[3/21, 22:27] Xahratty (OUM AJMAL): 👨🏽‍🦳 *_GALADIMA FAMILY_*👨🏽‍🦳 Story& Written By *FATEEMA ZAHRA LAWAL* Marubuciyar⤵️ A DALILIN'YAR TSINTUWA. MIJIN ZAHRA. DIAMOND LADIES (Daukar fansa) paid book. RUHIN AMRITA (FATALWA CE) Now *_GALADIMA FAMILY_* https://hausanovels001.com.ng Page 01 Tafe take cike da natsuwa kamewa,long Hijjab ne ajikinta sky blue Wanda ake cema jalbab fuskarta sanye da madaidaicin glashi wanda yasake fito da ainahin kalan fatanta sanye take da facemask sky blue tayi matuqar kyau ,kafanta sanye da halfcover golden colour,jakane rataye a kafadarta golden. Duk dacewa bazata gaza shekaru sha takwas ba sai dai natsuwarta nasa amata kallon tafiye haka. Taqaraso dai² kwanar layinsu,lokaci daya taji wani irin qunci da takaici ya lullubeta badon komai ba sai don masu zaman kashe wandon layin nasu(sunan da tasanya musu kenan),sake tamke kyakkyawar fuskanta tayi duk dakuwa facemask din da ke lullube da fuskarta,a hankali yasake qarfafa saurin tafiyan nata don burinta baiwuce ace kauce inda masu zaman kashe wandon suke ba. "Zuhra sannu da dawowa,fatan kindawo lafiya?kalmar da tatsinkayo daga cikin kunnenta kenan. Da hanzari tajuyo cike da mutumtawa tadubi inda maganar tafito tare da dan rissinawa tace"barka da gida baba me icce inayini?tayi maganar tare da fadada murmushinta. Amsawa yayi cike da mutumtawa tare da sanya mata albarka,sosai taji dadin albarkan da yake sanya mata. Walwala kwance akan fuskanta taqariso bakin gate din gidan nasu,madaidaici mai matuqar kyau da tsaruwa,hannu takai da niyyar knocking gate din,ahankali taga anbude taciki. Koda tadago ido four eye's sukayi dashi,sosai kirjinta yayi saurin bugawa wanda yasa da hanzari ta sunkuyar da kanta qasa,shiko ta bangarensa kallo daya yamata sannan yadauke kai,rabata yayi yawuce ta gefenta. Bayanshi driver dinsu ne janye da trolly bag yanufi wata mota dake fake a kofar gidan nasu,kafin zuhra tajuyo taji hayaniyar yaran gidansu nafitowa,maimoon ce tafito da gudu cike da yarinta da rigima tace"pls yah Sauban katafi dani mana inaso naje masarautar su bodejo. "A'ah ya Sauban kada kaje da ita dani zakaje saboda nayi missing din bodejo kuma bantaba zuwa masarautar ba,Amma maimoon ita taje. Wani dan murmushi wanda suke kira da ya Sauban din yaqaqalo tare da dafa kan ateek yaron dan shekaru goma cike sanyayyar muryan shi mecike da taushi yace"kada kadamu my aboki insha Allah bazan dadeba zandawo I know lokacin kunsamu hutu a school so insha Allah idan nadawo zan tafi daku,Ok? Cike da murna yaran suka hau tsallen murna,zuhra kuwa gabadaya tamkar andasata a tsaye ita batayi gababa kuma batayi baya ba,a hankali tasauke wata sihirtaccen ajiyar zuciya tashiga cikin gidan,direct apartment din mommy tanufa,bude kofan tayi tana sallama cikin siririyar muryanta,wanda idan mutum beyi dagaske ba bazaiji abinda tafada ba,mommy kuwa da tataso da alamu fita zatayi hannunta riqe da wani hadadden ledabag tace"My zuhra welcome! Murmushi zuhra tayi cike da gajiya tace"mommy!tayi maganar tare da langabar dakai tace"nagaji mommy gaskiya nikam nagaji da zuwa jamb class dinnan. Wucewa mommy tayi tare da cewa"kedai kije ki watsa ruwa kici abinci nasan meke damunki duk baiwuce gajiya ba so nasan dakin watsa ruwa zakiji dai² tayi maganar tana fita daga farlon. Ajiyan zuciya zuhra tasake saukewa akaro na biyu tanufi stairs tahaye,shiga dakin mommy tayi tare da cire hijjab dinta,wow Masha Allah tsarki yatabbata ga ubangijin daya halitta wannan halittan,Ashe zuhra kyanta ba'a fuska bane kadai harta da halintan sura Allah yahore mata,ahankali tacire kayan jikinta yarage daga ita sai undies farare tass. Addu'an shiga toilet tayi sannan tasakai cikin hadadden bathroom din wanda yatsaru kota ko'ina. Bata bata lokaci ba tafito daga toilet din,agurguje tasanya English wears na riga da wando purple wanda suka sake daukan suran nata,kobi takan lotion batayi ba.Hulan kayan tasaka a gyararren gashin kanta,tazura slippers,zare handbag dinta tayi taciro wayarta qirar iPhone 13 pro max tafito tare da sakkowa daga kan benen,kallo daya tayima dinning din tahango warmers dinda ke Kai anjejjera abinci. Fita tayi daga farlon tanufi dayan apartment din dake hannun dama,cike da qwarin gwiwa ta Isa farlon sai dai wacce tahango zaune kan one sitter din dake farlon yasa jikinta tsananin yin sanyi,cikin sanyayyar muryanta tayi sallama,ahankali taqarisa shiga tamkar wacce kwai yafashewa a ciki ta isa inda babban mace take zaune wacce aqalla zatayi shekaru hamsin da duriya, fuskarta sanye da medical glass ta'aza kafa daya kan daya. Gefe guda laptop ne akan cinyarta take sarrafashi,cike da fargaba zuhra ta isa inda take tare da rissinawa tace"Ummi sannu da gida! batare da tadago daga abinda take a ta amsa da "yawwa sannu dawowa. Cikin sanyin murya zuhra tare da tsantsar mamaki tafurta "yawwa. Miqewa tayi tanufi stairs,kai tsaye dakinta tanufa,ahankali tazauna akan tsadadden gadonta tare da sauke wata qarfaffan ajiyar zuciya a fili tace"Ummi yau tayi abin mamaki,yau ta amsa gaisuwata batare da kyara ko shakku ba,amma meyasa?kafin tabawa kanta ansa anturo kofan bedroom din nata. Nihal ce da Laila,murmushi tasaki kamar yanda suma suka saki,nihal tace"kai zuhra yau gaskiya kundade a jamb class dinnan meyafaru ne? Laila tace"tun sanda ya sauban ya dawo damu muke tambayarki akace ai kinshiga jamb class,wai kinanan akan bakanki na zuwa Danfodio din?kizo muyi joining gabadaya a ABU mana. Zuhra tace"hmmm Laila kenan bazaku gane ba nisam banason harkan takura,kunsan ya Aseef a ABU yake lecturing wallahi takurama rayuwa zaiyi muddin nashiga ABU kunsan halinsa fa tamkar bunsuru yake shiyasa nafison Danfodio akan ABU bawai don wani abuba sannan duk abinda yake aikatawa Ummi bata gani,kunsanta akan ya Aseef zata iya batama kowa rai so shiyasa nahaqura da ABU so Kuma kuyi a hankali dashi. Da mamaki suke dubanta Nihal tace"wai zuhra menene lefin ya Aseef don yace yana sonki dahar kike kiransa da bunsuru?don kawai yace yana sonki?to wallahi kikiyaye bakinki da furta wannan munanan kalmomin akansa don da zarar Ummi taji kema kinsan sauran. Laila tace"taya Ummi zataji inba wani yafada mataba gaskiya kila yanada wani boyayyen hali wanda zuhra ce kawai tasani. Dasauri zuhra tadago da daradaran idanuwanta tace"nibansan wani boyayyen hali dayake daba just bana ra'ayinshi ne kawai. Tabe baki nihal tayi tace"ke dama matsalarki kenan miskilanci. Murmushin iya labba zuhra tayi batare da tayi magana ba ta miqe tare da nufan bathroom. *-WASHEGARI-* Saukowa takeyi daga saman stairs inda tacidda gabadaya 'yan gidan zaune akan dinning sunan breakfast,a hankali tadubi kujeran da Abbie yake zama amma bashi hakan yasa sam bataji dadi ba,jikinta yaqara sanyi,mommy ce tace"a'ah zuhra qaraso mana da sauri kiyi breakfast don kinsan shagon saloon din hjy asiya akwai layi barinma yau Wednesday amareda dama zasuje gyaran kai. Qarasawa zuhra tayi tare dajan ajiyan zuciya,kujerar da take zama taja ta zauna a hankali cikin muryanta wanda batafiye son magana ba tace"Barka gida Ummie Ina kwana?batare da Ummie tadubeta ba tace"barka dai a takaice. Duban mommy da ya taufeeq daya Aseef tayi tace"gud morning mommy gud morning yaya's. Murmushi ya taufeeq yayi yace"morning sweet sister,shima Aseef murmushin yayi yace"morning sis, idanunta nakan ya taufeeq tana murmushi har tabude mouth daniyar sake magana Ummie tayi gyaran murya, duban inda take zuhra tayi a rashin sa'a kuwa sukayi four eye's da zuhra,wani rikitaccen kallo ta aika mata dashi wanda yasata saurin dukar da kanta,a hankali ta dauki spoon da plate ta aje agabanta tare da bude warmer din wanda chips ke ciki,kadan tadiba tazuba a ciki. Laila tace"shikenan abinda zakici?batare da tayi magana ba tadaga ma Laila kai alamun eh. Nihal kuwa kyabe baki tayi don Allah yasani tana tsananin takaicin wannan miskilancin na zuhra. A hankali tacigaba da cin abincinta aqasan zuciyarta kuwa tarasa dalilin da yasa Ummie tatsaneta tun tasowarta,inda sabo yaci ace tasaba sai dai sam hakan taqi yuwuwa,ita da zasubi ta nata dasun maidata maidugri wajen bodejo don tafi samun natsuwa da kulawa,maganar mommy ce takatse mata tunani. "Zuhra kiyi kigama ci mana yanzu fa kusan 11:28 yakamata ace kinje har kindawo. Cikin sanyin muryanta tace"tohm mommy ai yanzu zan gama,cikin natsuwa tagama cin abincin tare da daukan tisue tagoge bakinta, miqewa tayi tare da rataya jakanta tace"Ummie,mommy natafi,sister's sai nadawo. Laila tace"Bari nazo narakaki sis,murmushi zuhra tayi najin dadi tace"yawwa aiko naji dadi, duban ya taufeeq Laila tayi tace"Yaya pls ko zaka saukemu al shagon ne?kafin yayi mgn mommy tace"a'ah kuda kukeda shiririta?taufeeq sauri yake zashi company don yakusa ma late sai dai Aseef yakaiku. Wani irin dadi Aseef yaji a ransa,sai dai kafin wani yayi magana taufeeq yace"No no no no mommy bari na'ajesu sharp ² saina wuce. Fuska kwance da fari'a mommy tace"toh shikenan taufeeq ka ajesu,duban nihal yayi yace"keba zakiyi rakiyar ba nihal? Murmushi tayi tace"a'ah Yaya bazani ba,dariya Laila tasaki cike da sharri tace"ae Yaya nihal tana takaicin zuwa saloon taga yanda ake wankema masu gashi kai Amma ita kai kamar na jariri dan wata hudu😃 Gabadaya farlon dariya akasa harda Ummie idan kacire Nihal da tataso aguje tabiyo Laila tana zazzage mata kwandon masifa,da gudu Laila tafita tana dariya, Nihal dinma baya tarufa mata,mommy tace"Kai Laila Laila akwai sharri. Fita ya taufeeq yayi yana dariya, Ummie ma miqewa tayi tanufi main farlo. Daqyar ya taufeeq yadawo da Nihal ciki sannan suka tafi,a mota kuwa banda dariya babu abinda zuhra keyi,sosai hankalin ya taufeeq dana Laila yakoma kan zuhra don rabonda tayi irin wannan nishadin tun ana saura sati daya Abbie yatafi Indonesia,sai gashi yau tayi,hakan baqaramin dadi ya taufeeq yajiba dagashi har Laila,a haka suka karisa shagon saloon din,saukesu yayi sannan yajuya yatafi,sukuma suka shiga cikin shagon. WAI WACECE ZUHRA?MENENE MATSAYINTA A CIKIN GIDAN?AKWAI TURKA-TURKA DA HAUTSIMA ANAN GABA KUDAI KUBINI MUJE Xahratty Ce🥰 Lallai Alqalami 🖊️ yafi takobi🗡️ [3/21, 22:27] Xahratty (OUM AJMAL): https://chat.whatsapp.com/LNYjzpjYlHH8OHTK0bdHGw 👨🏽‍🦳 *_GALADIMA FAMILY_*👨🏽‍🦳 Story&Written By *FATEEMA ZAHRA LAWAL* Marubuciyar⤵️ A DALILIN'YAR TSINTUWA. MIJIN ZAHRA. DIAMOND LADIES ( Daukar fansa)paid book. RUHIN AMRITA (FATALWA CE). Now *_GALADIMA FAMILY_* Page 02 A can kuwa Zaune suke gabadaya a farlon Galadima Daddy,Abbiey,Abba,baba hasheem, Galadima ne zaune a lallausan kujeran sa mekama da gado na irin wanda ake kishingidar nan akai cikin muryanshi me kama dana babban mutum me cike da dattako yafara magana tare da gyaran muryan"Taleeb a matsayinka na babba acikin family dinnan idan kacire ni da bodejo da Kuma guggon ku Laure to kaine babba,magana guda ne ta taramu anan kowa yasan magana ce baiwuce na yaran nan ba tundaga kan Sauban har zuwa kansu mashahuda,wai boko hauka ne?meyasa kuke nema kukoma koyi da yaren yahudawa ne?yaranku sun girma kuma ko wannensu idan aka masa aure zama zeyi to akan mene?ga Sauban nan dashi da taufeeq sun cika ko wannensu ba master's ne dashi ba? Galadima yayi maganar yana dubansu cike da nazari, Daddy yace"hakane Alhaji munaso ne dama munemi yaran idan anzo saka ranar su mashahuda kan maganar saka nasu ranar idan yaso komai yazo yanda kowa keso sai a hada bikin nasu rana daya ayi ko sadeeq?yayi maganar yana duban Abbie. Abbie yace"Ea yaya nima inaso nakira Ummien yaran ne nace sutaho gabadaya dama abinda yahanasu zuwa maganar jamb class dinda zuhura keyi ne so zankirasu zutaho nan din kawai.Galadima yace "gaskiya kuwa,anjima idan an idar da sallar la'asar inaso muje daku gabadaya mu duba jikin Laure ance tanata zazzabi tana kwance. Gabadaya suka amsa da insha Allah sannan suka miqe suka nufi masallaci gabadayansu harda Galadima. Zaune yake a dakinsa yana duba wani saqo a laptop dinsa da aka turo masa ta Email dinsa,wani company a qasar maleyshia taturo dashi kan suna son daukanshi aiki idan babu damuwa suna nemanshi Nanda 4days kan yazo za'ayi musu interview a cikin su goma Sha shida 'yan nan Nigeria. Sosai yaji dadin hakan aransa wanda inba kalura dakyau ba bazaka fahimci hakan ba, duk da fuskanshi takasance me tsananin kyau tamkar jinin larabawa,dama shidin jinin shuwaarab ne,miqewa yayi a fili yafurta"ALHAMDULILLAH,Masha Allahu laquwwatu illa billah,jallabiya wata blue black yadakko ta yasaka wacce tayi tsananin yimishi kyau yafita,kaitsaye masallacin dake layinsu ya nufa. Koda aka idar da sallah tare suka fito dasu Daddy,wajen Abbie yanufa fuskanshi dauke da murmushi duk cikansu da mamaki suke dubansa baba hasheem yace"A'ah Sauban yaushe Kuma kadawo garin?Abba yace"tambayeshi dai kam.Dariya yayi tare da dan rissiniwa yafara gaggaishesu, cike dajin dadi gabadayansu suke amsawa. Murmushi yayi wanda yasa dimple din gefen kumatunsa lobawa yace"Ai Ina ajesu kawai najuyo don banma shigo gida ba sai wajejen asubah. Galadima yace"kunji koh?kunji irin gangancin nasa Koh?inbanda kasada mezesa kadawo a wannan lokacin kamar Wanda ake kora? Abbie yace"Sadauki ba na hanaka tafiyar dare ba?ai wannan ganganci ne kadena sam baida amfani. Rissinawa yayi kadan yace"insha Allah za'a kiyaye. Shiga cikin gidan sukayi gabadaya inda su suka nufi farlon Galadima,domin muddin Abbie da Daddy na garin sun shigo to a farlon Galadima akecin abinci,shiko Sauban kaitsaye apertment dinsu yanufa. Da sallama yashiga cikin farlon hayaniya yaran dake farlon keyi Amma jin sallamar shi yasa farlon yakoma shiru inda banda sautin amsa sallamar da yayi bakajin komai, 'yan matan kuwa dake zaune ko wacce wayarta tasaqe suka fara boyewa. "Barka da shigowa Bro Sauban!!!abinda 'yan matan suka fara fada kenan,suko sauran yaran oyoyo suka nufoshi suna mai,sai sai suna qarisowa gabansa sukaja birki suna dariya don sunsan basu isa suyi hugging nashi ba donbshi mutum ne wanda befiye son daqunar yara ba. Murmushi yayi iya lebe tare da cewa"yawwa sannunku,ina Ammi take?nuna masa wani dogon corridor sukayi,yamike kenan da niyyar zuwa sai gata tafito. Da murmushi yatare ta yace"sweetheart,dan hugging nata yayi,hararar wasa ta aika masa dashi wacce da alama babbace don zatayo sa'a da Ummie. Murmushi yayi yace"Me Kuma nayi sweetheart?irin wannan harara haka?Ammi tace"Hmmm zaka sani Ina ganin sanda kashigo gidan nan,wallahi Sauban bakajin tsoro zaka sani ne,muje dinning kaci abinci. Dariya yayi tare da dan kamo shoulder dinta suka nufi hanyar kitchen suka shiga,babu wani jimawa ya Sauban ya fito hannunshi rike da plate biyu ya aje akan dinning yajuya baijima ba yafito riqe da ruwan gora cup,zama yayi kan dinning din yadubi inda 'yan matan suke yace"Mashahuda kije kitchen ki amsa abincin su Daddy kikai farlon Galadima,kekuma muneefa kizo kidauki na boddejo,da to suka amsa don kafin ma ya ida maganar suk sun miqe. Sallama akayi tare da shigowa,Kareem ne yashigo abokin ya Sauban da sauri yaran suka nufeshi suna Oyoyo bro Kareem,bude musu hannu yayi duka su ukun suka fada jikinshi,itakuwa inteey kaitsaye inda ya Sauban yake tanufo,ta wutsiyar ido yadubeta don yasan yarinyar mayyanshi ce duk abinda zai mata tananan kwafufe dashi,kusa dashi tazo ta tsaya tace"ouncle mommy na tace zaka siyomin hollandia idan kadawo tace koka manta natuna maka idan batazo daukana ba kai zaka maidani gida. Dago manyan idanuwansa yayi yana duban yarinyar don yana tsananin mamakin wayon yarinyar don inteey bata wuce 4 yrs ba,murmushi yayi mata yace"bby inteey kenan ainasan mekike nufi nikadai nake gane dama wannan yaren naki,dakko ta yayi yadorata a cinyarsa yafara feeding dinta,idan yayi 1 spoon itama yabata.Sarai yagane abincin zataci shiyasa ta bullo masa ta wannan surutun,Hakeem ne yakariso inda yake yana murmushi donshi mutum ne wanda sam murmushi baya gushewa a fuskarsa,yaron abokin Daddy ne sosai suke zumunci shiyasa yaransu ma Sauban da Hakeem suka dinki. Mikomai hannu Sauban yayi alamun musabaha yace"mutumin Ashe kadawo?shine ko kakirani?Koda yake nayifa lefi ne shiyasa sorry,yaqarisa maganar yana kunshe dariya. A daidai nan Ammi dasu muneefa suka fito kowacce hannunta riqe da basket sai dai na mashahuda sunfi yawa,kowacce doguwar riga ce ajikinta sai veil,gaishe da Kareem sukayi suka fice,Ammi kuwa dinning din tanufo ta zauna tana fadada murmushinta tace"a'ah Kareem kashigo gidan ne? "Aikuwa Ammi inayini munsameku lafiya? "Lafiya lou ya hajiya sakinan dasu bahijja? Lafiya Lou Ammi,dubanshi Ammi tayi tace"tashi kaje kitchen kasa abincin mana don yau mutumin ka akayi. Murmushi Kareem yayi yace"Ammi gurasa kikayi?Amma 'yan matanki suka miki koh? Saboda naga kinaji da kanki don ma Allah yasa Ammin namu macece jaruma,yaqarisa maganar cike da zolaya. Harara Sauban ya aika masa dashi donshi yana mamakin surutun Hakeem haka ko gajiya bayayi,shiga kitchen din Hakeem yayi ya hada gurasar sa yafito abinshi. Inteesar ta sauka jikin ya Sauban takoma wajen Kareem tunda sun cinye nasu don shi Kareem ne wanda baifiye cin abinci ba. Harara yabita dashi tana dariya ta falfala da gudu tabar farlon don sauran yaran dama sunfice sun nufi sashen Mom. A bangaren su mashahuda kuwa suna mikawa su Daddy abincin suka nufi sashen Mom bayan sun gama tsokanar Galadima,don bodejo batanan tana wajen guggo Laure don haka suna bude bedroom dinta suka ajiye mata. Shiga apartment din mom sukayi,mom na kitchen don haka kaitsaye kitchen din suka nufa, Mom sannu da gida,cike da fari'ah tajuyo tace"yawwa sannunku daga ina haka? Muneefa tace"abincin su Daddy muka kaimusu farlon Galadima dana Galadima. Mashahuda kuwa batasan sanda tayi subul da baka ba tace"kai gaskiya matar ya Sauban wallahi ta shiga uku dashi,da yasani ma aikin soja kawai yashiga,tab irin wannan mazurai haka? Dariya mom da muneefa tasaka tace"ai shiyasa bansan sanda nasaqe wayata ba gudun kada ayi sezing dinta. Mashahuda tace"Kuma wallahi kar yagammu kawai dai ya share ni yayi kakar be ganiba. Muneefa ta diddilo Ido cike da tsoro tace"wai dagaske?mashahuda tace"Allah gashi ko amso gurasar mu bamuyi ba,ai wallahi bazan koma ba sai yafita. "Nima bazani ba don nasan halinki sai ki'iya cewa _don Allah muneefa jeki amso Mana abincin_,babu inda zani ahto kadama kiqarisa. Dariya Mom tasaka tace"lallai ne big broo yacika big broo ai haka akeso. Su Daddy Koda suka gama cin abinci basu wani bata lokaci ba suka shiga motocinsu,kaitsaye gidan guggo Laure suka shiga,itama tanada dan nata rufin asirin sai dai ko kwatan kafar na Galadima da iyalensa baikai ba,baba hasheem ne ke driving nasu,gefenshi Abba ne,sai abaya Abbie, Daddy, Galadima. Fitowa sukayi sannan suka budema Galadima shima yafito tare da hadadden sandarsa mai matuqar kyau da tsada yafara dogarawa yana gaba suna biye dashi,maqota sun leqo sai kallansu akeyi. Wani yaro ne da alamu jikan guggo Lauren ne yashiga da gudu yana cewa tayi baqi,duka da cewa flat dinta daban sai na yaranta su biyu maza kowa da nashi flat din da Alhaji sani da Alhaji mansir. Shiga dakin sukayi bakunansu dauke da sallama, bodejo ce ta amsa tana zaune akan kujera,tsohuwa me shakaru sai dai dayake tanada kyan jiki ga kuma arziqi yasa tsufan yamata kyau,itakuwa guggo Laure sallah take Amma tsaban farin ciki ko lazimi bata idar ba tajuyo ta sallame sallar tace"Yaya muhammadu yau Kaine a gidannan?tayi maganar tana dariya, a'ah a'ah a'ah gaskiya naji dadi gaka gasu taleeb da Alhaji sadeeq maraban ku sannu da zuwa. Gaisheta su Daddy sukayi cike da dattaku da muntuntawa suka mata ya jiki,sannan aka shiga gaida bodejo wacce murna da dadi yakasheta a zaune ganin zaratan yaran nata. "Yaya muhammadu nace magana akan akilan kazo ayi koh?dama nace najika shiru ai wallahi da nasan zakazo da banbari yau taje bikin nan ba!Guggo Laure tayi maganar. Galadima yace"wacece kuma haka Laure?ninazo duba jikinki ne,tun sassafe yaronnan sani takirani kan bakijin dadi shiyasa ma bodejo tamatsa zatazo duk da itama ba dadin jikin nata takeyi ba. Guggo Laure tadan tamke fuska tace"a'ah Yaya kamanta ne yarinyar wajen mansir dana maka magana kan inaso a hada aurenta da Sauban ko don zumuncinmu yaqara karfi! Kallon kallo akafara tsakanin Daddy da Abbie da Abba da baba hasheem cike da mamaki,bodejo kuwa hangame baki tayi tana duban guggo Laure. _TOFA🤔 WATA SABUWA INJI DAN CACA,ANYA TSOHUWAN NAN BA RIGIMAMMIYAR TSOHUWA BACE?DA ALAMA GALADIMA DA IYALENSA BASUYI AMANNA DA WANNAN MAGANAR BA._ Xahratty Ce🥰 Lallai Alqalami 🖊️ yafi takobi🗡️ [3/21, 22:27] Xahratty (OUM AJMAL): 👨🏽‍🦳 *_GALADIMA FAMILY_*👨🏽‍🦳 Story&Written By *FATEEMA ZAHRA LAWAL* Marubuciyar⤵️ A DALILIN'YAR TSINTUWA. MIJIN ZAHRA. DIAMOND LADIES ( Daukar fansa)paid book. RUHIN AMRITA (FATALWA CE). Now *_GALADIMA FAMILY_* Page 03 _please idan kunga kurakurai na typing ba'ayi editing bane so kuyahakuri._🙏🏽 Gyaran murya Galadima yayi tare da duban guggo Laure yace"Laure kenan keda baki da lafiya wani magana ne za'ayi yanzu data wuce ta samun lafiyarki?nikinga su taleeb ko tuntubar su ma banyi da zancen ba a inda mukayi zancen anan nabarshi. Da mamaki sosai a fuskan guggo Laure take duban Galadima. "Au Yaya kana nufin zancen nawa ma bashi da darajar da za'ayi ta?nifa Yaya so nake mu karfafa zumuncinmu tunda bamu samu hadawa ta hanyar 'yaya ba sai muhada ta hanyar jikoki,idan kacire rabi datake aure da Aliyu(Abba) waye nahada ?wannan kuwa jininmu da tsokar mune zamu hada. Galadima cike dattaku irin na tsofaffin mutumci yace"Laure kibari kisake samun sauqi sai ayi maganar sannan muji ta bakin yaran idan sun amince da juna. Salati guggo Laure tasanya tana tafa hannu tace"Yaya muhammadu!kada dai ace yaran zamanin nan sunaso su maidaka kaima dan zamani?bodejo da takasa haquri tuntuni tace"aiko Laure yanzu zamani yazo ba'a ma yara auren dole,to shi saudan dinne yace muku baida wacce yakeso? Cike da takaici guggo Laure tace" A'ah Yaya bodejo ko Sauban nason Akeela ko baya sonta dole ya aure ta tunda 'yar uwanshi ne,murmushi bodejo tayi tace"A'ah Laure kice Allah kin tuba don babu wanda ya isa yama Saudan auren dole?wayayyan yaro yaron da yayi gogayya da turawa ne za'a ce za'a masa wani auren dole?bazaiyuwu ba ahto. Tayi maganar tana Ciro gutsiran goronta ta bangala. Fashewa da kuka guggo Laure tayi,cikin muryan kuka tafara magana. "Wallahi Yaya bodejo tuntuni na lura dama kinamun wani gani-gani sam bakison a hada zuri'ah da talakawa,yo menene Sauban zai nunama Akeela?kyau ko mene?wallahi babu Kuma Akeela wayayyar yarinya ce itama don samari da dama ruhubin ta sukeyi. Wani shewa bodejo tasaka tadubi guggo Laure Ido cikin Ido tace"Laure tunda hakane ta aure mana masu rububin nata daidai ita. Daddy ne yayi gyaran murya ganin guggo Laure ta harzuqa tana Shirin maida martani yace"guggo don Allah kiyahakuri,bodejo kema kiyi shiru insha Allah za'a zauna asamu lokaci ayi maganar. Guggo Laure tace"kada Allah yasama ayi taleeb dolene Sauban ya aure Akeela muddin munfito ciki guda da Yaya muhammadu!tana qare fadan haka takauda fuska gefe tana huhhura hanci,bodejo kuwa goranta take ta bangala tare da karkada kafafuwa. Abbie ne yayi ajiyar zuciya yace"insha Allah za'a ma bullowa lamuran komai zai daidaita. Cike da masifa guggo Laure tataso mishi kamar zata dakeshi tace"toh karere kayahakuri badakai ake magana ba tukuna, Kuma bamaga ake akan danka taufeeq ba. Da mamaki duk suka dago suna dubanta,bodejo ce tabude baki da niyyar magana Amma sai Galadima yakatseta ta hanyar fara magana"Laure kenan har yanzu rashin iya maganarki yananan,kinada shekaru sittin da wani abu kina shirin cika saba'in Amma ace baki iya kalamai masu dadi ba?ai abubakar yafi karfin karere tunda jinina ne nine nan nahaifeshi kuma Sauban danshi ne tunda dan Dan uwanshi ne kingako yafi karfin karere a ciki. Yayi maganar yana me miqewa tare da gyaran sandar sa,duk miqewa sukayi harda bodejo ta gyara mayafinta tace"ai kafata kafarfu don nima zan wuce Laure dai taji sauqi,tayi maganar tana aikama da guggo Laure harara,inda itama akaikaice ta rama sam bazakace su din tsofaffi ne ba. Duqawa su Daddy sukayi har qasa tare da mata sallama Kuma kowannensu sai da ya ajemata kudi, murmushi tafara tare da samusu albarka tana memikewa. Harara bodejo ta aika mata dashi a fili tace"daso samune kadama a amsa na karere,duk cikansu sun fahimci abinda bodejo ke nufi amma kowanne ya basar. Guggo Laure kuwa tace"ai dadin abin ma na 'yayan Dan uwa nane. Ko wanne a cikinsu dariya suka sanya banda bodejo wacce dama duk ta rigasu fita,sai da akazo tafiya ne sukaga cewa motar bazai ishesu ba duk da cewa ba wani girma ne dasu ba Amma ko babu komai zasu so mutumta iyayen su susakasu a wake guda,motan Alhaji sani ne tashigo farfajiyan gidan da sauri ya fito daga cikin motan cike da muntuntawa,domin Daddy da Abbie da Abba duk sun girme mishi. Kai tsaye wajensu yafito fuskansa dauke da tsantsar fari'ah,cike da ladabi yaduqa yana gaishe da bodejo da Galadima,sukuwa sauran mazan hannu yamiqa musu tare da musabaha yana dan tsokanar su abinka da abokan wasa. Duban Galadima da bodejo yayi yace"Kawo ku shigo na maidaku gida a cikin tawa motar.Haka kuwa akayi don Kai tsaye suka shiga motocin biyu suka nufi old maidugri don ba wani nisane dasu tsakaninsu da gidan direbi ba. A garin kaduna kuwa zuhra ce tsaye a bakin kofan shiga farlon nasu sai dai ta kakire a tsaye ita bata shiga ba kuma ita bata juyawa ba inda ka kalli fuskanta kuwa zaka sha mamakin irin mugun kallon da take watsama wanda ke tsaye a bakin kofar. "Please ya Aseef ka kama mutumcinka don ina ganin mutumcinka ba kuma zan iya maka rashin kunya ba Amma inaso kasani nisam ba irin watsattsun matan da kake tunani bane.Tayi maganar cike da fusata. Matsowa Aseef yayi inda take tare da fara lasan labba yace"zuhra kenan 'yar kakkyawan kanwata kina tunanin bansan irin sheqe ayar da kikeyi bane?duk gidannan anhanaki saka English wears Amma kinki ji,idan zakisa kisa na mutumci mana irin wanda su Laila ke sawa Amma kinasa abu jiki a dame kiyi tunanin ire-ire na bazamu bibiyeka? Wani dogon tsaki taja saboda yanda ranta yayi qololuwan back,wanda kuma yayi dai² da isowar Ummie wajen zata wuce. Da sauri Ummie ta juyo tana duban zuhra cike da mamaki tace"zuhra!Ashe dama rashin kunyar taki har takai haka?kidubi idon Aseef kiyimasa irin wannan tsakin?saboda yace yana sonki?so hauka ne da har haka zai baki damar yimasa rashin kunya?to bari kiji zaki sha wuya a cikin gidannan muddin bazaki dena rashin kunya ba. Kai kuma kada son da kake mata ya rufe maka Ido ka kasa hukunta ta ka zaneta to nonsense ni nasa,mara kunyan banza kawai.Taqarisa maganar tare da gyara zaman medical glass dinta tana wucewa apartment dinta kaitsaye. Wani kuka ne ya tahoma zuhra saboda tsananin takaici tarasa menene tayiwa Ummie take nuna mata irin wannan tsaanar sam bata jawota a jiki irin na uwa da da,anya kuwa Ummie ce tahaifeta?a ranta tayiwa kanta wannan tambayar. Shiko Aseef cike da murna yayi wani irin murmushin gefen lebe yajuya yanufi BQ nasu kaitsaye. A haka ya taufeep yashigo ya iske zuhra da sauri yayi parking din motar sa yafito tare da karisowa inda take,miqar da ita yayi yace"me akamiki zuhra ke da wanene?bude baki tayi da niyyar masa bayani Amma ina?tuni kuka yaci karfinta. Lallashinta yashiga yi har yasamo tayi shiru banda ajiyar zuciya babu abinda takeyi. Kaitsaye apertment din Ummie yanufa cikin disasshiyar murya zuhra tace"zanje bangaren mommy ne. Ya taufeeq yace"Ok muje,shiga farlon sukayi sallama dauke a bakin taufeeq,sun cidda mommy dasu Laila,gefe guda kuma ateek ne ke wasa shida maimoon,da gudu yaran suka taso suna hugging din zuhra da taufeeq,daga ateek ya taufeeq yayi sama yaron na qyalyqalewa da dariya. Jikin mommy zuhra tafada tare da kara fashewa da kuka,a hargitse mommy tafara tambaya"A'ah taufeeq meyasameta daga dawowan ta jamb class dinnan? Murmushi ya taufeeq yayi yace"shagwaba gurl! Mommy kenan nafa rarrashe ta tun a wake kafin munshigo dama nasan shagwaban nata akanki zai kare. Hararan wasa mommy ta wurga masa tace"Allah taufeeq ka kiyayeni me aka mata kuma? Yace"ai kinsan halin 'yar mulkin taki ko nima rarrashin ta nayi batare da nasan ko dawaye neba don na tambaye ta bata fadamun ba. Dariyar qasa² Laila tayi tace"ko dai ita da Ummie ne? Zuhra kuwa kaman antsikare ta tadago tafara zayyane ma mommy abinda yafaru a waje tanayi tana kuka tace"Kuma wallahi ya Aseef dinnan dan iska ne gwara na konawa na gidan Galadima saboda nagaji. Gabadaya dariya suka saka,nihal tace"chabdi saboda wani nabar gidan mu gaskiya I can't kema fah kamar harda rashin fahimta da yashiga tsakaninku kedashi. Mommy kuwa tace"tabbas nihal ninarasa gabadaya irin wannan abu haka tsakaninsu gaskiya taufeeq kayima Aseef magana matsayinka na wansa nisam banga amfanin hakan ba. Ya taufeeq tace"sudai suka sani ai idan ma bazasu dena ba sai aje wajen Ummie don itace zata bulloma lamarin. Zuhra ta zunburo mouth gaba tace"ni bazanje wajen Ummie ba,Ummien ma da goyon bayansa take ni kullum cikin lefi nayi mata,wallahi Abbie zai dawo shizan fadawa don ma wayana babu credit ne kuma bani da kudi a ccount dina bare na siya dana kirasa na fada masa. Ya kabani wayarka nakira shi kaji? Harara ya taufeeq ya zabga mata yace"ni?lallai yarinyar nan bada wayata ba,sai akace miki nima mara hankalin ne irinki koh?ga dai mommynki nan ki amsa tata...da sauri mommy tace"wah don Allah taufeeq ka rufamin asiri sai kuma akace bamu da tunani gabadaya? Dariya su Laila suka sanya,zuhra kuwa a fusace tamike tafita daga farlon. Gabadaya dariya suka bita dashi. Koda tashiga farlon su bata samu Ummie ba don haka kaitsaye bedroom dinta tashiga tare da fadawa akan kayataccen gadon ta tafashe da kuka,itasam takan rasa abinda ke mata dadi sam ita da gidan su da mahaifiyar ta araye amma kamar wacce take mara uwa(niko nace hmmm zuhra kenan nibanga abinda akai miki nakaman rashin uwa ba.) Xahratty Ce 🥰 Lallai Alqalami🖊️ yafi takobi🗡️ [3/21, 22:27] Xahratty (OUM AJMAL): 👨🏽‍🦳 *_GALADIMA FAMILY_*👨🏽‍🦳 Story&Written By *FATEEMA ZAHRA LAWAL* Marubuciyar⤵️ A DALILIN'YAR TSINTUWA. MIJIN ZAHRA. DIAMOND LADIES ( Daukar fansa)paid book. RUHIN AMRITA (FATALWA CE). Now *_GALADIMA FAMILY_* Page 04 _Bismillahir-rahmanir-raheem._ _____Haka zuhra takarisa tunane tunaneta tamiqe tashiga toilet ta dauro alwalan sallan magrib kaman yanda taji anata kiran sallar harma wasu masallatan sun tayar. Babu bata lokaci itama tazo tafara gabatar da sallan ta. Bayan sallar isha'i Sauban yasamu su Daddy a farfajiyar gidan don a ka'ida nan suke dawowa su cigaba da hira abinsu cike da qaunar juna,sallama yayi cike da mutumci irin na hadadden yaron tare da kamewa yaduqa yafara gaishesu. Suma cike da jin dadi suke amsawa saboda natsuwar Sauban da Kuma kamewarsa,wanda wannan dalilin ne yasa yakeda jama'a da dama a cikin family din nasu. Abba ya dubeshi yace"Sauban ya akayi ne?dan murmushi yayi tare da sake sunkuyar dakai yace"Abba dama sako ne dazu aka turomin daga can maleyshia kan suna son muje za'ayi mana interview mu goma Sha shida 'yan Nigeria,nanda 4days shine nace bari nazo nasanar daku. Ko wannensu cike da farin ciki Daddy yace"Masha Allah! Abbiel kuwa murna sosai kwance akan fuskar sa yace"Sadauki Masha Allah, congrats my son! na tayaka murna sosai,yayi maganar yana masa musabaha. Inda sabo Sauban yasaba da halin Abbie don tun yana yaro yake tare dashi,murna sosai sukayi. Daddy yace"ka fadama su Ammin naka? "A'ah Abba yanzu nakeso nashiga wajenta na fada mata sannan na fadama mom itama. Sake mishi fatan alkhairi sukayi,miqewa yayi cike da qasaita duk da cewa hakan halittarsa ce domin Sauban tsayayyen namiji ne a cike wanda dai² da maza ma 'yan uwansa yana musu kwarjini balle kuma mata. "Yanzu Sauban kasar maleyshia zakaje yin aikin?Koda Allah yasa hakan shine yafi zama alkhairi nidai abinda nakeso dakai kada ka kawomin wata 'yar qasan kacemin aurenta zakayi don magana ta gaskiya ba lamunce maka zanyi ba,don ga 'yan uwanka nan cike da dangi. Dan guntun murmushi yayi yace"sweetheart ko aikin ma ba'a samu ba kinfara kawo korafi? Ammi ta sake tsuke fuska tace"ai gaskiya ce na fada saboda nasanku ku maza shiyasa tun yanzu ma nake gaggawan taka maka birki kada naji ko nagani Koda kuwa andace ne. "Shikenan sweetheart hakama sam bazai faru ba gobe nakeso naje gidan Aunty falmata. Ammi tace"Allah yakaimu!da ameen Sauban ya amsa nan suka cigaba da hirarsu. Washegari da safe wajejen goma saura sai ga Guggo Laure itada Akeela,tsayawa nayi naqare mata kallo tasss,kyakkyawa ce sai dai ko kusa bata kamo kafar yaran gidan ba duk da cewa a ciki akwai qalilan da tafi kyau,sanye take da lutfaya baki mai ratsin jan flowers sai kafanta sanye da halfcover ja,hannunta riqe da handbag shima ja fara ce tass wanda a farin ma akedan karawa da man bleaching daga gani zatayi sa'a dasu mashahuda. Baba mansir mahaifin Akeela shine Guggo Laure tasa ya kawo su don baisamu shigowa gidan bane saboda ana jiransa ujila. Kaitsaye bangaren su bodejo suka nufa, Akeela kuwa tamkar bazata take kasa ba,Koda suka shiga sun cidda bodejo da Galadima,bodejo tana hada masa brabusko da miyar kuka Wanda yaji nama zallan tsoka daga bangaren Daddy aka kawo. "Assalamu alaikum!ga bakin sassafe fa. Guggo Laure tana fada fuskanta dauke da tsananin fari'ah saboda ganin motocin yaran gidan da alamu ma basu fitaba hakan ne yasata sake fari'arta. Galadima yace"Laure!kece a gidan?lallai jiki yayi sauqi sosai tunda gashi kin iya fitowa yayi maganar fuskansa kadaran kadahan. A inda Akeela take tsaye ta gaishesu ko rissinawa babu qiqam ta gaidasu. Cike da mamaki su bodejo ke duban ta, Galadima yace"ke haka akace miki mata na gaida mijinta?duqawa akeyi har qasa bawai atsaya a tsaye kerere ba kinji? Akeela ta wayance ta hanyar cewa"toh ai saboda bana auren tsoho irinka yasa na gaisheka a haka saboda kada tsohuwar matanka ta huramin hanci. Bodejo kuwa Sarai ta ganeta sai cewa tayi"to ai tunda kikama wannan angon haka babu irin angon da bazakiyi wa ba. Guggo Laure tace"musake gaisawa kundawo lafiya?ya gajiya Yaya bodejo? Bodejo tace"ai gajiya tabi jiki Laure Kuma marasa lafiya kun fito balle kumamu? Guggo Laure tace"wallahi fah kedai Bari jiya najuya yafi sau nawa? narasa gabadaya abinda kemun dadi a gidan duniya naqosa gari ya waye nazo saboda nace da zafi zafi ake bugun karfe shiyasa,tadubi Galadima tace"kada dai agaji dani akan kokari na nason aikata alkhairi. "Maganace dai akan yaran nan Akeela da Sauban shiyasa ma nace Akeelar tashirya tazo muje ayi komai a gabanta. "Shima kuma Sauban din ayi komai a gabansa. Cike da mamaki duk suke duban ta. Galadima kuwa abin duniya ne ma ya isheshi yayi dan murmushi irin nasu na manya yace"Laure kenan kekam akwaiki da wutan ciki, gashi yaran ba dukansu ne suke nan ba don shi sadeeq yau ya koma kaduna,shikuma Hasheem yaje ta'aziyyar amininshi da yarasu. Guggo Laure tace"toh nidai Yaya hakanan za'ayi hakuri ayi maganar nan yau a wuce wajen. "Yarinyar nan tana tsananin son Sauban,duk cikin jikoki na babu mafi soyuwa agareni kamar Akeela. Galadima yace"toh shikenan bari nakira taleeb din,hannunsa yakai gefen lumtsememen leaderseat dinda yake zauna yadakko wayarsa kirar sumsung yafara nemo number,baiwani dau lokaci ba yakira har takatse ba'a daga ba,ko kafin yasake danna kiran,Kira yashigo wayan nasa. Dauka yayi tare da sallama,daga can bangaren Daddy yagaishe shi,amsawa yayi kaitsaye yace"inason ganinku kai da Aliyu idan anyi sallar azahar,daga can bangaren aka amsa da toh insha Allah,sannan Galadima yakatse wayan. Guggo Laure kuwa murna takeyi kamar yakasheta,dakin da take sauka wanda aka mata nan tanufa harzata shiga sai Kuma tajuyo tace"ke Akeela zo muje mugaisa da matan gidan tukuna koh? Akeela kuwa farin ciki takeyi kamar anmata kyautan hajji,aranta kuwa fadi take itace zata mallaki Sauban jinin GALADIMA FAMILY?tabbas tayi sa'a,don Sauban namiji ne wanda da dama mata ke bibiyan sa,don ko a yanar gizo maganar sa mata keyi namiji ne mai tsadan gaske. Kai tsaye apartment and Ammi Guggo Laure tashiga,sallama tayi itama Akeela tayi cike da kissa. Su mashahuda ne a farlon,hada idon da muneefa zatayi aiko tamike da gudu tanufi Akeela tace"Kai lallai ma Akeela yau kece a gidannan haka? Akeela ta watsa idanuwa tace"aiko gani ai muneefa bakida kirki ko Guggo bakizuwa gaishewa. Mashahuda ta dubi Guggo cike da mutumtawa ta gaisheta,inda kallo daya tama Akeela ta watsar don sam ita Akeela bata burgers barin yanda take ganin tanasa pic dinta a Instagram na shirme. Muneefa tace"Tabb yaushe zaki ganmu so kike ya Sauban ya babballamu?dariya sukayi. Kujera Guggo Laure tazauna, Akeela da muneefa kuwa daki suka shige inda mashahuda tashiga kitchen don kiran Ammi,Ammi bata zama duk da masu aiki suke aiki Amma girkin mijinta ita takeyi tunda yanada suger,masu aiki kuma suyi na gida gabadaya ko da ita bata dauki wata mai aiki tayiwa mijinta girki ba. Mashahuda bajima ba tafito kitchen hannunta dauke da tray inda ruwa kekai da lemo. Ammi ce tafito fuskanta dauke da murmushi tace"Guggo ce a gidan? Guggo ta amsa fuskar ta dai kadaran kadahan tace"yauwa sannu Aisha nice. Ammi tace"inayini Guggo,kunzo lafiya? Guggo Laure tace"lafiya lou,munsameku lafiya? Ammi tace"lafiya ALHAMDULILLAH ya karfin jiki?jiya zamuzo da Rabi sai mazan sukaci mubari suje mu mazo yau Ashe jikin ma yayi sauqi? Guggo tace"jiki Alhamdulillah sai dai tasowar na dole nayi saboda mahimmiyar maganar dake tafe dani. Ammi tace"Allah sarki sannu da zuwa. "Yawwa Aisha,inasu Yaya na muhammadu? Murmushi Ammi tayi tace"Sauban yana dakinsa anata shirye²n tafiya Malaysia. Guggo cike dason jin Karin bayani tace"mekuma zaije yi can? Mumushi ammi tayi tace"zaije interview ne idan da rabon yasamu aiki a wani company a can ne toh. Cike da farin ciki har zuciyar Guggo Laure ta yashe baki tace"Alhamdulillah Allah mungode maka,a zuciya Guggo Laure tace"(ya ubangiji Allah yakai damu ga harawa,lallai Akeela duniya sabuwa,duniya nakine.) Allah yabada sa'a ubangiji yadorashi bisa kawunansu. Da Ameen Ammi ta amsa. Nan Guggo tamike tamata sallama kai tsaye sasan Mom tanufa. Mom taji dadin ganin Guggo don ko babu komai da mijin Guggo da baban Mom uwa daya uban daya,anan suka gaisa Guggo tace"gaskiya Rabi bakida kirki yanzu kiri² dan naman nan ma kindena aikomin dashi sai dai kikaiwa hajiya habi?haka amana yace? Dama ana saka alheri da mugunta?a fakaice mom ta watsama Guggo Laure harara,a zabiri kuwa dan marairaice fuska tayi tace"toh yazanyi Guggo?kiri² baban Aseef ba siyowa yakeyi ba sai lokaci zuwa lokaci,nima kaina baya isata balle nabaiwa wani. Guggo Laure ta kama baki tace"Oh a haka Hasheem sumumi sumumi Amma duk Wanda yaganku yaganku cikin hutu don ke tunda kika shugo cikin a halinmu zaka sheda. Mom tayi dariya tace"gaskiya ne Guggo,amma bajiya akace bakijin dadi ba? Guggo Laure tace"hmmm aikedai bari ai tafiyar nan ta dole nakeyinta,nan Guggo Laure tazauna tabawa Mom labarin duk wani qudurinta kaf nason hada auren Sauban da Akeela. Kirjin Mom ne yayi wani irin mummunan bugawa hankalinta yayi qololuwan tashi,a diririce Mom tace"Guggo wani Sauban din? Harara Guggo Laure ta maka mata tace"Sauban nawa ne a gidannan?to dan uwanta mana nake nufi. Guggo tace"Bari naje rabi yanzu zakiji ankira azahar. Gabadaya har Guggo Laure tagama maganarta tabar farlon Mom bataji ba sai da taji karar rufe kofa tajuyo a hautsine. Mikewa tayi cikin gigita da rudewa tace"Inah? Sauban da Akeela?wallahi bazai yuwuba bazan taba bari Sauban ya auri Akeela ba. Duk irin son da Rammat takeyi masa ana nufin zaitashi abanza ne?wallahi bazai yuwu ba,qanwata Ina ganin yanda takeson Sauban kamar zata rasa ransa,Rana tsaka azo da maganar wata shegiya Akeela?wallahi bazai yuwu ba,Ina wayata? Tayi maganar tare da nufan hanyar wani corridor cikin gigita. _TIRQASHI ANA WATA GA WATA._ _MEKE SHIRIN FARUWA NE?ME MOM TAKE NUFI?DUK WANNAN ABINDA AKEYI SHI ME GAYYA ME AIKIN MA BESAN ANAYI BA,KUDAI KU KASANCE DA ALQALAMIN ÕÙM ÃJMÃL🖊️_ Xahratty Ce🥰 Lallai Alqalami🖊️ yafi takobi 🗡️ 12/2/2023. [3/21, 22:27] Xahratty (OUM AJMAL): 👨🏽‍🦳 *_GALADIMA FAMILY_*👨🏽‍🦳 Story&Written By *FATEEMA ZAHRA LAWAL* Marubuciyar⤵️ A DALILIN'YAR TSINTUWA. MIJIN ZAHRA. DIAMOND LADIES ( Daukar fansa)paid book. RUHIN AMRITA (FATALWA CE). Now *_GALADIMA FAMILY_* Page 05 _Bismillahir-rahmanir-raheem._ _______A tsananin rikice mom take shiyasa koda tashiga cikin bedroom dinta sam hankalin ta baikai wajen phone nata ba,fita tayi daga bedroom din tanufi wani corridor wanda kaitsaye ya sadata da parlon Abba,neman wayar tashiga yi sai dai duk iya neman da tayi bata gani ba ( _Nikoh nace su hajiya mom manya tsaban rudewa a bedroom dinki kika bar wayan😆_ ). Dan siririn tsaki taja tare da fita tanufi bedroom dinta dai,gabadaya ta hargitsa dakin bata gani ba,banda numfarfashi babu abinda takeyi cikin sa'a kuwa idanuwanta suka sauka akan bedside drower dinta,sake watso idanuwa tayi cike da tsananin mamaki,mikewa tayi ta dakko wayar tare da komawa tazauna a bakin gadon hannunta har rawa yakeyi wajen dialing number Rammat,ganin andauka ne yasa Mom kara wayar a kunne bakinta na rawa tace"Hello Rammat kina jina ne?kina gida? Daga can bangaren akace Eah, Mom ta cigaba da cewa"kiyi maza maza kizo inason ganinki yanzu fah,still dai da toh aka amsa mata. Katse kirar tayi inda tafara safa da marwa a cikin dakin. A bangaren su Guggo Laure kuwa bayan sallar azahar duk suka hallara a parlon na Galadima, Galadima,bodejo, Daddy,baba hasheem. Guggo Laure tace"Yaya ayi maganar da za'ayi don Allah saboda nisam bansan sharrin shedanu. Dan murmushi Galadima yayi yace"Laure kenan bari akira yaran duk aji ta bakunan su. Duban Daddy yayi yace"taleeb lalubomin Sauban a wayarsa daganan kace masa su taho da mashahuda.Da toh Daddy ya amsa sannan yafara neman Sauban a wayarsa. Cikin kankanin lokaci kuwa ya dauka inda Daddy yasanar masa da saqon Galadima. Ba'a dau lokaci ba yayi sallama mashahuda na biye da ita,duqawa sukayi cike da mutumtawa suna sake gaishesu,nan Baba Hasheem yadubi mashahuda yace"takira masa Akeela daganan tawuce,amsawa tayi da toh tare da miqewa. Basu wani jima ba itama tashigo sai wani sake karairaya take tamkar iccen da yake gaf da karyewa,samun gefen kafar Guggo Laure tayi ta zauna sannan tafara gaida su Daddy. Gyaran murya Galadima yayi yafara magana. "Toh Alhamdulillah Muhammad wannan taron da akayi akanku kune kai da kanwar ka Akeela gatanan!yayi maganar yana pointing din Akeela,yaci gaba"Toh 'yar uwata Kuma kanwata kakanka Laure gatanan tanaso musake danqon zumuncin mu ta hanyar hada auratayya tsakaninka da Akeela. Da sauri Sauban yadago tare da duban Galadima. "Ita kuma yarinya tana sonka shine nace kaima munason muji ta bakinka kana sonta kokuwa? Sauban mutum ne wanda sam baida boye² kaitsaye yake magana don watarana su Daddy har takaicin hakan sukeyi,bude baki yayi da sauri yace"wallahi Galadima bana sonta,nisam bata cikin jerin matan danake son na aura don haka ku bata haquri,saboda sam bana fatan abinda zai taba mana zumuncin m...... Ko kafin Sauban ya ida abinda zai fada Guggo Laure tafashe da kuka cikin tsananin fusata ta dubi Sauban tace"Baka Isa ba,baka isa ba muhammadu!ubanka Taleeb ma bai isaba balle kai karan kada miya,nikuke so ku watsama kasa a ido?mene nayi muku?lefi ne don Akeela nason ka? Akeela jininka ce kuma 'yar uwanka. "Ko babu komai so muke muqara danqon zumuntan mu. Sauban dafa kai yayi zuciyar sa na tsananin bugawa don har ransa shi baya son hadin zumunta. Cike da bacin rai bodejo tace"dakata don Allah Laure,wani zumunci kike maganar za'a gyara?a gyara ko a bata?yaro yafito yafada ra'ayinshi kuma a neme a tilasta sa,wallahi bazan lamunci cin kashin kowa ba a yanzu wannan son zuciyar taku tafara isatal! Tayi maganar tare da watsa ma kowa kallon banza harda Galadima ( _Omg🤔_ ) Mikewa Guggo Laure tayi cike da jin haushin bodejo tace"lallai ma Yaya bodejo sannu me jika kenan Akeela ba jikar ki bace sai Sauban?yanzu niba zan iya neman alfarman wani a gidan nan ayimun abu baaa?takarisa maganar tare da fashewa da kuka mai tsanani tamkar ba tsohuwa ba,gabadaya hankalin su yatashi idan kacire bodejo da Sauban. Bodejo tace"Laure nice bansan makircin ki ba?kukan d..... "Ya isa don Allah kubar maganar haka, Galadima ya katse bodejo. Wani kololuwan takaici bodejo taji a zafafe tanufi hanyar kofar parlon Galadima don fita,daga murya Galadima yayi yakira bodejo. Sai dai ko waiwaye batayi ba balle asa ran tsayawar ta. Jinjina kai Galadima yayi saboda hankalinsa yatashi,ransa Kuma yabaci,a zafafe ya daka ma Guggo Laure tsawa akan kukan da takeyi tamkar ba tsohuwa ba( _Koda aidama tsoho akwai rikici,sai dai guggo Laure macece see shu'uma._ ) Daddy ne yayi gyaran murya sannan ya dubi Guggo Laure yace"Am Guggo don Allah kiyahakuri kiyi shiru haka za'a San abinyi yanzu kuji gida insha Allah zakiji alkhairi. Galadima yace"Laure meyasa kikeso kibata zumunci gabadaya? Sakin baki Guggo Laure tayi tana duban Galadima,aituni zuciyar ta yayi mata wani fassaran saba. "Yaya! Saboda inason karfafa zumuncinmu shine zakace inaso na lalata?meyasa bodejo batason jinina? kuyahakuri insha Allah bazan sake maganar Akeela da Sauban ba,sai dai na haqura dakai da ahalin ka Yaya,don bazan zauna da wadanda basason jinina ba. Gabadaya a firgice suka dago suna duban Guggo Laure,dayake Galadima Sarai yasan halinta. Mikewa tayi a zafafe tacema Akeela" ki mike mutafi. Fuuuu kuwa suka kama hanya suka fita. " _Innalillahi wa Inna ilaihirraji'un! Allahumma ajirni fi musibati wa'aklifni khairan minha_. Kalmar da Daddy yafada kenan tare da duban Sauban. "Yanzu Galadima ya za'ayi a shawo kan wannan matsalar? matsala cefa wacce idan ba'a ma tufkar hanci ba to zai iya taba zumuncinmu da Guggo Laure. Jinjina kai Galadima yayi"Hasheem narasa ma mezamuyi,daga bodejo har Lauren kaf sun dauki zafi yakamata ace daya a cikinsu ya sauko,duban Sauban Galadima yayi yace"muhammadu Kaine sanadin wannan rikicin don haka kai zaka gyara. Sauban ya sauke wani nannauyan ajiyar zuciya don shi mutum ne mara son hayaniya yace"Galadima bana son ta Allah ma yasani kuma. "Keep quite Sauban! Daddy yafada cikin bacin rai. Bakaga abinda ke faruwa bane?meye yashiga kanka?kasan kuwa wacece Guggo Laure?kakuma son me ake nufi da zumunci?hmmm katashi kabamu waje,don mune muka haifeka bakai ne ka haife muba,kaje duk hukuncin da muka yanke zakaji. Mikewa Sauban yayi tare da rissinawa yace"Allah yahuci zuciyarku nabarku lafiya,yana gama fadar haka yajuya cike da mazantaka da salon tafiyarsa mai burge duk Wanda ke kallo yafita. Baba Hasheem yace"gaskiya Yaya kada kashiga haqqin Sauban. "Don Allah Hasheem kadena wannan maganar bana fatan abinda zai bata sunan GALADIMA FAMILY,kakira su Sadeeq a waya akwai meeting ranar Friday insha Allah,mukuma kafin lokacin mungama magana da bodejo don shawo kanta. Gabadaya jinjina kai sukayi, Galadima kuwa sosai yaji dadi don matansa da kanwar tasa sun gwara mishi kai. *KADUNA JABI ROAD* Gabadayansu zaune suke akan dinning din suna dinner cike da farin ciki zuhra tace"Abbie nayi missing dinka sosai. Murmushi Abbie yayi yace"nima nayi missing dinki mama na ya gida ya shirye²n jamb kuma? Zuhra tace"alhamdulillah munanan munayi. "Toh alhamdulillah agama cin abinci sai muje parlona inji wani jami'a kika cike a slip din jamb din. Dariya sosai zuhra tayi tace"toh shikenan Abbie. Ummie kuwa tsaban takaici jitayi tamkar tayi Aman wuta 😡 saboda bacin rai. ( _Ko na menene oho._ ) Basu jimaba suka kammala,duk suka hallara a parlon Abbie, Taufeeq, Laila, Aseef, Nihal, ZUHRA. "Abbie nafiso nayi Dan fodio don haka shinasa. Murmushi Abbie yayi irin nasu na manya yace"meyasa bakisa ABU Zaria ba ko Kuma KASU mamana? Dan Jim zuhra tayi sai Kuma tace"Abbie banason ABU nikam,kuma abinda yasa banason KASU afa kaduna nayi nursery, primary, secondary, shiyasa nakeson nacanza gari Amma nafison Danfodio Abbie. "Bakiga duka 'yan uwanki ba suna ABU?ga kuma yayanku Aseef,inaganin zakisamu kulawa sosai sannan zakiji dadi. Dan rau rau zuhra tayi da ido dama ita abin kuka baya mata kadan muryan ta na dan rawa tace"please Abbie nikam banason ABU don Allah. Laila tace"Abbie wallahi kada abari tayi Danfodio tazo ABU zataji dadi fa,takarisa maganar tana dariya kasa² Cikin barkwanci ya Taufeeq yace"wallahi Abbie yarinyar nan tana mana bakin cikin dan jellof rice dinda zata dinga mana ne. Gabadaya dariya aka Sanya,nihal tace"da dan sululu Koh Yaya?aka Kuma sa dariya. Ya Aseef yace"Abbie aiba sai abinda takeso za'a biba dole umarnin iyaye zatabi ko 'yar jarida. A kaikace zuhra ta dalla masa harara. Fira sukayi sosai da Abbie kafin kuma kowa yawatse yaje kwanciya bacci. *OLD MAIDUGRI* "Aunty wai don Allah dagaske kikeyi?inafa son sa wallahi bazanyi fatan Sauban ya kubucemun ba,idan nashigo zura'ar GALADIMA FAMILY wallahi cele zan sake zama a wajen kawaye na da abokaina. Wacce tayi maganar bazata gaza 27 yrs ba. Mom tace"Rammat kenan nafiki son shigo cikin wannan family din don arziqi yaci uban nada kinsan kuwa waye Sauban?hmmm awajen dangin Aisha kawai idan kikaga gatan da Sauban ke samu sai kin gigice, Rammat da arziqi agidan wasu gwara a gidanku a gidanku ma a dakinku,hmmm wai Akeela. Wani tsanar Akeela Rammat taji har cikin ranta saboda tsananin son da takewa Sauban. "Aunty nidai gaskiya asanar ma da Mama halin da ake ciki don ni babu dalilin da zaisa nayi zaman kishi da Akeela ( _Sauban kaga takanka,tun yanzu anfara maganar zaman kishi a dalilinka._ ) Mom tace"Ea zanje bari ko zuwa anjima idan su Yaya (Daddy) sun fita sallar la'asar sai mufita don kinsan dokar gidan nan namu. "Gaskiya kuwa Aunty don da zafi² ake bugun karfe. A gidan Guggo Laure kuwa banda kuka babu p abinda Akeela takeyi gabadaya ta tadarma jama'ar gidan da hankali, Guggo Laure kuwa sai girgiza kafa takeyi. Xahratty CE (ÕÙM ÃJMÃL )🥰 Lallai Alqalami🖊️yafi takobi🗡️ 15/2/2023 [3/21, 22:27] Xahratty (OUM AJMAL): 👨🏽‍🦳 *_GALADIMA FAMILY_*👨🏽‍🦳 Story&Written By *FATEEMA ZAHRA LAWAL* Marubuciyar⤵️ A DALILIN'YAR TSINTUWA. MIJIN ZAHRA. DIAMOND LADIES ( Daukar fansa)paid book. RUHIN AMRITA (FATALWA CE). Now *_GALADIMA FAMILY_* Page 06 _Bismillahir-rahmanir-raheem._ *NAGA SAKO NAGODE SOSAI MY SOFY ALLAH YASAKA DA ALKHAIRI UBANGIJI YAKARA RUFA ASIRI DUNIYA DA LAHIRA😊ALLAH YAKARA GIRMA ACEMA OGA SAUBAN MUNA GODIYA TARE DA AJMAL🙏🏽🙏🏽🙏🏽* https://www.facebook.com/profile.php?id=100074816894956 Guggo Laure tace"Haba Akeela meyasa kikeso tayarmin da hankali ne?nace miki indai ina raye Sauban mijinki insha Allah idan Kinga baki aure Sauban ba ki tabbaci hakikan bana numfashi ne. "Wai Guggo meke faruwa ne?tundazu kunshigo gabadaya Akeela tahana kowa sukuni a cikin gidannan,har yanzu bazata dena tabara ba kamar wata karamar yarinya?shekara ashirin da biyar Amma ace har yanzu mutum bai girma ba wallahi waje tasamu. Harara Guggo Laure ta aika mata dashi tare da watsa yatsu tace"Maimuna kinsan Allah kikiyaye ni kifita idona,to ina ruwan wani kokuwa nina nemi wani yazo?inbanda munafunci da tsugudidi meyakawo ku? Guggo Laure tayi maganar tare da watsama mama hajiya zainab harara matan baba sani,ganin hakan yasa sumi² tajuya tabar wajen. "Guggo kada fa kimanta tun Akeela na qarama mujaheed kesonta wallahi idan akayi haka ba'a ma Yaya sani da Aunty zainab karaba. "Maimuna kinsan Allah zan batamiki a gidan nan,ina ruwanki?ko kinfini son Akeela da mujaheed ne?duk son da mujaheed kema Akeela tunda ita batason shi aiduk zance ne. Banga dalilin da zaisa ayi abinda za'a zo ana danasani ba,kinga kiwuce kiban waje. Cike da bacin rai mahaifiyar Akeela ta wuce flat dinta tare da matsananciyar bacin rai. Da daddare kuwa Guggo Laure tasa aka kiramata Alhaji Sani da Alhaji Mansir nan tazauna taratsa su tare da shirya musu karya wai Galadima ya nemeta akan yanaso a hada Akeela da Sauban aure. Sosai sukayi murna duk da cewa sunsan maganar mujaheed da Akeela, Alhaji Mansir yace"Amma hajiya kinmanta da maganar mujaheed da Akeela ne? Cikin sauri Alhaji Sani ya katseshi. "Haba Mansir meyasa kake hakane?neman alfarma fa wan mahaifiyar mu yayi kan yanaso a hada jikinsa da jikanta aure,ba Kuma don komai ba sai don karfafa zumuncinsu to mezesa ayi haka? Guggo Laure tace"Hmm rabu dashi Sani kaji,nan dai ta sallamesu. Akwana a tashi babu wuya inda Allah yakawo mu yau Friday,gabadaya family din Galadima suna MAIDUGRI idan kacire matan Adda Labeeba da Adda Maryam. Abbie yazo tare da kaf iyalensa,haka kuma Mommy ma sunzo dama da Abbie da Abba ne suke zaune a kd. Zaune suke a parlon Galadima gabadayansu,bodejo, Daddy,Abbie, Abba,Baba Hasheem. "Alhaji kunason shiga hakkin saudan da yawa,yanzu fa lokaci ne na kowani dan Adam nada 'yancin kansa Amma tunda kun rijayene shikenan Allah yasa hakan shiyafi zama alheri Amma sam ba'a yimana adalci ba,tayi maganar tana sake tsuke fuska. Duk cikansu sauke nannauyan ajiyar zuciya sukayi,domin da bodejo bata amince ba to tabbas da akwai gagarumar matsala kuwa. Murmushi ne ko wanne akan fuskansa, Galadima cike da jin dadi yace"Allah yayi miki albarka fadimatu. Da Ameen su Daddy duk suka amsa. Bodejo ta qanqantar da idanuwa tace"wallahi an shiga hakkina ba kadan ba saboda ni tuni Sauban na zaba masa matar aure,amma babu komai in matan shi ne nan gaba Allah yabashi. Su Daddy suka sake amsawa da Ameen,duk da kuwa kowa yaso jin Karin bayani a wajen bodejo Amma gudun maido da hannun agogo baya yasa sai suka haqura. Anan aka tsaida magana inda Galadima yayanke shawarar da kanshi zaije yawa kanwar sa wannan albishir din. Tabe baki bodejo tayi tare da mikewa ta gyara zaninta tawuce ko sallama batayi musu ba. Abba ne yasauke ajiyar zuciya yace"Yaya taya zamu sanar da Sauban wannan batun?kaga yaron nan yanuna bayason wannan abin tunfarko. Daddy yace"yakuwa zaiyi auren biyayya shine abinda zaiyi ko kuwa Sadeeq? Abbie Wanda koda yaushe fuskansa baya rabo da murmushi yace"Allah yasa hakan shine abinda yafi alkhairi. Sunji dadin addu'ansa. Nan suka kammala tattaunawan su sannan suka miqe. Zuhra ce kwance akan kujeran Ammi ta lumshe idanuwanta saboda tsananin ciwon da kanta ke mata,sosai jikinta yadauki zafi alamar zazzabi nason saukar mata. Yaran gidan gabadaya suna wajen Ummie don Ummie macece meson yara sai dai tsakaninta da zuhra sai a hankali. Ammi ce tafito daga kitchen hannunta rike da wani plate tayo inda zuhra ke kwance,zama tayi a gefenta sannan tadauki kanta tadora akan cinyar zuhra. "Subhanallah zuhra ai ba ciwon kai kadaine ke damunki ba ga zazzabi nan a jikinki, tashi kisha wannan fruit salad din. Batare da tayi musu ba tamike,wani irin Sara mata kan yayi da qarfi,hannu takai tare da kama kan,jijiyoyin kan sun firfito. Sake rikicewa Ammi tayi domin sosai Allah yadora mata son zuhra tun sanda Ummie ta haifeta tare da wani burinta akan zuhran. Sanyayyan muryanta tabude a hankali,muryan inbanda rawa babu abinda yakeyi tace"Ammi ki Kama mun kaina inajin kamar zai fashe. Kama mata kan Ammi tayi tafara yimata addu'o'i a hankali wani wahalallen bacci yayi awon gaba da ita. Ajiyan zuciya Ammi ta sauke tare dajin wani tausayin zuhran a ranta. Samun gefen ta tayi ta zauna tana duban kofar parlo tare da amsa sallamar da akayi. Kareem ne yashigo fuskar sa dauke da murmushi dama shi mutum ne wanda baya rabo da murmushi. "Barka da gida Ammi,yafada tare da rissiniwa. Cike da fari'ah Ammi tace"A'ah Kareem har kadawo daga airport din? Kareem yace"Ea Ammi nadawo don sai da natsaya ma har jirginsu yatashi sannan nataho. "Allah sarki Allah YAKARA muku dankon zumuncin nan naku da kaunar juna Kareem anfa gode,angode sosai. Dariya Kareem yayi yace"Haba Ammi tsakani na da Sadauki ai babu haka, bari naje gida hajiya tanata kirana. Ammi tace"tohm Allah yayi albarka ka gaisheta,kace inanan zuwa,anfa gode. Fita yayi tare da satan kallon inda zuhra ke kwance,duk da yaso yaga fuskanta Amma Allah baibashi sa'a ba. Da daddare yaran gidan duk suna sashin bodejo harda zuhra. Bodejo tadubi zuhra tare da kyabe baki tace"waike yarinyar nan lafiyanki?tundazu kiketa yatsina ko bakijij dadi ne? Shiru zuhra tayi tare da sake lumshe idanuwanta. "Yarinyar nan haryanzu wannan shegen miskilancin naki yananan,nidai keda saudan bansan wanda yafi wani wajen miskilanci ba. Gabadaya yaran parlon suka sanya dariya,maimoon tace. "Bodejo bafa saudan ba, Yaya Sauban. Bodejo tace"Toh uwar feleke,ni ina ruwa na,haka na iya haka kuma zan fada. Murmushi Galadima yayi yace"zuhra zo nan kinji. Mikewa zuhra tayi a hankali kamar wacce kwai ya fashe ma a ciki ta nufi inda Galadima yake ta zauna a gefensa tace"granny mezaka bani na dadi. Duban Laila Galadima yayi. "Zonan Laila,jeki kitchen din bodejo saman fridge dinta zakiga bakar leda ki daukomin. Zuhra batasan sanda wani murmushi ya subuce mata ba jin amfani hakar leda. Daga murya Galadima yayi yace"ki kuma zo da plate guda biyu.Da toh Laila ta amsa. Tuni yaran parlon suka fara murna. Laila batajima ba tafito hannunta da wani dan leda baqa medan girma,tare da plates uku babba guda da madaidaita biyu,akan babban plates din tadora ledan. Galadima yace"hajiya bodejo azo akasa abawa kowa nashi. Bodejo takama baki tace"wa? Ai idan zuhra na waje bodejo bata tasiri ga tagaban goshi? Murmushi Galadima yayi yace"Toh ko nihal ta raba ne?nihal zoki raba mana. Tasowa nihal tayi aiko ta raba kashi uku kamar yanda Galadima yace tayi,shida bodejo kashi daya itada da Laila da zuhra Kashi daya sai su maimoon ma kashi daya. "Allah yasaka da alkhairi granny ubangiji yaqara budi, Allah yaqara daukaka GALADIMA FAMILY,zuhra tayi addu'an cikin muryanta mai sanyi. Da Ameen su Laila suka amsa. Sosai Galadima da bodejo sukaji dadin addu'an na zuhra,wanda a kullum suna yabawa da hankalinta. _SU WAYE GALADIMA FAMILY?_ Cikakken sunansa Muhammad Taleeb Muhammad haifaffen garin MAIDUGRI sai dai mahaifiyar sa ce 'yar nan wacce take shuwaarab,shi kuwa mahaifinsa buzaye ne irin masu tashin nan,adalilin haka Allah yakawo mahaifinsa da mahaifiyar sa garin MAIDUGRI inda wata rana suna kwance da daddare wata takama Wanda ba'asan daga inda wutar yafito ba. Mutane suka fara kawo dauki,a lokacin Muhammad nada shekara a duniya,atake anan Allah yayiwa mahaifinsa rasuwa garin ganin ya cece matansa da dansa maisuna Muhammad,don sosai yayi wani irin mummunan kuna,mahaifiyar Muhammad kuwa itama kokari take takare Muhammad tare da abinda ke cikinta. Asibiti aka kai mahaifiyar Muhammad,inda likitoci suka dukufa akanta,koda suka duba sai sukaga cikinta yana watan haihuwa ne babu bata lokaci suka yanke hukuncin ciro abinda ke cikinta,suna shirye²n yimata aikin ne Allah yadau rayuwanta,ganin haka yasa suka hanzarta yimata aikin. Aiko suka Ciro yarinya kyakkyawa mace, Muhammad kuwa sai kuka yakeyi,nan suka tattara akayi abubuwan da za'ayi aka amsa gawar Muhammad. A lokacin hakimin garin shine kakan bodejo don haka shine yayi komai,suka koma suka sallaci gawa biyu,babu bata lokaci hakimi da sauran dattawan anguwa suka yanke hukuncin baiwa hakimi su Muhammad,inda shi kuma hakimi yadamqasu a hannun danshi tilo namiji Harun mahaifin bodejo. A lokacin bodejo nada shekara bakwai mahaifiyar ta daga kanta bata sake haihuwa ba Allah yamata rasuwa,a lokacin matan baban bodejo na aure da kanin bodejo yakub sai aka bata jaririyar ta hadasu tana shayar dasu. Kamar yanda al'ada yazo ranar suna aka radama yarinya suna Lauratu inda mutane ke kiranta da Laure,sosai mahaifin bodejo da kakanta suka bawa su Muhammad gata,hakimi yasa aka tattaro masa raquman su Muhammad guda goma Sha biyar yabawa wani abokinsa dake cikin gari ajiyansu ana cigaba da kula dasu. A haka dai rayuwa ta cigaba da tafiya har akasa Muhammad a makaranta inda shakuwa mai karfi tashiga tsakaninshi da bodejo,a gefe guda kuma hakimi na cigaba da kula mishi da dukiyanshi shida mahaifin bodejo. Xahratty CE🥰 Lallai Alqalami🖊️yafi takobi🗡️ 16/2/23. [3/21, 22:27] Xahratty (OUM AJMAL): 👨🏽‍🦳 *_GALADIMA FAMILY_*👨🏽‍🦳 Story&Written By *FATEEMA ZAHRA LAWAL* Marubuciyar⤵️ A DALILIN'YAR TSINTUWA. MIJIN ZAHRA. DIAMOND LADIES ( Daukar fansa)paid book. RUHIN AMRITA (FATALWA CE). Now *_GALADIMA FAMILY_* Page 07 _Bismillahir-rahmanir-raheem._ _____A lokacin da Muhammad yagama secondry school lokacin Allah yadauki rayuwan hakimi,inda anan harun mahaifin bodejo yatura Muhammad cikin garin MAIDUGRI gidan aminin mahaifinsa inda gadon su Muhammad yake anan yaciga ba da karatunsa na gaba da sakandiri,a gefe guda kuma shakuwa sosai tasake dinkewa tsakanin bodejo da Muhammad lokacin tagama aji uku na sakandiri sai aka cireta, Laure ma tana samun kula sai dai takasance tun tana karama take da wasu dabi'u sam marasa kyau. A kwana a tashi babu wuya Muhammad yasamu kwalin diploma dinshi,a lokacin ne Kuma harun ya aura masa bodejo inda suka tare anan gefen gidansu bodejo din, Muhammad yataso mutum ne mai tsananin hazaqa da kokari uwa uba kuma kyau,auren su da wata uku yakoma makaranta. Lokacin da yagama Digree dinshi na farko a lokacin harun yadamqa mishi gadon su wanda tuni ansai da raqumayen,anjuya musu kudadensu inda ya habaka sosai,lokacin bodejo ta haifi danta mai santalele namiji kyakkyawa aka sanya masa Taleeb sunan mahaifin Muhammad,sai dai kiri² Muhammad ya hana a boye sunan,bayan bodejo tagama wanka Muhammad yadauke ta ya maidata cikin gari inda yayi musu gini, Laure Kuma tana zaune wajen harun da matarsa. Bayan shekaru 28 aiki ya maida Muhammad garin kaduna inda yake zaune a zaria akuma lokacin yaran Muhammad su shidda ne maza hudu mata biyu,Taleeb ne babba sai Sadeeq,Haroun,Labeeba, Maryam sai auta Hasheem. A lokacin anyi auren Taleeb da Sadeeq don rana daya akayi bikinsu. Taleeb ya aure matansa 'yar maidugri ne don shuwa ce itadin gaba da bayanta,inda Sadeeq ya aure 'yar zaria wajen fada,duk cikansu Allah ya hadasu da mata nagari. Matar Taleeb sunanta Aisha,matan Sadeeq kuma bilkisou. Shekarar da suka cika shekara guda da aure Allah yabaiwa Taleeb karuwar da namiji inda yaci sunan Muhammad Taleeb Muhammad,waton sunan kakansa inda ake cemasa Sauban,bayan cikin Sauban suka sake haihuwar mace inda aka sanya mata sunan mahaifiyar Aisha Safeena suna cemata falmata wacce take sa'a da Dan wajen Sadeeq wato Ahmad ake masa laqabi da Taufeeq. Wasa Wasa sai da Aisha tayi haihuwa hudu, Sauban,falmata, Mashahuda, Laila. Amma bilkisou tundaga kan Taufeeq bata sake haihuwa ba. A lokacin shima abba yayi aure sai dai matansa shima bata haihu da wuri ba 'yar kaduna mai suna hauwa'u. Hasheem yayi aure inda yake aure da 'yar wan mijin Guggo Laure, me suna Rabi.Yaransa uku,babban Bashir ana cemasa Aseef sai muneefa inda takeda ciki a lokacin itama bilkisou tasamu cikin nabiyu. Anyi bikin Labeeba da Maryam, Labeeba tana zaune a Canada tare da mijinta yaransu biyu muhsin da musaddiq.Inda Maryam ke Lagos sai dai ita bata haihu ba. Rabi ta haifi yaronta namiji Mai suna yassir tsakaninshi da Laila wata daya,inda itama hauwa'u ta haifi diyar ta mace akasanya mata Nihal. Alokacin da cikin jikin bilkisou itama ya bayyana sosai ahalin Muhammad suka shiga farin ciki kowa yaqosa ace tahaihu,sosai akayi zumudin cikin,lokacin haihuwa tayi ta haifi yarinyar ta kyakkyawa Masha Allah anan ne fa akashiga turka turka inda bilkisou tace sunan mahaifiyar ta za'a saka mata,shikuma Sadeeq yace sunan mahaifiyar sa zai saka Fatima. A lokacin rashin kawaicin bilkisou yafito muraratan inda tace to muddin yasa sunan bodejo to bazatayi farin cki ba,sosai ran Sadeeq yabaci dana ahalinsa sai dai su suka danne,bodejo kuwa duk bakinta haka tazuba ma bilkisou Ido, Guggo Laure kuwa tasamu bilkisou tayi mata tijara tundaga lokacin ta tsani bilkisou. Aiko aka sanya sunan bodejo wato fateematuz zahra'u suke cemata zuhra. Da farko bilkisou tace bazata shayar da jaririyar ba,sai da mahaifinta da mahaifiyar ta sukazo har gida sukayi mata tatas inda mahaifinta yace muddin Bata shayar da zuhra ba sai yayi mata baki,sannan yatasa ta taje tabaiwa bodejo hakuri da Muhammad da mijinta Sadeeq. MUHAMMAD kafin kace mene yayi fice saboda kudinsa da kuma ilimi irin na 'yayansa ga uwa uba kyau,don alokacin Taleeb Yana aiki a NNPC inda yaran gidan ke kiransa da Daddy,Sadeeq kuma yana aiki a wani company a Lagos inda yaran gidan kekiransa da Abbie sunan da Sauban yasa masa, Harun wanda suke cema Abba kuma yana lecturing a KASU ne,shima Hasheem wanda suke Kira da Baba yana lecturing ne a ABU zaria. Allah yarufama iyalensa Muhammad asiri da shi kansa dai² gwargwado,sosai sunanshi yayi fice inda a wancan lokacin zamanin sarkin lokacin ya nada masa sarautar galadiman zazzau shikenan kuma sai sunan yabisa,an nada masa sarautar babu jimawa kuma don ba'a wuce shekaru uku ba yakoma MAIDUGRI gabadaya da iyalensa,banda Abba da Abbie inda Baba Hasheem yakoma University of maidugri yacigaba da lecturing dinsa. Zuhra kuwa sosai tasha wahala a hannun mahaifiyar ta bilkisou vwacce suke kira da Ummie,duk da kuwa tataso 'yar gatace Amma sam batajij dadi ta wajen Ummie yana daya daga cikin dalilan da yasa Abbie yake tsananin son ta kenan,tunda yayi fadar har yagaji yasama Ummie Ido,mommy ce a kaduna tamaye mata gurbin mahaifiyar ta. Inda sosai mommy ke tsananin tausaya ma zuhra tare da bata cikakkiyar kular da tadace komai tare take musu ita da Nihal har Allah yabata ciki tasake haihuwar junior yasir,takuma sake haihuwan mace maimoon. Dalilin dayasa zuhra tataso da tsoron Ummie kenan tare da shakkar ta,idan kuwa ace Abbie baya gari zama takeyi kamar mara lafiya. Wannan kenan. _Cigaban labarin._ Ji kake tassss! Jikinta babu inda baya shaking tsaban rudun da take ciki hawaye ne kawai ke tsiyayowa daga idanuwanta,dafe kuncinta tayi don sosai Marin ya shige ta. Lokaci daya parlon yadauki shiru sosai Taufeeq, Mashahuda, Laila, Nihal jikin su yayi sanyi ganin irin marin da Ummie ta zabga ma zuhra,cikin kakkausar murya tayi pointin dinta tare da cewa. "Karyan rashin hankali kikeyi zankoya miki natsuwa ne,stupid kawai. Takarisa maganar tare da jan tsaki cikin muryan tsawa tace"Get out !!! Da wani irin sassarfa zuhra tafita inda jikinta babu inda baya rawa, Taleeb kuwa sunkuyar dakanshi yayi idanuwan shi sunyi jajazur. Kaitsaye apartment din Ammi zuhra ta wuce,kicibus tayi da Ammi a kofar hawa stairs din Daddy, fadawa tayi jikin Ammi tare da fashewa da wani irin kuka mai tsuma zuciyar duk wani mai sauraro,cikin rawar murya tace. "Ammi...Am...Ammi don Allah Ummie ne mama na? Ummie ne ta haifeni?meyasa Ummie tatsaneni?please kuje kubata hakuri kuce tasoniiii...taja kalmar saboda wani irin kuka da yazo mata. A hankali Ammi takai hannu tana shafa kan zuhra cikin tsananin tausayin ta wani kwalla taji ya taru mata a idanuwan ta,kama hannunta tayi tanufi hanyar wani corridor inda zai sadata da parlon ta,zaunar da zuhra tayi akan sofa. Facing dinta tayi tare da kakalo murmushi takira sunan zuhra, dago dara²n idanuwan ta tayi wanda suka tasa saboda kuka ta zubawa Ammi. "Kiyahakuri kinji?kidauki duk wani abu da zaifaru dake a matsayin kaddara da kuma jarabawa kinji?Allah Yana sane dake Koda wasa kuma kada nasake ji kinkuma fadar maganar nan,watarana fah sai labari kinji zuhra na? Daga kai kawai tayi tare da amsawa Ammi,murmushi Ammi tayi tace"kinci abinci? Cikin sanyin muryan ta tace"A'ah yanzu zanje wajen Mommy na amsa alale na. Ammi tace"yawwa to taaji kije Allah yamiki albarka. Mikewa tayi cikin sanyin ta tafita,kaitsaye apartment din mommy tanufa dai² dan lungun shuke shuke tsakanin apartment din Mom dana mommy taji anfisgo ta tafada jikin mutum. A tsananin gigice ta dago tare da kokarin sanya ihu,Ido biyu sukayi da Aseef inda yake binta da wani irin matsiyacin kallo Yana lashe lips. Jikin zuhra ne yatsananta kadawa,kirjinta na tsananin bugawa,baki yakai da zummar yimata sumba Allah kuwa yabata sa'a ta dunkule hannu takaimasa punch a hanci. Ai tuni yasaketa yana me dafe hancinsa,itakuwa zuhra dagudu ta falla bata tsaya ko inaba sai apartment din Mom banda nishi babu abinda takeyi,hawaye kuwa anan ya tsananta ambaliya. Gefe ta samu tafashe da kuka a fili ta furta"wa zankaiwa kuka na?wa zanfadama halinda nake ciki don ya magancemin? A hankali maganar wata 'yar ajinsu yafado mata inda suke fira dawasu can daban a cikin firar tace. _Fauziyya duk duniyar nan banda mahaifiyarka babu Wanda zaka fadama magana ya fahimceka sama da mahaifiyarka shiyasa Allah yakara ma iyayenmu mata lafiya da nisan kwana._ A fili tasake fashewa da kuka tace"banda nawa Ummien. Dafata taji anyi,da sauri tadago sai sukayi ido biyu da Taufeeq dan murmushi ya sakin mata yana kallon yanda hawayen idanunta kowanne yake rige²n sauka,zama yayi a dan gefenta tare da daukan kanta yadora akan kafadarsa. Sai dai ko wannensu yakasa cewa komai,katse shirun da cewa. "Tashi muje mommy na nemanki,yayi maganar yana miqar da ita tsaye,a hankali ya miqar da ita. Apartment din mommy suka nufa. ******** "Daddyn Sauban bazaka gane abinda nake nufi bane wallahi bilkisou sam bata kyautawa rayuwar ta,ni kaina bacin agaban mu bilkisou ta haifi zuhra sai nace ba itace ta haifeta saboda wannan dan kankanin matsalar amma ace bilkisou tadauki tsanar duniya tadorawa zuhra,anyi anyi anyi?iyayenta sunyi rokon har sun gaji wannan wane irin musifa ne? Daddy yace"Aisha nikaina hankalina na tashi, muddin zamu hadu da Sadeeq to maganar da zaifara yimin kenan, yarinyar tana shiga tsananin damuwa,ni tsoro na kada wani larura ya kamata. Ammi tace"narasa meya shiga kan bilkisou,bilkisou meson yarane kaduba fa,kuma sanda tasamu cikin zuhra ta dauki son duniya ta dorawa cikin don ko cikin Taufeeq batanuna zumudi haka ba,ko a sanda tahaifeta kamar ta hadiye abarta sai daga baya zancen ya canza. Daddy yace"Allah ya kyauta,ita kuma Allah yakara mata hakuri da juriya ubangiji ya bata ikon cinye jarabawarta. *MALAYSIA* Sosai Sauban yake cike da farin ciki saboda kaitsaye anamasa interview akace za'a daukeshi aiki a company kuma hazaka da kokari nashi sun burgesu sosai,inda sauran goma sha biyar din akace zasuji bayani daga baya. Anan suke sanardashi nanda 2 weeks zaifara shiga office,sosai yayi godiya inda yafara shirye shiryen dawowa gida Nigeria. Kwananshi biyar a Malaysia yafara shirin dawowa. A MAIDUGRI kuwa gabadaya yaran 'yan matan gidan suna cikin din Ammi inda suke aiki,zuhra ce kehada couslow don aikin da aka bata kenan. Cike da sanyin ta take aikin sai dai sam fuskanta babu walwala ko kadan,cike da barkwanci Mashahuda tace"Aunty zuhra kiyi kigama hadamana couslow dinnanfa don nasan yau akwai santi akan dinning. Dariya duk sukayi muneefa tace"Ai sis shiyasa Ammi tabata hadin couslow din. Dan murmushin gefen baki zuhra tayi tace"kai Aunty's. Xahratty CE🥰 Lallai Alqalami 🖊️ yafi takobi🗡️ 17/2/23. [3/21, 22:27] Xahratty (OUM AJMAL): 👨🏽‍🦳 *_GALADIMA FAMILY_*👨🏽‍🦳 Story&Written By *FATEEMA ZAHRA LAWAL* Marubuciyar⤵️ A DALILIN'YAR TSINTUWA. MIJIN ZAHRA. DIAMOND LADIES ( Daukar fansa)paid book. RUHIN AMRITA (FATALWA CE). Now *_GALADIMA FAMILY_* Page 09 _Bismillahir-rahmanir-raheem._ *This page is dedicated to my lovely son Ãjmãl,much love 😘 my rabin jiki* _____Wannan saurayin ne da suka hadu dashi a super market dazu,mirmushi ya sakar ma zuhra cikin sauri ta kawar dakai tare da basarwa. Maida dubansa yayi ga Aunty Mashahuda wacce batadena yimishi kallon mamaki ba,dan murmushi yamata yace"Auntymmu dama nan kukazo? Mashahuda tace"aiko nan mukazo sannu dai. Aunty Safeena tace"kunsan junane Shuraim?dan sosa kai yayi tare da murmushi yace"Ea Aunty munsan juna. Zuhra ce tadubi Abban inteey tace"Yaya Asheer sannu da zuwa, inayini? Fuskarshi cike da fari'a ya amsa da lafiya lou autan Abbie yaushe kuka shigo garin? Zuhra tace"yau sati daya. Yace"Masha Allah yasu Ummie da Abbie? Zuhra tace"duk suna nan lafiya lou harma sun koma yau kwana biyar da komawansu. Shiko wannan saurayin ke suna Shuraim tuni zuhra tatafi da imaninsa gabadaya hankalinsa yakoma kanta. Dubanshi Aunty Safeena tayi"Shuraim lafiya kuwa?firgigit yayi tare da maida dubansa wajen Aunty Safeena,daga Abban inteey har zuhra suma dubansu sukayi. Abincin Aunty Mashahuda tadauka tare da duban zuhra tace"Sis zo muje dinning muba su Yaya Asheer waje. Mikewa zuhra tayi don dama a takure take hannunta riqe da hannun inteey suka nufi dinning din zama sukayi inda zuhra tajuyama parlon baya. Cikin kasa kasa da murya Aunty Mashahuda tace"kinsan wancan mutumin ke yabiyo anya ba sonki yake ba zuhra? Sosai zuhra taji gabanta ya fadi amma sai ta basar tace"hmmm Aunty ni babu ruwa na dasu Daddy wallahi yaje can yaqarata,takarisa maganar tana kai lomar spaghetti din bakinta wanda yaji dakakken naman kaza. Itama bata sake magana ba mashahudan, can wayar Mashahuda yafara Ringing,hannu takai tare da dauka sunan ammi ne ya bayyana akan screen din wayar. "Assalamu alaikum ammi,bansan me akace mata daga can bangaren ba sai dai tazaro idanuwa gabadaya,ta marairace face tace"please ammi kice masa muna hanya yanzu zamu dawo,magana aka sake mata tacan bangaren. Sake marairaice face tayi"please ammi muna zuwa fah. Itakuwa zuhra tuni ta aje spoon din a cikin plate din taja tissue tagoge mouth dinta sannan tamike,itama Mashahuda mikewar tayi bayan ta aje wayar tadubi zuhra tace. "Wai Daddy ne yadawo yake tambayar inda muke,shine tace munje supermarket shine fa yafara fada. Tafiya zuhra tafara suka dawo parlon,mikewa Abban inteey yayi yace"Shuraim kamaidasu gida zanshiga inwatsa ruwa ne don yanzu za'a kira magrib,cike da girmamawa ya amsa key din yace"nima gida zan tafi yaya dagacan. Abban inteey yace"tohm shikenan ka gaida mutan gidan kacema Alhaji gobe zanshigo. Aunty Safeena tace"muje toh kutafi don nasan kuna wuce magrib sai sunyi fada musamman ma Baba Hasheem,fita sukayi suna yiwa Abban inteey sallama. Parking space suka isa nan suka shisshiga cikin motocin,shima Shuraim sallama yama Aunty Safeena sannan yashiga yatayar da motan,nan gate man yabude masa gate din yafita. Aunty Safeena kuwa sosai take farin ciki don idan harsashen ta ya tabbata to tabbas sai tafi kowa murna( _Ji wannan safeenan zaki hadu da bodejo ai_ )🤔 Suna cikin motar babu wanda yace da wani qala sai dai time to time Shuraim na duban mirror kuma cikin rashin sa'a su hada idanu,itako zuhra ta galla masa harara tare da murguda baki. Sai dai kawai yayi murmushi don shi masifar burgesa tsiwan nata keyi,a haka dai suka kariso anguwan su,kwatance Aunty Mashahuda tashiga yimishi,nankuwa yakawosu kofar gidan yadanna horn,da sauri Aunty Mashahuda tace. "Kada kadamu Baba mudi ma bayanan suna cikin masallaci ka ajemu anan ma ya isa,bude murfin motar sukayi suka fito, shima fitowan yayi yadan tsaya a setin zuhra duk da suna da tazara face nasa dauke da smile yadubi Aunty Mashahuda cikin zolaya yace"shikenan Auntymmu gashi dai a bonus naga gida da alama kuma tafiyar tawa akwai nasara,yakarisa maganar yana duban zuhra. Tunda yashigo layin idanunsa ya sauka akan kofan gate dinsu don gidan Galadima yana daya daga cikin manyan gidajen da akeji dasu a layin,a hankali yarage speed din motar,idanuwansa ne yafara sauka akan na wannan saurayin dayake wani irin murmushi,da sauri yaduba don ganin wanda yake ma murmushin,nandanan yaji kirjinsa yabuga ransa yayi kololuwan baci yamaida dubansa ga Mashahuda wacce take ta murnushi. Kara speed din motar yayi gefen su yafaka motar yaballe murfin motar yafito,daga Zuhra har Mashahuda gwalo idanuwa sukayi waje,ai kamar hadin baki su biyun da sassarfa duka shige cikin gate din. Da mamaki Shuraim yadubi inda yaga sun kalla har yasasu wannan razanar sai dai abin mamaki baiga kowa ba awajen. Abinda Shuraim baisani ba kuwa shine koda Sauban yafito daga motan ko kallon inda suke beyi ba ya shige cikin masjid din,amma su da take sun ganshi shine fah. Yadade sosai a bakin gate din daga karshe yashiga motan ya gyara parking din agefe yanufi masjid din yayi alwala yashiga ciki. Su kuwa daga Mashahuda har zuhra kowacce takanta tayi don kaitsaye apartment din bodejo zuhra tashige,koda tashigo bodejo bataji shigowanta ba tana kitchen itada nana mai aikinta itama dattijuwa ce suna abincinsu ita da Galadima don suna da diabetes. Shiyasa bataji shigowar zuhran ba,can bedroom dinta tashige tare da sanya key tafada kan bed tana dafe kirji,gabanta banda dukan uku uku babu abinda yakeyi,tadade anan kwance zuwa can tamike tashiga toilet don dauro alwala. Bata jimaba tafito koda tafito kunna dum light tayi ta shimfida praymat ta tada sallah. Koda ta idar zama tayi har akakira sallahn isha'i tayi sanna tabude bedside drower dinta tafito da cake da doughnut wanda mommy tamata kafin su koma,cake uku ta dauka doughnut biyo,tabude dan fridge dinda ke cikin dakin ta dauko lemon mountain dew. Kan bed din takoma tahau tare da dauko phone dinta tashiga tiktok,da videon wannan yarinyar da ta shahara a duniyar tiktok tafara cin karo,wato Aakeelah Mancy don tashi take amfani,bude videon zuhra tayi nan taciddata taci kitson attached,tana sanye da riga da wando murna takeyi tayi tanama fans dinta albishir din cewa ankusa samata rana,sai ihu da tsalle take . Dan siririn tsaki zuhra taja kasa kasa a ranta tace"Kai wannan yarinyar ta cika rawar kan tsiya. Bodejo kuwa sai da sunacin abinci hankalinta yadawo jikinta cewa su Zuhra fa basu dawo ba tun wajen biyar da suka fita,dai dai Sauban yayi sallama. Galadima da bodejo suka amsa masa idanuwansu na kansa cike da tsantsar soyayyan sa a zuciyoyinsu, cike da zolaya yace"Don Allah tsofaffin nan kada kucinye ni batare da nima naga 'yayana da jikoki na ba,ku gwara daku don da alama har tattaba kune zaku gani. Dariya suka sanya bodejo tace"Ungo nan,tayi maganar tana aika masa da daquwa,murmushi yayi tare da jan kujerar Galadima ya zauna,bude warmer din yayi yazuba lafiyayyen dambun accan Wanda yaji kayan ciki tare da vegetables. Duban shi Galadima yayi yace"ai shiyasa kaji muka damu dakayi auren kaima shiyasa muka zaba maka mata. Dan hade face yayi yana Kai lomar dambun bakinsa. Murmushi kawai Galadima yayi yana girgiza kansa don tabbas yasan cewa Sauban biyayya kawai yake kokarin yimusu amma batare da yanason yarinyar ba. Galadima yace"munyi magana da mahaifinka kan zasuje gidan Laure wajen Sani a tsaida ranar aurenku....cikin sauri Sauban yadago tare da sauke ajiyar zuciya. Dan yatsine face yayi cike da aji da natsuwa don kowata macen albarka yadubi Galadima yace"please Galadima kada asa ranar nan kusa nida so samune ma asa nan da two year's. Wani kallo Galadima yayi masa irin na yhu re not serious dinnnan,budejo kuwa dariya tayi. Sauban yace"bakace komai ba Galadima. Galadima yace"kabari anjima sai kaje wajen mahaifinka ka tuntubeshi abinda yace shikenan. Wani wawan ajiyar zuciya Sauban ya sauke yace"ai idan nayi magana kamar nayi rashin kunya ne inhar nayari Daddy da zancen. Murmushi Galadima yakuma saukewa a karo nabiyu yasake cewa"Kaje kasamu Hasheem kayi maganar dashi. "Huhhhhhh wannan tsohon sam bazai ganeba, Sauban yafada a ransa yana share gumin dake keto masa duk da kuwa AC dake a wajen. Koda suka kammala cin abincin mikewa Sauban yayi yamusu sai da safe, bodejo tace"kabiya sashin Aisha katuromin Zuhra. "Hmmmm kawai Sauban yace yafita kai tsaye apartment din Ammi yanufa,da 'yar siririyar muryansa yashiga parlon da sallama,babu kowa sai Mashahuda tana waya,ganin shi yasa takatse wayar tafara tsilla-tsilla da idanuwa,sake hade face yayi don yana sane dasu. "Ke ina yarinyar nan?sosai Mashahuda cikin rudewa tace"Tatafi apartment din bodejo,don tagani wanda yake nufi. Harara ya zabga mata tare dayin kwafa yace"zanyi maganin ki soon,yana gama fadar haka yanufi corrridor dinda zai sadashi da parlon Daddy don yasan Ammi nacan. *******^^^^^^^****** Cikin muryan kuka take magana"wallahi hajiya ina sonshi nidai gaskiya ayi duk yanda za'ayi aga wannan auren baiyuwu ba tsakanin shi da wannan yarinyar,don ni natsaneta kodan fans dinda takedashi a tiktok. Wacce aka kira da hajiya na duba sai karkade kafa takeyi,face dinta murmushi kwance daga ganinta kasan idanuwan ta kyar suke. "Haba Rammat to meye kuma abin kuka?nimafa inaso ki aure Sauban don yanzu shine tauraron sa ke haskawa, Mom tayi maganar tana dafa kafadar Rammat. "Hajiya gaskiya duk yanda za'ayi ayi don ganin Rammat tashigo cikin GALADIMA FAMILY,yanda kika shiga kika fita harnima nashiga to itama tashiga,kinsan kuwa nan da 1week Sauban zai koma Malaysia akan sun daukeshi aiki,Mom tayi maganar. Ai dasauri wacce suka Kira da hajiya tadubi Mom tace"Wai Rabi dagaske kikeyi?kinfasan burina baiwuce Koda yaushe ku aure manyan mutane ba kushiga dangina dana ubanku ana girmamaku,tuntuni nayiwa Rammat sha'awar auren yaron nan,Ashe makirar Laure tarigani hada nata tuggun?hmmm nasan Laure farin sani sai dai ita batasanni ba batasan koni wacece ba,amma muje zuwa a sannu zanyi maganinta. Ki kwantar da hankalinki Rammat,insha Allahu sai kin aure yaron nan Koda kuwa zakiyi kishi da wancan kodaddiyar yarinyar ne,tuni zamuyi waje da ita bayan auren. Rammat tace"A'ah hajiya ni gaskiya bazan iya zama da wannan munanan yarinyar ba,natsaneta. Mom tace"muma bamu fata insha Allahu bazakiyi zaman kishi da ita ba aikinfi karfinta wallahi. Hajiya tace"hmmm ku yarane bazaku gane me nake nufi ba amma a hankali zanyi muku bayani, Rammat ki kwantar da hankalinki indai Sauban ne kisa aranki kinsame ahi kingama. Dariya Rammat da Mom suka sanya cike da farin ciki. _TAB CAKWALKWALIN CAKWAKIYA KENAN SAUBAN KAIKAM KAGA TAKANKA_🥴 _YANZU FA WASAN ZAIFARA KUDAI KUCIGABA DABIN ALQALAMIN OUM ÃJMÃL._ Xahratty CE🥰 Lallai Alqalami 🖊️ yafi takobi🗡️ 22/2/23. [3/21, 22:27] Xahratty (OUM AJMAL): 👨🏽‍🦳 *_GALADIMA FAMILY_*👨🏽‍🦳 Story&Written By *FATEEMA ZAHRA LAWAL* Marubuciyar⤵️ A DALILIN'YAR TSINTUWA. MIJIN ZAHRA. DIAMOND LADIES ( Daukar fansa)paid book. RUHIN AMRITA (FATALWA CE). Now *_GALADIMA FAMILY_* Page 08 _Bismillahir-rahmanir-raheem._ ____Sai bayan sallar la'asar Taufeeq da Kareem sukaje daukoshi a airport yadawo gida cike da nasara inda gabadaya farfajiyan gidan GALADIMA FAMILY cike yake da yara da jikoki don taryan Sauban. A hankali motan tashigo cikin farfajiyan gidan bata tsaya ko inaba sai parcking space,su duka ukun suka fito daga motan kowanne dariya ne kwance akan fuskar sa. Yaran gidan ne suka fara tsalle da muryan dawowan sa inda suketa tururuwan yimasa barka da zuwa. Yassir babba ne yajawo trolly bag din. Uban gayyar kuwa direct wajen Ammi yanufa kaitsaye murmushi kwance akan fuskar sa ya furta "Oyoyo sweetheart yayi,yayi maganar tare dayin hugging nata. Murmushi kwance akan fuskanta tadan bubbuga bayansa tace"Oyoyo son hope kadawo lafiya? "Alhamdulillah sweetheart ! Ya ambata. Nufar bodejo yayi da niyyar yin hugging dinta itama,da sauri taja baya tare da mere baki tace"Allah yatsareni da wannan dabi'ar yahudawan inazan iya wannan shedancin saudan?boko yagama lalataka gabadaya😏 Murmushi su Ammi suka sanya. Nufar Ummie yayi fuskar sa cike da fari'ah ya miqamata hannu don musabaha,itama miqamasa tayi don gaisuwan su kenan muddin zasu hadu. "Ummie na yaushe kuka shigo Mai din?ainazata sai gab azumi zaku iso? dariya Ummie tayi tace"aikuwa wannan zuwan munzo da wuri amma jibi zamu koma saboda school dinsu Laila da Nihal. Gyadakai yayi tare da murmushi yanufi Mom tare da rissinawa ya gaisheta itama ciki da fari'ah ta amsa yanufi mommy,hannu ta miqa masa suka tafa duk dashi a kunyace yake. Bodejo tace"Uhm uhumm lalacewa yakai lalacewa yanzu ke hauwa ko kunya bakiji ba?kika miqama kusan danki hannu kuka kashe? Gabadaya wajen dariya aka sanya,a zahiri kuwa Aunty hauwa bata wuce shekaru uku zatabawa ya Sauban ba,Yan matan gidannan suka fara gaida cike da girmamawa. Zuhra kuwa tana gamai gaisheshi ta sunkuyar dakai tamkar wata munafuka,akanta ya tsaida idanuwan sa sai dai kallo daya yamata yakauda kai. Dunguma sukayi suka shiga cikin parlon Galadima don da alama yau anan za'ayi dinner akuma taba hira. "Sweetheart Inasu Daddy da Galadima? Ammi tace"Basunan sunje masallaci kuma daga can zasu wuce jana'izar ladan don Allah yamasa rasuwa dazu wajen 3:30. "Innalillahi wa Inna ilaihirraji'un yarasu? Ah muma zama baikama muba yakamata ayi jana'izar damu ko friend? Kareem da Taufeeq suka mike, Ummie tace. "Haka zaka kuma fita babu abinda zakasa abakin ka? Bodejo ya alhamis ina azumi ko kin manta ina azumin litinin da alhamis?yaqarisa maganar yana fita. A kaikace bodejo ta makama bayansa harara tace"Oho maka nina manta ma kanayin wani azumi. Bayan sallar isha'i gabadaya ahalin sun hallara a hall din cin abincin wanda yatsaru iya tsaruwa fada kuwa bata bakine sai dai kai maikaratu ka kiyasta irin tsaruwar Galadima family. Bayan Sauban yagama gaida iyayen nasa maza sun taba 'yar barkwanci da hausa shida Galadima anan akafara cin abinci harda matayen. Babu wanda yasake magana sai zuwa can ne mommy talura babu zuhra awajen cin abincin,gyaran murya tayi tare da duban nihal tace"Nihal ina zuhra ne?gashi anacin abinci batanan,tashi kije ki kirata. Miqewa tayi zata tafi Mashahuda tace"Bari nakirata a waya muji mommy,Kiran wayar zuhran tayi ba'a dau wani lokaci ba akayi picking. Da yake a handsfree wayar take cikin sanyin muryan ta maicike da natsuwa tare da shagwaba tace"Hello Aunty Mashahuda inayini? Mashahuda ta amsa tana me cewa"kizo dinning cin abinci anata jiranki fah,cikin shagwababbiyar muryan ta tace"Aunty Mashahuda na qoshi nikam shiyasa ma banzo cin abinci ba. Har Mashahuda zatayi magana Ammi ta amsa wayar,cikin muryan rashin wasa tace"Me kikaci?kiyi maza kizo kici abinci ina jiranki ne. Tana gama fadar hakan ta datse wayar. Mommy tayi murmushi tace"Zuhra hmmm batason cin abinci kwana biyu ina lura da ita. Cin abincin suka cigaba dayi. Ko 5minute ba'ayi ba tashigo tare da sallama cikin sanyinta,duk dagowa sukayi suna dubanta, Sauban kallo daya yamata sai dai kayan jikinta sun mata kyau,sanye take da riga da skirt English wears,long skirt mai budewa tundaga kugu sai rigar iya kugu mai gajerar hannu kalar ruwan hoda,hula ne akanta black sai black din flat shoe wanda suka hade da fatarta kalar half-caste sukayi mata kyau sosai hannunta riqe da wayarta iPhone 8+ da ita da Nihal da Laila wayarsu iri daya. Amsa sallamar sukayi,nan tafara gaida kowa tare da jan kujera tazauna. Bodejo tace"kawai saboda bakin hali saikishige kurya kiqi fitowa?akan wane dalili? Turo mouth gaba tayi tace"Kai bodejo uhumm,awara ta zuba da egg source tare da tsiyayan kunun gida tafara sha. A lokacin su Daddy suka kammala harma da Galadima suka miqe. Suma su Sauban basu wani jimaba suka tashi, dama a takure take saboda irin kallon da Kareem ke mata a sace. A hankali kowa yadinga tashi duk aka watse yarage daga Zuhra,Laila,Nihal da maimoon. Wajejen 9:30 kowa yana apartment dinsa inda su Zuhra ke apartment din Ammi dakin Laila. Sauban ne ya shigo bedroom din Ammi,cike da girmamawa yace"Sweetheart kenan haryanxu baki baccin wurin ko?duk da kallo daya zakama fuskansa zaka fahimci yana cikin damuwa. Kura mishi idon Ammi tayi tare da aje hisnul muslim din hannunta akan side drower tace"Son lafiya?naga kacanza ne bakamar sanda kadawo cike da farin ciki ba? "Sweetheart Daddy p suka sameni akan wani magana wanda Allah yasani tun farko nace banason yarinyar amma sunce umarni suke bani kan na amince inhar sun isa dani,bama kaman Daddy sweetheart bakiga yanda yakeyi ba. Shikuma Galadima harda rokona wai yana gudun lalacewar zumuncin su day rigimammiyar tsohuwan nan hajiya Laure. "Wallahi muddin akamin haka ba'a kyauta min ba sweetheart don sam yarinyar batamin ba,yaqarasa maganar tare da murza forehead dinsa da babban yatsan hannunsa. Ajiyan zuciya Ammi tasauke tace"Amma basun fadamaka dalilinsu na umurtanka da auren ba? Sauban yace"A'ah sweetheart kawai sunce sunyimin mata sannan umarni suke bani wai inhar sun isa, Galadima hardamin kuka gabadaya sun daddaure ni,mema sanyi a ciki shine Abbie, yanzu yazanyi da rayuwata?wallahi sweetheart banason yarinyar nan please kisa Baki.Yayi maganar idanuwansa nasake jajazur. Ajiyan zuciya Ammi tasauke tare dayin murmushin da baiwuce iya labba ba don Allah yasani har zuciyarta bata aminta da aurensa da Akeela da akeso a hada ba amma bazata hanashi yima iyayensa biyayya ba,kuma bazatayi sanadin abinda zai bata zumunci ba. "Kaine kajawa kanka Sauban tun tuni ake maka maganar kafito da matan aure amma kaqi to ya kakeso ayima nibazan goyi bayan kaqi yima iyayenka biyayya ba kacigaba da addu'ah Allah yasa hakan shi yafi alkhairi. Shiru ya ratsa na wani lokaci,mikewa yayi yace"shikenan sweetheart nizan tafi na kwanta ina furar da kika mun magana? "Yananan a cikin karamin fridge dincan. Nufar fridge din yayi yabude yadauki furar sannan yamata sai da safe tare da jan kofar yabar bedroom din,girgiza kai kawai Ammi tayi tacigaba da duba hisnul muslim dinta. Washegari zuhra zaune take a qasa kusa da Abbie tana saurarensa,gefensa Ummie ce fuskanta kadaran kadahan sai ya Taufeeq da yake zaune kusa da Ummie. "Kinji mamana anan zaki cigaba da zama saboda munyanke hukunci dasu Daddyn ku kan zaki shiga University of maidugri ne tunda kindage bakison zarian koh?baki kewar mune? Dago dararan idanuwan ta tayi tadubeshi cikin cool voice nata tace"ina kewanku mana Abbie musamman ma kai dasu maimoon da mommy,amma nafison nandin,takarisa maganar muryanta na rawa. Sosai Abbie yaji wani irin tausayinta saboda yasan badason ranta zata zauna anan ba amma saboda mahaifiyar ta tazabi nisantar su. Cike da barkwanci ya Taufeeq yace"Ai Abbie tagaji da ganinmu ne musamman ma ni. Turo mouth tayi tace"Kai ya Taufeeq wallahi niba haka nake nufi ba kawai dai....tayi shiru batare da takarisa ba,kasa² take duban Ummie wacce take lallatsa wayarta tamkar bata a wajen,ajiyar zuciya mai karfi ta sauke tare da rintse idanuwan ta. Dafa kanta Abbie yayi yace"shikenan Allah yayi miki albarka kinji Allah yabada sa'a akan KARATUN da zakiyi 'yar jarida,nan yashiga yimata nasiha masu shiga jiki,wanda har sai da zuhra jikinta yayi tsananin sanyi,duban Ummie yayi yace. "Ummien yara to kema kiyi naki nasihar mana. Barin lallatsa phone din tayi tace"Allah yabada sa'a ubangiji kuma yamiki albarka.Tana gama fadar haka tamike. Duk cikansu da kallo suka bita,sosai zuhra jikinta yayi sanyi. Shima ya Taufeeq 'yar nasihar yayi mata tare da dan zolayarta kamar yanda yasaba. Bayan kwana daya Abbie,Abba,Ummie,mommy,ya Taufeeq, Laila, Nihal suna shiga motoci inda Ummie, mommy,Abbie, Abba suka shiga mota guda Abba ne kejan motar sai dayar ya Taufeeq, Laila, Nihal dasu maimoon inda ya Taufeeq kejan motar sosai zuhra ke kuka na kewarsu don tunda take ko hutu bata taba zuwa ita kadai ba,inda Abbie yaturama da ya Sauban kudin shopping dinda za'a ma zuhra don before azumi zasu fara attending lectures,shiko ya Sauban yamaida masa yace ai za'ayi mata duk siyayyan daya kamata. Kowa haka ya watse cike da kewar mutanen kadunan. *_IDAN NAGA RUWAN COMMENTS ANJIMA NASAKI DAYAN PAGE DIN😃._* Xahratty CE🥰 Lallai Alqalami 🖊️ yafi takobi🗡️. 19/2/23. [3/21, 22:27] Xahratty (OUM AJMAL): 👨🏽‍🦳 *_GALADIMA FAMILY_*👨🏽‍🦳 Story&Written By *FATEEMA ZAHRA LAWAL* Marubuciyar⤵️ A DALILIN'YAR TSINTUWA. MIJIN ZAHRA. DIAMOND LADIES ( Daukar fansa)paid book. RUHIN AMRITA (FATALWA CE). Now *_GALADIMA FAMILY_* Page 10 _Bismillahir-rahmanir-raheem_ _____Ayau Saturday ne kuma su zuhra zasuyi jamb dinsu,tun wajen 7:30 tatashi tayi duk abinda yakamata. Don Daddy yace 8:00 zai dauketa su tafi wajen bodejo taje don mata sallama ita da galadima a parlon taciddasu su duka sanye da medical glass suna kallon tashan aljazeera. Amsa sallamar da tayi sukayi suna maida hankali akanta,duban tsanaki bodejo kemata sosai take mamakin girman zuhra don zakayi tunanin takai shekara 18 koma 20 saboda yanda Allah ya halicceta da diri sosai ko ina tubarkallah Masha Allah. Sanye take da Dubai gown Army Green sai white flatshoe duk da cewa face nata babu makeup sai dai tayi kyau sosai. Gaishesu tayi cike da kulawa suka amsa mata,bodejo tace"Har anfito za'a tafi? Daga kai zuhra tayi tace"Eah bodejo zanje wajen Daddy ne mutafi. Galadima yace"toh Allah yabada sa'a ubangiji yasa kifito da 300 score. Dariya suka sanya gabadaya zuhra tace"Ameen my Galadima na tafi. Fatan dawowa lafiya suka mata sannan suka fita, apartment Baba Hasheem tafara shiga, Mom tasamu a kitchen don haka tafara gaisheta tana tambayar Baba,cike da fari'a Mom ta amsa anan take sanar da ita baima tashi daga bacci ba. Sanar mata tayi da yanzu zata tafi wajen exam din jamb idan ya tashi ta gaisheshi. Fatan alheri Mom tamata. Koda tashiga apartment din Ammi a dinning ta taddasu itada Daddy,cikin shauki takarisa garesu face nata dauke da yalwataccen fari'a. "Good morning Ammi, good morning Daddy. Cikin fari'ah suke dubanta, Ammi tace"Morning my zuhra antashi lafiya? Daddy yadubeta yace"ah lallai mamana har anfito ne? Murmushi tayi tace"Ea. "To kizauna kiyi breakfast tare da Daddyn naku kafin shima Sauban yafito. Sosai kirjin zuhra yabuga saboda batason haduwa da Sauban din. Cikin sauri ta girgiza kai tace"A'ah Mom nayi breakfast Alhamdulillah bari naje dakin Aunty Mashahuda nayi mata bangajiyan jiya. Ammi tayi murmushi tace"ai bata tashi daga bacci takoma gashi ansamu hutun hadda. Cikin sanyin jiki zuhra tajuya don komawa parlon ta zauna, clashing sukayi da Sauban wanda fitowanshi kenan,suit ne a jikinsa blue black da covershoe black agogo kirara Gucci yake daura bakajin kamshin komai sai na perfume din da yasanya. Hada ido sukayi da zuhra wani harara ya gallamata,itakuwa cikin sauri ta dukar dakai tana murguda baki a hankali tace"Ina kwana. Ko amsawa beyi ba yasamu waje ya zauna,tare da gaisar da iyayen nasa. Cike da kulawa suka amsa,Ammi tace"Son kanwarka na gaisheka. Dan yamutsa face yayi sannan yace"Sweetheart banji bane hankali na na wani wajen,daganan sai ya cigaba dacin abincin sa. Daddy da Ammi kuwa murmushi kawai sukayi,a gurguje suka gama cin abincin,mikewa Daddy yayi Sauban ma yamike. kaitsaye parking space suka isa inda Daddy yashiga gidan baya zuhra kuwa gaba tashiga. Sauban ne yaja motan tare da sanya karatun alqur'ani na Abdullah Abba Zaria,zuhra kuwa a ranta tace"wannan mutumin mayen karatun Abdullahi Abba ne idan anbibiya ma baisan shi ba. "Idan ni bansanshi ba aike kinsanshi koh?taji muryan Sauban yajefeta da wannan tambayar a rikice zuhra tadago tana dubansa. Don sam batayi zaton karatun zucin da takeyi yafito fili ba,idanuwanta gabadaya ta diddilo waje tana duban Sauban. Shikuwa ko kallon inda take beyi ba yacigaba da driving dinsa. Koda suka kariso center da zatayi Jamba din Daddy dakanshi yashiga yakaita don har anfaffara shiga hall din. Nan Daddy yace tanatau tamaida hankali tayi exam din cikin nutsuwa,cike da girmamawa ta amsa masa da toh. Sai wajen karfe 11:30 su Zuhra suka fito daga wajen rubuta Jamb din,cike wajen yake da maza da mata,wasu sa'o'inta wasu sungirme mata wasu kuma ta girmesu sai hayaniya yake tashi a wajen cikin sanyin ta itakuwa take tafiya a kofan gate din center tatsaya tana tunanin ta inda zata koma gida gashi ita bawani sanin maidugri tayi ba. Hankalinta gabadaya yakoma gida saboda yanda taga anata zuwa daukan wasu daga gidajensu wasu kuma suna tsare adaidaita sahu,da yawansu zuwa daukansu akeyi. Samun gefen gate din tayi tatsaya. Duk wanda yazo wucewa sai yadubeta fuskar nan a hade wayanta taciro da niyyar kiran Ammi sai taji magana daga gefenta,cikin natsuwa ta dago don ganin me maganar. Wani saurayi tagani a tsaye yadubeta tare da nuna mata bakin titi yace"Wai kije inji brother naki,a hankali zuhra ta sauke wani gwauron ajiyar zuciya cikin nutsuwa tanufi motar. Sukuwa gabadaya student dinnan hankalinsu yakoma kan motar da ya Sauban ke ciki,'yan mata kuwa da dama ganinsa yasa sun susuce. Sallama tayi iya labba har tanufi gidan baya da niyyar shiga sai tatuno da maganar Aunty Mashahuda don haka sai tabude front seat tazauna,tare da gaidashi. Da kamar bazai amsa ba sai kuma zuwa can ya amsa. Sunyi tafiya babu wanda yayi koda tari sai zuwa can Sauban yadan dubeta, gyaran murya yayi tare da sake dan tsuke face yace"wannan Jamb din da kikayi tamkar aikin banza ne don basan karatun kike ba. Cike da rashin fahimta Zuhra ke dubansa,ta wutsiyar ido yake dubanta,gane bata fahimci abinda yake nufi ba yasashi cewa. "Zansamu Abbie nafada masa cewa keba karatu ne a gabanki ba aure kikeso tunda nakama ki sau biyu kenan. Da sauri tadago tana dubanshi tare da tsantsar mamaki da razana da kalamanshi mouth dinta har rawa yake tace"a'ah wallahi Yaya burina nayi karatu nazaba journalist don Allah kada kafada mai niba aure nakeso ba,kuma ma wazan aura?cike da yarinta tare da tsantsar shagwaba take maganar. Shi Aseef din dana ganku tare ba soyayya kukeyi ba?sannan yaron da yakawo ku gida keda Mashahuda ba soyayya kuke ba?cikin sauri tafara girgiza kai tace"wallahi duka babu Wanda nake soyayya dashi kuma nibansan wani abu soyayya ba niko friend namiji bantaba yiba Allah. Ta sake magana cikin tsantsar yarinta,shiko Sauban dage kafada yayi irin ko a jikinshin nan ya cigaba da driving dinsa cikin kwanciyar hankali. Itakuwa zuhra gabadaya neman natsuwa tayi tarasa burinta yace bazai fada ba.A haka dai suka karisa gida. Da sauri ta balle murfin motar tafito kaitsaye apartment din Ammi tanufa,shikuwa Sauban koda ya ajeta juya kan motan yayi yasake fita. Da sallama tashiga parlon babu kowa sai Aunty Mashahuda,ganin ta yasa tasaki murmushi tana cewa. "Yawwa Zuhra naje nemanki ai dazu shine bodejo tace kinje rubuta Jamb kinsan menene? Girgiza kai Zuhra tayi. Mashahuda tasaki murmushi tace"guy din jiyane da muka hadu a supermarket yakira wai Shuraim koh?shine fa yace nahadashi dake nace baki kusa kinje zana Jamb. Waro idanuwa Zuhra tayi tare da dafe kirji tace"please Aunty Mashahuda kirufamin asiri wallahi adena maganar sa kinsan idan Daddy ko Abbie sukaji zanshiga uku,sannan za'ace guda nawa nake. Mashahuda takama baki tace"toh yanzu zuhra cemasa za'ayi baki sonsa? gaskiya nibazan iya fada masa haka ba sai dai ke kice masa. Zuhra tace"ni bazan iya waya dashi ba Aunty wallahi inajin tsoro kawai abar maganar kirabu dashi Allah,takarisa maganar tana mike tare da fita daga parlon. Murmushi kawai Mashahuda tayi sannan tamike tanufi stairs din Daddy. _____+++_____ A bangaren su Guggo Laure kuwa sai shirye-shirye suke saboda Galadima yakirata cewa su Abba zasu zo daga kaduna a tsayar da magana asa ranar biki. Cike da farin ciki Guggo Laure da Akeela suke,don itama Akeela tsaban murna ma har walima tace zata hada,daga mamanta har Alhaji Mansir sunsamu Ido duk da abin alfaharinsa ne ace 'yarsa tashiga ahalin Galadima amma aida kunya amma wani alqawarin za'a bashi ita akuma zo a fasa. Akeela ce da qawayen ta a dakinta sunata tayata murna daya daga ciki maisuna Suby tace"nikoh akeey baki nuna mana hoton wannan mai sa'ar ba,dayan mesuna zuleey tace"ai da alama shidin ke tsadane fah,dayar maisuna siyama tace"komin tsadarshi ai mu dole tanuna mana shi don ko ba komai anatare duk wanda yaji cewa ma mu nakusa da ita bamusanshi ba ai wallahi dariya za'a mana. Suby tace"gaskiya ne siyama maganar ki Murmushi Akeela tayi wanda dama tun sanda suka fara maganar tashiga gallery dinta inda tayi saving din photos dinshi a IG account dinshi da yake sawa. "Hmmm bbys kenan ku kwantar da hankulan ku gashi tayi maganar tana mikamusu phone dinta. "Wow,suby tafada tana bude mouth, zuleey tace"handsome, siyama tace classic guy. Itakuwa Akeela banda mnurmushi babu abinda takeyi don tasan muddin Allah ya mallaka mata Sauban amatsayin miji to lallai tana daya daga cikin mata masu sa'a. "Kai bby akeey wannan Rich Man din?wanda ko wace mace ke burin aura kika samu?kinsan ko yanda mata ke hauka cewa akansa?to koni ina daya daga cikin fan dinsa. Dan tabe mouth Akeela tayi tace"aiko ko wacce mace kwalelenta don inada tabbacin ahalin da ake ciki babu macen da takaini daraja a wajensa. Suby tace"Lallai ne akeey dole ne team dinmu yasake haskawa dole muba haters wuta. "Yanda kikajin nan Suby,hmm lallai kinyi babban kamu kekam. Akeela tasake sakin murmushi akaro na babu adadi tace"ko babu auratayya tsakanina dashi shidin brother nane da hajiya Laure da Alhaji Muhammad Taufeeq Muhammad (GALADIMA) uwa daya uba daya. Duk zaro idanuwa sukayi waje cike da mamaki. Suby tace"lallai kam muntayaki murna,nanfa suka fara shirye-shiryen yanda party din sa ranar zai kasance don dole duniya Susan wannan abin ko ba komai zamu sake zama celebrates a duniyar tiktok musamman ma ke akeey,cewa zuleey nanfa suka hau ihu bakajin komai sai hayaniyar su da hirarrakin su. Acan fam din Galadima kuwa Daddy ne yakira Sauban bayan sallar isha'i yake tambayar sa wata nawa yake ganin za'a sa ranar. Wani gwauron ajiyar zuciya Sauban ya sauke cikin kamewar sa da nutsuwa yafara magana. "Daddy inda so samu ne asa nanda 1 year saboda inaso naje naga yacce aikin zai kama sannan nayi duk tsare-tsaren da zanyi kafin lokacin insha Allahu everything will be fine. Kura masa ido Daddy yayi tare da dan murmushi yace"gaskiya baza'a sa 10year ba to bari kaji koda mukayi shawara da Alhaji Mansir dasu Abbie dinku da za'a sa 4month ne shine Abbie naku yace a tuntube ka aji tabakinka,Amma wani irin 1 year Sauban babu dadin ji. Sake tsuke face yayi tare da sake rissinar dakai yace"please Daddy a duba a gani. Daddy yadaga masa hannu tare da dubansa face nashi babu alamun wasa ko kadan yace"Za'a tsaida ranar auren ku nanda 8month shikenan. Sosai ransa baiso ba kuma ko kadan baya farin ciki bare mara ba da auren,sai dai duk kwakwanka bazaka gane hakan akan fuskar sa ba. Dan rausayar dakai yayi gefe yace"Shikenan Daddy Allah yasa hakan shine yafi alkhairi. Da Ameen Daddy ya amsa,tare da sa masa albarka don har ransa yake farin ciki da irin danda Allah yabashi,duk da kasan zuciyansa cike yake da tausayin Sauban din. Mikewa yayi tare da masa sai da safe. BAYAN KWANA BIYU Zuhra tunda taji Abbie dinta zaizo takasa sukuni tsananin farin ciki ya dabaibayeta,kudi ta amsa wajen bodejo tabawa security mai bawa fulawa ruwa tace yasiyo mata kaji na turawa guda uku da wasu dai siyayyan,zama tayi ta hada ma mahaifinta lafiyayyen dambun kaza dasu cake da dubulan,da temakon Hannemai aikin bodejo tahada masa komai,ana gobe zasu taho shida Abba tahada komai ta adana,daren ranar cikin tsananin farin ciki tayi bacci. Washegari su Daddy suka shigo maidugri kuma kaitsaye gidan Guggo Laure suka sauka a hanya suka hadu da Baba Hasheem da komai na al'adar saka rana,nan aka musu tarba ta girma wajejen la'asar aka sanya ranar wata takwas. Itadai Guggo Laure ba haka taso ba amma tunda ansa babu yacce zatayi. Haka suka dawo gida, Baba Hasheem apartment dinsa yashiga, Mom yacidda tana hada abinci a dinning,koda yayi sallama da mamaki tajuyo tana dubansa. Murmushi yayi tare da cire hulan kansa ya zauna akan kujerar,sannu da zuwa tamasa sannan tace"wallahi nadamu Abban Aseef tundazu hankalina yaki kwanciya ganin baka dawo daga office ba gashi inata kirar wayar ka taki shiga. Cike da farin ciki Baba Hasheem yace"ya hakuri Rabi wallahi abubuwa ne suka shamin kai munacan wajen sa ranar auren Sauban ne da jikan Guggo Laure!! Wani gingirin gin Mom taji kanta ya mata cikin tsananin rudewa ta dubi Baba Hasheem. Xahratty CE🥰 Lallai Alqalami 🖊️ yafi takobi🗡️ [3/21, 22:27] Xahratty (OUM AJMAL): 👨🏽‍🦳 *_GALADIMA FAMILY_*👨🏽‍🦳 Story&Written By *FATEEMA ZAHRA LAWAL* Marubuciyar⤵️ A DALILIN'YAR TSINTUWA. MIJIN ZAHRA. DIAMOND LADIES ( Daukar fansa)paid book. RUHIN AMRITA (FATALWA CE). Now *_GALADIMA FAMILY_* Page:- 11/12 _Bismillahir-rahmanir-raheem._ *_Ba zaku gane maza security bane ga mata sai mijinki ya rasu ko kun rabu ..._* *_Duk ranar da akace baki da Aure toh fa sai ahankali kin zama hanya mai insecurity, keda hanyar Zamfara ko Rijana na Kaduna kusan daya 😃😃😃_* *_Yo harda wanda bai isa ya maki magana ba zaiyi.._* *_Amma in kina da Aure Koda mijinki baya tabuka maki komai ke kike ciyar dashi mutane ba zasu taba miki kallon banza ba ..._* *_Don Allah Yan uwa mata mune zamu gayawa juna gaskiya idan matsalar da kike fuskanta ba matsala ta transformer bace da baya kawo wuta , ba Kuma dukanki yake ba kiyiwa Allah kiyi hakuri ki zauna.._* *_Babu auren da ba a fuskantar matsala sai dai muce na wani yafi na wani..._* *_Babban matsalar Bai wuce talauci ba , kuyi hakuri lokaci ne , wannan keburan na taba kowa Dan dai mutane Basu fito sun Fadi matsalarsu bane ..._* *_Ina bawa duk wata matar Aure hakuri, a Kara hakuri, Allah yaci gaba da baku hakuri ya biya maku bukatunku na Alkhairi._* ____Au yau akasaka ranar?tayi tambayar fuskarta dauke da murmushi iya labba. Baba Hasheem yace"Eah yau akasa wata takwas muka sanya saboda yanzu za'a fara aikin so sai yaga kamun ludayin aikin,idanma komai yayi normal before lokacin so za'a iya dawo da ranar baya insha Allah. "Kai! Mom tafada wanda sam batayi zaton bakinta ya furta hakan ba,dubanta Baba Hasheem yayi yace"Kai mene kuma Rabi? Da sauri ta wayance ta hanyar sakin wani kayataccen murmushi yace"Hmmm kasan kuwa irin tsananin farin cikin da nayi?wallahi na taya maimuna murna da samun siriki irin Sauban. Wani murmushin jin dadi Baba Hasheem yayi"Tabbas kuwa don Sauban yaro ne wanda kuwa zaiyi sha'awar sa. Mom tasaki murmushi tace"Aikuwa! Zuhra tarasa inda zata saka ranta tsananin murnan ganin Abbie din nata bodejo ta tabe baki tace"Gaskiya Sadeeq duk kabi ka shagwaba yarinyar nan tare da sangarta ta. Dariya Abbie yayi"Bodejo to yaza'ayi? "Abbie kataso kaci abinci tundazu nahada maka lunch saboda nasanka da son cake da meat pie shiyasa namaka sannan na dama maka kunun gyada,takarisa maganar tana kama hannun Abbie din. Murmushi yayi tare da mikewa kai tsaye suka nufi dinning room. Tabe baki bodejo tayi"uhm uhummm tafurta. Dan dariya Galadima yayi yace"hajiya bodejo duk kishin ne haka? Bodejo tace"wane kishi zanyi kawai sai nahau yin kishi saboda wancan kwailar?takarisa maganar tana nuna zuhra. Itadai Zuhra akaikaice tasakin ma bodejo gwalo. *KADUNA JABI ROAD* "Lallai Bilkisou sai yau nasake tabbatar da baki da hankali gabadaya kin wofantar da diyarki ta karfi da yaji kinmaida ita abokiyar gabanki?yarinyar ki nutsattsiya karfi da yaji kinmaida ta marainiya?meye lefinta?itace tace a sanya mata sunan surukarki?ke kanki ba sunan mahaifiyar ubanki kikaci ba? To bari kiji wallahi wallahi ina sake jaddada miki muddin baki shiga hankalinki ba Bilkisou bazan taba yafemiki ba,yarinyar nan ko wajenmu baki kawota sam Fateema batasan niba yanzu ke kin kyauta?ke ba abin kunyarki bace ace 'yarki batasan gidanku ba?sai dai tadinga ganina a photo?tsaban hankali irin na yarinyar nan har kirana take a waya. Narantse da Allah Bilkisou fateeman ma tafiki hankali,har mahaifinki ya rasu da bakin cikin abin nan yatafi. Duk da kinkasance mai biyayya amma akan wannan abin kinkasa wa mahaifinki biyayyaaaaa...... Takarisa fashewa da kuka cikin takaici. "Mtsewwww ai wallahi Amma kinma mata da sauki da yacce tayi watsi da diyarta,kekuma kiyafeta a cikin 'yayanki.... Da sauri Ummie tadago tana duban yayanta Aunty Zainab tace"Haba Aunty mezesa kicewa Amma haka?kunsan kuwa irin zafin da nakeji a cikin zuciya ta?wallahi inajin sonta da kaunar sai dai tsanar da nake mata ya danne sonta da nake mata. "Innalillahi wa Inna ilaihirraji'un Bilkisou dinyar taki kike cewa kike tsana?lallai. Zainab tashi muje wallahi wallahi Bilkisou muddin baki kaunace diyarki ba All....da sauri Ummie ta rufe bakin Amma tana girgiza kai hawaye na tsiyayo mata. Fincike bakinta Amma tayi sannan tamike tadubi Aunty Zainab tace"Zainab tashi muje. Gyara mayafin gyalenta tayi tadauki jakanta sannan suka fita,Ummie tabiyo bayansu da sauri tana kiran sunan Amma dana Aunty Zainab Amma ko waige. Daidai nan Taufeeq yashigo a gigice yasamu daya daga cikin sofa din yazauna tare da duban Ummie yace. "Ummie meke faruwa ne?Kinga yadda Amma tafita tana kuka nagaishesu amma bata amsa ba infact ma ko tsayawa batayi ba Adda Zainab ce tatsaya muka gaisa. "Ummie nasan dama bazaki bani answer ba amma nasan akan maganar Zuhra ne hakan ke faruwa,wallahi Allah yasani koni banjin dadin abinda kike mata haba Ummie kamar bakece kika haife zuhra b..... "Tasssss!karar mari yafito. Ummie ce ta zabgama Taufeeq marin tana huci tare da nunasa da yatsa alamun gargadi tace"Tashi kafita. Sakin baki Taufeeq yayi yana duban Ummie cike da mamaki don tunda yake a rayuwa ko dunguri Ummie bata taba yimishi ba. "Kana mamaki ne?tashi kafita nace kafin nakuma yarfa maka wani marin. Mikewa yayi tare da duban ta yace"Allah yahuci zuciyar ki Ummie. Wani banzan kallo ta watsa masa. Sum sum Yaya Taufeeq yafice daga parlon. *BAYAN KWANA BIYAR* Ayau ne Sauban jirginsa yadaga sai kasar maleyshia. Bayan tafiyarshi da kwana biyu aka bashi aiki matsayin M.D na company,wadanda hada takalma sukeyi,sannan aka bashi gida hadadde Wanda ya kawatu matuka babu abinda babu a gidan,sannan anbashi mota kirar Benz G-Wagon tabbas duk wani masoyin Sauban yaji labarin nan dole yatayasa murna. Ranar monday shine ranar da yafara fita daga office babu abinda kakeji sai sautin tas tas tas tas sautin karar covershoe dinsa ne.Sosai ayau din kensa yasake fitowa na jinin shuwaarab da kuma buzaye,pink lips dinsa gunin sha'awa,sajen nan nasa yakwanta sai sheqi yake kamar balarabe gashin kansa baki sidik gunin ban sha'awa duk da cewa Ya Sauban ba fari bane amma yana da wata irin kyakkyawan fata irin na Zuhra wato half-caste haka colour nasu yake. Sanye yake da designer suit kirar company Gucci black colour,agogon dake daure a hannunsa Kuma Cartier. Hannayensa riqe da wayoyinsa guda biyu iPhone 11pro da iPhone 13 pro max. Kaitsaye inda motarsa take kirar Benz G-Wagon yanufa da sauri driver din yafito tare da bude masa bangaren back seat,dan rissinawa driver yayi tare da cewa. "Good morning sir! "Morning David hope everythig is Ok? "Yes Sir,David ya amsa dashi yana me yaba kyan da ogan nasa yayi a ransa. Bangaren driver David yashiga tare da tada motar,gate Man ne ya wangale musu gate din kaitsaye David yacilla motar kan kwaltan dake area din. ********** "Ranka yadade dangudelle haba taya zan raina aikinka nida nasanka kasanni shekaru 28 kenan munatare tabbas nasan aikinka yana kyau shiyasa ma koda yaushe nakeda yaqini agareka sam bana wasiwasi akan aikinka. "Hahahahahahahaha! Aka saki dariyar cikin wani murya marar dadi wanda gabadaya sai da sautin dariyar ya amsa dajin,itakuwa Mom banda rawa babu abinda jikinta keyi saboda tayi tasananin tsorata. "Biba kenan nasan abinda yakawoki nakuma san abinda yake tafe dake,yayi maganar cikin wata irin murya marar dadi. "Hahahahaha wannan yaron dakikeson hada 'yarki dashi tabbas hatsabibi ne don kuwa sam baya wasa da azkar,sannan ita yarinyar da akeson yanzu a hadashi aure da ita ba sonta yakeyi ba sai dai tabbas daga baya zaisota ta hanyar asirii....hahahahaha" Yakarisa maganar yana sakin wannan dariyar nasa da muryansa marar dadin ji. "Hmmm dangudelle nasani nasan komai so nake kamun aiki akansa ya birkice akan maganar aurensa da wancan kodaddiyar yarinyar,ajuyar da akalar maganar kan Rammat,don idan har Rammat bazata sameshi ba to itama Akeela bana fatan tasameshi. Wani irin kallo dangudelle yayiwa Biba tare da sakin wani dariya,zuwa can yatsuke fuska yace"tirkashi aiko bazai yuwuba sai dai suyi zaman kishi tare saboda wannan tsohuwar tsaye take akansa don so take da bala'i su mallake yaron. Share gumi Biba tayi tace"nikam yaza'ayi kenan?tabbas Biba itama saita shiga gidan idan yaso daga baya takoreta. Wani dariyan boka dangudelle yasanya yace"lallai yaron dangata ne don a kaddararsa yanuna daga baya da mace daya zaiyi rayuwa tare da yimata wani irin mahaukacin so,don ko ayanzu yana sonta. Dafe kirji Biba tayi cikin tsananin rudewa tace"wacece wannan yarinyar? "Bansanta ba!duk iya kokarina naganin gano yarinyar nakasa amma tabbas itace matarsa uwar 'yayansa,boka dangudelle yakarasa maganar yana diddilo da idanuwa waje. Itadai Mom banda rawa babu abinda jikinta keyi dukda kuwa yanda takejin daci aranta saboda ta tsani Sauban tun randa ta haifi ɗa namiji, saboda yanda Sauban keda kwarjini da farin jinin jama'a sam danta baidashi wannan dalilin ne yasa daga ita har Aseef din suka tsane Sauban. Biba tace"dangudelle so nake duk halin da ake ciki Sauban yafada tarkon son Rammat. "Hahahaha....Ke shedaniya! tabbas kinsan zan iya zanyi abinda yafi haka,yayi maganar yana jawo wani kwarya wanda babu komai sai toka yafara cakuda garin tokan da hannu,cike da al'ajabi hoton Sauban ya bayyana yana zaune a office dinsa. "Hahahaha.. dangudelle yasake sakin wata dariyar yace"Zoki ganshi tabbas yaron yasamu daula. Jikin hajiya Biba dana Mom har rawa yakeyi."Aiko tabbas Sauban ne hajiya,hajiya kinga wani irin office dayake zaune a cikinsa? Kafin hajiya Biba tayi magana dangudelle yadaga hannu tare da shafe tokar,nan take hoton ya bace. "Kutashi kuje tabbas zakuji sakamako mai dadi don yanzu haka na wada da dantsaka da lituwa suna hanyar dawowa daga masar kawon saqo kuje na sallameku". Hajiya Biba na shirin magana kenan dangudelle yabace bat,dole suka mike badon sunso ba kowacce da abinda take saqawa a ranta don Mom ita inda dayanda za'ayi kashe mata Sauban kawai za'ayi. _________**________ Yauma kamar kullum tashinta kenan dai² karfe hudu a dalilin wani mummunan mafarki da tayi wai anyi rasuwa ga mutane nan cike a Galadima fam sai dai bataga gawar ba sosai hankalinta yayi kololuwan tashi,koda tamike bathroom tashige tadauro alwala tafito tare da shimfida praymat tatada sallah. Koda ta idar lokacin anfara kiraye-kirayen sallar farko,sosai tayi addu'ah. Tadauki tsawon mintuna tana lazimi zuwa can aka tayar da sallar asuba don haka sai itama tamike tatada sallar. Acan gidan Guggo Laure kuwa Akeela ce ta tasata agaba wai ranar da akasanya yayi tsayi da yawa ai 'yan kauye ne kecika ranar aure ita gaskiya a rage. Guggo Laure kuwa sai lallashinta takeyi takuma tabbatar mata da cewa suna zaune ma Sauban din da kanshi zaizo yana neman alfarmar a rage. Dan yatsine face Akeela tayi cike da rashin jin dadi a ranta tace"Ni Guggo ina tsananin kishin sa ne wani irin zazzafan so nake masa,wallahi nida da yanda zanyi kan kada yaso ko wacce mace zanyi saboda ina tsananin kishin sa. Dariya Guggo Laure tayi"mekike ci nabaka nazuba 'yannan?kisa a ranki zai soki kedai kidage da kissa da kisisina sannan ki tabbatar da kin jawosa a jiki ya zamana babu macen da yake gani a matsayin mace saike. Dariya Akeela tayi tace"yanda kikajin nan Guggo kuwa sai dai nayi tsananin yarda dasu Suby su kansu zasu tayani shawo kansa. Mere baki Guggo Laure tayi"Hmmm kesam bakisan sharrin kawaye ba koh?ina gargadinki Akeela amma sam bakiji. "Wallahi Guggo basu da matsala don kawai bakisan su bane domin duk suna tsananin sona wallahi. Murmushi Guggo Laure tayi tace"Yaro yaro ne to shikenan Allah ya kyauta. Xahratty CE🥰 Lallai Alqalami 🖊️ yafi takobi🗡️ 25/2/23. [3/21, 22:27] Xahratty (OUM AJMAL): 👨🏽‍🦳 *_GALADIMA FAMILY_*👨🏽‍🦳 Story&Written By *FATEEMA ZAHRA LAWAL* Marubuciyar⤵️ A DALILIN'YAR TSINTUWA. MIJIN ZAHRA. DIAMOND LADIES ( Daukar fansa)paid book. RUHIN AMRITA (FATALWA CE). Now *_GALADIMA FAMILY_* Page 13/14 _Bismillahir-rahmanir-raheem._ ______Ummie abin duniya duk yataru ya mata yawa taje wajan Amma don bata hakuri amma gabadaya taki saurarenta tasake jaddada mata cewa muddin bataja'yarta a jiki ba to tamance itama tana da uwa a raye. Kiran number Aunty Zainab tafada mata duk yacce sukai da Amma,itama fir tarufe Ido tama Ummie sol. Tsakanin Ummie da hajiya Zainab tazarar shekara daya da rabi ne. Haka dai Ummie tadawo gida jikinta sam babu kwari tarasa wanda zataje wajensa suyi magana taji dadi ita ba kawaye ba,a yanzu duk wanda zataje wajensa neman shawara kara mata takaici zasuyi,banda huci babu abinda takeyi a fili tafurta"Natsaneki Zuhra tabbas bacin nice dakaina na haifeki zan iya tsine miki saboda kina daf da rabani daduk wasu masoya na,na haifawa kaina masifa na haifawa kaina jaraba? Sosai hankalin ya Taufeeq yatashi don yana gaf da shigowa parlon yaji zan tuttukan da Ummie keyi, idanuwansa sun kada sunyi jajazur juyawa yayi yafasa shigowa parlon,kaitsaye bq dinsa yanufa a daddafe, Aseef sai masa magana yake amma Ina baiji ba. Da harara Aseef yabishi a fili yafurta"Idiot"cikin murya kasa kasa. ****** Zuhra ce cikin shagwaba da sangarta take latso wasu hawaye mere dan mitsitsin mouth lip dinta tayi tana muttsike Ido cikin muryan son kuka tace"Toh yanzu Abbie idan kuntafi yaushe zaka dawo?ni wallahi bangaji da ganinka ba fah. Dan dariya Abbie yayi tare da shafa kanta yace"zamu dawo azumi mana kinmanta azumin saura 1month?so insha Allah I think sai lokacin zamu sake zuwa. Daddy ne suka kariso shida Abba da Baba Hasheem, Daddy ya dubi zuhra yace"A'ah mamana kema yau zaki koma ne bamu da labari? Dan sinnar da kai zuhra tayi cikin girmamawa tana wasa da yatsunta tace"A'ah Daddy narako su Abba ne da zasu tafi. Dan murmushi sukayi gabadaya Abba yace"hmmm kya fadi gaskiya,Yaya kuka take nema tamaka koh?yakarasa zancen cikin zolaya. Dan rissinawa tayi tadauki ledan dake gefenta tamika ma Abbie tace"Abbie gashi abaiwa Ummie na da mommy,akwai sweet da chocolate na maimoon da Ateek. Abbie ya amsa yace"toh shikenan Allah yamiki albarka. Da Ameen ta amsa tare da matsawa saboda gabadaya sun nufi mota daya motar Daddy kenan da ita zasu fita, Baba Hasheem ne ke driving gefensa kuma Abba ne,sai baya Daddy da Abbie cike daso da kaunar junansu suka fita,zuhra natsaye har Baba mudi yabude musu gate suka fice,hawaye ne ya zubu mata da sauri tasa hannu ta goge,saboda shigowar Aunty muneefa datagani da wasu 'yanmata biyu. Abangaren Abbie shima runtse idanuwa yayi yabude tare da sauke ajiyar zuciya yana mejin tsananin tausayin diyarsa duk Daddy na lure dashi shima girgiza kai kawai yayi,kaitsaye motar airport tanufa. Zuhra murmushi a face dinta tatare Aunty muneefa. "Aunty muneefa barka dama kece?muneefa na murmushi tace"Eah zuhra kwana biyu bananan ina school shiyasa. Haka kawai Zuhra taji sam wacce suke tare da muneefa batayi mata ba don haka ko kallonta batayi ba,a gefen ma haka ne don lokaci daya taji tsanar zuhra ta dirar mata,sake shaqa tayi a dalilin ko inkular da zuhran tanuna mata,yarinya qarama da sanabe,tafadi hakan a ranta. "Dawowata kenan yanzu nabiya gidan Guggo Laure shiyasa ko hutawa banyi ba,murmushi zuhra tayi. "Eyya Aunty nima apartment dinku zanshiga don ko jiya danazo gaida Mom batanan. Muneefa tace"ok muje koh? Dayar ce tayatsine face"Muneefa bari naje nafara miqa gaisuwa ta ga Ammi kafin nadawo. "Kai Allah don Allah kizo muje mu warware gajiya dududu yaushe muka shigo?dayarl budurwar tafAdal Zuhra kuwa ko sauraren su batayi ba tanufi sashen Mom,a kaikace budurwar ta dalla mata harara. Muneefa tace"Don Allah rabu da ita Suby kinsan Akeela da rawar kai. Zuhra kuwa koda tashiga sashen Mom tagaisheta sosai Mom din taji dadi don Allah yadora mata son zuhra tun sanda Ummie ta haifeta sannan takema Aseef sha'awar auren ta. Tana gafda shiga apartment din Ammi Akeela tafito, Zuhra dauke kai tayi kamar bata ganta ba itako Akeela wani banzan kallo ta watsa mata. Koda zuhra tashiga kai tsaye ta nufi kitchen don tasan Ammi tana can,ilaikuwa sunata aiki itada Aunty Mashahuda da maid dinta Amina. Murmushi kwance a face din Ammi ta tarbe Zuhra,dan rissinawa tayi ta gaishe da Ammi. Dan turo mouth tayi alamun shagwaba tare da karyar da wuya tace"kai Aunty shine ko ki aiko nazo nataya aikin?nasan Daddy akema abin shan ruwa. Hararar wasa tawatsa mata sannan tace"Aiba sai nace kizo ayiba keda kanki zakizo"takarisa maganar tana dan murmushi. "Ammi wallahi namanta Daddy yana azumi saboda naje raka Abbie ne shiyasa duk na shagala. Kallon ta Ammi tayi fari'a kwance a saman fuskarta tace"Don Allah kirabu da wannan Auntyn taki,aikinma da sauki don mesa ana masa girke girken bashi nan. Dan dariya kadan zuhra tayi batare da tayi magana ba tafara yanka cabej din dake kan mable din. Mashahuda tace"Hmm ai Yaya akwai shi da iyasa aiki ni wallahi tausayi matar sa kebani. Sallaman su muneefa ne yasasu juyawa gabadaya,kallo daya zuhra tamusu tadauke kai saboda ganin yarinyar nan tadazu. Da murmushi Akeela tamatso kusa da Mashahuda tace"sis kawo in tayaki goge carrot din,dan yatsine face kadan Mashahuda tayi tare da dan sakin yaqe tace"No kada kidamu munkusa gamawa ma ai tunda ga zuhra na gyara cabej. Akeela badon taso ba haka tahakura,ita kuwa Suby gabadaya hankalin ta yakoma kan zuhra faffadan kugunta kawai take kallo( _acewarta_). Muneefa tace"Sis muje kada kuyi magrib, Ammi tasaki murmushi tare da duban Akeela"Akeela ya hajiya maimunan take? Cike dajin dadi tace"wallahi tananan lafiya mommah. Murmushi Ammi tasake saki akaro na biyu tace"to don Allah kigaisheta mungude sosai. "Ai babu damuwa mommah nima fa 'yar gida ce. Ammi murmushi kawai tayi bata sake magana ba,muneefa tace"yee gaskiya ne Auntymmu, Allah dai yabar kauna keda ya SAUBAN! A gigice zuhra tadago tana duban muneefa sai dai kowa hankalinsa baya kanta,wani mummunan faduwar gaba ta tsinci kanta a cikin jin an ambaci sunan Wanda batayi zato ba,a kaikai ce tasake duban Akeela da wasu second's zuwa can ta sauke ajiyar zuciya,aranta tace toni meye damuwa na? Nanfa muneefa tafara magana"Ai wallahi bikin nan haba za'ayi abinda ba'a taba yiba sai ansan anyi biki na jinin Galadima auren ya Sauban ai dole muci uwar sabada. Akeela tace"ai gaskiya za'ayi biki nagani nafada hmmm kudai Allah yakaimu lokacin, mommah muntafi tayi maganar tana ma Ammi bye bye. Daga Zuhra har Mashahuda kallon mamaki sukabi Akeela dashi, Mashahuda tadubi Ammi tace. "Cabdi wallahi Ammi kinsan da matsala Yaya Maison mace mai kunya amma jibi wacce aka bashi matsayin mata?hmm wallahi nidai bana son Yaya ya aureta sam,tayi maganar tana daga hannu tare da nuna iyakacin gaskiyar ta, sauke ajiyan zuciya Ammi tayi tace"please Mashahuda ni bana son kananun zantuka haba abar maganar. "Hmm Ammi kema fa kinsan Yaya be dace da wannan yarinyar b.... "Allah Mashahuda zan saba miki,tayi maganar cikin muryan bacin rai. Itadai Zuhra ko tankawa batayi ba tanata yanka cabej dinta,sai dai hakanan tatsinci zuciyar ta cikin bacin rai lokaci guda. Hakanan taji tayi mugun tsanar Sauban din dashi da Akeela. *******^^^****** Sosai yaqara gogewa da kyau yazama wani classic guy wanda ko a malysia ma 'yan mata rububinsa sukeyi. Yarasa dalilin da yasa yake sake tsanar auren da ake nema a qaqaba mishi itakanta yarinyar bayajin zai iya aurenta duk da kuwa besanta ba. Messenger sane yashigo office din yace"Sir kayi baki. Duban CCTV camera dinda ke office din yayi yana duban mutanen dake Zaune a wajan office din nasa,maido da duban sa yayi ga massenger yace"Miracle who re those people? "I don't know Sir,yayi maganar cike da girmamawa. Dan girgiza kai Sauban yayi tare da cewa"Ok jeka shigo dasu. "Ok Sir,yayi maganar yana fita babu jimawa yashigo da baqin. ******** "Boka so nake a sauko da auren lokacin da aka sanya na bikin nan wallahi yayi tsayi ita kanta yarinyar takosa ace tayi aure tahuta,bari kaji nifa so nake a mallake mana yaron ya zama na bayajin maganar kowa sai nawa,kai yazama mai taurin kan tsiya. "Hahahaha,aka kyalkyale da dariya,wani dan wadan aljani ne wanda sam bayada kyan gani ko kadan kuma daga ganinsa baya da imani yace" _BANADA LAFIYA FANS DON ALLAH INA BARAR ADDU'AN KU👏🏽_ Xahratty CE🥰 Lallai Alqalami 🖊️ yafi takobi🗡️ [3/21, 22:27] Xahratty (OUM AJMAL): 👨🏽‍🦳 *_GALADIMA FAMILY_*👨🏽‍🦳 Story&Written By *FATEEMA ZAHRA LAWAL* Marubuciyar⤵️ A DALILIN'YAR TSINTUWA. MIJIN ZAHRA. DIAMOND LADIES ( Daukar fansa)paid book. RUHIN AMRITA (FATALWA CE). Now *_GALADIMA FAMILY_* Page 15/16 _Bismillahir-rahmanir-raheem._ PLS KUTAYANI DA ADDU'AH MASOYA ALLAH YAKARAMIN LAFIYA DON CIWO YASANI GABA SHIYASA KUKA JINI SHIRU KWANA BIYU BANJIN DADI, NAGODE SOSAI DA SAKONNIN GAISUWAR KU MUSSAMMAN MA KE *MAMAN HEELAL* KEDIN TA DABANCE. _____Zuhra ce zaune a parlon Bodejo tana yimata massage,sallamar Baba mudi gateman sukaji a bakin kofan parlon,amsawa sukayi inda Bodejo tabashi izinin shigowa. Cike da girmamawa ya rissina yace"Barka da warhaka Bodejo,inayini ina gajiya? fuskar ta kadaran kadahan tace"yauwa mudi lafiya Alhamdulillah ya kuma aiki? Baba mudi yace. "Alhamdulillah! Dama wani yaro ne a waje yazo yake cemin don Allah nakira masa Fateema. Cikin natsuwa Zuhra tadago tadubi Bodejo itama ita take kallo,maida dubansa tayi ga Baba mudi tace"Fateema kuma mudi?wa Fateema tasani a garin nan har zai aiko akira masa ita? Tayi tambayar cike da mamaki. "Wallahi kuwa Bodejo bansan shi ba nidai yanata roqona kan nakira masa ita. "Ikon Allah ko wanene haka oho?tashi kije kiji ko wanene. Dan tsamm Zuhra tayi tare da dan bata face tace"nikam bazani ba Bodejo wallahi bansan shiba kawai ina zaman zamana ya wani kirani? Takarisa maganar tana kokarin shiga hanyan corridor din Bodejo,sakin baki Bodejo tayi tana duban Zuhra,kallon Baba mudi tayi tace"shikenan mudi kace tana zuwa. Mikewa yayi tare da fita,murmushi kawai Bodejo tayi tana kokarin mikewa ne sai ga Mashahuda tashigo,dan gaida Bodejo tayi sannan tace. "Bodejo ina Zuhra ne tundazu Shuraim yazo nemanta Baba mudi yace yazo ya kirata amma taqi fitowa. Dan tabe mouth Bodejo tayi"Toh ni ina nasanin mata,bansan me take nufi ba,wanine shuraish?dan gwalo idanuwa Mashahuda tayi"kaji Bodejo kuma da bata suna bafa shuraish ba Shuraim ake cewa. "Uhum kudai kuka sani da wani iyayi da sanabe abinda dai nafada shikika maimaita. Rausayar dakai tayi kaitsaye ta nufi bedroom din Bodejo. Koda tashiga kwance taga Zuhra sai daddanna phone nata take hankali kwance,ganin Mashahuda yasa tamike cike da fara'a a fuskarta tace"Aunty Mashahuda kece? Hararar wasa ta zabga mata tace"kyace mana nice tun dazu mutumi yazo nemanki kina wulaqanta sa haba Zuhra menene haka? "Aunty nifa bansan shiba bansan koshi wanene ba akan me zan fitan masa?shiyasa ma ban fitaba,takarisa maganar tana dan babbata fuska. Itama Mashahudan bata fuska tayi tace"Lallai ma yarinyar nan kinci uwar rainin wayo to Shuraim ne yazo kitashi kuje ku gaisa mana. "Shuraim! Zuhra ta maimaita sunan alamun bata ganesa ba tace"Aunty ni bansanshi ba. Mikewa Mashahuda tayi tare da fita tace"idan kinje wajen ai zaki gane wanda nake nufi,takarisa mgnr tana barin dakin. Tsuru tayi tana bin kofan da kallo tadau kusan 6 minute's a zaune kamar wacce aka dasa,zuwa can tasauke ajiyar zuciya tare da mikewa,closet din ta tabude taciro wata Dubai gown mai taushi wanda yaji wasu irin flower's maroon colour,sannan tasaka viel din tayane kanta dashi,flat shoe baqi tasaka batare da tamurza ma kyakkyawan face dinta komai ba tafito parlon, Bodejo ta taras a zaune tana kallon Africa TV 3 dan sunkuyar dakai tayi like munafuka sum sum tafice. Cikin sanyin jiki take tafiya kamar mejin tausayin kasa acan gefen apartment din Ammi ta hango Mashahuda da wani don bata ganesa ba saboda ya juya mata baya,a hankali take tafiyar har ta isa inda suke zaune,sallama tayi cikin zazzaqar muryanta mai sanyi da dadi,da sauri yadago don jin muryanta. Da mamaki Zuhra take dubansa a hankali tace"Yaya dama kaine? murmushi kwance akan fuskar Shuraim yace"Ea nine Zuhra. Dan tsamm tayi tare da duban Mashahuda,mikewa Mashahuda tayi tare da duban Shuraim tace"bari nashiga na fito kafin ku gama gaisawa,sake fadada fara'a Shuraim yayi tare da cewa"Allah yafito dake lafiya Auntymmu,zuhr kuwa sakato tayi tana duban Mashahuda har tashiga parlon su,ajiyan zuciya ta sauke saboda muryan Shuraim da taji yana cemata ta zauna. Karasawa tayi kujeran da Mashahuda ta tashi ta zauna,dukar da kanta tayi kasa tafara wasa da yatsun hannunta. "Babu gaisawa ne Zuhra?Shuraim yace. Cike dajin nauyi da kunya cikin sanyin muryanta tace"eyya ba haka bane wallahi yaya don Allah kayahakuri, inayini? "Sai dana roka?yayi maganar still murmushi kwance saman fuskansa. "Kayahakuri,tasake maimaitawa cikin sanyin muryanta. "Lafiya lau Alhamdulillah ya kwana biyu? "Lafiya lau wallahi. "Ashe anata shirye-shiryen school ne?to Allah yabada sa'a Aunty Mashahuda take fadamun. Zuhra tace"Ea anata shiri munkusa fara zuwa school tafada cike da murna da zumudi murmushi kwance saman fuskanta,daidai nan Baba mudi yafara wangale gate,hancin mota ne ta shigo kirar Corolla ( _da take bansan kan motoci ba amma motar daga gani medan tsada ce._ ) duk cikansu maida dubansu sukayi kan motar,shikuwa tun sanda yashigo gidan idanuwan sa ke kafe a inda suke zaune,sosai yaji zafin ganinta da wani,balle murfin motar yayi ya fito,dole idan zai shiga apartment din Ammi ta gabansu zai wuce,koda yakariso fuskar sa a sake yake dubansu,mikawa Shuraim hannu yayi sukayi musabaha tare da cewa"Barka da warhaka.Duk da cewa ya girmi Shuraim din sosai ma don Shuraim ai sa'an kaninsa ne na biyu kuma akwai tazarar shekaru tsakanin su. Duban Zuhra yayi face dinnan cike da fara'a yace"kanwar mu bako akayi ne haka?dan rissinar da kai tayi tace"sannu da zuwa ya Kareem,cikin fara'a yace"yawwa mun sameku lafiya?ya shirye-shiryen school Kuma? Zuhra tace"Alhamdulillah. "To Allah yabada sa'a! A takaice ya fada. Da Ameen duk suka amsa. Wucewa yayi. Duban Zuhra Shuraim yayi yace"Ina me neman gafarar ki akan maganar da nazo miki dashi bansani ba dai ko zaki iya amincewa dashi? Zuhra tace"me kenan ya Shuraim? "Idan babu komai inaso kibani wani matsayi da wajen zama a jerin masu kula dake,cikin rashin fahimta take dubansa. Gane bata fahimci abinda yake nufi ba yasa yace"kibani matsayi na yayanki muzama Yaya da qanwa nidake don Allah. Murmushi tayi tace"Kai Ya Shuraim nina dauka wata magana ce,haba ai babu komai nabaka wannan matsayin Yaya. "Masha Allah kanwata godiya nake Allah yasaka da alkhairi. "Ai babu komai Yaya ta fada cikin sanyin murya,nan suka cigaba da hirarsu don Zuhra sosai ta sake da Shuraim. ** *MALAYSIA* ** Yauma kamar kullum shirinsa yayi yafito cikin suit blue black,takalminsa kamfanin Gucci ne dai cover shoe black colour sai agogon hannunsa Rolex,Kai tsaye driver yaje yabude masa back seat yashige shikuma yaja motar, gaisheshi gateman yayi sannan suka fice, laptop dinsa yafara daddanawa yana duba saqonni ta email daga wasu kasashe da dama nason takalman company nasu, wayar sace tafara neman agaji. Sai da yadau lokaci yana ringing kafin yakai hanny yadau wayar,sunan Kareem ne ya bayyana akan screen din,cikin kamewa ya dauki wayan batare da yayi magana ba,sallama Kareem yayi. Amsawa Sauban yayi nan suka fara gaisawa inda Kareem keta masa shikiyanci zuwa can yace"yawwa dama kira nayi na sanar dakai wani abu don kaine babban Yaya, kuma babban wa uba. "Malam katafi maganar ka kaitsaye, yafada cikin kamewa. "Dama akan kanwar ka nakira muyi magana don naga iri ina nema don alamu sun nuna idan banyi da gaske ba za'a mun shigo² ba zurfi,kai nifa idan na so samune ma a hada bikin mu tare. "Akan wa kake magana kenan? Sauban yayi maganar wanda ko driver din ba lallai yaji abinda yake cewa ba. Kareem yace"Akan zuhra mana nake magana gaskiya ni nagani inaso asan yanda za'ayi dani dazu na ganta da wani karamin yaro sa'an kabeer dinmu ne ma dagani wannan yaron wai yazo zance,so please ga dan gida nan. Lumshe idanuwana Sauban yayi tare da kwantar dakai dakai a jikin seat din motar wanda duk kwakwanka bazaka gane yanayin da yake ciki ba yace"menene haka Kareem?so kake ka zubar mana da mutumci yarinya karama tanemi ta raina mu?look gaskiya kada ma kafara wannan tunanin,guda nawa take wannan yarinyar neman zubda mana da mutumci gaskiya ban goyon bayanka",yayi maganar cikin kwanciyar hankali. Daga can bangaren Kareem kuwa baki da hanci yasaki yana sauraran Sauban sai da yabari yakai aya sannan yace"Nikam Sauban gaskiya bazan iya da wadannan halayyan naka ba menene aciki? "Komaima! Sauban yafada a takaice,a zafafe ya kuma cewa"inbanda jawo raini ina kai ina kula wannan kwailar yarinyar?yana gama fadar haka ya yanke kirar. Cigaba da danne dannensa yake a laptop din wanda sam baka isa ka karanci yanayinsa ba. Ta bangaren Kareem kuwa mamaki sosai ya gama rufeshi da halayyan aminin nasa shisam yafiye son girma da rashin son raini. ( _A daiji maganar babban Yaya Kareem don shine madaurin auren zuhra._ )😜 A haka suka isa babban company wanda gabadaya ma aikatan wajen sai girma suke bashi. **** *KADUNA JABI ROAD* Ummie ce zaune akan lumtsememen leaderseat din dake parlon ta kafa daya kan daya tana duban tashar aljazeera, Abbie ne yayi sallama tare da shigowa a hankali tadago tadubesa dan murmushi tayi tace"Sannu da zuwa yallabai. Murmushi Abbie yayi cike da zolaya yace"Yauwa yallabiya,zama yayi kusa da ita da yake cushion din two seater ne cike da gajiya yace"Am tired Madam. Dan dariya tayi tace"Toh bari naje na hada maka ruwa kayi wanka zakaji dan dama then sai kaci abinci kadan kwanta stressed ne kwana biyu baka zauna ba yallabai gashi jibi zaka tafi Indonesia. "Wallahi kuwa akan furnitures din su Mashahuda nakeso naje kinsan bikinsu 6 month akasa su ita da muneefa, shiyasa ma nakeso muje tare nida ke mu zabo musu kaya masu kyau,harda kayan kitchen. Ummie tace"iyye lallai Abbien yara ya shirya to shikenan Allah ya kaimu amma bazamu kawo komai gida yanzu ba ko? Abbie yace"to me za'a tsaya jira Bilkisou ai gwanda a kawo komai nasan kilama kayan su rigamu isowa. Kafin kuma na auta na yazo Allah yanuna min auren ta. Da Ameen Ummie ta amsa a maqoshi. Dan girgiza kai Abbie yayi yace"Bilkisou kenan Allah ya karkato da hankalin ki kan diyar ki. Cike da kwarin gwiwa Ummie ta amsa da Ameen,da mamaki sosai Abbie yadube ta saboda jin ta amsa cike da confidence. Ummie ta dubeshi murmushi kwance a fuskanta mai Kama da yaqe tace"kana mamaki koh?hmmm nima inason Zuhra sai dai tsanar da nake mata ya ninka son da nake mata,ina tsananin jin tausayin ta amma ya zanyi narasa meke damuna,takarisa maganar cikin raunin murya. "Huhhhh!Abbie yasauke ajiyar zuciya yana dubanta,zuwa can yace"Bilkisou bana fatan zagin da yakeyi yazama gaskiya. Cikin rashin fahimta Ummie ke dubansa. "Ea ina zargi,alamu suna nuna kamar akwai sihiri tsakanin ki da Zuhra. "Koh? Ummie tayi tambayar. "Kwarai da gaske, bilkisou inaso kisani bana fatan na mutu banga kin daidaita da Zuhra ba. Sosai gaban Ummie ya buga hankalinta yayi kololuwan tashi. ( _Duk da kin kasance Mai biyayya akan wannan abin kinkasa wa mahaifinki biyayyaaaaa._ _To bari kiji wallahi wallahi Ina sake jaddada miki muddin baki shiga hankalinki ba Bilkisou bazan taba yafemiki ba._ ) Kalaman Amma ne suka fara dawo mata a kwakwanta hankalin ta yasake tsananin tashi duban Abbie tayi idanuwan sa a rufe tace"Don Allah kadena fadamin haka kana tayar min da hankali na insha Allahu everything will be fine. Mikewa yayi jikinsa sam babu kuzari yanufi stairs,hawaye ne masu dumi suka tsiyayo ma Ummie. *_ADDU'AN DAI SHINAKE BUKATA NAGODE SOSAI MASOYA DA WADANDA SUKA KIRA DAMA WADANDA BASU KIRANI BA SON SO FISABILILLAH 🙏🏽 Happy birthday to you my rabin jiki baby Yusuf (Ãjmãl) Allah yaraya ka ya shiryaka yabaka ilimi Mai amfani da albarka ubangiji Allah ya albarkaci rayuwar ka Yusuf Imran Muhammad bature❤️🦋🔐_* Xahratty CE🥰 Lallai Alqalami 🖊️ yafi takobi🗡️ 07/3/23. [3/21, 22:27] Xahratty (OUM AJMAL): 👨🏽‍🦳 *_GALADIMA FAMILY_*👨🏽‍🦳 Story&Written By *FATEEMA ZAHRA LAWAL* Marubuciyar⤵️ A DALILIN'YAR TSINTUWA. MIJIN ZAHRA. DIAMOND LADIES ( Daukar fansa)paid book. RUHIN AMRITA (FATALWA CE). Now *_GALADIMA FAMILY_* Page 17-18 _Bismillahir-rahmanir-raheem._ ______A kwana a tashi babu wuya after 1 month da satittika gashi zuhra jibi zata fara zuwa school(UNIMAID) sosai take jin dadi da annashuwa gashi gefe guda kuma suna tsananin mutumci ita da Shuraim da yake shi mutum ne mai barkwanci sosai duk da haka ZUHRA takasa sakemai ssai. A bangaren Kareem kuwa hakan ba karamin sosa mai rai yake ba don yanason ZUHRA tun randa yayi tozali da ita suna zaune da Shuraim yaji yana tsananin kaunar ta,wannan kenan! "Hajiya kefa kika ce zakiyi wani abu gashi wasa² anci 2months da saka ranar auren su yanzu saura fa 6 months, Rammat tayi maganar tana latso hawayen da suke gangaro mata. Itakuwa banda girgiza kafa hajiya Biba babu abinda takeyi, Mom tadan mere baki tana duban Hjy Biba"Ni kam hajiya anya aikin malamin nan naki kuwa yanay........ "Ke...k..kke ke...keke kul! Meye haka rabi nema kike kidebomin tafasashen ruwa mai dafa duk taurin nama?ki rufamin asiri kinsan kuwa aikin dangudelle na yarda dashi na yarda da aikinsa,saboda shidin shedani neeeee takarisa maganar tana wani rimi dolen dole na hada zuri'ah da Galadima da wannan makirar tsohuwan Bodejo,inaso na bawa Laure mamaki tasan cewa ni nafita hatsabiban ci wallahi dani take zancen. Duban Rammat tayi wacce take kukan cikin takaici tace"dallah ke kimin shiru,sai kace kema din ba mace ba?yanzu ke ba zaki iya jawo hankalin yaronnan gareki ba?meye amfanin macen da bata iya kissa ba kwata²n ta? hajiya Biba takarisa zancen tana huci tare da babban kada hanci. "Hmmm aini Rammat wani takaici take bani hajiya,ga Akeela nan tanaji tana gani zata kwace mata shi. Dan bata face Rammat tayi"Kai Aunty fatan tsiya haka? Wani hararan Mom ta galla mata tare da mikewa ta dauki jakar ta duban hajiya Biba tayi"Hajiya zantafi bnson baban Aseef yadawo yaga bana a gida,Kinga ba'asan na fita ba. Hajiya Biba tace"shikenan sai munyi waya,nan sukayi sallama tafita a ranta da qudurori kalakala,don ta dauki alwashin koda Rammat zata mutu ba zata yarda ta aure Sauban ba. **** **** **** Zaune take a cikin class din suna sauraren lecturer din English don da abinda aka fara tarbansu kenan sosai ta maida hankalinta akan lecture dinda ake musu,sanye take da Arabian gown coffee tayi rolling viel din sosai tayi kyau fatanta kalar half-caste yasake bayyana,duk da sanye take da facemask amma sosai taja hankalin 'yan class din. Yadauki tsawon 20minutes yana musu bayani sannan yafita anan wani lecturer din yashigo yadauki 10 minute's kana yafita,na ukun ne yadauke fifteen minutes kuma daganan wajejen 11:30 suka fito daga lectures gabadaya, student's da dama sun sami bakin department dinnasu suna hira wasu na introducing kansu ga juna saboda asaba. Zuhra kuwa kaitsaye gate tanufa don tafiya gida,tare da wasu daliban da qyar tasamu napep tahau dropped yakaita gida,cike da gajiya ta shiga gidan kaitsaye apartment din Ammi ta nufa. Moryoyi ta fara jiyowa na 'yan mata koda tashiga parlon Aunty muneefa ne da Akeela,kan dinning kuma Aunty Mashahuda. Cike da fari'a muneefa tace"A'ah students,yau UNIMAID sunyi sababbin dalibai. Dan murmushi kawai Zuhra tayi tana karisawa wajen Mashahuda dake dinning,itama cike da zolaya tace"Wai yau 'yar gidan Ammi akwai rigima. "Kai Aunty Mashahuda nifa ban gaji ba,dudu lecture's uku mukayi muka fito, takarisa maganar cikin shagwaba. Ammi da saukowan ta kenan daga stairs tace"toh mene idan anmata tausar si auta ce,duk gidan nan itace auta yimata shine zaman lafiya. Cike da tsananin jin nauyin Ammin zuhra ta duqar da Kai tana murmushi,dariya mashahuda ta saki tace"Ammi kinga zuhra wai kejin nauyinki. Murmushi Ammi tayi dai-dai nan wayanta yasoma neman agaji, duban number tayi tare da sakin murmushi tayi picking. "Assalamu alaikum Son. Daga can bangaren Sauban ya lumshe ido cikin tsananin son Ammi yace"Sweetheart barka da rana. Murmushi kwance akan fuskanta tace"barka dai yakake ya aiki? Alhamdulillah Sweatheart jiya inata kiran number dinki yaqi shiga na Daddy ma haka nakira na Mash'huda kuma number busy tanata waya. Ammi tayi dariya me sauti tace"itada taufeeq ne nasani to ya aikin? Alhamdulillah,nima I think nanda sati biyu zan shigo zarian saboda branch dinmu na Abuja zanje naduba. Cikin jindadi Ammi tace"Masha Allah son Allah yakawo min kai lafiya cikin aminci da yardarsa. Cike da jin dadin addu'an ta ya lumshe ido yace"Ameen Sweatheart yasu Mom? don nayi waya dasu Bodejo. Ammi tace"lafiya lou Mom dinku ya kamata kkrata koh? "Ea Insha Allah haka za'ayi. Kana waya dasu Ummien naku da Abbie? Dariya mai sauti Sauban yayi wanda inba Ammi ko su Ummie dasu Bodejo ba bame ganin irinta yace. "Ahhhh kaji Sweatheart sosai ma muna waya dasu. "Yawwa son haka akeso Allah yamaka albarka. "Ameen Ammi sai anjima a gaida yaran gidan. "To Shikenan tafada tana me zare wayar daga kunnenta. Cike da zumudi muneefa da Mashahuda ke tambayar ta ya tambayesu? Ammi tace"kowa ma ya tambaya ya kuma ce a gaida kowa don nanda sati biyu zaishigo kasar. Akeela kuwa wani kululin bakin ciki dana takaici ne suka dirar mata ganin ko damuwa bai nunawa akan ta,kamar ma yamance da ranar wata akansa,hakan yasa cikin bacin rai ta tattara kwamatsanta tabar parlon,babu wanda ya lura da ita sai Zuhra,sai dai ita hakan ko a gyalen ta dan tabe mouth ma tayi. *BAYAN SATI DAYA* Zuhra ce zaune da ita da Shuraim suna hira cike da nishadi don Allah yabawa Shuraim nasarar samun Zuhra don sosai ta sake mishi. Cikin muryan dariya tace"Yaya to idan kasamu balarabiya bazaka iya auren ta ba? "Hmmm yarinya bazaki gane ba,nifa yarinyar da nakeso ko a larabawan ba lalai a masu mai kyanta da quality dinta ba,kedai kibari wataran zaki ganta. Cike da shagwaba Zuhra tace"Lallai ma yayan nan naqi wayon,kawai dai kasa ma mana lokaci wataran kakaini naganta. Zuhra tace"To shikenan Allah ya kaimu. Da Ameen ya amsa yana mejin wani nishadi a ransa na yanda yaga yarinyar tayi bala'in sake masa. Baba Mudi ne ya bude gate saboda horn din da aketa dokawa,ko gama bude gate din beyi ba aka shigo da motar a zafafe, cikin bacin rai ya balle murfin motar ya fito kaitsaye wajen Baba Mudi ya nufa,cikin rashin da'a yafara magana. "Meyasa kake hakane tsohon nan?tunda nataso a gidan nan kai nake ganin matsayin me gadi gashi karfinka yafara karewa,don Allah katafi kabawa me jini a jika shima daman shigowa ya daddale arziqi mana, mtsewwww. Yaja tsaki,shigo Baba mudi girgiza kai kawai yayi a zafafe ya nufi apartment dinsu. Dan siririn tsaki zuhra taja. "Yayadai?shikuma wancen wanene? Zuhra tace"Hmmm barshi cousin dina ne haka yake duk gidannan shine Mara da'a shine wanda baiganin darajar talaka. "Allah yakyauta ubangiji Kuma ya shiryeshi,da Ameen zuhra ta amsa,anan suka cigaba da hirarsu. "Mom Wai dagaske ne?nifa bansamu labari ba sai shekaran jiya dana ga pic dinshi a IG yanda 'yan mata keta rushing akansa har fada wasu sunayi,baya kasarnan to waya sama masa aiki? Mom tace"bansani ba,hmmm burika na biyu basu cika ba don haka bazanyi sake shima na ukun yaqi cika ba. Aseef yace"wasu burika kenan? Mom tace"naso ace ko Sauban ko taufeeq daya a ciki ya aure Muneefa amma gabadaya babu wanda yasamu,abin bakin cika wai Sauban yafika,nifa bana fatan rayuwar wanda zaifi dana ko wanene shi,shiyasa kota halin kaka sai ka aure Zuhra,takarisa maganar tana wani huci. Wani irin sanyin dadi Aseef yaji a ransa. "Ga sa ranar auren sa da akayi kasani ai koh? "Nasani Mom sai dai hakan bedameni ba don sanin wacce zai aura ba kowa bace face bunsura,ai mom idan Sauban ya aure akeey beb ai yaci baya. Mom tace"Toh meya shafeka da cin bayansa?idan yaso ma yaci uban baya,don kullum ni burina kenan dan iskan yaro. Sallama Baba Hasheem yayi ya shigo. Amsawa sukayi nan suka fara yimasa sannu da zuwa,sosai baba hasheem yaji dadin ganin Aseef"A'ah mutanen kaduna yaushe Kuma aka iso? Dan sosa kai Aseef yayi yace"wallahi Baba yanzu bandane da shigowa ba. "Ok to ya kabarsu Kuma? "Lafiya lou wallahi Baba,dama nace Bari nazo na duba ku kwana biyu bamu shigo ba. "Kashiga wajen su Galadima? "A'ah yanzu zanshiga dai. Alhaji kenan to inbanda abinka zaiki shiga ne?dole dai yafara gaisheni tunda nice na haifi abina. "Gaskiya ne wannan,abinda Baba Hasheem yafada kenan yamike yashige corridor din bedroom dinsa. Cikin farin ciki Aseef ya dubi Mom "Please Mom da gaske zan aure zuhra saboda gaskiya yarinyar tayi kota ina! Mom tace"na taba maka wasa ne Aseef? Girgiza kai yayi da sauri. ******** "Kai gaskiya naji dadi Allah yama Bashir albarka ubangiji yasake hada kawunan su, Bodejo ke mgn. Daddy face dinshi dauke da murmushi yace"Ameen ai gabadaya kayan na 15 millions ne yahada musu babu abinda bai siya musu ba har kayan kitchen. Baba hasheem yace"Allah dai yasaka ma Yaya da alkhairi. Da Ameen gabadaya suka amsa, Galadima yace. "To yaushe zasu dawo? Daddy yace"insha Allah yace"kaitsaye ma gobe nan zai iso don yanason ganin Zuhra. Dariya Bodejo tayi tace"Kai sadeeq na sangarta yarinyar nan matuka. Dariya duk aka sanya. Washegari wajejen bayan magrib Daddy ne da Ammi ke zaune sunayin lunch,wayar Daddy ya nemi neman agaji,da sauri ya dauka Yana murmushi saboda sunan Abbie da yagani,sallama yayi. Nan aka fara magana tacan bangaren. "Eah nine lafiya kuwa?Ina me wayar yake ne?daga can bangaren aka sake magana. A gigice Daddy yamike yana furta" _INNALILLAHI WA INNA ILAIHIRRAJI'UN_,Ammi ma mikewa tayi tana Daddyn yara lafiya kuwa? "Sadeeq!Sadeeq!! Aisha Sadeeq yayi hatsari shida bilkisou. "Innalillahi wa Inna ilaihirraji'un a lokacin ne Baba Hasheem yashigo shima apartment din Daddy cikin rudu"Yaya!Yaya!! Dagaske ne? Wani yunkurawa Daddy yayi cikin jarumta ya nufo Baba Hasheem,Kama hannunshi yayi. _YANZU FA WASAN ZAI FARA MASOYA GALADIMA FAMILY_💃💃💃💃 Xahratty CE🥰 Lallai Alqalami 🖊️ yafi takobi🗡️ 13/3/23. [3/21, 22:27] Xahratty (OUM AJMAL): 👨🏽‍🦳 *_GALADIMA FAMILY_*👨🏽‍🦳 Story&Written By *FATEEMA ZAHRA LAWAL* Marubuciyar⤵️ A DALILIN'YAR TSINTUWA. MIJIN ZAHRA. DIAMOND LADIES ( Daukar fansa)paid book. RUHIN AMRITA (FATALWA CE). Now *_GALADIMA FAMILY_* Page 19/20 _____A gigice suka nufi apartment din Galadima a dai-dai nan wayar Daddy yafara ringing, cikin rudewa ya dauki wayar,daga can bangaren aka fara magana. "Alhaji Taufeeq majinyacin yana cikin wani hali don sai sunan ka yake ambata yana cewa kazo. Bakin Daddy yana rawa ya dubi Baba Hasheem yace"Hashim mutafi asibitin ko kasan ko wane asibiti ne? Baba Hashim yace"sun sanar dani muje kawai nan suka nufi motar Baba Hashim. Tsananin rudewa kuwa Mashahuda tashiga don duk abinda ke faruwa akan idon tane da tsananin gigita tashiga apartment din Bodejo tana Kiran sunanta. Bodejo dake zaune tana shafama Galadima man zafi a kafa ta dago tana cewa"ke kuwa Mashahuda wani irin Kira ne kikeyimin haka mai gigitar wa? A rude takariso tara da durqushewa a gabansu tana sauke numfashi akai-akai. "Bodejo Daddy sun tafi asibiti yanzu aka kira a waya Abbie da Ummie sunyi accident a hanyarsu ta tahowa daga airport. "Innalillahi wa Inna ilaihirraji'un wane Abbie din? Bodejo tayi maganar tana gyara zanin ta da yake neman sabulewa. Galadima yace"natsu Mashahuda kiyimana bayani. Nan Mashahuda ta sanar musu da duk abinda ke faruwa a lokacin ne Kuma Ammi, Mom,muneefa da yaseer suka shigo parlon. Cikin muryan tsawa Ammi tace"menene haka Mashahuda waya aikoki?haka ake fadan sako. Daga musu hannu Galadima yayi cikin muryan dattaku yace"duk ku zazzauna. "Innalillahi wa Inna ilaihirraji'un!!! Kalmar da Bodejo take ta fada kenan,hankalin ta yayi kololuwan tashi ga tsufa ga rudu,sai da Ammi da Mom suka kamata suka zaunar da ita. GALADIMA wayansa yaciro yafara neman layin Daddy,sai dai ba'a daukan kiran,maida kiran yayi ga Baba Hashim ba'a dau lokaci ba tadauka,cikin kamewa Galadima yayi sallama. Daga can Baba Hashim yadauka saboda a rude yake don muryansa har neman disashewa tayi saboda kuka. "Hashim lafiya meke faruwa ne? "Galadima ga munan dawowa yanzu,yakarisa maganar muryanshi na rawa. "Mekefaruwa ne anan ina tamabayar ka meya same abubakar?fashewa da kuka Baba Hashim yayi yace"Allah yadauki rayuwansa wanda yafimu sonsa ya amshe abinsa Galadima.Runtse ido Galadima yayi batare da yasake magana ba yakashe wayan. Cikin daburcewa Bodejo tace"malam meyasame abubakar din? "Gasunan a hanyar dawowa gida,amsar da yabata kenan a takaice. Dai-dai nan Zuhra tashigo parlon sai dai babu wanda ya lura da ita. "Don Allah malam kamin bayanin meya same dana abubakar? Bodejo tafada tana me fashewa da kuka. Sukansu su Ammi hankalinsu a tashe yake. "Kuyi masa addu'ah Allah yakarbi rayuwarsa, Allah yamasa cikawa......wani irin kara da aka kwala ta bayansu yasasu gabadaya juyawa. Zuhra ce a take anan tafadi sumammiya. Innalillahi wa Inna ilaihirraji'un!!!!shine kalmar da gabadaya 'yan parlon ke ambata cikin tsananin rudewa, Ammi dasu mashahuda suka nufo wajen zuhra. Mom da Galadima suka nufi Bodejo saboda wani jiri da yadauke ta tanemi faduwa. 9:11 Kafin kace me gida yacika tam da jama'a bakajin komai sai tashin koke-koke na mata don ankawo Abbie gida,daga Daddy har Baba Hashim a gigice suke,me dauriyan ma Galadima ne. Makota duk sun cika gidan,ana haka sai ga Abba dasu mommy tare dasu Laila duk sun iso saboda shima sanda sukayi accident din ankirashi kaitsaye asibitin yanufa yacidda ai dan uwanshi yarasu sun nufo gida. Duk Wanda yaga ahalin nan a daren nan sai yayi musu kuka saboda tausayi, Zuhra kuwa tana apartment din Ammi ankira family doctor dinsu yaduba ta tare da samata drip da alluran bacci,saboda wasu sunbatu da mimmikewa da tafara. Gawar Abbie kuwa a daren suka shiryashi tsaf sai gobe karfe tara na safe za'a kaisa(kwanan keso,ake cewa Koh?🤔). Bodejo fifita su Mom ke mata saboda ta rude. Su Daddy kwana sukayi suna ma Abbie karatun kur'ani, taufeeq shikan shi a gigice yake yafita daga hayyacinsa. Washegari zuwa karfe takwas Galadima family yacika tam da jama'a dangi da masoya da makota,don abokan Abbie nanan Mai din da kaduna da yawa suna wajen, Maryam na Lagos ma ta iso abinka da jirgi itada mijinta da yaranta,labeeba dai suna hanya 'yan Canada. Mahaifiyar Ummie da kannenta maza Suma sun iso da hajiya Zainab. Duk Wanda yaga Zuhra sai ya tausaya mata saboda yanda takoma a kwana daya kawai ta gigice fuskarnan tayi jaa idanuwanta sunyi luhu luhu,mommy ce da Aunty Maryam rike da hannunta suka nufi babban parlon Galadima inda gawan Abbie take,mutane ne cike a parlon ana masa addu'ah,sallama sukayi suka shiga da ita,kowa hankalinsa yadawo gareta,dukar da ita Aunty Maryam tayi gaban gawar,dai-dai kunnenta ta mata magana"Banda kuka kinji? addu'ah zaki masa. Hawaye ne masu zafi suke rige-rigen zubo mata,hannunta na rawa tadan bude fuskan Abbie. Fuskan nan banda sheqi babu abinda yakeyi don zaka zata murmushi ma yakeyi kamar kace masa ya tashi. "Allah yajikan ka Abbie, Allah yagafarta maka ubangiji yamaka rahama, Allah yasadaka da mala'ikun rahama Abbie,kaine uwana kaine ubana wanda yafini sonka yadauke ka a lokacin da nake tsananin bukatan ka, Allah ne gata na kaine gatanaa.....takarisa maganar tana fashewa da wani irin kuka. "Abbie halinka nagari yab.....numfashinta ne yafara seezing da sauri Mommy ta kamata suka fita,kowa cike da tausayin ta yabita da kallo,anan aka fito da gawar. Nan fa gida yasake haumutsewa da koke-koke na mata, Laila ma atake anan ta fadi ta Suma garau. Guggo Laure da shigowan ta kenan da jiniyar kuka tafara"wayyo Allah mutuwa me yasa zaki Mana haka?me zesa kidaukar mana yaron kirki?ga sauran can,sai kika tafi mana da mai hakuri. Takarisa maganar tana Jan majina. Allahu akhbar kullu nafsin za'ikatul maut,duk Mai rai sai ya dandani dacin mutuwa Allah yajikan Abbie 🤧 Sai wajen la'asar ya taufeeq da Kareem da wani kanin Ummie suka daukota daga hospital sosai ta galabaita itama sannan mutuwan Abbie ba karamin girgiza ta yayi ba,takasa mance maganganunsa wadanda sosai su sukafi tasiri a zuciyar ta( _Bilkisou inaso kisani bana fatan na mutu banga kin daidaita da Zuhra ba._ ) sosai wannan maganar yake dawo mata a kai saboda sosai tafara tsorata da lamarin nata ita kanta hakan yasa hawayen idaniyar ta suka gaza tsayawa. Ammi ne da Mommy da Mom suka kariso tare da kama Ummie kaitsaye apartment din Abbie nanan suka nufa don su Amma da hajiya Zainab suna can zaune. Zazzabi ne me zafi ya saukar ma Zuhra saboda kukan da tasha gashi har muryanta ya dishe,mijin Aunty Safeena da mahaifiyar shi sai yayyen shi mata su biyu sunzo don Shuraim ma yajawo su a motar,su kansu sun tausaya ma ahalin musamman ma Zuhra don da alama Abbie irin mutanen nan ne masu tsayawa a rai. Koda Zuhra tafito don su gaisa da Shuraim kasawa tayi saboda kukan da yaci karfinta,ga abinci da sam ba cinsa take ba. Tabbas Galadima jarumin tsoho ne don kaf 'yayan sa yafisu dauriya kukan zuci kawai yakeyi wanda kowa yasan yafi na fili azaftarwa da radadi. A ranar Aunty Labeeba itama ta diro da mijinta sosai fa gida ya cika. *MALAYSIA* Sosai yashiga rudu da tashin hankali da rasuwar Abbie din,don har Saida zazzabi me zafi yanemi kwantar dashi,duk da a bayyane ba lallai ka fahimci hakan ba. Sosai Abba ya kwantar masa da hankali duk da yaso yazo kasar a ranar amma baisamu izinin haka a wajen na sama dashi ba dole ya hakura,sanar dashi halin da Ummie tashiga shima sai yasake gigitashi. A haka yadinga dai zuwa office din zazzabi nata cinsa a tsattsaye,duk da kullum cikin video call yake da Taufeeq ko Ammi akan jin halin da Ummie ke ciki. ****** Bayan kwana uku da rasuwar Abbie,anan ne wasu daga cikin dangi da 'yan uwa suka wawwatse sai dai na jikinsa suna nan. Anan Daddy yakira meeting parlon Galadima,sosai kowa ya halarta a cikin ahalin gidan,Banda Guggo Laure dai,'yayan Galadima kawai ake bukata. Nan Galadima ya bude taro da addu'ah yayi addu'o'i wa Abbie, Daddy kuma ya amshe. Nasiha maishiga jiki yafara yiwa Ummie,tare da sanar da ita abinda dan uwansa yamutu da burin ganin yacika shine shiryawan ta da diyar ta Daddy ya cigaba"Sadeeq yace muddin kika ja marainiyar Allah a jiki kingama masa komai,ga Hashim nan abinda yadinga maimaita wa kenan kafin Allah yadau rayuwansa yakuma CE shi yayafewa kowa don bashi da kullin kowa a ransa. "Bilkisou kiji tsoron Allah ki kula da diyarki ki cikama abubakar burinsa mudai a iya saninmu baki da matsala kuma Alhamdulillah a kullum abubakar cikin yabon kyawawan halayyarki yakeyi illa matsala guda shine wannan matsalar,Wai ko kin manta Zuhra nada ciwon zuciya ne?kinsan dalilin da yasa a koda yaushe abubakar ke debe mata kewa kenan?don Allah menene matsalar bilkisou? Cikin muryan kuka Ummie tace"inason ta amma narasa meyasa nakejin tsanar ta? wallahi ina kewanta da begenta sai dai sam banaso ta rabe inda nake. Gyararan murya Abba yayi yafara magana"Ina ganin Yaya kamar maganar Yaya Sadeeq gaskiya ne da koda yaushe yake cewa shi yana zargin sihiri a lamarin,nima kuma gaskiya na sake a minta,da sauri Aunty Maryam tace"wallahi kuwa Yaya nima haka nake gani. "Hmmm nidai nace saboda taya uwa zata ki danda ta duka ta haifesa?sannan ko son da aka haifi Zuhra Bilkisou na tsananin son ta daga baya ne komai ya canza,Ammi tayi maganar. Shidai Taufeeq kansa na duke don shikadai ne a yaran gida yake parlon. Baba Hashim yace"toh me zehana anemi malamai masana addinin islama aji ta bakinsu? "Wannan gaskiya ne Yaya, cewar Labeeba. GALADIMA ne yayi gyaran murya,gabadaya wajen yayi tsit magana yafara kamar haka. Xahratty CE🥰 Lallai Alqalami 🖊️ yafi takobi🗡️ 14/03/23. [3/21, 22:27] Xahratty (OUM AJMAL): 👨🏽‍🦳 *_GALADIMA FAMILY_*👨🏽‍🦳 Story&Written By *FATEEMA ZAHRA LAWAL* Marubuciyar⤵️ A DALILIN'YAR TSINTUWA. MIJIN ZAHRA. DIAMOND LADIES ( Daukar fansa)paid book. RUHIN AMRITA (FATALWA CE). Now *_GALADIMA FAMILY_* Page 21-22 _Bismillahir-rahmanir-raheem._ ___Sosai GALADIMA yayi nasihohi masu shiga jikin duk wani wanda yake zaune a wajen,inda a ka tsaida magana za'a ma wani aminin GALADIMA magana dake wani kauye anan maidugrin don masanin harkan sihiri ne kuma yana bada magani sosai,nan aka sake yiwa juna gaisuwa kafin kowa ya watse. Bayan kwana daya,ana masu amsan gaisuwa suka cigaba da tururuwar zuwa,hajiya Biba ma tazo ganin yanda Galadima family yasake tsaruwa ne yasa tasake kudira a ranta cewa lallai yakamata Rammat ta shigo gidannan,sawa tayi aka kaita sashin ammi,anan fa tadinga fadanci a wajen Ammi tare da yabon halayyan Sauban. Ammi tacika da mamakin hajiya Biba amma sai sam bata nuna ba,itakuwa Mom ta cika tayi Damm saboda yanda taga hajiya Biba na neman kwanta ma Ammi tayi wuff tace. "Hajiya kizo muje kiyima iyalen Abbie gaisuwa mana. Mikewa hajiya Biba tayi Rammat tana bayanta itama cike da kissa ta rissinawa Ammi tana mata sallama. Kaitsaye apartment din Abbie nanan suka isa sosai hajiya Biba tanuna jimaminta,itakuwa zuhra tana rakube gefen Ummie jikin kafar Adda zainab. A haka rayuwa ta cigaba da tafiya har yau gashi bakwan rasuwar Abbie a ranar ne kuma Sauban yadiro garin babu zato bare tsammani,idan kallesa baka isa ka tantance a yanayin da yake ba sai dai fuskar sa da take a dinke,ta gabanshi tazo ta wuce cikin sanyinta long hijjab ne a jikinta brown colour yayi mata kyau sosai,fuskar ta daka kalla kasan mutuwar tana dukanta. Ta wutsiyar Ido yabita da kallo har tashiga wajen Ammi,kaitsaye shikuwa apartment din Ummie yashiga bakinsa dauke da siririyar sallama,da Ummie suka fara hada ido,ai tuni tasaki kuka mai tsuma zuciya,da sassarfa yakariso gareta da sauri ya kama mata hannu. "A'ah Ummie don Allah kada kiyi kuka Abbie insha Allah ya dace,ko nima so kike kisanya ni kukan Ummie?please. Girgiza masa kai Ummie tashiga yi tanajan gunjin kukan hawaye wani na riga wani muryanta na rawa tace"Sauban Abbien yara ya tafi ya tafi yabarni da nauyij zuhra ya zanyi please? "Kiyahakuri don rashi mungriga da munyi Allah yajikan Abbie ubangiji yasada sa da rahamarsa. Da Ameen 'yan dakin suka amsa don a yau zasu bi jirgi su koma har da Ummien ma don tace can kaduna zata koma,shima Abba da mommy zasu tafi. ****** "Zuhra kifa dunga cin abinci koko so kike ki dora ma kanki wani lalurar? Ammi tayi maganar tana jawo Zuhra. Hawaye ne yashiga yimata sintiri, Laila takama hannunta"Zuhra please kici abincin kinji?ko so kike kitayar ma da mutane hankali? "Rashin Abbie bake kadai kikayi ba amma tabbas ke zaifi miki zafi kiyahakuri, Nihal takarisa maganar. "Yawwa ku kwantar mata da hankali, Laila maza kishiga dakina kidaukomin makullin dakin yayanku da aka gyara masa dazu. Mikewa Laila tayi tanufi bedroom din Ammi don dauki keys din. Cin abincin kawai takeyi badon tanajin test nashi a bakinta ba,sallamar mommy ne yasasu dagowa. "Zuhra yanzu kika fara cin abincin ne?mommy tayi maganar. "Eah mommy yanzu nafara. "Ok to kiyi kigama zamu koma kd yanzu tare da Ummien ki kizo muje kiyi mata sallama. "Nidai mommy kubarta tatafi don Allah nidai ina gaisheta".Tayi maganar cikin sanyin murya. "A'ah haba zuhra taya mahaifiyar ki zata tafi kice agaisheta? a'ah tashi kije kiyimata sallama. "Ammi inajin tsoro ne please Ummie tace nadena bari tana ganin bakar fuskata,tayi maganar hawaye suna zuba. Kamota Ammi tayi taahare mata hawayen sannan takama hannunta tace"Hauwa muje nasan sun fito tun dazu ko? Mommy tace"sunanan wajen mota. Farfajiyar gidan suka fito inda su Mom, Bodejo, Amma Adda Zainab suke tsaye dasu Aunty Maryam,zuhra kanta a kasa tana tafiya idanuwanta ya cika taf da hawaye. Har gaban Ummie Ammi takaita,da dan hanzari Ummie ta matsa,duk wadanda ke wajen basuji dadin hakan ba,cikin rawar murya zuhra tafara magana. "Ummie ku gaida gida Allah yatsare, Allah yakara hakuri da juriya",tana gama fadar haka tajuya tatafi. 'yan labba Ummie kawai ta amsa,anafa kowa yafara musu sallama don ya Sauban ne zai kaisu airport,mota biyu sukayi dayar Aseef kejanta,haka suka jera sukayi na airport din. Haka suka tafi suna dagawa juna hannu, Ummie kuwa haka tadake saboda kukan dake neman kwace mata,hajiya Amma tadan dube Ummie tare da tabe baki taciro medical glass dinta ta sanya tare da kankance idanuwa. "Yanzu ke fisabilillah Bilkisou bazaki iya daukar diyarki takoma hannunki ba?kijata a jiki? Nannauyan ajiyan zuciya Ummie ta sauke tace"To Amma taya zan daukota alhalin school tafara zuwa anan?kuma Abbie nata shida kanshi suka yanke hukunci dasu Galadima da Yaya kan tadawo nan. "Yo ba dole ba?ai dole suyi haka,kada kinemi sabauta masu diya,kinga ko babu komai sun nuna miki sunfiki sonta da sanin darajar ta,ance tana fama da ciwon zuciya zasu barmiki itace ki karasa musu?takarisa maganar tana kawar da fuskanta kamar ba itace tayi maganar. Duban Adda zainab Ummie tayi tace"Adda don Allah kiyima Amma bayani ta fahimceni bawai fa banson zuhra bane..... "Kinga Bilkisou ni babu wani bayani dazanyi miki kiyi kokari kawai kija diyarki ajiki,tayi maganar tana sake tamke fuska. Sosai Ummien nashi tabashi tausayi saboda ganin yanda duk suke mata kallon mai lefi. "Ni Amma sai nake ganin kaman maganar su Yaya da gaskiya da sukace lamarina da yarinyar can kamar akwai sihiri a ciki. Gyara zama Amma tayi tamaida hankalinta wajen Ummie tace"ko Bilkisou? Daga kai Amma tayi tace"Ea nima kuma sai nafara zargin hakan,saboda me zuhra tayimin ne da nake mata haka?nice fa uwar dana tsuguna na haifeta... "Kinji Kuma wani magana Amma?asiri kike nufi?to taya za'a muku asiri?kudai kudena daukar wa kanku jita-jita da zargi kuna sanyawa zukatanku,wallahi Bilkisou duk lefinki ne amma kinki yarda ai shikenan. A daidai nan suka kariso filin jirgin. Duk firfitowa sukayi daga motar,anan Amma kecewa bataga Taufeeq ba,shine Abba yace ai Galadima yace yabari sai jibi yakoma. Murmushi kwance a saman fuskar Amma tace"Haroun kunadai nema ku kwace duka yaran su koma maidugri da zama,ba za'a bar mata ko guda daya bane anan? Shima Abba cike da dattaku yace"a'ah hajiya Amma taya za'a kwacesu?ai Bilkisou tananan a gidanta shima Taufeeq din sako yatsaya ya amsar mata wajen Galadima. ****** Duk cikansu sunyi jugum suna sauraren babban Aminini Galadima, tsoho Mai ran karfe shima masani ne akan abinda ya shafi sihiri kuma yana karya sihiri da yardan Allah yazama kamar ba'ayi ba. "Lallai lallai muhammadu farraqu akayima yarinyar nan da uwarta don bokan da yayi wannan aikin bakaramin ahedani bane,sannan a yanzu haka ba zaiyuwu in karya asirin ba har sai anje kasan gadon ita mahaifiyar yarinyar andauko wani tukunyar kasa wanda aka tsafacesa sosai akawo. "Innalillahi wa Inna ilaihirraji'un!!!!sautin dake tahi Kenan a babban zauren Malam Baba. A kofar shiga sashen nata gefen fulawoyi shima anhaka rami anbinne wani abu, wallahi muhammadu ban isa nakarya wannan abin ba har sai an binno wadannan abubuwan don tabbas wacce tayi wannan abin ta zalincesu kuma taci amanar su. Bodejo tace"Malam Baba itakuwa wacece wannan?don Allah kafada don a hukunta ta. Dan murmushi Malam Baba yayi yace"ai hajiya bodejo fadar baida wani amfani saboda lokaci na dauka wacce tayi abin da kanta zata kawo kanta gareku amma tabbas hatsabibiya ce. Daddy yace"lallai koma wacece mu bazamu yafe mata ba Allah ma yagani. Duban Taufeeq Malam Baba yayi yace"yanzu malam Taufeeq Kaine aikin nan ke gabanka,zaka iya?. Cike da kwarin gwiwwa Taufeeq ya dagama Malam Baba kai yace"anya kuwa?saboda anason mai dakakken zuciya wanda sam bashida tsoro,yakarisa maganar yana kurawa Taufeeq Ido. Shiko tsakani da Allah Taufeeq yariga yasan kansa akan tsoro don haka sai ya girgiza kai. Murmushi Malam Baba yayi yace"toh kunemi wanda zaije Taleeb,idan kunyanke hukunci kubashi wannan man yashafa,man zaitun ne dana habba akayi mishi hadi da magunguna"yakarisa maganar yana dauko wata 'yar kwalba wacce sai kamshi take zubawa inda yacce da andauko ko kwana biyu kada abari yayi ba'a kawo masa ba. Sosai sukayi mishi godiya inda anan ne kuma akasa almajiran Malam Baba suka dinga shigo da buhunhunan abinci,dama duk shekara Galadima na aiko masa da zakka amma wannan ihisani ne kawai. Daddy anan yabashi dubu hamsin, Baba Hashim yakara mishi da ashirin. Almajiran kuwa Galadima yaraba musu 'yan dari bibbiyu. Anan akayi sallama suka baro kauyen su Bodejo sukayi cikin gari,da yake mota biyu sukayo a mota kowa da abinda yake sakawa,basu suka shigo gida ba sai bayan isha'i. ****** *KADUNA* ***** Anguwan rimi kaduna gidane hadadde na gani na fada sai dai ko kai gidansu Ummie beyiba. Hankalinta atashe yake banda gumi babu abinda takeyi jikinta har rawa yakeyi tana magana. "Hajiya Aliya don Allah kidena wannan maganar asirina nagab da tonuwa fa,nidai mushirya muje nijar din tunkafin su sa akarya musu asirin nan,kina gani a lokacin da akayi wani irin asara ne banyi ba na kashe kudade da kadarori. "A'ah ba nufina kenan ba ai ba asara bane tunda bukata ta biya nasani amma wallahi banaso akarya nibanki har Bilkisou tabar gidan duniyar nanba batare da tashirya da diyar ta ba. Tadan tsagaita saboda maganar da ake acan bangaren. "Toh menene?wancen ma ba maradin mukaje ba?nidai bukata kawai nake nema,ke ko nawane zan iya kashewa idan har zan samu abinda nakeso. Magana aka cigaba da mata tacan bangaren. To Shikenan kikirashin don Allah bakiga yanda na tsure ba inama taoro ne kada asiri na ya tonu,wallahi nayi zawo babu adadi tsaban tsoro. Nagode nagode hajiya Aliya babu abinda zance miki don kina temakona. Aje wayan tayi tana sauke ajiyar zuciya,gumi kuwa haka yake tsattsafo mata. ( _Itakuwa wannan ni fatsima🤔 reader's ko ku kunfahimci wacece ita?_ ) Xahratty CE🥰 𝐋𝐚𝐥𝐥𝐚𝐢 𝐀𝐥𝐪𝐚𝐥𝐚𝐦𝐢🖊️𝐘𝐚𝐟𝐢 𝐭𝐚𝐤𝐨𝐛𝐢🗡️ 19/3/23. [3/21, 22:27] Xahratty (OUM AJMAL): 👨🏽‍🦳 *_GALADIMA FAMILY_*👨🏽‍🦳 Story&Written By *FATEEMA ZAHRA LAWAL* Marubuciyar⤵️ A DALILIN'YAR TSINTUWA. MIJIN ZAHRA. DIAMOND LADIES ( Daukar fansa)paid book. RUHIN AMRITA (FATALWA CE). Now *_GALADIMA FAMILY_* Page 23/24 _Bismillahir-rahmanir-raheem. _____Acan gida kuwa bayan Daddy sun dawo daga sallar magrib anan suka sake tattaunawa inda Sauban ya daddage akan shine zai ciro duk abubuwan nan da akace don Taufeeq sosai ya tsorata yakuma nuna tsoron nashi a bayyane. Duk sunji dadi,anan aka yanke hukuncin jibi Sauban zasu koma dasu Aseef don daga Aseef har mahaifiyar shi babu wanda yasan halin da ake ciki. ***** "Gaskiya Guggo kiyi dagaske inba haka ba Sauban na gab da subucemun, Akeela tayi maganar tana turo mouth gaba. Dan harara Guggo Laure ta aika mata dashi tace"inyi dagaske?ko kema kiyi da gaske?bari kiji inaso ki shirya kikoma gidan da zama sannan ba sasan kowa zaki sauka ba saina Aisha,ke bakisan zamanin ba saida kissa da kisisina? "Amma Guggo kinsan Daddy da wuya ya yarda sai dai idan ke zakiyi mishi magana. "Badole ya yarda ba?yanzu kije kihada duk wani abin bukatanki yanzu zansa waya nakirashi,saboda da wuri nakeso kije gidan,koda nida kaina ma zankaiki. Akeela tayi murmushi tace"yawwa Guggo dama ke yakamata kikaini. "Aiko zankaiki kedai jeki hada kaya yanzu zankira manseer din a wayata,cike da farin ciki Akeela tafita tanufi gate kaitsaye dama ana jiranta a waje,Suby tabita da wani kallo tace. "Wallahi kina ruwa akeey kinsan mommy daharatu tana fushi dake tunda taji ansa miki ranar aure?tace kin munafunce kungiya? wallahi babu ruwana. A razane Akeela take duban Suby wani mulmulallen ashariya tasaki"kutumar ubancan uban waye yafada mata? wani munafuki ne zai sanar mata? Wani banzan kallo Suby tayi mata tace"lallai ma akeey kinmanta abubuwan da kika dingayi a tiktok da IG dinki?magana tariga tanata trending a social media?har 'yan bakin ciki suna bayyana kawunansu. "Mtsewwww to wallahi babu Wanda ya isa ya hanani aure kamar yanda babu wanda ya isa yahanani neman mata da binsu,ina son aure don kinsan nidama nimai son harkan nanne inason wancan abinma,haka kuma inason madigo,to aknme ban matsama wani ba wani yanemi matsamin. Kinga rakani naje wajen mommyn inshawo kanta nasan harda takaicin rashin ganina da batayi bane kwana biyu. Suby murmushi tayi tace"lallai akeey wai kinmanta mommy da sharrin ta kenan?juyar dakai Akeela tayi inda banda bugawa babu abinda kirjinta keyi. "Hmmm Suby nifa inaso ma nadena wannan harkan kwatakwata tunda Allah yabani miji wanda babu abinda yarasa. Suby tace"kina nufin zakibar kungiya?to kindebo ruwa kuma komai tayi miki kece kikaja. "Naji don Allah mubar maganar nan. Washegari wajen karfe 7:30 su ya Sauban suka nufi filin jirgi,a lokacin ne babu jimawa Guggo Laure da Akeela suka isa Galadima family,sosai Galadima da Bodejo bsukayi mamakin ganinsu,don shi Galadima ma yana bedroom dinsa Zuhra na matsamai kafafuwa. Cike da natsuwa take tafiya koda tashigo parlon kallo daya tama su Guggo Laure ta kauda kai saboda wani irin kallo da Akeela ta aika mata dashi,cikin natsuwa tasamu kusa da Bodejo ta zauna tace"Bodejo barka da safiya Ina kwana? "Lafiya Lou Zuhra harkin gama matsa masa kafafuwan? "Ea nagama don har na hada masa ruwan wanka yashiga kema yanzu zanje na hadamiki. "Yawwa Allah yamiki albarka yabaki miji nagari mejin kanki da kaunar ki. "Ameen Bodejo na,tayi magana kaitsaye tare da mikewa tace"bari nashiga wanka saboda zanje school"duban Guggo Laure tayi tace. "Guggo kune da sammako haka?sai kace wacce ake koranki daga gida?tayi maganar cike da zolaya. Guggo Laure tace"nida gidan mu?ai babu maganar sammako anan Fatima kinsan da zafi-zafi ake bugun karfe. Murmushi Zuhra tayi tace"gaskiya ne to sannu da zuwa,tana gama fadar haka tanufi dakinta. Basu dade da zama ba Galadima yashigo inda Bodejo tashiga hada masa breakfast,duban Akeela tayi tace"tashi kihado muku abin kari. Dan yatsina tayi tana mikewa tanufi kitchen din Bodejo tana wani karairaya uwa zata balle tanufi kitchen din. "Laure kece da safennan haka? Allah yasa lafiya dai? Dan murmushi Guggo Laure tayi tace"Yaya muhammadu kenan kunata fadin sammako kamar wacce tayi asibanci?nikam maganar yaran nan yakawoni......au Wai kaji,tayi subul da baka. "Au Akeela nakawo nan ta zauna koda sati biyu ne zuwa uku tayi anan tafara sabawa da gidan duk da gidan su ne. Kallon kallo aka shiga yi tsakanin Bodejo da Galadima. Sauke ajiyan zuciya Galadima yayi yace"toh ai Shikenan sai su zauna da Zuhra a dakin zuhran koh? Da sauri Guggo Laure tace"A'ah ba haka za'ayi ba,ni nace taje can,tanufi wajen Aisha ta zauna tadinga tayata ayyuka abubuwan bukata ko kuwa? Gwalo idanuwa Bodejo tayi cikin mamaki tace"a bangaren surukar tata zata zauna?tun kafin akawo ta gidan? Dan tabe baki Guggo Laure tayi tace"Toh menene aciki? Aisha fa uwarta ce koda kuwa ba maganarta da Sauban. Dan murmushi GALADIMA yayi yace"Laure kenan ninakan rasa a Ina kika samu wannan wayewar kamar jinin fulani baya yawo a jikinki,ita Aishan tanuna miki bukatan son akeela tazo ne?koko tace miki bata da maid's ne? Guggo Laure tatsuke fuska tare da kankantar da idanuwa tace"yanzu munkoma gida kenan?to ai shikenan babu komai takarisa maganar tana latso hawaye tare da mikewa. "Dakata!!! Inazaki a haka?Akeela dai kika kawo ta zauna koh?to Shikenan kidauke ta kikaita wajen Aishan. Guggo Laure tamike inda Akeela kuwa tuni taja trolley dinta tafice cikin jindadi. *******KADUNA******* Sosai Ummie taji dadin ganinsu ya Sauban tarasa inda zata Sanya kanta don murna,haka tasa me aikinta takawo musu breakfast don wajen 9:30 suka iso shikuwa Aseef kaitsaye BQ yanufa batare da yaje gaida Ummie ko Mommy ba,koda yashiga wanka yasakeyi yacanja kaya,don sunyi da wata yarinya zasu hadu zai kama mata daki daga adamawa. Gidan tsohon governor jahar kaduna sukaje shida Taufeeq wajen abokinsa Hamid anyi biki Sauban baisamu zuwa ba kuma sosai ran Hamid yabaci,don ko zuwan baisan dashi ba. Basu suka shigo gidan ba sai wajejen Tara nadare shiyasa Ummie tarufe ido yadinga yimusu fada sosai,abinci tace suje dinning suci ita tawuce bangaren Abbie don tunda tadawo acan take kwana. Sunji dadin hakan sosai,sai da suka jira dare yayi nisa sosai misalin karfe sha daya sannan suka nufi bedroom din Ummie kaitsaye, Taufeeq yamiko ma Sauban man da su Daddy suka bayar sukace wanda zai dakko da hannunshi a cikinsu yashafa. Ansa Sauban yayi ya shafa tare dayin wasu addu'o'i sosai kana yaduka yakai hannunshi. Jikinsa ne yakama rawa saboda damko tukunyar kasan da yayi,kokarin fadi takeyi daga hannunshi kuma tabbas idan tafadi da matsala,jikinsa kuwa jiyake tamkar anjona mishi shock kota ko ina. Taufeeq bakaramin tsorata yayi ba saboda yanda yaga Sauban nayi,gashi duk wata jijiya dake kansa tafito banda zufa babu abinda yakeyi. Sauban kuwa jikinsa jiyake kamar ana yankan naman sa,jiyake kamar yasaki tukunyar amma taurin zuciyar shi bazaisa yayi hakan ba. Cikin yardan Allah dai yajawo tukunyar yadaukota,wani irin hayaki ne ke fita daga tukunyar,cikin sauri Taufeeq ya watsa garin maganin da malama Baba yabada a watsa,zuwa can kuma hayakin yafara raguwa,haka rawar da jikin Sauban keyi shima yafara raguwa,a hankali kuma komai ya lafa. Da sauri Taufeeq ya nannade tukunyar da wata bakar kyalle da aka basu, Sauban kuwa kamar jira yake a amsa yazube kan gadon,kansa namasa wani azababben sarawa. Ruwa Taufeeq yadauko masa anan fridge din Ummie dake dakin,da qyar Sauban ya iya tashi hannunsa dafe da kansa,idanuwansa sun kada sunyi jazur,sai da Taufeeq yatsorata daganin idanuwan Sauban. A haka Taufeeq yakamasa suka nufi bq yakaishi dakinsa don kowa da nashi dakin,sannan yace zai kwana anan don bazai iya tafiya yabarshi a yanayin da yake ciki ba. A haka dai suka kwana jikin Sauban gabadaya babu dadi abin kama da jarumi don sosai yakeda dauriya acewar Taufeeq. Koda safiya tayi dakyar ya iya shiga toilet ya watsa ruwa yafito,wannan man shi yashafa a jikinsa tare da kundundunewa cikin duvet saboda zazzabin daya rufesa,shidai Taufeeq hankalinsa yayi kololuwan tashi don haka yafara neman layin Daddy. *OLD MAIDUGRI* "Lallaima yarinyar nan ni akeey babe zata yaudara?wallahi bata Isa tabar kunya ba kuma dole itadin mallakina ce ko tanaso ko bataso kubarni da ita dole nakira boka na yayimin aiki akanta ni zata ci amana?hajiya daharatu tayi maganar cikin fusata. Zuleey ta tabe mouth"hmm mommy kenan ai Akeela ta mutu akan gayen nan kumafa bason ta yakeyi ba da ita da wannan kwadayayyar kakan tatace suke wahalar da kawunan su. Murmushin jin dadi daharatu tasaki tace"kice akeey 'yar wahala ce,yo metake nema anjikin da namiji?me zata tsinta?wallahi saina bata mamaki saina hanata jindadin rayuwa. "Ai mommy saikinyi tsaye fa don bikin baiwuce saura six month ba,inji zuleey. "Hmm kisha kuruminki dani take zancen wallahi.Tayi maganar tare da sakin kwafan bacin Rai don sosai ranta yabaci. *GALADIMA HOUSE* Xahratty CE🥰 𝐿𝑎𝑙𝑙𝑎𝑖 𝐴𝑙𝑞𝑎𝑙𝑎𝑚𝑖🖊️𝑌𝑎𝑓𝑖 𝑇𝑎𝑘𝑜𝑏𝑖🗡️ 20/3/23. [5/4, 14:36] Xahratty (OUM AJMAL): 👨🏽‍🦳 *_GALADIMA FAMILY_*👨🏽‍🦳 Story&Written By *FATEEMA ZAHRA LAWAL* Marubuciyar⤵️ A DALILIN'YAR TSINTUWA. MIJIN ZAHRA. DIAMOND LADIES ( Daukar fansa)paid book. RUHIN AMRITA (FATALWA CE). Now *_GALADIMA FAMILY_* Page:- 25/26 _Bismillahir-rahmanir-raheem._ ‎اللهم بلغنا رمضان Welcome Ramadan 🌙 Wishing all our Muslim brothers and sisters good health, luck and wealth on its moon sighting tonight March 22, 2023 before fasting commences. Ramadan Kareem, may Allah bless you with happiness and grace your home with happiness & peace and may all your good deeds, prayers and devotions get acceptance by Allah Almighty during this blessed month of Ramadan. 𝐕𝐈𝐓𝐀𝐋 𝐋𝐈𝐍𝐊 𝐁𝐔𝐈𝐋𝐃𝐄𝐑𝐒 𝐀𝐍𝐃 𝐃𝐄𝐕𝐄𝐋𝐎𝐏𝐄𝐑𝐒. ______Sosai hankalinsu yatashi musamman Bodejo tunda taji halin da akace Sauban na ciki, Ammi ma yashiga sai dai sam bata bayyana damuwar da take ciki ba addu'ah tadinga yimasa a cikin ransa tare da rokon Allah yabashi nasara. Akeela na zaune a parlo kusa da Ammi don Mashahuda tunda taji ance wai tazo ta zauna ne tabar parlon takoma bedroom dinta. Wayarta ce tafara ringing ganin sunan mommy wato hjy daharatu yasa da sauri tamike tanufi kitchen,da kallo Ammi tabita batare da takawo komai a ranta ba. "Hello my sweet mommy.... "Dallah can rufemin baki munafuka,mukike kokari ki munafurta Akeela?to bari kiji wallahi Koda zanyi yawo tsirara baki isa kibar kungiya ba kuma baki isa kice zakiyi aure ba,sannan duk abinda kikeyi kizo inason ganin ki tana kare fadar hakan tadatse kiran. "Mtsewwww nikam wallahi babu wanda ya isa yace zai hanani aure kuma da mijin da nake burin aure mijin da kowace mace zataso kasance wa dashi haka kawai bazai yuwu ba. Komawa cikin parlon tayi fuskar ta cike da tsantsar damuwa ta isa ga Ammi cike da bariki tace"Ammi zantafi gidan su kawata Suby yanzu akakira ni wai tafadi tayi targade a hannu shine zanje naduba ta"takarisa maganar cikin marairaice fuska. "Subhanallah gaskiya ya kamata kuwa kije amma don Allah kiyi sauri don bayan la'asar kiyi maza kidawo don Daddyn ku kinsan baison fitan dare. Sake marairaice face Akeela tayi tace"Insha Allah Ammi nace please kibani number dear nakirashi na sanar dashi fitata. Ammi tace"wanene Kuma dear ni Aisha? "Oh ya Sauban nake nufi Ammi. Ammi tace ok to bari nabaki,daukan tsadaddiyar wayar ta tayi tabawa Akeela tasaka number,zuciyar ta cike da tsantsar farin cikin tasamu number mafarkinta,mikewa tayi babu jimawa tafito tare dama Ammi sallama tafita zuciyar ta cike da tsantsar farin ciki. Tazo dai-dai fita gate dinne kuma saiga muneefa da Rammat zasu shigo, wani banzan kallo duk cikansu su biyun suka watsama juna ,dogontsaki Rammat taja tana me tofar da miyau,da mamaki muneefa ke dubansu gabadaya. Akeela kwafa tayi tare da yima Rammat gargadi da yatsu taraba au tawuce tana karkada shafaffen boom boom dinta. "Useless kawai"Rammat tafada cike da bacin rai. "Aunty rahama meke faruwa ne tsakanin ki da Akeela?meyayi zafi haka? "Natsani wancan 'yar iskan yarinyar duk duniya bani da babban makiyiya sama da ita kuma wallahi sai nayi maganin ta ahankali. Muneefa tace"kiyahakuri mushiga daga ciki kawai banji dadin banzan kallon da tayi miki bane don ko babu komai wata kusan tafi wata mushiga ciki. ****** Daka kalleta kasan a fusace take zaune take akan wata dakakkiyar kujera banda karkada kafafuwa babu abinda takeyi tana huci,gefen daman ta matane masu irin shekarunta,daya gefen kuma 'yan mata ne ciki harda zuleey da Suby. Shigowa tayi parlon ganin fuskokin kowa yasa jikinta yin sanyi kaitsaye wajenta ta isa. "Mommy kiyahakuri nasan nayi lattin zuwa wallahi bansamu dan adaidaita bane da wuri,sorry my sweet mommy,tayi maganar tana shasshafa mata face. Da sauri hajiya daharatu tabige hannun tare da mikewa tadubi Akeela ido cikin ido tana huci tace. "Nizaki yaudara Akeela nizaki ci amana?to bari kiji wallahi baki isa kici amanata ba kisanni sarai kaf cikin wadannan,tayi maganar tana nuna mutanen dake wajen da yatsa tace"Babu wanda yasanni a cikinsu sama dake kinsan ni nasanki kinsan abinda zan iya da wanda bazan iyaba wallahi wallahi kinji na rantse muddin kika ce zaki bijirewa umarni na to saina illataki. Sosai gaban Akeela ke bugawa don tabbas tasan halinta matukar sani ta kuma San batada Imani ko kadan,muryan ta yana rawa tafara magana. "Mommy kiyahakuri walahi bazan taba barinki ba inanan tare dake babu abinda zai rabamu nida ke,inason ya Sauban amma son da nake masa baikai wanda nake Miki ba,idan babu damuwa zanso nayi magana ta sirri nidake. Banda harara babu abinda momy ke zubama Akeela,zuleey kuwa burinta kawai hajiya daharatu ta kore Akeela daga kungiya ita kuma tazaga tayi cuku-cukun rabata da Sauban din ita ta auresa. Daya daga cikin manyan matar ne tafara magana fuskar ta dauke da murmushi tace"haba baby kibata dama mana. "Auntyn kayan dadi bazaki gane bane Akeela ta gama kaini makura tasan duk cikin yaran nan babu wanda nakeso da kishinsa sama da ita amma shine ita take kokarin ganin taci amanata. "A'ah kifa dena saurin cewa cin amana kedai kuje bakisan mezata ce miki ba. "Hmmm shikenan muje,hajiya dahara tayi maganar tana fara fita,cikin nishadi Akeela tabi bayanta,da wanj banzan kallo zuleey tabisu tana sake jin matsananciyar tsanar Akeela a ranta. Samun wani lungu sukayi suka labe,anan Akeela tashiga shasshafe jikin hjy dahara,cikin muryan da takeyi najawo hankalinta tafara magana"sorry momy na kinsan koda zanyi aure ba'a son raina bane don babu harkan danafi so sama da wannan"takarisa maganar tana cusa hannunta cikin kirjin hjy dahara. Momy aure na da Sauban nasan na manufa ne shiyasa Guggo Laure tadage ayi shi,daga ni harke kinsan munada burin mallakar kudi banda wannan harkan,na amince da auren sa ne kawai badon komai ba sai don nadinga tara mana kudi nidake,sannan kwadayin Guggo ma nasan baiwuce akan kudin bane sam banason nayi maganar agaban wasu ne. Lullumshe idanuwa hjy dahara tafara saboda abinda Akeela take mata,bude idanuwa tayi tasaka cikin na Akeela tare da tsuke fuska tace"bakison auren shine harkina rawa da murna a shafinki na IG da tiktok? "A'ah wallahi momy nayi haka ne saboda mahassada na kinsan suna zagaye damu a duk inda muke. Dan murmushi hjy dahara tayi tace"Ok na fahimta to kikiyaye gaba maganar gaskiya kuma kada ki rufa a sonsa da yawa na fada miki. "Insha Allah momy"Akeela tayi maganar tana rungumo hjy dahara zuwa jikinta. ** *GALADIMA HOUSE* ** Zuhra cike da gajiya tadawo daga makaranta kaitsaye apartment din Ammi tanufa,babu kowa a parlon don haka tanufi dakin Aunty Mashahuda,koda ta isa tacidda ta tana waya kuma da alama da ya Taufeeq take wayan saboda yanda take maganar. "Shikenan Darling T bari zankira ka zuwa anjima ka gaishe da ya Sauban din Allah yakara sauki. Nan takatse kiran tana duban Zuhra. "Yanzu kika dawo? "Ea wallahi Aunty ai nadawo da matsananciyar gajiya ne a jikina shiyasa. "Ok toh kisamu ki watsa ruwa zakiji normal insha Allah. Zuhra tace"insha Allah yanzu kuwa Aunty,takarisa maganar tana zare turkey gown dinda tasanya kallon ruwan powder wanda yayi mata kyau sosai,towel din Aunty Mashahuda dake kofan bathroom tadauka tasanya. Dan murmushi kadan Aunty Mashahuda tayi bayan Zuhra tashige toilet a hankali tace"zuhra duk namijin da ya aure ke yamure, Allah ya hadaki da miji nagari. *KADUNA JABI ROAD* Daqyar yatashi yayi sallan la'asar shima da temakon Abba don mommy batanan taje gidansu suna,tare sukaje da Nihal da Laila,kuma sai gobe zata dawo. Zuwa wajen sallar magrib jikin nashi yadanyi dama sosai don haka bayan sallar isha'i yafara haka inda malam Baba yayi masa kwatance, Taufeeq na tayashi shidai Abba yana tsaye yana kallon wannan abin al'ajabin abu kamar a mafarki,suna cikin hakin ne hayaki yafara tashi sosai bakinkirin,sannan sai akafara wasu maganganu da wani irin yare wanda sam sunkasa fahimtar abinda ake cewa,jikin Sauban ne yafara rawa saboda jawo wani bakin tsumma daya farajawo wa daga ramin. "La'iala ha illalllahu muhammadan rasulillah"kalman da yaketa ambata kenan shikadai yasan azaban da yakeji gashi yaki sakin kyallen,yana gama jawo wa atake anan yafadi sumamme,daga Abba har ya Taufeeq wajensa suka runtuma suna ambatan sunan sa. Abba kuwa banda salati babu abinda yakeyi,a dai-dai kuma wannan lokacin ne itama Ummie tayanke jiki tafadi sumammiya don haka cikin rudewa Baba sa'a metayata zama kawar Amma ne tanufe ta tana ambatan sunanta tana girgizata. Da gudu tafito inda ta taradda wani tashin hankalin ma nufar su Abba tayi tana cewa"innalillahi wa Inna ilaihirraji'un haruna wannan wani irin musiba ne yau ya tunkaromu a gidan?ga Bilkisou can itama rai a hannun Allah ta yanke jiki tafadi.....ai ko gama magana batayi ba Taufeeq yanufi cikin sashin Ummie cikin tsananin rudu. Abba kuwa banda salati babu abinda yakeyi megadi yashiga kwala ma kira"safiyanu!safiyanu!!!kana inane?shima cikin rudu ya iso yace. "Ranka shidade gani,maza kamamin Sauban munufi dakinsa dashi,aiko nan suka ciccibeshi sukayi na dakin don dama Aseef baya gidan,number Galadima yashiga nema. Aiko babu jimawa yadauki wayar. "Assalamu alaikum, Galadima barka da rana?nace don Allah meza'a baiwa Sauban yaciro dayan abin ne gashi jikin yafi bayama rikicewa ance Bilkisou ma tayanke jiki tafadi kuma ina zargin duk sanadin Ciro abinne. Cike da dattaku da jarumta a muryan tsoho yasanar dashi cewa bari yakira Malam Baba yaji mezaice. Katse Kiran yayi ko minti goma ba'ayi ba yakira Abba nan yashiga sanar dashi abinda zaiyi wato zaihada garin maganin nan da wannan man nacikin kwalba ya cakuda tare da karanta suratu ikhlas,falaq,nass sai yashiga shafa mishi Yana durza mishi a goshinsa,da toh Abba ya amsa tare da fara shafama Sauban maganin. ***** Banda sintiri babu abinda takeyi tare da duban kawarta tsoro karara bayyane a fuskar ta tace"nashiga uku hajiya Aliya inatsoron tonuwan asiri na 'yan uwana sun yarda dani gashi kince boka yayi fushi dani. "Hmmm aminiyata cewa fah yayi kinja anata Kona masa aljanunsa gashinan sunyi mummunan fushi dashi don haka nema yace"gobe da sassafe yana neman mu a dajin katamu inba haka ba duk abinda yafaru kiyi kuka da kanki. Dora hannu aka tayi tafara kuka rurus tamkar wata karamar yarinya"innalillahi wa Inna ilaihirraji'un yazanyi hajiya Aliya?wani karya zanyi har Alhaji yabarni naje nijar?nashiga uku wallahi da nasan wannan tsinannen tsohon zai iya gano Shirin mu da dajin da babu wanda zai iya zuwa zansa abinne, "Sannan wayaje har karkashin gadon Bilkisou yaciro wannan tukunyar?kadafa kimance boka yace"duk Wanda ya koda taba tukunyar ne mutuwa zaiyi balle ace wai andauko shi kacokar? Xahratty CE🥰 Lallai Alqalami 🖊️ yafi takobi🗡️. 22/3/23. [5/4, 14:36] Xahratty (OUM AJMAL): 👨🏽‍🦳 *_GALADIMA FAMILY_*👨🏽‍🦳 Story&Written By *FATEEMA ZAHRA LAWAL* Marubuciyar⤵️ A DALILIN'YAR TSINTUWA. MIJIN ZAHRA. DIAMOND LADIES ( Daukar fansa)paid book. RUHIN AMRITA (FATALWA CE). Now *_GALADIMA FAMILY_* Page:- 27/28 _Bismillahir-rahmanir-raheem._ _____kamar yanda aka shafama Sauban maganin haka Baba sa'a ta shafawa Ummie,cikin hukuncin Allah Sauban yasamu dan dama sosai a jikin nashi,itakuwa Ummie da azababben ciwon kai tatashi dole tasa su Abba suka garzaya da ita asibitin giwa hospital ba'a dau wani lokaci ba aka bata gado saboda yanda Doctor din yasanar da Abba cewa jinin ummien yahau sosai. Don haka Abba yakira Daddy yasanar dashi, Baba sa'a itace tayi zaman jinyar inda su Abba basu bar hospital dinba har kusan 10:30. ***** Tunda Alhaji yakirata cewa bazai samu dawowa ba sai jibi yana da meeting aiko taji dadi don a daren gidan hajiya Aliya ta kwana. Washegari kuwa da sassafe driver dinta yajasu a mota suka nufi nijar duk da tafiya ce me tsaho kuma da alama za'a wahala hakan bata shafesu ba sudai burinsu susami biyan bukata. Haka yadinga falfala uban gudu dasu a hanya. *OLD MAIDUGRI* A washegari Sauban yadawo batare da taufeeq ba don shi yana tare da Ummie shima don saboda sakonin ne,koda yadawo babu jimawa suka kama hanya,Galadima, Daddy, Baba Hashim,Sauban suka nufi kauye don ganin malama Baba. Basu wani jima ba suka kariso,tarba na mutumci malam Baba yayi ma aminin nasa,don zabi guda biyar yasa aka gasa musu shi sai madarar shanu mai dumi wanda banda maiko babu abinda yakeyi. Sai da suka natsu gabadaya don har sallan azahar sukayi kafin malam Baba yayi musu ison shiga wani daki a cikin zauren nashi,ba wani wadataccen haske bane a dakin. Duban Sauban yayi yace"malam muhammadu kawo sakonnin,yakarisa mahanar cike da raha. Hannun Sauban na rawa yamika masa,aiko wannan kyallen yafara hayaqi inda akafara magana cikin wani yare,babu bata lokaci malam Baba yasaka kyallen cikin wata qatuwar kwalba,tare da rufe kwalban da murfinsa. Aiko abin al'ajabi kyallen ne kewani irin girgiza a cikin kwalban,inda hayaki ya turnuke cikin kwalbar. Tukunyar nan yadibo wani ruwa a kwarya yakafa baki alamun addu'o'i yakeyi kafin kuma yafara watsa ruwa a jikin tukunyar kasan,aiko nan tashiga daddarewa ko ina yana tsagewa a jikinta har yafashe dakansa inda wadu kulle-kullen layoyi suka shiga bayyana. Hankalinsu Daddy ne yayi kololuwan tashi saboda cin karo da sukayi da hoton Ummie da zuhra ranar suna fuskar ta dauke da murmushi a kasa an rubuta, _Mummunan farraqu,har subar gidan duniya basu babu juna wutar kiyayyar diyarta shi zai cigaba da wanzuwa a zuciyar ta._ "Innalillahi wa Inna ilaihirraji'un!!! Kalmar dasu Daddy suka shiga maimaitawa kenan, Baba Hashim yashare ruwan hawayen da yakawo masa, Galadima dukar dakai yayi Daddy da Sauban kuwa jijiyoyin kan nan tayi baro-baro. "Ya Salam hasbunallah wa ni'imal wakeel,malam baba wannan wane irin musifa ne haka?wane mara imanin ne ya aikata haka?tabbas ko waye wannan yacika cikakken mara imani. Galadima yayi maganar. "Huhhh Sauban yafitar da wani huci idanuwan nan sunyi jajazur,kansa har wani irin sara masa yakeyi. Haka malam baba ya cigaba da aikinsa. Zuwa can yadubi galadima yace"Alhamdulillah malam Muhammad nayi nasarar magance matsalar nan sannan na hada musu wani dafa'i wanda insha Allah babu abinda zai sake faruwa a tsakanin su,komin tsafin me tsafi kuwa da yardan Allah. "Sannan akwai wasu addu'o'i da zan basu da ita da 'yan wanda zasu lazumci yinsa da yardan bi'iznillah babu abinda zaifaru. Duban Sauban yayi yace"Shima takwaran ka na hada mishi wasu zan bashi domin tabbas za'ayi kokarin bibiyar wanda ya lalata aikin koda kuwa ba'a gano shiba sai sunyi kokarin sabauta ko wanene. "Mungode malam baba Allah yasaka da alkhairi ubangiji yaja kwana Allah yayima rayuwa albarka. Cewar Daddy kenan cike da tsananin jin dadin yadda malam baban ya warware musu komai da yardan Allah da temakon sa. Godiya sukayi sosai inda Galadima yake cemai ga sadakan abinci nan yayi ma almajiran sa sannan anbiya mishi kujeran hajji. Nan yashiga godiya duk da ya nuna musu sunfi karfin haka a wajenshi Amma ina. ********* Sai yamma lis suka isa qauyen wajen bokan inda shima driver hajiya Aliya dan gari ne don suna shiri sosai ita dashi don har aikoshi tanayi wajensa a sirrince. Gidan da suka saba sauka a dan quyen gefen gidan boka nan suka sauka,zuwa bayan sallan isha'i suka shiga wajenshi. Da wani banzan kallo ya tarbe su,nan danan hajiya Aliya tasha jinin jikinta,a dan tulluwan kasan da suka saba zama suka nufa zasu zauna. "Kulllll! Ahirrr dinku Aliya ka kasa nan ku zauna. Jikisu har tsuma yakeyi saboda yanda yayi maganar. "Aljanu su huci zuciyar ka,shedanu su huci zuciyarka yakai mebiya mana bukatun matsalolin mu( _wa iyazubillah_) "Ya isa hajiya Aliya kunfi kowa sanin abinda kukamin kun batamin aikinda tunda nake babu aikin da nasha wuya akansa sama da wannan,me kuke zaton yafaru?yayi maganar yana zaro musu mummunan idanun saasu kama da attarugu saboda ja. Kunsan aljanu nawa aka konamin a aikin nan?tabbas wadanda sukayi aikin nan ba kananun bane,duk sharrin dan dagiya da masanu sai da aka konamin su,duk cikin aljanuna babu jajirtattu irin su. "Wallahi bazan kyale ko waye ba sai na dauki fansa akan abinda akayi musu koba yanzu ba. Su dai su hajiya Aliya sun kasa magana banda rawar jiki ba abind sukeyi. Duban dayan yayi yace"yanzu me kikeso a musu?don shiryawa sun ruga sunyi itada diyar ta sai dai wani zancen ba wannan ba. Jikinta na rawa tafara magana cikin rawar murya. "Duk da 'yar uwata ce ubanmu daya amma nayi mata wani irin tsana mafi muni, duk da cewa mahaifiyar ta tafifitani akanta tanuna min soyayyar da bata nuna mata ba amma inajin muguwar tsanar ta a zuciya ta, takasance ta taso da soyayyar mutane da dama ne a zuri'ah mu harda mahaifinmu,wallahi boka hatsabibi bana sonta kuma ba zan taba sonta ba,inason ka sabauta min bilkisou yanda ba zata moruba. "Hhhhhhhh boka hatsabibi ya shiga qyalyqala dariya,zuwa can ya daure face. "Aikin ki sai na sake nemo wasu aljanun kuma shedanu saboda kinsanta da rukon addini bata wasa da azkar to zanyi shiri na musamman akanta,don yanzu haka tana kwance a asibiti jinita ya hau a dalilin karya sihiri nan da akay ......... "Allah dai yakashe ta ma kihuta aminiya,cewar hajiya Aliya. Wani kallo boka ya watsa mata. "Ba Amin ba nine nan ajalinta,mutuwar ta a hannu na take,sai dai wannan aikin ba kamar ko wanne bane don inada tabbacin duk me zatayi se yaci,amma kema zakiyi wani aikin daga bangaren wasu ayyukan. "Ni Kuma?tayi tambayar tana zaro idanuwa. "Eah ke!wannan karan mata biyu zasuyi amfani dake,bi ma'ana zasu mu'amalance ki. "Kamarya yaya boka? Duban hajiya Aliya yayi yace"kiyi mata cikakken bayani. Nan hajiya Aliya tashiga yima aminiyar ta bayani yanda zata fahimta,ai bata bari rakarisa ba tadafe kirji tace. "Ni Zainab bantaba madigo ba kuma banjin zan iya aikatawa. Daga hajiya Aliya har boka daure fuska sukayi. Boka yace"to duk inda zaki babu me yimiki maganin matsalar ki muddin baki aikata wannan abin da nace ba. "Mtsewwww!hajiya Aliya taja tsaki tace kika ma aikata wadanda sukafi wannnan muni da sabo wannan ne bazaki iya aikatawa ba lallai baki shirya ganin nasara ba. "A'ah ba haka bane aminiya da girma na da komai aganni ina madigo? "Waye zai ganki?cewar hajiya Aliya. "Boka hatsabibi yace a gabansa za'ayi fah 😥 "Mtseww Kinga idan bazaki iya ba tashi mu tafi makwancin mu zuwa safe mu tafi gida. "A'ah matsalata dake saurin fushi aminiya,cewar hajiya Zainab. "Toh ai ke dince da kayan haushi,idan kin shirya kiyi magana. Da sauri ta daga kai alamun ta amince. Nan boka hatsabibi ya rufe ido yana wasu yare kafin kace wani abu wasu katta kattan mata biyu bakake sun shigo ta kofan,babu sutturan arziki a jikinsu. Ba hajiya Zainab kadaiba,hatta hajiya Aliya sai da ta hadiye wani irin miyau na firgita. ***** *KADUNA* **** Ansamu Ummie ta farfado tana tare dasu mommy, Amma da kannen ta maza, Abba ma yana asibitin don su Daddy ance suna hanya. Hawaye kawai takeyi tana ambatan sunan Zuhra. "Amma na manta da Zuhra a babin rayuwata wallahi ni naman ce wai bayan Taufeeq inada wata diyar,meyasa na aikata mata hakane fisabilillah? Takarisa maganar tana zubar da hawaye masu dumi da zafi. "Ba laifinki bane Ummie wannan duk wanda yagani ko yaji labari yasan aikine na sihiri akwai farraqu a lamarinku,ba gashi ba yanzu da akayi magani komai ya warware? Mommyn yara bazaki gane me nake nufi ba,Abbie ya rasu batare da na cika mishi burin shi ba naganin naja diyata a jiki,ya rasu yana tausayin diyar shi da fargaban halinda zata shiga na kiyayyata bayan bashi,kuma hakan baitaba shafan zaman mu ba. "Allah yasani duk wanda da sa hannunshi akan wannan lamarin ban yafe ba kuma sai Allah ya bimin hakki na. "Wallahi kuwa bazamu yafe ba, Amma tafada tana kuka. Dai-dai nan ne kuma su Daddy, Galadima, Bodejo, Ammi, Mom, Sauban, Zuhra suka shigo dakin bakunan su dauke da sallama. Ummie jikinta har rawa yake ta sauko daga bed din ta nufosu,zazzaro idanuwa takeyi kawai tana laluben ta inda zata ga Zuhra. Zuhra kuwa ganin ta nufo inda take ne yasa jikinta kama rawa ta runtse ido tare ruqunqume kwankwason Sauban gam,fadi take. "Innalillahi wa Inna ilaihirraji'un don Allah Ummie kiyahakuri babu abinda na miki please bazan kara ba,na hadaki da Allah please kiyahakuri wallahi. Shesshekan kukan da tadinga ji daga maban bantan bakuna ne ya sata bude ido. Ummie tagani a durqushe tana kuka mai sauti, Amma ma da Bodejo kukan sukeyi. Duk da haka jikinta rawa yakeyi takasa sakin Sauban don ita batasan tama rikeshi haka ba,Ammi ne ta matso tare da kamota tazo da ita har gaban Ummie inda take durkushe. "Zuhra Ummien ki tadawo gareki, Ummien ki mai sonki tadawo gareki dama banace miki ba?kidena jin tsoro kinga kinsata kuka koh? Kamar wawuya haka zuhra takoma tana kallon Ummie tana kallon Ammi. Kamo hannunta Ummie tayi wanda gabadaya ilahirin jikinta yashiga rawa tafara magana. "Zuhra diyata kiyafemin bansan abubuwan da nake mikiba a baya hasalima nina mance ma na haihu tun washegarin sunan na manta ki a shafin rayuwa ta,don Allah kiyafemin. "Ni maisonki ne,ni me kaunar kine,ina tsananin begenki,please diyata forgive me my babe. Xahratty CE🥰 Lallai Alqalami 🖊️ yafi takobi🗡️ 14/4/23. [5/4, 14:37] Xahratty (OUM AJMAL): 👨🏽‍🦳 *_GALADIMA FAMILY_*👨🏽‍🦳 Story&Written By *FATEEMA ZAHRA LAWAL* Marubuciyar⤵️ A DALILIN'YAR TSINTUWA. MIJIN ZAHRA. DIAMOND LADIES ( Daukar fansa)paid book. RUHIN AMRITA (FATALWA CE). Now *_GALADIMA FAMILY_* Page 29/30 _Bismillahir-rahmanir-raheem._ *BARKAN KU DA SALLA MASOYA FATAN ANYI SALLAH LAFIYA,WADANDA SUKA RIGAYEMU GIDAN GAAKIYA ALLAH YAJIKANSU.....YAWWA NACE BA GORON SALLAH KADA A MANTA DUK WANDA ZAI BADA YAZO A BASHI ACCOUNT NUMBER😁HAR NAMAN SALLAH DA CIN-CIN ZA'A IYA TUROWA TA ACCOUNT.* *DUBUN GAISUWA A GAREKU MAMAN ASLAM,MMN TAUFEEQ,UMMU MEE'AD,GODIYA DA TARIN KULAWA.* ________Gabadaya dakin daga masu tayasu kuka sai masu juriya haka suka kasance, Zuhra kuwa wani irin nishadi takeji wanda tunda take bata tabajin irin sa ba. Nan Galadima yake sanar dasu abinda yafaru,babu wanda baishiga shocked ba, Ummie haka ta taso ta rungume Sauban tana me sake zubda hawaye cikin muryan kuka tace. "Nagode son Allah ya saka maka da mafificin alherinsa bazan taba manta kaba a rayuwa ta, Allah ya dafa maka a lamuran ka. Amma tace"ubangii Allah ya baka mata tagari me kula dakai Allah ya daukaka duniya da lahira. Gabadaya dakin sai amsawa akeyi da amin,ita kuwa Mom takaicin irin addu'o'in da ake kwaranyo ma Sauban takeji,domin ji take kamar ta shake shi ya mutu kowa ma ya huta,banda yaqe babu abinda takeyi. Anan suka sake godiya ga Allah akayi addu'o'i suka dunguma kuma jabi road don Ummie sarai ta warke, Zuhra na maqale a gefenta. Ko kafin su iso Abba yasa anyimusu oder lafiyayyun kalolin abinci,tuwon shinkafa miyan egusi,jollop din shinkafa,sakwara da miyan alayyahu sai snack's da drink's. A babban sashen Galadima suka zauna wanda idan yashigo da kaduna yake zama,matan kuma suka nufi sashen Ummie. Amma tace"Niko lafiya hajiya Zainab gabadaya number ta baishiga?nakirata ban sameta ba nakira number farida tace batanan tayi tafiya. Ummie tace"toh ina Adda Zainab taje ne?tayi tafiya kuma takasa sanar dake Amma? gaskiya da mamaki. "To nima dai shi nagani,ita takanta taci burin zuwan wannan ranar shiyasa nake nemanta fa, Allah ya kyauta bari zuwa anjima nasake gwada kiranta. ****** Hajiya Aliya da hajiya Zainab kuwa basu da wani choice da yawuce amsan bukatan boka,haka hajiya Zainab tanaji tana gani wadannan kattin matan sukayi amfani da ita sannan a gaban boka hatsabibi yana watsa musu wani irin ruwa yana cigaba da surkullen sa. Sai da suka shafe awa daya suna abu guda zuwa can suka kyale ta,boka yace suje zuwa anjima tazo ta amsa saqon magungunanta,su kuma matan suka zauna anan. Banda dariyar keta babu abinda hajiya Aliya keyi ganin yanda aminiyar ta ke tafiya a tattale,sosai hajiya Zainab ta kulu ta dubeta da niyyar tayi magana amma sai ta rigata. "Kada kice komai don tun kafin ayi hakan dake akayi dani fin sau goma,ke nifa idan har akan biyan bukata ne zan iya komai,ke ko boka hatsabibi ne yace yana son kaina zanbashi,ke ko dan mutum yace nakawo zankawo. Takarisa maganar tana taunar chwengum"kas kas kas". Sai yau hajiya Zainab tasake yarda lallai aminiyata hatsabibancin ta ko shedan tsoron ta yakeyi. "Nikam mu amsa maganin nan mutafi don wallahi Alhaji baisan da fitana ba kuma kowane lokaci zai iya dawowa,gashi layina ba za'a iya samu ba. Hajiya Aliya tace"toh mukoma mu gaya masa mukam tafiya zamuyi yanzu. Haka suka sake komawa inda babu abinda ke tashi a dakin sai hayaqi da wani irin wari,sun dauki minti biyar a tsaye kafin boka hatsabibi cikin muryan tsawa yace. "Tsayuwar me kuke musu a hanya alhalin zasu wuce,wallahi duk Wacce aka gurgunta babu ruwa na,duk cikansu jikinsu na rawa suka fada dakin. Zama sukayi a kasa,wani bakin kwarya boka hatsabibi ya dauko tare da yin wasu yare sai ga kullin magani guda biyu sun bayyana,hannu yasa ya dauka inda yadaure face tare da duban hajiya Zainab yace"Kinga wannan hajiya,kije kisamu dai-dai kan inda 'yar uwanki ke kwanciya ki barbada wannan garin maganin,babu wanda zai gane kinsa wani abu,ni kuma ina tabbatar miki da muddin anyi aikin yanda ya kamata to fa 'yar uwanki zata kamu da mummunan ciwon barin jiki(paralysis)wanda har tabar gidan duniya babu maganin shi. Sai kuma wannan kisamu abincinda kikasan shine abincinda tafiso duk cikin abinci ki barbada mata hhhhhhhhhhh....daga zarar kika barbada mata taci kowa gudunta zai dingayi harta 'yan uwanta da uwanta ke da kowama nata,don zata dinga magana ne bakinta na wani irin aman wari tare da fitar da wasu tsutsotsi. Wani irin dariya hajiya Aliya da hajiya Zainab suka sanya najin dadi. "Idan wadannan basuyi ba to dole sai munyi mummunan aiki akansu. "Ayi boka hatsabibi ka kasheta inaso ta mutu natsani in daga ido naga bilkisou. "Hhhhhhhhh kisa a ranki aikinki ya kammala gashi kutafi yanzunnan. Da sauri suka mike ko gidan da suke sauka basu koma ba don dama bawai sunzo da kayan canji bane,hand bags ne shima suka tura driver hjy Aliya yaje ya dauki musu,nanfa suka fafaro hanyar dawowa lajeria🤪 ______ *NIGERIA*______ Haka wadannan ahalin suka kasance cikin farin ciki inda a washegari Sauban zai koma Malaysia,ummie ma tace zataje maidugri kusa da diyarta ta kwana biyu ta dawo. Tunda babu daman ita ta zauna kodan school dinta,inda Amma itama atake anan tace zata bisu taje sosai sukaji dadi babu bata lokaci Abba da Daddy suka fita nema musu jirgi Wanda zaije borno kona 5:00 pm ne. Cikin yardan Allah kuwa suka samu jirgin inda nan suka tafi suka bar su mommy da Abba da kewarsu,maimoon ma sai rigima suke kan sai sun bi Ummie. Washegari tun 7:00 am Kareem yadauki Sauban don kaishi airport,jirgin 7:30 zaibi hakan yasa basu wani jima da isaba aka fara neman matafiya aiko nan Sauban yatafi suna ma juna waving hannu shida Kareem. Anan ma wani sabon kwarkwaryan walima aka hada don su Mashahuda sunyi farin ciki haka su nihal saboda babu wanda besan 'yar tsaman dake tsakanin Ummie da Zuhra ba. Duk da tasan yatafi Amma sai ta nemi walwalarta tarasa tunda taji labarin shine mutumin da yayi aikin haqo asirin da aka mata itada Ummien ta sai taji wani kiman sa da darajar sa a zuciyar ta,musamman da taji irin kasada da hadarirrikan dake cikin aikin tare da wahalar da yasha sai mutumcin sa ya ninku a idon ta,duk da tasan bawai yinsa take ba hasalima ba birgeta yake yaba yasata jan tsaki akasar ranta ta furta " _to meye abin damuwa da tafiyar nasa?kekam wawuya ce._" Yinin ranar kwanan farin ciki wadannan ahalin keyi,don saura kiris Zuhra tayi lattin School ko wanka batayi ba ta sulale tatafi gashi suna da test. *MALAYSIA* Yauma kamar kullum sanye yake cikin suit gray sosai yayi kyau duk da fuskar sa babu alamun fari'a ko kadan amma hakan 'yan matan company din nan keta binshi da mayataccen kallo,dan tsaki yayi kasa² tare da sake tamke fuskar a hankali ya isa office dinsa. Nan aka fara shigowa yimasa barka da zuwa maza da mata. Aiki yakeda shi sosai akan wani designer shoe da yafito wanda sam bema bayyana ba shine take su hada don ko babu komai a fara gani a company nasu shysa take so busy yaudin kam,don duk wanda yazo nemanshi ma baya ma samunsa saboda ya gayama secretary dinsa cewa duk wanda yazo tace yana aiki. Bashi yabar office ba sai kusa to 6:18 na yamma kaitsaye wani shagon coffee yanufa saboda wata hardaddiyar yunwar da yake jinsa. ****** *NIGERIA* ****** "Ni gaskiya yau zan dawo kanme zakice nakara lokaci?kinsan kuwa irin takurar da nake anan?ni da wallahi nasan yau zai jiya zai wuce da tun shekaran jiya na dawo gida,ganinan dawowa yanzu. Akeela takarisa maganar tare da datse kiran tana jan dan siririn tsaki a fili tace"mutum sai shegen taurin kan tsiya,yama kulani baikulani ba hasalima kamar besan da wanzuwa ta ba. "Lallai iska na wahal dame kayan kara! Taji an bata amsa ta bayanta. Juyowa tayi don ganin ko wace isasshiyar ce. Rammat ce zaune kan 2sitter din daya daga cikin set din kujerun guda biyu dake farlon,ta daura kafa daya kan daya sai girgiza su takeyi bakinta dauke da chwengum tana tauna,dagowa tayi akaro na biyu tasake watsama Akeela wani banzan kallo tare da cewa. "Ko mara aji nason mace me aji,ko wawan namiji nasan mace me aji kisama ranki cewa keda ya Sauban tazarar ku tamkar sama da kasa ne yayi Miki nisan da baki isa ki cimmasa sai dai kizo a 'yar aikinsa".Sosai kalaman Rammat suka batama Akeela rai wanda har yasata kasa control din kanta cikin tsantsan hargagi da masifa tataso ma Rammat"karya kikeyi karamar karuwa karamar kilaka,karya kike kice tazarar dake tsakanina da ya Sauban tamkar sama da kasa ne don ko babu komai nidin jininsa ce kuma dan gaba kadan zan zama uwar 'yayansa"takarisa maganar tana zabgama Rammat harara. "Ahayye cassss! Lallai saifa su jininsa su jininsa an wahala,shiyasa ai naga yana tattalaki tare da riritaki ko?ko kina tunanin bansan irin shige da fice da gwagwarmayan da kike bane don samu soyayyan sa?wallahi ba baki nake miki ba Akeela keda samun soyayyar ya Sauban sai Allah,muddin baki natsu ba kinsan Allah ya faku,maganar karuwan ci kuwa ke har kinda bakin magana akan wannan?ke wani irin badala da ta'asa ne bakiyi?kunna datan ki,kishiga cikin IG naki kiga abinda na wallafa. Tana kare faden hakan tadauki handbag dinta tare da barin farlon zuciyar ta fal farin ciki duk da taji zafin maganganun da Akeela ta fada mata amma tasan ko babu komai nata martanin yafi zafi. Da sauri Akeela ta dauki wayar ta da niyyar shiga IG dinta sai ganin kiran Suby tayi,da sauri tayi picking call din. Jin abinda Suby ke karanta mata tacan bangaren yasa zuciyar ta sake tsinkewa batare da tabari takai aya ba takatse kiran,babu zato sai ga Kiran zuleey itama.Dogon tsaki Akeela taja tare da rejecting call din tana meshiga cikin IG dinta inda tafara cin karo da sakon ni ta DM dinta,shiga tayi tafara duddubawa inda banda dakan lugude babu abinda zuciyar ta keyi,kaitsaye wall din Rammat tanufa nan taci karo da wani post da Rammat dintayi wai. _Wai Wanda akasa ma Rana da Akeela ba sonta yakeyi ba hasalima itace tashiga tafita tare da bin malaman tsubbu da matsafa aka shawo mata kansa har akasa rana,a hakan ma shidin baya sonta don yanzu haka tana gidan su don farauto soyayyar sa,inbanda karuwa ma jahila ce taya zatayi tunanin kamilin mutum irin wannan zai so karya kamanta? Tabbas ta yaudare kanta da bata tantance dai-dai da akasin hakan,mudai namu ido Allah yakaimu lokaci musha biki._ Abinka da celebrities kafin wani lokaci magana nata trending a social media wasu har screenshot sukeyi,wani kwallan takaici ne yazo ma Akeela a makoshi cilli tayi da wayar kan kujera tare da fita daga apartment din Ammi,kaitsaye apartment din Mom tanufa. Mashahuda da fitowan ta kenan daga apartment din Abbie don kaima su Ummie abinci taganta,dan tabe mouth tayi. Itakuwa koda tashiga ta cimmusu sunata aikin hira da shewa,ai tana Isa batayi wata wata ba cikake tassssssssssss! _KUYIMIN AFWA MAKARANTA MUNA FAMA DA MATSALAR WUTAN NEPA NE DON BA SAMU MUKE BA,SHIYASA NAKETA ASUSUN NA'URAN NAN NAYIN CAJI🤧, XAHRATTY MAI KAUNAR KUCE🥰._ XAHRATTY CE🥰 Lallai Alqalami 🖊️ yafi takobi🗡️ 1/5/23. [5/4, 14:37] Xahratty (OUM AJMAL): 👨🏽‍🦳 *_GALADIMA FAMILY_*👨🏽‍🦳 Story&Written By *FATEEMA ZAHRA LAWAL* Marubuciyar⤵️ A DALILIN'YAR TSINTUWA. MIJIN ZAHRA. DIAMOND LADIES ( Daukar fansa)paid book. RUHIN AMRITA (FATALWA CE). Now *_GALADIMA FAMILY_* Page:- 31/32 _Bismillahir-rahmanir-raheem._ _______Duk cikansu mikewa tsaye sukayi Mom,muneefa,banda Rammat dake zaune dafe da kunci baki a sake,aiko minti biyar ba'a kara ba itama tamike batayi wata wata ba tasauke ma Akeela tagwayen maruka dama da hagu wanda har sai da yasata yin taga² zata fadi,cakumo ta tayi tare da fara magana. "Ni sa'ar kice ko ko ancemiki ni irin yaran da kuka raina ne kuje har inda suke ku dakesu,tayi maganar tana me wujijjiga akeelar abinda da dama ba kiba. "To bari kiji idan kina cin kasa kikiyaye ta shori wallahi duk randa kika sakemin wannan jakan cin sai nabiki abinda a kungiyar kuma babu wanda zaiganeki usless kawai.Sosai Akeela tayi mmkin abinda Rammat tayi mata kuma bazata iya ramawa ba don tasan tafi karfinta amma tadau alwashin sai tasa anrama mata ko badane ko bajima,haka tamike jiki a sabule tana fadin"wallahi ki rubuta ki ajeyi sai nabaki mamaki sai namiki abinda baki zata ba.... "Kindade bakiyi ba don abu kaza naki ina jiranki",takarisa maganar tana me nufo Akeela,ai dagudu tabar farlon tana cigaba da zage². Mom da muneefa kuwa mezasuyi banda dariya saboda yanda Akeela tabasu dariyar. Koda nufar ta apartment din Ammi cikin sa'a tacidda babu kowa a farlon haka ta isa bedroom dinda tasauka tashiga hada kayanta,babu bata lokaci ta jawo trolley bag dinta nanma bata ci karo da kowa ba kaitsaye fita tayi daga farlon. Haka tafita gidan tare dajan dan akwatinta don barin layin,saboda a layin ba'a samun adaidaita sahu sai anfita don ma suna farkon layine. Haka tabar layin cike da bacin rai har neman number suby takeyi bata samu ba har kwallan takaici tayi. Sai wajen karfe takwas Ammi taga dai shiru shiru bata fito ba gashi za'a ci abinci amma babu ita duban Daddy tayi tace"Oh ni Aisha koyau Akeela lafiya bata fito ba,tashi Mashahuda kikirata kice tazo tayi dinner. "Please Ammi kirabu da ita wallahi ba yunwar takeji ba da tanajin yunwa ai zata fito yin dinner din, Mashahuda tayi maganar tana yatsine face. Dagowa Ammi tayi da niyyar sake mata magana wayar Daddy yafara ringing,ganin sunan Guggo Laure yayi cikin dattaku ya amsa kiran tare da fara gaisheta ko aya bekai a maganar ba tafara zazzaga fada. "Taleeb wai me akeso a maidani a gidan nan ne naku?yanzu fisabilillah wani ahalina bashi da iko a gidan nan har bare ace yafishi? "Subhanallah Guggo meyafaru ne haka? "Yanzu ramatu ne ta yayyarfa ma Akeela mari waye ubanta?dangartakan me mukedasu da har tasamu wannan zarrar?sosai Daddy kanshi ya kulle yarasa wacece take magana akai,cike da kamewan sa yace"Guggo wacece kuma ramatu wallahi bangane maganar da kike akaiba. "To bari nasanar maka da abinda ke faruwa,nan Guggu Laure tafada Daddy duk abinda Akeela tace mata ta ida zancen da cewa"kuma wai saboda raahin mutumcin irin na rabi a gabanta akayi komai amma ta kasa kwabawa. Nannauyan ajiyan zuciya Daddy yasauke tare da bawa Guggo Laure hakuri sannan ya cemata itama Akeela bata kyauta ba don kawai haka tafaru ta tattaro kayanta tadawo gida sam beyi ba ko bata fada musu abinda yafaru ba ai ta musu sallama. "Yo taya zata muku sallama tunda an sakota gaba da musifa tunda akace ansa ranar ta da Sauban makiya keta bayyana kawunan su gabadaya ansata a gaba. Shiru Daddy yayi tare da mamakin halayen Guggon nasu nakin gaskiya sam ita batason gaskiya kuma bataso ka gyara mata kuskurenta komai kankantar sa. "Shikenan Guggo kiyahakuri insha Allah za'a wa tufkan hanci,nan sukayi sallama. Cikin bacin rai Mashahuda ta dubi Daddy tace. "Wallahi Daddy sam Akeelan nan bata dace da Yaya ba,kuma wallahi bataji fa"wani mugun kallo Ammi ta watsa mata wanda yasata Jan bakinta ta dinke. A bangaren Ummie kuwa sai nan nan sukeyi da Zuhra ita da Amma har ma dama-dama Amma tana sakin mata amma sam takasa sakin jiki da Ummie duk da kuwa yanda Ummien ke nuna kukawar ta agareta,mikewa tayi tare da cewa"Ummie bari naje na amso abincin ku wajen Bodejo wai tasa ayi muku faten alkama takarisa maganar batare da tajira abinda ko wannensu zaice ba,da kallo duk suka bita dashi. Ummie ta sauke wani nannauyan ajiyar zuciya tare da goge 'yar kwallan da ta taru mata tace"kingani ko Amma? Zuhra bazata taba sakin Jikinta dani ba sam,duk wanda ya shiga tsakanina da diyata haka tsawon shekarun nan bazan taba yafemasa ba ko wanene. "Kiyahakuri bilkisou aikomai a hankali ake binsa kuma a hankali zata saki jikin nata dake,inace ba yau bane aka warware komai?to komai zai dawo dai-dai yanda baki tunani ki kwantar da hankali,insha Allah ninarasa meyasa mu number addanku duk idan nakira baya shiga. Tayi maganar tana me latsa layin Adda Zainab din,cikin sa'a kuwa taji tashiga. "Kinga kuma tashiga bari muji lafiya kuwa. Daga can bangaren akayi picking call din,nan suka shiga gaisuwa anan Amma ke sanar da ita abinda ke faruwa sannan tafada mata tana maidugrin. Sosai tanuna jajantawar ta tare da alhini ta Kuma ce insha Allah Alhaji yau idan yadawo zata taho gobe da sassafe. Anan sukayi sallama da junan su inda Adda Zainab tacika da tsananin farin ciki don ko babu komai burinta na gabda cika koma tace yacika,landanan ta latsa kiran aminiyarta hajiya Aliya anan ta sanar da ita yanda sukayi da Amma. Itama taji dadi ta Kuma ce lallai tafiyar da ita za'ayi don aiwatar da aikin yanda ya kamata,sallama suakyi cike da kosawa ma garin ya waye. *WASHEGARI* Su Adda Zainab tun 7:00 suka fita amma basu suka isa ba sai wajen 6:30 sosai suka wahala don motar haya suka bi inda suka samu tarba na girma da kulawa. Sai da aka bari sukayi wanka suka ci abinci sannan aka fara gaishe-gaishe har sashen Galadima sukaje don mika gaisuwan su agareshi,cike da dattaku ya amsa sannan suka koma sashen Ummie nan aka dasa hirar yaushe gamo inda Zuhra tadan saki jikinta sosai don hajiya Aliya macece mai barkwanci da ban dariya,itadai Ummie na kwance akan hadadden gadon ta, Zuhra ne tashiga toilet din Ummien. Tadan bata lokaci kafin tafito tare da duban Ummie tace"Ummie ga ruwan wankan can nahada miki da komai da komai a ciki",cikin jin dadi ta dubeta tace"tnx my lovely daughter Allah yama rayuwar ki albarka. Da ameen duk 'yan farlon suka amsa. Ammi tace"kawa muje sashen Bodejo na dan taba hira nadawo",Zuhra tace"to muje. Ummie ma mikewa tayi don shiga wankan,kallon juna Adda Zainab da hajiya Aliya sukayi tare da sakin murmushin jin dadi,bayan tashiga toilet din dama maganin na jikin zanin Adda Zainab da sauri ta kwantoshi tare da mikewa dai-dai inda suka ga Ummie nasa kai nan suka daga pillow din tare da dan yaye gefen bedshit suka cidda duvet still akasan bedshit din,suka sake daga duvet din sannan suka tarda matress din,cikin sauri suka barbade maganin tass tare da barbajeshi. Nan sukq maida komai normal tare da duban juna duka saki dariyar jin dadi,cikin sauri suka fita dakin tare da nufar masaukin su. ********** "Barki kiji hajiya Laure nibazan lamunci cin zarafin ki ba akan yara,ni ina ruwana da abinda yashiga tsakanin Rammat da Akeela?da Akeela da Rammat duk abu daya ne a wajena...... "Karya kike Biba ba haka kika daukesu ba,me kike nufi ko kiso ko kada kiso Akeela jinin Sauban ne kuma aure kamar anyi angama. "Hhhhhhhhh casss! Auren da auren manufa zaki hada?ai Yaya Laure duk wanda yayi hulda dake yasan halinki ciki da bai,dadin abin ragowa zai sama don nasan duk rashin jin diyata bata aikata munanan lefukan da jikanki ke aikata wanda ko karya sai haka. Bude baki Guggo Laure cike da mamakin irin kalaman hajiya Biba"Biba nizakiwa sharri kiyiwa jinina?wallahi sai nabaki mamaki sai na nuna miki dani kike zance. "Ina sauraren ki nidake kafasa,kuma niba sharri nake mata ba gaskiya nafada amma kijira lokaci komai zai bayyana kansa"! Tana gama fadar haka tajuya tashige daki tare da rufe kofar. Nanfa Guggo Laure tashiga zage-zage sai tsinewa Rammat albarka takeyi ta kuma ce tajira taga abinda zai faru sai ta bata mamaki. Hartana kwallan ta tsaban takaici haka tajuya gida. ******* Banda nishi babu abinda kakeji natashi a dakin hajiya daharatu,da ita da Akeela ne suke aikata masha'arsu cikin kwanciyar hankali. Hajiya dahara sai sumbatu take"please baby kada kibar ni koda kinyi,don nima inason abinda kikeso don Allah ki kara rikeni gam"nan ta cigaba da shirmenta Akeela nataya ta gabadayansu haihuwar uwayeensu da ubayensu( _wa'iyazubillah! Allah yakawo mu zamanin da aikata sabo yazoma ba abin komai ba,don Allah 'yan uwa me muke nema da wannan rayuwar?meyasa muka mance cewa duniya bafa ma tabbata bace? meyasa muke mance banda wannan rayuwar akwai wata da zamuyi anan gaba?Wai mun mance wancan rayuwar ba'a ciwo ne?ba tsufa ne?haka zalika ba'a mutuwa ne?duka ba'ayi,in wuta wutane idan aljanna aljanna ne straight babu kwana......don Allah 'yan uwa muji tsoron Allah mufa dunga tuna duk rintsi akwai mutuwa kuma dole ko wane mai rai yadandani nacinta.Yau ina annabi Adam AS?Ina annabi Ibrahim AS ina annabi Yusuf AS ina shugaban annabi Muhammad SAW? Duk cikansu sun koma ga Allah,to shin kai waye da bazaka koma ga Allah ba?ya Allah kajikan magabatan mu,kajikan iyayen mu,kajikan mu🤲🏽ya ubangiji kayima na karshe mekyau._ ) ++++ *MALAYSIA* ++++ Zaune yake a office dinsa kunnensa makale da waya sai dariya yakeyi"ah haba Galadima sai kace wani ragon namiji?wai me kadaukeni ne tsohon nan?nafa fika jarumta wallahi kaima kasan haka,dariya yasakeyi kana ya cigaba "To ya jikin Ummien?Masha Allah,aidama ita sai a hankali zata sakewa da ita Allah dai yakara lafiya da tsarewa,yanzu zan shiga meeting ne Galadima I will call yhu back,katse Kiran yayi yana mikewa tare da gyara suit din dake jikinsa. 𝐗𝐀𝐇𝐑𝐀𝐓𝐓𝐘 𝐂𝐄🥰 𝐋𝐚𝐥𝐥𝐚𝐢 𝐀𝐥𝐪𝐚𝐥𝐚𝐦𝐢🖊️ 𝐘𝐚𝐟𝐢 𝐭𝐚𝐤𝐨𝐛𝐢🗡️. 03/5/23. [5/7, 14:18] Xahratty (OUM AJMAL): 👨🏽‍🦳 *_GALADIMA FAMILY_*👨🏽‍🦳 Story&Written By *FATEEMA ZAHRA LAWAL* Marubuciyar⤵️ A DALILIN'YAR TSINTUWA. MIJIN ZAHRA. DIAMOND LADIES ( Daukar fansa)paid book. RUHIN AMRITA (FATALWA CE). Now *_GALADIMA FAMILY_* Page:- 33/34 _Bismillahir-rahmanir-raheem._ _____'Yan mata da dama sun mutu akan soyayyan Sauban a kasar sai dai wasu masu aji basu iya tunkararsa,wasu ko tsoro da shakkan sa ne yasa basu iya yimasa magana,wasu ko da kansu suke kai kansu office dinsa har sai da yahana sakatariyan shi bari ashigo saboda rashin hankalin 'yan matan yakoma bashi tsoro matuka,ya maida hankali sosai akan aikinshi daga can bangaren kuma yaron mai company din na shirye-shiryen dawowa zai amsa mukamin Sauban,dama can nashi ne rashin kammala master's din nasa ne ya hana abashi kujerun yana America karatu. **** *NIGERIA* **** Ummie kuwa a natse tafito daga bayin bayan ta kammala wankan,cikin nutsuwa tashirya tasanya wata Dubai gown fara tass tare da mayafinsa mai Kama da hijjab don har hannayenta ya rufe mata, gadon ta nufa tafara dube-dube sai dai da alama bataga abinda take nema ba, dai-dai lokacin Zuhra tayi sallama tashigo hannunta dauke da basket din kayan abinci,ajiyewa tayi tare da nufo inda take saboda ganin yanda taketa bincike. "Ummie lafiya?ko wani abun kike nema ne? dagowa Ummie tayi fuskar ta dauke da alhini tare da mamaki tace"Wai casbaha na nake nema amma ko sama ko kasa babu shi kuma akan bed din na ajiye don ko sanda nayi sallan magrib anan na aje gefen pillow dinnan amma kinga babu,gashi na kaku dana tada sallar,tayi maganar tana cilla pillow din gefe guda. "Ummie please kije kiyi sallan bari naduba kafin ki idar angani. "Ok my baby! Ummie ta ambata tare da tayar da sallan,nanfa Zuhra tayi dai- dai da gadon harda su yaye bedsheet da duvet din sai can gefen saqon tsakanin matress din da gadon tagani aiko tajawo tare da kokarin maida duvet din,fasawa tayi tare da sake yaye kayan shimfidan ta kakkabe kan katifar sosai tayi mai tatas sannan tadau bedsheets din da duvet din taje can corridor dinda zai sadaka da toilet tabude laundry basket ta saka su,adai dai nan Ummie ta idar da sallan. Ikon Allah Zuhra daga neman casbaha sai Kuma a bige da gyaran gado? murmushi kwance akan fuskar ta tace"Ummie wallahi sunyi datti ne naga sosai ga kuma datti harda kasa-kasa akan katifar shiyasa nacire"takarisa maganar tana bude closet,wanda bangare guda yake shake da bedsheets colours mabanbanta,duvets nd etc. Jawo wani tayi colour daya da wancan sai dai zane ne ya bambanta shima sai kalura ne zaka gane,wannan karan bata dauko duvet ba dama akwai wanda take lulluba dashi still a gefen bed din,shinfidawa tayi takuwa liliye gadon tsaf tare da sake gyaggyara pillows din,bayan ta kammala tajawo stool gaban kujeran da Ummie ke zaune ta ajiye,tana kokarin dauko basket dinne takatseta"Kinga ai kan carpet zan sauka naji kafata nayimin tsami,kije kikira addan ku kice nace suzo ga abincin idan kuma a kawo musu ne to.Zuhra tace. "Ok bari nasanar dasu,tayi maganar tare da fita,jingina ummie tayi da jikin gadon tare da rufe ido a haka taji sallamar zuhra. "Ummie sunce gasunan zuwa,babu kuwa jumawa da shigowan ta sai gasu suma sun shigo,da sauri Adda zainab tanufo ummie fuskanta cike da murmushi tace"bilkisou har kin fito wankan ne?Ummie tace"aiko nafito Adda ai ko kafin nafito naga kuntafi. "Ea muma munje muyi sallan ne,hajiya Aliya tace"sannu hajiya bilkisou ya jikin naki? Ummie tace"Alhamdulillah ai naji sauki wallahi. "To Masha Allah Allah dai yakaro mana lafiya dai,ubangji yabarki da diyarki"tayi maganar tana me shafa kan zuhra tana dariya. "Hajiya Aliya kenan Amin nagode. Nan Zuhra ta shiga zuzzuba musu abincin kowa na zabar abinda zaici, kallonta Ummie tayi tace"baby ke kinsa abincin kinci? "Ea Ummie naci tare dasu Bodejo da Amma aimu faten alkaman Bodejo mukasha,Kinga kuma itama Amma tanada diabetes in so sai yau akayi danan yawa,kuma fa nasa musu wadataccen kayan ciki. Adda zainab tace"ah lallai diyar albarka kinaji da wadannan kakannin naki,nikuwa bilkisou yanzu kindena cin dan gauda ne?dariya Ummie tayi"mekika gani Adda? "A'ah tambayace kawai naga kwana biyu banjin labarin dan gaudan. "Uhummm Adda kenan shekarun da yawa inaji rabona da cin dan gauda tun sanda nakeda cikin Zuhra,kuma Allah inaso cinshi sosai. Kama baki hajiya zainab tayi"cabb!gaskiya shekarun da yawa,Anya kuwa wannan ko kingani zaki iya ci kuwa ma? Dariya ummie tayi tace"ci kuwa sosai,inafa son shi don kawai bansamu bane,kai duk da haka ma nina mance da wani abu wai dan gauda. "Aikuwa insha Allah gobe da sassafe zan dauki driver muje kasuwa munemo garin dan gauda don acan zan siya masara ta kuma nabada nika a hada min komai da komai sai dai dana tashi nazo nayi miki,yajin ma musamu wanda yaji tafarnuwa don nasanki da son tafarnuwa,takarisa maganar tana dariya zuciyar ta fal nishadi. Nan ko suka cigaba da hirarsu suna dinner abin gunin sha'awa. Washegari kuwa kamar yanda hajiya zainab ta alkwaranta haka ne tafaru don wajen karfe sha daya na safe tafara kwabin dan gaudan ta tayi na ummie daban sannan ta kwaba nata dasu Bodejo daduk dai me sha'awan ci, zuhra na tayata,babu bata lokaci ta cewa zuhra tacigaba da zuba dan gaudan da wannan yayi za'a zuba na ummie ne. _____________ "Tab ai wallahi kinbani kunya Akeela kitsaya wannan yarinyar ta farfada miki magana haka?babu abinda ke cinta sai bakin ciki da hassada dole tasan kika mallaki guy dinnan kin mata fintinkau,na gaba yayi gaba na baya ai sai tsintar hula,aike dai kibari kawai zamuyi maganin tane karamar 'yar iska"Suby tayi maganar tana karkada kafafuwa. Akeela tasauke wani ajiyan zuciya tace"ni ba wannan nake tsoro ba kada watarana tace zata tonamin asiri kunsan fa tasammu farin sani ta kuma san abinda muke aikatawa. Tabe mouth zuleey tai tace"to sai mene?su da babu abinda suka sani sai Shan minti da samari fa?abi wannan saurayi abi wancan. "To ai inaso kisan nata me sauki ne akan namu namu yafi nata muni,wallahi ni da ace wani a cikinsu zaiji wannan labarin to nida shiga GALADIMA FAMILY matsayin mata wallahi sai gani sai hange don bazasu taba bari na aure ya Sauban ba,shiyasa nakeso Allah nadena wannan harkan fa don ni duk abinda zai shiga tsakanin aurena da ya sauban gudunsa nakeyi don rasa sa wallahi babban asara ne kuma bazan jura ba,wallahi na rasasa zan iya mutuwa. Wani harara zuleey ta watsa mata a ranta tace" _Hmmm indai ina raye bazaki taba auren saurayin da nake mafarkin aura ba tunda nataso nasan waye Muhammad Taleeb Muhammad Sauban yatafi da imanina,muddin bazan sameshi ba wallahi kema bazaki taba samun saba._ Suby tace"Lallai Akeela keko wani irin so kike ma Sauban haka?kinmance ba'a hada soyayyar mommy data kowa?ina guje miki randa zaki juyama mommy baya don kuwa kinsan sai kinshiga cikin gagaruman matsala. "Huhhhh! Suby don Allah kukasance koda yaushe cikin yimin fatan alheri ba fatan tsiya ba,meyasa kuke kokarin fasamin kwanya ne?inaso kugane cewa ko wanne da matsayinsa a waje na,amma banaso Kuna hada soyayyar ya Sauban data kowa please"takarisa zancen tana bata face. Da mamaki duk suka dubeta,zuleey tace"harda ta mommy?wani banzan kallo Akeela ta watsa mata tace"bansaniba mtsewwww,wallahi zuleey kwana biyu kaman kina neman zama munafuka ce,inafa lure dake kina kokarin shiga tsakanina da Mommy wallahi shiru kawai na miki,hmm kicigaba. "A'ah dakata mana Akeela"zuleey tayi maganar tana mikewa"akan me zakice min munafuka?menamiki na munafunci?kidubi tsaban ido na kicemin munafuka?ko a girme na girmeki kibar ganin ina binki kamar rakumi da akala wallahi bashi zaisa na dauki cin zarafi ba. Itama Akeela a fusace ta hayayyako mata"kada Allah yasa kidauk...... "Guys!guys!! Haba meye haka?kun manta mudin suwaye?meyasa kuke kokarin bawa haters damar shiga tsakaninmu?gaskiya banji dadi ba,gaskiya banson haka inkuwa ba haka ba sai atafi wajen mommy. "Bama sai anje ba!!duk su biyun suka hade baki,murmushi Akeela tasaki tace"Shikenan kiyahakuri zuleey,fuskan zuleey kadaran kadahan itama tace"Allah yabaki hakuri tana kare fadar haka tamike tare da daukan jakanta tadubi Suby tace"ni zan wuce gida yanzu Suby. Murmushi Suby tayi"Lallai zuleey Ashe baki huce ba?babban matsalata dake dama riko,meye amfanin hakan a tsakaninmu? "Ba maganar riko bane Suby zanje gida don nasan hajiya zatayi ta zuba idon ganina yanzu. "Shikenan kigaida gida sai munyi waya,Suby tafada. Akeela tace"adai yayyafewa juna akara hakuri,ko tankata zuleey batayi ba tafice tanajin zuciyarta namata wani irin tukuki. Tabe baki Suby tayi"banziya munafuka ainaji dadin abinda kika mata don yanzu Suby karfi da yaji takoyi munafunci da hassada" Akeela ta dubi Suby tace"Ashe kema kin fahimta?ai sainayi maganinta batasan ina raga mata bane saboda hater's kiris suke jira. Anan dai suka shige daki tare da rufo kofar rufff! *GALADIMA FAMILY* Sosai Ummie tadinga santin dan gaudan mai da yaji don yayi dadi sosai,suma su Bodejo kadan suka dan tsakura. Washegari su Adda zainab da Amma suka tattara komatsan su tare da Sha tara na arziki drivern Daddy yadaukesu don maidasu gida, Amma zata sauka gidan hajiya zainab ta kwana biyu sai takoma Zaria. Haka rayuwa yadinga tafiya tun ana abu saura kwanaki satittika watanni har takai dai yau saura 1month da 3 week's biki,indai aikin ya Sauban kuma yakoma Canada,aka bashi matsayin chairman na branch dinsu na Canada saboda sam basu fatan abinda zaisa su rasa sa matsayin ma'aikacin su jajirtacce mai amana, kafin kace me har ya Sauban yasake zama celebrity,kudi kuwa sun zauna masa sosai su Daddy ke alfahari dashi,shima ya taufeeq yasamu aiki a Abuja yana aiki a CBN, Aseef nedai har yanzu yake lecturing din a ABU wanda hakan sosai yake taba zuciyar Mom,kuma haryanzu bin malaman suke daga ita har hajiya Biba amma babu nasara don Sauban din ma baidawo kasar ba ballanta na aikin yatafi yanda akeso. A dai-dai wannan lokacin ne Kuma akatafi yajin aiki wanda yasa su Laila da nihal dawowa maidugri,su tattaro kayansu gabadaya a sashen Ummie suka tare saboda yanda gabadaya take sangarta 'yan matan. Mom tunda ta fahimci muneefa zata shiga gidan masu arziki kuma manyan mutane sai ta dora ma ranta salama tadena maganar wani hadin Sauban da muneefa kamar yanda ita takeso,don a zahirance iyayen yaron Suma sunada kudi sosai ga asali da nasaba. ________ "Hajiya don Allah kidena wahalar da kanki akan Sauban shidin yafi karfina wallahi ba ajina bane nasani kema Kuma kinsani,to mezesa muyi kokarin yaudarar kanmu?nina ma hakura dashi don ina rokon Allah yaciremin son shi,duk idan nayi sallah sai nayi addu'ah zabin mafi alkhairi. "Ke dalla tafi can kibani waje,wallahi bakinki yasari danyan Kashi Rammat,kinsan Allah kifita idona na rufe,meye Akeelan zata nuna miki?alhalin kinfita komai,yarinyar da ba abinda tasani sai gantali daga bin maza sai madigo,a haka kuma kikeso nabari suyi nasara? inason kudi Rammat!inason su,kina kallo 'yar uwanki duk a gidan mijinta ne baikai sauran karfi ba amma duk watan duniya shike ciyar damu cima mai kyau,shine kike kokarin yimin asaran samun mai kaini hajji da umara duk shekara?hajiya Biba takarisa maganar tana zaro ma Rammat idanuwa. "No hajiya ba haka nake nufi ba idan munada rabo ai ba lalai sai shiba kawai kimin zabin nagari. Tana kare fadan haka ta mike tare da wucewa kitchen. Da harara hajiya Biba tabita"ku kujimin 'ya 'yar bakin ciki,to baki Isa ba wallahi. XAHRATTY CE🥰 Lallai Alqalami 🖊️ yafi takobi🗡️ [5/9, 19:38] Xahratty (OUM AJMAL): 👨🏽‍🦳 *_GALADIMA FAMILY_*👨🏽‍🦳 Story&Written By *FATEEMA ZAHRA LAWAL* Marubuciyar⤵️ A DALILIN'YAR TSINTUWA. MIJIN ZAHRA. DIAMOND LADIES ( Daukar fansa)paid book. RUHIN AMRITA (FATALWA CE). Now *_GALADIMA FAMILY_* Page:- 35/36 _Bismillahir-rahmanir-raheem._ *THIS PAGE IS DEDICATED TO MY SWEET SISTER BILKISOU M BELLO,SHEKARU BIYU CIKIN NA UKU KENAN DA RASUWAR KI,ALLAH YAKAI RAHAMAR SA MAKWANCIN KI🤲🏽NAYI RASHIN AMINIYA,ABOKIYAR SHAWARA,WANDA SAMUN KAMARTA ZAIYI WUYA ALWAYS I MISS YOU AUNTY BILLY🥹* _____Guggo Laure ne zaune a daya daga cikin kujerun farlon Galadima,tsaban yanda masifa ke cinta idanuwan nan an kankance su,sauraran bayanan Galadima takeyi har yakai aya sannan tadora. "Yaya muhammadu nifa ba haka nake nufi ba,sam abinda Sauban yakeyi baya kyautawa,kamar yama mance da ranar auren shi da Akeela a kansa?tunda akasanya rana banaji yaron nan yataba nemanta a waya koda sau daya ne,sai kace wanda za'a aura masa makiyiyar sa?takarisa maganar tana sake tsuke fuska. Shidai Daddy shiru yayi gabadaya yana mamaki tare da shocked din halin guggon nasa wanda kullum babu alheri sai tashin hankali,gyaran murya Baba Hashim yayi yace"yanzu Guggo ita yarinyar ce duk ke fada miki haka? "Ai Hashimu koda Akeela bata fadamin ba abune da yake a bayyane domin kuwa ina gani da idanuwa na,ga damuwa karara tattare da ita,nasan baya sonta amma hakanan zai aureta kodan karfafa zumuncin mu,shi nakeso ta aura, Kuma ko baya sonta dole ya zauna da ita wallahi"takai aya tana zazzare idanuwa. "To yanzu menene abinda kikeso ayi Laure? "Tambayar da tuntuni ya kamata ace kamin kenan Yaya,sonake asashi yakira ta a waya kuma ko babu komai yadinga kulata ko yaya ne,amma yarinya tana neman ramewa da karewa a banza a wofi? "Shikenan Allah yashige mana gaba,insha Allah za'a kirashi amasa magana,amma maganar gaskiya Laure niban fiye son yawan korafe-korafe ba,haka za'ayi auren ana korafi dakawo kara?alhalin irin auren nan babu inda baya zuwa?gaskiya banso yakamata kizaunar da ita kikara fahimtar da ita menene aure?don shirmenta yayi yawa"Galadima yayi maganar yana bayyana bacin ransa karara. "Kayahakuri Yaya muhammadu za'a kiyaye. "Aini ba wani abu nace ba kuskuren da ake tatkawa nake kokarin gyarawa don bazamu zuba idanuwa muna gani ayita kawo korafe-korafen matsaloli ba,don Allah kinatsar da ita. Sosai jikin Guggo Laure yayi sanyi,gudun kada yayan nata ya botsare yasa tamike tare da yimusu sallama tafita,jingina Galadima yayi da jkin hadadden kujeran nasa yana me lumshe idanuwa,muryan Baba Hashim ya tsinkayo"ni wallahi lamarin auren Sauban da yarinyar nan fa yafara fitamin a rai,ace tun yanzu korafe-korafe sunfara shigowa ciki to inaga ma anyi?ita Guggo ko la'akari batayi da yaron nan fa auren dole za'a masa,auren biyayya zaiyi,yafada shi baya son yarinyar nd baya son abinda zai bata zumunci,to gaskiya za'a wa tufkar hanci tun wuri. Ajiyan zuciya Daddy ya sauke tare da cewa Allah ya kyauta nan suka cigaba da tattaunawan su akan tsaida ranar bikin tunda iyayen ma'aruf mijin da zai aure muneefa suka basu dama. Haka dai rayuwa ta cigaba da tafiya har takama yau saura wata guda biki,akuma ranar ne Ammi da Ummie suka shirya sai kasar Dubai don siyoma yara kayan kitchen don ko Mom bata sani ba,a gefen ta itama sai shiri takeyi batare da tasaka kowa a cikinsu ba don tayi alkawarin sai ta shayar da kowa mamaki da kayan kitchen din muneefa hakan ce yasa takira kawarta daga Lagos kan a turo mata da kayan kitchen na million 1. Bangaren su Ummie kuwa kwanansu biyu suka gama shirye-shiryen su don juyowa saboda kayansu tun a ranar suka isa Lagos daganan aka wutu dasu kaduna JABI ROAD wajen mommy,don agidan abokin Abbie suka sauka wani balarabe me suna Omerr Aslam,sun kuma samu tarba me kyau inda suka masu Ummie alkawarin zuwa biki insha Allah shida babban dansa,da zasu tafi suka musu kyautan sha tara na arziki don mahaukatan yadika da shaddo di yayi akwati guda yace na Taufeeq da Sauban,ko wanne 10 10 yrd kusan set biyar² zasu tashi dashi,sosai su Ummie sukayi godiya matan shi kuma hajiya Amna ta hadama amare akwati guda na dogayen riguna, zuhra ma ta mata akwati guda haka su Ummie suka bari Dubai cike dajin dadi,kwanan Ummie da Ammi biyu a kaduna suka wuceZaria kai tsaye dukkan su anguwan su Ammi suka nufa saboda ita iyayenta sun rasu sai 'yan uwa don haka zata ta kwana daya gobe da safe tazo gidan su Ummie don zasubi jirgin 4:30 ne sai su wuce gida. Sosai ko wacce 'yan uwa sunyi murna da ganinta, washegari kuwa suka nufi gida. ********** "Aminiyata nifa a tsorace nake haryanzu ba'a kirani ance gashi wani abu yasameta ba,ke in takaice miki ma har Zaria sunje itada matan Alhaji Taleeb sun kwana"Adda Zainab ne ke maganar nan. "Hmmm nifa lamarin matan nan hajiya Zainab yafara bani tsoro,kinsan Kuma aikin nan yanda aka umurce mu haka muka gudanar,to amma bari nakira boka hatsabibi"hajiya Aliya ta ida fada tana dauko wayarta dake aje kan center table,nan tashiga laluben number boka amma abin mamaki babu ita babu alamanta,sake dai bincika wa tayi amma still bata gani number,nandanan tamike tsaye cikin tashin hankali tare da dafe kirji tace"Nashiga uku ni Aliya,taya lefin wani zai shafe wani?da sauri Adda Zainab tamike tana dubanta. "Lafiya aminiya meke faruwa ne?naga hankalinki atashe kuma ga abinda kikace?duban hajiya Zainab hajiya Aliya tayi tace. "Narasa number boka hatsabibi kuma wallahi ko kaffara bazanyi ba munyi masa gagarumin aiki mun lalata masa aiki,nidai da nasan haka ne wallahi da nabarki ke kadai kinyi aikin ki da bansa hannu ba,nashiga uku gashi iya duba na naduba banga number ba,aikin banza kema ba number ne gareki ba. "Munshiga uku yanzu Yaya zamuyi. Yaya zamuyi kuwa tafiya ce ta ganmu don kuwa tunda kikaga babu number turo aljanu yayi suka goge don yasan dole mu nemesa kinsan abinda yace fa tun farko. "Nasani sai dai gaskiya nikam wannan karan da wuya nakoma don gudun zargi banso a zarge ni.Wani banzan kallo hajiya Aliya ta aikama Adda Zainab"mekike nufi kenan hajiya Zainab?kina nufin nikadai zanje?cabdijam!wallahi baki isa ba aikin kifa akeyi. Kasa da murya Adda Zainab tayi tare da marairaice fuska tace"A'ah ko daya ba haka nake nufi ba,banason abinda zaisa idon mutane sufara sauka kan mu kingane?ke widowed ce nikuma kinga matan aure CE so sai afi samin Ido ba'a samiki ba,sannan kinsan halin Alhaji na ciki da bai kinsan halinshi sarai,don Allah kiyahakuri kije mana duk abinda ke akwai inkin dawo sai muji kokuwa? Dan sakin fuska hajiya Aliya tayi tace"Ahto 😏 kada a maidani wata bican fa, saboda ni for sale CE. Dariya Adda Zainab tayi"A'ah ko daya wallahi matsayin ki ya wuce haka a wajena kedin ta daban ce so kisha kurumin ki nidake we're together"takarisa zancen suna tafawa da juna tare da kyalkyalewa da dariya. "Nima idan naje akwai aikin da nakeso yamin don inaso nayi wufff da wani Alhaji dana gani lokaci daya yashiga zuciya ta yayi kane-kane. "Au dagaske?Kai amma matan nan ke shedaniya ce shine bani da labari ko a sanarmin,?to a'ina aka samosa? "Hmmmm kedai bari nifa hajiya Zainab da kafar dama nashiga GALADIMA house don anan naga MIJIN Aure. 😳Diddilo idanuwa hajiya Zainab tayi gabanta na masifan faduwa cikin mamaki tace"kekuwa wanene wannan? Wani dariyan hajiya Aliya ta kyalkyale dashi tare da cewa kedai bari ayi sha'ani kawai,tana sake kyalkyala dariya. Itakuwa Adda Zainab gabanta ne yashiga dakan lugude a zuciyar ta tace _Da yarda bi'izinillah babu ke babu shiga gidan GALADIMA hajiya Aliya,shedaniya kawai niban shiga gidan bane kece zaki shiga?_ a fili kuwa tasaki dariya tare da cewa"Ayyoririrrriiiiii amarya amarya amarya a gidan GALADIMA house,pls kifadamun wa idonki ya kyallo ne? Fari hajiya Aliya tashiga yi da idanuwa kamar wata budurwa. *GALADIMA FAMILY* Kafin kace me sha'anin biki yagama kankama yinshi kawai akeyi babu kama hannun yaro, Rammat tayi kuka sosai saboda tasan cewa bazata taba samun Sauban ba sosai tamika lamuran ta ga Allah ta fawwala masa komai,inda hajiya Biba ko takasa natsuwa shige shigen malamai ko takasa sai canye mata kudade sukeyi ko wanne da karyan dayake lafta mata,hakan ba karamin sosa zuciyar Rammatc set yakeyi ba A lokacin da biki yarage saura sati uku da kafini daya dangin ma'aruf gobe zasu kawo lefe,kafin kace me anfara tarbansu tun daren ranar,duk wani kalolin girki Ummie da Ammi ne sukayi tare da Mashahuda da zuhra harda ma muneefan. Washegari kuwa takama asabar su Mashahuda,muneefa,duk basunan sunje gidan da ake musu gyaran jiki su kuma su zuhra,Laila da nihal suna gida. Wajen karfe daya mommy da Abba suka diro mota biyu sukayo don babu wanda yasan da zuwan su,sai karar Horn dana motoci akafara ji,ko kafin kace me ma'aikatan gidan sun bude dayar motar Sharon sunfara fiddo da akwatuna suna nufar sashen Galadima,a lokacin mutanen gidan suka firfito ko wanne baki bude cike da mamaki akwatuna sha shidda cif. Ummie tadubi mommy tace"Kai mommyn yara wannan wane irin zuwa ne haka?nuna Abba tayi tace"surprise ne daga Abba babu ruwana, dai-dai nan Zuhra tazo da gudu ta cafeta tsananin murna,Suma su nihal karisowa sukayi suna ihun murna,kafin kace me gida yafara hautsinewa da hayaniya don maimoon da Ateek ganin Zuhra suma yasasu murna nan su Ummie suka koma ciki don shiryawa su kuma suka mika apartment din Galadima don mika gaisuwa, da sallama suka shiga sashen inda suka cidda Bodejo rike da haba tana karewa lefen kallo. "Hauwa wannan lefen na waye haka kuka taho dashi?ni fatsuma. "Ai dai kyabari su sasara ko?daga shigowa ko hutawa ba'a yiba bare maganar gaisawa sai ki fara da lefe? Murmushi Abba da mommy sukayi,nan suka fara gaggaisawa da juna, sun gaisa sosai sannan mommy tamike tace bari taje tayi sallah. Anan Abba ke sanar dashi kayan lefen Taufeeq ne daya hado masa shine nasa gudummawar don har ya sanar dashi yace kada yahada,dama shida Sauban yaso hada musu amma sai yace shi tuntun-tuni ya gama hada lefen shi idan zaidawo zai taho dasu,naso duk da haka na masa amma sai yanuna min kada ayi almubazzaranci. Galadima yace"gaskiya ne kaga da da hankali ko, shikenan Allah ya musu albarka yanzu yaushe yace ma zeshigo?gaskiya bamuyi maganar ba amma ai dole next week yashigo Galadima. "Masha Allah Haroun Allah ya muku albarka ubangiji ya kara hada mun kawunan ku. Ameen suka amsa shida Bodejo. Nan yasake gyaran murya sai Kuma su matan na biya musu kujeran umra,shima Sauban da wannan nake tunanin na biyama yarinyar da zai auran. "Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Allah ya maka albarka harouna ka kyauta kaima Allah ya saka da alkhairi. Da ameen still ya amsa nan suka dasa hira Bodejo da Galadima zuciyoyin su wasai da jin dadi. Xahratty CE🥰 Lallai Alqalami 🖊️ yafi takobi🗡️ 10/3/23. [5/24, 17:48] Xahratty (OUM AJMAL): 👨🏽‍🦳 *_GALADIMA FAMILY_*👨🏽‍🦳 Story&Written By *FATEEMA ZAHRA LAWAL* Marubuciyar⤵️ A DALILIN'YAR TSINTUWA. MIJIN ZAHRA. DIAMOND LADIES ( Daukar fansa)paid book. RUHIN AMRITA (FATALWA CE). Now *_GALADIMA FAMILY_* Page:- 37/38 _Bismillahir-rahmanir-raheem._ ______Da la'asar family din ma'aruf suka iso,sosai suka samu tarba me girma da karamci a farlon Galadima don maza ne suka kawo lefen,su kansu sai da suka tabbatar da ba auren kwadayi dansu yayi ba tabbas ya aure 'yar gidan tarbiyya da mutumci saboda yanda Daddy, Abba Baba Hasheem suka tarbesu cike da mutumtawa,gefe daya ga tsoho me ran karfe yasha wata mahaukaciyar danyar shadda fara tasss sai maiko takeyi,shikanshi ya burgesu yanda sukaji Yana magana cike da dattaku da ilimin addini. An gabatar musu da abinci,namomi,lemukan gora, fruits kaloli inda suka so kin ci amma Galadima ya nuna musu ba ahaka dole kowa yaci abincin Yana santi don dama gaskiya surikan Galadima gwanaye ne wajen girki musamman Ammi, Ummie kuwa ta kware wajen iya na kasashen waje saboda rayuwar da sukafi yinta acan,mommy da Mom ma ba baya don idan Ammi da Ummie basu waje to sudinfa on top ne. Sai wajen karfe shida suka fita tare da tsaraban kalolin snaks sunfa kala biyar anyi raping nasu a kwalaye sai katan-katan lemuka da ruwa ammafa babu tukwici don anyi ba'ayi bane,wannan ma don gidan masu kudi ne shiyasa,sosai sukaji dadi su shidda ne haka suka tafi suna yabon wadannan ahalin. BAYAN magrib su Daddy sukasa ma'aikatan gidan maida akwatunan babban farlon Bodejo, nanfa mommy dasu nihal suka takarkare suka dinga sakin guda,don kaya kuwa Masha Allah komai washabban washabban don akwatuna goma sha hudu ne gasunan aka kawo,nanfa aka shisshigo dana Mashahuda akwatuna sha shida,gida fa ya kacame don sai da Galadima yayi musu gyaran murya don duk Wanda kaga fuskanshi kasan yana cikin farin ciki. Mom ma tayi murna don bata taba arzikin su ma'aruf dinma har takai haka ba,nanfa ta sulale tafara kiran 'yan uwanta da abokan arziki tana sanar musu, Ammi ma taji dadi sai dai damuwa karara ya bayyana kan fuskanta bayan mommy tamata bayanin abinda Sauban yace akan maganar lefensa. "Gaskiya yaron nan be kyauta ba memakon yayi komai nashi cikin kamata gaskiya sai na batama Sauban rai, Ummie ne ta dakatar da ita. "Haba Ammi kinaji fa anmiki Karin bayani yace yahada nasa bayason almubazzaranci ne shiyasa,don Allah ki kwantar da halinki ninasan yaro na wallahi ba daga baya ba", Mommy tace"Aifa kara tuna mata Ummie. *BAYAN KWANA BIYU* Akeela ce kwance akan gadon ta tana bacci, vibration din wayarta ne yatashe ta,dan tsaki taja kafin tayi picking cikin muryan bacci tace"Kai Suby barci fa nakeyi,kinsan da anshiga next week ba isasshen baccin za'ayi ba"daga can bangaren Suby tace"ke dalla can ba wannan ba ki shiga account din Rammat,kiga yanda tayi posting videos din lefen kannen mijinki,mahaukatan kayan lefe gashinan IG ta dauka. Zabura Akeela tayi ta tashi zaune cikin sauri tace"suwa kenan? "Hmm kannen mijinki da za'ayi bikin ku rada day.....ai Suby bata karisa magana ba Akeela ta datse wayar. Kaitsaye Instagram tahau,Nan ta watsa fiki-fikin idanuwan ta kan wayar,da sauri tamike tare da kama mouth"Ewwee!ai da gudu tafita bedroom dinta"Mom! Mom!! Tashiga kwalama mamanta Kira,da sauri tafito daga kitchen,"Akeela wane irin Kira ne haka? "Mom kallah,tayi maganar tana mika mata wayar,ansa tayi. Wannan lefen na waye haka?tayi mgnr ta diddilo idanuwa. "Hhhhhhhh! GALADIMA FAMILY Kenan ana fada miki, kayan lefen kannen bby Sauban ne. "Kai Masha Allah kaya sunyi kyau,Wai wai ko wacce gidan manya zata shiga kenan? "Ea daya zata aure Dan gidan maishanu family,dayan kuma dan Abbie daya rasu zata aura. "Kai Masha Allah kaya sunyi kyau,Allah yasanya alkhairi ya kade fitina,ubangiji ya basu zaman lafiya. "Mom saura nawa,amma ainima yaka mata ace ankawo nawa yanzu,tayi maganar tana bata fuska . Harara ta wugamata tare da shogewa kitchen din,da sauri itama Akeela tanufi kofan fita,kaitsaye sashin Guggo Laure ta nufa,itama nuna mata videon tayi,ai bata gama gani ba tafara sallallami"duk ankawo nasu amma ke basu kawo naki ba?to me mutanen nan suke nufi danine?sannan akasa kirana a amsa kayan dani?wallahi sai yau nasake tabbatar da Yaya Bodejo bata sona,bata son jinina,lallai ko yanzu zanje gidan. Caraf Akeela tayi"wallahi dani zaki Guggo don inason ganin lefen nan azahirance, shikenan maza ki shirya muje. Aiko cikin farin ciki Akeela ta fita, Guggo Laure bata jima ba tashirya tafito tana mitan har yanzu Akeela bata fito ba?Nan mujaheed dandan Baba sani yashigo gidan da mashin dinshi kirar jincheng roba -roba. "Guggo fita zakiyi ne haka? "Ea wallahi mujaheed zanje gidan Yaya muhammadu ne nadawo nida Akeela, murmushi kwance saman fuskansa yace"Au da amarya zaku fita?ni mumma dade bamu hadu da Akeela ba Guggo. Yatsine baki Guggo Laure tayi tace"to kunyar wa mujaheed?ai kunyarka,kuna gida daya bazaka shiga kaduba ta ba? "Guggo kenan,ko nashiga wataran mom zatace bata tashi ba ko batanan,to Yaya zanyi? Mere Guggo Laure tayi da baki tare da cewa"kaga bari nashiga naga dalilin da yasa ja'irar yarinyar nan shanya ni,takarisa maganar tana shiga sashen,nan tafara juyo fadar Mom. "Waike Akeela sai yaushe zakiyi hankali? meyasa baki da kunya?wallahi kika fita gidan nan nidake ne,bubbuga kafafuwa Akeela tafara. "To yayane meke faruwa ne?ni inacan waje inajiran ki ke kuma kinshanya ni. "To ba Mom bane wai bazani ba,haka kawai tace bazani ba,kafin Guggo tayi magana Mom ta cabe"fisabilillah Guggo taya za'a barta taje gidan surukai saura sati biyu biki?wallahi rashin kunyar Akeela kullum gaba yakeyi. "Maimuna kedai sai kayi bagidajiya ko mu tsofaffin da bazamu dinga wannan abinba bare ku yara,yanzu lefi ne don Akeela ta shirya munje gidan Yaya muhammadu da ita?ke don ma banyi niyya bane da wallahi ranar asabar mai zuwa zata koma can da zama,zo muje kinji",tana kare fadan hakan suka fita Akeela nabiye da ita tasha wani dan ziririn mayafi tana karkada shafaffen baya kamar andanne da iron. Mom din Akeela kuwa sakin baki tayi tana duban su har suka bar farlon,a fili ta furta"Wallahi sam abinda Guggo take bata dacewa,wannan ina mutum zai yarda yabata danshi?mtsewww taja tsaki tare da juyawa ta koma kitchen din. Su Guggo Laure kuwa koda suka isa gidan sun cidda ya sake kacamewa don Aunty Maryam ma ta iso,wasu daga cikin 'yan uwan Bodejo su uku suma sunzo,hannu bibbiyu aka tarbeta kamar yanda aka saba,nan aka shiga gaishe-gaishe Guggo Laure tace"Ashe kuma ankawo lefen yara banida labari don ba'a kirani a amsa kaya dani ba,shima a waya yanzu Akeela take nuna min shine nace bari nazo naga zahiri"tayi maganar tana dariya kasa-kasa. "To menene a amsan lefe Laure kinmanta shi taufeeq mune zamu hada mukawo? Harouna su suka kawo lefen Mashahuda shida hauwa'u daga kaduna,a ranar kuma aka kawo na muneefa,to ai ba wani abu bane,sannan yaranki duk maza ne ba mata ba balle ace suzo a amshe kayan dasu. "Amma Yaya Bodejo duk da maza ne ai naga suna da matayensu ko?ko babu komai ai ace ko su maimuna da uwar mujaheed ne a turo,ammaai babu komai dama idan ba'a dauke ka da muhimmanci ba babu abinda bazaka gani ba. "Guggo wallahi ko daya ba haka bane,kayan ma ba mata ne suka kawo ba mazane suka kawo kayan. Guggo Laure tace"Maryam to tunda mazane suka kawo,ba sai akira ko mansir bane? Aunty Maryam tace"To shikenan Guggo kiyahakuri ai akwai na wasu 'yan matan har guda uku bayan wadannan kibari idan za'ayi nasu zakiji komai mun amsa lefinmu dai wannan. Ture kaga tsiya Guggo Laure tayiwa dan kwalinta tare da hura hanci tace"da dai yafi kam. Bodejo kuwa tun sanda taji Guggo Laure tafara korafi ta yunkura tabar wajen. "To shi Sauban nashi lefen be isone kuwa ba? Dan murmushi Aunty Maryam tayi tace"Ea to ina tunanin sai next week zai iso dasu 'yan Dubai ba,kinsan shi acan yake hada lefensa"murmushi Guggo laure tayi cike da jindadi tace. "Ah Masha Allah, Allah dai ya iso mana dashi lafiya,da Ameen aka amsa gabadaya. Akeela sosai taji dadi a ranta,sai lokacin ta tuna bata gaishe da Aunty Maryam ba,cikin kissa tashiga gaisheta, Aunty Maryam itama ta amsa cike da kulawar don batasan itace Akeelan ba itadai taji ana cewa jikar Guggo Laure ce. A kwana atashi babu wuya yau biki yarage saura sati guda kuma ayau Sauban zai diro don taufeeq yatafi daukosa tare da wasu abokansa su hudu,don kayan kwana biyu kenan da isowar su yana hannun wata kawar Ammi an aje a gidan.Itama Aunty labeeba anjima zasu kariso,gida fa yacika yayi tam,a gefe daya kuma Guggo Laure ranta a jagule yake saboda rashin ganin ba'a kawo lefe ba don kuka Akeela ta tasata tafara mata,aiko ana cikin hakane baba sani yayi sallama yashigo farlon. Gaida Guggo yayi cikin kulawa face dinsa dauke da raha yafara magana"Guggo dama maganar kayan lefen Akeela ne ankawo sunzo bayan la'asar don yanzu suka taf......ai be karasa magana ba Guggo Laure tamike tare da sakin wani guda. "Ayyyiirirrrriiiii!Allah nagode ma,sani ina suke masu kawo kayan?. "Sun tafi tun dazu Guggo. Shigowa Alhaji mansir yayi, ya gaida Guggo,nanfa ta amsa baki a yage tsananin murna. "Sani to ina kayan suke yanzu? Baba sani yace"Suna farlona. Hade rai tayi tace"a sashen ka Wai kake nufi? Sake tsuke fuska tayi tare da dubansa tace"A'ah magana ta Allah niban yarda ba akan wane dalili za'a ajiye kaya a sashenka ga sashin uban 'ya?gaskiya ayi maza-maza adawo dashi sashin mansir,daga baba sani har baba mansir,mujaheed sakin baki sukayi suna duban Guggo laure,cikin bacin rai Baba mansir yadago zaiyi magana,katsesa Baba Sanj yayi ta hanyar daga masa hannu sannan yadubi mujaheed wanda ranshi yakai kololuwar baci yace"Mujaheed maza kaje parlo na ga key din ka kwaso kayan lefen kanwar ka kakawo dakin Guggo,cikin ladabi Mujaheed yasa hannu ya amsa key din tare da juyawa yatafi,da harara Guggo laure tabishi tana Jan tsaki kasa². Baijima ba yafara zhigowa da akwatunan,aifa nan Guggo laure tashiga guda daga Mom din Akeela har hajiya zainab murna sukeyi baki har kunne,kafin kace me gida yafara cika da makota zuwa ganin kayan lefe,sosai kayan sukayi kyau Masha Allah don Sauban yakashe kudi musamman hand bag da shoes nd Dubai gowns,kaya dai sunyi kyau sai dai makiyi akwatuna takwas yayi. Nanfa kafin kace me kawayen Akeela sunfara watsawa a duniya. Washegari ya Sauban yaturo mata da message kan yananan shigowa,murna Akeela tayi saboda aganinta yafara son tane da kula da ita a fili ta furta"Lallai bokan Guggo yasan aikin shi, hehehehe ya Sauban kenan ai kashigo hannu na kagama,takare maganar tana mikewa tare da fadawa toilet,sabulan ta na dilka dana bleaching da ake hada mata tafara muttsike jikinta dshi before tashiga wanka. Aiko washegari su Suby da Zuleey suka zo gidan inda suka je wani restaurant suka siyo musu snack's lafiyayyu,tare da shiryawa ala dole zakace su ne suka hada. Sai wajen 5:30 su ya Sauban suka iso dashi da Taufeeq da Kareem duk cikan su sunyi kyau musamman Sauban da Taufeeq duk da cewa manyan kaya suka sanya,shadda ya Sauban yasanya me ruwan kanwa inda aka mata dinki half jamfa sai hannun ma gajere hulan kanshi ya murzata brown sai cover shoe da ya Sanya brown,agogon hannun shi kirar Gucci me ruwan kanwa,inda farin fatan shi yafito yayi masifan kyau,face dinshi sanye da shade fuskar nan babu annuri ko kadan,shima ya Taufeeq shaddar ya sanya dark blue shima half jamfa amma shi besa hula ba takalmin shi da agogon sa bakake shima yayi kyau duk da daka gansu shida Sauban zaka san jini daya ne, malam Kareem kuwa kananun kaya yasanya jeans da t shirt sai dai yayi kyau don duk cikansu badai iya wanka ba,gabadaya sun rude da ganin zaratan mazan,sosai Zuleey da Suby suka hadiye miyau don gabadaya sunyi mutuwan tsaye da ganinsu musamman Sauban. "Hello sannun ku da zuwa,please have a sit, zuleey tayi karfin fada tana nunawa Sauban inda zai zauna,cike da karairaya ita da Suby suka samu 2 seater suka zauna,inda su Sauban ke zaune a 3 seater,cikin kissa Suby tasa wayar s kunne tare da fara magana"hello kawata wai mekikeyi ne?kifito mana haka gasu angon namu fa yazo,takarisa maganar tana lankwasa muryan ka,ta wutsiyar ido Zuleey ta gallamata harara tana me mikewa. Yake tasaki tana saka idonta kan na Taufeeq don sam kwarjinin da Sauban ya mata yasa takasa hada Ido dashi tace"excuse me!tayi maganar tana watsa yatsu wadanda suka sha kunbunan kanti,sanye take da wani riga da skirt na atamfa sunyi bala'in matseta duk da ba bayan ne da itaba amma karfi da yaji ake jujjuya su. Ko kallonta Sauban beyi ba don shi hankalin sa Yana ma kan wayan dayake daddanawa ne, Taufeeq ne da Kareem sukayi karfin halin amsa mata, Suby tace"ya shirye-shirye guy's?munji ku shiru Ashe yau dinma kuna tafe?shiru kowannen su ya mata yana danna wayansa,da mamaki Suby ta dubesu amma sai wata zuciyar ta bata amsa da kila basu jita bane. "Oyoyo sweetheart"Akeela tashigo farlon da gudu tare da nufar Sauban sai dai ganin face dinsa da rayi yasa dole ta ajiye duk wani kissa da bariki da taso aiwatar wa,cikin rawar jiki tashiga gaishesu,cike da kulawa Taufeeq da Kareem suka amsata amma gogan ko dagowa beyi ba balle tasa ran ze amsata,"amarya kina lafiya?karem yayi maganar yana dan murmushi, Akeela ma murmushin tayi tace"lafiya lou munjiku shiru ga events da zamu fara gudanar wa tun jiya amma baku iso ba sai yau. "Aikam kinsan ogan be gama wattaakewa da tafiya ba so munjira ya huta sai mu shigo agaisa, Akeela tace"eyya babu komai,duban Sauban tayi tare da langabar dakai tace"Baby inata magana amma kayi shiru, dagowa Sauban yayi tare da Kura mata ido duk da bata ganin eye ball nashi amma sai da kallon yasata taji babu dadi,agogon hannun sa ya kalla tare da duban su yace"please Taufeeq kuyi abinda yakawo mu cuz time yana tafiya, Taufeeq yace"Ok. Dagowa yayi cike da basarwa yadubi Akeela yace"amarya nawa kuke da bukata ne?na hidima nd everything? "10 millions naira! Sukaji ambasu amsa,duk cikansu suka dubi inda maganar yafito har shi gogan sai da yadago. Xahratty CE🥰 Lallai Alqalami 🖊️ yafi takobi🗡️ [5/28, 11:27] Xahratty (OUM AJMAL): 👨🏽‍🦳 *_GALADIMA FAMILY_*👨🏽‍🦳 Story&Written By *FATEEMA ZAHRA LAWAL* Marubuciyar⤵️ A DALILIN'YAR TSINTUWA. MIJIN ZAHRA. DIAMOND LADIES ( Daukar fansa)paid book. RUHIN AMRITA (FATALWA CE). Now *_GALADIMA FAMILY_* Page 39/40 ______Sosai maganganun hajiya Aliya suka tsaya ma Adda zainab a ranta domin tashiga fargaba tare da tsananin tashin hankali,lallai tasan wacece hajiya Aliya duk abinda ta sama gaba to tabbas sai ta cimma nasara,hankalinta a tashe yake sosai take safa da marwa a cikin dakin nata,a gefe guda kuma damuwar ta daya shine haryanzu bataji sakamako akan bilkisou ba,a koda yaushe cikin jiran tsammanin kira take amma shiru ga biki ya gabato saura kwana biyar kuma can maidugrin zasu nufa don acan ne ake taron biki,sosai hankalinta yakasu gida biyu,wani tunani ne yafado mata cikin rai don haka da sauri tadauki wayarta tafara laluban layin hajiya Aliya,sai dai kash!sanar da ita ake wayan fa haryanzu a kashe take alamu ya nuna tabbas bata dawo daga kasar nijar dinba. ****** Sanye takeda doguwar riga mai hannun armless,roba ce tasamu waje ta lafe a jikinta wanda har tayi sanadin bayyanan duk wani halittun ta saboda shape duk ya bayyana,musamman kugunta wanda yake a tsuke sai hips daya nemi waje ya baje ga tudun bom bom,hankalinta a kwance take tafiya da alamu video call takeyi don murmushi takeyi da surutai.Kallo daya ya mata tare da kauda fuskan shi cikin basarwa,idanunshi ne suka sauka akan wani security dake bakin gate ya kurawa mata idanuwa ko kiftawa bayayi like maye,maida dubanshi yayi gareta yaga tabbas ita yaron yake kallo,ranshi ne yayi kololuwan baci wanda har sai da yakasa control din kansa,idanuwan sa sun kankanci cikin bacin rai yanufo inda take gadan²,babu zato taji an fusgota tare da yarfa mata mari. Lokaci guda tanemi jinta da ganinta tarasa don sun dauki batasan sanda tasaki wani ihu ba tare da dafe kunci don rabon da ayi mata irin wannan marin ta manta,da sauri Ammi ta futo daga apartment dinta don yafi kusa saisu Mashahuda da suka fito daga apartment din Mom suma a guje saboda karar ihun nata,nunata yashiga yi da hannu bakinsa har wani rawa² yake amma yakasa furta komai."Menene haka Son?me ta maka lafiyan ka lau kuwa?gabadaya yakasa magana,da sauri yajuya kai tsaye gate din yanufa,koda yaje beyi wata² ba ya zabga ma security dinnan mari,a gigice ya dafe kuncin jikinsa babu inda baya rawa,cakumo kwalar rigansa yayi tare da diddilo masa idanuwa yace"idan nasake kama ka kana ma wata mace a gidannan irin kallon da kama wannan yarinyar yau,wallahi sai kabar aiki a gidan nan tare da tsarabar nakasa ka don sai na nakasa naga uban da ya tsaya maka,stupid son of a bitch!! Yakarasa maganar tare da hankada sa baya,a gigice security dinnan yanufi kofan gate yafice jikinsa na wani irin rawa,juyowa yayi kaitsaye yanufi parking space, Ammi ce tayi saurin isa garesa"Son wai ba magana nake maka ba kana jina meta maka da zaka mata irin wannan marin?kaga yanda shatin yatsunka suka fito a kumatun ta kuwa?bakinsa na rawa yace"Saboda rashin kamun kai na yarinyar nan haka taga sauran 'yan uwanta ke dressing a cikin gidan?ta fito tana karkada ma security jiki tana shaking body?ko kunya bataji?wallahi daga yau nasake kamata da makamancin dressing dinnan sai na lahira yafita jindadi"yakarisa shiga motar tare da kunnata yayi reverse yana dannan wani azababben horn. Juyawa Ammi tayi taga dressing din jikin Zuhra,babu wani aibu a shiganta amma yamata wannan marin?girgiza kai Ammi tayi tare da nufar Zuhra wacce banda kuka babu abinda takeyi gashi bakinta yakasa shiru cikin muryan kuka take magana"Ni me dressing dina yayi?kawai saboda cin zali zemun wannan marin wallahi sai Allah yasaka min tun ina karama yatsaneni saboda kawai yatsaneni shine zaizo yamin marin nan Allah nagani,kuma ban......"Zuhra!!! Bata karisa maganar ba taji ankirata cikin daga murya, Ummie ce,karisowa tayi fuskar ta babu wani walwala tace"mekike so kice?cewa zakiyi da baki yafe ba?shidin sa'an kine?kull kada nasake ji,meyasa bema sauran ba sai ke kidubi shigan su mana,amma ai basu fito ba suna killace a daki bari har idon security yakai kansu. Cikin muryan kuka Zuhra tace"amma Ummi aini shiga ta duk tafi tasu mutumci. Ummie tace"naki yaga yafi muni sai ki gyara gaba inba haka ba zakisha wahalar sa kuma niba zan hanashi hukunta ki ba,tana kare fadan hakan tajuya,kamota Ammi tayi tanufi apartment dinta da ita"Why? Why?dani kadai yasama ido a gidan nan baga su Aunty Mashahuda ba wallahi Ammi nima aurena zanyi na huta kawai ranar bikinsu Aunty Mashahuda a dauramin aure tare da nasu nima na huta"takarisa maganar cikin muryan kuka,dubanta Aunty Maryam tayi tace"Oh really?to a'ina kika samo mana mijin naki?sai ama Daddy magana idan yadawo.Duk dariya 'yan parlon suka sanya,Ammi tace"gaskiya kam Maryam ya kamata bari muji Koda wa za'a samata ranar. Shiru Zuhra tayi kamar ruwa yacita sai yanzu ta fanimci baran baramar da tayi,rufe fuska tayi da sauri, Mashahuda tace"kila da Shuraim ne Ammi, Ammi tace"wanene haka? Mashahuda tace"Shuraim fa cousin din su ya Asheer din Aunty falmata, Ammi tace"wannan yaron?lallai na ganesa kuma sosai na yaba da halayensa don yayi his very innocent,murmushi Zuhra tayi tare da nufar hanyar bedroom din Aunty Mashahuda cikin daga murya tace"wallahi Ammi niba da gaske nakeyi ba da wasa nakeyi wallahi niba yanzu zanyi aure ba sai na kammala degree dina tukuna. Duk cikansu dariya suka sanya. *** *NIJAR* *** Sosai ya kura mata idanuwa saboda yaji dadin maganarta,cigaba da magana tayi"nifa boka hatsabibi babu cin amana a cikin lamarin nan naga tana wasa da aurenta shiyasa ninakeso na aure Alhaji iliyasu zanyi tattalin sa tare da basa kulawa tunda ita tazama ballagaza,duk fa cin amanar da zanyi bekai Wanda takeyi,wallahi har gwara nawa raya sunna nakeson aikatawa ita kuma fa?wani irin dariya boka hatsabibi ya kyalkyale da ita tare da tsuke face yace"kisa a ranki aikinki yama yiwu ya gama,dole kishiga gidan Alhaji iliyasu matsayin matansa ta aure,domin nima hajiya Zainab tayi min lefin da dole namata mugayen hukuncin da bata taba zato ba,tasa nayi asaran aljanu bila adadin kuma sune sojoji duk ciki wallahi sai ta girbi abinda ta shuka,zaro idanuwa hajiya Aliya tayi bakinta na rawa tace"b..bo..boka wai shima wannan aikin ba'ayi nasara bane?juyowa yayi a fusace ya watsa mata idanuwan sa cikin daga murya yace"kada kija lefinta ya shafeki duk da cewa harda ke amma nata yafi naki domin aikinda akayi gabadaya babu wanda akayi nasara. Dafe kirji hajiya Aliya tayi da karfi tace"Nashiga uku ni Aliya,amma ya akayi aikin beyiba,wallahi boka da hannuna nataya ta barbada maganin a shimfidar ta kuma ta kwanta akan shimfidar,wani banzan kallo boka hatsabibi yama Aliya cikin muryan tsawa yace"shine nace miki beyi ba don asirin ya karye,kekuma ga wannan kwalin ki sanya a idanuwan ki,a ranar da kikaji Alhaji iliyasu zai dawo kafin yafara kallon kowa ki tabbatar da kece yafara kalla,sannan kada ki kuskura ki hada idanu da wani idan ba haka ba to tabbas wanda kika fara hada idanu dashi shine zaki aura"ya karasa maganar yana mika mata kullin maganin,jikin hajiya Aliya na rawa ta amsa tare da cewa"da yardan boka hatsabibi sai na mallaki Alhaji iliyasu,kuma aikina baza'a samu kuskure ba. Anan sukayi sallama inda sai da wadannan kattan munanan mata suka biya bukata da ita. ____*NIGERIA*____ Sosai shirye²n biki ya kankama ranar laraba su Mashahuda sukayi bridel shower,sosai events din ya hadu,don suyi kyau matuka, Shuraim yazo gidan don shine yakawo Aunty safeena,sosai yakema zuhra wani irin so wanda shikansa mamakin kansa yakeyi,fuskansa dauke da murmushi ya zubanya mata idanuwa,dan cuno mouth tayi cike da shagwaba tafara bubbuga kafa"To wai ni ya Shuraim kallon na menene?tayi maganar cikin shagwababbiyan murya tare da zaki da sanyi,"zakasa Allah nakoma ciki,tunda tasani zakayi kamar wata television kana kallo,sosai yanayin nata yakara rikitar dashi har ya rasa lissafin sa ajiyan zuciya ya sauke"Huh bazaki gane bane ina imagine ne wai na mallakeki,huhhh da ranar sai anyi sadaka na abinci,kudade, everything,yakarisa maganar cikin shauki,dariya Zuhra ta sanya"I am still young,dudu shekaruna 18 ne fa,why not?na gama degree na daura B8? Wani banzan kallo ya Shuraim ya mata cikin sigar Wasa yace"wa kike tunanin zai tsaya jiranki har wannan shekarun?ai malama kawai kya cigaba a gidana,dariya sosai ya bata don haka tasake tafara dariyar ta wanda dimple, Gap teeth dinta duk suka bayyana a kuma dai dai wannan lokacin ne motar su ya Sauban ta danno kai cikin gidan,fitowa sukayi su duka ukun,sai dai shi gogan face nasa a dore,ba kamar taufeeq da kareem ba,duk da shi Kareem na ciki na ciki. Cikin sauri Zuhra ta nufi inda suke sai dai kaitsaye ta wuce Sauban ko kallon sa batayi ba ta nufi wajen taufeeq,kamo hannunsa tayi,"yawwa Yaya ga ya Shuraim can kazo ku gaisa, bata jira mezece ba tafara jansa. Tun kafin su kariso Shuraim ya karisu,cike da girmamawa yadan rissina kadan tare da mikawa Taufeeq hannu yace"Yaya sannu da zuwa,shima Taufeeq face dinsa babu yabo ba fallasa yamika masa yace"sannu ko malam Shuraim ya mutanen gidan? Shuraim yace"kowa lafiya lou Yaya,dubansa Taufeeq yayi sannan yadubi Zuhra,sake maida duban sa yayi ga Shuraim din yace"Ko zan iya sanin matsayin ka a wajen kanwata malam Shuraim? Shuraim na kokarin magana cikin sauri Zuhra tace"he's my friend...tayi maganar tana sakin murmushi,gyada kai Shuraim yayi yace"yes Yaya,murmushi Taufeeq yayi yace"Ok nice to meet yhu malam Shuraim,insha Allah zansa mana lokaci musake gaisawa da kyau,dariya Shuraim yayi cikin jindadi yace"babu damuwa Yaya a shirye nake don amsa kiranka. Taufeeq yace"Ok ka gaida mutan gidan. "Insha Allah zasuji Yaya. Wucewa yayi a ransa yana kissima abubuwa da dama inda lokaci guda ya fahimci inda Shuraim ya dosa,kaitsaye apartment din Ummie ya nufa. "Kingani ba?tun yanzu nafara samun shiga a family naki ko?to dana fito da maitata nasan za'a amince,dariya Zuhra tayi tana kokarin yin magana ne ta hango Laila ta doso inda suke kaitsaye,nuna ma Shuraim Laila tayi tace"kaganta ko?duban inda tanuna masa yayi yace"who is she?dariya Zuhra tayi tace"her name is Laila, she's my lovely sister nd my abokiyar fada,dariya Shuraim yayi itama Laila dariyar tayi don taji amsar da zuhran ta bada,duban Shuraim tayi tace"Barka da zuwa! Dariyq Shuraim yayi yace"Barka dai fatan kina lafiya?ya shirye-shiryen biki? Laila tace"Alhamdulillah shiri ananan anayi sai dai mujira ranar daurin aure,maida dubanta tayi ga Zuhra tace"Ummie na kiranki, Zuhra tace"Okay to bari naje tayi magnan tana duban Shuraim"Ya Shuraim nizan wuce please don Allah kagaishe da mutanen gidan. Takarisa maganar tana me wucewa tabarsu tare da Laila yana janta da hira. Xahratty CE🥰 Lallai Alqalami 🖊️ yafi takobi🗡️ 26/5/23. [6/7, 15:49] Xahratty (OUM AJMAL): 👨🏽‍🦳 *_GALADIMA FAMILY_*👨🏽‍🦳 Story&Written By *FATEEMA ZAHRA LAWAL* Marubuciyar⤵️ A DALILIN'YAR TSINTUWA. MIJIN ZAHRA. DIAMOND LADIES ( Daukar fansa)paid book. RUHIN AMRITA (FATALWA CE). Now *_GALADIMA FAMILY_* Page 41/42 ______Kareem ne yadubi Sauban yace"Ango kiran kafa akeyi da alama kawayen amarya ne,kuma nasa akan maganar kudinsu ne"Cikin bacin rai Sauban yace"I don't have time for wadannan 'yan iskan ladies din masu fama da hayakin kai,nine zanbasu 10 millions naira na hidimar biki?to ai banfito a cikin jerin ahalin karuna ba idan har abinda nayi niyyar basu bazai musu ba sai dai subar hidimar da zasuyi. "Calm down! Friend abin bana daukan zafi bane haka,please kabisu a sannu nisam banason abinda zai sanya kabata ma kanka rai ka bata mata ita.... wayar ce aka kara Kira, Sauban ko kalla beyiba duk da face dinsa bazaka ga mahaukacin fushin nan ba,Kareem ne yayi picking call din. Cikin muryan shagwaba tare da karairaye murya,gyaran murya Kareem yayi yace"bashi bane amarya,barka da Rana amaryan bakya lefi koda kin kashe dan masu gida. Batare da gaisuwa ba Akeela tace"uhum Kareem kenan,nace please sweetheart din baya kusane kadauki phone din?dan murmushi Kareem yayi ta hanyar danne bacin ransa yace"aiko baya kusa yabar wayan a dakina ne kafin yaje yadawo but insha Allah idan yadawo zan sanar masa kinkirani"Da sauri Akeela tace"no ba wani abu bane dama tuni akan maganar hidimar kawaye naje haryanzu baku nemesu bane kuma time na tafiya ya kamata abasu abinda kikace. Kareem sosai yasan abokin sa magana daya yakeyi daganan baya canjawa"kingani Akeela abinda yasa bamu nemeku ba maganar gaskiya Sauban yace bazai iya bada 10 millions ba,idan kuma kum matsa sai hakan tofa sai dai ku fasa hidimar taku. Wani kululin bakin ciki da takaici Akeela taji ya ziyarce ta lokaci guda,tanaso tayi rashin kunya amma tsoro ya hanata,cikin karfin hali"Yanzu fisabilillah a ganinka Kareem ya kamata Sweatheart yace bazai bani wannan kudin ba?me akayi akai 10 millions please?meyasa yakeso yamaidani wata karamar yarinya wajen friend's dina?alhalin ansan wanda zan aura Muhammad Taleeb Muhammad nefa haba haba,dage kafada Kareem yayi tamkar tana gabansa yace"to kinji nidai abinda yacemin kenan kije kiyi shawara don yace daga 3 millions bazai kara wani abu b.....batare da yakarisa abinda zaice ba daga bangaren Akeela yaje tace"Kutumar uban can!!! Atake anan kuma wayar ta gimtse alamun ta gane katobarar da tayi kenan.Wani dariya Kareem ya kunshe saboda tabbas tasan Akeela ba irin tsarin macen da abokinsa yakeso bane,dogon tsaki Sauban yayi tare dayin kwafa batare da yace komai ba yamike ya shiga toilet. Acan kuwa gidansu Akeela tabotsare sai masifa take zazzagawa a dakin Guggo Laure tare da kuka,tana fadin itafa Sauban baya sonta,sosai hankalin Guggo Laure ya tashi ranta ya baci matuka amma haka ta danne gudun abinda zaije yadawo taja Akeela cikin dakinta tare da fara kwantar mata da hankali,nan fa tafara lallashinta magana tafara mata kamar haka"inaso ki saurare ni kiji da kyau, ni babban matasalata dake wutan ciki taya bikinki saura kwanaki kifara bacin rai da hayaniya? Cikin muryan kuka Akeela tace"Haba Guggo ni sam abinda guy dinnan yakemin sam baya min dadi,haka sauran mazan suke?koko don yaga ina son shi shiyasa yake min haka?nikawai Guggo kisa mallakemin shi sai abinda nakeso za'ayi"Ajiyan zuciya Guggo Laure ta sauke tace"Ai wannan dole ne kisha kurumin ki dama kina tunanin zamu barshi haka ne?ai wallahi bazai yuwu ba,gashi yaro Yana neman zama mante malloniya,dole ya zama na yana tafin hannu mu mune muke juyasa wanda ko Aisha sai tarasa kwanciyar hankalin ta,cikin tsananin farin ciki Akeela tasaki dariya"yawwa Guggo na shiyasa nake matukar son ki nufa kin fimun Mom wallahi,domin Mom bata damu da damuwa ta ba"... Mtsewwww! Don Allah dena tadin wannan shashan wake maganar ta?cewan Guggo Laure. Wayan Akeela ne yayi ringin cikin sauri tadauka"hello baby's ya akayi ne?daga can bangaren aka amsa"ok to bari nazo dama ina sasan Guggo ne amma ganinan fitowa,takarisa maganar tana mikewa wayar kare a kunnenta tana fita,cikin jin dadi Guggo Laure ke duban ta don ko babu komai tana mata murnan shiga ahalin GALADIMA FAMILY,a fili tace"Wane Mujaheed?ai Akeela ba tsarar ka bace,kuma ba sa'ar ka bace,duk da nice nan na haifi iyayen ku amma kuma da banbanci"Guggo Laure tayi maganar tana wurgama iska harara. Dai-dai sanda ta isa wajen su Suby alokacin wayar ta tadanyi kara alamar message yashigo cikin wayar,cikin zumud ta dago wayar tana dubawa,sai dai abinda taci karo dashi yasa murmushin nata gushewa,da karfi ta furta"kan ubancan,lallai ma mutanen nan nizasu maida wata 'yar iska wai ko mene?jibi don Allah Suby,tayi maganar tana mika mata wayar ta. "Wai iya kacin abinda suka turo kenan?Suby tayi maganar tana duban wayar,cikin hasala Akeela tace"Gashi kuwa kina gani,amma gaskiya ba'a mun adalci ba,inada hidima fa sosai,ga event din gobe,ranar Friday Kuma kamu haba!tayi maganar tana yatsine fuska. "Ai shikenan sai kiyi maleji da abinda yasamu kawai muma abamu kasammu,wani banzan kallo ta aika mata dashi"bangane me kike nufi ba,abaku kasanku kamar Yaya kenan?bata fuska Suby tayi tare da kura mata ido. "Ea mana ko kinmanta ana bawa kawaye wani abune?aka idama kudin nan bata account dinki ya kamata a turo ba, account din daya daga cikin mu zaki bayar mukuma muyi yanda mukeso da kudin"Zuleey tayi maganar tana tamke fuska"kwarai kuwa zuleey amma kinji abinda yarinyar nan ke cewa, Akeela wai me kika maida mu wawaye ko menene? Sauke ajiyan zuciya Akeela tayi tana kokarin danne bacin ranta"A tunanina million 3 bazai hadani da ku ba amma tunda kun matasa zanbaku 200,000 naira shikenan? "A'ah wallahi bazamu amsa ba ya mana kadan,inama lefin kibamu 1 million mu biyu? "Wallahi bazan iyaba,inama lefin 500,000?da wanne zqnji ga Kama hall da sauran su, Zuleey tana kokarin magana Suby ta hanata ta hanyar yi mata magana da ido,badon ranta yaso ba haka tadannne. "Okey to kuzo muje mufara tsare-tsaren yanda komai zai wakana,don inaso muje gidan mommy ne ko kuwa?dukka amsa mata sukayi da hakane. ******** Tarasa dalilin da yasa take tsintar kanta cikin bacin rai a duk sa'ilin da taji anyi maganar auren Sauban din,hakanan takejin wani kunci na ziyartarta tare da tsanar Akeela matuka a ranta,shikuwa mugun haushinsa takeji,a kullum cewa take bacin hadene dana su Aunty Mashahuda da wallahi bazata zauna ayi bikin ba,kai ita duk wanda taga yana rawar kafa akan lamarin na Sauban shima haushinsa takeji. Shigowa Laila tayi don bata jitaba,zama tayi tare da makama cinyar ta duka,da firgici tadago tana dubanta, ajiyar zuciya ta sauke"zuwa nayi nace miki kitashi muje mu amso dinkin mu,gasu ya Taufeeq zasu sauke mu a shagon"bata fuska tayi"Gaskiya nibazan bisu ba idan ku zaku bisu ku bisu amma ni adaidaita zan samu,takarisa maganar tana mikewa don shiga bathroom"Ummie tace nazo na fada miki idan kuma naje nabata amsar hakan to,tayi maganar tana mikewa tsaye.Cikin sauri Zuhra ta dawo tana shan gaban Laila tare da tsuke fuska"ni ban aikeki ba kice mata ganinan nashiga wanka ne,tayi maganar tana juyawa cikin sanyin jiki, dariya Laila ta kunshe tana me fita. Bata wani jima a toilet dinba ta fito ta shirya a gurguje don tasan basu fiye son delayed ba yayyen nasu,ba wani kwalliya tayi ba a fuskar ta,Dubai gown Army Green ta sanya sai sneaker black tayi Rolling kanta,dan karamin hand bag dinta baki tadauka tafita da sauri,ilai kuwa tana fita ta hango Laila da nihal a parking space jikin motar ya Sauban,wani kululin bakin ciki da bacin rai taji ya taso mata lokaci daya,harara Laila ta aikamata tace"Zaki gamu dasu Yaya wallahi babu ruwan mu kin bata musu lokaci,bata kulata ba suka bude motar suka shiga, Taufeeq ne ke driving,shikuwa Sauban laptop ne akan cinyar sa yaketa sarrafata,gaishesu sukayi duk suka amsa,cikin barkwancin sa yadube su"Allah yasa telan be mata muku dinki ba,don nasan teloli sai addu'ah,cikin raha Laila tace"Ai Yaya Ameer ya iya dinki sosai,tun daga Zaria yazo yima su Aunty Mashahuda dinkin biki,namune be gama ba yace sai munzo da kanmu,jinjina kai Taufeeq yayi yace"Ah gaskiya ne tunda aka dauko tun daga Zaria to lallai nima na sheda,don nasan gimbiyar tawa bata za6en tumin dare ko gimbiya?yayi maganar yana duban Zuhra ta jikin mirror motan,dariya Zuhra tayi wanda sai da point nata ya loma,sannan Gap teeth dinta suma suka samu damar bayyana,lankwasar dakai tayi cikin shagwaba tace"To yaya maganar saloon din bamuje bafa, gashi gobe mother's day,kuma mu a goben ne zamu henna ko?tayi maganar tana duban su nihal,daga mata kai sukayi gabadayansu,nihal tace"Kuma ranar Friday kamu ba! Zuhra tasake shagwabe muryan"Yes yaya and kamu. Tun sanda ta fara magana tatafi da duk wani kuzarinsa lokaci daya yaji wani kasala ta kamashi,banda bugawa babu abinda zuciyar sa keyi,shekara da shekaru kenan yake karya ta abinda zuciyar sa ke raya masa,sam takasa tunkarar wani da maganar balle yasamu sassauci,lumshe idanuwa yayi cikin natsuwa wanda mutum bai isa yagane ya yanayin sa ba. Cikin taushe tare da basarwa yafara ma Taufeeq magana batare da ya dubesa ba"inada baki da zasuzo,wasu daga maleysia wasu kuma daga Canada so ina bukatan hotel me kyau sosa and sai dai niban san kan hotel's din garin nan ba,jinjina kai Taufeeq yayi yace"Gaskiya nima bansan kan hotel's din garin ba sai dai mukira Kareem kan ya bincika mana,let me call him"yayi maganar yana jawo wayar sa daga aljihu,jinjina kai Sauban yayi batare da yayi magana ba. Zuhra kuwa ajiyar zuciya take ta sauke wa a boye batare da kowa ya fahimta ba,dai-dai lokacin da suka iso shagon dinki me tsananin kyau don dama yasan shagon shida kanshi yake dauko Mashahuda ya kawo ta. Bude kofan sukayi suka fito tare da rufo musu kofan,tsayawa Zuhra tayi gefen Taufeeq duban ta yayi yace"to yanzu maganar saloon din zaku wuce ne, idan mundawo zamu biyu ta shagon mu dauke ku,jijjaga masa kai Zuhra tayi,kudi yaciro a aljihu wanda shi kansa besan ko nawa bane yamika mata,godiya suka masa gabadaya suka shiga shagon. Ta wutsiyar ido yake hankalce da duk wani motsinta da wani babbasar wan da takeyi. Kai tsaye shagon suka shiga,basu jima ba suka fito dauke da kayan su Ghana most go guda medium,an dinka a goge duk da sunso dudduba kayan amma ganin mutanen dake cikin shagon yasa suka hakura,don Zuhra a takure take abinda ta tsana kenan a rayuwar ta,har bakin titi Ameer ya rakosu suka samu napep sannan yajuya,kaitsaye shagon saloon din suka isa me suna saleema hair beauty saloon matar tana da matukar kirki,gashi tana tsananin son Zuhra,basu jima ba bayan magrib suka gama ana Shirin Kiran isha'i,turama da Taufeeq address din Zuhra tayi,babu kuwa bata lokaci yadawo,wannan karan shi kadai kuma ta map ya dinga bin address din. Kudin saloon din yabiya sannan tadauki kayansu yasanya musu a cikin boot,kaitsaye suka isa gida. _________ Washe gari Biki yayi biki inda labarin event din su Akeela kawai akeyi,maisuna suger mommy's day,sosai suka kashe kudi a event din wanda akayi a gidan hajiya daharatu,wato mommy, sosai ranar 'yan less sukayi iskancin da suke so, Akeela kuwa a daren mutane uku sukayi masha'arsu da ita,sun cancare matuka gaya,sai karfe ukun dare suka watse. A dai-dai kuma wannan lokacin aka tura ma da Sauban video. Xahratty CE🥰 Lallai Alqalami 🖊️ yafi takobi🗡️ 7/6/23. [6/8, 21:41] Xahratty (OUM AJMAL): 👨🏽‍🦳 *_GALADIMA FAMILY_*👨🏽‍🦳 Story&Written By *FATEEMA ZAHRA LAWAL* Marubuciyar⤵️ A DALILIN'YAR TSINTUWA. MIJIN ZAHRA. DIAMOND LADIES ( Daukar fansa)paid book. RUHIN AMRITA (FATALWA CE). Now *_GALADIMA FAMILY_* Page 43/44 _______Ganin bakuwar number ce yasa yadanja siririn tsaki tare da kin bude message din a fili yafurta"Trash! Yana takaicin 'yan matan dake bibiyan sa wadanda sam basu da aji balle ayi maganar kamun kai,wayar ya ajiye a side yana mikewa tare da shiga toilet don dauro alwala,saboda Sauban mutum ne mai rukon addini tsantsa shiyasa lokuta da dama yake jin dan sanyi a zuciyar sa. Washegari da safe GALADIMA family suka tashi da shirye-shiryen mother's day,Ammi,Ummie,Mom,Mommy sunyi kyau sosai don babu wacce bakinta basu zoba musamman Ummie don da kawayen ta na kaduna da Zaria,haka ma Ammi kowa dai yatara mutanen sa,kanofi uku aka kakkafa,duk wannan shagalin su ZUHRA basa gidan suna can wajen henna,sun hada mother's day dinsu yayi masifar kyau,duk da iya kacinsu ne don ko maza basu shigo gidan ba, security ma suna can gate 1,haka zalika sunsa police mata kan su kula duk wacce tayi video Koda waya ne to aka mata,duk da cewa ba badala sukayi ba,sunyi wanka mahaukatan lace hadaddu,da Ammi da Ummie lace dinsu iri daya white,sai Mom da Mommy kuma orange sunyi kyau abinsu matuka,bodejo da Amma ma sunyi kyau cikin lace dinsu suma,inda Aunty Maryam da Aunty labeeba suma suka sanya coffe din lace, Adda zainab dai tana hanya tare da matan yayyen Ummie biyu basu kariso ba. Haka aka gama shagali lafiya inda kowa yatashi yana tsananin farin ciki tare da kyaututtuka. Sukansu amare sunyi matukar kyau inda acan company taje gidan ko wacce tayi mata danki,gidan muneefa Masha Allah kamar yanda na Mashahuda kuma baya faduwa ya kawatu,kananun magana ne yafara tashi saboda ba'a ga anyi dankin Akeela ba sai yau zasuje suyi. ******** "Hmmm suby kina kallon abinda Akeela take mana? kuma mu zuba mata ido?sauke ajiyar zuciya Suby tayi tace"To zuleey me kikeso ayi?zubanya mata ido zamuyi komai zai wuce by the grace of God cuz ayi komai agama lafiya. "Shikenan Suby yanda kika ce haka za'ayi,muje mu cigaba da shirye-shiryen mu kinga kudin ma a siyayyan kayan daki na kyale kyale ya kare,sai dai tabar 1 million na dinner gobe da tarban jama'ar mu duk da nasan wannan abune me sauki mommy tace zataji da wannan. Haka suka cigaba da zantukan su inda zaka fahimci zuleey tana cikin matukar damuwa tare da bacin rai don bini-bini kadan sai ta duba wayar ta,sai dai gnin babu alamlun message yasa ta basar tare da saka wayar a jaka,anje anyi dankin gidan Akeela,wanda ya gaji iya gajiya,tsaruwa da haduwa kuwa ba'a magana,anan jikin gidan akayi gidan,kayan dankin ne dai basu dace da gidan ba,don ma apartment din Sauban dabanne da abin kunyar yafi yawa,domin apartment din shi yayi balai'n haduwa komai oder ne, itakuwa Mashahuda a j K.d akaje akayi danki waje yayi balai'n haduwa, muneefa ma gidan ta yayi kyau sosai. Yau ta kama Friday kamu aka shirya guda narwa a Galadima family,amare sunyi kyau matuka gaya,anan ne su Aunty Maryam suka tura su Laila gidan su Akeela akaimata kayan kamun,don dama an amsa majorment nata,Anko sukayi su uku inda,angwayen ma sukayi ankon arniyar danyen shadda sky blue,su kuma amaren net ne sky blue su Aunty labeeba suka musu dinkunan. Wajen ya kawatu matukar kawatuwa,baka tatan su Suby suka tsinta maganar don su sun zata zasuyi abinsu daban ne,abinka da waje babba fili ne dake bayan gidan Galadima wanda yake mallakinsa,an katangeshi tare da zuba interlock da shuke shuke,lokaci guda masu decoration suka canza masa kamanni yakara wani masifar kyau da tsaruwa,kawayen Akeela da 'yan uwanta guda goma aka bukata,kamar yanda aka bukaci na ma'aruf saurayin muneefa,sukuwa sauran abinka da abu nasu ba'a maganar 'yan uwa,su Suby suma sunyi shigansu na tatattun 'yan duniya itada Zuleey anko sukayi. Waje fa ya hadu ya tsaru matuka gaya babu abinda kakeji na tashi sai sautin kidan wakar namej me taken "dama". ***** Kwance take akan gadon Ummien sam bata da alamun tashi ta shirya balle ayi maganar fita,su nihal sunyi maganar har sungaji sun wuce tare da wasu cousin's dinsu agemate, Ummie ce tashigo tana sanye da wata lace maroon tayi matukar kyau face nata dauke da tsantsar fari'a,turus tayi taja tatsaya tana duban ZUHRA cike da mamaki tace"Zuhra zaman me kikeyi anan?kowa yanacan yana watsa idanuwan ganinki ke kina nan kina kwance.Turu mouth gaba tayi tace"Ummie kaina na ciwo ne shiyasa ma banfita ba kuma bazanje ba,takarisa maganar tana sake gyara kwanciyar ta"Lallai to wallahi baki isa ba shashancin banza,yayanki sai kirana yake akan be ganki ba ke kuma kinzo kinrashe?maza² kitashi ki shirya kiwuce tun kafin raina yabaci,haba babyn Ummie kinaso ki batama sweat broo din naki rai ne ranar farin cikinsa? Girgiza kai Zuhra tayi tana me mikewa badon ranta yaso ba,nan Ummie ta cigaba da lallabata da lallashinta don ta fahimci tunda bikin gidan yakarato take cikin kunci da damuwa,a gurguje tafito ta shirya cikin wani hadadden yadin rose white sai net dinsa wanda Ameer ya zauna ya tsattsafa mata wani street gown me daukan magana,abinka dame kirar cikakkiyar halitta,shape dinta yayi balai'n fita,light make-up tama kanta,tashirya tayi matukar kyau,takalmin high heel shoe me siraran igiya tasanya a 'yar karamar kafanta wanda yaji jan lallen salatep,fitowa tayi cikin takunta me daukan hankali,nan tanufi sashin taron,duk da kowa zaune yake a mazaunin sa amma shigowan ta yasa da yawa hankulan su ya koma kanta,haka abokan angwaye ma, half-caste skin dinta shima yasamu damar sake fito mata da ainahin kyanta,kananun magana ne yadan fara tashi. Akeela kuwa ganin Zuhra ba karamin baci taji zuciyar ta tayi ba,jitayi kamar ta tashi ta shaqe ta don wallahi ita kanta da take amarya tasan yarinyar tayi bala'in finta kyau nesa bama kusa ba,wani banza kallo tashiga aika mata dashi zuciyar ta na tsananin tatarfasa, Zuhra kuwa ko kallon inda amare da angwaye suke batayi ba babu zato taji sallama ta gefen kujeran da take zaune,duk da kujeru uku ne table a tsakiya amma ita kadaice,dagowa tayi don jin muryar sa,murmushi suka sakin ma juna one time,da ido ya mata alama da ya zauna?cikin cool nd sexy voice dinta kamar me rada tace"yep have a sit,murmushi suka sake sakinma juna,shima yayi kyau sosai Shuraim don babban rigan ta masa kyau gaya. Wani bacin rai yake tsintar kansa a ciki amma haka yaketa dannewa har aka fara Kiran angwaye da amare su fito suyi rawa,duk da a takure yake jinsa sai dai hakanan yadaure yakamo hannunta suka sauko suma filin,dai-dai yadago idanunsa itama ta dago,ido cikin ido yasan ya mata musamman ganin yanda take hira cikin nishadi da kwanciyar hankali,basarwa tayi ta hanyar dena duban ta tana sake maida hankalinta ga Shuraim dake ta bata dariya. Tunowa tqyi da Taufeeq cikin hantsari ta dubi Shuraim,excuse me! just give me five minute"daga mata kai yayi masu ma amare manni sun ragu,a dai dai lokacin da aka saki sautin wakar "luwaiiii" na Ado gwanja,tafiya tafara tana karkada jikinta cike da jan aji da basarwa tabude pos dinta ta ciro 'yan dubu-dubun da Daddy yabata tafara manni,aiko nan aka saki tafi tare da shewa,rike hannunta Taufeeq yayi suna rawar cike da natsuwa tare,ai nan danan Nihal da Laila suma suka fito,sun burge mutane da dama,don shi kanshi ya Sauban sun matukar burgesa. Akeela kuwa face dinnan ansake cureshi lokaci guda,kafin kace me se ga abokan Sauban da suka zo daga abroad suma suna zubama Taufeeq da Zuhra manni,shima Shuraim tasowan yayi, Aunty safna ma haka tare dasu Aunty Maryam,su kansu amaren ba'a barsu a baya ba, Akeela kuwa zuciyar ta jitake kamar zata buga tsaban bakin ciki. Haka atashi taro lami lafiya aka gama kowa na farin ciki wasu kuma akasinsa. ***** Duk zaune suke a apartment dinsu na mazan,babban parlon ne da 3 bedrooms,firar dinner kawai sukeyi,daya daga cikin abokan Sauban mes suna Saif Ahmad Khan dan kasar India cikin muryan turanci ya dubi Taufeeq yace"Gaskiya Taufeeq kanwar nan taka tayimin matukar kyau nifa da zaku temaka ku bani ita na aura,wani me suna ishaq Adekunle mazaunin Canada yace"jibeka!taya zata aure wanda ba dan kasar ta ba?ai dani tafi dacewa Saif,harara Saif din ya gallamasa,shikuwa Taufeeq dariya kawai yake musu,mikewa yayi yana cemusu yana zuwa,don amso musu abincin su,duban Sauban Saif yayi yace"Oga magana nakeyi wallahi dagaske nake I love her so much"batare da yadago ba kuma be tanka ba ya cigaba da lallatse wayarsa,wani me suna Ashur shankeer ya kyalkyale da dariyan mugunta yace"lallai iska na wahal da me kayan kara sufa familyn su Oga da alama basu bama bare aure,auren zumunci sukeyi gabadaya,duban Sauban yayi yace"please Oga idan zakayi fighting din bamu ita nizaka mawa don ni nafi dacewa da wannan bby doll di.....dogon tsaki Sauban yayi tare da daure face babu alamun wasa ko kadan yace. "Look niba dan iska bane da zanje na tare yaran ciki na da shirme,inbanda abinku ai ku yafi dacewa dakuje kuyi ma kanki fighting,babu wanda ya isa ya siyamin raini wajen yarinya,ya karisa maganar yana mikewa tamkar ba shine yayi maganar ba domin kuwa face dinsa ko alamun bacin rai babu,toilet ya shige ya barsu sai surutu sukeyi, Taufeeq ne yashigo tare da sallama bayansa,zuhra ce da katon basket a hannu,shima hannunsa basket ne da flask na ruwan zafi suna tafi suna hiran nishadi,shigowan su parloun yasata dan tsuke face,cike da girmamawa ta rissinawa tafara gaishesu da turanci,ko wanne na amsawa cikin nishadi suke amsawa,tana ajewa ta musu sai da safe tafita cikin sauri,kicibus tayi da Aseef rataye da hakan baya,cikin sauri taja baya,shikuwa marairaice fuska yayi yana duban ta,takowa yafara yi zuwa inda take yana kanne mata ido irin na cikakkun 'yan barikin nan. Da wani irin gudu zuhra ta kwasa don harga Allah ita tana tsoron sa,tasan mummunan halinsa Wanda ba kow ya sani a family din ba,karasawa tayi apartment din Ammi don banda haki babu abinda takeyi. Su Adda Zainab da hajiya Aliya ma sunzo,sashen Ummie sosai ya cika da 'yan uwa da abokan arziki,haka sauran sashisshikan. ******* A gidan Guggo Laure kuwa shima gida yafara cika sosai da 'yan biki,Akeela sashin Baba sani ta koma da kawayen ta,inda banda hirar batsa babu abinda suke a tsakanin su,tare da kosawa gobe tayi domin kuwa an dauki buri a bikin nan musamman ma Akeela,banda dirkan magungunan mata dana matsi babu abinda takeyi,tagigita kanta a banza a wofi tana tsananin bukatan mijinta a cewar ta. *𝑨𝑺𝑨𝑩𝑨𝑹* 𝑿𝒂𝒉𝒓𝒂𝒕𝒕𝒚 𝑪𝒆🥰 𝑳𝒂𝒍𝒍𝒂𝒊 𝑨𝒍𝒒𝒂𝒍𝒂𝒎𝒊🖊️𝒀𝒂𝒇𝒊 𝒕𝒂𝒌𝒐𝒃𝒊.🗡 ️[6/9, 22:33] Xahratty (OUM AJMAL): 👨🏽‍🦳 *_GALADIMA FAMILY_*👨🏽‍🦳 Story&Written By *FATEEMA ZAHRA LAWAL* Marubuciyar⤵️ A DALILIN'YAR TSINTUWA. MIJIN ZAHRA. DIAMOND LADIES ( Daukar fansa)paid book. RUHIN AMRITA (FATALWA CE). Now *_GALADIMA FAMILY_* Page 45/46 ______Allah yasani tatsani Aseef hakanan tarasa dalilin da yasa take kokarin shiga rayuwata ita tama mance dashi a shafin zuri'ar su,to ina ya shiga kwana biyu da ba'a ganin sa yabace bat?tambayar da tama kanta kenan batare da tana tunanin samun answer ba,ajiyan zuciya ta sauke mai karfi tana karisa shiga apartment din na Ammi. *𝘈𝘚𝘈𝘉𝘈𝘙* Washe gari wajejen 11:30 babu abinda ke tashi sai muryoyin maroka suna sanar da daurin auren nasu Muhammad Taleeb Muhammad(Sauban) & Akeela Mansir,Taleeb Abubakar Muhammad(Taufeeq)&Mashhudat Taleeb Muhammad sai Ma'aruf Kabeer Mainaera&Habiba Hasheem Muhammad(Muneefa) sosai marokan nan suka saki makoshi asake,kafin kaceme sai guda shima kansa ya fara tashi,tsintar kanta tayi cikin wani irin bacin rai a hankali zazzabi yafara shiganta,fitowan ta kenan daga apartment din Ummie tana kokarin shiga apartment din Bodejo ne taji an fisgota,jitayi ta fada jikin mutum a tsananin rude tare da tashin hankali tadago,ido biyu tayi da Aseef,kirjinta ne ya shiga bugawa jikinta ya soma rawa,bude mouth tayi da niyyar sakin ihu,hannu yayi maza yadora a saman pink lips dinta yana furta"Shiiiii don't say anything baby,yakarisa maganar yana bin jikinta da wani irin mayetaccen kallo,karfin hali tayi na fusge jikinta sai dai ko kadan be bata damar hakan ba don ba rikon wasa ya mata ba,cikin rawar jiki tasake dagowa hawaye na sirnano mata cike da bacin rai da tsiwa tafara magana"ka sakeni please,niba 'yar iska bace wannan mummunan habits din da kake boyewa da yardan Allah wataran sai asirin ka ya tuno,murmushi yayi kamar ba dashi take magana ba yafara matso da bakinshi kan nata bakin,fusgewa tayi cikin karaji ta furta"ka sakeni la'ananne,kasakeni I hate you,natsaneka natsane halayen ka da yardan Allah nafi karfin ka bazaka taba samun galaba a kaina,yakarisa maganar tanajin wani mahaukacin karfi yazo mata lokaci guda,dagewa tayi ta turasa baya,aiko tasamu nasara don sai da yayi taga² zai fadi abinka da mashayi dama ba wani karfine a jikinsa ba,da gudu ta kwasa tana me sake zaginta. Karkada kai Aseef yayi yana mebin jikinta da kallo,idanun sa sun kada sunyi jajir,yaji zafin zagin da ta masa,alkawari ya dauka duk bala'i sai ya dandana yarinyar kalmar da ya fada kenan yana me juyawa tare da wucewa,kaitsaye bedroom dinta apartment din Bodejo. Kuka ta fashe dashi me tsuma zuciya tana sake me tsinewa halayyan Aseef"natsani gidan natsani kowa, Allah ya jikanka Abbiey na am always miss yhu,I love yhu lovely father da kananan da ka sharemin hawaye na,ina begenka da kauna me tsanani,wani ciwon kai taji me tsanani ya saukan mata,kukan ta tacigaba dayi tana fadawa kan gadon ta kwanta,tanajin sanyi na ratsa ko ina na jikinta. Da kakalle fuskokin su angwayen zakasan lallai suna cikin farin ciki,hotuna aketa tayi dasu,kowacce budurwa burinta tayi pic da Sauban da abokansa musamman Saif da ishaq don sunfi kyau a bisa Ashur,shikuwa Taufeeq wurga idanuwa yake ko zaiga ta inda Zuhra zata fito amma sam be ganta ba,sosai yadan damu haka ya saki aka cigaba da hotunan,shima Shuraim yazo gidan sai laluben numbers dinta yake amma is not reachable ake cemasa, Aunty safeena ya tambaya tace bata ganta ba amma yabari zatasa a dubo mata ita,biki yayi biki taro yayi taro harga Allah Saif ya kamu da son Zuhra shiyasa ma yaketa wurga idanuwa ko zaiga gilmawar ta amma be ganta ba. A can sashen Bodejo ko Zuhra taci kukanta har ta gode Allah,a take anan wahalallen bacci yayi awon gaba da ita,Saboda zazzabi da ciwon kai dake neman zautata. Anci ansha anyi shagulgula karfe hudu aka Kai amare sashen Galadima inda suka hadu da Daddy, Abba, Baba Hasheem suka hadu suna ma amaren nasiha mai shiga jiki sosai,daganan aka kaiso sashen iyayen su mata, Mashahuda kadai za'a wuce da ita don haka tayi kuka sosai,gefenta Rammat ne keta lallashinta,nanfa motocin daukar amarya suka iso da ita da Mashahuda aka dauka don Mashahuda zata rakata gidanta. Wajejen biyar angama kwashe duk wanda zashi gidan amarya anwuce dashi, Mashahuda kuma sai gobe za'a wuce da ita tare dasu Aunty Maryam, Aunty falmata(safeena)sai wasu 'yan uwan Ammi. Dangin Ma'aruf sun tarbe amare da 'yan uwanta cikin mutumci da kulawa,kai tsaye sashen mahaifin Ma'aruf din aka kaita,babban mutum mai cike da dattaku nan fa yafara mata nasiha mai shiga jiki tare da Ma'aruf don babu kwana,daganan sashen mahaifiyar Ma'aruf din aka nufa da ita,itama tamata nata nasihar. Bayan magrib akafara dawo da mutane,inda acan kuma masu kawo Akeela suma sun iso,ana tafe da amarya wanda babu abinda ke tashi sai kida a MP3,manyan mata wsu ma duk sun haifeta sune keta kwarkwasa,sai dai ba wanda ya fahimci wani abu,yan mahaifiyata kuwa mamaki yacika ta don bata sansu a dangi ba,ganin rashin da'an na neman yayi yawa tadaga murya"Meye haka?Wai wacece me mp nan da take cika gidan mutane da kida?haba bayin Allah meyasa muke hakane mutane? za'a fa kaita sasan sirikanta ne ba dakinta ba,yo ko dakinta nema ai be kamata a shiga da ita da mp ba,takarisa maganar cikin bacin rai,wacce mp ke hannunta ne tafara magana"wallahi mama hakan ba wani Abu bane,kawai mutanen mu na yanzu rashin wayewar kai ta musu yawa ne shiyasa,hajiya daharatu dake rike da hannun amarya tadubi yarinyar wata busasshiya da ita taci mai ta kwaile tace" 'Yar caras kashe mp nan mana. Kashewa tayi suka shiga katon gidan wanda da damansu sai da suka raina kansu atake anan wasu hassada ya darsu musu sukaji inama ace sune suka shigo cikin wannan ahalin, lallai Akeela ta dace saurasu,wasu kuwa da yake ba auren ne a ransu ba hakan be wani damesu ba sai dai suma sunji sha'awar kasancewa a gidan. Tundaga yanda Galadima family sukaga amarya da kawayenta sukeyi suka san lallai basuyi dace da sirikar kwarai ba amma ba anan gizo ke sakar ba kila tana da wasu halayyan, Ammi kuwa tayi bala'in jin kunyar kallon Akeela a matsayin sirika,don ko rufe fuska batayi ba,sai dai baka isa kagane hakan a face dinta ba Saboda murmushin da take tayi,tsakanin Rammat dasu Suby kuwa banda kallon banza babu abinda suke aikama juna,nan aka gama mata nasihohi aka fito da ita tare dasu Aunty Maryam don kaisu gidan amarya dake jikin nan gida,koda suka isa nanma mutanen Akeela sun raina kansu don ita da kanta ware ido tayi tana kashe kwarkwatan idanuwan ta. Barosu su Aunty Safeena sukayi bakunan su cike da abubuwan mamaki tare da tausayin Sauban don da alama zasu wahala. Bodejo ce tanufi dakin don dauko furar da ta'aje ma yallabai😂Turus tayi saboda ganin mutum da tayi kan gado"Wanene nan?shiru taji,dan matsawa tayi cikin tsoro tasake cewa"Nace Wanene nan?ina magana ana jina eyye?mutum ko aljani?wallahi ko aljanuni sharri na yafi naku, hatsabibanci na yafi naku"takarisa maganar zuciyar ta fal tsoro shahada tayi ta yaye duvet din, Zuhra tagani banda rawar sanyi babu abinda jikinta ke mata,da sauri ta taba goshinta,gau haka taji shi da zafi sosai"Oh ni fatsima dama yarinyar nan kina sashin nan kikazo kika boye kina neman kashe kanki da ciwo?kinji jikin ki kuwa?tayi maganar tana bubbuga mata jiki. A wahalce tadan bude idanuwan ta,tanajin wani irin azaba,sake lumshe idon tayi cikin tsananin azaban da takejin kanta na mata kamar zai rabe biyu. "Ke Zuhra tashi kizauna lafiyanki kuwa?meke damunki ne haka?kinji yanda jikin ki yadauki zafi gau?gaskiya ba lafiya ba bari nazo,tayi maganar tana fita batare da tadauki abinda tazo daukan ba,ko minti goma bata kara ba tadawo ita da Taufeeq dasu Aunty Maryam,suka shigo,duk cikansu nufar gadon sukayi"Taba jikinta kaji Taleeb,zazzabi ne mezafi ya lullubeta"Bodejo tayi maganar,hannu yadora akan goshin nata,da sauri ya cire"Kai gaskiya kuwa, Aunty labeeba tace"Zuhra!Zuhra!!tayi maganar tana tabata. A wahalce tadan bude ido tasake lumshewa,dagota Aunty Maryam tayi tasa kanta a cinyar ta tace"Zuhra bude idanuwanki, Zuhra"Uhum! Abinda tace kenan tana rufe idon ruffff "Ikon Allah jikin nata ya canza mata ne lokaci daya,duban Aunty Maryam Taufeeq yayi yace"Aunty ya kamata muje asibiti da itane ko? Aunty labeeba tace"Gaskiya kam don wannan zazzabin ya bigeta gaskiya,dagata.Kamata sukayi suka mikar da ita,jikinta babu inda baya rawa saboda sanyin da takeji,face din har wani pink pink yake na wahala,wani mahaukacin amai ne taji yazo mata,ai kafin kace me tafara kelayarwa,haka jikinta ke cigaba da rawa,amai take sosai,sosai su ma hankalinsu yatashi,cikin muryan kuka take fadin"Abbie!Abbie!! Kamata sukayi ai ganin zata wahala ga jikinta yayi bala'in saki wani yaraf kawai take yasa Taufeeq cak yadauketa,biyosa sukayi,anan ma parlon ragowar 'yan biki suka taso ana tambayar lafiya?kowa yaganta yanda ta canza sai ya tausaya mata. **** Daddy ne da Abba da Baba Hasheem suke farfajiyar gidan da alamun daga masallaci suke,gefensu Sauban ne kansa a tsaye,gani sukayi mutane duuuu sun fito daga apartment din Bodejo, Taufeeq dauke da mutum a hannu,cikin tashin hankali suka nufi wajen suna tambayar abinda ke faruwa,a rude Taufeeq ke tambayar ya Sauban akwai car key a hannunsa?batare da yabashi answer ba yayi saurin nufar motar sa yana mata key, banda bugawa babu abinda kirjinsa keyi,tambayar kansa yake me kuma ya sameta?batare da yasan maganar zucin da yayi tafito ba yaji Aunty Maryam na bashi answer"wallahi muma haka muka sameta a sashen Bodejo,sakata a motar Taufeeq yayi yana zaunar da ita kanta akan kafadar Aunty labeeba, Aunty Maryam ma tashiga,da sauri Ummie takariso a rude take sai tambayar inda zuhran take takeyi,tayi matukar rudewa,haka Ammi dasu Mom,nufar dayan motan tayi tana cewa Taufeeq ya tada"No Ummie ki zauna a gida insha Allah komai zaizo da sauki,wani kallo ta aika masa dashi jikinta yana rawa cikin rawar murya tace"Ace min ka dauko 'yata kamar gawa?shine kake tunanin zan iya samun natsuwa?lallai Taufeeq baka da hankali"cikin daga murya tace"kabudemin mota nace! Bude mata motar yayi Saboda ganin yanda ta canza lokaci daya,Ammi ma tashiga,Adda Zainab ne tabude bayan itama da sauri tafada banda salati babu abinda takeyi,nan fa kowa yayi jugum². Su Laila kuwa sai kuka da kuka Saboda a yanayin da kowa yaga anfito da ita hankalinsa dole yatashi,a 360 Taufeeq ya figi motar,tuni securities din gidan suka wawwangale gate din. "Ya Allah ya tayar da kafadunki Fatima, Amma ta fada hakan tana me juyawa,lallashin su Laila Rammat ta shiga yi tana yimusu fadan so suke su sake tayar ma da mutane hankali?su yahakuri insha Allah zata samu lafiya. Koda labarin ya isa ga Akeela sosai tayi farin ciki da hakan don har addu'ah tayi kan Allah yasa kada ma ta tashi daganan ta mace kota huta da kallon ta tana kwasar takaici da haushi. Xahratty Ce🥰 Lallai Alqalami 🖊️ yafi takobi🗡️. 9/6/23. [6/11, 12:36] Xahratty (OUM AJMAL): 👨🏽‍🦳 *_GALADIMA FAMILY_*👨🏽‍🦳 Story&Written By *FATEEMA ZAHRA LAWAL* Marubuciyar⤵️ A DALILIN'YAR TSINTUWA. MIJIN ZAHRA. DIAMOND LADIES ( Daukar fansa)paid book. RUHIN AMRITA (FATALWA CE). Now *_GALADIMA FAMILY_* Page 47/48 𝑾𝑨𝑵𝑵𝑨𝑵 𝑷𝑨𝑮𝑬 𝑫𝑰𝑵 𝑺𝑨𝑫𝑨𝑼𝑲𝑨𝑹𝑾𝑨 𝑵𝑬 𝑮𝑨 𝑴𝑼𝑯𝑨𝑴𝑴𝑨𝑫 𝑲𝑨𝑹𝑬𝑬𝑴,𝑮𝑶𝑫𝑰𝒀𝑨 𝑴𝑨𝑰 𝑻𝑨𝑹𝑰𝑵 𝒀𝑨𝑾𝑨 𝑨𝑳𝑳𝑨𝑯 𝒀𝑨𝑩𝑰𝒀𝑨 𝑴𝑨𝑲𝑨 𝑩𝑼𝑲𝑨𝑻𝑼𝑵 𝑲𝑨 𝑨𝑲𝑨𝑵 𝑵𝑼𝑵𝑨 𝑲𝑶𝑲𝑨𝑹𝑰 𝑫𝑨 𝑲𝑼𝑳𝑨𝑾𝑨 𝑨𝑲𝑨𝑵 𝑩𝑶𝑶𝑲 𝑫𝑰𝑵.......𝑨𝑵𝑮𝑶𝑵 𝑹𝑨𝑯𝑴𝑨(𝑹𝑨𝑴𝑴𝑨𝑻) 𝑨 𝑩𝑶𝑶𝑲 𝑫𝑰𝑵 𝑮𝑨𝑳𝑨𝑫𝑰𝑴𝑨 𝑭𝑨𝑴𝑰𝑳𝒀😆 ______wani Private hospital suka isa me kyau da tsada da alama nanne asibitin da ahalin suke hidimarsu,da isar su kuwa nurses din asibitin suka sanya ta akan gadon marasa lafiya kaitsaye emergency ward aka nufa da ita,likitoci uku ne suka tsaya akanta gefe guda kuma nurses biyu,su kuwa ahalin banda zarya babu abinda suke a dan dogon corridor din ward din sauran kuma duk sun zazzauna,idan ka kalle fuskokin su cike da alhini banda shi da yake zaune ya lumshi ido tare da jinginar da kai a jikin kujerar da yake zaune. Sunanan dai zaune har 9:30 amma babu wani likita da ya fito bare a musu cikakkiyar bayani,dubansu Daddy yayi ya soma magana"Ku tashi kuje gida dare nayi muzamu jira har Doctors din su fito muji abinda ke wakana,matan ku koma gida"yakarisa maganar yana juyar dakai gefe daya. Ummie ce tadago da niyyar yin magana amma sai takasa don Allah yasani tana tsananin girmama Daddy don musu bai taba hada ta dashi ba bare gaddama,cikin sanyin jiki suka mimmike,kallon Daddy Ammi tayi tace"Amma Daddyn su day kun bar daya a cikin mu ko kun manta cewa dole macece zata maida hankali wajen kula da ita?fuskan Daddy babu wani wasa yace"babu bukata zaku iya tafiya ga Sauban nan inma anbata gado zai zauna da ita ya kula da ita"Cikin mamaki suka dago suna dubansa,shima da sauri yabude idanuwan sa yana duban Daddyn nasa.Aunty Maryam tace"amma Yaya kamar hakan be kamata Saboda shidin ba muharraminta bane,kuma dole zata bukaci wani abu kamar shiga toilet da sauran su. Wannan karan sake tamke fuska yayi yana maida duban shi gabadaya akansu yana kokarin magana, Abba ne yarigasa"Hakan ba matsala bane kawai kuje gida don muma munsan da hakan kuma munzauna a islamiya ba jahilai bane mu. Babu wanda ya sake magana a cikinsu duk tashi sukayi suka fita ko wanne da tunanin da yake a cikin zuciyar sa, Ummie kuwa bataji dadi ba ko kadan sai dai bazata iya nunawa,cikin sanyin jiki suka nufi hanyar fita,duban Taufeeq Daddy yace"maza kaje ka maidasu gida dare nayi,amsa yayi cike da girmamawa yana me bin bayan su,muryan Sauban suka tsinkayo"Daddy taya zanyi jinyar ta?naga hakan sam be dace ba wallahi ni bansan ma yanda zan kula da ita ba. Kafin wani yabashi answer doctor's din sun fito ko wanne na share zufa,karisowa Doctor Ahmad yayi Yana duban su Daddy"Alhaji idan babu damuwa zaku iya samu na a office,yana gama fadar haka yanufi office dinsa,kaitsaye rufa masa baya sukayi. Waje yabasu suka zauna,nan suka shiga gaggaisawa da juna zuwa can ya sauke ajiyar zuciya yana duban fuskokin su"To Alhamdulillah munyi nasarar shawo kan matsalar tata ba wani abubane face damuwa wanda ya haddasa mata jinin ta yadan hau kadan tare da ciwon kai kunsan hawan jini ga zazzabi kuma a gefe daya,sai dai insha Allah munyi nasarar gano matsalar Allah yakara lafiya,amma gaskiya kuyi kokarin ganin kunji meye damuwar tata domin kuwa idan aka zuba mata ido a haka to akwai matsala,ajiyan zuciya suka sauke gabadaya Abba ne yayi karfin halin magana"insha Allah likita zamu kiyaye Allah yakara mata lafiya"Da Ameen gabadaya wajen aka amsa dashi suna me mikewa,rakasu Doctor Ahmad yayi yana tambayar me zama,duban shi yayi yace"ga Sauban nan shi zai zauna da ita yayi jinyar nata,da mamaki yake duban su don yasan alakar dake tsakanin Sauban da zuhra batare da nauyin baki ba yace"Amma Alhaji ina ganin da ansamo 'yar uwanta macece tayi jinyar ta idan ma babu sai mu duba muku a nurse's din mu. Daddy ya danyi murmushi yace"Babu bukatan Doctor Ahmad don shidin mijinta ne...... Yana kare fadar hakan sukayi gaba abinsu, daga Sauban har Doctor Ahmad kamewa sukayi a tsaye kamar status saboda mamaki,wani murmushin jin dadi Doctor yayi,yana me dafe kafadar Sauban wanda yayi suman tsaye banda bugawa babu abinda zuciyan sa ke masa yarasa me yakeji a zuciyar sa,farin ciki yake ko bakin ciki?baisani ba,cikin tsananin murna Doctor yace"Na taya ka murna oga Sauban Ashe auren gata aka maka? congratulation!wucewa yayi yana cigaba da mamaki don shima yaso ace ya mallake Zuhra a matsayin matarsa,yana tsaye jikinsa na sake sanyi,ganin tsayuwar babu abinda zai masa yasa ya juya,direct dakin yanufa cikin tafiyar da na izza da kasaita,a hankali yaka ma handle din ya murda,a makoshi yayi sallama tare da kutsa kai cikin dakin da aka canza mata (VIP) idanuwan sa kuri akan kyakkyawar fuskan ta wanda yini guda kawai yasa ya yamutse saboda ciwo,kallonta yakeyi kawai yakeyi jikinsa na sake sanyi a gefe guda yana jin taya shi zai iya rayuwa da mata har biyu?to ta inama shi zaifara?tambayar da yayi ma kansa kenan.Haka ya samu kan kujerar dake gefen gadon nata ya zauna batare da ya dena kallon ta ba yana kissima abubuwa da dama akanta,duban agogo yayi yaga sha daya da kusan rabi ne ma na dare,lumshe ido yayi batare da yanajin dadin zaman kujerar ba. A can gida kuwa duk da mamakin su Daddy suka dawo tare da tambayar kawunan su a zuciyoyi mezesa suyi haka?shi kanshi Taufeeq mamaki ne fal ransa,sai dai rashin samun me Basu amsa yasa kowa yakasa furta komai,koda su Aunty Maryam suka isa apartment din Galadima tambayan su me jiki sukayi tare da me kwana da ita,cikin alhini suka basu amsa da wai Sauban ne zaiyi jinyar ta,ganin fuskokin tsofaffin sukayi normal babu wani alhini, Galadima yace"Hakan ma yayi Allah yabata lafiya ya kuma tada kafadun ta,da Ameen suka amsa jikinsu nasake sanyi da lamarin ahalin nasu masu cike da abubuwan mamaki.A sashin Ummie kuwa sun tadda Amma har tayi bacci abinta don dama kafa ya matsa mata, Adda Zainab ne keta sababi akan mezesa su Daddy suyi hakan?ita kuma Ummie takasa magana kan abinda yake faruwa,ajiyar zuciya Ummie tayi tace"bazan iya tambaya ba Adda domin koni dana haife Zuhra bankai bayin Allah nan sonta da kaunar ta,ni ina tunanin suna da kwakkwaran dalilin su nayin haka don dai haka kawai bazasu yanke wannan hukuncin ba. Adda Zainab tace"Hmm to ai shikenan Allah ya kyauta meson dangin miji ke dama sam bakison a fadi lefinsu koma dai menene?ai hakan dai bedace haba jama'a sai kace ana garin ga6a²,shiru ita dai Ummie tayi bata tanka ba.Hajiya Aliya ce tadubi Adda Zainab tace"Niko aminiya yaushe Alhaji iliyasu zai dawo ne?saboda munada biki acan gombe inaso da muje tare da kene,kinsan hajara na zata aurar da 'ya next week,cikin mamaki Adda Zainab ke duban hajiya Aliya tana sakin dariya"Eyye aminiya kina nufin hajara har zata aurar mu muna zaune?lallai aiko ya kamata muje ma hajara biki ai komai zaizo da sauki nima gobe zan koma nafara tarban dawowar shi don jibi zai dawo yace jirgin 4:00 zai biyo, cikin farin ciki hajiya Aliya tace"Kai naji dadi ai nida kaina ma zan tambaye shi domin nasan zaiji dadin hakan sosai,dariya Adda Zainab tayi tace"gaskiya kam zaiji dadi sosai Allah yadawo min dashi dai lafiya kinsan yatafi yana fushi danine don naki binsa sai a waya muka shirya,hajiya Aliya tace"Ai tafiye²n nan irin nasu ba kowace mace bace zata jura kinji kiyi zamanki anan wallahi, Adda Zainab tace"yanda kikajin nan. Ummie najinsu sai dai bata tanka ba don asanin kanta duk abinda za'a cema hajiya Zainab akan hajiya Aliya ba yarda zatayi ba saboda son da take mata,tasani yanda takeson hajiya Aliya bata mata irin wannan son tun suna secondry school,sabanin ita da take tsananin son yayar tata,mikewa tayi don nufan dayan sashin nata don duba sauran jama'ar nata nan tabarsu suna cigaba da hirar su,da wani irin mugun kallo Adda Zainab tabita dashi tanajin kamar tatashi ta makure ta tahuta. Bayan fitanta cikin dacin murya Adda Zainab tafara magana"Aminiya boka hatsabibi bai kyauta minba,ba haka kukayi dashi ba nidai duk aikin da yabani nayi nayi amma kina ganin ma idon ki babu abinda yayi aiki ni garas ma naga takari,gaskiya zan canza wani bokan ki samo min wani nikam bazan iyaba wallahi so ake ciwon zuciya da bakin ciki su kashe nine ko mene?Hajiya Aliya tace"Kash!Kash!! Dadina dake Aminiya gajin hakuri,munyi magana dashi nayi masa korafi sai dai yace lefin ki ne wallahi domin kuwa duk aikin da kikayi sun lalace sai dai besanar dani yanda akayi suka lalace ba,amma kinsan idan kika fadi wani magana mara dadi akan boka hatsabibi kema baki masa adalci ba,shekara nawa yana miki aiki kuma anga dacewa don kawai wannan anyi kuskuren da kecema kikaja sai kifada haka?wallahi banji dadi ba idan yajiki kuma babu ruwana.Adda Zainab tace"gaskiya ne idan nafada wani abu nayi butulci aikam zanje nane mesa da kaina domin magance matsala ta. Hajiya Aliya tace"Da dai yafi kam,haka suka cigaba da tattaunawa akan matsalolin su har suka raba dare. ********* Wajen karfe 2:40 ta farka a hankali tashiga bude ido still tanajin kan na mata ciwo sai dai baikai na farko ba,kwata² babu karfi a jikinta ga wani masifaffen fitsari da takejin ya matseta,muryan ta da babu wani kwari ta bude tafara magana"Ummie! Ummie!! Ummie!!! Zanyi fitsari"kamar a mafarki yakejin muryan nata don shi mutum ne wanda beda nauyin bacci,bude ido yayi ya zubanya mata batare da yayi magana ba,magana tasake still"Ummie zan shiga toilet,mikewa yayi yana me kunna switch din,room din ya gauraye da haske,ido biyu tayi dashi wani irin kamewa tayi akan bed din duk da kuwa wani irin fitsari da takeji ga rashin karfin da bata dashi ko kadan jinta take kamar a wani duniyar,tamke fuska yayi ganin yanda ta kura masa ido alamun ta tsorata dashi,bata fuska yayi da kyar ya bude baki ya soma magana"Zaki tashi narakaki toilet dinne ko zakiyi a zaunenne?yayi maganar yana tsura mata dakwa-dakwan idanuwan nan nasa,cikin rawar jiki ta mike sai dai ko second biyu batayi ba tatafi luuu zata fadi,cikin hanzari yakarisa yana me tallabo ta jikinsa,duk cikansu sunjisu a yanayi na daban a dalilin hakan,kamata yayi suka nufi toilet din wanda yakejinsa fess kamar ba'a hospital ba sai kamshin Toilet freshener yake Dana hypo,kokarin sakinta yake amma sai yaga tatafi luuu,ita kuma ga azababben fitsari tanaji kuma yaki matsuwan mata,rasa yanda zaiyi da ita yayi a hankali yake jan kananun tsaki saboda takaici shi sam bema san yanda zai mata ba,ganin haka yasa Zuhra fashewa da kuka tanajin wani irin takaici don dai ba'a kyauta mata ba da aka barta a daki daga ita sai shi,tafada a cikin ranta,ita batasan tana hospital ba,karfin hali yayi ya jingina ta da bango tare da dukawa,doguwar gown din dake jikinta ya fara dagawa,jikinta babu inda baya rawa kafafuwan ta naneman gaza daukan ta don ita abune wanda be taba faruwa da ita ba,a hankali ya cire mata pant din face dinsa babu walwala yace" Oya yikiyi, am waiting for you. Ganin da tayi bata da wani mafita yasa tafara kokarin yin fitsari ai babu zato bare tsammani tafara sakin shi a tsayen,runtse idanuwa tayi da karfi tana mejin wani irin mahaukacin kunya tare da takaici,shima takaicin a gefensa yake ji don ma anci sa'a bata fallatso mai da fitsarin ba da ya kafa mata mari acewar sa,idanunta a rufe,bude tap taji yayi nan ya jinginar da ita daga jikin bangon sosai yana me matsawa tare da kauda kai yace"Yi tsarki mufita,duk kincika ma mutane toilet da zarnin fitsarin ki,mtsewwww! Yaja siririn tsaki. Zuhra kamar kuwa babu zato taji hawaye na sirnano mata,cikin rashin abin yi tayi tsarkin ta gama,kamata yayi suka fito yana zaunar da ita akan gadon,idanuwan ta arufe ta kwanta tana jin kanta na juya mata. Kashe switch din shima yayi yana me komawa yazauna kan plastic chair din,kowanne da abinda yake sakawa a ransa,babu jimawa bacci yayi awon gaba da ita saboda alluran da aka sa mata a drip din harda na bacci,jin yanda take sauke numfashi cikin natsuwa ya tabbatar mata da tayi bacci don haka yamike ya shiga toilet din don dauro alwala. *~DA ALAMA BA KARAMIN CAKWAKIYA BANE ZAI AFKU GABA,NINAGA LABARIN NATA TSAYINE ANYA KUWA ???~* 😂😂 Xahratty CE🥰 Lallai Alqalami 🖊️ yafi takobi🗡️. 11/6/23. [6/14, 10:59] Xahratty (OUM AJMAL): 👨🏽‍🦳 *_GALADIMA FAMILY_*👨🏽‍🦳 Story&Written By *FATEEMA ZAHRA LAWAL* Marubuciyar⤵️ A DALILIN'YAR TSINTUWA. MIJIN ZAHRA. DIAMOND LADIES ( Daukar fansa)paid book. RUHIN AMRITA (FATALWA CE). Now *_GALADIMA FAMILY_* Page 49/50 *_KUYAHAKURI PLEASE DUK DANI NA TSARA LABARINA NAKE KUMA RUBUTA ABINA SAI DAI WANNAN KARAN LABARIN SHIKE TSARANI YAKE KUMA JANA😂FATAN KUN GANE ABINDA NAKE NUFI?INA KOKARIN INJA BURKI,SHI KUMA YANA WASKEWA🤣* *PLEASE FORGIVE ME MAKARANTA🙏🏽GABADAYA LABARIN SADAUKARWA NE GA MASOYA BOOK DIN GALADIMA FAMILY.* ______Shi mutum ne me kyankyami gashi babu abin sallah don haka yabude kawai app din complete Qur'an dake wayan sa na Alaramma Ahmad Sulieman yafara karatun,itakuwa bancin ta takeyi cike da natsuwa,haka Sauban ya cigaba da karatun sa har aka kira sallar asuba,toilet yakoma yadauro alwala yafita don neman masallacin asibitin ya gabatar da sallah. ******* A can kuwa washegari haka suka tashi jiki a sassalube sai dai hakan be hana hidiman na bikin kawatuwa ba,cikin sauri su Aunty Maryam ke hada abin breakfast din 'yan asibiti su Laila na tayasu don bada su za'a koma Zaria ba, Rammat ma said tayasu aikin takeyi ta saje a cikinsu sosa,'yan aikin Ammi kuma suna na amare Akeela,sai wajen tara suka gama hada breakfast din. Da mommy dasu Aunty Maryam su Nihal sune suka nufi asibitin,don Abba, Daddy, Baba Hashim tun safe sukaje asibitin amma bata farka ba,haka suka dawo akan anjima zasu sake lekowa,Koda suka isa baya dakin sun ciddata tana zaune bayan ta pillow ne an jingina mata,ganinsu ba karamin murna tayi ba sai dai kallo daya zaka mata kasan tanajin jiki, basket din duk suka aje suna Isa bakin gadon suna mata ya jiki,shimfina dan babban carpet din da sukazo dashi sukayi,nan wasu suka zazzauna,mommy dafa kanta tayi tace"Sannu my baby ciwon nan naki na jiya ya tsorata mu sosai,ke Kinga yanda kikayi zuru-zuru kwana daya kawai,dan lumshe ido tayi cikin karfin hali tace"mommy nama ji sauki fa,duban su Aunty Maryam tayi tace"Mommy Maryam,mommy labeeba ina kwana?amsa mata sukayi cikin sakin fuska tare da tambayar ta ya karfin jikin nata?amsa tabasu da Alhamdulillah.Cikin tsokana Nihal tace"mufa munzata shekawa zakiyi har munfara tanadin gumba,duka akasa dariya,cikin karfin hali Zuhra tace"ai idan na sheka ku kanku bazakuji dadin zama a family dinba wallahi,cikin Wasa Laila tace"injiwa ya gaya Miki?lallai mudai kinmana bakin cikin cin gumba,kwafa tayi"hahaha kubari na warke zakuga yanda ake rashin mutumci.Duka 'yan dakin dariya suka sanya,dai dai sukayi sallama suka shigo dakin,shida Taufeeq ne,kallo daya ta masa ta kauda kai da sauri don harga Allah batason hada ido dashi,hada ido sukayi da Taufeeq wanda Kai tsaye yanufo inda take,langabar dakai tayi cikin muryan shagwaba tace"Yayaaaa sai yanzu ko? Murmushi dauke a face din taufeeq yace"sorry kanwaty aike dince kin tadama kowa hankali jiya kowa ya rude,tana kokarin magana aka turo kofar aka shigo. Shuraim ne da wasu 'yan mata biyu sai wata 'yar dai babban mace kamar su Aunty Maryam sallama dauke a bakunan su,hanayen 'yan matan kuma rike da ledoji riki-riki sai basket,cikin mutumtawa da girmamawa mommy dasu Aunty Maryam suka tarbesu,nuna musu wajen zama sukayi. Koda suka zauna gaisawa suka farayi da juna,shiko kaitsaye wajenta ya nufa face dinsa dauke da damuwa,tsira mata idanuwa yayi kamar zai lasheta cikin tausayin da wani irin murya yace"just one day?jibi yanda kikayi?gaskiya koban gani ba nasan kin wahala,yakarisa maganar kaman besan da mutane a dakin ba,duk sauraran sa sukeyi cike da mamaki. Dukar dakai tayi yashiga wasa da 'yan yatsunta masu daukar hankali da sukasha jan lalle,dan murmushi Shuraim yayi yace"kidago face mana nine kikejin kunya?ya karfin jikin naki? Ahankali tace"naji sauki Alhamdulillah. Cikin jindadi yace"Alhamdulillah to ga Aunty na, aunty safiyya wadancan kannena ne,khairat da khausar su din twins ne,yayi maganar yana nunasu,duk ya jiki sukayi mata,maida hankali yayi yashiga gaishe da 'yan dakin inda su kuma su Sauban musabaha sukayi,jiyake kamar ya shake yaron saboda wani mugun tsanar da da yaji da haushin sa lokaci daya,kawai yazo yanama mutane wani rawar kai,mommy ce tadube Sauban tace"Son ya kamata fa kazo kayi breakfast itama yanzu za'a Sanya mata,duban Aunty labeeba tayi tace"please labeeba zuba ma Sauban abinci. "No mommy kinsan wallahi bazan iya cin abinci a hospital ba yanzu ma zan wuce gida nayi wanka sai nayi breakfast. Da yake mommy Sarai tasan halinsa shiyasa bata jaba tace"To shikenan amma yakamata ka hanzarta don kada kayi ta zama da yunwa ko?cikin kamewa yace"insha Allah mommy yanzu zamu tashi. Duban zuhra tayi tace"Baby meza'a zuba miki?akwai Chip's nd eggs sai samosa,akwai faten Irish da hanta sai kuma doughnut wanne zakici,cikin sanyin murya tace"mommy nikam nakoshi mouth dina babu appetite ko kadan shiyasa,mommy tace"to da yunwa kike tunanin za'a barki?kitashi kici abinci ko Yaya ne sai kisha magungunanki,nannarke murya tashiga yi tana neman botsarewa,wani kallo ya aika mata dashi cikin sa'a kuwa suka hada ido. Mommy ki zuba mata abincin za'a tsaya jin tabakin ta ne?kamar bashine yayi maganar ba saboda ko dagowa beyi ba daga daddana wayan da yakeyi,kamar zatayi kuka take dubansa. Mommy tace"wanne zakici a ciki? Cikin sanyin murya tace"faten Irish din,zuba mata akayi dai-dai,dayake jikinta din ba wani kwari bane dashi, matsowa Aunty labeeba tayi ta shige bata abincin a baki,duk da bakinta babu dadi amma taji dadin faten ainun,dakyar aka lallabata ta gama shan faten shima saboda Sauban ne daya tsareta da idon dina.Shuraim kuwa jiyake tamkar yayi kuka don Allah yasani yana tsananin masifar son zuhran,duk abinda yake Sauban na ankare dashi shys gabadaya ya nemi walwalar sa yarasa jiyake kaman yaje ya kama yaron da duka. Duk suna zaune zuwa can sister's din Shuraim suka mike kan zasu wuce,'yan matan nan kuwa sun mutu akan Sauban,mommy tace"Haba kukuwa har zaku wuce da wuri haka?yarshi tadanyi murmushi tace"Ai mommy Shuraim dinne wallahi zanje gdn bikin wata cousin's dinmu but Saboda shidai nayi squeezing din time muka wuto,kinsan yanda yake son zuhra kamar ya maida ta cikin ciki yasake haifota"duk cikan 'yan dakin dariya suka Sanya har taufeeq,shikuwa ogan yasake cudu² da face sam babu walwala, Shuraim kuwa sosa kai yaketa tayi cike da kunya.Mommy tace"Allah sarki ai dama hakane,mungode sosai domin a haka ma mune da godiya matuka Allah yabar zumunci,da Ameen duk suka amsa,duban shi Aunty safiyyan tayi cikin zolaya tace"Ouncle Romeo oya let's go! Nan ma dariyar aka sanya,dan susa kai yayi yace"Aunty muje nadai taka muku don bazan iya barin ta ita kadai ba wallahi look at her Aunty gaskiya muje na taka muku,duk da mamaki ake duban sa wannan karan Sauban tsaban mamaki daskarewa yayi don ko dago face ya kasayi,yana mamakin rashin kunyar yaron,a ransa yace _Lallai dole ne yaron yayi nasarar sace zuciyar kanwar tasa,dole ya Mike tsaye._ Fita sukayi Mommy kuwa sai dariya suke, Aunty Maryam tace"Lallai zuhra wannan yaron yana matukar son ki gashi kunyi masifar dacewa don shima kyakkyawa ne,ga natsuwa da alama idan kika aure shi zakiji dadi don bai boye irin son da yake miki, Laila tace"wallahi kuwa Aunty Yaya Shuraim na matukar sonta sosai, cousin's din su ya Asheer din Aunty safeena ne,hada baki sukayi wajen fadin dagaske?Nihal tace"Allah kuwa yace mata shi idan ma akace yaturo yanzu Allah zai turo don hajiyan su da kowa nasu suma sunason hadin musamman da sukaji kanwar Aunty safeena CE, Mommy tace"Kai Nihal duk a'ina kikejin wannan labaran? Laila tace"wallahi Mommy dagaske ne ya Asheer ke fadama Aunty safeena da mukaje gidan,ai gaskiya wallahi.....batare data karisa ba ya Sauban yadaka mata tsawa yana diddilo mata wannan idanuwan da suka koma jajaye,tsit tayi daga ita har Nihal jikinsu babu inda baya rawa,ita kanta Zuhra banda rawa babu abinda jikinta keyi ganin haka yasa ta zamiye ta juya tana me rintse idanuwan ta.Maida duban sa yayi ga Mommy yace"haba Mommy meye amfanin ku tasa yaran nan a gaba ana firar samari?dudu shekaran su nawa da suke hirar samari?wato ana ma sane tana karatu take kula wasu 'yan iskan yara?cikin bacin rai da karaji yake magana,cigaba yayi"Lallai zaki zaba kodai auren ko karatu cikin daya kizaba daya ki aje daya,mtsewww! Yana kare fadan haka yafita yana mejin zuciyar sa na wani irin bugawa,Taufeeq ne yabi bayansa. Duk cikan su day kallon mamaki suka bisa har yafita,ajiyan zuciya Mommy ta sauke,a ranta tana ayyana abubuwa ita kadai, Aunty Maryam da Aunty labeeba suka mike suna duban mommy"Aunty Hauwa'u mu zamu wuce kinsan tafiya kaduna zamuyi akai Mashahuda gidan ta,kafin keda Ummie ku karaso, Mommy tace"Ea nasani babu damuwa ai Labeeba Allah yatsare don Allah ki tabbata tasha magunguna nan,muneefa ma na aika mata da nata,can gidan ta zamu wuce mu"Aunty Maryam tace"Insha Allah.zumbur Zuhra ta mike duk da kana ganin yanayinta kasan karfin hali take face dinta babu wani walwala kamar tayi kuka tace"Mommy!juyowa Mommy tayi tana duban ta,cikin rashin abinyi da damuwa tace"Mommy nifa inason karatu na kibawa ya Sauban hakuri nazabi karatun Amma wallahi inason ya Shuraim,duk da mamaki suke dubanta,su Laila kuwa sai guntse dariya suke. Aunty Labeeba tace"ke Zuhra ki rufama kanki asiri kibar maganar nan a yadda naga Sauban yafita a fusace ai idan kika cigaba d maganar nan zai kassara kine a banza,kuma wannnan abin tun zamanimmu ne ba kukadai ba,duk wacce karatu zatayi to bata aure sai tagama degree,bakiga su Mashahuda da muneefa bane?mu kanmu sai da muka gama diploma mukayi aure,wallahi ki rufama kanki asiri kada kikawo wani sabon tsari, Aunty Maryam tace"Ah to kidai fada mata. Mommy cike da tausayin ta take duban ta,batare da tayi magana ba suka fita ita dasu Aunty Maryam,cikin raunin murya mommy tace"wallahi Maryam inajin tausayin Zuhra,soyayya tayi gaggawan shigowa rayuwar ta da wuri duk da farin jinine ma yasake ruruta wutar wani abu,inajin tsoron abinda zaije yadawo kinsan yayyen nan naku?ita kanta tana son yaron haka zalika shima da baya iya boye sonta ko gaban wanene,a gefe daya Zuhra na matukar son karatu yana daya daga cikin abinda yasa sam tatsani wani ya mata maganar soyayya kenan to Amma kinga yaron nan yaci galaba a kanta?Suma ajiyan zuciya duk suka sauke, Aunty labeeba tace"Allah ya jishemu alheri,bari muje zamu tare me napep ne kawai tunda su sun wuce gashi munbar yara a gida. ****** Koda suke mota suna driving sam yakasa samun natsuwa,a gefe guda kuma sam zuciyar sa taki aminta da maganar da Daddy yafada yana kallonsa a just for raha,sam yakasa natsuwa shi ba abin yaje yasake tunkarar wani a cikin iyayen sa da magan ar ba,wayar sa ce tafara neman agaji,dauka yayi daga can bangaren aka fara magana,amsa yabada kamar haka"sorry Kareem muna hanya ne gamunan karisowa. Aje wayan yayi Taufeeq ya dubesa"Kareem ne ko?daga ma Taufeeq Kai yayi kamar wani me ciwon baki da kyar yace"Yana sanar dani azo ayi abinda za'ayi gasu Saif zasu wuce. Kara speed din motar Taufeeq yayi har suka karisa,a gurguje sukayi wanka suka shirya,sunyi bala'in kyau cikin wata danyar shadda cofee sunyi anko,abokin Abbie ma na Dubai bai samu zuwa ba. Nanfa aka fara hotuna. Amma ce keta surfama Ummie bala'i akan abinda ta aikata"bilkisou da hankalinki da komai da sanin addininki dai² gwargwado kina takaba amma kika zauna kinata caba ado na daukar hankali?anya bilkisou kinyiwa Sadeeq adalci kuwa?bilkisou haka ake takaba?wallahi baki kyauta ba,kinsan yanda maganganu zasuyi ta fita akanki tunda abune na yanar gizo yanzu?wallahi bakima kanki adalci ba bare 'yayanki,takarisa maganar cikin fusatacciyar murya. Cikin tsananin damuwa Ummie tace"wallahi Amma shaf na sha'afa ne ba wani abuba,amma nasan nayi kuskure Allah yayafe min don bada gangar nayi ba Allah natuba kayafemun,don Allah amma kema kibar maganar,bazan sake ba. Amma tace"Kinsan yanda ran yayyenki yabaci?niban ma hankalta da irin kwalliyar ki ba harsu mother's day dinda aka hada,sune suka kirani suna ta fada suna cewa inanan kike wannan kwalliyar da takaba akanki?kawai kija mana zagi?dama mutane kuskuren ka kalilan suke nema su kara maka da sharri, Bodejo tace"don Allah hajiya Amma kiyahakuri dagaske bilkisou da gangar bazatayi haka ba,Dan Adam dama ai yana kuskure don Allah abar maganar ta wuce ita kuma Allah yayafe mata. Dakyar aka samu Amma ta sauko,dayake suma su Adda Zainab yau zasu wuce tare da Amma gabadaya Sha tara na arziki Ummie tashiga hada musu da abin biki,don gabadaya zasu wuce da amarya ne,Amma kuma ta wuce gidan Adda Zainab washegari driver ya maidata Zaria,sosai take kewan bakin nata,hajiya Aliya kuwa jitake kamar tayi tsalle taganta a kaduna gashi ta kosa taji yaushe Alhaji iliyasu zaidawo? Xahratty CE 🥰 Lallai Alqalami 🖊️ yafi takobi🗡️ [6/18, 23:18] Xahratty (OUM AJMAL): 👨🏽‍🦳 *_GALADIMA FAMILY_*👨🏽‍🦳 Story&Written By *FATEEMA ZAHRA LAWAL* Marubuciyar⤵️ A DALILIN'YAR TSINTUWA. MIJIN ZAHRA. DIAMOND LADIES ( Daukar fansa)paid book. RUHIN AMRITA (FATALWA CE). Now *_GALADIMA FAMILY_* Page 51/52 ______Sun kammala duk wani shirye²n su haka aka dauke amarya tana kuka haka suka shisshiga tsaddaddun mutocin,motoci biyar suka nufi kaduna dauke da amarya,to amarya mashahuda sai dai muce Allah ya baku zaman lafiya keda ya taufeeq din naki. Ummie sam hankalita ba'a kwance yake ba tanaso taji halin da zuhra ke ciki amma bazai yuwu taje ba tunda tasan tana takaba,wayan ta kirar spark 10 tadauka tafara neman number Sauban,dauka yayi yana me Mika gaisuwa gareshi,kaitsaye tace tana son ganin shi idan yana kusane,amsa mata yayi dacewa yana nan gashinan shigowa,ajiya wayan tayi don sashin nata babu kowa bakin ta duk sun watse sai wadanda baza'a rasa ba abokan arziqi. Baiwani dau lokaci ba yashigo,cike da girmamawa yake gaida ummien nashi,cike da kamewan shi da basarwan shi yace"Ummie Allah yasa lafiya dai?dan murmushi Ummie tayi tace"Son kenan lafiya lou dama nakira kane naji ya jikin kanwar taka?duk da naso zuwa dubata but sai a hankali,takarisa maganar da dan damuwa,duban ta yayi cikin girmamawa yace"Ummie lafiyan ta kalau fa just I think fever ne yake damunta but insha Allahu everything will be okay so kila gobe ma da yardan Allah su bamu sallama,yakarisa maganar yana maida hankalinsa dungurun gun kanta. Ummie tace"Alhamdulillah naji dadi wallahi har nasamu natsuwa jiya sam ban iya bacci ba Saboda yanda muka baro yarinyar nan a asibiti. Dan murmushi yasake wanda yabawa kyansa Kara damar bayyana yace"Ummie kenan insha Allah gobe zasu sallameta, Ummie tace"babu komai Allah yakaimu,ya amarya kuma?dan sosa kai yayi yana dan munafikin murmushi yace"Aini Ummie tunjiya kinga Ina hospital sai yanzu da muka shigo Saboda tafiyan su Taufeeq,amma lafiya lau"dariya Ummie tayi tace"ai yau za'a samu me zama da ita kaikuma yau dole kaje ga amaryan ka, Allah dai yakara hada kawunan ku yabada zaman hakuri. Da Ameen ya amsa tare da cewa"Ummie nifa yunwa nakeji wallahi"mikewa Ummie tayi sanye take da babban mayafi babu kwalliya a face dinta sai dai kaya tadansa masu kyau sai casbaha da takeja"Okay bari nasa akawo maka,Nima daganan zan wuce parlour na sallami baki ance anata shigowa,takarisa maganar tana fita daga bedroom din. **** Zuhra tadan samu bacci,sai dai bata wani jimaba ta farka a suka cigaba da hirarsu dasu Laila da Mommy,jikin nata yadan samu babu lefi su Mommy na zauna doctor Ahmad ya shigo,gaisuwa suka fara da Mommy kafin sauran yaran suka gaida shi,fara duba ZUHRA yayi tare da tambayoyi,Koda ya kammala hamdala yayi yana duban Mommy yace"Alhamdulillah jikin nata yayi sauki sosai insha Allah gobe zamu sallameta,abinda yasa ma bazamu sallameta yau ba Saboda akwai drip uku da bata gama Sha ba sai wasu allurai da za'a mata so insha Allahu gobe zamu sallameta"Mommy tace"Masha Allah munji dadi Doctor Ahmad Allah yasaka da alkhairi,fita yayi,hakan yaba ma zuhra daman duban Mommy tace"Nidai gaskiya Mommy a samu yau wanda zai kwana dani don bazan yarda ya Shuraim ya kwana dani ba,to ma taya aka bari ya kwana dani ga 'yan uwana gasu Laila?takarisa maganar tana kwal² da idanuwa, Mommy tace"to ya zamuyi mu kanmu zuhra jiya harta su Ammi sai da suka ce beka mata Sauban yayi jinyar ki but su Daddy suka ce dole shi zaiyyi,so ansan dalilin su nayin hakan ne?ko ya miki wani abu ne?cikin sauri ta girgiza kai tace"ni babu abinda yamin Aunty amma nayi abin kunya a gaban ya Sauban,jiya fa dana tashi jiri nake gani cikin daren nan ga kuma fitsari da ya matseni,cikin muryan kuka tace"nayi kokarin rike fitsarin nakasa haka fa nayi a tsaye a gabansa...... "Hhhhhhhhhhh!!!! Su Laila suka fashe da dariya,ita kanta mommyn dariyar ta rike,tace"lallai zuhra kinyi abin kunya"to me yace miki shi?su Laila banda dariya babu abinda suke,zuhra tace"mezece min Mommy kinsan yaya da babbasar wa amma Allah naji bala'in kunya,shiyasa gaskiya nidai yau bazan kwana dashi ba,gashi shi yadinga fa rirrike ni Saboda ban iya komai jikina yayi very weak,banson hada Ido dashi inaji yatafi sallan asuba na lallaba na mike da kyar na koma toilet nayi alwala,rashin fa sallaya da yanayin kayan jikina yasa nahakura da salla ina tunanin bazasuyi sallah ba na fantsala musu fitsari"dariya su Laila suka sake saki. Cikin muryan shagwaba zuhra tace"mommy kingansu ko?please ki musu magana,takarisa maganar tana zabga musu harara cikin kuluwa,itama mommyn hararan ta maka musu,mikewa tayi tace"a lallai bari na hada ruwan zafi kiyi wanka zaki samu dadin jiki sai ki canza kaya kiyi salla nazo miki da kaya set biyu sai hijjab din sallah. Bayan tayi wanka tayi sallolin ta,sanye takeda da wata gown me umbrella tayi matukar yimata kyau,wajejen karfe biyu mommy tatafi tabar su Laila Saboda zasu tafi gidan muneefa budan kai,nan suka cigaba da zaman su suna hirarrakin su gwanin ban sha'awa,wajen hudu aka kawo musu abincin rana. Da magriba ta gabato gida duk ansake wawwatsewa,shikuwa gogan yana apartment din Galadima,duban Galadima yayi sam face dinsa babu walwala yace"Gaskiya an tauye min hakkina Galadima nida zaku yadda Allah gobe da sassafe zan kama gaba na na koma office,sam banjin zan iya rayuwar aure da wannan yarinyar don inada wacce nkso"dan murmushi Galadima yayi yace"da kana da wacce kkso da tun tuni kafito da ita amma kana ta mana yawo da hankali,ka maza katashi kanufi wajen amaryan ka,6ata fuska yayi batare da yayi magana ya cigaba da danne² wayarsa. A bangaren amarya Akeela kuwa ta maida hankali ta babbaki magunguna sosai,don tana tsananin yau su zama abu guda itada ya Sauban,haka zalika tana addu'an Allah yasa maganin da boka yabata yayi nasara domin ta mallakeshi ta mallake duk abinda ya shafeshi. Da yake duk kawayen ta sun kwana,sosai suka sake mata hudubar banza,zuleey kuwa har kuka sai da tashiga toilet tayi ganin cewa ba'a fasa bikin Akeela ba,sai dai tadau alwashin cewa duk bala'i duk wuya duk rintsi sai ta raba auren Akeela da Sauban ita kuma tashiga domin gani takeyi sam Akeela bata dace da mijin ba balle gidan. Rammat ma tayi kukan daya isheta sai dai tasa ma ranta dangana,ta kuma kudurta a ranta matan mutum kabarinsa, tayi addu'an Allah ya zaba mata wanda yafi zama alkhairi,haka hajiya Biba itama duk ta watsar da makaman yakinta musamman da taga ahalin da jikanta tashiga sai takoma yima autan ta addu'an samun makamancin hakan. Wajejen karfe takwas aka kawo mommy tare da abincin dare,sai su Laila Kuma aka maidasu gida,cike da kewan junan su. Sauban sai wajen goma da rabi yashiga gidan nashi kaitsaye apartment din sa yanufa,wanka yayi sannan ya shirya cikin pyjamas masu matukar taushi Gray colour,katsaye hadadden gadon sa ya hau tare da addu'o'in bacci yakashe fitilu tare da shigewa cikin duvet,duk kokarinsa na ganin bacci ya daukesa ya kasa domin tunanin yarinyar ya sakashi gaba,yakasa sukuni shiyasa bini² kadan yake jan tsaki,a hakadai ya samu bacci ya sacesa. Bangaren amarya Akeela kuwa ta shirya abinta cikin wata fitinanniyar night gown da ta tsaya mata iya kacin gwiwa,banda tashin kamshi babu abinda takeyi,a gefe daya kuma ta shirya kanta tsaf da magunguna kaloli,sai duban agogo takeyi amma babu ango babu alamun sa,har kusan 1:30 amma Sauban beshigo ba sai aikin matse cinyoyi take hankalinta yayi kololuwan tashi tarasa inda zata sanya kanta taji dadi,ga wani ciwo da mararta keyi mata,har kuka kuwa sai da tayi takuma sake tabbatar da lallai Sauban baya sonta dole ta tashi tsaye da kafafunta akansa,dan robar da suke amfani dashi ne don biyawa kai bukata ta lalubo don sam bata yarda ta barshi ba,nanfa ta shiga biyawa kanta bukata( _wa'iyazubillah._) banda ihu na dadi ba abinda Akeela keyi bata samu natsuwa har sai da tabiyawa kanta bukata,nan ta kwanta batare da wanka ba tafara bacci. *_WASHEGARI_* Shuraim sammako ya doka ya nufi asibiti hannunsa da basket na breakfast zuhran ko tashi ma batayi ba,mommy sosai ta cika da mamakin guy din,cikin mutumci ya shiga gaisheta,amsawa mommy tayi tana duban agogo 7:48,sama² zuhra kejin muryan sa a hankali tashiga bude idanuwan ta,four eye's sukayi atare suka sakin ma junan su murmushi a hankali tafara kokarin mikewa Mommy na temaka mata tare da kallon ikon Allah,tana mamakin yanda idanunsu ke rufewa a sanda suka ga juna basu tunawa da kowa gabadaya,dan sunkuyar dakai tayi tana wasa da zoben azurfan da abbien ta yasa mata tare da dan murmushi kasa² don jin nauyin Mommy kawai takeyi,ganin haka yasa Mommy cewa bari taje tasake dan zazzaga asibitin ta mike kafafuwan ta. Bayan fitan Mommy sosai Shuraim ya kura mata idanuwa kamar tsohon maye don ko kyaftawa bayayi,cikin sanyin murya yafara magana"Kinga yanda kika rame ne?just 2 days kawai amma kin zabge my Zuhra,gaskiya nidai da dayanda za'ayi da anyi bikin mu yanzu sai kiciga ba da school a gidana,diddilo idanuwa waje Zuhra tayi cikin shocked da maganar sa tace"please ya Shuraim nidai mubar zancen nan yanzu idan nakoma gida mayita"tayi maganar cikin marairaice face. Sake fuskan tausayi yayi yace"Meyasa?banyi miki kalan irin mijin da zaki aura ba ko?koko banyi kala irin na Ya Abiddeen MIJIN ZAHRA ba?kokari take tabasa amsa sai gani sukayi anturo kofan anshigo,idanuwan sa a kansu face dinsa babu digon fara'a ko kadan,yatsine face yafara,idanuwan shi na kanta ko kadan yaki dena kallon ta,wannan dalilin ne yasa duk tabi ta diriri ce, jikinta nadan rawa tashiga gaishe shi,ko amsa mata beyi ba sai dai still idanunsa na kanta,shima Shuraim sosai yasha jinin jikinsa da irin kallon da yaga yana mata,gaishe shi ya shiga yi tare da mika masa hannu,hannu kawai yadaga masa tare da amsa gsisuwar nasa,samun daya daga cikin plastic chair's din yayi ya zauna ya shiga daddana waya hankalina sa kwance,duk su biyun sunyi matukar takura.Ana haka ne kuma Mommy tashigo bakinta dauke da sallama,batare da tajira amsawar su cikin tsananin farin ciki tace"Ah Son kashigo hospital din kenan? duban ta yayi yace"Ea wallahi Mommy,gud morning!yashiga gaisheta,amsawa tayi tana tambynsa amarya batare daya amsa ba yake sanar da ita dama Abba ne yace yazo ya daukeso don sunyi magana da Dr Ahmad anbada sallama. Mommy tace"Kai Alhamdulillah naji dadi maida duban ta tayi ga Zuhra tace"daughter tashi mutafi me zamu zauna jira kum?wallahi sam zaman hospital badadi son komai kyansa,tanayi tana hada kayansu,shima Sauban din tayata yakeyi don ma basu da wani tarkace nan ya kwasa ya fita, Mommy tabi bayansa. Ajiyan zuciya suka sauke atare kamar hadin baki dubanta yayi yace"Allah yakara Miki lafiya my Zuhra bari nazo na wuce bacin anzo daukan ku dani zan kaiki har parloun Ummie,yayi maganar cike da barkwanci,murmushi tayi tace"ya Shuraim kenan ko yanzu idan kanaso sai nashiga motan ka kamaida ni gida"dariya sosai Shuraim yayi yace"rufa min asiri mudaije ga babban Yaya kinsan sune masu bani auren ki so don haka sai da biyayya fa,suna tafe suna hira a hankali take tafiya don dama ko ada can Zuhra yanayin tafiyar ta kace tana yanga bare yanzu da ba wani lafiyan gareta isassa ba. A cikin mota kuwa Shuraim ya cika yayi fam kiris yake jira yafita yaje yaci musu mutumci daga ita harshi,sai kuma ya hango fitowan su ta mirror inda suke sakin ma juna murmushi,runtse ido yayi da sauri,bata wani jima ba tabude bayan motan kusa da Mommy da niyyar shiga,cikin kakkausan murya suka jiyo muryan sa"waye driver dinki?Saboda rashin kunya Mommy na baya kema sai kishiga baya Saboda kin raina ni?batare da tayi magana ba tanufi gaban ta bude tashiga ta zauna,tayar da motan yayi yafiga kamar zai daki motan Shuraim,cikin tsarewan Allah dai suka isa gida lafiya, Mommy ce tafara bude motan tafita,itama Zuhra budewa tayi kokarin yi sai dai jitayi anfisgota,idanuwan sa sun kada sunyi jajawur tare da sake wani irin girma magana yafara cikin wani irin amo mai ban tsoro"kinaso kizama 'yar iska ko?tunda kika shiga University kikejin kanki watace ko?haka kikaga su Laila nayi?yayi maganar yana daka mata tsawa,jikinta na wani irin kyarma hawaye na zubo mata takasa magana,cigabawa yayi"uban me kuke a daki daga ke sai shi?nema kike ki bata mana sunan family?sosai maganar sa ya bata mata rai da yimata zafi shiyasa hawayen ta suka kasa tsayawa."Bari kiji as from today nasake ganin dan iskan yaron nan tare dake saina wulakanta ki a gabansa shima na wulakanta shi,mtsewww Idiot! Get out of my car!! Yayi maganar cikin daka tsawa,jikinta na bala'in rawa tafita daga motan da gudu tana toshe baki Saboda wani mahaukacin kuka data saki,a dai-dai wannan lokacin kuma su Daddy sun fito tare dasu Ammi,ko kallon su batayi ba saboda kukan daya ci karfin ta tanufi sashen Bodejo,duk da kallo suka bita har ta kule,maida duban su sukayi ga Sauban daya bude murfin mota ya fito face dinsa babu walwala. Xahratty CE🥰 Lallai Alqalami 🖊️ yafi takobi🗡️ [6/20, 22:09] Xahratty (OUM AJMAL): 👨🏽‍🦳 *_GALADIMA FAMILY_*👨🏽‍🦳 Story&Written By *FATEEMA ZAHRA LAWAL* Marubuciyar⤵️ A DALILIN'YAR TSINTUWA. MIJIN ZAHRA. DIAMOND LADIES ( Daukar fansa)paid book. RUHIN AMRITA (FATALWA CE). Now *_GALADIMA FAMILY_* 𝑷𝒂𝒈𝒆 53/54 _____Ammi ce tayi saurin isa gabansa face dinta babu walwala ta fara magana"me Kuma kayi mata daga dawowan ta?yanzu fa aka sallamo ta daga asibiti,haba son wai meyasa kake haka ne? Dukar da kai yayi cikin takaici yace"Sweatheart ni babu abinda nama yarinyar nan shagwaba ce kawai tayi mata yawa kuma zanyi maganin ta ne,kawai daga na fada mata gaskiya akan wancan yaron shine tafita tana koken banza?to kuma ji dakyau ku sani aure take so! Yakarisa maganar yana raba Ammi ya wuce,binshi da kallo tayi,wajen su Daddy ya isa tare da kamewa, Daddy face dinsa babu walwala shima ya rufeshi da fada sai dai wannan karan sam be tanka ba haka kawai yakejin wani irin takaici da bakin ciki a ransa yace _lallaima mutanen nan ba da bakinsu sukace itadin matata ce amma ace kada nayi kishi,zanyi maganinta._ Hakuri ya rissina yabasu sannan yajuya yabar gidan kaitsaye gidan sa ya nufa tundaga gate kakejin sautin kida tmna tshi daga apartment din Akeela,dogon tsaki yaja kaitsaye sashen sa ya nufa, Akeela kuwa sarai ta hango sanda yashigo don haka cikin sauri ta kikkintsa jikinta,tashirya cikin wasu damammun English wears riga da wando wadanda suka fito mata da ainahin halittar ta sam Akeela bata diri ko shape face nono,nonuwa ne kamar guga kunsan dai yanda nono masu yawa kema siririn mutum to haka ne itama Akeela,da kwarkwasa tashiga apartment din,sosai ta rude da ganin tsaruwar sashin nata,ita kanta tasan lallai ba komai akasa mata ba face kayan dakin me aikin Sauban domin sashen sa iyaka ne,zaune ta hangosa a gefe yana daddanna laptop Bluetooth a kunnen shi yana magana,tunda yashigo yaganta kallo daya yamata ya kauda kansa,yanajin sanda take isowa garesa,batare da tajira komai ba tazauna a gefensa,kwankwason su na gogan na juna,cikin muryan bariki da kissa tafara magana"kai horney meyafaru ne jiya?inata jiranka amma shiru baka shigo har nagaji nayi bacci,wat's happening? Sauban idan kintanka ya tanka don zaki rantse da Allah badashi ake mgn ba,bata face Akeela tayi tana kokarin kai hannunta jikinsa cikin muryan tsawa yace"don't touch me! Cikin gigita Akeela ke dubansa tana jin wasu hawaye suna neman kufce mata,hankalin ta yayi kololuwan tashi sake langabar dakai tayi tana duban sa akaro na biyu tace"Naroke ka da Allah horney ka daukeni a matsayin matarka,yakamata ka kwantar dakai mufaranta ma junan mu musan cewa lallai munyi aure koba komai mukasance masu biyayya ga iyayen mu"wani banzan kallo ya watsa mata mai cike da ma'anoni da dama,mikewa yayi yana duban ta face dinnan babu almamun wasa yace"please zaki iya fita inaso nashiga na watsa ruwa ne,cikin marairaice face ta mike tana me nufan toilet din tana magana"honey wannan ai aikina ne ba naka ba don Allah kabarni nasamu lada a gidan aure na"yakarisa magana tana shiga toilet din don hada masa ruwan wanka,sosai yake mamakin karfin hali da budewan Ido na yarinyar yarasa dalilin da yasa sam bata tsoron shi,wata zuciyar tace _Aibata yarda ta hada ido dakai balle takarance yanayinka._ Zama yayi zuwa can babu jimawa tafito jikinta har rawan farin ciki yakeyi ta nufosa tace"honey gashi can na hada ma,mikewa Sauban yayi batare da yayi magana ba yanufi toilet din,muryan ta yajiyo tana cewa"ko nazo na temaka maka ne honey?cikin sauri ya murza ma kofan key,kanshi nasake daurewa da bude idon yarinyar,kafin yafito tabude closet dinsa tafito masa da kayan da zaisa. Yadan Jima a toilet din kana yafito,waist dinshi daure da towel bata dakin cikin jin dadi ya sauke wata ajiyar zuciya,kofan bedroom din yanufa ya sanya key yarufe,gaban mirror yadawo yafara shiryawa,yanajin sanda take knocking yayi mata banza sai da yagama shirya ko kallon kayan da tafito masa dashi baiyi ba yabude yaciro wasu kayan ya shirya yayi matukar kyau,sosai kwarjinin sa da zatin sa suka sake bayyana,cikin takun sa na isa yafito.Kallo daya Akeela ta masa tasake rikicewa don tabbas ya hadu iya haduwa sai dai ganin face dinsa da tayi yasa tadan shiga taitayin sa,dubanshi tayi tace"ga lunch can an aiko dashi"batare daya dubeta ba yace"zanje masallaci daga can zanshiga cikin gida nayi acan,wani kululin bakin ciki taji yazo mata makoshi ya tokare cikin yanayi nanuna rashin jindadi tace"nikam gaskiya banajin dadin abinda kakemin don Allah idan bazaka iya zama dani ba ka sawwake mun yanzu natafi niba makiyiyar ka bace face masoyiyar ka don haka bazan tilasta maka saika so niba"takarisa maganar cikin muryan kuka sosai takashe masa jiki sai dai duk kwakwan ka bazaka fahimci haka,sam baya fatan abinda zai bata ran iyayen nasa kwana biyu da aure ace amarya tayi yaji,danne zuciyan sa yayi batare da yayi magana ba kaitsaye taga ya nufi kofan barin parloun,maganar sa tajiyo"idan nafito zandawo nayi lunch din"yana gama fadar haka yafita,wani murmushi Akeela tasaki a fili tace"Sauban nida kai dan halas kafasa lallai kuwa nagano lagon ka Wallahi koda bala'i sai ka soni,cikin farin ciki tanufi dining din,wasu pills ta balle a satchet nasu tacire guda biyu tazuba a cikin lemon Fairless ta girgiza sosai sannan tasake tamke murfin,ranta fal nishadi,batare da maganar sallah ba tasamu waje tazauna. Yadauki tsawon 35 mnt sannan yadawo,cike da kissa ta tarbesa kaitsaye dinning din yanufa,cikin bariki tafara serving dinsa,tuwon shinkafa ne miyan zogale sai farfesun kayan ciki,nan ta gabatar mai da komai itama ta zauna tafara cin abincin,cikin natsuwa yakecin abincin nashi yanayi yana sipping juice din,har ya kammala ya mike tare da daukan ragowar juice dinsa yakoma parloun sa yazauna,wani nishadi Akeela takeji donji take kaman ammata wani gagarumin kyauta,bayan kamar 5 minute Sauban yaji wani bakon al'amari duk da ada yana fama da matsalar sai dai yadan dade baitaso mishi ba,dannewa yaci gaba dayi,dai-dai lokacin Akeela takariso wajen tana zama agefenta jikinsu na gogan na juna hannunta tasa tasaqalo ta wuyansa,sosai Sauban yasake tsare gidan sa duk da wani mahaukacin feeling da takejin yana taso masa but haka yaketa dannewa,cikin tsananin shedanci Akeela tafara yimishi wasu shirmen hira tana shasshafa jikinsa.Sauban kuwa banda zufa babu abinda yakeyi sosai yake kokarin danne matsalar sa,mikewa yayi yana dan matsar da Akeela sai dai kokafin yayi magana yaji hannunta a federal government dinsa🙈wani rintse ido yayi yanajin wani takaicin ta agefe kuma ga azaba daya ishesa,juyowa yayi cike da niyyar yimata tijara,sai dai arban da yayi da maka-makan gugunanta yasa ya daskare a tsaye🏃🏾‍♀️🏃🏾‍♀️🏃🏽‍♀️sai dai duk yanda yaso yayi kokarin control din kansa kasawa yayi don yakai limit dinda shikansa bazai iya controlling kansa ba,su Akeela ansamu abinda akeso nanfa tafara aikama da ya Sauban wasu manyan sako,tun yana basarwa kai hardai yabada kai bori yahau,sosai suka fara al'amuran su batare dashi kansa Sauban din yana gane halin da yake ciki ba duk da a kasan ransa ba hakan yaso ba amma bayajin zai iya wasa da damanshi,a haka Allah yatemakesa yasamu natsuwa da Akeela batare da wani abu yashiga tsakaninsa da ita ba duk kuwa yanda taso wani abu yafaru yakiya,kuka tasanya masa tana cewa tunda shi yasamu ya faranta ma ransa ai dole ita ya maidata ko oho,cikin takaicinta ya dafe kai don gabadaya yagama fahimtar Anya yarinyar ba 'yar hannu bace?duba da wasu dabi'unta,ganin tagaza yin shiru cikin karfin hali yafara magana"Niba jahili bane inason na gudanar da Daren farkona wajen nuna godiya ga mahallicina,sannan mubi dokokin da aka sanar Mana a addinance,buyi sallah na nuna godiyan mu ga Allah ba sai mufara wani Abu?I can't! Yana gama fadar hakan yanufi bedroom dinsa kaitsaye toilet yafada, Akeela kuwa cij yatsa tayi a fili tace"Allah yakai damo ga harawa,yanda ka tayarmin da hankali nima dole nasamu me biyamin bukata bari nanemi Suby,takarisa maganar tana me mikewa tafita daga apertment din. Wanka Sauban yayi cikin dan natsuwan da ya samu shiryawa yayi cikin kananun kaya marasa nauyi yanufi gidan su,tundaga shigowan shi ya hangosu zaune akan plastic chair sai hira sukeyi cikin nishadi,hada Ido tayi dashi gsbanta yayi wani mummunan fadi,batare da komai ba yawuce ko sake dubansu beyiba,wani boyayyen ajiyan zuciya zuhra tasaki tana godiya ga Allah. ***** A KADUNA kuwa abubuwa sun fara cakude ma Adda zainab yanzu hk zaune take suna tattaunawa da aminiyar ta,cikin wani irin damuwa take magana"Wallahi bansan yanda zanyi ba aminiya,damuwa yamin yawa Alhaji tun dawowan shi da kwana biyu ya sauya nagaza gane kansa,Wai sai rannan na kamashi yana waya da mace harma da maganar wai yatura manyansa,hauka ne kawai banyi ba,ni Alhaji iliyasu zai tozarta? wallahi da naga Alhaji da wata mace gwara naga motuwar sa kowa ma yahuta"tayi maganar tana cire dankwalin ta ta ajiye a side, hajiya Aliya tace"hmmm namiji kenan su totally nasu abin kunya baya musu wahala bacin haka ina Alhaji iliyasu ina wani sure?Koda kinsan wani me budurwan zuciya ce,kuma kada kiyi mamaki yaje yadauko Miki budurwa.....batare da takai aya ba Adda zainab ta mulmulo wani ashar! "Tabbas da itama saina kasheta aminiyata kinema min mafita kada na hadiye zuciya na mutu wallahi bazan iya ganin Alhaji da wata mace ba,lokacin da nasha wahala na kafin yayi kudin wayasani?sai yanzu da yayi arziki ne yakeda muhimmanci?don Allah munje wajen boka hatsabibi"takarasa maganar tana tagumi da sakin wasu wahayen bakin ciki. Hajiya Aliya kuwa a ranta murmushi takeyi kawai najin dadi domin tabbas tasan idan tashiga gidan Alhaji iliyasu kashin hajiya zainab ya bushe don alkawari tadauka sai ta wulakanta ta,sai ta tozarta ta,gyaran murya tayi tafara magana"Kinga sai dai nakirashi a waya duk yanda mukayi dashi zan sanar dake amma Kisha kurumin ki muddin kinatare dani kindena zubda hawaye,me akayi akai kishiya aminiya?meyasa kike zubda hawayen ki a banza? Adda zainab dai takasa magana sai hmmm da hmmm take cewa, abubuwa sun taru sun mata yawa ga rashin samin nasara akan kanwarta bilkisou yanzu kuma ga matsalar miji ta kunno kai,sai dai taji dadi da sassaucin kalaman aminiyar tata sosai. **** Amare kuwa zama yayi dadi a gidajen biyu Mashahuda da muneefa amarcin su suke ci da tsinke ana zuba soyayya,Akeela kuwa Suby tadawo tatare a gidan tareda da wata yarinya sabuwan hannu suke biyawa Akeela bukatan ta,duk abinda ke faruwa shikam baisani ba,don shi yama fara shirye²n komawa nanda 5 day's,shedanci da kazantar da akeyi a gidan Sauban ya tsananta wanda ba kowane yasani ba,domin kuwa madigo babban bala'i ce a doron kasa don har su hjy daharatu Suma zuwa sukeyi, akwai wata rana da sukazo sun gama iskancin su duk suna zaune a parlour sukaji karar door bell,lekawa Suby tayi da sauri tadawo take sanar da Akeela Guggo Laure ce,kikkimtsawa suka sakeyi sannan akaje aka bude mata kofar,tunda taga bakin fuska a gidan tafara harhada rai fuskan ta babu wani cikakken annuri,gaisheta suka fara sai dai dakyar take amsa musu,ganin haka yasa suka tattara yanasu yanasu suka bar gidan,koda suka watse cike da masifa Guggo Laure tafara magana"Ashe Akeela har yanzu bakiyi hankali ba?har yanzu bakidena tara wadannnan tambadaddun yaran ba?wai nikam sai yaushe ne zakiyi hankali?wallahi kikiyaye wadannan yaran,daga ganin idanunsu a soye gogaggun 'yan iska nefa.A raina nace _hajiya Guggo Laure kenan ita Akeelan bakiga gogewan nata ba saina yaran wasu kike hangowa?_ bata fuska Akeela tayi batare da tayi magana ba don tasan yanzu tadinga naci kenan,can dai tace"Guggo zan kiyaye don Allah kibar maganar haka"katseta tayi cikin fada"bazan bar maganar ba aikece kikajawo tun yaushe nake rabaki da wadannan yaran amma bakijin magana?harda wadanda sunma haifeki amma kince a makarnat kuka hadu,wallahi zan gayawa mansir dinner tunda ke bakijin magana,ni don Allah tashi kisama min abin Kari me kyau da soyayyen kwai guda bakawai"tayi magana tana gyara zamanta a kujerar,mikewa Akeela tayi tana mejin haushin zuwan nata a dai-dai wannan lokacin,don harga Allah batason ba don bawai ta gamsu bane,da alama kuma Guggo Laure yini zatayi.Bata wani Jima ba tahado mata lafiyayyen breakfast. A dai-dai lokacin da su hajiya daharatu suka fito a lokacin ne kuma sauban yafito daga sashen sa don raka wasu bakinsa,ganin shi yasa duk suka gigice don kwarjinin sa da kyansa na tafiya da 'yàn mata da dama,jikinsu na rawa suka shiga gaisheshi shida abokansa,abokan duk sun amsa amma shi ko tankawa beyi ba illa nazarin su day yashiga yi ganin sam ba mutanen arziki bane,sai dai yaso yagane Suby,cikin sauri suka bar gidan. Shima raka abokan nasa yayi koda yadawo apartment din sa yawuce dai dai nan kuma wayansa tayi kara alamun message yashigo,bayan ya zauna ne yajawo 💻 dinsa har zai bude sai kuma yatuna abu yashigo dazu don haka yabude wayan,kaitsaye ta wahtsapp yaga notification din tunda always data a kunne ne,shiga yayi still da number da akaturo masa messag3 din kwanaki still dashi aka turo wannan kuma duk video's ne,shiga cikin profile din yayi,ko bude pics din dake DP din beyi ba,gani yayi an rubuta....batare da yabi takan komai ba yaja tsaki,jawo laptop dinsa yayi ya kunna don sunada meeting da ma'aikatan company nasu shi ta video call zaiyi don an bashi hutun amarci gashi saura 5 day's yakoma. Xahratty CE🥰 Lallai Alqalami 🖊️ yafi takobi🗡️. 20/6/23. [6/24, 17:31] Xahratty (OUM AJMAL): 👨🏽‍🦳 *_GALADIMA FAMILY_*👨🏽‍🦳 Story&Written By *FATEEMA ZAHRA LAWAL* Marubuciyar⤵️ A DALILIN'YAR TSINTUWA. MIJIN ZAHRA. DIAMOND LADIES ( Daukar fansa)paid book. RUHIN AMRITA (FATALWA CE). Now *_GALADIMA FAMILY_* Page 55/56 ______Zaune suke cike da so da kaunar juna suke hirarsu cikin kwanciyar hankali da jin dadi,zaune suke akan plastic chairs kamar dai yanda suka saba,bude gate din security sukayi anan motoci biyu suka kunno kai cikin gidan,motar gaba ta Daddy ce ta biyu kuma kirar Benz ta ya Sauban, ZUHRA jitayi kirjinta ya shiga dakan lugude don wannan shine rana ta farko dasu Daddy zasu kamata a irin wannan yanayin,sannan tabbas tasan dokan gidan,balle murfin motar sukayi suka fito Daddy da Baba Hasheem tun daga nesa idanuwan su Daddy ke kansu,shikuwa Sauban kallo daya ya musu ya kauda kai,ganin sun kawo kusa dasu tunda dai-dai apartment din Ammi dama suke zama cikin sauri zuhra ta nufesu, cikin girmamawa tafara magana"Daddy sannu da zuwa, Baba sannu da zuwa"amsawa sukayi duk cikan su suna duban Shuraim wanda yake karisowa,cikin girmamawa Shuraim ya duka ya shiga gaishe dasu Daddy,face dinsu Daddy kadaran kadahan suka amsa,zuwa can shiru yaratsa wajen,dubanshi Daddy yayi yace"gashi kuma bamu gane ba malam daga ina kake?dan sosa kai Shuraim yayi yafara inda² saboda ganin da yayi zuhra ta koma tsumu-tsumu. Baba Hasheem da yaga gane duk abinda suke 6oyewa da yanayin zuhra yace"tambayar ka ake daga ina kayi shiru?yayi maganar cikin dan hassala,cikin sauri Shuraim yace"Dama wajen zuhra nazo hira"Baba Hashim yace"Hira kamar Yaya?Shuraim yace"dama nida zuhra son juna muke kuma nida niyyar aure nake son ta bada wasa ba.Shiru duk sukayi suna zubanya mishi na mujiya,ita kuwa zuhra banda rawa babu abinda jikinta keyi don tabbas tasan idan ba'ayi wasa ba to tata takare yau. "Bakasan tana da iyaye bane da bakazo kanemi izinin su ba kafin kafara zuwa wajen ta? Baba Hasheem yayi ma Shuraim tambayar face dinsa babu alamun wasa ko kadan,shikan shi Shuraim yasha jinin jikinsa musamman da Baba Hasheem,cikin sauri yace"Nasani Baba,sai dai nayi kokarin zuwa sai.....yayi shiru batare da yakarisa ba,"Baba Hashim yace"sai kuma baka zoba?maida duban sa yayi ga zuhra yace"kin kyauta tunda kece keda iko da kanki? yanzu har kinyi girman da zaki kira saurayi yazo zance gidan ku batare da kingama makaranta ba?batare da annemi izinin iyayen ki ba?shiru zuhra tayi jikinta babu inda baya rawa. Cikin daka tsawa dayasa Ammi dasu Laila fitowa yace"Ba magana nake miki ba kike girgiza min kai kamar kadangaruwa? Cikin muryan kuka zuhra tace"don Allah Baba kuyahakuri"girgiza kai kawai Daddy yayi sannan yayi gaba, Baba Hasheem yace"kin kyauta domin duk abinda yafaru kece sila,kenan a school dinma samari kike kulawa ba karatu kikeyi ba kenan?da sauri zuhra tadago tana girgiza kanta hawaye na mata zarya. Batare da yasake magana ba ya wuce, Sauban ma bin bayansa yayi,zuhra kuwa atake anan ta duke tana me salkin wani irin kuka me ban tausayi domin bata kawo zuwan ranar nan kusa,shikan shi Shuraim hankalinsa ba karamin tashi yayi ba,duban ta yayi cike da tausayawa, Ammi ce takaraso wajen tana me kama zuhra suka nufi cikin apartment dinta,jikinsa yayi bala'in sanyi,a gefe daya kuma ga tausayin kawunan su,dama a waje yake parking motar shi,direct gate ya nufa ya fice daga gidan gabadaya. Haka dai takara sa yinin ranar tayi shi sukuku babu walwala ga tarin fargaba da ya hadu ya mata yawa don kuwa tabbas tanaji a jikinta shirun Daddy ba alheri bane. Bayan sallan isha'i zsune take a dinning sam abincin takasa ci tsakura wa kawai takeyi,sam bakinta babu apatite hakanan tarasa abinda ke mata dadi,Laila ce tashigo cikin sanyin jiki ta dubeta"Sis kitashi kije Daddy nakira wai suna parlour Galadima"jitayi kirjinta ya tsananta bugawa fargaban ta yakaru,ko kaffara bazatayi ba tabbas akanta ne za'ayi wannan zaman,mikewa tayi cikin sanyin jiki tana duban Laila idon ta na cikowa da ruwan hawaye,dafa kafadanta kawai Laila tayi tana mejin tausayin 'yar uwan tata. Cikin sanyin jiki ta yafa gyalin Egyptian gown din dake jikinta tanufi apartment din Bodejo,da sallama tashiga parlour,zaune suke Galadima, Bodejo, Daddy, Baba Hasheem, Ammi, Ummie, Mom sai kuma Sauban dake zaune gefen kafar Galadima ahankali takarisu parlour cikin sanyin jiki,wani irin kallo Ummie ke aika mata dashi don ita batasan meyafaru ba sai a bakin Mom takeji. Zama tayi akan hadadden carpet din wanda ya qawata parlour sosai,gaishesu tashiga yi cikin jam'i,cike da tsokana Galadima yace"feel free mana amaryas,sai kame² kikeyi ba?ai asirin ki ya tonu wato nema kike kimin Kishiya saboda kinga natsufa ko?to komin abinki ba'a canzawa tuwo suna"yakarasa maganar yana gyara zaman shade din fuskan sa, Bodejo tace"Hmmm ai kayi kagama ni me kishi dani sai ya shirya"duk dariya aka Sanya banda Sauban daketa daddana wayar,shiru ne ya gifta zuwa can Daddy yayi gyaran murya yana duban zuhra"mamana! Muryan zuhra na rawa tace"na'am Daddy, Daddy yace"kinsan zaman nan akan wa mukayi shi ba sai anyi dogon jawabi ba ko?daga kai zuhra tayi alamun Ea. Daddy yace"Masha Allah,tunda muke a gidannan tun kama daga kan Addojinki su Maryam babu wacce tataba kula wani saurayi kafin aure hatta su Mashahuda batare da anzo annemi izinin mu ba,kece ta farko da kika fara karya dokar gidan nan harki dinga kula wani saurayi ku kulla soyayya batare da duk munsani ba,bazan boye miki ba raina yayi mummunan 6aci domin kuwa hakan babban zunubi ne agareki. Shiru parlour ya dauka zuwa can ya cigaba"nema kike ki maida mu mutanen banza?a'ina har kika samu karfin gwiwwan haka?waye shi a'ina kuka hadu?jikin zuhra yasake sanyi muryan ta na rawa ta shiga basu labarin haduwar ta dashi tundaga farko har karshe,cikin muryan kuka tace"wallahi Daddy ba karya nakeyi ba ka tambayi Aunty Mashahuda da Aunty Safeena,domin dan uwan Ouncle Asheer ne,sosai tabawa su Daddy tausayi amma sukaki nuna mata hakan,cigaba da magana tayi"sannan yaso ya sameku nice na hanasa nace sai na gama school amma don Allah kuyahakuri bazan kara ba. "Hmmm abinda yasa muke hanaku kula da wasu mazan ba komai bane face gudun matsala,domin ke akanki hakan ne ke shirin faruwa dake domin akwai aure akanki"ai a gigice Ummie, Mom,zuhra ke duban Daddy, Ammi kuwa mamaki ne ya kashe ta,jikin ta babu inda baya rawa tamike tanaso tayi magana takasa saboda tashin hankalin da tashiga, Daddy ya cigaba da magana"Marigayi Sadeeq yabar mana wasiyyar idan yarasu yanaso ranar addu'an ukun shi a hada da auren ku,domin yace tun sanda aka haifeki da wannan kudurin a ransa,ranar da Sadeeq ya cika kwana uku da rasuwa a ranar aka daura auren ki da yayan ki Sauban!zuhra jitayi kanta na juya mata lokaci daya taji wata jiri na dibanta,wannan karan Mom ce ta zabura ta mike tsaye tana kokarin magana sukaji karar fadin mutum timmm!!! Gabadaya juyawa sukayi wajen inda sukaji karar faduwan,zuhra ce ta yanke jiki ta fadi a take anan, da wani azababben gudu Sauban yanufe ta yana me jawo ta ya rungume,duk cikan 'yan parlour zagayeta sukayi banda Galadima da Ummie da suke zaune, Ummie wani hawayen farin ciki ne ya shiga sirnano mata,tabbas abinda tadinga addu'an samu kenan tundaga sanda tadawo hayyacinta take fatan Sauban da zuhra su fahimci juna,sai dai rashin jituwar su ba karamin daga mata hankali yakeyi ba. Da sauri Ammi tabude fridge din dake nan parlour,bottle water medan sanyi ta dauko,balle murfin tayi tashiga tsiyaya ma Sauban a hannu,shikuma yana shafa mata haka sukayi har kusan sau biyu ana ukun ne taja ajiyar zuciya tana me sakin wani irin kuka,duk ajiyan zuciya suka sauke sannan suma suka koma suka zazzauna"zaunar da ita Sauban"cewar Baba Hasheem,zaunar da ita yayi sannan yana dan matsawa gefe cikin kamewa,rarrafawa tayi tana dafe kafar Daddy cikin muryan kuka gwanin ban tausayi tace"please...please Daddy don Allah kuyahakuri kada kubarni dashi bazan iya rayuwar aure da.....maganar ce tatsaya cak a dalilin marin da Ummie ta sauke mata,tana huci takai hannu zata sake mata wani marin cikin sauri Ammi ta tare,6acin rai kwance a fuskar ta tanuna ta"zuhra!maganar mahaifin ki kike nema ki butulce?yabar wasiyya kice ba haka ba?mekika sani ke?harkin san wani so ne ke?wallahi nasake jin kalmar nan abakinki saina miki bugun tsiya,mtsewww useless"tana kare fadan hakan tafice daga parlour,bakajin komai sai shasshekan kukan ta,shikan shi Sauban din sai yaji wani tausayin ta ya kamashi gabadaya. Cikin fusata Mom tamike tana duban kowa tace"tsakani da Allah ana rashin adalci a cikin family dinnan,ni nazata Aseef ne za'a bawa zuhra? maganar gaskiya nida 'yayana ba'a Mana adalci,domin kuwa ai wannan tsantsar rashin adalci ne,sai kace duk family din Sauban ne kadai da'? Anbashi Akeela ga kuma zuhra gaskiya....cikin bacin rai baban Hasheem yace"Rabi!! Kishiga hankalinki dani,waye sa'anki anan?itama Mom cikin bacin rai tace"ni iya gaskiya ta nake fada wallahi"tana gama fadan hakan tafice daga parlour tana 'yan kananun surutai. Daddy yace"koma mene duk abinda zakuyi kuyi babu me kwancen auren nan sai Allah,kutashi ku wuce"yayi maganar yana duban Sauban,cikin sauri zuhra tamike tariga fita,duk da kallon tausayawa suka bita,tafe take kawai tana hada hanya,jitayi tayi tuntu6e da wani interlock na gefen hanyar,gaba tayi zata tuntsira, Sauban dage bayanta cikin sauri yakarisa ya tarota tafada jikinsa, dai-dai kunnenta yace"Kidai kula Saboda wata can banziyar soyayyan ki kina neman kashe kanki a banza,to nina dakika ganni ba sonki nake ba domin kuwa amaryan matata tafimin ke"yana kare fadan hakan yasake ta tare da wucewa yabarta nan tsaye,wani kuka ne taji ya kufce mata tare da sake jin wani haushinsa da tsanar Akeela a ranta. Da kyar ta lallaba takai kanta sashen Ummie. Zuhra kuwa banda kuka babu abinda takeyi tarasa gabadaya meke mata dadi a rayuwar ta. Xahratty CE🥰 Lallai Alqalami 🖊️ yafi takobi🗡️ [6/24, 17:32] Xahratty (OUM AJMAL): 👨🏽‍🦳 *_GALADIMA FAMILY_*👨🏽‍🦳 Story&Written By *FATEEMA ZAHRA LAWAL* Marubuciyar⤵️ A DALILIN'YAR TSINTUWA. MIJIN ZAHRA. DIAMOND LADIES ( Daukar fansa)paid book. RUHIN AMRITA (FATALWA CE). Now *_GALADIMA FAMILY_* Page:- 57/58 _Bismillahir-rahmanir-raheem._ ______A gajiye ti6is ya isa yau ya isa sashen sa,koda yaje ya taradda kulolin abincin akan dinning dama da wata irin yunwa yashigo gidan kaitsaye dinning din yanufa,abinci yasaka jallop din spaghetti yaji busasshen kifi sai tashin kanshi da yakeyi,hadiye miyau yau duk da yasan Ammin shi ce tayi girkin,cikin nishadi yakecin abincin hakanan yakejin farin ciki da walwala,yana gaf da kammala cin abincin yaji sallamar ta,a makoshi ya amsa batare da ya dago ba,kariso wa tayi kaitsaye hannunta ta sakalo wuyansa tare da bashi Peck a kanshi cikin muryan jan hankali tace"welcome honey!hannu gawai ya daga mata Saboda kora lemon Fairless da yakeyi,wani killer smile tasaki,bada wani yawa yaci abincin ba Saboda shi dama ba ma'abocin cin abinci bane,ganin irin shigan da tayi bakaramin tashi hankalin sa yayi ba,ga kamshin body spray din da takeyi lokaci daya yanemi susu cewa, ganin hakan yasa Akeela tashiga yawo da hannunta zuwa ko ina na jikinsa tare da tsananin jin son kasancewa dashi,one time Sauban ya susuce,da kyar ya iya yakice kansa yadube ta"Tashi muje muyi sallah kikoma sashin ki kisanyo gown,cikin muryan shagwaba tace"Nifa honey nayi sallah kabari kawai"takarisa maganar tana dan langabar da kanta,tsinin bakinta na turowa,sai yaga tayi wani muni,kauda kansa side yayi muryan sa babu alamun wasa yace"wannan daban wancan daban,don haka ina sauraren ki,yana kare fadar haka ya mike ya haye stairs. Cikin tsananin farin ciki Akeela ta nufi apartment dinta,jitake dama kamar ta dannesa,wanka ta kumayi ta shirya sannan ta dauko wani dan turare a kwalba ta kalla tayi wani shu'umun murmushi,a fili tace"Guggo yau ga aikin turaren boka nan za'ayi,tayi maganar tana tuno abinda Guggo Laure tace mata _Kinga wannan turaren yana shafawa zaki mallakesa zeji babu abinda yakeso kamar sama da kasancewa tare dake,don haka kiyi shi kamar yannda boka yace!_ wani murmushi Akeela tayi sannan tasamu cottonwood ta dangwalo turaren sannan ta shafa a kasanta,tayi duk yanda Guggo tace mata,har zata fita sai taji wani irin firsari ya matseta,toilet din ta shiga tayi abinda zatayi tafito katsaye tanufi sashen nasa tare da long hijjab,koda ta isa tasame shi shirye tsaf?sanye yake da coffe din jallabiya yayi kyau ainun,ganinta yasa ya tada sallah,da sauri tabishi itama,koda suka idar kama kanta yayi yamusu addu'o'i da ganin yashiga yi mata tambayoyi akan ibadun ta da sauransu,kwarai ya shiga mamaki ganin baisamu amsar ko daya ba inbanda kame² da take masa,ganin da tayi yana mata wani irin kallo yasa ta latso wahayen karya,tare karyar da murya tace"Bazan iya baka amsa ba honey cuz na fahimci wannan ranar shine zai kasance first night dinmu,kuma ni tsoro nakeji"takarisa maganar cikin muryan kukan munafurci,sosai ya yarda da batun ta Saboda yanda lokaci daya ta koma. Jawota yayi yashiga lallashinta tare da shafa mata baya hakan yasa tayi luf a jikinsa,tun ana lallashi abin har ya zarce aka cire hijjab din.Ganin haka yasa Xahratty tattare alqalamin ta da littafinta waje daya tamike tafice tare da rufo musu bedroom din,sai da safe Sauban da Akeela. ******** Zuhra kuwa yanda taga Rana haka taga dare tana ganin miscalls din Shuraim but takasa picking Saboda kukan da takeyi,shikuwa ganin hakan da yayi sosai hankalin sa ya tashi don bai natsu da abinda yafaru dazu ba,yanaji a jikinsa tabbas da akwai matsala, sosai yanemi bacci yarasa,hakan yasa yajawo wayarsa yafara typing,text ya tura mata kan gobe yananan zuwa, Allah yasa lafiya,tana kwance tana ayyana irin mijin da aka aura mata,tabbas tasan ya Sauban ya hada duk abinda dole mace ta soshi but ita a nata bangaren su sonsa tarasa dalili,cikin kuka tace"nasan shima baya sona cuz yanada wacce yakeso shiyasa always he's happy"takarisa maganar cikin kuka,jitayi wayan ta tayi kara alamun notification a hankali takai hannu tajawo wayar ta bude da sauri Saboda sunan wanda tagani,ganin message dinsa da abinda yace yasa cikin muryan kuka tafara yimasa voice note"please kada kazo ya Shuraim ina cikin matsala, kawai addu'an ka ita nake bukata"tayi maganar tana me kecewa da kuka tare da kashe wayan gabadaya tana dunkule jikinta waje daya. A sanda yaji voice note dinta bakaramin gigicewa yayi ba,cikin saura yayi dialling number ta,sai dai jitayi ance switch off,nan ya cigaba da trying but kalma daya ake fada masa wato akashe,kama kansa yayi shima hawaye na silalo masa,cikin raunin murya yace"my zuhra wat's wrong with you?wat happing to you?yayi maganar yana sakin kuka ya cigaba da cewa"duk abinda yafara I know ninaja miki da nazo ,sosai yanemi natsuwa ya rasa tare da kosawa safiya tayi hankalinsa a tashe yake. _______ Adda Zainab hankalinta yayi kololuwar tashi jinda tayi wai kawar ta hajiya Aliya Alhaji zai aura,acan parlour sa tasame sa a gigice ba cikin natsuwar Saba,tasame sa yana waya da babban abokin sa,ganin yanayin ta yasa ya masa sallama da sauri yakashe wayar,idanuwan ta taf da hawaye ta karisu tana jefa idanuwan ta cikin nasa,cikin daga murya tafara magana"Alhaji da gaske ne abinda naji?da gaske ne hajiya Aliya aminiyata zaka aura?don Allah kayi magana,nace da gaske ne?tasake maganar cikin daga murya,hannu Alhaji iliyas ya nade a kirjinsa tare da kura mata idanuwa cikin natsuwa yafara magana"Kinga hajiya Zainab ki nutsu ki zauna muyi magana nidake na fahimta,ba tahaka ba"yayi maganar yana kamo ta,fusge jikinta tayi muryan ta na rawa tace"kasanar dani zargin da nakeyi gaskiya ne ko kuwa? Alhaji iliyasu yace"please mana hajiya have a sit! Cikin masifa Adda Zainab tace"ba zan zauna ba,saika answering question dina,if not.....tayi magana tana nuna masa yatsar ta tare da tsaida idanuwan sa akanta. "Hmmm! Hajiya magana ta gaskiya tabbas hakane hajiya Aliya zan aura! Menene don na aure ta?so nake zumuncin ku yakara karfi sannan ai ba haramun bane,ganin da nayi yanda kuke kaunar junan ku yasa na yanke wannan hukuncin,sannan dana auro miki bare ai gwara na gida"tunda yafara magana ta nemin jinta da ganin ta tarasa na wucij gadi, jitayi wani kululin abu yazo mata makoshi ya tokare,batasan sanda ta yanka ihu ba tazube anan parlour,a gigice Alhaji iliyasu yanufe ta. Hajiya Aliya kuwa a bangaren ta suna can sun sako Alhaji iliyasu gaba ita da boka hatsabibi kan duk abinda zaifaru bazai janye kudurinsa kan auren ba,don tana lure yau saura kwana uku daurin auren, katsaye tanufi gombe wajen yayar ta,kan bazata dawo ba sai lokacin tarewar ta tayi. Bangaren Adda Zainab kuwa sosai tashiga tashin hankali tayi kuka sosai ta tsinewa hajiya Aliya babu adadi,duk yaranta ukun na zaune suna sauraron ta babban danta namiji mesuna Ammar yace"don Allah mom kidena saka ma ranki damuwa, Daddy fa da alama auren nan yinsa babu fashi ko dazu yafada yace sai dai kisama ranki salama,karamar sa'an zuhra tace"ai wallahi momy Aliya taci amana kuma bamu yafe mata ba tarasa wanda zata aura sai Daddyn mu shine zata aura,ta biyun kuwa banda sauke ajiyan zuciya babu abinda takeyi tana rungume da bbyn ta,cikin muryan kuka Adda Zainab tace"nasani wallahi nasan Aliya ba hakanan tabar Alhaji ba,nasan halinta nasan abinda zata aikata,shedaniya ce. "Mom kenan sai yau ne kikasan da Aunty Aliya shedaniya ce?tun yaushe nake fada miki kinki yarda,aikinsan mugayen halayen ta tun ada,batare kuke aikata komai ba?sai yanzu data miki shine zaki dawo kifada haka akanta?takarisa maganar tana duban Adda Zainab,itadai shiru tayi ta cigaba dajan hawayen ta, Ammar ne yace"menene kike fada haka islaha?da wanne kiieso Mom taji?Yaya duk abinda nake fada nasani,itama Mom tasani kuma ita tagane karatun da nake nufi,wallahi akan Aunty Aliya har zaneni Mom ta ta6ayi daga nace ni zuciyata be kwanta da ita ba amma tarufe ido tamun duka tana cewa bazan raba zumuncin shekara da shekaru ba"ta ta6e baki sannan ta cigaba"kaga duk wani yake da faran² dinda nake ma Aunty Aliya?inayi ne don kawai Mom kartayi fushi dani don akanta zata iya komai. Kuka Adda Zainab tafashe dashi tace"please islaha kiyi shiru haka,banson jin ko sunanta wallahi sai nadau mummunan mataki akan cin amanar da tayi min"islaha tace"hmmm Mom kenan kidai bi komai a hankali,cikin 6acin rai Adda Zainab tace"naki nabi komai a hankalin don abu kaza naki,wai dame kikeso naji ne islaha? Ammar yace"gaskiyan ta ne Mom babu wanda beson yanda kuke tare ba,wallahi yanda kike son ta ko Aunty bilkisou bakiso haka,duk fa munsan komai Mom,kin fifita ta akan duk wani dan uwanki,kawai Allah ya kyauta aikin gama ya gama don gobe ne daurin auren"yana gama fadar haka yabar bedroom din. Kuka sosai Adda Zainab keyi,su dai su islaha suna zaune jugum² tare da tausayin uwar tasu. *** *GALADIMA FAMILY* *** Sauban dai yadanji sanyi a ransa jinda yama Akeela a matsayin budurwa sai dai ko kadan bayajin burbushin son,don ko irin tattalin nan da ake na mutum beyi ba da,sosai Akeela tasake jin wani irin son guy din ya ninku mata,sannan sosai ta yarda da cewa lallai tayi sa'a, lafiyayyen namijie ne wanda ko wace lafiyayyar mace take burin samu,lallai yasan sirrin sarrafa mace,sosai takejin ta cikin nishadi,bata farka ba sai wajen 11:16 bata sameshi a bedroom din ba,shikuwa yana mamakin yanda Akeela tazage tana masa abubuwa wadanda sam babu kunya a cikin su. Yana zaune tafito sanye da night gown,ganin sa yana daddana laptop yasa takariso a hankali tazauna kan rabin cinyar sa shafo gefen face dinsa tayi cikin muryan jan hankali tace"honey wallahi jiyan nan ka gajiyar nan dani don kawlai ni jaruma ce sam banda raki,da dai kamar bazaiyi magana ba sai zuwa can batare da yadubeta yace"sorry! Sosai Akeela taji dadi mikewa tayi da niyyar barin parlour,muryan shi tajiwo babu alamun wasa yace"A haka zaki fita saboda baki da hankali?juyowa tayi tapdubesa kamar bashi yayi maganar ba,cikin sanyin jiki tanufi bedroom dinsa,hijjab dinta ta dauka ta sanya sannan tafito tare da fita tabar apartment din,Suby ce takirata kan tanason zuwa,a take anan Akeela ta dakatar da ita kan cewa batanan yanzu zasu fita ita dashi,sallama sukayi dai-dai nan taja tsaki tace"yau nasamu babban nadau hutu ni kuma da komawa wannan harkan sai an kwana biyu. Acan gidan Galadima kuwa banda zazzaga ruwan rashin kunya babu abinda Mom keyi harta kaiga Baba Hasheem ya mareta tare da sanar da ita taje gida zai nemeta,sosai Mom ta gigita da wannan furucin nasa,sashin Galadima ta nufa cikin tashin hankali da kukan ta da komai. Duk hankalin mutanen gidan a ranar yatashi saboda yanda Baba hasheem ya rufe ido kan sai Mom ta tafi gida,sannan ya rantse da muddin bata tafi gida ba to saki ne zai biyo baya idan ta sake ko minti 20 ne,shi kanshi Daddy duk kokarin shi naganin ya shawo kan kanin nasa lamarin ya faskara,waya ya dauka yakira Abba tare da sanar dashi abinda ake ciki,inda yace yananan shigowa gobe da safe. Da kuka da komai Mom take sanar ma da hajiya Biba abinda yafaru,dogon tsaki hajiya Biba taja cikin fusata tace"wato ke ala dole ga 'yar bala'i ko?to wai ma rabi ina ruwanki da sha'anin gidan da har kika tsoma baki?koko ke kadaice mata a gidan? Mom tace"wallahi hajiya kaddara,ninaso ace Aseef ne ya aure Zuhra ba Sauban ba, saboda...sai kuma tasake karisawa,hajiya Biba tace"saboda ubanta nada kudi?wallahi Saboda haka ne yasa kikeson hada auren,rabi nasanki fa nasan halinki,nice nan na haifeki ba wani ba nasanki da bala'in son kudi to bari kiji koni da kika biyo akan wannan mummunan dabi'ar adace don kuwa yanzu nadaina na shiryu,Kinga Rammat? tayi magana tana nuna Rammat taccigaba"ina mata addu'ah kan Allah ya hadata da miji na gari me dan dai rufin asiri ko yaya ne wanda zai rikemin amanar ta domin Kinga nacire buri dason iyawa.Don haka shawarar da zanbaki kicanza hali rabi tun wuri in bahaka ba kinaji kina gani keda gidan GALADIMA family sai gani sai hange sannan kifadawa gidan wahala,a wannan marran,babu wanda bazaiso jininshi ya shiga gidan nan ba,duk akan maganar Aseef kika nemi kashe ma kanki aure,alhalin kinsan sa kinsan halayen sa wallahi Aseef ba kowa zaiso yabashi mata ba,a haka kamar mutumin arziki,kije ki bincika abinda yake aikatawa,kuma wallahi nida kaina zan sanar ma Taleeb komai kiji ma kisani,tana kare fadar hakn tajuya tashige bedroom dinta, Mom kuwa cike da nadama da danasani tafara laluban number Baba Hashim,sai dai ko dagawa ba yayi. Bayan sallar isha'i sai ga Ya Asher da Shuraim,kaitsaye sashen Daddy suka nufa don Daddy yasan da zuwar su a can suka cidda Sauban zaune,cikin girmamawa suka Isa parlour Daddy suna mika gaisuwa,duban Sauban ya Asher yayi yana me mika masa hannu yace"babban Yaya barka da dare,Ashe kana nanne?Sauban cikin kamewar sa yace"wallahi kuwa kwana biyu ya gida ya family? Asher yace"Alhamdulillah ya amarya?Sauban yace"amarya tana lafiya. Nan Shuraim shima yagaisa da Sauban,amsa masa Sauban yayi kamar wani abu baita6a faruwa ba. Kawo musu kayayyakin motsa baki akayi,duk da anyi-anyi suci amma sunki ci akan daga kan abincin ma suka fito, Daddy yace"Malam Asher abinda yasa na nemeka magana ce akan dan uwanka Malam Shuraim gashi!tare da mamana na wajen marigayi sadeeq,kasan alakar dake tsakanin su?Asher yace"Ea to Daddy kwanakin safeena ke fadamin,sannan take nuna min ai suna son junan su,sai nace to me ake jira basai magabata su shiga ba?sai take cemin ai sai ta gama degree dinta,sai nace to aje ko izinine a nema masa yasan anbashi saboda yanayin Shuraim ya nuna serious yake son ta,to nidai tundaga ranar bamu sake magana ba sai kuma dazu Shuraim yazo harda kukan shi. Bayan yakare magana Daddy yace"Malam Shuraim ya mana babban lefi a cikin family dinnan,wanda tunda muke ba'a ta6a mana makamancin sa ba,nafara kula yarinya kafin a nemi izini, ba don komai ba sai saboda gudun matsala"hakuri Asher da Shuraim suka shiga bawa Daddy. Daddy yace"No no no no aini everything will be gone cuz shine zamu bawa hakuri domin mamana akwai aure akanta.....ai wani irin zabura Shuraim yayi yamike tsaye,mouth dinsa yafara rawa,ko kafin yayi magana ruwan hawaye ya riga sirnano masa,kamar ba namiji ba. Xahratty CE🥰 Lallai Alqalami 🖊️ yafi takobi🗡️ [6/30, 07:41] Xahratty (OUM AJMAL): 👨🏽‍🦳 *_GALADIMA FAMILY_*👨🏽‍🦳 Page:- 59/60 ______Dukawa yayi da rarrafe yakariso wajen Daddy tare da kama kafansa cikin muryan kuka yace"please please Daddy help me I love her so much,I can't live without her don Allah kada ku rabani da Zuhra rasata babban asara ne a rayuwa ta da nakasu,tana da wasu qualities wanda ba kowa ya sani ba sai wanda yake zaune da ita,naroke ka kamin duk hukuncin da zaka yimin amma banda na rabani da ita"yakarisa maganar yana wani irin kuka mai tsanani,sosai yabawa duk wanda ke parlour tausayi banda Sauban don wani mugun jin haushin yaron yake jiyake kamar yatashi ya rufeshi da duka sai dai face dinsa yagaza nuna hakan,baka isa ka fahimci mode nasa ba. Daddy yace"kayahakuri Malam Shuraim nace maka da auren wani akanta, Daddy kamin alfarma kahadani da wanda ya auretan na rokesa.Kamashi Daddy yayi ya zaunar dashi domin kuwa yayi bala'in basa tausayi matuka"Kunga irin shi ko,kunga dalilin da yasa muke fighting akan kafin afara neman yara a nemi izini, Zuhra tana aure da yayan ta Sauban"da sauri Shuraim ya maida duban sa ga Sauban wanda shima shi yake kallo,haka ya rarrafa wajen shi yana me kama hannayen sa cikin kuka yace"please Yaya don Allah kabarmin zuhra,domin don ni akayi t.....baikarisa ba sukaji Sauban yace"you re very stupid?re you mad?matar auren kake cewa don kai akayi ta?nima inason ta!yes I love her!bude baki yayi zai sake magana amma sai yakasa kawai sai ya girgiza kanshi yafita daga parlour. Dafa kafadansa Daddy yayi yace"kayahakuri kaji ba'a aure akan aure,sai dai temako daya zan maka kaje kasamu natsuwa idan komai yawuce sai kazo ina son ganinka,kamashi Asher yayi yace"babu komai Daddy Allah yasa hakan shine mafi alkhairi,a'iya sanin da nayiwa su Daddy Shuraim da babu aure akanta Allah sai sun baka ita,gabadaya ko matsawa Shuraim yakasa a ransa kuwa fadi yake _Yanzu shikenan dama bashi ne yake da rabon mallakar zuhra ba?_ ganin da Daddy p yayi kamar ma yaron baya a hayyacinsa yasa ya kamasa ya mikar dashi da kanshi yarikeshi suka fito har parlour, Sauban na zaune a gefen Ammi,suma fitowa sukayi dai-dai lokacin ZUHRA sun shigo dasu Laila,idanuwan su ne suka shiga na juna,atake anan zuhra jikinta yadauki rawa,shikuwa Shuraim hawaye kawai yakeyi,cikin tsananin sauri hade da gudu zuhra ta juya tabar apartment din,kokarin binta Shuraim yakeyi sai dai rikon da ya Asher shima ya masa ya hanasa bintan. Duk wanda ke parlour sai da suka basu tausayi harta shikanshi Sauban din,daqyar Daddy ya lallabashi suka tafi a mota kuwa ko magana ya kasa lokaci daya zazza6i ya rufeshi,wajen 9:26 pm suka isa gidan su Shuraim din. ****** Sosai ciwo ya kwantar da Shuraim wanda sai da takai takawo ga anbashi gado,ya rame yayi baki inban da kuka babu abinda yakeyi, daga mahaifinsa har mahaifiyar sa da kannensa basu da natsuwa Saboda banda sumbatu babu abinda yakeyi. A bangaren Shuraim da Akeela kuwa sun dinke duk da ba wani zama yake suna hira ba sai dai yana kula da ita sosai tunda mutum ne mai yawan bukata, Akeela tun tanajin dadi idan akafara haryazo da kuka take kosawa a gama,son shi kuwa sake ninkuwa yayi a ranta,shirye²n tafiya yakeyi gobe da safe. Zaune suke shida Kareem a parlour sa suna kallon tashar aljazeera,duban shi Kareem yayi yace"Kai oga aini nashiga rudu dajin wannan labarin, gaskiya kai me sa'a ne don kuwa nima har ina shirin sulalowa nazo na kama kafa ta bangaren ka gudun kada wani yamin wuffff Ashe kadade dayin wuf din da ita?yayi magana yana sakin dariya,dan tsaki Sauban yaja yana kaima kafadun Kareem duka"kaifa matsalata da kai dan iska ne,nima bansan meke faruwa ba sai randa aka kaita hospital din nan,don su Daddy dagewa sukayi kan dole wai nice zan kwana da ita,aiko hakanan na kwana da ita,to sai akan wannan yaron shine sanadin da magana mafa ta fasu"yakarisa maganar yana picking call,magana akayi masa ta can bangaren,amsawa yayi da "okay gani nan zuwa Daddy, hanging call din yayi yana duban Kareem yace"Daddy na kirana tashi muje. Mikewa sukayi suka bar gidan gabadaya kaitsaye cikin GALADIMA house suka nufa,da yake Abba ya iso shida Mommy. Bayan sun hadu yagaishe da iyayen nasa nan Abba yake cemasa ya maganar tarewar na zuhra?domin shi bayason abinda zaisa ayita jan magana ana sake tada fitina,cikin girmamawa Shuraim yace"Abba ai tarewar nan ba yanzu ba,a bari komai yasake warwarewa tukuna,dan dariya Abba yayi yace"shikenan,mommynku ma kiri² tace ba yanzu zata tare ba da ita da Ammin ku,dariya Shuraim yayi yace"Abba ai gaskiyan su ne, Abba yace"To Masha Allah! Allah ya tabbatar da alkhairi,muzamu je gidansu Rabi tukuna",duban Kareem yayi yace"Muhammad Kareem kai ya maganar naka auren ne?naji shiru ya kamata kafin tarewar abokin ka kafito da mata idan kuma ba haka ba zan nema maka fulanin ruga",Kareem yace"Insha Allah Abba munkusa asamu a addu'ah kafin dai oga ya tare da.....shiru yayi yakasa karisawa,dariya sosai Abba yayi da yake shi din mutum ne mai barkwanci sai dai duk cikinsu yafisu fada sosai. ****** Mommy sosai tashiga bawa zuhra baki tana lallashinta,cikin muryan kuka zuhra tace"Mommy ya Shuraim ance yana kwance a asibiti anbashi gado,meyasa ba'a yima kowa auren dole ba sai ni?ko wacce fa ita takawo wanda takeso to taya ni za'a ce dole sai ya......bige mata baki mommy tayi batare da tabari takai aya ba,cike da takaicin wautan ta tace"Wai don Allah zuhra yaushe ne zakiyi hankali?to bari kiji wannan tamkar kinaja da maganar Abbie ne,bari kiji abinda yace a ranar"Nan Mommy tasaka mata recording din, tabbas muryan abbien ta ne sanda yake barin wasiyyar auren ta dana ya Sauban,kuka sosai ta kece dashi cikin muryan kuka tace"tabbas Abbie zanbi maganar ka,zan amince da abinda kskeso, kayafemun Abbie"takarisa maganar tana kece wa da kuka tare da fadawa jikin toilet,sosai tabasu tausayi matuka gaya. Washegari ta kama Monday a ranar su Abba zasu koma domin tun jiya sun dawo da Mom tayi nadama matuka, Sauban shima ranar zai koma Canada,sosai Akeela tasa rigimar sai yaje da ita dadai taga sam hakan bamai yuwuwa bane sai ta hakura,zuhra kuwa a ranta tsattsaye take ta ciwon ta na rabuwa da masoyinta,abin sam babu dadi. Alhaji iliyasu ma a ranar aka daura aurenshi da hjy Aliya,hauka ne kawai Adda Zainab batayi ba amma hankalin kuwa sai da yatashi haka rayuka sun 6aci,don a ranar da hajiya Aliya zata tare sai Alhaji iliyasu yace ta dakata idan yadawo daga tafiyan da zauyi sa tare,cikin dibara kuwa Hajiya Aliya taja hankalin shi tafiyan nan da zaiyi to dole tare sukayi shi ita da shi, jirgin su yadaga sai kasar Argentina,duk wanda yaga Adda Zainab sai ya tausaya mata sosai. Rayuwa kenan a kwana antashi babu wuya yau gareka gobe ga wanin haka,yanzu gashi anci wata hudu da bikin amare, inda Shuraim ya sake gogewa a cikin Galadima family ya zama dan gida don sun hada kansu da Laila harda ranar aure inda itama da ta gama degree dinta sai biki,ta bangaren Nihal ma haka wani yaron kanwar Mommy dake aiki a cotonou shima yafito ansa rana,ta bangaren Rammat itama Kareem yafito kan tabbas shifa yake son ta,to su ansa rana don biki bairi sauran 2 months ba,sosai zuhra ta maida hankali akan karatun ta,gashi ta bangare guda tasake cika da wani irin kyau na daukar magana,don haka samari suka sanyo ta gaba domin kuwa muddun tafita sai anbiyo ta kuma manyan mutane haka ake sintirin zuwa neman aurenta.Sosai hankalin su ya tashi a dalilin hakan yasa suka nemi Sauban ya samu lokaci ya shigo musamman ma don iyalinsa da suke ganin kwana biyu mata suna suntiri a gidan nata. *** *KADUNA* *** Zaune take a leadeseat din dake parloun glass cup ne a hannunta fresh milk ne a ciki,idanunta sanye da medical glass,kafa daya akan daya ta dora tana cigaba da kallon ta,waya takeyi hankali kwanci tana dariya"wallahi Yaya kinganni nan jiyama muka dawo kasan da Alhaji ina tunanin nan da 2 weaks ma zamu sake barin kasar"saurara tayi don da alamu daga can bangaren magana ake mata,dariya ta kyalkyale dashi tana taunar chwengum tace"Ai Yaya bamu gama honeymoon ba kinga Alhaji mutum ne me son kulawa sam baya son gidadanci to shiyasa nake zagewa nake basa kula"magana aka mata tacan barin,dariya ta kuma saki tace"Ah to kinga lefina?ai yama fada yace yanzu ne yasan yayi aure"takarisa maganar tana duban wajen dinning din da Adda Zainab ke zaune tana cin abinci. Adda zainab tsaban takaici da 6acin rai kasa cin abinci tayi tana sauraran ta ga zuciyar ta da take lugude,cikin zafin rai saboda jin irin maganganun da hajiya Aliya keyi yasata mikewa a zafafe ta nufeta, dai-dai ita kuma ta aje wayar,tana isa tatsaya a gabanta cikin 6acin rai tafara magana"Hajiya Aliya tsakanina dake wallahi Allah ya isa,banta6a tunanin ke mayaudariya bace sai da kika aure mijina,ke maciyiya amana ce daga ke har boka hatsabibi bazan ta6a yafe muku ba domin nasan da saka hannun sa azzaluma kawai karuwa"tana gama fadar haka yajuya zuciyar ta na mata wani irin rawa,muryan hajiya Aliya tajiyo tana kyalkyale dariya tace"Hmm Aminiyata kenan kace babban maciyiya amana domin kece ke cin amanar 'yar uwarki,babu babban maciyiya amana kamar ki,kuma ki rubuta ki ajiye wallahi wallahi wannan sakon da kika bani tamkar a kunnen boka kika fada"dogon tsaki Adda Zainab tayi tace"ki sanar masa don ubanku ke dashi"tana kare fadar hakan tajuya ta haye stairs,daga murya Hajiya Aliya tayi tana dariya tace"Oho kishin banza mijine dai na mallakesa. Koda Adda Zainab tashiga daki a tsorace take hankalin ta yayi kololuwar tashi da wani tunani da ya fado mata rai akan kada hajiya Aliya ta tona mata asiri, tabbas tana nan akan bakanta na kin 'yar uwanta sannan tana son kauda ta a doron kasa,sosai takejin 6acin rai. A can maidugri kuwa da yake Ummie ta gama iddarta shirye-shiryen komawa kaduna takeyi sosai hankalin zuhra ya tashi tadinga rokonta kan tazauna anan amma taki da yake jirgi zata bi ,don su Laila sun dade da komawa saboda school,da Ammi da Mom ne zasu rakata sai yaseer da zuhra don ita ke driving din ma motar,sun rakata airport tayi duk abinda zatayi basu baro can dinba sai da sukaga jirgin su Mom yatashi sannan suka nufi gida cike da gajiya wajejen karfe 8:07pm. A haka rayuwa take ta tafiya bayan kwana biyar,adalilin rashin napep da ake fama dashi yasa ta tafara takawa a kasa, motocin da suka tsaya yimata lift sunkai amma zuhra taki sauraran su sai wani wanda a yanzu sai binta yake yana rokonta kan tazo ta hau sosai gayen ba lefe kyakkyawane nd gently daka kallesa kasan dan gidan manya,sai binta yake ana cikin hakan ne taga wata motar tasha gabanta a zafafe kirar Benz G wagon duk cikan su tsayawa sukayi batare da ya fito ba yayi zipping tinted window motar tare da bude front door,hada ido sukayi ita dashi duk dashi kallo daya ya mata amma ita takasa dena dubansa saboda abune biyu ne suka darsu mata a rai,na farko yasake zama wani arrogant and sexy boss kyansa kullum sake fitowa yake ga tsoron sa da kwarjinin sa daya darsu mata a zuciya,bata da wani za6i dole tanufi motar ta shiga,ganin hakan yasa gayen nan juyawa. A motar babu Wanda m yace da wani kanzil,itadai banda wasa da finger's dinta babu abinda takeyi, duk yana kallon ta ta wutsiyar ido,sosai ta masa kyau sannan yaji dadin ganinta da wannan gown din da be kama mata jiki ba sam nd tayi rolling mai kyau gunin sha'awa,ga wani cika da yaga takara da kyau,wani numfashi yaja saboda wani abu da yaji ya taso masa,zuwa can face dinsa babu alamun walwala yace"Da auren nawa akanki ne kike kula kulan samari?kinsan lefin hakan kuwa?"yakarisa maganar cikin rausayar da kai,sosai mamaki ya kamata wanda har yagaza 6oyuwa,gabadaya sakin baki tayi kamar wawuya tana dubansa saboda taji alamar mutumin nan yana son yayi mata sharri,sassauta face dinsa yayi yana dubanta,da sauri Zuhra takau da fuskanta cikin sanyin muryanta da wani dadi da ya kara tace"Ba haka bane yaya,niban kula kowa ba ko suma din naci sukeyi amma ban kulasu"takarisa maganar tana sunkuyar dakanta kasa. "Amma wannan gayen da alama da banzo ba kila da yayi nasara akanki don naganshi yana da masifar naci sam baya sassauta wa"tajiyo muryar sa yana fadar hakan,ajiyan zuciya ta sauke me karfi batare da tayi magana ba,shima be sake magana ba suka cigaba da tafiya,kaitsaye gate din gidan sa yanufa yana danna Horn,da sauri ta dubesa,shiko ko kallon ta beyi ba,babu jimawa akazo aka bude gate. Xahratty CE🥰 Lallai Alqalami 🖊️ yafi takobi🗡️. [7/2, 23:53] Xahratty (OUM AJMAL): 👨🏽‍🦳 *_GALADIMA FAMILY_*👨🏽‍🦳 Page:- 61/62 ______Gama parking yayi tare da fitowa babu abinda ke tashi a gidan sai karar kida na waqar Ado Gwanja mai taken "chass" sosai Sauban ransa ya 6aci kaitsaye apartment din Akeela ya shiga,da yake batasan da dawowan sa ba shiyasa,ransa yayi kololuwan 6aci ganin yanda mata manya wasu ma sunyi 'yar ciki da Akeelan amma haka suka tike sai rawa sukeyi suna rungume da junayen su,duk cikan su ba kayan arziqi bane a jikinsu.Ji sukayi sautin wakar ya tsaya cak,wata hajiya ce tafara jiyowa ganin Sauban yasa tayi mutuwar tsaye don ba karamin kyau yaron yayi mata,tabbas a haife ya haifeta,ganin irin kallon da take masa yasa cikin bala'i ya qanqantar da idanuwa,muryan Akeela ne yafara tashi"Oh honey barka,hope kadawo lafiya?tayi maganar tana nufarsa tare da kokarin fadawa jikinsa,cikin zafin nama ya tureta side,tare da kololuwan 6acin rai ya nunata tare da fara magana"kafin nadawo sashen nan,ki tattara min wadannan 'yan iskan kazaman su barmin gida,if not nadawo wallahi sai na rufe kofan parlourn na muku dukan mutuwa"yana kare fadar hakan yajuya kamar wani zaki,cikin 6acin rai ya isa sashen shi,kaitsaye bathroom ya isa ya sakin ma kansa shower yana sauke ajiyar zuciya,face dinsa a runtse,idanuwan ta yafara haskowa da yanda tasake wani cika da tsananin kyau,murmushi kawai yasaki,a gurguje yafito ya shirya cikin kananun kaya wadanda suka masa matukar kyau. Fita yayi, dai-dai lokacin su kuma matan wadanda sunkai biyar suka fice daga gidan,yana mamakin yanda Akeela ke tara masa mata a gida musamman wadanda ma sun haifeta sun juya sannan daka kallesu kasan shedanu ne,sam baya son tabbatar da zargin da yake akanta hakan yasa ya saki dogon tsaki, Galadima house ya nufa direct apartment din Bodejo ya isa yana waya da Taufeeq akan rashin lafiyar da Mashahuda keyi,sai tsiya Sauban yake masa wai ko ciki ne. Sam basu kula da juna ba saboda saurin da take taje sashen Mom,sanye take da wata gown wacce tadan bude gabadaya iya gwiwwa ta tsaya mata rigar,sai dai duk da haka be hada tudun saman ta bayyana ba,haka kuma be hana tudun bom bom dinta bayyana. Garam!karar bugewar su ta bayyana,da sauri zuhra tadan dafe goshinta tare da cewa"ouch! Matsawa gefe tayi da sauri saboda kallon da taga Sauban na mata sosai tasha jinin jikinta,sake hade rai yayi dama da ragowar 6acin ran da Akeela ta hada masa yake,cikin tsukakkiyar fuska yace"Ina zaki da wannan dressing din haka?in ina Zuhra tafara"dama..d...dama leqawa zanyi nadubo abu shine,cikin muryan tsawa yace"Dallah go back my friend,wallahi akan ire-iren wadannan banzayen dressing din da kike a gidan nan sai na baki mamaki,yayi maganar yana ra6ata ya wuce, Bodejo da fitowan ta kenan daga palour Galadima tace"To sarkin kwarwa kadawo kenan,yanzu kuma ba zata samu wani sakewa ba,haba jama'a wai meyasa duk idan kashigo da masifar fadan ka baka saukewa kan matarka sai ita? Sauban fuska a daure yace"to ai itama matar tawa ce Bodejo,idan ki kaga na mata fada itama lefi tayi, Bodejo tace"to sannu me mata ai saika cigaba. Mikewa yayi yanufi parlourn Galadima batare da yasake bin ta Bodejo ba. Bayan kwana biyu,gabadaya Zuhra time din kanta ma wahala yake mata cuz exam da suke ta shirye-shiryen farawa sam lokacin ta na karatu ne,sai dai kullum tana shiga kowane apartment da safe gaishesu,a bangaren Ammi kuwa sosai take samun kalawa,don sam Ammi bata dauke ta wata surika ba,sunyi kusan kwana biyu basu hadu dashi ba hakan ba karamin faranta mata rai yayi ba saboda ta fahimci a duk sa'in da zasu hadu sai ya nemi lefi ya liqamata ya hauta da fada,Yau ma kamar kullum da wuri suka gama Exam dalilin hakan yasa kawai ta nufi gidan muneefa,sosai Muneefa tayi murnan ganinta ta dade sosai a gidan sai bayan isha'i sannan Mus'ab yadauko ta yadawo da ita,bude motan tafito tana dan rissinawa tace"to Yaya Mus'ab nagode sosai Allah yabar zumunci, murmushi yayi yace"Ameen kanwar mu kicema rigimammiyar tsohuwan nan bazan samu leqowa ba amma ga wannan ki bata"yayi maganar yana miko mata wani leader bag me kyau sannan sukayi sallama yazuge tinted window dinshi yaja motar,cikin natsuwar ta tashiga gidan,harta gota first gate sai taji kamar ana binta a baya ko kafin tayi yunkurin juyowa taji anfisgota,a gigice ta bude baki da niyyar ihu sai dai jitayi andane bakin da yatsu,sosai taji wani azababben zafi, face dinsa ta kalla sosai ya canza jikinta ne yadauki wani irin rawa da tsuma,bakinsa har rawa yake tsaban masifar dake cinsa fuskar nan tayi jajawur,hadata da jikin gate din yayi,da karfi Zuhra ta rintse ido domin kuwa ta sadakar yau me kwatar ta sai Allah,muryan shi tajiyo cikin amo yana magana"Wancan wane dan iska ne ya ajeki a mota?Fateema da aure na a kanki kike kula wasu mazan?da aurena akanki kike cin amanata?wai halan kina mance ke din matar aure CE koh?yayi maganar cikin muryan tsawa yana me matse mata hannu gam kamar zai balla,wani irin kuka Zuhra ta saki jikinta kuwa banda tsuma babu abinda yakeyi"Am talking to you teemah!!!yayi maganar yana daka wani tsawa wanda yasa Ammi fitowa ita da Daddy don apartment dinsu tadan fi farko duk da kuwa tazarar su,cikin muryan kuka Zuhra tace"wallahi ba wani na kula ba kuma ba wani ne yakawo ni....bata karisa ba yace"To uban waye ya sauke ki a mota?karya zanmiki? "Kai Sauban lafiyan ka kalau kuwa?Wai menene kakeyi haka ne?sakin mata hannu kafin ranka yayi mummunar 6aci wallahi a gidannan"Ammi tayi maganar cikin 6acin rai,yakasa sakin ta saboda bala'in kishin da ke cinsa a ransa, Daddy yace"Wai bada kai ake magana ba?sakinta yayi Yana me kafa mata idanuwan sa da sukayi jawur,itakuwa kanta na kasa banda kuka babu abinda take rusawa. "Meke faruwa ne Sauban? Daddy yayi maganar yana karisowa cikin kamewa,itako zuhra kamata Ammi tayi tare da maidata gefenta,yanaso yayi magana yakasa saboda ruwan kwallan da ya taru masa a idanuwa,juyawa kawai yayi yanajin kansa na sara masa yafita daga gate din, Daddy bece masa komai ba don yaga yanayin mode dinsa,"kamata muje ciki muji meyafaru"kamata Ammi sukayi har parlour ta ajeta kan carpet duk suka zauna,nan Daddy yake tambayanta abinda ke faruwa"Wai saboda yaga an sauke ni a mota shine yashigo yafara fada"tayi maganar cikin sanyin murya, Daddy yace"wanene ya ajeki a motar? Zuhra tace"Yaya Mus'ab din Aunty Muneefa ne"Daddy yace"A'ina kuka hadu dashi har ya dauko ki?nan Zuhra tafara in ina alamun rashin gaskiya"da...dag...daga gidan su naje wajen Aunty Muneefa daga school na wuce"Daddy yace"okay to karfe nawa ya saukeki?zuhra tace"wajen 8:17 kayahakuri Daddy"Daddy yace"wakika tambaya? Zuhra cikin tsananin tashin hankali tace"Bodejo kawai tasani. Girgiza kai kawai Daddy yayi yace"tashi kije da safe zan nemeku kedashi"cikin muryan kuka Zuhra ta mike tafita,da kallon tausayi Ammi tabita tana takaicin abinda Sauban kema Zuhra,duban Daddy Ammi tayi zatayi magana,hannu yadaga mata tare da cewa"Hmmmmm!"dole Ammi taja bakinta ta tsuke. Duk da ya fita apartment din da 6acin rai amma hakan be hanashi soyewa da matarsa ba,duk da bawai wani dadi da gamsuwa yake ba amma haka yake hakuri don gudun fadawa halaka. ********** "A gaskiya Alhaji nagaji da rashin adalcin da ake gwadamin a gidannan kada fa kamanta nima fa matarka ce,akan me tunda kazo duk inda zaka sai da hajiya Aliya kake zuwa?dame tafini?kyau ko kuwa ilimin addini dana boko?dan murmushi Alhaji iliyasu yayi yana girgiza kafa tare da sipping coffee"Alhaji magana fa nake maka"Adda Zainab tayi maganar damuwa tattare da a face dinta,ajiye cup din Alhaji iliyasu yayi yana duban Adda Zainab"Bata fiki da komai hasalima ke kika fita dashi,amma fa kuma ada,domin kuwa a yanzu tafimin ke sau dubun dubata,kin manta ada lokacin da kika fifita ta akan kowa naki,hatta ni mijina?sai nace miki kizo muyi tafiya kiki,amma ita da zarar tamiki kike binta ki tafi?to bari kiji a yanzu Hajiya Aliya tafimin ke nesa ma ba kusa ba. Wani kuka Adda Zainab tasa tace"wallahi baka isa ba Alhaji,wallahi sai na illata hajiya Aliya sai na maidata abar kwatance"tana karisa fadar hakan tafita tana share hawaye tare da jin matsananaciyar Hajiya Aliya da Alhaji iliyasu a ranta,zuciyar ta sai ingizata takeyi akan wani kuduri nata. Shikuwa Alhaji iliyasu sam baiji dar ba hasalima waya yadauka yakira hajiya Aliya akan tagama shirinta su wuce. Sosai komai ya dagulewa Adda Zainab,gashi boka hatsabibi yadena sauraranta kwata-kwata hakan yasa tafara bin malamai akan dai sabauta Ummie don tadau alwashin sai ta sabauta ta tana ganin duk abinda yake faruwa a gidan ta ba komai bane kamar matsalar ta da Ummie ( _Kai jama'a hassada mugun ciwo,mu guji kanmu da hassada domin kuwa masifa ne,gadai Adda Zainab nan haka kawai babu abinda Ummie ta mata amma ta tsaneta sam bata son ko bude ido tayi taganta a doron kasa, Allah yasa mudace ya rabamu da ciwon hassada Ameen 🤲🏽 domin maganinsa nada matukar wahala_. ) Tarasa me zatayi burinta ya cika ganin da tayi dukiyoyin ta zai tafi a banza a wofi yasa tadawo bangaren kuma Hajiya Aliya,itadai islaha sosai yakema mahaifiyar tata nasiha sai dai da alamun kamar tayi nisa batajin kira domin a duk sa'ad da tamata fada ranar kwana take zaginta har ta waya take kiranta ta cimata mutumci,hakan be hana islaha yima mahaifiyar tata nasiha. Satin su Alhaji iliyasu uku suka dawo gida daga honeymoon din tare da murnar samun cikin Hajiya Aliya,bakaramin razana da gigita Adda Zainab tashiga ba domin har Suma tayi ta tayi tare da sumbatu,wanda hakan ya haifar mata da kwanciyar asibiti,hankalin yaranta yayi kololuwan tashi yayi,su Amma duk sunzo fada sosai Amma tayi mata akan wannan halin da tadauka tadorawa kanta, Ummie ma da Mommy da Mashahuda sunje,jin yanda Adda Zainab keta sumbatun Hajiya Aliya ta ci amanarta yasa duk jikinsu sanyi,sai dai ita a bangaren ta ba haka bane domin kuwa gani Ummie ba karamin wani tsanar ta takuma ji ba. ****** Sosai ta wahala da abortion din da tayi,dubara ce tafado musu,cikin sauri suka hanzarta komawa gida,inda Akeela tayi kace-kace da toilet da jini,a hanzarce su Hajiya dahara suka bar gidan,a cewar su yanda plan dinsu zai tafi yanda suke so,haka Akeela tayi faca² da jini,takun Sauban tafaraji yanufo bedroom din nata,nanfa ta juyar da idanuwa tafara nishe nishen karya,a hanzarce ya nufota yana me tallafota izuwa jikinsa,kuka tafashe dashi tace"honey nayi miscarriage ka kallo jinin dake fita daga jikina....ai da hanzari Sauban ya dauke yafice da ita,dawowan sa kenan daga Kiran da Daddy yamusu shida Zuhra,inda aka samata tsauraran dokoki. Kaitsaye hospital din su Dr Ahmad ya nufa da ita,temakon gaggawa suka shiga bata,anan Dr Ahmad ke tabbatar ma da Sauban cewa lallai Akeela tayi miscarriage din cike na 1months nd 6days, Sosai Sauban yaji zafin hakan sai dai yasama ransa haka Allah ya tsara. ******* Babban tashin hankalin da ya taru a gidan Alhaji iliyasu shine anga gawarsa shida amaryarsa wadanda aka saka mudu Poison a cikin cofeeeeeee Xahratty CE🥰 Lallai Alqalami 🖊️ yafi takobi🗡️. 👨🏽‍🦳 *_GALADIMA FAMILY_*👨🏽‍🦳 Page:- 63/64 ____Sosai tashin hankali ya bayyana a cikin wannan family din da rudu inda su islaha banda kuka babu abinda sukeyi jin yacce ake la'antar mahaifiyar su daga bakuna da dama,ita kanta Amma tasha zagi duk da batasan hawa ba batasan sauka ba, domin dai a sashen Adda Zainab aka ga kwalaben poison dinda aka kashe su hajiya Aliya gashi kuma an nemeta an rasa,anzuba jami'an tsaro kota ko'ina, Ummie kuka takeyi sosai hankalinta yayi kololuwar tashi wanda yayi sanadiyar da tafadi,hawan jini yayi mata mugun hawa,daga mutanen kadunan har maidugri babu kwanciyar hankali,su Daddy cikin tashin hankali tare da Sauban, Baba Hasheem, Ammi, Mom harda Zuhra suka nufo kaduna,sosai suka taradda tashin hankali domin kuwa har gidan Ummie 'yar uwan Alhaji iliyasu ke zuwa suna tada kayar baya,sai da su Daddy suka iso sannan akasa jami'an tsaro shine fa komai yazo da sauki, Ummie na kuka Amma ma tanayi, cikin muryan kuka Amma tace"mezesa ki aikata haka Zainab?wani irin zafin kishi ne dake haka?wallahi ba irin tarbiyyan da namiki bane domin ko mahaifiyar ki ba haka take ba munyi zaman lafiya da amana, innalillahi wa Inna ilaihirraji'un kin cucemu kin cuce yaranki kin cuce kanki,sai lallashin ta akeyi. Acan kuwa cin zarafin da dangin Alhaji iliyasu kema su islaha kamar ba jinin su ba yasa itada da kanwar ta gudu daga suka nufo gidan ummie,duk da yaune akayi rasuwar amma a yacce suke musu kamar zasu kashesu Suma. Kota ina bincike ake koda Allah zaisa aga Adda Zainab amma ina ba'a ganta ba har dare,wannan ahalin dai haka sukayi kwana bakin ciki sam basu rintsaba, washegari su Daddy suka wuce harda Zuhra cuz tana da Exam,sun bar sallahun duk abinda ake ciki ummie ta sanar dasu. Washegari haka suka shirya suka nufi gidan Alhaji iliyasu,tare da manya²n kuloli na abincin sadaka,sun ma maza 'yan waje gaisuwa don sosai yayyen Alhaji iliyasu maza da kannen su suka amsa cikin kulawa sai da suka shiga gidan ne gida ya hargitse domin har masu iskokai sai da suka tashi kan idan su Amma basu bar gidan ba sai sun kashesu,sosai sukaga tashin hankali wata kanwar Alhaji iliyasu tana kuka tace"Dangin masifa dangin bala'i wallahi munyi dana sanin sanin ku,ashe Yaya iliyasu da ajalinsa yake zaune duk tsawon shekarun nan?wallahi bamu yafe ba kuma sai mun dauki fansa, Allah ya isa tsakanin mu daku"Amma kuka Ummie ma kuka haka su islaha ma, Ammar ne ya kariso yace"Haba Guggo mu bada son ranmu momy zatayi haka ba domin lefin wani baya shafar wani sannan muma mahaifin mu fa aka kashe,muma munajin zafin hakan fa matuka,sannan me su Amma sukayi da zaku hada dasu?yakarisa maganar cikin 6acin rai, cike da masifa tace"dalla can rufemin baki,wayasa dakai?ai bazaku ga lefinta ba tunda ba ita aka kashe ba, la'ananniya shedaniya"takarisa maganar cikin muryan kuka,yayyen Alhaji iliyasu maza biyu ne suka shigo cikin 6acin rai suka fara magana"Wai talatu lafiyan ki lou kuwa?ku meyasa idan baku tayar da fitina ba bakujin dadi?kubar mamata su samu salama ma ya isa,sannan kinada tabbacin hajiya Zainab ce takashe su?cikin muryan kuka tafara magana"Yaya waye zai kashesu idan ba ita ba?tunda yayi auren nan bata ta6a barin shi yayi sukuni ba,fitinar yau daban ta gobe daban sannan da bakinta take fadar mugayen abinda zata aikata musu,wani bincike ake so ayi?bayan ga hujjoji?cikin fada yace"talatu banson masifa wallahi yanzu zakibar gidan nan"maida duban sa yayi gasu Ummie yace"don Allah kuyahakuri kusamu waje ku zauna"cikin sauri Amma tace"A'ah Alhaji ai munyi gaisuwa yanzu zamu tafi Allah kajikan su Allah ya musu rahama,yanda 'yan uwankun nan suke a fusace sai su cinye mu danye ai anan"tayi maganar tana goge kwallar idon ta tasanya medical glass din. Haka dai rayuwa ta cigaba da tafiya da dadi babu dadi gashi a yau Alhaji iliyasu sun cika sati guda da rasuwa,inda bincike be tsaya ba neman hajiya Zainab ake ruwa ya jallo,su islaha sunyi kuka sun gaji me ma lallashinta mijinta ne da mahaifan sa. ****** Zuhra sun kammala Exam dinsu lafiya inda take dan hutun sati guda,bikin Kareem da Rammat kuma ya gabato shirye-shirye kawai akeyi domin saura wata guda. Sauban ma ya tattara ya koma Canada sai biki kuma kila yadawo,wannan dalilin yasa Akeela cin karenta babu babbaka da akwai ranar da Bodejo ta aike Zuhra gidan Sauban din,duk da bataso ba don har kuka sai da tayi amma Bodejo tace sai taje don duk wani guje²n ta gidan zata koma da zama,haka ta amsa sakon ta tafi badon ranta yaso ba,koda taje sallama tadinga babu response ganin hakan yasa tashiga parlon,abinda tagani sai da yasa ganinta daukewa na wucin gadi,domin kuwa Akeela tagani akan wata mata suna lesbianism inda Akeela ke goga al'auran ta ana matan ita kuma matan ta kama..... Akeela sai shansu takeyi,ihu gabadaya ya cika palourn,da wani mahaukacin gudu Zuhra tabar gidan don da alama ma basusan shigowar ta,sashen Ammi tanufa inda ta ciddata da Mom suna hirar bikin Kareem da Rammat,ganin yanda tashigo a gigice ne yasa Mom kamota"ke Zuhra lafiyanki kuwa?ganin banda zufa da rawa babu abinda jikinta keyi,hanyar waje tafara nunawa daqyar ta iya bude baki tace"s....sa....gidan ya sa....sau...ban. Mom da Ammi suka hada baki wajen cewa"me yasame gidan Sauban din,cikin gigita Zuhra tace"Akeel....ai bata karasa ba atake anan ta zube sumammiya,wannan abin yayi matukar tayar musu da hankali a dai dai lokacin ne kuma su Daddy suka shigo nanfa suka shiga tambayar abinda ke faruwa, Ammi tashiga sanar dasu yanda zuhran tashigo a gigice,ai da sauri Daddy, Baba Hasheem, Ammi suka nufi apartment din Sauban, Mom kuma ta zauna da Zuhra tana yayyafa mata ruwa,cikin tsananin tashin hankali. Ammi dasu Daddy dake bayanta haka suka nufi gidan Sauban,ganin kofan palourn a bude yasa Ammi fadawa,abinda tagani ne yasata sakin salatin me hade da kiran Daddy,a lokaci daya suka zabura Akeela da wannan hajiyar dake kanta cikin gigita,a kuma dai-dai lokacin ne kuma su Daddy suka fado parlour,inda Ammi tazube sumammiya. Tashin hankali su Daddy suka shiga ganin su Akeela a wannan mummunan yanayin,inda yanufi Ammi yadagata, Baba Hashim kuwa cikin sauri yafita daga palourn yana rintse idanuwa,wannan wane irin masifa ne? Ranga² Daddy yadauki Ammi yanufi gida da ita,nanfa Mom tashiga tambyar abinda ke faruwa,sai dai babu amsa, fifita aka shiga yiwa Ammi don Zuhra ta farfado banda kuka babu abinda takeyi,ta isa wajen Ammi tana mata fifita haka Mom ma"Wai Baban Aseef meke faruwa ne?na tambaye Zuhra tunda ta farfado batace min komai ba kuma bata bar kuka,kuku ma kunshigo da Ammi ranga²"batare da Baba Hasheem ya tanka mata ba yakara waya a kunne,babu jimawa akayi picking"Assalamu alaikum, Dr barka da warhaka,daga can 6angaren aka amsa,magana ya cigaba"don Allah Dr munason ganinka ne yanzu anan gida"amsa masa akayi tacan bangaren"To shikenan sai ka iso,yafada yana aje wayar ya cigaba da cewa"innalillahi wa Inna ilaihirraji'un, hasbunallahu wa ni'imal wakeel. ***** Babu jimawa Dr Ahmad ya iso,yanayin da yaga jikin Ammin ne yasa yace gaskiya sai fa anje asibiti,aiko haka suka dunguma asibitin, Zuhra akace taje ta sanar da Bodejo. Taimakon gaggawa aka shiga bawa Ammi don ceto numfashin ta,kusan awa biyar kenan ana kanta,ana cikin hakan ne kuma Galadima da Bodejo da zuhra suka shigo. "Ikon Allah Aisha kuma lokaci daya ace ciwo ya sauka?lallai Allah me iko"Mom tace"wallahi kuwa bodejo barka da zuwa,bodejo tace"yawwa Rabi,nan suka cigaba da tsayuwa, Dr Ahmad ne ya fito yadubi su Daddy yace"Alhaji muje office"da okay Daddy ya amsa sannan shida Baba Hasheem suka nufi office din harda Galadima,waje suka zauna nan Dr Ahmad yafara bayani"babu komai kawai firgice tayi da alama taga wani abu daya firgita,but Insha Allah everything will be okay,yanzu haka ma ta farfado zaku iya dubata"godiya sosai sukayi masa suna fiata daga office din,duk cikansu suka rankaya dakin, Ammi na zaune banda hawaye babu abinda yake mata,duk sannu suka shiga yimata, amsawa tayi tana me duban Daddy dakyar ta bude baki tace"Daddyn yara ALLAH yasa mafarki nake ba gaske ba,ina jin tsoron abinda na gani ya zama gaskiya,gyaran murya Daddy yace"Uhmm please Aisha calm down cuz likita yace baki bukatar hayaniya....carab bodejo ta ca6e"ku mana bayani mana Taleeb wai meke faruwa ne? Mom tace"gaskiya kam saboda kinga Zuhra tafara ganin abinda ke faruwa sannan a sashin Sauban, Galadima yace"ya isa haka kubarta ta samu natsuwa idan anje gida duk a tattauna. A ranar Dr Ahmad yabama Ammi sallama. ****** Akeela kuwa ganin abinda yafaru ba karamin rudewa da tashin hankali ta shiga ba,kuka takeyi tana fadar ta shiga uku shikenan tasan ita auren ta yanzu ya gama yawo,itakuwa hajiyar ganin abinda yafaru yasa ta tattara yanata yanata tabar gidan gudun wani mummunan abu ya auko,aiko Akeela cikin tsananin rudu da damuwa tanufi gidansu tana kuka kaitsaye sasan Guggo Laure ta nufa,da tashin hankali Guggo Laure ta tareta tana kamata suka shiga daki,ananfa Akeela ta shirga ma Guggo Laure karya da gaskiya ita kuma tahau ta zauna, bala'i tafara zazzagawa,nan kuwa ta shirya ta nufi gidan Galadima,a dai-dai lokacin su kuma suka dawo daga hospital,da kuka Guggo Laure da taresu don su sam basu lura da ita bama,duk cikansu mamaki sukeyi,musamman Daddy da Baba Hasheem,kaitsaye Ammi ta tunkara tana nuna ta da yatsa tare da kumfar baki"Aisha baki isa ki yanke abinda Allah shi da kansa ya kulla ba,dama tunda akafara maganar auren Akeela da Sauban na lura da take²n ki bakiso,taya za'ace tunda tazo gida kullum sai kinshiga gidan ta kin tayar mata da hankali?wai me ta tsare miki,kwanaki ma da tayi 6ari tace kece kika zuba mata abu a lemu tasha cikinta ya zub........bata karasa ba Baba Hashim ya katseta cikin 6acin rai,domin dai da alama yau Guggon nasu ta kure shi"Don Allah ya isa haka Guggo ya isa,ita shedaniyar jikan takice tafada miki wannan kanzon kuregen?wallahi da na kama yarinyar nan a gidan nan yau dukan mutuwa zan mata domin itadin annoba ce a cikin ahalinmu,ko makiyin mu bazamuyi fatan ya hada zuri'ah da me irin halayen yarinyar nan ba"cikin daga murya Galadima yace"Hasheem kana hauka ne? Guggon naka kake fadawa haka?gabadaya idon Baba Hashim ya juye da bala'i yace"Galadima kadena sauraren maganar Guggo,domin duk halin da Aisha tashiga Akeela ce sila,domin dai Akeela 'yar madigo CE!nan yashiga basu labarin abinda ke faruwa tundaga zuwan Zuhra da suman da tayi har zuwan su dasu Daddy da sumar da Ammi tayi,gabadaya Galadima, Bodejo, Guggo laure salati suka sanya Daddy na tayasu,cikin kuka Guggo Laure tace"Karya kukeyi hasheemu wallahi sharri kukeyi Allah ya isa tsakanina daku da yardan Allah sai Allah yasakama Akeela, Allah ya isa"tana fada tana kuka haka yafita tabar gidan. Taga² Galadima yayi zai fadi,cikin sauri suka taresa,fadi yake nine Laure yau takema 'yayana Allah ya isa? innalillahi wa Inna ilaihirraji'un,gabadaya gida ya hargitse kamasa sukayi suka kaishi bedrooms dinsa suna masa fifita, Galadima kuwa sai maimaita magana guda daya yakeyi abinka da tsufa yafara riska,shekaru 82 ba wasa ba ai"Nine Laure kema yarana Allah ya isa?a ranar dai sai da jinin Galadima yahau, Sauban ma ammishi waya kan gobe zai iso, Abba ma haka. Gabadaya ahalin kwanan rashin dadi da natsuwa sukayi domin tsiya sosai Guggo Laure takeyi Alhaji mansir na tayata, Baba sani kuwa cewa yayi abari ayi bincike,nanfa Guggo Laure da Alhaji mansir suka dirar masa wai shima ya yarda da sharrin da akama Akeela. Da daddare kuwa Akeela ba gida ta kwana ba,can tatafi suka sake cin Karen su babu babbaka,domin gani takeyi yanda tahada wannan maganar komai zaizo da sauki. Washegari kuwa da wajen 1:30 babu abinda kakeji na tashi sai hayaniya gidan Galadima family wanda har yaja koke koke domin kuwa Guggo Laure ta dage kan wallahi muddin aka raba auren Akeela da Sauban itama ta rabu da Galadima bata bashi babu zuri'ar sa rabuwa kuma ta har abada,a'inda Bodejo itama ta rantse kan wallahi sai Sauban ya saki Akeela don bazasu zauna da annoba,Sauban idanuwan nan sunyi jajawur nan yashiga recalling din abubuwa da dama,sannan tabbas shima yasha zargin sa da haka,nan yashiga bayanin komai shima,sannan Ammi tasamu shedar tunda akayi bikin Sauban bata shiga sashin ba sai jiya,sosai rayuka suka 6aci hankula suka tashi,ita kuwa shedaniyar batasan meke wakana tana can suna madigon su,duk da a gefe guda na zuciyan ta tanajin bazata iya rabuwa da Sauban ba.Gida kuwa sai kuka da kuka domin Guggo Laure tace"anuna musu sheda na kama Akeela da akayi tana madigo"Bodejo tace"sheda ai Allah ne shaida kuma insha Allah sai Allah yatoni asirinta mudaije zuwa. Wata kalma da ya girgiza su ne yasa mutane biyu zuciyoyin su rawa lokaci guda wato Galadima da Guggo Laure domin kuwa a take anan Sauban yace"ni Muhammad Taleeb Muhammad nasaki matata Akeela saki daya,biyu.....baikarisa na ukun ba yaji wani gigitaccen mari,da hanzari yadago lokaci daya, Daddy ne ya maresa"Sauban ka gwammace ka yanke zumuncin 'yan uwa biyu?Ashe baka da hankai? Sauban yace"Daddy ko na cigaba da zama da Akeela babu aure domin zargin ta zan fara,kuma aure da zargi babu aure. Ihu Guggo Laure tasa kamar mahaukaciya tana fadar"Allah ya isa tsakanina da ahalinki Yaya Muhammadu bani bakai,insha Allah abinda kukamin sai Allah yayi muku"tana fadar hakan tabar gidan tana kuka, Alhaji mansir yabi bayanta. Atake anan Galadima ya yanke jiki yafadi,wanda yayi sanadiyar karkacewan mouth dinsa tashi daya. *_LALLAI WADANNAN AHALIN SUNA CIKIN CAKWALKWALIN TASHIN HANKALI,A GEFE GUDA GA ADDA ZAINAB WACCE BA'A MASAN INDA TAKEBA,KOMAIFA YA RINCA6E YA LALACE😱_* [7/9, 13:44] 𝐗𝐚𝐡𝐫𝐚 𝐗𝐚𝐡𝐫𝐚𝐭𝐭𝐲🥰: 👨🏽‍🦳 *_GALADIMA FAMILY_*👨🏽‍🦳 Page:- 65/66 ____Hankulan su yayi kololuwan tashi a lokacin da sakamako yafito kan Galadima ya kamu da paralys daga 'yayan har jikokin hankulansu yayi kololuwan tashi,lokaci guda aka fara kokarin hadawa mishi Visa shida Daddy da Abba don zasu nufi Malaysia gidan Abbie nacan zasu sauka idan komai ya dai-dai ta,family kuwa sai kuka da kuka. Sauban yayi nadama matuka akan hukuncin da ya yanke domin Daddy lefinsa yake gani inda dashi kanshi ma yake ganin shine silar komai, Bodejo kuwa kuka take sosai cikin muryan kuka tace"Duk abinda ya samesa Laure ce sila babu ruwan saudan domin shidin ya kasance meson 'yar uwansa ne ganin su biyu kawai iyayen su suka haifa,sam baya son damuwan ta shiyasa yake mata abinda zai faranta mata duk da kuwa yasan halinta na rashin kirki amma haka yake shanye komai, Allah yasani wannan yarinyar ta cucemu. Basu tare da natsuwa, Taufeeq dasu ummie ma sun karaso,inda jibi zasu bi jirgin karfe 10:00. Duk an mayar da matan gidan mazan ne kawai suka kasance a asibitin da jikokin nasa,acan gida kuwa sai maida zancen akeyi, Mom nabawa Ummie da Mommy labarin duk abinda ya faru harda cin mutumcin da Guggo Laure tayi daya haddasa haka. "Innalillahi wa Inna ilaihirraji'un wannan abu sam beyi dadi ba,mezesa son ya yanke hukunci cikin fushi?da anbari duk an shawo kan matsalar ko don yankewan zumuncin nasu"sai a sannan Ammi tayi magana"Wallahi kuwa Ummien yara yayanke hukunci cikin fushi,ni a tsarina Sauban bazai sake Akeela ba yabarta duniya ma ta isheta. Carab Mom tace"Ca6! Kazanta wallahi ko jini bazamu yarda muhada da 'yar madigo ba,wai Aunty Aisha kin mance illarsa ne?kin mance girman zunubin sa? Ai wannan abinda yayi shine dai-dai kuma beyi lefi ba da yake dai ita Guggo Laure a yanda na fahimce ta sam batason lefin wannan yarinyar,ni tun sanda nafara ganinta bata kwanta min ba bata burgeni ba yarinya ido a bude sai kace sandar snooker?ai gara da Allah ya tona mata asiri,ga matansa nan kawai asa tarewan su kowa ma ya huta"takarisa maganar tana nuna Zuhra wacce tayi tsuru² dajin furucin Mommy na karshe. Mom tace"yanda kikajin nan Aunty Hauwa,ai mu munyi mummunan gani munshiga tashin hankali. "Nikaina a yanzu nafi bukatan asa kawai ranar tarewar su ko sati guda ma inda za'abi ta nawa kada ayi,shi kanshi ma ya samu natsuwa"Ummie tace. "Gaskiya ne idan aka gama wannan abin komai ya lafa sai ayi maganar"Ammi tafada,mikewa Zuhra tayi jikinta nayin bala'in sanyi don harga Allah ita tasan batajin san ya Sauban acikin ranta,zuciyar ta a dagule tashiga bedroom din Mashahuda nada inda tattada ta tana kwance tare dasu Laila da Nihal,da yake tanata fama da laulayin ciki shiyasa,kwalla ne ya taru mata a ido tanajin damuwa lokaci guda ya dirar mata. Muneefa ce ta shigo da 'yar dariyar ta tace"Amaryan mu gaskiya ya kamata ayi shagalin biki kafin ki tare, Mashahuda ta mike ta zauna itama dariyar take tace"anyi maganar tarewar ne? Muneefa tace"maganar dasu mommy suke kenan a palour"wani ihu Nihal da Laila suka sanya,cikin tsokana Nihal tace"ai wallahi kuwa gara kitare Yaya ya tafi dake can Canada kikarasa karatunki, Mashahuda tace"Ai banjin zai iya tafiya da ita yanzu kila nan zata fara zama"hawayen da take makalewa ne ya samu daman gangarowa,kamota Muneefa tayi ta zaunar da ita kan gadon tace"a'ah menene kuma abin kukan yanzu daga magana?dagowa Zuhra tayi cikin muryan kuka tace"Bazaku gane bane,ni ni bana son sa Allah yasani don Allah kusa baki yasakeni.....bata karisa taji Mashahuda ta buge mata baki,cikin 6acin rai tafara magana"kinada hankali kuwa Zuhra?kinsan abinda kike fada?to tun wuri kishiga taitayin ki domin wallahi idan su Abba sukaji kalmar nan daga bakin ki sai na lahira yafiki jin dadi,ke bama su ba ya Taufeeq naji sai kinsha mamaki,'yan mata nawa ne ke neman irin damar ki basu samu ba?kinsan yanda 'yan mata ke rushing kan Yaya?to wallahi kisan maganar da zaki na furtawa gudun kada ya koma kunnensu da Daddy, Muneefa tace"Hmmm Zuhra kenan duk wannan abin da kikeyi yarinta da wauta ne kawai yake damunki,Amma I know ko badade ko bajima keda kanki zakiyi alfahari da samun ya Sauban matsayin miji,don koni naso shi amma nasan ba lalai yasoni ba,gashi Allah yamin canji damafi alheri. Duk shiru dakin ya dauka banda shesshekan kukan Zuhra babu abinda ke tashi, Laila tace"Allah ya ganar dake,kuma ko mutum naso ko baiso dole ya tare"tayi maganar tana sakin ma Zuhra gwalo tare da ficewa da gudu tana dariya,kokarin binta Zuhra keyi tana karama kukan ta volume. Dayake asibitin su Dr Ahmad akwai kula don asibiti ne me masifar tsada nurse's ke kula da mutum,wannan dalilin yasa karfe 10 su Daddy duk suka baro asibitin. Taufeeq da Sauban apartment din Ummie suka wuce, Zuhra ce zaune a parloun kasa tana cin abinci,don Ummie tashiga ciki watsa ruwa,sallamar su ce yasata dagowa tana amsawa idanunsa akanta duk da yacce face dinsa yake a tamke hakan behanashi kashe ta dana mujiya ba kamar wacce ta masa lefi,cikin tsananin farin cikin ganin Taufeeq tataso tare da hugging dinsa"Yaya ur welcome,shafa kanta Taufeeq yayi yace"thank you little,hope kina lafiya? Zuhra tace"fine Yaya I think ma nafika cikakkiyar lafiya",dariya suka sanya itadashi,shikuwa Sauban remote ya dauka ya kunna Ball,wanda yau akwai wasa 10:30 tsakanin Manchester United da kuma Arsenal. "Ina Ummien take?tajiyo muryan sa yana tambayar ta,da kamar bazata amsa ba Taufeeq yace"little dakefa akeyi"cikin sanyin murya tace"tana sama. Babu wanda yasake magana duk da kuwa yanda Akeela kejin ta a takure zamansa a wajen, Ummie ce tafara sakkowa daga stairs din. Zama tayi inda nan suka shiga gaisheta da mata sannu da gida,amsawa tayi cikin dan damuwan dake kan face dinta tace"ya kuka baro jikin Galadiman?suma cikin alhini Sauban yace"Ummie jiki sai godiyan Allah,jibin dai za'a wuce dashi can,nima jibin zan koma office ana jirana,daga can nakesa ran naje na duba jikin nasa"Ummie ta girgiza kai tsce"Allah yabashi lafiya,kai kuma Allah yabaka ikon zuwan,dan duban gefen da Zuhra take tayi tace"kitashi ki zubo hado musu abinci mana. Mikewa Zuhra tayi duk kunya ta isheta saboda bomshort dinda ta sanya tare da vest,cinyoyin nan katar katar sai juyawa sukeyi,a sace yake kallon ta,yanajin wani abu na taso masa,bata wani jimaba tadawo inda suke dauke da basket,juyawa ta kumayi taje tadawo da tray,inda plates,spoons da glass cup da bottle water suke da drinks ta ajiye,tana kokarin mikewa tajiyo muryan Ummie"kihada musu abincin mana. Babu yanda ta iya nan tashiga serving dinsu,shikanshi sai da ya lumshe ido saboda kamshin abincin, Taufeeq kuwa kasa hakuri yayi yace"Little halan ke kikayi girkin nan?shiru Zuhra tayi tana murmushi,ganin hakan ya tabbatar masa da lallai itace tayi abincin"yi kizuba mana tun safe Muna asibiti bamu iya cin komai ba sai bottle water da muketa antaya ma cikin mu Ummie"Ummien tace"to ya za'ayi? hankali ne sam ba'a kwance ba. White Basmati rice wanda aka dan watsa Kara's,grean beans nd parsley sai gasmeat Wanda sosai yaji kayan hadi,shi ta zuba ma kowa a plate dinsa,sannan ta samusu farfesun kan rago dai-dai,ruwa ta zuba musu a glass cup batare da ta zuba lemo ba,bismillah,ta furta wanda hakan ya zama sabon ta kuma al'adar ta. Cikin natsuwa suka sakko kasa kan carpet suka fara jan girki. "Ummie wanka zanshiga idan kinji shiru nayi bacci"Zuhra tafada hakan tana hayewa stairs,wannan karan ba Satan kallon ta yayi ba,bude ido sosai yayi yana kallon ta ko kunyar Ummien ma bayaji. [7/9, 21:30] 𝐗𝐚𝐡𝐫𝐚 𝐗𝐚𝐡𝐫𝐚𝐭𝐭𝐲🥰: 👨🏽‍🦳 *_GALADIMA FAMILY_* 👨🏽‍🦳 Page:- 67/68 _____Sosai suka ci abincin don ko wannen su sai da yakara sai dai Taufeeq yafi karawa da yawa don dama shidin yafi Sauban cin abinci sosai, Ummie ma tayi mamakin abincin da Sauban din yaci,cuz a iya sanin ta shi din ba ba ma'abocin cin abinci ne ba,bashshi da kayan snack's musamman pizza da Burger,haka suka gama cin abinci sai da yafada musu sannan Sauban ya dubi Ummie yace"Ummie bari naje na duba Ammi gud night"murmushi Ummie tayi tace"Au dama ba can kuka fara zuwa ba?tayi maganar tana musu hararar wasa, Taufeeq yace"ai tare muka dawo dasu Daddy so kinga shima yana bukatan kulawa,shiyasa muka tawo nan ke kuma ki bamu tamu kulawar"dariya Ummie tayi Sauban kuma na sakin murmushi,dan kwalla ta share a dalilin tuno da Abbie da tayi,Sauban har yafita sai kuma yadawo tare da tsayawa kofan palour yace"Ummie please idan babu damuwa coffee"yayi maganar yana dan marairaice face, Ummie tace"Sauban har yanzu baka dena shan coffee ba? "Ummie ai sai dai arage" Ummie tace"ikon Allah to kaje zansa Zuhra ta hada maka"murmushin jindadi yayi"tnx my only Ummie"yayi maganar yan fita. "Zuhra! Zuhra!! Ummie ta shiga kwala mata kira,amsawa tayi tana sakkowa sanye da wani night gown har kasa maroon colour,ta ciki hannun vest ne,sai falmarar sama me gajeran hannu duk da ba kamata yayi ba sai dai da yake yadin silk ne irin me mannewa a jikin nan,a hankalin ta kariso"wayyo Ummie har fa nafara bacci"tayi maganar kamar me shirin kuka, Ummie tace"Kuma dole kitashi ba,dama yayanki ne keson coffee bani ba",da sauri Zuhra ta dubi Taufeeq tace"kai yaya yanzu fa wajen 11 ake nema"takarisa maganar tana mere baki da mutsitstsike ido,harar Taufeeq ya wurga mata,cikin sauri ta mike ta nufi hanyar kitchen din don duk a tunanin ta Taufeeq ne keson coffee din,bata wani jima ba tafito hannunta dauke da tray din coffee jug,gefe kananun glass cup din ne,a center table dinda ke gefensa ta ajiye. Ummie tace"Sauban ke bukata ba Taufeeq ba kishiga kidauko mayafi kikai masa"a hargitse Zuhra ta dubi Ummie tace"innalillahi wa Inna ilaihirraji'un,ni Ummie ina zangan shi yanzu?wani harara Ummien ta galla mata me dauke da ma'anar ina wasa dake ne? Zuhra da kwallan ta tace"A'ah ta furta sannan ta mike tadau tray din tanaji kwalla yana taruwar mata,fita tayi daga palourn ta fito farfajiyar gidan kaitsaye apartment din Ammi ta nufa,koda tashiga parlour Laila ta gani tana waya cikin nishadi wanda kp ba'a fada ba kasan da wanda takeyi wato Shuraim,ganin Zuhra da tayi da niki-nikin tray yasa tace mishi bari tana zuwa,a dai-dai gabanta ta ajiye tray din tare da cewa"Laila ya Sauban yafita ne? Laila tadaga mata kai alamar eah tana kallon ta,dan narkar da face Zuhra tayi"please dan kira shi muji yana inane kice mishi ga coffee din"wani murmushi Laila tayi tana dan mere baki koda takira ba'a dauka ba,sai dai ko minti biyu batayi ba kira yashigo,dauka Laila tayi cikin mutunmtawa kamar yana gaban ta tace"barka Yaya",Bata jira amsar sa ba ta cigaba"dama coffee dinka ne Zuhra takawo nan ta zata kananan ne,magana akayi ta can bangaren,ita kuma ta amsa da "Okay bari na fada mata"takarisa maganar tana kallon Zuhra da tayi sagalo, Laila tace"Yaya yace yana tsohon apartment din shi kikai masa can"da sauri Zuhra ta mike tana dafa Laila"please sis don Allah ki kai masa"Laila ta dafe kirji like taga wani abin tsoro"Ni?ki rufamin asiri,in mutu maza su kaini salin alin,ai yasan dani be ce nahada masa,ke matar sa kece yaga dacewan ki hada masa,so kike a faffala min mari kenan?wallahi bazan kai ba"tayi maganar tana watsa yatsu, Zuhra tace"shikenan naji tom muje kirakani nakai" ja da baya Laila tayi"wallahi wallahi bazani ba karfe nawa yanzu ne da bazaki iya zuwa apartment din ba?yasan zaki iya zuwan ne shiyasa yace ace kikai masa can"tayi maganar tana hayewa stairs tare da dariyar shakiyan ci,mikewa Zuhra tayi tadau tray din tafita,kaitsaye sashen ta isa,sosai kirjinta ke wani irin luguden duka gabanta na tsananta faduwa,hannu takai ta fara knocking,sai da tayi sau biyu ana ukun ne aka bude,kan ta a kasa, kamshi St.ives body wash ne ya cika mata hanci,"idan kin gaji da tsayuwan kya shigo"yayi maganar tare da juyawa,shigowa parlour tayi duk da karami ne amma yayi bala'in haduwa sannan babu tarkace a ciki,sosai dakin yayi kyau,dagowa tayi da niyyar duban stool din da zata aniye tray din,gabanta ne yayi wani mahaukacin faduwa a dalilin Ido biyu da tayi da murdadden jikinsa,wanda banda glowing babu abinda yakeyi,ruwane a jikin yayi masifan kyau,towel ne daure a waist dinsa,cikin gaggawa ta runtse idanuwan ta,jikinta na wani irin rawa"idan kika zubar min da coffee sai na faffala miki mari,kikawo min ciki"shigewa bedroom din yayi ita kuwa zuhra tsaye tayi kirjinta na wani faduwa,tana tsaye har na tsawon minti bakwai,fitowa yayi sanye da wata designer jallabiya coffee colour tayi masa kyau gaya"i amذ your mate? Yayi maganar face dinsa babu alamun wasa ko miskala zarratan,takowa tafara,shi kuma ya koma ciki, shiga tayi ganin sa kan sallaya yasa ta sauke wani ajiyan zuciya,nufan inda bedside drower tayi ta ajiye tray din sannan ta juya da niyyar fita,gyaraln muryan da taji yayi ne yasata duban sa da sauri,raka'a biyu yayi batare da tasan zai sallame ba tayi azamar fita a dalilin shawarar da zuciyar ta tabata,fisgota taji anyi,a gigice ta kwalla kara,babu tsato babu tsammani taji mouth dinsa kan lips dinta,jikinta ne yafara rawa,ta kwalo idanuwan nan ta saka cikin nasa wanda shima itadin yake kallo,mutsu mutsu tafara hawaye na sakko mata,wani karfi ne yazo mata aiko ta turesa a dalilin sakin da jikinsa yafara"cikin kuka Zuhra tace"banyafe ba Kuma sai na fada ma Ammi kai ma dan iska ne,mugu azzalum.....bata karisa ba taji ya damki bakinta da nasa bakin,cikin salon mugunta yake tsotse lip's dinta,wani radadin azaba takeji a bakinta,sai dai kukan ma bazai yuwu ba banda hawaye,daka kalle fuskan sa da idanuwan sa kasan cikin bala'in bacin rai da hassaluwa yake,yadau tsawon minti biyar kafin yasaki mouth dinta,anan Zuhra ta zamiye tafadi kasa tana fashewa da wani irin kuka tare da dafe bakin,muryan sa ne ta sauya da tsantsan bacin rai"Duk randa kika sake cemin dan iska mugu azzalumi,wallahi ranar sai na miki abinda yafi wannan,ni sa'anki ne?akan hakkina kike neman zagina da min rashin kunya?stupid kawa dalla tashi ki hadamin coffee"jikin Zuhra na rawa ta mike,ga hawaye takasa denawa,zuba masa tayi takai masa bakin gadon,amsa yayi yana Kura mata ido,sosai takejin zafin kukan nata hakan yasashi lumshe ido yana kai cup din bakinsa tare da sipping,duk tana tsaye tana ahare hawaye,muryan shi tajiyo"kishiga toilet ki share hawayen ki ki wanke face dinki"yayi maganar cikin murya Shiba sanyi ba kuma ba fada ba,juyawa tayi ta shiga toilet tana ja masa Allah ya isa"Nike zagi?tajiyo muryansa,ai a kidime tajiyo tana me sakin wani irin kuka ganin ya taso"wallahi ni ban zage kaba"tayi maganar da muryan ta da yafara dishewa,rumfa ya mata yana hadata da jikin bango,cikin muryan kuka tace"please Yaya don Allah kayahakuri ban zageka b"gani tayi ya lumshe ido ya matso da bakinsa saitin nata sai dai me?jitayi yabata peck a forehead dinta yana matsawa,face din nan a daure,kamo hannunta yayi,wani laushi yaji me masifar dadi,sosai hankalin sa ya tashi,a makoshi yayi magana"muje na kaiki apartment din ku"binshi tayi kamar rakumi da akala,cikin izzan sa yake tafiya don shi mutum ne me zafin nama a haka ya kaita har apartment din Ummie,bude kofan parloun yayi babu kowa,wani ajiyan zuciya Zuhra ta sauki har sai da ya kalleta"what! Ya tambaye ta yana tsura mata sexy eyes din sa wanda lokaci guda sun sauya,girgiza kai Zuhra tayi da sauri"No... nothing"shima Sauban girgiza kai yayi"ban yarda ba,tell me the truth"Zuhra cikin shagwababbiyan murya tace"Nace fa babu komai,tayi maganar tana zumburo mouth gaba"sosai hakan yayi bala'in burgesa sai dai bazaka fahimci hakan ba"Okay oya let's go"yayi maganar yana nuna mata stairs,cikin sauri ta nufi stairs,sosai yake kallon yanda ass dinta ke kadawa,muryan sa tajiyo"Babu sallama?dan juyowa tayi tace"Gud night"da sauri takarisa hayewa,murmushi Sauban yayi yana lumshe ido,firgitacciyan fuskan ta yake hangowa sanda take cewa wallahi Yaya ban zageka ba,shafa sajensa yayi yana fita daga apartment din,ita kuwa Zuhra jingina tayi a jikin kofan tana dafe da kirjinta,sosai wani irin tsoron sa ya shigeta,kaitsaye toilet ta nufa ta dauro alwala, alqur'anin dake kan bedside drower dinta tadauka tafara karanta suratul Muhammad,bayan ta gama ta karanta Suratul mulk wanda hakan yazama al'adar ta, addu'o'i tayi sannan taja blancket,bata wani jima ba sai bacci. Shikuwa Sauban koda ya koma shima Shirin bacci yayi bayan yayi addu'o'in sa sannan ya kwanta,kokarin bacci yake,Amma baccin yaki zuwa da ya runtse ido face din yarinyar yake gani"Oh my God, Sauban wat's wrong with you?yarinya karama ce fa, she's still young fa,idan ina lissafi dai-dai yarinyar nan zatayi 19?So why not am thinking about her?huh ya rabb,I know am not loving her"yayi maganar yana runtse ido da kyar bacci yayi awon gaba da shi. ******** Washegari kuwa duk sunje asibiti 'yan gidan Kama daga kan yara har manya,motoci biyar sukayi,ko wacce number mota sai kaga sunan G FAMILY muddin suka wuce ansan sune sai an daga musu hannu saboda temakon tsohon,wanda labarin laruran da yasamu har ya watsu a gari,mutane da dama na masa fatan samun sauki, Bodejo sosai take kuka a lokacin wajen 8:30 su Daddy da Abba ne zasu tafi kasar Malaysia da Galadima cikin muryan kuka Bodejo tace"haba Laure me Galadima yayi miki da ya cancan ci hakan daga gareki?mutum ne me kaunar ki tare da tsananin son ki amma akan jika kikayi sanadiyyar zamowan sa haka,meyasa?tayi maganar tana fadawa jikin Daddy, Daddy, Abba, Baba Hasheem duk rungume ta sukayi suma tana kokarin sasu kuka,sallama su Aunty labeeba sukayi,kaitsaye suna nufar gadon Galadima,suma kukan suka sanya suna fadawa jikinsa,wannan dalilin yayi sanadiyyar tashin sa. Shima hawayen ne ke zuba kawai a idon sa,komai baya motsi sai kwayan idon sa yana murmushi,duk nufar sa sukayi, Aunty Maryam cikin muryan kuka tace"Bodejo me yasame shi hakan?mun tafi min barshi lafiya lou, meyafaru? Bodejo cikin muryan kuka tace"kaddara mairo komai ya faru mukaddari ne sai dai da sanadi. Galadima kuwa kura ma Zuhra Ido yayi duk da murmushin nasa ba kowa ke ganewa ba amma angane,sannan yamai da duban sa ga Sauban yana murmushin,alama ya musu da kai dasu zo,don bakinsa babu halin magana,karasawa sukayi garesa,murmushi yayi yana girgiza kai alamun yana jin dadi. Dr Ahmad ne ya shigo tare da wasu doctor's din, duban Daddy yayi"Alhaji Taleeb lokacin wucewan ku yayi yanzu 9:00,duk juyowa sukayi hankalun su nadawo wa kanshi,wani daga cikin Dr din yace"sunana Dr Amjad Aliyu tare dani zamu tafi"nan kuwa suka fara shirye-shiryen su,gabadaya shisshiga motan sukayi don rakasu airport,goma saura minti 7 suka isa airport din,nan Sauban da Taufeeq sai Abba suka shiga ciki don tayasu kimtse kimtse na visa da sauran su dama already anyi. Karfe 10:40 aka fara sanarwan passengers,sosai Bodejo dasu Aunty Maryam ke kuka, Ammi da Ummie ma haka,sai Mommy da Mom ne suka koma rarrashi,sai da sukaga tashin jirginsu sannan suka nufi wajen motocin su,hannun ta taji an kamo a tsorace ta juya,kamar ba shine riqe da hannun nata ba don fuskewa yayi gabadaya,ita kuwa Zuhra a tsorace take tsananin kunya ya kamata,ga fargaban kada wani ya gansu sai dai abinda bata sani ba shine, Baba Hasheem, Ummie Bodejo, Mom duk sun gansu,sakinta yayi tashiga mota tare dasu Aunty Mashahuda don Taufeeq ne ke jansu, Mashahuda, Laila, Muneefa, Nihal,ita. Sai motan Sauban Baba Hasheem, Bodejo,sai dayar motan Aseef keja Mom ce a ciki,dayan kuma Aunty Maryam keja Ummie, Ammi,sai dayan Aunty labeeba keja Mommy ce sai kuma yara da akasa a wasu motocin,haka suka tafi abinsu gunin sha'awa. Koda suka koma a sashen Bodejo aka yada zango,nan aka shiga maida magana, Mom ce tashiga bada labarin abinda yafaru tun daga zuwan Zuhra da zuwan su Ammi dasu Daddy sashen Sauban din da abinda suma suka gani,sai zuwan Guggo Laure da cin zarafin da tayi har Sauban ya yanke hukuncin nan,cikin muryan kuka Ammi tace"Yanzu fisabilillah da Sauban be yanke saki a tsakanin sa da Akeela ba hakan zai faru? Aida Galadima bazai shiga halin da yake ciki ba,ga lalacewan zumunci"cikin sauri Bodejo tace" Xahratty CE 🥰 Lallai Alqalami 🖊️ yafi takobi🗡️. [7/10, 19:53] 𝐗𝐚𝐡𝐫𝐚 𝐗𝐚𝐡𝐫𝐚𝐭𝐭𝐲🥰: 👨🏽‍🦳 *_GALADIMA FAMILY_* 👨🏽‍🦳 Page: 69/70 ____Koda a lokacin Saudan be saki Akeela ba to wallahi sai ya saketa domin bazai zauna da shedaniya ba,yarinyar nan babu alamun shiriya a tattare da ita kuyi la'akari mana,wallahi ko bayan raina saudan bazaiyi rayuwa da alakakai ba"tana kare dadar hakan tanufi corridor din dakinta, Mommy tace"gaskiyan Bodejo ne sam babu lefin Sauban kawai Guggo Laure sai a hankali ne"Mom ta mere baki tace"Hmm kune bakusan halinta ba,itafa nata kawai tasani nata nata ne koba komai a wannan hargitsin ma tanuna"ajiyan zuciya Aunty Maryam ta sauke tace"Ni tun randa aka kawo yarinyar nan naga 'yan uwan mamanta masu budadden ido da ita kanta jikina yayi sanyi,don babu irin kunyar nan ta amare ko miskala zarratin a tattare da ita"Mom tace"Bana tunanin 'yan uwan maimuna ne gaskiya,don maimuna mutumiyar kirki ce,haka 'yan uwanta,itafa yarinyar nan daurin gindi kawai tasamu wajen Guggo,kunsan akanta sai da Guggo taje har gida ta zazzage hajiyan mu kafin bikin su?wai Rammat zata kwace mata Sauban,haka dai akayi maida zance batare da Ummie tayi magana ba, Baba Hasheem ne yashigo yana duban duk wanda ke parlour,don babu yara duk suna waje suna wasa,sai su Nihal tare da iyayen su,duban Mommy yayi yace"hauwa'u kufara shirye shirye,gobe insha Allah Zuhra zata tare a dakinta,domin hukuncin da aka yanke kenan,yanzu Bodejo tayi magana"Mommy zuciyan ta fesss tace"Insha Allah,mutanen parloun cikin tsananin farin ciki suke har Ummie sai dai bata nuna ba fuskan ta kadaran kadahan, Ammi kuwa kaman tayi rawa"Innalillahi wa Inna ilaihirraji'un don Allah kubashi hakuri ni banason auren wallahi banason Yaya ni karatu na zanyi"Zuhra ne ke magana cikin muryan kuka kota ina zufa ne ke tsattsafo mata kamar babu A.C a parloun,duk da mamaki suka tsaya duban ta parloun yayi tsit bakajin komai sai gunjin kukan ta, Mom ce fuska a daure tace"Amma wannan yarinyar anyi ja'irar banza, Kinga wallaphi kikeyaye mu,idan baki son auren mu munaso aikin banza kawai"Mom tayi maganar tana jan tsaki,sosai Zuhra take kuka wanda yasa jikin Ammi yin sanyi,mikewa tayi ta isa ga zuhra ta kamo ta tace"kiyahakuri Zuhra kinga mahaifinki wasiyya yabari na auren ki da son,ki temaka ki aure sa,inaji a jikina ke alkhairi ce agaresa"Ammi tayi maganar tana murmushi Wanda sosai tabama mutanen parloun tausayi, Ummie kuwa a fusace ta taso domin idan bata daki Zuhra ba bazatayi sukuni ba,ganin haka yasa Zuhra fusge hannunta ta nufi dakin da take zama,cikin muryan kuka tace"wallahi banason sa"kamo hannun Ummie Ammi tayi tace"Menene zakiyi haka bilkisou?wai meyasa kina mantawa da zuhra yarinya ce?dole a bita a hankali fa, menene amfanin abinda kike shirin yi? Ummie cikin bacin rai tace"Haba haba Ammin yara Zuhra ce yarinyar?hmmm taga ana lallabata ne"Mommy tace"babu maganar lallabo Aunty bilkisou gaskiya ne zuhra yarinya ce,so sai anbita a hankali,cikin bacin rai Ummie tabar apartment din, Mashahuda da Muneefa ne suka shiga bedroom din da Zuhra ta shiga, Aunty muneefa cikin bacin rai ta dubi Zuhra"yarinya ina guje miki ranar nadama,wai kuwa kinsan waye ya Sauban?kin kuwa san yanda mata suka rikece akansa?mata da dama sun mutu a son sa wallahi idan kika auresa keda kanki sai kinyi alfahari da auren",cikin kuka Zuhra tace"nidai bana son sa,meyasa Abbie zai yanke wannan hukuncin?i know Abbie bazai taba zabamin mijin da zai cutar dani ba,sai dai why not zuciya ta takasa amincewa dashi matsayin miji,bazan iya yarje ma batun iyaye nabaaa.....takarisa zancen tana sakin wani irin kuka me tsuma zuciya"meyasa aure na yazo a haka?duban Aunty Mashahuda tayi"Aunty Mashahuda meyasa baza'ayi irin shagulgulan da akayi a naku ba,bikin ku is d best biki a wannan year din"dafa ta Mashahuda tayi tana murmushi tace"bikinku ya fita daban dana kowa,kiyarda cewa rayuwar auren ku ne kukuma zai zama abin kwatance, cuz Allah zai albarkaci aurrn ku trust me"shiru Zuhra tayi tana jan ajiyan zuciya, Laila tayi dariya tare da cewa"Aunt duk fa munafunci ne itama tana son Yaya, amma zuciyar ta takasa yardan mata da haka, Nihal itama dariyar tayi tace"wallahi kuwa hhhhhh"a fusace Zuhra ta dubesu"Ni banson sa bantaba son sa ba,mutum daya naso a duk duniya akan shi nasan menene so,wato ya Shuraim.....Tasss! Karar mari ya sauka akan kumatun Zuhra,huci kawai yakeyi idanuwan nan sunyi jajawur,cikin sauri Mashahuda,muneefa, Laila, Nihal suka bar bedroom din, Sauban kuwa banda rawa babu abinda bakinsa yake masa,cikin muryan tsawa ya nuna Zuhra"ke...kk..kkee da aure na akanki kike fadar kina son wani?yayi maganar yana nufo Zuhra yana huci,girgiza kai Zuhra keyi"A'ah yaya don Allah kayahakuri bazan sakeb......hannu ya dunkule kamar zai kaimata punch,sai kuma yakaima wall din bedroom din,ita kuwa runtse ido tayi jikinta na rawa,juyawa yayi yafita,cikin takunsa wannan karan dai-dai da tafiyar cikin fushi yakeyi. Mommy ce tashigo dakin cikin sauri,kamo Zuhra tayi"Wai ke bakida hankali ne?sai yaushe zakiyi hankali my Zuhra,kike fadar bakison mutum agaban mahaifiyar sa gatsal haka?cikin kuka tace"Mommy shima fa baya sona"cikin fusata mommy tace"inji uban wa ya fada miki haka? kuka Zuhra ta fashe dashi hankalinta a tashe sai dai takasa furta komai,kukan kawai takeyi,ki tashi kije ki shirya zakije saloon,cikin sanyin jiki ta mike ta fita,babu kowa a palourn na bodejo,kaitsaye apartment din Ummie ta wuce,a palourn kasa ta taras da ita da Taufeeq suna magana,sallama tayi duk suka amsa sannan ta haye stairs,shiryawa tayi cikin riga da straight skirt,harta dau mayafi tasa kome ta tuna?sai kuma tanemo after dress ta dora akan kayan tafita. Duban ta Ummie tayi"inane zaki haka?cikin sanyin ta tace"Mommy tace nashirya nazo za'a wankin kai"daga mata kai Ummie tayi,hanya ta Kama har takai kofan palour tajuyo cikin raunanniyar murya tace"Ummie ki yafemun"tana karisa fadan haka da sauri ta fice. Sai la'asar suka dawo daga wankin kan,a lokacin ne kuma me henna ke jiranta,abinci taci tayi la'asar sannan Aunty Labeeba da Mommy suka fara yimata dilka,bayan an gama aka mata wankan lalle, fara shiryata cikin wata hadaddiyar net wanda aka mata dinkin wedding gown,blueblack tayi kyau dinkin ya hadu,me make-up tafara zane mata face dinta,light make-up aka mata,tayi balai'n kyau,fito da ita akayi farfajiyan gidan,kanofi ne guda uku,mutane ne zazzaune daga familyn gidan,sai makota da kawayen matan gidan don abune da akayi a kurarren lokaci,anyi decoration din filin sosai,kaitsaye aka kaita wajen rumfarta wanda yayi balai'n haduwa da tsaruwa sai wani walwalin wuta ke tashi ajikin wani rubutu ansa *_HENNA DAY,HAPPY MARRIAGE LIFE, MUHAMMAD TALEEB MUHAMMAD&FATEEMA SADEEQ MUHAMMAD._* Zaunar da ita akayi a hadadden carpet din dake wajen,gefe me lallen ne,aiko nan tashiga yima amarya lalle,sosai kida yafara tashi tare da gude² na farin ciki,haka me lalle ta cigaba har tagama na kafa ja dana hannu,anfara baki a kafa.....sautin kidan ne ya canza salo,nan Mc ya fara sanarwa"Ga ango nan ga ango nan don Allah a bashi waje,Zuhra kuwa zuciyar ta kaman tayi tsalle tafito,nan kuwa aka saki waqar illela bille illela,lamshi sharahni,sosai kidan ke tashi,ya Sauban ne a gaba cikin wata mahaukaciyar boyel blueblack,sai bakar zanna bukar,kafansa wani hadaddiyar covershoe ne kirar gucci baki,hannunsa dauke da agogon Cartier, yayi bala'in kyau,murmushi yake wanda yakara fito da ainahin kyansa,sosai aka fara tafi da ihu,bayansa abokan sa ne 'yan nan maidugri su biyar sai Taufeeq,Kareem,da Aseef su kuma cikin fararen boyel,kaitsaye wajen Zuhra ya nufo,nanfa yashiga watsa mata daloli,sai da ya watsa mata fin dari,ihu ne kawai ke tashi na mutane,hannu ya mika ya Taufeeq ya saka masa meant na 1000 aiko ballewa yayi yana watsa mata,aiko waje yasake kacamewa da ihu,Suma ya zuba sosa,dukawa yayi dai-dai saitin kunnenta inda kanta ke duke ya fara magana cikin rada tare da kamo hannunta"kinyi kyau matata sosai,am proud of you my beauty"cikin sauri ta dago,don tabbas jitake kamar tana mafarki,a dai-dai nan aka fara daukan su hotuna,waje nasake cika da ihu,nan yaja tawagar abokan sa suka bar wajen,aiko cigabawa akayi, ba'a watse ba sai wajejen 9:30 sannan. Cikin matsanancin gajiya Zuhra take,lallabawa tayi tanufi bedroom dinta ta rufe sai bacci,sosoai Sauban yaso ganinta amma ina Zuhra tayi bacci. ****** Washegari cigaba akayi da shirye-shirye duk da kuwa botsarewan da Zuhra keyi domin daru sosai tasa kan naqin auren,sai da Baba hasheem ya mata hauka² kana tashiga taitayin ta,karfe biyu akafara walima zuwa la'asar angama duk anwatse sai yarage gidan sai iyasu ahali,da yake Amma ma ta iso tare da matan yayyen Ummie da kannen ta,haka dai aka cigaba, hayaniya ce ta fara tashi,a dalilin shigowan Guggo Laure gidan. "Munafukan banza munafukanp wofi,ai dama tun tuni nasan Yaya Bodejo ta tsaneni tatsane jinina, Allah sai ya yimin sakayya tsakanina dakuu"takarisa maganar tana sakin kuka,tsit gidan ya dauka kowa yayi cirko-cirko, Akeela kuwa wajen Zuhra ta nufa tare da nuna ta da yatsa tana huci"matsiyaciya nadawo kanki,'yar iska karuwa kawai,dama tuntuni na fahimci manufar ki akaina kina kokarin rabani da farin cikina karuwa kawai"tayi maganar Cikin karaji,murmushi Zuhra tayi tana duban Akeela"Hmmm Akeela kike da suna ko wane?I don't have time for you cuz ni din nafiki ajiki,kima da kuma mutunci,niba 'yar iska bace,kuma ba karuwa bace,abarshi ma a hakan haka nake,ai gara karuwa da 'yara madigo la'ananniya,domin zunubi da girman madigo ya taka na Zina ya shany....a fusace Akeela tayi kan Zuhra tana cewa"nice kike gayama magana haka?da sauri Zuhra taja baya,aiko wani irin fusgota Akeela tayi tana shirin cacumar ta,jikake tassss! Sauban ne ya sauke wa Akeela lafiyayyun mari har biyu banda huci babu abinda yakeyi gabadaya kamsnnin sa sun rikide,dafe kumatu Akeela tayi tana sakin ihu"Ni ka mara akan wata banziya?nidin matark......daka mata tsawa yayi wanda duk wanda ke wajen sai da ya firgita"point of correction Akeela,you re not my wife,nadatse igiyoyin aure na akanki,sannan koda wasa kada ki kuskura kazantaccen hannunki ya ta6a jikin matata"Guggo Laure ne takariso tare da dauke Sauban da mari"kauu! Magana tafara"baka isa ba Sauban kayi kadan kaci zarafin jinina ina kallo dan iska kawai la'ananne. Cikin tsananin 6acin rai Baba Hasheem yace"Haba Guggo haba wannan cin zarafin naki yayi yawa,bazaiga la'anta ba,bazaiga la'anta ba Guggo"yayi magana cikin karaji,cigabawa yayi"me Mika miki haka da zafi?kin lalata zumunci,a dalilin ki mahaifin mu nacan kwance da barin jiki, Guggo mungaji da cin zarafin ki"yayi maganar cikin karaji,hannu ya hada waje guda yace"Don Allah Guggo kitafi,muddin ba alkhairi yake kawoki garemu ba so please nd please kidena zuwa kina tayar ma da ahalin mu hankali na rokeki"Guggo Laure kuwa sakin baki tayi tana kallon Baba Hasheem"Hasheem nikake fadawa magana son ranka?ka mance matsayin wa nake a wajenka?kafin yabata answer Aunty Maryam tayi carab cikin muryan kuka tace"Matsayi wani irin matsayi Guggo?kin mance keda kanki kin yanke alaqar dake tsakanin ki da ahalin nan?duk irin soyayyar da Galadima ke miki Amma haka kika rufe ido akan jika kika tozarta sa,duk akan wannan?tayi maganar tana nuna Akeela"meye ribar ahalinmu idan munma Akeela sharri alhalin mudin duk abu daya ne,wallahi Guggo indai shedaniyar yarinyar nan ne watarana sai kinji kunya. Shiru Guggo Laure tayi da alama jikinta ya danyi sanyi ganin haka yasa Akeela fashewa da kuka"Guggo kinajin su?kina jin irin cin zarafin da suke min?maida dubanta tayi ga Akeela"ke Kuma sai kinsan kin aurar wa kanki masifa da bala'i"tana kare fadar hakan tajuya,da sauri Guggo Laure ta take mata baya tana cewa"Allah ya mana sakayya! _Hoho Galadima family ko rikici family,nikam zanso naga randa wannan rikicin zai tsaya haka,gadai Sauban da Akeela ga kuma Kuma Zuhra a gefe guda,sannan ga alwashin da Akeela ta dauka akan zuhra._ Xahratty CE🥰 Lallai Alqalami 🖊️ yafi takobi🗡️. [7/12, 00:54] 𝐗𝐚𝐡𝐫𝐚 𝐗𝐚𝐡𝐫𝐚𝐭𝐭𝐲🥰: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/Cz6pFHyd9N68OmqNx3Vpqs 👨🏽‍🦳 *_GALADIMA FAMILY_* 👨🏽‍🦳 Page: 71/72 ____Sosai Zuhra ke wani irin kuka me tsuma zuciya,gabadaya sun sake 6ata gidan,bayan sallar magrib aka fito da Zuhra Cikin shigan alfarma na lutfaya Army Green tayi kyau matuka,ita kanta lutfayan daka kalleta kasan nera tayi kuka,kuka takeyi sosai kaitsaye apartment din Bodejo aka nufa da ita inda gabadaya a halin ke a palour a zaune,zaunar da ita akan carpet Mommy tayi kusa da Sauban din,nan Baba Hashim yayi gyaran murya tare da sallama,bayan yayi addu'o'i sannan yace ma Taufeeq yakira su Daddy ta laptop din,aiko lokaci daya sai ga Daddy da Abba sun bayyana. Anan aka shiga gaishesu,tare da tambayan su jikin Galadima,hadasu da Bodejo akayi suka gaishe ta,bayan sun gama gaishe²n ne kuma Daddy yayi gyaran murya,nan yashiga nasiha,sosai yama Zuhra nasiha me shiga jiki wanda dole yasata cigaba da kuka Saboda tunatar da ita da yasake kan hakkokin miji akan matanshi da abinda idan tayi zata samu zunubi,sosai yayi mata raga-raga da nasiha daga karshe ya damkawa Sauban amanarta,sannan yace idan ya zalunce ta Allah ya isa,shima Abba nan yayi nasa inda shima daga karshe ya damka amanar Zuhra ga Sauban,na karshe Baba hasheem ne yayi nasa,me hade da fada² don ya lura Zuhra zuma ce sai da wuta a cewar sa,su Daddy nan akayi sallama dasu,cikin tsokana Ummie ta dubi Baba hasheem tace"wallahi da ka hada da duka ina tunanin Zuhra zatafi gane yaren,duk dariya aka Sanya,shima mikewa yayi tare dasu Sauban don zuwa suyi sallah yana cewa"kuyi ku gama mata nasihar da zakuyi mata,don muna dawowa masallaci za'a bashi matansa ya wuce da ita,da to mommy dasu Aunty Maryam suka amsa, Bodejo tace"munafuka munanan daku sanda zasu hade suna kwasar soyayyan su babu meji"dariya palourn akasa, Aunty labeeba tace"yanda kikajin nan Bodejo,nan Ammi tafara mata nasiha,sannan Mommy, Mom, Aunty Maryam, Aunty labeeba,duban Ummie Ammi tayi tace"bilkisou bakice komai ba,dan tamke face Ummie tayi tace"Allah yasa albarka,idan har kika bijerewa umarnin mijinki akan abinda be sabawa mahaliccin ka ban yafe miki ba"tana kaiwa nan tamike ta fice,duk sake da baki suka bita, Zuhra kuwa kuka tasaki. A hankali aka dinga raguwa a palourn,yarage daga Laila sai Nihal,cikin zolaya Laila tace"Oh mu ko dan siyan bakin nan baza'a bari muyi ba?cab wannan auren manya ne"Nihal tace"Allah yasa Yaya ya jiki,haka suka zauna su Laila na taya ta hira a gefe Bodejo na mata tsiyan kuka gulma takeyi,sai wuraren 10 sannan Sauban ya shiga palour da sallama hannunsa dauke da leda wanda aka RUBUTA Delicious Suya,sannu da zuwa suka fara masa yana amsawa sannan suka mike suka fice,kusa da Bodejo yaje ya zauna yana ajiye mata ledan a gefen ta,murmushi Bodejo tayi tana jawo ledan"me kuma kakawo min ne Saudan?tayi maganar tana bude ledan,cike da farin ciki tace"uhmmm aiko ka kyauta kamar kuwa kasan nagaji da cin wannan farfesun gwanda daka siyomin suyan nan,amma dai na rago ne ba sa ba ko? Sauban dake danne-danne a wayansa yace"Ea na rago ne nasan baki cin na sa ai,keda Amma na siya muku"murmushi Bodejo tayi cikin jin dadi tace"amma kuwa mungode Allah yayi ma auren ku albarka"tayi maganar tana kai suyan bakinta tare da lumshe ido tace"kai naji dadin naman nan sosai,ai ina gaya muku kuda kanku sai kunyi alfahari da auren nan"tana tauna namar tana magana,a kaikaice Zuhra ke zabga mata harara don ta gama ramfo Bodejo santin naman takeyi,mikewa Sauban yayi tare da zura hannayen sa a aljihu,wani mugun faduwar gaba Zuhra taji, shikenan wai dagaske akeyi bin ya Sauban zatayi yau?sai hawaye sharrrr,duban Bodejo yayi"mu zamu wuce sai da safe kici nama lafiya"cikin sauri Bodejo tace"ai ban ba matarka naman ba, Zuhra ungo zo ki amsa"ko kallon ta Zuhra batayi ba tana bin bayan Sauban cikin wani irin kuka, Bodejo tace"Oho dai algunguma anaso ana kaiwa marke(Wai market🤣) suna fita ya wani irin fisgota gabadaya tafada jikinsa,face din babu walwala ko kadan yace"Wallahi idan bakiyi min shiru ba sai na baki mamaki,uban waye yace miki nima inason ki da kike damun mutane da kuka?nima ban son ki kakaba min ke akayi"sake fashewa da kuka Zuhra tayi tana toshe bakinta don tabbas taji zafin kalman nasa(su Zuhra Ashe ba dadi,shida kike cemasa bakison sa fa?yafiki jin radadi fa.) Wucewa yayi haka tabisa har suka fice daga gidan nan securities din suka rufe ko ina,gidan sa ya shiga,gate man din shima yarufe ko ina,kaitsaye apartment dinsa ya nufa,cikin sanyin jiki Zuhra ke binsa,wani mahaukacin kamshi ne ya buge hancin ta, tabbas apartment din ya Sauban aljannan duniya ne don apartment din ya hadu,tamkar don ita akayi shi,gani tayi ya nufi stairs ya haye,samun kujera 1 sitter tayi arakube ta zauna tana lumshe ido a dalilin wani irin sarawa da taji kanta na mata,a haka ta cigaba da zama batare da ta ankare ba bacci yayi awon gaba da ita. Sakkowan shi kenan sanye da pyjamas masu matukar taushi da tsaruwa bakake,hannun sa dauke da laptop dinsa,ganin ta yayi a kwance,cikin nutsattsiyar muryan shi ya fara magana don tabbatar da tayi bacci ko kuwa"Hey! Hey wake up kada jikinki yayi ciwo,shiru yaga bata motsa ba hakan ya tabbatar masa da tayi bacci,ajiye laptop din yayi yana nufar ta,hannu yakai yana cire mata hannun da tarufe face dinta,sosai tayi masa matukar kyau dama ita me kyau ce,hakan yake fada a ransa always, murmushi yayi yana shafa lips dinta wanda yasake pink a dalilin kukan da tasha yau"Rigimammiya! Yafada yana sakin smile,daukan ta yayi cak like bby yanufi stairs da ita yana cewa"wow ashe tanada nauyi?a haka ya isa da ita parlon ya wuce da ita bedroom dinsa yana kwantar da ita, squeezing face tayi tana dan turo mouth wanda yasa point din ta lomawa,cikin baccin tace"ummm"tana sake yamutse face din,kallon ta kawai yake yi yanajin son ta na sake nunkuwa a zuciyar ta. Warware mata lutfayan yayi,anan wata gown ta bayyana ganin da yayi kamar gown din bata da nauyi ne yasashi barin matashi yana ja mata duvet din,tare da dai-dai ta mata A.C ya kashe light din ya bar mata bedside dum light,yana fita daga bedroom din,kasa ya sauka ya rufe ko ina tare da kashe fitullu ya haye saman yana rufe shima ko ina,dan balcony dake saman yaje ya zauna yana kunna laptop dinsa gefe daya fresh milk ne sai shawarma,aiki yafara inda yaketa cin karo da sakonni na abokan aikinsa suna masa congrats akan auren sa,wasu Kuma na masa iya shige,yakai wajen karfe 12:30 sannan ya tattara komai ya nufi ciki,kikkimtsawa yayi sannan yadauro alwala yayi sallah raka'a hudu sannan ya kwanta,duban ta yayi yana shafa face dinta yanajin wani sanyi,abinda yadinga mafarkin zuwan shi kenan,tun sanda aka haifeta yake da burin kasancewa da ita,murmushi ya saki sannan ya jawota jikinsa yana manna mata kiss a forehead dinta"I love you so much my life"ya furta kaman wani me rada,babu jimawa shima bacci ya suresa. Ita tafara farkawa wajejen 5:30 jinta tayi kamar ammata daurin goro cikin sauri ta bude idanuwan ta,a hankali ya sauka kan face dinsa,diddilo idanuwa tayi cike da mamaki cikin sauri ta yunkura zata tashi,batare da ya bude ido ba yace"were re you going?cikin muryan bacci,kallon sa tayi still taga bacci yakeyi seriously,batare da tayi magana ba tasake kokarin mikewa,amma sai taji yaki sakinta"uhm am talking to you"yafada,wani kuka Zuhra ta kece dashi wanda yasa cikin sauri Sauban ware idanuwan shi akanta yana sakin ta,mamaki fal ransa,ganin ya saketa yasa ta mike da sauri tare da sauka daga bed din taje can gefe tayi tsaye tana cigaba dakai,dafe kai Sauban yayi yace"kaga takanka Sauban"tamke face yayi yana mikewa,toilet ya shiga ya barta nan tsaye,ruwa tafara jiyo zuban sa,hakan ya tabbatar mata da wanka yakeyi a gurguje yafito saboda lattin da yayi be samu asuba ba,jallabiya yasaka fara tas sannan yafita a gaggauce. Wani ajiyan zuciya ta sauke tana share hawayen ta,toilet din tashiga tana wani irin lumshe ido saboda tsaruwan sa,cikin sauri tayi wanka itama tayi alwala,koda tafito lutfaya dinta ta dauka ta nada,tare da tayar da sallah,koda ta idar azkar tayi sannan tafara rera karatun alqur'an,Suratul Yusuf,daka takeyi cuz wayanta bata gani a saman ba,a haka har bacci yasake awon gaba da ita akan dadduman. Sauban wajejen 7:00am yadawo gidan, kaitsaye sashen da yake gyming ya wuce,be fito ba sai wuraren 9:00 a lokacin Zuhra ta farka ta gyara bedroom din sannan ta sakko kasa shima tadan gyaggyara duk da bawani datti. Knocking tajiyo duk a tunanin ta Sauban ne hakan yasata rudewa sannan kamar wacce aka dasa takasa mikewa,kusan minti biyar sannan tajiyo muryan sa,ku shiga mana I think tana bacci ne,tsuru tayi ganinsa da tayi batare da ya dubeta ba yahaye stairs, bayan sa Mashahuda ne da Muneefa, Muneefa dauke da basket a hannu,nufota sukayi Mashahuda na dariya kasa-kasa tace"morning Aunty amarya"haka kannen miji ke cewa ko Muneefa? Muneefa da tanufi dinning cikin muryan dariya tace"kwarai kuwa yanzu biyayya dole don matan Yaya ne, Zuhra da idanuwan ta yayi luhu luhu muryan ta na rawa tace"kai Aunty Muneefa"Muneefa tace"wani kai Aunty Muneefa gaskiya ne ai, Mashahuda tace"kinyi wanka ne? Zuhra tace"nayi sai dai bani da kayan canji"Mashahuda tajawo wani dan akwati dake gefen ta tace"ga wannan kije ki shirya kafin su Laila anjima su kawo miki kayanki,amsawa Zuhra tayi da to tana mikewa,dayan parloun ta nufa anan kasa inda taga bedroom har biyu,nan tashiga daya,shima sosai yayi kyau, biyo ta sukayi a baya,anan suka fito mata da kayan da zata sanya,wani arnen lace silver suka fito mata dashi Wanda akayi masa dinkin half bubu da street skirt yayi bala'in kyau,sai Muneefa tace tadaura dan kwalin da kanta don sun santa gwana ce akan dauri,bayan ta gama daurin tadan shafa powder kwalli nd lipstick,ta dan tace girar ta,tayi kyau sosai,takalmin ta golden high heel shoe ta sanya sai mayafinta gold shima,dan kunne da abin wuya silver,tayi kyau sosai-sosai. "Wow Masha Allah wallahi kinyi bala'in kyau little sis"cewan Mashahuda tana zuba mata hotuna,kamo hannunta Muneefa tayi duk suka fito bedroom din. Sauban ne yafito sanye da wata danyen shadda fara tasss babu aiki ko dis a jiki,daka kalle shaddan kasan naira dai tayi kururuwa bama kuka ba,sai half cover shoe blue,hulansa ma blue,yayi kyau har yagaji sajen nan tasaka zama baki sidik akan farar fatar nasa sai sheki takeyi,gefen sa abokan sa ne Taufeeq, Kareem, Aseef,sai wasu guda uku 'yan nan maidugrin,ga Mommy da Mom,kannen Ummie,sai na Ammi,sannan Rammat. Sosai yake sakin murmushi saboda ganin Zuhra da yayi,a hankali ya fara takawa babu abinda ke tashi sai wakar ciza dani,manni kawai ake musu,yana zuwa ya rungumo ta gabadaya yana sakin wani irin ajiyar zuciya,goshinta yakai ma sumba,nan akasa ihu,kamo habar ta yayi yana laluban idanuwan ta wanda ta runtse su sosai,dukawa Sauban yayi yana ciro wani dan box a pocket dinsa,atake anan wani abun wuya na gold ya bayyana,aiko nan aka sake sa tafi da ihu,matsawa yayi yana Sanya mata abin wuyan, cikin wani irin murya ya furta"I love yhu Fateema Zuhra,I can't live without you,I love you so much,yafada yana kai mata kiss a baki,ai wannan karan daga mommy,mom har sauran iyaye rufe Ido sukayi. Zuhra kuwa sandarewa tayi saboda jin abinda yace mata,haka aka cigaba da shagali,hotuna kawai akeyi a parloun inda kowa na cikin farin ciki,zuwa la'asar kowa ya watse. Xahratty CE🥰 Lallai Alqalami 🖊️ yafi takobi🗡️. [7/14, 16:21] 𝐗𝐚𝐡𝐫𝐚 𝐗𝐚𝐡𝐫𝐚𝐭𝐭𝐲🥰: 👨🏽‍🦳 *_GALADIMA FAMILY_* 👨🏽‍🦳 Page:-73/74 https://chat.whatsapp.com/Cz6pFHyd9N68OmqNx3Vpqs _____Acan angano Adda Zainab wacce sai sunbatu take saki,nacewa ba ita takashesu ba kalmar da taketa ambata kenan kamar karatu tana kuka,duban ta wani police yayi cikin natsuwa yace"hajiya ki nutsu ki sanar damu asalin alakanki da hajiya Aliya har zuwa sanda ta rasu,kuka sosai Adda Zainab tasaki nan tashiga basu labari tun daga haduwar su na secondry school,daganan ta dakata,sannan cikin muryan kuka tace"officer don Allah ku kiramun 'yar uwata bilkisou tare da Amma nafiso duk labarin da zan bayar yazama suna wajen,sannan a hadani da hajiya kareema kanwar mijina suma duk suzo tare da yarana. Haka kuwa akayi a ranar aka kira Ummie tafiyan urgent sukayi ita da Amma da Taufeeq,don mota ma suka biyo, Mashahuda kuwa dasu Mommy zata dawo,don ita kanta Zuhra bata son Ummien ta wuce ba. Bayan komawar su kaitsaye gidan Adda Zainab suka isa sannan duk 'yan sanda ne a bakin gate din gidan,cikin gidan,kofan parloun da cikin palour,dama or ready family din Alhaji iliyasu sun hadu,su Ummie kawai ake jira,aiko nan police din ya dubi Adda Zainab"Hajiya ke muke sauraro,nan Adda Zainab ta cigaba da bada labarin sannan tace"babban sake dinkewar alaqar mu da Hajiya Aliya shine sanadin bilkisou,kowa kallon Ummie yayi nan ta cigaba tana duban Ummie"tunda na mallake hankalina nafara jin tsanar bilkisou a dalilin komai da tafini yasa nakejin tsanan ta,tsanan ta besake nunkuwa ba sai da tasamu miji daga ahalin da suka fi nawa sannan nasake jin wata iriyar tsanar ta,alhalin mahaifiyar ta bata ta6a nuna cewa ba itace ta haifeni ba,hasalima ta fifitani akan bilkisou,daya ke bilkisou ta rigani aure a lokacin hankalina yatashi wanda har Amma taso a fasa bikin Bilkisou abari nima na samu miji ko kuma Sadeeq ya aure ni ya hakura da bilkisou, Allah yajikan baban mu shine ya hana hakan a lokacin naji matsanancin haushin sa,ana haka ne na hadu da Hajiya Aliya inda ta hadani da wani boka da yake nijar,salati aka Sanya gabadaya palourn, Ummie kuwa kuka kawai takeyi. Ta cigaba da cewa"Nice nasa akayi miki farraqu da Zuhra nayi amfani da kyallen jininki na kaiwa boka akayi asiri,tun daga lokacin kika tsane Zuhra,nan fa Adda Zainab tadinga bada labarin irin abinda suka dinga kullawa da hajiya Aliya har asirin da tasake yi mata da wancan ya karye,har zuwa sanda hajiya Aliya ta aure Alhaji iliyasu,da irin rigimar da sukeyi sannan tayi shiru tana jan shasshekan kuka, Ummie ma kuka takeyi tare dasu Amma,cikin kuka Amma tace"Zainab dama kece duk kike musu wannan farraqun?mahaifinku ya mutu da fushin bilkisou akan haka, fisabilillah kin kyauta kenan?cikin tu ajjabi hajiya kareema tace"lallai Zainab shedancin ki yakai inda yakai,yo wanda yayi wannan aikin ai kisa bazai mishi wahala ba,domn tuni aka cire miki imaninki"Adda Zainab cikin dasasshiyar muryan ta tana kuka tace"wallahi bani ce na kashe su Alhaji ba, wallahi"Ammar cikin muryan kuka yace"idan bake bace wanene Mom?please wanene?yayi maganar cikin muryan tsawa,islaha da kuka yaci karfin ta tace"why?why Mom?kinja mana abin fade Mom innalillahi wa Inna ilaihirraji'un ya Allah,babu 6ata lokaci aka sanya ma Adda zainab ankwa a hannunta wata mace,kuka sosai takeyi haka yaranta dasu Amma, Ummie ta dubi police din tace"Please yalla6ai yanzu ina zaku kaita?dan sandan yace"hajiya kaitsaye daganan state CID zamu wuce da ita domin gudanar da bincike yanda ya kamata,munyi muku alqawari muddin babu saka hannunta zamu saketa,idan dasa hannunta kuma zamu turata court a yanke mata hukunci"yana gama fadar haka aka tisa keyan Adda Zainab akayi waje da ita,kowa kaganshi bashi da kwanciyar hankali. ******** Yau a bedroom dinta ta kwana domin kuwa tayi alqawari bata sake kwana daki daya da Sauban,hakanne ma yasa tun kafin yadawo ta koma dayan palour kasa tare da shigewa daya daga cikin bedroom din ta kwana,hakan kuwa sosai ya sosa ma Sauban rai tare da yanke hukuncin yau da la'asar zaibi flight,ta online yasai ticket da komai nasa ya gama batare da tasani ba,da safe tana tashi ta shirya musu lafiyayyen breakfast,babu abinda ke tashi sai na room freshener da turaren rushi,gefe guda kuma ga kamshin girki,tasan Sauban ma'abocin son macaroni ne,dalilin hakan yasa tahada masa lafiyayyen macaronin sa da yaji dakakken nama yayi kyau da dadi,sannan ta dama masa kunun gyada, Ammi ma ta aiko da breakfast din kosai da custard sai wainan kwai,shiryawa tayi cikin riga straight gown,wanda ya fito mata da cikakken surar ta ko ina yacika Masha Allah, tayi kyau sosai,abinka da atamfa me dan duhu sai tayi kyau kwarai,daurin Aisha buhari ta murza mai kyau,kafarta sanye da high heel shoe brown, fitowan ta kenan daga kitchen hannunta dauke da plates taji alamun tafiyan sa,turaren sa me kamshi Arabian Oud ya buge hancin ta,dan lumshe ido tayi tanajin faduwar gaba,daurewa tayi ta cigaba da shirya dinning din. Karisowa yayi yaja kujera ya zauna,sanye yake da wata yadi me kyau tare da maiko brown colour,daka ganta kasan lallai anyi fitan nera wajen siyan ta,kansa murzazziyan kube ce,wacce kudinta zasukai dubu 35 face dinsa babu wani walwala kamar koda yaushe, Zuhra kuwa gabanta ne ya cigaba da faduwa,a hankali tayi karfin halin furta"Ina kwana Yaya"kura mata ido yayi babu ko kiftawa,almost 5 minutes sannan ya girgiza kai kawai,ajiyan zuciya Zuhra ta sauke kirjinta na cigaba da bugawa daurewa tayi tace"Yaya meza'a zuba maka?hannunsa dauke da wayar sa yana latsawa batare da yadago ba yace"meda menene akwai?Zuhra tace"akwai jallop din macaroni with kunun gyada nama nd custard wih kosai,sai wainan kwai.Dagowa Sauban yayi yana zuba idanuwan sa akan warmers din dake kan dinning din,duk da a rufe suke yace"kisamun macaroni nd kunun gyada kadan inci tukuna"yanada tabbacin itace tayi wannan, cikin nutsuwan ta take serving dinta,gabadaya ya tsareta da idanuwan sa jinta kawai take a takure, shikuwa Sauban baiki yaji Zuhra akan cinyar sa ba, wani irin shaukin son ta kawai yakeji,batare da ya ankare ba yaji maganar ta"bismillah Yaya"dan sake hade face yayi yana daukan spoon din tare da duban plate din,lumshe ido yayi yanajin wani sanyi da dadi a ransa don dakakken mama yaji a cikin macaronin Masha Allah,hadiye miyau yayi, bismillah yayi yafara cin abincin cikin mutsuwa,jiyayi wani dadi ya ratsa masa har kwakwalwan kansa,sosai yake daurewa gudun kada yayi santi,ganin ta zauna tatasa kosai da yaji tanaci yasa ya dubeta"bazaki kiyayi kanki da cin yaji haka ba?wallahi idan kikazo kina min complain din basir da ulcer ko?sai kawai yayi shiru ya cigaba da cin abincin, Zuhra kuwa dagowa tayi cikin marairaice face,tare da wata shagwa6a66iyan murya wanda ita kanta bata ta6a sanin tana da ita ba tace"kai Yaya kosai fa idan babu yaji babu dadi"wani tsam!yaji a dalilin yanda tayi maganar,batare da yayi magana ba yadaga mata kai kawai,atake anan ya cinye plate din,gyaran murya yayi mata, dagowa tayi ta kallesa,da ido yayi mata alamun akara,kara mishi tayi ba da yawa ba,itako kosan biyar taci ta basshi cuz takasa sakin jiki taci yana wajen,shiko ko a jikinsa sakin jiki yayi yaci abincin sa yayi katt,yana gamawa yadau kunun gyadan sa yafara sipping,lumshe ido yayi domin har ga Allah yaji dadin kudun sosai,be yadda yabiye ma dadin ba yadaka,don a haka ma jin cikinsa yake ya cika don dama shi ba ma'abocin cin abinci bane,tissue yadauka yafara goge bakin sa,ji sukayi anwani daka kofan palour. Da sauri suka mike, Akeela ce tashigo jikinta sanye da wata doguwar riga fitted sai dai ko kadan batayi mata kyau,sai taunar chwengum takeyi tana kare ma palour kallo,ganin canja wasu abubuwa da akayi tare da kara gyara sa,ta6e mouth tayi tana jan tsaki,nan tashiga takowa a gaban Sauban ta tsaya idanuwan ta cike tafff da hawaye tafara magana"Kaine na mijin dana fara so a rayuwa ta wanda akansa nasan menene so,amma munafukai sunyi nasarar rabani dakai a lokacin da muka kasance tare,inaso kasani wallahi bazan ta6a rabuwa dakai ba koda kuwa zanyi yawo tsirara ne sai na farauto soyayyar ka,sai nadawo cikin gidan nan matsayin mata"takarisa maganar hawayen na zubowa,duban ta ta maida ga Zuhra tana nuna ta,ke kuma inaso na Miki wata zazzafan gargani duk sanda kikasan mijina a matsayin miji wallahi babu ke babu kwanciyar hankali,banza kawai jak.....ai bata karisa ba taji saukar gigitaccen mari Sauban ya shimfida mata a fuska,sannan yana huci ya nufi wajen extension wear ya ciro cabel din caja,ai Akeela na ganin haka ta nufi kofan palour tana fita da gudu,aiko binta Sauban yayi cikin zafin nama, Zuhra kuwa da taga ma tsorata da kalaman Akeela binsa tayi jikinta na wani irin rawa.Wallahi babu macen da ta isa ta haifa maka yara saini,ke kuma kijira kiga abinda zai sameki"tana kare fadan haka tafice kamar wata zararriya, Zuhra kuwa kuka ta fashe dashi tana juyawa don ta tsorata da kalaman Akeela gani takeyi tabbas kamar wani zai farun,babu zato taji Sauban ya mata wani irin runguma,ai a haukace ta fisge jikinta tanaja baya,tsayawa kawai yayi yana kallon ta,jiyayi ta saki kuka tana hade hannayen ta waje guda,kuka yasa ta gaza furta komai,nufota Sauban yayi da mugun sauri ta kuma jan baya,tsayawa yayi kawai yana kallonta"Naroke ka da Allah yaya ka sakeni,ni bazan iya auren nan ba inajin tsoro please kasakeni nac..... batare da taji sanda yakariso ba kawai saukan mari taji a kuncin ta me azaban zugi,wani ihu tasa tana dafe kumatun tare da duban sa,jikinsa ne ke wani irin shaking,idanuwan nan nashi sunyi jajawur bakinsa na rawa"Du....dduk..duk ranar da kika sake cewa na saki wallahi sai nayi miki dukan mutuwa"yana kare fadar hakan yajuya yana maida kwallan dake kokarin zubo masa,tabbas a yanzu ya tabbatar da yarinyar nan bata son sa, kaitsaye palour yafice jikinsa na cigaba da rawa,ita kuwa Zuhra inda yabarta nan ta zube tana sake fashewa da wani irin kuka( _Nikaina Zuhra kinfara bani haushi akan kalmar sakin nan da kike fada,da mene zaiji?_ ). Tana bedroom tana sallah taji shigowan sa yahaye upstairs,har taji sanda yake sakkowa da alaman ana jan trolley bag,cikin sauri ta mike tafito,shi tagani sanye da kananun kaya, security dinsa na daukan akwatin yana fita,kafadun shi dauke da wani jakan, Zuhra lokaci guda zuciyar ta tatsinke taji kuka kawai yataho mata,a hankali ya tako har inda take,face dinsa kadaran kadahan,hannunta ya kamo duka biyun tare da sumbatan goshinta"Zan tafi insha Allah zandawo nan bada jimawa ba,Zaki koma wajen Ammi before nadawo,ina miki fatan alheri"yana kare fadar hakan yajuya yafice,sai a lokacin makalallen hawayen da Zuhra ke makalewa suka samu damar sirnano mata,tana me zama kan sofa din sharaf,tana fashewa da kuka. Shiko Sauban a tunanin sa Zuhra zata biyo sa a baya amma sai yaga akasin haka,girgiza kai yayi yana sake yarda da lallai Zuhra bata son shi,mota yashiga driver yaja,dama ya masu Ammi sallama kaitsaye sai airport, Zuhra kuwa tasha kukan ta ta koshi sannan ta mike tashiga tayi wanka sosai ta kwanta atake wahalallen bacci yayi awon gaba da ita,sai wajejen biyar ta farka tasake wanka ta shirya cikin turkey gown me yankakken hannu,tadau hijjab tasanya,abubuwan bukatan ta tadauka,dama ba komai aka kawo mata ba na kayanta,fita tayi ta kashe kowane socket nd switch na sashen har saman shi sai da tahau ta kashe komai sannan ta rufe ko ina tafito tanufi Galadima house. Cikin sanyi tashiga sashen Bodejo tafara nufa,suka gaisa nan Bodejo tafara mata tsiya tana cewa ta canza lokaci daya saboda mijinta yayi tafiya sam babu walwala tattare da ita, Zuhra kuwa da baki be iya shiru tace"Cab Allah ya kyauta,ni wannan har nayi irin wannan shakuwan dashi ne? Allah yatsare a gayas,dariya Bodejo tayi tace"hmmm yaro yaro ne koma me zakice ba yarda zanyi ba. Nan suka ta6a hira ta mike ta nufi sashen Mom,tagaishe ta aiko nan ta cidda Rammat ai zama sukayi suka sha hirarar su sosai,duk da Rammat sa'an su Aunty Mashahuda ce amma akwai saukin kai gashi nasu ya hadu da Zuhra,ba ita tashiga wajen Ammi ba sai after magrib,aiko nan Ammi tafara nan-nan da ita,duk kulawar da take bata ada sai yakaru, Ammi kuwa sai taga kamar Zuhra na cikin damuwa ne na tafiyan mijinta yasa tace"ki kwantar da hankalin ki Zuhra, yayan ki baze dade ba zaidawo kuma idan zaidawo dake zai koma gaskiya"Zuhra tace"a'ah Ammi nifa ba komai,kawai dama Akeela ne..sai kuma tayi shiru,kallon ta Ammi tayi tace"dama Akeela mene?me Akeelan tayi miki? Zuhra tayi raurau,hawaye na silalowa,nan taba Ammi labarin abinda yafaru dazu da safe,sannan cikin muryan kuka ta cigaba"ni Ammi inajin tsoron abinda zatayi mun ne,tace"idan nasan shi,duk da ban fahimci me kalmar take nufi ba,kuma ninasan shi,ba Yaya na bane? Ammi ta sauke ajiyar zuciya don ta fahimci tabbas Zuhra bata gane me hausar idan kika sanshi yake nufi ba hakan yasa taji natsuwa tace"ki kwantar da hankalinki,kinfa je islamiya Akeela ke saukakkiya ce,kinsan bawa baya wuce kaddarar sa, Akeela bata isa ta miki abinda Allah be miki ba,kisa hakan a ranki, sannan kuskure ne Wanda kema kinsa ni nacewa miji ya sakeki,kinsan zunubin hakan,sannan kinsan wani irin so Sauban ke miki? Zuhra tace"Ammi wallahi Yaya beso na kawai ya aure ni ne. Xahratty CE🥰 Lallai Alqalami 🖊️ yafi takobi🗡️. [7/15, 10:35] 𝐗𝐚𝐡𝐫𝐚 𝐗𝐚𝐡𝐫𝐚𝐭𝐭𝐲🥰: 👨🏽‍🦳 *_GALADIMA FAMILY_* 👨🏽‍🦳 https://chat.whatsapp.com/Cz6pFHyd9N68OmqNx3Vpqs Page:75/76 ____Ammi murmushi kawai tayi tana jinjina ma yarintar Zuhra,haka Zuhra ta cigaba da zaman ta a apartment din Ammi tama mance da wani Sauban sai idan taji suna waya da Ammi take tunawa dashi,sannan tasake yarda da baya sonta tunda ko kiran ta yakasa yi yaji ya yabarta,sosai taji zafin hakan,da yake sun dan samu hutun sati biyu na school hakan yasa taji tanason zuwa wajen Ummie. GALADIMA kuwa jiki Alhamdulillah don sosai aka fara ganin sauyi don har mikewa yakeyi da kansa cikin yardan Allah kuma yana dan maganar sa,lokacin da yaji Zuhra ta tare da Sauban ba karamin farin ciki yayi ba shiyasa koda Sauban din yazo nasiha yadinga masa kan ya kula da Zuhra ya riketa amana,sannan dui abinda zai gani ya mata uzuri harda yarinta. Shi kanshi Sauban din yaji dadin ganin Galadima don jiki kam Masha Allah tunda maganar ba sosai yake fita kamar da ba,sai dai ana sa ran nanda 3 days za'a sallame su gabadaya, Bodejo ita kanta tayi farin cikin hakan don da sukayi video call da Galadima har kukan farin ciki tayi mara misaltuwa. ***** Bangaren su Adda Zainab bincike sosai akeyi,inda taki amsa lefin kisan,tadai ce taje sashen marigayi Alhaji iliyasu saboda tunda suka dawo kwana biyu be lekota ba sai taje taduba ko lafiya shine tana shiga ta cidda gawansu don har kumburi sun fara,ganin da sukayi kamar Adda Zainab tafara musu yawo da hankali ne yasa aka fara wahalar da ita,don har farcen ta sai da aka cire mata,wuyan da taji ne yasa ta amsa lefin don cewa itace ta kashesu,ta barbada musu guba a abinci,dama abinda jami'an suke so kenan hakan yasa suka tattare duk wani takardun ta suka mika court inda gobe itama za'a wuce da ita,sai dai mummunan abinda yafaru da Adda Zainab shine a daren tayi mafarkin wasu irin halittu sunzo suna amfani da ita ta bayan ta,sai sai farkawar da zatayi ta farka da hauka tuburan,don tsirara tayi ma kanta haihuwar uwarta,wasu tsutsotsi suna fito mata ta bayan ta,hauka sosai Adda Zainab keyi tana sanar da abubuwan da suka dinga aikatawa da nemanta ta baya da matan nan da sukayi,nanfa hankalin jami'an yayi kololuwan tashi,a a dai-dai lokacin Kuma Ammar da Taufeeq sunzo state CID din a dalilin hujjan da suka samo na ba Adda Zainab bace tayi kisan hajiya kareema ce kanwar Alhaji iliyasu,sai suka cidda wannan tashin hankalin,tsaban kuka da Ammar keyi kamar yayi hauka yasa hankula yatashi a office din, komai ya tabbata a computer ba Adda Zainab bace tayi kisan,ga inda Hajiya kareema tashiga har palour yayanta Alhaji iliyasu tasa maganin 6era a lemon da hajiya Aliya ta hada musu,har inda suka fadi tasake dawowa tana cewa"Nasan dole wannan kisan ace Zainab ce tayi itama a kashe ta idan yaso naji da suma wadancan tsinannun yaran ko kwangilar kisan su na bada",lokaci guda aka dauki Adda Zainab sai hospital don duk a tunanin ma'aikatan rudewa ne yasata hakan don su basu farga da tsutsotsin dake fito mata ba,kaitsaye akaje aka dauko hajiya kareema da safe aka maka ta a kotu tare da gamsassun hujjoji,don da farko taso ta musa sai da aka Sanya videon kowa yagani itama tagani sannan ta yarda tafara kuka da cewa sharrin shedan ne,yaranta ma kuka sukeyi,mijin ta kuwa atake anan yasake ta tare da mata Allah wadai,don anyanke mata hukuncin kisa ta hanyar rataya tare da horo me tsanani. *_BAYAN KWANA UKU_* Ummie itace ke tare da Adda Zainab a asibiti tare da islaha,sai matan yayan Alhaji iliyasu,kuka sosai Ummie keyi tana sumbatu"Allah na yafewa Adda Zainab ya ubangiji ka bata lafiya ka yafe mata wallahi nidai kam na yafe mata,gabadaya sai ta koma ita ake ma lallashi domin zuciyar Ummie tayi ma kowa naganin ta mace me yafiya,kamar wasa Ummie haka abinta keta gaba don harta kaiga hannu take sawa a bayanta tana jawo tsutsotsi,su Amma da yayyen ta maza suma kuka kawai sukeyi,abu kamar wasa duburan ta yafara zazzagowa yana jini ga nama duk a waje,dararrakun ta kawai kakeji tana ambatan boka hatsabibi sunan shi ya zauna a bakin ta zam. Duk wanda yaga Adda Zainab sai ya tausaya mata, Ummie har hawan jininta sai da yatashi, Taufeeq yakira su Daddy ya sanar dasu halin da ake ciki don yau suka dawo da Galadima domin jikinsa Masha Allah,maganar ne dai ana ganewa ma amma bedawo dai-dai ba dama sai a hankali. Washegari su Daddy suka iso,ya zamana Bodejo kawai da Galadima aka bari don Zuhra ma ta biyosu,duk da bata tambaye sa, Ammi ce tace tashirya,daga Ammi, Mom har Zuhra kuka sukeyi, Mommy da Mashahuda kuwa har su Saba gani don tare suke da Ummie koda yaushe. Kamar wasa Adda Zainab tadinga wani irin rama,naman ta na zagwanye wa don bata cin abinci,kashi kuwa idan yana fita babu control,kowa yaki jinyar ta sai Ummie. A wannan halin ne kuma Allah yadauki rayuwar ta bata ambatar komai sai sunan boka hatsabibi har tabar gidan duniya babu kalmar shahada babu komai ( _Innalillahi wa Inna ilaihirraji'un hasbunallahu wa ni'imal wakeel,shikenan fa duk abinnan antafi cikin babban lefi wanda mutum be Isa ya yanke hukuncin tsakanin bawa da mahaliccin sa ba,masu hali irin na Adda Zainab Allah ya shiryesu,ku duba duk abinda ya haddasa hakan "hassada" shine ya jefata cikin wannan bala'in, wallahi wallahi wallahi mukiyaye kanmu da hassada domin babu abinda be sawa, Allah ka mana tsari da ita Allah katsaremu da mugun ji mugun gani Ameen!_ ) Bayan sati daya,Yasmeen ta koma hannun Ummie inda islaha take gidan ta mijinta yarike ta hannu bibbiyu dashi da iyayen sa, Zuhra kuwa satin ta daya da kwana biyu yau a kaduna,gobe ne komawar ta maidugri hakan yasa ita dasu Laila suka shirya suka nufi saloon, sannan suka wuce gidan lalle,a hanyar su ta dawowa ne wani mutumi yadinga nacin suzo su shiga ya rage musu hanya,ga rashin abin hawa gashi tafiya ce me nisa tsakanin su da gida, babu abin hawa gabadaya,tunda layin da suke tadan shiga hakan yasa dole suka hau,sannan shi ba kowa yakeso ba da alama niyyar rage musu hanya kawai yayi,har JABI ROAD kofan gate dinsu ya kaisu, gaban Zuhra ne yayi wani irin mahaukacin yankewa ya fadi,a dalilin wanda tahango,ya Sauban ne ta hango jikin mota shida ya Taufeeq gabadaya shi hankalin sa nakan motar da tayi parking,cikin sauri Zuhra ta 6alle murfin motar ta fito,idanuwan su ya shige cikin na juna,wani irin kallo ya aika mata dashi mesa hanjin mutum kadawa,domin kuwa daka kallesa kasan ransa a 6ace yake duba da yanda lokaci guda face dinsa ya sauya da wani irin mahaukacin kishi,godiya su Laila suka ma me motar sannan suka nufota, Laila na cewa"tundazu ya isa ace kinshige har mun kariso...shiru tayi a dalilin wanda tagani,itama jikinta ne yayi sanyi da irin kallon da taga yayan nama Zuhra, Nihal kuwa gigita tayi da tsoro hakan yasa da wani irin azababben gudu tashige gate din. Laila ce ta kamo hannun Zuhra,sumumi-sumumi suka wuce suka shiga gidan,nannauyan ajiyar zuciya Laila ta sauke,itako Zuhra hakanan tanemi natsuwar ta tarasa,ko ada da sukafi 'yar tsama be ta6a mata irin wannan kallon na yau ba. Shiyasa suna shiga kaitsaye bedroom din Ummie ta shige tana sauke numfashi. Shikuwa suna shigowa yabiyo bayan su, tana cikin cire gyalen ta Laila tashigo tace tazo ya Sauban na neman ta,sannan daka kalle face din Laila kasan ba lafiya ba. Cikin sanyi suka fito sun cidda kowa cirko-cirko har mommy, Mashahuda, Taufeeq, Ummie,wani mugun kallo Sauban ke aika mata dashi,tsayawa tayi cak taki karasowa kanta a kasa, muryansa tajiyo kamar zai tsaga palour,idan kika bari nazo nan saina tattaka kanki,kirjinta ne ya cigaba da bugawa a hankali ta shiga takowa"Na hanaki shiga motan tsinannun mutanen nan bakiji ko?yayi maganar idanuwan shi na diddilowa cike da kishi"wallahi duk ranar da nasake ganin kin shiga motan wani da sunan lift sai naci uban shi,wallahi sai na dauresa ko dan gidan uban waye,ke kuma sai na baki mamaki tunda kunnen kashi ne dake,ku kuma"yayi maganar yana nuna su Laila"Duk sanda zaku fita wata tasake dauko min mata sai naci uban yarinya a gidannan"yasake maganar yana huci,duk tsit palour yayi don Sauban idan yana fada kamar mahaukacin Zaki yake komawa, Ummie da Mommy kuwa sunji matukar dadi don kishinta ne bayyane a idanunsa. Itakuwa Zuhra juyawa tayi tana turo baki sai da takai dai-dai stairs tajuyo sannan tace"Kai da baka so na sai kabar masu so na su soni,ai da wani irin firgita yake duban ta,sauran 'yan palour kuwa da wani tsananin mamaki suke dubanta,ganin hakan yasa da gudu ta haye stairs,aiko Sauban ya rufa mata baya,tana kokarin danno kofan bedroom dinne ya kuwa danno kofan yaturo,kamar mayun wacin zaki yayo kanta,fisgota yayi ya kifa mata mari,aiko Zuhra ta bude baki da niyyar ihu,ai babu zato taji mouth dinsa cikin nata,wani mugun cafka yama lips dinta wanda yasata kwakufosa saboda zafin da taji,aiko nan yashiga punishing dinta da mouth, sosoai Zuhra ke hawaye babu bakin ihu ita kadai tasan azabar da takeji juya kai kawai yakeji,don jitayi kamar ana yayanka mata lip to pieces,hawaye takeyi sosai. Acan downstairs kuwa Mashahuda ta dubi Mommy tace"Mommy please kije kinsan halin Yaya da zuciya kada yazo yana ta dukan ta ne kuma ya hanata ihu"Mommy tace"Sauban bazai ta6a dukan Zuhra ba sai dai punishing dinta"Ummie tace"ai baby sai ana maganin ta rashin kunyar ta yawa ne dashi, Allah ya kyau ta,tana gama fadar hakan tanufi kitchen, Taufeeq yaja hannun Mashahuda yana mata rada a kunne,aiko nan suka shiga dariya kasa²,su Laila suka bi Mommy apartment din ta,tsawon 4minutes Sauban ya dauka yana azabtar da ita,sai da ya tabbatar ta shiga taitayen ta sannan ya saketa,aiko ta daddage tasaki wani irin kuka Saboda yanda taji lip din kamar ba a bakinta ba,tsananin azaba,duk beyi jini ba sai dai yayi mugun komawa pink,kuka sosai Zuhra keyi,shiko Sauban ficewan shi yayi yabar ta nan yanajin kukan nata har ransa,sai dai yanda yakeji yasa ko tunanin tausaya mata bayaji. After sallan isha'i su Laila duk suna sashen Ummie harda Mashahuda da Taufeeq suna dinner, mommy nacan wajen Abba don yadawo, Ummie ta dubi Yasmeen wacce takoma silent sam batada hayaniya yanzu tace mata"Yasmeen jeki kicema Zuhra tasakko injini kafin nahayo stairs din, Yasmeen tace"tom Ummie"sannan tamike,babu jimawa tasakko tace ma Ummie gatanan zuwa,tuwon semo akayi miyar ugushi da yaji busasshen kifi,sai farfesun kayan ciki,wani zazza6i ne yayi mugun lullu6eta,da kyar take iya tafiya,tana sanye da night gown me dan kauri,kanta sanye da hula,kujerar da zata zauna tana gefen ta Sauban ne,yimusu Ammi da Taufeeq sannu da gida tayi sannan taja kujera ta zauna, serving dinta Laila tayi kokarin yi,cikin sanyin muryan ta wanda yadan dashe saboda kuka tace" bazanci ba banjin yunwa"Ummie tace"ba tun breakfast bane a cikin ki?Koda kuka fita taci wani abu ne"Ummie tayi maganar tana duban Laila, Laila tace"Babu abinda mukaci"Ummie tace"yi serving nata,cikin muryan jin jiki Zuhra tace"Ummie idan naci zanyi amai inajin fever p sosai"dagowa yayi ya kalleta,sosai yaga tayi wani irin yaushi,a hankali yakai hannu ya ta6a gefen neck dinta,cikin sauri ya janye hannun yana cewa"what's wrong with you? Zuhra tace"inajin fever me tsanani a jikina"Ummie tace"shine bazaki sauko kiyi magana ba?kenan da bance a kiraki ba sai nashigo kwanciya zan ganki a yanayin? Allah ya shiryeki"dariya Taufeeq yayi cike da tsokana yace"taji aikin manya,yau anyi punishing dinta"yakarisa maganar cikin dariya,hararar Sauban ya watsa masa,itako Zuhra shiru tayi kamar ruwa ya cita,ajiye spoon din hannunsa yayi yace"kije kisawo hijjab kizo muje hospital"yayi maganar ko a jikinsa, Zuhra kuwa wani irin nauyi taji ganin kowa a wajen shikam beda kunya,duban Ummie tayi wacce kamar ma batasan abinda ke faruwa ba,abincin ta takeci hankali kwance. "Magana nake miki"tajiyo muryan sa,a hankali ta mike tahaye stairs,zuwa can tafito sanye da jalbab maroon,mikewa Sauban yayi"Ummie bari muje mu dawo"yayi maganar yana wucewa ya fice, Zuhra karasowa tayi tace"Ummie mun tafi, Yaya muntafi"Ummie tace"Allah yakara lafiya,ya Taufeeq kuwa cike da tsokana yace"Asiyo mana tsaraba Mrs Muhammad!dariya su Laila suka, Mashahuda tace"Nima haka please"shiru Zuhra ta musu ta fice,jitayi ankamo hannunta cikin sauri ta dago don tabbas ta tsorata,kashe mata ido daya yayi yana shafo lips dinta,cikin wani irin murya yace"lips din yasakar miki da fever ko?shiru Sauban yayi,matse mata hannu yayi yace"I am talking to you Mrs Muhammad Taleeb Muhammad"dagowa tayi da sauri tana kallon sa. Xahratty CE🥰 Lallai Alqalami 🖊️ yafi takobi.🗡️ [7/15, 19:14] 𝐗𝐚𝐡𝐫𝐚 𝐗𝐚𝐡𝐫𝐚𝐭𝐭𝐲🥰: 👨🏽‍🦳 *_GALADIMA FAMILY_* 👨🏽‍🦳 Page:- 77/78 ____Kauda kai yayi cikin basarwa,bude mata motar yayi ya zaunar da ita,sannan ya rufe yazaga ya bude ya shiga,nan yaja motar suka bar anguwan kaitsaye wani Private hospital me kyau ya kaita,koda aka duba ta fever ne kawai ke damun ta,hakan yasa Doctor rubuta musu magani, Sauban besiya anan hospital din ba,daukan ta yayi yakaita wani hadadden eatery wajen yayi kyau,zama sukayi babu jimawa wani ma'aikacin gidan cin abincin yazo,cikin girmamawa yace"yalla6ai me za'a kawo muku?duban Zuhra Sauban yayi yace"Mrs MS me za kici?dan langabar dakai Zuhra tayi don harga Allah amai takeci,tanajin tsoron taci tayi amai hakan yasa tace"please Yaya banajin yunwa banso nayi amai,dan tsuke face yayi babu alamun wasa yace"zakisha magani kuma bazakici komai ba?malama dole kici wani abu"cikin sanyi da rashin mafita tace"shikenan! Kallon ta Sauban yayi da sauri don da alama bata da yanda zatayi ne amma tabbas batajin cin koman,shi kuma be yarda ta zauna da yunwa ba don zata sha magani,duban ma'aikacin Sauban yayi"kanaji?ka kawo mana pizza karamin box nd hollandia yoghurt,me strawberry flavor nd vanilla"da sauri Zuhra ta dubesa don tayi mamakin da yasan tafison strawberry, ma'aikacin yace"angama yalla6ai,wucewa yayi be wani dade ba yadawo hannunsa dauke da kayayyakin,a gefe ga extra leather bag"Sauban yace"yawwa sa mana a leather bag din kawai muwuce"amsawa ma'aikacin yayi da to yana sawa, tambayar shi bill yayi, nan yake sanar dashi 5500,hakan yasa yabashi 6000 tare da cemasa yarike canjin,godiya guy din yayi shi kuma ya kama hannunta suka bar wajen. Sai wajen 10 suka isa gida,kaita apartment din Ummie yayi sai da ya tasata don cin pizza din amma taki,tamke face yayi yace"farfesun fa? Zuhra gudun matsala yasa tace masa zataci,da kanshi yashiga kitchen ya hado mata,da kanshi yadinga bata farfesun,ai bata gama ba tafara yunkurin amai,duk kokarin ta na ganin ta tsaidashi ina takasa,nan tashiga kelaye amai, Sauban kuwa sosai yaji damuwa,bayan tagama toilet yakaita ya ajeta yace ta gyara jikinta,shikuwa duk kyankyaminsa zama yayi ya gyara palour sosai,sannan ya koma toilet din lokacin Zuhra tana daure da towel hakan yasa takasa fitowa,tambayar ta yayi koda matsala ne?nan take sanar dashi hijjab dinta. Komawa yayi ya dauko mata,sannan tabude toilet din ya tura mata,tasa sannnan tafito,kamata yayi ya zaunar da ita gefen gadon, magungunan yabata tasha,sannan yabata Hollandia shima sosai tasha,kamata yayi dakanshi ya haye da ita upstairs,ganin Ummie a palour yasa ya ajeta a palourn gefen Ummie, Ummie yi tayi kamar batasan meke faruwa tashiga tambayar su sun dawo?amsa mata Sauban yayi da ehh, Ummie tace"kashiga da ita bedroom kawai nima yanzu zan shiga kace gobe zaku koma right? Sauban yace"yesss Ummie insha Allah wajen 11:00am nakeso mu fita"Ummie tace"to ka kaita,kamata yayi suka shiga ya kwantar da ita, runtse ido Zuhra tayi a dalilin jinda tayi yabata peck a kumata,kamar me rada yace"kibar ganin ina lalla6aki bashi zai hana idan kika mun lefi na hukunta ki ba,Okay?shiru Zuhra tayi don harga Allah bacci takeji,babban damuwar ta kalmar Akeela takasa gane me hakan yake nufi tana neman me mata karin haske,gashi batajin zata iya tambayar Ummie,tun tanajin hirar Ummi da Sauban har bacci yayi awon gaba da ita. ******** Ba kajin karar komai sai na nishinsu da ihun su a dakin, Akeela ce da Suby suke aikata madigo ko wacce cikin fitan hayyaci take,domin sun riga sun lula wata duniya, Mom din Akeela ce tun sanda abinnan yafaru takasa samun natsuwa ta zauna tayi karatun ta nutsu tana ganin kamar ahalin GALADIMA ba zasu yima Akeela sharri ba,su me rufa mata ma asiri ne,hakan yasa tatashi domin taje suyi magana,don ita batanan taje makota da akayi rasuwa gaisuwa so batasan Suby ma tazo ba,murda handle din kofan bedroom din Akeela tayi,nishi tadinga ji kamar irin wanda ake.....hakan yasa cikin hanzari ta murda handle din,abinda tagani ne yasata sakin wani irin mahaukacin ihu wanda yajawo hankalin Alhaji mansir da dawowan shi kenan daga wajen Guggo Laure,cikin hanzari ya taho yana tambayar lafiya?abinda yagani ne yasa shi yin baya da sauri yana runtse ido, Akeela da Suby kuwa kokarin neman abinda zasu rufe jikinsu suke sun kasa,gabadaya sun rude,don kururuwa sosai Mom din Akeela keyi,hakan yajawo hankalin matan Baba Sani da mujaheed,ganin inda Mom din Akeela ke tsaye tana ihun yasa Mujaheed nufan wajen,dasauri ya juya yana runtse idanuwan sa, Mom din Akeela kuwa bata dena ihu me hade da salati ba,hakan yasa Guggo Laure shigowa,da sauri matan Baba Sani ta toshe ma Mom din Akeela mouth"maimuna!maimuna!!please kada kitara mana jama'a don Allah"jin wannan maganar da Mom din Akeela tayi yasata dawowa hankalin ta, Guggo Laure ta matso tana"meke faruwa ne ake kada a tar......shiru tayi takasa karisawa a dalilin tozali da tayi da Akeela da Suby haihuwan uwar su day ubansu, gefe guda kuma al'auran maza ne irin na roban nan daure a kwankwason Akeela"innalillahi wa Inna ilaihirraji'un innahu min sulaimanu wa innahu bismillahir rahmanir rahim,nashiga uku ni Laure na lalace,Ashe dama da gaske ne?kuka wiwi Alhaji Mansir,mom Akeela,da Guggo Laure keyi, Guggo Laure ta cigaba"wallahi Akeela kin cuce mu, yanzu da wani ido zan kalle Yaya Muhammadu da 'yayansa?dama sunce mune da jin kunya ashe da gaske ne"takarisa maganar tana wani irin kuka,da wani irin mugun fusata Alhaji mansir yadauko wayan radio aiko ya rufe ido yana dukansu kota ko Ina,ihu Suby da Akeela keyi suna rokonsa,amma ina dukan su yakeyi bayaji baya gani sai da ya musu jina-jina sannan ya rabu dasu don ko motsin arziki basu iyayi sai numfarfashi,sannan yadubi Suby yace kafin ya kirga ashirin ta tashi tabar masa gida,ko ya fice da ita tsirara,jin haka yasa Suby a hanzarce saka kayanta tadau long hijjab dinta tasa tafice tana kuka,baki ya kumbura yayi suntum! Komawa dakin Alhaji mansir yayi ya cigaba da dukan Akeela,gabadaya Baba Sani yakasa kwatanta, Guggo Laure kuwa fadi take"ai Akeela da haihuwar ki gwara asarar cikin ki,maimuna ta haifa mana kamiyamiya ta haifa mana annoba, cikin kuka Mom Akeela tace"kiji tsoron Allah Guggo,ki tuna akwai mutuwa akwai hisabi,duk abinda Akeela ta zama kinada kamasho,don duk cikin jikokin ki babu wacce kika sangarta kamar Akeela,kece bakiso a kwa6a mata,kika nuna duk abinda zatayi dai-dai ne,idan kin manta niban manta shekaru 24 baya Akeela ta zubar min da mangyada daga na dungure ta kika dinga fada har sai da takai ga Alhaji ya sakeni saki daya,ko kin mance ni?wallahi kece silar lalacewan Akeela"kuka Guggo Laure tasa takasa furta komai,domin duk abinda maimuna ta fada gaskiya ne. Sai da yaga tadena numfashi ya rabu da ita,don sai da ya zubar mata da hakora biyu na gaban bakinta,kuka wiwi kamar yaro haka yakeyi,duk cikan su suna zaune jigum-jigum,wani yaro ne yayi sallama,bayan sun amsa ne yake cewa wai mutane na sallama da Alhaji mansir a waje,gabansa ne yafadi aka shiga kallon², Baba Sani yace"mutane kamar yaya? yaron yace"su Malam sahabi ne dasu Malam Gaddafi"Baba Sani yace"tohm kace yana zuwa,su uku suka fita har da mujaheed,nan suka tadda dandazon matasa su shidda sai manya uku,hannu suka mika suna musabaha,su kuwa matansa sai wani ciccin magani sukeyi, Baba Sani yace"Malam sahabi lafiya kuwa?wanda akakira da Malam sahabi yace"Gaskiya ba lafiya ba kuka ganmu haka,wani video ne mummunan video,babu kyan gani yau muka wayi gari yanata trending a social Media,videon Akeela na wajen ku,videos kusan uku anwatsa a duniya tana aikata madigo,tsirara,zindikiya,haihuwar uwarta da ubanta? innalillahi wa Inna ilaihirraji'un,shine matasa sukazo suna cewa su bazasu yarda ba kada ta lalata musu yaran anguwa. Shiru duk su Baba Sani sukayi saboda sun shiga wani hali na kunya da tozarci,a dalilin yanda hankulan mutane yafara dawowa kansu, baba Sani yace"malam sahabi don Allah kuyahakuri anjima idan anyi bincike sai a tabbatar da komai"aiko nan matasan nan suka botsare inda kowa yadinga bada labarin irin shedancin da Akeela keyi,dakyar aka samu komai ya lafa sai dai magana fa ta tabbata Akeela 'yar madigo ce,kuka sosai Alhaji mansir yakeyi, duban Akeela yayi cikin muryan kuka"Allah ya isa tsakanina dake Allah, Allah sai yamin sakayya a irin tozarcin da kikamin,Baba Sani cikin 6acin rai yace"wai me kake fada ne haka mansir?idan fa hankali ya gushe hankali ke nemosa,wani Allah ya isa zaka mata? addu'ah shine mafita amma ba baki ba,cikin kuka Mom Akeela tace"kadai fada masa Yaya Kuna kallo a gidan nan,shida Guggo ne masu 6ata Akeela sai kuma da talalace ne yake kokarin mata baki?takarisa cikin fusata,shima Alhaji mansir yace"wallahi kika sake magana maimuna sai na mugun sa6a miki"cikin kunan zuciya Mom Akeela tace"duk abinda kamin abakin auren ka,don dama ni aka cuta don Akeela kadai na mallaka"tana kare fadar hakan ta wuce tana kuka,sukam sunga tashin hankali. ***** Cike da gajiya suke tunda suka dawo Zuhra ta kwanta bata farka ba sai yanzu don dama tanajin zazza6in sai dai bekai na jiya ba, toilet ta shiga ta watsa ruwa sannan ta sauko daga stairs din, kitchen tashiga saboda wata irin yunwa da take kwakular ta,dambun naman da Ummie ta musu ta zubo sai yoghurt da tadauko a fridge, bomshort ce a jikinta da vest,kasan carpet ta zauna sannan tafara shan magungunan ta,door bell taji yafara ring hakan yasa ta mike,budewa tayi aiko cikin farin ciki da harka tace"Aunty Rammat kece?sannu da zuwa shigo,itama Rammat murmushi takeyi zama tayi a dayan palour ba na baki ba, Rammat tace"nashiga ne shine naji ance baki da lafiya shiyasa nace bari na dubaki"cikin jin dadi Zuhra tace"Gaskiya naji dadi bari na kawo miki lemu da snacks wallahi banyi girki bane"Rammat tace"eyyah kada kidamu a koshe nake ma da kinbarshi"Zuhra bata saurare ta tawuce cikin kitchen,a tray ta hado mata komai tajawo stool ta ajiye tray din akai. "Aunty Rammat biki nata gabatowa sai jiya naga anko a wajen Mom,gaskiya lace din yayi kyau,atamfar kanuri day da za'ayi itama tayi kyau ga biki saura 3 week's"Rammat tace"Aikuwa dama ba wani events za'ayi ba banda wannan,shima don na matsane"Zuhra tace"ayya Allah ya nuna mana"Ameen Rammat ta amsa dashi sannan suka cigaba da hirarsu abinsu,sai wajen 2:00 Rammat ta tafi,shiru Zuhra tayi tana mamakin inda ya Sauban yaje haka bedawo ba,mikewa tayi tahau saman sa ta fara gyara masa duk da ba wani datti ba,juyawan da zatayi taci karo da wani dan book me kyau da tsaruwa,hannu takai ta dauka tana budewa cike da sha'awa,zaro idanuwa tayi a dalilin abinda taci karo dashi,pic dinta tagani ranar tana sanye da wata Dubai gown a kasa anyi rubutu kamar haka _My heartbeat_,cike da mamaki ta bude wani page din,cikin sauri ta samu waje ta zauna don ganin wani pic din nata akasa shima anyi rubutu kamar haka _Itadin duniya tace kuma rayuwa ta ina tsananin son ta tun randa Allah yakawo ta duniya har zuwa wannan lokacin,ina kaunar ta da dukkan rayuwata,cuz itadin numfashi na ne,duk wata mace dazan mallaka a bayan ta take,bata kaita ba kuma bazata ta6a kaita ba domin itadin ta musamman ce....i love you my Surur Qalbeey🥰_,ga date shima tun 12/4/2018. Zuhra zaro ido tayi a fili tace"shekaru masu yawa haka?cigaba tayi da budewa tana ganin abubuwa masu tsananin al'ajabi da mamaki wanda lokaci daya taji wani irin mugun tausayin yayan nata don har bayani yake akan yanda yakasa tunkarar ta da maganar soyayya shi kuma bazai zuba ido ta aure wani bashi ba,cigaba da karantawa tayi har zuwa randa aka kirasu ana sanar da ita an daura mata aure dashi,wani hawayen tausayin sa ne ya kamata a fili tace"Allah sarki Yaya dama duk abinda yakemin ba kiyayya bane tsantsar kishi ne?sorry yaya na,duban frame din gefe wanda pic dinsa ke jiki tayi,sanye yake da kayan cricket da sandar a kasar Malaysia ne yayi masifan kyau,shafa photon tayi tana juyawa da niyyar cigaba da aikinsa. Gabanta ne yayi wani mugun yankewa ya fadi a dalilin Ido hudun da sukayi dashi,hannayensa kalmashe a kirjinsa ya tsuke face,nan ya shiga takowa idanuwan sa a kanta,cikin sauri Zuhra ta sunkuyar dakai tare da runtse idanuwa,hannunsa taji ya riko waist dinta tare da turota ta fado kirjinsa,dayan hannun yakai yana kamo ha6arta"bincike kike yimun a bedroom?cikin sauri Zuhra ta bude ido tare da kauda kai, Sauban ya sake matse mata waist hakan yasa ta furta"Ouch! Yace"ba magana nake miki ba? Cikin shagwa6a66iyan murya tace"Nifa ba bincike nake maka ba"a yanayin yanda tayi maganar yasa yaji wani abu ya fisgesa,cikin sauri yakai mouth dinsa cikin nata,kwalo idanuwa Zuhra tayi don a tunanin ta muguntar da yasa ba yimata ne yau ma zai maita,sai dai sa6anin haka,jitayi yana mata wani irin salo, zazzafan kiss yake aika mata,wanda yasata jin wani iri,jin abinda bata ta6a jiba,tsintar kanta tayi da kokarin biye masa,hakan yasata tura yatsun hannayen ta cikin kwantacciyar suman kansa.🏃🏽‍♀️🏃🏽‍♀️🏃🏽‍♀️ Xahratty CE🥰 Lallai Alqalami 🖊️ yafi takobi🗡️. [7/17, 17:20] 𝐎̃𝐔̂𝐌 𝐀̃𝐉𝐌𝐄̨𝐑𝐋💜🤍: 👨🏽‍🦳 *_GALADIMA FAMILY_* 👨🏽‍🦳 Page:- 79/80 _____Sosai Sauban ke romancing Zuhra wanda hakan yafara bata tsoro,domin batasan yamutsa masa gashin da takeyi bane yasashi sake susuce mata,hankalin sa yayi kololuwan tashi ba tare da ya ankare ba yaji kukan Zuhra saboda mahaukacin romance din da yake mata dayasa yakai hannunsa state government,hakan yasata rudewa ta sakin masa kuka sosai. A hankali ya dena mata abubuwan da yake mata yana janye mouth dinsa cikin nata,maida kanta yayi kan kirjinsa yana shafa mata baya,alamun lallashi,bakinsa ya gaza furta komai,idanuwan sa sunyi wani laushi sun sake zama sexy eyes,tanajin bugawan numfashin sa abinda ya bata tsoro shine kalaman Akeela ne suka fara dawo mata kunne,cikin sauri tayi kokarin fusge jikinta tayi,shi kuma yaki bata daman haka,hakan yasata fashewa da kuka. Dagota yayi yana kamo face dinta"what's wrong with you?yayi mata tambayar yana kura mata ido,kasa kallon sa tayi saboda wani mugun jin nauyin sa da take,dakyar tayi karfin halin fadin"Nothing....ummm banyi komai ba"dubanta yayi"like wat?ya furta hakan, Zuhra tace"I mean banyi girki ba cuz..sai kuma tayi shiru, Sauban ya saketa tare da nufar kofan bathroom yace"don't worry nima yanzu fita zanyi,babu zato yajiyo muryan ta"Again!! Ita kanta batasan ta fada hakan ba,tsayawa yayi tare da juyowa gabadaya yana dubanta,murmushin gefen baki yayi yatako zuwa inda take,hannun ta ya kama yanufi bathroom din da ita,nan ya hada musu ruwa cikin jacuzzi,kayansa yashiga cirewa,hakan yasa Zuhra runtse ido gam tafara addu'o'i,murmushi kawai Sauban yayi yana taotsan lip dinsa na kasa,babu zato taji yafara ciremata vest dinda ke jikinta,da mugun sauri tabude ido ganinsa tayi daga shi sai boxes,hannunta takai kan nasa don kokarin hanasa,buge hannun nata yayi yana me tsuke face,cigaba yayi da cire mata vest din, Zuhra kuwa jikinta babu inda baya shaking,wani shocked Sauban yaji a dalilin cin karo da yayi da dukiyar fulanin ta,don batasan bra ba,duk da suna da girma hakan be sasu russunawa ba tsaye suke cak. Cikin sauri takai hannayen ta da niyyar karesu tana sakin kuka lokaci guda, Sauban kuwa jikinsa ne yadau rawa,da hanzari ya cire mata bomshort din,anamma saranda yayi Saboda kayan ruwan Zuhra,daukan ta yayi kacokar yasakata cikin jacuzzi din,gabadaya ya sake wani susucewa one time. ******* Sosai damuwa ya shiga cikin gidan su Guggo Laure gabadaya kunyar jama'an layin sukeyi musamman tunda anyi rasuwa hakan yasa maganar ta tunda yawo a society din, Akeela kuwa ba karamin tashi hankalin ta yayi ba,bata ta6a zaton Zuleey zatayi mata wannan cin amanar ba don itace ta watsa video's dinta a socially media,tayi kuka sosai sannan ita kanta tayi Allah wadai da irin rayuwar ta,a gefe guda ga mahaifin ta dake mata Allah ya isa, mahaifiyanta kuwa kuka kawai takeyi,ga maganganun da Guggo Laure keyi masu zafi tana yayya6a akanta. Cikin tsananin damuwa tafito palour su nan ta cidda hajiya maimuna,cikin muryan kuka takarisa gareta"Mom don Allah ki yafemun wallahi sharrin shedan ne,bazan sake ba ki roki Baba ya yafemun, Alhaji mansir cikin 6acij rai yace"Akeela idan kika sake kirana da Baba sai na canza miki kamanni, nayi dana sanin haihuwar ki, Allah kuma ya is......cikin 6acin rai Baba Sani ya fara magana"Wai Mansir kana da hankali kuwa?tundazu kake mata Allah ya isa,so kake tasake lalacewa?sai kuma ya sassauta"inaso kasan cewa hannun ka baya ru6ewa ka yar,duk abinda yafaru mubar shi a kaddara komai mukaddari ne,dole kuma muja Akeela a jiki jinin mu ce bamu da yarda zamuyi"Guggo Laure tace"gaskiyan Sani ne Mansir,me faruwa ya faru domin kuwa cuta dai Akeela ta cuce mu sai dai fatan mata shiriya"haka dai suka cigaba da tattaunawa cikin jimami da damuwa. ******* Ammi ce tafito daga kitchen hannunta rike da cup ta nufo Zuhra,samun gefen tayi ta ajiye cup din"kiyi maza ki shanye wannan kafin nadawo wajen Daddyn ku,idan kika shanye akwai wani ma"Zuhra amsawa tayi da to sannan ta dau cup din,tafara shan abin,lumshe idanuwa tayi tana sakin murmushi"Ummm ashe da dadi ai nayi tunanin magani ne Ammi tabani"Zuhra ta furta tana sake Kai spoon din mouth dinta,cigaba da sha tayi cikin natsuwa. Sallaman su tajiyo shida Kareem,amsawa tayi batare da ta hada ido dashi ba,samun sofa suka zazzauna, duban inda Kareem yake tayi"Yaya Kareem barka da zuwa"cikin murmushi Kareem yace"amaryan mu barka dai da wannan lokacin,ya gida ya garin? zuhra tace"Alhamdulillah ya shirye-shiryen biki? Kareem yace"Alhamdulillah ai gashi nan munata fama babu zama please ayi hakuri na rike oga abin ne sai a hankali"murmushi kawai tayi batare da tayi magana ba, Ammi ce ta fito, duban ZUHRA tayi tace"kin gama sha ne? Zuhra tace"Yess Ammi na gama,kuma yayi dadi juice me sunan shi?hararar wasa Ammi ta aika mata dashi,dariya Zuhra tayi tace"please Ammi ki karamin serious da dadi"Ammi tace"kitashi ki hado musu abinci tukuna kidawo"mikewa Zuhra tayi,da kallo Sauban ya bita yarasa dalilin da yasa yake kaunar tafiyar ta,nan suka shiga gaishe da Ammi,cikin kulawa take amsawa, Zuhra bata wani jima ba tadawo hannun ta dauke da babban tray wanda wamers ke kai sai plate nd spoon,bayan ta ajiye musu komawa tayi ta dauko wani madaidaicin tray wanda bottles water guda biyu ke kai da juice sai glass cup's biyu. "Sannu da aiki matar oga muna godiya"Kareem yayi maganar cike da tsokana, harara wasa Sauban ya galla masa yana cewa"kaji dashi munafuki da alama bakin ka da magana,guntse dariya Kareem yayi batare da yayi magana ba yajawo tray din don azababbiyar yunwa yakeji,serving dinsu yayi kowa da plate dinsa,sannan suka fara cin abincin, mikewa Zuhra tayi don basu waje,muryan shi ta jiyo"kada kiyi nisa don zamuje anguwa ne". "Okay! Kawai tafada tana nufar dinning taja kujera ta zauna,chat takeyi dasu Laila sai iskanci suke mata wai kila ma ta harbu. Basu wani jima ba suka g Kammala,hakan yasa yace mata tazo suje,mikewa tayi tahaye stairs don cema Ammi sai sun dawo, murmushin jin dadi Ammi tayi don taga kamar duk cikan su sun fara rike auren da muhimmanci,dama Zuhran ce abinji. Long hijjab tasaka onion colour da yake t shirt nd three quarter ne a Jikinta,sosai hijjab din ya rufe mata ko ina,shi ya bude mata motar da kanshi ta shiga sannan ya zaga shima ya shiga, Kareem shima ya bude ya zauna cike da bar kwsnci yace"Haba oga wannan ai son kaine nima ya kamata ka bude min motar ne nashiga"harara Sauban ya aika masa dashi,Zuhra kuwa murmushi tayi tana duban gefen titi, shi kuwa ta mirror yake kallon ta bini bini kadan,tafiyar minti 7 ta kawo su gidan su Kareem parking yayi a bakin gate din,bude motar Kareem yayi ya fita yana musu a dawo lafiya,ta jikin mirror Sauban ya dube ta"ki dawo gaba ki zauna"Zuhra gudun matsala yasa ta bude murfin motar ta fito tashiga ta rufe,tayar da motar yayi yana sakin ajiyan zuciya,da sauri Zuhra ta dubesa,daga mata gira yayi hakan yasa cikin sauri ta kauda kai,hannu yakai tare da kamo ha6arta yace"yadai 'yan mata na?na miki kyau ne?runtse Ido Zuhra tayi batare da ta tanka sa ba,babu zato taji mouth dinsa kan lips dinta,cikin sauri ta bude ido,a dai-dai lokacin me motan bayansu ya sakin musu wani uban horn,a hankali ya zare bakinsa cikin nata,yana maida hankali ga driving din. Da sauri ta dukar dakai,shikuwa bini-bini kadan sai ya kalle ta,wani hadadden boutique yayi parking a parking lot,fita yayi sannan ya zaga ya bude mata itama ta fito,nan suka shiga. Kaya nagani na fada ya hado musu ita dashi ya siya musu wata mahaukaciyar shadda 15 yrd 160,000 haka ya biya sai jaka da takalmin Zuhra 58,000,hulanshi da takalmin shi 52,000,sai 'yan kunne da abin wuyanta da agogo 37,000 sosai Sauban ya kashe mahaukatan kudi wanda ita kanta Zuhra binshi da kallo kawai takeyi,bangaren mayafai suka nufa. *_MURA YA SAKANI A GABA FA INAJI A CIKINA WALLAHI,MANAGE IT._* [7/19, 20:24] 𝐎̃𝐔̂𝐌 𝐀̃𝐉𝐌𝐄̨𝐑𝐋💜🤍: 👨🏽‍🦳 *_GALADIMA FAMILY_* 👨🏽‍🦳 Page: 81/82 ____Wani irin kulawa na musamman ke bawa zuhra duk da ba wani sakin jiki tayi dashi ba a dalilin kalmar da Akeela ta fada mata,kamar kullum suna zaune ne a dinning suna breakfast,wayar sa ce tayi ringing batare da yabi takanta ba ya cigaba da breakfast dinsa musamman da yaga baƙuwar lamba ce,wani kiran yasake shigowa still be waiwayi wayar ba sai da akayi 3miss call a na huɗun ne yakai hannu yaɗau wayar yana ɗan jan tsaki ƙasa-ƙasa,da yake a handsfree ya saka wayar hakan yasa akejin komai,sallama daga can ɓangaren akayi,lokaci guda Zuhran zuciyar ta tayi wani tsalle tare bugawa tana saurin duban sa,shima ita yake kallo yana amsa sallamar,daga can ɓangaren aka fara magana. "Ina kwana? fatan katashi lafiya? tsuke face Sauban yayi yana fadin"lafiya lou"dan murmushi akayi daga can ɓangaren sannan aka sake karya murya"Sunana Zulaihat wanda akema laƙabi da Zuleey wacce watanni baya nake turo maka saƙo ta wahtsapp sai dai da alama baka buɗe ba"Sauban yace"Okay then! cigaba da magana Zuleey tayi dama idan babu damuwa son ka nakeyi da aure don naji labarin duk auren da aka maka bakason ko daya a ciki,shine nakeso muhaɗu face to face,ka ganni na ganka,I know idan muka hadu zakayi accepting dina as your wife"da sauri Zuhra ta ɗago tana tunanin wacce banziya ce wannan?zuciyar ta na cigaba da bugawa kwalla ya taru mata ta kafeshi da ido,shima ita yake kallo yana samun natsuwa a zuciyar sa domin kuwa yau ya tabbatar kanwar tasa tana son sa tunda tana kishin sa,ba tare da ya farga ba yaji an fusge wayar,cikin ɓacin rai ta fara magana"Ke ki nutsu kisan da wanda kike magana,mijina ba ƙazamin na miji bane da yake bin ko wace ƙazama yace yana so,kin gama yawon ki kin gama ƙazantar ki sannan kidawo nan?wallahi kinyi kaɗan kije can kisamu ƙazami like yhu ki aura cuz shine ajinki ba mijina ba"Zuhra na gama fadar hakan ta ajiye wayar tana sake tsuke fuska ban da huci babu abinda takeyi, shi kuwa Sauban sai murmushi ya keyi,daukar wayar yayi jin muryan Zuleey tana magana,muryan shi tajiyo"enough baiwar Allah,matana ta riga ta baki answer please go nd check your husband,cuz nan babu space,bbyn bby ta tare komai"yana gama fadar hakan ya kashe wayar yana kwashe wa da dariya,kama mouth yayi"Ewwee! Ashe ana kishi na haka? wow naji dadi,ashe kina sona?hararar wasa Zuhra ta aika masa tace"Ni kam bana son ka kawai ni bana fatar irin wadan nan su shigo min gida gara ka nemi kamammu natsattsun mata ka aura,don su ko ɗari ka auro bazan damu ba"tana ƙare faɗan haka ta mike ta nufi stairs,da kallo Sauban ya bita yana jan ƙwafa yace"Hmm yarinya lokacin ki ne zaki shigo hannu ne" nufar stairs shima yayi,ya sameta akan kujerar palour sai share tires takeyi,rungumo ta yayi ta baya, kokarin fusge jikinta takeyi sai dai yaƙi bata damar haka,hakan ya sata sakin kukan da take dannewa babu shiru,cikin sauri yajuyo da ita yana kamo haɓar ta,tsura ma face dinta ido ya shiga yi kamar me shirin gano wani abu. Jan ta yayi suka zauna a kujera sannan ya dauke ta ya ɗora ta akan cinyar sa,wani kunya Zuhra taji tana ƙoƙarin sauka,cikin zafin murya yace"kinsan bansan haka ko?yanda taji murya sa ne ya sata duban sa,tsuke face yayi yace"yess abinda nake nufi kenan,yayi maganar yana kai mouth dinsa kan nata,nan yayi nasarar tura tongue dinshi cikin mouth dinsa,nan ya shiga aika mata da zafafan saƙonni,wanda ita ma tafara biye masa don da bata biye masa yanzu kuwa biye masa takeyi,sai aikin mutsi take a tsakanin cinyoyin sa inda take tsokano masa...... ******* Bayan sati daya shirye²n biki ya kankama tunda biki yazo saura sati guda,kuma yaup ne ake shirin kai lefe don Ammi tun safe tana gidan su Kareem da ita za'a kai kayan, Mom itama tana gidan su, Muneefa ma na can gidan su Mom don tarban kaya abu nasu,hakan yasa Sauban daukan Zuhra da kanshi ya kaita gidan su Mom yace itama a tarbe kayan da ita,sosai Zuhra tayi murna, Mom ma taji dadi,haka hajiya Biba don sosai ta nuna jin dadin ta tashiga sawa Sauban albarka duk da baya wajen. Sai karfe biyu su Ammi suka kawo lefe,sosai suka samu tarban girma don an karrama su sosai an kuma shirya musu abubuwa, bayani an gama gaishe² aka gudanar da duk wani abu na al'ada sannan suka tafi cike da ganin nagartar gidan su Rammat tare da dattaku,kaya kuwa Masha Allah ansawa Rammat kaya babu karya akwatuna takwas Kareem yayi,yayi kokari sosai don kaya kam babu na banza,cike da shauki Zuhra ta dubi Muneefa tace"Aunty Muneefa ni yaushe za'a kawo lefe na kamar kowa?kodai ni aure na daban ne?dariya Mom da Muneefa sukayi, Mom tace"Kisha kurumin ki inada yaƙini akan yayan ku lefe za'a hada miki naban mamaki. Muneefa tace"kwarai kuwa yanda yaya keji dake ɗinnan haka?hmmm zakiga lefe sosai. Murmushin jin dadi Zuhra tayi,nan aka cigaba da hira cikin farin ciki,sai bayan magrib Sauban yazo yadau Zuhra,kaitsaye Galadima family ya wuce da ita. Sashen Bodejo suka nufa don gaishesu,sun cidda ta ita da Galadima a palour sai hira sukeyi abinsu,ganinsu yasa Bodejo tamke face saboda yanda Sauban ya riƙo mata hannu,cike da masifa tace"munafuka kin gama cewa ke baki son shi?tunda aka kaiki muƙus mukeji ko yaji baki taɓa yi ba,ƙila ma kina dauke da ɗan tayin shi a cikin ki"ta ƙarisa maganar tana gallama Zuhra harara, Sauban yace"ke kam tsohuwan nan abun ya miki yawa,ga fitina ga sa ido,kodai duk kishi ne bake ke zaune a wancan haɗaɗɗen gidan ba?mere da baki Bodejo tayi batare da tasake magana ba, murmushi Galadima yakeyi yana duban Zuhra"kinji ƙariso rabu da ita duk cikin kishi ne"Zuhra tace"Ai ka rabu da ita Galadima lokacin ta ne yanzu nima nawa lokacin na tafe"Galadima yace”gaskiya ne kam wannan,nan akafara gaggaisawa,inda Galadima ya kalle Sauban"Muhammad ya maganar matar ka?ba zaka dawo da ita bane?,ɗagowa yayi ya kalli Zuhra akayi sa'a itama shi take kallo,ɗan murmushi Galadima yayi sannan ya cigaba"a wannan lokacin yafiya shine sama da komai ka manta komai,komai ya wuce ka dawo da matar ka ka haɗasu ka musu adalci". Cikin ɓacin rai boɗejo ta kalle Galadima"Wai Malam meyasa ka fiye dawo da hannun agogo baya ne?gaskiya bazan ɓoye maka ba nisam bana son dawowan ta gidan nan,ka barsu suyi rayuwar farin ciki itama Allah ya haɗa ta da wani mijin nagari me kula da ita"tana ƙare faɗan hakan ta mike ta nufi kitchen,murmushi Galadima yayi yace"Wato su mata kullum tunanin su ɗaya ne, menene a ciki don kadawo da Akeela?kuskure ne ta riga tayi kuma ƙaddara ce bata wuce kan kowa ba"mikewa Zuhra tayi gaban ta na masifar bugawa don har ga Allah tana tsoron Akeela,da kallo duk suka bita Sauban ji yake kamar yatashi yaje yabita. Still murmushi Galadima ya kuma yi sannan yace"kaje kayi shawara,amma inaso ka natsu tukuna kafin ka yanke hukunci"miƙewa Sauban yayi jikinsa na masifar sanyi yama Galadima sallama ya fice, apartment din Ammi ya nufa nan ya cidda ta da Zuhra zaune tana dafe da kafaɗun Zuhra wacce banda sharɓan kuka babu abinda takeyi,a hankali ya ƙariso,cikin ɓacin rai Ammi ta dubesa"mekayi mata ne Sauban?tsaban kuka tunda ta shigo ko magana ma ta kasa,meke faruwa ne?shafa kai Sauban yayi yace"magana Galadima yayi min akan dawo da Akeela shine fa taji take kuka,to wai ma menene abin kuka anan? Ammi idan fa Allah ya ƙaddara da sauran zamana da yarinyar nan babu yanda za'ayi dole kowa yayi haƙuri"Sakin wani irin kuka tayi tana faɗawa jikin Ammi a dalilin jin kalaman sa da tayi na ƙarshe,cikin ɓacin rai Ammi tace"Sauban! Sauban!! So nawa na kira ka? "Sau biyu Ammi". Ammi tace"To idan har nice na haifeka kada na sake ji ka tayar mata da maganar nan"cikin kuka Zuhra tace"Ammi idan zaiyi auren shi yayi ban isa na haramta masa abinda Allah ya halasta masa ba, kawai dai ni banson Akeela ta dawo ko uku ne ya ƙarosu a lokaci guda amma don Allah banda Akeelaaa"takarisa maganar tana sakin kuka,shikuwa wani ɓacin rai yaji don yana ganin yarinyar kamar fa har yanzu bata son shi tunda har tana cewa ko uku ne yayi banda Akeela. Ammi tace"kiyi shiru nace maganar ai ta mutu taso muje,kamata Ammi tayi suka haye stairs suka barshi anan zaune. Mikewa yayi shima ya fita don tun ɗazu Kareem ke kiran sa. **** Cikin dariyar shaƙiyanci Kareem yace"hhhhh idan bakayi wasa ba kanaji kana gani zan angwan ce na bar ka,kayi ta kallon ruwa dai kwaɗo yazo....mema karisan hausar?dalla masa harara Sauban yayi yana jan tsaki,sannan yace"kai nifa yarinyar nan sam bata so na,nan yashiga bashi labarin abinda yafaru,ajiyan zuciya Kareem ya sauke yace"haba oga wallahi yarinyar nan tana sonka kasan fa yarinya ce so sai kabita a sannu Kaine zaka koyar da ita soyayyan ka"Sauban yace"haka Daddy ma yace min". Nan suka cigaba da hirarsu. Acan Ammi sosai ta lallashe Zuhra sannan tabata good advise na yanda ake kula da miji da tattalinsa,sannan tabata wasu sirrika akan zamantakewar aure wanda insha Allah zaku jisu a book dina mezuwa in na gama wannan. Sai wajejen 9:00 Sauban yadawo inda ya biya yadauki Zuhra suka koma gida,koda suka shiga bata bi takansa ba,dayan personal palour dinta ta nufi,daya daga cikin bedroom din tashiga tayi wanka. Bayan tafito ta shirya cikin wasu night gown masu taushi,wandon gajere ne hannun kuma na vest peach colour,shiryawa takeyi tana muttsuke jikinta da khumra da kulakca masu masifan ƙamshin daɗi,wayar tane yafara ringing mikewa tayi tadauko akan bedside drower ganin number yasa taƙi ɗagawa har ta katse,sake kiran ta akayi,mamaki ta shiga yi kan waye ke kiranta cikin daren nan?shahada tayi taɗau phone din. Muryan shi ta jiyo"Ina sama ina jiranki idan kingama"Yana ida faɗar hakan ya datse kiran,bin wayar Zuhra tayi da kallo,sannan taje ta cigaba da shiryawan ta,sam bata kawo komai a ranta ba,batare da wani damuwa ba ta ɗau hijjab ɗinta long ta sanya ta fice. Samuj shi tayi sanye da kayan baccin shima riga da wando farare tass,shimfiɗa praymat yayi yace"kizo mu gabatar da sallah"wani irin bugawa Zuhra taji ƙirjinta yayi don idan bata mance ba ta taɓajin su Aunty Mashahuda na firar sallah da akeyi ranar da miji zai san matansa...tunanin ta ne yakatse a sanda taji muryan sa"Ba magana nake miki ba?Cikin sauri taƙaraso anan ya tayar da sallan, raka'a huɗu sukayi, anan ya kama kanta yashiga yi mata tambayoyi akan addinin ta,duk tambayar da yayi mata sai ta bashi answer,sosai Sauban yaji dadin hakan. Bayan sun kammala ya zubanya mata idanuwan yana murmushi,wani irin nauyi Zuhra taji,kamo hijjab ɗinta yayi yana kokarin cire mata,da sauri ta kallesa jikinta na rawa,shima kallon ta yayi yana ɗaga mata gira tare da cigaba da cire mata hijjab ɗin,bayan ya cire mata hijjab ɗinne ya miƙe,tare da fita daga bedroom ɗin, Zuhra kuwa banda dakan lugude babu abinda ƙirjinta keyi. Be wani jima ba yadawo hannunsa ɗauke da tray wanda plate da cup's biyu ke kai,zama yayi a gabanta yana jawo ledar gefen sa,buɗe ledan yayi atake anan ƙamshin gasasshiyar kazar tafara tashi,a plate din ya ɗora sannan ya ɗauko Hollandia strawberry ya zuba a cups ɗin. Kallon ta yayi fuskan sa ɗauke da wani murmushi yace"kina jin yunwa?cikin sauri Zuhra ta girgiza masa kai alamun a'ah.Sauban yace"kinaji mana i know Ammi munyi waya tace baki ci abinci ba na tabbatar yau na ciyar dake kin ƙoshi"yana faɗar hakan yakai hannu ya gutsiro tsokar bakin yakai bakinta,Zuhra babu yanda ta iya hakan yasa tabuɗe bakin,sam bataji daɗi da taste din kazar ba,daƙyar ta haɗiye,sake miƙo mata yayi,da sauri ta riƙe hannunsa tana fashewa da kuka"please Yaya bana jin yunwa naci abinci"taƙarisa maganar tana sakin kuka,da mamaki sosai yake duban ta,ɗauko cup ɗin Hollandia yayi yabata,bata musa ba tasha tashanye duka. Ɗaukar kazan yayi ya fita,babu jimawa yadawo lokacin Zuhra ta fito daga toilet,kan bed ɗin ta nufa saboda baccin da yake cinta,shima toilet ya shiga batare da ya kalleta ba,a lokacin da ya fito bacci ya ɗauke ta. Xahratty CE🥰 Lallai Alqalami 🖊️ yafi takobi🗡️ [7/21, 08:54] 𝐎̃𝐔̂𝐌 𝐀̃𝐉𝐌𝐄̨𝐑𝐋💜🤍: 👨🏽‍🦳 *_GALADIMA FAMILY_* 👨🏽‍🦳 Page:- 83/84 ____Wani sabon al'amari ta fara ji kamar ana shafata,cikin sauri ta buɗe idanuwan ta,ido biyu tayi da Sauban gabanta ne yayi mugun faɗuwa duk da bata ganin sa sosai saboda Dum light ce a ɗakin,wasu abubuwa yafara mata tun bata biyesa masa har ta koma biye masa,hakan yasa Sauban yasake samun ƙwarin gwiwa cikin zafi² ya cigaba da aika mata da saƙon ni,tun Zuhra na biye masa har ido yadawo ya fara canza fata domin kuwa tafara tsorata da lamarin nasa cin yafara karkata wani ɓangaren, addu'an kasan cewa yayi da iyali lokacin da yake kai hannunsa yana buɗe cinyoyin,koda yayi ƙoƙarin shiga kasawa yayi a dai-dai lokacin Zuhra ta ɗan saki ƙara jikinta babu inda baya rawa don tayi bala'in firgita. Sannan gashi yaji ruwan ni'ima sosai na guda na a jikinta dagewa kawai yayi don idanun sa ya rufe burin shi kawai ya ji shi a jikinsa kawai,babu zato ya dage yayi wani irin shigar ta,lokaci ɗaya Zuhra tasaki wani gigitaccen ihu tana ƙanƙame sa,tana faɗin"Wayyo Abbie" shikam Sauban sam baya bi takanta be masan inda kansa yake ba saboda wani mahaukacin ɗumi da yaji da daɗi sun mamaye kwanyar,ita kuwa Zuhra baƙin al'amarin da taji ba ƙaramin firgita ta yayi ba cikin tsananin tashin hankali banda kuka babu abinda takeyi tana jujjuya kai jitake kamar ana watsa mata barkono a ƙasanta, Allah sarki Zuhra, Sauban kuwa aikin gabansa yakeyi yana wani irin ihu da nishi cikin tashin hankali. After 1hr Sauban yafaru dawowa natsuwar sa saboda yasamu natsuwa,kamo Zuhra yayi ya ƙanƙame ta kamar zai maida ta cikin cikinsa,ji yayi gabaɗaya jikinta ya wani irin saki,cikin sauri ya tashi ya zauna yana ɗauko ta gabaɗayan ta hankalin sa a tashe,girgiza ta yafara yana kiran sunan ta tare da ɗan shafa mata kumatu,sam taƙi motsawa"Kekekeke keee! Yafaɗa yana girgiza ta gabaɗaya ta susuce yalwataccen gashinta me santsi ya hargitse ga busasshen hawaye, ɗaukar ta yayi cak ya ajiye ta cikin zafin nama ya nufi bathroom,ruwan zafi ya haɗa meɗan zafi ɗan dai-dai,sannan yafita yaje yaɗauko ta babu tunanin komai ya sakata cikin ruwan,wani ajiyar zuciya Zuhra ta saki tana sakin wani irin kuka ginin ban tausayi,sosai ta bashi tausayi,buɗe ido ta shiga yi tana sakin kuka tare da kama hannunsa da yake wanke mata pussy ɗin ta yana watsa mata ruwan yanda zai shige,mimmiƙewa takeyi tana ƙoƙarin tashi dannata yayi cikin muryan damuwa yace"Please Babyn baby ki bari na gasaki yanda zakiji daɗi please"wani irin kuka takeyi,haka ya cigaba da gasata har sai da ya tabbatar da ta gasu sannan ya canza ruwa yamata wanka tasss! Duban ta yayi yace"kiyi wankan tsarki Please"ɗaga masa kai tayi alamun to"wankan tsarki tayi duk yana tsaye yaji daɗin kasancewar ta me sani akan addininta,kama ta yayi daƙyar take tafiya tana runtse ido,kan gado ya kaita ya kwantar da ita tare da jan mata blancket,shi kuma ya koma toilet ɗin,ƙoƙarin ta fito tayi bacci, koda yafito kallon ta yayi cikin farin ciki,tabbas yasamu natsuwa da ita shikam beƙi koda yaushe yana jikinta ba,matsawa yayi gareta yajawo ta ya rungume ta. Misalin ƙarfe huɗu na asuba taji ana laluben ta cikin tsananin firgita ta buɗe ido,kuka tasaka masa saboda nipples ɗin ta har wani azaban raɗaɗin zafi yake mata,kuka take masa lallashin ta yakeyi cikin kalamai masu taushi da daɗi,sai dai ina Zuhra takasa mance azabar da tasha ɗazu,nan tashiga roƙon sa,sam Sauban ya kasa saurarar ta nan yafara kiɗar sa da rawar sa,wani irin kuka Zuhra keyi tana jan numfashi kamar zata shiɗe wannan karan Ammi, Boɗejo ya Taufeeq duk ankira,zafin da taji yanzu yafi na ɗazu saboda yanzu wajen ɗanye yake, Sauban be ƙyale Zuhra ba har sai da yaji ankira assalatu sannan ya samu natsuwa gabaɗaya ta susuce face ɗinta yayi jajawur tsaban wuya ko idanuwan ta bata iya buɗewa,toilet ya kaita ya gyara ta sannan yayi mata wankan tsarki da wanka ya mata alwala,ya fito da ita,zaunar da ita yayi kan praymat ya juya ya nufi toilet ɗin,alwala ya ɗauro dai-dai lokacin aka fara ƙoƙarin tayar da Sallah duban ta yayi cikin sanyin murya da wani mugun ƙaunar ta yace"zaki iya Sallah?ɗaga masa kai Zuhra tayi,yace "Okay to kiyi sallan bari naje masjid na dawo"yayi maganar yana kamo hannunta ya sunbace ta tare da fita,da kallo Zuhra ta bishi,miƙewa tayi ƙoƙarin yi cikin azama,wani ƙara tasaki saboda wani raɗaɗin azaba da taji a ƙasanta cikin sauri ta duƙe,ƙarshen shi a zaune tayi sallan tana jin wani raɗaɗi sai cije baki takeyi,tana idarwa daƙyar ta kalla a tanufi bed ta haye atake anan bacci yayi awon gaba da ita. Sauban ana idar da sallah ya nufo gida ko jiran gaisawa dasu Daddy beyi ba saboda tunanin Babyn Baby,koda ya shigo tayi bacci nufar wajen ta yayi yana cire jallabiyar jikinsa ya haye bed ɗin,jawo ta yayi jikinsa yana ƙura mata ido yana jin wani irin sonta na ninkuwa da ratsawa a jikinsa,a hankali yace"Tabbas ke ta daban ce Babyn Baby 🔐❤️🤍. Babu jimawa bacci shima ya ɗaukesa sai kusan 9:30 ya farka da sauri ya tashi yana duban ta saboda wani zafi rau da yaji jikinta ya ɗauka alamun zazzaɓi,idan ya lura ma haƙoran ta kamar kakkarwa yakeyi cikin wani irin murya ta furta"Yaya zansha rurrrruwa"Sauban da sauri ya miƙe ya nufi fridge ɗin dake bedroom ɗin ya ɗauko mata bottle water yazo ya ɗagata yafara bata,sosai tasha ruwan don tasha kusan rabi,kwantar da ita yayi cikin damuwa yace"sannu Babyn Baby nine ko?fashewa tayi da kuka tana sake lulluɓe jikinta da duvet. "Sorry bari nakira likita muji"ɗaukar wayarsa yayi ya lalubo number Dr Ahmad,kiransa yayi,gaisawa sukayi sannan yace masa idan babu damuwa yana buƙatar Dr mace tazo ta duba masa madam, Dr Ahmad ya amsa masa da Okay babu damuwa zai turo masa Dr Jamila yanzu,nan ya masa Godiya ya katse kiran. Kamar minti goma sai ga kira ya shigo masa,cikin sauri ya ɗauka nan take cewa itace Dr da tazo duba Zuhra gata a bakin gate, Sauban ya amsa da Okay gashinan fitowa. Miƙewa yayi yasa jessy riga da wando ya fice da sauri jikinsa har rawa yakeyi,be wani daɗi ba suka shigo shida wata babban mace don zata yi sa'ar Mom,ƙarisowa sukayi Sauban na kamata ya zaunar da ita sosai,daka kalleta zaka san tanajin pepper don gabaɗaya ta sukurkuce, Dr jamila hannu takai jikinta tana cewa"ayyah sorry meke damunki ne? Zuhra tace"zazzaɓi! Dr Jamila tace"babu inda ke miki ciwo? Zuhra tace"zazzaɓi nakeji,da headache sai ciwon jiki sosai"Dr jamila tace"ayya kada kidamu zaki samu sauƙi kinji,but bayan nan babu inda ke miki ciwo? Zuhra duban Sauban tayi idanuwan ta na ciko wa da ƙwalla,ɗaga mata kai Sauban yayi alamun tayi magana sai dai Zuhra takasa magana saboda wani irin nauyi takeji tana tsoron kada mutane su mata kallon 'yar iska. "Meke damunki eh?feel free kada ki damu"Dr jamila tayi maganar tana ƙoƙarin kwantar mata da hankali,juyawa Sauban yayi ya fita don ya gama fahimtar idan har be fitan ba Zuhra ba zatayi bayani yanda ya kamata ba. Sosai Dr jamila take lallashin Zuhra,da ƙyar ta iya buɗe baki ta sanar da ita,pussyn ta yana mata masifan zafi kamar an watsa mata barkono a wajen,anan ne Dr jamila ta fahimci abinda yafaru da Zuhra,murmushin jin daɗi tayi saboda sosai yarinyar ta burgeta da takawo budurcin ta ɗakin mijin ta,duban ta yayi tace"Please ki gyara inaso naga wajen"cikin jin nauyi Zuhra tace to,nan ta gyara Dr jamila ta buɗe wajen,gabaɗaya ya kumbura gashi yayi ja,ko ba'a faɗa ba kasan yaji mata ciwo ɗan kaɗan,sosai Zuhra taba Dr jamila tausayi,sai dai har ga Allah taga dauriyar yarinyar. Aiko nan tafito da kayan aiki,a dai-dai nan Sauban ya dawo yana ɗan sussunkuyar da kai,ɗauki allura Dr jamila tayi cikin sauri Zuhra tace"har da allura zakiyi min?Dr jamila tace"Ea na kashe zafi ne hannuna ai beda zafi sam"Zuhra ta yarfe hannu tace"nikam da kin barshi na warke ma"cikin kuka take maganar,sosai tabawa Dr jamila dariya saboda ganin ƙarfin halin yarinyar, Sauban ne ya ƙariso wajen dai-dai lokacin Dr jamila ta gama haɗa alluran so take tayi mata,zama Sauban yayi ya kamota jikin sa ya rungume ta,aiko nan Dr jamila ta tsira allurar,be gama shiga ba Zuhra ta yanka ihu"Wayyo yaya"aiko nan Dr jamila takarisa shigar da alluran ta mata,batare da ta liliya ba cikin tsokana tace"kinada raki alhalin banda zafin hannu"Zuhra dai jiki yayi sanyi sai sauke ajiyan zuciya takeyi. Harhaɗa kayan Dr jamila tayi tace"Toh daughter zan tafi Please kidage da shiga ruwan zafi zakiji daɗi sosai kinji?ɗaga kai Zuhra tayi gabaɗaya ta wani narke tace"Nagode mommy,miƙewa Sauban yayi don raka Dr jamila ya kuma mata ɗan ihsani. Da yake alluran da Dr jamila ta mata har bacci tana sakawa kafin yadawo ta ɓingire. Cike da kulawa ya gyara mata kwanciya ji yake kamar yasake samun natsuwa da ita sai dai tausayin ta ya ratsa ko ina nasa ga gargaɗin da Dr jamila tayi masa,toilet ya shiga yayi wanka ya shirya kaitsaye kitchen ya shiga ya haɗasu Chip sai ruwan zafi,ko breakfast ɗin beyi ba yafita lokaci 1:02,motar shi ya ɗauka direct airport ya isa,sai wajen 1:30 jirgin su ya sauka, Ummie ce tazo bikin Kareem da Rammat sai Yasmeen,cikin kulawa Sauban ya isa ga Ummie murmushi kwance kan face ɗinsa,cikin ɗan kamewa ya gaishe ta yana amsar hand bag ɗin hannun ta, Yasmeen ta gaisheshi,mota suka ƙaruwar,aiko yaja sai GALADIMA house. ****** Sai wajen biyu ta farka,jikinta da kanta da zazzaɓin juyayi duk sun sauka,ƙasan tane dai ke mata zafi,da ƙyar ta iya miƙewa tana jin wani irin raɗaɗi ta nufi toilet tayi alwala,a zaune tayi sallan,a dai-dai lokacin Sauban ya shigo hannunsa riƙe da tray,table ɗin dake gaban bed ɗin ya ajiye tray ɗin,a sanda ta idar a lokacin yayo hugging ɗinta ta baya,kamar me raɗa yace"Yanzu kika tashi?ɗaga masa kai Zuhra tayi jikinta na rawa"To taso muje kiyi breakfast"yayi maganar yana kamo hannunta a gaban table ɗin ya zaunar da ita,ruwan tea ɗin yafara bata sannan ya bata chips ɗin,loma uku tayi tace ya ishe ta, Sauban sai da yaga zatayi amai ya ƙyaleta,kamo hannunta yayi cikin kulawa ya kira sunanta,jin ya kirata with serious talk yasa ta amsa tana sake sunkuyar da kai saboda wani mahaukacin nauyin sa takeji. "I love yhu my Fateema with all my heart,Ina tsananin ƙaunarki kinbani abinda har abada banida abin biyanki dashi,Nagode Allah ya miki albarka Babyn Baby ❤️Allah yaƙara min son ki da ƙaruwar ki ya bamu Baby nan kusa"cikin sauri Zuhra ta rufe face cikin shagwaɓa tace"kai yaya nifa yarinya ce"Sauban dariya ya shiga yi sosai wanda yasa Zuhra sakin mouth tana duban sa"gira ya ɗaga mata sannan yace"ai da ba zaki iya ɗaukar ciki ba banjin za'a bari ki tare"Shiru Zuhra tayi takasa ɗago face,muryan shi tajiyo"Allah yabani ikon kula dake Mrs MS, Allah ya ɗorani bisa kanki kifara so na kamar yanda nima nake son ki"shiru Zuhra tayi taƙi magana,lakace mata hanci yayi yana miƙewa yace"tashi muje kiyi wanka"cikin sauri ta girgiza mishi kai alamun a'ah,dama wasa Sauban ke mata,yayi yayi ta miƙe taƙi,daga ƙarshe sai kuka ta sami shi,komawa lallashi Sauban yayi. Toilet ya nufa don wanka,hakan yasa sharp sharp kafin yafito ta gyara gadon ta lailaye shi,sannan ta sulale tabar saman gabaɗaya, personal palour ɗin ta ta nufa,aiko tasake faɗawa toilet,wanka tayi ta shirya cikin long truser sai ƴar top,gyara gashin ta tayi ta faka shi a gadon bayan ta. [7/22, 11:09] 𝐎̃𝐔̂𝐌 𝐀̃𝐉𝐌𝐄̨𝐑𝐋💜🤍: 👨🏽‍🦳 *_GALADIMA FAMILY_* 👨🏽‍🦳 Page:- 85/86 ____Gabaɗaya batajin daɗin komai nata,gashi jinta take sakayau kamar batada karfi,zama tayi a bakin bed ɗin tanayin tagumi,komai jitake ya tsaya mata cak,buɗe bedroom ɗin akayi aka shigo,cikin ta kunshi na uzza ya ƙariso shima sanyi yake da ƙananun kayan shirt ne me gajerar hannun sai three quarter wando yayi kyau ainun sai zuba ƙamshi yakeyi,da sauri Zuhra tayi nudding kanta,murmushi Sauban yayi yana kneeldown a gaban ta tare da tallafo haɓarta,jiyake kamar yasake don Allah ya gani be wani ƙoshi ba(😱 _Zuhra kinada aiki ashe sai kin koyi haƙuri da juriya da yayan naki._) ƙwalla ne ya taru mata cikin sanyin murya ya fara magana"Inason ki so me tsanani Fateema keɗin kin zamo min wata aba a rayuwa ta me muhimman ci,banjin zan iya nesa dake na kwana ɗaya yanda kika faran ta min Allah ya faran ta miki kenan,ina son ki,ina son ki,ina son ki!!! Wani irin kuka Zuhra ta fashe dashi don har ga Allah bata taɓa tsumayen wannan kalmar nan kusa ba,matsawa yayi yakai tongue ɗin shi ya dinga lashe mata tears ɗin dake fita,ita kuwa sai zuba shessheƙar kuka takeyi. "To menene abin kukan eyye?girgiza kai tayi,rungumo ta yayi"sorry Babyn Baby nine ko?cikin shagwaɓa ta ɗaga masa kai,lallashin ta ya fara yana shafa kanta dake kan ƙirjinsa"kinsan menene?girgiza masa kai tayi,zaki iya zuwa cikin gida?ɗaga masa kai Zuhra tayi,ɗago ta yayi yace"Okay to muje"tana rungume a jikinsa ya ɗauko mata wata egyptain gown da viel dinsa ya saka mata sannan ya mata rolling, hannun ta ya kama suka fice, yana riƙe da hannunta yanaji kamar za'a ƙwace masa ita,kallo ɗaya zaka masa kasan yana cikin wani irin niahaɗi,koda suka shiga wajen boɗejo suka fara isa,sai da Sauban ya nemi magana sannan suka fito,basu shiga wajen GALADIMA ba don da baƙi a palour dasu Daddy,nufar apartment ɗin Ummie sukayi,ɗagowa Zuhra tayi ta kallesa gabanta na mahaukacin faɗi don ita duk a tunanin ta wani abin zai kuma cewa suyi a apartment ɗin. Buɗe ƙofan palour yayi mouth ɗinsa ɗauke da sallama,cikin kulawa Ummie ta ɗago answer sallamar nasa,sandarewa Zuhra tayi a tsaye tare da tsananin mamaki,da wani irin zafin nama ta nufi wajen Ummie,azabar da taji ne a ƙasan ta yasata dakata wa tana sakin ƙara tare da cije lips,cikin sauri Sauban yaƙariso kamar me raɗa yace"kibi a hankali ga,ko so kike Ummie ta gane?kallon sa tayi da sauri tana girgiza kai,ita kuwa mamaki ya cika ta fal,muryan ta suka biyo"Lafiya dai ko?cikin sauri Sauban yace"yesd Ummie normal ne"Ummie ta ɗaga kai alamun gamsuwa,daurewa Zuhra keyi tana ƙoƙarin dai-dai ta tafiyar ta tana jin wani raɗaɗi,a take anan Ummie ta gama fahimtar duk abinda ke faruwa,zama Zuhra tayi cikin muryan shagwaɓa tace"shine zaki zo Ummie baki kirani ba?sai akayi surprise ɗina? Ummie cikin dariya tace"Ea mana ni biki kazo ai,kuma Sunday zan koma"Zuhra tace"kai Ummie wallahi yayi kusa ki zaman ki anan please"dariya Ummie tayi tace"kada ki damu su Laila zasu iso ranar Friday da yamma,but kina zuwa school ɗin ma ke?shiru Zuhra tayi,duban Sauban Ummie tayi tace"bata zuwa school ɗin ko?sosa ƙeya Sauban yayi yace"Ummie ranar Monday zata koma insha Allah,amma ina tunanin ƙila....sai kuma yayi shiru, Ummie tace"ƙila mene? Sauban yace"zamuyi magana anjima Ummie bari naje na dawo, haka kawai yaje yana jin nauyin Ummien sosai,duban Zuhra yayi cikin kulawa yace"mene zaki ci?Zuhra ta narkar da murya don har ga Allah batajin cin komai sai tuwon semo miyar kuka,kuma tasan da wuya idan anyi don sam mouth ɗin ta babu apertite"Babu komai"Sauban ya ƙanƙantar da idanuwa babu alamun wasa yace"mekika ce da zaki ce babu komai? Ummie yau da ko breakfast ɗin kirki batayi ba amma kinji wai babu komai"Ummie tace"au Allah wasa take da cikinta da yunwa ko?to ai shikenan karabu da ita son cikinta"girgiza kai Sauban yayi yace"a'ah Ummie dole sai taci abinci fa"duban Zuhra yayi"ehem ina jinki. Duban Ummie Zuhra tayi kamar zatayi kuka tace"tuwon semo da miyar kuka nakejin ci sam mouth ɗina babu apertite"Sauban yace"Okay I will be back soon,zan nemo miki,love yhu ki kula da kanki"cikin kulawa yayi maganar yana duban Ummie yace"Ummie bari na samo mata tuwon ko wajen Ammi ne"yana faɗar hakan yafita be jira jin mezata ce ba,don shi kanshi sai daga baya ya fahimci irin katoɓarar da yayi, Ummie kuwa kallon Zuhra kawai tayi. Da gangar tace mata taje stairs ta ɗauko mata hand bag ɗin ta,miƙewa tayi tana ƙoƙarin dai-dai ta tafiyar ta ta nufi stairs ɗin a fakaice Ummie ta ƙare mata kallo tsaf,sai da takawo mata jakan sannan tace mata"Me yasa mu ƙafar ki ne naga kamar da ƙyar kike tafiya?Cikin sauri Zuhra tace"A'ah Ummie bigewa nayi da nazo saukowa daga stairs ɗazu,amma na samu sauƙi ma saboda yaya ya duba min"sosai Ummie ke mamakin ƙaryan da Zuhra ta lafto take shirga mata amma sai ta wata ce da faɗin"Ayya to Allah yaƙara sauƙi kin shiga sashin Ammin kune?girgiza mata kai tayi,tace"to tashi kije ki gaishe ta ai can ya kamata ace kun fara shiga ma"da to Zuhra ta amsa tana miƙewa cikin sanyi tafita tanajin wani irin fever a dalilin fama ciwon da tayi. Sashin Ammi ta shiga nan ta taradda Aunty Safeena tazo,aiko cikin murna taƙarisa shiga palour, dai-dai lokacin Ammi ta fito daga cikin kitchen, ƙoƙarin dai-dai tafiyar tata tasake yi,ƙamahin dadawa duk ya ɗumi palour, Aunty Safeena ce tayi carab tace"a'ah me kuma ya samu ƙafar naki? Zuhra ta ƙaƙalo murmushi tace"gurɗewa ɗazu nayi a stairs"Aunty Safeena tace"eyya Allah yaƙara sauƙi, Ammi bta ƙariso tana kama Zuhra ta zaunar da ita tace"Son yanzu ya fita yaje siyo nama ninan nama na yaƙare yace tuwo zakici miyar kuka"duƙar dakai Zuhra tayi cikin jin nauyin Ummie,cikin tsokana Aunty Safeena tace"Eyye ya Sauban har ɗan tuwo ya samu?a lallai dole yaje samu nama"Ummie tace"uhum tana miƙewa, Zuhra ma miƙewar tayi tana jin wani nauyi, Aunty Safeena tace"ba kunya za jiki ba magana zakiyi"ita dai Zuhra ba tayi magana ba cigaba da tafiyar ta tayi sai dai azaba takeji don har kan ta sarawa yake mata. Ammi ce ta jiyo tana ƙura ma tafiyar Zuhra kallo,wani tunani ne ya faɗo mata,cikin sauri ta kauda wannan tunanin,Zuhra kuwa shiga bedroom ɗin palour tayi kaitsaye toilet ta nufa fitsari ya matse ta,shaf ta mance ta ɗibi ruwan sanyi tayi tsarki dashi,aiko ta kwala wani azababben ihu tare da mahaukacin zaɓura, Ammi ne da Aunty Safeena suka shigo cikin sauri, Zuhra kuwa kuka takeyi jikinta na rawa don tabbas ta fama ciwon nata, Ammi tace"meyasa meki Zuhra?shiru tayi tana kuka ga uban ciwon kai da takeji, Ammi tace"ki faɗamin gaskiya me yasame ƙasanki?nan ma Zuhra shiru tayi taƙi ma Ammi magana,sai uban zufa da take yi tana gunjin kuka, duban Aunty Safeena tayi tace"ka mata falmata kuyi gefe ina zuwa"cikin toilet ɗin Ammi ta shiga ta haɗa ruwa me ɗan zafi sannan ta fito ta fice bata jima ba tasake shigowa,don ko zama Zuhra ta kasayi, Ammi ce ta fito ta kamo hannun Zuhra tayi toilet ɗin da ita,face ɗin Ammi babu alamun wasa tace ma Zuhra"cire kayan ki"ai ko babu musu Zuhra ta cire tanayi tana kare cikakkun ƙirjinta,kamota Ammi tayi ta shigar da ita ruwan tayi,tana zaunar da ita. Aiko wani zabura Zuhra tayi tana sakin kuka tare da girgiza ma Ammi kai, Ammin sake tsuke face tayi tace"koma ki zauna"Zuhra cikin kuka tace"Don Allah Ammi ki ƙyaleni da zafiiii, taƙarisa maganar tana kuka"falmata! Ammi takira Aunty Safeena,shigowa tayi sai dai taji bala'in nauyin ganin Zuhra a haka,Ammi tace"muka mata mu zaunar da ita cikin ruwan nan"anan Aunty Safeena ta fahimci abinda ke faruwa,aiko kama ta sukayi suka zaunar,inda Zuhra ke sakin wani wahalallen kuka na azaba,sosai ta basu tausayi, Ammi ranta ya ɓaci wato Son ya jima yarinyar nan ciwo kenan?tayi tambayar a zuciyar ta,sake canza ruwan Ammi tayi wannan karan ban da ajiyar zuciya babu abinda Zuhra ke sauke wa don tabbas ta gasu don har wani bacci ne ke fusgan ta a cikin ruwan. Fito da ita Ammi tayi ta kamo ta ta kwantar da ita,sannan tace ma Aunty Safeena suje su bari ta huta,fitan su kuwa babu jimawa wani wahalallen bacci yayi awon gaba da ita tana sauke numfashin wahala. Sauban ko koda ya dawo bega wani face wajen Ammi ba don tsuke face ɗin ta tayi,ɗan shafa kai yayi yace"Sorry Ammi traffic ne yau a garin"Ammi tace"umm to bani"miƙa mata yayi yana fita don ɗauko ma Zuhra magungunan ta da ta mance dasu a gida,koda ya dawo sashin Ummie ya isa, anan Ummie ke ce masa ai tana wajen Ammi,mamaki ne sosai ya kamashi don shi be ganta a wajen Ammi ba,fita yayi ya nufi apartment ɗin,zama yayi akan sofa,a lokacin Ammi ta fito kitchen, Aunty Safeena kuma na ciki, zama Ammi tayi gefensa, Sauban ne ya dubeta"Ammi Babyn Baby nanan ne?cikin rashin fahimta Ammi ta dubesa,cikin sauri yace"Opps i mean Zuhra"harara Ammin ta galla masa sannan tace"me zakayi mata? Sauban ya sosa kai yace"Dama maganin ta zan bata saboda ta manta bata sha ba? Ammi batare da ta dubesa ba tace"Oh dama bata da lafiya ne? Sauban yace"na manta ince miki ɗazu taɗan gurɗe da stairs shine mukaje hospital aka rubuta magani but normal ne"Ammi ta dubesa cikin mamaki saboda yanda yake kafco ƙarya one time,tsarguwa yayi da kallon da Ammin nasa ke masa. "Ba cewa kayi fever ne ke damun ta ba? Sauban ya sosa kai sannan yace"Dama wannan ne ya saka mata fever"Ammi tace"Ok to tana bacci idan ta tashi ka bata"cikin sanyin jiki Sauban yace"Okay Ammi,miƙewa yayi yana ajiye ledan maganin akan stool ɗin side ɗin sofa. Da kallo Ammi ta bishi. Zuhra bata tashi ba sai wajejen magrib,sosai taji daɗin jikinta matuƙa gaya koda ta miƙe sai taji wajen be takura mata kamar ɗazu ba,miƙewa tayi tashiga toilet ta ɗauro alwala,nan ta shiga gabatar da sallolin ta a tsaye ba a zaune ba. Ammi ce ta shigo,ganin tana sallah yasa ta juya tana cewa"dama zuwa nayi na tashe ki cuz anata kiran magrib. Koda Zuhra ta idar ta gama addu'o'in ta kasa tashi tayi tafita saboda nauyin Ammi da takeji,ana haka Ammi ta dawo"Au kin idar shine kuma kike zaune?miƙewa Zuhra tayi Ammi tafita itama tabi bayan ta. Daddy, Aunty Safeena, Sauban da yaran Aunty Safeena mace da namijin duk suna dinning,cikin sauri Zuhra ta ƙarisa wajen Daddy,shima ganin ta yasa gabaɗaya ya dawo da kulawar sa gareta"Daddy barka da gida?sannu da zuwa,murmushi kwance face ɗin Daddy yace"Barka mamana kina nan lafiya? Zuhra tace"ina lafiya Daddy"Daddy yace"Masha Allah,son na kula dake kuwa?ko yana cin zalinki?yayi maganar cike da zolaya yana duban Sauban,shiru Zuhra tayi a kaikace tana duban shi wanda gabaɗaya hankalin sa na kanta,duban Daddy yayi yace"Daddy ina kula da ita itama ta sani sai dai bazata faɗa gaskiya ba. Murmushi Daddy yayi yace"haka nakeso Allah ya ƙara muku zaman lafiya da fahimtar juna,amsawa sukayi gabaɗaya banda Zuhra da kanta ke ƙasa, food flask Ammi ta turo mata dana tuwo dana miya tace"Ga tuwon kinan sannan nasa miki na ɗumame"cikin farin ciki Zuhra taja kulan tana nuna tsantsar jin daɗin ta a fili tace"Nagode Ammi na"hannu takai da niyyar ɗauko plate a lokacin Sauban har ya ɗauko mata,aiko nan ya shiga serving ɗin ta a gaban su Ammi waɗanda mamaki ya cika su tare da tsananin jin daɗi da farin ciki. Zuba ma ta tuwon yayi malmala biyu daƙyar ta iya cinye ɗaya tana squeezing face alamun ta ƙoshi,kallon ta yayi yace"Yhu mean kin ƙoshi?ɗaga masa kai tayi ba tare da ta yadda ta haɗa ido dashi ba, muryan shi tajiyo"Ai yarinya babu wannan maganar kici abinci kiyi ƙat kisha maganin ki"Zuhra kamar zatayi kuka tace"Allah yaya naƙoshi ne ba wani abu ba"Sauban yace"Ai baki isa ba yarinya"ɗaukar spoon ɗin yayi ya shiga bata abincin,sai da yaga tafara yunƙurin amai sannan ya sarara mata. Bata magungunan yayi tasha a lokacin Daddy ya tashi sai Ammi, Aunty Safeena ce wayarta tayi ƙara,koda ta duba number Shuraim tagani dama shine zaizo ɗaukar su tunda ya Asheer baya gari,ɗaukar wayar tayi"Hello ka shigo ciki mana"tana gama haɗar hakan ta yanke wayar,sallama Shuraim yayi ya shigo dai-dai lokacin kuma Sauban ya kamo hannun Zuhra zuwa palour,cikin girmamawa Shuraim ya fara gaida Ammi,duban Sauban yayi wanda ya fara ciccin magani tare da tsuke face yace"Yaya barka da dare ina yini? Sauban batare da ya ɗan saki face ba yace"Barka! ya mutanen gidan? Shuraim yace"Alhamdulillah kowa yana nan lafiya"kallon Zuhra yayi yana ɗan murmushi yace"Aunty Zuhra barka da dare"Zuhra da ɗan murmushin ta tace"ina yini?kasa amsawa yayi,ita kanta cikin jin nauyi ta gaidasa,wani ƙululin baƙin ciki ne ya tokare maƙoshin Sauban sallar kishi ya bayyana a face ɗin da saboda yanda ya sake turniƙe ta. Xahratty CE🥰 Lallai Alqalami yafi takobi.🗡️ [7/24, 15:10] 𝐎̃𝐔̂𝐌 𝐀̃𝐉𝐌𝐄̨𝐑𝐋💜🤍: 👨🏽‍🦳 *_GALADIMA FAMILY_* 👨🏽‍🦳 Page: 87/88 ______Ammi duk tana hankalce da sauyin sa,girgiza kai kawai tayi tare da murmushi,anan su Aunty Safeena suka tafi,shima Sauban duban Ammi yayi yace"Ammi zamu tafi sai da safe"Ammi tace"tom shikenan mukwana lafiya,duban Zuhra tayi tace"ki kula da kanki,ki kuma dinga shiga ruwan zafi kina sitbath inba haka ba babu ruwana"daga Zuhra har Sauban wani mahaukacin kunya sukaji, Zuhra takasa maga ɗaga mata kai kurum tayi,juyawa Ammi tayi ta haye stairs. Kamo hannunta sukayi suka fice basu samu damar leƙa Ummie ba saboda daren da yayi wucewa sukayi gida,suna shiga ya sanar da ita coffee kawai yake da buƙata sannan ya haye stairs,binshi da kallo tayi saboda gani tayi kamar yana fushi,tambayar kanta ta shiga yi"To me akayi masa?ɗage kafaɗar ta tayi tanufi kitchen,haɗa komai tayi a tea pot ɗin ta kunna electric ta fito ta nufi personal palour ɗinta,a gurguje ta shiga toilet ssi da ta fara gasa federal government ɗin ta sannan tayi wankan ta cikin natsuwa ta fito,ko shafa cream batayi ba taɗau kulakcha da humra ta murza,sannan ta gyara gashinta ta daure da band jelar ya sauko gadon bayan ta,ta feshe gashin da hear freshener ta buɗe closet ɗinta,wani top ta ɗauko wacce ta tsaya mata iya ƙirjinta,da kaɗan ta rufe dukiyar fulaninta,colour ɗinta white a gaban anyi rubutu da yellow an rubuta I can't live without you,sannan ta buɗe closet ɗin boomshort shi kuma yellow,iya ƙasa tudun boom boom ɗin suka tsaya,flat shoe white ta sanya cikin sauri ta fita kitchen ta faɗa,aiko ta shirya masa coffee ɗinsa tsab cikin tray ta ɗauka ta haye stairs din,cikin natsuwa ta buɗe bedroom ɗin ta shiga tare da ƴar siririyar sallamar ta. Kallo ɗaya ya ɗago ya mata ya kauda kai,juyayi wani abu na fusgar sa babu shiri ya rufe laptop ɗin da ke kan cinyar sa yana furzar da numfashi,a gaban sa ta ajiye tray ɗin sannan ta miƙe cikin sanyin ta tace"Yaya sai da safe,shikenan abinda kake buƙata? ƙura ma dukiyar fulaninta ido yayi dai-dai tudun saman,hannu ya miƙo mata"Zonan! Ya furta da wata iriyar shaƙaƙƙiyar murya,a hankali tafara takowa ƙirjinta na mugun bugawa,zaunar da ita akan cinyar sa yayi,suna facing juna hannun sa yakai kan pink lips ɗin ta yana shafawa yace"idan kin tafi wazai haɗa min coffee ɗin humm?bakisan raba kwanciya da miji haramun ne ba?Ni ban amince kije wani waje ki kwanta ba bayan nan"yayi maganar yana kai mouth dinsa kan lips ɗinta,nan ya shiga aika mata da wasu hot kisses masu gigita kwanya,ba shiri Zuhra ta shiga biye masa,nan fa aka cigaba da romance har yakai ga an koma kan bed ya kwantar da ita🤦🏽‍♀️ After 1hr komai yadawo normal,gabaɗaya ya rungumeta kamar zai maida ta cikin cikinsa sai shafa barbazajjen gashin kanta yakeyi, Zuhra kuwa idanuwan nan sun kukkunbura sai ajiyar zuciya takeyi,jitake ƙasanta na mata zafi,shiko Sauban banda samata albarka babu abinda yakeyi,wani irin farin ciki yakeyi mara misaltuwa har ga Allah yanzu ne yasan yayi aure,tabbas Zuhra nada matsayin da babu meshi a zuciyar sa,duban sa yayi yace"ina tsananin son ki ƴar baiwa,wallahi ke ɗin ta daban ce Babyn Baby",miƙewa yayi ya shiga toilet,haɗa musu ruwa yayi sannan ya dawo cak ya sunkuce ta ya nufi toilet da ita. ******** Akeela komai ya tsaya mata cak, Daddyn ta ya dena kulata ko gaishesa tayi ya dena amsawa,haka idan taje wajen Guggo Laure habaici kawai take sakin mata,yau ma kamar kullum tsaye take a bakin ƙofan palour Guggo Laure sai mita takeyi,cikin ɓacin rai da muryan kuka Akeela ta fara magana"Wai ya kuke so nayi ne da rayuwa ta?nace nayi nadama ina kuma neman yafiya na a wajen Allah to meyasa za'a tasa ni da cin zarafi? Guggo Laure tace"dole aci zarafin ki domin kin daɗe kina cin amanar mu tare da ɓata mana sunan ahali,ashe ba karya da sharri su A'isha suka miki ba amma kika zo kika faɗamin ƙarya da gaskiya kika sa naje na ma ɗan uwa na tujara har takai shi da samun mutuwar ɓarin jiki?wallahi Akeela ke sheɗaniya ce"sosai kalaman Guggo Laure ya ɓata ma Akeela rai,tana kuka ta fara magana"Kada ki mance Guggo kece kika fara tusa min son ya Sauban a raina tun bansan menene so ba,kece kika samin kwaɗayin son sa,wallahi Guggo har yanzu ina son ya Sauban banjin akwai na mijin da zanso bayan shi,don Allah Guggo kije ki roƙa min gafarar sa ya maidani"wani kallo Guggo Laure ta mata na baki da hankali sannan ta miƙe ta shige cikin uwar ɗakin ta tana jin baƙin cikin abinda tama yayan nata,tarasa da wani idon zata je duban sa. Kuka sosai Akeela keyi tana Allah wadai da irin rayuwar ta,ga kunyar duniya bata isa ta fita waje ba,aci zarafin ta iyayen ta da basu ji ba basu gani ba suma a zage su,share hawayen ta tayi tana miƙewa ta nufi apartment ɗin su. A tsakanin Bana sani da Alhaji Mansir kuwa sun yanke hukuncin zuwa su bama GALADIMA da su Daddy haƙuri akan abinda ya faru,don haka suka fito cikin shirin su suka nufi wajen Guggo yi mata sallama,anan suka ci karo da Akeela da ke tafe tana sharɓen kuka,wani dogon tsaki Alhaji Mansir yaja sannan yana nuna ta da yatsa cikin ɓacin rai yace"Ai inhar duniya ce Akeela baki ga komai ba"girgiza kai kawai Baba sani yayi harga Allah yana jin zafin abinda Akeela ta aikata ga tsananin tausayin ta. Koda suka shiga wajen Guggo Laure sanar mata sukayi da inda zasu nanfa ta tubure kan itama zataje,duk yanda suka so lallaɓata taƙi hakan yasa babu yanda suka iya suka ce to ta shirya suje. Fitowan su kenan daga apartment ɗin Zuhran Rammat tana ƴar dariya ta dubi Muneefa tace"wallahi kidai kula da amanar da yaya ya danƙa miki idan ba haka ba kuma babu ruwa na"duban Zuhra Muneefa tayi tace"wa? aidole na kulan ma yaya da wannan amanar tashi domin idan nasake wani abu yafaru hukunta ni zaiyi duk da yau saura kwana uku biki,ni fa banga wani wurin da akayi na zuwa saloon ba. Rammat tace"Gaskiya kam,suna ƙoƙarin fita second gate sai gashi anturo,su Guggo Laure ne,aiko cikin girmamawa su Zuhra suka shiga gaishesu,sosai suka amsa cikin kulawa inda Guggo Laure keta nuna kulawa akan Zuhra fiye da kowa,domin ko gausuwar Rammat ma bata amsa ba,sai su Baba Sani ne ke tambayar ta Hajiya Uban da shirye-shiryen bikin?(kunsan dama su ɗin ƴan uwa ne da Hajiya Biba da mahaifin su Baba Sani.) Wucewa sukayi inda Muneefa tace"To me kuma yakawo Guggo gidan nan?ita da ta nuna bata babu ahalin nan sannan sai wani basar damu takeyi"Rammat tace"mtseeww! Can ta matse mata ganina ne yasa take ta wannan abin ke bakisan sunje family ɗin su Hajiya sunyi tujara ba ita da Ouncle Mansir?suna cewa Hajiya ce ta kashe ma Akeela Aure tunda dama taso nine na aure Sauban?sai da ashirin Akeela ya tonu sannan da Hajiya ta wanku,anan kuma aka samu masu zuwa jin gulma,idan kika lura Ouncle Mansir ma cikin kunya ta ai yake tunda dama shine mataimakin ta idan tana tujara. Zuhra tace"Allah dai ya kyauta"Duk da Ameen suka amsa,inda suka isa bakin ƙofan motar, Zuhra ta fara shiga backseat ɗin sannan Rammat, Muneefa kuma tashiga gaba,dama Mus'ab mijin ta ne zaikaisu saloon ɗin. Acan ƙofan palour Boɗejo kam sallama suke ta dokawa, Boɗejo ta fito tana amsawa tare da bada izinin shigowa,sallama sukayi suka shiga da mamaki take binsu da kallo musamman Guggo Laure tamke face tayi don sometimes Boɗejo bata da dama,gaisawa suka fara yi,sannan shiru ya ɗan gifta, Guggo Laure tace"yaya Boɗejo yaya Muhammadun ko nanan? Boɗejo ta sake tsuke face sannan tace"Yana nan dame kuma yau akazo masa?don bazan yarda yau a kuma tayar masa da hankali ba"tayi maganar tana ɗauko cup ɗin goron ta ta ɗauraye ta ɓantara,cikin damuwa Guggo Laure tace"Wallahi ko kusa hasalima nazo na bashi haƙuri ne akan duk abinda yafaru,tabbas nayi kuskure wanda gashinan nazo ina nadama"Boɗejo tace"Ikon Allah to madallah bari na mishi magana ya fito nan,miƙewa Boɗejo tayi zuwa can sai gashi sun fito GALADIMA ne a gaba yana tafe yana dogara sandar me shegen kyau da tsada,bayan sa Boɗejo ce ta fito. Samun waje yayi ya zauna cikin kulawa GALADIMA ya dubi Guggo Laure yace"Laure kece a gidan?cike da jin nauyi Guggo Laure tace"ina wunin mu yaya?ya ƙarfin jikin naka?cikin fara'a GALADIMA yace"alhamdulillah jiki yayi sauƙi sosai,nan su Baba Sani suka shiga gaishe shi cike da girmamawa tare da tsananin jin nauyi,kunya da nadama. "Hanne!!! Boɗejo ta shiga ƙwala ma maid ɗinta kira,babu jimawa ta iso hango baƙin da tayi ya fahimtar da ita abinda zatayi,komawa kitchen tayi ta haɗo abin motsa baki a tray sannan ta iso ta ajiye tana gaishe dasu Guggo Laure,a lokacin da yake da la'asar ne sai Galadima ya ɗau waya ya kira su Daddy,babu jimawa suka iso shida Baba Hasheem sunyi mamaki ƙwarai,inda Baba Hasheem ya ƙudurta a ransa idan sunzo da niyyar cin wani mutumcin ne to shi zai sauke musu. Saɓanin haka domin kuwa sosai suka nemi yafiya inda Guggo Laure har kuka tayi, Baba Hasheem yace"ai Guggo an aikata abin kunya ne zalla,be kamata yara su haɗaki da Galadima ba,yana ɗaya daga cikin abinda a yanzu haka naji auren zumunci ya fita kaina,amma wannan ba komai bane face rubutaccen ƙaddara, Allah ya tsare gaba"da Ameen duk aka amsa,sannan Daddy ya dubi Guggo Laure yace"to meze hana ita Akeela ta dawo nan gidan da zama tunda kince acan babu halin ta fita sai hantara da ƙyamar?ta dawo nan kaw.....wani tsalle Boɗejo tayi ta dire cikin masifa tafara zazzaga ruwan bala'i"wallahi Taleeb zanci mutumcin ka duk abinda ya faru be isheku ishara ba ko?to wallahi ba zata dawo nan ɗin ba babu ruwan ka,aikin banza kawai aikin wofi"gabaɗaya palour shiru akayi kowa na sauraran masifan da takeyi, Guggo Laure tace"ai komai ma mai wucewa ne Taleeb mungode sosai muma a yanzu ba zamu tabbatar da nadamar Akeelan ba sai a dalilin zama a gaban mu tukuna zamu gane"taƙarisa maganar tana sharɓen ƙwalla da gefen mayafin ta, Baba Sani yace"Gaskiya ne wannan yaya gwara ta zauna acan gaban namu zafi, miƙewa Boɗejo tayi tare da mere da baki kamar ba tsohuwa ba tace"Da dai yafi ku gaida gida"tana gama faɗar hakan bata jira amsar su ba tanufi corridor ɗin da zai sadata da jerin ɗakunan ta sai ƙananan surutai takeyi tanaji kamar ta faffallama Daddy mari. Anan aka fahimci juna tsakanin Guggo Laure da Galadima sannan sukayi musu sallama suka miƙe,suma su Daddy miƙewan sukayi don taka musu. Wajejen magrib Suby da Zuleey ne aka tsinci gawar su a wani hotel room inda suke tsirarar su an musu yankan rago, wannan abin ba ƙaramin girgiza Akeela yayi ba don kamar zatayi hauka da ta samu wannan mummunan labarin,kuka take kamar ranta zai bita,cikin tashin hankali Alhaji Mansir ke magana"Kin gani?sune manya²n ƙawayen ki baki da ƙawaye sama dasu to wallahi Akeela Allah na Son ki da rahama domin kuwa ya miki da kyau abisa su,ki dage da istigfari da roƙon Allah yafiya,ki kalla ita wancan yarinyar suwaiba uban ta ƙin ɗaukar gawan ta ma yayi sai da ƴan uwa suka suturta,wannan kuwa"yayi maganar yana nuna Zuleey"Iyayen ta kuka suke kan ammata sharri ne, saboda bata taɓa ɓarin wata ƙofa da zakayi mata kallon mutumiyar banza ba,kullum cikin suturta jikinta takeyi,ina me baki shawara da kiyi tuba irin tuban taubatun nasuha,idan ba haka ba ƙarshen ki sai yafi nasu muni"cikin muryan kuka Hajiya maimuna tace"haba haba mana Alhaji kadena jifan yarinyar nan da mugayen kalamai haka,kune kukayi silar komai nata Akeela tun tana da 16 yrs ta nuna maka aure takeso amma kai da Guggo kuka nace sai tayi boko"taƙarisa maganar cikin kuka. Zira takalmi Alhaji Mansir yayi yana fita yace"kyadai daiji dashi,nidai gaskiya nake faɗama ta ( _Nikuwa nace gaskiyar ka ta banza Alhaji Mansir?sai da Akeela ta lalace kake faɗa mata gaskiyar?kana ina sanda take kwana a waje?kana ina sanda ƙasashen banza ke zuwa wajen ta?baka taɓa bincike ƙawayen ta ba,kuskuren da iyaye da dama keyi kenan a wannan zamanin, Allah yasa mudace alfarman Annabi da Alkur'ani._) [7/25, 09:30] 𝐎̃𝐔̂𝐌 𝐀̃𝐉𝐌𝐄̨𝐑𝐋💜🤍: 👨🏽‍🦳 *_GALADIMA FAMILY_* 👨🏽‍🦳 Page: 89/90 ____Sosai Sauban ke nuna ma Akeela soyayya da kulawa wanda be jin kunyar uban kowa,su Laila ma an sakko da bikin su nan da six months don har ga Allah yayi nesa a ce sai sun gama School tunda dududu 2000l yanzu suke,dama Zuhra ce dai bata shiga da wuri ba,yau ta kama Tuesday kuma yau ne ake event na Kanuri day,amarya tasha kyau ko ta ko ina. Zuhra sosai take kuka a dalilin hanata zuwa wajen event ɗin da ya Sauban yayi,har yau takasa sabawa dashi tun wajen 1 yake abu ɗaya har yanzu da ake neman 4 azaba ya ishe ta duk da ma juriyar da Allah ya saka mata amma tayi kuka har ta gaji,gabaɗaya a wahale take ko hannun ta bata iya ɗagawa,sai yanzu ya sarara mata,ɗaukan ta yayi ya shiga da ita toilet ya musu wanka,inda ita kuwa sai ƙananun koke² take masa da complain ɗin ciwon jiki,shiyasa suna fitowa daga toilet sallah yaja su sannan yafara aikin yi mata massage,a haka wani wahalallen bacci kuwa ya ɗauke ta,cike da wani irin ƙaunar ta yake kallon ta yana ji kamar ya haɗiye ta,peck ya bata a kunci sannan ya shirya cikin wata kaftani ɗinkin half jamfa me laushi tare da tsada,kwantancen gashinta a gyara suɓul sai sheƙi yakeyi batare da yasa hula ba yaɗau car key ɗinsa yabar gidan,kai tsaye wani lafiyayyen eatry ya nufa,shiga yayi ya haɗo musu take away na Burger sannan yadawo, ko a lokacin bata tashi ba hakan yasa kaitsaye ya faɗa kitchen inada ya feraye Irish nan ya haɗa musu chips nd egg,komai jera shi ya shiga yi akan dinning,batare da ya sake hawa upstairs ɗin ba,toilet ɗin palour ta ya shiga ya daura alwala ya tafi masallaci. Bashi ya shigo ba sai wuraren 8:30 don har isshan shi yayi,hayewa saman yayi nan yaje ya fara tashin Zuhra cikin kulawa,shafa mata kai ya shiga yi yana hura mata iska a kunne,cikin wani irin shagwaɓa ta tashi,cikin muryan shagwaɓa tace"Kai yaya nifa baccin be isheni ba sam"tayi maganar tana turo mouth gaba,rungumo ta Sauban yayi cikin kulawa yace"to ai dole ki tashi I know yanzu haka kinajin yunwa ga sallolin ki,Please wake up"yayi maganar yana kamo hannunta tare da miƙar da ita,kukan shagwaɓa ta saka masa,be sake ta ba,har toilet ɗin ya kaita tayi alwala sannan ya shimfiɗa mata praymat ta tayar da sallah, hakan yasa ya fita yaje ya haɗo komai a tray ya kawo saman anan palour ya ajiye. Waya yakeyi da ƴan office ɗin su sai iskanci suke masa kan yaƙi dawowa,fitowa tayi tana ɗan nesa dashi don har ga Allah wannan jarabar nasa tsoro yake bata,miƙewa yayi ya kamo ta ya zaunar tare da hanging call ɗin,cikin shagwaɓa ta dubesa"Shine bazaka jira na tashi nayi komai ba?ni nafi son kana cin abinci na sam bana son kana cin na eatry"kumatun ta Sauban yaja yana maimaita maganar nata,throw pillow ta ɗauka ta jefa masa tana sakin kukan shagwaɓa, kamota yayi ya ya shiga lallashin ta,hakan ya sata lafewa a jikinsa,shida kan shi yayi feeding ɗin ta sai da taci ta ƙoshi sannan ya ƙyale ta. Haka rayuwar su ta kasance gunin ban sha'awa da burgewa Sauban bashi da wata matsala sai na kishi,yana da zazzafan kishi sosai. ******** Ranar juma'a su Laila suka diro harda su ya Taufeeq,mommy ce kawai bata biyo su ba,sai ta haɗa su dasu Ateeq da maimoon a dalilin kukan da maimoon ta dinga yi kan sai tazo wajen Zuhra,gabaɗaya Zuhra ta tare acan da yake Sauban ranar yana busy saboda suna shirye-shiryen tarban abokan su waɗanda sukayi school,wasu ba'a state ɗin suke ba,wasu kuma suna can daga waje zasu shigo, Zuhra na zaune wayar ta tafara ruri, Nihal ce ta miƙa mata,ganin sunan Sauban ne yasa ta ɗanji sanyi a ranta don tunda ya fita be nemeta ba,duk da taso kiran shi amma sai hayaniyar ƴan uwan ta ya hana ta zuwa, picking tayi,daga can ɓangaren Sauban yake ce mata don Allah gashi nan zai turo da saƙo idan babu damuwa yana so ta haɗa ma baƙin su dinner da zasu iso yau ɗinnan. ZUHRa cikin sanyin murya tace"Tom babu komai tana jiran shi"sanar mata yayi da taje gida zai aiko da komai,miƙa tayi tana faɗin"Tom bari naje"kashewa yayi,ada yaso suyi Oder ne ta hotel sai yaga rashin dacewan hakan,shiyasa ya yanke wannan hukuncin,sun kama musu hotel rooms wanda sai da suka kama ɗakunan goma sha biyu,duk Sauban ya biya komai. Duban Nihal da Laila Zuhra tayi tace"kuzo muje ku taya ni aiki yaya zai aiko saƙo zamuyi ma baƙin su girki,cikin murna kuwa suka tashi suka tafi,maimoon kuwa tana biye dasu,don Ateeq na can wajen su Daddy. Su Laila sai sake santin apartment ɗin suke yi,wai kamar ya sake kyau, Zuhra ta basu amsa da Ea an ƙara wasu kayayyakin. Nihal ta riƙe waist tare da duban Zuhra tace"Matar nan nifa naga sai wani glowing kike ƙarawa me yaya ke baki ne haka?hararar wasa Zuhra ta galla mata tace"munafuka bari idan ya dawo ki tambaye sa"kama baki Nihal tayi tace"Wa? Rufamin asiri in mutu maza su kaini salin alin"Laila dariya tayi tace"kenan da wani tambaya kike Nihal,aiko abinda yaya ke bata da ya wuce rufaida yoghurt"da yake Zuhra ta fahimce lailai aiko ta maka mata duka tana kaucewa, Zuhra tace"ai kam zakiyi masa bayani bari ya dawo"kafin lailai ta bata answer door bell yafara ƙara,Nihal ce taje ta buɗe,aiko wani ɗan matashin ne ya sauke bako biyu na kaya,nan Nihal ta ɗau ɗaya, Laila ma tazo taɗau ɗayan. Kai tsaye kitchen suka dire komai da komai, Zuhra ce ta bisu kitchen ɗin,leda ta farko kayan miya ne sai kayan salad,sai egusi da owgun,sai ɗayar leda kaji ne daƙwa² guda huɗu sai saidin kifi,shiru Zuhra tayi tana tsura ma kayan,aiko nan abinda zatayi ya faɗo mata,ɗaya ke gashin a gyare ne, ɗauraye wa kawai tayi sannan ta dubi Nihal tace ta gyara kayan miyan,ta fara niƙa tomatoes daban sai kayan yajin daban,Laila kuma ta wanke kifin ta tsane a basket sannan ta barbaɗe kayan spices. Kowa kama aikin sa yayi, Zuhra koda ta ɗauraye kajin,kwaso kayan spices ɗin da Ammi duk ta kawo mata tayi tasa komai yanda ya kamata,ginger,cloves,gerlic tasa kaɗan,sai ɗiyar miya,ta ɗau ko ganyen parsley ta ɗan ɗora a sama tasa Curry bata sa tyme ba, seasoning ta kwaso, Maggi star 4, Maggi know 4,rayco 4 sai onga chicken flavour tasa biyu ta rufe, store ɗin da ke cikin kitchen ɗin ta ta shiga,ta ɗauko semovita guda biyu ta fito. Ɗauraye peas ɗin tayi da carrot ta fara gyarawa bayan ta ɗora ruwa a wata tukunya,bayan ta ɗora ruwan,komai dai tayi shi cikin natsuwa wanda su Laila suke mamakin inda Zuhra ta koya girki,komai daki² takeyin sa,perboiled ɗin shinkafar ta tayi ga ƴar souce na kayan yaji da tasa ma Nihal komai,gefe guda kuma Laila na soya kajin,acan kuma kuma ga peas nan nata nuna a ruwan da tayi sanwa ɗan dai-dai,tuwon ta fara tuƙawa dama tayi talge tun ɗazu, duban Nihal tayi tace ta zuba mata shinkafar koda ta zuba lokacin ta gama tuƙin hakan yasa tazo ta fara motsa shinkafar,gabaɗaya wani ƙamshi me shegen daɗi ya game apartment ɗin,bayan ta motsa shinkafar ne ta ɗan rufe ya ɗan turara,abinka da nonestick pot. Laila na gama suyan kajin dama tun ɗazu an sauke source ɗin da ɗan ruwa kaɗan a jikinta,kifin aka ɗora Nihal itama ta cigaba da kula da shi gabaɗaya hankalin ta nakan Zuhra don ganin komai Allah yasa ni cike take da mamakin komai, haɗa kajin nan Zuhra tayi aɗan bawo me balance sannan ta ɗauko source ɗin nan tafara haɗa komai,cikin natsuwa take komai, Laila ganin kamar ta gaji ne yasa ta amsa ta cigaba da motsawa,cikin natsuwa tace"naga ma kamar ya haɗu,ki buɗe wancan drower ki ɗauko set ɗin wasu foodflask mugani,miƙewa Laila tayi inda Zuhra kuma ta rage wutan tuwon don yanzu zata kwashe,kashe wutan shinkafar tayi,da yake kulolin babu lefi suna da ɗan girma duk da kuwa kyan su ana biyun ta juye shinkafa,na farkon kuma ta juye pepper chicken ɗin,kwashe sauran tayi ta maida carbenet ɗin,sannan ta fito da wasu set ɗin. Suma 4set ne sai ta cire biyu da babban dana ukun, babban suka fara ƙulla tuwo suna sakawa sai da suka ƙulla malmala goma ƴan dai-dai,sauran tabada wani foodflask ɗin tace a zuba shima malmala goman yaci,babu abinda ya rage akan gas sai miyan tuwon da kuma cooslow, already an goge kayan cooslow ɗin haɗi kawai yake jira,sauke miyar tayi wacce sai tashin ƙamshi takeyi sannan ta zuzzuba anasu foodflask ɗin sauran ta zuɓa a ɗayan foodflask ɗin shima,sannan ta ɗauko soyayyen kifin ta zuba a kowane kulan miya wada tacce,ragowar ta saka cikin fridge. "Ikon Allah nifa ina mamakin inda kika iya girki ne haka Zuhra musamman me yawa,kinji yanda ƙamshi ya game apartment ɗinn nan?Nihal tayi maganar tana kama haɓa,murmushi Zuhra tayi cikin zolaya tace"idan za'a ɗauki Course sai azo tunda bikin naku ma ya gabato"Laila tace"yanda kika jin nan" sauran jollop ɗin shikafan tukunyar tabasu foodflask tace su sake musu,fito musu da komai tayi harda su masarar gwangwanj,bama,waken gwangwani,babu egg dai tace su haɗa cooslow ɗin,ita kuma a gurguje ta haɗa musu lafiyayyen cucumber juice nd tamarind juice ta saka cikin fridge, duban su tayi tace"bari naje nayi sallolina gamunan babu magrib bare isha'i,sai na shirya,don ma yanzu aka kira isha'i,tana fita dai-dai lokacin kuma Sauban yakira ta,kan nan da 8:30 zasu shigo,amsa mishi tayi da to tana duban agogo,lokacin 8:06 cikin sauri tafaɗa bathroom tayi wanka tayi alwala,a gurguje tazo tafara sallolinta,a lokacin da ta idar 8:20 cikin sauri ta shirya cikin wata haɗaɗɗiyar lutfaya golden yellow,wanda ya mata kyau ainun,powder da kwalli kawai tasa sai ɗan kunne,agogo da sauran su,lalle nan ya fito tare da yin kyau sosai,high heel shoe me igiyoyi ta saka brown sannan tafice,shiga kitchen ɗin tayi da sauri tace su fito da kayan a fara shirya dinning,aiko cikin hanzari suka fara shirya dinning ɗin,komai suka jera sa a muhallin da,plates,glass cup's,spoons duk dai komai na buƙata,a dai-dai lokacin taji door bell,nufar ƙofan tayi tana buɗewa,babu zato taji ya wani rungomu to,nan ya shiga bata kisses kota ko ina,su Laila ganin hakan yasa cikin sauri suma suka fice suka nufi personal palour ɗin ta don gabatar da sallolin su. "Uhum kai yaya Please stop,tayi maganar tana maƙalƙale jiki"cak ya ɗauke ta ya shige da ita palour yana dariya,kukan shagwaɓa tasa mishi wai ya sauketa,dire ta yayi yace"Eyye kin ganki kuwa Mrs MS?kinyi 100% babu makusa dressing me kyau me kuma mutumci,tunda muka shigo ƙamshi ya buɗaɗe gidan nan"Zuhra ta rufe ido tace"kai yaya,to ina abokan naka? Sauban yace"yanzu zan shigo dasu,wai Taufeeq har dashi ya tsaya wai sai na bashi izini?ɗan rainin wayo"hararar wasa Zuhra ta zabga mishi sannan tace"ai gaskiyan shine ni banga lefin shi ba,yaya ya san ka da kishi ne shiyasa"Sauban yace"to kinga lefina?ke bakisan irin kyan da Allah ya miki bane shiyasa,ga diri na jan hankali dole na dinga taka tsantsan dake"yana faɗar hakan ya juya,itama Zuhra murmushi tayi ta koma kitchen,ɗauko juice ɗin da ta haɗa tayi,glass jug biyu ta fito dashi,suma a lokacin ta taradda su zazzaune sai hayaniyar fira sukeyi,ajiye komai tayi sannan ta koma ta shaƙu tray da bottle water shima ta ajiye ta koma ta ɗauko cooslow ɗin da sukayi ɗanɗane,ta ajiye wani tray ɗin ta ɗauko inda su samosa,spring rolls nd cake ke kai ta ajiye, Sauban ne ya ƙariso kamar zai rungume ta yana kallon dinning ɗin yace"yanzu duk wannan aikin Babyn Baby ce tayi shi?lallai yau da rigima"dukan wasa ta kaima chest ɗin sa tace"mun kammala bari naje palour su Laila na can"Sauban yace"Okay love yhu"Zuhra ta watsa hannu ba tare da ta jiyo ba tace"me too love". "Guys bismillah fa ku ƙariso"ya faɗa nan kuwa suka tattaso da yake dinning ɗin me cin mutane goma sha biyu ne,su kuma su goma sha ɗaya ne akwai ya Taufeeq da ango Kareem,sauran ne dai baƙin su,waɗanda in ka kallesu kasan kuɗi da sun zauna babu ƙarya, Kareem yace"Kai oga ƙarfi da yaji kasa Aunty Zuhra irin wannan aikin? murmushi Kareem yayi wani daga cikin su yayi carab yace"Nima idan zanyi baƙi Nihla nake sawa tayi komai,to ga iyalin ka ta iya mezesa kaje waje ci? Please Taufeeq yi ka serving ɗina"gabaɗaya dariya aka sanya harda Taufeeq kowa ya ƙagu ya fara cin abinci,inda kowa ya shiga zaɓan abinda zaici,sai dai daga ƙarshe ko wannensu sai da yaci komai dake wajen,babu abinda ke tashi sai muryoyin su da suke zuba santi [7/25, 21:43] 𝐎̃𝐔̂𝐌 𝐀̃𝐉𝐌𝐄̨𝐑𝐋💜🤍: 👨🏽‍🦳 *_GALADIMA FAMILY_* 👨🏽‍🦳 [7/26, 10:39] 𝐎̃𝐔̂𝐌 𝐀̃𝐉𝐌𝐄̨𝐑𝐋💜🤍: 👨🏽‍🦳 *_GALADIMA FAMILY_* 👨🏽‍🦳 Page: 91/92 ____Sun zuɓa santi,zuwa can Kareem yace"Allah Sarki Aure Aure me daɗi oga kaifa naka yayi kyau saura mu ƴan baya don wallahi Aunty Zuhra ta iya girki, shiyasa lokacin da suke Kaduna Taufeeq idan yazo nan yayi ta ɗafe-ɗafen yunwa ashe ashe"dukan wasa Taufeeq ya kai masa gabaɗaya suka saki dariya,wani a cikin su me sunan kabeer ɗan Gombe suna ce mishi kb ya dubi Sauban yace"Wallahi da a garin nan muke sai haseena tazo wajen yarinyar nan koyon girki"harara Sauban ya galla masa sannan yace"Matar rawa ce yarinya?Kb yace"Ea mana yarinya ce akan su haseena,a shegen girman kan haseena ma nasan ba zata taɓa zuwa ba"haka dai suka cigaba da tattauna wa domin sun ji daɗin abincin matuƙa. Basu suka bar gidan ba sai wajen 9:30 lokacin su Laila ma sun tafi,tare da tuwon Galadima, Daddy da Ammi, Ummie sai na Baba Hasheem,suma dai acan hakan ce don santi suka dingayi,sannan su Laila suka sanar dasu Zuhra tayi girkin ta abinta,don su shinkafar su da kajin su suka ce, Aunty Mashahuda kuwa kiran Zuhra tayi ta sanar da ita idan akwai ragowan tuwo ta bama ya Taufeeq ya kawo mata,da yake a wajen ta malmala ɗaya ya ragu kuma tana so taci don bata jin cin shinkafar,ce mata tayi bari su tafi idan sun rage zata bashi ya kawo mata,cike da farin ciki Mashahuda ta kashe wayar,abinka da me kitchen. Sauban ne ya shigo ɗakin yana aika mata da wani kallo me tafiya da zuciyar mutum,idanuwan sa sun koma so sexy yace"Wifey taso muje kuyi sallama"yayi maganar yana gyara mata lutfayar ta,hannun ta ya kamo ya miƙar da ita sannan suka tafi ajere. Nan Zuhra ta shiga gaishe su,cikin kulawa suke amsawa,wani me suna Kamal yace"Gaskiya Madam oga beyi zaɓen tumbin dare ba shiyasa yake ta sake zama young Alhaji ashe kulawa yake samu,wannan delicious haka"murmushi Zuhra tayi tana sunnar dakai,nan dai duk suka gaggaisa suna miƙewa don tafiya tare da mata sallama suna godiya,hannun Kb ɗin riƙe da tray ɗin snack's ɗin don sunce sai sunje otel zasu ci, Zuhra tace"babu komai ai,fita sukayi ya Taufeeq na jinjina mata hannu, Sauban ya bata wani peck a kumatu"ina alfahari dake matata kin fitar dani kunya Allah ya miki albarka,yasa ki haifa min Baby girl me kama dake sak!👌🏼yayi maganar yana ƙale yatsu,dukan wasa Zuhra ta kaima chest ɗin shi sannan ta nufi dinning ɗin tace"Kaga dare ya fara bari na fara kai kayan nan kitchen,kun rage tuwo? Sauban ya dube ta cikin kulawa yace"baki ci bane? Zuhra tace"Ea ban ci ba ina da ragowan malmala ɗaya a kitchen dama Aunty Mashahuda ce ta kira tana so"Sauban yace"Caɓ anya sun rage tuwon nan bari mugani"yayi maganar yana buɗe foodflask ɗin,ragowar malmala ɗaya ne ya rage,yace"kinga abinda ya ragu ki kira ta ki sanar da ita babu"Zuhra tace"Haba yaya a'ah gwara na bata ni naci jollop ɗin hakanan"Sauban ya wurga mata harara yana tamke face"wai kina nufin ki zauna da yunwa?to baze yiwu ba keda aiki wasu da lamushe daɗi ki kirata kice mata babu"marairaice face Zuhra tayi sannan tace"yaya ita fa me ciki ce inada ragowar miyan gobe da safe sai na tuƙa wani yanzu zanci jollop ɗin ka bari a bata"Sauban ya sake tsuke face yace"kika sani ko kema cikin ne dake?dariya Zuhra tasa kawai batare da tayi masa reply ba saboda kiran wayar sa da akayi. Batare da yayi picking ba yace"bari naje suna jira na zamu kaisu otel ɗin da suka sauka sai mu dawo,cikin sauri Zuhra tace"Please yaya ku sauke ni cikin gida sai na kaima Aunty Mashahuda tuwon"wannan karan tamke face ɗin yayi gabaɗaya Sannan yace"ba zaki kai mata ba a daren nan,idan ta buƙatu tazo ta amsa"yana gama faɗar haka yayi wucewar sa,ɗaga murya tayi tace"safe journey"juyaowo wa yayi cikin jin daɗi yace"tnx love"ya fice,kaya kayen kayan Zuhra tayi tana harhaɗa plates ɗin,kuɗi ta gani kashi da kashi kusan biyar,zato ido tayi cikin mamaki,wato ihsani sukayi mata kenan,ɗaukan kuɗin tayi ta irga na farko 10,000 na biyu 5000,na uku 10,000,na huɗu 15,000,na biyar 7000,cike da mamaki Zuhra ke kallon kuɗin lokaci ɗaya sun haɗa mata 45,000k kenan sun biya ta kuɗin aikin ta,hakan yasa sai taji bata wani murna da ganin kuɗin ba,ajesu tayi anan side ɗin dinning ɗin ta cigaba da gyaran wajen. Basu jima ba suka shigo shida ya Taufeeq,a lokacin ta shirya cikin wasu shegun night gown,sanin ƙila Taufeeq ya shigo yasa ta zunduma long hijjab abin ta, Taufeeq yace"Malama ina tuwon Madam ɗina? Zuhra na murmushi ta miƙe ta nufi kitchen,bata jima ba tafito hannun ta ɗauke da foodflask tare da wani ɗan take away tace"gashi tunda abin bin bashi ne,kada Babyn mu ya fito da taɓo yaya"Sauban yace"a samu hujjan yi mana aharri ba? Taufeeq ya amsa foodflask ɗin yana dariya yace"wallahi kuwa don haka kun fanshi kawunan ku,gud night"Yana ƙare faɗar hakan ya fice, Sauban na biye dashi ya sama ƙafan key,tare da juyowa ya rungume Zuhra a jikin shi,cikin kulawa yace"kinci abinci? ɗaga masa kai tayi,yana rungume da ita suka haye stairs yana cewa"shine za'ayi wankan ba za'a jirani ba?so wallahi sai kinyi sabon wanka don ke zaki tayani"bubbuga ƙafa Zuhra ta fara cikin shagwaɓa,don harga Allah idan aka ce dare yayi to always cikin fargaba takeyi,don tutur federal government ɗin ta a matse yake duk da ruwan ni'iman da yake shiyasa take wahaluwa,duk da ko kaɗan bata nuna masa gazawan ta,hakan ke ƙara masa son ta da ƙaunar ta,kamar yasan tunanin da takeyi ya matso dai-dai kunnen ta cikin muryan raɗa yace" sai kinyi haƙuri da yayan ki, cuz bana gajiya dake keɗin ta daban ce Babyn Baby"yayi maganar tare da ɗaukar ta cak ya shige da ita toilet. ******** Dama akace duk abinda ake sama rana sai idan lokaci beyi ba,domin kuwa yau ne ake shirin ɗaurin auren su Kareem. Zuhra tayi kyau har ta gaji,ankon colour sukayi da Sauban kayan da ya siyan musu,wani straight gown aka yima Zuhra me ɗaukar hankali,don ma veil ɗin babba ne,daga ita har Sauban ɗin duk wanda ya kallesu sai ya kuma, ga high heel ɗin ta da ga henna gaskiya Zuhra tayi kyau wanda me karatu ne kawai zai ƙiyasta irin kyan da tayi a zuciyar sa,saura five minutes daurin auren don daurin auren 2:30 ne gabaɗaya 'yan gidan su tun ɗazu suka fice, Ammi na gidan su Kareem, Ummie dasu Mashahuda dasu Laila suna gidan su Mom,sai da Sauban ya samu natsuwa sannan ya shirya Zuhra a bala'in gajiye take ƙarfin hali kawai takeyi duk abinda takeyi,da kanshi ya kamata ya shiga da ita gidan,nan fa maroƙa suka shiga roƙo,duk inda suka gifta kuwa kallon su akeyi ƴan jaridu ma na ɗaukan pic,haka zalika wasu daga cikin mutane,don Sauban yayi fice matuƙa kuma bikinsu da Zuhra duk da ba'ayi wani events ba amma hotunan da akayi yasa sosai sukayi trending a lokacin. Mom sosai ta tarbesu cikin kulawa ta kamo Zuhra,palour da aka kai Ummie nan Mom ta nufa da ita,Hajiya Biba ma cikin kulawa ta tarbe Zuhra,ita kuwa cikin girmamawa take gaida su, Zuhra tace"kai Mom kin ganki kuwa? Baba yaga kwalliyar nan?daƙuwa Mom ta mata tace"ƴar nema da har ina cewa Sauban ya rufe miki baki ashe be rufu ba"dariya Zuhra tayi tana ɗan rissinawa wajen Ummie tana gaishe ta, hararar Ummie ta kai mata tace"hamshaƙiya ai nayi tunanin bazaki zo ba"don har aiko su Nihal nayi tunda wayar ki kin kashe"Zuhra tace"Ummie fa yaya ne ya tsayar dani"Ummie tace"Okay to kije wajen amaren mana"Zuhra tace"ai bansan inda suke ba"dai-dai lokacin Muneefa ta shigo tasha kyau cikin lace me tsada ganin Zuhra yasa ta ƙarisu da sauri,kamo ta tayi taja sai da suka fita tace"Masha Allah maganar ku ya yaɗa ko ina ance kunyi anko da yaya kun haɗo shine nazo neman ki muje"Zuhra tayi murmushi kawai,a dai-dai lokacin ne kuma maroƙa suka shiga shela "An ɗaura auren Abdulkarim Usman Shugaba tare da amaryar sa Rahma Ahmad lakadan ba ajalan ba,nan fa mata suka shiga zazzaga ruwan guɗa. Sosai biki yayi armashi, Zuhra ta bawa Rammat gudummawar bikin ta da yaya ya bata ta bayar 50k Cass haka ta bata,tabawa Hajiya Biba 20k sosai sukayi farin ciki don Ummie ma 20k ta bawa Hajiya Biba Mom taji daɗin karan da suka mata. Ƙarfe huɗu akazo ɗaukar amarya a masu ɗaukar amarya kuwa harda Ammi,anan itama ta bawa Hajiya Biba 30k, Zuhra Sauban da Taufeeq suka ɗauke su ita da Mashahuda dasu Laila,aiko aka nufi new g r a maidugri da amarya,gida fa yayi kyau sosai ɗan dai-dai sama da ƙasa ne,sosai fa wajen yayi kyau Masha Allah,sannan babu lefi su Mom sunyi ƙoƙari wajen haɗa wajen,duk da saman Kareem da kanshi shi ya sanya komai,shima yayi kyau sai dai ko rabin rabin na Sauban be kamo ba, dai-dai ƙurji dai, dai-dai tsaki,haka kowa yafito cike da sanyi aka watse aka bar amarya don babu ƴan kwana, Zuhra kuwa daurewa takeyi saboda zazzaɓin da yake ta cin ta a tsattsaye. Cike da gajiya suka isa gida. Washe gari ya kama Sunday,koda Zuhra ta tashi wajen 9 bata ga Sauban ba tunda komawa bacci tayi abinda,gyara ko ina tayi sannan ta shiga kitchen,tuwon ta ta tuƙa malmala huɗu sannan shi kuma ta haɗa mishi lafiyayyar sandwich da coffee,ta shiga toilet tayi wanka sanda tafito lokacin taji motsin shi ya shigo gidan tunda ga ƙarar motar sa nan. A gurguje ta sakko cikin wata haɗaɗɗiyar turkey gown tayi mata kyau peach colour me hannun vest,sannan har ƙasa,sai hulan gown ɗin da ta saka,cikin da jin daɗi yayi hugging ɗinta tare da shinshina ko ina na jikinta yana lumshe ido,cikin wata kasalalliyar murya yace"shine zakiyi wankan kibarni?jin haka yasa Zuhra cikin zafin nama ta fusge jikinta da gudu ta ƙarisa wajen dinning tace"Allah ba zaka sani yin wani wankan ba"cikin muryan dariya tayi maganar, Sauban yace"hmmm yarinya zaki shigo hannuna ne"hayewa stairs yayi be daɗe ba ya fito cikin kaftani black anyi mishi ɗinkin halfjamfa yayi kyau ainun,gyararren baƙin gashin nan nashi sai sheƙi ya keyi,zama yayi nan Zuhra ta fara serving nashi tana cewa"Gud morning Babyn baby"murmushin jin daɗi Sauban yayi yace"morning to my everything,hope kintashi lafiya?Zuhra tace alhamdulillah, duban plate ɗin ta yayi yace"nima fa zanci tuwon"yayi maganar idanuwan sa ƙur akanta,murmushi Zuhra tayi tasa mishi malmala guda,nan suka fara breakfast ɗin su cike da soyayya tare da ƙaunar juna. ******** A ranar su Ummie suka koma, Zuhra kuwa kasuwa tasa Sauban ya wuce da ita tunda gobe shima zai tafi,sam bata son tafiyar nasa haka kawai taji damuwa inda ta alaƙan ta hakan a matsayin shaƙuwa. Koda ta dawo,dambun kaza ta shiga haɗa masa da doughnut sai cin-cin,tare sukeyin aikin don sosai ya sake yana taya ta suna komai cikin soyayya juna,basu kammala ba sai wajen 6:00,aiko Sauban bebi takan gajiyar da sukayi ba,ya nemi haƙƙinsa ya sauke,ita kuwa Zuhra sai ƙananun kukan shagwaɓa take masa,wanka ya musu sannan suka ɗauro alwala,kaitsaye masjid ya wuce,ita kuma ta tayar da sallan ta anan. Text ya turo mata kan yana wajen su Daddy kada tayi girki,reply ta masa cewa"Okay ka gaishe su"nan ya turo mata alamar sumba😘, murmushi kawai Zuhra tayi sannan ta miƙe,itama gobe suna da class sai dai wajen 11 zasu shiga,shiko Sauban 9 zai wuce,cike da gajiya ta kwanta ba ita tafar ka sai sanda taji anata shafa ta,cikin sauri ta buɗe idanuwa,a kyakkyawar fuskar mijinta ya sauke,murmushi tayi ta miƙe tare dukan chest ɗinsa"Kai Yaya shine kaje ka daɗe ko? Sauban yace"Sorry love Ammi tace na tsaya na taho miki da masa"yayi maganar yana kamo ta,cikin farin ciki Zuhra ta taso ta biyo shi,da yake anan palour saman nashi ya ɗauki duk wani abin buƙata,nan yayi serving nasu tare da feeding ɗin ta don yaga bacci ne sosai a idanuwan ta,koda suka kammala da kanshi yaje ya kwantar da ita yaja mata duvet,shi kuma ya dawo palour don yin aiki a laptop ɗin sa. Zuhra tunda ta farka da asuba basu koma ba nan ta tayashi haɗa duk wani abin buƙatan sa,inda shima ya nemi haƙƙinsa,(oga Sauban kenan sam ba'a ɗaga ƙafa,kana so Zuhra itama ka koya mata......ba) Lokacin har 9 ɗin yayi sosai Zuhra ke kuka don ko kunyar su Daddy bata ji ba,kuka takeyi sosai,shi kanshi Sauban daurewa yakeyi,ganin taƙi shiru ne yasa Baba Hasheem cewa to idan batayi shiru ba bazata rakasa airport ba,dole kuwa ta haɗiye kukan ta, Kareem da kanshi shida Rammat suka zo kaisa airport,sai Zuhra da Yasir,haka suka tafi Ammi da Boɗejo su Galadima na ɗaga masa hannu. Basu baro airport ɗin ba sai da suka ga tashin sa inda ya nuna mata soyayya a gaban mutane don rungume ta yayi ya bata sumba a goshi tare da mata magana a kunne yana shafa cikinta"Insha Allah nasan nayi ajiya anan,ko don dagewan da na dinga yi kwana biyu"sosai Zuhra ta saki murmushi tana faɗa wa jikinsa,cike da ƙaunar juna suka rabu. Har gida su Kareem suka kawo Zuhra suka ajiyesu ita da Yasir, apartment ɗin Ammi ta wuce,bata wani jima ba tayi shirin school 10:30 ta fita inda driver zai sauke ta. [7/26, 21:02] 𝐎̃𝐔̂𝐌 𝐀̃𝐉𝐌𝐄̨𝐑𝐋💜🤍: 👨🏽‍🦳 *_GALADIMA FAMILY_* 👨🏽‍🦳 Page: 93/94 _____Zuhra ta cigaba da resuming school ɗin ta duk da bawani daɗi takeji ba amma a haka take maida hankalin ta sosai akan karatun ta,duk tsananin kewar mijinta da takeyi ko da yaushe sai dai sam taƙi bada ƙofar da za'a fahimci hakan har shi don suna waya sosai tare da video call don ya aiko mata da tsadaddiyar laptop ɗin ta Apple. *AFTER 4 MONTHS* Abubuwa da dama sun faru na farin ciki,ciki kuwa harda ƙarin matsayin da Sauban ya samu aka maida shi Malaysia sosai yaji daɗin hakan don yafison ƙasar da Canada,ƴan uwa kowa ya taya shi murna da farin ciki, Zuhra kuma suna exam na shiga 200l inda bikin su Laila yayi saura 2 months,shirye-shirye duk sukeyi ta kowa ce ɓangarori haka aketa shiri. Akeela duniya ta ladabtar da ita duk da kuwa matsanancin Son da take ma Sauban nanan daram dam don babu abinda ya ragu sai ma ƙaruwa,kullum ka ganta a ɗaki cikin zubda hawaye takeyi tare da tsanan kanta da kanta,ta bayan fage kuma mommy(hajiya daharatu) nata ƙoƙarin ta dawo da ita ruwa tsundum. ******** Su Zuhra sai da sukayi 2 weaks suna exam sannan suka kammala a lokacin tafara shirye-shiryen zuwa kaduna don haka ta kira Sauban take sanar dashi sai dai duk ƙoƙarin ta na yabari taje yaƙi hakan yasa takai ƙarar shi wajen Daddy,nan kuwa Daddy ya rufe shi da faɗa sosai inda yace tare ma zasu je da Ammi,sai a sannan yaji sanyi har ransa ya gamsu,aiko ranar Monday da safe su Ammi suka bi jirgin ƙasa sai Kaduna. Sosai su Ummie sukayi murnan ganin su,sunji daɗi matuƙa nan aka shiga nan nan dasu. Zaune take a bedroom ɗin Ummie suna video call da Sauban,cemata yayi"Ni a tunanina kafin nabar Nigeria nayi miki ajiya?ashe babu abinda ya shiga?gaskiya ball ɗin nan bata shiga yanda akeso ba"dariya Zuhra tafara tana rufe face ɗin ta saboda kunya,hakan kuwa ba ƙaramin daɗi yake ma Sauban ba tace"Kai yaya wallahi kai kam baka da kunya,ni ina ni ina ɗaukar pregnant?ai i AM still young"hararar wasa ya cillo mata ta cikin wayar yace"a'ah kin manta ne,You re baby ne"dariya sosai ta shigayi zuwa can ta ɗan kwaɓe face tace"to yaushe zaka dawo nikam?wallahi am tired,I am always miss yhu hub"tayi maganar tana mummurza idanuwa,ƙasa Sauban yayi da muryan sa ya fara lallashin ta"Oh baby I really miss you too, don't panic ina dawowa soon but sai bikin yaran can"cikin sauri Zuhra tace"Nan da 1month 2 weaks? Sauban yace"Yess beb ai idan na dawo bazan baro ƙasar ba sai da ke tare da ajiyan bby na"dariya Zuhra tasa tace"but yaya anya ba punishing ɗina kayi ba? Sauban yace"meya ne wani abin punishing?me kika mun?aiki ne dai kawai da yamun yawa nd gefe guda ga damuwar rashin ki,ai shiyasa idan na dawo ko?hmmmm"yayi maganar yana ƙane mata one eye's,murmushi Zuhra tayi don ta gane abinda yake nufi. Haka suka cigaba da soyewar su cikin kulawa da ƙaunar juna. Zuhra wannan zuwan ta ɗan zazzaga gari sosai taji daɗi,ga shiga kasuwa da suka dinga yi da su Nihal kwashe² inji Ummie,kwasan tarkace. Duk wani gyara da ake ma su Laila tare da Zuhra ake musu,haka dilka da halwa,ta zauna har tafi amaren kyau da ɗaukar ido,sunyi kyau ainun,shiryawa sukayi da Ammi suka shigo Zaria gidan su Ammi,duk da mahaifan ta sun rasu but ƴan uwan ta maza da mata nanan,sosai suka samu cikakkiyar kulawa ta musamman,sai nan nan ake da Zuhra,kwanan su biyu gidan su Ammi,suka wuce gidan Amma suka mata yini a can ne driver Abba zai zo ɗaukar su,gabaɗaya sati ɗaya suka yi a Kaduna suka nufi Maiduguri cike da kewar juna,inda amaren kuma zasu iso ana saura 2 weaks biki. "**""*****"""""****** Ta kowane ɓangare haka aka cigaba da shirye-shiryen biki,Zuhra sai da Sauban ya turo mata da 500,000 kuɗin siyayyan ta ɗinki,takalma,jakunkuna,mayafin,da sarƙoƙi Aunty Safeena taje tayi mata siyayyan komai. Bikin su Laila kam zai kama za'ayi bikin saura 2 months azumi ne. A yau biki ya kasance saura sati biyu, Zuhra ce zaune a palour Ammi da sauran jama'a anata murnan lefen Laila da aka kawo gefe guda su Guggo Laure ne da surikanta,maƙota da abokan arziƙi duk sun shigo,dama yana sashen Boɗejo ne shine daga baya aka kawo nan, Hajiya maimuna sai satar kallon Zuhra takeyi cike da sha'awa don yarinyar natsuwar ta ta mata. Sallama Kareem yayi ya shigo hannun sa jaye da trolley bag,sai wani a kafaɗan sa,bayan sa security ne shima jaye da trolley bag ɗin,gabaɗaya kallo ya koma kansu ana amsa musu sallama,ana haka ne ya shigo mouth ɗinsa ɗauke da sallama ya sake cika yayi wani ɗanye-ɗanye,aiko nan aka fara mishi sannu da zuwa,amsawa yakeyi yana zama inda maƙota suka fara rarraguwa,nan yafara gaida waɗanda ke zazzaune a palour, Zuhra kanta na ƙasa ji takeyi kamar dream wai yaya ya dawo,ƙura mata ido yayi cikin wani irin shauƙi da ƙaunar ta,ba tare da kunya kowa ba ya taso ya nufo inda take,kneel down yayi a gaban ta yana kamo haɓarta,ido huɗu sukayi"tallafo face ɗin ta yayi yace"bakiyi murnan ganina bane Babyn Baby?ko fushi akeyi dani?yayi maganar yana ƙura mata ido don wani masifan kyau yaga tayi masa,atake anan ƴatr guntuwar feeling ɗinsa ta motsa,jiyake kamar ya....... Su Guggo Laure kuwa su aka bari da ganin abin kunya don sunji nauyi sosai,Hajiya maimuna kuwa tausayin Akeela ne ya faɗo mata tabbas tasan ƴar ta bata da gurɓi a zuciyar Sauban,hasalima ba sa'an aurenta bane,lallai ta fice kanta ta cuce su. Ammi tace"Sannu ko?duban Ammi yayi da sauri yana shafa kwantancen sunan sa tare da miƙewa yace"Opps Ammi sorry,ina rasa natsuwa ta idan naga Zuhra"duk zaro ido sukayi suna duban sa, Mom tace"Ja'iri to ai da kaje kayi wanka kaci abinci ka huta sai kaji daɗin tasa ta kamar tv"murmushi Sauban yayi yana fita kawai don dama su Kareem tun da suka shigo da kayan suka fice, Mom ta cigaba da cewa"wani irin soyayya Sauban ke ma Zuhra jiyake kamar ya maida ta ciki"murmushi Ammi tayi tace"ummm"Guggo Laure tace"Allah Sarki dama haka akeso Allah ya zaunar dasu lafiya"da Ameen duk aka amsa inda suka miƙe kan zasu wuce, Ammi dakatar dasu tayi ta shiga kitchen ta haɗo musu take away na snacks wanda a kama masu kawo kaya,driver Daddy ya maida su gida. Nan suka cigaba da hirar su da Mom sai wajen magrib itama ta wuce apartment ɗin ta,duban Zuhra Ummie tayi tace"Kitashi kije kiyi wanka kiyi sallah,kizo ki haɗa ma mijin ki dinner, kafin anjima yazo ku wuce"turo mouth Zuhra tayi cikin ƴar shagwaɓa tace"A'ah Ammi nan zan sake kwana gobe na koma"Ammi tace"wane ke yarinya?ai ƙafarki ƙafar mijinki ba'a sashin nan ba,ni nasan da dawowan shi shiyasa na roƙi Muneefa tare hanne sukaje suka gyara miki sashin,shiru Zuhra tayi sum-sum ta nufi corridor in. Ammi tace"shiryayyu yaran zamani". ***** Sosai Zuhra ta bawa mijinta cikakkiyar kulawa,daga ƙarshe suka tattara suka nufi gidan su ko duba Galadima ma basuyi ba,akwai ranar Zuhra ta gane jure ta,ta tantance Allah ɗaya ne,don ɓaƙaramin wahala Sauban ya bata ba,duk matse abinnan da yake ranar dai ya fanshe an kayanshi,yana kuka tana kuka,shi kukan da..Zuhra kuma na wahala,sosai Sauban yake ta zuba uban sumbatu yaƙi yin shiru,a daren dai kwana yayi yana abu ɗaya don be fiye wani hutawa ba sai kuma..... Hakan yasa koda asuba Zuhra tayi bala'in laushi tayi tiɓis da zazzaɓi gau ta kwana,da kanshi ya mata wanka ya gasa ta sosai,shida kanshi ya haɗa musu breakfast sai dai duk yanda yaso Zuhra taci kasawa tayi,ruwan zafi ma tana sha ta amayar dashi gabaɗaya. Gaba ɗaya Sauban ranar cikin jinya ya yini,su Laila suna dirowa gidan duka iso wajen Zuhra,sai dai ƙirƙiri Sauban ya hanasu ganin ta yace bata da lafiya tana bacci. Koda sukaje duk ana sashin Ammi har da su Ummie,Mom,Mommy, Mashahuda, Safeena. Mom tace"ai dole Zuhra taji a jikinta ta shiga hannun babban yaya,yanda Sauban ya dawo da ƙishin ruwan ta ai babu sauƙi sai na Allah"sum² su Laila suka bar wajen, Mommy tace"Ni kaina tausayi take bani kamar tayi ƙanƙanta"Ummie da Ammi dai shiru sukayi suna sauraran su. Aunty Safeena ta samu Mashahuda a kitchen tace"Ai yaya daga ganin shi za'ayi jarababben mutum ne"Mashahuda ta sanya dariya tace"Ai duk haka suke sai dai yaya fa kamar iyaka ne"dariya suka sanya gabaɗaya, Safeena tace"Zanje na duba lafiyar ta Gaskiya yanzu in haɗa mishi da pretending"Mashahuda tace"Nima zani,muje gabaɗaya"aiko haka suka ɗunguma suka fito,mayafan su suka ɗauka da dubara suka fice don sun san Ammi yanzu sai ta hana su. Gabaɗaya idanuwan ta sun kumbura da ƙyar take iya tafiya saboda ciwon da jikinta ke mata,shi kanshi Sauban yasan yau ya bata wahala hakan yasa hankalin sa sosai tashi,kama ta yayi suka sauko ƙasa,nan ya shiga tambayar ta mezata ci?girgiza mishi kai tayi wahaye na sirnano mata tace"banjin cin komai mouth ɗina babu apertite nidai ka kaini wajen Ammi"tayi maganar tana sakin kuka, Sauban yace"wajen Ammi kuma baby?why? Zuhra tace"Yaya pussy na baka tausayina zafi nakeji,Please ka kaini"sosai ta bashi tausayi ana cikin haka ne sai yaji door bell,share mata tears ɗin ta yayi sannan ya miƙe ya buɗe ƙofan,tamke face yayi yace"Lafiya? Aunty Safeena ta kama baki"kaji Yaya da wani zance,lafiya lou mana,su Ammi suka ce muzo mu duba jikin Zuhra don su Laila sunce bata da lafiya"tayi maganar tana raɓa sa ta shigo, Mashahuda sum² ta biyo bayan ta don tasan halin shi, Aunty Safeena tace"Wai kinji jikinki zafi garau?duban Sauban tayi wanda yayi fata-fata da face tace"yaya zazzaɓi ne ke damun ta wai?jiyake kamar ya galla mata mari don takaici saboda sarai yasan gulma ya kawota,yasan Safeena ciki da bai,yace"check her! Yayi maganar yana harɗe hannaye,wargazazzan gashin ta Safeena ta gyara mata tace"me zaki ci? Zuhra tace"babu komai ni ban son cin komai"to ko wanka zakiyi? Zuhra tace"nayi wanka,sai kuma tayi rau-rau da ido"Nidai ku kaini wajen Ammi na kwana acan"tayi maganar tana sakin kuka wanda hakan yasa sosai ran Sauban ya ɓaci,lallai ma yarinyar nan ni dodo ta maidani kenan?cikin ɓacin rai ya haye stairs,babu jimawa ya fito hannun sa ɗauke da hijjab ɗin ta,miƙa ma Mashahuda yayi cikin ɓacin rai yace"gashinan sa mata ku wuce"amsar hijjab ɗin Mashahuda tayi Safeena ta sa mata hijab ɗin suka kamata suka miƙar da ita,sosai ran shi ya ɓaci,juyowa Zuhra tayi tana ƙoƙarin mishi magana ya dakatar da ita"don't talk, please go"yayi maganar yana nuna mata hanya, Safeena tace"yaya kayi fushi ne?wani harara ya galla mata sannan ya haye sama, Zuhra kuwa bata damu ba tayi ficewar ta, suma binta sukayi,su Ammi na zaune suka gansu sun shigo riƙe da ita,cikin sauri Ammi da Mom, Mommy suka nufosa, Ammi tayi saurin kamo ta"yaya dai?jikin ne?Safeena tace"jikinta da zazzaɓi sosai sannan tasa rigima ita nan zata dawo hakan yasa yaya ya zuciya yace tadawo"shiru duk sukayi"Mom tace"ke kuma Safeena sai kika taho da ita?basai ki barta ba tunda kinga beso? Ummie kyaɓe mouth tayi tace"saboda taga tana gindin gida ne shiyasa"Ammi tace"kaji bilkisou da wani zance yarinya najin ciwo kice wani kaza?umm tayi maganar tare da kama hannun Zuhra ta zaunar don gani tayi kamar jiri na neman kada ta. Ummie miƙewa tayi tace"Sai da safen ku, Allah ya huta gajiya"tafice,duk da kallo suka bita don dama Ummie macece me kawaici ta fice, Mom ma sallama tayi musu, Mashahuda Taufeeq ya kirata dai-dai lokacin anzo ɗaukar Safeena suka fice tare, Ammi ta dube Zuhra tace"meyasa kika zaɓi dawowa nan? ZUHRa tace"Ammi yaya ne,ƙasa na zafi yake mun"tayi maganar kamar wacce take a firgice,wani nauyi Ammi taci hakan yasa tayi shiru, Mommy ce ta shiga da ita toilet da kanta ta sake mata wanka sannan ta gasa mata jikin ta,aiko atake anan wani daddaɗan bacci yayi awon gaba da ita. [7/28, 09:38] 𝐎̃𝐔̂𝐌 𝐀̃𝐉𝐌𝐄̨𝐑𝐋💜🤍: 👨🏽‍🦳 *_GALADIMA FAMILY_* 👨🏽‍🦳 Page: 95/96 _____Washegari ma koma wa baccin ta tayi kuma Ammi tasa kada a tashe ta,su Laila duk suna sashin suna breakfast Sauban ya shigo,zama yayi face ɗin nan babu alamun wasa ko misƙala zarratan ya shiga gaida Ammi cikin girmamawa da kamewa,amsa wa Ammi tayi tana babbasar dashi don ta fahimci dalilin shi nayin hakan. Nan su Mashahuda suka shiga gaishe shi,amsa musu yakeyi a daddaƙile,sannan ya miƙe ya haye stairs wajen Daddy,da kallo Ammi ta bishi sai da ya ɓacewa ganin su sannan Mashahuda tace"A yanda yau yaya yake ɗin nan duk wanda yayi ƙoƙarin takalar sa to ya bani"Ammi tace"Ai sai yayi tayi"tayi maganar yana miƙewa ta nufi kitchen,be wani daɗe a saman ba ya sakko cikin zafin naman sa,duk da kuwa idanuwan shi suna mararin ganin ta but haka ya daure ya fice ya nufi wajen Ummie,acan ya samu Taufeeq. Nan ya gaida Ummie cikin kulawa,sannan ya shiga haɗa abubuwan breakfast don dama a danning ya tadda su,sam beda walwala haka yake breakfast ɗin. Taufeeq yayi nazarin sa tsaf sannan yace"kai Malam lafiya kazo kana ta mana mazurai"Sauban batare da ya dubeshi ba yace"What do you mean? Sauban yace"lallai ma guy ɗin nan,I mean everything" Sauba ya ɗaga kafaɗa"norms Taufeeq yace"Okay then...sai kuma yayi shiru yana duban Ummie wacce take ta murmushi sannan tace"Sauban Zuhra tayi maka lefi ne ko? Cikin sauri yace"Ah Ummie no babu abinda tayi mun,just I am not feeling well"Ummie ta dubeshi cikin kulawa tace"Sure? Sauban cikin sauri yace"yeh yeh Ummie please normal ne". Nan sukayi zaman su zuwa can suka fice don duba Galadima daga can su wuce wajen tailor. ZUHRa kuwa ba ita ta farka ba sai around 11 sannan ta shiga tayi wanka,ragowar kayan ta da bata ɗauka ba ta zaƙulo wani lace white me kwalliyar golden yayi mata kyau sosai,ta shirya sai zuba ƙamshi takeyi, tana fitowa su Laila suka fara mata iskanci"Kaga matan big bro da girman kujerar ki,a kwana a hantse sai uwargida kuma amarya a gidan ya Sauban" dariya duk aka sanya banda Zuhra da ta gaggalla musu harara sannan tace"Aunty Mashahuda kina jin su fa? Mashahuda tace"Yess na...ai basu yi ƙarya ba,gashi babu rabon ku haɗu ɗazu ya shigo"Zuhra shiru tayi saboda tasan yayi fushi ne tunda ko neman ta beyi ba,wani ƙwallar takaici taji ya nemi silalo mata,batare da tayi magana ba ta nufi dinning ta haɗa abin kari,suko suna can palour suna zuba sharrin su,bata daɗe ba ta miƙe ta shiga kitchen wajen Ammi. Cikin jin daɗin ganin ta Ammi tace"Zuhra har kin tashi?nina ce su rabu dake ki samu bacci sosai ki huta"murmushi Zuhra tayi tace"Ammi ki koma palour Please ki zauna mu yau zamuyi girkin"dafa kafaɗun ta Ammi tayi tace"kada ki damu inaso ne ki warware sosai,jikin naki yayi dama?wani nauyi Zuhra taji saboda ta tuna meyafaru jiya da daddare. Ammi ganewan da tayi kamar tana jin nauyin ta yasa tace"kije ki gaisa dasu Ummien ki kidawo, Zuhra tace"Okay Ammi sannu da gajiya ina dawowa". Murmushi Ammi tayi tare da girgiza kai,tana fitowa daga apartment ɗin su kuma suna parking lot, Taufeeq ya shiga Sauban ne yake ƙoƙarin shiga tafito,sosai ya ganta da yake shade ne a face ɗin sa sai yayi saurin shigewa motar ba tare da yabi takan ta,sosai Zuhra ke mamakin yayan nata,to meye abin fushi da zaiyi fushi haka?tana tsaye har suka fice a second gate aka rufe,cikin sanyin jiki ta nufi ɓangaren Ummie,itama Ummie koda taje nan ta shiga balbale ta da faɗa. "Saboda baki da hankali ki fito batare da son ran mijinki ba kuma sarai kinsan fushi yakeyi dake kika ɗebo jiki kika zo nan wai nan zaki kwana?saboda ana sangarta ki da yawa?to ni bazan lamunta ba"Ummie tayi maganar tana huci. ZUHRa kuwa sai shessheƙar kuka takeyi, Mommy ce ta shigo ta cidda su a wannan yanayin samun waje tayi ta zauna,nan Ummie ta cigaba"Ko don kinga kin samu miji mai son ki shine kike gara sa?kiyiwa kanki faɗa kafin duniya ta miki"taƙarisa maganar tare da zama tana ɗaukar ruwan dake kan glass center table tasha. Mommy ta dafa Zuhra tace"Zuhra ki koyi juriya kidena nuna ma mijinki gazawar ki fa"kuka Zuhra ta fashe da shi tana duban Mommy cikin muryan kuka tace"Mommy ina jurewa bana nuna ma yaya gazawa ta, Mommy da zafi kuma yaya ya dinga maimaita abu ɗaya kenan sam baya gajiy.....bata ƙarisa ba Ummie ta daka mata tsawa"come on keep your mouth shut"kowa ce mace da kika ganta da haka ta fara kema kuma zaki saba ne domin gado sukayi idan na jaraba ne"Mommy tace"please Aunty bilkisou Zuhra yarinya ce sai anbita a sannu a nuna mata komai step by step". Ummie wani kallo tabi Mommy dashi tace"yarinya?lallai Hauwa look at her chest,nd look at her boom boom"tayi maganar tana nuni da jikin Zuhran sannan tace"Mu sanda akayi mana aure ko ƙirgan dangi ba mu fara ba, Zuhra da waje ta samu,kinsan Allah idan baki tattara yanaki yanaki kin koma gidan ki before dare yayi ba?sai naci ƙaniyar ki am telling you" Tayi maganar tana watsa ma Zuhra idanuwan ta,kuka Zuhra tasa ta kasa magana,nan Ummie ta dasa"Hauwa ina takeso yaje ya zubar da abinda ke jikinsa?cikin sanyin mommy tace"Babu! Ummie tace"Oh nema take yaje ya fara neman mata oh what? Cikin sauri Zuhra ta dubi Ummie,Ummie tace"Yes idan kuma ba haka ba,nida kaina zan shige mishi gaba kan yayi aure,wallahi komai ni zan tsaya mishi.....wani irin kuka Zuhra ta kece dashi tare da miƙewa da gudu tayi na apartment ɗin Ammi. Zaune suke suna ta zuba chapter su tazo ta wuce da gudu tana kuka,duban juna suka fara,kafin Ammi tayi wani abu Zuhra ta fito riƙe da hijjab ɗinta tana sanya wa tana kuka,kamo ta Ammi tayi. "Ke Zuhra lafiyar ki ƙalau kuwa?keda wanene ina zaki? ZUHRa face ɗin nan yayi jajawur tace"Babu kowa Ammi,gida zan koma"taƙarisa maganar muryan ta na rawa,da yake ta samu Ammin ta sake ta da gudu ta fice, Ammi sai ƙwala mata kira take amma bata juyo ba. Security na ganin ta ya buɗe mata gate ɗin ta shige,koda ta shiga babu key a hannun ta,hakan yasa ta shige wajen da yake ajiye baƙi tayi zaman ta,sai aikin sauke ajiyar zuciya takeyi akai-akai,don har ga Allah ta gama zuciya,taɗau alƙawarin koda Sauban kasheta zeyi zata jure. ******** Ammi kuwa ranta bala'in ɓaci yayi don duk a tunanin ta Sauban ne ya mata wani abu, hakan yasa ta ɗauki wayar ta tashiga kiransa, cikin sauri yayi picking daga can ɓangaren,sudai su Mashahuda sunyi sage². Cikin ɓacin rai Ammi tace"where have you been?daga can Sauban ya bata answer. Sanar mishi tayi da yayi maza-maza yazo tana jiran sa now. Sauban kuwa cikin sauri ya jiyo don yaji muryan Ammi so angry. Babu jimawa ya ƙarisu gidan, Ammi face ɗin ta babu walwala tace"Ƙarar Zuhra kakai wajen bilkisou ko?saboda ita akan ka na lura bata son gaskiya kasa ta rufe ɗaya da faɗa Allah kaɗai yasan abinda ta mata.....nan fa Ammi ta rufe ido ta dinga zazzaga ma Sauban ruwan masifa, shidai shiru yayi kamar ruwa ya cisa kanshi a ƙasa sai da ta gama sannan ya ɗago yace"Don Allah Ammi kiyahaƙuri". Ammi tace"Ni babu abinda kamin kada dai ka manta Zuhra ba kamar Akeela bace shekarun su ba ɗaya ba,so ka bita a hankali,don kagan ta da jiki kada yasa ka mata kallon babba"tana ƙare faɗar hakan ta haye sama. Ɗan sosai kai Sauban yayi tare da fita,gidan shi ya nufa,hango ta yayi a zaune a cikin ɗan rumfan,zuwa yayi ya buɗe ƙofan yana ƙoƙarin mata magana security ɗin gidan yazo wajen shi cikin sauri,magana ya fara masa koda ya juyo babu ita alamu sun nuna ta shige ciki,shima cikin ya shiga yana ƙoƙarin lallashin ta,koda ya shiga palour ta ta rufe bedroom ɗin da key, knocking yafara Mma Zuhra taƙi buɗewa sai ma kukan ta da yake ji nan ya shiga lallashin ta amma fir taƙi zuwa ta buɗe ƙofan,kai daga ƙarshe ma bathroom ta shige yana jin san da ta bugo ƙofan,kama kai Sauban yayi tare da juyawa ya koma kan sofa ya zauna,wasa² har 4 Zuhra taƙi buɗe ƙofan,hatta su Laila sun shigo taƙi buɗewa haka suka tafi,shima Sauban ɗin da ya gaji fitowa ya fice. Jin fitan shi yasa ta fito cikin kwalliyar ta duk da batayi make up ba idanuwan nan a kumbure,kitchen ta shiga,ta buɗe friedge ta ɗauko naman dake ciki,nan tashiga tsince zallar tsoka,bayan ta gama ta wanke tasss sannan tasa a abin niƙa nama ta niƙa shi,gyaran kayan miya tayi sannan ta zauna tafara haɗa kayan girkin ta lokacin ma an kira magrib,komawa tayi tai sallah bayan ta idar ne ta koma kitchen ta ɗora dakakken naman ta, gabaɗaya ƙamshi ya buɗe gidan koda ya shigo wani lumshe ido yayi yana jin natsuwa har cikin zuciyar ta,tare da tausayin ta da soyayyar ta,kai tsaye kitchen ɗin ya shige,bata ji shigowan sa ba sai dai ji tayi anyi hugging ɗinta ta baya,ɗan fusge jikinta tayi tana nufar wajen gas ɗin ta buɗe tukunyar ta shiga motsa naman ta,nan ta zuba duk wani kayan ɗan ɗano,na ƙamshi da duk abin buƙata ta sake motsawa,sannan ta ɗauko ruwan kwakwan ta ta ɗan zuba ta rufe. Sake matsowa yayi ya fisgota suna facing juna,da sauri ta sunkuyar da face, Sauban yace"Idan kin isa ki ɗago mana ƴar rainin wayo kinje kin haɗa ni da Ammi kinji daɗi?yayi maganar yana tsare ta da ido, Zuhra kuwa wasu hawaye ne suka taru mata batare da ta ɗago ba tafara magana"kada Allah ya nuna min ranar da zan haɗa ka da mahaifiyar ka yaya,amma ka yahaƙuri"tayi maganar voice nata na cracking,wani mugun tausayin ta yaci da wani irin son ta kamo haɓar ta yayi yace"Sorry Babyn Baby kiyahaƙuri nasan bazaki iya dama ji dani ba,hakan yasa na yanke wani hukunci"Zuhra bata saurare shi ba ta matsa taje ta cigaba da aikin ta,zama yayi a dinning ɗin dake kitchen ɗin me kujeru huɗu yana kallon ta,ganin yanda take komai cike da kulawa,jin da yayi an fara kiran isha'i yasa ya miƙe ya fita don zuwa sallah. Zuhra kuwa a take anan ta haɗa lafiyayyar jollop ɗin cuscus wacce taji dakakken nama tare da Irish potatoe,tasa nasu a wani foodflask ɗin sannan tasa ma Galadima don shi mutum ne me son cuscus,gashi yaji kayan lambu,plantain ɗin da ta soya ta sa mishi a gefe, coslow kuma tasa mishi a wani ɗan glass bowl. Nan ta fara shirya komai a dinning table ta kawo duk wani abin buƙata,sannan ta shige bedroom ɗin ta,wanka tashiga bayan ta fito ta tayar da sallah,nan ta shirya cikin wasu English wears,mini skirt tasa wacce ta tsaya mata iya kacin cinyoyin ta,sai wata bodyhug ta ɗora skirt ɗin a saman rigar tunda skirt ɗin dama me umbrella ne,banda wani sassanyan ƙamshi babu abinda takeyi, dai-dai tana fitowa dai-dai lokacin shima ya shigo,sosai tayi mishi kyau jiyayi kamar ya kamota ya dinga shilla ta sama,ɗan gyaran voice yayi yace"Nida Taufeeq ne"hakan yasa Zuhra komawa ta cire skirt ɗin ta ɗauki long trouser ta sanya tare da ɗaura P-cap a kanta,a dinning ta tarad dasu,cikin fara'a ta ƙariso. "Yawwa yaya kamar kuwa kasan ina tunanin me kaiwa Galadima saƙo sai gaka"harara Taufeeq ya aika mata dashi sannan yace"idan har zaki iya aikena to wannan ma zaki iya aiken shi"yayi maganar tare da nuna Sauban. Shiru Zuhra tayi tana ɗan murmushi, Sauban kuwa kallon ta yayi yana ɗan tsadadden murmushin sa yace"and so what?ai dama ni ɗan aiken ta ne,Please Baby ki aikeni duk inda kikeso kinji?murmushi Zuhra tayi, Taufeeq yaje"da dai yafi,nikam kiyi ki serving nawa kina ta yin namijin ki, ƙamshi ya cika min hanci"yayi maganar tare da ɗauko foodflask ɗin ya shiga serving ɗin kanshi. Lafiyayyar jollop da taji dakakken nama ne da Irish,da carrot,grean beans,soyayyan plantain sai coslow da kowa ya ɗan kaɗan don dama kaɗan ɗin tayi gudun lalacewan ciki. Gabaɗayan su suka fara cin abincin Sauban kuwa natsuwan shi kacokan ya maida ga Zuhra,ko yaya ta motsa sai ya bita da kallo,duk tana hankalce dashi. [7/29, 00:20] 𝐎̃𝐔̂𝐌 𝐀̃𝐉𝐌𝐄̨𝐑𝐋💜🤍: 👨🏽‍🦳 *_GALADIMA FAMILY_* 👨🏽‍🦳 Page:- 97/98 *~SECOND TO THE LAST PAGE~* ___Kwatsam Kuma sai labari ya canza inda mutuwar su Alhaji iliyasu da hajiya Aliya ya kasance shine,a sanda Hajiya talatu ƙanwar Alhaji Mansir taje gidan kai tsaye sashin Hajiya Aliya ta nufa batare da ko gate man yaga shigowar ta ba,aiko tana shiga ta ƙofan kitchen ɗin ta ta shiga nan ta hangota ta buɗe wani wammer tana ɓarɓaɗa garin wani abu,dakata wa tayi taƙi shiga sai da tabari ta gama sannan tayi wufff ta shige kitchen ɗin bayan Hajiya Aliya ta fice,aiko taɗau maganin ta ɓarɓaɗe a cikin tukunyar dake kan gas ɗin ta motsa ta ajiye ragowar sannan tayi wufff ta fice, don ita domin duk a tunanin ta maganin mallaka ne hakan yasa tayi haka. Hajiya Aliya kuwa boka hatsabibi ne sukayi magana tace ya bata maganin da zata sama Alhaji yaci ya mutu tunda tana da ciki anyi scanning anga twince ne kuma duka maza so ita bata buƙatar cigaba da zama dashi kuma tana so taci gado,aiko nan boka hatsabibi ya bata inda ya sanar mata wannan maganin koba wanda yayi asirin bane yaci to shima fa zai mutu,sannan sai bayan awa goma sha biyu zaiyi aiki,aiko Hajiya Aliya tayi farin ciki ta amsa a ranar ta juyo don kada ya gane. Shine washegari wajen ƙarfe 2 na rana ta zauna tayi musu girki ta ɓarɓaɗe masa a abinci bata sana angansa ba,koda ta kai mishi saman shi yayi yayi suci amma taƙi tace ita nata tayi mishi haɗi na daban ne na masu ciki ta cika yaji don dama tasan beson yaji,nan kuwa yaci abincin shi cikin natsuwa,itama taje ta zuba nata taci tana yi tana wani irin murmushin nasara. Aiko ranar har anguwa zunje can babban family house ɗin su Alhaji iliyasu,daga can sukaje shopping ya haɗu ma babes ɗin shi kaya sosai suka dawo,a ranar Adda zainab har kuka sai da tayi,aiko cikin dare wajen ƙarfe biyu na dare cikin Alhaji iliyasu ya fara murɗawa,nan itama Hajiya Aliya nata cikin yafara nan fa suka dinga neman ɗauki,ai ko 5mnt basu haɗa ba rai yayi halinsa ba tare da kowa yasani ba. Washegari da safe ita kuma Adda zainab nason fita ganin har wajen 9 bata ji motsin shi ba yasa ta nufi apartment ɗin nashi,nan ta cidda gawan su cikin bedroom ɗin sa,wannan abin ne ya firgita ta yasa ta fice da gudu tana faɗin Alhaji ya mutu,duk iya ƙoƙarin gate man na ya kamota ya kasa,hakan yasa yayi gaggawan kirar Ammar yazo suka nufi apartment ɗin Alhaji suka ci karo da mummunan abu,sannan gate man ya sanar masa Adda zainab ga yanayin da tafice,nan ya kira yayan Alhaji da ƙannen sa. Shine Hajiya talatu na zuwa ta sake hargitse waje cewa Adda zainab ce ta kashe su don kullum iƙirarin ta kenan,kuma gashi ai ta gudu ya tabbata ita tayi kisan kenan?wannan dalilin yasa aka ɗora alaman question mark akan Adda zainab kenan har zuwa inda aka ganta da mutuwar ta. To wannan CCTV camera footage shine ya bayyana komai tun dawowar su Hajiya Aliya garin har zuwa abinda ya faru,nan kuwa akayi ram da Hajiya talatu tare da kaita kotu koda akaje batayi ja ba sai dai tace ita arashin sani tayi duk a tunanin ta maganin mallaka ne,aiko kaitsaye aka yanke mata hukuncin shekaru hamsin a prison tare da horo me tsanani. Hajiya talatu tayi kuka tayi nadama mara adadi. Wannan kenan. ****** Sauban sam ya kasa gane kan Zuhra don da yayi mata magana sai ta masa banza idan ma ya matsa mata kuka take sa masa,sai dai muddin yazo amsar haƙƙinsa tana bashi,hakan ba ƙaramin tayar mishi da hankali yayi ba,haka dai suka cigaba da tafiya daƙyar da siɗin goshi ya shawo kanta komai ya dai-dai ta suka cigaba da shan soyayyan su ba sassauci. Biki ya kama saura 5 day's hakan yasa shirye-shirye gidan suke babu kama hannun yaro,amare ana ta shiri inda ƙawayen su wasu duk sun shigo su shida,don haka a sashin Boɗejo suka sauka tsohon ɗakin Zuhra don nanne babu cikan jama'a,inda Ammi da Mommy ƴan uwa na jiki duk sun iso saboda events ɗin da za'ayi. Yau ma kamar kullum zaune suke akan kujera 2 sitter kanta na cinyar shi sai wasa da gashin ta yakeyi zuwa can yace"Baby kamar jikin ki da fever fa ko?Zuhra tace"Something like that hub,cuz tun jiya nakejin hakan ga tashin zuciya sai dai ina haɗa hakan da ulcer dake tashi mun kwana biyu" Sauban yace"Okey but ba kina Shan maganin ba? Zuhra tace"Yesss. "To kodai zamuje hospital ne?Sauban yayi tambayar,zumbur Zuhra ta miƙa tana kwaɓe face,cikin shagwaɓa tace"Ni..Ni..dai gaskiya A'ah nifa ba sosai nake jinsa ba yaya,ni kasan abinda nake son ci yanzu?girgiza mata kai yayi tare da shafo face ɗin ta, Zuhra tace"Gullisuwa me daɗi Please" Sauban yace"Eweee this girl na kwaɗayayya,kinga mouth ɗin nan naki?so ni ina zan samu gullisuwa? Zuhra tace"Nidai shi zanci katashi muje munema Please"tayi maganar tana bubbuga ƙafa, miƙewa yayi yace"Okay to tashi muje,muje na shiryaki,"yayi maganar yana kamo hannunta. Fita sukayi don nemo gullisuwa sosai Zuhra tabawa Sauban wahala don kuka sosai tasa masa da sukaje trade biyu basu samu ba,ƙarshen shi wani getto area suka nufa anan suka,don Sauban da kanshi ya fita suyo mata ya hanata fitowa saboda masu zaman majalisar da ya gani a layin group group hakan yasa yaji wani masifar kishinta ga idanuwa da duk yadawo kan motar nasa,yana zuwa 1k ya miƙa ma yarinyar ya tambaye ta na nawa ne?nan take ce masa na 650 ne,cewa yayi ta juye masa,ledar ta baƙa me kyau ta zube masa gullisuwar sannan ta shiga laluben canji,ce mata yayi ta barshi,sosai ta shiga godiya. Shikuwa tuni yaja motar,mamakin ta yakeyi yan da take shan gullisuwar hannu baka hannu ƙwarya tare da lumshe idanuwa tana jingina kanta a sit ɗin. "Sai kuma mene bayan wannan?ta tsinkayo voice nasa. Zuhra ta dubeshi tare da murmushi tace"Allah yaya sai agwaluma,but nasan ba za'a samu ba cuz ba lokacin shi bane yanzu". Sauban yace"lallai ma yarinyar nan yau da kwaɗayi ma kika tashi kenan?,bata tankasa ba ta cigaba da shan agwalumar ta har suka isa gida,koda suka koma farfesun kayan ciki kawai yace mata yanaso ya ɗan yi yaji saboda muran da yakeji. Amsa masa tayi sannan ya fice shima saida suka tattake waje ya cema ta Daddy ke neman sa sannan ta barshi ya tafi. A lokacin kusan ana gabda magrib ne hakan yasa ta shiga kitchen ɗin tafara ɗora masa bata bar kitchen ɗin ba sai da aka kira magrib,ga wani mahaukacin bacci da ya sakota gaba sai dai bata son yi sai ta gama masa pepper soup ɗin,shiga bedroom tayi ta wuce toilet ta watsa ruwa sannan ta ɗauro alwala,sallah ta tayar tana idar wa ta shige kitchen nanfa ta zauna anan cuz bata so ta koma bacci ya kwashe ta,ɗan rage gas ɗin tayi, dai-dai ana kiran isha'i ta sauke don tasan shi yafi son ta tayi laushi,plaintain guda ɗaya da ta yanka ta soya masa,sannan ta shirya su, plaintain ɗin tasa a plates ta rufe, pepper soup ɗin kuma ta sa a wani bowl ta rufe abinka da kayan tangaras riƙe zafi,a tray ta haɗa masa tare da spoon da pork sannan ta ɗauko ta fito,komawa tayi ta haɗo masa fresh milk nd Fairless a wani tray ɗin,glass cup nd bottle water ta fito dasu ta ajiye,palour ta koma ta cigaba da shan gullisuwar ta babu jimawa bacci yayi awon gaba da ita. Babu jimawa kuwa ya shigo yagan ta tana barci,aiko peck ya bata a kumatu ya wuce dinning ya fara dinner ɗin shi,yana gamawa yakai komai kitchen sannan cak ya ɗauke ta,ya ɗau mata gullisuwar ta ya haye da ita upstairs, bedroom din shi ya wuce da ita sannan yayi mata addu'a yaja mata duvet tare da ƙara mata A.C don ita mejin zafi ne,toilet ya faɗa yayi wanka be wani jima ba ya fito yayi duk abinda ya kasance al'adar sa,aiko ya haye gadon a buƙace yake,hakan yasa shikaɗai ya fara kaɗan sa da rawar sa sai dai wani gigice wa yayi saboda wani daɗi da yaji ta sake,a bacci takejin komai sai dai sam takasa tashi,don sam Sauban be san ko isha'i batayi ba. Bayan ya kammala komai yaje yayi wanka tare da dawowa ya rungume ta sai bacci. Zuhra ko wajejen uku da rabi a yanayin jikinta kawai tasan yaya yayi aiki murmushi kawai tayi da ƙyar ta miƙe ta shiga toilet,wanka tayi sannan ta ɗauro alwala tazo ta tayar da isha'in ta,a daddafe ta koma ta sake kwanciyar ta. ********* Bayan kwana huɗu yau ta kasance ana gobe biki,events an yishi babu magana,yau kuma dinner za'ayi duk yanda Zuhra taso zuwa Sauban ya hanata saboda zazzaɓin da takeyi,itama bata wani damu can ba,fita yayi saboda zasu kama ma mijin da zai aure Nihal hotel don yanzu haka suna hanya, shida Taufeeq da Kareem suka fice. A can Ummie da Mom su suke abincin tarba,babu abinda kakeji na tashi sai hayaniya a Galadima house, Zuhra tana zaune ta jiyo motoci anzo ɗaukar mutane don tafiya dinner,hakan yasa Zuhra taji wani iri kamar ta ƙwala ihu. Haka dai suka tafi sauban kam be wani jima ba ya shigo lokacin Zuhra tayi baccin ta abinta shi kam yana mamakin wannan baccin na kwana biyu da takeyi yauma har ɗaki ya kaita,haka ya cigaba da rainon ta like baby. Washe gari kuwa da wani azababben zazzaɓi ta tashi da mugun ciwon kai duk da kuwa taƙi yarda ya gane,sa mata abin wuya yakeyi ta jikin mirror yana kallon ta. "Baby kinyi balai'n kyau kinganki?har naji wani kishi"ɗan shagwaɓa face Zuhra tayi tace"kai yaya nidai ka barni na shiga cikin ƴan uwa na Please". "But Baby kamar baki da lafiya right? Cikin sauri Zuhra tace"Nop yaya mene kagani kuma?Ni lafiya ta ƙalau" Murmushi Sauban yayi yace"Okay to muje,anko sukayi duk da ita lace tasa doguwar riga blue Black ta sanya veil white takalmi high heel white da ƴar hand bag ɗin ta white tayi kyau ainun. Shima shadda ɗanya yasa sai maiƙo take blue Black,hulan kansa light blue haka halfcover ɗin ƙafarsa,hannun ta ya kamo suka fito,anan masallacin Alhaji Mai Deribe aka ɗaura auren sosai mutane suka halarta tare da sheda auren. Muhammad Shuraim & Lailah Taleeb Muhammad,Aliyu Abdulhakeem& Barakah Haroun Muhammad (Nihal). Aiko gida ya cika tanƙam da ƴan uwa da abokan arziƙi, Zuhra tana sashin Mom don acan su Aunty Mashahuda suke,itadai tunda ta ƙyallare ido taga wannnan jollop ɗin shinkafar da yaji curry hankalin ta ya tashi,wani mugun amai taji ya taho mata,duk iya ƙoƙarin ta na ganin ta danne ina,da masifar gudu ta shige toilet. Gabaɗaya su Aunty Safeena suka bita suna lafiya?sai dai Zuhra amai takeyi sosai don jikinta har wani irin rawa yakeyi,cikin sauri Aunty Safeena ta kamota daƙyar ta gama aman nan,haka tatafi luuuuuuuu. Yaraf! Ta zube a jikin Safeena,salatin suka sanya suna tattaɓa ta sai dai babu numfashi babu alamun sam babu numfashi a jikinta. Gabaɗaya sun gigice, Mom ma ta taho,ruwa aka ɗauko a fridge aka shafa mata sai dai ko ajiyan numfashi batayi ba, Mom ta dubi Aunty Safeena cikin ruɗewa"Me yafaru da ita ne haka Safeena? Aunty Safeena taba ma Mom labarin komai. Mom tace"To ai zama be ganmu ba,maza² kikira Sauban"nan Safeena ta lalubo Number sa tahau kira,har 2 times beyi picking ba,tana shirin sake kira ya kira ta. "Hello yaya kana inane?daga can Sauban ya amsa mata, gamu nan a apartment ɗin Mom don Allah idan babu damuwa kazo"cikin sauri ya Sauban yace"What is happening Safeena? where's her Zuhra? In Ina Aunty Safeena tafara,ko kafin tayi magana ya yanke don a lokacin fitowan shi kenan daga apartment ɗin Ammi yaje gaida ƴan uwan ta,cikin zafin nama ya shigo palour ko bi takan mutanen palour beyi ba,ya danna ma Safeena kira,hakan ya tabbatar mata da ya shigo palour. Mom tace"bari ni naje. Aiko babu jimawa sai gashi sun taho da ita,tambaya ya shiga yi meya same ta?hankalin shi tashe ya ɗauke ta ya fito,nan duk suka biyo shi. Mutanen palour suka mimmiƙe Hajiya Biba tace"Subhanallah meya sameta ne haka?nan duk mutane suka fiffito,Mom da Hajiya Biba sai Aunty Safeena suka bishi don motar shi dake bakin gate ya ɗauka gabaɗaya hankula ya dawo kansu kafin kace me magana ya zagaye gida. Aiko Mommy itama shiryawa tayi tare da yayar Ammi suka bi bayan su Taufeeq da Kareem suka kaisu,duk da kuwa jama'an da Mommy keda su haka ta tsallake su. Kaitsaye hospital ɗin su Dr Ahmad suka nufa cuz sun fi zaton suna can. ******** Sauban kuwa suna isa a take anan aka nufi VIP da ita Doctor's sukayo kanta cuz gabaɗaya Sauban ya ruɗe ganin ko motsi batayi ga jikinta ya saki gabaɗaya. Aiko nan aka ɗebi jininta tare da nasarar dai-dai ta numfashin ta,alluran bacci aka mata tare da sa mata drip suka fito,nan Dr Ahmad ke sanar dasu su kwantar da hankalin su insha Allah jikin da sauƙi ya bada jini aje lab a gwada su ɗan jira akawo result,yayi maganar yana dafa kafaɗar Sauban ganin yanda ya susuce lokaci guda. Babu jimawa su Mommy suka ƙariso tare da tambayar meyasame Zuhra sannan wani hali take ciki? Nan Mom ta shiga basu labari,can babu daɗewa Daddy, Abba, Baba Hasheem, Boɗejo, GALADIMA, Guggo Laure duk sun ƙariso suna neman cika asibitin. Wata nurse ta dubi abokiyar aikin ta tace"Oh sis su kuwa waɗannan wasu ahali ne suna neman tarewa a hospital? murmushi wancan nurse tayi tace"Galadima family kenan,kinga wancan tsohon to shine Galadiman"tayi maganar tana nuna Galadima, ɗayan tace"Wow but familyn so nice sunyi ko ta ina ga kyau"dariya wancan nurse ɗin tasa tace"ke duk wata mace zata so ta shiga family ɗin nan da sunan aure don a yanda ake bada labarin family ɗin komai sun haɗa Masha Allah"wancan nurse tace"kuma fa patient ɗin nasu ba wani ciwo bane me damuwa,don Allah ki kalli kayan alfarman dake jikinsu"wancan nurse ta sake cewa"Galadima family aka ce miki fa,I think wancan ne mijin me blue Black ɗin shaddan can,kinsan yanda ƴan mata ke rushing guy ɗin can?sai dai ance ɗan wulaƙanci ne gashi yana bala'in son matar shi,ance ma fa yarinya ce ƙarama don baza ta wuce 19yrs ba,yana son ta sosai"ko kafin wancan tayi magana Boɗejo ta katse su"kai kuwa waɗannan yara da tsinannen gulma kuke,duk a ina kukaji wannan?domin basuyi tunanin suna jin hirar su ba, gabaɗaya hankalinsu ya koma kan nurse's ɗin,su ko tsitsitsi suka shiga yi da idanuwa. Dr Ahmad ne ya leƙo tare da kiran Sauban,jikin shi na rawa ya shiga office wani mahaukacin bugu ƙirjinsa keyi. Dr Ahmad yace"bismillah Malam Sauban have a sit"zama Sauban yayi tare da ƙosawa yaji me zaice mishi,wani takadda Dr Ahmad ya miƙo masa yace"take this result nd da abinda ya ƙunsa. Ɗagowa Sauban yayi ya dubi face ɗin Dr Ahmad. [7/30, 14:53] 𝐎̃𝐔̂𝐌 𝐀̃𝐉𝐌𝐄̨𝐑𝐋💜🤍: 👨🏽‍🦳 *_GALADIMA FAMILY_* *~LAST PAGE~* ___Hannu ya miƙa masa sannan yace"Congratulation Mr Sauban Madam ɗin ka na ɗauke da juna biyu na tsawon 2weeks Allah ya sa albarka"Wani mugun farin ciki ne ya kama ya Sauban wanda ya sashi rungume Dr Ahmad babu shiri,sakin sa yayi tare da yin sujudur shukur,babu ɓata lokaci Sauban ya fice da result a hannu sai a sa ilin da ya hango su Daddy ne yaji wani irin nauyi da kunya,hakan yasa shi babu shiri ya kame kansa duk da kallo suka bisa tare da tambayar shi me Dr ɗin yace,saboda har ga Allah hankulan su a tashe yake, Sauban cikin kamewa yace"sunce da sauƙi sai dai ga results ɗin"yayi maganar yana miƙawa Mommy da tafi kusa dashi,aiko ta warware don dubawa,inda wasu suka shiga tambayar me result ɗin yace,ai kafin abada answer Mommy ta daddage ta saki guɗa wanda ya jawo hankulan mutane da dama, Mom itama ta amsa result ɗin cikin farin ciki ya shiga furta"Alhamdulillah Allah mungode maka"Boɗejo ta mere baki tace"dama sai da jiki na ya bani yanzu haka ciki ya shiga ne tunda akace tayi amai,to Allah ya ƙara lafiya,don ciwon me ciki sai haƙuri,kai Abdulkarim kuzo ku sauke ni a gida mun bar jama'a"duk dariya aka sanya,su Daddy duk wanda ka kalla fara'a ne a face ɗin sa,haka zalika Ammi wani farin ciki ne ya ziyarce ta wanda ko a cikin Mashahuda da Safeena ba taji hakan ba,a ranta tashiga gode ma Allah. Don haka yasa duk suka shiga ɗakin har lokacin tana bacci sosai,lokaci ɗaya tayi wani fayau ta faɗa,nan suka dudduba jikin ta inda duk suka tafi aka bar Sauban da Mom don su Taufeeq sunyi² ya taso suje yaƙi. Acan gidan biki kuwa anbar jama'a da jimami,koda suka koma nan suka cema mutane jikin nata da sauƙi, Ummie ce kawai aka sanar da ita abinda ke faruwa,nan fa su Mashahuda suka dasa chapter tsegumi wai dama ai wannan haske kwana biyu da tayi ga ƙirjin ta daya cika,nan dai suka dinga. A hospital kuwa Zuhra bata farka ba sai wajejen magrib,shima tana farkawa aman tafara ga cikinta da babu komai da ka kalleta kasan a matuƙar wahale take, Sauban kuwa gabaɗaya ya ruɗe har sai da yabawa Mom tausayi,da ƙyar aman ya tsaya,anan Mom ta kamata suka shiga toilet tayi alwala tayi sallah la'asar,sannan aka ɗan jinginar da ita saboda complain ɗin da takeyi na jiri da take gani. "Yaya yunwa nakeji"ta furta cikin wahalallen murya wanda daka ji kasan na marasa lafiya ne, Sauban cikin kulawa yace"mezaki cine baby?Girgiza kai Zuhra tayi tace"ina jin yunwa amma banjin cin komai"Mom tace"A'ah Zuhra ai dole kici wani abu ba zai yiwu ki zauna da yunwa ba fa gaskiya"ZUHRa wani wahalallen ƙwalla ne ya ziraro mata daƙyar tace"Mom idan naci amai zanyi na sani Kum.....ai bata ƙarisa ba aman kuwa ya taho ga uban wahala,don cikinta babu komai sai kakarin aman da takeyi,a lokacin nurse's ɗin ɗazu dake ta gulma ne suka shigo,nan suka shiga yi ma Zuhra ya jiki,a gefe guda suna satar kallon Sauban wanda ya tsuke face,ya tattare gabaɗaya hankalin shi ya koma kan matar sa. "Yaya nidai a maida ni gida bansan warin asibitin nan amai yake saka ni"tayi maganar a wahale, miƙewa Sauban yayi yace"Okay so bari nama Dr Ahmad magana gaskiya"sannan yasa kai ya fice,daga Mom har nurse's ɗin da kallo suka bita,kamo kafaɗun ta mom tayi tace"Zuhra kidaure kici wani abu koda zakiyi amai saboda idan cikin ki da akwai wani abu bazaki wahala kamar irin wanda kikeyi da cikin ki babu komai ba"ɗaga ma Mom kai Zuhra tayi,a dai-dai lokacin ne kuma Sauban suka shigo shida Dr Ahmad,hakan yasa nurses ɗin ficewa. Dariya Dr Ahmad yakeyi ya dubi Zuhra"Madam kinfi dai son komawa gida right? ɗaga mishi kai Zuhra tayi don har ga Allah warin asibitin damun ta yakeyi,a take anan kuwa ya rubuta mata sallama,inda Dr jamila zata dinga zuwa dubata, sannan sai ruwan hannun ta yaƙare zasu wuce. Godiya Sauban yama Dr Ahmad a kuma take anan ya tura masa 250,000 tukwicin sanar da wannan daddaɗan albishir ɗin,wani baccin Zuhra ta koma sai wajen magrib lokacin ma Sauban na masallaci, Mom ma sallan takeyi sannan Zuhra ta farka,yunƙurin miƙewa take yi amma jirin dake nema kada ta ne yasa takoma ta jingina tare da rintse idanuwan ta gam. Muryan Mom taji"Ya yadai Zuhra?jikin ne? ɗaga ma Mom kai tayi tace"jiri ne ke neman wahalar dani Mom,ga aman da nakeji har yanzu nina rasa meke samun jin aman? Mom tace"Ai haƙuri zakiyi Zuhra yanzu keda jin dai-dai kuma sai Allah ya sauke ki lafiya"wani kallo Zuhra ta ma Mom na rashin fahimta don har ga Allah bata son abinda ke faruwa ba,dariya Mom kawai tayi a lokacin Sauban yayi sallama ya shigo duk cikan su suka amsa,nufo su yayi tare da zama gefen Zuhra yace"Mom Yaya jikin nata?ta sake aman ne?? Mom tace"Jiki alhamdulillah Sauban complain ɗin ta ɗaya jirin da take gani ne kuma Dr Ahmad yace insha Allah zaiyi sauƙi a hankali tunda Dr jamila zata dinga zuwa gida kula da ita,don bayan fitan ka ma ta shigo mun daɗe da ita lokacin ma Zuhran tana barci". "Masha Allah, Allah ya ƙara lafiya,to ai sai muyi shirin tafiya ko Mom? Mom tace"Okay muje Toh. Duban Zuhra Sauban yayi yace"hey beb zaki iya tafiya?Zuhra tace"ka mance nace ma ina ganin jiri kawai kama ni zakayi muje"kama ta yayi Mom ta gyara mata mayafin ta sannan suka fice,har mota ya saka ta don yaso shiga office ɗin Dr Ahmad but ya tashi. Haka ya ɗauko su,suna tafiya da yake hanyoyin akwai street light hakan yasa duk inda ka wuce haske ƙau,har zasu wuce ya jiyo muryan ta,da yake suna baya ne kanta na kan kafaɗar Mom"Yaya ga me balango can"dakata wa yayi yace"zaki ci ne? ɗaga masa kai Zuhra tayi,samun waje yayi yai parking sannan yafice, yaɗau almost 4mint sannan ya shigo,hannunsa ɗauke da ledoji uku ɗaya madaidaici, ɗaya ya fishi, ɗayan kuma duk ya fisu yawa,haka suka ƙarisa, dai-dai wani shagon da ake saida yoghurt ya tsaya ya sai manyan robobi huɗu sannan ya dawo ya shiga motan ya tayar. A haka suka isa kaitsaye Galadima family ya wuce da ita sashin Ammi,kama ta yayi ya kaita, Mom kuwa apartment ɗin ta tawuce saboda Hajiya Biba tana nan,don biyo su Ammi sukayi suka dawo ɗazu. ******** Kowa tambayar jikin nata yakeyi,haka amare duk sun shisshigo sun tasa ta a bedroom ɗin da aka sauke ta,su Aunty Maryam da Aunty labeeba duk suna tare da ita sai sannu ake mata masu sharri nayi,ita dai Zuhra kunya ta saka ta a gaba duk bakin ta takasa furta komai. Sauban da kanshi ya kaima Mom na manta har apartment ɗin ta da yoghurt,godiya sosai tayi masa,inda shida Kareem suka ɗauki Hajiya Biba don maida ta gida,suna zaune har kusan 9:00 sannnan ya shigo,hakan yasa siɗif² suka fara ficewa cikin su na ɗuran ruwa,turo mouth gaba, Zuhra tayi tace"ƙarfi da yaji ka zama kaman wani mala'ikan mutuwa da angan ka sai a shiga taitayi"harara Sauban ya galla mata yace"kema ai saboda kin ganni tsirara ne shiyasa kika rainani haka,kuma zanyi maganin ki"dariya Zuhra tasa tace"Sorry Babyn Baby". "Kinci abinci?yayi mata tambayar tare da jawo ledojin, Zuhra tace"ai baka zo ka bani balangon ba"ɗan murmushi Sauban yayi sannan ya buɗe komai ya shiga bata tana amsa idanuwan ta akan shi tana jin wani soyayyan shi,sai da yabata yaga taci ta ƙoshi sannan ya ƙyale ta suka cigaba hira,wanda rabi da kwata duk romance ɗin junan su sukayi,har sai da Zuhra ta mishi abinda ya samu natsuwa( Su Sauban manya😁🙄). Sai wajen 11:43 ya tashi shima sai Ammi ta shigo ta kora sa sannan wanda Zuhra kuwa a lokacin amai ta dinga sheƙawa,basuyi wani kwanan daɗi ba daga ƙarshe bedroom ɗin Ammi ta koma. *WASHEGARIN BIKI* Nihal da Laila kuka kawai sukeyi kamar ransu zai fita don sai da suka tayar ma da mutane da dama hankali sun saba komai tare gashi aure zai raba su duk da Laila after 2weeks zata koma saboda school hakan yasa Shuraim ya sama mata gidan haya a can,duk weekend zai dinga shiga kaduna, Nihal ita ta raka Laila gidan ta wanda yayi kyau ɗan dai-dai kasha Allah,wajen 10 aka kaita,ana dawowa ƴan k.d suma suka ɗauki amarya tare da duk wanda zai tafi motoci bakwai suka wuce. Zuhra dai nata ido don Sauban wayo ya mata anfito tafiya da amarya yaja ta gidan su,yaci karen sa babu babbaka,wanda sosai zubar ke kuka don wani mugun tsanar abin ta tsinci kanta daji duk da kuwa itama ta samu natsuwa,ko kaɗan bata so taji ya....a ciki,shiyasa ya koma yi a waje. Sai wajejen magrib sannan ya maido ta gida,hararar kawai Ammi ta masa inda tace"to lallai Zuhra ta koma ɗakin ta don ba za'ayi abin kunya a sashin ya ba. Laulayin cikin na damun ta don ma ta samu sauƙin jirin sannan Dr jamila tana iya ƙoƙarin ta wajen bata kulawa,ranar Laraba Sauban yayi mata kyautar motar ta ƙirar MERCEDES_BENZ G - CLASS G500 MODEL 2022,babu wanda beyi farin ciki ba don motar babu ƙarya ta haɗu iya haɗuwa,ƴan uwa hakan suke kira suna taya Zuhra murya,da yake su Aunty labeeba duk basu tafi ba,kai kowa da murna yake, Zuhra kuwa jitayi kamar ta zuba ruwa a ƙasa ta shiga,don koda wasa bata taɓa kawo za'a siya mata mota nan kusa ba,ba wai don babu ba a'ah sai don ko maganar sam basuyi dashi,ya bata a matsayin tukwici akan abubuwa da dama a cewar sa ma harda baiwar da Allah ya mata. ******* After one week gidan kamar ba'ayi sha'ani ba don duk sun wawwatse,inda Sauban shi ya cigaba da rainon cikin Zuhra tare da yimata duk abinda takeso,aikin gida ma kuwa tare sukeyi,shi yake kai ta school ya ɗauko inda da haka yake mata dubarin koya driving,weekend kuwa me gasken sukeyi, sosai Sauban ya dage da koya ma Zuhra driving Kuma lokaci guda ta iya,duk wanda ya gansu sai yaso kasancewa tare dasu,ranar da zata dawo daga school haka suka ci karo da Akeela inda wani me daidai ta sahu ke ta mata rashin mutumci kan kuɗin da tabashi be kai ba,har yana kiran ta ƴar maɗigo sai wulaƙata ta yake mutane har sun fara taruwa. Akeela kuwa sosai take kuka,idan ka ganta duk tayi laushi tunda bata rame ba,kawai da ka kalle ta zakasan lallai Akeela ta tuba tayi nadama,long hijjab ne a jikinta , gabaɗaya tayi sanyi, Zuhra da kanta tafita taje ta ƙwato Akeela don Sauban hanata yayi ita kuma taƙi, a motar tazo ta sanya ta,inda kuka sosai Akeela keyi, ta buɗe hand bag ɗinta takaima me adaidaita kuɗin da ita kanta bata san ko nawa bane, sannan tazo ta shiga sai lallashi Akeela take, sauvan ko yayi kicin kicin da face,babu alamun rahama ko kaɗan,nan Zuhra ta shiga bata baki har gida suka kaita, Zuhra na ƙoƙarin fita Sauban ya galla mata uban harara hakan yasa dole ta haƙura, Akeela buɗe motar tayi sannan ta zagayo ta dubi Sauban tace"Don Allah Sauban ka yafemin nasan ni mai lefi ce a gare ka,naci amanar ka amma Allah sheda ne na tuba,tuba irin na taubatun-nasuha don Allah ka yafemin"tayi maganar tana fashewa da kuka, Sauban yace"Allah ya yafe mana,ai ke yanzu duniya ma ta isheki"yana gama faɗar hakan ya zuge glass's ɗin motar ya mata key,beyi wata² ba ya fisgeta ya bar layin,wani irin kuka Akeela keyi don harga Allah tasan cewa lallai ta cuce kanta rashin Sauban matsayin miji asarar ne. 1months Sauban yayi suna zuba soayyayn su daga ƙarshe ya tattara yana shi ya nashi ya koma,wanda Zuhra taji kamar tayi ta kururuwa. ____________ Sauban koda ya koma sau biyu ya dawo a lokacin har anyi azumi har anyi babban salla don lokacin Zuhra cikin ta kusan six months ne dawowar da yayi na farko,cikin yayi girma na hankali duk wanda ya gani sai yayi magana,a lokacin da ya cika seven months wani kumburi Zuhra tayi kota ko ina,ga damuwa da ta sanya ma ranta na mutuwa,ita a kullum gani takeyi mutuwa zata yi hakan yasa lokaci guda jininta ya hau,sosai su Daddy ke mata faɗa don ransu ya ɓaci,gashi wannan karan da yake sun samu hutu har na wata guda hakan yasa duk inda ta zauna sai ta tsaya ma kowa a rai kowa na jinta,ita kanta Boɗejo wani nan nan takeyi da ita,haka Ummie itama sosai ke nuna mata kulawa, ɗaki guda suka cika da kayan baby unisex,don Sauban duk kayan da akasaa ɗakin daga abrod ne. A lokacin Mashahuda ta haihu baby boy ne hakan yasa yaci sunan Abbie suna kiran sa da Ashraf, hakan yasa tadawo gida bayan anyi suna acan,don ko sunan Zuhra bata je ba Sauban ya hanata,shiyasa bata da aiki kullum sai na tambayar Mashahuda yaya haihuwa yake da zafi ko kuwa? Sometimes Mashahuda murmushi takan mata tace"kada ta damu idan lokaci yayi zataji don shi haihuwa ba lallai wahala da wancan ya sha ba shi wannan ke sha,wani yana zuwa masa da sauƙi"kowa cikin tattalin ta da nuna mata kulawa. Sai alokacin Muneefa ta samu ciki na wata huɗu,inda daga Laila har Nihal ke ƙunshe da cikin su ɗan wata bibbiyu. Rammat itama haihuwa yau ko gobe. Haka rayuwa ta cigaba da daɗi babu daɗi har Rammat ta haifi Baby boy inda mahaifin Kareem ya sanya masa sunan Daddy suna kiran sa Aslam. ******** Bayan wata biyu lokacin Sauban ya dawo gida gabaɗaya saboda Zuhra cikin ta ya shiga watan haihuwa,sosai ta sake kumbura sai dai anci Sa'a jinin ya sauka,kullum da la'asar sai Sauban ya jata zuwa struggling hakan yasa yake ɗan jin dama dama. Wata ranar Lahadi ƙarfe 11 na dare naƙuda ya sako ta gaba,tun tana abinta ita kaɗai har Sauban dai ya tashi dama baccin sa rabi da rabi ne hankalin sa na kanta always. "Innalillahi wa Inna ilaihirraji'un"ta furta tana yarfe hannu tare da duƙewa,cikin azama Sauban ya diro daga kan gadon a gigice ya nufeta yana faɗar haihuwa ce Baby? ɗaga masa kai Zuhra tayi ta kasa magana saboda azaba. Hakan yasa a gigice Sauban ya fice daga gidan ƙoƙarin fita yake but ya kasa hakan, gabaɗaya ya gama ruɗewa da gigice wa lokaci guda. Wayan shi ya ɗauka ya lalubo number Ammi,kusan 2misscall sannan ta ɗauka muryan ta da alamun bacci tace"Assalamu alaikum Sauban ya akayi? "Ammi Zuhra kizo don Allah"cikin sauri Ammi ta miƙe tace"haihuwar ce? Sauban yace"i think cuz tana shan wahala"Ammi ce tayi hanging call ɗin, Daddy ma tashi yayi,hakan yasa cikin sauri ta nufi apartment ɗin Mom ita da Daddy, Daddy da kanshi ya kira Baba Hasheem a waya ya sanar dashi,babu jimawa suka fito shida Mom ko wacce zani ɗaure akan kayan bacci tasa hijjab. Wayan Ammi ne yayi ringing cikin sauri ta ɗaga Sauban yace"Ammi ganinan a mota a waje". Amsa mishi tayi sannan suka fice wajen su suka shiga inda su Daddy suka ce duk halin da ake ciki su sanar dasu. Sauban kiran Dr Ahmad ya sanar dashi,inda akayi Sa'a Dr yana asibitin cuz night duty zaiyi. Suna Isa cikin hanzari aka karɓe ta sai labour ward. Nan fa aka shiga bata kulawa gabaɗaya Sauban ya ruɗe,cikin yardan Allah wajejen 3:00 ta sunkutu yaran ta biyu mace da namiji,ihun su ne ya cika ward ɗin. Aifa nan su Ammi sukaji sanyi ya ratsa musu,babu jimawa Dr jamila ta ƙarisu hannun ta ɗauke da Baby wata nurse ma ɗauke da Baby,atake anan Sauban yayi sujudur shukur,inda banda hamdala babu abinda su Ammi keyi, Sauban cikin sauri yace"yaya take?zan iya shiga na ganta?cikin sanyin jiki Dr jamila tace"dama tace"akira mata kai, Ammi tace"muma zamu iya shiga? Dr Jamila tace"Ea ai angyara ta". Koda suka shiga a kwance suka taradda ita inda sai murmushi takeyi,hannu ta miƙa ma Sauban tace"Yaya kaga Babyn mu ko?nasan ni ba wani kula dasu zanyi ba Please ga amanar su nan a hannun ka,ka tarbiyyar tattadasu,ina son ka mijina, ina so ko a aljanna nayi rayuwa dakai"taƙarisa maganar sai hawaye, Sauban cikin sauri ya kamo hannun ta ya matse"wani irin magana ne kike yi haka?wani waje na miki ciwo ne?girgiza masa kai tayi tana kwance hawaye na mata wani irin zarya,duban su Ammi tayi tace"Mom, Ammi Ina son ku kuce ma Ummie na ina son ta koda na mutu kada tamin kuka zanje inda Abbie yaje ne"wani kuka Mom ta fashe dashi Ammi kuwa jikinta har tsuma yakeyi tace"Zuhra wani irin magana kikeyi haka?meya kawo zancen mutuwa?girgiza kai Zuhra tayi tace"Ni kaɗai nasan azabar da nakeji wallahi,kuna jin wani ƙara kamar abu na turowa a gabana?ga cikinana wani irin karta?duk shock suka shiga Sauban jikinsa na rawa ya fita saboda ya fara tsora babu jimawa suka dawo da Dr Ahmad da Dr jamila, ɗan ɗaga doguwar rigar asibitin Dr jamila tayi,wani jini ne ke gudu yana wani zubowa a gaban Zuhra tare da wasu dunƙule²,cikin tashin hankali tace"Ya Salam Dr da matsala jini fa ya kece mata". Gabaɗaya tashi hankulan su yayi,nan ya danna wani ƙarar rawa kafin kace me Dr uku sun shigo tare da roƙan su Ammi su fita, Sauban kuwa dagewa yayi kan bazai fita ba,daƙyar aka samu ya fita,don a lokacin Zuhra har ta suma, nan yaran dake hannun su Mom suka shiga tsala wani irin kuka. Duk iya ƙoƙarin su don dakatar da jinin yaƙi tsayuwa,don wani numfashi Zuhra ta saki tare da fara kalmar shahada a take anan rai yayi halinsa. ******** After 5 minutes doctor's ɗin suka fito ko wanne na share zufa, Dr Ahmad ne a ƙarshe,da sauri suka nufe shi,girgiza kai ya shiga yi yana dafa kafaɗar Sauban,ko kafin yace wani abu Sauban ya yanke jiki ya faɗi, dai-dai lokacin su Daddy sun iso don Ammi ta Kira shi. Da gudu su Mom suka nufi ɗakin da Zuhra take,ga shi nan an rufe face ɗin ta da farin ƙyalle sai sheƙi yakeyi murmushi kamar yin sa takeyi ta sake wani irin kyau. Ammi jikinta rawa ya kama suna sakin wani irin kuka inda suma su Daddy suka nufo ɗakin suna salati. [7/30, 15:31] 𝐎̃𝐔̂𝐌 𝐀̃𝐉𝐌𝐄̨𝐑𝐋💜🤍: Muryoyin Mom da Ammi kakeji cikin kuka suna salati saboda kwata² babu rai a tattare da Zuhra ko kaɗan,ga Sauban likito ci na kansa don ceto rayuwar sa. Ƙarfe biyar na a asuba su Daddy suka taho da gawar Zuhra,inda a hospital kuma Kareem ne ke zaune da Sauban, gabaɗaya idan kaga ahalin nan a wujijjige suke,wani irin kuka Boɗejo keyi,haka su Rammat ma su Guggo Laure kafin takwas gida ya cika tanƙam,mutuwa kenan me tambari. **** A Kaduna kuwa koda Baba Hasheem ya Kira Abba ya sanar dashi shima tashin hankalin yakeyi, Mommy da taji wanda ya rasu kuka sosai takeyi wani irin zazzaɓi lokaci guda na rufe ta,ita ta shiga wajen Ummie ta sanar da ita sai dai ta nuna mata Galadima ne sannan gashi yanzu zasu tafi,ƙarfe huɗu na asuba suka fito duk cikan su ahalin har da Nihal da Laila motoci uku sukayi tunda shima Shuraim na garin lokacin,duk kazan sunji wanda ya rasu,a mata kuwa Mommy ce kawai, itama Ummie gaban ta faɗuwa yake hakan ya saukar mata da ruɗu da tsoro ta saki kuka,basu isa Maiduguri ba sai azahar a lokacin su kawai ake jira,tun daga farkon layin har ƙarshe jama'a ne,tunda suka shigo gidan kallo ya dawo kan Ummie da Taufeeq,abin mamaki gawan a sashin Ammi ne hakan yasa suka nufi can,dafo kafaɗun Ummie Ammi tayi lokacin Sauban na duƙe gaban gawar yana wani irin kuka duk da babu sauti ga baby ɗaya a bayan Muneefa ɗaya bayan Rammat sai kuka sukeyi,domin kukan su shine yake sake tayar ma da mutane hankali. Nan fa jikin Ummie ya kama rawa a sanda aka buɗe fuskan Zuhra. A take anan Laila da Nihal suka zube sumamnu,ita kanta Mashahuda sai da aka riƙe ta. "Innalillahi wa Inna ilaihirraji'un, hasbunallahu wa ni'imal wakeel!!!shine kawai kalmar da Ummie furta idanuwan ta kan Zuhra jikinta na kyarma. Nan tashiga faɗin"Allah ya jiƙan ki Fatima,Ubangiji Allah yayi miki rahama,ashe kece me bin mahaifin ki?kin mutu kinbar ni kin bar ƴan uwa? innalillahi wa Inna ilaihirraji'un, addu'o'i ta shiga zubo mata wanda yasa a take anan ta burge mutane da dama, majority kuka kawai suke,mutuwar Zuhra mutuwa ce me tsayawa a rai,mutuwar ƙuruciya Wanda mantawa ba nan kusa ba,nufar yaran Ummie tayi sai a lokacin tafara zubda hawaye,shi kan shi Taufeeq kukan yake yana jijjiga, addu'o'i shima ya shiga kwaranyo wa,atake anan aka kira duk wani makusan cin ta ya fara mata addu'a saboda za'a kaita gidan ta na gaskiya. ****** Laila kam jiki yaƙi har jini tafara zubarwa aka nufi asibiti da ita,lokacin da za'a wuce da ita kuwa haka wasu suka sake shinsshin fiɗewa a ƙasa sumammu,ita kanta Boɗejo tana can ana mata ƙarin ruwa. *******" Innalillahi wa Inna ilaihirraji'un mutuwa mutuwa mutuwa babu daɗi,daka kalle Sauban kasan a gigice yake,ko abinci be iya ci, gabaɗaya ya rame ya sake wani haske,haka ake zuwa mishi gaisuwa tun daga uwa duniya,idan kuwa yaran suka fara kuka kamar zai shiɗe shima tsaban kuka,yana tuno soyayyar su bai taɓa kawowa ɗayan cikin su mutuwa nan kusa ba, Zuhra ta daban ce a cikin mata baijin sai samu me maye gurbin ta har randa shima nashi mutuwar zaizo. Wasa wasa har anyi bakwai masu tafiya sun tafi su Aunty Maryam nanan sam ahalin gidan mutuwar ya kasa goge musu, Sauban ya kasa dawowa dai-dai,haka rayuwa ta cigaba da tafiya inda Mashahuda ita ta cigaba da shayar da yaran Sauban,bayan sati biyu suka tafi dasu Kaduna. ******* Boɗe idanuwan shi yayi waɗan da sukayi jajawur,yana ɗaukan hanky ya share tears ɗin da suka zubo mishi,wata yarinya ce da bazata gaza 3 yrs ba ta taho da gudu ya faɗa jikinsa"Daddy kaga Ajmerl ko?tayi maganar yana faɗawa jikinsa,wanda aka kira da Ajmal ne ya ya ƙariso zabori a hannun shi,duk da ba manya bane amma idan ka gansu zakayi tunanin ƴan 5yrs ne saboda girman jiki da shegen wayo, yaran kyawawa sosai kamar ka sace. Shafa kan macen Sauban yayi yace"Idan yaya Ajmerl ya daki mun little Zuhra sai na zane shi"ƙarasowa Ammi tayi duk da bata wani canza ba Amma ta girma,duban Sauban tayi tace"Yau ma kayi tunanin naka ko? Sauban duk cikan mu haƙiri zamuyi kafin lokacin mu yayi tabbas mutuwar Zuhra manta shi ba nan kusa ba,amma banjin daɗin rashin walwalarka mundena ganin fara'an ka, kayahakuri ka sake kamar da ka bita da addu'a" tayi maganar tana share hawayen da ya gangaro mata,"insha Allah zaka samu wata ta gari itama" Duban Ummie Sauban yayi tare da yin yaƙe yace"har abada Ammi bazan samu makwafin Zuhra ba,na rasa ta ban kallon sauran mata a mata yanzu don haka banjin zan ƙara aure nan kusa". Da mamaki Ammi ta kalle shi tace"Galadima tun kafin ya rasu yake maka nasiha da lallashi,haka ma Boɗejo duk da tsakanin su shekara guda ne,tabbas munga tashin hankali ya Allah kajikan bayin ka"da Ameen Sauban ya amsa. Rayuwa kenan duk abinnan Sauban ne yake tunanin rayuwar shi da Zuhra da ahalin Galadima family,ga Galadima ya rasu,haka Boɗejo rasu, duk bayan rasuwar Zuhra,inda Mashahuda yaran ta uku, Laila da Nihal bibbiyu, Muneefa ɗaya, Rammat biyu,sauran jikokin gidan duk sun girma, Ummie ma tana can a Kaduna don tace ita bata sake Aure duk da su Sauban suna ƙoƙarin Daddy ya aure ta. za ku samu duk novels din da ku ke so a shafin mu https://hausanovels001.com.ng ALHAMDULILLAH DUKDUKA ANAN NA KAWO ƘARSHEN LITTAFIN GALADIMA FAMILY,KURAKUREN DAKE CIKI ALLAH YA YAFE MIN,BADA CIN ZARAFI NAYI BA SANNAN ƘIRƘIRARREN LABARI NE,INA GODIYA MASOYA TABBAS NAGA SOYAYYA INA KAN GANI DUK DA WANNAN BASHI NE BOOK ƊINA NA FARKO BA AMMA NAGA KULAWA ALLAH YASAKA DA MAFIFICIN ALHERI. JINJINA. Muhammad Kareem kaima kayi iya ƙoƙarin ka Nagode Allah ya saka da alkhairi Allah yabar zumunci. Ban manta da GALADIMA FAMILY group ba ina miƙo gaisuwa a gare ku Allah yasa ka da alkahiri,haka mutanen facebook musamman HAFSAT HAUSA NOVE H² Allah ya saka muku da alheri. Gargaɗi Kada a canza min komai na book yin hakan babban kuskure ne akiyaye😡 Sai kun sake jina a zazzafan next book ɗina Wanda zaizo bada jimawa ba,kudai ku kasan ce da alƙalamin XAHRATTY ✍🏽 za ku samu duk novels din da ku ke so a shafin mu https://hausanovels001.com.ng