta sheka kwalliya da sabuwar atamfar data dinka,kayan sun bi jikin ta dinki ya zauna a kafadarta gwanin sha'awa. Kaka tace Salamatu kin zuba kyau fah, Allah ya kafaki a gidan ki zauna lafiya da kishiyoyin ki, zuciyar ki daya domin na fuskanci babu ha'inci tare dake Salamatu,a zaman mun nan baki taba wani abuba,baki taba gundurata ba ga biyayya ga hankali,in Shatima ya fahimceki nasan zakuyi zama mai cike da amana da tsafta. Salma tace" Kaka nima naji dadin Zama dake na koyi abubuwa da dama ga tarbiyya kala kala, Kaka Allah ne kadai zai biyaki........ Sallamar da Shatima ne ya ratso gidan Maryama wacce ta fito daga falo ta amsa ta bishi da kallo ya yi matukar kyau a cikin yadi mai ruwan kasa wanda layinshi ke nuna tsadarshi,kamshin sane ya bude ko'ina, Maryama ta juya da sauri tana fadawa Salma cewa kinga Yaya Shatima kuwa tamkar wani ango ya yi kyau sosai. Salma ta kosa ta ganshi lekowa tayi ta zubamashi ido,kallo juna suke har saida Kaka tace "to Ina wuni? Shatima yadan zabura ya dubeta da sauri " Kaka kiyi hakuri don Allah" yahau hannun kujera suka gaisa,yace Salma tazo yakaita ta sallami su Inna,Kaka tace sai sun dawo . [8/26, 01:59] Ummi Tandama😇: 📚4️⃣ Page 21 Tana shiga soran da zai fiddasu waje, Shatima ya rungume ta tamkar zai maida ita cikin jikinshi don kauna yace "Salma wannan kamshin naki tun jiya nike jinshi har cikin bacci na,ta shafi kumatunshi,muje kada wani ya shigo ya ganmu," iya daukarki na zagaye garin zaria da ke a hannu na,in gwada masu ke tawace. Salma tace"mu tafi kawai" a cikin mota Shatima da hannu daya yake tuki dayan na rike da hannun Salma ya gamesu guri guda,jefi-jefi saiya kalleta ya yi murmushi jiyakeyi kamar su biyune kadai a rayuwar duniyar nan gaba daya, Salma kallon Shatima takeyi tana yiwa Allah godiya da baiwar da ya yi mata na samu miji mai tsananin sonta,irin mijin shiga taro,bawai mugun kyau Shatima yake dashi ba amma akwaishi da iya wanka ga kwarjini gashi yanzu yana samun kudi hankalinsa ya kara kwanciya,a gidan Inna suka jeru Dan ma Salma takine da hannun ta yakeson ya rike, Inna ne take yankar kubewa taji sallamar su da sauri ta fito daga kitchen tana fadin,sannuku da zuwa. Taji dadi sosai da ganin su da tayi kuma tayiwa Allah godiya. Shatima yace"munzo yi maku sallama ne,tayi masu nasiha sannan suka mike suka nufi gidan su Hajiyan Shatima inda suka sameta a falo zata nufi kitchen ta tsaya da fara'arta wacce Salma tasha mamaki,har kasa tabi Salma inda ta durkusa ta kamo hannun Salma tace "tashi-tashi yata ta sakata jikinta ta rungume ta tare da fadin "Allah ya yi maku albarka" Badi'atu ta fito da murnar ta taja Salma sukayi daki daga nan suka balle da hira, Badi'atu tacewa Salma "akwai wasu magunguna da aka kwaso a kayana Zan kawo maki har gida, Salma tace nifa banma taba shansu ba,ko lokacin aurena ma,na banyi wani abuba,kuma bansan ya zanyi dasu ba. Sun jima suna hira kafin suyi bankwana su fice sunje sundebi kayan Salma tana kuka domin batason rabuwa da Kaka,Kaka ta mike cike da kewar rabuwa da Salma,tace "Shatima ka kula da Salma,ka kula da ita sosai yarinyace mai biyayya da girmama mutane gata da shiga rai,idan harka kuskura ka cutar da ita ko ta dawo gidan nan ta kawoman kararka,hummm,,,, Shatima yace"insha Allah zan kiyaye kuma baki fadi diyyar da za a bayar ba?" Kaka tace"diyyar ta kawai ka kula mani da ita,nan suka rabu da kewar juna,tun kafin su isa Shatima ya tsaya ya siya mata kayan abinci,sun iso ana kiran magriba ta shige dakinta wanda tayi kewarshi a lokutan baya bata zaci zata sake shiga cikin dakin nan da sunan zama ba ko jiya da sukazo gyarashi batayi tsammanin zata kuma dawowa da sauri haka ba. A fili tace "Allah ka kore duk wata fitina da zata taso a wannan sabon zama da zamuyi tayi sallah domin shi ya nufi gurin su Aliya ne. Bayan ta gama ta tashi tana kara kimtsa abinda yake bukatar gyara a dakin, sannan ta nufi bandaki tayi wanka tare da alwala isha'i bayan ta idar ta zauna tana shafa mai, zuciyar ta cike da tunanin cigaban data samu sakamakon karance-karancen litattafan hausa da takeyi,ta tuno da tana kallon karance-karance yadda ta dauki littafin hausan nan duk bata lokacine kawai da shirmen banza, amma haduwar ta da Hauwa'u a A.B.U sai kawai ta jinjinawa marubuta, domin yanzu tasan yadda zata kula da mijin ta,ta koyi abubuwa da dama wadanda mahaifiyar ta ko yayarta bazasuyi tunanin koya mata ba. Tana fesa turare Shatima ya shigo hannun shi dauke da leda,ta amsa kayan marmarine daya siya masu a hanya tana dubanshi "a yanka yanzu?" Yace "bazaki sha bane?" Tace "humm inkasha ainima nasha, cikin jindadi yace hakane "me Hajiya ta zubo mana ne a wannan doguwar cooler? Tace "burabusko ne sai miyar kaji data bani ita tace kwana biyu zanyi ina amfani dashi" Shatima yace"yanzu kin zama 'yar gatan Hajiya fah" Salma cikin wasa tace "to ya son ranka? Yace"fari kar" sukasa dariya. A ranar Salma da Shatima haka suka kwana cikin farin ciki sun raya daren da soyayya ta ma'aurata, Shatima ya yi alfahari da samun Salma cikakkiyar budurwa dama ya zaci haka. Salma batayi wani raki ko nuna wahalar ta game da ranar ta ta farko ba,kuma ta cire kunya ta nuna farin cikin ta tasa mijin ta farin ciki,sosai batare da wani noke-noke ko kunyar banza ba. Washegari tamkar kar Shatima yabar dakin Salma jinshi yake kamar wani sabon mutum ayau. Banda makarantar Salma da kuma yaron shi da yake can Abuja da gaskiya saidai su koma da Salma. Da zai tafi ya shiga dakin Salma,tana shara yace "Salma" ta ajiye tsintsiyar hannun ta ta rungume shi tace "zaka tafi ko?" Zan tafi Salma Ina sonki zanyi kewar ki,ta dubi fuskar shi hawayene a idanunta suna bin kumatun ta. Ya cika da mamaki "Salma menene kuma? Tace yanzun ya zanyi? Banason kayi nesa dani, yasa hannu ya share mata hawaye" ______tare da fadin Salma zakisa inje cikin damuwa kenan don Allah ki dena hawayn nan,tayi murmushi banason ka zauna da damuwa mijina Allah ya tsare min kai,tamkar kada ya barta haka suka rabu cike da kewar jina, Safwan kuwa ko yaushe indai yana gari to yana zarya a wurin duba lafiyar Badi'atu hidima yake mata kawo wannan kawo wancan,tun tanajin kunyarshi saboda kinshi datayi a baya,gashi yanzu yanata fama da hidimar ta,har ta dake ta dena jin nauyin shi ko be mata maganar so ba ta gane kuma tana sane har yanzu yana sonta. Kuma duk da yaga batayi iddah ba,sai dai tana shirye a duk randa ya furta mata kalmar so zata amsa. A gefe guda kuwa Aliya dai kam kima ta riga ta zube ko magana idan zata fadawa Shatima to tana shakka domin taga yanzu duk hirar ta be shafi shi da ita ba to bazaiyi ba ko zancen danta indai ya wuce wannan shikenan,tana dauko masa wata maganar zataga ya yi mata shiru domin shi a gurin shi yanzu duk sauran matanshi sun fita mutumci da kima. A gefe guda kuwa ranar wata asabar a gadon shi na dakin Salma yana danne danne a waya Salma tana cikin kitchen tana yan girke girken ta,ta dora tuwo ta dawo ta kwanta jikin Shatima ya sake janyo ta sosai yace "wai me kike dafa mana ne?" Tace bakace kajima bakaci tuwon semo ba?" Yace "miyar me kikeyi kenan danyar kubewa....wayar shi tayi ruri Amna ce ya daga da sauri domin tun jiya tace mashi batajin dadi. Baban Jafar zazzabi ne ya rufeni fah" tashi yayi da sauri "to bari ina zuwa". Salma ta kalleshi da mamaki ta rasa meyasa kullum Shatima yake rawar jiki akan Amna,ya kalleta tare da miko mata hannu "zo muje ki gaisheta" babu musu ta mika hannu ya kama suka tafi,tanason sanin abinda Amna take masa wanda ke sashi yake rikicewa yake maida lamuranshi haka. Har cikin dakin ta suka shiga tana kudundune kan gado cikin bargo Shatima ya zauna tare da bude gefen fuskar ta yasa hannu a dokin wuyan ta,ta bude ido,suka hada ido kuwa da Salma har suna hada baki kuwa wajen yi mata sannu Salma da Shatima. Shatima yace kinsha magani kuwa? Tace "a'ah" Salma tace"kodai asibiti za ajene Yaya? Yace ina ganin zaifi ma,Amna tace" ka bani parasitamol kila zai sauka, Salma tace "da kin daure munje asibitin" "A'ah ku bani maganin kawai" ta nunawa Salma maganin ta dauko ta mikowa Shatima,ta bude firij ta dauko ruwa,anan ne taga gororin tsumi da suke wani lungu ga gumba, Salma ta yi murmushi dama tayi zargin haka. Tana gani a cikin littattafai, Shatima ya bata da kanshi tasha. . [8/26, 06:35] Ummi Tandama😇: 📚4️⃣ 22 Ta kwanta basu bar dakin ba sai da bacci ya dauke ta, Salma Yarinya ce mai dubara ta samu karin basira a karance karancen da tayi sannan cudanya da wayayyun yan boko yasa ta zama wayayya,girke-girke ta kware sosai dana gargajiya duka gidan Kaka na zamani kuma a karance karancen ta, sannan kuma ta fahimtar abinda mijin ta yakeso da wanda bayaso. Sabuwar rayuwa ta bude a gidan nan nata cikin dubara ta shigewa duk wani daya danganci Shatima tundaga kan matanshi ya'yanshi zuwa danginshi. Azumi ya kankama ga makaranta sai dai cin goman farko da aka tafi yajin aiki duk lokacin jami'o'i na garin an rufe ko kuma ince na kasar saidai dai dai ku wadanda basuda wata matsala a kasar,domin kuma zai wahala ka samu jami'a wacce ta kware ba tare da kaci karo da matsalar yajin aiki ba mai bata lokaci. Salma ta lura da Shatima yanada matsala sosai da matansa biyun nan, wadanda suke cikin gidan nan Amna da kuma Aliya kwarai kuwa tasha mamaki akan na Aliya,batasan ya zatayi ba tasan abune mawuyaci taji a bakin shi,ta fahimci na Aliya ba kadan bane idan yazo ya sauka a dakin ta wanka zaiyi ya fice wani guri inya komo washegari zai sake ficewa. In ya kwana a gurin Amna baya fita sai lokacin tafiyar shi sannan zai wuce,idan ya sake zuwa ita kuma a dakinta zai sauka,haka zalika baya fita har washegari. To kuma ita Amna sai a yanzu Salma ta lura idan yana dakinta baya zama itama,lallai kuwa akwai wani abu tsoronta kardai Shatima ya canza hali. Ya dawo da safe bayan sunyi sallah da karatun qur'ani sun koma sun kwanta,sai Salma taji wayar Shatima na ruri bata motsa ba dan tasan shi dinma yanaji. Yana dagawa sai taji yana gaisuwa cikin girmamawa tace a ranta kamar Alhajin sa sai kuma ya tashi daga gadon yana tafiya daf da fita tare da fadin Dady ba haka bane,bansan Amna da karya ba sai dai in yanzun zata fara tunda idonta ya rufe tanason cutar dani. Wancan karan Dady kun saka baki akan maganar tsarin iyali na hakura Dan bana jayayya da iyayena,tana ta tsarinta don nidai naira ban bayar ba kuma banida niyyar bayarwa sai gashi Allah ya nuna ikonshi duk da tsarin iyalin da takeyi sai da ciki yazo. Shine takeson ta zubar dashi in bata tsoron lafiyar ta ni inason cikina,wallahi Dady na fada mata gaskiya ne komai zai iya faruwane idan har ta cire wannan cikin bazan iya yin hakuri ba. Dady yace "ka saurara kaji shifa ciki yarjejeniya ce ta mutane guda biyu idan kai ka yarda ita bata amince ba kenan kaga babu dole abarshi musamman da yake itace zata dauki nauyin cikin a jikin ta sannan kana fadin cewa in ta cire komai zai faru,kasan dai bazaka iya shari'a da ita bako? Karkari dai kawai kace zaka saketa ko? To ta fada mani ta shiryawa hakan ni na kiraka ne in baka shawara bawai rokon ka zanyi ba akan dole sai kayi hakan din,dan haka kasan me zakayi shawara zan baka ka lallaba ta ka lallashi matar ka sai ku shirya bawai kanada wasu yaran ba? Kuma sauran matanka zasuci gaba da haihuwa, wannan shine kawai". Shatima yace "gaskiya nidai wannan shawarar ba Zan dauke taba dady domin bazan bari ta cireman ciki kamar yadda tayi na baya ba,babu saki a tsarina amma zanbi hakki na duk inda yake". Dady yace"shikenan nan tunda kaki kayi yadda kaga ya dace" ya kashe waya. Shatima yaja dogon tsaki tare da fadin za'ayi aika aika,dama nasani suna bayan yar su dan son rai da kuma kin gaskiya kiri-kiri bazan zama sakarai ba,yana kwanciya tare da kara sakin tsaki, Salma ta kai hannu ta rungumoshi zuwa jikinta,"kayi hakuri Yaya duk dani Yarinya ce be kamata insa baki a zancen ku na manya ba a yadda dai na fahimci komai daga zantukan ku kuma ince da amsar ka,ka lallaba ka bita a hankali kuma kasa hikima a cikin lamarin" "Wane hikima kuma zansa? Wane hikima zan sa mata ga gaskiya a na kallo" Salma ta ce yanzu in ka biye ta tata zaku cigaba da fada da gaba a wannan rikicin ma sai taje ta cire kaga shikenan, amma inka lallabata ka nuna mata kamar ka yarda zata saki jiki har ta nemi shawarar ina za aje ayi,idan ta fada maka kai kuma kasan yadda za kayi ka samu wani a asibitin ko likita kanada zabi biyu kodai kace masa idan kunzo ya yi dubara ya bata abinda bazai zubda cikin ba,inyaso daga baya sai ya nuna mata cewa idan ta nace sai ta zubda cikin zata iya rasa ranta to dole zata hakura,kayi mashi kuma gargadi akan matukar ya cire cikin hukuma ce zata rabaku. Saidai fa Yaya inason kayi hakuri shawara na baka bawai dole ka dauka ba, amma ka gwada kwakwalwarmu ta yara ce in kaga beyi ba kayi watsi da zance na. Cike da al'ajabi ya dubeta har zai yaba mata sai kuma ya tuno da Aliya da sigar da tazo masa kenan a farko ya saki jiki a karshe kuma yazo ya bashi mamaki,yaja numfashi bazai cigaba dayin shawara da wata akan matsalar wata ba, abinda kawai zaiyi shine kowacce zai tafiyar da ita akan matsalar ta. Yace "Salma ba lallai ne in dauki shawarwarinki ba duk da cewa kinyi basira a nan" ta ce "dama bance lallai kayi amfani da ita ba,kadai saurareni,kuma daka saurareni na gode. Duk shawarwarin da Salma ta bada dasu din ya yi amfani kuma cikin sati hudu ya cimma nasara,Amna ta hakura bisaga tsoratar wa da gargadi da likita ya yi mata wadda ya samu suka tattauna bayan Amna ta fada masa wurinshi zataje harma ya tambaye ta ta yadda akayi ta sanshi tace "shine ya saka mata abin tsarin iyali kuma ta sanshi ta hanyar kawar ta Mama Afra wacce taki yadda da shawaran ta a wannan karan,harma suka danyi sa insa sakamakon taki baiwa Amna goyon baya akan cire cikin. Shatima yaji dadi yadda shirin Salma ya kaishi ga ci,kai tsaye be samu ko wacce tangarda ba. Haka wata juma'a a wajen Salma daya diro da wuri ya taho da yake jirgi ya biyo Dan cike yake da kewar ta wancan zuwan da ya yi be samu kwananta ba duk da kwana biyun dayakeyi dama a wancan sati biyun daya gabata kafin wannan ya samu bata sallah ne. Ta zuba kitso kanana ga lallenta na hannu da kafa Wanda ta watsa tamkar amarya kayan turawa tasa riga da wando,wandon siririne be kai kasa ba,rigar kuwa tadanyi fadi ta gwiwa. Tunda Shatima ya shigo da runguma ta tareshi haka kuma kai kawon shirya mashi abinci da takeyi sha'awa take bashi ga mayen kamshin ta da yake mugun damunsa. Waina tayi masa da miyar tantakwashi da kuma lemun zobo me sanyi haka yaji cucumber ba kadan ba,tare suka ci abinci cikin wasanni tare da hirarraki na miji da mata da fahimtar da juna,wayar Shatima tayi ruri Nafisa ce ta kirashi domin jin ko ya sauka lafiya, wannan halin ya cikin halayyar Nafisa wadda Shatima keso wato nuna kulawa da tafiyar sa idan baya tare dasu,lura da haka yasa Salma kwaikwayon Nafisa domin itama ta kara samun ma zauni a zuciyar shi. Shatima yana daga wayar cikin jindadi yake fadin "Matata" Salma ta kalleshi cike da murmushi tare da fadin "ace ina gaisuwa musamman ga yarana" kai ya daga alamun yaji sannan suka cigaba da zance yace a bashi Ashraf,suna gaisawa yaron yace "Dady bakace momi ta dena shiga gidaje ba" be jira amsa ba yace "to jiya ma ta shiga kuma tabarmu a gida" Shatima ya gane nufin yaron nan dayace jiya wato yana nufin dazun, Nafisa ta amshe wayar tare da danawa yaron duka tace "shegen surutun tsiya." Shatima bayason dukan yaranshi don haka take ya... . [8/26, 06:35] Ummi Tandama😇: 📚4️⃣ Page 23 Ya bata rai ya sake kiran Nafisa don ta kashe wayar tana dagawa yace "ki bawa Ashraf"ta mika masa,yaron cikin kuka yake fadin"Dady dukana tayi" ka dena kawo karar mamanka kaji ka dena fadaman inda taje, Ashraf yace " to na dena" yace "to ina Babana?" Gashi nan akan gado,to bashi waya,ya yi magana dasu sannan yace su bata wayar ta fita gefe guda dan bayason magana a gabansu dubi yanzun bemasan lokacin da yaron yaji kashedin da yayiwa uwar tasu ba,amma gashi nan ya kawo kara. Ta katse mashi tunani da cewa "sun fita" yace "meyasa kika fita ba tare da iznina ba? Shiru tayi yace "na rabaki da matan layin nan bamason huldarki dasu amma kin ki "tufa haihuwa akayi" Yace "to ko uwar wacece ta haihu na hanaki hulda dasu, sannan kuma inaso ki sani karki kara dukanmu yara bazan dauka ba,tunda kin kasajin magana ta zaki baro Abuja kema ki dawo nan,indan yarane makaranta zan canza masu wata, tace "ni gaskiya sana'ar zanin gadona za a katseman kuma..... ya katseta "wannan ba matsala ta bace ribarkice babu wani abu danike amfana daga cikin sana'ar ki,kinga kenan dan kinbar inda kikeyin kasuwa ba damuwa ta bace, akwai abin dubawa ni nace kiyi bakiyi ba to taya za ayi haka? Nifa damuwa ta idan nace ayi to ayi in kuma nace abari nan ma abari,tunda na lura ba damuwa tace a gabanki ba kije kiyi nasa matakin da zan dauka,ya kashe wayar tare da jefata gefen kujera. Salma tayi tsam tamkar ita yakeyiwa fadan,yana gama cin abinci ya tashi,ta tashi ta wanke hannu domin itama abincin ya ginshe ta,kusada dashi ta zauna tasa hannun ta gefen kumatun sa tadan shafo "Yaya kayi hakuri ko" cikin sanyi murya tayi magana. "Banason ganinka cikin damuwa ga fushi baya yi maka kyau ko kadan idan kayi fushi bakayin kyau,danyi murmushi mana don Allah" Ya kalli fuskar ta tace "kayi murmushi mana yaro mekyau haba dan yaro mekyau" Dariya ne ta kwace masa yace "nine yaronki?" Tace "sosai ma gashi nan kuwa ina lallashinka cikin kulawa yarona" dariya ta kara kwace masa "lallai kam" Kuma gobe inna fitama zan siyo maka fida na rinka dama maka madara kaji ko yarona" sa hannu ya yi ya rufe bakinta yace "Salma kin zama mara kunya yanzu" tace to shikenan ai nima dan kai nikeyi. Da wannan dubaru ta mantar dashi fushin dayake ciki sannan ta kawo zancen Nafisa akan batun dawo da ita kaduna, musamman da ita tasan da in har ya dawo da ita to kila da ita zai tafi karatun ta kuma yasha ruwa tunda dai yayi zancen nan,shi kuma beki sauraren ba domin yana ganin cewa tanada wata baiwa tace "Yaya nayi wani Karan bani akan maganar maman Ashraf mana dawo da ita gida bashine mafita ba,kenan kanason ta tabbatar batajin maganar ka kena kai kuma zakayi abinda zai bata mata rai itama zatayi, kyakykyawan zaman ku zai lalace Aunty Nafisa tana sonka sosai na tabbata idan kafi hanyoyin da suka dace gurin sulhuntaku to abin zai maku kyau hakan zaifi. Bada haka ma ai kai Yayan tane zaka iya zuwa ta wannan sigar, Shatima yace"a tunanin ki kenan,ba lallai ne ma ya zama irin nataba,amma bansan hanyar da kikeson in biyo mata ba,tunda na zauna da ita nace mata banason yawo." Salma tace"to shikenan tunda wannan karon kayi mata fada sosai zata tsorata musamman ma da yake batason dawowa nan,kai kuma yanzu gashi ka nuna mata zata dawo. Wannan shine karo na karshe da damar da zaka bata inhar ta kitare dokar ka to zaka sauki matakin dawo da ita, sannan ka shinfida mata dokoki amma ba masu tsauri ba nasan zata kiyaye. Shawarar ta shige shi sosai amma ya nuna wannan shawarar shiririta ce baki kawai ya tabe tare da fadin" wannan zancen naki fa ba lallai ya yi aiki ba, amma nasan yazan mata. Lokacin Salma ta shiga debe kayan da sukaci abinci, Shatima mamaki yakeyi da baiwar ta,in be mata ba itace ta bashi shawarar kasuwancin da yakeyi a yanzu Wanda har ya zama wani abu,e zuwa yanzu kasuwancin yana sama da aiki. Katse mashi tunani tayi da cewa "don Allah ka dena cewa sana'ar matarka bata kara maka komai ba,"to duk abinda yake a wuyana inayi mata" Salma tace "umm nagane ai shine burgewar kowanne namiji kuma shine cikarsa namiji kuma nasan dole kudin ka zai kare ka koda kuwa akan yaranka ne ko wajen siyen takalmi ne. "To naji sarkin jawabi da Allah kizo kiman tausama muyi bacci tukunna na gaji duk jikina ya yi nauyi" "to muje gado mana yadda yaro mekyau kayi bacci ko yarona?" Dariyar daya kamashine dariya ya yi harda rike ciki suka nufi daki. A can gida kuwa bayan Badi'atu ta gama iddah tana zuba idon ko Safwan zai ce yana sonta, amma sai taji shiru kamar an shuka dusa,daga lokacin kuma sai ya dauke kafarshi a gidan hakanne ya tayar mata da hankali ba kadan ba,kuma gashi babu wanda zata tunkara da wannan batun akan Safwan a tattauna ko zataji dadi. Salma ta soma yiwa zancen da suke chatting tace wai son Safwan take a ranta gashima ya dauke kafa tana tunanin zai bar tane tunda ita yanzu ta riga ta zama bazawara, Salma tace" wannan bazai zama silar dena sonki ba,tunda shi so babu ruwan shi da wannan sai dai kuma in wata yasamu" Badi'atu tace "dana shiga uku na kuma,dan na dora raina akanshi sosai." Salma tace"amma ki gwada tura mashi gaisuwar juma'a kota WhatsApp ne" Badi'atu tace "shikenan zata gwada" Juma'a uku tana masa babu amsa hakan ne ya dada karya mata gwiwar ta,ta soma samun kanta da zubda hawaye a wasu lokuta, kullum Salma takewa zancen wadda haka yasa tashiga damuwa tare dason taga ta fidda Badi'atu cikin damuwa,ba tare da shawara da Badi'atu ba ta kira layin Safwan cikin mamaki taga ya daga. Dan be zarci har yanzu tanada number shi a wayar taba,tayi Salma ya amsa tare da cewa "matar Shatima Allah dai yasa lafiya kika kirani"? To lafiya dai ba lau ba kodayake karanbani zanyi ba sani ba,"to inajinki me yafaru ne matar Shatima?" Tace "Aunty na Badi'atu" da sauri yace "me yasame ta?" Tana sonka,sonka take wallahi kuma a cikin damuwa take batasan ma zan fada maka ba ta hanani. "To don me ta hanaki ki fada mini?" Ita wai bazata iya fada ba,"saboda dama can ba sona take ba" Salma tace"tana matukar sonka da gaskiya" cewa tayi koda ta fada maka yanzu kila zakace dan wani yayi mata wulakanci ne da kuma ta zama bazawara. Safwan ya yi dariya Dan hakane mana" Salma tace"badan haka bane Yaya domin na lura da abubuwa da dama wadanda babu lokacin da zan yima bayani, amma kazo muyi magana mana nasani kai din malamine a bangaren soyayya zaka fahimceni inhar ta kamu kuma dan ta rasa wanine. Yayi dariya gaskiya kuwa har yanzu inason Badi'atu amma ada na hakura tunda kinzo min da dadin bakin nan naki zan gwada zuwa yau,bayan Salma da sukayi murna takeji sosai ta kira Badi'atu tace" ke albishirin?"ki tace goro"Salma tace"wallahi ni banacin goro, wannan takalmin zakiban me igiyoyin nan" Badi'atu tace"zan baki" Safwan yaceman ya mutuwar sonki"yana nan zuwa yau din nan. Badi'atu tace"don Allah da gaske kike zai zo yau? Ya akayi kika sani? "Tace baiwace kawai da Allah ya yi mani,nasan dai zai zo naji a jikina, amma fa ki sani idan har yazo yau takalmi ya zama nawa,kin yarda? Da sauri Badi'atu tace na yarda wallahi" Salma tace"shawara idan yazo babu kunya ki fito da tsantsar son da kike masa ki nuna masa,karki tsaya wani kunya in kikai haka kanki zaki cuta" Tace insha Allahu zanyi haka. Safwan yaje kuma ya yarda Badi'atu nasonshi kwana kadan zance ya zaga dangi aka soma shirin biki,ba a sa rana ke Tsawo ba akasha biki inda aka kai Badi'atu dankareren gidanta Wanda aka dankara a unguwar turawa,Wanda yake zaria kwanakin su shida suka shiga duniya domin zagayawa sukaci amarci. Haushin Badi'atu daya ma shine kawai dashi ya riski budurcin ta tun farko. Kwanci tashi dai Salma an shiga shekarar karshe a jami'a lokacin ne Amna ta haifi danta mekyau, Shatima ya zama babban mutum kuma Baban maza,ansha suna lokacin Nafisa ta je makka Shatima ne ya biya masu da Amna yace wata shekarar sai taje ita,bata damu ba dan taje hajji taje umara batasan adadi ba. Salma tanason ta samu ciki duk da karatun da take,shiru har ga Badi'atu da nata cikin, hakane yasa Hajiya harma da Kaka nema mata magani,da yake ita tace Allah ne be kawo ba. ..... [8/26, 09:52] Ummi Tandama😇: 📚4️⃣ Page 24 Sai ga Aliya da wani ciki Nafisa ma haka, Shatima ya lura da sallar dare da Salma keyi a wasu lokuta harda kuka,sai ya fara lallashinta tare da bata misali da Aliya,haka ta dangana tana jiran lokacin ta in kuma bata cikin waɗanda zasu haihu a duniya Allah ya sa haka shine mafi alkhairi a gareta. A gefe guda kuwa ta gama karatun ta cikin nasara Shatima har biki sai da ya shirya mata dan faranta mata rai,a lokacin aikin hajjine zasu tafi su uku har dashi da Amna sai ita Salman. Amna tace ya bata kudin kawai zata siya mota,ya bata shida Salma suka tafi, Salma bazata taba mantawa da wannan tafiya ba domin kuwa bata taba samun lokaci ita da mijin sunyi tafiya irin haka ba,sai da taji inama ace daga ita saishine kadai a duniya. Sun dawo inda Salma aka zubo hakorin makka tayi kyau ta murje,Aliya da Nafisa duk maza suka haifa, Shatima dai gida ya cika da ya'ya guda bakwai duka maza ga arziki na karuwa ya sai sabuwar mota,ya bawa Nafisa da Aliya nashi, domin an danyi gyara,shine ya koya masu. Yanason halin Salma sosai domin bata daga kai ta kalli komai abinda ya yi masu bare kuma batun motoci ko a yayin zuwa koyoma da akayi aka gama baduwar ta ko akan fuskar ta ba,zaman gidan Shatima yanzu ya dawo zamane da ko da halinsa ya ke zaune burin Salma shine taga ta shiga jikin Shatima a kowacce fuska, ta samu wannan damar kuwa domin ita kadai yake yawan zancen ta, kasuwancinsa kuwa cikin dubara ya nemi shawarar ta sosai,tana bashi shawara haka zalika Badi'atu yanzu komi nata da Salma take shawara itace abokiyar ta. Tana gama hidimar kasa ta samu aiki a gidan talabijin mai zaman kansa wanda dama tana zuwa sanin makamar aiki sun yaba da kwarewar ta. Salma ta cika burinta a halin yanzu na zama yar jarida ita takanyi labaran hausa da turanci, lokacin Auwal kuma yaransa biyu sun hada gwiwa da Hadiza da Salma sunyi gini a filin da Salma ta siyawa innar su daki hudu da bandaki da kuma kitchen, Shatima ne ya rufa masu tare da karasa sauran gyaran da ake bukata da Auwalu. Inna ta dage sai Salma ta dauki dan gidan Auwal,matar bataso ba dan haka Salma tace "Inna a barshi gidanmu fa cike yake da yara zasu debeman kewa banida matsala" abinda Salma ta yarda dashi shine ba komai da kake so Allah yake baka ba don haka ta yarda da kaddara. komai yana da lokaci Salma ,tana zaune Shatima yace lokaci ya yi da zaki koyi mota" tayi murna sosai shi ya koya mata mota bayan ta iya ya bata ta hannun shi, kwana uku da yin haka ya siyo sabuwa dal, Salma a cikin albashin ta take hidima da duk Wanda ya rabeta ko kuma ya rabi mijin ta idan dai intaga abu tanaso takansiya dan ta burgeshi basai ta jira Shatima ba, hakan ne ya kara mata kima da daraja a gun shi ita kuma kullum tana kallon ai komai ta zama a duniya shine sila domin shine ya tsayawa karatun ta. Shatima yakan zauna ya kalli labarai yana alfahari da matar sa abar sonsa. Salma sadik Dankasa zatai aure lokacin tana aiki a wani kamfani na babansu,ansha biki inda aka kaita Abuja,andawo biki da kwana uku Salma ta kamu da wani irin mura ma tsanani,jurewa takeyi lokacin taji labarin cewa Shatima yana can kwance ranga ranga,dukansu sunje dubashi a asibitin da yake kwance Salma da Amna ne a gurin shi su kuma Nafisa da Aliya,sunje kawo abinci Salma tashi zatayo alwala sallar la'asar, kawai sai jiri ya debe ta zubewa tayi itama dole aka bata gado. Binciken da akayi likita ya gano tanada ciki wata daya, Shatima ya mike ya isa wajen gadon ta ya kamo ta ya rungume yanayiwa Allah godiya,sai kawai ai shi ya samu sauki Salma kuma kuka tasa wanda bazata iya tantance kukan na menene ba. Tana cikin farin ciki,taimako daya ta samu cikin ba mai laulayi bane dan haka tacigaba da aikin ta, Shatima yana kula da ita da lelenta duk da mamakin ciki irin nata wanda be hanata kula dashi ba cikin kowanne irin yanayi tana kula dashi. Lokacin ne Kaka jiki yaki har saida aka kaita waje kafa dai,anyi mata aiki sun dawo da ita sati daya ajali ya sauka inda rai ya yi halinsa Kaka da ta rasu. Salma taji mutuwar nan tamkar ita kadai akayiwa mutuwar,anyi bakwai sun dawo gida Badi'atu lokacin sai ga ciki danta kuma watanshi goma,ta kira Salma harda kuka wai Safwan yace kar ta sake ta cire masa ciki, Salma tace"wane tsautsayi ne da zai kaiki har kiyi haka? Wane tsautsayi ne zai kaiki zagin mahaifi? To wallahi ki saurare ni yanzu na samu shiyasa inajin in zanyi ciki yau na haihu gobe na kara samun wani to bazan cireshi ba, shawara da zan baki kada ki kuskura ki fusata ko kiyi fushi da mijin ki,idan yan goma zaki haifa mijinki nada karfin rikewa to karki samu damuwa dan haka ki taka a sannu". Badi'atu ta ce "dama yasoma cewa bana sonshi tun a asali shine dalilin da bana son cikin shi" Salma tace "ai kinji ko,kinji daya" to wallahi ta biyu sai tafi haka muni daga nan kuma kinsan batun da zai biyo baya basai na fada maki ba,me yiwuwa na karin aure ya biyo . Badi'atu tace "na hakura ni kishine dani bazan iya ba" Salma ta ce kuma ai tanada dadi ni yanzu duk da kowa harkar ta takeyi, Allah in dayanmu tayi tafiya duk sai naji babu dadi a gidan. Badi'atu tace"aiku kun riga kun sabane,nifa dagani sai mijina kullum muna manne da juna" Salma tace "to shikenan inkin tsaya yanga kuma yanzu zai je ya samo wata a waje." Cikin bacci taji ciwon baya, shiyasa ta farka,bata saka ran cewa haihuwa bace dan lissafin likitoci suna hasashen saura kwana hudu kenan dan haka bata tashi Shatima ba dan kwana hudun nan dai sai ya cika,ta kyaleshi a baccin da yakeyi. Kai kawon da takeyine ciwo ya yi yawa yanata karuwa "innalillahi" abinda take ta ambato kenan ta farkar dashi be jira komai ba ya sureta zuwa asibiti cikin dare suna zuwa aka kaita dakin haihuwa cewa ya jira. Kafin minti goma sai gashi ya jiyo kukan jariri komai na Allah ne. Salma komai na maza ta siya domin takardar hoton da akayi mata a ciki gashi nan namiji akace mata sai gashi ta haifu Yarinya mace kyakykyawa damkar yayyenta, Shatima ta kwaso Yarinyar nan don yaran kaf idan kagansu zakasan cewa nashi ne har kudi Shatima ya bawa me kawo mashi albishir na haihuwar nan, nan ya yi ta waya yana shela Salma ta mashi yar budurwa kyakykyawa, kafin wani lokaci asibiti ya cika harda su Hajiya kowa yazo ace ansamu Hajiya. Salma ko tunda ta dauki jaririyar ta soma hawaye taso ace Kaka taga yar nan tata na duniya babu irin maganin da bata nemo mata ba dan ganin ta samu ciki,kuma ita a gaskiya sunan Kaka ya dace asawa Yarinyar nan bawai Hajiya ba har yanzun bazata manta da tarbiyya da Kaka tayi mata ba, Hajiya tace ai da Salma zata tafi Zaria Shatima be kiba domin shima alfaharinsane Hajiyarsa ta zama me kula da Salma haka zai sa Salma ta sake mantawa da abinda Hajiya tayi mata duk da cewa ya shedi Salma batada riko bare gaba,tunda ta haihu suka kebe da Shatima gashi yar tana neman cin sunan Hajiya,sako ta tura masa a waya cewar tanason ganinshi sai gashi yazo washegari da safe tayi mamaki dan ta zaci yana Abuja. Ta fito wanka kenan wanda Hajiya ke mata,yana zaune bakin gado yana kallon kofin da Hajiya take sheka mata shayi, shiyasa ma kiketa karuwa ashe" "Yanzun hakama nayi katuwa" Ashema kuma gashi kinfi kyau tace " ruwan nono yaki zuwa Saida tea din nan,Hajiya ta damu nama gasashe duk ya ginsheni," Yace inyeh kinji yar gata amma yanzu ruwan nonon ya kawo ko? Ta janye zaninta tana fadin "gashi nan kana gani har ciwon kirji suka sakani sunyi wani irin girma sunyi yawa" cikin mamaki ya kalli maman nata suna tsaye kem har yanzu kuma suna cike yace "Ni banga sun kwanta ba kamar yanda sukeyi idan an haihu" Tace kwanciyar mama aishi halittane haka zalika tsayuwar dinma hakane,irin tawa kirar da Allah ya yi masu kenan. Yace "Salma kedin ta daban ce banason na fada maki amma don Allah kar kiyi amfani da hakan gurin yakata,tace wane irin yaki zanyi maka? Saidai na yaki kaina. Yace "Ina Maman tawa ne?" Tace "Hajiya tana mata wanka dama dan haka na kiraka,don Allah kayi hakuri sunan Kaka nikeson asama Yarinyar nan,dan Kaka ne tayiman komai a rayuwa" Shatima yace"nimafa na raya haka sai naji kowa yace Hajiya shiyasa nayi shiru" tace nasan Hajiya bazata ki ba muyi shawara da ita. Lokacin da Hajiya ta shigo dakin dauke da Yarinya tayi mamakin ganin Shatima tace "kai jirgin safe ka biyo ne?" Salma ta nemoni akan wata shawara ne suka fada mata,tace "hakan ma yayi" nan take ta shaidawa Alhaji batun murna ya yi sosai tare da godiya agun Salma da za a saka sunan mahaifiyar shi. Nan take kuwa ranar suna Yarinya taci halimatu sadiya saboda sunan Kaka kenan, Yarinya kuwa taga jama'a da abin arziki kala-kala domin ya'yan Kaka sunce lallai kam za asan an sa sunan uwarsu. Mejego tasha kyau ita da Yar ta abokan aikin Salma duk sunzo,su kuwa Salma Dankasa har da kwana a Zaria. Daga nan maijego ta cigaba da wanka cikin kulawa da tattali Yarinya dai Iftihal suke kiranta wasu kuma suna tsokanar ta sai suke kiranta da Kaka. Shatima dai ya yi nasara yanzu wajen hada kan iyalanshi da 'ya'yanshi haka kuma ya cuka masu son Iftihal Yar uwarsu yace masu ita karama ce kuma mace tanada rauni,ya zama dole su tausaya mata,sai ya zamana koda yaushe idan sun zauna kowa zai ce Iftihal kanwarmu yaushe za a kaimu mu ganta? Yakan nuna masu hoton ta wadanda ya ke daukar ta idan yaje,ko kuma wanda Salma ke daukar ta tana turo mai,wani zuwa ta yayi kuwa ka ya taho dasu Ashraf suka kwana gurin Aliya washegari ya hada da jafar da Abulkhairi ya nufi gurin kanwar su Iftihal,tasha dauka kuwa ba kadan ba, Salma kuwa hadasu tayi baki dayansu tayi masu hotuna,yara kamar su daya hakan yasa Shatima alfahari tare da godiya ga Allah. Salma ta dawo ta dora daga aikin ta sannu sannu wayewar ta ta karu saboda basirar ta tasamu cigaba har ya zuwa babbar tasha ta kasa baki daya, hakan yasa Salma dole ta tattara ta koma Abuja na ta samu nasara da abubuwa da dama. Kalubale data fuskan ta wasu lokacin sukanzo tare wani lokacin kuma daya yakan riga daya yayin da kalubale da nasara dama haka suke tafiya wannan yazo wannan ya tafi,samun ilminta shine nasarar ta haka halayyar tama itace ta sakata zaman lafiya da kishiyoyin ta musamman Nafisa mai banzan kishi amma gashi zama ya hadasu,tafi duk wani hali mekyau ta koya wanda Shatima keso, yanzu kuma yana samu daga wajen sauran matan shi duk ta kwashe ta hada da halin ta mai kyau tanayiwa mijinta. Shatima dai ya dora rai akan Iftihal yana tausayin ta kullum zancen sa Iftihal,ya kance shidai duk mijin da zai auri Iftihal to sai yasha bincike don bazai kaita inda zata wahala ba. Idan yana wannan magana kuwa Salma ta kance to in an samu wata macen fa? Yace itama haka zan sota sai dai son Iftihal daban ne. Lokaci yaja Salma ta mallaki abubuwa da dama na kashin kanta haka kishiyoyin ta kowa yanada bakin rabonshi,zama kuma yanzu babu wanda zai dagawa wani kai,Aliya dai wacce take da yara biyu har yanzu bata kara ba kullum tana son kari,don Shatima dai bunkasa yake,duk inda ita din ta zauna daukaka dai a wurin aikin ta ta samu har ta bude khemis a Zaria amma nashi take kallo,kuma izuwa yanzu ba Salma ce kadai ta gane ita din annamimiya bace har ma dasu Nafisa da Amna duk sun gane, saboda taso ta rinka rura wuta tsakanin su wannan ne yasa duk wacce ta kawo wa magana sai dai ya gwasale ta, haka ta zauna a babu nauyi. Amna kuwa batada wata matsala domin bata damuwa da shirgin kowa ba,bata sake haihuwa ba domin ta cire wani cikin Shatima bema sani ba, sannan idan kajisu da Shatima suna sa'insa to ana maganar hakki ne kila dai za abar kasa ne tare dasu ko kuma wani abu shine abinda zakaji ya hadasu. Nafisa kuwa kishin ta kawai take,sai zargi haka zalika lokacin da Salma suke guri daya sai son yaran nan Wanda kusan kowanne lokaci Shatima sai sun hau sama da Nafisa. Salma dai mai bakar dubara yanada wahala kaji komai a gefen ta da mijin ta saidai in tsautsayi ya ratsa wanda take maza ta kashe wutar kafin ma ya tashi,yar mace take goyo lokaci data sake haihuwa ma mace ta kara haihuwa inda aka samata sunan Hajiya batayi farin jini da kwarjini kamar Iftihal ba domin ita Iftihal irin yaran nan ne masu shegen shiga rai,ko a hanya aka ganta sai an tanka gakuma gyaran da take sha. Babu laifi a gurin Shatima duk yana sonsu kuma kowacce yana zama da ita busaga halinta haka kuma yana kokari yaga ya sauke duk wani hakki ko nauyi da yake kanshi nasu,haka zalika hadin kan yaranshi ya jajirce shine ya burge kowa,kuma ya fadawa matansa ma kada wacce ta raba masa kan ya'ya ko bayan ya mutune be yafe ba,yaran nan suna son junansu musamman ma Iftihal duk yayunta suna matukar sonta komai nasu nata ne,Aliya ce dai takeson canza ra'ayin ya'yan ta,dayake Shatima ya cusa masu ra'ayin in Abulkhairi yace "wannan na kanwa tane sai tace baga kaninka nan ba kusadakai zakaje ka ajewa wacce bata nan,sai yace "aishi namiji ne Iftihal kuma kanwata mace ce Dady ne yace mu tausaya mata" dole haka ta saki wannan ra'ayin domin tana tsoron kar yaron yaje ya shelantawa ubansa harma da yanzu ba kima takesashi ba,don haka indai yaje ya yi haka lallai akwai matsala. Salma tana linke kayansu cikin akwatin yara hutun makarantar yazo dai dai da hutun data ne tanason zuwa Zaria da kaduna taga dangi anyi abubuwa da yanayin aikin ta yasa babu damar zuwa,rigace da wando siriri a jikin ta irin kayan nan da tafi Zama dasu a gida,taji anturo kofa ta zaci Iftihal ce ko su Ashraf dan haka bata waiwaya ba tana dai yan wakokin ta na wani film din data kallah sai kawai taji an rungume ta ta baya da sauri ta dago ta juyo tare da rungume shi,ya lumshe ido tace mashi "ka shigo mutumi na?" Zo nan mana,ya dago habar ta kina hada kayane ko wato kin kosa ki tafi ki barmu ko? Humm.. ta kalli cikin idonshi taya za ayi na kosa da rabin raina muje kayi wanka kaci abinci, lumshe ido ya yi Ni na gaji yau a kuma kwana biyun nan bakiman tausa ba,inaga ma ki matsaman jiki kafin magriba nayi bacci koda na minti goma ne. Tace "to bari nayi maganin waɗannan yan biri birin yaran nan domin nasansu da sa ido bazasu barka ka runtsa ba, makulli ta dauka ta kulle dakin sannan ta sameshi ya yi runda ciki gadon bayan ta haye tana matsa masa jiki idanunshi a lumshe yake fadin "nagode Salma tah inkin tafi wazai kula dani ne kin shagwaba ni da yawa". Salma tace "dole in shagwaba ka kaifa babban yaro na ne, dariya ya yi yace kaiyanzu kam a yayeni mana. Ta matse wuyanshi tace "humm ai bazan taba yayeka ba" yace "Salma yau zan baki wata amsa da kika jima kina tambaya ta" tace "wane amsa kenan?" Yace "ai yanzu kin gaji gar kin dena tambayar wanafi so? Salma tace"ai kaki bani amsar ne duk da dai nasan so dayane tak kuma dole mutum daya za ayiwa haka" yace "na jima Ina fada maki sirrika na ba tare da nasan ina fada maki ba,sai dai ina matukar alfahari da ban kasance awani guri nike yada sirrikana ba,ko ga kanwata da take babbar aminiyar ki, tace haba Yaya kaifa na musamman ne a rayuwa ta tilo a duniya ta babu irin ka taya za ayi in rinka bayyanar da sirrikanka har wani yaji. Ya juyo ya rungume ta tsam Ina sonki,Ina sonki Salma, amsar tambayar ki kenan a duk cikin matana ke nafi so,duk inda nike zuciya ta na gurin ki,a gurin nike samun duk abinda nakeso matana basu iya yiman in bake ba, Salma wannan sirrin zuciya ta ne,na baki amana bai kamata in fada ba sai dai na sani tuni ni dake mun Zama abu daya, hawayen Salma da yaji a kirjinshi ne cikin sauri ya dagata zaune yace "Salma akwai wani abu da nayi maki na bacin rai a kalamai na? Ta sake kamkameshi humm Yaya wannan shine babban burina Allah na gode maka da naga wannan rana,nasan tsananin sonka da nikeyi yawaita addu'a da nayi ne nasan Allah bazai barshi haka ba. Tasa hannu biyu ta tallabo kumatunshi jafar nida kai amanace kwantar dashi tayi tana fadi to kayi bacci ka huta kafin magriba sai kayi wanka kaje masallaci,in kadawo kuma in baka abinci kaci kayi bacci,ta shiga yi masa tausa har bacci ya daukeshi itama ta manne jikin shi tayi shiru duk da ba bacci takeji ba tunani kawai ta tsunduma, lallai kam duk matar data jajirce ta zauna da kowa da zuciya daya to babu shakka zata zama tauraruwa a mijinta. Alhamdulillah anan muka kawo karshen labarin littafin Rana Daya.