[22/08, 12:28 pm] Mom Islam Ce 💃: *YARINYA MAI TAƁARGAZA* BOOK 2 Bismillahir rahmanir rahim. Zubawa ta shiga yi tana dariya tana gama zubawa ta mai da robar data ɗibo miyar kitchen ta dawo ta kwanta , Afnan na kwance tana gursheƙen kuka , gani take su Ammi sunfi son Aisha fiye da ita ,tunowa tayi ai bataci abinci ba ga wata yunwa da ta addabeta da sauri miƙe ta yaye blanket ɗin da ta rufe jikinta ta fito tana shirin ƙarasa fitowa ta faɗi timmmm wani uban ihu ta sake tana cewa " Ammi ki temaka min dan Allah zan mutu wayoo kwankwaso na na shiga uku wayo , Ammi na can tana bacci bataji faɗuwar Afnan ba , Afnan kam na ganin Ammi sarai ta jita bazata fito bane , faɗuwar Afnan da ihunta duk a kunnen Aisha dan haka ta dinga ƙyal ƙyala dariya tana ƙarawa , hakan ma bai isheta ba har sai da ta taso ta nufo inda Afnan ke jaɓe kamar wace aka shuka a gurin , riƙe ƙogu Aisha tayi ta tuntsire da dariya tace " wlh in baki bar mana gida ba zan saki ki barshi ni da kaina , dariyar yaƙe Afnan tayi tace " dan ubanki ni kike cewa " nan gidanku ne to wlh ki kiyayeni inhar nasaki a gaba ruwa ma bazaki sha a gidannan ba , cire ɗankwalin kanta Aisha tayi ta ɗaure a ƙugunta tana rawa tana tafi ,wanan abin ya ƙonawa Afnan rai sosai hakan yasa tayi sa'ar janyo Aisha ta fara duka kamar an aikota , ihun da Aisha ke dararawa ne yaja hankalin Ammi da baccinta yayi nisa ta farka , ta sakko daga gado tanajin kamar muryar Aisha , fitowa tayi zatayi palo ta jiyo shasheƙar kukanta a gurin ɗakin Afnan ,ya salam Ammi ta faɗa tana mai ƙarasawa da gudu ,kasancewar wutar lantarkin gidan a kunne yake yasa ta hango Aisha jini na zuba ta hancin ta , zaro ido Ammi tayi ga Afnan a zaune riƙe da ƙugu tana kuka , a fusace " Ammi tace " Afnan ina tunanin lokacin ɓatawarmu dake yayi walh bazan lamunci cin mutunci ba ,dukan da kikayi mata jiya da yazo da ƙarar kwana shikenan ? to maza ki tattara wlh ki koma gurin momynki inhar Aisha ta warke kya dawo dan naga bakida tausayi ko kaɗan, harara Afnan ta gallawa Ammi Allah yayi temako bata ganta ba , cikin muryar kuka Afnan tace" Ammi kina jina ina ihu na fito daga ɗaki na zame baki fito ba sai da kikaji ihun wanan yarinyar , a ina kikayi ihun nikam ban jiki ba Ammi ta faɗa tare da kamo hanun Aisha ta nufi bedrom ɗinta da ita. Kuka kam Afnan tasha shi dan tayi baƙinciki sosai ace Ammi zata lura da bare ita ta ƙyaleta tabbas sai momynta ta ɗauki mataki , da haka Afnan taja tayi ɗaki haka ta kwana da yunwa kasancewar bazata iya zuwa kitchen ɗinba dan da nisa kaɗan. Wanke ma Aisha baki Ammi tayi tace " ta hau gadonta ta kwanta , wanan karon taji maza babu musu ta hau batare da ɓata lokaci ba bacci mai nauyi yai nasarar ɗaukarta. Washe gari da asbha ana fitowa daga masallaci Khamis ya shigo part ɗin Ammi ƙwanƙwasa wa Ammi ƙofa yayi kasancewar gari bai gama haske ba yasa tana zaune kan sallahya tana azkar ,Aisha kuma ta koma bacci , Ammi na kusa da ƙofar tasa hannu ta buɗe masa tare da yu masa alama da ya jirata , zama yayi kan wata farar kujera mai ɗauke da katifa mai laushi an rufe jikinta da leda mai ruwan shuɗi , Ammi na idarwa ya sauka tare da durƙusaw gabanta yace " barka da safiya Ammi , ywwa barka ka tashi lpy my son Ammi ta faɗa cikin fargaba dan batasan me zatace masa ba inhar ya kuma ganin tabo a jikin Aisha , yana shirin miƙewa ya nufi gurin da Aisha ke kwance Ammi ta dakatar dashi a siyasance tace " haba my son kasan fa bata cika lpy ba so ka barta ta huta man , dawowa yai da baya dan har cikin zuciyarsa yana son ganin kyakyawar fuskarta babu inda ya iya haka ya dawo ya zauna Ammi na lura da yanayinsa hakan yasa ta ƙara shiga damuwa . Gari yayi haske suna zaune suna hira shi da Ammi har ƙarfe takwas na safiya lokacinne Aisha tayi miƙa alamun zata tashi wani mumunan faɗuwa gaban Ammi yayi . Juyowa Aisha tayi ta ɗora idonta kan Khamis , Khamis da yaga kamar fuskarta ta dauje ga kumburi da ta daɗa yi ga hancinta shima ya kuɓbura ya mutsike idonsa alamun gasgatawa yace "Esha meke faruwa ne naga face naki ya daɗa kumbura , yanzu kam Ammi batada abin cewa bazata hanata faɗar gaskiya ba . Wata ce mai kamada arniya ta dukeni kuma jiya ma ita ta dakeni fuskata ta kumbura Aisha ta faɗa ko a jikinta , juya kai Ammi tayi taƙi haɗa ido da Khamis whattttt .....kam bala'i Khamis ya faɗa ya miƙe yana tambayar Ammi wacece arniya ?" tambayeta Ammi tace " tare da basu guri dan taji kunyar cewa" da Aisha tayi jiya ma Afnan ce ta duketa , bata yiwa Khamis ƙarya a wanan karon tayi masa dan kare ƴar, ƴa uwarta da tayi . Dawowa yai ya zauna tare da cewa " gayamin wacece ta illataki my Esha ?" naji mama tana ce mata Afna..kafin Aisha ta ƙarasa sunan ya miƙe ya fice kai tsaye ɗakinta ya nufa da ko sallah batayi ba sbda ciwon da jikinta keyi , cikin sa'a ya samu kofar a buɗe hankaɗawa tayi ya taka gadon da takalmin ƙafarsa tare da fincikota yace " ke mahaukaciyar ina ce ?" an taɓa so dole na tsaneki na tsaneki i hate you banza jaka wa wuya dabba marar tunani kirasa da wacce zakiyi faɗa sai da ƙanwar ƙanwar bayanki ya wanka mata mari tare da ciro bel ɗin wandonsa ya fara kai mata duka ta ko ina, Ammi na kitche ita da baba mairo bata ko sauraresu ba ,sai da taji wani razannen ihu sanan ta fito ta riƙe hanun Khamis tana bashi haƙuri akan ya ƙyaleta , ina bayaji baya gani idanunsa sun sauya i zuwa kalar ja zuciyarsa na tafasa , janyeshi Ammi tayi tana huci , a tsorace Ammi ta kalli Afnan duskarta duk ta dauje da ciwo ba ƙaramin duka yayi mata ba , bayan ya fice ne Ammi ta janyo Afnan tace " kinga irinta ko ?" duk da karekin da nayi jiya bai san ke kika doketa ba gashi kin ƙara yi mata mafiyin wancen nikam bansan ya zanyi muku ba ran Ammi a ɓace ta fice. Zauna ta sami Khamis a ƙasa ya haɗe kai da guwaiwa jijiyoyin kansa duk sun tasa cikin firgici ta taɓashi tana kiran sunansa , bai yi mata magana ba sai ɗago kai da yayi ya ɗora jajayen idonsa a kanta , cikin kwantar da murya Ammi tace " haba ubana ka sanyaya zuciyarka Aisha zataji sauƙi da yardar Allah ka kwantar da hankalinka , miƙewa yayi baice komai ba yabar part ɗin ya nufi nasu yana huci , kwanciya yayi a ɗaya daga cikin kujerun ya ɗaga kansa sama yana tunani, yanzu Aishansa ce haka ?" gaskiya ma beyiwa Afnan dukan da ya kamata ba wlh , amma taci darajar Ammi da saiya karyata. Fitowa Aisha tayi daga bedroom ɗin Ammi ta dawo palo ta zauna , ganin Ammi zaune tana ta gursheƙen kuka yasa Aisha ruƙo hanun Ammi tace " mama waye ya taɓa ki kiyi shiru ai kyakkyawan zai dawo barin kirashi , ƙara bawa Ammi tausayi tayi hakan yasa Ammi ƙara ƙarfin kukan ta, ficewa Aisha tayi da gudu ta nufi part ɗin su ganin Khamis tayi a zaune dafe da kai idonta ya ciko da hawaye tace " mama na kuka waye ya taɓata ?" nima ban sani ba Khamis yace " tare da janyota jikinsa ya fara shafa mata baya , tunowa da Aisha tace " Ammi na kuka yasa shi miƙewa ya goyata ya nufi gurin Ammi a zaunen da ya barta a haka ya sameta tanata kuka har yanzu.....! dan Allah kar a fitarmin dashi 👏🥰. [22/08, 12:28 pm] Mom Islam Ce 💃: 3&4 Ammi ki kwantar da hankalinki Afnan sai tabar gidannan yau , dakatar dashi Ammi tayi tace " yau fa kace abi komai a hankali son , to Ammi ki dena kuka Khamis yace " yana mai riƙo mata hannu , share hawaye tayi ta miƙe kana tace " muje dining ga farfesu can anyi maka nima naji ina sha'awarsa yau ɗinnan , duk suka ɗunguma har da Aisha kowa aka zuba masa a plet Aisha da yawunta ya gama tsinkewa taga anata jan aji ba'a zuba mata ba tace " kyakkyawa , babu rabona ne ?" kallonta Ammi tayi dan tana mamakin zarar zance irinna Aisha , Khamis ne ya miƙa mata nashi ya jira ƴar aiki ta zuba masa wani , cikin lokaci kaɗan Aisha ta cinye tana girgiza kai tarw da lashe plet ɗin , sunkuyar da kai Ammi tayi yayin da takai kallonta ga Aisha , shikam Khamis hamdala yayi da Allah yasa Ammi ce a gurin ba wani ba , a daɗo min nidai Aisha tace " tana shirin kuka , mai aikin dake kai wa da komowa a palon tace " babu farfesun kaza sai na naman rago a zubo miki ?" eh Aisha tace " ku har wani zaɓe kukeyi nama nama ne fa , babu shiri Ammi ta tuntsire da dariya dan iya dauriyarta ta kasa ,shugaba Khamis shima ƙunshe dariyar yayi yana mai ƙara ƙare mata kallo gata yarinya amma tana abin manya , baba mai aiki ?" na 'am baban tace " tare da dawowa gurin Aisha taɗan sunkuyar da kai alamun girmamawa , tace " gani ƴar nan , ki zubomin harda romo kuma da yawa cewar Aisha , to baba tace " kana ta nufi kitchen ta zubo naman nan da uban yawa romo kam ba'a magana gashi yaji yaji kuma da ɗuminsa ta kawowa Aisha ta ajiye a gabanta tare da cewa " gashi hajiya , wani juya ido Aisha tayi tace " hajiya kuma ?" ta ƙyal ƙyale da dariya tana tafi, Allah ya shiryeki baba tace "tana dariyar itama , miƙewa Ammi tayi ta nufi bedroom ɗin Afnan samunta tayi kwance tana rawar sanyi , family doctor ta kirawo cikin ƙanƙanin lokaci ya shigo , samun su Khamis a dining yai tasowa Khamis yayi suka gaisa kana yace " zomuje muci abinci abokina , no doctor yace " yana dariya ina amarya doctor ya tambayi Khamis , cikin rawar kai Aisha tace " baka gani ne ?" nice amaryar , cikin jin kunya Khamis yace " Aisha kenan dama doctor nada labarin auran Khamis yasashi cewa " amarya bakya lefi dariya Aisha tasa tana farr da ido doctor ya wuce , hakan sam baiyiwa Khamis daɗi ba ya iso inda take zaune yace " my Esha mai yasa kike haka ne ? to ba nice amaryar ba ?" ta maida masa da tambayarsa hakan da tayi a shagwaɓe sai ya birgesa ya sureta zai fice da ita ta fara ihu tana cewa " ban gama shan romon ba ka saukeni wlh ko ka kaini dawowa zanyi , tana maganar ne da ƙarfi har Ammi dake ɗakin Afnan taji abinda Aisha ke faɗa , murmishi tayi dan Aishan akwai bada dariya , sa da ya kaita part ɗinsu ya direta zata ruga da gudu ta koma part ɗin su Ammi ya riƙo ta tare da sunkuyawa sbda ya fita tsayi ya rungumeta yana shafa gashin kanta , a hankali har wani lumshe ido yake , Aisha da ta lura da abinda ya keyi tace " ji inda ka wani rufe ido kamar maijin bacci kamar illun anguwar mu ya sami tuwon masara ta gimtse fuska tana shirin guduwa , abinka da riƙon da yayi mata bana wasa ba yasata kuka tana cewa " daga yau na dena kwana a nan gidan tunda gurin mama anfi cin daɗi can zani nikam na gaji da cin shinkafa , kallan ɗan mitsitsin bakinta yayi sai yaji sha'awar ya haɗa da nashi ai ko cikin wayo da dabara ya haɗe bakinsa yana kissing ita dai har ga Allah batasan meye wanan ba tasan dai iskanci ne ƙarara a fili yake yi mata , gashi babu damar magana , ya daɗe yana tsotsar lips ɗinta kamar ya sami sweet daga ƙarshe ya saketa tare da janye jikinsa gefe yana maida nunfashi , wlh bakinka ƙamshi kamar turare , Asha ta faɗa tana daɗa turo bakinta ta gurin hanci , Khamis dake jinshi cikin wani yanayi yace " ko in ƙara ne ?" a'a Aisha tace " iskanci ne kanaso Allah ya tsine maka ko dan babu ni a ciki kaine kayi , to ai kece kikace akwai daɗi zonan zanyi miki wanda yafi na ɗazu kinji , ƙara matsawa gefe tayi tana cewa " babu ruwana mama zata gane ina fita tace " nayi iskanci , miƙewa yayi tare da kunna kallo a tashar mbc 2 wani fil suke wanda ya hana Khamis kula Aisha , budurwa ne da saurayi zaune tana kuka yana kuka duk akan soyayya da turanci sukayi film ɗin hakan tasa Khamis ƙara gyara zama , Aisha da ta gaji da magana babu mai kulata tace " ni banga abin kallo a nan ba kagani ko zasu ƙara koyama iskancin bazaka kashe ba ?" tana maganar ne da gasken gaske , wow Khamis ya faɗa yana janyo Aisha idanunsa na kan tv , na shiga uku na lalace wayo ni wayo malam , dariya Khamis yasa yace" keee natsu babu abinda zanyi miki ɗauko min cup da flks a dining , komai dining komai dining mtsw Aisha tace " tana turo baki ni wlh halina daku kenan ƴan gayun nan komai turanci to baza'a faɗi sunansa da hausa ba ?" to me kikeson ince my Esha ?" yana cikin magana Ammi ta kirasa a waya tare da ce masa yazo tana son ganinsa , miƙewa yayi da sauri yace " my Esha ki jirani ina zuwa maƙe kafaɗa tayi alamar a'a am sorry insha Allah yanzu zan dawo harda ragowar romonki , tsalle ta buga tace " yauwa ina jiranka kayi sauri dan Allah ta zauna tana buga ƙafa , tana cewa " idan be zai da romon nan ba har na fara tuno kalar muguntar da zanyi masa anjima. gidan su anty Fiddausi anyi suna lafiya yarinya taci sunan Aisha saboda soyayyar da yaya Zakari keyi mata , kaka ce zaune tana baza tsintsiyar da taje jeji tayi tana waƙarsu ta mutanen da , leƙowa anty Fiddausi tayi tace " kan bala'i kaka tace " ya sauka a kanki mai neman fitina , riƙe da ƙugu Fiddausi tace " nidai wlh kina ɓatamin gida ki wani je ki kwasowa mutane datti ni bansan dalilin ma da aka zaɓeki a mai zuwa gidanan ba , kinwa Harira , kaka tace " tare da wurga mata daƙuwa , oho nidai ba mamana ba anty Fiddasu ta faɗa tana girgiza , to sai wa ?" nace sai wa?" marar mutunci kawai in tashi tun farar safiya in ɗora miki ruwan wanka in dafa muku shayi in wanke kayan jaririya in wanke naki ga wanke wanke ga shara amma abinda zaki sakamin dashi kenan san zanci arziƙi koda na koma gida insami na siyan kalanzir kaka ta fashe da kuka tana share hawaye da gefen zaninta Khamis dake shigowa yanzu yace " kaka ai gidannan da kike gani ki ƙaddara kin zauna din din din a cikinsa amma Ummi zatazo anjima kinga kinsami ƴar taya kwana ko , cikin fara'a kaka tace kai masha Allah aiko da mutanen ƙauye sunyi kewata ,bubuga ƙafa Anty Fiddausi ta fara tana cewa " babu mai zama min a gida itama Ummi ta kama gabanta tun wuri ni na gaji da damuwa , zaro ido yaya Zakari yayi kana yace " damuwa ko ? inhar mutane sune damuwa yanzu kika fara ya juya ya fice , bakin kaka kamar zai taɓo kunne tsabar daɗi dama tana tunanin ɗan biredin safennan da in ta koma ƙauye taena ci sai ɗumamen tuwo , haka taci gaba da gyara tsintsiyarta tana cewa " ai bama sai na adana ba tallah zan fara tunda naji ance tana wuya anan anguwar ita dai anty Fiddausi ƙala bata ce ba dan angma dagula mata lisaafi....! Dan Allah kar a fitarmin 👏 nayi typing read more huɗu ya goge kuyi haƙuri da wanan pls [22/08, 4:00 pm] Mom Islam Ce 💃: 5 & 6 Tana shirin shiga ɗaki taji sallamar Ummi kurma ihu tayi tare da ɗora hannu a kai tana na shiga uku an cikamin gida , ita dai kaka tana aikinta bata bi ta kanta ba , Ummi da bataso zuwa gidan ba ta shige ɗakin da yake mazaunin nasu ta kwanta kan katifa tana kuka ita har ga Allah gidan Aisha take son zuwa gashi anƙi kaita , kaka tana daga can waje taje barka da zuwa yan nan , Ummi batasan da ita ake ba dan bata ma lura da kowa a tsakar gidan ba hakan yasa taci gaba da kukanta , sallamar yaya Zakari da taji ne yasa ta goge hawayenta ta kifa kai a katifa , sannu ya yiwa kaka ya shiga ɗakin da Ummi take ciki sallama yayi amma shiru ba'a amsa ba , da mamaki ya ƙarasa kusa da ita ya zauna ga shi ga ta yace " haba OUM pls ki dena wanan kukan ɗaukokin da nayi akwai dalili wlh kinada muhimmanci a rayuwata ba kaɗan ba so kawai na ɗauko ki ne ki huta duk da nasan bakya aikin komai a gida , to kawai Ummi tace " kana ta kwanta , kamo hanunta yai ya haɗe da nasa yana jin ɗumin hanunta hakan ya daɗa ƙara jin wani lamari game da ita , bargo ya ɗauko ya rufa mata kana ya fice daga ɗakin , ɗakin mai jego ya nufa samunta yayi a zaune idanunta sun kumbura tsabar kuka ,nesa da ita ya zauna gudun matsala yace " my Fiddy karki sawa kanki damuwa akan abu kaɗan dan Allah ki yi haƙuri ɗan adam ma rahama ne fa , share hawayen fuskarta tayi kana tace " ni duk ba shine damuwata ba damuwata shine ka mayar da Ummi gidansu inajin wani abu game da ita , cikin sauri yaya Zakari yace " me kikeji ? gayamin , kamar zatayi magana sai ta fasa ta miƙe tana ci gaba da kuka ta shige uwar ɗaki ta kwana kan gado tana mai ci gaba da rera kukanta san ranta , baiyi ƙoƙarin binta ba ya fito ya nufi masallaci kasancewar anata kiraye kirayen sallah , yana fitowa ya kama hanya zuwa gurin aikinsa zuciyarsa cike da tunani kala kala na rayuwa ga wata sabuwar fitina kuma wai in koma da Ummi Yaya Zakari ya faɗa yana mamaki , iska mai zafi ya furzar yaci gaba da aikinsa . Da sallama ya shiga part ɗin Ammi bayan ya zauna ne ta ke gaya masa gobe insha Allah zai fara suwa Aiki , faɗuwa gabansa yayi a take , lura da hakan yasa Ammi cewa " ya naga baka farinciki alhalin kaine watannin baya ka dameni maganar ka gaji da zama , am Ammi nayi farinciki to wa zai dinga kula da Aisha ne ni shine damuwata , eyeee Ammi ta faɗa tana tafa hannu kasan dai Aishar nan ba jaririya bace da za'a goyata koni bazan kula da ita ba ko ka raina abinda nake mata ne ? a'a Ammi to Allah ya bamu haƙurin zama Ammi ta faɗa dan lamarin na Khamis ya fara bata mamaki , miƙewa yayi ya fice , yana fita Afnan ta fito tana ɗingishi , taba Ammi tausayi matuƙa ,tashi Ammi tayi ta riƙo mata hannu ta zaunar da ita tare da tambayarta me za'a kawo mata , shayi Afnan tace" tana mai kwantar da kanta jikin kujera da alamu jikin dai har yanzu akwai sauran zazzaɓin, Yana shiga ta diro daga kan fridge ɗin da tahau kasancewarsa bashida wani tsayi sosai tace " ina romona ?" fuska babu wal wala yace " na mance kana ya zauna , shiga ɗakinsa tayi ta fara tattaro kayanta na sawa tana watsosu falo da sauri yai gurinta yana cewa " mekuma ya faru ke bakya rabo da sa mutum magana , bata saurareshi ba ta ƙudundune kayan guri ɗaya tayi hanyar fita , ina zaki , na koma gidan mama ne dariya Khamis yayi a fili cikin ransa yace " yaro yaro ne in Afnan ta kuma sauya miki halitta zaki nemeni ne, har ta fice baice da ita komai ba. Shi lissafinsa ma duk ya kwance wanne zai kama oho hannu yasa ya bugi kansa yana furzar da iska mai zafi , a fili yace " yanzu ban isa in goce maganar aikin nan ba ran Ammi zai ɓaci gaskiya hakan zan tafi dole. Aisha na shiga Afnan da Ammi suka bita da ido data ƙaraso ne Ammi tace " ɗiyata me zakiyi da wanan kayan na gansu a hanunki , na dawo gurinki ne mama , murmishi Ammi tayi kana tace " to ƴata kai bedroom ɗin da kika kwana shekaran jiya kinji to Aisha tace " tunda Aisha ta shigo Afnan ke yi mata mugun kallo wanda bashida maraba da na tsaneki , hira suka ci gaba dayi da Ammi maganar Aisha ne ya katse musu tunanin, mama ina ragowar romon nan na jiya , tuntsirewa da dariya Afnan tayi kana tace " yarinya taji gidan masu kuɗi ba irin naku na talakawa ba , kamar ta wurgawa Ammi mashi a ƙirji haka taji saukar kalmomin ya ilahi , Ammi tace " tana kallon Afnan mai yasa bakida lafazi mai daɗii ne Ammi ta tambayi Afnan , cuno baki Afnan tayi alamar jin haushi. Washe gari tun da asbha yai wanka yana dawowa daga masallaci ya ɗauki abubuwan buƙatarsa ya tafi ɗakin Ammi , yau sarautar ce ta motsa hakan yasa ya zauna a palo ya danna lambar wayarta , idar da sallahar ta kenan ta fito , ganinshi zaune da jaka a hanunsa yasata cewa " wai har ka shirya ne ?" eh Ammi na ya durƙusa ya gaisheta bayan ta amsa ne ya dawo ya zauna dai dai , zama Ammi tayi tace " to bakaci komai ba ?" no Ammi na bana buƙata yau ba lallai bane in karya da wuri yau monday , cewar Khamis adu'ar kariya Ammi tayi masa da kuma faɗan ya kula da aikinsa da mutunta mutane , insha Allah Khamis yace " kana ya miƙe ya bada ƴar wata leda mai ɗauke da dambun nama yace " a ajiywa Aisha ya tafi, bayan ya fita ne Ammi tace " son kana son Aisha sosai fatana Allah yasa lokacin da tasan kanta da zafin kanta ya ƙara sonka so mai tsananj , ta koma ɗaki ta kwanta. Malam ne zaune a tsakar gida kan tabarma masifa yake ta zubawa san ransa a dole sai mama ta gaya masa lefin da yayi mata ta dena yawan magana , amma tayi shiru itama ɗin tana tskar gidan bata kulashi ba bare ta nuna alamun taji abinda yake faɗa , aure zan ƙara wlh dan naga iskancin yayi yawa acce kanada mata bazaku zauna ku kashe ku rufa ba , in na ƙara auren nasan zaki dawo da biyayyar da da bakyayimin , har yanzu batace komai ba , zuciya ce ta ɗibi malam ya shiga ɗakinsa ya ƙirgo kuɗi dubu ɗari ya fito tsakar gida ya zubesu gaban mama dake ɗinke bakin hijab ɗinta da alura , kinga wanan kuɗin sadaki zankai budurwa gangariya mai jini a jika , yai murmishi ya ɗauki kuɗinsa a karo na uku ma batace dashi komai ba ya fice , cikin sa'a ya sami baban Ummi a waje yana jin redio gaisawa sukayi malam ya nemi guri ya zauna kana yace " aure nakeson yi kuma banason bikin ya wuce wata biyu , da mamaki baban Ummi ya dubesa yace" haba malam ana fama da abinda za'aci a ciki ne ko ana fama da maganar aure dan Allah kabar wanan maganar kaji ?" rurɓune fuska malam yayi kana yace " oho kaima tanan ka biyu wato ni itace ne ? bana buƙatar kulawa ?" to yanzu babu ɗaya ƙanwar biyu duk ƴan uwanta sun zugeta kuma aure da kaji na ambata babu makawa wlh sai nayi budurwa gangariya akwai wata yarinya mai tallan kunu munyi magana da iyayenta mahaifinta dattijon arziƙi ne yace " in kawo dubu hamsin to yanzu kai na wakilta , malam ya ƙirga dubu hamsin ya bawa baban Ummi yace " gashi ka kai zuwa gobe kuma sai in fara maganar akwati muga inda abin zai kaya , babu yadda baban Ummi ya iya dole ya ɗauki kuɗinnan inhar bai ɗauka ba zasu iya samun matsala mai girma , hakam yasa ya ɗauki kuɗin yace " Allah yasa a dace " malam na shirin yi masa kwatancen gidan yace " ai na gane zan tafi zuwa anjima insha Allah sukayi sallama malam ya wuce ya barshi nan a zaune, Tabbas ya jinjina wanan aure na malam to babu yadda zai yi ana yin la'asar ya tafi gidan su yarinya me kunu suka gana da mahaifinta cikin sa'a aka sami nasara harda sa rana akayi kwana hamsin kowa yayi wa kowa fatan alkairi , baban Ummi na dawowa ya kira malam a waya ya gaya masa inda sukayi farinciki fal zuciyarsa a dole zai bawa mama haushi. Yaya Zakari ne yai parking ɗin motarsa a gefe ya shigo gidan su tare da sallama , mama na nan zaune a gurin da malam ya barta har yanzu bata tashi ba , amsa sallamar mama tayi tare da tura masa tabarma tace " shinfiɗa ya gidan naku ya mai jego ?" duka muna lafiya yaya yace " yana gyara zama to masha Allah mama tace " tare da sunkuyar da kai ƙasa , na lura kamar kina cikin damuwa mama duk kin rame ko kayan abincin ya ƙare ne ? yaya ya jero wa mama tambaya a'a basu ƙare ba bana cikin damuwa , hmm yaya yace mama dan Allah ki sanar dani yai rau rau da ido kamar ƙaramin yaro , babanku zai ƙara aure mtsw yaya yace " to yayi man sai me ki kwantar da hankalinki mama wlh karkisa damuwa a ranki insha Allah zan share miki kukanki , zan baki jari kici gaba da sana'ar ƙuli ƙulinki , aljihunsa ya taɓa ya ƙirgo kuɗi dubu goma sha biyar ya damƙawa mama , yana damƙa mata hawaye suka zubo a kan kuɗin ,hannu yasa ya shate mata hawayen shima idanunsa sun ciko , malam ne ya shigo da sallama yace " to anzo kenan ?" juyawa yaya yayi ya gaida malam bayan sun gaisa malam yace " ya masu jego lafiya laou yaya yace , malam yace " madallah , tabbas ya yarda da zancen mama tunda yaji malam yau bai haushi da faɗa ba zancen aure ya tabbata shima dan ya kwantar mata da hankali ne yasa shi cewa " karta damu Amma koshi beji daɗin jin zancen ba gaskiya , haka ya miƙe yayi musu sallama ya fita . Yana fita ya wuce gurin aikinsu da tunanin halin da mamanshi take ciki wani lokacin yaji kamar yai kuka amma babu hali . Koda Khamis ya isa gurin aiki office ya wuce kasancewar ma'aikatar tasu ce ma 'aikata ce da ake sarrafa robobi mai suna K &K wato Khamis Kabir sunan mahaifinsa kenan , shine babba gaba ɗaya a gurin hakan yasa ba wani aiki na shan wuya zaiyi ba ƴan cicike takaddu ne kawai sai abubuwan da ba'a rasa ba, sosai kamfanin ya birgeshi yana jin yanzu zai kauda komai ya duƙufa gurin kawo gyara da daɗa ƙawata kamfanin yakuma samun karɓuwa ta fannoni masu yawa , yana zaune yana tsaka da tunani yaji ana nock yes yace " come in murɗa handle ɗin ƙofar akayi , tare da shigowa , ƙamshin turarenta ne ya doki hancinsa , bai ɗago kai ba sai da aka sami mintuna sanan ya ɗago ya kai dubansa ga reta bai taɓa ganinta ba wani irin faɗuwa gabansa yayi lura da kyau irin nata kamar balarabiya gata fara doguwa mai dara daran idanuwa gashin girrar nan sun kwanta da gashin idonta suma zara zara bakinta ƙarami ne yayinda hancinta yake kamar biro dogo masha Allah nidai a ganina batada makusa dan in aka titsiye mutum zai ce ya haɗu da balarabiya , to ni meye na wani ƙare mata kallo bayan inada Aishana a gida mtsw yaja tsaki.....! Dan Allah kar a futarmin da shi pls 👏. [23/08, 3:31 pm] Mom Islam Ce 💃: 7&8 Have a sit Khamis ya yace " yana mai sunkuyar da kai kan takardun dake gabansa , zama budurwar tayi kana tace " thnks sunana Muhibbat nice sakatariyar ka , ok masha Allah Khamis yace " kana ya kuma maida hankalinsa kan takardun a karo na biyu , to na barka lafiya Muhibbat tace " ɗago kan da zeyi ta jefesa da wani sihirtaccen kallo mai wuyar fassara , tana fita yaja tsaki kana yace " inhar zan dinga haɗuwa da irin wa innan gaskiya da sake babu zancen zaman office gara zaman gida sbda ba matsalar kuɗi yasa na fara aikin ba , duk shi kaɗai yake wanan zancen , zuwa yamma ƙarfe biyar lokacin tashi yayi kowa yana haramar tafiya gida banda Muhibbat , zaune take kan ɗaya daga kujerun da aka tanadar a farandar ma'aikatan domin zaman mutane , buni buni ta duba agogon hanunta lokaci zuwa lokaci , ƙarfe shida dai dai gabanta yai wata mumunar faɗuwa , jin takun tafiyar Khamis wani gwauron nunfashi taja ta sunkuyar da kai alamun damuwa , abinka da mai tausayi ya dawo da baya cikin takunsa na ƙasaita yace " lafiya kowa ya tafi ke kona nan ?" lafiya lou Muhibbat tace " tare da kwaɓe fuska tace " temako nakeso kayimin dan Allah ka dubi girman Allah da ma'aikinsa ka ceci rayuwata taci gaba da maganar idanunta na zubar da hawaye , ina jinki Khamis yace " yana mai neman gurin zama dan jin meke faruwa, na taso cikin gata da nuna kulawa mahaifina da mahaifiyata suna sona so mai tsanani kowa na ƙoƙarin yaga ya faranta min , cikin ikon Allah Allah ya karɓi ran mahaifiyata lokacin inada shekara goma sha biyar a duniya , dady na yaci gaba da nunamin gata babu abinda baya siyamin na buƙatar mace kwatsam suka haɗu da wata bazawara mai suna Sajida , cikin ƙanƙanin lokaci ta ɗaukewa dady na hankali ya dena saurara ta tun kafin ma ayi auransu , anayin aure ta tare a wani katafaren gida da dady na ya gida mai tsadar gaske , har dani aka koma gidan kullum da safe sai tayi min duka ga ƴan aiki a gidan sai ta dinga sanya ni wahala nice wankin ta da wanke wanke dady na baya magana sam wani lokacin ma cewa " yakeyi ya mance dani , inyi kuka har in gaji , godiyar da nayiwa Allah shine kuɗin makaranta ta tundaga jami'a har sama ya gama biya amma badan haka ba karatun ma bazan samu ba , samun sauƙi na yanzu shine gurin aikinnan da nake zuwa , yanzu gashi nakai munzalin aure burin kowacce mace ta ganta a ɗakin mijinta to ni ko samarin sunzo matar dady na wato Sajida ita ke koremin su tace " wai anyimin baiko za suyi asarar kuɗinsu ne kawai , su kuma in sukaji haka sai su tafi , nisawa tayi kana taci gaba da cewa " ina zaune da daɗi babu daɗi wata rana kakata wato mahaifiyar momy na tazo gidan ta ganni ina kuka da girmana ganin jikina duk tabon duka yasata tattara min kayana muka bar gidan ko uffan Sajida batace ba shine na koma gidan kakata da zama mahaifina ma baya tambayata bare ya tambayi halin da nake ciki , da kuɗin aiki na nake komai na rayuwa . Shirun da Khamis yaji tayi ne ya kalleta yaga ta share hawaye ta kifa kanta cikin matsin ƙafafunta tana kuka , kiyi haƙuri dama kowane ɗan Adam da tashi jarabtar ki daure ki ƙara yiwa Allah godiya to ni yanzu wane temako zanyi miki ?" ƙara fashewa da kuka tayi tace " ka aureni nasan bakada mata , ta share hawayeta , kana tace " tun lokacin da nakeda damar samari aka kore min su yanzu duk kyawun da Allah ya bani babu mai zuwa ƙofar gidan mu . Hmmm Khamis yace " dan lamarin babba ne waye yace " miki banida aure ?" to aurena ko s weeks beyi ba , zaro ido tayi kana tace " nidai ina jiranka ka tausayawa rayuwata dan Allah bakada ƙanwa ne ? in itace a irin halin da nake ciki dole kayi yunƙurin samo mata mafita , mu talakawa ne , lokaci ɗaya tausayinta ya kamasa sosai tausawa rayuwar da ta shiga , Allah ya baki mafita , ƙirgo dubu hamsin yayi a aljihunsa ya miƙa mata kana ya nufi mota , tasowa tayi kamar zatace " ya temaka mata , taga yaja motar da uban gudu ya tafi , lokacin ƙarfe shida da arba'in anata kiraye kirayen sallahar magrib bakin titi ta nufa ta sami abin hawa ta wuce gida . Yana parking ya fito da sauri bai jira an buɗe masa murfin mota ba , ya buɗe ya fito da sauri kai tsaye part ɗin Ammi yazo samun Aisha yayi zaune a palo ita kaɗai da hawaye shaɓe shaɓe a fuskarta , tana ganinsa ta rugo da gudu tana cewa " kyakkyawa gobe dani zaka tafi ko ? eh kawai yace " mata ya riƙe mata hannu suka nufi sashin Ammi bedroom suka shiga batanan dan haka suka dawo kitchen aiki suka ganta tanayi itada baba mai aiki , sannu Khamis yayi musu tare da cewa " my Ammi na gaji sosai , ayya Ammi tace " maza kayi wanka ga special food ɗinka na jiranka oya , tom Ammi na Khamis ya faɗa kana ya wuce part ɗinsu. Da gudu Aisha ta bishi ta ɗafal fale masa dole ya ɗauketa yana dariya , suna isa ya sauketa kana ya nufi toilet dan yin alwalah , yana gama alwalar ya je masallaci yana fitowa yadawo yai wanka ya canza kaya , boyel yasa baƙi da farar hula da farin takalmi ,kyakkyawa kasan me ?" Aisha ta tambayeshi tana daga zaune kan gadonsa , sai kin faɗa my Esha Khamis ya faɗa yana murmishi , inkaje gurin budurwarka kace ta bani tsaraba kaji , ɓata rai yayi kana yace " ke a rayuwarki bakida damuwa banda ta tsaraba ?" iye , to naga kayi kyau ne haka fa yayanmu yake kwaliya yake tafiya hira gurin anty fiddausi , to ni ba shi bane gurinki zanzo hira , dariya tasa tace " ƴar ƙarama dani ta rufe fuska , tana ganin zai fita tace " nima zan bika , no part ɗin Ammi zani ki zauna yanzu zan dawo naga ma kamar bakiyi sallah ba , zan da asbha sai in haɗasu hakama jiya nayi , zaro ido Khamis yayi yace " to Allah ya kyauta amma dole in nemi bulala kodan marar yin sallah, ai mama tace " ba'a dukan matan aure inka dakeni sai na rama Aisha ta faɗa ko a jikinta , ring wayarsa ta fara dubawa yai yaga Ammi ce da sauri ya fice Aisha ta ruga da gudu tasha gabansa tare da cewa " sai na rigaka zuwa wlh ta ƙara da gudu , tana shiga taci karo da Afnan taci kwaliya leshi tasa mai tsadar gaske milk color mai ratsin jan zane gyalenta siriri ja da takalminta mai tsini shima ja , fuskarta na ɗauke da glass baƙi wanda ya mamaye ilahirin fuskar tata , ke gurin wa kikazo Afnan ta jefo ma Aisha tambaya tana harararta hakan yayi dai dai da zuwan Khamis yace " gurinki tazo tunda gidan naki ne ke kaɗai , shiru tayi kamar ruwa ya cinyeta ta koma gurin Ammi da ta shiga bedroom ɗinta ta cire kaya zata shiga wanka , turo ƙofar tayi tare da sallama , har kin shirya ne ?" Ammi ta tambayeta eh na shirya Ammi one week zanyi Ammi , to ki gaida momyn naki ga wanan ki kai mata , haɗin turaruka ne Ammi ta bawa momyn Afnan masu kama jiki sosai ga tsadar gaske , ficewa Afnan ɗin tayi ba tare da ta kalli su Khamis dake dining suna cin abinci ba , kira Ammi ta ƙwalawa Afnan , Afnan na zuwa Ammi tace " karki tari mashin a titi kiyiwa haliru magana ya kaiki tom Afnan tace " idonta na kan Khamis ko ƙiftawa batayi , ta fice Ammi dake sanye da hijab bata shiga wankan ba ta dubi Khamis tace " son ya kamata zuwa gobe akai yarinyar nan gidansu taga iyayenta fa , tom Khamis yace " Allah ya kaimu Ammi ta tafi ta barsu a gurin tsalle Aisha ta doka tace " waya ganni a cinyar mamanmu kai tasa dariya zani inga Ummi tanata surutunta shikam hankalinsa na kan soyayyar taliyar da Amminsa tayi masa, da gudu Aisha ta fice ta nufi part ɗinsu gurin kayanta tayi ta fara haɗawa a fili tana cewa " idan naje wata ɗaya zanyi in dawo .....! 😥ina fama da ciwon kai ina buƙatar adu'arku fans [23/08, 8:02 pm] Mom Islam Ce 💃: 9 &10 yana kammala ci ya wuce masallaci sai da yayi shafa'i da wutiri kana ya dawo part ɗinsu , samunta yayi ta cika gadonta da kaya waro ido yayi yace " mezan gani wanan kayan fa ?" duk na tafiya gida ne Aisha ta faɗa tana ci gaba da haɗo kayan , sai da ta cika akwati da kaya tam har tana hawa kansa dan ya rufu tana zuge zip ɗin ta fito yau bakin yaki rufuwa , ƙarfe goma na dare bacci ne a idon sa sosai amma tsabar murnar gida da takeyi yasa taƙi koda rintsawa , sai yayi bacci sai tazo tana yi masa waƙa a kunne , kamar zai rafza ihu haka yake jinsa sai wajen ƙarfe ɗaya ya samu bacci ya ɗauketa gashi babu halin duka. Washe gari tun asbha Aisha ta tashi ta shiga toilet ta ji jiƙa wankanta ta fito ta mulka mai ɗakinta ta nufa domin sa hoda ,tana sauko da akawatin kayan make up ta gigice dan ma mama ta rage wasu kayan , kwalliya ta fara tana yi tana kallon mudubi. Jan baki ta ɗauko ja 24 hours ta damɓara tana ta gogawa har sai da saman bakinta ya samu idanunnan sunsha jan jambaki ga kwali data sashi kamar mai siyarwa , fitowa tayi sanye da ɗinkin doguwar riga na shadda da farin gyale duk da gogawa gyalen janbaki , cin karo sukayi da Khamis daya dawo daga masallaci innalilahi yace " bai kai ga ƙarasawa ba yaga ta wangale masa fararen haƙoranta tace " kyakkyawa nayi kyau kuwa ? dama akwai kayan kwalliya a wanan ɗakin shine kaƙi gayamin ko ?". toshe bakinsa yayi kana yace " to ai kinfi kyau inbabu kwaliya , cuno bakinta tayi alamar fushi hakan ma ya kuma basa dariya . " me ya sami gyalen ki naga duk jan abu ?" Khamis ya tambayeta yana dariya , ban sani ba ta bashi amsa tana mai ci gaba da tafiya ta fice daga sashen nasu ta nufi na Ammi , tana cikin tafiya sukaci karo da mai gadi zaro ido mai gadi yayi yana jinjina kai , " yada kallo ido ba kwalli Aisha tace " masa tana murguɗa baki ,bai dai kulata ba yasan halin ogan nasu ya wuce ya barta tayi part ɗin Ammi , Ammi dake zaune da ƙaramin cup a hanunta tana ganin Aisha ta zaro ido tare da cewa" mezan gani ?" ƴata kwalliyar ce haka , eh mama kinga kyakkyawa sai dariya yake yimin wlh kuma munyi faɗa dashi ma , " kiyi haƙuri to muje bedroom in wanke miki fuska inyi miki wata kwaliyar , maƙe kafaɗa Aisha tayi tace " ko a gida haka muke kwaliyar mu kuma munfi ƴan matan anguwarmu iya kwalliya nida Ummi. " wacece Ummi ?" Ammi ta tambayeta , ƙawata ce mama dan Allah in munje ki taho da ita zamu dinga tayaki aiki , Aisha rigima Ammi tace " a cikin zuciyarta, zodai muyi mu shirya kar son yazo yana jiran mu Ammi tace " tare da janyo hanun Aisha. Wanke mata kwaliyar tayi ta goge mata fuskar kana ta ɗauko mai da powder ta shafa mata ta kawo man baki ta goga mata da kwali ba ƙaramin kyau Aisha tayi ba kasancewarta ƴar fara mai manyan idanu "to jeki palo ki jirani nima barin shirya , tom Aisha tace " tana tafe tana rangwaɗa kamar zata faɗi ƙasa inka ganta abin sai ya baka dariya duba da yadda take karai raya ita a dole ƴan mata , Cikin shigarsa ta alfarma ya shigo palon Ammi, Ausha ya tarar a zaune ta ɗora ƙara ɗaya kan ɗaya tana zaro ido , gimbiya my Esha zo inyi miki photo Khamis ya faɗa yana murmishi , abin nema ya samu wai matar bakanike ta haifi sifana ,Aisha ta miƙe tare da tahowa tana yanga , Khamis bai san lokacin da ya tuntsure da dariya ba , cikin jin haushi Aisha tace " nama fasa ɗaukar hoton kalan in na ɗauka ka nunawa budurwarka kuyi ta yimin dariya , ta haɗe rai kamar mai shirin kuka " am sorry my Esha na tuba Khamis ya faɗa yana ɓata fuska alamar damuwa , fitowar Ammi ne yasa Khamis kama kanshi tace " kowa ya shirya ko ?" eh su Khamis da Aisha sukace , ficewa sukayi baba mai aiki tayi musu Allah ya kiyaye suka shiga mota , sai anguwar su Aisha Ammi ce tace " driver ya kaisu wata plaza dake gaban anguwarsu zasuyi siyayya ,babu musu ya kaisu yai parking a inda motoci suke fakawa , suka fito dukkan su hanun Aisha a na Khamis kai tsaye katafaren shagon suka shiga mai ɗauke da kayyayaki na amfani kayan abinci Ammi ta lodar musu da su maggi da kayan ƙamshi katan katan harda buhun shinkafa ƴar gwafnati lol. ma'ai katan gurinne suka dinga loda musu a mota ana gamawa Khamis yaje gurin biyan kuɗi ya biya suka tafi. Drivern yayi gudu cikin ikon Allah sai gasu a anguwar suna zuwa Aisha ta hau dariya tana yi musu shirme , ana parking Ammi na fitowa itama ta buɗe ta bugo ƙofar da gudu ta shige gida , mama da ta fito daga bayi har zata ruga sai taga Aisha ta faɗaɗa fara'arta tace " oh kekam bakya girma ko kaɗan keda wa kukazo ? nida maman kyakkyawa zaro ido mama tayi tace " waye kuma kyakkyawa , kodai mijin naki ne ?"eh Aisha tace tare da hayewa bishiyar mangoro , faɗa mama ta kama yi mata akan ta sako amma ina tayi nisa ko saurarar mama batayi ba , sallama su Ammi sukayi itada Khamis , cikin fara'a da karamawa mama ta karɓesu tare da yi musu marhabum , ku shigo mama tace " tana shirin shiga ɗakinta da ta gyareshi tsaf babu datti tabarma ta shimfiɗa musu akan sabuwar ledae ɗakin suka zauna tare da gaisawa , bayan sun gaisa ne Ammi take tambayar Aisha , ƙwala mata kira mama tayi tace " bazaki zoba ana kiranki , a ina take ne ?" Khamis ya tambaya " daga zuwa ta haye bishiyar mangoro wlh mama ta faɗa tana nuni da hannu , oh Khamis yace " Aisha rigima ya miƙe ya fita , tsayawa yayi a dai dai saitin bishiyar yace " haba mana my Esha pls ki sauƙo Ammi na kira. "Taɓɓ Aisha tace " bazan sauƙo ba kasan kewar bishiyarnan da nayi kuwa ?" to a ita nake wuni kullum garama ka tafi , inkuma zakayi min tari to dan naga akwai wanda suka bra wata dariya ce ta tahowa Khamis banda so ba kamar Aisha ta dinga yi masa surkulle yana saurarar ta shima kansa ya fara mamakin irin son da yake yi mata har baya ganin yarintarta ko wautar ta, naji zanyi miki ai zamukai yamma a nan ki sauko dan Allah , to Aisha tace " ta sauko hanunta ɗauke da wani jan mangoro tace " wanan mama zan kaiwa tasha tasha taji irin mangoron gidan mu , hanunta ya kama suka shiga ɗakin mama , suna shiga Ammi ta kamo ta tace " baki fa gaida mamanki ba kika haye bishiya murmishi mama tayi daɗi ya kamata taga Aisha harda kumatu ga wata ƙiba da tayi. " yiwa driver mgna ya shigo da kayan nan son , ok Khamis yace " tare da ɗaga wayarsa ya dannawa driver kira , driver dake zaune a mota yana ganin kira ya fito tare da amsawa , ka shigo da kaya inji Ammi to drivern yace " Khamis ya kashe waya. Niƙi niƙi driver ya kwaso kaya ya fara shigowa dasu sai da yayi sahu huɗu sanan ya kammalah , tun daga nesa malam ya hango ana shiga da kaya gidan washe baki yayi kana a fili yace " kai masha Allah ga sabon aure ga abinci na warke wlh , yana isowa daf suka gaisa da drivern ya shige gida , yana shiga su Ammi na fitowa zasu tafi , da gudu Aisha taje tace " malam ina kwana a'a ƴar albarka ya gida ya ƙiriniya?" malam ya faɗa yana faɗaɗa fara'arsa....! *MOM ISLAM* [24/08, 6:33 pm] Mom Islam Ce 💃: 11 & 12 Bayan su Ammi sun gaisa da malam suka yiwa mama sallama , Khamis ya kira Aisha da gudu ta biyoshi kasancewar daya kirata waje yayi , Ammi dake zaune a gidan gaba ta jinjina kai tayi tana mamakin wanan soyayyar da Khamis ke nuna ma Aisha. Yana tsaye ya harɗe hanunsa ɗaya kan ɗaya idanunsa a kanta , tana ƙarasowa ya lumshe ido kana yace " my Esha kizo mu tafi dan Allah ya marai raice fuska kamar mai shirin yin kuka , tuntsirewa da dariya Aisha tayi kana tace " a hayeee namiji da shagwaɓa zaro ido Khamis yayi yace " Ammi fa na jinki kiyi a hankali yanzu dai kizo mu tafi , maƙale kafaɗa Aisha tayi tace " inason zuwa gidan yaya gobe kuma anjima zani kasuwa , eh kasuwa fa kikace ?" wlh kar inji labari kina matar aure zakije kasuwa ? uhm ni fa ka dena cemin matar aure yarinya dani , innaje kasuwar ma innaga budurwa zanyi maka magana , janyo mata hannu yayi kana yace " aiko kinban kwana gobe na kawoki gidan yayan naki ya turata a mota shima ya shiga kana yace "wa driver muje karka tsaya , kafin Ammi tayi magana driver ya figi mota . Faɗa ta kama yiwa Khamis akan mai yasa zai yi wa Aisha haka. " Ammi kasuwa fa zataje tana matar aure , murmishi Ammi tayi tace " bafa sharaɗin da za'a gindaya wa babbar mace zakayi mata ba dole tana buƙatar wasu abubuwan na yara. Fuskar Khamis a haɗe ya kalli Aisha yaga kuka take wiwi wanan hawayen dake zuba daga fuskarta kamar ana zuba masa wuta yake ji amma ya riga ya cika aiki dan har sun hau titi ya rungumeta , tana shash sheƙar kuka bacci mai nauyi yai awon gaba da ita , suna isa gida driver na parking ya fito ya buɗewa Ammi mota kana ya buɗewa Khamis dake back side shida Aisha , fitowa Ammi tayi bata tsaya kallonsu ba tayi part ɗinta , ɗaukar Aisha yayi shima ya nufi nasu part ɗin da ita , kwantar da ita yayi a bed ɗinsa kana ya shiga toilet ya watsa ruwa tare da ɗauro alwalar azhar , yana fitowa ya sanya farar jallabiya ya nufi masallaci , bayan an idar da sallah ne ya dawo gida yana dawowa yai part ɗin Ammi , a zaune ya sameta tana waya zama yayi yana jiranta gama yayi mata magana , tana ajiye wayar yace " my Ammi zani office yanzu , duba agogo Ammi tayi ƙarfe biyu da minti biyar ,tace " kayi haƙuri gobe kaje man ?" no Ammi akwai wasu fils da ban samu na cike ba shiyasa , Allah ya tsare Ammi tayi masa ya fice tare da cewa " Amen. Part ɗinsu ya koma ya sauya kaya kana ya daɗa luluɓe Aisha ya kira baba mai aiki yace " ki kularmin da ita dan Allah kisamo min ƴar aiki kunyi kaɗan gaskiya , washe baki baba tayi tace " insha Allah ranka shi daɗe dama gobe zani ƙauyenmu akwai ƴar gurina tana ta so ta biyoni ina hanata kaga sai tazo ko ? ok Khamis yace " yana sanya farin gilashi a idanunsa ya fice . Drivern sa na ganinsa ya fito da motarsa kana ya buɗe masa ya shiga yana shiga suka ɗauki hanyar zuwa ma'aikatar tasu , Sunyi tafiya mai nisa kana suka iso ana parking ya fito yai hanyar office yana shirin shiga ma'aikata suka taho suna gaishe sa ,amsawa yayi cikin ƙasaita suke tambayarsa ko lafiya bai zo da wuri ba ?" lafiya Khamis yace " naje anguwa ne shiyasa , ya shige office , zama yai a ƙayatacciyar kujerar dake juyi ya fara juyi yana nazarin wani abubuwa , nocking aka fara sai da yai jimm kana yace " yes , budurwar jiya ce dai wato muhibbat tana sanye da wani material yellow mai ratsn flower fari yana da adon duwatsu masu kyau , zama tayi batare da jiran izini ba ta dubi Khamis tace " barka da war hakan ranka shi daɗe dafatan dai lafiya muka jika shiru yau ?" lafiya lau sai alkairi Khamis yace" cikin ƙosawa da tabar office ɗin dan yasan abinda ya kawota , am nace ya maganar mu ta jiya ka amince ?" cewar Muhibbat wani kallon banza yayi mata kana yace " ke ki shiga hankalinki banison takura kikayi wasa zaki bar ma'aikatar nan gaba dayanta , zaro ido Muhibbat tayi kana tace " Allah ne ya haɗa jininmu ka yarda dani . cikin faɗa faɗa Khamis yace " saboda rashin hankali da tunani baki sanni ba bakisan koni waye ba yaya halina yake mai kyau ne ko marar kyau amma kina iƙirarin in aureki aure abin wasa ne ?" to bari kiji Allah da kansa yace " ku zaɓawa ƴaƴanku iyaye na gari haka itama mace ta zaɓarwa ƴaƴanta uba na gari duk mazan da suke kai kawo bakiga wanda yayi miki ba sai ni ?" to wlh kina cikin matsala ya buga takardun daya ɗauka ya fice ya barta cikin zafin rai , ko kiran driver baiyi ba ya figi motar a ɗari yabar ma'aikatar , kuka ta fashe dashi mai tsuma zuciyar mai karatu . Miƙewa tayi ta fice ta nemi guri ta zauna tana ci gaba da kuka har yamma tayi idanunta duk sun kumbura tsabar hawaye , ƙarfe shida nayi ta nufi bakin titi ta hau a dai daita ta nufi gida . Yana komawa gida direct part ɗinsu ya shiga samun Aisha yayi tayi wanka tana cin soyayyen dankali , ganinta cikin kwanciyar hankali ba ƙaramin daɗi yayi masa ba hakan yasa ya sa hannu a aljihunsa ya ciro kuɗi ƙirga dubu biyar yayi yaba baba mai aiki dake zaune kusa da Aisha tana yi mata hira , gashi baba " Khamis ya faɗa yana miƙa mata . Hannunta na rawa ta karɓa tana murna ta fara sanya masa albarka , sai da Aisha ta cinye tsaf sanan tazo gurinsa ta zauna kusa dashi tace " shine kayimin wayo ko ? murmishi kawai yayi sbda a halin yanzu bayason magana komi ƙanƙantar ta , kama kunnensa Aisha tayi tace " nifa ka kulani kokuma inta kuka sai ka maidani gidanmu , shiru yaƙi kulata , ihu ta zunduma tana shure shure a tsorace ya tashi tsaye dan wata maganar da take yi ba jinta yake ba kasancewar yayi nisa a kogin tunani , cak ya ɗagata sama yana juyi da ita tana dariya ga kuma hawaye , shima dariyar ya keyi amma ta dole dan karta dameshi da kukanta mai rikita mutum . Na gaji ka saukeni , Aisha tace "tana dariya , sauketa yayi ya koma ya zauna , haka ya kwana cike da tunani iri iri. Washe gari ji yayi gurin aikin ya fice masa a kai kwata kwata baya ma sha'awar zuwa , bayan ya fito daga sallah ya shiga sashen su , samun Aisha yayi har tayi wanka ɗakin ya gaure da ƙamshin turare iri iri ga wata kwalbar a ƙasa ta fashe , innalilahi wa ina illaihir raji'un Khamis yace " tare da cewa " Aisha mezan gani haka ta 'adi kikayi min ne ? jikinta a sanyaye ta rakuɓe gefen gado tana bashi haƙuri , kinsan tsadar wanan turaren kuwa Esha kika fasa min ?"cikin tsoro ta hau girgiza kai alamar a'a to dubu ɗari ne ya nuna kwalbar data fashe , kuka Aisha ta fara tana cewa " dan Allah karka dukeni wlh bazan ƙaraba bada sanina nayi ba nazo sawa a jikina ne kawai kwalbar ta faɗi , goshinsa ya buga kana ya nemi guri a gefen gadon ya zauna yana ƙarewa Aisha kallo , kwaliyar dai irinta jiya ita ta kuma yi yau kuma janbaki tasa mai ruwan toka inka ganta kamar wacce ta shafa farar ƙasa a baki , ga ɗige ɗige da tayi kamar yammatan ƙauye , bayajin yin dariyar yau ga fasa turare ko kwana uku ba'ayi ba da siyoshi ga Muhibbat da take neman juya masa kwanya. babu abinda zanyi miki amma ki kiyaye kinji ?" to tace " kanta a sunkuye , a cikin akwatunan nan ai akwai turaruka ki duba zaki gani sai ki dinga shafawa , to Aisha tace " jiki a sanyaye ta ɗauka dukanta za'ayi sai sha biyu zan kaiki fa garama ki dena wani zumuɗi ,cuno baki Aisha tayi kana tace " ayya kyakkyawa in munje zakace ba kwana zanyi ba mu tafi yanzu . No Khamis yace " yana girgiza mata kai daɓas ta zauna kusa dashi ta riƙe masa hannu zatayi magana ta kalli fuskarsa , a turɓune take kamar bai tama dariya ba , na fasa zuwa yanzu mu bari sai anjiman Aisha ta faɗa tana kuma kallon fuskarsa ko zaiyi dariya , duk da haka taga baiyi ba , juya baya tayi ta fara kuka , jin kukanta yasa Khamis ankara da ita kai Khamis yace " tare da ɗora hannu a ka yana mai jin zuciyarsa a cunkushe, wai Aisha ya kikeso inyi da rayuwata ne ko so kike nima kiga ina kukan? da sauri ta girgiza kai ta share hawayenta ta juyo tana masa dariya , shima dariyar ya mayar mata kana ya rungumota ya kwanta tare da ita yace " shafa min bayana my Esha yau babu musu tana gudun kar tayi magana yaƙi kulata , haka ta dinga shafa masa baya har ta gaji bata ce masa ta gaji ba sai sharar hawaye takeyi , jin ɗumin saukar hawaye ne yasa shi ɗagowa yace " mai kuma ya sake faruwa my Esha ?" na gaji Aisha tace " tare da rufe bakinta , am sorry nama mance kiyi haƙuri ankalina yayi gaba yau ko gaishe da Ammi banje ba barinje in dawo ko ?" cikin marai raicewa tace " zani no karki biyoni ki zauna da baba zanyi mata magana ta shigo ki gaya mata abinda kikeso a dafa miki inyaso sai tayi miki , dariya Aisha tasa tace " wayo daɗi yau zan wahalar da baba kuma ko tayata bazanyi ba bari ta shigo ta kuma ƙyal ƙyalewa da dariya , shikam yau duk abinda Aisha take ya kasa dariya sbda halin dayasa kansa ficewa yayi yana fita zau shiga palo yaga baba maj Aiki tana goge kujeru , sannu tayi masa tana yawa Khamis yace " kana ya dubeta yace " baba dan Allah in bada wuri zaki tafi ba kije gurin Aisha ta gaya miki abinda takeso a dafa mata , to ranka shi daɗe sai zuwa azahar zan tafi , to Khamis yace " ya nufi bedroom ɗin Ammi dan bata palo, sallama yayi Ammi tace " ya shigo guri ya samu ya zauna kana kuma ya sauko ya durƙusa ya gaida Ammi bayan sun gaisa ne Ammi tace " yau lafiya kuwa ? son naga yanayin ka duk ya sauya ?" shafa sumar kansa yayi kana yace " lafiya Ammi me kika gani ?" ina tambayarka kana tambayata son ?" sunkuyar da kai yayi yasan inhar matsala ta samesa in bai faɗa mata ba babu kwanciyar hankali ko kaɗan , son akwai abinda ke damunka baka saba ɓoyemin damuwarka ba kana kuma baka saba ƙin baiyana min damuwarka cikin gaggawa ba ina jinka maza gaya min meke faruwa da kai baza kaje office bane yau ?" eh Ammi Khamis ya bata amsa , meyasa ?" babu komai ya kuma bata amsa . Akwai komai mana Ammi tace " tare da gyara zama , ka gayamin inba so kake raina ya ɓaci ba , uhm am Ammmmi ...katse shi Ammi tayi kana tace " ka fito kayimin magana sak banason jan layi ina sauraronka , gyaran murya Khamis yayi kana yace " ranar sana fara zuwa office wata budurwa ta shigomin office ta gabatar min da sunanta da rayuwar data fuskanta a gidansu ta ƙara da cewa " zan aureta ?" gaskiya bisa ga yanayinta koda banyi aure ba bazan aureta ba gaskiya bata yimin ba ya kwashe labarin duk inda sukayi yaba Ammi....! [24/08, 6:34 pm] Mom Islam Ce 💃: 13 & 14 Nisawa Ammi tayi kana tace " a kanta ne zaka dena zuwa aiki ina ka zamo jarumi man babana karka zamo rago mace ɗaya tana neman hargitsama rayuwa . Dafe kansa yayi kana ya miƙe yace " Ammi kaina ciwo zani in kwanta kuma anjima zan kai Aisha gidan su yayanta , badan Ammi taso rashin zuwansa office ba babh inda zatayi hakan yasa tayi masa fatan samun lpy mai ɗorewa ya fice , yana isa sashen su ya sami Aisha ta baje a kan kafet tana ta yagar naman kaza tana zaro ido , dariya ma ta basa ya ƙyalƙyale yana kallonta , murguɗa masa baki tayi tare da jefo masa harara , ni kike harara yau kuma ?" Khamis ya tambayeta yana ɓata rai kayi haƙuri bazan sake ba Aisha tace " tana gudun kar a ɗauke plet ɗin naman kazar , shigewa bedroom ɗinsa yayi ya barta a gurin ya kwanta , bacci yaƙi ɗaukarsa kasancewar yasa damuwa a ransa tashi yayi ya ɗauki key ɗin sabuwar motarsa da in ba shiba babu mai hawanta ya fito palo ya cewa " Aisha tazo su tafi ya fice , leda ta samu baƙa ta ƙulle ragowar kazar a ciki romon kuma ta shanye taje kitchen ta ɗibo ƙwai guda biyu suma ta zuba a ledar da magi ta ƙulle tasa hijab har ƙasa ta fito , kije ki yiwa Ammi sallama Khamis yace " mata to kawai Aisha tace " taje part ɗin cikin sa'a ta tarar da Ammi a palo cewa " tayi mama mun tafi , Ammi dake ƙarewa kwalliyarta kallo tace " haka zaki tafi da wanan kwalliyar maza zonon in gyar miki , da gudu Aisha ta ruga ta dawo gurin Khamis tace " mama tace " Allah ya tsare amin Khamis yace " tare da cewa " shiga mu tafi , gaba ta shiga ba suka bar gidan , yana hawa titi yace " da sharaɗi tun a nan zan fara faɗa miki kar muje kice ba haka ba tare zamu dawo ba kwana zakiyi ba , eh Aisha tace " ita dai burinta tana jaririya da kuma Ummi , suna isowa zata fice da gudu ya rungumota , ya ɗorata kan cinyarsa ya haɗe bakinsu guri ɗaya ya dara aika kisses yana lumshe ido ɗago kan da Aisha zatayi suka haɗa ido da Ummi , a zabure Aisha ta zamo tace " kyakkyawa na shiga uku Ummi zata iya gayawa malam muna iskanci kuma wlh ta ganmu yana shirin kamo mata hannu ya kamo ledar dake hanunta , meye wanan a ciki ?" Khamis ya jefo mata tambaya , babu komai , tana jujuya hannu aka fasa ƙwai anan ne Khamis ya gane ko me ta sa a ledar dan harda ƙashi yaji murmushi yayi kana yace " ƙuruci kenan yace " zo ki karɓa ki kaiwa Antyn naku , dubu biyu ya bata kana yace " zani gurin abokina anjima zanzo mu tafi tana zumuɗi tace" to tana ganin Ummi ta ɓata rai tace " to munafuka me kikaga munayi ?" zaro ido Ummi tayi tace " ke Aisha kice kinzama ƴar iska kuma sai na faɗawa yaya wlh bari ya shigo , matsalar ƙwallah Aisha ta fara tana haɗa Ummi da Allah akan karta gayawa yaya tayi haƙuri , nafa ganku keda wanan wanda ya kawoki , ke dallah can so kike suji to wlh nazo da abin daɗi bazakici ba kuma tunda naje kaza nake ci da dankalin turawa ke har girki ake yimin Aisha ta faɗa tana juya kai irinna yara , kee Allah Ummi ta faɗa tana tsalle , aiko zan biki wlh dariya Aisha tasa kana tace " kwaɗayayya kawai ,Ummi tace " kekuma ƴar iska kawai bin juna suka kamayi da gudu sukaci karo da yaya Zakari yana tahowa a ƙafa, durƙusawa Aisha tayi har ƙasa tace " ina yini yaya . Lafiya lau yayan yace " yana ƙare mata kallo , Yaushe ki kazo ya tambayeta yana daɗa kallonta , ɗazu banama shiga gida ba Aisha tace " tana sunkuyar da kai to ku muje ,yayan ya faɗa yana kallon Ummi . Da sallama suka shiga kaka suka samu zaune tana gyara tsintsiya , gaisheta Aisha tayi kana ta wuce ɗakin Anty Fiddausi a zaune ta sameta tana bawa jaririya nono suna kiranta da Afnan , a'a kaga amare anty Fiddausi tace " tana washe baki , sunkuyar da kai Aisha tayi tana dariya , miƙa mata yarinyar anty Fiddausi tayi tace " kinganta tana kama dake ko , dariya Aisha ta kumayi tace " ai batada dogon hanci suka sa dariya , fitowa Aisha tayi da yarinyar a hanunta suka shiga ɗakin da da yake mazaunin nata zama tayi ta bugi cinyar Ummi tace " wlh ki biyoni zaki dinga cin daɗi sosai har sawa za'ayi ayi miki girki , a gidan , cikin zumuɗi Ummi tace "ko ta bayan mota nabi ku ,dariya Aisha tasa tana kunce ɗaurin zani ta fito da baƙar ledar da ta ɗaure nama da ƙwai , ta mance ta rugur guje ƙwan duk ruwan ya ɓata mata jiki shirin kuka ta fara Ummi ta karɓi ledar taga nama ga kuma ƙwai shima ya haɗe sai ƙarni , kinsan me za'ayi Aisha zomuje kicin mu soya haɗe da naman , uhm wlh tsoron anty Fiddausi nakeyi cewar Aisha , dallah yaya na nan bazai fito yanzu ba zo muje , cikin sauri suka fito kaka na cewa ina zaku kuka haɗa kai kamar ƴan matan amarya , ganin sun nufi kitchen tace " me kuma zakuyi , duk cikinsu babu wanda ya kulata bare su nuna sunji abinda take faɗa , har suka gama suyarsu suka cika mangyaɗa da maggi anty Fiddausi bata sani ba kaka ce data jiyo ƙamshi take ta faman yi musu magana sunƙi kulata , fitowa sukayi da plet a hanun Ummi suka nufi ɗakinsu , jin maggi yayi yawa yasa Aisha cewa " bazanci ba nasan inna koma ma za'a soyamin ta cire hanunta , giwa ta daɗi Ummi sai murna ya daɗu Ummi tace " tana dariya kana ta kuma cewa " oh su Aisha ankoma masu kuɗi kina hutawa , kuɗin da Khamis ya bata taba anty Fiddausi ta ciro tace " kinga kuɗinnan me zamuyi dashi cewa " fa yayi inba anty Fiddausi , tashi muje kasuwa wlh mu kashe wa idonmu ƙwarƙwata , Ummi ta faɗa tana tafawa da Aisha aiko kin kawo shawara cewar Aisha . Kayan kwaliyan da yaya Zakari ya siyawa Ummi suka ɗauko aka fara kwaliya ta hauka , kaka na ganinsu tace " tunda waccan yarinyar tazo mai kamada fulawa ido kamar gurjiya nake yi miki magana Ummi kinƙi kulani ko?" sai mun dawo kaka Ummu tace " tana ruƙo hanun Aisha , suna fita sukaci karo da motar Khamis Ummi bata san ko waye a motar ba dan ta mance motar da aka kawo Aisha , Aisha na ganinsa ta juya da gudu tayi gidan yaya ɗakin anty Fiddausi ta faɗa abinda ta gani ne yasata sunkuyar da kai anty Fiddausi akan cinyar yaya sun haɗe lips ɗinsu guri ɗaya. oh Aisha ta faɗa ashe suma sunayi to ba iskanci bane ?" duk a cikin zuciyarta take wanan zancen .maganar da taji ne yasa ta ankara da taji ana cewa " bazaki fita ba marar kunya , muryar yaya ta tsinkayo yana yi mata faɗa , kafin ta fice tace " ga Khamis nan yazo gaishe ku zai shigo ta fice , ɗakinsu na da ta koma tasa hannu a baki tana tambayar kanta to wai shin ba iskanci bane ?" ai kyakkyawa ma yana yimin haka aiko zan tambayi mama duk ranar dana koma , zama tayi sai ga Ummi nan ta shigo , ke wlh mijinki ne yazo kuma yace " kizo ya aikeni yace " incewa Anty Fiddausi zai shigo kuma tayimin faɗa jiya tace " in yaya ya shigo kar in sake in shigo mata ɗaki cewar Ummi . Ke wlh karki sake ki shiga iiiskanci sukeyi kina shiga zai ɗura miki zagi dan haka karkishiga muje wajen gurin kyakkyawa , dakatar da ita Ummi tayi kana tace " zaku tafi dani ɗin? ke yaya ya dawo wlh kinsan basa shiri da kyakkyawa , to bazaku tafi dani ɗin ba kinenan Ummi tai rau rau da ido tana shirin yin kuka zomuje ko zamu sami kuɗi.....! Mom Islam [25/08, 4:34 pm] Mom Islam Ce 💃: 15 & 16 Suka fice , fitowar yaya Zakari ne yasa su dai daita nutsuwarsu ya miƙawa Khamis daya fito yanzu hannu suka gaisa , bayan sun gaisa yaya ya tambayesa ya al'amura yace lpy ya wuce , Khamis ne ya dubi Aisha yace " wanan ce Ummi ?" eh Aisha tace " tana washe baki , to ku rakani in gaida mutanen gidan , Khamis ya faɗa yana kamo hanun Aisha , a tare suka shiga ya da sallama ya durƙusa ya gaishe da kaka dake ta fama da haɗa tsintsiya , da gudu Ummi tayi ɗakin anty Fiddausi tace " ka shigo , babu musu ya shiga ya zauna kan kujera suka gaisa ta miƙa masa yarinya , miƙewa yai yace " zai tafi ya ajiye musu dubu goma yace" gashi a siyawa yarinya riga ya fita , ashe an bada kuɗi a kunenen kaka , tana ɗingishi ta taso kasancewar ta gashi da zama tace " a raba a bani nawa dama ina sha'awar cin kifi yau sai in shiga kasuwa , farr da ido anty Fiddausi tayi tare da kai kuɗin uwar ɗaki ta ɓoye su tana zaro ido tace " ai jaririya yaba ba kowa ba dan haka babu wanda zanba kuɗinnan a to . Kambun uba wlh baki isa ba dole a raba ke Ummi nawa ya bayar ?" dubu goma Ummi tace " tsalle kaka ta buga tace " kan uba taɓɓ amma wlh baki isaba kai kinyi kaɗan bari zakari ya shigo ,Ummi ta ƙyalƙyale da dariya tace " kaka anji kuɗi an ruɗe , ke ƴar nan dole in ruɗe kuma tilas taban kaso na . Ummi na gurin masu rabon kuɗi har Khamis ya tafi da Aisha bata sani ba tana fitowa taga wayam babu su babu alamar su ihu ta fasa tare rushe wa da kuka , yaya Zakari da yake tahowa yana waya ya ɗaga mata hannu alamar meke faruwa?" bata bashi amsa ba ta zauna tana ta shure shure , ɗagota yayi ya rungumeta ya kaita gida suna shiga yaji ana drama tsayawa yayi daga nesa da ɗakin anty Fiddausi yana fahimtar abinda ke wakana , murmishi yayi ya sauke Ummi yace " jeki kwanta . Ɗakin anty Fiddausi ya shiga kaka ya samu a zaune tayi tagumi kamar wace aka yiwa mutuwa , ƙunshe dariyar data taho masa yayi yace " kaka lafiya kuwa naganki haka?" lafiya ɗannan kaka tace " tana nuna anty Fiddausi tace " kaganta nan kuɗi wanan yaron daya shigo ɗazu ya bamu har dubu goma shine ta ɓoye wlh kazo ka karɓar min haƙƙi na , dariyar da yake ɓoyewa ce ta kuɓuce masa sai da yayi mai isarsa kana ya dake ya dubi anty Fiddausi yace " ki bata rabi , cuno baki anty Fiddausi tayi kana tace " ko sisi bazan bata ba kamaji da kyau. Ina wasa dake ne FIDDAUSI cikin kakkausar murya yake maganar , tun wuri kibata nace miki , anty Fiddausi na bubuga ƙafa ta shiga cikin ɗaki ta fiddao dubu biyu ta miƙawa kaka kafin ya kai hanun kaka ta hango kuɗin dubu biyu ne ihu tasa tare da sanya hanunta a kai ta rushe da kuka , a razane Ummi ta fito jin kuka a gidan batare da neman izini ba ta shigo ɗakin anty Fiddausi samun kaka tayi a durƙushe da hawaye shaɓe shaɓe a fuskarta , nuna kaka tayi kana ta ƙyal ƙyale da dariya tace " Allah shi ƙara akan kuɗi kina kuka , dariya yaya Zakari ya ƙarayi a karo na biyu yace " kin ɗauko kuɗin ko sai na je na ɗauko nabata duka ?"sanin zai iya aikata hakan yasa ta shigewa da gudu ta kwashe kuɗin ta ƙaro dubu ɗaya akan dubu biyun da taba kaka ta miƙa mata ,share hawaye kaka tayi kamar ƙaramar yarinya tace " ai nasan tunda akaba kura ajiyar nama sai taci amana , gwalo anty Fiddausi tayi mata ta nemi guri ta zauna , miƙewa kaka tayi kana ta fice waje ta nemi guri ta zauna kusa da tsintsiyarta ta fara lisaafo abubuwan da zata siya da dubu uku , sai da ta lissafa inda kuɗin zai ƙare kaf ciki kuwa harda tsire , kana taci gaba da gyaran tsintsiya . Fitowa Ummi tayi ta kalli kaka tace " su kaka anji jiki wlh harara kaka ta watsa mata tana murguɗa baki , dariya Ummi tasa tace " wai dama tsofaffi suna murguɗa baki kai abin dariya , wurga mata tsintsiya kaka tayi, Ummi ta shige ɗakinsu da gudu . Suna mota Aisha na kuka wai sai dai Khamis ya koma ya taho da Ummi duk da haƙurin da yake bata taƙi saurararr sa parking ɗin motar yayi a gefen titi ya janyota jikinsa yana aikin rarrashi , jijigata yake kamar wata baby " am sorry my happiness pls kiyi haƙuri insha Allah za'a kawo Ummi zansa driver ya je ya ɗauko ta , yana ta shafa mata kai yana bata haƙuri da ƙyar ta haƙura sai da yace " zai sa ayi mata farfesu ta haƙura ya tada mota suka ɗauki hanya , suna isowa yayi parking a parking spice , drivern shi da ya taso jin shigowarsu yazo yaɗe masa mota kana ya buɗe na Aisha fitowa tayi ta ruga part ɗin Ammi da gudu tana dariya idanunta da alamun hawaye , janyota Ammi tayi tace " zauna kun dawo lafiya ?" lafiya lau Aisha tace " tana wasa da hijab ɗinta , naga kamar kinyi kuka Ammi ta watso mata tambaya " ba kyakkyawa bane ba yaƙi ɗauko Ummi kuma tana can tana kuka , ta karashe maganar tana shirin kuka , sorry Ammi tace " mata karki damu zansa a ɗauko ta ai sai an tambayi iyayenta , ko ?" girgiza kai Aisha tayi alamar eh. Ammi ce tace " wa Aisha gobe mai yimiki lesson zai zo ku fara kafin a kaiki school , faɗaɗa fara'arta Aisha tayi tana tsalle akan kujera tace " to mama . Su Ammi na fita malam ya leƙo ɗakin mama ganin kayan abinci lodi lodi yace" aiko sai dai a raba dan bazan yarda ba an jido kayan an kawo ɗakinki kece mai gidan ?" Kai malam abinda kake yimin ya fara isata wlh dan kaga ina ƙyaleka kake yimin kowane abu to sam bazan lamunta ba dan zakayi aure shine zaka cigaba da wulaƙanta ni , mama tana huci ta faɗa cikin rashin jin tsoro , taɓɓ lallai wuyanki ya isa yanka wato ni kike gayawa baƙaƙen maganganu irin wanan ko ?" malam yaci gaba da cewa " aure kam babu fashi ko baƙin kishi ne ya taso to ya kwanta aure sai nayi . Komawa ɗaki mama tayi tana mai jin ɗaci a zuciyarta , da takalmi malam ya shigo kana yace " a raba biyu a bani nawa in haka ne ma ai nine na yarda da maganar auran sbda ke baso kike ba , dama nasan zamu sami alkairi Allah sarki Aisha ɗiyar kirki malam ya faɗa yana share hawaye mama da dariya tazo mata tace " daga baya kenan wai anyi sadaka da bazawara , janyo kayan mama tayi ta fara rabawa kamar inda malam ya buƙata ta cire nata ta tura masa nasa kwasa yayi ya kaisu ɗakinsa kana ya fice. Afnan na isa gidansu ta tarar da dadynta yayi tafiya zuwa india gurin aikinsa kasancewarsa baban likita , momynta ta samu zaune a palo tana kallo bayan tayi sallama momyn ta amsa ta faɗa jikinta tare da sakin kuka , cikin tsoro momyn nata tace " lafiya kuwa daughter maiya faru ?" ta jero mata tambayoyi , share hawayenta tayi kana tace " momy ya kusa kasheni duka yayi min har sai da aka kira doctor , kan uba ita yayan tana kallonsa ?" momyn ta jefo mata tambaya , to wlh bazata saɓu ba kema can da shegen son dangi gashinan kina matashiyar budurwa ya bar miki tabo a fiska dallah matsa ki bani guri , cikin tsanantar kuka Afnan ta ƙara riƙe momynta tana cewa " akan na daki wanan matsiyaciyar yarinyar nan ne fa shine yamin duka Ammi ce ta ƙwaceni wahattt momyn Afnan tace " kema anyi banza uban me kikeyi da baki rafka masa wani abun ba , buɗe baki Afnan tayi kana tace " ina sonsa fa momy inya ji ciwo fa ? dan ubanki in yaji ciwo kece kikaji banza wawuya kin damu dasu daga shi har uwar tashi amma basu damu dake ba , share hawayen fuskarta Afnan tayi kana tace " Ammi akwai milk a fridge ?" eh mazai hanashi samuwa , momyn ce ta ƙwalawa ƴar aikinsu mai suna Hanne kira , da sauri ta shigo momyn tace "kawowa daughter milk, tom Hajiya Hanne tace " tare da tashi daga durƙuson da tayi taje ɗauko milk, yanzu dai me kika fahimta a zaman yaronnan da figigiyar yarinyar nan ?" momyn Afnan ta tambayi Afnan , Afnan ce tace " am gaskiya na lura zata basa wuya Ammi kasancewar a haka kamar yanada buƙatar mace " amma soyayyar wanan shegiyar ta rufe masa ido wlh ta yarfe hannu , turrr wlh momyn Afnan ta faɗa tare da miƙewa tana zagaye palo , ta ƙara da cewa " shin yaya bazata lamunci haɗa auran zumunci bane ko yaya ?" tunda nayi mata magana tun kafin ya rakito wanan ƴar talakawan nake magana amma tayi yimin banza , ni banda tulin dukiya da ubansa ya mallaka wlh babu abinda zai sa in matsa da inason ya aureki , Afnan da ke shan milk ɗin da aka kawo mata yanzu tace " nidai gaskiya momy soyayya nake yimasa ta tsakani da Allah kuma ina fatan ya zamo min abokin rayuwa , ta ƙarashe maganar tana rufe fuska , banza wawuya momyn Afnan tace " tana hararrar Afnan , kenan ko kunyi auran bazaki yi mana hanyar tara dukiya ba ko ?" momyn ta faɗa tana kallon Afnan a kai kaice , no momy ba cutarsa zanyi ba , tsinka mata mari momyn tayi ta gurin da Khamis ya daketa , jin zafin dukan momyn nata yasa ta ganin wasu taurari na yawo , sai da jinta ya ɗauke na tsawon daƙiƙu kana ta dawo dai dai bata sami damar kuka ba sai da ta dawo normal ta fashe da kuka tana cewa " wlh sai na aureshi , momyn nata dake shirin ƙara mata wani tace " ki aureshin mu gani inhar bazaki cika min burina ba wlh keda auran Khamis kunyi hanun riga , kuka ta kuma fashewa dashi tana bawa momyn nata haƙuri , tureta tayi ta shige bedroom ɗinta tare da yiwa ƙofar key ta kwnta tana nazarin maganar Afnan na cewa " soyayyyar tskani da Allah za suyi , wato duk huɗubar da nake yiwa yarinyar nan duk a banza to inhar bazata nemo mana kuɗi ba to wlh babh ita babu auranshi ko da a mafarki , momyn ta faɗa tana cigaba da surutu kamar mai shirin yin hauka , bubuga ƙofar Afnan take amma momyn taƙi buɗewa a dole tayi fushi da ita tunda batason abinda take so , kuka take sosai mai ban tausayi ko a jikin momyn cikin ɗaga murya tace " ki koma inda kika fito , no momy karkiyimin haka dan Allah Afnan ta faɗa tana zubarda hawaye , palo ta dawo ta zauna jin zaman ya gundureta ya sata kwanciya ta lumshe ido , ƴar aikin gidan Hanne dake kaiwa da komowa ta ce " wa Afnan Hajiya da abinda za'a kawo ne ?" Afnan na huci ta wanke Hanne da mari tace " ubanki za'a kawo ko nace miki yunwa nakeji banza wawuya wuce ki bani guri ko in takaki , sum sum Hanne ta wuce tana tafiya tana waige ta shige kitchen tana gyare gyare tana kuka, a haka bacci ya ɗauki Afnan tana daga kwance tayi mafarki ga momynta nan da wuka tazo zata yankata , wani mahaukacin ihu ta darara ta miƙe da gudu zata fice , a take momyn ta fito cikin tsoro tace " daughter menene ?" babu komai Afnan tace " kana taci gaba da baccinta...! [25/08, 8:47 pm] Mom Islam Ce 💃: 17 & 18 Itama momyn koma ɗaki tayi abinka da uwa da ɗa , ƴar aiki kam tunda taji mari bata kuma dawowa ba . Khamis na shigowa ya sami Ammi da Aisha a zaune suna ta hira da fara'a ya zauna yace " Ammi na yunwa na keji , miƙewa Ammi tayi tace " aikin yau yayimin yawa baba mai aiki ta tafi gida , on Khamis yace " Ai nasa ta taho min da ƴar aiki saboda Aisha , juyowa Ammi tayi tace " wace ƴar aiki kuma ?" mai kula da ita Khamis yace " yana kallon yanayin fuskar Ammi da yaga sauyi tashi ɗaya , Ammina akwai wata matsalar ne ? ya jefo mata tambaya , Ammi na yin hanyar kitchen tace " babu komai , ta shige abin ya ɗaure masa kai amma bai fahimci komai ba , ɗauke da abinci a hanunta Ammi ta fito ta ajiyesu a dining ta koma ta ɗauko jug da ta haɗa kunun aya mai sanyi , zama Khamis yayi ya bude flaks ɗin abincin wani ƙamshi ne yayi masa sallama shinkafa ce mai miya taji kifi da naman kaza ga salad da akayi masa haɗi da bama coslw yaji yankaken ƙwai ga dankalin turawa da faffae Aisha na hangowa tayi gurin da gudu ta zauna a tata kujerar tace " kabeji za'a zubo mata , babu musu Khamis ya zuba mata kaɗan , ɓata rai tayi tace " a ƙara mata no Khamis yace " yana ɓata ciki inhar bai karɓeki ba , nidai ka samin Aisha tace "tana bubuga ƙafa , Ammi ce tace " zuba mata mana dan cikinka na lalacewa sai akace na kowa ma haka zaiyi ? yau da gudawa Aisha tace " tana buga tsalle , basu kulata ba amma Khamis ya kusa dawo da abincin bakinsa daurewa yayi , kyakkyawa zubomin romo harda kazar , Aisha ta faɗa tana shafa ciki , bazan zubo romon ba an faɗa miki kayan ɓata ciki ne nima yau cikin nawa sai ta Allah Khamis ya faɗa yana ci gaba da cin abincinsa , Ammi da ta gaji da damuwarsu tace " son wai maiyasa kakeson bawa yarinyar nan kuka ne ?" sa mata duk abinda tace " tana buƙata , sawa ya shiga yi a zuciyarsa ko yana tayata da adu'a , yawaa Aisha tace " ta hau tafi tana wurga ƙafafuwa ci take babu kama hanun yaro ta maida hankali inta tsoma ƙashin a cikin romon sai ta lashe haka ta dingayi tana ƙazantar ta miƙewa Ammi tayi dan ta gaji da surutu da kuma ganin ƙazanta tace "ni zani in kwanta , to Khamis yace " yana ganin Ammi ta shige yace " wlh ki dena shan romon nan haka , ina ko saurararsa Aisha batayi ba illa fari da ido da take yi masa tana gwalo , shima tashin yayi ya koma part ɗinsu ya kwanta kan kujera yana tuno maganganun Muhibbat . Aisha na zuwa ta zauna kusa dashi tace " zan faɗa maka wani abu amma sirri ne kuma amanatul amana alahira azaba inka faɗawa wani wuta bal bal , zaro ido Khamis yayi kana yace " taɓɓ bar abinki wanan fitina haka ya faɗa yana jinjina kai , kayi shiru kaji in faɗa maka, ɗazu naga yaya da Anty yana yi mata kalar abinda kake yimin kuma nace anjima zan tambayi mama , ido Khamis ya firddo waje yace " wace maman ?" maman gidannan Aisha tace " tana dariya , haɗe hannayensa biyu yayi yace " dan girman Allah karki faɗa mata zatayi min faɗa , kai kai kai ashe babu kyau ma ko ?" akwai kyau man amma ai mu munyi yara da yawa shiyasa Ammi zata yimin faɗa , to bazan faɗa ba amma sai kayimin alƙawari , ina jinki Khamis yace " rufe ido Aisha tayi kana tace " danbun naman nan da ka siyomin to shi zaka ƙara siyomin , kawo kuɗi Khamis ya faɗa yana miƙo hannu , a firgice ace " ya akayi kasan na boye kuɗi kai nifa mancewa nayi , Khamis da idonsa ke rufe sai yanzu ya gane maganarta , yace " dama baki basu kuɗin ba ?" da kuma ban basu bafa , oho ga wanan dai Aisha ra kunto bakin zaninta ta miƙa masa kuɗin daya bata , karɓa yayi ya ajjjiyesu a gefe , my Esha zo kiyimin tausa pls da sauri tazo ta haye kansa tana ta tsalle yana cewa " ouch tana dariya jin yayi shiru ya sata sauka tare da kiran sunansa kyakkyawa , bacci ya ɗaukesa hakan yasa ta koma kitchen ta ɗibo cin cin da ruwan sanyi swan tana ci tana gama ci taji cikinta ya murɗa da gudu tayi toilet tana gamawa ta tsuguna tana maida nunfashi , jin wani kashin ya taho yasa ta riƙe ciki dama bata fita a toilet ɗin ba taji gaba da tsugawa tana nunfarfashi , tana gamawa tayi tsarki ta fito bedroom ɗin Khamis ta shiga ta faɗa gado tare da kifa cikinta hanunta akan cikin ta shiga zaro ido , ba shiri wani kashin ya biyo baya ta miƙe da gudu ta faɗa toilet tana yinshi gashi irin mai ƙarar nan ne , tana tsaka da kashi taga Khamis ya faɗo bayi da gudu yace " kekuma me kikeyi anan ne Esha , gudawa ta bashi amsa tana nishi , inkin gama sauƙo ki bani guri walh yanzu na fara Aisha na gudun kar ta sauka Khamis ya hau inkashin ya kuma matsarta ina zataje tayi shiyasa taƙi tashi , sai matse ƙafafu yake ya rasa inda zeyi da yaji alamun kashin ya kusa fitowa da gudu ya shiga bedroom ɗin Aisha ya fara sakewa yana nishi harda ruƙe bango , yana fitowa ya nemi bakin gado ya zauna tare da zuba tagumi , zai tashi ya fito wani kashi ya kuma tahowa da sauri ya koma toilet yana tafiya a sunkuye , Aisha na can tana aikin kashi shima gashi yana nashi aikin kashin , bayan ya fito ne yaji cikin nasa ya ɗan lafa masa fitowa yayi ya dawo palo ya ƙara gudun AC da fanka nanda nan palon ya ɗauki sanyi , laƙwam yayi a kujera kamar wanda yayi ciwon sati sai ido zuru zuru , leƙowa Aisha tayi tace " wai naka kashin ya tsaya ne ?" gimtse fuska Khamis yayi kana yace " waye ya gaya miki kashi nake ?" oho gani nayi kuma wlh ina bayinka naji ƙarar kashinka , bai kulata ba yace " ke naki ya tsaya ne ?" a'a har yanzu Aisha tace " tana yarfe hannu jiri na ɗibarta , to Allah ya sawwaƙe zo ki bani wayata in kira family doctor , bazan iya ƙarasowa ba Aisha ta faɗa tana ɗingisa ƙafa , shima jikinsa babu ƙarfi ya miƙe ya ɗauko wayar dake kan kujerar dake nesa dashi ya danna lambar doctor , kazo akwai mara lafiya Khamis ya faɗa bayan sun gaisa to doctor yace " kana yace " gashinan zuwa , ajiye wayar Khamis yayi ya gyara kwanciyarsa jin cikin nasa yake babh komai kamar wanda baici abinci ba , bubuga ƙofar da akeyi ne yasa Khamis miƙewa doctor ne shida Ammi suka shigo , Ammi ce tace" doctor yazo yace " min wai ka kirashi shine nace to barinzo inga ko lafiya , Aisha dake tsugunne tama kasa tsayuwa tace " mama gudawa mukeyi wlh , zaro ido Ammi tayi kana tace " dukkan ku ? eh Aisha tace " tana riƙe da ciki , kiranta doctor yayi ganin ta kasa tafiya yace " bari yazo ya ɗauketa , a hassale Khamis ya taso duk da jikinsa babu ƙarfi bai hanashi zuwa gurin Aisha ya ɗaukota ba , doctor dai yaga ikon Allah yarinyar da batafi shekara sha biyu ba ake yiwa haka duk cikin zuciyarsa yake magana , Ammi dai sai ido dan yanzu ko kunyarta ma bayaji . doctor ne yace " sai an ƙara mata ruwa amma zai je ya dawo , kwanciya Aisha tayi tana juyi kasancewar cikinta dake murɗa mata, sannu Ammi tayi mata kana ta zauna kusa da ita take tambayarta ko tana buƙatar wani abun , a'a tace " mamaki ne ya kama Ammi sbda badai ka tambayi Aisha tace " a'a ba ko bazata ci ba tace " eh haka takeyi , lallai manyan mata babu lafiya Ammi ta faɗa a fili . Khamis da idanunsa suke rufe yana shirin gyara kwanciya Ammi tace " amma gobe zaka office ko ?" Allah ya kaimu Khamis yace " badan yanajin zai je ɗin ba...! [26/08, 7:41 pm] Mom Islam Ce 💃: 19 & 20 Bayan an gama yi mata ƙarin ruwa har wanda zai koya mata lesson ya zo Ammi tace "masa bata da lafiya haka ya koma. Magani aka haɗawa Khamis kasancewar basa shiri da allura. Washe gari jikin Aisha yayi sauƙi sai dai ƙarfi da babu sosai , Shima Khamis ɗin jinkin nasa alhmdulilh , Amma bai ko leƙa part ɗin Ammi har ƙarfe takwas na safiya , fitowa Ammi tayi kana ta shiga part ɗin nasu Aisha na cikin ɗaki Khamis ne zaune a palo da waya a hanunsa , shigowar Ammj yasa shi ajiye wayar ya maida hankali gurin jin abinda ya kawota , durƙusawaKhamis yayi ya gaida Ammi ya koma ya zauna . Bayan Ammi ta amsa tace "son yaushe zaka fita ne naga ko shiri bakayi ba , haɗe fuska Khamis yayi yace "Ammi dan Allah kibar maganar zuwa aikinnan babu abinda muka rasa na rayuwa dan haka ni nadena zuwa , Yaro yaro ne Ammi ta faɗa tana ƙara kallon Khamis taci gaba da cewa "to kasani shi nema yanada amfani yanzu inhar ka rasa dukiyar me kake tunani baka taɓa wahalar da kanka ba kullum a cikin daɗi kake so ka kiyayye nidai inason komawarka gurin aiki , tom Ammi Khamis ya faɗa a baki amma cikin zuciyarsa sam baya buƙatar sake zuwa , miƙewa Ammi tayi kana tace " ya mai jikin ?" " da sauƙi Khamis yaba Ammi amsa kana ta fice . Bedroom ɗinsa ya shiga ya sauya kaya kasancewae yayi wanka ya feshe jikinsa da turare masu sanyin ƙamshi ya fito, Har yanzu Aisha nata sharar bacci sbda magani da tasha. direct part ɗin Ammi ya shiga a palo ya sameta tana goga kwakwa oh my Ammi baba ta barki ke kaɗai kinata wahala , murmishi Ammi tayi kana tace " wahala kuma ai bashida wuya inason dafa shinkafa ne anjima shiyasa nake aikin da wuri , amma zansa a cigiya min ƴan aiki gaskiya mutum ɗaya tayi kaɗan Ammi ta faɗa tana dariya , ywwa mai Ammi zan wuce gurin aiki ammafa yunwa nakeji , to ai na gama shayi maza kaje dining ka fara dashi kafin in sauke indomie , "No Khamis yace "zan wuce kawai yau ko driver bai buƙaci ya rakasa ba haka ya tafi zuciyarsa cikin ƙunci yana isa bakin get ɗin tangamemen ma'aikatar mutane suka fito suna gaishe sa , ɗaga musu hannu yayi alamar yana amsawa , kana ya shige office. fils na mutane ya ɗauko kana ya ciro biro a aljihunsa zai cicike sbda tun ranar daya fara zuwa aka bashi bai duba ba sai yau, Saura guda biyu ya gama cikewa ya tsaya tare da juyi a kujera tunanin yayi masa yawa. Aslamu alaikum akace daga waje , bazai iya mance mai muryar ba tabbas kamar Muhibbat . Walaikissalam Khamis ya amsa tare da cewa " zaki iya shigowa cikin takunta mai jan hankali ta shigo ta zauna kan kujera tare da gyara gaban mayafinta ilahirin ƙirjinta a waje ta sunkuyar da kai kana tace " ka temaka ka bani amsa rankashi daɗe ni marainiya ce ka duba pls ta kuma marai raicewa tana kashe masa ido , tana zaune a gurin har aka ci minti talatin yunwa Khamis yaji ta addabesa ,ya kalli muhibbat ya kawar da kai kana yace " kiramin masinja zan aikesa siyan abinci , lallh ranka shi daɗe badan karkace girkina babu daɗi ba ai da na baka ka taɓa kaji , wani mugun kallo yayi mata a kai kaice tai shiru da bakinta tare da miƙewa dan taga yau babu fuska bare ma ya tsaya suyi magana ficewa tayi tana mai dana sanin shigowarta na yau. Bata daɗe da fita ba sai ga masinja nan ya shigo , 5k Khamis ya miƙa masa kana yayi masa bayanin kalar abincin da yake so . Aisha na tashi taga babu Khamis palo ta fito sbda duba shi amma babu shi babu alamarsa , part ɗin Ammi ta wuce Ammin baya palo hakan yasa ta kwanta kan kujera, Ammi na fitowa tace " a'a ɗiyata jiki yayi sauƙi ko ?" eh Aisha tace " to Allah ya ƙara lafiya Ammi ta faɗa tare da cewa "to me kike son ci ?" babu komai Aisha tace "kasancewar bakin babu daɗi , bafa zaki zauna da yunwa ba tashi ga shinkafa na gama inkuma faten dankali kikeso akwai , uhm sai anjima Aisha tace " tana gyara kwanciya . Zuwa yamma sai ga Khamis ya shigo yana riƙe da leda a hanunsa , miƙawa Ammi yayi bayan tayi masa sanu yace "keda Aisha ,buɗewa Ammi tayi taga dambun nama ne a roba mai murfi Allah yayi maka albarka Ammi tace "tare da ajiye ledar, plet taje ta ɗauko a kitchen ta juye na Aisha a ciki tace " ƴata nasan kina cin wanan sosai taso , shima sai anjima tace " Khamis da jikinsa yayi sanyi ya zauna a ƙasa kan kafet yana kallon Aisha da duk ta rame lokaci ɗaya , ka samu ka bata wanan taci ko zataji ƙarfi a cikinta ko ka ɗauko mata maltina tasha cewar Ammi , Tom yace " tare da miƙewa ya ɗauko mata tare da kofi ya tsiyaya mata ya bata tasha kaɗan tace "ta ƙoshi dambun naman ya ɗibo a cokali yace " maza buɗe bakin kiga zan baki wani abu , Da ƙyar ta buɗe bakin ta karɓa zai bata cokali na biyu tace " ta koshi . Baiji daɗi ba haka ya tashi jiki babu ƙwari Ammi dake kallonsu ta girgiza kai sbda Khamis na bata tausayi . Tashi yayi ya koma part ɗinsu ya zauna a palo ya ciro wayarsa ya shiga gallery yana ƙarewa hotunanta kallo gata lokacin da tayi kwaliya zasu gidan su murmishi yayi kasancewar kwaliyar da tayi kafin Ammi ta gyara mata , kiss ya yiwa photon tare da rungume wayar tsamm a ƙirjinsa yana jin soyayyarta na ratsa ko wani sassa na jikinsa . Washe gari yau kwanan watan Aisha biyu a gidan taji sauƙi kamar ba ita ba ,hakan ya yiwa Khamis daɗi . Ƙarfe tara na safiya mai lesson yazo bayan su Ammi sun gaisa dashi ya buƙaci Aisha da tazo su fara , zama Khamis yayi a ranshi ya aiyana duk ranar da malamin nan yazo nima zama zanyi karya dinga kallemin Esha wlh badan ƙiuya ba ai da nina dinga koya mata , tamayar da aka fara yiwa Aisha ne ta katse masa tunani. "kin taɓa zuwa makaranta kuwa?" eh Aisha tace " ina aji huɗu muka dena zuwa " wasu ƴan tambayoyi yayi mata game da karatu , amsa ta shiga bashi hakanne ya tabbatar masa da yarinyar tanada brain sosai , ta burge Khamis hakan ya ƙara rura wutar soyayyar ta a zuciyarsa , Ammi da ta shigo yanzu tace " oh kai kuma zama kayi ?" murmishi Khamis yayi kana yace " my Ammi nima ina tuni ne . malamin ne ya dubi Ammi yace " wanan bazata bada wahala ba sbda tanada saurin fahimtar abu , masha Allah Ammi tace " to "kamar zuwa yaushe kake ganin zata fara zuwa School ?" Kamar nan da two month haka , ok Ammi tace " kana ta shige ta barsu a gurin . Zuwa ƙarfe sha ɗaya sun kammala yayi musu sallama ya tafi , Tsalle Aisha ta buga tace " wayaga Aisha a boko wlh da nafi kowa jin daɗi bakinta yaƙi rufuwa sai fara'a take " ganinta cikin farinciki yasa Khamis shima jin farinciki a zuciyarsa tana ta tsalle tana rawa , wayarsa ya ɗaga ya hau yi mata video yana murmishi yana ganin zata ankara ya sauke wayar . mayafi kaka ta ɗauka tace "wa anty Fiddausi zani anguwa dan Allah ki kulamin da tsintsiyata , anty Fiddausi dake tsaye bakin ƙofa ta riƙe ƙugu tace " wlh koda ruwa yazo yayi musu duka ta koma ɗaki , riƙe baki kaka tayi tace " yarinyar nan kwai ƴar iska ko bata sanni ba ta dinga gayamin magana haka kamar tanayi da marar galinhu kaka ta tattara tsintsiyarta a buhu ta wurga ɗakin su Ummi dake kwaliya tayi wanka , Ummi na cewa "meye a ciki kaka tai kunen shegu da ita tace "nidai naje kasuwa , babu wanda ya kulata daga anty Fiddausin har Ummi haka ta tafi tana masifa a hanya . Tana cikin tafiya taga mai tiren tsire , mai tsiren na ganinta yace "baba a kawo ne ?" a'...! Ƴan VIP grp kuyi haƙuri dan Allah nayi baƙi ne bansami damar typing ba 👏 [27/08, 1:32 pm] Mom Islam Ce 💃: 21 & 22 Kaka dake gyara mayafinta data ɗora a kanta tace "ba anan zan siya ba sai naje kasuwa ƙila nasu zai fi araha , jin haka yasa mai tsire saukewa ya buɗe shi yawun kaka ne ya tsinke ba shiri tace " samin na ɗari biyu amma fa canji ne , to mai tsiren yace "kana ya zuge tsinke biyu ya baɗe shi da yaji wanda yaji ƙuli , gyara zama kaka tayi ta zauna a kan takalminta kana tace " karfa kayimin tsada dan zan baka abinka , mai tsire na yar yaɗa mangyaɗa yace " haba kaka ai ni ɗanki ne . Kaka da tsire yayi mata daɗi har mai tsire ya tafi da canji bata karɓa ba sau da ta gama cin tsire ta duƙunƙune takarda sannan ta tuna da ai bata karɓi canji ba , kuka tasa tana salati haka ta miƙe tana tafiya tana jera masa Allah ya isa ace mutun kamar na Allah ya rasa wacce zai cuta sai tsohuwa ?" nikam na shiga uku waccan yarinyar ƴar duniya ta cuceni yanzu kuma gashi wanan ma cucin ya cuceni Allah ka bimin kadi na taci gaba da magana tana mita , har tayi nisa bata sani ba har sai da taji ta gaji ta tsare mai mashin tace " ya kaita bakin dogo nawa ne ?" kaka ta tambayesa ki barshi Allah ya kaimu lafiya baba "mai mashin yace " yana mai karkatawa kaka ta hau , cikin ikon Allah sai gasu sun iso godiya tayi masa tare da sa albarka ta shiga cikin kasuwar, wani dakali ta samu ta zauna kana ta fito da lalitarta ta fito da kuɗin ciki duka tana ƙirgawa , dubu uku da ɗari biyar ne kasancewar taba mai tsire ɗari biyar kuma tanada dubu ɗaya dama , tana cikin haɗa kan kuɗin taga an biyu wani da gudu ana cewa " ɓarawo ɓarawo ba shiri ta tattaro kuɗin a guje ta faɗa gidan da ta gani a gefen ta , wata mata dake shirin fitowa daga ɗakin tana ganin kaka ta dannawa ƙofa saƙata dama ita ɗayace a gdan gashi faɗa ya ɓarke a ƙofar gida , haka kaka ta nemi guri ta zauna tare da miƙe ƙafa , takai minti talatin a gidan sai da taji an dena faɗan sannan ta fita a gidan , tana fitowa ta riƙe baki tace " daga shiga gidanki sai ki gudu sai kace kinga mutuwarki kaji min shegiyar mata kaka ta faɗa tana daɗa ɗaure lalittar ta , mai tallan rama da zogale ta gani yana tafiya ƙwala masa kira tayi kana tace " bani na hamsin amma ɗari biyar ce "to akwai canji yaron yace "yana duba aljihunsa , ɗari huɗu da hamsin ya miƙa mata ita kuma ta miƙa masa ɗari biyar , kashi biyu ya bata kana ya barbaɗa mata ƙuli ya sanya mata a leda . asi kilishi asi kilishi kaka taji ana cewa "kai mai kilishi kawo dama tunda na shigo kai nake nema "to mai kilishin yace " tare da ajiye kujerar hanunsa ya ɗora tirai a kai . "na nawa za'a baki?" Mai kilishin ya tambaya yana gyarawa yawwa bani na ɗari biyar kasa min a babbar leda saboda har gida zani dashi , to yace " mata yana sawa ya miƙa mata ya tafi kuma zama tayi taci rabi ta ƙulle rabi bata si komai ba sai wani bugujejen sikel ta tari mai mashin ta dawo gida . Tana dawowa Ummi dake share tsakar gida tace " oyoyo Kaka kawo ledar , maƙale hannu kaka tayi kana tace " da zan tafi akwai wanda ya bani sautu dan haka a barni in huta ,ta shige ɗakin Ummi kasancewar anan take kwana wuni ne kawai take zama a waje , tana zama ta buɗe takardar nama ta fara ci tana suɗe hannu , faɗowar Ummi ɗakin ba tare da sallama ba yasa kaka ɗura mata zagi tana mata faɗa , zama Ummi tayi tana jira itama ace ga nata amma kaka ko kallonta batayi ba taci gaba da ci tana murguɗa baki ,duk da ran Ummi ya ɓaci hakan bai hanata dariya ba . Ummi ce tace " anty wlh kaka ta siyo tsire, da ƙarfi take maganar, To shikuma aka kwaso Anty Fiddausi dake fitowa tace " muma ɗazu muka yanka kaza muka soyeta , kitchen anty Fiddausi ta shiga ta ɗauko bokitin da ta juye naman kana ta shigo ɗakin da kaka take ta nuna mata , Kaka dake naɗe takarda tana hamdala ta kuma ruɗewa tana cewa " to in dan wanda naci ne na hamsin fa naci zaki tada hankali , anty Fiddausi dake dariya tace " ƙwalele . Washe gari haka Ammi ta kuma matsawa Khamis akan yaje gurin aiki ranshi a ɓace ya tafi ko sallama bai yi mata ba hakan bai yiwa Ammi daɗi ba yaƙi fahimtar ta ko kaɗan amma tasha alwashin gobe insha Allahu bazata ce masa yaje ba inyaje dan kansa in kuma yaƙi to itama ta ƙyaleshi , yana parking bai kula masu gaishesa ba ya shige office zama yayi idanunsa sun kaɗa sunyi ja tsabar damuwa , har ya kai ƙarfe biyu Muhibbat bata shigo ba cikin zuciyarsa yace " lpy to ?" kawar da zancen yayi ya janyo takardun dake buƙatar dubawa . Zuwa yamma ƙarfe biyar ya tattara komai ya ajiye ya haye mota ya dawo gida yana shigowa yaga Aisha zaune tana wasa da furannin gidan ta bar baza z tsakar gurin , yana parking ya fito yaje gurinta my Esha maiyasa kike haka ne ?" Khamis ya tambayeta ransa a ɓace " mai gadi ne yace " wlh oga babu inda bamuyi da ita ba amma taƙi denawa daga ƙarshe cewa " tayi inhar muka sake magana zata fasa mana kai tana nunomu da duwatsu , dariya ce taso kufcewa Khamis bai yita ba ya tare ta , riƙe da hanunta suka shiga part ɗin Ammi ' Ammj na ganinsu tace " dama yanzu zan fita nemanta a ina ka ganta ?" a gurin flawoyi na ganta tana ta 'adi oh ɗiyata "kinason a fara dukanki ne ?" girgiza kai Aisha tayi ta daka tsalle ta haye kan kujera tana wasa , ƙarfe shida da arba'in Ammi ta kammala girki ta jere a dining tace " wa Aisha taje tayi sallah , sai gobe Aisha tace " tana cigaba da tsalle , waro ido Ammi tayi tace "naga takaina nikam ace yarinya bata son yin sallah bari in haɗaki da son ya zaneki , da gudu ta duro tare da shiga toilet ɗin da yake a mazaunin na mutane yake nesa da palon amma a palon yake , alwalah ta tayi ta fito sa gudu ta bubuga sallah tace "fatiya da ƙarfi Ammi dake ɗakinta tana sallah sai da ta jiyota , batare da jiran kowa ba ta wuce dining ta ɗauki plet ta jiye rabin farfesun kifi ta fice da gudu ta nufi part ɗinsu, tana shiga taga Khamis yana waya yana dariya , a bayan kujerar daya zauna ta zauna tanayi tana tsotse ƙayar kifi bai san da ,zuwanta ba sai jin tauna yayi da sauri ya miƙe yana dube dube , hangota yayi kamar munafuka ta takure gefe ɗaya tana suɗe kwanon data cinye kifin , kyakkyawa inkaje gurin mama kace mata na ƙoshi tace " wa Khamis tare da yin hanyar bedroom tana shiga ta kwanta babu ko wanke hannu , abinka da yaro ko a jikinta sam bata san tayi wani abu ba, Khamis da ya bita da ido ya miƙe ya tafi palon Ammi samun Ammi yayi a dining tana zaune ta zuba tagumi ita fitinar Aisha ta fara damunta . Khamis ne ya katse mata tunani ta hanyar cewa " Ammi lafiya na ganki haka ? lafiya son kaga yarinyar nan ta kwashe farfesun kifin da nayi kaga wanda ta bari Ammi ta buɗe foodflaks ɗin tana nuna masa kiyi haƙuri Ammi maganar da ta fito daga bakin Khamis kenan , bata kulasa ba ta zauna shiru tana daɗa zurfafa a tunani shima ya shiga damuwa ganin Ammi babu walwalah , a haka dai sukaci abincin sama sama ya yiwa Ammi sallama ya tafi part ɗinsu , samun Aisha yayi tayi ɗai ɗai a gado tana bacci ƙare mata kallo ya shiga yi tabbas kyakkyawa ce , yasan inda abinda ke ɓatawa Ammi rai bai wuce a ɗaukar mata abu ba'a tambayeta ba wanan abin yana yi mata ciwo , to shikam ya zaiyi gurin gayawa Aisha karta sake ɓatawa Amminsa rai oho , kwanciya yayi tare da rungumeta yana shafa cikinta , ganin cikin nata kamar ba komai yasan tsoron faɗa yasa taƙi komawa cin abinci yaci gaba da shafa cikinta yana wani tunani, a wanan cikin my Esha zata ajiye min baby sai kuma yayi murmishi yana shafa fuskarta , ƙara matseta yayi a jikinsa suna jin nunfashin juna yayi musu adu'a bacci yai nasarar ɗaukarsa asuba ta gari. Guɗa ake rangaɗawa a gidan su mama , mama bata ma san ranar ɗaurin aure ba bare tasan ranar da za'a kawo amarya malam bai gaya mata komai taga anzo anyi jere a ɗakin yaya zakari na da ciki da palo ne , ita dai mama nata ido ƴan kawo amarya sunyi habaici sun gama shugowar maman Ummi ne yasa mama jin sanyi a ranta , maman Ummi bata bar gidan ba har sai da taga ƴan kawo amaryar sun watse tana ta yiwa mama nasiha gami da ban haƙuri dakuma tunatar da ita adu'oi kana da jan girma banda sanya ido ta kawar da idonta , hankalin mama ya ɗan kwanta kasancewar nasihar maman Ummi ta shigeta. Washe gari da safe ƙawayen amarya suka zo gurin malam wai ya basu abin karyawa , ce musu yayi suje gurin mama suce ta ɗora musu abinci inji shi , da yake su ƴan aika ne sukaje suka isar da saƙo, mamace tace " kuce masa inya bada a nashi zan ɗora amma ni banida shi , haka sukazo suka gayawa malam wanan abu ya yiwa malam ciwo ɗakinsa yasa key ya buɗe kasancewar key yake sawa ɗakin indomie ya ɗibo musu guda goma ƙawayen ma basu wuce huɗu ba aiko suka karɓa suna far'a sukace kuɗin cefane , babu musu malam jiki na rawa ya miƙa musu ɗari biyar suka fice , Kai tsaye ɗakin mama ya shiga babu sallama yace " wato shine kika tsinkani a gaban ƙawayen matata ko ? mtsw mama taja tsaki tace " kaga malam ban shiga harkarka ba dan haka ka fitarmin a ɗaki karka janyomin raini in tusa tana hura wuta ayi dai mu gani ,a zuciye malam ya fice ya fita waje ya zauna kowa yazo wucewa sai yace " na gaida ango malam na washe baki , bayan ƙawayen sun ƙammalah girkinsu sunci harda amarya sukayi wanka suka yi kwaliya kowacce ta ɗauko jakarta , amaryar ce tace " bari in kira malam, waya ta ɗaga ta danna number sa tace " ƙawayenta zasu tafi cikin ƙanƙanin lokaci ya shigo yana washe baki ya miƙawa kowa 1k cikin farinciki sukayi masa godiya kana suka tafi. inbaku manta ba Aisha taje gurin wata dillaliya a maƙotansu siyo anko. To yau tazo yiwa mama Allah ya sanya alkairi, tun daga ƙofa ta fara sallama malam dake zaune da plet ɗin cin cin a hanunsa ya fito yana amsawa kasancewar mama na bacci , ganin dillaliya yasa malam cewa " maza koma nayi amarya banason munafurci itama wacce kikazo gurinta zan taka mata birkin fita ko ina bazan lamunta ba sam haka dillaliya ta koma tana jinjina kai . Hayaniyar malam ce ta tada mama daga bacci fitowa tayi tana cewa " malam kai da waye naji kamar muryar dillaliya ?" eh itace korarata nayi ko da akwai wani abinne ?" a' a mama tace " dan taga yana neman faɗa ne ita kuma tana taka tsan tsan ɗin kar yarinyar da aka kawo ta rainata....! [27/08, 5:50 pm] Mom Islam Ce 💃: 23 &24 Shiru mama tayi ba tare da ta tanka masa ba ta koma ɗaki. Dare na yi kaka tayi sallama a ɗakin su anty Fiddausi tsaki anty Fiddausi tayi kana tace " ko me tazo yi oho kwance take kan cinyar yaya Zakari tana shafa sajen fuskarsa duk cikinsu babu wanda Allah ya bashi ikon cewa "shigo duk suna shirin yin nisa bankaɗo labule kaka tayi ta fara sababi abinda ta gani ne ya sanya ta mutuwar tsaye ta juya babu magana sarai anty Fiddausi ta ganta ta kuma kamo yaya Zakari tana riƙo hanunsa , tunda kaka ta fara tafiya ba ita ta tsaya ba sai da ta kai ƙofar gida ta sami dakali ta sunkuyar da kanta ,kana ta rafka tagumi gami da cewa " na shiga uku nikam naga abinda ya isheni yanzu da wane ido zan kalli yarannan on ta dinga zuba surutai tana riƙe haɓa, Jin anata kiraye kirayen sallahar magrib yasa ta komawa gidan ta yi sauri tayi alwalah ta shige ɗakinsu Ummi har tana bugewa da bango , tanajin gyaran muryar yaya Zakari taji gabanta ya bada dummm ,zan tattara in tafi gida kaka tace " tana share hawaye ,Ummi dake kwance tayi kamar mai bacci ta tuntsire da dariya kana tace "kaɗan ma kika gani ashar kaka ta mulmula mata wanda ya bawa Ummi damar yin shiru , haka kaka tayi sallah zuviyarta babu daɗi . Anty Fiddausi ce ta ƙwalawa Ummi kira tace " tazo ta ɗauki yarinya , ficewa tayi tana cigaba da darawa. bayan malamin da yake koyawa Aisha karatu yazo ya tafi ,Khamis yace " wa Ammi zai kai Aisha gurin wankin kai da kitson Allah ya tsare Ammi tayi masa suka fice kasancewar tayi wanka , Bai buƙaci driver ya kaisu ba hakan yasa da kansa yai driving suna tafiya yana tambayarta wane subject tafi so a karatu yafi yi mata daɗi , hausa Aisha tace " tana dariya suna zuwa gurin wankin kan ya bada kuɗi aka gyare mata kanta ana cewa " za'ayi kitso Aisha tasa kuka tana cewa " bataso haka aka bar kan , juya kan motar yayi yace " bari muje gidan maman abokina ki gaisheta murna Aisha ta fara sbda yau zasuje anguwa tanason yawo a rayuwarta, sunyi tafiya mai nisa kana suka zo wata ƴar kasuwa da ake siyarda kayan marmari , parking Khamis yayi ya fito ya siyi lemu da abarba da kankana da ayaba da apple aka sanyasu a leda aka kai masa both ya biya kuɗin suka ji gaba da tafiya , Cikin ikon Allah sai gasu a anguwar anguwa ce ta masu kuɗi komai a tsri yake gunin sha'awa , horn yayi aka buɗe get ɗin ya shige yana shiga yayi parking suka fito yace " ma ɗan aikin gidan ka kwaso kayan cikin both ɗinnan da gudu ya taho ya buɗe ya shiga dasu cikin gidan , riƙe hanun Aisha Khamis yayi suka shiga cikin gidan ilahirin mutanen gidan suna zaune a palo da mahaifiyar abokin nasa da matar abokin nasa kana da yaran maman abokin nasa akwai mai shekara goma sha biyar kana akwai mai shekara sha ɗaya wato sa'ar Aisha , lale Momma take yi musu kasancewar sunan da yaran auke kiranta kenan , shiga sukayi hanunta a na Khamis suka zauna guri ɗaya , durƙusawa yayi ya gaida Momma kana suka gaisa da matar abokin nasa yace "ina Bashir ?" ya tafi bakin titi yanzu zai dawo matar tashi ta faɗa tare da ƙwalawa ƴar aiki kira ta kawowa baƙi drinks , Momma ce take tambayarsa ya Ammi kana tace " abokinka ya bani labarin kayi aure ya matar taka ? lafiya lau yace " sai a lokacin Aisha ta durƙusa tace " ina wuni ta gaida matar abokin Khamis bayan sun amsa ta koma ta zauna , godiya Momma tayi masa na tsaraba kana ya miƙe yace " zasu tafi janyo hanun Aisha Momma tayi ta shiga da ita bedroom ta bata hijab har ƙasa na makkah da doguwar riga sabuwa da turare kana ta bata wani ƙaton turare tace " ta kaiwa Ammi godiya Aisha tayi suka fito , Momma ce tace " amma wanan ƙanwarka ce ko ?" naga kuna kama , eh Khamis yace " Aisha ta nuna masa hanunta godiya ya yiwa Momma kana suka wuce , Suna tafe tana bin waƙar da yasa wato jirgin so wanda Umar m Sharif yayi dariya ma ta bashi har wani kareraya take tana rawa, har suka isa gida yana dariya , da ana buɗe mota Aisha ta fice da gudu tayi part ɗin Ammi tare da cewa " albishirinki Ammi -Ammi na dariya tace " goro ƴata maiya faru "Ammi na washe baki ta tambayi Aisha kamo hanun Ammi Aisha tayi ta haɗa da ledar hanunta , shigowar Khamis ne yasa Ammi tambayarsa taga Aisha na farinciki maiya faru " dariya yasa yace " Ammi gidan Momma mukaje fa shine aka baku abu take ta murna ayya Ammi tace " shine baka faɗamin ba ?" ka sameta lafiya ?" eh Khamis yace " ai tace " in gaishe ki, ina amsawa Ammi tace " tare da zama ta buɗe ledar dake hanunta , kayan da ta gani ne ya sata buɗe baki tace " kai kai amma nayi farinciki irin turaren dana dinga nema a garinnan na kasa samu tunda nawa dana taho dashi daga saudiya ya kare nayi baƙinciki ksi naji daɗi dole in kira inyi mata godiya ,murmishi Khamis yayi yace " na Aisha ma na ciki , cigaba da duba kayan Ammi tayu tace " kai masha Allah Allah ya biyata da aljannah maza kai part ɗinku ta miƙawa Aisha da gudu tayi part ɗin nasu ta watsa kan gado ta fito ta dawo a mai makon ta wuce gurinsu Ammi sai ta nufi bishiya tunda jiya sunzo fita ta hangi jan magoro to yau kwananka ya ƙare Aisha tace " tana sanya hannu a baki , bishiyar ta haye can sama sai da ta ciro mangoron sannan ta sauƙo ta hau bishiyar gwaiba itama ta tsinki ɗanyu ta sauko ganin sauran bishiyoyin basuyi ba yasa ta zaman dirshan tana maida nunfashi sai da ta gama shan mangoron sanan ta je gurin mai gadi tace " ka buɗemin , ina zaki" mai gadi ya tambayeta zani anguwa ne ,kallon sama da ƙasa yayi mata kana yace " yarinya dake kike maganar anguwa kafin ya ƙarasa zancen ta shatale ƙafarsa ta buɗe ta ruga a guje ta gane hanyar da suke bi ita da Khamis hakan yasa ta dinga tafiya tana waige ita kanta batasan ina zata ba , wani mai katafaren shago ne ya watso kwalaye ƙofar shagonsa , da gudu Aisha taje ta kwaso biyu ta juyo da nufin dawowa gida , tafiya take amma har yanzu bata isa gidan ba , zaman hutu tayi tana mayarda nunfashi dan ta gaji sosai tayi mamakin tafiyarta. Koda Khamis ya je part ɗinsu bai ga Aisha ba ya shigo toilet nanma shiru ya fito ya shiga ɗakinta shima shiru , fitowa yayi ya zage gidan harda gurin bishiyoyi babu ita babu alamarta , gurin masu gadi yaje da suke zaune suna ta hirarsu , yace "musu dan Allah bakuga Aisha ba ?" mai gadi ne yace " tazo nan tace " sai na buɗe mata nikuma nace bazan buɗe ba shine ta shammace ni ta fice da....kafin ya ƙarasa Khamis ya zuba masa maruka uku lafiyayyu yana haki dan ubanka in Aisha ta ɓata kaine sanadi wlh tunda ai bata fi ƙarfinka ba maza kaje ka nemota duk inda ta shiga wlh ko in saɓa maka. tafe take da alamun gajiya a tare da ita ita kanta batasan a tahowa tayi wanan uwar tafiyar ba taɓɓ zaman hutunta biyu a na ukun ne tana shirin zama ta hango wani gida ƙofarsa a buɗe amma fa haɗaɗɗe ne gidan na ƙarshe tace " barin shiga ko da wanda zai temakeni tana shiga taci karo da wani mahaukacin kare ya biyota da gudu , itama da gudu ta ƙara ta fice daga gidan ta miƙi hanya , hango mai gadin gidansu tayi da driver cikin ihu tace " kuzo ku temaka min dan Allah....! Kuyi haƙuri da wanan👏 [29/08, 2:46 pm] Mom Islam Ce 💃: 25 & 26 Yawwa dama ita muke nema su mai gadi suka faɗa suna ƙarasawa gurinta da gudu, itama gurin nasu ta nufa kana ta baje a ƙasa tana mayar da nunfashi tace "dan Allah ku kaini gida ta fara hawaye , riƙo mata hannu mai gadi yayi zai tasheta su wuce tace " bazan iya tafiya ba ƙafafuwana zafi sukeyi , goyata yayi a baya suka ci gaba da tafiya shida driver buɗe get ɗin sukayi kana suka shiga cikin gidan , tsaye suka gansa a jikin mota yana karkaɗa keys ɗin dake hanunsa , sallamar su ce yasa shi ɗago kai bai ankara ba yaga Aisha a bayan mai gadi , baisan lokacin da yace " kutumar uba ya tafi gurin yana gurnani kamar mahaukacin zaki, cukumo wuyan rigar mai gadi yayi da ya sauke Aisha yana mata sannu " dan ubanka waye yace ka goyamin mata baka da hankali ne ko kanka ya kunce ne zaka goya matar wani ?" ya ƙara da sake masa mari har biyu kana yace " last worning wlh yaja hanun Aisha suka shiga part ɗin Ammi ,ganinshi fuska a murtuke yasa Ammi cewa " son lafiya kuwa?" lafiya Ammi " ya zauna kanshi a ƙasa yana tuno goyo da mai gadi yayi wa Aisha, mtsw Khamis yaja tsaki ,ita ko Aisha tunda ta samu ta dawo ta kwanta kan kujera da taga babu wanda ya kulata ta diro tana ƙyal ƙyalewa da dariya tace " wani mahaukacin kare dana gani kamar kura na tsorata sosai , shuru har yanzu duk basu kulata ba , mama mama Aiaha ta kira sunanta na'am kawai Ammi tace " can kuma ta kalli Aisha tace "ina kikaje ?" Aisha ce tace " walh kayan wasa naje samowa shine kare biyoni , karki sake fita Ammi ta faɗa da kakkausar murya , Aisha ta tsorata tace " to mama . Wani mugun kallo Khamis ya wurga mata kana ya miƙe ya nufi part ɗinsu , tana shirin tashi amma tayi azamar riƙota kana ta zaunar da ita tace " mai yasa yayanki ɓacin rai " wai dan ya ganni a bayan mai gadi ya goyoni nikuma ƙafafuwana zafi suke shine ya wankawa mai gadi mari, zaro ido Ammi tayi tace " murmishi amma tayi kana tace " Khamis masu mata ta miƙe tace " jeki itama ta shiga bedroom ɗinta , Aisha na isa part ɗin nasu ta shiga da sanyin jiki ta zauna kan kujerar da Khamis ke kai ta riƙo hanunsa tace " kyakkyawa bakada lafiya ne ?" eh Khamis yace " yana lumshe idonsa . "To kasha magani man" "nasha" oh kyakkyaww kayi haƙuri na gaji ne shine ya goooo....a tsawace Khamis yace " ki tsaya iya nan pls karki ƙaramin damuwa , haka ta zauna kamar marainiya shima shiru ya zauna yana tunani yayi zurfi sosai yaji kiran Ammi a waya yana ɗagawa tace " yazo " To Khamis yace "kana ya miƙe ya isa kiran nata , zama yayi a kujera kana yace " Ammina gani" Ran Ammi a ɓace tace "tunda kayi aure ka sauya kwata kwata nan da nan kayi fushi ga sa abu a rai da kakeyi kaga ramar da kayi kuwa ?"yanzu dai ga shawara ka zaɓa ko a kai Aisha makarantar kwana ko a kaita gidansu in ta girma kamar 15yrs sai ta dawo gida muci gaba da zama , cikin fargaba Khamis yace " Ammina babu ko ɗaya dan Allah kimin rai kaf abin da kika faɗa babu mai yiwu wa " Murmishin takaici tayi kana tace "ka ɗauki san duniya ka ɗorawa yarinya ƙarama bata gudun ɓacin ranka ko kaɗan amma har zaka dinga damuwa miƙewa Ammi tayi kana tace " na zaɓi makarantar kwana in akayi hutu ai zaka dinga ganinta duk da jiya aka ce akwai taro a england da za'ayi a kamfanin dadynka yau saura one week " Allah ya kaimu Khamis yace "kana yaci gaba da cewa "Ammi a duba lamarin nidai banason ko ɗaya , na ƙare magana ai cewar Ammi tace " ana kiran sallahr magrib kaje masallaci . anty Fiddausi na fitowa zata zuba abincin da ta gama bayan ta zuba ne tace " Ummi tazo ta ɗauki nata dana kaka , bayan Ummi ta kwaso abincin ta kawo wa kaka ta zauna tana ci taji kaka tace " ke Ummi ina naman da yarinyar nan ta soya ina ta kai ?" gidan su man gurin mamanta , zaro ido kaka tayi tace " bayan naman suna da aka kai mata harda wani kuma ?" shiru Ummi tayi ba tare da ta kulata ba taci gaba da cin abincin ta. Washe gari tun safe anty Fiddausi take shirin ,zuwa gida kasancewar sun daɗe dayin arba'in yaya Zakari na zaune da waya a hanunsa yana game ya kalleta yace " yanzu kin dena yimin kwaliya Fiddy amma yau da zaki fita kamar sabuwar amarya "farr tayi da ido tace " ai koma menene kai ka jawo ka cika mana gida da mutane nikam nayi arba'in kace kaka ta tafi itama Ummin duk kace su tafi , waro ido waje Khamis yayi kana yace " na isa kuwa ?" nifa nayiwa kaka alƙawari in baki manta ba nace mata zata zauna a gidannan ai sai tace "mun koreta "anty Fiddausi dake ɗaura ɗankwali tace "kai tsoronta ma kakeji nifa bama shiri da ita dan ko ƙauyensu bana zuwa dan haka inhar kana son farinciki to wlh kace subar gidannan , kana ta rungumoshi tana sakar masa hot kiss irin haka kake so ko?" anty Fiddausi ta faɗa tana ƙara rungumo shi , idanunsa a lumshe harta miƙe ta goya babynta a baya ta janyo mayafi ya riƙota ta faɗo jikinsa kana yai ƙasa da muryarsa yace " my Fiddy ki tausayamin pls kwana arba'in fa mugun kallo tayi masa tace "ai sai kaka tabar gidan nan inhar kana son farinciki "idanunsa sunyi ja tsabar ɓacin rai kana da kuma buƙatuwa yace "karki manta mala'ikun Allah zasu tsine miki Allah kuma yayi fishi dake "ƙarawa gaba tayi tana cewa "yau ba sai kaba da kuɗin mashin ba akwai ragowar kuɗinnan" ta fice tana tare mai mashin aka sauketa a ƙofar gidan su da sallama ta shiga ta sami mamanta zaune tana yanka kuɓewa, oyoyo da masu jego murmishi anty Fiddausi tayi ta zauna a tabarmar da maman ke zaune suka gaisa maman take tambayarta ina kaka "yatsina fuska Fiddausi tayi tace " nifa wlh wanan kakan ta isheni mama dan Allah kice ta dawo" anty Fiddausi tayi kamar mai shirin yin kuka ,to wato Fiddausi na lura har yanzu bakida hankali bakiso ɗan uwanki yazo yaci arziƙi musamman ma yanzu da naga Allah ya buɗawa mijinki ranar nan fa sai ga soyayyun kaji an kawo min to tun wuri ki farka in kika bita a hankali zaku kashe ku rufa ƴan dabaru namu na mata duk zata koya miki ke harda haɗin magunguna kinsan tayi aure a mai duguri harda su turare duk ta iya haɗawa ,jikin anty Fiddausi ne yayi sanyi tace "to mama ai yanzu da garaje bazata fuskanceni ba "katse ta mama tayi ta hanyar cewa "kinsan komai na son kyautatawa ki kyautata mata kiga aiki kinsan tsofi akwai son cin mai maiƙo "murmishi anty Fiddausi tayi kana tace " aiko inhar zamu tara dukiya tilas kanmu ya haɗu ko be ashirya ba , sukaci gaba da hirarsu zuwa la'asar sai ga babansu Fiddausi ya dawo cikin farinciki yaja kujera ƴar tsugunno ya zauna suuka gaisa da anty Fiddausi kana yake tambayarta ya kaka da mai gidan ?" duk suna lafiya tace "ya miƙe dan zuwa masallaci itama tashi tayi bayan tayi alwala tayi sallah tana idarwa ta goya babyn ta tace "mama zan tafi to maman tace " dan Allah inkinje ki kirani a waya mu gaisa da uwata , har zata gyatsine fuska sai ta tuna ai zasuyi wani shiri da kaka dole fa ta dinga danne rashin kunyar da take yi mata dubu biyu taba mama kana ta bada dubu ɗaya tace "taba baba cikin murna mama take sanya mata albarka gami da godiya". An fara shirye shiryen tafiyar Aisha makarantar kwana palon Ammi cike yake da kayan abinci iri iri kana dasu drinks da kayan ciye ciye kama daga dambun nama da dai kayan ƙwayi haka aka jeresu a gurin . Tunda Aisha taga haka ta dinga tsalle a dole zataje makarantar kwana murna fal cikinta zata dinga cin daɗi har wani rawar kai take, Khamis duk ya shiga damuwa gashi gobe ne tafiya duk da ba amfanin wani abin take yi masa ba ta wani fanin amma yana ganin rashinta a kusa dashi zai iya haifar masa da larura ,zama yayi a palon Ammi yace " Ammi har yanzu baki faɗi makarantar da za'a kaita ba "ta gwamnati man Ammi ta faɗa tana kallon ƙwayar idonsa"zuciyarsa da gangar jikinsa kana da fuskarsa sun nunarwa Ammi bai amince ba kawai ita kuma tanada dalilin yin hakan , ganin bai amince ba tace "nabaka wuƙa na baka nama ka nemo mata duk wacce kaga ta dace " ina murna wlh tom yace "tare da miƙewa ya fita , kai tsaye motarsa ya ɗauko aka buɗe masa get ya fice tafiya yake cikin sanyin jiki kamar wanda ƙwai ya fashe masa a ciki yana zuwa wani mall yai parking ya ajiye motarsa a inda aka tanada kana ya shiga yana shiga ya nufi gurin su sweet ne coconut mai sugar da chocolate da sauransu sai da ya cika basket dashi yaje ya biya kuɗin aka sanya masa a leda, ya fito ya dawo gida ya jibge kayan inda wa inan suke . Bai sami Aisha a nan ba ya tafi part ɗinsu a palo ya sameta tana rawa tana cewa "kai gaskiya na fito a mai sa'a ina muruwar son makarantar kwana yau gashi Allah ya cikamin tana juyi zatace burina kawai ta rungumo mutum ihu tasa tana sakinsa dan Nagano shigowarsa ba " my Esha Khamis ya kira sunanta tare da ƙara rungumeta tsammn a jikinsa yana mai da nunfashi yace " mai Esha yanzu kinason tafiya ki barni ?"mai nayi miki da kikafi buƙatar ki bani rata Allah ne ya ɗoramin sonki a cikin zuciyata amma kina neman hawalani , kayi haƙuri yaya infa naje makarantar nan walh daɗi zan dinga ji mitsw yaja tsaki kana yace " nifa kina bani mamaki a gidannan duk abinda kika buƙata bakya rasawa way zakice wai ke makarantar kwana shine farincikin ki ko kinsan shekaru nawa zakiyi shera shida fa wlh nidai bazan yarda ba Khamis ya faɗa yana ƙara janyota jikinsa "hawayen me kakeyi Aisha ta tambayesa jin ɗumi a hanunta dake gefen fuskarsa, wani irin ruƙo yayi mata kamar wanda ya kama ɓarawo yana jijigata, tayi tayi ta fincike abin ya gagara hakan yasa ta sanya kuka tace "ka matseni , haɗe bakinsu yayi yace "an matse ɗin nida kika zaɓi kibar gidan ya faɗa yana lumshe idonsa futowar dimple ɗinsa yasa ta cewa "kanata ja min rai kace zakayi min wanan abin amma kaƙi yayi ko ?" inhar kikace kin fasa tafiya makarantar nan to yanzu zama ki jishi karki damu , maƙale kafaɗa tayi kana tace "bazan zauna ba" haka dai suka dinga hirar babu daɗi , Khamis har bayason gobe tazo, kayanta ya ciro mata kala biyar yace "kinga wa innan kayan to sune zaki dinga sawa ba 'a tafiya da kaya masu yawa ,har yanzu murnar take kasancewar ta biyoshi har bedroom ɗinsa , ya ciro mata hijab da pant kana yace " akwai sabon hijab a ciki , godiya tayi masa kana tace "da wuri zamu tafibko ?"harara ya watsa mata kana yace " inhar kika sake labarin nan to ranki zai ɓaci "cuno baki tayi tace "yaushe zani yiwa su mama sallama? kuma naji mama tace "gobe ne tafiyarmu cewar Aisha , "wasa take yi miki ba gobe bane yau muna lahadi monday mai zuwa ne"to mai yasa naji kaima kace gobe?" maƙale murya yayi yace "dama inason sanin kinfi son makarantar kwana a kaina shiyasa "shigowar Ammi ne ya katse musu magana Ammi tace "son ka kai Aisha gidansu tayi kwana uku ta dawo suyi sallama "ok Ammi Khamis ya faɗa cikin yanayin damuwa , tashi mu tafi , ledar dake hanun Ammi ta miƙawa Aisha tace " ki kaiwa mamanki kice ina gaisheta "to Aisha tace " suka fito ita da Khamis yace " diriver yazo ya kaisu dan bayajin daɗin jikinsa har wani gumi yake a dole yau zai kwana shi kaɗai babu Aisha ita ko sai murna take kamar wacce aka bawa kujerar hajji, shiga back side sukayi driver ya tada mota sai anguwarsh Aisha cikin ikon Allah sai gasu a anguwar parking drivern yayi a ƙofar gidan su da mamaki ta kamayi ganin an gyara ƙofar gidansu ga fenti , kamo hanunta Khamis yayi yace " Esha maiya faru ?"shiru tayi ba tace komai ba suka shiga suka bar driver a mota kasancewar zai koma da Khamis, da sallama suka shiga mama dake zaune tana waya da alama da yaya Zakari ma take wayar ta ƙatse tana yi musu maraba ,tsalle Aisha tayi ta rungume mama , mama tace " ka shiga ciki "shiga Khamis yayi kadancewar da tabarma kuma ɗakin tsaf yake mama ta aika aka siyo masa maltina da fanta kana da swan ta ajiye masa a gabansa bayan sun gaisa mama take tambayarsa ina Amminsa yace "lafiya Aisha dake zumuɗi tace "albishirinki mama?"goro mama tace " rufe baki Aisha tayi kana ta buɗe tace " ranar monday zani makarantar kwana , wani irin farinciki mama taji har tana hawaye dan daɗi ganin haka yasa Khamis shima farinciki duk da bayaso tafiyarta, Khamis ya ɗan jima a gidan mama daga ƙarshe har zai fito sai kuma ya dawo ɗakin ya ƙirga dubu goma ya bata ,daƙyar mama ta karɓa tana yi masa godiya yace "Aisha tazo ta karɓi abinda Ammi ta bata ta kawowa mama , mama ce tace "ka tsaya ku gaisa da matar ɗakinnan , tsayawa mama tayi daga bakin ƙofa tace "amarya ga baƙo zaku gaisa , cikin isa amaryar tace "ace ina gaishe sa aiba dole sai na fito ba , wani uban ashar Aisha ta mulmulo tace "ƙundun uba wacece wanan mama ?"murmishi Khamis yayi ya nufi ƙofar gida baiyi mamaki ba sbda ya zauna a duniyar" miƙowa Aisha leda yayi kana yace "my Esha sai yaushe kuma ?" zan dawo amma zani gidan yaya da kuma kasuwa siyo aya da taura ƙila makarantar babu , gudun kar ya ɓata mata rai yasa shi sanya gannu a aljihu zai ciro kuɗi tace" ka barshi inada shi ina dashi "bai ƙara magana ba ya shiga mota tare da ɗaga mata hannu suka tafi da gudu ta dawo cikin gidan su ta bankaɗo labulen ɗakin amaryar tace " wai haya akasa ne mama?" mama dake fitowa yanzu tace " amaryar malam ce fa " malam kuma aure yayi?" Aisha ta tambaya cikin mamaki "amaryar ce ta fito tace " ke wacece ƴar ƙarama dake sai iyayi da kwainane banza kawai tai tsaki ta koma ɗaki, sai dai kece banza Aisha ta faɗa da ƙarfi a zuciye amaryar ta fito zata mari Aisha malam yayi sallama jin sallamar malam yasa Aisha faɗuwa ƙasa tayi kamar mai suma tasan yanzu yana ji da ita zai yi wani abun.....! Kuyi haƙuri yau baku samu da wuri ba jiya na dawo duba mara lafiya na samu Abban islam shima ya dawo babu lafiya ina fata zakuyi haƙuri dan Allah🙏 [29/08, 5:26 pm] Mom Islam Ce 💃: 27 &28 Da sauri malam ya taho kanta yana subhanallahi mai ya sameta ?"maman Aisha ta shige ɗaki ita kuma amarya tana tsaye riƙe da ƙugu tana girgiza Aisha sai maida nunfashi take kamar da gaske adu'a ya shiga yi mata cikin lokaci kaɗan ta dawo normal kana ta yunƙura ta miƙe tana kuka tace " waye wanan malam ?"malam shaƙemin wuya tayi wai sai ta kasheni " kan uba amaryar ta faɗa tana shirin kamo Aisha malam ne ya fara yi mata magana yace "wanan fa ƴata ce to "to ina ruwana da ƴarka ce kasan abinda tamin kiwa ?"tunda ba'a koya mata girmama na gaba da ita ba wlh bazan zauna ana yimin cin kashi ba "amaryar ta faɗa kamar zata yi dambe da baban mutum "wato ke da ƙaramar yarinya ma zakiyi faɗa wacce take ƴa a gurinki" mtsw amaryar taja tsaki tare da wucewa ta barshi a gurin ta shige ɗaki kuma Aisha tasa tana share hawaye malam yace " kiyi shiru Aishana nida ita ne wlh zamusa ƙafar wando ɗaya mama na daga ɗaki uffan batace ba , bankaɗa labulen ɗakin amaryar malam yayi ya fara surfa bala'i kamar zai ari baki , wani irin kuka ta fara mai kamada na ƙissa tanayi tana jijiga ,zaro ido malam yayi yace "iskancin banza ya nemi guri ya zauna yana jijiga ƙafa , komawa ɗakin mama Aisha tayi tana dariya mama tace "Aisha ba sa'arki bace karki kuma kinji?" ɓata rai Aisha tayi kana tace "wlh kafin inbar gidannan sai na janyo mata asara"tasowa mama tayi daga wanciyar da tayi tace "har yanzu bakiyi hankali ba ko to wlh ki kiyaye wannan ta fiki garama ki sawa kanki ruwa dariya Aisha tayi ta fice gidansu maman Ummi a zaune ta sameta a ɗaki tana ninke kaya" a'a yaushe a gari maman Ummi ta faɗa tana dariya "ɗazu mukazo ya Ummi Aisha tace "maman Ummi ce tace "ai tana gidan yayanku tunda yazo ya ɗauketa "nima zan tafi makarantar kwana ranar monday Aisha tace "wa maman Ummi ". "ikon Allah maman Ummi tace " tana murmishi to Allah ya kaimu Aisha "amen Aisha tace "kana ta fito daga gidan. tana dawowa yamma tayi dan haka mama tace "mata me takeson ci ?"indomie Aisha tace "da kifi "mama ce tace "kinga babu mai siyomin maza ga kuɗin ki siyo manya guda huɗu koda bamu cinye ba gobe a ɗumama ki siyo kifin na ɗari uku munada mangyaɗa da maggi "to Aisha tace "kana ta ruga da gudu bata jima ba sai gata ta dawo karɓar jajjage tayi bayan ta gama mama ta bata yanka albasa suyar da amaryar malam taji ne ya sata ƙwafa tace "zai shigo ya sameni yau za 'ayi bala'i a gidannan ta zauna a kujera tana jiran shigowar malam "gida ya kaure da ƙamshi sosai ga ƙamshin kifi gana indomie abin yayi yawa komawa ɗaki mama tayi ta fito da buta ta zuba ruwa taje alwalah tace "wa Aisha inta gama ta zubawa amarya a roba "tom kawai Aisha tace " tana gamawa ta cika robarta dashi ta sawa mama a kwano ya zamo saura kaɗan ta ɓoye tukunyar inda mama bazata gani ba ta shige ɗaki ta fara ci lemun da aka siyowa Khamis bai sha ba shi ta sha tana ci tana waƙa. Bayan isha'i malam ya shigo da fara'arsa ya shige ɗakin amarya haba amarsu bakya lefi fa ko faɗan da nayi miki akasi aka samu zo mana ya washe haƙora, wata uwar harara ta doka masa kana tace "ai bazanyi lefin ba daka basu kuɗi suketa soye soye ni ka wareni tun yazu ka fara nuna kafi sonta kenan ni wlhi bazan iya ba ta ƙarashe maganar tana kuka"malam ne ya janyota jikinsa yana yi mata tafiyar tsutsaya yana adu'a lol kome yake karantawa oho hhh. cikin ƙanƙanin lokaci ta miƙe tare da kawo masa dublan da cincin da fresh a jug washe haƙora yayi yana cewa " Allah yayi miki albarka amarya ta kinsan inda nake sonki kuwa ƙara fasa mata kai yayi tama mance da su Aisha na can suna cin daɗi , haka ya shashantar da ita har bacci yayi gaba da ita , miƙewa yayi ya je ɗakin mama sallama yayi ya samesu a zaune kowa da kwanon indomie a gabansa ga kuma lemon kwalba , eyeeee malam yace "ke Aisha ya nunata da yatsa yace "dan ubanki bakida tausayine duk daɗi da kuɗin da suke kashe miki bazaki dinga tunawa da mahaifinki ba ko ?" wlh ki yiwa kanku faɗa ,mama dai tana zaune kamar kurma ya ƙara da cewa "ko da yake wanan uwar taki bazata barki kiyi arziƙi ba nasani ba laifinki bane , kayi haƙuri malam ga dubu biyu yace "in baka Aisha tace " washe baki yayi kana yace "ashe dai ƴar malam tana tattali kai Allah yayi miki albarka dama banida kuɗi kamar kin sani , yana karɓa yace " to a kwana lpy ƴar malam "malam na fita Aisha tace " mama wlh kuɗin da kyakkyawa ta bani inbawa anty Fiddausi ne wanan tun zuwanmu fa"ahine baki bata ba " cewar mama Aisha ce tace "ai ya basu dubu goma shine na ɓoye wanan gashi naba malam ai "to Allah yayi miki albarka mama tace " amma karki sake shiga sabgar amaryarnan na roƙeki Aisha kinason raina yayita ɓaci ko ?" a'a Aisha tace "tare da miƙewa kai roba waje ta wanke hannu tayi alwalah tazo tayi sallah tana idarwa ta hau gado ta kwanta. Washe gari da asbha mama ta dinga tashinta taƙi tashi har sai da ƙarfe bakwai tayi sai faɗa mama take yi mata , bayan tayi sallah ne mama tace " tazo ta siyo ƙullu a dama koko ɓata rai tayi kana tace "ni wlh tunda naje gidannan bansha koko ba sai yau taɓɓ wlh na dena sha a siyo madara da buredi a haɗa shayi da suga , to mama tace "kuma ance baƙonka annabinka dole tayi mata sbda ma duk ta dalilinta suketa samun alkairai sosai, bayan Aisha ta siyo an haɗa shayi tanajin amaryar zata fito Aisha ta fito da kofin shayi tana cewa "mama sugan beji ba wlh , mama dake shan nata tace " karyaji ɗin mai bakin shan zaƙi ,dariya Aisha tasa tana ƙarawa ,wanan abin ya ƙular da amaryar malam kamar zatayi kuka har so take taga ranar da Aisha zata bar gidan tayi murna dan in tana nan to babu ita babu zaman lafiya. "a'a Aisha me kikeyi a nan ?" malam ya tambayeta "shayi nakesha malam "Aisha ta bashi amsa" to to ƴar malam asha shayi a daɗo miki madarar ne koko wanan taji ?"eh taji Aisha ta faɗa tana dariya , malam na shiga ɗakin amarya tana ganinsa ta dashe da kuka tace "yau gidanmu zani bazan zauna baƙinciki ya kasheni ba a sati mun taru mun cinye garata gobe fa zaka koma ɗakin matarka gashi ka sake musu kuɗi sai daɗi suke ci ni ka barni kamar dutse nikam bazan yarda ba tunda kaima bazaka sauya ba wlh, haƙuri malam ya shiga bata tare da cewa "indai shayi ne zai siyo mata ta kwantar da hankalinta , ganin zata tada masa bori yasa ya ɗauki kofi yaje gurin mai shayi ya siyo da bredi ya kawo mata , sai a lokacin tayi dariya hhh harda haɗowa da hanun malam akayi irinna masoyannan wato kiss lol abin dariya , ƙyl ƙyl abu yayiwa malam daɗi yasa dariya , jiyo dariyarsa da Aisha tayi ne yasata cewa "mama wai malam lafiyarsa "ke banison gulma kina yarinyarki dake mama ta faɗa tana zarewa Aisha ido ,gum Aisha tayi bata ƙara magana ba . Zuwa azhar amarya taci kwaliya yau malam zai fita daga ɗakinta ya koma na maman Aisha zuwa yamma tana tafe tana cin cingam dariya Aisha tasa tana tafi , maman Aisha dake ɗaki tace " kekuma lafiya?"lafiya mama Aisha tace "bayi ta nufa amaryar da buta a hanunta, a hankali Aisha ta shiga ɗakin ta ɗauki kwalbar turaren wuta guda uku ta fashesu ta kuma ɗauko plet plet na tangaras shima ta rotsa shi, da gudu amaryar ta fito yana harsashen kamar a ɗakinta akeyi cikin sa'a taci karo da Aisha Allah bai bata sa'ar kamata ba.....! [29/08, 9:19 pm] Mom Islam Ce 💃: 29 & 30 Ihu tasa tana cewa "shegiya kin kasheni ,ficewa ƙofar gida Aisha tayi taga malam a zaune da redio a hanunsa cikin firgici tace "malam aljanun amaryarka sun tashi tana ta fasa kayan ɗakinta kazo ka gani"malam har yana tuntuɓe ya taho ya samu tana ta gursheƙen kuka buta ya ɗauka ya kuskure bakinsa kana ya fara yimata karatu ture ƙafar malam tayi tace " ance maka aljanu ne dani da zaka wani zo baka yimin jaje ba kazo kana yimin adu'a ?" ci gaba da adu'a malam yayi kuka takeyi sosai dan abin yayi mata ciwo Aisha kam ta gudu batama anguwar ta sshiga kasuwa ranta fess , mama ce ta fito cikin sanyin jiki dan tama kasa fitowa tsabar takaici tace " dan Allah kiyi haƙuri , kan uba amaryar tace "tare da bangaje malam ya faɗi ƙasa tace "wlh yau sai anyi gobara a gidannan dan bazan yarda ba "malam da ya kasa gano komai yace "wai meke faruwa ne"mama da bataso yimasa magana ba tace "ka tambayi ƴarka ta shige ɗaki "zabura amarya tayi tayo ɗakin maman Aisha da niyar duka cikin kakkausar murya malam yace "ko da wasa karkiga na auroki kice zaki rai nata sam ban yarda ba koda wasa "malam ya faɗa yana girgiza hannu , baƙinciki gami da damuwa ya ishi mama ta zauna ta fara kuka tana salati malam na fita amaryar tayo ɗakin mama da icce zata daki mama shigowar Aisha kenan tana waƙa amaryar ta ɗaga iccen sai a kan Aisha ta sauke mata shi ji kake gimmm sumammiya ko mai rai Allah ne kaɗai yasan dai dai "da gudu mama ta miƙe tana salati tana kuka bata tunkari kan amaryar ba tayi kan Aisha tana kuka kamar ranta zai fita , bangaje amaryar mama tayi tana kuka ta fice dariya amarya tasa tana cewa "sa'a tafi sammako mama babu hijab ta leƙa ƙofar gida hakan ya bawa malam mamaki ya leƙo yace "wane irin hauka ne haka ?"da muryar kuka mama tace " an kashe Aisha "malam ne ya wurgar da redion hanunsa kana yace "me kika ce ?" mama bata ƙara bi takan malam ba ta koma ɗakinta inda tabar Aisha haka ta dawo ta sameta babu nunfashi hankalin malam a tashe yace "waye yayi mata haka ko faɗuwa tayi ?" mama dake sharar hawaye tace "amaryarka ta bigeta da icce a kai , ya salam malam yace "tare da ɗaukar Aisha Allah yasa suna fita sukaci karo da mai mashin sai asibiti , emergency aka wuce da ita inda aka fara bata kulawar gaggawa , hatta likitoccin sun fara karaya sosai da lamarin in suka fara aiki har wani uban gumi sukeyi kaf cikinsu babu wanda bai tausayawa Aisha ba" Mama da ta koma kamar kurma sai sharar hawaye take tana ƙarawa malam kam ya kiɗime dan zirga zirgar da yake ne zai tabbatar maka yana cikin damuwa innalilahi yake ta mai maitawa yayinda ƙasan zuciyarsa ke tafasa kamar garwashi , da likitoci sun fito zaiyi kansu da gudu yace "musu lafiya ?" babu mai kulasa. Washe gari har yanzu sunata ƙoƙari kan Aisha abin ya girmama har yanzu basu faɗi halin da take ciki ba , mama kwana tayi babu bacci malam kan ta kwana yana sallah , sai da yayi haske sosai malam ya fita ya siyowa mama abinci yace "mata ya tafi gida yana zuwa gida ya sami amarya ta sake waƙa a waya tana ta tiƙar rawa , a fusace ya buga wayar da ƙasa yana yi mata bala'i tana magana ya wanketa da mari kana ya janye ƙafarta ta faɗi ƙasa yace " wlh karki ɗauka kinci banza sai na zubar miki da jini kema "mtsw amaryar taja tsaki tace "a banza zama daram dan ɗan wanan abin sai ka tada hankalinka garama kazo musha soyayya nayimaka tanadi oyoyo mijina "kukane malam baiyi ba sai da ya nisa yace soyayyar ubanki shegiya mai mugun hali dana san gaka kike babu abinda zai sa na aureki ƴar iska kawai jaka jahila "amarya ce tace "nasan ta gama da kai kome zakace ba yin kanka bane nasani Allah ya bakaaa lpy malam malam dake ɗauko wa mama kaya yace " amen tare da ubanki shegiya jaraba ya fice daga gidan yana shirin fita ya hangi motar Khamis wani mummunan faɗuwar gaba ne ya riskeshi ,Khamis na shirin fitowa malam na shirin zuwa jikin Khamis tun jiya yake jin babu daɗi ko abinci bai ci ba jiya yace "wa malam ina wuni tare da durƙusawa malam ne yace "lpy ya iyayen naka ?"suna lpy Khamis yace "masu gidan sunan ko ?" Khamis ya tambaya "malam ne yace " suna asibiti ,gaban Khamis ne ya yanke ya faɗi yace "waye babu lafiya ?"malam ne yace "ƙanwar Aisha ce "Khamis ne yace "dama Aisha nada ƙanwa ne ?"malam bai iya bashi amsa ba zai shige yace " baba in asibitin zaka kazo muje nima zani ya faɗa murya kamar zaiyi kuka , shiga motar malam yayi suka tafi , cikin ikon Allah suka iso asibitin suna shiga hanyar da zai sadaka da ɗakin mai jinyar Khamis yaji gabansa na dukan uku uku , mama ya hango bai hango Aisha ba to ina take ya tambayi zuciyarsa" ƙarasawa gurin mama sukayi dake zaune a benchi ta ɗaga kai sama , durƙusawa Khamis yayi ya gaida mama tare da cewa "ya mai jiki ?"da sauƙi mama tace "Allah yasa su barka ka shiga " malam ne yace "wai har yanzu bata motsa bane ?"eh bata motsa ba wlh mama ta faɗa da alamum damuwa a fuskarta" miƙewa Khamis yayi kana yace "inane ɗakin marar lafiyar ?" gashinan mama tayi masa nuni da hannu buɗewa yayi da sallama yaga likitoci sunkai biyar akan wata kamar Aishansa diri diri yake gani kasancewar ganin Aisha da yayi kanta ɗaure da bandeji kamar babu nunfashi ,waya ya ɗaga ya kira Ammi taga ɗagawa yace " Aisha babu lafiya muna asibiti ya gaya mata sunan asibitin ,suna gama waya ya faɗi ƙasa sumamme jin hayaniya tayi yawa a ɗakin yasa malam shigowa ganin Khamis a kwance yasa shi salati ya ƙwalawa mama kira nan da nan aka bashi gado aka fara bashi kulawa , cikin mintuna ƙalilan sai ga Ammi nan ta iso tana cikin tambaya ne suka haɗu da malam yace " ga ɗakin da aka kwantar da Aisha can shiga Ammi tayi jiki a sanyaye ta zauna hawaye nabin fuskarta yarinya mai barkwanci" tambayar ina Khamis tayi" cikin in ina malam yace " ya ya ya....yaje ina ?" Ammi ta faɗa hankali a tashe tasan in akan Aisha ne babu abinda bazai yi ba. Yana kwance an bashi gado , a kiɗime Ammi ta tambayi ɗakin aka gaya mata tana shiga ta gansa kamar wanda yayi ciwon shekara duk ya rame sosai shafa fuskarsa Ammi tayi tare da cewa "Allah ya baku lpy my son ta share hawayen daya kwaranyo mata ta nemi kujera ta zauna . Malam da mama babu mai iya magana kowa da abinda yake kitsawa a zuciyarsa wani doctor ne ya fito kana yace "ana neman mahaifin yarinyar nan da take wancan ɗakin doctorn ya nunawa malam da hannu , cikin fargaba malam ya isa gurin yana salati a zuciyarsa samunsu yayi sun rufeta baya ko hangota bare yasan meke faruwa, ganin basu kulashi ba yasa shi ficewa ya zauna ya maida tagumi , tunowa yayi rabonsa da abinci tun jiya da rana tabba hausawa sukace inkaji ance baka iya kuka ba to uwarka bata mutu ba , tashi ɗaya mama ta rame Ammi na can ɗakin Khamis dake ta bacci anyi masa allura , zuwa can anjima sai gashi yana motsi da jikinsa cikin farinciki Ammi ta daɗa matsowa da kujerar da take zaune tace "my son ga Amminka ta share wasu hawayen da suja ƙara yi mata sintiri buɗe idonsa yayi a hankali ya kalli Ammi tare da kamo hanunta ya haɗe a nasa yana kallonta [30/08, 4:41 pm] Mom Islam Ce 💃: 31&32 "Ammi na Aisha ta mutu ko ?"Khamis ya jefowa Ammi tambaya "bata mutu ba my son tana nan lafiya "Ammi ta faɗa tana kallonsa, Khamis ne yace "to Ammi riƙemin hannu muje in ganta "riƙe masa hannu Ammi tayi suka isa room ɗin da Aisha take babu likitocin sai mama da malam dake zaune fuskar su wasai suna dariya da sauri Khamis ya ƙarasa kan Aisha yace "ta warke ne ?"eh mama tace "amma ta koma bacci "ina Khamis ya faɗa da ƙarfi ta mutu ne kuke ɓoyemin walh Ammi ce ta riƙe hanunsa ta jashi zuwa gaban Aisha ta riƙo hanun Aisha ta haɗa da nashi jin haka yasa Aisha buɗe ido cikin murya irin ta marar lafiya tace "kyakkyawa "wayo Aisha na Allah nagode maka haƙiƙa ni mai sa'a ne a rayuwa wayo Allah Aisha taji sauƙi natafi masallaci yin sallah dan in nuna godiya ga Allah ya fice ya nufi masallaci, Malam da mama da Ammi mamakin irin soyayyar da Khamis ke yiwa Aisha sukeyi tabbas samun kamar Khamis sai an tona , bayan ya idar da sallah ne ya fara kwararo wa Aishansa adu'ar daɗin samun lafiya mai ɗorewa ya dawo ɗakin cike da fara'a har lokacin idon ta biyu , janyo kujera yayi ya zauna daf da gadon da take kwance su mama ficewa sukayi dukansu , kamo hanunta yayi yana kissing yace "my Esha bana son ki tafi ki barni ko a mafarki , Aisha dake shirin kuka tace " kyakkyawa amarya ce ta ƙwalamin icce a kai na shine na faɗi "waye amarya ?" Khamis ya tambaya , amaryar malam fa Aisha ta faɗa tana taɓa bandejin kanta , a zabure ya fice ya fito waje Ammi na ganinsa yana huci tace "son me kuma ya faru ?"tasowa malam yayi a firgice yace "jikin Aishan ne?" zani ɗaukar fansar bugawa Aisha icce ne ya faɗa babu ko jin ɗarr a zuciyarsa ,idanun malam na zubar da hawaye yace "ka rabu da ita kowa yayi nagari dan kansa ni kaina badan kar ashe nayi aure da wata manufa ba sati ɗaya na saki mata wlh da saina saketa , dakatar da Khamis Ammi tayi kana tace "abi komai a hankali Aisha ta gama samun lafiya. Kwa nan su Aisha biyar su yaya Zakari da anty Fiddausi sukazo duba su tare da kawo kayan tsaraba Ammi kam kullum tana zuwa ta koma gida washe gari ta kuma dawowa Khamis kam sai wajen ƙarfe goma na dare yake barin asibitin . Sosai taji sauƙi dan jikin ya ɗan warware har ana shirin sallamarsu gobe insha Allah, murna gurin Khamis abin babu sauƙi har yana gayawa Ammi ana sallamar Aisha tace "zata wuce da ita gida shiru Ammi tayi masa tafison ta ƙara samun lafiya sannan ta dawo . Washe gari ana sallamar Aisha suka wuce gida suna shiga suka ci karo da amarya tana wanke wanke , ko kallon su batayi ba suka shige da malam da mama da Aisha , kai tsaye ɗakin mama suka wuce ta kwanta a gado kasancewae jikin babu ƙarfi. kwana goma da faruwar hakan jikin Aisha yayi sauƙi har tana fita waje tayi wasa da safe ƙarfe 7:am amarya taje maƙota siyo kunu Aisha ta cinno wuta a icce tasa jikin labulen amarya kana ta ɗauki ragowar kananzir ɗin dake gorar da mamanta take hura wuta ta wartsa nan da nan wuta ta kama sosai kayan ɗakin ya fara cin wuta , buta Aisha ta ɗauka da gudu tayi bayi ta tsuguna tana jiran shigowar amarya. Amarya ta shigo da waƙa harda tafi taci karo da ɗakinta na cin wuta salati tayi kana ta ƙwala ihun neman agaji wuta ta cinye kayan ɗaki harda gado da katifa jin muryarta a sama yasa malam shigowa da sauri ya ɗauka mama ce jikin Aisha ya tashi , yana shigowa ya sami amarya tana ta ɗaga hannu sama alamun temako mtw malam yaja tsaki tare da cewa "kin ɗauka Allah zai barki a haka ne ?"gashi banyi miki komai ba Allah ya sakawa baiwar Allah cikin ƙanƙanin lokaci , malam ka fita a idona in rufe wlh Allah daga kai har matsiyaciyar matarka sai kunyi dana sani wa yasani ma ko shegiyar ce ta sa wutar inko naje naji ance itace to ba shakka sai na daɗa fashe mata kai , a lallai malam ya faɗa yana jinjina kai tabbas biri yayi kama da mutum dama jiya akace min kin taɓa hauka nace ƙarya ne amma babanki ya cuceni da bai gayamin gaskiya ba , wani wawura ta kawowa malam ya ruga da gudu dan tsoronta yake ji amma bai nunar mata ba tana guduwa tace "daka tsaya dana nuna maka ni babbar ƴar iska ce kuma kaci bashi ai tunda kukace haka to an gama zaman lafiya a gidannan kowa sai ya kwashi kayansa a hannu , kana ta kuma rushewa da kuka tana nuna ɗakinta babu wanda ya shigo duk mai shirin shiga malam zai ce ai hauka yana tunanin ta fara anjima kaɗan zai kaita asibitin mahaukata sai su ja baya , maman Ummi da taji abin yayi yawa ta yafo gyalenta tana shirin shigowa taci karo da malam babu damar ya hanata dole ya barta ta shiga tana shiga taga amaryar gidan na kuka tare da sanya hannu a kai , gefen ɗakinta maman Ummi ta kalla taga duk ya kama da wuta Allah ya kyauta maman Ummi tace "tana shirin wucewa ɗakin mama amaryar tace "munafuka a haka zaku ƙare taci gaba da kururywarta , sai yanzu Aisha ta fito daga bayi tana cuno baki, saitin ɗakin amarya Aisha ta kallah suna haɗa ido amarya tace " to yarinyar munafukai, uban me kike kallo?" amarya dai ta koma kamar mahaukaciya sai bala'i take tana gamawa tasa kuka haka ta dingayi duk wanda ya shigo sai ta zageshi , maman Ummi ce tace "wa mama ya jikim Aisha bansami zuwa ba wlh baban Ummi ne babu lafiya jiya ma ya ban tsoro , subhannalah mama tace " Allah ya bashi lafiya mai ɗorewa amen maman Ummi ta faɗa kana tace "naji abu kwam a gari wai waccan ce ta bugawa Aisha icce a kai ?" hamm mama tace " eh itace ai da saidai kuji saƙon mutuwa wlh dan daga ni har malam bamuyi tsammanin Aisha zata tashi ba , taɓɓ to Allah ya ruda asiri maman Ummi ta faɗa tare da miƙewa ta fice, lokacin d tazo fita amarya ta koma ɗaki tana kuka tana surutai . mama ta fito daga ɗakinta da niyar haɗa wuta sai yanzu ta lura da cin wutar da ɗakin amaryar yayi kuma hakan bazai sa tace "da ita Allah ya kyauta ba mama ta jinjina kai. washe gari yau kwanansu biyu da sallamowa Khamis ya zo da safe lokacin ƙarfe goma da rabi ya kaawowa Aisha kayan marmari aiko yasha hira dan bata gayawa mama itace tasa wuta a ɗakin amarya ba amma Khamis na bata sweet tana cikin sha tace " kyakkyawa na rama abinda amarya tayi min na ƙona mata ɗaki waro ido Khamis yayi kana yace "da hankalinki kuwa Aisha sai na gaya mata , tsaki Aisha tayi tace "wlh jeka ni ba tsoranta nakeji ba , jinjina kai Khamis yayi kana yace "taɓɓ duk wanda ya taɓo Aisha ya taɓo wa kansa tsiya , dariya Aisha tasa tace "har monday ta wuce ba'a kaini makaranta ba kyakkyawa?" bakya ganin bakida lafiya ne my Esha amma tunda kinji sauƙi kina komawa za'a kaiki kwantar da hankalinki , tsalle Aisha tayi tace "jibi zan dawo gidanku kaji kyakkyawa ?"ywwa my Esha Khamis yace " aiko zansa a soya miki kaji da farfesun naman rago suka sa dariya , yace " to ni zan tafi sai jibin nima nakusa tafiya amma naji ance kamar tafiyar zata fasu , bata shi takeyi ba sai tsallenta take iya san ranta ,niko nace kaji kamar yana magana da babbar mata , ficewa yayi ransa fess a nesa da bakin ƙofa ya sami mama ya ƙirgo dubu biyar ya bata ƙin karɓa tayi sai da ya nuna bazai mayar aljihu ba sannan ta karɓa , amarya najin Khamis ya fita ta fito ta riƙe ƙugu tace "a bani nawa kason dan baza'a zalinceni ba ina gani ehe [31/08, 2:24 pm] Mom Islam Ce 💃: 33 34 Ko ɗago kai mama batayi ba Aisha ce ta bata amsa tace " to ai ba mijin ƴarki bane "kan uba amarya ta faɗa cikin ɗaga murya to wlh yau za'ayita a cikin gidannan ace ko tausayina baza ayi ba nayi gobara ban ɗauki komai ba ace baza'a bani koda dubu biyu ba tana maganar tana tafi kamar ƴar dambe "malam da ya shigo ajiye buta yace "meke daruwa ne ?" kuɗi aka basu shine ta hanani malam ne ya shiga ɗakin mama yace "ki bata koda ɗari biyar ne a cikin kuɗin "babu musu mama ta bata shima darajar taga malam ya sakko tunda suka kwanta a asibiti , miƙa mata kuɗin malam yayi cikin masifa tace "kambu wlh baku isa ba dubu biyar fa naji wanan munafukar na cewa "taɓɓ ta wurgawa malam ɗari biyar ɗin , ɗauka yayi ya fice kai tsaye gurin mai shayi da indomie ya nufa yace "ayi masa haɗi yaji albasa da maggi kana yace "mai shayi ya bashi aron plet ,ana gamawa malam ya shigo da plet da baƙar leda a sama amarya dake tsaye tana jijiga tana surfa bala'i ta gansa da plet a hannu bata kulasa ba ta tsaya taga gudun ruwansa ,zama yayi kan kujera ƴar tsugunno kana ya buɗe indomie da ƙwai haɗe da shayi,ya fara aikawa cikinsa ,aikin banza harara a duhu amarya ta faɗa lokacin da ta fito da jakar kayanta wai tayi yaji , Allah ya kaiki lpy malam ya faɗa , kuka tasa tace " bakada tausayi ko kaɗan ɗakin nawa yayi gobara amma ka kasa temakamin da koda wani abu kwanan da zanci abinci ma bani da shi malam dai kansa a ƙasa bai kulata ba ta fice ta tafi. Bayan kwana uku. tun safe Khamis yazo yai parking kana ya shiga gidan samun mama da Aisha yayi a gaban murhu durƙusawa yayi ya gaid mama Aisha ta gaishe shi tare da cewa "kyakkyawa nafasa tafiya "Aisha ta faɗa tana maƙalewa a jikin mama "dariya mama tasa tace "aiko tafiya babu fashi shima Khamis murmishi yake , barin jiraki a mota Khamis yace "kana ya fice , zama yayi a mota ya ɗaga kansa sama yana murmishi mai sauti Allah yasa shi kaɗai ne a motar babu driver kasancewar in zaiyi tafiya da Aisha bayason driver ya kaisu .nhg gb Ya daɗe a cikin momta sai gata cikin wata koriyar shadda riga da sket, duk da ba wata babba bace kayan sunyi mata kyau ta yafa farin mayafi ta iso gurinsa da wata leda a hanunta da jaka kuma , buɗe mata motar yayi ta shiga ta zauna a gaba shi da yake mazaunin driver ya jangota tare da zuge glass ɗin , kasancewarsa baƙi yasa bazaka hango kowa ba sai dai shi da yake ciki yana iya ganin masu wucewa "kyakkyawa ka dena fa wlh babu kyau kuma za'a dinga ce mana ƴan iska "murmishi Khamis yayi ya kuma janyota har sai da ta dawo kan cinyarsa ya haɗe fuskarsu guri ɗaya yana cewa "ina miƙa godiyata ga Allah da mafarkina bai kasance gaskiya ba tabbas na shiga ruɗu my Esha na ɗauka zaki tafi ki barni ne ashe zamu sake haɗuwa my Eshana , dariya Aisha tayi kana tace "kyakkyawa in baka labari naji ana cewa "amaryar malam tafara hauka "zaro ido Khamis yayi kana yace " innalilahi shine kike dariya my Esha suk da ta cuceki amma ai Allah yace "AL MUSLIMU AWUL MUSLIMU" musulmi ɗan uwan musulmi ne . "Dan haka ki zamo mai tausayi ko gobarar da kika sa mata banso ba wlh amma karki ƙara kinji "kuka Aisha tasa tare da cewa "nama fasa binka buɗemin ƙofa na fita baza'aje ɗin ba , rungumeta yati tsamm yana shafa bayanta yace " dan nayi miki faɗa shine kikaji haushi ?"to ai Ammi tace "in baki koma yau ba maganar makaranta tasha ruwa ,ƙara ƙanƙameshi Aisha tayi kana tace " zani muje zani "jikinsa duk ya mutu haka ya tada motar suka bar anguwar sai gidan Ammi . cikin ikon Allah sai gasu a ƙafar da horn yayi mai gadi ya buɗe masa get suka shiga , yana parking ɗin motarsa a parking spice Aisha ta buɗe da gudu zata ruga ya cafko ta yace "nafison in dinga ganinki kina tafiya irinta ƴammata my Esha "ya raɗa mata maganar a kunenta , dariya ta kwashe dashi tace "yaya kenan ni ka sakeni inje in cewa "mama na dawo yaushe za'a kaini makaranar ?" ok tom muje suka fito yana riƙe da hanunta ,suna shiga suka sameta ita da Afnan suna kallo ko kallon inda Afnan take Aisha bata yiba ta koma gefen Ammi ta zauna kana tace " mama na dawo , oyoyo ɗiyata Ammi tace "tare da rungumeta Afnan ce tace "brother ina wuni ?"lpy lau ya amsa fuskarsa babu yabo babu fallasa yace "ya momy ?"tana lpy Afnan tace "cikin jin daɗi ya miƙe ya tafi bedroom ɗinsa dake part ɗin Ammi "Aisha bakiga antinki bane ?" Ammi ta tambayeta "na ganta ina wuni ?"lafiya Afnan tace "cikin harara a fakaice ba tare da Ammi ta gane ba "mama yaushe zan tafi makarantar ?"Aisha ta tambaya da alamar tausayi "Ammi ce tace "ki bari ki ƙara samun sauƙi man "na warke Aisha ta faɗa tana taɓa ɗinkin da aka yi mata da ka gansa kasan faɗarta ce ta yarinta , to naji maza jeki part ɗinku akwai abinci da yarinyar baba tayi miki zama ta dinga kwana a nan akwai ɗakin ƴan aiki , da tsalle Aisha ta tashi kana ta wuce tana murna ,tana zuwa ƙamshi ya bugi hancinta ta zauna a dining ta buɗe abincin kalolin abinci ta gani sunkai kala uku a cikin harda haɗin salad , zaro ido tayi tace " kabeji nayima bankwana wlh koda a mafarki bazan cika ba ta faɗa tana jujuya hannu , Khamis ne ta shigo yana sanye da koriyar shadda tasha aiki bayan yayi sallama Aisha ta amsa ,tace "laaaah kalar shadda ta ko kyau ma bakayi ba tunda kana gasa dani , murmishi Khamis yayi kana yace "akwai salad a gurin idan kina buƙata ya faɗa yana dariya ,wlh bazan ci kai kazo kaci ni banga ma naman bane ,taci gaba da bubuɗewa , kodai ba'a dafa bane ?" ta jefo masa tambayaa "kidai bude zaki gani Khamis ya faɗa yana kallonta ,cikin sa'a ta buɗe wani kwano mai murfi mai kyau taga soyayyun kaji harda yaji a gefe ,Khamis dake kusa da ita sai da yaji alamun haɗiyar yawun ta , mamaki yake shikam da har yanzu ta kasa sabawa kullum ƙwaɗayin cin kaza oh ,Aisha ce ta katse masa tunani da cewa " kallona kake ko ?" a'a Khamis yace "yana dariya "sai da ta cika cikinta damm sanan ta sauko ta dawo kan 2sitter ta zauna tana shafa ciki , kallo Khamis ya kunna a tashar Arewa 24 wani film suka sanya mai ban dariya , tunda Aisha ta fara kallo ko ƙiftawa batayi sai dariya take , Khamis ne ya canja kallon izuwa tashar mbc action turɓune fuska Aisha tayi ba tare da tayi magana ba ta juya baya , bacci ya fara ɗaukarsa juyowar da zatayi taga ankai wa wani mutum naushi itama ta kaiwa Khamis naushi a jinya ,a zabure ya miƙe tare da cewa "innalilahi lafiya kuwa ?" juyawa Aisha tayi tana dariya ciki ciki "Esha meke faruwa ne ?" Khamis ya tambayeta shiru tayi babu amsa dariya ta kuma sawa tace " nifa na matsu inganni boko wlh ko mutum ya sami sake ku nan ku dinga kulle mutane kamar masu lefi nama fita samo kayan wasa na samu wani mahaukacin kare ya biyoni wanan wacce irin jaraba ce ni duk gidan ma ya isheni namafi son in koma gida inga amaryar malam , duk wanan maganar da takeyi Khamis na jinta cikin zuciyarsa yace "tabbas hausawa sunyi gaskiya sukace in daɗi yayiwa mutum yawa sai yace "Allah kasheni shine wanan tabbas yaji haushin wata maganar a ciki amma bai kulata ba....! Abban islam babu lpy shiyasa kuka jini shiru kuyimin afuwa😥🙏 [01/09, 3:55 pm] Mom Islam Ce 💃: 35 & 36 Kwananta biyar da dawowa taji sauƙi sosai har an kunce ɗinkin da akayi mata anfara maganar tafiya makaranta , yau Ammi ta matsawa Khamis akan sai yaje dubo office yaga abinda suke ciki duk da akwai shugaba a gurin shima zuwansa nada muhimmanci sosai, ransa bai soba ya shirya cikin ƙananun kaya yana fita zai ɗauki mota driver yazo da gudu da katar dashi Khamis yayi kana yace "ɓacemin da gani a hassale "Allah ya huci zuciyarka ranka shi daɗe driver yace "yana ranƙwafa kai yabar gurin "kasancewar tunda ya fito mai gadi ya lura da yanayinsa yasa ya buɗe get da wuri ya dawo ya zauna a guje Khamis ya fice daga gidan kamar mai shirin tashi sama ,tafiya yake zuciyarsa na ƙuna ikon Allah ne kawai ya kaishi ma'aikatar tasu , bama a gurin da aka tanadar yayi parking ba kawai ajiye motar yayi ya fito tare da buga murfin motar ya nufi office ɗin nashi ya zauna yana juyi a kujera ya kai minti ashirin bai kalli takardun dake zube a gurin ba wani irin takaici yake ji takaicin kuma na haɗuwa da muhibbat ne , nocking aka fara a zuciyarsa bai kawo ita bace tunda bai ganta a gurin da ta saba zama ba ,yes come in Khamis ya faɗa da sassanyar muryarsa , murɗa handle ɗin ƙofar tayi kana ta shigo tana mai turo ƙinjinta tare da janye mayafi gefen kafaɗa ,Khamis bai lura da abinda takeyi ba ,zama tayi kan kujera tare da ƙara maƙale murya tace " ina yini yallaɓai "lpy Khamis yace "yana turɓune fuska "hawaye ta fara ta dubeshi tace " Allah ya yiwa kakata rasuwa banida gata a duniya ta ci gaba da zubar da hawaye , a razane Khamis ya ɗago ya kalleta yace " ta rasu ?"eh Muhibbat tace "alamun tabbatarwa , muje inyi gaisuwa a gidan ya miƙe tare da kwashe wayoyinsa suka bar office ɗin , a kai tsaye motarsa suka shiga ta zauna a gaba suna tafiya tana satar kallonsa shiko hankalinsa na titi , sai dai nunin anguwar da take yi masa ,cikin sa'a sai gasu a ƴan kifi K.D kenan nuna masa kwanar anguwar tayi duk kwata ga cakwalkwali motarsa duk ta ɓaci da datti haka ya dinga shiga wani ɗan madai daicin gida suka zo gida ne mai ɗan kyau baza'a kira gidan na talakawa ba kana kuma baza'a kirashi na masu kuɗi ba , yana da ɗan ƙaramin get da mota zata iya shiga , nuni tayi masa da ya shiga nan ,ya shiga yayi parking a tsakar gidan kasancewar babu gurin parking , fitowa tayi kana shima ya fito tayi masa jagora tunda suka shigo gidan babu kowa sai ƙarar tsuntsaye ,tace "ya shigo bari ta kira antina nan gidan antin ta ne gidan rasuwar na gaba da nan , to babu damuwa Khamis yace "sai kuma yake jin tausayinta yanzu sosai gata marainiya sai binta da kallo yake na tausayi " barin kawo ma drinks kafin ta iso wai ta shiga maƙota , ok Khamis yace "idonsa a kan tv dake jikin bango , fitowa tayi da fanta babba ta gora da cincin kana da ruwa shima na gora ta dire masa a gabansa , fanta ya ɗauka ya buɗe murfin ya fara sha , shiru shiru har ƙarfe ɗaya tayi su da sukazo tun sha biyu da minti goma zai ce har.....yaji jikinsa ya mutu over babu ƙarfi ko kaɗan ga wani juyi da kansa ya keyi.. Anty Fiddausi na dawowa gida ta samu kaka tayi shara tayi wanke wanke ta gyare gidan tsaf sallama anty Fiddausi tayi , kaka ta amsa batare da ta kalleta ba , murmishi anty Fiddausi tayi tace " kaka na siyo miki gadashiyar kaza "da sauri kaka ta taso tazo tana washe baki ta nemi kujera ta zauna miƙa mata anty Fiddausi tayi kana tace "ta samma Ummi " babu musu kaka ta kira Ummi tace "tazo ta karɓa da sauri Ummi ta fito tare karɓa tace "nagode , kaka na ci tana sawa Anty Fiddausi albarka "murmishin ai nima zan ƙaru dake tayi kana ta shige tana cewa "mama na gaisheki , da fara'a kaka tace "ina amsawa anty Fiddaushi ta wuce ɗaki . Washe gari kaka ta fito zatayi shara anty Fiddausi ta karɓi tsintsiyar tace " kaka aiki na yimiki yawa barin tayaki "washe baki kaka tayi tace "aiko dana gode "haka anty Fiddausi tayi sharar tare da ɗora abincin dare . Murmishin mugunta Muhibbat tayi kana ta dai daita nutsuwarta tace " ranka shi daɗe kana lafiya kuwa ?" eh Khamis yace "murya can ƙasa ,daɗa buɗe gaban rigarta tayi dama anyi mata irin ɗinkinnan da shida tsirara duk ɗaya , ta sunkuyo suna jin nunfashin juna tace "ko inzo ne ?" eh danaji daɗi my Esha taho gareni dama na daɗe ina jiran ranar da zanyi miki ajiyar baby a wanan ɗan cikin naki taho gareni ya miƙe ya rungumo Muhibbat suka faɗa kujera ,ƙara langwaɓe masa tayi tana shafa sumar kansa tana ƙara aika masa da murmushin mugunta , kwance ɗaurin ɗankwalinta yayi yana shafa ƙananun kitson dake kanta yace " wow haka nakeso "wani salo Muhibbat ta fara yi masa da ya sanya sa jin kamar wanda ya fita daga duniyar mu lol janyo hanunsa tayi zasu shiga bedroom ɗinta yana shafa ko ina na jikinta sai yai firgit a zabure ya juya ya kuma juyawa kana yace "uban meye haka zaki cire kayan jikinki ?"ba cewa "kikayi in bari antynki ta dawo ba ?" kuka Muhibbat ta fara tare da cewa "kaine fa ka cire min kaya wlh ba nice ba , kansa ya buga tare da tsaki ya fice a ɗakin ya ja motarsa ya fita kana ya fice , driving yake hankalinsa a tashe yama kasa mai ya faru dashi sai photon surar jikin Muhibbat zuciyarsa ke mai maita masa innalilahi ya dinga ammata kana ya ɗan sami sauƙi a zuciyarsa , bai wuce office ba ya zarce gida bai ma shiga part ɗin Ammi ba ya shige bedroom ɗinsa ya kwanta rufda ciki yana mamakin ya akayi har ya gansa a hanyr zuwa wani ɗaki bashida mai bashi amsa hakan yasa ya runtse idonsa ko bacci sai daukesa ya sami ɗan sassauci . Washe gari ta kasance monday yau ake shirye shiryen kai shugaba Aisha makaranta , tun asbha Aisha ta kintsa komai zuwa ƙarfe biyar da ashirin ta tashi Khamis sallah nafila ya fara kana ya wuce masallaci ba shi ya dawo ba sai da gari yayi haske zuwa ƙarfe bakwai Aisha tayi wanka kasancewar yarinyar baba mai aiki tana part ɗinta tana yin wanka ta sanya uniform ɗin da ta karɓo a gurin Ammi kasancewarsu masu ruwan hoda ba ƙaramin kyau sukayi mata ba ,zama tayi a dining ta fara aikawa cikinta farfesu tana ta tattare hijab wai karta kwashi manja , dariya Khsmis yasa yana daga zaune kan kujera yace " a boko dai babu farfesu sai garin kwaki da ƙuli " ya tuntsire da dariya, cuno baki Aisha tayi tace "idan nayi ilimi sosai bazan dinga kulaka ba "tashi ɗaya hankalin Khamis ya tashi yana tunanin inta waye fa zata iya ƙin kulasa Ammi dake haɗa mata kayan abinci a jaka tana ankare da yanayin Khamis da kuma maganar da Aisha tayi ,murmishi Ammi tayi tana jiran taji mai zaice , tasowa Khamis yayi ya zauna kan kafet kusa da ita ya riƙe hanunta kana yace " Ammi dan Allah a fasa tafiyar nan shekara shida ba wasa ba Aisha inta girma zata iya guduna Ammi "ya ƙarashe maganar yana marai raicewa "no son karka damu Allah na tare damu kuma ina tare da Aisha zan nusar da ita komai karka sami matsala "faɗaɗa murmishinsa yayi kana yace " na gode wa Allah daya haɗani da uwa ta gari mai tsoron Allah da kuma san ganin farinciki na " albarka Ammi ta sanya masa kana tace "kaje ka dubo Afnan yau ta tashi da ciwon kai "baya yiwa Amminsa musu dan haka ya nufi bedroom ɗinta tare murɗa handle ɗin ƙofar yai sallama , amsawa tayi tana daga cikin blanket zama yayi kan stool ɗin dake gaban mirror ɗinta yace "ya jikin naki ?"yayi sauƙi Afnan tace "tana ɗan rage murya....! UZURI👏pls inada marar lafiya [01/09, 8:19 pm] Mom Islam Ce 💃: 37 & 38 Kawar da kai yayi gefe kana ya miƙe ya fice daga ɗakin ya dawo palo gurin su Ammi ya zauna a kujera , Ammi ce taja Aisha ɗakinta ta zaunar da ita kana tace " Aisha ki riƙe mutuncin ki karki sake ki dinga wasa da malamai duk da nasan makarantar babu maza amma akwai malamai maza so ki kiyayye kinji " tom Aisha tace "kanta a ƙara ,Ammi ce ta ƙara da cewa "karki manta kinada aure ko bakida shi ?"ina da shi Aisha ta faɗa tana shirin kuka to koda wasa koba yanzu ba karki sake ki kula wani namiji kinji ?"to Aisha tace "Ammi ta kamo hanunta suka dawo palo tace "wa Khamis to ta shirya jikinsa a sanyaye ya muƙe tare da kamo hanun Aisha yace "suje mota ƴan Aikin gidan zasu kwashi kayan abinci su kawo mota ,binsa tayi itama tanajin rashin daɗin rabuwarsu da ahalin gidan gashi Ammj ta zaɓa mata da itama kanta ta zaɓawa kanta makarantar kwana , bayan an gama saka kayan abincin Ammi ta leƙo idanunta taff da ƙwallah tace " ƴata Allah ya bada sa'a yasa a sami abinda akaje nema "amen Aisha tace "tare da riƙo hanun Ammi ta saki kuka mai sauti " da sauri Ammi ta koma part ɗinta ganin motar tasu na shirin tashi kasancewar Khamis ne driver bai buƙaci kowa ba ,a hankali suka fita a gidan ya hau titi kusan tsakanin Kaduna da Kano akwai tafiya ,sunsha tafiya babu laifi cikin ikon Allah sai gasu a Dala boarding school kasancewar yabi umarnin Ammi da tace "a sanyata a ta gwamnati , parking yayi a bakin get ɗin makarantar kana ya rungumota hawaye na zuba a fuskarsa ya haɗe bakisu guri ɗaya tausayin sa yasa bata ƙwace ba har sai da ya raba nashi da nata itama kukan take amma nata kukan harda kururuwa , rufe mata baki yayi alamun tayi shiru , yayi horn aka buɗe get ɗin makarantar suka shiga, mai gadi na gaishe sa amma bai ma gansa ba kasancewar hankalinsa na kan Aisha , kai tsaye office suka wuce yayi musu bayanin komai dake lamarin na masu nera ne basu wani sha wuya ba , aka bata jss 1 tare da nuna mata tsare tsaren makarantar kana da kuma wacce zata zame mata uwar ɗaki Khamis yaji daɗi an sami wacce zata dinga kula da Aishan sa dubu biyar ya bawa budurwar kana ya janyo Aisha sukayi gefe yace "koda wasa karki cewa " kowa ke matar aure ce kinji "to tace "ya ƙirga dubu biyar itama ya bata kana yace "kisan inda zaki dinga ajiya zan dinga zuwa dubaki lokaci zuwa lokaci ki dinga kula da karatunki dan Allah ,kana ya shiga mota leƙowa tayi tace " nafasa zama komawa zanyi tana maganar tana kuka zaro ido Khamis yayi yace " Aisha kenan zan dawo ai yaja mota ya tafi , faɗwa tayi a gurin ta dinga shure shure wata ƴar aji uku ce ta fito da bulala a hannu tace "ke uban me kike yiwa kuka ?" yaya na ne ya tafi ya barni "kambu nan ance miki gurin shagwaɓa ne dallah tashi ki wuce ani ko in ɗaye miki jiki , ƙin tashi Aisha tayi taci gaba da shure shure ,ɗaga bulala tayi ta zuga mata a gadon bays tace " tashiii cikin tsawa ,wani malami ne ya leƙo yaga sabuwar zuwan da aka kawo ake duka , faɗa ya shiga yiwa yarinyar tare da faɗa mats ai sabuwar zuwa ce , haƙuri taba malamin kana tace "bata sani bane taja hanun Aisha suka wuce ajinsu , samu tayi ana karatu dan haka ta tuno da maganar Ammi ta tsaya ta nutsy dan jin mai ake cewa , ana tashi tayi ɗakinsy ta hau gado ta kwanta , masu duba na zuwa sukaga Aisha a kwance da nama a hanunta , zaro ido babbar cikinsy tayi tace "dan ubanki waye ya baki nama kuma waye ya baki izinin kwanciya ance miki hutu akazo yi a makaranta ?" Aisha na ƙwalalo ido tace "oho ku kuka....kafin ta ƙarasa magana ɗayar cikinsu ta sauke mata bulala a ƙafa , kuka Aisha tasa tana cewa "shegu mugaye kuma sai na rama"dariya suka sa kana sukace "zaki rame kuwa ina naman da kikece ki fito mana dashi ko mu dakaki ,baza'a fito dashi ɗin ba Aisha ta faɗa tana zare musu ido , toƙare ta da ƙafa sukayi kana suka fice daga ɗakin , suna fita Aisha tace "duk na ƙirgaku wlh sai na rama ko waye ubanku taci gaba dacin naman ta. kasancewar tazo lokacin karatu ,karatu suke babu kama hanun yaro basu da wani lokaci na wasa hakan yasa Aisha maida hankali ga karatunta , wata ranar Asabar basuda boko sai islamiya suna tasowa tazo ɗaukar nama taga an kwashe mata pikmilk ɗinta guda huɗu zaro ido tayi tana tunanin waye zai ɗauka , office ta wuce da kuka tacewa "malamin da aka fara kaita gurinsa tace "masa an sacemin madara har guda goma ,ta ƙara fasa ihu a rikice malamin ya miƙe tare da ajiye biron hanunsa yace " goma fa kikace abin mamaki ,tunanin abinda Khamis ya gaya masa yake akan idan bai kula da Aisha ba to zai iya yin sanadiyar dena koyarwarsa a makarantar ,tashi muje yace "wa Aisha "binsa tayi suka fara tun daga aji ɗaya yace " an sace madara waye a cikinku ?"kuka ta fara tana cewa "kuɓa gashi banida wasu , ƙusa malamin ya ciro a jikin wata kalanda yace " a haɗamin taro yanzu yanzu kowa ya kawo madararsa anjima wanan yarinyar ta ɗanɗana inhar taji yayi kalar nata to nata ne ,zaro ido ɗaliban sukayi tare da rufe baki basuda ta cewa " mintuna ƙalilan ƴan makarantar suka taru dukkansu , kowa da madararsa a hanunsa ya karɓa ya fasa da ƙusa yace "Aisha tasha taji ko nata ne ,kowa na gurin sai da tasha madararsa tace "ba tata bace haka kowa ya koma ya ajiye kayansa ransa babu daɗi yayinda wasu ɗaliban suka ɗau alwashi sai sunyi mata duka kokuma su sace kayan abincin ta tunda sunga ƴar masu kuɗi ce , ran Aisha fess ta ƙoshi koba komai , kwanci tashi babu wuya a gurin Allah yau suke zana jarabawar hutu kasancewar taje ana gaf da jarabawa kowa na murna zashi gida ya ga iyayensa , yau aka bada hutu wasu daga cikin ɗaliban har sun tafi wasu kuma suna jira a zo a ɗaukesu , yayinda Aisha ke zaune cikin kayan gida da jaka a hanunta hango wata mota da tayi ne motar ta tafi da hankalinta , yana parking a gabanta ya fito yana dariya itama dariyar tayi kana tace " oyoyo kyakkyawa ta rungumeshi yanajin kamar sun shekara basu haɗu ba , kasancewar rabonsu da juna wata biyu da kwanaki , babu kowa a makarantar sai sauran ɗalibai haka ya ɗauki Aisha sai gidansu a mota sai surutu take yi masa yana dariya farinciki ya keji kamar me . cikin ikon Allah sai gasu a KD suna zuwa gida yai parking bayan yayi horn mai gadi ya buɗe masa da gudu Aisha ta fice tana dariyar murna cikin ɗaga murya tace "mamaaaa da ɗan gudu Ammi ta fito tana dariya suka rungume juna zama Aisha tayi tace "mama wlh makarantar akwai cin zali sosai sunata dukana "dariya Ammi tayi tace "to ai makarantar kenan sai anyi haƙuri , tashi kije kiyi wanka kici abinci ga farfesu kifi gana kaza Ammi ta faɗa tana nuna mata dining wani uban tsalle Aisha ta doka kana tace "wayo daɗi kasheni ta fice da gudu tana waƙa. Sai da tayi wanka ta sauya kaya kana ta fito ta zauna a dining Khamis dake zaune sai binta da kallo yake yana murmishi , sai da ta cika cikinta damm sannan ta dawo kan kujera ta fara bawa Khamis labari tare da tambayarsa mamanta da yayanta ,ce mata yayi yace "gidansu sau biyu amma basa haɗuwa da yayanta...! [01/09, 8:20 pm] Mom Islam Ce 💃: 39 & 40 Abubuwa sun faru da dama bayan tafiyar Aisha makaranta ciki harda barin Afnan gidan Ammi bayan sunyi kaca kaca da Ammi akan sai dai Khamis ya auri Afnan Ammi tayi iya bakin ƙoƙarinta Khamis yace "zai iya yi mata biyayya a komai amma bazai auri Afnan ba "hakan yasa momynta babu shiri ta sata tattaro kaya tace "su tafi Afnan na kuka haka tabar gidan su Ammi badan ta soba . Ɓangaren su malam amarya ta nemi saki akan bazata iya zama da shiba cutarta sukeyi a cewarta mama ta mallakeshi sai abinda ta ce masa . Ɓangaren su anty Fiddausi kuwa sun gyarota da kaka tana faɗa mata sirruka na dabarun zama da miji kana da inda zata sami kuɗi nanda nan cikin sauƙi hhh. Yau hutun su Aisha ya ƙare ganin ranar take kamar ranar baƙincikinta tayi kuka har ta gaji Ammi tayi rarrashi tayi har ta gaji , zuwa ƙarfe tara na safe suka ɗauki hanyar kano ko gidansu bata jeba wanan karon tace "sai sunyi hutu na gaba Ammi tayi tayi amma ina , suna tafe suna hira zuciyar Khamis dai babu daɗi karatun alƙu'ani mai girma yasa yanayi yana bin karatun dan rage raɗaɗin da yakeji a zuciyarsa buni buni ya kamo hanun Aisha ya haɗa da nashi ya matse haka ya dingayi har suka iso makarantar ,horn yayi mai gadi ya buɗe masa ya shige kana yayi parking ɗin motarsa can gefe suka fito a tare da Aisha, hannu ya riƙe mata suka tafi office bayan sun gaisa yabi malaman makarantar kowa da dubu uku uku kana yayi musu godiya suka fito , suna fitowa yace "mai Esha ki kularmin da kanki dan Allah karki kula kowa hatta ƙawaye kinji "to Aisha tace "tana kuka haka ya tafi ya barta , ta wuce ɗakinsu da gudu , tana shiga ta samu sun sami ƙaruwar mutum ɗaya , yarinya ce amma zata girmeta dan zata kai shekara goma sha shida , gaishe da Aisha tayi Aisha taƙi kulata ta haye gado tana kuka sai da tayi mai isarta sanan ta haƙura ta dawo suka ɗanyi hira da yarinyar har take gayawa Aisha sunanta Khadija yarinya ce nitsatsiya mai kamun kai daga ganinta zaka gane hakan , tun daga ranar jininsu ya haɗu da Aisha komai zasuyi tare sukeyi babu abinda sukasa a gaba banda karatu amma ana yawan cin zalinsu , wata ranar lahadi kowa yayi wanki ya shanya yana jira ya bushe Aisha taje ɗakinsu ɗauko hijab ita kuma Khadija ta shiga wanka aka sace hijab ɗin islamiyar Aisha , ihu ta fara tana buge buge tare da cewa "wlh bazan yarda ba koma waye sai ya biyani , duwatsu ta fara tarawa ƙanana masu ɗaɗin jifa mutane basu lura ba ta fara sakin duwatsu wanda Allah ya bawa sa'a ta fasa mishi baki wata taji mata ciwo kowa dai da nashi kuma duk da haka akaƙi fito mata da hija , da malamai sukazo aka gaya musu abinda ke faruwa wani malami yace " kai matsala kuɗin dai da ya bamu shi zan fasa in siya miki yadin hijab a office dan nasan wanan yayan nata na zuwa zai iya sanadiyar barinmu makarantar nan tunda taƙamarsa nera mtsw malamin yaja tsaki duk wanan maganar da yakeyi a zuciyarsa yake har malamai suka watse bai sani ba sai da Aisha tace "laah juya bayanka , tana dariya juyawa yayi yaga ba kowa cikin mamaki shima ya juya ya nufi office. tun daga ranar da Khamis ya haɗu da Muhibbat taso yi masa sharri ya dena zuwa Aiki kasancewar yayi wa Ammi bayanin komai kuma Ammi mace ce mai lura da abubuwa da dama na rayuwa ga fahimta. ******************** RAYUWA KENAN MAI JUYI JUYI GIRMAN ƊAN ADAM BABU WUYA YAYINDA ZAKAJI RANI YAZO DAMINA TAZO KAKA TAZO DUK SUN WUCE KO WANNE DA LOKACINSA . Zaune take a harabar makaranta suna hira itada Khadija, hango kyakkyawar budurwar nayi kamaninta basu ɓuya ba dan haka banyi wuyar gano ko wacece ba karkuyi mamaki idan nace muku Aisha ce...tanada shekara goma sha shida a duniya farinta kyaun ta duk sun ƙara baiyana ga ƙirjinta da ya ciko da na fulani Allah ya azurtata dashi babu laifi tanada tsayi ga hips komai na jikinta kamar dan ita akayishi , wata yarinya da bazata wuce 12 yrs ba tazo gurin su Aisha tace "anty Aisha wai kizo inji malam Nazifi "ina zuwa Aisha tace "tare da cuno baki , Khadija ce ta dakatar da ita kana tace "Aisha a labarin rayuwarki da kika bani kin bani labarin kinada aure amma mai yasa bazaki fa ɗawa malamin nan cewar kinada aure ba ?" juyi Aisha tayi kana tace yayana yace " kar in faɗawa kowa shiyasa "ta wuce ta tafi tunda ta shiga office ɗin yake binta da kallo kasancewae shi kaɗai ne a office ɗin sbda yanada babban matsayi shine principal babu mai shigo masa sai in wani abu ne ya kawo mutum ,haba mana ƴar kyakkyawa ya sai in aika kizo kiƙi zuwa ?"wlh kikayi wasa duk da kowa ya yaba da ƙoƙarinki sai in ɗauki takardar jarabawarki in bayar in sanya miki bakida ƙoƙari a sakamakon ki, tsaki Aisha tayi kana tace " ni ba inayin karatu dan na sami sakamako bane inayin karatu dan na iya zama da mutane ne zats fice ya rungumota ta faɗo jikinsa ido ta ƙwalalo tana jifansa da mugun kallo tace "ni ka sakeni ko ka mance tsinuwar Allah ko , zare mata ido yayi kana ya tare bakin ƙofa yace " wlh ko kibani abinda na nema daga gareki ko in yimiki rashin tausayi da imani , hannu Aisha ta ɗaga tace " Allah kaga halin da nake ciki Allah ka kawomin sauƙi a cikin lamurana Allah ka dubenj dan isar annabi , ta kuma zuwa zata wuce ya cafko mata bobs tare da shirin rungumeta , tattaro ƙarfinta tayi cikin ikon Allah tasa masa ƙafa ya faɗi ƙasa ,ta ruga da gudu bata tsaya ko ina ba sai gaban Khadija dake zaune hankalinta a tashe , ganin Aisha tayi zufa har tana kwaranyo mata yasa ta cewa "kardai yayi miki wani abunne ?" naganki a zabure "Aisha na mayar da nunfashi tace " kedai bari inaga lokacin barina makaranta yayi dama saura aji biyu na gama to na haƙura bazan iya ba wlh ko kaɗan, a'a Aisha karkice haka inhar kikace kinbar makaranta zaki tadawa iyayenki hankali wlh ,cikin muryar kuka Aisha tace " bakiganin da karatuna gara mutunci na ?"me zancewa wanda yace "min shi mijina ne ?" mekike so ince masa ta kuma fashewa da kuka "ace malaminka shike neman watsa maka tarbiya nikam me nayi musu suke neman yimin haka ya ilahi wayo Allah na ta kuma rushewa da kuka , duk dauriyar da Khadija takeyi sai da tayi kuka, suka miƙe suka shiga aji jiki a sanyaye babu ƙarfi , yau kam mai karatun ma yasa jaruman ajin babu lafiya tambayarsu yayi ko lafiya ?"eh sukace lpy ciwon kai ne yace " su biyoshi su karɓi magani ƙin binshi Aisha tayi sai Khadija ce taje ta karɓo maganin tace " gashi ta koma ɗakinsu ta ɗauko musu ruwa suka sha , sai da sukasha maganin Aisha tace " wanan shine babu ciwo akwai magani ana gama karatu kowa ya fice masu duba littafansu nayi masu uzuriruka nayi , yayinda Aisha da Khadja ke zaune sun zuba uban tagumi. Kwance Ummi take a ɗakinta itama ta ƙara girma shekarunsu ɗaya da Aisha komai ya fito masha Allah . Kwance take a kan katifar su jikinta yai zafi sosai ,yaya Zakari ne ya shigo hanunsa ɗauke da ruwa da magani idanunta a buɗe yace " tashi Ummina kisha magani bazan iya tashi ba " Ummi ta faɗa tana shirin kuka , ɗago kanta yayi ya ɓallo maganin ya bata ,ya rungumeta a ƙirjinsa yana jijigata kamar ƙaramar yarinya....! [02/09, 2:04 pm] Mom Islam Ce 💃: 41 & 42 Wani irin kuka Ummi ta saki mai kamada na shagwaɓa tace " yayana kai na kamar zai fita taci gaba da kuka ,hankalinsa a tashe ya miƙe ya fita yaje ɗakin anty Fiddausi ya sameta ita da kaka a zaune suna kallo hmm kawai yace "kana ya ɗauki mukullin motarsa a saman tv zai fita Anty Fiddausi tasha gabansa tace "kace ka dena fita ranar Asabar da Lahadi to ina zaka ?" kallon banza yayi mata cikin sauri yace "zankai Ummi asibiti " kan uba Anty Fiddausi ta faɗa tana riƙe ƙugu ta ƙara da cewa " lallai biri yayi kama da mutum tabbas ace in raini yarinyar tun batasan kanta ba amma ta nemi ƙwacemin miji wlh bazan yarda ba kan bala'i ,tana shirin shiga ɗakinsu Ummi ya tareta yace "zan wanka miki mari bakida tausayi da imani ne ?"yarinyar na kwance itafa ke tayaki aiki amma kina can kina kallo "in baki kauce ba wlh zakiyi mamakin abinda zanyi miki , sanin kanta faɗansa babu daɗi hakan ya sata haƙura ta matsa ta bashi guri tana gunguni , koda ya shiga ɗakin Ummi jikinta ya ƙara zafi sai rawar sanyi take ,anty Fiddausi na tsaye ya fito da Ummi rungume a hannunsa da gudu ta shige ɗakinta tare da kurma uban ihu tace " wayo Allah na na shiga uku kaka wlh sonta yake ga maganarki nan ta tabbbata kaka ki temakeni" kaka ce tace " kwantar da hankalinki akwai wani hamshaƙin malami fitacce a ƙayenmu aikinsa kamar yankan wuƙa wlh inhar kinada kuɗi to ki kawo gobe gobe zantafi kwana biyu zanyi in dawo kafin ma in dawo zakiga aiki ya fara kyau , idanun anty Fiddausi sun rufe tsabar kishi tace " aiko nagode kaka kamar nawa ne zayi , jimm kaka tayi kana tace "ƴan bariki ne suka buɗe masa ido da kuɗi to ni nawa ma zamce kar inzo in ƙayyade azo kuɗin yaƙi kaiwa gashi ba lamuni yake ba , anty Fiddausi ce tace " bari mu gani zuwa gobe zanyi amfani da maganin nan na mallaka da kika bani ko shi waye nasan dole ya sake bakin aljihu , yawwa ƴar arziƙi ai kishi halak ne cewar kaka " haka anty Fiddausi ta wuni babu walwalah sun ɗan daɗe sai gashi ya riƙo mata hannu sun shigo suna shigowa anty Fiddausi ta bisu da kallo ba tare da tace "komai ba ,kaka ce ta fito tayi ɗakin kana tace "Ummi ya jikin ?" da sauƙi Ummi tace "tana matse kanta, washe gari yaya Zakari na rungume da anty Fiddausi yace " gaskiya naji daɗi jiya Allah yayi miki albarka , farr tayi da ido cikin ƙissa tace "to mijina miye amfanina inhar ban sanyaka farinciki ba ?" shafo sumar kansa tayi tace " wlh matsala ce ta dameni kana ta fashe da kuka , cikin tashin hankali ya daɗa rungumota tare da cewa " matsalar me kuma ?" ƙara shagwaɓe fuska tayi kana tace " kaka ce zata tafi gobe kuma banida ko sisi "mtsw yaya Zakari yaja tsaki kana yace " shine kike wani neman ɓatawa mutane rai ?" amma kunso yimin rashin adalci yanzu kakan zata tafi kuƙi gayamin ko ?uhmm uhm anty Fiddausi tace " to ai itace tace " kar in gaya maka wai zan sanyaka ɗawainiya "ta ƙarashe maganar tana shafo sajen fuskarsa "amma ko taje ba daɗewa zatayi ba ko ?" eh anty Fiddausi tace "kwana biyu zatayi oky yace " kana ya janyeta a jikinsa ya shiga cikin ɗaki murmishin mugunta ta farayi tana murna , fitowa yayi da kuɗaɗe a hannunsa ya bawa anty Fiddausi kyautar dubu goma ya bata dubu biyar yace " ta bawa baba , gadiya tayi maga kana ta miƙe zata tafi ya kirawo ta , tana zuwa yace "in kinyi wanka ki haɗamin shayi "to tace "kana ta fice babu kowa a tsakar gidan ta shige wanka tana fitowa ta sanya doguwar riga ta shiga kitchen ta haɗo masa shayi ta dawo tana bashi ta fice " gurin kaka dake can tsakar fida tana gyara tsintsya ,kasancewar ba lallai ka jiyo abinda suke faɗa ba tace " kaka wlh magani yayi aiki gashi mun sami kuɗi naki dubu biyar nawa dubu goma yanzu nawa zan ciko ?" cikin murna kaka tace "kai aiko na gode ki ciko dubu goma kinga aikin da yawa kince a mallake mijin naki kuma kince a rabashi da wanan yarinyar tabar gidannan , cikin zumuɗi anty Fiddausi tace " aiko zan ciko Allah ya kaimu goben. Washe gari ta kama monday kaka nata shiri yaya Zakari ne zai sauketa a tasha yana fitowa ta yi masa godiya yace " babu komai bayan anty Fiddausi ta sallameta ta fito Ummi ta riƙe mata kaya kasancewar jikin da ɗan dama dama ta raka kaka mota , kaka na gama shiga yaya Zakari yayiwa motar key suka nufi tasha , suna zuwa ana cewa " jos saura mutum ɗaya , kuɗin motar ya biya ta shiga tare da ƙara yi masa godiya a karo na biyu , sunyi tafiya mai nisa inda suka wuwuce garuruwa da da dama suka iso jos cikin ikon Allah ,parking driver yayi ya sauke kowa a tashar da suke sauke pasinja , tare da saukewa kowa kayansa mai mashin kaka ta tare ya kawota wani ƙauye ana kiransa da yalwa ,yara da manya sai murna ga kaka ta dawo ga kaka ta dawo suka karɓar mata kayanta , aka shigar mata dasu gida , tana shiga gida mutanen gidan suka fara yi mata sannu cikin farinciki suka gaisa ta buɗe ɗakinta ta shige , bayan an gana gaggaisawa matar ɗanta ta shigo kaka take tambayarta dabbobinta matar ce tace " ai kuwa suna lafiya jiya ma Sunusi ya kawo tallan wasu nace da kina nan da kin siya , cikin sauri tace "maza aika yaro ya kirawo shi zan siya guda nawa ne ?" kaka ta tambaya matar ce tace " guda biyu ne " amma kin tabbatar da lafiyansu lau ko ?"kaka ta tambaya eh tace " matar miƙewa tayi dan zuwa nemo yara ta aikasu, cikin sa'a taga ɗanta babban ta aikeshi nan da nan sai gashi tare da Sunusi sun taho yana janye da awakan fitowa kaka tayi ta tambayesa nawa ?" cewa "yayi to tinda kece ki kawo wanan babbar dubu goma wanan ƙaramar dubu biyar , cikin murna kaka ta haɗa kuɗi harda na anty Fiddausi data bata ta kaiwa malam ta bawa mai akuya , godiya yayi mata kana ya fice , tasa aka ɗaure mata awakan, dabbobin a halin yanzu sunyi biyar yanzu kuma burin siyan kaji take kamar guda biyar , mutanen gidan sai gulmar kaka sukeyi akan tana ta wadaƙa da kuɗi , dawowa ɗakinta kaka tayi kana tace "dole insan abinyi wlh inhar nace ban komawa yarinyar nan da komai ba zata cimin mutunci tunda batada kunya , barin shiga jeji in samo ganye in daka mata shi, jan mayafi kaka tayi ta tafi jeji ta samo sassaƙen mangoro da na ɓaure da sassaƙen ɗorawa ta kankare bayan ta bazasu a tirai ta ɗauko wani maganin mayu da ta barshi a gida tace "wanan zance ta sanya masa a abinci wanan sassaƙen kuma ta dinga sha zanyi tunanin abinda zan faɗa mata ,sai a lokacin hankalin kaka ya kwanata taji gaba da harkokinta , washe gari ta ɗaure kayanta tare da bawa matar ɗanta dubu uku tace "ta dinga siyawa dabbobi abinci , bayan ta karɓa kaka tace " to zamu koma dama nazo duuba awakai na ne to tunda suna lafiya masha Allah ,yara suka riƙe mata jaka ta fito domin tarar abin hawa,cikin sa'a sai ga mai mashi nan Bauchi road kaka tace "masa ɗari biyu yace "ba tare da neman ragi ba ya kaita suna isa ta shiga motar KD saura mutum biyu cikin ikon Allah sai ga wata mata ta shiga driver ya tada mota suka ɗauki hanya sai KD sunyi tafiya mai nisa , cikin ikon Allah sai gasu a Kaduna bayan an saukesu a tasha kaka ta nemi mashin ya kaita anguwarsu yaya Zakari tana sauka ta basa kuɗinsa ta shiga gidan , anty Fiddausi dake tsakar gida tana wanki tana ganin kaka ta buga tsalle ta rungumeta kamar wacce sukayi shekara basu haɗu ba. [02/09, 3:11 pm] Mom Islam Ce 💃: 43 & 44 Cikin murna kaka tace " bari mu shiga daga ciki , ajiye wankin anty Fiddausi tayi tabi bayan kaka , suna shiga suka tarar da Ummi da littafin boko a hanunta kasancewar yaya ya sanyata , a tsawace anty Fiddausi tace " dallah tashi ki fice babu shiri Ummi ta fice jikinta a sanyaye , ta fita waje ta zauna tana tsane da tsinke a ƙasa , wani kyakyawan saurayi ne yazo ya tsaya a kanta tare da cewa "ƴan mata barka da wanan lokaci " ywwa Ummi tace "tana ɗago kai tare da miƙewa daga tsugunnen da take , dan Allah in bazaki damu ba inason ki bani numbern ki tare da daddaɗan sunanki nasan inda kike da kyau haka naki sunan ma , murmishi Ummi tayi kana tace " sunana Ummu Salma bani da waya gaskiya , tunda yaya Zakari ya karyo kwana ya gansu a tsaye suna hira baƙinciki da takaici duk sun dirar masa a zuciya , yana zuwa dai dai saitin inda suke yace " an yi mata miji inhar na sake ganinka a nan wlh sai kayi nadama , saurayin ne yace " kayi haƙuri itace bata faɗamin ba ya wuce " jan hanunta yaya Zakari yayi suka wuce gida suna shiga yaji kaka na cewa "wai koɗan soye soye ba'ayimin ba , da sallama ya shiga ɗakin da suke zaune Allah yasa duk kaka ta gama yiwa anty fiddausi bayanin maganin sun mayar jaka ya zaunar da Ummi yace " inga kin sake fitowa ya durƙusa ya gaida kaka bayan sun gaisa yace " Fiddausi kizo inason magana dake " to anty Fiddausi tace " tare da miƙewa tabi bayansa , tana shiga ta samesa kamar wanda aka yiwa saƙon mutuwa , zama tayi a gedensa ta ɗauka zai ce Ummi taje gida sai taji yace " baki jan yarinyar nan a jiki sam na ɗaukota domin ta tayaki aiki kina wulaƙantata yau zan mai data gida insha Allah taci gaba da karatu a gaban iyayenta , ayiri yiri wayo daɗi anty Fiddausi ta faɗa tare da manna masa kiss a kumatu ga mamakinta sai taga ya miƙe ya fice ya leƙa ɗakin su kaka yace "Ummi fito da kayanki mu tafi , cikin murna Ummi ta fito da komai nata aka sa a bayan mota suka ɗauki hanya , tunda suka fara tafiya babu mai yiwa kowa magana shikam tunani ne fall zuciyarsa da kuma fargabar abinda zuciyarsa ke nanata masa , ita kuma farincikin zuwa gidansu take dan ta gaji da cikashin da suke mata , cikin ikon Allah sai gasu a ƙofar gida , hanunta ya riƙe suka shiga gidan su Ummi a tskar gida yaga maman tana zaune da redio a hanunta tana ganinsu ta buɗe tabar ma tana cewa "sannunku da zuwa , bayan sun gaisa tace "Ummi ta ɗibo masa ruwa bayan ta ɗibo yasha yace " wa maman Ummi na kawo Ummi ne tayi hutu zanzo in ɗauketa "cike da farinciki maman Ummi tace " to ai babu damuwa mun goode Allah ya bar zumunci ya miƙe tare da ajiye maman Ummi dubu ɗaya ,godiya tayi masa tare da sanya albarka ya fita , kai tsaye gidan su ya shiga ya sami mamansa da malam suna zaune kan babbar tabarma , shima tunda yaga malam ya dena wulaƙanta mamansa shikenan yake jin daɗi a ransa har yake yi musu alkairi tare , bayan sun gaisa da iyayen nasa suke tambayarsa ya iyalan ?"suna lpy yace " kana sukace madallah , yaya Zakari ne ya kalli murhu yace " mama naga rana tayi bakiyi abinci ba ?" hmm mama tace " wlh duk kayan abincin ya ƙare dan ma mijin Aisha na zuwa yana kawo mana kayan abinci shiyasa wlh , malam ne yace " aikam bamuda bakin yi musu godiya gaskiya ,ficewa yaya Zakari yayi ya nufi gurin mai kayan abinci ya siyo galan ɗin manja da mangyaɗa a gora da shinkafa mudu bakwai da maggi da gishiri ,ya dawo da babban buhu a kansa , malam ne ya miƙe ya karɓesa yana cewa "Allah dai yayi maka albarka Allah yasa ka gama da duniya lafiya kai mungode ,malam harda ƴar ƙwallarsa kasancewar kaf kuɗinsa ya ƙarar dasu akan hidimar bikin amarya kuma aikin malintar ma babu sosai shiyasa jikinsa saurin yin sanyi , dubu biyar yaya Zakari ya ciro yaba malam dubu uku yaba mama dubu biyu , godiya suka dinga yi masa tare da sanya albarka , yaya Zakari ne yace " malam inason muyi wata magana , mama na shirin tashi malam ya dakatar da ita yace "ina zaki ?" dawowa tayi ta zauna "yaya Zakari yace "malam dama akan maganar Ummi ne sai kuma yayi shiru , malam ne yace "ina jinka ?" dama dama ,mama dake dariya dan ta harbo jirgin tace " ikon Allah dama tasa dariya , yaya Zakari ne yaci gaba da cewa dama inason Ummi ne murmishin su na manya malam yayi yasan dama za'ayi haka tabbas akwai wanan rana , ga mamakinsa sai yaji malam yace "Alhmdulilh mungode Allah tabbas naji daɗi , to zanyi wa mahaifinta magana muji ya abin zai kasance , cikin farinciki da maganar malam yaya Zakari ya tashi dan ya kasa cewa "komai sai murmishi da yake yi yana ƙarawa , yana fita ya shiga mota sai gida , yana dawowa gida ya wuce ɗakinsu ya kwanta kan gado yana ta murmishi anty Fiddausi da tayi amfani da maganin da kaka ta kawo mata ta ɗauka hankalin nasa ne ya fara dawowa gurinta , ta shigo ta zauna gefensa ta shafo sumar kansa tace "mijina har ka dawo ?ina fatan dai bazata sake dawowa ba ko ?"haɗe rai yayi yace " ai ta tafi kenan ya janyota cikin zuciyarsa yace "tun yanzu zan fara lallaɓa ta inba haka ba intaji maganar aurannan sunana sorry. Yau ta kama ranar visiting kowa da kowa danginsa na zuwa Zaune Aisha take riƙe da wani littafi na hausa Khadija ce ta bata tace "ta dinga karantawa " tana cikin duba littafinne taji mutum ya rungumeta ta baya , har zatayi zagi sai kuma ta fasa ta juyo wa zata gani yayanta wato kyakkyawa dariya tayi kana tace "yaya baka taɓa yimin irin wasannan ba sai yau kuma babu kyau wlh , hannu Khamis ya haɗe yana murmishi yace " na dena ƙanwata yakk ya zagayo ya zauna ɗan nesa da ita , lafiya tace " tana murmishi dariya tasa tace " naga kayi ƙiba da haske ne "kaci kaji da romo ko ?" sukasa dariya " to ya karatu ?" yaya Zakari ya tambayeta yana ɗaga mata gira , karatu alhmdulilh ina " mamana ?" Aisha ta tambayi Khamis Ammi na lafiya tace "in kawo miki wani abu , amma ki rufe idonki har naje mota na dawo tana dariya ta rufe ido tace " nagaji fa cikin ɗaga murya , dawowa yayi da foodflaks a hanunsa ya ajiye mata a hannu yace " gashi buɗe ido , tana buɗewa taga farfesun kaji ne cike da kular wani irin farinciki taji dama tana sha'awar shi Allah sarki mamana ta faɗa a fili. cokalin dake ciki taauka ta fara ci kasancewar duk an cire ƙashi sai tsoka yasa ta dinga cika baki tana ƙarawa , yana zaune yana ƙare mata kallo inda ta ƙara kyau sosai , komai nata yana brgesa musamman in tana shagwaɓa , wanan zan ajiyewa Khadija ne ta kalli Khamis , waye Khadija kuma ?" Khamis ya tambaya wata ƙawata ce wlh tana sona sosai , kirawo ta in ganta Khamis yace " yana kallon yanayin tafiyar Aisha, tare suka taho da Khadija ta ɗan risina ta gaishesa ya amsa zata juya ya sa hannu a aljihunsa ya ciro dubu biyu ya bata kana yace "dan Allah kici gaba da kularmin da ƙawarki "dariya Khadija tayi tace "insha Allah ta basu guri "yaya bayan kaza sai me kazo min dashi na ci ?"cewar Aisha , dai awara ya ƙyalƙyale da dariya ya tuno lokacin da taci awarar mutane ta gudu ya kuma sa dariya ,tashi tayi alamun tayi fushi zata wuce ya riƙo mata hannu yace " am sorry matata , zaro ido Aisha tayi kana tace " wai da gaske ni matarka ce yaya ?" [03/09, 8:02 am] Mom Islam Ce 💃: 45 & 46 Eh man Khamis ya bata amsa "shiru tayi ba tare da ta sake magana ba , lokaci nayi yayi mata sallama ya tafi. Washe gari , Aisha da Khadija na zaune kasancewar sun zamo manya babu mai takura musu sai malamai d s.. Wanan malamin da tayiwa laƙabi da ɗan iska shine yazo ta gabansu yace "Aisha ina san ganinki a office "cikin dakiyar murya tace "to koda ya tafi ya ɗauka zata taso nan da nan inaa taƙi tasowa har sai da Khadija tace " ba girmaki bane ki tashi man ki tafi da adu'a a bakinki kinji ?" tom Aisha tace " ta miƙe jiki a sanyaye ta nufi office ko da taje ta samesa zaune yake kan kujera ya tura mata jujera da ƙafa , Aisha ce tace "ba zama zanyi ba , kizaunaa....ya daka mata tsawa a razane bai lura ba ta fice da gudu , Khadija ce ta nufota tana cewa "menene zai kasheni ki kaini gida Khadija , rungumeta Khadija tayi kana tace "haba Aisha maiyasa kike haka ko yayi miki wani abinne ?" a'a Aisha tace " tana ware ido , zake Khadija tayi kana ta ruga da gudu taje office ɗin da Khamis yake shiga in yazo , kafin ta shiga ta saita nutsuwarta kana ta shiga , samun malamin tayi zaune a kan kujera da jarida a hanunsa , durƙusawa tayi ta gaishesa kana tace " malam dan Allah ka kiramin yayana dan girman Allah , a nitse malamin yace " me zakiyi masa ?" babu komai jiya nayi mafarki ne shine nakeson inji yana lpy ?" Aisha ta ƙarashe maganar a marai raice , ɗaga waya malamin yayi ya kira number Khamis cikin sa'a ta shiga yana ɗagawa ya miƙawa Aisha , karɓa tayi tare da rugawa waje da gudu sbda gudun kar malamin yaji abinda zata faɗa , lungu ta samu tace "hello yaya "ina jinki Aisha yi magana Khamis ya faɗa" walh yaya ratuwata nacikin matsala wani ya sani a gaba a cikin makarantar nan wai sai dai inbashi kai na whattt....Khamis ya faɗa tare da kashe waya ya miƙe , Ammi dake zaune tace " lafiya kuwa son , Ammi zanje in ɗauko Aisha walh ta gama karatu gaskiya kinga irin abin ko Ammi ?"Khamis ya faɗa yana janyo keys ɗin motarsa , janyoshi Ammi tayi kana tace " to zauna man kayimin bayani "yama kasa gaya mata komai sai da ta matsa sosai ne yace " mata wani ne ya keson lalata rayuwar Aisha ,a tsorace Ammi ta miƙe kana tace "Ai maganar barin ta makaranta bata taso ba , ayi wa malaman magana kawai . Inaaa Khamis yace " yana girgiza ka kana yace " Ammi kiyi min haƙuri wanan karon banbi son ranki ba nasani da tafiya jiya nace makarantar gashi yau ta kirani tana kuka kuma insha Allah yauma zan koma amma dirver zai kaini kiyimin adu'a Ammi na pls ,ya haɗe hannayensa guri ɗaya . Ammi tasan inhar Aisha tabar makaaranta a wanan time ɗin to ta gama kenan dan bazata kuma yiba babu inda ta iya kamar yadda yake jin maganar ta da kuma kawo mata damuwarsa yasa ta cewa "Allah ya kiyaye hanya son "amen ya Allah yace "tare da ficewa yana fita driver yazo da gudu ya durƙusa tare da cewa "mai gida za'a kaika ne ?"eh Khamis yace "kano zamu tafi yi sauri , driver ne yace "a shirye nake muje ya buɗewa Khamis mota Khamis na shiga suka ɗauki hanya , tafiya suke amma Khamis na ganin kamar basa sauri ,dakatar da drivern yayi yace " sauko ni zanyi driving yana shiga mazaunin driver , shikuma driver ya zauna a gurin da ya tashi wani mahaukacin gudu ya fara kamar zasu tashi sama a titi ikon Allah ne ya kawosu Kano bai gama farinciki ba sai da ya gansa a bakin get ɗin makarantar a waje ya bar motar tare da driver shi kuma ya fice , kai tsaye office ɗin wanan malamin ya nufa wanda Aisha ta ari wayarsa , ya sameshi a zaune bayan sun gaisa ne Khamis yace " bakuda tsaro a makaranta tabbas yau zan cire ƙanwata ko ku yarda ko karku yarda zan tafi da ita da rayuwarta ta salwanta , yana fita cikin zafin rai ya hango Khadija ta fito daga wani aji , kira ya ƙwala mata kana yace "inason ganin Aisha bayan sun gaisa , tom tace " amma Aisha na ɗaki tana kuka nayi nayi ta gayamin damuwarta taƙi , da sauri ya shiga ɗakin da Khadija ta nuna masa ya hangota ta ƙudundune tana ta kuka ,my Esha Khamis ya faɗa cikin muryar damuwa maza haɗa kayanki mu tafi gara kibar makarantar ya faɗa yana cewa "tayi sauri , cikin mamaki Aisha tace" yaya kaine ta miƙe ta har haɗa kayan zata ɗibi kayan abinci yace "ki barwa Khadija man "Aisha ce ta ƙwalawa Khadija kira bayan Khadija tazo ta miƙa mata ragowar kayan abincinta sunada yawa , godiya Khadija ta dinga yiwa Aisha tana jin Aisha tace " ai tafiya zasuyi ta fashe da kuka sai da tayi mai isarta ta rakasu mota , kuɗi Khamis ya bawa Khaɗija dubu ɗaya tayi masa godiya suka wuce ,kaf malamai sai da suka fito amma babu mai magana kasancewar sun san ko waye shi , yanzun ma driver ne yaja su suka ɗauki hanya , sai da taga sun shiga wani gari sanan ta share fuskarta ta kalli fuskar Khamis taga yana kallon gefe , cikin zuciyarta tace " yanzu shikenan bazan kula samari ba "taɓɓ aikuwa duk wanda ya kulani zan kulasa taji gaba da zancen zuci ,taɓo hanunta da taji anyi ne ya sanyata zare ido alamar tayi shiru yayi mata da hannu ya juya da ita kana ya kwantar da ita kanta a kan cinyarsa yana mammatsa hanunta a hankali , ashe dama bacci take ji nan da nan tayi bacci , bata san har sun kawo KD ba , kai tsaye anguwarsu Khamis suka nufa horn driver yayi mai gadi ya buɗe get , suna shiga driver yayi parking tare da zagayowa ya buɗewa Khamis a kafaɗa ya rungumota kamar baby ma'aikatan gidan nata kallonsa sunata mamakin girman Aisha babu wuya , kai tsaye part ɗin Ammi ya wuce da ita dama tunda ta girma ko tazo a part ɗin Ammi take kwana , kwantar da ita yayi a kan kujera kana ya tafi bedroom ɗin Ammi , nockinh ya fara kana ya tsaya tare da jingina a jikin bango buɗewa Ammi tayi kana tace " har kun iso ? Eh Khamis yace "yana murmishi , fitowa Ammi tayi tana yiwa Aisha sannu da zuwa, ganin tana bacci yasa Ammi kallon Khamis tace "ka tasheta taje ɗaki man zaka barta a nan , ba hakan yaso ba yaso Ammi tace "ya wuce da ita part ɗinsu fuska babu walwalah ya ɗaukeya cak riƙe baki Ammi tayi dan tana mamakin rashin jin kunyarta da bayayi yanzu ko kaɗan , harda iya ɗaukar budurwa , yaje kwantar da ita ta tashi ta zauna tare da cewa "har munzo ne ?gaki a ɗakin Ammi ma "Khamis ya bata amsa , cikin murna tace " barinje dubo mama ƙila tana palo "kamo hanunta yayi ta faɗa kan cinyarsa ta zare ido tare da shirin zubawa da gudu , daɗa kamota yayi ya haɗe bakinsu guri ɗaya tare da matseta a jikinsa sun ɗau lokaci a hakan can kuma ya saketa ta goge bakinta tana cewa "kai ba mijina bane ma , zaro ido yayi kana yace "me kike cewa " wll zakisa ranki ya ɓaci inhar na kuma jin kalar wanam kalmar to bazakiji da daɗi ba , ficewa tayi ta sami Ammi dake zaune zata yiwa Ammi magana sai ga Khamis nan , Ammi ce ta dubesa tace "daga kai mai bacci shine na jika shiru ko ?" sosa kansa yayi kana yace "Ammi labarin abinda ya faru take bani "Aisha na daga gefe ta rufe baki tana zaro ido , to maza tashi ka bamu guri zanyi magana da ɗiyata , Khamis na dariya ya miƙe kana ya fice . juyowa Ammi tayi ta kai kallonta kan Aisha tace "ƴata "Aisha tace "na'am Ammi ce taci gaba da cewa "inason in tunatar dake kinada aure yanzu ko kin sani ?"eh mama Aisha ta faɗa tana kallon Ammi ta sunkuyar da kai "son mijinki ne kuma ni ki ɗaukeni a matsayin uwa ba suruka ba kinji ?" eh Aisha ta faɗa tare da share hawayen fuskarta. [03/09, 2:08 pm] Mom Islam Ce 💃: 47 & 48 Ammi ta ci gaba da cewa "zan kula dake kamar inda zan kula da ɗan cikina ina fata kin ɗaukeni a matsayin mamanki ? eh Aisha tace good Ammi ta faɗa , zo muje bedroom Ammi tace "tare da riƙo hanun Aisha "binta Aisha tayi suna shiga Ammi ta zaunar da ita kan kujera ta ɗauko cup da cokali ta ɗibo wani garin magani da zuma ta bata ta shanye ta kuma ɗibo wani garin maganin ta haɗa mata da madara ta bata babu musu tasha , wani kwano Ammi ta buɗe da yake ɗauke da farfesun kaji sai tashin ƙamshi take amma jikinta duk magani , haka Ammi tace "sai ta cinye naman nan tsaf ai masoyayyarsa ce " shima babu musu ta fara ci tana gyatsa kasancewar taci abinci daga zuwanta tace "mama zuwa anjima zan ƙarasa na ƙoshi "to Ammi tace "ta rufe kwanon tace zan baki wasu turaruka inhar kikayi sallahar isha'i ki dinga shafawa a fuskarki kinji ?"to Aisha tace " kana Ammi tace " jeki kokuma zo babu gama ba , gobe insha Allah zaki koma ɗakinki banason ƙazanta duk da nasan ba halinki bane kuma ki iya magana kinga iya magana da sanyaya murya tana ƙoƙarin sanyawa mai gida yaji yana ƙara sonki ,ki iya tafiya da zarar kinga yana kallonki sauya salon tafiyarki kuna haɗa ido kiyi masa murmishi ,ki rage kunya bance ki zamo mara kunya ba inason inga kin yi fice kema kin zamo tauraruwa kin kawar da ƴan matan dake yi masa layi , dariya Aisha tasa kana tace "mama kenan "cikin gasgatawa Ammi tace "tom shi kenan "in kikayi wasa wata seta ƙwace miki mijin wlh ,dai daita nutsuwarta Aisha tace " tunda Ammi tace "ta cire kunya to bari tayi mata wata tambayar "Aisha ce tace "mama dama inason yi miki tambaya ne ?" ok ina jinki "Ammi tace "Aisha ce tace mama dama yaya ne yake riƙe min hannu kuma a islamiya ance babu kyau , bugar goshinta Ammi tayi kana tace "duk faɗan da nayi miki bai shiga jikinki ba kenan ?"da wane yare zan faɗa miki ne ?"kiyi haƙuri mama Aisha tace " da alamun damuwa " no ba zancen haƙuri bane amma zuwa gaba zan faɗa miki jeki kuma ban amince zuwanki gurinsa yau ba Ammi ta faɗa tana kallonta koda ya kiraki kice nace "karki fita ,to Aisha tace "jikinta a sanyaye ta fita , Ammi na zaune a bakin gado tace "wato wanan yarinyar akwai aiki na lura har yanzu ƙuruciya na yawo a kanta hhmm Ammi ta nisa kana ta miƙe ta nufi kitchen , samun baba tayi har ta gama aiyuka sannu Ammi tayi mata kana tace " tafasa min wanan maza pls , cikin ladabi baba ta karɓa tasa a tukunya ta kunna gas tasa ruwan da Ammi ta umarceta , bayan Ammi ta koma bedroom ɗinta ta zauna tana wasu tunani barkatai. Washe gari mama suka shirya zuwa gidan su Aisha tare da kai mata ragowar akwatunanta malam ne yaba mama dubu biyu yace "ta shiga kasuwar nan anguwar ta siyowa Ammi lalle tunda sunga ƙafarta baya rabuwa da lalle da kuma citta da kaninfari ,bayan mama tayi masa godiya taje ta siyo , tana dawowa suka tari mashina suka wuce , basu sha wuya ba gurin samun gidan kasancewae mai gidan ba ɓoyayye bane duk da anguwar ta masu kuɗi ce ,mai sun sallami masu mashin sum sauka suka fara bubuga gidan suna ƙwaɗa sallama , cikin sauri mai gadi ya buɗe ƙaramar ƙofar kana yace "wa kuke nema ?"maman Ummi ce tace "nan ne gidan su Aisha ?"eh mai gadi yace " to barin isarwa masu gidan ya rufe ƙofar tare da komawa cikin gidan ,mama da ta gaji da tsayuwa tace "nifa shi yasa ban fiye san zuwa gidan masu get ɗinnan ba sai an dinga jawa mutane rai kafin a barsu su wuce mtsw, ba'a ɗau lokaci ba sai gashi yadawo yace "nace su maman Aisha kukace ko ?" eh suka amsa Aisha ce ta fito mai gadi ya durƙusa yace "Allah ya temaki amarya , ko kallonsa batayi ba ta buɗe get ɗin tare da kururuwar murna ta rungume su mama da maman Ummi tace "ku shigo , mama ma kanta taga saurin girman Aisha cikin fara'a suka bi bayanta ta shiga dasu cikin gidan kai tsaye palo ta kaisu nanfa kallo ya koma sama Allah yayi temako palon babu kowa , maman Ummi sai kallon kwaliyar dake malale a saman take tana jinjina kai mama ko bata tsaya kallo ba sbda karta nuna ƙyauyan cinta a gefe , dawowar Aisha daga kiran Ammi yasa maman Ummi kallon Aisha tace "ƴata ta girma , durƙusawa Aisha tayi ta gaishe su bayan sun gaisa ne Ammi ta fito zama tayi tana faɗaɗa fara 'arta suka gaisa bayan sun gaisa sai ga baba da plet plet na abinci har huɗu ta jere a gabansu da drinks da ruwan gora kana ta gaishe su , mai gadi da dirver da mai bawa flawa ruwa da mai kula da masu share share ne suka shigo da akwatunab da su mama suka zo dashi , masha Allah Ammi tace " nan suka ɗan taɓa hira mama taba Ammi kayan data siyo mata , godiya Ammi tayi kana tace "kuzo muje kuga part ɗin ƴata "dariya su mama sukasa kana suka miƙe , tafe suke suna kale kale har suka iso sashen Aishan da sallama suka shiga suka fara bin ɗakin da kallo wani farinciki da iskar ni 'ima ce ta fara ƙaɗa mama tana mai jin daɗin inda suka ɗauki Aisha kamar ƴarta gashi ta shigo cikin gata ɗakinta kamar na wata sarauniyar , sai da Ammi ta rakasu ko ina na gidan kana suka fito suka dawo part ɗin Ammi sukaci gaba da yi mata godiya da sanya albarka kasancewar basuda abinda zasu biyata komai muhimmancinsa , sosai Ammi taji daɗi da hakan Aisha kam baki yaƙi rufuwa gata gasu mama ,sai murna take cikin zumuɗi tace "da fa gobe zanzo amma tunda kunzo sai sati mai zuwa zanje harda gidan su yaya , Allah ya kaimu su mama da Ammi suka faɗa , maman Ummi ce tace "in kinzo kwa haɗu da Ummi dan ta dawo gida "cikin murna Aisha tace "ai kuwa , miƙewa Ammi tayi ta basu guri kunsan ance tsakanin ɗa da mahaifi sai Allah ta koma bedroom ɗinta tana ƙara tuno adu'oin da su mama suka dinga yi mata tare da godiya , haƙiƙa taji daɗin wanan abu . Mama ce ta dubi Aisha kana tace " Aisha ki riƙe baiwar Allahan nan tsakani da Allah dan a halin yanzu bakida kamarta ko mijinki ne ya ɓata miki rai karki sake ki nuna mata bare ki faɗa mata , ki zamo mai ɓoye sirrin mijinki haka kuma karki dinga yi masa gatsali dan zata iya dena yi miki duk wasu abubuwa , ki nunawa mijinki so na tsakani da Allah yin hakan zai sa ki sami gurbi a zuciyarta , bayan haka ki zamo mai tsafta duk da kunada ƴar aiki kena ki dinga taɓuka wani abin karkice dole sai ita , kuma kar ya zamo kina bada wanki harda wandon mijinki gajere da ƴar shimi lol ki cire ƙiuya ki wankesu lada zaki samu , banda faɗar maganar da bata dace ba banda rashin tausa murya banda ganin kayansa kice ai bai san dasu ba ki ɗauka ko ki kyautar wanan ba hali mai kyau bane tun wuri ki yi hankali yanzu fa kin girma ibada zaki fara wato neman aljannar ki inkinbi waɗan nan hanyoyin zaki sameta cikin sauƙi, Aisha na zubarda hawaye tace ,ɗazu mama tayimin faɗa sosai har ta bani wani abu ta haɗa da madara da kuma wanda ta haɗa da zuma da kuma kaza amma akwai magani a ciki "murmishi su mama sukayi kana mama tace "nikam bansan da me zan sakawa wanan baiwar Allahan ba wlh mama ta share hawayen fuskarta tace " duk mai son ɗanka ai yana sonka fatana karki watsamin ƙasa a ido kamar inda ta riƙeki tsakani da Allah kema ki riƙe ɗanta da amana , wlh kin gama min komai , ki zamo mai tattalin kayanki ko da yake ku bakwa jin garin amma kidai tattala shima yanada muhimmanci malam yace "a gaisheki , ina amsawa Aisha tace "idanunta sunyi ja alamar tayi kuka ta gaji , to bari mu tafi suka miƙe tare da cewa "Aisha tace "wa Ammi sun wuce , tafiya kiran Ammi tayi bayan tayi sallama Ammi ta buɗe ƙofa tace " wai su mama zasu tafi [03/09, 3:53 pm] Mom Islam Ce 💃: 49 & 50 Fitowa Ammi tayi hanunta riƙe da wata leda mai kyau ta miƙawa Aisha tace "ta kai musu ga sunan tahowa "to Aisha tace "taje ta miƙawa maman Ummj kayan "godiya maman Ummi tayi wa Ammi dake tahowa suka fita Ammi ta kira driver tace "ya kaisu "shiga motar sukayi driver ya ɗaukesu sai anguwar su sunyi tafiya mai ɗan nisa kana suka iso anguwarsu , godiya suka yiwa drivern kowa yayi gidansa , mama na shiga ta samu malam harya gama dafa shinkafa dariya tasa tace "yau ga malam da aikin mata ,snnu da dawowa yayi mata ,a tsakar gida mama ta zauna kana tace "munsha tafiya wlh kuma mun samo abin arziƙi dawowa malam yayi ya zauna kana yace " to masha Allah , mama ce tace "aiko munga Aisha tayi dimir mir abinta har wasu kumatu ta ajiye wlh ,dariya malam yasa yace "Allah mun gode maka daka azurtamu da surikar arziƙi wanan mata tanada halin kirki wlh , suna tsaka da hira maman Ummi ta shigo da ledar da Aisha ta bata ta zauna bayan ta gaishe da malam tace "maman Aisha gafa abin arziƙi "mama ce tace "me muka samu ?"fifito da kayan maman Ummi tayi ledar maggi kala kala har huɗu ga mangyaɗa na gora ga manja roba bibiyu cikin farinciki malam yace "aiko mun gode Allah ya saka mata . Washe gari yau ne Aisha zata koma part ɗinta Ammi ta gama yi mata duk wani shirye shirye da zata yi mata ,tun jiya Khamia yasa aka gyare part ɗin yau kam sai tashin ƙamshi yake kamar yau ta fara shigowa , Ammi da kanta ta kaita part ɗinta tare da dafa kanta ta dinga kwararo mata adu'a ,daganan ta barta ,kasancewar bayan isha'i ne yasa Aisha tashi ta buɗe drower ta ciro kayan baccinta riga da wando gajere iya guwaiwa , mai ruwan pink da hularsa tana da kwaliyar wani farin stone a gaba , kwanciya tayi bayan ta ɗauro alwalah tayi adu'ar bacci ta kwanta , ƙarfe tara dai dai Khamis ya shigo hanunsa ɗauke da kaza leda biyu yasa ɗaya a fridge ya shiga part ɗinta da ɗaya da sallama ya shiga kasancewar ƙofar a buɗe take ya shige , samunta yayi har tayi bacci ya zauna tare da ƙarewa kyakkyawar fuskarta kallo ya ɗau lokaci mai tsayi yana kallonta daga ƙarshe ya miƙe ya nufi bedroom ɗinsa ya sauya kaya i zuwa na bacci ya dawo ɗakinta ya kwanta gefenta tare da rungumeta yaja musu blanket asbha ta gari. Bayan malam sun gama magana da baban Ummi akan Ummi mahaifin nata yace "ai ƴarshi ce malam kaima mai aurar da ita ne ,godiya malam yayi suka yake sadaki malam yace "insha Allah zan sanar masa , cikin sa'a zuwa yamma sai ga yaya Zakari ya shigo da malam ya sanar masa murna kamar me yace "tafe nake da kuɗina malam ba tun yanzu nake tarasu ba , mamaki ne ya kama malam yace "wato ni yanzu kama dena jin kunyata ko ?"dariya yaya Zakari yayi yana sosa kai wata leda ya janyo ya miƙawa malam kana yace "dubu ɗari ne malam zaro ido malam yayi yace "a kai musu duka ?"eh malam insha Allah har kuɗin da za'ayi hidimar komai baza'a rasa ba insha Allah "to malam yace "ya karɓi kuɗin da bismillah . Washe gari komai ya kammalah an yanke biki saura wata biyu , murna gurin mama abin ba sauƙi a cewarta tayi surukar kirki masha Allah . Yau da dddaddare yaya Zakari ya dawo daga gidan su mama ya shiga ɗakin anty Fiddausi kasancewar kaka har tayi bacci yana shiga ya sami anti Fiddausi ta haɗe cikin gajeran wando bai ƙarasa cinyarta ba tasa riga iya cibiya ,yana shiga da sallama taje ta runfumesa cikin farinciki ya riƙe mata hannu tare da shafo gefen fuskarta yace "ya kike da fatan kin wuni cikin farinciki , a ƙasan zuciyarsa kuma yana tunanin inda zai fara yi mata magana , hardai ya kare yace "muje mu zauna inasan magana dake "cike da murmishi tace "to gani zo muje hannunta ya riƙe ya zaunar da ita kana ya fara shafa sumar kanta a hankali ya dawo fuska yana yawo da hanunsa a jikinta har wani lumshe ido take tana cewa " yau da wani salon kazo ?"naganka cikin cikin shauƙi "lumshe idonsa yaya Zakari yayi kana yace "komai naki birgeni yake , a ƙasan zuciyarsa kuwa cewa "yake nakasa sanar mata da abinda ke cikin zuciyata wayo Allah na ,tallafo kansa tayi ta haɗe bakinsu guri ɗaya ta fara rikitashi da kisess masu zafi jin haka yasa yaya Zakari cewa " fiddausi nitsu muyi magana idonsa a lumshe zama tayi ta nitsu kana tace "ina jinka " aure nake san ƙarawa badan in cuceki ba sai dan ki sami matemakiya kuma ƴar uwa shiyasa , bayan haka karki ɗauka zanyi ne da nufin na wulaƙanta ki, bawai dan bana sanki ba ya ƙarashe maganar da bata haƙuri "sai da ta bari ya gama zubar surutunsa sanan ta fincike jikinta daga rungumar da yayi mata lokacin da zai fara magana ta ɗauki cup ɗin dake kusa da ita ta jefeshi dashi ta ɗauki ta duk wani abu dake kusa da ita ta dinga wurga masa tana kuka kana tace "nayi dana sanin haɗuwata da kai wlh wanan wace irin rayuwa ce ?"wlh bazan yarda ba ai dan ni kaɗai akayi gidannan badan ni ba bazakayi ginin ba ta dinga masifa tana ƙarawa , zata buga masa dutsen guga ya fice da gudu ya koma ɗakinsa ya rufo ƙofa yana dana sanin gaya mata abinda ya faɗa tare da kiran innalilahi wai dama haka mata suke inko haka suke sun shiga uku dan akan kishi , yaci gaba da maganar yana mamaki , da gudu ta nufo ɗakinsa tana kururuwa ta shiga bubuga ƙofar tana cewa "wlh ka buɗe ko in ɓalla ƙofar yau kaima sai kayi kwanan baƙinciki kamar yadda ka sani nayi taci gaba da ihu , Shidai yana zaune a takure takaici ya ishesa . Washe gari da asbha Khamis ya tashi Aisha yin sallah salai tayi ta sauko daga gadon ta shiga toilet tayi alwalah ta fito shi lokacin ya wuce masallaci , bayan tayi sallah ne ta ninke sallahyar ta cire kayanta ta shiga wanka , tana fitowa ta shafe jikinta da mayuka masu ƙamshi kana ta shafa powder simple make up tayi kana tazo sauya kaya tayi zigidir tana duba kaya sai ga Khamis nan ya shigo ,a kunyace ta shige cikin drower kamar biri ta rufo kofar ta kulle ta ciki kasancewae drower tanada zurfi sosai , murmishi yayi mai sauti kana yace "my Esha kenan Allah ya barmu tare "ya juya ya fice, yana fita ta fito tana zare ido kana tace "oh na shiga uku nikam bazan iya haɗa ido da yaya ba wlh kalan yace "iskanci ne ya sani yin hakan taci gaba da surutunta tana dariya , doguwar riga ta ciro ja mai adon farin duwatsu masu ƙyali tayi rolling ɗankwalin a kanta kana ta buɗe akwatin sarƙa da ɗan kunne ta zaɓi farar sarƙa itama mai kwaliyar duwatsu farare ta sanya ta zauna tana tsoron fita ,turare ta ɗauko ta feshe ko ina na jikinta dashi nan da nan ta ɗau ƙamshi mai rikitarwa, tsayuwa tayi jikin mudubi ta kalli kanta ta juya tana farr da ido sai ta tuno faɗan da Ammi tayi mata na sauya tafiya , yanga ta fara tana yarfe hannu sai ga Khamis nan ya shigo bata sani ba , harɗe hannayensa yayi ya tsaya daga bakin ƙofa yanata kallonta , ta taho da gudu idonta a rufe ya caraf rungumeta yana murmishi ,zaro ido tayi batayi magana ba amma taji kunya shima bai yi maganar ba yana ta murmishi ya waye wanan ta fara faɗa kuma tasan ko waye ƙin yin yin magana yayi a karo na biyu yana tafiya da ita a hankali a hankali dan Allah koma waye ya sakeni bada niyya nayi ba pls ta haɗe hannayenta idonta a rufe sai da suka kai kan bed ya kwantar da ita tare da cewa "mijinki ne . END END ALHAMDULILH ALLAH NA GODE MAKA DAKA BANI IKON KAMMALA BOOK 2 Kura kuran dake ciki Allaj ka yafe mana Allah ka karemu daga dukkan sharri Allah ka tabbatar mana da alkairi a rayuwar mu alhmdulilh Mu haɗu a book 3 08141799224.