HTTPS://HAUSANOVELS001.COM.NG BOOK 3 Page 1 ALhaji Isa ya shiga cikin Falon yana kiran, "Hajiya!" ' Badi"atu ta fito daga dakinta tana yi wa Alhajin sannu da zuwa,sannan ta ce, "Yaya Mustapha ya kai ta Kaduna". Ya kalli agogon bangon falon tare da fadin, *Nan da Kaduna shine har yanzu sai ka ce wadanda suka tafi Abuja? Badi'atu ta ce, "Sai da suka yi sallar azahar sannan suka tafi" Ya ce, "Kai Hajiya tana da shiririta sosai. Ni da muka yi da ita za su tafi tun safe?" " Ya ja tsaki tare da fadin, "Yanzu dubi fa shida saura, kuma ta san ina azumi" Badi'atu ta ce, *Ga shayinka can yanzu na gama dafawa, na sa a flask" Ya ce "*Shayin ne kadai matsala ta kenan? Tana sani na tsani in dawo ba ta gida. To wai su nawa suka yi tafiyar ne?" Badi'atu ta ce, "Su da Mama Ya nufi dakinshi yana fadin, *Bari in kira ta" Daidai wannan lokacin Shatima yana tsakiyar falon cikin tsansnin damuwa, da tashin hankali. Minti daya tak din da Hajiya ta ba shi ne ya yi mugun tsorata shi. Sam ba ta ba shi isasshen lokacin da zai yi tunani ba. Ya nufi kujera da nufin zama ko zai samu basirar shawo kan matsalar. Don rudewa sai ya kai zaman kafin ya isa kujerar. Hakan ya sa shi zubewa a kasa Salatin da ya ji dakin ya dauka gaba daya ne yasa shi lunshe ido, tare da fatan Allah ya sa mafita ce wannan Ya saki jikinshi tamkar wanda hankalinsa ba ya tare da shi Nan duk suka yi kansa suna kiran sunansa. Hajiya tana fadin, "Na shiga ukuna! Shatima don allah ka tashi! Ku debo min ruwa Mama ta ce, "Tsaya mu gani ko dai juwa ce ba suma ba ne?" Aliya da su Amna sai nanata sannu suke yi. Hajiya ta dibi ruwa ta wanke mishi fuksa tare da fadin, "Sannu Shatima, ka tashi don Allah Duk yana jinsu, ko babu komai sanyin ruwan ya rage masa zufar da take tsiyaya a jikinsa. Sannan ya sauke wata irin ajiyar zuciya. Mustapha cikin bacin rai ya ce, "Ban ga dalilin yin wannan zantukan ba tunda ba su ne suka kawo mu ba" Shatima kuwa addu'a yake a cikin zuciyarsa,yana kiran sunayen Allah tsarkaka. Fatanshi Allah ya fidda shi cikin wanna fitina. Miyan bakinshi ya tsaya cak! Lokacin da ya ji muryar Hajiya tana maimaita ya wartsake a yi ta ta kare, don ba zan bar wannan damarba. Mama tace, "Haba Hajiya! Don Allah ki bar wannan maganar, a bi komai sannu Alhaji ya yi ta duba wayarshi a daki, sai ya tuna tana mota inda ya jona ta a caji. Ya cire kayanshi ya maida jallabiya mai gajeran hannu, sannan ya fita. Missed calls ashirin na Mustapha ya gani, Tsoro ya kama shi, tare da fargaba suka darsu a zuciyarshi. Tuni ya Raya cewa sun yi hatsari ne. Cikin rawar hannu ya bi kiran. Da sauri ya daya, Alhaji don Allah ka kira Hajiya yanzun tazo tana ta fada da abubuwa a gidan ga shi nan har Ya Shatima ya fadi!* "Faduwa?" Alhaji ya tambaya da karfi. Mustapha ya ce, "Faduwa kuwa, yanzun haka ba ya cikin hankalinshi Alhaji ya ce, "Ai babu batun kira, bari kawai inkira Babanku Musa muzo gidan Mota ya fada a hakanshi, sannan ya kira layin dan uwansa Alhaji Musa. Lokacin da Alhaji Musa ya daga wayar Alhaji ya kusa fitowa daga layinsu. Alhaji Musa ya ce, ga shi a Jaji sun z0 duba jikin Alhaji Yakuba abokinsu, wanda ya hadu da ciwon mutuwar Barin jiki. Alhaji ya ce, "Gani a hanya, jira ni a titi zan dauke ka mu wuce" Alhaji Musa ya ce, "Ina zamu Wuce!?" Alhaji ya ce, "Kaduna gidan Shatima, Hajiya Amina da suka je dubiyar jikin Nafisa ta tada musu wata fitinar. Ga shi can an ce jikin Shatima ya tashi har ya fadi yana da rai ko ya mutu ma? Ni ban sani ba" Gudu sosai Alhaji ke yi, cikin mintuna ya iso Jaji, ya dauki Alhaji Musa ya kuma daukar hanya Cikin lokaci kalilan Shatima yana jingine da kujera kanshi yana cinyar Aliya wadda wadda idanu suka yima jajir don kuka. Page 2 Yace Hajiya, Ki saurare ni zan yi mikI bayani yanda za ki fahimta' Ta mike tana fadin, "Kana bata min lokaci, ga shi can ana kiran magariba. Ni kawai cewa na yi ka saki waccan abin", Ta nuna Salma wadda ke durkushe a kan Kafafunta, tun gurin da aka titsiye ta Kafatunta sun yi sanyi sun sage, har ba ta san ta yi motsi mai karti don azabar da suke yi mata. Shatima ya ce, "Hajiya.Ta sake katse shi, "Bana son jin komai daga gare ka, sakinta kawai na ce ka yi. Ba zan fahimci komai ba" Alhaji ya fado Takin babu sallama, ya amshi zancen Hajiya da cewa, "Wa za a saki?" Shatima ya mike da sauri tare da fadin, Alhamdu lillahil. Alhaji Musa ya ce,Zauna Babana, zauna kar ka sake faduwa Alhaji ya isa gaban danshi da sauri ya kama shi, ya zaunar tareda fadin, "Zauna abinka Shatima ya zauna cikin farin ciki, tare da ci gaba da yi wa Allah godiya. Hajiya ta yi matukar girgiza, mamaki ya cika ta da ganin Alhaji. A zuciyarta ta ce, "To wa ya fada ma Alhaji?" Alhaji ya dube ta rai bace, fuska daure, "Yanzu Hajiya Amina kin yi daidai kenan? Ki taso tun daga Zaria da sunan gaida mara lafiya don ki samu lada, amma ki buge da tada husuma cikin gidan danki? Ina hankali da tunaninki suka shige? To wa kike fadin a saki ma?"Ya kalli Alhaji Musa, "Dubi wani abin kunya don Allah Alhaji Musa ya ce "Ga wadda za a ce ta yi abin kunya nan. Kin z0 gidan"yarki gaban kishiyoyi, gidan suruki kin tada hankali? Wannan abin fadin da me yayi kama? To da kin yi sanadin rayuwarshi, me za ki Ce?" Hajiya cikin borin kunya ta ce, "Ni ban tada wata husuma ba. Wane munafuki ne ma ya kira Alhajin?" Ta kai Karshen maganar tare da kure Mustapha da ido. Shatima ya ce, "Alhaji, don Allah ku zauna, nidai na gode wa Allah da ya turo mini ku a daidai wannan lokacin. Don Allah ku taimaka min ku zauna don a warware wanna matsalar. Domin duk wata matsala a duniya ana warware ta ne ta hanyar zama a tattauna ba ta 鈥瀉nyar tashin hankali ba. Ba kuma ta hayaniya ba Alhaji yace "'Mu yi sallar magariba tukunna ko?" Hajiya ta ce, "Ni fa kawai a yita ta kare, ya saki *yar can mu kama gabanmu". Ta fada tare da nuna Salma. Duk suka dubi gurin da Salman ta ke a tsugunne, sai lokacin Alhaji ya ga Salma din. Hajiya ta ci gaba da fadin, "Ni fa duk wannan abin lafiyarsa ni ke yi ma wa, ku ba za ku fahimta bane an fada min cewa uwar yarinyar nan ta je ta kai sunan Shatima an tsaface shi don ya dinga kashe musu kudi. An hada asirin da yawun bakinta, an yi surkulle an ba shi ya ci. Kuma asirin ya ci shi domin ga shi yanzu duka yaushe aka yi auren ma ya sa ta a makaranta mai tsadar gaske, kullum sai ya ba ta dubu da dari biyar. Ita na haifar ma shi kenan?" Salma ta fashe da sabon kuka tana fadin. "Na rantse da Allah Hajiya, Innarmu ba ta zuwa gurin masu asiri. Ko Babanmu da yake da ciwon Barin jiki cewa tayi yi kar a kai shi grin masu maganin gargajiya ciwonshi na asibiti ne kar su bata masa jinya su ce wani ne ya yi masa asiri. Allah na rantse ba mu taba yi wa Yaya asiri ba. Allah ma ba zai barmu ba, domin shi taimakonmu ya yi. Na sani ban kai Yaya Shatima ya aure ni ba, mu tsoro ma muka ji da ya ce shi zai aure ni. Ga ma Yaya din a tambaye shi, ko ruwan gidanmu bai taba sha ba bare har ma mu ba shi nama ya ci" Ta saki ajiyar zuciya, sannan ta karasa maganar a hankali, "'Ko yanzun da nike matarshi bai ci abincina ya kai sau goma ba. Cewa yake ni ban iya girki ba" Ta jero shesshekar kuka a tare, sannan ta ci gaba da gunjin kuka.Alhaji ya kalli Hajiya, "To ke da ki ka ce an fada miki, wane ne ya fada miki din?" "Hajiya Azumi ta yo min tambaya a gurin malamai, kuma ta ce guri biyu ta je duk bakinsu daya Alhaji ya kalli Alhaji Musa ya ce, "Ka ji ko? Imaninta ta saida a gurin makaryatan bokaye. To da izinin wa ki ka je?" Ta zaro ido cikin firgici, ta ce, "A'a Alhaji, Niba zuwa nayi ba. Ina fada maka Hajiya Azumi na aika Shatima ya amshe zancen da cewa, *Alhaji,kamar yanda Salma ta fada ne, ko ruwan gidansu ban taba sha ba. Hajiya ma da ta yarda da wanna karyar ta so ta yarda ne. domin ta fi kowa sanin yanayina domin ba kowane abu ni ke iya ci ba, Kuma kudi da Hajiya take magana ina ba Salma, ita ce ma ba ta samu gatansu ba, komai na sauran matana ya fi na Salma. Gida da Hajiya ke magana haya ce na kama musu, ba siya na yi ba don ko alakar aure ba ta hada ni da 'yarsu ba ina yi musu. Taimako irin wannan ban san adadin da na yi ba, Munnir ya san haka ba sai na zo na ce Hajiya, ko Alhaji na taimaki wasu ba. Haka ko a hanya na sha kashe rigimar kudi da aljihuna in wucce Ba ina fada ba ne don alfahari ko gori ba, ina son a fahimce ni. Maganar kud矛 wane magulmaci ne ya fada?" Aliya ta ce, "Ai na sani kudin nama ne ka ke bata, mu kuma kana saka mana nama a fridge. Na fadama Hajiya" Shatima ya kalli Alhaji, "Ga su nan rago na dubu talatin-talatin nike siya musu su uku, kowacce a gyara a saka mata a fridge ga kaji guda goma-goma na wata daidai kenan, amma cikinsu na Amna ne kawai ya kai watan. Su kafin haka nasu ya fare, ita ko Salma dubu daya a wata, dubu talatin, sannan bana sai mata kaza. In na siyo gasasshiya har da su nike saye. Haka kuma akwai kudin kati da nike saka musu duk sati, ita ko ko wayar ma ba ta mallaka ba bare kudin kati ya je mata Shatima ya dubi Hajiya, "Zancen makaranta kuwa,alkawari na dauka tsakanina da mahaliccina cewa, zan taimake ta tu帽 kafin in yanke shawarar zan aure ta Ya numfasa sannan ya kalli Mama, "Akwai abin da ba ku sani ba. Babu son Salma ko digo a cikin zuciyata, so na soyayya dai sam babu wannan. Na auri Salma ne don in taimaki rayuwarta ta yi karatu. Ta so in aura mata wani ne, in mata kayan daki don ta cika burin Babanta. Ni kuma na aure ta don ta cika duk burikan guda biyu ne. Zan iya zama da Salma har karshen rayuwarmu, in kuma da zuri'a a tsakaninmu har mu samu rabo, ba zanyi Ki ba. Amma ba don so ba. In kuma tana bukatar rabuwa da ni yayin da burinta ya cika, zan iya sahale mata ta je ta auri wanda ta ke so, yake sonta. Ban fadi haka don cin fuska ga Salma ba, sai don hakan shine gaskiya, kuma Hajiya ta gane cewa,Salma ba su yi min asiri ba Salma kanta a sunkuye wasu zafafan hawaye ke zuba a idanunta masu radadi. Tun da aka soma rigimar bata tsinci kanta cikin bakin cikin da ya kai na yanzun nan ba. Kalaman Shatima sun yi tsauri, kuma sun yi ma zuciyarta daci, sannan sun yi ma kwakwalwarta nauyi. Har ma ta ji da ma ya bi umarnin mahaifiyarsa ya sake ta din zai fiye mata jin wadannan munanan kalaman da suka fito daga bakinsa. Ta soma rainon zuciyarta, har ta soma koyon sonshi, da tantance son Page 3 Don ta samar da sotsan tsamara gauraye. Ashe ita tana aikin banza ne, gara ma da ta sani tun da wuri. Ta dago jajayen idanunta ta kalle shi, yana da Kimar da ba za ta iya maida mishi magana ba, don haka ta sake sunkuyar da kanta. Alhaji yace "Duk abin bai kai a yi wannan tone-tone ba, kada in Kara jin an yi zancen saki, ko asiri Ya dubi Hajiya Amina, yace "In kin ci gaba da dagewa a kan wannan maganar zan ta sa ki har gaban Hajiya Azumin, sannan mu je gurin malam su bani hujja' Ya nuna ta da yatsa, "Kin san zan iya Alhaji Musa ya ce, "Wannan shine gaskiyar magana Mama ta ce, 芦Ni wallahi duk wannan abu ba a son raina suka faru ba. Ban so aka tono wadannan zantukan ba, tunda ban san komai a kai ba. Mun dai z0 duba mara lafiya Alhaji yaja tsaki, "Ga shi mun rasa jam'in magariba a kan zantukan nan marasa tushe, bare makama Ya kalli Hajiya, '"Ke ce babbar mai laifi a cikin wannan al'amarin" Ya kalli Salma 芦Tashi yarinya kin ji daga wanna durkuson Salma ta sauke ajiyar zuciya, sannan ta yunkura da niyyar tashi. Kafafunta sun yi tsami, ba za su iya daukarta ba, don haka ta koma ragwat! Ta zauna. Alhaji Musa ya ce, '"Sannu, Kafafun naki duk sun yi tsami ko?" Ya sa hannu a cikin aljihunsa ya ciro kudi ya kirga naira dubu goma sha biyar ya mika wa Shatima, ya ce, "Ga shi ka sai mata waya ko karama ce, don ita ma ake saka mata katin ko da iyayenta sa gaisa Ta dubi Alhaji Musa ta ce, "Baba na gode".Muryarta tana rawa. Yace "Babu komai "yata" Yaci gaba,'da Kowacce ta koma gurinta ta zauna lafiya da mijinta da "yar uwarta, zuciya daya Amna ta kalli Hajiya, "Babu maganar asiri-asiri ko?" 鈥� Alhaji ya amshe, "Babu wata magana da ta shafi asiri, duk sharri ne' Ta ce,To, ku gaida gida". Ta nufi sashenta cikin jinjina abin da ya faru. Aliya ta mike tana fadin, "Ga shi ko abincin ma ba ku ci ba. To ku gaida gida" Salma ta bi Aliya da kallo, ba ta shakka ita ce ta hada komai. Ta soma tuno wasu abubuwa da ta yi mata masu kama da ingiza mai kantu ruwa. Salma ta yunkura ta mike da kyar ta dubi su AlhajiBaba ku gaida gida" Ta kalli su Hajiya, - "Sai anjimanku, Allah ya tsare hanya Su Alhaji suka ce, "To sai anjima, ki yi hakuri kin ji ko?"Hajiya ta tabe baki tare da raka Salmar da harara. Nan Alhaji ya yi ma su Hajiya fada sosai,sannan suka ce, "Ku shirya bari mu yo sallah mu zomu wuce" Salma ranar da zazza6i ta kwana, haka kuma ba ta jin cewa za ta je a yau. Lokacin da Shatima ya shiga gurinta da safe tana nade a zanin gado a can tsakiyar gadonta. Ya kira sunanta, "Salma". Da kyar ta daga idanunta jajir ta ce, "Na'am." Ya ce, "Ya ya dai, ba ki da lafiya ne?" Ta maida idanu ta rufe, zuwa yanzu ba ta son taji ko ta ga Shatima. Ta ce, *"Dan zazzabi ne' Ya hau gadon ya saka bayan hannunshi a sassan wuyanta. "Kai! Haka jikin naki ya yi zafi? Tashi in kai ki asibiti Ta yunkura tare da fadin, "Ka barshi kawai, zai bari anjima kadan Ya ce, "To in turo Aliya ta duba ki?" Ta ce, "Ka barta anjima kadan zan warware" Ya ce, "Yaushe ki ka soma gardama da ni?"Salma ta yi shiru, Ya kama hannunta, "'Sakko in kai ki asibiti" Jallabiya ta saka suka tafi.A bakin makarantarsu suka tsaya, ya rubuta *yar takarda ya bawa mai gadi ya ce ya kai ofishin shugaban makaranta. An ba ta allura da magunguna, ya dawo da ita gida. Ya shiga gurin Aliya. Da ma ta ga fitarsu, ya ce, don Allah ta lura da ita ba ta da lafiya. Aliya tace, "To"Yana fita ta zauna cikin fargaba, kar dai ita ma wannan cikin gare ta? Na ba ni ni Aliya, nice kenan zan zama karshe?" Ta mike da sauri tare da fadin, "Bari na je dakin Salmar na gani" Ta same ta kwance kan kujera. Salma tana gaminta a ranta ta ce, "Allah ka yi min tsari da duk sharrin da matar nan ta zo min da shi Aliya ta je gabanta ta tsaya tare da rike kugu, "Ashe ba kya jin dadi?" Salma ta ce, "Uhum". Aliya ta ce, "*Ko ke ma cikin ne?" Salma ta ce, "Oho! Ni ma ban sani ba" Ta sake matsawa kusa da ita, "Wane irin gwaje- gwaje aka yi miki?" Salma ta yi mata banza. Tsaki ta ja ta fita tana mitar, yana fadin ba ya sonta amma ga shi nan da cikinsa a jikinta. Salma ta shiga kunci da bakin ciki sakamakon kalaman Shatima. Duk da wautarta da Kuruciya ta san Shatima ya ba da ita badawa ta karshe, ya kunyatata gami da tozartata. Ta yanke ma kanta dakatar da son Shatima, sannan za ta ja baya da shi. Za ta ci gaba da kallonshi a matsayin Yaya kurum *** Kwanci tashi asarar mai rai inji masu iya magana. Amna da Nafisa ciki na ta girma. Domin Amna tana da shidda, Nafisa tana da wata biyar. Shatima ya samu Amna da batun zuwa awon ciki, ta ce masa ita sai sun dawo daga umara. Ya dube ta cikin al'ajabi, "Za ku je ummara yaushe?" Tace "Jibi insha Allahu za mu tafi da su Momy Yace, "Ikon Allah, shine ban isa ki fada min ba bare ki nemi izinina? Ta ce, "Jiya Mom ke fada min ni ma' Shatima ya yi shiru cikin bacin rai. Ya sauke ajiyar zuciya, abu daya zai sa ba zan hana ki ba, amma gaskiya a guji shigar min hakki" Ta dube shi. "Ban gane ba? Kana nufin da saika hana?"Yace "Kwarai kuwa Ta yi *yar dariya irin ta rainin wayo, ta ce, "Kai kana da son rigima" Ya kauda zancen don ba ya son su fara sa'insa, don haka sai ya ce, "Ke nan ba ki nan za a yi bikin su Hannatu, yaran Yayan Alhaji marigayi na Kaduna?" Ta dan yatsina baki, "Ko ina nan ka san bai zama lallai inje ba don bana son hayaniyar mutane Shiru ya yi yana kallonta, don tuni ya lura ba ta son duk wani al'amari da ya shafi danginsa, domin ko kwanan baya da Hajiya Kaka ta yi rashin lafiya babu yanda bai yi ba a kan su je a duba ta ba, amma ta ki, kuma sauran duk sun je. Amma bari ya yi mata uzuri ta haihu. Bikin "ya'ya biyu za a yi, babban dan Kaka wanda ya rasu, bikin a Zaria za a yi shi. Haka kuma bikin zai kama ana saura sati daya azumi. Da Amna ta Page 4 shirya za ta tafi Kano don yin tatiyarsu, Shatima ya yita maza ya ce, "Allah ya tsare hanya". Ya kuma kawo dubu goma ya ba ta. Kanwar su Alhaji Hajiya Sauda ita ce ta fito da anko, ta kira Shatima tana sanar da shi cewa, ga na" matanshi kala bibbiyu, kudinsa naira dubu arba" in. Ya ce, "Anty na mutum uku za a cire, Amna bata nan anty tace To zan barsu gurin Kaka" Ya ce, "*Shi kenan, ki turo account in tura miki kudin Da ya sanar da su batun anko, Nafisa ta ce za tasa Hamida ta je ta amshi nata a gurin Kaka din. Aliya ma cewa ta yi za a zo daga gidansu a karba mata. ' Salma kuwa cewa ta yi, nata a bai wa Anty Badi 'atu ta bai wa mai mata dinki. Ya ce, "To telan ya sanki ne?" Ta ce, "Ta yi masa kwatance na kawai Salma Bash shine sunan da *yan makarantar su Salma ke kiranta da shi. Kawarta Salma Sadik Dankasa ita ce ta rada mata shi. Zuwa wannan lokacin Salma ta waye, ta goge, ga turanci tana gane karatu sosai. Haka nan in ka ganta tana tsalle-tsallenta sam ba za ka ce tana da aure ba. Salma da ma yarinya ce, sannan ga ta da son wasa, shi ya sa kawancensu ya dace da Salma Sadik. Suna cikin group din Kwallon tebur da kuma rawa irin ta makaranta. Wani lokacin ma wayarta ta kan kunna a gida tana cashe rawarta. Yau Shatima dakin Salma yake. Dafadukan taliya ta yi, ta zubo masa don ta lura yanzun yana cin abincinta, tunda aka yi wannan hayaniyar. Ta aje a gefensa yana zaune kan kujera yana aiki da laptop. Ta koma ciki tana atisayen rawar da za su yi gobe in sun je makaranta. Ya kwalla kiranta. Ta fito ta durkusawa a gabanshi, ya ce, "Wai ke duk lokacin da zan shigo sai in ji kina jin wannan sautin, ina ki ka samo shi?" Ta ce, "Muna amfani da shine a club dinmu na rawa" Ya kware da abincin da ke bakinshi, nan ya shiga tari. Salma ta ce, "Ya salam!" Ta tsiyaya ruwa a kofi ta mika masa. Ya amsa ya shanye, ya ajiye kofin sannan ta dube ta murya a shake ya ce, "Rawa? A wane club kuma?"Ta ce, "Yaya na makaranta ne, an ce mutum ya zaba ko rawa ko waka Ya ce, "Kina manta cewa kina da aure ko?" Ta ce, "Ban manta ba". Ta sunkuyar da kai. Ya ce,Gaban maza ku ke rawa ko?" Ta ce, 'A'a Ya ce, "To kar dai ki sake in ji an ce kin shiga gasar rawa, balle a zo ana yinta a gaban mutane Ta ce, "Ba zan yi ba, jibi ma za a yi mana hutu' Ya ce,Shi kenan. . Yauwa Badi'atu ke ta damuna wai dinkin anko wane kala za a yi miki? Na ce in na dawo zan neme ta. Bari in kira miki ita" Salma ta ce, "Mun yi waya dazun Yaya, da ma wai ba ta same ni ba ne ta kira ka. Nida zaka barni inje Zaria din da na kai wadansu kayan Ya ce, "A'a sai biki za ki je gaskiya Ta ce,Allah sarki Yaya, kayana sun sha ruwa wadanda aka dinka min" Ya ce,Yau saura kwana goma sha daya bikin,zan je ranar asabar sai ki ba ni sako Ta ce, *Badi'atu za a bai wa, zan amshi wasu style a hannun Salma Sadik" Ya dago ya dube ta, "To wa zai biya kudin dinkin?" Ta yi murmushi, "Ni zan biya kayana Ya tattara hankalinsa a kanta, "Ina ki ka samu kudi?"Ta ce, "Wanda nike tarawa.Ya yi murmushi, "Kawo su mu gani, sun kai) dubu goma?" Ta yi dariya tare da nufar daki. Ledar da ake saka zanin gado ta dauko ta zo gabanshi, ta juye kudin a Kasa. Mamaki ya kama shi, ya ce, "Wannan duk sune?"Ta ce, "Sune mana" Ya ce,Lallai kudi wawaye ne, sun, kai nawa Yanzu tace , "Sai dai a kirga a gani". Ya dauki yan dari biyar, bari in hada wadannan, ke kuma ki hada sauran "Bari in hada Ta soma hadawa tana cewa, Kila su kai irin dubu talatin din nan Sun gama lissafi abin da yaba su mamaki, sai ga kudi dubu dari da biyar har da naira sittin. Salma tace, "Kudina ne kadai kuwa?" Ya ce, "Ana ba ki ajiya ne?" Ta ce, "A'a, ni dai to ko aljanu suna saka by Mistake? Ya yi dariya, "Kin dauki watanni kina tara su' Ya dube ta, "Ni ma za ki ba ni aron dubu hamsin Ta ce, "a,a dai a raba zan dai ba ka kyauta. Toni ban ma san ya zan yi da su ba. Ka amsa duka mana?"Ya ce, "A'a ba zan amsa ba, ai kudinki ne"Y脿 Kirgi hamsin, "Wannan ma na ara ne, zan baki insha Allah". Tace Ni dai bar maka na yi gaskiya Shi ma ya sake cewa, "A'a zan ba ki su. wadannan kuma in kin je gida sai ku yi shawara da su Inna, ki yi yanda ki ke so" Ran'- da za su tafi Zaria ita ce ranar farko da dukkansu za su je gidansu, don haka duk suna cikin murma da doki sunje wajen shiga mota nan ne akadanyi wasan kwaikwayo nafisa da aliya duk sunata harin gaban mota salma tana ganin haka sai tayima kanta mazauni a baya Aliya da yake ta fi Nafisar lafiya sai ta yi maza ta fada gaban. Nafisa ta kama kugu ciki ya yo gaba, ta ce, "Ni ce zan zauna a gaban mota, don nice da girki" Aliya ta kalle ta, da dan murmushi, "Ai gaba mazaunin babba ne" Shatima ya riske su cikin wannan musun, don ya je gurin Baba maigadi ya sallame shi da abin da zai rike kansa kafin su dawo. Ya kalli Nafisa da ke tsaye,ya ce, "Kina nufin sai na zo za ki shiga?"Cikin dan wasa ya yi maganar. Ta ce, "Ni gaba zan zauna . Ya kalli gahan, Aliya ce a ciki, ya ce, "To ki shiga baya tunda ta riga ta zauna" Nafisa ta ce, "Oho, da ma kai ne ka ce gaban mota na uwargida ne?" Aliyar ta yi *yar dariyar kissa, "Da ke sai ki bar babba a baya?" Shatima ya ja tsaki, wai har shiga motar ma sai an yi masa wata ka'ida? Aliya ta ce, "Shi ne na gani" ". Cikin 'yar dariya ta yi maganar.? "Maimakon ki shiga baya ga ciki inda za ki sake abinki" Nafisa ta koma baya ta coge, tare da dafe ciki, ta ce, "Sai dai ko a bude but din a fito min da kayana,don kuwa babu dole sai na je a cikin motarsa' Kar in sake in ji kin bi motar haya. Inba za ki shigo ba, to ki koma ciki ki bude dakinki ki shiga Ta tura baki, "Ai dai ka san wanna bikin dole in je shi. Domin yanda ka ke jin cewa 'yan uwanka ne za su yi aure, haka ni ma 'yan uwana ne" Page 5 Ya ce, "To za kiyi min rashin kunya ne ko zaKi fada min magana ne?"Ta yi shiru tana rike da Kugu. Ya koma ya zauna, ya sauke ajiyar zuciya sannan ya soma magana da Aliya, "Yi hakuri ki koma bayan" Aliya ba ta so haka ba, amma sai ta wayance ta bude Kofar tana fadin, "Zo ki shiga ba don halinki ba, kuma kar ki sake ki takura min yaro na fada miki"Nafisa ta shige tana zumbura baki. Salma duk tana jinsu, ita neman layin kawarta Salma Sadik takeyi. Aliya cikin son daba ma Nafisa magana tace, "Ke baki fadan shiga gaban motar? Da yake yanzun Salma ta Gama sanin wace ce Aliya sai ta tabe baki, tace, "Anty ai ni gaban motar Yaya in da gundira ya kamata ya gundure ni. Kullum sai na hau zuwa makaranta" Aliya ta tabe baki ba ta sake magana ba. Suna hawa babban titi layin Salma ya shiga.Kuka suka soma shirmansu, "Hi kawata ya ki ke?"Ta ce, "Ya ki ke Kawas? Gamu za mu je Zaria din Tace Haba ki ce yau sai City?" Salma ta ce Ga mu a hanya, in na dawo zan Zo in kawo miki kayanki" Salma ta ce, "Ke din ce zaki zo? Lallai Salma ta ce, "Allah zan z0. Zan roki yayana ya barni inz0 ko ya kawo ni in maido miki style dinki dana ara kin ga mun yi hutu, kuma za a shiga azumi Salma Sadik ta ce "Ki bari dai zan z0 miki da sallah Salma tace "Za mu sake zuwa Zaria da sallah, amma duk da haka zan jira ki". Ta ce, "Shi kenan". Suka yi sallama. Shatima yace, "Ina za ku je yawon sallah din?" Salma ta ce, "Uhm Ya ce"Na san kin ji ni", 'Ta ce, "Zaria mana da sallah fa" Ya ce, "A'a ba za ku z0 ba, kun je daf da azumi sannan ku je da sallah:" Ta yi shiru. Aliya da Nafisa har suna hada baki gurin cewa, "Haba dai, sallah guda!"?" Ya ce, "Au kuma kuna son zuwa ne?" Aliya ta ce, "Haba my love, sallah lokacin ziyara ne Ya ce, "To ni dai ba dinkin sallah zan samu damar yi muku ba, don akwai abubuwa a gabana" Aliya ta ce, "My love ta ya ya ma za mu ce maka sai ka yi mana kaya, ga' zannuwan nan na lefenmu za mu dinka". Nafisa ta ce -Ni kam zanyi da ace tun muna gida aka yi wannan zancen da na zo da kayana na bada dinki". Shatima ya ce, 芦Wannan ai mai sauki ne, in zan sake shigowa Zaria zan z0 miki da shi" Ya kai hannunshi daya ya shafi cikin Nafisa tare da fadin, "Ke kuma wa yace miki kwalliya ba tayi miki kyau?" Cikin shagwabar da ta san yana so, ta ce, " In jika mana Ya maida kanshi titi, "Kin ma san me ye? Ai kin ma fi kyau a haka. Ina kallonki da dan yarona 'Ta ce, "Ni nace maka yarinya ce fa" Ya ce, "Ai ni na yarda da batun likitan, duk da shi ba Allah ba ne. Amma Allah ya ba shi ilimi a kan haka Aliya bakin ciki ya hana ta magana; sai da Shatima ya ce, "My love wannan layinku ne, hoto ya nuna namiji amma tana musu". Ta yi dariyar yake, "Ai kin dai ji an ce namiji ne to hakan ne" Nafisa ta ce, "Ni dai Allah ya ba ni mace ba zan daina wannan addu'ar ba Aliya ta ce, "Ki dai roki alkhair kawai". Yace, "Abin da ya fi kamata ma kenan Sun isa Zaria cikin tukin da yake na nutsuwa da kwanciyar hankali. Kai tsaye gidan su Hajiyarshi ya nufa da su. Ta sa an gyara gurin bakin ta dauka har da Amna za azo ta sa an yi girki na alfarma da kaji. Tafito da fara 'a tana fadin, "Sannunku. 鈥� sannunku"Ta dube su, "Ina Amna?" Shi ma wanda ke kokarin fita ya ce, "Sun je umra Hajiya tace "Masha Allah, Allah ya dawo mana da ita lafiya Sannan ta kalli salma "Kowa ya nemi gidan uwarsa in- yana da shi, tunda dai ku ba baki ba ne, dama na sa an gyara sasan ne saboda Amna, don nice uwarta ta Zaria Shatima yaCe, "Naso Su zauna anan gabadaya Hajiya tace, "A'a sam ba zai yiwu ba, ga dai abinci nan su ci, kowa ta kama gabanta Nafisa tace "Har ni Hajiya?" Hajiya ta ce, "Ai ke nan gidan ubanki ne, in zaki zauna zauna mana Salma dai hakan ya yi mata dad矛, don tana kewar Innarsu. Abincin ma ita ba ta ci na kirki ba saboda doki. Ita da Aliya ya dauka don ya kai su gidajensu, Nafisa ta ce, sai Alhaji ya zo sun gaisa. Aliya ya soma saukewa, sannan ya nufi kofar gidan su Salma. Cikin doki ta fito za ta dauki kayanta. Ya yi saurin riko hannunta, "Kina ta sauri za ki rabu dani ko?" A hankali ta kalli hannunsu, sannan ta dago ta kalli fuskarshi. Babu ko digon son Salma a zuciyata Kalaman da suka dawo mata gar a zuciya kenan. A hankali ta zame hannunta,Cikin sauri ya sake rike hannun gam! "Fadi abin dake ranki" Ta Kirkiro murmushi, "Ba ni da magana" Ya ce Ba za ki yi kewata ba?" Ta ce, "Ko dakina zan yi kewarshi bare kai. Ina da sabo sosai Ta kuma janye hannunta daga nashi, tare da Fadin, "Bari in shiga ciki' Ya sauke ajiyar zuciya, "Ban yarda ki je ko ina ba ba tare da kin sanar da ni ba' Ta ce, "Ni kadai kacema haka Don Anty Aliya ban ji kace mata haka ba". Cikin shagwaba tayi maganar. Shatima ya ce, "Ai ita ta san me ta ke yi" Salma ta ce, "Humm, kai dai kana yinta dayawa Yace Me ya sa ki ka ce haka?" Salma ta ce Komai ita".Ya ce, "To shi ne ya sa ki ka ce na fi sonta?" Tace "To wa ka fi so a cikinsu?" Ya ce, "Ya aka yi ki ka cire kanki?' Ta ce, "Yaya kenan, ai da ma ni ba na cikinsu sam"Ta yi murmushin Karfin hali sannan ta fice daga motar da sauri, tare da fadin, "daga min baya in Dauki kayana Ya ce, "A bude yake, ki daga ki dauka Tana fito da kayan shi ma yana fitowa daga motar yana kallonta. "'Kin cire kanki a cikin matana saboda har yanzu ba ki san so ba?" Ta ce, "Humm, ka tafi abinka Yace" Duka kika kwaso kayanki?"Ta ce, "Ba ka ce in dauka duka ba? Amma ka cire wanda ka ce in ba ka ko?" Ya ce,A gabanki na dauka, har kin manta?" Page 6 Ta ce,"To ba za ka shiga ku gaisa da su Inna ba?" Ya dubi jikinshi,A,a zanzo na musamman Kananan kaya na saka yanzun".Ta ce, "Shi ke nan, amma don Allah ka kawo min Badi'atu ta kawo min kayana Ya ce, "In ban samu zuwa ba sai Mustapha ya kawota Ta ce, "Duk daya ne". Salma ta yi murna da dinkunanta da Badi'atu ta kawo, sun yi kyau sosai da yake ita ma Salma Dankasa kusan Kirarsu daya da Salma din. Sai dai Salma Dankasa ta fita cika idanu. Salma ta dubi Badi"atu ta ce, "Anty Badi'atu nawa ne kudin dinkin?" ido A Badi' atu ta ce, "Yaya fa ya bada Salma ta CE Kai! Ya bada kuma shi da ba shi da kudi? nage Badi'atu ta ce, "Ai tun lokacin da ya kawo kayan ina kai wa ana fadin kudin ya biya" Sai da Salma ta yi wanka ta shirya, sannan suka tafi tare da Badi'atu. Can gidan Hajiya Kaka suka nufa, sun bar Inna cikin murna ganin yanda Salma ta yi kyau, ga shi ta waye abinta. Da dare suka bar gidan Hajiya Kaka, Salma ta dawo su Badi'atu suka wuce. Ta ciro kudin da ta zo dasu ta ba Inna dubu arba' in a ciki, ta rike goma. Ta ce a sai mata wani abin. Sauran da ta cire ta sa a jakarta tace gobe daurin aure zan so ace da kudi a jikina, mutum ya dan yi alheri. Abin da ya ba Aliya mamaki, ranar daurin aure sun hadu a gidan kaka, duk kowa ya zo ya kai gaisuwa ana zaune, Salma ta shigo ta yi kyau sosai cikin atamfar ankon, doguwar riga. Ga dauri ta sha abin sha'awa. Ita ma ta je gaban Kaka ta durkusa har Kasa ta gaida ita. Kaka ta ce,Wace ce wannan?" Aliya cikin gadara da son ganin an wulakanta Salma ta ce, "Salma ce kaka, matar Shatima" Kaka ta dube ta, "Masha Allah, to Allah ya yi muku albarka dukkanku". Salma ta bude jakarta ta ciro leda baka babba,ta mika ma Kaka da hannu biyu ta ce, "Ga shi KakaTa amsa tare da tambaya, "Me muka samu?"Salma ta zauna gefe ba ta ce komai ba. Kaka ba ta bari ba, ta bude ledar. Turmin zani ne da turaruka sai "yan dari biyar guda hudu. ta kalli Salma, "Allah ya yi miki albarka. Ina jin ke ce za ki saka ma uwar Shatima da abin da ta yi min" Nafisa ta mike ta fice, Aliya kuma aka yi tsuru cikin jin kunya. Dole ta shiga jerin masu cewa, "Amin" In Kaka ta yi ma Salma addu,a, ga shi Kaka ba ta raina abin fada, kow脿 ya zo a zuri'arta sai ta nuna. "'Kun ga abin da matar Shatima karamar ta kawo min" Dole Aliya daga sallah ta sulale ta gudu; Salma ko da yake kanta a waye yake, tuni ta shige cikin sa"anninta suna ta hotuna. Karyar kowa dai ta turanci ne, kuma ita ma yanzun ta kware gurin fesoshi. Hakan ya sa wasu daga cikin dangin Shatima sha'awarta. Sai da aka dau amare sannan Salma ta je ta sallami Kaka, ta samu Hajiya a gabanta zaune. Ta durkusa tana gaida Hajiya don ba ta ga zuwanta ba Dole Hajiya ta amsa, ta kuma yi mata godiya don Kakar ta riga ta fada matA kuma ta bukaci Hajiyar da ta yi mata godiya a gurin Salma. Kaka ta ce, "Allah ya yi miki albarka, ki gaida manyan naki, ki wa 'yar uwar taki ban gajiya Da yake Yaya Hadiza tazo Tana fitowa don ba nisa ta hau hanya. Wata mota tana ta yi mata horn t脿 yi banza, Kila ma irin mazan nan ne sun ga duhun dare. Motar ta yi gaba kadan ta tsaya, Salma ta fusata, ta ce, kila zan ji me motar nan. Ta zo za ta wuce, ta jikin motar ta ji an ce, "Yammata ji mana". Ba ta tanka ba, amma muryar da ta ji ya sa gabanta faduwa, har ma ta waiwayo ta kalli motar,. Bata san motar ba, amma muryar irin ta Shatima ce. Ji tayi an kara cewa, "Don ana miki magana shine za ki share mutane?" Ta waiwaya da sauri, tare da fadin, "Kai ina da miji? Maganar ta makale ganin Shatima. Tayi muryar shagwaba, "Haba Yaya, ka ba ni tsoro dayawa Ya ce, "Wa ya ce ki fito titi? In wani ya taka ki kamar yadda na yi din nan fa?"Ta ce, "Ai na ga babu nisa ne Ya kama hannunta"Muje in kai ki gida禄. Baya ta shiga, sai ta ga ashe Munnir ke jan motar. Ta gaida shi, sannan suka sauke ta kofar gidansu. Ya miko mata leda, "Ga shi rabonki ne Ta amsa, ko ba ta buda ba ta san kaza ce, don taga suna ci suna hirar gidan biki. * Tana nuna wa Innarsu hotunan da suka dauka, Inna ta ce, "Na ga abubuwan da Hadia ta zo da su na rabo Salma ta ce, "Sun yi rabo sosai. To auran fa yara biyu, kuma kin san Babansu ya rasu, amma an yi musu komai. Gaskiya zuri'arsu suna da yawa, ga zumunci" Inna ta ce, "Gaskiya sun more, don duk zuri'ar da ke rike da zumunci ba ta tabewa" Salma bata bada wani labari da zata bata sunan mijinta ko na danginsa ba. Har Hajiya da su Yaya Hadiza suka dauko zancenta, sai ta nuna ai yanzun Hajiyar ta daina nuna mata kiyayya. Inna ta juya zancen da Salma ta kawo mata, ta ce, "Lokacin da na fita takaba ma Hadiza ta sai min turmin zani, sai su Babarku sun hado min zannuwa uku, har da hijabai daga kauye" Salma ta ce, "Ai kuwa an gode. Ni ma na so zuwa Ya Shatima ya hana, wai sai ka ce biki?" Inna ta ce,Gara da ya hana din, tunda lokacin duka kwananku nawa?" Ta ce,"Mun dan jima fa Inna"Ta ce, "Ai yanzu komai ya wuce" Washegari za su koma gida Yaya Hadiza tazo dan -su shawarta kan kudin Salma, ita Yaya Hadiza cewa ta yi,; a canza mata kujeru tunda guda uku ne sai a siyo mata saiti. Salma tace duk yadda aka tsara, amma wa zai Siya nawa? Hadiza ta Ce, "Gun Lami dillaliya aka sai naki,kuma za ta siye su sai a cika a sai wasu Salma ta ce,To motar da za ta kwaso wadancan fa?"Hadiza tace "Ai tana da masu mota, illa dai Ki kira mijinki ki tambaya, sai mu je gidan a zaba Suna tsaka da hira da Hajiyarshi akan abin da ya shafi haihuwar matanshi, da kuma zuwan azumi da sallah wanda ake kan shirinsu, sai ga kiran Salma ya shigo! Ya daga tare da sallama, ta amsa sannan ta gaida shi. Ya amsa tare da cewa, "Ya ya dai Salma?" Ta ce, "Da ma za mu je gidan wata mai saida kaya ne za mu duba kujera". "Ke da wa za ku?" Ta ce, "Yaya Hadiza" Yace "To kar a zauna anjima za mu tafi" Ta ce,Insha Allah Sun je sun zaba, kuma ta amince amma da yarjejeniyar za ta bi motar kaya don ta ga wadancan. Sun amshi lambar juna don mai kaya ba sanin gidan tayi ba. Karfe uku tana kwance a kan tabarma a tsakar dakin Inna, sai ta ji sallamar Yaya Auwal. Su biyu ne suka aje buhun shinkafa karamin da buhun gero, sai suga da kayan tea. Salma ta ce, "Daga ina?"Sallamar Shatima ya sa ta samu amsarta. Kan tabarmar da ta tashi daga kwance nan ya zauna kusa da Page 7 Ita. Ya rusuna yana gaida Inna, duk da cewa a zaune yake don girmamawa. Salma ta zuba idanu tana kallonshi, ya yi kyau cikin yadi mara nauyi mai ruwan madara. Hular kansa ta yi matukar dacewa da kayan. Ya kalle ta, ta lumshe ido, tare da fadin, "Barka da zuwa". Ya ce, "Yauwa. Na ga ko shiryawa ba ki yi ba?" Ta ce, "Wai har tafiyar ta tashi? Na zaci sai dare" Ya yi mata hararar wasa, tare da fadin, "Amma na ce miki ki shirya ba?" Ta mike, "Bari in yi wanka" Ya ce, "Wane wanka kuma? Tashi kawai mu tafi ki yi shi a gida in mun koma". Inna ta ce, "Gaskiya kam, domin ba zama zai yi yana jiranki ba". Salma ta tura baki don yin shagwaba ga Inna, tace, "Kuma hijabi kadai zan zira?" Inna ta ce, "Oho! In ma a haka za ki babu hijabin je ki" Shatima cikin murmushi ya ce, "Inna fada mata dai". Inna ta dubi Shatima tana 'yar dariya, tare da yin godiya da dawainiyar da ya kawo musu, Ya ce Haba Inna, a yi hakuri da shi, garin ne sai a hankali" Salma ta hada kaya tana tura baki, ga su da dan yawa saboda dinkunanta da ta amsa. Shatima ne ya kinkimar mata kayan. Ita kuma ta rataya hijabi a katada.Shatima ya ce, 鈥濨a ki fa san gatse ba fa ke? Ki saka hijabin mana .Salma ta yi mamakin ganin Aliya a cikin mota, ashe ya dauko ta. Salma ta yi ta maza ta dube ta, but ya zuba kayan Salma sannan ya shiga. Ita ma ta shiga baya suka nufi gidan su Nafisa. Suna isa Abin da ya bai wa Salma mamaki sal taga Aliya ta fita ta nufi cikin gidan su Nafisa tare da Shatima, ita ma saita Fito ta bIsu. A zuciyarta kuma tana tambayar me ya sa ba ta shiga nasu gidan ta gaida Innarta ba? Sun samu duk yan gidan a falo, Da alamu Nafisa tuni ta shirya don jiran zuwan Shatima. Aliya cikin kissa da irin salonta ta nufi Nafisa. Yar uwa ya ya dai?" Natisa ta yatsina, fuska, "Lafiya, ya ki ke?". *" Aliya ta ce, "Lafiya Ta rusuna tana gaida Mama,wadda Suke magana da Shatima. Salma ma ta rusuna tana gaida Maman. Hamida cikin fara'a ta dubi Salma, "Za ku tafi?" Salma tace Eh. Yauwa Hamida ina hotunanmu na wayarki?"Ta ce, "Bari in dauko in tura miki Aliya ta kalli Shatima, "Taso mu je Nafisa karmu yi tafiyar dare Tuni Salma ta fahimci Aliya tana fadin haka ne don taji Hamida za ta tura mata abu a cikin waya. Saita zauna tare da fadin, Dauko ki tura min, ni ban yi hotuna sosai da wayata ba, kin san ba ta da kyan hoto Ko da Aliya ta azalzala su tafi hakan bai saka Salma ta tashi ba, sai da Hamida ta gama tura mata sannan suka fito a tare zuwa gurin motar. Aliya ta kalli Salma wadda ke rike da jakar Nafisa ta taya Hamida dauka. Ta ce, *Ai na zaci ke ba yau ba Salma ta yi tamkar ba ta ji ta ba, suka yi sallama suka hau mota. Salma ta yi dan murmushi ganin Aliya an dawo bayan mota, Nafisa ta hakimce a gaba. Nan suka nufi Kaduna. Sun dawo da 'yan kwanaki aka soma azumi. Ranar farko dai Salma daure ta yi domin makara ta yi, washegari ta yi Kudirin tashi nan ma daure ta yi har da zuwa rana ta uku, a rana ta hudu Shatima a dakinta yake, ya zaci za ta tada shi kamar yanda sauran suke yi,amma sai shine ya tada ta. Ya ce, "'In don saboda ke ne makara za mu yi Ta ce,Ai ni ban taba yin sahur ba' Ya ce,Saboda me?"Ta ce, "Makara nake yi" Ya ce, "Shirme kenan, bacci ki ke kwanciya ki ta sharawa a wannan watan mai albarka?" Ta yi shiru, ya ce, "To daga yau 'na kashe baccin nan. A tashi a kai kuka gurin Ubangiji" Salma ta ce, "To zan tashi, amma sai ka taimaka gurin tashina Ya ce Shi kenan, zan dinga kiran wayarki, sai ki dinga barinta a bude Ran da ya koma gurin Aliya, sai da ta nuna rashin jin dadinta da tashin Salmar duk da bai tahimci ta damu din ba. Cewa ya yi ta miko mishi wayarsa a caji, sai tace wa zai kira? Ko mutan Saudi zai kira? Sai da ya soma kiran layin Salma din sannan ya ce,Salma zan tada daga barci Ta yi 'yar dariya, "Salmar yanzu don lalaci sai an tashe ta! Ya kalle ta da dukkan gaskiyarsa, " Salmar! Baki ganin yarinya ce, wai ashe duk azumin nan dore take yi, wai makara take Ta tabe baki daidai lokacin da yake sake kiranta, bayan kiran farko ya katse. Cikin barci ta ji " Karan wayar ta farka da sauri cikin mayen bacci tadaga wayar tana fadin, "Yaya na tassshhhi!' Ya ce, "Kin tashi ko dai na tashe ki?" Ta yi murmushi mai sauti, cikin amsar gyaranta ta ce, "Yaya to ka tashe ni' Ya ce, "To a yi maza kar a makara. Ya dubi Aliya wadda takaici ya cika ta, yana yar dariya ya ce, "Kin ji ta wai na tashe ta amma tana fadin ta tashi" Aliya tace "To wai ita bata sallar dare kenan?" Yace ai dole in matsa mata takeyi. Aliya tace "To kai ma kaci abincin kar kai kuma ka makara. Ta mika mishi kofin shayin da ta gama hadawa. Haka kuma a dakin Nafisa randa ya je sai da tayi Korafi da zai tashi Salma, wai ita bai taba tashinta ba in ba ya dakinta. Ya ce, "Kar wannan ya dame ki, ita ai yarinya ce ke,ki ke tashina wani lokacin ma fa Ta ce, "Ba wani, don dai ta san za ka tashe ta din ne shi ya sa take shantakewa Azumi ya soma tafiya, har lokacin Amna ba su dawo ba, a zatonshi sati biyu za su yi, "amma shiru! Yana dai jira ya ga ikon Allah. Hankulan mutane ya karkata kan sallah, Aliya ta matsu da son ta samu kudi domin ta lura neman suna sai da kudi, ga shi ba ta nemi komai ta rasa ba, amma ba ta da kudi a hannunta. Wata dabara ta fado mata, bari Shatima ya zo ta kallallame shi ko zai ba ta kwangilar siyan kayan jarirai don ta so a ce ita ce da ciki domin da tayi tatsa sosal. Suna kwance bayan idar da sallar asham wadda yake jansu a falon Aliya. Salma da Nafisa sun tafi lokacin, ta ce, "Wai masoyina sai yaushe za a sayi kayan jarrai? Ka san fa ana yin sallah za su haihu. Yanzun ya kamata kawai ka siya a wuce gurn in sallah tazo sai aji da hidimar sallah*. Ya kai hannu ya janyo ta zuwa jikinshi tare da fadin, "'Shawara mai kyau, amma kin san dole sai Amna ta dawo sannan mu je a siya. Ban ma san ko me da me za a siya ba . Ta tashi zaune, "Haba dai, kar ka fara da haka, ka zama namijin da kowane lokaci a gidansa shine mai tsarawa, kuma shine mai zartarwa. Ni na san duk abin Page 8 MUN TSAYA Wai masoyina sai yaushe za a sayi kayan jarrai? Ka san fa ana yin sallah za su haihu. Yanzun ya kamata kawai ka siya a wuce gurn in sallah tazo sai aji da hidimar sallah*. Ya kai hannu ya janyo ta zuwa jikinshi tare da fadin, "'Shawara mai kyau, amma kin san dole sai Amna ta dawo sannan mu je a siya. Ban ma san ko me da me za a siya ba . Ta tashi zaune, "Haba dai, kar ka fara da haka, ka zama namijin da kowane lokaci a gidansa shine mai tsarawa, kuma shine mai zartarwa. Ni na san duk abin ZAMU TASHI da ya kamata a saya game da jarrai da kuma maijego, don haka ka bar komai a hannuna Ya dago ya kalle ta Fuskarsa dauke da murmushi, ya ce, "Haka ne, amma bana son korafin Natisa. Bari in yi magana da ita, sai in kai ku ku zabo har da na Amna tunda an tabbatar mana cewa duk maza ne" Aliya ta zaro ido, "Da ma ita ma Amna namiji ne?"Ya ce,Eh" Ta hadiye wani wahalallen yawu sannan ta kirkiro murmushi, *Ka ce gidan namu duk sojoji ne ashe?"Ya kai hannu ya shafi cikinta, "Ke kuma sai ki kawo mana 'yar budurwa ko?" Ta saki dariyar yake, *Eh mana" A cikin ranta kuwa fadi ta ke, "Allah ba zai biya bakinka ba, ni ma namijin zan santalo, Kila yan biyu ma". Cikin wasa ya lakaci kumatunta tare da fadin, "Ga shi ma kinki ki yi cikin" Maganar ta sosa mata rai har ta kasa dannewa sai da ya gani a kan fuskarta. Ya ce Ki yi hakuri banyi da nufi ba. Ina yi miki wasa ne Ta dai cije suka canza hira. Washegari Shatima ya tunkari Nafisa da batun siyan kayan jarirai. Ya ce, "Ina son ki shirya mu je kasuwa ke da Aliya ku za6o kayan jarirai naki da na Amna, in kuma babu damuwa sai mu je ni da ita"Natisa ta fusata, "Nima fa na san hanyar nan ba sai an je min ba ko an raka ni"Ya ce, "To amma ai ke daya ga ciki, kuma ina ki ka sani a Kaduna ba sai ku je tare ba?" Nafisa ta ce, "Ni dai a ba ni kudin kawai Ya ce, "To na ji, yanzu nawa zan ba ki?" Ta Ce, "Abin da za ka bai wa Amna, ko don ita daban ce tunda su masu kudi ne?" Ya ce, "Au abin da ki ka tsiro da shi kenan? To bari in ta dawo na baku tare don bana son zargi Ta ce, "Na yarda Ana jibi sallah Shatima ya shigo da shanu gidan don bai san ko kaji nawa zai siya ba. Ana gobe sallah ya sa aka gyara shanu aka raba hudu, ya bai wa kowa nata, aka zuba na Amna a freezer. Nafisa ta yi waya aka zo mata da Hamida har ta zo mata da dinkunanta, don ta taya ta aiki. Ita ma Aliya 'yar wansu ce Amira tazo don ta taya ta aiki,. Haka kuma ita ma ta zo mata da Dinkunanta, Shatima da ma shine ya kai musu kuma ya biya kamar yanda ya biya na Salma. Salma sanye cikin riga da wando cikin irin kayan da ta siya gurin wata makociyarsu da ta kawo musu tallah. Sauran ba su siya ba, amma Salma ta zazza6a ta biya abinta. Tana ta aikin namanta, matsalarta cincin don gaskiya ba ta iya ba. Ga dai kayan fulawa ya kawo musu kamar yanda Aliya da Nafisa suka rubuta mishi, amma ba ta san yanda za ta sarrafa shi ba. Ta san kuma in har ta tambayi Aliya baza ta fada mata gaskiya ba, Kila ma ta sa tayi Bata. Bayan ta gama suyan naman ta nufi gurin Nafisa domin ta jiyo tashin Kamshin cincin. Hamida ta samu a kicin din, ta ce, "Ke ce ma ki ke aikin?" Nice sannu da zuwa Salma tace Ina Anty?" Hamida tace "Tana cikin dakin Yaya ta kulle kanta, wai ba ta son Kamshin cincin din nan' Salma tace, "To fa! Ga shi nazi ta koya min yanda zan kwaba cincin da sauransu?* Hamida tace, "Wai! Gaskiya da kyar in za tayi, don wannan ma ni na kwaba" Salma tace, "To don Allah dan kwaba min". Hamida tace, "Da kamar wuya in miki, don aiki ya yi mini yawa. Sai dai ga wannan littafin na baki aronsa, zai taimaka miki gurin yin duk, irin cincin din da kike so Salma ta amsa tare da godiya, sannan ta nufi sasanta. Ranar idi da safe Salma ta dora abincinta na sallah da wuri, shinkafa fara ta dafa ta yi miyarta tun jiya. Tana wanka tana ta sauri don kawarta Salma Dankasa zata zo mata yau. Shatima ya gama shirinsa tsaf don dakin Nafisa yake. Ya kalli Nafisar tana zaune turus kan kujera tana cin nama, yace Wai ba zaki je sallar idi din bane?" Ta ce "Ba zan je ba Aliya ma ta ce ba za ta je ba aiki, Salma kuwa yana shiga ya ce mata, "Zo mu je masallaci" Babu damar musu tace to Hijabi ta zura suka nufi motarsa, wai kuma halin kishi sai hakan ya bai wa Aliya haushi. Sun yo sallah cikin murna da farin ciki, suka nufo gida. A hanya ne take fada mishi zuwan Salma Kawarta. Ta ce, "In da hali ya sai mata lemon roba. Ya ce jiya ya siyo *lemuka, ya manta suna cikin but Din wannan motar hard脿 na kwali. In sun je gida zai ciro musu kowaccensu ta dauka. Ta ce, "To mun gode". Salma ta Ki yin kwalliya tana jiran sai Salma Dankasa ta zo ta yi mata kwalliya, don ta iya sosai. Sha biyu da mintuna maigadi ya z0 kofar Salma ya ce tana da bakuwa mai suna Salma. Tare da maigadin suka nufi gate din, cikin doki Salma da Salma suka rungume juna. Cikin murna suka shiga falon, Salma tace, "Ina su Anty in gaida su?" Salma ta ce," "Suna sashensu, kun gaisa kafin ki wuce' Ta shiga jera mata abinci da na sha, nama da kayan cincin. Sai da suka ci suka yi dam, sannan suka yi gaban madubi don a yi wa Salma kwalliya. Tun kafin su gama Salma ta ga irin kyan da ta Yi haka kuma Salma Dankasa take ta koda kwalliyar. Salma tace, "Da bana kwalliya, amma yanzu zan koya ina yi wa kaina" Salma da aka daura mata dankwali, ita da kanta take fadin ta hadu karshe. Hotuna suka yi ta dauka kala-kala. Suna zama za su soma hira sai wayar Salma ta yi ruri. Da sauri ta daga ganin sunan Yaya a fuskar wayar. Ta ce, "Yaya?" Ya ce, "Ki z0 ku gaisa da baki". Tace.' "A gurin Anty Nafisa?" Ya ce, "Eh'Ta ce, "To ga ni nan" Ta kalli Salma Dankasa, "Zo mu je" Ta ce, "Ina?" Salma ta ce, "Ciki gurin su Anty sai ku gaisa da Yayana Salma Dankasa ta yafa mayafinta sannan suka fita. Tun kafin su shiga suka jiyo hayaniyar mutane a falon Nafisa, a ran Salma ta ce, to fa, ga shi ban ko yafa mayafi ba. Suka shiga da sallama, Shatima ya canza kaya daga yadin da ya saka suka je idi zuwa shadda mai ruwan hoda mai duhu. Tana da matukar tsada, ya yi matukar kyau, kanshi da aski yayi masa kyau. Salma a ranta ta ce su Yaya har da canza kaya? Ta shiga gurin su ta tsuguna tana gaida su. Shatima ya cire gilashin idonsa yana kallon Salma, ya zaci ko gilashin idanunsa ne ya sa yake kallon salma ta dan kara girma, kuma ta yi kyau sosai. Sai kurum ya ji kishinta musamman da ba ta yafa mayafi ba. Salma Dankasa ta gaida su. Ya dubi Salma, "Wannan ce bakuwar?" Salma ta ce, "Sunanta Salma Sadik Dankasa" Ta kalli Salma, "Ga yayana" Salma ta sake dubanshi tare da sake fadin, "Sannu Yaya Ya amsa tare da cewa, "Kullum ina jin labarinki, yau mun hadu. Sannunki da zuwa" Salma ta sake duban abokan su shida, da alama akwai wadanda ba musulmi ba. Ta sake yi musu sannu. Ta dubi gurin da Nafisa,ta ke zaune, ta ci kwalliya Page 9 Ya dubi Salma, "Wannan ce bakuwar?" Salma ta ce, "Sunanta Salma Sadik Dankasa" Ta kalli Salma, "Ga yayana" Salma ta sake dubanshi tare da sake fadin, "Sannu Yaya"Ya amsa tare da cewa, "Kullum ina jin labarinki, yau mun hadu. Sannunki da zuwa" Salma ta sake duban abokan su shida, da alama akwai wadanda ba musulmi ba. Ta sake yi musu sannu. Ta dubi gurin da Nafisa,ta ke zaune, ta ci kwalliya shadda mai ruwan jibi, ta yafa mayafinta kalar kayan. Ta kama hannun Salma ta ce, "Zo ku gaisa da Antyna Nafisa cikin jan aji ta gaisa da Salma, Salma ta kalli Hamida wadda take kwashe kayan da su abokan na Shatima suka ci abinci, ta ce, "Hamida ya sallah? Kin yi kyau fa". Hamida cikin "yar dariya ta ce, "Na gode. Kema kin yi kyau Salma, dube ki kamar amarya". Suka saki dariya a tare. Ta dafa kafadar Salma Dankasa ta ce, "Ga kawata ita- ma Salma sunanta Hamida tace, "Sannunki fa, ni sunana Hamida" Salma Dankasa ta ce, "Sannu, ya sallah?" Salma ta ce,Lafiya Shatima wanda idanunsa suke kansu suna burge shi, yanda suka yi gaisuwar. Salma ta katse shi da fadin, "Yaya zan iya tafiya?"Ya c猫, "Eh, ku je abinku, da ma gaisuwa ce kawai"Ta dube su, "Sai anjima, mun gode". Wani daga ciki ya mika mata sabbin *yan dari biyu da dan yawa, "Ga goron sallarmu". Ta kalli Shatima tana fadin, "Ku barshi kawai, mun gode" Wani daya cikin abokan yana fadin, "Kina dai neman izimi n茅 a gurinsa kafin ki karba Shatima ya yi dan murmushi, "Ki karba, ai goron saliah ne* Da hanna biyu Salma ta amshi kudin tare da rusunawa tqce "An gode" Ta nufi gurin Shatima ta nuna masa tare da cewa,Ka gani?' Ya ce,Na gani, kin god'e" Ta mika ma Nafisa "Anty mu raba Harara ta sakar ma Salma domin wannan kinibibin ya ishe ta, duk ta dauke hankalin Shatima ta kosa ta tita. Shatima yace 芦Wannan naiki ne, ita ma sun bata" Salma ta dafa kawarta tare da fadin, "Mu je"Bayan ta dube su ta ce, "Ku gaida gida" Suna fita Salma Dankasa ta dubi Salma ta ce, "Kawas wannan yayan naki ya hadu fa" Kafin ta yi magana sai ta hango Aliya ta fito sanye da farin leshi doguwar riga, ta yafa mayafi shima fari. Salma ta ce, "Sannu anty, ya sallah?" Ta dube su a yatsine, ta ce, "Lafiya" Salma Dankasa ta ce, "Wannan fa?" "Duk matansa ne!" Dankasa ta zaro ido tare da fadin, "Salma Bash da gaske ki ke yi? Har su nawa ne?" Salma ta nuna dakin Amna, "Ga dakin wata can ma ta tafi ummara Salmar ta kai dubanta dakin sannan ta ce, "Tabdi, kuma yaranshi nawa?" Salma ta Ce, "Ai auran bai shekara ba, duk kuma rana daya ya aure su Salma ta zaro ido tare da fadin, "Rana daya?" Salma ta sa dariya, "Kar ki sa ya jiyo mu, ki yi magana a hankali" Ta ci gaba da fadin, "Rana daya wallahi" Salma tace "Tabdi, amma kun sha bidiri.wace.ce uwargida?" Salma ta ce, 'Wannan da ta wuce". Dankasa ta ce, 'Tabdi,, ni mamaki ma naji, gashi gaye da shi. Ko da yake ni kaina zan yarda, in shiga jerin matansa da zai so ni Salma ta dube ta da sauri, "Da wasa ki ke?" Dankasa ta ce; "Za ki min hanya?" Salma ta ce, "Ba ruwana"鈩� Dankasa ta kai mata duka, tace Kina tsoron matansa ko? Don naga ba sa wani yinki" Ta yi dariya, *Ni dai ina yinsu". Da suka koma daki suka ci gaba da hira: Salma ta kula Dankasa ta fi son a yi hirar Shatima, in kuma taci gaba da amsa: tambayoyinta akwai yiwuwar ta gane,ita ma matarsa ce don haka ta ce, "Ashe fasalin gininku iri daya ne da na matansa, wai ni uwa daya. uba dayas ku ke ne?" Salma a ce, "Nice auta, kuma nan ya sa ni nake kula da nan din in zai yi mata ta hudu sai in koma gurin daya daga.cikin matan"Dankasa tace Iyayenku na raye? Wallahi ni nice ba zan zauna ba, sam-sam. Ina son zama da mamana Salma ta ce, "Ni mun shaku da shine sosai, ba kin ga na nuna miki Mustapha da Badi'atu ba? Su ke binshi, amma da tazara tsakaninshi da Mustapha Salma ta ce, "Mu canza labari, kin damu da batunsa"Ta kurbi lemun da ta dauka "Saura kwana nawa mu koma makaranta?Dankasa tace "Saura kwana tara Ta ci gaba da fadin, "Ni ya min ne shi ya sa ko a dakin ina ta kallonsa, shi kuma sai ke yake kallo. Da muka shiga fa har da cire gilashin idonsa Salma ta tashi ta nufi cikin daki, don ba ta son zancen ya ci gaba. Turaruka da kayan kwalliya ta dibar mata, sannan ta dauko mata mayafi daya wanda ba ta taba sawa ba. Ta hada mata kaya masu yawa, ta aje a kan gado. Tana fitowa Salma ta ce, "Ni zan tafi Salma ta ce, "Ba kin ce sai kin yi la 'asar ba?" Dankasa ta ce,Na fasa Salma ta ce, "Ba ki isa ki tafi ba". Da Kyar ta kai uku. Ta kira Hajiyarsu wai direbansu ya zo ya dauke ta. Hajiyar ta ce ta aike shi Marafa zai kai abincin sallah gidan kakarsu. Salma tace, "To bari ta taho. Salma ta ba ta kayan da ta ari style, sannan ta ba ta wanda ta yi niyya, sannan ta ba ta dubu biyu acikin dubu biyar din da abokan Shatima suka ba ta. Ta ce, "Gaskiya kin ba ni abubuwa da yawa, nagode sosai. Yanzun sai ki raka ni titi" Salma ta ce, "Wai bari dai in kira Yaya ko zai bar ni"Ta ce, "Ai ko ba ki isa ki bar ni a bakin ni daya ba"Salma ta ce, "Ba za ki gane ba ne". ta daga wayarta ta kira shi. Ya daya, ta sa a handsfree don Salma ta ji, tace "Yaya Kawala zata tafi" Ya ce, "To mun gode, ki ba ta dubu daya zan ba ki"Ta ce, "To Yaya, daman ba ta san hanyan titi ba ne, shi ne zan raka ta" Ya ce,A'a, me na ce miki?" Ta ce,Please Yaya, ka ga a motar gidansu aka kawo ta, kuma. Kashe wayarsa ya yi.Ta kalle ta, "Kin gani ko kawata?' Salma ta ce, "Zo mu je har gabansa Ta ce, "Kai! Ina tsoro Salma ta ce, "Ke dai zo mu je" Sun fito su ma za su fita, Shatima ya tsaya suka isa gurin motar. Kafin Salma ta yi magana ya ceKi koma, ke kuma titi ne ba ki sani ba?" Dan Kasa ta ce, "Eh" Ya ce, "Bari mu sauke ki" Ta ce,To" Salma ta ce "To sai mun yi waya kawata". Shatima ya ce,Ina ne unguwarku?" Ta ce, "N.D.C Ya ce, '"To bari mu sauke ki a kan layinku" Tana idar da sallar isha ta shiga hada kayanta, in ta tuno gobe za su je Zaria farin ciki a gurnta kamar me, hatta kayan da za ta sa tuni ta aje su. Takirga kudinta dubu sha biyu da 'yan canji don ba makaranta, kuma wanna lokacin naman dubun take saya, saboda azumi. Ta yi komai jiran zuwan washegarin take yi. Page 10 Tana wanka ta fito don ta yi shirin bacci. Kan gado tasamu Shatima a kishingide. Tayi mamakin ganinshi, saboda bai cika zuwa ba, sai in zai saka kaya. Ta nufi gurin da ta aje kayan baccin ta saka, sannan ta dube shi, "Sannu da shigowa Ya ce, "Ke ma sannu da wanka Ta yi yar dariya, sannan ta fita zuwa kicin. Yaga tana ta jero masa tukwane dauke da nama. Ta ce,Kalli kason da na yi Ya ce,Kason me?" Ta ce,Nama mana, ga naka, ga nawa, ga na su Hajiyarka, ga na kaka, ga na Innarmu Ya yi yar dariya, "Da ma haka ake yi?" Ta ce,To da mu kadai za mu ci?" - Ya ce, "To yanaga na Inna,ba shi da yawa. Kara musu da nawa"Ta ce, "Ai ba su da yawa Ya sauka ya dauki tukunyar ya zuba mata kusan rabin nashi. Ta rike, "Barshi hakaYa ce, "Da kin bar su Hajiya, don nama yana can kamar ya yi magana a gidansu 鈥� Ta ce,Ai namu daban, tana son ta ga na gidankaYa ce, "Salma!"Ta dago ta dube shi, ya ce,Kina da manyance ko da yake na ga kin girma. Maida naman kizo *Sai kawai ta ji gabanta ya fadi. ni Tana dawowa sai ya janyo ta zuwa, jikinsa. Abubuwan da yake mata ne suka tsorata ta. Ta ce,Yaya don Allah ka bari"Ya ce, "Salma yau zan amshi hakKina matsayin mijinki, domin naga kin soma girma Ta ce,Na shiga uku Yaya, ba zan iya ba Ya ce, "Zan koya miki, kar ki damu' Yana dora ta kan gado ta rarrafa zuwa karshen gadon ta makure. Ya cire kayan sannan ya dube ta. Daga shi sai gajeran wando, ta boye fuskarta a cinya,tana fadin, "Yaya don Allah ka sa kayanka. Yaya na shiga ukuna Yana janyo ta sai suka hau kokawa. Sai kyarma take tana kuka. Ya ji haushi har ma komai ya fice masa a rai, ya hankade ta, sannan ya tashi ya fita zuwa falo bayan ya saka jallabiya. Ya kwanta kan kujera cikin bakin ciki. Tun kusan kwana uku yake a matse, Nafisa ta Yi nauyi dole ya tausaya mata, Aliya kuma tana al'ada. Ya kwana da takaici, ita ma dai Salma ba ta runtsa ba,ga shi tana son ta yi masa abin da yake so, amma ta kasa don tsoro Yana yin sallar asubahi ya nufi dakin Amna, ya bude ya shiga. Gadonta ya hau ya kwanta cike da kewarta, ya dauki filo ya rungume. Bacci ya dauke shi, karar wayarshi ce ya tashe shi, ya mike zaune. Amna Ce, ya daga cikin jin dadi yana fadin, "Zuma ta ina cike da kewarki, da mafarkinki"Ta ce, "Amma ga shi sai ni na kira ka, tun ranar jajibiri da ka kira ni?" Ya ce, "Yanzun haka ina Dakinki, ina kwance kan gadonki rungume da filonki ke da yarona kawai nike son jin duminku' 'Ta ce, "To yau zamu taso" ."Ki ce inzo Kano in jira ki?'A'a, sai na huta "To yau za mu je Zaria ranar da za mu dawo sai in zo mu taho' Tace Haka ya yi". A nan dakin ya yi wanka ya shirya tsaf? Lokacin da ya koma dakin Salma ta kammala abin kari don haka yana zama ta fito daga kicin ta aje a gabansa,tare da yi masa zannu. Bai ko kalle ta ba bare ya amsa. Tana kallo ya dauki wayarsa ya kira Aliya ya ce ta kawo masa abin kari dakin Salma. Salma" ta soma sabon kuka tare da fadin, "Yanzu Yaya ba za ka yi min hakuri ba?" Ya daka' mata tsawa, Tashi a nan!" Ta tsora ta sosai cikin hanzari ta dauki tire din kayan shayin ta maida kicin. Ta zo da gudu ta shige daki, sannan ta banko kofa. Tana jin shigowar Aliya saita daga labulen window tana kallonsu: Ta hada shayi ta mika masa, ta saki labulan ta koma kan gado ta kwanta tana kuka. Tsaf ta gama shirin zuwa Zaria tana jiransu. Nafisa da Aliya sun shirya tsaf, Salma ta kulle namanta da ta kasa da cincin. Shatima ya shigo zai dauki wayarsa, ya ga Salma ta fito da kayan tafiya. Ya dubeta cikin tsawa, "Ko kofar gida na ji labarin kin fito sai na yi mummunan sa6a miki Ta ce, "Yaya don Allah, to ka z0 yanzu na yarda ko zan mutu, Allah zan yarda kada ku bar ni, ina son in je Zaria" Ya ce, "Ki bar abinki bana so, na tsani duk wani abu da ya fito daga gare ki" Kalaman Shatima sun yi tsauri a gurin Salma Ba ta kara magana ba, ta dauki kayan sawarta ta maida ciki. Ta dauko kudin jiya sababbi ta Kirga dubu biyu ta Kulle a leda ta sa a cikin Kullin Kaka. Ta sa dubu biyu ana Innarsu, sannan ta dauka ta nufi gurin Nafisa. Ta samu suna ta saka kaya a mota, ta kira Hamida ta ce "Don Allah ki ba ni dama in ba ki sako". Hamida ta ce, "Ba za ki ba?" Hawaye suka soma sulmiyo mata, ta ce, "Ya ce ba zan je ba. Don Allah ki ba Anty Badi atu wannan daurin kayan za mu yi waya. Wannan kuma ki ba Hajiya na san can za ku fara zuwa". Hamida ta amsa tare da cewa, "Insha Allah zan ba su. Ki yi hakuri ki daina kuka' Ta ce, "Na gode". Ta juya. Aliya ma ta fito da kayanta, ta cema Salma, "Ke ba ya ce ban da ke ba?" Salma ba ta tanka ba ta wuce, sai ta ji Aliya ta saki dariya kyalkyal. Ba ta waiwaya ba ta shige daki ta banko kofar. Ta hau gado ta kwanta, sannan ta kira Badi'atu, ta ce, "Ga sako nan ta taimaka mata da shi zata amsa a gurin Hamida. Badi atu ta ce, "Au ba za ki zo ba!" Ta ce, "Eh na yi laifi ne, ya ce ba zan zo ba" Badi'atu ta ce, "Mayafin da na miki message jiya?"Salma ta ce, "Ban gani ba wallahi, me ki kace?" Ta ce,, "Pink din gyalanki za ki ara min". Tace '"Au, bari in kai ma Hamida ta kawo miki, amma ba'aro-ba, na ba ki duka" Badi'atu ta yi godiya, ta je ta ba Hamida mayafin.Salma tana jin fitarsu ta koma ta kwanta cike da da ta sani. Ta lumshe ido tana tuno irin rokon da yake mata a kan ta ba shi hakkinsa, amma ta kasa. Dole yayi fushi da ita, fatanta Allah ya huci zuciyarsa kafin su dawo. Ita daya a gidan ta kwana tsoro ya ishe taba ta yi baccin kirki ba. Washegari ta ce, bari ta je gidan makociyarsu mai gwanjo inda shi ta siya, ko ta dan yi tattaki. Tana zuwa maigadi ya ce, "Yata ki koma ciki;, maigida ya ce kar a barki ki fita, kuma kar a bar kowa ya shiga har su dawo Salma ta ce, "Tofa!" Ta juya ta koma ciki, ita ba talabijin ba bare ta kunna ta kalla. Kwana hudu suka yi cif sannan suka dawo,Salma ta leka ta windo ta ga Mustapha ne ya kawo su da motar Shatima, sannan ta ga ya dauki motar Amna ya fita. Ba ta kara bi ta kansu ba ta koma ciki. Amna da Shatima sun yi matukar murna da ganin juna. Ya dauko ta suka nufo gida. Ranar gurinta Page 11 Ta juya ta koma ciki, ita ba talabijin ba bare ta kunna ta kalla. Kwana hudu suka yi cif sannan suka dawo, Salma ta leka ta windo ta ga Mustapha ne ya kawo su da motar Shatima, sannan ta ga ya dauki motar Amna ya fita. Ba ta kara bi ta kansu ba ta koma ciki. Amna da Shatima sun yi matukar murna da ganin juna. Ya dauko ta suka nufo gida. Ranar gurinta ya' kwana suka sha soyayyarsu. Tsaraba ta yo masa masu yawa, kayan sawa, agogo da sauransu. Tana sonshi da kananan kaya, kuma su ta kwaso masa. Ya ce,Da na sani na ba ki kudin kayan baby kin sayo a can Ta ce,Momy ta ce, sai an je Dubai don mun duba babu wasu sabon yayi a can Shatima ya ce,Amma online za ku siya ko?" Ta ce, "A'a su Momy za su je karshen watan nan"Ya ce, "Nawa zan bada?"Tace Ka bada yanda ka ke da shi, Dady ya cika".Ya ce, "Hamsin ya yi?" Ta dube shi tare da zaro idanu, "Hamsin kuma?Ko kudin durowa ba zai kai ba庐 ' Ya ce, "To ni dai kin san Allah a cikin account dina dubu dari biyu ne da arba' in. yanzun sai dai in baku dari-dari ke da Nafisa. Can kudin makarantar Salma in脿 zaton za su koma Monday din nan Amna ta ce,Ka bada haka din Ya kira Natisa, ga ta ga Amna, ya ce, zai ba su dubu dari-dari kudin siyayyar haihuwa. Nafisa ta ce, to sun gode. Bayan fitarta Amna ta ce, "Kawai ka yi transfer zuwa account din Momy, don ba zan iya ce mata komai ba. Kudin durowar baby din ma ai ya fi darin"Ya ce, "To ni kam karfina kenan' Ta ce,Ai ita ma jikanta ne sai ta cika Ya yi murmushi, tare da fadin, "Haka ne Salma tana cikin damuwa, Shatima ba ya zuwa duba ta da safe kamar yanda ya saba. Ta kan leka ta window ta ganshi yana shiga dakunan sauran. Ta yi kuka ta gaji, domin ta san karatunta ya zama labari. Kuma ko ranar girkinta da wuya ya shigo dakinta. Ya daina ba ta kudin nama, komai dai ya tsaya mata cak!A lissafinta yau litinin, kuma yau za su koma makaranta, ta ce ba za ta shirya ba, sai wata zuciyar ta ba ta shawarar cewa, ta shirya ta ga me zai faru? Tsaf Ta yi cikin kayan makaranta, amma ta kasa kari. Ta je window ta tsaya tana leken fitowarsa. Tana kallo ya shiga gurin Aliya da Amna, don akin Nafisa ya _kwana. Tana ganin ya yi gurin motarsa, Nafisar ta raka shi, ita ma ta fito ta gaida Nafisa. Da kyar ta amsa sannan ta nufi motar, ya riga ya shiga ya tada, har yana yin baya. Ta dan bubbuga gilashin. Yanda ya waiwaya cikin harara ta san ya ganta tunda ta zo gurin.Ya waiwaya ya kalli Nafisa, ta shige dakinta sannan ya sauke gilashin. Da sauri ya katse ta daga gaisuwar da ta soma yi cewa,Yaya ina. Ya cE "Adana gaisuwarki bana bukata" Ya sa hannu a gaban aljihunshi ya ciro dari biyar ya jeho mata, "Ga shi ki hau mashin, ba za ki Kara shigar min mota ba Ta duka ta dauka, sannan ta dago ta kalli fuskarshi, a tamke bai ko kalli inda take ba ya zuge gilashi. Salma ta juya fuskarta fal damuwa, don sun yi kadan ta sani ba dakatar da karatunta ba sai dai tana jin ya rage ma karatun nata karsashi A makaranta babu wanda bai gane tana cikin damuwa ba, Salma Dankasa ta matsa da son jin damuwar aminiyar tata, sai ta ce mata ba ta jin dasi ne kawai. Ko da ake musu karatu tana dai sauraro, amma ba ta fahimta. Salma Dankasa ta ce, ta raka ta asibitim cikin makaranta. Salma ta ce, a'a ba za ta je ba, tana da magunguna a gida. Ranar ita ce da miji, ga shi kuma bai ba ta kudin cefane ba, don haka sai ta dumama sauran miyarta ta dafa farar shinkafa. Karfe shida da rabi na yamma tana wanka sai ta ji motsin shigowa da kaya. Ta san Shatima ne, amma ba ta san kowane irin kaya ba ne. da ta fito shi ta gani tare da wani suna kokarin shiga da katifa cikin daya daga cikin dakuna biyun da babu komai. Ya dube ta, "Zo ki kwashe tarkacen da ke cikin dakin nan" Da sauri ta shiga, babu wani tarkace sai *yan kayan da ba ta fara amfani da su ba. Ta maida su a durowar kicin. Dakin babu datti don kullum sai ta share shi ta goge ko da babu komai. Ya sa katifa da filo guda biyu. Kafet din tsakar daki duk a Kasa ita, dai tana zaune tana kallonshi, da ya gama kuma suka fita. Ta Ieka dakin, har zanin gado ya saka. Bayan is'ha'I taji shigowarshi, ta fito sai ta ganshi da talatijin, da tasoshi ana canzawa. Sai tara da rabi ta ji fitarsu tare, taje kicin ta hada mishi abinci. Tana fiowa yana shigowa, don haka yana shiga dakin i'ta ma tana shigowa Tun kafin ta yi taku na uku a dakin ya katse mata hanzari da cewa, "Ko ma da shi, na koshi" Washegari ma da safe bai dubi abin karinta ba, ya aje mata dubu daya wai na cefane da kuma na makaranta. Salma ta ce, "Na gode Bai tanka ba ya fice. Ta shirya ta nufi makaranta. Duk satin ba ta da sukuni, babu walwala bata damu da kudin da ya rage mata ba. Damuwarta ya yafe mata su koma Kamar da. Sai dai yiwuwar hakan da kyar ne, domin yanda Shatima ke mu'amalantarta a yanzu tamkar bai taba saninta ba, ko kuma babu wani sabo a tsakaninsu. Duk ranar da yake dakinta ba ya zama a falonta sam in ya dawo ma ba zai shigowa sai bayan isha, kuma abincinta tuni ya daina ci, ya ma fada mata cewa ta daina zuba mishi. Tana kallo tsakanin Aliya ko Nafisa duk wadda ya ga damar cin abincinta sai ya sa ta kawo masa har dakin. Haka kuma da safe yana da "yar karamar hiter da kayan tea sai ya hada abinshi, in kuma yana son dankali ko wani abu haka, sai ya sa matansa su kawo masa. Tun Salma tana kuka har ta dake ta saba da sabuwar rayuwar da ya tsirar musu ita da shi. Ba za ta tuna dariyarshi da ta gani ta karshe ba. Ba ta taba tsammanin haka yake da daukewa da dakewa ba sai da matsalar nan ta shigo. Yanzu shakkarsa ma take yi, da wani mugun tsoronsa da ya darsu a zuciyarta. Wataranar asabar tana shanya kayanta tana sauri taje ta yi assingment sai ta ga shigowar motoci guda biyu. Ko ba a fada ba ta san bakin Amna ne, dan su ke zuwa akai-akai, kayan haihuwa ta ga ana shiga dasu, tun daga kan gadon jarirai zuwa durowa da sauran kaya. Salma ta yi murmushi har zuciyarta ta yi doki zasu sami jarirai a gidan. A fili ta ce, "Ashe zamu sha suna?" Kayan da ke cikin akin baki aka fito da su zuwa barandarta, aka jera kayan jaririn a ciki komai blue mai haske. Amna ta kalli dakin ji take yi tamkar ta haihu yanzu. Ta sa hannu tana shafa cikin ranta fal farin ciki Haka da Shatima ya shigo ba a dakin yake ba, dakin Nafisa yake amma sai ya nufi dakin saboda ganin gadon Amna a waje. Ya shiga, tana zaune a kan kujera a falo tana kallon wani shiri da take bi a tashar Africa. Ta dube shi tare da amsa sallamarshi, ya isa gurinta da tambaya, "Shin me ya faru a dakin can na ga kaya a waje?" Ta ce Kama ni in mike" Ya kamata tare da fadin, "Sannu". Suna shiga dakin, Shatima ya rungume Amna ta baya yana shafa cikinta, ya ce, "Har na kosa baby ya zo gaskiya dakin nan ya yi kyau, sai na ji kamar ya zo yanzun" Amna ta shafa hannuwansa da ke kan cikinta, taCe, "Wallahi honey ni ma haka na ji. Allah dai ya saukeni lafiya Ya ce,Ameen-ameen kullum addu'ata kenan "To kin ki mu je a yi miki awo Ta ce,Ni fa ba a nan zan haihu ba, Dad ya ce England za mu je a can aka haife ni" Shattima ya saki amna cikin sauri ranshi yai mugun baci yace, 12 Shatima ya saki Amna cikin sauri, ranshi ya mugun baci ya ce, "Gaskiya wannan karon ba zan amince da abin da ki ka zo da shi ba, shi ya sa ki kaqi in kai ki kowane asibiti?" Ta ce, "Wai me ya sa ka ke son mu yi rigima ne? Duk abin da iyayena suke yi saboda lafiyata ina tsammanin jin dacinka ne, da kuma hutar da kai a kan wasu abubuwan?"Shatima ya ce, "A bar ni mana in yi daidai Karfina. Ni fa sai ina ganin kamar ana nuna ban isa ba,ko kuma na kasa Ta ce, "Ok, in lokacin ya zo sai ka fada wa Dad din ba zan je ba". 鈥� Ta juya ta fita cikin fushi. Ya yi shiru a cikin dakin, wata zuciyar ta ce masa, kada ka bi da fushi, ka bi komai a sannu. Ya fito shi ma, ba ta falon kai tsaye dakinta ya nufa ya same ta kwance a kan gado. Ya zauna ya dafa ta, "Kin yi fushi kenan?" Ba tare da ta dago ba ta ce, "Ta ya ya ba zan yi fushi ba, kowane lokaci sai ka dinga nuna bacin ranka in an ba ni kulawa. Har ka sa na soma tunani, na saka shakka a cikin son da ka ce kana min Ya tashi ya dago ta zaune, sannan ya rungumeta, "Ki yi hakuri matata. Tsananin sonki ne ya sa bana son ki yi nisa da ni" Ta sa hannuwanta ta ta dago fuskarshi, "In haka ne ba sai mu tafi tare ba?" Ya kalli cikin idonta, "Akina fa?" Ta ce, "Shine kadai matsala"Yace "Ina son mu je asibiti a duba ki, don a tabbatar min cikin lafiya Ta ce, "Yana lafiya fa, ko a saudi da muka je sun auna ni sosai" Ya ce, "To ,,,,,,,,,fa?" Ta ce,Cikin watan da za mu shiga ne, biyar ga wata"Ya ce,Yaushe ne tafiyar?" Ta ce, "A na kan shirin tafiya kenan, zai yiwu ma cikin satin nan don na ce ma su Dad bana son in fara labour kafin a kai ni"Ya ce, "Aiki ki ke so a yi miki?" "'Ni na fi son aiki in samu baby ba tare da na wahala ba Shatima ya ce, "To Allah sauke ki lafiya Ta ce, "Amin Ya ce, "To ya za a yi da kayan gadon can na waje?"Ta ce, "Ni na san ya za a yi da shine? In akwai gurin da za ka ajiye ta ka ajiye kawai" Ya ce, "In ba dakin Salma zan kai ba, ba ni da gurin da zan aje" Ta ce, "Ni fa ba abin da zan yi da shi" Salma tana juye shinkafa a kula don ranar mai da yaji take son ci, sai ta ga maigadi da Shatima suna shigo da kayan gado. Ba ta ce komai ba, suka shiga da su dayan dakin suka jujjingine har da sif. Ta yi musu sannu, Baba maigadi ne kawai ya amsa. Yana fita Shatima ya kalle ta, "Kayan Amna ne kada ki Bannata musu" Salma ba ta iya amsa masa ba, domin dai ta san duk cikinsu babu wacce za ta yarda a kai mata ajiyar kayan kishiya. Wata zuciyar ta ce Ki ka sani ko don ba ki da kaya a dakin ne, da kina da shi ba zai zo ya cire naki ya sa ba Sai ta amince da hakan, kuma ta ji ta sauke haushin da ta ji. Wannan shine ya sa kullum Salma take da kyakkyawar zuciya, don tana da kyautata wa kowa zato. Duk da Shatima ya yi iya kokarinshi don kada Amna ta fita wata Kasa da sunan haihuwa sai dai hakan ya ci tura don ya yi kokarin kai ta asibiti dan ya hada baki da likitan ya kara a kan lokacin da ake tsammanin haihuwarta. Sun je an samu nasarar yin hoton, kuma an Kara kamar yanda aka sa. Nufinshi kafin su yi shirin tafiya ta haihu. Amma sai dabarar tashi ta tada musu da hankali, har ma ta sa suka soma haramar tafiyar. Amna ce ta yi mugun daga hankalinta tunda ta ga takardar hoton, kusan wata daya da kwanaki ya Karu a kan dukkan hotunanta na baya. Cikin damuwa ta kira mahaitinta ta sanar da shi, ya ce lallai ta shirya su tafi a cikin satin nan maimakon na sama. Dole Shatima ya sa ido suka aiko aka dauke ta suka tafi. Abin da bai sani ba ma iyayenta suna shake da shi, domin nasu ganin ya kamata ya dauki uzuri gurin aikinshi su tafi tare. Amna ce ta ke nuna musu cewa, aikin babu damar hakan. Ya shiga mugun tashin hankali da damuwa. Aliya ce ta rungume shi tana lallashi tare da ba shi magana. Hakan ya sa shi son kasancewa tare da ita a 'yan kwanakin nan. Sati uku da tafiyar su Amna aka ciro santalelen yaro mai kyau kama da ubansa, mahaifin Amna da kanshi ya kira Shatima yana masa albishir da samun karuwar. Murna sosai Shatima ya yi tare da kiran nasa mahaifan ya sanar musu. Nan da nan labarin haihuwar ya watsu a dangi. Hajiya aka shiga shirya kayan barka. Shatima yana kwance a kan katifarsa ranar dakin Salma yake. Kwanaki uku kenan da haihuwar, amma maijegon ta ki daga layinsa. Ya san tana fushi ne tunda suka tafi sau daya ya kira ta, shi ma Aliya ta matsa masa. Ya tura mata sako yana mai rokon alfarmarta cewa ta daga, sannan ya sake kira. Ta dauki wayar ta yi shiru duk da tana jin sallamar da yake dokawa. Ya ce, "Ki yi hakuri Honey, ko mene ne tunda mun zama iyaye bai kamata muna fushi ba. Zafin rabuwa da ke har kuka na yi, shi ya sa bana kiranki"Cikin shesshekar kuka ta ce, "Ka nuna min matsayina, kuma na gani. Sai dai kullum in tayi Momy karyar mun yi waya kana gaida su, don kawai kada mutuncinka ya zube amma ba ka gani" Nan Ya yi lallashinta, da kyar ta sauko sun yi waya sosai, kuma za su dawo cikin satin da za a shiga.Ya ce, "Suna fa?" Ta ce, "Sai satin sama" Ya ce,A nan za a yi mishi huduba?" Ta ce, "Dad zai masa dama ya ce mu yi maganar sunan da za a sa mishi da kai" Don ya sake faranta mata, ya ce, "Na ba ki zabi zumata Ta ce,Kamanninka da yaron ya sa na darsa sunanka a zuciyata, in ni zan zaba ina son a sa mishi Muhammad Ja'atar"Ya ce, "Yanda ki ke so haka za a yi, amma nasa za a yi taron rada suna a gidanmu can Zaria, bikin mata sai kun dawo" Ta ce Haka ya yi" Ya Ce. "To a turo min hoton yaron nawa in ganshi"Ta yi dariya, "Ka ci sa'a da na ce sai randa 鈥� muka dawo ka ganshi". Ya ce, "Da ma ni mai sa'a ne tun daga lokacin da na mallaki zuciyarki Ta sake sakin dariyar jin dadi sannan ta ce, "Zan turo maka yanzu ta whatsapp" Ya kalli yaron cike da so tsantsa da kauna, fari ne tas cikin kayan jarirai masu kalar sararin samaniya. Tabbas yaron yana kama da shi sosai. Ya mike ya dauki jallabiyarsa ya zura. Salma tana zaune tana assignment ta dago ta dube shi, shi ma ya kalle ta tamkar zai yi magana amma sai ya fasa. Ta maida kai ta ci gaba da rubutunta domin inda sabo ta saba da yanda Shatima ya rikide yanzun. Ta kula kwanakin nan yana cikin farin ciki da walwala. Dakin Aliya ya shiga ya nuna mata hoton kyakkyawan yaronsu. Ta yi farin ciki tare da fadin, "Yaron nan kama yake da kai sak!" Page 13 MUN TSAYA Tabbas yaron yana kama da shi sosai. Ya mike ya dauki jallabiyarsa ya zura. Salma tana zaune tana assignment ta dago ta dube shi, shi ma ya kalle ta tamkar zai yi magana amma sai ya fasa. Ta maida kai ta ci gaba da rubutunta domin inda sabo ta saba da yanda Shatima ya rikide yanzun. Ta kula kwanakin nan yana cikin farin ciki da walwala. Dakin Aliya ya shiga ya nuna mata hoton kyakkyawan yaronsu. Ta yi farin ciki tare da fadin, "Yaron nan kama yake da kai sak!" Ya rungume ta tare da fadin, "HaKika kin san kama Y谩 mike, "Bari in gwada wa Nafisa, Aliya ta yi 'yar dariya tana sake bin hotunan da kallo. Ya fita ya barta nan tsoron zuciyarta cike da takaici. Tunda aka yi haihuwar ta lura Shatima ya zama kamar wani soko. Natisa kuwa da ta kalli hoton cewa ta yi, yaron mai kyau abinshi. TA shafa cikinta tare da fadin, "Ni ma Allah ya sauke ni lafiya"Ya dora tafin hannunshi a kan nata, "Ameen Sweetyna. Amma da wa ki ka ga yaron yana kama?"Ta dan yatsina fuska, "Da mamansa mana" Ya ce,Kin duba da kyau?"Ta yi zooming din hoton, "Ga hancin nan irin na Mamanshi" Ya san kishin Nafisa don haka sai ya ce, "Ni nafi ganin kamarshi da ke" Ta kalle shi, "Da ni kuma?"Ya ce, "Eh mana kin san da ni ki ke kama" Ta yi murmushi,Wai da gaske ina kama da kai?禄 Ya ce, "Sosai ma, in na cikinki ya fito kin ga shi ke nan mun samu "yan biyu, don na san da mu zaiyi kama"Ta sake kallon hoton, "Guda daya ta tura maka?" Yace "Suna da yawa, bude ki gansu" Tana kallon hotunan tana fadin, "Ka tura min hotunan a wayana Ya ce,To kin kirata kin mata barka?" Ta ce, Ba ni da lambarta, kira min ita da kanka Nafisa da Amna sun gaisa, inda Amna ta yi wa Nafisa fatan sauka lafiya, bayan ta yi mata barka. Ran Shatima ya yidadi, domin kullum yana addu'a Allah ya hada kan iyalansa. Salma ba ta san da batun haihuwar ba, sai da taga Shatima da Aliya za su je Zaria wai za tayi wa su Hajiya barka. Ta tsinci zancen ne a bakin Aliyar lokacin da ta zo daukar zanin gadonta da ta shanya a kusa da motar da suka hau, tana fada ma Nafisa.Nafisa ta Ce, "Ku gaida su, ni na kira ta a waya ba iya zuwa zan yi ba Salma ta kalli Shatima, sannan ta kalli Aliya tace,Anty wace ce ta haihu?" Aliya ta kalli Shatima, ya daka mata tsawa, Da Allah ni shiga mu je" Ya yi baya da motar tamkar zai ture Salma,tana jin lokacin da Aliya ke fadin, "Ba ka fada mata haihuwar Amna ba?" Ba ta ji me ya ce ba suka wuce. Baki Salma ta _tabe tare da fadin, "Allah ya raya". Har zuciyarta ta ji dadin labarin. To sun dawo tana Zaria din ne ko ko?Ba wanda zai ba ta amsa don haka a fili ta ce, "Oho"A daki ta kira Badi' atu ta ce, "Ashe Amna ta haihu?"Badi'atuta.ce *Kina nufin ba ki sani ba?" Salma ta ce, suna Zaria din ne?"Cikin mamaki Badi'atu ta ce,Bakya gidan ne Kin yi tafiya? Salma ta ce, "Hmm, ina nan wallahi, amma Yaya bai fada min ba" Badi'atu ta cE "Wai kun samu matsala da shine na ga rannan da ya zo na tambaye shi ke sai na ga ya hada rai, sannan ya ce kina gida. Da ko da kanshi yake min zancenki" Salma tace "Tun laifin da na ce miki na masa da sallah shine har yanzu bai huce ba. Ko magana da kyar yake amsa min' Badi' atu ta Ce, "Wai ba ki ba shi hakuri ba ne?" Salma ta ce,Na ba shi har sau ba adadi, amma ya ki hakura Badi'atu ta ce, "Wai wane irin laifi ne haka mai zafi?" Salma ta yi shiru, Badi'atu ta ce, "Kina jina?" Salma ta Ce, "Ina jinki, sai dai in yi miki sako ki karanta"Badi' atu ta ce, "To ki yi min sakon" Ta rubuta mata sako kamar haka. "Ya neme ni ne na kasa yarda, don ina jin tsoro shine yake fushi Badi"atu ta kira Salma ta ce, *Ke ma kin san dole ya fusata" Salma ta Ce, 芦To ai daga baya na zo na ce na yarda; kuma na bi duk wata hanya don in ba shi hakuri amma yaqi, har ma na saba da yanda ya koma min yanzu" Badi' atu cikin tausayawa ta cE "Sai dai in ba ki hakuri in ce ki ci gaba da addu'a da kuma yi masa biyayya tunda ni ma ba wai na yi auran ba ne bare insan ko akwai wata dabara. Hajiya kuwa bawai tana yinki ba ne bare in kai mata kara Cikin sauri Salma ta ce, "Don Allah ki taimaka Karki fada, ke ma na fada miki ne don in ji sanyi a raina, ba wai don ki ba ni mafita ba. Ina son in yi wa Hajiya barka ne" Badi'atu ta ce,Bari in turo miki lambarta, amma ai maijego England ta haihu sai ta dawo za a yi suna Salma ta ce, "Na ji tafiyar, na za ta ta haihu sun dawo ne. to ki turo min lambar har da ta kaka Badi'atu ta ce,To, ko kuma ki fada ma kaka din tunda na ga ita tana yinki sosai, kin ga murna da na kai mata sakonki na sallah? Ta ce, Shatima ke ce zai ci riba a cikin matanshi" Salma ta ce, "Allah sarki Kaka, Anty Badi'atu ba zan kai mata Kara ba, kema amana na ba ki, insha Allah ba zan taba kai Karan mijina ba har abada Badi'atu tace "To Allah ya ba ki ikon jurewa" Nan suka yi bankwana. Ba a fi minti uku ba sai ga sakon lambobi sun shigo. Ta kira Kaka ta yi mata barka, Kaka ta yi ta saka mata albarka, sannan ta kira Hajiya. Salma ba ta sha mamakin yanda Hajiya ta amsa mata ba don ta zaci abin da ya fi haka ma. An rada wa yaro sunan mahaifinshi Muhammad Ja"afar, walima sosai Alhaji yayi a kofar gidan, Shatima ma ya kasance a abokansa. Dan sammako suka yi shi da Aliya. Salma ta cire duk wata damuwa ta aje ta dage da karatunta, yanzu burinta shine ta shiga islamiyya Ta bari sai ranar da babu aiki ta same shi ko a dakinsa yake. Tunda akwai islamiyya kusa da su, kuma babu tsada in dai ya barta to za ta shiga ko a aljihunta ne duk da ya rage abin da yake ba ta, ba ta fasa adanawa ba.Gaban Salma yana faduwa ta nufi dakin Aliya. Cikin sa'a sai ga shi ya fito sanye da jallabiya, da alamu ba fita zai yi ba don takalmin tsakar gida ne a kafarshi. Ya kalle ta har zai wuce, ta yi sauri ta rusuna ta sunkuyar da kai cikin tsananin faduwar gaba. Ya katse mata tunani, ta ce, "'Amma da ma Yaya ina son in roke ka ne ko za ka saka ni a islamiyya. Saboda duk na manta da karatun da na iya Shiru tayi, ta dago ta dube shi dan ta ga yanda ya amshi maganar. Sai ta ga yana yi mata wani kallo mai cike da tsana, za ta fassara shi ko wulakanci, sai kuma ta ga ya sa kai ya fita abinshi. Ta dan yi jim a tsugunne, sannan ta mike ta nufi dakinta. Sati daya tsakani ya zo ya aje mata wata leda akan kujera, ta fito kicin ta yi masa sannu da aiki ya amsa, dan ta samu ma yau ya amsa mata tunda watarana ko kallo ba ta ishe shi ba. Ya ce,Ga shi nan kayan islamiyya ne, ki shirya anjima za ki soma zuwa Cikin murna Salma ta ce "Na gode, Allah ya Kara budi Page 14 MUN TSAYA Ta sunkuyar da kai cikin tsananin faduwar gaba. Ya katse mata tunani, ta ce, "'Amma da ma Yaya ina son inroke ka ne ko za ka saka ni a islamiyya. Saboda duk na manta da karatun da na iya Shiru tayi, ta dago ta dube shi dan ta ga yanda ya amshi maganar. Sai ta ga yana yi mata wani kallo mai cike da tsana, za ta fassara shi ko wulakanci, sai kuma ta ga ya sa kai ya fita abinshi. Ta dan yi jim a tsugunne, sannan ta mike ta nufi dakinta. Sati daya tsakani ya zo ya aje mata wata leda akan kujera, ta fito kicin ta yi masa sannu da aiki ya amsa, dan ta samu ma yau ya amsa mata tunda watarana ko kallo ba ta ishe shi ba. Ya ce,Ga shi nan kayan islamiyya ne, ki shirya anjima za ki soma zuwa Cikin murna Salma ta ce "Na gode, Allah ya Kara budi Ya fita ba tare- daya saurareta ba. Ranar ta soma zuwa islamiyya, har da hadda za ta dinga zuwa sati da lahadi. Maijego Amna sun dawo ranar Shatira da Aliya da su Hajiya suka dira Kano. Sun samu gidan tankam da mutane, har sun soma tunanin ko sunan ake An yi musu tarba, kuma an amshi kayan barkan da suka kawo. Shatima yana jin dadin zai ga kyakkyawan danshi, Hajiya kuma tayi tam da ganin yanda aka ajebkayan barkan kamar a wulakance, domin ta zuba kudi a kan wanda ta amsa a gurin Alhaji sannan sun z0 da manyan raguna guda biyu wadanda Alhaji Musa mahaifin Nafisa ya siya. Ita dai Hajiya suna zaune ita da Aliya da maman Nafisa a dakin mahaifiyar Amna. Sun gaisa da mahaifiyar da sauran bakin da ke dakin. Anty Amarya ita ce ta gabatar da su da kuma kayan da suka kawo. 'yan dakin tareda Momy tunda sukace an gode ba su sake bi ta kansu ba, kuma ba su samu damar matsar da kayan daga inda suke ba. Amna ta nufi dakin da aka sauki Shatima saboda lokacin da suka iso sannan take wanka. Ba su jima da tashi ba, Anty Amarya tace ta shiga dakin Momy su gaisa da su Hajiya. Ta shiga ta rusuna tana gaida su. Hajiya cikin son nuna itace surukarta, ta fara fadin "Sannu 'yata, sannu da arziki. Allah ya raya mana Muhammad Ja'afaru je gurin Shatima Amna dai ta mike, tare da fadin, "Momy bari inje gurin Shatima Hajiya ta wage baki cikin murna, ta ce, "Ai ko dai yana can dakin ko? To ina jaririn Momy ta kalle ta, ta yi murmushi ganin zumudin da Hajiyan ke yi, sannan tace "yana tafe Hajiya, za a kawo muku shi. Yanzu ake shirya shi" Aliya tace "Ni ma shi na Kosa in gani" Amna ta yi sallama ta shiga dakin da Shatima yake, ya aje wayarshi cikin sauri da doki ya nufi Amna suka rungume juna. Suka sumbaci bakin juna sannan suka zauna kan cinyarsa ya dora ta. "Ina yarona ne?" Ta sa hannu ta tallafi fuskarsa, "Ana shirya shine, ba mu dade da tashi ba ka san shigowar asubahi muka yi, sai kawai muka ci gaba da bacci" Ya sa hannu ya shafa cikinta, "Baby ya fito ko?" Suka sa dariya, ya ce, "Kin kara kyau Amna" Ta ce "Ko?" Ya ce, "Sosai kuwa". Aka kwankwasa Kofa, Amna ta mike da sauri don ta san Sumayya ce. Shatima shi ma ya mike tsam ya tari Amna, ya amshi jaririn. A Kirji ya manna shi tare da lumshe ido. Wata irin Kauna mai tsanani yakeji, da tsantsar son yaron. Kamshin jaririn ya sa shi kara jin wani shauki, ya dago cike da matsanancin farin ciki ya kalli fuskarta. 'Amna na gode,Allah ya saka miki da mafificin alkhairi, don kin gama min komai a rayuwata Cikin jin dadi da alfahari tace, "Allah ne ya ba mu ba wayonmu ba ne" Ya ce, "Duk da haka kin yi dawainiya da cikin,kin ba ni dan fari mai kama da ni, kuma ki ka zaba mishi sunana Ya sa bakinsa a kunnen yaron ya yi masa kiran sallah, ya jaddada masa huduba. Sun jima har aka kawo abinci, tare suka ci cikin kulawa da Kaunar juna. Hajiya dai ta kasa cin abinci saboda har lokacin ba taga jikanta ba. Aliya ta ce, "Wai ni a raka ni inda yaron nan yake don shi muka zo, amma har yanzu ba mu ganshi ba" Anty Amarya tace, "Au na manta, ina zuwa".Can ta dawo, "Suna gurin Babanshi" Hajiya tace "A karbo mana shi" Aliya ta mike, "Nuna min inda yake in karbo shi' Suka fita da Anty, Aliya ta Kwankwasa kofar. Shatima ya ce, "Shigo". Don a zatonshi Sumayya ce. Tana sako kai ta ga suna kicin-kicin ba shi nono, Shatima ne ma ke rike da nonon. Aliya ta yi saurin sakin fara'a tare da danne wani Kululun takaici da ya taso mata, ta ce, "Haba! Ashe kuna nan da dan muna can muna jiran gain jariri?" Shatima ya ce. "Au ba ku ganshi ba? Yanzun yana cin abinci" Amna ta kalle ta, "Da ma har da ke aka zo?"Cikin mamaki Aliya ta ce, "Ai mun gaisa kuwa lokacin da ki ka zo kuna gaisawa dasu jiya" Amna ta kalli yaron, sanna ta ce. "Ban luraba Yaron ya ja nono da karfi, amna ta lumshe ido tare da fadin, "Wash!" Ya ce, "Sannu". Ya sa hannunshi yana shafa mata baya Aliya ta tabe haki tare da kau da kai, Amna ta kalle ta, "Zauna mana' Ta ce Bari in je kun kawo shi, muna dakin Hajiyarku Amna tace Momy kenan?!" Aliya ta fice cike da jin zafinsu, amma tana zuwa dakin sai ta saki fara a, "Za ta kawo shi. Maman su Nafisa ta ce, "To ke me ya sa baki karbo shi ba?" Maimakon ta ce nono yake sha tunda ita mata gani, amma sai ta ce, "Ina, gani dai Qila yunwa yakeji" Hajiya ta dan yi shiru, domin yanzu ta yarda Zarginta wulakanci ne kawai. Ita da jikanta na fari sai an mata wulakanci zata ganshi, bayan ta fi su iko dashi ma? Gashi ita kanta uwar maijegon sai wani jin kai takeyi, taki ko da hira da su sai labarinsu suke da "yan uwanta da kawayenta. Aliya ta katse tunanin Hajiya da cewa, "Dubi yanda aka bar kayan yaron can sai zama a kan akwatunan ake yi. ko magana za a yi musu su bude su gani Kan Hajiya ya sake sosuwa tace Kar wanda yayi musu magana, in mun tafi su zubar da shi Mama tace Kar ki dau fushi da sauri Majiya,kin san manyan nan sai a hankali, da ma hulda dasu sai hakuri* Hajiya tace "Uhum'! Tafiya ma zan yi" Ta ciro wayarta a jaka, tana nemo lambar Shatima yana dagawa, tace "To ya kamata mu tafi haka ko?" Ya ce, "Da sauri haka Hajiya? Ki bari mana Sai yamma?" Ta ce, "Ni yanzun zan wuce, in kuma ba za ka tafi ba to mu je mu hau ta haya Ko ba a fada masa ba ya san Hajiya ranta ya baci, ya yi tsaki cikin tunanin me ya faru? Amna ta mike, "Tunda ya gama bari a kai shi su Hajiyar su ganshi ko?' Yace Yauwa, kai shi" Sai yanzun ya gane abin da ya sa Hajiya jin zafi. Tana ta zumudin ganin yaron, amma har yanzun ba ta ganshi ba. Amna ta shiga ta mika yaron ga Aliya tare da fadin, "Ga shi" Hajiya cikin *yar gajeriyar fara"a mai boye damuwa tace "Da kun barshi ma Allah ya raya Amna wadda ba ta cika damuwa da damuwar mutane ba bare ma ta gane wai haushi Hajiyan ta ji, tace, "Badi'atu ba ta z0 ba ne?" Hajiya ba ta tanka ba, sai Aliya ta ce, Sai ranar suna Amna ta fita ta koma gurin mijinta. Page 15 Mun tsaya Amna ta shiga ta mika yaron ga Aliya tare da fadin, "Ga shi" Hajiya cikin *yar gajeriyar fara"a mai boye damuwa tace "Da kun barshi ma Allah ya raya Amna wadda ba ta cika damuwa da damuwar mutane ba bare ma ta gane wai haushi Hajiyan ta ji, tace, "Badi'atu ba ta z0 ba ne?" Hajiya ba ta tanka ba, sai Aliya ta ce, Sai ranar suna Amna ta fita ta koma gurin mijinta. Da Kyar Mama ta lallashi Hajiya ta dauke shi domin da ta ki, ta ce, ai ta ganshi a hannunsu. Duk wannan abu da su Hajiya ke yi sam Momy da 'yan uwanta ba su san ma arziki tana bori ba. Shatima tamkar ya tafi da dan gudan jininsa haka yake ji. Sun yi batun kayan suna, ya ce zai sa Anty Momiyo ta turo mata lesissika da atamfa don ta zaba, ya kuma tambaye ta ko nawa zai ba da game da abincin suna? Amna ta ce, "Ni ban sani ba, amma bari in tambayi Anty Amarya Anty amarya ta ce, "Tabdi! Gaskiya ban san ya zan ce maka ba sha'anin gidan nan ana kashe kudi sosai, ka dai kimanta ka bada kawai Ya ce, "In na ba da dubu hamsin ya yi?" Duk suka yi shiru, duk da sun san karfinshi baikai nasu ba, amma dai dubu hamsin bai kai ko kudin kajin da za a dora a kan abinci ba. Ban da Sada ya zama.ka'ida dole a yanka, ga nau 'o' in abinci da na sha. Jin sun yi shiru Shatima ya ce, "Anty abin ne da yawa, yanzu haka Nafisa a watanta ta ke Anty ta ce, "Duk da haka sun yi kadan sosai". Ya ce, "To insha Allah zan kara". Amna ta ce, "Ni ka bada dari da hamsin ko dari biyu sai ka bar kayan da za ka sai min na fitar suma, tunda ina da kaya ko na lefena ban taba ba, sai nadauka a ciki" Anty amarya ta ce, "Momy ma ta dinka miki kayan suna tun zuwansu Dubai" Ya kalli Amna, "Shi kenan, in dari biyu ba ta samu ba zan yi kokarin ko dari da hamsin ne. na gode da karamci, in ina da kud矛 kin cancanci in kashe duk abin da na mallaka a kanki da dana" A mota Hajiya tana ta mitar abin da aka yi musu a gidan su Amna, fadi ta ke, "Ban da isa sai a wani share mutane ana nuna irin wannan iko? Kai da gudan jininka sai an wulakantaka sannan za a ba ka? Mu ba rokonsu muka je ba, ba ruwanmu da abinsu"Mama tace "Ke ma kina da gajen hakuri ne Hajiya, shi fa shi'anin masu da shi din nan sai da kai zuciya nesa, don sai ka iya zama da su" Shatima ya Ce, "Wai me ya faru?" Hajiya ta shiga rattafa mishi abin da take ganin an yi mata. Cikin sauri Shatima ya ce, "Laifina ne, nine na kasa ba da shi, ki yi hakuri"Daga nan ta dan saurara. Ranar suna gidan tankam da dan Adam. Da masu masu zuri'a ne sosai, dangin Shatima da matansa sun z0, amma ban da Salma. Nafisa ma tazo ta gane wa idonta. An ci an sha kuwa komai sai da aka barshi, ga maijego da jariri suna ta shiga suna fita.Nafisa kuwa a ranta fadi ta ke, ai gara da na zo na gane ma idona don kar in haihu ba a yi min wani abin ba. Kyauta kuwa ta kaya da kud矛 har da mota yaro ya samu, babban wansu Amna ya sai mishi. Aliya kuwa tamkar "yar aiki haka ta zamar da kanta, duk wanda yazo ita ce mai zuba abinci duk da cewa akwai wasu da aka tanada don raba abinci. Da ma neman suna take yi a gurin dangin Amna, kuma ta samu. Don in sunata yaba mata. Da za su tafi aka hada musu kaya rigijit Sai Karfe takwas da wani abu suka isa Zaria. Nafisa ta ce, ita kam ba za ta tafi Kaduna adaren nan ba, gobe a kawo ta.Cikin wanna daren ciwon haihuwa ya taso ma Nafisa, aka nufi asibiti da ita. Hamida ce ta kira Shatima a waya ta sanar da shi. Ji ya yi tamkar ya yi tsuntsu ya nufi Zaria. Ta sha wahala sai asubahi ta haifi danta mai kyau. An yi mata dinki don sai da aka karata. Da sassafe su Hajiya suka je asibitin da Alhaji, sun yi murna sosai, Alhaji ya rungume yaron yana yi masa addu'a. Ba tare da neman shawarar Shatima ko Nafisa ba ya yi wa jaririn huduba da Musa, sunan mahaifin Nafisar, Kaninsa. Ya mika wa Hajiya shi tare da fadin, "Karbi Musa na yi masa huduba Hajiya ta ce, "Alhaji ka yi shawara da iyayen dan ne, ka san fa su *ya yan yanzun kafin a haihu an zabi suna Nafisa ta yi dan murmushi tana daga kwance, Tace A'a ba mu zabi suna ba Alhaji ya ce, "Ko ma dai kun zaba ta sunan dan uwana Allah ya ci da shi". Sallamar Shatima ce ta sa Hajiya canza abin da za ta fada zuwa amsa sallama. Gurin Nafisa ya wuce kai tsaye ya kama hannunta yana yi mata sannu. Mama ta fito daga bandaki tana yi musu sannu da zuwa. Suka gaggaisa, ta dubi Shatima ta ce, "'Har ka zo?" Yace Eh mama Sai lokacin ya gaida su duka. Hajiya ta mika mishi jariri tare da fadin, Babanka Musa" Mama tace "Wa ya yi masa huduba da sunan tsoffi? Don ita da ma sunan kakanta ne. Alhaji ya ce, "Su sai su ce ba sa son sunan Baban nasu in ji Shatima ya manna dan a Kirjinsa tare da fadin "Wane mu? Allah ya sa ya biyo halin Baban namu Duk suka amsa, sannan suka koma kan shawarar inda za a kai Nafisa gidanta ko nan Zaria.Shatima ya ce, shi dai ta koma dakinta. Hajiya ta ce, "Wane ne zai kula da ita can?" Mama ta ce, "Tunda dai mijinta ya fi son ta zauna a can a barta ta koma can"Hajiya ta ce, "A'a in ba za ki tafi da ita ba, ni in tafi da ita" Shatima ya ce, '"To duk yanda ku ka yi".Ya dubi Nafisa, "Ina ki ka fi so?" Ta ce,Ni gurin Mama zan tsaya"Ya ce, "Shi kenan. Aliya ta ce in gaida ki kafin ta zo. Ni ma yanzun zan wuce gurin aiki ne" Kaka ta ji dadin yanda a ka sa wa jaririn sunan kakansa don ita tana son ake yi wa juna kara. Kwana biyu da haihuwar Nafisa kwatsam sai ga Hadiza da Innarsu murna a gurin Salma ba a magana. Ta yi musu girki mai dadi ta kuma hada musu abin sha. Sun yini sun sha hira amma ko da wasa Salma ba ta sanar da su Inna rashin jituwarsu da Shatima ba. Ta dai fada musu haihuwar Amna da kuma ta Nafisar da ta ji a bakin Aliya, don ko shi ma ba ta samu ta yi masa barka ba.Inna ta ce, in ta koma za su je da Hadiza su yi wa Hajiya kaka barka. Salma ta ce, har da can gidan Shatima duk ku je. Sai a nuna muku gidansu Nafisar tunda tana can Zaria din. Inna ta ce, "Insha Allah za taje" Da za su tafi, Salma ta kawo dubu' biyar ta bai wa Inna ta ce, ta yi jari ko na kayan miya ne don Inna ta yi kuka da rashin sana"a. Ta raka su suka tafi. A bakin Aliya Shatima ya ji cewa Innar su Salma tazO, ya same "ta a dakinta tana rubutun islamiyya, ya ce, "Ke wato su Inna sun zo shine ba zaki iya kirana ki ce min sunzi ba ko?". Ta ce, "To ai Yaya ba ka daga wayata shi ne dalili? Ya CE, "T貌 me ya hana ki yi min message?" Ta yi shiru ba ta son jayayya ne kawai, amma message nawa ta yi masa babu amsa. Ya ce, "Kar ki sake yi min irin haka. To me ki ka ba su?"Ta dago "ta dube shi a dan tsorace, "Kudin hannuna ne kawai na ba ta duka". Ya juya zai fita, ta ce, "Ashe Anty Nafisa ma ta haihu?" Sai da ya saka Kafa a waje sannan yace"Eh". Gidan su Nafisa ta koma, Hajiya ta hada kayan barka ta kai. Alhajin su Shatima ya sai raguna. Ranar barka ko in ce ranar kauri, gidan cike da dangi da yake su ma akwai zuri'a. Page 16 Mun tsaya T貌 me ya hana ki yi min message?" Ta yi shiru ba ta son jayayya ne kawai, amma message nawa ta yi masa babu amsa. Ya ce, "Kar ki sake yi min irin haka. To me ki ka ba su?"Ta dago "ta dube shi a dan tsorace, "Kudin hannuna ne kawai na ba ta duka". Ya juya zai fita, ta ce, "Ashe Anty Nafisa ma ta haihu?" Sai da ya saka Kafa a waje sannan yace"Eh". Gidan su Nafisa ta koma, Hajiya ta hada kayan barka ta kai. Alhajin su Shatima ya sai raguna. Ranar barka ko in ce ranar kauri, gidan cike da dangi da yake su ma akwai zuri'a. sunan Amna, Aliya da ke zaune kusa da maijego a bakin gado tana sauraron hirar da su Nafisa suke yi ita da yan uwanta. Nafisa ta ce,wai da sunan Mus'ab wa ta yi muku cake na ji ana ta labarin dadinsa Ta ce, Gidan Alhaji Sani ne Nafisa tace "Don ni ma duk abin da ya yi ma wacca matar a sunanta ni ma fa haka zai min Aliya ta ce, "Kar fa ki ce komai, kin dai san su suna da halinsu, wani abin da kansu za su yi Nafisa ta ce, "Ina ruwana, dole dai ya yi min duk abin da ya yi mata"Aliya ta ce, "Ni ban ce kar ya yi miki ba, amma kar ki ce komai Safina tace "Dole ya yi mata mana, don su masu kudi ne?" Nan dai suka shiga surutu. Aliya ta ji dadin haka, domin ita ba taqi su kwabe ita da Shatima ba. Nafisa tace "Ni ya zo mu yi maganar kayan fitar suma, don su ma irin nata nike so' Aliya ta ce, "Sun ko yi kyau kayan sosai" - Nafisa tace "Ai irinsu sak zai min". Haka dai suka yi ta mata famfo tana hawa kamar farashi. Salma tana son zuwa suna, amma ta san ba za a barta ba. Hanya daya ce kawai ta saka Aliya ta nemar mata izini, Ta san Aliyar za ta yi tunda tana son irin haka. Ta riski Aliya a dakinta, tace "Anty ina son don Allah ki rokar min Y盲ya, ina son zuwa suna ko zai bar ni" Ta balla mata harara, "Ke ba ki da baki ne?" Salma ta ce, "Ai ba zai saurare ni ba ne Anty, ke kadai yake jin maganarki ba ya miki gardama Salma ta fada cikin son tula mata kasa. Aliya ta saki murmushin jin dadi, ashe har mukaminta ya kai haka? Kishiyoyinta har sun gane ita din babba ce, gaskiya abin ya yi mata dadi. Wannan sokuwar ma ta gane bare sauran, lallai ita ce a sama. Cikin isa ta ce, "Shi kenan, je ki zan tambayar miki" Salma ta ce, "Na gode" Shatima ya zauna a bakin gadon fuskarsa dauke da murmushi, ya amshi jaririnsa daga hannun Hamida. Ya kalli Nafisa wadda ke cin gasasshen nama a cikin faranti, ga yaji tana dangwala. "Sannunki mai jego" Ta ce,Sannu mijin maijego"Suka yi"yar dariya. Ya kalli yaron Babana din nan fa yana kama sosai da Jafar" Ta kalle shi, "Wane ne Jafar?" Shatima ya ce, "Yayanshi mana Ta dan tabe baki, "Ni dai wannan ya fi min kama da kai" Ya yi murmushi a ransa ya ce, Nafisa sarkin son kai. A sarari ya ce, "'Duk su biyun suna kama da ni ne. Wannan ya nuna karfin jinina ne" Ta yin murmushi, "Menene kuma na yin al fahari?" 鈥簃urmushi yayi Yace "Dole in yi don duk wanda ya dube su ya san yayana ne babu bata lokacin kwatance"TaceKa, Ni lokaci yana ta tafiya amma ban ji kayi maganar kayan suna ba Yace,Kayan suna kuma?" Ta sake kallonshi,na fitar suna mana Ya ce, *Shi nazo mu yi magana. Anty Momiy ba tazo ba?" Ta ce, "eh bata zo ba Yace,zatazo takawo miki kayan ki zaba.Kala uku za ki dauka, Aliya ma a bata guda daya"Nafisa ta Ce, "Irin kayan Amna kawai za a kawo min, ko.ba ita c猫 ta kawo mata ba? Ya ce, a,a bansan inda suka sai kayansu ba, Nafisa ta dube shi cike da zargi. Tace Kawai dai ka ce ita ka yi mata irin nasu na masu hali, ni kuma ka yi min na daidai ni Ya. tausasa murya da nufin. kwantar mata da hankali, ya ce, "Nafisa in na fada miki cewa.banyi,. wa Amna kayan fitar suna ba za ki yarda?" Ta sake hade rai, "Ba zan yarda ba gaskiya? Ya ce, "To ban yi mata ba, kuma ita da kanta tace in barshi" Ta tura baki, "Ni dai a yi min adalci ah to!" Ya dan daga murya don nuna jin zafinsa, *Kina sa ran zan cuce ki kenan?"Ta yi shiru. Yace "To na gode" Ya mike ya kwantar da yaron a kan gadon ya yi ficewarsa. Suka yi kici6is da Mama ta fito kicin da Fulas na ruwan zafi za ta dakin mai jego. Ta ce, "Ba dai har ka fito ba? Ga abinci can Hamida za ta kawo maka' Ya ce, "Na koshi Mama. Nafisa ce ta bata min tai? Ta ce, "Nafisa ko?" Ta aje kayan tare da fadin,Zo nan" Ta shiga dakin su Hamida. Ya fada mata duk yanda suka yi, ya ce, "Mama Amna ban sai mata kaya ba, saboda ta ce kudin abincin da zan ba ta ya yi kadan kuma ba ta son a ce na kasa" . Ya fada mata duk yanda suka yi da Amna. Mama ta Ce, -Kai Nafisa kishi yana son ya maida ta mai hassad Ta dubi Shatima, "Kana ji ko Baba, ka kwantar da hankalinka, shirme ne ma in tace za ta hada kanta da Amna. Abin da za a yi idan Momiyo tazo kawo Kayan, to ka zabi wanda ranka ya yi maka kuma daidai Karfinka ka siya. Batun abinci kuwa babu takura, duk abin da Allah ya hore shi za a yi. Duka yaushe aka gama waccan sabgar? Mu ne fa iyayenka, mune masu yi. Don Allah ka kwantar da hankalinka ka ji ko?" Ya Ce, "Balle ma ita ma zan mata komai da yardar Allah. Na fi son ta kwantar da hankalinta Mama ta ce, "Babu komai ka kwantar da naka,ita ma za ta kwantar da nata hankalin" Ta so ya ci abincin, yace ya koshi. Gidan Hajiyanshi ya wuce: Tana zaune a falo, Ya gaishe ta, ta ce, "Zuwan kenan?" Ya ce, "A'a tuni na zo, daga gurin su Nafisa nake Ta ce, "To ka sallame su ko?" Ya ce, '"'Abin da na je kenan. Anty Momiyo bata kai mata kayan ba ma" Ta ce, "Ni dai ka yi mata komai kamar yanda da yi wa Amna, bana son ka yi rashin adalci tsakani, bare wasu zantuka ma su shigo. Allah ma ba zai bar kaba Yace "Insha Allah bazan canza daga tarbiyyarku ba Hajiya, kuma Amna kudi na bata shi ne Da na so da Anty Momiyo ta zo ta kawo kayan da na san ko na nawa ta dauka, sai in ba ta sauran kudin kamar daidai adadin kudin da na ba Amna Hajiya cikin gamsuwa tace, To ka kira Momiyo din kawai mana' Ya ce, "To, bari in kira ta".Bayan sun gaisa ya ce, "'Anty ashe ba ki kawo mata kayan ba?" Ta ce, "Kai dai bari Shatima. Autana ne ba shida lafiya, ka ganshi nan yanzun nan na gama ba shi magani ya kwakkwara amai"Shatima ya ce, "Allah sarki. To Allah ya ba shi "lafiya. Ya za a yi kenan?" Tace "Gobe insha Allahu zan zo in kawo mata" Ya ce, "Uku za ta dauka. "Yan nawa-nawa ne?" Page 17 Mun tsaya Daidai adadin kudin da na ba Amna Hajiya cikin gamsuwa tace, To ka kira Momiyo din kawai mana' Ya ce, "To, bari in kira ta". Bayan sun gaisa ya ce, "'Anty ashe ba ki kawo mata kayan ba?" Ta ce, "Kai dai bari Shatima. Autana ne ba shi da lafiya, ka ganshi nan yanzun nan na gama ba shi magani ya kwakkwara amai" Shatima ya ce,"Allah sarki. To Allah ya ba shi "lafiya. Ya za a yi kenan?" Tace "Gobe insha Allahu zan zo in kawo mata" Ya ce,"Uku za ta dauka. "Yan nawa-nawa ne?"Ta ce, -Atamfa ishirin da biyar, leshi kuma talatin da biyar Ya Ce, "Ta Gauki leshi guda daya, atamta biyu. Nawa kenan?' Tace, "Tamanin da biyar Shatima yace "To a bata haka. Sai kuma ita Aliya a bata leshi guda daya" Ta ce, "To 'yar gidanka fa?" Ya ce, "Barta wannan, ba lallai ta zo sunan bama. Kuma ga biyan kudin makarantarta. Gaba daya kudinki zai zama dari da goma ko?" Ta ce, Haka Yace "To za a dai daga min Kafa Ta ce, Babu komai" Bayan sun yi bankwana ya dubi Hajiya, "Cikin dari da hamsin an cire tamanin da biyar, saura nawa?"Hajiya ta ce, "Sittin da biyar" Ya ce, "Shine abin da zan ba su su yi girki. Domin Amna ma dari da hamsin na ba ta Ta ce, "Na ji kana a ba Aliya leshi, ita gudar fa?"Shatima ya ce, "Kyale ta ba dole ma ta je sunan ba fa" Hajiya ta yatsina fuska, "Ni dai bana son a ja - sunana a ce ni ce na hana a yi wa wani - Shatima ya ce,Ga kudin makarantarta, sannan ta shiga islamiyya da hadda kwanan nan' Hajiya ta tabe baki tare da fadin, Umm, ku dai ku ka sani Ya mike, "Bari in leka gidan Munnir in wuce" Ana gobe suna Salma ta koma gurin Aliya, don ranar dakin Aliyar ya kwana, tace "Don Allah Anty kin ko tambayar min zuwa gidan sunan din?" Aliya ta tabe baki, "Na manta sam. Amma bari dai ya dawo" Duk da haka Salma ta tura mishi sakon cewa. za ta je kitso da Talle a makota. Ok kawai ya turo mata. Aliya don ta nuna ma Salma gadara, bari ta yi sai da Shatima ya dawo ya shiga dakin Salma, sannan tabiyo shi za ta tambaya mata unguwa a gabanta. Kai tsaye ta shiga dakin Shatima yana zaune a tsakiyar katifa yana aiki a laptop. Ta zauna a bakin katifar tare da fadin, "Sannu da dawowa Ya amsa da, "'Sannunki. Kafin ki ji dadin zama hado min shayi"Ta ce, "To mijina, ko kwanciya nayi ai dole in tashi in hado maka shayi". Ya ce, "Yau dare zan raba ina aiki, don ina da aiki. Ga shi za mu yi sammakon tafiya Zaria, saboda taron suna Ta ce, "Yauwa, da ma na zo in maka magana ne a kan ya kamata Salma ta je sunan nan. Fisabilillahi yarinyar nan bana jin dadin yanda ka ke mata. Ka ga ko zanin nan da ka sai min ita ba ka sai mata ba, banso ba na yi shiru ne kawai Ya ce,Ki bar wannan zancen". Ta ce,Na bari, yanzu dai ina son don Allah ka barta goben sai mu tafi tare" 'Zai yi magana ta ce, "Don Allah ni za ka yi ma wannan Yace Shi ke nan ta ci albarkacinki" Tace,Na gode". Ta jima sannan ta fito ta samu Salma zaune a 'falo, a hankali ta ce, "Ki shirya za ki je" Salma ta ce,Na gode Anty. Washegari suka nufi suna, Salma ba ta ji komai ba da ta ga Aliya ta saka sabon leshi irin na maijegon,sun yi armashi duk da bai kai na Amna ba, amma taro ya yi kyau tunda an tashi lafiya. Kwanansu daya suka dawo. Kwanci tashi masu jego suka yi arba"in. sai da Nafisa ta gama zaga dangi sannan ta dawo. Jaji gurin Antynta sai da ta kwana biyu, Anty Maimuna ta sa aka hada mata *yan gara masu kyau. Da ma da suna cewa tayi ba za ta ba ta komai na gudunmawa ba,ta ce za su hadu in ta yi arba"in. tun a lokacin ma ta hada mata wani tsumi wanda ta ke sha a cikin jego. Don haka Nafisa a shiryenta ta dawo, Amna kuwa saida tayi wata biyu da kwanaki sannan ta dawo. Lokacin ne aka gama zuba zama. Aliya ta soma shige ma Nafisa kafin dawowar Amna, ta dauko Ashraf shi ne sunan da suke kiran yaron Nafisa. A goya shi, ta yi ta wannan fi'ili bare ma in ta ga Shatima yana nan, ko in ya shigo da shi, a amshe shi a goye a baya ram! Da Amna ta dawo sai kuma aka koma gurinta,sam Amna ta hana danta in ta zo sai tace yana bacci, ko za a yi masa wanka da dai sauran uzuri, har dai ta gane ba a son ba ta shine ta hakura. Sai ma wani sabon haushi da ta tsinci kanta,wanda kuma ba ta da damar magana. In Shatima yana dakin Nafisa ko Amna ba ya fitowa da wuri, ta san yana can yana wasa da yaranshi. Haka dai ya kan zo da Ashraf don Amna ba ta bada yaronta. Ya kan ba da duk hankalinshi a kan yaron, yana yi masa wasa. Wani 'lokacin ma ko tana magana ba ya ji, sai in ta yi dabara ta amshi yaron ta goya, sannan za su yi hira. Hakan yana matukar kona mata rai. 鈥� Salma kuwa karatunta ta sa a gaba. Sannu-sannu su Salma sun zana jarrabawar fita daga J.S sun shige SS 1, har lokacin Salma ba ta kara Kiba ba sai ' tsawo. Amma cudanya da yaran masu kud矛 irin su Salma Dankasa da sauransu ya sa ta waye sosai. Babu yanda za a yi ka ga Salma ba ka yi tunanin cewa "yar masu kudi ba ce Zuwa yanzu ta manta yanda Shatima yake fara"a, ta fi sabawa da yanayinsa na yanzun. Tana Kallonshi matsayin wanta mai kula da ita, kuma wanda take shakkarsa. Sai dai ta kasa manta kalaman nan masu muni da ya yi mata, hakan ya taimaka kwarai gurin Kara nesanta zuciyarta da son Shatima. Har zuwa yau za ta yarda cewa, ba ta san so ba,kuma ba ta damu da ta sanshi ba. Haka lokuta da dama ta kalli kanta a madubi ta san cewa, ita ba mai kyau ba ce, amma kuma ba ta da munin da Shatima zai ki ko da sake nuna sha鈥檃warsa a gare ta matsayinta na matarsa. Ta yarda rashin so ne kawai dalili. Domin don ya neme ta sau daya ba ta yarda ba bai isa ya zama dalilin da zai sake kasa gwada sa'arsa ba. Zuwa yanzu ta fi daukar kanta a ba matar aure ba. Hakan ya fi saka ta kwanciyar hankali. Haka kuma ba ta tambayarshi komai sai in fita unguwa za ta yi. Game da kudi ko wani abu ba ta ce masa tana son kaza, sai abin da ya kawo ya ba ta. In ko kudin makaranta ne, sai dai ta kawo masa takardar banki na islamiyya kuma da ma na shekara yake biya mata. Daga cikin kudin motanta *yar dari biyar din nan take makalewa shine take siyan dan kayan bukata irin na mata. Aliya dai tun tana boye damuwarta na rashin samun ciki, har ta dawo tana nunawa. Sai dai ta kan ji sauqi kadan in ta tuna cewa ba fa ita kadai ba ce ba tayi cikin ba, ga Salma nan. Shatima kullum yana lallashinta a kan haka, sai yake ganin kamar tana zargin shi ya kasa. Don haka da ta zo masa da batun son neman aiki a asibiti baiqi ba, don yana son ta rage kewa. Ganin in har tana fita aiki za ta dan samu kwanciyar hankali. Ta hanyar abokin aikinsa ya sama mata aiki a asibitin Kawo, Amna kuwa wata plaza yayanta ya siya a kan titin Ahmadu Bello da ke Kaduna, don haka Momi ta ce a ba ta shago daya don ta zuba kaya. Shago biyu aka ba ta tunda suna tausaya mata, suna ganin tana auren mara karfi. Daya aka sa mata kayan kicin, daya aka saka mata na yara. Aka nemi masu saida mata aka zuba, kullum take zuwa don da office dinta a ciki. Shatima bai so- ba, amma dole ya yi shiru don ya san ma ba za ta yarda ba ko ya hana ta. Lokacin Jafar wanda suke kira da Junior Mamansa kuma tana ce masa Honey. An yaye shi don shekararsu daya, Nafisa dai ba ta yi niyyar yaye Ashraf ba, sai ya shekara da rabi cif? Sai dai ita ma ta tada balli a kan cewa za ta shiga makaranta, don ko ba za ta yarda ba 18 Mun tsaya Jafar wanda suke kira da Junior Mamansa kuma tana ce masa Honey. An yaye shi don shekararsu daya, Nafisa dai ba ta yi niyyar yaye Ashraf ba, sai ya shekara da rabi cif? Sai dai ita ma ta tada balli a kan cewa za ta shiga makaranta, don ko ba za ta yarda bace kullum tana gida kowa ya fice ba. Cikin haka kwatsam sai ga Nafisa ta soma jinya. Suna zuwa asibiti aka ce ciki, Nafisa ta daka tsalle ta ce,Saidai a zubar, Shatima kuma ya ce, wallahi in ta sake ta zubar masa da ciki zai mata hauka, za ta sha mamaki. Rikicin da sai da ya kai su gaban Mamanta, inda Mama ta yi mata tas, ta kuma cc kar ta sake jin makamanciyar irin wannan maganar. Dole Nafisa ta zo ta dangana, amma sai da Shatima ya nemo mata mai aiki saboda kulada Ashrat, tunda ita laulayinta ba ya mata da wasa. Wani abu da ya sa Shatima cikin wani mugun Bacin rai, Amna ta saka Jafar a makaranta mai matsanancin tada. Ajin wasan yara, kuma sai da ta kaishi ta yi komai ba tare da ta sanar da shi ba. Sun yi rigima sosai ba tare da kowa ya sani ba. Kinyarda da ka^idojin da ya saka. mata ne na cewa, lallai ta ciro yaron daga makarantar domin dan ikonsa ne ba nata ba. Abin da ya sake bata masa rai da ya kira mahaifinta ya sanar da shi, sai ya nuna cewa, ai shi ta taimaka kasancewar ba ta ce ya bada kudinshi ba. Haka kuma ita ma tana da ikon yi wa dan komai tunda ita ta haife shi. Rikicin bai Kare ba, sai da ta kai kara gurin Hajiyarsa. Hajiyarsa ta hada su ta yi musu nasiha inda ta nuna ma Amna cewa ba wai laifi ba ne don ta saka dansu a makaranta, amma komai ya zama cewa za su ke yin shawara. Shi kuwa Hajiya ta ce ya yi hakuri komai ya wuce. Da ma Aliya ita ce ta yi ta kara tunzura shi. tana nuna masa cewa kan ya yan zai bambanta in har ba makaranta daya suke zuwa ba Sannan yaran Amna za su raina shi a nan gaba matsawar suka gano cewar uwarsu ce ta ke yin dawainiya da su, shi za su ga kasawarshi. Irin wannan zantukan na Aliya suke saka shi jin tsanar Amna da jin zafinta. Bugu da Kari, Amna ta je ta saka maganin hana daukar ciki don tace masa baza ta iya haihuwa duk bayan shekara biyu ba. Nan ma sun sha rigima da jin zafin juna. Ranar wata litinin Salma sun je makaranta, sai aka ba su hutu domin mataimakin shugabar makarantar ya rasu, Salma Dankasa ta ce bari ta je gidan su Salma Bash sai ta yi waya a z0 a dauke su tunda direbansu ya wuce. Su Amina Hamza da su Jamila A Ramalan sukace suma za su je. Salma kuwa ta ja su suka je, ta yi musu girki suka ci, suka sha hirarsu har suna tambayarta wai nan sashenta ne ita daya sai ka ce wata matar aure? Salma ta ce, ai yayanta yana ji da ita, "Ni yayan nata ne ma wallahi ya yi min, akwai aji Salma dai ta bi su a haka, kowa ta nufi gidansu, Salma kuwa direbar,u ya zo ya dibe su da kannanta. Aliya aikin rana gare ta, tana gida lokacin, nan ko ta kira Shatima a waya ta ce, ga Salma nan ta debo zugar " yan makarantarsu sunzo suna ta yi wa mutane hauka. Nan ko Shatima ya cika dam, don in har Aliya ta fada mishi magana tamkar wahayi ba ya bincike. Ya kira lambar Salma a kashe, bai san ta yi wata ba ta da waya ba. Domin wayarta da Baban Nafisa ya sai mata ce kuma ta samu matsala. Yana dawowa dakin Salma ya nuta, tana zaune tana yanke farce. Ya fado tare da sallama. Cikin tsoro Salma ta dube shi, tareda amsa sallamar. Yace, "Wane zugar yaran ki ka debo min zuwa gida yau?" Ta zaro ido, cikin rawar baki tace "Salma ce fa da Kannenta. Ya katse ta, "Wace Salma? Na lura rawar kai yana damunki, in kin yi wasa zan cire ki daga makarantar nan. Ina son ki sani kar ki sake ki sake janyo min wani tarkace gidan nan" -Jikin Salma a sanyaye, cikin sanyin murya ta ce,Ka yi hakuri, insha Allahu ba zan sake ba" Tsaki ya ja, sannan ya juya ya fita. Sannu a hankali su Salma suka yi jarabawar shiga S.S 2 suna gida suna hutu, sai dai islamiyya,Lokacin Shatima ya samu karin girma a gurin aikinshi inda aka maida shi ofishinsu da ke Abuja. Hakan ya sa sai bayan sati daya yake zuwa Kaduna, Nafisa ya fi tafiya da ita don ita ce ba ta zuwa ko'ina, Aliya ba ta so hakan ba, amma babu yanda za ta yi tunda ga aikinta. Cikin haka Nafisa ta haihu, danta namiji. Wannan karon a gidan Shatima aka sha suna, inda yaro ya ci sunan Alhajin su Shatima. Tunda ta haihu ta lashi takobin cewa fa sai ta yi tsarin iyali, kuma sai ta koma makaranta. Lokacin ne Shatima ya samu damar biya musu kudin aikin hajji shi da Aliya. Da lokacin tafiya ya y矛 suka tafi, Aliya ta tsananta rokon Allah a kan haihuwa.Ta yi roko sosai, ita dai Allah ya ba ta haihuwar ya'ya maza ita ma. Da aka gama aiki ta hakuri, kuma ta Kara kyau da yar Kiba.Lokacin tafiyar ne dai kansu tafi har aka yi dan rikici, Nafisa ta nuna damuwarta, tare da koratin yanda yake nuna Aliya ta fi kowa, shi ya sa ma zai je makka da ita. Ya ce, ba haka ba ne, duk yana sonsu don dai ita babba ce, kar ta damu duk za su je. Amna kuwa ko a jikinta don Saudiyya ba bakuwarta ba ce. Salma kuwa ba ta ji batun tafiyar ba har sai da suka z0 mata sallama, har Aliyar tana fadin a yafi juna. Sun yo tsaraba, ko da Aliya ce ta yo tsarabar,don shi bai siyo komai ba tunda ba zuwanshi ne nafarko ba. Ana ta rabon tsaraba, Salma dai an ba ta wata "yar yaloluwar riga kamar ta bacci, ita dai ta yi godiya ta amsa. Cikin ikon Ubangiji ko wata ba a yi ba sai ga Aliya da ciki, murna gurinta da shi kanshi Shatima ba a magana. Nan ko ta shiga kaudi da salo, Shatima kuma ya kama biye mata. Ita Salma yanzun damuwarta daya, duk yan ajinsu mafi yawa za su yi SSCE, ita ma ta so a biya mata, amma tana tunanin tunkarar Shatima, ga shi an kusa bikin Badi'atu da su Hamida, da Mami kannen Nafisa. Ta sani duk harkar kudi ce shi ya sa ta kasa tunkararshi da zancen. Zuciyarta tana yawan fada mata cewa, ta same shi kawai ta ji abin da zai ce, amma ta yanke shawarar sai in ya dawo dakinta za su yi maganar.ranar da ya dawo dakin nata tana jinshi yana kallon labarai amma ta kasa yi masa magana. Sai ta yi kamar ta tashi, sai kuma ta koma ta sauna. A karo na uku ne ta yi ta-maza ta tunkari dakin. Sanye ta ke da kayan bacci masu dan kauri, don yanayin sanyi ne lokacin. Duk da cewa, ba wannan ne karo na farko ba da ta shiga dakin, amma bai hanata diriricewa ba, kamar dai kowane lokaci in ta shiga. Yana kwance tsakiyar katifar ya ware A.C duk da sayin da ake yi, amma ya rufa da bargo. Hankalinsa kaf yana kan talabijin da yake kallo. Ya maido da kallonsa ga kofar da aka turo, ya kalli fuskar Salma sosai, kaman mai yin nazari a kan abin da ta z0 da shi. Sannan ya sake maida kallonshi ga labaran da yake kallo. Ta rusuna gwiwa biyu a gaban katifar, sannan tace, "Ina yini Yaya?" Ya amsa ba tare da ya sake kallonta ba. Hakan ya sa ta ji dan karfin gwiwar da ta shigo da shi ta rasa. Jin shirun ya yi yawa yace "Lafiya?" Ta dago ta dube shi, har lokacin idanunsa suna kan talabijin, tace *鈥aya dama na z0 ne. Sai kuma ta yi shiru.Ya dube ta, "Kinzo me?" Cikin sauri ta dube shi. Ya tsare ta da idanunshi ta sake sunkuyar da kai, "Yaya a ajinmu ne aka ce duk wanda yake son ya zana jarrabawar fita, to ya biya sake yin shiru, ga sanyin A.C din ya soma ratsa ta, har ta soma kaduwa Ya ce, -Ke kina ajin fita ne?" Page 19 Mun tsaya Ta dago ta dube shi, har lokacin idanunsa suna kan talabijin, tace *鈥aya dama na z0 ne. Sai kuma ta yi shiru.Ya dube ta, "Kinzo me?" Cikin sauri ta dube shi. Ya tsare ta da idanunshi ta sake sunkuyar da kai, "Yaya a ajinmu ne aka ce duk wanda yake son ya zana jarrabawar fita, to ya biya sake yin shiru, ga sanyin A.C din ya soma ratsa ta, har ta soma kaduwa Ya ce, -Ke kina ajin fita ne?" Ta Ce "A'a. 'yan dai ajinmu ne mafiyawa an biya musu za su fitan; shine ni ma nace bari in fada maka ko kana da halin biya min Ya yi shiru yana kallonta yanda take kaduwa kanta a Kasa ya san sanyin A.C dinshi ne, sai ya dauki remote ya kashe, sanan ya canza harshe daga Hausa zuwa Turanci. "Ba ni da tabbacin kin san me ki ke yi a makaranta har da zan biya miki ki yi jarabawar fita"Ita ma cikin harshen Turanci ta ce, "Yaya bari in debo maka dukkan sakamakon jarabawa ta ka gani,har ma da kyauttukan da na yi ta samu a lokaci daban-daban in za mu yi hutun canjin aji". Ya daga hannu, "Barsu, kar ki kawo min me yasa ba ki nuna min ba, tun a lokutan da ki ka same su?"Ta ce, "Yaya ina tsoro ne kar in maka magana ka.Ya katse ta, "In cinye ki? Ko ba haka ba ne? kina tsorona kar ki fada min in cinye ki mana!"Cikin d盲ga murya ya ce, "Bari in fada miki wani abu. Zan biya miki kudi ki yi jarabawa Amma ina son ki sani matsawar ki ka fadi jarabawar ko ki ka rasa darasi daya aciki, to fa kin gama karatun boko. Baza ki je jami a ta Cikin sauri ta ce, , "Na yarda Yaya".YaCe. "Shi kenan, ki je zan je makarantar taku Tace "Na gode sosai da yawa Yaya" Bai ce komai ba, ta tashi ta fita. Suna cikin aji a zaune suna rubutu, sai ga wata ta z0 tace "Salma A Bashir ta zo" Tana zuwa ofishin shugaban makarantar sai taga Shatima. Sun tabbatar masa zata ci jarabawar domin duk ajin an san Kwazonta. Shatima ya biya aka ba shi takardar shaida, ita kuma aka ce ta koma aji in an tashi tazo za a yi mata hoto da sauran abin da ya rage. Kwanci tashi lokacin jarabawa ya yi, Salma suka zana suka koma gida jiran sakamako da kuma lokacin zana jamb. Cikin wannan hutun ne bikin su Anty Badi atu da su hamida, Don haka ta tattara dukkan kokarinta ta bada shi a islamiyya da hadda. Balle yanzun da ta ke ajin sauka. Wata juma'a Salma tana tsaka da muraja'a sai ta ji sallamar Salma Dankasa, da murna ta tare ta suka rungume juna. Ta kalli Habiba Sulaiman ta ce,Yau wace rana ga ki a gidanmu?" Habiba tace Duk suka sa dariya.Sun zauna ta ba su abinci da na sha, suka ba ta katin biki da anko na bikin Habibar ne. Salma tana juya katin ta ce, "Ku saka ni a addu'a a bar ni zuwa wannan biki ko da rana daya ne" Salma Dankasa ta zaro ido,Har yanzu bai daina takurawa a kan fita ba yayan nan naki?"Salma tace "Har yanzu baya bari. Sai dai wani lokacin ba na ganin laifinshi in na ga yanda 'yammata ke lalacewa a wannan zamanin namu. Bugu da Kari ina karanta littattafai ina Kara samun wayewar kai"Habiba ta ce, "Dalilin Babanmu kenan da ya tattara mu yace aure. Har da Fatinmu wadda ko sakandire ba ta gama ba. Sai dai ya lura tana da janye janyen kawaye Salma Dankasa ta ce,' "Mu ko Babanmu yana da son karatu, kuma ba ya kawo komai a cikin ransa game da mu. Sai dai mu ma fa muna karance-karance mun san abin da zai cuce mu, don haka waye zai kai kanshi?" Sun yini sannan suka tafi. An kusa sati Salma tana tufka da warwara kafin ta iya tunkarar Shatima da katin biki, cingam da kuma anko. Ranar yana dakinta tuwon shinkafa ta yi da miyar ganye Shatima yana cin duk abinda ta girka yanzun, musamman in ta yi abincin gargajiya. Domin ta koyi kalolin girki a cikin littattafan Hausa da take karantawa. Ranar dai ta yi karambanin gyara masa dakinsa,don kullum tana son ta gyara, amma tana jin tsoro. Wani lokacin ma kulle dakinsa yake yi. Ta goge kayan wutar ta sa turare, sannan ta jera masa abincin. Tun kafin ya dawo sallar isha ta gama komai, Da ya shiga dakin ya yi ta kallon ko'ina dakin yana ta kamshi da kyalli, babu kura. Ya yi wanka ya saka jallabiya ya zauna kan katifar yana cin tuwon cikin nishadi, har yana zance da zuciyarshi cewa,akwai kuwa abin da ya kai tuwo dadi? Ga labarai yana kallo abinshi. Salma ta yi sallama tare da dan tura kofar. Ya amsa idanunsa na kan wayarsa da ke ringin. Ya daga yana waya, ta kwashe kwanukan don ya gama ci. Ta dawo ta tsuguna tana jiran ya kare wayar da Hajiyarshi suke magana a kan bikin Badi' atu. Da ya gama ya dube ta, "Mene ne kuma, don na san ke ba a ganinki sai kina da bukata' Fadin hakan yasa ta kasa magana. " Yace Ina jinki" Ta Ce, "Da ma yaya zan tambayi zuwa bikin 'yar ajinmu ne". 鈥� Ta kai karshen zancen cikin faduwar gaba da zullumi. Ya tsura mata ido kamar mai tuhumarta, yace, "Wace ce " yar makarantarku?" Ta zazzage ledar hannunta, ya bi cingam da katin da kuma kyallen da kallo. Ya sa hannu ya dauki katin ya karanta, sannan ya aje ya dauki kyallen, "Wannan kuma fa?" Ta ce, "Kyallen anko ne'.? Ya Ce, "'Maimakon a sako zanin sai a sako kyalle?"Ta ce,Sun saka ne in mutum ba zai saya a hannunsu ba sai ya yi amfani da wannan kyallen' Ya ce,Nawa suke saidawa?"Ta ce, "Dubu uku ne yace "Ina ne ake saidawa ' Ta ce, "A sabon Kawo ne gidan su amaryar Ya ce, "To su kawo miki amma a cikin bashi da kike bina zan sai miki"Ta tsura mishi ido, "Wane bashi?" Ya ce, "Dubunki hamsin da na ara, ai ban manta ba Salma ta CE, "Yaya tun a ranar na fada maka ba bashi ba ne, baka fa na yi" Ya ce, "Ni ma tun a ranar na fada miki cewa ba shine. ki kira su kawo miki zanin Ta ce, "Ba ni da waya, ta lalace Ya tura mata karamar wayarsa, "In kina da lambarta kira Salma tana ta mamakin yayan nata a yau. Ta juya bayan katin inda ta sa Habibar ta rubuta mata lambarta, ta ce,Yauwa, ga lambar Ta sa lambobin ta kira, babu kati, ta dube shi, "Babu kati a wanna layin Ya turo mata katuwar,Kira da wannan Ta dauki wayar cikin tsoro tana juya ta, ba ta san ina za ta shafa ta kawo ba. Ya kalle ta,Shafa tsakiyar" Tana shafawa wayar ta kawo. Hoton Ashraf da Junior da Shahid ne. Ta tsura ma yaran ido. Ba ta san a fili ta ce, "Suna kama". Ba sai da ta ji ya ce, "Duk ni suka biyo Ta yin murmushi, sannan ta soma saka lambobin. - Habiba ta daga, Salma ta ce, "Ni ce Salma Bash"Habiba ta ce, "Oho, ya ki ke?" Suka gaisa, ta ce, "Ina son anko guda daya, su Salma Dan kasa sun amshi nasu?" Ta ce, "Gobe da safe, za ta zo ta amsa". Salma ta ce, "Ki bata nawa ki ce ta bada a yi mana dinki iri daya da nata Page 20 Ta ce, "Zan ba ta, ba za kisai na dinner ba?"Salma ta ce, "Dinner kuma?" Ta kalli Shatima, "Kuma karfe nawa ce dinner Din Habiba ta ce, "Karfe tara dai za a tafi". Salma ta ce, "Wai! Ba za a bar ni ba. Ki dai ba ta atamfar sai ki z0 ki amshi kudin". Ya ce, "Ko ta turo account dinta" Salma ta ce, "To ki turo account dinki zan tura da kudin dinki don Allah ki ba Salma" Ta ce, "Zan ba ta"." Suka yi sallama, Shatima ya kalle ta, "To me za ki je mata tunda Dinner ta yi dare?" Ta ce,Kamu za ni" Ya ce,Har da maza?" "A'a ban da maza". "Shi kenan"Har za ta mike, sai ta ce, "Ina son ma nayi magana da Anty Badi'atu" Ya kalle ta, "Kina son cinye kudin cikin wayata ko?"Ta girgiza kai, tare da yunkurin mikewa. Ya ce, Kira ta dai minti biyu za ku yi". Salma ta yi murmushi, sannan ta soma saka Lambar Badi atu. Sai sunanta ya fito ya saka mata sister. Ta daga tare da fadin, Yaya Salma ta ce, "Na'am Badi"atu tayi dariya,Salma ya ki ke?" Ta ce, Lafiya lau, da ma kwana biyu ba mu gaisa ba. Bikinki saura kwana sha tara ko?"Badi' atu ta ce,Au kina ma tambaya ne?" Nan Salma ta sa dariya, "Ina dai son in kara tabbatarwa ne"Badi' atu ta ce, "To saura sati biki za ki z0?" Salma ta ce, "Sosai ma tun saura sati daya zan zo Zaria tare za mu raba kati" Hira ta yi wa Salma dadi har da zama dirshan kamar ma ta manta cewa a waya take magana, kuma ta manta da aron wayar ta yi, ta manta da mai wayar a kusa da ita, suna ta tsara yanda shagalin zai kayatar. Shatima shiru ya yi yana kallon Salma komai in tana yi burge shi take yi. Bai taba ganin tana hira haka cikin sakin jiki ba, ya kasa katse ta sai kallonta kawai yake yi. Har sai da ta ji daga ciki an soma gargadin saura minti daya kudin su Kare. Da sauri ta dube shi tare da ciro wayar a kunnenta ta katse, sannan ta ce, "Yi hakuri Yaya Sai ta ga ya yi murmushi, "Kin manta kina waya ne ko? Kati fa na zuba ba wai bonanza ba ce" Da hannu biyu ta mika mishi wayar tare da sake maimaita," "Yi hakuri" Ya dubi gefen katifarsa, ta gane nufinsa ta aje masa a gurin, don haka ta aje ta mike cikin sauri ta fita. Ya bi ta da kallo. Ranar kamu ta kama alhamis, karfe biyar aka rubuta a jikin katin. Salma ta so bari sai karfe shida saboda sanin wannan mummunar al'adar ta African time, amma kuma ta san in ta kai shidan nan Shatima zai iya dawowa, kuma zai iya hanata tunda ya san ya bata kudin motarta dubu daya, kuma yana zaton tunda rana za ta tafi biyar da rabi ta gama kwalliyarta,ta yi kyau cikin anko, dauri mai hawa-hawa ta yi don yanzun ta kware sosai grin tsantsara kwalliya da kuma daurin dankwali. Takalmi mai tsini ta saka,mayafi da 'yar poss dinta mai igiyar chain. Sun dace da atamfar, _ tana kulle kofar dakinta, Shatima yana shigowa. Har zai wuce-sai kuma ya tsaya, ta nufo shi bayan ta gama rufe Kofar ta rusuna, "Yaya sannu da dawowa 鈥� Ya daure fuska, *"Kina nufin cewa yanzu za ki tafi?禄 Gabanta ya fad矛, ta ce,Ai Yaya da yamma ake Yin kamu fa".Kina nufin titi za ki tafi yanzu a haka ki hau mota?" Ta ce, "Ai dole mota sai a titi" sai Ya je ya yi baya da mota ya juya, daidai ita ya tsaya sannan ya ce, "Shigo in kai ki" Ya kalli fuskarta bayan ya miki layin nasu don zuwa titin, yace Da haka za ki biyo ta nan da wannan shafe-shafen? Dubi maza cike a nan Ta yi shiru. Suna shiga sabon Kawo ya ce, "To inane gidan?"Ta zaro ido, "Lah na manta in z0 da katin saboda duba adress . Ya rage tafiya yace "Au da ma haka za ki zo Kiyita garari a layi Ta ce, "Wallahi yaya na manta katin ne Ya nuna wayarshi a caji, "To dauki waya Ta ciro wayar cikin murnar ta samu madita sai kuma ta yi turus da ta tuna ai a bayan katin na rubuta lambar Habiba. Shatima ya ja tsaki tare da fadin, "Ki hakura da bikin bari mu juya gida .Cikin sauri ta CE, Bari in kira Salma Dankasa, har ta sare saboda Salmar ba ta daga ba,domin wannan ne kashi na biyar da ta kira Salma amma ba ta daga ba. Gab da tsinkewar kira na shida,sannan Salma ta daga, Salma cikin fushi ta ce ma Dankasa, "Banza kawai mara aji, ina ki ka aje wayar?"Ta ce, "Salma Bash, Allah ban san ke ba ce. Wayar tana hannuna na zaci wani ne da yake ta damuna, naqi dagawa a zatona shine ya canza lamba"Salma ta ce, 'Kuna ina ne yanzu mun shigo Sabon Kawo, ga shi ba mu san adireshin ba" Salma tace, "Ga amarya ta yi muku 'kwatancen inda muke tare za mu tafi da ita' Habiba ta yi musu kwatance, ashe ma suna kusa da gidan, ta ce, "To Salma Dankasa ta fito mu ganta a waje Daidai gate din suka samu Salma, ita ma ta yi kyau cikin anko, ta sha kwalliya. Ta zo da sauri ta gaida yaya, Salma za ta fita ya ce, "Kar ki kai magriba Ta ce, "Yaya yanzun fa karfe shida, kuma Karfe bakwai saura ake yin magariba, ga shi kuma ko ramarya ba a dauka ba". Ya ce, "To yanzu karfe nawa ki ke nufin za ki dawo?"Tace Sai dai mun je ko ba a tashi ba ni sai in dawo Wannan shi ne karo na farko da za kiJe biki. To ki sani ana wanke tukunya don gobe ne" Salma tace "Insha, Allahu zan dawo da wuri". Ihu suka saki lokacin da suka hadu da sauran Kawayensu. Amarya kuwa ta ci gayu sosai ana kan shirya ta. Sai kusan magriba suka isa hall din, inda suka dafa wa amaryarsu zuwa gurin zamanta. Da yake har da kanwar Habiban ita ma da nata Kawayen.Ango sun shigo da abokansa, sannan aka yi kamu kawayen amarya da amarya sun shiga rawa ana ta ruwan kudi. Salma duk ta tsorata da wani saurayi cikin abokan ango da ya zo yana yi mata liki. ta canza guri ya bi ta, har dai ta fita a filin ta samu guri ta zauna. Sam ba ta ji zuwansa ba, sai magana ta jita bayanta, "Yammata kin gaji da rawar ne?" A tsorace ta kalli gurin da yake, sannan ta kauda kai. Ya ja kujera ya zauna, "Ki fada min sunanki da kwatancen gidanku" Page 21 Salma ta firgita matuka gani take ma magana ma idan ta yi wa wannan mutumin alhaki ne, amma dole ta tanka ko don ta roke shi. Ta dube shi, sannan ta -waiwaya baya ta kalli gefe da gefe, sannan tace "Ina da miji bawan Allah, ni matar aure ce Ya yi dariya,. ' "Ta ya ya zan yarda da ke? Ba kiyi kama da matar aure ba. Ni sunana Yusuf Bashir, muna zaune a Malali, dalibi ne a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria, kuma yanzu ina shekara ta karshe, ina karantar. Salma ta daga mishi hannu, "Malam, don Allah ka tashi a nan! In kuma ba za ka tashi ba ni bari ka ga". Ta mike da sauri ta koma filin, ta rike hannun Salma Dankasa, tace Salma zan tafi gida, ku zo ku raka ni" Salma Dankasa ta dube ta, "Haba don Allah,yanzu fa aka fara, kuma ko abinci ba ki ci ba". Ta ce, "Kin san da ya yaya aka bar ni? Don Allah ni dai zan tafi, ga shi gurinmu da nisa, zan iya rasa abin hawa fa" Salma ta ce, "Ki bari komai yayi dai dole akai ki har gida" Salma ta hakura ta ci gaba da zama, amma a darare. Ko da aka soma ciye-ciye Salma kawai ta yi ta ajiye. Ta kalli agogonta, tara saura ta mike da sauri ta nufi gurin Salma inda suke ta daukan hotuna. Tace "Salma ko ba za ku raka ni ba Nina wuce dare ya yi Salma ta ce je ki sallami amarya in raka ki, tunda kinki bari a tashi Sukayi bankwana har da sauran kawayen suka fito don raka ta, Salma tana rike da jakar da aka raba ta biki, suna fita hall din sai ko saurayin da abokansa guda biyu ya tsaida su. Salma ta kalle shi ta ja tsaki, ta ce, "Don Allah ku zo mu je" Ya dubi Salma Dankasa, ya ce, "Don Allah ki shiga, maganata da kawarki. Ina sonta na fada mata, amma ta ki ta saurare ni Salma tace Ba kada matsala, ZanYi magana da ita, kuma za ka ji sakamako Ya ce, "Za ku tafi ne in kai ku?"Salma Dankasa ta ce, "Yauwa gida za ta ka kai ta Salma cikin daga murya, tace Dankasa kina hauka ne? Ya kai ni ina?" Cikin fushi ta wuce fuu ta barsu tsaye. Duk suka saka dariya Kawayen Jamila Umar ta ce, "Na ras脿 mai yasa Salma ba ta so ace ana sonta sam Dankasa tace "Yayanta take tsoron. Amma ku zo mu je". Ta dubi saurayin, "Yusuf mu raka ta ka kai ta mu dawo tare kafin a tashi. Amma bari ka ga dabarar da da za a yi a wace mota ce?"Ya nuna motar, tace "Jamila bita ki lallashe ta, ku shiga motar, don ni yanzun ina je fada za muyi Da Kyar Jamila ta sha kanta suka shiga motar.duk baya suka zauna ta nuna ma Salma motar saurayinta ce Fatima ma ta zo ta shiga, Dankasa ta shiga gaba. Sam Salma ba ta san wake jan motar ba,sai da suka hau babban titi. Ta ji haushin ganin Yusuf amma sai t脿 yi shiru don yanzun ba ta da burin da ya wuce ta ganta a gida. Kafin su Karasa gidansu ta ce, "Ku aje ni nan in karasa' Yusuf yace "Bari dai mu karasa ina ne gidan?" Dan Kasa ta nuna mishi da hannu, "Ga gidan Can Salma tace "Subhanallahi, kada ki ja min matsala. Salma wallahi kar fa ya zo gidanmu Salma tace "Eh ba zai zo ba, ku ke yin waya Salma cikin gadara tace, "To ki ba da lambata?" Ta bude motar ta fita, Salma ta saki dariya, "Na tuna ba ta da waya Ita dai ba ta waiwayo ba, burinta ta shige gida.Allah ya sa lokacin Shatima ba ya gida, goma saura ya shigo sasan Salma. Tuni ta cire kayanta tayi sallar isha tare da shirin bacci ya juya ya fita. Bikin Badiatu ya kusanto, Aliya kuma an shiga watan haihuwa, in tana tafe ta dafe kugu, Salma takan sha dariya domin dai tana ganin masu ciki kala-kala, amma ba ta ga mai gwadare irin na Aliya ba. Ko su Amna dai iyayen son jiki ba ta ga tana irin wannan yatsinar ba. Salma dai ta yi sabbin dinkuna ban da wanda Shatima ya yi musu, kudinta da ta ke dan makalewa ta ba Salma Dankasa ta sai mata ya diddika irin nata masu kyau ta bada aka dinko mata su, sun yi kyau sosai kayan. Salma ta zaci Shatima zai barta tun ana saura sati daya bikin, sai ya daure fuska ya ce, ba ya son shirme. Da kyar da rokon da Badi'atu ta yi ta masa ya barta ana sauran kwana uku biki, cikin kawaye Salma ta saje suka sha lalle ana ta shirye-shirye. Bikinsu uku ya tara mutane sosai, Salma ta yi aron kudi dubu goma gurin Yaya Hadiza da ta kwashi adashe za ta canza gado, Salma ta ce, "Don Allah ta ara mata ta yi wa Badi'atu gudunmuwa ta kashe kudinta duka ne, amma da zarar an gama bikin za ta tara ta biya ta. Wani saitin agogo ta sai mata mai guda uku dubu goma sha daya. Sun yi kyau sosai kowa ya gani sai ya yaba, Nafisa da Salma dama rana daya suka zo. Amna cewa, ta yi ita sai ranar biki. Aliya kuma shida kanshi ya ce ta bari sai ranar biki. Salma gidan Hajiya Kaka ta sauka gidan Kaka don za ta fi sakewa, can jama'a tayi yawa,Amna gidan Anty Momiyo suke da Badi'atun da kuma kawayenta. Duk shagulgula tare aka hada da nasu Hamida kamar kamu, sisters day da sauransu. Dinner ce wadda abokan ango suka shirya ita ce ta Badi"atun kadai, wadda aka yi ana gobe daurin aure da zasu wuce zuwa Katsina inda mijin Badi'atu yake aiki, domin Costom ne babba. Amarya ta yi kyau har ta gaji a gurin Dinner,su Salma an sha gayu babu yanda za a yi ka ce tana da miji. Sai faman kashe hotuna suke yi da sauran kawaye da 'yan uwansu Shatima sa'anninta, lokacin da aka zo soma rawa su Salma mazari nan suka shige tare da amarya ana ta rawa, "yan uwa da abokan arziki suna ta yi wa amarya liki. Kallo sai ya koma sama lokacin da wani ya zo yana yi wa amarya ruwan "yan dubu-dubu. Gurin ya Dauki ihu, Salma ta tsura masa ido cikin mamakin ko wane ne wannan,ga shi ita kadai yake wa likin ban da ango. Da ya gama kuma ta ga ya nufi kujerar da su Anty Momiyo suke zaune, Salma ta taba Aishan Anty Momiyo tace, *Wai wane ne wannan?" Aisha ta ce, "Yaran yayansu mamanmu ne. ya so Anty Badi' atu sosai ta ki yarda". Salma ta ce, "Shi ma yana da mata?" Aisha ta ce, *A'a, ita dai ya so ya aura, ga shi yana da kudi sosai, kasuwanci yake yi komai suna yi irin su shinkafa, taliya da dai sauransu' 8/22/22, 17:00 - Ummi Tandama馃槆: 馃摎3锔忊儯 Page 22 Salma tace "Kash! Da ma ta yarda ga shi mai kyau. Wannan ko ga shi har da mata da yara biyu" Aisha ta ce, "Ai kowa ya ji haushinta bare Hajiya. Babanshi shine babba a dakin su Hajiyan fa,kuma ya rungume su kamar me, komai shi yake musu don shi ma dan kasuwa ne. yana da kudi, da dan ne ya taso sai ya fi uban kudi" Salma ta ce,Allah ya yi wannan ne mijin nata Aisha ta ce, 'Kuma haka ne, Allah ya ba su zaman lafiya Sunanta da ta ji Imran ya kira ne ya sa Salmawaiwayawa da sauri. Imran Kanin Aisha ne, ya ce,Anty Salma wai ki zo Ta ce, 'In ji wa?"Ya ce, 'Ke dai ki zo" Ta bi shi ta gun su ta fit脿 waje. Tana mamaki sosai ko su wane ne? dan Yaya Hadiza da Inna su ne za su zo mata, amma sai gobe gidan daurin aure. Har Kosawa ta yi sukai ta ga ko wanene. mamaki ya kamata ganin Yusuf. Da sauri ta isa gurinsu tana fadin, "Na shiga uku, wa ya ce ku zonan? Me ya kawo ku?" Tana yi tana waige-waige. Duk ta firgice. Ya ce,Kwantar da hankalinki mana, mene ne don na zo miki biki? Salma kawarki ita ce ta bani katin bikin yayarki, Tun yamma muka zo ni ma ina da yan uwa a Kaura, can muka sauka shine na ce bari mu zo Dinner, gobe mu je miki Daurin aure daga nan ma sai ki gabatar da ni" Salma tace "Yusuf ka taimake ni., wallahi ni matar aure ce, ina da mijina fa" Ya ce.Salma sai dai kawai in ba ki sona kawai ki fada min, amma Salma kawarki ta tabbatar min cewa ba ki da wani miji": Salma ta ce, "Ai ba ta sani ba ne. to na ji din ma bana sonka, don Allah ka tafi mijina yana nan gurin auren kanwarsa ake yi fa" Ya ce, "Ni dai ban yarda da zantukanki ba, ki kai ni kawai yanzun gurin danginki". Abokinsa da suka zo tare kuma ya ce, In kina jin kunya ko tsoro fada mana gurin wanda zamu, sai mu je da kanmu. In kuma sun fi son ganin magabatanmu sai su zo" Ganin mutane sun fara fitowa daga dakin taron sai Salma ta yi baya da gudu, jikinta yana bari ta nufi cikin dakin taron. Karo ta ji sun zabga da wani, a rude take fadin, "Subhanallahi禄 " Domin wanda suka yi karon yana kokarin fitowa ne, yana yin waya. Wayar ta fad矛 kasa, cikin sauri ita da shi suka kai hannu da nufin dauka. Salma ta riga shi kai hannu ta dauki wayar kirar Samsug ce wadda ake yayi, karshen tsada a wannan lokacin. Ta juya wayar a hannunta bayan wayar ya yi kwatsa-kwatsa dai shi ma bayan gilashi ne. da sauri ta dago ta kalli mai wayar da nufi ba shi hakuri, sai ta kasa ganin wanda ya yi wa Anty Badi'atu ruwan kudi ne. ga shi ya zuba mata ido yana kallonta, bakinta yana rawa tace "Don Allah ka yi hakuri. Bai ce Kala ba sai kallon Salma yake yi Ta mike da sauri ta nufi ciki tana yi tana waiwayenshi, shi yana tsaye yana kallonta mamakin barnar da ta mishi ne yake yi mata irin wann谩n kallon, ko kuwa mene ne dalili? Gurin da su Aisha suke ta nufa, ta ce,Ina mayafin kuma?" Ta taba kafadarta, "A'a ina to mayafin?" Ta soma waige-waige, ta kalli Aishan, "Bana baki ba? Tace, "A ina ki ka ba ni?禄 Salma ta ce, "'Tun da za mu yi hoto" Aisha ta ce, "Kuma da aka zo kiranki bakin karba ba" Salma ta ce, "Allah dai ya sa ban yar ba Ta soma dube-dube, ba ta ganshi ba ta soma duban inda za ta hango Shatima. Ta kasa tashi daga inda take zaune duk ta tsani taron ta kosa a tashi. Ta mike tare da fadin, "Bari dai in duba gurin can da na buge ma mutumin nan waya" Ba ta ga mayafin ba sai su Shatima da ta hango shi da wannan da suka yi karo suna magana a gurin motocinsu, Muryar Yusuf ta ji yana kiran Salma. Da sauri ta dubi gurin su Shatima don ta tabbatar bai ji kiran sunanta da aka yi ba, kuma cikin sa'a Shatima ya ji kiran tunda tsakaninsu babu nisa, domin ta ga ya kai dubanshi gurin Yusuf din, sai ta yi sauri ta juya cikin addu' ar Allah yasa Shatiman bai ganta ba. Bayan an tashi ta bi ayarin amarya zuwa cikin motoci suka nufi gida ranar dai gidan Anty Momiyo ita ma ta kwana Tun Karte goman safe suka dawo gidan Hajiya kaka domin nan za a daura aure, duk amaren ma nan suka hadu. Ana ta wanka da kwalliya. Salma ta makale ana gama yi wa amare kwalliya ita ma aka rangada mata, suka sha ankon daurin aure ana ta hotuna. Aliya da Amna sai ga su, Salma tace "Da ma Yaya a daren nan ya koma Kaduna kenan!" Sai ta ji Aliya tana fada ma Nafisa wai Mustapha ya je ya dauko su. Salma ta dauki Jafar yaran Amna tare da fadin. "Zo mu yi hoto" Ko don ganin mutane ne ya san Amna fadin wannan katon za ki dauka? Salma da ma sau daya ta taba daukarshi lokacin da suka dawo ta je ta yi musu barka. Salma ta amshi wayar Aisha tana yi musu hoto, Aisha ta ce, "Ke dai don Allah Anty Salma kisa Kawu Shatima ya sai miki waya, wayar kowa cike da hotunanki Salma ta Ce, "Kuma don Allah kar ki goge min ko daya anjima duk zan tura su a wayar yaya Aliya ta kalle ta, "Shi kuma sai ya ba ki wayarsa babba ki masa wasa" Salma ta Ce, "Ai ba wasa zan masa ba, in ya hana kuma sai in amshi ta Anty Badi atu in nayi Waya sai ta turo min ko ta whatsapp ne Su Inna da Hadiza sun zo ta kawo su gurin Kaka suka yi mata murna. Sun ci waina sannan suka bari su je can gurin Hajiya da kuma gidan su Nafisa su yi ma mama murna ita ma. Bayan an gama daurin aure Shatima ya shigo yana neman daya daga cikin matansa, Amna ya iya samu a waya, ya ce, suna son abinci shi da abokansa. Ta ce, "Ni ina zan je nemo abinci?" Aliya kuma tana Zaune turus tana son gwaninta ga ciki ya yi nauyi, ta ce, "'Amna ta yi wa Anty Momiyo magana" Amna tace "Ni fa gaskiya ban iya surutun abinci ba Salma ta gama saka dayan yadinta, ta yi kyau sosai riga da siket an sha Dauri ta fito kenan Mustapha ya shigo, ya ce, "Kai su Anty na an sha kyau. Yaya na son abinci shi da abokansa' Salma kuwa ta je har dakin abinci ta debo kaloli, tuwo, waina, shinkafa dafa duka da nama da abin sha, tire biyu. Mustapha ya dau daya, ita ta dauki daya. Shatima ya amshe ta tareda fadin, "Sannu Tace "Yaya ina wayarka?"Ya dube ta, "Me za ki yi da ita?" Page 23 Ta ce, Zan tura abina ne daga wayar Aisha ka aje min. bai san dalilin da ya kasa hana taba, illa dai ya ce. "Kar ki yi min wasa da way脿. Tun kafin ta nemo Aishar ta soma daukar sabbin hotuna da wayar ta Shatima ta sake zuwa ta Dauki Jafar suka yi wasu. Aliya ta sha mamaki ganin wayar Shatima a hannun Salma, ta tura duk hotunan da ta yi a wayoyin jama'a sannan ta je ta kai masa. Lokacin saura su 'uku a cikin dakin da suka ci abinci. Ta mika mishi tare da godiya, sannan tace Yaya ni ma fa zan je kai Anty Badi' atu". Ya ce,Ina?" Ta yi shiru don jin yanda ya amsa da karfi. Munnir yace "'Katsina mana Shatima ya hade rai, *Koma ciki malama babu inda za ki je Za ta yi magana ya ce, "Bana son jin komai" Salma jiki babu Karfi ta fita ta koma cikin gida. Dakin Hajiya Kaka ta shige ta takure a bakin ~ gado. Hajiya Kaka da take zaune kan sallaya suna hira da wasu *yan uwansu ta kalli gadon tare da tambayar wane ne nan ya yi rijib a gado? Salma cikin damuwa tace "Nice Hajiya Kaka tace "Salamatu ce?' Salma ta ce. "Ni ce Kaka' Ta ce.A'a na ga kin saka kaya kin fita yanzu?" Salma cikin shagwaba ta ce, *Yaya Shatima ne wai ba zan je raka Anty Badiatu ba, kuma Kaka yadace a ce shi yana babba ya mu hudu matansa ace babu wanda ya je rakiyar Kanwarsa gidan miji?" Kaka tace *Zance yake yi, dole kuwa a samu mai zuwa a cikinku. Ina Shatima, a kira min shi"Salma ta ce, "Sal dai in sa a kira shi kar ya ce Karansa na kawo Hajiya Kaka ta ce, *Kira min Saude ta sa a yi min magana da shi" Salma ta fita cikin murna ta bar Hajiya Kaka tana fadawa wadanda suke zaune tare, kirki da hangen nesa irin na Salma. Tace "Yarinyar nan ga ta karama amma lissafi gare ta irin na manya, ga ta da kokarin kyauta ga girmama mutane Saude ta shigo tana fadin, "Ga ni kaka, ina shiryawa ne za mu kawo amare ki musu fada a kai su gurin iyayensu a zo a tafi, don Badi' atu tuni Alhaji ke waya su zo tafiya da nisa" Kaka ta ce, "To ku kokarta ko a tafi. Yanzu, ban da shirme irin na Shatima a ce ko daya cikin matansa babu mai zuwa?" Anty Saude ta ce Ai ba zai yiwu ba, tunda ita babbar cikinta ya girma ita karamar mu je tare ko kuma Maman Jafar tunda Nafisa babu hali ita wanna ga tsohon ciki' Kaka ta ce, "Kira min shi an ce yana dakin 鈥akina Salma tana jiyo muryar Shatima yana gaisawa da mutane a falo ta shige bandakin Hajiya Kaka. Tana jin lokacin da yace "Kaka ga ni, an ce kina nemana ruwa a jallo Ta ce. "Zauna dan nan ka fada min in ji ko gaske ne. wai babu wanda zai je a cikin matanka Yace 'Me za su je kuma su yi kaka?" Tace Ka ji zancen banza, kai ne fa babba a cikin gidanku, matanka hudu amma babu wadda zata raka kanwarta, ai ko dai da ka ji haushi. Babu wadda fa ta je jere cikinsu' Shatima ya ce, "To wa za shi cikinsu, Nafisa suma cikin hidima suke, Aliya ta yi nauyi, ita ko Amna ba son shiga jama"a take yi ba' Salma ta bude Kofar bandakin ta fito daidai lokacin da Kaka ke fadin, "To ai ga Salamatu" Ya kalli Salma, "Kin zone kin kawo karata?" *Yan dakin suka sa baki da cewa, *Gaskiya matanka ya dace su wakilceka a wanna tafiya' Jin baki ya yi yawa ya ce, "To shi kenan Kaka su je duk wadda za ta" Ya dubi Salma, "Ki same ni a dakin baqi Kaka ta ce, "Kada in ji ka yi mata fada, ba Kara ta kawo ba"Ya ce, "Kar ki damu Kaka kudin shan ruwa a hanya zan ba ta Salma ta kalle shi don ta, ya sakar mata harara. A tsorace tabi bayansh, motarshi ya shiga ita ma ta bude ta shiga. Ya rufe ta da fada, ta sunkuyar da kai yana fadin, "Ke shegen yawo ki kasa a ranki shi ya sa har ki ka kai Karata, ina ta lura da rawar kanki da ki ka kama yanzu. Jiya ina kallonki Salma ta yi saurin dubanshi tare da fadin, "Mene?'Ya ce, "Mayafi ma aje shi ki ka yi ki ka kama yawo haka jiki duk a matse, kina manta cewa kina da aure ma ko?" Salma ta sauke ajiyar zuciya ta godw ma Allah da ya sa iya rashin mayafin ya gani. Ta girgiza kai tare da fadin, "Bana mantawa Allah kuwa Ya ce, "Kuma tunda kin matsa sai kin je ki je din, amma ki sani duk wani motsinki zan sani, sannan kuma ko naira ba zan ba ki ba Ta saki fara'a, "Babu abin da zan yi ma, babu komai in b脿 ka da kudi Yace, "Ina da shi, ba zan bada babe Salma ta ce, "Yaya in har kana ga zuwana din ba ka so Allah a barshi. Da ma dai rashin dacewar aCe mu ba mu je bane kana kai babba shi ya sa har nayi magana Yace "In kin zauna ma me za ki yi min? kije kawai abinki"Ta ce, "To na gode, bari inje in shirya" Har ta fita, yace "Amsa Dubu biyu ya ba ta, ta sa hannu biyu ta karba, ta ce, "Na gode A Katsina gidan amarya ya yi kyau, duk da cewa kowa da barinsa. Ita da kishiyarta amma gida daya suke, irin tarbar da suka samu daga dangin mijin su ne suka saka ran cewa ta karbu gurinsu. kishiyar ce dai sai dai a ce Allah ya kade fitina,domin kanta tsaye washegari bayan an yi budar uwargidan don a hada su, tace "Kar ku ce min amana, don ba a bada amanar kishiya Anty Saude ta ce, "To, mu dai fatanmu a zauna lafiya, zama na amana" Ta ce,Idan ta so haka za a zauna Duk suka sha mamaki, don haka da suka dawo dakin Badi'atu suka yi ta mata nasiha, tare da jaddada mata hakuri. Da za su taho Badi'atu ta sha kuka, haka ma Salma. A Zaria kuwa bayan tafiyar'yan kai amaryaKatsina, Shatima ya samu su Aliya ya ce su shirya su koma don gobe zai wuce Abuja. Amna dama a takure take, nan suka koma gidan Hajiyan Shatima don shiryawa. Aliya kuma ta ce, bari ta je gidansu su gaisa tunda ba taje ba. Har ta ce da zai barta zuwa gobe. Yace a' a, su gama komai zuwa bayan magariba. Ya dauki mota ya nufi gidan su Nafisa lokacin motocin daukar amare sun fita da suke nan an kuma kwashi jama' a. Har,zai juya don ya san kila Page 24 Nafisa tana cikin yan kai amare, sai dai ya ce yasan gidan ya ragu da jama'a bari ya shiga ya yi sallama da su Mama ta sun yi waya. Cikin sa a da ita ya fara cin karo a falo, tace "A'a Baban Ashrat?'Ya ce, "Na'am, kin gama shiri ko? Tace Wane shiri kuma?" Ya ce To mu je inda babu mutane mu yi magana Nafisa cikin mamaki tace Shigo nan Ta tura akin su Hamida. Wasu yara ne a ciki, ta ce, "Kuje falo Ta kakkabe mishi bakin gado tare da fadin, Zauna Ya zauna yana cewa, "Ina yaran?"Ta ce, "Ashraf ya makale wa Babata tun da muka zo. Babanmu kuma yana bayan Mama Shatima ya yi murmushi, "Ai dole ya makale ma takwaransa?Ta dub猫 shi, *Ina yini?"Yace Lafiya lau,tunda an kai amare ai biki ya Kare saimu tafi ko, don gaskiya gobe da ke za mu nafisa ta yi yar dariya, "tace gobe fa za,a yi budar kai, ka ga ya dace in tafi?" Yace an gama budar kai tunda an kai amar猫 dakinsu, kuyi musu addu,ar zaman lafiya-kawai"Tace yaya gaskiyal ba zai-yiwu ba, kannai na har biyu na kasa halartar budar kan kansu Ya ce, "To na ji, zan jira ki goben ki taho da wuri na fada miki Abuja za mu wuce, jibi office Ta ce,Wai ni Yaya me ya sa ba ka min adalci? Ni kadai ce matarka? Ga Salma ai tana htun ba makaranta take zuwa ba, kuma ga Amna in ma Aliya tana da ciki. Amma ko yaushe sai a kace dani zakaje Abuja, kuma ni anki saka ni makaranta,Fisabilillahi adalcin kenan?"Shatima ya yi shiru yana kallonta, har da kuka. Gunjin kukanta ya sa Anty Maimuna ta leko tare da fadin,A'a bayan an gama kukan daukar amaren wa muka samu yake gunji a nan?"Ganin Shatima da Nafisa sai ta ce, "Au dama ku ne?" Shatima ya gaida Anty Maimuna, ta ja kofarta nufi dakin Mama, ta kira ta gefe, tace *Mama? Nafisa ce mijinta ya z0, sai kuma na ga tana kuka Mama ta ce. "Suna ina?"Anty Maimuna taCe, "Suna dakin Su Hamida Mama ta ce, "Nafisa da ki ke gani sarka ce sarkin rikici. Bari in je in ji mene ne kuma Bakin kofar ta tsaya tana jin muryarshi yana fadin,Karatu dai ko ina ana yinshi ba sai Zaria ba,kuma in kin kwantar da hankalinki Abuja zan nema miki. Inma da za ki yarda akwai wata makaranta da wata mata ta bude irin ta koyan sana'o'in nan kayan yara da zannuwan gado, da rigunan aure. Na yi magana da matar Nafisa ta ce, Tab! Nizallar karatuna zan yi" Yace Kin fi so ki koma baya? Kina ganin Amna a waje tayo karatunta tana da kwalinta na digiri, amma me ta yi da shi? Yanzu gata kasuwanci ta koma. Ta ce,amma dai iliminta yana kanta ko?" Shatima ya ce, "Shi kenan, yanda ki ka so.Amma ina fada miki Abuja za mu tafi gobe, don haka goben lallai ki taho da wuri Ta ce, "Ni fa ba zan dawo gobe ba. Ta yi shiru ganin Mama ta shigo. Kamar an jeho ta, Shatima ya rusunar da kai yana yana gaida Maman. Yanda ta amsa gaisuwar yasan ranta a bace yake. Ya dago ya dube ta, Nafisa take kalla, ta ce, *Duk da ban ji zantukan ku duka ba, abin da na ji ya gamsar da ni. Ban san lokacin da za ki san darajar mijinki, ba, yana ga abin da za a yi kina ke ba shi kike so ba. Wannan ba tarbiyya ta bace, ban san kuma A ina ki ka samo su ba Nafisa cikin kuka ta ce, "Mama wai a ce mu hudu ne fa amma kullum Yaya ni yake dakilewa karatu, sai dai in bi shi Abuja. Marin da Mama ta sakar mata ne ya sa ta dafe bakinta, shi kuma Shatima bai san lokacin da ya rike hannun Mama ba, yana fadin,Don Allah Mama kiyi hakuri abin bai kai haka ba Mama tace "ta tashi ta hada nata ya nata ta bi mijinta.Yace a'a ta bari sai gobe ta zo, Mama ta ce "Kai ka fi ba ni haushi, ka tsaya kana lallabata tana botsewa, maimakon ka shasshara mata' mari, mata sun sa ka canza daga Shatiman da na sanka Ya ce, "Mama ai ba za a biye ba a yi ta rigima, a barta sai zuwa goben'Ya mike; "Mama ni zan je in yi sallah mu wuce"Mama tace "Don Allah ka yi ta hakuri daSu Shatima ya ce,Babu komai"Yayi godiya ya fita. Anty Maimuna tana gain fitarshi ta shiga dakin tana tambayar abin da ya faru, Mama ta fada mata komai. Nan suka rufe ta da fada, Anty Maimuna ta ce Sokuwar banza, cikin ku hudun harda 'yar yarinya wadda ba ta kai ku shekaru ba, ya za6e ki kece fa tauraruwarshi, ya taba zuwa da sauran?"Tace "Sau daya ya je da su, Salma kuwa bai ta6a zuwa da ita ba Anty Maimuna ta ce, "To kin gani? Gyaran da ki ke yana amfani, kuma wannan shigar da ki kasamu a gurinsa ta fiye miki duk wani karatu da za kiyi". Mama tace "Kuma da za ta shiga makarantar koyon sana'ar sai tafi mata karatun, tunda na gasa ne za ta yi karatun ba na ra'ayin kanta ba ne"Nan dai suka bar fadan, suka dawo bata shawara da nuna mata abin da ya dace Washegari tun karfe Daya Mama ta tattara Nafisa da yaranta direba ya maida ta. Lokacin Shatima baya gida suka dawo, da ya zo ya same su murmushi ya yi tare da kara ganin darajar mama,matsayin suruka ta gari. Sai dai ya san sai ya yi lallashi game da marin da Mama ta yi mata. Lokacin da suka shirya tafiya Salma ba su dawo daga Katsina ba, don haka ya bar abin da yakan dan-ba ta na nama a hannun Aliya. Salma ta samu nasarar zana jarrabawar share fagen shiga jami'a (jamb), suna jiran Samun sakamako. Wani yammaci maigadi ya yi sallama a kofar Aliya ya tambaye ta ko Alhaji yana ciki? Ya yi baki. Aliya wadda ta kumbura saboda cikinta ya ma fita a watanshi, ta ce, "Yana nan, bari in fada mishi,ko da sai sun dan jira yana wanka Shatima ya fito sanye da jallabiya ruwan madara, ta yi kyau sosai a jikinsa duk da bai sa ta don kwalliya ba, sai don shan iska: Wata mota ce a gefe ya gani, Danbaba maigadi bai bari sun shiga ba,tunda sun ce bai san da zuwansu ba. Samari matasa sa'annin su Mustapha ya gani sun fito daga motar sun nufo shi, duk suna sanye da dogayen kaya da huluna,shigar mutunci. Suka gaida shi cikin girmamawa, Shatima ya sake dubansu, sam bai sansu ba, ya ce, "Samari daga ina?"Suka ce,Daga cikin gari" Ya ce, "Kuma ni ku ke nema?" Suka ce "Eh, yayan Salma dai muke nema" Shatima cikin mamaki ya ce Salma?" Suka ce, "Eh" Ita Ya ce, "Ni ne, lafiya ko?" Daya cikinsu ya ce' "Eh to gaskiya dai lafiya lau Ya nuna Yusuf, "Wannan abokin namu ne dama yake sonta, to amma ta ki saurarenshi shi ne wata kawarta ta ba mu shawara a kan muzo gurin yayanta Duk da wanka Shatima ya fito sai da ya ji wata zufa ta keto masa. Cikin matsanancin bacin rai ya ce Amma ita Salma ba ta fada muku cewa tana da aure ba?" Yusuf ya zaro ido tare da dafa kirji, gami da fadin,Dama da gaske take yi?" Ya cire hular kanshi yana fifita, nan da nan idanunsa suka yi jajir. Yana fadin, "Na shiga uku, da ma da gaske Salma tana da aure? Wallahi ina tsananin sonta Shatima ya daka mishi tsawa, "A ina ka ganta? Page 25 Yusuf yace gurin biki na ganta ranka ya dade a taimaka min Shatima ya sake furzar da wani huci mai zafi sannan yace kanasin kace min kunyi hira da ita kuma ita ta kwatanta maka nan gidan ? Yusuf yace magana daya kawai tayi min wai in barta wai tanada miji Daidai lokacin salma ta turo kafar gidan sanye da kayan islamiya zata tafi turus ta tsaya tana kallon shatima da yusuf shatima cikin tsawa yace ke zonan jikin salma ya dau rawa tazo ta taugunna tace gani yaya Ya nuna yusuf kinsan wannan? Tace eh Yace meke tsakaninku? Babu komai don inma zai fadi gaskia aina fada masa inada miji Shatima ya zabga mata harara yaya akayi yasan gidannan? Hawaye suka soma zubowa daga idanunta tace ni bani na nuna musu ba yace to waya nina muku? Ya tambaya tare da kallon yusuf Yace kawarta ce ta nuna min Shatima ya kalli salma fada masa ko wanene mijin naki don ya sani Salma ta dubi yusuf cike da jin haushinsa sannan ta nuna shatima wannan shine yayana kuma shine mijina Shatima ya kalli yusuf to kaji kuma ina fatan ka gamsu sannan kuma ka fita hanyarta Ya dubi salma ke kuma koma ciki ina zuwa Cikin tsoron kar ya hana ta karatu; tace Wallahi ni.... Ya daka mata tsawa, "Na ce ki wuce ko?" Salma ta nufi ciki. tare da fadin, "Na shiga ukuna Ya bi bayan Salma ba tare da ya kara kallon gurin su Yusuf ba. Tana Kokarin bude dakinta da makulli ya iso kusa da ila, makullin ya fadi don tsoro. Gani take yi dukanta zai yi. Yace Ke tsaya ki amsa min, kuma ki fadamin gaskiya Salma ta tsuguna jiki yana Bari, ya ce,Kina son yaron?" Ta zaro ido da fadin,Haba Yaya, ina da miji kuma zan so wani kamar jahila?" Ta fada mishi duk yanda abin ya faru Ta ce,Kuma Kawayena ba su san cewa ina da miji ba Ya ce, "To daga yau ina son duk Kawayenki su san cewa ni mijinki ne, sannan daga yau kin gama saka mayafi sai hijabai" Tace *To ai banida hijabai, sai wanda aka kawo kwanaki kasai mana Ya ce. "To a kara kawowa in sai muku. Tashi ki tafi islamiyya Salma ta wuce tana gode wa Allah da ya tsare ta. Amna cikin motarta ta nufi gidan Maman Afra, sun Kulle da Maman afra ne saboda yawan yin siyayya da takeyi a shagonta, mijinta sojan samane babban soja. Maman Afra jininsu ya hadu sosai da Amna, don suna zuwa gidan juna tare da bai wa juna shawara. Ta kofar kicin ta shiga bayan tayi fakin Ta samu Maman Afra tana saka danwake, tace A'a yau kuma ke da kanki a kicin?!" Ta ce. "Ke dai bari duk na saka su aiki, ga shi yunwa ta ishe ni, kuma danwake nake son ci" Amna ta ce Dole ki ji yunwa sha biyu fa ta gota Maman Afra tace, "Kin san mai house ya dawo jiya da yamma yanzun na dawo daga kai shi filin jirgi ya wuce Lagos" Amna ta zaro ido, "Kwana daya rak?" Maman Afra tace "Don ni kadai ya zo,kuma na samar masa da nutsuwa ya tafi yana kewata Suka sa dariya, tace "Maman Jafar a wannan zamanin mu fa ba a sanya, mata suna nan a waje birjik suna jiran wanda za su dafe mawa. Ke da mijinki kina kallo wata a waje tana mulkinsa.Domin yanzu mata ba sa jira a taya su, Ta dauki danwaken tana fadin, "Mu je ciki Maman Jafar, game da miji bana sanya, ban hada shi da kowa ba wallahi. Duk lokacin da ya z0 sai na bar masa wata alama wadda za ta sa in kasance a zuciyarsa kowane lokaci庐 Amna ta isa ta dafa kafadarta, *Tsaya Maman Afra, wace alama ce wannan? Ni fa dama matsala ce da ni Ta dube ta, "Wace irin matsala ce? Kodayake mu karasa dakina Ta kwala wa 'yar aikinta kira, "Haula!" Yarinyar ta z0 da sauri, ta ce, "Kawo min fulas din shayi da dafaffen kwai* Kan gado Amna ta haye, don tace ba ra ta ci dan waken ba. Maman Afra ta zube kan kafet din Wai Maman Jafar wace matsala haka dake Amna tace "Humm, mijinmu ne in muna tare kowane lokaci a hira da lokacin sirri sai ya dinga kira min sunan kishiya. Ko fa magana zai min sai kiji ya ce Nafisa, sannan yace au Amna? Maman Afra abin yana damuna wallahi' Maman Afra ta zaro ido, "To ke kuma ki ka ce me? Page 26 Amna ta ce, "in Na yi magana sai ya ce shi bai san ya ce ba, mantuwa ce "Tabdi yarinya ta tsare muku Maman Jafar bacci ku ka yi ne haka! In fada miki ni nan ba ni da kishiya, amma na yi kishiyoyin waje. Da baban su Afra kwararren dan neman mata ne, ni ma farkon haduwarmu da haka ya zo na nuna mishi ni fa ina da tarbiyya, shine ya Billo da batun aure, da yake ina sonshi ban Qi ba na amince. In fada miki anyi aure muna ta soyayya daga samun cikin Afra sai wulakanci ya shiga. Ai ko ya shiga neman matanshi har ba ya shakka in sani. Ina haihuwa Yayata ta hadi ni da wata mai saida maganin mata a Kaduna. Kafin in yi arba'in ta yi min gyara tare da shawarwari yanda ya kamata.Ranar ko da ya dawo ban da tona sirrin aure babu kyau da na ba ki labarin yanda muka kwashe kin sha dariya. Mutum ya koma tamkar soko, ko inCe bawana, Ni ina sonsa tsakani da Allah haka bai sa na wulakanta shi ba. Cikin hikima dubara da addu'a Allah ya taimake ni ya bar duk wata macen waje,sannan in na yi magana yana karba, duk abin da nace ina so in yana da hali yana mana. Daraja da Kimata ta dawo idanunsa, Ke shawararsa wadda ba ta shafe ni ba ma sai ya kawo min ita. Ni ko in ba shi iya fahimta ta sakamakon ina karance-karance littafan Hausa ina samun kaifin basira"Amna ta tabe baki "Ni fa duk wannan karance-karancen na Hausa bana yin su, gara English Novel, sannan wadannan abubuwan ban yarda da su ba. Ga likitoci kullum suna gargadin shaye-shaye da matse-matsen nan" Maman Afra ta ce, "Ina mamakin irinku"yan gayu masu karatun al'adun wasu ku bar naku. Hikima da basira ai tanaga marubutanmu cikin hikima da basira, kuma kin san wannan matsalar da ki ke fad矛 da kina karatun da tuni kin magance ta batare da kowa ya sani ba kuma game da kayan gyaran jikin nan, sai dai in ba ki nemi ingantattu ba kuma basu baki shawara daga masu saida kayan ba. Kin san cewa ni ma na yi irin abin da ki ka yi?"Amna ta tabe baki, "Ni fa ban iya wannan aikin, ko da aurena ban sha sosai ba, ko yanzu na fi ga dan irin na waje din nan Maman Afra ta ce,Ai wannan ba su zama a jiki in za ki dawo hanya ki dawo kawai" Amna ta ce,Mu bar wannan zancen, ni muyi wanda nike miki Maman Afra ta ce, "Mun bari. Amma in kin canza shawara kina iya tuntuba ta zan kuma hada ki da ita. Don kullum ina fada ma mata sai sun gyara zasu ga daidai Amna ta ce, "Yanzun ni ya zan magance wannan matsalar, yanzu haka fa ita tana Abuja gaba daya mu sai dai ya zo ya yi mana kwana daidai don ita Karamarmu ma da yake ya maida ta sakara, sai yayi zuwa ka ga bai kwana gurinta ba Maman Afra ta sheke da dariya tareda fadin, "Lallai na jinjina ma wanna Nafisar, har ta burgeni" Amna ta ce "To mene ne abin dariya a nan. Maimakon ki taya ni bakin ciki miji yana tare da ni,kuma yana ambatar kishiya. Akwai ranar da har kuka na yi saboda kiran sunan Nafisan, na yi wai sai ya ce min wai sun yi fada ne shine abin yake ransa Maman Afra ta sake shekewa da dariya har da kwalla. Amna ta mike za ta tafi tana fadin, "Tunda abin dariya ne bari kawai in tafi" ". Ta yi maganar cikin fushi. Maman Afra ta riko ta, "Tsaya ki ji kawata, rainin hankalin da namiji nike yi wa dariya. Ya rasa lokacin da zai tuna sun yi fada da ita sai irin wannan lokacin mai tsada a gurinki?" Maman Afra ta dafa kafadar Amna, "Yi tunani da kyau ki gani. Yarinar nan tana matukar gyara jikinta, inda za ki tambayi sauran kishiyoyinki Kila su ma yana kiran sunanta a gurinsu. Ai bai san lokacin da zai yi barin ba Amna ta ce, "Kin ganta ne, busasshiya. Na fita komai fa! Har na fara zargin ko ta yi masa asiri ne" ta ce, "Ba wani asiri in fada miki isassun mata yanzun ba sa zuwa gurin bokaye, kayan gyara suke siya suna gyara jikinsu, ki ga mace birtintin amma ta isa' a gurin miji, kuma ita ma har bushewarta ta fi ku a idonshi. Shawara ta daya ku dage kawai ki gyara, amma fa tushi babu inda zai kaiki" Ita dai Amna har ta tafi ba ta gamsu ba. Cikin dare nakuda ta kama Aliya, ranar asabar ce Shatima yana dakin Amna, Aliyar ta yi ta kiran layinshi ba a daga ba. Haka ma layin Amna tayi ta kira, wayoyin duk suna falo su kuma suna cikin daki, sam ba su ji kiran ba. Karfe biyar na asubahi Aliya ta haifo danta santalele shi ma mai kama da Babansa. Cikin bacci Shatima ya yi mafarki wai Aliya ta haihu. Da sauri ya farka, falo ya nufa ya ciro wayarsa a caji da nufin kiranta tunda likita yace lallai tana fara nakuda a kai ta asibiti, domin ta gota lokacin da ake saka ran za ta haihu. Adadin kiran daya gani nata a wayarsa shine ya sa shi ficewa daga dakin babu shiri, ya nufi sashen Aliyar, Ya same ta tana numfarfashi a gefe ga da yana ta tsala kuka. Da alama ba ta jima da haihuwar ba. Ya kai hannu ya kama ta tare da fadin, "Tashi"Ta ce. "Ka bani reza a cikin can in fara yanke mishi cibiya" Ya dubo ya ba ta, ta yanke cibin, sannan ta ce ya ba ta zani. Ta nannade yaron, sannan ta ce ya kwantar da shi. Ta ce ya taimaka mata ta shiga wanka. Ya tara mata ruwan zafi ta shiga wanka, layin Amna ya kira da wayar Aliya, ba ta daga ba ya Nufi dakin da sauri ya tashe ta, ya fada mata haihuwar Aliya.Juyi ta yi tare da fadin, Allah ya raya Ta maida kai ta kwanta. Yace Ki tashi ki taimaka mata' Amna ta ce, "Me ni gaskiya ba zan iya zuwa wani taimako ba Ya ce, "Ita kadai fa ta haihuTa ce, "Ina asibiti ne Can ya kamata ka kai ta Ya nufi dakin Salma da sauri, ya taso ta, yace ta zo ta taimaka wa Aliya. Suna shiga suka samu掳 Aliyar zaune tana goge jiki, ta fito wanka. Salma ta ce, "Sannu Anty Ya nuna mata gurin jinin, "Ki gyara nan Salma ta nufi gurin zuciyarta ta tashi, amma haka ta daure ta kwashe ta kulle uwar a ledar da Aliyar ta ce ta dauko a store, ta goge ko ina tsaf da Detol sannan ta fesa turaren daki; ta koma dakinta zuciyarta a tashe, ta shiga ta yi wanka, sannan ta yi sallah,"Da safe Shatima ya dauki maijego da danta ya kai su asibiti don likita ya duba lafiyarsu. A ranar dangin Aliya suka cika gidan daga Zaria, Amna sai da ta tashi fita zuwa shago sannan ta shiga don yi wa 'Aliya barka. Kusan tunda take a gidan wannan ne karo na farko da ta shiga gurin Aliya, gara ma gurin Page 27 Salma ta shiga lokacin da aka z0 daukan gadonta da Shatima ya taba ajewa a daya daga cikin dakunan Salma. Aliya ta ce ma matar yayanta su yim脿 Shatima magana su tafi da ita Zaria tunda shi ba ya nan, yana Abuja, babu kuma wanda zai taya ta aiki. Shatima bai musa ba domin shi ma hakan zai fi masa sauki, don Salma ba za ta iya yi mata aiki ba, saboda aikin jini da ta yi sai da ta yi ta amai, har sai da ya amso mata magani, Don haka zuwa yamma ya kai suda wasu yan uwanta. Washegari kuma ya koma inda ya kai su Alhajinsa, nan kuwa aka yi wa yaron huduba da sunan wani Kanin su Alhaji da ya rasu, ubansu daya, Aminu. Shatima ya bada duk abin da ya san zai bada duk da za su zo suna shi da Nafisa, ita ma Hajiya tayi kayan barka kamar yanda ta yi ma sauran. Salma ta yi nasarar zama daya daga cikin daliban da suka samu gurbin karatu a jami'ar Ahmadu Bello ta Zaria, Shatima ya yi tsayin daka don ganin Salma ta zama daga cikin sahun farko na daliban da za su fara karatu. Ta so ya barta ta zauna Zaria ya c茅, ya yarda kullum a kai ta a dawo da ita. Ya ce, nan gaba in ta yi hankali sai ya koya mata mota take zuwa da kanta. Hakan ya Kara kunna Nafisa ta bijir茅 da zancen nata karatun a karshe dai ta yarda ya sa ta makarantar koyon dinkin da ta je ta ga irin aikin da suke yi. Safwan yana karya kwanar ya ce a ranshi, Wannan ai layin su Anty Momiyo ne" "Yana gangarawa sai ko ga gidan. Ya kalli gidan da murmushi, a fili ya ce, "Bari in dawo Anty zan shiga mu gaisa Kiran abokinshi ya sake shigowa, ya ce,Na shigo layin yanzun, ai na san layin, domin layin su Antyna ne, ga ma gidansu nan鈥�. kai wane gidan ne naka din?"Ya ce, "Nine na karshe a layin, don layin baya fita"Safwan yace "Fito waje to".Nan kuwa ya samu abokin nashi, aure abokin ya yi lokacin Safwan yana Chaina shine ya zo ganin amarya. Sun shiga ya ganta sun gaisa, ya dai sha ruwan da aka kawo, amma bai ci kayan garar ba, ya, yi wa amarya alheri ya taso. A gurin motar da abokin ya raka shi, ya ce, "Ga gidan Antyna can, zan shiga mu gaisa Abokin ya ce,To bari na je mu gaisa tunda makota muke"Bai shiga da motar ba a waje ya aje, suka kwankwasa. Aisha ce ta zo ta bude, cike da murna tace, '"'Oyoyo Yaya Safwan"Ya ce, "'Anty tana ciki?"Ta ce, "Ku shigo Ta shiga tana kiran, *Mama ki fito ga Yaya Safwan" Sun zauna a falo Anty Momiyo ta fito daga kicin tana fadin, 芦Batan hanya ka yi ko Safwan"?"Ya yi *yar dariya, "Anty dai ba ni da ta cewa, don ba zan tuna rana ta karshe da na z0 gidan nan ba 'Ta ce,Yau ma na san ba na musamman kazo ba Ya dubi abokin, *Ga wanda ya jawo ni,abokina ne ya yi aure ya tare a layin nan, ba na kasar aka yi bikin shine na zo ganin amarya, yana min kwatance ina shigowa sai naga layinku Ta ce, "Ko da na ji, na san dai kazo ziyara. musamman da wahala Ta dubi abokin,Allah ya sanya alkhairi. Ko shine aka yi wancan satin yara sun ce an kawo amarya?"Ya ce, "Shine kuwa, amin na gode" Aisha ta aje musu abinci da ruwa, Safwan yace, 'Dauki abincin n盲n, yanzu za mu tafi",. Suna cikin hira wayar Aisha ta yi ringin,wayar tana kusa da Safwan ya dauko tare da fadin,Wayar wane ne?" Sai kiran ya yanke Yana kallon wayar gabanshi ya fadi, hoton Aisha ne da yarinyar da yake ta nema. Ya sake kallon fuskar wayar tare da fadin, "Wannan wayar ta wane ne?"Aisha ta ce, "Tawa ce Ya shiga gurin hotunan yana kallo. Ya bude tashi wayar ya tura hotunan Salma, sannan ya mika mata wayarta. Ya kalli Anty Momiyo, '"'Anty bari mu tafi Ta ce, "Da wuri haka?"Yace; "Zan zo na musamman Ya. kalli Aisha, "Bari in ba kuna siyan kati". Ya ciro yan dubu-dubu ya mika mata, sannan ya mike, Anty tana taya ta godiya. Suna fita ya sauke abokinshi, sannan ya dauki hanya. Sai da ya yi nisa sannan ya tsaya ya ciro wayarsa ya fiddo hotunan da ya tura na Salma, ya tsura musu ido. Tunda ya rasa Badi'atu sai wannan karon ne ya sake ganin yarinyar da yake matukar so, ya yi kwatancen duniya wa Mustapha bai gane yarinyar da yake nufi ba. Haka dai ya yi ta neman wanda zai taya shi gano yarinyar ya rasa har mahaifiyarshi ya yinwa zancen yarinyar, da kuma kwatancenta amma ba a gane ba. Cikin murna ya ce, "Yau ga ta na ganta a sama, wa zan tambaya ne labarin yarinyar nan? Ina ganin bari dai in kira Anty Momiyo Sai kuma ya fasa ya tada mota ya nufi hanyar gidanshi, zai bi a hankali har ya gano ta. Sa'ida Kanwar Safwan tana kallon hotunan da ya ce ta duba na wasu takalma da ya yi Oder , yace ta zabi kala biyu. Ta ci karo da hotunan su Aisha, tace Yaya Satwan ina ka samu hoton Aisha da matar Yaya Shatima?" Da sauri ya ce, "Me kika ce Sa'ida?"Tanuna mishi tare da cewa, "Wannan hotunan da bikin Anty Badi'atu ne Ya ce, "Ki ka ce wace ce dayar?" Tace "Salma ce fa matar Yaya Shatima, amaryarshi"Ya amshi wayar, "Ita ce wannan?" "Eh Ita ce"Safwan ya fasa shiga bandakin da zai shiga, ya zauna bakin kujera yana kallon Sa'ida. Ya sake kallon hoton Salma zuciyarsa ta ce, Sa'idar da ba ta shiga cikin jama a ina ta santa? Ya dube ta, "Ke da ba ki shiga mutane, ina ki ka santa?"Ta yi dariya, "Allah yaya ita ce, sau nawa ina ganinta a gidan Hajiya?" Ya ce,To je ki, wanka ma zan yi"Ta ce, "Yaya ban zabi takalmin ba Na turo ta wayarki ki zaba, yanzu sauri nike yi"Ta Ce, 芦Yaya kai din fa sabga ta yi maka yawa, kafin ka samu damar turo min. Ya ce, "Ki je dai". Page 28 Wankan da bai yi ba kenan ya dauki makullin mota ya fita, dole ya tabbatar da wannan zancen. Ya kalli agogon hannunsa, karfe nawa yanzu Biyu da rabi, yace -Ina da lokaci" Layin Shatima ya kira, "Kana gari kuwa?" Ya tambaya bayan sun gaisa. Shatima ya ce, "Karfe uku dai zan taso zuwa Kaduna yace Dama gorin da ka ke min ne zan wanke laifina Bros" Shatima yace Ni fa da na ga kiranka sai da na yi mamaki, har na yi zaton ko wani ka je kira wayar ta danno sunana' Tare suka sa dariya, ya ce, "Da yanzun na so da zuwa, amma bari na jira in shigo gobe" Safwan dai ranar bai samu barci ba, yana ta tufka da warwara. Bai san ya zai yi ba in har ta tabba matar Shatima ce. Salma ta kalli Shatima, Yaya ina zan samu caf茅 a nan unguwar ne?" Ya ce.Me za ki yi a gurin? Ta ce, "Akwai wasu takardu da za mu yi kwafinsu, sannan akwai wasu tambayoyi da zan duba a yanar gizo Na so siyan miki waya yau, abubuwa ne suna da yawa. Amma bari mu ga zuwa gobe" Wayar Shatima ta sake yin ruri, ya kalla, "Safwan ka iso?' Yace "Ga ni a gate" Shatima ya mike, "Koma tukunna in Safwan zai fita ma hada hanya sai in kai ki Shatima ya fita suka shigo da Salwan, dakin Amna ya kai shi da ma ranar ya hana ta fita, ya ce tunda zai yi bako daga Zaria, Aliya batq nan, Nafisa tana Abuja. Salma tana kwashe shanya ta hangi bakon a fili ta ce, Wannan ai wanda na fasa ma waya ne Ta dan makale har suka shige zuwa gurin Amna, Shatima da Safwan suka gaisa, sannan suka soma hira. Amna ta zo suka gaiva, Shatima ya bi ta daki, ya ce ta kawo masa abinci mana. Ta ce, bari tasa masu aiki su kai. Ya ce, "A'a bari". Ya kira Salma Tamkar kada ta fito, amma ba ta da damar gaddama. Ta saka mayafi sannan ta nufi dakin. Ta rusuna ta gaida shi, ya amsa jiki babu kwari, domin gaskiya ya kamu da tsananin son Salma. Shatima ya dube ta, "Shiga kicin ki kawo masa abinci Salma ta nufi kicin, Safwan ya bi ta da kallo. Sai da ta bace, sannan ya maido kanshi ga Shatima, wanda shi kuma yake kallon Safwan din. Ya ce, Wai wannan ma matarka ce?"Shatima ya yi dan murmushi, "Ita Ce karamarsu Safwan yace "Sauran ba su nan kenan?" Shatima yace Daya tana Abuja, daya ta haihu tana Zaria Salwan yace Kana KoKari, na yi zaton kafin shekara biyu za su tsular da kai da matsalolinsu, sai naga har yanzu kana nan a gayenka Suka sa dariya, Shatima ya mike don kunna talabijin, lokacin Salma ta fito da tiren abinci ta aje. Taje ta tur貌 teburin da ake dora abinci in ba a bukatar hawa teburin. Ta Dora masa a kai, sannan ta koma kawo abin sha. "Amna ta fito tana cewa Shatima, Jafar bari in Dauko shi a islamiyya. Shatima yace "Kada ki jima Tace *Yanzu zan dawo Salma tana gama jerawa za ta fita, Shatima yaCe Wai ke da Allah yaushe za ki daina tsoron mutane? Dawo to in gabatar miki da shi, ba bako bane, dan gida ne, zumunci ne ba shi da shi. Kinsan "gidan Alhajin G.R.A? Ta ce, "Ba mun jeba, gidan su Sa' ida ko?" Shatima ya ce, Yauwa, to shine babban yayan su Sa"ida. Da babanshi da Hajiyarmu uwarsu daya ubansu daya, shine babbansu Shatima ya kalli Salwan, "Don Allah ka yi aure Ya kalli Salma wadda ta zuba ma talabijin ido. Shatima ya ce Kin ganshi tare aka yi goyonmu, amma ina da yara hudu shi har yanzun ya ki aure' Salma ta kalli Satwan suka hada ido, gabanta ya fad矛, tayi saurin dauke kai saboda wani irin kallo da ta ga ya yi mata. Muryar Safwan ta ji yana cewa. "Lokacina ne baiyi ba. kuma mu ture batun wasa bana sa'a ne akwai masu sona da yawa, amma na lura suna son abin hannuna ne. Su kuma wadanda nike son sai a samu matsala Shatima yace "Ban da Badi'atu wa ka so?' Safwan ya tsiyaya ruwa a kofi ido ya kurba, "Yanzu haka akwai wadda nike tsananin so, amma ina zaton ita ma na makaro Shatima ya dube shi, "A ina take? Safwan yace "A nan Salma ta kalle shi da sauri, daidai lokacin da Shatima ya ke cewa, "Nan Kaduna?" Safwan ya ce, "Eh" Shatima yace Yar gidan waye?"Safwa- ya girgiza kai, "Ban san mahaifinta ba" Salma ta dubi Shatima a sanyaye ta ce, "Yaya wayarka tana ringin tun dazu. Ya mike ya nufi cikin dakin Amna, tare da fadin,Ina jin ringin din tun dazu. Ki zuba mana abincin Salma ta mike ta nufi gaban teburin ta tsuguna tana zuba musu dafa-dukan taliya da dankalin turawa. Safwan ya ce, "Na zone ki biya ni wayata Ta zaro ido, "Don Allah kada ka fada ma yaya "To fada min lambar wayarki" -Ya dauko wayarshi yana dannawa, kanta na Kasa ta ce! "Ba ni da waya Ta mike da sauri cikin mamaki ta koma kan kujera, me kuma zai yi da lambarta? ' Shatima ya dawo ya zauna tare da fadin, ".Ashraf ne wai ya matsa wa Mamansa sai ta kira masa ni Safwan ya ce, "Mu ma dai bari mu zo mu aje yaran nan Salma ta kalli Shatima, Yaya zanJe islamiyya Yace "To ki je in mun fita da wuri zan sai miki wayar* 'Ta ce, "Caf茅 din kuma fa?" Shatima ya dan yi shiru, yana son ya ga ya ya ma zai mata, Safwan ya katse masa tunani da cewa,Ba ka da computer a gida?"Yace, "Ta amfanina dai akwai, amma ai ba zan bata ta bata ba, ko ta goge min abubuwa Safwan ya yi yar dariya, "Sai ka ce wata mara wayo, ko kuma wadda ba ta san computer din ba?" Page 29 Shatima yace, Yarinyar da ba ta taba rike babbar waya ba bare computer?" Safwan yace Wannan duk laifinka ne, in mun fita yanzun muje a sai mata waya da laptop Shatima yace -To kin ji".Salma ta ce,Na gode" Shatima ya ce,Ki masa dai godiya, shi zai sai miki Salma ta cube shi, "Yaya na gode sosai Safwan yace Kar ki wani damu" ' Salma ta yi murna sosai da ganin wayarta dankareriya da laptop, Shatima ya ce, "Ko dai in miki canji ne don wannan laptop din ta fi tawa kyau da tsada Salma tace To ka dauka mana" Yace Wasa nike, ga shi ya kashe mik kudi duka fa kin ga rasist din Ya bude ledar wayar ya ciro su duka biyun.dubu dari shidda da talatin. Salma ta zaro ido tana kallon Shatima; *Yaya ya aka yi ka bari har ya kashe irin wanna kudin?" Yace Gurin Safwan wannan karamin kudi Ne Ta ce, "To na gode, don Allah Yaya ka yi masa godiya".Ya ce, "Bari in kira miki shi ki masa, ni tuni na yi masa-godiya Safwan ya daya wayar Shatima tare da fadin, "Na yi nisa, amma ban kai gida ba Yaa ce, "Na kawo sako tace nayi maka godiya. Ya ce, "Haba babu damuwa Salma ta amsa tayi sallama, ya amsa tare da cewa, " Sun yi miki ko? Tace "Sosai ma, na gode sosai Yaya, Allah ya kara arziki" Yace "Zan iya yi miki komai Salma, a cikin ledar laptop din nan za ki ga sakona, sai na ji kiranki"Bai jira amsarta ba ya kashe wayar. Salma ta kalli Shatima sai tana ganin kamar ya ji abin da Safwan din ya fada. Ya ce, "Mu je duk ki hada su Ta saka layinta a waya, randadau gwanin shi'awa, Shatima ya ciro laptop din yana kunnawa. Salma ta duba cikin ledar katin Safwan din ta gani,ta dubi Shatima, hankalinsa yana kan laptop din dayake dubawa. Ta dubi katin an rubuta, Safwan EL Nasir, ga lambobinshi nan. Ta juya bayan katin ya rubuta, "Ina jiran kiranki Salma ta yi saurin maida katin tare da tambayar kanta abin da Safwan yake nufi. Sai ta ji duk ta tsani wannan kayan, tana fa da aure ya sani, to ita abin duniya ba zai rude ta ba. Shatima yana nuna mata yanda Za ta sarrafa computer, amma yaga duk ranta a jagule ya ce, "Ya ya ba kya murna ne?"Tace Ina murna mana, kaina ne ya kama ciwo Yace To bari na aje gobe na nuna miki" Ta ce,To ". Yana fita ta shiga tunani. "Bari dai kada ta yanke masa hukunci har sai in ya bayyana nufinsa, kuma babu damar ta dada ma Shatima don ba za ta zama sanadin lalacewar zumuncinsu ba.Har sati ya zagayo ba ta kira ba, kuma bata da niyya, illa dai ta yi wa katin boyo na gaske. Salma Dankasa an shiga KASU university ta Kaduna. Ita dai English take karantawa, sabanin Salma da ke karantar Mass Communication. Burin Salma jarida, amma in ba ta samu ba komai ta samu za ta yi, sai gashi ta samu tana ganin za ta iya cinma burinta. Tana girki ta jiyo kukan wayarta, tana zuwa ta ga bakuwar lamba. Ta dan yi shiru tana son tuna ko ta taba ganin lambar, kiran yana daf da tsinkewa ta daga da sauri, yar siririyar murya ta ji an ce, "Salma?"kafin mu yi nisa wacece don Allah?" Ta ce, "Ni ce Sa'ida daga G.R.A" Salma tace "Ah Sa'ida abin mamaki, ina ki ka samu lambata?"Ta ce, "A gurin wata yarinya Saddika S. Tata Tace min department dinku ta ke" Salma ta ce, "Na santa, muna shiri sosai, S. Tata yar G.R.A ce ita ma?" Sa'ida ta ce, "Nima ai nan nike, amma ni Hausa nike karantawa Salma ta ce, "Wuuu a languges ki ke, sannu fa da kokari, kuna shanta Sa'ida ta ce, ' "Kuma da yake ina son Hausar bana ganin wuyarta Salma ta ce, "Haka ne" Suka dan yi hira, sannan suka yi sallama da alkawarin sai sun hadu a makaranta, ta yi kamar tace ta gaida mata Safwan, sai kuma ta ga rashin dacewar hakan. Aliya an yi arba"in an dawo, kuma an koma bakin aiki. Sai dai ita ma ta sa Shatima ya daukar mata mai aiki, dawainiyar gidan Shatima ta yi yawa har ta sa albashinsa yana neman ya gagari rike gidan. Ko da ya yi batun da Aliya, sai ta ce, to tunda haka ne kawai ya rage abin da yake kashe musu. Ya yi batun da Nafisa don so yake ya ji ta bakin kowa. Sai ta ce, tunda Aliya tana aiki ta dauki nauyin wani abin nata, ni ma tunda na fara yin kayan yaran nan da zannuwan gado kuma suna tafiya a Zaria sai na rage maka wani nauyin. Amna ma haka, ita ko Salma saita dakata da karatu Ya samu Amna da zancen, ta ce, "Ni dama ban dora maka nauyina dari bisa dari ba, don haka wannan ba zancena ba ne" Kamar kada ya yi batun da Salma, don yana ganin har yanz煤n ba wai tana da hankali bane. sai Kuma ya ga ya dace ya ba ta hakkinta ita ma. Tana karatunta ya shigo har uwar dakinta, ba za ta tuna rana Ta karshe da Shatima ya shigo dakin baccinta ba. Har a ranta tana cewa, in dai har Yaya hakkinshi ya kawo shi dakina, to yau kuwa zan sauke wa kaina nauyi Ya zauna bakin gado, "Kina karatu ne?" Tace "Eh Yaya, ya gajiyar hanya? Ina su Ashraf?"Ya ce, "Suna lafiya. Salma' ina son za mu yi magana, amma ban sani ba ko za ki fahimta?" Ta ce,Yaya mai zai hana ni fahimta in dai Ka fahimtar da ni?" Ya yi dan murmushi tare da fadin, "Haka ne.wato Salma abin da ke faruwa dawainiyar yau da kullum din nan ne yanzu haka bana iya samun rara a cikin asusuna wannan watan har sai da mai kayan abinci ya bi ni bashi fa" Salma ta ce,"To yaya a rage abubuwa Kamar me?"TaCe, "Farko ni maimakon direba ana biyanshi a wata, kullum dubu daya zai isa in je makaranta in dawo nawa ne Zaria? Dari uku ne, ko Ka koya min kamar yanda ka ce, ka ga an samu sauki. Nama da sauran abin da bai zama dole ba sai a rago, sannan da za ka yarda Yaya ka hada da Page 30 Kasuwanci mana. Na tabbata in ka samu irin su Yaya Safwan zai ba ka shawara tunda shi din dan kasuwa ne Shatima ya zuba ma Salma ido, zancen kasuwancin ya ratsa shi. Ya ce, "Amma ke ba kya ganin kasuwa sai da jari?" Ta ce, Wannan ko su Hajiya da Alhaji za su Iya juya maka Ya ce, "Kice gobe in tafi Zaria kenan. ZanJe inyi shawara da su Hajiya Salma da Sa'ida da kuma Saddika S. Tata suna tafe zuwa gurin motar Sa'ida, duk suka jingina jikin motar hirar dai ta karatu ce. Salma ta ce, "Jikina ni har ya soma sabawa da suntirin Kaduna zuwa Zaria din nan kullum, ga shi duk na rame Saddika ta ce, "Humm, ai karatu fa babu sauki" Sa'ida tace "Bari in tafi dama na zo na duba kune Har ta shiga mota, ta ce,Au? Na manta, Salma Yaya Safwan ya ce in ce miki ya gode, amma na ba shi lambarki dazu da safe. Wai menene ma?"Salma ta yi yar dariya, "Sako ya ba Yaya Shatima ya kawo min, shine ban masa godiya ba"Saida ta yi murmushi, "Kai Yaya manya, to sau nawa yana kyauta ba ya waiwayawa? Na zaci wani abin kirki ne ma, don na ga shi ba mutum ba ne mai son shiga shirgin wasu"Salma ta yi 'yar dariya, sannan suka juya. Shatima ya tallauna da mahaifanshi biyu kan batun kasuwanci, amma bai nuna musu cewa ya gaza da gidanshi ba. Sun ji dadin shawarar kuma sun yi alkawarin taimaka masa da jari. Sun kuma goyi bayan ya tuntubi Safwan. Ya kira Safwan ya sanar da shi cewa yana son ganinshi, Safwan yace babu matsala, in ya samu lokac zai zo har gida a cikin ranakun karshen mako. Wani dare Salma tana shirin kwanciya sai ga kiran yayarta Hadiza, ce suka gaisa, tace Salma kina lissafin bikin Auwal kuwa?" Salma tace "Ina lissafe Yaya, saura kwana ashirin ko?"Ta ce, To cikon dubu biyuna ki Kokarta ki samo min. to ke me za ki masa?" Salma ta ce, "Dubu biyunki suna nan aje, ki bari zan fada wa Yaya gobe in na zo makaranta in karaso gidan Inna sai mu yi magana a tsanake, don kam mu nan sai a hankali, Yaya Shatima abubuwa sun yi masa yawa Hadiza tace "Mun 'yi maganar da Inna da taga wannan karon kudin haya da guntu-guntu ya biya musu Salma tace "Allah sarki Yaya, bai ma fada min ya biya kudin ba. Allah ka ba ni ikon gama karatun nan, ka albarkace ni da samun aiki, zan taimaka masa da dukkan abin da zan iya sannan in taimaki iyayena"Suka yi bankwana a kan sai gobe.Hajiya ta dubi Momiyo.Ni fa Allah tunda Aliya matar Shatima tazo lokacin da ta yi arba' in din nan take ba ni labarin irin kudin da Shatima ke kashewa kan konanniyar yarinyar nan du tsanarta ta karu a raina, ga iyayenta shine cinsu da shansu, shi ne kudin haya Momiyo ta ce,Karatun jami'a kam da kashe kudi, amma tunda shi ya ga zai iya ke ki daina damun kanki mana Hajiya taCe,Allah dole in damu. Shekaran jiya Aliyar ta sake kirana tana fada min,wai ga shi har ya kai matakin kasawa da su. Duk da albashinsa mai tsoka da yake dauka, har bashi yaci na abincin gida Momiyo taCe Bashi kuma? Wane iri? Shatima gaskiya gara a san abin yi Hajiya ta ce, Ba ina fada miki ba ya z0 da son shiga kasuwanci ba, har kina murna? To na fasa bashi kudina, karshe ni zan kwana ciki a bashi ya kashe musu anty Momiyo ta ce, "Kar ki hana shi, amma ki masa kashedi, kuma ki nuna masa kin. san me gidan nasa yake ciki" Tace Ai in na nuna masa na san abin da gidan nasa yake ciki sai ya yi mata magana, kuma daga nan zan daina jin komai. Zan dai san yanda zanyi in ga na raba su, don bala'I ita ba haihuwa ba ba komai ba sai tsatsibar kudi kawai suke yi" Momiyo tace "Kaka dai tana yinta sosai" Hajiya ta ce, "Ta yi ta yinta din, ni dai dole ya rabu da ita ba zan iya ba. Na soma yi wa Alhaji mitar yayu tsalle ya ce kar ya kuma jin haka Momiyo tace, "Allah dai ya kyauta, amma dai Hajiya ki bi a hankali" Shatima yana tafe cikin motarsa gida ya nufa,don shi ba shi da dabi'ar yawo babu dalili. Kyakkyawar yarinyar da yake yawan gani a kusa da gidansa ce ta sa mishi hannu alamun ya tsaya. Kamar ya wuce, sai kuma ya tsaya. Ta iso da dan saurinta gefe da ba kowa ta kalle shi, "Don Allah Baban Ashraf gida za ka?" Ya dauke kai daga dubanta, don wani salo da ya ga tana yi da idanunta, sannan ya ce, "Eh" Ta ce,In shigo ka taimaka min, na rasa abin hawa Ya ce,Bismillah" Ta bude ta shiga tare da fadin, "Na gode" Bai tanka ba ya figi mota. Ta dube shi, hankalinsa yana kan tukinsa, tace, "Ba ka yi mamaki da na kira sunanka ba?" Ya dube ta, fara ce tas ga kyau, ya maida kai Kan titi Ban yi wani mamaki ba gaskiya, don an fada min haka Ta ce, Ka san ni to, da ba ka ji mamaki ba?" Ya ce,Ban sanki ba gaskiya, amma na taba ganinki a layin da nike"Ta saki wata yar dariya, 芦Tunda nike ban taba ganin mutumin ddaya ganni sau daya ya kuma ganina bai gane ni ba. In na tambayi dalili sai ace kyauna ne sila'Shatima ya sake kallonta cikin mamakin maganarta. Ya maida kai titi, "Hakika kina da kyau. Ta ce, "Kai ma ka yaba kenan?"Ya ce,A'a, na dai fad矛 abin da yake zahiri" Ta dan yi shiru kamar mai nazari, sai ta sake dubanshi.Kusan kowa ai yana yabawa da mai kyau, musamman ku maza Ya ce, "Haka ne, amma kowa da ra'ayinsa ba a komai kyau ke burge ni ba, musamman ga mace.Don bana son abin yayi da kuma wanda kowa ke so. Ina ki ke ganin yanda Kuda sukan taru a kan alkakin da ya ji suga Maganar ta shige ta, don haka ta ce, "Ai kuma irina ba kowa nike ba fuska ba?". Daidai lokacin ya tsaya a kusa da gidansa, "Kina iya sauka zan shiga gida" Ta bude, "Har mun iso?" Page 31 Bai tanka ba, ta dube shi bayan ta fita, " Na gode Nan ma bai tanka ba. Ya karasa gidansa. Nafisa da yara suka fito suka tari Shatima, sai yanzu ta gane cewa zamanta a Abuja jin dadi ne, don tana manta cewa tana da wasu kishiyoyi. Ta taimaka masa ya yi wanka sannan ta zauna suka shiga cin abinci, Saura sati daya bikin Auwal, Salma tana wanki sako ya shigo wayarta, har kashi biyu a jere. Hakan ya tabbatar mata ba "yan gidan waya ba ne. ta dauraye hannu sannan ta goge ta dauki wayar. Daga ganin rubutun ta san wanda ya iya' ne ya yi shi. Da turanci ya turo sakon kamar haka; Salma, barka da war haka, na san cewa yau hutu ne na karshen mako kina gida. Ina fatan kina cikin Koshin lafiya. Safwan ne, babu mamaki ba ki da lambata, don na ce ki kira in samu lambarki amma kin ki. Ban ga laifinki ba, domin kina kare aurenki ne. salma na so in hakura da tsananin sonki da ya kama ni a ranar da muka yi karo da ke, amma inna tuna wasu kalamai da mijinki ya yi a lokacin da muka je siyan wayarki, sai in samu kwarin gwiwa tare da yarda cewa zan iya cimma burina. Ya sanar dani ke da shi ba auran soyayya ku ka yi ba, kuma ya ce shine dalilin da ya sa bai kuma tunkararki da huldar auratayya ba tun sau daya da ya gwada ki kaKi yarda. Kuma ya tabbalar min da rashin son da ki ke masa ne ya sa ki Kinsa, amma ba rashin wayon da ki ka nuna masa a lokacin ba tunda yara ma wadanda ba su kai ki shekaru ba sun san rayuwar aure, kuma in na tuna yanda ya nuna ba zai takura miki ba in kin fidda wani mijin zai barki, sai ince tattala min ke yayi. Kuma ban da Allah ya hukunta cewa ba shi da rabo ya za a yi ya zuba wa mace kamarki ido? Salma cike da karfin gwiwa nike fadin ina sonki, so na hakika, kuma na shirya daukan duk wani kalubale da zai taso a dangi in ma da shi. Sannan zan nuna miki soyayya irin wadda ba a taba nuna ma wata ba a duniya ba cika baki ba. Fatan za ki yi nazarin zancena sosai, kuma kar ki damu kanki da cewa sai kin ba ni amsa, na fi son ki yi nazari. Na barki lafiya abar kaunata Salma ta jike sharkaf da rufa, ta maimaita karanta dogon sakon ya kai sau goma sha biyu, sannan tuni ta manta da batun wanki ta hau gado don son yin nazari. Duk da ta yi bakin ciki da sakon Safwan, amma ba ta ji haushinsa kamar yanda take jin na Shatima ba. A fili take fadin, "Lallai Yaya Shatima ya kai makura a rashin sona. Na zaci tuni ya bar Wannan zancen?" Ta tashi ta je gaban madubi. "Mene ne laifina? Duk da ban kasance kyakkyawa ba, amma ban zama mai munin da za a guje ni ba Gaskiyar Safwan ne Shatima ba ya ra'ayina, da ko bai sona zai bukace ni. Na yi ta yin tunani a lokuta da dama ina neman dalilin da tun tayin farko Yaya bai sake kula ni ba, ashe Kaunata ce ba ya yi" Ta ja numfashi, sannan ta saki kuka. Ta yi kuka sosai domin tana tuna lokacin da ya fada a gaban kishiyoyinta da iyayenshi. Lallai ya kaita babbar hujja, kuma daga yau ta ja layi da Shatima, ta shirya yaki da tallarta da yake yi. Ta sake fadawa kan gado, ta ce, "Ban san adadin mutanen da ya fadamawa ba ya sona ba. Gara ma ya sauwake min in huta, matanshi ma duk a banza suke kallona'Yar karamar hauka dai Salma ta yi ta a ranar, kuma ta lashi takobin nuna wa Shatima cewa ta gaji da zama da shi, wanna satin in ya zo sai ya sake ta. Ranar dai wanki bai gamu ba, sai washegari. Ta kwana cikin fushi da ko abincin dare ba ta ci ba.Ta zuba idon ganinshi a washegari lahadi, amma bai zo ba, kila wanna satin ba zai zo ba, don ya kan yi haka yanzu. Ranar litinin ta dawo makaranta da dare tana kwance, duk ta gaji har ranar ba ta da walwala. Ta dauki wayarta tana kara karanta sakon Safwan. Ta samu kanta da rubuta mishi amsa duk da yace ba ya bukata. *Yaya Safwan ban ji haushinka ba, da na zaci ko kana son yin hulda da nine a munafunce lokacin da ka sa min katinka cikin laptop din da ka sai min. In ka shirya za ka aure ni zan yi yaki in bar wanda ba ya sona, in koma ga wanda yake sona. Da ma ni ban damu da so ba bare in ji haushi, ina nufin ban san so ba. Sai dai na yi imani in na zauna da mai sona Zan koyi so, tunda ance zama da madaukin kanwa. Na gode sai dai ba za mu sake magana ba har sai na zama bazawara ko in ce sakin wawa Ta tura a layin Safwan. Salma me take shirin yi? Domin yau talata kwanaki uku-kenan ba ta daga kiran Shatima, sakon dubu biyar din da ta gani a account dinta ba ta gansuba ta gani ba. Ranar talatar ba ta je makaranta ba,don ba za su yi komai ba tunda sun gama jarabawa.Tana yin tuwonta tana kallon kiran Shatima yana shigowa yana tsinkewa har kashi uku.A gefen Shatima, ya shiga damuwa da rashin samun Salma. A iya saninshi ko missed calls dinsa in Salma ta gani za ta mishi filashin ko sako. Ya fi tunanin ba ta da lafiya ne, amma Aliya ta ce masa lafiyarta lau kuma tana zuwa makaranta. To me yake faruwa? Ya kuma kiran Aliya, ya ce,Salma tana gida?" Ta ce, "Eh, don yau ba ta je makaranta ba Shatima ya ce, "Ki je ki gani lafiya? Sannan ki ce nace ta daga wayata yanzun nan Aliya ta sabi danta wanda suke kira da Abulkhairi ta nufi akin Salma. Ta same ta zaune tana. cin tuwo, ta yi sallama, Salma ta dube ta a wulakance, sannan ta amsa. Aliya cikin mamaki ta kalli Salma, ta daure tace '"Baban Abulkhairi yace ki daga waya yana ta kiranki, ko kin yar da wayar ne'?" Salma ta dube ta cikin son jin Karin bayani, "Waye kuma Baban Abulkhairi?" Aliya tace, "Tofa! Yau kuma har mijin naki ba ki. sanshi ba?" Salma ta saki *yar dariya irin ta rainin wayo,sannan ta ce, "Baban Jafar, Baban Ashraf, Baban Abdul wa kikace ma?" Aliya ta ce,Kai yau wata rashin kunya ki ke ji ne haka? To ko Baban wa aka ce an ce don ya haifa ne. kuma ke ma da kin haifa na san sai kin ce baban wane. Tunda kuwa ba a da da sai a bari masu ya' ya matansa mu yi"Salma taCe, Tofa! Har dasu gorin haihuwa?" Ta saki dariya, har da "yar shewa. Aliya ta ce, "An yi miki, in fitsari banza ne kaza ta yi mana" Salma cikin fusata tace, "Ni don Allah ki je kin sa tuwona ya huce ina surutu". Aliya tace "To da ma mijinki ya ja min wanna rashin kunyar da ki ka yi min, don shi ya turo ni" Salma tace "Ki fada masa ba ni da lokacin daga wayarsa" Ta dago wayarta daidai lokacin da kiran ya Kara shigowa, "Gashi nan ya sake kira banji dagawa ba Ta maida wayar ta aje. Aliya ta zaro ido tana kallon Salma, ta mike ta dauki robar tuwon ta nufi kicin tana cewa, "Ki je ki fada masa sakona, don nasan ko ban ce ki fada ba kai tsegumi aikinki ne Aliya ta juya cikin tsananin mamaki, jiki har Bari yake, ta kira Shatima tana fada mishi wai Salma ta zage ta tas! Har da kuka, kuma ta ce ba ta da lokacin daga wayarsa.Shatima ya cika da mamaki, ba don Aliya ta fada mishi da, ba zai yarda ba. Duk da haka sai yana tantama, don haka sai ya tura mata sako kamar haka.Kin ce ba za ki daga sakona ba a kan me?Sai Salma ta tura masa amsa kamar haka.Haka na fada'. Ta tura mishi. Mamaki da tsoro suka dirar ma Shatima, ji yake tamkar ya kulle ido ya bude ya ganshi a Kaduna. Ya soma lissafin ranaku, kwana uku ya yi masa nisa. da ya zo gida bai iya daurewa ba yana fada ma Nafisa wai Salma ce ta yi kaza da kaza.Dariya Nafisa ta saki tare da cewa,Ai dama _karshen alewa Kasa, kuma dama tunda kace ta je jami'a ai dole idonta ya bude" yace ni kuma nafi tunanin ko aljanu ne suka shigeta nafisa tace aljanun iskanci ba Ranar juma'a Salma ba ta je makaranta ba ta bari ne sai in ta koma Zaria. Kayanta ta ke ta linki tana. loda su cikin akwati, ta kalli lodin kananan kayanta wadanda ta dinga siya tana sakawa lokula da dama in Shatima yana dakinta. Ashe ita aikin banza take yi? Ta girgiza kai tare da fadin, "Humm Allah Ya dawo da mutumin nan lafiya ya sha mamakina Takwas da mintuna na safiyar juma' a Safwan yana kwance kan gadonsa kamar ba shi ne zaibi jirgin karfe tara zuwa Abuja ba. Din yanada sabgogi da yawa kuma yanason ya ga Shatima. Ya kai hannu ya dauki wayarshi da nufin ya sanar da Shatiman cewa, yau fa zai shigo Abuja, kuma yanason in zai zo a kan son ganinshi da Shatima ya ce yana yi, sai dai kuma yana dauko wayar bai dire ko ina ba, sai kan rubutun Salma. Duk kwanakin nan matsawar ya dauki wannan wayar, tofa sai karanta rubutun Salma kafin ya yi abin da zai yi. kuma fa ba wai yana farin ciki da zantukan nata bane, domin ya gama nazarinsu kaf babu so a zantukan illa haushin mijinta da ta ji sakamakon abin da ya ce a kanta. Kuma hanyar da ta biyo don yin bore ga mijinta ba za ta bayar da masalahar da ake so ba, illa ma a samu matsala in ba a yi sa'a ba rikicin ya shafi dangi. In ya yi tunanin rubuta mata sakon dakatar da ita ta bari har sai lokacin da ta gama karatun kamar yanda y盲 ce, sai kuma ya fasa in ya tuna da gargadin da ta masa cewa ba zasu sake ji daga juna ba har saita zama ba matar Shatima ba. Agogon dakin ya buga tara, da sauri Safwan ya danna kiran Shatima. Ya dauka sun gaisa, sannan Safwan ya fada masa cewa zai shigo Abuja, kuma zai zo don ya ji neman da yake yi masa. "Ya ce, to shi ma dai yau zai tafi Kaduna don wancan satin bai je ba. Safwan ya ce, to ya jira shi sai su dawo tare. Karfe uku da rabi daidai Safwan suka isa gidan Shatima, inda Shatiman ya je ya dauko shi.Nan suka ci abinci har ya yi wa su Ashraf kyautar kudi. Suna cin abinci Shatima ke fada masa bukatarsa ta son gwada kasuwanci. Safwan yace, "Gaskiya kayi tunani.kasuwanci yana sama da duk wani aiki a gurina, ko don da shi na bude ido?" Shatima ya ce, "Haka ne, ba wai don ka bude ido da shi ba, haka batun yake. A rana sai ka ci ribar albashin wani na wata daya Safwan ya sa dariya, ya ce, "'Na wata kadai. na shekaru ma Sun tattauna sosai. inda Safwan ya ba 'Shatima shawarar ya shiga harkar man fetur, ya ce,amma jarin naira miliyan goma sun yi kadan saidai ya zuba kar ya waiwaye su yanzu a yi kamar shekara. Shatima ya gamsu da duk shawarwarin da Safwan ya ba shi Sun nufo Kaduna tare shi da Shatima, zuciyar Shatima tam da tambayoyi a kan Salma.Ita kuwa Salma zaman jiran zuwan Shatima take yi, don ta hada kayan sawarta gaba daya gadonta ta jingine, ta tattara kujerunta gefe guda ta Zuba kayan kicin dinta a buhu ta daure, ta tara komai a falo, sannan ta ci uban kuka idanunta sun kumbura suntum! Muryarta ta dashe, sai dai ita baza ta ce ga dalilin kukan nata ba. * Shatima bai san dalili ba, yana shigowa gidan ya ji wata mummunar faduwar gaba. Idanunsa suka dira kan dakin Salma, dakin a bude yake a wangame. Kai tsaye can ya nufa da kayan da yake dauke da su a hannuwanshi. Baki ya saki ganin babu labulan a kofar, ya karasa falon nan ya yi turus! Ya zube kayan da ke hannuwanshi ya shiga cikin falon tsibi-tsibin kayan yake bi da kallo.Ya yi karfin halin kwala mata kira, "Salma! Salma!!" Ba ta amsa ba, sai dai ta fito daga cikin dakin tana rataye da jaka da kuma akwatin da za ta iya dauka tana janshi. Ya kalle ta tare da fadin,Lafiya?" Harara ta watso mishi da jajayen idanunta, "Lafiya ka ke tambaya? To ita ta kawo haka, ba don ina jiran takardar saki ba da babu abin da zai saka tarar dani a gidan nan yanzu kam ka bani takarda ta don bazan sake kwana a cikinshi ba Ta daga murya shatima ka sakeniiiii Mu hadu a littafi na hudu kuma na karshe wanda za ku samu a shafin mu https://hausanovels001.com.ng