Assalamu Alaikum, Thank you so much for choosing to read this document... NO COPYING OF THIS STORY IN ANY FORM. NO TRANSLATION IN ANY LANGUAGE. THE UPLOADING, SCANNING AND DISTRIBUTION OF THIS BOOK IN ANY FORM WITHOUT THE OF THE AUTHOR IS ILLEGAL AND PUNISHABLE BY THE LAW. KU SANI CEWA LAIFI BAYA BUYA! Labarin WAYE SHI zai tafi ne akan soyayya tsakanin mutum da wata halittar. Kuna ganin hakan abu ne mai yiwuwa? Biyo ni ciki mu tarar da gwagwarmaya da kuma k'addarar rayuwar Sa'adha, duk akan rashin sanin WAYE SHI. Ina fata labarin zaiyi muku dad'i da kuma ma'ana! AYSHA MAHMOUD SHAFI'EE. WAYE SHI? AYSHA SHAFI'EE 01 (☆_☆) "Nanne! nanne! nanne!!...ki tashi nace koh?" Yarinyar da aka kira da nanne ta motsa sannan ta cigaba da baccinta. "Zaki bude ido ko sai na tashe ki da ruwa..." Inna ta fada tana dad'a girgizata, jin haka yasa ta zumb'ura baki sannan ta mike tana murza ido ta cikin dogon gashin kanta daya hargitse ya rufe fuskarta. "Ki tashi ki wanke ido ki fita tun kan salisun ya tafi, kin san tun jiya muka yi haka dake." Nanne ta dago ta kalli agogon dake kafe a dakin, k'arfe takwas da kwata na safe, gabadaya baccin da tayi bayan sallar asuba ma bai kai fi na awa biyu ba. Kwata-kwata ta manta sunyi da inna cewar yau zata je da safe ta gayawa salisu irin audugar da zai d'ebo mata a gonar baffansu wajen daza'a fitar da auduga yau kafin masu siyen kamfani su d'ebe masu kyan ciki, wai da ita zata yi sak'ar mayafan da amare zasu yafa ranar wankan amarya (Hakan wata al'adarsu ce ta wata kabila daga nijer) "Allah inna da kin san gajiyar da na kwanta da ita da kin hakura wani daga cikin su yaya umar kawai ya fad'a masa. "Kema kin san ba ganinsu zanyi kafin su fita ba don haka ki tashi ki d'auraye ido kije tun kan salisun ya tafi na san zasu fara yin gaba, don tun dazu nake jin dirin motoci zasu fara tafiya." Nanne tasa hannu ta tattara gashinta baya sannan ta tufke shi, ta shiga band'akin dake jikin d'akin ta zuba ruwa a buta ta wanke bakinta da fuska sannan ta fito, inna ta miko mata hijabi daga inda take zaune. "Haba dai, wannan ya cukurkude, bari in duba wani." Ta bud'e wardrobe ta janyo wani mai d'an tsaho ta zura sannan ta karbi k'atuwar ledar da innan ke nuno ta dashi. "ki masa bayani kamar yadda na fad'a miki jiya dan Allah." Yadda ta marairaice murya yaso ya bata dariya sanda ta fita daga dakin, da yake a hawan farko suke tana iya hango k'aton tsakar gidan da ba mutane sosai saboda safiya sai daidaikun 'yan aikin dake wucewa akai akai. Ginin gidan nasu dake cikin wata unguwa a katsina, dad'ad'd'e ne da akayi shi da dakakken gini da ko k'usa ba kasafai take huda shi ba, sannan gabadayansa hawa uku ne, daga bakin gingimemen gate din dake jikin zungereriya katangar data zagaye gidan, faffad'ar haraba ce da tsaf zata d'auke bikin masu dangi, akwai manyan rumfuna na ajiyar motoci da kuma shukar fulawowi data zagaye filin gabadaya. Daga can jikin ginin gidan kuma doguwar baranda ce data bi tsawon fad'in wajen inda d'akunna ne a jere guda shida na yayyansu maza, a tsakiyar su kuma k'atuwar kofa ce data shigo ciki zuwa bangaren baffansu dake daga dama, inda ya had'a da k'aton falo na saukar bak'insa da kuma d'akuna biyu a ciki da bandaki, daya gefen hagu kuma k'aton kicin din gidan ne wanda shi kansa waje biyu ne dashi, da b'angaren da aka kafe da durowoyin ajiya, sai madafi inda ake jibge tarin itace da kuma manya-manyan tukwanen girki. Bayan shi babu komai a k'asan sai manyan sito guda biyu, da ake ajiyar kayan gona, matattakalar hawa sama mai fadi ce data d'auka daga tsakiyar katon tsakar gidan kuma ta rabu hagu da dama saboda kowanne b'angare a zagaye yake da d'akunan matan baffansu su hudu ras!, inda kowacce take da falo da kuma manyan dakuna guda biyu kowanne da band'aki a ciki, sai wajen inna wato mahaifiyar baffansu inda itama take da katon falo sai dai daki daya ne da kuma band'aki. Hawa na biyu kuma na karshe faffadar baranda ce inda wajen yafi ko'ina a gidan girma, a d'an zagayeta da gini daidai misali yadda in ba d'age mutum yayi ba ba zai iya gano k'asa ba, a nan suke shanyar kaya, kayan miya da kuma zaman shan iska kasancewar akwai kujeru kala-kala harda 'yan furanni na tukwane. Kuma daga nan kana iya hango gabad'aya kewayen unguwar da tsilli-tsillin gidaje ne kawai wanda da yawansu ba mutane a ciki, wasu ma ba'a gama ba. A kaftanin 'ya'yan baffansu Nanne ce ta goma sha bakwai, sannan akwai mutum biyu mata 'ya'yan aunty amarya data girma a k'asanta. Uwargidan baffa ta farko, hajiya Nasiba da ake kira da hajiya babba, 'yar maigidansa ce dake can cikin garin katsina, kasancewar baffansu d'an asalin nijer ne ya shigo katsina. tana da 'ya'ya shida, Ahmad, Nasir, Muhammad, ishaq, farida da kuma Aisha. Maza hudu mata biyu, kuma 'ya'yanta sune manya a gidan, don Ahmad da farida sunyi aure saura maza uku da mace daya Aisha. Sai Mama Rabi wadda ita kuma 'yar uwarsa ce ya auro daga nijar, ita 'ya'yanta hudu, Ibrahim, sulaiman, umar da macenta daya jamila. itama ta aurar da babban d'anta ibrahim. Sai Mama halime wadda itama 'yar nijar d'ince amma ba 'yar uwarsa ba, 'ya'yanta hudu duka mata, khadija, maryam, nafisa, da kuma zainab. Khadija ce kawai tayi aure a cikinsu. Sai aunty Amarya mai 'ya'ya biyar kasancewar haihuwarta ta farko tagwaye ne maza, salim da suraj, sai mai bi musu sadiq, safiya da kuma surrayya. A duk cikin 'ya'yan baffan, nanne ce kawai bata da uwa a gidan, mahaifiyarta bafulatanar adamawa ce kuma tana can tare da 'yan uwanta, baffansu ya aureta ne lokacin da wani sab'ani ya shiga tsakaninsu da mama Rabi har ya sake ta, toh a wannan lokacin ne yaje adamawa halartar wani taro na manoman nijeriya da akayi kusan sati ana gudanarwa, anan yaga mahaifiyarta a d'aya daga cikin masu goge-gogen wajen da suka kwana. Farko abokananshi ne suka fara tsokanarshi da cewar ya kamata ya koma gida da bafulatanar adamawa tun lokacin da suka ganshi yana tambayarta wani abu, shikenan kuwa zance ya koma gaske inda a satin basu baro adamawa ba sai da suka je har gidansu nuratu aka tabbatar musu kuma an bashi ita, anan suke ji ma ashe bazawara ce ta taba aure harda yara biyu. Ko da ya dawo, ya sanar da inna mahaifiyarsa, bata hana shi ba sai dai matansa da suka nuna rashin son abin, hankalin mama rabi yafi na kowa tashi tunda a lokacin tana ta yawon bin 'yan uwa kan a bashi hakuri ta koma darajar 'ya'yanta. Sai dai ubangiji ya riga ya tsara al'amarinsa don ba'a fi wata daya ba aure ya tabbata tsakanin baffansu da nuratu, ta kuma tare a b'arin mama rabin, duk da kasancewar nuratu bazawara, amma baffa ya nuna mata so wanda har hakan ya dinga b'atawa matansa rai, kasancewar baya b'oyewa koda kuwa a gaban 'ya'yansa ne. Shekarar nuratu daya da rabi a gidan, ta haifi diyarta mai kama da ita, sai dai ta d'auko hasken fatar baffan tunda ita nuratu ba fara bace, baffa ya sanya mata SA'ADHA nuratu kuma ta lak'aba mata NANNE wanda shine ya bita. Tun daga haihuwarta ne kuma nuratun ta sauya hali, ta fara rashin mutunci kala-kala a gidan, rashin kunya tun daga kan baffan har inna ba wanda ta kyale. Nasiha da kyaliya ba wadda baffa baiyi ba amma a kullum abin gaba yake. Ganin haka, ya sawwak'e mata saki d'aya ba da son ransa ba, don har a lokacin yana k'aunarta, tayi niyyar tafiya da nanne amma ya hana. Saboda haka ta dire ta ta koma adamawa, daga baya ne suka samu labarin cewa ashe gidan tsohon mijinta take son komawa kuma ta koma d'in bayan ta gama idda. A lokacin da hakan ta faru, mama halime tana shayar da autarta zainab, baffa ya roki da ta hada da nanne amma kiri-kiri ta rantse ba zata shayar da 'yar kishiya ba sai dai in itama ya saketa. Aunty amarya ma da bata dad'e da yaye d'anta na biyu sadiq ba tace bata san zancen ba. Hajiya kuwa ba mai tunkararta da irin haka, kasancewar ba shirgin kowa take shiga a gidan ba har dashi baffan kuwa, kuma ma 'ya'yanta duk sun riga sun girma a lokacin. Daga karshe dai inna ce ta dauki nanne, duk da cewa da farko itama bata shiga zancen ba don tana cike da d'acin abinda nuratun tayi musu. Da taimakon tatacciyar madarar shanun da a kullum ake tatsowa daga gonar baffa nanne ta girma a hannun kakarta, inda kuma innar ta dauki son duniya ta dora akan nannen, ya zama tamkar bata da jika ko d'aya a duniya sai ita, har ta kai ma in kana son farin cikinta to ka yiwa nannen wani alkhairi. Sannan tun tashinta sau uku baffa yasa aka kaita adamawa wajen mahaifiyarta, sai dai ita nuratun tana yawan yi mata aike ta hanyar turo 'yan uwanta. Gabadaya ilahirin jama'ar gidan baffa, har kuwa da tulin ma'aikatan dake cikin gida da gonaki, nanne zata iya kirga masu nuna mata kulawa a cikin 'yan yatsunta kawai, don daga wad'anda suka tsane ta sai masu nuna cewa Allah baiyi halittar ta a cikinsu ba, saboda kuwa dalilai biyu, na farko ta tashi a cikin bakin fentin mahaifiyarta daya shafeta, don da yawansu tsanar da suke mata ta samo asali ne daga irin abinda nuratu tayi a gidan bayan haihuwarta, sai kuma saboda tsananin rashin kunyarta da ba ta kan wanda bata bi in abinta ya tashi, harda manyan mazan gidan kuwa da take d'an shakkarsu. Hakan kuwa ya samo asali ne daga rashin kwab'ar data samu daga inna, don duk gidan har baffa ba wanda ya isa yayi mata tsawa akan wani abu in tayi ba daidai ba sai anga b'acin ran inna, wani lokacin ma ta yini tana sababin cewa don anga yarinya bata da uwa a gidan ne. Shi yasa ta tashi kusan a sangarce, saboda kowa a gidan na shakkar bacin ran inna, don in bata yi da kai shi kansa baffan baza ka samu fada a gunsa ba. Mutane da yawa in suka kalli fuskar nanne baza su ce tana da magana bama balle rashin kunya, tafi kama da irin miskilan nan dake takama da wani abu nasu, amma yini d'aya tare da ita zai rusar da wannan ma'anar. Duk cikin jama'ar gidan, babu wanda nanne take ganin tsana b'aro-b'aro a wajensa irin mama rabi da 'ya'yanta, kasancewar baffa bai dawo da ita gidan ba sai bayan an yaye ta. Amma hajiya babba babu ruwanta da ita in ba aiken inna ne ya kaita wajenta ba, haka ma 'ya'yanta, shi yasa su take ganin mutuncinsu. Mama halime kuwa nunawa take yi Allah bai halicci inuwarta a gidan ba, bata ko ambatar sunanta balle tabi ta kanta a duk harkokinta, tafi karkata ga yadda baffa zaifi fifita ta a cikin matansa, hakan yasa suma 'ya'yanta basu damu da ita ba, sunfi damuwa da samun harkar kyale-kyale kamar yadda ta d'ora su akai, sai dai kuma duk randa wani abu ya had'o su da nannen, kowa sai ya san ana tashin hankali a gidan kasancewar da sauran 'yan uwansu ma ba mutunci suke ba. Aunty amarya ce mai kyararta da kuma hantara in bata ga idon inna ba, wanda ita kuma nannen in dai babu 'yan biyunta da take shakka a wajen zata rama ne da irin maganar data fito bakinta kafin ta bar wajen, ita kuma ta bita da zagi. Ma'aikatan gidan ma basa shiga harkarta, don data had'a ka da inna hanyar samunka a wajen baffa ta fara rawa kenan. ●﹏● WAYE SHI? AYSHA SHAFI'EE 02 (☆_☆) Nanne na sauka k'asa taci karo da Mama Azumi shugaban ma'aikatan dake kula da girke girke. Mace daya a cikin kalilan d'in 'yan aikin gidan dake nuna mata kauna. "A'ah uwata ce da sassafen nan?" Ta sake turo bakin daya zame mata jiki. "Wallahi ba yadda na iya ne inna ce ta taso ni, ya akayi Kema kika fito da sassafen, wani abun za'ayi yau?" "Yo, mu ai fitar safe yanzu ta ganmu, kin san masu kawo lefen jamila da safe suka taso, kuma kila wajen azahar zasu iso tunda a gobe zasu koma, ga aikin tarbar tasu da yawa." Nanne ta d'an zare idonta tace. "kice yanzu gabad'aya gidan zai tashi." Don lefen jamila shine na karshe da za'a kawo kuma wanda kowa yafi d'okin gani a cikin na yayyen nata hud'u da za'a aurar, kasancewar wanda zata aura din a can nijar yake, d'an wata yayar baffan nasu ne da suke kamar cousins ita da baffan, kuma k'anin mahaifin baffan ne ma ya had'a auren, a cewarsa sunyi nisa da danginsu hakan zai dad'a kusanci tsakaninsu ya kuma sa zumunci ya d'ore. Shine da akace baffan ya bada 'yarsa ya had'a da jamila 'yar gidan mama rabi, wanda zuwan yaron d'aya wajenta, aka tsaida maganar auren tare da nasu Aisha d'iyar hajiya babba da zata auri cousin d'inta, da Nafisa da maryam 'ya'yan mama halime. Dama kusan duk sa'anni ne su hud'un, har ana zasu tafi su bar ita jamilan kasancewar ta dorawa kanta akidar sai mai kudi zata aura, don kowa shaida ne a gidan bata saurayi sai d'an wani babba ko mai nauyin aljihu, to sai abin yazo a daidai, don wanda zata aura d'in mai suna Al'ameen, mahaifinsa shahararren mai kudi ne a nijar d'in, shi kansa baffan ma bai sanshi sosai ba saboda gabadaya karatunsa a k'asashen waje yayi, shi yasa ma da akayi had'in babu wanda yaji bakin jamilan ko ita mama rabi akan basa so. Wanda da ace bashi da kudi, kowa a dangi sai yaji masifar da zasu yi wadda zata sa a fasa auren. Amma yanzu mama rabin bata da magana sai habaicin cewa ana yiwa 'yarta kishi. Kuma kusan hakane, don hajiya babba ce kawai bata sa ido akan auren ba, saboda ita irin k'ananan abubuwan nan wani bata ma sanin anyi, danginta na uwa da uba kaf! masu arziki ne, shi d'an wan nata ma da Aisha zata aura in bai fi su Al'ameen d'in kudi ba zasu iya karawa. Amma mama halime ba wanda ya kaita kishi, ganin ita har 'ya'ya biyu zata aurar, amma duk cikin mazajensu ba wani mai shahararren arziki sai dai rufin asiri, duk da cewar kuwa 'ya'yanta sunfi kowa gayu a gidan. Don a lokacin da taji zancen ma cewa tayi kamata yayi tunda itace mai 'ya'ya mata baffa yayi had'in da zainab, wai ai jamilan tana da tarin samarin dake sonta. Sai dai sanin kanta ne baffa ba zai taba yin hakan ba, tunda jamilan itace gaba da zainab. Ita kuwa Aunty amarya bak'in cikinta bai wuce na cewa 'ya'yanta sune k'anana a gidan ba basu kai minzalin da za'a fara damawa dasu ba, tunda 'yan biyunta manya sai yanzu suke jarabawar fita daga sakandire, Kuma ko a cikin mazan sune k'anana, don muhammad da nasir ma 'ya'yan hajiya babba aiki suke yi banda Ahmad ma da yayi aure, ishaq ne kawai ya koma k'aro karatun masters, suma 'ya'yan mama rabi bayan ibrahim da yayi aure, sulaiman da umar duk aikin suke yi. **** "ke don uw**ki ina zaki da sassafen nan?" Muryar sulaiman ta katseta a daidai barandar waje, d'a na biyu a wajen mama rabi, yana tsaye daga jikin 'yar karamar katangar data raba k'ofofin d'akunansu da hanyar shiga gidan yana danne-danne a wayarsa, har tayi tunanin me yasa bai tafi aiki ba ta tuna cewa duk ranar da za'a fitar da kaya a gonar baffa tare da mazan gabadaya yake zuwa, har da masu auren ma kuwa, ita ko kadan bata kula ta wuce shi bama, a ranta tace. Ba dai uwata ba sai dai taka. "Nace ina zaki?" "Inna ce take son auduga, shine zanje in yiwa salisu bayanin irin wadda za'a kawo mata." Ya d'ago ya kalleta. "Duk mutanen da zasu je ba wanda zai iya fad'a masa sai ke?" "Ni ta yiwa bayani ne don zai fi saurarata." Ya kalleta da mamaki. "Saboda ke k'anwar babbarsa ce?" Tayi kamar tace wani abu amma sanin hakan zai iya zama kamar ta zage shi ne yasa ta had'e rai ta juyar da kanta gefe. "Koma ciki kafin in take ki." Dama abinda take jira kenan, saboda haka tun kafin ya rufe baki ta taho fuuu! ta wuce shi. "Yo, daya dawo min dake shi ya san irin wadda nake so ne koko ma zai fad'awa salisun ne?" Inna ta tambaya tana kallon nanne dake cin d'umamen da mama Azumi ta kawo bayan fitarta. Hankali a kwance ta daga kafad'unta. "Nima ban sani ba...tunda har ya iya zaginki ina ruwansa da wata audugar da kike so." "Wai ni ya zaga b'aro-b'aro?" Ta saki lomar data d'auko cikin hannunta. "Toh inna uwata fa yace, a duniyar nan ina da wata uwar ne bayan ke..." Inna ta sake kwafa tana kokarin tashi. "Rabu dashi dani yake zancen, Allah zai kawo shi har nan wajen ina zaune, daga shi har tasa uwar kuwa da yake tak'ama da ita." Awanni hud'u bayan haka, Sadiq d'an wajen Aunty amarya dake sa'an Nannen ya shigo rik'e da wata k'atuwar leda cike taf! da farar audugar. Ya dire ta a gaban inna wadda ta hau dubawa tana sababinta, sannan ya matsa kusa da nanne dake yankan farcenta ya d'an sunkuyo yace. "'Yan mata..!" Taja wani dogon tsaki ba tare da ta d'ago ba, tun lokacin da ya samu labarin cewa in tana yarinya aka tambayeta ita mace ce ko namiji sai ta fara kuka tana cewa ita 'yanmata ce shikenan ya addabe ta, dama k'iris yake jira ya samu wani abin da ya san bata so, tunda a duniya burinsa kawai yaga ya tsokane ta. "ke kika d'aukewa ya suraj kayansa da aka shanya a baranda? tun jiya yake nemansu." Jin haka yasa ta d'ago da dara-daran idanunta ta kalle shi. "Shi yace maka ni na d'auka, a ina zanga wasu kayansa ma balle in d'auka." "Na san zaki iya daukar ne shi yasa na tambaya, in ma kece gwara tun wuri ki mayar masa, don wallahi ransa ya b'aci kuma yanzu zasu dawo, nima don yaya sulaiman yace in biyo su Aminu ne da tare zaki ganmu." Caraf! kuwa inna ta karbe zancen. "Kaga ni bana son neman tashi hankali da safiyar nan, daga aiko ka kuma sai ka soma bin ta da sharri, ina nanne ina wasu kayan surajo?" "Rabu dashi inna, in ma na d'ebo ai dole nan zan kawo kuma zaki gani." Sadiq yayi dariya kafin ya juya yana fad'in. "Ni dai na fada miki, don wallahi kin san halinsa." Ta sake jan tsaki sannan ta mike ta shiga bandaki don d'auraye hannunta. sai dai wani b'arin na zuciyarta tsoron kar da gaske sadiq yaje ya fadawa suraj cewa ita ta dauki kayansa ne, don ta tabbata ko muryar inna zata dushe wajen fad'a sai ya jibgeta kamar yadda ya saba, shi yasa ko kad'an basa shiri da inna. Tana fitowa ta nufi can kasan kayan wankinsu inda ta cusa kayan nasa, kala biyu na shaddar gezna, wadda baffa ya bayar akayi musu aiki tun daga maiduguri, ta sake duk'unk'une su a ranta tana fad'in. Ba dai ni zaka yiwa tsawa a gaban abokanka ba, wallahi haka zanyi ta kwashe duk wani abun da kake so. Ta fada a zuciyarta. ●﹏● WAYE SHI? AYSHA SHAFI'EE 03 (☆_☆) Yana tsaye daga jikin wata tsohuwar container data raba gate din gidajen biyu yana lura da masu aikin feshi da suke yi a k'ofar gidan. "Wai dama da gaske gidan nan tarewa za'ayi?" Nanne ta tambayi rahama dake tafiya a gefenta lokacin sun dawo daga islammiyya. "Tun jiya naji mama na fad'a, wai har sun fara kawo kaya ma...gwara ku sami makota ai  gidan ya dad'e ba kowa." Sun iso daidai bakin gate din kenan zasu wuce, d'aya daga cikin masu aikin feshin ya juyo da bokiti cike da ruwa zai watsar a kasa, cikin rashin sa'a sai abin yazo daidai da sanda suka k'araso wajen, ruwan gabadaya ya sauka a jikinsu, tun daga hijabi har kan takalmansu. "Malama dan Allah kuyi hakuri, wallahi ban san kuna bayana." Nanne ta d'ago da mamaki ta kalleshi. "Kamar yaya muyi hakuri? Ta yaya zaka jika mu da k'azamin ruwan nan sannan kace muyi hakuri?" "Toh in ban baku hakuri ba me zance?" "Wallahi ba wani zancen hakuri sai ka biya kud'in kayan nan tunda uniform ne, ko kana tunanin zamu sake saka su ne a haka?" Ya girgiza kansa rike da bokitin. "Wannan ma zancen banza ne, ta yaya daga jik'a ku za'ace sai in biya kudin kaya?" Jin muryar mutumin a sama yasa imran juyowa daga wayar da yake yi, idonsa ya gano masa ita tsaye daga jikakken uniform a kusa da kawarta, ta hade rai tana dallarawa mutumin nan harara sanda yake magana, abin yaso ya bashi dariya ganin yadda take fiffikewa wajen magana kamar zata cakume shi. "Ka san Allah malam ba wani zance sai ka biya kudin kayan nan...." "Na rantse da Allah in dai baku hakura sai dai ku san yadda zaku yi." Wani daga cikin abokan aikinsa ya juyo yace. "Haba 'yanmata ku baku san tsautsayi bane?" "Bamu sanshi ba...abinda muka sani kawai a biya mu kudin da zamu sake kaya." Rahama ta janyo hannunta. "Dan Allah ki rabu dasu, yanzu in ya baki kudin ma karba zaki yi?" "Wallahi karba zan, ni da hakkina...?" Bata kai karshe ba, muryarsa ta katseta mai taushi daga gefe. "Uhm kaga..." mai aikin ya juya. "...Ka tambaye su nawa ne kudin kawai." Ta juya ta kalle shi, jingine da container kofar gidansu, yasha farar shadda da hula mai kyau, ranar data fara ganinsa kenan, ranar da ya fara shiga cikin tunaninta.... "Baffanki ya fara fad'a kan bakya zuwa gaishe da su hajiya, don jiya yake ce min ya bawa halime shadda a dinka muku ke da zainab tace masa ai ita tafi sati biyu ma bata ganki ba, don haka da kin gama shiryawa yanzu kibi dakin kowacce ki gaishe ta." Inna ta katse tunaninta tana kurb'ar koko, Nanne ta kalleta sannan ta cigaba da shafa man da take bayan ta fito daga wanka. Ko kad'an bata so haka ba, don duk cikinsu babu dakin wadda take son shiga, tafi son tayi harkarta kowa ma yayi tasa...in sun hadu a tsakar gida ko a baranda ta gaishe su da kai. "Inna ni wallahi da wani waje zamu da rahma, in d'inkin ne ayi min iri d'aya da zainab kawai, waccar atamfar ma da baffan ya bayar ai ba'a tuntube ni ba suka yi min wata 'yar mitsitsiyar riga." Zainab itace 'yar autar mama halime, kuma kusan sa'ar nanne don da watanni bakwai kawai ta girme ta. "Ni ba ruwana da zancen dinki, in sun ga dama ma su dinke mata shaddar duka, nace dake kawai kije ki gaishe su, in sun ganki ai shikenan ba mai sake zuwa ya fadi wani abu akanki." Ta hade rai kan ta nufi wajen kayanta don daga yanayin muryar innan, ta san da gaske take sai taje. Dakin mama halimen ta fara shiga bayan ta shirya cikin wata doguwar riga ta jan material, sannan ta yafa dankwalin kawai akanta, hannunta rik'e da bak'ar leda mai cike da kanwa wadda inna tace ta kai can kicin wajen su mama azumi. Maryam kadai ta tarar a falon, zaune akan kujera tana karyawa da alama bata dade da tashi ba, don kuwa akwai ta da son bacci musamman na safe. "Maman tana ciki ne?" ta tambaya tsaye daga bakin kujera. Kamar baza ta amsa ba, don sai da ta gama taune abinda ke bakinta sannan tace. "eh." "Gaisheta nazo yi." Ta d'ago ta kalleta sarere. "sai ki jirata ta fito." Tana rufe baki kuwa Nafisa da zainab suka shigo, hannunsu rike da wasu manyan ledoji, kallo d'aya nafisa tayi mata ta shige, zainab d'ince kawai ta mata guntun murmushi kasancewarta mai saukin kai, don ba don rashin yawan maganarta ba da sun d'anyi shiri da nannen. "Kar dai wai an samo?" cewar maryam da saurinta lokacin data sauko tana ajiye kofin hannuta a k'asan kujera. Nafisa ta mik'a mata ledar da take rike da ita tana fadin. "Zauna nan, ina tashi daga bacci naga sak'onsa wai an samu kayan ba shiri na azalzali idris (direbansu), in gaya miki sha d'aya muna can, mun ma riga shi isa shagon." Maryam ta hau zaro wasu tsantsara tsantsaran lesuna masu kalar milk da orange tana fadin. "Sune kuwa, yanzu guda nawa ne anan?" "sha tara ne, amma bamu bar shagon ba sai da nasa ya kulle guda talatin da daya a store kinga hamsin din kenan...don kar ma yace mana an siya wasu." "Wooo...." ta d'an yi ihu sannan ta had'a da zagi. "Wallahi kowa sai ya san anyi ankon da har a gama bikin gidan nan baza a sake yin irinsa ba." Nanne ta kalli lace din da akewa ihu, don kyau yayi kyau don ba karya sun san harkar gayu, amma ya za'ace har a gama bikin kowa a gidan baza'ayi mai kyansa ba, ta tabbata ma wanda su hajiya babba zasu fitar sai yafi nasu tsada don ba had'i tsakaninsu. Idonta ya kai kan kofin da maryam ta ajiye, ta juya taga duk hankalinsu ya tafi wajen kirga kayan, zainab kuma ta dauki wayar maryam din tana dubawa, a hankali ta matsa dab! da kujerar sannan ta damk'o k'ura-k'uran kanwa guda biyu, ta dubi tean da yasha madara kamar me, ta jefa ba tare da sun ankara ba. "'yan kasuwar ne har suka dawo..." muryar mama halime ta ratso daga cikin d'akin kafin ta dage labulen ta fito, sai dai ganin nanne tsaye daga jikin kujera ya tsaida ta, cikin kissa tayi murmushi tace. "Yau bak'uwa muka yi ne?" Nanne ta kalle ta daga inda take tsaye, sanye cikin wata hadaddiyar shadda data sha aikin dutse, abin yaso ya bata mamaki, don ta san ba wani shiri suke da mama rabi ba da har zata yi wannan kwalliyar don karb'ar lefen 'yarta, sai dai fa ko don ta cusawa mutan gidan haushi. "Ya kika tsaya daga nan, zainab baku ce ta zauna ba, shigo ciki mana." Kamar gaske. Ta ayyana a ranta kafin tace. "Nan ma ya isa mama, dama zuwa nayi in gaishe ki, ina kwana." "Lafiya kalau, ya innan da k'afa jiya na fita tun safe ai bamu gaisa ba." "k'afarta da sauki, tace a gaidaku kuma." "Muna amsawa, zauna mana." "Ba komai mama, tafiya zanyi ma sai anjima." Har ta juya maman tace. "A'ah dawo kici abinci mana, maryam kina kallon kanwartaki ba kiyi mata tayi ba?" Abin ma yaso bawa nanne dariya, wai a cikin gidansu ake mata tayin abinci kamar taje wani bak'on waje, abincin da a yanzu in ta tuburewa inna bashi take so ba, dole ta fad'awa mama azumi a canja in yaso wanda ba zai ci ba, ya nemi wani abin. Ta girgiza kanta. "A'ah mama taci abinta wallahi, a k'oshe nake." Tana fadin haka ta juya ta bar dakin, sai dai kafin ta gama zura takalmanta taji sanda maryam ta furzar da wani abu sannan cikin muryar fushi tace. "Meye wannan?" Da murmushinta ta nufi falon aunty amarya, inda ta tarar gabad'aya yaranta na nan banda 'yan biyu da suka tafi wajen fitar da auduga, safiya da surrayya sun baje suna kallon wani film d'in larabawa, ta tab'e baki ganin yadda hankalinsu ya tafi gabadaya akai, ita abinda baya gabanta kenan kallo, don tvnsu ta dakin inna sai tayi kusan sati biyu bata kunna ba, tunda itama inna ba kallon take ba, sadiq dake can kan dining ya d'ago daga cin abincin da yake yi bayan su safiya sun amsa sallamarta. "Kayan kika kawo a ledar? don wallahi na tabbata suna hanya yanzu." "Sadiq na gaya maka ka fita harkata, don wallahi daga kai har kayan gabadaya sai in had'a in zage ku." Ya kyalkyale da dariya harda buga table din gabansa. "Na zata ai zaki ce harda mai kayan, tunda baki ji waccan shawarar dana baki ba bari in sake miki wata, kije ki canja kaya kisa masu nauyi-nauyi da zasu kare miki duka ba wannan fale-falen ba, don jawur zaki koma yanzun nan." Taja tsaki kafin ta juya wajen surayya 'yar autarsu da bata fi shekara tara ba tace. "Ina Aunty?" "wanka take yi." Kamar ta jira ta fito kuma ta tuna sadiq yace yanzun nan su suraj zasu dawo, kuma ba lallai ma ta samu wata tarbar arziki daga wajen Auntyn ba don haka tace. "In ta fito kice nazo gaishe ta." Har ta juya safiya mai bin sadiq ta tsaida ita. "Yaya Aisha tace zata samu a gad'ar da cousins dinta zasu yi ranar kamu, in kina so ki fada mata kema ta saki." Kamar tace mata eh kuma ta tuna rawa ce, daya daga cikin abubuwan da bata iya ba, saboda haka tace. "Gaskiya bana jin inna zata barni." Safiya ta gyada kanta sannan ta maida hankalinta kan tv. Dad'in nanne dasu kenan ita da surrayya basa taba mata rashin kunya ko wani abu, duk ko da cewar mahaifiyarsu bata sonta. Shi yasa itama take jin dadinsu musammam ganin sune kadai wad'anda ta girma a gidan. Tana isa falon hajiya Babba ta tarar kanwarta mai suna Aunty hadiza da wata mata da bata sani ba sunzo ana lissafin adadin labulayen da za'a siya na gidan Aisha kasancewar sunje sun gano gidan. Ta gaishe su suka amsa mata ba yabo ba fallasa sannan ta tambayi inda Aishan take, hajiya babba ta shaida mata tana dakinta, tayi zaton zata kirata ne don haka ta cigaba da zama a wajen, sai dai ga mamakinta kai tsaye hajiyan tace ta tashi ta shiga dakin. Tun daga kofa take k'arewa dukiyar da aka narka a dakin kallo, tana iya tunawa shigarta ta karshe komai na dakin lemon green ne amma yanzu an canja zuwa milk and ash, gaskiyane da inna ke cewa ita kanta hajiya babba mai kudin kanta ce, su mama rabi kawai haukansu suke a gefe. "A'ah daga nan, karaso mana." Aisha dake kwance a gado tana waya tace da nanne. "...zaka d'an ara min miti biyu?" ta tambaya cikin wayar, wanda suke wayar da ba tantama nanne ta fahimci wanda zata aura ne ya fadi abinda ya sata murmushi kafin ta katse kiran ta mike zaune. "kina lafiya? Kwana da yawa?" "Lafiya kalau." Nanne ta amsa da murmushi, a ranta tace 'ya'yan hajiya babba kenan, ko basa sonka baza su taba nunawa ba shi yasa a duk sanda ta gansu gaisuwar mutunci ke hada ta dasu, duk ko da kafin ta gansu din aiki ne, don ko ita Aisha da take mace sai tafi sati bata ganta ba don kusan kullum a makaranta take yini, balle kuma mazan dake aiki, kuma yawanci ma sunfi shiga dangin mamansu. Daga nan bata ko kalli hanyar d'akin mama rabi ba wanda ke cike da mutane tayi kasa ta nufi kicin. Anan ta tarar gabadaya ma'aikatan gidan harda wanda ba b'angaren girki suke ba anata hada hadar abinci kala-kala da kuma snacks fal duk cikin umarnin mama rabi. Ta wuce can karshe inda mama azumi dasu lami ke packaging wasu snacks d'in a foil paper. "Farar mace alkyabbar mata, balle kuma in tasa jan kaya, haba wa!." "Kai mama azumi, kema ai jan kayan ne a jikinki." "Yo ke kya had'a fatar budurwa data tsohowa irina." Tayi murmushi sannan ta mik'a mata ledar. "Gashi inji inna." "Me muka samu....kinga kanwa mai kyau wallahi, a ina ta same ta haka?" "Wa ya sani...." ta fada tana d'anewa kan durowar data zagaye k'aton kicin d'in, bata ko kalli su lami ba dake ta faman d'auke kai suna maganganu don su nuna kamar basu ganta ba. "...Naji kamar tana kawo mata akayi. Mama azumi a d'an zubo min kad'an yunwa nake ji." "Kai uwata, na san fa tare kuka ci tuwon nan da inna, ina yunwa ta isa ta kamaki?" "Toh dan Allah a d'an bani ladan k'anshin da naji." "Haka dai zaki ce, kuma wannan ai ko baki fad'a ba." Ta yago foil paper dake hannunta ta shiga zubo mata su samosa da meatpie wadanda ke cike taf! da nama bisa umarnin mama rabi. Tana ci suna hirarsu da tare, don dad'i sai shilla k'afafunta take yi tana zuba santi wanda kesa mama azumin dad'a tsokanarta. "Toh ga fa 'yan gona nan sun dawo." Mama azumi ta fada tana duban windon dake bayanta, nanne na juyawa ta ci karo da samarin gidansu kaf! Su tara, har kuwa da yaya Ahmad da yaya ibrahim masu aure, sun sako baffa a tsakiya kowanne cikin shadda mai kyalli da hula kalar kayansa, baffan sai murmushi yake yana yiwa ya Ahmad magana, idonta ya kai kan 'yan biyu da suka yi ankon shudiyar shadda daga gefen yaya umar, kamar kodayaushe suraj ya had'e girar sama data k'asa kamar me shirin lailayo zagi, ta inda ake gane su da salim kenan don shi ba laifi yana da d'an sakin fuska. Cikinta ya bada k'ara lokacin da tayi saurin juyowa don kar su ganta, mama Azumi kuwa sai fadi take. "Masha Allah, masha Allah...Allah ya bawa kowannen ku zuri'a irin haka kuma." Ta had'iye abinda ke bakinta kafin tace. "Haba dai in kowannensu ya sami 'ya'ya irin haka, ai ina jin sai mu shiga tarihi a matsayin zuri'ar da suka fi kowacce yawan haihuwa." "Yo ai ba abin gudu bane uwata, 'ya'ya fa suna d'aya daga cikin rahamomin duniya." Daga nan ta juya tana bawa su lami odar a shiryawa 'yan mazan abinci don ta san yanzu kowannensu zai fice ganin mata sun fara cika gidan. Nanne ta dad'e a kicin d'in tana ta ganin hada-hadarsu kafin Rahma tazo ta tarad da ita. Rahma ita kadai ce k'awar da take da ita bayan kawarta ta makarantar boko Amina, jikar d'aya daga cikin tsofaffin ma'aikata gidan ce wadda ake kira da hajiya, a yanzun haka ita hajiyan ta rasu sai babar rahman ce ta maye gurbinta kasancewarsu masu k'aramin hali, wanda a yanzu shekara biyar kenan tun rahman na 'yar karama take zuwa da ita har ta fara wayon da take d'an kama mata wasu abubuwan, dalilin da yasa ma kenan ya zama kullum tare suke zuwa, don gidansu ba nisa daga nan. K'awancen nasu ya fara ne tun suna k'anana lokacin da kowannensu bai san ciwon kansa ba, in sunzo za'a had'u dasu zainab da nannen ayi ta wasa wani lokacin ma har da sadiq da yazama sune sa'anninsa. Sai dai tsakanin nannen da rahma ne kawai abotar ta d'ore saboda ita rahman tana da tsananin hakuri, tana jure duk wani rashin mutunci da abubuwan da nannen ke saka ta har zuwa yanzu da don kanta take ragwanta mata ganin irin hak'urin da take yi da ita. "Wai tun d'azu dama kinzo ina nan inata jiranki?" "Kiyi hakuri yau aikin gidan ne da yawa, kin ganni ko hijabi ban cire ba wallahi tun zuwanmu." "Toh ya zancen zuwan? Zamu je fa." "Ki bari dai zuwa d'an anjima in anci karfin aikin, yanzu in na tafi mama zata iya yin magana." "Saboda ke sai a kasa yin wani abin, kin san fa anjima 'yan kawo lefe ne zasu zo, gidan k'ara cika zaiyi." "Toh bari in gaya mata inji." "Ki dai wanke hannunki bari inje in d'auko mayafina." Ta mik'a mata ragowar meatpie da samosan hannunta kafin ta diro k'asa. "Nagode." Ta k'arb'a da murmushi. Nanne na d'age labulan kofar d'akinsu tayi turus! Ganin 'yan mazan gabadaya sun baje a cikin falon, inna na daga tsakiyarsu tana ta washe baki, kowannensu kuwa ya d'ago ya kalli kofar d'akin harda yaya sulaiman dake maitar danna waya. Ta had'iye yawu lokacin da yaya Ahmad ke fad'in. "Ke dama kina nan?" Duk da da gabanta dake fad'uwa a ranta saida tace. "Ina zani nida gidan ubana." Tayi kamar ta juya ta koma amma muryar hadiza ta katse ta daga baya. "Zamu wuce." Ta juya ta gansu kusan su biyar d'auke da manyan-manyan tire shak'e da kayan abinci. Ba musu tayi cikin d'akin, sannan ta dan durkusa ta gaishe su lokacin da ake ta faman dire musu abincin. "ke zo nan!" Tar! muryar suraj ta kirata a cikin hayaniyar da aka fara ta zuba abincin, ba damar tace bata ji ba don saboda wani tsautsayi yana magana ta kalle shi. "An shanya min kaya a baranda jiya kuma daga nan ba'a gansu ba." Ya fada kamar mai bata labari bayan ta isa gabansa, zuciyarta cike da tsoro ta daure tace. "Toh ni meye had'ina da kayanka?" A cikin hayaniyar nan suka tsinci muryar innan na fad'in. "Surajo me tayi maka ne?" Bai ko bi ta kanta ba yace. "Kije ki d'ebo min su yanzu kafin in mik'e in fasa kanki." ya fad'i kalmar fasawar kamar zata fashe da bakinsa. "Ban gane ba, kana nufin ni na d'auka? Toh ni ba barauniya bace, kuma ko zanyi sata ma sai in k'are a kayanka..." Kafin ta rufe bakinta kuwa taji saukar wani azababben mari a fuskarta wanda ya taho tare da salatin inna. "Kai meye haka?" Yaya Nasir da yaya umar suka had'a baki wajen fad'a, nanne ta rusa wani irin kuka da rabinsa na k'arya ne. "Me tayi maka?" ya muhammad ya tambaya, kafin ya amsa kuwa inna ta karbe. "Me ko zata yi masa banda tsananin azaba irin tasa." "Nace me tayi maka?" ya muhammad ya sake tambaya. A dak'ile ya amsa. "Yaya kayana na shanya a courtyard ta d'ebe." Kafin a tambayeta nanne ta k'ara rushewa da kuka tana fadin wallahi tallahi k'arya yake ita ba abinda ta dauka. "Kai dama tana d'aukan kayan ka ne?" yaya Ahmad ya shigo zancen. "Ba wai tana d'auka bane, na san ita ta d'auka don ita kadai ce a wajen lokacin da aka shanya." "Toh ai hakan baya nufin ita ta dauka...ke kuma kar in sake ji kince k'arya yake, tashi ki tafi." Dama abinda take jira kenan, saboda haka yana fad'a ta mike tayi ciki. "Guda nawa ne kayan?" Taji yana tambayar suraj bayan ta shiga d'aki. Ta wanke fuskarta sannan ta yafa d'an karamin mayafi lightbrown akan doguwar rigar, ta nufi wajen kayan wankinsu ta janyo kayan suraj d'in dake can k'asa ta cusa su a bak'ar leda tana fadin.. "Kai da kayan nan har abada wallahi." Ta fito har a lokacin suna hayaniyarsu ana ta dariya, kanta a mik'e ta fita, Allah yaso idon inna bai hango ta ba lokacin ta juya tana ganin adadin abincin da yaya ibrahim ke zuba mata. Tana sauka k'asa ta tarar Rahma na jiranta a bak'in k'afar bene. "Me tace?" "Tace dai kar mu dad'e, don wai an tafi markad'en Alala zamu yi k'ulli." "Ai dama ba dad'ewa zamu yi ba, abinda ya kaimu kawai zamu yi." Ko dai abinda ya kai ki. Rahma ta fad'a a zuciyarta. Don inda zasu je d'in gidan wata 'yar islamiyarsu ce Hafsa, a sati biyun da nanne bata je makaranta bane hafsan ta tada ballin cewa nanne na neman kwace mata saurayinta, wanda kullum aka tashi zai zo ya raka ta gida. Ta dinga masifar cewa wai duk sanda aka tashi sai ta dinga binsa da kallo wani lokacin ma harda murmushi. Abin ya zama topic d'in ajin nasu kullum sai an tada zancen da za'a zazzage ta, ganin ma taki dawowa yasa suka rubata takarda aka gaya mata bak'ak'en maganganu sannan aka bawa safiya ta kawo mata shekaranjiya da yamma, jiya kuma ta titsiye rahma sai da ta gaya mata dukkan abinda yake faruwa da bata nan. "Zamu biya ta shagon khalid kafin muje." "Wane khalid?" "Mai shagon bakin titi mana." Khalid irin 'yan karyar samarin layin nan ne da ba abinda suka sani sai d'aukan wanka, iyayensa masu rufin asiri ne daidai nasu, amma shi inda yake kai kansa yafi haka, shagon da yake dashi ma na soft drinks da recharge card wani Alhajin layinsu ne ya bud'e masa. Dalilin haduwarsu da nanne kenan wajen siyan lemo. Suna isa kuwa ya tsuke bakinsa yana murmushi, kafin ya fito ya fara shafa sumar kansa irin ta fulani. "Kin b'uya fa, kwana wajen shida kenan ban ganki ba." "Shida?"... Ta zare ido tana kallonsa. "Har wani kirgawa kake?" "Sosai ma, ke d'in ai ta daban ce." Ta tab'e baki kafin ta mika masa ledar hannunta. "Kaga rik'e, kaya ne na kawo maka ban sani ba ko zasu yi maka?" "waww! Ai ko nagode sosai zasu yi ma insha Allah..." Ya d'ago ya kalleta, idonsa d'aya a kanne. "Thank you, har na hango ni a ciki." "Wai me yasa kika damu da Khalid d'in nan ne." Rahma ta tambaya bayan sunyi gaba. "Saboda bashi da matsala, kuma yana yin duk abinda nace." Ta amsa kanta tsaye wanda kuma hakan ne, in dai mutum zai jure halinta ya kuma dinga yi mata biyayya toh fa zasu yi shiri dashi. Rahma bata kara cewa komai ba, tunda ita ta san abinda khalid ke tunani daban ne, don har ya fara yad'awa a unguwa cewa nanne sonsa take yi, zaiyi auren jari. ●﹏● WAYE SHI? AYSHA SHAFI'EE 04 (☆_☆) An kawo lefe kamar yadda kowa ya zata, akwati goma sha shida da kuma bayanin cewa bayan auren a can nijar jamilan zata zauna, anci an sha a gidan kamar gidan biki sannan kuma an tarbi mutanen nijar cikin girmamawa kafin su tattara su tafi wani guest inn dake bakin titin unguwarsu inda baffa ya kama musu d'akunan kwana. Su mama rabi an samu abinda ake so, wato lefen 'yarta yafi na kowa, don na Aisha guda goma sha biyu ne, nasu maryam da nafisa kuma takwas-takwas. Saboda haka sai washe baki take yi anata hidima. Duk wannan abin ya faru ne bayan an gama tashin hankali da bala'i a gidansu hafsa, inda nanne ta rufe idonta ta zage ta tas! a gaban 'yan gidansu, ba don rahma bama da abin ya kaisu harda kokawa don sun tarar maman su hafsar da kishiyarta basa nan sai 'yan matan gidan kawai, amma duk da yawansu ba wanda nanne ta kyale a cikinsu, sai da rahma taga abin zai koma kokawa sannan ta jata da kyar suka bar gidan. Suna zaune bayan sallar isha a barandar dake kofar kicin itada Rahman dake b'arar maggi, ta sake yin kwafa tace. "Na rantse da Allah rahma don dai ba zan iya kula wannan jagwal din yaron bane, amma wallahi da sai yarinyar nan ta zama 'yar kallo tsakanina dashi sai na mayar mata da tunaninta ya koma gaske." "Dan Allah ki bar maganar nan, tunda dai kinje kin ja mata kunne ai komai ya wuce." "Ba abinda ya wuce, in dai bala'i ne yanzu aka fara, saboda da sai wani satin nake tunanin komawa makarantar, amma wallahi ranar asabar d'in nan zanje muyi ta da sauran 'yan iskan k'awayen nata da suke biye mata, sai naci mutuncinsu d'aya bayan d'aya." "Kin san fa malam murtala ya dawo, wallahi aka kai masa ku kuna fad'a ba zai muku da sauki ba, don ranar litinin d'in nan kusan bulala talatin yayi wa su Anisa." "Ko d'ari zaiyi min wallahi sai nayi musu kacakaca a ajin nan..." Ganin bata da niyyar sauka yasa ta karkato da farantin kan cinyarta tace. "Allah ya kaimu asabar d'in toh....yanzu dai d'an taya ni b'arar maggin nan." Suna cikin yi, rahma ta sako mata zancen saurayinta daya nace akan zai turo iyayensa, ita kuma ta dage sai ta gama makaranta tukunna tunda dama ss3 zata shiga yanzu, tare dasu nannen. "Toh wai meye? Tunda dai mamanki ta yarda dashi ki bari ya turo mana." Rahma ta kalleta da murmushi. "Kalli wadda take cewa ba wani abu bane, ke da har yanzu ba wanda kika taba saurara...kuma kin san in dai za'ayi auren zainab baffa dake zai hada tunda ba dole sai kun fara jami'a ba, gashi ita tana da wani." Nanne ta tabe baki. "Nifa na gaya miki harkar samarin nan duk wahala ce, ni in zanyi auren ma cewa baffa zanyi kawai ya zabo min babban mutum mai hankali, don duk samarin nan 'yan duniya ne." "Haka dai kike gani don baki taba tsayawa kin saurari wani ba, ga masu son miki magana da yawa." Da jin haka, idonta ya hango mata fuskarsa, wani mutum guda daya da ta kasa cire shi daga tunaninta, tun ranar data fara ganinsa har yanzu da baya nan, yanzu da take jin kamar tana kewarsa, kewar yadda take ganinsa tsaye a kofar gidansu duk sanda ta dawo daga islamiyya, a saman mota yana danna waya ko tare da abokansa. Yawanci iya haduwarsu kenan, sai ko da safe wani lokacin in zasu makaranta ta hango shi ya dawo daga morning training, ita ko sanin gabadaya 'yan gidansu ma bata yi ba don bata taba shiga ba, duk da cewa yanzu zasu yi kusan wata hudu da dawowa, kuma wata k'anwarsa ma sun saba da safiya don ta shiga islamiyarsu. "Wai tunanin me kike?" Rahma ta katse ta. "Ba komai, me kike cewa?" "Wannan purple jakar ta lefen aunty jamila tayi kyau sosai, kinga d'an flat takalminta kuwa?" Daga nan ta shiga santin abubuwan ciki, wanda a lokacin da ake d'agawa ita nanne hankalinta ya tafi wajen zirawa Aunty nanah (k'anwar mama rabi) fara cikin rigarta, don sun kusa yin karo da ita a hanyar bene ta zageta har tana fad'in tayo halin rashin mutunci irin na Nuratu mahaifiyarta. Ai kuwa ba'a gama ganin kayan ba, ta hau make-make a jikinta, kafin ta tashi da gudu tayi d'aki. ***** ***** Sati d'aya bayan haka rayuwar gidan ta cigaba da tafiya tare kuma shirye-shiryen biki daga kowanne b'angare, don kuwa kowa ya dage wajen ganin bajintarsa tafi ta sauran saboda wata guda ne kawai ya rage ayi bikin, baffa ya saiwa kowacce amarya dank'ara-dank'aran gadaje guda biyu da kuma furniture saitin kujeru suma guda biyu, sai manyan-manyan tvn plasma da sauran kayan saitinsu. Sauran abubuwa irin na kitchen da kuma k'arin wasu abu na ado wannan duk na iyayensu mata ne, sannan ya bawa kowacce a cikin matan nasa dubu d'ari tasa gudunmawar don yaga take-takensu na cewar bayan events d'in daya had'a za'a yi gabad'aya, kowacce na shirin kama waje tayi wani bikin da 'yan uwanta. Hatta Aunty amarya saida ya bata dubu hamsin yace tayi d'inki itama da 'ya'yanta. Don haka a kowacce rana gidan cike yake da mutane na 'yan uwa dake zuwa anata faman hada-hada tsakanin gidan da kasuwa. A lokacin an koma makarantar boko daga dogon hutun da akayi na sabon zango, wanda su nanne suka shiga aji shida itada sadiq da zainab, safiya kuma na aji uku, surrayya ce kad'ai a ajin na k'arshe a primary. 'yan biyu kuma sun sami abinda suke so sunyi candy, sai aikin baccin safe kamar baza su tashi ba, da yamma kuma su tafi ball ko yawon eatery da abokai. Da safe nanne na zaune a falo ta hard'e k'afa d'aya kan daya tana shan tea, uniform d'in makarantarsu ne a jikinta na farar riga da bak'in wando, ba d'ankwali a kanta sai jelar manyan kalbar da rahma tayi mata sun zubo har k'asan kafad'arta. Inna ta juyo ta kalleta daga kan sallayarta data gama lazumi. "Yanzu nanne baza ki dubi girman Allah da magiyar da nake miki ki tsefe kalbar nan ba? Tafi sati biyu fa akanki." Ta yamutsa fuska. "Inna na fad'a miki sai na wanke kan ne kafin in sake kitson kuma wankin wahala yake bani, so nake in samu lokaci inje saloon tukunna." "Ai shikenan. sai kiyi ki gama kafin su fara jelan kiranki." Tana rufe baki kuwa safiya ta shigo falon, ta durkusa har k'asa ta gaishe da innan sannan tace. "Nanne tun d'azu fa muke jiranki, kowa ya fito kuma yaya umar ne zai kaimu yau." "Yaya umar?...ina idris d'in?" "Wai ya aiko bashi da lafiya." "Toh maza tashi, don kin san halinsa." inna ta fad'a da sauri. Ta zura hijabi sannan ta dauki jakarta tare da safa da dankwali tabi bayan safiya, tun daga waje sadiq dake zaune a gaban sienna da ake kaisu ya langwab'e kai yana mata murmushi, hakan ya tabbatar mata sun dad'e suna jiranta kenan. Suna isa safiya ta shige baya sannan ta zauna a kujerar gefen surrayya ta rufe kofar motar, umar ya ajiye tab d'in da yake dannawa a gefe sannan yayi magana ba tare daya juyo ba. "Ke kina jina?" "Eh." Ta fada kanta tsaye. "Idan kin dawo kije wajen mama Azumi ki karbi key din d'akina, ki gyara shi tas! Ki wanke band'akin, sannan kuma for the whole week ni zan dinga kaiku makaranta, idan kin ga dama ki bari kullum in dinga riga ki shigowa motar nan." Yana gama fad'in haka yaja motar suka yi gate, ta had'a ido da sadiq ta cikin mudubi ya sake sakar mata murmushi motsin fatar bakinsa na fad'in 'yan mata! Ta gallara masa harara kafin ta sunkuya saka safarta. Suna isa makarantar ta tarar har malami na farko ya shiga, wata malamar biology mai tsanani rashin son surutu ta juya kan allo tana rubutu, bata bari ta ganta ba ta shigo a hankali ta wuce bencinsu ita da Amina, dukkan 'yan ajin na kallonta ba wanda yayi magana, don duk da cewa ba tsoronta suke ji ba kowa yana d'an shakkar surutun ta, irin dai karar da akewa mutum mai baki. Tana zama Amina tasa hannu ta cusa mata jelar gashinta da ta fito ta gefe. In da akwai abinda ya banbanta halin nanne da Amina to rashin kunya ce, saboda ita magana ce kawai da ita amma bata da rashin kunya irinta nanne. "Ya akayi yau kika zo da wuri?" ta tambayeta a hankali. "Azababben yaya umar ne ya kawo mu wallahi." "Ina idris d'in?" "Wai bashi da lafiya." "Kice kin daina missing first period." Taja guntun tsaki. "Wai a tunaninsa ma fa haka na makara ban fito ba." Amina ta d'anyi dariya kafin tace. "Zaki saka mai wani sabon tunanin ne." "Ke bari a fita break, akwai maganar ma daza muyi." "Haba? Ko munyi first catch ne?" Ta juyo daga kokarin d'auko littafin da take, ta gallara mata harara. "Ke dai 'yar iska ce, baza a taba wani abu a duniya ba sai saurayi." A daidai nan malamar ta juyo ta kalle su. "Surutun me kuke yi?" Ta tambaya da turanci. Kai tsaye Amina ta d'ago tace. "Malama rasuwa aka mata ne shine nake mata gaisuwa." "Ajin nawa ne gidan gaisuwa?" Ta sake gyara murya tace. "Ma, ai yadda mutuwa take zuwa ko'ina haka gaisuwarta ma ana iya yi a koina." Ta kalle ta da mamaki kafin ta nuna musu hanyar kofa. "Toh ku fita waje kuyi zaman makokin." Inda sabo dama hakan yasha jawo musu fitowar bakin aji, don Amina irin mutanen nan ne da basa taba rasa amsar fad'a, ko waye mai tambayar kuwa. Har sun kai k'ofa ta tsaida su da tambayar waye ya rasu, Nanne tayi rau! da ido kafin ta amsa da kazar da take kiwo ce, abinda ya jawo dariyar gabadaya ajin kenan wanda ya jawo musu kneel-down a gaban aji, next period ma english ba suka shiga aji ba, tunda malaman k'awaye ne haka suka zauna har aka fita break. Da break d'in ma basu samu damar maganar ba saboda haduwa suka yi da 'yan click dinsu akayi ta hira kala-kala, wata maryam tayo musu dan malele ana sha ana cafta. Bayan an kada kuma suka tafi wanko farantan da suka aro a kicin din makarantar, suna dawowa kuma aka tafi physics lab, suka ci uban note sannan aka fara practical, last period ya kasance geography ne, wani malami mai azabar dictation shima. Sai da aka tashi sannan suka tsaya daga k'asan wata bishiya a harabar parking lot din inda ake d'aukarsu. Nanne ta kalli Amina sosai tace. "Ta yaya aljanu suke shiga jikin mutum?" Amina ta d'an had'e girarta. "Ban gane ba, nifa ba malama bace." "Dalla ina nufin kamar yanzu ni in inaso aljanu su shiga jikina me zanyi?" "Sa'adha aljanu? Me zaki yi dasu?" "Wani malami nake so na waskawa mari a islamiyarmu." "Me yayi miki?" "wai kawai daga cacar baki ta had'a mu da wasu mahaukatan yara a aji, ya kama ya mana bulala ashirin-ashirin." "Toh kiyi na k'arya mana, me zai sa ki jawo wa kanki bala'i?" "Malamin ne mugun d'an izala ne, yanzu sai ya iya ganewa." "Wallahi ba ta yadda za'ayi ya gane tunda aljanu dai ba ganinsu ake ba, kuma a yadda na sanki zaki iya, kawai abu d'aya ne kar ki tab'a bari ya dake ki da sunan ruk'iya tunda kin san ke za'a jibga." Ta d'anyi shiru tana tunani. "Kuma fa hakane, ba dai ihu ake ba da zare ido?" "Sannan ki cire d'ankwalinki ki tsaida idonki tar! ko waye yazo kar ki nuna kin sanshi ma balle wani tsoronsa, ki zagi duk wanda kike so kuma." Nanne ta tsaida idonta waje d'aya, tunaninta na hasko mata ita a hoton da Amina ke zanawa. **** **** BAYAN SATI BIYU. Da maghriba ta dawo daga bayan layinsu gidan wata hajiya talatu, ta karbowa inna tarin adduwa a cikin bakar leda wai ta gaji da cin goro. Tana tafe tana cilla ledar a hannunta, layin ko'ina da haske saboda wuta da aka kawo a lokacin kuma babu mutane da yawa, daga tsillin masu wucewa sai masu gadin gidaje da suka fito waje da 'yar rediyonsu. Cilla ledar da zata sake yi sama sai kawai ta yage a daidai sanda ta karyo kwanar layinsu, gabadaya adduwar ta tarwatse wasu ma suka shiga gangarawa cikin kwalbatin dake gefenta, taja karamin tsaki. "Ai wallahi dama na san sai ledar nan ta yage, matar nan tana tab'a bada wani abin arziki ne?" Ta tsaya tana kallonsu kamar su zasu kwashe kansu kafin ta tsugunna ta shiga bin wadda bata fada kwalbatin ba tana sakawa a hijabinta. "ledar bata da kwari ne?" Kamar a irin tunanikan da take yi kunnenta ya jiyo mata wannan muryar, wannan muryar mai taushi daga bayanta, ta juya da sauri daidai sanda yake kokarin tsugunnawa. Yana sanye da farar t-shirt da kuma farin wando, ya kara wani fresh akan yadda ta sanshi a baya. Bata san lokacin da ta d'aga kanta ba. "Ina jin dama ta fara yagewa." "Ko kuma kin cilla ta sama da yawa." "Cillawa sama ba zai sa ta yage ba." "Inji wa? Bayan da nauyi a cikinta." Ta mike tsaye rike da karshen hijabinta. "Watakila baka san adduwa bane, amma bata da nauyi." Ya karaso gabanta hannayensa cike da wandanda ya tsinto. "Na san adduwa mana harda sauran 'yan uwanta, su taura, magarya, d'inya da kuma d'ayan mai kwallo da yawa a ciki." Ta daga siririyar girarta d'aya. "Kad'anya...?" "Right! Kad'anya." Ta girgiza kanta alamun ta gane sannan ta kalli hannayensa tace. "Nagode." Maimakon ya zube mata a ciki, sai ya zaro handkerchief daga aljihunsa ya zuba a kai, sannan ya kwashe na hijabinta ma sannan ya fara tafiya, ta kalli bayansa kafin ta bishi. "Sunana Imran, baki taba gaya min naki ba." Tayi shiru kamar baza ta amsa ba. "Baka taba tambaya ba." "Baki taba bani damar tambaya bane." Ta kalle shi da gefen ido. "A ina kake ganina?" "In dai ina garin nan kullum ina ganinki, da safe in zaku tafi makaranta, da rana in zaki je islamiyya, da yamma in kin dawo...ko kuma sau da yawa in kin fito keda k'awarki." "Ta yaya kasan duk wannan abubuwan?" "Abubuwan da na sani naki sun fi cikin kirga, d'azu ma kin raka inna asibiti wajen gashin k'ashi." Daidai sannan suka iso kofar gidansu, ya mika mata handkerchief din ta karba. "Zaki fada min sunan...?" Ta sauke gashin idonta kan hannayenta dake rike da adduwar. "...Don Allah" muryarsa a hankali ta fito. "Idan ka san duk wadannan abubuwan, sunana ba zai maka wahala ba, sai da safe." Tana fadin haka ta tura gate d'in ta shige gida. A ranar ko inna ta shaida cewa cikin farin ciki take. Sai dai kuma me? Ta kwana da wani matsanancin ciwon kai! ●﹏● WAYE SHI? AYSHA SHAFI'EE 05 (☆_☆) "Inna wai ina cokulan, nifa bangansu akan tray d'in ba." Nanne ta tambaya daga falo bayan ta dawo daga makarantar boko ta saka kayan islamiyya. Inna ta amsa daga cikin d'aki. "Toh watakila basu sako ba, don yau ance ba azumi bace akan rabon, iyami ce." "kuma a rashin hankalinta haka zamu ci abincin da hannu?" Don a yadda tsarin abincin gidan yake, duk matar da ranar girkinta ce, ita zata bada odar abincin da za'ayi ta kuma tsaya a kicin d'in har sai an gama an rarrabawa kowanne d'aki, har da 'yan mazan kowa tray d'insa daban mai d'auke da flask, plate da cokula harda jug saboda ba'a taba yin abinci a gidan ba babu abin sha, musamman zob'o kusan kullum akwai shi a gidan nan. Sannan ba wanda zaici abincin yace na gidan yawa ne don ma'aikatan gidan gabad'aya an bi musu da tsari akan tsafta, sannan ma girkin kamar gasa ya zama tsakanin matan, kowacce na son ace ranar girkinta abinci na dad'i saboda hatta baffa shi yake ci, bai taba son a banbanta nasa ba. "Kije ki karbo mana." "A wannan yunwar da nake ji yaushe zan iya sauka k'asa." "Toh ai sai kisa hannunki tunda daga wanka kika fito." Ta zuba abincin, ta koma kan kujera ta fara ci, idonta na kan agogo tana lura da lokaci. Bata san me yasa jikinta yayi sanyi ba duk da sun gama tsara komai ita da Amina, kuma ta dake ranta cewa zata yin, amma jikinta kwata-kwata ba kwari. Ta rufe idonta tana tauna abincin, haka kawai taji ko dadi ma baya mata, saboda haka ta rufe shi ta zura dogon hijabinta. "Ina zaki da tsakar ranar nan." "Islamiyya mana, kin manta tun wancan satin na koma." "Yaushe naji kina cewa canja ta zaki yi?" "Na fasa ai." "Ai miki wannan dukan kuma ki cigaba da zuwa?" Ta hadiye yawu cikin makogwaronta. "Inna ba lallai bane ma malamin ya kara shigo mana, bari inyi sauri kar su safiyya su tafi." Tunda ta isa cikin ajin nasu ba wanda ta yiwa magana, da yake ma kusan rabin ajin na jin haushinta akan dukan data jawo aka musu sai ba wanda ya kulata, iyaka kad'an dake binta da sannu kawai. Ko da rahama ta iso ma da ka kawai ta amsa tambayar data mata. Malamin fiqhu ya shigo ya biya karatunsa yayi bayani sannan aka fita sallah, ana dawowa malam murtala ya shigo aka fara bita, tunda aka fara kuwa nanne bata ko d'ago da kanta ba balle tayi karatun, har akayi izu biyar,  sannan ya biya k'ari yace suma su biya. A nan ma ta k'ara dankwafar da kanta ta, tun yana kyalewa har zuciya ta kawo shi yace kowa yayi shiru. "Sa'adha tashi ki biya karin da aka yi!" Bata ko motsa ba balle ta nuna taji me yace. Ya sake maimatawa ba wani canji, Rahma dake gefenta ta tabo cinyarta bata d'ago ba, gabadaya 'yan ajin sun juyo kowa na kallonta, ai kuwa bai k'ara magana ba ya janyo bulala yayo kanta, Rahma tayi saurin matsawa sanda ya k'araso ya sauke mata guda d'aya a tsakiyar bayanta. Ai kuwa tana jin vibration d'in bulalar a jikinta taji wani irin karfi da bata san tana dashi ba ya shige ta, kafin kwakwalwarta ta iya wani tunanin taji wata bulalar a jikinta ba shiri kuwa ta mike tsaye, ta fito bakin bencin ta tsaya daf dashi idanunta a tsaye kyam! "Keh baki da hankali? ni kika tsayawa a kai haka, koma ki zauna...nace koma ki zauna!" Tak'i zaman, ta tsare shi da dara-daran idanunta da bata san sunyi jawur ba, ya d'aga hannunsa ya k'ara mata wata bulalar, ba tare da tunanin komai ba kuwa nanne ta waska masa mari, mai kauri sannan ta cakumi wuyan rigarsa, ta d'aga shi sama har sai da kafarsa ta rabu da k'asa. Ajin gaba d'aya ya rude da ihu wasu kuma suka yi waje, malam murtala yayi-yayi ya raba hannun nanne da rigarsa amma ya kasa gashi bata ko ihu balle magana, sai zazzare jajayen idonta take yi ga kuma radadin marin na shigarsa. A haka wasu malaman biyu suka shigo suka ratsa ta cikin cincirindon daliban suka raba su da kyar. Tana sakinsa kuwa ta sulale ta fadi kasa kamar an zare wani abu daga jikinta. Aka fita da malam murtala, d'aya malamin kuma ya shiga bada umarnin a daga ta, rahama ce ta fara zuwa kanta tare da wasu mutum biyu, suka maida ita kan bencin. Nan fa makaranta ta rude daliban wasu ajujuwan suka dinga shigowa, malaman sukayi-sukayi kowa ya koma aji amma suka kasa, sai tururwar ganin nanne suke da kuma malam murtala da aka kai staffroom. Har aka tashi, Rahma da sadiya suka raka nanne gida bata san inda kanta yake ba, don wani irin ciwo yake mata da kuma juyawa. Saboda haka koda rahama ta cewa inna bata da lafiya ne, bata d'aga hankalinta ba ta barta ta kwanta. Tana yin sallar isha kuwa ta nemi kan gado, a lokacin tasha panadol ya kai hudu amma ba abinda ya ragu, da kyar ta samu bacci ya dauketa. A cikin baccin, tayi mafarki da fuskarsa, fuskar IMRAN, muryarsa mai taushi ta cika kunnuwanta, a hankali kamar sanda yake mata magiyar sunanta. Sai dai wannan karon sunan ya fad'a, sunanta kad'ai. "Sa'adha!." ****  **** "Wai don Allah meya same ki?" "Rahama nace miki ki daina zancen nan koh? Wai sai inna taji ne?" "Nanne abin ne ya bani mamaki, na san baki da aljanu, amma d'aga malam murtala fa kika yi har sama, ta yaya kika iya?" Nanne ta had'iye yawu, itama tun tashinta take wannan tunanin, ta rasa ya akayi taji wani irin karfi a daidai wannan lokacin, karfin da har ta iya daga mutum. "Nifa ban sani ba, watakila kawai don na sa kaina zanyi ne, saboda haka ni kawai kiyi shiru kar wani ma ya jiki." Tana fad'in hakan ta cigaba da cillo kayan wankinta daga cikin wardrobe. "Bari in gama hadawa ki tayani sauka k'asa dasu bello zan bawa wankin, na nasiru baya fita wallahi." "Nanne..." Rahma ta kira sunanta a hankali. "Su malam murtala fa sunce zasu zo gidan nan yau, d'azu na hadu da malam mukhtar yake ce min anjima zasu zo." Ta juyo a hankali rike da wata riga. "Zasu zo? Me zasu zo suyi?" "Wai hankalinsu ya tashi aljanin da ya shige ki mai karfi ne, malam murtala yace yaga alamunsa a cikin idonki." Sakan daya-biyu tana kallonta kamar abinda ta fada ya tsorata ta, kafin kuma ta kyalkyale da dariya harda rik'e murfin wardrobe din. "Kice malam yaji shak'a, wato a aljanun ma nawa mai karfi ne, aiko zan nuna masa wasu k'arin moves din da aljanin ya iya ne ma duk sanda ya sake dukana wallahi." Rahma ta girgiza kanta. "Yanzu toh ya zaki yi in sun zo?" "Yafi ince karya suke min, ba dai baffa zasu gayawa ba...kar su fasa Allah ya kawo su." **** Ya lumshe ido yana lokacin da muryar gefensa ke fita cike da bacin rai. "...me yasa kake tunanin yin abinda ba zai tab'a yiwuwa ba? Me yasa zaka fara abinda ba zai d'ore ba?" Ya ciza gefen lebb'ensa yana sauraren yadda iskar saharar ke kad'awa da karfi. "Tana da kyau jamil, idan tana fad'a zaka ga kamar lebbenta zai koma ciki ne." Jaamil yaja tsaki kafin ya sulale yabi cikin iskar saharar. ●﹏● WAYE SHI? AYSHA SHAFI'EE 06 (☆_☆) A daidai kofar shiga falon baffa nanne ta tsinci muryar ya sulaiman cike da bacin rai yana fadin. "A tunani na baffa gwara a takawa yarinyar nan birki wallahi tun yanzu, abubuwan nata sun fara yawa." Bata bari baffa ya bashi amsa ba ta murda handle din kofar ta shiga, sulaiman din ne kuwa zaune a katon falon yayin da baffa ke daga can karshe kasan kujerarsa, jaridu kusan uku a gefensa da kofin coffee dinsa. Ta zube daga tsakiya tana gaishe shi, fuskarsa ba yabo ba fallasa ya nuna mata gefen hagunsa, ta mike ta koma can. Ba yadda sulaiman ya iya dole ya fita don ya san baffan baya bukatarsa a lokacin. "Sa'adha me ya faru a makarantarku jiya?" Muryarsa taso ta yanke karfin gwiwar da ta shigo dashi, ta hadiye yawu a hankali kanta na kasa tace. "Wace makarantar? Islamiyya ko boko?" "Islamiyyarku ta bayan layin nan." "Babu komai, jiya ma da wuri aka tashi." "Ya akayi akace kin mari malami jiya?" Da saurinta tace. "Duk wanda ya gaya maka karyane baffa, ni ba abinda nayi." Ya gyara zamansa yana kallonta sosai. "Baki san kin mare shi ba?" Ta d'aga kai. "Kenan in yarda da abinda malamanki suka fada?" Tayi shiru. "Nan wajen yayanki ya rako su suka zauna suna fada min wai ba'a hankalinki kika yi komai ba, aljanu ne suka shige ki kuma suna tunanin masu k'arfi ne." Ta bata rai, ta kirkiro hawaye. "Wallahi baffa karya ake min ni babu aljanin daya shiga jikina, kullum sai nayi addu'a kafin na kwanta." "idan haka ne sa'adha, toh me zaisa ki daga hannu akan malaminki, ni dai na san har ga Allah ba'ayi miki wannan tarbiyar a gidan nan ba. Wadda ta raineki ita ta raine ni, kuma na tabbata inna baza ta taba cewa kije ki mari malamin ki ba." Ta shiga rera kuka tsakaninta da Allah tana bashi hakuri, yayi ta nasiharsa akan girman malami da kuma girman laifinta kafin ya sallameta, sai dai har ta gama bashi hakurin ta fita, ransa bai dawo daidai ba. Tana zuwa daki ta tarar inna ta fara gyangyadinta na maghriba, ta shiga toilet ta wanke fuskarta tana fadin. Ta Allah ba taku ba, wato a tunaninku baffa yace ku tafi dani ayi min ruk'iya, a sami abin jibga...ba sai kun sake ganina ma a islamiyyar ba. Ta fito falo ta zuba abincinta sannan ta kunna tv. Abinda ya tashi inna kenan ta mike da salati. "Me ya sami idanunki suka kumbura?" ta tambaya tana kare mata kallo. Nanne ta dan ja tsaki, matsalar fuskarta kenan, ko hawaye tayi sai idanunta sun kada. "Ba komai, kaina ne kawai ke ciwo." "Ke anya lafiyar ki kalau kuwa? A satin nan sau nawa kika yi wannan ciwon kan?" Ta d'anyi shiru, duk da ba ciwon kan take ba amma abinda inna ta fada haka ne. Bata fiye ciwon kai ba amma kusan a satin nan sau uku tana yinsa. Anya lafiyar tata kalau kuwa? Sai kuma tayi saurin kawar da zancen kar inna ta shiga damuwa. "Watakila wahalar komawa makarantar nan ce, in zubo miki abincin ko sai kinyi isha?" Lokacin da taje jera kayan da aka kawo mata daga wanki, handkerchief din daya bata ya fado, ta sunkuya a hankali ta dauka, tun a wancan daren data ninke shi ta ajiye bata kara bi ta kansa ba, babu ko kanshin turare a jikinsa amma sai taji gabanta ya fadi sanda ta kaishi kan hancinta, wani irin faduwar gaba mai nauyi, kamar an cilla katon dutse cikin ruwa. Ta ware shi gabadayansa, anan wani mamakin ya tsaida numfashinta, d'an karami ne da baifi a dunkule shi ba. Toh amma yaya akayi a wancan lokacin ya d'auki tarin adduwar data yi kusan rabin leda? Adduwar da kusan sati d'aya kenan har yanzu bata kare ba? ***** Gari ya waye, rana ta bude a sararin sama. Yana bud'e idonsa yaci karo dana jaamil zaune akan stool d'in mudubin dake dakin. "Barka da tashi, ashe ka canja gida?" Ya mutsika idonsa. "Wallahi, kwana waje tara kenan da dawowa ta." "Allah ya sanya alkairi, bamu sani ba ai da munzo mun taya ka d'iban kaya." "Ai da yake abin ne yazo ba shiri, amma kar ka damu kanka ma ban debo komai na can ba, komai sabo na..." Bai karasa ba jaamil ya dauki wata kwalbar turare dake kan mudubin ya jefo masa, amma maimakon ta same shi sai ta wuce ta cikin jikinsa ta daki bango ta tarwatse. "Kwana na uku kenan ina faman nemanka yarima, ina tunanin ba gidan da ban shiga ba a garin nan." Imran ya mike zaune. "Toh saboda me zaka shiga nemana? na san dai ba wani abu ne ya taso daga gida ba." "Idan a wajenka babu wani abu, ni dole ne inyi taka tsantsan da kai don duk abinda ya faru Naani zata ce laifina ne." "Me zai faru? Ba dai zancen zamana haka bane kuma ta sani?" "Banda wannan, kaima ka san me nake nufi." "Baka yarda da rantsuwar da na maka bane?" "Ina tsoron sha'aninka ne yarima, don tunaninka daban ne." Imran yayi gajeriyar hamma sannan ya lumshe kyawawan idonsa. "Ka san me? Yunwa nake ji, bari in hada mana wani abun sai ka cigaba da gaya min maganganun daka saba, nima ina baka amsa da wadanda na saba...so, me zaka ci?" Jaamil ya girgiza kansa yana masa kallon Ba inda zaka. Mintuna goma bayan haka ya gaji da zaman d'akin ya bishi can kan dining d'in dake tsakiyar had'ad'd'en kicin d'insa (island). "Ga ruwan zafi nan a kettle sannan akwai differents tea-bags a cikin cabinet din can ka zabi wanda kake so." A wannan lokacin jaamil ya san hanyar kawai da zai iya samun had'in kansa shine ya biye masa, saboda haka ba musu ya nufi jikin durowoyin ya d'auko wanda hannunsa ya fara kaiwa kai sannan ya dawo ya zauna a kujerar dake fuskantarsa. Ya had'a tean kamar yadda yasha ganin imran na yi sannan ya shiga juyawa, idonsa na kan yadda yake ta cin kwan daya soya da fork yana kuma duba cikin wayarsa. "Me yasa ka tashi daga wancan gidan?" ya tambaya kai tsaye. Ba tare daya d'ago ba ya amsa. "Na fada maka kwanaki nayi mistake wani mak'ocina ya ganni na shiga ta jikin katanga, bana son suspense!" Jaamil ya gyada kansa. "Toh me yasa ka dawo nan wajen?" "Saboda ina son unguwar and yayi kusa da wajen aikina." "Kuma yayi kusa da gidansu." Da jin haka imran ya tsaya da taunar da yake da kuma danna wayar. jaamil ya sake maimaitawa. "Yayi kusa da gidansu yarima kuma ka sani." "Ka san me? lets get this straight..." ya dire wayar hannunsa da fork din. "...Ka kai karata wajen Naani, ka fada mata duk abubuwan da nake tunanin sirri ne tsakanina da kai, and yes! na yarda cewa nayi kuskure, nayi kuskure dana bari ta sanni har kuma nayi mata magana, sannan nayi rantsuwa ba zan k'ara zuwa kusa da ita ba, toh me ya kawo wannan zancen yanzu?" "Saboda ban yarda da rantsuwarka ba." ●﹏● WAYE SHI? AYSHA SHAFI'EE 07 (☆_☆) "Wai ya na gansu ne kala-kala?" Amina ta tambaya tana warwara katunan dake kan bencinsu. Nanne ta tsotse kwallon agwalumar bakinta tace. "Wai fa bayan events ukun da za'ayi kowacce sun had'a nasu daban zasu yi da yan'uwansu, shine baffa yace shi 'yanuwansa kala d'aya ne kuma dole zasu je na kowa don haka suyi a rana daban-daban." "Toh ai dates din sun hargitse min, kati wajen bakwai wanne za'a fara?" "Kinga fa, event din farko shine wankan amare ranar litinin, shi inna ce ta hada da daddare za'ayi, sai kamu washegari talata shima a gida za'ayi, laraba mother's eve na kowa da kowa a wannan event center din, Alhamis shine bikinsu hajiya Babba suma ga inda zasu yi, juma'a na mama rabi itama da wajenta, Asabar kuma nasu mama halime, sai lahadi a d'aura aure kowacce ta kama gabanta." "Tabdijam! Wannan ai gajiya zaku yi, bikin ba zai taba dadi ba." "Ko dai su gaji, an gaya miki kowanne zanje, ni kawai bak'in cikina za'a hana ni baccin safe weekend." "Toh ba kowanne zaki ba ni kika tattaro ki kawo min gabadaya?" "Ai wai ki zab'a ki darje, wad'ancan guda biyun fa na mama rabi da mama halime duk card admits ne, inda zaki san abin k'aranta ne, ita hajiya babba data isa babu wani sai da kati, kowa shiga zaiyi kuma yaci ya koshi." "Toh wanne zaki a ciki?" "Duk wad'anda za'ayi a gida ina nan, sai mother's eve da kuma na hajiya babba." "Biyun nan ne baza ki ba kenan?" "Gaskiya dai, kuma fa mama halime harda wani aiko min da anko." "Ke dai kawai ba kya son matar nan ne amma wallahi tafi mama rabi kirki. Bar ma zancen bikin nan, baki ban labarin ba." Nanne ta tsotse wani kwallon, tana tand'e baki. "In gaya miki sai ga sallama wai malam mukhtar ne yazo, inna har tana washe baki da taga zan fita ta zata na fara sauraren irin mayun nan ne masu nacin aike, na fita na gaishe da bawan Allah nan...ya kuwa hau bayani tiryan-tiryan wai wallahi akwai abinda ya same ni da ban sani ba, malam murtala har wace k'asa ce yaje akan sannin sirrin aljanu kuma wai wallahi ya ga aljani a jikina sanda na shake shi." Amina ta kyalkyale da dariya harda buga benci. "Na yarda dake wallahi sa'adha, nina san zaki iya shi yasa nace miki kawai ki zare idonki ki mari mutum!" "...mhmmm ina kaiki ke dai, ya gama bayanansa ya kawo wani k'ullin leda, wai ingattattun magunguna ne da aka kawo daga madina, dana wanka, na sha da madara ko nono, na shafawa a kai, na wace tsiya-wace tsiya, ni dai na karba nayi godiya, ina shigowa gida kuwa na jefa a sharar compound kar ma wani ya ganni dashi." "Ke amma fa sunyi kokari, magungunan aljanu fa ance da tsada." Nanne ta galla mata harara. "Toh in gaya miki a satin dana koma na bada kudin makaranta, na tabbata dashi suka siyo tunda sun san ba dawowa zanyi ba." Amina ta sake kyalkyalewa da wata dariyar. "wallahi ko hakane sunyi kokari, tunda zasu iya cinyewa." "Can musu da iyayi, ni yanzu abinda ke gabana daban." "Allah koh? meye a gaban naki?" A lokaci d'aya bugun zuciyarta ya k'aru, don duk duniya abinda ke d'an damunta guda d'aya ne, ji take yi kawai tana son sake ganin IMRAN, a kwanakin baya da bata ganinsa bata damu kanta haka ba, amma tun daga wannan 'yar maganar da suka yi shikenan kuma take jin wani abu kamar damuwa a ranta na rashin ganinsa kusan sati biyu. Gashi ba wanda ta sani da zata tambaya, k'anwarsa ma da take gani tare da safiya yanzu basa haduwa tunda ta bar islamiyyar,  ba sau daya ba, ba sau biyu ba tasha leka bakin gate da zummar ko zata ganshi, har ta gaji ta yardarwa kanta cewa da gaske baya nan, ya sake irin tafiyar da yayi kwanaki. Wai meye had'ina dashi ne ma da zan damu kaina da son ganinsa. Ta ayyana hakan a wani gefen zuciyarta lokacin da yatsunta suka matse agwalumar har saida wani kwallon ya bullutso. ***** Ya jingina da kujerar bayansa yana juyawa a hankali, idanunsa a rufe yana sauraren assistant dinsa dake gefe yana karanto report din karshen wata shida na ma'aikatarsu. Kwakwalwarsa na jin komai daki-daki yana saving d'insa, daga yanayinsa kad'ai wani zai zata shine shugaban kamfanin gabadaya. Kamfanin nasu na 'ORZ' dake kula da duk wasu harkokin talla da ake gudanarwa a media platforms da kuma billboards na kan titi. Ya bude idonsa da sauri sanda yaji wani abu daya dau hankalinsa. "Kaji koh? Kaji abinda nake fad'a masa exactly last six months?" Mr. Marvin ya rufe file din. "Shima ana kai masa result din abinda ya fara cewa kenan, yace abinda imran yake fad'a ya tabbata." "Ba irin bayanin da banyi masa ba a lokacin amma ya kasa fahimta ta, na fada masa 'G&M' ba kamfani bane da za'ayi trusting d'insu da makudan kudi haka, amma ya samu wannan yaron yana gaya masa kawai adadin hundreds din da suke biya per week, gashi nan yanzu just in a half year budget d'inmu yayi kasa da 20%, who knows me zai faru nan gaba?" "Ni naji fa ana cewa zai janye ne, kawai a maida contract d'in ya zama iya rabin shekara. Imran ya girgiza kansa. "Wallahi ba zasu yarda ba, ai yau ko karamin kamfani ne akayi wannan yarjejeniyar dasu baza su taba yarda da haka ba, kuma we can't force them tunda an riga an rubuta komai da sa hannu." Sunyi kamar minti goma suna tattaunawa kafin mr. Marvin ya mik'e. "Akwai wasu files da zanyi compling, sai na ganka anjima." Bayan fitarsa, Imran ya cigaba da ayyukansa, sai da yayi nisa sannan wata mak'ociyar office d'insa maryam ta shigo, ya d'an ja tsaki a k'asan numfashinsa, ko kad'an baya bukatar surutun ta a lokacin. Don a cikin mutane masu irin zuciyarta ma daban ne, yayi tunanin zata daina shiga hanyarsa tun lokacin da ya gaya mata kiri-kiri cewa abinda take tunani tsakaninsu ba zai taba faruwa ba. Amma sai ya zama kamar ba'ayi ba. "Good afternoon dear, aiki ne da kai yau haka?" Muryarta mai sanyi ta shiga kunnensa. "Afternoon." ya amsa a gajarce ba tare daya kalleta ba. Ta tsaya daga karshen bencin ta dafa hannayenta da suka sha kunshi akai. "Akwai wani project na oil company da shamsu yace min zamu yi aikinsa tare, an kawo maka ne?" "No, banyi signing akai ba, so yanzu ke dashi ne kawai zaku yi handling." "Amma saboda me? Zaka bamu guidance fa." ta marairaice murya. "kinga maryam..." ya d'ago da kansa. "In the next 3 months ma bani da aiki dake, kuma kina iya gani yanzu wani abin nake yi, so if you will excuse me." Ya nuna bayanta hanyar kofa. Da yake 'yar duniya ce ko a jikinta, sai kawai ta gyara zaman d'an mayafinta tace. "Okay, lets discuss something then...nayi zaton baka da relation a kusa kamar yadda yake a file dinka da komai, amma yau sai Allah ya had'a ni da brothernka." Ya had'e kakkaurar girarsa waje daya yana kallonta, itama ta nutsar da idanunta cikin nasa sannan ta kiftasu a hankali. "I'm serious Imran har kama kuke." Jin haka yasa gabansa ya fadi, don daga yanayin muryarta ya tsinci k'anshin gaskiya a ciki. Sai dai ya riga ya san halinta, sai ta gama juyashi kafin ta gaya masa gaskiya, kuma bashi da wannan lokacin da zai iya jiranta saboda haka a lokaci d'aya ya tsaida duk wani abu dake motsi a cikin office d'in sannan ya mik'e ya isa wajenta, jikinta ya sandare kamar a k'ank'ara ga hannayenta a iska, sannan bakinta slightly a bud'e alamun tana shirin yin magana ne, bugun zuciyarta ne kadai abinda ya rage mai motsi a tare da ita. Imran ya tsaya cak ya kalli cikin idanunta, nan take ya shiga ganin abinda ya faru da ita tun daga tashinta a yau har zuwanta office, ya dinga wuce mutanen data hadu dasu kala-kala da abubuwan data yi har zuwa sanda ta koma wajen motarta dauko wani flash, yaga sanda ta juya ta kalli wani kyakkyawan matashi dake mata murmushi daga gefen mota a dai parking lot na office dinsu, bai tsaya yaji maganar da suka yi ba yayi sauri ya nufi kofa, har zai bud'e ya tuna ya murza hannunsa, take komai ya dawo daidai. "Ko kana tunanin karya nake..." Maryam ta zarce da maganar data makale a bakinta. "Idan kin gama ki rufe min office din." Yana fada yayi ficewarsa. Ta juyo a kid'ime ta kalli kofar da tsananin mamaki sannan kuma kujerarsa. Yana isa parking lot d'in ya hango wannan matashin dai tsaye jikin motar nan kamar yadda ya gani a idanun maryam. "Wallahi na raina haukan yarinyar akanka, na zata tun sanda ta ganni zata je ta fada maka amma kusan mintuna talatin ina tsaye." Imran ya bashi amsa yana k'arasawa wajensa. "Waya sani ko tana tunanin canja shek'a ne tunda ta ganka." "Kuma ka san har number wayarta ta bani." "A ina ka samu waya?" Ya d'ago masa tsinken dake hannunsa. "Shi ta gani a matsayin waya." Ya girgiza kansa yana k'are masa kallo. "Wallahi daka san yadda kayi kyau, da kayi sujjada a wajen nan ka ta rokon Allah ya maida kai haka." "Bana son wannan zancen, kaima ka san ba don abu mai muhimmanci ba, babu abinda zaisa inzo nan." "Meya faru?" "Tafiya ce ta dole ta kama ni zuwa k'asar Nepal, kuma zan d'auki kusan wata guda don maganin da zanje karb'owa sai an hada shi tukunna." "Maganin waye?" "Bwama ce ke fama da ciwon b'arin kai." Imran ya girgiza kansa. "Ya salam, Allah ya bata lafiya...amma da kun gwada panadol yana aiki sosai." jaamil yaja tsaki. "Bani da lokacin rainin hankalinka yarima, abu d'aya ne ya kawo ni nan..." "Na sanshi..." Bai saurareshi ba ya cigaba. "Naani bata san da tafiyata ba, ka dubi girman Allah, ka tafi da komai daidai har na dawo, zuwa sannan na san baifi wata biyu ba mu huta da duk wannan wahalar." Imran ya cigaba da kallonsa gira d'aya a d'age, kamar akwai wani abu da bai fada ba yake jira. Jaamil yayi ajiyar zuciya sannan yace. "Kar kaje wajenta." **** Ranar Asabar tunda ya tashi yake gida yana ta harkokinsa, kwana biyu kenan yana rayuwar 'yanci tun tafiyar jaamil ranar alhamis, a yanzu bashi da wani mai takura masa ya san yayi nesa daga duk wani idon sani, jinsa yake kamar a farkon watanni hud'un da suka wuce, watannin da ya canja rayuwarsa gabadaya zuwa wata siffar da har yanzu ya kasa yardarwa kansa cewa hakan ba zai d'ore ba. Wajen karfe uku yana kitchen, ya gama cin abincin daya dafa, ya wanke kayan da yayi amfani dasu ya kife a dryer, sannan ya wanke sink din, yana aikinsa ya sauraren cool wakokin da yake so daga cikin bluethoot a gefe. Sai da ya kimtsa komai sannan yayi wanka ya shirya cikin wani light blue yadi mai kyau, d'an fitted dinkin kuwa ya zauna daidai a jikinsa, ya gyara sumar kansa sannan ya feshe jikinsa da turare, wanda ko bai sa ba kanshinsa baya taba barin kayansa. Kafin ya gama shiryawa ya kunna wayarsa tare da data, messages suka dinga kokawar shigowa kota'ina harda voicemail, yana danna na farko muryar maryam ta karad'e dakin. "Imran na kira ka several times wayarka bata shiga, please if you got this message call me, na kasa nutsuwa da abinda ya faru ranar thursday..." Ba bari ta k'arasa ba ya danna na biyu, muryar wani ta maye tata, ya cigaba da saurarensu d'aya bayan d'aya kafin ya fito falo, ya kashe Tvn dake nuna tashar football da duk wasu switches na gidan sannan ya fita. Bai d'auki mota ba don strolling kawai yake son yi yaga unguwar sosai. A wani masallaci dake can gaba da gidansa yabi jam'in sallar la'asar, ya dad'e ma a ciki yana addu'oinsa kafin ya fito ya nufi hanyar gida ta cikin wani layi mai yawan bishiyu. Sai dai me? yana shan kan kwanar yaji gabadaya duk wata jijiya ta jikinsa ta shiga aiki da sauri. Tar! idanunsa suka hango masa sa'adha ta fito daga wani k'aramin gida, fararen hannayenta sun sha jan k'unshi mai kyau, sannan ga bak'i a sama tana ta hura shi da iskar bakinta, tana yi tana wa k'awarta mitar zaman bin layin da suka yi, wanda duk da tazarar su yana jiyo komai. Saura kad'an yayi wani abu daya kusan manta shi a rayuwarsa, saura kad'an ya sulale yabi jikin bishiyar bayansa sanda idanunta suka d'ago suka kalle shi. ●﹏● WAYE SHI? AYSHA SHAFI'EE 08 (☆_☆) Da sauri ya janye idanunsa daga cikin nata sannan ya d'auke kansa yayi kwanar dake damansa, ya zaro wayarsa ba tare da ya ko juyo ba ya b'acewa ganinta. A lokaci daya nanne taji guntun murmushin da take shirin yi yabi iska, wani abu mai kama da mamaki ya maye gurbinsa, ta rufe idonta ta sake bud'awa ta kalli inda ya tsaya sannan kwanar da yayi, tabbas ba karya idanunta suka mata ba ya ganta, ya ganta ya kalleta sannan ya d'auke kansa yayi gaba. "Me kike kallo ne wai? Kizo muyi gaba baza mu sami abin hawa ba anan." Ta tsince muryar rahma daga nesa kamar ba'a kusa da ita take ba, ta juyo da sauri tace. "Rahma kinga mutumin daya wuce yanzu?" "A ina?" "Anan wajen, wanda yayi can kwanar da light blue kaya." "Anya? kin san na sunkuya d'auko kudin mota....waye shi?" "Wani ne." Ta fada a hankali idonta na kallon hanyar, kamar tana jira ya dawo ya fada mata dalilinsa na kin mata magana, Toh amma saboda me? Ta tambayi kanta, bata da wata alak'a dashi, me yasa in ya ganta zai mata magana? Don kawai ya taimaketa sau d'aya kuma ya tambayi sunanta a ranar? "Nanne muje mana la'asar fa ta wuce, ko sallah bamu yi ba." Ba yadda ta iya haka tabi Rahma da hannayenta a d'age suka yi titi. Har bayan magriba wani iri take ji a jikinta, ta rasa kuma dalilin hakan, ko don zuciyarta ta damu da son sake ganinsa ne a baya, yanzu kuma ta ganshi ya d'auke kansa. Ta dafe kanta sanda take zaune a kan kujera tana hango tarin 'yan aikin da suka baje a tsakar gida anata packaging sabulun salo dana magarya a roba wanda za'a rabawa mutane jibi ranar wankan amare. Tayi tunanin tashi daga wajen amma bata san inda zata ba, don koina a gidan cike yake da mutane, hatta dakinsu yanzu tarin 'yan niger ne fal, 'yan uwan inna tsofaffi sun had'u anata hirar yaushe gamo, inna ta basu labarin abubuwan da suka faru da ita, suma su bata nasu na can. Rahma ta d'ago mata hannu daga tsakiyar matan wai tazo ta zauna amma ta girgiza kanta. Abu na karshe da zata so yanzu shine ta shiga cikinsu duk da cewa anata irin hirar da take so ana dariya, don sun samu taimakon wasu 'yan niger masu barkwanci, amma zuciyarta ba dadi a lokacin. "Ko zaki taimaka mana da kujerar nan dan Allah kitso zamu yi." Ta juya taga wata mata tsaye akanta da kibiya a hannu. Ta san ta sarai daga cikin 'yan uwan mama halime take, su da suka fara zuwa tun cikin sati masu aurar da 'ya'ya biyu. "Gaskiya ba yanzu zan tashi ba." "A'ah uwata..." mama Azumi da zata wuce ta katseta. "...Taimaka ki basu mana, gidan ne yayi albarka duk kujerun an zaune." Kamar baza ta tashi ba, don dai kawai mama azumin ce yasa ta mike. "Ko kefa, zo muje ta kicin akwai abinda na ajiye miki." Dama yunwa take ji, don sun dawo daga kunshin ta tarar jollof akayi tun rana tayi shape din flask, ita kuma taki ci don babu ko zob'o tunda yanzu yawan gidan ya kai intiha. Ta tarar cake ne k'anana wajen guda takwas, ta karb'a da murna ta dauki ruwa sannan tayi wajen compound, ta samu k'arshen barandar d'akunan mazan ta zauna, ta zame dankwalinta saboda zafi da ake d'anyi a lokacin. Bata ci ya kai uku ba sanda taji Alamar an turo gate din gidan, wannan k'iii! din k'ofar ya shiga kunnuwanta, ta rufe idonta gami da d'an jan tsaki, don ta san in d'aya daga cikin su ya sulaiman ne yanzu za'ace ta shiga gida, musamman ace da wani abokinsu suka shigo. "Sa'adha..!" Wannan muryar mai zurfi da taushi ta shiga kunnenta, tana juyowa taci karo dashi tsaye daga d'an gaba da ita. Bakinta ya bud'e saboda mamaki, a lokaci daya taji zuciyarta da tayi sanyi ta shiga bugawa da karfi. Tayi saurin jawo mayafinta ta rufe gashinta. "Yaushe ka shigo? ta ina?" Ganin gashinta da yasha gyara dakuma hanbayenta masu kunshin nan yaso dauke hankalinsa, don sai da yayi shiru sannan ya amsa a hankali. "Yanzu na shigo ta gate." "Dama kana shigowa gidan nan?" "Wani lokacin ina zuwa wajen umar." ya nuna kofar d'akin dake gefenta. Ta mike da sauri kafin tace. "Ina ga baya nan yanzu." Bata jira komai ba ta juya tayi hanyar komawa ciki. "Sa'adha..!" "Ba wajensa nazo ba, ke nake son gani." Bata juyo ba ta girgiza kanta. "Ba zan iya tsayawa ba, in wani ya ganka za'a min magana." "I'm sorry, d'azu na ganki bamu gaisa ba ina sauri ne." Kanta yayi duumm! Ta kasa gasgata abinda kunnuwanta suka ji, da gaske shi din ne?  Ya shigo har compound d'insu don kawai ya bata hakuri? ta juya a hankali rik'e da plate d'in cake d'in. Yana tsaye kuwa, ya d'an biyo bayanta kad'an. Dogo ne sosai, ba fari ba sai dai yana da hasken fata irin ta murjewa, sumar kansa a dunk'ule take kamar ta jinsin larabawa, ta taho tun daga saje ta zagaye bakinsa, Ga wani irin k'anshi dake tashi mai dadi wanda tabbas daga shi din ne, Taji bugun zuciyartu ya karu akan da, kamar yana barazanar tarwatsa kirjinta. "Ba komai, sai da safe." muryarta da kadan tafi rada. Imran yayi ajiyar zuciya sanda ta b'acewa ganinsa, bai san me yake shirin faruwa ba dashi ba, amma zai daurewa koma menene tunda yanzu ya sauke wannan nauyin,  nauyin daya dame shi tun lokacin da ya ganta d'azu yayi tafiyarsa. A lokacin ya dake zuciyarsa ne cewa zai cika alk'awarin daya d'aukarwa Jaamil da Naani, na cewa ba zai bari wani abu ya shiga gabansa ba, zai tafi da tsarinsu kamar yadda suka shirya komai a farko, amma tunda ya koma gida ya kasa wannan dauriyar, ya kasa cire fararen idanunta daga ransa, yadda ta bishi da kallon mamaki  sanda ya juya, da yadda take ta kallon hanyar da yabi, yana iya ganin zafin dake cikin idonta tunda daga nesa. Rauninsa kenan a duniya, baya taba son ya zama sillar bacin ran wani, ya shigo cikin rayuwarta da salama ba zai so ace hakan ya zama rabuwarsu ba. Da wannan tunanin ya samu kwarin gwiwar zuwa wajenta. Ya gayawa kansa cewar abinda Naani da jaamil ke tunani ba zai taba faruwa ba don yazo wajenta sau d'aya, yana da enough focus d'in da ba zai taba zama distracted ba, sai dai ma ya zama distracted in wani abu na damunsa. Yayi saurin yin baya sanda wasu mata suka fito daga cikin gidan rike da kaya niki-niki, ya matsa wajen duhun rumfar adana motocin dake gefe, sannan ya bar wajen, a tunaninsa ya barshi kenan har abada. Sai dai kuma wata kaddarar bata ma soma ba! ●﹏● WAYE SHI? AYSHA SHAFI'EE 09 (☆_☆) "A daidai ina muka tsaya wancan karon?" Muryar da kaushi ta fita, cikin wani irin amo mai girgizawa, don yana iya ganin yadda 'yan k'ananan decor's d'in dake kan center table na gabansa ke jijjigawa. Imran ya d'ago da idonsa ya kalli manyan-manyan hallitun dake tsaye a bayan kujerar falonsa, basa bada ko karamin motsin da zai nuna cewa suna raye. A tsakiyarsu akwai wani dunkulallen haske dake lilo a iska, haskensa ya tarwatse ya baje ko'ina a cikin d'akin, daga kasa kuma jikin inuwarsa, wani tambari ne ya fito, tambari irin na adon sarautarta. "A ina muka tsaya yarima...?" Muryar tasa kowacce tsigar jikinsa mik'ewa, A kullum girmanta da matsayinta karuwa suke a wajensa. "Ki min gafara Naani, abinda kike tunani ko kadan ba haka bane, a wancan lokacin kinyi fushi ne dani sosai shi yasa na kasa miki bayani, amma an samu sab'anin fahimta ne tsakanina da jaamil, don kinfi kowa sani na a duniya, kinfi kowa sanin cewa ba zan taba yin abinda zai bata ranki ba." Maganarta ta fito a gajarce. "Ina saurarenka." Ya gyara Gwiwoyinsa dake zube akan tattausan carpet d'in sannan yace. "Farkon zuwana garin nan, na had'u da ita ne a layin da nake tunanin zama, daga baya na fahimci wajen yana da yawan jama'a sai na barshi, kuskurena na farko shine ban rabu da ita ba, na cigaba da bibiyarta bayan nan, kuskurena na biyu shine a lokacin da jaamil ya gane, sai na maida abin kamar sigar tsokanarsa, har nayi mata magana don ya gani, amma babu komai a raina game da ita, kuma tun a huduwarmu a baya nayi miki rantsuwa cewa ba zan kara zuwa kusa da ita ba." Shiru mai yawa ya biyo kafin murya ta sake fitowa. "Me ake ciki game da tsarinmu?" Ya lumshe kyawawan idonsa sannan ya amsa. "komai yana tafiya daidai, bana tunanin zamu kai watannin da aka d'iba don YA RIGA YA FARA YARDA DANI YANZU!" **** ~_~ Ta zama tazama...ta zama d'auko riga, tazama d'auko wando, ta zama tazama...ta zama dama furar nan...! ~_~ Wak'ar ta karade katon filin farfajiyar gidan su Nanne, wajen ya tsaru sosai kamar bashi ba, yasha ado da kayan al'ada na gargajiya kala-kala. Rumfar da amaren ke zaune a tsakiya akayi ta kuma ba'a shimfida komai a k'asa ba saboda 'yan kujeru ne irin na tsakar gida guda hud'u inda kowacce amarya ke zaune akan d'aya, a gefenta da katuwar roba da aka cika da ruwan d'umi, duk wanda yazo gaban amarya zai d'ebi ruwan ya watsa a jikinta, sannan ya ajiye gudunmawarsa a k'asan k'afarta wanda ake kira da 'kudin sabulu.' Amaren gabadaya farin zanin da inna ta sak'a sukayi d'aurin k'irji dashi sai da kowacce tasa farar t-shirt daga ciki kuma sunyi yafen farin mayafi. Sannan gabad'aya 'yanmatan da suka sa anko daga kowanne b'angare na amaren, ankon plane zani suka yi suma da riga buba. Nanne na zaune ita da Amina daga can kujerun baya suna cin gasasshiyar awarar nono wadda aka raba a wajen da kuma fura. Itama irin ankon 'yanmatan ne a jikinta, sai dai ba ko hoda a fuskarta kuma ta cokala d'auri gaban goshi. "Wallahi da kin fada min da nazo munje gidan kunshin nan tare, yaushe rabon hannuna da lalle." Nanne ta juyo daga kallon wasu 'yanmata a gefensu tace. "Nima rahama ce ta takura min, kwata-kwata banyi niyyar kunshin ba, kuma in gaya miki gidan d'an banzan layi kamar da sallah, tun wajen goma fa muka fita bamu muka dawo gidan nan ba sai bayan la'asar." "Ai baku yi jiran banza ba, ta iya wallahi." Nanne ta kalli hannunta sannan tace. "Kuma lallenta nada kyau, tunda fa tun ran asabar, gashi kamar yau akayi." "Ai gaskiya zanzo bayan bikin nan ki raka ni." Har Nanne zata ce wani abu wata murya ta tsaida ta. "Kinga dan Allah tambaya muke." Ta juya taga d'aya daga cikin 'yanmatan dake gefensu ce ta d'an juyo da kujerarta saitinsu. "Naga kamar kin san 'yan gidan nan ne?" Nanne ta d'aga kai tana kallonta. "Dan Allah kin san wannan?" Ta miko mata hadaddiyar wayar hannunta, Nanne na juyo da fuskar wayar taci karo da hoton Suraj tar! akan screen d'in. Wani hoto da salim ya dauke shi a jikin motar ya Ahmad, a ranar sati biyu kenan da bikinsa sunje gidansa gabad'ayansu ganin Amarya. Amina ta sunkuyo da kanta kad'an tace. "Ba suraj bane wannan?" Nanne ta mika wa yarinyar wayarta. "Eh na sanshi anan gidan yake." Da jin haka ta juya ta kalli sauran k'awayen nata biyu. "Kun ji koh? Na gaya muku wallahi shine...." ta dawo kan nanne. "Dan Allah yaushe ya dawo daga cyprus d'in?" "Wace cyprus?" "Inda yake karatu.." Nanne ta kalli Amina suka kyalkyale da dariya. "Shi yace miki a cyprus yake?" "Eh mana ba'a can yake karatu ba?" d'aya kawar ta tambaya. Nanne tayi k'okarin danne dariyarta. "Tsaya ma tukunna wane karatun?" "Degree mana..." Aiko bata k'arasa ba suka sake fashewa da dariya. "Dan Allah tambayarku fa muke..." Basu ko kulasu ba saida suka kyakyata mai isarsu sannan da kyar Aminah tace. "Yi hakuri, wallahi k'arya yake muku, kwanan nan suka gama waec da neco a makarantar mu." "Ke toh anya kuwa shine, shi fa har facebook account dinsa gabad'aya komai na can ne." "Ai shine..." d'ayar ta karba. "...Ba kince mana harda outside number yake kiranki ba?" Nanne ta kalle su tace. "Wallahi duk karya ce, in gaya muku nan ne gidansu kuma ni k'anwarsa ce, in baku yarda bama kuzo in kaiku ku gaishe da Babarsa." "Dan Allah da gaske kike?" Ta sake kyalkyalewa da dariya kafin tace. "Wallahi da gaske nake muku, d'azun nan ma ya gama fito da kayan wankinsa akan barandar can, ga d'akinsu can a kulle." Ba shiri kuwa suka matso da kujerunsu kusa dasu. Yarinyar tace. "Shifa ce min yayi a Abuja gidansu yake, toh d'azu da muka je sallah a cikin gidan sai naga wani family hoto a d'akin da muka shiga, harda wani a ciki kamar shi, muka yi ta doubting, shine fa na tambaye ku." Tana maganar kamar zata yi kuka, Nanne na k'ok'arin matse dariyarta amma ta kasa saboda Amina data sunkuyar da kai tana ta kyalkyalawa tana mintsininta. "Dan Allah ku bar dariyar nan, kuyi magana mana..." "Yo me zamu ce? Karya ce dai ya riga ya tafka muku, don wallahi makarantar daya gama ma a tsakiyar garin nan take ba wani waje ba, kuma ko result d'in waec d'insu bai fito ba balle ya tafi wata jami'a, kullum suna gidan nan shi da twin brother dinsa, in banda bacci ba abinda suke sai yawo..." Tun suna dariyar su biyu, har k'awayen yarinyar ma mai suna Ameerah suka bi sahun su, aikuwa basu rabu dasu ba sai da nanne ta sauke musu duk wani in and out na Suraj data sani, harda kuwa abinda yayi tun yana k'arami data ji labari. Bayan sun rabu dasu, suka matsa wajen rumfar amaren Aminah tace zata dauke su a hoto, suka yi hotuna kuwa masu kyu abin mamaki jamila sai washe musu baki take, lalle buri ya cika an samu abinda ake so, Nanne ta ayyana a ranta. Suna fitowa daga wajen, wayar Aminah tayi kara. "Anzo d'auko ta, sa'adha ba zanzo kamu gobe ba sai jibi ranar mother's eve." "Toh shikenan, bari in d'auko miki dankwalina ki taho min da mayafi kalarsa a wajen Aunty maimunah (yayar Aminan)." "D'an 3 thousand ko 5?" "Three d'in dai, an gaya miki kudi ne dani." "Toh yi sauri don Allah hashim azalzala ce dashi wallahi." "Kije wajen motar, zan same ki acan." Ta cikin tarin jama'a da kuma kujeru nanne tayi ta kutsawa har taje can k'arshe wajen fulawoyi inda inna ke zube akan carpet da jama'arta 'yan tsofaffi wanda basa iya hawan kujera. Da kyar ta samu innar ta saurareta saboda jama'ar da suka yanyanmeta anata gaisuwa da Allah sanya alkhairi. "Inna muk'ullin wardrobe zaki bani." "Me kika ce?" "Mukullin wardrobe wanda nasa a jakarki d'azu." "Yana ina?" "A cikin jakarki, na saka d'azu." Ta miko mata 'yar purse d'in hannunta gabadaya, ta d'auka sannan ta mika mata. Da kyar ta iya tsallake su ta wuce, saboda kowa duk'awa kawai yake ana gaida 'yan tsofaffin. Daga cikin gidan, sautin kid'an kad'an ake ji sannan ba mutane sosai, daga wajen kicin ne kawai da mutane suma kad'an. Har zata hau benen ta gano rahama da wata sun jawo buhun takeaway d'in sabulun salo,magarya da kuma turaren wuta wanda za'a rabawa mutane. Tausayinta ya kamata don wallahi tun yanzu ta san rahma ta gaji, sun aikatu sosai, ga kuma biki yanzu aka fara. Ta hango ta itama. "Nanne akwai na k'awayenki dana ajiye a kicin, bari mu kai wannan in d'auko miki." "Kinga ni mutum daya fa na gaiyata, kuma yanzu zata tafi ma, miko min d'aya kawai." Ta jikin hannun benen ta miko mata sannan suka yi gaba. Tun daga k'ofar d'akin nasu ta jiyo karar tv na tashi, mamaki ya kamata don ta san tunda satin bikin nan ya kama ba wanda yake kunna tvn. Ta d'an ja tsaki. Watakila ma yara ne, tunda kowacce ta jajibo 'ya'ya anzo an cika musu gida. Ta k'arasa ta kashe ta sannan tayi cikin d'aki. Ta bud'eshi da mukulli don shi a k'ulle yake saboda sha'anin biki, ta kunna fitila sanna ta bud'e wardrobe d'in ta shiga laluben d'ankwalin a wajen sababbin kayanta. Kawai sai jikinta ya bata alamun wani ya shigo cikin d'akin yana tahowa wajen wardrobe din. Ta rufe murfin ta juyo, sai dai me? Babu kowa. Ta d'an tsaya da mamaki sannan ta sake bud'e wardrobe din. Sai dai hannuta na kaiwa kan d'ankwalin ta sake jin alamun mutum na tahowa, ta tsaya tayi shiru tana saurare, sai da taji motsin ya karaso dab! da ita sannan ta sake rufe wardrobe d'in da wani irin sauri ta kalla..... Irin dai d'azu babu kowa ba alamun mutum, sai dai kuma idonta ya kula da kofar d'akin tana lilo a hankali. Ta janyo mayafin da sauri kawai ta fito, ta kulle d'akin sannan ta juyo, abinda ta gani ya razana 'yan hanjin cikinta. Tvn data kashe yanzu an sake kunnata, amma yanzu ba sound ko kad'an sabanin d'azu da yake kusan a k'ure. "Waye a d'akin nan?" Ta fad'a a fili tana kallon kowacce kusurwa. Shiru ya biyo bayan maganarta, babu motsi a ko'ina sai tvn dai dake ta aikinta tana nuna tashar cartoon. Tayi ajiyar zuciya sannan ta k'arasa ta sake kashe ta. Sai dai kuma me? Tana juyowa taci karo da kofar falon a rufe. Wani abu da rabon data ga anyi baza ta iya tunawa ba, don ko da daddare cikin d'aki kawai suke rufewa ita da inna. Sannan labulen ma da ya rufe k'ofar an d'age shi an mak'ale a gefe. Ta k'arasa da sauri ta murd'a handle d'in. A rufe take gam! Alamun da muk'ulli aka k'ulle! ●﹏● WAYE SHI? AYSHA SHAFI'EE 10 (☆_☆) Ta murda ta jijjiga, ba alamun kofar zata bude. Zuciyarta ta shiga dukan tara-tara don a cikin tunaninta ba zata iya tuna inda mukullan k'ofar nan suke ba, in ma suna nan din kenan. "Akwai mutum anan?" Ta daga muryarta da karfi ta kira. "Idan wani na jina dan Allah a bud'e kofar ta rufe dani." Shiru ba motsi, sai tashin kid'an waje da take jiyowa kawai daga nesa. Hannayenta dake rike da k'ofar suka shiga rawa, ta cigaba da tsayawa a wajen tana rarraba zuciyarta waje-wajen neman mafita, aikuwa take ta tuna da tagar dake cikin d'aki wadda zata fitar da ita jikin barandar saman, ta koma da sauri wajen ta shiga kokarin zura mukullin, sai dai bata kai ga sawa ba lokacin da hasken tvn bayanta ya sake kamawa, sannan muryoyin cartoon d'in dake magana da larabci ya karad'e ko'ina a d'akin. Ba shiri ta cusa mukullin ta murda sanna ta fad'a ciki, ta ture net d'in daya rufe tagar sannan ta dira waje, bata san cewa sauri take ba sai da ta kusa yin karo da wata mata dake kokarin shigowa gidan bayan ta sauka k'asa. "Ke hankali mana, bakya gani ne?" Bata ko bi ta kanta ba tayi cikin tururuwar mutanen ta nemi hanyar gate, kafin ta karasa kuwa ta hango Aminan na sake shigowa. "Ke na taho dubawa fa, kin dad'e wallahi." "Yi hakuri." Ta mika mata dankwalin da sauri. "Toh shikenan sai jibin, Allah huta gajiya." "Ameen." Ta amsa a hankali. Saboda saurin da Aminan keyi, bata ko lura da yadda jikinta yayi sanyi ba, ta d'an rungumeta kawai sannan ta juya. Daga nan mik'ewa tayi wajensu Inna, ta samu waje a gefenta ta zauna ta dunk'ule jikinta waje daya tana jinta wani iri, zuciyarta sai k'ara hasko mata da duk abinda ya faru take, tana ganin komai kamar Almara ko wani labari. Bata kara tashi ba sai tare su innan, lokacin mutane sun fara tafiya, sannan cikin gidan ma an daddawo anata kacaniyar sallar isha, don cikin d'akinsu ma sanda suka shiga wasu ne ke ta sallar a falo. Sannan tvn a kashe. "Nanne bud'e cikin d'akin muma mu dauro tamu alwalar." Muryar inna tasa ta kalli kofar d'akin dake k'ulle, wani yawo ya zarce cikin makogwaronta don ta san sanda ta bud'e bata ko tsaya rufewa ba ta fita, ya akayi yanzu take a rufe? Kawai sai ta matsa kusa da innan sosai tace. "Inna akwai wanda keda muk'ullan d'akin nan ne bayan na wajenki?" "Kamar k'ak'a? Da kika shigo kinga an d'auki wani abu ne? Shi yasa fa nace dake tun shekaranjiya ki maida duk wani abu mai amfani cikin d'aki saboda mutane ba kowa ne...." "Inna ba wani abu aka dauka ba.." tayi saurin katseta kar mutanen gefensu suji. "Toh menene?" Har ta bude baki zata ce wani abu kuma ta maida shi ta rufe, don bata san ta ina zata fara bayanin ba, irin wannan bayanin da ba kowa ne zai yarda ba, koda innan ce kuwa, don ita kanta a yanzu gani take kamar a tunaninta ne komai ya faru. "Ba komai." Ta juya ta bud'e kofar aka fara layin alwala. Har tayi sallar ta saka kayan bacci tunanin abin nan bai fita daga ranta ba koda minti d'aya. Wata dattijuwa mai suna falmata ta taimaka ta d'auko mata bargo daga can saman wardrobe d'insu, ledarsa duk tayi kura ta kakkabe shi ta d'auko, sannan ta d'auki filonta ta fito falo. "Inna zanje wajen mama azumi acan zan kwana yau." "Saboda me? Ku uku ne ma fa yau kawai a d'akin, mu da kiga ganmu duk nan zamu yada kai mu kwanta." Kan ta amsa wata tsohuwa tace. "keh rufa mana asiri kar daga zuwanmu ace mun kori 'yar masu gida." Tayi guntun murmushi tace. "Wallahi Gwaggo ba haka bane, can din kawai nake son kwanciya." "'Yo ku kyaleta mana..." wata daga gefen inna ta karba. "...Ran da muka zo nata bikin ai ba inda ta isa taje, sai mun ga dama ma zamu bawa angon." Suka kyalkyale da dariya gabadaya. A haka ta juya ta bar d'akin, don ta sa a ranta cewa ba zata kwana anan ba. **** Washegari da akayi kamu, Nanne bata kara bari ta zama ita kad'ai a waje ba, saboda haka babu wani abu daya k'ara faruwa irin jiya. Sai dai kawai jikinta ba dadi, yayi wani irin shafal! tana jin kamar bacci take ji amma ko ta kwanta baya tab'a zuwa. A haka har akayi kamun aka gama, da daddare ma ta sake d'ebo kayan kwanciyarta tayi d'akin su mama Azumi, sai dai a yau ta lura da kallon da inna ke mata, kallo irin na rashin yarda cewa k'in kwananta a d'akin ba don wani dalili bane. Washegari da rana wajen uku tana kwance a tsakiyarsu innan da wata Gwaggo ladi, a lokacin an fara shirye-shiryen tafiya wajen mother's eve d'in, masu wanka da shiryawa nata yi. Aunty maryama ta shigo (D'aya daga cikin 'ya'yan kanwar inna) tana kara rok'on su akan su shirya aje wajen event d'in dasu suma, inna ko ta dora daga inda ta tsaya a daren jiya, wai biki in ya wuce cikin gida ya koma party, su ko tsoffai-tsoffai dasu ba zasu party ba. "...in banda abin su hajiya Babba suma ai ba inda ya kamata suje, wajen da akace surikanka maza zasu zo, me zai kai k'afarka?" Nanne ta tab'e bakinta. "Inna duk wannan abin fa kauyancin da ne, don kawai surikansu zasu zo sai suk'i zuwa bikin 'ya'yansu? Kenan duk randa suka zo gaishe su har gida ma sai suk'i fitowa." Kan inna ta amsa gwaggo Ladi ta karb'e. "Rabu da 'ya'yan yanzu Ramatu, ba abinda zasu gane ai, abinda yanzu za'ayi auren yarinya washegari ta fito tsabar rashin ta ido? Ni sanda aka kaini d'akin miji sai da na shekara biyu cur! Sannan da yarsa ta haihu yace in shirya inbi 'yanuwansa ranar suna, ke zo kiga farin ciki wankana uku a ranar nan." "Yo komai ai ya canja, bikin ma dai ana yinsa ne kawai, amma ace abu baza a fara ba sai bayan la'asar a dawo tsakar dare. A da biki ai tunda duku-duku maza na dawowa daga asuba zaku tafi aje a yini, da anyi sallar magriba kuma kowa ya dawo gida, kuyi abinku a mutunce." Nanne tayi shiru tana sauraren hirarrakinsu, idonta na hasko mata komai da suke fad'a cikin nutsuwa. Doguwar riga ce a jikinta sai bata d'aura dankwalin ba kawai ta yafa shi, fuskarta tayi fayau! filon da take kwance na daga tsakiyarsu, sannan ta jawo jelar kitsonta d'aya tana kanannad'ewa da yatsunta. Zuwa can taji inna tace. "ke baza ki soma shirin bane, an kusa la'asar fa." "Inna nayi wanka ai, kaya kawai zansa kuma sai Aminah tazo." Suka juya suka cigaba da hirarsu. Tun tana jinsu har bacci ya fara shirin d'ibanta a cikin hayaniyar d'akin, sai dai me? Ba zato ba tsammani kawai taji alamun wani abu kamar hannu mai taushi ya shafa fuskarta, tun daga farkon sumarta har zuwa gefen hab'arta. Ta bud'e ido da sauri ta dafe wajen, zuciyarta na bugawa ta d'ago ta kalli su inna ko sun lura da ita amma hankalinsu na kan kulolin abincin da ake shigowa dashi d'akin. Ta shafa wajen taji yayi sanyi k'alau kamar an d'ora k'ank'ara. Kowacce jijiya ta jikinta ta shiga aiki, Ta kasa d'auke hannunta gabanta na cigaba da fad'uwa. A lokacin ne abin ya faru. Wannan muryar...wannan muryar mai taushi ta cika kunnuwanta. "Kinyi kyau!" ●﹏● WAYE SHI? AYSHA SHAFI'EE 11 (☆_☆) "Wallahi Aminah da gaske nake miki a dakin nan k'ofa ta rufe dani tv tayi ta kunnuwa ita kad'ai, jiya kuma gaba d'aya jikina ba dadi, yadda kika san wata bugaggiya haka na koma, duk inda na samu waje in kwanta amma ba baccin. Sannan yanzu na gaya miki murya naji sosai ta min magana a cikin kaina." Aminah tayi shiru zaune daga bakin gadon. "Kuma kin tabbata ba wanda yaji maganar." "Ba wanda yaji, a cikin kunnena kawai naji ta fa, kamar irin nasa earpiece." Suka sake yin shiru gabad'ayansu. "Me kike tunani?" Kamar ba zata yi magana ba sai kuma tayi ajiyar zuciya tace. "Anya sa'adha kina tunanin ba aljanun ne suke tsorata ki ba?" Ta girgiza kanta da sauri. "Ni dake fa mun san ba haka bane tunda pretending nayi, kawai dai ina tunanin wani abu ne daban." "Wani abu daban kamar me? Kin san dai mutane basa jin irin haka, kuma aljanu ne kawai zasu iya irin wannan abin." ta sake girgiza kanta. "Duk da haka gaskiya ba aljanu bane, bana ji a jikina hakan ya dangace su, sai dai wani abin daban." "A'ah, dama kuna nan?..." Aunty ni'imah ta shigo tana fad'a, biye da ita wasu matan ne guda biyu. "Nanne baki shirya bama? An fara tafiya fa." "Yanzu zansa kayan." Suka juya suka fara kwalliya da d'aurin d'ankwali a gaban mudubi, suna yi suna hirar dangin mijin jamila da suka zo daga nijer a yau d'in. Aminah ta jawo wata leda a kusa da kafarta tace. "Ga d'ankwalinki da mayafin." "Material d'in ya min kyau, ankon su waye?" "Nasu hajiya Babba ne." Ta amsa a tak'aice tana zaro rigar daga cikin wardrobe. Kamar yadda yake a al'adarta, doguwar riga ce akayi da material d'in (lemon green&milk) mai bud'ewar umbrella da d'an karamin hannu. Ta saka sannan tayi d'auri mai kyau, ta yafa lemon green mayafin da Amina ta kawo mata a kafad'a, hoda kawai ta shafa da lip balm mai kyalli ta saka silver d'ankunne da abin hannu, amma tayi kyau sosai fuskarta tayi fresh da kuma kyau. A wajen event d'in suka cigaba da tattauna matsalar, sai da Rahma tazo wajensu ne sannan suka yi shiru, don Nanne ta nuna bata so wani d'an gidansu yaji. Wajen biyar da rabi Amaren suka shigo tare da Angwayensu, kowacce da irin kalar kayanta itada angonta. Jamila da take Babba ce ta fara shigowa itada zugar k'awaye da cousin d'inta masu anko, tayi shigar ash and black shima Angon nata yasa shadda ash da aikin black, sai wani d'add'age gira yake yana kallon mutane d'aid'ai. Abokansa mutum hud'u ne kawai a bayansu. Nafisa da maryam su ankon Maroon colour suka yi duk su biyun kayansu iri d'aya, don dai su nuna cewa su 'yan d'aki dayane, 'yanmatansu masu ankon lace d'in da akace yafi na kowa suna farko da bayansu. Sunyi kyau sosai, don Angwayensu ma duk brown shadda suka sa amma kowa da aikinsa. Kafin Aisha da Angonta su shigo sai da aka canja wak'a aka sa na step dance d'in 'yanmatanta, su safiya da surrayya na ciki suna bin rawar kamar kowa, abin ya burge mutane yadda suke takawa a hankali, daga bayansu kuma Aisha ta shigo da nata Angon cikin kwalliyar Royal blue da milk, shima yasa milk shadda sai washe baki yake yana dariya. Ga tarin abokansa a baya suna shigowa kamar baza su k'are, kafin su k'arasa wajen zamansu ya sunkuya ya rad'awa Aishan wani abu, aiko ta tuntsire da dariya tana sunkuyar da kai. Duk wannan abin, Nanne bata ga ko d'aya ba, don tana zaune bata tashi ba, tunaninta gaba daya ya tafi wajen neman abinda ke damunta. Sai da suka gama zama Mc ya kiran masu bud'e taro da addu'a sannan tace dasu Aminah tana zuwa, ta mike tayi wajen fita, a hanyar ta had'u dasu Aunty maryama sun d'ebo jakunkunan souvenirs, kowannensu ya kama fad'an wai me yasa bata shiga tawagar su Aisha ba, ga anko a jikinta amma ta zauna kamar 'yar gaiyata. Ta juya idonta, ita ba abinda ke gabanta kenan a yanzu ba, so take kawai ta fita ta samu waje a tayi tunanin dake cikin kanta. "Rike wadannan maza, mu fara rabawa daga can." Ba yadda ta iya haka ta karb'a ta bisu. Har aka tashi daga bikin kuwa bata sami wannan hutun ba, don daga k'arshe ma sai sulalewa tayi tabi Aminah da aka zo d'aukanta suka sauke ta a gida. Har aka gama bikin ranar lahadi aka kai amare Nanne bata k'ara samun walwala ba, mutane suka yita tambayar meya sameta ganin duk ta rage tsiwarta da surutu amma duk cikin tarin jama'ar nan ta rasa mutum d'aya da zata gayawa matsalarta, don in ba harkar taro ba bata fiye ganinsu ba, ba wanda sabonsu yayi karfi da ita a cikinsu. Inna ce kawai kuma bata jin zata fahimce ta a wannan lamarin. Saboda haka Aminah bata yi niyyar zuwa ranar d'aurin auren ba amma ta takura mata sai da ta shigo, tayi ta mata k'orafi na yawan farkawar da take yi a kullum cikin dare ba tare da dalili ba. Aminan tayi-tayi da ita akan su fad'awa wani amma taki yarda don a tunaninta duk wanda yaji zaice aljanu ke damunta, ita kuma tayi rantsuwa cewa ba aljani a jikinta. A haka sati biyu cike da taraddadi a wajenta suka wuce, 'yan k'ananan abubuwa kala-kala suka yi ta faruwa da ita. Kamar yawan maganganun da take ji a cikin kanta wanda yanzu bata iya fahimtar abinda muryar ke fad'a, ko kuma kamar ana binta a baya in tana tafiya ko mutum ya tsaya a daidai bayanta, yawan kiran sunanta da take ji daga can nesa, da kuma alamun wani abu na tab'a fuskarta ko jan jelar gashinta. Tun Inna bata lura da ita har tazo ta fara fahimtar wani abu, saboda yawan tsoratar da take yi da kuma azabar ciwon kai, sannan sau biyu tana tashinta cikin dare tace ana kwankwasa musu kofa alhalin ita bata jin komai. Abu d'aya kawai dake sawa taji sauk'i a ranta da kuma rage mata tsoro shine yawan addu'o'in data rik'e bisa shawarar Aminah, Sannan bata tab'a zama ba d'ankwali a kanta. Amma kallo d'aya mutum zai mata ya tsinto rashin kwanciyar hankali a idanunta, don gabad'aya sun d'ashe sannan sunyi fari fat! Ta rame kuma ta rage yawan magana. Ko sadiq yazo da tsokanarsa sai dai yayi ya gama bata iya biye masa, inna ma idan tana hirarta sai dai tayi ta binta da eh ko A'ah. Mama Azumi da Rahma ba tambayar duniyar da basu yi mata ba amma tace musu ba abinda ke damunta. Daga k'arshe sai mama Azumin kawai ta b'ige da kawo mata jik'e jik'e tana tunanin ko shawara ce ke damunta. A sati na uku baffa ya kirata akan rashin walwalarta da ya lura kwana biyu, shima ta kasa gaya masa abinda ke damunta sai shiru kawai. Ba yadda ya iya haka ya sallameta da umarnin ta koma islamiyarsu wani satin. Ta amsa sannan ta tashi ta tafi. Sai dai kuma dukkaninsu ba wanda ya san me wani satin zai zo da dashi, satin daya rufta da wani b'angare na rayuwar gidan! **** RANAR LARABA! ●﹏● WAYE SHI? AYSHA SHAFI'EE 12 (☆_☆) RANAR LARABA! Wajen karfe biyar da rabi na safe, inna ta fito daga cikin band'aki da alwalarta, ta tashi Nanne dake dunk'ule a cikin bargo sannan tayi falo inda daddumarta take. Nanne ta bud'e idonta a hankali tana jin kamar baccin bai isheta ba, amma ba yadda ta iya ko bata tashi yanzu ba, ba zata kara minti talatin ba saboda tafiya makaranta. Tayi yunkurin tashi, a nan ne fa taji wani irin nauyi ya danne ta, gabanta ya fad'i ta sake yunk'urawa amma ta kasa, taji kamar wani gingimemen abu aka d'ora a jikinta, Ta tattaro dukkan k'arfinta ta tara shi a hannayenta amma ta kasa mik'ewa, tsantsar mamaki ya rufe ta, me ya same ta kuma? Ta yaya zata kasa tashi? Meye akanta? Ta juya idanunta ta kalli jikinta babu komai sai wannan bargon da take lullube. Toh me ya faru da ita? Sai kawai ta bud'e baki da niyyar kiran Inna ko har a lokacin bata tayar da sallar ba, anan ne zuciyarta tayi tsalle ta fice daga k'irjinta, don ta bud'e baki har ta furta sunan Innar amma babu sautin daya fito. Ba tare da ta tsaya wani tunani ba ta  d'aga muryarta ta sake kiran, amma ta gagara tsinto sautinta. Ta maida idonta ta rufe lokacin da k'arar bugun zuciyarta ya cika kunnenta, yana jijjiga ta kan cewa ta farka daga mafarkin da take, saboda haka ta tamke idonta ta sake bud'ewa sannan ta yi yunkurin tashi game da furta kalmar Bismillah amma ba abinda ya canja daga d'azu. Zuciyarta ta k'ara tsalle cikin fargaba, kanta ya shiga juyi? Me kuma yake shirin faruwa da ita? Bayan duk abubuwan da take jurewa? Tana tunanin zasu wuce zuwa wani lokaci. Ta sake yunk'urawar dai da dukkan wani k'arfi na jikinta amma wannan nauyin, wannan nauyin dake samanta ya hana jikinta d'agawa. Da gaske ne wani abu ya faru da ita ko kuma yana faruwa a yanzun, in ba haka ba ta yaya kawai zata kasa tashi, taji duniyar ta tsaya mata cak! Yanzu in bata mik'e ba me zai faru da ita kenan? Zata dauwama ne a haka? Koma mutuwa zatayi? Wannan tunanin ya k'ara rura mata wutar sabon k'arfi a cikin jikinta, tayi ta yunk'uri tana motsa yatsun hannu da k'afarta amma ba wani abu daya sauya. Har k'arfe shida lokacin da inna ta idar da duk wasu nafilfilunta bata ji motsin Nanne ba, hakan yasa ta dawo cikin d'akin ta tsaya daga k'ofa ta kira sunanta. "Har yanzu kina kwance? Yaushe kika koyi nauyin bacci ne...ga lokacin shiga wankan ki har yayi." Shiru bata yi magana ba kuma bata motsa ba, ta sake kira ba amsa, sai ta k'arasa a hankali ta yaye bargon. "Idonki biyu ashe? Ko ba zaki...." Bata k'arasa maganar ba sanda ta lura bakin nanne na magana amma bata jin me take cewa. "Baki da lafiya ne?" Nanne ta girgiza kai tana kara gaya mata cewa ta kasa tashi ne da kuma magana amma ba alamun innar ta fahimce me take cewa. "Yi magana mana inji, muryarki ce ta rike ko mura kike yi?" Ta cigaba da girgiza mata kai tana fad'ar wani abu amma maimakon ta fahimta sai kawai hakan ya k'ara hargitsa ta, ta hau salati tana kokarin taso da ita, nan ma abu ya gagara sai kawai ta kara rud'ewa tayi waje da d'an saurinta tana neman wani. Kafin k'arfe bakwai na safiyar, gabadaya kowa na gidan ya shiga tashin hankalin abinda ya sami Nanne, don wani abu ne da a tarihin rayuwar kowannensu bai tab'a gani ba, yayyunta maza haka suka yi ta  k'ok'arin ciccib'arta daga kan gadon amma abu ya faskara, daga k'arshe suka yanke shawarar kawai a kira likita har gidan amma baffa ya hana, don tunda ya shigo cikin d'akin yaga yadda take dunk'ule a gado tana ta k'ok'arin yiwa kowa maganar da ba'a iya ji ga kuma hawaye ko'ina fuskarta, sai ya koma falo kawai ya kira waya yace da na ciki yazo. Bai k'ara cewa komai ba daga nan, sai sanda hajiya Babba ta shigo yace ta taimaka ta taya su mama rabi bawa Inna baki ta rage kukan da take, don da mama Azumi ce ke bata hak'urin itama kuma daga baya ta fara nata. Mama halime ita ta tsugunna a gaban Nanne ta dinga karanto addu'o'i kala-kala tana tofa wa a koina na jikinta. Sadiq kuwa tunda ya shigo yaga yadda Nanne ke kuka sosai tana ta motsa bakinta alamun magana, ga kuma yayyansu duk sun taru sai kokarin d'ago da ita akeyi, ya koma d'aki yaci kukansa. Hatta Aunty amarya da mama rabi sai da jikinsu yayi sanyi, don suna tsaye daga cikin d'akin kusan awa biyu kafin malaman da baffa ya kira su iso. Anan suka umarci duk matan su fita, inda da kyar aka fita da Inna tana kuka tana a barta taga abinda zasu yi da idonta. Su uku ne malaman, wanda yake Babbansu shi ya tsaya daga daidai kan Nanne ya d'ora hannunsa akan goshinta. yayi ta wasu addu'o'i tana kuka tana raba ido tsakanin yayyenta da kuma baffa dake zaune akan stool d'in mudubi. Kusan mituna goma sha biyar kafin ya kammala, sannan sauran guda biyun suka fito da wasu papers da aka rubuta wasu keb'antattun ayoyin alqur'ani suka fara karantawa cikin had'in baki a tare kuma da karfi. Me zai faru? Basu yi nisa ba sanda idon kowa dake d'akin ya gane masa komai. K'afafun Nanne dake dunk'ule suka mik'e a lokaci guda, haka ma hannayenta, sannan jikinta ya shiga wata irin jijjiga yana d'agawa sama kamar dukka gab'ob'inta zasu b'alle! ●﹏● ***** WAYE SHI? AYSHA SHAFI'EE 14 (☆_☆) RANAR LARABA! Wajen karfe Takwas saura kwata, Imaran yayi parking motarsa a cikin kanfaninsu, ya fito ya d'an kalli yawan motocin gurin sannan ya gyara tie d'insa ya nufi cikin building d'in. "Barka da zuwa ranka ya dad'e." malam iliya dake zaune a kusa da k'ofar elavator ya gaishe shi. "Barkan mu dai Baba, fatan ka tashi lafiya." Ya amsa da murmushi, ya san yanayin kallonsa da yake masa na cewar yau ya makara ne, wanda shima bai san ya akayi hakan ta faru ba, da kyar ya iya tashi yau saboda nauyi da jikinsa ya masa da kuma wani irin jiri da ya dinga ji. Sai da yasha duk wasu magungunan kariyarsa harda wanda ya shanye gaba daya ma sannan ya iya shiryawa da kyar ya fito. Ya shiga cikin elevator d'in ya danna floor na shida, ya d'an jingina kansa da gefe yana kallon yadda numbobin ke canjawa suna yin sama. Tunaninsa ya koma kan jaamil da ya dawo shekaranjiya, dole ne a yau ya neme shi su san yadda zasu shawo kan matsalar nan, tunda ba jikinsa ne ke ciwo ba balle yace irin rashin lafiyar bil'adama ce, tun daga cikin ruhinsa yake jin juyawar komai, kuma hakan ba karamin abu bane. K'ofar ta bud'e, ya fita da sauri ya nufi office d'insa, kafin ya shiga ya hango Sales  Personnel dinsu yana fitowa daga office d'insa, bai ko tsaya ba ya bud'e nasa office din ya shige, don a nasa matsayin na Marketing Manager ba yadda za'ayi ace sun hadu dashi su rasa abin tattaunawa, kuma a halin da yake baya bukatar magana a yanzu, yafi son ya samu waje ya d'an kwanta kad'an ko zaiji daidai. Sai dai me? Yana isa teburinsa yaci karo da file d'in da aka ajiye masa jiya da yamma, na cewa k'arfe tara zasu shiga meeting da stakeholders d'in kamfanin G&M akan matsalar da suke fuskanta, kuma a matsayinsa na marketing manager kusan shine mai magana a wajen. Yaja k'aramin tsaki sanda ya ajiye briefcase d'insa akan table din, speech din ba abu ne mai wuya ba, ko a wajen he can come with something kawai k'arfin zama a meeting d'in ne matsalarsa. Ya koma ya sawa kofar key sannan ya nufi kan couch d'in dake gefen window, ya zuge curtains d'in yayi kwanciyarsa anan yana jin kowacce jijiya ta jikinsa na fitar da rad'ad'i. Har karfe tara aka fara taruwa a hall na meeting d'in babu alamun Imran saboda haka shugaban company DR. SULAIMAN TURAKI, ya bada umarnin aje office d'insa duba shi. Imran ya bude idonsa da kyar sanda aka fara knocking d'in kofar, ba zai iya tashi ba saboda haka ya mik'a hannunsa kawai ya bud'e daga nan. Shamsu ya turo k'ofar ya shigo, ba hasken fitila sannan an rufe labulayen. Yana ganinsa ya fara k'ok'arin mik'ewa. "Ya salam, Imran baka da lafiya ne?" "Wallahi, kaina ke d'an ciwo." "To ai da kayi reporting kawai ka zauna gida, iI'm sorry, bari in fad'a musu." "A'ah karka damu, yanzu nake shirin tashi dama...Its nothing." Ba zai taba iya missing meeting d'in ba, don abinda zaije yayi sune 'yan kananan abubuwan da zasu hadu su gina masa YARDA a wajen Dr. Turaki, kuma YARDA, itace zata sa ya cimma manufar zuwansa cikin wannan rayuwar, itace zata sa ya cimma burin daya dad'e a zuciyarsa. Saboda haka da kyar ya tattaro duk wani karfinsa suka nufi meeting hall din. Suna shiga Dr, Turaki ya yafito shi, ya zagayo ya biyo ta seat d'insa. "Where have you been? Ka san we can't keep this people waiting..." sai kuma ya lura da idonsa. "...baka da lafiya ne?" "I'm fine, just a minor headache. Bari mu fara." Ya samu waje ya zauna, aka fara meeting d'in. Da kyar ya iya jurewa har d'aya kamfanin suka gama presenting reasons d'insu na kin amincewa da janye contract din da zasu yi sannnan ya tashi ya fara opposing komai da suka fad'a, tun suna iya protesting har ya d'aure su da jijiyoyin jikinsu, ba yadda suka iya haka suka yadda aka janye contract din. Wani abu da shi kansa Imran d'in bai san zai yiwu ba, kowa yayi ta zuwa yana taya shi murnar k'ok'arin da yayi sannan Dr. Turaki ma yayi ta shaking hannunsa yana murna, wanda hakan ya k'ara sawa kansa cigaba juyawa. Saboda haka nan da nan ya nemi izinin tafiya gida, aka bashi kuwa da full assurance. Har ya kai k'ofar fita ya tuna ba zai ia driving ba, saboda haka ya dawo ya samu malam iliya ya bashi key d'in motarsa. Sannan ya juya ya nufi bayan building d'in, sai da ya tabbatar babu wani ido dake ganinsa sannan yayi wani abu daya kusan manta shi a rayuwarsa, ya rufe idonsa a hankali ya sulale yabi iskar wajen. **** Zuwa dare jikin Imran yayi tsanani sosai ta yadda baya iya ko mik'ewa, a lokacin sunyi duk wani k'ok'arin da zasu yi shida jaamil amma sun kasa gano komai. Ko sallah ma sai a zaune yayi. Wajen sha biyu na dare, jaamil ya shigo d'akin ya zauna daga gefen gadon da yake lullube ya dafa goshinsa, har a sannan jikinsa da zafi sosai. Ya d'an ja tsaki sanda Imran d'in ya bud'e idonsa. "Na gaya maka ka fita daga jikin nan watakila zaka ji sauki." "Nima na gaya maka ba ruwan jikin da abinda nake ji, tun daga cikin ruhina ciwon yake." "Dole ne fa akwai dalilin ciwon nan, irin wannan abin baya faruwa haka kawai." "Nima tunanin da nake kenan, amma na kasa gano komai." Jaamil ya d'an yi shiru kafin yace. "A tunani na kamar wani yana hukunta ka ne akan wani laifi da kayi, kuma a yanzu baka mu'amala da kowannenmu balle muyi tunanin wani, ko kuma ana son wani abu daga jikinka na asali, ko....." Bai karasa ba ya tsaya, Imran ya juyo a hankali ya kalle shi, idanunsa sun tafi alamun tunani, kamar zai nemo wani abu daya sani ne amma ya manta. "Me kake tunani?" ya tambaya da muryarsa mai zurfi da taushi. "Ina tunanin na gano dalilin rashin lafiyarka...." "Mene shi?" Maimakon ya bashi amsa, kawai sai ya mike ya fita daga d'akin. Tun Imran na jiran dawowarsa, har ya samu wani bacci mai nauyi ya tafi dashi wanda bai farka ba sai washegari da safe. A lokacin jaamil ya dawo yana zaune daga gefe yana juya wayarsa a hannunsa. "Yaushe ka dawo?" ya tambaya yana murza idonsa. Jaamil ya d'ago ya kalle shi sannan ya jefo masa wayar. "An kira daga wajen aikinka na gaya musu cewa baza ka iya zuwa ba." "Da baka fada ba, don jikina yayi kwari zanje yau." "Ba zaka samu damar zuwa ba, akwai abinda zamu yi yau din." Jin haka yasa ya juyo sosai ya kalle shi. "That reminds me, kace ka gano dalilin rashin lafiyata, so ina kaje jiya?" Jaamil yayi ajiyar zuciya sannan a hankali yace. "Ya sunan yarinyar nan?" A lokaci d'aya kwakwalwar Imran ta soma aiki, don mace daya ce jaamil zai tambayeshi ita haka, yarinyar daya riga ya goge komai daya dangance ta daga cikin rayuwarsa ya ajiye a gefe. Me zai kawo zancenta kuma yanzu? Ya had'iye abinda ke bakinsa kafin yace. "Sa'adha...?" sunan da bai taba tunanin zai sake furtawa ba. Jaamil ya gyada kansa sannan yace. "Itama bata da lafiya!" ●﹏● NB. Me kuke tunanin ya samu Nanne? Meye had'in rashin lafiyar Nanne data Imran? ***** WAYE SHI? AYSHA SHAFI'EE 15 (☆_☆) Bata taba tunanin yaya ake mutuwa ba, ko yadda ruhi ke fita daga cikin jiki. Duk da cewar koda ta yin ba zata taba yarda cewa haka mutuwar take ba. Ta tsaida idanunta akan siffofi biyun dake tsaye akanta, bata iya ganin fuskokinsu don a cikin duhu ne, saboda haka bata san ko su waye ba, amma tana ji a jikinta cewa kamar ta sansu ne tun asali, kamar sune wani b'ari na jikinta da ta dade tana nema. Saboda haka, hankalinta ya kwanta, zuciyarta ta sami nutsuwa, ta maida idanunta ta rufe a hankali sanda hannun d'aya daga cikinsu ya sauka a goshinta, wani sanyi ya ratsa kowacce jijiya ta jikinta sannan duk wani ciwo nata yabi iska! ***** Lokacin da ta farka da safe, wani abu ya canja, wani abu daban da yadda ta saba gani, ta shiga zagayawa da idonta cikin d'akin. Akwai dai hasken rana dake shigowa ta cikin labule, wanda yayi tar! Kamar an kara masa kala. Sai kuma ta lura ba hasken bane kadai yayi wannan tar d'in. Komai na d'akin ne idonta ke dauko mata shi haka. Kamar taje wankin ido an cire duk wani datti dake cikinsa. Muryar inna ta fara shiga kunnenta, tana karb'ar gaisuwar mutane da yawa da d'akin ya d'auka da maganganunsu. "Lafiya kalau mun gode Allah, ya wajen naku kuma." Muryar wani namiji ta amsa. "Lafiya kalau inna, ya kuma mai jikin? Mun shigo ne sai Hajiya take fad'a mana wallahi." "Da sauki, da sauki wallahi an gode Allah." Jin haka yasa ba shiri ta juyo da kanta b'arin da suke, anan idonta ya gane mata dakin cike taf da jama'a, bayan inna akwai su Aunty maryama da Aunty nafisa, da kuma wasu mata biyu da bata sansu ba. Sai hajiya Babba dake tsaye daga bakin k'ofa ta rako k'aramin k'aninta da yayi aure kwanaki da matarsa, yana rik'e da d'ansu a hannu, sai yanzu ta gane muryarsa ce taji. Aunty maryama ta taso da sauri ta nufo kan gadon. "Nanne kin farka, sannu ya jikin naki?" Jikinta? Me ya sameta? ta kalli sauran jikin nata, sannan kwakwalwarta ta tuna da duk abinda ya faru. Aikuwa da sauri ta mike daga kwancen da take, a tunaninta zata sake jin wannan nauyin irin na jiya. "Yi a hankali karki fad'i." Aunty Nafisa ta fad'a rike da 'yarta, ilham a hannu. "Aunty naji sauki, ba wani ciwo a jikina." "A'a Nanne jikinki ba kwari, maryama jinginar da ita da filon nan." "Inna bana son sake kwanciyar dan Allah." Ta fada har cikin ranta, don da gaske gani take in ta sake kwanciya zata kasa tashi. "Inna a barta ta sauko k'asan, ai da alamun sauki a jikinta." hajiya babba ta fad'a tana k'arasowa cikin d'akin. Aunty maryama da d'aya daga cikin matan nan suka kama ta aka sauko da ita kan carpet, kowa sai faman yi mata sannu yake. "Toh mu zamu koma inna, Allah ya kara sauki ya bata lafiya." Wannan k'anin hajiya Babba ya fad'a, sannan suka yiwa sauran sallama suka fita shida matarsa. Itama hajiya Babban daga baya tabi su. Aunty maryama ta mike tana fad'in. "Sannu Nanne, bari in had'a miki tea." Dama abinda take shirin fad'a kenan, don yadda take jin jikinta shafal, ta tabbatar harda yunwa ke damunta, aikuwa Aunty maryaman ta hado mata tea mai kauri harda pepper soup din nama da dankali (irish) wanda da alama don ita akayi dama. Ta cika cikinta fam! Sannan tayi wanka da ruwa mai zafi ta canja kayan baccin dake jikinta tun daren shekaranjiya. Aikuwa har yamma mutane shigowa suke ana duba ta, 'yan gidan kaf! ba wanda bai shigo ba, harda su ya Ahmad da ya ibrahim masu aure sai da suka zo da matansu bayan sallar maghriba. Nanne taji wani b'angare na zuciyarta ya fad'a, bata zata kowa na sonta haka ba. Rahma kuwa harda kukan murna data ganta ta farka, a wajen su Aunty Nafisa taji ashe a gidan ta kwana a falonsu, sai da safe ne ta tafi gida saboda zuwa makaranta. Duk wanda yazo dubiyar nan kuwa, sai inna ta labarta masa abinda ya faru tun daga farko har karshe, har sai da Nanne ta haddace kalma bayan kalma na abinda take fada. Sai dai kuma wani abin mamakin shine a duk labarin Inna bata ji ta danganta rashin lafiyarta da Aljanu ba, haka ma dukka 'yan gidansu da 'yan dubiyar babu wanda ya ambaci hakan, sai kawai fatan sauki da kariya suke. Saboda haka itama ta ture duk wani tunani a ranta ta sake tana ta cin kayan dubiyar da kowa ke rik'owa in zai zo. Don hatta sadiq sai da yaje can wani bakery na hanyar makarantarsu ya siyo mata irin sandwich cake d'in da ya san tana so. Amma duk da haka saida ya dameta da tsokana, duk sanda ya shigo d'akin zai ta dariya yana cewa 'yanmata taji azaba idonta yayi wuri-wuri. Da daddare mama halime ta kawo mata potate d'in dankali da alaiyahu, aunty amarya da mama rabi ma duk sun kawo 'yan fruits dinsu. Hajiya Babba kuwa manyan carton d'in madara da Bournvita ta kawo wai zasu sa taji kwarin jikinta. Inna sai washe baki take ganin yadda kowa ke nuna kulawarsa. Baffa ma sai da ya shigo da kansa da daddare yaga jikin nata. Washegari da yamma Amina tazo, don sai a ranar Safiya ke gaya mata a makaranta, duk ta rikice tana ta tambayar jikin nata, Nanne tace ta kwantar da hankalinta don wasai take jinta, tsoronta d'aya ne in dare yayi bata son kwanciya, don a jiyan ma kusan a zaune tayi baccinta. Aminah ta tambayeta abinda malaman suka ce tace itama bata sani ba, don tunda ta tashi, ba wanda yayi mata zancen, kowa ta ganin ta wartsake yake. Sai da mutane suka lafa sannan Baffa ya kirata falonsa, yace da farko dukkansu sun danganta ciwonta ne da shafar aljanu, amma malaman da suka zo sunyi duk wani k'ok'arinsu basu ga alamar aljani a jikinta ba, Saboda haka ga magunguna nan sun kawo ta dage da shansu da kuma addu'o'i. Tun daga nan, Inna ta tsaya akanta a kullum sai tasha magungunan sannan zata kyaleta, ga litattafan addu'o'i da carbi har kala uku duk ta siyo mata. Bayan sati d'aya ta warware sosai ta koma makaranta, sannan ta canja sabuwar islamiyya ta koma wata a hanyar gidansu Rahma, hakan yasa itama Rahman ba yadda ta iya, ta bita suka shiga tare. A cikin sati biyu, rayuwarta ta koma kamar da, komai ya dawo mata daidai...tsiwa da rashin kunyarta ta d'ora daga inda ta tsaya, don har ya sulaiman saida ya zane ta wata ranar juma'ah. Da magribha ne ta lab'e a wajen barandarsu ta gama jin wayar da yake da  girlfreind d'insa duka, sai a k'arshe da taji yayi k'asa da murya yana fad'a mata how much he loves her sannan bakinta ya sub'uce tace A'uzubillahi. Ai kuwa karaf yaji a kunnensa, ya biyo ta har cikin d'aki ya mammake ta, bai ko saurari kwaroroton inna ba. Sai dai bayan sati biyu, komai ya fara dawowa sabo... Maganganun da take ji a cikin kanta suka dawo tare da yawan kiran sunanta da kuma alamun wani abu na tsaye a bayanta. Sannan ga azababben ciwon kan nan da kuma yawan tsoratar da take yi. Wannan kwankwasa kofar ma na cikin dare ya dawo...! ●﹏● WAYE SHI? AYSHA SHAFI'EE 16 (☆_☆) Ya d'ago da kansa a hankali sanda aka rufe main kofar shigowa falon. "Watarana idan na gaji, zan shak'e wuyanka ne kowa ya huta." Imran ya juyo daga cire takalmansa da yake ya kalli jaamil dake zaune daga kujerar dining na falonsa. "Yaushe kazo? Ka dade kana jirana ne?" "Tun sanda ka bar wajen aikinka ka tafi yawon zagaye gari nake zaune anan." Imran ya k'araso da murmushinsa. "Toh me yasa kawai baza ka dawo nan bane, kaga ka huta zirga-zirga, kuma akwai spare d'aki...biyana kawai zakayi ka shiga." Jaamil bai saurari k'arshen zancen nasa ba ya kalli ledar daya ajiye akan table din. "Meye wannan kuma?" "Abinci ne nayi takeaway, don har yanzu bana jin k'arfin jikina, ba zan iya girki ba." "Wai me yasa ka damu kanka da abincinsu ne?" Ya d'aga kafada kad'an. "Saboda yana min dadi." "Ranar da komai zaizo karashe zanga yadda zakayi." "Me kuwa zanyi, zan cigaba da zuwa ne ina siya." Har jaamil zai bashi amsa suka tsinci knocking daga k'ofa. Ya juyo ya kalleshi. "Meye kake kallona? Gidanka ne fa." Yaja k'aramin tsaki. "Ba sai ka tuna min ba ai, ban taba yin bak'i bane thats why." Yana bud'e k'ofar, yaci karo da wasu 'yanmata biyu a balcony d'in. Ya d'an bude baki saboda mamaki sanda kowaccensu ta fad'ad'a murmushinta. "Ina wuni." suka fad'a a tare. "Uhm...lafiya kalau." "Dama mu mak'otanku ne, tunda aka tare ne bamu shigo ba shine muka ce bari yau muzo mu gaida matar gidan." Imran ya d'anyi shiru sannan ya cusa yatsunsa cikin sumar kansa yace. "Mungode...sai dai kuma ba mata a gidan." Suka zare idanunsa sannan d'aya ta kalli daya. "Oh sorry, bamu sani bane wallahi...sai anjima." "Its nothing, sai anjima." Ya rufe k'ofar ya dawo ciki. Jaamil yana dariya k'asa k'asa yace. "Yanzu a kawo maka ziyara ka hana su shigowa? Bayan kaine matar gidan?" "Wallahi k'arya suke, ina ganinsu fa in na dawo sun san babu mace a gidan." "Kaima ka san me suke nufi ai." Bai saurare shi ba yayi hanyar d'aki kawai. Bayan kamar minti talatin ya fito sanye da wasu kayan, ya jawo kujerar gefen jaamil ya zauna ya fara cin abincinsa. "Meya faru?" Ya tambaya ba tare daya kalle shi ba. "Ciwon yarinyar yana shirin dawowa." Da jin haka imran ya saki cokalin hannunsa. "Tun yanzu...? Jaamil gaskiya dole mu sami wata hanyar, ba zan iya ba wallahi nayi losing k'arfi da yawa kuma i'm still picking up." "Na sani." "Na san ka sani mana, I'm asking me ka samo? Don ba abinda zan iya nan gaba idan dai ni zan cigaba da controlling d'inta." "Da ace ban samo komai ba yarima, bazaka ganni anan ba." "Okay ina jinka." Jaamil yayi ajiyar zuciya mai nauyi yana kallon set d'in cokula da table knife d'in dake jere a cikin gidansu na katako daga tsakiyar table din. "Wai taya ka iya tsara komai na gidan nan ne ma?" "Wani Decoration company na biya suka had'a min. Ina jinka me ka samo?" Jaamil ya sake yin shiru, abinda zai fada nauyi yake masa, kuma shi kansa har yanzu ya kasa yarda cewa hakan shine kad'ai a hanyar samun saukinsu, wani abu da babu shi a tsari ko tunaninsu. "Yarima abinda na samo mai girma ne, ni kaina na san ba zai yiwu ace duk bayan sati biyu kana k'arar da k'arfinka wajen controlling d'inta ba, amma ka yarda dani ba yadda zamu yi ne." "Nima na san da hakan, saboda haka ka fad'a min kawai me ka samo?" "Hanya d'aya da zai sa ciwonta ya tafi gabad'aya shine in yarinyar tana kusa da kai!" Imran yayi shiru yana kallonsa, hannunsa rik'e da cokalin daya d'ebo abincin. Sai kuma ya sake shi cikin plate d'in sannan ya gyara zamansa sosai. "Ban gane me kace ba..." Jaamil yayi ajiyar zuciya, yana jin shima kamar abinda ya fad'a ba daidai bane. "D'aya b'arin jikinka ne kad'ai zai iya controlling wanda ke jikinta, saboda haka idan kuna tare a kullum d'aya b'arin zai dinga jin alamun d'ayan a kusa dashi saboda haka ba zaiyi k'arfin da zaiyi tasiri ba, kamar dai sanda duka biyun suke jikinka. Amma in har d'aya yayi nesa da d'ayan, ciwonta zai ta taruwa ne ta yadda duk sanda ka tashi zuwa kwantar dashi, sai kayi amfani da k'arfi mai yawa. Wanda in kuma kana yawan yin hakan toh k'arfinka zaita tafiya kullum ka zama baka da kuzari." Imran ya tsura masa ido, yana jin kowacce kalma tana bi ta kan fatarsa tana nutsewa cikin kwakwalwarsa. Amma kuma ya gagara fahimtar ma'anarsu. zuwa can ya daure yace. "Jaamil ban gane ba fa, ta yaya yarinyar zata zama a kusa dani? Ka san dai ba zan iya zuwa inda take kullum ba?" "Na sani." "Toh ta yaya hakan zai yiwu? Kuma ka san ba zamu iya sace ta mu cigaba da zama a garin nan ba, dole za'a nemo mu ko kuma yarinyar ta gudu...sannan in muka bar gari kuma zan samu matsala da wajen aikina. Wajen da saboda shi muka shigo rayuwar nan kuma nayi abubuwa da yawa ba zai yiwu mu b'ata komai ba...mu bar abu mai muhimmanci don gyara kuskurena." "Nima duk nayi wannan tunanin yarima, kuma na ga hakan ba zai yiwu. Shi yasa na ture komai na samo hanya d'aya kawai da zata fitar damu, mu sami komai kuma a sauk'ake." "Wace hanya kenan?" Kai tsaye jaamil ya amsa. "Shine ka AURE TA!" ***** Jikinta kwata-kwata ba kwari, yayi wani irin shafal kamar fallen paper, ta rufe idonta tana sauraren maganar Inna, tana ta gaisawa da amare, zainab ce a kusa da ita tana kira mata su d'aya bayan d'aya, kowacce sai ta tambayi jikinta kasancewar duk sunji labarin. Ji take yi kamar zata yi bacci amma kuma yak'i zuwa, ko sallar azahar d'azu da kyar tayi tana jin layi, abinci ma bata ci ba saboda ko kad'an bata jin sha'awar komai. Ta cusa yatsunta cikin gashinta tana rokon baccin ya d'auketa. "Zainab mama na nemanki." muryar safiya ta shigo d'akin. "Ta dawo ne?" zainab d'in ta tambaya. "Eh yanzun nan da zamu hawo suka shigo." "Toh bari in kira wa inna jamila tukunna." Nanne ta bud'e idonta a hankali sanda safiyyan ta k'araso wajen kujerar da take kwance. A gefenta wata yarinya ce da a lokaci d'aya ta cilla zuciyarta cikin tunani, tunanin wannan fuskar da ta kasa fita daga ranta....IMRAN. Tun ranar da ya shigo cikin gidansu da daddare, bata kara jin labarinsa ba balle ta ganshi. Sannan rashin lafiyar da tayi ta kwanan nan ta ture duk wani abu dake zuciyarta, dalilin da yasa bata k'ara tunawa dashi ba kenan. "Wai bacci kike yi?" safiyya ta fad'a tana zama a hannun kujerar. "A'ah wallahi kawai jikina ne ba dadi." "Sannu, ya jikin?" yarinyar ta tambaya, ta juya ta kalle ta sosai sannan ta amsa. "Walida ce take son style d'in doguwar riga, shine nace bari muzo wajenki kece mai su." "Ta kuwa yi sa'a jiya aka kawo min wanki, ki d'ebo mata suna wardrobe." Bayan safiyya ta d'ebo wajen kala goma suna d'agawa ne ta kalli walidan tace. "Wai kowacce kice tayi miki, toh guda nawa zaki d'auka ne?" "Ko duka ne fa ni d'auka zanyi, sauran sai in karbi na riga da skirt a wajenki." "Kaya nawa zaki d'inka ne wai?" "Goma sha hudu ne, ummah tace harda na sallah amma ni wallahi duk d'inke su zanyi." Safiyya ta gyad'a kai tace. "Gaskiyane, dama ke kad'ai 'yarta dole kiyi abinda kike so." Kamar a mafarki Nanne taji kalmar, saboda haka ta bud'e idonta da sauri ta kalle su sanda walida ke fad'in. "Kowa wai sai yace don ni kad'ai ce, kuma wallahi abubuwa da yawa ba haka bane, kinga yanzu fa na d'an kwana biyu banyi d'inki ba." Kafin safiyya ta bata amsa, Nanne ta riga ta magana. "Baki da yayye dama?" Walida ta gyada mata kai tana murmushi. "Ita kad'aice fa a gidansu daga ita sai mamanta da babanta, 'yar gata ce ai." Nanne taji kanta k'ulle, komai ya tsaya mata cak! Kamar yaya? Dama Imran ba wanta bane? Toh ya akayi kullum take ganinsa a k'ofar gidan duk tsawon watannin nan? Idan ba anan yake ba toh daga ina yake zuwa. Ta sake kallon walidan tace. "Akwai wani da yake zuwa gidanku Imran?" "Imran? Kai anya kuwa na sanshi? Ganinsa kika yi a gidan?" "Ina yawan ganinsa ne a k'ofar gidan naku." Ta kalli safiya tace. "Kin gane wa take nufi?" "Ta yaya zan gane, nina san duka 'yan uwanku ne?" "Toh ai kina yawan zuwa." Safiyya ta jiyo ta kalli Nanne tace. "Waye shi?" Ganin dai da gaske basu gane ba yasa kawai ta rabu dasu ta cigaba da kwanciyarta, suka d'ebi kala takwas sannan safiyya ta mayar mata da biyu suka fita. Har dare tunanin Imran bai bar cikin kanta ba, mamaki take yi in ba gidansu walidan yake zuwa ba me yake kawo shi? tunda dai bayan gidan nasu ba wani gida a gefensu duk kangwaye ne. Ta tuna kuma yace mata wani lokacin yana zuwa wajen ya umar, amma in har wajensa yake zuwa ya kamata ace ta tab'a ganinsa a cikin gidan nasu ba sai ranar ba kawai, tunda duk wasu abokan yayyunta masu zuwa ta sansu. Sai kuma ta tuna a cikin samarin nan dake yawan zama akan wata mota take ganinsa, in har hakane su zasu sanshi kenan, saboda haka tayi niyyar tambayar sadiq gobe. Sai dai har ta kwanta bacci a ranar, kwakwalwarta tambaya d'aya take nanata mata. WAYE SHI? ●﹏● ***** WAYE SHI? AYSHA SHAFI'EE 17 (☆_☆) Imran ya shigo kicin ya dauki 'yar kettle d'in da yake had'a coffee ya nufi jikin despenser ya fara tsiyayo ruwa a ciki. "Wai ta yaya ne zanyi ta binka tun jiya akan magana d'aya?" Muryar jaamil ta fad'a daga bayansa. "Wai ta yaya ne zanyi ta maka bayani guda d'aya tun jiya?" "Yarima ya kamata ka zauna muyi bayanin nan sosai, ka fahimci abinda nake nufi." Ya juyo ya bud'e cabinet d'in sama ya d'auko containers guda uku, na coffeee powder, madara da kuma sugar, ya zuba kowanne sannan ya maida kettle d'in jikinta ya kunna socket. "Na fahimce ka tun jiya jaamil kuma na gaya maka cewa ba zai yiwu ba." "Bamu da wata hanya bayan hakan yarima, saboda haka ba abinda zai hana shi yiwuwa." "Okay then, let's talk." Yaja kujera daga jikin island d'in ya zauna. "Zauna." ya fad'a ganin jaamil d'in bashi da niyyar zama. yaja kujerar a hankali shima ya zauna. "Ka saurareni da kyau don Allah....sanda kayi wannan tunanin Auren a cikin kanka, na san kayi la'akari ne da abubuwan da suka faru a baya, so lets make things clear, Bana son yarinyar nan kuma ban taba sonta ba, kawai da farko ne kafin in san rayuwar nan, yanayin maganarta ke burgeni shine har ka tab'a ganina a wajenta. Amma tun daga ranar da na yiwa Naani alkawari cewa ba zan k'ara zuwa kusa da ita ba, na goge duk wani abu daya shafeta a zuciyata, kuma tun daga wannan lokacin i try my best to keep away from her. So abinda kake tunani ba zai taba yiwuwa ba!" Jaamil yayi shiru na kusan minti d'aya yana kallonsa, sannan yace. "A yaushe aka tsara cewa zamu yi iya abubuwan da kake so ne?...nayi tunanin muna yin duk abubuwan da zasu samo mana mafita ne." Bai amsa ba ya cigaba. "Ya kamata nima ka saurerini da kyau yarima, sanda ka shiga jikinta baka yi wani tunani ba balle shawara, kayi abinda ka san cewa kuskure ne, yanzu kuma da matsala ta b'ullo me yasa kake zaton zaka sami zab'i a cikin kuskurenka? Dole ne ka hak'ura ka karb'i duk wata dama da muke da ita hannu biyu. Sannan dama bai kamata ka so yarinyar ba, saboda gabad'aya auren zai zama cikin abinda baifi wata biyar bane kawai, duk lokacin da Naani ta fito zamu ciro d'aya b'arin naka ba tare da ta sani ba sannan ka rabu da ita, mu k'arasa abubuwan da zamu yi mu koma rayuwarmu. A ina kaji dole sai da zancen so abin zai yiwu?" Imran yayi shiru yana saurarensa, abu d'aya kawai ya fahimta tun farkon zancen, shine duk wannan abin laifinsa ne bana jaamil ba, saboda haka da gaske ne bashi da zab'i, bai kamata ma ya samu ba, don in har ya samu d'in za'a iya kiran hakan da son kai. Abinda yayi wani kuskure ne da babu shi a lissafinsa, bai ma tab'a tunanin abu makamancinsa ba, a rayuwarsa yana taka tsan-tsan da komai mai muhimmanci, baya tab'a bada k'ofar da wani abu zai kawo masa cikas! Watakila shi yasa jaamil d'in ma yaji haushinsa a baya, yayi tunanin ko ya canja ra'ayi ne akan abinda suka tsara tun farko. Kafin daga baya shima ya gane cewar tsautsayi ne ya fad'a masa, ko kuma k'addara wadda bata wuce kan kowa. Cikin tunaninsa ya tsinto muryar jaamil yana cigaba da magana, ba yadda zaiyi, dole ne ma ya yarda da shawarar nan, in ba haka ba zai cutar dashi ne, shi d'in dake ta fad'i tashi wajen ganin komai ya tafi musu daidai, komai kuwa...komai d'in da ba laifinsa bane. Ya lumshe ido yana sauraren k'arar tafasar coffee d'insa daga baya. Ya riga ya yarda da duk abinda yake fad'a, saboda haka babu amfanin sauraren, sai da yaji ya kai k'arshe sannan yace. "Ta yaya aure tsakaninmu zai yiwu?" ya tambaya daidai sanda kettele d'in ta kashe kanta da k'arar k'assss! Alamun tafasa. "Yarima, na fad'a maka na tsara komai kafin na tunkare ka da wannan zancen, in har ka amince insha Allah komai zai yiwu cikin k'ank'anin lokaci." Lokaci. Kalmar lokaci ta d'auki hankalinsa, ya bud'e idonsa sosai sannan yace. "Jaamil aurensu yana d'aukan lokaci, ta yaya zanje har ta sanni na aureta kafin wata biyar kawai?" ***** Sulaiman ya shigo cikin falon baffa da sallama. Babu kowa a ciki don haka ya samu waje ya zauna, don a lokacin k'arfe goma ne saura na safe. Kusan mintuna goma kafin Baffan ya fito daga cikin d'akinsa. "A'ah ashe kaine..." Ya fad'a sanda ya taho kan kujerarsa ya zauna, a lokacin sulaiman yayi saurin saukowa k'asa. "Nayi zaton ai Ibrahim ne yayi sammako, don yau zamu je wajen commissioner dashi akan maganar kwangilar nan." Ya zauna sosai, sannan sulaiman d'in ya gaishe shi ya amsa. "Dama wad'annan malaman da suka duba Nanne jiya ne suka zo, da tun jiyan ma suka so ganinka sai kuma baku k'araso da wuri ba." "Toh...toh suna nan ne yanzu?" "Eh, suna tsaye a compound." "Toh shigo dasu mana, jeka ce dasu su k'araso. Koda kuma Ibrahim d'in yazo kace dashi ya dakata mu gama tukunna." Minti biyu bayan hakan, malaman nan su biyu suka shigo falon baffa, suka yi musabaha d'aya bayan d'aya tare kuma da gaisuwa kafin su zauna a kujerun dake gefe. "Ashe kuma jiya ma kunzo. Munje kaduna ne kuma mota lalace mana a hanya, shiya sa dare yayi mana." Babban cikinsu ne ya amsa. "Ya salam! Allah ya kiyaye gaba, haka shi sulaiman d'in yake fad'a mana wallahi, Da yake hajiya ce (yana nufin inna) tasa aka kira mu akan dai batun yarinyar nan." A daidai wannan lokacin lami tayi sallama ta shigo, ta ajiye musu tray d'in hannunta dake d'uke da flask, sukari da kuma k'ananan cups d'in shan tea sannan ta fita. "Alhaji a gaskiya munyi duk wani iya k'okarinmu harda taimakon wasu ma, don jiya mu bakwai muka zo gidan nan amma wallahi duk k'ok'arin namu ba muga wani aljani tattare da yarinyar nan ba. Shi yasa muka sami matsaya d'aya wadda itace kowannenmu ya yarda da ita, cewar Aljanun ne ke k'ok'arin shafarta, kuma da alama daga cikin jinsi mai k'arfi ne duba da yadda take wahala tun yanzu." Baffa ya gyad'a kansa alamun ya fahimta. "Sannan kuma kamar yadda muka yi bayani ne a baya, hanya mafi k'arfi da yarinyar zata kiyaye kanta shine dole sai tayi rik'o da addu'o'i, da kuma yawan zama da alwala da karatun alqur'ani, idan har babu wad'annan magungunan da muka bayar ma ba lallai ne a samu tasirinsu ba." "Toh su cikin gidan kun sake yi musu duk wannnan bayanin?" "Eh duk mun fad'a musu, amma akwai wani dalilin daban wanda dole kai ya kamata mu samu, shine ma dalilin dawowarmu." "Ina saurarenku.." ya amsa a hankali. Malamin ya d'anyi shiru kamar yana jin nauyin abinda zai fad'a. "Alhaji inda ace yarinyar tana da aure, ko kuma za'ayi mata aure nan da wani lokaci, hakan ba k'aramar kariya zai zame mata ba, don irin wad'annan Aljanun suna mu'amala ne kawai da matan da basu tab'a aure ba. Amma in har mace bata da aure, da kyar ne su rabu da ita." Baffa ya k'ank'ance ido ta cikin glass d'in dake fuskarsa yana kallonsa. Ba zaka yi iya banbace wane irin yanayi ne a fuskar tasa ba. Haushi? Mamaki? Nazari ko kuma rashin yarda? ●﹏● Please share this story with your freinds and family. Thank you for reading this document ***** WAYE SHI? AYSHA SHAFI'EE 18 (☆_☆) A cikin mafarkinta na biyu, duhu ne sosai kamar wancan karon, sannan dogwayen mutanen nan biyu na tsaye a kanta. Jikinsu na daga karshen gadon amma kuma sunyi kusa sosai yadda bata ganin wata tazara tsakaninsu. Bata iya ganin fuskokinsu, iya kafad'ansu ne kawai, kuma duk iya kokarinta, duk yadda ta kokarta ba abinda take gani a wajen da ya kamata ace kansu ne, bata ganin komai sai duhu. Taji ta k'agu, kamar ta bud'e baki ta roki daya daga cikinsu ya d'ora hannunsa akan goshinta kamar wancan karon, wancan karon da tunda sanyin fatarsa ta ratsa jikinta, duk wani ciwo nata yabi iska. Ta rufe idonta a hankali sanda ta hango hannun nasa na tahowa kan fuskarta, a hankali sanyin fatarsa ya ratsa kowacce jijiya ta jikinta sannan duk wani ciwo nata yabi iska! ****** A satin da tayi wannan mafarkin, bata k'ara fuskantar wani ciwo ba, jikinta ya koma k'alau kamar yadda take a da, sai dai kuma ba wanda ya yarda da ita akan hakan. Kowa yana binta ne da kallon mara lafiya musamman inna, dake takura ta akan yin abubuwa, bata isa ta tsallake wani tsari na shan magungunanta ba koda kuwa sau daya ne a rana. Duk da cewar tasha yiwa inna bayani cewa ita bata ganin magungunan zasu kawo mata sauki, don wani abin ma kamar k'asa ce kawai, amma inna ta rantse ba abinda zai hana ta daina sha, a lokacin taji kamar ta bata labarin mafarkin da tayi har sau biyu amma ta fasa, don wani abu ne da cikakken mutum ma ba lallai ne ya yarda ba, Balle kuma Inna da rikicin tsufa ya fara kamata. Saboda haka ta barshi a ranta kawai don babu na biyun inna a wanda zata fad'awa sirrinta. Babban abin mamakin daya same ta ya faru ne bayan ta koma sabuwar islamiyyar data canja, anan ne ta gane cewa gidan da Imran yake a layin dake gaba kad'an da islamiyyar yake, Don ba sau d'aya ba sau biyu ba tasha jin wasu daga cikin 'yan makarantar na hirarsa, hirar had'uwarsa, da kuma abubuwa da yawa wanda muhimmi shine zancen shi kad'ai yake zaune a gidan da yake, don akwai wadda ta rantse ma ta san wadda taje har k'ofar gidan nasa ya tabbatar musu cewa ba mata a gidan. Kuma a kullum shi kad'ai ake gani yana shiga gidan. Ranar data fara jin zancensa daga bak'in wasu 'yan ajin nasu, bata tab'a kawowa shi bane, sai da yazo wucewa a mota daidai lokacin tashinsu taji suna nuna shi tare da bayanin da aka gama a aji. A lokacin k'afafunta kusan mak'alewa sukayi a inda take tsaye, don tun ranar data fahimci ba'a gidansu walida yake ba, bata k'ara sake ganinsa ba kusan wata sati uku. A lokacin har sadiq saida ta tambaya amma yace bai gane shi ba, duk da ya san kusan mazan dake layinsu. Tun daga wannan ranar kuwa sai ta fahimci kusan rabin hirar 'yanmatan makarantar in an had'u a masallaci kafin a tayar da sallar la'asar ta Imran ce. Kuma kowa da irin albarkacin bakinsa da yake fadi game dashi. 'yan k'alilan ne ke fad'an abubuwan alkhairinsa, kamar yawan sallah a jam'i da kuma kyakyawar mu'amalarsa da suke ji daga bakin yayyensu, amma da yawansu sunfi sukar zamansa shi kad'ai a gidan ne da cewar wani abu ne da ba'a saba ba, kuma ake masa kalon laifi, wasu kuma zancensu bai wuce yabawa komai na tsarin halittarsa da kuma yadda suke mafarkin samun miji ko saurayi irinsa ba. A cikin satin, Nanne ta ganshi har sau uku amma ko kad'an bata bari ya ganta, duk da cewar daga cikin mota take hango shi kamar ya dawo daga aiki ko wani waje. Sai dai har cikin ranta tana so ko sau d'aya  magana ta shiga tsakaninsu, watak'ila hakan yasa ta samu yi masa tambayoyin dake cin ranta game dashi. Tambayoyin da a kullum k'aruwa suke musamman yanzu da take jin hirarsa wajen mutane daban-daban. **** Ranar Alhamis tana tsaye daga jikin mota a cikin asibiti tana jiran fitowarsu inna, wadda suka shiga ita da aunty amarya wajen gashin k'ashinta. Da a cikin motar take kuma sai ta fito waje shan iska, don yau kwata-kwata bata son shiga ciki, Allah yaso sun taho da Aunty amarya ne itama zata ga likitanta, da ta san ba yadda za ta yi dole sai ta shiga. Ta jingina bayanta tana kallon dogwayen bishiyun wajen, suna kad'awa a hankali kamar masu rangwada. Ta juya gefe ta kalli tsilli tsillin mutanen dake harkokinsu a harabar wajen, tana son irin yanayin nan, kamar ruwa zai sauka sannan kuma kowa na harkar gabansa. Daga can ta hango wani container na kanti saboda haka ta tafi da niyyar siyan ruwa. Har ta siyo kuwa ta dawo da kusan mintuna goma sannan su inna suka fito. Tana hango su ta bud'e gaban motar ta shiga. Idris direba ya taho shima daga jikin famfon da yake wankewata jarka ya shigo motar. "Zamu biya ta Al-karama idris zan tsaya in sayi magani dan Allah." Aunty Amarya ta fad'a daidai sanda idris d'in ya tada motar. "Toh shikenan hajiya." Nanne taji dad'i ak'alla tana so su dad'e a waje saboda yanayin garin, kuma Al-karama yana da nisa daga gidansu. Ta juya ta karbo wayar inna wadda kusan tasu ce su biyu, ta d'auki earpiece akan dashboard d'in motar ta cusa a kunnenta, sannan ta jingina kanta da glass d'in motar. Iskar dake shigowa na kad'a ta kota'ina. A cikin wak'ar da take ji ta jiyo inna na fad'an wai bata sa dankwali ba, don abaya ce a jikinta sai kawai ta dauko d'an bakin mayafi mai adon jajayen dutsuna ta yafa, tunda suka fito innan bata lura da ita ba kenan sai yanzu da taji dad'in k'afafunta. Ta k'ara lumshe idonta tana jin Aunty Amarya na gaya mata cewar ai haka yaran yanzu suke wai safiyya ma na yawan yin hakan, ta rasa wak'ar take ji ko hirarsu saboda haka ta ware volume d'in ta juya tana kallon titi. Sun iso daidai Al-karama dake d'aya tsallakensu, idris yace ba sai ya juya ba bari ya tsallaka kawai ya karb'o, saboda haka Aunty amarya ta shiga binciko takardar maganin da kud'in daga jakarta sai dai bata kai ga d'aukowa ba wayarsa tayi kara, ya d'auka ya shiga magana k'asa-k'asa, daga baya kuma sai ya fita waje ya koma bayan motar. Inna tace. "Yo kinji shakiyanci, maimakon ya karb'a kuma ya tafi yana wayar sai mun jira shi ya gama abinda yake kenan?" Aunty Amarya ta juya bayan motar ta ganshi yana ta sunkuyar da kai saboda haka tace. "Toh watakila wayar mai muhimmanci ce, tunda naji ance ya fara neman aiki." "Au ya gama karatun ne?" "Inna tun yaushe kuwa, har ya kawo takardar gamawar tasa gida ana tayi masa murna, shekara biyu ne ai da yake diploma suka yi." "Wallahi na manta, bawa Nanne toh ta tsallaka ta k'arbo miki, kan nan ya gama." Da kyar Nanne kuwa ta karb'a ta fito, don ta riga taji dad'in zaman da tayi. Ta kashe wakar, ta ajiye wayar akan seat d'in sannan ta rufe k'ofar motar ta matsa gefe. Ta tsallaka titi na farko kafin almarar da ta zama sanadin k'addararta ta faru. ALMARA. Don banda ita da ta tabbatar babu mota a kusa kafin ta tsallaka titi na biyu, babu wani d'an adam a wajen da zai iya bada shedar ga ta inda motar ta fito. Kawai sunji k'arar takewar birki ne da kuma wani irin ihu wanda karad'e wajen baki d'aya. Nanne taji tayi sama, numfashinta ma yana tafiya tare da ita, sannan a lokaci d'aya kuma taji ta fad'o da k'arfi ta daki k'asa. Wata irin k'ara mai amo ta fito daga makogwaronta ta ratsa cikin kowacce gab'a ta jikinta. Taji kamar bayanta ya b'alle ne sannan dukka jikinta ya mata nauyi. Numfashinta ya tsaya cak! a iya kirjinta, ta dunkule hannunta wajen k'ok'arin jawo iska ta shiga jikinta, a lokacin ne taji wajen ya rud'e da salatin mutane, muryoyi da yawa suka cika kunnenta, taji bata gane komai. Idanunta suka shiga k'ok'arin rufewa, amma tana iya ganin dishi-dishi na tarin mutanen dake ta shigowa cikin ganinta. A lakacin ne, taji wani ya d'aga hannunta dake da nauyi, sannan wannan muryar, wannan muryar mai taushi tayi magana. Kunnenta ya ture duk surutan mutanen dake wajen ya d'auko mata abinda muryar ke fad'a. Abinda muryar ta saba fad'a. "SA'ADHA!" ●﹏● WAYE SHI? AYSHA SHAFI'EE 19 (☆_☆) Nanne ta bud'e idanunta a hankali tana jin kamar ta tashi daga bacci. K'amshin turare da warin izal ne suka fara shiga hancinta kafin hayaniyar mutanen d'akin ta ziyarceta. Idanunta suka ci karo da silin fari, a jikinsa kuma akwai fanka wadda ke juyawa da k'arfi. A ina take ne? Don tabass nan ba d'akinsu bane. Sai kuma kwakwalwarta ta tuno mata da dukkan abinda ya faru kafin sumanta, tun daga tahowarsu titin Al-karsma gar zuwa sanda tazo tsallaka titin nan da sanda wata mota da bata san daga ina take ba tayi sama da ita. "Ta farka ne?" wata murya da bata san kota waye ba ta kutsa cikin kunnenta. "Ai kuwa kamar idonta a bud'e yake." Wata ta matso jikin gadon sannan ta kira sunanta, a lokacin maganganun mutane daki suka fara raguwa, saboda haka ta yunk'ura sosai sannan ta ware idanunta, ai kuwa fuskar Aunty nafisa ta fara cin karo da ita, sai ta Rahma sannan kuma Inna. Tayi k'okarin mik'ewa amma gabadayansu  suka  dakatar da ita. A sannan ne inna ta fara kuka tana fad'in. "Sannu Nanne, ke dai kina ganin jarabawa daga Allah, ba don da sauran numfashinki a duniya ba, da yanzu wani zancen ake..." "Inna dan Allah karki fara kukan nan, tun da ta farka ai godiya zamu yiwa Allah kawai." mama Azumi dake gefe ta katse ta. "A kuma yi fatan samun sauki ba." mama rabi ta k'arasa. Daga nan dukkan 'yan d'akin suka shiga matsowa ana yi mata sannu, wanda yawanci 'yan gidansu ne sai kuma k'alilan daga cikin matan layinsu. Ita dai bin kowa take da kallo don ba wani ciwo da take ji a jikinta...Bata kuma yi magana ba don ta tsinci muryar Aunty maryama na fad'in ba lallai ne ta gama wartsakewa ba. Yaya Ahmad da ya umar suka shigo sai kuma suka juya don kiran likita ko nurse. A lokacin nanne taji wani irin fitsari ya cika mararta saboda haka ta kalli Rahma dake gefenta tace. "Ke fitsari nake ji, raka ni toilet." Rahma ta kalle ta sosai. "Ai baza ki iya tashi ba, ban san ya za'ayi ba." Sai kuma ta juya gayawa aunty nafisa. Nanne ta yunk'ura da karfi ganin abinda zai hanata, anan ne idanunta suka ci karo da suntumemiyar k'afarta d'aure cikin plasta an rataye ta a jikin wani abu. Mamaki ya kamata, ta motsa 'yan yatsun daga ciki taji suna motsi kuma ba wani ciwo, toh me zaisa a d'aure ta haka?" "Nanne..." muryar aunty nafisa tasa ta juya. Tana magana k'asa-k'asa daidai saitin kunnenta. "Baza ki iya tashi ba, akwai robar fitsari a jikinki saboda haka in kina ji kiyi kawai." "Kamar yaya?" ta tambaya don a baiyane yake bata gane ba. "Kin tuna me ya faru dake koh?" Ta gyada kanta. "Toh kin samu karaya ne a k'afarki, don haka baza ki iya tashi ba, amma an sa miki robar yin fitsari a jikinki." Kanta ya kasa d'aukar zancen a lokacin d'aya, ta sake kallon k'afar tata, dama haka karaya take babu zafi ko kad'an. Sai kuma ta tuna da wanda ya kade tan, indan har ya karyata ai bai kamata ace baya nan ba. Kamata yayi yazo ya biya duk wani abu daza'a biya na asibitin  nan, tunda ba akuya ya buge ba. Ta juya da niyyar tambayar Aunty nafisan, sai kuma likita ya shigo tare dasu ya Ahmad, don haka kowa ya matsa ya basu guri, ya d'anyi mata tambayoyi akan yadda take ji ita kuma ta tabbatar masa ba wani abu da take ji a jikinta, amma da alama bai gamsu ba, don har allura ya sake mata a k'afar sannan yayi ta zuzzura mata wani abu a baki yana reading daga jikinsa. Daga k'arshe yace a bata wani abin taci sannan tasha tulin magungunan dake zube a side drawer. Kafin ya fita ya sake tab'a kafar tata, sannan yace gobe zasu sake dressing. Bayan sun fita aka mikar da ita zaune, ta jingina da filon bayanta sannan mama Azumi ta shiga bata abinci a baki. A lokacin ne ta tambayi inna dake zaune a gefensu ina mutumin da ya kad'e ta yake. Ga mamakinta sai ji tayi innan tace. "Yaro d'an Albarka, Nanne ki gode Allah, tun jiya d'an nan dashi ake ta fafutukar komai...yana tsaye anan wallahi har safe, sai d'azu sulaiman ya takura masa ya koma gida ya huta, amma anjiman nan na san zaki ganshi ya dawo." Kafin ta amsa mama Azumi ta k'arba. "Wallahi dai kuwa an samu d'an kirki, a wannan zamanin wani ai guduwa zai yi." Zata yi magana inna ta sake katseta. "Ai kowa yaga k'ok'arinsa wallahi, har su hajiya babba zuwansu d'azu saida suka yita yaba masa, banda tsautsayi ya gifta ai yaron da alamun hankali, bai kamata ace yana wannan gudun ba." Ganin abinda zata fad'a ba zaiyi tasiri akansu ba yasa ta maida bakinta tayi shiru. Ita taso taji inna ta fara fad'a ta kara tunzura ta akan a damk'e mutumin sai ya biya komai da za'a tambaya na asibitin. Wajen k'arfe uku, rahma ta matso kusa da ita. "Kin san me?" Ta gyara kwanciyarta sannan tace. "A'ah me ya faru?" "Kin san waye ya kad'e ki?" "Ta ya zan san d'an rainin..." "Kar ki karasa...Wannan mutumin ne fa." "Wanne?" "General topic d'in islamiyya." Ba tare da wani tunani ba bakinta yace. "Imran...?" "Au sunansa kenan? Wanda dai muka tab'a gani a jikin gidansu walida kafin su tare." A lokaci d'aya Nanne taji komai ya tsaya mata, imran ne ya kad'e ta? Ta yaya hakan zata faru? Me zai kaishi Al-karama a wannan lokacin? Taji zuciyarta ta shiga bugawa kamar lokacin da yaje gidansu, anya kuwa shi din ne, ko dai gizo idon rahma ya mata. Taya in shine zai tsaya kamar yadda inna ta fad'a...Amma me zai hana shi? Wata zuciyar ta tambaya, laifinsa ne ya kad'eta dole ya tsaya yaga samun lafiyarta, sannan ma ai ya santa. Sai kuma tayi saurin goge hakan, ta nemo zahiri tasa a zuciyarta, ya taimake ta ne kawai sau d'aya ya kuma tambayi sunanta amma ba lalkai bane ya iya rike saninta har yanzu. "...Na san abubuwa game dake fiye da cikin yatsu..." Ta tuno abinda ya fad'a wancan karon. Idan har yana nazarinta ne a da, yanzu ya daina don rabon data ganshi a layinsu kusan wata uku kenan. "Shi yasa nace miki kar ki k'arasa don duk sanda akayi zancensa, sai kin fad'a irin wannan tunanin." "Ta gallara mata harara da gefen ido. "Me kike nufi?" "Ke zan tambaya me kike nufi tunda har sunansa kin sani." Har ya yamma duk wanda ya shigo sannu yake mata, ita kuma ta tabbatar musu da ba wani ciwo a jikinta. Amma ko sau nawa ta fad'a babu alamun cewa suna yarda da ita saboda haka ta kwanta kawai ta rufe fuskarta. Bayan sallar la'asar, wajajen karfe biyar mutane da yawa suka tafi, sannan masu zuwa ma aka dakatar dasu, sai da kyar ma aka bar Aunty maryama tare da inna don su kwana a wajenta, don a yadda aka tsara Aunty maryaman ce kad'ai zata kwana amma inna ta kafe cewa baza ta bar asibitin nan ba tare da Nanne ba. Wajen karfe takwas saura, Nanne taji wani irin bacci ya fara fizgarta saboda haka ta rufe idonta, ta daina saurarar hirar da Aunty maryama keyi ita da mijinta wanda ya tafi aiki can abuja, tana bashi labarin dukkanin abinda ya faru. Inna kuma na daga k'asan d'aya gadon da ba kowa, tana nafilarta. A lokacin ne suka ji an kwankwasa k'ofar  dakin a hankali, inna da tayi sallama ta bada izinin a shigo, don dukkansu sun zata nurse din da tace zata dawo da daddare akan x-ray d'in da akayi a kai ne, wanda nanne ta kasa gane alak'arsa da karyewar k'afa. "Assalamu Alaikum." Wannan muryar, wannan muryar mai taushi ta ratsa kunnen Nanne. Kafin tayi wani tunani inna ta amsa. "Wa'alaika salam, har ka dawo? Sannu da zuwa." "Eh na shigo wallahi, munyi waya da sulaiman ne yake gaya min ta farka shine nace bari inzo inga jikin nata." Muryar ta sake ratsa kowacce kusurwa ta d'akin, cikin amonta a hankali, Nanne ta bud'e idonta da sauri ta kalli bangon dake fuskantarta, A lokaci d'aya tunaninta ya dawo mata da sanda taji muryar ta kira sunanta kafin idanunta su rufe, da kuma muryar imran sanda suka yi magana har sau biyu. Da gaske Rahma take kenan, da gaske ne shine ya kad'e ta ba wani, ta yaya k'addara zata sake had'a ta dashi a haka? "Ai wallahi da kayi zamanka ma sai gobe ka shigo, don tunda ta farka ba kukan ciwon da take, da alama abun da sauki ba kamar yadda muka zata ba." Taji numfashi ya zarce cikin kirjinta sanda ya sake magana. "Toh Alhmdlilah, Allah ya k'ara afuwa." "Ameen Ameen, k'arasa wajen gadon ku gaisa ai inajin idonta biyu." A daidai lokacin Aunty maryama ta gama wayar da take, ta mike daga kujerar da take kai sanda ya karaso suna gaisawa. Sai kuma ta sunkuyo daidai kunnenta tace. "Sa'adha juyo ku gaisa, mutumin d'aya hadu da tsautsayin buge ki ne." Nanne taji duk wani silin gashi na jikinta ya mike tsaye, ta gyara zaman d'ankwalinta a hankali sannan ta juyo, k'amshin turarensa ya cika mata hanci sannan zuciyarta ta k'ara girma a cikin kirjinta. Yana nan dai yadda ta sanshi, yadda ta fara ganinsa, yadda take hango shi daga nesa da kuma yadda ta ganshi ranar da ya shigo har gidansu. Shi kad'ai amma kwarjininsa ya cika ko'ina na dakin. Taji ta zama wata 'yar mitsitsiya a gabansa. "Sannu Ya jikin naki?" muryarsa kamar yana rera magana ne. Ta had'iye wani abu a cikin makogwaronta kafin ta iya amsawa. "Da sauki, bana jin kowanne ciwo." amsar da take fad'awa kowa kenan. Ya kalli kumbuarriyar k'afar tata sannan yace. "I'm sorry, tsautsayi ne ya riga ya faru amma banso muka k'ara had'uwa a haka ba." Idonta ya kai inda Aunty maryama ke tsaye sai taga bata nan, gwara da Allah yasa hakan, don baza ta so daga baya ta tsare ta da tambayar yaya akayi ya santa ba. Amma duk da haka sai ta kasa amsawa, saboda kamar yadda ya faru ne sau biyu a baya, sanda ya fara mata magana da kuma sanda ya shigo gidansu, ji take yi ta takura a gabansa, balle kuma yanzu da yana tsaye a jikin gadon da take ne, babu wata tazara tsakaninsu. "Allah ya k'ara miki sauki, na tabbata kafarki zata warke nan da k'ank'anin lokaci." Ya tabbata? Shi likita ne dama? Abinda inna ke nufi kenan da tace yana tsaye akayi mata komai? Ko shi yasa ma maganarsa take da sanyi da taushi? Tunda ance da baki ma likita kan warkar da mutum. Kamar ya karanci zuciyarta sai taji yace. "Ni ba likita bane, daga dai yadda kika ce bakya jin ciwo ne, kowa zai iya cewa da alamun sauki." Ta gyad'a kanta alamun ta fahimta. "Ina k'awarki? Da safe tana ta kuka anan." "Rahma?" ta tambaya kai tsaye don ta san itace. "Sun tafi gida sai gobe kuma." Daidai sannan nurse d'in ta murd'o k'ofa ta shigo. "A'ah sauki ya samu kenan, har ana hira haka?" Ta fad'a da dariya sanda ta nufo gadon. "Alhmdlilahi ai, taji sauki kam." Aunty maryama ta taso daga gefen inna tana fad'a. Ganin haka yasa Imran ya d'an ja baya kad'an sannan yace. "Toh ni zan tafi Aunty, sai gobe in Allah ya kaimu, Allah ya kara sauki." "Toh mungode fa, mungode Allah ya kaimu." Nanne ta juyo ta kalle shi sanda ya tsugunna yana wa inna sallama. "Da fatan bakya kukan Allura don ita zamu yi yanzunnan." Nurse d'in ta fada sanda ya d'ago shima ya kalleta, kawai sai tayi murmushi ta juya d'aya gefen. ***** A cikin sati d'aya da kwanaki, Nanne ta maida 'yar k'ibar jikinta data rasa a baya na rashin lafiya, mutane suna ramewa a asibiti amma banda ita, don ciwo kanta baya mata balle kuma k'afar da aka daure, sannnan ga kulawa da take samu kota wane b'angare. Sai dai ranar da aka fara mata dressing da taga wani dogon yanka a kafar tata, ga kuma k'ashinta yana lilo, ita kanta ta tsorata ace bata ji ko d'igon zafi a wajen. Su kansu likitocin suka rikice da tunanin ko wajen ya zama paralysed ne amma duk yadda aka taba tana ji, saboda haka a next dressing suka gaiyato wasu likitocin akayi ta bincike akanta, sai daga baya suka tsaya kawai akan cewar jijiyoyin wajen ne suka daina aikin d'aukar zafi zuwa kwakwalwarta. Suka kira Baffa da zancen za'ayi mata aiki a wajen amma ba wanda ya san ya amince ne ko A'ah, don sadiq da yazo ya gayawa Nanne cewa yaji su ya ibrahim na fad'in wai ba zancen aikin kad'ai suka yi masa ba. Ita kam! tun lokacin da taji ance jijiyoyinta ne suka daina aiki ta hutar da kanta da tunani. Fatanta ma kar su dawo da aikin don ba wanda ke son ciwo. Shi yasa ma da taji baffan baice komai ba ta mike k'afafunta ta cigaba hutawarta. A cikin kwana biyar imran yazo sau hud'u. Kuma a duk sanda yazo gaisuwa zata shiga tsakaninsu har da 'yar hira. Shi yasa a kullum take tashi da kwarin gwiwar ganinsa. Wanda itama a lokacin bata san me yake faruwa game da ita ba, bata iya wani tunani mai kyau ba tare da fuskarsa ta shigo ba. Da gaske ne abinda Rahma ta fad'a ya kamata ta tambayi zuciyarta me take nufi? Me take nufi da yawan damuwarta akansa? Amma ya zata yi? Fad'ar manzon Allah ce cewa zuciya na son wanda yake kyautata mata, tun da aka kawo ta asibitin nan, daida da kud'in magani Imran bai bari sun biya ba, yace shi yayi laifi kuma alhakin komai na wuyansa, saboda haka kullum 'yan uwanta da ita kanta cikin ganin k'ok'arinsa suke, a gefe d'aya kuma zuciyarta na k'ara rugurgujewa da tunaninsa. Kullum tana tashi da fatan cewa zai baiyana a d'akin da zarar ya dawo daga aiki, da wannan annurin fuskar tasa mai k'ara masa kyau da kwarjini, hakan yasa ba'a tab'a karanto gajiyarsa, a kullum ka ganshi, zaka iya rantsewa a lokacin ya fito daga wanka bayan ya tashi daga baccin hutu. A cikin sati biyu kawai, Nanne ta yardarwa kanta ta fad'a cikin yanayin da bata taba kawowa kanta ba. Yanayin damuwa da wani bayan harkokin gabanta, ta ayyana a ranta abubuwa baza su taba dawo mata daidai ba. Rayuwarta baza ta taba komawa kamar da ba, don ta d'auko wani abu ne da ba zai tab'a faruwa ba. Ta fahimci cewa ta fad'a son IMRAN,  ta shiga k'aunarsa ba tare da sanin me take yi ba! ●﹏● WAYE SHI? AYSHA SHAFI'EE 20 (☆_☆) Iyaye.... Wasu mutane ne da Allah ya hallice mu daga b'angare na jikinsu, soyayayarsu wani abu ne da tun farkon halitta aka manne jikinmu tare da ita, shi yasa komai irin halinsu, komai tarin laifinsu, akwai wannan d'igon k'aunar da zai sa kaji cewa kaga wani naka. Nakan da har abada baza ka tab'a samun irinsa ba. Nanne ta tsirawa matar dake gabanta ido, matar da ta ajiyeta tun bata kai shekara guda a duniya ba ta kama gabanta da sunan aure. A kullum ta ganta sai ta nanatawa zuciyarta wannan laifin, don ta samu ta iya jin haushinta ko sau d'aya ne amma ta gagara hakan, duk sanda ta ganta sai zuciyarta ta tsinke, gwiwoyinta suyi sanyi, taji kamar taje ta rungumeta ta lalabo duk wannan k'auna da d'umin uwar data rasa a baya. Suna zaune ne daga cikin bedroom d'insu, a lokacin anyi wani ruwa mai yawa an d'auke. Saukarsu kenan daga adamawa ana dab! da fara ruwan. "Inata magana kamar kina tunani, duk sunce a gaishe ki." Ta sunkuyar da kanta a hankali sannan tace. "Ai ban sansu bane Addano." Ta kira ta da yadda taji 'yanuwanta na kiranta duk lokacin da taje. Ta d'anyi tsaki kad'an. "Shi yasa nake ta nacin a kawo ki ai, kwanaki nayi aike ya kai sau uku daga ace min baku yi hutun makaranta ba, sai a bada uzurin wai za'ayi biki a gidan ne." "Da gaske ne ai, anyi bikin su yaya Aisha kwanakin baya." Bata ce komai ba sai ta juya ta kalli k'afarta da a yanzu aka kwance sannan tace. "Ance bayan karayar wai akwai wani ciwon ma koh?" "Eh bayan anyi aikin ne bana jin zafi a wajen, shine likitocin suka yi bincike suka ce jijiyoyin k'afar ne keda matsala, suka yi magana da baffa akan za'ayi aiki a wajen." "Ya yarda kuma?" Ta girgiza kanta. "Bai yi magana ba dai tun bayan nan." "Ai gwara a kyale ki, in waje ya warke me yasa kuma za'a tafi neman wani ciwon." A sannan wata mata da suka zo tare ta shigo rik'e da 'yar karamar 'yarta da take goyo. (k'anwar nannen kenan.) "Addano gata ta tashi yanzun nan." Ta mik'o mata yarinyar wadda ke ta mutstsuka ido, nanne ta kalleta, k'anwarta a suna amma bata ma san sanda aka haife ta ba, 'yar kyakkyawar bafulatana da ita, mai dogon gashi kamar nata. Sai dai kuma an b'ata fuskarta da bille. Ta kai hannu ta tab'a 'yan kafafuwanta. "Yaya sunanta?" "Miryam. Koda haihuwarta ai na aiko kizo baffanki yace jarabawa kuke." Bata ce komai ba ta cigaba da murza k'afar yarinyar. "Gobe in Allah ya kaimu da safe zamu koma." Sai ta d'ago ta kalle ta. "Baza ku biyo ta nan ba kenan?" Nuratu ta girgiza kanta. "Toh ai basu fad'a min da wuri ba, sai shekaranjiya fa aka aika, kuma gobe Babansu miryam zai dawo daga china. Kinga dole in koma da wuri." Sai ta gyada kanta kawai tayi shiru. Don mijin nata d'an kasuwa ne dake yawan tafiye-tafiye, bai cika zama a gida. "Nanne wai ajinki nawa ne?" 'SS3...wannan shekarar zamu gama insha Allah." "Toh meye a ranki game da nan gaba, kema karatun zaki biye musu kiyi, koko zaki rufawa kanki asiri kiyi aure?" Kalmarta ta k'arshe taso bata dariya, tayi aure a yanzu? Toh ta auri wa? "A'ah zan fara karatun dai, idan auren yazo ina cikin yi, sai ayi." Nuratu tayi ajiyar zuciya kafin tace. "Na san dama sun cusa miki irin ra'ayinsu, idan zan baki shawara a matsayina na mahaifiyarki kuma ki d'auka, gwara kiyi aure tun yanzu ki samarwa kanki 'yanci. Karatu zaki iya yinsa koda aure goma akanki, kuma shine ma zaki fi yinsa cikin 'yanci." Tayi shiru tana juya maganganun. Ba wai tana shirin yarda dasu bane, don ta san abu ne mai kamar wuya saboda haka sai kawai  tace. "Toh Addano ni a yanzu ma ba wanda nake kulawa ai." Ga mamakinta, sai taga ta fuskanceta sosai, sannan ta gyara zaman miryam dake kan cinya tana shayar da ita. "Wannan ba matsala bane Nanne, dama akwai zancen dana taho dashi tun daga gida, idan kin amince zan turo d'an wata yayata Nura, yaro ne mai hankali  kuma shima d'an boko, don har ya gama karatunsa ma yana aiki a cikin adamawa, na tabbatar miki in kika amince dashi zaki ji dad'i nan gaba, kuma ta hanyarsa zaki dawo cikin 'yan uwanki." Nanne taji kanta ya daure ta kasa fahimtar farko da k'arshen zancen, amma abun da yafi daukar hankalinta da tace zata dawo cikin 'yanuwanta. "Addano wadannan su ba 'yanuwana bane?" "Yan uwanki ne amma bana uwa ba, kuma ke mace ce, duk girmanki dangin uwa sune martabarki, yanzu ki duba fad'in gidan nan kaf! Duk randa akace babu ran inna wallahi ko kinyi aure kika zo sai dai kiyi ta kame-kamen wajen zama. Amma inda cikin 'yanuwana kike sai inda kike so zaki jefa k'afarki." Tayi shiru kawai tana jinta, don ta san abinda take fad'a wani abu ne da ba zai tab'a yiwuwa ba, ita a yanzu kwata-kwata ma harkar aure bata cikin lisaafinta, abinda ke gabanta daban ne. Kuma ko zata yi auren ma, ba zai yiwu da wani wai shi Nura ba, mutanen da basu santa ba, basu damu da saninta ba, sai a yanzu ne zata yi musu amfani? Baza ta iya musa mata ba, sai kawai ta dinga binta da kalmar toh, a k'arshe kuma tace mata zata yi tunani, ita kuma tayi ta jaddada zancen akan ta kira ta duk lokacin da ta gama amincewa zata turo Nuran. Da haka aka zo d'aukansu daga can gidan da zasu kwana bayan garin ya d'an sha. Bayan sallar magriba Nanne ta kwanta akan bargon inna dake shimfide a k'asan window na falo, yanayin garin na yadda iskar damina mai sanyi take kad'awa da kuma k'anshin jik'akk'iyar k'asa ya taimaka mata wajen ture duk wani tunani a kanta, ta janyo abinda ke cin ranta. Tunanin Imran! Tun bayan sallamarta da akayi daga asibiti sau biyu kawai yazo, na farko ma bata ganshi ba tana bacci. Sai a na biyu shi kuma bai dad'e ba yana ta sauri. Gashi har yanzu bata fara fita ba balle ta ganshi a hanyar islamiyya. Kuma a kullum, a kowacce rana tana jin zuciyarta ta k'agu da son sake ganinsa. Sai a yanzu take sake tabbatar wa kanta da gaske son Imran take, kuma ba tun yanzu ba, tun ranar data fara ganinsa ta kasa manta shi, har zuwa yanzu da komai ya cakud'e mata. Ta san koda ta ganshi d'in ma, ba abinda zai faru ko ya canja, sai dai ta k'ara d'aukarwa kanta wahalar da zuciyarta ta jawo mata. Wahala mara yankewa, wahalar da a 'yan shekarunta bata san zata fad'a ba. Wani b'angare na zuciyarta ya fad'a mata cewa ta taimakawa kanta tun yanzu ta cire imran daga ranta, donshi matsayin daya d'auke ta daban ne. Ya taimaka mata a farko kuma ya taimaka mata a yanzu da tsautsayi ya had'a su, kuma babu komai bayan hakan. Amma duk sanda tayi wannan tunanin sai maganar daya tab'a fada mata tazo ta ture komai. "Abubuwan dana sani game dake, suna da yawa...." Ko ba komai akwai lokacin da shima ya damu da ita. Ta lumshe idonta a hankali tana kallon yadda iska ke turo labulen windon, su inna na daga gefenta suna firfito da kayan da Nuratu ta kawo ana gani. A lokacin ne rediyon inna dake kunne ta fara playing wata wak'a sakamakon gama wani shiri da akayi. ....Sitting wide eyes open behind this four walls hoping you'll call, It's just a cruel existance i guess no point hoping at all. Baby, Baby.. I feel crazy, up all night! All night! Everyday, you give me something...but you said nothing. Whats happening to me?! (if u can relate dix moment, Allah muku albarka!) ***** BAYAN SATI DAYA. Tana zaune tana jiran isowar Rahma, yau a gidan zata kwana don haka ta tafi siyo musu wainar fulawa a can bayan layinsu, inna ta fito daga d'aki sanye da hijabinta a karkace. "Baffanku ne ke kiranmu tare dasu hajiya, da sune ma zasu zo nan nace A'ah gwara mu zauna a can falon nasa." Haka kawai Nanne taji gabanta ya fad'i ta juyo ta kalli inna. "Ke dasu hajiya? Har dasu mama rabi kenan." "Eh mana da duka matan nasa, na san dai wani abun ne ya taso, in ba haka ba yaushe rabon da ayi irin wannan zaman...tun lokacin da tsautsayin nan ya fad'a kan muhammad daya kad'e yaro a mota." Nanne ta tuna lokacin, ya muhammad na wajen hajiya babba ne ya tab'a kad'e wani yaro a mota bisa kuskure, abinda yasa bata manta ba saboda azumin da yayi tayi har sittin, kullum su mama Azumi suyi ta hidimar kayan shan ruwansa. Tabass kafin baffa yayi irin wannan kiran sai abu mai muhimmanci ya taso tukunna. Ta had'iye yawu cikin makogwaronta sanda inna tayi hanyar k'ofa. "Inna ki gyara hijabin naki." Bayan kamar minti biyar Rahma ta shigo d'auke da leda da kuma faranti. "Na dad'e ko? Wallahi layi ne da ita kamar me." Ta sauko k'asa ta karbi plate din. "Baki ma wani dad'e sosai ba...juye mana ita a ciki." Rahma ta zauna tana zubawa. "Kin san har na taho na tuna bata bani yaji ba, saida na koma." "keh na tuna Amina ta bani wani flash da film d'in india a ciki, bari in d'auko in sa mana." Ta tashi da sauri ta nufi d'aki, da fatan film d'in zai d'auke mata hankali daga tunanin dalilin meeting d'insu inna, don haka kawai take jin jikinta wani iri. Ta dawo, tasa flash d'in a jikin TV sannan suka zauna cin wainar. Sai dai tana kai lomar farko bakinta, sadiq ya d'age labulen d'akin ya shigo. "Ai tunda naji dama kina cewa anan Rahma zata kwana na san wani abin kuka shirya, wato ga waina fulawa mai zafi da zob'o ga kuma TV kunsa a gaba." Nanne tana kallonsa tace. "Kai kuma gulma na cinka sai kazo kaga me akeyi...Rahma dan Allah san masa ya bar nan wajen." Ya tab'e baki. "Allah ya kiyaye inci wannan abar, ni baffa ne ya aiko ni yana kiranki." A lokaci d'aya taji k'arar wani abu ya tarwatse a k'irjinta, shikenan abinda take tsoro ya faru, akanta za'ayi meeting d'in nan shi yasa dama tun d'azu jikinta ya bata. "Da gaske kake dan Allah?" Ya langwab'e kai ganin ta tsorata a lokaci d'aya, ya sami abinda yake so. "Da gaske nake 'yan mata, kije ki girbi abinda kika shuka." Ta d'auki kofin robar dake gabanta ta jefe shi dashi, yayi saurin kaucewa sannan ya fita yana dariya. Sanda ta tura k'ofar falon baffa ta shiga da sallama, jikinta gabad'aya yayi sanyi sannan zuciyarta ta sallama cewa duk abinda zai faru bai zai mata dad'i ba kuma dole ne ta karb'e shi hannu biyu, tunda wad'anda ke cikin d'akin sune da iko da ita da kuma duk wani abu nata. Inna tana zaune daga k'asan labule hajiya Babba na gefenta, sai Aunty Amarya, mama halime da kuma mama rabi. A d'aya gefen, ya Ahmad ne da ya ibrahim wanda bata san yaushe suka zo daga gidajensu ba, sai kuma sauran, ya sulaiman, muhammad, ishaq, Nasir da kuma ya umar. 'yan biyu ne kawai basa nan, inda ta fahimci daga kansu aka tsaya kenan. Toh me zai sa a tsallake su, a tsallake sadiq a taho kanta? D'akin ya mata girma, ta rasa inda zata zauna sai da Baffa dake tsakiya ya yafito ta da hannu ya nuna gefensa. Ba yadda ta iya haka ta tsallake kowa ta nufi inda yake zaune a k'asan kujerarsa. "To tunda kowa yazo, Babban yaya sai kayi mana addu'a koh." ya fad'a yana kallon yaya Ahmad wanda yayi d'an murmushi kafin ya fara. "Salati goma ga Annabi(SAW)...." Har aka shafa Nanne bata tabbatar duk abinda aka fad'a tayi dukka ba, don zuciyarta lugude kawai take kamar wadda tayi gudu mai nisa sannan ta tsaya a lokaci d'aya. Cikin nutsuwa Baffa ya bud'e baki ya fara magana! ●﹏● WAYE SHI? AYSHA SHAFI'EE 21 (☆_☆) Cikin nutsuwa baffa ya bud'e baki ya fara magana. "Dalilin taruwarmu anan akan matsala ce data shafi Nanne, kowa ya san irin rashin lafiyar data fuskanta kwanakin baya, wanda bayan anyi duk wani k'ok'ari da kuma taimakon Allah ta samu sauki na 'yan kwanaki. Daga baya kuma ciwon ya sake tashi, bayan an kuma warkar dashi ya sake dawowa dai a cikin k'ank'anin lokaci. Toh a zuwan da malaman suka yi na k'arshe ne suka same ni da zancen cewar har a lokacin basu iya gano ainihin abinda ya same ta ba, duk da rashin lafiyar tata tayi kama da shafar aljanu amma basu ga wani abu na alamar aljani a jikinta ba. Saboda haka dasu da sauran k'arin malaman da suka zo a ranar, suka bada tabbacin cewa bak'ak'en aljanun ne ke son shiga jikinta, bana irin shafar aljanu da aka saba gani ba, saboda duk wani alamun hakan ya baiyana a jikinta. Sunce su irin wannan aljanun suna da wahalar fitarwa in dai har suka riga suka shiga jikin mutum, sannan suna mu'amala ne da mata da basu da aure kawai. A lokacin sun bani shawarar cewa da za'a samu tayi aure nan bada jimawa ba, toh da tabbas aljanun baza su sami k'arfin cigaba da bibiyarta ba balle har su iya shiga jikinta. Toh tun daga wannan lokacin sai nayi ta bibiyar malamai wad'anda suke da ilimi akan irin wannan abin, amma kowa magana d'aya irin tasu dai yake maimaita min, in zan sami k'ari ma bai wuce wani yace anyi sa'a ma da har yanzu aljanin bai gama shiga jikinta ba. Ana cikin haka ne kuma ta gamu da wannan tsautsayin, kuma wani abu ya sake faruwa na cewa taji ciwo a k'afa har an sami karaya amma bata jin zafi a wajen. Suma likitocin suka kira ni bayan sunyi duk bincikensu akan cewa jijiyoyin k'afarta ne keda matasala basa iya aikawa da wani abu zuwa kwakwalwarta, sannan ita kanta wai kwakwalwar tata akwai wani abu da suka gano a ciki kamar k'ari wanda basu tabbatar da menene ba. Suka bani takardu gasu can a kujerar can akan inje insa hannu za'a sa ranar yi mata aiki. Sai dai ni tunda na karb'o su hankalina bai kwanta ba. Bayan kwana biyu sai d'aya daga cikin likitocin ya kira ni a waya. Yace yana so ne ya fad'a min gaskiya akan zancen aikin nan, duk wani abu da na gani a rubuce basu tabbatar dashi ba kawai hasashe ne, amma shi yana danganta rashin lafiyar Nanne da shafar aljanu don haka yake bada shawara a fara gwada magungunan hausa tukunna. Da naji haka sai naga an sake dawowa kan dai zancen malaman nan ne, saboda haka sai na tafi wajensu da kaina sulaiman shi ya kaini, suka kuwa sake tabbatar min da abinda suka fad'a a baya, magunguna zasu bata sauki na d'an lokaci amma babu tabbacin cewa nan gaba aljanun baza suyi nasarar shiga jikinta ba sai dai in har tayi aure. Don haka na yanke shawara cewa yi mata auren a yanzu shine kad'ai mafitar da muke da ita, wadda zata sa ayi fatan dacewa." Ya juya a hankali ya kalli inna. "Inna wannan shawara tace kawai, amma ina so inji ra'ayinki duk abinda kika fad'a a yanzu dashi za'ayi amfani." Inna ta gyara zamanta sannan tace. "Yo ni dama ai ka san me zance. Shekara biyu kenan harda watanni ba zan manta na tako k'afata har d'akin nan akan zancen auren uarinyar nan, nace maka ni a tsarin da iyayenmu suka raine mu, 'ya mace daga sha uku, hudu, biyar an kawar da ita. Amma ba irin zancen da baka kalailayeni dashi ba akan kai a cikin 'ya'yanka baka tab'a aurar da d'a bai gama sakandire ya fara ta gaba ba saboda haka inyi hakuri. Nace maka sam! Ni ina yiwa yarinyar nan kallon 'ya ne tunda nina ci kashinta da komai ba zan yarda tayi ta zama a gabana ina kallonta haka ba, toh Inace a yadda muka tsaya da kai cewa data k'are sakandiren zaka aurar da ita ne koh?" Baffa ya d'aga kai. "Haka ne inna." "Toh yanzu me ya rage a gamawar da har zakayi ta wannan dogon bayanin kamar mai shirin laifi? Koko kana tunanin bata isa auren bane?" "Ba haka bane inna, shawara ce kawai na nema don kece da iko akanta." "Toh in haka ne ko gobe ka tara jama'a ka d'aura mata aure, Allah ya hore min abinda zan had'a nan da sati d'aya a kaita gidanta." Ya Ahmad yayi saurin gyara zama yace. "Toh Baffa zancen karatunta fa? Tunda yanzu SS3 take, bai kamata ai ace ta tsaya kenan ba." Inna ta gallaro masa harara. "Ai zancen kenan, karatu...karatu ko uwar me yake muku oho." "A'ah inna da gaskiyarsa shima, nima kuma nayi wannan tunanin. Zata cigaba da karatunta insha Allah, in lokacin yin WAEC da NECO yazo za'ayi mata registration tayi kuma ta cigaba har jami'a da yardar Allah." "Toh amma Baffa..." Mama halime ta fad'a daga gefe. "...Nace ana ta zancen aure, dama ita Nannen ta kawo wani tsayayye ne ko kuwa ya za'ayi?" "Wannan dalilin shi yasa nasa aka kirawo ta nan itama, dan taji komai da kunnenta kuma in bata dama nan da wata guda ta gabatar min da wani, in har akayi bincike akansa babu matsala shikenan, idan kuma ba haka ba dama akwai tarin mutanen dake min magana akanta, don ak'alla abokaina uku suna min zancen nemawa 'ya'yansu kuma na tabbata kowanne a cikinsu ko nan da wata gudan nace baza a sami matsala ba." Hajiya Babba tayi gyaran murya sannan tace. "Toh Allah ya tabbatar mana da alkhairinsa, kowannenmu kuma sai ya taya da addu'ar nema mata sauki. Sannan kema Nanne sai kin kula sosai da kanki, tunda kinji duk abinda akace koh?" A lokacin kowa ya juya ya kalli Nannen, wadda fuskarta ta jik'e sharkaf da hawaye da kuma gumi. ****** "Me suka tattauna?" Imran ya tambaya yana kallon jaamil. "Komai ya tafi daidai, na gama nawa aikin saura naka." Imran ya ajiye wayar hannunsa a gefe sannan ya kalle shi. "Kana nufin dukkansu sun amince?" "Na gaya maka komai ya tafi daidai, yanzu kai ya rage ka fara naka." Ya ciji k'asan lebbensa yatsunsa a sark'e yana kallon 'yar vase flower dake can jikin tv-stand. Zuwa can kuma ya maida yatsun kan hab'arsa sannan ya huro iska daga bakinsa. "Ta ina zan fara kenan?" "Yarinyar ta riga ta fara sonka, kuma a yanzu bata da isashshen lokaci, saboda haka baka da matsala, inaga kai kad'ai ne zab'inta." Imran ya juyo ya kalle shi, yana zaune daga kan two seater dake gefe yana kallon tvn dake kunne tana nuna tashar News, sun kashe fitila sai hasken tvn ne kad'ai a d'akin yana reflecting akan fuskarsa. Har wajen dining ba fitila sai hasken switches kawai da kuma na fitilar kitchen. "Meye ne kake kallona?" "Tunowa nayi da yadda kake damuna akan na rabu da yarinyar lokaci kadan daya wuce, yanzu kuma kaine me cewa inje wajenta." Bai kula abinda ya fad'a ba yace. "Ya kamata ka saba fad'ar sunanta tun yanzu. Don bana son abinda zata gane cewa kamar akwai wani dalilin da zaisa ka aureta." Kafin ya bashi amsa wayarsa ta fara haske da vibration akan kujerar. Ya kalli screen d'in sannan yaja tsaki. "Waye?" "Maryam." ya amsa a tak'aice. Jaamil ya juyo ya kalli wayar sannan yace. "Kar ka damu, idan ka zama ANGO zata kyale ka ne." ●﹏● WAYE SHI? AYSHA SHAFI'EE 22 (☆_☆) Nanne ta tsirawa fuskarta ido a mudubin toilet tana nazari. A cikin sati d'aya kawai ta wani irin zabge kuma idanunta sunyi fari fat! sun d'ashe, kamar masu shirin fad'awa duk wanda ya kallesu irin adadin hawayen da suka zubar, ta kai hannu ta tab'a wuyanta a hankali inda wani rami ya fito tsakanin k'asusuwanta biyu. Watakila na rashin cin abincin da bata yi ne, ko kuma  na yawan tunanin dake faruwa a cikin kanta. A sati d'aya kawai, kwakwalwarta tayi sak'a da warwara akan dubunnan abubuwan da a gabad'aya shekarunta na baya bata yi ba. A kullum zata tashi da fatan cewa wannan zaman da akayi na falon baffa bai faru ba, amma cikin awa daya kawai fatanta zai ruguje saboda irin hada-hadar da inna keyi kamar a satin ne za'a d'aura mata auren. Aure. A kullum ta fadi kalmar ta sake maimaita ta tasan cewa bata shirya masa ba, don wani abu ne da kwakwalwarta bata taba hasko mata shi nan kusa, bama haka ba, ba zata iya tuna ranar da wai ta hango kanta a gidan aure ba. Balle kuma yanzu da akace za'a tura ta cikinsa nan kusa. Kwallar da ta taru a idonta d'aya ta ziraro kan kumatunta, tasa bayan hannunta da sauri ta share. Ta riga ta yiwa inna alkawarin daina kuka, tayi mata alkawarin karbar al'amarin nan hannu biyu tun ranar data tasa ta a gaba da rok'on ta taimaka ta dawo da rayuwarta kamar da. Don tun bayan fitowarta daga falon baffa a waccan ranar komai nata ya canja, ta daina magana, ta daina dariya, ta daina shiga mutane, bata da aiki sai ta dukunkune kanta a gado tayi ta turkar kuka. Ba irin magana da bin bakin da kowa a gidan bai mata ba amma bata ko fahimtar abinda suke fad'a. Sai da inna taga abin nata na neman d'orewa ne yasa ta sameta ita kadai ta ajiye duk wani fad'anta a gefe ta rok'e ta akan ta taimaka ta yiwa mahaifinta da ita biyayya, tace su iyayenta ne, bai kamata su nemi abu a wajenta ba amna da sunan baffa da kuma ita yau tana neman alfarmata da ta basu had'in kai wajen gyara rayuwarta, don abinda suke k'ok'arin yi d'in taimako ne ga ita kanta. Abin ya bata tsoro ganin innan na shirin durk'usa mata, a lokacin sai ta manta da komai tayi mata alkawarin cewa ta amince baza ta sake nuna damuwarta ba, tana hawaye itama innan nayi. Kuma tun daga wannan ranar, take kokarin ture duk wata damuwarta ganin ta farantawa innan. Bata k'ara kuka ko nuna b'acin ranta ba, sai dai kuma ta koma wata sabuwar halittar daban. Bata magana, sai bada amsar abinda aka tambayeta kawai, bata dariya bata kuka, abinci ma tana cin iya wanda ta san zai hana ta galabaita ne kawai. A kullum zuciyarta cikin tarawa da d'ebe tunani kala kala take kawai. Tunanin yadda zata yi ta fad'akar da kowa cewa ita ba wasu bak'ak'en aljanu dake shirin shafarta, rashin lafiyarta cuta ce kawai ba komai ba. Musamman baffa, tasha  had'a irin kalaman da zata je ta tsugunna a gabansa ta fada masa ya gane cewa ita lafiyarta kalau, ya taimaka ya janye maganganunsa rayuwarta ta koma daidai, amma a kullum ta tashi taga wannan farin cikin na fuskar inna, sai tunani ta ya karye ta shiga lalubar wata hanyar da zata fitar da ita. "Yanzu Nanne har yanzu kina cikin band'akin nan?" Muryar inna ta dawo da ita cikin zahirin da take. Da sauri ta bude fanfaon sink d'in sannan ta taba butar dake gefe da kafarta, jin k'arar yasa innan tace. "Toh Allah kuwa ya sawwake miki. Kiyi ki fito Rahman tun dazu take zaman jiranki, ga dare nayi." Jin sunan Rahma yasa ta tuna da cewar yau zasu je can gidan malaman ta karbo magunguna, abinda yasa dole saida ita saboda akwai wani turare da malamin yace za'a dinga mata duk sati, kuma matarsa ce take yi. Sunje wancan satin anyi mata saura na yau kenan. Ta ja tsaki a k'asan numfashinta. Allah ya sani bata ko son ganin mutanen nan. Don a tunaninta, sune silar duk wani hali da take ciki a yanzu. Ta d'auko sabulu ta wanke fuskarta sannan ta fito. Ta d'auki hijabi milk dogo mai hannu ta zura akan kayanta kafin tayi falo. Tana fita inna ta kalleta tace. "Koma ki d'auro dankwali." Bayan abinda da bai kai minti d'aya ba ta sake fitowa ta d'aura dankwalin, bak'i irin na abaya. "Toh ungo nan...ance idris ya fita da motar kuma yayyenki ba wanda ya dawo, ku hau adaidaita sahu kuje ku dawo kuma dan Allah kar ku dade, ana gamawa ku taho, ko sadiq za'a kira ya raka ku ne ma?" Rahma tace. "Inna kin manta sun tafi kaduna. Ba komai zamu iya zuwa mu dawo, ai ba nisa sosai." Har suka fita bakin titi, Nanne bata yi magana ba, sai da suka hau adaidaita sahun sannan Rahma ta kalle ta tace. "An kawo irin takalmin nan da kika ce kina so, wanda ake siyarwa a mak'otanmu." Ta kalleta kawai sannan tace. "Mhmmm." Kamar Rahman zata sake magana kuma saita yi shiru. Haka kawai sai Nanne taji ba dadi, babu laifin rahma ko d'aya a cikin halin da take, bai kamata ta canja mata haka ba. Ta tuno yadda ta damu sosai lokacin da take ta kukan nan, a kullum zata shigo d'akin ta dubata sau ba adadi kuma bata tab'a gajiyawa ba akan bata hakuri. Sai ta juya ta kalleta tace. "Kuma akwai kalar wanda na gani a wajenki d'in?" Jin haka yasa ta amsa da sauri. "Akwai mana, ba dai kamar baby pink ba? Har na d'aukar miki ma." "Kiji zumudi, to da na fasa siya fa." "Sai in karbo kud'in a wajen inna in sai miki." Taji wani abu kamar murmushi zai fito ta gefen bakinta. Wanda a 'yan kwanakin nan ta manta cewar fatar baki na da wani aikin sab'anin magana da kuma karbar abinci. (Gimbiya ruwaila- daga d'aya labarina na komai Nisan Dare!) Basu wani dad'e a gidan ba suka gama abinda zasu yi suka fito. Sai dai har sun kai bakin titi, Nanne ta tuna ta manta purse d'inta da kud'in motar ke ciki a gidan. saboda haka tayi sauri ta koma Rahma kuma ta tsaya jiranta a kofar wani shago. A inda gidan malamin yake, cikin wani k'aton gida ne irin na  mutanen da, irin Family house d'in nan dake d'auke da waje-waje, kuma gidan nasa na daga tsakiya ne, saboda haka da kyar ta iya ganewa, sai dai kafin ta shiga ciki ma wani yaro ya fito rik'e da purse d'in nata da gudu, da alama  cewa akayi ya biyo bayansu. Ta karb'a sannan ta juya, sai dai kuma ta kasa gane hanyar data biyo, kawai sai tayi ta bin lungu-lungu har ya fitar da ita ta wata k'ofa daban da bata nan suka saba shiga ba. Amma sai tayi tunanin ai duk titi ta zata kaita saboda haka kawai ta fita ta nan. Sai dai me? Layin ya zama daban da wancan, kamar ta koma cikin gidan kuma taga k'ila ta sake b'ata gwara kawai tabi hanyar ta fitar da ita titi inda rahma take. Layin babu wani haske dake fitowa daga dukkan gidajen wajen kuma babu mutane sosai, saboda haka ta k'ara sauri ta nufi inda take tunanin zai fitar da ita titi, a lokacin ne ta hango wasu mutane biyu su kad'ai sun karyo kwanar dake gabanta. Suna tafe suna magana da karfi tare da kyalkyala dariya. Gabanta ya fad'i, sannan zuciyarta ta buga da k'arfi. Tayi saurin matsawa gefe don ta basu hanya. A lokacin suma suka ankara da ita sabada haka tayi saurin sunkuyar da kanta. "'Yanmata..!" d'aya daga cikinsu ya kira sanda suka zo dab da ita, ta san da ita suke tunda babu kowa a wajen amma sai tak'i d'agowa ta cigaba da tafiya. "Yanmata tsaya mana." mutumin ya sake fad'a sanda ta wuce su, suka juyo suka biyo bayanta. Ta k'ara damk'e purse d'inta sannan ta k'ara sauri. "Tambayarki kawai zamu yi." muryan d'ayan ta fada da alamun dariya yake yi. Ta juya baya ta hango suna binta, ga gidan data baro daga can bayansu ba yadda za'ayi ta koma, sai tayi kwanar gefenta kawai da sauri tana jin takunsu a bayanta. Ta hango wani haske kamar na mota ya tahowa, wani dad'i ya ratsa zuciyarta sai dai a lokaci d'aya tafi kasancewar motar bata ko tsaya ba ta karya wani layi ta b'ace. "Idan kika tsaya ba abinda zai same ki, zaki koma gidanku lafiya." Ta sake jiyo muryarsu daga bayanta, sai kawai ta nufi kwanar da motar ta shiga da sauri idanunta kuma na lalube a hanyar, ko zata ga wani abin da zai iya taimaka mata wajen kare kanta, katako, dutse, k'arfe ko duk wani abu da zai zame mata a matsayin makami. Ba tsammani kawai taji hannu ya fizgo kafad'unta ta baya, ta dawo tangal-tangal sannan tayi yunk'urin fizge hannunta, bata san cewa ba da karfi aka rik'e ba saida taji tayi baya ta daki ginin wani kango. "Haba 'yanmata, tambayarki fa kawai zamuyi." Katuwar muryar mutumin ta fada. Ta damk'e purse dintama hannayenta na rawa sannan idonta na kallonsu d'aya bayan d'aya. A daidai sannan ne fitilun mota suka haske wajen gaba d'aya, motar ta taho da sauri kamar zata bige su gabadaya kafin a taka wani irin birki da k'ararsa ta karad'e wajen! ●﹏● WAYE SHI? AYSHA SHAFI'EE 23 (☆_☆) Nanne ta k'ara ware idonta ganin wanda ya fito, mamaki ya kusa cinyeta amma kuma sai taji duk wani tsoronta da fargaba sunbi iska, taji kamar ta riga ta kub'uta ne daga hannun mutanen, sannan taji bugun zuciyarta ya dawo daidai. "Lafiyarki kalau? Ba abinda ya same ki? Ba abinda suka yi miki?" Wannan muryar mai taushi ta jefo tambayoyin a lokaci guda. Maimakon ta bashi amsa sai ta juya inda mutanen ke tsaye, ga mamakinta sai kawai ta hango su daga can gaba suna gudu. "Ba abinda ya sameki?" Imran ya k'ara fada tsaye kusa da ita." Ta juyo ta kalle shi, sannan motarsa dake gefe k'ofa a bud'e. "Ta yaya kazo nan? Ta yaya ka san ina nan?" "Kin tabbata ba abinda ya same ki?" Ya tambaya kamar baiji me tace ba, sai kawai ta d'aga kai har a lokacin tana damk'e da purse d'inta. "Mu bar wajen nan." Ba musu tabi bayansa ta bud'e k'ofar gaba ta shiga, wani sanyi da kamshi ya ziyarci koina a jikinta. Ya tada motar sannan yayi kwana ya bi hanyar data baro a baya. Har a lokacin hannayenta rawa suke saboda haka bata ce komai ba, Bayan sun fita titi ya juyo ya kalleta. "Kin tabbatar ba abinda ya same ki?" Ta daga kanta da sauri. "Baki buge ba? baki fadi ba? bakya jin jiri ko..." "Bana jin komai." ta katse shi a hankali idonta na kallon titi. Kawai sai ya rage saurin motar sannan yayi parking a gefen titin, kusa da wani shagon saida robobi. Ta juyo ta kalle shi, shima ita yake kallo. "Sa'adha kin tabbata mutanen can ba abinda suka yi miki?" "Ba abinda suka min, ta yaya ka san ina can? Me ya kaika wajen?" "Na wuce ne ta hanyar sai na hango kamar ke, shine na dawo in tabbatar." Idanunta suka hasko mata wannan motar da ta wuce ta gabanta. Har a lokacin da mamaki a fuskarta tace. "Me ya kaika wajen toh?" "May be ke ya kamata in fara tambaya, ni namiji ne zan iya zuwa koina kuma ina da mota, amma ke a daren nan, sannan wannan wajen...." Taji idanunsa sun mata nauyi saboda haka ta juya sannan tace. "Hanya ce ta b'ace min bayan na fito daga wani gida." Ya gyada kansa. "Okay, toh ta yaya kika zo unguwar ke kad'ai?" Amsar da zata bayar ya tuna mata da Rahma, ta kalle shi da sauri. "Ba ni kadai bace nida rahma ne, tana can tana jirana." "A ina?" "Ban san wajen ba, amma...." Ta juya ta kalli yanayin wajen. "Ina tunanin mun wuce shi a baya." Ya juya kan motar a hankali sannan ya sauka daga kan titi, suka koma baya tana ya zare ido har suka zo daidai shagon nan da Rahma ta tsaya. "Ga wajen nan...amma kuma bata nan." ta k'arasa a hankali tana kallon koina a wajen. Tayi nufin bude k'ofar motar amma yayi saurin danna lock din gefenta. "Ki zauna a ciki, bari inje in duba." Duk da zuciyarta ba'a nutse take ba a lokacin amma ta kasa hana kanta kallon yanayin takun tafiyarsa da kuma yadda kafadunsa suke a k'ame kamar ba motsi yake ba. Ya k'arasa cikin kantin suka gaisa da mutumin ciki, tana kallon yadda mutmin keta masa bayani har sanda ya fito bakin kantin ya dauko waya ya kira sannna dawo cikin motar. "Bata nan, ta koma gida." "Kamar yaya? Ya akayi ta tafi?" "Ta koma gidan da kuka je ta tarar bakya nan sai mutanen wajen suka ce mata watakila kin b'ace hanya ne kika tafi gida saboda haka ta tafi." Nanne ta jingina kanta da seat din tare da yin ajiyar zuciya. Ta riga ta tsira daga koma me wadancan mutanen ke shirin yi mata amma zuciyarta ta kasa nutsuwa, tambayoyi da yawa ne ke yawo akanta na yadda akayi imran yaje wajen a lokacin, ta kasa yarda da abinda yace d'azu, don motar data wuce da farko ba itace wannan da take ciki ba sannan ita ko kad'an bata tsaya ba balle na ciki ya ganta. Idonta ya kai kan titi, a lokacin ne ta lura da yanayin garin, kamar mutane sun fara raguwa sakamakon daren daya fara yi. Ta kalli agogon kan dashboard, karfe tara da minti goma sha biyu. Ta san dole Rahma ta koma gida yanzu kuma hankalinsu zai tashi. Me yasa ne a cikin kwanakin nan take zama silar tashin hankalin kowa? Kamar ya karanci damuwarta sai taji yace. "Karki damu na kira sulaiman yanzun nan nace masa muna hanya." Jin an ambaci ya sulaiman yasa ta juyo da sauri ta kalle shi. "Bai tambayeka a ina ka ganni ba?" Haske fitilar wata motar ya haska mata fuskarsa sanda yayi murmushi a k'asan numfashinsa. "Bai tambaya ba, watakila yayi tunanin ko na k'ara kade ki ne." Abin yaso sata murmushin itama amma sai tace. "Wannan ranar ma tsautsayi ne amma ko keke bai taba buge ni a hanya ba, sannan a lokacin ma na....." Sai ta kasa k'arasawa saboda yadda idonta ya hango mata titin a wancan lokacin, sai da ta riga ta tabbatar babu mota a kusa sai wani babur daga can nesa sannan ta tsallaka, toh ta ina motarsa ta taho da bata ganta ba? Abin yaso yi mata shige da wanda ya faru yanzu. "Ya kika yi shiru?" ya tambaya a hankali sanda taji suna k'ok'arin sauka daga kan titi. "Ba komai." Ta fad'a sannan da sauri ta juya ta kalli window, sai dai sab'anin k'ofar gidansu sai taga sun tsaya ne a wani k'aton chemist mai cike da hasken fitilu. Ta sake dawo da idonta kansa. "Me zaka yi anan? Dare yana yi ban koma gida ba." Ya kashe motar nan sannan yace. "Ke na kawo." Ta kalli chemist d'in sannan ta sake kallonsa. "Me ya same ni? Na fad'a maka lafiyata...." Ta kasa k'arasa zancen sakamakon juyowa da yayi ya kalle ta, idanunsa masu kyau suka tsaida duk wani tunaninta. "You don't look fine to me sa'adha, its like you are kind of distracted." "Abinda ke damuna daban." Ta ayyana a ranta. Amma a fili sai tace. "Dan Allah ka maida ni gida." Minti uku bayan hakan, wata mace na tsaye a kanta a cikin chemist din. Daga ta zura mata wani abu sai ta gwale idonta kamar zata ciro tsakuwa a ciki. Duk abinda ake yi, idonta na kan agogo da kuma shi da yake ta zagaye a cikin wajen daga kanta zuwa kanta, yana kallon magungunan dake zube akai. "Kina jin jiri?" matar ta tambayeta bayan ta zaro wani abu kamar tsinke data sa mata a baki. "Ba abinda nake ji, lafiyata kalau." Tayi murmushi tana kallonta. "Kar ki damu madam, lafiyarki kalau." Sai ta jawo wata 'yar takarda tayi rubutu sannan ta zagaya d'ebo magunguna. Daidai sanda imran ya dawo hannunsa d'auke da k'atuwar robar yoghurt guda biyu. "Tace ba abinda ya same ni, mu tafi yanzu?" Lebb'ensa ya motsa cikin murmushi. "Ko in zauna ne a gwada ni a tabbatar miki cewa bana cin mutane?" Kafin ta amsa matar ta dawo da 'yan maguguna a hannunta. Ta nufi inda yake tsaye. "Yawwa ga wannan su zata sha, na duba na gani lafiyarta k'alau, kawai fargaba ce da kuma gajiya a jikinta." Daga inda take zaune, Sa'adha ta san matar nan karya take, kawai dai tana son samun hanyar da zata ci kud'insa ne. Ya mika mata robobin yoghurt d'in yace ta had'a har dasu ta fadi kud'in. Ai kuwa abinda ta fad'a ko waye zaiji ya san ko kusa kud'in abubuwan basu kai haka ba. "Zan iya ganinki gobe?" Ya tambaya bayan sun koma motar. "Me za'ayi?" Itama ta tambaya a hankali idonta na kallon titi. Taji wani abu kamar k'arar murmushinsa kafin yace. "Karki damu ba nan zamu dawo ba, akwai abubuwa da yawa da nake son in tambayeki ne." Taji kamar ya karanci zuciyarta ne, don watakila ita tarin tambayoyin ma dake k'ulle a kanta game dashi sun ninka nasa. Saboda haka ba tare da tunanin komai ba tace. "Allah ya kaimu." "Ameen. Amma da yaushe zan same ki?" "May be da yamma?" Ta amsa kamar tambaya. Ya sake yin murmuushi yana kallon titin. "Baki tabbatar ba?" Tun lokacin da ta fara sabawa dashi a asibiti, ta lura yana da yawan murmushi, amma bata yi tunanin yawan ya kai haka ba. "Na tabbatar. Allah ya kaimu." "Ameen." ya sake amsawa. Taji wani iri, yadda d'an wannan alkawarin yasa jikinta yayi sanyi bayan duk gwagwarmayar data sha a daren. Sun shigo layinsu a lokacin, komai yana nan kamar yadda yake, fitulun k'ofar kowanne gida sun haska tar! masu gadi na waje da 'yar rediyonsu sannan tsilli-tsillin mutane na wucewa. Sai taji kamar duk abinda ya faru a mafarki ne, yanzu ta farka. Yayi parking a k'ofar gate d'insu amma bai bud'e lock d'in ba. ya miko mata ledar magungunan. "Ki tabbata kinsha maganin kafin ki kwanta." Ta kalli ledar sannan shi, abinda ke idonta ya nuna masa tana shirin k'in k'arba ne saboda haka ya sauke muryarsa k'asa yace. "...Don Allah." Hakan ya tuna mata da ranar daya fara mata magana, lokacin da yake tambayar ta sunanta. Sai ta sauke gashin idonta kan ledar sannan ta karb'a. "One more thing...." ya katse godiyar da bakinta ke shirin yi. Muryarsa ta canja, ta zama so serious. "Zaki iya min wani alkawari?" Ta gyada kanta, a lokaci d'aya kuma tayi dana sanin hakan, ta san me zai tambayeta ne? in kuma wani babu ne da bazata iya ba fa? "Kar ki sake zuwa inda baki sani ba ke kad'ai." Ssi tayi ajiyar zuciya, wannan ai ba wani abu bane. "Insha Allah, sai da safe." "Allah ya kaimu." ya amsa sannan ya bud'e lock d'in. Ta juya ta bud'e k'ofar motar, sai dai tana zura k'afarta d'aya waje, ya sake tsaida ita. "Sa'adha...." Me yasa ne muryarsa ta saba fad'ar sunanta, watakila don bai san yadda hakan ke sawa taji bane. Ta juyo da sauri ta kalle shi.  Saboda shirme wani b'angare na zuciyarta na fatan zaice kar ta tafi ne. "Sleep well." Amon muryar tasa ya amsa a kowanne lungu da sako na jikinta, taji zuciyarta ta buga kamar tana neman hanyar fitowa daga kirjinta. Ba shiri ta fita daga motar ta tura k'ofar gate d'in ta shige. Babu kowa a harabar compound d'in amma duk fitilun d'akunan mazan a kunne suke alamun ba wanda yayi bacci. Da sauri ta shige ciki kar wani ma ya fito ya ganta. Akwai 'yan aiki da d'an yawa a kicin din amma bata bari kowa ya ganta ba tayi hanyar sama da sauri. Tana shiga d'aki ta tarar inna na zaune akan sallayarta. "Alhmdlilahi, har kin dawo?" Ta fad'a bayan ta amsa sallamarta. mamaki ya kamata. "Inna har ne? Ban dad'e ba?" "A'ah baki dade ba, yanzun nan fa sulaiman ya bar d'akin nan yake ce mana wai kin b'ace hanya ne, amma kin had'u da d'an albarkar yaron nan zai maido ki, itama rahman fitarta kenan ta tafi gida." Nanne ta juya ta kalli agogo, karfe tara da minti ashirin, tun kafin su tsaya a chemist d'in nan taga k'arfe tara da minti goma sha biyu, ta yaya za'a ce duk sauran abubuwan da suka faru a minti takwas ne kawai? "Inace ba dai abinda ya same ki koh?" Ta girgiza kanta da sauri. "Ba komai inna, dana koma gidan ne sai na fito ta wata k'ofar, na kasa gane hanya, sai Allah ya had'ani dashi ya dawo dani." "Toh Alhmdlilahi, ai baki ji yadda naji ba da Rahma tazo min da zancen wallahi, wannan bawan Allah dai Allah ya saka masa da alkhairi..." Tayi cikin d'aki ta bar innan nata sa masa albarka. Ta ajiye ledar hannunta a kasan gado sannan ta shiga toilet, ta tara ruwan zafi tayi wanka, ta fito tasa kayan bacci tayi sallah sannan tayi wa inna sai da safe ta kashe fitulun ko'ina sannan ta dawo d'aki. A yanzu ita kad'ai take kwana don Inna ta koma da shimfid'arta falo, ta jawo ledar nan ta fito da magungunan, guda uku ne daga wani pain reliver sai paracetamol da vitamin C, ta san ba abinda take ji a jikinta amma ta d'auko ruwa ta tura su bakinta, sannan ta sa vitamin C d'in a baki. Idan bata sha ba, zata yi ta tuno muryarsa ne sanda ya miko mata ledar. Ta d'auko robar yoghurt din nan tana juya ta, abubuwa da yawa game dashi suna d'aure mata kai, amma gobe ta san komai zai warware, don in har zai mata tambayoyi, itama zata yi masa tambayoyin da zasu sa ta san WAYE SHI. Ba zata b'oye komai ba, zata tambayeshi gabad'aya abubuwan da bata fahimta ba, tun daga ranar data fara ganinsa har zuwa yanzu. Ta koma cikin bargon ta dunk'unk'une jikinta rik'e da robar a hannunta. Wani irin dad'i da fresh take ji a jikinta, kamar an sauke mata nauyin wasu abubuwa, ta manta da halin da take ciki, ta manta da maganganun Baffa, ta manta da abinda ke shirin faruwa da ita, ta manta da wa'adin da Baffa ya bata, ta manta da duk wani zumud'in Inna. Ta janyo tunanin Imran da duk abinda ya faru a yau da kuma fatan ganin gobe kawai tasa a ranta, goben da take fatan sanin... WAYE SHI? ●﹏● WAYE SHI? AYSHA SHAFI'EE 24 (☆_☆) Bai san me ya same shi ba, bai san me yasa tunda ya dawo zuciyarsa ta kasa nutsuwa ba. ya san ya riga yayi kuskure tun a jiyan, kuskuren fad'a mata cewa zai ganta a yau, abinda ya san ba zai tab'a faruwa ba. Watakila ko don ganin yadda ta tsorata da mutanen nan ne. Shi kansa har yanzu da ya rufe ido su yake hangowa, musamman d'ayan, wanda yafi matsawa kusa da ita sosai yana dariya. Da ace Allah bai kawo shi a daidai wannan lokacin ba, baya jin zai iya tsayawa abinda zai faru. Daga office ne suka je gidan wani abokin aikinsu daya takura musu da gaiyata tun wajen watanni uku a baya da yayi aure, sai a jiyan Allah ya k'addara zasu je, kuma ya riga sauran da suka je tare tahowa, ganin dare ya fara yi amma su basu da niyyar tashi. Saboda haka yayi musu sallama ya taho, sai dai tunda ya shiga motarsa ya fara jin gabansa na fad'uwa sannan zuciyarsa tana bugawa, ya rasa dalilin hakan tunda ya san ba abinda ya same shi kuma ciwon Sa'adha a lokacin bai isa ya tashi ba. Abin ya cigaba da k'aruwa bayan ya fita daga layin yabi hanyar da zata kaishi titi. A hanyar ne idanunsa suka hango masa wasu mutane daga gefe sannan bugun zuciyarsa ya k'aru a daidai wannan lokacin saboda haka ya juyo da kan motarsa ya dawo. Anan ne ya hangi abinda ya sashi mutukar mamaki, wasu maza biyu suna kokarin ritsa Sa'adha a jikin wata kantanga, mamaki ya kamashi na ganinta a wajen, kenan abinda yasa shi fargaba kenan? Saboda daya b'arin jikinsa na cikin matsala? Bai san lokacin daya k'arawa motar gudu ba yayi kansu gabadaya. Abu d'aya ne ya hana shi bin bayan matasan nan lokacin da suka gudu. Idanunta. wad'annan idanun nata da suka cika da d'imbin tsoro, yaji ba zai iya tafiya ya barta ita kad'ai a wajen ba, don bai yarda cewa in har ya tafi wasu irinsu baza su sake zuwa ba. A zahiri da kuma yadda ta fad'a masa, ba abinda suka yi mata amma har suka hau titi fad'uwar da gabansa yake da kuma bugawar zuciyarsa basu canja ba, alamun har a lokacin tana cike da tsoro, saboda haka yayi tunanin ko sunyi mata wani abun ne ta b'oye masa. shi yasa a lokacin daya tabbatar k'awarta ta koma gida yanke shawarar tsayawa a wannan chemist d'in. Sannan bayan matar ta gama dubata ta zagaya d'ebo magunguna, ya tsaida duk wani abu dake motsi na cikin chemist d'in ya isa gurinta ya kalli idanuwanta, ya lalubo cikin tunaninta daga sanda suka shigo chemist d'in har zuwa lokacin da ta gama duba ta. Babu wani abu data gani a jikin sa'adhan, hasali ma tunaninta baya cike da komai sai k'ok'arin ganin meye a tsakaninsu. Tayi tunanin sa'adha k'anwarsa ce ko cousin, don a cewarta ba zai yiwu ace ita matarsa bace, he's too classy for her. (ya girmewa ajinta.) Yayi murmushi sanda ya tuna hakan. Daga baya kuma sai ta koma tunanin yadda zata karbi kud'i da yawa a wajensa, tana tunanin idan ta k'ara akan wanda take dasu zasu isa ta samu ta kai 'yarta asibiti gobe. Ganin ta bar zancen sa'adhan yasa ya juya ya nufi can k'arshen ginin, wajen da aka jera fridges sannan ya murza hannunsa komai ya dawo daidai. Ya lura har suka koma cikin mota, bata da nutsuwa sosai, tunaninta ya rabu kashi-kashi sannan hankalinta ya tafi gida, kamar tana ganin wani  abu zai faru in bata nan, Yayi tunanin yi mata magana don hankalinta ya kwanta ko shima ya sami nutsuwar zuciyarsa. "Zan iya ganinki gobe?" Bai san abinda ya tambaya kenan ba sai da tace "Me za'ayi?" Yayi murmushi a hankali saboda yadda muryarta ta fita kamar tana tsoron zai sake dawo da ita chemist d'in ne, saboda haka yace mata kawai yana son yi mata tambayoyi ne. Kuskuren da yayi kuma kenan, na neman kauce tsarin da suka yi shida jaamil. Don a yadda suka tsara ba zai k'ara ganin ta ba sai nan da wani lokaci, lokacin da zata shigo cikin rayuwarsa ya k'arasa daga inda jaamil ya tsaya. Tsarinsu ya tafi ne a cewar ta riga ta fara sonsa, don haka zata yarda dashi in har komai yazo a k'urewa amma shi bai yarda ba. Ya san Kawai tana cikin Delusion ne irin na mata da yawa da yake gamuwa dasu. Bata san WAYE SHI ba, bata san komai game dashi ba, toh ta yaya zata so shi? Soyayya shine a lokacin daka yarda ka kuma amince da mutum a kowanne irin hali na rayuwa. Don haka baya tunanin akwai wanda zai so shi, SHI d'in dake bayan wannan fuskar. Ya san zata shiga damuwa a yau d'in na rashin zuwansa amma ba yadda zaiyi, yayi kuskure da yawa a baya ba zai so ya cigaba da lalata musu abubuwa ba, alhalin jaamil yana iya k'ok'arinsa wajen gyarawa. Ko ganinta a jiyan ma, ba zai taba bari ya sani ba. Ya kalli had'dd'en agogon dake facing d'insa a saman TV.  K'arfe hudu da rabi. ******* "K'arfe hudu da rabi." Sa'adha ta fad'a tana mikawa inna wayar. Inna ta karb'a ta kara a kunnenta tana fad'in. "Toh ni kuwa ina suka tsaya haka? ace kasuwa tun safe har yamma..." Tayi saurin katse maganar sakamakon d'aukar wayar da akayi daga d'aya gefen. "...Maryama yanzu Allah baza ku taho ba sai wannan ruwan ya sauko a kanku, kuna ganin wannan hadari haka..." Nanne ta mik'e a hankali ta isa jikin taga inda iska ke kad'owa ciki kamar zata taho da labulen, garin yayi bak'ik'irin kamar da magariba sakamakon hadarin daya game sararin sama baki daya. A kusa da tagar akwai fridge, sannan a cikin fridge d'in akwai wannan robobin yoghurt d'in guda biyu, ta bud'e ta d'auko d'aya, sannan ta jingina da tagar tana wasa da ita a hannunta, babu d'ankwali akanta sakamakon 'yan k'ananan kitson da Rahma ta gama yi mata wanda ya dameta da zafi, saboda haka iskar ta shiga d'aga gashinta tana turo shi kan fuskarta. Ta tuna murmushin da yayi lokacin daya rik'o robobin a hannunsa. "Ko in zauna ne a gwada ni a tabbatar miki cewa bana cin mutane?" Taji kamar itama zata yi murmushin amma ya mak'ale daga wuyanta, akwai abinda yake ba daidai ba yau, duk da ta saba a kwana biyun nan bata da walwala amma yau tana jinta ne kamar tana tsaye a k'arshen wani abu mai tsawon gaske, k'arshen da zata iya fad'owa a kowanne lokaci. Ta sake hasko gabad'aya tambayoyin data shirya tun jiya a cikin kanta. Bata da matsala ta riga ta had'a komai da zata tambayeshi amma ita bata san me zai tambayeta ba kuma ta matsu taji ya nasa tambayoyin zasu kasance. Ba irin tunanin da bata yi hasashensa ba tun daga jiya har zuwa yau. Ta hasko cewar imran zai zo wajenta, kuma zai cigaba da zuwa har su saba. Watakila ma har suyi sabon da zai iya neman aurenta kafin adadin lokacin da Baffa ya d'ibar mata. Don in bashi ba, bata tunanin zata tab'a saurarar wani, balle har a zuciyarta ta yarda dashi tace zata kaishi wajen Baffa. Waye ma zai yarda a yanzu daga fara zuwa wajenta a fara zancen aure? In har dama ba ya shirya bane. Sai kuma wata zuciyar ta tambayeta game da Imran, meya banbanta shi da sauran? Me yasa take tunanin in shi d'in ne zai yarda a d'an k'ank'anin lokaci ya aureta? Tayi saurin ture wannan tunanin kar ya b'ata ranta. Ta maida robar cikin fridge sannan ta dawo ta zauna akan kujera, a lokacin inna ta gama wayar, kuma iskar da akeyi ta k'aru, sannan gari ya dad'a duhu alamun a kowanne lokaci ruwan zai iya sauka, ta dunk'ule a cikin kujerar tana sauraron zancen inna da take mita akan dad'ewar su Aunty maryama. Kowacce kalma tana shiga kunnenta, amma bata fahimtar komai. Har aka d'auke ruwan, dab! Da maghriba akayi sallah, babu Imran ba alamun zuwansa. Zuciyarta tayi nauyi, sannan jikinta yayi ba dad'i. Amma kuma sai ta dinga bawa kanta uzurin cewa watak'ila ruwan ne ya hana shi zuwa. Washegari rana ta fito har ta fadi, babu alamun zuwansa. Kwana d'aya, kwana biyu. Sai ta fara tunanin ta karb'i shawarar da d'aya b'arin zuciyarta ke bata, na cewar ta cire imran daga ranta, yaci ace ta gane cewa shi bai dauketa a matsayin data dauke shi ba. Watakila ya riga ya manta da abinda ya gaya mata tun a daren nan. Koma ya manta da ita ya shiga harkokinsa. Ya isa ta gane cewa duk sanda suka had'u chance d'in k'ara ganinsa  yana sake mata nisa ne. Kuma bai kamata ta cigaba da damuwa dashi a ranta ba. Damuwa da mutumin da bata san waye shi ba. Ya isa ta gane cewa ba daga Baffa yayi mata maganar aure bane imran zai zo yace zai aureta. Akwai abubuwa da yawa yanzu a gabanta, su ya kamata ta fuskanta ba wani abu da ba zai taba yiwuwa ba. Sai dai a duk sanda ta tuna tarin taimakonsa gare ta sai wani b'arin na zuciyarta ya sake rik'e fatan cewa zai zo a ranar ko gobe. Amma bayan sati d'aya sai ta hakura ta cire wannan fatan. Komai na gidan ya sake dawo mata kamar da, shirye-shiryen inna ya k'aru, zancen aurenta kuma ya biye gabad'aya danginsu, sannan a kullum kwanakin da Baffa ya d'ibar mata k'ara matsowa suke, komai ya sake cakud'e mata. Fatan da zuciyarta ta samu game da Imran a dare d'aya kawai yayi mata nisa ya zama kamar bai tab'a faruwa ba. BAYAN SATI DAYA. BAYAN SATI BIYU. BAYAN SATI UKU. BAYAN SATI HUDU. Baffa ya kirata! ●﹏● WAYE SHI? AYSHA SHAFI'EE 25 (☆_☆) Lokaci yana tafiya a kullum kuma a kodayaushe. Walau cikin farin ciki ko bak'in ciki. A duk motsawar agogo guda daya, lokacin ne yake wucewa, lakacin da baza a sake maimaita irinsa ba. Sau da yawa kuma, d'an adam baya fahimtar saurin zuwan lokaci sai ya tsara wani abu yasa masa rana. Anan ne zaka ga kamar ansa igiya ne ana jawo wannan lokacin. Hakan ce ta faru da Nanne, adadin kwanakin da baffa ya d'ibar mata ya k'are saboda haka a kowanne lokaci ta san tana iya samun kiransa. Muryar Inna ta kutsa cikin kanta. "Ni na gaji wallahi, had'a kayanki zaki yi ki tafi can wajen babar taki, watakila tunda ita ta kawo ki duniya ita kya iya hak'ura ki sake a wajenta, duk randa aka saka ranar auren kya dawo." Nanne ta d'ago daga juya abincin hannunta da take yi maimakon ci ta kalle ta, kwata-kwata ta manta magana innan ke mata balle har ta iya rik'e abinda take cewa ko wanda ta fad'a a karshe. "Inna me nayi?" Ta tambaya a lokaci d'aya kuma taji kunyar tambayar. Ita kanta ta san ko makaho ne yake tare dasu ya san cewa ta canja daga Nannen da kowa ya santa zuwa wani abin daban. Wani abu da ita kanta bata sanshi ba. Ta zama kamar wani gunki dake tafiya a doron k'asa, tayi losing duk wasu emotions d'inta. "Ba abinda kika yi, kuma matsalar kenan, ba abinda kike yi Nanne!" Ta rufe idonta a hankali, a cikin wata d'aya da 'yan kwanakin da suka wuce me nene bata yi? bata tab'a fashin makaranta ko sau d'aya ba, karatun da a da bata yi yanzu a kullum cikinsa take, anyi jarabawar first term tazo ta shida a maimakon na goma sha da take d'auka a baya, sannan a iya wannan lokacin ta had'a haddar izu bakwai a islamiyya. Sai dai bata hira, bata dariya, bata kuka sannan bata tsokanar da kowa ya santa da ita, ta koma kamar wancan lokacin da baffa yayi meeting akanta, lokacin da imran baizo yasa mata wani fata a dare d'aya kawai ba. "Inna me kike so nayi?" "Au tambayata ma kike yi? Da lokacin da kike harkokin ki ni kike tambaya me zaki yi?" Tayi shiru tana cigaba da juya abincin, kafin a hankali kuma tace. "Kiyi hakuri." "Ni ba hakuri nake so ki bani ba." "Toh me kike son inyi?" Har ta bud'e baki kamar zata yi magana kuma sai tayi ajiyar zuciya sannan tace. "Nanne, kin san dai ba'a kanki aka fara zancen irin wannan auren ba koh? Ba akanki aka fara aure a irin wannan shekarun ba sannan kin san ba'a kanki aka fara aure kafin a kammala makaranta ba koh?" "Na sani." "Toh me yasa zaki sa kanki a cikin damuwa irin haka? Koh auren ne kwata-kwata bakya so?" Tambayar tasa ta d'ago da kanta da sauri ta kalleta. Tunda aka fara zancen nan ba wanda ya tab'a bata zabi, ba wanda ya tab'a tambayar ra'ayinta. Kowa yaji zancen ko aka gaya masa, fatan alkhairi kawai zaiyi wasu ma su fara binta da shawarwarin da suka danganci auren. Amma yanzu ga inna na tambayar ra'ayinta, innar da'a yanzu in ta bude baki tace bata amince ba shikenan an rufe babin zancen sai wani kuma. Zuciyarta tayi zurfi cike da rokon Allah yasa ta fahimce ta. Ta gyara zama a hankali sannan ta d'aga kai. A lokacin taji inna ta rafka salati sannan ta ka'rashe da... "Na shiga uku ni saudatu, wallahi yau na dad'a tabbatar da zancen malaman nan, dole akwai abinda ke faruwa tare dake Nanne amma banda haka ni ina na tab'a jin macen data bud'i baki tace bata son aure? Sannan don har ance za'a yi mata ta fita haiyacinta ta shiga kunci tana wannan ramar? Toh wallahi tun wuri ki fita idona in rufe kafin in sassab'a miki..." Bata bari ta k'arasa ba ta d'auki plate d'in tayi cikin d'aki. Wani k'ololon abu ya makale mata a wuya, taji ina ma kuka zaizo mata a lokacin, watak'ila in ta samu tayi zata samu sauk'i a ranta. Sai kawai ta zube a k'asan gado sannan ta kwantar da kanta a gefe, ta jawo wayar inna dake kusa da filo, one missed call ya nuna akan screen d'in, ta bud'e ta a hankali sannan ta shiga cikin call log d'in. Sunan Addano ya nuna tar akai, yadda tayi saving number Nuratu dashi. A cikin sakan d'aya kawai, tunaninka da yawa suka faru a cikin kanta. Ta tuno da zancen da suka yi da ita a wannan zuwan nata na k'arshe, zancen da a lokacin ta d'auke shi ta ajiye a gefe tana tunanin ba na lokacinta bane. Ta tabbata yanzu idan taji abinda ke faruwa zata fi kowa cikin farin ciki, watakila ma har tafi inna. Sai kuma ta tuno da zancen d'an yayarta da tayi mata, wanda tace har yana aiki a cikin adamawa, kwakwalwarta tayi k'ok'arin tuna sunansa amma ta kasa. Idan har abubuwa sun cakud'e mata a yanzu ana shirin aurar da ita ga wanda bata sani ba, me yasa ba zata bi shawarar Nuratu ba ta yarda da wanda take tunanin had'asu? Tunda kamar yadda tace ne ko ba komai zata shiga cikin dangin mahaifiyarta. Amma kuma ta san wane irin mutum ne shi? Ta san halayensa? Sannan zai yarda ya aureta a iya lokacin da Baffa ya fad'a? Idan ta aure shi adamawa zata koma kenan? Zai barta ta cigaba da karatunta? Wace irin rayuwa zata yi a can? Tambayoyi da yawa suka dinga yawo a cikin kanta har ta kwanta a ranar, komai ya cakud'e mata, tana ganin kamar an d'ora rayuwarta ne akan faranti dake hannun k'aramin yaro yana gudu. kuma a kodayaushe zata iya fad'owa. Ta san in har tayi kuskure guda d'aya a yanzu zai shafi rayuwarta ne har abada. Don zai iya yiwuwa tayi kuskuren barin baffa ya zab'ar mata mijin da ba lallai taji dadin aurensa ba, sannan zai iya yiwuwa ita da kanta tayi wannan kuskuren. Ta rufe idonta a hankali sanda ta sake k'udundunewa cikin bargonta. Kanta cike da tunani fal! Wanda bayan ta farka washegari ta takura kanta ta samu matsaya d'aya. Ta d'auko wayar inna ta turawa da Nuratu sak'on text. Abu mai muhimmanci a ciki shine. "Addano na amince da zancen, ki turo SHI!" BAYAN SATI DAYA! Baffa ya kirata! ******* "Naji dad'i kwarai da bin maganata da kika yi Sa'adha. Haka ya tabbatar min da cewa baki d'auki fushin da wasu 'ya'ya ke d'auka da iyayensu ba a irin wannan lokacin. Kin kab'i kaddararki da hannu biyu ba tare da kin bari ta tauye ki ba, sanda naga result d'inki nayi farin ciki sosai fiye da yadda zan misalta miki. Amma a lokacin da mutanen da kika turo suka zo min da zancen neman aurenki, a ranar nayi sallah ta musamman ga Allah Sa'adha, na godewa wa Allah sannan nayi alfari dake fiye da koyaushe. Kin d'auki hanya mai b'ullewa wadda zaki ga amfaninta, kinyi min biyayya duk da cewa hakan zai tauye abubuwa da yawa na tsarin rayuwarki, amma ina tabbatar miki zaki yi tutiya da abinda kika yi nan gaba, biyaiyarki baza ta tab'a cutar dake ba. Nayi bincike akan yaron da kika turo, kuma daga kowanne b'angare ban samu aibinsa ba, saboda haka zamu zauna da iyayensa, mu yanke duk abinda ya dace. Tashi kije Allah yayi miki Albarka." Nanne taji kwalla na taruwa a idonta bayan ta fito daga falon baffa a lokacin, kwalla ce wadda ta manta yaushe rabon da taga irinta a idonta, kwallar dake tabbatar mata komai yazo k'arshe kenan, ta rufe idonta a hankali sanda d'uminta ya gangaro ya taho kan kumatunta. Shikenan abinda take wa hangen nesa ya kusa faruwa, Baffa ya yarda da mutumin da a yanzu ta san sunansa Nura. Mutumin dake shirin zama wani b'ari na rayuwarta! ****** WAYE SHI? AYSHA SHAFI'EE 26 (☆_☆) Another day... without your smile. Another day... just passes by. But now i know, how much it means. For you to stay right here with me. The time we spent apart will make our love grow stronger. But it hurts so bad I can't take it any longer... I wanna grow old with you..... Wakar ta katse a daidai nan sakamakon kiran daya shigo cikin wayar.  yadda ya tallafe bayan kansa da duka hannayensa biyu ya masa dadi, saboda haka bai ko motsa ba har kiran ya katse. Yana kwance ne akan irin dogwayen kujerun nan na bakin beach, yana jin iskar wajen mai sanyi da dad'i na kad'a kowanne particles na gashin jikinsa, ya mak'ala earpiece a kunne sannan idanunsa a bud'e yana kallon adon taurarin dake haskawa a samansa. Adonsu mai kyau, yadda suke shining akan black universe d'in samansa. ya had'e dogwayen gashin idanunsa waje d'aya sannan ya sake bud'e su, taurarin na da kyau, idonsa ya gane masa kuma kwakwalwarsa ta fad'a masa, amma hakan ya kasa tafiya cikin zuciyarsa. Zuciyarsa da ta kasa nutsuwa tun zuwansa k'asar nan. sati hudu kenan, sati hudu yazo da niyyar hutu amma abin ya zama kamar yazo ne don ya samu isashshen lokacin da zai dinga tunaninta. tunanin wadannan idanun nata. Ya salam! me yasa ne ya dawo da wannan tunanin, a d'azu har a sallarsa yayi wa Allah alk'awarin ba zai sake kawo ta a ransa ba, amma awa biyu kad'ai ta karya hakan. Fararen idanun nan nata masu kamar an zuba musu madara, su suka fara jan ra'ayinsa gareta. Bayan ya samu ya takura kansa ya rabu da ita kuma k'addara ta sake hada su, a yanzu kuma da k'addarar ke shirin sake had'a su, so yake ya ture wannan intrest d'in daya samu akanta tun baya, baya so ko kad'an ya sake dawowa cikin kansa. Don abinda zai had'a su d'in na dan lokaci ne kawai, kuma da komai yazo k'arshe zai fita daga rayuwarta ne har abada, Abada wadda bata da k'arshe. Saboda haka yake k'ok'arin hana kansa jawo musu wata matsalar. Don shi kansa zaman da zasu yi tare ma wani k'alubale ne da sai yayi mutuk'ar taka tsantsan da kansa. halittarta da tasa ba d'aya bace, in dai yana tare da ita dole ne sai koyaushe hankalinsa ya zamo hundred percent a tare dashi, in ba haka ba zai iya mantawa ko wajen rik'e hannunta ko tab'a kyawawan idanunta, ya rik'e ta da karfi irin nasa da zai sa k'ashinta ya rugurguje. Ya salam! me ya same shi ne kuma? yanzu ya gama yiwa kansa fad'an tunanin idanunta yanzu kuma ya koma tunanin rik'e ta? me zaisa ya rik'e ta? auren da zasu yi ba na gaske bane, zai aureta ne don samun kariyarsu su duka biyun ba don wannan shirmen da zuciyarsa ke kawo masa ba. Dole ne ma tun a yanzu ya nemi hanyar da zai nesanta zuciyarsa da ita, ko don ma jaamil.  ya tuno maganganun da suka yi na karshe kafin tahowarsa nan. Komai zai tafi mana daidai yarima, dama a lokacin da na kawo zancen nan, tsorona d'aya ne na yadda zamanku zai kasance. Don yadda kake da intrest akan yarinyar nake tunanin zaka iya jawo mana wata matsalar, ko a lokacin zamanku ko kuma a lokacin da zaman zai k'are. amma tunda ka tabbatar min da baka sonta hankalina ya kwanta, na tabbatar baza ku sami matsala ba. Ya rufe idonsa sanda ya tuno hakan, yasha gayawa jaamil abubuwan da yawa wanda yake nufi da gaske amma baya yarda dashi, sai a lokacin da ya gaya masa wani abu da shi kansa bai tabbatar ba sannan kuma ya yarda. Don shi kansa a lokacin daya fad'awa jaamil cewa baya son Sa'dha, yayi amfani ne kawai da kalmar don a tunaninsa hakan zaisa jaamil yace ya fasa wannan shawarar. Saboda tun lokacin da ya fad'a masa ita, hankalinsa ya kasa nutsuwa don bai yarda da kansa in yana tare da ita ba, bai yarda da zuciyarsa ba. lokacin daya sake bud'e idonsa akan taurarin, sai yaga kamar ansa hannu ne an jera su cikin wani tsari da yayi kama dana fuska. fuskar mutum d'aya a duniya wadda ya tab'a jin irin wannan abin game da ita. Gimbiyarsa Sareefa, 'yar uwarsa kuma 'yar uwar halittarsa dake can wata nahiya tana jiransa. Ya kamata yayi wa kansa fad'a, Sa'adha ba abokiyar rayuwarsa bace, zata shigo ciki ne kawai kuma ta wuce a lokaci daya. kamar mutum ne ya shiga d'aki mai kofa biyu, ya shiga ciki ya fita ta d'ayar kofar ba tare da tsayawa ba. Saboda haka ya san zai daure, shi ba matsoraci bane kuma bai tab'a tsoron wata gwagwarmaya a rayuwarsa ba, yana fuskantar komai da kwarin gwiwarsa kuma ya tsallake shi.  me yasa yanzu zai damu kansa da tunani akan Sa'adha? K'arar tsinin takalman dake taka floor din da akayi na katako ya ziyarci kunnensa, kuma ya san waye ba tare da ya bud'e idonsa ba. a sati na hudu da yazo wajen nan don hutawa ba zai iya k'irga iya adadin matan da  ya ture daga hanyarsa ba, wasu sun hakura wasu kuma har a yanzu suna cigaba da nacinsu. Wadda take tahowa a yanzu sunanta, Kathy,  kwananta hud'u kenan da fara aiki a hotel d'in da yake, kuma kamar sauran tunda tazo take fatan kawo kanta gare shi. "Hello, my name is Kathy, and i'm the server tonight. What can i get you to drink?" Muryarta ta fad'a daga gefe, wai bata fahimce cewa ta fad'a masa sunanta wajen sau biyar bane? Ya bud'e idanunsa a hankali ya kalleta. "Nothing."  ya fad'a da muryarsa mai zurfi. Sai da ta d'auki ta wasu sakanni kafin ya lura ta fahimci me ya fad'a, kamar ta tafi wani tunanin daban. Tayi murmushi da sauri sannan tace. "Okay, but if you ever change your mind..." Sai ta fito da wata 'yar paper  daga dan k'aramin aljihunta na gaba ta dora akan jikinsa. sannan tayi murmushi ta juya. Imran ya bita da kallon mamaki, kodayake ba abin mamaki bane inda ya bar kansa tun farko yaji me tunaninta ke cewa. A lokaci daya al'adar bahaushe musulmi ta burge shi, ya hango tarin matan dake damuwa dashi, ko kuma da siffarsa data fi kama da tasu, amma babu wadda ta tab'a fito masa kirikiri da bukatarta, sai dai 'yan kewaye-kewaye kawai. Ya godewa Allah da dalilin zuwansa cikin mutane bai kasance a cikin turawa ba, wayarsa ta sake katse  sabuwar wak'ar dake playing. Ya mik'e zaune sosai, iskar dake kad'awa ta d'auki paper tayi wani waje da ita. yana sliding answer button muryar jaamil ta shiga cikin kunnensa. "Me ya same ka yarima?" Maimakon ya amsa masa sai yayi murmushi mai k'ara sannan yace. "Wallahi kullum kara komawa more human kake, its a miracle, yau kaine ke kirana a waya?" jaamil yaja tsaki sannan yace. "Ba dole in kiraka ba, na duba duk inda nake tunani ban ganka ba." "Kamar yaya? ba na gaya maka inda zani ba?" "Ko dai ka fada min inda zaka je da farko, don gani a k'asar Bulgaria d'in kuma baka cikinta. Imran ya cusa yatsunsa cikin gashin kansa da iska ke kad'awa. "Oh my god, na manta ban fad'a maka bane, ina maldives sanyi ne ya koreni daga bulgaria kwana na d'aya." "I don't care, yaushe zaka dawo?" "Yaushe zan dawo? gaskiya ba rana. I have almost 2 weeks a cikin leave d'ina fa, meya faru?" "Komai ma ya faru, lokacinmu ya k'are sannan ciwon yarinyar na shirin dawowa. Sai da numfashinsa ya d'auke jin jaamil ya fara maganar sa'adha, sati hud'u kenan yana hirar ta a zuciyarsa amma bai furta ko sunanta a fili ba. Daga d'aya bangaren jaamil ya rage sautinsa sannan yace. "lokaci yayi yarima, ina fata ka shirya." ******* From the first time i met you... There was something about you I can never forget the way you thief my heart. I didn't try to pretend you I ain't like gonna send you But i know like we're friends too. Cuz you gave me a spark I just can't help myself, I want be your all And i see no one else.... "Rahma dan Allah kashe wak'ar nan..." Nanne ta fad'a lokacin da take goge tv da tsumma a hannunta. "Me yasa? wallahi ina son wak'ar duk da dadewarta." Bata ce komai ba sai ta d'auki bokitin ruwan omon dake kusa da k'afarta ta matsa jikin window ta fara goge shi. "Anya fa su inna yau zasu dawo, nifa banji kowa yace suna hanya ba?" Rahma ta fad'a daga gefe inda take jera tarkacen inna cikin wata cupbaord.  kwanan inna biyu kenan a niger, tun shekaranjiya suka tafi ita da baffa kuma a yau ake sa ran dawowarsu. A kwana biyun kuma Rahma tana tare da ita, tare suke kwana a dakin kuma tana iya kokarinta wajen ganin ta saki jiki suna harkokinsu tare kamar da amma bata iyawa, ko ta fara sai tunani da yawa yazo ya danne sukuninta. Musamman a yanzu da tunanin dalilin tafiyar Inna da Baffa yafi damunta, wani abu ne da bai tab'a faruwa ba, in dai za'a je niger toh kusan rabin gidan ake tafiya a tare. amma yanzu daga su sai direban Baffa kawai suka tafi. kuma bata san me yasa ba, tana danganta tafiyarsu ne da lamarinta. "Dazu kina wanka, Mama halime ta shigo tace sun taho." Ta amsa mata a hankali. "Toh Allah ya kawo su lafiya, in munyi sallah zamu je gidan Sumayyan?" "Eh zamu je, na gayawa Mama Azumi ma zamu fita." "Yawwa kinga sai mu tsaya in kai...." No one else can do the things that You do for me... I wanna be there for you Baby i really love you. There is something about you that i cannot explain... Wak'ar ta sake shigowa cikin kanta ta ture k'arshen maganar Rahman, sai kawai  ta ajiye tsumman hannunta da sauri sannan ta nufi kan kujera ta lalubo wayar ta kashe. "Na gaya miki bana son wak'ar nan." Rahma ta juyo ta kalle ta, da gaske ne abubuwa da yawa sun canja game da Nanne, abubuwa da yawa da bata sansu ba bata kuma tab'a tunanin zasu faru kanta ba. Bata k'ara cewa komai ba har suka gama aikin. ta zubo musu abinci suka ci sannan ta tattare kwanukan da niyyar sauka dasu k'asa. Sai dai bata kai bakin k'ofa ba wayar inna da bata tafi da ita ba ta shiga ringing a kusa da Nanne wadda ta baje magungunanta tana k'ok'arin sha. Nanne ta kalli wayar a gefenta,  bata san number ba, don haka ta barta ta gama rurinta sannan ta tsinke. bada dad'ewa ba aka sake kira, sai tayi tunanin ko inna ce tace a kira ta, tunda basu yi waya ba kuma ance sun taso. "Assalamu Alaikum." Imran ya rufe idonsa a hankali jin yadda muryarta mai sanyi ta ratsa jikinsa. "Wa'alaikum salam." Shima ya amsa ba tare da ya bud'e idonsa ba. A lokaci d'aya bugun zuciyarta ya tsaya, me yasa a kullum taji muryarsa take jin kamar wata murya ce data sani tun farkon rayuwarta, sab'anin sanin data yi masa na 'yan watannin baya ne kawai? Mamaki ya kamata, ta cire wayar daga kunnenta ta kalli numbar, da gaske imran ne ya kirata? imran d'in data sani? bayan tarin kwanakin da suka wuce ba alamarsa? Ta maida wayar a hankali kunnenta. "Zan iya ganinki gobe?" Muryarsa ta sake ratsa cikin kanta,  ta juya ta  kalli kofa inda Rahma take tsaye, babu kowa a wajen. "Me za'a yi?" Tana iya jiyo sautin murmushinsa daga daya b'angaren kafin yace. "Hak'uri zan baki na tarin laifukan dana yi." Nanne taji kanta ya fashe a lokaci d'aya. ita zai bawa hakuri. "Laifin me kayi?" "Suna da yawa, kuma in kika bani dama duk zan zayyano su duka da reasons d'ina." Sai ta gyara zamanta, yatsunta na kanannad'e ledar dake gabanta. "May be da yamma?" Wannan karon sautin murmushinsa ya k'aru. "Baki tabbatar ba?" Ta lumshe idanunta sannan tace. "Na tabbatar, Allah ya kaimu." "Ameeen..." Yaja Ameen d'in da d'an tsawo, sannan yace. "...Nagode sosai." Maimakon ta amsa sai kawai tace. "Sai anjima." Har ta cire wayar daga kunnenta, muryarsa ta katse ta. "Sa'adha..." Me yasa ne wai ya iya fad'ar sunanta fiye da kowa? bata ce komai ba amma sautin numfashinta ya tabbatar masa tana jinsa. "Thank you!" Dib! wayar ta katse. Ta cire wayar ta kalli screen d'in, da sauri kuma ta shiga call log don ta sake tabbatar ba tunani take ba. Sannan ta d'ago da ta kalli agogo. K'arfe uku da rabi. ●﹏● Please ignore the songs in the chapter,  i'm just kind of musical at that time. But if you are intrested,  the first one was. I wanna grow old with you by westlife. And the second. Kedike by Chidinma. ****** WAYE SHI? AYSHA SHAFI'EE 27 (☆_☆) Wajen cikin daji ne, dajin da bata tab'a zuwa cikinsa ba, amma somehow sai take jin kamar ta san wajen, kamar ruhinta ya tab'a zuwa...kamar wani waje ne da yake rik'e da wani tarihi na rayuwarta. Inda k'afafunta suke tsaye fili ne kuma daga gabanta akwai tarin bishiyu, tarin bishiyun da take ganin kamar abinda tazo nema yana cikinsu ne. Sai dai tana motsa k'afafunta, taji muryoyi da yawa na kiranta daga baya, muryoyin da ta kasa tantance su, kuma da yawa sunanta suke kira. ba tare da ikonta ba taji k'afafunta sun cigaba da tafiya wajen bishiyun nan, kamar tana zaune akan wani abu ne ana tura ta gaba. "Nanne..!" muryar inna ta fito daga cikin muryoyin nan, daga nan kuma sai ta fara tsintar sauran, akwai ta Rahma, Baffa, Sadiq, Amina, Mama halime, Mama Azumi, ya sulaiman da kusan rabin 'yan gidansu. kowannensu yana kiran sunanta da alamun gargad'i Taji tana son juyawa taga kiran me suke mata, don a yadda take jin muryoyin kamar bata yi nisa dasu ba, sai dai kafin ta iya juyawa ta hango shi. Imran ya fito daga cikin bishiyun nan yana kallonta da lumsassun idanunsa, kamar koyaushe yayi wani irin kyau sanye da light kaya, fuskarsa ta haska, sannan kyakkyawan murmushinsa ya kwanta sosai a gefen fuskarsa, sai da ta shagala da kallonsa sannan ya d'ago yatsansa guda d'aya yayi mata alamun ta biyo shi sannan ya juya ya koma cikin bishiyun. k'arar muyoyin suka k'aru a cikin kanta. Amma sai taji duk basu dame ta ba, bata damu taje wajensu ba, bata damu ta san kiran me suke mata ba. Tafi son ta k'arasa wajen Imran, ta tambayeshi tarin abubuwa da yawa da suka shige mata duhu, abubuwan da take son sani game dashi. Taku daya kawai ya shigar da ita cikin duhun bishiyun, amma sai wajen ya zama sab'anin tunaninta, a maimakon duhu wajen mai haske ne da kuma kyau, korayen ciyayi da fulawowi sun baje a koina, ga wani dutse daga can gefe yana zub da ruwa. Taji wani ya rungumeta ta baya, hannayensa sun zagaye k'ugunta sannan ya d'ora hab'arsa a daidai lungun wuyanta, ko bata juya ba ta san Imran ne kuma zuciyarta ta riga ta nutsu dashi, saboda haka ta cigaba da tsaiwa ba tare da ta juya ba tana jin d'umin jikinsa akan fatarta da kuma yadda numfashinsa ke busawa a k'asan kunnenta. A lokacin ne abin ya faru, taji an caka mata wani abu mai tsini a wuyanta, abin ya huda tun daga farkon wuyanta ya fito ta d'aya gefen. Numfashinta ya tsaya cak, sannan jini ya shiga gangarowa kan fatarta, tayi k'asa ta fad'i da baya sannan zafi ya shiga bin kowacce jijiya ta jikinta, taji ruhinta na barin jikinta a hankali sannan idonta na shirin rufewa. Amma kafin komai ya d'auke mata, fuskar Imran ta shigo cikin ganinta, yana tsaye akanta da wannan murmushin dake murkushe zuciyarta, sannan hannayensa na d'igar da jini! Nanne ta farka da wata irin ajiyar zuciya mai k'arfi idanunta a zare, wayar inna dake gefenta ta fad'i k'asa ta gangara wajen dressing mirror. Ta juya kowanne b'angare ta kalli wajen da take, cikin d'akinsu ne ba wani waje ba, Rahma na kwance a kusa da ita tana baccinta hankali kwance, ta kalli agogon dake saman dressing mirror. K'arfe uku da rabi na dare. Ta koma da baya ta kwanta akan filon, sannan ta shiga tofa adu'o'i a jikinta, amma har kusan mintuna ashirin baccin yaki dawowa, Sannan hankalinta ya kasa kwanciya, tunanin mafarkin ya cika kanta, saboda haka ta mik'e ta shiga toilet ta d'auro alwala da niyyar sallah. Tana fitowa idonta ya kai kan wayar inna dake k'asan mudubi, ta sunkuya a hankali ta d'auka, hannunta ya shiga call log ta lalubo number da Imran ya kirata jiya, tana nan rad'au a rubuce ba'a tunaninta ne komai ya faru ba, idonta ya kai kan time d'in da kiran ya shigo. K'arfe uku da rabi na rana. A lokacin fuskarsa ta cikin mafarkin nan ta sake haskawa a idonta, da sauri ta ajiye wayar gabanta na fad'uwa, me mafarkin ke nufi? wannan kiran dasu inna ke mata, wannan murmushin imran din sannan yadda ya rungumeta, yadda take jin numfashinsa a wuyanta kamar gaske da kuma sanda ta fad'i k'asa, ta hango hannayensa da jini? Jini? jinin waye? ita dai ta san taji zafi a wuyanta amma bata ga fitowar jini ba. Ta rufe idonta a hankali sannan ta bude su akan mudubin dake gabanta, idanunta sunyi zuru-zuru kamar tayi kuka. Ta k'iftasu a hankali tana k'arewa yanayinta kallo, a sannan ne abin ya faru, a sannan ne gabanta ya fad'i sannan dukkan tsoro ya shigeta. Ganinta ya koma dishi-dishi, sannan wani hayak'i ya fito daga rabin fuskarta ya tarwatse a iska! ●﹏● WAYE SHI? AYSHA SHAFI'EE 28 (☆_☆) "Wai Rahman ta tafi ne?" Inna ta tambaya tana kallon Nanne dake kokarin sa hijabinta, a lokacin karfe bakwai da kwata na safe. "Ta tafi tun d'azu kina sallah, zata je makaranta ai." Ta fad'a a hankali, saboda kanta dake tsabar ciwo. Tun bayan lokacin data farka daga mafarkin nan da kuma abinda ta gani a cikin mudubi. Bata san iya adadin sallar da tayi a lokacin kafin gari ya waye ba sannan ta iya samun nutsuwa. "Amma kuwa Rahma bata kyauta ba, ga tsarabarsu tun jiya na ware tana kallo shine zata tafi bata fad'a ba." "Inna zata dawo ai, ga kayanta ma fa bata d'auka ba." Nanne na rufe bakinta ta jiyo horn d'in idris daga compound saboda haka ta d'auki jakarta tayi waje tana fad'in na tafi. "Yau kar ki tsaya wannan lesson d'in naku, ana tashi ki biyo su safiyya ki taho." Daga k'afar bene ta amsa da toh ba tare da tayi la'akari sosai da abinda innan tace ba. A makaranta gabad'aya bata da walwala, duk da cewa kusan kwana biyu haka take amma yau ko hirar da take dagewa suyi da Amina ta kasa, tunaninta ya rabu kashi kashi, ga azabar da ciwonta yake sannan ga tsoron mafarkin da tayi a jiya da kuma fuskar da ta gani a mudubi, don ta tabbata taga wani abu kamar hayaki ya fito daga fuskarta, ta shafa wajen a hankali tana so ta cusawa zuciyarta cewa ba da gaske bane. Sannan ga Babban abun dake gabanta a yau, zuwan Imran wajenta, mafarkin da tayi ko kad'an bai girgiza zuciyarta akansa ba, ji tayi ma ta k'agu sosai yazo ya warware mata tarin k'ullin dake cikin kanta game dashi. Amma kuma bata san ya zasu had'u ba don ko Rahma bata gayawa zancen kiran da yayi mata ba, amma ta san in har zai zo d'in zai gaya mata lokaci. Ta kwanta akan bencinsu  sanda ajin nasu ya rud'e da surutu sakamakon rashin shigowar malami a last period d'in da suke da ita, wasu sun had'a group-group suna ta hira wasu kuma na daga can gaban ajin suna kid'a da benci suna rawa, a cikin masu rawar harda Amina, saboda haka ita kad'ai ce a row d'insu dake can k'arshe, kowa ya tafi harkarsa. Ta rufe idonta a hankali tana sauraren wak'ar sa'adu bori da masu rawar suka had'a baki suna yi. Haba yarinyar nan...dan Allah juya, idan baki juya ba...kinci amanata, mai abin dad'i kawo eh mara abin dadi ko.... Sai da aka kad'a k'ararrawar tashi sannan ta tuna da abinda inna tace mata, saboda haka ta yiwa Amina sallama ta fito tare da wad'anda basa yin lesson d'in. Zuciyarta cike da tunanin me za'ayi a gidan da inna tace ta dawo da wuri, amma har suka koma bata hango wani abu da ake shirin yi ba tun dawowarsu innan a jiya da rana. Sanda ta shiga d'akinsu, Mama Azumi na zaune suna magana da inna wanda shigowarta yasa dukkaninsu sukayi shiru sannan Mama Azumin ta mik'e tana fad'in wa inna sai anjima zata shigo. Bata nuna komai ba ta gaishe su sannan tayi d'aki, ta fad'a toilet tayi wanka da ruwan zafi sosai don ta samu k'arfin jikinta, har a kanta ta dinga kwarawa ruwan da fatan zai wanke tunanin wannan mafarkin da tayi. Ranar Alhamis ne saboda haka ta zura doguwar rigar wani light material ta fito falo. "Nanne k'araso nan magana zamu yi." Inna ta fad'a ganin tana shirin zuba abinci, ba musu ta rufe flask d'in sannan ta dawo ta zauna a kusa da ita. "Ina so ki nutsu sosai ki saurareni da kyau, abinda zan fad'a ba neman ra'ayinki nake ba ko son jin shawarki, abu ne da manyanki sun riga sun gama yanke komai kuma in ba wani ikon Allah ba, ba abinda zai sa a canja shi." Nanne ta tsura mata ido kawai tana jiran kalamanta na gaba, don ta tabbatar ita a yanzu babu wani abu da zai sake girgiza zuciyarta. "Tafiyar da muka yi nida baffanki akan maganar ki ne. Ni ban san yaushe kuka shirya da yaron nan ba don baki gaya min ba amma bayan baffanki ya tara mu akan zancen rashin lafiyarki yaje wajensa da sati biyu, ya nemi izinin zuwa wajenki amma baffan yace masa ya dakata tukunna. sai da yayi bincike akansa ya tabbatar da halayensa sannan yace dashi ya turo iyayensa. Toh wani abu na ikon Allah kuma bayan sun zo, sai suka nuna cewa shi yaron ya shirya kuma da wuri suke son ayi auren duk da haka baffa bai tsaida wata magana ba sai bayan sati guda da suka dawo, anan aka tsayar da lokacin aurenki nan da wata guda kamar yadda shi baffan yace ko kafin nan  ko kun k'are jarabawar wane ne term oho... Yana gaya min zancen nan na d'aga hannu na godewa Allah, don dama ni inda nake tunanin yin magana sai in har ya had'a ki ne da wanda bamu  sanshi ba, toh shine zance a d'an dakata mu dake mu fahimci halinsa tukunna. Amma tunda har Allah yasa an sanshi kuma shima baffan ya yaba da hankalinsa shikenan nayi shiru da bakina. Don haka zuwan da muka yi niger, mun tattauna ne da duk 'yan uwan mahaifinki kuma Alhmdlilahi kowa yaji dad'in zancen wallahi. Abinda yasa nace ki dawo da wuri kenan yau, don yace zai zo ku gana kuma na san kema ya gaya miki." Nanne taji ta zama kamar gunki ne zaune a wajen, abu na farko daya d'aure mata kai shine, tana cikin gidan nan har ake jelan zuwa neman aurenta bata sani ba? don ita baffa kawai ya gaya mata cewa yana bincike akan wanda ta turo wajensa ne amma ko Addano bata kira ta tace mata har iyayensa sunzo ba. Sannan ita ta zaci baffa ko inna  zasu nuna rashin amincewarsa akan cewa Nuran daga dangin mahaifiyarta yake sai gashi har komai ya tafi daidai an  tsaida ranar aure wata d'aya? wata d'aya kawai? Sannan zai zo wajenta yau? ita bata shirya ba, tana bukatar lokaci amma ba yadda ta iya, tunda inna ta fad'a mata tun farko cewa bata da zab'i abinda zata fad'a mata umarni ne kawai, muryarta na rawa tace. "Amma inna ba wanda ya fad'a min duk wannan abubuwan da suke faruwa ko ita kanta Addano bata kira ni ba." "Nuratu kuma? yo ina ruwanta da wannan sha'anin? koko bamu da ikon mu yanke abu akanki sai da izininta? tunda ita kad'aice me iko dake? toh  bari kiji kalma d'aya akan lamarin nan bata sanshi ba kuma habu abinda zai canja, ban k'i ba dai yanzu da aka yanke lokacin a gaya mata." Cike da mamaki Nanne ta kalleta tace. "Inna na san dole zata sani ai tunda wanda kuke zancen akansa d'an uwanta ne." "Ban gane ba, Imranan ne d'an uwanta? toh ni a yadda baffa yace min game da asalinsa banji wata dangantaka data had'a shi da adamawa ba." Wani irin bugawa zuciyarta tayi, gabanta ya fad'i, sannan kwakwalwarta ta yanke daga fahimtar komai, me inna ke cewa? wane Imran d'in take nufi? wane Imran d'in ne yazo neman aurenta? watak'ila dai mafarki take irin na jiya, kuma zata iya farkawa a kowanne lokaci, saboda haka ta tsura mata ido kawai ta cigaba da kallonta kamar wadda kammaninta suka canja gabadaya. ****** WAYE SHI? AYSHA SHAFI'EE 29 (☆_☆) Sai dai kafin k'arfe biyar na yammacin ranar, inna ta tabbatar mata da cewa da gaske imran ne yaje wajen Baffa neman aurenta kuma har an amincewa iyayensa an bashi ita. Ta zauna tayi mata bayani sosai akan cewa ba ita ta tura shi wajen baffa ba, ita irin wannan maganar ma bata tab'a had'a su ba amma inna ta kasa fahimtarta, zance d'aya kawai take maimaitawa cewar ai daman abinda ya dace kenan a shari'ar musulunci, a fara tuntub'ar iyayen yarinya kafin ayi mata magana, kuma gwara shi akan baffa ya bada ita ga d'aya daga cikin 'ya'yan abokansa da bata san ya suke ba, tunda dai ko babu imran aurenta ba zai d'auki lokaci ba. Ta san cewa a zuciyarta tana son imran, amma yanzu da kawai maganar aure ta shigo tsakaninsu, bata san yaya zuciyarta zata dauki abun ba. bata san me ya kamata taji game dashi ba, tunda shi bai taba fad'a mata yana sonta ba, kuma a tsawon lokacin daya kai kansa wajen baffa bai nemeta ba, yayi amfani yawunta ya gabatar da kansa, sai a jiya daya san zai zo yau sannan ya kirata a waya, ita kuma ta kasa daure zuciyarta ta ja ajinta, kawai ta amince da zuwan nasa. A sannan ne kuma ta san abinda inna da mama Azumi ke tattaunawa sanda ta dawo daga makaranta, kayan tarba sosai aka had'a masa na snacks da lemo har kala biyu, don ta hango su a hannun lami sanda ta shigo d'akin karb'ar muk'ullin falon waje da aka sa su halliru suka share. "Nace miki ki maida wannan rigar ko? ina hankalinki yake tafiya ne wani lokacin?" Inna ta katse tunaninta, ta juya ta kalli rigar da ta d'auko, ash doguwar riga ce mai kama da abaya sannan mayafinta yana had'e da d'an k'aramin hijabi a jikinsa. ita bata ga abinta tayi ba da inna zata ce ta mayar, kuma ma ai ita ta siyo mata a makka, in har bata da kyau me yasa ta d'auko mata. Kamar tayi magana taga yanzu sai inna ta fassara zancen da wata ma'anar, saboda haka ta cukwuikuye ta mayar, ta d'auko riga da skirt na atamfa coffee da milk da kuma dogon hijabinta mai hannu milk. "Su zaki sa?" "Inna meye laifinsu to dan Allah, shifa bata shigata yake ba, tunda har zai iya zuwa neman aurena ba tare da amincewata ba na tabbata shigata baza ta sa ya fasa ba." Ta saka kayan kamar gaske sannan tayi waje, ta tsakanin k'ofar gate d'in ta hango shi. Yana tsaye daga jikin motarsa yana danna waya, sanye cikin wani milk yadi wanda ya kwanta akan fatarsa sosai, yana da d'an shara-shara kad'an don har ana iya hango layin singlet d'insa dake ciki, sannan yasa hula mai kyau kalar brown shigen aikin dake jikin kayan da kuma takalmi k'afarsa, zata iya rantsewa a rayuwarta tab'a ganin halitta mai kyau irinsa ba, Zuciyarta tayi nauyi da tunanin cewa wannan jiran da yake nata ne, abinda tayi mafarki da tunaninsa fiye da cikin k'irga a baya, sai gashi a yau yake faruwa, yau d'in da komai ya cakud'e mata. Tunaninta ya tsinke, taji kamar baza ta iya bin shawarar data yanke ba, amma in har bata yi ba, ta san sai tayi regretting  hakan daga baya sau cikin carbi. Tayi baya ta koma ciki sannan ta kira wani hanif d'an wata mai aikinsu dake wasa a gefe tace masa. "In ka fita gate d'in nan zaka ga wani mutum a jikin mota kaje kace masa wai ance sa'adhan bata nan." "Yaron ya d'an kalleta. "Wace ce Sa'adha?" "Nima ban santa ba a gidan nan take kuma bata nan, kaje ka fad'i abinda naka gaya maka." Ta tsaya tana kallon tafiyar yaron, kowanne taku d'aya da yake ji take kamar taje ta jawo shi tace ya koma ta fasa ta fita wajen imran d'in dake jiranta. Amma kuma tunanin ya danne-danne abinda zuciyarta ke so, saboda haka tana gani har yaron ya fita ya rufe gate d'in sannan ta juya ta koma cikin falon da akace ta shigo dashi. Bata tab'a tunanin cewa hannun mutum zai iya gyara d'akin ba tunda kusan kodayaushe a k'ulle yake cike da ku'ra, amma a yanzu yasha gyara tas! harda carpet aka shimfida da kuma wasu manyan tin-tin guda uku, sannan daga gefe turaren wuta mai dad'in k'amshi yana tashi a kaskonsa. A tsakiya wannan farantin ne da ta hango a hannun lami cike taf! da duk irin snacks d'in da take so, a lokaci d'aya taji yawunta ya tsinke. Ta koma gefe guda ta jingina da bango sannan ta cusa hannunta cikin lallausar sumarta kamar zata tsinto duk wata damuwarta waje. Har a lokacin kanta na ciwo sama-sama. Komai ya cakud'e mata, kuma ta san ba sai ta fahimce su duka ba, abu d'aya ne kawai ya kasa shiga kwakwalwarta har yanzu, cewa Imran shine k'arshen duk wannan k'addarar tata. Ta tuno da mafarkin data yi a jiya, mafarkin da su inna ke kiranta kar taje wajensa, a yanzu kuma su ke k'ok'arin had'a ta dashi, sannan wannan jinin hannun nasa sanda ta fad'i k'asa. sai tayi saurin ture wannan shi kuma, mafarki k'arya ne, ba zai tab'a zama gaskiya ba. Ta dad'e zaune a d'akin kafin daga k'arshe ta janyo plate d'in nan ta cika cikinta dam, sannan ta kulle d'akin ta shigo cikin gida. ******* Bayan ta idar da sallar magriba, ta cigaba da zamanta akan sallayar tana lissafo dukkan damuwarta ga jalla wata'ala, ta bud'e zuciyarta sosai ta rok'e shi akan Allah yasa duk abinda ke faruwa da ita ya zame mata alkhairi, tunda wani abu ne da baza ta iya canjawa ba. Tana shafawa wayar inna ta shiga ringing, ta juya ta ga har a lokacin bata idar ba saboda haka ta d'auka ta kai kunnenta. "Assalamu Alaikum." A lokaci d'aya, taji tunaninta ya tsaya cak! Wannan muryar, wannan muryar  mai taushi ta cika kunnenta. taji tayi kewarta kamar ba'a jiya ne taji ta ba. Calm down Sa'adha! just calm down! B'arin zuciyarta mai hankali ya shiga bata warning. "Waalaikum salam." Ta amsa a hankali. "Sa'adha kina lafiya?" Bani da lafiya kuma hankalina a tashe yake imran, komai ya cakud'e min a lokaci d'aya, sannan ga al'amarinka da na kasa ganewa, ka san irin halin dana shiga a baya? kace min zakazo na jiraka har dukka hope d'ina ya kare ban ganka ba, me ya hana ka zuwa?  me yasa baka fad'a min kana sona  ba? me yasa ka tafi wajen baffa kai tsaye? sannan tsawon lokaci baka neme ni ba? in kowa yak'i fad'a min halin da ake ciki atleast i deserve an explanation from you, amma kaima ka share ni, sai a jiya kawai ka kirani, babu tambayar lafiyata balle wani explanation kace zaka zo wajena, ni kuma banyi tunanin komai ba na biye maka, sai a yanzu ka damu da sanin halin dana ke ciki? me yasa ma zaka damu? bayan ka riga ka samu go ahead akaina? a yanzu ko da yardata ko babu ka san ba zan iya fasa aurenka ba, saboda ko ba komai nima na san har yanzu wani side d'in zuciyata yana sonka... Maimakon duk wannan sai tace. "Ina lafiya, Alhmdlilah." This is clumsy. ta fad'a a ranta "I'm sorry, ban tambayeki haka jiya ba." Huff. wannan kuma ya wuce. "I'm so sorry sa'adha, na san ban kyauta miki ba, na san nayi abubuwa da yawa wanda ba haka ya dace ba..." "Me ya hana ka zuwa ranar da kace min zaka zo?" Tayi saurin katse shi, in har zata saurareshi gwara ayi komai tun daga farko, tana bukatar bayani da yawa. Ya danyi shiru kafin a hankali yace. "Sulaiman ne ya hanani zuwa wajenki sa'adha, ba'a ranar kad'ai bama harda duk sauran lokutan da ban nemeki ba." Taji wani k'aton abu ya fad'a daga zuciyarta, ya sulaiman kuma? ta ina ya shigo zancen? "Tun ranar dana fara ganinki a k'ofar gidanku rayuwata ta canja, duk wani tsari da nake dashi ya ruguje, na zama ba abinda nake iya yi ba tare da tunaninki ba, tun ban fahimta ba har nazo na gane cewa sonki nake yi, irin son da zuciyata bata taba yiwa kowa ba. Zan so in iya fad'a miki kuma ki fahimci irin son da nake miki sa'adha, duk sanda na rufe idanuna ke nake gani, in na bude su kuma sai inji ke d'in kawai nake son gani, duk da bana iya samun ganinki kullum amma i always feel your presence around me. Every second, every moment, every hour, my eyes search for you only, call this love, craziness or the beat of my heart... it is all same for me. I love you very very much Sa'adha and i don't want to lose you, ever! Shi yasa a ranar dana ce miki zanzo naje na sami yayanki sulaiman na gaya masa damuwata, shi yace inje wajen baffa sa'adha, shi yace kar in neme ki na tsawon lokacin nan sai na samu yardar baffa tukunna. a duk tsawon lokacin ba mantawa nayi dake ba, ina ta fad'i tashin neman amincewar baffa ne har na samu ya saurare ni, don da farko yace min yayi maganar ki da wani d'an abokinsa ne. Da Sulaiman da umar su suka yi ta min kokari a wajen baffa har na samu ya saurare ni, daga nan kuma yace zan iya turo magabata na, ko a lokacin na so zuwa in sanar dake komai amma sulaiman yace in bari inji me zasu tattauna tukunna. Kamar yadda aka fad'a miki nima haka naji zancen sa'adha, bayan tattaunawarsu, sun yanke mana rana zuwa nan da wata guda kuma wallahi duk da bani na tambaya ba i'm more than happy. Shi yasa jiya dana kira ki na kasa cewa komai...nace miki laifina da yawa sai nazo zan fad'a miki duka reasons d'ina, kuma nazo kika ce min bakya nan." Ya k'arashe zancen muryarsa can k'asa kamar k'aramin yaro. Nanne taji duk wata jijiya a jikinta tayi sanyi, gabad'aya fushin da take ji game dashi yabi iska, maganganunsa kamar sun sa hannu ne sun yaye rabin duhun da take ji game dashi, bakinta ya k'ulle ta rasa me zata ce. sai ta jingina kawai da jikin gado ta dunk'ule jikinta waje d'aya. Shiru ya biyo baya ba tare da yayi magana ba. "I'm sorry Sa'adha, i'm reeeeallly sorrry, dan Allah kiyi hak'uri if i've hurt you in anyway." Yadda muryarsa ta fita a hankali da kuma zurfi, yasa taji kamar zata narke gabad'ayanta. I'm so sorry nima da na kasa fahimtarka a baya, i'm sorry da duk wahalar da kasha akaina, i'm so sorry dana kore ka d'azu. Ta ayyana hakan duk a zuciyarta, sannan ta sake k'ank'ame wayar a hannunta ba tare da tace komai ba. "Sa'adha..." Sai da zuciyarta ta buga da k'arfi jin yadda muryarsa ta nannad'o sunan kamar tun asali shi ya bada shawarar a rad'a mata. "Na yarda kiyi punishing d'ina duk yadda kike so amma dan Allah kar kice kin fasa." "Na fasa me?" "Aure na." Kalmar tayi mata nauyi sosai, don duk sauran dauriyarta ta tattare ne wajen yadda muryarsa ke shiga kowanne lungu da sak'o na jikinta. "Na san ba zaki fad'a ba koh?" A hankali ta daure tace. "Baffa ya riga yayi magana ai ba zan iya masa musu ba." "Saboda Baffa ne ba saboda kema kina sona ba?" Ta damk'e k'arshen hijabinta  da k'arfi  sanda sallamar sallar inna ta shiga kunnenta. jin tayi shiru yasa yayi murmushi sannan yace. "Karki damu, zan koya miki yadda zaki so ni, for now wanda nake miki ma ya ishemu mu biyu." Taji maganganun suna shirin yi mata yawa a rana d'aya kawai da komai ya kwance mata saboda haka tace. "Sai da safe." "Zaki kore ni? dan Allah sa'adha kar ki d'auki fushin nan da nisa, so nake mu sake komai afresh, in sanki sosai kema ki san ni." Tayi shiru tana cije lebb'enta na k'asa. "Kinjiii....?" Da sauri tace. "Naji, sai da safe." "Ya na iya...sai da safe, Allah ya tashe mu lafiya." "Ameen." Tana shirin d'auke wayar daga kunnenta taji abinda ya d'auke numfashinta gabad'aya. "I love you!" ●﹏● Next chapter zamu ji yadda akayi imran ya iya tsara duk wad'annan abubuwan. Sannan zamu ji yadda zata bashi damar da zai gaya mata WAYE SHI. Kuna tunanin zai gaya mata gaskiya? Ko rabin gaskiyar? **** WAYE SHI? AYSHA SHAFI'EE 30 Assalamu Alaikum...i can't beleieve we are up to chapter 30 already! ya Allah kamar jiya ne fa kawai naci na qoshi na rasa me zanyi na jawo wayata na fara typing...gashi har mun fi rabi na cikin labarin nan. Kuma Allah ba don ku ba, da tuni na jefa shi a dustbin d'in da nake tara irinsu, cox i have lots of uncompleated stories kamar meh? Nagode da dukkan support d'inku...dix shapta is dedicated to o laf yuuu!...(lol😁) I mean all of you! Enjoy!😘 (☆_☆) "Nanne...?" muryar Rahma ta kira ta. "Mhmmm." ta amsa halfway cikin barci ba tare da tunanin komai ba. "Yau baccin me kike yi haka, sha d'aya fa ta wuce." Jin haka yasa ta bud'e idanunta da sauri ta kalleta. "Da gaske kike sha d'aya?" "Na gaya miki ma fa ta wuce, inna har ta fita asibiti nima shigowata kenan." Ta mirgina a hankali ta juya kan bayanta. "Ni kaina ban sani ba, na dad'e banyi bacci irin haka ba." "An kawo miki sak'o yanzu wani yaro ne ya kawo daga waje, shi yasa ma na tashe ki." Nanne ta had'e girarta waje d'aya. "Sak'o? meye a ciki?" "Sak'o fa nace miki, ta yaya zan bud'e." Ta matsa jikin dressing mirrow ta d'auko wata brown leda k'atuwa mai logo d'in hannaye biyu. "Kamar wani kwali ne a ciki." Nanne ta mik'e sosai akan gadon  ta karb'i ledar, tana bud'ewa taci karo da wani pink box medium size a jikinsa akwai large prints d'in flowers purple. Ba tare da tunanin komai ba ta bud'e cikinsa, idanunta suka ci karo da ledoji na different kinds of chocolate, tun daga kan wanda ta sani harda wanda bata tab'a gani ba, gasu nan fal! a ciki. "Lallai kayan dad'i ne ashe, daga ina haka?" Rahma ta fad'a tana zama akan gadon, ita dai tayi turus! da murfin a hannu tana kallon su, daga can gefe idonta ya hango mata wata takarda ta janyo ta a hankali ta bud'e. Sa'adha....! Yau ina tashi da safe naji a News wai sugar yana kwantar da anger dake jikin mutum, zaki taimaka kisha wannan ko zamu samu fushin da kike dani ya ragu? Bata san lokacin da wani d'an guntun murmushi ya sub'uce daga fuskarta ba. Bayan ta fito daga wanka ta zauna a gefen gado tana shafa mai tana kallon fuskarta ta cikin mudubi, akan mudubin wannan box d'in alawar yana facing d'inta. Wayar da tayi da imran a jiya kawai ta wanke abubuwa da yawa a cikim kanta, idan ta tuno cewa duk tsawon lokacin nan ba share ta yayi ba yana ta neman hanyar da zai same ta ne sai taji wani dad'i ya wanke zuciyarta, sannan idan ta tuno kalaman daya gaya mata cewa shima yana sonta sai taji kamar tana daya daga cikin wadanda suka fi kowa sa'a a duniya, don Imran daban yake daga irin mutanen data sani kuma take gani. Ance mutum baya taba zama cikakke, amma ita gani take shi komai nasa perfect ne! komai da ta sani a yanzu, kamar ice cream mai dad'i ayi topping d'insa da m&m's... Ta ina za'a sami matsala a cikinsa? Ta kalli box d'in ta tuno da d'an short text d'in nan, wani dad'i ya ratsa ta, kamar an saka k'ank'ara a cikin zuciyarta. Da gaske Imran yana sonta. Da gaske ne ba mafarki take ba. Yace yana so suyi starting komai afresh, kenan zai gaya mata waye shi da duk sauran details d'in rayuwarsa, kamar yadda ya fad'awa baffa har ya yarda ya bashi aurenta, in ma bata san duka a yanzu ba, ta tabbata zata sani nan gaba. Tunda k'addararsu ta riga ta zama d'aya. A lokacin ne taji wani abu a gefenta yace zut! tana juyawa taga ashe tana zaune ne kusan akan rabin wayar inna, aikuwa idonta ya gane mata number da taje tana kira, number Imran ce da yake itace ta farko akan call log d'in. Da sauri tasa hannu ta katse kafin ya kai ga shiga, me zai kaita kiransa a yanzu? tace masa me? Ta mik'e ta nufi sa kaya, sai dai kafin ta zak'ulo kayan da zata saka k'arar shigowar message ya shigo. A wayar inna dai ta san banda layin gidan waya babu masu turo da text, sai ko wani lokacin wrong number, amma kawai sai ta samu kanta da matsawa ta d'auko wayar. Da gaske text d'in ne kuwa, kuma ba daga layin waya ba balle wrong number ba. Daga number Imran. Missing me already?...ki min afuwa zan kira ki anjima yanzu zamu shiga meeting ne. nima nayi missing d'inki Habibty... ...like crazy! Hannayenta suka shiga rawa, dama kiran ya shiga kenan? ya salam! yanzu me zaiyi tunani akanta? zaice har ta fara kiransa kenan? ta ya zata ce masa bata san ta kira ba? Ta ajiye wayar ta koma wajen wardrobe ta jawo kayan da hannunta ya fara kaiwa kansu, ta saka rigar amma kafin ta zuge zip ta koma ta d'auko wayar ta sake karanta text d'in. Habibty. Ta fad'a a hankali. He just call her habibty! ******* "Toh ina jinka...sai kuma kayi me bayan nan?" Jameel ya tambaya yana kallon Imran dake zaune a study room d'insa yana signing wasu papers. shi kuma yana zaune ne akan wata couch dake jikin glass wall na d'akin. D'akin triangular ne mai bango uku, bangon k'arshe shine aka yishi da glass gabad'aya inda daga ciki kana hango d'an k'aramin garden d'in gidan mai d'auke da flowers. "Na kira ta a waya, na bata hak'uri kuma nace mata nima ina sonta kamar yadda itama take sona, sannan nace mata zanyi mata bayanin ko ni waye saboda ni da ita mu fahimci juna." "Yarima...." "Na sani jamil..." yayi saurin katse shi. "...Ba sai ka tuna min ba, na san bamu tsara haka ba, na san na dawo yanzu ne saboda ciwonta yana shirin dawowa sannan na san bamu yi da kai zan kulata ba har lokacin da za'ayi auren. Amma idan har muna tsarinmu dole ne mu dinga duba yanayin rayuwarsu suma. ba zai yiwu don iyayenta sun yarda da auren ba kawai ace babu wata alak'a da zata shiga tsakaninmu a yanzu, a tsarinsu dole ne a samu fahimtar juna tsakanina da ita wanda in babu hakan, ba yarinyar kad'ai ba har iyayenta zasu fara suspecting wani abu, kuma babban abinda zai fara rusa mana shiri, shine in har wani ya fahimci cewa akwai wata manufar da yasa nake son aurenta. Saboda haka dole ne jaamil sai nayi acting cewa da gaske ina son ta ne. kamar yadda ka fada a baya ka gama naka aikin saura nawa, don haka ba sai anyi auren zan fara zan fara part d'ina ba, zai fara ne tun daga yanzu." Jaamil ya d'anyi shiru yatsunsa akan lebb'ensa yana nazari, daga can kuma yace. "In dai zaka tafi da hakan akan tsarinmu ba matsala bane yarima, I'm just afraid kar ka zama so close da ita nan gaba...." "Na gaya maka bana sonta jaamil, abinda ya faru tun farko ya riga ya wuce, har yaushe zaka yarda dani ne wai? Sannan ni kaina ina da hankalin da zan san cewa Sa'adha ba abokiyar rayuwata bace, halitta ta da tata daban ce, ko banzo cikin mutanen da wannan manufar ba, ba zan tab'a fad'awa wannan kasadar ba. Rayuwata daban ce da irin tasu kuma na san a kowacce halitta aure shine cikar rayuwa, to ta yaya zan k'arashe rayuwar da ban fara anan ba?" Jaamil yayi shiru baice komai, hakan ya bawa imran tabbacin cewa ya d'aure shi ne da jijiyoyinsa. *** K'arfe sha biyu saura na rana, Imran na cikin office d'insa yana harhad'a takardun da ya gama signing, sha biyu daidai zasu shiga meeting da wani sabon company da suke son fara bussiness dasu. Wayarsa tayi haske, wani d'an mitsitsin haske da ba don idonsa na kusa ba zai gani ba. ya mik'a hannu ya jawo ta gabansa, mamaki ya kamashi ganin number Sa'adha, ya sake kallon agogo, yau friday...bata je makaranta ba kenan? Ya tuno da fuskarta a jiyan nan, sanda ta lek'o tana kallonshi daga cikin gate din gidansu. a lokacin yaji kamar ya shekara ne bai ganta ba, duk da cewa bata canja ba, amma wad'annan fararen idanun nata cike suke da damuwa wanda ya tabbatar masa da cewa abinda ya karanta da ita a sanda yaje don kwantar da ciwonta gaskiyane kenan. Zuciyarta tana cikin damuwa, damuwa mai yawa kuma rabi akansa ne, ya fahimci cewa in har zasu tafi akan tsarin da suka yi da jaamil kawai to dole zasu fuskanci matsala nan gaba, don ba zata k'i aurensa ba amma zuciyarta baza ta yarda dashi ba wanda hakan dole zai jawo matsala nan gaba. A daren ya lura kamar kuka take, daga baya kuma ya fahimci mafarki take yi kuma kamar wani abu ya same ta ne a cikin mafarkin, ya san zata iya farkawa a kowanne lokaci saboda haka yayi sauri ya d'ora hannunsa akan goshinta sannan ya shiga kwantar da d'aya b'arin ruhinsa dake tare da ita. Sai dai kafin alamun cewa hakan yayi, ya fito, ta bud'e idonta da sauri tare da yin ajiyar zuciya, a sannan ya tabbatar da cewa mafarki tayi wanda ya tsorata, yana cikin d'akin har sanda tayi alwala ta fito sannan ta tsaya gaban mudubi, ya matso dab da bayanta ya tsaya don yaga abinda take gani a cikin wayar data d'auka. Number daya kira yace mata zaizo ce, ita take ta kallo kamar tana so ta tantance ko shima kiran da yace mata zaizo a mafarkinta ya faru, ya lura ta haddace number saboda haka dole ya nemo layin duk inda ya shiga, don bayan ya kirata ba zai iya tuna inda yasa shi ba. Ta d'ago ta kalli mudubin, a lokacin ne alamun cewa ciwon ya kwanta ya faru, wani hayak'i ya fito daga rabin fuskarta ya tarwatse a iska, kamar yadda yake yi kullum. Tun daga yadda yaga ta tsorata a lokacin, ya san sai ya kwantar mata da hankali in ba haka ba abubuwa ne zasu k'ara cakud'ewa a cikin kanta. Shi yasa bayan yazo ta hana shi ganinta, ya san sai yayi amfani da dabararsa don ya saita tunaninta, saboda haka ya kirata bayan sallar magriba. Amma kamar yadda ya sani ne, bai yarda da kansa in yana tare da ita ba, bai yarda da zuciyarsa akanta ba. Saboda haka tun lokacin data amsa sallamarsa bai k'ara bi ta kan tsarinsu  ba, yayi amfani ne da hanyar daya san zata kwantar da hankalinta kawai. Bayan nan kuma ya tafawa kansa da shirmen da yayi, shirmen da ya fara tun ba'aje koina ba, shirmen da yayi k'ok'arin lullub'ewa jaamil d'azu cewar ba wani abu bane da zai b'ata tsarinsu, shirmen da yayi d'azu na aika mata da sweets d'in nan, sannan shirmen da yake shirin sake irinsa yanzu. Ya bud'e cikin wayar ya shiga typing mata message. Missing me already?...ki min afuwa zan kira ki anjima yanzu zamu shiga meeting ne. nima nayi missing d'inki Habibty... Ya tsaya ya kalli abinda ya rubutu, sannan a hankali ya k'ara da.. ...like crazy! ●﹏● WAYE SHI? AYSHA SHAFI'EE 31 (☆_☆) "Kin min shiru Sa'adha don Allah kiyi  magana, ko har yanzu fushin ne?" Nanne ta sake tankwashe k'afarta akan gadon tana nannad'e bakin rigar filon dake kan cinyarta, a hankali tace. "Kana lafiya?" "Ina lafiya kuma yanzu da kika tambaya sai na k'ara jin lafiyar ta kama ni." Tayi murmushi mai fad'i. "Ina jinki ki fad'a min sau nawa kika tuna ni bayan lokacin da kika ce min sai da safe?" Bata ce komai ba kamar yadda ya zata. "Ko sau d'aya ne kawai sanda kika yi min flashing?" Da sauri tace. "Ni ba flashing nayi ba ban sani bane kawai kiran ya shiga na zauna a kusa da wayar." "Irin wannan bayani haka kamar laifi kika yi?...yanzu toh ba wannan ba, baki tambayeni sauran bayanin jiya ba." Ta d'an hade girarta kad'an. "Wane bayanin?" "Bayanin koni WAYE mana, ko ba kya sonp kiji abinda nace wa baffa ya bani aurenki? ko kuma ki san wane irin miji zaki aura?" "Na san zaka fad'a min ai." "Ta yaya kika sani? saboda kin san ina sonki?" Kamar baza ta amsa ba sai kuma tace. "Mhmmm.." "Toh mhmm kema kina sona?" Ta sake yin shiru. "Ya Allah! Sa'adha kin mayar dani d'an jarida sai tambaya nake tayi akai-akai." "Toh ina jinka, ka fad'a min." "Shikenan mu ajiye wannan a gefe zamu dawo kansa daga baya, bari in fara baki tarihin mijinki tukunna. Sunana Imran kamar yadda kika sani, amma full name d'in Imran Siddiq, ni d'an garin bauchi ne iyayena sun mutu tun ina yaro saboda haka a hannun k'annin mahaifina na tashi, A bauchi nayi duk karatuna da komai, sai daga baya na samu aiki anan garinku. Aiki a company ORZ dake kula da harkokin talla na media platforms, shi yasa nake zaune ni kad'ai ba tare da kowa ba, don dukkan 'yan uwana suna can." This is it! just simple kamar yadda suka tsara a farko zuwansa, haka normal rayuwar matashi irinsa ya kamata ta kasance. Jin tayi shiru yasa ya cigaba da cewa. "Tun daga bauchi 'yan uwana suka zo nema min aurenki kwanansu biyu a garin nan, kuma a duk kwanakin suna ta yabawa da irin tarbiyyar gidanku, sunce baffa mutumin kirki ne zanyi sa'ar auren 'yarsa." Ta cigaba da nannad'e rigar filon a hannunta. "Tun da suka koma kuma ake ta min waya daga gida, masu son ganinki na da yawa Sa'adha, basu san cewa ni kaina an hana ni zuwa ba." Ya k'arashe zancen a hankali yana jin nauyin kalamansa na baya, tun farkon sanda ya fara wannan rayuwar, yana tafiya ne akan wannan tsarin, wannan k'aryar...amma tunda yake bai tab'a jin komai ba sai a yanzu da yake gayawa Sa'adha. Saboda daga yanayin bugun zuciyarta da yake ji ta cikin wayar, ya san ta yarda dashi ne, ta yarda da duk abinda ya fito daga bakinsa. Amma duk da haka yaji yana son sanin me take tunani a yanzu, meke faruwa a cikin kanta, ya rufe idonsa da k'arfi amma ya kasa jin komai, zuciyarta tayi masa nisan da ba zai iya reaching ba. Saboda haka yayi shiru shima yana sauraren fitar numfashinta a hankali da kuma bugun zuciyarta. kusan minti biyu kafin ya kira sunanta, ga mamakinsa sai yaji ta amsa nan take. "Zan iya ganinki gobe?" "Me za'a yi?" Kamar a lokutan baya, tana iya jiyo sautin murmushinsa daga d'aya b'angaren kafin yace. "So nake inzo inyi hira da iyalina." Kalmar tayi mata nauyi da kuma dad'i a lokaci daya, taji son da take yi masa ya k'aru a cikin zuciyarta, kamar a d'ebo yayi ne a k'ara akan wutar dake ci. A hankali ta fad'i abinda take fad'a a kodayaushe. "May be da yamma?" "Baki tabbatar ba?" Ta rufe idonta sannan tace. "Na tabbatar Allah ya kaimu." "Ameen Noory!" Jin wani sabon sunan yasa ta bud'e idanunta kad'an sannan ta lumshe su. Noory yau kuma? Sunan ya mata dad'i sosai. ****** Har k'arfe hud'u na yamma Imran na jin kuzari a jikinsa da wani irin annashuwa daya manta lokaci na k'arshe da yaji haka. Wayar da yayi da sa'adha d'azu k'arya ce, haka ma duk maganganun daya gaya mata, amma the fact that ta yarda dashi kuma a cikin duniyarta babu tunanin cewa k'aryar ne shi yake masa dad'i, yana son ya ture gaskiyar shima ya tafi da tunaninsa a hakan, ba don komai sai saboda yana jin dad'in abinda yake yi, yana jin dad'in duk wani moment d'in da yake tare da ita. Duk cewa da yana tsoron kar biyewa son zuciyarsa ya jawo musu wata matsalar kamar yadda a baya ya jawo wadda suke cikinta a yanzu. Amma wannan tunanin baya tab'a zuwa duk sanda yake tare da ita. "Uhmm....Siddiq are you with us?" Muryar Ibrahim ta shigo cikin tunaninsa, ya d'ago da sauri ya kalle su, sai yanzu ya tuna suna zaune a cikin office d'insa su biyar suna tattaunawa akan advert d'in sabon company da suka yi meeting dasu d'azu, wanda har sunyi signing contract da komai yanzu zasu fara shirya yadda za'a baiyana wa al'umma kayaiyakinsu ne, wato irin tallan da za'a yiwa jama'a. "I'm sorry dan Allah, wani abu ne ya d'an shiga kaina." Ya karb'i file d'in da yake mik'o masa ya shiga karantawa, sai da ya gama tsaf! sannan ya d'ago ya kalle su yace. "I don't think i like this idea, can't you come up with anything that will leave an immediate and strong impression?" Wani usman ya d'an duba paper gabansa sannan yace. "We just thought since the products are fibres, a simple advert will do." Imran ya girgiza kansa. "You should'nt have thought that, advert komai k'ank'artarsa komai rashin amfanin kayan ga al'umma, hakk'in mune mu tallata shi in a way da zamu iya karkata tunanin mutane daga kan neccesssities d'insu zuwa shi. Saboda haka zuwa gobe, just keep thinking about something any idea that wiil catch the mind of viewers, prepare something more spectacular please. Usman after that, I think you can work with Director Phillps to come up with a way to convey it. Ibrahim you will be in charge of the copy writing, and Maryam... Ya juya ya kalleta, tana zaune a gefensa cikin shigarta ta matsatstsun kaya kamar kullum d'an karamin mayafinta na reto a kafad'a. Ba abinda  ya sashi tsayawa da maganar kenan ba, hannayenta, hannayenta da suka sha wani had'add'en kunshi daya zauna d'as akan farar fatarta. Bai san ya akayi tun farko ya bari ta fahimci cewa yana son k'unshi ba, shi yasa duk sanda ta san zasu had'u take zuwa tayi don ta san ko ba komai zata samu alfarmar ya saurareta. Ya had'iye wani abu a mak'ogwaronsa kafin ya cigaba. "...make a list of all the client that we will work with for the next quarter by tomorrow." Ya juya ya kalli wata dattijuwar mata da kowa a companyn ke kira da Aunty Fati, mace ce mai tsananin kirki da sanin hakk'in al'umma, shi kansa yana ganin girmanta sosai saboda yadda ta maidashi kamar d'anta, don  babban d'anta ma Abdullahi ya girme shi kuma ya sanshi duk sanda suka had'u suna gaisawa sosai. "Aunty can you make me an appointment with Dr Turaki? I need to see him tomorrow." Tayi murmushi kafin tace. "Insha Allah Imran." "Okay, we can call it a day." Da haka kowa ya d'auki takardunsa suka mik'e, sai dai kafin Aunty fati ta kai ga fita, Imran ya tuna da abinda jaamil ya gaya masa jiya. "Abu biyu ne da suka rage mana yanzu, wai akwai kaya da ake kaiwa gidansu yarinyar sunansa lefe, ni ban san ta yaya zamu had'a su ba. Da kuma zancen gida, dole ne sai ka tashi daga gidan nan, saboda yayi kusa daga gidansu kuma ance min suna kawo kayan gida daga wajensu suma. Saboda haka inda zaka nema bana tunanin sai ka sayi komai. Tuno hakan yasa yayi saurin tsaida ita, ta dawo ta zauna a kujerar dake gefensa. "Aunty Faty wani abu ne ya taso min wallahi, kin san families d'ina ba'a nan kusa suke ba kamar yadda na fada muku..." Ya d'an yi shiru yana juya abinda zai fad'a, amma murmushin fuskarta ya sashi cigaba da magana. "...Toh aure na ne ya tashi, kuma bana son har sai na tafi can kafin a had'a lefe, shine nake so in tambaye ki ko zaki taimaka..." "Kar ka kuskura ka k'arasa Imran, in har kace taimako kenan baka yin uwar dani kamar yadda ni na d'auke ka, Alhmdlilahi, wallahi naji dad'in wannan zancen sosai, dama na dad'e ina maka sha'awar aure a wannan lokacin, don shine cikar mutuncin kowanne mutumin arziki. Zancen lefe kuma kar ka sami damuwa, insha Allahu za'a had'a ba da wata matsala ba, dana koma gida zan samu 'yan uwana, mu zauna muyi lissafin yadda muka had'a na Abdullahi, zaka ji duk wani bayani daga baya. Nayi murna sosai wallahi, Allah ya tabbatar mana ya sanya alkhairinsa a cikin lamarin. Allah yasa kuma ta zama alkhairi a gare ka da kuma 'ya'yan da zaku samu a gaba." ******* A cikin sati uku, kusan komai ya koma daidai a rayuwar Nanne, sunyi jarabawar first term sun k'are har an bada hutu na wata d'aya. Hutun data san ita ta gama zuwa makaranta kenan, don baza ta koma second term ba sai lokacin Waec da Neco kawai kamar yadda baffa yace. Shirye-shirye ya kankama sosai daga kowanne b'angare, don hatta iyayen Imran maza sun kawo lefe akwati goma sha uku, Sannan ya had'a ta da'yan uwansa a waya sun gaisa. Daga b'angaren inna kusan ba abinda bata tanada ba na harkar kayan d'akinta, ko baffa abinda ya bayar kad'an ne inna tace ta yafe masa tunda bai dad'e da bikin mata hud'u ba. A cikin wannan lokacin ma Nuratu tazo da nata gudunmawar ita da 'yan uwanta, a sannan ne kuma Nanne take jin cewa shima Nuran da tayi mata zancensa an kusa bikinsa a lokacin itace bata sani ba a lokacin. Ranta yayi fari kal! da tunanin shawararta Nanne ta karb'a ta yarda da aure a yanzu, musamman kafin su tafi da Imran yazo suka gaisa, sai farin cikinta ya k'aru, tana ganin ba k'aramar sa'a Nanne tayi na samun miji irinsa ba. A kullum kuma alak'ar dake tsakanin Nanne da Imran k'aruwa take, a yanzu ta saba dashi sosai don har tana sakewa tayi masa hira a waya ko kuma in yazo. Duk da cewar wayar tasu tafi yawa, don a k'aida ne kullum zai kirata sau uku, da safe in ta tashi, da rana in yana office, da kuma da daddare in zasu kwanta. Da gaske ne ya dad'a koya mata yadda zata so shi, don ko kad'an yanzu ba alamun wannan damuwar data shiga kwanaki sanda baffa yace aure zai mata, ta daina tunanin duk wasu abubuwa da zasu faru nan gaba, burinta kawai a kullum Imran ya kirata ya kara tuna mata cewa ta kusa zama tasa, duniyar gaba da take hangowa mai tsananin kyau ce tunda tana tare dashi. Don hatta karatun da take tunanin zata cigaba a yanzu ji take yi meye ma amfaninsa in dai Imran yana cikin duniyarta. Kusan komai ya gama kammala a satin da aka tsayar na auren. Imran ya bada muk'ullin gida a can wata unguwa dake nesa dasu. Gini ne na zamani mai kyau sosai, d'an moderate house mai d'auke da falo biyu da three bedroms, dining da kitchen da kuma toilets uku. Ba wai tamfatsetsen gida bane amma yadda ya zama well furnished ya k'ayatar da kowa akayi ta santinsa. A yadda inna ta tsara, babu wata hayaniyar biki da za'ayi. Kamu da walima ne za'a fara ranar juma'a anan cikin gidan nasu, sai washegari asabar ayi d'aurin aure da yini. Da yamma kuma akai amarya. Nanne ta gaiyaci kusan duk 'yan ajinsu na islamiyya da kuma boko, don har islamiyar data bari sai da taje ta kai musu cards d'in, kowa yayi ta mamakin yadda basu tab'a jin zancen ba sai kati kawai suka gani, don lokacin da ta gayawa Aminah komai, sai da ta gargad'e ta kar ta fad'awa mutane saboda gudun surutu. 'Yan islamiyya kuma ba wajen wanda zasu ji tunda Rahma ba fad'a zata yi ba, kuma ko wasu daga 'yan layinsu ma basu ji ba sai da komai ya matso kusa. Amma duk da haka sai da zance ya fara yawo a makarantar bokonsu cewa auren kud'i zata yi, wai irinsu dama basa gama makaranta suke samun Alhazan birni su aure su. Sai dai da yake shine bikin 'yar Ajin na farko da zasu fara, sai d'oki ya hana wannan gulmar tasiri, kowa ya shiga fafutukar siyan an anko wanda Amina ta fitar da kuma shirye-shirye. Sanda Nanne taje ita da Rahma suka kaiwa su Malam Murtala katin d'aurin aure, ba karamin farin ciki da murna suka nuna ba, ta san tunaninsu iri d'aya ne da malaman da suka cewa Baffa aljanu na shirin shigarta kuma aure ne kawai abinda zai iya kore su. A yanzu da sune silar farin cikinta bata sani ba gode musu zata yi sab'anin a farko da take ji sun juya duniyarta upside down? Ranar laraba da daddare bayan ta wanke lallen da aka tsantsara mata, tayi wanka sannan ta saka kayan bacci, da kyar ma ta iya samun wanda zata saka don inna ta riga ta gama had'a dukkanin kayanta da zata tafi dasu sauran kuma duk ta rabar, harda wad'anda take tsananin so ba damar tace a bar mata. Ta kwanta a kan gado cike da gajiya, daga nan tana iya jiyo hayaniyar 'yan falo wanda ke cike taf! ana musu nasu lallen. Idan wani ya shigo cikin ba zaice dama bayan bikinsu ya Aisha 'yan niger sun koma ba, don wannan karon harda k'arin wasu aka samu tunda bikin na inna ne. Banbancin kawai shine na 'yan uwansu mama halime, mama rabi da kuma hajiya Babba da basa nan wannan karon. Duk inda ta juya taga mutane sai ta kasa yarda cewa wai bikinta za'ayi, wai duk sunzo ne duk saboda ita kawai... Wayar inna a kusa da ita tayi k'ara, Amina ce, ta d'aga ta kara a kunnenta. "Toh Wallahi dole jibi sai mun fita da wuri, don su Aysha mahmoud naji duk sunce wajen suma Zarah zasu je kwalliya, kuma kin san ita first come first serve take yi, zata iya miki ni tawa tace sai ta musu tukunna ta b'ata mana tsari." "Toh Allah ya kaimu sai mu tafi tun sha d'aya, me ake ciki da masu ashoken?" "Gobe zanje in karb'o insha Allah, don sun kirani sunce sun gama, sai dai mai beads ne zai b'ata min rai da alama, don jiya sai masifa yake wai an bashi a k'urarren lokaci." "Kiji sai kace ba biyansa za'ayi ba, shi kad'ai ne ya iya, in kinje bai gama ba ki bar masa kayansa aje wani wajen, na san ko ya aka k'ara musu kud'i akai da gudu zasu yi wallahi." "Nima tunanin da nake yi kenan, yawwa ki cewa Rahma mu had'u goben wajen sha biyu, tace zata kai kayanta itama a mata beads d'in." "Toh shikenan, in mun fito saloon sai ku had'u kawai, don wajen goma dama nake tunanin mu fita." "Amma dai Sa'adha ba mai zaki sawa kanki ba koh?" "Wallahi da nayi niyya amma Aunty nafisa ta hanani, steaming kawai zanyi." "Ai gwara, in ba haka ba b'ata gashinki zaki yi, duk laushinsa me zaki k'ara akai." "Toh kar dai ki manta gobe duk ki d'ebo kayanki, dazu na k'ara kiran umma (maman Aminar) tace da kwana biyu da uku ai duk d'aya ne." "Eh nima dazu ta fad'a min, zan d'uro akwatuna na a motar Sani, da daddare ya kawo min in na gama zagayena a gari." "Toh shikenan sai goben." Tana kashe wayar Aunty maryama ta shigo da kofi a hannu, Nanne taji ranta ya b'aci a lokaci guda, d'azu har tana murna cewa sun manta ashe yana tafe, kusan sati biyu kenan ana d'ura mata jik'e-jik'en da ita ba amfaninsu take gani ba. Ance na gyaran jiki ne, bayan na gidan matar da kusan satinta biyu tana zuwa sai jiya ta sallameta, wai don ma za'ayi k'unshi yau ne, da ta tabbata sai yau d'in ma taje. "Wata yamutsa fuskar ki fa baza ta sa in fasa ba wallahi..." Aunty maryaman ta fad'a bayan ta tsaya a jikin gadon, ta mik'a mata. "...ban kofin yanzun nan." Nanne ta had'e rai sannan ta k'arb'a ta rufe idonta, ta had'iye shi a lokaci guda. "Kya gama had'e ranki ne, Allah ya kaimu ranar da zaki zo da kanki ki tambayeni, anan zaki ga nawa had'e ran nima." Bayan fitar ta, ta jawo ragowar katinan bikin dake kan bedside drawer. Sau ba adadi kenan take karantawa, amma har yanzu gani take kamar ba nata bane, kamar ba sunanta ne a jiki ba. Idonta ya kai kan sunasa, wanda aka rubuta da italian font mai lankwasar nan. Imran Siddiq! Me yasa ne shi komai nasa ya had'u? Wayar inna ta sake k'ara a kusa da ita, ba sai ta duba ba, tariga ta san ko waye, don a lokacin k'arfe goma ne daidai kuma ringtone d'in ma daban yake. "Assalamu Alaikum." Tayi murmishi sosai, a k'aidar waya wanda ya d'auka shi zaiyi sallama amma shi kullum ita ke amsa masa sallama, tana d'auka ya sani. "Wa'alaikum Salam." Muryarsa can k'asa-k'asa kamar mai jin bacci yace. "Sweetheart anyi k'unshin?" Murmushinta ya k'aru sanda ta d'go da hannayenta tana kallo, daga nan ta san abinda zai zama topic d'in wayar! ●﹏● I'm sorry for all d turanci in dix shapta, na san labarin nan na hausa ne but nayi editing d'in wani labarina ne na turanci, toh sai hausar take ta had'e min... I'm so sorry... kunjiii...... Hhhha! forget dat ni ba Imran bace.😁😁 **** WAYE SHI? AYSHA SHAFI'EE 32 Da fatan duk kun shirya don yau biki zamu yi, zan gaya muku komai kamar kuna wajen akayi.😀 (☆_☆) Iye di dide Ayye yaraye nanaye 'yanmata... 'Yan matan yanzu sun saka kallabi ga coge Hannayensu d'auke da zobe, 'yan gayu! Iye di dide Ayye yaraye nanaye 'yanmata... Amarsu ta ango, ki kika ce kina so ungo Jeki ki bashi tutar k'auna, 'yar gata! "...Dan Allah jama'a a marmatsa daga hanya don Allah, amarya da k'awayenta sun shirya...hanyar da zasu shigo suke nema...masu d'aukar hoto da video dan Allah ku matsa gefe, amarya zata shigo." Muryar Mc ta karad'e wajen yana yi yana kallon hanyar gate d'in gidan wadda ta cunkushe da tarin mutane jin ance Amarya ta k'araso. Daga gabansu train d'in k'awayen amarya ne wanda suka yi ankon wani dark yellow material sun jeru sai faman selfie suke yi wasu kuma na bin kid'an  suna rawar, wajen ya cakud'e da hayaniya sai ka d'aga murya zaka ji na kusa da kai tukunna. Nanne na zaune a cikin wata hadadd'iyar Hyundai da Imran ya aiko aka d'aukota daga wajen kwalliya, tana ciki sai kallon mutane take tana murmushi. Wani material ne mai kyau pitch da red na fitted gown a jikinta, daurin head d'in kanta mai kyau dark red yasha duwatsu, sannan kwalliyarta light ce sosai, ba blush, ba fake lashes sannan ba heavy janbaki, lips d'inta light pink ne sosai sai kyallin gloss kawai da suke, sannan eyakeup dinta ma light ne, kohl d'in kawai aka sa suka fito. Muryar Mc ta cigaba da karad'e wajen. "Dan Allah jama'a a bawa amarya da k'awayenta hanya, ance mutanen Niger ne a wajen, dan Allah a matsa ba cukwi ake rabawa ba...amarya ce zata shigo ciki ku ganta.." Abin ya bawa Nanne dariya, Bata ga Rahma ba amma ta hango Aminah nata k'ok'arin sake jera layin 'yan ankon wanda yawanci 'yan makarantar bokonsu ne, itama cikin shigar material d'in amma harda head, wani dark colour mai kama da golden, tayi kyau sosai musamman beads d'in data sha wahala kafin a had'a musu shi ya k'ara haskata, Ta kalli na wuyanta, yayi kyau shima dark red don tun a wajen kwalliyar ake tambayarsu inda aka had'a musu. Tana d'ago da kanta taga Anty maryama tazo gaban windon tana kwankwasa screen. "Bana son rashin mutuncinki Nanne, ya ana ta jiranki zaki yi zamanki kina kallon mutane?" Ta bud'e kofar da sauri tana dariya. "Toh Aunty gani nayi duk an cakude hanyar...." Kafin ta karasa muryarta ta b'ata a cikin d'imbin hayaniyar mutanen da suka matso da niyyar fara d'aukan hoto. A lokacin Zainab ('yar autar mama halime) ta k'araso ta cikin mutane ta miko wata sabuwar atamfa mai kyau Ash da red. itama tayi kyau sosai kayanta light pink harda head, sai kallon Nanne take tana murmushi, itama tayi ta washe mata baki tunda ta san ba magana zata yi ba, ita haka Allah yayi ta kafin kaji muryarta da wuya. "Yawwa Zainab, rik'e min d'aya kiga..." Ta ware zani d'aya ta shiga d'aura mata a k'ugunta. "Kayan meye kuma wannan?" "Kayan kamu ne...sai anyi tukunna zaki cire su..." Ta karb'i d'aya zanin ta yafa mata tun daga kan gwaggwaron har ya rufe fuskarta lokacin da Aunty Nafisa ke rabawa Aminah da wasu 'yan mata uku k'ananan kaskon turaren wuta dake hayak'i. Nanne ta jawo hannun Aminah bayan ta k'arb'a tace. "Gaskiya a canja wak'ar nan, ni ba zan shiga da ita ba." "...Aikuwa ba ta yadda zan ga Mc anan? kin san dai ba zan kutsa in shiga..." Kafin ta rufe baki, kid'an ya canja, nan take 'yanmatan suka fara bin takun wak'ar... Ga turare k'amshi..k'amshinsa yana gun amare. Ga turare... Cikin takun steps mai kyau aka shiga da Nanne filin harabar gidansu a matsayin amarya, mutane sai cincirindon d'aukan hoto suke duk da fuskarta da kayanta na rufe. aka kaita can gefe inda aka tanada wata 'yar karamar rumfa mai kujera d'aya. Anan ta zauna har Inna da danginta tsofaffi suka k'araso, aka kuma nemi wasu daga cikin dangin ango da suka zama abin kallo kafin zuwan amarya suka zo wajen suma. Abin daya d'auki hankalin mutane dasu shine yadda dukkaninsu suke farare tas! kuma kyawawa, daga tsofaffinsu har yaransu kuwa. Wata tsohuwa da Nanne ta gane a lokacin bikin su ya Aisha tayi ta rangad'a guda mai zak'i, sauran tsofaffin kuma na tsokanarta wai yau ranarsu ce, sai sun ga dama ma zasu bawa angon ita. Inna ta bud'e sabon turaren a kwalinsa ta shiga fesawa Nanne tana ta zubo Addu'o'inta, wasu irin adduo'i masu kashe jiki wanda suka sata kuka wiwi sai dai kyar su Aunty Nafisa suka sa tayi shiru, suna fad'in zata b'ata kwalliyarta, ga 'yan biki na jiranta a waje. Bayan an gama kamun ne, aka cire mata atamfar sannan 'yan matan suka sake jeruwa don raka ta main rumfar da zata zauna, tana fitowa wajen ya d'auka da wak'ar 'Duru' ta kowanne b'angare. See the love i dey see for ur eyes.. I love you baby i no talk am twice Your beauty making me do realize.. Say nepa don bring light.. So you must marry mee... Eh eh... You go love me you go killing me baby.. you go follow me...eh you are my remedy you're my melody.. Eh baby na harmony you go give me Baby palanga... i'll show you love dat you never seen....! Tun Mc na magana akan d'aukar hoto har ya hak'ura yayi shiru. don kowa son d'aukan hoton yake saboda yadda 'yar k'aramar amaryar ta burge kowa cikin shigarta da kwalliyarta mai kyau. Aka raba abinci mai dad'i cikin nutsuwa wanda hakan ya burge kowa, sannan kuma aka shiga rabon souveneirs a jaka ga duk wanda yazo zai tafi. Duk cikin wannan hargitsin idon Nanne na kan mutanen da akace 'yan uwan mijinta ne, tun bayan da akayi kamu, basu kara tasowa ba sai da aka kira su d'aukan hoto, sannan basu sake ba balle har su d'an shiga cikin 'yan uwanta, iyaka wanda yayi musu magana kawai su bishi da murmushi. Gasu farare tas! dasu kamar wani jinsi na shuwa Arab, sannan ta lura yawanci attention d'in mutane yana kansu. "'Yan uwan mijinki miskilaine, amma fa akwai kyau kamar shi, zaki haifo beauties in gaya miki." Aminah ta rad'a mata a kunne, ta kai mata duka sanda tawagarsu Inna ke shigowa rumfar don d'aukan hoto suma. K'arfe bakwai daidai Mc ya fara shelar cewa Ango da tawagar abokansa sun k'araso. Nanne taji wani irin farin ciki ya kamata ashe rok'on da tayi ta masa yana cewa ba lallai yazo ba dama duk jinta kawai yake kenan, ko d'azu a wajen kwalliya daya kirata yawo yai ta mata da hankali da zancen zai zo ko ba zai zo ba. A lokacin mutane sun fara raguwa, amma daga jin ance Ango yazo, sai taga kamar dawo dasu akayi, saboda yadda kowa yake mik'a wuya yana jiran yaga wane ne Angon, hatta k'awayenta na makaranta da 'yan islamiyya ta lura duk hankalinsu ya tafi wajen ganin adadin girman Alhajin da suke zaton ta aura. Mc yace k'awaye biyu su raka amarya ta taho da Angonta, sai a lokacin taga Rahma da kuma wata Sadiya Awwal, don Aminah ta tafi can fafutukar karb'owa 'yan ajinsu jakar souveneirs. A lokacin da suka k'arasa bakin gate d'in ta hango Imran a tsakiyar abokansa, ji tayi kamar zata narke a inda take tsaye saboda tsabar kyan da yayi, yasa kaya shade d'in brown da babbar riga wadda akayi mata aikin da darkbrown zare, sannan hular kansa ma darkbrown ce, yayi wani irin fresh yayi kyau kamar a cikin zane yake, murmushin fuskarsa ya k'ara dulmiyar da ita, taji kamar ta juya baya ne ta hango wata amaryar na tahowa wajensa, don ji take yi kamar ba itace dashi ba. he's too good for her! "Ya salam!... kinyi kyau sosai Sa'adha i can't breath." Ya rad'a a daidai kunnenta sanda ya k'araso gabanta, tayi saurin juyar da fuskarta kan hasken flashers d'in dake ta dallare su. Ta gefen idonta tana iya hango bakin Sadiya Awwal a bud'e, idanunta na nuna tsananin mamaki, kamar taga wani abu ne da a zahiri ba zai tab'a zama gaskiya, to ba ita kad'ai ba kusan dukkanin mutanen ciki da kuma sauran k'awayenta haka suka cika da tsantsar mamakin ganin had'uwar Imran. A lokacin kowa ya san hotonan da aka d'auka a baya ba komai bane, don har Mc ya fara shirin yace Amarya da Ango su shigo tsakiyar fili, yaga abin ba zai yiwu ba ya samu kujera kawai ya zauna, wajen ya zama ba abinda akeyi sai d'aukan hoto da kuma wasu 'yan mata dake rawa. A sannan ne ma yayyenta maza gabad'aya suka zo, bata san wa ya tsara hakan ba amma abin ya burgeta, suma su san ana biki a gidansu ba ace iya d'aurin Aure kawai zasu ba, Sadiq yayi ta tsokanarta dashi da tarin nasa gaiyar na 'yan ajinsu maza wato 'yan B class, daga baya kuma suka koma kan 'yan matan ajin nasu wajen ya koma musu kamar School party. Akayi ta hotuna sannan aka kawo musu abinci tare da sauran abokan Imran, filin ya koma na 'yan samari da k'awayenta 'yanmata kawai. Kusan duk mutanen da suka d'auki hoton Amarya da Ango sun d'auka ne Imran baya kallon camera, idonsa da hankalinsa gaba daya na kan 'yar Amaryasa dake ta murmushi kamar ba ita ce tasha kuka d'azu ba. Har abokansa data fahimci 'yan wajen aikinsu na tayi masa tsiya wai 'Gobe ne fa' Sai wajen goma sannan tawagar Ango suka bar wajen kasancewar a lokacin kusan kowa ya tafi. Aka bar Nanne da sauran 'yan gidan nata cigaba da d'aukan hoto, musamman 'yan niger wanda ak'alla kowaccensu tayi fiye da kala goma, sai da mai hoton yaga abin nasu ba zai k'are ba ma sannan ya tattara ya tafi shima. "Na shiga uku, sallah Rahma ko maghriba fa banyi ba." Nanne ta fad'a lokacin da rumfar ta zama daga ita sai su Rahman kawai. "Wallahi muma bamu yi ba yanzu zamu je mu had'a da isha, sai dai Allah ya yafe mana." Aminah ta kalleta tace. "Ki zauna in samo ruwa da hijabi kawai muyi anan, don wallahi kina shiga ciki ba samu zaki yi su barki ba, mutane ne kamar ba wanda ya tafi ciki aka koma." Bayan an k'are duk wata hayaniya ta daren, Nanne ta samu tayi wanka sannan ta lalubi gadonta, wanda inna ta hana kowa kwanciya a d'akin sai ita da Amina da Rahma kawai. A lokacin k'arfe biyu saura na dare, amma ko'ina a gidan da hayaniya don da yawa basu da alamar yin bacci. Tana kwanciya akan gadon taji kamar an dake ta da guduma a tsakiyar kanta, shikenan fa yanzu wannan ne daren ta na k'arshe a gidan nan, darenta na k'arshe a d'akinsu sannan darenta na k'arshe akan gadonta. Daga gobe rayuwarta zata canja, komai zai canja game da ita, za'a d'aura mata aure da wani ta tafi ta bar kowa data sani, ta bar Innarta ta tafi wani gidan daban ta fara rayuwa tare dashi, shi kad'ai kawai a gida d'aya...ta yaya zata fara hakan? anya zata iya kuwa? Ita fa duk bata hango wannan ba sai yanzu, yanzun da taga cewa da gaske ne fa, da gaske gobe za'a sallamata. wani irin tsoro ya kamata, ta tashi zaune ta rungume filon da k'arfi sanda hawaye ya cika idonta. "Me ya faru?" Rahma da ta fito daga band'aki da brush a hannu ta tambaya tana kallonta, hawayen daya taru ya gangaro kan kumatunta masu d'umi dasu. Aminah ta juyo daga lalubo kayan baccinta a cikin akwati tace. "Me kuwa ya faru? taraddadin barin gida ne ya fara kamata...sai hak'uri Sa'adha, wani kukan ma ai sai gobe..!" Ta fad'a da murmushinta, wanda hakan yasa hawayenta k'aruwa. Rahma ta zauna a gefenta. "Toh meye abin kuka Nanne, aure ai abin farinciki ne da godiyar Allah, don Allah kar kiyi kuka, keda ba nisa zaki yi ba a garin nan fa zaki zauna, duk sanda kike so zamu zo kuma shima na san zai dinga kawo ki kiga inna.... Maimakon kalaman su kwantar da hankalinta sai taji kukan ma ya sake k'aruwa, ta kifa kanta akan gadon ta shiga rera shi kuwa, tana jin wani k'ullutun abu a k'irjinta. Tun Aminah na tsokanarta har taga dai abin da gaske ne ta sauko ta fara bata hak'uri itama. ****** A cikin wannan daren mai d'aukar hoton nan ya shiga aikin editing pictures d'in daya d'auka shi da yaransa, saboda kar aiki ya musu yawa don gobe ma zai je yayi na d'aurin aure da yini kuma a satin suna da biki uku da zasu je. Suna ta editing d'in suna kuma printing wasu har wajen k'arfe uku na dare, a sannan ne suka ci karo da wani abu mai tsananin mamaki daya d'aure musu kai. Wani abu da kowannensu ya kasa yarda cewa daidai idonsa ke gane masa, wani abu da yasa kusan dukkaninsu suka cika da tsantsar tsoro. Gabad'aya hotonan da suka d'auka na mutanen da akace dangin ango ne, babu abinda ya fito a cikinsu sai Amaryar kawai, amma dukkaninsu...dukkaninsu yadda suka tsaya a kowanne gefen babu siffarsu, sai siffar Amaryar kawai da kuma mutanen can baya. Kuma ga alamun cewa da mutane a kusa da ita daga yanayin tsaiwarta amma kuma babu kowa. Suka binciko gabad'aya hotonan da suka d'auka, kowanne daidai yake sai iya na dangin angon da akace ne kawai. Wanda a yanzu, babu su ba alamarsu! ●﹏● WAYE SHI? AYSHA SHAFI'EE 33 (☆_☆) Sautin kid'an algaita, kid'an marok'a, hayaniya da turereniyar mutane a layin gidan Alhaji Mustapha Bashir shi zai tabbatar maka cewa ba'a dad'e da d'aura auren ba. Auren... IMRAN SIDDIQ DA SA'DAH MUSTAPHA Ko ina ka duba mutane ne cikin kaya masu kyau anata d'aukan hotona da kuma k'ok'arin kaiwa wajen ango don taya shi murna. Imran yayi kyau cikin fararen kaya, hula kalar Ash wadda ta dace da aikin kayansa, sai faman murmushi yake yana gaisawa da kuma d'aukan hoto da mutanen da yawanci ba saninsu yayi ba. Daga cikin gidan kuma mutane ne koina fal! anata hidima da hayaniya, masu rabon abinci nayi, masu rawar kid'an kwarya nayi, masu hira had'e da gud'a nayi, kowa nata farin ciki da annashushuwa sai dai duk wannan abin da ake, Nanne na can d'akin Aunty amrya inda su Aunty maryama suka tsaya akanta da abinci, don tun jiya ba wani abin kirki da taci sai kame-kame kawai. Tana cin abincin tana share hawaye kamar k'aramar yarinya, jikinta wani lallausan lace ne colour maroon and pitch da akayi masa d'inki mai kyau, adon rigar yasha stones sannan skirt din 8 pieces ne mai bud'ewa sosai. Aunty Nafisa ta shigo cikin d'akin da kwalliyarta itama. "Akace kuna d'akin mama halime, can naje ban ganku ba." "Ai can ta tafi ita da Aminah ta b'oye d'azu, yanzun nan muka kawo ta nan, gata nan tana ci kamar guba ake bata." Nanne ta k'are hade rai jin haka, ita fa yunwar ce kwata-kwata bata jinta, saboda gabad'aya jikinta dama tunaninta wani iri take jinsu kamar ba'a jikinta suke, ga kuma fad'an Aunty maryama da tun safe take binta dashi, ita bata tab'a ma ganin amaryar da akewa fad'a ranar bikinta ba sai ita. "Idan ta gama, tazo falon inna babarta da 'yan uwanta sun zo." Nanne ta had'iye lomar bakinta jin haka, a d'an tsukin nan taga Nuratu kusan sau hud:u kenan, wanda a da sai ta shafe kusan shekara biyu bata ganta ba, hakan na nufin cewa da gaske rayuwarta ta canja kenan, ko kuma tana shirin canjawar don bata sani ba ko a yanzu an d'aura au.... Aaaayiryiryiryiri....! Wata tsohowa ta bankad'o labulen d'akin ta shigo ita da wasu matan. "Aure ya d'auru...an d'aura shi yanzu yanzun nan....Sadakinki dubu d'ari 'yan nan...kin zama matar aure, Rana bata k'arya, girma ya hau kanki sai fatan... Nanne taji kamar a daidai lokacin nan matar ta d'auko wani k'aton dutse tad'ora mata a kai, shikenan yanzu ta zama matar AURE? kuma matar Imran? duk mutanen nan sun shaida kuma ba wanda ya isa ya kwance? "....Allah ya tabbatar da alkhairinsa, Allah yasa bad'i war haka muzo suna...." Hayaniyar matan ya cika kanta, sai kawai ta ajiye plate d'in hannunta ta koma ta duk'unk'une akan gadon Aunty Amarya, ta cusa kanta tsakanin cinyoyinta sannan a hankali hawaye masu d'umi suka shiga bin kumatunta. "Kuka ba naki bane 'yar nan, ke da Allah ya kashe ya baki zankadeden saurayi kamar a manna a goshi...Tashi zaki yi kiyi sallah ki godewa Allah...." Mutane suka cigaba k'aruwa a d'akin, kowa sai faman shigowa yake yana 'Nanne Allah ya sanya alkhairi' Tun tana jinsu har tunaninta ya zame daga d'akin ya tafi yadda zata iya zuk'e kowa na gidan ta mayar dashi inda ya fito, bata son ganin kowa a yanzu, so take kawai a barta daga ita sai Inna a d'akinsu ko ta samu ta rok'e ta cewa a bar zancen tafiya da ita yau, a bari sai zuwa nan da sati d'aya watak'ila kafin nan ta shirya tukunna. Kusan minti talatin sannan Nuratu da tawagar 'yan uwanta su shigo d'akin, shima da kyar don sunga Nannen bata da niyyar fitowa ne. Da kyar ta iya sakewa dasu don Nuratun ta dage sai bayaninsu take mata wanda ita ba ganewa take ba. "Nanne mun kawo kaya suna d'akin Inna, akwai standing fan da kayan kitchen set wajen goma sannan..." Da sauri ta katse ta. "Toh Addano madallah." Bata san me yasa in suka kawo abu sai tayi mata bayanin komai dalla-dalla ba, ko gani take su innan zasu rik'e ne ko me? Karfe sha d'aya da rabi, Aunty Maryama ta janyeta daga d'akin, zuwa can d'akin su Mama Azumi dake k'asa inda ba muyane sosai. Ta d'auko mata wata doguwar farar riga ta material daga cikin kayanta, rigar tayi kyau sosai saboda tana da bud'ewar umbrella. "Ga mai kwalliya nan zata gyara miki fuska kisa wannan kayan, Sulaiman  yace zasu taho da angon da abokanansa daga wajen reception su zo nan ayi hotuna." Nanne ta juya ta kalli budurwar dake zaune akan kujera, ta baje kit d'in kwalliyarta, ita sai yanzu ta lura ma da ita tun da suka shigo d'akin. "Bari inje kar su lami su tafi." "Aunty dan Allah ki turo min Aminah." Tana fita ta juyo ta kalli mai kwalliyar tace. "Hoda kawai zaki sa min sai kwalli." ******* Karfe Sha biyu da 'yan mintuna tawagar 'yan d'aurin Aure suka karaso gidan. A lokacin Nanne ta gama shiryawa cikin kayan da suka mutukar karbeta, anyi mata rolling da wani farin mayafi mai taushi a saman rigar, tayi kyau kamar zanata akayi, sai dai duk da adadin kwallin dake idonta, sunyi fulufulu almun kowa ya ganta ya san tasha kuka. A falon baffa kusan kowa ya taru aka yi ta d'aukar hoton, akayi da ita da Imran da inna, sannan akayi su hud'u harda baffa, sannan akayi da inna da su hajiya babba, sannan akayi da 'yan mazan gidan, da 'yanmatan gidan sannan akayi tayi da mutane da yawa. Anan ne ma taga jamila, don taji ance duk amaren sun zo amma ita ko a bikin jiya bata ganta ba, su nafisa da maryam 'ya'yan mama halime kawai ta gani sai Aisha da har kyautar sababbin English wears ta mata kusan akwati guda. Gabad'ayansu su hud'un sun canja daga yadda ta sansu, sunyi wani fresh dasu sun murmure, wani gefen zuciyarta ya hasko mata cewa itama haka zata zama nan da wani lokaci. A sannan ne ta kalli Imran sosai  sanda ya tsugunna shi da abokansa suna yiwa Baffa sallama, tun daya kirata a wajen kwalliyar nan, basu sake waya ba, koda yake ko ya kiratan a jiya ba d'auka zata yi ba, amma yau ma bai nemeta ba, tun safe har kuma aka d'aura auren. Ta kalli kayan jikinsa yayi mutuk'ar kyau fiye ka da jiya, farar colour da Ash, ta dade a rayuwarta bata ga mutumin da komai ke yi masa kyau irinsa ba. Idonta na kansa har sanda shida abokansa suka bar d'akin, abinda kuma ya dad'a bata mamaki shine, ko kad'an bai kalle ta ba, balle taga wannan murmushin nasa. hankalinsa ma gabad'aya baya kanta har suka tafi, kamar ita d'in bata da banbanci a yanzu da sauran mutanen d'akin. Ta ture wani abu mai kama da damuwa dake shirin samun waje a zuciyarta, A lokacin Sadiq ya shigo ya biyo ta cikin mutanen ya kirata, tabi bayansa suka fita. A daidai barandar wajen d'akinsu Sulaiman, Imran na tsaye yana kallonta, shi kad'ai ba tare da abokansa ba, akwai mutane dake ta hadaniyarsu a compound d'in, kwarjininsa ya cika idonta saboda haka ba musu k'afarta ta k'arasa wajensa. "Kinyi kyau sosai Sa'adha, I just want a picture." Kafin ta gama fahimtar maganarsa, ya rik'o tafin hannunta na hagu sannan ya juyar da ita gefe, masu hoton nan na tsaye suka shiga dallara musu. A wannan lokacin Nanne taji d'umin hannunsa kamar yana zuk'e  damuwar dake tare da ita ne, jikinta yayi wani irin sanyi sannan a hankali ya shiga rawa, amma abu d'aya ke yawo a ranta, Me ya sami Imran? tayi zaton zata ga murnarsa fiye da haka, a  yanzu da ta riga ta zama tasa? amma ko murmurshi irin na jiya bata samu ba. ******* Wajen karfe d'aya Addano da 'yan uwanta suka yi sallama suka tafi ganin gidan amarya daga nan kuma zasu wuce adamawa. Yini bikin ya cigaba da wakana, a kowanne lokaci mutane k'ara zuwa suke yi, musamman wad'anda basu samu zuwa jiya ba, k'awayenta ma da d'an yawa sun zo, anata d'aukan hoto da rawar kid'an kwarya, Har saida aka d'ora wata tukunyar abincin a gidan sab'anin da farko da duk kawowa akayi daga wajen da akayi order. Kafin La'asar muryar inna ta dashe saboda yawan magana da amsa gaisuwa. A sannan ne kuma aka fara shirye-shiryen kai amarya. Motocin da Imran ya aiko dasu tun daga farkon layin aka jera su har bakin titi, saboda yawa mutane har canja mota suka dinga yi, sai a shiga wannan a fito. Aka sa Nanne ta sake wani wankan sannan ta shirya cikin wata lallausar lafaya kalar lemon green, jikinta sai tashin sassanyan k'amshi na turarurruka daban-daban yake yi, a lokacin zuciyarta ta riga ta gama tsinkewa, gani take ko ku'da ne ya hau kanta zata iya fashewa da kuka. ******** "....Aljannarki tana wajensa Nanne, shi yasa nake ta maimaita miki biyayya da hak'uri, hak'urinki shi zai sa miki tausayinki a ransa sannan biyayyarki ita zata maye gurbin duk wani abu da zaki nema a wajensa..." Kukanta ya k'aru sosai to the point that duk wata doguwar maganar data biyo bayan nan bata iya jinta, tunaninta ya cakud'e gabad'aya ya tafi can wani waje, ta damk'e hannayen Aunty Nafisa dake gefenta tana sheshshek'a jikinta har d'agawa yake saboda ajiyar zuciya. Inna da muk'arrabanta suka yi tanasiharsu suna zaiyano abubuwan da ita a lokacin ba fahimtar su take yi ba. Daga k'arshe aka kaita wajen Baffa, a nan ma taci wani kukan ta k'oshi don bud'ar bakin sa da farko hak'uri ya fara bata, zuciyarta ta tsinke...ta yaya baffa zai bata hak'uri? akwai abinda zai tab'a yi mata a duniya da zai sa ya bata hak'uri? Tayi niyyar ta gaya masa ita ba abinda yayi mata, ita ba a cikin damuwa take ba, auren Imran ba zai zame mata matsala ba, amma kukan dake cinta ya hana ta, tana ji tana gani aka fitar da ita daga gidansu aka sata a mota, gidan da ta taso tun yarintarta, gidan da mahaifiyarta ta tafi ta barta a cikin sa, gidan da Inna ta raine ta da dukkan kulawarta, gidan ta fara gina rayuwarta a cikinsa, da gaske ne da ake cewa aure yak'in mata, yau ta fahimci wannan yak'in da ake nufi, don a yanzu ji take kamar runduna guda zata tafi tunkara. ●﹏● Pheeewwwwww......mun gama harkar biki, duk wata hayaniya ta k'are...komai yazo k'arshe an dai tafi da Nanne gidan Imran, abinda muke jira tun farkon labarin nan ya faru. Anyi auren, d next agenda shine yadda zaman zai kasance, zaman wata halitta da kuma mutum a matsayin zaman aure? yadda Nanne zata san waye Imran, tunda a yanzu da gaske ta zama b'arin rayuwarsa. Amma me kuke tunani yasa Imran ya fara canja mata tun a rana d'aya kawai? Ina zancen masu daukan hoton nan? May be zamu ji a next chapter.😊  *** WAYE SHI? AYSHA SHAFI'EE 34 (☆_☆) Mutane sun ragu sosai a lokacin duk an tafi d'akin ya rage daga su Aminah sai Aunty maryamah da Aunty Zainab kad'ai, har a lokacin Nanne na k'udundune a cikin lafayarta tana sheshshek'ar kuka. Aunty zainab dake kan stool ta kalli agogo tace. "Gaskiya tafiya zamu zo muyi, babu alamun zuwan dangin ango a wannan daren." Daidai sannan wayar aunty maryama tayi k'ara, bata nan tana kitchen ita da Rahma saboda haka Aunty zainab d'in ta d'aga. Abu daya ta fad'a Nanne ta gane inna ce mai kiran. "Gamu nan, yanzu zamu taho wallahi bari in gaya musu." Ta kashe wayar sannan tace da Aminah. "D'auki jakarki, bari in kira su tafiya zamu yi." Tana fita Aminah ta cigaba maganar da take mata. "....Sa'adha dan Allah ki rage kukan nan, kar ya shigo ya ganki kina tayi ba k'akkautawa." Da kyar ta had'iye shi a mokogwaronta tace. "Yau zaki tafi?" "A'ah sai gobe dai, ai yanzu dare yayi su Rahman zan bi." "Dan Allah toh kizo goben." "In naga wasu zasu zo, zan biyo su amma gaskiya ba zan miki alkawari ba." Tayi raurau da ido kamar k'aramar yarinya. "Gaskiya ne ai sa'adah, aure fa kika yi, dole ne ki hakura da komai ki saba da canjin rayuwarki." Canji rayuwa, canjin rayuwarta...tun jiya take maimaitawa kanta wannan kalmar amma har yanzu ta kasa nutsewa cikin kanta, tana kallo ba yadda ta iya haka suka tafi suka barta, bayan su Aunty maryama sun k'ara binta da nasihohin da ita ba fahimtarsu take ba. Tashin motarsu da kuma rufewar gate d'in data fahimci akwai maigadi a gidan ya dawo da hawayenta, ta sake dukunkune jikinta akan gadon tana jin gidan ya mata girma, kamar wata tsakuwa guda d'aya akan faranti. Bata san iya adadin mintunan da suka wuce ko lokacin da ya tafi ba kafin ta jiyo wani k'arar bud'e gate d'in, ta san dai kawai a lokacin hawayenta sun k'afe, sai ajiyar zuciya da take yi a hankali. Ta rufe idonta sanda ta jiyo k'arar taku daga inda take tunanin corridor ne, ba sai an gaya mata ba ta san waye ya shigo, Imran ne, mutumin da a yanzu kowa ke kira da mijinta. "Assalamu Alaikum.." Wannan muryar, wannan muryar mai taushi ta shiga cikin kunnenta, sai dai yau ba a waya ba, ko kan kan hanya ko gadon asibiti, a cikin gida ne, gidan dake mallakinsu su biyu a matsayin mata da miji. Ba tare da ta d'ago kanta daga tsakanin cinyoyinta ba ta amsa a hankali, ba lallai ne ma in yaji ba. "Hey...." muryar ta sake shiga kanta da wani irin amo sanda ya zauna a gefen gadon sannan bata zato taji ya lalubo hannuta daga cikin lafayar. Numfashinta ya d'an d'auke a lokacin da d'umin hannunsa ya ziyarci fatarta, kamar dazu taji wani abu na shiga jikinta yana soothing damuwarta. "Kuka kike yi?" Kamar mai bashi amsa sai tayi ajiyar zuciya tare da jan hanci, shima ya d'auki hakan a matsayi amsa. "Kukan rabuwa da Inna ne?" Bata amsa ba yace. "In dai haka ne dan Allah kiyi shiru, ko gobe in kina so zan kaiki wajenta..." "Kinjiiii...?" Taji kamar ta d'ago a lokacin ta tambaye shi da gaske yake? da gaske gobe zai iya kaita gida? amma hannunsa dake nannad'e da nata ya hanata magana, wani abu ne daga cikinsu yake shiga jikinta yana goge duk wata damuwarta. "Sa'adha..." ya kira sunanta a hankali. "Ko mu koma yanzu sai mu dawo anjima?" Ta d'ago da kanta da sauri ta kalle shi. Ya salam! yayi kyau cikin wani bak'in yadi d'inkin fitted mai kyau, sannan yasa bak'ar hula wadda ta fito da d'an hasken fatarsa. Yana kalonta da idanunsa masu kama da maik'o a cikinsu, da kuma d'an k'aramin murmushi a lebb'ensa, murmushin da a d'azu taso ganinsa kamar me. Ta sauke kanta k'asa sannan muryarta ta fito. "Yanzu dare yayi ai." ita har ga Allah a lokacin ta yarda cewa zai iya mayar da ita gidan ne a yau, saboda haka ta k'arashe da cewa. "A bari kawai sai goben." Taji k'arar murmushinsa kafin ya lalubo d'aya hannun nata. "Zo muje kiga..." Ya mik'e tsaye rik'e da hannayen nata, ba musu kuwa k'afafunta suka mik'e suma, ya jata har jikin wata k'ofa dake gefen wardrobe, wanda ta san toilet ne, aikuwa yana bud'ewa mamaki ya kamata ganin girmansa da bata yi zato ba, gashi komai na cikinsa light Ash ne, daga toiletries har tiles d'in, sannan ga wata fitila mai k'arfi da ko allura ce ta fad'i tana zaton za'a ganta. Ya tsayar da ita a jikin sink sannan ya koma ta bayanta ya rik'o kafad'unta, daga cikin mudubin da suke facing tana iya ganin tazarar kafad'arsa da kanta, ta san yana da tsawo amma bata san cewa banbancin ta dashi ya kai haka ba. "Sa'adha... I want to tell you something." Ya fad'i kowacce kalma a hankali kuma da nutsuwa, idanunsa kuma basu bar kallonta ta cikin mudubin ba, rudani da wata irin kasala suka saukar mata sanda taji ya zamo hannayensa daga kafad'arta, ya rik'o tafin hannayenta, zuciyarta ta dinga bugawa har tana jin kamar zai iya jinta. Sannan tunaninta ya tsaya cak! ta tsura masa ido ta cikin mudubin, kwarjininsa na k'ara dulmiyar da ita, musamman idanunsa da suke da kyalli kamar ya d'iga mai a cikinsu, They were clear and deep! taji zata iya nutsewa a cikinsu ta manta da duk damuwarta. "I want to share a part of my life with you, kiyi hak'uri na san kin gaji...amma in ya wuce yanzu, ya wuce yau bana tunanin zan iya sake fad'a miki." Ya sake shiru yana sauraren fitar numfashinta, kamar iya abinda zai fad'a kenan kafin ya fara. "Sa'adha tun da na tashi a rayuwata ban tab'a sanin iyayena ba, sun rasu tun kafin in san kaina, haka kuma bani da wani dan'uwa na jini, sannan rayuwata tana had'e da k'alubale da yawa, na fuskanci wahalhalu da yawa a lokacin yarintata, sai daga baya na sami tallafin wata halitta da ta rik'e ni da dukkan kulawarta, ta jawo ni jikinta, ta bud'e min sabuwar duniyar dana sami komai dana rasa a baya, 'yan uwa, d'aukaka, matsayi da kuma tarin abubuwan da a da nake musu hangen nesa. Shi yasa nima a lokacin na d'auki dukkan soyayyata na dank'a mata, na yarda cewa bani da wani farin ciki a duniyar nan daya wuce nata. A cikin haka sai k'addara ta jefo ni wajenki, tun daga ranar dana fara ganinki kuma rayuwata ta canja. ban san taya zan fad'a miki ki fahimta ba amma zuciyata ta fara sonki tun ranar da kuka dawo daga islamiyyar nan ke da Rahma, tun ban san ko ke wacece ba, da farko nayi kok'arin takura kaina da cewar ni da ke bamu dace ba, amma duk lokacin da nake tare dake ko na ganki sai zuciyata ta kasa daurewa. For the first time tun lokacin da na sake sabuwar rayuwa nayi failing a wani abu, nayi failing wajen controlling zuciyata akanki, shi yasa na fara bibiyarki tun baki sani ba, har kika fara lura dani. Daga nan kuma abubuwa da yawa suka dinga had'a mu, har zuwa yanzu da Allah ya k'addara aure zai shiga tsakanin mu. So, kome zai faru Sa'adha, kome zai faru nan gaba, I want you to keep in mind that son da nake miki da gaske ne, and it will forever be real." Yana rufe bakinsa, ta juyo da fuskarta ta kalleshi, yana tsaye dab! da bayanta ne, saboda haka numfashinsa ya shiga busawa akan goshinta. "Me zai faru nan gaba?" mamaki ya fito sosai a 'yar karamar muryarta. Ya lumshe idanunsa akanta. "I don't know, abubuwa da yawa suna faruwa a rayuwar nan, i just felt like telling you saboda gudun mistunderstanding nan gaba." Sai tayi shiru kawai kwakwalwarta na nazari, amma nazarin ma ya kasa yiwuwa saboda yadda yake tsaye dab? da ita, tunda take bata tab'a tsayawa kusa da wani namiji haka ba, sai a yau ranar farko da ta zama matar aure. Tunaninta ya katse, sanda ya d'ago da hannunsa a hankali ya sake juyar da ita tayi facing sink d'in, sannan ya kunna fanfon ruwa ya fara zuba. "Kiyi alwala muyi sallah Sa'adha, mu rok'i Allah ya kore duk wani abu da zai shiga tsakaninmu." Har tayi alwalar ta bishi jam'in sallah raka'a biyu, kwakwalwarta nazari take yi sosai na maganganunsa, amma har a lokacin abubuwa da yawa ta kasa fahimtarsu. Bayan sun idar da sallar, ya juyo ya sake rik'e tafin hannayenta sannan yayi addu'o'i wanda da yawansu na nema musu zaman lafiya ne sannan yace da ita taje tayi wanka ta rage kayan jikinta. Yana fita daga d'akin ta murd'a muk'ulli sannan ta cire lafayar jikinta, akwai heater a band'akin ta had'a ruwa mai d'umi sannan tayi wankan, tana yi tana kallon band'akin tana tuno nasu itada inna, tana ganin kyansa kamar me amma wannan ya ninka shi a komai. Ta zura wata doguwar rigar bacci har k'asa bayan ta fito sannan ta feshe jikinta da turare. Har ta kashe fitilar ta kwanta sai kuma wani tunani yazo mata, ta taso ta bud'e muk'ullin sannan ta koma tana sak'e-sak'en yadda daren yau zai kasance mata. Maganganun Imran suka yi ta yawo akanta, ta san addu'ar neman zaman lafiya abu ne mai kyau da ya dace su fara dashi, amma yadda yayi ta maimatawa da kuma addu'o'insa da suka fi yawa akai, ya sata wani tunanin. Ta dunk'ule hannayenta tana tuno yadda a dare d'aya kawai ta fara sabawa da yadda yake rik'e su. Kusan minti biyar sannan ya turo k'ofar d'akin ya shigo, da alamun shima wanka yayi, don ya canja kayansa zuwa wata light jallabiya, gashinsa alamun a jik'e sannan k'amshinsa ya cika d'akin. Ya shigo cikin bargon lokacin da ta sake duk'unkune jikinta daga can k'arshen gadon, bata ko d'ago da kanta ba don idanunta na kan yatsunta, amma taji alamun kamar ya kalleta kafin yaja bargon jikinsa sannan yace. "Allah ya tashe mu lafiya wifey." Wani dad'i ya ratsa ta, abinda take fatan taji kenan, sai kuma yazo har da k'arin wani sunan mai dad'i. Wifey! tayi murmushi a hankali sannan ta amsa. "Ameen." Asuba ta gari! ●﹏● Me kuke tunani game da abinda Imran ya gayawa Sa'adha....? Da gaske ne maganganun ko hakan ma na daga cikin tsarinsu? **** WAYE SHI? AYSHA SHAFI'EE 35 Allah abin godiya, kwana na uku ina tunanin yadda zan k'arasa chapter nan, sai d'azu ina cikin wanke gashina komai ya fito POP!....so i was tynking duk ranar dana rasa idea kawai toilet zan tafi in tara kaina a famfo.....hehehehehe!😁😁 Don't mind me please! Enjoy!😘 (☆_☆) "Zaka jira nan da kamar minti goma ayi warming d'insu sir." Matar dake zaune a kujerar cashier ta fad'a fuskarta d'auke da mirmushi. Good. Imran ya amsa a cikin ransa a fili kuma sai ya d'aga mata kai sannan ya juya ya fita daga restaurant d'in ya nufi cikin motarsa ya zauna. Yana bukatar lokaci dama, alone time d'in da zaiyi tunanin dake cikin kansa kala-kala. A driving seat yake zaune amma senses d'in hancinsa na iya jiyo masa wannan cool k'amshin da yaji a jikinta jiya, alamun har a yanzu motar bata rabu da k'amshin inda ta zauna sanda za'a kawo ta gidansa. Komai ya riga ya kammala a yanzu, Sa'adha ta zama matarsa bisa k'okari da fasahar jaamil, saboda kusan komai daya faru shi ya tsara, shi ya tsara duk tarin abubuwan da suka faru a d'an tsukin nan, tun daga kan iyayen daya gabatar a wajen Baffanta har zuwa matan da suka je a matsayin danginsa wanda duk babu su a gaske, ya rufewa mutane ido ne kawai sunga alamun siffarsu amma babu su d'in a zahiri. Hallucination ne kawai yayi planting a cikin idanunsu. don da ace an samu wanda zai haska su a wajen da mudubi ba zai gansu a ciki ba. Shi yasa ma mai hoton nan ya kusa kawo musu matsala, ba don Allah yasa jamil ya.... Tunaninsa ya katse, sanda wani saurayi ya kwankwasa masa glass. "Yawwa yallab'ai gasu nan gabad'aya ne, harda receipt d'in." Ya fad'a yana zuro masa ledojin hannunsa, Imran yayi godiya sannan ya rufe glass d'in, ya tada motar ya cilla ta saman titi haka ma zuciyarsa ma ta cilla can inda ya nufa a yanzu wato gidansa. Tsawon shekara d'aya kenan da uzirinsu ya shigo dashi wannan rayuwar, ya bar al'adarsa da komai ya canja yanayin halittarsa, amma duk tsawon wannan lokacin bai tab'a jinsa more human ba irin jiya da yau, watakila har gobe ma da jibi...har zuwa ranar da komai zai k'are. Sau ba adadi ya sani aurensa da Sa'adha ba abu ne mai d'orewa ba, don ko a yanzu baya tunanin suna da abinda ya wuce karfin watanni, shi yasa a jiya bayan an gama d'aura auren zuciyarsa ta karye da ganin irin d'imbin farin cikin dake faruwa a gidansu, ya hango ranar da shi d'in da kowannesu ke yabo a yanzu, zai zama abin la'ana a wajensu, a lokacin da shi d'in baya nan kuma, baya cikin wannan jikin da mutane suka sanshi dashi. Ranar da shi kansa zai ji haushin kansa, zai k'ara yin nadama da regreting abinda yayi sau ba adadi, mistake d'in da yayi tun farko na shiga jikinta, don da ba hakan ba, da komai dake faruwa a yanzu bai kasance ba. Da Sa'adha na can na karatunta bata zama matarsa ba, da watakila shima ya gama abinda ya kawo shi ya koma nahiyarsu, can wajen gimbiyarsa Sareefa. Amma k'addara ba haka ta tanadar masa ba, ta shigo da sa'adha cikin rayuwarsa a wani irin yanayi da yafi k'arfin tunaninsa, don da gaske ne abinda ya fad'a mata jiya. A yanzu, ya yardarwa kansa cewa da gaske yana son ta, zuciyarsa ta nutsu da ita kamar yadda ta amince da Sareefa a baya, shi yasa ya bud'e mata wani b'arin zuciyarsa da yake babu shi a tsarinsu shida jaamil, a lokacin tausayinta ne ya kamashi ganin tana kuka, ya san ya yaudareta ne ya rabo ta da iyayenta ya kawo ta cikin fake rayuwarsa, atleast she deserve to know something that is true about him, duk da cewa ma baya tunanin ta fahimci dukkan zancensa. ba lallai ne ma ta gane ba. Sannan yayi ta nanata zancen nema musu zaman lafiya ne saboda zamanta dashi had'ari ne, ita d'in ba abokiyar halittarsa bace, dole ne yayi taka tsan-tsan da kansa a wajenta, dole ne in yana tare da ita hankalinsa ya zama fully a jikinsa don she's so fragile to him, kamar mutum ne ya rik'a wasa da circle d'in kwanduwar kwai a hannunsa, kuma ya na yi da zummar cewa ba zai fasa cikinta ba. Saboda haka ba zai tab'a bari zamansa da ita ya samu matsala ba, zai iya k'ok'arinsa wajen nuna mata dukkan kulawarsa yadda ba zata fahimci rashin wasu abubuwa ba, don kamar yadda ya sani kuma jaamil ya dad'a fad'a masa a jiya, akwai abubuwan da ba zai tab'a bari su faru tsakaninsu ba. Ya tuno d'azu da yazo tashinta sallar asuba, tana baccinta peacefully a lokacin, hular kanta ta zame gefe kad'an sannan strands d'in gashinta mai kyau ya kwanta smoothly akan filon, ta rik'e fuskarta da tafin hannayenta biyu a kowanne gefe kamar k'aramar yarinya, sannan bakinta slightly a bud'e. Yana iya jin fitar numfashinta a hankali daga tsakanin leb'b'en nata, a lokacin yaji kamar ya matsa kusa da ita ya d'ora yatsansa akan leb'b'en, yaji irin taushi da d'umin da suke dasu amma ya hana kansa. Yadda ya barta tayi baccinta hankali a kwance jiya ba zai so ya tashe ta da wani abu da bata saba ba. Ya lashe gefen lebb'ensa sanda ya k'araso bakin gate d'in. Tun kafin ya danna horn maigadin ya fara k'ok'arin bud'e gate din. Sunansa Malam Aminu, wani tsohon dattijo a kamfaninsu da ya d'auko shi tun sanda ya siya gidan a matsayin mai gadi. "Sannu da zuwa Alhaji, Sannu da zuwa." Ya fad'a lokacin daya shigo da kan motar cikin gidan. Maimakon ya amsa sai yace. "Ina kwana Baba, mun tashi lafiya?" "Alhmdlilahi Alhaji, Alhmdlilah. Jiya ina taso in tuna maka zancen tankin nan na baya daya fashe kuma sai naga dare yayi." "Ya salam, na manta ne amma da kayi magana ai, yanzu to babu ruwa a ciki ne?" "A'ah ai da yake jiya na sami b'arin wasu robobi a can baya na aikin gidan, sai na k'ona su na manne shi, to ya ragu dai amma har yanzu ruwan na zuba." "Toh shikenan Baba, zan fita anjima sai in taho da wanda zai canja shi....ga wannan." Ya d'auko d'aya daga cikin ledojin gefensa ya mik'o masa, ya karb'a da godiya sannan ya k'arasa ciki, ya ajiye motar a daidai balcony k'ofar falo sannan ya fita, ya kwaso ledojin ya rufe motar. Sai da ya tsaya a gaban k'ofar sannan ya fara k'ok'arin lalubo key d'in a cikin na motarsa. sai dai kafin ya kai ga budewa ya jiyo wasu 'yan k'ananan taku daga ciki, sannan hannu yana fumbling da k'ofar, a sakan d'aya k'ofar ta wangale Sa'adha ta tsaya a gabansa cikin shigar wata doguwar riga ta orange material, rigar ta haska kalar fatarta da tayi fresh sannan ga hannayen nan nata da suka sha kunshi d'as, ya illahi! ya had'iye yawu da kyar sanda ya lura da idanunta. Me ya same ta? Kuka take yi! ●﹏● WAYE SHI? AYSHA SHAFI'EE 36 (☆_☆) Da sauri ya taka steps d'in ya shiga ciki, sai da yazo dab! da ita sannan ya tsaya. "Sa'adha me ya faru? me ya same ki? wani yazo ne?" Yayi tambayar duk a lokaci d'aya sanda hannunsa ya lalubo nata, jikinta ya d'anyi b'ari amma nan da nan ya saki sanda ya shiga murza babban yatsansa a bayan hannunta. Cikin sheshshek'ar kukan ta girgiza kai. "Ba wanda yazo, na tashi ba kowa a gidan sai ni kad'ai, kuma nayi ta jin tafiya kamar za'a shigo amma ba kowa, sannan...." "Shshhh..." yasa d'aya hannunsa yana goge mata hawayen a hankali. Zuciyarsa ta matse da tausayinta, ya tuna cewa ba taba zama a gida ita kad'ai ba, ta tashi a gida mai mutane da yawa ne dole yanzu taji bata saba ba. "I'm sorry habibty...kina ta baccinki mai dad'i sanda na fita shi yasa ban tashe ki ba, kiyi hak'uri dan Allah." A lokacin wani gefen tunaninsa ya ayyana masa cewa shine Babban abin tsoron da ya kamata ta guda ma a yanzu. yasa hannunsa a bayanta yana zagaya shi a hankali sannan yana k'ara rada mata tayi hakuri har sai da ya tabbatar zuciyarta ta nutsu sannan ya d'an sunkuya da fuskarsa side d'in kunnenta yace. "Ban tab'a dawowa gida wani ya bud'e min k'ofa ba Noory, this is my first time...Nagode!" Tayi murmushi a hankali cike da kunya sannan ba tare da ta d'ago ba muryarta tace. "Ina kaje?" Yaji murmushin shima na shirin kub'uce masa, irin wannan courage d'in nata na burge shi, bata cika k'umbiya-k'umbiya ba. "Baki ga note d'in dana ajiye miki ba." Ta girgiza kai. Ya rufe k'ofar da k'afarsa sannan ya d'ago mata ledojin hannunsa. "Naje samo miki abinda zaki ci ne." Idanunta suka kara girma da tambayar abinci ya siyo. "Come on, na san jiya da za'a kawo ki anyi ta fad'a miki cewa ki kula dani koh?" Bata amsa ba ya cigaba. "Nima haka kowa yayi ta fad'a min, to ta yaya zan fara barin ki da yunwa da sassafen nan?" Ta d'ago ta kalle shi da jik'akk'un idanunta da kuma d'an mitsitsin murmushi a lebbenta. Kwayar idanunta farare tas suka d'auki hankalinsa, yaji kamar zai fad'a cikinsu ne ya nutse. Subhanallah! ya fad'a a ransa. She's so beautilful...very stunning and deadly gorgeous! Ba tare da wani dogon tunani ba ya ajiye ledojin sannan ya kai hannunsa ya shiga tab'a doguwar jelar kitsonta da suka fito ta gefe, a lokaci d'aya kuma yana k'ara sunkuyo da fuskarsa saitin tata, ya lura ta ki'fta idonta a hankali tana kallonsa, sai da ya matso da kansa dab! da ita sannan ta rufe idanunta gabad'aya. A hankali lebb'ensa ya sauka akan cheeks d'inta, wani waje just a mere inch from the side of her lips. Sannan a hankali yaji wani abu da bai tab'a experiecing ba a rayuwarsa, wani abu daban, wani abu sabo da babu shi a register kwakwalwarsa. Cikin kiftawar ido jijiyoyin jikinsa suka daina aiki sannan jikinsa ya k'ame kamar dutse, yaji zuciyarsa na bugawa da k'arfi kamar zata tsaga kirjinsa ta fito, ya kasa koda kwakwaran motsi, Hannunta d'aya dake rike da nasa shine kad'ai wani abu dake rike da jikinsa, jikinsa da ya tsaya a k'ame kawai, frozen! kamar mai jirin wani abu, wani abu da zai dawo dashi duniyar zahiri. Ring Ring Ring Ring Ring. Wayarsa dake gaban aljihu ta zama wani abun daya janyo shi zuwa senses d'insa. ******** BAYAN KWANA UKU. Imran bai tab'a tunanin cewa akwai wani farin ciki a duniya da ya kai wanda yake ji a yanzu ba, ya yarda cewa duk wani farin cikin duniya ya taru ne a gefe guda sannan farin cikin aure ma ya tattara a gefe guda. Ya k'ifta dogwayen gashin idonsa a hankali yana kallon fuskar Sa'adha dake kwance a gefensa tayi pillow da kafad'unsa tana baccinta hankali a kwance, tunda yake bai tab'a ganin wanda ke bacci so innocent kamar ita ba. Ya tuno yadda ta dinga dariya jiya da daddare lokacin da tasa rigarsa, tana cewa tayi kama da irin masu film d'in abinda dariyar nan, amma shi a idanunsa ba haka ya gani ba. she look so flushing and radiant! A cikin kwana uku kawai yayi mugun sabawa da ita kamar yadda ya san itama ta saba dashi, don ko bata fada ba kyallin farin cikin idanunta da kuma yawan murmushinta zai shaida masa hakan, sannan ko daga yanayin maganganunta ta sake dashi saboda tana iya masa doguwar hira har ta bashi labari, wani lokacin ma tana indicating da hannunta cikin tsiwarta. Matarsa mai tsiwa ce, ya riga ya sani, Shine farkon abinda yaja hanakalinsa game da ita. Bayan hakan ya kula ta fara sabawa da yadda koyaushe hannusa ke cikin nata, good morning kisses d'in da kullum yake raining a fuskarta da kuma sauran abubuwan da kullum yake iya k'ok'arinsa wajen daure zuciyarsa akanta, don ko sau d'aya a rayuwarsa bai taba experiencing irin feelings d'in dake nukurkusar zuciyarsa game da ita ba, wasu irin feelings ne kamar electricity suke yawo a kowacce jijiya ta jikinsa duk sanda yake tare da ita. Kuma a yanzu tare suke yin komai na gidan, tare suka gyara setting d'in d'aya falonsu da tace baiyi mata ba sannan tare suka gyara kitchen d'in gidan, suka mayar da dukkanin kayan da aka jera cikin kwalinsu suka bar iya na amfani kawai, ya fahimci bata fiye son tarkace da kaya da yawa ba, she prefferd everything plain and simple! kamar yadda nature dinta take itama. Tare suka zauna suka yi lists d'in dukkanin abinda suke buk'ata na gidan sannan suka fita suka ciko boot da bayan motarsa dasu, a kwana uku kawai rayuwarsa ta canja, yaji kamar duk zaman da yayi a da cikin wani kango yake sai yanzu ya shigo gida. Murmushi ya sub'uce a kumatunsa amma bai motsa ba, ya kwanta very still yana kallonta, Sai wajen karfe biyu suka yi bacci jiya, ba zai so ya tashe ta tun yanzu ba, don ko da asuba, sai da ya d'auketa ya kaita har cikin toilet d'in sannan ta bud'e idanunta. Kullum baya iya barinta tayi bacci da wuri, in suna tare lokaci tsaya masa yake yi yaga kamar ba wani sauran abu mai motsi a duniya sai su biyu, sai yaga idonta ya fara rufewa sannan yake fara rage tambayoyin da a kullum yake cika ta dasu, ya dinga jefo su d'aya bayan d'aya a hankali yana tracing k'unshin hannunta, k'unshin da a yanzu in za'a sake irinsa ya san ko mai k'unshin da tayi baza ta kaishi yin mai kyansa ba. Ta gefen idonsa ya kalli agogon dake mak'ale a d'akin, lokaci ya nuna masa karfe sha biyu saura na rana, a yau ya kamata ya koma office don kwata-kwata bai d'auki hutu ba, sai iya 2-days leave d'in kawai da ya zama dole na ma'aikata, amma baya jin daga yau har zuwa satin ya k'are zai koma office, he wanted to spend his time with her, akwai abubuwa da yawa game da ita da bai gama sani ba. he wanted to know every single detail of her life. Tun daga kan abubuwa masu muhimmanci har zuwa silly-silly abubuwan da bata d'auke su a komai ba. Ya riga ya tanadi tarin tambayoyin da yake son yi mata dama, amma a kullum ya tashi ya kalli fuskarta, sai jerin tambayoyin list d'insa su k'aru. ya rayuwarta take kafin ya had'u da ita? Wadanne irin mutane take mu'amala dasu? Me take so me nene bata so?  His list grew. Koyaushe cikin tambayarta yake yi, in suna wani aikin, in suna cin abinci, in suna girkin da a yanzu tare suke yi ko kuma mafi yawan lokutan da zai jawota jikinsa yana absorbing duk wasu information d'inta. Amsoshin da take bashi, tun daga kan yanayin fuskarta da body language d'in da yake fahimta su suka bud'e kwakwalwarsa ya fahimci halayenta da yawa bayan iya wanda ya sani. Sa'adha wasn't just good, she was perfect! kamar wani box guda ne da aka had'a complete set na duk abinda d'an adam zai buk'ata a rayuwarsa. Kuma tun a yanzu tsoro ya fara kama shi, tsoron ranar da lokacin tambayarta zata zo, ranar da zata fahimci shi d'in ba komai bane mai daraja, don ya san k'aryar da duk zai had'a ba zata tab'a tashin wani abu mai daraja irinta ba. "Wane irin chewing gum kika fi ci?" Ya tuno tambayoyin daya mata na k'arshe jiya kafin tayi bacci. A lokacin tana kwance a jikinsa yana janye wani strand d'in gashinta da ya shiga bakinta. Ta d'ago da idonta ta kalle shi, yaji d'umin jikinta yana fitowa directly akan fuskarsa, k'amshin turarenta ya cigaba da nannad'e kowanne senses na hancinsa, ya k'ifta idanunsa a hankali sanda tunaninsa ke sulalewa kan plumpy lips d'inta da yake facing. "Kowanne... banda d'an goma dana biyar." Yayi murmushi a k'asan numfashinsa kafin yace. "Na Ashirin fa?" "In ka bani zanci." "Wane colour kika fi so?" "Suna da yawa." "Fad'a min first daya fara zuwa ranki." "lemon green." Ya sake yin wani murmushin, ba tun a lokacin ba ya fahimci Sa'adha tana da ra'ayin kanta, bata tab'a yin wani abu don wai hakan ya zama zab'in mutane da yawa. Hannunsa ya koma gefen fuskarta ba tare da amincewar zuciyarsa ba, ya sake janyo wasu tarin gashin nata, idonsa akan lips d'inta yana jin kamar ya d'ago da fuskarta sannan ya sunkuyo da tasa, zai iya had'uwa da bakinta halfway... Enough! Yayi saurin dakatar da kansa, in har hakan ta kasance, zai iya losing controll d'insa yaji mata ciwo. "Meye last music d'in da kika ji?" Her lips twisted, alamun tunani daga can tace. "Last wak'ar da akasa ranar bikin mu." Ya dage girarsa d'aya. "Seriously? wacce kenan?" "I beleive in you." Yayi murmushi a hankali. "I beleive in you too Noory!" "Kai wanne ne last da kaji?" "Mhm-mhm..." Yayi saurin dakatar da ita. "Har yanzu time d'ina bai kare ba, sai gobe turn d'inki zai fara." "Zuwa yaushe toh?" "Wannan ma tambaya ce, ki bari sai goben yayi tukunna sai ki tambaye ni." Tayi murmushi mai fad'i tana lumshe idonta a kansa... Her smile was infectious to him! Imran yaji duk wata kafa a jikinsa ta tsaya da aiki, sannan dauriyarsa ta k'are, a hankali ya sunkuyar da kansa cikin ramin wuyanta. ●﹏● WAYE SHI AYSHA SHAFI'EE 37 (☆_☆) Hannun Nanne ya mik'a zuwa d'aya b'angaren gadon, babu kowa kamar yadda tunaninta ya bata, ta bud'e idonta a hankali, babu Imran a kwance a wajen sai alamun imprint d'in kansa a jikin pillown daya kwanta. Tayi murmushi a hankali sanda ta tuno event d'insu jiya da daddare, a yanzu ta k'ara yarda cewa Imran yana sonta har cikin zuciyarsa kuma ba abinda zai canja hakan. Tana ganin soyayyarta fal a cikin idanunsa duk sanda ya kalleta, sannan ko kad'an baya jin nauyin fad'a mata how much he loves her tun tana kirgawa a rana har sai tazo ta b'ace k'irgar. Rayuwarta ta canja a iya kwanaki uku kawai da aurenta, Imran ya kaita  wata duniyar daban mai cike da d'imbin kulawarsa da tarairaya. Ta riga ta saba dashi sosai a yanzu, ta saba da hirarsa sannan ta saba da jikinsa, yadda yake yawan tab'ata da yadda hannunsa kullum yake cikin nata. Sannan baya taba barinta tayi abu ita kad'ai, komai tare suke yi cikin hirarsa, hirarsa ta tambayoyi kala-kala da suka had'a da dukkan wani insignificant detail of her existence, films d'in da take so da wanda bata so, wajajen da taje a rayuwarta, wajajen da take son zuwa, sannan tambayoyi game da ita...endless tambayoyin da suka shafe ta. Ba zata iya tuna lokaci na k'arshe da tayi magana mai yawan wadda tayi a kwanakin nan ba, don ta tabbata in za'a tattaro jarabawoyin data amsa a rayuwarta kaf! a had'a dana Imran a yanzu nasa zasu fi yawa. Sau da yawa jikinta yana ta bata cewa zata dame shi da yawan maganarta, amma absolute yanayin fuskarsa da kuma yadda baya tab'a tsayawa da tambayoyin, suke bata kwarin gwiwar cigaba da magana. Yawanci tambayoyin nasa masu sauki ne, 'yan kad'an-kad'an ne suke sata tunani ko kuma murmushi kafin ta amsa, kuma duk sanda tayi murmushin  sai an sake new sets na wasu tambayoyin. Akwai lokacin da fita ta kamashi kai wasu takardu office jiya, baifi minti goma ba yaje ya dawo, amma a lokacin taji ba dad'i, gidan ya mata wani iri da girma, bata san ta saba dashi har haka ba sai da ya dawo sannan taji komai ya koma mata daidai. Da daddare suka zauna a falo da Tv a kunne, suna zaune a k'asan carpet da tulin eatries d'in daya siyo amma hankalinsu baya kan tvn, tambayoyi yake ta mata akan gidansu, da duka 'yan gidan, yana son ya san me da me tayi missing da kuma bayanin yadda komai yake dalla-dalla. Tayi masa bayanin yadda fasalin gidansu yake tun asali kafin azo a canja abubuwa daga baya, yadda wajen baffa yake, yadda kitchen d'insu yake da tarin 'yan aikinsu da kowanne sai da tayi masa bayanin nasabarsa da gidan tun asali, sannan ta dawo kan jerin d'akunan yayyenta har zuwa kan bene, hawa na farko, na biyu da kuma barandar can sama, ta dinga kwatanta masa yadda wajen yake da yamma, cike da iska mai dad'i da kuma yadda mutum ke iya ganin yadda rana ke faduwar a yamma. Ta dinga bayanin tana kwatance da hannunta, yadda yayi shiru yana saurarenta ta cikin dim hasken tvn, yasa ta zama freely tayi ta magana. Daga k'arshe ta k'are da bayanin yadda setting d'in dakinsu yake, d'akin kwanansu ita da Inna. Murmushi tayi a hankali data tuno cewa yau kuma ranar tace, daga yau nata tambayoyin zasu fara, jerin gwanon tambayoyin da tara akansa fal! gasu nan kwando-kwando zube a kowanne lungu da saqo na zuciyarta. Tun daga lokacin data daina ganinsa a k'ofar gidansu d'in nan har zuwa yanzu, ta k'ara ta jera su perfectly akan wanda ta tsara kwanakin baya, wancan lokacin daya maido ta gida da daddare yace mata zaizo washegari, wancan lokacin da ya zama mafarin rayuwar da take ciki yanzu. Excitement raced through her at all the thoughts she would unlock today. Ta mike ta nufi toilet, idonta na kaiwa kan reflection d'inta a mudubi mamaki ya kamata, wani k'aton tabo ne jazur dashi ya fito a gefen kumatunta, tasa hannunta da sauri ta tab'a wajen, babu tudunsa akan fatarta sai jan kawai, kamar irin bruise d'in dake fitowa in mutum ya buge ko jini ya taru a wajen. Ta wanke fuskarta da sauri sannan tayi brush, anan taga wani mark d'in a gefen wuyanta da k'asan kunnenta, ta tuno yadda Imran yayi kissing d'inta a wajen jiya. Matsalar jikinta kenan, very sensitive yake akan komai, a gida ko kurjewa tayi sai wajen gabad'aya yayi jawur. Tayi tunanin concealer zata shafa duk su b'ace amma kuma duk a cikin kayan kwalliyarta yanzu bata da ita, sannan na cikin lefe ta gansu duk masu duhu ne, in ta shafa zaiyi daban da farar fatarta. Ta koma cikin d'aki ta tsaya a gaban full body mirrow d'in dake gefe, tana binciko su d'aya bayan d'aya, akwai da yawa a wuyanta da k'asan hab'arta, ta zame hannun doguwar sleeping dress d'inta nan ma akwai su da yawa, abin ya fara bata mamaki yadda suke da yawa haka, kamar wani abu na ciwo. A lokacin taji k'arar bud'ewar kofar d'akin. Tana juyawa idanunta suka ci karo da Imran rik'e da breakfast tray a hannunsa, singlet ce kawai a jikinsa sai wando three-quarter, lallausan gashin kansa a barbaje har yana saukowa goshinsa sannan fuskarsa d'auke da wannan murmushin dake dulmiyar da tunaninta, taji kamar ta d'auke shi ta kaishi can k'asan zuciyarta ko zata samu sauk'in abinda take ji duk sanda ta ganshi a ranta. "Good morning Habeebty!" Ya fad'a yana lumshe dogwayen lashes d'insa akanta. Hancinta ya jiyo mata daddad'an had'in wani abu kamar scrambled egg da fries, sannan ga sandwiches tana gani a bowl da kuma had'add'en Oats a mug guda biyu. Ta maida hannun rigarta a hankali sannan ta k'arasa gabansa. Sai dai kafin tace wani abu idonsa ya hango masa tarin bruises d'in dake jikinta, idanunsa suka zare da tsantsar mamaki ya lalubi kan dressing mirror ya ajiye tray d'in sannan ya matso ya shigo jikinta. "Me ya same ki? Meye wannan?" A hankali tace. "Nima ban sani ba, yanzu na tashi na gani." Daga yanayinsa ta lura ya tsorata sosai, sai faman dubawa yake yana shafa wajen, saboda haka yace. "Ba ciwo bane bafa, may be wani abin ne ya same ni, I easily get bruises like this... amma ina shafa concealer zai tafi." Sai a sannan taga reaction d'insa ya d'an kwanta. Ya lalubi kunnenta a hankali ya rad'a mata. "I'm sorry!" Maimakon ta amsa sai tace. "Zamu je mu siyo anjima?" Taji sautin murmushinsa kafin amsar ta biyo baya. "Zamu je mu siyo kwalayensu da yawa Sa'adha, don zasu mana amfani sosai." ●﹏● WAYE SHI? AYSHA SHAFI'EE 38 (☆_☆) Nanne ta taho da sauri daga cikin d'aki don bud'e kofar main  falonta da ake ta knocking, Wani dad'i ya kamata sanin cewa bak'i tayi, bakinta na farko a gidanta da tayi sati d'aya a ciki. Don ta san cewa ba Imran bane tunda basu fi minti talatin da gama waya ba, kuma ya gaya mata sai yamma zai dawo, yauce ranar farko daya koma aiki, ranar farko data fara rabuwa dashi ta fara zama a gidan ita kadai. Dazu da tana gyara d'aki ta d'auki filonsa ta shinshina k'amshinsa dake jiki, awa uku kad'ai amma tayi missing d'insa kamar kwana uku, tayi missing muryarsa mai taushi da babu ita a gidan, tayi missing yawan bibiyarta da yake yi a komai, tayi missing tambayoyinsa da har yanzu basu k'are ba, God...! tayi missing hannunsa ma da kullum ke cikin nasa. Kwanakin shidan da tayi tare dashi  gani take kamar shekara shida ne saboda yadda ta saba dashi sosai, He's the best husband anyone could ever wish for! Dukkan irin rayuwar da tayi mafarkinta a baya tare dashi ta same ta har ma fiye da hakan, Imran was caring, loving and showers her with so much affection. A iya tambayoyin data ware a yanzu wanda taga su ya kamata ta fara sani game dashi, ta fahimci mutum ne mai saukin kai sosai, baya tab'a d'aukan abu da zafi a rayuwarsa kuma ra'ayinsu da yawa yazo d'aya wajen so da k'in abubuwa. Sannan bai cika complain ba, rana farko da suka fara yin girki a gidan kusan k'onewa yayi amma haka ya zauna ya cinye baice komai ba, sannan komai tace masa za'ayi ko tana so zai biye mata suyi da dukkan iyawarsa sau da yawa tana jin kamar tana ordering yaro k'arami ne, (D'aya daga cikin abubuwan da take so a rayuwarta.) Sannan in har abu nada matsala zaiyi mata bayani in a simple way da zata gane ba tare da taji haushi ba. Tun a cikin weekend d'in nan yake bata hak'urin komawarsa wajen aiki wanda a lokacin ita bata ga komai, ba sai a yanzu da ta jita a gidan tsit tukunna! Ta tuna yadda yayi ta kissing cheeks d'inta da safen nan yana gaya mata zaiyi mata misssing d'inta da yawa. Taji tarin abubuwa sun tsaya mata cak a lokacin, ta rasa wanne zata fara tunkara, ta riga ta saba komai tare dashi take yi, komai k'ank'atar abu kuwa, da kyar ta tsaida ranta ta fara share gidan tas! sannan tayi mopping, kafin ta gama taji bayanta na shirin k'agewa kamar ta share wani waje mai tarin datti. Ta gyara kitchen ma sannan taje tayi wanka, tana komawa kitchen d'in ta sake tunowa dashi, kullum sai su shafe lokaci mai yawa ana debating me za'a dafa, in ta tambaye shi me zai ci, shima sai ya tambayeta me zata ci yana yi yana wasa da gashinta da a yanzu ta manta yaushe rabon data d'aura d'ankwali, don ko tasa ba zaifi minti biyu ba zai cire shi. Da kyar ta tsaida ranta akan me zata dafa, ta duba fridge taga lemukan da suka hada jiya wajen kala uku suna nan, ta ciro wanda aka had'a da gwanda, ayaba, madara da kuma sugar ta dawo dashi k'asa don ya rage sanyi. Sai da girkin ya kusa gamawa sannan ta koma d'aki d'auko kud'in da zata bawa malam Aminu ya siyo mata Slippers d'in da zata saka a toilet d'in cikin d'aki, a sannan ne taji bugun k'ofar falon. Tana bud'ewa idanunta suka ci karon da tarin mutanen da bata san tayi missing d'insu kamar hauka ba irin yanzu. Ta daka wani irin tsalle tare da ihu. "Na shiga uku, Nanne yaushe zaki yi hankali ne wai?" Aunty maryama ta fad'a sanda ta d'ane kanta, ta sake ta ta koma kan Aunty Nafisa sannan Aunty zainab, ga Rahma, ga wata 'yar uwarsu Sadiya... idonta ya ware da taga harda Amina, Ta sake daka wani tsallen kafin itama ta rungumeta. "Anya Nanne k'alau kike kuwa? sai kace kin shekara baki ganmu ba, kwana shida ne fa kawai." Ta juyo da bakinta a washe tana kallon aunty maryaman da suka yiwa kansu masauki a cikin falon. Tayi missing fad'anta ma kamar me. "Haba Aunty toh yaushe na tab'a zuwa wani waje na kwana shida, sannan bani da ko waya fa balle in kira gida." "To sai kiyi kuka yanzu..." Aunty zainab ta kwaikwayi muryarta, dukkansu suka fashe da dariya. Basu ko gaisa ba ta fara tambayar. "Inna inna? tace a gaishe ta? yaushe zata zo? muryarta ta washe yanzu? jikinta bai mata ciwon gajiya ba? ya k'afar tata? ta koma asibiti bayan bikin..." "Mu nan duk ba mutane bane ai da bama zaki bari mu gaisa ba." Sai kuma 'yar kunya ta kamata, ta fara gaishe su d'aya bayan d'aya, Aminah tace. "Rufa min asiri ke yanzu ai Aunty ce, matar Aure guda." Ta juya idonta tayi magana yadda Aminan ce kadai zata ji. "Kamar kuwa kin san dama in nayi waya da Aunty Sa'adah zance kiyi saving numberta." "Ai in baki fad'i haka ba, ba zan tabbatar ke d'in bace. Rahma dake gefe hankalinta na kansu  ta kyalkyale da dariya. Ta tashi taje kitchen ta kashe girkinta sannan ta d'auko musu lemon data fito dashi da ruwa sannan ta had'o da ragowar cupcakes d'in daya siyo. "Mu fa yanzu zamu wuce, kasuwa zamu kar rana tayi mana." Ta kalli Aunty Nafisan sanda ta mik'a hannu ta k'arbi 'yarta Shukra. "Kasuwar ina?" "Ta can k'ofar gabas, gobe duk zamu koma gida." "Wayyo, zaku bar inna ita kad'ai." "Ke ba tafiya kika yi kika barta ba." Kafin ta amsa Aunty maryama tace. "Ke ni kamar ba haka kujerun d'akin nan suke da farko ba koh?" "Eh, mun canja tsarinsu ne, wancan style din yasa sun had'e a waje d'aya." "Ke da wa?" "Nida shi, shi ya taya ni." Amina ta kalleta baki a sake sannan tace. "Gaskiya Aunty nima aure zaku min, yarinyar da muka bari tana kuka kamar ranta zai fita ita ke wannan bayanin..." Nanne ta d'aka mata duka a bayanta. Suka yita hirarsu ana dariya, kasancewar su Aunty Nafisa basu fiye d'aukan kansu da girman kai ba ganin su Nannen ba sa'anninsu bane. Sai da zasu tafi Aunty Maryama ta jata d'aki tana tambayarta game da zancen 'yan uwan mijinta da basu ga ko d'aya ba ranar kawota. "Wallahi Aunty nima banga ko d'aya daga cikinsu ba har yanzu, ya dai ce min ne dukkansu sun koma saboda wai basu da wajen zama anan garin sai kuma ranar da muka gaisa a waya da matar k'anin baban nasa daya bani labarin ta taimake shi sosai a rayuwarsa, amma bayan ita ni ba wanda na sani." "Toh dole ne kuwa ki dinga tambayarsa game dasu, tunda a yanzu dole danginsa kema sun zama naki, kuma shi mutumin kirki ne Nanne kinyi sa'ar miji dole ki san yadda zaki dinga kula dashi, ince dai kin rike duk abinda na gaya miki ranar nan koh?" Ta had'iye wani abu a makogwaronta, don ko kalma d'aya baza ta iya tunawa a tarin zancen da akayi ta d'ura mata ranar ba, don a lokacin abinda ke gabanta daban ne, amma sai ta d'aga kanta da sauri tace. "Na rik'e komai Aunty." "Toh madallah, ga numbobin wayoyin mu nan duk jna rubuta a wannan paper, harda tasu inna da sauran 'yan gidan naku, duk randa kika samu waya ki kira kowa ku gaisa kafin ki samu zuwa." Kanta tsaye tace. "Ai watakila ma a cikin satin nan zani gidan, tunda tun ranar da aka kawo ni yace zamu je." Aunty maryama ta d'auko salati tun daga farko har k'arshe ta dire. "Ai na san zaki aika uwar san yawo...wato har kin fara tambayarsa zuwa gida ko sati baki gama rufawa ba, toh kar ki fasa...yi ta tambayarsa ya kaiki gidan, in kinje bayan fad'an Baffa na inna ma kad'ai ya ishe ki." Ta had'e rai a lokaci d'aya. "Toh dan Allah meye dan naje gida yanzu, gidanmu ne fa ba wani waje ba, daga tafiyata da kwana shida har sai a fara korata?" Bata kai amsa mata ba Aunty Nafisa ta shigo d'akin. "Daga kitchen d'inki nake Nanne, komai tsaf-tsaf an zama matar gida, amma tun yaushe kika fara girki?" "Tun washegari muka je muka siyo komai." "Danginsa basu kawo muku komai ba?" Ta girgiza kanta. "Da safen ma sai da ya siyo abinci." Aunty maryama ta karb'i zancen. "Yanzu nake gaya mata ai, dole ne a hankali ta dinga tambayarsa game dasu gar ta gano wani abin in akwai." "Gaskiya dai, idan matsala ce yake dasu dole ne ki gano ta ki kuma san yadda zaki gyara tsakaninsu, in ba haka ba ke kanki bak'in jini zaki yi a wajensu da kuma 'yayan da zaku haifa, saboda haka dole ne ki gyara bakin zaren tun yanzu." Nanne tayi shiru kawai tana jinsu, a tunaninta dangin Imran ba matsalarta bace, dasu da babu su duk uwarsu d'aya ubansu daya a wajenta, indai har tana tare dashi kuma yana cigaba da nuna mata kulawar da a yanzu suka fara. Zancen Aunty Nafisa na farko ya d'auki hankalinta, da tace 'ya'yan da zasu haifa, Ya Allah! Zuciyarta ta narke da tunanin 'yan little babies d'in da zasu zama combination d'inta ita da Imran. Zasu yi kyau sosai ta san, musamman ace su d'auko kammanin Imran sosai..... "Kina jin mu wai kuwa?" Muryar Aunty maryama ta katse tunaninta. Da sauri ta kalleta tace. "Aunty Naji komai, kuma insha Allahu zanyi yadda kuka ce." Da haka suka yi ta cika ta da wasu shawarwarin suka tafi bayan Aunty maryamah ta mata dogon kashedin daura d'ankwali. Aka bar Rahma da Amina kad'ai. "Wai ta yaya kika biyo su, ko har yanzu kina gida." "Haba dai na koma tun washe-gari,  Rahma ce ta kirani jiya tace zata biyo su Aunty Nafisa yau ko zanzo, shine naje muka taho tare." "Kin kyauta wallahi, baku san yadda nayi missing d'inku ba kamar me?" "Ni ban gani ha, kinga wani irin fresh da kika yi?" "Dan Allah? ni kuwa ban gani ba." Ta kalli Rahma da tayi kwanciyarta akan kujera tana facing Tvn dake nuna tashar Bollywood tace. "Wai kin koma islamiyya?" "Eh ranar laraba kawai naje." "Yawwa ai dai kinje, ko bakya so kuwa sai kin bani labarin irin gulmata da aka kafa a makarantar nan, don na san tabbas za'ayi." Rahma tayi murmushi tace. "Kema kin san wannan dole ne, don yanzu maimakon mijinki ke kika koma General topic d'in islamiyyar." "Dan Allah, me da me suke cewa?" "Ina zuwa dai su maryam suka hau ni da zancen wai dama ni da ke mun san shi zaki aura muke jinsu suna ta b'ab'atu akansa. Su kuma su Aysha suka dame ni da tambayar wai in gaya mata ta yaya kuka had'u, a ina ya ganki yace yana sonki, da wasu tarin tambayoyi dai." "Ni ba wannan na tambaye ki ba, negative d'in zancen nake son inji." Rahma tayi shiru tana murmushi, Nanne ta tashi daga gefen Amina ta koma wajenta. "Ai na rantse ko ba kya so sai kin fad'a min." Ta cafki hannayenta ta murd'e su ta baya, ta kwallara k'ara had'e da dariya tana fad'in ta sake ta. "In kina so in sake ki fara bayani." Rahma ta dinga k'ara tana neman taimakon Amina wadda ke ta kyalkyala dariya tana kallonsu. Sai da taga da gaske Nanne baza ta sake ta ba sannan ta lallab'a tace zata gaya mata. "Ina jinki toh." "'Yan ajin malam isma'il ne suke yad'a zancen wai k'ila wani abu kika yi masa ya aure ki tunda har kika shigo islamiyyar baki sanshi ba, kuma kowa ya san ba wadda yake kulawa a unguwar tun zuwansa." Nanne tayi kwafa tace. "Toh me kika ce musu?" "Me kuwa zan ce musu? masu fad'a fa da yawa ba wai mutum d'aya bane kuma nima tsintar zancen nayi." "To ba kince daga ajin malam isma'il aka fara ba, nan zaki je kici mutuncinsu gabad'aya." "Kema kin san ba zan iya ba, da dai kina nan ne." "Yanzu ma ai bai wuce duk ranar da zanje gida sai na tabbatar ranar makaranta ne, inje inci uw*rsu wallahi, yadda suka fara zancen nan haka zasu san yadda zasu tsaida shi." Ta sake yin kwafa. "Wato ma wani abu nayi masa, toh zanje in gaya musu asiri nayi ba wani abun ba kuma gwara ni nawa yaci akan nasu." "A'uzubillahi..." cewar Amina. "Wannan wace irin magana ce?" "Ke baki san yaran nan bane Aisha, tun da haushinsu nake ji wallahi." Rahma tace. "Wato Nanne yara, duk fa sun girme mu." "Ke kuwa yanzu tayi aure ai muma duk kallon yara take mana." Nanne ta kalleta da gefen ido tace. "Ga ku nan 'yan matasa dai haka." Amina ta jefo mata d'aya daga cikin throw pillows d'in gefenta, suka yi dariya gabad'ayansu. Bayan sunyi sallah, Nanne ta zubo musu abincin da ta dafa sannan ta mik'awa malam Aminu ma nashi, suka ci suka k'oshi sannan aka sake dasa wata hirar, Nanne tayi ta dariya tana jin dad'i, ji take a yanzu kamar duk sanda Imran ya fita suzo suyi ta hira. ●﹏● Thank you so much for reading this far! WAYE SHI? AYSHA SHAFI'EE 39 (☆_☆) "Tunda kazo garin nan baka da abokai ne? Su waye freinds d'inka ? ban tab'a ji ka fad'i sunan kowa ba, ko baka dasu?" Muryar Nanne ta wancan lokacin ta dawo cikin tunanin Imran, yana zaune a cikin office d'insa a lokacin amma ya kasa k'arasa ayyukan dake gabansa, tunanin tambayoyin da tayi masa kwanaki uku keta yawo akansa. Kafin lokacin yasha tunanin yadda zai amsa mata su a cikin kansa, ta yaya amsarsa ya kamata ta kasance? da k'arya mai ma'ana ko kuma da k'aryar da baza tayi kama da gaskiya ba? Sai gashi tambayoyin sun fito a yadda bai zaci zasu kasance ba, don duk cikinsu ba wanda ke da alak'a da nasabarsa, nasabar da zata kaita ga sanin WAYE SHI..? sun ta'allak'a ne kawai akan sanin intrest d'insa akan abubuwa da kuma Habit d'insa, kuma masu sauk'i ne, they gave away nothing! sannan shima duk amsoshin daya bata masu tsafta ne, suna dacewa da labarin k'aryar daya d'orata akai tun farko, k'aryar da ya fad'awa Iyayenta suka amince da bashi aurenta. Bai bada ko k'aramin hint d'in da zaisa ta fahimci wani abin daban game dashi ba, sai dai ma shi daya gane inda tunaninta ke tafiya akansa, and it was nowhere close to suspense! Kwakwalwarta a goge take game al'amuransa, babu wani abu koda d'igo na zarginsa a cikin kanta, son da take masa ya lullub'e hakan, ta riga ta yarda da al'amuransa d'ari bisa d'ari. Shi yasa a kullum ya d'aga ido ya kalleta, ya kalli irin tarin yardar dake cikin idanunta, sai yaji rauni ya kama shi, yaji kamar ya zaunar da ita ya gaya mata gaskiyar dake b'oye a zuciyarsa, ya amsa tambayoyinta da dukkan gaskiyarsa, ba wai don abin ya daina damunsa ba ko don ya samu yardarta, A'ah sai don kawai yana son ta sanshi, ta san shi d'in na gaskiya. his real personality! kuma yana fatan in ta san hakan, wad'annan chocolate eyes d'in nata su cigaba da kallonsa da trust d'in da take bashi a yanzu. Sai dai wani abu ne daya kwana ya tashi da sanin cewa duk yadda ta kai ga sonsa, kwakwalwarta ba zata tab'a iya karb'ar irin sirrikansa ba. Wani abu ne beyond expectation d'in tunanin d'an adam! Don shi d'in wata halitta ce daban, d'aya daga cikin d'imbin halittun ubangiji da babu saninsu a wajen mutane, shi yasa ranar da yaga wadannan marks d'in a jikinta, ya la'anci kansa fiye da sau d'ari akan kasa fighting emotion d'insa da yayi har ya bari yayi kissing d'inta so deep haka, ya k'ara tabbatarwa kansa cewa da gaske confidence d'in da yake dashi a da ya juye zuwa luck yanzu, baya tab'a iya controlling zuciyarsa indai akan Sa'adha ne, abinda ya jawo masa komai tun farko. Shi yasa tun daga ranar yasa a ransa cewa zai dage da dukkan iya k'ok'arinsa kar ya sake maimata irin mistake d'in ya nemi wata hanyar da zata d'auke hankalinsa daga kan jikinta ba tare da ita d'in ta fahimci komai ba, saboda haka a duk sanda yake tare da ita, sai yayi k'ok'arin maida full attention d'insa kan gashinta...sassalkan gashinta mai santsi da tsawo dake sashi manta duk wani shirmen cikin kansa. And it worked! Ya tuno 'yan kad'an d'in tambayoyinta da sauka sashi tunani kafin ya iya bata amsarsu... "Sanda ban sanka ba, sanda kawai nake ganinka a layinmu, daga baya nazo na daina ganinka, wani wajen ka tafi a lokacin?" Babu inda naje. ya fad'a a cikin zuciyarsa don ya tuna lokacin sarai! wannan lokacin ne da ya takura kansa ya daina bibiyarta kusan watanni biyu, lokacin daya lura idanunta na iya ganinsa duk da cewa yana zuwa ne a yanayin da mutane basa iya ganinsa...wani abu da har yau bai san dalilinsa ba. "Na manta lokacin Sa'adha, amma ina tunanin ko na tafi gida ne lokacin hutuna." Kamar sauran amsoshin da yake bata, ta yarda dashi ba tare da tayi tunanin komai ba. "Toh wajen wa kake zuwa? har sadiq na tambaya a lokacin yace min bai sanka ba." "Da gaske? tun a lokacin kin damu dani haka? har kina tambaya a kaina?" Kumatunta suka yi flushing zuwa red, abinda ke faruwa duk sanda ya fahimci tana jin kunya. "Kawai na tambayeshi ne..." "Don't budge please...zuciyata har ta fara tsallen murna, kar kisa ta tsaya dan Allah." Tayi k'ok'arin fighting murmushin bakinta, his words pleased her! a hankali tace. "Ina jinka toh, wajen wa kake zuwa?" "Watakila Sadiq bai gane kwatancen da kika yi masa ba, amma wajen mutanen da kike gani na nake zuwa, akwai wani d'an office d'inmu da muke zuwa tare." Karya ne, amma sai ta gyad'a kanta alamun ta fahimta. "Ka tuna ranar da ka shigo gidanmu da daddare?" "Na tuna Noory, bana tab'a manta duk wata rana da idona ya ganki." "Me yasa a sanda muka had'u baka min magana ba, sannan da gaske dama kana zuwa wajen ya umar? saboda ni ban taba ganinka ba." "That's more than one..." Ya fad'a a k'asan numfashinsa, amma yayi deciding ya bata amsa kai tsaye, don tambayar bata da matsala, dole ne ta san akwai dalili, kuma shima yana da dalilai da yawa da zasu dace da amsarta. "Na san bakya kula kowa a waje lokacin, na san duk namijin da yayi miki magana a hanya bakya amsawa shi yasa nima banyi wannan gangancin ba, sannan da gaske ne ina zuwa wajen umar amma a ranar kamar yadda na fada miki wajenki nazo ba wajensa ba." "Toh me yasa kazo bani hak'uri?" Ya d'an hadi'ye yawu, tayi tambayar ne ba tare da wani tunani ba, amma amsarsa zata iya sa mata wani tunanin, saboda haka yayi deciding sirka zancensa da gaskiya. "Bayan na koma gida, zuciyata ce ta kasa nutsuwa da tunanin abinda nayi ban kyauta ba, tunda har na tab'a miki magana kuma kin amsa min, kin tuna ranar?" Tayi murmushi a hankali sannan tace. "Adduwa, kad'anya, taura, magarya, d'inya da kuma d'ayan mai kwallo da yawa a ciki...." Yayi murmushi shima. "Right, wannan ranar...shi yasa nazo na baki hakuri saboda a rayuwata bana tab'a son in zama sillar b'acin ran wani...musamman ma kuma ke." "Ka kyauta sosai saboda da baka zo ba, bana jin zan iya wani baccin kirki a a ranar." Zancen ya masa dad'i sosai, yayi dariya a hankali amma kuma mai zurfi har saida jikinsa ya jijjiga tare da nata, tunda tana kwance ne a jikinsa ne wajen karfe sha d'aya na dare, ya murza 'yan yatsunta dake sarke da nasa kafin yace. "Nagode for ur cocern Noory!" Daga nan dukkan wata tambayar data biyo baya ta shafi likes and dislikes d'insa ne da take son sani, kuma baya tunanin akwai kalma d'aya da ba ainihin gaskiyarsa ya fad'a ba anan. ******* "Tunanin me kake yi Imran?" Muryar ta janyo shi daga duniyar space d'in daya tafi a cikin office d'insa. ya d'ago da kansa a nutse ya kalli Shamsudden dake tsaye a gaban table d'insa. "Na tabbata baka yi sallama ba shi yasa kake zaton tunani nake yi." "Amma nayi knocking kuma har na shigo baka jini ba." Yayi murmushi a gefen kumatunsa kafin yace. "May be tunanin amaryata nake." Shamsudden yayi murmushin shima tare d'aga hannayensa sama. "Afuwan, ai na manta kai d'in sabon ango ne, watakila ko don bamu ga ka d'auki hutu bane." "Karka damu, Kwanan nan zan d'auka insha Allah." "Allah ya kaimu, dama kayi baqo ne nazo in gaya maka." Girarsa ta had'e waje d'aya. "Baqo? me yasa bai shigo ba toh?" "Ban sani ba, shigowata kenan malam hamisu masinja yace in taimaka in gaya maka don Dr. Turaki ya aike shi." Ya gyad'a kansa a hankali. "Well nagode, bari inje in gani." Shamsudeen na fita ya rufe file d'in dake gabansa, wanda bai ko yi halfway na signing sababbin arrangement d'in da zasu fara da wasu companies ba. Ya bud'e drawer gefensa yasa shi a ciki, idanunsa suka gane masa kwalin hadaddiyar wayar da ya siyowa Sa'adha d'azu, murmushi ya sub'uce a kumatunsa hango irin farin cikin da zata yi yau, ya maida drawer sannan ya fita daga office d'in ya nufi hanyar elevator, yana sauka ground floor yaci karo da malam hamisun ya dawo daga aikensa. "Yawwa yallab'ai wallahi aiken Alhaji ne ya tsaida ni, shi yasa nace da maigidana ya taimaka ya gaya maka." "Ba komai Baba, a ina yake mai jiran nawa?" "Yana daga wajen ajiyar motoci ranka ya dade." Da jin haka Imran ya fahimci waye baqon nasa. Yana isa parking lot d'in ya hango wannan matashin tsaye a jikin wata mota kamar wancan lokacin daya wuce a baya. "Na san dai sati d'aya ya isa ace ango ya huta, tunda gashi har ya fito aiki." Muryar jaamil ta shiga kunnensa. "Kwana bakwai fa jaamil, ka san dole zan neme ka amma kayi zamanka saboda ka san ba ta yadda zanyi na sameka." Maimakon ya amsa sai yayi murmushi ya kalli wajen yace. "Abin da mamaki, last time da muka tsaya anan nazo ne in k'ara jaddada maka cewa kar kaje wajen yarinyar nan...yanzu kuma gata a matsayin matarka." "Sunanta Sa'adha." "Ko kuma habeebty ko Noory." Mamaki ya kama Imran a lokaci d'aya. "You're spying on me?" "Ba komai ba, kawai irin part d'in da kuke hira a falo, kuke cin abinci tare da kuma in kana wasa da gashinta ko..." Kafin ya k'arasa Imran ya jefe shi da wayar hannusa, tana k'arasowa ya cafe ta da wani irin sauri irin wanda idanun mutum ba zai iya d'auka ba. "Ka kwantar da hankalinka yarima, I assure you baka yi wani abu ba daidai ba, ya kamata dama kayi komai yadda zai dace da tunaninta, 'yan mistake d'in kad'an ne kuma I didn't blame you, yarinyar tana da d'auke hankali." "Ba wannan nake son ji ba, me ya hana ka contacting d'ina har tsawon sati d'aya?" "Wani dalilin ne yarima, wanda ya shafe naka." "Wane dalili ne da kai a yanzu da yafi abinda yake gabanmu?" Maimakon ya amsa sai yace. "Ya ciwon nata?" Imran yayi shiru kamar ba zai bashi amsa ba shima kafin yace. "Kamar yadda ka sani ne ai ba abinda zai faru in har muna tare, yana nan kwance a jikinta." Jaamil ya gyad'a kansa a hankali yace. "Allah yayi wahalarmu ba zata yi tsawo ba yarima, don a yanzu komai yazo k'arshe. Naani ta dawo kuma zata raba yarinyar da b'arin ruhinka a yau d'in nan!" ********** Imran ya bud'e k'ofar motarsa da wani irin k'arfi da yasa handle d'in  b'allewa ya fito gabadaya, Alarms d'in jikinta suka hau k'ara da k'arfi, amma bai damu ba tunda har kofar ta bud'e, ya tayar da ita sannan ya danna button d'in hood d'in jikinta alarms d'in suka yi shiru. Ya juya ya sata a reverse sannan ya bar cikin parking lot d'in da dukkan saurin da zai iya, ya canja gear jiki zuwa ta farko sannan ya shiga canja k'afarsa daga wajen clutch zuwa danna accelerator da sauri, hakan yasa motar ta cilla kan hanyar da zata kaishi main gate d'in fita daga wajen cikin wata irin k'ara data dauki hankalin gabadaya mutanen dake wajen, amma bai damu ba, burinsa kawai a lokacin tayoyin su cigaba da cillawa dashi zuwa inda hankali da ruhinsa ya tafi. Ya canja gear zuwa ta biyu sanda yasha kwanar data hau dashi kan titi, ya sake danne accelerator sannan ya maida gear zuwa uku, injin motar yayi wani irin kuka kamar shima yana fad'in amincewarsa game da yadda motar ke tashi akan titi. Maganganun jaamil suka karad'e kunnensa kamar daga cikin speakers d'in motar suke fitowa. "Bama buk'atar wani b'ata lokaci, ina tunanin komai zai gamu a yau..... sai mu nemi hanyar kuma da zaka rabu da ita cikin sauqi. Naani tace abinda muka yi ba kuskure bane, sai dai garaje....munyi garajen yanke hukuncin cewa ka aureta.... Ya kalli agogon kan dashbord d'in motar, minti uku ta wuce tun sanda jaamil yake fad'a masa wad'annan maganganun, minti uku ya k'ara akan halin da Sa'adha ke ciki a yanzu, yaji kamar ya cillar da motar ya fita yabi iska amma ya kasa saboda ya riga ya d'auki hankalin mutane da yawa kuma kowa na kallonsa. Yayi ta kurd'awa ta tsakanin motoci baya ko lura da ihun horn d'in da ake danna masa da kuma yadda hannuwa suke fitowa ta window alamun zagi, kwakwalwarsa kawai aunawa take da tunanin hanyar da ta rage a gabansa kafin ya isa ga Sa'adha, wani irin abu mai zafi ya yanke kwakwalwarsa da tunanin wane hali take ciki yanzu, meke faruwa da ita ko kuma me ya riga ya faru? Yayi rantsuwa a zuciyarsa tafi cikin k'irga cewa in har wani abu ya sameta, sai ya dagargaza ruhin jaamil, sai ya dagargaza shi yadda ba zai sake amfanuwa ba tunda har zai iya yanke wani abin a cikin al'amarinsu ba tare da shawararsa ba. Ya sake danna pedal d'in k'asan k'arfasa da k'arfi sannan ya tura gear zuwa ta hud'u, RPM d'in motar ya tafi zuwa wajen Eight thousand, motar ta sake cillawa saman titi. Zai isa wajen Sa'adha ba tare da komai ya faru ba, ya cigaba da gayawa zuciyarsa da fatan zata fahimta ta rage k'arfin bugawar da take yi, ba abin da zai same ta, ba'a yanzu zamansu zai zo k'arshe ba...komai zai cigaba zuwa tsawon watanni kamar yadda tunaninsa ya tsara tun farko. Ya danne clutch d'in motar da k'arfi sannan ya maida gear zuwa biyar, motar ta k'ara gudu akan mahaukacin wanda take yi da farko, ya dinga wuce motoci da ginunnukan da suka zama blur a idonsa. Daga can gaba idonsa ya hango masa wani had'dd'en traffic na jerin motocin da basa ko motsawa, taraffic a wannan lokacin? taya zai zauna yana jira alhalin bai san halin da Sa'adha ke ciki ba? kowanne wucewar second d'aya ji yake kamar lattin awanni yake yi. Kawai sai ya maida gear zuwa uku sannan ya juya kan motar cikin wani irin sauri ya shiga wata kwana daga gefensa, bai tab'a bin hanyar ba kuma bashi da tabbas d'in inda zata kaishi, yayi ta binta kawai yana yin kwanoni lokacin da mutane da yara ke ta gudu suna matsawa gefe don kar ya buge su. A haka ya samu ya lalubo wata hanyar data maida shi kan titi, yana fahimtar inda yake ya sake danna accelerator k'asa, ya d'ane kan titin tare da tura clutch sannan ya maida gear zuwa hud'u. Ya dinga wuce shaguna da mutane a hanya suna ta harkokinsu ba tare da sanin had'arin dake faruwa gaba dasu kad'an ba. Idonsa ya kai kan wani sign dake jikin street d'in da yake kai, few more minutes! ya sake fad'awa zuciyarsa, few more minutes suka rage ya k'arasa wajen Sa'adha, a da in yazo wajen gani yake kamar ya zo gida ne, amma a yanzu titin ya k'ara yi masa tsawo, yaga kamar ba hanyar da ya sani bace, sai da kwakwalwarsa ta jiyo masa bugun zuciyar Sa'adha sannan ya tabbatar hanya daidai yake bi, wani irin releif ya sauka a jikinsa, releif sosai da yasa zuciyarsa matsewa cikin zafi...sai dai bugun zuciyar tata was weak, bata bugawa a normal rate d'in data saba. Me ya same ta? Har ya k'araso kwanar gidansa bai rage gudun motar ba, sai da yazo dab! da kwanar sannan ya taka birki da k'arfi motar tayi sliding sideways ta shiga kwanar. Tun daga nesa idonsa ya hango masa malam Aminu ya bud'e kofar gate d'aya kamar yana gyara wani abu, ya danna masa horn wanda ya karad'e layin gabadaya, yana d'agowa yaga shine yayi sauri ya rarumi d'aya kofar ya bud'e, da kyar Imran ya iya tsaida motar sanda ya shiga cikin gidan, 'yan inches ne kawai suka rabata daga hawa balcony da zai kaika k'ofar falo. In one swift move ya tura k'ofar motar da kad'an ya rage ta b'alle daga hinges dinta, ya nufi kofar falon ya b'alle handle d'inta don ba zai iya tsayawa bud'ewa ba. K'ofar na wangalewa idonsa ya gane masa abinda yake tsoro, abinda zuciyarsa ke taraddadin faruwa, yaji yaji dukkan jijiyoyin jikinsa sun tsaya cak da aiki, bugun zuciyarsa ma ya d'auke na wani lokaci...idanunsa suka tsaya akan abinda ke gabansa. Wani dunkulallen haske dake lilo a iska, haskensa ya tarwatse ya baje ko'ina a cikin falon, daga k'asa kuma jikin inuwarsa, wani tambari ne ya fito, tambari irin na adon sarautarta! ●﹏● WAYE SHI? AYSHA SHAFI'EE 40 (☆_☆) Imran ya tattaro dukkan wani ragowar k'arfi na jikinsa ya k'ifta idanunsa a hankali sanda wannan hasken ya d'auke cikin abinda baifi second d'aya ba, daga shi har inuwarsa suka dunk'ule suka bi cikin iska. Yana taka k'afarsa cikin falon, k'amshin wani daddad'an turaren wuta ya shiga hancinsa ba tare da shawara ba, gidan yana nan kamar yadda yake a kullum, komai zaune a muhallinsa cikin gyara tsaf! sannan shiru babu alamun wani abu mai rai a cikinsa, tunani kala-kala suka karad'e kwakwalwarsa a lokaci d'aya, yaji kamar ya ture bagwayen gidan, koina ya fito a lokaci d'aya. Zai iya yiwuwa Sa'adha na d'aya daga cikin d'akunan a wani irin hali, watakila tayi ihu da kuka har ta gaji maigadi ba jiyota ba tunda yana can bakin gate, watakila tana dunk'ule a waje daya cikin muryarta ta dashe cikin mawuyacin hali... watakila kuma abinda ya faru da ita ya shafe duk wani hasashensa. Ba abinda bai kawo ba cikin zuciyarsa kafin ya isa k'ofar d'akin da yake iya jiyo bugun zuciyarta a hankali kamar irin bugawar zuciyar jariri, ba tare da wani tunani ba ya buga k'ofar d'akin da karfi ta bud'e. Kunnensa ya jiyo masa k'arar shak'ar numfashi cikin tsoro kafin idanunsa su gane masa Sa'adhan, tsaye cikin wata had'dd'iyar riga royal blue data wuce gwiwarta kad'an, gashin kanta a tufke cikin bun sannan hannunta rike da kunnenta na hagu tana mak'ala wasu 'yan kananan silver d'ankunne. Cikin giftawar abinda bai kai second d'aya ba, Imran ya manta duk wasu rules na mu'amalar d'an adam yayi appearing a kusa da ita, Idanunta suka zare cike da tsoro tana kallonsa. "Yanzu ka dawo? me ya faru...?" "Sa'adha me ya same ki? me ya faru.?" Tambayoyinsu suka had'e a lokaci guda hakan yasa kowannensu yayi shiru, ta had'iye yawu tana kallonsa kafin ita ta fara magana. "Ba abinda ya same ni, me ya faru?" Maimakon ya bata amsa sai kawai ya shiga lalubar gabad'aya jikinta kamar me neman wani abu daya rasa. "Me ya faru ne? me ya same ni?" Ta sake tambaya muryarta na shaida alamun tsoro. Ya cigaba da duba koina a jikinta yana yayyage rigar wajen da duk hannunsa ba zai iya kaiwa ba. Nanne taji zuciyarta ta cika da wani irin tsoro, hannayenta suka shiga rawa, meke faruwa? meya same shi? ko kuma ita me ya sameta yake nema a jikinta. Tasa hannayenta duk biyu ta rike nasa sanda yake kok'arin yage d'aya kafad'ar rigar, wanda ya zama shi kad'aine abinda ya rik'e ta a jikinta, ta kalli idanunsa sosai sannan tace. "Me ya faru dan Allah? meya same ni? in bruises d'in nan kake nema gabad'aya sun tafi, dama na gaya maka baza su dad'e ba, guda d'aya ne kawai ya rage a nan..." Ta k'arasa tana nuna masa k'asan hab'arta, ya d'ora hannunsa a wajen sannan ya zamo dashi kan k'irjinta daidai saitin zuciyarta, yayi shiru kamar yana sauraren wani abu sannan a hankali da muryarsa mai zurfi yace. "Me ya sami zuciyarki?" "Huh? zuciyata kuma?" ta tambaya blankly tana kallonsa. "Bayan na fita wani yazo?" Ga mamakinsa sai yaga tayi murmushi mai fad'i sannan tace. "Su Aunty ne suka zo, su wajen biyar baka ji dad'in dana ji ba wallahi, harfa dasu Amina da Rahma, su basu dad'e ma da tafiya ba..." Jin haka yasa yayi saurin katseta. "Yanzu suka tafi?" "Eh, baza sufi minti talatin ba dai..." Minti talatin, a cikin minti talatin komai zai iya faruwa ba tare da ta sani ba...sai ya juya da sauri ya bud'e wardrobe dinta, ya d'auko first kayan da hannunsa ya fara kaiwa yazo ya sasu a cikin hannunta. "Ki saka yanzu ki fito ina jiranki." Bai jira me zata ce ba ya juya ya koma main falon, ya tsaya daidai tsakiyar carpet d'in inda wannan hasken ya fito, hasken dake nuna cewar gabad'aya duk wani hoto na gidan ya riga ya baiyana ga Naani, ta riga ta ga komai a can wajenta, sai dai abinda bai tabbatar ba shine in har ta shafi jikin sa'adha, zata iya yin komai ta gama cikin abinda baifi minti biyu bama amma in har hakan ne ba lallai yazo ya sami Sa'adha a yadda take yanzu ba. "Na shirya, ina zamu je?" Ya juya ya kalleta, ta saka wata doguwar riga ta atamfa mai kyau da mayafinta sky blue, gloss d'in da ta saka a bakinta mai kyalli ya taimaka wajen haska manyan kyan fuskarta, tana kallonsa da idanunta so innocent masu d'auke da tsantsar sonsa. Ya Allah! taya zai iya bari a cutar da wannan halittar ta dalilinsa. Har ta bishi cikin mota suka hau titi suka bar gidan, baice mata komai ba itama ka bata k'ara tambaya ba, don ko maigadi baiyi tambaya akan yadda ya shigo gidan d'azu ba, watakila fuskarsa ta nuna musu alamun rashin son magana a lokacin. "Da ka shigo falo d'azu kaga wani abu?" Sa'adha ta katse shirun motar sanda suka hau kan main titi, a lokaci d'aya ya d'auke idonsa daga kan titin ya kalleta. "Wani abu me?" zuciyarsa cike take da fatan amsarta ta zama sab'anin tunaninsa. ilai kuwa! "Wani abu ne kamar k'adangare kamar tsaka ya mak'ale a jikin taga muka yita korarsa ni dasu Rahma yak'i tafiya." Yaji zuciyarsa ta fad'a can k'arshen k'irjinsa, kamar ka cilla katon dutse cikin rijiya mai zurfi kana kallon tafiyarsa har lokacin da zai daki ruwan ya nutse, abinda suka gani ba k'adangare bane balle tsaka, d'aya daga cikin hakiman Naani ne, kuma in har sunzo gidan tun kafin tafiyar su Rahma kenan sun dad'e kenan. Dole ne akwai wani abu da ya sami Sa'adha wanda daga shi har ita basu sani ba. "Ina zamu je?" Muryarta a hankali ta k'ara tambaya, ba tare da tunanin komai ba ya bata amsa. "Asibiti." Can d'in suka nufa, don in har bashi da tabass d'in abinda ya faru, dole neya sami mafita a yanzu, Sa'adha bil'adama ce, kuma jikinta irin na mutane ne, don haka in har wani abu ya canja a jikinta, asibiti zasu iya ganewa duk da ya san cewa baza su tab'a iya gano musabbabin abinda ya sameta d'in ba. "Asibiti? waye bashi da lafiya? na fad'a maka ba abinda ya sameni..." "Shshshsh...." Yayi saurin katseta a k'asan numfashinsa ba tare da ya d'auke idonsa daga titi ba. Allah ya sani baya son magana a lokacin don abubuwa ne da yawa ke tarawa da d'ebewa a cikin zuciyarsa, sai akayi sa'a itama ta fahimci hakan bata k'ara magana ba. Wani private hospital ya kaita, irin k'ananan asibitocin nan masu jiran suci kud'in patients. Yace a mata general check-up na komai da komai a jikinta, aka yanka masa kud'i ya biya, sannan suka shiga da ita. Ya samu waje a waiting area d'in da ba kowa ya zauna jira, a lokacin ne jaamil ya turo glass door d'in ya shigo cikin siffar wannan matashin. Imran bai ko d'ago da kansa ba har ya zauna a kusa da shi, jikinsa ya riga ya bashi cewa d'an uwansa ne wanda ba mutum ba. Ransa ya k'ara b'aci akan wanda yake a da, bai taba jin haushin jaamil kamar yanzu ba. Don me yasa zai tafi ya cigaba da abubuwa ba tare da saninsa ba, me yasa har Naani ta dawo bai sanar dashi ba? ta yaya ma ta dawo? a yadda lissafinsu yake ai har yanzu suna da kusan watanni biyu a gaba. "Me ya same ta?" jaamil ya tambaya shima ba tare da ya kalle shi ba. Bai ko nuna alamun yaji shi balle yayi niyyar bashi amsa, yana zaune perfectly still, ya dunk'ule yatsunsa na hannu d'aya akan bakinsa, kamar yadda dutse ke zama stiff a waje d'aya babu ko alamun fitar numfashi a tare dashi. "Na san laifina kake gani a yanzu yarima, amma dan Allah ka saurare ni, ka san ba zanyi komai don na b'ata maka rai ba." Imran bashi da niyyar magana saboda ya cigaba da cewa. "Ranar da na koma muzaffar, ranar bwama ta same ni da zancen cewa sun sami labari Naani zata fito a daren, ban yarda da zancenta saboda a yadda Ma'amun ya shaida min lokacin dawowarta bai yi ba. Sai dai abinda nima ya bani mamaki shine a wannan daren Naani ta dawo d'in kuma ban sami ganinta ba har kwanaki biyu, saboda a washegari ta zauna da mukkarrabanta kan matsalolin da suka faru bayan bata nan, saboda haka sai a rana ta biyu na same ta. Tun kafin in fad'a mata komai yarima ta riga ta san zancen da zan gaya mata, ta riga taga komai ta san dukkan abinda muka aikata, sannan ta shaida min cewa abinda muka yi ba laifi bane, sai dai nayi garajen yanke hukuncin cewa ka aure ta, tace da ka cigaba da zuwa duk sanda ciwon ya tashi kana kwantar dashi da hakan yafi, amma na fada mata cewa kana loosing k'arfi ne da yawa duk sanda kayi hakan kuma baka iya maida hankali akan abinda ke gabanmu. Saboda haka tace min zata cire ruhin daga jikinta sannan mu san hanyar da zaka rabu da ita ba tare da bil'adama sunyi wani tunanin ba a cikin abinda bai kai wata daya ba. Don tace lokacin da take jira yana k'aratowa kuma har yanzu bamu cimma manufar ba. Naso sanar da kai hakan a washegari amma sai ciwon bwama ya sake tashi saboda haka ban sami kaina ba sai a yau da Naani ta sake kirana, nayi directing haskenta zuwa gidan da kuke. Amma banyi tunanin cewa raba jikinta da ruhin zai iya tab'a matsalarta ba yarima, saboda ni shaida ne akan wahalar da nasha kafin na iya juya zuciyar mahaifinta zuwa son yi mata aure yanzu, naga irin tarin k'aunar da iyayenta da 'yan uwanta ke mata, ba zanso ace cikin sati d'aya kawai mun yi mata lahani ba. Sai dai tunda har an cire...." "Ba abinda aka cire." ●﹏● WAYE SHI? AYSHA SHAFI'EE 41 (☆_☆) "....Amma banyi tunanin cewa raba jikinta da ruhin zai iya tab'a matsalarta ba yarima, saboda ni shaida ne akan wahalar da nasha kafin na iya juya zuciyar mahaifinta zuwa son yi mata aure yanzu, naga irin tarin k'aunar da iyayenta da 'yan uwanta ke mata, ba zanso ace cikin sati d'aya kawai mun yi mata lahani ba. Sai dai tunda har an cire...." "Ba abinda aka cire." Muryar Imran ta katse shi cikin kaushi. Ya juyo ya kalle shi har yanzu yana zaune so stiff ha tare alamar motsi ba, fuskarsa fayau take babu wani yanayin da zaka iya tsinta a ciki. "Kamar yaya? Na tabbatar... "Na sani..." Imran d'in ya sake katse shi. "...hasken yaje har gidan, amma ba abinda ya faru." jaamil ya cigaba kallonsa mamaki na nunawa akan fuskarsa ko kuma rashin yarda ne? "Amma ta yaya toh..." "Nima ban sani ba." Dukkaninsu suka yi shiru na wani lokaci kafin jaamil ya sake juyowa ya tambaye shi. "Toh me kake yi anan?" "Bugun zuciyarta ne baya bugawa daidai, I wanted to be sure saboda in nemo me ya same ta." "Look yarima, na san cewa a idon mutane yanzu yarinyar nan matarka ce, amma ya kamata ka dinga tunawa kanka matsayinta a gurinka, matsayin da nan da wani lokaci zai shafe, saboda haka bai kamata ka d'auki lamarinta da girma haka ba, ni na zata wani abu ya sameta ne da na ganka anan, amma canjawar bugun zuciyarta kawai shi zai sa ka rud'e da tunanin zaka tafi neman me ya sameta? Ka manta da abinda yake gabanmu ne? ko ka manta rantsuwar da ka min na cewa ba son yarinyar nan kake ba kuma intrest d'in da kake dashi akanta ya riga ya tafi, ita kanta Naani da wannan kalaman naka ta dogara bata yi fushi damu akan abinda muka yi ba, ta yarda cewa tunda har baka son yarinyar, rabuwarku ba zata sa ka kasa cigaba da abinda muka fara ba...amma yanzu canjawar bugun zuciyarta kad'ai yasa ka a wannan halin me zai faru kuma ranar da ka rabu da ita?" "So, wannan shine jaamil d'in?" Muryar Nanne tasa kowannensu ya d'ago da kansa cikin wani irin sauri suka kalleta, tana tsaye d'an taku kad'an daga gabansu tayi folding hannayenta a k'irji. A lokaci d'aya Imran ya mik'e yaje kusa da ita. "Me suka ce?" Ta d'an kalle shi ta gefen ido amma hankalinta na kan jaamil wanda ya sandare a wajen da tsananin mamakin yadda akayi ta sanshi, ta san sunansa...for real? kenan Allah kad'ai ya san adadin sauran abubuwan da Imran ya fad'a mata, dole ne ya damu da lafiyarta ashe. His sharing a part of him with her! "Allaura biyar fa aka min, kuma a hannu d'aya wai duk test ne." Muryarta mai dad'i ta fad'a tana nunawa Imran hannunta. Jaamil yaji wani abu mai kama da tausayinta a cikin zuciyarsa, tana cikin wani sirad'i mai had'ari amma bata sani ba. Her voice was innocent! Imran ya murza 'yan yatsun nata yana fad'a mata wani abu da bai maida hankali yaji ba, sannan yayi kissing saman goshinta, ta ture shi a hankali tana murmushi. "Naji dadin ganinka Jaamil, ka taimake shi don har na fara tunanin ko bashi da freinds ko d'aya." Jaamil ya juya ya kalli Imran, da ido yayi masa alamun zaiyi masa bayani daga baya, saboda haka ya kalleta yace. "Nine da laifi amarya, kamata yayi inzo har gida in gaishe ki amma na d'anyi tafiya ne." "Tafiya?" Ta juya ta kalli Imran. "Bai fad'a ba kuma." Kafin Imran d'in yayi magana wata Nurse ta k'araso tace da Sa'adha likitan da zai fad'a musu result d'in tests d'in na jiranta, tare da Imran suka tafi bayan ta rok'i jaamil akan kar ya tafi. Ba yadda ya iya haka ya zauna har suka fito, daga nan suka koma gida. Inda sa'adha ta rik'e shi da hira da d'awainiyarta har sai bayan sallar maghriba sannan ya samu ya tafi, Imran na tayi masa dariyar yadda a dole yau yaci abincin da Sa'adha ta tarkata masa kala-kala, tun yana iya ci har sai da ya fito k'iri-k'iri ya gaya mata ya k'oshi sannan ta daina kawo layin cimar da bai tab'a ci ba kala-kala. Imran ya gaya masa cewa ta tambaye shi su waye freinds d'insa ne shi kuma ya rasa sanda bakinsa ya furta mata sunansa, amma ya tabbatar masa bayan hakan babu wani abu nasa data sani. Bayan jaamil ya tafi, ya taya ta suka yi tarin wanke-wanken data tara, zuciyarsa cike da farin cikin irin karb'ar da ta yiwa jaamil, yaji dama yana da wasu 'yan uwan da zasu taya shi ganin kyautatawar matarsa, saboda itama tana masa tambayoyin da suka shafi 'yan uwansa amma bata cika matsawa sosai ba. Zuciyarta a kullum tana danganta shine da abubuwa masu kyau kawai, alhalin shi d'in akasin hakan ne a wajenta. Ya tuno bayanin likitan nan da yake gaya musu cewar komai a jikinta lafiya k'alau yake, kawai bugun zuciyarta ne ya ragu kuma shima 'yan dalilan dake sashi ba masu k'arfi bane. Hankalinsa ya kwanta a lokacin amma tunanin abinda zai faru nan gaba kuma yazo ya rugurza komai. Don kamar yadda jaamil ya fad'a masa ne kafin ya tafi, rashin jin komai da suka yi daga wajen Naani ba lafiya bane, dole akwai wani dalilin da har haskenta ya shigo gidan amma bai iya tab'a Sa'adha ba, don haka dole suyi tsammanin jiran koma meye a yanzu. "What's with d'ankwalin kanki yau?" Ya tambayeta da daddare lokacin da suke zaune a falo, ya d'auko system d'insa yana k'arasa wani kwantan aikinsa dake ciki, ita kuma tana gefensa tana b'are tulin maggin da take tarawa a cikin wata jar, idonta na kan tv tana kallon wani tsohon indian film da wata channel ke nunawa. Ta kai hannu ta tab'a d'ankwalin kamar tana so ta tabbatar in yana nan d'in. "Aunty maryamah tace in daina zama ba d'ankwali." Ya juyo ya kalleta. "Saboda me." Tayi shiru kamar ba zata fad'a ba sannan ta kalle shi tace. "Wai saboda aljanu zasu iya shiga jikina." Yadda tayi maganar ya bashi dariya kamar itama bata yarda da abinda ta fad'a ba, yayi murmushi a k'asan numfashinsa sannan ya jawota jikinsa. "Aljanu kike tsoro?" Ta girgiza kanta. "Su suke fad'a dai, bana fad'a maka wasu malamai sunce har bak'ak'en aljanu ne wai suke son shiga jikina ba." Har yanzu da murmushin a fuskarsa yace. "Duk ki rabu da wannan zancen Noory, in dai har kina tare dani ba aljanin daya isa ya shiga jikinki... babu shi a duniyar nan!" Ta d'ora idanunta sosai a kansa. "Ta yaya ka san hakan?" Ya kai hannunsa a hankali ya cire d'ankwalin sannan ya cusa yatsunsa ya warware bun d'in da tayi da gashinta. "Saboda su kansu Aljanun suna tsoron irin jinsi na Sa'adha." Kanta ya d'aure da mamaki. "Wane irin jinsi ne kai d'in?" Ya tura kansa gefen wuyanta yana shak'ar dadd'an k'amshin shampoo d'inta kafin ya amsa. "Jinsina na masu yawan addu'a mana." Tana jin hakan mamakin fuskarta ya kwance, sannan murmushi ya maye gurbinsa. ******* K'ARFE BIYU DA RABI. K'arfe biyu da rabi na daren wannan ranar abinda Imran ke tsammanin jira ya faru! ●﹏● WAYE SHI? AYSHA SHAFI"EE 42 Wannan chapter ta k'unshi zallar bayani na abubuwa da yawa da muke son kwancewa daga farkon labarin nan. (☆_☆) MUZAFFAR! Ta tsirawa taswirar fuskarta ido ta cikin garai-garai d'in ruwan dake wucewa a gabanta. Watakila ta shafe awanni biyar zaune a wajen koma fiye da hakan, ba zata iya tantancewa ba, don dad'ewarta a wajen ba damuwarta bane, fatanta kawai abinda  take zaman jira ya k'araso, ya k'araso gareta ta sashi a idonta ko ta samu nauyin dake zuciyarta ya kauce, wani nauyi daya taru tun tsawon shekara guda data wuce. Tana zaune ne a bakin wani rafi, ta d'age rigarta kad'an ta zira k'afafunta ciki, sunkuyawar da tayi ta zura hannuta yasa dogon gashinta ya bita cikin ruwan, yana motsawa a hankali tare da gudunsa, sannan daga kowanne gefe na lambun tarin hadimanta ne ke tsaye suna gadinta. Duwarta ta fara ne tun lokacin da YARIMA ya bar cikin duniyarta da niyyar yiwa Naani wani aiki da har yau bata san mene ne ba, bayani d'aya kawai ta sani wanda ya fad'a mata kafin tafiyarsa na cewar sai tayi hak'urin jure rashinsa don ba zata iya ko jin muryarsa ba daga can inda ya tafi d'in, a lokacin komai zai kasance ne cikin watanni hud'u kawai, amma a yanzu, shekara d'aya itace k'irgen da kowa keyi na tsawon tafiyarsa. Tayi hak'urin har ya k'are ta sake lalubo wani ta d'ora ya cigaba cinyeta, cinye siffar da take mutuk'ar so a rayuwarta. Idonta ya sake kaiwa kan ruwan, watak'ila da ita bil'adama ce da in ta samu biyan buk'atunta nan gaba kad'an hankalinta ya kwanta da sai jikin ya koma yadda yake, amma abu ne da ta san ba zai tab'a faruwa ba wanda ya tafi ya riga ya tafi kenan! A tsawon rayuwarta ba abinda take mutuk'ar k'auna irin siffar bil'adama da kuma son shiga cikinsu, amma sai ya zama kamar abubuwa da yawa a rayuwar tata, Naani tayi mata katanga dashi akan dalilin da ta san ba zai rasa nasaba da d'aya tilo da idonta kad'ai ke gani ba. Gata d'aya da tayi mata shine mayar da jikinta da tayi ya koma irin na bil'adaman, wani abu da ita kad'ai ke dashi a duk fad'in nahiyarsu. Amma duk da haka ta k'udirce a zuciyarta cewa sai ta fanshe duk wata wahala data sha a wajen dukkaninsu, duk wanda keda hannu a cikin bak'in cikin data tashi dashi. Mussaman shi yariman, wani halitta data tsana fiye da kowa a rayuwarta, ta tsane shi tun lokacin da hankalinta ya iya banbance tarin k'aunar da Naani ke masa akanta, Bata tab'a ganin Uwar dake fifita d'an wani sama da nata ba irin tata uwar, ita kad'aice 'yarta a duniyar nan, amma hankalinta da tunaninta baya tab'a zama akanta, ita d'in koyaushe tana zuwa ta uku ne a jerin al'amuranta. YARIMA DA JAAMIL sune sunayen data tsana fiye da komai a rayuwarta, kuma sunayen data yi alkawarin sai ta kawar dasu a duniyar nan, sai ta zama ajalinsu, ta yadda dukkan wani abu da Naani ke shirin mallaka musu zai dawo gareta, ya zama dukkan tanadin da take shirya musu ya k'are akanta, yadda bayan taga hakan itama daga baya ta kashe ta. Ta dad'e da tsara wannan shirin a cikin kanta, abu d'aya ne ta tsaida faruwarsa har yanzu, shine tafiyar yarima, domin komai zai fara ne bayan ya aureta. Shi yasa a yanzu take zaman jiran wannan nauyin zuciyar tata ya kauce! "Ranki ya dad'e sak'on ya iso...yarima ya shigo cikin masarauta yanzu." Wata hadima daya shigo lambun a daidai wannan lokacin ta fad'a kanta a k'asa. A hankali wani murmushi ya sauka a gefen kumatun SAREEFA, wani murmushin da tayi tanadinsa tsawon shekara guda! Lokacin data k'arasa cikin masarauta, komai ya canja...a jiya ne kad'ai Naani ta sanar da zuwansa amma a jiya kad'ai aka canja fasalin komai gabad'aya. K'erarren ginin masarautar yana tsaye kyam! cikin wata irin k'awa da ado na alfarma, an canja launin kalarsa zuwa kalar rawaya da fari, yanayin lokacin yamma ne mai cike da lumshi da kuma iska mai dad'i, amma duk da haka tsuntsaye ne birjik! tun daga hanya sunyi rumfa da fuka-fukansu cikin wani tsari mai ban sha'awa, sannan ga tarin halittu nan taf! jinsi kala-kala suna durfafin isowarsa, ko'ina ka juya fuskoki ne cikin farin ciki, ga kuma tashin wani kid'a mai dad'i dake tashi a ko'ina. Zuciyar Sareefa ta matse ganin irin tarin k'aunar dake fuskokinsu, a dawowarta na k'arshe masarautar, bata samu koda rabin wannan tarbar daga wajen kowa ba, hatta daga Naani kuwa saboda ta tabbata k'awata masarautar ma anyi ne bisa umarninta. A ranta ta ayyana cewa saura lokacin kad'an duk wannan ikon ya dawo mallakinta, ta tsaida hadimanta daga bin bayanta sannan tabi iskar wajen ta baiyana a cikin masarautar! ******* Imran na tafe cikin siffar da al'ummar nahiyarsa suka sanshi a matsayin YARIMA, a gefensa jaamil ne shima cikin ainihin tasa siffar suna ratsawa ta cikin tarin halittun da suka yi durfafin ganinsa, kowannensu cike da farin cikin ganinsa bayan wani tsawon lokaci. Nan d'in shine k'asarsa, mahaifarsa inda jinsinsa da duk wani gatansa yake, kuma ya saba da rayuwa a cikinsa tun zamanin k'uruciyarsa, ya saba da wannan matsayin da ake bashi sannan ya saba da wannan yanayin da jikinsa ke ciki, amma a yanzu ji yake komai ya dawo masa sabo, kamar ansa wani abu an goge wani waje a kwakwalwarsa da yayi saving duk memories d'insa na baya. Gani yake kamar shi d'in a yanzu baqo ne, komai ya canja masa, komai d'in da baya tunanin d'imbun halittun dake gabansa sun fahimta, koma jaamil dake gefensa, don watakila canjin da yake ji yafi nasaba ne da cikin zuciyarsa, wadda bata tare dasu a lokacin, tunaninsa ya koma can nahiyar da ya baro kusan awanni uku baya, k'irgawa yake cewa Sa'adha ta kusa tashi a yanzu, tunda ya saka mata Alarm a sabuwar wayar daya kawo mata wanda zai tashe ta sallar Asuba. Yafi sau d'ari a cikin zuciyarsa yana hasko yadda yanayinta zai kasance in ta farka bata ganshi ba, kowanne reaction na duniyar nan ya d'ora akan fuskarta amma ba wanda ya gamsar dashi cewa hakan zata yi. Sweatheart, Wani uzuri ne ya taso min urgently kina bacci, i'll be back soon! don't panic dan Allah, zanyi miki bayanin komai in na dawo kinji? I love you... ...like crazy! Ya tuno d'an k'aramin note d'in da yayi scrambling a papers wajen hamsin ya ajiye a kusan koina na gidan daya san idonta zai kai. kusa da pillow, kofar toilet, kan slippers d'inta, kan fanfon sink, kan kujera, kan dining table, kan drawers d'in kitchen, kan gas, kan sink, da duk wani waje daya san zata yi amfani dashi, he wanted to make sure hankalinta bai tashi ba ta fahimci uzurinsa. "Da alama al'amarin ba zai kasance yadda muke tunani ba, tunda da tayi fushi sosai, ba zata sanar da al'ummah ba har ayi wannan taron." Jaamil ya fad'a lokacin da suke takawa cikin hanyar da zata kaisu ga fadar Naani. "Na san koma meye ta riga ta samu hanyar da za'a magance shi yanzu, saboda haka ka yiwa Allah yarima ka karb'i dukkan wani abu da zai faru a yanzu da hannu biyu." Kamar yadda tun lokacin da yazo masa da saqon neman da Naani ke musu wajen k'arfe biyu da rabi na dare baice komai ba, haka ma yanzu baiyi magana ba har suka kai ga cikin tamfatsetsiyar fadar, da bata da wani fasali da kwakwalwar mutum zata iya fahimta. Suna isa ciki, jaamil ya nufi wajen mahaifiyarsa 'Bwama' da ya hango a gefe, a sannan ne kuma idanun Imran suka hango masa Sareefa tsaye daga gaban karagar Naani cikin siffarta ta bil'adama, bai tab'a d'aukan yanayinta da daraja ba irin yanzu, a da baya ko damuwa yaga banbancin siffarta da tasu don a tunaninsa son da takewa bil'adama shirme ne, matsayin da Allah ya basu ya isa rayuwarsu ba sai sun kwatanta dana bil'adama ba. Amma a yanzu, gani yake sareefa ta yiwa dukkan al'ummar daya had'u dasu zarra a idanunsa, kamar tana tuna masa cewa zai koma wajen Sa'adha ne nan da k'ank'anin lokaci. Kafin ya k'arasa tunaninsa ta baiyana a gabansa sannan cikin sauri ta rungume shi. "Maraba da sauka yarima, maraba, maraba...nayi kewarka fiye da tunanin duk wata halittar Allah." Muryarta ta fad'a a cikin jikinsa. Imran yaji jikinta yayi k'arfi a cikin hannayensa, ya saba da irin wannan rungumar tata a baya sau da yawa, amma yanzu daya saba da jikin Sa'adha na mutane, sai yaji kamar yana rik'e da dutse ne. "Da kinyi kewata da yawa, da na dinga samun sak'on ki akai-akai wajen jaamil." Ya fad'a sanda ya matsar da ita daga jikin nasa, idonta ya nuna rashin gaskiya kafin tace. "Kullum ya dawo zai koma wajenka, sai na tare shi da saqona, watakila shine baya fad'a maka." Rashin gaskiyarta ya fito k'arara har a muryarta, sai kawai yayi murmushi yana kallonta. "Ka canja yarima, ka canja sosai ka k'ara kyau fiye da baya, watakila duk inda kake ba a cikin wahala kake ba." "Babu wahala ko kad'an, na saba da komai kuma ina ji ma kamar..." Bai k'arasa ba ta katse shi, muryarta cike da mamaki. "Me ya sami ruhinka? me ya sami b'arin ruhinka?" Yaso ya manta ne sareefa tana da baiwar ganin duk wani abu dake jikin wata halitta ta duniya, bama iya jinsinsu kad'ai ba. "Akwai matsala tare da jikinka, ta yaya kake iya rayuwa da b'ari d'aya kad'ai? kuma d'aya b'arin baya kusa da kai?" Ya lumshe idanunsa a hankali. Yana kusa dani sareefa! Sa'adha tana kusa dani! ******* "Me ake ciki game da aikin da ya kaika..." Muryar ta fito cikin kaushi kamar kodayaushe tare da amo mai girgizarwa, a yanzu da ya dad'e bai jita ba, sai yake jin kamar sautin ta yana tab'owa ne har k'asan zuciyarsa. don yana iya jin yadda zuciyar tasa ke amsawa. Imran ya d'ago da idonsa ya kalli hallitar dake zaune a gabansa, wata halitta data zama gata da tallafin rayuwarsa, a kullum ya d'aga ido ya kalleta sai yaji girma da matsayinta ya k'aru a idonsa, ya gyara murya a hankali sannan yace. "Komai ya kammala Naani, a yanzu haka muna jiran wani taro ne da za'ayi na cikar kamfanin shekaru Ashirin. Na tabbatar a wannan lokacin buqatarmu zata biya, tunda a yanzu haka ya riga ya amince dani yadda ba wani abu da ake zartawa a kamfanin ba tare da umarni na ba. Shi yasa a lokacin da jaamil ya fad'a min lokacin fitowarki, nayi tunanin zamu kammala komai kafin nan." "Komai yana nufin har da matsalar data k'aru bayan bana nan?" Muryar tasa tsigar jikinsa mik'ewa, bata danganta abin da laifinsa ba saboda haka ya samu kwarin gwiwar bada amsa. "Matsalar data faru Naani wani tsautsayi ne da yafi k'arfin mu, shi yasa muka yi amfani da hanyar da iya tunaninmu ya bamu kawai wajen neman mafita, amma koda mun samu buqatar data kaini cikin bil'adama, zamu jira ne har ki dawo, don ba wanda zai iya raba ruhin da jikinta." "Na samu labarin komai tun ina can, kuma na shaidawa jaamil cewa abinda kuka yi garaje ne, akwai hanyoyi da yawa da za'a sami mafita bayan cewa ka aureta, saboda a kowacce halitta aure ba k'aramin zance bane, tunda yanzu in har zaka rabu da ita, sai a nemi wata hanyar da zamu shafe batunka daga tunanin duk wani bil'adaman daya shaida aurenku, wanda hakan ba k'aramin aiki bane. Sannan nayi k'okarin b'oye wannan zancen daga wajen sareefa, don na sani baza ta tab'a jin dad'i ba, taji kayi aure acan koda na wucin gadi ne, bayan tsawon jiran da take yi maka anan." Imran ya had'iye yawu jin hakan, zancen aurensa da sareefa ba sabon abu bane, amma a yanzu da yaji shi sai yake tunanin wane irin tunani ne dashi a da? ta yaya ya yarda da auren sareefa alhali bai tab'a sonta ba? da baije cikin mutane ya had'u da Sa'adha ba haka zai rayu kenan bai taba sanin mene ne so ba? "Aiki ya riga ya zama guda biyu a yanzu, zan raba yarinyar da ruhinka sannan a fara k'ok'arin hanyar da zaka rabu da ita, abinda na gayawa jaamil kenan, kuma a jiya na duba yarinyar a cikin haskena, sai dai abinda na gani Yarima ya wuce tunaninku." Sai a sannan ya d'ago da idonsa ya kalleta, kwarjinin siffarta ya cika kowacce gab'a ta jikinsa. "Ruhinka ya riga ya had'u da jikinta sosai, ba zan iya raba shi tun daga nan ba, dole ne ka kawo yarinyar nan!" Gabansa ta fad'i a lokaci guda, zancen ya masa girma. "Ta yaya hakan zai yiwu Naani? ta yaya zan iya kawo ta cikinmu? har yanzu bata san ni WAYE ba." Shiru ya biyo baya kafin ta amsa. "Ba abu ne mai wuya ba, zamu iya komai mu gama har ka maida ita cikin abinda baifi awa biyar ba, sai dai kawai zata fita daga haiyacinta ne." Sa'adha ta fita daga haiyacinta? Shine zaisa ta fita daga haiyacinta? Ta yaya zai iya hakan? "Da bakinka ka shaida min cewa ba son yarinyar kake ba, kuma jaamil ma ya tabbatar mun da kyar ka yarda ka aureta, toh me ya kawo tunani yanzu fuskarka?" Ya had'iye yawu a hankali, abu na k'arshe da zaiso a yanzu shine Naani ta fahimci wata matsalar daga wajensa, ita d'in wata halitta ce da duk duniyar nan bashi da kamar ta, kuma baya jin zai tab'a sab'a mata a rayuwarsa. "Ina tunanin yadda hakan zai kasance ne." "Zuwa nan da sati d'aya, zan sanar da kai lokacin da zaka kawota, kafin nan ka cigaba da dukkan harkokinka, komai ya kusa zuwa k'arshe ka dawo cikin rayuwarka, ina baka hak'urin dukkan wahalhalun daka sha." Daga haka ya san maganarta ta k'are kenan ta sallame shi. A yanzu zai iya komawa wajen Sa'adha, can nahiyar da rabin ruhinsa yake, don ji yake kamar a takure yake yanzu, ta yaya ne wai ya iya rayuwa shekara da shekaru a wannan wajen? Ya tattara dukkan zancen da suka yi a yanzu ya tura can k'arshen zuciyarsa, ba zai bi ta kansa a yanzu ba, sai ya koma inda hankalinsa zai kwanta tukunna, inda zaiyi tunanin wata mafitar ba wannan ba, don ba zai tab'a iya cutar da Sa'adha da hannunsa ba. Bayan ya fita jaamil ya shiga kamar yadda Naani ta umarta, sai dai k'afafunsa suka kasa barin wajen, yaji ba zai iya motsawa zuwa koina ba in dai har ba barin wajen zaiyi gabad'aya ba saboda haka ya tsaya anan yana jiran fitowar jaamil, don ba zai iya komawa cikin tarin al'ummar dake jiran fitowarsa avwaje shi kad'ai ba. A lokacin ne kuma kunnensa ya jiyo masa muryar Naani daga ciki. "Ka tabbatar Yarima ya bar wajen?" "Na tabbatar ranki ya dad'e." jaamil ya amsa. "Zan fad'a maka wani abu ne dana kasa gayawa masa, don yau shine rana ta farko a rayuwarsa da ya fara min k'arya, shi yasa nima ya zama rana ta farko dana fara b'oye masa gaskiyar lamari na. Saboda haka ina so kai ka bani had'in kai mu k'arashe abinda kuka fara, wanda shine dalilin dawowata da wuri." Imran yaji mamaki ya sark'e kafafunsa dake rik'e dashi a wajen, abinda yake ji wani abu ne da bai tab'a zatonsa daga wajen Naani ba, Muryar ta cigaba da shiga kunnensa. "Abinda kuka yi babbar matsala ce da zata iya jawo tab'arb'arewar komai a cikin rayuwarmu gabad'aya, amma nayi shiru ban fad'a muku bane saboda ina tunanin duka zan samu had'in kanku mu shawo kan matsalar,    don haka ko ban sami amincewar yarima ba, kai ka saurareni da kyau kaji abinda zan fad'a maka. Dalilin da yasa ban iya raba ruhinsa da jikin yarinyar a jiya ba shine ruhin ya riga ya kusa had'ewa da nata, ba zai tab'a yiwuwa a raba su ba kuma a sami dukkaninsu, dole sai an rasa d'aya. Ko dai in an raba su a sami na yarinyar a rasa na yarima, ko kuma a rasa yarinyar a sami nasa, kuma daga yadda na karance shi, ya riga ya gina wata alaqa da yarinyar da ba zai so ya rasa ta ba, kuma ka san cewa idan har babu cikakken ruhinsa a tare dashi burinmu ba zai tab'a cika ba. Saboda haka na yanke shawarar zamu cire ruhin nasa koda kuwa yarinyar zata mutu. Nayi masa bayani akasin naka, kuma zan gaya masa ranar da zai kawo ta nan, idan har mun gama komai sauran abubuwan zasu zo da sauqi tunda in har ta mutu, danginta ma zasu karbi hakan ba tare da wata matsala ba!" ●﹏● Akwai lauje da yawa a cikin nad'i game da chapter nan. Da farko munji irin tunanin Sareefa akan Imran...na irin kishin da take yi akan yadda Naani ke fifita shi akanta. Ga ainihin gaskiyar dalilin da yasa take son aurensa ka kuma son kasancewarta bil'adama, me kuke tunani zai faru in har ta san Imran cikin mutane yaje? Kuna tunanin cewa da gaske Naani tana son Imran ne kamar yadda kowa da kuma shi kansa yake gani? Me zai faru a yanzu da ya san ainihin abinda zai faru ga Sa'adha? **** WAYE SHI? AYSHA SHAFI'EE 43 (☆_☆) "Munyi waya dasu Inna, kowa yace a gaishe ka." Nanne ta fad'a tsaye a gaban Imran wanda yake zaune a hannun kujerar falo, kusan awarsa guda kenan da dawowa gidan amma banda waya ba abinda yake yi, zata iya k'irgawa yayi waya da kusan mutane sun kai goma kuma duk daga kamfaninsu, umarni yake ta bayarwa na yadda zasu k'arashe ayyuka kala-kala sannan a lokaci guda kuma kamar yana neman izinin wani abu daga wajen wasu manyansa. Bata san meya faru ba ko kuma me yake faruwa ba tun jiya da ya dawo a gigice, lokacin da yake tambayarta me ya sami zuciyarta da kuma sanda ya kaita asibiti, ita ta san ba abinda ya same ta amma daga yadda taga ya damu, sai zuciyar tata ta fara kokwanton ko dai akwai abinda ya same ta ne, tunda sau da yawa a gida ma inna ce ke fara gane rashin lafiyarta kafin ita ta fahimta, musamman in zata yi zazzab'i. Amma tunda likitan nan ya tabbatar musu da cewa a yadda suka aunata bugun zuciyarta ne kawai ya sauka k'asa kad'an mamaki ya kamata...ta yaya Imran ya iya gane hakan? ta yaya mutum zai iya gane abinda ya sami zuciyar wani ba tare da an gwada ba? tayi tunanin zaiyi mata wani bayani bayan sun dawo amma taga ya d'auko aiki a computer ya fara, kuma daga yanayin fuskarsa tunda yamman ta fahimci baya buqatar yawan magana saboda haka tayi shiru da tunanin zasu yi maganar washegari. Sai gashi ta tashi baya nan sai tulin takardunsa a ko'ina, notes d'in da basu nuna mata ainihin lokacin daya bar gidan ba, tunda wajen k'arfe biyu na dare ma ta farka ta ganshi a kusa da ita. Yanzu kuma k'arfe tara na safe ya dawo da alamun gajiya fal! a tattare dashi amma tun shigowarsa  daya zauna a hannun kujera bai tashi ba, danne-danne kawai yake yi a waya yana lalubo numbobin mutane. Duk abinda tazo ta gaya masa sai yace mata yana zuwa, sai dai har ta gama dukkan harkokinta bashi da alamun tashi daga wajen. Saboda haka tazo ta tsaya a gabansa da sak'on dake cin zuciyarta tun tashinta a yau da suka yi waya da dasu Inna, Sadiq ta fara kira kasancewar number Innan a kashe take, suka gaisa dasu Surrayya abin mamaki harda Aunty Amarya da kuma Salim, amma banda Suraj uban 'yan cusguna, wanda ta tabbatar kuma yana tare dasu a lokacin, a hanyar kaiwa Inna wayar ya had'u da Mama Azumi itama suka gaisa, a cikin d'akin Inna kuma Mama halime taje gaisheta itama ta karb'i wayar, daga k'arshe tana jin muryar Inna hawaye ne suka fara zubo mata, masu d'umi da bata san tayi tanadinsu ba sai a lokacin. Imran ya kamo hannunta a hankali yana cigaba da aika message d'in da yake a waya, sai da ya tura sannan ya d'ago da kansa daga kan screen d'in ya kalle ta. Nanne taji numfashi ya zarce cikin makogwaronta, ta gagara janye idanunta daga cikin nasa, wanda dogwayen gashin jikinsu yayi musu rumfa, hakan yasa a kullum suke da wani irin yanayi dake tsaida tunaninta, yanzu kuma da yake cikin damuwa sai suka juye zuwa kamar na mai jin bacci, ko kuma wanda ake cewa drunken eyes d'innan, D'an tafiyar da yayi kawai tsakanin tashinta da yanzu taji tayi kewarsa fiye da zatonta. Mata nawa ne wai a duniya suke yin sa'a irin tata? "Ina amsawa sosai Noory, yau kika kirasu?" Muryarsa a hankali ta fita, kamar wani mai jinya, dole akwai wani abu daya same shi wanda ya kamata ta sani. "Eh, d'azu muka gaisa dasu harda su mama halime, kowa na gaishe ka." "Nima ina gaishe su, duk da ina jin gobe ma zamu je muyi musu sallama." Mamaki ya fito a fuskarta sosai. "Sallama? wani wajen zamu je?" Ya murza 'yan yatsunta a hankali. "Wani wajen nake tunanin zamu je, but I'm not yet sure Sa'adha, na kasa tsaida tunani na waje d'aya...abubuwa da yawa sun had'e min a cikin kaina, and It's like I'm scared of all of them!" Tayi shiru tana juya zancen nasa, kamar lokuta da yawa a baya, bata cika fahimtar duka maganganunsa ba. "Me yake faruwa toh? na zata zaka min bayani tun jiya da muka dawo shi yasa ban tambayeka ba, gashi kaima kuma ka canja tun jiyan, kamar baka da lafiya, me ya faru?" Taga giftawar wani abu a cikin idonsa kafin ya sunkuyar da kansa kan hannunta ya murza shi a hankali, Sau da yawa tasha tunanin ko Imran jinin sarauta ne, yadda yake abubuwa cike da isa, magana misali...kamar ka'ida ne yin shirunsa kafin ya amsa. A cikin tunaninta taji ya janyo kafad'unta k'asa, ya durk'usar da gwiwoyinta a gabansa, sannan ya kalle ta sosai, kamar yana shirin fad'a mata wani babban Secret na rayuwarsa. "Na tab'a fad'a miki cewa hannunki na da laushi?" "Me yasa kake son canja zancen? ka gaya mun da Allah inda zamu je.." Ta fad'a da murmushi tana kwace hannayen nata. "Ni wa? Sa'adha ban tab'a ji fa kin kira suna na ba, ko sunan nawa bashi da dad'i ne?" Ta kalle shi sosai. "So kake in dinga fad'ar sunanka?" "A'ah..."  Ya sake kamo hannun nata. "...So nake ki samo wani sunan mai dad'i ki dinga kirana dashi, yadda zan san duk duniya sunana daban ne a wajenki." Ta shiga motsi da yatsunta dake k'asan nashi, tun da take a rayuwarta bata tab'a ganin mutumin da a duniya bakinta ke mutuwa a gabansa ba irin  Imran, kowa ya riga ya san halinta, sau da yawa bakinta ke bada amsa ba tare da kwakwalwarta tayi nazari ba, amma in a gabansa take sai ta biya zance a cikin zuciyarta sannan ta fad'e shi. Yanzu daya tsireta da wad'annan lumsassun idanun nasa so yake ta shiga jero masa sunayen da zata dinga kiransa dasu kenan? don ba d'aya bane balle biyu, suna nan da yawa ta tara su a kanta sai dai ta rasa hanyar da zata fara fad'a ne. Ya sunkuyo da fuskarsa dab da tata, sannan a hankali cikin husky muryarsa yace da ita. "Bari in shirya habibty zanyi miki bayanin komai insha Allah." Kalaman sun fito ne kamar yana jin tsoronsu. Zuciyarta ta buga a hankali, ta d'ago da idonta ta kalle shi, tsinin hancinsa ya sauka a gefen nata sannan numfashinsu suka had'e waje d'aya. "Kin dafa wani abu yau?" K'amshin bakinsa na fresh mint ya hura akan lips d'inta, oh God! this felt so good, taji dama su tsaya a haka tsawon awanni, ta girgiza kanta a hankali wanda hakan yasa hancinsa yayi grazing akan nata, Adam's apple d'insa ya motsa sama da k'asa kafin yace. "Toh kina da ragowar na jiya? yunwa nake ji." Dad'in maganarsa ya rungume zuciyarta, ya mamaye kowanne lungu da saqo na cikin kanta, tayi murmushi mai fad'i tana kallon cikin idonsa. "Sai kace dan Allah tukunna." Sai ya d'an karkata kansa dab da kunnenta na dama, ya sauke muryasa can k'asa sosai yace. "Dan Allah... iya d'an malam!" Ta kyalkyale da dariya jin dad'i kafin ta zare hannunta daga nasa, sannan ta mik'e ta nufi kitchen. k'asa-k'asa yabi takun k'afafunta da kallo, rangad'ed'an jan k'unshin bikinta har yanzu bai gama fita ba. Zuciyarsa ta matse da tunanin yadda nan da d'an k'ank'anin lokaci zai karya tata zuciyar da mummunan labarinsa a cikin kwanakin da ya kamata su zama na farin cikin rayuwarta, kwanakin da ko lallen bikinta bai gama fita ba. ●﹏● WAYE SHI? AYSHA SHAFI'EE 44 (☆_☆) Tun shigowarsa gidan, tunaninsa cike yake da abubuwa biyu da yake ta k'ok'arin daurewa, Rud'ani da kuma tashin hankali, yana cikin ryud'anin kalaman da jaamil ya gaya masa tun a Muzzaffar, lokacin da ya shak'e shi a jikin bangon fadar Naani bayan fitowarsa. "Me ya same ka ne yarima? me ya shiga kwakwalwarka? wannan dalilin shi yasa Naani tak'i gaya maka ainihin abinda zai faru, yanzu kuma da ka jiyewa kunnenka me ya kamata kayi? kamata yayi ka shak'e ni kana zargin harda ni za'a kasheta? ita wace ce a wajena ko wajenka? kar ka manta fa ta shigo cikin rayuwarka ne saboda kuskuren da kayi tun farko, kuma nine sanadin da yasa ka same ta. Sanadin da muka yi na k'arya wanda zai k'are nan da wani k'ank'anin lokaci, nan wajen shine rayuwarka yarima, anan danginka da duk wani tallafinka yake, can d'in da kake hangowa wani abu ne da ba zai tab'a d'orewa ba. Ya kamata ka janyo hankalinka daga duk inda ya tafi, nida Naani da kake tunanin zamu yi maka ba daidai ba mune sanadin duk wani abu daka samu a can, don ba don Naani ba babu ta yadda zaka iya samun jikin bil'adaman da zaka iya rayuwa a cikinsu, ba don ni ba kuma babu ta yadda zaka yi ka samu yarinyar a matsayin matarka. Kaje cikinsu ne don aikin da Naani ta saka, ba don ka gina wata rayuwar da a yanzu kake mana kallon wad'anda zasu kwace ta ba, karka manta ko an cire ruhinka daga jikinta kuma ta rayu ba zai tab'a yiwuwa ka cigaba da zama da ita ba. Mun tsara hakan tun lokacin dana same ka da zancen ka aure ta kuma ka tabbatar min da zaka bada had'in kanka mu gyara kuskuren daka jawo tun farko. Ko sau d'aya zuciyata bata tab'a yarda da zancenka na cewar baka son yarinyar ba amma nak'i nuna maka ne saboda na san bani da wata mafitar data wuce wannan a lokacin, sannan nayi zaton idan komai yazo k'arshe zaka iya daure zuciyarka mu k'arasa abinda ya kaimu tun farko wato aikin Naani, nayi zaton zaka daure zuciyarka ka farantawa halittar data tallafe ka har ka kai wannan matsayin da kake a yau, na zata zaka iya daurewa zuciyarka kamar sauran abubuwa da yawa a baya da muka sadaukar don samun farin cikinta...amma ban san cewa ka raba zuciyar taka gida biyu ba, ban san cewa ka bawa yarinyar irin matsayin da kake bawa Naani ba, ban san kuma cewa zaka iya had'a Naani da wata k'ask'antacciyar halittar..." Imran ya tuna marin daya d'auke fuskarsa dashi a lokacin har saida jini ya fito ta idonsa, sannan a hankali muryarsa tace. "Sunanta Sa'adha, ka sake kiranta da k'ask'antaciyar halitta ko sau d'aya ne kaga yadda zanyi kaca-kaca da fuskarka." ya fad'a kamar iya abinda yaji yace kenan. Jaamil yasa hannu ya shafo jinin daya fito sannan ya d'ago ya kalle shi, baice komai ba sai ajiyar zuciya kawai da yake fitarwa kamar yana son danne wata zuciyar dake gaya masa cewa ya rama. Imran ya sake shi sannan ya matsa baya yana cigaba da kallonsa. Ya riga ya sani, duk abubuwan daya fad'a gaskiya ne haka suka tsara tun farko, sai dai a yanzu baya jin zai cigaba da biyewa wannan gaskiyar, don zuciyarsa ta riga ta yadda da wata gaskiyar da yake ganin duk duniya babu wata halittar data isa ta kore hakan, gaskiyar cewa yana son Sa'adha kuma ba wani abu da zai bari ya shiga tsakaninsa da ita ko ya kawo k'arshen zamansu. Aikin da Naani ta tura shi cikin bil'adama ba zai yiwu ba sai da b'arin ruhinsa wanda yake jikin Sa'adha, abinda suke kwad'ayin samu kenan da har suke ikirarin zasu fitar dashi unrespect of duk wani hali da Noorynsa zata shiga. Amma yadda ya tsaya a wajen nan, ya d'aukarwa kansa alk'awarin cewa abinda su Naani ke shirin yi ba zai tab'a faruwa ba, zai kare Sa'adha da dukkan iyawarsa, zai d'auke ta zuwa wajen da d'ayansu ba zai tab'a ganota ba har sai ya sami hanyar da zai iya kawowa Naani abinda take buqata zuwa nan da wata biyun da komai zai faru, zai nemo yadda zaiyi ya iya rik'e DUTSEN NIL da b'arin ruhinsa guda d'ayan ba tare da na jikin Sa'adha ba, zai nemo dukkan k'arfin da zai iya kawo shi har gaban Naani, In ta samu abinda take so ya san zata barshi ya samu damar da zai iya k'arasa rayuwarsa ba tare da takurawar d'ayansu ba. Don a yanzu ya riga ya yarda cewa dukkan wani farin cikinsa yana tare da Sa'adha ne, ba zai tab'a iya sake dawowa cikin su ya cigaba da rayuwa ba, zai zauna cigaba da zama a matsayin bil'adama koda Naani baza ta cigaba da tallafarsa ba, koda kuwa hakan zai zama sillar rasa ransa! Ya taka k'afafunsa baya a hankali yana cigaba da kallon jaamil kafin ya juya da sauri da niyyar barin wajen. Daga can gabansa tarin cinkoson al'umma ne taf! dake jiran fitowarsa, amma bai damu ba, zai wuce ta cikinsu ya koma wajen Sa'adha tun kafin Naani ta samu labarin abinda ya faru yanzu tsakaninsa da jaamil. "Do you think she wants you!?..." Muryar Jaamil ta tsaida shi cak! a wajen. "Bata san WAYE kai ba yarima, bata san ainihin waye kai ba, labarin wani Imran kawai ta sani, wanda babu shi a duniyar nan...akwai tarin dalilan da zasu k'alubalanci zamanku ko daga 'yan uwanta. Idan kana son shirmen daka tsara a cikin kanka ya cigaba da faruwa dole sai ka sami had'in kanta tukunna wanda ba zai tab'a faruwa ba, daga lokacin da ka gaya mata gaskiya daga lokacin zata rabu da kai, saboda ba kai take so ba, Imran d'in da muka yi planting akanta ta sani kuma shi kad'ai take so!" Wannan zancen shi ya kawo tashin hankalin tunaninsa na biyu, don gaskiyane Sa'adha bata san ainihin waye shi ba kuma bashi da tabbas cewa in har ta sani d'in zata cigaba da bashi trust d'in da yake samu a wajenta, saboda haka bashi da zab'i a yanzu illa ya fad'a mata gaskiyar da yake ta yiwa ado da k'arya, in ba haka ba dukkan wani abu daya tsara ba zai tab'a yiwuwa ba. Komai ya riga yazo k'arshe, kuma amsar da zai samu a wajenta ita zata yi determining k'addarar da zata faru nan gaba a rayuwarsa! "Toh wanne zaka fara, wankan ko cin abincin?" Ya d'ago idonsa ya kalleta tsaye daga jikin dining area, sannan tarin warmers d'in dake zube a gefenta.! Yaya rayuwarsa zata kasance bayan yau? Me zai faru dashi anjima? Zai sake ganin irin wannan kulawar ta Sa'adha? Zai sake ganin irin wannan kallon daga gareta? Ya Allah! ***** "Me kika dafa mana?" Ya fad'a sanda yaja kujera d'aya ya zauna, Nanne ta fito daga kitchen rike da cups a hannunta ta kalle shi, ya canja kayansa zuwa wata jallabiya mai kyau light brown. K'amshin turaren jikinsa ya had'e dana sabulun da yayi wanka. "Me kika dafa Noory?" Muryarsa can k'asa ta sake fitowa yadda duk sanda yayi hakan yake sata jin wani iri. Me yasa ne muryarsa take da tasiri akanta? Ta matso kusa dashi ta bud'e warmers d'in, k'amshin wani abu curry, albasa da kayan k'amshi ya cika hancinsa, bai san cewa da gaske yana jin yunwa ba sai a lokacin don hargitsin dake cikin kansa yasa ya manta da sunan wani abu abinci, kuma a d'azu ya fad'a ne kawai don d'auke lokacinta daga amsarsa sa da take jira, don yana fatan kowanne k'arin lokaci ya taho masa da k'arin karfin gwiwa. Ta zuba abincin a plate d'aya kamar yadda suke ci a koyaushe, yadda ya koya mata sannan ta zauna, a lokacin ya lura cewa akwai abinda yake damunta, idanunta sun nuna masa hakan duk da irin k'okarin da take na kar ya gane. Shigarta ta dark purple kaya ya mata kyau sosai, duhun kayan ya k'ara fito da hasken fatarta da a yanzu ta zama So fresh mai laushi, d'ankwalin kanta ya zame kad'an yadda yana iya hango lallausar sumar kanta, bak'a wuluk sai shek'i take yi, yaji yana son zura hannayensa ciki yadda zasu lume cikin laushin gashin, ya salam! ya janye idonsa daha kanta da sauri don idan ya cigaba da kallonta zai iya mance duk wani abu dake gabansa a yanzu ya jawo ta zuwa jikinsa. "Duk sanda nake cin abincinki Noory sai inyi ta mamakin me nake ci ne a baya." Ta d'age gira d'aya tana kallonsa. "For example kinga irin wannan abincin, a kwakwalwata gabad'aya babu irin tunaninsa, ban san ana yi irin su ma ba balle inje in siya." "Irin wanne kake ci toh?" "Sau da yawa nafi shan tea ko duk wani abu cereal, amma duk ranar da zanyi girki, to ba wuce taliya ko farar shinkafa...shi yasa a yanzu nake mamakin yadda akayi na rayu a baya." Ta d'anyi murmushi kad'an. "Kuma kin san duk sanda zanyi girki ban fiye amfani da plate ba?" "A tukunya kake ci kenan?" Ya d'aga kansa ya na kallonta. "Kuma akan wuta, saboda in nazo d'and'anawa inji ko ya dafu, full cokali nake d'iba kuma sai in d'and'ana fiye da sau ashirin..." Dariya ta kamata a lokaci d'aya. "Ashirin fa? ai ka cinye abincin." "Kamar kin sani, in na gama sai in ganshi d'an kad'an a tukunya, gashi kuma ni na kusa k'oshi...kinga ba amfanin plate kenan, sai kawai in k'arashe abuna da serving spoon d'in dana fara ci." Nanne ta kyalkyale da dariya tana rufe bakinta, ya lumshe idanunsa a hankali yana kallon yadda take dariyar sosai. She's so innocent! mintuna kad'an tana cikin damuwar da har fuskarta ta nuna yanzu kuma ta koma farin ciki, yaji kamar ya jawo ta ya rungume ta sannan ya b'oye ta daga dukkan wani hargitsin dake gabansu. Idanunsa na kanta gabad'aya ranar, yana kallon dukkan activities d'inta kamar yana yi musu kallon karshe, bai san me zai faru ba, so he wanted to capture every single memory of her, yadda daga baya zai samu abinda zai rarrashi zuciyarsa kafin sanda da zata yi rauni ta karye gabad'aya. A lokacin da ya dawo daga sallar maghriba, a sannan ya zab'i lokacin ya zama sanadin k'addarar rayuwarsa, ya zaunar da ita a falo lokacin da ta kawo masa yankakkun fruits masu sanyi a cikin bowl, ya zaunar da ita a gaban zuciyarsa dake bugawa kamar zata fito waje. Ya zaunar da ita don gaya mata gaskiyar WAYE SHI! ●﹏● I promise ba wani kewaye-kewaye, chapter k'asa tazo da direct bayanin WAYE IMRAN, and d intresting part...daga bakinsa zamu ji komai...!😀 ***** WAYE SHI? AYSHA SHAFI'EE 45 (☆_☆) "Sa'adha kin san a yanzu ke matata ce koh?" Nanne ta d'aga kai a hankali tana kallonsa, ya sake damk'e hannuta a cikin nasa kafin ya cigaba. "Kin san kuma cewa babu wani secret tsakanin mata da miji koh? tun daga ranar da aka d'aura mana aure komai namu ya zama d'aya, walau farin ciki ko bak'in ciki bai kamata d'ayan mu ya b'oye wa d'aya ba..." Yayi shiru tare da yin ajiyar zuciya yana kallon hannusa dake sarke nata, zuciyarsa na tattaro dukkan kalaman da yayi bitarsu  fiye da kirgen mai kiga. Yayin da Nanne ta cigaba da kallonsa blankly tana jiran taji abinda yake shirin fad'a mata, taji dalilin da yasa yake cikin damuwa kwana biyu. "Ina so ki fahimce ni sosai a yanzu, ki bud'e kwakwalwarki ki fahimce ni dan Allah...Sa'adha na miki wani babban laifi tun daga farkon had'uwata dake har zuwa yanzu, nayi miki laifi dake dasu Baffa dama duk wanda ya san labarin auren mu..nayi muku laifin da za'a iya kira da yaudara koma wani abu fiye da hakan." Zuciyarta ta buga amma a hankali sakamakon mamaki daya zagaye tunaninta a lokaci d'aya. Laifi kuma? wane irin yaudara? Ya sake wata dogowar ajiyar zuciyarsa yana kallon carpet d'in da suke kai unseeingly, sannan ya cije gefen lebb'ensa kamar zai datsa shi. Lokacin daya d'ago da kansa, yanayin idanunsa sun canja daga haske zuwa wata kala da tayi kama da silver, wani abu da Nanne bata tab'a gani ba. "Sa'adha ni ba irin jinsin halittarki bane, I'm not human.!" Ya fad'i kalaman da dukkan wata dauriyarsa yana cije bakinsa kamar baya son su fito, don ba don tana kusa dashi sosai bama ba lallai bane taji me ya fad'a ba. Ya cigaba da kallonta da idanunsa so stiff a kanta, yana karantar yadda fuskarta take absorbing kalaman, bata ce komai ba? me take tunani? anya kuwa taji abinda ya fad'a? ya tsirawa idanunta ido bada ko k'iftawa ba amma ya kasa tsinto wata ma'ana guda d'aya a cikinsu, they were blank! watakila can k'asansu lullube yake da tarin tsoro, watakila kuma tana tattara dukkan k'arfinta ne waje d'aya yadda zata kwalla ihu a kowanne lokaci. Wani abu mai kama da lokaci ya tsaya cak! a cikin kan Nanne, ta maimata abinda ya fad'a a cikin kanta sau ba adadi, tana rarraba su filla-filla don ta nemo real ma'anarsu. "Kai ba mutum bane?" She tried the words out, ko zata ji ma'anar ta fito akan lebb'enta amma ta gagara fahimtarsu, sai mamakin yadda harafan suka had'u suka yi forming sentence d'in. "Yes, I'm an illusionist, wata halittar daban da taku." Ta tsira masa ido tunaninta baya aiki a lokacin, shima kallonta yake da idanunsa a tsaye kyam! zata iya rantsewa tunda take dashi bata tab'a ganinsa so serieos irin yanzu ba, taji tana nutsewa cikin a idanun nasa zuwa wani k'arshe mai nisa, miles and miles away! amma duk nisan da ta kai ta kasa gano ma'anar abinda ya fad'a. "Okay." Ta fad'a a hankali cike da mamakin yadda muryarta ta fito so calm, watakila don tunaninta ya riga tsaya ne a lokacin. "What?" Ya fad'a a fili yana kallonta, gaya mata yayi fa shi ba mutum bane and the best amsar data samo shine Okay? "Sa'adha ki fahimce abinda nace kuwa?" Ta girgiza kanta da sauri. "Ban gane ba Imran, ban gane me kake nufi ba." Da gaske ya yarda bata gane d'in ba, don tunda yake da ita bai tab'a jin ta fad'i sunansa ba sai yanzu. Zuciyarsa ta cika da wani sabon hope d'in daya manta yaushe rabon da yaji irinsa, ya sake damk'e hannunta kamar yana tsoron zata iya kwacewa a kowanne lokaci ta gudu. "Ki kwantar da hankalinki kinji? zanyi miki bayanin komai tun daga farko...you don't have to talk." Ta had'iye wani katon abu a mak'ogwaronta tana kallonsa da idanunta so wide kamar zasu fito. "Ni ba mutum bane Sa'adha..." Ya sake maimata abinda bata ganewa. "...na fito daga jinsin wata halitta da ake kira ALBIE, na san baki tab'a jin koda irin sunan ba, saboda bama shigowa cikin bil'adama mu'amalarmu tafi yawa ne tare da Aljanu wanda sune 'yan uwan halittarmu, duk da cewa akwai tarin banbanci tsakanin halittarmu da tasu." Nanne bata san ko akwai iskar dake fita da a kirjinta ba koma tana iya numfashi ba a lokacin, kwakwalwarta ta riga ta gama cakud'ewa, da kyar ta iya maida tunaninta kan muryarsa dake cigaba da magana. "Aljanu basu da jiki amma mu muna dashi, suna iya shiga jikin bil'adama mu kuma bama iyawa ba tare da bin wata hanyar ba, sannan jinsin Aljanu yana da yawa a doron k'asa yayin da mu kuma 'yan kad'an ne a duniya, bamu da yawa sosai. Sannan akwai abubuwa da yawa wanda muka fip aljanu k'arfin yi, sai dai kamar yadda mutane suka fisu daraja haka suma suka fimu daraja saboda suna iya mu'amala dasu, mu kuma bama iyawa Wasu daga cikin mutane da suke da sani akan aljanu da rabe-rabensu su sun san wani abu game damu amma ba komai ba, kuma suna danganta mune da jinsin bak'ak'en aljanu tunda sun san muna posessing wasu abubuwan da aljanun basa iyawa sai dai manyansu. Akwai wajaje da yawa a duniya inda irin jinsinmu suke rayuwa, amma sunan nahiyar dana fito 'Muzzaffar" "Ta yaya...." Muryarta fito daga can k'asan makogwaronta amma yayi saurin katseta. "Shshshsh... you don't have to talk remember?" Ta d'aga kanta a hankali, har yanzu hannayenta na cikin nasa. "Kin tuna abinda na fad'a miki ranar da aka kawo ki gidan nan? every single word a lokacin gaskiya ne Sa'adha, tun da na tashi a rayuwata ban tab'a sanin iyayena ba, sun rasu tun kafin in san kaina, haka kuma bani da wani dan'uwa na jini dana sani, duk sun mutu a wani yak'i daya had'amu da wasu irin jinsinmu dake wata nahiyar. Na tashi babu gata a cikin wata irin rayuwar da babu komai a cikinta sai fafutukar neman yadda zan rayu, nayi bauta a wajen irin jinsinmu da yawa kafin daga bisani na koma bawan wani mai suna 'Darshan' na shekara uku a wajensa kafin daga baya ya tattara dukkan dukiyarsa da nufin komawa Muzaffar, don a lokacin muna wata nahiya ne da ake kira 'Sabeel'. Dukiyarsa ta had'a harda tarin bayinsa wanda yayi niyyar zuwa Muzaffar d'in ya sayar dasu da tsada, kuma a cikin bayin nasa har dani Sa'adha. Sai dai a ranar da muka shigo Muzaffar a daren ya rasu, lokacin yana kwance a d'akin hutawar daya kama na cikin kasuwar garin, mutuwarsa tasa kowa ya rud'e a wajen kasancewarsa baqo a gurin, a cikin wannan hayaniyar na samu na kwance sark'ar da aka d'aure ni na gudu. Na fad'a can cikin Nahiyar muzaffar na samu wani wajen da ba wanda ya san ni na cigaba da rayuwata. Kin tuna na fad'a miki na samu tallafin wata halitta bayan duk wahalhalun dana sha a baya? wannan halittar itace Naani, Shugabar Nahiyar Muzaffar, na had'u da ita ne lokacin dana rasa duk wani tallafi a rayuwa, ita ta rik'e ni da dukkan kulawarta, ta jawo ni jikinta, ta bud'e min sabuwar duniyar dana sami komai dana rasa a baya, 'yan uwa, d'aukaka, matsayi da kuma tarin abubuwan da a da nake musu hangen nesa. Ta maida ni tamkar d'anta ta lak'aba min sunan YARIMA. Nima a lokacin na d'auki dukkan soyayyata na dank'a mata, na yarda cewa bani da wani farin ciki a duniyar nan daya wuce nata, saboda haka duk wani abu daya zama na taimako gareta bana tab'a kasawa wajen aikata shi. Jaamil d'a ne a wajen 'yaruwarta kuma suna zaune su duka biyun a wajenta, tare dashi na taso a masarautar Naani, ya zama tamkar d'an uwa na kuma abokin da nake dashi duk duniyar nan. A cikin haka ne ta kirani da buqatarta na son samun wani dutse da take wanda za'ayi amfani dashi don samun k'arin kariya a nahiyarmu, ta shaida min a lokacin cewa dutsen yana hannun bil'adama ne a cikin wani kamfani da suka nannad'e shi a matsayin Award d'insu banda haka su basu san wani amfaninsa ba. Naani zata iya bani damar da zan shigo cikin mutane a dare d'aya in d'auko mata shi in koma, sai dai in muka yi hakan ba zai taba yi mana amfanin da muke so ba, dutsen yana aiki ne kawai ga duk wanda ya same shi ta tsaftatacciyar hanya, wato ko dai mai shi ya d'auka ya baka da yardarsa, ko ka same shi ta hanyar guminka ko kuma duk wata hanya da zata kawo shi hannunka da take mai tsafta. Saboda haka ta kira ni a lokacin ta gaya min cewa zata tura ni cikin mutane, inje wannan kamfanin a matsayin ma'aikaci, inyi aikin da zaisa har su yarda dani, wannan dutsen a matsayin Award ya shigo hannuna. Sa'adha tunda nake a da, ban tab'a bada hankalina akan sha'anin bil'adama ba, a kullum ina musu kallon wasu halittu dake can nesa damu wanda bamu da alaqa ko kad'an tare, a iya inda nake samun labarinsu shine in na shiga cikin Aljanu wanda su suka sansu sosai. Saboda haka a sanda ta fad'a min hakan, ban kawo komai a raina ba, naji a jikina ne cewa zanje inyi mata aiki kamar sauran dukkan ayyukan da take sani. A cikin abinda baifi wata biyu ba, Naani ta samar mana da jiki mai irin siffar mutanen da zamu shiga cikinsu nida jaamil tunda na gaya miki bama iya possesing siffar mutane, jaamil zai zama mai taimakamin a komai saboda haka Naani ta bashi damar da zai iya komawa ainihin halittarsa a kowanne lokaci kuma ya iya komawa Muzaffar, ni kuma bani da ikon yin hakan saboda kar hankalina ya rabu gida biyu. Naani ta had'a ni da wani aljanin daya karanci halayen mutane ya koya min abubuwa da yawa na mu'amalarsu da kuma yadda suke rayuwa. A lokacin na dinga jin kamar ba zan iya komai ba, don ganin rayuwarku nayi kamar irin tamu ta kurkuku, lokacin da za'a kulle ka a hana ka duk wani freedom na pissibilities d'inka. Amma tun daga ranar dana sauko cikin mutane Sa'adha, tun daga wannan ranar rayuwata ta canja, ta canja in a way da ban san ta yaya zan miki bayani ba, naji ne kawai kamar a dawo min da rayuwar dana rasa a baya, rayuwar da zanga iyayena da dukkan 'yan uwana. Naje kamfanin ni da jaamil nayi dukkan wasu cike-cike irin na mutane da Naani ta shaida min cewa an gama samo min aikin da komai kawai abinda zanyi kenan, daga nan muka tafi neman gida. Aka kaimu wani gida da ake masa gyara har na biya deposit, wannan gidan da yake layinku, inda na fara ganinki kin dawo daga islamiyya..." Ya d'anyi shiru kafin a hankali yace. "Kin tuna....?" Bata ce komai ba sai kallonsa da take kawai tana k'ifta ido, ya sa hannayensa biyu harda wanda yake had'e da nata yayi cupping fuskarta a tsakanin tafin hannun nasu. Numfashinta a lokacin fita yake tare da nasa cikin nutsuwa kamar sunyi setting d'insa a tare. Imran ya kalli cikin wad'annan chocolate idanun nata, cike suke da d'imbin tambayoyi da kuma confusion, It was the same experession da yake hangowa a cikin kansa zata yi tun ranar da aka d'aura musu aure. And as he stared into those deep brown eyes, ya gano banbancin tunaninsa da yanzu, a tunaninsa bayan duk wannan experessions d'in akwai tarin tsoro fal a cikinsu - amma a yanzu babu koda d'igon wannan tsoron, babu shi ko kad'an! "I can't go on...ki fad'a min me kike tunani dan Allah." Ta sake k'ifta idonta a hankali ba tare da tace komai ha, shima yayi shiru yana kallonta, he couldn't read her thoughts amma yana iya karantar abinda ke idonta clearly...tana cikin rud'ani kuma shima abinda yake ji kenan, sai dai yadda idanunta ke fluttering akansa yasa masa jin wata irin kasala a jikinsa, yaji d'umin  fuskarta dake cikin hannunsa yana tura wani abu kamar electricty a kowacce jijiya ta jikinsa, a cikin tunaninsa ya hango yadda zai iya sunkuyawa a hankali yaji d'umin dake kan lips d'inta. Yayi saurin k'ifta idonsa kafin yace. "I don't want you to be afraid... kar kiji tsorona Sa'adha dan Allah." Muryarsa mai taushi ta fito a hankali kamar cikin rok'o, amma shi kansa a lokacin ya san abinda ya fad'a bashi da ma'ana, abinda ya kamata taji kenen, TSORO. Taji tsoron shi d'in dake zaune a gabanta yana gaya mata cewa shi ba mutum bane, shi wata halittar ne daban sab'anin tata ta mutane. Nanne ta sake k'ifta idanunta a hankali tana kallonsa, his eyes were watching her, kyakkyawar fuskarsa kusa da tata sosai! kamata yayi ta fizge daga rik'onsa, tashi ta bar d'akin, ta bar gidan, ta bar unguwar ma gabad'aya, ta tafi duk wani waje da zai nesanta ta dashi. Imran yayi shiru yana jiran abinda zata ce, gabad'aya duk wasu senses na jikinsa su d'aure tamau wajen sauarenta, ji yake kamar yaune rana ta farko da zai fara jin muryarta, Idonsa ya d'auko masa sanda ta rufe idonta a hankali sannan ta matso da fuskarta cikin wuyansa. "I'm not afraid of you...!" ●﹏● Alhmdlilah 😃😃😃! yau kowannenmu zaiyi bacci da minshaaari...🤤🤤Imran ya fad'a mana WAYE SHI da bakinsa bana wani ba. I tynk abinda kowannenmu yake jira kenan daga tiltle d'in ma littafin...nd phewww! munji shi a yau.😍 Do you tynk d story ends here??? I say Nahh, yanzu ne wasu abubuwan zasu fara unfolding. Yanzu ne stanza littafin zata fara fitowa wato "Soyayya tsakanin mutum da wata halittar." Yanzu ne zamu ji dukkan wani abu daya shige mana duhu a labarin. Yanzu ne komai zai fito fili a fara battle d'in dake kwance a k'asa. Yanzu ne Imran zai fahimci ainihin intention d'in Naani akanshi, da gaske tana son shi ko kuwa akwai wata manufarta ta taimakonshi? Yanzu ne zamu ji in Imran zai gayawa Nanne irin had'arin dake gabanta. Yanzu ne zamu ji yadda za'ayi burin sareefa ya tabbata. Akwai abubuwa fa da yawa dake kudundune har yanzu.😃 Masu rok'ona kan cewar Imran ya zama mutum na san na karya zuciyarku yanzu...don haka ina baku hakuri kwando-kwando. Imran yace wai yaji a news cewa sugar yana kwantar da anger dake jikin mutum, zaku taimaka kusha wannan ko zamu samu fushin da kuke dani ya ragu...?😜😜🍫🍫🍫🍫 Thank you for the support on this story so far. I feel like with each chapter I become a better writer and if it wasn't for those of you who have been reading it and reviewing I probably would have never gotten this far!..🙏🏻 ***** WAYE SHI? AYSHA SHAFI'EE 46 (☆_☆) Nanne ta k'ifta idanunta a hankali tana kallonsa, his eyes were watching her, kyakkyawar fuskarsa kusa da tata sosai! kamata yayi ta fizge daga rik'onsa, ta tashi ta bar d'akin, ta bar gidan, ta bar unguwar ma gabad'aya, ta tafi duk wani waje da zai nesanta ta dashi. Amma ta kasa ko motsi, idanunta na kallon nasa wanda ke cike da  matsanancin rok'o irin na yaro k'arami sanda ya maka laifi, bayan hakan kuma akwai hanqoro na jiran abinda zata fad'a, a hankali ta shak'i sassanyan k'amshin dake fitowa daga jikinsa, wani k'amshi mai sanyi da dad'i, Taji zuciyarta na ayyana mata cewa k'amshin zai iya kwantar da hargitsin dake cikin kanta, saboda haka ta matsa a hankali ta cusa kanta cikin wuyansa sannan ta fad'i abinda yake gaskiyar zuciyarta. "I'm not afraid of you...!" Da gaske ne ko kad'an babu d'igon tsoronsa da kalamansa suka sa mata, sai dai tarin mamaki fal da kuma rud'ani, gani take yi kamar a mafarki ko labari ne kad'ai abinda yake gaya mata zai faru, ta ture tunanin dake shirin kawo mata tsoro ta janyo b'arin zuciyarta dake cike da tausayinsa, tausayin irin rayuwar bautar da yayi a baya, wani abu da kwakwalwarta ta kasa hasko mata. "I'm so sorry Noory, dan Allah kiyi hak'uri." Muryarsa ta fad'a daga saman kanta amma bata ce komai ba, sai yayi shiru  kamar me jira. Zuwa can ta d'ago da kanta ta kalle shi, idanunsa har a lokacin basu canja daga launin silver, Ta yaya ne suka koma haka? akwai tambayoyin da yawa a cikin kanta a lokacin, saboda haka ta saka wannan ma a cikin jerinsu. "Wace irin halitta ce ALBIE? ni ban tab'a jin sunan ba ko a tarihi." Ya kalleta sosai kafin ya amsa. "Akwai tarin jinsin halittun Ubangiji a duniyar nan Sa'adha wanda tunanin d'an Adam bai sansu ba. abinda kowa ya sani kawai sune manya-manyan halittun; Mutane, Aljanu, Tsirrai da kuma Dabbobi. Amma a k'arkashin kowannensu akwai jinsi kala-kala, idan kika d'auki dabba misali, akwai su da yawa, na k'asa da cikin ruwa, kuma ba kowanne irin jinsi kika sani a cikinsu ba ko aka ambata a alqur'ani ko hadisi, akwai wanda ma baza'a tab'a saninsa ba har duniyar ta ka're. Ko a cikin ku mutane akwai jinsin k'abilu fal! wanda ba wanda ya san yawansu kuma ba kowanne aka ambata ba, toh haka a cikin jinsin Aljanu ma akwai irinmu da yawa da ba kowa ya sani ba. Mu ba Aljanu bane amma za'a iya danganta jinsinmu dasu tunda bama cikin mutane ko dabbobi." "Kuma kuma musulmai ne?" Ya d'anyi guntun murmushi yana kallonta. "Yadda addini yake kala-kala a cikin mutane da aljanu, haka yake ma a wajenmu, bayan musulunci akwai wasu da yawa, sai dai a nahiyarmu, musuluncin shi yafi k'arfi." Tayi shiru tana motsa yatsunta a hankali kafin tayi tambayar da take ganin itace jigon komai. "Me yasa ka aure ni?" Ta fad'a tana kallon labulen dake can bayansu, it was difficult for her ta fad'i kalmar aure tsakaninsu a fili. "Saboda ina sonki Sa'adha." kalaman suka fito cikin muryarsa mai taushi, muryar da sai a yanzu Nanne ta lura cewa tayi dad'i da yawa ta kasance ta mutane. Mutane musamman maza basu da irin wannan taushi da zurfin muryar. It was so velvety-husky! Ta dawo da kallonta kan fuskarsa, cikin d'an guntun tunani tace. "Ban gane ba, nayi tunanin kazo yin aikin da aka turo ka ne ba wai kayi rayuwa a cikin mu ba." Yayi shiru kafin ya k'ifta idanunsa a hankali. "Ta yaya zan miki bayani ba tare da na tsorata ki ba..." Sanda ya fad'i hakan yaji hannunsa d'aya da baya rik'e da nata yayi sanyi, saboda haka ba tare da ya nemi izini ba ya lalubo d'aya hannun nata yayi sliding nasa a ciki, nan da nan kuwa tunaninsa ya zama distracted. "Hannayenki suna da laushi, ina son d'uminsu." muryarsa can k'asa tare da yin ajiyar zuciya. Bata ce komai ba shima yayi shiru kamar mai jera tunaninsa. "Kin tuna ranar dana fara ganinki kin dawo daga islamiyya?" Ta d'aga kanta. "Zuciyata ta fara sonki tun a wannan ranar Sa'adha, tun a ranar dana fara shigowa cikin bil'adama, a lokacin da ban san komai ba kuma ban san ya rayuwar zata tafi dani ba, sannan ban san ko ke wacece ba amma zuciyata ta karb'e ki wholheartedy, duk da cewa ban fahimci hakan ba a lokacin nayi zaton kawai abinda kika yi ne ya burge ni don ban tab'a ganin hakan ba. A ranar jaamil ya gaya min cewa wannan gidan na layinku ba zaiyi min dad'in zama ba saboda yawan mutane a wajen, saboda haka na canja wani a can wata unguwa, bayan nayi settling komai kuma na fara bibiyarki ta hanyar zuwa layinku, a haka na gano lokacin da kuke fita makaranta da safe, sai inzo in wuce ku kamar na dawo daga morning training don in ganki, da kuma sanda kuke tashi daga makaranta, sau da yawa zanje a siffar da bazaki ganni ba, in tsaya a parking lot d'in da ake zuwa d'aukarku, don in saurari dukkanin hirarki..." Nanne taji k'arar wani abu kamar murmushinsa can k'asa, ta d'ago daga kallon hannayensu da take ta kalle shi, murmushin kuwa yake kyallin siver idonsa ya haska a cikin nasa. "...Na san duk wata fitinarki a lokacin Sa'adha, kin tuna ranar da kuka tsayar da wani tsoho mai turmi?" Ta maida kallonta k'asa a hankali, ta tuna lokacin sarai, ita da Amina ne da kuma wata Aisha, suka tsaida tsohon nan suka yi ta cinikin wani k'aton turmi daya d'auko, kusan minti ashirin yana ja suna ja har dai ya sallama musu akan wani farashi mai sauk'i, sannan suka ce wai ya dawo gobe zasu taho da kud'in, ai kuwa ya d'auki turminsa ya tafi yana zaginsu tare da Allah ya isa. She smiled, and he smiled ruefully back. "Bayan haka Noory kullum da yamma lokacin dawowarki daga islamiyya zanzo in tsaya daga wajen wasu samari da mafi yawa suke taruwa daga jikin mota a sigar da ba mai ganinna. Sai dai a kullum ina gayawa zuciyata cewa abinda nake ba daidai bane, zai iya zama min matsala musamman idan Naani taji, amma kuma duk sanda na kwana biyu bai ganki ba, bana iya focusing akan aikina, Saboda haka a kullum zan cewa kaina daga ranar ba zan k'ara zuwa wajenki ba, amma gobe zan dawo. Ban ankara da cewar abinda nake yi da gaske zai zame min matsala ba sai ranar dana ga cewa kina iya ganinna bayan kuma ina zuwa ne a sigar da idon mutane ba zai iya d'auka ba. Sau da yawa zaki juyo kamar kin kalle ni sai kuma kiyi saurin juyawa ki kalli Rahma da kuke tafiya tare. Tun daga wannan lokacin ne na takura kaina na daina bibiyarki kusan watanni biyu, shine wannan lokacin da kika ce  kin daina ganina." "Me yasa a lokacin dana tambayeka wajen wa kake zuwa ka min k'arya?" Ya d'ago hannayensu yana kallo sannan yace. "Ta yaya zan gaya miki a lokacin cewa ba wanda ya san ni saboda ina zuwa ne a siffar da ba wanda ke ganina?" "Toh me yasa ni kad'ai nake iya ganinka? kana tunanin inada wata matsalar ne?" "Nine nake zuwa a siffar da mutane basa ganina, and you're worried that kice mai matsala?" Imran ya fad'a da d'an guntun murmushi a fuskarsa, ta fahimce dukkan manyan abubuwan da ya fad'a amma wannan kawai ya sata tunani? ya kalli fuskarta, wani abu kamar damuwa etched deep between her eyes, sannan tana ta tauna lebb'enta. "Karki damu, ba wani matsala bane, ina tunanin alama ce na cewa ni dake are meant to be together." Ta sake tauna lebb'enta sannan tace. "Shi yasa na tambayi Sadiq a lokacin yace min bai sanka ba." Maimakon ya bata amsa sai ya zare hannunsa daga cikin nata ya kaishi kan bakinta, ya janyo lebb'en daga cikin bakinta. "Zaki ji wa kanki ciwo..." Kalaman suka rataye a iska kamar ba iyakar abinda yayi niyyar fad'a ba kenan. Nanne ta kalli cikin idanunsa har yanzu suna kyallinsu na silver ga wannan sassanyan numfashin nasa yana kad'a fuskarta a hankali, zata iya zama tare dashi haka zuwa tsawon lokacin da baza ta iya tantancewa ba, amma a halin yanzu akwai tarin abubuwa da take son sani, labarin bai kai k'arshe ba saboda haka ta d'an matsa baya kad'an sannan tace. "Bayan nan ban k'ara ganinka ba sai ranar daka fara min magana." "Right... lokacin da nake zuwa ganinki, jaamil ya lura da abinda nake yi, saboda haka ya dawo daga Muzzaffar lokacin dana riga na daina zuwa wajenki yayi min gargad'in cewa in daina abinda nake tun kafin Naani ta sani, ganin yadda ya d'auki abin da zafi yana ta b'ata rai, sai nayi tunanin in k'ara tsokanarsa saboda haka a ranar muna tare dashi na hango ki nazo nayi miki magana don ya gani, sai dai wannan maganar ta rushe duk wani tarin k'ok'arin da nake na avoiding d'inki, naji cewa ba zan iya sake nesanta kaina dake ba, saboda haka na dawo da zuwa ganinki." "A wannan ranar na kwana da wani irin ciwon kai, hakan yana da alak'a da kai?" "I'm afraid yes, saboda na tab'a jikinki a karo na farko." Ta kalle shi da mamaki, idonta na nuna tambayar da bata furta ba. "Sanda nazo baki handkerchief d'in nan, yatsana ya tab'a naki kad'an yadda ke baki ji bama." Ta had'iye wani abu a mak'ogwaronta kafin tace. "A lokacin nayi tunanin handkerchief d'in Babba ne, amma daga baya dana d'auko sai na ganshi d'an karami." "Mhmm Mhmm..." Ya girgiza kansa yana kallonta. "That's not something important...Ki gaya min ciwon kan naki ya dad'e a ranar?" Ta girgiza kanta a hankali. "Dana tashi da safe babu shi." A cikin kanta, ta tuna mafarkin da tayi da muryarsa a lokacin, muryarsa mai taushi data ambaci sunanta. "Bayan wannan ranar na kasa daurewa da daina ganinki, na cigaba da zuwa duk da irin magiyar da jaamil yake min, a sannan ne kuma nayi wani abu da ban tab'a yi ba tunda nake a rayuwata..." Ya tsaya a lokaci d'aya sannan ya kawar da kansa daga kallonta. Itama bata ce komai ba ta cigaba da kallonsa har zuwa sanda yayi deciding cigaba da magana. "Naje makarantarku lokacin da kike gayawa k'awarki kina son aljanu su shiga jikinki don ki mari wani malaminku...i was instantly jeleous! da naji kina nenan aljani a tare dake, kuma na san a wannan lokacin da an sami aljanin da ya jiki zai shiga jikinki ne da hujja and i don't think i can stand that... ba zan iya jure ganin wani tare dake ba, alhalin nima zan iya taimaka miki ta wannan hanyar, saboda haka ba tare da nayi shawara da kaina ba na shiga jikinki a islamiyyarku." He sounded ashamed, kamar yana admitting wani rauninsa. Nanne taji kanta ya d'aure, tunaninta ya hasko mata Malam Mukhtar, sanda yazo k'ofar gidansu yana gaya mata cewa Malam Murtala ya rantse cewa yaga aljani a jikinta, ashe Imran ne? Ta yaya ya ganshi a matsayin aljani? Ta yaya ma ya iya shiga jikinta? Common sense d'in kwakwalwarta na gaya mata cewa kamata yayi ta tsorata amma tambayar da take son yi ta ture hakan. "Nayi zaton kace kuna da jiki, nayi zaton kace an canja maka jikin ne zuwa na mutane, ta yaya toh ka iya shiga jikina?" ●﹏● @Shamsiyer ranar da kika fara karanta labarin nan, kika ce min in taimaka in turo next chapter kiji wane ne Imran d'in da Nanne take ciwon kai ta had'u dashi..😀....I tynk muna chapter 4 ne lokacin, toh gashi yau na amsa tambayarki. _@Zz kin tambaye ni jiya akan k'arin bayanin mene  ne halittar ALBIE...I hope kema na amsa tambayarki._😊 **** WAYE SHI? AYSHA SHAFI'EE 47 Kuyi hak'uri da Ingausar da zaku tarar a wannan chapter, wani abun ne baya fitowa sosai a hausa.🙏 (☆_☆) "Na fad'a miki muna possesing wasu qualities irin na aljanu kuma mun fisu k'arfi ma a wasu b'angaren, muna iya b'atar da jikinmu yabi iska a wasu lokutan amma ba frequently ba kamar yadda aljanu suke a kullum." Ya k'arasa yana kallon yadda tayi shiru tana jinsa, yatsunta dake cikin nasa suna motsawa a hankali, kowacce kalma dake fita daga bakinsa ji yake kamar wani nauyi ake sauke masa, he felt free! Saboda tun daga lokacin da aka kawo ta gidansa yake son fad'a mata wannan gaskiyar daya lullub'e da k'arya, yana son ta ainihin shi waye kamar yadda itama ta bud'e masa zuciyarta ya san komai game da ita. "Tun daga wannan ranar, na san cewa nayi wani babban kuskure saboda haka na kasa samun nutsuwa tare dani, jaamil bai san me ya faru ba, amma sai ya zab'i wannan lokacin ya kai k'arata wajen Naani, A karo na farko tun bayan zuwana na koma Muzaffar, na durk'usa a gabanta nayi mata rantsuwa ba cewa ba zan k'ara zuwa kusa dake ba. Bayan sati biyu da kuma hakan, jaamil yayi tafiya nemowa mahaifiyarsa maganin ciwon kanta, a wannan lokacin ne na had'u dake kin fito daga wani gida da k'unshi a hannunki, banyi miki magana ba saboda alk'awarin dana d'auka na nesanta kaina dake, amma bayan na koma gida sai naji cewa ba zan iya sawa rabuwarmu aya daga nan ba, saboda haka na dawo na baki hak'urin wannan zafin dana gani a cikin idonki, if not...i knew they will hunt me forever! Nanne tayi shiru tana jinsa, ya gaya mata b'arin wannan gaskiyar sanda take masa tambayoyin nan, abinda kawai ya b'oye shine dalilin da yasa baiyi mata magana ba, a wancan lokacin yace saboda ya san bata kula kowa a waje ne, sai yanzu take jin ainihin gaskiyar. "Daga nan kuma na takura kaina na goge komai naki daga cikin zuciyata don a tunanina hanyata da taki sun rabu kenan har abada, ashe wata k'addarar bata ma soma ba saboda ba'afi sati d'aya ba na tashi da wata matsananciyar rashin lafiya da ban tab'a yin irinta ba, da kyar na iya k'arasa meeting d'in da nake dashi a ranar, wani meeting mai muhimmanci kan abinda ya kaini kamfanin. Na kira jaamil yazo yayi jinyata, muka yi ta k'ok'arin gano abinda ya same ni muka kasa, sai daga baya wani tunanin yazo masa, amma bai gaya min ba sai da yaje ya tabbatar tukunna sannan yazo ya sanar dani cewa kema baki da lafiya." Ya d'anyi shiru kafin ya cigaba. "Kuma wai rashin lafiyata da taki ta faru ne saboda na shiga jikinki na bar b'arin ruhina tare dake." Yaji wani abu ya fad'a zuciyarsa sanda ya fad'i hakan, sannan yaji hannun Sa'adha dake cikin nasa yayi rawa, amma bai tsaya ba ya cigaba. "Ransa ya b'aci sosai daya gano cewa har na shiga jikinki amma na b'oye masa, ya kasa karb'ar dukkan uzirina da hujjar cewa bana tab'a wasa da duk wani abu mai muhimmanci da Naani ta sani saboda haka ina sane nayi komai, bai san cewa tun lokacin da kika shigo rayuwata na rasa wannan confidence d'in ba, bai san cewa tun daga lokacin da nayi failing wajen controlling zuciyata akanki komai ya zame min sa'a ba." Idanunsa suka lalubo fuskarta a sannan, ta sunkuya kad'an tana kallon hannunsa dake cikin nata, he wanted to tell her that itace abu mafi muhimmanci yanzu a rayuwarsa amma ya kasa samun k'arfin yin hakan, yana fata ta fahimta a kowacce kalma da yake fad'a. A nutse muryarta ta fito. "Nasha wahala lokacin, abubuwa suka yi ta tsoratani kala-kala, ya zama bana iya wani baccin kirki a kullum, sannan na tashi k'afafuna sun rik'e bana iya tashi, sai da Baffa ya kira wasu malamai suka yita addu'a sannan na samu sauk'i." "Bayan taimakon addu'arsu Nima na taimaka wajen d'orar da sauk'inki Sa'adha." Ta d'ago da idonta ta kalle shi. "Lokacin da jaamil ya gane dalilin rashin lafiyar, ya gano cewa d'aya b'arin ruhin dake jikina zai iya kwantar dana jikinki zuwa wani lokaci, saboda in har suna tare ba abinda zai faru, sai sunyi nesa da juna ne sannan jikinki zai kasa rik'e wanda yake tare dake hakan yayi resulting a abubuwan dake tsorata ki. Saboda haka muka je gidanku a wannan daren kina bacci." Nanne ta zare idonta lokacin da kwakwalwarta ta hasko mata wannan mafarkin da tayi na farko, wanda taga siffofi biyun nan tsaye akanta, da sanda d'aya daga cikinsu ya d'ora hannunsa akan goshinta taji gabad'ya ciwon jikinta yabi iska. Kafin ta iya samun damar tambaya Imran ya cigaba. "Bayan wannan lokacin, ina zuwa in kwantar da ciwonki duk sanda ya fara k'ok'arin tashi yana tsorata ki yayin da jaamil ke can yana kokarin gano yadda zamu ciro b'arin ruhina daga jikinki, sai duk sanda naje na kwantar da ciwon naki ina rasa k'arfi sosai a jikina wanda har hakan yake shafar kuzarina a wajen aiki. Jaamil ya k'are bincikensa, amma bai iya samo hanyar da zamu iya ba tare da taimakon Naani ba, kuma a lokacin ta shiga bautarta na tsawon watanni biyar saboda haka ya kawo shawarar cewa in aure ki, saboda in har b'arin ruhin yana tare da d'an uwansa zai zauna ne kamar sanda yana jikina ba tare da wani abu ya faru ba. A lokacin da naji haka nak'i yarda Sa'adha saboda girman da zancen yayi min, dukkan intrest d'in da nake dashi akanki bai tab'a gangarawa kan maganar aure ba, saboda haka nak'i yarda da shawararsa shi kuma yayi ta bina da ita, daga k'arshe har ce masa nayi ni ba sonki nake yi ba don ya kyale ni amma sai ya k'ara kafa hujjar cewa dama ba zan aure ki bane don ina sonki, zan aureki ne don in gyara kuskuren dana jawo, a haka har yaci galaba akaina na amince cewa zan iya. Daga nan muka fara tunanin yadda auren zai yiwu, na kawo shawarar cewa dole sai kin amince dani haka ma 'yan uwanki sannan komai zai tafi daidai, saboda haka jaamil ya bada shawarar na kad'e ki lokacin da kika je tsallaka titin nan siyo magani, ta haka na samu dukkanin wani contact dake da 'yan gidanku, kowa ya sanni kuma muka yi healing k'afarki ta yadda baki ji zafin ciwon jikinta ba ko kad'an. A lokacin da hakan ke faruwa, jaamil yaje yayi controlling tunanin Malaman da suka yi miki addu'a, suka je suka gayawa Baffanki cewa bak'aken aljanu ke shirin shiga jikinki kuma aute ne kawai hanyar samun sauqinki." Tunanin Nanne ya k'ulle a wannan lokacin, kallonsa kawai take yayin da magangamunsa ke shiga kanta kamar an tara bokiti a bakin famfo. "Baffanki bai so yi miki aure a yanzu ba ko kad'an, don duk da k'ok'arin da jaamil yayi wajen sa zuciyarsa ta yarda da hakan, sai da yayi ta bin malamai kala-kala kuma kowannensu jaamil yana sawa su k'ara tabbatar masa da maganar dana farko suka fad'a." "Baffan....." Muryarta ta fito involuntarily cikin rawa. "We didn't hurt him Sa'adha...wallahi ba abinda muka yi masa, jaamil yayi controlling kwakwalwarsa ne ba tare ma daya sani ba, kamar yadda kike jin tunaninki yana canjawa a cikin kanki haka komai ya faru." Ta kifta idanunta a hankali, tunaninta ya hasko mata sanda aka kaita wajensa sallama, sanda yake ta nasiha yana kuma bata hak'uri, Allah kadai ya san yadda yake ji a lokacin. Imran yayi shiru don ya bata damar da zata wanke tunanin cikin kanta, yana murza hannunta a hankali cikin wani salo na rarrashi. Nanne taji jinin dake cikin jijiyoyinta na gudu da wani irin sauri, wani irin saurin da taji dama tana da ikon da zata iya tsayar dashi, saboda hakan dad'a sawa yake taji komai ya had'e mata, sai dai yadda hannunsa ke motsawa akan nata a hankali ya shiga taimakawa wajen calming condition d'inta. Bata san iya dad'ewar da suka yi a haka ba, zai iya yiwuwa kusan awa d'aya kafin ta iya samu dukkan maganganunsa su shiga kwakwalwarta. Bai motsa ba shima balle yayi magana yana rike da hannunta kawai, ta san a wannan lokacin bayan k'ok'arin yarda da maganganusa da tayi kamata yayi kuma taji tsoro, tsoron yadda rayuwarta ta gaba zata kasance ko abinda zai faru da ita, amma kwakwalwarta ta kasa hasko hakan, she couldn't think of anything except that he's touching her! hannunsa yana tab'a nata. "Ka cigaba..." muryarta ta fito a hankali. Taji sanda yayi ajiyar zuciya kafin shima muryarsa ta fito. "Bayan Baffa ya tara ku ya fad'a muku cewa ya yanke shawarar aurar dake kuma ya baki wata d'aya ki gabatar masa da wani - sai naje wajensa bayan sati d'aya, Na fad'a masa labarin da kika sani kamar yadda muka tsara tun farko ni da jaamil, cewa ni d'an bauchi ne aiki ya kawo ni nan kuma iyayena sun rasu a hannun k'anin mahaifina na tashi. Yayi maraba dani sosai sannan ya buk'aci in bashi lokaci cewa zaiyi bincike akan lamarina, bayan sati d'aya sai ya sake kirana ta hanyar yayanki Sulaiman wanda muka saba tun sanda kina asibiti, dana je ya buqaci in turo da iyayena suyi magana saboda haka jaamil ya sake yin aikinsa, ya turo dattijan mutane irin wanda ya san Baffa zai ga girmansu ta hanyar rufe masa ido amma a zahiri babu kowa, babu wasu mutanen da suka je. A wannan lokacin na d'auki hutu naje Maldives. Wajen da tunda naje ba abinda nake iya tab'ukawa sai tunaninki Sa'adha, duk da cewa inata ture hakan daga zuciyata amma na kasa, tunanin yadda zaman mu zai kasance kawai nake, yadda zan iya rayuwa dake a matsayin matata alhali ba jinsinmu d'aya ba, tsoron cewa zan iya cutar dake ne yafi yawa da kuma tunanin yadda zanyi controlling zuciyata akanki. Saboda a lokacin ina kokarin sawa zuciyata ta yarda da kalaman jaamil ne, na cewa sai na ture dukkan intrest d'ina akanki don zamana dake ba mai d'orewa bane, zai k'are a duk ranar da Naani ta dawo ta raba ruhina dake." A daidai nan, yayi shiru yana shak'ar kamshin jikinta da kuma na gashinta wanda ya fito ta k'arshen d'ankwalinta, a lokaci d'aya kuma yana sauraren bugun zuciyarta, wani lokacin sai ya buga da k'arfi wani lokacin kuma ya tsaya gabad'aya, bayan wani lokaci sai ya koma daidai ya cigaba da bugawa a normal rate d'in da ya saba, a wannan lokacin ya fahimci cewa bugun zuciyarta shine sauti mafi muhimmanci a rayuwarsa. Duk cikin wannan lokacin bata motsa ba, saboda haka bayan ya tabbatar kwakwalwarta ta gama absorbing kalamansa na baya, ya cigaba. "A sannan jaamil ya kira ni da cewar lokaci yayi, saboda haka hutuna bai k'are ba na tattaro na dawo. Bayan dawowata na sake zuwa na sami Baffa, shi ya bani ranar da zanzo in same ki, saboda haka na kira ki na tambaya, amma dana zo kika hana ni ganinki. A wannan lokacin na fahimci cewa bayan had'in kan Baffa da muka samu, dole ne kuma sai na nemi naki in har ina so abubuwa su tafi mana daidai, ba tare da son ran jaamil ba na dinga kiranki a waya da duk wata hanyar dana san zan shawo kanki, har na fara koya miki yadda zaki so ni kamar yadda na fad'a miki." "Saboda me?" Ta tambaya. Imran ya kasa gane dalilin da yasa ta tambaya, bata san cewa b'acin ranta koya yake can cause him physical pain ba? Bata fahimci cewa yana k'aunarta fiye da tasa rayuwar ba? "Sa'adatu." Ya kira full name d'inta yadda zata fahimci cewa he's so serious, ya d'ago da d'aya hannunsa da baya rik'e da nata ya kamo gefen fuskarta. "Ba zan tab'a iya rayuwa mai kyau ba in har na zama sanadin abinda zai dame ki, you don't know how it tortured me to see you hurt." Nanne ta sake damk'e hannunta dake cikin nasa tana kallonsa, ya lumshe idanunsa a hankali by the pleasure, zai sake magana tayi saurin tsayar dashi ta hanyar d'ora yatsunta akan lebb'ensa, Bayaninsa bai kai k'arshe ba, akwai sauran abubuwan da suka rage itama kuma akwai sauran tambayoyin dake cikin kanta, amma wannan kalaman nasa ya ture komai, taji iya su kad'ai sunyi convincing zuciyarta sun ture duk wani sauran duhu dake cikin kanta game dashi. A hankali tana kallon idanunsa da suke kyallin silver har yanzu tace. "You are the most important thing to me too! the most important thing to me ever Ulfat!" ●﹏● Did we just heard the first nickname d'in da Nanne ta kira Imran? Me ne tunaninku akan duk wannan gaskiyar da Imran ya bud'ewa Sa'adha a yau? Kuna tunanin zai fad'a mata ma had'arin dake gabanta game da Naani? Me zai faru a next chapter? **** WAYE SHI? AYSHA SHAFI'EE 48 (☆_☆) "Kin gansu koh?" Inna ta tambaya daga falo zaune akan dardumarta. "Eh na gansu, ashe suna da d'an yawa ma." Nanne ta amsa sanda ta dawo cikin falon ta zauna a kusa da ita. "Toh na nan ne masu yawan kenan, ai na zata na wajen Azumin sune suka fi  yawa." "Au wai da akwai wasu ma a wajen mama Azumi?" "Akwai mana, wad'annan ai ina jin na wajen Nuratu ne da suka kawo ran d'aurin aure da kuma na sauran mutanen da suka dinga kawowa daga baya, toh na wajenta kuma ina jin sune ragowar wanda su Nafisa suka je kasuwa aka manta ba'a kai ba." Nanne ta mik'a hannu ta d'auki sala d'aya na lemon dake gaban Innan kafin tace. "Wallahi dama an barsu anan kawai, ki dinga yin gudunmawa dasu tunda a can d'in ma fa sai kiga wani abin har guda biyu iri d'aya." "A'ah, d'iban kayanki zaki yi ki tafi dasu ni yaushe zan d'ebi kayan kitchen in tafi kai gudunmawa, ai duk wanda zan bawa gudunmawa yanzu kud'i yake zato daga gurina. Kuma kayan har fa da wanda su Nuratu suka kawo, me zai kaini tab'a su? a ranar ma da zasu tafi har tambayar su maryamah suka yi wai ko su tafi dasu ne tunda zasu je gidan naki kafin su wuce tace musu su barshi za'a kai, nayi ta fad'a da tazo ta gaya min anan, nace don me zata hana su, su kwashi tarkacensu mana suyi gaba idan gani suke zamu rik'e wani abin zamu yi, in banda ma....." Nanne kawai murmushi take tana kallonta, tayi missing hirar nan tata kamar me? yadda zasu zauna irin yanzu wajen k'arfe d'aya kafin tafiyarta islamiyya suna ta hirarrakinsu, na 'yan uwa da kuma yanayin zamantakewar yau. Tun wajen k'arfe tara na safiyar yau da Imran ya ajiyeta a k'ofar gidansu take jin wani canji a zuciyarta, gani take kamar ta dawo duniya ne daga can wani baqon wuri da aka kaita, sanda ta shigo taga inna kuma sai kewar komai ta dad'a kamata, ta rungumeta da k'arfi su mama Azumi da suka rako ta tun daga tsakar gida suna ta fad'in wai zata b'allata, amma itama innan bata damu ba, ta rik'e ta sosai tana ta lale maraba da Amarya. Da kyar ta iya barin d'akin maq taje ta gaishe dasu hajiya Babba, kowa sai fara'a yake mata ana kuma bata wani girman da a da bata san dashi ba, don mama rabi wai harda rako ta bakin kofa, matar da a da kanta a d'age take amsa gaisuwarta. Babban abin mamakin data gani shine daga wurin yayyenta maza, duk wanda ya lek'o yiwa Inna sallama zai fita, in ya ganta sai ya tsaya su gaisa, a baya kuwa wani ma hamb'are kafarta zaiyi ya shige wajen innan. 'Yan biyu ma da suka shigo bayan sun tashi daga baccin asarar su Saleem da murmushinsa yayi ta tambayarta ya sabon waje da kuma mijinta, Suraj ne kawai ya d'an mata wani guntun murmushi daya d'auke in second sannan yace 'kin zo dama.' "Yanzu Inna to ke kad'ai kike kwana a d'akin nan?" Ta tambaya sanda take taya innan rarraba goron da take bayarwa a kai masallaci sadaka duk ranar juma'a. "A'ah bayan tafiyar su maryamah ai Azumi nan ta dawo, tare muke kwana kiga mu sha hirar mu ma har fare ya raba." "Kai Inna, wai harda kusha hira...irin kin samu wadda ta fini d'in nan." Ta fad'a kamar zata yi kuka. "Yo kiji min 'ya, ke ba wanda ya fini d'in kika samu ba? yanzu da za'a ce kizo ki kwana biyu ai ba yarda zaki yi ba." "Haba dai Inna, wallahi ba'a fad'a d'in bane." Ta fad'a tana d'aukar wani lemon, sai dai me? duk yadda ta kai ga d'okin gidan ana yin sallar la'asar taji ta fara tunanin sanda Imran zai zo su tafi, sau da yawa tana irin wannan dad'ewar bata ganshi ba in yana wajen aiki, amma yau da banbanci, a wani waje take da ba inda zai dinga tuna mata da abubuwansa, inda ya zauna yayi wani abin, inda yayi magana, abinda ya d'auka ko kuma inda ya tsaya yace mata wani abun. Rahma ma tazo sun sha hira amma duk inda ta kai ga jin dad'in hirarsu ita da Inna, tunaninta yana zamewa wajen hasko mata wad'annan kyawawan idanun nasa da yake yawan lumshe mata su, ko muryarsa, ko yadda yake rik'eta, dama sauran tarin 'yan k'anan abubuwan da bata san tana lura dasu ba. Da gaske ne ta yarda cewa rayuwarta ta canja, tun daga lokacin da aka d'auketa aka kaita gidansa, rayuwarta ta canja ta hanyar da baza ta iya fassarawa ba sai dai kawai wanda ya san irin hakan ya gane. Wajen k'arfe biyar, Sadiq ya shigo d'akin da tsokanarsa yana fad'in. "Yan mata ta zama matar aure...!" Nanne ta juya idonta tace. "To ya ranka? girma ne dai dole yanzu Allah ya riga ya bani kuma inda mutunci ma kamata yayi ka dinga kirana da Aunty, tunda yanzu ka san na wuce ajinka." "Wallahi ba matsala..." ya fad'a yana zama a kujerar da take kai. "Ni yanzu ko gwaggo kika ce in fad'a miki fad'a zanyi, don kwanan nan zaki tsufa bari ki fara haihuwa ki gani, sai anzo ana musu dani ina wallahi k'anwata ce ana Sadiq wannan ai babarka ce." Suka kyalkyale da dariya har Inna kafin ta d'auki filo ta maka masa. "Toh ina d'an handsome mijin naki? Kin san kwanaki su Abubakar d'in bayan layin nan suka tare ni wai dan Allah in gaya musu a ina kuka had'u, wai sun san gayen tun zuwansa unguwar na ba wadda yake kulawa, maza ma sallama ce kawai ke had'a su." Tace. "Toh me kace musu?" "Kin san ni bana son irin wannan munafuncin, ce musu nayi wani mai dalilin aure ne a can baya ya had'aku." Nanne ta sake kyalkyalewa da dariya. "Kuma sun yarda?" "Wallahi sun yarda, harda cewa wai zasu sa rana in raka su suma, na bisu da toh kawai." A cikin hirarsu Inna ta tambayeta sanda zasu dawo daga tafiyar da tace mata zasu yi. "Inna wallahi ban sani ba don bai fad'a min ba, kawai yace in gaya muku zamu yi tafiya." "Ina zaku je?" Sadiq ya tambaya. "Nifa ban sani ba, amma tunda da waya duk inda muka je zan kira ai." "Kaga hajiya Amarya, wato honeymoon d'in ma baza'a fad'i ina ne ba don kar a dame ku." Ta sake d'aukan filo ta maka masa. "Ni nace maka honeymoon zamu je." Inna tace. "Duk inda dai zaku ya kamata a sani, tafiya irin wannan da zata iya yin nisa." Sai bayan sallar isha sannan Imran yazo, ya d'an dade tare da Inna suna hira sannan yaje ya gaishe da baffa, kamar yadda yayi ta addu'a da sawa Nanne albarka haka shima yayi tayi masa, tare kuma da kallon da Imran ya fassara da cewar Ka kula da ita. I will, da dukkan iyawata Baffa! Shima ya amsa da idanunsa. Aka lodawa Nanne kayanta a mota sannan suka tafi bayan Inna tasa tabi su hajiya Babba duk tayi musu sallamar tafiyar da zasu yi. "Kayan meye wannan?" Imran ya tambaya sanda suka hau titi. "Kayan ka ne." Ya juyo sosai ya kalleta. "Ni kuma? a ina na sami wannan kayan?" Tayi dariya kafin tace. "Wasa nake yi fa, wai ragowar kayan da ba'a kai min bane, yawanci ma na amfanin kitchen ne." Yana jin haka ya maida idonsa titi, fuskarsa ba alamun murmushi balle dariya, Nanne tayi sensing wani abu na damunsa saboda haka tace. "Ka san cewa kafi kyau in idanunka suka zama so light." Kafin yayi magana tunaninta ya dawo mata da amsar daya bata kwanaki biyu da suka wuce, sanda ta tambayeshi game da idonsa dake kyallin silver. "Shine na farko da kika fara gani Sa'adha, a yanayin halittar mu, mood d'in mu yana reflecting ne a idonmu, I'm being myself aroud you now, zan dinga sakewa duk sanda ina tare dake akan k'ok'arin b'oyewar da nake a baya, Saboda haka zaki ga yanayin idona na canjawa a lokuta da yawa." A yanzu kuma taga sanda ya ciji lebb'ensa kafin yace. "Wane color yayi yanzu?" "Dark. So dark!" Ya sake datsa lebb'ensa. "Ban san me nake ji bane Sa'adha, I don't know what I'm feeling, 'yan gidanku sun yarda dani da yawa alhalin ina yaudararsu ne...kowannensu yana min kallon wani mutumin arziki, Wallahi bana son abinda nake Noory." Nanne ta maida kanta gefe tana kallon titi, ita kanta a lokacin da Inna ta tambayeta game da zancen 'yan uwansa, da kyar ta iya lalubo karyar da tace mata sun zo basu dad'e bane suka koma garinsu. Zuciyarta tayi nauyi da tunanin, in har su Inna suka ji gaskiyar WAYE Imran ya zasu yi? ya zasu ji in suka san wa suka aura mata? in har akwai matsalar da take hangowa a zamanta da Imran, bai wuce yadda zasu yi ta lullub'e komai ga iyayenta da 'yanuwanta ba, amma ita ta riga tayi deciding zuciyarta, ta tsaida ita a waje d'aya...zata zauna da Imran a kowanne hali in har ba zai cutar da ita ba. Tana son shi, kuma tana sonshi har cikin zuciyarta! ******** "At least ka d'an bani hint mana, ko don in san irin kayan da zan d'auka." Nanne ta fad'a tana kallon Imran dake kwance akan gado yana cafe kayayyakin da take jefowa daga cikin wardrobe, ya d'ora kafarsa akan d'aya, sannan hannunsa d'aya cikin gashinsa. "Hint kike so? toh dogwayen rigunan ki ma zasu yi, akwai musulmai a inda zamu je." "Musulmai? wane yare suke yi?" "Kala-kala, amma karki damu za'a samu wanda kika iya." Ta matso kusa da gadon tace. "Toh farare ne ko bak'ake mutanen wajen?" Ya d'age girarsa d'aya yace. "I think suna da haske." Nanne ta tsuke baki tana kallonsa sanda durk'usa a gefen gadon rike da wani pink mayafi. "Toh wajen zafi ne dashi ko sanyi?" Ya d'an tsaya yana kallonta. "Wai wayo kike son yi min?" Ta karkata kanta kad'an. "Ta ya zan maka wayo so nake kawai in sani..." "Mhmm-Mhmm baby girl, wannan k'ifta idon ba zaiyi tasiri akaina ba..." Ya karb'e mayafin hannunta sannan ya jawo ta kan gadon. "...In kina son ki san inda zamu ki bari gobe insha Allah zaki fara gani." "Fara gani ba waje d'aya bane kenan?" Imran ya juya idonsa, sannan ya mik'a hannunsa sama ya kashe switch d'in d'akin. "Enough talking for today, in ba haka ba zaki sa in fad'a miki komai da komai yanzu." "Ban k'arasa had'a kayana ba fa." Ta fad'a a cikin duhun. Ya lalubi gefen kunnenta ya rad'a mata a hankali. "Wanda ya shiga cikin akwatin sun isa Sa'adha, beside bana jin ma duk wannan kayan zasu yi miki amfani sosai a can." Ta lumshe idanunta tana shak'ar k'amshin jikinsa. "I give up Ulfat! na hak'ura da sani Allah ya kaimu goben." "Ameen Habibty." Bayan kamar minti talatin, har Imran na tunanin tayi bacci, yaji muryarta ta kira shi a hankali. Can k'asa-k'asa ya amsa shima kamar ya fara bacci. Ta b'alle buttun d'in gaban rigarsa a hankali sannan tace. "Yaushe Naani zata dawo? Kuma me zai faru in ta dawo?" ●﹏● WAYE SHI? AYSHA SHAFI'EE 49 (☆_☆) "Naani ba yanzu zata dawo ba, kuma kafin ta dawo we will figure a way out, ba abinda zai faru insha Allah Sa'adha, kuma ba zan tab'a rabuwa dake ba." Wannan sune kalaman Imran na jiya da suka kwantar da hankalin Nanne kuma suka bata kwarin gwiwar tashi a yau ta kammala komai na tafiyarsu, ta gyara gidan ta rurrufe komai da ta san zaiyi k'ura. Karfe goma sha biyun rana tayi musu ne a cikin airpot, har Imran ya gama duk wasu shige da ficensa tana tsaye bata san inda zasu ba, sai da suka shiga cikin jirgin ne sannan ta tambaye shi. "Zamu dad'e bamu dawo ba?" Maimakon ya bata amsa sai ya kamo hannunta cikin nasa ya murza a hankali. "I love you!" Hakan ya tabbatar mata cewa ba zata sami amsarta ba, saboda haka ta kwantar da kanta a gefen kafad'arsa kafin a hankali tace. "That's why we're here." ******* "Lagos..?" Nanne ta tambaya sanda suka sauka daga jirgin bayan tafiyar kusan awanni biyu. "Itace hanyar da zamu bi ta farko." Ya fad'a da murmushi sanda yaja hannunta suka nufi hanyar building d'in terminal, anan bayan wasu cike-ciken da kuma b'ata wani lokacin suka k'arasa international counter inda suka yi boarding wani flight d'in. "Australia?" Ta sake tambaya sanda ya karbi tickets d'in suka mik'e wata hanya. "Itace hanyar da zamu bi ta biyu." ya fad'a da wani murmushin. Tafiyar daga lagos zuwa Australia awa bakwai ne, but it was comfortable tunda suna zaune ne a fad'ed'en seat d'in first-class. Abinda ya sata  tunanin irin kud'in da Imran ke dashi. "Ayunie..." Ta kira a hankali tana kallon hannunsa dake nannad'e a cikin nasa, Babbar hanyar communication d'insa, sau da yawa zasu zauna suyi shiru amma in har hannunsa na cikin nata, sai taji kamar magana suke yi. Sai da Imran ya d'anyi shiru sannan ya fahimci sabon sunan da ta kira shi dashi, wani dad'i ya ratsa shi, yayi murmushi kad'an sannan ya amsa. "A ina kake samun kud'i, na zata tunda baka dad'e da shigowa cikinmu ba, bai isa ka tara kud'i da yawa ba." The question is so silly, Yayi k'ok'arin kar yayi dariya amma ya kasa hana kansa. "Na gaya miki Naani ta tanadar min komai kafin zuwana, akwai account guda da dimbin kud'i wanda a lokacin ban san adadinsu ba, sannan tunda na fara aiki, ina samun kud'i a kowanne wata da har wani amfani nake dasu sosai ba." Ta gyada kanta alamun ta fahimta. Ya matso da bakinsa dab! da kunnenta sannan a hankali yace. "I like the name...AYUNIE...yana da dad'i sosai Noory." Tayi murmushi tana b'oye fuskarta a jikinsa. Zuwa can ta d'ago ta kalle shi. "Ka tuna ranar da ka maida ni gida da daddare?" Ya d'anyi shiru kafin ya amsa. "I dont want to talk about it, bana son tuna wannan ranar habibty." "Saboda me?" Saboda mutanen nan. Ya amsa a cikin kansa, mutanen daya kasa d'aukan wani mataki akansu saboda ita, saboda kar taji tsoron da zai sa mata wani zarginsa a lokacin. Amma yaso ko da motarsa ne ya take su, ko kuma ya shak'e wuyansu ta yadda k'ashin wajen zai kakkarye, ko yayi ta marin su har sai jinin jikinsu ya gama fita ta baki. He wanted to kill them so bad, yadda duk sanda ya tuna hakan sai yaji kamar zai danne hak'oran bakinsa har sai sun marmashe. Bata damu da rashin bata amsa da yayi ba ta zarce da tambayarta. "Ranar ma yana cikin tsarinku?" Ya girgiza kansa da sauri. "Baya ciki ko kad'an, i swear to you k'addara ce kawai ta had'a ni dake a ranar, naje gidan wani d'an office d'inmu ne a hanyar daya takura mana da gaiyata ni da sauran mutanen office d'in, tun yamma ma muka je muka kai har bayan maghrib, ni na riga su fitowa shine lokacin da na hango ki a hanya..." Ya kasa k'arasawa saboda tunanin wad'annan mutanen. "Lokacin da ka kaini wannan chemist d'in? k'arfe tara da minti goma sha biyu amma har na koma gida tara da minti ashirin, ta yaya hakan..." "I was driving so fast..." Ya katseta. "...Na kare idanunki ne kawai daga gani amma sauri nake yi sosai, saboda bana so hankalin Inna ya tashi duk da cewa Sulaiman ya fad'a mata." Ya fad'i kalaman da gaskiya har cikin zuciyarsa, ya riga yayi wa kansa alk'awari ha zai sake b'oye mata komai ba a zamansu zai fad'a mata dukkanin amsar da take nema da dukkanin gaskiyarsa sai dai banda abu d'aya. Abu d'aya daya san cewa yafi k'arfin tunaninta, abu d'aya da in ta sani zai zama sanadin rasa nutsuwarta, abu d'aya da zai sa ta daina sakewa dashi, ba zai tab'a iya fad'a mata cewar Naani ta dawo kuma baza'a iya raba ruhinsa da nata ba tare da a rasa ransa ko nata ba. Tun tana masa tambayoyi kala-kala na wasu 'yan k'ananan abubuwan da bata fahimta game dashi ba har tafiyar ta mik'a bacci ya kamata, wani bacci mai nauyi da bata ko farka ba sai lokacin da suka isa k'asar Australia, da daddare ne lokacin saboda haka bayan sun sauka da kyar take iya bud'e idonta a cikin hasken fitulun dake dallare a ko'ina, kwata -kwata bata san abinda Imran keyi ba, kawai janta yake yi tana binsa a cikin hayaniyar Airport d'in mai cike da yare kala-kala a lokaci d'aya kuma tana k'ok'arin bud'e idanunta. Bayan kamar minti talatin suka yi connecting to wani jirgin da bata san ina ya nufa ba don suna shiga ta sake k'udundunewa a jikinsa ta koma baccinta. Sai bayan kusan awa biyu sannan ta farka, har a lokacin basu sauka ba, ta tsakuri abinda zata iya ci a cikin abincin da a kawo, sannan ta shiga tambayarsa inda zasu je kuma, amma yak'i fad'a mata kuma ya hanata ganin takardun airport d'in dake hannunsa. Haka ta hakura ta sake langab'ewa a jikinsa tana jin kowacce gab'ar jikinta na amsawa sakamakon kusan zaman awa goma a jirgi, ta tabbata yanzu a Nigeria tsakar dare ne su da suka taso tun wajen karfe biyuna rana. Lokacin da jirgin ya sauka bayan tafiyar awa uku da 'yan mintuna, Nanne ta ware idonta ganin k'aton signboard mai d'auke da haken fitilu dake ta dallare ta yana walk'a kalmomin. WELCOME TO MALE! "Ina ne kuma Male?" Ta tambaya sanda aka gama X-ray d'in kayansu wani bature mai uniform ya d'ora su akan gurney ya biyo bayansu. Yayi murmushi yana kallonta kafin yace. "Itace hanyar da zamu bi ta uku!" Daga haka bai k'ara mata magana ba ya rik'e hannunta har suka fita daga cikin airpot d'in, wannan mutumin na ta binsu ture da gurney d'in. Nanne in banda zare ido tana kallon mutane ba abinda take, jinsi ne kala-kala na dangain fararen mutane ke ta harkokinsu, tsilli-tsilli kawai take hango bak'ar fata shima ba irin wanda ta saba gani ba, don fararen ma gani take kamar ba'a gaske take ganinsu ba, das-das dasu, ga gashi yala-yala daga mazan har matan. Da yawansu sanye suke da dogwayen riguna irin na jikinta, wasu matan ma harda Niqab so she didn't felt so different in banda fuskarta data kumbura sakamakon baccin data sha. Ta tuna maganar Imran a jiya ne ko shekaranjiya. "...dogwayen rigunan ki ma zasu yi, akwai musulmai a inda zamu je." Saura kad'an tayi tuntub'e ba don yana rik'e da ita ba sanda ta hango wata 'yar yarinya fara tas! mai bak'in gashi dogo, kayan jikinta masu kyau harda wata 'yar karamar jaka ta goya a bayanta, ita da mamanta ne maman nata waya ita kuma tana tsaye a kusa da ita sai 'yan juye-juyenta take, taji kamar ta koma ta d'auko ta ace ma an bar mata ita har abada. Sanda suka fita can harabar airport d'in, Imran ya d'auko wayarsa data lura ya canja sim tun a cikin jirgin ya kira waya cikin wani yare da bata idea wanne ne. baifi minti biyu ba, wata shuttle bus ta k'araso inda suke, mai gurney d'in nan ya saka musu kayansu Sannan suka shiga, babu kowa sai driver da yake kamar bafaranse don ta tsinci wasu 'yan kalmomi a maganar da suka yi shida Imran, mamaki take yi na adadin yaren daya iya. "Mun kusa insha Allah Noory" Ya fad'a yana kamo hannunta, bata ce komai ba sai murmushi kawai data masa. Motar ta cigaba da tafiya ta cikin manya-manyan titunan masu d'auke da fitulu rutu-rutu da kuma mutane, mutanen da Nanne ke gani wasu iri a idanunta, a hankali kuma yawansu dana gine-ginen ya ragu har suka k'araso edge na titin, a gabansu duhun wani k'aton ruwa ne daya mamaye gabansu gabad'aya. Motar ta tsaya a k'arshen wani titi daya tsaya a daidai hanyar da zata d'auke ka zuwa port d'in dake gabansu, 'tashar jiragen ruwa' gasu nan fal manya da k'anana, wadu daga can nesa a cikin ruwan wasu kuma a tsaitsaye. Nanne taji ta had'iye yawu sanda ta d'aga ido ta hango wani tafkeken jirgin a tsaye cikin ruwan, taji wani imani ya ratsa ta ganin yadda duk girmansa yake tsaye a cikin ruwan ba tare da nutsewa ba. Imran ya rik'e hannunta zuwa wata doguwar hanya ta katako data kaisu can bakin ruwan, yana ta magana da mutane kala-kala cikin yaren da bata ganewa. Daga k'arshe suka ka'rasa wajen wani d'an madaidaicin jirgi fari tas dashi, sai kyalli yake alamun sabunta, aka saka kayansu da wani ya d'auko lokacin da matukin jirgin ke warming d'insa. Ya juyo ya kalleta a hankali tare da mik'o mata hannunsa d'aya. "Bismillah..." Nanne ta juya ta kalli k'aton tekun dake gabansu, bakikirin ba wani alamun haske, ga manya-mayan jirage a cikinsa ga kuma iska na kad'awa kota'ina, sanna ga tarin fararen mutanen da bata taba ganin irinsu ba. Ina zasu je a cikinsa? Sai kawai ta girgiza kanta da sauri. "Ba zan iya ba, ba zan iya shiga cikin ruwan ba, ina zamu je a cikinsa?" "You have already trust me Sa'adha, kin riga kin yarda ba zan cutar dake ba, So you don't need to be afraid" Yayi maganar a hankali cikin husky voice d'insa, Nanne taji iskar dake kad'awa ta hura koina na jikinta, zuciyarta tayi nauyi a kirjinta cike da tsoro, amma ta kasa daurewa kyawawan idonsa da kuma hannunsa dake jiran nata saboda haka ta had'iye yawu sannan a hankali ta d'ora hannunta akan nasa. "I'm here.." Ya fad'a a cikin kunnenta sanda ya rik'e waist d'inta ya shigo da ita cikin jirgin. Ta d'aga kanta kawai ba tare da ta d'ago daga kallon deck d'in ba. Daga tsakiyar akwai wata rumfa mai d'auke da wata doguwar kujera mai taushi, daga gaba kuma rumfar mai tuk'a jirgin ce, ya rik'e ta a hankali cikin lilon da jirgin yake suka zauna kujerar nan, hannayenta a duk'unkune cikin rigarsa ta cukwikuyeta, bayan kamar minti biyu mutumin ya tada jirgin suka figa cikin igiyoyin teku, wata iska mai dad'i tayi spraying akan fatarta, tana jin sanyinta koina na jikinta, ta juya baya a hankali tana ganin yadda suke wa fitilolin garin Male nisa, a hankali taji  tsoron nata yana tafiya tare da iskar wajen atleast hakan yafi da ace ta kalli bak'in tekun dake gabansu. Bak'in tekun da bata san inda zai kaisu ba, bayan kamar minti goma ta tambayeshi in sun kusa, ya kalli agogon hannunsa sannan yace. "About another ten minutes." Tayi ajiyar zuciya sannan ta sake binne kanta a cikin wuyansa.  Watakila Muzzafar d'in tasu zai kaita, inda zata ga ainihin 'yanuwan halittarsa. Bayan kamar minti goman kuwa, ya kira sunanta a cikin rugugin k'arar injin jirgin. "Sa'adha d'ago kiga." Hannunsa ya mik'e straight zuwa gabansu. Nanne ta juyo a hankali tabi hannunsa da kallo, a lokacin taji ragowar tsoron dake kwance a zuciyarta ya washe gabad'aya...ta kifta idonta ta sake k'iftawa, ba karya bane su d'in ne dai suke dosar wani waje mai cike da yawan fitilu kala-kala da kuma dogwayen bishiyun kwakwa kyawawa, wasu irin dogwaye da hata taba ganin irinsu ba, tun daga nan kuma tana hago wasu irin had'addun gine-gine masu sa zuciyar mutum tsayawa, gabad'aya wajen is a combination of beauty wanda bata tab'a gani ba. "Ina ne nan?" Ta fad'a a hankali muryarta can k'asa, sanda jirgin yayi kwana ya nufi wata hanya inda ta hango wasu jiragen tsaye daga k'arshen gab'ar wajen. Yaji me tace duk da rugugin injin da kuma k'arar iskar dake kad'awa. A hankali ya rad'a a cikin kunnenta. "Welcome to Maldives Island!" ●﹏● Dan dan dan dan dan.... Honeymoon starts here!😁 You don't wanna miss d next chapter!😍 Babi na hamsin ba wasa bane.😎 ***** WAYE SHI? AYSHA SHAFI'EE 50 (☆_☆) A hankali take taka marbles d'in cikin gidan mai wani irin santsi da barefoot kafafunta, Saboda ta ajiye takalminta tun a cikin jirgin nan, sanda ta fara fitowa ta nutsar da k'afarta a cikin yashin beach d'in da aka sauke su mai sanyi, a haka ta k'araso har cikin d'an k'aramin gidan da Imran ya nuno mata a matsayin inda zasu zauna bayan ya fito daga reception d'in da yayi musu booking. Tana tafe tana barin d'igon yashin a duk inda ta taka sannan tana kunna fitulun kowanne corridor, mamaki take na yadda gidan yake da girma fiye da yadda ta ganshi ta waje, tana ganin komai kamar a irin mafarki ko irin tunanin yadda take hango Aljanna a idonta, saboda haka yadda zuciyarta ke bugawa cike da d'oki yasa komai ya zama blurry a idonta. Dogowar hanyar data bi daga inda yayi kama da falo mai d'auke da luntsuma luntsuman kujeru guda biyu da k'arama d'aya, ya kaita wata k'atuwar k'ofa data ganta 'yar mitsitsiya a gabanta, tasa hannunta a hankali ta tura ta sannan ta kunna switch d'in fitila dake jikin bango a gefe. D'akin k'ato ne kuma komai na cikinsa fari ne tas! daga kan furnitures d'in har carpet din dake gaban gado, bedsheet, labulaye da kuma fentin komai fari ne, sannan bangon k'arshe dake gefen gado na glass ne gabad'aya dake nuna glistening view d'in waje, amma bata lura sosai da nan ba hankalinta yafi tafiya kan k'aton gadon dake tsakiyar d'akin, ta matsa ta tab'a lallausan bargon dake kai sannan ta danna hannunta ciki, she wanted to be sure everything was real! Bata jin ko a hoto ta tab'a ganin waje mai kyau irin wajen nan, ta dinga zagaye d'akin tana tab'a komai cikin mamaki, akwai tarin kayan electronics harda wanda bata san amfaninsu ba, ta tura k'ofar inda ya mata kama da toilet ta shiga, toilet din ne kuwa, sai dai cikin wata irin haduwa da bata taba gani ba, drawers koina kamar kitchen sannan wai harda wani center carpet a tsakiya, abu d'aya idonta ya gane da wuri shine bathtub, amma sink ma da kyar ta iya lalubo shi tsakanin drawers d'in. Akwai wasu irin dogwayen tagogi daga gefe, ta bud'e guda d'aya a hankali, hasken wata daga sama ya haske beach d'in dake can gabansu da kuma ruwan tekun, yashin wajen yayi wani haske a idon mai kallo sannan ga wata iska mai dad'i tana kad'awa. A sannan ne ta jiyo maganganun Imran shida Room service d'in daya d'auko kayansu daga can reception din, ta rufe windon sannan ta fito daga cikin toilet d'in. Daidai sanda shima ya bud'e k'ofar d'akin ya shigo. "Do you like white?" ya fad'a yana k'arasowa dab da ita, ta d'aga fuskarta kad'an tana kallon tasa. "Kai kayi choosing colour?" Numfashinta ya busa a fuskarsa, tana ganin yadda ya lumshe idonsa kafin ya amsa. "Na zata kina son fari." "Ina son kowacce colour Ayunie, white is great, also this place is great." Gefen kumatunsa ya lotsa alamun yaji dad'in maganarta. "Baki ga komai ba Noory, zan nuna miki duk sauran abubuwan da nayi wancan karon." "Ka tab'a zuwa dama?" "Na tab'a zuwa lokacin dana d'auki hutu sau d'aya, amma tun a lokacin ba komai na iya yi sosai ba saboda tunaninki." Sai ta sunkuyar da kanta k'asa tayi murmushi. "Yanzu kije kiyi alwala muyi Sallah." Magriba da Isha, abinda take tunani itama kenan, tunda sunyi azahar da la'asar tun a Nigeria da zasu taho. Kafin ta motsa taji ya lankwaso da kansa cikin wuyanta, lips d'insa suka yi brushing a gefen mak'ogwaronta daidai k'asan kunnenta, ta rufe idonta sannan ta damk'e yatsun k'afarta da k'arfi, kamar ya gani sai yayi dariya a hankali numfashinsa mai d'umi yana busawa akan fatarta. Da sauri ta d'an ture shi ta juya ta koma cikin toilet d'in tayi alwalar, akwai dogwayen hijabanta guda biyu a cikin akwatinsa da tasa saboda nata ya cika, d'aya daga cikinsu ta d'auko ta saka yayi musu jam'in sallolin guda biyu . Bayan sun idar order d'in abincin da yayi daga can reception d'in da suka fara tsayawa ya iso, akwai abubuwa da yawa amma in banda snack d'in samosa da fried naman kaza ba abinda Nanne ta gane a ciki toasted bread da ta gani guda uku. Sai dai duk sauran abubuwan nan da bata gane ba, haka Imran yayi ta d'ura mata su yana cewa taci shima k'arin experience ne, wani ta had'iye da kyar wani kuma ta fito masa dashi, haka zai sa hannunsa ya k'arb'a bai ko damu ba. Ita dai har a lokacin dad'a kallon wajen take tana gayawa zuciyarta cewa ta yarda ba mafarki take ba. ******** "No...!" Nanne ta fad'a tana zare idanunta. "Yes." Imran ya fad'a tsaye daga bayanta, suna tsaye daga wani balcony da ya fito ta cikin falon inda akayi wani d'an karamin pool da aka jawo ruwansa daga cikin tekun sannan ga grass carpet mai taushi da kuma flowers da fitilu masu haske kala-kala a wajen, wajen yayi kyau it felt like a dream to her! Har yanzu gani take kamar ba da gaske itace a wajen ba, kamar zata iya bud'e ido a kowanne lokaci ace mafarki take yi. Dazu taga k'ofar amma bata tab'a tunanin cewa wani wajen ne ba, tayi zaton toilet ne ko kuma d'an store kawai. Bata san sanda ta juyo da sauri ta kalle shi ba tace. "Please Ulfat zamu zauna anan har abada?" Ta fad'a tana kifkifta masa idonta alamun rok'o. Yayi dariya mai zurfi yana kallonta. "In kina so me zai hana, amma me zaki cewa su Inna?" Inna. kiran sunan da yayi ya sata tuna cewa bata kira su ba. "Ya salam! Ayunie ban kira su ba, ya kamata ace na kira su na fad'a musu inda muke tunda muka sauka." Yayi saurin rik'ota sanda take kokarin komawa ciki. "Kin san k'arfe nawa yanzu?" Ta janyo d'aya hannunsa dake rik'e da wayarsa ta kalli agogon. "K'arfe tara fa ai bata kwanta ba yanzu." "Wannan setting d'in k'asar nan ne saboda na canja Sim amma k'arfe hud'u na asuba yanzu a Nigeria." "Huh..?" Ta ware ido tana kallonsa. "Ko so kike tayi tunanin wani abun?" Ba tace komai ba ya sunkuyo da kansa daidai fuskarta. "Zamu kira ta first thing zuwa gobe, yanzu kin gaji da yawa Sa'adha, kije kisa ruwan zafi a jikinki kizo mu kwanta." Ya Allah, kunya ta kamata sanyin iskar wajen gabad'aya yasa ta manta da wani abu wai shi wanka. Ta d'aga kanta a hankali ba tare da ta kalle shi ba. A minute alone would be perfect! "Ko muje ne in taya ki?" Bata san sanda ta kalle shi da sauri tana zare ido ba, ya sake yin dariya cikin husky voice d'insa, sannan yasa kansa cikin wuyanta, wani waje dake fitting d'insa perfectly. Ya rad'a mata wani abu da muryarsa data koma can k'asa yadda taji kamar yana lasar fatar jikinta ne, taji k'afafunta sun daskare a wajen kamar k'ank'ara, tunaninta ya gwamutse a lokaci d'aya kuma kwakwalwarta ta kasa tab'uka wani tunanin. A haka yaja hannunta suka koma ciki har bakin toilet d'in. "I'm waiting for you." Yaja saman hancinta sannan ya juya ya koma ciki. Tabi bayansa da kallo kafin ta tattaro dukkan k'arfinta taja numfashi cikin k'irjinta, sannan ta kalli kafad'arta don taga ko ta kama ne da wuta, don hakan wani abu ne da Imran bai tab'a mata ba, kullum tana jikinsa amma tun lokacin da ta tashi da wannan marks, ya daina mata irin wannan abubuwan. Taji a cikin ranta cewa wajen zai k'ara kusanci a tsakaninsu. Babu wutar a kafad'arta, atleast babu a fili sai ta cikin fatarta da take jin wajen kamar an d'ora gaushi, ta lalubo jakar toiletries d'inta sannan ta koma toilet d'in, sai dai tana bud'ewa taga ta manta brush dinta, saboda haka ta shiga bud'e drawers din anan wani mamakin ya kamata, akwai komai da aka san d'an adam na iya buqata a harkar toilet, brands kala-kala masu kyau bama irin na Nigeria ba. Saboda haka ta zuge jakarta ta ajiyeta a gefe, don ba ta yadda za'a had'a kyan kayan da nata, ta d'auko wani shampoo mai ainihin k'amshin extract d'in strawberry ta wanke gashinta tsaf sannan tayi wanka, shi kansa ruwan wani irin santsi ne dashi akan fata, bayan ta gama ta d'auko wani katon towel a cikin drawer ta nannade jikinta sannan tasa wani karami ta tsane ruwan kanta, ta jona hand dryer ta taje gashinta, yayi d'umi ya kwanta smoothly har gadon bayanta. Sanda ta fito ta bud'e akwatinta, wani mamakin ya kamata, gabad'aya kayan da ta san ta jera da hannunta babu su, instead kayan da bata tab'a gani bane, k'ananan riguna da three-quarter skirts da wando, bayansu sai kayan bacci kala-kala masu mutuk'ar kyau. Undies d'inta da kuma wasu dogwayen riguna uku na material sune kad'ai abinda ta sani nata. Ta fiffito da kayan, gabad'ayansu sababbi ne da tag d'insu, bata san yaushe ya siyo ba kuma bata san yaushe ya canja su da kayanta ba, ita kad'ai amma kunyar kayan ta kamata, ta tuno da abinda ya fad'a mata a gida. "...bana jin ma duk wannan kayan zasu yi miki amfani sosai a can." Da kyar ta iya zab'ar wata rigar mai gajeren hannu kalar Pitch da kad'an ta wuce gwiwa ta saka, Ta juya wajen mirrors d'in dake kan wani dogon counter a gefenta, ai kuwa tana kalla ta juya da sauri ta juyawa mudubin baya, gaskiya ba zata iya fita a haka ba, ita da ta saba kullum cikin dogwayen rigunan barcinta...ta koma cikin akwatin ta d'auko doguwar rigar material d'inta guda d'aya, toh ai kuma yanzu dare ne, ta yaya zata zumbula wannan rigar ta kwanta? Numfashinta ya shiga fita kamar tayi gudu sannan hannunta ya fara rawa, sai kawai ta zauna akan sassayan tiles d'in d'akin ta cusa kanta a tsakanin k'afafunta, Zuciyarta ta shiga addu'ar kar ya gaji da jiranta yazo ya ganta, ta san in har ya ganta a haka shima hankalinsa zai tashi ne. Zai yi tunanin she's freaking out saboda tsoronsa ne, ba zai yarda cewa she's freaking out saboda bata san ta yadda komai zai fara ba, ba zai yarda cewa shes freaking out saboda bata san ya k'addararta zata kasance ba lokacin da ta fita daga cikin d'akin nan. Tana ji ne kamar zata fita cikin dubunnan jama'a wad'anda suke jiranta ba tare da ta san me zata fad'a ba. Ta yaya ne mutane suke iya had'iye tsoro da kuma taraddadinsu su tunkari wani abun? ta yaya zata iya zuwa wajen Imran a yanzu? Saboda kina son shi. Zuciyarta ta amsa, Da ace ba imran bane ke jiranta, Da ace zuciyarta b ata riga ta amince dashi ba, da ace kowanne particles na jikinta basu san cewa yana sonta unconditionaly ba, ba zata tab'a iya daurewa zuciyarta ba, amma Ayuninta ne ke jira saboda haka ta rad'awa kanta cewar kar taji tsoro. "Don't be a coward." K'ofar d'akin ta bud'e a lokaci d'aya, lokacin da itama ta juyo daga kallon kanta da take a mudubi. "Sulaiman ya kira ni yanzu, I don't know ke da inna wa yafi..." Maganarsa ta katse lokacin da idonsa ya gano ta, kyawawan idanunsa suka sauka akan nata, sannan a hankali suka soma sulalewa zuwa jikinta, ya tako a hankali ya k'araso gabanta, sannan yasa hannayensa ya nannad'o ta cikin jikinsa. Tana kallon yadda mak'ogwaronsa ya motsa alamun ya had'iye wani abun. "Kinyi kyau." Ya rad'a cikin kunnenta. "Kinyi kyau sosai Mine!" Ta k'ifta idonta hankali tace. "Yaushe ka siyo kayan?" Maimakon ya amsa mata sai ya d'ago hannunsa zuwa gashinta ya warware Bun d'in data k'ulle shi. "I preffered your hair loose!" Ya fad'a cikin husky voice d'insa, muryarsa mai taushi dake d'auke hankalinta. Zuciyarta ta buga da k'arfi sanda ya sunkuyo daidai fuskarsa yayi pressing lips d'insa a gefen bakinta. Ya Allah! Tunaninta ya d'auke gabad'aya, taji bakinta ya bushe sannan numfashinta ja fita da sauri, kamar zai janye gabad'aya ta suma, a cikin haka kwakwalwarta ta jiyo masa sanda ya fad'i wani abu, bata tabbatar ba amma taji kamar yace ne "Please" Sannan ya d'an tsaya kamar mai jiran wani abu, amma ta gaza yin komai, ta tsaya cak kawai hannayenta rik'e dashi ba tare da ta san me zata yi na, bayan wani d'an lokaci taji yana shirin d'aga kansa. No! not so soon...! Duk wani sauran tunaninta babu shi a lokacin, saboda haka tasa hannayenta dake rik'e da rigarsa ta janyo shi ya dawo...daga nan ta daina gane komai, magana d'aya kawai daya fad'a kwakwalwarta ta iya fahimta. "If you feel something wrong...If I hurt you, ki gaya min at once." Hasken ranar dake shigowa directly ta cikin windon shi ya tashe ta da safe. can safiya koma tsakar rana ne bata sani ba, Idonta ya bud'e tar tana ganin komai clearly, kuma ba sai tayi wani tunani ba ta san ina take, wannan farin d'akin mai k'aton farin gado, wajen tsit! k'ara d'aya ce kawai ke yawo, na kad'awar tekun dake waje. Taji zata iya kwanciya a haka tsawon lokaci tana jin dadin yanayin, amma ba abinda ya dace kenan ba, a wani waje suke mai cike da d'imbin abubuwan da take d'okin gani, She'd to get up nd face all the wonders that awaits her! Imran ya bud'e k'ofar d'akin ya shigo a daidai lokacin, sanye da wasu kayan bana jiya ba, annurin fuskarsa ya dawo mata da dukkan memories d'in da suka faru jiya, taji alamun kumaunta sunyi ja like she's blushing, and she wondered dalilin da ya kawo tsoronta da farko jiya, it seem silly a yanzu tama yi tunanin tsoro game dashi. A lokaci d'aya ya k'araso kan gadon. "Ka tashi lafiya" Ta fad'a a hankali tare da yin murmushi, maimakon ya amsa,  sai ya kwanta a gefenta sannan ya jawo hannunsa yayi stroking a hankali. Nanne ta kalli cikin idonsa, kalarsu ta canja daga bright zuwa wannan dark d'in alamun damuwa. Damuwa? me zai kawo masa damuwa a yanzu? "Ayunie me ya faru?" Muryarta ta sake fitowa a hankali fiye da d'azu. "Baki san me ya faru ba?"  Sautin muryarsa was so deep sanda ya tambaya yana tracing hannunta kamar mai bin layin wani abun. Ta k'ifta idonta a hankali tana kallonsa, sanda tunanin ko laifi ta masa yazo cikin kanta. kwalkwalwarta ta shiga lalube akan duk abinda ya faru jiya amma bata ga komai ba, ta shiga tace kowanne single memory da take iya tunawa amma ta kasa ganin wata tangard'a ko 'yar k'arama kuwa, to be honest komai ya tafi ne cikin sauqi ba kamar yadda ta zata ba, ita dashi sun dace ta hanyar data k'ara yardarwa kanta cewavana halicci kowannensu ne a matsayin abokin rayuwar d'aya, they fit together perfectly ta yadda har yanzu ta kasa gano abinda zai sa shi cikin wannan damuwar. A hankali taji hannunsa yana tab'a tattarewar da fatarta tayi a tsakanin girarta.. "Tunanin me kike yi?" "Tunanin abinda zai saka damuwa.." "Wane irin ciwo kike ji a jikinki?" Yayi saurin katse ta. "Ciwo...?" Fatar goshinta ta k'ara tattarewa lokacin da tayi focusing idonta akansa. Jikinta k'alau yake in banda gajiya kad'an da take ji a wajen gab"ob'inta ba komai, sai ko damuwar da take yi a yanzu na yadda yake son b'ata safiyar da tafi kowacce a wajensu. "Lafiyata k'alau Ulfat, ba abinda ya same ni I'm..." "Shashshsh..." Ya katse ta tare da rufe idonsa. "I'm sorry Noory, I made a mistake...Nayi laifin da nake jin na tsani kaina, dan Allah kiyi hakuri, I'm so sorry fiye da yadda zan iya fad'a miki." A wannan lokacin tasa hannayenta duka biyu tayi cupping fuskarsa. "Dan Allah ka gaya min me ya faru, me ka min? hak'urin me kake bani?" Bai bud'e idonsa ba har a lokacin kamar baya son ganinta. "Ayunie..." Ta kira shi cikin wata irin murya kamar zata yi kuka. A hankali ya tattaro ta cikin hannunsa sannan ya mik'e tsaye, bai tsaya koina ba sai gaban mudubin nan ya dire ta cikin carpet d'in har a lokacin fuskarsa take kallo, a sannan shima ya bud'e idonsa da suka k'ara rinewa suka koma so dark sannan ya juya kafad'unta hankali tayi facing mudubin. "Look at yourself Sa'adha." Cikin umarnin idanunta suka tafi cikin mudubin sannan bugun zuciyarta ya tsaya a lokaci guda. Marks, Bruises....bruises koina jikinta fal! ja jawur dasu kuma manya, gasu nan fal har wani na had'ewa da wani yadda ba wani sauran space da babu su. Tayi burd'in-bird'in da ita! ●﹏● WAYE SH? AYSHA SHAFI'EE 51 So wannan itace longest chapter da na fara rubatawa a labarin man, hope you will enjoy it!😁 (☆_☆) "Kayi shiru, I want to watch it quietly." Nanne ta fad'a a hankali idanunta na kallon can gabansu, inda rana ke shirin fad'uwa, Tana kwance a jikinsa daga k'asan wata dogowar bishiyar kwakwa a bakin tekun dake ta ambaliya wani har yana tab'o kafafunsa dake mik'e. A can gabansu rana ce ke shirin fad'uwa, wani abu ne da bata tab'a gajiya da gani tun zuwansu wajen, wani abu dake k'ara mata jin kamar ba'a cikin duniya take ba sannan wani dake k'ara k'arfin imani a zuciyarta...ranar tayi wani irin ja sannan brightness d'inta yayi reflecting a kowacce kusurwa ta yadda ya bada hasken rainbow, tana kuma yin k'asa a hankali kamar tana lumewa cikin makeken tekun dake gabansu. A sannan satinsu biyu kenan da zuwa wajen, wani lokaci da Nanne tayi wa tambari a matsayi ranakun da suka fi kowanne farin ciki a rayuwarta, the most happiest days of her life! Rayuwa ce ta kwanciyar hankali da nutsuwa, ba ruwan kowa dasu don wajen ba mutane sosai...saboda haka yadda zasu farantawa junansu rai shine kad'ai a gabansu. Sun ziyarci wajaje da yawa har da wasu island d'in dake kusa da nasu cikin irin speedboat da suka zo, a yanzu Nanne ta riga ta kware a shiga jirgin don har rige-rigen wajen zama suke ita dashi wajen da a karshe dai su biyun ne zasu zauna, har cikin ruwan sun shiga amma ba can zurfi ba, gefe kawai inda 'yan k'ananan kifaye da kuma kunkurun ruwa suke amma sai da suka sa snokel tukunna, (Wani glass d'in ruwa dake rufe ido da hanci saboda shak'ar iska.) Har da wani paddle na ruwa da ake tafiya a tsaye, abubuwa kala-kala yadda kullum suka fita sai rana ta fad'i suke komawa cikin cabin d'insu. Bayan fad'uwar rana kuma har fitowarta suke gani, Inran ya saka alarm a duk lokutan sallah saboda haka bayan sun idar da sallar asuba kullum zasu fito da overnight mat din da suka samu a cikin gidan su shimfidaa wannan balcony din na wajen pool, mat din na da laushi kamar katifa anan zasu kwanta suna facing fitowar ranar, yadda haskenta ke fitowa a hankali yana canja kalar duhun sama zuwa kamar royal blue da kuma shade d'in golden da kuma orange. Sai dai a cikin kwanakin nan, Nanne ke fuskantar wani azababben barci da kusan kullum bata san lokaci da kuma inda yake d'aukarta ba, wani lokacin suna cikin cin abinci, wani lokacin suna zaune a falo, wani lokacin ma a cikin toilet kafin ta gama brush, sai dai ta farka da safe ta ganta a d'aki. Sau da yawa zaice mata ta huta kar su fita, amma tsananin d'okin ganin sababbin abubuwa shi zaisa tayi ta rok'onsa da magiya har sai sun shirya sun fita. A yanzu bata da matsalar abinci don Menu guda suka kaiwa can wajen dake kawo musu abinci na irin simple-simple abubuwan da suka san zasu iya yi wanda su kuma zasu iya ci, don haka a kullum warmers d'insu cike suke da cima kala-kala, wani lokacin ma har sai an koma da wasu. ******* Wajen k'arfe uku na rana, dawowarsu kenan daga waje, bayan sun bawa cleaning crew d'in wajen awa biyu na gyaran cikin cabin d'in nasu. Nanne ta shiga wanka ta wanke fatarta tas! data k'ara wani sulb'i da haske a cikin kwanakin, bruises d'inta sunyi sauqi a lokacin sai dai basu tafi duka ba, har a lokacin akwai alamunsu a wani wajen, sunyi shade d'in pink kad'an. Bayan ta fito ta saka wata 'yar k'aramar riga mai kyau dark pink da d'an short da bai kai gwiwa ba, a yanzu ta riga ta saba da duka kayan nan, kullum su take saw kala-kala har gani take da ta taho da dogwayen rigunanta ba lallai ta iya sasu kullum ba, tunda wanda Imran ya bar mata ma amfaninsu in zasu fita ne kawai, amna duk inda suka je tattare abinta take tasha iska da dogon wandon da take sawa a ciki tunda ba wasu mutane a wajen. Tayi k'ok'arin b'oye murmushinta sanda idanun Imran suka zare bayan ta fito daga toilet d'in, amma cikin wucewar second d'aya yayi k'ok'arin controlling fuskarsa sannan yayi gyaran murya kad'an. "You look beautiful Noory, kinyi kyau da yawa, kamar kullum!" Ya fad'i abinda take shirin tambaya. "Awwn..." Ta dunkule hannayenta a k'irji sannan ta d'an turo bakinta tana kifta ido. "Thank you Ayunie." Ta fad'a sanda ta hau kan gadon da yake kwance yana karanta wata bussines magazine, ya mik'o hannunsa ya jawo ta jikinsa tayi hamma kad'an sannan ta d'ora kanta a kirjinsa. "Yaushe zamu koma gida?" "Har kin gaji? ke da kika ce mu zauna anan har abada." Tana murza idonta da hannu d'aya tace. "Wajen da dad'i Ulfat, amma ina missing su Inna." "Kullum fa sai kunyi waya." Ta turo bakinta kad'an. "Yau bamu yi ba." Sai ya mik'a hannunsa gefe ya jawo wayarsa yana fad'in bari a kira su toh, ta rik'o hannun nasa da sauri. "A'ah ba yanzu ba sai anjima, bacci nake ji." "Bamu ci abinci bafa...I'm afraid bana feeding dinki sosai." "You're trying, ka bari sai na tashi sai muci, na gaji yanzu." Ya ajiye magazine d'in hannunsa ya sake kwantar da kanta a jikinsa. "Ofcouse you're tired, Sleep, Love." Muryarsa can k'asa ya fara mata humming wani lullaby a hankali yana shafa bayanta. "Ban san me yasa nake yawan baccin nan ba Ayunie..." Ta fad'a a hankali idonta na shirin rufewa. "...I hope hakan bashi da alaqa da kasancewarka ba mutum ba." Yayi murmushi kad'an sannan ya cigaba da humming d'in. "Tunda nake ban tab'a irin wannan baccin mai yawa ba, kuma akai-akai haka." Ta sake fad'a muryarta so low. Humming d'in nasa ya tsaya a lokaci d'aya. "Nima I was wondering, baccin naki yaso yayi yawa habibty, ba don minshirin da kike ba, har zato nake ko kin shiga Coma ne." Da sauri idanunta suka bud'e, ta d'ago ta kalle shi. "Wallahi bana minshari." Ya d'age girarsa duka biyun. "Har da rantsewa? ni da nake tare dake kullum? To ranar da muka zo nan da kika ji iska sosai, a firgice na farka na zata wasu ne suka tayar da inji." Wani haushi ya cika mata wuya, bata san sanda ta wawuro pillon gefenta ba ta shiga maka masa, yana ta kyalkyaka dariya yana fad'in tayi hak'uri wasa yake yi! **** BAYAN SATI BIYU. "I'm sorry!" Jaamil ya sake fad'a karo na biyu yana kallon yadda tekun gabansu ke tambal-tambal cikin wani salo mai ban sha'awa. Ganin Imran bashi da niyyar amsawa yasa ya juyo gefe ya kalle shi, suna zaune a wata kujera dake facing bakin tekun. "Yarima." Ya kira sunan sa a hankali, maimakon ya amsa sai ya gyara zamansa ba tare da ya kalle shi ba yace. "Ta yaya ka san muna nan?" "Saboda na sanka, na san duk wani possibilities d'inka." "Amma ka ture wannan sanin kake son biyewa plan d'in Naani? kake kokarin yin abinda ka san zai cuce ni?" "Karo na uku kenan da nake maka bayanin cewa daga ni har Naani bamu yi wannan zancen don cutar da kai ba sai don kawai abinda muka tsara tun farko ya tafi daidai sannan a lokacin baka tsaya kaji ra'ayina ba yarima, ina fitowa ka shak'e ni da tambayoyinka." Imran yayi ajiyar zuciya sannan yace. "Naani ta sani?" "I never told her, ta cigaba da tsarinta na yadda duk lokacin da ka kawo yarinyar zata raba ruhin da jikinta, a kwanakin baya ma ta kirani da saqon cewa in gaya maka zata nemeka nan gaba, saboda da farko ta gaya maka zata kira ka ne bayan sati d'aya." "Ba zan taba kawo ta ba." Muryarsa ta fito kai tsaye. "Na sani, amma ta yaya zaka iya karb'ar dutsen in lokaci yayi? tunda ka san b'arinka d'aya ba zai taba iyawa ba." "I'm figuring a way out Jaamil, ban san wace hanya zan samo ba amma definetly zan samo hanyar da zan kare Sa'adha, I will, surely!" Jaamil ya juyo ya kalle shi kamar mai karantar wani abun sannan ya koma da kallonsa kan tekun. "Sooo..." yaja maganar yana kallon yatsunsa. "Ta yarda dani." Imran ya fad'i amsar tambayar da bai furta da dogon kalamai ba. "Na gaya mata komai kuma ta yarda dani jaamil, tace it doesnt matter ko ni meye, zuciyarta ta riga ta amince kuma zata zauna dani." Jaamil ya d'aga kansa kafin yace. "Kuma ka fad'a mata abinda Naani tace?" "Ba zan iya fad'a mata wannan ba, ba zan iya karya zuciyarta bayan yardar data riga ta bani ba, saboda haka na gaya mata Naani bata dawo ba, kuma kota dawo zan san hanyar da zan kare ta." "Insha Allah, zamu samo mafita yarima." Sai a sannan Imran ya kalle shi cike da mamaki. shima ya juyo yayi focusing sosai yana kallonsa. "Tun tasowarmu tare muke komai yarima, bamu tab'a banbanta wani abu namu ba, sannan tare muka fara wannan abin, tare Naani ta turo mu yin aikin nan, tare muka samo mafitar waccan matsalar, me yasa kake tunanin don wani abu ya faru yanzu hakan zai canja?" Imran ya had'iye yawu kafin ya maida kallonsa kan tekun, a hankali muryarsa ta fito. "Thank you." Jaamil ya juyar da kansa shima sannan suka yi shiru. Zuwa can yace. "And I like your wife, tana da kirki." Imran yaji murmushin jin dad'i ya cika bakinsa, ya kasa daurewa har saida hakan ya fito. Daga nan suka shiga tattaunawa akan yadda zasu b'ullowa lamarin ba tare da Naani ta sani ba, sun dad'e sosai kafin su fitar da wani kwakwaran plan wanda babu makawa shi zai zame musu mafita. Kafin su rabu hirarsu ta dawo daidai kamar ba abinda ya tab'a had'a su, dama haka yake kowannensu baya iya fushi da d'an'uwansa. *** Mafarkin ya fara ne a wannan wajen, wannan filin mai tarin bishiyun da ta san cewa abinda tazo nema yana cikinsu, sai dai a wannan karon babu muryoyin su inna dake kiran sunanta daga can nesa. Sannan kamar wancan lokacin Imran ya fito daga cikin bishiyun nan yana kallonta da lumsassun idanunsa, kamar koyaushe yayi wani irin kyau sanye da light kaya, fuskarsa ta haska, sannan kyakkyawan murmushinsa ya kwanta sosai a gefen fuskarsa, sai da ta shagala da kallonsa sannan ya d'ago yatsansa guda d'aya yayi mata alamun ta biyo shi sannan ya juya ya koma cikin bishiyun. Taku daya kawai ya shigar da ita cikin duhun bishiyun, amma sai wajen ya zama sab'anin tunaninta kamar wancan karon, a maimakon duhu wajen mai haske ne da kuma kyau, korayen ciyayi da fulawowi sun baje a koina, ga wani dutse daga can gefe yana zub da ruwa. Taji wani ya rungumeta ta baya, hannayensa sun zagaye k'ugunta sannan ya d'ora hab'arsa a daidai lungun wuyanta, ko bata juya ba ta san Imran ne kuma zuciyarta ta riga ta nutsu dashi, saboda haka ta cigaba da tsaiwa ba tare da ta juya ba tana jin d'umin jikinsa akan fatarta da kuma yadda numfashinsa ke busawa a k'asan kunnenta. A lokacin ne abin ya faru, taji an caka mata wani abu mai tsini a wuyanta, abin ya huda tun daga farkon wuyanta ya fito ta d'aya gefen. Numfashinta ya tsaya cak, sannan jini ya shiga gangarowa kan fatarta, tayi k'asa ta fad'i da baya sannan zafi ya shiga bin kowacce jijiya ta jikinta, taji ruhinta na barin jikinta a hankali sannan idonta na shirin rufewa. Amma kafin komai ya d'auke mata, fuskar Imran ta shigo cikin ganinta, yana tsaye kamar lokacin baya akanta da wannan murmushin dake murkushe zuciyarta, sai dai wannan karon a gefensa akwai wani d'an karamin yaro fari tas! mai mutuk'ar kyau dake ta b'angala mata dariya, a hankali idonta ya dawo kan hannun Imran wanda ke ta faman d'igar da jini! Ta mik'e da wani irin sauri lokacin data farka daga baccin. D'akin yayi duhu sakamakon yamma data yi sosai kuma an saki curtains d'in gabad'aya harda na jikin glass wall din an zuge shi, akwai sanyi air condition kad'an, amma taji gumi na gangarowa ta cikin gashinta. Ta kai hannunta jikin bango ta kunna fitila, haske ya dallare koina, hasken daya nuna mata cewar Imran baya d'akin, a sannan ne kuma Idonta kan tarin takardun dake baje kusan koina a d'akin. Kan drawars, gado, mudubi, da duk wani abu da yake da space a d'akin, ta mik'a hannu ta d'auko guda da'aya dake gefenta akan side-drawer. I'm hoping ba zaki karanta takardar nan ba saboda ba dad'ewa zanyi ba, amma in har kina karantawa yanzu, wani abu ya rik'e ni kenan...but I 'll be back very soon, kiyi sallah kici abinci sannan ki koma baccinki kinjii...? Zaki ganni lokacin da kika sake tashi insha Allah. I love you... ...like crazy! "I love you too." Ta fad'a a hankali sannan ta maida ninkin paper ta rufe, ta mik'e ta tattaro dukkan sauran na d'akin da abu d'aya suke fad'a ta zuba su a handbag d'inta. Ta shiga toilet tayi alwala tayi sallar La'asar data nemi ta kub'uce mata sannan ta sake wanka, kamar wancan karon bata sa mafarkin nan a cikin kanta ba, abu d'aya ne kawai ya tsaya mata a rai...wannan kyakkyawan yaron dake tsaye a kusa da Imran yana b'angala mata dariya. Bayan ta shirya ta fito don samun abinda zata ci kamar yadda Imran yace, ba wai yunwa take ji sosai ba amma tunda ya fad'a dole ne taci, tana tafe tana kunna duk switches d'in data san shi ya kashe da zai fita. Ta k'ara jin gidan ya mata shiru fye da koyaushe sannan ta dinga ganin koina wani iri. Different somehow. A kan stool d'in jikin counter ta zauna tana ta kallon abincin dake cikin warmers d'in, haka kurum take jin bakinta ba dad'i saboda haka tayi tagumi tana tunanin me zata ci. Da kyar ta tsaida zuciyarta ta janyo wani bowl dake cike da potato soup yasha yankan vegetables round kala-kala. Yawu ya taru a bakinta tun kafin ma ta fara ci saboda haka ta ajiye cokalin data d'auko tasa hannunta ta fara, tana ci tana lashe hannu kamar wadda aka sanmata. Sai dai bata kai ga ko ci da yawa ba ta fara rage taunarta a hankali... Me ya same shi? wani irin k'amshi yake, ko dai ya fara lalacewa ne? Ta kai hancinta ta shinshina, ai kuwa wani irin k'amshi ne ko wari ya daki hancinta, bata san sanda tayi wulli dashi ba ta matsa da sauri jikin sink ta shiga kwara amai. Sai da ta fito da duk wanda taci sannan ya tsaya ta d'auraye bakinta a hankali ta had'a har da fuskarta, tana d'agowa taji kuma kamar jiri ya kamaya, gidan ya fara juya mata saboda haka ta lalubi kujera ta dunk'ule akai, a can d'aya side din kujerar akwai wani blanket, amma kafin ta iya d'auko shi ta lullub'a wani sabon baccin yayi awon gaba da ita. Sanda ta sake farkawa duhu yayi sosai, kuma Imran na zaune a gabanta, gaban kujerar da take kai. "I'm sorry, ya fad'a yana shafa fuskarta a hankali. "I'm sorry na barki ke kad'ai, wani uzurin ne..." Bata ji k'arshen zancensa ba ta ture hannunsa da sauri sannan ta tashi da gudu tayi d'aki, ta banka k'ofar toilet din ta nufi sink ta shiga kwara wani sabon aman kamar zai had'o da hanjin cikinta. "Noory me ya faru? me ya same ki?" He was there in an instant! ya rik'o ta yana janye gashinta daga fuskarta. sai da numfashinta ya dawo daidai, sannan ta kalle shi, idanunta sun ciko da kwalla tace. "You don't need to see this, dan Allah kaje, amai fa nake yi." Bai ko kula ta ba ya mik'ar da ita tsaye, ya bud'e fanfon aman ya wuce sannan ya d'auraye mata baki suka fita. "Abinci naci ya fara lallacewa." Ta fad'a sanda ya zaunar da ita akan gadon. "Wane iri ne?" "Yana nan akan counter." Ya mik'e da sauri ya koma falon sai ta maida kanta kan pillow ta sake dulunkunewa. Bayan kamar minti ashirin ya dawo d'akin, ya tsugunna a gabanta ya d'ora hannunsa akan goshinta. "Ya kike ji yanzu?" Ta daure tayi murmushi tana kallonsa. "Lafiya k'alau." "Zan kira likita yanzu ya duba ki." Da sauri tace. "Amai ne fa kawai Ayunie, ba wai ciwo bane I'm fine, dan Allah kar ka kira su." "Allura kike tsoro?" "Harda magani ma bana so." Yayi shiru yana kallonta, ba yadda ya iya saboda haka yace. "Nasa an fitar da duk abincin an kawo sababbi, ki taso muje kici tunda ba komai a cikinki yanzu." Da kyar ta samu taci meatpie guda uku sanda ya d'auke ta ya maida ita falon, yana bata a baki yana tab'a jikinta da k'ara tambayar yadda take ji, tunda tana bashi amsar cewa ba komai, har in ya tambayeta sai ta lankwasar da muryarta ta fad'o wani k'aton ciwon, hakan ke sawa su kyalkyale da dariya. Bayan sunyi sallar isha, ya kunna t.v suna kallon wani funny American film na wasu teenagers, don shelf guda ne cike da movies kala-kala harda cartoons, tana zaton ma wajen yafi wani gidan saida CD's d'in yawansu. Tun ita kad'ai ke dariyar yana karanta bussines magazine d'insa har dai ya ajiye shima ya biye mata. Kafin su kwanta, she was so happy da har ta manta da jirin da take d'anji. Sai dai k'arfe biyun dare, ta tashi da wani irin ciwon cikin da yasa ta amayar da dukka meatpie d'in nan. "Sa'adha...." Imran ya fad'a yana kwankwasa k'ofar toilet d'in don ta k'ulle wannan karon. "Open the door, ki bud'e min." Bata ko motsa ba, idonta na kan cikin toilet sink d'in wanda ya rine jawur da jini, aman nata ya had'o da wani rin jini mai yawa da har dunk'ulewa yake, kamar wani abu ya fashe a cikin ta, ta mike da sauri tayi floushing, da ragowarsa har a lokacin saboda haka ta sake dannawa sanda taji hannun Imran ya rik'o ta. Ta juya da sauri ta kalle shi, sannan k'ofar wadda handle d'inta yake a karye. "I'm calling a doctor now." "Ayunie amai ne fa..." "I don't care..." ya katseta. "...Baki da lafiya shine kad'ai abinda na sani." Ta d'ora kanta akan k'irjinsa shi kuma yasa hannunsa ya rungume ta. "Aman da nayi harda jini." She finally admit a hankali. taji yadda k'arar bugun zuciyarsa ya canja a lokaci d'aya sannan rik'on da yayi mata ya d'an saki, daga can yayi ajiyar zuciya sannan yace. "Abin yayi yawa Noory, dole ne muga likita...yawan bacci, tashin zuciya amai kuma har da..." Sai dai kafin ya k'arasa kwakwalwar Nanne ta ta tsinci wani abin, ta d'ago kanta da sauri tana kallon fuskarsa, kamar me shirin d'auko wani abu nata daya fad'i. "Me ya faru? Tunanin me kike?" Bata ce komai ba ta cigaba da kallonsa blankly, fatar goshinta na tattarewa alamun tunani. Ya d'ora hannunsa akan goshinta. "What's wrong?" Maimakon ta amsa masa sai ta sake shi da sauri ta fita daga toilet d'in, ta kunna fitilar d'akin haske ya dallare koina, a jikin mudubi ta lalubo wayarta, hannayenta na rawa ta shiga k'ok'arin bud'ewa. "Sa'adha, I'm loosing my mind...me yake faruwa ne?" Muryarsa ta biyo bayanta. Tana bud'e application d'in da take nema, wayar ta sub'uce daga hannunta ta daki tiles din k'asa. Ya k'araso gabanta ya rik'e hannayenta da suke rawa. "Sa'adha...." Kafin ya k'arasa muryarta ma dake rawa tace. "Yau wane Date?" "25th...gida kike son tafiya?" Ta girgiza kanta da sauri sannan ta had'iye wani k'aton abu a makogwaronta. "Period d'ina yayi latti da kwana bakwai!" ●﹏● Zan muku alqawari saura couple of chapters mu rufe labarin nan!😊 ***** WAYE SHI? AYSHA SHAFI'EE 52 (☆_☆) "Is it possible? zai iya yiwuwa?" Abinda Nanne ta iya fahimta a cikin kalaman Imran dake waya kenan kawai, wayar da yayi kusan awa d'aya yana yi da wani irin yaren da bata ganewa, bayan wannan hausar da yayi ta farko, sunanta kawai ta iya tsinta wanda ya had'o tare da gwamutsin kalmomin da bata san ma'anarsu ba. Mamaki take na shi dawa yake waya haka? me yake son tabbatarwa bayan likitan da ya kira yazo ya tabbatar musu cewa da gaske ne tana da ciki. CIKI. Ciki wai... Ta rufe idonta a hankali, tunda take a rayuwarta tunaninta bai tab'a hango mata kanta a matsayin UWA ba, ta san dai cewa tunanin 'ya'yan da zata iya haifa da Imran yazo cikin kanta, amma d'aukar cikin da haihuwarsa wani abu ne da babu shi a register kwakwalwarta. Ta kai hannu ta shafa saman cikin nata a hankali, a yanzu halitta ce a jikinsa, halittar da take combination dinta ita da imran, halittar da zai girma zuwa wani lokacin ya fito a matsayin d'an baby, irin babies d'in da take hangowa a hannun mutane, itama zata samu nata...nata na kanta da zai zama cikin ikonta sannan nata itada Imran! A hankali kwakwalwarta ta shiga imagining yadda kammanin babyn zai kasance, ko mace ce ko namiji zata fi so ya d'auko kammanin Imran sosai, yadda duk sanda ta kalle shi zata ga abinda zuciyarta ke k'auna guda biyu awaje d'aya, don duniyarta ta canja daga lokacin da likitan nan ya furta cewa taba d'auke da cikin Imran, taji kamar zuciyarta ta k'ara girma ne ta fito da tsiron wata k'aunar sab'anin ta Imran, abu d'aya da take ji ba zata iya rayuwa babu shi ba a yanzu ya zama biyu. K'aunar abinda ke cikinta ya mamaye dukka ilahirin jikinta, irin wannan k'aunar da zaka ji kamar zuciyarka na fitar da tiriri ne na son tabbatar da abinda kake so, Allah ya sani a lokacin tana son Babyn cikinta kamar yadda take k'aunar ranta, watakila ma fiye. She wanted him so badly! Hannun ta yana kan cikinta kuma zuciyarta nata sak'e-saken abinda zai faru nan gaba sanda taji hannun Imran ya dafa saman nata. "Ciwon yake sake yi?" Muryarsa ta fito da alamun tsananin damuwar da yake son kwantarwa. Ta girgiza kanta da sauri. "Bana jin komai." Ta amsa idanunta na kallonsa cike da mamaki, fuskarsa _was hard!_ babu wani emotion da zata iya tsinta a ciki, ita tayi zaton ganin farin ciki ko yaya ne a fuskarsa... for crying out loud ba'ayi ko awa d'aya ba fa da gaya musu sak'on da yafi kowanne muhimmanci a rayuwarsu, amma tun wannan d'an guntun murmushin da yayi wa likitan babu wata sigar farin ciki data gani tare dashi. Ta juyo da hannunta ta rik'o nasan tana cigaba da kallonsa, Kafin tayi magana ya rigata. "Ki kwantar da hankaliki dan Allah Noory, ba abinda zai faru kinji?" Ba abinda zai faru kamar yaya? itafa bata gane me yake nufi ba, anya kuwa ya fahimci ma me aka ce? ciki fa akace tana dashi, cikin dake shirin kawo d'a a tsakaninsu, ita ta zata daga fitar likitan zai k'ank'ameta ne saboda farin ciki ko ya d'auke ta ne yayi ta juyi da ita a cikin d'akin suna godewa Allah. "Me kake nufi? Ba abinda zai faru a ina?" Ta yanke shawarar tambaya. "Ba abinda zai same ki insha Allah ba abinda zan bari ya same ki, Nayi kuskure tun farko wanda ba zai gyaru ba, amma nayi miki rantsuwa ban taba tunanin cewa haka zai iya faruwa ba, da tuntuni na kare hakan...saboda waninmu bai taba shigowa cikin mutane ba, irin haka bata taba faruwa ba." Kanta ya d'aure ta kasa fahimtar komai a cikin zancensa. "Na kira jaamil yanzu munyi magana, akwai mahaifiyarsa bwama itama tana da jiki irin na mutane saboda yawan rashin lafiyarta da take zuwa kasashe daban-daban neman magani, zasu zo tare a cire wannan abun Noory insha Allah, tun kafin ya cutar dake." Abu? d'an da zata haifa shine abu? Imran baya son Babynsu kenan? Baya son abinda zata haifa? Me yake nufi? Ta yaya d'an mitsitsin halitta zai cutar da ita? A lokaci d'aya tunanin dake cikin kanta ya canja, hoton da take gani Imran d'auke da ita yana murna ya juye zuwa shi da jaamil suna k'ok'arin kashe d'anta, d'an kyakkyawan Babynta, kunnenta ya karad'e da k'arar kukansa. Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! tunaninta ya hargitse a lokaci d'aya, ba zata taba yarda ba, ba wanda zai rabata da d'an dake cikinta, ba zata taba bari a cutar dashi ba, ko waye kuwa, ko shi Imran d'in ne kansa! Taji sanda ya zame hannunsa daga cikin nata ya mik'e tsaye yana amsa wata wayar, cikin yare irin na d'azu, ta tabbata jaamil d'in ne suke sake tattauna abinda ba zai tab'a kasancewa ba. Juyowar da Imran zaiyi cikin wayar ya kula da hawayen da take yi, Ya salam! ba dai wani ciwon take sake ji bada sauri ya kashe wayar ya dawo gabanta. "Sa'adha me ya faru?" "Ayunie so kake ka kashe Babyn mu?" muryarta ta fito cikin rawa. Ya d'an tsuke ido yana kallonta, Baby? tunanin da take kenan? tunani take abinda ke cikinta Baby ne? "Sa'adha we don't know what's in there...na gaya miki irin haka bai tab'a faruwa da irinmu ba, sanda nake wannan kuskuren ban taba sanin cewa ciki zai iya shiga jikinki ba, so for all we know a yanzu abinda ke jikinki zai iya cutar dake." Ta girgiza kanta da sauri. "Ta yaya zai cutar dani wai? ta yaya zai cuce..." "Kin manta ni ba mutum bane?" Yayi saurin katseta, ganin alamun bata fahimce shi ba ko kad'an. A lokacin d'aya fuskarta ta koma blank! idanunta suka zare kamar yaune rana ta farko data ji hakan, don har ga Allah ita mantawa take Imran ba mutum bane tunda bata tab'a ganin wata alamar hakan a tare dashi komai nasa irin na mutane ne sak! ba wata tangard'a. "Kin manta waye ni? ni ba mutum bane Sa'adha, saboda haka bana tunanin abinda ke cikinki zai iya zama mutum, zaki iya haifarsa da wata jirkitattiyar halittar or worse yazo a irin siffar mu... Look bama wannan ba, ba zaki iya ba,  jikin mutane da namu ba iri d'aya bane, halittarmu tana da k'arfin possesing abubuwa da yawa while mutane are weak, you're not strong for this Noory!" Duk wannan bayanin da Imran yake yi, kwakwalwar Nanne ba fahimta take yi ba, abu d'aya kawai take gane shine Imran baya son Babynsu saboda baya so ko kad'an a samu wata alama da zata tab'a nuna cewa shi ba mutum bane, amma ita bata damu da wannan ba, in har Imran ya kasance k'addararta toh zata rik'i wannan ma a matsayin wata k'addarar tata, zata yi k'ok'ari da dukkan iyawarta ta raini Babynta, tana ji a jikinta cewa hakan wani alkhairi ne nata... So atleast she would try! "Dan Allah ki fahimce ni." Ya fad'a yana sake rik'o hannunta. Ta tsaida idonta sosai akansa sannan tace. "Na fahimceka Ulfat, kuma nima ina son ka fahimce ni, ina son ka fahimci cewa ba zan tab'a iya kashe shi ba." A lokaci d'aya kalar idanunsa suka yi duhu sosai alamun b'acin rai. "Sa'adha, ba lallai irin Babyn da kike tunani bane a cikinki, for one second ki bud'e kwakwalwarki ki gane me nake nufi, abin nan zai cutar dake ta irin hanyar da baki sani ba, it's not some pretty Babyn da kike tunani." Itama nata ran ya b'aci, ta d'age girarta d'aya. "Zamu gani toh." Tana fad'in haka ta mik'e tayi hanyar d'aki, ba tare da wani tunani ba Imran ya b'ace cikin iska ya baiyana a gabanta, a lokacin da bugun zuciyarta yayi wani irin bugawa cikin kunnensa, a lokacin yayi dana sanin abinda yayi, don ba sai ta fad'a masa ba ta tsorata sosai da hakan, amma tunanin zancen da suke yi ya danne wanda ke cewa ya bata hak'uri. "Me yasa ba zaki gane abinda nake nufi bane? i can't stand to see you in pain,_Sa'adha abin nan zai iya kashe ki!" Nanne ta had'iye tsoron dake kanta, yanzu ta k'ara fahimtar wani abin, yana tunanin zata iya mutuwa shi yasa ya damu kansa haka, baya son ya rasa ta, watakila sunyi daidai kenan a haka, itama tana tsananin son abinda ke cikinta baza taba iya bari ta rasa shi ba, saboda haka tace. "Ba zai kashe ni ba Imran, I can do this." Tana fadin haka ta k'arasa cikin d'aki ta rufo k'ofar, yaji sanda ta murd'a lock d'in ta k'ulle alamun bata buk'atar company d'insa, amma ba wannan ne ya dame shi ba, the fact that ta kira shi da Imran, wani abu ne da ya kwana da sanin cewa duk sanda ta kira sunansa toh ko tana cikin rud'ani ko kuma fushi, wanda a yanzu ya tabbata fushin take ji, A hankali ya zame k'asa ya zauna akan dandaryar tiles d'in, bayansa ya jingina da bangon corridor d'in. Ya kai hannunsa don ya share gumin daya fito masa, amma sai yatsunsa suka nutse kamar zasu d'ago da fatarsa, duhun kwayar idonsa ya sake haskawa cikin sockets d'insu sannan bakinsa ya bud'e kamar zai yi ihu amma ba abinda ya fito. Sa'adha fushi take dashi? ta yaya zaiyi mata bayanin cewa ba zata iya d'aukar abinda ke cikinta ba, ta yaya zai zai fad'a mata ta fahimce shi su gyara kuskuren da yayi. Me yasa ne abubuwa basa tab'a zama masa daidai game da ita? me yasa baya iya controlling zuciyarsa akanta? Baya tab'a behaving rules d'in da suka dace... he's just being himself around her! Saboda tana sawa yaji shi complete yaji shima wani ne mai iko, don tunda yake bai tab'a jin yana son abu kamar yadda yake son Sa'adha ba. Yana zaune a wajen bai motsa ba har lokacin da alarm d'in wayarsa ya buga k'arfe d'aya lokacin sallar Azahar, bai san ya akayi taji alarm d'in ba don bayan wani lokaci yaji karar zubar ruwa daga can toilet d'in d'akin hakan ya tabbatar masa yau jam'in da suke yi ba zai samu ba kenan, saboda haka ya fita can balcony yayi tasa alwalar sannan ya shigo yayi sallah, sai dai har wajen k'arfe uku Sa'adha bata fito daga cikin d'akin nan ba shi kuma yayi alqawarin ba zai takura mata ba, zai barta tayi dukkan irin tunanin cikin kanta wataqila hakan zaiyi knocking sense cikin kanta ta fahimci abinda yake nufi. Yaji gabad'aya ya takura gidan ya masa wani iri, duniyar ta tsaya masa cak! sannan zuciyarsa ta matse na rashin sanin ainihin tunanin da take game dashi. Ya kasa yin komai, Jaamil ya sake kiransa fiye da sau goma amma yana kallo ya kasa d'auka. There had never been something like you and sa'adha before, dole sai kayi hankali da kasancewarku tare... Banbancin halittarku shi zai iya jawo wata matsalar a zamanku, akwai abubuwa da yawa da sai kayi taka tsan-tsan game dasu, strong emotion d'inka zai iya kawo wani abun yarima. Ya tuno maganganun da jaamil ya fad'a masa ana gobe d'aurin aurensa da Sa'adha, gashi bai kiyaye komai a ciki ba. Sai bayan La'asar sannan Nanne ta fito daga cikin d'akin, ta same shi daga jikin counter saboda haka ta tsaya daga nan, Zuciyarta tayi wani irin nauyi sanda ya d'ago ya kalleta, da lumsasun idanunsa dake cike taf da damuwa. Imran ya gyara zamansa sosai yana kallonta, tayi wanka ta canja kayanta zuwa wata 'yar pink riga mai kyau iya gwiwa, ya tuna sanda ya hango rigar daga can sama bayan ya gama d'ebo sauran yazo biyan kudi, haka kurum tayi masa kyau yace a d'auko ta a had'a da ita. k'afarta ta dama a tsaye take, ta hagu kuma akan babban d'an yatsanta tana juyawa, kamar abinda yaro yake yi in zai tambayi abu yana kuma shakka. "Ina so in tambayeka wani abu." Ta yanke shawarar magana lokacin da taga bashi da niyyar barin kallonta. "Ina jinki habibty." Ya fada shima daga inda yake zaune. "I want to go home, ina son inje gida." Ya gyad'a kansa a take. "Zan duba inda flight gobe zan mana booking." Ta gyad'a kanta a hankali, sannan ta juya ta koma ciki, Imran yabi bayanta da kallo yana jin kamar ya mik'a hannunsa ya jawo ta, _this is toture!_ bata san yadda rashinta a d'an lokacin nan ke azabatar dashi ba. Ya kifa kansa akan counter lokacin da itama ta buga k'ofar d'akin ta rufo. Wasa-wasa har sallar isha Nanne bata da alamun fitowa daga d'akin, saboda haka bayan ya idar da salkar isha ya hada mata tea mai kauri sannan ya d'ebi wani abincin da wasu snacks d'in ya nufi d'akin, yayi niyyar b'alla k'ofar amma ga mamakinsa ya turawa ya ganta a bud'e. Ya shiga ya kunna fitilar dake kashe, a lokaci d'aya ya hango ta lullub'e daga tsakiyar gadon ta takure kanta. Ya ajiye kayan da sauri ya isa gareta. "Sa'adha me ya sameki? Ciwo kike ji?" Ta d'ago da jikakkun idanunta ta kalle shi. "Sai yanzu kaga damar zuwa? Ayunie tun d'azu nake jiranka." Bai san sanda ya janyo ta gabad'aya jikinsa ya rungume ta ba. "I'm so sorry Noory, na zata kina buqatar lokaci ne ke kadai." "Wane lokacin nake buqata ni kad'ai ulfat? wane lokacin nake buqata da babu kai?" Ya sake rungumeta yana shafa bayanta. "Kiyi hakuri, na zata fushi kike dani." Ta dunk'ule hannunta ta shiga dukan kirjinsa. "Fushi nake yi da kai mana, fushi nake yi da kai sosai, kuma tun d'azu nake jiran kazo ka bani hak'uri..." "Toh ai kin k'ulle k'ofarki." "Ba ka iya b'allawa ba, jiya ba ka b'alla k'ofar toilet ba, ba sai ka b'alla ka shigo ba." Ya d'ago da fukarta daga jikinsa ya kalle ta. "Toh Noory sai in ta b'alla musu k'ofofi?" Ta sake kai masa wani dunk'ulallen naushi, shi kuma ya k'ara rungumeta a jikinsa! A can cikin rigarsa ya jiyo muryarta. "Ba zan mutu ba Ayunie, I will keep my heart beating, inada k'arfin da zan iya rik'e Babynmu insha Allah, ina son shi Ulfat...ina son shi sosai!" ●﹏● So we just had our first fight! Nanne da Ayuninta sunyi fad'a...!😜 Me kuke tunani game da abinda Nanne ta fad'a a k'arshe? Kuna ganin Imran zai bar mata Babyn?...ko kuma ince littlle monster kamar yadda Imran yake tunani?_😁 **** WAYE SHI? AYSHA SHAFI'EE 53 So I tynk ban tab'a dedicating chapter to kowa ba, amma yau i would lyk to dedicate dix chapter to all my university fans... wad'anda makaranta ta b'oye min su bana jin comments kwana biyu...I feel you guys Allah ya taimaka muku!🙏 Sauran readers d'ina kuma na gaishe ku, hope kuna cikin farin ciki, if not Allah sa kuji alert!😁 (☆_☆) "Zamu iya shiga yanzu." Jaamil ya fad'a yana kallon mahaifiyarsa, suna tsaye daga balcony main k'ofar da zata shigar dasu cikin gidan Imran. A lokacin zuwansu kenan daga can Muzzaffar cikin tafiyar da suka kusan kwana suna yi saboda rashin lafiyar jikinta sosai. Daga lokacin da ya zauna ya shaida mata dukkan abinda ya faru da Yarima da kuma irin taimakonta da suke nema daga sannan hankalinta ya tashi ta rasa nutsuwarta sai da tasa suka taho a lokacin. Ya riga ya sani a koyaushe mahaifiyarsa tana d'aukan al'amarin yarima da daraja, duk sanda wani abu nasa ya taso zata bada dukkan kulawar da zata iya, don har cikin zuciyarta ta amince shi d'a ne a wajen 'yar uwarta NAANI, ta yarda da hakan tun daga ranar da Naani ta d'auko shi ta kawo shi cikin masarautar, zai iya cewa mahaifiyarsa itace sanadin abokantakarsa da yarima, don a farkon zuwan yariman basa shiri ko kad'an, sai da taimakonta da kuma yadda take jawo shi a jiki sannan suka zo suka fahimci juna. Baya manta ranar da Naani ta kira mahaifiyarsa tayi ta mata fad'a akan yadda take kokarin janye shi daga wajenta, a cewarta tana masa abubuwan da ita bata yi masa saboda haka ta mata gargadin shiga harkarsa, a wannan ranar ya tabbatar da cewa Naani zata iya b'atawa da kowa akan yarima, daga wannan ranar kuma alaqar mahaifiyarsa da yariman ta nesanta, amma bata tab'a gaza bashi taimakonta ba a duk lokacin da zata iya, saboda haka ya san ba abin mamaki bane don ta rikice jin irin matsalar da yake ciki a yanzu, matsalar da ko Naani bata san da ita ba. Kamar yadda shima baiyi mamaki ba lokacin da yariman ya kira shi ya shaida masa halin da Sa'adha take ciki, don tun daga ranar daya same su a asibitin nan, kuma yaje har gidansu yaga irin rayuwar da suke shimfid'iwa, zuciyarsa ta gaya masa cewa Imran ya bar cikinsu har abada, banda b'arin ruhinsa zuciyarsa ma tana tare da ita kuma baya jin akwai wani dalili a duniyar nan da zai iya sawa ya rabu da ita. "Ka tabbata da yardarta zan ganta? ka san fa ban tab'a had'uwa da bil'adaman daya san ainihin koni wacece ba." Jaamil ya kamo hannayenta duka biyun. "Bwama, ni ban san mutane ba kuma ban san halaiyarsu ba, amma na san cewa yarinyar nan tana d'aya daga cikin d'aid'aikun mutanen da ba a koina ake samunsu ba, tana da kyakkyawar zuciya, k'arfin hali da kuma rashin tsoro, ta amince da yarima ta bashi yardarta duk da sanin da tayi na waye shi, sannan a yanzu tana shirin saudakar da rayuwarta saboda wani abu nasa, me yasa kike tunanin ganinki zai girgiza zuciyarta?" Bwama ta gyad'a kanta a hankali cike da fahimta sannan jaamil ya saki d'aya hannunta ya bud'e k'ofar dake gabansu. "Na yarda da ita Noory, ba abinda zata miki." Ya tsinkayi muryar Imran cikin whisper lokacin da suke taka corridor d'in da zai sada su da falon gidan. "I trust you too Ulfat!" Soft muryarta ta fito bayan tasa, a hankali kamar mai rad'a, ya runtse idonsa kad'an da tunanin yadda take bawa Imran wata irin makauniyar yarda da baiyi deserving ba. A lokacin da suka yi kwanar cikin main falon, a lokacin idanun bwama suka hango mata Sa'adha tsaye daga jikin Imran d'in, hancinta ya shak'o mata k'amshinta a take. The warm clean k'amshin bil'adama! Kusan tana b'oye a jikinsa sanye da doguwar rigar abaya bak'a, ta yafa jan mayafi d'an k'arami a kanta. A cikin sakan d'aya bata ga komai ba sai ainihin kammanin bil'adama kawai, fatar ta mai kyau mai taushi, sannan idonta manya chocolate colour...lips d'inta a tsuke kamar tana tamke wani abin. A sannan ne kuma bwama ta lura da kammaninta sosai, kammanin dake can k'asa suna fara rarake ta a hankali, so slowly yadda idanun mutane ba zai iya gani ba...k'asan idanunta sun fara rami suna zurmawa k'asa, fatarta ta wajen kuncinta ta tattare kamar zata tsinke, gashinta daya fito ta saman mayafin ya fara dunk'ulewa sannan akwai alamun yatsunta da k'ugunta sun fara ramewa. Hakan ya tabbatar mata cewa duk abinda ke cikin Sa'adha a lokacin ya fara janye karfin jikinta ne yana gina nasa. "Barka da zuwa bwama." Imran ya fad'a cikin yaren hausa, ta fahimci yayi hakan ne don matarsa saboda haka itama ta amsa masa da murmushi. "Barkanmu yarima, Barkanmu dai!" Nanne ta kalli Imran da gefen idonta d'aya, da kai ya mata alamar cewa zata iya magana saboda haka ta kalli bwama tace. "Barka da zuwa Mama." Ta fad'i hakan ne saboda bata san ma'anar bwama ba, saboda ba zata iya fadar sunanta kai tsaye ba, sai dai kuma hakan yasa bwama jin wata irin kauna da tausayinta, ta ayyana a ranta cewa Nanne nada zuciya mai kyau duk da wannan shine farkon had'uwarsu, amma zuciyarta mai kyau ce tunda har bata iya hasaso mata irin had'arin data ke shirin sa kanta a ciki ba, had'arin dake shirin tauye rayuwarta, saboda haka maimakon ta amsa sai ta k'arasa da sauri ta fito da ita daga jikin Imran sannan ta rungume ta. A lokacin Imran yaga cewar ya dace su basu guri, saboda haka ya murza yatsunta da basu gama fita daga cikin nasa ba a hankali sannan yayi wa jaamil alama da zasu iya fita. Ta saman kafad'un bwama Nanne tabi bayansa da kallo tana jin zuciyarta wani iri, a yanzu ta riga ta saba da communication d'insa ta hannu saboda haka ta san sarai abinda yake nufi da yayi brushing hannunta a hankali, ta san wace kalma kowanne yatsansa daya tab'a ta yake nufi, kalmomin da suka had'u suka had'a sentence d'in da yake ta fad'a mata tun dawowarsu daga maldives har zuwa yanzu. You will be fine! **** "Ka tabbata da abinda muke shirin yi yarima? are you sure about this?" Jaamil ya tambaya sanda suka zagaya bayan gidan suka zauna akan wasu kujeru dake cikin d'an karamin wajen shan iska, wajen da ana iya fitowa ta k'ofar kitchen ta baya. Imran ya sunkuyar da kansa sannan ya fito da iska ta bakinsa. "I don't know jaamil, wallahi ban san ya zanyi ba kome zai faru, kullum cikin magiya take min kala-kala ta safe daban, ta rana daban, ta dare daban duk akan a bar mata shi, ba irin bayanin da banyi mata ba tun muna can amma ta kasa fahimta ta, da farko ma zargi na ta fara yi akan wai zan kashe Babynta, yanzu kuma bayan duk taji komai tana ganin kamar ina underestimating d'inta ne, gani take kamar tana da k'arfin da zata iya." "Baby? Tunani take Baby ne a cikinta?" "Haka take gani saboda har a yanzu mantawa take ni ba mutum bane sai na tuna mata tukunnan, yadda ka san tatsuniya kawai na bata a baya." "Tana matawa ne saboda baka nuna mata what you're capable of." "Ba zan iya ba jaamil don koda ta yarda dani ita bil'adama ce, dole akwai tsoro irin nasu...ba zan iya dinga b'acewa a gabanta ba ko in dinga yin abubuwa da mutane baza su iya ba, ko in dinga baiyana mata ainihin halitta ta...I have to blend in for her sake!"   (I tynk na amsa wanda ke tambaya ta me yasa Imran baya nuna powers dinsa.😊) "Haka ne." ya amsa curtly. Suka d'an yi shiru na wasu seconds kafin jaamil yace. "Bwama ta gaya min Naani ce kad'ai zata iya ganin ainihin abinda ke cikinta..." "And she will never be involved!" Imran ya katse shi sharply. Jaamil ya gyad'a kansa a hankali ba tare daya kalle shi ba, bayan wani lokaci ya sake magana. "The good news...itama bwama bata so a rabata dashi." Imran ya juyo ya kalle shi da sauri. "Tana ganin cewa zai yiwu ne?" "Ba zata tabbatar in zai yiwu ba sai ta gama ganinta yanzu, amma ta fad'a min ne k'aunar uwa ga d'anta wani abu ne da babu irinsa a fad'in duniya, tace kowacce uwa tana son jininta komai irin munin halayya da siffarsa, so inaga ta fahimci abinda Sa'adhan take ji ne a yanzu, shi yasa ta matsa min a lokaci d'aya cewa sai mun taho don taga irin halin da take ciki." Imran ya had'e tafukan hannayensa sannan ya d'ora su akan lebb'ensa, kwakwalwarsa ta tuno masa hirarsa da ita jiya da yamma. "Ina ji a jikina ulfat Babyn nan alkhairi ne a garemu, ba zai tab'a zama irin tunanin da kake ba...ina son shi sosai Allah, kuma kaima na gaya maka zaka zo ka so shi fiye da tunaninka insha Allah." A lokacin suna zaune yana bata yoghurt a baki, abinda a yanzu suka gano cewa shi kad'ai cikinta ke d'auka ba tare da ta amayar daga baya ba. "So habibty Babyn namiji ne?" Ya tambaya yana goge mata smudge na yoghurt d'in a gefen bakinta. A lokacin d'aya kumatunta suka yi blushing zuwa pink... wata kala mai kyau, mai kyau sosai da yaji kamar an caka masa wuk'a a cikinsa, wata wuk'a mai tsini da kuma tsatsa saboda zuciyarsa ta kasa tantance wace irin k'auna Sa'adha ke masa, he'd hurt her in so many ways amma har tana iya wannan farin cikin around him. "Yau ce rana ta farko daka fad'i wani abu good akan Babyn nan Ayunie..." Kafin yayi magana ta cigaba. "...ban sani ba ko mace ne ko namiji , amma ni a mafarkina namiji nake gani." "Har mafarki kike yi da Babyn?" A lokacin da ya fad'i haka zai iya rantsewa yaga giftawar wani abu cikin idanunta, kamar akwai wani sauran bayanin tattare da mafarkin nata da take k'ok'arin b'oye masa amma sai ta sake yin murmushi tace. "Zanso in iya nuna maka shi a mafarkin, yana da kyau sosai saboda da kai yake kama!" Kafin fuskarsa ta iya rik'e wani reaction d'in ta rik'e hannunsa dake shirin kai mata wani spoon d'in baki tace. "Kaci abinci?" Ya langwab'ar da kansa kad'an irin abin tausayin nan yace. "Noory ba abinda naci." "Awwn...I'm soory na barka da yunwa, kaine kuma kak'i bari na in tashi." Ta fad'a tana cupping fuskarsa a cikin hannunta, a lokaci d'aya kuma ta tashi ta nufi kitchen, bai b'ata lokaci ba shima ya rufe robar yoghurt d'in yabi bayanta. A gaban deep freezer ya same ta ta bud'e tana kallon kayan ciki, ya matsa a hankali ya juyo da ita, hannunsa d'aya zagaye da waist d'inta, d'aya kuma ya karb'e bowl d'in markadadd'en kayan miyan data d'auko. "Me zaki yi?" ya tambaya fuskarsa dab da nata. "Abinci zan dafa maka." "Yaushe nace ina jin yunwa." Ta d'age girarta d'aya. "Kace baka ci komai ba." "Amma bance ina jin yunwa ba." Ya fad'a yana kallon bakinta da idanunsa masu d'auke da emotions kala-kala da take hango su ta cikin maik'on idon. "Toh ai zaka nemi abinci anjima kuma sai mu zauna ba'ayi girki ba don ni ba zan..." Kafin ta k'arasa kawai ya had'e lips d'inta da nasa and just like that...ta manta k'arshen zancenta, kwakwalwarta ta tafi cloud 9 ta nutse can cikin duniyarsa. Ya k'ara manna ta a jikinsa yana jin kamar ya cusa ta cikin zuciyarsa ta gano yadda yake mutuqar k'aunarta, ita kuma ta rik'o wuyansa kamar tana tsoron zata fad'i. "Kasha tea Ayunie, bakinka na k'amshin madara." Ta fad'a breathlessly sanda ta d'an ja baya kad'an. Yayi murmushi so soft idanunsa kusan a rufe, kafin ta k'ara magana ya sake sunkuyowa yana k'ara kissing d'inta, wannan karon itama ta taya shi, k'arar heartbeat d'insu ya had'e waje d'aya. "I want to tell you something, abinda zan gaya maka yana mutuk'ar muhimmanci." Muryar jaamil ta jawo shi daga tunanin da yayi tafi, ya juyo a hankali ya kalle shi. "Mene ne?" Kamar bai ji ba, sai da yayi shiru kafin yace. "Ban san ta ina zan fara maka bayani bama." Ya sake fad'a ba tare da ya juyo ba, Imran ya d'an tsuke gira yana kallonsa. "How about the begining?...ka fara ta farko." Maimakon ya amsa, sai ya d'ora hab'arsa akan hannayensa duka biyu sannan yace. "Yaushe ne lokacin da Naani take jira?" "Jiya na koma company, sunyi fixing date nan da kwana goma sha shida, atleast dai sati biyu, so i was thinking zamu iya samun mafita kafin nan." Jaamil ya girgiza kansa har a lokacin bai juyo ba. "Babu wata mafita da zamu nema yarima, Allah ya riga ya kawo mana sauk'i." "Ka samo wata hanyar kenan?" "Ban samo ba, kuma ba abinda zan samo, hasalima ba zaka je karb'ar award d'in ba, wannan dutsen ba zai tab'a shigowa hannunka ba." "Ban gane ba..." Da tsananin mamaki Imran ya furta reaction d'in dake kan fuskarsa. "Me kake nufi jaamil? ka san wannan dutsen shine dalilin duk abubuwan dake faruwa yanzu, shine dalilin shigowarmu cikin bil'adama kusan shekara guda kenan..ta yaya sai yanzu da komai ya kammala, Dr. turaki ya gama amincewa dani a matsayi wanda za'a bawa award d'in sannan zaka ce ba zan karb'a? Idan har matsalar b'arin ruhina dake jikin Sa'adha ne na san zamu iya samo wata mafitar kafin sati biyun, amma ba zamu tab'a k'in cikawa Naani alk'awarin da muka d'auka ba..she has sacrificed alot don a kawo wannan lokacin saboda haka zamu k'arasa komai ba tare da saninta ba, na san in dai har na iya karb'ar dutsen na kai mata, ba zata takurani akan matsalar Sa'adha ba tunda ta samu abinda take so...sai dai kuma in nemi yadda zanyi da sareefa don Allah jaamil a yanzu ba zan iya rabuwa da Sa'adha ba." Har ya kai k'arshen zancen jaamil bai katse shi ba, sai da yayi shiru sannan yace. "Ban san ta yaya zan fara maka bayani ba yarima, amma abinda kake shirin ji yanzu zai karya zuciyarka." Imran yayi focusing idonsa sosai yana kallonsa kwakwalwarsa na son tsinto yanayin da fuskarsa ke nunawa, yasha ganinsa cikin fushi, cikin b'acin rai, tashin hankali, mamaki, rud'ani da kuma ciwo... Amma yanayin fuskar tasa a yanzu wani abu ne daya girmewa tashin hankali ko rud'ani, a cikin idanun bil'adamansa yana iya hango ainihin kwayar idonsa da tayi jawur duk da cewar baya kallonsa, ya tsirawa wata 'yar k'aramar flowerpot d'in dake gabansu ido ne kamar an cinna masa wuta, duk zagayen tunanin Imran ya kasa gano dalilin da zaisa jaamil cikin wannan yanayin. "Naani ta yaudare mu yarima... bata turo mu samo dutsen nan don kariyar nahiyarmu ba kamar yadda ta fad'a." Imran ya k'ifta ido jin hakan, kwakwalwarsa ta maimaita zancen ta k'ara maimatawa amma ya kasa gane me suke nufi. "Kamar yadda kaji zancenmu da Naani, haka nima naji zancensu da Sareefa jiya bayan ta kira ni da saqon cewa in gaya maka ka kai Sa'adha wajenta gobe. "Gobe? Ta gama dukkan shirin da tace zata yi kenan na cire ruhin daga jikinta?" "Ba wannan ne mai muhimmanci ba." Jaamil ya fad'a yana ciro wani dunk'ulen abu daga aljihunsa, Imran ya riga ya san mene ne...HABLER, wani abu da suke recording murya dashi. Ya bud'e shi a cikin tafin hannunsa, take wasu abubuwa kamar fuka-fiki biyu suka fito ta kowanne b'angare suka shiga kad'awa, a lokacin muryar dake ciki ta shiga fitowa. Wannan muryar mai cike da kaushi da kuma k'arfin amo mai girgizarwa, kamar koyaushe Imran yaji sautin ta yana tab'owa har k'asan zuciyarsa. don yana iya jin yadda zuciyar tasa ke amsawa. "Na fahimce cewa zuciyarki ta fara karkata akaina sareefa, kina ganin kamar bana sonki, kamar ina fifita su yarima fiye dake...a yau zan shaida miki wani abu da babu mahalukin daya sani...ina amfani da yarima da jaamil ne kawai don cimma manufar da zata gyara rayuwarmu ni dake, shi yasa na d'auke su na nunawa al'umma su na fifita su duk don zuciyarsu ta amince dani suji zasu iya sadaukar da rayuwarsu don yi min komai...! Kamar yadda tun tasowarki kike ganin suna yi min aiki kala-kala, haka a yanzu ma na tura su yin aikin da shine dalilin d'auko yarima da nayi daga kwararo na gyara rayuwarsa na bashi dukkan wata kulawa daya rasa a baya. Na taba gaya miki a baya cewa ina neman dutsen Nil, wani dutse da zai bani k'arfin da zaisa zuri'ata ta d'ore wajen mulkar nahiyar nan...toh daga baya mun samo dutsen a cikin bil'adama, wad'anda basu san amfaninsa ba sai kawai kyau da yayi musu suke ado dashi a matsayin kyauta, a lokacin yana wajen wani mutumi dake shugabantar wani kamfani saboda haka nayi niyyar d'aukowa amma sai farme ya shaida min cewa kona d'auka dutsen ba zai tab'a min amfani ba, k'arfinsa yana aiki ne kawai ga duk wanda ya same shi ta hanya mai kyau, ma'ana sai in har mai shi ya bani da yardarsa inba haka ba ba zai tab'a min amfani ba. Tun a lokacin nayi niyyar tura dalak (Babban bawanta) a matsayin bil'adama yaje kamfanin mutumin har yayi aikin da zasu yarda dashi a bashi dutsen amma sai muka sake ganowa cewa ba kowa ne zai iya rik'e shi ba, sai irin d'aid'akun halittun cikinmu masu k'arfin ruhi, saboda haka nasa farme ya shiga nemo min irinsa. A sannan ne ya gano wani bawa dake can nahiyar Sabeel, saboda haka mu karkata zuciyar mai shi ya taho muzaffar da niyyar saida bayinsa ya samu kud'i, bana so ko kad'an matashin bawan ya san inada hannu a cikin lamarinsa don haka muka shirya komai ya tafi a tsare, Farme ya kashe ubangidansa a daren da suka shigo Muzaffar sannan ya taimaka wajen kwance sark'arsa ya gudo. Sai bayan sati d'aya da shigowarsa cikin muzaffar sannan na shirya had'uwa dashi, shine a ranar da muka fita cikin kasuwa har dake ya taimaka wajen cetona daga fad'awa rami da Farme ya shirya komai, ni kuma nayi amfani da wannan damar na 'yanta shi na kawo shi cikin masarauta. Ban tsara komai da jaamil ba saboda bana son cutar dashi a matsayinsa na d'an 'yar uwata, amma daga baya na fahimci alaqarsu tayi karfin da ba zan iya raba su ba saboda haka na barshi a matsayi mai taimakonsa nake tura su yin abubuwa kala-kala duk don su saba da hakan, sai da na fahimci zuciyar kowannensu ta yarda dani sannan na bijiro musu da buqatar samo min dutsen Nil, kuma ba wanda yayi musu a cikinsu duk da cewa basu tab'a wani abu makamancinsa va wato canja siffarsu su shiga cikin bil'adama. Na tsara komai ba tare dana gaya musu ainihin manufata ba, sannan na tura su da dukkan wani abu da zasu nema yadda komai zai tafi daidai su samo dutsen kuma su danqa minshi da yardarsu! sai dai gabad'ayansu sun sab'awa umarnina a yanzu sunyi wani abu da babu shi a cikin tsarinmu...wani abu da zan d'auki mataki akansa duk ranar da suka gama abinda na tura su. Saboda haka ki kore dukkan wani tunanin dake cikin kanki game da ina fifita su yarima akanki, K'arshensu ya kusa zuwa kwanan nan , daga lokacin da suka kawo min dutsen Nil, daga lokacin zan shafe tarihinsu daga tunanin al'ummar nahiyar nan gabad'aya, don hatta aurenki dashi na yarda da baikon ne wai don in k'ara samun yardarsa game damu ba wai don hakan zai kasance ba. Ke kad'ai ce d'iyata Sareefa, ke kad'ai ce zan iya sadaukar da komai akanki...kuma saboda ke kad'i nake duk wannan tanadin!" ●﹏● So i can recall wata ta tab'a cewa Anya Naani son da take wa Imran na gaske ne ba wai don yana da wani abu ba?....so whoever you are nayi saluting d'inki! u guess right!...😀 My humble readers, what do you think of this chapter ...? And me kuke tunani Bwama zata ce game da cikin Nanne? ****** WAYE SHI? AYSHA SHAFI'EE 54 (☆_☆) "Toh kin gansu nan, kala biyu ne...wannan da nono zaki samu ki dama shi wannan kuma da ruwa kawai in kinga dama ma ki watsa shi a bakinki haka, cikin cokali d'aya ya isa." Nanne ta d'age hanci da gira tana kallon k'ullin magungunan da inna ke nunawa a gabanta, ita tunda aka bud'e k'ullin wani yellow taji cikinta ya juya, yoghurt d'in data sha na safe na shirin fitowa. "Wai daga ina ma aka samo su?" "Tun zuwan da nayi Niger na taho dasu a wajen malam na vonni." Mamaki ya kamata, ta saki baki kawai tana kallon inna, ta kasa yarda cewa tun sanda suka je Niger da zancen aurenta inna ta karb'o mata maganin ciki. "In zaki sha tea da safe ma kawai ki saka shi a ciki tunda na san baki fiye son nono ba." "Inna nifa bana jin zan iya shan wannann abubuwan, ba komai ma nake iya ci ba." "Haka kuwa zaki sha, ko kina sha zasu dawo baza a rasa mai amfanin da zai tsaya ba, wad'annan d'in da kike rainawa sune masu amfani amma ku kunfi ganewa kwayoyin turawa da zaku yi ta sha ana haifar 'ya'ya da cututtuka." Ta fad'a tana janyo manyan ledojin da aka shigo dasu na tsarabar kayayyaki masu kyau da Nannen tazo dasu, komai a rabe yake don kowa a gidan saida ta d'auko wani abu da sunansa,  hatta 'yan aikin gidan su lami sai da ta d'auko musu mayafai irin na mutanen can, inna ta shiga warewa tana fad'in kuma ya biye miki kuka yita kwaso kaya haka, amma can k'asan ranta farin ciki ne fal! na ganin tarin alkhairin da  kowannensu baisa rai dashi ba, ta riga ta sani tun da Nanne bata da rowa ko kad'an, abin hannunta bai dame ta ba don bata k'i tayi kyauta da komai nata ba har kuwa ga wanda ba shiri suke ba, rashin kunyarta iya ta baki ce kawai. "Ki d'auki fa magungunan kisa a jakarki." Ba yadda ta iya haka ta d'auka tasa a handbag d'inta ba da niyyar sha ba, don tun zuwanta a yau da inna fahimci cikin dake jikinta tayi ta tambayarta game da zancen sunje asibiti da kuma yadda take jin jikinta, ba sai an fad'a ba ta san murna ce tsantsa a can k'asan ranta don tana iya hango kyallin hakan daga cikin idanunta sanda take gayawa Mama Azumi data shigo. Zuciyarta ta karye da tunanin yaya zasu ji a lokacin da suka san irin sirrin da take b'oyewa, kafin zuwan Imran cikin rayuwarta bata taba tunani akwai wanda zuciyarta zata amince har tayi sharing sirrinta dashi bayan Inna ba, sai gashi a yau innan take b'oyewa sirrinta, sirrin wani abu da take ganin ya zama jigon rayuwarta...take kareshi da karya kala-kala a wajen innar tata. Don ko awa d'aya bata rufa da zuwa gidan ba ta fara tambayarta game da zancen 'yan uwan Imran, ba yadda ta iya haka ta bud'i baki ta fad'i k'aryar cewa ai daga dawowarsu can bauchi suka fara sauka, sai da suka suka kwana biyu aka zagaya da ita cikin danginsa sannan suka taho. Jin haka yasa hankalin innan ya kwanta ita kuma nata ya karkasu waje da yawa. A cikin wajajen harda wani waje mai kama da damuwa ganin cewar dukkansu basu san irin cikin dake jikinta ba kuma basu kawo zaton komai a ransu ba, mama halime ce kawai data shigo tace mata in ta koma asibiti tayi complain akan idanunta don k'asansu yayi rami kad'an, basu san cewa ko sau d'aya bata bi hanyar asibiti ba, kuma bata jin har lokacin haihuwarta zata nemi asibitin. Bwama ta riga ta gama yi mata duk wani therapy da take buqata kuma ta gaya mata abinda a kwanakin baya take jin zata iya saida ranta don ta ji shi, Abinda ya zama dukkan wani fata da burinta a lokacin da Imran ya dasa ayar tambaya game da cikin nata. Allah ya sani a lokacin da yake gaya mata b'arin ruhinsa yana tare da ita, taji tsoro kad'an don bata son sake experiencing abinda taji a baya, har wani part na zuciyarta yayi fatan dawowar Naani don a cire shi, amma daga sanda bwama ta dubata, ta ganocewar wannan b'arin ruhin shike rik'e da cikin nata, ta mik'a godiyarta ga Allah da har a lokacin ya kasance a jikinta, don tace ba don shi ba, babu ta yadda za'ayi cikin Imran ma ya iya zama a jikinta kona 'yan mituna...jikinta is too weak d'in da zai iya rik'e shi! Amma a yanzu tana fatan cewa k'arfin zai iya rik'e shi har zuwa watannin da abinda ke cikinta zai fito, watannin da bwama ta tabbatar mata ba zai zamo d'aya dana mutane ba, don they grow so fast ba irin halittar d'an adam ba. Ta tuno yanayin Imran sanda ya shigo gidan bayan tafiyar Bwama, ga mamakinta emotion d'in fuskarsa was weak! zata iya fassara yanayinsa da kamar na d'an karamin yaron a lokacin da yaga mamansa bayan ya b'ata na kwana biyu. "Come here." Ya fad'a a hankali yana bud'e hannayensa ba tare da ya bar tahowa wajenta ba, ai kuwa yana rufe baki ta ajiye sassak'en itacen da Bwaman ta bata ta tafi da sauri ta had'e distance d'in dake tsakaninsu, yadda ta cusa kanta cikin jikinsa ya tabbatar masa da kuka take shirin yi. "Wani abu ya faru ne sweetheart?" Ya tambaya daga saman kanta. Muryarsa kad'ai a lokacin ta tabbatar mata da dole akwai wani abu daya same shi a lokacin, akwai wani abu da suka tattauna jaamil bayan fitarsa, bata san ko meye ba amma taji zuciyarta ta sake tsinkewa, hawayenta ya k'aru har yana gangarowa kan kuncinta. Ya jijjiga ta a hankali yana share hawayen da d'aya hannunsa. "Me ya saki kuka?" Ya tambaya yana d'auke hawayen da yatsunsa masu taushi, amma raunin muryarsa da take ji yasa suka kasa daina fitowa. "I'm so happy Ayunie, murna nake yi..." Ta amsa muryarta a karye. "...Bwama tace we can keep it!" Ya fad'i abinda ya san zai zama next words d'inta, daga can saman kafad'arsa ta d'aga kai sannan ta k'ara rungume shi. "Alhmdlilah." His voice was low again, saboda haka ta d'ago ta kalle shi, a lokacin ne zuciyarta ta girgiza sosai don ganin wani abu da bata tab'a zata ba, wani abu da tunaninta bai kawo mata ba. TEARS! ********* HAWAYE. Wani abu ne da Imran bai san ya d'uminsu yake akan fata ba, wani abu da bai tab'a using ba tun shigowarsa cikin mutane. Amma a lokacin da yake rungume da Sa'adha bayan tafiyar Bwama, a lokacin yayi experiencing yadda mutane keji sanda suke fitar da kwallar farin ciki da godiya ga Allah kan wata baiwa da yayi musu... Ya k'ara yarda cewa itace shi a yanzu, itace dukkan wani hope da zaisa ya cigaba da rayuwa mai kyau a gaba, Sa'adha k'addararsa ce da Allah ya shigo da ita don ta tallafe shi a lokacin daya rasa kowanne gata...kamar yadda jaamil ya fad'a ne zuciyarsa ta karye gutsi-gutsi ta dagargaje bayan muryar Naani da ya gama ji, muryar data fallasa dukkan wani zargi da zuciyarsa ta fara d'arsa masa tun lokacin da Naani ta d'auko shi a matsayin wanda ta 'yanta kamar d'anta, amma sai tarin alkhairinta suka ture masa komai a lokacin. Sai a yanzu yake hasko dukkan abinda ya faru a baya tar! a idanunsa, kamar a da yana cikin wani d'aki ne mai duhu a yanzu kuma aka kunna fitila mai haske yake ganin komai a gabansa. Ya godewa Allah da yasa komai ya baiyana a yanzu, a yanzun da abubuwa basu zame daga hannunsa ba, a yanzun da yake da Sa'adha... wata mace guda d'aya da ta san dukkan wani secrets d'insa but she still stood beside him, a woman who love and trust him da dukkan zuciyarta, wadda ta bashi hope d'inta 100% ba tare da ta tab'a zarginsa ba, macen data bashi wata irin kulawa da bai tab'a experiencing irinta a wajen wani mahaluki ba, a woman who had every reason d'in da zata guje shi amma bata yi ba, ta baro iyayenta da kowa tayi sacrificing rayuwarta da zata iya gyarawa a gaba and choose to stand by him! Ya rantse da ubangijinsa zai so Sa'adha ya kula da ita, ya kare ta da dukkan wani iyawarsa a duniyar nan, saboda ya fahimci cewa iya abinda zai iya yi mata kawai kenan! *** A cikin mota lokacin da yaje d'aukarta bayan ya shiga gidan ya karb'o godiya kala-kala a wajen kowa, Nanne tayi ajiyar zuciya mai nauyi, ya mik'o hannunsa da baya kan sitiyari yayi squeezing nata a hankali. "Me ya faru? how did it went?" "Ba abinda ya faru Ulfat, Inna ta fahimta tun kafin ma in bata slightest hint...kuma kowa da yaji yayi farin ciki komai ya tafi daidai." Ya gyad'a kansa  ba tare da ya kalleta ba idonsa na kan titi. "Komai zai tafi daidai insha Allah Noory." "Insha Allah." Itama ta amsa. Ta san cewa ya fahimci akwai 'yar damuwa a tare da ita amma bai tambaya ba, and she was glad that ya barta tayi keeping abun a cikin zuciyarta, in ba haka ba bata san ta yaya zata gaya masa cewa zuciyarta a tsinke take na ganin irin farin cikin da inna ke ciki game da Babynta ba alhalin ita tana b'oye mata wani babban abu da ya kamata ace ta sani, ta yaya zata gaya masa cewa zuciyarta ta dagargaje kamar irin yadda tasa tayi ranar da aka d'aura musu aure, ranar da yaga irin tarin al'ummar daya d'ora akan fake labarinsa. Maimakon ya kaita gida a lokacin sai ya canja hanya zuwa wani k'aton mall dake d'auke da wajaje da yawa a cikinsa, watakila ya fahimci damuwar da take ciki ne a lokacin, ya fahimci yanayinta ya canja kamar yadda itama take gane komai nasa da duk wani slightest bit na motsinsa, cikin sa'a kuma sai frozen vanilla yoghurt din da suka siya ya taimaka wajen lifting spirit d'inta, taji sanyinsa har yana barin wani danshi a can k'asan zuciyarta. Kusan minti talatin suna zaune a d'aya daga cikin kujerun park d'in wajen ba tare da sunyi magana ba, shiru da sanyin bishiyun wajen ya saukar da wani peace of mind a zuciyar kowannensu. Sai da Nanne ta d'aga robar yoghurt d'inta taji ya k'are tas! sannan ta yar da ita a gefe, ta juya ta kalle shi sannan tace. "Ayunie we need to talk... akwai abinda kuka tattauna da jaamil lokacin da Bwama tazo, You need to tell me, ina son inji me ya faru." Imran yayi squeezing robar chocolate ice-cream d'in da ya gama sha shima, he'd seen this coming...ya riga ya san Sa'adha ta fahimci damuwar da yake ciki tun wancan lokacin kuma ya dad'e yana jiran zuwan tambayarta dama, tambayar da ya riga ya shirya amsarta daki bayan daki. Sai dai kafin yayi magana, idonsa ya hango masa text d'in da ya turawa jaamil a d'azu. Komai zai cigaba da tafiya kamar yadda muka tsara jaamil, ba abinda zai canja ko ya tsaya, zanje in karbo dutsen Nil....zan kare Sa'adha dashi kuma zan d'auki fansa akan Naani dashi! ●﹏● Revenge guys! What do you think? **** WAYE SHI? AYSHA SHAFI'EE 55 This page is yours! My amarya freind..It's your day SHAMSIYYA ADO MA'AJI...Happy Birthday dear! 😍 Chill Out Mrs. Abdullahi...we love you! (☆_☆) "Naani ce ta dawo kuma ta san da dukkan abinda ya faru amma bata san da zancen cikinki ba...so mun tattauna yadda zamu b'oye mata sanin hakan ne har zuwa lokacin da zaki haihu, saboda in har ta sani ba zata yarda ba Sa'adha, ba zata yarda muyi abinda baya cikin tsarinta ba." Imran ya fad'i k'aryar da zata lullub'e ainihin gaskiyar da yayi niyyar gaya mata a da, ainihin gaskiyar da zata sa ya daina barinta a duhu game da al'amarin Naani, don a yanzu yana ganin ta cancanci ta san ko wane gutsiren al'amari game dashi, he can't hide anything fom her! amma sai kalaman da Bwama ta fad'a masa suka hana shi furta mata ainhin gaskiyar... "Kar ka tab'a bari ranta ya b'aci har ta shiga damuwa yarima, dole ne ka dinga b'oye duk wani abu da kasan zai takura zuciyarta...oum veri nah kour menku rajern! (stress will only make her more ill.) irtou nah kalabg daer waqatu harvil jourda gnawyer bayadda ferl...(Zuciyarta da duk wani k'arfin jikinta sun ta'allak'a ne yanzu akan abu guda, she can't be distracted.) hazar fumerbe ferl don sartu nah, gzarde ser tah ngam!  (You have to he composed, you can't make it harder for her.) Wad'annan kalaman su suka hana shi fad'a mata ainihin yadda zuciyarsa ta dagargaje da kuma irin ciwon da take yi bayan yaji kalaman Naani daga cikin Habler nan, Amma kwakwalwar Sa'adha was so sharp than tunaninsa. Ta tsuke idanunta kad'an sannan tace. "Ayunie ka tabbata ba wani abu da Naanin take shiryawa da zai cutar dani ko kai?" A lokacin data fad'i hakan wani abu a k'irjinsa ya tarwatse sannnan harshensa ya k'ulle... ta ya zai fara gaya mata cewa he just found out cewa Naani bata tab'a nufinsa da alkhairi ba, ta d'auko shine kawai don ta gyara rayuwarta daga k'arshe shi kuma ta tsaida tasa... Daga yanayin fuskarsa Nanne ta fahimci cewa ba zai bata amsa ba, saboda haka ta kwantar da kanta a kafad'arsa sannan ta zuro hannunta ta cikin nasa. "Koma meye Ulfat, na san I'm safe with you!" Matsalar kenan! gabad'aya tunaninta akansa were all backwards... bata tab'a gane hatsarin da rayuwarta ke shiga akansa, a koyaushe tana bashi wata yarda ne da shi bai cancanta ya samu daga gare ta ba, maimakon guduwa tana k'ara cusa kanta ne wajen da yake da hatsari...watakila kuma laifinsa ne da tun farko bai nuna mata hakan ba. Amma ta yaya zai kare ta daga kansa alhalin dukkan zuciyoyinsu basa son hakan? Sai ya jingina kansa shima a saman nata a hankali, idanunsu na kallon k'ayatattun lilukan park d'in dake can gabansu! **** BAYAN WATA UKU. "Kina da popo pos?" Hidaya ta tambaya zaune daga kujerar island na kitchen d'in. Nanne ta k'ara d'auraye bakinta daga d'an guntun aman da tayi a sink sannan ta juyo ta kalleta da murmushi, wani murmushi da ya fad'a can cikin ramin kumatunta kamar yadda idanunta da suka d'ashe suka yi zurfi a can cikin lungunsu. A cikin watanni uku kawai wanda ya san Nanne a baya zai yi mutuqar wuya ya gane siffarta a yanzu, wata siffa da a kullum innarta ke kira da kwarangwal... don d'an karamin jikinta ya yamushe sosai cikin abinda za'a iya kira fata da k'ashi kawai, fuskarta ta sirance sosai ta yadda k'ashin gefen hab'arta ya fito k'arara yana haska idanunta da suka d'ashe tas! Gashin kanta mai cika a yanzu duk ya yamushe ya kuma wani d'an yalolo sai tsawo ne kawai dashi...sai dai duk wannan canjin babu shi a cikin zuciyarta... zuciyarta da take b'ul-b'ul cikin k'oshin lafiya kuma cike da murnar sanin Babynta yana raye cikin k'oshin lafiya, don a kullum in banda k'ara girma ba abinda yake yi, girman dake tada hankalin 'yan uwanta ganin yadda ita take k'arewa kullum a tsaye. Sai dai tunda har bata jin wani ciwo ko kad'an sai inna ta kashe bakin kowa da cewar ko wacce mace da irin yanayin cikinta, ita nata laulayin a haka yazo mata... amma duk da hakan tana ganin tashin hankali kwance a k'asan idanun innar ko yaushe taje gida, tashin hankalin da duk girmansa bai kai na Imran ba, shi da a kullum suke kwana da tashi tare, ya san cewa bata cikin wani ciwo in banda rashin tak'amaiman abincin da bata iya ci...duk kuwa da duk irin k'ok'arin da Bwama ke zuwa bata na magungunansu kala-kala amma bata iya cin wani abun kirki, abinda ke bata mamaki kenan na ganin yadda kuma babyn ke ta girma a cikinta. Babyn da har yanzu bata san ya yake ba, don taje asibiti sau d'aya, a wata rana da ya zama ya zama silar fad'uwar wani jigon a rayuwarta, taje gida ta had'u da ya Ahmad sunzo shida matarsa da 'ya'yansa, tunda cikinta ya fara baiyana bata ganshi ba sai a wannan ranar...inda yayi mamaki ganin yadda duk ta k'are saboda haka yace zai dubata don bai tab'a ganin ciki irin nata ba, inna kuma ta bada goyon bayanta da cewar itama a lokacin taga ramar tata ta fara yawa, Ba irin hanyar da bata bi ba don ta zille masa amma sai da inna tasa ya d'auketa ya tafi da ita can asibitinsa. Inda wani al'amari ya faru daya jijjiga tunaninsa, gabad'aya injinan ultrasound na asibitin suka k'i aiki a jikin Nanne, ba abinda suke nunawa sai tarin wasu alamomi da suke fad'in... The membrane is too hard! Wato fatar dake lullub'e da babyn tayi karfin da ultrasound d'in ba zai iya ratsawa ya haska cikinta ba. A lokacin ne ya karb'i wayarta ya kira Imran da cewar yazo ya same su a asibitin, wanda kafin zuwansa ba irin magiyar da bata yi masa ba akan ya fad'a mata abinda ya gani amma yayi shiru kawai yana kallon hawayen da take yi, hawayen da ya kasa tantance na tsoro ne ko kuma na son kare abinda take b'oye musu. Lokacin da Imran ya k'araso cikin asibitin a d'an k'ank'anin time, lokacin ya Ahmad ya bud'e baki ya fad'i abinda Nanne bata tab'a zata ba. "Imran ka san cewa abinda ke cikin matarka ba mutum bane?" Zata iya tuna yadda fuskar Ayuninta take hard a lokacin, wani emotion da ya tabbatar mata cewa abinda take tsoro ya faru, baiyi magana ba ko sau d'aya har sanda ya Ahmad d'in ya sake tambayarsa. "You need to tell me, wane asibitin kuke zuwa suna yaudararku tun farkon samun cikin nata?" "Ya Ahmad dan Allah...." "Shshshsh...." yayi saurin katse ta idonsa cike da b'acin rai da kuma wani abu kamar tashin hankali. "Da mijinki nake magana, kar ki sake kisa min baki.!" Daga yanayin idanunsa da muryarsa ta riga ta san what he's capable of a lokacin, ta san halinsa sarai, ta san babu abinda zai hana shi tunkarar Baffa a ranar da zancen, saboda haka ta juya wajen Imran dake zaune kamar gunkin da aka sassak'a ta rik'o hannunsa sannan ta kira sunansa... sunansa direct don ya san cewa abinda zata gaya masa da gaske take, hakan kuwa yasa ya juyo da kansa ya kalle ta, idanunsa were so dark! alamun feelings kala-kala a tare dashi amma bata kula da wannan sosai ba, abinda zata fad'a a lokacin shine priority... a hankali muryarta ta fito ta cikin fuskarta dake shab'e-shab'e da hawaye. "Wipe his memory please!" "What? Me kika ce?" Muryar ya Ahmad tayi ihu daga gefensu. "Ka goge tunaninsa Ayunie dan Allah, in ba haka ba komai zai ruguje mana ne...za'a illata Babynmu." Ta sake fad'a idanunta akan Imran. "Nanne kina da hankali kuwa? me kike cewa? me ya same ki? me zai yi..." He trailed of cike da tambayoyi kala-kala, amma bata juya ta kalle shi ba, idanunta na kan imran da take rok'o da dukkan wani senses na jikinta akan ya taimaka yayi hakan, daga yanayin idanunsa kad'ai ta tabbatar baya son aikata abinda ta fad'a amma kuma ba zai iya mata musu ba, don shi kansa ya san basu da wata mafitar data wuce hakan, ya Ahmad ya riga ya san wani b'ari na sirrinsu da ba zai tab'a rufuwa ba saboda haka ya gyad'a kansa a hankali sannan ya mik'e ya juya wajen ya Ahmad dake k'ok'arin lalubo wayarsa a lokacin. Nanne ta juyar da kanta zuwa kallon k'ofa hawaye na bin idonta daidai sanda Imran ya tsaida duk wani abu dake motsi a cikin office d'in cak! har kuwa da nata tunanin.... Sannan irin abinda ya faru ga masu hoton nan ya kasance ga ya Ahmad, memory d'in abinda ya faru tas! ya d'auke daga cikin kwakwalwarsa. Daga wannan ranar kuma suka tattara komai nasu suka bar cikin garin katsina zuwa Abuja, Nanne ta bar cikin mahaifarta don kare abinda take ganin shine rayuwarta a yanzu, kuma hakan yazo musu da sauqi tunda a yanzu Imran ya riga ya bar aiki a kamfaninsu, abinda ya kaishi ya riga ya k'are kuma ba zai tab'a iya cigaba da zama ba tun bayan abinda ya faru tsakaninsa da Naani. Wani abu da ya zamo..... "Baki da popo pos d'in?" Muryar 'yar yarinyar d'azu ta janyo kwakwalwar Nanne daga tunanin data tafi, ta k'ifta idonta da sauri sannan ta kalleta sosai, tayi tagumi da hannayenta akan island table d'in kamar sanda take tunanin ita kuma ta tsaya ne tana kallonta. Sai data d'anyi gajeren tunani sannan ta gane me yarinyar ke nufi. "Coco pops kike so?" Ta d'aga kanta da sauri. "Eh nawa ya k'are kuma Daddy bai shiyo ba." Yadda tayi maganar tana turo d'an plumpy lips d'inta ya burge Nanne ta shafa kumatunta ta hannunta d'aya sannan tace. "Karki damu hidaya zaki sha coco pops yanzun nan, amma zaki yi game kafin a kawo?" "Yey! kina da candy crush?" Ta tambaya with pleading eyes. "Oww...bani da candy crush amna akwai garden scapes, yana da dad'i." "I'm in!" Ta fad'a da sauri tana d'aga hannayenta, Nanne tayi dariya ta koma falo ta d'auko mata tablet d'in Imran, ta nuna mata yadda zata yi gane d'in sannan ta d'auko wayarta ta kira shi, zuciyarta na fatan ya amsa kafin ta tsinke, don wajen sabon aikinsa na yanzu, aiki yake sosai fiye da wancan tunda suka gano irin kwarewarsa a harkar advertisiment d'in nasu, abinda take gani ya taimaka wajen lifting spirit d'insa da bashi kwarin gwiwa wajen manta abinda ya faru tsakaninsa da Naani. Wani abu da ya zamo.... "Hello! sweatheart ta tashi?" Muryarsa ta silalo ta cikin speaker wayar, tayi murmushi kad'an. "Na tashi Ulfat, kuma gidan ba dad'i, na saba da kai a cikinsa, kana tunanin weekend d'in nan ya b'ata ni?" Taji sautin murmushinsa kafin yace. "Ina tunanin ni na b'ata ki baby." Ta ciji gefen lebb'enta tana danna hannunta cikin shinkafar data d'ebo a wani bowl zata wanke. "Tell me how much you miss me Noory...ina nan inata ganin fuskarki akan screen d'ina, I kept checking time kowanne minute a wayana don inga fuskarki, (Picture d'inta was his wallpaper) And beleive me it's getting out of hand don na kasa ko gama project d'aya. So tell me naki storyn." Ya Allah! wai yaushe ne zata saba da irin wannan kalaman na Imran, maimakon ta biye masa sai tace. "Dan Allah zamu samu Coco pops in zaka dawo?" "Coco pops?" Tana iya jiyo mamaki a cikin muryarsa. "Are we talking Babies?" Murmushinta ya k'aru, ta sake nutsar da hannunta cikin shinkafar. "Ni dai in za'a samu dan Allah ka taho dashi." "Sure Babe kar ki damu... your wish  my command." Ta gyad'a kanta a hankali kamar yana ganinta sannan tace. "Come back soon!" "I will habibty." Tana ajiye wayar ta koma kan girkin da take yi, tun dawowarsu gidan bata tab'a d'ora wani abun arzik'i ba, kullum girkinsu 'yan kame-kame ne kawai, saboda haka a ranar tayi niyyar zama ta yiwa Imran girki sosai tunda ita ba iya ci take ba, sai dai tunda ta fara zuciyarta ke tashi tana ta yin k'ananan amai akai-akai, amma bata fasa ba don ta dake zuciyarta cewa zata yin. Kusan minti talatin tana aikin suna 'yar hirarsu jefi-jefi da hidaya tana mata tambaya game da kewayen unguwar da kuma makarantarsu, wata amsar ta gane, wata kuma ta had'e cikin jagwalgwalon gwarancinta... Bayan wani lokaci ta tsinci muryar Imran daga k'ofar kitchen d'in lokacin ta gama sauke abincinta, tana had'a samosan da take yi, kafin ta k'arasa amsa sallamarsa taji hannayensa guda biyu sun zagaye k'ugunta. "I'm back!" Muryarsa mai taushi ta fad'a dab da kunnenta, numfashinsa ya busa akan fatarta, taji tsigar jikinta ta tashi. "Sannu da zuwa." Ta fad'a a hankali. "Mhmhmm." Ya amsa softly yana grazing fuskarsa a cikin wuyanta, taji k'afafunta sunyi sanyi amma duk da haka ta karkata kanta kad'an don ta bashi more space. "You feel warm habibty..." Abu ne mai mutuqar wuya idan Imran na tab'a ta ta iya wani tunani mai kyau, saboda haka it took her a minute of scattered concentration kafin ta iya tuna cewa Hidaya na zaune a bayansu, da sauri ta juya game da d'an ture shi amma ga mamakinta ba kowa a zaune wajen island d'in nan, sai tablet dake kan table. "Ayunie Hidaya tana ina?" Girarsa biyu ta had'e waje guda. "Hidaya? Wace ce ita?" "Baka ganta ba, tana zaune fa anan." Kafin yayi magana ta kwance hannunsa dake rik'e da ita sannan ta bazama cikin gidan tana ta faman kiran sunan Hidaya. Imran yabi ta da kallo cike da mamaki, wace ce kuma Hidaya, a ina ta samo ta? A ina ta sami wata yarinya mai suna Hidaya? yaji gabansa ya fad'i wani abu mai kama da zargi ya d'arsu a zuciyarsa, tun bayan abinda ya faru tsakaninsa da Naani, zuciyarsa bata tab'a hutawa ba, don wani abu ne da ya zamo.... "Hidaya...kina ina?" Muryarsa ta katse tunaninsa, yana iya jiyo yadda bangwayen saman gidan ya d'auka da sound d'in muryar tata. Ba shiri ya ajiye ledar Coco pops d'in daya shigo dasu har guda uku yabi bayanta. ●﹏● So wacece Hidaya? Me ya faru tsakanin Naani da Imran a cikin watanni ukun da muka tsallake? Just hang in there...muna ta gangarawa dai! 😀 Waye ya iya karanta yaren su Imran a muryar Bwama?😁 @Shamsiyer, The Gardenscapes game is dedicated to you...!😉 ***** WAYE SHI? AYSHA SHAFI'EE 56 I'm so sorry na san nace zanyi updating jiya but Allah bai bani dama ba! @RashidaMuhammad4...😉 (☆_☆) TARIYAR BAYA! (FLASHBACK) ABINDA YA FARU TSAKANIN IMRAN DA NAANI WATA UKU BAYA. "Duk sanda kake tare da ita wannan b'arin na jikinta yana mstsowa dab da gab'ar nata ruhin, yadda wanda ke jikinka zai iya sensing nata, saboda haka in har tana kusa da kai... zaka iya karb'a ba tare da wanda ke jikinka yayi raunin da zai  maka illa ba." Imran ya gyara zamansa yana kallon zanen taswirar bayanin da jaamil ke nunawa a gabansa, idonsa ya kai kan zanen wani dunkulen abu dake tarwatsewa kamar yana fitar da wani hayak'i, ba tare da ya tambaya ba jaamil ya bashi amsar da yake nema. "In har aka samu matsala, ta haka ruhin dake jikinka zai fara k'onewa." "Bai kamata mu saka matsala a cikin lissafinmu ba, insha Allah komai zai tafi daidai, sai dai abinda nake tunani kayi wannnan binciken ne tun kafin mu san da cikin Sa'adha, a yanzu kuma baka tunanin k'arfin dutsen zai iya shafarta ta wata hanyar?" Jaamil ya d'anyi gajeren tunanin kafin yace. "Ai d'aya b'arin ruhinka yana jikinta, kuma karka manta a zuciyar Dr. Turaki kai ya nufa da zai bawa, saboda haka bana ganin wani abu zai faru tunda har da wanda ke jikinka da nata kusan d'aya ne, saboda haka k'arfin dutsen ba zai illata ta ba ko kad'an." Imran ya gyad'a kansa alamun ya fahimta, yayin da idanunsa ke nuna zurfin tunanin yadda komai zai kasance kamar yadda suka tsara. "Har yanzu bata fara susupecting komai ba?" Muryarsa ta tambaya sanda jaamil yake nannad'e takardar. "Ba abinda tunaninta ke kawo mata, zuciyarta ta riga ta yarda damu cewa baza mu tab'a fasa bin umarninta ba kamar yadda a baya ta sa mana yardarta, shi yasa da na gaya mata cewar sai nan da jibi zaka kawo ta ba tayi tunanin komai ba, ta yarda cewa bama son a samu wata hanyar da mutane zasu zarge mu ne... shi yasa zamu bari ta fara rashin lafiya tukunna kafin a fitar da ita daga haiyacinta." Imran ya d'ora tafin hannayensa da ya had'e waje d'aya akan lebbensa sannan ya huro iska ta cikinsu, dogwayen gashin idonsa suka had'e da 'yan uwansu na k'asa sannan muryarsa ta fito cikin kaushi. "Zata sha mamaki jaamil, I will make her pay!" **** Taron kamfanin ya fara gudana ne da misalin k'arfe hud'u na ranar Alhamis a watan August, a wani open park dake can hanyar barin gari waje ne k'ato da aka cike shi da shuke-shuken bishiyoyi masu cikar ganyayyaki kuma cikin wani tsari mai ban sha'awa, sannan k'asan wajen gabadaya grass carpet ne mai taushi anyi cutting dinshi so low ga kuma shukar flowers kala-kala a zube ko'ina da suke serving as fragrant! Daga farkon inda zaka shigo wajen ma wasu tarin  fulawoyin ne da aka rataye su daga can sama cikin haruffan da suka bayar da... ORZ  AT  40! Anyi setting din wajen kamar yadda turawa suke irin parties dinsu, babu kujera ko daya da aka jera in ka d'auke ainihin resting chairs na cikin park d'in, tebura ne kawai a ajiye tsill-tsilli cikin adon yadi da flowers pink, akansubakwai tarin lemuka da snacks da aka jera, kowanne gaban table kuma akwai mutanen dake tsaye rike da lemukan ko snacks anata gaisawa da murmushi ta cikin cool music d'in dake tashi a wajen. Wani abin sha'wa kuma, akwai wasu  fitulun ado dake rataye a jikin bishiyun cikin different colours pink, blue, yellow, red...round dasu irin fitulun 'yan china. Daga can inda yake facing tables d'in high floor ne cikin ado na pink flowers akwai mike da kuma tarin Awards d'in da aka kange cikin wani box na glass. K'arfe hudu da rabi daidai Imran yayi parking hadaddiyar Hyundai d'insa cikin jerin gwanon motocin dake jere a wajen. "Welcome to my success habibty!" Ya fad'a yana kallon Sa'adha dake zaune a gefensa. "I'm so so proud of you Ayunie!" Ta fad'a da murmushi. A lokacin cikinta baiyi girma sosai ba, saboda haka ya b'oye tsaf! cikin doguwar maroon rigar da tasa mai small prints d'in pitch flowers a jiki, tayi rolling da wani tattausan mayafi shima pitch colour, fuskarta ba kwalliya sai rambad'eden kwallin da ta saka a sama da k'asan idanunta wanda ya k'ara fito da girmansu ya kuma b'oye d'ashewar da  suka yi. Rigar was so flowy da bayan sun fita ta dinga ja akan grass carpet d'in, Imran ya rike hannunta cikin nasa suka nufi wajen wasu kofofin glass masu duhu da suke hanyar shiga wajen, Nanne ta d'aga kai ta kalli hadaddun flowers d'in nan da suka rubuta. ORZ  AT  40! Ta shak'i fresh k'amshinsu ya arce har k'irjinta, tun kafin su shiga ta san cewa wajen ya had'u saboda haka taji ta matsu d'imbin mutanen da Imran ke introducing d'inta a wajensu su k'are don su shiga ciki, sai dai ta kula kowannensu d'okin ganinta a matsayin matar Imran yake. "Ah, Imran tun d'azu nake jira...you're a bit late." Wata sassanyar murya tasa Nanne juyowa daga kallon hanyar da mutane ke shiga, idanunta suka ci karo da wadda ke k'arasowa gabansu, wata kyakkyawar mace cikin shiga da kwalliya ta alfarma, kalar fatarta so cream mai kyau, sannan manyan idanunta cike da kyallin farin ciki sanda ta tsaya a gaban Imran, matsatstsiyar doguwar rigar jikinta kalar fara nata haskawa cikin lumshin yammar, yankan rigar was so skillfully ta yadda hakan ya fito da duk wani rise and dent (d'agawa da tashi) na jikinta. Imran ya d'an taka baya kad'an ganin yadda ta tsaya dab! dashi, sannan ya juya da fuskarsa yana murmushi ya kalli Nanne. "Noory ce ta tsaida mu, she kept redoing her veil wai baiyi kyau ba kafin a samu wannan ya tsaya." Shi bai gani ba, amma Nanne da idanunta ke kanta tsaf taga giftawar b'acin rai k'arara a fuskarta kafin wani munafukin murmushi ya maye gurbinsa. "Let me introduce you to my wife." Taji ya sake rik'o hannunta, tun da suka tsaya a wajen abinda yake fad'a kenan, amma Nanne bata ji dad'in kalaman ba irin yanzu da yake fad'a a gaban wannan mai kama da shahararrun 'yan duniyan da bata san ko wacece ba, shi kansa a cikin muryarsa ta fahimci wani abu kamar tink'aho da kuma alfahari. "Habibty wannan itace maryam 'yar office d'inmu, and maryam this is my Sa'adha!" Ta had'iye k'ullutun wani abu a mak'ogwaronta sannan ta matso ta kamo hannun Nanne. "Barkanki da zuwa duniyarmu ta ORZ Sa'adha, it's nice to finally meet you." "Ofcourse." Nanne ta amsa cikin sanyin muryarta. "Its nice to meet you too!" Maryam ta gyad'a kanta sannan ta juya tace da Imran. "Ina jin su Ibrahim sun k'araso bari in duba." Da wannan excuse d'in ta saki hannun Nanne da yasha wani jan k'unshi tar! dashi sannan ta juya cike da d'acin rai, Imran ba zai tab'a zama nata ba, ta biyawa zuciyarta abinda ta shafe wata da watanni tana haddacewa, amma maimakon zuciyar ta karb'a sai ta dawo mata amsar cewa. Dama kema kinyi jan k'unshin! Kafin Nanne ta k'are kallon rigar jikin maryam, Imran ya jata zuwa gaba inda mutane ke ta layin shiga, sasassanyar yammar watan August ta sake haska kyan da kowannensu yayi! Sai dai suna taka k'afarsu cikin wajen, duk wata jijiya ta jikin Imran tayi sensing k'arfin radiation d'in dake jikin dutsen Nil, a lokaci daya kuma idanunsa suka masa zooming can cikin wannan box d'in dake d'auke da tarin Awards, kuma ba tare da b'ata lokaci ba kyallinsa ya haska a idanunsa fiye da duk sauran stones d'in dake jikin kowanne Award... "This is beautiful! Zamu dad'e a wajen nan dan Allah?" Muryar Sa'adha a gefe ta katse tunaninsa tana kallon adon wajen. Bayan kusan minti talatin, gaisuwa da  gabatarwa suka cigaba da gudana wajen, kusan saida Imran da Nanne suka gaisa da kowa a wajen har kuwa da 'yan other companies d'in da aka gaiyata, daga nan kuma bayanai suka fara...Shamsudden da yake a matsayin MC shi yayi leading taron wajen kiran mutane d'aya bayan d'aya dake zuwa suna bada speech d'insu kan abinda ya shafi kamfanin... success, challenges, failure, competition, achievements da duk dai wani abu da ya kasance da kamfanin tun farkon had'a shi, don an gaiyato manyan mutane ma da tun farko aka kafa kamfanin dasu. Imran shi yayi bayanin achievements d'in da kamfanin ya samu cikin shekara d'ayan da yake nan, wajen ya d'auka da lallausan turancin dake fita daga bakinsa yayin da idanunsa ke kan Sa'adha, wadda tayi masa tsananin kyau fiye da kowa a wajen, kalar mayafinta ya k'ara haskawa da fito da kyan fuskarta. Sannan ga d'an bump d'in cikinta da yake iya ganowa, bump d'in dake bearing babynsu ita dashi... his child! wani abu da bai tab'a tunanin zai samu da ita ba, abun dake dad'a tabbatar masa cewa itace duniyarsa... gabad'aya duniyarsa tsaye tana kallonsa da alfahari cike a idanunta. Sai wajen Shida da rabi sannan lokacin da Imran ke jira ya k'araso, lokacin da yayi tanadi ta tsumayinsa tsawon shekara guda, lokacin da duk wani canjinsa ya faru saboda shi, lokacin da ya zamo silar gata da tallafin rayuwarsa tun a farko, lokacin da ya shigo da Sa'adha cikin k'addararsa kuma ya mayar da ita duk wani hope d'insa a yanzu, sannan kuma lokacin da zaiyi determing fansar da zai d'auka akan Naani, fansar da zai hana ta abinda ta dad'e tana muradi, abinda ta sadaukar da abubuwa da yawa nata don kawai ta same shi. Shamsudden ya sake gaiyato Dr. Turaki kan high floor d'in a karo na uku bayan bayanin da yayi a baya don zuwa ya mik'a tarin Awards d'in nan ga duk wad'anda aka zab'a! "I would first like to say my hearty congrats to each and every member that will come up here... Muryarsa ta disashe a cikin kan Imran lokacin da ya lura wani a gefe na kallonsa sabanin yadda hankalin kowa ya ta'allak'a wajen sauraren Dr. Turakin, ya juya da sauri amma mutumin was so fast fiye dashi, ya d'auke idonsa da wani irin sauri kafin Imran d'in ya kai ga kamashi. Bayan kamar minti biyar lokacin da aka fara kiran mutane suna karb'ar Awards d'in, Imran ya sake juyawa yaga ba alamar wannan mutumin. "They are here! Ban san ya akayi ba yarima, amma Naani ta san cewa muna nan!" Da sauri Imran ya juya ya kalli jaamil wanda a lokaci d'aya ya k'araso ta cikin mutanen nan ya tsaya a kusa dashi. Kafin ya bud'e baki yayi magana, muryar Dr.Turaki a cikin speaker ta karad'e wajen da kiran sunansa. Ya juya kansa a hankali ya kalli can kan high floor d'in, a hannun Dr. Turaki wannan Award d'in ne, Award d'in dake d'auke da dutsen Nil... haskensa ya haska cikin idanunsa Sannan a gefen damansa Sa'adha ta sake damk'e hannunsa dake cikin nata! **** Zuciyarsa ta gaya masa cewa dole ne ya k'ara tsananta duk wasu matakai daya d'auka a baya, don canjin wajensu bashi ke nufin cewa Naani ta hak'ura da tunkararsa ba... abinda yayi mata wani abu ne da ba zai tab'a goguwa a ranta ba kuma ba zata tab'a hak'ura dashi ba, hak'ura da abinda ta riga ta d'ora zuciyarta akai tun wani zamani da bai sanshi ba, hak'ura da abinda take masa kallon duk wani fatan da burin da da take dashi har ma da wanda zata samu a gaba. Hak'ura da abinda ta riga ta ta'allaka zuciyarta akai tayi sacrificing abubuwa da yawa akansa... sannan hak'ura da abinda shine dalilin 'yanta shi ta bashi duk wani gata na duniya, abinda ta yarda cewa har cikin zuciyarta zai yi mata shi, ta yaya don ya tarwatsa duk wannan burin nata a rana d'aya kuma yayi tunanin cewa zata rabu dashi cikin sauk'i...? har yayi saken da zai bar Sa'adha under protection din da a yanzu yake ganin baya amfanin komai. Tunda har zasu iya turo wani abu nasu har cikin gidan da yake tak'ama baza su iya shigowa ba, don wani b'ari na zuciyarsa bai yarda ko kad'an da yarinyar dake zaune a gaban Sa'adha yanzu ba, yarinyar da tunda ya shigo gidan yaji tana nemanta zuciyarsa ta d'arsa masa wani abu game da ita. Bayan ta gano ta kuma a can sama da cewar fitsari tayi a toilet ba abinda ya canja game da zarginta a zuciyarsa, don daga yadda take mu'amala da Sa'adha kamar ta riga ta saba da ita ne tun wani lokaci na baya, ba wai yau kawai daga fitarsa suka shigo ita da mamsnta a matsayin mak'otansu ba kamar yadda ta gaya masa, k'arin wani abu kuma yarinyar was too beautiful fiye da irin mutanen da ya saba gani. Yaso koda sau d'aya ya bawa Sa'adha hint d'in da zai sa ta gane bai yarda da  ita ba amma hankalinta gabad'aya baya kansa, ya tafi wajen tarairayarta da bata duk wata kulawa data buk'ata. "Daddynki baya dariya ne?" Ya tsinkayi muryar yarinyar lokacin da take shan Coco pops d'in da aka kira shi ya taho dashi, Sa'adha ta juyo ta kalle shi. "Yana dariya mana harda kyakyatawa." Da idonta da kuma baki tayi masa inkiya da "Smile mana." Kawai sai ya mik'e daga kan kujerar da ya zauna yana kallonsu yace, bari in shiga in shirya. Sai dai har ya gama wankansa ya fito yasa kaya ba alamar Sa'adha ta biyo shi d'akin, yaji zuciyarsa ta k'ara matsowa wuya akan yarinyar, ta yaya zata d'auke hankalinta gabad'aya har haka? Bai ko taje kansa ba ya juya ya koma k'asa. A kitchen d'in ya samesu sun baje bowls cike da fulawa tana koya mata yankan wani abu akan chopping board. "Daddynki ya dawo!" yarinyar data d'ago tana kallonsa ta fad'a. In one swift move ta d'ago ta kalle shi sannan tayi wannan murmushin nata mai dulmiyar dashi cikin duniyarta. "Awwn you look fine, come sit... ga abincinka na gama." Ta fad'a tana nuna mishi kujerar dake facing d'insu, yarinyar ta zagayo da sauri ta janyo masa kujerar alamun ya zauna, yayin da Sa'adha ta d'auraye hannunta a sink din jikin island din sannan ta shiga jero masa warmers da plates d'in data had' tana fad'in. "Samosa muke yi Ayunie, don haka a bar space d'inta." Ba yadda ya iya haka ya k'araso ya zauna yana jin kamar ya shak'e yarinyar ta b'ace daga cikin rayuwarsu. "Baza kici ko kad'an ba?" Ya tambaya sanda ta gama zuba masa ta saka spoon d'aya. "I don't feel like eating, may be ko anjima." Da haka bata k'ara cewa komai ba ta koma suka cigaba da aikinsu, suna yi suna hirar da take sako shi a ciki amma baya magana, daga gefen idonsa ya hango sanda yarinyar ta rad'a mata cewa. "Daddynki bai combing gashinsa ba." Ransa ya kai karshe a b'aci, kawai sai ya ajiye spoon d'in hannunsa ya mik'e ya fita daga kitchen d'in tun kafin Sa'adha tayi magana, maganar da yake zaton zata yi daga lokacin daya shigo cikin kitchen d'in, amma bata ma lura dashi ba balle wai gashinsa, sannan for the first time tun zuwansu gidan ta shirya masa abincin da yaji dad'insa amma bata ko bashi hankalinta ba balle taji complimemt d'insa. Bai samu sauk'in b'acin ransa ba saida ta gaya masa zasu maida yarinyar gida, bayan ta cika ta da dukkanin wani abu da a san tana dashi, don leda guda ya d'auka sanda ita kuma ta rik'e hannunta suka nufi gidan nasu wanda ke d'an gangarensu kad'an, kasancewar unguwar yanayin gine-ginenta kamar irin tsarin turawa ne. A lokacin da suka tsaya jikin front door d'in gidan, matar da Nanne ta kira da maman yarinyar ta bud'e k'ofar, a lokacin Imran ya san cewa ba yarinyar ce abinda ya kamata zuciyarsa ta zarga ba, MAMANTA CE! ●﹏● WAYE SHI? AYSHA SHAFI'EE 57 Lenghty chapters for you! 😉 (☆_☆) "Are you free?" Muryar Sa'adha ta fad'a daga k'ofar d'akin, Imran ya d'ago ya kalleta, tayi wanka tasa wata 'yar k'aramar rigar Bacci, ta tufke gashinta baya sannan jela biyu na kalbar da tayi a gaba na reto, girman cikinta ya k'ara fitowa ta fragile jikinta, a hannunta wani k'aton littafi ne mai hardcover da rubutun... 100 THINGS YOU SHOULD KNOW ABOUT BABIES. "Come here." ya fad'a yana ajiye tablet d'in daya rik'e, ta k'araso ta shige cikin hannun nasa ya rungumeta sosai, k'amshin turare sabulun wanka da kuma shampoo d'inta suka had'e cikin hancinsa, ya lumshe idonsa a hankali. "I miss you!" he breathed. Da dariyarta tace. "Ina naje? tunda ka dawo fa muna tare." "Mhm-mhm, kina tare dai da yarinyar nan, hankalinki baya wajena." Ta d'ago da kanta ta kalle shi. "Amma na ta maka magana baka amsa ba." Ya d'an had'e girarsa waje d'aya. "Noory i hate to tell you this, but hankalina bai kwanta da mutanen nan ba, akwai wani abu a tare dasu." Itama ta had'e tata girar. "Kamar yaya?" A cikin kansa yayi tunanin gaya mata gaskiyar abinda ruhinsa da kwakwalwarsa suka ji game da matar nan, amma sai yayi saurin dakatar da kansa, damuwa hakan zai sa a cikin kanta, damuwar da zata iya sake illata wani abun na jikinta, saboda haka ya canja zancensa da cewar. "A halin da muke ciki Sa'adha da kuma yanayinki, kamata yayi muyi taka tsan-tsan da kowa, kinga dukkan abinda ya faru da idanunki, bana so mu sake experiencing makamancinsa." Maimakon ta bashi amsa sai ta sunkuyar da kanta k'asa kawai, da alama kwakwalwarta ta tafi irin tunanin da take yi duk lokacin da zancen abinda ya faru tsakaninsa da Naani ya gifta... don abinda ya faru wani abu ne daya tabbata banda b'arin ruhinsa dake jikinta a lokacin ba abinda zai hana zuciyarta bugawa. Shi yasa tun daga wannan ranar in har ba dole ba, basa tab'a yin zancen abinda ya faru. Shirunta yayi yawa, sai yasa hannunsa ya janyo littafin da take rik'e dashi sannan yace. "A module nawa muke?" Jin haka yasa ta d'ago da kanta ta kalli littafin daya bud'a akan cinyarsa, da sauri ta fara flipping cikin pages d'in sannan tace. "Inajin 20 ne." Imran ya k'ifta idonsa yana kallonta, Allah ya sani bai san wani irin so Sa'adha ke yiwa d'an cikinta ba, d'aki guda ne a yanzu ta ware da ba abinda take tarawa sai kayan 'yan babies, don duk inda suka fita ko 'yar feeder ta gani sai ta siya, da suka je siyan kayan abinci kuwa rabin siyayyar ta koma ne ta kayan yara da kuma tarin littattafan da suke guiding iyaye akan rayuwar yara, tun daga girmansu kuwa har teenage years. Wani abin dariya har gaya masa take cewa in babynsu ya kai shekara sha biyar za'a d'inka masa kaya da yawa, saboda wai teenagers na buqatar kaya sosai a wannan lokacin. **** A cikin kwanakin da suka biyo baya alaqar Nanne da maman yarinyar nan mai suna Safiyya ta k'ara habb'aka duk kuwa da rashin son hakan da Imran ke nuna mata a kullum, amma koyaushe sai ta kawo uzirin cewa su suke zuwa wajenta kuma ba zata iya korarsu ba. A cikin haka ne wata rana ya dawo daga aiki ya tarar bata nan, kuma bai fita da motar dake da key d'in gidan a jikin nata ba, mamaki ya kamashi sosai lokacin daya kira ta tace masa wai tana gidansu Safiyyan. Ransa yayi mutuqar b'aci ta yadda bai ko shiga gidan ba ya tsaya a waje yana jiranta har ta k'araso, yanayin yadda take tafiya kad'ai a hankali ne saboda girman da cikinta ya k'aru sosai, amma a haka har ta iya d'aukar k'afa ta fita ba tare da ta fad'a masa ba. "I'm so sorry Ulfat!... Safiyya ce ta kira ni urgently wai..." Ta fad'a sanda ta k'araso tana k'ok'arin lalubo key d'in a cikin bunch d'in dake hannunta, bai ko tsaya saurarata ba ya janyo hannun nata sannan ya b'alle handle din k'ofar ya cire shi gabad'aya ya jata ciki, bai tsaya ba sai da suka isa can cikin falo na biyu sannan ya zaunar da ita akan d'aya daga cikin kujerun. Idanunsa cike da tsantsar damuwa yace. "Sa'adha yauce rana ta k'arshe da magana ma zata had'a ki da mutanen nan ko a hanya ne kuwa, ban yarda ki sake barinsu su shigo cikin gidan nan ko ke kije wajensu ba." Da mamaki a fuskarta tace. "Kamar yaya Ayunie? me suka maka? na gaya maka wallahi matar tana da kirki, basu da wani aibu... ta kira ni ne kawai don in taimake ta hidaya ta makale kafarta a cikin kujera, and i call your phone busy kana ta waya..." "Ban yarda ba Sa'adha, and that's it! kawai na gaya miki ban yarda ba!" ya katseta da sauri. A yanzu girarta biyu ta had'e cikin b'acin rai. "Kana nufin kenan haka zan zauna ba zan kula kowa ba, Ayunie na baro dukkan dangina fa a can, nan d'in wani waje ne da bani da kowa and for goodness sake i need some company, ta yaya zan zauna a gida ni kad'ai ba zan yi mu'amala da kowa ba kuma kullum ka fita ka barni?" Ya k'ank'ance idanunsa yana kallonta. "Kina nufin ba zaki rabu dasu ba?" Duk da nauyin da idanunta suka yi mata a lokacin, amma Sa'adha ta daure zuciyarta ta fito da irin rashin kunyarta ta baya tace. "Haka nake shirin fad'a." Bai ce komai ba sai ya saki hannun nata kawai ya mik'e sannan yayi hanyar d'akinsa. Wasa-wasa har dare Imran bai k'ara mata magana akan hakan ba, sannan bai fasa al'amuransa a cikin gidan ba, yaci abincinta, sunyi sallah tare har ya bata wayarsa sun gaisa da Inna, sai dai duk cikin hakan fuskarsa ba fara'a ko kad'an, hakan yasa ta takura don basu saba irin wannan zaman ba, zuciyarta ta dinga gaya mata cewa maganar da ta gaya masa bata kyauta ba kuma bai dace ba, saboda haka bayan sallar isha ta nufi cikin study room d'insa da niyyar bashi hakuri. A jikin wata shelf ta same shi yana kokarin zaro wani littafi, ta tsaya dab da bayansa sannan ta kira sunansa cikin wata murya a hankali, hakan yasa shi juyowa rik'e da littafin ya kalleta ba tare da yace komai ba. kanta na sunkuye tana wasa da yatsunta tace. "I'm sorry dan Allah, kayi hakuri, bai dace in fad'i abinda na fad'a maka d'azu ba kayi hakuri." Imran yaji k'afafaunsa sun manne a inda yake tsaye? Sau nawa ne wai zuciyarsa take son Sa'adha, a yanzu yake shirin zuwa ya bata hakuri don zuciyarsa ta gaya masa cewa abinda yayi mata bai kyauta ba, tayi sacrificing abubuwa da yawa a rayuwarta saboda shi amma shi ya kasa hak'ura da wani abu guda d'aya kawai da take so? kamata yayi ya kyaleta ta cigaba da mu'amalarta dasu, tunda har yana bincike ta baya akansu ba tare da ta sani ba. Jin yayi shiru yasa ta d'ago ta kalle shi idanunta alamun hawaye. "Ayunie kayi hakuri mana, na gaya maka na daina, kuma Allah na kira wayarka har..." Lips d'insa masu d'umi suka sauka akan nata, bakinsa na k'amshin permanent chewing gum d'insa na mint, hannayensa suka jata cikin jikinsa tare da rungumeta baki d'aya! Ta rufe idanunta a hankali sanda kwakwalwarta ta shafe komai da ya faru a wannan ranar, ta manta zancen wata Safiyya da 'yarta, ta manta zancen da suka yi d'azu, ta tuno kawai cewa Imran yana sonta, he wanted her and she was all his! saboda haka ta nannad'e hannayen ta a wuyansa sannan ta bud'e kowanne waje a zuciyarta don ta karb'i sak'onsa. A lokacin ne kuma abin ya faru, wani abu da bai tab'a kasancewa ba, wani abu da ya tabbatar mata cewa da gaske ne ita d'in a lokacin ta zama UWA, halittar dake cikinta yayi motsi da wani irin k'arfi! *** Karfe d'aya na daren wannan ranar Nanne ta fito daga d'akin rik'e da waya a hannunta, sleeping dress d'in jikinta iya gwiwa, ta d'ora 'yar top akai. "Ayunie ka gaya min inda kake mana." Ta cikin wayar yayi murmushi sannan yace. "Kina ina yanzu?" "Ina falo." "Good, now ki nemo letter N a falon." Girarta biyu ta had'e waje d'aya. "Letter N kamar yaya?" "Just find it." Mamaki ya kamata, me kuma Imran zaiyi da tsakar daren nan? ita dai ya san tayi bacci tun wajen sha d'aya saura lokacin da suke kallo, shi yasa lokacin da k'arar wayarta ya tashe tayi tunanin alarm din asuba ne, amma sai taga kiransa ne kuma k'arfe d'aya na dare, ya kira kusan sau uku kafin ta wartsake daga baccin ta d'auka... mamaki ya sake kamata da yace wai ta fito falo zai fada mata wani abu kuma kar ta kashe wayar, ta lalubo 'yar top din rigar baccinta ta dora sannan ta fito, yanzu kuma yace wai ta nemo letter N wano mamakin ya sake cinye ta, amma sai ta biye masa ta shiga bincikawa cikin falon. "Atleast give me hint mana, ya letter N d'in take?" Yayi murmushi sosai kafin yace kawai ta cigaba da dubawa, sai tayi kusan minti d'aya tana d'aga abubuwa sannan ta gano ta wani sabon pillow mai shape d'in N a tsakanin kujerun. "A ina muka sami wannan pillown?" Ta tambaya a cikin wayar da har yanzu ke kunnenta. "Bravo habibty! yanzu ki taho dining, ki nemo double O. Ta d'age girata d'aya kamar yana kallonta. "Is This a game?" "I think so, just find the O's." Tana iya picturing yadda bakinsa ya zagaye a fad'ar O's d'in, tayi murmushi sannan ta nufi dining d'in rik'e pillown N. A can ma tasha duba kafin ta samo O's d'in guda biyu a tsakanin serviette tissue. "Now find the last letter Y a kitchen, sai in gaya miki inda nake." Tana shiga kitchen d'in letter Y da aka hura ta ballon was waiting a saman island. Ta zube sauran gabad'aya suka had'u suka bada sunanta, sunanta a wajen Imran. NOORY! "Awwn... this is too awesome! Thank you Ayunie." "Thank you too Babe. Ki bud'e back door d'in ina jiranki." Jin haka yasa ta juya da sauri ta bud'e k'ofar kitchen d'in wadda take leading zuwa bayan gidan, wajen kamar gidansu na can ne, d'an karamin garden ne da wajen shanya. At first ba abinda idonta ya gane mata sai duhun shuke-shuken, Sai da Imran ya kunna fitila ne sannan ta hango shi tsaye a tsakiyar wajen, samanshi katuwar Banner ce an rubuta. I'M SORRY NOORY..! AND CONGRATULATION FOR THE FIRST KICK...! Ta rufe bakinta da dukka hannayenta biyun saboda tsananin mamaki, This is just out of the world. Oh my heart, oh my heart! Ta fad'a a hankali lokacin da ya ware mata hannayensa alamun ta taho, sai a lokacin ta janye wayar daga kunnenta sannan ta ruga da saurinta ta shige cikin hannayen nasa shi kuma ya binne ta a jikinsa. "I'm sorry akan abinda ya faru d'azu habibty... I shouldn't have told you ki daina kula su, kawai zuciyata ce ke bani...." "Shshshsh...." Tayi saurin katse shi tana d'ago da kanta. "Abinda ya faru d'azu ya riga ya wuce Ulfat.... and this is just.... WOW!" "I'm glad you like it." Ya fad'a da murmushi. "A ina ka samu duk wannan abubuwan?" Ta tambaya tana kallon flowers d'in da aka jera a jikin Banner. "Interior Company da suka yi mana tsarin gidan nan na kira." Ta jinjina kanta tana sake kallon abun, wato komai inda kud'inka da shagalinka, a yaushe har ya kira su suka had'a wannan abun. Hasken flash d'in wayarsa ya dallare idanunta. "You look beautiful in kina tunani." Ta rufe fuskarta da hannayenta tana fad'in ta yaya zai d'auketa fuskarta muzu-muzu daga bacci amma ya janye su ya k'ara d'aukarta wani hoton, tun yana d'aukarta ita kad'ai har daga k'arshe ya shiga had'awa dashi, sai da suka kusan cika camera d'insa da selfie sannan yace. "Noory do you care for a dance?" Ta zare idonta a lokaci d'aya. "Rawa yanzu?" "Yes, I just thought we should celebrate the first kick." "Kusan fa k'arfe d'aya da rabi yanzu na dare Ayunie." "Me kike tsoro?" "Aljaanu mana." Ta fad'a kai tsaye. Ya kifa kansa cikin kafad'unta yayi dariya sosai kafin ya d'ago da kansa. "You can't be serious dear, wane aljaani zaki tsoro in kina tare dani, beleive me ko cikin gidan nan ba zasu iya shigowa ba balle kusa dake." Murmushin da tayi ya bashi damar sake tambaya. "May I have this dance habibty?" "Dance ba wak'a?" Ta tambaya girarta d'aya a d'age. Da sauri ya matsa baya ya d'auko bluethoot d'insa. Yana dannawa wakar ta karad'e wajen cikin mid volume. Ya k'araso ya miko mata hannunsa, ta d'ora nata akai sannan yasa d'aya hannunsa ya nannad'e kugunta... "So slow..." Ya rad'a a kunnenta sanda suka fara bin takun wak'ar. Darling, just kiss me slow, Your heart is all I own And in your eyes you're holding mine Baby, I'm dancing in the dark With you between my arms Barefoot on the grass, listening to our favorite song When you said you looked a mess, I whispered underneath my breath But you heard it, Darling, you look perfect tonight... Ya sake rik'e ta a cikin jikinsa, sannan ya sunkuyo da fuskarsa ya d'ora goshinsa akan nata, tsinin hancinsa na tab'a nata, a hankali muryarsa mai taushi da zurfi ta shiga bin wak'ar... Well I found a woman Stronger than anyone I know She shares my dreams, I hope that someday I'll share her home.. I found a love, to carry more than just my secrets To carry love, to carry children of our own... Nanne ta rufe idanunta a hankali tana jin zuciyarta kamar zata kumbura ta fashe saboda dad'i, that moment was the PERFECT and most wonderful moment a wajenta, tun lokacin data samu cikin nan suke fuskantar abubuwa kala-kala, ba irin tashin hankali da tudun da basu fad'a ba, amma yanzu da take cikin hannunsa a wannan lokacin ta manta da duk abun da ya faru a baya, ta manta da komai... She wanted to start everything afresh! ***** "Yanzu toh shi ya fita?" Inna ta tambaya daga cikin wayar. "Eh ai kusan kullum sai yamma can yake dawowa, asabar da lahadi ne kawai yake gida." "Toh gaskiya kuwa zamanki bai kyautu a haka ba, kinga tun wancan watan nake faman lalubawa in samo wadda zata zauna dake amma abun na neman gagara, don can niger duk yawanci zawarawan sunyi aure wasu kuma sun koma d'akin mazajensu. Anan kuma su lami ne kad'ai da ba shiri kuke yi ba, in ba suba kin san duk sauran ma'aikatan da aurensu... wancan satin ma muku yi zancen da Azumi take cewa ko ita zata zo, nace ai tafiyarta ba zai yiwu ba, don kusan komai na harkar kitchen din nan yanzu a hannunta take, don haka ki tambaye shi shi a nasa 'yan uwan a samo wata dattijuwar tazo ta zauna daku, amma ba zai yiwu ace a wannan halin kina zama ke kad'ai a gida ba." Nanne ta damk'e wayar a kunnenta lokacin da ta lalubi kujera ta zauna, bata dad'e da gyara gidan tsaf ba, saboda haka sai k'amshin turare yake, a gabanta flat screen d'in Tv ne ke nuna tashar "Star life" a lokacin k'arfe uku saura ne na rana. "Ko ba kya jina ne?" Inna ta sake fad'a daga cikin wayar. "Eh naji inna, in ya dawo zan fad'a masa insha Allah." "Yawwa kinga inda wata ai ko haihuwar ce ta kama ba sai kin taho ba, daga nan ma a samo wata kafin sannan, tunda dama banda su maryama da suka rako ki ai ba wanda yaga inda kuke." Jin haka yasa Nanne ta turo baki kamar tana ganinta. "Gaskiya Inna ni nafi son in taho nan, kome za'a yi maka ai ba kamar a gida ba kinga." "Toh wannan kuma sai kin shawarta dashi, tunda shi ba 'yan uwa a kusa ne dashi ba, yaushe za'a barshi ya zauna shi kad'ai?" "Karki damu Inna, na san ma zai yarda." "Ko kuma zaki rok'e shi ya yarda ba." Tayi dariya sosai kafin tace. "Jiya ma sunyi waya da yaya sulaiman yace ya gama yi min registration na WAEC da NECO din." "Toh ke da ba lafiya ba, yaushe zaki yi wata jarabawa." "Inna ai kafin lokacin ina jin ma munyi wata d'aya." "Da d'anyan jego zaki kenan kamar dole?" Sai da ta sake wata dariyar sannan tace. "Inna koh a yanzu fa ba wani ciwo nake ji ba, balle a lokacin insha Allah, kawai dai ramar ce." A sannan ne taji kamar ta gaya mata motsin da a yanzu kusan kullum cikin nata keyi, alamun cewa ko meye a ciki yana da rai da kuma k'oshin lafiya, amma haka kawai sai taji bakinta ya k'ulle. "An kawo kud'in auren Rahma jiya." Idanunta suka zare a lokaci d'aya. "Amma shine bata gaya min ba? shekaranjiya fa muka yi waya da ita." "Yo ai itama bata san za'ayi haka ba, tambaya kawai suka zo a jiyan kuma aka b'ige da karbar kudi, ai kin san ma yaron, d'an mak'otansu hajiya karima... yaro mai hankali wallahi." "Ai shikenan na kira ta yanzu in mun gama wayar, Allah ya tabbatar da alkhairi." "Ameen, ina Aminatu kuwa?" "Tana nan ranar juma'a ma munyi waya harda ummanta tace a gaishe ki." "Ita ba'a fara zancen nata auren ba?" "A'ah gaskiya, sai dai nan gaba tukunna." "Toh Allah ya had'a kowa da rabonsa." "Ameen, mama Azumi bata kusa ne?" "Eh, ta fita nan baya gaisuwa, k'anwar iyan shehu ce ta rasu wajen haihuwa." Haka kurum Nanne taji gabanta ya bada wata irin k'ara data amsa har cikin kunnunwanta, jikinta yayi wani iri a lokaci d'aya, da kyar ta iya lalubo muryarta tace. "Allah sarki, Allah ya jik'anta." "Ameen dai, tayi shahada wallahi, ance 'yarta tana nan kyakkyawa da ita." Kafin Nanne ta amsa, falon ya karad'e da sound din bell da aka danna daga waje, Saboda haka tace. "Inna zan kira ki anjima, inaga nayi bak'i ne." A hanyarta ta bud'e k'ofar text d'in Imran ya shigo yayi appearing akan screen d'in wayar. I'll be home a bit late habibty, zan yi miki bayani insha Allah when I'm back, love you Babe. ...like crazy! Da murmushinta tayi locking wayar sannan ta bud'e k'ofar. A lokaci d'aya k'arar b'allewar wani abu kamar k'ashi ta d'auka a bangwayen falon sanda wayar hannunta ta fad'i ta tarwatse a k'asa. "Owwwh..." Muryar Nanne ta fito a hankali yayin da ta zare idanunta, kwakwalwarta ta kasa fahimta, ta kasa d'aukar abinda ke faruwa, A cikin cikinta wani abu ya fizge zuwa opposite direction d'insa. Ripping. Breaking. Ciwo. Wasu k'ananan bakaken spots suka shiga rufe hasken dake cikin d'akin a idanunta lokacin da k'afarta ta kasa d'aukarta ta fad'i k'asa akan cikin nata, a lokacin tayi k'ok'arin lalubo zuciyarta, find it! amma she was so lost inside the pain, komai ya d'auke mata, makogwaronta ya cika da radad'i sannan duk wata iska ta d'auke mata. Hannayenta dake rawa suka lalubo kan cikinta da niyyar kare abinda ke ciki, amma d'aya ya karasa d'ayan kuma ya kasa kaiwa, she couldnt feel it, she could'nt feel herself! Bak'aken spots d'in nan suka sake cika idonta gabad'aya. A half second later, ta kwalla wata irin k'ara da wani abu kamar shak'ewa ya katse ta, and then... Bakinta ya bullutso da wani tarin jini daya tarwatse har cikin falon! Matar dake tsaye daga waje tayi murmushi a hankali sannan taja k'ofar ta rufe! ●﹏● How many cliffhangers do you notice in the two chapters? Meye k'arashen abinda ya faru tsakanin Imran da Naani a ranar da zai karbi Award din nan? Shin ya ma karb'a tukunna? Ina jaamil yake all this while? Wacece Safiyya maman Hidaya? Me Imran yayi sensing game da ita ya b'oyewa Sa'adha? Me ya faru da Nanne? Wacece matar da ta gani da ta bud'e k'ofar? Me tayi mata? Me ya tsaida Imran a ranar? What will happen next? Do you think the Baby is coming? Allah ya sada mu da alkhairi! WAYE SHI? AYSHA SHAFI'EE 58 (☆_☆) TARIYAR BAYA (FLASHBACK) K'ARSHEN ABINDA YA FARU TSAKANIN IMRAN DA NAANI WATA UKU BAY'A. "Me yasa?... Muryar ta fito da kaushi kamar koyaushe, cikin amonta mai girgizarwa. "Me yasa zuciyarka ta juya min baya?" Imran ya d'ago da idonsa ya kalli manyan-manyan hallitun dake tsaye a gabansu basa bada ko karamin motsin da zai nuna cewa suna raye, a wancan lokacin d'akin da suke tsaye nasa ne shi kadai, amma a yanzu wannan d'akin da suke ciki mallakinsa ne shi da Sa'adha. Sa'adhar dake rik'e cikin jikinsa a sume, tun bayan kallon farko da ta yiwa halittun tsananin tsoro ya d'auke numfashinta, tsananin tsoron ganin irin siffar da Allah bai halitta idanunta na bil'adama jurewa kallo ba. Zuciyarsa a rikice take, yana fatan suman nata ya tsaya a iya suma kawai, kar ya lahanta jikinta ko kuma halittar dake cikinta, amma duk da haka idanunsa sun gagara d'aukewa kallon wannan dunkulallen hasken dake lilo a iska, hasken daya tarwatse ya baje ko'ina a cikin d'akin, hasken dake nuna tambarin irin na adon sarautar NAANI. "Na dad'e da sanin cewa Bil'adama butulun mutane ne, amma ban taba sanin cewa butulcin nasu har zai iya shafar jinsin daba nasu ba don kawai kwaikwayon halitta ya shiga tsakaninsu... haka ban taba sanin cewa akwai ranar da umarnina zai zama abin wofantarwa gare ka ba yarima, ni din dana zama duk wani gata da tallafin rayuwarka, wane daraja kake dashi bayan tawa? wace rayuwa kake da ita bayan wadda na baka? Nice zahirinka! nice sanadin duk wani abu daka samu a cikin jinsinka da kuma wannan rayuwar da  baza ta taba d'orewa ba, na kawo ka cikinta ne don ka cika min burina ba wai don ka gina sabuwar rayuwar tare da wannan k'azamar halittar ba, k'azamar halittar da har zata sa ka iya yaudara... "Yaudara...?" Muryar Imran ta katse ta cikin kaushi da kuma tsananin b'acin rai, abinda ya haddasa motsin wad'annan halittun dake gabansu don hakan wani abu ne na farko da d'ayansu bai taba gani ba, in har akwai wanda ya tab'a yin katob'arar hakan, toh tabbas baya raye balle har ya iya bada labari. Shi kansa Imran sai da yaji sanyin jikinsa lokacin da idonsa ke manne akan hasken daya tabbata tana iya hango shi ta ciki, shugaba kona kwaikwayo ne kuwa akwai kwarjinin da yake dashi, amma ya yak'i zuciyarsa da tunanin maganganunta na cikin habler nan ya fadi abinda yake ganin gaskiyarsa ne. "Har zaki iya amfani da kalmar yaudara akaina? har zaki iya furta ta bayan kece abu na farko daya kasance a cikinta... rayuwar da kike tak'amar kin bani bata cike da komai face tarin yaudara wadda kika lullub'e don samun amfanin kanki, ba don tallafina ba kamar yadda kike tink'aho tsawo shekarun nan. Munji komai daga gare ki lokacin da kike gayawa Sareefa sirrin da kika dad'e kina b'oyewa, babu sauran wani abu da zaki kara rufe mu dashi, maganganun da duka fito daga bakinki sun haska mana duhun da kika dad'e da samu a ciki don amfanin kanki da kuma diyarki , ba don kariyar al'umarmu ba kamar yadda kike ikirari, Allah ya sani na soki kuma na girmamaki da dukkanin zuciyata, ina ganin cewa kin maye gurbin duk wani dangi nawa dana rasa, ban fahimci cewa kina sani hak'a ramin dake ta yin k'asa dani bane... kuma abin mamaki harda d'an 'yar'uwarki, wadda ta sadaukar da abubuwa da yawa a rayuwarta saboda cigaban ki, amma kike tanadin sa mata bak'in cikin da zai tsaida zuciyarta, ki kashe d'anta saboda samun cigabanki. Farin ciki na daya ban taba d'ora raina akan kwadayin samun sarautar da kika yi ta mak'ala min ba, balle har in d'ora raina wajen son d'iyarki, saboda haka a yanzu bana tunanin tsakani na dake akwai wani abu kuma da yayi saura. Da gaske ne, na karbi dutsen NIL a yau, dutsen da kika d'auko ni kika 'yanta ne saboda shi, dutsen da kika sadaukar da abubuwa da yawa akansa, sannan dutsen da a yanzu ya zama mallakina zan iya sarrafa shi ta hanyoyi masu yawa, hanyoyin dana yanke shawarar baza su taba giftawa ta gabanki ba. Na riga na san amfanin dutsen nan a yanzu, na san irin kariyar da yake bawa duk mamallakinsa, irin kariyar da duk karfin iko da tsafinki ba zaiyi tasiri akansa ba, shi yasa kike nemansa ido rufe... don ki k'ara girma da martabar sarautarki yadda ba mai iya ganin bayanki, saboda haka tsarin da muka yi tun farko ya wargaje Naani, ba zan taba baki dutsen nan ba kuma kema ba zaki tab'a iya tunkarata ba, na zabi in zauna a wannan rayuwar fiye da rayuwar k'aryar da kika d'ora ni akai. Wannan shine zahirina Naani, saboda haka godiya d'aya zan miki, ta jikin bil'adaman da kika iya sarrafa min!" A wannan lokacin Imran ya tabbata in har Naani tana jinsa toh tabbas mamaki da rud'anin maganganunsa sun lullub'e kwakwalwarta, saboda kowacce kalma daya fad'a.. every single word abu ne da bata taba zata ba, bata taba zaton sunji kalamanta da sareefa ba sannan bata taba zaton akwai ranar da zasu san b'oyaiyiyar manufarta game dasu ba. Sunfi karfin awa d'aya zaune a hakan ba tare da ta sake magana ba, Imran ya riga ya sani, ita din a koyaushe ba mai tada hankalinta bace, duk yadda abu ya kai ga rikicewa da kuma hargitsi, zata bishi ne a sannu har ta sami lagon da zata ci galabarsa, Abu d'aya dake burgeshi game da tsarinta, sannan kuma abu d'aya da yasa ta sami sarauta akan 'yar'uwarta! A cikin tsawon wannan lokacin, Imran ya san ba don k'arfin radiation d'in dutsen Nil dake fita daga hannunsa ba, babu abinda zai hana wad'annan halittun kawo k'arshen rayuwarsa shida Sa'adha dake rike a jikinsa, don suna fahimtar umarnin Naani ba tare da ta furta ba... sai dai a wannan karon daga ita har su d'in basu da karfin karasowa kusa dashi. "Zamu gani yarima, lokaci zai baiyana abinda alkalami ya riga ya bushe akansa!" Ya lumshe idonsa a hankali lokacin da daga hasken har halittun suka b'acewa ganinsa, ya san sarai me maganganunta suke nufi, zata nemo jaamil ta hukunta shi akansa, bata san cewa nasu tsarin yafi gaban tunaninta ba, yadda yayi wa kansa katanga daga gareta, haka ma bazata taba iya tunkarar jaamil ba. A hankali ya ware tafin hannunsa d'aya, rabin dutsen Nil ya baiyana akansa, rabi kuma yana tare da jaamil da Bwama. **** Jikin Nanne wanda gabad'aya ya baci da jinin dake fitowa daga bakinta ya shiga jijjigawa tare da d'agawa kamar wutar lantarki na janta sannan idanunta dake zare basa d'auke da wani emotion. They were pale and blank! Hargitsin dake faruwa a cikin cikinta shine jigon girgizar jikin nata, don daga kowacce kusurwa ta k'aton falon kana iya jin k'arar karyewar wani abu da kuma ruk'urkushewarsa. A cikin k'arar, muryoyin Bwama, jaamil da kuma Imran ke amsawa cikin k'arfi da kuma ihun da baza ka iya rarrabe kalmomin da suke fad'a ba. "lazzu nah se ka our tad to jikal vanmbiyarda jo! (Ka rik'e ta sosai yarima, kar ka bari ta fita daga hannunka, we can do this!) Muryar Bwama ta fad'a tana kallon Imran wanda ke rik'e da Sa'adha a jikinsa tana jijjigawa da wani irin k'arfin dake neman gagararsa, ba zaka iya tantance cewa k'arfin abinda ke cikinta ne kusan d'aya da nasa ba ko kuma raunin dake mamaye dashi ne na ganin Noorynsa cikin wannan mummunan halin, idanunsa na manne da nata dake a zare hawaye na zirara ta kowanne gefensu, don ba zai iya kallon sauran jikinta ba, sauran jikinta dake cikin azaba... sauran jikinta da k'arar karyewarsa ta cika kunnunwansa, he was afraid to save the memory in his head! "Babu iska a cikinta... jijiyar dake bada iska ta tsinke!" muryar Bwama ta sake ihu a cikin kunnensa. Somewhere in the lost zone, Nanne ta dawo haiyacinta a wannan lokacin tayi magana da wata irin murya mai k'arfi da bata yi kama da tata ba. "Ku cire shi!" Ta fad'a da k'arfi! "Do it now! ku fito dashi zai mu..." Kafin ta k'arasa wani tarin jinin ya bullutso daga bakinta ya fallatsa a kowanne direction, da sauri Imran ya d'ago da kanta kad'an yadda ragowar na bakinta zai fito. "Wourjuoni!" Muryar Bwama ta fad'awa jaamil da karfi cikin abinda baifi kiftawar ido ba ya mik'o mata wani dogon abu mai kama da allura, a cikinsa wani koren ruwa ne irin nasu dake kashe zafin waje, Imran na ganin haka ya k'ara rik'e ta yayin da Bwama tasa hannu ta yage kusan rabin doguwar rigar jikinta, jaamil ya juyar da kansa gefe. "Ka samo mata iska... ka samo mata numfashi, lour ni biryam!" Muryar Bwama ta sake bashi wani umarnin. Imran ya sunkuyar da fuskarsa kan tata da sauri, yayi pressing lebb'ensa akan nata masu laushi sannan ya shiga hura iska cikin mak'ogwaronta da dukkan k'arfin da zai iya, zak'in ragowar jinin dake bakinta ya gauraye a nasa bakin, yana iya jin yadda zuciyarta ke bugawa a hankali daga can k'asan k'irjinta. Keep it going! Ya ayyana da k'arfi a cikin kansa. You promise Sa'adha, kin min alkawari! Stay with me, kina jina? Stay! keep your heart beating! Ya tsaya da hura mata iskar sanda Bwama ta zura abun cikin fatar hannunta, zafin wannan koren ruwan da ya shiga bi cikin jijiyarta yasa jikinta k'ara girgizawa da k'arfi, Imran yasa karfinsa ya k'ara damk'e ta sosai cikin hannunsa, Sai da ya gama shiga duka sannan Bwama ta zare abun da sauri, a lokacin ne kuma wata k'arar karyewar wani abun tayi cracking daga cikinta sannan jikinta ya bar girgizawar, k'arar data sa kowannensu ya tsaya cike da tsananin tsoro, sannan idanunsu suka k'ame akan nata cike da tsabar hanqoro da kuma rok'o, rok'o kar tunaninsu ya zama gaskiya wajen fatan samun wata alama daga gareta, any single thing! ko da kuwa motsin gashin idonta ne amma ba abinda ya biyo baya... Jikinta ya tsaya cak! kamar wani abu ya daskarar da ita ne a lokaci guda. "Me ya faru??" Muryar Imran choked in horror sanda ya juyo yana kallon Bwama da tsananin fargaba. "Lakarta ta karye... Ba abinda jikinta zai iya yi yanzu!" **** A wannan lokacin, azabar da Nanne take ji ya maye gurbi da wani irin rad'ad'in ciwon baya wanda yasa taji numfashi ya tsaya a makogwaronta, taji kamar kowanne k'aramin particles na jikinta yana b'angarewa ne daga jikin d'anuwansa... slicing apart! Zafin ya cigaba da blazing a jijiyoyinta, taji kamar ta mike ta tafi a guje ko zata oya barin ciwo anan inda take amma ta kasa motsa koda hannayenta, wani irin nauyi ya manneta a jikin Imran dake rik'e da ita, kamar an dora k'aton dutse akan kirjinta, wanda nauyinsa ya binne ta cikin azababben ciwon dake tafiya yana mamaye sauran gab'ob'in jikinta, spreading with impossible pain through her shoulders and stomach! Me yasa jikinta ya bar girgizawar da yake yi? me yasa ta kasa motsi? me yasa take jin nauyi a jikinta? Tunaninta a fik'e yake da azabar da take ciki saboda haka kwakwalwarta was so clear da ta fahimci abinda Bwama ta fad'a a daidai wannan lokacin, kamar mai amsa tambayarta. "Lakarta ta karye... Ba abinda jikinta zai iya yi yanzu!" This was'nt part of the story, ta san tasha gaya wa kanta irin mutuk'ar wahalar da zata sha duk sanda da wannan ranar tazo amma bata tab'a kawowa wai abubuwa zasu rincab'e haka ba, Lakarta ta karye? Ta yaya lakarta zata karye? Kenan shikenan yanzu ba zata iya motsa jikinta ba? Ta yaya kenan Babynta zai fito... da wane karfin zata iya kawo shi duniyar da take ta tanadar masa tsawon lokaci? A sannan hankalinta ya d'aukar mata cewa babu muryoyin da a d'azu take iya ji sun zagayeta suna k'okarin ceto ransu, ransu ita da babynta... saboda bayan wannan maganar da taji komai ya d'auke, ya d'auke gabad'aya. Ina Imran yake? me yake tunani alhalin yaji me ya faru, ance jijiyar dake bawa Babynsu iska ta tsinke me yake jira? jiran me ake bayan Babynta yana mutuwa... Babu shiri ta yunk'ura da dukkan iyawarta ta kira sunansa, sunansa direct don ta janyo hankalinsa. Sai dai rabin harafan suka fito k'arashen kuma ya koma sakamakon wani sabon ciwon daya dawo ya soke ta a tsakiyar cikinta, ta tattaro dukkan k'arfinta ta daure hakan kuwa yasa idonta ya sake cika da duhu, ta kasa ganin komai amma kunnenta na iya d'auko mata sautin muryoyin da a yanzu suka cigaba da fafutuka da kuma ihu akanta sakamakon alamar data basu cewa tana raye, fuskar imran ta sake sunkuyowa sannan iska ta cigaba da shiga cikin huhunta, tana busawa da zafi a ki'rjinta. "Stay Sa'adha, dan Allah... you promised!" Muryar tasa ta busa a cikin bakinta, so weak yadda bata tab'a jinta ba. I'm trying...! Taso kwarai ta iya gaya masa hakan, ta gaya masa cewa tana kokartawa da dukkan iyawarta wajen cigaban bugun zuciyarta ba don kanta ba sai don ta raya abinda ke cikinta har ya k'arasa fitowa kar burinta ya tashi a banza... sannan kuma don tarin mutanen da tasan zata ruguza wani b'angare na rayuwarsu in har babu ita. Imran a farko, mijinta da rayuwarta da tasa ke nannad'e jikin zare d'aya, in har babu ita bata san ya duniyarsa zata kasance ba. Sannan Inna-- tsohuwar data raine ta lokacin da ta rasa duk wani gata da tallafin UWA, tsohuwar dake mutuk'ar sonta fiye da kowa da komai a rayuwarta, Would she hurt her again? bayan b'oye mata sirrin Imran da tayi? Ga Baffanta ma, bawan Allah dake ganin ya cuci rayuwarta wajen aurar da ita da wuri, me zai yi tunani a yanzu in har babu ita? Ta san kuma ko yaya ne Nuratu ma zata azabtu da rashinta, bata da shak'uwa da ita amma akwai k'auna da Allah ya halitta a tsakaninsu irinta d'a da mahaifi. Ga tarin 'yan gidansu ma, Rahma, Mama Azumi, Sadiq da duk wasu ahalinta... she'd to survive for them, in ba haka ba a wannan azabar da take ji her life means nothing to her! ciwon da take ciki mai tsananin azaba ne da take jin kamar zata iya sakin komai ta sallamawa duhun dake shirin lullub'e idanunta, ta barshi yaci galaba a kanta, yaci galaba wajen tura ta zuwa wannan k'arshen da ta san zata rabu da duk wani ciwo... Mutuwa! Amma wannan tunanin shi ke sawa ta tattaro duk ragowar k'arfin jikinta wajen rik'e Babynta, don duk yadda ta kai ga son rayuwa saboda ahalinta, it was not the same as the gut- wrenching terror da take ji wajen tsoron rasa shi, dole ne ta sami hanyar da zata cece shi ko da kuwa hakan zai zama abu na k'arshe a yanzu da zata iya yi... Don shine Babban fatan zuciyarta, zata iya hakura da duk wata wahalar da zata sha amma banda rasa Babynta. It was the only thing she had to save! Sai dai ciwon dake yankar k'irjinta a daidai wajen saitin zuciyarta felt so real... tayi k'okarin ture shi tare da sake lalubo tunanin Babynta... abinda ta san cewa dashi zata iya yak'ar kowanne irin ciwo a jikinta. Zafinsa ya cigaba da k'aruwa. Sosai da sosai, Sosai data kasa tantance ko yanka wajen akeyi ko kuma ruhinta ne ke kokarin fita, the pain was too much! Taji kamar ta mik'a hannayenta ta danne wajen ko zata ji sauk'i... but there was nothing a jikin hannayen nata, not a single twitch! su d'in a yanzu ba komai bane face wasu matattun abubuwa dake rik'e cikin hannun Imran, hannunsa da baza ta iya sake shafawa ba har abada! Ciwon ya cigaba da d'agawa-- yana k'aruwa yana d'agawa har saida ya shafe duk wani ragowar k'arfin jikinta! A lokacin ne kuma abun ya faru, abinda ya zamo fata da kuma jigon rayuwarta tsawon wani lokaci... abinda ya zamo sanadin dukkan wata gwagwarmaya da kuma k'addarar rayuwarta! THE BABY! Kicking her ribs apart! yana b'alla duk wani abu na cikinta da ya zama a hanyarsa ta fitowa lokacin da wani abu mai kaifi ya yanka fatar cikin nata hanya ta bud'e, hanya mai fad'i data zama mafarin fitowar halittar dake cikinta tsawon watanni bakwai! **** Imran ya runtse idonsa lokacin da k'arar yankawar fatar Sa'adha ta cika kunnensa, ya damk'e hannayeta sosai a cikin nasa wajen tsaida kansa kokarin hana Bwama tsaga jikin nata da zuciyarsa ke tursasa shi yayi... ya san its for their own good babu wata hanyar bayan haka, babu wata hanyar da zasu raya abinda ke cikinta bayan a bud'e cikin nata don a yanzu ko yatsanta baza ta iya d'agawa ba, balle ayi zancen karfin da zata iya haihuwarsa da kanta. Ya cije lebbensa na k'asa har sai da hak'oransa suka datsa ciki yayi zurfi. Bayan wannan k'arar yankawar fatar cikinta, wata k'ara ce ta biyo baya... wata k'ara da ta firgitashi yaji kamar an jona wutar lantarki ta cikin jijiyoyinsa, it was terryifying and unexpected! k'arar b'allewa da dagargajewar abu daga cikinta, alamun koma meye a cikin nata yana fighting hanyarsa ne ta fitowa a yanzu da ya sami hanya. Don hana kansa ganin hakan da kuma k'ara bawa jikinta k'arfi, ya sake sunkuyar da bakinsa kan nata ya cigaba da hura mata iska cikinta, hakan yasa tayi wani d'an guntun tari idanunta dake kusan a rufe suka juya blindly kamar mai k'ok'arin lalubo wani abun. "You stay with me now Sa'adha!" Ya fada da k'arfi sanda k'arar fitowar Babynsu daga jikinta ya cika kunnensa. "Kina jina? stay! Ba zaki tafi ki barni ba... keep your heart beating! kinyi alqawari!" Idanunta suka sake juyawa, kamar tana so ta lalubo shi a cikin blankness d'insu, duk da bata ganinsa ya tsaida nasa a cikinsu sannan ya k'ulle su bada niyyar daina kallonta ba. And then, sai jikinta ya tsaya a lokaci d'aya, yayi sanyi k'alau cikin hannunsa amma numfashinta mai nauyi na cigaba da fita kuma zuciyarta na bugawa a hankali, hakan yasa ya fahimci cewa komai yazo k'arshe kenan... hargitsin dake azabtar da ita yazo k'arshe, abun da ke cikinta ya fito duniya... duniyar da a yanzu take a hargitse! At long last, it was out of her! Shiru na wani lokaci ya biyo baya kafin muryar Bwama ta karad'e cikin falon a hankali kamar mai rad'a. "Masha Allah... Ourjaani yam!" ( He's so beautiful!) Imran bai d'auke idonsa daga kan na Sa'adha ba, wad'annan chocolate idanun nata masu kyau da a yanzu suka hargitse suka koma jawur! "Ayunie zan ganshi." Muryarta ta fito tar! amma cikin rashin kuzari. Bai ko k'ifta idonsa balle ya motsa don kwakwalwarsa bata aiki a lokacin, yaji me ta fad'a amma bai san ma'anar kalaman ba, hankalinsa yayi cilli can wajen tunanin yadda zai iya had'a jikinta ya koma daidai a yanzu da burinta ya gama cika. Yana iya jin sanda Bwama ta matso ta zuro abun ta tsakanin fuskarta da tasa, da sanda idanun Sa'adha suka k'ifta a hankali wajen saita ganinta akan abun, amma bai d'auke ganinsa daga kanta ba balle shima ya kalli abun da ya zama silar K'ADDARAR RAYUWARSU! "Alhamdlilah." Muryarta ta sake fitowa amma wannan karon da wani irin amo da zaka iya sensing irin azabar da take daurewa. For a second, babu wani motsi dake faruwa a cikin d'akin sai na hawayen Sa'adha dake gangarawa kan kuncinta da kuma sanda ta juyar da kanta gefe a hankali ta kalli wani wajen sannan ta dawo dashi kan halittar dake tsakaninsu, wanda kafin ya iya yunk'urin kallonsa Bwama tayi saurin janye shi daga jikinsu sannan yaji muryarta na umartar jaamil da ya karb'e shi, bai fahimci me ke shirin faruwa ba sai da tarin jini ya bullutso daga bakinta ya fallatsa akan fuskarsa. **** Hoton da idanun Nanne ke d'auko mata a lokacin was blurry! a hargitse kuma yana rawa, ta kifta idonta a hankali don saita ganinta wajen kallon d'an k'aramin halittar dake gaban fuskarta yana d'igar jini. Fatarsa mai d'umi ta manna akan tata yadda taji kamar tana rik'e dashi ne, jik'akkiyar fatarsa mai d'umi da tayi flooding wata irin nutsuwa zuwa ilahirin jikinta gabad'aya, idanunta suka yi focusing sosai akansa. Baiyi kuka ba ko kadan sai numfashinsa dake fita da sauri kamar a tsorace yake, kansa sunkuf yake da yala-yalan gashin daya damule cikin jini... a k'asan jinin kuma wata irin fata ce mai tsananin kyau da haske, komai a cikin 'yar k'aramar fuskarsa was so perfect! da take jin kamar ba gaske bane, he was even more handsome than Imran tun a wannan stage din! duk da cewa kammaninsa sun fito a tare dashi amma idanunsa sak irin nata ne. Wata irin nutsuwa ta sake kamata ganin cewa tunaninta, hasashenta, mafarkinta da kuma zuciyarta basu yi mata k'arya ba tsawon wannan lokacin, sannan wani b'angare na addu'arta ma ya karb'u, Her Baby was beautiful! yana da tsananin kyau kamar yadda kwakwalwarta ta ayyana mata tun daga lokacin d'in da ta fahimci cewa tana da CIKI. "Alhamdlilah!" Taji ba abinda ya dace irin ta mik'a godiyarta ga ubangiji jalla wata Allah da ya karb'i roko da fatanta ya cika mata burinta. A sannan ne kuma idanun Babyn suka d'auki hankalinta, kwayar idanunsa was familiar to her kamar ta tab'a ganinta a wani waje, ba tare da b'ata lokaci ba kuwa wannan mafarkin da take yi ya dawo cikin kanta. Sanda fuskar Imran ta shigo cikin ganinta, yana tsaye kamar lokacin baya akanta da wannan murmushin dake murkushe zuciyarta, sannan rik'e da wannan d'an karamin yaron fari tas! mai mutuk'ar kyau dake ta b'angala mata dariya. Ta tuna da kwayar idanunsa sarai! iri d'aya ce data Babyn dake rik'e a gabanta yanzu, a hankali ta juyar da idonta kan hannun Imran dake rik'e cikin nata a lokacin, a b'ace yake gabad'aya da jinin dake fitowa daga jikinta, wanda har naso yake yana d'iga a k'asa. Ya salam! mafarkinta ne yake faruwa... mafarkin da ta dad'e tana turewa daga zuciyarta, mafarkin da bata tab'a d'aukarsa da wata daraja ba balle ya dame ta, mafarkin da bata san cewa shine hoton dake nuna k'addarar rayuwarta ba! Da gabad'aya sauran k'arfin jikinta ta maida idonta kan Babyn but he was gone kafin ta iya sake ganinsa sosai! D'an kyakkyawan Babynta was snatched away, taji kamar tayi ihu a dawo mata dashi amma zafi da kuma jinin daya bullutso daga bakinta ya d'auke komai. A cikin wannan azabar, a cikin wannan ciwon, a cikin wannan lokacin tunaninta ya gangara da ita can baya, lokacin data fara had'uwa da Imran, lokacin da ta fara ganinsa tsaye daga jikin wannan tsohuwar container ta dawo daga islamiyya, lokacin da ya fara shiga cikin tunaninta...  wannan lokacin da bata san WAYE SHI ba, wannan lokacin da bata san komai game da rayuwarsa ba, wannan lokacin da zuciyarta ta fara sonsa ba tare da wani tunani ba, Sannan wannan lokacin da duk wani hargitsin rayuwarta bai faru ba! Babu wani abu guda d'aya da taji zuciyarta tayi regretting yinsa tun daga wancan lokacin har zuwa yanzu, saboda daga sanda da ta fahimci fara son sa, she knew she would follow him anywhere... and she have! kuma inda ubangiji zai sake dawo mata da komai baya, she beleived she would'nt change a thing! game da rayuwarta. Imran k'addararta ne kuma tana sonsa, tana sonsa da dukkan ruhinta! Ta san cewa a lokacin dukkaninsu a hargitse suke wajen ceton ranta daga yadda take jin ana tab'a kowacce gab'a ta jikinta da sauri da kuma k'ok'arin had'e yankan dake cikinta, da abubuwan da ake zura mata a baki da shigar tarin abubuwa cikin jikinta... amma kwakwalwarta bata d'auko mata dukkan hayaniya da maganganunsu, sai 'yan k'ananan abubuwan da bai kamata ace su take iya fahimta ba. Tana iya k'irga kowanne sauti na fitar numfashin Imran dake kusa da ita, na Bwama da jaamil da yayi nesa dasu sannan 'yan k'ananan shallow numfashin da ta tabbata na Babynta ne, Tana iya iya jin faint k'arar A.C dake cikin d'akin, daga can kuma sautin k'arar wani abu, tana iya jin k'arar iskar dake kad'awa daga wajen gidan, tana iya jin fitar numfashi da kuma motsin abubuwa dake a can wajen... Tana iya jin komai! Tana iya jin komai d'in da bai kai muhimmancin bugun zuciyar Imran dake bugawa kamar zata fito daga cikin k'irjinsa a kusa da ita ba, Sannan tana iya jin komai d'in dake zamewa daga cikin kwakwalwarta kamar lokacin da mutum ke k'okarin rike ruwa a tafin hannayensa. Bayan Second d'ari shida da tamanin da uku komai yazo k'arshe, komai yana nufin duk wani fata da burin rayuwarta! Komai kuma yana nufin komai... sannan komai kuma yana nufin duk wata gwagwarmaya da k'addarar rayuwar SA'ADHA/NANNE! *** Hannayen Imran rawa suke sosai sanda yake rik'e da wani abu da yayi kama da Allura wanda Bwama ta bashi da cewar ya cigaba da d'inke farkewar gefen cikinta yayin da ita ta koma k'ok'arin had'e fatar dake tsakiyar cikinta. Idanunsa a jik'e suke sharkaf da baya iya gani sosai ta cikinsu sannan tunaninsa yana k'ara hargitsiwa ne da kowanne motsin dake faruwa a cikin d'akin, wannan sautin zuciyarta dake bugawa da k'arfi a k'asan hannayensa, luguden tasa zuciyar da ya d'auke concentration d'insa, sannan wata k'arar da bai san daga ina take fitowa ba. Gabadaya kwakwalwarsa bata aiki a lokacin, kallon komai yake cike da rud'ani kamar dukkan tunaninsa ya gushe... don a yadda ya d'auka a baya ya fuskanci dubunnan tashin hankalin da bai san adadinsu ba, amma a yanzu ya tabbatarwa kansa wannan shine tashin hankali na farko da ya fara gani a rayuwarsa, koma a kira shi da wani abu da yafi hakan. Ya damk'e hannayensa da k'arfi rik'e da allurar, wani irin karfi da yasa har k'ashin d'an karamin yatasansa na hagu ya b'alle. A wannan lokacin Bwama ta fahimci cewa ba abinda ya iya k'arawa kan wanda ta bashi, saboda haka ta juyo da sauri ta karbi abin hannun nasa sannan ta bashi wani umarnin cikin k'arajin muryata. "Waffa goure yelim! (pump her heart!Ka danna k'irjinta!) Bai san ya akayi ya iya fahimtar hakan ba, watak'ila don hakan yana nufin wata direct hanya ne ta dawo mata da numfashinta, da sauri ya d'ora hannayensa akan k'irjinta ya shiga danna shi da dukkan sauran nutsuwarsa... it was harder! kamar jinin dake kwance a wajen ya daskare ne, wajen yayi tauri sosai. Bai damu da zafin da karyayyen yatsansa keyi ba, hankalinsa ya tafi gabadaya wajen danna kirjin nata a hankali yadda ba zaiyi kuskuren b'alla shi ba, Bwama ta gama d'inke wajen sannan ta d'auko wani abu mai tsini da ruwa a ciki ta tsira shi a gefen hannun nata, Imran yana iya jin yadda jijiyoyin jikinta suka girgiza kamar shocking ya kamata. Ki k'okarta Sa'adha, keep your heart beating! Muryarsa ta fito da kaushi, da sanyi da kuma hasala, a mace take wannan karon babu wannan taushi da dad'in nata dake murk'ushe zuciyar Nanne, ya cigaba da danna hannayensa yayin da Bwama ta cigaba da sokawa da kuma had'e duk wani waje mai rauni a jikin nata. Tun Imran na iya jin nauyin k'irjin nata har ya koma ya k'ame k'am! ya zama matacciyar d'agawa ce kawai ke biyo bayan hannunsa... amma bai daina ba, ya cigaba da pumping zuciyar tata while Bwama was working to put her back together. Tsawon lokaci babu wani abu dake wanzuwa a falon sai fafutukar da Bwama da Imran keyi akan GAWAR dake gabansu! Saboda abinda ya rage kenan, abinda ya rage daga karyayyen jikin Nanne dake kwance so still a gabansu, siffarta dake b'ace baja-baja da jinin jikinta. Wa'adi ya cika, alk'alami ya riga ya bushe, Allah yayi hukuncinsa, Lalle ne kowacce rai lokacinta k'ayyadadde ne... Babu wani k'ok'arinsu kuma da zaiyi tasiri! Amma duk da haka Imran bai daina danna kirjinta ba, ya cigaba da kokarin pumping iskar da bata da wani tasiri a jikin da ya zama gawa. Ta mutu... ... ya sani. Amma, ta mutu... ... bai yarda ba! ●﹏● WAYE SHI? AYSHA SHAFI'EE 59 (☆_☆) K'arfe bakwai da 'yan mintuna na safiyar juma'a a cikin garin katsina, wayar Sulaiman ta shiga vibrating a kusa dashi, yaja tsaki a hankali cikin baccin nasa... don ya san kiran ba zai wuce na yazo ya kai 'yan makaranta ba in har an samu wani uzirin daga Idris direba. Allah ya sani dole ne ma ya k'ok'arta a had'a aurensa dana 'ya'yan hajiya Babba Nasir da Muhammad da za'ayi cikin shekarar nan, don kusan duk wani responsibilty na gidan yanzu akansa aka d'ora, tunda ya d'auki annual leave d'insa bai samu ko kad'an ya huta ba, sunansa ne ke fara zuwa kwakwalwar kowa a duk sanda wani abun ya taso. Yasa hannun ya jawo wayar zuwa kunnensa. "Hello." Daga d'aya bangaren muryar cikin wayar tace. "Sulaiman kana gida koh?" "Eh." ya amsa ransa a b'ace. "Sunana jaamil, ni dan'uwan Imran ne mijin k'anwarka Sa'adha." Jin haka yasa ya d'ago da kansa yana kallon silin kafin yace. "Okay na gane.." Muryar ta d'anyi shiru bata amsa ba, hakan yasa shi k'ara bud'e idanunsa sosai sannan yace. "Ina sauraronka." Kusan sakan talatin kafin muryar ta sake magana da wani irin tattausan amo da ya ratsa har cikin jijiyoyinsa. "Sulaiman, Sa'adha ta rasu jiya da daddare wajen haihuwa, a yanzu haka muna hanya tare da gawar tata zamu iso nan gida, ina maka ta'aziyya kafin k'arasowarmu." A cikin abinda baifi kiftawar ido ba Sulaiman yaji tunaninsa ya zille daga cikin kwakwalwarsa ya rataye a iska, Mutuwa? Nanne ta mutu? Wace irin Mutuwa? Nannen da jiya ya shiga wajen Inna yaji suna waya da ita? "Dan Allah malam ka gaya min gaskiya, wace Sa'adhan kake nufi?" "Babu wanda yake wasa da mutuwa sulaiman, ba zan taba kiranka in maka karya ba Sa'adha k'anwarka nake nufi, Allah ya amshi ranta jiya wajen haihuwa, muna... Bai ji k'arashen zancen ba saboda ya kasa gasgata kunnunwansa, ya kasa gasgata al'amarin, ya kasa gasgatawa wai da gaske Sa'adhan/ Nannen da yasani ce ake gaya masa ta rasu, rasuwa ta mutuwa irin wadda in ta kasance mutum ya tafi kenan har abada! Hannunsa dake rik'e da wayar ya shiga rawa lokacin da muryar wanda ya kira kansa da jaamil ke cigaba da bayani wajen gaya masa cewa ya taimaka yayi wa su Baffa bayani cikin nutsuwa kafin k'arasowarsu, Nutsuwa? wace irin nutsuwa ke tattare da labarin mutuwa? Sai ya ajiye wayar ya d'ora hannayensa aka kawai ya shiga rero Inalillahi wa Inna ilaihir raji'un! Inalillahi wa Inna ilaihir raji'un! Inalillahi wa Inna ilaihir raji'un! Yanzu wa zai tunkara da wannan labarin? Baffa zai samu yace masa 'yarsa ta rasu ko kuwa wajen inna zai je ya gaya mata Nannenta ta mutu? wannan wane irin sak'o ne ya rataya a wuyansa haka? yaji kwalla ta cika idanunsa lokacin da tunaninsa ya cakud'e ya rasa madafa, sai kawai ya janyo wata T-shirt dake gefensa ya d'ora akan wandon shaddar jikinsa sannan k'afafunsa suka nufi d'akin hajiya Babba, bai ko tunkari na mahaifiyarsa ba don ya yardarwa kansa cewa wannan aikin na manya ne, a yanzu Hajiya Babban ce kad'ai zata iya samun Baffa da wannan hargitsatstsen bayanin.! **** Kafin k'arfe takwas na safiyar ranar, labarin rasuwar Sa'adha yayi tambari a cikin unguwarsu, haka nan kuma ya cigaba da watsuwa kusufa-kusafa na garin Katsina, sannan gidan ya fara cika da 'yan uwa da kuma mak'ota na kusa wanda hakan ya dad'a sanya hargitsi a zukatan al'ummar gidan. Lokacin da motoci uku nasu Imran da kuma su ya Ahmad da suka je taro su suka k'araso cikin gidan, hawaye ko d'igo bai fito daga idanun Baffa sai sannan, sai a lokacin da ya d'aga ido yaga manyan 'ya'yansa na kiciniyar fito da gawar daga cikin mota, ya kalla yaga wai yau Nanne dake dake zagaye gidan da kafarta ce ake d'aukowa babu numfashi kuma babu wani abu dake motsi a jikinta, jikinta sanye da doguwar riga kamar zasu sauke ta ne ta taka da k'afarta duk da cewar an rufe fuskarta da hijabin kanta. Yaji wani sabon Imani ya shige shi sai ya shiga salati yana k'ok'arin maida kwallar dake shirin tunkud'uwa daga idonsa. Wai Sa'adha ta tafi a yau, Sa'adha mai tsananin biyayya a gare shi, ta tafi a k'ananan shekaru masu cike da k'uruciya, ta tafi bayan tayi masa biyayyar da yake ganin ya tauye wani b'angare na rayuwarta... "Allah ya jikanki Nanne, Allah ya yafe miki kurakuranki, Allah ya baki Aljannatul firdausi mad'aukakiya, Allah ya ingata shahadarki, Allah ya shafe zunubanki, Allah ya kyautata aiyukanki na alkhairi, Allah ya karbi ruhinki cikin daraja, Allah ya kyautata zuwanki, Manzon tsira ya karbi bakuncinki, Allah yasa mutuwar ta zamo hutu a gareki, na yafe miki duniya da lahira, Allah yayi miki rahma da gafararsa...." K'okari yake kar hawayensa ya fito a gaban 'ya'yansa, kar ya fiddo da raunin da zai haddasa karyewar zuciyarsu alhalin yana iya ganin tsananin dauriyar kowannesu a cikin idonsu. A lokacin kuma gidan ya k'ara rud'ewa, mata suka shiga kuka mai d'agawa kamar a da suna tunanin jiran da suke zai zo musu da wani abun ne sab'anin hakan. Aka shiga da gawar Nanne har cikin d'akinsu ita da inna, Innar da a lokacin bata cikin haiyacinta, tun bayan shaida mata labarin da akayi take ta hailala mai cike da maganganu, maganganun da suke nunawa tar! cewa bata cikin haiyacinta, don har fad'i take cewa Nanne bata mutu ba watakila tayi bacci ne kawai a mota kuma zata tashi da zarar sun kawo gida, sai dai duk da wannan sambatun harshenta na kiran Lailaha ilallahu muhammadur rasululahi duk sanda ta juya taga irin kukan da mutanen dake gewaye da ita keyi, tana yi tana fad'in. "Na gaya muku ku bar fidda hawayenku, ba dai ance suna hanya ba? da sun iso zaku ganta garau... Azumi ki gaya musu mana ba jiyan nan nake ce miki munyi waya da ita ba? har nake gaya miki tace zata sake kirana bamu gama magana ba tace tayi bak'i? Ke Halime dauki wayar mana ai zaku ga lambarta a ciki..." Lokacin da aka shigo da ita cikin d'akin, da saurinta ta kwace hannayenta dasu Mama Azumi ke rik'e dasu ta rarrafa ta bud'e fuskarta dake lullube da hijabin, kyakkyawar fuskar Nannenta da ke fes! cike da annuri da kuma alamun nutsuwa irin ta mai bacci, kamar za'a kira sunanta ta bud'e wad'annan fararen idanun nata ta amsa. A lokaci guda ta d'anyi sororo tana kallonta, kamar mai son lalubo wani abu nata daya fad'i akan fuskar, amma ba wani abun take son lalubowa ba face fahimta da tayi cewa  babu alamun rai a tattare da ita, babu rai a jikin Nannen da take mutuqar so a rayuwarta, Babu rai a jikin Nannen da taci burikka da yawa akanta, Babu rai a jikin Nannen da taci burin ganin 'ya'yanta na yawo a tsakar d'akinta, Babu Nannen da taci burin ganin ta samar mata rayuwa mai kyau da inganci, Babu Nannen da take tsananin so fiye da 'ya'yan da ta haifa a cikinta! Sai kawai ta hau girgiza kafad'unta tana fad'in. "Da gaske suke kenan? Da gaske ne abun da suke fad'a kin mutu? Ta yaya zaki mutu a yanzu? Don kawai jiya mun yi waya na gaya miki k'anwar iyan shehu ta rasu wajen haihuwa sai kema ki mutu? Ki dubi girman Allah kiyi hakuri ki tashi wallahi ba zan kara gaya miki zancen mutuwar kowa ba, wayar ma zan yar da ita, ke da kika ce min watan gobe zaki taho gida haihuwar? ina nan ina tanada miki kayan wanka, me yasa zaki haihu yanzu? me yasa zaki haihu ki mutu Nanne? me yasa zaki mutu da k'uruciyarki bayan nice tsohuwa? me yasa zaki tafi ki barni? me zanyi da rayuwar....." Bata kai k'arshe ba idanunta suka juya luu sai kuma ta tafi ta fad'a kan jikin nata... nan d'akin ya kara rud'ewa aka d'auke Inna zuwa cikin d'aki, yayin da Ya Ahmad ta koma motarsa da sauri don d'auko first aid box d'insa, Kafin ya kai ga dawowa Rahma wadda tana shigowa tayi ido hudu da gawar ta fad'i itama. Haka waje ya k'ara rudewa cike da alhini da kuma tashin hankali, Ya Ahmad ya dinga zarya tsakanin Inna da Rahma don ceto nasu ran, yayin da mutane suka cigaba da cika a gidan, musamnan maza kowa na son samun sallar jana'izar da ake shirin yi. Duk wannan abin da akeyi, wannan d'an kyakyawan Babyn na k'udundune cikin hannun Bwama dake zaune daga can wani b'angare na d'akin, rikicin ganin gawar Nanne ya hana mutane da yawa biyowa ta kansa, kuma 'yan k'alilan din dake zuwa ganinsa, ba wanda take mik'awa don ta kafa sharad'in cewa shima ba cikakkiyar lafiya ce dashi ba don haka ba'a d'aukarsa, sai dai duk da haka tsananin mamakin irin kyawunsa ya fara zagaye cikin al'ummar gidan. Wajen k'arfe goma na safiyar juma'a aka gama shirya gawar Nanne tsaf cikin farin kyallen dake jiran duk wani mai rai! Mama Halime, Aunty Maryama da wata malama zahra'u su suka wanke jikinta da babu ko kwarzane sai alamun warkewar ciwo a k'asan mara da gefen cikinta, suka tufke dogon gashinta cikin tufka biyu, wadda tasa fuskarta ta koma kamar ta k'aramar yarinya saboda kyau, Aunty Maryama ta fashe da kuka sanda suke nannad'eta cikin likkafanin, gani take kamar jiya ne suke shiryata cikin kwalliyar aure yayin da taron gidan ya kasance na farin ciki, gashi ko shekara bata zagayo ba suna yi mata shirin tafiya kabari, yayin da taron gidan ya kasance na makoki. A wannan lokacin Inna ta farka daga suman ta, kuma abin mamaki wannan karon bata rikice irin d'azu ba, rarrafowa ta sake yi cikin tsakar falonsu da aka sake dawo da gawar don yi mata addu'a kafin a fita da ita. Ta durkusa a gabanta daga gefen Baffa wanda ya bud'e tafukan hannayensa yana ta zubo addu'o'in neman yafiyar ubangiji da gafarsa akan ruhin d'iyar tasa, Idon Inna baya iya gane kowa ne a lokacin amma zagaye da ita ta kowanne gefe 'yan gidansu ne kaf! daga mazan har matan su ashirin da uku, jaamila dake can Niger ce kawai bata nan, sai ko mahaifiyarta Nuratu da a lokacin suke kan hanyar tahowarsu, Kowannensu na zubo kalar addu'oinsa, wasu kuma amsawa Baffa... daga bayansu ne 'yan uwa na kusa irinsu Aunty Maryaama ke tsugunne suma suna nasu addu'o'in. Zuciyarta na zafi jikinta na girgirza tasa hannu ta janye likkafanin da yayi mata katanga da fuskar Nanne, fuskarta dake cike da annuri kamar wadda ke cikin tsananin farin ciki, kamar wadda ba taba fuskantar wani b'acin rai ba a cikin 'yar gajeriyar rayuwarta. Yafiya har yafiya, albarka har albarka, neman gafarar ubangiji da neman Rahmar ubangiji ba wanda Nanne bata samu daga wajen Inna ba, tun tana fadar addu'oin cikin hankalinta, har komai ya kai k'arshe ya zamo maimaci kawai take yi. Allah ya sani, zuri'arsu irin mutanen nan ne da basa mutuwa da wuri, kafin kaji mutuwa a danginsu toh ka tabbata ta tsoho ce ko wanda ya bawa hamsin baya, Saboda haka mutuwar Nanne ba k'aramin girgiza su tayi ba, kamar wata katanga ce daga wani b'angare na gidan ta fad'i ta rugurguje har garinta! Nanne mutum ce mai d'imbin kirki da alkhairi, tana da mutuk'ar kyautayi da son 'yan uwanta, tana hak'uri da tsananin biyayya ga iyayenta, tana da kuma tsanani kulawa kan duk abinda take so a rayuwarta! tana iya sadaukar da komai nata don samun farin cikin wani... ita d'in mai nasibi ce da faffad'ar zuciya, ga duk wanda ya fahimci halinta, toh tabbas zai so ya zauna da ita tsawon rayuwarsa! A lokacin da aka zo fita da gawarta daga gidan a lokacin komai ya sake rudewa da cakudewa, Inna ta rik'e k'afarta ta shiga yiwa Baffa magiya akan kar su tafi da ita, a bar mata ita haka ita zata iya zama da ita, rantsuwa take har cikin ranta cewa zata zauna da Nannenta a haka koda ba zata iya komai ba, duk wanda ya ganta a wannan lokacin sai ya zubar da hawayen tausayi, domin komawa tayi kamar k'aramar yarinya tana rik'e da k'afar Nanne tana rok'on Baffa dake tsaye daga bakin k'ofa. Wanda ganin mahaifiyarsa cikin wannan halin ya sashi kasa daurewa kukan dake nuk'urkusar zuciyarsa, sai kawai ya saki labulen yayi hanyar waje ta cikin dimbin jama'ar da suka cika gidan a lokacin. K'arfe Goma sha d'aya daidai na ranar juma'a aka fitar da Nanne daga gidansu a matsayin gawa, gidan da ta taso tun yarintarta, gidan da mahaifiyarta ta tafi ta barta a cikin sa, gidan da Inna ta raine ta da dukkan kulawarta, gidan ta fara gina rayuwarta a cikinsa, gidan da ta fara haduwa da Imran a k'ofarsa, sannan gidan da aka d'aura mata aure a cikinsa! Da da gaske ne da ake cewa duniya ba matabbatace, Lalle ne komai mai k'arewa ne... can d'in shine gida na gaskiya! *** Imran na sahun gaba hannayensa cikin na jaamil dake jansa tamkar rak'umi da akala, don da ace zai sake shi, ba zai iya cigaba da tafiya ba, zai tsaya ne kawai saboda kwakwalwarsa ba abinda take ganewa a wannan lokacin sai abu d'aya, abu d'aya da Bwama da jaamil suke gwagwarmaya akansa tun daga jiya, abu d'aya da ya zama dukkan fata da burinsa a halin da ake ciki, abu d'aya da yake ganin sai ya yishi sannan kwakwalwa da tunaninsa zai iya karb'ar labarin mutuwar matarsa. Don komai dake faruwa ganinsa kawai yake yi yana wucewa kamar a shirin wasan da aka zauna aka tsara shi, baya yarda da dukkan abinda idanunsa da kunnuwansa ke d'auko masa, har kuwa sanda ya kama gangar jikinta shida Baffa suka zura ta a cikin ramin kabarinta, da sanda ake jera tukwane a kanta, da sanda ake zuba k'asa akan tukwanen, har saida ta shafe hasken farin likkafanin dake lullub'e da ita, da sanda k'asar tayi tudu aka kafa allon alama akanta. Da sanda aka kusan shafe awa guda ana jero addu'o'i a gefen kabarin, da sanda jaamil ya sake jan hannunsa suka koma cikin motar da suka zo, da sanda kowanne motsin tayar motar ke k'ara nesanta shi da Ayuninsa, da sanda suka dawo cikin layin gidan nasu, da sanda suka fito daga mota saboda cunkuson mutane da ya fara yawa, da sanda suka iso daidai jikin wannan tsohuwar container data raba gate din gidajen biyu.... Sai kawai ya zame hannunsa daga na cikin jaamil ya tsugunna har k'asa a wajen, wajen da ya zama mafarin had'uwarsa da Sa'adha, ranar da ya fara ganinta sun dawo daga islamiyar nan, gashi wai a yau yaje ya raka ta cikin kabarinta ya dawo, ya dawo daidai wannan wajen dake cikin duniyar da babu Noorynsa! Sai ya kifa kansa cikin tafin hannunsa ya shiga rero kuka tamkar karamin yaro, jikinsa na girgizawa tare da zuciyarsa, jaamil na shirin sunkuyawa ya bashi baki, Baffa ya tsaida shi ta hanyar d'aga masa hannu, ya yarda cewa duk duniya ba wanda ke da hurumin hana Imran kukan da yake yi a lokacin... Matarsa ce ta mutu, irin matar da ba'a koyaushe Allah ke azurtar bawa da ita ba, don haka hakk'insa ne yayi makokinta! Zai iya yiwuwa mintoci, ko kuma awanni, irin wanda suke dunk'ulewa cikin jimla, jikin Imran bai bar girgizawa tare da kuka ba, Abu d'aya kawai da ya sani kuma yake ganewa a wannan lokacin shine zai kashe NAANI! Zai kashe ta dukan iyawarsa! ●﹏● Ehem  Ehem  Ehem! Did I do you wrong? A yafe min albarkacin ranar idi! Ina son inji ra'ayinku dai... me kuke tunani da wannan aika-aikar da nayi? Enough votes, and i will post the last chapter zuwa dare Insha Allah! BARKA DA SALLAH WAYE SHI? AYSHA SHAFI'EE 60 (☆_☆) MURFI. Har zuwa ranar da aka shafe zaman makokin Nanne da kwanaki bakwai, Bwama na cikin gidan a matsayin mai kula da Babyn nan, domin har a lokacin hankula da yawa baya kansa, sai bayan sadakar uku ne ma su Aunty maryama suka fara karb'ansa don yi masa wanka da kuma bashi abinci, wanda ba komai bane face tatacciyar madarar shanun da ake kawowa daga gonakin Baffa, wanda shi da kansa ya bada umarnin hakan, a cewarsa mahaifiyarsa ma da abinda ta rayu kenan. Sai dai abinda basu sani ba shine, a duk sanda aka kawo madarar, Bwama na fakar idonsu ta zuba garin wani abu mai suna 'jerul' a ciki, abu ne da suke amfani dashi ne wajen dakushewa irin halittunsu possibilities d'insu a duk sanda suka yi laifi don a samu a iya hukunta su, saboda haka a yanzu da bata san irin abinda Babyn zai iya ba wanda  ta san zai fi k'arfin hankalin bil'adama, yasa take amfani da jerul wajen dakushe koma wani irin abu ne ke tattare da jininsa. A ranar sadakar bakwai ne, Baffa ya kira taro a gidan gabad'aya wanda ya hada harda Nuratu da itama take kwana da tashi a gidan ita da 'yan uwanta, Nuratun da basa shiri da Inna a yanzu tana d'aya daga cikin mutane mafi soyuwa a wajenta, don duk sanda ta kalleta sai taga kamar taga wani b'ari ne na ragowar Nannenta da ya rage, saboda haka kullum tana gefenta suna karb'ar gaisuwa tare... gaisuwar tarin mutanen da cincirindonsu baya tab'a raguwa a gidan, don har daga can Niger ba'a daina zuwa ba. Hakika mutuwar Nanne ta girgiza duk wani mahaluki a gidan, ta guntule farin cikinsu, ta wargaza tunaninsu kuma ta k'ara sanya musu tsoron Allah a zukatansu. Don haka fuskar kowa na falon in ka kalla a wannan lokacin d'auke take da alhini irin na rashi. Bayan doguwar addu'a daga bakin Muhammad, Baffa ya fara bayanin cewa ya kira taron ne don ya gaya musu cewa anyi rad'in sunan Babyn da asubahin ranar kuma Imran ya rad'a masa sunan mahaifin Inna wato HISHAM. Anyi yanka kuma su mama Azumi har sun gama suyar naman. Yanzu abinda ya rage shine inda rik'on yaron zai kasance, za'a barshi anan wajensu ne, ko kuwa Inna tana ganin a bawa dangin Imran su rik'e shi. Daga yadda ya fad'a kowa ya san cewa ya fad'i hakan ne kawai don a kwatanta adalci a kowanne b'angare, amma ba ta yadda za'ayi Inna ta bari d'an nan ya matsa daga kusa da ita. Ai kuwa yana rufe baki, tayi tsalle ta dire cewar ba inda za'a tafi dashi, ai hakk'in dangin uwa ne kula d'a karami yaro irin haka, saboda haka yadda ta raini Nanne, a bar mata shi zata raine shi da dukkan iyawarta. Aunty maryaama kuma tace Inna ta tsufa, d'awainiyar yaro k'arami zata yi mata wahala a wannan shekarun saboda haka ita a bata shi, ta san mijinta zai amince, amma bata k'arasa ba Inna ta hau sababi wanda ya had'a da kuka tana fad'in bata yarda a matsa koina dashi daga cikin gidan ba, saboda haka Nuratu ma dake shirin magana tayi shiru da bakinta. Sai Aunty amarya tace ita zata karb'e shi amma Inna tayi saurin katse ta tun kafin ta k'arasa. "Kar ki kuskura ki k'arasa zancen nan, Hadiza, kar ki kuskura ki k'arasa, yau har kece mai bakin cewa a baki d'a? Duniya makaranta! Shekaru ashirin kenan baya muka yi irin wannan zaman a d'akin nan, ba irin yadda bawan Allahn nan bai rok'e ku ba akan ku taimaka ku rik'e masa marigayiya ke da Halime, amma kuka k'ek'ashe idanunku kuka ce baza ku raini 'yar kishiya ba, shine kike da bakin magana a yau? yo me kuma zaki yiwa d'anta a yanzu? me...." Bata k'arasa ba Baffa ya katse ta da girman Allah akan tayi shiru, abinda ya faru a baya ya riga ya wuce. Bayan ya gama 'yan koke-kokenta da rantsuwar baza a bawa Aunty Amarya ba, Baffa ya tambayi Imran game da ra'ayinsu, a karon farko cikin kwanaki bakwan nan ya bud'i baki yayi magana, don hatta jaamil ba yadda baya yi dashi ba wajen tambayarsa abubuwa amma baya tab'a cewa komai, ko wajen karbar gaisuwar baya zama, a kullum yana can cikin dakin Baffa inda yake kulle kansa yayi ta kukan da har hawaye sai sun daina bin kumatunsa, don Allah ya sani daya zauna a waje wani yace masa. Ya hakuri? Gwara ya shafe yinin ranar bai ga kowa ba, yana faman yi mata addu'ar da bata k'arewa! Tun lokacin da karfin rabin ruhinsa da ya bar na Sa'adha ya dawo jikinsa yake fatan k'arshen zaman makokin yazo don ya sami damar yin abinda Bwama da jaamil keta hana shi tsawon kwanaki. So yake yaje Muzaffar ya gayawa Naani cewa abinda dake fata ya dawo jikinsa, dama tace ruhinsa ba zai taba barin jikinta ba sai in har ta mutu, zai gaya mata tayi nasara ta kashe ta, b'arin ruhinsa ya dawo jikinta kuma zaiyi amfani dashi itama ya kashe ta! Amma Bwama da jaamil sunce alamar tambaya zata d'arsu akansa in har ya bar gidan zaman makokin ya tafi Muzzafar a wannan lokacin, sunce yayi hakuri ya daure wad'annan kwanakin don ya rufe asirin sanin WAYE SHI daga dangin Sa'adha, sunce bai kamata ya bada wata k'ofar da zata sa su fahimci wani abin ba kamar yadda ta rufa asirinsa da dukkan iyawarta, shi yasa jaamil ya sake dawo da wad'annan tarin mutanen a matsayin 'yan uwansa suka zo suka yi gaisuwa kamar yadda kowa yake zata. Yayi gyaran murya kad'an lokacin da hankalin kowa ya dawo kansa. "Baffa duk abinda Inna ta fada gaakiyane, a yanzu wajenta ne mafi cancanta da yaron ya zauna, sai dai kuma abinda Aunty maryama ta fada itama gaskiyane, bai kamata a d'ora mata d'awainiyar jariri a shekarunta ba, tunda kuma bata yarda da kowa ya rik'e shi ba ina rok'on alfarmar ta bar 'yar uwata (yana nufin Bwama) a wajenta ta taya ta rainonsa." "Wallahi na amince, ko su nawa suzo, idan har zaku bar min shi a gabana." Inna ta amsa kai tsaye. Cikin wannan tattausar muryar tasa mai zurfi, Imran ya cigaba da magana. "Sai dai ina rok'on ya dawo wajena daga lokacin da shekarunsa suka kai na shiga makaranta, na riga nayi mata alk'awarin zan kula dashi." Ba sai ya fasa ba, kowa ya san yana nufin Nanne ne, yayi wa Nanne alkawarin cewa zai kula da Babynta/Hisham tsawon rayuwarsa! "Wannan ba wani abu bane Imran, kai ubansa ne kana da hakkin karb'arsa a duk sanda kaga dama, saboda haka ko bayan raina kowa ya shaida nayi alkawarin zamu baka shi daga lokacin da ya shekara uku." Da wannan alkawarin taron ya tashi, Inna bata ja da hakan ba saboda itama ta san yana da hakki akan d'ansa kuma ko ba komai an had'a da cewar alk'awarin da aka yiwa Nannenta ne. Da hakan kuma Imran da jaamil suka had'a bangarorin dutsen Nil suka dank'a a hannun Bwama a matsayin abinda zai cigaba da  bata karfin da zata iya maintaning jikin bil'adama a cikin shekaru ukun da zata yi na kula da Hisham, da hakan kuma aka yi sadakar bakwai aka share zaman makokin Sa'adha, gidan ya sake shiga sabon yanayi na alhini, kewa da kuma k'unci. Ance sabo akewa kuka ba mutuwa ba, duk da auren da tayi, d'aukacin al'ummar gidan kaf! sun saba da Nanne, don ita d'in mai tsokana ce da  karamniya, ko mutum bai shiga shirginta ba, dole zata nemi abinda zai had'oka da ita, wanda daga baya za'a zo ana dariyarsa, hatta su Lami da ba shiri suke ba sun sha kuka da idanunsu akan rashinta, saboda haka dole alhini ya shafi wani b'angare na walwalar gidan. Da hakan kuma Imran ya shirya tsaf! ya d'auki hanyarsa ta zuwa Muzzaffar!! **** BAYAN SHEKARA GOMA. Yamma ce, amma gari yayi duhu sosai alamun bak'in had'arin dake manne a sama na iya narkewa ya sauko a kowanne lokaci. Imran ya bud'e k'ofar cikin d'aki da saurinsa ya fito... Nanne ta biyo bayansa da gudu ta cikin corridon da ya kawo su main falon gidan, tana sanye da wata 'yar k'aramar vest kalar ja da  kuma da d'an blue short da bai ka gwiwa ba, hannuta rik'e da wani k'aramin towel yayin da Imran ke sanye da dogon wando da singlet kawai, lallausar sumar kansa na d'iga da ruwa. "Ayunie dan Allah mana sau d'aya." Ta fad'a tana turo d'an bakinta alamu shagwab'a. D'aya daga cikin manyan abinda Imran baya so shine a goge masa gashi in ya wanke shi, ita kuma tunda ta fahimci hakan shikenan ta samu hanyar tsokanarsa. "Dan girman Allah kiyi hak'uri, wallahi ba dad'i ne." "Dan girman Allah nima ka barni inyi sau d'aya.." Ta fada tana k'okarin zagayowa ta bayan kujerar da yake tsaye, aikuwa yana fahimtar haka ya fara matsawa shima. "Toh kije ki d'auko hand dryer, amma ba da wannan ba." "Saboda me?" Ta d'age girarta d'aya. "Towel d'in nan yana da laushi, zaka ji kamar massage nake maka." "A'a Noory, ki hak'uri dan Allah." Ta matse kafad'arta d'aya. "Allah ba zan hak'ura ba." Da haka ta fyalla da gudu ta nufe shi, suka shiga zagaye kujerun falon da gudu tana ta kyalkyala dariya, shi kuma yana ta rokonta don har ga Allah baya so, a haka yayi tuntub'e da wayar extension ya fad'i k'asa, ai kuwa ta d'ane kansa ta shiga murza towel din a cikin gashinsa, da kyar ya iya cafke hannayenta ya wullar da towel d'in. "Ba kya jin magana you sweet little dickkins!" Ya fad'a yana ware tufkar gashinta itama, ta dinga dariya sanda yake hargitsa shi da hannayensa har saida ta fad'a kan jikinsa tana fadin. I'm sorry! Muryar ta mai sanyi ta ratsa dukkan jijiyoyin jikinsa, it was so real da yaji ko kad'an baya son ya bud'e idonsa ya koma wannan zahirin da babu muryar. "Noory... Ya kira sunanta a hankali, ta d'ago ta k'ifta chocolate idanunta masu d'auke da kwalla a hankali, so slow ta yadda yana ganin yadda dogwayen lashes d'inta suka had'e dana k'asa kafin ta sake bud'e su, gashinta a hargitse kan kafadunta wani ma ya zubo kan fuskarta... the way he always wanted it! the he always missed it! "I've missed you, I'm always missing you..." Muryarsa ta rad'a mata a hankali sannan ya k'ara da. "... like crazy!" Sai tayi wani guntun murmushi da ya k'ara fito da yawan kwallar idonta, sannan a hankali ta ware hannunsa d'aya dake rik'e da ita, ta d'ago shi sama sannan ta lankwasa yatsunta a tsakanin nasa, ta juya kanta da wani irin slow motion ta kalli hannayen nasu sanda shima ya lankwasar da nasa yatsun a cikin nata, amma bai bar kallon fuskarta ba. "I miss you too Ayunie!" Lallausar muryarta ta fito kamar rad'a, Imran ya kalli yadda kwallar ke gangarowa gefen fuskarta a hankali tana shigewa cikin sassalkan gashin kanta, yaji zai iya nutsewa cikinsu ya manta da duk wata damuwarsa. Ring. Ring. Ring. Ring. Ring..! K'arar wayar dake ajiye a gefensa ta farkar dashi zuwa zahirin da yake gujewa. Ya kalli inda yake, kan sallayar nan ne dai a gefen gado inda yayi nafila bayan tafiyar Hisham makaranta. Ya dafe kansa cike da takaici sanda idanunsa suka koma suka lumshe, zuciyarsa ta dagule ta hasala kamar yadda hakan ke faruwa duk ranar da yayi mafarki da Sa'adha ya farka. Wayar data katse a gefensa ta sake d'auka da wani ringtone d'in, ya zamo da hannunsa ya shafa kwantaccen sajensa sannan ya mik'a hannu ya d'auke ta. "Hello mr. Siddiq?" Muryar baturiyar daga d'aya gefen wayar ta ambata. "Yes." ya amsa cikin husky voice d'insa. "There's an emergency about your son, we need to see you at the school now." ( Muna nemanka da gaggawa akan wata matsala data shafi d'anka.) "Okay." Hankalinsa a kwance ya amsa sannan ya kashe wayar, saboda hakan ba wai bak'on abu bane a wajensa, in dai matsala ce akan Hisham ya san yanzu suka fara, don makarantar da ya cire shi bayan dawowarsu daga madina, daga shi har malamar tasu sun riga sun saba da irin wannan wayar, tana d'auka zata ce. 'The usual.' Shi kuma ya shirya ya tafi yaje Office d'in guidance and counselling yayi shiru yana jin dukkan k'orafinsu in sun gama ya basu hak'uri sannan ya d'auko shi su taho, a hanya shima ya bud'ewa Hisham nasa babin fad'an daga k'arshe kuma ya koma biya nasihar da dukkanninsu sun haddaceta. Wannan shine kusan rabin yadda suke tafiyar da rayuwarsu a wani d'an karamin gari mai suna "Bottesford" dake k'ark'ashin birnin Nottingham a k'asar England. A zamansu na madina ne suka fuskanci k'alubale kala-kala saboda su da gaske hukunta Hisham suke yi duk ranar da yayi wani abu da ba daidai ba wanda hakan ya dad'a janyo baiyanar abubuwa mamakinsa saboda duk lokacin da ransa ya b'aci ko yayi fushi ne baya iya controlling kansa. Dalilin da yasa har suka tafi dashi babbar headquarter d'in da ake hukunta masu laifi don yin bincike akan genesis d'insa saboda bayan sun d'ebe extraodinary possibilities d'insa, abubuwan da yake yi gabad'aya sun wuce irin abinda yara masu shekarunsa su kanyi. Wannan dalilin yasa ba shiri Imran ya tattaro suka dawo England da niyyar zaiyi dedicating rayuwarsa wajen canja k'asashe da kuma garuruwa har zuwa lokacin da Hisham zaiyi hankalin da zai dinga b'oye possibilities d'insa, yayi wa kansa wannan alkawarin kamar yadda yayi wa Sa'adha alqawarin zai kula dashi har tsawon rayuwarsa. Ya tuno rayuwar da yayi tsawon shekaru uku a hannun Bwama tana kula dashi kafin ya dawo hannunsa, rayuwar da yayi a cikin garin katsina kuma a cikin gidansu Sa'adha, rayuwar data sanya tsananin shak'uwa tsakaninsa da al'ummar gidan ya zama kamar ya maye musu gurbin mahaifiyarsa ne, rayuwar da Bwama bata tab'a barinsa ya baiyana wani abu daban nasa ba har ya gama zamansa tare dasu, bata taba bari ya bada wata kafar da zata kaisu ga sanin ainihin WAYE SHI ba. Abinda har yau har gobe ya kasa sanin da irin abinda zai gode mata, in banda tarin addu'ar da yake binta dashi a kullum. A hankali ya mik'e ya ninke sallayar sannan ya shiga toilet yayi wanka sosai, bayan ya fito ya shirya cikin wata jacket mai kama da jallabiya data wuce gwiwarsa da kuma wandon jeans, ya taje gashinsa sannan ya d'auki key d'in motarsa ya fita, har ya kai waje ya tuna da wani abu, ya dawo ya shiga kitchen, ya d'auko robar lemo mai sanyi guda biyu sannan yayi locking gidan. **** "Mr. Siddiq I just don't know how to explain but look at this and tell me how in the world can a 10- year old do this?" (Ban san ta yaya zanyi maka bayanin abinda ya faru ba, amma ina so kalla sosai ka gaya min ta yadda yaro d'an shekara goma zai iya hakan.) Mrs Judy, Malaysian-British Principal d'in makarantarsu Hisham ta fad'a tana kallon Imran dake zaune akan kujerar tsallaken teburinta. Imran ya cije gefen lebb'ensa na k'asa yana kallon zungureriyar jelar kitson dake ajiye a gabansa, a gefensa na hagu, Wani ba'indiye ne rik'e da hannun 'yarsa wadda tasha plaster a gefen gashinta kusa da irin kitson da yake kallo a gabansa. Daga d'aya gefensa kuma Malamin ajin su Hisham d'in ne da wasu Malamai biyu zaune suna jiran amsar sa.... Sannan hisham d'in kansa a tsaye daga gefe, wani kyayawan yaro mai kama da siffar mahaifinsa sak! in ka d'auke farin fatarsa da kuma da wad'annan manyan chocolate eyes d'in irin na Nanne sak! ya cije gefen lebb'nsa na k'asa shima kamar yadda mahaifinsa yayi sannan yana tsaye da wata irin tak'ama da kuma isa irin wadda ta wuce na yaro mai shekarunsa, yana sanye da wandon jeans da kema jar T- shirt, sai top mai had'e da hood wadda ya jawo hular ya rufe tarin gashin kansa da yake kar na jinsin jar fata, wanda duk da haka ya fito ta gaba perfectly styled dashi, girman jiki irin na yanayin abincinsu da weather ta can yasa zaka ce ya kai shekaru sha biyar. Tun shigowarsa cikin office d'in, manyan idanunsa na kallon k'asa kawai ya zura hannayensa cikin aljihun wandon, ya had'e girar sama da ta k'asa yadda wani zai rantse ba akansa ake magana ba, yana jira ne a gama ya fad'i abinda ya kawo shi daban. Cikon lallausan turancin nan nasa Imran ya bud'e baki yace. "Ni kaina ban san me zan ce muku ba principal, ba san ta yaya yaro irin hisham zsi iya aikata hakan ba, saboda haka sai dai mu danganta al'amarin da tsautsayi kawai, ina mai basu hakiri da kuma fatan zasu yafe masa sannan a gaya min tarar nawa hakan ya kama, zan biya yanzun nan." Duk yadda principal din nan da mahaifin yarinyar suka kai ga jin haushin Hisham ba yadda suka iya haka suka hakura, aka fad'awa Imran tarar cire gashin ya fito da card d'insa nan take ya biya yana k'ara basu hak'uri, da haka ya bar office d'in Hisham na bin bayansa ba tare da ya ko kalli inda Malamansa suke binsu da kallo ba. "How many times do we have to talk about this Rhea, I told you he's a single father." (Sau nawa zamu yi mafanar nan ne wai Rhea, na gaya miki bashi da aure.) "I know, I knew! but I can't control myself everytime he came into the view, and he's an african you said? oh my God! I swear Africa never look this beautiful and handsome an dashing and..." (Na sani, Na sani! amma bana iya rik'e kaina ne duk sanda na ganshi, kince daga Africa yake koh? na rantse Africa bata taba min kyau irin haka ba, da shek'i da kyau da...) "Hello Rhea, he's not Africa, he's from  Africa! and you better be careful.. he's Emily's crush as well!" (Kinga Rhea, bafa shine African ba, k'asar ce, kuma ya kamata kiyi hankali.. don Emily ma tana son shi!) Imran ya tura main k'ofar fita daga makarantar ya fita, ya riga ya saba da jin irin wannan hirar daga wajen mata a kusan duk inda ya taka ya shiga cikin k'asar turawa, k'asa irin wadda kunya tayi k'aranci a cikinta, ire-iren abubuwan dake sawa yaji kewar arewacin Nigeria ta kama shi, wajen da yake cike fal! da tari al'adun Hausa-fulani masu tsananin kyau da burgewa, abin alfaharin duk wanda ya kasance a cikinsu. Amma ba yadda zai yi ne, ya riga ya yiwa Sa'adha alk'awarin kula da Hisham tsawon rayuwarsa, kuma alk'awarin ya had'a har fa bashi kulawa ta gari da kuma d'ora shi akan hanyar da zata fi karkarta ga rayuwar bil'adama, shi yasa yake bin makarantun turawa dana larabawa, wad'anda suka fi Nigeria wajen bada ingantaccen ilimi boko da kuma na addini, don duk wani abu da zai bawa Hisham a duniyar nan, sai ya tabbata mafi kyau ne! Ya sawa hadaddiyar motarsa k'irar 'Venza' key suka juya suka fita daga harabar makarantar suka cilla kan titi, hasken ranar da yayi tar! a lokacin ya haska kyawawan fuskokinsu su duka biyun, wadda banbancinsu ya kasance abu biyu, na farko fuskar Imran cike take da kwantaccen saje da gashin baki wanda a yanzu suka k'ara yawa fiye da lokutan baya, yayin da na Hisham sid'ik take, in banda lallausan gashi kad'an da ya fito har wajen hab'a, alamun nan gaba shima sajen ba zai masa wahala ba. Sai kuma banbancin yarinta da ta alamun matashi d'an shekara talatin da takwas. Imran ya janyo wani bak'in space ya saka saboda hasken ranar da ya masa yawa, sai ya k'ara wani kyau kamar yana shirin gabatarwa da kamfanin space d'in talla ne, ya d'ago robar lemon nan guda biyu da har yanzu ke d'igar sanyi ya mik'awa Hisham d'aya. "Ina jinka." Ya fad'a ba tare da ya d'auke idonsa daga titi ba. "Daddy cewa tayi tana sona." Sai da Imran ya kware a lemon da yake sha kafin ya rage gudun motar ya juyo ya kalle shi. "What?" Hisham ya d'aga kafad'unsa shima ba tare da ya kalle shi ba. "Ai ba ita kad'ai ce bama, ita nata abin ne yafi bani haushi tayi ta zuwa wajena, wallahi da an barni sai na cire gabad'aya gashin kanta." Imran ya buga kansa da jikin kujerar sannan ya tura hannunsa cikin gashin kansa. "Hisham for goddness sake! shekarar ka fa goma, kana grade 4... me mamanka zata ce in taji haka?" Ya riga ya saba masa, suna maganar Nanne ne a kullum kamar zasu koma gida su same ta, don ya yarda in ba da hisham ba babu wanda zai iya hirarsa da ita, kuma shima ya kamata ya san wani abu na mahaifiyarsa. Hisham ya kurb'i lemonsa kafin yace. "Cewa zata yi duk wanda ya sake cewa yana son Babyna, kabi su duk ma mare su sai sun koma ja kamar tomato." Imran ya d'anyi murmushi kafin shima yace. "Sannan kuma tace dukkansu ka had'a musu da Allah ya isa!" Hakan yasa suka kyalkyale da dariya gabad'ayansu kafin kuma dariyar ta mutu a hankali, yadda suka saba duk lokacin da suka tuna cewa babu ita d'in. Kusan a tare suka cusa hannunsu d'aya cikin gashinsu sannan hisham yace. "Yaushe zamu je Nigeria?" "Yaushe zaku yi hutun Summer?" "In the next three weeks." "Then ka had'a kayanka!" Suna isa gida Hisham wayarsa ya fara lalubowa ya kira number Sadiq, bugu d'aya biyu ya d'auka. "Man, ya akayi ne?" Cewar Sadiq daga d'aya b'angaren, wanda shigarsa d'akin Inna kenan bayan ya dawo daga wajen aikinsa, tunda a lokacin har ya gama masters dinsa a b'angaren economics. A yanzu sune samarin gidan Baffa shi da 'yan biyu, duk sauran yayyen nasu sunyi aure da 'ya'yayensu. Aunty Amarya ta sami abinda take so, 'yayanta ke juya kusan komai na harkar gidan tunda tsufa ma ya kama Baffa baya iya abubuwa da yawa. Cikin irin hirar da suka saba Hisham yake gaya masa zai zo Nigeria nan da sati uku, daga k'arshe kuma ya bawa Inna dake ta mik'o hannu jin ance Hishaam ne ke wayar. "Hey, Baby girl! ya k'afar taki?" Imran na tsaye da jikin dining hannunsa d'aya a aljihu d'aya kuma rik'e da mug din coffee yake kallon Hisham, yana iya jin magiyar Inna ta cikin wayar wadda a kullum bata gajiya da ita kan suzo taga Babanta, koda kuwa a yau suka je suka dawo in an sake waya sai tace su taimaka su dawo, a yanzu tsufa ya kamata kwarai! don ko tafiya bata iya yi sai an kamata. Hisham nata dariya cikin wayar kamar bashi ba yana tsokanarta, Imran yaji wani sanyi a kasan zuciyarta daga yadda yake kallonsa daga nan. Kaf! duniya yanzu baya tunanin akwai abinda yake k'auna sama da d'an nasa, dama Sa'adha ta riga ta fada. "Ina ji a jikina ulfat Babyn nan alkhairi ne a garemu, ba zai tab'a zama irin tunanin da kake ba...ina son shi sosai Allah, kuma kaima na gaya maka zaka zo ka so shi fiye da tunaninka insha Allah." "That's true Noory!" ya fad'a a hankali yana kub'ar coffee d'insa. "So true!" Muryar jaamil ta amsa a gefensa. Yayi saurin juyawa ya kalle shi sannan yaja tsaki. "Jaamil don muna k'asar turawa fa haka baya nufin an daina sallama kenan." "Ko kuma ya kamata mutum ya daina tafiya zurfin tunani yana amsa sallama in anyi ba." Ya fad'a yana karbar mug d'in hannun nasa. "Me ya kawo ka ma ne wai? it's less than a week fa da kazo? An gaya maka haka ake shugabantar al'umma?" Jaamil ya d'age kafad'unsa yana zama akan dining d'in. "Ya zanyi, kewarku nake kullum kamar me... can din ba wani abu mai gamsarwa daga hukunci sai zartarwa! inaga ya kamata in canja tsarin abubuwa da yawa wallahi." "Ko kuma ya kamata ka sami wadda zata canja ka ba, nasha gaya maka it's high time wata ta shigo cikin rayuwarka, ya kamata kayi aure." Imran ya fad'a yana zama shima akan kujerar dake fuskantarsa. Shekaru goma kenan baya, da jaamil ya kasance shugaban nahiyar Muzzaffar! sakamakon kashe Sareefa da Imran yayi, don a lokacin da ya isa Muzaffar bai tarad da Naani a raye ba, Sareefa ta kashe ta bayan dukkan abinda ta tanada saboda ita, bayan dukkan d'awainiyar data yi mata, ta kashe mahaifiyarta sakamakon tsananin k'ullatar ta da tayi da kuma son mulkinta, wanda a lokacin kuma take fafutuk'ar ganin yadda zata ga bayansa shi da jaamil. Saboda haka a lokacin da ta ganshi, bata b'oye masa komai ba na yadda ta kashe mahaifiyarta saboda ta fahimci bata da niyyar d'aukar fansa akansa, sannan ta shiga ganin bayan matarsa kafin ta k'araso gare shi. Ta gaya masa dukkan abinda yaji daga cikin habler nan Naani ta fad'a mata ne saboda ta kwantar da hankalinta ba wai don haka komai yake a zahiri ba, Tace da gaske ne tun farko Naani ta d'auko shi ne saboda wannan aikin da take so yayi mata, amma daga baya zuciyarta ya so shi tsakani da Allah, So irin wanda ita da take d'iyarta bata taba mata. Saboda har a lokacin da ya hana ta dutsen Nil, zuciyarta ko kad'an bata da nufin cutar dashi, tace mata ne kawai zata kyale shi don ta san bayan wani lokaci zai dawo gareta shi d'in mai tsananin biyayya ne, Saboda haka a tunaninta na son farantawa Sareefa itama, sai ta bata kusan dukkan karfin jikinta, sannan tayi murabus ta nad'a ta a wanda da wannan damar Sareefan tayi amfani ta kashe ta bayan kwanaki biyu. Sannan ta shiga kokarin ganin bayan matarsa, don tayi rantsuwar sai ta guntule farin cikinsa tukunna kamar yadda suka hana ta itama kafin shima ta kashe shi, sannan tazo kan jaamil da mahaifiyarsa Bwama. Sai dai a lokacin bata da ikon kusantarsu saboda karfin dutsen Nil dake cikin gidan da suke, saboda haka daga nesa ta karanci halayen Sa'adha tsaf! da kuma mutanen da take mu'amala dasu. Ta haka ta gano cewar hankalinta yafi karkata ga Safiyya maman yarinyar nan Hidaya, ta gaya masa cewa matar bata tab'a zama muguwa ba kamar yadda yayi tunani a baya, kawai bai yarda da ita bane saboda jikinsa ya bashi alamar da bai iya ganewa ba a lokacin, alamar cewa rayuwarsa zata hargitse ne ta dalilinta, saboda da ita tayi amfani, ta shiga jikinta taje har kofar falonta, ta bugawa Sa'adha 'Kambun Turaz' a cikinta, wani abu da suke hukunci dashi wajen karya gab'ob'in irin halittarsu. Sai a lokacin Imran ya fahimci Sa'adha ba karamin k'ok'ari tayi ba na iya tsaida bugun zuciyarta har sanda Hisham ya fito duniya, don in har za'a bugawa irin halittarsu wannan kambun gab'obinsa su karye inaga an bugawa halittar bil'adama wadda take mai rauni? Mummunar kisa irin wadda in ido ya gani zai rikice, kwakwalwa ta hargitse hankali ya tashi, ita yayi wa Sareefa a lokacin da take ganin tayi k'arfin da ba zai iya galaba akanta ba, ya kashe ta amma bai cigaba da farfasa halittar jikinta ba har saida jaamil ya janye shi da k'arfin tsiya. Bayan nan kuma bai k'ara zama cikin hankalinsa ba tsawon watanni, jaamil shi yayi fafutukar kula dashi a duk lokacin nan, alhali ya karbi sarautar nahiyar Muzzafar! domin shai kad'ai ne jinin sarautar da ya rage a cikin zuri'ar Naani. Damuwa da depression kala-kala ba irin wanda bai shiga ya tafi ta gaba ba, saboda ba don d'aya b'arin ruhinsa dake jikinsa ba ya tabbata da tuni zuciyarsa ta dad'e da bugawa ya mutu! don sai a shekarar da rik'on Hisham zai dawo wajensa ne sannan ya samu ya fara dawowa haiyacinsa... amma Allah ya sani, ya azabtu fiye da tunanin mai tunani! "Kar ka damu, zanyi aure kwanan nan yarima." Imran ya zare idanunsa a lokaci d'aya, sannan ya matso da jikinsa ta kan table d'in. "Kace min mafarki kake nake yi jaamil, kaine yau kake fadar kalmar aure da bakinka? ya salam! you seriously need to tell me this, wacece haka?" Kafin jaamil yayi magana Hishaam ya taho da wani irin sauri da yafi k'arfin ganin idanun d'an Adam ya d'ane kan jaamil yana ihun murna. "Hishaam sau nawa zan gaya maka ka daina irin wannan saurin?" Imran ya fad'a da k'arfi amma Hishaam bai ko saurare shi ba, ya dinga kyalkyala dariya yana jijjiga jaamil har sai da ya suka sauka daga kan kujerar suka shiga birgima a k'asa. Imran yayi murmushi kawai sannan ya janyo wayarsa ya kunna ta. Hoton Sa'adha tar ya baiyana akan screen d'in, ta lumshe idanunta tana murmushi, shima ya lumshe nasa idon a hankali yayi murmushi. "I love you so much Nanne!" Sunan da baya tab'a jin ya kirata dashi a tsawon rayuwarta! "Allah yayi miki gafara!" KARSHE. *** Alhamdlilah! Alhamdlilah!! Alhamdlilah!! A yau mun kawo k'arshen labarin WAYE SHI? munji komai kuma ina k'ara baku hak'uri da ta'aziyya akan rashin Nanne da muka yi. Ba yadda muka iya ne, k'addarar labarin tafi soyayyar da muke yi mata! Nagoode! Nagoode!! Nagoode!! For all d love u guys show me along the way. Allah ya faranta muku da d'imbin alkhairi🙏😍 A big shout out a to all wad'anda zasu zo bayan mun gama labarin nan, na gaishe ku kyauta! Allah ya saka muku da alkhairi!😊 Kuma kuyi min dropping ra'ayinku game da labarin nan ta wannan number, 08067794315 zan dinga samun lokaci ina dubawa don in dinga baku dukka amsoshinku Insha Allah. Allah ubangiji yasa zamu sake had'uwa a next labarina, wanda nake ganin zai ma fi WAYE SHI, dad'i saboda I'm becoming a better writer now!🙈😁 Contact me via dat number for more Information, Allah ya sada mu da alkhairinsa.!😁 Thank you guys!💓💓💓