🍃 *DANGIN UBA*🍃 Story & Written By Milhart Na zo muku da littafi Mai ban tausayi,cike da abun al'ajabi,wannan salon na daban ne. *🌍MANAZARTA* *WRITERS ASSOCIATION📚🖊* *M. W. A* *Wannan labarin kirkirarren labarine ban yarda a chanza min labari ba Wanda ya chanza bamu yafe ba.* Ina alfahari da rubutu,sabida alkalami yafi takobi🗡️🗡️🗡️ *BISMILLAHIR RAHAMANIN RAHIM* Page 1 and 2 Haisam shine kad'ai d'a a gun Mahaifiyar sa Wacce ta kasance talaka, Mahaifin sa ya rasu tun Haisam na 'dan shekara biyu a duniya.Mahaifin sa mai kud'i ne sosai shiyasa wasu daga cikin yan uwan sa suke bakin Ciki. Duk da ya kasance Mai taimakon mutane sosai ga duk Wanda yake neman taimako daga gareshi, hakan bai Hana Yan uwansa Shirin kashe shi ba sabida su mallaki dukiyar sa. Da sun so shi sabida shine kad'ai Wanda Allah Albarka ce shi da d'a na miji. A Haka, wani daga cikin su ya sa mishi guba a abinci. Mahaifin Haisam yayi duk abinda yaga zai iya don ya ceci ransa daga guban Amma ya Riga ya Masa illa a jikin sa. Bayan rashin lafiya na watanni biyu sai ya rasu, Amma Kan ya rasu ya bawa matar sa wasiya akan ta tabbar ta ilmantar da Haisam Boko da addini komin tsadan sa. Bayan wata d'aya da rasuwar sa, wannan d'an uwan sa da yasa Masa guba yazo ya kwace dukkanin dukiyar, ya bar su ba ko sisin da za su rike. Rayuwa duk ta lalace wa Haisam da mahaifiyar sa, da kyar suke samun abinda zasu sa a cikin su, Amma duk da wahalan da suke Sha Bai Hana ta sa shi a makaranta Mai kyau ba, sabida shine wasiyar Mahaifin sa. Haisam yaro ne Mai kokari a makaranta, ya kasance shine yake zuwa na d'aya a cikin shekaru uku da yayi a junior secondary School, tunda da ga Nan ya kafa record. Ya cigaba da kokarin da ya Saba har ya Shiga senior secondary School. A yanzu Yana aji SS3 babban matsalar sa shine inda zai sami kud'in registration na W. A. E. C. MAKARANTA A ko da yaushe Haisam na Zama shi kadai, baya kula kowa harkan gaban sa kawaii yake yi sannan bashi da abokai, Duk da ya kasance Yan ajinsu sukan Zo gun sa don ya ganar dasu darasussukan da ya shige musu duhu ko basu gane ba, Yana da kirki sosai ga ilimi sannnan a shirye yake da ya ga ya taimaka musu, wata Rana a aji, darasin English ake musu, Haisam na zaune kusa da Ma'isha wacce ta kasance sabuwar zuwa ce a makarantar tasu, Ma'isha yarinyar kirkice daga gidan masu kudi, Bai dad'e da aka zabi Mahaifin ta a matsayin chariman na karamar hukumar su ba. A Lokacin da ake darasi malamar su Tace "Who can define phrase?" Duk Wanda suka amsa ba dai dai ba aka sa su kneel down. Haisam ya San amsan Kuma ya lura da Ma'isha na tsoro sabida bata San amsar ba, yayi saurin rubuta amsar a paper ya Mika mata. Nan take Ma'isha ta karb'a, malamar ta juyo gareta Tace "Ma'isha Mus'ab Aminu, answer the question, what is a phrase?" Ma'isha mikewa tayi ta tsotsa keyan ta wasu daga cikin Yan ajin suka shiga yi mata dariya a ganin su baza ta iya bada amsar Amsar ba "A phrase is a group of words that does not contain a finite verb and cannot stand alone to make a complete sentence" ta bada amsar cikin hikima da basira, malamar Tace " Excellent, class give her a round of applause." bayan sun fita break cikin sauri ta sayi biscuits da soft drink wa Haisam. "Hy Haisam, I want to thank you for your kind heartedness. You really saved me from the teacher's punishment and embarrassment." Ma'isha ke Wannan maganar. "You are welcome"kawai yace mata "Please take this snacks for my appreciation" Murmushi yayi yace "No thanks, no need for these really" Cikin murya kamar zatayi kuka Tace "But please am trying to show my appreciation, Dan Allah ka karb'a" " Na sani I don't think I need it, ko da yake ban ga dalili da zaisa ki dami Kanki ba" " Ban damu ba, ni dai Dan Allah ka karb'a Dan Allah, idan baka karb'a ba bazanji dad'i ba". Musaddiq, da tun dazu yake kallon su ya matso kusa yace "He does not want it, is it by force? Ko da yake, ni ina bukata bari na taimaka masa. " Haisam da Ma'isha hararar sa sukayi Rai a 'bace, ganin hakan yasa yayi saurin barin wajen, Haisam karb'a yayi sannan ya mata godiya, Ma'isha ba karamin farin ciki tayi da hakan ba. "Na sani dama ka na jin yunwa, but you're just pretending" ta yi maganar a sigar tsokana. Yace " Kul, ki iya bakin ki",hakan yasa ta bar zancen. Haisam na ci suna Hira suka gabatar da Kan su wa juna ba dad'e wa aka tashe su, wasu iyaye na zuwa d'aukan 'ya 'yan su, Driver a ka turo ya Zo d'aukan Ma'isha, Haisam na daga cikin yaran da, da kafa suke zuwa makaranta sannan su Koma da kafa, A Lokacin da Ma'isha ta ganshi ta umurci driver da ya tsaya Tace "Haisam ban San sanda ka tafi ba, Amma ka shigo mota , mu ajiye ka gida." "A a nagode, hanyata da Taki ba d'aya bace, Kuma na ma kusa Isa gidan namu baida Nisa da Nan" " Kar ka damu zamu Kai ka, komin kankancin nisan gidan naku" ganin tana neman takura shi, yayi tafiyar sa. Suman tsaye tayi tana bin shi da kallo, tana mamaki "wai shin Haisam wani irin mutumne haka?" A zuciyarta ta ayyana hakan, d'aga kafad'a tayi ta shige mota, d'aliban da suke gun Wanda suka ga abinda ya faru suna cewa ina ma ace sune Haisam, idan suka samu wannan damar baza su bari ya wuce su ba. Bayan ya Isa gida ya tarar babu abinci a gidan nasu kamar kullum, uniform d'insa ya cire sannan ya nufi kasuwa don ya taimakawa mahaifiyar sa, Koko take yi da kosai dashi suke rufa wa kansu asiri, Bredi ta saya Masa, had'awa yayi da kosai yaci Shine abincin ranar nasa. Da yamma, Kosai da doya ya d'auka a Tray ya fara talla a bakin titi, Yana cikin tallan ne ya hango wata mota kamar wacce aka Zo d'aukan Ma'isha da shi d'azu yayi saurin 'buya a bayan wani shago yana kallon motar ga mamakin sa sai yaga Ma'isha ce da mahaifiyar ta, sun Zo sayayya a kasuwar gwari. Kasa motsi yayi don baya son Ma'isha ta ganshi yana tallan Kosai a bakin titi, Ma'isha da mahaifiyar ta sun d'auki lokaci sosai Wanda hakan yasa shi kasa sakin jikinsa, Wani mutumi Wanda ya kasance kullum sai ya saya kosai da doya a gunsa ya hango shi ya shiga kiransa sunan sa Amma Haisam yayi burus kamar bai jishi ba,sabida idan yaje Ma'isha zata iya ganin sa. "Ka kyale ni don ni ba zuwa zanyi ba,gara ma kayi Shiru " zancen zuci yake. Mutumin ya zago ta bayan sa,dafe shi yayi a kafad'a yace "Haisam lafiya kuwa? Ko Kuma ka kurmance ne?" "Eemm... kiyi hakuri nayi nisa ne a tunani" "Mene haka da har yafi kasuwancin ka muhimmanci? Ko da yake kosai zaka bani na naira saba'in sai doya na talatin" ba musu ya sauke tray din ya sa a bakin leda ya mika masa. Bayan Ma'isha da mahaifiyar ta sun gama sayayyar da zasu yi a Lokacin gari har ya fara duhu, hakan yasa bai sayar da kosan ba, hakan yasa yaji duk ransa a 'bace. A hanyar sa ta komawa shagon su ya hango Ma'isha da mahaifiyar ta na sayan kosai a gun Mahaifiyar sa. Iska mai zafi ya hura ya kuma neman wuri ya 'buya. " Wai meyasa mutanen Nan suke bina duk inda naje? Hmm Allah yasa ba kullum zasu Rika zuwa Nan wurin ba, mutuncina da Ma'isha take gani zai zube" ya fad'a a bayyane. Sai da ya jira suka tafi sannan ya Koma shagon, Mahaifiyar sa tayi matukar mamaki da ganin bai sayar da kosan ba. Comments and share 🍃 *DANGIN UBA*🍃 Story & Written By Milhaart Na zo muku da littafi Mai ban tausayi,cike da abun al'ajabi,wannan salon na daban ne. *🌍MANAZARTA* *WRITERS ASSOCIATION📚🖊* *M. W. A* ```Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.🤙🏻``` https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa ____________________________________ *Wannan labarin kirkirarren labarine ban yarda a chanza min labari ba Wanda ya chanza bamu yafe ba.* Ina alfahari da rubutu,sabida alkalami yafi takobi🗡️🗡️🗡️ *BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM* Page 3 and 4 Da sassafe, Haisam ya shirya don zuwa tallan Kosai Kan yaje makaranta, yana kokari yaga ya had'a kud'in w.a.e.c d'insa , Amma Kan ya dawo daga talla lokacin zuwa makaranta har ya kure, a ranar ya shigo school a makare ya tarar ansa wa anda sukayi letti shara, bayan sun gama yayi saurin shiga aji yana had'a zufa, cikin rashin sa'a ya tarar da malamin Mathematics d'insu a aji yace "Haisam Ahmad Umar, Why are you late to school and why are you sweating like a Christmas goat?" Yan ajin suka shiga dariya Ma'isha ce kad'ai batayi dariya ba don ita bata ga abin dariya anan ba, Haisam shiru yayi baice komai ba, sabida bai San me zaice Masa ba hannu ya Masa alamun ya shigo. Lokacin break, Ma'isha da kawayenta suka nufo inda yake, suna rokon sa akan ya Kara musu bayani akan darasin da akayi dazu da safe, ya na cikin koya musu kwasam wayar Haneef ya soma ringing, Afnan 'daya daga cikin kawayen Ma'isha Tace "Haneef meyasa kake kokarin distracting din mu? " " How am I distracting you, wannan ba Lokacin break bane?" Cikin 'bacin Rai Ma'isha tace " Na lura kana da neman magana Haneef, Mr trouble" Haneef mikewa yayi ya ture Ma'isha ta buge kanta a bango, Haisam ransa yayi mugun 'baci bai tsaya wata wata ba ya tsinke shi da mari, fad'a Mai Karfi ya parke a tsakanin su d'aya daga cikin d'aliban ya Kai karar su gun Form master din su. Zane su yayi sosai kana yasa su yanka ciyawa, Ma'isha da kawayenta suka Zo da niyar taimakawa Haisam, Amma yaki yace su taimakawa Haneef sabida shi aka bawa wurin noman dayawa sabida shine silar fad'an Ma'isha Tace "A'a baza mu taimaka Masa ba, shi ya jawo wa kansa jiki magayi, yaron yana da matsala sosai" " Ma'isha ba a Rama mugun ta da mugunta, da babu Wanda zai tuba ya gyara laifin sa, Dan Allah kuje ku taimaka Masa" " okay , zamu taimaka Masa Amma da sharad'i" " What? " " Sai dai idan zaka Bari driver na ya ajiye ka a gida" "Inaa bazaiyu ba, I won't, I can't, can't you see that my uniform is very dirty? " Afnan tace " that's even more you should allow her to take you home, bai kamata ka tafi acikin kaya Masu ditti haka ba" "Okay, agreed, na amince" Ma'isha da kawayenta sunji dad'i sosai, yanda Haisam yace sukayi hakan sukayi suka taimakawa Haneef, abin ya bashi mamaki sosai, bayan sun gama yaje ya bawa Haisam hakuri, Haneef yace "am awfully sorry for everything, Dan Allah kuyi hakuri, all of you should forgive For all the trouble I caused, Dan Allah ku barb'e ni a matsayin aboki" girgiza Kai Haisam yayi yace "Kar ka damu komai ya wuce" Ma'isha zuwa tayi ta sayo musu ruwan sanyi duk suka Sha sannan suka koma aji.. Bayan an tashe su, Ma'isha babu inda bata duba ba Amma bata ga Haisam ba, taji ba dad'i, shigewa tayi mota ta wuce gida, bayan ta bar gun ya fito ya fashe da dariya "Hahaha come and take me home Mana, so kike kije Kiga gidan mu don ki gane cewar mu talakawa ne, inaa bazaiyu ba" sai da ya tabbatar Ma'isha sunyi nisa da barin gun, kana ya fito ya wuce gida. WASHE GARI Ma'isha na Isa school ta tinkare shi "Na tabbata kana sane kake guje min, But Haisam, meyasa kake guje min? Why are you hurting me like this? Bani da kowa shiyasa nake so ka zame min d'an uwa kwalli d'aya, please stop avoiding me Dan Allah." "Am sorry,kiyi hakuri, forgive me please" " You're forgiven, yau zamu Kai ka gida" "Dan Allah ki bar maganar kaini gida, akwai inda nake zuwa ne Kan na tafi gida" Kan ta bashi amsa principal ya shigo yace "Good Morning class, today is the last day for those who have not paid for thier w.a.e.c fees. starting from tomorrow , personally will be coming to send home any student who comes to school without his or her Money, have I made myself clear?" Duk suka amsa da "Yes Sir" bayan ya fita, Haisam kansa yasa a Kan benci ya shiga tunani mai nisa, har aka tashi bai kula kowa ba tunanin yanda zai samu kud'in ne ke damun sa. "Yaya zanyi?" Zancen zuci yake "mahaifiya ta bata da Kud'in da zata biya min sannan Dangin Ubana Babu Wanda yake da niyar biya min, Ya Allah ka kawo min mafita" Ma'isha Tace "lafiya kuwa? Haven't you paid the money?" Haisam yace "Eem.....Eem.... Eh but I hope to pay soon" baya cikin yana yin magana da kowa. Ana tashi ya Kama hanyar gida shi kad'ai yake tafiyar. Ma'isha ta Shiga damuwa ta rasa abinyi daga bisani ta yanke shawarar bin Haisam. Sai da ta tabbatar driver d'inta bai ganta ba a silale tabi bayan Haisam amma Haisam bai San da cewar tana biye dashi ba, yana isa gida ya Shige, Murmushi tayi tace "Finally, yau nasan gidan su. Sai ta juya ta koma makaranta, driver yayi jiran Duniya bai ganta ba hakan yasa ya koma gida. Ma'isha na zuwa taga wayam ba driver hakan ya tabbatar mata da ya tafi, bata da wani zab'i da ya wuce ta taka da kafa. Kan ta Isa gida mahaifiyarta ta shiga tashin hankali kasantuwar bata tab'a aikata hakan ba, ranta yayi mugun 'baci da driver sabida ya dawo ba tare da Yar ta ba, a tsawace tace "Idan wani Abu ya sami 'yata I'll make sure you spend the rest of you life in jail" Cikina Rawar murya driver yace "Is not my fault Ma, na dubata ta ko ina a makarantar Amma ban ganta ba, sannan bata makarantar don nine mutum na karshe da ya rage a makarantar, Kuma har na bar gun ban ganta ba" "Zaka yimin Shiru a wurin Nan ko Sai na buge maka baki? Kaje ka Nemo min 'yata....." Kan ta karasa maganar da zatayi ta hango Mai gadi ma Bud'e gate,Yana Bud'ewa sai ta ga shigowar Ma'isha, da gudu ta nufi inda take. 🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃 Milhat ce Yar Terawa Please comment and share 🍃 *DANGIN UBA*🍃 Story & Written By Milhaart Na zo muku da littafi Mai ban tausayi,cike da abun al'ajabi,wannan salon na daban ne. *🌍MANAZARTA* *WRITERS ASSOCIATION📚🖊* *M. W. A* ```Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.🤙🏻``` https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa ____________________________________ *Wannan labarin kirkirarren labarine ban yarda a chanza min labari ba Wanda ya chanza bamu yafe ba.* Ina alfahari da rubutu,sabida alkalami yafi takobi🗡️🗡️🗡️ *BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM* Page 5 and 6 WASHE GARI Haisam bai je makaranta ba, hakan ya tadawa Ma'isha Hankali, duk ta rasa sukunin ta a makaranta har aka tashe su. Bayan an tashi musu ta ce wa driver ya kaita gidan su Yar ajin su, ta karb'i assignment ba musu ya amince ta Masa kwatancen gidan ya kaita gidan su Haisam. Haisam karar motar yaji ya tsaya a kofar gidan su hakan ya sashi fitowa don ganin wane ne, ga mamakin sa yaga ma'isha ce. Rai a d'an 'bace yace "me kike yi anan? And how on Earth did you trace my house?" Ma'isha tace "Am I forbidden from coming to your house? Sannan Kai kuma irin salon naka Kenan na karb'an baki?" " Ba haka bane, kawai ban tab'a sammanin ganin ki anan bane anyway you're welcome" "Thanks, meyasa yau bakaje makaranta ba?" Kan ya bata amsa, yaji mahaifiyar sa na tari da gudu ya koma ciki, Ma'isha bin bayan sa tayi, mahaifiyar sa a kwance tana matsanancin zazzab'i. Ma'isha na ganinta ta gane itace matar da ta sayar musu da kosai ranar. Cike da kulawa tace "Me ke damin ta?" "Ban sani ba tun jiya take fama da zazzab'in Nan" "Ka kaita asibiti kuwa?" Shiru yayi ya kasa bata amsar tambayar sai hawayen da yake zubowa daga idanun sa. Kan kace me ita ma ta Fara kuka, ta rasa abinyi hakan yasa ta koma cikin mota tana kuka, driver na ganin tana kuka hankalin sa ya tashi, cikin sauri ya Shiga cikin gidan su Haisam a tunanin sa Haisam ya dake tane, Amma yana ganin mahaifiyar Haisam sai jikinsa yayi sanyi, ya fito ya Maida ta gida. Idanun ta a cike yake faal da hawaye suka Isa gida, mahaifiyar ta na ganin ta hankalin ta ya tashi, a tunanin ta wani abun aka mata, tayi tambayar duniyar Nan taki fad'a Mata daga bisani driver ne ya mata bayanin dalilin kukan nata, tana jin haka ta Shiga rarrashin ta. Tace "Nasan yanda kike ji daughter, Amma Kar ki damu zanyi wa Mahaifin ki magana idan ya dawo, so that we should know how to take your friend's mother to the hospital" ma'isha tayi mutukar farin ciki da jin hakan. Mahaifin ta na dawowa ta Sanar dashi halin da Haisam ke ciki Shi da mahaifiyar sa, ta karasa bashi Labarin cikin kuk,hakika sun bashi tausayi sosai, yace "Karki damu Ma'isha, Babu abinda zai Sami mahaifiyar Haisam, Kuma Kinga gobe Saturday ne Babu inda zanje Kinga gobe da safe sai ki kaimu gidan su Haisam d'in, sai mu kaita Asibiti" "Thanks Dad, Amma meyasa baza mu kaita Asibitin yau ba, ina tsoron Kar wani ya same ta" "Kar ki damu Insha Allah babu abinda zai sameta, Kuma Kinga dare ta Riga tayie, Amma na Miki alkawari gobe da sassafe zamuje." Ma'isha na alfahari da iyayen ta ganin yanda suka d'auki damuwarta tasu ce, tasani tunda yace zasuje to tabbas zasuje d'in amma yanda taga rana Haka taga dare, duk a tsorace take, gani take kamar mahaifiyar Haisam zata iya rasa ranta, Kan gari ya waye ta tashi ta Shiga ban d'aki ta d'auro alwala ta jero raka'a biyu kana ta fara rokon Allah da ya bata Lafiya bayan ta idar ne ta kwanta tana jiran wayewar gari,a Haka bacci 'barawo ya sace ta. Washe gari itace ta Fara tashi duk da ba tayi bacci da wuri ba, jiki na rawa ta gyara gidan tsaf tun kan, Mummy na fita ta rike baki tace "Oh Ma'isha ke da a weekend bacci kike sai nayi da gaske ki tashi yau me ya faru haka?" "Mummy ina so muje gidan su Haisam da wurine shiyasa, Wallahi Mummy da ita na kwana a rai, gani nake kamar wani abu zai sameta" Murmushi tayi tace "Inshallah babu abinda zai sameta, Naga kin gama gyara gidan ma" "Eh Mummy" "Toh yanzu kije ki shirya Ni kuma Zan had'a mana breakfast, Daddyn ki ma ya na wanka" Ta amsa da Toh ta shige d'aki bayan ta gama shiri ta fito ta tarda mummy da Daddy suna karyawa, cikin Ladabi ta gaida su, suka amsa, Ma'isha kasa cin abincin ma tayi, wainar indomie da kwai Mummy tayi sabida zaifi saurin gamawa. Bayan sun gama karyawa suka nufi gidan su Haisam, Haisam na ganin su tsuman tsaye yayi cike da mamaki yake kallon su, Yana ganin mahaifiyar ta ya shaida ta, har kasa ya durkusa ya gaida su, cike da sakin fuska suka amsa, Daddy yace "Yaro ina mahaifiyar ka?" Murya na rawa yace "Tana.....tana.... d'aaaa ki" Murmushi Mummy tayi tace "To ka kaimu mu ganta ko?" Jiki na rawa ya shige d'aki Suma suka Mara Masa baya, Ma'isha kuwa sai Murmushi take har cikin ranta take jin dad'in ganin mahaifiyar Haisam na raye, suna had'a da Haisam kuwa kallon tuhuma yake mata,tana ganin haka sai ta Fara dariya kasa kasa. Banda tari babu abinda mahaifiyar Haisam keyi, cike da tausayi yace "Ki kimsa ta ku fito" hannun Haisam ya riko, sannan ya cewa Ma'isha "Daughter zo mu jira su a mota" ba musu ta bi bayansu,suna isa inda motar take yace haisam ya zauna a gaban motar,shi Kuma ya zauna a gun zaman driver,Ma'isha Kuma tazauna a baya. Bayan mummy ta gama gyara ta, da taimakon Mummy da Ma'isha suka sa Umma a mota, Kai tsaye asibiti suka nufa, likitoci sunyi matukar jajincewa wurin kula da ita hakan yasa acikin Yan kwanaki ta samu sauki kamar ba ita ba. Wata rana Mummy ta kaiwa Umman Haisam ziyara, zaune suke suna Hira zuwa yanzu sun saba sosai, Nan take tambayar ta dalilin da yasa haryanzu bata biya wa haisam Kud'in WAEC ba, Bata 'boye mata ba ta Sanar da ita cewar Mijinta guba aka sa Masa a abinci da yanda kanin sa kwace Masa dukiya, ta tausaya musu sosai, a haka har suka gama hirar tasu ta dawo gida. Cikin dare ta kasa bacci, tashin Daddy tace "Am sorry na katse maka bacci" Zama yayi cikin muryar bacci yace "Kar ki damu,me ya Faru?" Nan ta shugay fad'a Masa Labarin da Umma ta bata, bayan ta gama basa Labarin ne tace "Darling ina so mu taimaka wa haisam da mahaifiyar sa" "Ina sauraron ki" "Me zai Hana tunda Boys Quarters d'in Nan babu kowa aciki a Basu part d'aya su zauna, Naga jikin nata bai gama warwarewa ba, sannan Ina so a biya wa Haisam WAEC" Murmushi yayi ya riko hannun ta yace "Madallah da samun mace kamar ki a rayuwa, tabbas ke d'in rayuwa tace, Maryam Allah ya Miki Albarka, a irin Rayuwar da muke ciki yanzu kowa kansa ya sani Amma ke kullum cikin taimakawa na kasa dake kike" Murmushi tayi Tace "To mijina mene ne amfanin Kud'in namu? Idan baza mu taimakawa na kasa damu ba,Kuma na lura Ma'isha tana so a taimaka musu ne kuma ina matukar son farin cikin ta,nasan idan taji Haisam zai dawo gidan nan kuma taji za a biya Masa WAEC zatayi matukar farin ciki" " Hakane Yar Albarka,Halin ki ta d'auko tana da tausayi sosai,ga son mutane" "Kaji ka da wani zance kai ta d'auko dai" "Zancen kike so,yanzu dai naji dukkanin maganar ki, Kuma zanyi yanda kike ce, Kuma Insha Allah zan rike Haisam tamkar d'ana, da niyata gidan nasu nake so a gyara musu" "A a tun da ga nan Kuma gidan ya mana girma mu kad'ai, su dawo Nan kawai" "To ba matsala, idan Allah ya Kai mu gobe zanje makarantar tasu na biya Masa, sannan ina so kije gidan ki d'auko mahaifiyar Haisam d'in, ban yarda ta 'dauko komai ba, Zan tura miki Dubu d'ari biyu, ki saya mata kaya, idan na nadawo zamu fita da Haisam d'in Shima na Masa sayayya" Farin ciki da Murna yasa ta rungumi mijinta had'e da yi masa godiya, a haka sukayi bacci. Washe Gari Daddy Kan yaje gun aiki ya biya ta makarantar su Haisam ya biya masa Kud'in WAEC harda NECO. Mummy na fad'a wa Ma'isha maganar da suka tattauna Akan Haisam da Umma tayi farin ciki sosai harda tsalle, tayi ta musu godiya da musu addu'a Wanda ya dace d'a yayiwa iyayen sa. Tana Isa school a kusa sit d'in Haisam ta zauna, tunda ta lura shi d'in ba mai son magana bane Hakan yasa sai ya kulata take kulashi. Principal ne ya shigo yana Kiran sunan wa'anda basu biya Kud'in WAEC d'in su ba, ga mamakin Haisam har aka gama ba a kira sunan sa ba, hannu ya d'aga yace "Excuse me sir!!! Yace "Yes" Mikewa yayi yace "I haven't paid and you didn't call my name" Cike da mamaki yace "You didn't pay? What's your name?" "Haisam Ahmad Umar" Ya shiga dubawa Bai ga sunan Haisam ba Yana duba list d'in wa'anda suka biya yaga sunan Haisam yace "Mr Man you already payed" Cike da mamaki yace "I payed? But sir please can you check the date of the payment for me?" "Sure" Yana dubawa ya Maida kallon sa ga Haisam yace "It was payed today"Yana Kai Nan ya sa wa'anda basu biya ba a gaba har Saida ya kai su bakin gate ya jaddada wa Mai gadi Akan Kar ya bari su shigo ya koma ciki. Haisam mamakine ya rufe, a zuciyar sa yake fad'in "Wa ya biya min Kud'in nan?" Da sauri ya d'ago kansa ya kalli Ma'isha ita ma kallon sa take, murya kasa kasa "kin San wani abu Akan haka ko?" Kai ta girgiza Tace "Ni ban sani ba" ta karasa maganar tana rufe bakin ta alamun dariya take son yi. Cikin sanyin murya yace "Ma'isha Please" Tace "Daddy ne ya biya" "Dan Allah dagaske?" "Uhmn gashi ka gani" "Amma....... " Shigowar malamin sune ya Hana shi karasa maganar da yayi niya, suna fita break ya Shiga neman ta bai ganta ba, Murmushi yayi yace "Alhamdulillah Allah na gode maka, yau Dole. Naje gidan su Ma'isha da Umma muyi musu godiya" Ma'isha da tun d'azu take tsaye a bayan sa tayi gyaran murya Tace "Anya zuwa gidan mu zakuyi ko Kuma Zaku koma gidan mu?" "Hmm zuwa Zamuyi dai" "Za dai ku koma gidan mu" "Ban fahimce ki ba?" "zaka fahimta idan driver yazo sannan ko ka gudu zamuje har gida mu d'auko ka" tana kainan ta ruga a guje, Yana Kiran ta Amma ina tayi nisa. _____________________________ Please comment and Share 🙏🏻🙏🏻 Milhat ce Yar Terawa 🍃 *DANGIN UBANA*🍃 Story & Written By Milhaart Na zo muku da littafi Mai ban tausayi,cike da abun al'ajabi,wannan salon na daban ne. *🌍MANAZARTA* *WRITERS ASSOCIATION📚🖊* *M. W. A* ```Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.🤙🏻``` https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa ____________________________________ *Wannan labarin kirkirarren labarine ban yarda a chanza min labari ba Wanda ya chanza bamu yafe ba.* Ina alfahari da rubutu,sabida alkalami yafi takobi🗡️🗡️🗡️ *BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM* Page 7 and 8 Haisam duk a kage yake a tashi sabida shi Sam bai fahimci Ma'sha ba, bayan an tashe su ne ya shiga neman ta, ai kuwa yana hangota da gudun sa ya nufi inda take Tana ganin sa tayi Murmushi, ya "Ma'isha wai me ke faruwane?" Cikin muryar dariya Tace "Ga Nan driver yazo" shiga tayi ya tsaya Yana kallon ta, ganin baida niyar shiga Tace " Haisam come in Mana" Ba musu ya shiga. Bayan ya gaida driver ya Maida kallon sa gare ta, yace "Ma'isha please tell me Mana" Dafe kanta tayi Tace "Ya Salam, Haisam Dan Allah ka kyaleni Idan muka je gidan zaka ga koma mene ne." Gyara Zama yayi yace "Tell me something Ma'isha" "Uhhmnn ina jinka" "idan Kika fada min mutuwa zakiyi ne kome?" "A a ko 'daya baza ka mutu ba" " So tell me" " No I won't." Cikin muryar dariya driver yace "Haisam ga naci, Ma'isha Kuma taurin kai to duk kuyi hakuri in muka koma gidan zakaji Kan zancen" "Hakan na nufin kaima kasan abinda ke Faruwa kenan ko?" "A a ba abinda na sani nikam" Girgiza kai yayi babu Wanda ya furta komai har suka Isa, Kai tsaye parlor suka nufa, Haisam duk ya kasa sakin jikin sa, ganin Umman sa a zaune a gun yasa mamaki ya rufe shi. Cike da mamaki yace "Umma kina kema Nan aka kawo ki?" Murmushi tayi, Mummy tace "Eh Nan aka kawota" Tsosa keya yayi ya durkusa ya gaida su,Daddy dake zaune yayi Murmushi ya amsa ba yabo ba fallasa. Yace "Tashi ka zauna akan kujera" Kai ka sa yace "A a Alhaji Nan ma yayi" Murmushi yayi yace "Haisam wannan umarni ne, ba shawara ba ne ba." Tashi yayi ya zauna gyaran murya yayi yace "Haisam naji tarihin ka, mahaifiyar ka Bata boye Mana komai ba hakika na tausaya muku, sannan na nemi ganin kune sabida ina so ku dawo Nan da Zama,sannan zan dauki nauyin karatun ka daga yanzu har Allah yasa ka gama" 'daga kansa yayi da sauri ya kalli Daddy sannan ya Maida kallon sa ga Umma, 'daga Masa Kai tayi alamun eh, a zuciyar sa yace "Wato Umma ta ta San da zancen" Gyaran murya Daddy yayi ya daura da fad'in "Nayi maka alkwarin zan dauke ka a matsayin d'an da na Haifa da ciki na, sannan kofa Bud'e take duk Sanda kake neman wani Abu kar kaji tsoro ko shakkar tinkarata ko Maryam" " Nagode Alhaji Allah ya saka, ya biya ka da gidan aljanna" " Umm Haisam, daga yanzu bana so na sake ji ka kirani da alhaji, ka Kirani da Daddy kamar yadda Ma'isha take kirana kaga Kenan Ma'isha ta samu wa" " To Alhaji, auu daddy nagode" Duk sukayi dariya, Maida kallon sa yayi ga Ma'isha yace "Daughter kuje kuci abinci, don zamu fita da Haisam din" Mikewa tayi Tace "Ya Haisam Tashi muje ko?" Mikewa yayi ba tare da yace komai ba ya bi bayanta, Umma tace "Alhaji, hajiya nagode sosai Allah ya saka da alkhairi, ban San wani irin godiya zan Muku ba" Mummy Tace "haba ke kuwa tun dazu fa kike ta godiyar nan, ya Isa haka, mu Dan Allah mukayi ba don komai ba, sannan mun lura akwai shakuwa a tsakanin yaran Nan Baki ga yanda ta tada Mana hankali ba nikaina mamaki ne ya kamani" "Ikon Allah, Amma ni Haisam bai tab'a min maganar ta ba ko da da wasa ne" "Ai bazaiyi ba don na lura Haisam na da zurfin ciki" Murmushi tayi tace "haka yake kamar ubansa" Alhaji dake Danna wayar sa, jin ta ambaci uban sa, yace "Yauwa please a ina baffan Nan nasa yake?" "Ya Nan cikin garin Nan" " Kina nufin cikin garin Gombe?" "Eh" " Abun zaizo Mana da sauki insha Allah" Mummy da Umma a tare sukace " Allahu yasa" Ya amsa da amin ya daura da fad'in "Maryam ku samu kuje shopping din Nan kar dare yayi, sannan please kar su d'auko komai a chan, za a Saya musu duk abubuwan da suke bukata, sannan idan kudin Bai Isa ba ki Kirani" Ta amsa da "to Alhaji" Mikewa yayi yace "idan yaran Nan sun gama ina ciki" "To alhaji a fito lafiya" 'bangaren su Haisam da Ma'isha kuwa abinci kala kala ne aka jera su,akan dinning duk ta bud'e Masa, Haisam Kan sa ne ya kulle ya rasa ma wani abinci zai ci,daga bisani yace ta sami fried rice din, bayan ta zuba Masa a plate ita ma tayi serving kanta sannan ta tsiyaya musu juice Wanda mummy ta had'a na Banana,kwakwa da Madara, Yana ci yana Santi har Saida ya cika cikin sa tam, yayi hamdallah, Ma'isha Tace "Ya Haisam na Kara makane?" Kallon ta yayi da lulu eyes dinsa yace "So kike ki hallakani?" "Laaa yaushe abinci ya tab'a hallaka mutu?" " Baki da Labari ko?" "Eh gaskiya ban tab'a ji ba" " To yau kinji" " Na daiji Amma ban yarda ba,taya za a yi abinci ya hallaka mutum?" "Yanzu ai a koshe nake idan na Kara sa wani abincin a cikina ko da kuwa spoon 'dayane mutuwa zanyi" Kama baki tayi tace "Mutuwa Ya Haisam nikam ban shirya kuka ba" "Ma'isha ke dai kin samu sabon salo" "wani irin salo Kuma?" "Naga kin dage Sai Yaya kike ce min,ni yayan ki?" "Eh Mana ko baka ji abinda daddy yace bane?" " Naji Mana Wai ke katuwa dake ki wani Rika cemin Yaya" Ajiye spoon din dake hannun ta tayi Tace "Nice katuwar?" "Eh Mana" Nan wasu siraran hawaye suka Fara saukowa daga idanun ta,Kama baki yayi yace "ikon Allah Dan Allah ki rufa min asiri,me yasa ki kuka?" Cikin muryar kuka tace " Ba Kai bane kace min katuwa" "Shiyasa kike min asarar hawayen ki?" Bata ce Masa komai Sai sautin shesshekar kukan da take kawaii yake iya ji, cikin murya Mai sanyi yayi yace "Yi hakuri Yar Kanwata ke baki San wa bane?" "Kanwar ka bayan kace ni katuwa ce?" "Ni na Isa na ce miki katuwa tuntuben harshe ne,bazan sake ba kiyi hakuri" " To naji zan hakura Amma Sai dai in zaka dauke ni a matsayin kanwar ka sannan idan na Kira ka da yayana zaka amsa?" "Na amince Sai Kuma me?" " Shikenan?" "Ah to ai hikenan baki da case kanwata" Rufe fuskar ta tayi wai ita a lallai taji kunya, Murmushi yayi yace "to kije ji fad'awa daddy na gama ko ina zamuje?" "bari naje na tambayo maka shi" "a a ni ban saki ba." Tashi tayi Tace " bari naje na fad'a Masa" Kai kawaii ya d'aga mata,d'akin Daddy ta nufa ta Sanar mishi da cewar Haisam ya gama. Bayan daddy ya shiga ciki Mummy Mikewa tayi ta d'auko makullin motar ta, Tace wa ummu "Tashi muje ko" Ba musu ta Mike a dai dai Nan Ma'isha ta shigo parlor cikin muryar shagwa'ba tace "Mummy tafiya zakuyi ku barni bayan nace Miki zan biku" "afwan daughter na sha'afane" "To Dan Allah mummy ku jira ni bari na canza Kaya" "To ki same mu a mota" Suka fice. A dinning daddy ya tarar da Haisam ya umurce sa da ya ajiye jakar sa, su fita hakan akayi, a tare Suka fito da Ma'isha, motar mummy ta Shiga yayin da Daddy da Haisam suka shiga motar Daddy, Mai gadi ne ya wangale musu gate, su mummy ne suka Fara fita sannan su daddy suka fita. A hanyar su ta tafiya daddy ke tayi masa Hira shi Kuma Sai dai yayi Murmushi idan ya Masa tambaya ne ya amsa da eh ko a'a a haka har suka Isa inda zasuje, kananan Kaya da shaddodi masu tsada daddy ya Saya Masa Sai kallan da Haisam ya zab'a a bashi, takalmomi da huluna Kuma ba a cewa komai. Haisam tsabagen farin ciki bakin sa ya kasa rufuwa don shi a iya sanin sa bai tab'a rike Kaya masu tsada haka ba bare ace nashi ne, bayan sun gama da shagon Kaya suka kaiwa telan Daddy sannan ya umurce sa da Yana son kayan Nan da kwanaki uku, ya amsa da to, ya cika Masa aljihu da kudi suka Kara gaba. Shagon sayar da waya suka nufa, daddy yace "Haisam ka zabi duk wayar da kake so anan" Haisam kallon daddy yayi yace "Daddy ka dai za'ba min ni ba sanin waya nayi ba" Daddy Har cikin ransa yaji dadin kiransa da Haisam yayi Daddy, Murmushi yayi yace "To why not mu d'auka maka iPhone 14?" Zaro Ido yayi yace "iPhone 14? Daddy naji ance wayar nada tsada sosai Kuma ma ban iya amfani da ita ba" " Kar ka damu Ma'isha zata nuna maka yanda ake amfani da ita, itama iPhone d'ince a hannun ta" " To Daddy nag....." Hannu ya 'daga Masa yace " A'a Haisam bana son godiyar Nan, daga yanzu bana so kalmar godiya ta Kuma Shiga tsakanina da kai" "Amma ai daddy masu iya magana sunce yaba kyauta tukuici ce" "Wannan Hakane Amma ni ban bukata" Shiru kawaii yayi don baya son jayayya da daddy. Kallon Mai shagon daddy yayi yace "Sa Mana iPhone 14 a leda sannan ka bani acct number ka na maka transfer" "Ai Alhaji babu wayar ba a ma samun ta anan sai dai idan kana so za a yi Muku order" "Okay to zuwa yaushe zai iso?" " Nan da sati haka" " Sati ai yayi nisa, anyways bamu iPhone 13 in yaso daga baya Sai a saya Masa wanchan d'in." Sa musu yayi leda sannan ya Saya Masa sim, had'e da earpod, Haisam farin ciki bazai misaltu ba, bayan sun gama suka wuce gida, daddy ganin mummy basu dawo ba ya "Na sani ai za a rina,Mata mata" Kallon Haisam yayi yace "Zo muje na nuna maka side Dinki" Bin bayan Daddy yayi wani d'an madaidaicin flat ne ya had'u iya had'uwa, Wanda tsaya kwatanta muku yanda take zai d'auke mu lokaci Mai tsawo. Tunda suka Shiga cikin gidan Haisam Sai kallon gun yake baki a bud'e a haka har Daddy ya gama nuna masa, daga karshe ya kaisa wani d'aki Wanda makeken Italian bed Ne a ciki,da wall drop Shima kalan gadon sannan da sofa masu kyau guda uku,'daya three sitter sauran biyun Kuma 1 1 sitter ne. Yace "Haisam wannan ne d'akin ka" Haisam durkusawa yayi Yana kuka Mai sauti yanayiwa Daddy godiya,da kyar daddy yasa shi ya Mike ya umurce sa da yayi wanka ya huta Kan su Mummy su dawo yayi ficewar sa. Haisam ya dad'e Yana zaune Yana mamakin abubuwan da daddy yayi musu,Ashe dama akwai mutanen kirki a Duniya, da wannan tunanin ya Shiga wanka,bayan ya fito ne yayi sallar la'asar dake suna shagon sayan wayar akayi sallar la'asar,bayan ya idar da sallar ne ya hau Kan gado ya kwanta,tunanin sabowar rayuwar da ya shiga yake a haka har bacci Mai nauyi ya d'auke Shi. Daddy ma wankan yayi bayan Nan yayi sallah ya kwanta Shima ya hau baccin sa Mai dadi. 'bangaren su mummy kuwa San Hussain suka Shiga zannuwa masu tsada da dogayen riguna,mayuka,gyalalluka takalmomi da jakkakuna baza su irgu ba, ta loda wa Umma,Umma kuka ta Shiga yi. Matsowa mummy tayi daf da ita tace "Haba Hajiya Fatima kisani fa muna cikin mutane,Zaki sa ayi ta kallon mu" Ma'isha ta miko Mata handkacif had'e da fad'in " kiyi hakuri Umma ki daina kuka" Murmushi tayi Tace "Na daina Ma'isha" Bayan sun gama sayyayan duk abui da zasu Saya suka nufi saloon,Umma rabonta da zuwa saloon tun Abban Haisam na Raye,wani irin iska Mai dadi take ji Yana Shiga kanta duk da kusan kullum saita wanke,Amma wankewan Kai a saloon Daban yake da wanda zakayi a gida. Bayan sun gama da saloon suka nufi gida suna Shiga Ana Kiran sallar magrib,a dai dai Nan daddy ya fito da alwalar sa,ya hango motar su tana parking girgiza kai kawaii yayi ya tsaya kallon su. Ma'isha na fita daga motar taje ta Kira Haisam su Shiga masallaci,da saurin ta,ta nufi part d'in da Haisam yake hannun ta dauke fa ledodi,a parlor ta ajiye su ta nufi d'akin sa,dake da ita aka gyara d'akin shiyasa tasan d'akin sa. Tana sa hannu taji kofar a bud'e take,lekawar da zatayi ta hangosa a Kan katafaren gadon sa yana sharban baccin sa hankali kwance. _________________________ Please share and comments Milhaat ce Yar Terawa 🍃 *DANGIN UBANA*🍃 Story & Written By Milhaart Na zo muku da littafi Mai ban tausayi,cike da abun al'ajabi,wannan salon na daban ne. *🌍MANAZARTA* *WRITERS ASSOCIATION📚🖊* *M. W. A* ```Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.🤙🏻``` https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa ____________________________________ *Wannan labarin kirkirarren labarine ban yarda a chanza min labari ba Wanda ya chanza bamu yafe ba.* Ina alfahari da rubutu,sabida alkalami yafi takobi🗡️🗡️🗡️ *BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM* Page 9 and 10 Shiga d'akin tayi ta tsaya kallon sa, Haisam a baccin sa yake ji kamar akwai mutum a Kan sa, a hankali yake bud'e idanun sa har ya sauke su Akan ta, Murmushi yayi cikin muryar bacci yace "Ya dai malama? Kin wani sani a gaba kina ta kallo na am in safe?" Murmushi tayi Tace "Of course you are safe, Daddy ne yace na Kira ka ku tafi Masallaci" "Daddy ne yace na Kira ka ku tafi Masallaci" ya fad'in hakan ne Yana kwaikwayon muryar ta ya daura da fad'in "Kuma kika tsaya kallo na ko?" Cikin muryar shagwa'ba Tace "Yaya shine kake kwaikwayata ni dai ba haka muryata take ba." Mikewa yayi ya nufi hanyar ban d'aki ya waigo ya kalle ta kyaji dashi" ya shige ban d'aki a gaggauce yayi alwala ya fito ganin Ma'isha na tsaye a inda ya barta ya sashi Kama Baki, kallon ta yayi cike da mamaki yace "Wai ke dama baki tafi ba? Ko so kike sai kin sani a gaba tukkunna?" Kai ta d'aga Masa alamun eh, girgiza kai yayi yace to muje Yana gaba tana biye dashi. Daddy na hango su yace "kaji yaran Nan har na ma manta na aiketa" Suna karasowa inda yake yace "Daughter ke kuwa daga aika ai ki zauna Sai kace an aiki baiwa gidan su?" Yar karamar dariya tayi Tace "Daddy ai Yaya ne, yake ta bacci dakyar na tashe shi" Haisam yace "Ji Dan Allah ko kunyar karya ma ba kyaji bayan...... " Daddy ne ya yanke Masa zancen yace "Ya Isa ya Isa, yanzu sai ka wuce muje Masallaci idan muka dawo sai ku cigaba da musun naku, kema ki wuce kije kiyi sallah" Ta amsa da "To daddy sai Kun dawo a Mana addu'a" Ya amsa da to ba tare da ya waigo ba,cikin gida ta wuce su Kuma suka wuce Massallaci" A parlor ta tarar da Mummy da Umma, mummy na ganin ta tace "daga zuwa aika Ma'isha sai ki zauna abunki?" "mummy ya Haisam ne da surutun sa" "Da surutun ku dai, ina sauran kayan Nan kike ajiye su?" " Yana part d'in su Umma, na d'auko ne?" "A a bar su kawaii d'auki wannan d'in ki Kai su Chan" Ta amsa da to had'e da d'aukan sauran kayan ta wuce dasu part d'in su Haisam, Umma ta rufa Mata baya. A chan Ma'isha tayi sallar maghrib da Isha, Haisam da daddy tunda suka fita basu dawo ba har Sai da aka yi Isha suka dawo gida. Mummy na ganin su Tace "Alhamdulillah to ba komai nasan yanzu bani kad'ai bace a gidan" Murmushi daddy yayi ya ce "Toh me Kuma ya Faru rankishidad'e?" "Duk fita kuka yi kuka barni Mana ni kad'ai kamar mayya" "Ahh ina su Ma'ishan suke?" "Tunda nace ta Kai Mata Kaya shiru kake ji ba ta dawo ba" Yar karamar dariya yayi yace "Ai Ma'isha ta iya zuwa aika, Haisam je ka kirawo min ita" Ya Mike Kenan ya hango shigowar su yace "Daddy ai ga sunan ma sun shigo" ya koma ya zauna. Girgiza Kai yayi yace "Wato shine kuka bar min Mata ita kadai ko?" Murmushi Ma'isha tayi Tace "Daddy wallahi Hira muke tayi muna kallon zee world bamu San lokaci ya tafi har Haka ba" "To kun kyauta, Hajiya yunwa fa nake ji" Mummy mikewa tayi Tace "Muje Dining dama dazu na kirb'a sakwara na sa a food flask" " Yauwa Yar Albarka na" ya Maida kallon sa ga Haisam yace "Son muje ko?" Mikewa yayi ba tare da yace komai ba ya bi bayan sa, Ma'isha hannun Umma ta rike tace "Umma muje" Mummy Tace "Shikenan nikuma an yaye ni ko?" Dariya kawai sukayi suka nufi dinning suna cin abinci suna hira har suka gama, bayan sun gama ci Haisam yayi musu Sai da safe ya koma part d'in su, Umma da Mummy da Ma'isha a parlor suka zauna suna Hira a yayin da daddy ya shiga bed room dinsa, sun dad'e suna Hira har karfe 10 ta wuce Umma sai hamma take cikin muryar bacci Tace "Ni ina gani zan wuce bacci nake ji sosai ga gajiyar da muka kwaasa d'azu" Yar karamar dariya mummy tayi tace "Ni kaina baccin Nan nake ji muje na d'an taka Miki" "To Shikenan" mikewa Umma tayi had'e da Mika tana ambaton "La'ila ha illallalah Muhammaddar rasulullah" Ma'isha cikin muryar shagwa'ba tace "Umma zan biki mu kwana tare please" Murmushi tayi Tace "To Muje daughter" riko hannun ta tayi sukayi wa mummy Sai da safe suka fice, mummy Murmushi tayi ta girgiza Kai ta shige d'akin ta. WASHE GARI Bayan sun idar da sallar asuba Ma'isha ta dawo part d'in su, Kai tsaye d'akin ta tashiga ta yi wanka sannan ta fito don Taya mummy aiki a kitchen, Tana Shiga kitchen ta tarar da mummy juya ruwa a flask. "Mummy ina Good Morning" "Ahhhh 'yar Umma har Kun tashi?" Murmushi tayi Tace "Eh mummy" "To ya kuka tashi,ya Umman taku?" "Lafiya Lau Alhamdulillah" "Amma meyasa baki tsaya kin tayata aiki ba Kika dawo?" "Itace Tace na dawo, shiyasa Kuma Kinga , zamuje school, bara nayi wanke wanken" "A'a ki bari yarinyar nan zata Zo ta yi kije ki samu ki shirya naga har kinyi wanka je ki kawaii ki shirya" "mummy tun yanzu? Karfe 6 fa" "Ki dai sake dubawa 6:30 ne" Agogon bangon dake manne a kitchen d'in tace "Gaskiya lokaci yana gudu Bari naje na sa uniform" "Okay" Ta fice a kitchen d'in Bata d'auki lokaci mai tsawo ba ta dawo, a lokacin bakwai har ya wuce, a dining room ta tarar da mummy da Daddy bayan sun gaisa ta karya, a gaggauce ta fice tana musu sai ta dawo, inda ake parking mota ta nufa, ta tarar da driver da Haisam suna Hira cikin girmamawa ta gaida driver kana ta maida kallon ga Haisam tace "Good Morning Yaya" Murmushi yayi yace "Morning" Duk suka shige motar suka, ba su tsaya a ko ina ba sai makaranta. Haka rayuwa ta kasance wa ma'isha da Haisam a tare suke zuwa school Kuma su dawo a tare, sun shaku sosai haka ma mummy da Umma kusan komai tare suke, sannan daddy yana iya bakin kokarin sa wurin ganin ya cika alkwarin da ya d'auka wa Haisam, duk abunda yake so yanayi masa, a hakan har suka rubuta WAEC and NECO d'in su Kuma Alhamdulillah paper su duk yayi kyau. Daddy yayie matukar farin ciki hakan yasa bai 'bata lokaci ba wurin yi musu registration na JAMB ba,Kuma Alhamdulillah sun ci yanda a ke bukata duk su biyun a gombe state University sukayi(GSU) applying,suna zaman jiran admission. Da gudu ta shigo ta murna had'e da tsalle tana Kiran sunan Daddy da Mummy, Mummy dake kitchen ita da Umma cikin Sauri suka fito a tare sukace "Lafiya? Me ya faru?" Tambayar su yayi dai dai da lokacin da Daddy ya fito cikin Sauri daga d'akin sa, yace "Ma'isha me ya faru?" Sai tsalle take Haisam kusa hard'e hannu yayi Yana kallon ta, Umma Tace "Kai kunci gidan ku ana muku magana baza ku amsa ba?" Da gudu ta rungumi Umma tace "Admission ya fito kuma duk mun samu" Girgiza kai daddy yayi yace "Dad'i na dake ba a raba ki da shirme wallahi, shiyasa Kike Mana ihu a cikin gida?" " Daddy ai Dole ni da Yayana mun samu admission a department d'in da muke so" Umma Tace "Masha Allah, kice yanzu muna da Doctor da Kuma pharmacists a gida" Ta amsa da "Insha Allah" Mummy maida kallon ta tayo ga Haisam cike da kulawa Tace "Son ya naga Kai baka tsallen? Ko bakaji dad'in admission d'in bane?" "a'a mummy kawaiiii...... " Daddy ne ya katse shi yace "Toke Banda abunki hajiya Ma'isha tayi Shima yayi ya za a banbanta yaro da babba" Duk dariya sukayi, ya d'aura da fad'in "Allah ya taimaka, Haisam yaushe zaku karb'o admission d'in" " Ai daddy mun karb'o" "Sharp sharp Kenan, anyways congratulations to you both" A tare Ma'isha da Haisam suka amsa da "Thank you daddy." "Emmm yanzu abunda za'ayi ku biyuni sai muyi maganar kud'in registration d'in don Ina so a Fara Lectures daku" ya wuce d'akin sa su biyun suka bi bayan sa mummy da Umma Kuma suka koma kitchen. Daddy ya Basu dukkanin kud'in da suke bukata,washe gari a tare sukaje sukayi registration tun safe suka fita basu dawo har sai dab da magrib a gajiye suka dawo,hakan yasa dawuri sukayi bacci. Bayan sun gama registration,suka Fara Lectures d'insu yanda ya kamata. Daddy na gani zaune a office, kwankwasa kofar da akayi ne yasa ya d'ago kansa yace "Come in" sannan ya cigaba da rubuce rubucen da yake, Jin an shigo ya d'ago kansa don ganin Wanda ya shigo Murmushi yayi yace "Bismillah zauna" Ba musu mutumin ya zauna, hannu ya Mika Masa suka gaisa, mutumin ne ya ce "naji Labari kaje gida har Sau Uku baka sameni ba, gashi kuma ban Sanka ba" "eh hakane kamar yanda nace maka a waya wata magana nake so muyi da Kai Mai muhimmanci, shiyasa ma kaga na takura kazo office Dina" Murmushi yayi ya gyara Zama yace "Business ne Kennan, kasan na dad'e ina so na fara business da company ku Amma Allah baiyi ba" Daddy yace "Malam Hassan zamu Zo Nan d'in ma Amma kamun Nan....." Wayarsa ya zaro a aljihun gaban rigar sa gallery ya shiga ya Mika Masa wayan yace "ko Kasan wannan?" Karb'an wayan yayi ya dad'e Yana kallon sa, a zuciyar sa yace "Wannan kamar Haisam, Kai ba shi bane ya akayi ya Zama Haka maybe kamane" A bayyane Kuma yace "Yallab'ai ban sanshi ba Gaskiya" ya Mika Masa wayan, Kan wani hoto ya koma ya Kuma Mika Masa wayan yace "Wannnar fa da fatan ka gane ta?" Yana karb'an wayan yana ganin Hoton a raza ya Mike hannun sa rawa yace "Zainab, wannan kamar Zainab dama tana raye ne, Zainab ce fa matar Yayana ko? Ko dai Kama ne ya naga ta canza?" _______________________ Please share and comments Milhat ce Yar Terawa 🍃 *DANGIN UBANA*🍃 Story & Written By Milhaart Na zo muku da littafi Mai ban tausayi,cike da abun al'ajabi,wannan salon na daban ne. *🌍MANAZARTA* *WRITERS ASSOCIATION📚🖊* *M. W. A* ```Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.🤙🏻``` https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa ____________________________________ *Wannan labarin kirkirarren labarine ban yarda a chanza min labari ba Wanda ya chanza bamu yafe ba.* Ina alfahari da rubutu,sabida alkalami yafi takobi🗡️🗡️🗡️ *BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM* Page 11 and 12 Daddy Shima mikewa yayi yace "hakan na nufin ka santa Kenan?" Malam Hassan Sai kallon sa yake ya kasa cewa komai, girgiza Kai daddy yace "calm down, calm down ka zauna" Jiki a sanyaye ya zauna Idon sa akan hoton Sai zare Ido yake Yana kallon Hoton, daddy yace "Na dad'e ina neman ka tsoratan da kayi hakan ya tabbatar min da maganar da Zainab ta fad'a min Akan ka gaskiya ce" Murya na rawa yace "me me me ta taa fad'a maka? Kar ka yarda da ita makaryaciya ce" "Give a good reason da zan gano cewar makaryaciya ce" "Ashe dama tana raye ni na d'auka ta mutu" Maganar da yake ta maimaitawa Kenan. Daddy yace "Bata mutu ba,ko ince Basu mutu ba,Ashe dama Kaine Wanda yasa aka Kona musu gida ina da labarin gidan ya Kama da wuta nayi iya tunanin Duniyar Nan ya akayi wuta ya Kama,ashe Kaine?" Mika Masa wayan yayi ya Mike,ba tare da ya bashi amsar Tambayar da ya Masa ba,har ya Kai bakin kofa Daddy yace "Ka dawo musu da dukiyan su ko Kuma mu had'u a kotu,kuma idan kace zaka bar gari wallahi tallahi duk inda ka shiga a fad'in Duniyar Nan zan Nemo ka" Waigowa yayi, yayi tsaki yace "To hell with you mu had'u a kotun" Sai ya fice, motar sa ya shiga duk hankalin sa a tashe Sai zufa yake ta goge wa da hannun sa, farar shaddan da ke jikinsa duk ya jike, Kai tsaye gidan sa ya nufa, yana parking d'akinsa ya shiga matar sa na ganin sa ta gane ba lafiya don ko sallama baiyi ba ya shige. Cikin sauri tabi bayan sa tarar dashi tayi a d'aki yana kaiwa Yana kawo wa, cikin nuna kulawa da damuwa Tace "Malam lafiya me ya Faru na ganka haka sai safa da marwa kake?" Murya na rawa yace "Rabi akwai matsala, akwai matsala wallahi" "Malam zauna ka fad'a min me ke faruwa?" "Zama? Ai banga ta Zama ba, ina naga ta Zama bayan asirina yana kokarin tonuwa?" "Asirin ka? Ban fahimta ba Malam me kake nufi da hakan?" "Ashe dama Munafukar matar Nan tana raye? Ashe bata mutu ba ita da d'anta?" Cikin rashin fahimta take kallon sa, yace "Dad'i na dake kanki baya ja wallahi ko kad'an Zainabu nake nufi Zainabu na Raye ita da d'anta" Dafe kirjin ta tayi Tace "Innalillahi wa Inna ilaihirraji'un, suna raye Malam? Amma ya akayi ka sani, na d'auka kasa an Kona inda suke?" "eh ni da ido na, na gani to Amma abinda ya d'aure min Kai hakan na nufin fa basu cikin d'akin don Babu yanda za a yi su tsira gas fa nasa aka sa hatta Wanda yasa wutan ya mutu da idona na gani fa" "ka gani ko Malam tun wanchan lokacin na Hanaka Amma kaki ji, yanzu gashi wa gari ya waya" "Rabi yanzu fa ba lokacin wannan bane..... " Nan ya sanar Mata yanda sukayi da Daddy, Rabi Tace "Malam ka maida musu dukiyar su, ai yanzu ka samu fiye da abinda ka samu agun su, idan ka bari ya kaika kotu duk abunda ka Tara za a Basu" "inaaa bazaiyu ba kin San tsawon shekaru nawa na yi ina tara kud'aden Nan kuwa?" " Ni kuwa na sani malam, ko dai barin garin zamuyi ne Kam?" "ai cewa yayi ko na bar gari Sai ya Nemo Ni" "Nikam wane ne haka? Da yake kokarin tozartamu?" "chairman ne fa Mus'ab Aminu" Zaro Ido tayi Tace "Eh lallai malam baka nemi zaman lafiya ba wallahi in dai baza ka maida musu ba, kasan mutumin Nan yanda yake da taimakon al'uma baya bari a cutar da kowa" "Na San da hakan, dole zan nemi mafita amm....." Kwankwasa kofar da akayi ne ya katse maganar da yake niyar yi. Cikin tsawa yace "Waye anan nace Waye ne?" Cikin sanyin murya Tace "Daddy wani mutumine ya kawo sako yace a baka" Rabi Tace "Shigo" Tana Mika Mata ta fita, Yana bud'ewa yaga tsammaci daga kotu kallon paper da yake ne yasa ta karb'a don ta gani girgiza Kai tayi Tace "lallai malam mutumin Nan dagaske yake, ranae Monday fa zaku shiga kotun" Tashi yayi ya fice ba tare da yace Mata uffan ba, ya shiga motar sa kenan ya hango Yan sanda guda biyu, jiki na rawa ya fito Yana kallon su, bayan sun gaisa 'daya daga cikinsu yace "Kaine Malam Hassan Umar?" Murya na rawa yace "Eh eh nine" ID card d'insu suka zaro suka nuna masa, "Yan sanda ne an turo mu da warrant arrest d'inka" "Ni Ni kuma, me me Kuma nayi?" "Idan mukaje office zakaji koma mene ne" Nan take suka zaro handcuffs suna kokarin Sanya Masa a hannun sa, cikin tashin hankali yake Kiran sunan ta "Rabi !! Rabi!!! Da gudu ta fito ita da 'ya'yan ta guda uku, Yaran na kuka rabi ma na kuka, har suka fice dashi suka sashi a mota. Suna zuwa police station suka tarar da Daddy, mummy, Umma, Ma'isha da Haisam duk suna zaune, cike da mamaki yake kallon su, hannu Daddy ya d'aga musu hannu, gani nayi sun cire Masa handcuffs din. Mikewa daddy yayi yace "Malam Hassan tun wuri ka taimaki kanka ka maida musu dukiyan su yanzu zan sa a sake ka idan Kuma kaki wallahi wallahi sai ka Raina kanka" Kallon Umma yayi yace "Zainabu kina jin abinda yake fad'a ko? Ki fad'a Masa gaskiya cewar dukiyar Nan Yaya nane ya bani" Umma fashewa tayi da kuka ta fice daga gun, mummy, Ma'isha da Haisam suka bi bayanta. Daddy ciza le'be yayi yace "Na lura kana da taurin kai, Amma kar ka damu...." Maida kallon sa yayi ga police d'in dake gefen sa yace "A kulle shi Kuma ban yarda a yi bailing sa ba, sannan kar a bari kowa yazo ganin sa ko da kuwa matarsa ce" Yana Kai Nan ya fice. Tarar dasu yayi a jikin mota Umma na kuka mummy na rarrashin sa, a yayin da Haisam ji yake kamar yaje ya shake baffan sa ya mutu ko zaiji sanyin abinda ke damin sa. Daddy yace "Ki daina kuka insha Allah komai zai wuce" "Alhaji dole nayi kaji abinda yake cewa fa, shi ya kashe min miji ya kwace dukiyar sa,sannan nima ya so kashe ni da d'ana Amma yana rayuwar sa hankali kwance" Mummy Tace "Kar ki damu ranar Monday komai zaizo karshe insha Allah, ke dai kawai ki fad'i duk abinda kika sani shine kad'ai zai sa a mishi hukunci dai dai da abinda ya aikata" Haisam yace "Amma mummy bamu da wani hujja, kinsan komai sai da evidence karshe ma a nemi a karyata mu" Daddy yace "matsala d'aya zamu samu shine evidence d'in da shi ya kashe shi Amma duk sauran zaizo Mana da sauki insha Allah, ku shiga mota mu tafi" mikawa Haisam key d'in motar akan ya jaa su, karb'a yayi duk suka shige, Kai tsaye gida suka nufo. Zaune suke a parlor,duk jikin su a sanyaye yake ganin kukan da Umma take yake ci yaki cinyewa Mummy Tace "Kukan na mene ne haka ya Isa Dan Allah" Cikin shesshekar kuka Tace "Wallahi ina ganin sa hankali yayi mugun tashi, tsayuwar da yayi a gabana sai naga kamar Ahmad ne Kai hatta muryar sa ma irin ta Ahmad ce, Hassan ya cuce ni bazan tab'a yafe Masa ba" ta karasa maganar tana kuka, Haisam Tashi yayi ya fice, Kai Tsaye d'akinsa ya nufa da gudu Ma'isha ta bi bayan sa. Daddy girgiza Kai yayi yace "Allah ya kyauta" ya nad'e garen sa ya shige d'akinsa. Ma'isha har cikin d'akin ta bishi, ya zauna a baki gado ya had'a Kai da gwiwa kuka yake sosai Mai sauti, Zama tayi a gefen sa baiji shigowar ta ba sai muryarta da yaji Tace "Ya Haisam." 'daga kansa yayi a hankali ya sauke idanunsa akan ta, kirkirerren Murmushi yayi, wata farar kyalle ta Mika Masa Murmushi ya Kuma yi yasa hannu ya karb'a ya share hawayen sa, bayan ya gama ya Mika Mata yace "Thank you" Murmushi kawai tayi tace "Ya Haisam kuka fa ba naka bane, addu'a ya kamata muyi Allah ya d'aura mu a Kan sa" " Ma'isha ba kukan dukiyar nake ba ko wani abu ba a'a ganin Umma ta a cikin irin wannan halin shi yake tada min hankali ko kad'an bana son zubar hawayen ta, ba sanin mahaifina nayi ba shiyasa bana jin kewar sa duk da cewar na San na rasa gata na Amma Umma itace uwata itace ubana bazan juri ganin ta a haka ba" "I know how you feel insha Allah komai zai dai daita" "Allah yasa." "Ameen" Ma'isha sai surutu take Haisam kuwa sai aikin kallon ta yake tun baya kulata har ya Fara kulata suka Sha Hira sosai, a yayin da Mummy na chan tana rarrashin ummu, wannan Kenan. RANAR LAHADI Daddy na zaune a garden Yana karanta jarida, yayin da Haisam da Ma'isha na daga gefe suna Shan hirar su, mummy ce ta fito cikin Sauri ta miko Masa waya tace "Tun d'azu ake ta kiran ka da sabon number" Karba yayi ya Kara a kunnen sa banji me akace ba ya Mike yace "okay gani Nan zuwa" Mummy Tace "Ina Kuma zakaje?" Bai Bata amsa ba yace "Haisam maza d'auko makullin mota akwai inda zamuje" Da gudu Haisam ya shiga d'akin Daddy ya d'auko makullin motar ya shiga ya tada motar, Mummy Tace "Alhaji lafiya?" "Lafiya Lau police station zamuje kar ki fad'a wa Zainab sai mun dawo" ya shige motar suka fice daga gidan, mummy da Ma'isha suka kalli Juna, Mummy tab'e Baki tayi Tace "Allah ya kyauta. ________________________ Watan March 2022 ya kasance wata mara Dad'i a gare ni a cikin sati biyu na rasa mutane na kusa dani. Kakata ta rasu washe gari kanwar mahaifina ta rasu, basu cika sati ba cousin brother na da abokanan sa guda uku sukayi hatsari duk su ukun suka rasu, shiyasa duk na kasa typing naso ace kamun Ramadan na gama littafin Nan Amma kana naka Allah na nashi, dole zan dakatar da Rubutun sai bayan sallah insha Allah, Dan Allah kusa Yan uwana a addu'a, Allah ya jikan Musulmai idan tamu tazo yasa mu cika da imani ameen. Please comment and share Milhat ce Yar Terawa 🍃 *DANGIN UBANA*🍃 Story & Written By Milhaart Na zo muku da littafi Mai ban tausayi,cike da abun al'ajabi,wannan salon na daban ne. *🌍MANAZARTA* *WRITERS ASSOCIATION📚🖊* *M. W. A* ```Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.🤙🏻``` https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa ____________________________________ *Wannan labarin kirkirarren labarine ban yarda a chanza min labari ba Wanda ya chanza bamu yafe ba.* Ina alfahari da rubutu,sabida alkalami yafi takobi🗡️🗡️🗡️ *BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM* Page 13 and 14 Da gudu Haisam ya shiga d'akin Daddy ya d'auko makullin motar ya shiga ya tada motar, Mummy Tace "Alhaji lafiya?" "Lafiya Lau police station zamuje kar ki fad'a wa Zainab sai mun dawo" ya shige motar suka fice daga gidan, mummy da Ma'isha suka kalli Juna, Mummy tab'e Baki tayi Tace "Allah ya kyauta." Ta shige cikin gida. Basu zarce ko Ina ba Sai police station,bayan sun shiga ciki Kai tsaye office din DPO suka shiga bakin su d'auke da sallama,ga mamakin su suka tarar da Baffan Haisam a zaune a cikin office d'in,DPO ya nuna was daddy kujerar dake gaban sa yace "bismillah yallab'ai" Ba musu ya nemi wuri ya zauna,bayan sun gaisa DPO yace "Nasan kayi mamakin Kiran ka da nayie ko?" Ya amsa da "Eh sosai ma" Gyaran murya DPO yayi yace "Dama malam Hassan ne ya bakaci ganin ka shiyasa ma na Kira ka" Daddy maida kallon sa yayi ga Malam Hassan yace "Ina sauraron ka" Malam Hassan yace "Na yanke shawara ne zan maida musu da dukiyar su" a gadarance. Girgiza Kai kawai daddy yayi yace "Ni Kuma ban amince da hakan ba, a lokacin da nake ta bibiyar ka da ka dawo da duk abinda ka San nasu ne Amma kamin kunnen uwar shegu, maganar kotu Kuma bazan janye ba Sai munje" Malam Hassan yace "A lokacin da kace na bayar banji zan iya bane ba Amma a yanzu na shirya" Daddy ransa yayi mugun 'baci sabida ganin yanda malam Hassan yake magana a gadarance, mikewa yayi yace "Haisam tashi mu wuce gida" ya nufi kofar fita, DPO yace "Yallab'ai Dan Allah ka tsaya" waigowa yayi yace "Na tsaya nayi me da na San sabida Shirmen Nan ka kirani wallahi da banzo ba" "Hakane yallab'ai dole ranka ya 'baci Nima cemin yayi zakuyi Sulhu shiyasa na Kira ka" ya maida kallon sa ga Malam Hassan yace "Malam Hassan ba haka mukayi dakai ba, Ce min kayi zaka nemi gafarar su kuyi Sulhu Amma ya za'ayi Kai da kake Neman Abu daga gare su kana musu magana a gadarance? Ka bashi hakuri ka fahimci juna don wallahi idan ka bari kuka shiga kotu da dukiyar d'an uwan ka da naka duk za a had'a a karb'a, Amma fa ba tilasta maka nake ba shawarace idan kaso ka d'auka" Malam Hassan Jin za'a raba shi da komai da komai ya Fara wiiki wiki da ido Nan take zufa ya Fara keto Masa duk da AC dake cikin office d'in, Chan ciki yace "Alhaji kayi hakuri Dan Allah" ya maida kallon sa ga Haisam yace yace "Dan Allah kasa baki Haisam" Haisam dake tsaye Yana kallon su yace "Daddy mu saurare shi a gama abin Nan once and for all ko ba komai hankalin Umma zai kwanta" Ajiyar zuciya daddy yayi ya koma ya zauna yace " Shikenan DPO wani formalities za a bi don a tabbatar da zai bada komai da komai don wallahi I don't trust him ko kad'an" "Kar ka damu yallab'ai zan kula da komai, Na maka alkawari Nan da 2 days zan kammala komai,amma zamu ciga ba da ajiye anan d'in ne ko Kuma mu sake shi?" " A a no need ai Ku sake shi" ya maida kallon ga Malam Hassan dake zaune a kasa ya nuna sa da manuniya yace "Mind you if try acting smart with me I'll deal with you and make your life miserable" Yana Kai Nan ya fice Haisam ya bi bayan sa, tunda suka shiga mota babu Wanda ya sake cewa komai har suka Isa gida. Horn Haisam yayi Mai gadi yayi saurin bud'e musu kofa, parking lot ya nufa yayi parking motar, Mummy , Umma da Ma'isha na zaune a garden d'in gidan suna jiran dawowar su, daddy d'akin sa ya wuce abinsa suna mishi sannu da zuwa ko kallon su beyi ba bare ya amsa. Haisam kuwa inda suke ya nufa ya nemi wuri ya zaunan, Mummy Tace "Son lafiya me ya Faru ne haka na ga ran Alhaji a 'bace?" Gyara Zama Haisam yayi ya fara jero musu yanda sukayi a police station, tunda ya fara magana suke kallon sa har ya Gama Babu Wanda yace komai, Mummy girgiza kai tayi ta tashi ta shige cikin gida, d'akin Daddy ta shiga taje tana ta aikin rarrashi. Ma'isha ganin Umma ta shiga cikin damuwa Ta d'an dafe kafad'arta tace "Umma wannan ba abin damuwa bane ba, tunda shi da kansa yayi ra'ayin zai dawo da dukiyoyin ai farin ciki ya kamata muyi, matsalar kawai gani nake bazai dawo dasu duka bane" Umma Tace "uhmm yaro yarone baza ki tab'a ganin abinda nake hangowa ba" Haisam yace "Umma Me hakan yake nufi, kina nufin akwai wata matsalane idan akayi hakan?" "babba ma kuwa Haisam, Baffan ka mutum ne Mai had'ari ni dukiyar Nan wallahi bataw dame ni ba , dama don kai ne nake so a karb'a maka hakkin ka, ina ji ajikina akwai abinda yake Shirin aikatawa" Ma'isha Tace "Insha Allah babu ma abin da zai faru Umma, aniyar shi ya bishi" Ta amsa da "Amin Allah ya shiga tsakanin mugu da na gari" duk suka amsa da Amin.Nan dai Haisam da Ma'isha sukayi ta kokarin jaan ta da Hira tun bata kulasu har aka fara hirar da ita. "Ka gani ko malam ai tun farko Haka nace maka kayi Amma kayi kunnen uwar shegu da ma baza a kai Nan ba" "Kinga Rabi ni bana son Mai maita magana, Allah ya kaddara hakan Sai ya Faru in ma maganar kulleni da akayi ne ai ba yau na fara shiga cikin cell ba so Dan Allah ki kyaleni naji da abinda yake damina ko Kuma na sauke 'bacin ran a Kan ki" Rabi na jin hakan ta shi ta fice daga d'akin ba tare da tace komai ba, binta yayi da kallo ya ja wani dogon tsaki. 'dakinta ta nufa tana Zama Kenan taji an turo kofa, kallon kofar tayi ganin irin kallon da take mata tayi kirkirerren Murmushi Tace "Ayra Shigo ciki mana" Wacce aka Kira da Ayra naga ta Shigo ta zauna a bakin gadon dake d'akin Tace "Mamy wai Dan Allah me ke faruwane, naga duk kina cikin tashin hankali, nasan hakan bazai rasa nasaba da Abinda ya faru da daddy bane ba, Dan Allah me daddy yayi har aka Kama shi" "Babu komai Ayra, ai daddyn naku ma ya dawo komai ya Riga ya wuce kar ki tashi hankalin ki" "Amma Kuma Mamy ke naki hankalin ai a tashe yake just in 2 days ki duba Kika yanda Kika rame Kika lalace" "Ayra kin San fa bana son ina magana Kuma kema kina yi sabida haka ko ki bar maganar Nan ko ki fice min daga d'aki bana son Shir........" "Me yasa baza ki fad'a mata ba, ai Ayra ba karamar yarinya bace ba, ta girma ya kamata ta San halin da ake ciki tunda baza ki iya sanar da ita ba Ni zan fad'a Mata" Wuri ya samu ya zauna, yace " Ayra" ta amsa da "Na'am Daddy" "Kin tuna cousin brother d'inki Haisam?" "Eh daddy d'an Uncle Ahmad" "Good" Nan ya shiga jero mata abubuwan da ya Faru shekarun baya kamo yanzu, Murmushin gefen baki tayi tace "Daddy wai dama suna Raye na d'aukan sun mutu fa" "Suna Nan a Raye" "To shi Alhaji Mus'ab d'in me had'in shi dasu da yake son taimakon su kalen dangi kawai" Mamy Tace "Na Allah Kenan ba, tun ba yau ba nake nuna wa mahaifin ki abinda yake ba dai dai bane ba, Yana ciyar damu da haram, sanan yana tufatar da mu da haram" "Haba Mamy so kike daddy ya kashe kansa da wanne zaiji? Ni daddy dama mu gudu mu bar kasan wallahi" Mamy yarfa hannu ta shigayi tayi tana sallalalami ta ce " Ayra Ashe baki da hankali ban sani ba? Kina nufin goyon bayan mahaifin ki zakiya bayan Kin San abubuwan da yake yi haramun ne, dukiyan maraya fa yake ci, nasan kinyi karatu kinsan kudin da mahaifin ki yake ci wutane Amma wallahi kin bani Mama....... " "Ke ke ke, me haka nace me haka? " Mikewa yayi ya nufe ta yace "So Kika kisa mata tsanata a ranta ko me kike nufi, wannan wani irin mumunar hud'uba kike Mata haka" "Amma malam kasan....." " Amma me, nace Amma me wallahi tallahi Rabi zan sab'a miki akan wannanw maganar wallahi daf kike da rasa auren ki" Mikewa itama tayi Tace " In rasa Mana ai auren Nan da shi da Babu duk d'aya" Cike da mamaki yace "Oh haka ma Kika ce ko?" "Eh Haka nace" "toh Shikenan kije ki na sak....." Ayra Tace "A'a daddy kayi hakuri Dan Allah, kar ka aikata, Dan Allah kar ka saki mamy" ta karasa maganar tana kuka. Tsaki yayi yace "Kinci Albarkacin Ayra, Allah ya miki Albarka Ayra" Ta amsa da amiin, yace "Naji dad'in maganganun ki hakan ne yake kara tabbatar min da cewar bazan wahala wurin d'aukar fansan da nake sonyi ba, Akwai aikin da nake so kimin, idan Kika min hakan na yafe Miki duniya da lahira." "Inshallah zan maka ko ma mene ne Daddy don samun albarkar ka" "Malam kar ka saka yarinyar Nan acikin matsalar ka ka fama Kai kad'ai" "a'a mummy mahaifina ne fa, matsalar da ai tawa ce, so kar ki damu" Murmushi daddy yayi yace "Good My Girl wuce muje kafun tayi poisoning mind d'inki" Ficewa sukayi a d'akin a tare suka bar ta ita kad'ai, Mamy ta rasa abinda yake mata dad'i, ajiyar zuciya tayi Tace "Ya Allah ka shirya min su ka ganar dasu gakiya." *BAYAN KWANA BIYU* Daddy na zaune a parlor shi da Haisam suna kallo suna Hira sama sama kasantuwar Yau lahadine yasa bai fita office ba, Mai gadi ya shigo bakinsa d'auke yake da sallama, suka amsa. Cikin girmamawa yace "Yallab'ai kayi baki" "Baki Kuma su wane ne Haka?" "Wai DPO ne da malam Hassan" "okay Ce musu su Shigo" " To yallab'ai" ya fice. Daddy yace "Son wai ina mutanen gidan Nan suke ne?" "Suna part din Umma" "Okay je ka Kira min su duka" Mikewa yayi tare da fad'in "to daddy." Tun daga bakin kofar parlor yake jiwo muryar su suna Hira suna dariya , da sallama ya shigo shima Yana daruyay duk da bai San dariyar me suke ba, yace "Nima nazo ne ayi hiran Dani" Umma tace "A'a you're not welcome here, yau ranar ta Mata ne" Yar karamar dariya yayi yace "Nikam dama nasan ba'a yina a gidan Nan Ma'isha kawai ake so" Ma'isha Tace "Ji Yaya fa dan Allah ni Kuma me ye nawa acikin maganar ku?" " Oh ma baki sani ba?" "Eh ban sani ba" "To ki taso Mana kawai ki shake min wuya na fad'a maki" Taso wa tayi ta nufe shi tana dariya yace "Ki karaso Nan kiga abinda zan Miki" Mummy Tace "Yaran Nan Basu da kunyan wallahi,Amma alhaji duk baya gani" Haisam yace "Laaa Kinga na Manta wallahi daddy ne ma ya aikoni wai nazo na Kira ku" Umma Tace " Kuma ka tsaya shirme ba" Mummy Tace "Lafiya dai ko? Nifa bana son irin Kiran Nan" Murmushin yayi Wanda ya kara bayyana kyawun fuskarsa yace "Lafiya Lau, Baffan hassane suka Zo" Dukkanin su Saida suka ji gaban su ya fad'i kallon juna Mummy da Umma sukayi a tare suka Mike suka fice a tare suka shiga dasu Malam Hassan. Mummy gefen daddy ta zauna yayin da Umma, Haisam da Ma'isha suka zauna a Kan three sitter dake d'akin DPO da Malam Hassan suka zauna a one one sitter dake kusa da su Daddy. Daddy yace "DPO shine kazo da kan ka? Ai da ka kirani zuwa office d'in" " A a y'allabai kasan an rufe case d'in Kuma naga maganar yanzu na gidane ba sai a office zamuyi shi ba" "Wannan ma hakane" Mikewa DPO yayi ya Mika wa daddy wasu files, karb'a daddy yayi ya shiga dubawa, bayan ya Gama dubawa yace "Ka tabbata ka had'a komai da komai?" Murya na rawa yace "Eh Alhaji" Daddy yace "Son Zo ka karb'a, har ya sa hannu zai karb'a yace "Daddy da dai ka bar su a wurin ka tukanna, Ni ban San me zanyi dasu ba a yanzu gaskiya" Yar karamar dariya daddy yayi yace "Son Kenan dukiyar kace fa, ba nawa ba" "Eh na sani daddy shiysa nace ka rike su tukunna" "A a son ba za a yi Hakaba" Umma Tace "Alhaji haryanzu Haisam yaro ne ka rike d'in kamar yadda ya bukata" " Toh Shikenan" Sai ya ajiye su a Kan side table dage gefen kujerar da suke zaune. Ya maida kallon da ga DPO yace "Nagode sosai dpo Allah ya saka da alhairi" "a a Alhaji bakomai aikina kawai nake yi" ya maida kallon sa ga Malam Hassan yace "Mu tafi ko?" Yace "Umm umm Dan Allah Alhaji alfarma nake nema a wurin ka" "Babu wata alfarma da zan maka ka tashi ka fice min daga gida" Mummy ce ta dafe shi a fad'a alamun plz ka saurare shi Sai Kuma yace "Fad'i ina jinka" "Alhaji Dan Allah so nake a taimaka min da muhalli ko da gidan da muke cikine naci Albarkacin yayana Dan Allah, bani da inda zan zauna da iyalai na" Kallon kallo a ka Fara yi a d'akin Haisam Kuma Murmushi kawai yayi. Daddy yace "Hakan ba Mai yiwuwa bane ko da yake bani da iko da dukiyar nan, dukiyar Nan ta Haisam ce shi zaka roka ya maka wannan alfaramar bani ba" Malam hassan har kasa ya durkusa a gaban Haisam yace "Haisam Dan Allah ka taimaka min , nasan ban chanchanchi yafiyar ka ba amma dan Allah find a place in your heart and forgive me" Haisam kallon Umma yayi da tun dazu take ta aikin kallon sa, Murmushi tayi shima ya maida Mata. ___________________ Please kuyi min sharhi, shi kad'ai zai bani karfin gwiwar typing. Sannan Kumin sharing Milhaat ce Yar Terawa 🍃 *DANGIN UBANA*🍃 Story & Written By Milhaart Na zo muku da littafi Mai ban tausayi,cike da abun al'ajabi,wannan salon na daban ne. *🌍MANAZARTA* *WRITERS ASSOCIATION📚🖊* *M. W. A* ```Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.🤙🏻``` https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa ____________________________________ *Wannan labarin kirkirarren labarine ban yarda a chanza min labari ba Wanda ya chanza bamu yafe ba.* Ina alfahari da rubutu,sabida alkalami yafi takobi🗡️🗡️🗡️ *BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM* Page 15 and 16 Kallon Baffan sa yayi yace "Dan Allah ka tashi baffa meyasa zaka durkuwa a gabana bayan kana matsayin ubane a gare ni, Ni na yafe maka duniya da lahira, maganar gida Kuma na bar maka shi halak malak hatta company d'in da kake aiki a Cikin na mallaka maka" Malam hassan kirkirerren kuka ya Fara yi yana fad'in "Nagode, Nagode Haisam Allah ya maka Albarka" ya maida kallon sa ga Umma yace "Zainabu kiyi hakuri ki yafe min Dan Allah" "Bakomai na yafe maka, Allah ya yafe Mana baki d'aya." Duk suka amsa da amiin, Malam Hassan Banda godiya babu Abinda yake har suka fice daga gidan, Nan su Daddy suka shiga hirar su suna farin cikin nasarar da suka samu. Tana ganin shigowar sa ta mike tana fad'in "Daddy ya dai? Da fatan anyi nasara" Murmushin irin zasu gane kuren su yayi yace "Yar daddy ai daddyn nakin ba daga nan, plan d'inmu zai Fara ne daga yau, na gama nawa saura naki" Murmushi tayi Tace "Insha Allah Daddy kasa ranka anyi an gama kawai" "Allah ya miki Albarka Yar Daddy" Ta amsa da "Ameen." Umma da Haisam hankalin su kwance ko bakomai sun karb'i hakkin su, Basu da sauran damuwa a rayuwar su, duk wanni abu da suke bukata na jin dad'in Rayuwa suna dashi. Wannan Kenan Haisam da Ma'isha shakuwace Mai karfi ta shiga tsakanin su tare suke zuwa makaranta su dawo tare, kullum Haisam ke Kai su school, ko da kuwa bai da lectures yakan kaita ta idan sun tashi ya koma ya d'auko ta wasu lokutan Kuma ya jira ta har sai ta gama su koma gida. Umma da Mummy komai tare suke hatta unguwa zasuje tare suke zuwa shopping, har kauyen su Mummy tare suke zuwa. Haisam ke zaune a Cafeteria yana cin abinci,Yana jiran Ma'isha ta Gama lectures,cin abincin sa yake hankalinsa kwance yayin da d'ayan hannun sa yake Kan wayar sa, wata budurwa da baza ta haura shekaru 20 ba ta nufi inda yake, da sallama ta karasa inda yake a hankali ya d'ago kansa had'e da amsa sallamar ta, kallon ta ya tsaya yi, Murmushi tayi Wanda hakan ya kara bayyana kyakkyawar fuskar ta Tace "Sannu dai" Dai dai ta nutsuwar sa yayi ya amsa da "yauwa sannu da" "Dan Allah idan baza ka damu ba zan iya Zama anan?" Tana nuna kujerar da ke fuskan ta nasa. Yace "Eh... Eh zauna Mana" Tace "Nagode, ta jaa kujerar kana ta zauna tana Murmushi, waige waige ta Fara yi kana ta hango wata ta d'aga Mata hannu had'e da fad'in "Waiter!!!" Cikin sauri ta karaso inda take Tace "Welcome ma what will I offer you?" Kallon Haisam budurwan Nan tayi da ya maida hankalin sa Kan wayarsa, Murmushi tayi Tace "Ki bani irin abincin da yake" Haisam d'an d'agowa yayi ya kalleta ya girgiza Kai had'e da Murmushi ya cigaba da cin abinci sa, ba a d'au lokaci ba ta dawo plate d'in chicken and chips, tasa hannu ta karb'a. Ganin Haisam bai kulata ba tayi gyaran murya Tace "Ni suna na Aysha kaifa?" Ba tare da ya d'ago ya kalleta ba yace "Haisam" Tace "Wow Nice name, kai a school d'in Nan kake ne?" "Eh" "Wani department?" "Medicine" "Nima a medicine nake Amma ban tab'a ganin ka ba, Amma aji nawa kake?" "200 level" "Oh shiyasa ni a 100 level nake" Yace "Maybe" Duk maganar Nan da suke bai d'ago ya kalleta ba. "Lalle gayen Nan akwai rainin hankali duk yanda nake so muyi Hira ya kasa sakin jikinsa , dama ance kyawawan mazan Nan haka suke da girman kai" duk maganar Nan a zuciyar ta take. Bata lura ba har ya Kira Waiter ya biya su kud'in su ya Mike zai tafi, karar kujeran da ta jaa Ne ya dawo da ita daga tunanin da ta lula da murya mai d'an karfi Tace "Ina Kuma zaka?" Kallon ta yayi cike da rashin fahimta yayi d'an Murmushi yace "Gida" ya juya zai tafi tayi saurin mikewa Tace "Dan Allah ko zaka iya bani number ka?" "Number ta Kuma?" "Eh number ka" " Da fatan dai ba laifi nayi bako?" Murmushi tayi Wanda hakan yasa Beauty point d'inta ya nuna tace "A a kawai so nake muyi wata magana da kai idan bazan takura maka ba" Yace "Okay" ya Mika hannun sa alamun ta Mika Masa wayar ta, cikin sauri ta Mika masa wayar Yana sawa ya Mika Mata ya fice daga gun, bata samu damar yi Masa Godiya ba, Yar karamar tsaki tayi Tace "Anya gayen Nan zai Soni kuwa?" Komawa tayi ta zauna ta Fara cin abincin ta, Haisam kuwa zuwa yayi ya tarar da Ma'isha na tsaye a jikin mota tana jiran sa, ta had'a raai, tun daga nesa ya fara dariya don yasan ta dad'e tana jiransa tun Kan Aysha tazo dama ta kirashi yace mata sai yaga cin abinci tazo ta same shi Kuma Taki. Yana karasawa yace "Yar karamar Kanwata har an fito?" Cikin Muryar Shagwab'a Tace "Ba a sani ba" "Haba Mangana me yayi zafi wai fushi kike dani?" "Nikam ka bud'e min na shiga so nake naje gida" Kai kawai ya girgiza da kansa ya bud'e mata motar ta shiga sai turo baki take ita a lallai an 'bata mata raai, Yana shiga ya tada mota suka nufi hanyar gida, sai surutu yake Yana bata Labari bata kulashi sai da Tace Umm ko hmmm har suka Isa gida, suna Isa ta fice ta shige gida ba ta Tsaya jiransa ba kamar yadda suka Saba ba, mummy na ganin ta Tace "Ke Kuma yau ko sallamar ma baza ki iya ba" Cikin sanyin murya tace " Sorry mummy na shafa'ane" wuri ta samu ta zauna tace "Mummy ina wuni" "Lafiya daughter ya school d'in dai?" "Lafiya Lau Mummy, ina Umma?" "Tana part d'inta, yanzu ma tashi a inda kike zaune zatayi wanka zamu je saloon wanke Kai" "Yauwa Mummy Nima zan biku" "Ahhh yau Kuma ba yayan naki bane zai kai ki?" "Eh zan biku" Haisam da sallama ya Shigo mummy ta amsa har kasa ya tsuguna ya gaida ta kana ya nemi wuri ya zauna yace "Ni zan kai ki, aiki nane wannan" Turo baki tayi Tace "Bana so zanbi su mummy" Yace "In ko hakane baza ki ba don bazan bari ki fita a gidan Nan ba" Mikewa tayi Tace "To an fasa wanke Kan" ta shige d'akin ta, Haisam yace " Kin ganta ko" Mummy tayi saurin fad'in "Ah ah ba ruwan nikam kun fi kusa in sa muku baki ku kunyata ni ba dani ba" ta Mike ta shige d'akin ta itama Haisam Yar karamar dariya yayi ya bi bayan Ma'isha ya tarar da ita tana kwance a Kan gado tana kallon saman d'akin. Turo kofar yayi a hankali tasan ba mai shigowa sai shi hakan yasa ta juya Masa baya, Murmushi yayiw ya zauna akan couch d'in dake d'akin ajiyar zuciya yace "Please princess kiyi hakuri duk da ban San laifin me nayi ba, don na tabbata fushin Nan da ni akeyi, Amma duk da hakan kiyi hakuri" Hmmm kawai Tace ba tare da ta juyo ba, tashi yayi ya zauna a Kan couch d'in dake fuskantar ta, Kama baki yayi yace "Laaa ila kuka Princess? Me yayi zafi har Haka Dan Allah ki fad'a min laifi me nayi haka?" A zuciyar ta Tace "Taya za'ayi na fad'a maka cewar ganin ka da nayi da watane ya sani kuka? Taya za'a yi na fad'a maka cewar bana son ganin wata mace ta rab'e ka? Taya za'a yi na fada maka ganin ka da wata da nayi cafeteria ne ya sani kuka?" Cikin wani irin salo ya ambaci sunanta "Ma'isha!!! A hankali ta d'ago kanta ta sauke su akan kyakkyawar fuskar sa kasa jure kallon da yake mata tayi ta Kuma rufe idanun ta. Yace "Ma'isha tell me please ko Nima so kike nayi kukan?" Girgiza Kai tayi had'e da fad'in "A'a" Yace "To tashi ki zauna" Ba musu ta tashi ta zauna yace "Princess ina jinki Dan Allah me ya same ki?" Shiru tayi sai kokarin 'boye hawayen da ke idon ta take Amma ta kasa, daga bisani ta fashe da kuka Mai sauti. Haisam har cikin ransa baya jin dad'in kukan ta, musamman ma ace shine silar kukan nata ajiyar zuciya yayi yace "Dan Allah Dan Annabi na roke ki fad'a min dalilin kukan naki , bana jin dad'in ganin ki a hakan karya min zuciya yake Dan Allah kiyi shiru" Bata ce mishi komai ba ta cigaba da rera kukan ta. Mikewa yayi yace "Shikenan tunda ban kai matsayin da Zaki fad'a min matsalar ki ba na kyale ki, sannan yanzu nasan matsayina a wurin ki" har yasa hannu zai bud'e kofar d'akin yaji saukar Muryar Tace "Yaya kayi hakuri" Murmushi yayi yasan hakan ne kad'ai zai sa ta kula shi, kin juyo wa yayi jin ta nufo shi ya had'a raai kamar bai tab'a dariya ba Tace "Yaya na" Joyowa yayi Yana kallon ta , kanta a kasa tana wasa da yatsunta yace "Uhmn ina jinki?" "Kayi hakuri Dan Allah" "Hakurin me Kuma? Ni baki min laifi ba, kawai dai yanzu nasan matsayina a wurin ki Ni ba komai bane a wurin ki" "Wallahi Yaya ba Haka bane ba , wallahi bayan mummy da daddy bani da Wanda ya fika a wurin Kuma Kai ma ka sani" "In da hakan ne kamar yanda kikace ai da zaki fad'a min matsalar ki, da Allah fa nake ta had'a ki tun a hanya Amma kin ki kulani Kuma a hakan Zaki wani cewa ina da matsayi a wurin ki? In dai da Gaske ki ke ki fad'a min abinda ya same ki" Turo baki tayi Tace "Ba Kai bane" "Bani bane me?" "Ai Kaine ka shanyani nayi ta jiran ka, ga Rana" Murmushi yayi ya jaa hancin ta yace "yanzu dama don wannan ne kike uban kukan nan?" Ka ta d'aga Masa alamun eh, yace "Ai Saida nace miki kizo Kika ki zuwa, abinci fa nake ci princess, Amma kiyi hakuri na Miki laifi" yasa hannun sa biyu ya rike kunnuwan sa, Murmushi kawai tayi yace "Kin hakura? Idan baki hakura ba bazan sake kune na ba" "na hakura" Ajiyar zuciya yayi yace "Kai na gaji" "Laa d'an rike kunnen ka da kayi da bai Kai minti d'aya ba har ka gaji?" " Eh Mana da wahala fa" Dariya tayi harda tafi Shima dariyar ya shiga yi yace "Zo mu je dining nasan princess d'in yayanta tana jin yunwa" Tace "kamar ka sani Yaya" Shima yace "Kamar ka sani Yaya" Yana kwaikwayon Muryar ta. Dariya sukayi a tare suka fita, shigan su parlor yayi dai dai da shigowar mummy parlor baki a bud'e take kallon su suna Hira suna dariya Mummy Tace "Ahaaaf ni da sani za'a Rina ai, mutum ya shiga tsakanin ku kunya zaiji" sosa keya yayi yace "Mummy in gaya miki da kyar da makerkyasa na rarrashe ta" "Uhmnn to maza je ki d'auko mayafin ki mu je saloon d'in" Cikin Muryar Shagwab'a Tace "A a mummy sai kun dawo Yaya zai kaini" Mummy Tace "Kinci gidan ku ja'ira kawai Ni Zaki jawa raai" tsaki tayi ta fice a hanyar ta tafita suka had'u da umma hakan yasa suka juya kawai hannu Ma'isha da Haisam suka d'aga musu suna a dawo lafiya. Mummy Tace "Yaran Nan sun maida mutane kamar kakannin su" Umma Tace "Bakamar Haisam bama sai a hankali" Mummy Tace "Kin samin son a gaba wallahi ke Sam bakya ganin laifin yarinyar Nan ko kad'an" "Hmm Hajiya Kenan ai ni gaskiya nake fad'a ke dai da son d'a ya rufe Miki Ido bakya gani" a haka suna Hira har suka Isa parking lot already dama driver yasan da fitan su yana hango su ya fito da motar a baya suka zauna, ya Danna wa motar key suka wuce saloon. Haisam da Ma'isha suna zaune a dinning tana cin abinci shi Kuma sai tad'i yake ta mata tana ci tana dariya har kamar zata kware,kwasam wayaey sa ta fara ringing hannu yasa a aljihun rigar sa ya zaro wayan ganin sabon number yasa bai d'auka ba, sai da aka sake Kira a karo na biyu yayi picking sallama yaji jin Muryar mace ya sa shi tunanin Wace ce wannan da zakin Muryar da bai tab'a jin irin ta ba, a ransa yake ayyana hakan, ta sake sallama a karo na biyu ya amsa bayan sun gaisa daga d'ayan 'bangaren Tace "Ka gane mai magana kuwa?" Yace "A'a " a takaice. Murmushi tayi Wanda Yana iya jinsa Tace "Nice na karb'i number ka d'azu a Cafeteria d'azu, ka tuna" Yace "Eh na tuna, ya kike? " Tace "Lafiya, idan baza ka damu ba Dan In na so muyi wata magana dakai idan baka komai?" " For now am busy gaskiya sai zuwa anjima when am less busy I'll call you" Tace "promise?" " Yeah Insha Allah" "Okay sai na jika" Kiit ya katse wayar, tunda ya fara wayan hankalin Ma'isha yake kansa Tace "Yaya who is that?" Yace "A friend" Tace "Okay" Yace "Yau ina Baki Labari........ " Nan suka cigaba da hirar su Saida ta cita koshi suka koma parlor suna kallon favorite series d'insu a zeeworld Mai sun I Do. ___________________________ Ina barar addu'ar ku fansa ina cikin wani yanayin da yake hanani komai hatta typing ma shiyasa kuka jini shiru. Please Comment Share Milhat ce Yar Terawa 🍃 *DANGIN UBANA*🍃 Story & Written By Milhaart Na zo muku da littafi Mai ban tausayi,cike da abun al'ajabi,wannan salon na daban ne. *🌍MANAZARTA* *WRITERS ASSOCIATION📚🖊* *M. W. A* ```Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.🤙🏻``` https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa ____________________________________ *Wannan labarin kirkirarren labarine ban yarda a chanza min labari ba Wanda ya chanza bamu yafe ba.* Ina alfahari da rubutu,sabida alkalami yafi takobi🗡️🗡️🗡️ *BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM* Page 17and 18 Haisam da Ma'isha kallo suke hankali kwance har Saida aka Fara kiraye kirayen sallar maghriba, mikewa yayi ya kashe TV turo baki tayi Tace "Yaya meyasa zaka kashe min Kallo na?" "Lokacin sallah yayi baki ji ana Kiran sallah ne?" "To ai Ni bana sal...... " Sai kuma tayi shiru ta kasa karasa maganar dariya yaso yi sai Kuma ya matse yace "karasa abinda zakice bakya me?" Mikewa tayi da sauri ta nufi d'akin ta tana dariya kasa kasa,dariya yayi ya kad'a Kai yasa Kai zai fita knn sai ga shigowar su Mummy, d'an Jaa da baya yayi ya basu wuri suka wuce Yana fad'in "Har kun dawo?" Umma Tace "harne? Bayan munfi 2hours" Yace "Naga kunyi sauri ne ai" Mummy Tace "Son ana Kiran sallah kana Nan kuna ta aikin surutu ko?" Murmushi yayi Yana Jin dad'in yanda mummy ke nuna kulawa a garesa tamkar ita ta haife shi yace "Yanzu Masallacin nayi" Tace "To a dawo lafiya" Ya amsa da "Ameen" Sai yayi ficewar sa. Ma'isha na shiga d'aki ta kwana abinta ta d'auki wayarta tana chatting da kawayen ta, Bata fito parlor ba har sai da ta ji shigowar Daddy, da gudu ta fito tana Masa sannu dazuwa. Daddy yace "Daughter baki san kin girma bako, ya kamata ki rage Shagwab'ar nan Haka" Haisam yace "Daddy ai saima abinda ya karu, Mijin ta zai Sha wahala sosai don na tabbata ko da bayan ta haihuwane Reno biyu zaiyi" A zuciyar Tace "Zaka Sha Reno dai, don kaine mijin nawa Insha Allah" a bayyane Kuma Tace "Uhmnn daddy kace Masa ya daina tsokana ta" har da bubbuga kafar ta kamar yarinya Yar shekara biyar daddy yace "Son ka daina tsokanar ta" Haisam dariya kawai yayi baice komai ba, mummy ce ta Shigo parlor taci kwalliya sai zuba kamshi take Tace "Daga dawowar sa kun sashi a gaba da shirmen ku babu Wanda yayi tunanin karb'ae jakar sa" Ma'isha saurin karb'an jakar hannun da tayi tace "Laa sorry daddy wallahi farin cikin ganin sa ne yasa na manta" Haisam yace "Hakane mummy 2 weeks fa dad baya Nan Dole muyi kewar sa" "Naji yanzu dai ku bari idan yaci abinci ya samu ya huta sai kuyi hirar taku" A tare sukace toh. Karb'an jakar hannun Ma'isha tayi, Ma'isha Tace "Mummy ki bari Mana na kai Masa d'akin sa" "Anki d'in mijinkine ko mijina?" Ma'isha hannu tasa ta rufe bakin ta Tace "mummy abin harda gorine Kuma?" Hararar ta mummy tayi ta bi bayan Daddy da tun d'azu ta wuce d'akin sa. Zama Ma'isha tayi a Kan couch d'in dake gefen na Haisam bakin sa ya kawo dai dai kunnen ta yace "kinji abinda mummy Tace ko dama maza ki Nemo miji in yi miki aure idan bakya son Gori" Dariya tayi Tace "Na baka huka da nama yaya ka Nemo min mijin aure na maka alkawarin ko wane ne ka kawo zan aure shi" "kamar dagaske, confidence d'inki dariya yake bani wallahi kina nufin ko Mai gadi na kawo miki zaki aura? " "Da gudu ma, ai Mai gadi mutum ne kamar kowa ko?" "Shikenan tunda kince haka Zaki Sha mamaki." Dariya kawai tayi suka cigaba da kallo. Umma ce ta Shigo parlor Tace "Kun samu sana'a ku Kam, a haka za'a samu likitocin?" Haisam yace "Ai gobe ba school ne Umma Sunday ne fa ranar hutun d'an boko" " Gafara Chan ka zauna kana kallon zeeworld kamar wata mace" "Wallahi umma ba laifina bane, laifin Yar kice itace ta koya min Kallo" "nasan abinda zakace Kenan ai" wuri ta Samu ta zauna suna kallon tare. Daddy ne da mummy suka fito baka Jin abinda suke cewa Sai dariyar su kawai, Haisam kasa kasa yace "Kin gani ko princess kiyi aure ki Rika samun farin ciki abunki" "sai na fadawa Daddy abinda kace yanzu" "a a yi hakuri nayi shiru" Dinning suka nufa, Umma, Ma'isha da Haisam Suma suka wuce dinning d'in Tuwon shinkafa da miyar kuka mummy tayi yaji daddawa da citta sai nama da kifi da suke ta shawagi a ciki, suna ci suna Hira har suka gama suna gamawa Haisam ya Mike yace "Yau bacci nake ji sosai zan kwanta" Ma'isha a take ta 'bata Rai Tace "Yaya but kace min zamuyi Kallo tare fa" "Am sorry Kanwata wallahi a gajiye nake akwai gobe wuni zamuyi muna Hira kinji?" Bata so hakan ba Dole ce tasa ta hakura yayiwa su mummy sai da safe ya wuce part d'insu Yana tafiya Ma'isha itama tashi ta shige d'akin ta. Haisam na shiga d'aki ya ban d'aki ya fad'a yayi wanka ya sanya vest da d'an gajeren wandon sa ya d'ale Kan gado ya bud'e datar sa ya Fara chatting, emoji da stickers na kuka ya Fara cin karo dasu Ma'isha ta jero Masa dama yasan za'a Rina Nan ya shiga rarrashin ta suna cikin chat d'in ne bakuwar number ta kirasa. Yana picking Tace "Haba yallab'ai kasa ina ta jiran ka, nan ne ma ya tuna cewar yace zai kirata dafe kansa yayi yace "Am so sorry Aysha na d'anyi busy ne gafar ce ni" Murmushi tayi ko ba komai bai manta sunan ta ba, tace "Bakomai yallab'ai Ni da na damu da nayi magana da kai ai na kiraka" Murmushi yayi yace "Afwan ina jinki" "ummm dama ba wani abu bane ba, so nake Dan Allah ka Zama Tutor na" "Tutor dai? 'dan Ni d'in Nan bani da wannan ilimin ai Ni dolo ne fa" Yar karamar dariya tayi Tace "na amince ka koya min dolon cin naka, duk da nasan Kai ba dolon bane ba sai dai in rowa zaka min Kar na karu da kai sai na hakura" Murmushi yayi yace "Toh yaushe kike so mu Fara?" Tace "Ko gobe ma" "A a gobe Sunday ba inda nake zuwa ina gida, ki dai bari idan muka had'u Monday mayi maganar" Cikin murna Tace "Toh nagode sosai" "Bakomai sai da safe" Ya katse wayar Aysha bin wayan tayi da kallo tace "Mtssw ya katsewayar kamar shi ya Kirani" wurga wayan tayi akan gado ta kwanta ta fara sharar baccin ta dama ta Riga ta shirya cikin kayan baccin ta. Ma'isha kuwa ganin bai mata reply ba tayi tunanin ko bacci ne ya d'auke sa, ta shiga kiransa Amma busy, ji tayi kamar ta kurma ihu, cikin sanyin jiki ta tashi ta shiga wanka ta d'aura da alwala,bayan ta fito tayi shafa'i da wutiri bayan ta idar ta shiga rokon Allah da ya yaye Mata sayayyar da take Masa in shi d'in ba alhairi bane a gareta ba, in ko alhairi ne yasa ya Sota kamar yadda take son. Wayar Tace ta fara ringing tana dubawa taga yayana Yar karamar tsaki tayi Tace "wato ya gama waya da ita" Sai da ya kusa yankewa ta sa hannu ta d'aga ta Kara a kunnen ta, yace "Haba princess kin shanyani bacci Kika yine?" "a'a wanka na shigane" "Shine baki fad'a min ba?" "gani nayi kana wayar da tafini muhimmanci" " Ki daina fad'in haka princess waya nake da wata course mate d'ina" "Oh mace ce ma ko?" Yace "Eh" "Na sani ai" "Me Kika sani?" "Babu komai" " To hau online d'in mu cigaba da hirar mu" Tace "Nikam bacci zanyi kaina ke ciwo" Babu yanda baiyi ba ta hau Amma taki hakan yasa ya kyale ta,katse wayar yayi, yayi wurgi da ita Yana tsaki yace "Yau na kasa gane Kan yarinyar Nan ko me ya same ta oho" Da wannan tunanin bacci yayi awun gaba da shi. Ma'isha kuwa kasa bacci tayi, tana kuncewa sa sakawa idan har bata mallaki Haisam a matsayin miji ba zata iya samun matsala, Kila ma ta rasa rayuwar ta a dalilin hakan, Amma meyasa haryanzu bai nuna Yana sonta ba? A bayyane Tace "Ya Allah kasa Yayana Yana Jin abinda Nima nake ji akan sa, Allah yasa ba Ni kad'ai nake haukataba" a Haka har bacci ya d'auke ta. WASHE GARI Ma'isha tunda tayi sallar asuba ta koma bacci bata tashi ba har sai da aka Fara Kiran sallar azahar, tana farkawa wayarta ta fara dubawa taga missed calssy da dama, amma na haisam yafi yawa harda texts shi a tunanin sa fushi ta Kuma yi dashi. Murmushi kawai tayi ta tura Masa text *"am sorry Yaya na bacci nake , wayar na silent ne shiyasa banji ba"* Yana gani ya Mata reply da *"okay idan kin shirya ki Sanar dani Ina d'akina sai na kai ki saloon d'in"* Ta amsa reply da *"Alright"* tashi tashiga wanka,sai da tayi sallar azahar kana tashirya cikin wasu lallausar riga da siket na voyel less dark blue wanda aka mata ɗinkin tamkar ajikinta aka dinka yayinda adon jikin kayan pink ta yafa pink din mayafi da takalminta hill da kuma handbag ɗinta pink yar karama ,ta saka wayarta aciki ,Batayi wani kwalliya ba abisa dabi'arta na rashin damuwa da ɓata fuskar ta wajan ciki masa hayaniyar kwalliya ,Ta fesa turaren ta mai kamshi ta fito. Tana fitowa ta samu mummy da Umma a parlor suna Hira sannan suna Kallo sama sama Umma tace " masha Allah daughter kinyi kyau" Ma'isha kanta akasa tana murmushi tace "Nagode umma " Mummy Tace "Yau sai ina Haka?" "Saloon zani" "uhmnn" kawai Tace Tace "Sai mun dawo" Mummy kallon ta kawai tayi Umma Tace "A dawo lafiya,Allah ya tsare" Ta amsa da Ameen, part d'insu Haisam ta shiga Kai tsaye d'akin sa ta nufa,ta tarar ya gama Shima hakan yasa basu 'bata lokaci ba fita sukayi atare, sadaddiyar mota suka shiga da Alama sabuwace an wanke ta sai sheki take. Bayan sun shiga motar ya kalleta ta yace "Princess irin wannan kyawu Haka, kamar Zaki je gasar sarauniyar kyau" Turo baki tayi cikin Shagwab'a tace "Sai yanzu ka ganni?" Dafe Kai yayi yace "kefa na lura Sam bana Miki gwanin ta ko?" "Ni dai bance ba, ai tun Shiga na d'akin yakamata kace nayi kyau"for "kyau din naki ne yayi yawa baki ga sai kallon ki nake ba na kasa magana,Kuma nayi maganar baki ji bane, yanzun ma dakyar maganar ta fito" Dariya kawai tayi tana Jin dalilin kalaman sa masu sanyaya zuciya, shiyasa Bata gajiya da magana dashi bataki ace tana tare dashi ba a ko wani lokaci ba. Sunyi tafiya kusan na minti uku sai Tace "kaima fa kayi kyau sosai Yaya" "Au ramawa zakiyi? Sai yanzu Kika ganni Kennan?" "A a na Isa ramuwa Kuma, tun d'azu nake son fad'a maka cewar kayi kyau sosai Amma ya kasa fita yanzun ma dakyar sai da na dage na furta" Dariya ya Shiga yi, itama tana dariya tuki yake a hankali har suka Isa saloon ta fita shi Kuma ya zauna a mota Yana jiran ta. Fitar ta ke da wuya wayar sa ta Fara ringing Yana dubawa yaga Aysha, picking yayi bayan sun gaisa ta Fara Jan shi da Hira har ta a ka Gama wanken Kan nata suna waya da Aysha bud'e motar tayi ta zauna, yace "Aysha am sorry please zan kira ki anjima" Tace "Tohm bye" ya katse wayar. yace "Princess har kin Gama?" " yau Kuma Yaya? " "Yau Kuma me? " "To ai ka Saba cewa na dad'e ne,yau Kuma nayi sauri ko?" Dariya yayi yace "Wallahi Aysha ce ta ke ta bani dariya" "Wace ce Aysha Kuma?" "course mate d'inace" " Wato da ita yake waya Kennan jiyan ma koma wacece ke baki Isa ki rabani da Yayana ba,baki Isa ki rusa min ginin da na dad'e ina ginawa ba" take ayyanawa a ranta. Tafi yayi Tace "Na'am" "Lafiyan ki kuwa tunanin me kike haka?" "Bakomai bacci nake ji yaya" "Shopping d'in fa?" " Na fasa mu koma gida kawai" "Ikon Allah yau wa zai Mutu princess ce tace Bata son shopping" Kirkirerren Murmushi tayi yace " Your wish is my command" Ya tada motar suka bar gun. Suna Isa gida bata tsaya jiran sa ba ta bud'e motar ta fita, tarar da su Mummy ta musu sannu ta shige d'akin ta. Umma Tace "mutanen ki sun fara" Mummy Tace "Chan ta matse mu Basu da damuwa ne ko kad'an" __________________________ Please comment and share Milhat ce Yar Terawa 🍃 *DANGIN UBANA*🍃 Story & Written By Milhaart Na zo muku da littafi Mai ban tausayi,cike da abun al'ajabi,wannan salon na daban ne. *🌍MANAZARTA* *WRITERS ASSOCIATION📚🖊* *M. W. A* ```Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.🤙🏻``` https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa ____________________________________ *Wannan labarin kirkirarren labarine ban yarda a chanza min labari ba Wanda ya chanza bamu yafe ba.* Ina alfahari da rubutu,sabida alkalami yafi takobi🗡️🗡️🗡️ *BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM* Page 19 and 20 Haisam na shiga parlor cikin girmawa ya gaidasu mummy suka amsa, Umma kallon tuhuma take Masa Tace "Haisam me kayi wa 'yata?" Cikin rashin fahimta yace "Umma ce Miki tayi na mata wani abun" "Gidan ku Haisam ina tambayar ka kana maida min amsa da tambaya?" "Wallahi Umma Ni ba abin da na Mata, sai dai Kuma in sharri ta fara yi" " Wani irin sharri yarinya ta fita tana walwala da farin ciki ta dawo cikin 'bacin Rai ka dai..... " Mummy ce ta dakatar da ita tace "Ki daina shiga maganar yaran Nan wataran Zaki ji kunyane Tohm" "To ai abun ne da mamaki daga fitan su ta dawo Haka?" "Da dai kinyi shiru da kin taimaka wa Kan ki sabida kunya zakiji, Ni da ranar na shiga maganar su ba kunya tani sukayi ba, ina Nan ina goyon bayan Son Ashe ya lallab'a sun shirya, kawai nazo wucewa naji Muryar su suna Hira suna dariya tun daga Nan na fita harkan marasa kunya" Haisam yace "Ma'isha dai akwai abinda ke damin ta nayi nayi da ita ta Sanar dani taki daga bisani ma kuka tayi tamin dakyar na rarrashe ta" Mummy tab'e baki tayi Tace " Kwaji dashi" Umma Kuma Tace "Nikam ai baza taki Sanar dani ba" mikewa tayi ta shige d'akin Ma'isha ta tarar tana kuka ta kwanta ruf da ciki, Bata ma San da shigowar Umman ba. Dafe ta tayi had'e da Kiran sunan ta cikin murya Mai sanyi "Daughter!!! A firgice ta tashie ta zauna tasa hannu tana share hawayen dake fuskar ta, kirkirerren Murmushi tayi Tace "Umma kece ban ji shigowar ki ba" Ganin irin kallon da Umma take mata yasa ta sunkuyar da kanta kasa tana wasa da yatsunta Umma tace "Ma'isha me ke damun ki? Yayan ki ya Sanar dani kina cikin damuwa Kuma kin ki fad'a Masa sannan yace min kina kuka na d'auka shirmen sane Ashe da Gaske ne tunda na gane wa Ido na, me ke damun ki? Ki saki jikin ki Nima tamkar mahaifiyar kice" Murya na rawa tace * "Ba ... Babu komai fa Umma" "Baza dai ki fad'a min ba, ko kina ganin ban Kai ki fad'a min bane?" "A'a Umma har kin wuce ma, kawai ban San ta ina zan fara Sanar dake damuwata bane" "ki fad'a min ta ko ina zan fahimta Kuma Insha Allahu zamu samu mafita" "idan na fad'a mata dalilin kuka na tabbas nasan zata Sanar da Haisam sannan idan na 'boye Mata Kuma baza taji dadi ba Dole ma nasan yadda zanyi, na gwammaci nayi ta dakon soyayyar a zuciya ta har izuwa ranar da zai bud'i bakin sa yace Yana so na" Dafe kafad'ar Ma'isha Umma tayi hakan yasa ta dawo daga tunanin da take Umma Tace "Ki Sanar dani matsalar ki" "Umma...... Ina.... Ina son... " "Kina son me?" "Inaso na Sanar dake Amma this is not the right time idan lokaci yayi Zaki ji Insha Allah, Amma for now ina bukatar addu'ar ki please" "hmmm Shikenan Daughter Allah ya yaye Miki damuwar ki" "Ameen Umma" "To tashi muje parlor muyi Kallo" "Ya Haisam na parlor ne Umma?" Mikewa tayi Tace "Dama zan karb'i sako a wurin sa" "Ai na d'auka fushi kike da yayan naki" "Umma ai ni da Ya Haisam sai Allah" "Allah ya muku Albarka" Ta amsa da ameen. Suka fice, suna isa parlor ba taga Haisam ba Tace "Mummy Yaya na fa?" Wani irin Kallo ta mata Tace "Sandan kiwon sa ya 'bata" Turo baki tayi zatayi magana Umma Tace "Jeki d'akin sa maybe yana chan" Tace "To umma" da saurin ta ta fice. Mummy ta bita da Kallo kana ta maida kallonta ga Mummy Tace "Kinga abinda nake fad'a Miki ko?" Umma Murmushi tayi Tace "Na gani." Babu Wanda ya sake cewa komai suka cigaba sa kallon su. Tun daga Baki kofar d'akin sa take ji yana waya yana dariya d'an tsayawa tayi Tace "Waye Yaya samu haka?" Jin ya ambaci sunan Aysha yasa taji kamar an soketa da kibiya a kirji, shiru tayi har ta juya xata koma sai Kuma ta dawo ta bud'e kofar had'e da sallama, Yana ganin ta yace "Am Sorry zan Kira ki anjima" ya katse wayar, Ma'isha Murmushi tayi har cikin ranta taji dad'i ko ba komai tana da muhimmanci a gun sa, sai wata zuciya Tace Mata "idan Kuma 'boye Miki wani Abu yake fa?" Yace "Princess ya dai kin tsaya kina kallona ki zauna Mana" "Yaya meyasa ka katse wayar da kake yi?" "Sabida princess d'ina ta Shigo lokacinta ne ba na kowa ba" Taji dad'i sosai hakan yasa ta zauna Nan fa suka fara Shan hirar su sosai suna cikin farin ciki. Aysha kallon wayan ta ke Tace "Ya Rabbi gayen Nan zai bani wahala, a hakan zan samu soyayyar sa? Amma ba komai insha Allah sai nasan hanyar da nabi na sa ka Fara Sona ko ta wani hanya ne" *MONDAY* 7:45am Kiranta yayi a waya murya cikin fad'a fad'a yace "Wai me kike haryanzu ne? So kike na makara?" "Am sorry gani n...... " Kitt ya katse wayar cikin sairi ta fito ta bud'e motar ta shiga tana Zama bata ma rufe kofar ba ya ya tada motar tana rufewa ya jaaa motar suka nufi hanyar school kana kallon fuskar sa zaka gane ransa a 'bace yake cikin sanyi murya Tace "Yaya Dan Allah kayi hakuri wallahi na tashi da ciwon Kaine" "Dama kin tab'a rasa abin fad'a ne? Inaga ma Dole na bar driver ya Rika kaiki aini ba driver d'inki bane ba" "Yaya har abun ya kai ga Haka?" "Wuce Nan ma" "Ai Yaya naga lectures d'in naka karfe 8 ne Kuma haryanzu da sauran time" "Malama test nake dashi Kuma malamin Nan ba imani bane dashi, 8 na cika yake rufe kofa ba Mai Shiga ba Mai fita, sabida Kinga baki da lectures sai 9 yasa Kika 'bata min Lokaci" "Wallahi ba haka bane Yaya" "Hakane Mana, wallahi ki ka Kuma maimata irin haka tafiya zanyi na bar ki" "Insha Allah bazan sake ba kayi hakuri" "Da kuwa kin taimaka wa Kanki, don Kanki kika taimaka bani" "Kayi hakuri" "Naji" kawai yace Mata har suka Isa cikin makaranta babu Wanda ya ce uffan a cikin Saida yayi parking Tace "Yaya ka saki ranka Mana in ba haka ba test d'in bazai maka dad'i ba" "Kin San da hakan ai Kika bata min raai? Fita yayi a motar ganin zai iya kulleta a ciki itama tayi saurin fita jakarsa kawai ya d'auka a back sit yayi tafiyar sa ba tare da yace Mata komai ba. Ma'isha mamaki ne ma ya kamata bata tab'a ganin sa haka ba, "ko da yake ni na 'bata Masa raai zuwa anjima nasan zai huce tunda hakan ba halin sa bane ba." Haisam sauri yake sosai sabida saura minti biyu kachal time ya cika, Yana Shiga LT zaman sa kenan zai ga shigowar malami, ai kuwa yana Shiga yasa aka rufe Masa kofofin, Nan ya Shiga arranging d'insu zaman da sukayi babu Wanda zai iya magana da wani inko kayi za'a jika sanan baka Isa Kati satar amsa ba layin medicine ba wasa kwata kwata su sha Tara ne a ajin bayan mutum sama da talatin ne suka samu admission sauran tun a aji d'aya aka zubar dasu GSU Kenan ba wasa. Alhamdulillah test yayi wa Haisam dad'i mintuna 30 aka basu Amma shi a cikin sa'a ya gama cikin mintuna 20,bayan sun gama duk suka fita, wurin motar sa ya nufa jin an Kira sunan sa yayi saurin juyowa Murmushi yayi yace "Kaga manyan mutane" "Su ku Kenan ko?" Hannu suka Sha yanda samari suke Haisam yace "Ya test d'in dai?" Yace "Alhamdulillah" "Masha Allah, Allah ya bamu sa'a ya amsa da amiin. Haisam yace "Dama cafeteria zanje ban samu na karya a gida ba muje Mana" "Wallahi Nima ban karya ba muje d'in" Sai da ya ajiye jakarsa a mota kana suka wuce suna tafiya suna Hira sabida dakwai d'an tafiya daga College of medicine zuwa commercial area. Inda ya Saba cin abinci Suka nufa, as usual chips and chicken yace a kawo Masa, abokin tafiyar tasa Kuma ya ce Fried Rice suna cikin cin abincin su ya hango Aysha Wanda itama tana d'ago Kai Kennan suka had'a Ido dashi Murmushi ta sakar Masa Shima ya maida Mata. Karasowa sukayi da ita da kawarta sallama sukayi suka amsa musu, Tace "Zamu iya Zama?" Haisam yace "Bismillah Ku zauna" Bayan sun gaisa Tace "Yallab'ai wannan kawatace Sunanta mardiya a pharmacy take" Murmushi ya Wanda a ko da yaushe shine abun yinsa yace "Nice to meet you pharmacists" Ta amsa da "Nice to meet you too" Ya maida kallon sa ga Aysha yace "Yallab'iya wannan abokina ne sunan sa Farukh a medicine yake" Yar karamar dariya tayi Yallab'iya da yace ne ya bata dariya Tace "Sannu Dr Farukh" Zaro Ido yayi yace "Dr? Da saurana tukunna, cemin Farukh d'in ma kad'ai ya wadatar" "Hahaha to shikenau Sannu Farukh" Yace "Yauwa ai yafi dad'i ko? " Dariya sukayi dukkan su, suna cin abinci suna Hira, wayar Haisam ce ta Fara ringing ajiye spoon d'in hannun sa yayi, Yana picking cikin Muryar Shagwab'a Tace "Yaya" Ya amsa da Na'am "Princess" Cikin sauri Aysha ta d'ago kanta suka had'a Ido da mardiya, ji tayi kanta ya fara sarawa a ranta take maimaita sunan Princess? Shin Yana da matane ko kuma budurwa,inaa duk yadda akayi budurwar sace taya ma za'ayi ace wannan yarin santalelen Saurayi ace bayi da budurwa? Lallai aikina ya jiku zanyi fafutakan neman soyayyar sa sannan ne rabashi da so called princess d'in nasa. Haisam yace wayan sa yake hankalin sa kwance, tunda ya fara wayar bai daina Murmushi ba alamun Yana Jin dad'in wayan, yace "To princess kizo Mana ki sameni a cafeteria Sai kici abincin" Dariya yayi yace "Na Amince zan saya miki duk abinda kikaso Kuma sai kin cinye ehe." Bata d'au lokaci Mai tsawo ba ta karaso cafeteria dake dama ba wani nisa tayi ba tun daga nesa da ta hango Aysha taji gaban ta yafi a bayyane Tace "Itace na gansu tare ranar, ba shakka itace Aysha" Ajiyar zuciya tayi Tace "Koma mene ne zanji gaskiyar a yau" _____________________________ Please comment and share Milhat ce Yar Terawa 🍃 *DANGIN UBANA*🍃 Story & Written By Milhaart Na zo muku da littafi Mai ban tausayi,cike da abun al'ajabi,wannan salon na daban ne. *🌍MANAZARTA* *WRITERS ASSOCIATION📚🖊* *M. W. A* ```Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.🤙🏻``` https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa ____________________________________ *Wannan labarin kirkirarren labarine ban yarda a chanza min labari ba Wanda ya chanza bamu yafe ba.* Ina alfahari da rubutu,sabida alkalami yafi takobi🗡️🗡️🗡️ *BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM* Page 21 and 22 Tafiya take kanta a kasa, hannun ta rike yake da Yar karamar jaka Wanda bazai wuce handout biyu bane aciki, a hankali take tafiya hankalin ta kwance har ta Isa inda suke sallama tayi had'e da jaan kujerar dake gefen Haisam ta zauna. Murmushi Haisam yayi yace "Barka da zuwa the only princess in Haisam Palace" "Uhmn Yaya Kenan princess kawai ashe da saura na" "Wa ya gaya miki? Ke Kanki kin San ke ta dabance" Murmushi tayi sai Yanzu ta maida kallon ta ga su Aysha dake aikin kallon ta Murmushi tayi Tace "Sannun ku fa" Mardiya ce ta amsa da "yauwa" Ganin Aysha tayi nisa a tunani ta d'an tab'a ta, a d'an razane Tace "Yauwa sannu ya kike" "Lafiya Lau" Haisam yace "Princess meet Aysha and Aysha this is My princess bani da tamkar ta a Rayuwa" Kirkirerren Murmushi Aysha tayi Tace "Nice To meet you, to Amma ita d'in bata da suna ne? Haisam Yar karamar dariya yayi yace "Tana dashi Mana kawai dai sunan ne yayi min nauyi bana iya Kiran sa sai on special occasions" Aysha zaro Ido tayi sannan Kuma ta tab'e baki had'e da girgiza Kai Tace "oh lallai" Yace "Sai dai idan ita zata fad'a miki da bakin ta" Aysha Tace "Ya sunan ki?" "Ma'isha"kawai Tace a takaice. "Suna Mai dad'i" " Thank you" Ma'isha ta maida kallon ta ga Farukh da aikin cin abincin sa kawai yake, Ma'isha dariya tayi Tace "Haba Ya Farukh duk don Kar naci ne kake ta sauri ko?" Sai da yasa hannu ya kurb'i ruwa kana yace "Na Isa Ma'isha kawai dai naga baku da niyar gama surutun nakune kin San ance kowa da damuwar sa Ni abincin ne damuwa ta" Haisam yace "Zaka ji da shi ai" Cikin sanyin Murya Tace "Yaya My promise yunwa nake ji" "Me Zaki ci?" "Ka zab'a min komai ma nikam" "To kin San Ni abinci na d'ayane idan Zaki ci sai a kawo miki" "Ai Yaya tun bana son chips ka sa na Fara son shi" Murmushi yayi yace "Barka na kinnga ko ba komai Zaki Rika yi Mana a gida" Murmushi kawai tayi Nan da Nan yasa aka kawo Mata ta hau ci, har ya karb'i spoon d'in ya Fara Bata baki. Aysha kamar zata had'iyi ranta ta Rasa abinda yake Mata dad'i tsinta kanta tayi da mikewa ta bar wurin ba tare da Tace komai ba, mardiya ma ta bi bayan ta. Haisam kuwa bai ma San sun tafi ba , Yana Nan Yana feeding princess d'insa Saida taci ta koshi ya lura ba su Nan, kallon Farukh yayi dake Kallo a wayar sa yace "Haa'ah yaushe Kuma suka tafi?" "To ka Zama Romeo ina zaka ji tafiyar su? Duk da ma na ga Kamar sauri suke don Nima ba kulani sukayi ba suka tafi" Tab'e baki yayi ya d'aga kafad'ar sa irin halin ko in kula d'in Nan ya maida kallon sa ga Ma'isha yace "Karfe nawa zaki gama lectures d'in?" "Karfe 4" "Ni Kuma sai 6 ya zamuyi Kenan? Zaki jirani ko Zaki koma da napep don bazan barki Kiri driving ba" d'an turo baki tayi Tace "sabida me Yaya?" "Umarnin daddy ne, akan Kar na barki kiyi driving sai kin Kara girma" "Yanzun wai ni yarinya ce?" "Eh Mana sosai ma Amma..... " Farukh ne ya dakatar dashi da fad'in "Malam kana da niyar Shiga lectures d'in Nan kuwa ko kuma na tafi na Barka da kanwar ka ku gama surutu?" "A a tashi muje, princess ki jirani kinji?" Kai ta d'aga Masa alamun to basu fita ba sai da ya biya su kud'in su, a tare suka fita ta nufi Lt din da zata yi lectures Suma suka nufi nasu. 'Bangaren Su Aysha Aysha Rai a 'bace ta nufi garden d'in cikin makaranta inda d'alibai sukan zauna su Sha iska, wasu suna karatu wasu Kuma hirar su suke Maza da mata. Zama tayi ta dafe kanta da hannun bibbiyu, ji take kanta ba tsarawa Kamar zai rabj gida biyu, mardiya ce ta zauna a gefen ta tana kallon ta ba tare da tace Mata kala ba. Aysha ta d'ago kanta ta kalli mardiya kana ta maida kanta kasa cikin Muryar kuka Tace "Mardiya I need your help ki taimaka min wallahi Ina son gayen Nan har cikin Raina Dan Allah give me advice" Cike da mamaki take kallon ta tunda ta Fara maganar,Baki a bud'e ta ce" Wai ke dama dagaske son gayen Nan kike?" Hararar ta tayi Tace "Eh Mana" "ikon Allah Amma ya akayi Haka bayan ranar Asabar d'in Nan kika ce min kun had'u ko dama kin San shine?" "Ba wani sanin sa nayi ba, kawai dai ina yawan ganin sa a cafe ne tun ina ji yana burgeni har naji na fara son sa, ranar Asabar d'in ne Naji bazan iya jurewa ba na tinkare sa har na samu damar karb'an Number sa" Kad'a Kai mardiya tayi had'e da fad'in "Eh lallai gayen Nan na daban ne, nifa duk tunani na shi ya tinkare ki ashe kece, Amma wallahi ba girman ki bane ki zauna kina kuka akan na miji ba, ki dube ki fa kyakkyawa dake babu na mijin da bazai so ki ba sabida kina da duk qualities na kyau" "Hmm mardiya Kenan ai wallahi duk kyawuna yau da naga yarinyar Nan na Raina Kai na, kamar ita tayi kanta,moreover ki ga yanda yake rawar jikin akanta, alamu sun nuna Yana sonta sosai" "Gaskiya Allah yayi halitta a wurin Nan,kamar ka sace ta,Amma Ni a gani na ai wannan ba babbar matsala bace ba, kawai ki mata snatching just shot your short, Amma kamin Nan ki fara tabbatar da cewar ba Soyayya suke ba tukunna" Cikin damuwa ta maraice fuska Tace "Tayaya Kenan zanyi hakan? Guy d'in Nan fa haryanzu ba wani sake min yayi ba bare har na sa ran samun soyayyar sa" "hmm Qawata Kennan, sai kace ba mace ba ai kiransa kawai zakiyi cikin dabara irin Tamu ta mata Zaki tambaye sa" "Shikenan zan kirasa zuwa anjima insha Allah" "Yauwa ko kefe, idan Kuma bamu samu yanda muke so ba sai mu had'a shi da malamai su mana maganin sa" Wata shu'umin dariya sukayi suka tafa Aysha Tace "Shegur Qawata shiyasa nake yinki ta hannun damana" Dariya mardiya tayi Tace "Sa wasa ni d'in ai ba daga Nan ba" "Tabbas Ni shaidace" Mardiya Tace "Ya labarin mutuminki?" "Wa Kenan fa?" "Wa kuwa banda Abdul" Doguwar tsaki tayi tace "Please spare me wa ke ta tashi Yanzu?" "Hahahaha Qawata ba ji,kice Haisam ke ruling yanzu" "ai fad'a ma 'batawa,shi Yana ruling anan" ta nuna kirjin ta,ta d'aura da fad'in "Shi kuma wachan Abu ke ruling a tasa zuciyar" "hahaha ki yayyafawa zuciyar ki ruwan sanyi Qawata Haisam da kansa zai nemi soyayyar ki, alkawarina ne wannan" "Nagode Qawata" Mikewa Tayi Tace "mu tafi ko?" Cikin rashin fahimta mardiya Tace "Ina zamuje?" "Gida Man" "Lectures d'infa" "na yafe" tana kaina ta fara tafiya,bakiea bud'e mardiya ke kallonta,ganin da Gaske take ta Mike ta bi bayanyanta da d'an sauri had'e da gudu, motar Aysha suka nufa,tada motar tayi suka bar cikin school d'in, dropping d'in mardiya tayi kana ta wuce gida,dage unguwar su d'aya hatta layin su ma d'aya hakan yasa bata 'bata lokaci ba ta isa gida. Karfe 4:10pm Bayan ta gama lectures ta tsaya jiran sa har sai karfe 6 da Yan mintuna ya Zo suka Kama hanyar gida, yana driving sunan sharar hirar su. Chan Tace "Yaya Ayshan Nan a ajinku take ne?" "a'a Yar aji d'ayane?" "To how comes Kuka Saba?" "Sabawa a hakan? It's just this Saturday muka had'u fa, itace ma ta karb'i number na" "sabida me?" "Wai so take na Zama Tutor d'inta" "Tutor kuma, Kuma ya yarda Yaya?" " So kike nace Mata bazaiyu ba? Nifa Musulmi ne itama haka so hakkina ne Akan taimakawa ko wani Musulmi tunda ina da halin taimaka Mata me zai Hana naki amincewa" Iska ta hura Tace "Hakane" "Amma irin tambayoyi Haka princess am I safe?" Murmushin yake tayi Tace "You're safe Mana Yaya, kawai dai naga sai aikin kallon ka take Kuma bata ji dad'in bani abinci a Baki ba, nayi tunanin ma itace auntyn tawa" Dariya yayi yace "Haba princess ai da kece Zaki Fara sanin hakan,ni ba Soyayya muke da ita ba,hasali ma ban tab'a zaman minti 30 da ita ba" "Amma fa Yaya Na lura Kamar son ka take" "ah haba Dan Allah?" "Allah kuwa" "Lalle d'an Ni d'in Nan?" Murmushi kawai tayi yace "Well bani da wannan lokacin Yanzu idan na tashi soyayyar ma ke zansa ki nema min Matar aure" " Kamar dagaske" "Allah kuwa dagaske nake miki na rantse miki da kauyen kakana" Dariya tayi sosai Harda tafi, a Haka suna Hira har suka Isa gida. Har cikin ranta taji dad'i ko ba komai hankalin ta ya kwanta, tunda tasan ba sonta yake ba, Bata da sauran damu sai na soyayyar sa da fatan ya fahimci hakan. Suna isa gida suka tarar da su Mummy da Umma shigowar su gidan Kenan Suma, bayan sun gaisa ta wuce d'akin ta Shima Haisam ya wuce nasa d'akin, dake dukkanin su biyu suna da assignment basuyi kallon da suka Saba ba, hatta chat d'in ma basuyi ba. Haisam na zaune akan gadon sa yana browsing yaga shigowar Kira ba wayarsa kallon time yayi yaga Karfe 11:38pm a bayyane yace "Aysha da Daren Nan?" Picking yayi ya Kara a kunnen sa daga d'ayan 'bangaren tace "Barka da war haka yallab'ai" Murmushi yayi yace "Yauwa Barka dai Yallab'iya" Yar karamar dariya tayi Tace "da fatan dai ba bacci Kake ma tashe ka ba?" "umm umm ba bacci nake ba, assignment nake yi" "Oh so sorry na dame ka,duk da ma na ce ka Zama Tutor d'ina kaki ko?" "No Kar ki damu, ba ki nayi ba ai na fad'a miki idan kin shirya ki Sanar dani" " To na shirya gobe idan Allah ya Kaiimu" "To Allah ya Kaiimu" Ta amsa da "Ameen ya Allah" Yace "ya kike d'azu kawai Kika tafi ba sallama" "Uhmnn gani nayi ka fad'a lambun soyayya baka ji baka gani" Dariya yayi yace "Soyayya Kuma Ni d'in?" "Eh Mana Kai da princess d'inka harfa abinci naga kae Bata, nace lallai kud'in masoyan asaline" Girgiza Kai yayi Kamar tana gaban sa yace "Ni ba Soyayya nake ba" "Kiyayayya Kake yi Kennan?" "Hahaha a a, to Shima dai d'an uwan soyayyar ne, amma taya za'ayi nayi soyayya da Kanwata?" Cikee da farin ciki tace " Au dama kanwar kace? " "Eh kanwatace da me Kika d'auka?" "Na d'auka budurwar ka ce" "To ki ajiye Kanwata ce,ai Ni bank da budurwa ban ma tab'a soyayya ba" "Na dai ji ban yarda ba" "Allah kuwa trust me ba wasa nake Miki ba,sai dai idan ke zaki nema min Yanzu" "A a idan Kuma na nema maka waccce Bata maka ba Kuma fa?" "Zata ma yi insha Allahu" "To Insha Allah zan nema maka waccce zata dace da kai" "Da kuwa naji dad'i sosai" Nan sukayi ta hirar su kusan na mintuna 20 kana ta Masa sai da safe suka sauke wayar a tare, kwanciyar ta tayi yayin da Haisam ya cigaba da abinda yake yi. ________________________ Ba na ganin comment d'inku Please kuyi sharhi sannan kuyi sharing. Taku a kullum Milhat Yar Terawa 🍃 *DANGIN UBANA*🍃 Story & Written By Milhaart Na zo muku da littafi Mai ban tausayi,cike da abun al'ajabi,wannan salon na daban ne. *🌍MANAZARTA* *WRITERS ASSOCIATION📚🖊* *M. W. A* ```Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.🤙🏻``` https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa ____________________________________ *Wannan labarin kirkirarren labarine ban yarda a chanza min labari ba Wanda ya chanza bamu yafe ba.* Ina alfahari da rubutu,sabida alkalami yafi takobi🗡️🗡️🗡️ *BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM* Page 23&24 *...............WASHE GARI* Kamar kullum a tare suka shiga school tun karfe 7 na safe, Yau Haisam ya Riga Ma'isha Gama lectures hakan yasa ya zauna zaman jiranta a Mango garden na cikin School. Kiran Aysha ne ya Shigo wayar sa, picking yayi da sallama daga d'ayan 'bangaren ta amsa da "Wa'alaikassalam yallab'ai kana lafiya?" "Ina lafiya ke fa?" "Nima haka" "Masha Allah ka Shigo kuwa?" "Eh na Shigo" "Ok please kana ina ne nazo na same ka" "Ina mango garden" "Okay muna kusa ma gani Nan karasowa" Ya Masa da " okay" ya kashe wayan. Girgiza Kai Aysha tayi Tace "Qawata Kinga bawan Allan Nan, Yana da wani habit d'in da bana so wallahi" "Me Kenan fa?" "Bai tab'a Kirana ba tunda Amma idan na kirasa shi yake fara cutting call d'in which is very bad" ta karasa maganar kamar zatayi kuka. Mardiya Tace "It's not a big deal qawata tunda in Kika kirasa yana d'agawa Kuma yana sauraron ki ai Shikenan Kuma Nan gaba da kansa zai Rika neman ki" Huci tayi tace "Shikenan tunda kince Haka shiyasa a ko wani lokaci idan ina bukatar shawara Kai tsaye ke nake nema nasan zan samu solution" " I will always be here for you Qawata,yanzu dai tashi kije ki same shi before it's too late" Aysha tace "I thought tare zamu" "A a kaaai, kamata ai daga ke sai shi zaki fi fahimta" ta kashe mata Ido d'aya,duka Aysha ta Kai Mata ta kauce. Mikewa tayi ta Masa sai anjimu da jaddada mata idan ta gama zata kirata sai su koma gidan tare,tayi tafiyar ta, ba d'au lokaci mai tsawo ba kasantuwar LT d'in da take da mango garden ba nisa hakan yasa tayi saurin Isa inda yake. Da sallama ta karasa inda yake bayan sun gama gaisawa Nan ya mata umarnin da ta fito da handouts d'inta, Nan ya zari d'aya ya Fara mata tutorial d'in sunfi awa d'aya yana mata, Amma fa hankalin sa na Kan wayarsa minti minti yake dubawa daga bisani Tace "Akwai abinda kake jirane? Naga sai faman duba time kake" "Hmmm eh, Time nake dubawa kar princess tayi ta jirana karfe 3 zata gama lectures" Tab'e baki tayi Tace "Wai dole Kai Zaka kaita gida ne?" "Eh Mana to wa zai kaita in bani ba?" Ganin yanayin sa ya canza tayi saurin fad'in "Lallai kana ji da ita sosai Naga karfe 2 yanzu da sauran time ai" Yace "Eh gashi wayata ta kusa d'aukewa ba chaji Kuma na baro cable a gida Dana saka a mota, kar ta Kira bata same Ni ba" Ta amsa da "Hakane" Yace "Anyways mu cigaba ko?" Ta amsa da "Toh" Nan ya cigaba da Mata tutorial d'in, ganin hankalinsa yayi nisa a abinda yake koya Mata tasa hannu ta kashe wayar tasa sannan ta maida ta ajiye. Sun dad'e a zaune a gun ya d'auki wayar sa ya Danna yaga a kashe tsaki yayi yace "Damn it!!!" Tace "Lafiya kuwa?" Yar karamar tsaki yayi yace "Wayar ta d'auke" "In time ne bari na duba maka a wayata" Yace "Yauwa please duba min." Aysha na duba time taga karfe 3 da kwata Tace Masa "2:30" Zaro Ido yayi yace "Wai tun d'azun Nan 30 mints kawai mukayi?" Tace "Eh" "Lallai time baya gudu" "Ko dai ka gajine? Mu bari sai gobe?" "A a kar ki damu mu cigaba kawai." Murmushin kyeta tayi ba tace Masa komai ba ya d'aura daga inda ya tsaya. Ma'isha tafi minti 20 tana jiran sa, Kiran wayarsa take Amma switch off sai ta tuna tana da Number Farukh ta shiga dialling har kusa yankewa ya d'auka cikin Muryar ta mai dad'in sauraro Tace "Ya Farukh ina wuni?" Ya amsa da "Lafiya" cikin Muryar bacci, Tace "Am sorry kana bacci na tashe ka ko?" Yace "Eh wallah but kar ki damu ya akayi?" "Dama na d'auka kuna tare da Yayana ne" "A'a mun rabu tun d'azu da mukayi sallar azahar but yace min zaiyi wa Aysha tutorail but ki kirasa ki ji" "Uhmn number a kashe, Amma Bakomai nagode sai anjima" ta katse wayar tayi ba tare da ta ji amsar sa ba. Girgiza kai yayi yace "kishi kumallon Mata, Amma guy d'in nan don ya raina min hankali yace min ba Soyayya suke da Ma'isha ba mtss" ajiye wayar yayi ya koma baccin sa, Ma'isha kuwa Mango garden ta nufa dake tasan wurin zaman sa Kenan yawanci. Tun daga nesa ta hango su suna zaune dai dai lokacin da Aysha take dariyan sunan wani scientist da ya fad'a dariya take sosai Shima ya fara taya ta a Fili Tace "Tutorial d'in kenan" har ta nufi inda suke sai Kuma ta Canza shawara ta koma, gate na makarantar ta nufa tana fita ta tari napep ta wuce gida, ita kanta taji ta wani iri sabida shine karo na farko da ta shiga napep sannan shine karo na farko data Koma gida ba tare da Yayan ta ba. Kiran sallah da akayi ne Haisam ya Mike a zabure Aysha ma mikewa tayi tace "Lafiya?" "Kamar kiran sallah fa nake ji?" "Eh Kiran sallah ne" Ajiye Mata handout d'in yayi da saurin ya bar gun ba tare da yace mata komai ba, baki bta bud'e ta tsaya kallon sa har ta daina ganin sa bata bar mamaki ba, wa'anda suke zaune a gefen su Kuma suka tsaya kallon ta, tsaki tayi ta wurga musu harara da sauri suka kau da kansu Tace "magulmatan banza kawai Mtssw" ta d'auki Jakarta da handout d'in da Haisam ya ajiye ta bar gun. Ma'isha na Isa gida ta tarar da su Mummy suna part d'insu Umma, hamdallah tayi ta shiga d'akin ta wanka ta fara yi ta d'auro alwala bayan ta idar da sallah ta kulle kofar d'akin ta kana ta kashe wayarta ta kwanta taso yin bacci ta kasa ta dad'e a haka kamun bacci ya d'auke ta. Haisam wurin motar sa ya nufa duk a tunanin sa tana jiran sa, ganin bata Nan yace "to ina tayi ne?" Sa hannu yayi a Goshen sa yana ta waige waige bai ganta ba sai Kuma yace "Maybe bata zo ba nasan dai zata jirani" Daga bisani ya shiga Masallaci don yin sallah, har ya idar ya dawo Bata Nan Zama yayii a motar har wuri ta Fara duhu, tsaki yayi ya jaa motar yabar gun. Yana shiga gida d'akin ta ya nufa ya tura yaji a rufe, d'akin mummy ya nufa ya ga bata Nan, da sauri ya fice ya nufi part d'insu da sallama ya Shigo a tsatsaye ya gaida su yace "Mummy Ma'isha fa?" Cike da mamaki suke kallon sa Umma Tace "Lafiyan ka kuwa meya same ka Shigo a rud'e Haka?" "Umma banga Ma'isha ba, na d'auka ta dawone Kuma ban ganta ba" Mikewa Umma tayi Tace "Shirmen banza Kenan dama ta tab'a dawowa ba tare da Kai bane?" "Umma wall....... " Mummy ce ta katse shi da fad'in "Son kasan dai baza ta 'bata ba ko? Ka Kira wayar ta man" "Wallahi mummy wayata ce ta d'auke to nafi sa ran ta kirani ne bata same ni ba" Umma ce ta zaro wayar ta dake chaji ta Shiga dialling number ta Amma switch off kallon Haisam tayi Tace "A kashe" Kallon ta kawai yayi ya ma rasa abin fad'i,kana ganin sa Zaka gane Yana cikin tashin hankali, Ya dad'e a tsaye mummy Kam kallonta ta cigaba dayi yayin da Umma sai safa da marwa take tana Kiran layin Amma haryanzu a kashe. A tsawace Tace "To uban me kake jira anan? Kana ji an Fara Kiran sallar maghrib yarinyar Nan bamu San a wani Hali take ciki ba ka fita kaje ka Nemo min yarinya,Kuma wallahi kar ka kuskura ka ka dawo gidan Nan ba da daughter na ba kaji na Gaya maka." jiki ba karfi ya Shiga d'akin sa , cable d'in wayar sa ya d'auko ya fice ya fad'a motar sa, wayarsa ya zaro daga aljihun wandon sa kana ya sa a chaji, zaro Ido yayi don ganin fuskar wayar tasa da kyau a bayyane yace "15 percent to ya akayi wayar ta d'auke?" Tsaki yayi ya kunnata ya Shiga dialling number ta haryanzu a kashe, jaan motar yayi ya fita Masallacin unguwar su ya nufa yayi sallah, bayan sun idar ne ya Kama hanyar makaranta, duk inda yasan Ma'isha ke zuwa babu inda baije ba Amma Bata Nan, duk da cewar dare ne Amma Akwai student a school d'in. Haisam hankali a tashe ya Shiga motar sa ya nufi gidan su Ameerah, Ameerah qawar Ma'isha ce tun a secondary school yakan kaita gidan idan sun gama hirar su ya koma ya d'auko ta, Kiran layin Ameerah yayi da yaw Isa kofar gidan su. Mamaki ma abin ya bata sabida ba ya kiranta haka kawai sai da dalili, picking tayi bayan sun gaisa yake fad'a Mata yana waje had'e da tambayar ta suna tare da Ma'isha ta tabbatar Masa da rabuwar ta da ita yafi 2 weeks tun bikin kawar su da suka je yace "Ya Salam" Cike da kulawa tace "Lafiya kuwa? Wani abun ne ya Faru?" "Lafiya lau, sai anjima bari na wuce" "Baza ka Shigo ku gaisa da Mama ba? " "Zanzo wani lokacin ki gaishe ta" kitt ya katse wayar. Ma'isha kuwa tana chan tana ta baccin ta, da sallati ta farka ta kalli agogon dake d'akin ta taga karfe 7 saura mikewa tayi ta watsa ruwa kana ta tayi alwala tayi sallah wani uban yunwa take ji hakan yasa ta nufi kitchen food flask ta bud'e, farar Shinfa ta gani ta bud'e d'ayan taga stew tsaki tayi Tace "Mutanen gidan Nan da shinkafa nifa in ba tuwo ba duk shirme ne" plate ta d'auko ta zuba, kujerar dake Kitchen d'in ta samu ta zauna sai da ta cinye abincin Tass har ta Kara tasha ruwa tayi hamdallah, tasa Kai zata fita suka ci karo da Mummy Tace "Sorry mummy ban ganki ba ne" cike da mamaki mummy Tace "Ma'isha kece?" "Eh Mummy" "Yaushe Kika dawo?" "Tun kan la'asar" Mummy ta Shiga ta yarfa hannu Tace "Innalillahi wa Inna ilaihirraji'un Amma Ma'isha Allah ya shirye ki,Ashe dawowa kikayi Kika sa Yayan ki wahalan neman ki yanzu ga chan Umman ku ta Hana shi zaman gidan na tace kar ya kuskura ya dawo ba tare dake ba Ashe kina Nan kina ta baccin ki" Turo baki tayi tace "To ai mummy...... " "Ai mummy me ke? Ki fita daga idona Ma'isha wannan wani irin rashin hankaline, me ya sami wayar ki mukayi ta Kira a kashe?" "Kashe nayi" Kai a kasa Tana wasa da yatsunta. "Ka jimin ja'irar yarinya ki tadawa mutane hankali ba gaira ba dalili, dama kije ki Kira shi yanzu, tun d'azu yaron Nan baya gida gashi tun safe bai sa abinci a cikin saba kuka tafi makaranta ke Kuma kina Nan kin zauna Kinci abincin ki in ba mugunta ba" "Mummy kiyi hakuri Dan Allah, wallahi na Kira layin sa ban same shi ba Kuma na gaji da jiran sa shiysa,Kuma na dawo a gajiye shiyasa fa na dawo gida Amma kiyi hakuri please" "Dallah gafara ki bani wuri ko na had'a kanki da ginin Nan Mara hankali kawai" Ficewa tayi da sauri don taga alama mummy zata iya buga Kan natan ta dad'e bata ga 'bacin ran mummy irin haka ba, da gudu ta Shiga d'akinta tana matsar kwalla, tana kunna wayar shigowar kiran Haisam ne ya shigo. Haisam a kishingid'e yake a cikin motar, parking motar yayi a kofar gida ya kasa shiga cikin gida don bai San irin masifar da zai Sha a gun sa ba, ta dad'e baiga umman sa a cikin irin 'bacin ran Nan ba. Jin Kiran ya Shiga ya zauna cike da kulawa yace "Princess Lafiyan ki kuwa? Kina ina nazo na d'auke ki?" Cikin sanyin murya Tace "Ina gida" Cike da mamaki yace "Gida wani gidan? Yaushe Kika dawo?" "Gida man Ya Haisam akwai wani gidane bayan namu? Kuma tun kan la'asar nake gida" Kashe wayar yayi, yayi horn Mai gadi ya bud'e Masa, Yana Shiga ya kashe motar ya fita ba tare da ya Kai motar parking lot ba, ya shige cikin gida da sauri, d'akin ta ya nufa, kofar d'akin ya tura da d'an karfi ganin ta Akan gado ya d'an ji sanyi a ransa sai Kuma ya fice daga d'akin tana Kiran sunan sa yaki kulata. *FEDERAL LOW-COST* Ayra kwance take Akan lallausar katifan ta, da sallama daddyn ta ya shigo tana ganin sa ta tashi Tace "Sannu da zuwa daddy Ashe ka dawo?" "Eh Yar daddy na dawo tun d'azu mummyn ki Tace min kina school, ya school d'in dai?" "Lafiya Lau daddy" "Komai normal ko?" "Eh Daddy" "Masha Allah, to ya maganar mu ta kwana? Da fatan kin Fara aikin da na saki?" "Hmm daddy Kennan ka kwantar da hankalin ka alkawari na maka sai na Kai makiyin mu kasa ko ta wace hanyance Kai dai kawai ka tayani da addu'a" "I trust you Yar daddy, I trust you shiyasa na saki wannan aikin sabida nasan Zaki iya but mind you kibi a hankali kar kaikayi ya koma Kan mashekiya" "hahaha insha Allah ba za'ayi hakan ba daddy your girl is very smart" "Allah ya dafa Miki" "Ameen daddy nagode, Ina tsarabata?" "Yana Nan Zo muje ki karb'a" Cike da murna ta Mike ta bi bayan sa. Bayan ta karb'o ledan da ya Mika ma ta ta nufo d'akin ta, ji tayi an Kira sunanta cikin sauri ta juya don ganin Wacce ke kiranta ganin mahaifiyar Tace tayi Murmushi Tace "Na'am Mamy" "Zonan ina da magana dake" tana Kai Nan ta shige d'akin ta Ayra ma tabi bayanta. __________________________ Please comment sharhi, ku duba yawan typing da nayi Amma wasu thanks kawai nake Samu please kuyi min sharri sannan kumin sharing. Milhaat ce Yar Terawa _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._ *DANGIN UBANA*🍃 Story & Written By Milhaart Na zo muku da littafi Mai ban tausayi,cike da abun al'ajabi,wannan salon na daban ne. *🌍MANAZARTA* *WRITERS ASSOCIATION📚🖊* *M. W. A* ```Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.🤙🏻``` https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa ____________________________________ *Wannan labarin kirkirarren labarine ban yarda a chanza min labari ba Wanda ya chanza bamu yafe ba.* Ina alfahari da rubutu,sabida alkalami yafi takobi🗡️🗡️🗡️ *BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM* Page 25&26 ..................Da gudu tabi bayansa , ya nufi part d'insu da gudu ta Sha gaban sa "Yaya Dan Allah ka saurare Ni" Kallon ta ya tsaya yi kamar zai tanka mata sai Kuma ya kauce ya Shiga cikin gida da sauri, d'akin sa ya nufa Yana Shiga ya sa key ya rufe kofar Yana ji tana Kiran sunan sa had'e da bubbuga kofar tana fad'in "Yaya Dan Allah kayi hakuri wallahi kuskure aka Samu, bazan sake ba" Umma jin Karan buga kofa ta fito daga kitchen cikin sauri hannun ta d'auke da cokalin Miya alama tana girki ne, kofar d'akin Haisam ta nufa ganin Ma'isha na bubbuga kofar tana kuka Tace "Daughter lafiya? Ina Kika Shiga ne Kika tada Mana hankali iye?" Cikin kuka tana share hawayen da ke sauka a kuncin ta Tace "Umma ina Nan fa tun d'azu" "Ban gane kina Nan tun d'azu ba, bayan Haisam shi kad'ai ya dawo Kuma yana neman ki, hankalin mu ya tashi sosai sabida a tare kuka Saba dawo wa" "Umma da na gama lectures nazo inda yake ajiye motar sa, nayi ta jiran sa ban gan sa ba, Kuma na Kira layin sa a kashe a tunani na wani abun yake na shiga neman sa kawai sai na ganshi da wata suna hi....... " kukane yaci karfinta ta kasa karasa maganar dake bakin ta. Umma ruko hannun ta tayi suka dawo parlor,zaunar da ita tayi ta sa ta a gaba tana kallon ta , ita ko Ma'isha kukan ta to ta Rai rawa "lallai abinda nake zargi ya tabbata Soyayya ce a tsakanin yaran Nan tunda gashi har kishi take" zancen zuci take A bayyane Kuma gyaran murya tayi Tace "Daughter ki daina kuka wa ya gaya miki ana wa na miji kuka kiyo shiru ki daina kuka sai ya raina ki,kuma ma naga ai shi ya Miki laifi so shi ya kamata ya baki hakuri ba ke ba." Cikin shesshekar kuka Tace "A'a umma Ni na Masa laifi, da ban jira shi ya gama abinda yake ba, ni nayi tunanin kashe wayar sa yayi Ashe ba chajine, Kuma ku ma na tada muku hankali Dan Allah kuyi hakuri" ta karasa maganar tana kuka Mai tsuma zuciya. " Yi shiru daughter yi shiru tunda kin dawo ai Shikenan, duk tunanin mu wani abun ne ya same ki har shi kanshi Haisam d'in ya damu don yafi kowa ma damuwa 'bacin Raine kawai Amma zai huce ki daina kukan haka, zo muje kitchen ki tayani aiki." Riko hannun ta Umma tayi suka nufi kitchen, Nan ta Fara Taya ta wanke wanke da sauran abubuwan da ya dace. Haisam kuwa tunda ya Shiga cikin d'akinsa ban d'aki ya fad'a ya kunnawa kansa shower ba tare da ya cire kayan jikinsa ba, tsantsan 'bacin Rai da Jin haushin abinda tayine ya sa shi hakan, sannan ya kunna shower d'in ne don kar yaji kukanta, sabida bazai iya jure Jin kukan ta ba, Dole ne ya horata. "Ayra kiji tsoron Allah ki fad'a min abinda kuke shiryawa da mahaifinki, Ayra Ina guje miki abinda zai je ya dawo" "Uhmn Umma Kenan Amma kin San Daddy bazaiyi abinda zai cutar dani bako?" "Hakane nasan da hakan Amma ina so ki fad'a min abinda kuke shiryawa" "Mamy kiyi hakuri bazan iya fad'a miki ba , sabida daddy fa gargad'i yamin akan kar na kuskura na sanar da kowa Shirin mu" " Amma ai ni uwarkice ina da hakki Akan ki" "Shima Kuma yana dashi a kaina, please Umma ki fita daga cikin maganar nan, daddy yaki fad'a miki ne sabida yasan baza ki bada had'in Kai akai ba" " Hakan shi zai tabbatar da tsiya kuke Shirin aikatawa, ina so duk abinda zakiyi a rayuwar ki sa tsoron Allah a zuciyar Ayrah, shifa rayuwar Nan gajera ce, mahaifin ki bazai tab'a fahimtan hakan ba sabida shi na mijine ciwon 'ya mace na 'ya mace ne" Mikewa Ayrah tayi tare da fad'in "Kar ki damu Mamy nasan Kina Sona Baki son abinda zai cutar dani insha Allah Babu abinda zai sameni" "Ayrah Ni ba take nake ba, in tunanin abinda kuke Shirin aikatawa nee, Kar ki manta Haisam d'an uwan kine mahaifiyar sa Kuma kamar uwa take a gare ki, kamata ai idan Kika ga wani zai cutar dasu ki Kare su Amma ke da kanki?" Dafe kanta tayi Tace "Ya Rasullullah, Mamy wai wa yace miki cutar dasu zamuyi after all haryanzu ban shirya abinda nake sonyi ba, amma wallahi sai ya d'an d'ana kud'ar sa na wulakanta min mahaifi da yayi" tana Kai Nan ta d'auki ledar ta da ta Shigo dashi ta fice daga d'akin. Mamy Tace "Allah kana gani nayie iya bakin kokari na wajen ganar dasu Kuma sunki saurarata Allah ga bawan ka Nan Haisam bawan Allah da mahaifiyar sa ka kare su daga sharrin su, sannan ka Kare Musulmi a duk inda yake, ya Allah ka Shiga tsakanin mugu da na gari" Ni ko na amsa da ameen. Da guda na koma gidan su Haisam don ganin Wace wainar ake Toyawa. Bayan Umma da Ma'isha sun gama girki suka zauna zaman ci, Umma da kanta taje ta Masa magana Akan yazo suci abinci yace Mata ya koshi, ta dawo abinta Ma'isha kuwa duk yanda take son Tuwo ta kasa ci , gashi Nan tuwon shinkafa sukayi da Miyar alaiyahu yaji gyad'a sai zuba kamshi yake. Har karfe 9 Haisam yaki fitowa hakan yasa tayi wa Umma sai da safe ta koma part d'insu. Mummy da Daddy ta tarar a parlor ta musu sannu ta Shige d'akin ta Bata zauna sukayi Hira ba kamar yadda suka saba, gyara Zama daddy yayi yace "Hajiya baki lura ba kamar yarinyar Nan akwai abinda ke damin ta" "Na lura da hakan ya wuce ita da Yayan nata?" "hmm Haisam da Ma'isha Kenan wannan karon Kuma me ya Faru" Nan mummy ta Sanar dashi abinda tayi, tsaki yayi yace "Ni kaina ta 'bata min Rai banji dad'i ba bare shi da akayi wa, ko da yake zasu shirya kansu" Mummy Tace "Sanin hakan ne yasa ban Shiga cikin maganar tasu ba, sun fi kusa" Nan suka cigaba da kallon su suna Hira, daga bisani suka kashe TV suka koma d'akin su. "Allah kawata kice kin kuntata mata yau?" "Trust me mana, nice fa Kuma kin San me abun burgewar?" "A a sai kin fad'a" "A lokacin da na kashe wayar naga kiranta ya fara shigowa na kashe , bayan Nan kusan thirty minutes sai na hango ta tsaya tana kallon mu sai ta juya ta tafi" Wata irin shu'umin dariya Mardiya Tace "That's my girl idan kina haka Zaki Shiga tsakanin su a saukake ba tare da sun gane ba" "Hmm ke dai bari zan so da Kinga fuskar ta d'azu Amma Anya Qawata yarinyar Nan ba son shi take ba kuwa?" "Haba ke kuwa ya za'ayi ta so shi bayan d'an uwan tane?" "Ina ta tunanin hakan Amma zan Kara tambayar sa nayi don ina tunanin na uwa d'aya uba d'aya suke ba, babu yanda za'ayi suna uwa d'aya uba d'aya su shaku har haka" "Da wannan ma to ki kirashi Mana tunda kuka rabu kunyi waya kuwa?" "A a 'bata min Rai yayi Kinga wani saurin da yake ya barni a gun kamar wata wawayi yasa aka tsaya kallona" "Fushi fa ba naki bane ki kirashi kawai, don na tabbata tana fushi dashi Kinga kin samu damar waya dashi ko ba komai zaiji dad'i" "Wannan hakane, bari na kirashi" Sai da safe sukayi wa junan su, Aysha wanka ta Shiga abinta Akan in ta fito tazo kwanciya sai ta kirashi. Haisam har karfe goma ya kasa bacci sai juyi yake , Yana ta jiran Kiran Ma'isha Amma Bata kirasa ba a bayyane yace "wato ma baza ta iya Kirana ba ta bani hakuri bayan tasan tamin laifi" Yar karamar tsaki yayi ya d'auki wayar sa ya Shiga kiran Aysha, fitowar ta Kenan daga wanka jikinta sanye yake da bath robe, Murmushi tayi Tace "Alhamdulillah" Picking tayi cikin sanyin Murya ta Masa sallama ajiyar zuciya yayi ya amsa kana ya Shiga Bata hakuri Akan tafiyar da yayi ba tare da yayi Mata sallama ba, ta nuna Masa ba damuwa. Nan tayi ta jaan shi da Hira har ya manta da Yana cikin 'bacin rai, suna cikin wayar ne yaji shigowar wani Kiran dubawa yayi Yana ganin sunan *Princess* yayi Yar karamar tsaki. Aysha Tace "Lafiya kuwa ya da tsaki?" Yace "Wani ne yake ta damina da call" "To ka d'aga Mana" "Kar ki da mu it's not important, Uhmn kina bani labari" Yar karamar dariya tayi Tace "Yauwa bayan na gama......" Nan ta cigaba da bashi labarin shimen ta shi Kuma ya biye mata, har wayar ya Kai awa d'aya yanke ya Kuma kiranta suka cigaba da hirar su, Ma'isha Kuma ta Kira yafi sau ashrin idan taji yana waya sai ta katse, har karfe Sha biyu na dare suke waya jin ta Fara hamma ya mata sai da safe ya katse wayar missed call 57 na Ma'isha ya gani da message guda d'aya _"Yaya Dan Allah kayi hakuri, na yi ta jiran ka baka Zo ba Kuma wayar ka akashe bayan naje neman ka Kuma naga Kuna Tutorial da Aysha shiysa na dawo gida don kar na katse ku am sorry please"_ Bayan ya gama karantawa tsaki yayi ya ma kashe wayar Baki d'aya ya yi baccin sa, Ma'isha ta sake Kira taji switch off kukane Mai karfi ya kwace mata tana fad'in "Shikenan Shikenan dama na San Yaya ba so na yake ba ni kad'ai ce nake hauka na, insha Allah daga yanzu na cirewa kaina soyayyar ka" Kasa bacci tayi yanda taga rana haka taga dare, idan tayi kukan ta gajie sai tayi shiru tana tuna abinda ya mata Kuma sai ta fashe da kuka a Haka har gari ya Waye, tana Jin an Kira sallar asuba ta Mike tayi wanka sannan tayi alwala, bayan ta idar da sallah ta nufi kitchen breakfast ta d'aura bayan ta Gama ta dawo d'akin ta ta Fara Shirin school. Bayan ta gama ta d'auki Jakarta ta fice daga d'akin, dinning ta nufa ta tarar da su Mummy da Daddy na karyawa cikin girmamawa ta gaishe su suka amsa. Ta sa wa kanta abincin ta hau ci bayan ta gama ci ta musu sai ta dawo, tayi ficewar ta Mummy da Daddy kallon junan su sukayi yace "Haryanzu fa Basu shirya ba" Mummy Tace "zasu shirya don na tabbata yana waje yana jiranta" Haka kuwa akayi tana fita ta hangosa a mota Yana jiran ta, Kuma waya yake hankalinsa kwance da kamar baza ta Shiga ba sai Kuma ta fasa ta bud'e gaban motar ta Shiga Kallo d'aya ya Mata ya cigaba da wayar sa. Ya d'auki tsawon minti uku Yana waya kamun Nan yace "karfe nawa Zaki Shigo?" Daga d'ayan 'bangaren ta ce "Karfe 4,kaifa?" "Ni bani ma da Lectures yau" Cikin wani irin murya Tace "Yau bazan ganka ba Kenan?" " Me zai hana idan kina son gani na zaki ganni, Kuma kinsan Dole na Kai princess makaranta" "Albarkacin ta zanci Kenan" "Umm umm ko don ke zan Shigo ai idan kin bukaci hakan" Murmushi tayi Tace "Nagode Amma yallab'ai uwa d'aya uba d'aya kuke da ita ko naga Kuna Kama?" "A a Yar Baffana ne" "oh Masha Allah ka gaida min ita sai na Shigo d'in" " Okay bye" Ma'isha tana Jin su kamar zuciyar ta zata fashe Amma tayi kokoran saita kanta, ganin ya tada motar Tace "Ina kwana?" Ya amsa da "lafiya" kawai yace mata a takaice, yasa wa motar key suka wuce makaranta. _______________________ Please comment and share Milhat ce Yar tarewa _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._ 🍃*DANGIN UBANA*🍃 Story & Written By Milhaart Na zo muku da littafi Mai ban tausayi,cike da abun al'ajabi,wannan salon na daban ne. *🌍MANAZARTA* *WRITERS ASSOCIATION📚🖊* *M. W. A* ```Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.🤙🏻``` https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa ____________________________________ *Wannan labarin kirkirarren labarine ban yarda a chanza min labari ba Wanda ya chanza bamu yafe ba.* Ina alfahari da rubutu,sabida alkalami yafi takobi🗡️🗡️🗡️ *BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM* Page 27&28 _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._ _Continuation.............._ Ma'isha ganin har sun Isa bai kulata ba cikin Murya kamar zatayi kuka Tace "Yaya yanzu Dan Allah baza ka kulani ba? Duk hakurin da nake baka baza kayi hakuri ba tsakani da Allah, bayan Kuma Kai ne kamin laifi" Kallon kin Raina min hankali ya Mata sannan yace "Ni ne ma nayi Miki laifi?" "Eh Kaine" A dai dai suka Shiga School d'in sai da yayi parking kana yace "Uhmn ina jinki laifin me na miki?" "Kasan time d'in da zan gama Lectures sannan ka kashe wayar ka bayan Nan Kuma kaje ka zauna da yarinyar Nan kana hiran ka hankali kwance ka ma manta dani" ta karasa maganar tana matsar kwalla. Murza goshinsa yayi ya ce "Amma meyasa baki min magana ba?" Bud'e kofar motan tayi Tace "Haka kawai" ta rufe kofar motan da d'an karfi yayi Kara har Saida yayi saurin rufe idon sa, hatta mutanen da ke tafiya da Wanda ke zaune suka kalli inda suka jie karar wasu suna magana kus kus. Haisam kuwa fita yayi daga makarantar Sai da ya daidai ci lokacin da Aysha zata Shigo ya dawo,Bayan sun had'u suka Shiga hirar su har ta manta da wani abu Wai shi Lectures, ganin karfe 6 ya kusa yace ta tashi ta wuce gida maghrib ya kunno Kai, ba musu tayi yanda yace. Har wurin motar ta ya raka ta sai da ta Shiga ta tada motar ya bar gun ya d'aga mata hannu ya nufi gun motar sa, daga nesa Ma'isha ta hango su girgiza kai tayi a tare suka nufi wurin motar, zagayo wa yayi ya bud'e mata ta Shiga ta zauna sannan ya rufe, kana yanzagaya Shima ya Shiga ya tada motar suka wuce gida. *AFTER 1 WEEK* Wata shakuwace mai karfi ta Shiga tsakanin Aysha da Haisam, yayin da tsakanin shi Ma'isha ina kwana ina wuni ne kawai. Wata ranar lahadi, ta shirya ta Sanar da Mummy zata gidan su Ameerah Mummy ta mata fatan a dawo lafiya sannan ta jaddada mata kar ta dad'e, Haisam ta hango a garden d'in gidan kanta ta kawar kamar bata gansa ba, gun Driver ta nufa ta umurce shi da ya d'auko mota ya Kai unguwa, cikin sauri ya d'auko yayie parking ita kuwa ta Shiga gidan baya. Haisam kallon ikon Allah yake a bayyane yace "Wato yarinyar Nan ta ganni Amma tayi kamar bata ganni ba, Kuma ma ina zata je da Rana tsaka haka?" Ganin ba samun amsa zaiyi ba ya zaro waya ya kirata. Tana ganin call d'in tsaki tayi ta kashe wayar ma gaba ki d'aya, Haisam bin wayar sa yayi da kallon ganin ta danna Masa Line busy,ciza leb'en sa yayi,ya Shiga cikin d'akin sa ya d'auko key d'in motar sa ba fice daga gidan,basu d'au lokaci Mai tsawo ba suka Isa, sai da ta fita ta waigo ta kalli driver Tace "Baba kabiru kar ka manta karfe biyar Zako d'aukana" A d'an rutsune yace "Inshallah rankashidad'e, karfe hud'u da rabi anan zata same ni" Murmushi tayi Tace "To sai anjima" Ta shige ciki. Ma'isha ne zaune a Kan gadon Ameerah suna kallon juna, tana kwararo Mata bayani, sai da ta gama bata labarin duk abinda le faruwa tsakanin ta da Haisam kana ta fashe da kuka mai cin Rai. Ameerah taji tausayin kawar tata sosai, ta Shiga rarrashin ta har sai da tayi kuka mai isan ta don kanta tayi shiru. Ajiyar zuciya Ameerah tayi Mai d'an sauti tace "Isha gaskiya Yayan ki bai kyauta ba tun ba yau ba nake fad'a miki kin nunae damuwa sosai akan shi na miji ba a mishi haka, in fact ma d'an Adam haka yake idan ka nuna masa ka damu dashi sosai sai ya d'auka duk duniya baza ka tab'a samun irin sa ba ko Kuma baza ka iya Rayuwa babu shi ba, Ni shawarar da zan baki shine ki cire Shi a ranki alamu sun nuna Yana son So Called Aysha d'in Nan, Don iya abinda Kika fad'a min Haisam a matsayin kanwa ya d'auke ba masoyayi ba" Murmushin takaici Ma'isha tayi Tace "Nayi kokarin fahimtar hakan Ameerah Amma na kasa ke Kanki kin sani tun muna makaranta nake crushing d'insa, in fact tun muna primary, Har Saida muka Isa SS 3 da ya bani amsar tambayar da ake kana na Samu damar Shiga rayuwar sa, yanzu Kuma kice na rabu dashi?" "To Isha fad'a min me zakiyi idan baki hakura ba? Cutar dake zaiyi Isha, na damu da lafiyar ki" "Gaskiya Ki kawo wata shawarar banda wannan rabuwa da Haisam tamkar rabuwa da numfashi nane" "Hmm isha Kenan" mikewa Ameerah tayi ta nufi Yar karamar fridge d'in dake d'akin ra d'auko ruwa Mai sanyi da Hollandia, had'e da glass cup ta dawo ta zauna Tace "wanne zan sa Miiki?" "Hollandia" kawai a takaice zuba mata tayi ta cika cup d'in kamar zai zuba ta Mika Mata, Ma'isha tasa hannu ta karb'a, bismillah tayi ta kafa a bakin ta bata sauke ba har sai da ta shanye Tass. Ameerah Tace "Should I add more?" Cike da kulawa Girgiza Kai Ma'isha tayi had'e da fad'in "No Thanks" Tissue ta zaro a jakar ta, tagoge bakin ta. Ameerah Tace "As I was saying isha, rabuwa da Haisam is the best solution, cos Haisam baya son ki ya kamata ki gane hakan" Kallon ta Ma'isha tayi sai Kuma ta sunkuyar da kanta kasa. Dafe kafad'ar tayi Tace "Isha!!" 'dago kai tayi a hankali ta na kallon ta, Tace "I know how you feel son Wanda baya sonka babbar matsala ce but you can't force him to love you" Cikin Murya kuka Tace "Kin fad'i gaskiya, Dole na rarrashi zuciya ta" sai Kuma tayi Murmushi bayan hannun ta tasa ta share hawayen dage gangaro wa a fuskar ta d'aya nabin d'aya kana ta d'aura da fad'in "Insha Allah zan cire Ya Haisam a raina please ki taya ni da addu'a" "Insha Allah dear" Ma'isha Tace "Kwana biyu ba mu had'u ba ba wani gulma ne?" "Hahaha Allah ya shirye ki Isha kina cikin damuwar ma baza ki Canza Hali ba?" "Ahhh ya zanyi to? Kefa Kika ce min na cire shi a raina to it starts from now" Dariyar ta Kuma yi Tace "Akwai su dayawa har sai kin gaji da fatan wuni zakiyi?" "Eh sai 5 zan koma" "Kai Amma naji dad'i wallahi" Murmushi kawai Ma'isha tayi bata ce komai ba. Ameerah Tace "Yauwa mutumin ki kullum sai ya tambayeni ke" Cike da rashin fahimta Tace "Wa Kenan?" "Ma'aruf Mana" "Mtswww wai dama yana Nan? Ni wallahi na ma manta da wani ma'aruf" "Hmm to na tuna miki, please give him a chance" " I can't dallah,Ni yunwa nake ji ma me Akwai?" Girgiza kai Ameerah tayi ta fahimce ta so take ta kawar da maganar sabida tun shigowar ta Tace zata kawo mata abinci tace a koshe take, riko hannun Ma'isha Ameerah tayi had'e da fad'in "Zo muje kitchen mu duba me suka girka don dama Nima tun breakfast ban ci komai ba" Nan suka nufi hanyar kitchen, a hanyar su ta Shiga kitchen suka ci karo da mahaifiyar Ameerah har cikin girmawa wa ta gaida ta ,ta amsa ba yabo ba fallasa, suka shige cikin kitchen. Haisam kuwa Yana fita gidan su Farukh ya nufa, a d'akin Farukh na hango sa yana zaune hannu a goshin sa yana murzawa Wanda hakan ya zame Masa jiki da zaran ransa a 'bace yasa hannu yayi ta murza goshinsa a Haka har ya huce. Farukh yace "Look nifa banga laifin yarinyar Nan ba, Bayan Kaine ka mata ba dai dai ba Kuma ta baka hakuri sannan ka nuna Mata Kai d'an iskane" Gyara zaman sa yayi kana yace "Jiman ya za'ayi na fad'a maka matsala ta Kuma na tsaya kana goyon Bayan ta?" "Ba goyon Bayan ta nake ba,Ina dai fad'a maka gaskiya ne, yarinyar Nan fa son ka take Amma ka kasa gane hakan" A zabure ya Mike yace "so bangane tana Sona ba" Shima farukh mikewa yayi ya ce "Eh Mana baka lura da hakan ba,kishine yake cin Ma'isha" Yar karamar dariya yayi yace "No No it can't be ba so na take ba nifa Yayan tane" ya koma ya zauna. "Eh kai Cousin Brother d'inta ne like you told me and Akwai aure a tsakanin ku,Kuma kaima kana sonta baka gane hakan bane haryanzu" "Yes she is my cousin but,bazan tab'a son Ma'isha ba, a matsayin Kanwata na d'auke ta wallahi Bayan hakan babu komai a raina,And wani abunda baka sani ba,ina ji na Fara son Aysha" Zama farukh yayi yace "nasan za'a Zo Nan, Amma Ni Kam am not in support gaskiya Wai Aysha mtsww" "Me Ayshar tayi bata had'u bane? Ko tana da wani mugun Hali Wanda Ni ban sani ba?" " NO NO ko kad'an kyakkyawa ce Kuma na lura kanta na d'an rawa ba kamar Ma'isha ba,Gata kyakkyawa,ga sanin ya kamata sannan Bata da rawan Kai" "Nifa Kuma a hakan nake son kayana,idan Kuma kana son Ma'isha ne zan maka jagorawa har wurin daddy" "Ai da kuwa na Rika sa maka Albarka har karshen rayuwata in dai na mallaki Ma'isha a dalilin ka,Amma bazan iya son maso wani ba so count me out" "Shirme kayi rawa kayi kid'a duk Kai kad'ai" mikewa yayi yace "Tashi muje Masallaci daga chan zan wuce gun habibaty" Dariya Farukh yayi yace "Wata sabuwa inji yan cha-cha wai har an Canza ma Aysha suna?" "sa wasa" yayi maganar yana shafa kirjin sa,Yana jin kansa a sama. Tab'e baki Farukh yayi yace "Nawa Ido Allah sa kar kazo daga baya kana da na sani,Ni dai bata min" " Ni Kuma tamin" Yana kai Nan yayi hanyar fita har ya bud'e kofar ya waigo yace "gwamma ka fara sonta sabida she is my wife to be idan ka gama Kallo na ka same Ni a waje." Yayi ficewar sa da d'an gudu Farukh yabi bayan sa. Bayan sun idar da sallar la'asar ya Kira Aysha ya Sanar da ita yana hanyar gidan su, da kwatancen ta ya kai kansa gidan su, abinka da unguwar manya bai Sha wahala ba ya Isa kofar gidan su a GRA. Har cikin gidan ya Shiga yayi parking motar sa,kujera tasa a ka fito musu dashi suka zauna ta sa aka jera Masa kayan shashaye da fruits ruwa kawai yasha Nan ya fara kwararo mata da abinda ke zuciyar sa, Aysha ba 'bata lokaci ta karb'i bukatar sa,Hira suka Sha sosai sai har Saida ya ji an fara Kiran sallar maghrib ya Mike ya yi Mata sallama,har wurin motar sa ta raka shi Yana fita ta koma cikin gida zuciyar ta fal farin ciki. Ma'isha hira suka Sha sosai karfe 5 saiga mallam kabiru ji sukayi kamar kar su rabu, har jikin mota ta raka ta, da tabbacin Sunday Mai zuwa Ameerah zata Zo gidan su, Nan ya tada motar suka wuce gida. Isowarsu yayi dai dai da Shigowar Haisam gidan, Zama yayi a motar Yana kallon ta, ta ganshi Sarai su Amma tayi kamar bata gansa ba ta shige cikin gida, kitchen ta Shiga ta tarar da Mummy da masu aiki suna girki tana supervising ta baya ta rungumeta had'e da fad'in "Mummy na, na dawo" Mummy dariya tayi Tace "Daughter so kike ki karyani ko?" Sake ta tayi had'e da fad'in "A'a mummy na Isa, idan na karyaki ina zan sa kaina?" "Ina fa zaki zauna da Umman ki da Yaya ki da Daddyn ki" Rufe Mata baki tayi da hannun ta Tace "Yi shiru mummy bana son kina fad'in hakan" "Nima zolayar ki nake Ma'isha" "Yauwa, Mummy naga kuna ta aiki daddy zai dawo ne?" "Eh Kuma zaiyi baki shiyasa" "Gaskiya daddy Kwanan nan baya Zama baya yin sati a gida fa" "Aikin Kenan sai dai mu bishi da addu'a" "Allah ya taimaka Masa, ya dafa Masa" "Ameen daughter je ki Samu kiyi sallah ki Zo ki tayani" Ta amsa da to ta nufi d'akin ta Tora kofar tayi a hankali, wurin ajiye takalmi ta nufa ta cire takalmin ta sannan ta rataya jakar ta juyowan da zatayi ta hango mutum a kwance a Kan gadon ta, dafe kirji tayi tana ambatan "Innalillahi wa Inna ilaihirraji'un" _______________________ Please comment and share Na kusa na Fara removing marasa comment, and please idan na cire ki kar kiji haushina Milhaat ce Yar Terawa 🍃*DANGIN UBANA*🍃 Story & Written By Milhaart Na zo muku da littafi Mai ban tausayi,cike da abun al'ajabi,wannan salon na daban ne. *🌍MANAZARTA* *WRITERS ASSOCIATION📚🖊* *M. W. A* ```Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.🤙🏻``` https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa ____________________________________ *Wannan labarin kirkirarren labarine ban yarda a chanza min labari ba Wanda ya chanza bamu yafe ba.* Ina alfahari da rubutu,sabida alkalami yafi takobi🗡️🗡️🗡️ *BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM* Page 29&30 _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._ _Continuation.........._ Hannun ta ta sauke daga kirjin ta, ta sauke ajiyar zuciya Tace "Kai Yaya ka tsoratani yaushe ka Shigo?" Tashi yayi ya zauna daga kwanciyar da yake yana kallon cikin idonta tabbas ta tsoro ta, yace Mata "Yanzu na Shigo, Ashe dama kin ganni?" Kawar da kanta tayi kamar bata ji abinda yace ta hard'e hannun ta, ba ganin bata da niyar bashi amsa ya taso ya nufe ta, dab da ita ya tsaya ganin har yanzu bata kula shi ba ya hannu ya riko hannayen ta, wani abu taji yarrrr tun daga tsakiyar kanta I'xuwa tsakiyar kafan ta, da sauri ta zare hannun ta. Murmushi yayi yace "Princess wai haryanzu fushi kike dani?" 'dan ja da baya tayi ganin haka Shima ya matsa kusa da ita ta Kuma yin taku biyu ta baya shi Kuma yayi Taku biyu ya iso ta haka sukayi tayi har ta Kai jikin bango, hannu yasa ya riko hab'arta ya juyo kanta ta kalle shi. Idonta cikin nasa, idanun ta sun taro ruwa kiris suke jira su zubo ganin hakan yaji duk ba dad'i kasa da murya yayi yace "I Know I hurt you, Dan Allah ya Isa Haka bana jin dad'in hakan duk kin Canza min kamar ba princess d'ina ba" Hawayen da dama jira suke suka fara bin juna suna sauka da sauri yasa hannu yasa ya fara share mata yana girgiza kansa, ya kuma cewa "Am sorry My princess" Ma'isha runtse idanun ta tayi tana Jin dad'in sunan My princess wani 'bagaren Kuma ji take kamar zuciyar ta zata fashe sabida gani take kalmominsa na yaudara ce kawai. Haisam ganin hawayen Ma'isha ba karamin tada masa hankali yake ba ji yake kamar yasa harshen sa ya lashe hawayen ta yana Kuma ji kamar ya rungumeta a jikin sa ko zata ji saukin abinda take , amma bazai iya hakan ba sabida tun ba halaliyar sa bace. Riko hannun ta yayi ya zaunar da ita a bakin gado, ya durkusa a gaban ta hannun ta d'aya ya rike yasa hannun ta a tsakiyan hanyen sa, murza hannun nata yake a hankali yana kallon ta, banda hawayen dake zubiwa daga idanun ta Babu abinda take yi, har sai da ya ga ta daina kukan ya sake hannun nata sannan ya mike ya zauna a gefen ta. Still yana kallon ta yace "Please ki daina kukan haka bana son ganin ki haka, sannan dama na kawo miki labari ne Mai dad'i Amma na fasa" ya karasa maganar kamar yaro d'an shekara 3. Kirkirerren Murmushi tayi Tace "Na daina kukan fad'a min me ya faru?" "Zan fad'a miki but da sharad'i" "Ina jinka" "Sai kin min alkawarin kin daina fushi dani tukunna zan Sanar dake" " Toh ai Yaya Kaine kake fushi dani bani ba, tunda ko magana ma ka daina min ko da na maka ma amsa mara dad'i nake Samu ko Kuma kaki kulani, Kuma in ba Ni na maka magana ba bakayi min" "I Know, kin 'bata min raai ne wallahi, Amma yanzu komai ya wuce am sorry kinji?" "Hmm Shikenan" Mikewa yayi Tace "Haa'ah ina zuwa Kuma?" "Sallah zanyi kema na San bakiyi ba, so ki tashi kiyi" " Labarin da kace zaka fad'a min Kuma fa?" "zan fad'a miki anjima ki tashi kiyi sallah, bye" ya d'aga mata hannu kana ya fice. Murmushi tayi tana kallon hannun ta da ya rike ta dad'e tana kallon hannun ta tana shafawa da d'ayan hannun nata, sai gani nayi ta Mike firgit ta shige ban d'aki ko me ta tuna oho. Haisam Bayan yaje Masallaci ya dawo ya koma d'akin sa yayi wanka, wando three quarter baki ya saka sannan ya saka Riga armless Shima baki kana ya fito yazo part d'insu Daddy zaman sa ke da wuya daddy ya Shigo da Baki sun Kai su Shida cikin girmawa ya gaidasu suka amsa, Kai tsaye dinning suka wuce, mummy da Umma suka fito daga kitchen da sauran abincin Nan aka Shiga gaishe gaishe, Bayan sun ajiye suka koma d'akin mummy suka fara hirarsu a chan. Bayan su Daddy sun gama cin abinci suka d'an zanta har karfe takwas da rabi kana suka gama meeting d'in, fita sukayi duka a tare har wurin motocin su ya raka su duk suka wuce Amma banda mutum d'aya a tare suka sake shigowa a parlor suka zauna Haisam ya musu sannu suka amsa Nan fa daddy suka fara Hira ba kakkautawa da mutumin nan. Ma'isha kuwa Saida tayi sallar Isha kana ta fito daga d'akin doguwar Riga ce Mara nauyi sannan ta saka baby hijab ta fito parlor ganin su daddy da gudun ta karasa inda suke ta fad'a jikin Daddy tana fad'in "Daddy sannu sa dawo wa" Ya amsa da "Yauwa Daughter." Dariya sukayi mutumin nan da suke tare da daddy yace "Oh daddyn ki kawai Kika gani baki ganni bako?" "Laaah Abba wallahi ban gan ka ba, ina wuni?" Ta d'an duka ya Masa da "Lafiya su Isha manyan mata kaga yarinyar Nan yanda ta girma" Daddy ya amsa da "Wallahi kuwa kasan girman mace" "girman mace ai kamar Taki ake saka musu, ya school d'in dai dafatan ana kokari?" "Eh daddy Alhamdulillah" "Allah ya taimaka" "Ameen nagode Abba" Wanda ta Kira da Abba ne ya Kara maida kallon sa ga Haisam a karo na sau ba adadi ya maida kallon sa ga daddy yace "Yaya ina ta zuci zucin tambayar ka wane ne wannan?" Murmushi daddy yayi yace "Ai shine yaron da nake baka labarin sa kwanaki" "Ohhhh" girgiza kai yayi alamun ya tuna kana ya d'aura da fad'in "Haisam ko?" Yana kallon Haisam d'in, cikin girmawa Haisam yace "Eh yallab'ai" Murmushin gefen Baki yayi yace "Yallab'ai Kuma Haisam Kuma ka Kira Yaya na da Daddy? Ko Ni ban Kai a kirani da Daddy bane?" Ya karasa maganar a sigar wasa, sosa keya Haisam yayi yace "A'a ba Haka bane" Gyara Zama Abba yayi yace Sunana Abdallah Aminu Tahir, d'aga Malam Tahir Mus'ab wannan da kake gani.... Yana nuna daddy haisam ya kalli daddy kana ya maida kallon sa gare shi,ya d'aura da fad'in "Yaya nane uwa d'aya uba d'aya muke dashi shi ya sha nono ya bar min kaga Kennan Ni Abban Ma'isha ne zanzo ka Kirani da Abba kamar yadda Isha take Kirana" Murmushi Haisam yayi yace "Insha Allah Abba" Daddy Har cikin ransa ya ji daddy, hakan zai tabbatarwa da Haisam ya zama d'an gida. Daddy yace "Daughter jeki ki Kira su Mummyn ku" Mikewa tayi had'e da fad'in to, tana Shiga d'akin da sallama ta Sanar dasu cewar daddy na Kiran su a tare suka fito, gaisawa suka Kuma yi Nan sukayi ta Hira tare yayin da Alhaji Abdallah sai Satan kallon Umma yake ta lura da hakan, hakan yasa duk take jinta wani iri, sai da karfe 11 tayi ya mike da zummar zai tafi daddy da mummy sukayi duk yanda sukayi suka sa ya Kwana. *TSOKACI* ```Shin wane ne Alhaji Mus'ab Aminu??``` Alhaji Mus'ab Aminu d'ane ga Alhaji Tahir Mus'ab da Hajiya Maryam Muhd, Tahir Mus'ab cikekken bafulatanin Gombe ne gaba da baya, shaharen Mai kud'i ne Wanda yayi suna a fad'in Nigeria suna da 'ya 'ya biyu dukka maza Mus'ab Wanda yaci sunan mahaifin sa sai kanin sa Abdallah sun taso cikin gata dukkanin su kuma sunyi karatu ne a kasan waje Sannan dukkanin su Business suka karanta, Bayan Mus'ab ya gama karatu a India ya dawo gida Nigeria, Bayan ya dawo ne ya da Yan kwanaki karayar arziki ya Kama mahaifinsa kasantuwar asarar da yayi zuciyar sa ta buga. Tun daga sannan mahaifiyar su ta kwanta rashin Lafiya yau da lafiya gobe ba lafiya a haka har ta shekara daga bisani ita ma ta rasu, da Taimakon Allah da na Mus'ab ya farfad'o da business d'in mahaifin nasu har ya samu Abdallah ma ya Zama mutum Shima ya fara business d'in. Tare suke koman su har suka samu sukayi aure, a Rana d'aya suka yi aure, Shi Mus'ab Yar Gombe ya samu ya aura Mai suna Maryam, shi Kuma Abdallah a yawon business d'insa ya had'u da fauziya, fauziya bahaushiyar kano ce, Bayan shekara biyu Fauziya ta haifi d'a na miji sai yayi wa Yayan sa Mus'ab takwara, Bayan shekaru uku ta haifi Yan biyu dukka mata wata hassana da Hussaina,daga Nan suka koma Kano da Zama sabida ya cigaba da lura da business d'insu na Kano d'in. Maryam hankalin ta kullum a tashe yake bata da wani buri da ya wuce ta samu ciki, kullum cikin kuka take Mus'ab shine Mai rarrashin ta. Cikin Muryar kuka Tace "Mus'ab Zaka rabu har dani ko? Ko Zaka karo min kishiya" Rungumeta yayi tsam a jikin sa yace "Bani da wacce ta fiki maryam, bazan tab'a miki kishiya ba insha Allah, kullum ina fad'a miki ki daina tada hankalin ki shi fa Haihuwar Nan na Allah ne" "Amma ai ganan Fauziya a Rana d'aya akayi auren mu yanzu yaran ta uku yanzu haka tana d'auke da cikin wata hud'u Ni ko 'batan wata ban tab'a yi ba, sama da shekaru 7" ta karasa maganar cikin kuka. Bubbuga Bayan ta yake yace "Amma ai ba dabarar ta bane Kuma kema ba laifin ki bane, tunda munsha zuwa asibito ci da dama har kasar waje munje duk zancen d'ayane dani dake duk bamu da matsala Kinga Kenan lokacin Haihuwar ne bata Zo ba, ki daina tada hankalin ki mu cigaba da addu'a" *AFTER 10 YEARS* Maryam ta tashi da zazzabi Mai zafi banda amai babu abinda take, cikiin tashin hankali ya kaita asibiti, Likita ya Sanar dashi labari Mai dad'in da ya dad'e yana son ji, farin ciki fal ransa ya Kira Abdallah ya Sanar dashi, dashi da Fauziya sunyi muran matuka, Bayan wata 9 Maryam ta sami yarta, yarinya kyakkyawa kama take sak da ubanta Amma da d'auki hasken fatar Maryam, kasantuwar Mus'ab ba wani haske yake dashi sosai ba. Abdallah najin labarin Haihuwar ya sa suka shirya dashi da matar da yaran sa hud'u , Mus'ab, hassana da Hussaina sai Autan su Faisal, Wanda a lokacin Mus'ab nada shekaru 10, Hassana sa Hussaina 8 years sai Faisal a lokacin bai cika shekaru 4. A Ranar suna Mus'ab ya Sanar musu da yarinya taci sunan mahaifiyar su wato Maryam Amma ana Kiran ta da Ma'isha, tun da sassafe suka shirya suka Kama hanyar Gombe a hanyar su ta zuwa gomben sukayi hatsari,Fauziya da 'ya'yan ta duk 4 suka rasu,yayin da Abdallah ya bugu sosai Yana kwance a asibiti Rai a hannun Allah. ________________________ Please comment and share Milhaat ce Yar Terawa 🍃*DANGIN UBANA*🍃 Story & Written By Milhaart Na zo muku da littafi Mai ban tausayi,cike da abun al'ajabi,wannan salon na daban ne. *🌍MANAZARTA* *WRITERS ASSOCIATION📚🖊* *M. W. A* ```Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.🤙🏻``` https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa ____________________________________ *Wannan labarin kirkirarren labarine ban yarda a chanza min labari ba Wanda ya chanza bamu yafe ba.* Ina alfahari da rubutu,sabida alkalami yafi takobi🗡️🗡️🗡️ *BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM* Page 31&32 _Continuation........_ Tun daga Nan Abba yake kwance a asibiti, Rai A hannun Allah buguwar da yayi ne ya sa bai farka ba yayi dogon Suma, Satin sa d'aya a kwance. Su Fauziya Kuma da 'ya'yan ta tun a ranar aka kai su makwancin su, bayan ya farfad'o mutuwar tasu ta girgiza shi Kennan, tun daga Nan ya ji baya bukatar aure sabida gudun kar ya sake rasa su, hakan yasa ya bar kasan gaba ki d'aya ya Koma dubai, Yana kula da harkokin su na chan,sai lokaci zuwa lokaci yake zuwa duba su, Nan ma kwanaki biyu zuwa uku kawai yake musu ya koma,wani lokacin Kuma ya kwana hotel. Wannan Kenan. *CIGABAN LABARI* Abba ba don yaso ba ya Kwan,washe gari kuwa Ma'isha Bata sa Lectures a ranar akayi sa'a Haisam ma bayi da shi, a tare sukayi breakfast karfe 10 na safe flight d'in su Abba zai tashi. Bayan sun gama karyawa Abba yace dasu su fito waje akwai abinda zai nuna musu,Bayan sun fitane ya zaro key a aljihun sa ya mikawa Ma'isha, sa hannun tayi ta karb'a had'e da fad'in "Abba ajiye maka zanyi?" Yar karamar dariya yayi yace "A a My Isha,Taki Ce na Saya mikine sabida kokarin sa kike a school" Benz Ce baka sidik sai sheki yake wani uban ihu tayi had'e da salle,da gudu ta rungumi Abba had'e da yi Masa godiya "Abba Thank You Thank you" Shima rungumeta yayi Yana "fad'in mention Not Daughter, ki dai Kara kokari akan Wanda kike yi kinji?" Ta amsa da toh da gudu ta nufi gun Mummy tana nuna Mata,Duk sukayi Masa Godiya, Sannan suka koma cikin,Abba lokacin tafiyan sa ya kusa Amma bai ga Haisam da Umma ba,cike da kulawa yace "Yaya ya Banga sauran mutanen gidan ba?" "Eh suna part d'insu Amma yanzu nasan zasu Shigo" Aiko Yana rufe baki sai ga shigowar Haisam cike da girmawa ya gaidasu Duk suka amsa. Ma'isha da saurin ta Tace "Yaya ka gani Nima an Saya min mota babu ruwana da jiran ka bare ka jaa min ajii" Murmushi yayi yace "Masha Allah , congratulations gaskiya na tayi ki murna" Mikewa tayi Tace "Kazo muje kaga motar" wucewa tayi shi Kuma ya bi Bayan ta mummy girgiza Kai tayi Tace "Alhaji bari na Shiga daga ciki" ya amsa da "Toh." Ya rage daga Abba sai daddy a parlor ,gyaran murya Abba yayi yace "A gaskiya Yaya bazan yi shiru na cuci kaina ba Umman Haisam ta kwanta min a Raina,da fatan zaka bani auren ta?" Yar karamar dariya daddy yace "Ikon Allah daga ganin ta sau d'aya kace min ka kyasa?" "Eh Mana love at first sight kake ji,look Yaya ka daina min dariya Kai da ya kamata kayi farin ciki ma" "Sosai Kam,naji dad'i sama da 20 years kaki aure ai abin a duba ne,Kuma Insha Allah baka da matsala sabida Zainab bata da matsala ko kad'an tana da kirki" Shafa kirjinsa Abba yayi had'e da fad'in "Alhamdulillah abinda nake son ji Kennan tunda ka yabe ta magana ta kare,yanzu dai ya za'ayi?" "kar ka damu zansa Maryam ta Mata magana Insha Allah,Allah dai yasa ta amince" "Amiin ya Allah Ni da kaina zanyi Mata magana ma, Maryam Uwar Maryam" Fitowar Mummy Kennan ta ce "To me Kuma ya Faru naji ana Maryam Uwar Maryam nasan cuta ta za'ayi" Dariya sukayi daddy yace "A'a ba cutar ki za'ayi ba alfarma Zaki Mana ko ince taimako" Zama Mummy tayi Tace "Ahaaaf na sani ai da wala kin goro a miya, nasan ba a banza ba wannan kirarin" Daddy ya Sanar mata da abinda Abba yake bukata, Murmushi tayi Tace "Kai Alhamdulillah finally addu'ar mu zata karb'u, a gaskiya idan ka auri Zainabu zan ji dad'i sosai sabida mutuniyar arziki ce, gata da tsoron Allah, mace Ce ta gari, fatana shine Allah ya Sanya alhairi yasa Kuma ta amince kasan dai baza'a mata Dole ba" Abba yace "Nima ban bukaci hakan ba, in dai Bata so ki kyaleta Amma fa zanzo ki sa mata ra'ayi na gaskiya" "Kar ka damu Insha Allah ma zata amince kaga Shikenan ta Zama ta gida Duk da dama Yan gida ne" Nan sukayi ta hirar su har karfe 9:30 daddy da kansa ya kaisa Airport yaso ganin Umma Kan ya tafi Amma bata fito ba, Ma'isha Kuma da Haisam d'akin Haisam suka nufa suna ta Shan hirar su. Suna cikin hiran ne Tace "Yauwa Yaya Kace Akwai maganar da kake son fad'a min, mene ne?" "Yauwa kin tuna min, ba kince kina so na sama Miki aunty ba?" "Eh hakane" "To burin ki ya kusa ciki" "Ban gane burina ya kusa cika ba? Soyayya ka fara ne?" Murmushi yayi yace "Dad'i na dake kanki naja sosai princess, hakane soyayya nake Kuma ina sonta sosai" Ma'isha jin maganar Nan dai dai yake da kamar wuka aka dab'a Mata a kirjinta ji take d'akin na juya Mata, shiru tayi kana tace "Wace Ce haka Yaya?" Murmushin Jin dad'i yayi yace "Kin santa ai" "Haba dai ya sunan ta?" "Aysha!!! A razane ta Mike Tace "Aysha?" Shima mikewa yayi yace "Eh Aysha lafiya naga kin razana haka?" Ma'isha a ranta ji take kamar ta shake mishi wuya ya Kuma cewa "Princess kuka, meyasa ki kuka?" "Yanzu duk soyayyar da nake maka baka gani, da abun da zaka saka min Kennan? Baka san cewa ina sonka ba, me zakayi da wata Aysha? Dame ta fini? Kiran sunan ta da yayi da d'an karfine yasa ta dawo daga tunanin da take ya Kuma cewa "Princess tell me please what happened, why are you crying?" Cikin Muryar kuka Tace "Yaya ba Kai bane?" "Me nayi princess?" "Har zaka Fara soyayya ba tare da ka fad'a min ba" Dafe Kai yayi ya sauke wani ajiyan zuciya "Na d'auka maganar Farukh zai tabbata ne Ashe ba hakan bane ba?" " Me Farukh d'in yace?" Girgiza kai yayi had'e da Murmushi yace "Nevermind Amma princess Allah ya shirye ki komai kuka komai kuka gaskiya mijin ki zai Sha fama Kam, don wallahi aka Kai Masa ke raino zaiyi" Murmushi tayi "Nikam bari na tafi Kan Abba...... " Ganin agogon dake d'akin yasa Tace "Wayyo karfe 10 da rabi" ta nufi kofa da gudu Haisam yace "Lafiya me ya Faru?" "Abba zai tafi bamuyi sallama ba Kuma idan ya tafi sai yafi 3 years bai dawo ba" Ta fita da gudu, parlor ta nufa, tana Shiga ta tarar da Umma da Mummy a zaune mummy da d'an fad'a fad'a Tace "lafiyan ki Kike Mana gudu a gida haka?" "Mummy Abba da Daddy fa?" "mtsww sun fita" kawai Tace Mata had'e da kawar da kanta. Dafe goshin tayi Tace "Kai Amma naso mu yi sallama wallahi Amma ba komai zan kira shi a waya" tana Kai Nan ta shige d'akin ta, ba ta dad'e ba ta fito ta shirya cikin sutura mai kyau Tace "Mummy zanje gidan su Ameerah" "Aikin Kenan ai bare yanzu kinyi mota" Murmushi tayi Tace "Sai na dawo Umma sai na dawo" Umma Tace "Ai Ni munyi fad'a dake" Kama baki tayi Tace "Na Shiga uku Umma laifin me nayi kiyi hakuri" "Uhmn wai ace a miki babbar kyauta haka Amma baki fad'a min ba" Fad'awa jikin Umma tayi tana fad'in "Kiyo hakuri Umma wallahi d'azu ma da na Shiga da niyaan fad'a miki ne Amma Yaya yasa na manta kiyi hakuri kizo muje kiga motan" "To na sani dai Dole mantawa kikai, kar ki damu kije sai kin dawo ki kaini d'ani" Da murnar ta ta Mike Tace "To Umma sai na dawo d'in" Ficewa tayi tana ganin Haisam hannu kawai ta d'aga Masa ta shige motar ta key ta sa wa motar ta fice abin ta girgiza Kai yayi ya Koma ciki wayar sa ya d'auka yan kirata tana gani taki d'auka a bayyane Tace "Chaap ina driving d'in zan d'aga call d'in ka sai na Isa" Har ya katse Bata d'aga ba text ya tura Mata yace ```"Wato yanzu na Zama 0 a gun ki kinyi mota ba komai nagode"``` Bud'e text d'in tayi ta karanta Murmushi tayi parking tayi ta Masa ```"reply da ba Haka bane Yaya zanje gidan su Meerah ne, Kuma zan dad'e sai na dawo"``` ta ajiye wayar tana Isa gidan su Ameerah ta nuna Mata motar ta ta taya ta murna sosai, sai da suka gama kallon motan kana ta suka koma d'akin ta, wani irin Kallo Ameerah takeyi Mata Wanda yasa har ta Fara tsarguwa Ma'isha kallon kanta tayi Tace "Lafiya me ya Faru kike min Kallo haka?" Cike da kulawa Ameerah Tace "Isha wai ke Dan Allah baza ki cire damuwa a ranki ba? Haka Zaki cigaba da Zama?" Kirkirerren Murmushi tayi Tace "Me Kika gani ni Lafiya na Lau fa" "Haba Isha na sanki fa over 10year you're my best friend ko da baki fad'a min ba na miki sanin da zan iya gane farin ciki da bakin cikin ki, tell me maganar Haisam d'in ne haryanzu?" Ajiyar zuciya tayi sannan Tace "Shine kin San d'azu yake fad'a min wai Ashe soyayya suke da Aysha?" "I said it, ai na fad'a miki ki cire shi a ranki ko Kuma ki fad'a masa Amma kinki and now it's late" "Anya Ameerah kin San soyayya kuwa? Kar ki manta fa shi so halittace ba yin kaina bane wallahi abun ya fi karfi nane" ta karasa magani cikin kuka. Hannu Ameerah tasa a goshin Ma'isha Tace "Akwai zazzab'i a jikin ki" Mikewa tayi ta d'auko BP apparatus kasantuwar ita d'in a school of Nursing take tana final year yanzu, gwada BP d'inta tayi ta Kuma gwada har sau uku zaro Ido tayi Tace "Isha jinin ki ya hau sosai har 200 Inna wa Inna ilaihirraji'un, gaskiya dole in fad'a wa Ya Haisam gaskiyar magana bazan bari ki cutar da kanki" wayar ta d'auka zata Kira shi Ma'isha tayi saurin kwace wayan Tace "Me haka Ameerah me kike Shirin aikatawa haka?" "Ke zan tambaya Isha me kike Shirin aikatawa, zaki ja wa kanki matsala a banza Bayan wannan matsalar idan kina so a Yau d'in Nan za'a yi maganin sa" "kince na cire shi a Raina Insha Allah zan cire shi I just need some time please" Hawaye wani na bin wani haka ya rik'a fita daga cikin idon Ma'isha,ta kalli Ameerah ta rik'e hannunta tace "Please Dear ki taimaka min dan Allah karki fad'a,baki san irin son in da yaya yake ma Aysha ba ,haka itama wallahi suna son junansu bani son lalata masu farin ciki muna k'aunar junanmu ni da d'an uwana" Haushi yasa Ameerah ta fara magana cikin fad'a "oh kenan kin fiso ki mutu?kina so mu rasa ki kenan?shin keda Aysha wa ya fara son yaya Haisam? tun kafin ya dawo gidan ku a school baki da wata magana sai tashi shin idan ba'a fito fili an fad'a masa gaskiya ba ya kike so muyi?kina so ki dawwama cikin damuwa Kenan?" Kukanta a yanzu ya fito fili ta saka hannayenta ta rufe fuskarta tace "alkawari kika d'auka Meerah karki manta girman alkawari da mahimmancin sa ki rufa min asiri"dan Allah karki fad'awa kowa" Itama Meerah kuka ta fara, ta jingina kanta a kafad'ar Ma'isha ta cigaba da fad'in "karki damu da duk halin da nake ciki ni dai fatana karki fad'awa kowa kamar yadda kikayi alk'awari" "Shikenan Insha Allah bazan karya alkawarin da na d'auka ba Amma kema kimin alkawarin Zaki cire shi a ranki" "Insha Allah." "Hajiya wai kina nufin Kanin Alhaji ne wannan ko da yake na d'an ga kama Kam" "Eh kanin sane uwa d'aya uba d'aya....... " Nan fa Fara bata labarin sa da halin da ya Shiga girgiza kai Umma tayi Tace "Allah sarki na tausaya mishi, wato Duk halin da ka Shiga a Rayuwa idan Ka ga na wani sai ka Raina naka" Mummy tace "Wannan hakane" riko hannun Umma mummy tayi Tace "Please Zainab ki taimake mu ki maye Masa gurbin abinda ya rasa" Cikin rashin fahimta take kallon ta, "ban gane na maye Masa gurbin abinda ya rasa ba?" Nan mummy ta kwararo mata bayanin yanda sukayi da Abba a razane ta Mike tace "Gaskiya bazaiyu ba, bani ba aure kice Masa bana son sa ban amince ba, Kai baza ma na tab'a son sa" Mummy mikewa tayi ta fara Mata magiya, hakan yayi dai dai da Shigowar Daddy a tsawace yace "Maryam!!! Ba Mummy ba har ita Umman ta tsorata , sai da ta maso inda suke, sai Kuma yayi kasa da murya yace "Ba haka mukayi dake ba Akan me Zaki matsa mata Tace Bata so then let her be" sai ya wuce d'akinsa, Haisam kuwa Jin Muryar daddy ya Shigo da gudu, karaf maganar da daddy yayi ya sauka kunnen sa. Mummy cikin kuka Tace "Haba Zainab yanzu da abinda Zaki saka Mana Kenan" ta juya tabi bayan daddy. __________________________ Alhamdulillah naga yanzu ana comments ba laifi Amma fa ina Kan baka na, na removing Insha Allah Kuma zanyi. Nanarh Ummu Ziyad Ayusher Da sauran masu comments bazan iya irgu sunayen ku duka ba, nagode sosai inajin dad'in comments d'inku musamman Nanarh Allah ya bar Kauna. Please comment And share Milhaat ce Yar Terawa _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._ 🍃*DANGIN UBANA*🍃 Story & Written By Milhaart Na zo muku da littafi Mai ban tausayi,cike da abun al'ajabi,wannan salon na daban ne. *🌍MANAZARTA* *WRITERS ASSOCIATION📚🖊* *M. W. A* ```Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.🤙🏻``` https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa ____________________________________ *Wannan labarin kirkirarren labarine ban yarda a chanza min labari ba Wanda ya chanza bamu yafe ba.* Ina alfahari da rubutu,sabida alkalami yafi takobi🗡️🗡️🗡️ *BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM* Page 33&34 _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._ _Continuation........_ jiki a sanyaye mummy ta nufa part d'insu Haisam na Mata magana Amma Bata kulashi ba, a parlor ta zauna tana matsar kwalla, Haisam cikin tashin hankali ya zauna a gaban ta had'e da riko hannayen ta, cike da kulawa yace "Umma me ya Faru ne ban tab'a ganin daddy acikin irin Wannan yanayin ba a iya zaman da mukayi dashi ba, Haka ma mummy har kuka naga tana yi kema gashi kukan kike yi what Happened Umma?" Cikin shesshekar kuka Tace "Nothing Haisam, babu abinda ya Faru" "Dan Allah Umma ki fad'a ya za'ayi kice babu abinda ya faru Kuma kike kuka Dan Allah ki fad'a" Mikewa tayi a d'an tsawace Tace "Nace maka Babu ko" Ta shige d'akin ta. Ya dad'e a wurin yana zaune daga baya ya tashi ya bar gidan ma gaba ki d'aya. "Kin 'bata min Rai Maryam, Akan me Zaki sa ta agaba dole sai ta amince kar ki manta fa kece Kika sa na d'auko su na ajiye su akarkashina ba takura babu takura Jan su da mukayi a jikine yasa har suka sake jiki damu muka Zama one and family, tunda tace Bata so let her be ana Dole ne? Bafa yarinya bace ba tasan me take so da abinda bata so, Shima Abdallah zan Kira sa na fad'a Masa ya bar maganar sabida na lura ya na neman sata a Rai daga jiya zuwa yau" "Uhmn Alhaji Kenan yanzu duk abinda mukayi masu da abinda zata saka Mana Kenan, Alhaji dama don mu ba wallahi nasan inda Bata mutu ba da ta kusa mu...... " A tsawace yace "Ke Zaki kashe ta? Nace ke Zaki kashe ta?" Ta girgiza Kai had'e da sunkuyar da Kai, iska ya hura kana ya sassauta Muryar sa yace "Maryam zaki goge ladan da Kika Samu idan Kika cigaba da fad'an haka mun taimaka Mata don Allah Ne ba don ta biya mu ba, kar ki manta fa kece Kika kawo shawarar taimaka musu har Kika sa na dawo na su cikin gidan nan, Dan Allah idan na Isa dake ki bar maganar nan ban yarda ki sake Mata maganar ba bare ki nuna Mata a fuska" " Insha Allah zanyi yanda kace kayi hakuri" Ma'isha da Meerah Havilla Ice cream suka nufa, Bayan Meerah ta tabbatar da ta kwantar wa da Isha hankali, ice cream suka Sha har sai da akayi la'asar tayi suka koma gida, sai da Isha ta ajiye ta a gida kana ta wuce gida. Haisam kuwa school ya Shiga, Duk da bayi da Lectures jiran ta yayi ta gama Lectures suka Sha hiran su ya samu hankalin sa ya kwanta , sai Kuma yayi sa'a yau bata fito da motar ba hakan ya bashi kaita gida. Bayan sallar Isha Umma kasa zuwa gun Mummy tayi suyi hirar da suka Saba, Ma'isha na d'akinta taji Duk bata jin dad'in zaman hakan Yasa ta fito parlor ganin ba kowa ta nufi d'akin Mummy da sallama ta shiga Tace "Mummy ya na ganki a kwance yau baza a yi hiran parlor bane?" "Uhmnn bani Jin dad'i ne" "Subhannallah me ya same ki?" "ciwon Kaine ba wani Abu ba" "Amma kinsha magani ko?" "Eh Nasha" "To Allah ya sauwaka" "ameen" Mikewa tayi Tace "Bari naje part d'insu Umma" "Okay" tab'e baki Isha tayi ta nufi part d'insu Umma. Ganin Umma Bata parlor ta wuce d'akin ta cike da mamaki Tace "Umma kema a kwance ko kema bakya Jin dad'in ne?" Kirkirerren Murmushi tayi tace "Eh wallahi bana Jin dad'in jikina" "Oh ikon Allah sai kace Kun had'a baki ga mummy ma a chan ta kwanta wai kanta na ciwo" Umma a ranta Tace "Oh Allah kar dai ita ma tasa maganar a ranta kamar Ni" a bayyane ta ce "Lallai kamar mun had'a baki" "Allah ya baku Lafiya" "Ameen" "Ya Haisam fa yana Nan?" "Ki duba shi a d'akinsa d'azu dai baya Nan ban San ko ya Shigo ba" Ta amsa da "Ok sai da safe Allah ya sauwaka" "ameen daughter nagode." 'dakin Haisam ta nufa ta shige d'akin taga wayam Bayanan, kwan kwasa kofar d'aki tayi ko Yana ciki taji shiru hakan ya tabbatar mata da Bayanan d'aga kafad'a tayi irin I don't care, ta fice. A hanyar ta, ta fita suka had'u da Isha yace "Princess kin dawo Kenan?" "Eh na dawo tun d'azu" "Su Umma fa" "Suna kwance wai Basu da lafiya" "Duk su biyun?" " Eh Umma wai zazzab'i take ji Mummy Kuma Wai ciwon Kai" "Hmm kin San d'azu bakyanan me ya Faru?" "A'a sai ka fad'a" Nan ya jero Mata abinda ya gani da idon nunsa , cike da mamaki tace "eh Lallai no wonder biri yayi Kama da mutum, to Amma me ya faru haka?" "Allahu a'a lam, Umma taki fad'a min amma ki gwada tambayar mummy muji ko menene" "kaji ka ya Haisam mummy ce zata fad'a min sai kace baka San halin ta ba, dama kaine maybe zata fad'a maka" "Okay muje hope tana d'akinta ba d'akin Daddy ba?" "Eh tana d'akin ta" "Alright muje" Yana tafe tana biye da shi da sallama suka Shiga d'akin mummy sunyi sa'a bata rufe ba don tashin ta Kennan zata rufe, tana ganin si tayi Murmushi Tace "ku Kuma fa daga ina?" "Daga d'akin Umma" Ma'isha ta bata amsa ba. Mummy ta amsa da "okay" Haisam yace "Mun Zo gunki ne mummy" "Lafiya dai ko?" Ta kalli Haisam ta kalli Isha Haisam murya na rawa yace "la.....Lafiya lau,kawai magana zamuyi mummy" " To ku zauna mana" ta koma ta zauna a Kan gado ta d'auki Pillow ta d'aura a cinyar ta sannan ta d'aura hannayen ta akai tana kallon su. Zama sukayi akan kushin d'in dake d'akin kasa kasa Haisam yace "kiyi magana Mana" Ita ma Tace "Kayi magana Mana" "Princess kiyi magana Mana Dan Allah" "A a wallahi Yaya ai kai kace min zaka mata magana mun Zo Kuma ka kasa" Mummy na Kallo ikon Allah, sai kuskus take ji bakin su na motsi Amma bata jin abinda suke fad'i,a d'an fad'a fad'a Tace "Idan baza ku fad'a min ba ga hanya Nan ki fice min bacci zanyi" tana nuna musu kofar fita. Haisam ne ya gyara Zama Yana wasa Yana d'an bubbuga kafar sa da hannun sa yace "mummy dama.....dama.....dama d'azu da na Shigo ne naji Abba na fad'a,naga Kuma kin Fad'i kalma wa Umma Sannan kina kuka Kika shige ita ma kukan naga tana yi,mummy dukkanin ku bamu tab'a ganin ku a cikin Wannan yanayin ba a iya zaman da mukayi daku bamu tab'a Jin Kan ku ba,shine muka zo ki fad'a mana Inda Hali,don naga duk Kuna cikin damuwa" Ajiyar zuciya Mummy tayi Tace "Son ina da niyar yi maka maganar ko da kuwa baka Zo ba, sabida nasan Kai kad'ai Umman ku ke Jin maganar ka Idan mukayi sa'a ta amince da bukatar mu,ba wani abu bane ba dama Abban kune............ " Nan ta bayyana Masa komai Kama daga Kan mutuwar Matar sa da 'ya'yan sa da kuma dalilin sa na kin yin aure. Murmushi Haisam yayi Wanda yake Kara bayyana kyawun fuskar sa yace "Mummy yanzu dama Akan wannan ne kike kuka Duk kuka tashi hankalin ku? Ni a ganina wannan abun ba abin tashin hankali bane ba, zanyiwa Umma magana Kuma Insha Allah zata amince, ko ba komai ai abun farin cikine wannan duba ga irin tsawon shekarun da Abba ya d'eba bayi da niyar aure ace Rana d'aya ya ce zaiyi, Kuma na tabbata Insha Allahu Abba zai rike ta da zuciya d'aya sabida na lura Shima Yana da son Mutane Shima kamar daddy, insha Allah zata amince fatan mu shine Allah ya tabbatar da alhairi" "Kaai Amma naji dad'in maganganun ka son, Allah yasa ta amince d'in" "Ameen Mummy" Ma'isha da tun d'azu take kallon su Tace "Ni Idan akayi auren Nan ai barka na sabida Abba na auren mummy gidan su zan koma da Zama in huta da....... " Turo kofar da akayi ne da d'an karfine yasa ta kasa karasa maganar ta Duk su ukun suka Mike a razane mummy baki na rawa Tace "Al.... Alh..... Alhali Lafiya? Tana leka Bayan sa ganin ba kowa ta cigaba da magan "Alhaji Lafiya na gan ka a Haka?" Rai a mugun 'bace yake nuna ta da d'an yatsa Yana fad'in "Haven't I warned you not to talk about it again? Haven't I?" "Alhaji Amma...... " "Shut up!!! Amma me? Nace amme? Akan me Zaki zauna kisa yaran Nan a gaba kina fad'a musu abinda bai shafe su ba iyee? Answer me?" Mummy kasa magana tai ta sunkuyar da kanta a kasa tana kuka Mai cin Rai Duk yanda taso ta Hana kukan ta ta kasa sabida yanda daddy ya ke mata tsawa da fad'a a gaban yara, da su ya sune abun Sam bazai Dame ta ba. Ma'isha Murya na rawa Tace "Daddy please Daddy kayi hakuri wallahi ba laifin mummy bane mune muka sata a gaba Dole tasa ta fad'a Mana, Kuma....... " "Ma'isha!!! Ya Kira sunan ta a wani irin Murya Wanda hakan yasa ta rike bakin ta da hannun ba tare da tasan tayi hakan ba, ba tare da ya kalleta ba yace "Idan na Kuma Jin bakin ki a wurin Nan sai na 'ballaki" Ya cigaba da fad'in "Taya za'a yi ni da gida in kafa doka Amma ki take shi? Yaushe Kika Zama Haka Maryam?" Haisam cikin girmawa yace " Daddy please kayi hakuri Dan Allah Ni a gani na wannan abun ba abin tada hankali bane ba, yes kamar yadda princess Tace mune muka Masa wa Mummy Akan ta fad'a maana abinda ya faru sabida d'azu a gabana naga kana Mata fad'a, abinda ban tab'a gani ba Kennan tunda na dawo gidan, ta fad'a min ne sabida tasan Idan nayi wa Umma magana zata amince, sannan Abba nasan Idan hakan ta kasance zaka fi kowa farin ciki, Amma Dan Allah kayi hakuri" Shiru Daddy Yana sauraron sa jikin sa Duk yayi sanyi, tabbas maganar Haisam hakane zaifi kowa farin ciki sannan idan Haisam yayi wa Umma magana babu Makawa zata amince, shiru d'akin yayi na d'an wasu lokuta Banda kukan mummy da na Ma'isha babu abinda ke tashi a d'akin jiki a sanyaye Daddy ya nufi inda Mummy me tsaye tana matsar kwalla, bai tsaya 'bata lokaci ba ku Jin kunyar su Haisam ba ya rungume ta Sam a jikin sa Yana d'an bubbuga Bayan ta a hankali, yace "Am sorry Maryam, am sorry please wallahi raina ne ya 'baci jin kalaman Zainab a Jan d'an uwana Sai na kasa jurewa yanda na ga ta ki Abdallah karara naji zafi sosai da kalaman ta, Amma bani da ikon da ita bazan iya tirsasata ba, na d'au lokaci Mai tsawo na ganin irin wannan ranar da Abdallah zai kawo min maganar aure, nayi matukar murna sosai Allah Allah nake na dawo gida don Jin labari Mai dad'i sai Kuma najie akasin hakan, ke Kuma da na hanaki magana akai sai Kuma Kika ki jin magana Amma maganar da Son yayi sai na gane kuskure na" d'an d'ago Kan Mummy yayi yasa hannu Yana goge mata hawaye yana fad'in "am sorry am sorry" Haisam d'an Buge kafar Isha yayi da kafar sa ta juyo ta kalle sa murya kasa kasa yace "Kinga ko mijin ta ya rarrashe ta,Yana share Mata hawaye ta daina kukan, gwamma kiyi shiru don ba Mai rarrashin ki anan" 'dan Buge shi tayi da kafan ta yana gumse dariyar da ke kokarin kwace Masa. Mummy zare jikin ta tayi a hankali daga jikin daddy tasa Bayan hannun ta, ta share hawayen ta kana ta gyara murya Tace "Son kaci gidan ku" Kama baki yayi yace "Laaaa Ashe ta ji" da gudu ya fita isha ta Mara Masa baya, Tace "Ja'irai kawai" suka bar daddy dashi da Matar Nan, suka Shiga soyewa abinsu. Haisam da Ma'isha kuwa a parlor suka zauna Banda dariya babu abinda suke yi, su Haisam harda rike ciki itama Isha dariya take sosai ba kakkautawa tana cikin dariyar ne kwasam ta Mike a zabure ta wuce d'akin ta da gudu, Haisam kuwa baki ya sake Yana kallon ta har ta haura d'akin ta sai da yaga ya daina kallonta kana ya kawar da kansa Yana mamakin Shagwab'a irinta Ma'isha , a bayyane yace "Mutum bata da aiki sai kuka" Ma'isha kuwa tana Shiga d'akin ta ta had'a kai da gwiwa ta fara rera kuka son ranta, tunawa tayi da Haisam na son wata ita ba, yanzu duk dakon soyayyar sa da ta dad'e tana yi ya tashi a banza Kenan? Karar shigowar Kira taji ya shigo wayar ta mikewa tayi ta duba fuskar wayar ta ganin sunan Meerah yasa ta daina kukan ta yi picking ba tare da Tace komai ba, Meerah Tace "Hy Isha kin koma gida kalau, da fatan kinsha maganin da muka saya d'azu?" "Nikam Na manta da wani magani" a ranta ta ayyana hakan Amma a bayyane Kuma Tace "Uhmmn Nasha" "Subhannallah Isha kuka kikayi yana ji muryar ki haka Lafiyan ki kuwa?" "Uhmn Lafiya na Lau daga bacci na tashi" "oh sorry na tashe dama so nake na ji ko kinsha maganin nakin gudun kar jinin naki ya sake Hawa" "Kar ki damu Nasha" "Tohm Shikenan zan Zo gobe Insha Allah na gwada BP naki ko ya sauka, da fatan baki da Lectures gobe?" "Akwai But da safe ne zuwa la'asar zan dawo" "alright sai mun had'u goben please take care" " Insha Allah thank you" a tare suka katse wayar d'ago kanta da tayi ta sauke kanta a Kan haisma da tun da ta Fara wayar Yana tsaye Yana kallon ta, Murmushi tayi Tace "Yaya ka Shigo Mana" Girgiza Kai yayi yace "Ba Zama ya kawo ni Nan ba, Princess meyasa ki kuka? Kuma ke da wa kike waya naji kina maganar kinsha? Me ke damin ki baki da lafiyane?" Yar karamar dariya tayi Tace "Yaya irin wannan tambaya haka wanne zan amsa a ciki?" "Dukka" ganin ba wasa a fuskar sa Tace "Uhmn dama kaina ne yake ciwo" "Uhmn sai akayi Yaya? Da wa kike waya?" "Ameerah ce dama da naje gidan su ne, saai.... Umm kaina ya Fara ciwo shine ta bani magani Nasha Akan in na dawo na Sha, shine ta Kira taji ko Nasha" "Toh naji shi Kuma kukan na mene ne?" "umm... Ummm..... Kai na.... Kaina ne yake ciwo" "Ciwon Kan ne ya saki kuka?" Kai a kasa ta amsa da "Eh shine" ganin ya kure Idanun sa yana kallon ta Yana kokarin gaskata maganar da. "Ya ciwon Kan, kin Sha maganin?" "Eh Nasha" " Alright, sai ki samu ki kwanta kar na Dame ki, good night" ya jaa kofar ya rufe Mata bai tsaya Jin abinda zata ce ba. Ajiyar zuciya tayi Tace "That was closed I thought yaji" girgiza Kai tayi ,ta Shiga ban d'aki ta yi wanka tana fitowa ta Sanya sleeping dress d'inta ta kwanta sannan ta kunna datarta, ta Shiga WhatsApp, ganin Haisam a online yasa ta Masa "Hy Yaya ba kayi bacci ba?" Sai da ya d'auki kusan 5 minutes kana ya mata reply da "Eh banyi ba me ya hanaki bacci?" Emoji na kuka ta jero masa had'e da tura masa "Sai yanzu Zaka kulani?" "am sorry Video call muke da auntyn ki" Tana bud'e wa ta kashe datar ba tare da ta Masa reply ba, ta gyara kwanciyar ta tana ta tuna abubuwa dayawa daga bisani bacci yayi awon gaba da ita. ```Washe Gari``` Haisam ne ya Shigo ya tarar da mummy da Daddy a parlor suna karyawa gaishe su yayi suka amsa kana ya tamabaya Ma'isha fa. Mummy ce ta amsa Masa da "Bata fito ba kana da Lectures ne?" "Eh Umma Lectures na karfe takwas nake dashi" ya maida kallon sa ga daddy yace "Daddy naga jaka tafiya zakayine?" "Eh son zani abuja zanyi 3 days a Chan" "Gaskiya daddy sun sa makan Kai a gaba Sam baka Zama Ni na manta ranar ma da kayi one week a gida" Dariya yayi irin tasu ta manya yace "To ya zanyi Dole ce tasa" Haisam ya ce "Hakane Allah ya dafa maka daddy" "ameen son Mike ka Duba ta kar ku makara, mikewa yayi da sauri ya haura sama, a hankali ya tura kofar had'e da lekawa ya hango ta Akan gado ta na sharar baccin ta hankali kwance, a bayyane yace "lallai yarinyar Nan" Ban d'akinta ya Shiga ya bud'e tap ya d'an Tara da hannun sa ya fito ya watsa Mata a fuska a razane ta farka tana ambaton sunan Allah ganin Haisam yasa Tace "Haba Yaya me Haka" ta koma ta kwanta. "Princess ya haka baki da Lectures ne ki tashi please Karki makarar da mu" Ido a rufe ta amsa Masa "Sai 10 kaje kawai sai anjima zan Shigo" 'daga kafad'a yayi ba tare da yace Mata komai ba, Yana fita yaga mummy na shigowa ciki yace "Har ya tafi?" "Eh " "Allah ya tsare, sai na dawo" ta amsa da "a dawo Lafiya" Ya shige motar sa ya fice daga gidan ya wuce school. Ma'isha sai karfe 9 ta tashi ta shiga ban d'aki ta shirya, a gurguje ta karya tayi wa Mummy sai ta dawo ta fice itama da motar ta Shiga school yau, Bayan sunyi Lectures karfe 1 suka Samu break ta nufi Masallaci domin ta gabatar da sallar azahar Kan su koma , Bayan sun idar suka koma class karfe biyu sai karfe 3:30 suka gama Lectures d'in wurin motar ta, ta nufa, tun daga nesa ta hango Haisam da Aysha suna Hira suna dariya alamu ya nuna Duk su biyun suna cikin farin ciki, ki tayi jira na d'aban ta da sauri ta nufi motarta ta bud'e ta Shiga, kwantar da kanta tayi steering motar ta dad'e a haka tana ambaton La'ila ha ila anta subhanaka inni kuntu Minal zalimin take har Saida taji d'an dama dama ta jaa motar ta fice daga cikin makarantar ranta ba dad'i. Bayan ta Isa gida, ganin mummy da Umma a garden tasa ta d'an ji dad'i alamun babu wacce ta rike kowa a Rai, Bayan ta gaida su ta shige d'akin ta ruwa ta watsa kana ta gabatar da sallar la'asar ta kwanta tana tunani kala da iri har karfe biyar da rabi kana Meerah ta Shigo cikin gidan Bayan ta gaida su Mummy ta shige d'akin Isha. Tana Shiga d'akin ta Ciro BO apparatus d'in ta ta hau gwada ta cikin Murya kamar fad'a Tace "Haba Isha Haba Isha 220 Isha, jinin ki ya hau har 220 ina mamakin ma yadda akayi har kike tafiya, Anya kinsha maganin da na ce Kisha" Turo baki tayi ta ce "Nasha Mana" "Wallahi baki Sha ba da kinsha da ba Haka ba, kin San Allah Idan baki cire shi a ranki ba Wallahi tallahi zan fad'a Masa" " Karki min haka Dan Allah" "Isha Ni Banga dalilin 'boye Masa ba, gara ya sani ya San halin da kike ciki a dalilin sa, jinin ki Kara Hawa yake wallahi zuciyar ki zata iya bugawa" "Insha Allah baza ta buga ba, ki tayani addu'a d'azu ma na gansu sai kin gansu gwanin sha'awa" "oooh no wonder yanzu nasan inda matsalar take ganin su da kikayi ne yasa hankalin ki ya Kuma tashi ko? Isha soyayyar da kike Masa na gaskiyane baza ki iya cire shi a ranki cikin sauki ba" Haisam ne ya turo kofar Yana kallon su, wani yawu Mai zafine ya wuce ta makoshin Isha murya na rawa tace "Ya... Yaya ka dawo?" _________________________ Please comment and Share Milhaat ce Yar Terawa 🍃*DANGIN UBANA*🍃 Story & Written By Milhaart Na zo muku da littafi Mai ban tausayi,cike da abun al'ajabi,wannan salon na daban ne. *🌍MANAZARTA* *WRITERS ASSOCIATION📚🖊* *M. W. A* ```Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.🤙🏻``` https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa ____________________________________ *Wannan labarin kirkirarren labarine ban yarda a chanza min labari ba Wanda ya chanza bamu yafe ba.* Ina alfahari da rubutu,sabida alkalami yafi takobi🗡️🗡️🗡️ *BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM* Page 35&36 _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._ _Continuation.........._ Kofar d'akin ya tura ya nemi gu ya zauna kana yace "Eh na dawo maganar me kuke tattaunawa?" "Uhmnn ba komai fa" Kallon ta yayi kana yace "Oooh really ba komai? Naji Ana maganar Isha na son wani wane ne wannan lucky guy d'in?" Daram daram kirjin ta ya buga, Meerah Tace "Ya Haisam dama........" Ma'isha katse ta tayi da fad'in "Yaya ya school d'in d'azu na ganka da Aunty na Kuna ta soyewar ku a love garden" "oh ashe dama dagaske ked'in ce , Dama habibty Tace min ta ganki Amma na karyata ta, har ina fad'in inda kece zaki min magana, Ashe yaudaran kaina nayi" idon sa ya Kai kan gado ya hango BP apparatus kallon abun yake da mamaki. Murmushi tayi Tace "Ba Haka bane dama........ " Katse ta yayi da fad'in "Princess ya naga BP apparatus baki da lafiyane?" Ganin baza ta amsa ba yamaida kallon sa ga Meerah da take aikin kallon sa yace "Likita me ya sami princess d'in?" "Yaya jinin ta ne ya d'an hau Amma insha Allah zai sauka na bata magani ta Sha" "jinin ta ya hau how comes?" " Ga ta Nan ask her" Murmushi tayi ta Fara inda inda yace "Tell me princess me ke damin ki? Na lura a Yan kwanakin Nan Akwai abinda ke damin ki Amma kina 'boyewa mene ne?" "Ummm Yaya kasan Exam ya sako kai to yawan tunanin exam ne da rashin samun hutu yasa" "Oh Hakane please ki rika samun hutu sosai, kar ki wahala karatun Kuma exam yazo ki kasa Exam , Kinga anyi ba'a yi ba Kenan" "Hakane Insha Allah zan kiyayye" Mikewa ya musu sallama ya fice. Sai da Meerah tayi sallar Isha , Ma'isha ta maida ta har gida da kanta. Haisam ne a d'akin Umma cikin sanyin Murya da kamar rarrashi yace "Umma please, Dan Allah ki duba lamarin nan" "Haisam Kenan, haryanzu baka fahimce ni ba Sam, bazan iya auran wani ba Bayan mahaifin ka zan cigaba da Zama haka har nima mutuwa ta riske Ni" "Umma ki dubi girman Allah ki sake tunani a Kai, kar ki manta fa Daddy shi ya taimaka mans muka fita daga cikin kuncin Rayuwa har muka dawo Mutane, kin San abubuwan da bazan iya lissafa su ba, yau yana neman abu a wurin Wanda zamu iya bashi Kuma mu hana shi, Idan mukayi hakan ba muyi Masa butulci ba kuwa?" A razane ta d'ago kanta ta kalli Haisam d'in kana ta sake kawar da kanta, ba Tace Masa komai ba magana yayi tayi Yana bata hakuri Amma bata tanka Masa ba har ya gaji yayi shiru mikewa yayi da niyar fita, har yasa Kai ya tsinkayo Murya Umma tana fad'in "Shikenan Na amince" Da d'an saurin sa ya dawo cikin d'akin ya d'an rungumeta ta kana ya sake ta yace "Yauwa Umma ta ai nasan Zaki amince" mikewa yayi Yana fad'in "zani na fad'awa Mummy" "Wa ya aike ka? Ka bari da kaina zan Sanar da ita dama yanzu zan Shiga part d'insu" Murmushi yayi yace "Shikenan Umma" Mikewa tayi ta d'auki mayafin ta, ta nufi part d'insu mummy ta tarar a parlor sun dad'e suna Hira sama sama kamun ta fad'a Mata cewar ta amince mummy murna yasa ta Kira daddy a waya ta Sanar mishi, yayi farin ciki sosai shima Nan take ya Sanar da Abba, Abba baiyi kasa a gwiwa ba yasa aka tura masa number ta Sannan mummy ta bata na Abba, Ba 'bata lokaci ya neman Soyayyar ta. Haisam kuwa d'akin Isha ya Shiga ya Sanar da ita labari Mai dad'i tayi murna sosai, Nan sukayi ta hirar su. *BAYAN WATA 5* Shirye shiryen biki su ke tayi duk da ba wani events zasuyi ba daga walima sai walima shima anan gidan su Ma'isha kawai za'ayi. Yayin da Haisam da Aysha wata soyayya ce Mai karfi ya Shiga tsakanin su kusan kullum suna tare, Ma'isha kuwa damuwa Sai abunda ya karu, Meerah kuwa kusan ko wani sati zata Zo ta duba lafiyar ta sannnan ta bata shawarwarin da ya Dace Amma Duk da hakan Isha ta kasa daina son Haisam. Alhamdulillah an d'aura Auren Umma da Abba sannan Amarya ta tare a gidan ta anan cikin garin gombe, Daddy ne yayi iya bakin kokarin sa ganin ya dawo da dukkanin aikin Abba a gombe. Ma'aruf kullum cikin Kiran Meerah yake Akan maganar Ma'isha, Amma Ma'isha Taki bada had'in Kai shi Kuma ya kasa hakura. Wannan Kenan "Isha please think about it Mana, Wallahi ma'aruf na sonki ke ko tausayin sa bakya ji? Ki duba kiga ni fa tun d'azu Yana waje Yana jiran ki Amma kin ki, ki saurare shi" "Nifa na Riga na fad'a muku bana son sa Kuma bazan tab'a son wani ba bayan Haisam meyasa Kika kasa fahimta na ne?" "To ai Banga amafanin hakan ba, tunda kin kasa fad'a Masa har yayi nisa da soyayyar wata hakan zai tabbatar miki da cewar kin rasa shi Kennan har abada" Hawaye na a idanun Ma'isha d'aya na bin d'aya, taji zafin maganar Meerah Amma Kuma tasan gaskiya ta fad'a mata sabida masu iya magana sukace shi Gaskiya d'aci gareta. "Na Sani Meerah, nasan kin damu dani kin damu da farin cikina gami da lafiya ta Amma Dan Allah kar kiyi kokarin sani Dole sai na Kula shi" Mikewa meerah tayi Tace "fine then Ni zan tafi dama shine ya ce na rako shi, ki sani baza ki sake gani na ba a gidan ku, sannan zan fad'awa Haisam halin da kike ciki" ta Kama hanya zata wuce Ma'isha ta Sha gaban rike hannayen ta tayi tana kuka "Please don't do this to me Meerah ke ce kad'ai kike saurarata ke ce kad'ai Kika San damuwa ta Akan me zakimin irin wannan hukuncin Kuma Kar ki manta kin min alkawarin baza ki tab'a fad'a wa kowa matsala ta ba" Fin cike hannun ta tayi da karfi Tace "Dallah malama gafara min na wuce idan ke baki da shi to ni Ina dashi, idan baza ki bawa ma'aruf dama ba ya maye miki gurbin Haisam ba to Dole ne ki samu Haisam" Har kasa ta durkusa ta rike kafafun ta tana Mata magiya Akan Kar ta fad'a Masa. Meerah Sam Bata Jin dad'in ganin kukan ta Amma Dole ce tasa tayi Mata hakan, Dole ta samarwa kawarta farin ciki gudun Kar ta kamu da ciwon zuciya. Cikin murya Kamar fad'a Tace "Wallahi tallahi sai na fad'a Masa in dai baza ki kula ma'aruf ba ai zab'i na Baki" mikewa Isha ta tayi ta share hawayen ta Tace "Shikenan na amince wallahi zan kula ma'aruf, Dan Allah kar ki fad'awa ya Haisam Dan Allah" Murmushin samun nasara Meerah tayi kana ta sa hannu tana share Mata sauran hawayen dake fuskar ta. Cike da kulawa Tace "Am sorry Isha, ki daina kuka Sam bana jin dad'in ganin ki a Haka ne shiyasa nabi ta wannan hanyan, yanzu ki d'auko mayafin ki muje Yana chan yana jiran mu Amma ki wanke fuskar ki tukkunna" Ba musu tayi yanda Tace mata suka fita suka tarar dashi a cikin motar sa, jiki na rawa ya fito suka gaisa, Mai gadi tasa ya kawo musu kujera ya ajiye musu a inuwa, suka zauna daga bisani Meerah ta koma d'akin Isha tana jiran su, sai da suka gama hiran ma'aruf ya kirata ya maida ta gida, tun daga wannan ranar Isha ta fara kula ma'aruf lokaci zuwa lokaci Kuma Yana zuwa gidan su tun bata sake Masa har ta Fara Duk da ba son shi take ba, ma'aruf mutum ne mai abin dariya yakan sa taji ta manta Duk wata damuwar da take dashi in dai suna tare. *AFTER 1 YEAR* Sosai Ma'isha ke mayar da hankalin ta Akan karatun ta, Sannan Duk weekend a gidan Umma take yi, Haisam kuwa tunda Umma tayi aure aka rufe part d'insu ya dawo part d'insu mummy Yana d'akin sa kusa da na Ma'isha , idan suna gida sukan zauna a parlor suyi Hira Duk sanda ya kawo maganar Aysha kuwa sai tayi yanda tayi ta kawar da maganar. Ma'isha ne zaune da Ma'aruf a garden suna hirar su, labari yake Bata dariya take Sha sosai yayin da shi Kuma sai aikin kallonta yake. Haisam kuwa dawowar sa Kenan daga gun Aysha tunda ya Shigo gidan yake kallon su, ji yayi ransa ya 'baci Amma bai San dalilin hakan ba, ya d'auki kusan mintuna biyar Yana kallon su su kuwa Basu ma ji shigowar sa ba, kasantuwar motan da tint yasa Basu ganshi ba, ajiyar zuciya yayi Sannan ya fice daga cikin motar har ya wuce Ma'isha Tace "Yaya ka dawo?" Kirkirerren Murmushi yayi Sannan ya dawo mikawa ma'aruf hannu yayi suka gaisa turo baki Isha tayi Tace "Dama Yaya wuce wa zakayi Kamar baka ganmu ba?" "Am sorry princess , kin San hankali shine gani ban lura bane" kallon Ma'aruf yayi Wanda shima kallon sa yake yi, da sauri ma'aruf d'auke Kan sa gani yayi ya Masa kwarjini, maganar su sukayi tayi kana ya shige cikin gida. Ma'aruf kuwa natsuwar sa ya rasa yace "Wannan fa Yayan kine?" "Eh Yayana Ne" "Amma ya kuke dashi?" "My cousin, meyasa kake tambaya?" "No..... Bakomai naga Kuna Kama ne shiyasa" Murmushi kawai tayi gani kawai tayi ya mike yace zai tafi, ba don taso ba ta rakashi jikin motar sa, sai da taga fitan sa ta koma cikin gida. Kamar wasa Ma'isha tana final year kasantuwar pharmacy 5 years akeyi shi Kuma Haisam saura Masa shekara d'aya ya gama, Meerah kuwa ta dad'e da gamawa har tana aikin ta a medical center dake cikin garin gombe. Bayan Ma'isha tayi graduating Abba ya sa ma mata aiki itama a medical center hakan yasa kullum suna tare da Meerah, Haisam kuwa kullum cikin bibiyar Aysha yake da ta gabatar dashi gun iyayen ta Amma taki kullum amsar d'aya take bashi zan had'a ku idan lokaci yayi. Yau ma hakan Tace Masa "haba Habiby saurin me kake Ne Kam" "Aysha!!! Jikin ta ne yayi sanyi da jin yanda ya Kira sunanta ta amsa da "Na'am" tashi yayi ya zauna daga kwanciyar da yake wayan dake hannun sa ya maida d'ayan kunnen nasa yace "Anya kina Sona kuwa?" "Wannan wace irin tambaya ce Haka, kafi ko wa Sanin irin soyayyar da nake maka Kuma kake min irin Wannan tambayar?" "I doubt much gaskiya in dai dagaske kina sona ki barni na tura su Daddy gidan ku gudun Kar wani ya shige min" "Allah kar ka damu habiby next year fa zaka gama karatun ka kaga Ni Kuma sai Nan da 2 years na maka izini kana gamawa kazo ko da kuwa baka Sanar dani ba in yaso sai na gama a gidana ko" Dad'in maganar natan yaji Amma ya basar yace "Shikenan sai anjima zan Zo gidan" Da sauri Tace "A a kar kazo" Cike da mamaki yace "Meyasa?" "Umm.... Umm... Dama.... Dama Mom ce ta aike Ni zanje gidan kanwarta sai dai idan zamu had'u a Chan" "Okay wani unguwa ne?" "Federal low cost" "Oh unguwar mu nema idan kin Zo let me know" Bai jira yaji abinda zata ce ba ya kashe wayar, d'akin isha ya nufa ya tura kofar yaga wayam Bata nan. Layin ta ya Kira tana picking yace "Yau weekend ina Kika shi ne, tun safe ban ganki ba?" "Wallahi Yaya ina gidan Umma ne" "Shine baza ki fad'a min ba mu je tare?" "Am sorry na Shiga d'azu na ga kana baccine shiyasa" "okay Nima gani Nan zuwa" Ta amsa da "okay" sai ta kashe. Haisam dama da already yayi wanka Kaya kawai yasa ta fice, ya nufi gidan mummy, sai Bayan da iya sane ya tuna ya bar wayan sa a d'akin, ganin yanda Umman sa tayi kyau tayi fresh hakan yasa shi jin dad'i sosai. Umma na zaune a kasa, gata da babban ciki Wanda haihuwa yau ko gobe, Isha ganin tana wahala sosai ta fad'awa mummy zata zauna anan har sai Umma ta haihu Kuma ita kad'ai take aikin ta ga ciki, ita Ma'isha kullum mamaki take meyasa su Daddy basa son Yar aiki a gida. Aysha kuwa ta Kira layin Haisam yafi sau a irga har ta koma gida bai kirata ba , a ranar Kam raba dare yayi Yana rarrashin ta dakyar ya Samu ta hakura. Ma'aruf kuwa Duk sanda yake son ganin Isha Yana zuwa asibiti su gaisa sama sama yayi tafiyar sa ganin ta koma gidan su Umma yasa ya Fara zuwa gidan nasu, shi Sam bai San dalilin da yasa baya son ganin Haisam ba, Kuma hankalin sa ya kasa kwanciya shi duk tunanin sa Soyayya suke, sai da Meerah ta tabbatar Masa da cewar shakuwa ce kawai irin ba Yan uwa da Yan uwa. Wata Rana, cikin dare Isha taji Umma na Kiran sunan ta , da gudu ta fita ganin Umma a cikin jini yasa tayi matukar tsorata gashi Abba baya gari Sannan Kuma karb'an haihuwa ba 'bagaren ta bane, da gudu ta d'auko wayan ta ta Kira Haisam, kasantuwar unguwa d'aya suke bai Kai mintuna goma ba ya Isa da taimakon Sa da Isha suka sa ta a mota, suna Isa asibitin aka tabbatar musu da nakuda ce. _____________________________ Please comment Vote And share Milhaat ce Yar Terawa 🍃*DANGIN UBANA*🍃 Story & Written By Milhaart Na zo muku da littafi Mai ban tausayi,cike da abun al'ajabi,wannan salon na daban ne. *🌍MANAZARTA* *WRITERS ASSOCIATION📚🖊* *M. W. A* ```Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.🤙🏻``` https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa ____________________________________ *Wannan labarin kirkirarren labarine ban yarda a chanza min labari ba Wanda ya chanza bamu yafe ba.* Ina alfahari da rubutu,sabida alkalami yafi takobi🗡️🗡️🗡️ *BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM* Page 37&38 _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._ _Continuation........_ Haisam da Ma'isha na zaune a reception, Haisam Kam kwata kwata ya kasa nutsuwa ya zauna ya tashi ya fara kaiwa Yana kawo wa, ya dawo ya zauna. Ma'isha tausayin sa ya kamata sai ta tuno lokacin da Umma bata da lafiya, cike da kulawa Tace "Yaya please ka zauna Mana addu'ar mu take bukata a yanzu" "Princess wallahi na tsoratane sosai, mata suna wahala sosai wallahi duk Wanda yace zai tozarta mace ko ya wulakanta ta bai san ciwon kansa bane bare Kuma ace uwa" "Uhmn hakane Kam Amma fa ga Wanda ya sani, sabida wani abun idan kaji sai kaji Kamar Duniyar Nan an Tara zallan mahaukatane, kwanaki naji labarin wani ya Mari mahaifiyar sa akan kawai Tace Masa ya aske gashin Kan sa" "kin gani ko to wannan ina zaiga dai dai fisabilillahi" "Allah dai ya rabamu da iyayen mu Lafiya" Ya amsa da "Ameen summa ameen" Tace "Amma Yaya ka fad'a wa mummy zaka zo kuwa?" "A a wallahi a birkice na fito, Amma bara na Kira daddy" "shi da baya Nan?" "Eh gara shi d'in ya fad'a mata" "Toh" Kiran daddy yayi ya Sanar Masa shi Kuma ya Kira mummy ya fad'a Mata, mummy Kiran Haisam d'in tayi, tayi ta fad'a akan bai Sanar Mata ba suna Yara sun kaita asibiti idan ana bukatar wani abu fa, cikin Daren ta bugawa driver kofa kasantuwar yana zaune ne a boys quarters shi da Matar sa, d'auko motar sukayi gidan Umma suka fara nufa ta d'auko Duk wani abunda za a bukata kana suka wuce asibitin. Bayan ta Isa asibitin na had'a su duka tayi ta masifa Banda hakuri Babu abinda suka ce mata, haka Umma ta kwana ba ta haihu ba sai uban wahalar da take Sha, har gari ya waye sai abin ya tashi ya sake kwanciya. Ganin har karfe 8 tayie bata Haihuwa ba Umma Tace su koma guda Ma'isha ta had'o musu breakfast ta kawo, a gidan Umma Haisam ya ajiye ta ya Koma gida yayi wanka ya dawo gidan Umman sai da ya karya Ma'isha ma tayi wanka suka koma asibitin. Abba na Abuja ji yake kamar ya dawo Amma ba hali kasantuwar washe gari yana da meeting da zasuyi, Daddy Kuma yana bauchi yaje yin wasu harkokin sa a Chan, anan asibiti sukayi sallar azahar, Haisam banda matsar kwalla ba abinda yake yi Mummy da Isha Kuma sai aikin rarrashin sa suke suna kwantar Masa da hankali Likita ce ta fiti fuskanta d'auke yake da Murmushi gunsu ta nufa Tace "Alhamdulillah Allah ya sauke ta lafiya, ta Samu Twins duka Mata" A tare su Umma suka Shiga hamdallah, Likita kuwa Tace "Amma ta zubar da jini sosai Gaskiya tana bukatar jini" Haisam a rud'e yace "To a d'i a nawa mana" Hannu ta d'aga Masa had'e da fad'in "Come with me." Yabi bayanta. Sai da aka gyara su tsaf da jariran ta Mummy da isha suka Shiga suka gansu Yara kyawa Masha Allah, wayar Ma'isha ce Fara ringing picking tayi ta dafa Kai "Tace am sorry wallahi yanzu haka ina specialist ne mom d'ina ce take labour, Amma gani Nan zauwa yanzu" Mikewa tayi Tace "Mummy zan tafi ni na manta ma yau afternoon nake karfe biyu ya kamata na karb'e ta gashi har quarter to 3 yanzu" "Yi maza kije Allah ya tsare" Ta amsa da "Ameen Mummy" sai da ta d'auki hoton jariran kana ta fice, napep ta Tara ta koma gidan Umma ta d'auko lab coat d'inta kana ta d'auki motar ta ta wuce asibiti, tana Isa wacce zata karb'e ta, ta tafi, wayar ta ta zaro ta turawa Daddy da Abba hotunan, Abba na gani ya kirata Yace "Dama ta haihu ne babu Wanda ya fad'a min" "Eh Abba d'azun Nan ta haihu" "Amma shine baku fad'a min ba tun d'azu hankali na a tashe yake" "Yi hakuri abba wallahi Mun shafa'a ne, Kuma ance tana bukatar Karin jini" "Subhannallahi an samu an Sa Mata?" " Ban sani ba wallahi nima yanzu ina bakin aikine" "okay bari na Kira su naji" Ya katse wayar Murmushi tayi Tace "Lalllai Abba bai ma damu da yaran ba matar sa kawai ya sani" Nan ta cigaba da aikin ta. Haisam kuwa jinin sa bai Dace da na Umma ba sai da suka saya sannan aka sa mata, bacci Tasha sosai har sai yamma lis ta farka, Murmushi kawai tayi ta yi, tana kallon 'ya'yan ta. Mummy kanta ne ya kulle ta rasa yadda zatayi , Ma'isha na gun aiki gashi suna bukatar abinci yau ga ranar Yar aiki, Kiran abba tayi ta rarrashi shi cikin ikon Allah ya amince dama akwai wacce take son Fara aikin a gidan mummy Amma ya Hana, Mummy ba tayi kasa a gwiwa ba ta kirata, ta fad'a mata Duk abinda zatayi tana zuwa Mai gadi ya bud'e mata gate ta shiga sabida mummy ta Riga ta fad'a Masa hakan yasa bai tsaya tambayar ta ba. Duk abubuwan da Mummy ta fad'awa Sadiya duk tayi su kasantuwar ita d'in Mai nutsuwa ce, Bayan ta gama ne ta Kira Hajiya ta Sanar mata akan ta gama, Mai gadi mummy ta Kira tasa ya kawo ta asibitin ta kawo musu abinci da duk da duk wani abun da zasu bukata. Kwanakin su uku a asibitin aka sallame su, a ranar Kuma Abba ya dawo, bakin Nan a wage an kasa rufe shi, Mummy Kam gaba ki d'aya ta dawo gidan Umma tana kula da ita, bayan Nan mummy tasa Dole sai da aka samawa Umma ita ma Yar aiki, sai Bayan suna Mummy ta koma gida kasantuwar Daddy zai dawo, Twins kuwa Ana Kiran su da Aaima da Aymana. Sosai suke samun kulawa a gun familyn gaba ki d'aya kun San Twins da Shiga Rai musamman ma ace identical Twins ne. Kwan a tashi ba wuya a wurin Allah, Haisam ya samu ya gama makarantar sa sabida good Results d'insa ma Asibitoci da dama suna son su d'auke shi aiki, Amma Isha ta kafa ta tsare Dole ya karb'a a inda itama take aiki, acikin shakara d'aya komai ya canza, Haisam kuwa dama a kage yake ya gama don ya samu damar mallakar Aysha, Ma'aruf kuwa Ma'isha ta kaishi sun gaisa da su Daddy an San da zaman shi, komai tafiya normal yake sai godiyar Allah. Haisam ne zaune shi daddy suna Kallo a parlor sai yayi Kamar zaiyi magana sai Kuma ya kasa, mummy Ce ta fito hannun ta rike take da Plate fruits ne a ciki ta ajiye a gaban Daddy, Kallon Haisam tayi Wanda ya Shiga duniyar tunani, Kiran sunan sa da tayi "Son!!! Ne ya dawo da shi daga tunanin da ya Lula ya amsa da "Na'am Mummy" "Lafiyan ka kuwa?" "Lafiya Lau Mummy" Murmushi daddy yayi yace "Tun d'azu na lura dashi Akwai abinda yake damun sa amma yayi shiru, ka fad'a Mana Son me ke faruwane? Ko dai matsalar daga gun aikine?" "A a daddy dama.... " Sai Kuna yayi shiru yana Sosa keya daddy yace "Feel free man, ka Fad'i Duk abinda kake so ni Kuma na maka alkawari zan maka shi in bai fi karfina ba" "Umm dama... Dama Akwai wacce Muke soyyaya da itane , to ina so a nema min auren tane" Murmushi mummy tayi Haka shima daddyn yace "Wace ce Kuma Yar gidan wace ce?" "Sunanta Aysha,Amma Gaskiya daddy tun da muke ban samu damar ganin mahaifin ta ba, Amma na San gidan su" "Toh Shikenan ba matsala, sai ka Sanar da ita su sa mana Rana" "Daddy Kuna iya zuwa gobe ma don munyi magana da ita" "To Shikenan dama Abban Kuma yana gari kaga sai muje goben kawai" "To Shikenan Allah ya kaimu." Mummy tunda Haisam ya ambaci sunan wata ba sunan Ma'isha ba sai taji ba dad'i Haisam mikewa yayi ta Shige d'akin sa, mummy cikin damuwa Tace "Alhaji wallahi na d'auka yaran Nan soyayya suke" Cikin rashin fahimta yace "Wasu yaran Kenan?" "Ma'isha da Haisam Mana Gaskiya na dad'e ina burin naga an had'a su aure" "hmm bake kadai ba har Ni kaina na yaba da halin yaron Nan, Amma tunda ya ce ga wacce yake so ai baza mu Masa Dole ba ita Ma'ishan sai ta fad'awa wannan yaron da yake zuwa gun ta ya turo Iyayen sa sai a had'a ayi rana d'aya." Ma'isha ce ta Shigo cikin parlor bakin ta d'auke da sallama da kayan aiki ajikin ta da alama daga asibiti take Zama tayi a Kan kujerar da yake fuskantar su Daddy a kasalan ce ta gaida su suka amsa daddy yace "Yauwa daughter kin dawo a dai dai, ki fad'awa wannan yaron da yake zuwa wurin ki ya turo magabatan sa in har da gaske yake sai a had'a Rana d'aya da na Yayan ki shima gobe zamuje mu nema Masa aure" Zumbur ta Mike Tace "Innalillahi wa Inna ilaihirraji'un Aure Kuma? Yayan aure zeyi?" Mummy cikin fad'a Tace "Ke Lafiyan ki kuwa me haka?" Jiki a sanyaye ta d'auki Jakarta ta haura sama da gudu tana kuka, Daddy yace "Meyasa Kika yi Haka?" "Alhaji me Kuma nayi?" "Baki San ma me kikayi ba?" "Umm to Alhaji maganar aure fa akayi, sai kace zancen mutuwa akayi, Kuma Alhaji ban ma San nayi hakan ba,Amma Alhaji nifa ina ganin yarinyar Nan tana son Haisam" "Kamarya Kenan fa?" "Baka lura da hakan ba yanzu fa maganar auren sa da kayi ne ya razanar da ita yanzu Nan tabbata kuka takeyi" Ajiyar zuciya daddy yayi yace "Maybe shakuwa ce kawai ba soyayya bace , Amma shekaru nawa sukayi suna tare a gidan Nan ai in da Soyayyar ce da mun sani ko? " "Hakane Kam, to Allah ya tabbatar da Alhairi" "ameen." Kamar yadda mummy Tace Isha kuka take tun da ta shiga d'akinta take aikin kuka Haisam kuwa Yana kwance hankalin sa kwance Yana waya sa masoyoyar sa, ya sanar da ita su daddy zasu zo gobe, tayi murna sosai harda Yar tsallen ta, Tace "Yanzu bari naje na fad'awa Mom ta sanarwa da Daddy" "Toh ki bari mu gama wayar Mana tukanna" "Aaa wallahi za dai muyi waya anjima zanje na fad'a mata" "Uhmn habibty zumud'i Kenan?" Cikin muryar Shagwab'a Tace "Toh habib ranar da nake jira Kenan fa kaga zumud'i dole, so kar kaga laifina" "A a Banga laifin ki ba ko kad'an ni kaina na kosa goben tayi, don a gaskiya ban so auren mu ya wuce Nan sa da 3 Months" Zaro Ido tayi kamar yana kallon ta tace "Har 3 Months Gaskiya yamin Nisa Habib" "A hakan yayi nisa? To ya ya kike so ayi?" "Nan da 2 months dai,kaga dama muna Shirin Exams ne zamu samu hutu Mai d'an tsayi kawai sai ayi" "To Shikenan hakan za'ayi zan Sanar wa su Daddy idan sun amince Shikenan" "Zama su amince,yanzu dai bye naji kamar daddy ya Shigo" "Bye" ta katsewayar, da kanta ta Sanar da dad halin da ake cike Murmushi yayi yace "Yaran zamani ba kunya wato ma zan yi baki Shikenan Allah ya Kai mu goben sai sun Zo" "To Daddy." Ma'isha kuwa sai da tayi kuka Mai isarta kana ta fito parlor mummy Tace "Dama yanzu zan Shiga na duba ki Lafiyan ki kuwa?" "Lafiya Lau Umma" "Ya naga idanun ki sun Kumbura?" "Bacci nayi Mummy,an gama abinci?" Ta fad'i hakanne don ta kawar da maganar ba don tana Jin yunwa ba. Mummy ta amsa da "Eh an gama,Yau anan Zaki Kwana ba gidan su Abba ba?" "Eh Mummy sai jibi zan koma chan d'in" "To Shikenan Allah ya kaimu,zo muje dining d'in." A tare suka zauna Ma'isha Tace "Mummy ina daddy?" "Ya fita yaje gidan Abban ku zasuyi maganar zuwa gidan su budurwar Yayan ki" Ma'isha ji tayi kamar zuciyar ta zata buga,ganin irin kallon da Mummy take Mata tana son gane wani abu tayi kirkirerren Murmushi Tace "Nifa na d'auka Yaya is not serious about her" "Dama kinsan tane?" "Eh na santa ita ma a school d'in mu take course d'insu d'aya da yaya" "Kina so kice min course mate d'insa ce" "Eh to kusan hakanne Amma fa ba aji d'aya suke ba,sune zasu Gama a shekarar Nan" "Oh Masha Allah, Yayan naki Kinga na manta kije ki kirashi yazo yaci abinci" Ta Mike Kenan ta hango shi Yana saukowa hannun sa a manne a kunnen sa yana waya Yana dariya,Zama tayi Tace "Gashi Nan ma" "Okay" Sai da ya gama wayar yazo ya ja kujera had'e da fad'in "Barka da Dare Mummy" "Yauwa Barka son,yanzu nake ce mata ta Kira ka sai ga kanan,waya ake tayi haka da surkuwa ta?" Murmushi yayi kawai baice mata komai ba, Ma'isha tace "Yaya ina wuni" "Lafiya Lau princess, pharmacists of the house ya na ganki haka? Baki da lafiya ne?" "Bacci na wuni yi Yaya" Mummy Tace "Wai wuni naga Bayan la'asar Kika dawo" Uhmn kawai Tace ta cigaba da cin abincin,ci kawai take Amma bata jin dad'in abincin Sam kasantuwar bakin ta Duk d'aci,mikewa tayi ta ajiye plate d'in a kitchen kana ta wuce d'akin ta ba tare da tace musu komai ba. Haisam yace "Mummy Amma baki lura kamar princess na cikin damuwa ba?" "Gata Nan dai nima na lura da hakan Amma na tambaye ta Tace min bakomai" Mikewa yayi yace "Bari naje naji ko mene ne." Bai jira yaji amsar ta ba ya haura sama da sauri, tun daga kofar d'akin yaji tana ta dariya, a hankali ya tura yaga tana waya Zama yayi tana kallon sa Amma Bata kashe wayar ba,ta d'auki kusan 5 minutes Kan ta katsewayar da fad'in "Sorry Love zan Kira ka yanzu" Haisam ji yayi wani abu ya tokaresa a wuya Ma'isha Tace "Am sorry yaya wallahi Ma'aruf ne yake ta bani dariya" Cikin rashin Jin dad'in maganar nata yace "Waye ma'aruf?" "Saurayina man Yaya Wanda yake zuwa gidan Nan" "Oh that guy? Ni ban San sunan sa ba" "Ma'aruf sunan sa" "Ban San me Kika gani a jikin sa ba Ni Sam bai min ba" "Yaya saurayin nawa ne bai maka ba? Aiko shi nake so Kuma zan aura" "Hmm lallai gani nake Sam baku dace ba" Ma'isha wayanta ta bud'e ta Shiga gallery ta Mika Masa wayan had'e da fad'in "have a look" Karb'a yayi ganin hotunan da suka d'auka tare sauran selfies ne sauran Kuma d'aukan su akayi suna dariya a wurare da dama,sauran gun wurin cin abinci ne da ice cream Rai a 'bace ya Mika mata wayan yace "ba laifi maybe ranar kallon tsoro na Masa,Kuma yana sonki?" "Eh Mana sosai ma yana sona ga alamu Nan, hotunan Nan da ka gani ai sun Isa ka gane hakan" "Hakan.......yanzu auren sa zakiyi?" "Eh insha Allah,daddy ma yace na fad'a Masa ya turo don Yana so a had'a ayi rana d'aya" "Me za'a had'an" "My wedding and yours" Mikewa yayi yace "Yayi kyau" Ya fice Isha kuwa d'aga kafad'a tayi irin halin ko in kula d'in Nan ta Kira Ma'aruf ya katse kana ya kirata suka cigaba da wayar su. Haisam kuwa Yana Shiga d'akin sa ya kasa tsaye ya kasa zaune ya rasa dalilin da yasa yaji duk ya damu baya son Ma'isha ta auri gayen Nan, dafe kansa yayi yace "Maybe ko don gayen baya burgeni ne?" Ya kuma bawa kansa amsa da "Hakanne ma?" Wayar sa ya d'auka kamar zai Kira Aysha sai kuma ya fasa ya kashe wayar gaba ki d'aya ya kwanta dakyar da makyar kyasa bacci ya sace shi. *Washe Gari* Karfe hud'u na yamma,Daddy da Abba suka shirya don zuwa gidan su Aysha , Haisam ke Jan motar yayin da Abba ke gefen sa daddy Kuma yana baya suna tafiya suna Hira har suka Isa. Kasantuwar an san da zuwan su aka musu iso cikin gidan,Amma Haisam a mota ya zauna ya kira ta a waya suna ta Hira daddy da Abba suka gabatar da Kan su,shima Dad d'in Aysha da kannen sa maza biyu suka gabatar da kan sun,sun fahimci juna sosai kasantuwar Daddy sa nannen mutum ne, sannan basu 'boye musu asalin Haisam ba gudun Kar wani abu ya gifta suce an musu karya, Bayan sunji bayanin su Daddy suka amince da had'in tunda yara suna son junan su babu 'bata Lokaci suka amince da bukatar su, hakan yasa aka sa ranar aure Nan da wata biyu, drinks ne Niki Niki a gaban su daddy da namomin kaji Amma basu tab'a komai ba suka fice. Haisam na ganin su Daddy yace "habibty ganan su Daddy sun fito zamuuyi waya anjima" Cikin muryar Shagwab'a Tace "Bazan ganka ba Kenan?" "Zan dawo anjima insha Allah, bari Muji yanda sukayi tukunna" "Insha Allah,Mai dad'i ne sabida dad yasan ina son ka,Kuma yana son abin da nake so" "To Masha Allah,I'll call you later." ya katse wayar. Su dad kuwa har jikin mota suka raka su daddy hakanne ya tabbatar Masa da cewar bashi da sauran matsala,ai kuwa suna fita a gidan daddy ya Sanar Masa da and ranar bikin Nan da wata biyu, Haisam farin cikin da yake ciki ya kasa 'boyewa, gidan Abba Suka nufa Umma taji dad'i ta wani 'bangaren wani 'bangaren Kuma bata ji dad'i ba Sam,sabida kullum burinta shine Haisam ya auri Ma'isha tayi wa Abba korafi yayi saurin dakatar da ita akan ba a yi wa d'an yau auren Dole. Shiri suka Shiga yi duka family Ma'isha ma ba'a barta a baya ba,idan tana cikin Mutane ta nuna tafi kowa farin ciki yayin da idan tana d'akin ta Kuma taci kukan ta,son ranta idan ta gama ta wanke fuskar ta. Yau saura sati d'aya bikin Aysha da Haisam, Ma'isha da Meerah na gani zaune a cikin Masallacin asibiti da alama sun idar da sallar ne "Isha kiyi hakuri Dan Allah, Rana ita yau fa auren su,kema sai da nace miki ki tura Ma'aruf Amma kinki har karya fa kikayi wa Daddy cewar Ma'aruf baya Nan Bayan kuma yana Nan,ban San dalilin ki nayin hakan ba" " Dalili d'aya ne kema kin sani,Haisam nake so ba Ma'aruf ba" "Na sani amma ai Haisam d'in aure zaiyi ko?" "Eh Ana gama auren sa zan fad'awa Ma'aruf ya fito" "Ikon Allah,to Allah ya nuna Mana" "yanzu Meerah ya Haisam aure zaiyi fa ko? Kuma wata zai aura bani ba?" Ta fashe da kuka Mai cin raai har Saida sauran staffs d'in suka Fara kallon su rarrashin ta Meera keyi sai da tayi mai isarta ta Mike Kenan ta yanke jiki ta fad'i sumammayi. ____________________________ Please Comment and share Mihaat Ce Yar Terawa 🍃*DANGIN UBANA*🍃 Story & Written By Milhaart Na zo muku da littafi Mai ban tausayi,cike da abun al'ajabi,wannan salon na daban ne. *🌍MANAZARTA* *WRITERS ASSOCIATION📚🖊* *M. W. A* ```Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.🤙🏻``` https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa ____________________________________ *Wannan labarin kirkirarren labarine ban yarda a chanza min labari ba Wanda ya chanza bamu yafe ba.* Ina alfahari da rubutu,sabida alkalami yafi takobi🗡️🗡️🗡️ *BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM* Page 39&40 _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._ _Continuation........._ Cike da fargaba da tsoro suka chiccibeta suka kaita A&E (Accident & Emergency) Nan da Nan likitoci sukayi kanta, kwata kwata bata numfashi da taimakon Oxygen ta fara numfashi, Haisam kuwa yazo wucewa ne don duba patient d'insa ya hango meerah na ta aikin kuka, da sauri ya karasa inda suke ganin Isha ce a kwance bata motsi ya birkice Yana tambayar su "Me ya same ta ne?" Wurin Meerah ya nufa Yana tambayar ta "Meerah what Happened to her? Me ya same ta? Please ki Sanar dani" Cikin kuka Tace "Yanke jiki tayi ta Fad'i" Likitane ne ya juyo yace "Dr Haisam, itace sister d'inka ko?" Cikin rawar murya yace "Eh itace" "To ya akayi kuka bari har ciwon zuciya ya kamata?" Zaro Ido yayi yace "What ciwon zuciya dai? But how comes?" Kafad'ar sa ya d'aga had'e da fad'in "I don't know, thank goodness ma ta samu kulawa cikin gaggawa da an rasata Kai ma kasan irin wannan lokaci d'aya mutum yake mutuwa ko Kuma ya kamu da mutuwar 'barin jiki" Haisam dafe kan sa yayi ya jaa da baya ya jingina da bango yana kallon Ma'isha da haryanzu oxygen na hancin ta, d'an bubbuga shi likitan yayi kana ya fice dashi da sauran nurses d'in. Kallon Meerah yayi yace "Dan Allah ki Sanar dani me ke damun Princess nasan kisan komai a kanta sabida kinfi kusanci da ita fiye da kowa" Kai a kasa tace "Ni ban san komai ba, babu abinda na sani" Girgiza Kai kawai yayi ya Koma kusa da ita ya zauna ya sanya hannunta a cikin nasa Yana ta kallon ta, sai yamma ya tuna bai Kira su Mummy ba, Nan ya kirasu ya Sanar dasu, ba dad'ewa Mummy da Daddy suka zo, mummy na ganin halin da yarta ke ciki ta Shiga rera kuka dakyar daddy ya samu ya rarrashe, a takaice dai Ma'isha a haka ta kwana bata farka ba ta kwana ta wuni tana bacci, sai yamma lis ta bud'e idon ta haisam da kanshi ya duba ta, ya mata alluran da ya kamata, aiko ta sake komawa bacci. A takaice dai Ma'isha Kwanan ta uku a gadon asibiti, sai da ta d'an Samu sauki aka sallame ta, a cikin Yan kwanakin Nan ta rame ta lalace Kamar ba ita ba, kuka kuma sai abinda ya karu,mummy da daddy sunyi rarrashin sunyi fad'an Amma taki fad'a musu, mummy Tace "Ma'isha idan baki fad'an min damuwar ki ba wa Zaki fad'awa umm? Ki duba kiga yanda kika lalace fisabilillahi baki kyauta wa Kanki ba wallahi" "Mummy nifa ba abinda yake damina" "Idan babu abinda ke damin ki me ya kawo miki ciwon zuciyar?" "Uhmnn mummy ciwo ne kawai daga Allah ba wani abinda yake damina" "Toh naji kukan da kike Kuma fa? Ki duba abincin Nan da sadiya ta kawo miko tun na safe baki ma tab'a shi ba" "Zanci Mummy" "A gaskiya Ma'isha bana Jin dad'in ganin ki a haka Dan Allah........ " Sallamar da akayi ne ya katse ta amsawa tayi had'e da kallon kofar don ganin wane ne, Murmushi Umma tayi Tace "Ameerah kece?" "Eh Mummy ina wuni?" "Lafiya lau ya gida ya su maman naku?" " Suna lafiya sunce a gaishe ku da maie jiki" "Allah sarki muna amsawa , sannu Ameerah Allah ya biyaki sai faman wahala kike " "Aaaa haba Mummy nida Isha ai Mun Zama d'aya nima idan hakan ta same ni nasan zata min fiye da hakan,fatan mu shine Allah ya bata lafiya" "hakane Allah ya bar zumunci" "Ameen Mummy" "Please kiyi Mata magana ta fad'a miki abinda ke damin ta, Kuma taki cin abinci, rabonta da abinci tun jiya da dare" "Kar ki damu mummy zataci insha Allah" Mummy fita tayi ta barsu da ga ita sai Isha, plate da d'auka tasa abincin d'an dai dai ta ajiye Sannan ta zaunar da ita ta Shiga bata a baki ba musu ta karb'a. Cike da kulawa Tace "Haba Isha, Isha so kike ki kashe Kanki?wannan fa ba alkawarin da Kika d'aukan min ba Kennan, kin zabi ki mutu Kennan?" "uhmn zan mutu idan kwana na ya kare,kema kin San da hakan ko?" "Amma kuka ai gangancin kine zai saka ki rasa ran naki tun kwanakin ki bai kare ba, wallahi Isha na gaji da ganin ki a Haka, a gaskiya lokaci yayi da zan fad'a Masa da dasu mummy" "Meerah please ki tuna alkawarin, Duk Wanda ya karya alkawarin to ba Makawa alkawari zata cishi, kin fiso a rasa rayuka biyu ne?" "Ban gane a rasa Rayuwa biyu ba, wa Dawa Kenan?" " Ni da Ya Haisam, wallahi farin cikinsa matters allot to me, bazan juri ganin sa a cikin damuwa ba, moreover ba Sona yake ba" "Shima Kuma bazai tab'a jin dad'in abinda kike Shirin aikatawa ba, ko da ace baya sonki na tabbata zai so ki Nan gaba" Maganar Meerah a kunnen Haisam ya sauka, turo kofan yayi ya shigo gaisawa sukayi kana Meerah ta Mike Tace "Zan wuce asibiti dama nazo  na duba jikin nakin ne, sai gobe zan dawo insha Allah, Allah ya baki Lafiya" Suka amsa da ameen tayi ficewar ta, tana fita ta nufi gun motar ta Muryar Haisam taji yana kiranta a hankali ta juya tana jiran sa. Karasowa yayi yace "Meerah wane ne Wanda Ma'isha take so?" In a serious tone yake tambayar ta, mamaki ma ya bata don ita ta manta ranar da ya Kira Ma'isha da sunan ta in bata manta ba tun suna school, ajiyar zuciya tayi Tace "like I said to you ban sani ba ni kaina taki ta fad'a min, sai anjima Kar na makara" ta shige motar ta har ta fice daga gidan Haisam na tsaye yana nazarin maganar ta a bayyane yace "Dole na sanarwa su Mummy sabida jinin ta sake Hawa yake Yi" Ya shige ciki ai kuwa Yana shiga har d'akin mummy yayi zama yayi ya Sanar mata da halin da Ma'isha Ke ciki tace "yanzu Isha dama akan na miji ne ta kamu da ciwon zuciya?" "Wallahi mummy Ni kaina abin mamaki yake bani" Daddy ne ya shigo Zama yayi Bayan sun gaisa ta Sanar mishi da halin da Isha take ciki Murmushi irin tasu ta manya yayi yace "Habae biri yayi kama da mutum, Dole mu nema Mata farin ciki ta samu abinda take so, koma wane ne zan Nemo shi sanan Nan da sati uku za a d'aura musu aure" "Haba alaji ko waye fa kace idan Kuma ba mutumin kirki bane fa?" "I trust my daughter baza ta tab'a son abinda bayi da kyau ba." Uhmnn kawai mummy Tace Haisam yace "am in full support Daddy Dole a nemo shi ko ina yake don wallahi idan bata Samu abinda take so ba zamu iya rasa ta" Daddy yace "Insha Allah, zan mata magana." Mummy ta ce "Amma ya kamata a bita a hankali gudun kar rashin Lafiyan nata ya kuma tashi ya kamata ace tana samun kulawa ne" "kar ki damu insha Allah zan San yanda zanyi ta fad'a min." Mikewa daddy yayi ya nufi d'akin ta babu yanda baiyi da ita ba ta fad'a masa Tace Masa "Babu wanda nake so Daddy." Matsa mata yayi Sosai daga bisani ta fashe da kuka daddy ransa a mugun 'bace ya bar d'akin. 'Dakin mummy ya nufa ya tarar haryanzu Mummy da Haisam maganar suke,hushi yake Yana fad'in "Taki ta fad'a min,ban san wani irin taurin kai Isha take da shi ba,tana chan tana kuka don kawai na bukaci ta fad'a Mana gaskiya" Mummy mikewa tayi Tace "Ka gani ko Alhaji,sai da fad'a maka mubi ta a hankali" tana kai Nan ta fice da sauri tayo d'akin Isha. Haisam shima mikewa yayi yace "Daddy kawarta fa tasan komai" Kallon sa yayi kana yace "Wacce kawarta Kenan?" "Daddy ai kawarta d'aya ce Ameerah,I over heard them suna maganar sa but na bita ta fad'a min Taki ta Sanar dani" "Ta kwana gidan sauki,Ni zan same ta da kaina kasan inda zamu same ta?" "Eh har gidan su na sani,Kuma Nurse d'in mu ce" "Shikenan idan Allah ya kai mu gobe sai muji" "Allah ya Kaiimu" sai ya fice. Mummy na Shiga d'akin Isha ta tarar da ita kuka take Sosai rungume ta tayi tana rarrashin ta amma Taki yin shiru, ganin Kamar numfashin ta na kokarin tsayawa ta shiga kwalla wa Haisam Kira, Haisam kuwa dama yazo fita ne yaji irin kiran za take masa, da gudu ya dawo ya Shiga d'akin, Daddy da sadiya suka shigo a tare. Duk kanta suka nufa Haisam kuwa Bayan ya duba ta d'akin sa ya Koma ta d'auko first aid box ya fara duba, Duk abubuwan da yakamata yayi Mata kana ya mata alluran bacci, mummy kuwa kuka take Sosai daddy na rarrashin ta, sadiya kuwa tausayin Ishan ce ya kamata sai matsar kwalla take, sabida Isha ta kasance tana kyautata Mata. Haisam ne yace "Mummy!! daddy!! Ya kamata mu bar ta ita kad'ai ta samu damar bacci, mummy Dan Allah ki daina kukan hakan Nan, Kar kema ki jaa wa kanki wata matsalar please." Hannun ta daddy ya rike suka fice daga d'akin,sadiya tafita, Haisam kuwa kallon ta ya tsayayi na d'an wasu lokuta kana ya fice daga d'akin. A hanyar sa ta fita ya jiyo Muryar Umma da Abba a parlor da sauri ya karasa Bayan ya gaida su ya Mika hannu ya d'auki kannen sa wata Aaima da Aymana,  mummy dai haryanzu kukan take Umma hankalin ta tashi yayi ganin mummy a Haka, cikin Muryar kuka Tace "Dama jikin Daughter yayi tsanani har hakane? Nifa tun a asibiti da na ga har munyi Hira na d'auka taji sauki Sosai." Ajiyar zuciya daddy yayi ya Sanar Mata abinda yake damin ta dama sun 'boye Mata Tace "Innalillahi wa Inna ilaihirraji'un, Ciwon zuciya a d'an karamin shekarun Nan nata? Kuma akan na miji? Dan Allah wane ne shi? Ni zanje na durkusa har gaban sa ya aure ta" ta fashe da kuka, cikin Muryar kuka Mummy Tace "Bamu San shi ba, Taki fad'a mana Wanda take so" Daddy yace "Yanzu kukan da kuke me zai amfane mu dashi? Dan Allah da wanne zamuji?" Tsaki yayi ya fice daga gidan, Abba ma yabi Bayan sa, a garden suka zauna suna ta tattaunawa har Abba ya bukaci da a d'aga auren daddy yace "A a Abdul baza a d'aga auren Nan ba" "Amma Yaya ka duba halin da isha ke ciki, shi Karan kansa baya cikin hayyacin sa" "Uhmn bikin Nan fa saura 4 days, 4 days kawai me zamuce wa jama'a?" "Amma Yaya Ana uzuri ko?" "Eh Ana uzuri, Amma baza a d'aga bikin Nan ba, ranar jumma'ar Nan za'a d'aura auren. Abba ganin Daddy dagaske yake hakan yasa ya bar maganar suka Fara maganar kasuwancin su, Haisam kuwa Zama yayi dasu mummy Yana Basu hakuri had'e da wasa da kannen sa, sun girma sai wayo idan sukayi wata maganar zakace fad'a musu akayi, dab da sallar magrib Abba ya Shigo akan su koma gida. Umma ta kekashe Tace babu inda zata je anan zata kwana sabida ta kula da Ma'isha, Dole daddy ya hakura, Daddy ne yace "To kaji, kaima sai ka kwana anan, tunda gidan babu kowa baza ma kaji dad'in gidan ba." Murmushi yayi irin nasu na manya yace "To ya na iya da garen da ba wuya? Dole nima na kwana" Daddy ne ya maida kallon sa ga Haisam yace "Toh masu kanne taso muje Masallaci" suka wuce. Sosa keya Haisam yayi ya bi Bayan su. Ma'isha sai da gari ya Waye kana ta farka, mikewa tayi ta Shiga ban d'aki ta wasa ruwa    kana ta d'auro alwala Sannan ta Shiga jero sallolin da ake binta, Bayan ta idar ne ta sauko parlor Jin muryar su Mummy a dinning room ne ya sa ta nufi gun, da sallama ta karasa inda suke ta jaa kujera ta zauna dukkanin su kallon ta suka Shiga yi cike da mamaki Umma tace "d'azun Nan fa na leke ta tana bacci, Amma gashi ta fito." Abba ne cike da kulawa yace "Daughter ya jikin naki?" Ta amsa da "Sauki Alhamdulillah" Daddy yace "Sannu daughter" Ta amsa da "Yauwa nagode Daddy." Mummy mikewa tayi ta shafa kanta had'e da tab'a wuyan ta Tace "Jikin naki da d'an zafi har yanzu" "Uhmn da sauki mummy" Haisam kuwa gyaran murya yayi yace "Princess ya jikin naki? Da fatan bakya jin komai yanzu?" Kirkirerren Murmushi tayi kana tace "Eh bana jin komai , sai Kaine da yake d'an sarawa kad'an kad'an" "Allah ya sauwaka, shima zai daina a hankali." Duk suka amsa da "Allah yasa" Kallon Mummy Ma'isha tayi Tace "Mummy nima a Samin abincin" Jika na rawa ta sa mata abinci, kallon ta suka tsaya yi Murmushi tayi Tace "Dan Allah ku daina kallo na haka sai ku sa na kware." Haisam yace "Ai Dole ne mukalle ki, Duk da Yan kwanaki kikayi bakya cikin mu, ji muke Kamar shekara kikayi" ya maida kallon sa ga su Umma ya d'aura da fad'in "Ko ba Haka ba" Umma ta amsa da hakane, dariya sukayi suna ta hirar su, dukkanin su sunji dad'in ganin Ma'isha a haka. Sai da aka Fara kiraye kirayen sallar azahar ,Duk mazan Suku fice zuwa Masallaci, Bayan sun idar da sallar kuwa asibiti suka nufa, Haisam office d'insa ya bud'e musu suka zauna kana ya fita, bai wani dad'ewa ba suka ya Shigo Meerah kuwa na biye da shi. Har kasa ta durkusa ta gaida daddy ne yace "Tashi ki zauna" Yana nuna mata kujerar dake fuskantar su, Bayan ta zauna ne ya Fara magana yace "Meerah nasan Daughters bata da kawar da ta wuce ki, sannan nasan kin San sirrukanta Dan Allah ina so ki fad'a min abinda Kika sani game da Wanda take so" Kai ta d'aga ta kalle shi kana ta maida kanta kasa Tace "Daddy ban sani ba, ban San Wanda take so ba" Abba yace "Please ki fad'a Mana gaskiya nasan Dole Akwai abinda Kika sani akai" Meerah har cikin ranta take so ta Sanar dasu gaskiya Amma idan ta tuna alkawarin da tayi wa Ma'isha sai ta fasa Tace "Abba da na sani wallahi zan fad'a Muku" Haisam ransa ya yi mugun 'baci cikin 'bacin Rai yace "Wallahi karya take Daddy, da kunne na fa naji lokacin da suke maganar Amma yanzu Kuma don ta Raina Mana hankali tace bata sani ba" Daddy yace "Son calm down" Abba yace "Kinji ko Ameerah, Dan Allah ki fad'a mana wane ne, kece kad'ai zaki taimaka Mana wajen sama wa zuciyar ta abinda take muradi" Shiru tayi tana matsar kwalla, a tsawace haisam yace "Shegen taurin Kan tsiyane da ita, ranar babu yadda banyi da ita ba Akan ta fad'a Min Amma taki, na rantse da Allah idan wani abu ya sami princess...... " Daddy ne ya d'aga Masa hannu yace "Ya Isa , ya Isa " mikewa yayi ya kalli Abba yace "Mu tafi ko?" Abba Rai ba dad'i ya mike yana girgiza Kai, Sai da suka Isa kofar fita, Abba ne ya juyo ya kalle ta yace "ki yiwa girman Allah ki ceci rayuwar Isha wallahi tana cikin wani matsanancin hali dan Allah ki fad'a mana gaskiya wane wannan wanda Isha take so a ina yake kuma d'an waye?" Cikin Muryar kuka Tace "Wallahi ban sani ba,da na sani da na fad'a Muku" Girgiza Kai Daddy yayi yace "Allah shi kyauta" suka fice Haisam Rai a 'bace yace "Tirrr da qawa irin ki, Wallahi ko kaffara bazan yi ba kin San komai" "Ya Haisam ban....... " A tsawace yace "Get out of my office" a tsorace tayi hanyar fita sai da ta kusa fita yace "Kuma ki sani idan wani abu ya same ta kece sila" cikin kuka ta fice. Tana fita shima ya fita, rufe kofar office d'in yayi ya nufi gun su Daddy dake tsaye a jikin motar sa suna jiran sa , hakuri ya basu Duk suka shige motar suka koma gida, Bayan ya ajiye sune ya koma office don cigaba da aikin sa. Daddy da Abba ganin Isha na walwala hakan yasa suka d'an ji dad'i, ta wuni cikin farin ciki sai fara'a take,Nan suka Cigiba da shirye shiryen biki, Isha kuwa Duk lokacin da ta Shiga tashin hankali sai ta Rika ambaton '''la'ila ha illa anta subhanaka inni kuntu Minal zalimin''' hakanne yasa ta ji sauki abun Sosai. Rana bata karya sai dai uwar d'iya taji kunya, yaune ranar da Haisam da Aysha suke jira, shine ranar da yafi shekaru har hud'u yana jiran wannan ranar, Bayan sallar jumma'a za a d'aura auren amma a kofar gidan su Aysha za a d'aura dalili kuwa shine mahaifin Aysha ne ya bukaci hakan. Bayan sallar jumma'a jama'a sun taru, ga Nan waliyin Ango Amma babu waliyin amarya, Abba ne ya bukaci da a d'an jira su, wurin shiru yayi kwasam suka jiyo horn d'in mota da gudu motar ta karasa rumfar da Mutane suke zaune, Kura motar ta tada mutanen daga masu Allah ya wadai sai masu zagi, sai wa'anda Kuma suke kokarin toshe hancin su. Kowa hankalin sa a Kan motar take kowa son ganin Wanda ke cikin motar suke son gani, ai kuwa Mahaifin Aysha suka gani da Kanin sa, inda su daddy suke suka zauna, Haisam kuwa fararen jamfa da garen sa Sannan kansa bakar hulace Kamar yadda takalmin sa yake Baki,sai baza kamshi yake,  Murmushi yake abokanan sa na tsokanar sa babu ma Kamar Farukh, Malamin da zai d'aura auren ne yayi hamdallah zaiyi magana mahaifin Aysha ya dakatar dashi malam yace "Lafiya dai ko?" Ya amsa da "Uhmn lafiyar Kenan Akwai Wanda ya kamata ku gani kamun a d'aura auren na" Abba yace "Wane ne? Kuma yana ina?" Hannu ya d'aga ya nuna Masa jikin motar, Haisam, Abba da Daddy naga sun mike Daddy ne yace "Innalillahi wa Inna ilaihirraji'un" _____________________________ Naji dad'i Sosai da addu'oin kuyi hakuri ban samu damar muku reply ba nagode Sosai Allah ya saka da alhairi. Please comment and share 🍃*DANGIN UBANA*🍃 Story & Written By Milhaart Na zo muku da littafi Mai ban tausayi,cike da abun al'ajabi,wannan salon na daban ne. *🌍MANAZARTA* *WRITERS ASSOCIATION📚🖊* *M. W. A* ```Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.🤙🏻``` https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa ____________________________________ *Wannan labarin kirkirarren labarine ban yarda a chanza min labari ba Wanda ya chanza bamu yafe ba.* Ina alfahari da rubutu,sabida alkalami yafi takobi🗡️🗡️🗡️ *BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM* Page 41&42 _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._ _Continuation........_ Abba kallon su Daddy yayi ya dafe kafad'ar sa had'e da fad'in "Yaya Lafiya naga Duk kun rud'e" Haisam cikin rawar murya yace "Kanin Mahaifiyi na" a dai dai lokacin Malam ya iso Haisam karo zaro idon sa yayi da ganin Aysha a bayan sa, cikin kid'ima yace "Habibty dama kin San shine?" Yar karamar dariya tayi tace "Na San shi mana" "Amma.... Amma ta yaya? Kin San shi Kuma baki sanar dani ba? Why?" "Yaya Haisam kenan, Dole na sanshi sabida jinin sa ke yawo a jinin jiki na" Tana maganar tana kallon jikin ta, Haisam kama baki yayi Nan da Nan zufa ya keto masa yace "Kina nufin...." Tayi saurin katse shi da fad'in "Eh mahaifina ne, Nayi mamaki da ba ka gane kanwar ka ba" Zaro Ido yayi waje yace "Ayrah!!! Dariya tayi Tace "Yaaap you got it right, d'azu ka tambayeni meyasa ban fad'a maka na San shi ko?" Shiru yayi Yana kallon ta bashi kad'ai ba kowa da kowa na son Jin dalilin ta, gyaran murya tayi Tace "To ga amsar ka Nan, nayi hakan ne saboda na karya maka zuciya, na sa maka soyayya ta a ranka sabida na ga bayan ka" Idon sa fal da kwalla Yana Fara magana suka fara gangarowa yace "Amma me na miki what have I done to deserve this?" "Oh so you don't know? Kar ka rainawa kan ka hankali mana don't act innocent" Murmushin gefen baki Malam hassan yayi yace "Just tell him Yar daddy, fad'a masa ya kamata ki tunatar dashi" "Toh daddy" kallon ta ta maida ga Haisam Tace "Dr Haisam, wannan shine sakamakon tozarta mahaifina da kayi ka kwace Masa dukiyar sa sabo son zuciya irin naka" Daddy Rai a 'bace yace "Dukiyar sa? Ko Kuma dukiyar Haisam?" Kallon mallam Hassan yayi yazo ya tsaya gaf dashi yace "Bayan ka kashe shi yanzu Kuma so kake ka kashe d'an sa?" Cikin rashin fahimta Ayrah ko ince Aysha 😁 Tace "Wa aka kashe?" Girgiza kai Daddy yayi "Hakan ne ya tabbatar min da baki San komai ba, you are just dancing to your father's tone amma Ni zan fad'a miki gaskiya wannan mutumin da kike gani...." ya nuna malam Hassan ya d'aura da fad'in "Shi ya Kash........ " Da sauri malam Hassan yace "Kul ka fita daga idona na rufe Kar ka d'auka don kana da kud'i ka d'auka kafi karfina Wallahi ka fita daga harkan family na" Kallon Haisam malam Hassan yayi yace "Kuskuren ka shine da ka d'auko zuciyar yafiya irin na iyayen ka shine ya cutar da Kai da ace ka koreni daga gidan Nan da company da ka bani da Duk hakan bai Faru da Kai ba" Daddy kallon su yayi yace "Amma ya akayi kune kuka bamu aure ba shi ba?" 'daya daga cikin sune yace "Wallahi biyan mu yayi bamu san komai ba" Haisam Banda zubar da hawaye babu abinda yake. Abba yace "Amma baku kyauta ba sabida kud'i a had'a baki da ku a cutar da wani, yanzu fisabilillahi baku ji Kunya ba?" Jikin sune yayi sanyi d'ayan yace "Wallahi tallahi bamu San Shirin su Kenan ba, mu ce mana sukayi baya gari Kuma zai dad'e bai dawo ba, Sannan ya tabbatar Mana da cewar Kun matsane in ba ayi baikon ba zai iya fasawa" Haisam kallon Ayrah yayi kusa da ita ya tsaya suna iya shakan numfashin juna yace "Naji kin yi hakan ne sabida ki d'au fansa a kaina Amma Dan Allah Duk rintsi Kar ki rabu dani don wallahi idan na rasa ki zan iya rasa Raina ko Kuma nayi karamin hauka." Jikin ta sanyi yayi tasan tabbas ta cutar dashi amma lokaci d'aya ta tsinci kanta da rashin tausaya Masa maganar da mahifinta ya fad'a mata ta tuna "Haisam har marina yayi sannan yaci mutunci dakyar na roke shi ya bar Mana wannan gidan da 'dan karamin company Bayan duk wannan gumi nane hassada ce da kyashi irin na d'an Adam" Muryar Haisam ce ta dawo da ita daga tunanin da take Yana fad'in "Dan Allah Kar kice zaki rabuna dani Dan Allah, please ki bari a d'aura Mana aure and I'll make things right." Tace "Over my death body, Bayan abunda kayi wa mahaifina Wallahi ko mutuwa zakayi bazan tab'a auren ka ba, idan ka mutu ma bani da asara" Tari Haisam ya Fara yi ya rike kirjin sa Nan da nan ya fara tarin jini, Abba da Daddy ne sukayi saurin rirrike shi, tsaki tayi had'e da fad'in "I hate you, fool Wai soyayya, soyyaya my foot" Malam hassan ne yace "Allah ya miki Albarka daughter ina alfahari dake" hannun ta ya rike suka shige motar da suka zo dashi, suna barin gun kuwa Haisam ya yanke jiki ya Fad'i a sume, Abba ne ya d'auko mota da taimakon daddy,da Farukh da wasu daga gun aka sashi a mota, Basu Zarce ko ina ba sai asbiti. Nan da Nan Mutane suka Shiga jinjina lamarin Nan kowa na tofa Albarkacin bakinsa wasu suna ganin hakan da aka yi wa Haisam ba dai dai bane wa'anda suka yarda da maganar malam Hassan kuwa suna Allah ya kara. Emergency aka kaishi, daddy ne ya Kira Mummy ya fad'a mata Umma najin hakan ta fashe da kuka a lokacin suna tare Kuma wayar na handsfree ne, Isha fitowar ta Kenan taji wannan mumunar labarin Duk da bata San dalilin sumar tasa ba, driver suka Kira ya kaisu asibiti, Isha hankalin ta yayi mugun tashi Bayan sun Isa asibitin aka hana su Shiga. Duk suka tsaya zugum kowa da abinda yake ayyanawa a ransa, ganin Shirun yayi yawa Ma'isha cikin kuka Tace "Daddy me ya sami yayan, me ya faru haka har ya suma? Kuma naji kace yana aman jini how comes" Daddy kasa magana yayi haka ma abba, dukkanin su basu tunanin kowa sai Umma. Inda Farukh yake ta nufa cikin kuka Tace "Ya Farukh Dan Allah ka fad'a min me ya faru nasan kana gun kasan me ya sa meshi" Nan ya Sanar mata da komai Duk da shi bai San me dangantakar ta da Haisam ba, Umma fashewa tayi da Kuka Kan mummy ta karasa inda take tsaye ta Fad'i a sume, da gudu sukayi kanta, mummy Ce ta fara Kiran sunan "Nurse Nurse" nurses biyune suka karaso inda suke da gudu, gado suka d'auko suka tura ta suka kaita d'akin da yake kusa da Haisam,Nan Nan likitoci sukayi kanta. Abba Zama yayi a kasa ya fashe da kuka, kuka yake Sosai Kamar karamin yaro daddy ne ya durkusa a gaban sa yace "Haba Abdallah mene haka kake kuka Kamar wani karamin yaro, be a man mana." Cikin kuka yace "Dole nayi kuka Yaya Dole nayi kuka, why me? Why me wani laifi nayi wa Allah da yake horani Haka first was fauziya with my four kids and now Zainab and Haisam sannan fa Tana da karamin ciki, Yaya ina tsaron rasu Suma don wallahi idan na rasa su kuma zaku rasani" Daddy yace "Subhannallah haba Abdallah Kar kayi sab'o Mana, Allah Yana sonka Allah Yana jarraba bayin sa da yake so ne, ka d'auki hakan amatsayin kaddarar ka" "I can't Yaya bazan iya ba, fi kowa Sanin halin da nake ciki I was a sad and lonely man over 25 years sai yanzu da na fara samun kwanciyar hankali Kuma ace na rasa wannan am back to square one" Ma'isha kasa jurewa tayi ta bar gun ta na kuka mai tsuma zuciya, Farukh ne yabi bayan ta don ya samu ya kwantar mata da hankali kasantuwar yasan tana da ciwon zuciya. Abba sai surutai yake Kamar ya fara zarewa, mummy itama kukan take daddy ya rasa yadda zaiyi mikewa yayi yana safa da marwa ji yayi Mummy ta fashe da "Ihu Innalillahi wayyo mun Shiga uku da gudu tayi Kan Abba da ya Fad'i Daddy shima yayi kansa yana jijjiga shi yana Kiran sunan sa, nurses d'in da suke Kan Umma ne suka fito da gudu da taimakon Daddy suka kai shi d'akin da mummy ke ciki suka kwantar dashi a gadon dake gefen nata dama d'akin gadaje biyu ne aciki, Nan da nan wani likitan ya shigo shima ya fara duba shi. Mummy kuka take Sosai daddy ne ya rike ta suka fita suka zauna a kan kujera irin Wanda ake ajiye wa a ko wani ward, kwantar da ita yayi Yana d'an bubbuga Bayan ta yace "Ki daina kukan Nan please addu'a suke bukata a yanzu Dan Allah kiyi Shiru" "Alhaji taya za'ayi na daina kuka, son fa da Zainab Innalillahi wa Inna ilaihirraji'un ga Nan Abdallah shima Wallahi tausayin sa nake ji, a cikin Yan awanni ta fita hayyacin sa" "To ya zamuyi? Haka Allah yaso Dan Allah I need you now kukan ki na tada min hankali Dan Allah Kar ki daina kina karya min zuciya" shiru tayi bata sake cewa komai ba ta cigaba da kukanta, shi Kuma bai daina bubbuga Bayan ta ba a haka har ta d'an samu relief. Likitocin Dake d'akin Su Abba da Umma ne suka fito a tare d'aya daga cikin su yace "Ku kwantar da hankalin ku, Suma sukayi duk su biyun, munyi musu allurar bacci zuwa anjima kadan zasu farka" Daddy ne ya amsa da "Mun gode" sukayi wucewar su, Bayan sun tafine likitocin da ke kan Haisam suka fito su uku, shugaban sune yace "Me ya sami Dr Haisam Haka?" Shiru sukayi d'ayan yace "Ya kamata musan me ke damin sa sabida musan ta yanda zamu 'bullo wa al'amarin" Daddy yace "Nasan Kun San yau ranar d'aurin auren sane ko?" A tare suka amsa da "Eh mun sani" 'dayan ya d'aura da fad'in "maganar zuwa gun dinner sa ma muke aka Sanar da mu an kawo patient Emergency, ga mamakin mu da muka zo muka tarar ashe shine Mara lafiyan" Ajiyar zuciya Daddy yayi yace "Auren ne aka fasa" A tare suka ce "subhannallah Abu baiyi dad'i ba" Sai kuma sukayi shiru suna kallon junan su. Farukh ne yabi bayan Ma'isha inda Meerah take ta nufa Meerah na ganin Isha a haka ta yi saurin tare ta had'e da zaunar da ita tana fad'in "Lafiya Isha? Me ya same ki Haka? Mutuwa akayi ne?" Muka take Banda sunan Haisam babu abinda take kira, cikin kukan ta Sanar da ita abinda Aysha tayi ka karasa maganar da fad'in "I know something was fishy about her,Ya Haisam ya cutar dani Kuma ya cutar da kansa Bayan irin Soyayyar da nake Masa Amma Baya gani Akan sa fa na kamu da ciwon zuciya,Ashe haukata kawai nake akan wata fa ya shiga halin da yake ciki"ta karasa maganar cikin kuka. Farukh Bayan ya karasa inda suke Jin maganar da Ma'isha keyi ya jaa da baya ya tsaya don Jin abinda take fad'a,sai da ya gama jin maganar da take ne ya samu gu ya zauna yace "Isha Yayan ki fa ba mutuwa yayi ba Suma yayi kuma Wallahi shima yana sonki kawai na kasa gane wane dalili ne yasa ya kasa fahimtar hakan, Dan Allah ki daina kukan Kuma Insha Allah hakan da ya faru zai Zama alhairi kinji" Meerah hannu tasa tana share mata hawaye Tace "kinji ko ai na Sha fad'a miki shima yana sonki, da ace kin bi shawarata kin Sanar Masa da Duk wannan bai faru ba" Farukh ne ya amsa da "Wannan hakane Amma kin san bamu muke sarawa kanmu Rayuwa ba we plan but Allah knows what is the best for us, kawai dai sai dai muyi fatan dacewa" Nan sukayi ta mata baki har ta samu ta daina kukan, sai ajiyar zuciya take sabida tayi kuka sosai Farukh pharmacy ya nufa ya Saya mata magani kana ya sayo ruwan sanyi bai dad'e ba ya dawo ya Mika Mata ta Sha, Duk su ukun suka nufi inda Su Daddy suke, suna Isa ganin daddy da mummy a tsaye sai Kuma likitoci biyu a gefen su, Farukh Mika musu hannu yayi suka gaisa yace "Dr Musa, Dr Sani ya jikin Haisam d'in hope everything is okay?" Dr musa yace "Gaskiya Akwai matsala Dr Farukh" Ma'isha Tace "Please Dr Musa wace matsala Kuma Bayan Wanda muke da ita a yanzu? Me ya sami Haisam d'in? Ko dai ya mutu ne kuke 'boye Mana?" Ta Karasa maganar tana matsar kwalla. Dr sani yace "No no bai mutu ba Pharm isha, yana Raye" "So tell me, what's wrong?" Ajiyar zuciya yayi yace "Ya Shiga comma." Ma'isha jaa da baya tayi ta jingina da jikin bango tana girgiza Kai had'e da fad'in "Shikenan Shikenan Shikenan Nima lokacin mutuwa ta tazo" Farukh yace "Haba Isha sai kace ba health practitioner ba? Kin fa San yanda comma take wani aranar ma zai farka wasu Kuma sukan d'auki sama da shekaru 20 suna comma Kuma ana sa ran zasu farka watan watarana, misali Kamar d'an sarki saudiya tun da yayi hatsari ya shiga comma yafi 20 years bai farka ba Kuma bai mutu" Mummy Tace "To me banbancin sa da mamaci ya mutu kawai" Dr sani yace "Bai mutu ba Mummy sau dayawa Akan binne Mutane ba tare da sun mutu ba wasun duguwar Suma ce amma rashin sani sai a binne su" Daddy ne yace "Allah ya Basu lafiya, don comma fa babban tashin hankalin" Ganin sukayi Isha ta tsuke sai ganin ta sukayi a kwance mummy kuka ta fara Farukh yace "Mummy kwantar da hankalin ki ni na bata maganin bacci,tayi kuka sosai gudun Kar ciwon ta ya tashi,na d'auka ma zata gane" Meerah Tace "Aikuwa nima shi nake Shirin bata, baza ta gane ba sabida ai ba a hayyacin ta take ba" Murmushi Daddy yayi yace "Madallah da samun Mutane irin ku a gaskiya daughter da Son sunyi dace" Mummy Tace "Hakane Kam na dad'e Banga Qawa ko aboki Haka ba, Allah ya muku Albarka ya barku tare" Duk suka amsa da ameen. Mummy da Meerah ne suka kai Isha wani d'aki don ta samu damar baccin da kyau,Nan tayi ta baccin ta. ____________________________ Ga masu bukatar Shiga WhatsApp group kumin magana 07083818353 Mata zallah pls , sannan idan kin San baza kiyi sharhi ba Kar kimin magana Dan Allah,don sharhi nake so ba Thanks ko Allah ya kara basira ba,idan ba kyayi zan cire ki. Please comment and share Milhaat ce Yar terawa [7/6, 1:26 PM] Miilhaat: 🍃*DANGIN UBANA*🍃 Story & Written By Milhaart Na zo muku da littafi Mai ban tausayi,cike da abun al'ajabi,wannan salon na daban ne. *🌍MANAZARTA* *WRITERS ASSOCIATION📚🖊* *M. W. A* ```Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.🤙🏻``` https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa ____________________________________ *Wannan labarin kirkirarren labarine ban yarda a chanza min labari ba Wanda ya chanza bamu yafe ba.* Ina alfahari da rubutu,sabida alkalami yafi takobi🗡️🗡️🗡️ *BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM* Page 43&44 _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._ _Continuation........_ "daddy wai me Mutanen Nan suke fad'a ne? Wa aka kashe?" Ayrah keyi wa Daddyn ta da yake tuki tayi wa wannan tambayar, cikin inda inda yace "Don't mind them please,shirme ce da irin sharrin su da suka Saba" "To Shikenan, Amma daddy har naji tausayin sa Wallahi, Ya haisam na da kirkii Sosai" Taka birki yace "Tausayin..... Tausayi Kika ce" Ganin yanda ya ke zaro Mata Ido kana Yana maganar cikin fad'a ya tsorata tata Sosai. Murya na rawa Tace "Am sorry" Tsaki yayi yace "You better be, Banda wawiya irib rashin mutuncin da ya min baki ji tausayi na ba sai Tausayin sa? Kuma kul na sake jin kin ambaci sunan sa sai na sab'a miki shasha kawai" A dai dai Nan suka Isa gida zata fita yace "Dawo Nan" Dawo wa tayi ta zauna bata ce Masa komai ba, ganin bai yi magana ba Tace "Daddy gani" "Mtsss ai na zaci Zama zakiyi kina Kallo na tunda na Zama sa'an ki, kina jina?" Ta amsa da "Eh daddy" "Good, Kar ki kuskura naji kin fad'awa maman ki maganar Nan" "Toh" "Wuce ki fita min a mota." Tur baki tayi kana ta fita, likowa yayi yace "Ni kike turawa baki ina zan Shigo gidan na same ki Sai na ci mutuncin ki" Da guda ta shige gida, shi Kuma ya fita daga gidan. Bayan farfad'owar Abba da umma, Tunda mummy ta fad'a mata cewar Haisam ya Shiga comma ta bud'e sabon babin kuka Daddy kuwa yayi ta fad'a Yana fad'in "Ai dama sai da na Hana ki fad'a mata Amma kinki ji, yanzu ki ga halin da Kika sata a ciki" Abba yace "haba Yaya ya Isa haka Mana tun d'azu kake ta fad'a Kuma, ai dama Dole ta sani ko idan bata sani ba Dole gaba zata sani so ni Banga abun tashin hankali anan ba" Shiru kawai yayi bai ce Masa komai ba, Ma'isha na farfad'owa Meerah ta gani a gefen ta, da taimakon Meera Isha ta zauna abinci ta bata da ruwa da kyar ta karb'i spoon 3 ta Sha ruwa, ta tashi zata fita, Meerah ce ta rike ta had'e da fad'in "Ina Kuma zaki?" "Gun Ya Haisam" "Amma......" Dakatar da ita tayi da fad'in "Yanzun ma hanani ganin sa zakuyi? Bayan d'azu maganin bacci kuka bani?" Sake ta tayi kana Tace " ya akayi Kika sani?" "uhmn Kar ki manta fa Ni pharmacists ce nasan drugs" tana Kai nan ta fice d'akin da Haisam yake ta nufa taga wayam. Da sauri ta fito ta hango Bayan Meera Kiran sunan ta tayi ta tsaya, su Daddy najin Muryar ta Duk suka fito , da sauri ta Karasa inda take Tace "Ya ban ganshi ba?" "To ta ya za'a yi ki ganshi ce miki akayi ya shiga comma to where do you expect za a Kai shi pharmacists?" "Oh so that's mean yana ICU" Hannu ta d'aga mata alamu oho, ta juya tayi tafiyar ta tana ganin su Umma ta nufi inda suke, dukannin su Sannu suke Mata ta amsa. Abba ne yace "Ya kamata mu koma gida ko tunda duk Mun farka" Umma Tace "A bar Haisam d'in dawa?" Ma'isha Tace "Umma Kar ki damu ina Nan, Kuma baza a bari a Rika Shiga kansa ba , kin san ba'a son motsi ko kad'an a ciki" "Hakan na nufin bazan sake ganin sa ba ko?" Ta karasa maganar tana matsar kwalla, Ma'isha rungumar Umma tayi Tace "Please Umma ki rage kukan Nan haka Kinga nima na daina ko muyi ta Masa magana, Kuma Insha Allah zan nemi hanyar da Zaki Rika ganin sa lokaci zuwa lokaci, Kuma fatan mu shine Kar ya d'auki tsawon lokaci a ciki" Mummy Tace "Allah yasa hakan ne don nifa Sam ban yarda da likitocin Nan ba, a Haka sukayi wa wata makwanbciyar mu ba Ashe kashe ta sukayi ance fa yawanci likitocin Nan mayu ne" Ma'isha tayi saurin fad'in "Laaah mummy Kenan Nima mayya ce ko?" Duk sukayi dariya a Haka suna Hira har suka fita, Umma da Abba suka Fara ajiyewa a gida kana su daddy suka wuce gida. "Qawata ya akayi haka? Meyasa zakiyi wa Haisam haka? Dama ba son shi kike da Gaske ba?" Mardiya ke yiwa Ayrah wannan tambayar, mikewa Ayrah tayi Tace "Na fad'a miki kwanaki a kwai wani buri nawa Wanda nake so na cika, Wanda Wannan burin nawa burin mahaifinane, Wanda na cika Masa burin sa Amma na rasa dalilin da yasa bana farin ciki da hakan" Amma "Ayrah me ya Kai ki aikata irin Wannan d'anyan aiki tunda kinsan ba auren shi zakiyi ba, me yasa Kika had'a harda asiri?" "uhmn Qawata Kennan to ai da ba don ke ba ai bazan samu damar Shiga ransa ba, kinga Kenan amfanin bokan Kenan ko" Mardiya mikewa tayi cikin rashin fahimta Tace "I don't get you please ki Kara min Karin haske Akan abinda ban sani ba" "zauna kiji" Zama sukayi Nan ta Fara Sanar da ita duk abinda mahaifin ta ya Sanar da ita da hanyan da tabi har akayi maganar aure, Kama baki Mardiya tayi Tace "Innalillahi Ayrah Amma gaskiya banji dad'i ba Kuma Ni gaskiya ina kokonta Akan maganganun kin Nan Haisam Sam bazai aikata hakan ba" Rai a d'an 'bace Ayrah tace "Kina nufin kice Daddy na makaryaci ne?" Cikin inda inda tace "A....A'a Ni Sam ba Haka nake nufi ba Amma..... " Murya Mamy sukaji ma'ana mahaifiyar (Ayrah) tana fad'in "Tabbas karya ya miki" A razane ta Mike jikinta na kyar ma Tace "Mamy dama... dama kina Jin mune?" "Kwaraai Yanzu ke Ayrah kin kyauta wa Kanki Kenan? Ashe dama abinda kuka aikata Kenan ko da yake Banga laifin ki ba kina amfani da abinda mahaifin ki ya d'aura ki a Kaine, to bari na fad'a miki gaskiyar maganar, mahaifin ki shi ya kashe Yayan sa, sannan ya kwace komai da komai nasa........ " Nan ta Sanar da ita komai da komai harda yadda ya aika a kona Haisam da mahaifiyar sa. Ayrah Zama tayi a kasa, kasa motsi tayi sai hawayen dake gangarowa daga fuskar ta bakin ta rawa ta ma rasa me zata ce, Mardiya ce ta karasa inda take tasa a hannu ta d'aga ta ta zaunar da ita a kan gado fashewa tayi da Kuka tana fad'in "Innalillahi wa Inna ilaihirraji'un me na aikata wa kaina, me nayi na Shiga uku" Tsaki Mamy taja Tace "Kuka ba? Baki ga komi ba tunda kin biye wa ubanki zaki ji dashi" tana Kai Nan ta fita, Mardiya ce tayi ta rarrashin ta tana Jin jina lamarin tabbas mahifin Ayrah abun tsorone. Ayrah tun daga Wannan ranar ta Shiga tashin hankali mara misaltuwa tundaga wannan ranar take kiran layin Haisam Amma baya Shiga tayi kuka tayi kuka har ta godewa Allah. Yau ta kudiri aniyar ko ta halin Kaka sai ta ganshi, har asibitin da yake aiki taje aka tabbatar mata da bayi da lafiya, jiki ba karfi ta fita a hanyar ta ta fita sukayi kicibus da Farukh. Farukh na ganin ta ya kawar da kansa Kamar bai tab'a ganin ta , da sauri ta bi Bayan sa tana Kiran sunan sa baiyi niyar kulata ba ganin yadda take kiran sunan da ya ja attention d'in Mutane yasa ya tsaya, kallon ta yayi kana ya kawar da kansa had'e da fad'in "Lafiya kuwa kike ta bina?" "Am Lafiya lau dama Kaima anan kake aikine?" Kallon ta yayi yasa hannu a aljihun wandon sa kana yace "umm umm a specialist nake, tambayar Nan ce ta sa Kika tsayar Dani?" Jiki a Sanyaye Tace "A a dama ina Kiran layin sa ne baya Shiga shine nazo neman sa aka ce min bayi da lafiya me ya same sa ne Haka?" Ciza leb'en sa yayi cike da takaici yace "As if you care ta ina ruwanki da lafiyar sa bayan burin ki Kenan? To Haisam ya Shiga comma a dalilin ki kinyi farin ciki ko? Mtswww" ya tafi ya barta a tsaye a gun baki a bud'e. Ta dad'e a tsaye a gun kana ta wuce gidan su mardiya ta sanar mata da halin da Haisam ke ciki "tab wai yanzu a dalilin ku, a gaskiya Wallahi Allah bazai bar ku ba, idan kuma ya Rasa ransa a dalilin ki kema kin Zama Kamar mahaifin naki" "look mardiya nasan mahaifina ba mutumin kirkii bane ba, Amma that's not give you the right to disrespect him kin gane ko" "Am sorry am sorry abun ne ya dameni, yanzu mene ne abinyi?" Cikin Muryar kuka Tace " I don't know, I don't know am in a mess Wallahi, idan Haisam bai yafe min ba Nima bazan yafe kaina ba" "kiyi ta istigfari Sannan muyi fatan Allah ya bashi Lafiya, kin san fa Allah ba ya yafe laifin wani wa wani" "Ba Wannan ba, asirin Nan nake so a karya shi, don kin San Boka yace bazai tab'a daina Sona ba har ya mutu sai dai idan Mun tone abinda muka binne" "Ta kwana gidan sauki sai muje mu cire shi" "Shikenan hakan za'a yi zamu had'u gobe Insha Allah" Ta Mike kana ta Tace "Ni zan tafi sai anjima Amma Banga Mama ba bata nan ne?" "Eh sun fita da Ya Ma'aruf" "Oh Ya Ma'aruf d'in kin Nan yaki aure ki had'a ni dashi Mana" "Taaab d'i" " Me na wani tabd'i?" " umm babu babu muje na raka ki" a zuciyar ta Kuma Tace "Allah ya sauwake mu had'a jini da ke" Har jikin motarta ta raka ta, sai da taga fitar ta ta koma cikin gida. Ma'isha tundaga Wannan ranar kullum a asibiti take kwana take ta wuni idan ta koma gida to dalili ne Mai karfi dake a kwai bathroom na staffs hakan yasa ta kanyi wankan a Chan Amma ta fiye yi a gida, Bayan likitocin dake kula dashi ita kadaice ake bari ta Shiga kansa Nan ma sai ta sa wani irin rigar Wanda baya Kara dama an tanadar dashine sabida Shiga ICU sannan suna da takalmi na musamman idan ta Shiga takan d'auka wa Umma hoton sa ta tura mata ko kuma in taje gidan ta nuna Mata. Duk sanda ta Shiga gunsa idan ta fito Sai tayi kuka, ga Nan mutum amma ba Hali yayi magana. Kwan a tashi asarar Mai Rai, wasa wasa Haisam ya kaie shekaru har biyu bai tab'a motsi ba. Daddy,mummy da Ma'isha ne zaune a parlor, gyara Zama Daddy yayi yace "Daughter na Kira ne don ina so muyi wata muhimmiyar magana" "Toh daddy ina sauraron ka" " Yaron Nan Ma'aruf magabatan sa sun Zo nema Masa auren ki Amma nace sai na ji ta bakin ki tukunna, kina son sa?" Ma'isha ji tayi gabanta na duka uku uku baki na rawa Tace "Daddy aure Kuma?" Mummy Tace "Eh Mana Ma'isha so kike mu zauna mu zuba miki ido kina abinda Kika ga Dama? Isha idan ma bacci kike ki farka kina neman kusan shekaru 29 a duniya Amma har yanzu kin kasa fidda miji Kuma bawai kin rasa mane ma ba" Cikin Muryar kuka Tace "Mummy ni gaskiya ban shirya aure yanzu ba" Mummy Tace "Kana ji ko Alhaji, kana ji ko? Yarinyar Nan so take ta jaa Mana zagi a gari shiyasa tun farko nace ba sai kaji ta bakin ta ba asa rana kawai" "Hakane Hajiya sai yanzu na fahimci abinda Kika hango sabida haka Isha zan sa ranar auren ki da Ma'aruf Nan da 2 weeks ki Fara Shiri" Yana Kai Nan ya mike ya Shiga d'akin sa Mummy ma ta Mara Masa baya suka barta a zaune a gun ta rasa me ke mata dad'i abin duniya Duk ya bi ya ishe ta. ____________________________ Please comment Vote And share Milhaat ce Yar Terawa [7/6, 1:26 PM] Miilhaat: 🍃 *DANGIN UBANA*🍃 Story & Written By Milhart Na zo muku da littafi Mai ban tausayi,cike da abun al'ajabi,wannan salon na daban ne. *🌍MANAZARTA* *WRITERS ASSOCIATION📚🖊* *M. W. A* *Wannan labarin kirkirarren labarine ban yarda a chanza min labari ba Wanda ya chanza bamu yafe ba.* Ina alfahari da rubutu,sabida alkalami yafi takobi🗡️🗡️🗡️ *BISMILLAHIR RAHAMANIN RAHIM* Page 45&46 _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._ _Continuation........._ jiki ba karfi Isha ta fita, asibiti ta nufa Wanda shine ya zame Mata wurin wuni da Kuma Kuma kwana ko da kuwa ranar aikin tace ko ba ranar aikin ba achan ta ke Zama, Bayan ta Isa asibitin ne ta tarar da Meerah ta tashi, Isha hannun Meerah ta rike suka fita waje suka zauna a inda ba hayaniya Sosai Tace "Meerah ina cikin matsala Ina cikin tashin hankali" "Kwatar da hankalin ki ai ko baki fad'a ba na fahimci hakan a tattare dake, Amma me ya Faru?" "Uhmn Daddy ne Wallahi" "Me ya sami Daddyn?" Cike da kulawa Meerah ke mata tambayar. Isha Tace "Daddy wai aure zai min Nan da 2 weeks" Murmushi tayi had'e da fad'in "Alhamdulillah Kai Amma naji dad'i Wallahi" Wani irin Kallo ta mata Meera cikin rashin fahimta Tace "ikon Allah Wannan mugun kallon fa, nifa ina Taya ki murna ne" "Zaki taya ni murna ne only if am happy with it" "what do you mean if you're happy wi.....? Hold on kina so kice min bakya son auren ne, nasan Babu Wanda daddy zai aura miki a yanzu da ya wuce Ma'aruf" "Bana farin ciki gaskiya Kuma eh Ma'aruf d'in ne" " Meyasa bakya farin ciki?" "Sabida bana son auren nan ke Kanki kin San Wanda nake so ba Ma'aruf ba, and yanzu fa Dole zasu min" ta karasa maganar tana matsar kwalla. "Isha Kenan ke ma kin Samu zakiyi auren Amma Ni Kuma fa tunda na rabu da wannan d'an iskan shiru babu Wanda naga ya kwanta min" "Uhmnn kefa issue d'inki daban nawa daban, yauwa that reminds me, ya maganar Farukh ne Kam?" "Wai kina nufin Abokin Ya Haisam" "Eh Mana Akwai wani Bayan shine" "Yana nan kin San ya dage sai dai ya turo gidan mu" "Then what are you waiting for? Then ki turashi Mana" "Banfa Gama sanin wane ne shi ba tukunna so Ina bukatar lokaci gaskiya" Zaro Ido Ma'isha tayi Tace "Wani irin sani kike bukata yau kusan 3 years Kennan fa da kwanciyar ya Haisam Kuma tun lokacin kuka fara Soyayya, ke dai kice bai miki bane kalas" "Ba haka bane kin San ai gayen ya had'u ban San meyasa na kasa bashi dama ba" "a gaskiya ki cire Duk wani kokonto Wallahi Yana da kirkii Sosai" "To Shikenan inshallah zan duba na gani, Amma seriously Isha Kar ki tashi hankalin ki Akan maganar auren Ma'aruf Wallahi yana sonki" "nifa bana son shi kin fi kowa sanin hakan, Haisam nake so kuma sho zan cigaba da so" "Haka zaki zauna kina jiran ranar da Haisam zai farka? Kin San ranar da zai farka ne? Kibe abinda su mummy sukace shine kad'ai kwanciyar hankalin ki" Ajiyar zuciya tayi Tace "Hakane I always have faith in Haisam will wake up sooner or later but it seems like...... " Kuka ne ya ci karfinta ta kasa karasa maganar dake bakin ta, Nan Meerah tayi ta rarrashin ta, sai da tayi ta bata baki har hankalin ta ya kwanta suka rabu. "Mamy Dan Allah horon yayi yawa Dan ki yi hakuri ki yafe min" Kallon ta tayi kana Tace "Ayrah na fad'a miki ba sau d'aya ba sau biyu ba, baza ki tab'a samun sakin fuska daga gareni ba har sai Haisam ya farka sannan ya yafewa miki, nifa baki min laifi ba" "Toh Mamy tunda ban miki laifi ba Dan Allah ki daina maltreating d'ina nifa 'yar kice" Mikewa tayi Rai a mugun 'bace Tace "Ni ce ma nake Maltreating d'inki? Oooookaaay wata kin samu dama ina kula ki shiyasa kike fad'a min magana son ranki ko? Tashi ki fice min daga d'aki, Kuma ko da wasa na sake ganin kafar ki a d'aki na sai na karya miki su." Ganin yanda mamy take mata fad'a ta tsorata matuka,Bata tab'a ganin ta a Haka na, hakan ne yasa ta fice da gudu tana kuka, Kanwar Tace ta bi Bayan ta tana tambayar ta "Aunty Ayrah Dan Allah ki fad'a min me ya Faru kullum cikin kuka kike" 'daga kai tayi ta kalle ta kana Tace " Babu komai" tasa hannu tana shara hawayen ta cike da kulawa Tace "Haba Aunty sai dai in baza ki fad'a min ba, na rasa dalili Duk sanda kuke tare da mamy sai kinyi kuka ko wani laifi Kika Mata ne?" Kai a kasa Tace "Eh Nabila, nayi mata laifi kuma ta gindaya min wasu sharud'a Kan ta yafe min" "To ai ni a gani na abu mai sauki ne tunda kin San abinda take so kiyi, sai ki aikata hakan" "Uhmn lamarin Nan ya wuce tunanin ki, Amma ki tayani da addu'a insha Allah komai zai dai daita" "Allahu yasa" Ta amsa da "Amiin." Ma'isha Bayan ta baro asibiti gidan Umma ta nufa, Bayan sun gama gaisawa Umma tace "Amma yau Kam zaki kwana mana ko? Kannen ki suna tambayar ki" "Eh Umma kwana zanyi ina Twins d'in suke ne ma ban gan su ba?" " Sun tafi islamiya" "Haka Auta fa?" (Auta shine d'an da Umma ta Haifa Bayan kwanciyar Haisam zuwa yanzu yaron na da shekaru biyu a duniya da Yan watanni, sunan sa Aayan, amma suna kiransa da Auta). Umma ta amsa da "Yana bacci kin San shi da son bacci" "Wallahi yafi mishi ai, Ni da zan samu hakan ma ina so" "Uhmn daughter Kenan, ki dai bi abin hankali ko da yake yanzu da sauki ma tunda kin kwana biyu ciwon ki bai tashi ba" "Hakane Umma abin ne sai a hankali, gashi Daddy na son d'aura min wata damuwar Kuma" Gyara Zama tayi tana kallon Isha tace "Me kuma ya Faru?" "Umma Daddy wai aure zaimin Nan da sati biyu" "To me abin tashin hankali anan ai dama tare da na Yayan ki za'a had'a rashin lafiyan naki ne yasa aka d'aga, ma'aruf sunan saurayin naki ko?" 'dan tab'e Baki tayi tace "Eh" "Amma Isha me aibun sa naga yaron na da nitsuwa tunda yasha zuwa gidan na ganshi" Cikin Muryar kuka Tace "To Ni Umma yaushe ni zan Sami abinda na ke so ni Wallahi bashi nake so ba, Ya Haisam nake so kuma shi nake so na Aura" Umma Tunda Isha ke magana Baki a bud'e take kallom ta Muryar Mummy suka ji daga bakin kofa tace "Biri Yayi kama da mutum, Ashe dama Soyayya kuke da Yayan naki?" Wuri ta samu ta zauna Umma tana mata Sannu da zuwa ta amsa a gaggauce kana ta maida hankalin ta ga Isha dake kuka tace "Isha dama kina son Yayan ki? Kika cuci Kanki Kar dai ma shine Wanda a dalilin sa Kika kamu da ciwon zuciya?" Kai ta d'aga alamun eh, Umma Tace "Haba Isha Amma baki kyauta Mana ba, Kuma kin cuci Kanki" Cikin kuka tace " Umma ya kuke so nayi ne? Baku ga yanda Yaya yake sonta bane? Idan ma ya sani babu abinda zai Canza tunda ba Sona yake ba" Umma Tace "Ai mune gaba daku Isha da kin sanar damu da Duk Wannan bai faru ba, Kuma da Yayan naki Bai Shiga comma ba" "uhmn Umma Kenan, zafa ku raba su ne kuma yana sonta yanzun ma ai rashin natan ne yasa ya Shiga comma, Kinga da ko an gudu ba lallai bane a tsira." Mummy Kam shiru tayi tana Jin tausayin Yar tatan chan sai ta ce "Idan bakya son Ma'aruf d'in zan fad'a wa mahaifin ki a kyale ki kawai" Umma tace "A kyale ta Kamar yaya? Kina nufin ta cigaba da zama haka tana jiran babu?" Cikin rashin fahimta mummy Tace "Ban gane babu ba?" "Babu man Haisam da shi da Babu ai duk d'ayane, gaskiya to me a bar yarinyar nan tayi auren ta, wa yasan ranar da zai farka?" Mummy Tace "Haba Dan Allah meyasa kike fad'in hakan, Haisam fa d'anki ne" "Isha ma 'yata ce" kallon Isha tayi Tace "Daughter kiyi auren ki kiyi fatan hakan shine alhairi a gare ki dake da Haisam d'in baki d'aya" Kirkirerren Murmushi tayi Tace " Shikenan Umma nagode Sosai Kuma na amince da auren Ma'aruf d'in" Umma Tace "Masha Allah, Allah ya miki Albarka" Ta amsa da "Ameen." Girgiza kai mummy tayi tace "To dama Nazo ne muyi list na abubuwan da ya kamata mu saya mata in yaso zuwa next week sai muje turkey, muyi sayayyan a Chan" Umma Tace "Ai a gani na ba sai munyi list bako?" " Gara dai ayi kin San Akwai mantuwa" "Eh hakane Kam" Nan suka shiga listing kayan d'aki da kayan kitchen d'in Isha mikewa tayi Tace "Nikam zan Shiga bacci nake ji" ta shige ciki abinta ba tare da taji abinda zasu ce ba. Kwanciyar ta ke da wuya Ma'aruf ya Kira wayar ta da Kamar ba zata d'aga ba har dai da ya kusa yankewa ta d'aga bayan sun gama gaisawa yace "Am sorry Isha na tura gidan ku ba tare da sanin ki, Isha na gaji da ganin ki a haka ina sonki kuma ina tausayin ki sabida halin da Kika tsinci kanki a ciki" Tashi tayi ta zauna Tace "Bangane kana tausayin halin da na tsinci kaina a ciki ba?" "Uhmn Isha Kenan na Riga na San komai, Meerah ta Sanar dani halin da kike ciki and please Karki yi fushi da ita ko ranki ya 'baci a Kan hakan nine na takura ta Akan ta fad'a min Nan ma da kyar ta Sanar dani irin Soyayyar da kikeyiwa Yayan ki since from day one na fahimci hakan daga gare ki na d'auka Soyayya ce ta jini, Amma Dan Allah ina so ki bani dama na Shiga rayuwar ki ko da kuwa bazan iya maye miki gurbin sa ba zan kwatanta baki kulawa iya bakin karfina" "Lallai Meerah wato shine ta je ta gaya maka ko zamu gamu" "Yi hakuri ban sanki da fad'a ba" "a a yanzun ma ba fad'a zanyi ba" "Yauwa nasan nayi dace ai" Murmushi kawai tayi yace "Isha Aurena da ke is in two weeks da fatan kina farin ciki da hakan?" "Hmm eh" "Dan Allah dagaske kike?" "Eh dagaske nake" "Kai Alhamdulillah ya kamata mu Fara Shiri ko?" Murmushi tayi kana tace "Eh" "Masha Allah, yanzu kina ina?" "Ina gidan Umma" "Okay ina zuwa yanzu Amma da Kanwata zamu Zo" "To Shikenan sai kunzo d'in" Bayan sallar la'asar yayi horn a mamakeken gate d'in gidan Abba, mai gadi bai tsaya 'bata Lokaci ba ya wangel musu gate d'in sabida zuwa yanzu yasan Ma'aruf da Kuma gun Wanda yake zuwa, Kamar kulluma kud'i ya zaro a aljihun sa ya Mika Masa kud'i ne sun kai kimanin naira dubu biyar murna ya Shiga yi yana kwararo Masa addu'a. Kiran ta yayi akan sun iso, Yar aikin gidan ta aika ta Shiga dasu parlor bakin, kana ta kai musu abin sha da snacks bayan yan Mintuna ta Shigo bakin ta d'auke yake da sallama, Ma'aruf da Kanwar sa a tare suka suka amsa sallamar. 'dago kanta tayi don ganin wacce take sallama, ai ko tana ganin fuskar Isha ta Mike zumbur, Isha ma tayi mamakin ganin ta, Ma'aruf mikewa yayi yace "Ya dai Kun san juna ne dama?" Kirkirerren Murmushi Isha tayi Tace "Eh kamar nasan fuskar Nan a wani wuri" shiru tayi tana kallon ta don tuna inda tab'a ganin ta, Yayin da ita Kuma jikinta sai rawa yake duk ta rasa sukunin ta, gani take kamar Isha tasan Duk Shirin su. Muryar Isha ta tsinkayo tana fad'in "Yauwa kawar Aysha ko? Ko ince Ayrah?" Murmushi kawai tayi bata ce komai ba Isha Tace "Zauna Mana" zama tayi kanta a kasa Isha Tace "Rankashidad'e Kai ma ka zauna Mana" Zama yayi yana kallon yadda yanayin kanwar tasa ya canza, Isha tace "Ya kike ya kwana da yawa da fatan dai an sami abinda ake so" Jin hakan tayi saurin d'ago Kai tana kallonta Isha ta d'aura da fad'in "Ina nufin an fita da result Mai kyau?" Ta maida kallon ta ga Ma'aruf Tace "kasan lokacin su suke bin mu a school" Ajiyar zuciya yayi yace "Ai ni Duk kun tsoratani ne" " Me abun tsoro anan don kawai Mun San juna" "To baki ga yadda Mardiya bta sauya ba?" "Oh dama sunan ta Kennan ai ban sani ba, ikon Allah Kenan back then ina ga sau d'aya ko biyune muka had'u dake ashe zaki Zama sister in-law na" Mardiya da tun d'azu ta kasa cewa komai kirkirerren Murmushi tayi kana ta amsa da "Allah Kenan" Wayar Isha ce ta fara ruri picking tayi Tace "Haba Dan Allah, to ki Shigo parlorn baki man muna ciki" ta ajiye wayan Ma'aruf yace "Wane ne?" Ta amsa da "Meerah ce" Ya amsa da "Oh okay" Bata d'au lokaci Mai tsawo ba ta Shigo bakin ta d'auke yake da sallama, Zama zatayi ta kalli fuskar Mardiya Tace "What me ya kawo Wannan munafukar gidan Nan?" Duk su ukun suka Mike suna kallon juna Meerah Tace "Isha me ya kawo Yar iskan yarinyar Nan gidan Nan?" Murya na rawa Tace "Dama kin santa ne?" Wani irin mugun kallo ta mata sama da kasa Tace "Nasan ta mardiya Kenan, itace wacce nake baki labari Wanda suka Shiga tsakani na da Bashir da kawarta Ayrah" Kallonta mardiya Isha tayi Tace "Tirkashi to ai nima itace kawar Ayrah da sanadiyar ta Yaya na ya Shiga comma" Ma'aruf Duk ya rikece ya kasa fahimtar inda maganar su ta dosa cikin rashin fahimta yace "Wai me ke faruwane Kun sani a duhu?" Meerah Tace "Ni zan fitar da Kai daga cikin duhu ko Kuma ince zan kunna maka haske,in dai Wannan yarinyar kanwar kace Wallahi Sam bakayi dacen kawa ba sabida wannan da kake gani tafi bakar macijiya mai mugun dafi" Isha Tace "Please Meerah maganar nan ta wuce, please kiyi hakuri ki manta komaai dan Allah" "Isha ke Shaida Ce kin San halin da suka sa na shiga, Duk duniya zan iya yafe komai Amma banda abinda Sukayi min" Ma'aruf yace "Isha please Kar ki hanata Dan Allah, Meerah Sanar dani me Kanwata ta Miki?" Mardiya kuwa duk da AC da ke d'akin bai hana jikinta jikewa da zuwa fa, sai rarraba idanu take, juyawa tayi da niyar fita daka Mata tsawa ma'aruf yayi yace "Dawo Nan" Jiki Sim sim ta dawo ya nuna mata kujerar dake gaban sa yace "Zauna anan" sai da ta zauna ya maida kallon su ga Meerah da Isha yace "Please ku zauna, Meerah ki Sanar dani abinda ya kamata na sani" Kallon Kallo Meerah da Mardiya suka shigayi wa juna. Ana wata sai ga wata shine mene ne wannan abun da Mardiya tayiwa Meerah? Ku cigaba da bibiyata, don Jin yanda labarin zata kasance. _____________________________ Ina Jin dad'in comments d'inku Group d'in Dangin Uban dama sauraun groups d'in, bana samun damar yi muku reply Amma ina gani sannan hakan na faranta min Rai nagode Sosai Allah ya bar Kauna. Please kuyi min sharing sannan ku cigaba da Sharhi ni Kuma na Rika yi muku typing Milhaat Ce Yar Terawa [7/6, 1:26 PM] Miilhaat: 🍃 *DANGIN UBANA*🍃 Story & Written By Milhart Na zo muku da littafi Mai ban tausayi,cike da abun al'ajabi,wannan salon na daban ne. *🌍MANAZARTA* *WRITERS ASSOCIATION📚🖊* *M. W. A* *Wannan labarin kirkirarren labarine ban yarda a chanza min labari ba Wanda ya chanza bamu yafe ba.* Ina alfahari da rubutu,sabida alkalami yafi takobi🗡️🗡️🗡️ *BISMILLAHIR RAHAMANIN RAHIM* Page 47&48 _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._ _Continuation......._ Ma'aruf ganin sunyi shiru ya Kuma cewa "Meerah kinyi Shiru, Ina sauraron ki, Dan Allah ki Sanar dani Kar ki boye min komai" Ajiyar zuciya Meerah tayi kana Tace "Na San ka San kawancen dake tsakani na da Mardiya Bayan Isha bani da wata kawa da ta wuce Mardiya" Kai ya d'aga had'e da fad'in "Wannan Hakane" "Mardiya tayi amfani da yardar da na Mata ta cutar dani" gyara zama tayi kana Tace "Bayan na gama secondary school, ina burin Shiga School of nursing Amma Abba yaki ya fi so sai na yi aure in yaso na cigaba da makarantar, Already dama ina da saurayin da yake son Aurena Mai suna Bashir, Bashiir mutum ne mai bala'in kishi, Kuma yana yawan fad'in shi idan ya auri mace ya same ta ba a budurwa ba zai rabu da ita" Ma'aruf yace "Ina sauraron ki" "To akwai wani d'an unguwar mu , Kama sanshi sunan sa Usman ana Kiran sa da Usu" "Eh na gane shi" "Akwai wata rana Mardiya ta shigo gidan mu ta zo take min labarin sa, akan yana da kirki Kuma yana Sona, sai nace Mata kina da shirye me wallahi an fa Riga da ansa ranar biki na Nan da yan satikai Kuma kike min maganar wani, sai Tace min "Ai ba a d'aura ba tukunna ai ansha yin hakan" Nace Mata "Bana so ayi hakan akai na gaskiya kima bar maganar Nan kawai." sai ta Ciro wasu kud'aden da ni ban San adadin su ba, Wai Usu ne yace a bani, babu yadda batayi da ni ba naki karb'a, a haka ta maida masa, ba shine na farko kuma ba shin na karshe ba tana yawan kawo min maganar sa Duk da na nuna Mata Bana son hakan. Sau dayawa takan kawo min kud'i da turaruka akan shi yace a kawo min ban tab'a sa hannu na karb'a ba, tunda bana son sa bazan so abin hannun sa, akwai wata rana ana saura 5 days da bikina tazo gidan mu nace "Mardiya ya batun lalle ne, wa Kika Sanni wacce ta iya, don Gaskiya ina so a fitar Dani" Tace "Eh akwai wata mata da take yi gidan ta bayi da wani nisa sai muje a Miki,Amma fa sai munje Mun tambaye ta,ta San da zaman ki" "To yaushe kike ganin zamuje?" "Zuwa gobe,idan Baki da abin yi" "Okay zan fad'a wa Mama Sai muje,zan ma Kira Isha sai muje tare" "Ki bari ranar lallen sai muje tare da Isha d'in tunda yau ai tambayar ta zamuyi ko?" "Eh to da Wannan ma, Allah ya Kaiimu goben" Nan muka cigaba da hirar mu, washe gari Bayan sallar azahar sai ga Mardiya ta shigo gidan mu,dama na sanarwa Mama inda zamuje tana zuwa na Sanar da ita zamu fitan, ta min a Dawo Lafiya Kuma tace Kar ka na dad'e,muka tafi, napep muka hau wani gida d'an madaidaici muka nufa, kusa kan mu mukayi muka Shiga ciki Bayan mun Shiga har parlor muka zauna. Bayan Mun Zauna ne naga wani Saurayi ya fito daga shi sai gajeren wando da singlet, Ya mana Sannu kana ya wuce, Yana fita nima na miki na Fara masifa ina fad'in "Dama Nan gidan zaki kawo ni, gidan maza, kince Nan gidan mai lalle ne Amma Banga mace ko d'aya ba tunda muka Shigo" hannu na ta rike Tace "Haba Meerah Nan gidan Mai lallen ne wallahi tana ciki shi Wanda ya wuce d'an tane fa" Kan na bata amsa wata budurwa kamar sa'ar mu ta fito Hannun ta d'auke yake da drinks da ruwa ta Shigo da sallama, tace "Sannun ku da zuwa,tana wanka zata fito yanzu" sai ta fice, jin hakan sai naji hankali na ya d'an kwanta, sai na samu wuri na zauna. Mardiya da kanta ta zuba min a kofi na karb'a nasha Sannan ta d'auki d'ayan ta bud'e ta zubawa kanta ta Sha, nace Mata "Big cola ne fa, ai da baki bud'e wani ba" Sai tace min "Eh Wallahi kan ne ba dad'i kin sanni da shirme" girgiza kaai kawai nayi na shanye Tass, kasantuwar ni masoyiyar coca cola ce. Tunda na Sha Wannan naji idanuna sun fara rufewa tun daga Wannan lokacin na manta kaina ban San a Ina nake ba Kuma ban san a wani Hali nake ciki ba, ji nayi na farka a razane d'ago kaina da zanyi na gan ni a kwance a jikin Usu, a razane na Mike nayi kokarin d'aga kafana naji sun min nauyi kallon kafan nawa nayi naga jini na bin kafana. Usu kuwa Kallo d'aya yamin ya kawar da kansa a kaina hakan ne ya tabbatar min da Usu ya min fyad'e, kuka na fara yi ina ja Masa Allah ya Isa shi da Mardiya bazan tab'a yafe musu ba, hijabi na d'auko Nasa ina tafiya da kyar har na fita bakin fate napep na Tara ya kaini gida, ina Shiga gida naci sa'a Mama na d'akin ta hakan yasa na Shiga ban d'aki na gyara jikina. Fitowa ta Kennan daga ban d'akin Mama ta Shigo d'aki na, ganin irin tafiyar da take ta tsaya Kallo na Tace "Me ya same ki a kafa na ga kina limping?" Cikin inda Inda nace "Mun dan yi accident ne a hanya na sai na d'an buga kafa na" Tace "Subhannallah Baki ji ciwo Sosai bako?" "Eh d'an bugewa nayi kuma nasha magani" "sannu Allah ya sauwaka, Ita Mardiya fa babu abinda ya same ta" ji nayi kamar na fashe da kuka da naji ta anbaci sunan ta amma nayi kokarin dannewa nace "Eh babu abinda ya same ta nice kadai na d'an buge" "toh Allah ya tsare na gaba" Na amsa da "Ameen" sai ta fice. Kwana nayi da zazzab'i chemist d'in unguwar mu na nufa na sayi magunguna nasha shine na samu zazzab'in ya d'an sauka, washe gari kuwa da mamaki na ina kwance a d'aki na ga shigowar Mardiya da Wannan Yarinyar da ta bamu abin Sha. Mikewa nayi saye cike da takaici nace "Ke me ya kawo ki gidan mu? Ke don ke karamar Mara kunya ce har kin iya tako kafar ki Cikin gidan mu har cikin d'akina?" Mardiya tace "Kiyi hakuri Wallahi ban San gidan su Usu bane" Murmushiin takaici nayi nace "Ke d'ince baki San gidan su Usu ba? Bayan gidan su Usu a unguwar nan yake? Mardiya kin cuce ni kin lalata min Rayuwa kin ruguza min tanadin da na dad'e ina yi,laifin me na Miki? Wallahi tallahi bazan tab'a yafe Muku ba" Wacce suka shigo tare ce tayi duguwar tsaki Tace "To sai me in baki yafe ba, kar fa ki d'auka Mun Zo neman yafiyar kine, munzo gidan ku ne don muga yanayin da kike ciki" Ji nayi kaina Yana juyawa na rasa abinda yake min dad'i cikin kuka nace "Dan Allah me na muku me na muku" Mardiya Tace "Wallahi babu abinda Kika Mana, Kin san ance mutunci ya fi kud'i but to me kud'i yafi mutunci, 5 mil ba wasa, zuwa yayi ya same mu, Akan mu taimaka Masa ya cimma burin sa Akan ki, kin San ke d'in akwai kayan Jin dad'i " dariya sukayi suka yi tafi kana ta d'aura da fad'in "Ya mana tayin 5mil each ni ko ina ganin Wannan kud'in bazan bari su wuce ni ba" Ji nayi kukan ma na kasa yi ina kallon su baki a bude nace "Yanzu akan kud'i? Akan kud'i Kika min Haka kefa kawatace?" "mtssw Wannan kuma ke ta shafa na samu kud'i na babu abinda ya Sha min Kai, Kuma idan Kika kuskura kikace Zaki Kai karan mu, ina mai tabbatar miki da sai Bashiir yaji labari, Kuma idan yaji kema kin San ba zai tab'a auren ki ba" Ayrah dariya ta Shiga yi Tace "Sunan wani abu wai fanko, anyways kar ki damu baza mu fad'a Masa ba , Amma idan Kika kuskura muka ji maganar nan a wani wuri sunan ki Sorry, Kinga Nan" wayarta Ciro a jaka ta nuna min Video d'ina da na Usu Ashe sunyi Mana video yanda yake lalata dani, ta d'aura da fad'in "Nasan Mardiya baza ta rasa number sa ba zamu tura Masa" Mardiya Tace "Idan kunne ya ji?" Had'e da rike kunnen ta, Ayrah ta karasa mata zancen nata da "Jiki ya tsira" suka yi dariya had'e da barin d'akin na dad'e a tsaye agun kukan da nake yi ma na kasa yi. Zama nayi na had'a Kai da gwiwa ina kuka Jin an turo kofar ne na yi shiru had'e da d'ago kaina don ganin Wanda ya shigo ina ganin Isha ce ta nufeta da gudu na fad'a jikin ta ina kuka, Allah sarki Isha kawar arziki Nan ta zaunar dani tayi tayi ta rarrashi na, Bayan na fad'a mata abinda aka min har ta fini Shiga tashin hankali, tashi tayi akan zataje ta sanarwa su Mama don a bi min hakki na, na hanata sannan na fad'a mata dalili na da farko taki Amincewa bayan hakurin da nayi ta bata ta fasa fad'a musu ba don ta so ba. Ana saura kwani hud'u bikina Bashir yazo gidan mu, ina ganin yanayin sa, sai da naji gaba na ya Fad'i dama a parlor baba muke Hira Bayan Mun gama gaisawa sai nace "Kana Lafiya kuwa,naga fuskar ka wani irine" "Lafiya na Lau,akwai maganar da nake so muyi dake ne" Na amsa Masa da "ina sauraron ka" yace "so nake ki rakani wani wuri yanzu" Zaro Ido nayi nace "Yanzu da daren nan? A a gaskiya Ni ba inda zanje Mama ba za ta bari na fita ba yanzu" Murmushin gefen baki yayi yace "Amma Kuma kin iya zuwa 'dakin samari ko?" Cikin rashin fahimta nace "Ban fahimce ka ba" Yace "Kar ki rainawa kanki hankali don wallahi kinyi kad'an ki rainan hankali" wayan sa ya ciro ya nuna min Video nan, kuka na fara yi ina fad'in "Wallahi ba da sani akayi ba" Amma yaki yarda da magana ta mikewa yayi yace "A Daren nan Nima ina so ki bani abinda Kika bashi in ba Haka ba goben Nan zan turo a karb'a min kayana da na kowo gidan ku" Durkusawa nayi a akasa da gwiwowina ina rokon sa "Dan Allah Bashir Kar ka min haka, Dan Allah da wanne zanji Dan Allah ka rufa min asiri." Yace "Idan kina so na rufa miki asiri kiyo yadda nace kawai" ganin dagaske yake hakan yasa na share hawayena na Mike had'e da fad'in "Bashir idan baka fasa aure na ba kai ba d'an halak bane, kayi Duk abinda zakayi Amma Ni bazan bika" Cike da mamaki yace "Oh haka kikace, kinje ki ba wa wani ni da zan aure ki ne baza ki bani ba?" "Tunda aure na zakayi sai ka jira idan aka d'aura auren sai na baka kaina Amma wallahi bazan tab'a aikata abinda kake so na aikata ba" Yace "Allah ya sauwake na had'a jini na da Yar iska karuwa" "uhmn naji na gode Amma Allah Shaida nane ban a hayyacina aka yi hakan ba" "Dallah gafara makaryaciya inda fyad'e aka miki ai da kin fad'a a gida ko ni Nan bazan bari ba, bare ma karya kike da son ranki akayi hakan" "Ban fad'a wa kowa bane sabida sun tsoratani Akan zasu nuna maka, shiyasa na yi shiru" "Makaryaciyar banza, Ni zaki kalla ki fad'awa hakan an gaya miki ni yaro ne, Wallahi Meerah idan baki biya min bukatata ba zan fasa auren ki" "Sai akace maka Ni d'in wawiyace ko? Oh in baka kaina ka yi yanda kake so dani sannan kaki aure na, Ni ba mazinaciya bace, sannan na tabbata bani da zunubi a agun mahaliccina, sabida haka kazo ka karb'i kayan ka mtssw" tafiya nayi na barshi a gun baki a bud'e shikan sa yayi mamakin yanda akayi ban amince da bukatar sa ba Duk da dama niyarsa ko da kuwa nayi abinda yake so bazai aureni ba. Bayan na Shiga gida Isha na Kira na Sanar mata da yanda mukayi da Bashir, Isha cike da mamaki Tace "Bashir ya bani mamaki, insha Allah, zai had'u da dai dai shi" Cikin Muryar kuka nace "Isha yace zai fasa aurena Dan Allah yazanyi ina tsoro Kar ya sanarwa iyayena" "Kar ki damu, inshallah Allah na tare dake" Nan tayi ta rarrashina, daga bisani ta katse wayar. Washe Gari Da safe Bashir ya turo magabatan sa, gidan mu Akan a maida Masa kayan sa, Baba na jin dalili a take hawan jinin sa ya tashi Mama ta Shiga tashin hankali a gurguje aka kaishi asibiti, Bayan ya farfad'owa yayi kuka har ya tsine min Albarka, Albarkacin Mama ita kadaice ta yarda da magana ta. Baba yafi shekara baya kulani ni kuma ban gaji da bashi hakuri ba duk da ba saurarona yake ba, bayan wasu watanni nayi wani rashin lafiya kamar bazan tashi ba, sanadin rashin lafiyar Nan ne Baba ya saurareni har ya fahimci komai yayi da na sanin fushin da yayi dani sannan ya kudiri aniyar sai yasa an Kama su. Amma mama ta hana a fad'in ta idan akayi hakan tamkar an tona min asiri ne, dakyar ta shawon Kan Baba ya bar maganar, Bayan na samu sauki ne yasa na Shiga school if nursing, tun daga Wannan ranar da zaran mijin aure ya fito Sai a same shi a sanar dashi Kuma na tabbata aikin Mardiya da Ayrah ne. 'dago Kai tayi tace "Ma'aruf kaji abinda Kanwar ka tamin sabida son zuciya irin nata" ta karasa maganar tana kuka. Ma'aruf Banda ambaton Innalillahi wa Inna ilaihirraji'un babi abinda yake yace "Mardiya Ashe haka kike? Innalillahi am finding it Very difficult to believe my ears" Isha Tace "Ya fa Riga ya wuce dan Allah" Cikin Muryar kuka Tace "Hakika nayi abubuwa da dama Wanda ban tab'a da na sani ba sai yanzu Wallahi nayi na dama Dan Allah ku yafe min" Isha Tace "Ni baki min komai ba, Meerah kikayiwa Kuma Insha Allah zata yafe miki" Mardiya Tace "Isha kema na miki laifi kawai dai baki sani bane" Isha cike da mamaki Tace "Laifin me ni Kuma Kika min?" *ina masu son koyon humra da kwalacha na jiki da kuma kwalacha na gashi da turaren wuta da kuma kyaran jiki na uwar gida har amarya akan naira #250 kawai, duk mai bukata ya tuntube ni a wannan number 07053599651* _____________________________ Please comment and share Milhaat ce Yar Terewa [7/6, 1:26 PM] Miilhaat: 🍃 *DANGIN UBANA*🍃 Story & Written By Milhart Na zo muku da littafi Mai ban tausayi,cike da abun al'ajabi,wannan salon na daban ne. *🌍MANAZARTA* *WRITERS ASSOCIATION📚🖊* *M. W. A* *Wannan labarin kirkirarren labarine ban yarda a chanza min labari ba Wanda ya chanza bamu yafe ba.* Ina alfahari da rubutu,sabida alkalami yafi takobi🗡️🗡️🗡️ *BISMILLAHIR RAHAMANIN RAHIM* Page 49&50 _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._ ```Continuation..........``` kallon Yayan ta Mardiya tayi kana ta sunkuyar da kanta kasa tace "Tun ranar da na ganki a cafeteria da Haisam na gane ki, sabida nasha ganin hotunan ki a wayan Meerah, Ayrah ta nuna min tana son sa nice na zugata mukaje gun Boka aka asirce shi, sannan ta bini akan muje mu tona naki, Haisam bazai tab'a son wata ba in har Wannan layan na kasa" Isha Mikey tayi cikin Muryar kuka tana ambaton sunan Allah tana fad'in "Mardiya why? Mardiya me muka miki haka da kike son ganin mun wulakanta?" Kai a kasa tace "Meerah Qawata ce tun muna Yara dake unguwar mu d'aya ke Kuma kawar Tace a makaranta, Meerah tana samun Duk wani gata da jin dad'in Rayuwa iyayen ta sunfi nawa karfi bayan hakan Kuma suna sonta sosai kasantuwar ita kadaice Yar su shiysa da Usu ya Zo min da bukatar sa na amince sabida nasan Dole iyayen ta zasu tsane ta, maganar ki da Haisam Kuma hoton ku na gani ke dashi a wayar Meerah sai naji na kamu da son sa ganin irin Soyayyar da kukewa junan ku nasan bazan tab'a samun Soyayyar sa ba, shiyasa na yi kokarin raba ku, duk Wanda ya ganku zai gane Kuna son junan ku Amma, Haisam bai gane ba shiyasa mukayi amfani da wannan damar wurin rabaku,amma Wallahi tallahi ban san Shirin rabuwa take dashi ba plan d'inta ne da mahaifinta Wanda ni ban sani ba, Amma a yanzu nayi na dama kuma na miki alkawarin yau d'in Nan zanje na cire layan Nan" Cikin Muryar kuka Tace "Kin cuce ni kin cuci masoyina bazan tab'a yafe miki, a dalilin Kune na kamu da ciwon zuciya, sannan a dalilin kune Yayana Yana chan yana kwance Rai a hannun Allah, bazan tab'a yafe muku ba" Durkusawa mardiya tayi ta had'e Hannayen ta wuri gudu alamun roko Tace "Dan Allah kuyi hakuri ku yafe min, wallahi alhakin kune yake ta bina gashi na gama makaranta sama da 3 years Amma babu Wanda ya tab'a zuwa gidan mu da sunan yana Sona, in ko an min zancen Soyayya to jikina suke so Dan Allah kuyi hakuri ku yafe min" Meerah itama mikewa tayi a tsawace Tace "yafiya? Har kina da bakin neman yafiya a wurin mu? Shin zakiyi iya Dawo min da budurcina da kimata da na rasa a dalilin ki?" Isha ta d'aura da fad'in "Shin Zaki iya Dawo min da Yayana? Zaki iya sa ya tashi? Ko Kuma zaki iya bani lafiya" Cikin tuhuma suke mata maganar. Meerah Tace "Baza ki iya bako? To kamar yadda baza ki iya Dawo da wa'an nan abubuwan da muka rasa a dalilin ki ba Haka baza mu iya yafe miki ba" riko hannun Isha tayi da niyar barin d'akin har sun Isa kofar fita, Ma'aruf yace "Isha please " a hankali suka juyo suna kallon sa, ya karasa inda suke yana matsar kwalla yace "Nasan an zalin ce ku, har abada abinda kuka rasa baza su Dawo ba, Dan Allah ina rokon ku, ku yafe mata on my behalf, and please Isha Kar abinda Kanwata ta aikata a gare ki ya sa ki janye maganar aurena dake" Murmushin gefen baki tayi kana Tace "It can never happened" Cikin rashin fahimta a d'an kid'ime yace "What? Isha please Kar kice baza ki aure ni ba Dan Allah" Girgiza Kai kawai tayi ta fice Meerah na ta bi Bayan ta yana Kiran sunan su basu juyo ba bare su saurare shi ya dad'e a tsaye a gun ya rasa abinda ke Masa dad'i d'akin shiru yayi Banda sautin kukan Mardiya babu abinda kake iya ji a parlorn, cike da takaici ya kalle ta Kiran sunan ta yayi da d'an karfi "Mardiya!!! A d'an razane ta d'ago kanta had'e da mikewa jikin ta na kyarma cikin rawar murya Tace "Na...naaa..... Na'am Yaya" Cike da takaici ciza leb'en sa yayi yace "Are you happy now? Kinji dad'i ko? A dalilin ki na rasa masoyiyata" "Wallahi yaya ban sani ba, ban San itace wacce kake so ka aure ba da ban....... " A tsawce ya katse yace "Da bakiyi me ba? Oh sai kin San cewar zan aure ta ne tukkunna kisan abinda ya kamata? Who gave you the right to mingle in someone's life? Me suka miki? Nace me suka Miki?" Ya karasa maganar cikin tsawa har Saida ta razana ta jaa da baya a tsorace cikin Muryar kuka Tace "Yaya please" daka mata tsawa yayi ya nuna ta da 'dan yasa yace "This will be the last day da zaki sake kirana da wannan sunan Ni ba Yayan ki bane, daga yanzu na yanke ki daga jikina" ya Kama hanyar fita da gudu ta karasa inda yake ta rike kafafun sa tana kuka had'e da bashi hakuri, hankad'e ta yayi da kafar sa ta buge bakin ta a Kan tiles d'in dake gun Nan da nan bakinta ya Kumbura ganin ya fice ta bi Bayan sa cikin sauri. Wurin motar sa ya nufa ya shige ganin tasa hannu ta bud'e motar zata Shiga a tsawace yace "Kul Kar ki soma Wallahi Kika kuskura Kika Shiga min mota sai na karya ki kinji na gaya miki" marfin motar ta rike ta sandare tana kallon sa tsaki yayi ya sa hannu ya ja marfin motar sa da karfin gaske ya rufe ya had'a da yatsanta , wani Kara ta saka har da ya tsorata, da sauri ya fice daga motan, hannun ta ya cire ya na mata sannu had'e da hura mata hannun (Nace Allah sarki jini kennan duk da yana fushi da ita amma ya damu da lafiyar ta) yana tuna abinda tayi ya ture ta had'e da rufe marfin motar sa ya zaga ya shige ya sa wa motar key Mai gadi ya wangale Masa gate,Mai gadi yana masa sannu da fitowa Amma bai kalle sa ba bare ya amsa,ficewar sa kawai yayi. Mai gadi girgiza kai yayi had'e da fad'in "Anya Lafiya kuwa?" Sai ya hango Mardiya a tsaye tana kuka ta rike hannu ta tana kallon raunin da Yayan ta ya ji mata, da sauri ya karasa inda take yana mata sannu ganin jinin da yake zuba a hannun ta, yana mata magana bata kulashi, hanyar fita tayi Yana kallon ta har ta fice, tab'e baki yayi had'e da fad'in "Tooooh Allah shi kyauta." Da sallam ya shigo parlor kallon da take Masa ne yace "Mama Lafiya kuwa kike min irin wannan kallon?" Ma'aruf keyiwa mahaifiyar sa Wannan tambayar. "Ina fa Lafiya ina ka baro min yarinya, Kun fita tare Kuma ka Dawo kai kadai" Shiru yayi a zuciyar Kuma yace "Kash Ma'aruf ka kwafsa kasan Dole sai an tambaye ka inda take" a karo na biyi ta Kuma cewa "Ina magana kayi Shiru Ina take?" "Umm... Ummm" Muryar ta ya jiyo a ta Bayan sa tana fad'in "Gani Nan Mama" "mtsww dama kuna tare Kuma shine ina tambayar ka kayir Min shiru" Shiru yayi baice mata komai ba, mardiya inda Mama take ta nufa ta zauna a gefen ta, idon Mama ne ya sauka a hannun ta da yayi jajir jini yana d'an sauka a hankali cikin tashin hankali Tace "Subhannallah Auta me ya same ki?" "Mama na....." Charafff ma'aruf ya kase ta da fad'in "Wurin rashin hankalin ta man, ta datse hannun ta a marfin mota" Hannun ta rike tana mata sannu Tace "Amma shine Kuka Dawo gida baka kaita asibiti ba? Haryanzu fa jini yana zuba" Yace "itace fa, Babu yanda banyi da ita ba muje Taki wai in muka dawo gida zata sha magani shiyasa na kyale ta" Mardiya kallon sa tayi cike da mamakin karyar da yake,ganin tana kallon sane hakan yasa ya mata wani irin muguwar Kallo,da sauri ta kawar da kanta. "idan ita bata da hankali kaima baka dashi Kenan? Maza ka d'auke ta kuje asibiti" Ba don yaso ba ta fita tabi Bayan sa, ta tarar ya Shiga mota har ya tada ta, ta bud'e gidan baya zata zauna a tsawace yace "Ni d'in driver kine da Zaki zauna a baya don gidan ku?" Jiki na rawa ta Dawo gaba, tana zama Bai jira ta rufe kofar ba ya fizgi motar, Mai gadin gidan nasu ya bud'e musu gate suka fice, babu Wanda yayi wa d'an uwan sa magana har suka Isa wani clinic tare suka Shiga yasa aka wanke mata had'e da sa bandage, ya biya sa hakkin sa kana suka fice. "a gaskiya Isha wannan shawarar da Kika yanke bata yi min ba Sam" Meerah kewa Isha Wannan maganar. Isha kallon ta tayi da kamar baza ta tanka mata ba sai Kuma tace "Koh?" Meerah ta amsa da "Kwaraai ma kuwa" "To ni yamin" "Uhmn Isha Kenan, ya kamata ki gane wani abu Mardiya daban haka ma Ma'aruf daban, so please kar laifin wani ya shafi wani please" "Dole ya shafe shi sabida kanwarsa ce, Akan me zan zauna da irin Wannan mutanen sai su kashe ni ai" "Babu Wanda zai kashe ki Isha, sanin Kanki ne Ma'aruf mutumin kirkii ne, shikan sa baiji dad'in abinda tayi ba please ki bar maganar nan iya mu Dan Allah" Kallon ta tayi kana ta girgiza Kai tace "Da ce miki nayi zan kai maganar wani gun?" "To what's the difference Tunda Kince kin fasa auren sa, idan Kika fad'awa daddy dole sai kin Sanar Masa da dalili Kinga Kenan bak tsaya a iya Nan ba" "Uhmn Wai yaushe nace miki bazan aure shi ba? Kawai dai naji kamar na fasa ne" "To Dan Allah Kar ki ji kin fasa,Wallahi mutumin kirkine Kuma yana sonki" "To naji,ke dama ai bakya son laifin sa" "A'a gaskiya dai na ke fad'a idan yayi laifi Kam Dole a hukunta shi" "Meerah sarauniyar dad'in baki" "No kema kin san ni ai gaskiya nake fad'a miki" "To naji mubar zancen please kaina har wani sarawa yake" " Dole ai ni kaina hakan nakeji" "Allah ya kyauta ya mana Mai kyau" Meerah ta amsa da "Ameen" Nan sukayi ta hirar su har Saida akayi sallar Isha ta tafi. Mummy kuwa bata tafi ba har Saida daddy ya taso daga gun aiki yazo ya d'auke ta suka wuce gida. Ma'aruf na kwance ya rasa me ke Masa dad'i kallon silin d'akin ya tsaya yi yana tunanin mugun Hali irin na kanwar sa jin an turo kofa ne yayi saurin d'ago kansa ganin ta yayi a tsaye tana kallon sa wani dogon tsaki ya jaa had'e da fad'in "idan kina tunanin kinzo bani hakuriy ne to kin makaro don ba sauraron ki zanyi ba sabida haka ki fice min daga d'aki" ji ba karfi ta fice tana fita ya mike ya kulle kofar da key ya Koma ya kwanta, wayar sa ya d'auka da niyar Kiran Isha a waya har yayi dialling yayi saurin kashe wa tsaki ya jaa yace "mtsww to me ma zance mata, she has all the right to be angry, Mardiya kin cuce Ni" da Wannan tunaniin bacci ya sace shi. Washe Gari "Auta je ki dubo yayin ki har karfe 9 bai fito ba ko Lafiya" Jin an ambaci sunan sa sai da taji gaban ta yayi mugun fad'iwa , Mama ganin bata Mike ta a d'an tsawace Tace "Ke Lafiyan ki kuwa? Tunanin me kike haka?" Zumbur ta mike had'e da fad'in "Babu" tayi saurin barin gun, d'akinsa ta nufa, kirjin ta na duka uku uku ta kwankwasa kofar had'e da sallama, jin bai amsa ba ta tura kofan a hankali ta shiga, hangoshi tayi a kwance yana danna wayar sa har ta Isa kansa bai sani ba, zagayawa tayi don ganin abinda yake, hoton Isha ta gani yake kallo Duk ya manta kansa , gyara Murya tayi a razane ya d'ago kai ya kalle ta, a tsawace yace "Ke Wace irin dakikiyace da zaki shigo min d'aki ba sallama?" Cikin sanyin murya Tace "Nayi sallama baka ji bane" "Oh na Zama makaryaci kenan ko?" Ka ta d'aga Masa alamun a'a. Yace "Uban me ma ya kawo ki d'akina" "Mama ce tace Nazo na Kira ka karya" "Naji fice min daga d'aki" Tace "Yaya Dan Allah kayi hakuri nasan ban kyauta ba ,Dan Allah ka rufa min asiri Kar ka fad'awa su Mama" "mtsww Ce miki akayi ban San me nake ba? Dole ma na gaya musu jira nake Baba ya Dawo na Sanar Masa komai da komai ya kamata su San shaid'aniyar da suka Haifa" Durkusawa tayi tana kuka Tace "Dan Allah Yaya Kar kamin haka Wallahi zasu tsane ni" " Mtsww Wannan Kuma ke ta shafa, indai na rasa Ma'isha Wallahi kema sai kin rasa farin cikin ki, sabida Ma'isha itace farin cikina" "Inshallah baza ka rasa ta ba yaya,zanje har gidan su na bata hakuri Dan Allah Kar ka Sanar musu." Nagode kwaraai da Addu'an ku, Allah ya bar kauna,gamo da Typhoid da malaria nayi Kun san Basu da mutunci😅 Ina sonku fans Allah ya bar Kauna _________________________ Please comment and share Milhaat ce Yar Terawa [7/6, 1:26 PM] Miilhaat: 🍃 *DANGIN UBANA*🍃 Story & Written By Milhart Na zo muku da littafi Mai ban tausayi,cike da abun al'ajabi,wannan salon na daban ne. *🌍MANAZARTA* *WRITERS ASSOCIATION📚🖊* *M. W. A* *Wannan labarin kirkirarren labarine ban yarda a chanza min labari ba Wanda ya chanza bamu yafe ba.* Ina alfahari da rubutu,sabida alkalami yafi takobi🗡️🗡️🗡️ *BISMILLAHIR RAHAMANIN RAHIM* Page 51&52 _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._ ```Continuation.......``` "Naji na amince bazan fad'a musu ba, Amma da sharad'i" "Mene ne shi Wallahi zanyi Koma mene ne in dai Bai fi karfina ba" "Okay kije ki bata hakuri idan ta hakura Shikenan" "To Amma yaya kana ji fa ranar Tace Baza ta tab'a yafe min ba" "Wannan Kuma ke ta shafa, don wallahi idan Isha taki aure na hmmmm...... " Girgiza kai yayi had'e da ciza leb'en sa yace "Idan taki aure na, na rantse da girman Allah sai na muzguna Miki mark my words" ya karasa maganar yana nuna ta da Yar yatsa mikewa yayi kana ya fice. Bin Bayan sa tayi da Kallo girgiza kai tayi Tace "Za'ayi auren nan,Kuma Insha Allah daga Kai har ita sai kunyi dana sani." Sai ta fice d'akin ta ta nufa ta Kira Ayrah ta Sanar da ita abinda ke faruwa, Sannan ta Sanar mata da zata je gidan su Isha anjima Kuma tana so ta mata rakiyi, Ayrah ta amince don daga jin muryar kawar tata tasan tana cikin damuwa. Mama na ganin sa Tace "kana Lafiya kuwa? Meyasa baka fito ba tun d'azu?" "Ina kwance ne mama" "Okay zauna ka Karya sabida ina so mu yi maganar kayan lefen Nan" Ji yayi gaban sa ya fad'i, zama yayi had'e da fara cin abinci. Bayan sun gama wayar ne ta fita, dinning itama ta nufa suka zauna suna cin abinci, Bayan sun gama ne ta fita da niyar zuwa gun Aiki, Amma ba gun aikin ta nufa ba, gidan su Ayrah taje, Basu d'au wani lokaci Mai tsawo ba suka nufi gidan su Isha, Suna Isa Kwankwasa karamin gate d'in gidan Sukayi bayan sun gaisa da Mai gadi Mardiya Tace "Dan Allah Baba gun Ma'isha muka Zo da fatan tana ciki?" "A'a bata Nan" Ayrah Tace "Dan Allah ka San inda taje ne?" "Eh to Dama gun zuwan ta Basu wuce wuri biyu ba zuwa uku" Tace "Ina da ina Kenan?" "Gidan Baffan ta ko asibiti, Amma na fi sa ran tana asibiti" A tare suka ce "Toh Mun gode" motar da suka Zo da ita suka Shiga kana sukayi hanyar asibiti, Bayan sun Isa asibitin da Isha ke aiki Kai tsaye pharmacy suka nufa, wata pharmacists suka gani Bayan sun gaisa ne suka tambaye ta Ma'isha ko tazo ta tabbatar musu da cewar yau bata Zo ba tana shift. Tsaki Ayrah tayi kana Tace "Ai na fad'a miki da Mun fara zuwa gidan Baffan nata tukunna" "Mtsww kina da matsala Wallahi Yanzun da kafa muka zone? Kar ki manta fa sa motata muka Zo Kuma man ciki ni Na saka bake Kika samin ba mtsww" tana kai na tayi gaba bin Bayan ta Mardiya tayi Tace "Banga laifin ki ba, Ni na jawo wa kaina da na rako ki, Sannan sannin Kanki ne mu ba matsiyata bane bare kice zaki min gorin Mota" Yar karamar dariya mardiya tayi a dai² Nan sun Isa jikin motar ta, Jingina jikinta tayi a jikin motar tana fuskantar Ayrah had'a hannayen ta tayi kana Tace "To Yar a Karuna Ni ba Gori nake Miki ba ke d'ince kin fiye mita dayawa, and karfa ki manta Ni dake Duk muna cikin matsala, Kud'in da ma na wani kuke ci" ta karasa maganar kasa² , Ayrah gyara tsayuwar ta tayi cikin Muryar tuhuma "Me kike ce?" Kirkirerren dariya tayi kana Tace "Nothing Shiga mu tafi please" Ayrah Tace "Anki a shigan salon ki sake min gori tafiya ta zanyi" ta juya da niyar tafiya, mardiya tayi saurin taro ta tana fad'in "Am sorry am Sorry Qawata ke Baki San wasa bane" tsaki kawai Ayrah tayi tana kokarin tafiya, rike hannun ta "kiyi hakuri Dan Allah , kizo muje gidan Baffan nata kin San karfe 4 zan Koma gun aiki" "Ke da aikin ya dama ba inace Ni gashi haryanzu na kasa samun aikin" "zaki samu Insha Allah, zo mu tafi" a zuciyar ta kuma Tace "Abinda ka shuka shi zaka girba (Niko nace ke d'in ma Allah ya barki da halin kine na wayon ki ko dabarar ki bace tasa Kika samu aiki ba). Motar suka Shiga suna Hira sama² har suka Isa gidan Abba, horn sukayi Mai gadi ganin Mardiya ya gane fuskar ta sabida jiya suka zo da Ma'aruf hakan yasa bai tsaya tambayar su gun wa suka Zo ba ya bud'e musu gate , a parking lot tayi parking motar ta kana suka fito. Cikin gidan suka nufa tun daga nesa suka hango Meerah da Isha, Ayrah Tace "Wai nikam Wannan wasu irin mayune kullum suna tare?" Mardiya Tace "Ni kaina ina mamakin irin qawancen Nan nasu, ban tab'a ganin qawaye irin suba" Wani irin Kallo Ayrah ta mata kana Tace "Kina nufin qawancen mu bai kai nasu ba?" Girgiza kai tayi had'e da dariya kana Tace "Ke dai ayi sha'ani Qawata namu ai ba irin nasu bane" suna maganar suna tafiya. Meerah na hango su ta tsaya chak, yayin da isha ke danne² a wayan ta jin Meerah ta tsaya ne yasa ta juya tana kallon ta had'e da fad'in "lafiya? ya naga kin tsaya mu tafi mana kin San Mummy na jiran mu." Meerah takaicine ya sa ta kasa magana, Isha ganin inda take Kallo hakan yasa ita ma tayi saurin kallon gun da take kallo, baki a bud'e take kallon su, a dai² Nan suka iso kallon kallon suka tsayi yiwa juna, Mardiya ce Tace "Kiyi hakuri Mun Zo gidan ku ba notice and we know that we're not welcome here, Amma Dan Allah inaso ku d'an ara mana Lokacin ku kad'an idan baza ku damu ba please" Cikin 'bacin Rai Meerah Tace "As you can see we are about to go out and you interrupted us so bamu da Lok....... " Isha ce ta katse ta da fad'in "Calm down Meerah let's listen to what they want to say" Meerah Tace "But Isha.... " "Please Meerah kiyi hakuri mu saurare su Kinji?" Shiru tayi had'e da kawar da kanta gefe. Isha Tace "Uhmn ina sauraron ki" Ayrah Tace "Da so samune mu zauna please" tab'e baki tayi had'e da d'aga kafad'a Tace "If you say so why not? mu shiga ciki" Riko hannun Meerah tayi don taga alama bata da niyar motsawa, ba don taso ba ta bi bayan ta, Isha juyowa tayi ganin suna tsaye Tace "ku Shigo Mana" sukayi gaba su Kuma suna biye da su. Mardiya da Ayrah kallon parlor suka tsaya yi ganin yanda aka Tsara gidan, gidan ya had'u iya haduwa sabida kud'i sunyi kuka anan gun, inda d'akinta yake suka nufa, Bayan sun Shiga d'akin ne Isha da Meerah suka zauna a bakin gado kana ta nuna musu sofa dake fuskantar su had'e da fad'in "Bismillah ku zauna" Zama sukayi, Bayan sun zauna ne Isha ta Mike had'e da fad'in "Ina zuwa please" Bata d'au lokaci ba ta Dawo hannunta d'auke da exotic sa glass cup guda biyu a gaban su ta ajiye kana ta koma ta zauna Tace "Bismillah ga abin Sha" A tare sukace "Thanks." Mardiya Tace "Isha nasan na cutar dake da kawar ki ko ince mun cutar daku Dan Allah find a place in your heart and forgive us what we did was very terrible but please Forgive us" Meerah Tace "hmm And what if we decide not to Forgive? Look idan baku da abin fad'a muna da abinyi" Ayrah Tace "Meerah ko kad'an Banga laifin ki ba, kina da right d'in da zaki Fad'i ko ma mene ne sabida an cutar dake, har ga Allah ko nice aka min haka da na dad'e da d'aukan mataki akai but please have a second thought on this" Mardiya Tace "Hakane zancen ki gaskiya ne Ayrah, and Isha please Kar laifina ya shafi Yayan Wallahi yana cikin wani hali bazai jure rashin ki ba" Murmushin gefen baki Isha tayi kana Tace "Da nayi niyar fasa auren nasa Amma zuwan ku yasa na Canza shawara zan auri Yayan ki Amma fa da sharad'i idan kikayi abinda nake so ina mai tabbatar miki da cewar bakina da Ma'aruf ranar Friday mai zuwa babu abinda zai sa a fasa shi sai dai in bana numfashi" Ajiyar zuciya Mardiya tayi kana Tace "Insha Allah Koma mene ne zanyi Wallahi" Meerah Tace "har da rantsuwa da dai ki bari kiji bukatar ta kamun nan ki rantse ko da yake ma baki San illan sa ba mtsww" Ayrah Tace "Isha Insha Allah zamuyi dukkanin abinda kukace muyi, ina da na sanin abinda na aikatawa d'an uwana na jini, na bi hud'ubar mahaifina sannan nayi amfani da maganganun sa na karya da gaskiya, a dalilina Ya Haisam ya kusa rasa ransa yana neman Almost 3 years kenan a kwance, bazan tab'a yafe wa kaina ba" ta karasa maganar cikin kuka. Isha Tace "Uhmn Haka Allah yaso kuma shima insha Allah zai farka ko ba yanzu ba" Ayrah Tace "Allah yasa" Duk suka amsa da ameen. Mardiya Tace "Isha ina sauraron ki mene ne sharad'in naki?" Isha kallon Meerah tayi, Meerah ma ta kalle ta Yar karamar dariya sukayi Wanda na kasa gane dalilin dariyar tasu, hankalin Ayrah da Mardiya yayi mugun tashi, kallon Kallo suka Shiga yiwa juna, Turo kofar da akayi ne yasa dukkannin su kallon kofar don ganin Wanda ya turo kofar. Kuyi hakuri da wannan please,ba yawa,haryanzu jikin ne ba dad'i, dakyar nake samun Daman typing d'in, nagode sosai da Addu'oin ku. _________________________ Masu tambayar complete d'in littafin Nan babu sabida 6th/01/2022 na fara typing, sabon littafine am just typing it. Ina Jin dad'in yanda kuke son book din Allah ya bar Kauna. Milhaat ce Yar Terawa [7/7, 10:02 PM] Miilhaat: 🍃 *DANGIN UBANA*🍃 Story & Written By Milhart Na zo muku da littafi Mai ban tausayi,cike da abun al'ajabi,wannan salon na daban ne. *🌍MANAZARTA* *WRITERS ASSOCIATION📚🖊* *M. W. A* *Wannan labarin kirkirarren labarine ban yarda a chanza min labari ba Wanda ya chanza bamu yafe ba.* Ina alfahari da rubutu,sabida alkalami yafi takobi🗡️🗡️🗡️ *BISMILLAHIR RAHAMANIN RAHIM* Page 53&54 _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._ ```Continuation......``` Da gudu suka shigo d'akin suna fad'in "Umma kin ganta ko, mun fad'a miki bata tafi ba" Aymana da Aima ke Wannan maganar. Umma dake biye dasu Yar karamar dariya tayi had'e da fad'in "Eh lallai Kun fini Gaskiya" kallon inda Isha ta ke tayi Tace "Daughter Kince min Zaku fita Ashe Kuna Nan?" "Eh wallahi Umma, munzo fita ne muka had'u da Mardiya da Ayrah" Umma jin ta ambaci sunan Ayrah hakan yasa tayi saurin kallon inda suke, tana ganin fuskar Ayrah ta gane fuskar ta sabida tana Kama sosai da mahaifiyar ta. Jiki na rawa suka durkusa har kasa a tare suka ce "Ina wuni?" A d'an yasine ta amsa da "Lafiya" riko hannun Aima da Aymana tayi suka fice daga d'akin, jiki a Sanyaye suka koma ma zaunin su, Meerah dad'i taji wani irin Murmushi tayi Mai d'an sauti. Isha Tace "As I was saying zan auri Yayan kine on one condition, and the condition is zamuje inda kuka binne Wannan layan ku kona shi da hannun ku" Ayrah zaro ido tayi tana kallon Isha Tace "Amm.... Amma ai... " Sai Kuma ta kasa karasa maganar da take son yi Isha Tace "Amma me" Cikin Murya Mai sanyin Tace "Babu komai" A zuciyar ta Kuma Tace "Ya Rabbi ya zanyi zasu ruguza min shiri gashi yanzu ina son Haisam sosai" muryar Meerah taji tana fad'in "Kunyi Shiru? Bazaiyu bane?" Mardiya Tace "Me zai Hana yanzu ma sai muje in Kun shirya" Mikewa Meerah tayi had'e da fad'in "Good Sai ku tashi muje bari na Shiga kitchen nasha ruwa" sai ta fice. Isha, Ayrah da Mardiya fita sukayi suka tsaya a katafaren compound na gidan suna jiran fitowar Meerah , fitowa tayi hannun ta d'auke da jakar ta tana wasa dashi ta karaso inda suke Tace "Muje ko?" Tafiya suke ganin Su mardiya da Ayrah sun nufi motar su cikin Muryar fad'a Tace "Excuse me ina Kuma zaku? Wai Kuna nufin motar ku zamu shiga Bazaiyu ba" Ayrah Tace "Uhmn to kin San inda aka binne abin ne? Idan kin sani to bismillah mu shiga motar taku" Kawar da kanta kawai tayi Isha Tace "Meerah you know they are right let's use their car" Meerah Tace "Oh stop it please Duk abinda sukace sai kice they are right? Ai mu ba baki bane a garin ko? Gombe fa garin mune anan aka Haife mu so zamu sani" Mardiya Tace "zaiyi wuya kusan gun gaskiya Amma babu komai mu yi amfani da motar taku sai na Rika nuna muka hanya" Isha Tace "A'a ai wannan wahalane goma da ashirin muje kawai" jaan hannun Meerah tayi tana bata hakuri dakyar ta shiga motar, Meerah da Isha a baya suka zauna Mardiya ke jaan motar sai Ayrah a kujerar Mai zaman banza, fice wa sukayi daga gidan suka kama hanya. Tafiya suke Babu Wanda ke magana da d'an uwan sa, Meerah ganin tafiyar taki karewa Tace "Irin Wannan tafiya haka kamar zamu bar gari are we safe?" Murmushi Mardiya tayi kana Tace "Of course you're safe, kusa da makabarta ne" Zaro Ido Isha da Meerah sukayi a tare suka ce "Makabarta dai?" Ayrah Tace "Eh Makabarta" shiru sukayi basu ce komai ba, ko wacce da abinda take tsakawa a ranta, a Haka har suka Isa gun. A bakin hanya sukayi parking motar su, kana suka Fara Shiga wani daji sun d'auki tsawon mintuna 20 suna tafiya mardiya ce Tace "Mun iso ganan gun" tana nuna gun da d'an yatsan ta. Meerah Tace "kin tabbata Nan ne?" "Eh Nan ne" Isha Tace "But ya akayi Kika gane gun shekara kusan bakwai Kenan fa ko?" Ayrah tace "da wannan bishiyar muka gane shiyasa muka binne a karkashin bishiyar" Isha girgiza kai tayi alamun ta fahimta had'e da fad'in "Oh." Ayrah Tace "To yanzu ya zamuyi mu tona Ni shaf na manta ma da Mun d'auko ko da wuka ne" Meerah Tace "Worry Not na d'auko" had'e da zaro wuka a Jakarta ta mikawa Ayrah, Ayrah hannu tasa ta karb'i wukan tana juyashi tab'a Kara kallon wukan tace "Mardiya gashi ki tone" Tana Mika mata wukan, banka Mata harara tayi Tace "Kila kin manta ko,kece Kika binne Kuma kece zaki tona shi bani ba" Girgiza kai tayo ta Mika Mata Jakarta da durkusa ta Fara tonawa, tono take yayin da su Kuma suna tsaye suna kallon ta, har sai da ta fara jin alamun abu a kasan ta ajiye wukan ta sa hannun ta tana kokarin cirewa, Isha da Meerah ganin abinda ta Ciro suka jaa da baya a razane, ajiye shi tayi Kana tace "Gashi Nan" had'e da kakkab'e Hannayen ta. Isha cike da tsoro Tace "Me nake gani haka kamar kad'agare, sannan kamar alluraai ne a jikin sa?" Ayrah Tace "Eh hakane" Meerah Tace "Duk tsawon shekarun Nan Amma bai Rub'e ba ya akayi haka" Mardiya Tace "Eh bazai rube ba sabida abubuwan da akayi amfani dashi, inda ya Rub'e to zai daina sonta ma'ana asirin ya karye Kenan Kuma ba abu bane Mai sauki" Meerah Tace "Lallai asiri Gaskiya ne" Mardiya Tace "To gashi nan Mun cire what's next" Isha Tace "Burn it" Ayrah ji tayi gabanta ya Fad'i, "Bazan tab'a bari ku 'bata min shiri ba" a zuciyar ta take maganar a bayyane Kuma Tace "Dame za'a Kona?" Mardiya Tace "I wonder" Ayrah Tace "Mu tafi dashi kawai in yaso idan na Koma gida zan kona" Meerah charab ta karb'i maganar Tace "Tabd'i kalle mu dakyau ce Miki akayi mu illiterate ne? To da ilimin mu, shiyasa ma na kawo wukan Nan, da Kuma ashana" tana maganar ta sa hannu ta ciro Ashana, ta wurga Mata. Yar karamar dariya Isha tayi Tace "Inayin ki Qawata" tafi Sukayi suna dariya meerah Tace "Ooops I almost forgot ganan kerosene sai yafi konewa" ta Mika mata dariya suka Kuma yi. Ayrah gaba ki d'aya taji hankalin ta ya tashi ba don ta so ba jiki na rawa ta zuba Kerosene akai kana ta kunna ashana ta wurga akai sai da ya kone kurmus kana suka bar gun, kan su Shiga mota wayar Isha ya Fara ringing. Ganin Dr Ali (likitan dake kula da Haisam Kenan) hakan yasa tayi saurin picking murya na rawa ta amsa daga d'ayan 'bangaren yace "Good News,Haisam ya farka Yanzun Nan ya bud'e idon sa." Ajiyar zuciya tayi had'e da fad'in Alhamdulillah, sauke wayar tayi daga kunnen ta suna tambayar ta Amma ta kasa basu amsa key d'in motar ta fizge daga hannun Mardiya ta fad'a cikin motar baki a bud'e Duk suka tsaya kallon ta, ganin ta tada motar Kuma tana niyar tafiyane sukayiw saurin Shiga motar su ma. Suna Shiga ta fizgi motar da wani mugun speed. "oyoyo oyoyo Yarana" da gudu suka nufi inda mummy take suka rungume ta , Zama sukayi, Mummy kallon sa tayo Tace "Haba Auta baza kamin magana ba?" Turo baki yayi kana yace "Ai ni bakya Sona Su Sister Aymana da Aima kawai kike so" "Kai ma ina sonka nama fi sonka Akan kowa, kazo muje na baka chacolate" Jin an ambaci sunan chacolate da gudu ya nufi inda take, hannun sa ta rike, d'akin ta suka shiga Aymana da Aima na biye da su chacolate da Biscuits ta Basu kana suka fito, Channel ta Canza musu Tasa Nicklodeon suna ganin favorite channel d'insu ki wannen su ya samu gu ya zauna suka cigaba da kallon su. Mummy ganin Umma tayi shiru hakan yasa tace "Umman Yara lafiya dai ko? Ya na ganki haka?" Cike da kulawa take tambayar ta. Gyara Zama Umma tayi kana Tace "Uhmn Mummy Yara ina cikin damuwa Wallahi" "Sanar dani mene ne kuma ya faru?" "Yarinyar Nan Ce tazo har gida wajen Daughter" " Wace yarinya Kenan?" Mummy ta tambaya cikin rashin fahimta. Umma Tace "Aurajy Yar gidan malam Hassan" Zaro Ido mummy tayi tace "Ayrah kuma tare da Isha? Amma kin tabbata ita d'in ce?" "Kwarai kuwa ga Nan kamannin uwarta na gane ta" "Allahumma ajirni fii musibati, to ita Ma'isha me ya had'a ta da tsinanniyar yarinyar Nan? " "Allahu a'alam na biyo tane don naji dalilin zuwan ta har gida ta same ta, a ina take nema banji motsin ta?" "Ha'aa ai na d'auka suna chan sabida ba ta dawo ba" "Ikon Allah ko ta wuce asibiti ne?" "Anya yau ai tana off" "Shikenan Duk inda taje zata dawo ta same ni inji dalilin ta na magana da shaid'aniyar yarinyar Nan, da har zata zauna inuwa d'aya da ita" tana maganar cikin tsananin 'bacin Rai. Umma Kam kasa magana tayi, don ta ma rasa abinda zatace. "Rabi Anya kina tsoron Allah kuwa? Anya kina so ki Gama da duniya Lafiya kuwa? Shin kina son Shiga aljanna kuwa? Karfa ki manta cewar aljannar ki a karkashin kafata yake, Wallahi sai in take ta muga yanda zakiyi" "Mtsww kaga malam Dan Allah Kar ka Dame ni kaji ko kazo ka tsaya akaina kana damina da surutu" Nuna kansa yayi cike da mamaki yace "Ni Rabi? Ni malam Hassan kike fad'awa haka? Kar ki manta fa ni mijin ki ne" "Kai ka sani don ni Wallahi na dad'e da daina kallon ka a matsayin mijina idan kana son kwanciyar hankalin ka a gidan Nan ka sauwake min na tafi gidan mu" "Na fad'a miki bazan sake ki ba, Wallahi ko mutuwa zakiyi bazan rabu dake ba in ko Kika bar gidan nan to ki sani ban yafe miki ba, Wai ma shin kin San hukuncin Matar da ta nemi Mijinta ya sake ta kuwa?" "Ayyirriiiiiii har Kai ka Isa ka nuna min sanin Allah me ka sani a game da adddin ka, da ka sani baza ka Rika aikata abubuwan da kake ba" "Oh kina nufin ni jahiline Kenan ko?" "To me banbancin?" "Oho Wannan Kuma kai ta shafa, Dan Allah idan ka gama ka fice min daga d'aki" "Naji zan fita Amma ina bukatar ki yau a turaka ta" "Allah ya sauwake na had'a jikina da naka, a Bayan ma ban San abinda kake aikatawa bane yasa na saki jikina da kai" Kasa kasa yayi da murya yace "Rabi kiji tsoron Allah tun lokacin da yaron Nan ya Shiga comma kika kaurace min, ya kike so nayi ne Dan Allah Kar ki manta Ina da hakki fa Akan ki" "Kaje chan inda aka saba baka karb'a idan Kuma kaji haushi Kaje ka kara Aure mtsww" ta cigaba da kallon da take, kallon ta ya tsaya yi kana yace "Zanyi maganin ki dani kike zancen" Yana kaina ya fita. Da d'an karfi Tace "Do your worse, d'an halak ka fasa, tasan yaji abinda tace Amma yayi kamar bai ji ta ba, fita yayi daga gidan gaba ki d'aya Bai Kai awa d'aya ba ya Dawo tare da wata yarinya wacce baza ta wuce sa'ar Ayrah ba, a lokacin Mamy ta fito parlor Suna Kallo da ita da Nabila, Faisal da Sunusi kannen Ayrah. Malam hassan har cikin parlor suka Shiga da yarinyar , Mamy ko kallon inda suke batayi ba bare ya dame ta, Nabila ce tabi su da Kallo har suka haura sama sai da suka Shiga d'aki Nabila tace "Mamy Wace ce wanchan suka shigo tare suka da daddy?" "Kije ki tambaye shi mana, ba uban ki bane" Faisal yace "A gaskiya Mamy Wannan cin fuskan yayi yawa, har cikin gida daddy ya fara kawo Yan matan sa Bayan maganganun da muke ji a unguwa yana zubar Mana da mutunci Mana" (Yaran Malam Hassan guda hud'u ne, Ayrah sai Nabila da take binta sai Faisal sannan karamin cikin su Sunusi). Kallon su kawai Mamy take batace musu komai ba, Nabila Tace "Mamy Yanzu Dan Allah haka zamu zubawa baba Ido yana abinda ya ga Dama a gidan nan?" "Nabila!!! Nabila!!! Nabila!!! Sau nawa na Kira sunan ki?" Kai a kasa Tace "Sau uku Mamy" "Good idan Kika sake min maganar uban ku Wallahi tallahi sai na miki baki, ba ke Kad'ai ba har daku" ta karasa maganar tana nuna Faisal da Sunusi. Mikewa tayi ta shige d'akin ta, kallon juna su sukayi sannan ko wanne su ya Shiga taitayin sa. Isha gudu take sosai, tana driving d'inne ta Sanar musu da cewar Haisam ya farka. _________________________ Please comment and Vote Milhaat Ce Yar Terawa [7/13, 8:42 PM] Miilhaat: 🍃 *DANGIN UBANA*🍃 Story & Written By Milhart Na zo muku da littafi Mai ban tausayi,cike da abun al'ajabi,wannan salon na daban ne. *🌍MANAZARTA* *WRITERS ASSOCIATION📚🖊* *M. W. A* *Wannan labarin kirkirarren labarine ban yarda a chanza min labari ba Wanda ya chanza bamu yafe ba.* Ina alfahari da rubutu,sabida alkalami yafi takobi🗡️🗡️🗡️ *BISMILLAHIR RAHAMANIN RAHIM* Page 55&56 _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._ ```Continuation........``` Su Ma'isha na Isa asibitin fita tayi ba tare da ta kashe motar ba, gudu take sosai har ta isa ICU Dr Ali ta gani yana kaiwa yana kawo wa murya na rawa Tace "Dr Ali ina yake? Yana ciki ne?" Kan ya Bata amsa da sauri ta kusa kanta cikin d'aki Meerah, Ayrah da Mardiya Suma suna kokarin Shiga ciki yayi saurin d'aga musu hannu had'e da fad'in "A a please ku jira ta anan" sai yabi Bayan Isha. Isha inda ake Canza Kaya ta nufa ta cire takalmin ta,ta sanya Wanda ake Shiga cikin ICU dashi, da sauri tayie inda Haisam yake, ganin Haisam tayi yana rarraba idanu yana son gane inda yake Isha tsuman tsaye tayi tana kallon sa, suna had'a Ido dashi ta masa Murmushi shima Murmushin ya mata sannan ya rufe idanun sa. A dai dai Nan Dr Ali ya Isa inda suke fuskar Haisam ya kalla cikin kid'ima ya nufi kansa duba nakurar da ke Kan Haisam ya Shiga yi ajiyar zuciya yayi ya fita, Isha ma tabi Bayan sa. Sai da suka fita waje tace "Dr ya naga Kuma ya rufe idon sa?" Ya amsa da "I don't know isha, ban San ya akayi hakan ya Faru ba, baifi mintuna 30 da farkawa ba fa, ina ganin ya farka na Kira ki" Dafe kanta tayi Tace "This is not what I asked you Dr meyasa ya rufe idanun sa?" Kallon ta yayi kana yace "I don't know and I just told you that, look Isha hakan na faruwa dama Kinga Kenan akwai alamun ya kusa ya Dawo" Cikin murya Mai d'an kara tace " What? Kana nufin ya sake Shiga comma ne?" Kai ya d'aga Mata alamun eh. Jiki a Sanyaye ta zauna a kasa hawaye d'aya na bin d'aya daga nesa suka hango su da sauri suka karasa gun, Meerah ce take kokarin d'aga ta Amma ta kasa hakan ne yasa Ayrah tayi saurin riko ta, Ma'isha da dukkanin karfinta ta ture ta har sai da ta Fadi a kasa cikin zafin nama Ma'isha ta Mike cikin tsawa tace "How dare you Ayrah? Who gave you the audacity to touch me?" Meerah baki a bud'e take kallon Isha don Bata tab'a ganin 'bacin ran Isha har haka ba, cikin sanyin Murya Meerah Tace "Isha calm down please,muna asibiti ne fa ki duba kiga kin sa ana ta kallon mu" "A kalla Mana I don't care,gara su kalle mu su san cewa akwai Mutane mugaye azzalumai kamar Ayrah a dalilin ta na rasa d'an uwana kuma masoyina ta rabani dashi,Kuma kice min I should calm down?" ta karasa maganar cikin kuka. Meerah Tace "Na sani Isha Amma kiyi hakuri Insha Allah, Allah zai bashi Lafiya,but ba Kince ya farka ba?" "Eh ya farka don har na kalli cikin idanun sa Amma ya sake rufe idanun sa,Ayrah bazan tab'a yafe miki ba Idan wani abu ya sami Ya Haisam" Ayrah da tun d'azu take durkushe a kasa ta Mike had'e da kakkab'e Kuran da ke jikin ta tace "To hell with You Isha,so what Idan baki yafe min ba? Did I asked for your Forgiveness? Haisam d'an uwana ne jinin da ke yawo a jikin sa shi yake yawo a jikina,na fiki son sa" Dariya Isha ta Shiga yi sosai harda rike ciki Amma fa hakan baisa ta daina zubar da kwalla ba sai da tayi mai isarta kana Tace "Su d'an uwa manya,so tell me Soyayyar da kike masa ne yasa Kika Masa hakan? A dalilin ki ya Shiga wannan halin shima Duk Soyayyar ce?" "Ai ba'a..........." Da sauri mardiya Tace "Please ya Isa Haka,Ni Banga amfanin chachan bakin da kuke ba Kar ku manta fa a asibiti Muke Kuma akwai marasa Lafiya moreover a bakin ICU Muke kunsan ba a son surutu Dan Allah ku yayyafa wa zuciyar ku ruwan sanyi please" Dr Ali yace "Finally" ya maida kallon sa ga Isha yace "Kamar yadda nace miki ya kusa farkawa inshallah zai farka......." Maida kallon sa yayi ga Meerah yace "Please ki maida ta gida" Riko hannun isha kawai tayi suka bar wajen ba tare da ta ce Masa komai,ba girgiza kai yayi had'e da fad'in "Allah shi kyauta." Ya bar wajen. Mardiya na ganin yayi d'an nesa da su ta finciko Ayrah magana kamar rad'a Tace "Wai meyasa ke Sam baki da hankali ne" Cikin 'bacin Rai Ayrah Tace "Nice ma ke Ni dake waye Mara hankali?" Murmushin takaici mardiya tayi kana Tace "Ke Kanki kin San baki da hankali, to in ba rashin hankali ba me zai sa ki tsaya kina biye mata harda maida Mata da magana?" "Mtsww Amma dai a gaban ki ta ture ni ko? Ni banji haushin ta rabani da d'an uwana ba ita sai taji haushi" "Iyeeee jimin zafin raai Shirmen banza inda kin d'auke shi a matsayin d'an uwan ki ai da baza ki Masa hakan ba" "Amma dai kin san ina son sa ko? The love she have for him is nothing compared to mine" Tafi ta Shiga tana fad'in "Wow wow bravo bravo, so now you love him? It seems like Baki San mene ne Soyayya ba, Soyayya fa sacrifice ne, Soyayyar da Isha keyi wa Haisam shine soyyayar gaskiya" "meyasa kike ce Haka?" Cikin sanyin Murya ta mata tambayar. Mardiya rungumar hannun ta tayi kana Tace "It's clear ai,Isha tana son Haisam sosai ita kanta ta San rabuwa dashi zai mata illa Amma fa hakan baisa ta danne zuciyar ta ba sabida tana son abinda yake so" Cikin rashin fahimta Ayrah Tace "What do you mean? Why are you siding with her?" "Am not siding with anyone,am just saying the truth,look malama bank da lokacin miki bayani sabida komai a bayyane take" tana kaina ta juya da niyar barin gun. Ayrah Tace "Mardiya please help me I really love him" Ba tare da juya ta kalle ta ba Tace "I can't help you this time sabida kinyi wasa da chance d'in ki,kizo mu tafi gida" ta cigaba da tafiyar ta, Ayrah kuwa ta Tsaya tana kallon Bayan ta,ganin fa dagaske tafiya zatayi ta bi Bayan ta jiki a Sanyaye. Gun motar suka nufa Mardiya Duk a tunanin ta zata tarar dasu a gun motar , Kallon Ayrah tayi Tace "Laah sun tafi fa" "Mtsww to sai me in sun tafi dama bana bukatar ganin ta a kusa Dani" " Kyaji dashi nikam ina bukatar hakan sabida bana so asirina ya tonu, mun shirya komai yanzu kin Zo kin 'bata komai" " Ban fahimce kiba me kuka shirya?" "Mtsww Allah ya shirye ki maganay auren Yaya Ma'aruf da Isha Mana kin manta shine dalilin sa ya sa muka fita?" "mtswwwwwww matsalar kuce wannan ba tawa ba , ni mamaki ma kike bani da har Kika damu da auren nan Bayan na san kin tsani yarinyar Nan tun kan ma ki San Yayan ki na neman ta" "Amma dai na fad'a miki sharad'in Yaya ko? Inda banyi hakan ba kashi na ya bushe so Dole Nayi abinda yake so for the meantime ba gidan mu ba? Allah ya Kawo ta sai ta Raina kanta" " Naji naji Dan Allah ki maida ni gida kaina ke ciwo" Mardiya Kallon agogon hannun tayi kana Tace "gaskiya zaki makarar dani fa" "Oh to ko na taka da kafa ne?" " a'a bance ba muje nayi dropping d'inki" tsaki Ayrah tayi ta shige motar, girgiza kai Mardiya tayi a zuciyar ta tace "Zanyi maganin kine" motar ta Shiga suka bar asibitin. Su Ma'isha kuwa tunda suka bar wajen napep suka Tara suka wuce gidan su Isha, a parlor suka tarar da Mummy da Umma gaishe su sukayi suka nufi hanyar Shiga d'akin Ma'isha Murya mummy sukaji tana fad'in "Ku Dawo Nan" Isha kallon meerah tayi itama ta kalle ta alamun Lafiya ta Mata da Ido Isha ta girgiza Kai alamun ban sani ba, jiki ba karfi suka Dawo had'e da neman Wurin Zama mummy tace "Isha ina miki kallon mai wayo da sanin ya kamata Ashe Baki da hankali ban sani ba?" Cike da rashin fahimta take kallon Mummy tun da ta fara maganar cikin rashin fahimta Tace "Kiyi hakuri Amma Dan Allah me Nayi?" "Kinci gidan ku Isha, nace Kinci gidan ku, uban me ya had'a kie da tsinanniyar yarinyar Nan Yar gidan matsiyata wacce bata gaji arziki ba?" Isha kallon Mummy tayi kana ta maida kallon ga Umma da fuskanta ya bayyana damuwa karara. Mummy ta ce "Ina Miki magana kin min shiru? Ko bakya jina ne?" "Mummy itace tazo har inda nake kawar Mardiya ce kanwar Ma'aruf shiyasa suka Zo tare Ni ban ma San ta santa ba sai da suka Zo d'azu" Meerah wani irin Kallo ta Mata hakan yasa mummy ta fahimci akwai abinda sume 'boyewa, "Meerah!!!" A 'dan razane ta kalli inda mummy take had'e da fad'in "Na'am" Mummy Tace "Akwai wani matsala ne?" "Umm mummy Dama..... Dama....." Isha tayi saurin katseta da fad'in "Dama Ya Haisam ne ya farka yanzu ma daga gunsa muke." Zumbur Mummy da Umma suka Mike a tare suka ce "Yana Ina?" Kai a kasa Isha Tace "Yana asibiti" Mummy Tace "Shine baki Sanar damu ba" Umma Kuma Tace "Alhamdulillah" Isha Tace "Mummy akwai wata Yar karamar matsala ce shiyasa ban Sanar daku ba" Umma Tace "wace irin matsala Kuma Bayan Wanda muke cikin ta?" "Ya farka har na ga kwayon idon sa Amma ya sake rufe idanun sa" Cikin rashin fahimta mummy tace "Ban fahimta ba me hakan ke nufi?" "hakan na nufin ya kusa farkawa" Umma zama tayi had'e da dafe kanta, mummy ma zaman tayi Isha kuwa mikewa tayi ta haura d'akin ta, Meerah ta bi Bayan ta. A bakin gado suka zauna Meerah Tace "meyasa baki Sanar musu Gaskiyar dalilin zuwan su ba?" Shiru tayi kamar baza ta amsa mata ba sai Kuma Tace "sabida dalilai guda biyu" "Me Kenan?" "Na farko Idan su Mummy sukaji dalilin zuwan su maganar fyade da aka miki da taimakon su zai zama ba sirri ba don tabbas Abba da Daddy zasuji harga Allah Ni ban so ma Ma'aruf yasan maganar ba sabida wannan sirrin ki ne" "Haka ne to mene ne dalilin ki na biyu?" "Dalilina na biyu shine idan daddy yaji abinda Kanwar Ma'aruf ta aikata na tabbata zai wargaza batun aure na da Ma'aruf Kuma bana son hakan gaskiya" Meerah rike habarta tayi kana Tace "I thought ba son auren kike ba?" "Eh bana so Amma su Daddy suna so ,so I have no option Dole nayi abinda suke so" "Toh Allah ya tabbatar Mana da alhairi, ranar ma ai tazo tunda saura Yan kwanaki ne, ya kamata mu Fara shirya events d'in da zamuyi" " Babu event d'in da zanyi Bayan walima, bani da ma lokacin wani abu bayan shi, Kuma kin San jibi zamu wuce Turkey da su mummy" " Hakane har na manta ma Allah ya nuna Mana, amarsu ta ango" ta karasa maganar cikin tsigar tsokana. Murmushi kawai Isha tayi suka cigaba da hirar su. Mardiya Bayan tayi dropping d'in Ayrah ta juyo ta koma domin zata gun aiki, Ayrah na Shiga cikin harabar gidan ta hango mahifin ta Yana rugume da wata yarinya matashiya wacce baza ta wuce sa'ar ta ba, Kan ta karaso inda suke har sun Shiga mota, ta gefen ta suka wuce waigawa tayi tana kallon motar , Mai gadi ya wangale gate d'in suka fita, Saida Mai gadi ya rufe gate d'in kana ta Shiga cikin gidan da d'an sauri sauri. Nabila Kad'ai ta tarar a parlor tana kallo Amma Sam hankalin ta baya Kai, magana take mata Bata ma jinta sai da ta tab'a ta a d'an razane Tace "Aunty kin dawo?" Ba tare da ta bata amsar tambayar da ta mata ba Tace "Wace ce wacce naganta tare da Abba?" Tab'e baki tayi had'e da fad'in "Karuwarsa Mana" Wani gigitaccan mari taji ya sauka a fuskar ta a razane ta Mike tana kallon wacce ta mare ta hannunta Akan kumatun ta sabida zafin Marin da taji. _________________________ Da fatan anyi sallah lafiya , Allah ya maimata mana , ameen. Milhaat ce Yar Terawa [7/18, 8:33 AM] Miilhaat: 🍃 *DANGIN UBANA*🍃 Story & Written By Milhart Na zo muku da littafi Mai ban tausayi,cike da abun al'ajabi,wannan salon na daban ne. *🌍MANAZARTA* *WRITERS ASSOCIATION📚🖊* *M. W. A* *Wannan labarin kirkirarren labarine ban yarda a chanza min labari ba Wanda ya chanza bamu yafe ba.* Ina alfahari da rubutu,sabida alkalami yafi takobi🗡️🗡️🗡️ *BISMILLAHIR RAHAMANIN RAHIM* Page 57&58 _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._ https://www.wattpad.com/1246873923?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp ```Continuation.......``` cikin Muryar kuka Tace "Mamy Mari?" Cikin hargitsi da d'agawa tace "Eh Mari idan na kuma Jin makamanciyar maganar nan daga bakin ki sai na sab'a ki wawiya Mara hankali, mahaifin ki kike had'awa da mugun kalma irin wannan" Ayrah cikin sanyin Murya Tace "Amma Mamy gaskiya ta fad'a Kuma kema kin San gaskiya ne, why won't you fight for your right?" Mamy tunda Ayrah ta fara magana ta kawar da kanta tayi kamar bata jinta, Ayrah ganin tayi shiru Kuma bata ga alamar zata kulata ba ta Kuma cewa "Mamy Dan Allah kiyi hakuri ha horo Haka Mamy, da wanne zanji Dan Allah da rashin kulani da kike zanji ko kuma da matsalar da take tsakanin ku da Daddy Wanda Nasan duk nice sila" Ajiyar zuciya Mamy tayi kana fuskanci Ayrah dake tsafe a bayan ta tace "Sam ba Wai bana son kulaki bane sabida abinda kuka aikata da mahaifin ki ba a'a so no na nuna miki kuskuren ki" Langwabe kai tayi Tace "Mamy Wallahi na gane kure na, 3 years ba wasa ba, Dan Allah mamy ki yafe min Kuma yanzu daga gun Haisam d'in nake ya farka" Murmushi Mamy tayi cikin Murya kamar dariya tace "Dan Allah dagaske?" Kai a kasa Ayrah tace "Eh Mamy amma fa bai dad'e ba ya kuma komawa" "Ban gane ya kuma komawa ba?" " Ya sake Shiga comma" Dafe kai mamy tayi Tace "Ai ga irin tanan Wallahi Ayrah kin cuci d'an uwanki kun biye wa son zuciya da uban ki, Dole Mutane suji tsoron *Dangin Uba* kuma Wallahi idan Haisam bai yafe muku ba baza ku tabay ganin rahamar ubangiji ba" tana kaina ta haura d'akin ta cikin tsananin 'bacin rai da takaicin abinda Mijinta da yar ta suka aikata. Ayrah fashe wa tayi da kuka mai sauti da karfi ta saki jikin ta a kasa ta cigaba da rera kukan ta,da gudu Nabila ta karasa inda take cike da kulawa ta fara rarrashin ta tana tambayar ta laifin da tayiwa Mamy cikin Muryar kuka ta Sanar mata da komai, baki a bud'e Nabila ke kallon ta Tama rasa abin Fad'i hakan yasa ta tsaya kallon Yar uwar tata. Muryar Faisal sukaji yana Fad'in "Tabbas biri yayi kama da Mutum Wai ace abinda Daddy yake aikatawa Kenan? Taya na za'a ce alhakin su zai barmu gaskiya daddy ya cuce mu" Sunusi yace "Ka duba kaga ni fa Yaya abin fa bai tsaya Akan sa shi Kad'ai ba harda big sis yayi involving a ciki and abin haushin ma she blindly did what he ask to do" Nabila Tace "Sunusi didn't you heard the story since from the beginning? Bata fa San komai akai ba, and ni ina blaming Mamy ma for not telling her the truth since from day one" Sunusi yace "Uhhh here you go again look sis Nabila Mamy bata da laifi had it been lokacin da Dad ya Fad'a mata abinda zatayi ta Sanar da Mamy ai da zata hanata Amma ta boye mata gaskiya" Faisal yace "Ya Isa please this is not the solution here, fad'in wa yake da laifi ko baiyi da laifi duk bai taso ba, sabida bazai amfane mu da komai let the bygones be gone please" ya karasa maganar yana hard'e Hannayen sa alamun roko. Shiru Sukayi na d'an wasu lokutan Babu Wanda yace komai sai kukan Ayrah dake tashi a d'akin Faisal ne ya matso kusa da ita ta durkusa, handkerchief ya ciro daga aljihun sa ya Mika mata had'e da fad'in "Please ki daina kuka hakan ya Isa Dan Allah karfa ki ja wa kanki wani matsala" Cikin shesshekar kuka tace "Faisal idan banyi kuka ba mezanyi kaina ya kulle duk duniyar bata yimin Dad'i" Yace "Ki fawwala wa Allah komai Insha Allah komai zai dai daita" Ciza le'be Sunusi yayi yace "Wato a cikin Haram aka Haife mu haryanzu kuma muna cikin ta Allah ya isan mu Wallahi......." kallon da Faisal yayi masane yasa ya shiru. Mardiya na Isa gida da murna ta Shiga d'akin Yayanta ta Sanar dashi cewar zancen auren sa da isha na nan yace "Idan na Kira ta naji akasin hakan fa?" Shiru tayi na d'an wasu sakonni kana tace "Ka d'auki Duk matakin da ya Dace" Yace "Okay" had'e kiran Layin Isha,duka biyu ta d'aga da sallama ajiyar zuciya yayi yace "Na d'auka na rasaki" "Uhmn baka rasani ba,Ina mardiya ta Isa gida kalau?" Kallon mardiya yayi kana yace "Eh kalau gata Nan ma muna tare" "Okay ka gaida min ita" Ya amsa da " tana amsawa" Nan ya fara Jan ta da Hira tun bata kulashi har ta saki jikin ta Sukayi ta Hira. Da Yamma Ma'aruf ne zaune da Mummyn sa da Daddyn sa suna ta shirye shirye Don a yau suke so sukai kayan lefe,Daddy tace "Yauwa Babana Nikam ya batun gidan naka ne an gama had'a komai ko?" "eh dad an gama had'a komai" Mummy Tace "Dan Allah yallab'ai ka bar min su anan tunda ka chan part d'aya ba kowa su zauna in yaso daga baya su zauna a Chan" "in dai ya amince da hakan ai bani da matsala" Kallon Ma'aruf yayi Yar karamar dariya yayi yace "mummy irin wannan Kallo haka?" "Eh so nake naji ta bakin kane ko bakaji maganar da muke bane?" "naji Mummy yanda kikace Haka za'a yi" Murmushi kawai tayi suka cigaba da abinda suke. Lefe ya had'u iya had'uwa in tsaya muku bayanin sa 'bata lokaci ne sabida haka just imagine it in your imagination,su Umma ne Kan gaba an karb'i baki yanda ya dace sai dai muce Allah ya nuna mana ranar biki. *WASHE GARI* Ma'isha tun da ta farka tayi sallah Bata Koma ta kwanta ba, had'a kayan ta tashigayi har sai da gari ya soma haske ta gama ban d'aki ta fad'a tayi wanka a gurguje sabida karfe 8 na safe jirgin su zai tashi, bayan ta gama shirine ta sauko kasa hannun ta rike yake da handbag d'inta d'ayan Kuma d'an madaidaicin akwatin ta take jaa, Driver da tun d'azu ya kai kayan Mummy mota yayi saurin zuwa ya karb'i akwatin natan yasa a jaka. Mummy da Daddy da hango suna saukowa daga stairs ya rungume ta a jikin sa suna tafiya suna Hira had'e da dariya gyaran murya Isha tayi kana ta sunkuyar da kanta a kasa. Murmushi daddy yayi had'e da fad'in "Har kin fito?" Ba tare da kalle sa ba ta amsa da "Eh Daddy Good morning" Ya amsa da "Morning" kallon Mummy yayi yace "Naso na kaiku Airport da kaina Amma Kuma zamuyi baki Kuma 8 ne yakamata mu had'u" " Bakomai Alhaji gaba da yawa fatan mu shine mu Isa Lafiya kawai" " To Hajiya Allah ya kaiku Lafiya ya Dawo daku Lafiya" Ta amsa da "Ameen" Ta d'aura da fad'in "Muje ko Isha? Driver na jiran mu dafan ba kiyi mantuwa ba?" "Eh mummy banyi mantuwa ba, Amma ina Umman take ban ganta ba ko zamu biya mu d'auke ta ne?" " A'a Umman Ku baza taje ba" 'dan Turo baki tayi Tace "To Amma mummy mai yasa haka bayan tafiyar Nan da ita aka shirya?" " Gashi Nan ki tambaye shi da Abban kune suka Hana" tana nuna Abba had'e da tab'e baki. Turo baki Isha tayi had'e da d'an buga kafa tace "Daddy why?" Ta karasa maganar kamar zatayi kuka. Yar karamar dariya yayi yace "wato Hajiya so kike ki had'a min wuri ko? Daughter idan Umman ku ta tafi wa zai kula da yaran? Abban ku baya nan Kinga bazai yu a bar su da masu aiki bako?" "But daddy 2 days fa kawai zamuyi" "Yeah I know kawai kuje da mummyn naku, kinji kiyi hakuri" Ba don tasa ba tayi shiru bubbuga kafa ta Shiga yi had'e da fita waje, motar ta fad'a, ta zauna had'e da rungume hannun ta sai faman Turo baki take, Mummy a gefen ta tazaun, Driver ya kunna wa motar wuta kai tsaye airport suka nufa, Basu dad'e da isa ba jirgin su ya Lula a sararin samaniya Nigeria to Turkey. Bayan sun Isa ne a ranar hutawa sukayi basu fita ba sai washe gari suka fita, tun da suka fita basu dawo ba sai yamma liss, washe gari ma hakan Sukayi a takaice dai kwanaki uku sukayi sabida basu samu damar gama sayayyar tasu ba, sai a rana ta hud'u suka koma gida. Yau saura 3 days biki shiri ake both families, sosai suke shiri ba kakkautawa, Isha dai sunan zatayi aure ne amma Sam bata farin ciki da auren babu abinda tayi na gyara jikin, Umma ce ta zage dantse wurin ganin ta gyara yar ta. A yaune dubannin Mutane suka shaida Auren Ma'aruf da Ma'isha, Bayan an d'aure aure walima akayi a gidan su Amarya, karfe 8 na dare aka kaita d'akin mahaifin ta nasiha ya mata sosai mai Shiga jiki da fatan Allah ya basu zaman Lafiya, mummy Kam kasa magana tayi tana kuka Isha na Kuka rungumar ta tayi tana fad'in "Daba don aure ba babu abinda zai rabani da ke 'yata Allah ya miki Albarka ya baku zaman Lafiya" karar motoci suka fara ji alamun an Zo d'aukan Amarya Nan take sautin kukan Isha ya Karu mummy na taya ta Umma ma Saida ta zubar da kwalla, dakyar ta 'ban'bari Isha a jikin Mummy aka sata a mota , Mummy,qawayen Mummy Guda biyu,da Meerah da kawayen Isha guda biyu na wurin Aikin sune suka Rakata har gidan ta. Umma nasiha ta Kuma mata tana mata fad'a akan tabi Mijinta sau da kafa, wani sabon babin kuka ta bud'e ganin Umma zasu tafi su bar ta, Dakyar ta bari suka fita aka barta da ga ita sai kawayen ta. Karfe goma da Yan Mintuna Ango ya shigo tare da abokanan sa bakin su d'auke da sallama suka amsa ba 'bata lokaci sukayi duk wani abinda al'ada ya tanadar kana suka fice, Ma'aruf raka su yayi har gun motar su, Cikin kawayen ta babu wacce ta fito da motar ta hakan yasa Dole sai sun Kai su gida. Sai da yaga fitar su kana ya shige part d'insu, Zama yayi kusa da ita a hankali ya d'aga mayafinta, wani ajiyar zuciya ya sauke had'e da fad'in "Alhamdulillah Allah na gode ma ka da ka mallakamin wannan kyakkyawar baiwa taka" Isha lokaci guda ta tsinci kanta da jin haushin sa, surutan sa yayi tayi bata tanka Masa ba, ganin bata da niyar kulashi sai yayi tunanin ko kunyar sa take ji, hakan yasa umurce ta da taje tayi alwala bata Musa ba ta Mike ta shige ban d'aki ta d'auro alwala bayan ta fita shima ya Shiga Bai dad'e ba ya fito sallaya ya shimfida musu Sannan ya jaa su sallah bayan sun idar da sallan ne ya dad'e yana roka musu zaman Lafiya a gun mahaliccin su sannan ya mata Duk wani tambayar da ya kamata Ango yayi wa Amaryar sa a, dukkannin tambayar da ya mata ta bashi amsar su dai dai yadda ya Dace hakan yasa yaji ta Kara Shiga ransa. Ledan kajin da suka shigo dashi ya janyo ya ajiye a gaban ta mikewa yayi ya nufi kitchen bai dad'e ba ya shigo hannun sa d'auke yake da plate sai Kuma glass cup, da kanshi ya fara bata abincin Duk da taso tayi masa rigima, sai da ta koshi kana ya tsiyaya mats yogurt ya bata tasha kana shima ya sakar wa cikin sa shima. Plate d'in ya mayar kitchen parlor ya nufa ya sa key kana ya dawo d'akin ganin ta yayi har ta kwanta, Canza kayan jikin sa yayi ya Sanya jallabiyar sa shima ya haura Kan gadon, hannunta ya rike kana yace "A haka zaki kwanta?" Tace "Eh" a takaice "Amma kayan Nan basu miki nauyi ba?" "Basu yi ba" " A a dai bari na rage miki su" hannu yasa zai tab'a ta da saurin Gaske ta Dirko daga Kan gadon tana kallon sa, cikin rashin fahimta yace "Isha Lafiya?" Cikin Muryar kamar fad'a Tace "Me kake shirin aikatawa ne?" Murmushi yayi kana yace "Babu komai kwanta abinki babu abinda zan Miki" Gani kawai yayi ta d'auki Pillow da bargo ta nufi hanyar fita da sauri yasha gaban ta had'e da fad'in "ina kuma Zaki?" "Zan bar maka d'akin ne, don ni gaskiya bazan iya had'a jiki da Kai ba" Cikin sanyin Murya yace " Amma meyasa Isha Kar ki manta fa ni mijin ki ne ina da iko Akanki" Fashewa tayi da Kuka Tace "Dan Allah kayi hakuri ban shirya ba" "Kar ki damu ni bazan miki Dole ba, Kuma Dama ba dalilin da yasa na auri ki ba Kennan soyyayar da nake miki yasa na aure ki zan iya jiran ki har zuwa ranar da Kika shirya" sa hannu yayi karb'i pillow da bargon dake hannun ta yace "Je ki kwanta ni zan kwana a parlor" Yana Kai Nan ya fice abinsa. Isha jikinta ne yayi sanyi tabbasa tasan bata kyauta masa ba, tunda Yana da hakki akanta Amma fa alkawari ta d'auka wa kanta babu wani mahalukin da zata bashi kanta in ba Yayan ta ba, da wannan tunanin ta kulle kofar ta koma ta kwanta abinta. Ma'aruf kwance yake Akan kushin ransa Duk ba Dad'i a bayyane yace "Yau fa ranar da na dad'e ina jira Kenan Amma a parlor zan kwana, hmm bazan miki Dole ba Isha sabida nasan halin da kike ciki" tunani kala da iri yayi tayi har dare ya raba ya kasa bacci, ji yayi bazai iya hakura ba, mikewa yayi ya nufi d'akin da Isha take Wanda shine d'akin su Tura kofar yayi yaji ta a rufe Murmushin takaici yayi kana ya juya ya koma ya kwanta a haka bacci 'barawo yayi awun gaba dashi. _________________________ Masu tambayar complete book d'in Nan Babu pls sabon book ne Milhaat ce Yar Terawa https://www.wattpad.com/1248497695?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_pageb=create_on_publish&wp_uname=Milhaat&wp_originator=yyYOiPWOf9d70htdRqg7I1%2F4ucy6HsOlgByapt3Dnb2JGUd5QVGMPXeC%2Bp0YdiBDdt6TP4swRtJhg2tXkbgWfc9O3T2b4yf1jRUCMIvqFOmhE71dThk0eS8%2FT5G%2F00JG 🍃 *DANGIN UBANA*🍃 Story & Written By Milhart Na zo muku da littafi Mai ban tausayi,cike da abun al'ajabi,wannan salon na daban ne. *🌍MANAZARTA* *WRITERS ASSOCIATION📚🖊* *M. W. A* *Wannan labarin kirkirarren labarine ban yarda a chanza min labari ba Wanda ya chanza bamu yafe ba.* Ina alfahari da rubutu,sabida alkalami yafi takobi🗡️🗡️🗡️ *BISMILLAHIR RAHAMANIN RAHIM* Page 59&60 _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._ *WASHE GARI* Alarm d'insa ne ya fara bugawa mikewa yayi ya kashe, d'akin su ya nufa ya Shiga babbuga mata kofa, zumbur ta mike a d'an tsorace, bedside lamp ta kunna kallon d'akin ta shigayi tana mamakin a wani d'aki take, sunan ta da taji ya Kira ne kamar rad'a yasa ta kalli kofan shiru Bata komai ba, a karo na biyu ya Kuma cewa "Isha!!! Cikin Muryar bacci Tace "Na'am" "d'an bud'e kofar asuba tayi" Mikewa tayi jiki ba karfi ta bud'e Masa kofar,Kan gado ta koma ta zauna shi Kuma ya Shiga ban d'aki,alwala yayi Bayan ya gama ne ya fito ya wuce Masallaci ba tare da yace Mata uffan ba. Itama mikewa tayi ta Shiga ban d'aki tayi alwala ta shimfid'a sallah ya Shiga yin sallah,Bayan ta idar ta zauna Akan sallayar tana azkar. Ma'aruf Kuma bai dawo cikin gidan ba har sai da gari ya fara haske,ya Shigo har cikin d'akin bakin sa d'auke yake da sallama,tana zaune akan sallaya, d'ago kanta tayi ta kalle shi suna had'a ido ta kawar da kanta a hankali, amsa sallamar sa tayi had'e da fad'in "Ina kwana" Ya amsa da "Lafiya how was your night?" Tace "Alhamdulillah" had'e mikewa,sallayan ta nad'e kana ta Shiga ban d'aki, Jin saukar ruwa a shower ne yasa ya fice daga d'akin,Bayan ta gama ne ta leko taga baya d'akin fita tayi cikin sauri ta nufi kofar ta sa key. Gaban Mirror ta nufa ta zauna,kallon kanta tayi a mirror ko me ta tuna Naga ta girgiza kai had'e da Yar karamar dariya mai d'an sauti,Mai ta Shiga shafawa a jikin ta Bayan ta gama ne ta ciro kayan da zata sa, Riga da skirt d'in atamfa ta sanya a jikin ta, ba tayi wani kwalliya ba powder ta shafa sai kwallin da ta saka a idon ta sai lip glow. Fita tayi daga d'akin, parlor ta nufa kallon d'akin ta tsaya yi tana ganin kokarin iyayen nata had'e da sa musu Albarka, komai na d'akin Royal Blue ne da Sky blue ya haska d'akin sosai ga wani uban kamshi da d'akin keyi. Motsin da taji ne yasa tayi saurin maida kallon gun, a hankali take ta fiya har ta Isa kofar da take jin karar,a hankali ta Turo kofar had'e da kusa kanta ciki, kallon kitchen d'in ta tsaya yi tana Murmushi,ta shagala da kallon kitchen d'in har ta manta dalilin da yasa ta Shigo. Ido hud'u sukayi,kallon kallon suka Shiga yi wa juna,wani irin kallon yake binta dashi ganin yanda tayi matukar kyau Duk da ba wani cika take dashi sosai ba kayan yabi jikin ta,kamar a jikinta aka d'inka shi. Ganin kallon da yake mata yayi yawane yasa tayi sauri juyawa da niyar fita cikin Murya mai sanyi yace "Isha!!! A hankali ta juya tana kallon sa murmushi yayi kana yace "Kinyi kyau" Murmushi itama tayi had'e da fad'in "Thanks" ta juya zata fita yace "Hold on mana" ajiye spoon d'in dake hannun sa yayi ya nufe inda take hannun ta ya riko ya jaa ta izuwa gun gas cooker da yake girki da ita. Marfin tukunyar ya bud'e yace "Look Waifa gwanin ta zan miki Kuma sai naga baiyi yanda nake gani idan Mama tayi ba" Isha kusa dariya ta Shiga yi Tace " Me ne wannan d'in?" "Bakya gani Irish potatoes ne" "Eh na gani ina nufin me kake son girkawa?" "Chips Mana ai tunda kwanaki ka ka fad'a min kina son chips sosai sai na kudiri aniyar yi miki shi da kaina" Dariya take yi sosai shi Kuma ya rungume hannun sa yana kallon ta cikin Muryar dariya Tace "chips fa kace" ya ama da "Eh Mana" Dariya ta kumayi Tace "ba dai chips ba sai dai pourage" yace "Pourage Kuma gwate kenan fa?" "eh Mana ina ka tab'a ganin chips haka,ai da ka dage ka koya Kan irin ranar Nan tazo" " Uhmn Gaskiyar ki,ai ni yanzu ma gani nake kamar mafarki nake" Jin abinda yace ne yasa ta daina dariya kamar anyi ruwa an d'auke Tace "Ban gane kamar mafarki ba?" "Umm na d'auka bazan tab'a samun ki ba Isha" Murmushi tayi Tace "Kasan mene ne?" Yace "A a sai kin fad'a" Sauke tukunyan tayi kana Tace "bari na nuna naka yanda akeyin chips sabida gaba" Kai ya d'aga had'e da fad'in "to" Nan ta Shiga fere Irish d'in shima wani wukan ta d'auko Yana Taya ta ,sai ta fere biyar bai fere d'aya ba tayi ta dariyar su sunayi suna Hira sama sama,Bayan sun gama ta soye shi had'e da soya kwai ta d'aura a gefe, a tare suka kai abincin dinning,zama yayi tayi serving d'insu suka fara ci. Bayan sun gama cin abincin a tare suka kai kitchen, a parlor ta zauna da niyar Kallo taji yace "d'auko mayafin ki mu shiga mu gaida su Mom" Mikewa tayi had'e da fad'in to, d'aki ta shiga ta d'auko hijab dinta har kasa, tana fitowa suka wuce part d'in su Mom, da sallama suka shiga mom ce na gani a tsaye ita da Mardiya. Baki a bud'e take kallon su Tace "Har kun tashi? Yanzu fa na ke cewa yarinyar Nan ta kai muku breakfast" Neman wuri yayi ya zauna had'e da fad'in "ai mun karya" "Shine kasa 'yata girki daga zuwan ta?" "A a ni nayi girkin fa" Mom kallon Ma'isha tayi Tace "Wai hakane?" Murmushi tayi kana Tace "Na daiyi Mom" "Yauwa nasan za'a Rina" Kama baki yayi yace "Lallai bakya tsoron Allah ina laifin ma kice mata tare mukayi?" Dariya kawai tayi Bata ce masa komai ba, mom Tace "Sai ka nemi wuri ka zauna ka bar ta a tsaye" Gyara Zama yayi kana yace "Yan zun Nan fa Kika ce Yar kice meaning ba sai ance Mata ta zauna ba tunda a gidan su take ko?" Tab'e baki Mom tayi, zuwa tayi ta riko hannun Isha ta zaunar da ita, Ma'aruf kallon Mardiya yayi cikin Murya kamar fad'a yace "Ke baki iya gaisuwa bane? Ko baki ga Mutane bane?" "Uhmn Yaya Kenan ai gani nake kamar Duk Kun manta dani shiysa, ina kwana?" Ya amsa da "lafiya" Maida kallon ta ga Isha tayi taace "Ina kwana Aunty Isha" Murmushi tayi had'e da fad'in " lafiya Lau kin tashi lafiya?" " Lafiya ya Amarci?" Murmushi kawai tayi bata ce Mata komai ba, kallon da Ma'aruf ya mata ne yasa ta ajiye food flask d'in dake hannun ta , had'e da kokarin barin gun. Mom ce Tace Mata "Ya haka Kuma anan Zaki bar min abincin? 'dauka ki Kai musu part d'in su" Cikin sauri ta d'auka ra fita. Ma'isha har kasa ta durkusa Tace "Mom ina kwana?" Cike da fara'a ta amsa da "Lafiya Lau ya kwanan bakonta?" Murmushi tayi had'e da fad'in "Alhamdulillah" Ma'aruf ma gaishe ta yayi Bayan sun gama gaisawa yace " Dad ya fita ne?" Ta amsa "Yana d'akin sa , ku shiga ku gaishe shi" mikewa yayi had'e da kallon Ma'isha yace "Zo muje" mikewa tayi Sim sim tana binsa a baya, d'akin Dad suka nufa Bayan sun gaishe shi ya musu nasiha da fatan Allah ya basu zaman Lafiya Mai d'aurewa, Nan suka tashi suka koma part d'insu kasantuwar Mom bata parlor d'in. "Mamy yanzu haka zamu zuba Ido muna kallon Daddy yana abinda ya ga dama a gidan Nan ki duba kiga yau ma ya shigo da mace" Faisal ke wannan maganar. Sunusi yace "Mata dai ai su biyune yau Kam" Faisal yace "Innalillahi wa Inna ilaihirraji'un, that's it Wallahi yau d'in Nan zan yi maganin Yan iska" ya mike Yana huci yayi d'akin sa. Mamy kallon sa kawai tayi ta kawar da kanta, Sunusi yace "Mamy Wai baza kice wani abu bane ba?" "To me zance muku tunda ku kuka Haife Ni bani ce na haife kuba na fad'a muku ba sau d'aya ba ba sau biyu ba Akan Ku bar zancen Nan Amma kunki, ina guje muku fushin uban kune, Duk lalacin sa fa shine mahiaifin ku ya Kamata ku San da wannan" "Amma Mamy........ " Wani irin ihu sukaji ya d'auki cikin gidan Duk su biyun a razane suka mike, Ayrah da Nabila ko wacce da gudu ta fito daga d'akin su suna son ganin mene ne ke faruwa. Sunusi yace "Mamy kamar ihu na ji ko?" "Eh Nima naji" Wani ihun suka Kuma ji wannan karon Muryar mace ne take kuka had'e da ihu, Ayrah Tace "Kamar daga d'akin Daddy ne" Nabila Tace "Eh daga d'akin sane" Mamy ce ta haura da saurin Gaske Suma suka bi Bayan ta,Kai tsaye d'akin ta fad'a ba tsuman tsaye tayi tana kallon sa. Faisal Ne hannun sa rike da Adda jikin sa duk jini sannan malam hassan da Yan matan Nan Guda biyu suna cikin jini,dukkanin su tsirara,wani Kara Ayrah ta sake, Nabila Kuma ta fashe da kuka. Mamy Zama tayi da d'an karfi a kasa tana kallon su cikin jini, d'ago kanta tayi ta Kalli Faisal dake huci cikin Murya Mai sanyi Tace "What have you done Faisal? What have you done" Cikin d'aga murya yace "Abinda ya Dace dasu Mamy ya Isa Haka na gaji da ganin ki Cikin kunci da tashin hankali" "Faisal ka kisa? Faisal ka kashe su, ka kashe har Mutum uku" Jin maganar da Mamy keyi ya sanyi shi ya yatsar da addan dake hannun sa jiki na rawa yace "A a Mamy ni Wallahi banyi niyar kashe su ba, kawai inaso ne na rau nata su" Sunusi ne yayi kansu murya na rawa yace "Suna motsi Basu mutu ba mu Kai su asibiti" Nan suka Shiga Sanya musu kaya, Basu tsaya 'bata lokaci ba sai medical center suka kaisu ,a A&E (accident & emergency) aka ajiye su, likitoci na ganin su suka ce baza su tab'a su har sai hukuma sun sa hannu, babu yanda basuyi dasu ba Akan su basu taimakon gaggawa in yaso zasu je suyi report Amma suka ki sabida Haka law yake, Faisal da Sunusi ne suka nufi motar da suka Zo dashi suka wuce Police station. Bayan sun Isa police station d'in sukayi narrating abinda ya faru Nan take aka Kama Faisal, hankalin Sunusi yayi mugun tashi ganin ansa d'an uwan say cell. Police d'aya aka sa suka Dawo asibitin tare da Sunusi, sai da police d'in yasa hannu kana aka Shiga basu taimakon gaggawa, Mamy Jin an Kama d'an ta tayi ta kuka, ita kuka su Ayrah kuka Sunusi ne ke ta aikin rarrashin su. "To ya zanyi Meerah, na amince na aure Amma Wallahi gangar jikina da zuciyar ta bata aminta dashi ba har yanzu" "Yau 5 days da bakin ku Amma na Jinjina wa Ma'aruf ya kwanta dake a gado d'aya ba tare da ya tab'a ki ba?" " Mtsww ni Nace miki muna kwana tare? A parlor yake kwana" " Isha kin bani kunya wallahi Sam bata tunaniin zakiyi hakan ba, tunda kin San baza ki aminta dashi ba ai da baki aure shi ba" " Na d'auka Zan iya ne shiyasa na amince da hakan, bazan iya ce miki bana son Ma'aruf ba kuma bazan iya ce miki ina kin sa ba , I don't know what the problem is" "Dallah malama Kar ki 'bata min Rai mu bar maganar please don wallahi ji nake kamar na daka ki wallahi" "Ban fahimce ki ba Isha kina nufin baki bashi hakkiin sa ba, kinsan Allah na fushi da ke ko?" Ganin tayi shiru yasa tace "Nasan kin San abinda Kika aikata ba dai dai bane Kuma wallahi sai Allah ya tambaye ki, tunda kin San bakya son sa ai da baki bari an d'aura auren ba" " Ni nace miki bana son sa?" Cikin Muryar tuhuma " Baki ce ba Amma actions speaks louder than words" "To ina son sa shiyasa ma na aure sa kin gane ko? So mu bar maganar ya wurin aikin?" "kalau" a gajarce ta bata amsa. "Yau fa almost a week banje Naga ya Haisam ba, Wallahi Duk na Shiga damuwa" "Laa kin tuna min ma, kin San me ya Faru?" "A'a tell me" " Kina nufin baki ji labarin da yake ta yawo a gari ba?" "Umm umm banji ba, tunfa da aka kawo ni gidan Nan ko waje ban leka ba, in takaita miki ma part d'in mom kawai nake zuwa shima baifi sau uku naje ba" "To Kar kad'a kunnen ki ki Sha labari" ta karasa maganar tana Murmushi. Gyara zama tayi tana kallon ta a kage tace "Tell me, me ya Faru" "Malam hassan na kwance a asibiti Rai a hannun Allah" ta karasa maganar cikin Murya kamar zatayi dariya, zaro ido Isha tayi Tace "Wani malam Hassan d'in?" "Malam Hassan dai Wanda Kika sani" "Tooooh me ya same shi" "Wai Yan Mata ya Kawo har cikin gidan sa" " Ban gane Yan mata ba?" "To bara na fito miki a Mutum karuwai ya Kawo har cikin gidan sa, shi Kuma d'an sa ya fusata ya sassare su da Adda, yanzun Nan da nake gaya miki Yan matan sun mutu shi Kuma yaji mummunan rauni" ta karasa maganar tana dariya, Isha Tace "Meerah baki da hankali Wallahi, yanzu me abin dariya anan?" "Komai ma, this called for a celebration Wallahi" "Bai Kamata ace Musulmi ya Shiga tashin hankali ba Kuma kice ki tsaya kina murna" "Wai ko baki gane maganar wa nake bane Kam?" " Na gane mana ba mahaifin Ayrah ba, Baffan Haisam,har naji tausayin su wallahi?" "uhmnn lallai shine har kike cewa kina tausayin su?" " Uhmn gara ke" mikewa tayi ta d'aura da fad'in "Ni Zan wuce gida" Itama Isha mikewa tayi ta amsa da "muje na taka miki" Ma'aruf da tun d'azu ya shigo Yana tsaye a bakin kofa yana Jin maganar da suke musamman ma maganar sa yasa shi ya kasa Shiga d'akin yana jin suna kokarin fita yayi saurin komawa parlor ya zauna, Yana danna wayar sa. ________________________ Please comment and share Mihaat Ce Yar Terawa 61&62 '''Continuation.......'''  cike da mamaki suke kallon sa, murya chan ciko Isha Tace "Yaushe ka Dawo?" 'dago kansa yayi ya Kuma maida kansa Kan wayar sa kana yace "Yanzun Nan shigowa na" Meerah cikin tsigar tsokana Tace "Ango Ango kasha kamshi" Yar karamar dariya yayi yace "Meerah manyan gari ashe kina Nan gaba ki d'aya kin kimu"     "Aaaaahhh wane ni kawai dai na baku lokacine kuci amarcin ku da kyau, Amma har sai kun gaji dani"     " Baza mu gaji ba gaskiya, so ya aikin dai?" "Alhamdulillah, Amma ba Dad'i Wallahi aminiyata bata Nan so wurin ya Zama min so boring,ya Kamata ka bar min ita haka ta Dawo bakin aiki"      Murmushi yayi yace "Zata Dawo ai da zaharan hutun ta ya kare" "To Shikenan, Allah ya nuna Mana" Ya amsa da amiin, Tace "Sai anjima" Ya amsa da "A gaida gida" " Gida zaiji" Tayi gaba Isha Tace "Bari na rakata" Yace "Alright"      Har wurin mota ta rakata, sai da taga fitar ta kana ta Shigo cikin gida, ta iske shi Yana zaune a inda ya bar shi, Zama tayi yace "Ba Zama zakiyi ba ki d'auki mayafin ki, zamu fita" magana yake ba tare da ya kalli inda take ba          Tace "Ina zamu?" 'dago kai yayi kalle ta kana yace "Sayar da ke zanyi" sai ya ki cigaba da danna wayan sa. Tab'e baki tayi ta mike ta shige ciki, bata d'auki lokaci mao tsawo ba ta dawo jikinta sanye yake da hijab, d'ago kansa yayi ya  kalle ta, Murmushi yayi kana yace "Kinyi kyau " Murmushi tayi Tace "Thanks" Mikewa yayi yace "Mu tafi ko?" Yayi gaba bai tsaya jin abinda zata ce ba, kallon sa tayi ta girgiza kai kana ta bi Bayan sa.       Motar sa ya Shiga baka sidik Mercedes Benz sai sheko take, ganin ta nufo shi ne yayi saurin fita ya zaga ya bud'e mata kofar motar ta Shiga, ya maida ya rufe zagayawa ya kuma yi kana ya Shiga, Yana Shiga bai Tsaya 'bata lokaci ba ya sa wa motar key, tun Kan ya Isa yayi wa Mai gadi horn, da sauri ya wangale kofan Yana musu a Dawo Lafiya, suka fice daga gidan.      Kallon ta yayi kana ya maida Kan sa Akan tukin da yake, yace "Isha" cikin wani irin low voice , kallon sa tayi had'e da fad'in "Na'am"     "Kina so na kuwa?" "Uhmn Haba Ya ma'aruf wanann wace irin tambaya ce?" "Don't feel bad kawai akwai abinda nake so na fahimta ne"      "Uhmnn ina sonka Mana , idan bana son ka me zai sa na aure ka?" Wani dogon ajiyar zuciya yayi bai ce mata komai ba ya cigaba da tukin sa itama ganin bai da niyar magana tayi shiru abin ta.     Ganin sun doshi hanyar FTH ne hakan yasa Tace "Kar dai yaji maganar da muke d'azu da meerah?" A zuciyar ta take ayyana hakan.          A bayyane kuma Tace "Me Kuma zamuyi a anan?" "Gani nayi kin kwana biyu baki ga Yayan ki ba" Kallon sa kawai tayi tana mamakin Hali irin na Ma'aruf "shi ko irin kishin Nan baya yi Kuma yasan irin soyyayar da nake yi wa Haisam?"      Muryar sa taji yana Fad'in "Nasan zakiyi tunaniin ko bana sonki ko Kuma bana kishin ki, Isha Ina son ki Kuma ina kaunar ka babban burina shine na ganki cikin farin ciki da kwanciyar hankali, n aure kine a ganina zan iya Zama wani 'bangaren rayuwar ki Amma Naga alaman hakan bazaiyu ba"      A dai dai Nan suka Shiga cikin asibitin sai da yayi parking kana ya kwantar da kansa a Kan kujera yace       "Isha" d'ago Kai tayi ta kalle sa kana yace "ko yau d'in nan Haisam ya farka in dai zai karb'i soyyayar ki sannan ya soki kamar yadda kike son sa a shirye nake da na sake ki"                zaro Ido tayi tana kallon sa, hannun yasa ya share mata hawayen da ya ke gangarowa daga fuskan ta Wanda ita kanta bata San sun zubo ba kirkirerren murya yayi "Isha I can sacrifice anything for you in this world har da ni kaina"        bud'e marfin motar yayi ya fita ya Fara tafiya, ganin ta kasa fita daga motar ne ya dawo da baya ya bud'e mata marfin motar, kallon sa ta tsayayi ya zaro idanun sa had'e da mata gwalo yace "Rankashidad'e am a I safe?" Bata amsa mishi ba sai shesshekar kukan da take, ganin bata da niyar fita hakan yasa ya riko hannun ta suka bar wajen.    ICU suka nufa, Zama yayi a waje yana jiran ta, itako Isha tafiya take kamar kwai ya fashe Mata a ciki.             Bata dad'e a ciki kamar yadda ta Saba ba, ta fito ta hango shi Yana zaune Yana latsar wayar sa, Kallon sa ta tsayayi a zuciyar ta ce "Ya Allah me nake aikatawa ne haka, Innalillahi wa Inna ilaihirraji'un, Ma'aruf mutumin kirkii ne mai yasa ni bana son sa, gashi kyakkyawa son kowa kin Wanda ya rasa ,Astagfirullah ya Allah ka yafe min"     Ma'aruf na d'ago kansa ya hango ta tana kallon sa murmushi yayi ganin irin kallon da take Masa hakan ya nuna hankalin ta baya jikin ta, mikewa yayi cikin tafiyar a nitse ya karaso inda take, ganin bata ma San ya karaso inda take ba yayi tafi, a razane ta kalle shi yace "Kina Lafiya kuwa?"     Fashewa tayi da kuka, ta Fad'a jikin sa, rungumar ta yayi sai ta tsinci kanta da shigewa jikin sa, sai faman kuka take tana chusa jikin ta a nasa, Ma'aruf kuwa rikice wa yayi shi a ganin sa wani abunne ya sami Haisam d'in a gigice yake tambayar ta "Isha tell me what happened?" The more yana tambayar ta the more shi cries.       " Isha please tell me what happened, me ya faru ne kike kuka haka?" 'dago kanta tayi ta Kalli fuskan sa kana ta Kara rugumar sa tana kuka, "Ya Salam" Ma'aruf yace.     Ganin attention d'in Mutane ya faro dawo wa kansu ya janye ta daga jikin sa, hannun ta ya rike suka nufi motar sa, sata yayi a mota kana ya zaga ya Shiga haryanzu bata daina kukan ba. Iska ya hura murya kamar Fad'a yace "Oh My God , could please stop crying, Isha bana jin dad'in ganin ki a haka ki Fad'a min abinda ke damin ki Mana" ta tsorata da yanayin da ta gansa hakan yasa tayi shiru tana kukan kasa kasa, ganin Bata da niyar magana ya sa wa motar key.     Kai tsaye gida suka nufa, a parking lot yayi parking, cire key d'in yayi ya shige cikin gida rai a 'bace da sauri tabi bayan sa , ganin yana kokarin haurawa bedroom da sauri ta nufi inda yake ta rungume shi ta baya, tana kuka mai tsuma zuciya, tsayawa yayi chak ya kasa motsi, Yana Jin kukan ta har cikin ransa shima hawayen ya fara zubarwa yana cizan leb'en sa.    Cikin Muryar kuka Tace "Am sorry, am sorry Dan Allah ka yafe min" rike hannunta yayi had'e da juyawa yana fuskantar ta  yace "Isha Ni fa babu abinda Kika min ki daina kukan Nan haka please" Yana mai share mata hawaye Tace "Bazan daina kuka ba har sai ka yafe min"          "Sai na yafe Miki?" Cike da rashin fahimta ya mata tambayar. 'dago kanta yayi yace "Look at me Isha babi abinda Kika min ko da ma kin min to Wallahi na yafe miki duniya da lahira" fashewa Tayi da kuka tana fad'in "Ina son ka mijina Dan Allah ka yafe min, na kasan ce ba mace ta gari ba a gare ka, na kasa sauken hakki ka dake kaina"        Shima rungumeta yayi Yana juya ta tamkar suna rawa , Murmushi yayi Mai d'an sauti yace "Wannan shine yasa kike kuka" Kai ta d'aga alamun eh, yace "Kar ki damu when ever you're ready ina Nan ina jiran ki, ban damu ba by The way bamu fa Kai sati ba so take your time Nasan abinda kike ji"          Janye ta yayi daga jikinsa yana kallon fuskan ta jaaan hancin ta yayi yace "Cry cry baby Duk kin tada min hankali na d'auka wani abune  ya Faru"    Cikin shesshekar kuka Tace "Yanzu Dan Allah baka fushi dani?" Murmushi yayi yace "ko kad'an" Kallon kallon suka shigayiwa junan su, ko wannnen su da abinda yake rayawa a ransa.      A hankali yake kusanto fuskar shi da na nata, had'e kansu yayi wuri guda suna jin numfashin shin junnan su sun d'auki tsawon dakika 6 a haka, tsintan Kan su sukayi suna sumbatar junan su, a hankali suke Shan bakin junan su, sun dad'e a haka, a tare Kuma suka janye bakin su suna wani irin numfashi yanda kasan sunyi gudu ne.       Hannun ta ya rike suka shige bedroom d'insu, a Kan gado ya zaunar da ita, ya shige bathroom yayi wanka, Bayan ya fitone itama ta shuga, Bayan ta fito ne ta hango shi Yana ki shin gid'e a Kan gado daga shi sai Vest da gajeren wando, d'ago Kai yayi ya kalle ta, jikinta ya ke bi da kallo daga ita sai towel, zumbur ya mike ya nufe, Sa hannu yayi ya raba ta da towel d'in jikin ta, rintse ido tayi, Murmushi yayi ya sa hannu ya d'auke ta kamar wata Yar Baby, Akan gado ya dirar da ita Nan ya Shiga raba kansa da kayan dake jikinsa, niko ina ganin  hakan nayi saurin barin d'akin na ja musu kofa, Nace bari na leka asibiti Naga a wani hali su malam Hassan suke. asha Amarci Lafiya.         "Sister nifa gaskiya na gaji da yawon asibitin nan kullum Kenan mu muna hanyar asibiti, gashi Yan iskan Nan sun hana mu komawa makaranta wai strike"   Murmushi Ayrah tayi Tace "Sunusi Kenan to yanzun me kake nufi? Zuwa asibitin ne baka so ko Kuma haushin ASSU kake ji?"      " Duka" yace a takaice, Nabila Tace "Ni kaina na gaji Wallahi, kullum asibiti kullum asibiti"     "To ai rashin Jin Faisal ne ya ja mana hakan, gashi Nan Yana chan a tsare na tabbata ba sake shi zasuyi Nan kusa ba"    Nabila Tace "Nifa yamin dai dai Wallahi" Sunusi yace "To yanzu wa gari ya waya? Kin San dai hukunci Wanda ya kashe shine a kashe shi ko?"     Cikin Muryar kuka Ayrah Tace "Innalillahi wa Inna ilaihirraji'un wannan masifa dame tayi Kama?" Sunusi girgiza kai yayi ya fice abinsa , Nabila ganin Ayrah ta Shiga tashin hankali sosai Tace "Sister ya labarin Adnan ne Kam?"      Hannun tasa ta share hawayen dake fuskan ta kana Tace "Yana Nan, kin San tun lokacin da yaji labarin aurena da Haisam ya rikice babu yanda baiyi dani ba Akan Kar na Masa hakan, na so na Fad'a Masa plan ne Amma na kasa gudun karya tarwastsa Mana shiri"    " To yanzu ya ake ciki?" " Ya daina kulani babu yanda banyi dashi ba Amma yaki kulanai shiyasa na hakura Amma to my surprise jiya ya turo min da wani sakon da ya tsorata ni" Zaro wayar ta tayi a d'an karamin purse d'in dake hannun ta ta Shiga text d'in ta Mika wa Nabila ta fara karanta shi kamar haka. "Na tabbata kina cikin tashin hankali Sabida iftila'in da ya dirin muku a gida, Allah Kenan baki ga komai ba this is just the beginning" Nabila kallon ta tayi kana Tace "Me yake nufi da hakan?" Tab'e bako tayi Tace "I don't know Wallahi, and I love this guy so much"     Muryar Mamy taji tana fad'in "Kwarai kuwa baki ga komai ba ko ince bamu ga komai ba, Ai Allah ba azzalumin bawan sa bane ba, sai Wanda ya zalunci kansa bare Kuma Kun tab'a maraya, yau tsawon shekara nawa haisam yake kwance rai a hannun Allah, ai naso da yana Raye yaga halin da mahaifin ki ya shiga kuma Wallahi masifa da bala'i yanzu kuka Fara gani, gashi chan Faisal shima taurin Kan Nasa abinda ya jaa wa kansa"     Nabila Tace "Haba Mamy maganganun ki sunyi tsauri dayawa Kar ki manta fa ke uwace, Mamy idan uwa tana yawan sawa d'anta Albarka tab'arbarewa yake bare kuma kin Masa mugun fata Dan Allah, Mamy ki Mana addu'a Allah ya Kawo Mana d'auki"     " Ni bazanyi musu mugun baki ba, Sannan ni bazan musu addu'a ba" tana kaina ta fice daga gun, ta shige d'akin Malam Hassan, hawaye ne ke gangarowa daga idanun sa kallon sa tayi ta jaa wani uban tsaki Tace "Nasan maganar da mukayi ne da yaran Nan yasa kake kuka to Wallahi baka ga komai ba, Duk Wanda yaci Amana to ba Makawa amanar Allah zata ci shi." Ta jaa kujera ta zauna ta d'aura kafa d'aya akan d'aya ta Shiga danna wayar ta. Malam Hassan kuwa tunda wannan abin ya same shi ya daina magana, sai dai Ido kawai. Tun daga Wannan ranar Isha da Ma'aruf wani soyyaya mai karfi ya shiga tsakanin su kullum a like suke da juna idan kaga sun rabu to ya fita office ne, a haka har suka gama cin amarcin su, har ta koma bakin aikin ta, sannan lokaci zuwa lokaci ta kan je gidan Umma ko kuma gidan Mummy wasu lokutan Kuma tare da Ma'aruf d'in suke zuwa. Mardiya kuwa,tun ranar da ta kai musi abinci bata sake Shiga part d'insu ba,idan sun had'u a gun Mom sukan gaisa, kawancen nata da Ayrah tayi baya sosai ba kamar da ba kasantuwar Ayrah idan bata gun aiki to tana gun mahaifin ta, Itace Kad'ai take kula dashi Mamy kuwa da ta gaji da jinya gidan su ta koma, Ni ko Nace Anya Mamy bata d'auki zafi dayawa ba kuwa? *AFTER SOME MONTHS* Meerah ce ta Kawo wa Isha ziyara , Bayan sun gama hirar su ne suka fito tare har gun motar ta ta rakata, suna tsaye suka hango motar Ma'aruf parking yayi ya fice a motar yazo inda suke, Bayan sun gaisa ne ya ce "Barina na shiga part d'insu mom Dad ne ya dawo" "okay Nima gani Nan shigowa yanzu" "Okay ya shige ciki" Yana wasa da key d'in motar dake hannun sa,Isha binsa tayi da Kallo tana Murmushi , Meerah Tace "Wannan kallon fa?" "Hmm Bangane ba mijina ne fa"     "Oh sai yanzu Kika San cewa mijin kine ko?"     " Tun da dad'ewa Nasan da hakan" "Uhmnn manyan Mata, Amma naji Dad'i Gaskiya da Kika kwantar da hankalin ki no wonder Mana Naga sai Fresh kike kina kyau, Anya ma ciki kike dashi ba?"         "Dallah malama bana son sa Ido...... " Motar  Mardiya ce ta shigo ta faka, Bayan ta fito wurin su ta nufa, Isa wurin su ke da wuya suka jiyo wani uban Kara, juyawan da zasuyi suka hangi part d'insu Mom ne yake ci da wuta ga Warin gas ya maimaye gun gaba ki d'aya. Dukkanin su babu Wanda ya Isa mosawa a gun, suna Tsaye suna kallon ikon Allah, Mai gadi be ta fito daga ban d'aki hannun sa rike yake da buta yana kokarin d'aure mazargin wandon sa, Yana fad'in "Innalillahi wa Inna ilaihirraji'un, ba kowa a ciki ko?"    Nan ne fa Isha ta d'aura hannu a kai ta kwarma wani uban ihu, ta yanke jiki ta Fad'i , Mardiya kuwa suman tsaye tayi daga bisani ta Fad'i sumammiya, Meerah kuka ta shigayi tana nemon taimako. ________________________ Rashin comment d'inkune yasa jikina Duk ya mutu da typing d'in,Dan Allah ku bani had'in kai Nasan Kuma Kun kosa da kuji yadda labarin zai kasance Please Comment and share Milhaat ce Yar Terawa 63&64 '''Continuation.....'''  da gudu Mai gadi ya nufo su, Yana ta ambaton Innalillahi wa Inna ilaihirraji'un, Nan da Nan jama'ar unguwa suka Fara shigowa cikin gidan kowanne da abinda yake tufawa.       Fire service aka Kira ,basu d'au wani lokaci Mai tsawo ba suka iso , suka Shiga kashe wutan, Isha da Mardiya kuwa a motar Meerah aka sasu sai asibiti.     Bayan wutan ya d'a tsagaita suka Shiga ciki don duba 'barnan da wutan yayi, Mutum uku suka gani a parlor, Mutum biyu suna zaune a kujera Wanda Mom da Dad ne, yayin da d'ayan Yana kwance a kasa shine Ma'aruf. Nan aka Shiga fitar da gawakin su a waje kowa ya jinjina al'amarin cike da tausayi suke ta kallon su,yayin da masu saurin kuka Kuma sai kuka suke suna yabon hayyyan su musamman ma Dad da Ma'aruf.       Bayan sun Isa asibiti, taimakon gaggawa aka Basu, yayin da Meerah ta Kira Dad ta Sanar dashi abinda ya faru, anyi sa'a Yana gari, a lokacin suna gidan Umma shi da Mummy, a razane ya mike zufa na keto Masa, mummy da Umma a tsorace suke tambayar sa abinda ke faruwa, Daddy kallon Abba yayi kana yace "Zo muje" ya fice Abba kuwa yabi Bayan sa ba tare da yaji inda zasuje ba, bin Bayan su sukayi suna tambayar ko Lafiya.    Daddy waigo yayi cikin Murya kamar Fad'a yace "Ku koma ciki" Jin yanda yayi maganar Umma ta riko hannun Mummy suka koma ciki, motar daddy suka Shiga.        Daddy ne yake jaan motar, a hanyar ne yake Sanar dashi abinda ya faru, Banda ambaton sunan Allah babu Abinda yake har suka isa asibitin dasu Isha suke, suna dosan d'akin da Isha take suka jiyo ihun ta cikin Muryar kuka take fad'in "Dan Allah ku sake Ni, Meerah Ma'aruf fa wayyo na Shiga uku" Meerah itama kukan take Amma bata sake ta ba, da taimakon wata nurse suka rirrike ta, Isha na ganin su Abba da Daddy da dukkanin karfinta ture su ta nufi inda suke cikin kuka Mai sautin gaske, tana fad'in "Daddy Mijina na Shiga uku" ta maida kallon ta ga Abba tana fad'in "Abba ya mutu ko? Shikenan Shikenan na shiga uku, yanzun Nan fa mukayi magana dashi, Innalillahi wa ilaihirraji'un"    Daddy ne ya rungume ta Yana fad'in "Ya isa Isha ki daina kukan hakan" Amma kamar cewa yayi ta Kara kukan ne, Abba waje ya fita yace su Umma suzo asibitin, Amma bai Fad'a musu dalilin kiran suba.      Isha tafi Mintuna talatin tana kuka, Abba da Daddy suna rarrashin ta, Meerah kuwa ta rakub'e a gefe itama kukan take sosai, Su Mummy suna shigowa suka halin da take ciki, cike da rashin fahimta suke kallon su.   Abba ne ya Sanar dasu abinda ya faru, mummy fashewa tayi da kuka da zaran ta kalli Isha sai ta fashe da kuka, Umma ma kukan take, Isha mikewa tayi ta rungumi Umma tana kuka.    Meerah fita tayi bata dad'e ba ta dawo hannun ta rike yake da goran ruwa Tace "Umma ki bata tasha, ko zata d'an ji sanyi" tayi maganar cikin sanyin Murya da jin tausayin kawar ta.     Dakyar da makyar kyasa Isha ta Karb'a tasha, bata d'auki mintuna biyar ba ta fara Jin jiri, Umma na ganin hakan tayi saurin kaita Kan gado.      Nan hankalin su ya Kuma tashi Meerah Tace "Ni Nasa mata maganin bacci zata kwana tana bacci, ina tsoron Kar ciwon ta ya tashi" Abba yace kin kyauta, Duk suka tsaya zugum suna kallon ta, Nan Abba yace " Meerah ya akayi hakan ta faru?"    "Abba muna tsaye ne a compound d'in gidan, ya Dawo cikin gidan da fara'a yace ya Dawo ne ya sabida mahaifin sa ya Dawo, yana Shiga cikin gidan bai dad'e ba kawai muka ji wani irin Kara, sai wuta ya kama"    Daddy yace "Ha'aaah karar me?" "Ina tunaniin gas ne ya fashe sabida gidan Duk ya d'auki Warin gas" ta karasa maganar cikin Muryar kuka.      Abba yace "Allah sarki yaron kirki ya mutu da kuruciyarsa da rabon bazai bar baya ba" Yana girgiza Kai, Meerah bayan hannun ta ta saka ta share hawayen dake fuskan ta tace "Ya bari, sabida yanzu haka Isha na d'auke da cikin wata har na tsawon wata biyu"   Duk da hankalin su ba a kwance yake ba bai hanasu murmusawa ba, suna Mai hamdallah, ganin Isha na bacci hakan Yasa suka fita, d'akin da Mardiya take suka Shiga, tana zaune akan gadon marasa Lafiya tayi shiru bata vko motsi har suka shigo bata sani ba, Umma ce ta zauna a gefen ta Tace "Kiyi hakuri 'yata iyayen ki da Yayan ki sunyi mutuwar shahada, sai dai muyi hakuri"   'dago kai tayi ta kalle ta kana ta maida kanta kasa tana wasa da yatsun hannun ta.       Nurse ce ta Shigo da sallama Bayan sun gaisa Tace sun sallame ta, Mardiya najin hakan zumbur ta Mike zata fita mummy ce tayi saurin rikota tana tambayar ta "Ina Zaki?" "Gida" tana kokarin ficewa, daddy yace "Umman yara driver na waje ne?" " Eh" "Okay ku tafi gida tare, please ki kula da ita" ta amsa da to had'e bda mikewa, hannunta ta rike suka fice, mardiya bin Umma kawai take kamar wata sakarya har suka shige cikin motan, suka fice daga asibitin.      Ayrah na gun aiki ta ji labarin abinda ta faru a gun wasu staffs da ke Hira da saurin ta, ta fice daga asibitin motar ta ta Fad'a ta fice.     Driving take kwasam motarta ta 'dauke, buga steering motar tayi ta fad'in "Damn it!!! Fita tayi tana dubwa ko zata ga mechanic Amma Babu, kwasam wata mota tayi parking a gaban ta, ga mamakiin ta Adnan ta hango ya fito daga motar, baki a bud'e take kallon sa.             Cike da tsoro ta ke kallon sa a hankali yake takawa Yana tafiya cike da izza, Jikin sa sanye yake da T-SHIRT da Jeans,fuskan sa d'auke yake da eye glass hannayen sa a cikin aljihun sa, sai da ya isa daf da ita kana ya zaro Hannayen sa ya rungumi kirjinsa sa yace "I told you idan Kere na yawo zabo na yawo wataran Dole a had'u ko?" Ya karasa maganar yana matsowa kusa da ita a hankali take ja da baya jikinta na rawa, don a matukar tsoro take, sabida irin kallon da yake mata Kallo ne na tsantsar tsana.     Murya na rawa Tace "Adnan please, ka kyaleni na tafi Dan Allah, me na maka, nifa Babu abinda na maka"      "Shutttt up jaka wawuya" a tsawace yake maganar, Yar karamar wuka ya zaro a aljihun sa yana nuna Mata had'e da fad'in "wuce muje" "Inaaa..... Inna.. Ina zamuje.....?" "Zaki wuce ne ko Kuma zaki tsaya tambaya ta na Burma miki wukan Nan a ciki?" Yana Mai nuna Mata motar sa.     Ayrah ganin gun shiru ba kowa, Kuma zai iya cutar da ita hakan yasa ta nufi motar nasan da d'an sauri Tana yi tana waigawa ko zata ga wani Amma har ta shige motar babu Wanda ya gifta ta wajen.       Shima motar ya Shiga ya jaa motar suka bar wajen, tafiya suke har Saida suka fita a cikin gari, parking yayi kana ya kalleta ya murmusa, handkerchief ya zaro a aljihun sa ya Mika Mata  had'e da fad'in "Kar b'i ki share hawayen ki"     Kin Karb'a ta yi a tsawace yace "ki Kar 'ba Nace" hannu na rawa ta sa hannu ta Karb'a, ta samo share hawayen ta, bata d'auki tsawon lokaci ba ta ji idanun ta sun fara rufewa tayi kokarin ganin bata yi bacci ba Amma ta kasa.     Adnan kuwa kallon ta yake sai da yaga ta fita cikin hayyacin ta, ya jaa motar, wani gidan gona ya nufa Babu kowa sai da ya sauka ya bud'e gare d'in da kansa, ya ja motar ciki kana ya sauka ya rufo gate d'in.      Bud'e side d'in da Ayrah take yayi, yana ganin ta a haka ya kyalkyale da wani shu'umin dariya, d'aukan ta yayi chak, kamar wata Yar baby ya shige cikin gidan, Kai tsaye bedroom ya nufa.      Wanka ya Shiga yayi kana ya fito ya nufi kitchen ya nemi abinda zai d'an say cikin sa, Bayan ya gama ne ya Dawo d'akin, ganin ta yayi a zaune sai kallon d'akin take.         Kallon ta yayi yace "Ohh kin farka?" Bata ce Masa komai ba, yace "Dama nima na Shigo da niyar na tada ke, da naso na cimma burina a yayin da kike bacci Amma sai Naga idan nayi hakan bazan wani gamsu ba"     Cike da rashin fahimta take kallon sa Tace "me.... Me kake nufi?" Nufo ta yayi hannun sa a konkoson sa yace "Ina nufin zamuji Dad'i mu mure, sabida Haka undress yourself"       Zaro Ido tayi Nan da Nan hawayen da suka makale suka fara zubowa cikin Murya kuka Tace "Me kake nufi da hakan?"      "Ohhhh come on, sai kace ba wayayyiya ba, to Bari na fito miki a Mutum, so nake na d'and'ani zumar ki, Duk da ma bana tunaniin ba a Riga Ni ba, Amma I'll give it a try"     "Adnan Dan Allah kayi hakuri, Wallahi Ni ba haka nake ba, Kar ka raba ni da mutunci na" "ke malama just do as I say, Kinga already na shirts, vest d'in jikina da boxers d'in kawai zance"       "Adnan kaji tsoron Allah, ka tuna Allah ya na kallon ka" "shashashar banza kin San da Allah da had'in bakin ki a ka yiwa Yar uwar ki mace fyade? Ita d'in bata San mutuncin kanta bane?"      Kai a kasa ta kasa bashi amsar tambayoyin da yake mata sabida bata da amsar da zata bashi, "Tabbas nayi babban kuskure ban tab'a  Dana sanin actions d'ina ba, and now my past is hurting me, but ya akayi ya San da maganar?" A zuciyar ta take wannan maganar muryar sa taji yana Fad'in "Kina mamakin yanda akayi ja sani ko?" Kai ta d'aga Masa alamun eh, yace "Well shi Usun is a frnd of mine" ji tayi gaban ta ya Fad'i, a tsawace yace "ki cire kayan ki, bani da Lokaci sannan idan kina tunaniin zakiyi ihu ba Mai jinki, sannan zan iya kashe ki anan hatta gawan ki ma baza a gani ba"     Ganin bata da niyar yin abinda yake bukata ya zaro belt a Jikin wandonsa da ya cire ya nufo ta gadan gadan, tana ganin hakan ta Mike da sauri tana fad'in "zan cire..... Za cire Wallahi" Murmusawa yayi had'e da fad'in "Good girl" Jika na rawa ta soma cire kayan Jikin ta, Yana tsaye Yana kallon ta, sai faman lashe baki yake kamar sabon maye, sai da ta gama cire kayan Tass ya Mata alama da hannu tazo.          Tafiya take tana d'an rufe Jikin ta da Hannayen ta har ta Isa inda yake, hannun ta ya cire daga Kan kirjin ta, Nan da Nan ya kara rikicewa, bai tsaya 'bata lokaci ba yasa Hannayen sa biyu ya shiga wasa da Dukiyar Fulanin ta da karfin gaske Yana yi yana cizan leb'en sa. Ayrah kuwa kuka take a hankali kara sauti, bakin sa yasa a ya fara shansu kamar zai cinye.     Wani irin azaba take ji, ta fara kokarin tureshi da dukkanin karfinsa ya riko ta cikin sauri ya sa hannun sa a kasan ta, don mugunta yatsunsa guda hud'u yake kokarin chusa mata Jin yaki shiga , hannun ta ya riko ya ajiye ta Akan gado , ya ware kafafun nata,ganin yanda wurin yake a tsaftace sannan ga kamshin da ke tashi a gun,hakan ba karamin kunna shi yayi ba,ya Kara gigicewa.       Saurin Sanya bakin sa yayi yana Sha kamar ya Sami alewa, Ayrah kuwa tun bata Jin komai har ta Fara sauke wani irin nishi, Adnan na Jin hakan yayi sauri cire vest da garen wando da ke Jikin sa, ya Haye kanta, Babu tausayi babu imani yake kokarin shigar ta bai Sha wani wahala ba sosai kasantuwar gun a jike yake ya shige jikin ta wani irin Kara ta sake, tana kuka tana ture shi Amma ina yafi karfin ta, sai da ya yi Mai isar sa kana ya mike, har yanzu kuka take.    'ban d'aki ya shiga  shower ya Kuna Yana tsaye ruwan na sauka a Jikin sa, "Mtswww What happened? Meyasa nake ji ina tausayin ta Kuma?" Da wannan tunaniin ya gama ya fito.      Har yanzu kukan take yace "Ki tashi kije kiyi wanka kin dame ni da kuka, Bayan kema kinji Dad'i"    Cikin Muryar kuka Tace "Dan Allah ka barni na tafi gida" Hanyar fita yayi da kamar bazai tanka mata ba sai ya juyo yace "Idan Kinga kin bar Nan to Wallahi sai ranar da naji na gamsu na daina Jin sha'awar ki ko da kuwa zan Kai shekara ne." Yana Kai Nan yayi ficewar sa.    Kuka ta Shiga rairawa a haka baccin wahala ya d'auke ta.         A razane ta farka tana kuka, Meerah da sauri ta nufi inda take tana kokarin rike ta Tace "Isha please zaki ji wa kanki ciwo"   "Meerah meyasa kike min haka? Meyasa kike bani maganin bacci kin maidani kamar wata tab'ab'biya"     "am sorry but I have to do it, bana son wani mummunan abu ya same kine" "To me ya rage? Me ya rage Meerah, Na rasa Haisam, gashi yanzu zan rasa Ma'aruf Dan Allah ki Fad'a min cewar Ma'aruf na Raye" ta karasa maganar tana kuka. Ganin Meerah tayi shiru ne hakan ya tabbatar mata da Ma'aruf ya mutu cikin kuka Tace "Na sani na sani Shikenan, Shikenan shima ya tafi ya barni"     "Isha calm down please, Duk mai Rai mamacine muma tamu muke jira" cikin Murya mai Sanyi take maganar "mom da dad fa?" Ajiyar zuciya Meerah tayi kana Tace "Duk sun mutu sun kone kurmus" Isha dafe kanta tayi wani irin ciwon kai take ji kamar kanta zai fashe, Meerah Tace "Isha Kar ki cutar da kanki Dan Allah, sabida Kinga bake Kad'ai bace yanzu"      " Ban gane ba ni Kad'ai bace yanzu ba?" "Ina nufin kina da 2 months pregnant" Mummy da Daddy da Shigowar su Kenan suka ji maganar da suke da sauri mummy ta karaso inda suke tana fad'in "Meerah pregnant? Are you sure?"      "Eh mummy, ai tun zuwan mu ma suka tabbatar min da hakan, Amma dake Naga halin da kuke cike Ne d'azun yasa na kasa Fad'a Muku" Murmushi Mummy tayi Tace "Allah ya miki Albarka" "Amiin Mummy" Mummy kallon daddy tayi Tace "Alhaji kaga ikon Allah ko?" Murmushi yayi yace "Allah Kenan" Wayar Isha da ke hannun Meerah ne ya fara ringing, da sauri ta fice ganin Wanda ke Kiran layin Isha, da sallama tayi picking, daga d'ayan 'bangaren yace "Kina kusane? Haisam ya farka" kashe wayan tayi da saurin gaske ta bar gun.     ICU ta nufa daga nesa ya hango ta kasantuwar yasan ita d'in kawar Isha ce yace "Ina take?" Nan ta Fad'a mishi incident d'in da ya faru, yaji tausayin ta matuka, Nan ta nemi alfarma ya bari ta Shiga a madadin Isha, bai Musa Mata ba, suka Shiga, suna Shiga taga Haisam a kwance sai rarraba idanu yake Yana son gane inda yake. Idan sa ya sauke a Kan Meerah, Cikin tsarkewar murya yace "Prin.... Ceessss" (Princess) Kama baki Meerah tayi Nan da nan hawaye suka Fara kwararowa daga idanun ta, "wannan Wace irin shakuwace a tsakanin Ma'isha da Haisam,sabida nasan da sunan Princess yake Kiran Isha,tabbas ita yake son gani,tunda ya farka bai yi magana ba,sai da yaga kawar ta" Dr Ali ne yake ayyana hakan a ransa. Da gudu Meerah ta fita, ta nufi ward d'in da Isha take, tana Shiga d'akin ta fashe da kuka su, mummy da Daddy suna tambayar ta ko Lafiya Amma sai kallon Isha kawai take, Isha ma kallon ta take. ________________________ Please Vote and comment Milhaat ce Yar Terawa 65&66 '''Continuation........''' daddy kallon ta Meerah yake cikin Muryar mai Sanyi yace "Meerah speak up Mana, what happened?" Mummy ce ta karasa inda take, hannunta ta rike hadey da fad'in "Kina Lafiya tsorata mu Meerah, me ya farune kike kuka Haka? Wani mugun abune Kuma ya Faru, sabida a cikin Yan shekarun Nan duk kullum cikin tashin hankali muke da ga wannan sai wanchan" Daddy yace "Kar kiyi sab'o Mana, Ko wani bawa da tasa kaddarar mu Tamu Kenan muyi fatan Allah ya bamu ikon cinye jarrabawar" Meerah hannun tasa ta Shiga share hawayen ta, murmusawa tayi had'e da fad'in "Mummy wannan karon ba mumunar labarine ba, abinda Muka dad'e muna jira ne" Cike da mamaki suke kallon ta, musamman ma Isha da ta kosa taji maganar dake bakin ta,mummy Tace "Please stop beating into the bush,just go straight to the point Mana" "afwan mummy......" Kallon Isha tayi Tace "Haisam ya farka" Isha da Bata San sanda ta Dirko daka gan gadon asibitin ba,bata tsaya tambayar ta komai ba ta yi hanyar fita,Duk suka bita da Kallo,Mummy Tace "Are you sure of what you're saying?" "am sure mummy har sunan Isha ya Kira" daddy yace "Ta fita fa a haka jikinta ba ko mayafi" ai kuwa a sannan ne mummy da Meerah suka bi Bayan ta,a guje Mutanen dake gun sai aikin kallon su suke, suna Kiran sunan ta Amma inaaa kamar cewa suke ta Kara gudu. Tana Isa ICU,zata Shiga aka hanata,ganin yanda take a birkice kamar mahaukaciya,Dr Ali ne ya karaso gun sabida hanyaniyar da yake ji,Yana ganin Isha ya bi Jikin ta da Kallo da ga sama har kasa ,a cikin kwana d'aya har ta lalace tayi baki ta rame, tabbas tana cikin damuwa. Muryar tane ya Dawo dashi duniyar Mutane tana fad'in "Dr ka Fad'a musu su barni na Shiga please" tana maganar tana kuka hawaye ya wanke mata fuska, Dr Ali yace "Ai Haisam baya Nan Isha" "Ban gane baya Nan ba?" "Ina nufin Yana ward,an fitar dashi daga Nan,kizo muje na kaiki inda yake shima Yana tambayar ki" a dai dainan su mummy da Meerah suka Isa inda suke,suna ganin sun juya suka bi Bayan su ba tare da sunce komai ba,Isha tafiya take har tana kokarin fad'iwa. Da sauri Dr Ali ya taro ta cikin sanyin Murya yace "Be careful" Murmushi kawai tayi suka cigaba da tafiya, suna Isa kofar d'akin da Haisam yake yace "Ki Shiga Nan ne d'akin nasa" Kasa motsi tayi tana kallon kofar, Meerah ve ta dafe ta a kafad'ar ta had'e da fad'in "isha kin dad'e kina jiran Wannan ranar, ki Shiga Mana" "Meerah ina tsoron Shiga ne, bana so ya Kuma rufe idanun sa kamar na ranar idan ya sake rufe idanun sa na tabbata bazai sake tashi ba" Dr Ali yace "No Isha Kar kice haka Mana, I told you d'an sarkin Saudi tun yana da shekara 17 a duniya yayi accident ya Shiga comma, tun 2014 Kuma a yanzu Muna 2022 bai farfad'o ba Kuma bai mutu, Kuma Haisam bai koma ba , tun da kiga mun dawo dashi nan, ya farka kenan" Mummy Banda kallon Isha babu abinda take yi,wasu zazzafan hawayene suke gangarowa daga fuskar ta tana mutukar jin tausayin Yar tata,fatan ta shine wannan ya Zama shine wahalar ta na karshe a Duniya. Ajiyar zuciya tayi ta Fara 'daga kafa a hankali, ji tayi kafar ta ya mata nauyi Duk da babu takalmi a kafarta,Jan kafar ta farayi har ta sa hannu ta murd'a kofan ta bud'e, kamar baza ta Shiga ba, sai Kuma ta Shiga da d'an sauri. Haisam naji motsin kofar ya waigo, don ganin Wanda ya shigo, Yana ganin Isha, kallon ta kawai ya tsayayi, itama kallon sa take Hannayen sa ya ware alamun come and give me a hug, cikin kuka da had'e da dariya ta nufi inda yake, ta rungume shi , wani ajiyar zuciya suka sauke a tare, Isha kuka take yayin da yake d'an bubbuga Mata baya alaman rarrashi Yana zubar kwallar Farin ciki, Shigowar su Mummy ne yasa tayi saurin janye Jikin ta. Mummy wurin Haisam ta nufa, shafa kansa tayi cikin so da Kauna irin na uwa da d'anta, Tace "Son kana lafiya?" Ya bud'e baki da niyar magana Amma ya kasa, Isha kallon Dr Ali tayi Tace "Ya baya magana Dr?" "Eh ai dama bazaiyi magana Nan take ba, sabida shekarun da ya d'iba Yana bacci, yanzu Haisam ya zama kamar yaro babu abinda zai iya yiwa Kan sa" Mummy Tace "For how long Dr?" "Uhmn I can't really say gaskiya, Haisam have been sleeping for four years, so Allah ne Kad'ai yasan sanda koman shi zai Zama normal" Haisam kallon su yake Yana mamakiin maganar da Dr Ali yake yi, Wai shi ne yayi bacci har na tsawon shekara 4,shi Duk a tunaniin sa Suma yayi ya farka, a Sannan ne ya tuna da a gun d'auri auren sa ne ya Suma, kokarin tashi ya Shiga yi, da sauri Dr yasa hannu ya kwantar da shi Yana fad'in "Calm down Haisam, Calm down" Kuka ya farayi Yana kokarin tureshi, yace "Haisam me kake so? Akwai abinda kake so a Kawo maka ne?" Murya a hard'e yace "Ayrah" Isha, Mummy da Meerah kallon juna suka Kuma suka mayar da kallon su ga Haisam d'in, Isha fashewa tayi da kuka ta fice daga d'akin, tana fita suka ci karo da Daddy, Abba da Umma. Daddy ne ya rike ta yace "Isha ina Haisam d'in" Cikin kuka Tace "Yana ciki" Umma tace "Ya Mutu ko Isha?" Kallon Umma tayi a razane ta girgiza kai had'e da fad'in "A a bai mutu ba" Abba yace "To kukan me kikeyi?" "Kawai tausayin sa nake ji" tana Kai Nan tayi gaba suka bita ta da Kallo, d'akin suka Shiga, da sallama, haryanzu Yana kokarin ture Dr Ali,Umma na ganin Haisam cikin Muryar kuka tace "Haisam!!!" Haisam naji Muryar Umman sa ya d'ago ya kalli inda yaji Muryar ta, cikin tsarkewar murya yace "Umma" Da sauri ta nufi inda yake, Dr Ali na ganin hakan ya jaa da baya, rungume shi tayi Yana kuka tana kuka. Meerah na ganin hakan ta fita tabi Bayan Isha, hango ta tayi ta durkusa tana ta kuka mai tsuma zuciya, cike da Jin tausayinta ta d'ago ta tana fad'in "Isha kuka?...... Tasa hannu tana share mata hawaye " please ki daina kuka Isha, nasan ambaton Ayrah da yayi ne ya saki kuka ko?" 'dago rinannun idanun ta tayi cike da mamaki Tace "Ya akayi Kika gane hakan" "Hmm haba Isha we have been friends for a very long time, ya za'a yi bazan gane ba?" " Hakane Amma Meerah abun ya bani mamaki, Amma meyasa ya ambaci sunan ta, hakan na nufin asirin da ya mata bai Karye ba?" "A a baki ga actions d'insa ba, ya tuna abinda ya faru ne, don na tabbata Haisam zai d'auka kamar bacci yayi ya farka, ya Kamata ki Masa uzuri kinji, bazai ma so Ayrah ba sai dai ya tsane ta sabida abinda ta aikata masa" Hijab ta saka Mata kana ta ajiye Mata ta kalmi, sawa tayi, Meerah riko hannun ta tayi suka koma cikin d'akin. Dukkanin su murna suke sosai yau Haisam d'insu ya Dawo. Mardiya tana kwance a d'akin da Mummy ta ajiyeta, taji lokacin da suke waya da Mummy Akan Haisam ya farka, kuka ta Shiga yi tana fad'in "bazan tab'a yafe miki ba Isha, kin kashe min Yayana da Iyeye na, gashi Yayan ki ya farrka wayyo Allah na, ya zanyi na Shiga uku na lalace" kuka take sosai kamar ranta zai fita. Kwankwasa kofar da taji akeyi ne yasa ta tsagaita kukan nata, hannu tasa ta share hawayen ta kana ta Mike ta nufi kofar d'akin, bud'e kofar tayi tana kallon ta. Tace "Hajiya Lafiya naji kina kuka?" Mai aikin Umma ke yi Mata wannan tambayar. Kirkirerren Murmushi tayi kana Tace "Lafiya Lau, nagode" ta koma ciki had'e da rufe kofar. "mtswww Amma Ayrah bata da mutunci na tabbata taji labarin abinda ya same Ni, tun da safe Amma har yanzu Bata Kira ni ba bare tazo inda nake" Dialing numberta ta Shiga yi Amma swich off, cike da mamaki take kallon wayan nata a bayyane Tace "Yau Wace Rana? Wayar Ayrah a kashe?" Tab'e baki tayi ta wurgar da wayar a gefe ta yi tagumi tana tunaniin yanda rayuwar ta zata kasance, ba uwa ba uba ba yayanta Wanda yaje sonta fiye da komai, ta cigaba da rera kukan ta. "Nabila wai yau ina Ayrah ne, tun safe da na Zo ban ganta ba, wato dama haka takeyi Bata Zama a gu d'aya?" Mamy kiyi wa Nabila Wannan tambayar. "A'a Mamy kullum tana Nan Wallahi, Sunusi ne ma ya daina zuwa kwata kwata" " To ina taje?" "A Facebook muka gani Wai gidan su Mardiya ya kone, shine ta fita don taje ta Duba ta Amma haryanzu bata Dawo ba, Kuma na Kira Layin ta baya shiga" "Innalillahi wa Inna ilaihirraji'un, Ashe dama gidan su Mardiya ne? Ance fa Duk mutanen ciki sun mutu" "Eh Mamy gidan sune" Mamy yarfa hannu ta Shiga yi ta Kama habarta Tace "Oh Allah, Allahumma Ajurni fii musibati, Kinga rayuwar Nan ko, ita fa da Ayrah suka had'a Kai suka cutar da Yayan ku Haisam sabida hud'ubar uban ku, gashi duk Allah ya soma nuna musu ikon sa" Nabila "uhmmmn" kawai tace.. Mamy Tace "Kira Mardiyar muji ko suna tare" "To Mamy" Ta Shiga Kiran layin Mardiya, mardiya naji wayan ta ya Fara ringing tayi Tsaki bata Duba wayar ba bare tasan Wanda ke Kiran an Kira har sau biyu na ukun ne tace "mtsww Wane ne hakane?" Ganin sunan mardiya ya bayyana a fuskar wayarta tayi saurin d'agawa, ta'aziyya ta mata kana ta tambaye ta ko suna tare da Ayrah. "A'a bata Zo ba, nayi tunaniin ma bata ji abinda ya faru bane ba" "A a taji, har ta fita da motar ta Akan zata je gidan naku" "okay bata iso ba maybe tana hanya ne" "Anya kuwa tun fa lokacin da abin ya faru ta fita, ai ko barin gari zata yi Albarka" "Hakane Kam, Kuma ko da taje gidan namu ma baza ta sameni a Chan ba" " Toh Allah yasa Lafiya" Ta amsa da amiin. Mamy ce ta karb'i wayar suka gaisa ta mata ta'aziyya sannan ta mata nasiha, ta Kuma jaddada mata cewar kuka ba nata bane yanzu tayi ta musu addu'a kuka take sosai, Mamy na Jin hakan tayi saurin katse wayar, Mardiya kuwa ta Shiga rera kuka Mai cin raai. Bacci take har ta manta Jikin ta , ruwan da aka watsa mata ne yasa ta farka a razane a had'e da dirkowa daga Kan gado, kallon sa take yi da d'an karamin bucket d'in dake hannun sa ta kalli Jikin ta, zaro ido tayi tana ganin jikinta har yanzu ba kaya da sauri ta sa hannu ta d'auko zannin gadon ta d'aura a Jikin ta. "Mtsww me zaki 'boye anan me ban sani a Jikin ki ba?" Adnan keyi wa Ayrah wannan maganar Kai ka sa tana matsar kwalla Sam bata ji dad'in maganar da yayi mata ba, yace "Ba Kya sallah ne? Bakiyi azahar da la'asar ba gashi magrib ta sako Kai, wato ma kinji dad'in abinda mukayi d'azu tunda har Kika iya bacci, to ki shirya anjima zamu sake, kije kiyi wanka" Yana kainan ya fice abinsa. Bin bayansa tayi da Kallo tana Jin tsanar sa a cikin zuciyar ta, ajiyar zuciya tayi ta nufi hanyar ban d'aki, shigowa d'akin ya sake yi Amma wannan karon da wata Leda ne a hannun sa, wurga mata yayi yace "Kaya ne idan kin yi wankan kisa" Bud'e ledar tayi, kananan kayane aciki, daga mini skirt sai wanduna da riguna sharara Wanda su da babu Duk d'aya, hawayebe masu zafi suke gangarowa daga fuskan ta Tace "Wai me ya maida ni ne?" Ji tayi ya amsa da "Karuwa ta" kallon sa tayi tana mamakin yaushe ya shigo, Kuma ya akayi yaji abinda Tace ganin kallon da take Masa ne yasa ya kashe Mata ido had'e da fad'in "Ya akayi" Yana maganar cikin gadara da nuna Isa. Wurgar da ledan tayi ta Shiga ban d'aki, tana ji kamar ta shake mishi wuya. _________________________ Please comment and Share Milhat ce Yar Terawa 67&68 Continuation.......... Tana fita daga wankan jikin ta d'aure yake da towel,sai da ta leko taga baya nan kana ta sa Kai ta fita, ledan da ta yatsar ne ta tsuguna ta d'auka,zazzagen kayan tayi ta shiga dubawa wani wando ta gani Wanda shine d'an dama dama ta saka taga ya Kai gwiwanta, Wani riga ta d'auka ta sa, Wanda armless ne kamar vest Amma ya rufe mata cibiyar ta.            Bayan ta gama sakawa ne ta hango kan gadon,da mamaki ta Kara gun hannu tasa ta d'aga ga mamakinta hijab ta gani girgiza kai tayi a bayyane tace "Adnan kenan,hijabi ya kawo min" ajiyewa tayi ta koma ban d'aki tayi alwala bata dad'e ba ta fito,sallayan da ta hango a bedside ne ta d'auka ta shimfid'a kana ta Sanya hijab din ta tada sallah.              Ta yi raka'a biyu ta ji shigowar sa,har ta gama jero sallolin da ake binta kana ta sallame,tana d'aga Kai suka had'a ido dashi,tayi saurin kawar da kanta,murmushi yayi kana yace "Tashi muje muci abinci" mikewa yayi daga kwancen da yake ya fita, Yana fita ta bi bayan sa,a parlour ta tarar dashi ya zauna gaban shi da abinci kallon sa ta tsaya yi,Shima kallon ta yake yace "Kin tsaya kallo na zauna mana"              Zama tayi tana mamakin a ina ya sami abincin,ta Kai hannun ta kenan yace "daga ta malama wai kina nufin a tare zamuci abinci? A kwano d'aya haba,matsayin ki bai Kai Nan ba" taji ba dadi hakan yasa ta mike cikin fushi ta nufi d'aki,da sauri yace "Gara ki zauna kici abinci,sabida bazan sake fita ba,idan ma na fita a chan zanci kayana,yanzun ma tausayin ki naji yasa na kawo miki take away,sannan inaso ki samu karfin d'auka na,ki ga take away chan...... "Yana nuna mata ledar dake gefen sa "ki d'auka rice and stew ne"          Sai da ta gama kallon sa kana ta shige d'aki abinta,girgiza kai yayi had'e da Murmushi ya cigaba da cin  abincin sa,tana shiga ta sawa kofar key,zama tayi akan sallaya wayar ta ta shiga dubawa taga babu,hakan ne ya tabbatar mata da cewar ya d'auke mata, mikewa tayi ,tayi sallar Isha kana ta kwanta akan gado.              Tunanin halin da Nabila zata shiga ne yake damun ta,Fatan ta shine Allah yasa su gane sace ta akayi,kuka ta fara yi ganin yanda Adnan ya Maida ta tamkar matar sa a Rana d'aya kawai Kuma ta tabbata zai Kuma Neman ta shiyasa ma ta rufe kofar, tunani take mai kyau da mara kyau tana da na sanin abubuwan da ta aikata,ta dad'e a haka kana bacci ya d'auke ta,chan cikin bacci taji alamun ana cire mata wando,a razane ta Farka tana jaan jikinta,ganin Adnan ne hakan ya Kara tsoratar da ita,kuka ta shiga yi tana Masa magiya akan Kar ya mata haka Amma ina baya ma sauraron ta,a haka har ya raba ta da kayan dake jikin ta,ya afka mata bakamar d'azu ba da Saida ya yi wasanni da ita,zafi taji sosai tana kokarin tureshi Amma ta kasa sabida Adnan na mijine kakkarfa,yafi karfin ta,sai da yayi mai isarta kana ya kyaleta, tare suka kwana a wannan ranar idan yayi barci da zaran ya Farka sai ya afka mata yayi hakan kusan sau Hud'u kan gari ya waye,sai da aka Kira sallar asuba kana ya kyaleta ya koma d'ayan d'akin,ya watsa wa jikinsa ruwa yayi sallah kana ya koma baccin sa,ayrah kuwa ko motsi Mai kyau ta kasa yi,i wani azabebben zazzab'ine ya rufe ta,ta ja bargo ta rufe jikinta tana rawar sanyi.              Sai karfe 10 na safe ya tashi daga bacci Nan ma yunwace ta tashe shi, weekend ne hakan yasa bazai fita aiki ba,d'akin da take ya nufa Yana shiga ya hango ta tana rawar sanyi da sauri ya karasa inda take ga mamakinsa zufa take had'awa Amma kuma tana rawar sanyi, first aid box ya d'auko ya bata maganin zazzabi dakyar ta karb'a Tasha zaunar da ita yayi Yana kokarin d'agata,wani Kara ta saka Wanda yasa ya razana bargon ya d'aga yaga irin aika aikan ta yayi zanin gadon duk ya 'baci da jini,dafe Kai yayi a zuciyar sa yace "What have I done?" Cike da Jin tausayin ta ya Mike ya d'aga ta Chak sai ban d'aki ruwan wanka ya had'a mata tana tsaye a rigingine tana kallon sa, had'e da ciza leb'en ta magana yake mata Sam bata Jin sa,ganin hakan kawai ya d'aga ya saka ta acikin bathtub da already ya had'a ruwa Mai zafi,wani nkarabta saka tana kokarin fita ya danne ta da dukkan karfin sa,Yana mata sannu kuka take sosai har ta fara Jin dadin ruwan bayan ta d'auka tsawon mintuna kana ya cire ta,ya Mika mata towel ya fita,bed sheet d'in ya cire ya canza wani a dai dai Nan ta fito,kallon ta yayi ya fice daga d'akin.           Tun daga wannan ranar yake tausayin ta ya d'an d'aga mata kafa,sai da ta warware kana ya d'aura daga inda ya tsaya.          Mardiya tana samun kulawa sosai agun Umma ta d'auke ta kamar Yar da ta Haifa a cikin ta,haka ma su Twins sun saba da ita sosai, idan suka dawo daga school sai su zauna a d'akin ta suyi ta cika ta da surutu,wannan dalilin ne yasa ta d'an saki ranta a gidan. *AFTER ONE MONTHS*         Haisam na samun kulawa sosai from both families,musamman ma Isha tafi kula dashi sama da kowa,Ayrah kuwa cigiyan ta ake sabida alamu sun nuna sace ta akayi an samu motar ta a pake a bakin hanya Amma an kasa gano Indo take.              Adnan kuwa duk lokacin da yaji amfani da ita zai afka mata ba dare ba rana,da safe zai fita yaje gun aikin sa da dare kuma ya dawo,wasu lokutan kuma ita kad'ai take kwana tafiya yake ya barta Amma baya barin ta ba tare da ya ajiye mata abinda zata ci ba,sau dayawa idan ta shiga d'akin sai ta rufe Amma cikin dare sai taji motsin sa hakan ne ya tabbatar mata da cewar Yana da wani key d'in daganan ta hakura,kullum cikin kuka take tana rokon sa akan ya kyaleta ta tafi gida,Adnan na matukar Jin tausayin ta kuma yana kaunar ta shi Kansa bai San dalilin da yasa yake mata haka ba,har cikin ransa Yana so ya bar ta tafi,Amma idan ta tafi ya zaiyi,ya Saba da ita,Yana sonta Yana kaunar ta sannan Yana son kasancewa tare da ita,hakan yasa ya yanke shawarar bazai tab'a rabuwa da ita ba.           Mamy tayi kukan tayi kuka har ta gaji,babbar Yar ta 'bata duk da cewar tana fushi da ita Amma hankalin ta yafi na kowa tashi,kullum cikin kuka take tana addu'ar Allah ya bayyana ta ko da kuwa gawan tane tasan cewar ta mutu,tayi mata addu'a,suna cikin wannan halin ne aka yankewa Faisal hukuncin kisa duk Wanda ya kashe a kashe shi. Kasantuwar Familyn su Mamy suna da kud'i duk da ba wani kud'i suke dashi ba babban yayan tane ya shiga ya fita har aka kashe case d'in aka sake Faisal,tun daga Nan Faisal ne yake kula da business d'in Daddyn nasu duk da har yanzu Yana Jin haushin uban nasa yaso ace da shine ya mutu ba wa'annan Yan matan ba,Amma duk da hakan bai hanashi biya masa kud'in asibitin ba.          Ganin babu Wanda ya kira yayi demanding kud'i yasa polisawa suka gane cewar ba kidnapping d'inta akayi ba,hakan yasa suka ma daina Neman ta sabida su kansu sun gaji .             Kamar yadda ya saba tafiya ya barta haka yau ma yayi,sai washe gari ya dawo,Yana Bud'e kofar ya hango ta a zaune kan koshin ta zuba Uban tagumi ga TV na aiki Amma hankalin ta Sam baya Kai,bata ma San ya shigo ba,har gaban ta yazo ya tsaya bata sani ba,har Saida ya tab'a ta,a razane ta d'aga kai ta kalle shi,ganin shine ta kwar da kanta gefe Don a ko wani Rana tsanar Adnan karuwa yake a zuciyar ta, cikin murya Mai sanyi yace "Ayrah me yake damun ki?"              Kallon ka raina min wayo ta masa kana ta kawar da kanta had'e da yar karamar tsaki, murmushi yayi kana ya zauna a gefen ta yace "Nasan kin tsane ni baki ki ma ace na mutu ba ko?"           Shiru bata ce masa komai ba,murmusawa ya kumayi kana yace "Am sorry Ayrah babu yanda zanyine,sabida Ina son ki Ina so na kasance Dake na har a bada,idan kin amince wallahi zan aure ki kuma na miki alkawari daga yau bazan sake kusantar ki ba har sai na mallake ki a matsayin matata ta sunnah."         Mikewa tayi Tace "Bayan abubuwan da kamin Adnan? I won't fall for your lies anymore, ka cuce ni, ka wulakanta Ni, yanzu Kuma kazo kana gaya min maganar banza maganar wufi" ta karasa maganar tana kuka Mai tsuma zuciyar Mai sauraron.     Ledan da ya shigo dashi ya ajiye, har kasa ya durkusa ya hard'e Hannayen sa alamun roko, hawayene suke gangarowa daga idanun sa Zuwa kuncin sa, cike da mamaki take kallon sa, cikin sarkewar murya yake fad'in "Dan Allah Ayrah, Kar ki min haka kiji tausayina Wallahi ina sonki Kuma Ina kaunar ki, bazan iya Rayuwa babu ke ba Ayrah"        Tunda ya Fara maganar take kallon sa cike da mamaki, ji take kamar ta shake Masa wuya ya mutu.             "Kana Sona kace?" Cikin sanyin Murya take magana. "eh Wallahi , ina sonki sosai fiye da tunaniin Mai tunanina" "Hmm to ina so ka bud'e kunnuwan da kyau kaji abinda zan Fad'a maka yanzu" magana take in a serious tune, ganin hakan ya mike ya tsaya da kafafun sa, Duk Jikin sa yayi sanyi.     Matsowa kusa da shi tayi,har suna iya jin numfashi junan su, cikin Murya Mai d'an karfi Tace  "Ni Ayrah Hassan na tsane ka, na tsane ka kuma bazan tab'a son ka ba"     Yace "Ni Kuma ina sonki ina sonki Kuma bazan tab'a daina son ki ba" " Ohh haka kace? Haka kace?" Cikin d'aga Murya yace "Eh haka nace" "To tabbas nice ajalin ka Adnan" Murmushi yayi kana yace "Da nafi kowa Farin ciki idan Kika kashe Ni" Wani abu taji ya tokare ta a kirji, Bata Jin dad'in yanda Sam bai da mu da maganganun da take Masa ba, tsaki tayi ta shige d'akin ta.      Kallon ta ya tsaya yi  har ta shige d'akin, a bayyane yace "Wallahi sai na sace zuciyar ki kamar yadda nayi a baya." Kofan d'akin ta ya nufa ya tura a hankali ya hango ta zaune Akan gado tana aikin kuka, ji yayi ba dad'i, ledan hannun sa ya ajiye Mata ya fita gaba ki d'aya daga gidan.          Alhamdulillah Haisam na samun sauki sosai don har ya Fara takawa, maganar sa Kuma ya Dawo normal, Duk da wasu kalmomin idan ya furta su kamar yaro.       Wata Rana, Yana kwance a Kan gadon jinyar sa, Isha Kuma na zaune a gefen sa a Kan plastic chair kallon ta yake yayin da ita Kuma hankalin ta na Kan wayan ta.       Muryar sa taji ya kira sunan da ya saba kiran ta dashi "Princess!!!" Ajiye wayar hannun ta tayi tace "Akwai abinda kake bukata ne?" Ta mike  tana kallon sa shima kallon ta yake, da ta lura da yana kallon cikin ta, itama kallon cikin natan tayi Wanda a yanzu Yana cikin wata hud'u, ya Fara fitowa, da sauri ta koma ta zauna.    Murmushi yayi kana yace "Princess Fad'a min abubwan da nayi missing Bayan na Shiga comma" Wasa ta shigayi da hannun ta kana ta Fara fad'in Duk abubuwan da ya faru, Kama daga yanda ya Shiga comma har aka Kawo shi asibiti, da shekarun da ya d'eba Yana kwance, Sannan ta Fad'a Masa tayi aure Amma Bata shekara ba mijinta ya rasu, sannan ta Fad'a Masa halin da Malam Hassan ke ciki da  'batan Ayrah. Ta karasa bashi labarin tana matsar kwalla, hankalin sa yayi mugun tashi Jin abubuwan da ya faru bayan kwanciyar sa, cike da jin tausayin ta yace "Yanzu ciki kike dashi?" Kai a kasa Tace "Eh" Ajiyar zuciya yayi kana yace "Allah ya raba lafiya" Ta amsa da amiin.       Yace "ban San meyasa Baffana ya tsane ni ba , Bayan ya kashe min Uba Nima ya so ya hallaka ni, sunyi wasa da zuciya ta shi da Ayrah na kudiri aniyar d'aukan fansar abinda suka min Amma jin kaddarar da ta same su na tsinci kaina ina matukar tausaya musu, yanzu abinda yafi damuna shine Ina Ayrah take?"       "An bin cika ta ko ina Amma ba labari, gidan TV da gidan radio Duk ansa cigiya Amma shiru" " Allah ya Kare ta" "amiin" " Amma ya Jikin Malam Hassan d'in?" "I don't know gaskiya but Yana nan a asibitin nan" "really tashi ki rakani" " A a Ya Haisam, babu inda zaka ce a haka Kar ka manta fa ba cikekken Lafiya gare ka ba, tunda haryanzu kafar ka na rawa, by the way meyasa ma zaka damu da wa'annan mutanen Bayan irin abubuwan da suka maka?"     " It's simple...... " Mike Yana Mai gyara jallabiyar sa, ya d'aura da fad'in "They are my Family Princess, ai ba'a Canza wa tuwo suna" kallon sa ta tsaya yi tana tunaniin irin hali irin na Haisam ace Duk abubuwan da suka masa Amma ya damu dasu, ganin bata da niyar magana yace "Muje ko?" Ba don ta so ba, ta Mike tayi gaba yana biye da ita, girgiza kai yayi.     Ward d'in da Malam Hassan yake suka nufa, kofan Isha ta tura had'e da yin sallama kasantuwar, uniform ne na asibiti a jikinta hakan yasa suka d'auka tazo Duba shi ne, Mamy na ganin Haisam biye da ita ta Mike tana kallon sa, shima kallon ta yake don bazai tab'a manta fuskar ta ba, sabida ta kasance tana nuna Masa so da Kauna tun Yana yaro ba kamar yadda Baffan nasa yake ba, Murya na rawa Idanun ta fal da hawaye Tace "Hai......sam!!" Malam Hassan da ke kwace Yana fuskantar bango yaji an Kira sunan Haisam ya juyo a hankali, yayin da Nabila ita ma ta Mike tana kallon sa, sabida ita Sam bata tab'a ganin d'an uwan nata ba. _________________________ Please comment & vote Milhat ce Yar Terawa [8/13, 8:26 PM] Miilhaat Writer✍🏻: 🍃 *DANGIN UBANA*🍃 Story & Written By Milhart Na zo muku da littafi Mai ban tausayi,cike da abun al'ajabi,wannan salon na daban ne. *🌍MANAZARTA* *WRITERS ASSOCIATION📚🖊* *M. W. A* *Wannan labarin kirkirarren labarine ban yarda a chanza min labari ba Wanda ya chanza bamu yafe ba.* Ina alfahari da rubutu,sabida alkalami yafi takobi🗡️🗡️🗡️ *BISMILLAHIR RAHAMANIN RAHIM* Page 69&70 _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._ ```Continuation......``` Murmushi Haisam yayi Wanda yake Kara bayyana kyawun fuskar sa, rike shi Mamy tayi tana kallon sa daga kafan sa har tsakiyan kansa, idanun ta cike yake da hawaye, tana matukar son Haisam, tana Kuma Jin tausayinsa, hannu yasa ya share Mata hawayen da suka fara gangarowa daga idanun ta, Yana girgiza Kai alamun ya Isa. Murya na sassarkewa Mami Tace "Haisam Ashe ka farka? Kai Allah mun gode maka" Malam Hassan kallon Haisam d'in yake Yana daga kwance a Kan sick bed d'insa, a hankali a Haisam ya zare hannun Mami a Jikin Sa ta fara takawa a hankali, har ya nufi gun malam hassan, wani irin Kallo malam Hassan keyi wa Haisam Mai cike da ma'anoni, Haisam d'in ma kallon sa yake, mamy ce ta matsa kusa dasu ganin Shirun yayi yawa, Tace "Haisam!!! "d'ago wa yayi ya kalleta ba tare da yace komai ba. Tace "Yanzu Babu abinda kake ji ko?" Murmushi yayi kana yace "Eh Mami" ya maida kallon sa ga malam hassan da ya juya masa keya kana yace "Ya Jikin Daddy?" "Da sauki za'a ce kullum Babu improvement" "Allah ya bashi Lafiya" Mummy da Nabila suka amsa da Amin. Jin Muryar Nabila ne yasa ya kalli inda take a tsaye bai ma lura da ita a gun ba, Yana kallon ta ya Gane Yar Mamy ce sabida duk yaran Kama da ita suke, hatta yaranta mazan ma Babu Wanda yayi Kama da malam Hassan, duk da shid'in bafulatani ne na usul Amma bakine, Nabila ce ma ta d'an d'auki kalar fatar sa, hakanne yasa duk ta fi su kyau, Kun San ance black is beauty. Kallon ta yayi kana yace "Farida ko?" Murmushi tayi kana Tace "A'a Nabila" "oh sorry My Bad,Nabila amma Mami yarinyar Nan ta girma fa sosaiii" Yar karamar dariya Mami tayi duk da haryanzu hawayene fal a idanun ta, Tace "Eh ta girma nan ma baka ga Auta ba" Nabila turo baki tayi kamar zatayi Kuku, ita ta tsani daji ance mata wai ta girma, ganin yanda take ta kunkuni ba karamin bashi dariya yayi Amma ya gimtse dariyar tasa. Babu Wanda ya Kuma cewa komai kusan na mintuna uku, mami Tace "Baka tambayi kanwar ka Ayrah ba" Kai ya sane a kasa, kamar wani Mai nazari yayi ajiyar zuciya kana ya d'ago Kai ya kalli mami yace "Eh Mamy ban tambaya bane ba sabida ina da labarin abinda ya same ta" " kaga Allah ko Haisam? Baka da hakkin su shiyasa Allah ya Kama su, ban San me ka terawa malam ba, babu yanda banyi dashi ba Akan ya d'auke ka kamar d'an cikin sa, Amma ina son zuciya da son Kai irin nasa ya rufe Masa Ido, bai tsaya a iya Nan ba ya had'a har da Yar sa wacce bata da ji ba bata gani ba yayi amfani da ita wurin biyan bukatar sa....... " Kuka ne yaci karfinta ta kasa karasa maganar, Nabila ce ta sa hannu tana d'an bubbuga mata baya alamun rarrashi, mamy hannu tasa ta share hawayen ta,kana ta had'e Hannayen ta wuri gudu alamun roko kana Tace "Haisam Dan Allah na roke ka ka yafe Mana a Karo na sau ba adadi, kila in ka yafe mana Rayuwar mu zata Koma dai dai" ta cigaba da kukan ta. Haisam da d'an saurin sa ya nufo ta Yasa hannu Yana share mata hawaye, yace "Mami Wallahi ban tab'a rike Daddy a Raina ba ko da na minti d'ayane, Kuma maganar yafiya tun a ranar na yafe Masa wannan kadara tace Ni Musulmi ne na yarda da kaddara Mai kyau da Mara kyau,a ranar da Daddy yasa wa Abba guba na ganshi,Amma yace idan na kuskura na fad'awa,kowa sai ya kashe Ni ya kashe Umma,sannan a ranar da muka Koma gidan su Isha,na fito naje gidan mu don na d'auko Abu,babu Wanda ya sani daga ni sai maigadi,da idona naga daddy yana fad'a musu su sa petir ta ko ina,hmm su mutu kowa ya huta,a ranar na gane Isha is an Angel to me sends from the almighty Allah........." Ya d'aga Kai ya kalli Isha,da take ta matsar kwalla tana jin tausayin Yayan ta, ya maida kallon sa ga Mamy yace " let the bygones be gone Mamy, Allah baya barin wani don wani but am Very sure that ya barni a Raye ne to make things right and I'll surely do that insha Allah yanzu abinda ya Kamata muyi shine mu maida hankali gun Nemo Ayrah" Fashewa Mamy tayi ta kuka Tace "Innalillahi wa Inna ilaihirraji'un, Haisam kaga rayuwa, kaga rayuwa sabida dangin Uban ka, tun kana yaro kaga jarrabawa kalala" Murmushi yayi yace "Kuma Yanzu ya zama tarihi ba, please Mamy ki daina kuka haka, nasan kin Soni tamkar d'an da Kika Haifa a cikin ki, har Yanzu ban manta lokacin da idan Kika sayo abu sai ki ja ni d'aki a 'boye ki bani sabida Kar Ayrah ta gani duk ina tune dasu Mamy" Hannun ta ya rike ya zaunar da ita akan Plastic chair dake d'akin,ya durkusa a gaban ta Sannan ya Mika hannun ya d'auki bottle water ya bud'e kana ya Mika mata, ba musu ta Karb'a tasha, goran ta sauke kana sauke wani ajiyar zuciya, tana kallon Haisam da shima yake aikin kallon ta, shafo fuskar sa tayi had'e da fad'in "Allah ya maka Albarka" Ya amsa da "Amin Mamy" Kiran wayan Isha akayi, ta d'aga ji nayi Tace "Mun d'an zagayane Umma Amma ga munan muna dawowa" ta sauke wayan da ga kunnen ta tana kallon Haisam, mikewa yayi daga sugunawan da yayi yace "Mamy bari muje Umma ba neman mu" ya kalli Isha yace "Muje" Ta juya ta fice, Mamy Tace "Tsaya muje tare naga d'akin da kake" Murmushi kawai yayi ya rike hannun ta suka fice. Malam hassan najin sun fita ya d'ago Kai, yayi ajiyar zuciya, Nabila da sauri ta nufi inda yake tana fad'in "Daddy Lafiya? Kana son wani abune?" Girgiza Mata Kai yayi alamun a'a hawayena na zubowa daga idanun sa , da sauri ta d'auki tissue tana share Masa. Umma da Mummy sai mardiya ne zaune a d'akin Ma'isha ta Shiga, sannan Haisam da Mamy a biye da ita, Umma na ganin mamy ta Mike a d'an razane tana kallon yanda Haisam ya rike mata hannu, Rai a mugun 'bace Tace "Haisam Ashe baka da hankali me ya Kai ka gun mugayen Nan?" Saurin sakin Mamy yayi ya Shiga d'akin Yana fad'in "Haba Umma" juya Masa baya tayi Tace "Haisam kace matar Nan ta fice min daga gani bana son ganin ta na tsane ta da ita da duk wani abunda ya shafe ta" " Harda ni?" Cike da mamaki ta juyo tana kallon Haisam d'in kallon baka da hankali take Masa, ya Kuma maimaita tambayar sa a karo na biyu "hardani Umma?" "What are you saying Haisam? Are you in your normal sense?" Umma ke Masa wannan tambayar. "Of course Umma am okay, Umma have you forgotten who this woman is?" Yana nuna Mamy da d'an yatsa, "Itace fa matar da mijin ta ya kashe min miji, ya so ya kashe mu, sannan ya sa Shiga comma for almost five years" "Alhamdulillah Mijinta Kika ce ba ita ba, and wannan matar Itace matar da take Kawo Mana abinci a 'boye ba tare da Mijinta ya sani ba, sannan itace matar da take kullar miki dani a lokacin da babu Wanda yake tare da ke, ta d'auki risk da dama akaina, shin Umma laifin wani na shafan wani dama?" Ya karasa maganar cikin sanyin Murya. Shiru Umma tayi , Jikin ta ne yayi sanyi tabbasa mamy mutunce ta taimaka musu da ita da 'danta a lokacin da basu da kowa basu da komai, kosan da ta sayar a baya ma Itace ta bata jarin, tana cikin wannan tunaniin ne ta ji an Kama Mata kafa da sauri ta kalli a kasa, ganin Mamy tayi ta zube a gaban ta, tana kuka Tace "Dan Allah maman Yara kiyi Hakuri nasan an cutar dake, nasan Hakurin da zan baki bazai Canza komai ba, but please find a place in your heart to forgive and believe me, Wallahi I know nothing about this, hatta ita Ayrah ma bata San komai ba, you know how Hassan is he a very manipulative human being, yayi manipulating d'inta ne Wallahi bata San komai ba Yanzu haka maganar da nake miki ayrah ta 'bata kusan watanni hud'u kenan bamu San inda take ba ko ta mutu ko tana raye bamu sani ba, babban tashin hankali na ace ta mutu bamu gana ba sabida nayi fushi da ita tsawon shekarun Nan da muka rasa Haisam, Akan sai ya farka na yafe mata gashi ya farka and she is nowhere to be found" ta karasa maganar cikin kuka. "Tabbas ni shaida ce, Mamy bata kula Ayrah, Wanda hakan ba karamin tada Mata hankali ba" duk suka kalleta, sai Kuma tayi shiru kamar ba ita tayi maganar ba, Haisam kallo d'aya ya mata ya gane ta, ya dad'e Yana kallon ta kamar Mai son gano wani abu, sai Kuma ya kawar da kansa. Umma hannu tasa ta d'ago Mamy suka rungume juna, Umma na fad'in "Kiyi Hakuri Maman Yara, da na kasa fahimtar ki na manta duk abubuwan da suka faru a baya, na rasa madafa, Ina cikin tashin hankali" " Ko kad'an Banga laifin ki ba, Amma Dan Allah ki yafe min" "Allah ya yafe Mana duka" Duk suka Masa da amin Amma fa Banda Mardiya da take ta taunan chewn gum tana latsar wayarta. Duk wuri suka samu suka zauna, kasantuwar d'akin babba ne ya d'auke su, Hira suka Fara yi harda Mummy, cikin hiran ne suka yanke shawarar zuwa ganin Jikin malam hassan, Mummy, Umma da Mamy suka fita,suna fita Haisam ya Koma Kan gadon sa ya kwanta suna Hira da Isha,daga bisani sukayi shiru baka jin komai sai karar chewn gum d'in da Mardiya ke tauna. Suna cikin wannan yanayin ne faruk da Meerah suka shigo, Isha na ganin Meerah da d'an saurin ta Mike ta rungume Meerah, Meerah d'an ture ta tayi tana fad'in "Kaaai mai ciki zungurina fa kike da tumbin ki" sai a sannan mardiya ta d'ago kai ta sauke Akan tumbin Isha, zaro Ido tayi tana kallon Isha, Meerah da ta lura da kallon da take mata Tace "Allah ya sauke ki lafiya mu samu Ma'aruf junior" Mikewa tayi tana kallon Isha cikin Muryar kuka Tace "Ciki? Ciki kike dashi Isha? Cikin Yayana?" Duk lokaci Guda ta jero mata tambayoyin Nan, Murmushi Isha tayi kana Tace "Uhmnn eh" mardiya Rungume Isha tayi ta fashe da kukan farin ciki. _________________________ Please comment and share Milhaat ce Yar Terawa [8/15, 8:02 PM] Miilhaat Writer✍🏻: 🍃 *DANGIN UBANA*🍃 Story & Written By Milhart Na zo muku da littafi Mai ban tausayi,cike da abun al'ajabi,wannan salon na daban ne. *🌍MANAZARTA* *WRITERS ASSOCIATION📚🖊* *M. W. A* *Wannan labarin kirkirarren labarine ban yarda a chanza min labari ba Wanda ya chanza bamu yafe ba.* Ina alfahari da rubutu,sabida alkalami yafi takobi🗡️🗡️🗡️ *BISMILLAHIR RAHAMANIN RAHIM* Page 71&72 _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._ ```Continuation.......``` Isha Murmushi kawai take ta kasa bata amsar tambayoyin ta, mardiya sakin Isha tayi hawayen fal a kwarmin idanun ta, Tace "Allah ya sauke ki lafiya" Duk suka amsa da Amin, Farukh ne ya zauna kusa da Haisam musabaha sukayi, sannan ya tambaye shi ya Jiki, hiran su suke hankali kwance, yayin da Meerah da Isha ma tasu hirar suke, Mardiya kuwa ta yi saye tana kallon su kamar gunki, kallon ta Farukh yayi yace "Hajiya ki zauna Mana" kamar dama jira take ta koma mazaunin ta Jiki a Sanyaye. Farukh yace "Baby ya Kamata mu tafi fa, kin San akwai wuraren da bamu je ba tukunna" Mike wa Meerah tayi fuskar ta d'auke yake da Murmushi, kallon ina zakuje Isha take Mata, hannu tasa a jakar ta ta cire IV (invitation card) ta zaro su dayawa bata San Guda nawa bane ma ta Mika wa Isha had'e da "fad'in tare ya Kamata mu raba, amma Kuma kina tare da patient, ga wa'annan ki bawa Wanda ta dace" Kallon kati Isha tayi tana Murmushi Tace "Kai Masha Allah, katin yayi kyau, ikon Allah baikin saura 1 months" ta karisi maganar tana kallon Meerah, Murmushi tayi Tace "Eh." Gyaran Murya Haisam yayi kana yace "Amarya to ni ina katin nawa ko baza a gayyace Ni bane?" Yar karamar dariya tayi kana Tace "Ai sai dai kayi gayya ba dai a gayyace ka ba" Faruk yace "You're right kaifa babban abokin angone" " Isha Kuma babbar kawar Amarya ba, an bata Amma Ni ba'a bani ba" a Shagwab'ance Haisam yayi maganar kamar karamin yaro. Isha dariya ma ya bata ta Mike ta Mika Masa Tace "Gasu Nan Yaya" Meerah Tace "Bakwa gajiya da drama, to ai Ishan ba nata bane na bata ne don tayi gayyar ta itama" " To Nima a bani tawa" ai kuwa da sauri Meerah ta Sanya hannu a jaka ta miko Masa masu yawa, dariya ya shigayi had'e da fad'in "Ni Wallahi zolayar ki nake, Allah ya nuna Mana ranar" Suka amsa da Amin. Mardiya kuwa ji take kamar ta Burma musu huka, ta tsani taga Meerah na cikin farin ciki duk da ta kasance kawarta ce tun na yaranta, mardiya irin mutanen ne masu bakin hassada da Kuma kyashi. Meerah da Farukh suka nufi hanyan fita, sai Meerah ta juyo kamar tayi mantuwa, inda Mardiya take ta nufa,ta zaro kati d'aya ta Mika mata had'e da fad'in "Be my guest" kallon katin ta tsaya yi kamar Mai tunani kana tasa hannu ta Karb'a, ta mata Kirkirerren Murmushi da duk Wanda ya gani yasan a iya fuskane kawai, Meerah da Farukh sukayi ficewar su. Shiru d'akin yayi sai kara IV da Isha take ta kallo, Haisam yace "Ya dai Princess?" "Me ka gani?" "Naga sai kallon katin kike tayi, ko dai.....? " " Ko dai me?" " Baaaa......buuu" yace babun yana jaan sa, girgiza Kai Isha tayi ta mike had'e da ajiye IV d'in a Kan kujerar da ta tashi, yace "Ina zaki?" "Toilet, alwala zanyi" Yace "oh" ta shige toilet ba tare da ta ce masa komai ba, shiru sukayi kowa da abinda yake tunani ransa, Haisam tunani yake Akan yadda zai kula da Isha ya gyara dukkanin abun da ya 'bata ya sani da ace baiyi na'am da Ayrah ba da Yana Nan tare da ishan sa, idan bai zame mata farin cikin ta ba Tabbas Hakkin soyayyar ta (sunan book d'ina na gaba *HAKKIN SO*) bazai barshi, a Yanzu ya shirya zama da Isha ko ta halin Kaka ne,sabida yana matukar kaunarta, a ranar da ta gaya masa cewar tayi aure kwana yayi baiyi bacci wani irin wutar kishi ne take tashi a zuciyar sa, Amma daga bisani yace haka Allah yaso. Mardiya kuwa tunani take ta ina zata bullo wa al'amarin Auren Meerah sai ta gama da ita tukunna ta Dawo Kan Isha da Haisam, baza ta tab'a bari Isha tayi farin ciki ba in ta kuskura Tace zatayi aure. (Oh ni milhaat ina mamakiin karfin Hali irin na Mardiya, ita idan baza ta samu Abu ba to gara kowa ya rasa, muna da ire iren mardiya a cikin al'umar mu Wanda they can even do worst ya Allah ka Shiga tsakanin mugu da na gari, Amin). Bayan Isha ta fito daga toilet ta kalli Haisam da ke kallon sling na d'akin yayin da Mardiya kuwa tana kallon kofar d'akin, dukkanin su sunyi nisa a duniyar tunani, gyaran Muryar da Isha tayi ne yasa duk suka kalleta ta, a lokacin ta d'auko prayer mat ta shimfid'a, ta hau kai ta tada sallarta. Haisam ma sauka yayi daga Kan gadon ya nufi toilet din shima da niyar d'auro alwala, mardiya wayan Haisam ta hango a Kan gado a hankali ta Mike tasa hannu ta d'auka tayi sa'a ba password hakan ba karamin dad'in ya mata, sai da ta ji motsin Haisam na kokarin fitowa tayi saurin ajiye wayar a mazaunin sa Takoma ta zauna, Isha taji motsin ta Amma kasantuwar ta juya mata baya bata ga abinda take ba. 'dayan prayer mat d'in ya d'auka ya shimfid'a ya tada sallar. Su Umma kuwa suna shiga d'akin da Malam Hassan yake, Umma har kusa dashi taje tana Masa ya jiki ya kawar da kanta ya juya mata baya, Nabila har kasa ta duka ta gaida su Mummy da Umma suka amsa ba yabo ba fallasa, ganin Wanda suka Zo gaishe sa bai kula su ba, sukayi hanyar fita, Mami Tace "Dan Allah ku d'an zauna Mana,wurin shiru duk muna cikin kewa" Ba musu suka zauna suna hiran sama sama,Nabila kuwa tana ta chatting a wayar ta. Isha Bayan ta idar da sallan ta zauna tana azkar d'in da ta Saba,Bayan ta shafene ta d'auki sallayar ta nad'e kana ta ajiye shi a mazaunin sa,ta koma ta zauna. Haisam Bayan ya idar da sallar shima ya zauna Yana Addu'oin,ya dad'e Yana rokon Allah yafiya da Kuma biyan bukatunsa na alhairi,yaji shigowar su Abba da Daddy,ganin yana Addu'oin ne Suma suka d'aga hannu a tare suka shafa, fuskar su d'auke yake da Murmushi,gaishe su yayi suka amsa,Isha ma haka, Mardiya kuwa bata ma San da Shigowar su ba,Daddy ne ya mata magana Amma bata ji ba bare ma ta bashi amsa. Mikewa Isha tayi ta d'an tab'a ta,a d'an razane Tace "Na'am.. " Isha Tace "Su Daddy na miki magana Amma baki ji ba" Murya na rawa Tace "Sannun ku da zuwa ina wuni" A tare suka amsa da Lafiya,Abba yace "Mardiya ki rage yawan tunani gudun Kar ki cutar da kanki, kullu nafsin za'ikatul maut,ko wani rai sai ya d'an d'ani zafin mutuwa muma tamu muke jira,Kiyi ta musu addu'a,Kuma Kinga mutuwar shahada sukayi, insha Allah chan yafi musu Nan kinji" tunda ya fara magana kanta a kasa, tana matsar kwalla,su duk a tunanin su maganar da Abba yake ne yake sata kuka,ita Kuma kukan Nan na haushin Isha ne,ita duk ta d'auki tsanar duniya ta d'aura Mata,gani take kamar ita ta kashe Mata ahalin ta,cikin Muryar kuka Tace "Nagode Abba, Insha Allah zan kiyaye" "Yauwa Allah ya miki Albarka" ta amsa da Amin. Daddy ne ya tambaya ina su Mummy suke, Isha Ce ta shaida musu cewar sun je duba Jikin Malam Hassan, kwatancen d'akin suka sa aka musu suka fice a tare, suna fita Mardiya ta Mike tayi hanyar fita Isha Ce Tace "Ina Zaki?" A zuciyar ta Tace na tsani shisshigi wallahi, Amma a bayyane Tace "Wurin aiki, karfe shida ya Kamata na koma bakin aiki" "Amma this is just 4:03 ki d'an jira su mummy Mana tunda tare kuka Zo" "a a akwai abinda zanyi before lokacin yayi, idan su Umma sun shigo kice musu na wuce gida" ba ta jira amsar Ishan ba ta fice, tana fita Haisam yace "kema akwai nacin tsiya Wallahi" "Me Kuma nayi Yaya?" "Oho ba'a sani ba" Murmushi kawai tayi ta cigaba da dannan wayarta, Bayan su Abba sun Isa d'akin Malam hassan suka gaisa da mamy sannan Nabila ta gaida su, har suka gama tsayuwar su malam Hassan bai kula su ba. Gani suke kamar baya son kula sune Amma shi Kuma kunyace da Dana sani take daminsa , ji yake kamar ya tsaga kasa ya Shiga, shiysa yake pretending cewar baya magana ne. Sallama suka musu, Daddy ne yasa hannun a aljihun sa ya ajiye musu kud'i masu yawa yace a sayawa Mara Lafiya lemo. Mami ta masa godiya sosaiii suka fice. 'dakin Haisam suka nufa Umma na ganin Isha a zaune Haisam kuwa sai sharar baccin Sa yake, Umma Tace "Isha kina Nan haryanzu baki wuce bakin aiki ba?" "Eh Umma" "Why?" "Umma hutu na d'auka har sai na haihu, ina wahala sosai wallahi" "to in ko hakane kin daina Zama akan Haisam d'in Zaki koma gida sai kiyi ta hutawan" "A a Umma Dan Allah, to idan ta tafi wa zai kula Dani?" Baki a bud'e suke kallon sa Umma tace " ja'iri dama ba bacci kake ba?" " A a Yanzu na farka, Dan Allah Umma ku bar Isha anan" "Lallai Haisam, kai ko tausayin ta ma baka ji?" Kallon Isha yayi sai ya maida kallon sa ga Mummy alamun kisa baki Mana, Murmushi Mummy tayi tace "Maman Yara ayi Hakuri a barta ta kula da Yayan ta" Umma dariya mummy ta bata data Kira ta da Maman Yara , sunane da suke Kiran junan su ita da Mami, Abba yace "To tunda Tace zata iya a barta Mana, ko ya kace Yaya?" Yana maganar Yana kallon Daddy, Daddy yace "eh a barta kawai" Umma Tace "Kuna biyewa yaran Nan Wallahi, Shikenan nayi shiru tunda kunfi karfina" duk sukayi dariya. Daddy ne ya fara magana, "Son Bayan kwanciyar da kayi ajiyar ka da ke wurina nayi amafani dasu wurin gina maka asibiti, sannan na zuba maka ma'aikata aciki Ana gudanar da aiki yanda ya Kamata, a gaskiya Haisam ka samu aboki na Kwarai, da taimakon Farukh ne komai ya tafi dai dai tun Bayan wannan lokacin shi yake kula da komai, a halin Yanzu asibitin yana d'aya daga cikin manyan asibitocin da ake ji dasu a garin gombe, sannan na gina maka gida, na zuba maka dukkanin abubuwa na more Rayuwa" Mikewa Haisam yayi ya rungumi daddy yana kuka kamar wani karamin yaro Yana ta Nagode Allah ya saka, daddy Murmushi kawai yake Yana d'an bubbuga Masa baya alamun rarrashi, Umma ma godiya ta Shiga Masa, tana Kara godewa Allah da Ma'isha sabida itace silar komai, shiysa take matukar son Isha, fiye da ka yadda take son Haisam d'in, Abba yace "Kan mu shigo, mun biya gun Dr Ali yace anjima da Yamma za'a sallame ka" "Alhamdulillah dama Wallahi na gaji da asibitin Nan, Yamma tayi ai Abba" Duk dariya sukayi. Suna cikin maganar ne sai ga shigowar Dr Ali, Bayan sa biye yake da wata nurse hannun ta Kuma rike yake da patient file, Bayan sun gaisa ya Shiga Duba Haisam, Bayan ya gama ya rubuta Masa magunguna da za'a saya ya mikawa Ma'isha had'e da fad'in "Pharmacists a samawa patient magani" Karb'a tayi tana dariya tace "Ai na samu hutu" " Yet ke staff d'inmu ce" Charafff Haisam yace "She was dai, don Canza mata wurin aiki zanyi" girgiza Kai Isha tayi Dr Ali yace " Fatan alhairi" sai ya fice nurse din tabi Bayan sa. Tattara kayan su Umma da Mummy suka farayi Isha ma bata zauna ba da ita ake had'awa su Daddy da Abba Kuma suna Kai kayan mota, farin cikin da Umma take ciki bazai misaltu ba yau Bayan shekaru 4 d'anta zai Koma gida, har kuka Saida tayi mummy na ta aikin rarrashin ta. Bayan sun gama kai tsaye gidan Umma suka nufa Haisam zai zauna a gunta Kan ya gama murmurewa, Isha dama already tana gidan Umma, Ni ko nace Anya zaman Isha, Haisam ga Kuma mardiya zaiyu kuwa a gida d'aya? Muje zuwa. Mardiya Bayan ta koma gida ta shirya cikin doguwar rigar atamfamfar ta, Atamfa less ne, brown an Masa Flowers da kallan ja da yellow sannan less d'in Jikin farine hakan yasa tayi Rolling da d'an figegen gyale fari hannun ta Kuma rike yake da labcoat d'ayan hannun ta Kuma fashion bag d'intane shima fari Sannan takalmin ta ma fari, a gogon hannun ta take Kallo sai Kuma tayi Tsaki , a bayyane Tace "wannan Wace irin Rayuwa ce, a gaskiya zan d'auko mota na tun d'azu nake ta jiran abun Hawa Amma babu." Wata dankararriyar mota ce tazo ta faka a gaban ta, ta kawar da Kai Jin an Kira sunan ta Yasa ta kalli Wanda taji ya Kira sunanta Tace "Laaaa Adnan" Murmushi yayi yace "Mardiya manyan gari ana ganin ku dama?" Itama Murmushin tayi Tace "Gashi kuwa" "Hakane, ina zaki ne haka?" "Gun aiki ina ta jiran napep Amma ban samu ba" "Hoop In Mana mu rage Miki hanya" Ba musu ta bud'e gidan baya sabida daf take da yin latti,jaan motar yayi yace Mata "Wani asibiti kike aiki?" "Specialist hospital" "Okay " Babu Wanda yace komai sai chan yace "Wannan abokina ne sunan sa Abdallah" "Barka" Shima ya amsa da yauwa barka,nan suka fara hirar yaushe gamo,suna Isa specialist hospital har ta bud'e marfin motar Tace "Baka tambayeni mutuniyar ka ba?" Sai da yaji kirjin sa ya fara duka uku² cikin rawar murya yace " Wa Kenan?" "Ayrah Mana" "Ummmm...... Ya take ne? Tayi aure ko?" " Wai kana nufin baka ji abinda ya same ta?" Gyara zama yayi ya waigo Yana kallon ta kana yace " A'a me ya same ta?" _______________________ Please comment And share Milhaat ce Yar Terawa [8/17, 1:06 PM] Miilhaat Writer✍🏻: 🍃 *DANGIN UBANA*🍃 Story & Written By Milhart Na zo muku da littafi Mai ban tausayi,cike da abun al'ajabi,wannan salon na daban ne. *🌍MANAZARTA* *WRITERS ASSOCIATION📚🖊* *M. W. A* *Wannan labarin kirkirarren labarine ban yarda a chanza min labari ba Wanda ya chanza bamu yafe ba.* Ina alfahari da rubutu,sabida alkalami yafi takobi🗡️🗡️🗡️ *BISMILLAHIR RAHAMANIN RAHIM* Page 73&74 _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._ ```Continuation.......``` Ba Adnan Kad'ai ba hatta Abdallah sai da yaji zufa na sassafo Masa, Adnan kuwa wani abu ya ji ya bi ta makoshin sa ganin irin kallon tuhuma da take masa, Dakyar ya aro jarumta yace "Umm umm bani da labarin komai" Ajiyar zuciya tayi kana Tace "Ta 'bata ba a San inda take ba" Gyara zama yayi kamar Bai San komai ba yace "Whatttt!!!! Da d'an karfi kana yace "when, how? Yaushe hakan ta faru,taya ma za'a ce ta 'bata sai kace Yar tsana?" Ya maida kallon sa ga Abdallah kana yace "kana Jin wani zance ko,wai ta 'bata kamar babyn roba?" "Wallahi da mamaki Kam" "Umhn to maganar da ake ma ta kai 4 months ba a San inda take ba" Adnan yace "Ashhha abu baiyi Dad'i ba, Allah ya bayyana ta" Duk suka amsa da Amin. Ficewa tayi daga motar Bayan ta bawa Adnan Number wayar ta, Motar ya tada suka Kama hanya, Abdallah ne yace "Abokina I think is high time fa da zaka bar yarinyar Nan haka ta koma gida, ina gudun abinda zai biyo baya gaskiya" "I wish zan iya hakan, I wish zan iya cire ta a Raina I wish lokacin da ta nemi mu na shirya na amince da duk ba a Zo Nan ba" " Bar maganar wish wish d'in Nan ka bar yarinyar Nan haka ta koma gida" "Bazan iya" Yana maganar ya maida hankalin sa kan tukin da yake. "Ka fahimce ni Adnan, wallahi idan asirin ka ya tonu abun bazai Mana kyau ba sabida duk abinda ya shafe ka Nima ya shafe Ni" " Nima ka fahimce ni, wallahi Allah ina son yarinyar Nan har cikin Raina" "Ita Kuma Tace Bata son ka just let her be" "Kana ganin idan na barta ta tafi zata rufa min asiri ne?" Shiru Abdallah yayi na Yan sakanni kana yace "No, I don't think so" "Good that's my point, ina so na jefi tsuntsu biyu da dutse d'ayane you understand what I mean?" " Yeah I do, Allah ya shige Mana gaba" "Ameen" " But fa ina son kawartar Nan Wallahi" Kallon bana son rainin hankali Adnan ya Masa kana yace "To wani sabon iskancin naka xaka Fara Kenan" "A a wallahi tallahi sonta nake Kuma da aure" "Hmm lallai fa" " Kana ganin zata amince kuwa?" "Can't tell, but try your luck" Bai Kuma ce masa komai ba har suka Isa inda zasu. Mardiya ce zaune a office d'inta ta Lula duniyar tunani, ajiyar zuciya tayi kana a bayyane Tace "Meyasa nake ji kamar akwai abinda Adnan yake 'boyewa? Anya Adnan baida sa hannu acikin 'batan Ayrah kuwa? Mtswww ko ma mene ne zan bin cika" ta d'auki wayarta ta Fara latsawa. Bayan ta Dawo daga gun aiki ta tarar da su Umma, abba, Daddy, Isha, Mummy da Twins Sannan da Auta suna dinning suna cin abinci suna Hira, manta jiki tayi tana kallon su, ganin yanda suke farin ciki basu da wata damuwa, tsanar Isha ne ya sake ninkuwa a zuciyar ta. "You don't deserve to be happy, yayana ya rasa ransa Amma ko kad'an abun bai dame ki ba, hankalin ki kwance dake da ahalin ki, to wallahi Ni zan Zama sanadin rushewar farin cikin Nan tunda Ayrah ta kasa, Allah sarki Mummy da Daddy, Ina kewar ku sosai Yaya kasance kana son farin ciki Isha sama da komai a duniya Amma Bata damu da Kai" magana take a zuciyar ta tana matsar kwalla, batayi aune ba sai jin murya Umma tayi Tace " 'yata kin Dawo?" Had'e da dafe kafad'ar ta. Umma kallon fuskar ta tayi, cike da tausayi tasa hannu ta share mata Tace "Ki daina Kuka Mardiya, nasan is not easy ki d'auke mu tamkar family d'inki kinji, ki cigaba da musu addu'a kinji" Girgiza Kai tayi cikin Muryar kuka Tace "Nagode Umma" ta fashe da wani irin kuka, Umma rungume ta tayi tana rarrashin ta, Suma kallon su suke suna jin tausayin ta Amma Banda Haisam ya rasa dalilin da yasa ya ji bai yarda da yarinyar Nan ba, cigaba da cin abincin sa yayi hankali kwance, Roku hannun ta Umma tayi har dining table kaita ta jaa mata kujera ta zauna , sannan ta karb'i jakanta ta ajiye mata daga gefe, plate ta d'auka ta sa mata abinci sannan Tace "kici abinci" ta shafa kanta kana ta koma mazaunin ta, shiru wurin yayi baka jin komai sai Karan cokula, abincin take ci Amma Sam bata jin dad'in da, taci Kad'an kana ta mike had'e da fad'in "Nagode, bari na shiga ciki" Mummy Tace "Ki samu kiyi wanka sannan ki Dawo ki same mu a parlor ki daina zama ke Kad'ai" cike da kulawa take maganar, Murmushi Mardiya tayi had'e da fad'in "to mummy." Bayan ta Shiga d'akin ta ruwa ta watsa duk jikinta a Sanyaye , Bayan ta gama ne ta zauna a bakin mirror tana shafa mai, karar wayar ta taji tana ringing, ta duba don ganin wane ne, number ta gani ba suna, tsaki tayi bata d'aga ba an Kira har a karo na uku kana ta d'aga ta Kara a kunnen ta ba tare da tace komai ba daga 'dayan 'bangaren akace "Assalamualaikum" Murya kasa kasa ta and da "wassalam" " Barka da war haka Hajiya Mardiya" Jin an Kira sunanta ta d'an d'aga girar ta kamar yana kallon ta Tace "Yauwa barka dai" tana son gane ko wane ne. "Suna na Abdallah, abokin Adnan" Yar karamar Murmushi tayi had'e da fad'in "Oh Abdallah barka kana lafiya, ya gajiyan ku na d'azu Nagode fa" Shima Murmushin yayi yace "Bakomai, da fatan kina Lafiya?" "Alhamdulillah" "Ya aikin? An taso ko?" "Eh" "Allah ya taimaka dama na Kira ne naji lafiyar ki" "Allah sarki Nagode sosaiii" "Goodnight" Ta amsa da Night. "Ayrah Wai meyasa kike da shegen taurin Kaine?" A tsawce yake maganar kallon sa tayi sama da kasa kana ta kawar da kanta, ajiyar zuciya yayi ya Saira kansa ya lura idan ya mata da zafi bazai tab'a samun kanta ba. Durkusawa yayi a gaban ta ya hard'e Hannayen sa alamun roko kana yace "Ayrah Dan Allah Dan Annabi give me chance na tabbatar miki da cewar ina son ki, so na Haki ka" Kallon sa tayi kana ta murmusa Tace "Naji zan amince da hakan Amma ina da sharad'i" "Ina sauraron ki just name it and Ni zan yi miki shi" Mardiya na Gama shafa mai simple duguwar Riga ta Sanya a Jikin ta kana ta fito parlor kamar yadda mummy ta umurce ta, hirar su suke hankali kwance, sunayi suna dariya. Wuri ta samu ta zauna had'e da fad'in "Mummy na d'auka Kun koma gida fa" Murmusawa Mummy tayi kana Tace "A a yau muna nan, Umman ku ta kafa ta tsare akan dole mu kwana" "har naji dadi zamu Sha Hira kam" Isha ta ce "Sai kace dama tana hirar" " Ina yi man, gashi nazo ayi Dani" "toh you're welcome" Haisam zaman ta a gun duk yasa yaji ransa ya lalace mikewa yayi had'e da Mika yace "Nikam zan kwanta, bacci nake ji, sai da safe" Duk suka amsa da Saida safe, Kallon Isha ya tsaya yi ita ma kallon sa take gira ta d'aga Masa alamun ya dai? Sai da ya tabbatar hankalin su Mummy baya kansu kana murya kasa kasa yace "I Love You" rufe fuskar ta tayi da tafin hannun ta tana Murmushi, Mardiya kuwa duk abinda suke Akan idanun ta, tsaki tayi Wanda yasa Haisam yayi saurin kallon ta, wani irin Kallo ya mata Wanda yasa tayi saurin kawar da kanta, tana jin kirjin ta na duka uku², Isha ta lura da sauyawan fuskan nasa, cikin sanyin Murya Tace "Ya Haisam what happened?" Murmushi yayi mata Kana yace " Nothing ki hau online" Yana Kai Nan ya haura sama bai tsaya jin me zata ce ba, bin Bayan sa tayi da Kallo, kana ta maida kallon ta ga Mardiya wacce ta manta kanta tana kallon Haisam d'in, Isha da d'an karfi Tace "Duk maita Mutum wannan halittan ya fi karfin sa" sai kuma tayi kamar ba ita tayi ba, Abba yaji abinda Tace Sarai Amma bai gane da wa take ba, kawai ya batsar. Mardiya kuwa hararar Isha tayi had'e da mikewa Bata ce musu komai , Babu ma Wanda ya San ta bar gun Isha kuwa Tace a ranta "sai nayi maganin Yar iska dani kike zancen" Datan ta ta bud'e suka cigaba da chat d'insu da Yayan ta, Yana nuna Mata shi sam Baya son zaman Mardiya a gidan, Isha da itama ranta a 'bace yake da Mardiyan sai ta danne 'bacin ran natan tana ta bashi hakuri. "Ayrah kinyi shiru? Fad'a min mene ne sharad'in naki?" "Na'amince zan aure ka" Wani uban tsalle Adnan yayi yana Fad'in "Yessssssss!!! Yaja yes d'in sabida tsantsar farinciki, ita kanta Ayrah abinda Adnan d'in yayi ya bata dariya, sai taji ya burge ta, matse dariyar tayi Tace "Not so soon, Kar kayi farin ciki tsaya kaji sharad'ina tukunna" Zama yayi a gefen ta Yana kallon ta yace "Uhmnn, ina jinki" "Zaka barni na koma gida daga nan sai muyi auren mu" Murmushin gefen baki yayi kana ya mike yace "Zaki koma gida Amma Nima kiji nawa sharad'in" Tana kallon sa don Jin me zai ce. _______________ Toh fans me kuke ganin Adnan me zai bukata daga gare ta? Ina jiran amsoshin ku. Please comment and share fisabilillah. Milhaat Ce Yar Terawa 75&76 '''Continuation.........''' sai da ya Kai bakin kofa yasa hannu ya bud'e kofan kana ya waigo ya kalle ta, Murmushi yayi yace "Zaki Koma gida a matsayin Mata ta, idan kin amince ki same ni a d'akina, and kir ki wani damu da batun waliyi, Zanyi handling na komai" ya fice kana ya rufe Mata kofar , duk da ya fita Amma baki a bud'e take kallon kofan, tana mamakin karfin Hali irin nasa. Zama yayi yana jiran ta Amma shiru har bacci yayi awun gaba dashi, alarm d'insa ne ya buga na karfe 5 ,jaan wayar yayi ya kashe kana ya Shiga ban d'aki ya d'auro alwala ya tada sallah , Bayan ya idarne ya Koma baccin Sa. Ayrah kuwa kasa bacci tayi tana ta kuncewa da tsakawa ta rasa abinda zatayi, sai da taga wuri ya fara haske ta shige ban daki tayi alwala, Bayan ta idar da sallah, zaune take Akan prayer mat d'in haryanzu dai maganar Adnan ke Mata yawo a kwakwalwar ta, Bayan ta gama tsakawa da warware a bayyane Tace "Zan amince na aure ka, Amma da zaran na fita anan dole ne ka sake ki, in Kuma kaki kotuce zata rabani da Kai" Kofar d'akin sa ta nufa, ta kwankwasa kofar had'e da kusa Kai ciki, duk zaman ta a gidan bata tab'a zuwa d'akinsa ba, daga d'akin da take sai kitchen, baccin Sa taga yana yi, ta koma da niyar fita Muryar da taji yace "Ina Zaki?" Cikin Muryar bacci ya mata tambayar Nan. "Na d'auka bacci kake" "Umm yanzu na farka Shigo Mana" Kujeran dake gaban Mirror ta ja ta zauna a kusa dashi kana Tace "Nazo muyi magana ne" Zama yayi yana d'an goge idanun sa da yatsunsa kana yace "Ina jinki" Shiru tayi kanta a kasa kana Tace "Na'amince zan aure ka, Amma Dan Allah Kar ka cutar Dani" hawaye fal a idanun ta, hannu yasa ya share mata kana yace "Insha Allah, I will never guv you the chance to regret, Is a promise" Murmushi tayi, shima ya maida mata mikewa yayi da d'an saurin sa ya shige ban d'aki karar ruwan da taji ne hakan yasa ta gane yana wanka ne, Zama tayi tana jiran sa, tana jin ya fito ta sunkuyar da kanta, ta cigaba da wasa bda yatsun ta, abun ma dariya ya bashi, me bata sani a Jikin sa ba? Sai da ya gama Shirin sa tsaf yace "Muje muyi breakfast ko?" Ta amsa da toh, had'e da mikewa tayi gaba yabi bayanta, yau tare sukayi girki, sunayi suna Hira abin birgewa kamar wasu amarya da ango, ko da yake sun kusa su fad'a lambun ma'aurata. Bayan sun gama karyawa ne, ya fita da niyar tsara komai na yanda za'a d'aure auren sa da Ayrah, hakan kuwa akayi bai dawo ba har sai da ya tabbatar an sa ka ranar d'auren su Nan da sati d'aya hakan kuwa akayi,dama ba wuya a wurin Allah muddin an sa Rana, a yau aka d'aura auren Adnan da Ayrah Akan sadaki dubu d'ari. (Oh Ni Milhat jikar Mutum hud'u, Adnan ya d'aura auren da masoyiyar sa ba tare da iyayen sa ko iyayen ta sun sani ba, yayi hayan iyaye ba tare da Wanda ya d'aure ya sani ba, Ko ya zasu wanye? Mu cigaba da zuwa). Adnan ya sa an yi Masa video don ya tabbatar wa da Ayrah cewar an d'aura musu aure ta Zama mallakin sa, Allah sarki Ayrah a duk sanda aka d'aura wa yarinya aure tana samun kula ta musamman a gun dangin ta, za a rako ta har d'akin ta ana nuna mata so da Kauna sannan su rabu cikin kuka da kewar juna, Amma kashhh ita ta samu aka sin hakan, video d'in da yayi shine shaidar auren su, tayi kuka sosai Adnan tun yana rarrashin ta har ya daina ya fita ya bar mata d'akin ma gaba ki d'aya. Tun daga wannan ranan Ayrah kullum cikin kuka take,shi Kuma Adnan baya gajiya da bata hakuri a haka har ta sake Jiki dashi ta bashi dama Yana nuna mata irin soyayyar da yake mata,yana Kuma saka ta tana Kara son shi,duk da cewar tana kokarin taga ta 'boye,Amma masu iya magana sunce shi so baya 'buya. Haisam ta samu sauki sosai har ya Fara fita gun aiki,farin ciki da kwanciyar hankali Kuma sai dai ace Alhamdulillah,Isha na samun kula sosai musamman ma gun Umma da ta hana ta fita ko ina,idan ta fito to tare da Haisam suka fita Nan ma idan suka dad'e Umma tayi ta Kira Kenan Kira Kan Kira. Shirye shiryen Biki Meerah ake yau saura kwanaki Uku, events Kam sun Sha shi,sunyi friends day,bridal shower da dai sauran isha ba a barta a baya ba duk da ba wani Abu take ba sai dai ta zauna tana kallon su. *Ranar Biki* Farukh ne zaune da Haisam da sauran abokan sa suna shiri zuwa gun d'aurin aure sai tsokanan sa suke musamman ma haisam da dama sarkin tsokana ne,wayar Farukh ce tayi kara har da bazai d'auka ba sai Kuma ya zaro wayar a chaji ,sakon da ya shigo wayar sane yasa shi tsuman tsaye,Nan da Nan hawaye suka cika idanun sa,Kallo d'aya Haisam ya Masa ya Gane ba lafiya,hakan yasa ya mike ya nufi inda yake kafad'ar da ya dafa had'e da fad'in "Ya dai ango Lafiya kuwa ga na ganka Haka?" Farukh Mika Masa wayan yayi ba tare da ya Ce Masa kala ba, Haisam da d'an saurin sa ya sa hannu ya karb'a. Yana ganin abinda faruk d'in ya kalla zaro ido yayi dq d'an karfi yace "whaaaaatttt!!!! Hakan yasa dukkanin abokan su hankalin su yayi ta Dawo kansu,d'akin shiru yayi baka jin motsin komai sai Karan AC da kumma TV dake aiki. _________________ Please comment and share Milhat ce Yar Terawa 77&78 Continuation.......'''  'daya daga cikin abokan sune yace "Ya dai Guys? Lafiya kuwa?" Murmushi Haisam yayi had'e da fad'in "Good" beyi aune ba sai jin karar an rufo kofa, farukh ne ya fita Yana mugun sauru.     Haisam ne yace "Ku cigaba da shiri bari muzo" Bin bayansa sa yayi, har ya bud'e marfin motar yaji Muryar Haisam "Farukh ina zaka?"     Cike da tashin hankali Farukh yace "zanje ne na dakatar da auren Nan, I can't marry Meerah, Ashe dama haka Meerah take? Duk irin soyayyar da nake mata Amma ace da abinda zata saka min Kenan" ya karasa maganar Yana kuka, Haisam kwace key d'in motar yayi ya zaga ya Shiga gun zaman driver, farukh kuwa kallon sa ya tsaya yi ya kasa motsi, Haisam lekowa yayi yace "bamu da Lokaci Shiga muje"     "Ina zamu?" "Idan munje zaka gani" Tada motar yayi Mai gadi ya wangale musu gate suka fice daga gidan, gudu sosai haisam keyi sai da ya Isa inda yake son zuwa kana ya tsagaita gudun, a bakin gate d'in ya tsaya ba tare da ya Shiga ciki ba, wayar sa ya d'auka ya Shiga yayi dialling number, duka biyu ta d'aga da sallama, kai tsaye yace "Ki fito ki same ni ina waje, and please ke Kad'ai zaki Zo." Ya katse wayar ba tare da yaji amsar da zata bashi ba.     Farukh ji yayi kansa Yana mugun sarawa, ji yayi duniyar tana juya Masa, ji yake kamar ya fasa auren Amma wani 'bangare na zuciyar sa tana matukar kaunar Meerah.    Isha ce naga ta fito, ta nufo su da d'an kuttun cikin ta, Bayan motar Haisam ya bud'e Mata, ta Shiga ta zauna kallon su take tana Jin gaban ta mugun Fad'uwa sabida yanayin da ta ga Farukh a ciki, murya na rawa Tace "Ya Haisam Lafiya?"     Wayar Farukh d'in dake hannun sa ya Mika Mata, tana kallon video ta rike baki tana ambaton sunan Allah.                "Inna lillahi, wannan videon a ina kuka same shi?" Da sauri Farukh ya waigo ya kalle ta yace "Kin San da videon dama?" Kai a kasa ta amsa da Eh.       Farukh baki a bud'e yake kallon ta wasu sabbin hawayene suke gangarowa daga idanun sa yace "Kin sani fa Kika ce Isha? Amma kuma baki Sanar dani ba? Na d'auka ina matsayin Yayan kine kamar yadda kike Kirana Taya za a ce kin San halin kawar ki Amma ki bari na aure ta, Bayan kin San ita d'in ba alhairi ce a gareni ba"     Isha cikin kuka tace "Tabbas Meerah tayi kuskure da ta 'boye maka, duk da nasan tayi hakan ne gudun Kar ta rasa ka kamar yadda ta rasa Bashir"       "Ban gane ta rasani ba, me kike nufi da hakan?" "Wallahi ko kaffara bazanyi ba nasan wannan aikin Mardiya ne, ita kadaice zatayi hakan, Mardiya da kake gani ya Farukh, babu abinda baza ta iya ba don ganin ta 'bata Meerah, na rasa dalili Haka kawai ta d'auki Karan tsana ta d'aura mata, 8 years ago there where friends, Amma........ Nan ta bashi labarin yanda akayi mata fyad'e da yanda  suka mata video da Kuma yanda suka mata barazana sannan suka rabata da mijin da zata aura a satin da Za'ayi bikin su.     Ajiyar zuciya tayi Bayan ta gama bashi labarin, Jikin sa ne yayi sanyi , kallon Haisam yayi yace "Dama kaima kasan da maganar?" "Eh not long ago, bayan na farfad'o Isha take Sanar dani, nifa ko shiyasa duk na tsani yarinyar nan wallahi, bana son ta kwata kwata, Dole ma ta bar gidan Nan yau d'in Nan"     "A a Ya Haisam Kar kayi haka Dan Allah su Umma baza suji Dad'i ba" "Amma Princess Kinga dai abinda tayi ko? Kika San mene ne Shirin ta na gaba?"     " Ban sani ba , Amma inshallah ta Allah ba tata ba" Shiru yayi baice mata komai ba.     "Ya Farukh" ta Kira sunan sa cikin sanyin Murya. Had'a Hannayen ta tayi wuri guda alamun roko Tace "Dan Allah, Dan Annabi, Kar kace zaka fasa auren Meerah wallahi tallahi ba laifinta bane ba, Bata San komai akai ba, wallahi duk sharrin Mardiya da Ayrah, idan kace ka fasa auren ta zuciyar ta zata karye Dan Allah" ta karasa maganar tana kuka sosai kamar ranta zai fita,haisam hankalin sa yayi mugun tashi,don shi idan akwai abinda ya tsana shine yaji ko ya gani Isha na cikin damuwa bare ma ace tana kuka.    Murmushi gefen baki Farukh yayi yace "Ki daina kuka Isha, bazan fasa auren ta ba, hasali ma labarin da Kika bani ya sa naji ina bukatar na rayu da ita zan goge Mata wannan bakin tabon da aka Mata, Kuma zan miki wani alkawari sai Nasa an d'aurte wallahi wallahi bazan tab'a kyale ta ba" Murmushi Haisam yayi yaji dad'in maganar abokin Nasa,su isja sarkin kuka Kuma Aka cigaba da kuku.     "Ya Salam Princess,kukan Nan fa na mene ne,inace ya fad'a miki baza a fasa auren ba,meyasa Kuma kike kuka,kin San fa bana son kukan ki"     Cikin Muryar kuka tace "Ya Haisam, Dole nayi kuka ina tausayawa rayuwa tane dana Meerah,tun tasowar mu,bamu samun abinda muke so,idan mun gama da wannan matsalar sai wata ta 'bullo" ta karasa maganar tana kuka Mai sauti, Haisam rarrashin ta ya Shiga yi yace "Ma'isha"      Cike da mamaki ta d'ago tana kallon sa,don a iya zaman su dashi bata tab'a ji ya Kira sunan ta ba,idan ma ya Kira to ta manta, Murmushi yayi kana yace "Ni Haisam na miki alkawari zan share duk wata kunci da damuwar da kike ciki,kawai dai wannan d'an nawa na cikin ki ne yake katse min hanzari" ya karasa maganar kamar zaiyi kuka Isha kuwa hakan dariya ya Bata,tana kuka had'e da dariya.     Farukh yace "Wa yace maka namiji ne?" "A jikina nake Jin hakan" "Mtsww dallah malama ka tada mota mu tafi ya fa rana na ce, nasan suna chan suna jiran mu"    Dariya Haisam yayi ya kalli Isha kana yace "Princess ki Shiga ciki ko,zan Zo na d'auke ki anjima,kin San Umma Tace Kar na bari ki kai la'asar so ki kasance cikin shiri" Ta amsa da toh, had'e da bud'e marfin motar, Farukh ne yayi saurin fad'in "Dan Allah ki kwantar da hankalin ki auren da Meerah babu fashi sai dai idan mutuwa nayi, Sannan please bana so ki fad'awa Meerah ko ki nuna Mata cewar an turo min wani abu,ita Kuma wannan Kanwar zanyi maganin ta"       Dariya sukayi dukkan su, Haisam yace "me Kuma kanwa?" "Kanwa mana,kanwa uwar gami had'a su kasa rabasu"     Dariya suka Kuma yi cikin dariya Haisam yace "Princess jeki suturun sa ba karewa zaiyi ba" ficewa tayi ta shige,ai kuwa Isha na Shiga, Meerah na ganin ta ta fahimci akwai matsala,Jan ta tayi suka keb'e tana tambayar ta dalilin da yasa ta ganta a haka,Isha Tace Mata bakomai,ganin Meerah ta nace yasa Tace Mata marar ta ke mata ciwo,ta Mata sannu sannan suka Koma cikin kawayen nasu.     Dubbanin Mutane ne suka shaida Auren Dr Farukh Sani Usman da Ameerah Murtala, cikin mutanen kuwa harda Daddy da Abba.      Mardiya ne kwance akan gado,tana taunar chewn gum wata iriyar dariya tayi,Zama tayi Tace "waima taya Za'ayi kiyi aure  Ni banyi ba? Dr Farukh? Hmm kyakkyawan saurayi haka bai dace dake ba Sam dani  ya Dace,na tabbata duk inda yake yanzu yaga sakona" ta Kuma fashewa da dariya.    Muryar Umma taji tana Kiran sunan ta kanta amsa har ta Shigo kallon ta Umma tayi Tace "Lafiya ke da waye?" Murya na rawa Tace "Ummmmmm....waya nake"    "Ok ,ya naga baki shirya ba baza ki bikin bane?" " Wani biki Umma,Bayan an fasa bikin?"     " Wani bikin ne aka fasa? Bayan tun karfe 11 aka d'aura aure" Zumbur ta Mike Tace " No no inaa bazaiyu ba, wahala na ya tashi a banza Kennan?"   Umma Tace "Ke Lafiyan ki kuwa?" Shan jinin jikinta tayi ta zauna ta ce " kaina ke ciwo Umma,sai kun Dawo" wani irin Kallo Umma ta mata har ita mardiyan ta tsargu,ta fice abinta,tare da mummy zasuje tana jiran ta a parlor tana Isa parlor sukayi tafiyar su. Ciza leb'en ta tayie kana Tace "wato Farukh ya auri Meerah? Ko dai baiga sakon bane? Anyways idan ita Meerah ta tsira, Ma'isha baza ta tsira ba muje zuwa, wallahi sai na ga Bayan ku,I'll disgrace you to extend that you'll be ashamed of yourselves." Ta kwanta ta cigaba da danna wayanta tana jinra duk ba dad'i.     Umma da Mummy  dasu akayi bud'an Kai da kamu,a ranar amarya ta tare a gidan angonta.Allah ya bada zaman lafiya amiin.           *After 4 months* Malam Hassan duk wasu raunuka na jikinsa sun warke Amma sabida tashin hankali da ya Shiga ya had'u da shanyewan 'barin Jiki, duk wani kud'i da ake kashewa Faisal ne yake bada su, yayin da Mamy har ta cire Rai da ganin Ayrah, kullum sai tayi kuka.      "Mamy nifa na gaji da 'bata kud'i na Akan wannan mutumin" Faisal ke wannan maganar Kama hab'a mamy cike da mamaki tace "Kaci gidan ku" had'e da masa dakuwa.      "Yanzu  Kai Faisal rashin hankalin naka ya Kai haka? Ubankane fa duk lalacin sa, ni na d'auka kayi Dana sanin abinda ka aikata Ashe ba haka ba, ka godewa Allah ma da ya kowa abun da sauki da yanzu Ana irga kwanakin da ka mutu, daba don Allah yasa yaran basu da gata ba wallahi na tabbata da yanzu baka raye"      "Mamy dama tun chan kwanakin mutuwa ta basu yi bane, Kuma wallahi ko kad'an bana Dana sanin abinda na aikata, Ban so hakan ba, naso da shi d'in ne ya mutu ko hankali ya zai kwanta"     Tasss Tass Mamy ta shafa Masa maruka har sau biyu, rike kuncin sa yayi Yana matsar kwalla.    Mikewa Mamy tayi Tace "Ka fice min daga gani Kar Kuma na Kuma ganin ka anan, Kan kazo ka karasa min shi"        Faisal kwallon mahaifin sa yayi da yake kallon su, cike da hawaye a idanun sa, Murmushin Takaici Faisal yayi kana yace "Mamy mari na kikayi? Akan mutumin da bai damu dake ba, mutumin da bazai San mutuncin ki ba? Shin kin San irin bakin cikin da muke ciki da ni da Yan uwana Akan irin abubuwan da yake aikata Amma ke sabida.......... " Shiru yayi ya kasa karasa maganar kallon mahaifin nasa ya Kuma yi ya fice yana matsar kwalla.       "Zainabu!!! A hankali cikin sanyin Murya taji ya Kira sunan ta, da sauri har kafarta na hard'ewa ta nufi inda yake tana tambayar sa "Malam wani abun kake buka ne?"     Kai ya girgiza mata alamun a'a cikin Muryar sa Wanda baya fita mai kyau yace "Da baki mare shi ba sabida duk abinda yake fad'a gaskiyane, na kasa Mai son zuciya da son Kai, ban damu da kowa ba, ban damu da komai ba in dai zan samu abin da nake so...... " Ajiyar zuciya yayi Mai d'an tsawo kana yace "Na cutar dake da ke da 'ya'yan mu, ban kasance miji na gari ba sannan ni ba Uba na gari bane da ko wani yaro yake fatan samu, ki yafe min Abu, Dan Allah"      Cikin muryar kuka Tace "Na yafe maka mallam, dama ban rike ka a Raina ba irin wannan ranar na ke jira Wanda zaka gane koren ka kuma kayi Dana sani , Alhamdulillah Allah nagode maka" ta karasa maganar tana kallon sling na d'akin tana matsar kwalla.          Faisal da dawowar sa Kenan ya manta wayar sa , yaji dukkanin maganar da suke Yar karama tsaki yayi a zuciyar sa yace "Yanzun ma tuban muzuru ne don dama halin sane" kofar ya bud'e ba tare da yayi sallama ba ya sa kai ya shige,Mamy da Malam Hassan duk suka kalle shi,kawar da kansa yayi kamar baiga kowa a gun ba, ya nufi inda wayarsa take ya sa hannu ya d'auka sannan ya fice, girgiza Kai many tayi a zuciyar ta Tace "Allah ka shirya min yaran Nan" kwasam Ayrah ta Fad'o mata a rai mikewa tayi ta fice ta samu d'an corridor ta zauna tana kuka mai cin Rai, tana Jin zuciyar tana mata zafi,tana addu'ar Allah ya bayyana mata Yar ta,ko da kuwa gawar tane,sai da tayi mai isarta kana ta koma ciki. Soyyaya ce Mai karfi ta Shiga tsakanin Abdallah da Mardiya musamman ma Mardiya da take ji baza ta iya Rayuwa babu shi ba, don ta shaku dashi.     Adnan na bawa Ayrah duk wata kulawar da miji ke bawa matar sa, tasan tana son Adnan Amma da zaran ta bar gidan dole ne ma ya sake ta taya ma Za'ayi ka 'boye Mutum har na tsawon watanni 8?     Mardiya da Abdallah na hango  a wani d'an madaidaicin shopping complex , Hirar su suke suna d'aukan abinda suke so kana ganin su kasan masoyan Nan suna suna cikin farin ciki, Bayan sun gama suka nufi inda zasu biya kudi, Mika mata wayan sa yayi Sabida ya samu damar ciro wallet d'insa.       Tana rike da wayar a hannun ta yayin da take Danna wayarta da d'ayan hannun ganin ana ta Kiran sa Tace "Baby ana ta Kiran ka fa" a Shagwab'ance tayi maganar ba tare da ya kalle ta ba yace "wane ne?"    "Adnan" "Bari in na gama zan kira sa" "Okay" A dai dai nan ya gama dasu suka nufi hanyar fita,Yana gaba tana biye dashi,booth ya bud'e ya sa kayan dake hannun sa.     Mardiya na tsaye tana kallon sa ji take kamar ta sace shi,Jin Shigowar message yasa ta kalli fuskar wayar nasan,zaro Ido tayi ta bude sakon, kasantuwar wayar ba Key, sai da ta gama karanta sakon tayi saurin fita a ciki,tayi kokari dai dai ta kanta.       Sau biyu yana Kiran sunan ta Bata ji ba,a d'an razane ta amsa da ya Kira sunanta a karo na uku,cike da kulawa yace "Lafiyan ki kuwa?" Turo baki tayi Tace "Bana jin dad'ine" "Ban gane ba yanzun Nan fa lafiyar ki kalau"      "Uhmn Nikam ka maidani gida" "Kin fasa cin kifin ne?" "Eh na fasa ka maidani gida" ta karasa maganar kamar zatayi kuka. "Ikon Allah,to Shiga muje" Had'e da bud'e mata marfin motar ta Shiga ta zauna,ganin ya zaga tayi saurin ciro karamar wayarta a jaka ta wurga a Bayan mota, ta yi saurin gyara Zama kana ganinta kaga Mara gaskiya.         Kallon ta kawai yayi ya girgiza Kai kana yace "Baby na Mai abun mamaki" Murmushi kawai ta masa,suna Isa gida Bata Tsaya Hira dashi kamar yanda ta saba ba, ajiye masa wayarsa tayi,tayi saurin fita,bai Ankara ba har ta isa gate,da d'an karfi yace "Kin manta ledan naki"       "Au Na manta" ta dawo da d'an saurin ta karba had'e da fad'in "Thank you bye" ta shige gida da sauri,ya d'anyi Jim yana tunanin canzawan ta, kafad'ar Sa ya d'aga kana ya Shiga,Yana tada motar  ya bar wajen,hannun ya sa d'auki wayar sa ya Shiga dialling number Adnan.       Da sauri ta Shiga cikin gida bata ma lura da Haisam da ke zaune a parlor ba ,shi Kuma tab'e baki yayi ya girgiza Kai ya cigaba da danna wayarsa,tana Shiga d'akin ta yatsar da ledojin da jakar dake  hannun ta kana ta cire gyallen dake Jikin ta,Zama tayi a bakin gado kana ta Kara wayar ta a kunnen ta.         Ta dad'e a haka kana Naga ta miki zumbur ta d'auki jakar ta da mayafinta ta yafa ta fita da sauri, Haisam da Ma'isha ta hango Amma tayi kamar bata gansu ba tayi ficewar ta da sauri had'e da d'an gudu.     Ma'isha Tace "Ita kuma  wannan fa?" Hararar ta yayi kana yace " miko mini takalmin ki na rike miki Naga Alama sun miki nauyine sai kije ki tambayeta" dariya kawai tayi.      Mardiya kuwa motarta ta fad'a tun Kan ta Isa gate take Masa horn, da sauri ya bud'e don ya razana sosai, tana fita daga gidan ta Kara gudun motar. Su Mardiya ko ina za'a je, me take Shirin aikatawa oho? ________________________ Kumin afuwa mun koma school shiyasa kuka jini shiru, Amma Alhamdulillah yau muka Gama exam. Please comment and share. Milhaat Ce Yar Terawa. 79&80 Continuation..............'''            "Yane abokina"  "Dallah Malam ina ka ajiye wayar Kane ina ta Kiran ka Amma baka d'aga ba, Ina ka Shiga ne?"     " Afwan mun fita da baby ne ya ake cikine? " " Baka ga sakon da na tura maka ba" "A a ban gani ba Wallahi, dake wayar bata hannu na" Waro Ido yayi yace "Ban Gane ba Abdallah a hannun wa wayar take?" "Mardiya ce fa ta rike min wayar ne"       "Innalillahi Shikenan asiri na ya tonu idan har mardiya taga sakon Nan don Wallahi nasan baza ta rufa min asiri ba"    "Wai  me ka turo min ne duk Naga ka Riki ce?"     " Ka duba ka gani please ta bud'e ko bata bud'e ba" 'dan cire wayan yayi daga kunnen sa ya duba, Murmushi yayi kana yace "ba a bud'e ba ka kwantar da hankalin ka bata gani ba" Wani ajiyar zuciya ya sauke kana yace "Alhamdulillah dama Ayrah ce ba Lafiya nake so ka kawo Mana maganin zazzabi please" " Okay bara na je na sayo, yanzu zan Shigo gidan" " Okay" a tare suka katse wayar.         Direct police station ta nufa, tana parking da saurin ta ta fito tana gudu ta Shiga, Police din dake Kan canter har ya tsorata sabida irin gudun da ta Shigo da dashi leka Bayan ta yake ko wani ne ya biyo ta yayinda mardiya Kuma sai faman haki take kamar numfashin ta zai d'auke, sai faman kallon ta yake Yana kifkifta Ido yace "Madam Lafiya wa ya biyo ka?" Da Yar hausar sa da bata gama nuna ba .      Murya na rawa ta fara magana "Qawata wacce ake nema kwanaki ba a ganta ba naji labarin inda take" "To yallab'ai wani kawarki Kenn....... " Bai karasa maganar ba sai ga shigowar DPO Sara Masa yayi had'e da bankare kirjinsa Kallo d'aya ya Masa yace "relax" maida kallon sa yayi ga Mardiya yace Wace ce kike magana akai sannan ya sunan ta"     "Ayrah..... Ayrah Alhassan" zaro Ido yayi had'e fa fad'in " kin tabbatar da abinda kike fad'a?" "Eh na tabbata" Maida kallon sa yayi ga Police din kana yace "Take her statement, Sannan ku shirya don dani za a fita" Sara Masa yayi had'e da fad'in " okay sir" Nan ta Basu dukkanin details din, dama ta bar karamar wayar tane a cikin motar Kuma wayan is on call taji maganar da suke, Luckily ya sa wayan a handsfree hakan yasa taji dukkanin maganar da suke.      Number ta bawa Police din don yin tracking ai kuwa ba a d'au lokaci Mai tsawo ba aka gano inda Abdallah yake Nan da Nan suka Fara binsa a sace, da motar Ayrah sukayi amfani sabida bai santa da wannan motar ba, Bayan Abdallah yayi horn a gate d'in ba d'au lokaci ba Adnan yazo ya wangale Masa gate d'in, Yana Shiga tun Kan ya rufe kofar motar Mardiya ta sa Kai cikin gidan nan da nan polisawa sun fi biyar suka sauko daga cikin motar dukkanin su day bindigogi , Suna pointing din Adnan. Nan da Nan Adnan hankalin sa ya tashi, Abdallah da ya fito daga motar baki a bud'e yake kallon su, hannun sa rike yake da ledan magana, cikin wata iriyar murya kamar zaiyi kuka Adnan yace "Abdullah ya zaka min Haka?"     "Wallahi tallahi ban San sun biyo ni ba" Mardiya ce ta fito tana wani irin Taku tana tauna cin gum , tazo daf da Adnan Tace "Hello Mr Adnan" kana ta kauda Kai had'e da Murmushi Tace "Hello baby"      "Mardiya kece?" Abdallah ke mata tambayar Nan cike da mamaki, tace "Eh nice kayi mamakin gani na ko?"     "Ai dama na fad'a maka yarinyar Nan idan ta gani baza ta rufa Mana asiri ba" "ya Isa haka,ina yarinyar take?" DPO ya yi magana a  tsawace .       Adnan tun da ya gansu ya San Shikenan ya rasa Ayrah, shi ba hukuncin da za a Masa bane ma damuwar sa baya son rabuwa da ita, d'aya daga cikin Police din ne ya ture shi had'e da fad'in "wuce muje" jiki ba kwari ya Fara tafiya Yana tafiya biyu daga cikin polisawan Suna biye da shi sauran Kuma suna tsaye a waje, har da Mardiya aka Shiga ciki, har cikin d'akin da Ayrah take ya kaisu, Mardiya na hango kawarta ta saurinta  ta ture Adnan ta nufi inda Ayrah ke kwance tana baccin ta hankalin ta a kwance.      Kamar a mafarki ta ji Muryar Mardiya tana Kiran sunan ta, a hankali ta Fara waro Ido har idon ta ya bud'e duka ta tabbatar ba mafarki take ba, daga Chan nesa ta hango Adnan ya rakube a gefe Yana kallon ta daga shi sai vest sai boxer Yana kallon ta, idanun Sa sun canza daga launin fari suka koma jajir kamar zaiyi kuka.      Kiran sunan ta da Mardiya tayi ne a karo na ba adadi ta ya dawo da tunanin ta gare ta, rugumar juna sukayi dukkanin su suna kuka.     Basuyi wata wata ba suka sa masa handcuffs dashi da aminin sa Abdallah, Ayrah na ganin hakan ta yanke jiki ta fad'i.      Haisam na kwance a d'akinsa dawowar sa kenan daga masallaci ya cire jallabiyar sa daga shi sai wando Wanda bai Kai gwiwarsa ba, ya Zo zai kwanta yaji ihu Kuma kamar Muryar isha, tsawaya yayi daga kwanciyar da yake son yi ya Kuma kin ihun ta tana Kiran sunan sa "Ya Haisam zan mutu" da gudu ya fita d'akinta ya fad'a, ya hango ta Akan gado tana mirginawa har tazo Fad'uwa yayi saurin tare ta kanta babu ko d'an kwali.      Gashin kanta ya baje kamar wata mahaukaciya kuka take tana yarfa hannu had'e da rike Bayan ta a kid'ime yace "Princess mene ne, me ya same ki?"      "Zan mutu Yaya, zan mutu bayana, Inna lillahi wa Inna ilaihirraji'un" "You're in labour princess" Blanket masu nauyi ya d'auko a Waldrop ya shimfid'a,Sau Kar da ita yayi a  kasa yayi ganin ruwan ya fashe,  ya gyara mata kwanciyar ta, bata kulawa ya farayi kasantuwar sa na likita, d'akinsa ya koma ya d'auko duk wani abunda zai bukata, ba wannan bane karo na farko ba da yake ganin mace a haka Amma bai San Meyasa hankalin sa ya tashi sosai ba, ko don Yana sontane oho.         Duk wani abunda ya kamata ayi wa mace Mai haihuwa ya Mata, Yana d'an matsa Mata baya Yana Mata sannu had'e da fad'in "push princess" kusan awa d'aya suka d'auka a haka, gashi Umma bata gida dukkanin dasu Twins suna gidan Mummy, Abba da Daddy Kuma sunyi tafiya suna Germany sunje wani business trip, Mai aikin Kuma taje kasuwa don yi sayyaya.          Wani nishi ta saki Mai d'an Kara , jariri ya Fad'o sai Jin kukan jaririn sukayi, wani ajiyar zuciya ya sauke shi zufa ita zufa, mikewa yayi ya gyara kwanciyar jaririn kana da taimakonsa mahaifa ya fito, Raba jaririn yayi da mahaifan, zanin ya sa ya nad'e jaririn a Kai kana ya kwantar Mata a kirjin ta, da sauri ya Shiga toilet d'an karamin roba ya Samu ya tari ruwan zafi ya sirka ya dawo d'akin.      'daukan jaririn yayi ya Shiga Toilet din ya wanke  jaririn tass yanda dai akewa sabbin jarirai, Kaya mai kyau ya d'auka  ya sakawa jaririn, ya kwantar da jaririn kana ya koma Kan Isha dake kwance idon ta lumshe duk kunya ta ishe ta Murmushi yayi ya girgiza Kai kana ya d'aga ta chak sai ban d'aki, tsayar da ita yayi kana yace "kiyi wanka bari na Kira su Mummy" Kai kawai ta d'aga Masa ya fice ya barta a ciki.        Yana Fad'awa Umma Isha ta haihuwa sukayi ta fad'a wai Meyasa Bai Kira suba, Murmushi yayi yace "Umma Kennan kin manta da Dr Haisam kike magana ko?" Sai tayi shiru, fizge wayar mummy tayi daga hannun Umma tace "Sannu da kokari son gamunan zuwa" Ta kashe wayar, Kan Isha ta fita ya tattare gun tsaf, ya sa jik ya goge back yard ya nufa da blankets din da suka baci sai ga Yar aikin ta dawo, tana ajiye ledan a kitchen tazo ta karb'i wanki ta hau wankewa, ya koma d'aki yayi wanka ya sanya kaya marasa nauyi ya koma d'akin Isha ya tarar ta fito wanka har ta Sanya kayan tana tsaye tana kallon jaririn, Murmushi yayi yace "Ya dai maman baby?" Kallon jaririn yayi a kwance a inda ya bar sa, cike da mamaki yace ya Naga Baki d'auki Baby ba?"       "Uhmn Wai me na Haifa ne mace ce ko na Miji?"         A sume aka Kai Ayrah asibiti, yayin da Abdallah Kuma da aka wuce dasu police station,mardiya batayi kasa a gwiwa ba ta Kira Mahaifiyar Ayrah, Nabila ta kwala wa Kira Akan ta Shigo ta kula da Malam Hassan an ma yi sa'a a asibitin da Malam Hassan yake aka kwantar da ita, Malam Hassan yace suje su kawai zai kula da kansa.      Shigowar mami yayi dai dai da fitowar likitan dake Kan Ayrah, inda suke ya nufa yace "babu wani damuwa kawai dai fargabane and congratulations tana d'auke da ciki na tsawon wata uku" Yana Kai Nan ya tafi ya bar su agun Baki a bud'e. ____________________________ Please comment and share Milhaat ce Yar Terwa 🍃 *DANGIN UBANA*🍃 Story & Written By Milhart Na zo muku da littafi Mai ban tausayi,cike da abun al'ajabi,wannan salon na daban ne. *🌍MANAZARTA* *WRITERS ASSOCIATION📚🖊* *M. W. A* *Wannan labarin kirkirarren labarine ban yarda a chanza min labari ba Wanda ya chanza bamu yafe ba.* Ina alfahari da rubutu,sabida alkalami yafi takobi🗡️🗡️🗡️ *BISMILLAHIR RAHAMANIN RAHIM* Page 81&82 *End page* _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._ Continuation............... Mardiya ce tsaye tana kallon d'an jaririn Isha Kuma d'a agun Yayan ta , jiki na 'bari ta d'auki d'an tana kallonsa kamar yayanta ne yayi kaki ya zubar, Kuka tayi sosai sabida mutuwar yayanta da iyayen ta sun dawo Mata sabo fil, har kasa ta durkusasa ta roki yafiyar Isha dama Mutanen gidan gaba ki d'aya, duk wani munafurcin da tayi ta kullawa ta fad'a musu hatta 'bata auren Farukh da Ameerah da tayi Niyan yi, kowa sai da yayi mamakin abubuwan da ta aikata Amma ance d'an Adam ajizine, Isha ta yafe Mata, anan take shaida musu anga Aurahi suyi murna matuka musamman ma Haisam da haryanzu Yana sonta Amma a matsayin soyayyar ya da kanwarsa. Har gida taje ta nemi yafiyar Meerah da Farukh, Kuma sun yafe Mata,duk da Farukh da kyar ya hakura sabida ya d'au alwashin sai ya d'auki fansar abinda ta yiwa meeran sa. "Ayrah me hakan yake nufi? Congratulations? Ciki kike dashi?" Duk a jere mami ta jero mata tambayoyin nan. Kallon ta kawai Ayrah take yi sai ta kawar da kanta tana fuskantar bangon d'akin. "To Wallahi Dole ne a zubar da cikin Nan, wannan abun kunyan ba dani ba Baki Isa ki haifa min shege a cikin zuri'a ta ba" "Mami!!" Ayrah ta kira sunan ta kamar ba ita tayi maganar ba, Zama tayi ta jigina jikin ta ta pillow kana Tace "Mami bazan zubar da cikin Nan ba sabida ba d'an shege bane" Baki a bud'e take kallon ta Tace "Ashe baki da hankali Ayrah ban sani ba? Ko dai kin samu tabin hankali ne?" "Ni Lafiya ta kalau au..... " Bata karisa maganar ba taga shigowar Mardiya wani irin Kallo ta mata sai Kuma ta kawar da kanta. Mardiya karasowa tayi ta dafe ta a kafad'a had'e da fad'in "sannu Qawata" ture hannun ta Ayrah tayi cikin tsawa Tace "Kar ki tab'a Ni" a d'an zabure ta jaa da baya tana mamakin abinda ke damun ta, mardiya Tace "Ayrah lafiyan ki kuwa, me ke damin ki?" "ina mijina?" Shine tambayar da ta wurga mata kallon Kallo Mami, Mardiya da Nabila suka Shiga yi kana suka maida kallon su gareta, Mardiya ta ce "Mami bari naje na Kira likita don na lura bata cikin hayyacin ta maybe ya tab'a mata kwakwalwar ta" "Ke malama da hankalina Kuma a cikin hayyacina nake nace miki ina Kika Sa aka Kai min shi" "Auuu Wai Adnan kike nufi? Yaushe Adnan ya Zama mijin ki Kuma, Ayrah na lura baki da hankali" "Kar ki Kuma cemin bani da hankali Adnan mijina ne Kuma ina son sa" mikewa tayi Tace "ina yake?" Kallon ta Mardiya tayi kana Tace "Me nake gani kamar cikine a Jikin ki Ayrah? Fyad'e ya Miki?" Zafin zuciyar Ayrah ya Shiga yi mata saisaita kanta tayi kana Tace "Kina 'bata min lokaci ina yake?" "Mutumin da ya sace ki? Ya Miki fyad'e? Sannan yayi kidnapping d'inki shi kike Kira da miji Ayrah?" Mami ne tayi karfin halin rike hannun Ayrah ta zaunar da ita cike da tausayin Yar nata don zuwa yanzu a tsorace take ga kukan da Ayrah ta fara, cikin Muryar rarrashi Tace "Ayrah ki fad'a min abinda ya faruwa tun daga ranar da Kika barni a asibiti Akan zaki je gidan su Mardiya?" Shiru tayi tana kallon ta zancen zuci take " Taya za'ayi na fad'a mata abubuwan da ya faru,Taya za'ayi na fad'a mata cewar ina son Wanda yamin fyad'e a karo na ba adadi? Taya zan fad'a mata irin abubuwan da Adnan yamin?" Sai ta tsinka kanta da fad'in "Mami a hanya ya tare ni sannan yayi barazanar zai kashe ni idan ban bishi ba,Ni Kuma naji tsoron Kar ya cutar Dani sabida nasan na yaudare shi,Bayan na Shiga motar sa sai ya kaini gidan gonan sa tun daga wannan ranar take bani duk wata kulawa sai nake mamakin meyasa ya d'auko ni in dai bai cutar dani yake Shirin yi ba? Dana tambaye shi dalili yace Yana so ya hora nine Amma Kuma bai tab'a cutar dani ko na second d'aya bane....." Ajiyar zuciya na ta sauke ta cigaba da fad'in "Tun a wannan lokacin yace zai dawo dani gida Amma da sharad'in zan aure sa,Ni Kuma a wannan lokacin wutar tsanar sace a zuciya ta naki amincewa da bukatar sa,aiki kawai yake fita idan ya dawo yana Nan a cikin gidan sai abinda nake so yake yi ,Mami kin San zuciya Kuma ya Hadu da dama Nima inason shi tunda akan sa ne na San mene ne soyayya, soyyaya ce Mai karfi ta Shiga tsakanina dashi daga bisani muka yanke shawarar a d'aura Mana aure,Bayan Yan watanni ya nemi mu dawo gida sai naki sabida ina tsoron zaku rabani dashi" ta fashe da wani irin kuka Mai cin raai. Kallon ta Mami tayi ji take kamar karya take mata,Amma duba da yanayin jikinta da bata rame ba ,jikinta yayi kyau tayi fresh hakan ne ya tabbatar mata da cewar gaskiya take fad'a mata. Rungumar ta Mami tayi tana patting Bayan ta kamar wata Yar baby,babu Wanda ya Kuma cewa komai sai sautin kukan Ayrah da AC dake aiki a d'akin,Mami Tace "Ayrah lamarin kin Nan ya d'aure min Kai,wannan wani irin rashin hankali ne Ayrah kin sani cikin damuwa,bana iya bacci bana Kuma iya cin abinci duk a kanki Ayrah, ga Jikin baban Kuma abin Sai Kara gaba gaba yake yi" ta fashe da kuka, cikin tashin hankali Ayrah Tace "Mami Dan Allah ki daina kuka,kinsan kukan uwa Akan 'ya'yan ta ba abu bane Mai kyau" Murmushi mami tayi Wanda yafi kuka ciwo Tace "Kin San da hakan Kika yanke wannan d'anyen hukuncin? Kin tab'a tunanin a wani Hali nake ciki ko da na second d'ayane?" Ayrah kasa magana tayi idan mami tasan wahalar da tasha baza Tace haka ba idan Kuma ta kuskura ta fad'a mata tasan cewar ita da Adnan har abada. *Bayan kwana biyu* Adnan da Abdallah horo ake musu mai tsanani, duk sun lalace sunyi baki, musamman ma Adnan da shine babban Mai laifi, dakyar Ayrah ta shawo Kan Mami suka dunguma zuwa asibiti, tu daga waje take jiyo ihun say da gudu ta Shiga cikin Suma Mami suka rufa mata baya, Ayrah na kokarin shigewa inda take Jin kukan sa, wani police dake tsaye yaga shigowar ta ya daka mata tsawa ba ita kadai ba hatta su Mami Saida suka tsorata. "Ina Zaki?" Cikin kuka Tace "Dan Allah kace su daina dukan shi ni ba sace ni yayi ba" Isha da jaririn ta na samu kulawa sosai a gun Umma da Mummy , harda Haisam da yake ji kamar d'ansane, ranar suna yaro yaci sunan mahaifin sa wato Mansur (Mansur Mansur) su Mardiya sai rawar kai ake, su Meerah uwaye ita ma da d'an katon cikin ta anci ansha daga bisani kowa ya watse anan Mummy ta bukaci Isha ta koma gida Sam Umma bata ji dadi ba dakyar ta amince ta koma gida. Rikici akayi sosai tsakanin family d'insu Adnan dana Ayrah sabida Mahaifiyar shi sama taki amincewa da wannan auren, Adnan kuwa ya kafa ya tsare bazai tab'a rabuwa da matar Sa ba musamman a a yanzu da yasan tana son shi duba da irin karyar da tayi don ta kare shi ya tabbata da ayanzu yana gidan yari. Dakyar mahaifin Adnan ya shawon Kan hajiya larai(Mahaifiyar Adnan) Akan idan ta haihu za'a kawo Masa matar sa, Adnan ya nuna shi Sam bai San da wannan zancen ba a haka yasa dole aka kawo Masa matar sa. 'bangaren Malam Hassan kuwa hankalin shine ya kwanta ganin yarsa ta dawo , Kuma ya amince da auren nasu, Haisam ne ya d'auki nauyin jinyar sa zuwa India inda mami da Faisal ne suka tafi, ya daina fushin da yake da mahaifin nasa. Mardiya kuwa Abdallah ya daina kulata tayi kuka har ta kamar idanun ta zasu Fad'o da taimakon Adnan ya hakura har ya tura iyayen sa a nema Masa auren ta. Zuwa yanzu Little Mansur Yana wata shida a yayinda kamanin sa da ubansa yake sake fitowa , a sanadin sane mardiya ta canza ta daina duk wani mugun hali nata, idan bata gun aiki kullum suna tare dashi bata ma barin Isha ta d'auke shi idan kaga ta kaishi gunta to don yasha nonone hatta wanka ita take mishi. *Bayan shekara d'aya* Abubuwa da dama sun faru, Meerah ta haihuwa yarta mace,taci sunan aminiyarta Ayrah, Ayrah don farin ciki har kuka Saida tayi, Malam Hassan Lafiya ta samu sannan Abdallah da Mardiya sunyi auren su babu wani shamaki, a yayin da Haisam Kuma zallan so yake nunawa Isha, don ita kanta ta Fara tsorata da irin soyayyar da yake Mata, Daddy da Abba suka yanke shawarar d'aura musu aure da zaran ta yaye little mansur. Bayan an yaye little mansur, aka sa ranar Auren Isha da Haisam anyi hidama sosai Saida garin gombe ya amsa, Bayan aure kuwa Isha ta koma aiki a karkashin asibitin Haisam, daga bisani Haisam ya hana ya bud'e Mata babban chemist yasa mata masu aiki tana gida kud'i suna Shiga account d'inta, sai da ta suka mori amarcin sa kana ya koma bakin aiki a hakan ma idan ba wani serious abu bane ba Zama yake a gida. *After 5 years* Dukkanin family suna cikin kwanciyar hankali , a yanzu Isha yaranta 6,3 mata 3 maza da Mansur ya Zama Yara 7, Ayrah kuwa yaranta 4,3 mata d'aya na miji Wanda shine d'an farin ta, sai Meerah yaranta biyu da Mai sunan Isha sai kanin ta daga Nan Kuma haihuwan ya tsaya, Nabila ma tayi aure, haka ma Faisal, a haka family din suke cikin kwanciyar hankali sannan kullum suna cikin mutunci da mutun ta juna. Alhamdulillah Alhamdulillah, a yaune na kawo karshen littafina Mai suna DANGIN UBANA, Nagode sosai da goyon Bayan da kuka bani har na samu na kammala. Kuskuren da nayi aciki Allah ya yafemin abinda na fad'a dai dai Kuma Allah ubangiji ya bamu ladan sa dani daku baki d'aya, har kullum Ni din ce Milhaat taku Yar tarewa ku kasance dani a littafina na gaba Mai suna *HAKKIN SO* da fatan zaku bani had'in Kai Nagode.