(01)  Ta sauke labulen bayan mashin dinsu yabar harabar gidan. Ta koma ta zauna cike da tausayin KB,kwarai tasan KB yana sonta sosai,yasha zuwar mata da zancen aure amma sai tayi buris karshe ma ta share zancen ko kuma ta nunamishi bacin ranta akan aure. Bawan Allahn nan haka zaiyi hakuri ya bita yanda taso. Yau gashi an wayi gari ta zama mallakin amininsa dan uwansa. Ita kuwa da wane ido zata dubi Kabir. Tana ji a ranta inda ace yau shine ya mallaketa da babu ta yanda zai nuna mata muguwar tsana irin wacce take ganin Haris yana nuna mata. Duk wannan saukin kai da mutunci da rashin son magana da take gani Haris yana dashi ashe duk ba haka bane yakan iya runtse ido yaci mutuncin d'an adam. Koda dai ta lura ita kadai yake yiwa hakan saidai tana da tabbacin wasu ma zai iya yi musu.                       *****      Baharu tunda suka taho daga gidan Mamma yake ta tunani ganin hoton Tasleem a wayar Kabir,yanaso ya tambayeshi ko daman ya santa birni amma sai ya rabu dashi ganin fuskarsa a daure tamau. Yana saukeshi kofar gidan yaga ya hau motarsa ga mamaki kuma ya jata ya dauki hanyar da zata sadaka da barin garin. Toh wai meke faruwa haka? Yana shirin komawa ciki,yaji muryar almajirin gidansu Kabir yana kiransa,ya juyo ya amsa.     "Hajiya na nemanka." Jin haka Baharu ya shiga da sauri sai ya iskesu tsaye cirko cirko da sauran mutanen gidan a tsakar gida.      "Kai ina Kabirun? Ance tare kuke."     Baharu ya bata amsa    "Tare muke, munje domin yaga amaryar yaya Haris amma ance bacci takeyi shine kuma yanzu ya hau motarsa naga ya dauki hanyar barin cikin gari."    Suka sa salati,Hajiya tace  "Amma yaron nan bashi da hankali,ace da yammacin nan zai juya zuwa Kano? Toh meke faruwa ma mutumin da yazo da niyyar kwana?"      "Allah masani,gwanda a kirayi wayarsa aji." Cewar Hajiya Atine.      "Ina da kudi a waya saidai bani da lambarsa." Baharu ya fadi yana kokarin zaro wayarsa a aljihun riga.      "Ga lambarsa nan,shiga ka dauko wayata akan talabijin." Ya shiga dakin Hajiya ya dauko wayar, ta fadamishi sunan da akayi mata saving dashi ya lalubo ya kwafa ya soma kira. Saidai tana ta zabga ringing yak'i dagawa dolensu suka hakura,yayinda Hajiya ta shiga don sanarwa Malam Babangida.                         *******   A gefen KB kuwa,tuk'i yakeyi a fusace. Taimakon Allah da tsarewarSa kadai ta shigo dashi garin Kano ana kiraye kirayen sallar isha'i. Kai tsaye bai zarce ko'ina ba sai gidan Haris.                      *******    Haris yana zaune a falonsa yana shan ice cream mai sanyi, kallo daya zaka yiwa fuskarsa ka gane bashi da wata damuwa ta kowane fanni. Yana sha hankali kwance yana kallon wani american film. Buga kofar da akeyi ta sanyashi tsayawa cak yana dubanta. Baiyi mamakin ganin wanda ya turo kofar ya shigo ba asalima sai ya ajiye robar ice cream din yana mai daure kansa jikin kujera yana kallonshi fuskarsa dauke da murmushin mugunta.          "KB manya,daman kana gari? Zauna mana."      Kallon da yake watsawa Haris wanda duk tsawon zamansu bai taba yi mishi irinsa ba yasa Haris gane cewar tabbas labarin komai ya fito gareshi.       "Meyasa zakayimin haka?!  Daman zaka iya zagayawa ka auremin matar da nafi so da kauna duk duniya. Why Haris???"     Ya karashe da babbar murya,wanda ya harzuka Haris! Wannan bacin ran nasa na satuttuka akan KB ya dawo sabo fil. Nan take annurin fuskarsa ta dauke,ya mike tsaye cikin matukar fusata      "An gayamaka so da kauna yasa na auri 'YAR BARIKI? Ko an gayamaka ina da bukatar rayuwa kwatankwacin wacce ka daukarwa KB! No! Ban aureta ba don farantawa rayuwata,na aureta ne don tseratar da rayuwarka daga cigaba da halaka! Sannan ka sani, aure na riga da nayi babu mai warware min igiyar aurena da ita! Zahra is the only girl that I love,Tasleem kuwa babu wata soyayya tsakanina da ita. So,kabar zargina da cin amanarka! Na aureta ne don nuna maka kuskurenka na zama D'AN BARIKI wanda ya janyo kake cutar rayuwarka da na iyalinka da kuma b'ata sunan iyayenmu. Babu abunda zanyi da Tasleem,ba komai bace a wajena saidai yes! A yanzu she's my wife! Nine kadai mai ikon sanyata da hanata don haka stay away from her!"     KB wanda ke tsaye cak yana sauraron lafuzzan bakin Haris,ya jinjina kai kafin yayi dariya mai ciwo a gefe guda hawaye sun kwaranyo akan fuskarsa           "Baka isa ba Haris,kayi kad'an ka rabani da Tasleem. Idan bakasani yau ka sani,Tasleem ni kadai takeso! Baka isa ka samu gurbi a zuciyarta ba. Baka isa kuma baka kai matsayin da zaka juyata ba saboda nasan kayata."    "KAYATA?" Wanna furucin ya tunzura Haris,       "KB get out of my house!!"     Kb yayi dariya ya soma ja da baya baya      "Zan fita ba saikayimin shouting ba. Amma kasa a ranka,Tasleem tawa ce ni kadai! Bazata taba zama taka ba."     Murmushi Haris yayi wanda acan k'asan zuciyarsa ya d'an daku sakamakon hawayen da KB ke zubarwa ba shakka KB nason Tasleem saidai idan za'a hada da son da shi kuma yake yiwa kanwarsa Yasmeen fiye da dukkan sauran kannensu bazai misaltu ba. Hakanan ita din tun tana karamarta tana fama da ciwon zuciya wanda dashi aka haifeta hakan ya janyo take yawan motsa jikinta koda tayi fushi nan da nan zata soma numfarfashi. Dole ya kula da ita da rayuwarta.        KB tuni ya fice a fusace,Haris ji yayi komai ya fice a ransa. Yaji ya k'ara jin haushin Tasleem,duk itace ta janyo matsalar nan. Tsaki yaja kafin ya koma ya kwanta rai babu dadi......! Kallonsa kawai yakeyi da mamaki na yanda yake d'ura ruwan barasar a cikinsa ba tare da tunanin illarsa ba,a yanda yasan KB bai fiye shanta ba sai ransa ya b'aci da wani abun. Ganin ya shanye rabin babbar kwalba ya k'ara zubo wani akan kofi mai dauke da kankarar yayi saurin damk'e hannunshi. "Why KB? Me yayi zafi haka ne?" Mugun kallon da KB ya watsa mishi ne,yasa ba shiri Nas ya matsar da hannunsa. Saida yayi mankas sannan ya dubi Nas da idanunsa rinannu cikin muguwar buguwar da tunda yake da KB bai tab'a yin irinta ba. "Kaje ka samu Haris ka gayamishi Baby tawa ce ni kadai! Ya sakarmin matata if not kotu zata rabani dashi." Nas ya tuntsire da dariya,tabbas KB yasha tayi mishi over,Ustaz da 'Yar bariki? Bamai yiwuwa bane,yo menene gamin kashi da fura? Ya mike tsaye yana nufar dakinsa inda ya baro budurwarsa Rita tana jiransa. "Mutumin kwanta ka huta kaji,zuwa gobe sai muyi magana." KB ya bishi da kallo cikin rinannun idanunsa na maye, ya sanya yatsa yana shafa lebbansa,daidai lokacin da hawaye suka kwaranyo mishi yasa yatsa ya shafosu kafin cikin muryar maye ya kyakyale da dariya "Yanzu ka fara zuba wallahi,dan iska kawai. Saika dawomin da matata zan rabu dakai." Ya dora kansa jikin kujera bai bar zubar hawaye ba yana sumbatu yana maganganu duk akan Baby da Haris kafin kuma ya tuntsire da dariya. Haka har bacci ya daukeshi mai nauyin gaske. Tashinsa yaji anayi kamar a mafarki,ya bude idanunsa wadanda sukayi mishi nauyi hakanan kansa yakeji yana ciwo. A sannu sannu idanunsa suka washe ya saukesu akan Nas wanda ke juya mishi hannuwa kamar yana (bye bye) "Morning Loverboy." Tuni KB ya mike zaune ganin hasken rana a kanshi. "Oh no,anan na kwana?" "Tayaya zakasan duniyar da kake, tasha kayi tatul." Nas ya fada yana dariya,tsaki yaja mishi kafin ya mike ya nufi dakin Nas. Can ya hango Rita nad'e saman gado tana sharar bacci,tsaki yaja na takaicin kwashe kwashen Nas wadanda wasu ma ka kallesu abun kayi amai ne. Toilet ya shiga ya kama ruwa kafin ya dauro alwala ya fito. Can ya hangi darduma ya dauka ya fito falon inda Nas ke zaune yana faman chanja tashoshi. Ganin KB da darduma yayi murmushi "Yau ustazancin ne ya motsa kenan,toh a sanyamu a addu'a muma." Ko kallo bai isheshi ba,ya gabatar da salla hadi da yin istigfari da hailala a k'arshe kamar yanda ya saba da kuma salati. Ya jima yana rokon gafarar Allah kafin ya shafa ya mike. Halayyar KB kenan,duk abinsa baya wasa da sallolinsa. Saida ya mike ya ajiye darduma kafin ya dubi Nas "Ni zan wuce gida." "A'a malam,bafa ka gayamin damuwarka ba. Jiya dai naji kana surutanka wai Haris sai ya sakar maka Baby. Mene da menene. Meke faruwa ne?" Fuskar KB ba walwala yace "Anjima mu had'u a gidana by 4pm yanzu banjin dadi ne." Daga haka yayi gaba "Mukullin motarka fa?" Ya dawo baya yana karamin tsaki ya dauka,sannan ya zura takalmansa ya fita daman wayoyinsa ya barsu a mota. ****** Yana zaune a gidansa yana sauraron zuwan Nas,Daddy yayi kiran wayarsa. Ya dauka,bayan gaisuwa ya tambayeshi ko lafiya akace ya baro Kazaure a fusace? Yace mishi babu komai wani uzuri ne ya manta baiyi ba. Daddy ya bishi da toh kafin yayi mishi umarnin kiran Hajiya don kwantar da hankalinta. Ya amsa da toh kafin suyi sallama. ****** Gama wayarsa da Zahra kenan ya nufi sif dinsa don saka kaya da niyyar fita zuwa gida sakamakon wasu takardu na ofis da zai kaiwa Daddy. Ya fiddo kananun kaya yana shirin shiryawa idanunsa suka kai ga sark'ar k'afar nan ta Tasleem wacce ta barshi a motarsa ajiye saman madubinsa. Cak ya ajiye kayan ya nufi inda yake ya dauka. Idanunsa ya zuba musu cikin murmushi koda ya tunano irin yanda ta kaya tsakaninsu dashi a wannan yini d'ayan na mota. Saidai tunano rikicin dake gudana duk a kanta yasa shi dire sark'ar yana tsaki kafin cikin fusata ya cigaba da shirinsa.....! ****** Gama jin labarin abunda ke faruwa daga bakin abokin nasa, ya sanya yanayin fuskarsa chanjawa zuwa yanayi na mamaki karshe ma sai yayi murmushi. "Wai KB meke damunka ne? Tun jiya sai faman alak'anta Haris kakeyi da Baby,I'm sorry saidai wallahi na kasa gaskataka." KB ya dafe kansa cikin tsananin takaici,ai ba Nas kadai ba shi kanshi sumtyma sai yaga al'amarin kamar cikin mafarki ne akwai ranar da zai farka amma abu ne da yake a zahirance ba wai shaci fad'i ba......!‬     Farin cikin da Yasmeen take tsammanin zata sameshi a wannan ranar bata sameshi ba sakamakon KB wanda kwata kwata ma ya kauracewa dakinta zuwa nasa. Tasha kuka ganin yanda gaba daya ya sauya ta tabbatar 'Yar Bariki ta tab'oshi ta barta da jangwam. Dakyar ta dangana tayi kwanciyarta. Da safe ma ta bishi a ladabce tayi mishi dukkan hidindimun data saba kafin kuma ta shige dakinta bayan yaci yasha ya fice.       Misalin goma na safiya ta dannawa hasina kira. Hasina tana dauka ta kyalkyale da dariya       "Yadai tawan? Komai ya tafi daidai ko?"     Yasmeen tayi murmushin yak'e     "Uhum,bari kawai Hasina,wallahi wannan yanayin nashi dai na koyaushe haka ya shigomin ke gwara a baya ma yakan hada shimfida dani amma jiya kam rabawa yayi ma."     "SubhanAllah ya haka?"    "Ina zan sani."     "Kada wannan ya d'aga hankalinki Yasmeen,hakuri babu abunda bazai baki ba. Ki bishi sannu yanda kika saba har ki shawo hankalinshi ya kusanceki ina mai tabbatar maki ko yaya saikin samu chanji daga Kabir a sannu sannu hankalinsa zai dauke daga kan kowace mace ta waje. Sannan ba hakan yana nufin wai bazai iya aure ba,no,shi aure mukaddari ne daga Allah tunda daman ba hanyar kaucewa muka bi ba. Kin gane ko?"     Yasmeen cikin gamsuwa da jin dadin shawarwarin Hasina,ta murmusa     "Na fahimceki yar uwa."    "Yauwa tawan,kedai kada ki fasa gyara kanki."   Daga haka sukayi sallama suka rabu.                        *******      Cikin bacci taji muryar humaira na ihun fad'in    "Yaya oyoyo! Yaya oyoyo!!"  Kafin kuma taji muryar Mamma na fadin     "Ashe da gaske take? A'a Hasina sannunku da zuwa."     Jin an ambaci Hasina tayi azamar mikewa,batasan sadda ta fito a guje ba daga ita sai riga doguwa iyaka k'aurinta sai zani dake daure a samansa. Ai tuni itama Hasina dayake ta hangota tana saukowa daga matattakalar bene ta yada jakarta ta isa suka rungumi juna cike da tsananin murna da farin ciki. Sai kuma Baby ta sanya kuka itama Hasina ta sanya. Saida Yaya Abdullah yayi magana kafin su bari.     Hira kam ta barke babu ji babu gani,Baby ta kasa barin Ummi ta matsa daga wajenta. Sai rukunkumeta takeyi tana mata wasa. Ba itace ta samu tayi wanka ba sai wajejan uku na rana sakamakon hira da kuma girki da sukayi tare da Hasina duk kuwa da tace mata ta bari zatayi.      Ta fito wanka daure da towel,ta durkusa saitin Ummi dake wasa da ribbons din kanta tana jijjiga mata gashinta ruwa yana fallatsar mata. Dariya sukeyi kafin ta daga yarinyar tana mata wasa. Hasina dake zaune gefen gadon tana kokarin fiddowa Ummi kaya don yi mata wanka kallon chanjawar Baby takeyi kawai. Kwarai ta goge irin na "yan barikin,ta lura kuma jikinta bai lalace ba hakanan tayi fes da ita duk da dai ta rame sosai.         "Gaskiya a barmin ummina tare dani. Wannan kamannin namu yayi over." Cewar Baby kenan bayan ta zauna a kujerar gaban madubi tana yi mata wasa ita kuwa dariya take b'angalawa.       "Hum,ai sai a bar maki ita."    Murmushi Tasleem tayi lokacin da take gyara mata ribbons dinta.     "Wannan yayan nawa kam bazai yarda ba."    "Mijin naki fa?"    Baby ta ajiye Ummi gefen mamanta kafin tabe baki ta juya ga kallon madubi ta soma sharce kanta.      "Au babu amsa? Ke wai kuna waya kuwa?"     Kallonta tayi ta cikin madubi    "Ina fa? Mutumin da baya kaunata ta ina zai wani nemeni? Bar dai 'yan uwansa,sai kiga anzo wai ganin amarya."     Hasina tayi murmushi cike da tausayawa Tasleem.    "Kada ki damu sister,wuyarta ya shigo hannunki." Tasleem murmushi tayi,tana mamaki idan ance wuyarta ya shigo hannunta,hakama Anti hafsa ta gayamata. Ajiye comb din tayi ta juyo idonta cike da kwalla        "Me kike ganin ya rage ina dashi da zan siye zuciyar Haris? Kin manta yana da budurwa fal a leda anti?"      Hasina ta rike hannunta    "Kada wannan ya dameki,kowacce fa da takunta! Kada kisa komai a ranki,Haris bazai amince da aurenki ba face sai yana sonki.(Kasancewar Abdullah ya labartawa Hasina komai). Bana tsammanin Haris yana k'inki. Kedai ki bishi sannu kada kuma ki k'osa da yin biyayya a gareshi."         Washegari hasina ta sanyata daki tayita nuna mata kayayyaki kala kala na mata datayo mata tsarabarsu. Murmushi kawai Baby keyi,ai ita batayi zaton akwai mata wadanda basu yin sake wajen gyaran kansu ba. Kallon Hasina kawai takeyi yanda ta dage sai jawabi takeyi mata akan abunda ta tsufa da sanin harma fiye dasu. A karshe ta soma amfani dasu gudun kada Hasina taji babu dadi. Washegari Abdullah ya koma ita kuwa Hasina saida sukay sati cif sannan yazo ya daukesu suka tafi bayan ta shiga dangi an gaggaisa.       Tsakaninta da Haris kuwa,ko waya babu saidai ta ji suna waya da hirarsu da Mamma harma take mamakin shakuwarsu.                              ANA SAURA SATI DAYA BIKI.....!‬ "Ni kaina wasu lokutan nakan karyata abunda gashi a gabana a gaske ba wai mafarki ba Nas,amma ka yarda dani. Haris ya rabani da Baby,ya auremin ita saboda ganinsa itace silar da rayuwata ta lalace har haka. Bansan ya zanyi ba Nas."     "Amma in har hakane,Haris sam bai kyauta ba wallahi. Ya za'ayi yayi maka haka bayan ka sanar dashi kudurinka na auranta?"     KB ya lumshe ido yana mai jin wani iri a ransa. Shi kansa baisan ta inda zai b'ullowa Haris ba.      "Toh why not ka gwada samun iyayenku ka sanar dasu wacece ainahin Baby?"    KB yayi shiru yana tunani kafin kuma ya girgiza kai    "Bazan iyaba Nas,kai son da nakeyiwa Baby fa ba'a baki ya tsaya ba. Bazan iya b'ata mata suna wajen iyayenmu ba. Nasan waye Haris,yana da sanyi da kuma hakuri amma idan ya zuciya ya kafe akan abu toh fa babu sauki. Wallahi Haris zai iya bin dukkanin wani hukunci da iyayenmu suka yanke akanshi amma bazai saketa ta ruwan sanyi ba. Yanzu abu daya na hanga wanda shi zai zamemin mafita."      "Menene shi?"    "Tunda kaji Haris yace bayason Baby kuma har ya furta da bakinsa,toh gaskiyar kenan. A yanda nasan kayata,bata jurar a wulakantata ko yayane,ina mai tabbatar maka aurensu bazaije ko'ina ba. Saidai a zahirin gaskiya zan nunamishi na share komai. Kaga a sannu sannu zan samu damar kara shigewa Baby har mu bullowa lamuran yanda Haris zai saketa don na tabbatar kuma na hakikance ni kadai takeso take kauna."     Nas yayi murmushi     "Tabbas hakane,ina mai tabbatar maka abi abun a sannu. Banda ma abunsa,mai zaiyi da sauran maza?"  Kb ya daure fuska    "Ya isheka please kada ka nemi zagarmin matata."    Nas yayi dariyar wannan karfin halin na KB.                          ******      Yasmeen ta tarbi bakuwarta kuma school mate dinta a baya,wato HASINA da bebinta,Ummi wato Tasleem. Cikin fara'a suka zauna har hira ta kankama ba kakkautawa.     "Keda kikace tun sha biyun rana zakizo sai gaki da karfe biyu."    Hasina tayi dariya tana kallon yanda Ummi ke mikawa Nasreen yarinya mai shekaru biyu da watanni hannu alamar wasa.       "Bari kawai na biya gidan Hajiya Fatima Aminu Garba ne,kin santa akwai customers wallahi dakyar na samu ganinta."    Yasmeen ta yamutse fuska alamar rashin fahimta     "Wane irin customers kuma?"     Hasina tana kokarin zame dankwalin kanta tace       "Kedai kada kicemin duk zamanki a Abuja bakisan Hajiya Fatima Aminu Garba ba? Toh ai duk fadin Abuja babu inda zaki samu kayan harka masu kyau da tsada sai a gidanta. Kinsan idan ka haihu musamman ma haihuwar fari saida gyara."  Yasmeen ta zubawa Hasina ido bayan ta tafka tagumi       "Toh har wani gyara akeyi bayan an haihu? Kedai kin cika iyayi."     Jin haka,yasa Hasina zamowa ta zauna akan carpet d'abas     "Ke Yasmeen,kada kicemin zero kike zaune tun aurenki babu wani motsi na taimako na kuma gyara da kika yiwa kanki?"     Yasmeen wacce ita batasan ma dawan garin ba domin duk abubuwan nan ba damunta sukayi ba(ga inda matsalarta take!)ta girgiza kai     "Wallahi ba abunda nakeyi Hasina,hakanan nake zaune ke nifa tun kafin na haihu ma banyi wani abu ba."     Ai sai Hasina ta sanya salati tana tafe hannu     "Na shiga uku ni Hasina,me kikayi kenan Yasmeen? Kedai wallahi banza ce. Daman haka kike zaune shiyasa koyaushe kikemin korafin mijinki na ci miki fuska? Eh lallai,laifin naki ne nabar ganin laifinsa. Ke a zamanin nan ana zama haka ne? Wallahi inajin wai wai a gari ana maganar irinku masu zama haka salam ashe kuwa ga wata shashashar a kusa dani ta jikina ma bansani ba. Yasmeen ya kikayi wannan gangancin?"      Hasina ke maganar cikin tsabar takaici da bacin rai.     "Ji jikinki lukwui lukwui kamar a tab'a jini ya fito,bak'ar fatarki sai shek'i take,ga cika da kike k'ara yi amma sammank'al.         "Nifa kina sakani cikin duhu Hasina,wai menene?"    Hasina ta karkato tana dubanta    "Look Yasmeen,hakika zamanki a haka zai iya sanyawa mijinki kara aure ko bibiyar matan banza. Wannan kuskurene babba da kike gani."    Dogon jawabi Hasina ta yiwa Yasmeen kafin ta janyo jakarta ta fiddo tsarabarta na gidan Hajiya Fatima ta shiga yi mata bayanai masu gamsarwa a karshe kuma ta kara da cewa     "Had'inki yafi karfin wannan,dole fa kafin dawowar mijinki ki nemi izninsa muje dake gidan Hajiya Fatima."    Yasmeen wacce harda kwallarta,sai lokacin ta fahimci tayi sake ba kad'an ba. Ta fiddo waya ta nemi iznin kb akan zata fita. Kasancewar cike yake da bacin rai      "Jeki." Shine kawai amsar daya bata. Babu bata lokaci ta sanyo afterdress akan riga da zanin dake jikinta na atamfa ta yafa mayafinsa a saman dankwalin dake daure a kanta. Ta shirya Nasreen ta fiddo kudade har dubu talatin suka kama hanya a motar Hasina.      Hajiya Fatima ta bata taimako sosai yayinda itama ta saki kudade kafin tayi mata doguwar nasiha inda ta nuna mata cewar komai fa bazai yiwu ba saida ladabi da biyayya ta k'ara k'aimi gurin aikatasu. Yasmeen taji dadi kwarai ta hau godiya. Ai kuwa hasina tasha addu'a a wajenta. Hasina na sauketa a gida tayi gaba bayan Yasmeen ta cika Ummi da kayan dadi.     A ranar ta cinye hadin kaza biyu ta kora da ruwa ko abinci bai samu gurbin shiga cikinta ba. Tabbas taji alamar chanje chanje. (Mata a kula!!!)                      ********      KB bai dawo ba sai safiyar Litinin. Direbansa na daukarsa yace yayi ofis dashi. A ranar Yasmeen ta kara yin waya da Hasina a inda ta kara bata wasu shawarwarin da zata kula dasu karshe sukayi sallama.      "Wai me kuke k'unsawa ne?"    Hasina dake kokarin hadawa Abdullah tea tayi dariya      "Da wa kuma?"    Abdullah yana murmushi yace    "Naga kamar kuna kulle kullen mallakemu."    Ta harareshi da wasa    "Toh laifine? Ai dominku mukeyi."    Abdullah ya gyada kai yana dariya      "Hakane kam,saidai kada ki manta da kanwar taki itama,a shiryata zan baki ko nawa kike bukata kinsan fa karshen satin nan zamuje."    Hasina na dariyar yanda mijinta ke neman zama marar kunya akan kanwarsa Tasleem,tace     "Ba ruwanka da sha'aninmu,kud'inka ba kabar abinka. Ai na fika k'aguwa naje gareta."      Abdullah dariyar yake shima bayan ya yiwa shayin data had'a mishi kurb'a d'aya      "Ai shikenan,nabar lamarinku."  Sai kuma yaga Hasina ta zauna cike da damuwa a fuskarta     "Wallahi ina tausayawa Tasleem matuka,banji dadi da fushina ya janyo a farko ka koreta ..."     Ya daure fuska    "Maganar nan ta wuce My dear,abarta please. Ya labarin Hayat kuwa? Ya koma gida?"    Ya chanja darasin,ta tabe baki    "Ya koma jiya da daddare,wallahi Yaya hayat sai addu'a,iskancin nasa ma gaba yake k'ara yi. Kar kaso kaga 'yar iskar daya kawo a matsayin wacce zai aura. Baba yace bai amince ba amma naji ana batun ya kamata a bishi a sannu kada b'atancin yayi yawa,saidai a tuntub'i asalin yarinyar a gani."     "Allah Ya shirya mana zuri'a. Zai daina wataran."     "Uhum,Allah Yasa toh."                .       ********‬ "Princess! Princess please wait!"    Bata ko kalleshi ba har saida ta dangana da falonta ta zube saman kujera tana kuka. Kb ya matso ya dafata,ta fisge hannunsa         "Ka rabu dani,kaje ga Baby na tabbatar ta fini a wajenka. Idan har haka zamanmu zai dunga tafiya na hakura da rayuwa dakai Yaya kabir!"    Yayi mamaki don ya mance rabon data kirayi sunansa na ainahi saidai tace prince. Tabbas baiji dadin yanda bakinsa yayi ta subucewa wajen tarayya da ita ba yayi ta ambaton Baby kai harma da wasu kalamai na soyayya masu girma wanda a bakin Baby kadai yakejinsi kuma ita ta koyamishi. Ya dafe kai,saidai a daren yau daya kasa danne feelings dinsa domin shi din mabukaci ne ya nemi matarsa yaga bambanci a zahiri wanda watakil hakan yasa ya tsammaci da Baby yake tare.     Rungumo kafadunta yana rarrashinta hadi da bata hakuri kai harma da yi mata kalamim da idan Yasmeen bata manta tun farko farko aurensu rabonshi da yayi mata su. Dakyar ta hakura amma hakika abun yana cin zuciyarta,ta yaya ma za'ace namiji ya kusanceta yana ambaton sunan wata can wacce batasan da zamanta ba? Kai abun akwai ciwo ma ganin yanda ta soma shawo kan mijin nata yasa ta d'an saki jiki harma ta amince ta bishi suka koma d'aki mai yiwuwa a zatonta ya gano bai kyautata mata ba hakanan ta hangi tausayinta k'arara shimfid'e a kwayar idanunsa.      Kasa bacci yayi a wannan daren, lissafe lissafe yakeyi a zuciyarsa da kuma sak'e sak'e. Wai ana nufin sauran sati bikin Haris da Tasleem? Ya salam! Meke shirin faruwa? Shi fa dannewa kawai yakeyi amma abun yana cin ranshi. Ya fahimci cewar lallai kaunar da yakeyiwa Baby tsakani da Allah ce bawai don komi nata ba kamar yanda a farko yakesonta domin shi. Saidai ba don yaso ba dole ne ya tattara ya komo Kano yabar komai na kamfanin nasu a hannun mataimakinsa bisa umarnin da Abba ya bashi na yazo suyi shirye shiryen aure da Haris.      Akan dole suka shirya gaba daya har Yasmeen washegari suka kama hanyar Kano.  Wajen sha daya suka isa,Haris da kansa shine yaje daukosu. Yasmeen ta kankameshi tana murna da farin cikin ganin yayan nata gashi har wata kiba yayi tun ma kafin ya angwance. Ya saketa ya rungume KB. Basu iya fushi na tsawon lokaci da juna,saidai can kasan zuciyar KB kishi ne fal yake nukurkusarsa. Haris yana murmushinsa mai k'ara fiddo sirrin kyawu na halittarsa ya d'an bubbuga kafad'ar KB      "You are welcome to my wedding dear brother."     Murmushi yayi mishi  da gefen kumatunsa d'aya,ya jinjina kai kawai batare da yace mishi uffan ba. Yana kaunar Haris a matsayinsa na amininsa kuma dan uwansa saidai ya kasa jin zuciyarsa ta hakura da Baby. Hakanan a gefe guda ya gaza samun kwakkwarar matakin dauka. Mai yiwuwa dai yanda ya cewa Nas hakan zai aiwatar a sannu sannu ya raba Baby da Haris cikin sauki.     Suka dunguma zuwa gida. Wajen Abba suka soma shiga. Baya gidan sai Hajiya Aisha(Momi) mahaifiyar Haris. Tayi farin cikin ganinsu hakanan sauran kannen Haris,a karshe bayan gaisuwa da komai suka wuce gidan Daddy inda anan Yasmeen tayi masauki. Suna zaune wajen Hajiya Mariya mahaifiyar KB(Mami),Momi tayi kiran Haris tace yazo tanason ganinsa.       "Akwai abunda ya hadaku da dan uwan naka ne?"  Ta tambaya fuska a murtuke daman ba wani sakarwa Haris fuska takeyi ba.      "Babu ko daya momi,kinga wani abu ne?"     "Kwarai na lura da chanjawar fuskarsa hakanan na lura baku fiye sakin jiki da juna ba kamar da."     Haris baiso sam iyayensu su fahimci komai har a samu tangard'a a shirinsa.      "Babu komai Momi,a gajiye yake ne kuma banje daukosu akan lokaci ba shine dalilin fushinsa dani."    Ta gyada kai cikin gamsuwa    "Kana iya tafiya."    Ya mike ya fita, a farfajiyar gidan Daddy yaci karo da KB yana waya       "Nas kana ina ne?...Ok ok, saika dawo "     Ya katse wayar sukayi ido hudu da Haris wanda ke sakarmishi murmushin da shi kuma yake dauka matsayin na rainin hankali. Dauke fuskarsa yayi yana kallon harabar gidan da murmushin shima dauke saman fuskarsa.      "Dan uwana,mu mance komai kazo mu zauna musan abokan da zamu gayyato dinner. Kasan fa budurwa shafal nake shirin dauka."      Lallai Haris dagaske ya raina ajin Baby,ya dubeshi       "Ka manta harda saurata a matanka?"     Kirjin Haris ya buga,ya tsani KB ya danganta Baby da kayarsa. Kamar ya gayamishi magana sai kuma ya fasa ya shanye hadi da sakin dariya kad'an      "Gwara da kace sauranka. Me zanyi da ita? Zahra ce a gabana,ba saina tsaya ina k'ara nanata maka dalilina na aurenta ba. Tun farkon ganina da ita kai kanka kasan I hate her."     Kwarai shine yasan da wannan,ya jinjina kanshi tuni idanunsa sun sauya      "Meyasa baka bar masu sonta sun aureta ba?"     "Saboda su fahimci kuskuren da suka jima suna tafkawa da hakkokin Ubangiji dake kansu."     Kb ya cije lebbansa na k'asa kafin ya jinjina kai baice komai ba,yana shirin juyawa Haris ya riko hannunsa a sanyaye.     "Kada muyi haka aminina kuma dan uwana,mace bata isa b'ata zumuncinmu ba bare kuma 'YAR BARIKI. Muje muyi abunda ke gabanmu."    Zuciyar KB ta tab'u jin yanda Haris ke nuna tsanar baby k'arara,tsananin kishi ne ko tsananin kaunarta ce? Oho amma tunaninsa yafi bashi cewar Haris baison Baby. Shi kuwa zai jira iyakar tsawon kowane lokaci don mallakarta....!                         ******‬   KB ya saki jikinsa akayi dukkan wani shirye shirye dashi,bai nuna komai ba ga Haris. A gefe na Momy tayi kiransa game da son sanin labarin Baby. Ya sanarmata abunda ya girgizata. Wai baby tayi aure. Babbar magana...!   Rana Bata K'arya.....!!   Tun safiyar ranar asabar wanda ya kama ranar kamun amaren haris,amarya tasleem tun sallar asubahi ta kasa komawa bacci sakamakon fargaba da damuwar da take ciki na rashin sanin takamaiman irin zaman da zasuyi da mijinta wanda har zuwa lokacin babu wani fahimtar juna dake a tsakaninsu,hasina dake sharar bacci batasan tana yi bama. Tun tana zubar hawaye har bacci ya fisgeta a saman darduman. Sai wajen takwas taji hasina tana tashinta. "Amarya baccin ya isa hakanan,yau fa ba ranar bacci ne ba." Murmushi baby tayi wanda ya kara fiddo da kyawun fuskarta wacce tafi sati tana daukar gyara. Haka hasina ta sanyata a gaba saida ta fada bandaki sannan ta fiddo mata leshi mai kyau ta ajiye a gadon na inna,don tuni ta komo nan.  Bayan ta fito ta dubi kayan dake ajiye ja girgiza kai kawai. Ta janyo kenan da niyyar dubawa wayarta wacce mamma tayi mata dole wajen kunnawa ta dauki k'ara. Gabanta ya fadi sanin kowane. Kamar bazata daga ba,saidai ta daure ta dauka. Sallama ta soma yi kafin ya amsa daga can bangaren,shiru ya biyo baya."Baki iya gaisuwa bane?" Ta dan tsuke baki kamar bazatayi magana ba sai kuma ta gaisheshi. Haris ya lumshe ido yana mai jin dadin muryata yayinda yake sosa sumar kansa da mukullin motar dake a hannunsa."Bazan amsa ba tunda saida na rok'a,kina da bukatar wani abu ne?" Cikin jin takaicinsa tace"Ni bana bukatar komai." Murmushi yayi "Shikenan." Daga haka ya katse daman MURYARTA yaso yaji. Haka kawai takan yi masa dadi,karaf sukahada ido da Kb wanda ya fito daga daki,murmushi ya sakar mishi "Har ka shirya?" Ya kauda kansa yana mai numfasawa har zuwa lokacin ya kasa gane hakikanin sirrin dake ran Haris akan Tasleem"Na shirya,muna iya tafiya." Suka fita don zuwa kama wajen dinnerparty wanda zai kasance ranar litinin‬ Misalin uku na rana,tuni an soma  cika a filin farfajiyar gidan Alhaji babangida kasancewar  amaren biyu tare aka hada bikinsu. Babu wani kwalliya da sukayi ko kunshi basuyi ba sai washegari zasuyi. Baby tana zaune gefen gadon inna ta chanja shiga zuwa wata ruwan hodar atamfa mai ratsin fari,duk da ko hoda bata shafa ba amma tayi kyau kwarai. Hasina tana tsaye tana murza daurin dankwali taji muryar da bata zata ba tana sallama. "Yasmeen?" Ai kuwa ita dince ta shigo tana fadin "Wai ina amaryar tamu?"Ganin Hasina ya dakatar da ita kafin su sanya ihu su rungumi juna suna murna."Shegiya,daman kina zuwa Kzu?"Hasina tayi dariya baby kallon yasmeen takeyi yanda sukayi kama sosai da haris. "Mijinafa anan yake,ga kanwarsa." Yasmeen ta dubi baby sukayi murmushi kafinta dubi hasina"Toh ai nima prince dan kzu ne,gidan da zaayi bikin nan ne gidansu." Gaban baby ya fadi,taji hasina ta katseta"Kada dai kicemin wai Kabir dai?" Baby ta baza kunne sauraron amsar da yasmeen zata bayar"Eh mana." Ai saita mike tsaye a razane.  Basu lura da yanayinta ba. Ta juya musu baya cikin matukar razana da yanayi na tashin hankali.Yasmeen kanwar haris kuma matar kabir? Menene manufar aurenta da Haris,FANSA KO KADDARA? Zai ramawa kanwarsa wulakancin da Kb yake mata ne kodai kawai auren kaddara ce? "Ya kuke ciki yanzu dashi?" Maganar hasina ta katse tunanin baby.Hakan yasa ta waigo kadan ga son jin amsar yasmeen. "Hum,bar prince,dakyar bakinsa yabar ambaton shegiyarnan wai baby idan muna tarayya.Ai ina kara godewa Allah da zumuncinmu ya kara karfi na tabbata idan muna tare dake,matsalata zaizo karshe in sha Allah." Hasina tayi dariya"Kinga yanzu ba lokacin wannan bane,muje muga Zahra sai mu hadasu mu fita dasu." Baby tana jin fitarsu ta juyo da azama fuskarta ga hawaye shabe shabe,ta datse kofar,gidan ita kadai suna wajen kamu acan ake aikin girki. Wayarta ta janyo a fusace ta dannawa Haris kira. Alokacin yana haramar shiga wanka saboda zafi da akeyi na damuna. Yayi mamakin ganin lambarta,ya dauka"Haris menene manufar aurenmu?Ayau inaso na sani.  Yayi murmushi wanda ya danne faduwar gabansa saboda muryarta dake rawa"Hey,bayan da bakin alkalami ya riga ya bushe kike tambayata?Kin makaro Tasleem,ashe tunanin nan bai riski kwakwalwarki ba sai a kurarren lokaci?Hum! Bazaki gane waye Haris ba." "Ni kuwa nasan wanene Haris,mutum ne mai son kansa wanda zai iya cutar rayuwar wani don kyautatawa na jikinsa!Na tsaneka haris!Kasancewata YAR BARIKI a baya bazai zamana cewa bansan kima da darajar kainaba. Kayi nasarar rabani da kb,amma banajin zakayi nasarar daga darajar soyayyar kanwarka Yasmeen a zuciyarsa!Son kb yanzu na soma!" "Shut up!!" Tsawan ya daki zuciyarta ta tsorata.Gumi ya wanke Haris,jikinsa b'ari yakeyi sosai ya daki bangon dakin,muryarsa a kausashe"Kinyi kadan ki gayamin magana,ina kara sanar dake cewar baki kai darajar zamowa matar Haris ba!Ina maki rantsuwa da Allah idan bakinki ya kara ambaton wani Dan Bariki saina gwadamaki waye ni! Abu na gaba kinemi sanin bambancin zaman aure da rayuwar bariki.Namiji da muna maza!"‬ Tasleem ta tunzura saidai jin maganar hasina yasa tayi azamar kashe wayar ta ajiye. Acan kuwa,Haris zama yayi gefen gadonsa ciki tsananin damuwa da bacin rai.Meyasa har zuwa yanzu tasleem bata fahimtarsa ne? Wace irin matsala kenan zasu samu a zaman aurensu?Kunyar kansa ta kamashi,yau shi da kansa yake zagin amininsa kuma dan uwansa akan mace. Tasleem bata isa lalata zumuncinsu ba,bazai kyale hakan ta faru ba. Game da aurenta da yayi kuma..Murmushi yayi mai fassarori daban daban kafin ya mike ya shiga wankan da yayi niyya. Tambayar duniya hasina ta yiwa baby nason sanin abunda ya bata ranta saidai gabadaya batayi nasarar samun amsa ba asalima baby haushinta takeji tana ganin kamar ita da yasmeen bakinsu daya kuma suna da labarin komai. Haka dai akayi kamun nan fuskar amarya tasleem ba yabo ba fallasa,gwara gwara Zahra ita da take murna ta samu zabinta,ga tasleem kuwa,ko oho.   Washegari da safiyar yini aka kawo lefe na gani na fada karshe aka adanasu a gidan gwaggo hajara saboda idon mutane.Anyi yinin nan ma dai har lokacin baby bata da walwala,da yamma suna zaune a dakin anti hafsa,taji hasina na fadin"Bismillah,ku shiga tana ciki." Wadanda taga sun shigo yasa cikinta murdawa ba kadan ba. "MOMY!" Baby tayi maganar cikin rawar murya. Momy da manal sukayiwa juna murmushi. Baby ta dubi mutanen dakin,Safiyya ce sai humaira"Safiyya ku fita." Suna fita ta rufe kofar,ta juyo ta dubesu hawaye tuni sun soma zubomata kan fuska."Manal haka zakimin?" Manal tana murmushi ta dafa kafadar tasleem"Kada ki kawo komai baby,bamu zo don rusamaki farincikinki ba saidai momy nayiwa rakiya." Baby ta dubi momy,momy ta dan daure fuska bayan sun zauna gefen gado"Kin bani mamaki da har kika iya gujemin,kika yankewa kanki shawarar fita daga kungiya batare da kin cika sharuddanta ba.Hakikanin gaskiya koda kb ya bani labarin kinyi aure na kasa gaskatashi sanin yanda kika tsani auren saida ya bani tabbacin hakan kafin na gaskata. Na nemi Alhaji ubale daya bani aron manal tayimin rakiya saboda tabbacin dana samu wajen dalal akan cewar tasan garinku wanda a baya na dauk a Abuja kuke kamar yanda na samu labari daga bakinki."   Momy ta numfasa"Kaunar da nake maki yasa ban zurfafa daukar mataki akanki ba,illa dai saboda gudun gulmar mutan kungiya ya zama dolene na yanke hukuncin.Sanin kanki ne duk wacce ta shirya barin kungiya dole ta ajiye dukkan abunda ta mallaka a wannan tafiyar."Murmushi baby tayi"Momy ban taho da komai nawa dana mallaka ba sai mota da atmcard,daidai da takardun gidan suna cikin lokar kayana acan." Ta mike"Ina zuwa." Suka bita da kallo,ta kara kyau da cika sosai.Cikin takaici momy ta dubi Manal.   "Inajin takaicin rabuwa da baby. Karbar kadararta bazar rageta da komai ba domin a rayuwa bata rasa komai daya danganci dukiya ba." Manal tayi murmushi,ai tasleem taji dadinta tunda gatanan tare da danginta ita kuwa data taso a shegiya a wulakanttacen rayuwa fa? "Momy kina manta cewar dalal ta bamu tabbacin haris baya kaunarta ne? Da wuya ta samu wannan farincikin kuma na zaman aure,kalli fa kiga tsaleliyar yar shilar data zo a matsayin kishiyarta?"Momy tayi murmushi mai tarin ma'anoni"Kina tunanin wannan wacce bata da ilimin komai na harkar aure ta isa tasha gaban baby?"Momy ta girgiza kai"Ture wannan batun kawai,saidai bana tsammanin koda aurensu zai mutu a gaba,zata dawo bariki.Nasanta fiye da kaina,kaifi daya ce.!" Shigowar bby ya katsesu,atmcard da mika mata hadi da cewa"Miliyan biyar da wasu chanjina ne a ciki,mukullin mota kuma zan karbo wajen haris na damka maku." Momy ta karba "Kin zabi fita daga cikinmu har abada?" Murmushin bakinciki tasleem tayi.....  "Sanin kanki kece kika tsundumani a wannan harka wanda ko a mafarki bantaba ganoni cikinsa ba.Kwarai nabarshi kenan har abada,bana kuma marmarin k'ara yinsa.A karshe nasihata a...." Mikewar da momy tayi ya dakatar da baby daga cigaba da zancenta,cikin daure fuska tace"Munyi abunda ya kawomu,babu bukatar nasiharki,ki rike ke daya idan da riba zamu gani a k'as." Daga haka momy tasa kai ta fita,Manal ta mike tana gyara zaman mayafin doguwar abayar jikinta,tasleem ta dakatar da ita ta hanyar riko hantnunta"Idan na tuna ta sanadina kika fada wannan halakakkiyar rayuwar nakanji kamar Allah bazai yafemin ba,kiyi aurenki da zuciya daya na tabbatar maki in sha Allah bazakiyi kaico ba."  Manal tana duban bby da idanunta da suka  kad'a sukayi ja tasa dayan hannunta ta matsar da hannun baby"Nike da iko da rayuwata bake ba,kin barmu kink'i sanardamu labarin aurenki koda mutum daya cikinmu ne,wannan ya nuna dagaske kina kyamatarmu ayanzu.Toh zamu barki zamuyi nesa dake har abada."Daga haka manal ta fice,baby na hawaye.  Yasmeen ta dago hab'arta tana murmushi wanda ya kara ruda Baby ganin tsantsar kamanninta da Haris ya kara fitowa."Masha Allah,nidai nakan rasa wanda yafi wani kyau cikin matan yayan nawa."Baby murmushin dole tayi mata a inda su hasina ke bata amsarta.A karshe dai akayi shirin tafiya,waje daya aka hada amaren anan gidan malam hussein akayi musu nasiha mai ratsa zukata wanda yasa baby kuka harda sheshsheka,kaiconta?Inama bata amince da usman ba a farko,da bazai soma kusantarta ba har ta hau tubalin ruguza rayuwarta,inama ace bata bayar da kanta ga rilwan ba.Kaiconta da ayau bata da wani abu mai daraja da zata tafi dashi dakin aurenta ba! A karshe dai tsoffin suka sanyamusu albarka kafin tasleem ta shiga wajen hajja dasu hajiya da atine nan ma nasiharce sannan suka hau hanyar kano,taso ta kara ganin mamma amma babu ita,motarsu tasleem da hasina da sauran yanuwan mamma kai tsaye suna isa Kano aka nufi gidan waziri da ita...!  Sunyi mamakin ganin taron jama'ar gidan da sukazo don tarbarsu,gashi harda anko sukayi.Juwairiyya wacce ta kasance diyar Alhaji nasir waziri kuma kawar tasleem a baya ta taho a guje suka rungume juna suna murna.A karshe da gwaggo amarya(maman juwairiyya)da wata mata sukaja tasleem ciki har zuwa wani daki inda wasu mata  'yan nijar suke ciki,suka rufa dakin. Aka mika su anti hafsa da sauran jama'ar wani kayataccen falo aka cikasu da kayan makulashe a gefe ga na'urar sanyaya daki yana aiki.A bakin wata sukejin ashe wani walimar suka shirya nan zuwa karfe uku za'a soma kuma suna bukatar dangin miji suzo harda angon.Su hasina sukaji magana banbarakwai,tayi kiran yasmeen ta sanar da ita,yasmeen tace ba matsala daga garesu zata nemi yayanta.         ******   Yabar kokarin tayar da motar ya tabe baki kafin ya dubeta ta cikin bakin gilas din idonsa"So what?" Yasmeen cikin langabe kai tace"So,suna bukatarka da abokanka."Murmushi yayi na gefen kumatu daya kara fiddo kyawun Haris."Sai yanda ta yiyu malama."Yaja motarsa!‬. Yasmeen tayi murmushi kawai don tasan halin yayannata,zai wuya yak'i zuwa.           ******   Acan kuwa matan nan haka sukayita dirje yasmeen da kurkur da dilka duk da sun yaba da gyaran 'yan kazaure,daga karshe ta kara yin wanka da ruwan dumi,suka hada turarukan wuta masu kamshi suka sanyata ta tsaya hayakin yana gauraye jikinta kafin kuma gwaggo amarya ta fita bayan tasleem tayi sallar azhar an bata abinci taci kadan, tayi kiran hajiya nafisa omar wacce ta kasance gwana a wajen make up na amarya,(talla agareku kenan mata!),aka bar musu dakin sai gwaggo kadai a ciki da tasleem wacce ke tashin kamshi. Awa daya ta kaisu ga yin kwalliya. Kwarai tasleem ta yaba da hannun nafisa,kafin gwaggo amarya ta fiddo wani rantsastsan leshi kalar skyblue mai adon duwatsu wanda dinkin ya dace kwarai da leshin,sunata fargaban kada yak'i shigarta saidai cikin ikon Allah ya zauna d'as ajikinta duk da cewar ya kamata sosai,sukace ba matsala tunda alkyabba zata d'ora...  Misalin uku a rabi,filin cikin gidan waziri cike yake da yan uwa da abokan arziki,ga kid'a dake tashi daga gefe kuma yanmata ke tik'ar rawa abinsu.Hasina da sauran jama'ar da sukazo daga kazaure tuni sun zauna suna baza idon ganin ta inda amarya zata fito.Karshe dai amarya bata fito sai bayan la'asar,sukaji an tsaida kid'a kafin ayi sanarwar zuwan amarya sannan aka ware wakar da basusan da zamanta ba,na biki wanda a farkon farawa mawakin yayi godiya ga yayan ango daya bashi damar yiwa kyakkyawa jinin sarauta,gimbiya tasleem wak'a.Anan suka gane aikin Abdullah ne,hasina tafi kowa mamaki tunda batasan da zaman wakar ba.Juwairiyya da wata aminiyarta Nadiya sai yara kananu masu kaya iri daya sune suka jagoranci shigowar tasleem wacce kanta yana k'asa tana takowa a sannu bayan tayi kokarin maida hawayen dake taho mata.Wata dattijuwa take faman rangad'a bud'a ga masu hotuna nayi kada kuso kuga yanda amarya ke kyalli kai kace watan daren sha biyar ne.Waje ya rude da sowa da daukar hotuna har dai aka ta zauna.  Tsawon minti goma ango bai iso ba,tana ganin yanda yasmeen ke zaryar kiran waya tana tsaki cike da takaici.Murmushi kawai baby tayi,inama yasmeen zata bar wahalda kanta don abune mai matukar wuya Haris yazo wajen nan.Ga mamakinta kuwa,saiga mota ta tsaya adaidai saitin inda aka shimfida jan darduma don shigowar bak'i.Kabir ne ya soma bude mazaunin direba ya fito,kafin Abdullah ya fito,sai abokinsu soja dake kaduna,da musty abun mamaki kuma harda Rilwan a dayan motar ta baya,daman ya dawo daga kasar wajen ne?Shine tambayar da tasleem ke yiwa zuciyarta.A karshe sai ga ango ya fito cikin farar shadda data sha aiki daidai dana sanyawar maza,hular kansa ta zauna d'as,sunyi kyau matuka.Matasa ne masu ji da kudi da kyau.Kb idanunsa na boye acikin bakin gilashi wanda hakan da yayi ya boye sirrin dake cikinsu a fuska kuwa murmushi yakeyi bazaka taba kawowa akwai wata damuwa tattare dashi ba. Ina gefe tare da jama'ata na duniyar facebook muna ciye ciye.Mafi yawa sun tausayawa kb,banda ni dasu o'o....‬ Tun daga nesa yake dubanta baya ko kifta idanu,suna hada ido ya basar gami da dauke kanshi a hankali ya sauke nannauyan ajiyar zuciya sai kuma MATSANANCIN KISHIN NAN dayakeji tun farko akanta ya dabaibaye zuciyarsa.Da ace yana da ikon hana wadannan matasan da suka sota a baya(Kb,musty da rilwan)kallonta,da tuni ya yanke wannan hukuncin.Kamar yanda gwaggo amarya ta nusar da ita hakan kuwa ta aikata,wato mikewa tsaye ta nufi daidai inda mijinta ke tsaye a hanyar shigowa filin,cikin takunta na isa da jin kai,kai kana ganinta kasan ba'a k'asa ta tsinta ba gado ne.A gefe ga yara goma,kowane biyar a gefenta.Kanta yana k'asa cike da fargabar fuskokinsu take tafiya,dukkan zuciyoyin ukun nan wadanda suka so samunta babu wanda bai raunana ba musumman rilwan wanda ya jima baiyi tozali da ita ba saidai sunyi kokarin kore abunda shaidan ke raya musu sakamakon. tunawa da sukayi,matar wani ce!Saida ta isa gefensa kafin kuma abun mamaki ta tsinci yatsunsa ,batasan sadda ta dubeshi ba... Murmushi dauke saman fuskarsa baya ko kallonta.Ta ayyana cewar ganin idanun mutane ne yasa shi hakan.Suka taka har mazauninsu suka zauna.Ta soma kokarin kwace hannunta a hankali saidai ya dubeta ido cikin ido,bata tab'a ganin wadannan manyan sakonni ba acikinsu kamar yanda bata taba kawowa akwai randa zata samesu ba.Murmushi mai ban mamaki ya sakarmata wanda ya jefata a tunani,duk saita raina haduwarta akansa.Ta daure fuska ta kauda kanta tana kallon masu daukarsu hotuna,hakan yasa ya zare hannunsa a hankali. A gefena nima na kasa hakuri na maida dubana ga yan uwana bayan na kurbi lemo"Kun fahimci sakon da Haris ke isarwa tasleem?"Ai nan kowa ya soma fadin albarkacin bakinsa,ummu aliyu da ummu faruk ba'a barsu a baya ba,gasu elkanawy da mai babban suna.Hakanan na hango mutan hannu da yawa writers dana dm suma suna tofa nasu,ga zee town wacce itace karshen magana.Shakkah babu mun gano Haris na yiwa matarsa so mai wuyar fassarawa saidai bamu san dalilinsa na b'oyewa ba! Sannu bata hana zuwa...!!!! Haka aka gama taro lafiya,koda ango ya tashi tafiya,tasleem ta gaisa da abokansa, kamar bata taba wata mu'amala dasu ba haka ta nuna.Ta tambayi rilwan namesake dinta da matarsa,ya sanarmata tare sukazo kano tana can gidan antinta.Tace ya gaishesu,bayan duk sun shiga mota,haris ya matso dab da ita har kafadunsu na gogar juna"Ki zama cikin shiri,da misalin karfe takwas zamu tafi dinner."Cikin marairaitar fuska wanda batayi hakan da wata manufa ba saidai gogan yaji a jikinsa tace"Nikam banajin zan iya zuwa,kuje da hasken idaniyarka,na gaji da yawa." Yaji dadin maganar saboda abu biyu,bayason ayi rashin sa'a ta hadu da fuskar data santa a rayuwar da tayi na baya,hakanan bayason kallon da wadannan mayun ke jifanta dashi."Kin kyautawa kanki kuwa,zuwanki ba alheri bane.Karki samu damuwa,zahra ta wadatar." Maganar ta daki zuciyarta,kenan ko a jikinsa? Haka kawai taji kishin Zahra ya mamayeta,wanda bata tabajin irinsa ba."Juya ki koma,ya dace ki goge kwalliyarnan haka,kamar aljana."  Batasan sadda ta watsamishi kallo da dara daran idanunta ba shima kallon ya jefeta dashi alamun ramuwa."Malama kada ki dungamin gezau idan na tafi,yi azamar komawa ciki please,sannan fuskarnan a wanketa."Murmushi taso tayi saidai ta fasa, ta bude baki zatayi magana saidai ta fasa.Juyawa tayh tayi gaba ta barshi anan.Ya numfasa bayan ya bita da kallo tana takunta mai fisgarsa,ya shige motar suka tafi.          *****  Tana kallon su juwairiyya dasu hasina anata kyalkyale fuska da zummar tafiya wajen dinnerparty,ita kuwa doguwar rigar bacci ta zura mai kauri ta dora zani samansa.Matar musty,Fahima sai faman zolayarta takeyi wai yau angon na Zahra ne ita kam murmushi kawai takeyi.Haka suka fice bayan sun dauki gayu,ta matsawa hasina tabar ummi awajenta,ita kuwa hasina daman batason tafiya da ummin tafison daga ita sai abdul dinta ko don su tunanowa zukatansu ranar nasu dinar da wannan soyayyar.Tasleem tana kwance ta dora ummi saman kafafuwanta tana mata wasa,taji shigowar gwaggo amarya.Kira ne daga mahaifinta!!  "Tasleem bakiji abunda nace bane?Ki tashi kije,suna nan a rumfar waziri."Idanunta tuni sun soma kawo ruwa,gaba daya tarihinta ya dawo mata.Kalamansa na karshe agareta ya dawo sabo fil a kwakwalwarta."Yanzu yana sona kuwa gwaggo?"Cikin jin tausayinta,gwaggo amarya tasa hannu ta dauki ummi kafin kuma ta bata amsa murya a sanyaye"Akwai uban da zai haifi diyarsa yace baya sonta?Wancan ma kuskurene ke kanki kinsan an kauce hanya amma bayin kansa bane.Banda haka ma,ba'a fushi da iyaye,kije ki nemi gafararsa kafin ki soma rayuwarki ta aure kinji ko?Albarkarsu ne ke kai mutum matakin da bai taba hasasowa ba(love you mom nd dad)."Tasleem ta share hawayenta ta mike,hijabi taja ta zura sannan ta zura silifas din juwairiyya ta fita.Gaba daya ta manta fasalin gidan,saida ta nemi taimakon wata baiwa tayi mata jagora har sashen waziri.Dogarawan dake zaune anan waje suka gaisheta itama gaidasun tayi,gabanta na dukan tara tara yayinda wasu ruwan hawayen suke ta bulbulowa,haka ta shiga da sallama.Muryoyi biyun nan suka amsa!  Ta daga kanta sukayi ido hudu da mahaifinta wanda rabonta dashi shekaru uku da watanni kenan.Alhaji Khalil Abba kasa hakura yayi har diyarsa ta karaso wajenshi,ya mike ya nufeta itama jikinta rawa yakeyi,gabanta na dukan tara tara.Rungumeta yayi yana hawaye"Nagodewa Allah da Yasa inada rabon ganinki kafin mutuwata ta riskeni tasleem."Kuka sosai tasleem takeyi,farin cikin data rasa a baya wanda har ya kaita da jin tsanar mahaifinta,ya wanke mata zuciya.Dakyar abba ya jata suka zauna.Ya dubi waziri wanda zuciyarsa ta gama mamaya da tausayawa uba da d'iyarsa"Tasleem ta girma yallab'ai,duba yanda ta kwaso kamannin Maryama?"Waziri yayi murmushi.Tasleem ta ankara da bata gaishe dasu ba,hakan yasa ta zamo jikinta daga kan kujera zuwa k'asa tayi gaisuwa.Waziri ya dafa kanta,cikin murmushi ya amsa mata.Saida ta nutsu ne,sannan waziri ya soma da bismillah kafin yayi dogon jawabi game da girman iyaye har yana hadawa da ayoyi masu tsarki na k'ur'ani da hadisai kafin ya nemi tasleem data yafewa mahaifinta.  Tasleem cikin rawar murya tace"Baffa ni yafi cancanta na nemi gafararsa saboda nice 'ya a wajenshi.Saurin fushi da zuciya irin tawa wacce ta kaini ga mugun dana sani ya haneni hangen hakan da farko,tabbas iyaye basu zamto masu cuta ga yaransu ba,sunfi sonmu sunfi nuna mana kauna akan kowane mahaluki a duniya saidai ya biyo bayansu,na tafi nabar mahaifina banko k'ara bincikar lafiyarsa ba,ban nemi zuwa inda yake ba,na mance iyaye suma suna da hakki akanmu." Ta mike daga zaman da take zuwa durkuso gaban mahaifinta wanda ciwo duk yabi ya ramar duk da dai yanzu alhamdulillah yana samun waraka."Ka gafartamin abbana,nayi babban kuskure,bazan k'ara ba."Abba ya rungumota shima hawayen ne wani ke bin wani,harda na bakincikin rabuwa da mahaifiyarta da yayi."Komai ya wuce diyata,Allah Yayi maki albarka,Ya baki zaman lafiya da mijinki.Sannan Ya kara tsareminku gaba daya." Ranar ta jima anan tana hira da iyayenta maza biyu kafin kuma wajejan goman dare tayi musu sallama ta miko hanya zuwa ciki,burinta tasa hindu a idonta!  Tunda ta samu labarin itama ai tana gidan a wajen abbanta take mamakin yanda akayi bata hadu da ita ba,koma dai sun hadu amma hindu bata kulata bane?Oho. Tanason kanwarta don ko sadda tayi rayuwar bakin ciki a gidannan harda ita cikin masu tausayamata idan an cire direbansu da kuma kulu.Allah Sarki kulu,itama ko tana wace duniyar? Hamida daman bata daga lissafinta amma ance jini daya yafi gaban wasa(lol,hope hakane?),dole akwai wannan son na yan uwantaka a ranta. Tazo daidai hanyar shiga sashen gwaggo amarya,taji an rufe mata idanuwa da hannu.Tasan su Hasina baici ace sun dawo ba yanzu,tsoron da taji na kada ya zama namiji ne kasancewar gidan baya rabo da gayyar maza yasa tayi azamar juyowa. Bak'a ce saidai bata da bak'i sosai,hakanan doguwa ce don a tsayi ta taddo tasleem,tana da siririyar fuska.Wannan kamannin nata da Abba har yanzu yana nan.Kafin zuciyar Tasleem ta gama hasaso mata kowacece,budurwar da bata fice shekaru ashirin da daya ba ta rungumeta tana ihun murna"Yaya Tasleem ashe da rabon haduwarmu?"‬ Tasleem ta dago fuskarta,"Hindu,haka kika girma?"Kome hindatu ta tuna,tayi azamar riko hannun tasleem"Zo muje sister."Ta bita har suka isa wani karamin garden wanda ya wadatu da hasken wutar lantarki,saman wasu kujeru suka zauna.Hindatu tana murmushi ga fuskarta duk hawaye ta dubi baby"Nace muzo nan ne saboda banaso mutanen gidan suji tattaunawarmu.Basu da labarin bakya wajensu brother ba acan Abuja,kamar dai yanda waziri yace muyi gum da bakinmu ko hamida Abba bai bari na fadawa ba hakane yasa ma ba'a barina yawan zuwa garin na saboda dole wataran su gane muddin muna yawan zuwa." Cikin murmushi mai hade da kuka tasleem tace"Ya hakurin rashin dan uwanmu hamid da mamanku?" "Da godiya,don Allah sis ki yafewa..""Komaiya wuce hindu,na jima da yafe musu."Hindu na zubar hawaye tace"Ashe daman yaya usman ne ya lalata rayuwarki?Nima sai bayan kwana uku da tafiyarki naji yana gayawa mama,naso sanarwa abba sai tsoro ya haneni,wallahi ya cuci.."Tasleem tana dariya mai ciwo ta dakatar da ita, "Haba hindu,nace maki komai ya wuce abar tuna baya ko?Ni ba wannan ba,anti hasina ta sanarmin kuna jarabawa bazaki samu zuwa biki ba,ya akayi kuma har kikazo baki nemeni ba?" Murmushi tayi tana mai share hawayen fuskarta"Kiyi hakuri,na hana antina da brother su sanarmaki ne cos i want to surprise you,sai kuma ya zamana bayan na sauka garin nan anti hamida ta kirani wai sunyi fada da kishiyarta tayi mata duka shi ya tashi hankalina na zarce gidanta na mik'ata asibiti saida akayi mata dressing don taji rauni a fuskarta.Toh bayan mun dawo ma nan mijinta yace tunda har ta fita bada izninsa ba wallahi bazata shiga gidansa ba,kinsan kuma anti hamida ba hakuri,yana zaginta tana ramawa a karshe dai ya nemi dukanta dakyar makwafta da suka bashi hakuri ya barta ta shi shiga ciki yana goranta mata cewar ko b'atan wata bata tab'a yi ba a gidansa.Hum!Wallahi ni masifar nan ma ta gidan Anti hamida yawa ne da ita,shi kuwa nataccen yak'i sakinta kamar yanda take mahaukacin son hakan.Bata sonshi shine ya hanata ganin girmansa.  Tasleem ta tausayawa rayuwar kanwartata,maganar hindu ta katseta"Tace na gaisheki,sannan na rokeki ki yafemata kafin ta warware tazo gidanki ku gaisa." Ranar sun jima hira kafin su tashi su kama hanyar komawa ciki inda anan hindu ke bata labarin hamza yayanta,wanda tun yayashe dukiyarsa da matarsa tayi ta gudu ta barshi da yaransu uku har yanzu bai dawo hayyacinsa ba don ya zama kamar wani tab'abbe,yaran dai suna hannun dangin matar domin mayar mata dasu yayi saidai su kansu iyayen nata basusan duniyar da take ba daman ba wani ganin girmansu takeyi ba.Hindu ta k'ara da cewa"Yanzu haka yana nan a daya daga cikin gidajen da Abba ke zuba 'yan haya,gashinan dai koda kaje gurinsa banda labarin matarsa da tsinuwa da ashar da yakeyi gareta ba abunda yakeyi.Ai alhaki kwuikwuiyo ne fa,kawai dai wanda ya mutu ya mutu sai fatan samun rahmar Allah garesu amma..Hum."Tayi shiru,tasleem ta jinjina kanta,tabbas Allah tun anan duniya yake nuna ishararSa ga dan adam,yanzu ina raliya da usman? RAYUWA CE! Gashi itama ta chanja.  "Daman nasan hira ce ta tsaidake,ga wayarki tana rurin neman agaji tun dazu,maza kije ki duba ko mijinki ne."Tasleem ta nufi dakin tabar hindu na kiran neman abinci wanda hakan itama hakan ya tunano mata da tsohuwar yunwar cikinta.A gadon ta tara da Ummi na sharar bacci,ta nufi gurin wayarta dake blinking,ta duba,ai kuwa shi dinne har missedcalls biyar,ta tabe baki,mai yiwuwa dai abunda ya saba na cin zarafinta shine yasa shi bid'arta.Ta jefa wayar kan gado ta cire hijabin jikinta,tana niyyar ficewa falo don ita dinma yunwar ta addabeta,wayar ta dauki k'ara a karo na shida.Kamar bazata dauka ba sai kuma tunanin da tayi na a yanzu fa yanda iko akanta yasa ta dagawa."Hello,assalamu alaikum."Ta fada cikin sassanyar muryarta.Shirunminti biyu baya har tana shirin katsewa ta jiyo muryarsa inda ya amsa sallamarta,tana iya jiyo hayaniyar jama'a da ababen hawa watakila dai an tashi taron"Menene dalilinki nak'in d'aga kirana alhalin kina sane cewar.."Kome ya tuna sai kuma ya katse maganar da yayi niyya...  Yaja karamin tsaki"Ina kika shiga?"Ita dinma duk da taso taji abunda yaso fada saita basar,ta soma hango wasu abubuwa amatsayinta na wacce bata dauki kanta yarinya ba,akwai ta da son girma sai kuma akayi sa'a Allah Ya bata baiwar hangen nesa daidai da abunda kwakwalwarta kan iya dauka.Tafiso ta gani a k'as kada ya zamana ba hakan bane tasha kunya.Numfasawa tayi"Ina wajen Abba ne." "Ok,mu kwana lafiya." Ya kashe wayar,ta tsinci kanta da murmusawa tare da yin kwafa ita kadai tasan abunda zuciyarta ke ayyana mata.Daga haka ta fita. Dawowarsu anti hasina,hira ta kacame a rumfar gwaggo amarya wacce tuni ta nemi makwancinta.Nan suke nunawa Tasleem hotunan ango da amarya,sunyi kyau ainun,hotuna biyu duk angon danna waya yakeyi,daya kuwa cikin damuwa yake.Yayinda wasu yake dariya,hatta da inda aka tanada domin zamanta ta gani,wani wurin cake yake sanyawa Zahra a bakinta harda wani rumgumota jikinsa.Tabbas zuciyarta ta soku,ta kauda kanta a wayance ta barwa hindu rikon wayar.Sukayita hira kafin bacci.‬ Washegari tun safe akaje akayi jere da kayayyakin da Abba ya bada aka siyo duk na bukatar gida.Misalin bakwai na dare aka soma shirin kai Amarya Tasleem gidanta.Tayi wanka tsaf,aka turareta da turarukan wuta na jiki masu kamshin gaske.Kuka takeyi ba don komai ba saidai doguwar nasihar da abbanta yayi gareta,shima yayanta ya d'ora da nasa.Bata tab'a kawowa ko a ranta ba cewar akwai ranar da zata tsinci kanta ba a gidan aure.Haka ta shirya dakyar,ana sanar da zuwan masu daukar amarya duk saita k'ara rikicewa saboda tausayawa rayuwarta a gidan da zata shiga. Misalin bakwai da rabi kuwa,tuni baby ta tsufa a gidanta,hakanana ranar dai aka kawo Zahra wacce take a matsayin amarya. Bata saka ran shigowar haris ba,hakanan ita kanta a wannan ranar tsananin kunyarsa ne ya dabaibayeta,menene yayi mata ragowa da har Haris zai d'okantu da ita a wannan daren?Tana cikin kukan kuma ga mamakinta taji muryarsu.Hakan yasa ta tsaida k'arar kukanta,ta lura daga haris sai abokinsa soja. Addu'a da 'yar karamar nasiha saidai mai fa'idoji da yawa yayi musu kafin daga bisani ya ajiye mata ledojin hannunsa yayi mata saida safe.Tare suka fice da Haris din zuwa sashen Zahra. Har wajejan tara bata ga Haris ya shgo a,wannan ne dalilin da yasa ta fidda rai da shigowarsa,mikewa tayi ta cire alkyabbar jikinta sannan ta fidda farin leshinta dinkin riga da siket daya kama jikinta sosai.Babu bukatar tayi wanka tunda daman tuni a wanke take tas saima kamshin dake tashi a dukkan jikinta.Riga doguwa har k'auri na bacci mai hawa biyu ta zura kalar bak'i wanda ya k'ara fiddo da farar fatarta sai ta fito a bafulatanarta sak!Ba wani gashin azo a gani ne da tasleem ba saidai babu laifi ya sauka a kafadunta,ta k'ara gyara zaman ribbon din kanta,sai lokacin ta lura da kwalliyar komai a d'akin,fari da purple ne,abun ya burgeta.Batayi wata wata ba ta kashe fitilun ta kunna na gefen gadon,kwanciya tayi ta rufe rabin jikinta da bargo,a sannu taji hawaye ya gangaro bisa kuncinta."Baki jiran mijinki?"Taji muryarsa. Tayi azamar share hawayenta,tuni haske ya gauraye dakin,wani kamshi na sabulu da turare ya bugi hancinta.Bata ko dubeshi ballantana yasa ran zata mike zaune.Bai damu da yanda ta shareshi,darduma ya janyo ya shimfida a gefen gadon sannan ya tada sallah.Kasancewar gefenta yake tana kallonshi,cikin kira'arsa mai dadi yake karanto suratul A'ala,kafin a raka'a ta biyu ya jawo suratul Kafirun wanda ya bata tabbacin shafa'i da wutri yakeyi.Jallabiya ce marar nauyi a jikinsa fara tas,fuskarnan tamkar an k'ara sirantata,ga wani shek'i da yakeyi.Murmushi tayi wanda ya zubo da ruwan hawaye,tun hankalinta yana gareshi har ta fada kogin tunanin yanda ta maida kanta tamkar dustbin a baya wacce kowane datti ake kwasa a zuba cikinta.Yau ga ranar k'in dillanci,da ace abun ya tsaya kadai a wannan kaddarar na fyade da Usman yayi gareta,toh da damuwarta batakai har hakan ba,ashe wannan ne alfaharin kowace macen kwarai?Lallai ta tafka kuskuren da takeji inama inama hannun agogo ya dawo baya ta gyara.Hannunsa taji akan fuskarta.. Wannan ne silar dawowarta cikin hayyacinta,tayi azamar dubansa bata ko kifta idanunta.Ko me ya tuna sai ya sauke hannunsa cikin sassanyar murya yace"Ya dace zuwa yanzu ace kin fahimceni,banason kukan mace."Daga haka ya mike,"Kinci wani abu kuwa?"Bai saurari amsarta ba  ya dauko ledojin,inda ya shimfida darduma ya zauna."Taso nan."Ta soma jin ya takura mata,a ranta tana tambaya daman Haris yasan bata da sallah ne ko kuwa dai ya mance da batun nafila da akeyi don nuna godiya ga Allah a irin wannan daren? Ido hudu sukayi,yayin data yaye bargon ta zuro kafafunta kasa"Nifa ban tare da yunwa."Harararta yayi"Kizo dai."Ta lura da mayataccen kallon da yake watsa mata.Toh menene laifin shigarta ita da a baya ma tayi wanda yaci uban wannan ta fita?Ai wallahi ba karamin kunyata surarta tayi ba a baya kamar wacce batasan darajar killacewa ba da suturtawa,tabi umarninsa don kaucewa mayatattun idanunsa.Ya bude ledojin,daya kazar yahuza suya ce cikinta,dayan kuwa furarsu ce sai ruwa da lemo.Ya tura mata ledar kazar fura yaja, Dolenta ya sanyata a gaba da kallo tana tsakura tana ci,haushinsa takeji na yanda ko 'yar tarairayarnan da ango ke yiwa matarsa baiyi mata ba,fura yake kurb'a abinsa ya nuna kamar baimasan tanayi ba saidai duk d'agowar da zatayi idanunsu kan shiga na juna,hakanan sukanyi kokarin kaucewa sakonnin dake yawo acikinsu.Tattarawa tayi ta mayar ledar,ruwan kawai ta kurb'a kafin ta mike ta barshi zaune bakin saman dardumar yana kurb'ar furar hannunsa.Bandakin ta shiga ta wanke hannunta ta goge da karamin towel sannan ta fito.Cikin jin haushi irin kallon da yakeyi gareta ta kauda idanunta wadanda fitowarta daga bandakin kuma bisa kuskure suka shiga cikin nasa.Ta nufi gado zata kwanta"Badai kwanciya zakiyi ba daga cin abinci?Kada ki kwanta ki tsaya ya d'an fad'amaki ko?" Batace komai ba,"Kashe fitilar nan." Tayi mishi wani irin kallo yayi kamar bai gani ba,ya rufe murfin furar ya kora ruwa kad'an kafin ya zagaya toilet.Ita kuwa tana kashe fitilar tayi kwanciyarta taja bargo.Minti daya sai gashi ya fito,taji bak'on abu. Kwanciyarsa da janyota jikinsa,ya faru ne a lokaci guda,ta zaro ido tana mamakinsa."Allah Ya tashemu lafiya,sweetdreams."Ya fada kamar mai rad'a.Wanda ya janyo mata kasala,ta lumshe ido tana shakar kamshinsa har batasan sadda bacci ya sureta ba.          ****   A hankali taji kamar ana jan yatsun kafafunta,taja tsaki ta k'ara janye kafafunta ta kudundune cikin bargo"Please barni mana."Tayi furucin cikin magagin bacci,batason ta daina wannan mafarkin da fuskar Haris,taji anja kumatunta ana cewa"Wai nan kece uwargida,amma kin kwanta bacci har kanwarki ta kammala had'a breakfast." Ta shafa kumatunta tana yamutse fuska cikin jin haushin mintsilinta da yayi,ta bude ido tarr tana dubansa,yayi wankansa ya had'e cikin kananun kaya,jan tshirt ne marar kauri sosai sai wandon jeans bak'i.Sumarsa yake k'ara gyarawa,muskutawa ta k'ara yi tana murmushi,wani irin so da kaunarsa takeji matukar gaske,batasan tana kaunarsa har haka ba sai yanzu."Kada ki cinyeni madam,bar kallona."Kunya ta kamata,ta tsuke baki ta mike. Akwatinta karama ta dauka wanda ta zuba abunda tasan zata nema a wannan safiyar.Undies dinta ta zaro da auduga.Kafin ta fiddo sabon tawul dinta ta rufe jakar.Koda ta juyo tuni yabar dakin taja kofar ganin a bude ya barta sannan ta fada wanka.Takai tsawon minti talatin,daman fa shirin baby sai a sannu.Ta kimtsa kanta ta fito daure da tawul iyakarsa gwuiwarta,karamin tawul cikin ukun data gani a bandakin tayi amfani dashi wajen goge kanta.Ta kammala ta shafa mai kafin kuma ta shirya cikin wata atamfa holland mai kalar orange da ratsin fari fari.Dinki mai hannu 3quarter hakanan gaban rigar yasha adon duwatsu ya kamata tsam,siket din ya zauna mata sosai,ta sanya dankunnenta da sarka fashion fari mai kyalli kai ka rantse wani diamond dinne.Hoda kawai ta shafa ta sanya jan baki ja kadan,sannan ta murza daurinta ta k'ara feshe jikinta da turare.    Kofarta ta bude bayan ta zura takalminta mai karamin tudun dunduniya,basunan a falon nata,hakan yasa ta fito sai kuma ta tsaya jiyo muryarsa yana saukowa daga bene. Wayar yakeyi yana cigaba da kallonta har ya karasa saukowa,ta lura sallama yakeyi da soja wanda zai koma Kaduna.Ta dauke kanta tana duban corridor din,dubanta yayi tun daga kasa zuwa sama,shigar ta burgeshi matuka hakanan kyawun nan nata ya kara fitowa ga wannan azababben son daya jima yana nukurkusarsa nata."Wallahi bansan yawan kallo,ka gayamin inda kanwata take."Ta fada tana murmushin mugunta ganin yanda ya shagaltu da kallonta."Ta rama kenan."Ya fada a ransa,a fili kuwa harararta yayi yana murmushi kafin ya tabe baki ya juya ya nufi hanyar sama"Bake nake kallo ba,ja girarki ce tayi yawa."Dariya ta subuce mata,a iyakar saninta batayi jagira ba.Ya tsaya ya juyo,har saida ta dan ja baya sakamakon kusancin da sukayi tunda daman tana biye dashi ne.Hannu ya daga zai kai saman fuskarta yana fadin"Dariya na baki?" Wayarsa tayi k'ara yayi azamar matsawa idonsa a kanta ya zaro daga aljihun wandonsa."Dan uwana an tashi lafiya?"Tabi gefensa ta wuce,acan ta iske zahra cikin brown shadda tayi kyau itama. Gaisuwa cikin mutunta juna ya shiga tsakaninsu,kafin zahra tayi mata bismillah zuwa dinning table.Katon frame din data gani mai dauke da hoton haris a jikin bangon daidai tebur din daka doshi wajen,ya tabbatar mata bangarensa ne.Kishingide yake saman kujera ya tallafo kansa da hannuwansa,hakora a waje yana dariya aka dauka,sanye yake da kananun kaya farare tas riga da wando.Yayi mata kyau ainun,ta zauna saitin inda zata fi kallon hoton ta darje.Cikin murmushi tace"Afuwan kanwata na barki da aiki." Zahra tayi dariya"Haba antina,yan uwan juna ne mu ai.Yiwa kaine."Daidai lokacin haris yakaraso ya ja kujera masterchair ya zauna"Yunwa fa nakeji aji dani."Ya fada yana duban Zahra,murmushi ta sakarmishi a kunyace,ko a jikin baby,ta soma kokarin hadawa kanta tea,zahra zata hadamishi ya dakatar da ita"Zauna abinki ba dutynki bane yau,rabu da ita ta hadamin."Baby batace komai ba,ta dauki kofinsa ta hadamishi kafin ta zubamishi dankali da kwai da sauce ta tura mishi,sannan ta hada nata.  A sannu sannu take kurb'ar shayin,yayinda jefi jefi idanunta suke tafiya ga kallon hotansa.Har dai ta kammala ta ci dankalin kad'an,tana jinsu suna hira saidai bata ko maida hankali ba ballantana tasan batun da suke.Dariyar da suka sanya ita ta maidota cikin hayyacinta ta bar kallon hoton wanda a zahiri ta fada kogin tunani ne."Antina don bakisan yanda yayan nan namu ke daure mana fuska ba a kzu,banyi zaton yana dariya ba."Murmushi baby tayi ta dubeshi shi dinma idanunsa na kanta,"Ba lallai tasan abunda muke maganar akai ba,hankalinta bai jikinta."Ya karashe yana mai mikewa tsaye"Bari naje muyi sallama da mutane."Sukayi mishi addu'ar sauka lafiya,tasleem ta mike tsam,Zahra tace ta bari zata kwashe kayayyakin,ba musu ta sauka zuwa sashenta.Komai saida ta k'are mishi kallo kafin ta zagaya 'yar k'aramar barandar dake acan hanyar kicin dinta,wajen shukokine kawai.Bata jima ba taji ana kwankwasa mata k'ofar falon,ta koma ta bude.Zahra ce,ta bata hanya ta shigo sukayi zaman hira har zuwansu yasmeen da hasina.  Ai saifa hira tayi gaba harda matar mustapha,Ramla dasu hindu da matar ridwan,fadila.Tasleem ta rukunkume takwarorinta,da ummi da tasleem ta wajen ridwan,ga kuma diyar kb,nasreen.Mace ce mai son yara sosai,sukan burgeta hakanan takan shagala wajen biyewa shirmensu.Can kuma hindu da yasmeen suka fita zuwa sashen zahra,inda gayyarma gaba daya ta koma can,sun dora girki nan ma akayita hira. Sallamar haris da kb harma  ta katsesu.Kb gaba daya dai ya saduda duk da babu wani abu da zai tabbatar maka da ko akwai wani kullin ne a ransa ko kuma babu,amma hakan yayiwa Haris dadi don a yanzu mutuwa kadaice zata iya rabashi da matansa.Babu saki a tsarinsa.  "Dakyau hira ce haka?"Cewar kb,suka gaisa,baby bata ko dubeshi ba gudun zargi.Basu tsaya anan ba suka nufi sama wajen haris.Awa daya suka kammala komai,hindu ce da zahra suka kai sukayi serving dinsu sannan suka juyo.Basu suka bar gidan ba sai dab da magriba nan ma saida umma ta kira yasmin a waya tayita fadan jimawarsu.Suna tafiya,tasleem ta kara wanka ta cakare.  Wannan karon doguwar riga 'yar kanti tasa dark green mai laushin gaske kuma kakkaura.Ya fiddo coca cola shape dinta matuka,ta sanya hular da tayi daidai da shigarta a kanta.Hoda kawai ta shafa da jan baki kadan,ta sanya dankunnen data saka da safe batare da sark'ar ba,turaruka kuwa kamar ruwa hana ta dunga feshe jikinta dashi.Wayarta tayi k'ara,ta dauka ,mamakin ganin lambar Haris ya kamata,daman baya gidan ne kodai k'ara fita yayi?"Ta d'aga ganin kiran na neman yankewa"Ki sameni a falona."Ya kashe,ta sanya takalminta ta fita.    Zaune yake yana chanja chanjan channels ta bude kofar ta shigo da sallamarta,kasancewar kana shigowa akwai bango daya kare yasa baiyi saurin tozali da ita ba,ya maida kansa ga abunda yakeyi har ta isa kujerar kusa dashi ta zauna.Kamshi daddad'a daya gauraye hancinsa yasa shi kasa jurewa har saida ya dubeta.Cak yabar danne remote din,dukkan wani ilahiri na jikinsa saida ya amsa.Ita kuwa hankalinta yana ga tv ganin tashar cartoons ke haskawa,ta rasa abunda ya dauki hankalin haris anan.‬. Jin shirun yana neman yawaita yasa ta dubansa don son sanin dalilin kiran nasa,murmushi tayi saidai fa kamar malamin nata baisan tanayi ba yakai kololuwa har ya manta wani aji da shan kamshinsa gareta.Lebbenta ta ciza ganin ta d'ana mishi tarko,taso tayi huhuhuhu amma ta fahimci ba hakan ya dace ba,wannan ne dalilinta na jan kunnensa kadan.Ya dawo hayyacinsa ba shiri,dariya ta saki yayinda cikin yanayin borin kunya ya hade gira yana mai hakimcewa a kujerar.Gyaran murya ya d'anyi ya jawo wayarsa saima ya fasa kiran"Kiyi kiran Zahra."Ta tsuke bakinta bayan ta hadiye dariyarta,lallai Haris dinnan,zata nuna mishi rashin wayonsa.Wai ya akayi tun farko ta gaza gano wannan kauna mai wuyar fassara da yakeyi mata?Ta fahimci kamar dai Haris ya rasa hanyar bi domin nuna mata a zahirance ko kuma dai salonshi ne haka oho.Taci alwashin shawo kan mijinta ta hanya ingantacciya tunda itama a yanzu bata da abun so da kauna kamarsa.Ji takeyi babu macen data kaita son Haris."My haris."Ta fada a fili.  Ta tarar da Zahra a kicin tana juyewa abinci a flask abun ya bata mamaki matukar gaske"Sister,ba nace kibar girkin ba musha koda tea?Nikam banji dadi kinata sanya kanki aiki." Dariya Zahra tayi tana mai kokarin danne kishim tasleem dake taso mata,ganin kwalliyarta na yanzu duk sai ita kuma ta raina nata kwalliyar duk da dai riga da wando na Pakistan ta sanya amma tasan wutsiyar rakumi tayi nesa da k'asa"Gani nayi tunda ga kayan cefane menene hujjarmu ta shan tea?I really love to cook,kada ki damu."Baby ta yaba kwarai da wannan hali na Zahra,ta bambanta da sauran mata masu nuna kishi k'arara a irin wannan ranakun.Tare suka shirya komai suka nufi saman dashi.Yana kishingide cikin jin mutuwar jiki,baby ta tafi ta barshi da tunani kwarai,ya rasa dalilinsa na kasa bayyana mata sirrin zuciyarsa.Yasan dai yana sonta baida bakin karyatawa.Shigowarsu ta katse tunaninsa,ya zuba musu ido suka shige suka ajiye kayan hannunsu saman tebur,a ransa godiya yake ga Allah kan wannan kyauta da Yayi masa na Tasleem da Zahra.  Bayan zamansu a tsakar falon,yayi musu nasiha inda ya nuna musu shi ya daukesu yan uwansa na jini kuma mata wadanda a yanzu ya basu daraja daya babu bambanci,kamar kuma yanda yasan ba wacce zata bashi kunya gurin kyautatawa gareshi da tsakaninsu.Ya yarda da tarbiyyar dukkaninsu.Ya nusaq da tasleem kan ta rike girmanta matsayinta na babba,itama zahra haka.Karshe yace kwana bibbiyu ya warewa kowaccensu.(A ganinsa shiga hakkin daya ne ace sati dayan nan sai an cikata). Kowaccensu tayi na'am da hakan kafin kuma su garzaya tebur.Santi haris da tasleem sukayita zubawa Zahra,abun ya burgeta tayita dariya,karshe dai Haris ya rigasu tashi ya koma kallon ball wanda tun tsawon lokacin nan daman ita yake jira a soma.Su kuwa hirarsu sosai da dariya sukeyi,karshe tasleem ta tayata sauke kayan kasa suka wanke wadanda suka b'ata suka zauna anan kasa bisa cewar tasleem,ita kam batason ball."Barshi ya kalli abunsa sisna,muyi zamanmu nan muyi hira."Murmushi Zahra tayi,tana mamakin tasleem,ashe haka take da mutunci?‬ Farkon ganinsu da ita yanda sukaga tana ji da gayu sunyi zaton samunta cikin masu wulakanci sai kuma ta basu mamaki,ashe harma tafi hakan a mutunci.Labarin makarantar kwana da Zahra tayi take saurare,da irin wuyar da sukasha a hannun seniors,baby tana dariya,har basu ankara ba sai ganinsa sukayi a kansu yana cin magani.Duk suka dubeshi,daman tuni ya chanja,baby ta kauda kai."Tun yanzu kenan kun soma nunamin wariyar launin fata?Kun barni acan ko?"Zahra ta narkar da murya"Nidai bani da laifi,kaga dai antina ce da girki kuma tace batason kallon ball shiyasa ta biyoni."Ya zubawa tasleem ido kafin kuma ya girgiza kansa ya fice.Cikin tsoro Zahra tace"Antina kinsan halin yayannamu,please ki tafi."Ta tabe baki"Rabu dashi."Zahra ta zaro ido a tsorace,ganin yanayinta ya bawa baby dariya ta mike tana fadin"Shikenan,naji dai kin koreni daga dakinki." "Wace ni na koreki,gaskiya nake fadamaki."Murmushi baby tayi sukayi sallama ta fita zuwa sashenta.Duhu falon,tana rufe kofa taji an rik'ota.  Ta ambaci sunan Allah,saidai kamshin turaren ya fallasa mata shi.Kafin tayi magana ya rigata"Ke haka akeyi,kinje kin bar mijinki kina ragewa wata dare?Ina maki kallon mai wayo?Idan kin gama ki sameni a sashena nabar biyo mace dakinta."Ya saketa suna numfarfashi ya kunna fitila haske ya gauraye dakin,sukayi ido hudu ta dauke kanta kawai ta shige dakinta.Bai biyota ba shi d'inma ya fita ya koma sama.Saida numfashinta ya daidaitu kafin ta saki murmushi,ta gama hakikancewa Haris na daban ne a dukkan sauran mazajen da wata mu'amala ta had'asu a baya,tayi godiya ga Allah da Ya shiryata har gashi Yasa ta samu miji nutsastse.Wanka tayi saboda zafin da garin yayi ga kuma hadari dake had'uwa hakanan walkiya sai haskawa takeyi,kowane lokaci ruwan nan mai iya sauka ne da ikon Allah. Ta jima kafin ta fito tayi shirinta cikin kayan bacci saidai ba mai zafi ba,riga da wando wadatattu tasa na cotton ta fesa turaruka bayan na jikinta data farfesa.Hoda da lipstick kadai ta shafa kafin ta dauki hijab a hannu ta rufe sashenta.  Sanin da tayi ba ita kadai ce matar gidan bane,yasa ta dauki hijabin,ta nufi saman,babu shi a falon,a d'akinsa ma wanda ya k'ayatu bayanan taji motsin ruwa a bandaki,ta ajiye hijabinta a gefe ta fito taja mishi kofar,kai tsaye wajen hotonnan daya gama tafiya da ita,ta nufa.Tsayawa tayi hannuwanta rungume saman kirjinta tana karewa kyakkyawar surar mijinta kallo,babu abunda ya fado mata rai sai farkon haduwarsu a gidan kb wanda tun anan ta jinjina imaninsa,tunda har ya iya dauke dubansa a kanta duk da ta yarda cewar Allah Yayi mata baiwar k'ira mai ban sha'awa ga kowane namiji,ta tuna haduwarsu a daren data nufi partyn hibba da nasiharsa gareta,ta tunano hatsarinta da taimakonsa gareta.Haris wani haske ne a rayuwarta.Hawaye ya kufce mata ta taka sannu har gaban hoton takai hannu ta shafi fuskarsa"I love you Haris." "Really?"Taji tambayar saidai tayi nisa "Yeah,i really do." Saida ta amsa ta ankara,da sauri ta juya sukayi ido hudu,yana tsaye ya dafe hannunsa da tebur.Ta daure fuska,shima yasha mur."Repeat it."  Ta basar ta hanyar kauda kai ta goge hawayenta kafin ta juyo ta soma tafiya"Bada kai nake ba." Murmushi yayi ya k'ara gyara zaman tawul d'in dake d'aure a k'ugunsa sa'ilin da ita kuma tuni ta koma kujerar falon ta zauna.Yakai dubansa ga hoton wanda tunda safe ya gama fahimtar irin burgewar da hoton keyi mata.Ya nanata furucinta da mamaki,wani sanyin dadi ya kewaye zuciya da gangar jikinsa,ashe itama tana sonsa amma meyasa take kokarin nuna mishi halin ko'in kula har haka?Kwafa yayi" "Ai idan ji da kaine gidansa tazo." Ya fada a fili,har ya iso kunnuwana dani da tawagata,mukayi tsuru tsuru,wannan ya kalli waccan,waccan ta kalli wanda."Ta ratsa!"Cewar wata tak'adariyar cikinmu,hanne cillare,a nufinta mutuwa. "Amma bata dauki kowannenmu ba,mamaki ne fa ta yanda wadannan masoya ke kokarin nunawa soyayya aji,sun manta cewar shi so ba'ay masa wannan ko kuwa dai son baije ko'ina ba?"Ummu abdool tayi furucin nan,Msmart Zee data k'urawa hoton ido ta juyo"Mu bisu muga wanda zai riga russuna,Mazan ko Matan??"  Muka mara musu baya jikkunanmu kamar wadanda akayiwa duka. Bai dubi inda take ba,ya shige daki yayi shirin kwanciya kafin yayi shafa'i da wutri.Tunani da kunya sun dabaibayeta na yanda soyayyar Haris ta gaza b'oyuwa kamar yanda take matukar kokarin yin hakan.Bataso ya kasance itace zata soma bayyanawa,dole ta cigaba da kokarin dannewa,babu batun k'in bin kowane umarninsa,saidai zata nuna mishi itama mace take.Ta kwantar da kanta jikin kujera tana mai lumshe ido yayin data fada cikin kogin tunani.Tsakar kanta taji muryarsa"Bakijin baccine?"Tayi saurin mikewa batare data yarda sun hada ido ba"Kashe fitilun."Daga haka ya wuce ciki,tabi umarninsa daga nan ta bude firij,tasha ruwa ta nufi dakin. Kwance ta iskeshi ya dora kafa daya kan daya,ta dauke kanta ta kashe fitilun.Zagayawa tayi da niyyar kwanciya ta tsinkayi muryarsa"Taimaka ki dannamin kafafuwa,sunamin tauna."Murmusawa tayi"Tun baka tsufa ba kenan."Ta fada a sarari,aka soma ruwa sosai."Gado nayi wajen Abba."Ta danyi dariya,haka har yay bacci.Ta kwanta‬ Koda girkin Zahra yazo,tasleem ce tayi mata,washegarin girkin zahra,ta shirya musu kari takai har dinning ta ajiye anan b'angarenta kasancewar taje basu bude kofa ba.Tayi adonta cikin riga da siket yan kanti daman tun a baya manyan kaya ba damunta sukayi ba,ta zauna cikin faduwar gaba da tunani.Tasan babu dalilin da zai hana haris tarayya da Zahra,ta soma tunanin ko wane irin farin ciki zasuji da wannan ranar?Inama ya kasance itama ta kawo budurcinta gidan mijinta?Tausayin kanta ya dabaibayeta,hawaye suka zubo tayi azamar sharesu jin ana kwankwasa mata k'ofa.Ta mike da sauri ta bude,haris ne cikin yanayin damuwa bai bari sun gaisa ba yace"Kin dafa shayi?"Bata kawo komai ba ta amsa da cewa"Nayi mana kayan kari saidai dana zo na tadda falon a k'ulle."Ya shigo ciki sosai yana fadin"Zahra ce ke fama da ciwon kai,zo mu dauka mukai."Wani malolon kishi ya k'ara turnuk'eta,ta riga tasan kanun zancen.Bata nunamishi komai ba har suka isa,yace ta hadamata.Ya fada dakin,can sai gasu sun fito tana tafiya sannu,fuska daure. Idanunta ya sauka akan hannun Haris dake saman k'ugun Zahra,tayi azamar dauke kanta har suka karaso.Saidai mamakine k'arara a saman fuskar baby yanda Zahra ke cin magani ko ma dai menene can ta matse musu,ta daure bayan ya zaunar da ita ta mika mata tea data hada.Cikin murmushi mai kama da yak'e Zahra ta gaidata tamkar bataso.Ita dinma ta danne kishinta ta amsa."Sannu sisna,ashe bakiji dadin jikinki ba?" Zahra ta amsa."Kisha sai na baki magani ko?" Tasleem batasan sadda ta watsa mishi wani kallo ba idanunta sun kad'a,baisan tanayi ba don kallonsa yana ga Zahra.Ranar dai tasleem bata yarda tayi wani zama mai tsawo a dakin ba ta sauka daga kwanuka. Muka bi tasleem da ido kafin mu maido dubanmu ga zahra wacce aka bari ita daya a falon da kumburarran fuska.Na dubi tagawata wadanda duk idanunsu sun cicciko,mata masu rauni cikinsu harda hawayen tausayin baby"Ku saurara,bangane chanjin fuskarnan na Zahra ba fa.""Akwai walakin dai goro a miya."Cewar abdulaziz dake kuka kamar mace. Kukan zahra ya tsaidamu duka. Meyasa yayi mata haka?Zata iya tunawa da abunda ya faru a daren na jiya.Komai ya soma tafiya daidai tsakaninsu kafin yayi wuf ya dauki rigarsu ya fice zuwa falo ya bar mata dakin dukansa.Wannan abu ya tsaya a ranta kamar yanda ya shayar da ita mamaki matukar gaske.Kukan data kwana tana yi shi yayi sanadin data tashi da matsanancin zazzabi da ciwon kai.Sai asubahi ya shigo dakin,hankalinsa a tashe ganin yanayin jikinta,zai taimaka mata wajen mikewa don yin alwala ta kara fashewa da kuka ta nuna bata so.Yayi kokarin janyota jikinsa ta kufce"Ka rabu dani nace,daman nasan makala maka ni akayi bawai son tsakani..."Ya rufe mata baki,cikin tausasa murya"Kibar fadin haka Zahra,wallahi ina sonki,kada kiyi mummunan shaida akaina."Bata yarda da kalamansa ba saboda gaba daya ya gama kaita bango.Dakyar ta amince ya rakata tayi alwala ga wani jiri dake kwasarta,sallar ma a zaune tayishi sannan ta kwanta.Wannan ne dalilin fushinta,har take zargin yafison tasleem akanta.Hakan yasa ta kasa sakewa tasleem ko kallonta batayi ba. Acan kuwa,tasleem ce rungume da filo a kuryar dakinta,taci kuka har ta gode Allah.Kaiconta!Tir da bariki,me akeyi da ita? A baya tana yiwa kanta kallon isashshiyar mace ashe isar ba'a waje take ba,ba'a tarayya da maza ko wani barikancin waje bane,a'a,isar a gidan aure take! Isar a wajen miji take.Muddin kika isa awajen mijin,har zai iya bugar kirji gaban dubban jama'a ya tabbatar musu cewar ke d'in kin isa awajenshi,kina mishi komai da yakeso,kina binsa sau da k'afa,kwarai anan isar take,zai dunga tattalinki ya nuna maki zallar so da kauna.Yau kam taga wannan tattalin amma ga watanta ba ga ita ba!Karar wayarta ta katse tunaninta,ta duba,ganin lambar mamma yasa ta saita muryarta.Sun gaisa,taji lafiyarta.A karshe ta kara yin nasiha gareta sukayi sallama.Wannan ne ya kara karfafa mata gwuiwa ta share komai ta hau kimtsa dakinta. Ranar kuwa ba wacce ta leka dakin wata da zummar hira,saima bayan da tasleem ta kammala girkin rana tayi kamar ta sharesu,sai taga rashin dacewar hakan.Dauka tayi zuwa saman... Da sallama ta shiga saidai taji shiru,hakan ya k'ara k'ular da ita,kenan suna d'aki.Har ta ajiye kayan abincin ta juya da niyyar fita ta hangeshi kwance saman kujera,ya rungume karamin filo na kujera,daga shi sai singilet da dogon wando na farar shadda,rigarta na ajiye a d'ayan kujerar,yayinda ya rufe fuska da hularsa.Bata da tabbacin baccin yake ko idanunsa biyu,harara tayi cikin duhu don baisan tana yi ba,daganan ta fice.A hanyar steps din ta had'u da Zahra an kara cin ado cikin riga da siket 'yan kanti.Murmushi ta sakar mata"Sister ya jikin?Ga abinci fa nakai." Murmushin itama tayi gareta tana mai danne kishinta"Da sauki anti,banjin ma zan iya cin komai yanzu saidai ko yayanmu." Giftata tayi ta cigaba da sauka"Hum,ki tashesi yaci,nima ba yunwar a cikina."Cewar baby,daga haka ta bude kofar bangarenta ta shige harda sanya mukulli don bata bukatar dukkansu biyun.Rashin abunyi yasa ta janyo waya ta hau game... ***** INA LABARIN KB?. A sannu sannu zuciya ma'abociyar zafi da rashin hakuri ta soma sanyaya,babban dalilin kuwa bai wuce samun kyautatawa da kulawa ta hakika ba a inda bata tsammata ba.Mamaki da zallar kauna da kokarin mayarda martani sune suka taka rawa a wannan gab'ar har ya zamana mantuwa da juriya bisa kaddara sun samu gurbin zama sosai acikinta,ba don anfi karfinta bane,a cewar mallakinta.Sam!Ba hakan bane,saidai kauna ta don Allah ta dangin juna ya janyo ta tausasa,ta kuma rungumi abunda ke gabanta.   Kuskure daya yayi,wanda shi dinma mantuwa ce tasa.Barin hotunan tasleem a wayarsa,wanda ya kusan janyo mishi asara,ya kusan yin BIYU BABU.A yanzu da yake zaune a gefen gadon asibitin,ido ya zubawa Yasmeen cikin tsananin tashi hankali da matsanancin kunyarta daya lullubeshi.Hawaye suka zubo mishi ganin har lokacin bata farka daga doguwar suman da tayi ba,ya kara rungume nasreen dake bacci saman kirjinsa ya sumbaci goshinta.Baya fatan wani cikin ahalinsu ya samu labarin abunda ya faru. TUNANI...! Ya fito daga bandaki bayan ya kama ruwa,ya tsaya cak cikin yanayi na firgici ganin wayarsa a hannun yasmeen,hannuwa nta sai rawa sukeyi,ta dago rinannun idanunsa tana dubansa,ya karasa da sauri zai rikota,taja baya a tsorace,dakyar take numfashi saima haki da takeyi kamar wacce tayi tsere."Menene princess?"Ya fada yana kusantarta tana ja baya,ta nuna mishi fuskar wayar,hotonsa ne na selfie daya daukesu da tasleem.Tana kwance tsakankanun kafafunsa,dagashi sai singilet da shortnicker ita dinma vest ce sai wando threequarter,ta yi kwai da cingam dake bakinta shi kuwa yana dariya.Duka wannan kallon ya faru ne a sakan biyar kafin muryar Yasmeen ya katseshi"Daman itace baby? Akanta ka rabani da walwalata?Yanzu kuma ka cuci yayana ka bari ya aureta?Ka..cuce...ka" Tuni idanunta ya rufe."Yasmeen!"Ya fada da karfi yana mai sakin wayar a gigice,tun kafin takai k'asa ya tareta,har lokaci rike take da kirjinta tana numfarfashi,baiyi wata wata ba ya sureta sai asibiti! **** Ajiyar zuciya ya saki adaidai nan...! Ya zubawa matarsa ido a yayinda ya tunano da sukayi da likitansa satin daya wuce. "Ka rage shaye shaye kabir,matsala ce kuma illah ga lafiyar jikinka.Tana janyo matsaloli da dama,kamar na makogaro da hakora,wani sa'in har takai ga zubar hakori,tana rage kuzari yayin saduwa,kamar yanda take kawo tabin hankali da sauransu.Yanzu dai na duba baka da matsala,amma tabbas idan ka cigaba zaka janyowa kanka matsala ta liver.Duk idan ka ajiye wannan,ka manta da cewar Allah Yayi mana hani da shan giya?Dama duk wani abu mai bugarwa?Please kayiwa kanka fada."Doctor Bilyamin kenan,wanda ya kasance likitansa,kuma shi kadai yasan cewar kb yana shaye shaye amma baisan da neman matan banza ba saidai yana zargin bazai gaza ba.Idan ya tuna,baby ma sun sha fada da ita akan batason yazo gareta drunk,yasan ita d'in banda sigari bata ta'ammali da komai,sigarin ma sai idan ranta a b'ace yake take sha wajen tsinke uku.Cikin muguwar nadama,ya sauke ajiyar zuciya.   Salatin da yaji Yasmeen tayi,shine yasashi dubanta,ya kwantar da nasreen. Dafa kanta yayi yana mai sanya hannunsa cikin nata,"Sannu princess." Ta kura mishi idanu,hawaye tuni suka zubo mata tunano abunda idanunta ya gane mata.Wai wannan shine d'a a wajen dattijon kirki mai kokarin tsare kansa daga wuce iyakokin Allah,Alhaji idris babangida?Shine dai kuma dan uwan nan nata na jini da suka taso cikin tarbiyya d'aya,amini kuma dan uwan yayanta,farin cikinta.Kanta ta girgiza,a fili ta karashe maganar zuciyarta"Kuma mijina,uban 'ya'yana wanda na damk'awa amanar rayuwata da farin cikina,ashe zaku iya cin amanar yaya haris har haka?Ka bani mamaki kabir."Ta fadi sunansa babu jin shakkar komai,ya saki hannunta ya zauna gefen gadon da take,zaiyi magana kawai saita fashe da kuka a rikice,cikin muryar tsawa tace"Ka tashi ka rabu dani!Idan mutuwa zata ziyarceni a wannan gab'ar sonta nakeyi!Ka kiramin yayana!Ka nemominshi ko kuma ka kaini wajensa!"Kuka sosai takeyi babu kakkautawa,a guje ya fita yana kwalawa likitan kira ganin numfashinta yana hawa da sauka.Likitan ya taho a rikice ya shiga ciki. Ya lura har lokacin bata da nutsuwa wanda idan aka barta haka zai iya janyo barazana ga rayuwarta,allurar bacci yayi mata,kafin tana sumbatu baccin yayi awon gaba da ita.Ya maida dubansa ga kb wanda yake rike da Nasreen da hayaniyar ta tasheta,duk ya birkice."Hakikanin gaskiya ya dace ka nemo Haris koda ta waya ne ka gayamasa yazo Abuja,idan kuwa ba'ayi mata abunda takeso ba kwarai akwai babbar matsala." Furucin doctor nuhu kenan,wanda ya kasance kwararren likitan zuciya(cardiologist)kuma shi Haris ya d'orawa alhakin kula da yasmeen,hakanan shine ke d'orata akan magunguna.KB ya sauke ajiyar zuciya cikin tashin hankali da rud'ani.         **** A gidan Haris kuwa,matan babu yabo ba fallasa,kowacce dai tana kokarin boyewa.Ga mijin kuwa ya fahimci damuwarsu,dariyar mugunta kawai yayi ya tafiyar da baby a hakan,cewar yayi tarayya da zahra. Misalin takwas na dare,Tasleem ta shirya musu abinci kasancewar girkinta ne,taci ado ta nufi saman.Bayan ta ajiye zata juya,takai dubanta ga hoton,ga mamaki taga ya chanjashi. Katon frame ne na sunan Allah,ta sauke ajiyar zuciya,taji takaicin yanda akayi ya gane tana son hoton.Juyawa tayi ta fice,dakin Zahra taje ta kwankwasa,bude mata tayi suka gaisa kafin tace mata ta fito suci abinci.Ta yamutse fuska"Banajin zan iya sanya abinci a cikina anti,kuci kawai zan sha lipton."Daga haka ta rufe kofarta,karamin tsaki tasleem taja,yarinyar da ta tabbatar ta girmeta koda da watanni ne amma take mata haka?Ita dinma ganin maigidan bai dawo ba yasa tayi zamanta a sashenta.Hasina ta laluba a waya suka gaisa,kafin ta tambayeta lafiyar ummi.Sun kammala wayar bayan hasina ta jaddada mata tasha boma boman nan tunda tayi tsarki.Da toh kawai ta bita ta katse wayar.A ranta cewa take,mutumin da bata gabansa ne zatayi abunda zai burgeshi?Ta kunna socket da zummar kallo,taji wayarta ta dauki kara.Da sauri ta dauka,ganin haris ne ta sha mur."Ki sameni a sama."Ya fada kamar a fusace,jiki a sanyaye ta fito ta hau saman.Yana zaune a falo da alama shigowarsa kenan,ta zauna.Harara ya watsa mata"Meke damunki?".  Cikin rashin fahimta ta dubeshi,shi dinma ido cikin ido yake dubanta"Meka gani?"Ta fada a sanyaye,ya kauda kansa"Kamar ba girkinki ba,bakiga yanda yar uwarki keyi ba?Ranar girkinta bata barin falon nan,takan zauna anan har ta jirayi isowata."Taji ciwon misalin da yakeyi mata ga wata,ta daure tace"Kayi hakuri."Yayi dan shiru,can kuma yace"Zo ki kaimin jakar nan daki."Ba musu ta dauka takai,zata fito ya shigo dole ta koma da baya.Saida ya shigo tayi niyyar fita ya dakatar da ita."Toh wankan nawa fa?Zahra fa tana hadamin ruwa."Yayi furucin cikin yanayin damuwa,har ta juyo ta dubeshi,murmushi ya sakarmata,kanta ta girgiza ta shiga toilet din,ya zama dole ta takamasa burki akan zahra,menene dalilinsa na hadata da ita adukkan lamuransa?Ta hada ta fito,dagashi sai singlet da wando"Kina nufin banda wankan?"A fusace ta dubeshi"Kana iya kiran Zahra tayima."Ta fice ta banko kofar,dariya ya saki"Kadan kenan,saikin magantu tasleem."Yayi shigewarsa. A falo tana zaune tana aikin karkad'a k'afa,ta gama kuluwa,can ya fito. Me yake nufi da ita ne?Tana jinsa ya karaso ya tsaya a kanta"Kirawomin Zahra mana,ban ganta ba."Kamar tak'i zuwa saidai ta mike a kufule ta shuri takalmanta,ya dubi takalmin kafin ya dubeta"Ke kam baki tsoran ki fad'i kan tiles dinnan?" "Waye ya hadamin lefen?"Ta tambayi zuciyarta,a fili kuwa kallo ma bai isheta ba ta juya ta fita.Wannan karon taji kofar a bude,hakan yasa ta murdawa ta shiga da sallama,Zahra bata falon,ta zauna hannun kujera tana jiranta.A hankali take bin jeran zahra da kallo,komai nasu iri daya sai bambancin kala.Idanunta suka tsaya cak akan hoton da take matukar muradinsa,shi d'inne kwarai dagaske bawai gizo yakeyi mata ba.Ta tabbatar da gayya Haris ya kyautarwa da Zahra shi,jin taku yasa a kauda kanta daga hoton.Kamshi ya ziyarci hancinta kafin Zahra ta fito,tayi kyau cikin shigar atamfa ruwan hoda.Ganin tasleem yasa ta murmushi tuni bacin ranta ya kau,daman can ita din bata da riko,toh idan ma ta riketa a rai ai ba ita takai zoman ba"Antina kiyi hakuri,gani." Furucin da Zahra tayi sai ya zamana kamar ta tunasar da ita wani abu,wani irin murmushi ta saki."Bakomai sisna,kizo muci abinci." Zatayi magana,ta tari numfashinta"Karki min korafi,please muje."Ba don zahra taso ba,ta bita suka tafi.Yana zaune saman kujerar dinning din yana danne wayarsa,riga da wando bak'ak'e na Adidas ne a jikinsa.Bai dubesu ba har suka karaso,tasleem tsayawa tayi gefensa ta janyo faranti ta hau zuba mishi,lumshe ido yayi yana mai jin dadin turarenta."Barka da zuwa yayanmu."Ya maida dubansa ga zahra,ya "Barka dai my lady,ya jikin naki?Kina shan magani ko?"Ta gyada kanta"Eh."Ya saci kallon tasleem wacce ko kusa bata nuna wata damuwa ba saima murmushi dake dauke saman fuskarta,kasan zuciyarta kishin ne fal.Yakai hannu kan faranti"Bari na taimaka na zub da maki kada..aush!" Yayi furucin jin radadi a yatsar kafarsa,da sauri tasleem tayi baya"Lafiya?"Cewar su biyun,dago kafar yayi yana duban baby"Daman tunda naga takalmin nan nasan zaiyi ta'adi,kin ciremin yatsa."Murmushi tayi,wayarsa tayi kara!. Ya saki kafar ya dauka,cikin murmushi baby ta zauna,dole Zahra ta cigaba da zuba abincinta tana mai jin dadin yanda Haris ke nuna mata kulawa,a nata wautar har ta soma tunanin cewar yafi son nata dagaske kamar yanda tsohuwa hajiya kaka ta gayamata a baya.   "What?!"Ya fada cikin tsawa da yayi sanadiyyar sanyasu kallonsa a firgice,tuni ya mike tsaye yana cigaba da kasa kunnuwa.Nan take tashin hankali ya bayyana karara saman fuskarsa."Yanzu ina Yasmeen din?"Jin wacce ya ambata yasa dukkansu mikewa tsaye.Ya dafe goshinsa kafin cikin daga murya yace"Kabir!?Idan na rasa kanwata saina kasheka!!"Wayar ya kashe,ya nufi dakinsa da sauri,Zahra tabi bayansa da tambayar ko lafiya.D'abas!Baby ta koma ta zauna saman kujera,hawaye suka kwaranyo saman fuskarta,jikinta yana bata cewar ko menene itace silah."Leave me alone!!"Ai saita mike a rude cikinta yana murd'awa,da gudu taga Zahra ta fito daga dakin,ji kakeyi b'am!,ya rufo dakin.Zahra ta karaso inda baby take jikinta yana rawa,kamar tayi magana saita fasa ta fice aguje..! Garam!,kofar falon ta koma ta rufu bayan Zahra ta fice.Tasleem kirjinta sai k'ara dukan tara tara yakeyi ga hawayenta sun gaza tsayuwa.K'arar bude kofar da akayi ne ya dawo da ita tunaninta,ya chanja sutura zuwa riga da wando kananu,hannunsa rike da jaka,baikai dubansa inda take ba ballantana ma ya gane da ita a wajen.Ganin yana shirin ficewa ne ya sanyata gudu ta tari gabansa,ya dubeta duban da bai taba yi mata irinsa ba"Move aside!" Ya fada da karfi,ta juya aguje ta sanyawa kofar mukulli kafin ta tura cikin rigarta"Wallahi bazan barka ka kama hanyar wani gari da daren nan ba haris! Koma menene sai gari ya waye."Ta fada bayan ta tattaro jarumtarta,ya cakumo wuyan rigarta bayan ya jefa jakar kasa,cikin shak'akk'iyar muryarsa yace"Ke da Kabir baku isa ku kashemin kanwata ba Tasleem!Kunyi kadan!Mutuwarta mutuwarku ce!Ki sani bazaku taba cimma burinku ba!"Ya saketa har tana kokarin faduwa,cikin muryar kuka ta soma magana bayan data dubeshi yayi zaune saman centertable"Ashe haka kake Haris?! Idonka zai iya rufewa?. "A baya inayi maka kallon mutum mai tausayi da karbar uzuri,ban mance yanda ka dunga nusar dani ba a sadda rayuwa ta ficemin a raina,haris yau kaine ke shirin yanke danyen hukunci?Daman abunda nake tsoro kenan,nasan da wuya idan zargi bai shiga tsakaninmu ba.Wace irin kalar rantsuwa zanyi maka ka yarda cewar rabona da Kb tun kafin naje kazaure?Haba,nasan menene aure,kabar ganin nayi bariki a baya,inada ilimin addini daidai gwargwado." Ya numfasa,zuciyarsa ta sanyaya har ya gano rashin kyautatawarsa.Kishine kawai!Amma kb kawai bayanin rashin lafiyar yayi mishi,shaid'an ne ya d'osana mishi zargi.Mikewa yayi tsam ya mik'ar da ita kafin ya rungumeta,sun shafe mintuna biyu tsaye k'ik'am,yayinda so da kauna ke k'ara ratsa sassan jikkunansu,cikin rawar murya yace"Ki taimakamin da addu'a,kada na rasa Yasmeen,ciwon zuciyarta ya tashi." A razane ta dago kanta daga kirjinsa tana kallonsa,bakinta na rawa saidai ta kasa magana tsabar kad'uwa da jin wannan bak'on zancen ma tashin hankali.Yaja hannunta suka zauna kan kafet. Ciwon zuciya fa kace?" Kansa yana jingine da kujera ya lumshe ido ya bude"Kwarai,tanada ciwon zuciya,dashi aka haifeta amma yanzu da sauki.A iyakar sanina yanzu ba karamar damuwa ko tashin hankali ke tayarmata dashi ba,inada yak'inin wani abun ne ya hadasu.Hakanan ina fargabar ya kasance akanki ne Tasleem."Ta dubeshi da idanunta masu zubar hawaye"Inajin nauyinka kamar yanda nakejin nauyin Yasmeen,inama wata alaka bata tab'a giftawa tsakanina da Kb ba.Ashe mijin yar uwata ne." Ta rufe fuskarta da tafukan hanneyenta tana kuka ainun,ya mike zaune yana fuskantarta,numfashinsu har yana gauraya da juna,hannuwanta ya zamar yana mai rikesu,idanunsa kuwa suna nuna tsantsar damuwa"Banason tuna baya Tasleem,yanzu ba gashinan kina zaune dakin mijinki ba?Ina ga wadanda suke zina da mahaifinsu basu sani ba?Kada ki manta fa har yanzu kawayenki basu bar bariki ba,ki godewa Allah da Ya cetoki,Yayi maki kyautar miji mai tsananin.."Kallon da take watsa masa mai nuni na tsananin so da kauna ya dakatar dashi,sakin hannunta yayi. Daki ya shige,ta sauke ajiyar zuciya tana mai murmusawa kafin tabi hanyar dakin da kallo,a fili tace"Koda baka fito ka fad'a ba Haris,ina da tabbacin kanajin irin yanda nakeji game dakai saidai har zuwa yau ban fahimci abunda yake hanaka nunamin ba a zahiri."Ta sauke ajiyar zuciya,sannan ta mike,dubanta takai ga kulolin abincin kafin tunanin Zahra ya fadomata tayi dariya kadan,zubawa tayi ta rufe sannan ta bude kofa ta fita,bata yarda tabar kofar a bude ba,nan ma ta kulleshi ta sauka.Tayita bugun kofar Zahra,cikin muryar tsoro zahra ta tambaya"Waye?""Haris ne ki budemin."Baby ta fada da katuwar murya,sukayi dariya kafin ta bude,har tasleem ta shiga dariyar sukeyi musamman ma ganin yanda Zahra ta k'ara datse kofar.Tasleem ta ajiye plate din saman centertable"Matsoraciya."Zahra tana dariya tace"Aa wallahi kiyi jam'u,ai gwara ni nayi kokarin shiga inda yake,ke kuma fa hawaye kika tsaya fitarwa."Sukayi dariya,"Daman haka yayanmu yake da zuciya?Tab,aini na k'ara jin tsoransa ma."Cewar Zahra,baby ta nunamata keys. Kinga mukullayen,rufeshi nayi ruf." "Ai nagode Allah daba dutyna bane yau,tab,wallahi saidai na gudo wajenki mu b'ame."Suka k'ara tuntsirewa da dariya kafin kuma yanayin damuwa ya sauka saman fuskar Zahra"Allah Yasa ba ciwon maman nasreen ne ya tashi ba,da wuya ma idan ba hakan bane domin yaya bayason damuwarta.Yana kaunarta sosai kamar ita kadaice kanwarsa a duniya.Toh menene laifin yaya kb kuma?Alhalin yayanmu yana sane da cewar ciwon maman nasreen,abu ne da aka haifeta dashi?"Tasleem ta jinjina kanta"Mai yiwuwa saboda rud'ewa da yayi ne,ke niyyarsa fa ya wuce Abuja yanzu,don dai na hanashi ne." Zahra ta zaro ido"Lallai ma yayanmu,toh banda abinsa wane jirgin ne zai kaishi?Ko mota zai bi?Ai kawai muyita addu'a."Tasleem ta gyada kai"Kada fa kice zaki fadawa su Umma hankalinsu zai tashi."Tayi wannan dabarar gudun tonuwar asirinta.Zahra ta girgiza kai"So kikeyi yayanmu yayimin duka kenan?Ai bazan soma ba." Sukayi dariya kafin tasleem tayi mata sallama ta fita zuwa dakinta don shirin bacci..! Saidata kimtsa a tsanake kafin ta nufi saman.Budewa tayi,baya falon hakan yasa ta tura kai dakin.Sallah ta tarar yana yi,damuwa fal a saman fuskarsa.Hakan yasa itama ta shimfida darduma kusa dashi ta hau nafila,bayan ta idar sukayi addu'oi masu tsawo akan nemarwa Yasmeen sauki,daga haka kuma suka shafa.Damuwar dake cunkushe kasan ranshi,ya hanashi maganin kishirwaryarsa,baik'i ya rab'u da jikinta ba suna 'yar hirarsu yana bata labarin irin wuyar da Yasmeen tasha wajen kb har bacci ya dauketa,ganin hakan shima yayi shiru kafin ya samu runtsawa. Washegari da sassafe yayi shirin tafiya,tana ajiye kayan kari ya fito, har ya kammala shiri ga jaka a hannunsa,a sanyaye ta karasa"Tafiyar ce?Bazaka karya ba?" Ya danyi murmushi"Kina wace duniyar na tashi nayi sahur da tea?Azumi nakeyi." Ta tuna yau lahadi ba litinin ko alhamis ba,mai yiwuwa dai na lada ne."Ai bansani ba" Tare suka sauko,ya bugawa Zahra kofa,ta bude,ganinsa duk sai tayi sanyi,da sauri ta gaisheshi,yayi mata sallama sannan suka takamasa kadan,ya fice. Zaune suke a falon kb lokacin karfe biyar da mintoci na yamma.(Kasancewar an sallamosu domin kuwa ta tubure bazata zauna a asibitin ba.)Yasmeen tana jikin yayanta cikin yanayi na zubar hawaye,shi kuwa kb yana dafe da kansa bayan ya gama labartawa haris abunda ya faru,ya kara dago kansa yana duban Haris"Ka yarda dani,wallahi kabir din da kake gani yanzu ba wannan kabir bane a baya.Kuskure nayi wajen barin hotunan.." "Ya isheni haka!"Cewar Yasmeen cikin fusata,ta dubi haris daya rasa bakin magana"Yayana kana sane da wacece Tasleem?Sun cuceka,sun cuci rayuwar..." "Yasmeen nasan komai game da hakan."Ta zaro ido a mamakince,kukanta ya karu hakanan ta rasa ta bakin magana.Nan ya labarta mata kadan daga cikin abunda yaga ya dace,ya dora da cewa"Ki sani,na auri tasleem domin tseratar da ita da kuma mijinki daga cigaba da fad'awa halaka.Musamman dana gano yar uwace awajenmu,ina rokonki da ki yafi mijinki,ki dauki komai matsayin kaddara.Kada ki sanya komai a ranki."Ya dubi kb fuska daure"Ka gaggauta goge hotan iyalina! Kb yayi murmushin karfin hali"Ko baka fada ba,bata gabana yanzu asalima nafi damuwa da yawan zunuban laifukan dana aikata a baya,fatana Allah Ya gafartamin."Murmushi Haris din yayi,a zuciyarsa yake godiya ga Allah da Ya bashi sa'a akan niyyarsa.Kb ya kara da cewa"Princess kadai ke gabana yanzu,banda ita bansan kowace mace ba,zan kula da ita har tsawon rayuwat.Ka taimaka ka nemamin gafara awajenta."Yana gama fadin haka ya mike yana dan duban yasmeen wacce ta dan sassauto,kodayake dai daman soyayyar da take yi mishi bata wasa bace,har mamaki yakeyi.Ko tasleem da idonsa ya rufe akanta,bayayi mata irin son da Yasmeen keyi mishi.Hakanan sau da yawa shine mai nemanta akai akai amma ita ko oho.Lallai SO MAKAHO NE(In sha Allah my next),duk tunanin nan yana yinsa ne a hanyarsa ta shiga daki. Sunfi awa suna maganganu da haris da kanwar tasa kafin ya bar maganar ya dubeta ganin yanda take murmushi tana dubansa"What happen?" "You love her so much,don’t you?" Ya sosa karan hancinsa...!‬ Murmushi yayi ya mustsika karan hancinsa"Inason matana mana."Tayi 'yar dariya,ta gama gane ba karamin so yakeyi ga tasleem ba,duk da matar ta fice mata aka,hakanan babu abunda yayi mata zafi da shiga huruminta,har lokacin tanajin radadi cikin ranta,wai tasleem ce ta karkatar mata da hankalin miji?Itace sanadiyyar rasa kulawar kb? Haka dai tayi amfani da shawarwari da nasihun Haris,ta kuma yi alkawarin bazata sanarwa iyayensu komai ba.Suka sasanta kansu da kb,washegari Haris yayi musu sallama ya biyo jirgin safe,sai ta dabo! Matan nasa sun kammala kimtsawa musamman ma Tasleem wacce ya kasance girkinta ne,saidai gogan kai tsaye daga airport,ofis ya umarci direban nasa,malam abdulaziz ya kaishi. Zahra ta ajiye wayar"Bai iso ba?" Cewar tasleem wacce hankalinta ke ga tv,zahra taja numfashi"Harma ya wuce ofis."Murmushi tasleem tayi,a ranta Allah ya kara,tace.Ganin yanda zahra tak'i cin abincin rana,ita tana jiran miji,ita kuwa zagewa tayi ta cika cikinta taf! "Yanzu ai ya zama dole kici ko?"Tasleem ta furta. Zahra ta mike don haushi"Bari naje sai anjima." Ko kallonta Tasleem batayi ba,ta fice.Ta sauke ajiyar zuciya,kasan ranta damuwa fal wanda idan suna tare da Zahra take kokarin dannewa,a jiya wajen karfe uku,habiba diya ga kawu usman,kanin mahaifin haris kuma yar uwa ga zahra ta kawo musu ziyara don daman ita kadai ce bata koma ba,anan kano zata cigaba da karatunta na jami'a anan gidansu kb wajen mami wato hajiya mariya. Tasleem ta daga hannu da zummar kwankwasawa zahra kofa don dama habiba ta leko wajenta amma lokacin wanka takeyi,yanzu tazo domin su gaisa, saidai ta tsaya sa'ilin data jiyo muryar habiba na fadin"Wai kina nufin babu abunda ya shiga tsakaninku dashi? Amma me kikayi mishi har haka?" Zahra tace"Wallahi ban mishi komai ba,nafi tunanin yafi son matarsa akaina,kema kinga dai ta yanda akayi auren,ba don a baya yana kirana musha hira ba da sai nace k'aka'ba masa ni akayi." Gaban tasleem ya fadi,ashe haka Haris ya aikata? Meyasa yake nuna mata anyi wani abu? Meyasa zai yiwa Zahra haka.Ta juya rai b'ace. A ranar har habiba tabar gidan bata sakarwa tasleem fuska sosai ba hakan ya kara sanyaya jikinta. Tana kaiwa nan a tunaninta ta numfasa cikin jin tausayin zahra,koda dai ita dinma abar a tausayawa ce."Kada kiyi zalunci,kada ki bari a zalunci yar uwarki. Kada ki yarda ki zama mai nuna kishinki a fili,duk da nasan halinki da zuciya da fushi,ki gane,harisu mijinki ne,dolenki ki bishi, ki kasance mai adalci a rayuwa. "Wadannan kalaman sun fito daga bakin mahaifiyarta ne a sadda take nusar da ita akan rayuwar aure, kwarai duk da zuciya irin nata bazata bari a shiga hakkin yar uwarta a musulunci ba.Game da Haris kuwa? Hum!!Tayi kwafa kafin ta mike don gabatar da sallar la'asar daganan kuma ta fada kicin. Kafin bayan magrib ta kammala komai takai samansa, a hanyar ma sai mita takeyi, hawa da saukar nan matsala ce,yafi a dunga ci adakin mai girki.    Wanka tayi ta hade cikin riga da wando,gaba daya saman rigar wajen wuyanta a bude take,ta kamata, daman gata gwanar iya wannan dressing din, ta tsuke da wando dogo,tasha kwalliya. Tabi jikinta ta fesheshi da turaruka masu sanyin dadi marar hawa kai.Takalminta dai mai tsini ta saka saika rantse wata balarabiya ce,rigar pink ce wandon kuma bak'i ne mai jikin leather sai shek'i yakeyi.Shape dinnan na baby mai daukar hankalin dukkan mutane don har cikin kawayenta a baya sukanyi mamakin irin halittarta,cikin nan saika rantse bata zubamishi abinci.Ta kalli lebbanta,jan bakinta kalar pink ya zauna d'abas sai sheki yakeyi,murmushi tayi kafin ta sanyawa jelar kitsonta tafka tafkan ribuna.Juyawa tayi ta fito zuwa falonta,yayi daidai da buga kofar sashen nata da akayi.Tafi zaton Zahra ce,don haka cikin takunta wanda babu inda baya vibrating ta nufi kofar ta bude.  A take idanunsu suka hadu da juna,wani abu tun daga yatsa har zuwa tsakar kansa yaji yana yawo, tun daga sama har kasa ya dubeta, ya rasa bakin magana bare ma daya ankara da murmushin da take sakar mishi.Yayi dakiya ba kadan ba ta hanyar yamutsa fuska "Mene kika kashe wayarki? Idan kingama kizo kibani abinci da yunwa nazo."Ya wuce sama!  Murmushi tayi,kwarai ya dauko ruwan dafa kansa don kuwa zaiyi nadamar abunda yake aikata mata. Kafin ta kwankwasawa Zahra sai gatanan ta bude,itama dai yan kantin taci,riga da siket, bata taba karambanin saka wando ba wai a ganinta tunda ba ita kadaice matar gidan ba. Ganin Tasleem da wando sai tayi turus,gaba daya taji wani mugun kishi ya taso mata. "Yanzu ai nake shirin kwankwasa maki." cewar tasleem, tayi murmushin karfin hali "Hum, ai ya sanarmin ma. "Tasleem batace komai ta nufi saman,zahra ta rufa mata baya. "Kinsan fa kanawan nan, gani sukeyi sunfi kowa iya kissa da wayewa, koda wasa kada ki dunga nuna kishinki a gabanta, kuma wallahi kar kiyi gangancin gayamata babu wata mu amala tsakaninki da yaya haris, saiki bada kanki. Me zata nuna maki? Kema fa macece! "Ta tunano maganar habiba, ta kuma jin karfin gwuiwa don kuwa haris har wajenta ya shigo ya sanarmata dawowarsa harda yabon kwalliyarta, tana saurararsu bayan daya kwankwasawa baby, daga nan waje taji muryarsa yana mata magana, lallai ta hakikance dagaske yana sonta!‬ Koda suka isa, baya falon, hakan yasa Tasleem shigewa kuryar d'akin.Yana zaune gefen gado yana amsa waya.Ganin haka yasa ta juyawa ta koma falon. Jimawa kadan sai gashi ya fito, bayan ya zauna suka kara gaisheshi gami da tambayar jikin yasmeen, ya amsa musu. Tasleem tayi serving dinsa, kamshinta duk ya gama hawa kansa, yanason yayita kallonta saidai bai kaunar ya bada maza tun wuri, don haka ya dake.Ya juya akalar hirar tasa ga Zahra inda yake tambayarta course din da takeson karantawa. Jin wannan yasa tasleem jin wani sanyin dadi, ashe yana da ra'ayin karatu. Muryar Zahra ta katse tunaninta inda cikin jin dadi ta amsa mai "Masscom nakeson karanta." Ya jinjina kansa yana murmushin nan nasa mai wuyar gani awajen mata "Nasaka a nema maki admission keda Habiba, baki da matsala tunda results dinki sunyi kyau sai ki dage da addu'a. Idan har zaki tsaremin kanki da mutuncinki, baki da matsala dani Tawan". Baby ji tayi tamkar ya buga mata guduma a kirji, suka hada ido da Zahra, ta daure ta murmusa, Zahra kuwa baki ya gaza rufuwa!.  Ta daure ta hadiye bacin ranta, ya nuna k'arara kenan bayason karatunta ita? Eh mana! Gashinan a zahirance tunda har yana batun cigaban karatun Zahra, ita kuwa ko oho! Ranta ya sosu, har suka kammala batace uffan ba. Ta tattara komai takai k'asa,a zuciye take wanke kwanukan tana tunanin zantukansa, koda dai ita tayiwa kanta tunda a baya ta samu damar yi saidai Allah bai nufa ba. Koda ta koma zama tayi,hankalinsa yana ga ball da ake haskawa, game ta hau yi a wayarta, Candy Crush, tana matukar sonsa, hakan yasa ko a baya take nacin yinsa, ga ipad dinta ma abun takaici ta barshi gidan Mamma. Wayar taji an warce, tayi azamar dubansa, game din yake kallo kafin yayi exiting. Ta tsuke baki "Zaka fad'ar dani fa". Yana mata dubansa mai k'ara sanyaya mata jiki, kafin ya kishingida har kafadunsu na gogar juna. Cikin murya kasa kasa yace "Inada kishi fiye da tunaninki, banaso a dunga mayarda hankali ga wani abu ko wani matukar muna tare da mutum, wannan ne babban dalilina na rashin ra'ayin kula yan mata. "Yayi murmushi kafin yace..! "A baya kb da sauran abokanmu suna dauka cewar ban iya yanda zan tsara mace bane, kuma da hakan. Ke nifa na tsani mace tayimin kallon mayaudari, duk wata soyayya wacce iyakarta a waje idan an shigo gida ba'a kwatanta toh bata burgeni, bada kaine na dunga batawa kaina lokaci wajen jaddadawa mace ina sonta yazo kuma ban aureta ba, nan gaba Allah Ya kaddara na auri yar uwarta nazo muna jin kunyar juna. "Ya dan mike zaune yana tabe baki wanda tuni baby ta fahimci hakan d'abi'arsa ce "Babu dadin fada a baki ma". Wani irin murmushi tayi "Ni kaina nafi gaskata cewar baka iya soyayya ba, baka ma santa ba". Ya karkato bayan ya lankwaso kafarsa daya, ya rungume hannuwansa yana fuskantarta kafin ya daga mata gira yana murmushi "Really?" Ta lumshe ido ta bude, wannan na nufin "Yes!" Ya juya kai yana 'yar dariya, ta gama tafiya dashi, a sannu kuma salo ya chanja. Tunda take bata taba jin abunda taji awajen Haris da wani namijin ba. Bata cikin nutsuwarta, saida taji muryarsa cikin dodon kunnenta "Mazan ko matan? Goodnight". Daga haka ya fice!‬ Takai mintuna uku kafin ta mike da sauri ta fice zuwa sashenta. Ashe daman GABA DA GABANTA? Ta murmusa tana numfarfashi, tana rantsuwa cewa Haris is special guy, ya iya wani abu wai shi soyayya. Ashe a zahirance ana samun irin wadannan? Hum! Bata jin akwai wani d'a namiji daya tab'a sanyawa ta raina gwanancewarta sai shi, duk da dai ba wani tarayya da sukayi ba amma ita kanta jikinta ya fahimtar da ita hakikanin wanene Haris Aliyu Kazaure! Kauna da soyayya tsagwaronsa, sune suka k'ara mamayar zuciyarta har tana jin cewar (she can't leave without him!).   "Mazan ko matan?!" Furucin daya tsaya kuma yake mata yawo cikin kwakwalwarta, menene manufarsa? Gasa ya maida rayuwar auren nasu ko me? "No ba haka bane! Watakila dai kema gwanantarki yakeson gani!" Tayi mugun murmushi, ai mace take, ba lallai saita mik'a kanta ba, dole ta hukuntashi! Ta daukarwa kanta alk'awarin karkato da hankalin mijinta gareta a KWANA UKU tal! Sai ya furta yana sonta! Sai ya ganewa kansa cewar matan ma suna suka tara! Saida tayi wanka ta kimtsa cikin kayan bacci riga da wando ta fita bayan ta dauki hijab da zaninta tasa a karamar jaka saboda sallah, kafin ta dauki sauran kayan amfaninta na safe. Kwarai tayi mamakin taddashi yayi nisa a bacci, ta hadiye kwadayinta itama tayi addu'ointa ta kwanta bayan ta kudurce a ranta sai Haris yadawo yana bibiyarta! RANA TA FARKO!!! Baccinsa yake cikin kwanciyar hankali da nutsuwa, da alama ya sha'afa da batun ofis, a hankali yaji ruwa yana fallasa a saman fuskarsa, wannan tasa dolensa ya bude ido fuska daure. Karon da idanunsa yayi da kyakkyawar fuskarta ya sanyaya ran nasa "Amincin Allah da rahmarSa su tabbata gareka my king, ka tashi ko yau baka zuwa ofis?" Tayi maganar ne cikin kwantar da murya, yayinda shi kuwa ya zuba mata ido, daga ita sai tawul ko cinyoyinta basu gama rufuwa ba ga dukkan alamu fitowarta kenan daga wanka don fuskarta ma da jikin akwai digo digon ruwa, nan ya tuno farkon ganinsa da ita. Duk wannan tunane tunanen yana yi ne yana bibiyarta da kallo, tuni ta juya tana shiri! Bata yarda data dubeshi ba ta madubin, har ta kammala goge jikinta, tana cikin shafe jikinta da cream dinta mai kamshi ne kuma yayi dauriya wajen mik'ewa ya cire jallabiyarsa dagashi sai gajeran wando ya fada toilet. Tabi bayanshi da kallo kafin tayi murmushi. Kadan ma ya gani. Kafin ya fito ta hade cikin leshi kalar darkbrown, mai b/curve. Riga da siket ne, siket din ma ya kamata, kamar yanda rigar ma saida ta dauke numfashi ta zurata. Daurin ma ya zauna d'abas, tuni ta gama da fannin kayan karin kumallo. Ta fente fuskarta ta feshe ko'inanta da turare kamar koyaushe. Ta maida komai jakarta, sannan ta fiddowa Haris manyan kaya duk da tasan lokuta da dama yafi kaunar zuwa ofis da kananun, saidai yau zab'inta tafison Haris dashi. Milk colour shadda ta zab'o mishi, wanda ya hau sosai da leshinta kasancewar katuwar fulawar da aka sanyamata a gefe milkcolour ce da kuma sauran kwalliyar da leshin yazo dashi. Daidai da hula saida ta ajiyemishi, tana kokarin gyara gadon ne ya fito, takowa yakeyi saidai ya gaza dauke kansa daga dubanta! Yana tunkaro cikin dakin amma idanunsa yana kanta har yana buge kafa da gado, yayi sauri ja baya. Cikin nuna halin ko'in kula ya nufi wajen dressingmirrow. Ba zato yaga ta janyo man ta lakato a hannu, ya dubi hannun sannan ya dubeta. Fuskarta har lokacin yana dauke da murmushi mai burgewa. Ai saiji yayi an jawo hannunsa, yana ji yana gani ta gama shafa mishi man, sannan tayimai farr da ido "My king, kafin ka kammala bari na had'a maka tea ko? Naga kamar zaka makara". Ta sumbaci kuncinsa sannan ta nufi hanyar fita tana tafiyarnan dai nata. Saida yaji bugun kofar ya dawo hayyacinsa, yana son yarinyarnan, wai kuwa tasan da haka? Kodai nema takeyi ya bada kai da wuri? No bazaiyi hakan ba, toh amma har tsawon wane lokaci da kwanaki zai d'iba cikin juriyar k'arya. Ya dafe saitin zuciyarsa, tanan yakejin wata kibiya tana sukarsa, tanan kuma yake jin zafi da radadin so da matsanancin kauna yana kara shigarsa. Dakyar ya tattaro nutsuwarshi ya cigaba da shiri, kayan data fiddo mishi ya saka kafin ya dora agogo ya dauki jaka da wayoyinsa..! Fitowa yayi ya sameta tuni ta hadamasa. Zama yayi sai ya ankara babu Zahra. Hakan yasa shi tambaya "Ina Zahra?" Ta murguda baki gefe kadan tana murmushi "Bata tashi ba." Ya gyada kai ya soma karyawa "Daman inada wata shawara, please inaso ya zamana girkin rana ne kadai za'a dunga haduwa tare ana ci, na safe da dare akaiwa mara girki sashenta." Kallonta yayi da wannan dara daran idanunsa masu lumewa acikin na mata harma su janyowa zuciyarsu matowa akan Haris "Akan wane dalilin" Tak'i janye idanunta daga nasa, ta kara k'aimi wajen kwantar da kwayar idanunta "Inaso kowaccenmu ta dunga samun enough time dakai. My king ka duba zancena". Tasleem batasan wani abu ba, my king da take fadi birkita lissafinsa yakeyi shi kadai yasan me yakeji, ya kawar da kansa daga dubanta ya maida ga filet din gabansa "Bani da matsala, kiyi shawara da kanwarki". Murmushi ta saki kafin tayi godiya. A ganinta hakan yafi, babu wata alama da wata zata fuskanta harma ta fahimci yanda alak'arta da mijin ke tafiya. Koda sukayi magana da Zahra, ta fita jindadi Itama tayi na'am da shawarar nan, murmushi baby tayi kawai. Zaune yake a ofis ya kasa katab'us, kansa yana jingine jikin kujera idanunsa a lumshe, a hankali yake juyi da kujerar yana tunani. Shifa ba dutse bane, yau duniyar tunaninsa akan mata ya fada, ya kasa daina hasko tasleem, hannu yakai ya shafi kuncinsa kafin ya murmusa, yes! Yana sonta, hakanan yana tsananin bukatar keb'ewa da ita. Buga tebur dinsa da akayine ya maidoshi hayyacinsa, ya bude idanunsa wadanda tuni sun kad'a ya zubawa mai shi ido, kafin yaja guntun tsaki ya mike ya shiga toilet, can sai gashi ya fito da tawul a hannu yana goge fuska."Ka daina shigomin babu sallama malam." Sayyid abokin aikinsa, sun saba har sun zama tamkar abokai yayi dariya yana duban Haris dake korawa mak'oshinsa ruwa "Ta yaya zakaji sallamata harma ka amsata alhalin kayi nisa cikin tunanin matanka? Ka gode Allah, a farko darakta da kanshi yayi niyyar zuwa amma sai akaci sa'a ya hakura ya aikoni, ka manta da meeting na 1pm. "Da sauri ya zari laptop da hularsa, shaf ya mance. Suka fita! Ya dawo da rana cike da d'oki da son ganinta. Numfashinsa ya kusan daukewa sakamakon kyau da shiga doguwar riga ta atamfar tayi mata. Zahra itama taci adonta tayi kyau, shi dai Haris ya k'ara godewa Allah bisa sa'ar daya ci na dace da samun zuk'a zuk'an yan matan nan. Wannan karon ma itace ta zubamishi yaci, tamkar kada ya koma ofis haka yaji, can dai ya daure ya fice. Mintuna uku da barinsa daga gidan, taslim kwance a gadon dakinsa ta jawo wayarta ta soma tsara mishi kalamai "The king of my heart, har na soma kewarka. Please and please idan ka taso ka taimaka kayo gida kai tsaye, tun kafin rashinka yayimin yawan da zan kasa jurewa na b'alle da ruwan hawaye. Tasleem, yours forever!" Murmushi yayi yayin daya kammala karantawa, lokacin yana tsaye a junction, kibiyar so na kara sukar k'ahon zuciyarsa. Ba k'arya, tasleem tana kara rura wutar kauna a zuciyarsa! Ya kara muryar wakar da cikin sa'a aka sanyo a tashar Wazobia, wato Fall in love na dbanj kamar ansan yanayin da yake ciki, ransa yayi fari. A gefen Tasleem kuwa, bata damu da rashin maido martanin sak'onta da Haris baiyiba, tana da yak'inin tarkonta yana matukar kokarin kama kurciya.Ta kirayi hasinat suka sha hira abinsu kafin ta kirayi hindu, anan kuma ta nemi data aikomata lambar Hamida saboda zumunci. Mammanta da Abbanta kuwa, kai harma da waziri takan nemesu su gaisa. Bayan magrib ya shigo gidan cike da buri da d'okin son yin tozali da ita, saidai kuma kash! Zahra ya tarar zaune a tsakar falon nasa tana kallo, ta cancara kwalliyarta kamar mai zuwa wajen wata liyafa. Da murna ta tarbeshi, a ladabce ta mishi sannu da zuwa sannan ta karb'i jakar hannunsa. Ya amsa yana murmushi, saida yayi wanka ya shirya cikin kananun kaya, kafin ya fito zuwa falon. Ya dubi Zahra yana murmushi kafin ya shafi gefen fuskarta "Myn bari naje masallaci lokacin sallah yayi". Wani sanyi ya ziyarci zuciyarta. "Myn?" Wancan karon ya kirata da tawan a gaban tasleem, yau kuma myn? Wow ta yarda kwarai yana matukar kaunarta. Shi kuwa gogan yana dawowa daga masallaci, ya kwankwasawa bby. Ta budemishi kafin ta bude baki "Lah, daman ka dawo? Shine banji ma shigowarka ba ballantana nazo yin sannu da zuwa gareka? I'm sorry". Tuni ya karasa shigowa ciki, farar shirt bodyhug ne ajikinta, sai wani wando pencil jeans wanda daf yake da karasawa gwuiwarta, kanta babu ko dankwali. Numfasawa yayi kafin ya juya ya dubi tv,Arabica tv take kallo, muryar nancy  yana tashi cikin d'ayan wak'okinta. Ya juyo "Wa kika yiwa wannan kwalliyar? Please ki dunga suturta jikin if you are alone. Nasha gayamaki banason kishiya, koda aljanu ne!" Jin haka yasa ta hau mutsitstsika ido, kafin ta kauda hannuwanta sai ga hawaye sun zubo, yayi mata kuri da ido kafin a tausashe yace "Me akayi toh?" Ta juya da gudu ta fada kan kujera tana kuka, kamar ya shareta ya fice saidai bazai iyaba, da sauri ya karasa ya durkusa gefenta, numfasawa yayi kafin yakai hannu ya dago hab'arta "Hey,menene kuma?" Ta share fuskarta, ta tsuramai ido "Kai na yiwa kwalliya baka yaba ba". Yanda tayi maganar yaji har kwanyarsa, ya share mata fuskar "Ok, i'm sorry kinji" Ta gyada kai. Ta sanya hannuwanta ta kama yatsunsa kafin ta saukesu daga saman fuskarta, still dai tana rike dasu tace "Kabar kanwata cikin kadaici". Tab! Ai abunda Tasleem bata sani ba shine, bawai kanwartata ba, daidai da duniyar gaba daya ya manta da mutanen cikinta. Ya kara kama hannuwanta sosai "Kinmin iznin tafiya?" Tasan da ace da dama zata sakashi yin fiye da haka, murmushi tayi tana wani lumshe ido kafin taja hannuwansu ta sumbaci nasa sannan ta tsaida idanunta kansa, har lokacin murmushin nan takeyi "Muje na rakaka". Suka mike. "Oh ni rufaida yau naga ikon Allah, kuga yanda jaruman maza ya zama solob'iyo gaban mace?" Na fada ina duban iyalan Hannu da yawa writers dake facebook, na lura mazan sun daure fuska, don gasa mukeyi tsakani aga wandanda zasu ciri tuta, can na hango matan suna shewa da tafi, idan an cire sayyada muhd k'awar Zahra! Muka maido hankulanmu ga ma'abota nunawa juna tsantsar soyayya. Har sun kawo kofar dakinta, takai hannu da niyyar budewa, taji runguma, sunkai 2mins kafin ya sumbaci kuncinta "Ki chanja shiga, gud nyt". Daga haka yayi ficewarsa, ta kulle kofar kafin ta jingina da kofar tana dariya, kai musamman ma idan ta tuno wani jiji dakai, da shan kamshin haris gareta a baya sai abun ya k'ara bata dariya, ta wuce daki ta chanja shigarta tunda dai kwalliya ta biya kudin sabulu, a yau ta d'ana mishi babban tarkon da bazai iya ganin mace ya kyale ba. Sai kuma ta zauna d'abas saman gadon, a fili tace "Ba mu'amalata da Haris kadai nake gyarawa ba Zahra, ke kanki da mijina inaso naga komai ya daidaita". Duk da cewar tasleem tana da kishi matuka, don har wasu lokutan takanji haushin Haris daya auri mata biyu batare daya bari sun more rayuwa ba, amma saidai hakan bai zame mata dalilin da a zuciyarta taji muguntar son ta kori Zahra daga gidan ko kuma miji ya juyamata baya ba. Kowa yayi takunsa kawai!    Acan kuwa zuciyace ta shiga cikin wani yanayi, ta kasa daina tunani, ta kasa yakice dukkan sak'onnin da aka aika zuwa gareta. Kasancewar gangar jikin, bai taba kuskuren hada kansa da haramun dinsa ba a rayuwa, sai halaliyarsa, ji yake inama su dauwama haka. Saidai da komai ya nisanceshi, dole ya rungumi abunda ke kan idanunsa. Baiyi k'asa a gwuiwa ba wajen yakice wannan tashin hankalin akan daya halal din tasa! A bangarenta itama ta cika da mamaki tsantsa, saidai ta gurzu matuka da har a karshe ta fashe da kuka wanda dole bayan kwarnafi ya kwanta, ya mike tsam ya hada ruwan dumi a toilet kafin ya bata kyakkyawan agaji, da kansa ya sanyamata kayan barci ya shiryata, kafin kuma ya bata paracetamol ta sha. Saida ya kimtsa tsaf ya dubeta yana neman iznin tazo suci abinci, cike da tsananin kunyarsa ta tura kai bargo "Na koshi". Yayi yayi amma tak'i tasowa dolensa ya fito falon bayan ya kashe mata fitilu. Bude fuskarta tayi tana mai murmusawa, Haris daban ne! Ta yarda da wannan, a karshe ta hau mamakin yanda yana shigowa falon ya kawo mata runguma bata wasa ba. Kalamai na so da kauna kam tasha su har saida ta tsorata da rawar k'afarsa.          A gefen Haris kuwa, kwarai ta burgeshi matsayinta na budurwa data iya kokarin tsare mutuncinta har gashi ya bata wata daraja mai girma a ransa!! Kasancewar baisanta ba, ya sanya koda suka shigo falon da kallo kawai ya bita kafin ya maida dubansa ga Tasleem dake nuni da tambayace. Tana murmushi, ita kuwa Hamida zubewa tayi tana gaisheshi, gaba daya yayi mata wani mugun kwarjini, daman haka Haris din yake? Namiji ne wanda yakeji da kudi da kuruciya, uwa uba kuma kyakkyawa ne na gani na kwatance. Kwarai Tasleem tayi mugun sa'a a rayuwarta, wannan miji haka? Inama inama hum! Ta ayyana a ranta tuni ta koma kalar tausayi.   Ya amsa gaisuwarta duk da dai fara'ar dake saman fuskarsa ragagga ce na rashin sanin kowacece. Ya dubi Tasleem. Murmushi ta k'ara sakar mishi "Hamida ce kanwata, d'iya ga Marigayiya Raliya". Ya k'ara kallon Hamida da murmushi saman fuskarsa, ikon Allah kenan, wato dai Hamidar data tab'a bashi labarinta ce kenan? Shi kam baiga wani abu da take dashi ba da har yasa ta nunawa Tasleem k'iyayya "Sannu fa kanwarmu, ya maigidan naki?" Hamida ta amsa "Lafiya kalau yake." "Toh madallah, a gaisheshi ko?" Ya fada yayinda yake zura hannu cikin aljihun wandonsa, ita kuwa hamida tuni ta amsa da toh gami da mikewa, ya mik'awa Tasleem dubu biyar "Ki bata." Hamida ta amsa cikin rawar jiki ta koma durkushe tana godiya, yace bakomai. Zahra dake kokarin zuba abinci ta dubi Hamida "Hamidah kinci abincin ko?" Tasleem ta bata amsa da cewa "Taci." Daga haka sukayi sallama da Zahra kafin tasleem ta fice domin yi mata rakiya, saida suka isa farfajiyar gidan sannan ta mik'awa Hamida ledar da tun shigarta falon Haris take a hannunta, kayan kwalliya ne, sai sabbin dinkunanta kala hudu da bata tab'a sakawa ba sannan kudi har dubu goma cikin wadanda take dasu bata kashewa, hamida ta soma hawaye da godiya, Tasleem ta dafa kafad'arta "Menene haka? Na gayamaki banaso kina damuwa, kefa yar uwata ce". Daga haka sukayi sallama, sai sukaji muryar Haris, ashe yazo. "Ba'a mota take bane?" Jin haka duk suka kai dubansu garesa. Tasleem ta amsa "Eh." Ya dubi Tasleem cike da takaicin yanda ta fito, don daga ita sai yalolon mayafi wanda bai gama rufeta ba "Ok, ki koma ciki zansa a kaita." Tasleem ganin yanda yayi kicin kicin ne yasa ta komawa ciki. Shi kuwa Abdulaziz direba ya kwalawa kira kafin ya bashi mukullin mota "Ka mik'ata gidanta". Daga nan suka k'ara sallama da juna, hamida tayita godiya bisa karamcin da Haris yayi mata daga haka yayi ciki. Tasleem ta fito daga sashenta zata hau sama don yin lunch sukayi arba. Harara ya wurga mata ya wuceta zuwa sama. "Toh menene kuma?" Ta tambayi kanta kafin ta tab'e baki ta bi bayanshi. Tuni ya zauna saman kujerar dinning, tana k'arasowa ta zauna, Zahra har ta kammala zubamishi itama ta zauna. "Na sanya muku doka, duk wacce tayi bak'i ban yarda ta wuce daga baranda ba, ta tsaya anan suyi sallama koma da wacece. Daga yanzu ku kula, ke kuma". Ya dubi Zahra, "Admission naku ya samu, ranar monday mai zuwa zaku soma halartar karatu. Ki kiyayemin darajarki, banaso kina zuwa daukar darasi da sutura marar dacewa, ko kuma kice zakiyi kwalliya, duk wannan ban amince masa ba, sannan kisan irin wadanda zakiyi mu'amala dasu, banason k'awaye sune masu lalata tarbiya, don haka ki kula, ki gane kuma ki fahimta, kada ko kusa ki bari naga wani chanji daga kulawa ko kuma biyayyar da kikemin, hakan ga tarbiyyar da kika taso cikinta. Nidai babu wacce ta isa ta juyani cikinku, kamar yanda ya zamto dole agareku kuyimin biyayya, nayi alk'awari zan k'ok'arta wajen kulawa daku da sauke hakk'ok'inku da suke akaina. Aurenku nayi bisa kauna da soyayya ta don Allah, don haka kuji tsoron Allah ku kiyaye hakkin aure!" Yana magana cikin damuwa matsananciya wanda daga Tasleem d'in har Zahra basusan abunda ya jaza damuwar tasa ba. Sun dai amsa da toh kafin kuma ya tsakuri abincin ya koma ofis!. Bayan tafiyarsa, tasleem tana kwance saman doguwar kujerar falonta, kwayar idanunta yana ga fankar dake juyawa, tunani takeyi game da makomar karatunta, tasan ta riga ta yiwa kanta, bata zaton koda wasa Haris zai amince mata ta cigaba. Musamman tunawa da maganganun daya gama fad'a yanzun, ji takeyi inama ace itace da wannan opportunity da Zahra ta samu, ai karatu har saita dangana da masters, da ace ta maida hankali a baya da tuni ta zama cikakkiyar lauya, ta muskuta tana mai numfasawa, ko giyar wake tasha tasan Haris bazai barta ta cigaba, hakanan dai zata hakura. Bayan magrib tana jin shigowarsa ta nufi saman. Lokacin tayi wankanta tsaf, ta chanja shiga zuwa riga doguwa marar nauyi, mai fad'ad'd'an hannu daga k'asa. Ta yafa karamin mayafi tayi talha, babu kwalliyar komai saman fuskarta. Ta shiga da sallama, lokacin hira suke harda dariya, yana sanye da jallabiya bak'a marar nauyi kuma shara shara. Suka amsa mata sallamarta, wani sassanyan kallo yake jifanta dashi yana sakin murmushi. Ta maida mishi martani kafin ta dan russuna tayimai sannu da zuwa. Ya amsa yana kokarin ganin kwayar idanunsu ya had'u da nata saidai kokusa bata dubeshi ba, ta mike, tana kaiwa kofa ta juyo akayi sa'a yana kallonta. Murmushi mai burgewa ta sakarmai kafin ta kashe masa ido d'aya, daga haka ta fice. Ajiyar zuciya ya saki, a hankali kuma ya shafi sumarsa yana mai lumshe ido. Ko kusa Zahra bata kula ba, hankalinta yana ga tv ganin ansoma series din da take matukar so da kaunar gani, Laali. Shi kadai yasan yanayin da zuciyarsa ke shiga akanta, baik'i su kwana su wuni tare ba koyaushe. Ya kanyi iyakar k'ok'arinsa wajen ganin ya b'oye damuwa da azalzalar da zuciyarsa keyimishi akan Tasleem. Muryar Zahra ta katse tunaninsa inda take dariyar film. Ya daki bayanta "Cry cry baby, kinbar mijinki da yunwa". Kunya ta kamata, ta mike da sauri! Ta rigaya tasan me yake nufi, cikin shagwaba murya tace "Gaskiya nidai nagayama banaso". Ya kwaikwayi muryarta "Ni kuma inaso". Ta turo baki, sukayi dariya yakai hannu da nufin rik'ota, a guje ta bar wajen tana fad'in "Taso ka cika cikinka". Misalin goma na dare, Zahra ta sauko sashenta da niyyar shirin bacci, shi kuwa yana kwance saman gado yana browsing, wayarsa tayi k'aran shigowar sak'o. Murmushi yayi ganin daga inda yazo. Ga abunda take cewa "Zuciya ta kasa daina tunaninka, hakanan na kasa samun sukuni. Kai kadai ka zamto abun muradina, inama inama mu kasance tare kullu yaum! Sweetdreams my king! *hugs nd kisses*. Oh God! Ya lura tanason kasheshi, ya karanta yafi a k'irga kafin daga bisani ya yanke hukuncin maida martani, saidai jin motsin dawowar Zahra ya sanyashi fasawa gami da jona wayar chaji. Daren sun kasance masu faranta ran juna kamar jiya, hakanan so da shak'uwa suka k'ara wanzuwa a zukatansu.! RANA TA UKU       AIKI SAI MAISHI!! Kamar koyaushe, ya gama shirinsa cikin nishadi da walwala, yana yi suna hira da matarsa kafin su fito yayi breakfast sannan ta rakoshi zuwa k'asa. Ya kwankwasawa Tasleem, suna hada ido suka sakarwa juna tattausan murmushi, hakanan kwayoyin idanuwansu suna aikawa juna sak'onni na musamman. Kasancewar ba gaba daya ta bude kofar ba, hakan yasa Zahra bata gane wainar da suke toyawa ba. Sai lokaci Tasleem tayi jarumtar bud'e k'ofar, tana mai russunawa ta gaisheshi, ya amsa fuskarsa dauke da murmushi. Zahra ta gaisheta, ta amsa ta tambayeta lafiyarta. Kafin Haris yace "Zan wuce, saina dawo". Har lokacin murmushi bai gushe ba saman fuskarta "Toh a dawo lafiya my king, Allah Ya bada sa'a". Ya amsa kafin ya nufi hanyar fita, Zahra tayi mai rakiya batare data sab'a iyakar da yayi musu ba. Ya rungumeta ya sumbaci kuncinta kafin kuma ya daga mata hannu "Gudbye my baby, Kularmin da kanki". Ba tare da gajiyawa ba, Tasleem wajejan sha biyu ta k'ara tura mishi text mai nuni da tsananin kauna da bege. Kafin kuma ta cigaba da girkinta. Fankaso da miya sai romon kayan ciki da tayi kafin kuma ta had'a lemun citta da fosterclarks na pineapple guda biyu, karshe ta had'a komai takai sama ta jera, lemun kuwa ta sanyashi a firij kafin ta sauko, saida ta kimtsa kicin d'in, harda wanke wanken data tsana a rayuwa tayi, don yafi kowanne aiki wahalar da ita. Ta fad'a wanka, kwalliya sosai tayiwa fuskarta, ta murza lebb'anta har saida taga jan janbakin data sanya ya zauna d'abas ya daidaitu, kafin ta mike don saka kaya. Riga da siket ne na atamfa skyblue da fari, ta zura rigar dakyar, kafin taja zip. Daga daidai gaban rigar, an bud'e da shape na circle har kana iya hango halittar wajen. Hakanan siket d'in shima ya kamata kwarai, ya kuma zauna d'as a jikinta. Ta sharce gashinta wanda tuni ta tsefe kitson, tayi murmushi, tunawa da gashin dokin da a baya take sakawa duk da daidai gwargwado tana da gashinta. Ta murza daurin dankwali duk da bata gwanance sosai a d'aura d'ankwali ba saboda bata fiye shigar manyan kaya ba. Saidai koyaya ta murza sai kaga ya amsheta kamar daman can ita d'in ta saba. Tana fesa turare taji hon na motarsa. Ta kammala, saida ta bawa minti goma baya kafin ta zura takalminta mai tudu bak'i da kwalliya ruwan toka, wanda ya k'arawa k'afarta kyawu da haske, sannan ta bude ta fito. K'amshinta ya karad'e corridor d'in, tana tafiya cikin salo na nutsuwa, a hankali take taka steps din har ta isa ga k'ofar, tana murd'awa ya bud'u alamun daman can a bud'e yake. Sallamarta ta doki kunnuwansu, fitowarsu kenan daga d'aki, da alama cikin nishad'i suke saboda rike yake da hannun Zahra suna dariya. Tsayar da idanunsa yayi cak ga abunda yafi muradi a rayuwarsa, ganin idon Zahra yasa shi basarwa ya taka zuwa dinning chair ya zauna. Idanunsa sun gaza daina satar kallonta, yayinda ita kuwa take takunta mai fisgar hankali, tana murmushi ta duk'a saitin kujerarsa "My king barka da rana". Ta fada tana watsamishi salon kallonta da murmushi saman fuskarta. Ajiyar zuciya ya saki, bazai iya magana ba, har lokacin idanunsa sun gaza daukewa daga kanta, gyada mata kai kawai yayi yana murmushi. Cikin dauriya ba kad'an ba, ya kauda idanunsa daga muradinsa yana maida dubansa ga Zahra wacce tuni kishi ya tafaso zuciyarta. Ido ya kashe mata "My baby a zubamin abincin mana". Jin sunan daya kirata dashi ya sanyayata. Shi kuwa sai kallon tasleem yake awajen firij. Bud'ewa tayi ta dauko lemu da ruwa duka ta ajiye, kafin ta zauna ta janyo filet itama. A sannu suke cin abincin bayan kowannensu yayi bismillah. A hankali kamar kuma da wasa taji kafar mutum saman nata yana shafawa. Wannan yasa ta dubansa, akayi sa'a ya kallota, saidai fa kallon ya bambanta dana koyaushe, ta nuna masa Zahra (da kanta ke kasa tana kai fankaso baki) da ido, ya harareta kadan kafin ya murmusa, mintsilinta yayi da yatsu biyu, ta yamutse fuska don zafi, kafin ta sanya takalminta ta d'an takeshi. "Aush!" Ya fada da karfi, ganin Zahra ta kalloshi ya wayance da firfita bakinsa "Abincin zafi fa". Zahra ta hau sannu kafin ta mike tana fadin "Bari na k'ara fanka, please yayana kaci sannu".  "Sannu".Cewar Tasleem, idan ka dubi fuskarta saika rantse batasan abunda ta aikata ba, harararta yayi kafin cikin rad'a yace "Kinci bashi". Murmushi mai bayyana hak'ora tayi batare da tace uffan ba. Misalin biyar na yamma, Tasleem ta kammala girki har ta zubawa Zahra nata ta mik'a mata, kafin ta hau saman ta ajiye nasu da maigidan nata daga bisani ta sauko ta fada wanka. Zama na musamman tayi bayan ta goge jiki ta shafeshi da cream dinta mai kamshi sosai. Tayi kwalliya mai fiddo kyawu kwarai kafin ta mike. Kayanta ta shiga sanyawa, english wears ne,riga da wando. Hum! Ba'a magana, na bar maku alkalam, ku hasko tasleem mai kyawun diri cikin shiga ta kananun kaya maroon colour. Jikinta kuwa kamar anyi ruwan turare sai mutum ya rasa kalar turaren data fesa, game da makaman aiki kuma, tun safiyar ranar tayi aiki da kayanta. Murmushi ta sakarwa kanta kafin ta dauki wayarta tayi hotuna. Bataso ya dawo bai sameta a saman ba wannan yasa ta yin azamar daukar wayarta da jakar data riga ta had'a, domin daga yau tasa a ranta matukar ta hau wajen mijinta toh ba abunda zai kara sauko da ita sai wata safiyar. Saida akayi sallah yazo! Itama ta idar da salla harta maida doguwar abayar salla da hijab daki, jin ana kwankwasa kofar yasa tayi saurin mikewa ta bude mishi. Lokaci daya suka sakarwa juna tattausan murmushi kafin ta amshi jakar hannunsa, rik'ota yayi gaba d'aya, ya janyota zuwa jikinsa, a hankali ya tura kofar dakin da k'afarsa. Salo ya soma chanjawa, har ya zamana tsayuwa tana neman gagararsu, tasleem ce ta soma ankara da sautin takalmi dake nufowa saman, hakan yasa tayi azamar janyewa tana mai daukar jakarsa zuwa daki, cikin kasalallan duba yake binta da ido yanajin takaici yanda a katse hanzarinsa. Jin ana shirin turo kofar, ya gyara mab'allin rigarsa, kafin ya amsa sallamar yana mai sa hannu ya gyara sumar kansa. Zahra ce ta shigo, sukayi murmushi, kafin tayi mishi sannu da zuwa. A karshe ta sauka. Wannan ya bashi damar kutsa kai cikin d'akin, batanan ya jiyo motsin ruwa, ganin bata rufe kofar bane ya sanyashi shiga ciki. Ruwa yaga tana had'amai, ta juyo da murmushi kafin ta hau b'alle mishi botilan riga har lokacin bata yarda koda wasa ta dauke kwayar idanunta daga cikin nasa ba. "Ya dace ayi wanka haka ko my king?" Baida niyyar amsawa don baiji wannan kuzarin ba, hakan yasa kawai ya hau bata amsa ta musamman! Dakyar ta goce ta fita tana dariya. Ajiyar zuciya yayi, wani zugin kauna yana k'ara k'arfi cikin ransa.   Madallah da wannan dare mai wuyar fassara yanayi da jin dadin masoyan nan! Godiya da yabo sun cancanta ga Sarkin sammai da k'assai wanda Ya halattawa namiji da mace aure, Ya kuma sanya so da kauna marar yankewa tsakaninsu! Kwarai Allah mai iko da baiwa ne! Mak'agin kowa da komai! Zukata biyu ne da basu gajiya da begen juna, burin kowace zuciya bai wuce ta kyautatawa yar uwarta ba, ta nuna mata tsantsar kauna da tsananin begen da take kwana da yini a ciki. Babu wacce ke fatan rabuwarsu, karshe ma sai zuciyoyin suka raunana bisa tunawa da baya! Har dai baiwar Allahn ta kasa dannewa kawai ta d'ora kanta saman kirjinsa ta fashe da kuka mai tsanani wanda hawayen ke zuba kamar famfo a saman kirjin nasa. Cikin tashin hankali yasa hannu ya d'ago kanta kafin cikin muryar rad'a yace "Queen, nayi wani laifin gareki ne? Please ki sanar dani, kukanki yana tayarmin da hankali, banason damuwarki. Tab'a kiji yanda kirjina ke bugu tamkar zuciyata zata fito, gayamin me Haris yayimaki, na rantse da Allah zan hukuntashi". Ta dago kwayar idanunta tana dubansa, tuni idanunsa sun kad'a da alama dai hawaye ke shirin fita daga cikinsu. Ta riko hannunsa "Na tsani kaina ne!" A gigice ya tallafo fuskarta "No please, kibar cewa kin tsaneni, domin wallahi duk wanda zai tsaneki shakka babu ni ya tsana, kuma nima banajin zan k'ara ganinsa da k'ima, amma ke menene ya zafi zaki tsaneni, ko ban gamsheki ba?" Kwayar idanunsa kadai zai baka tabbacin cewar dukkan abunda yake fad'i tsantsar gaskiyarsa ce. Bakinta yayi nauyi, dakyar ta sunkuyar da kanta tasamu kwarin gwuiwar yin magana. "Ka gafarceni my king, ai kai d'in namiji ne cikakke wanda babu macen da bazata yabawa bajintarka ba, saidai inajin nauyi bisa yanda ka riskeni, da...". "Ke mene haka wai? Bana son shirme!" Ya fada cikin fusata, kafin ya cigaba da magana "An fadamaki wannan kadai shine so? Ko an fadamaki Kauna ce? No tasleem, son da nakeyi gareki so ne na gaskiya wanda babu algus cikinsa. Ina yi maki so wanda baki bazai iya misaltawa ba, na soma sonki tun sadda naji labarinki, tun lokacin nake kwana da wuni cikin tunaninki. And you know what? Tun kafin faruwar wani lamari, inada niyyar aurenki. Son da nakeyi maki bai danganci wannan hanyar ba, duk da kwarai nasan wannan ne mutunci da alfaharin diya mace, don wallahi ba don kauna ta gaskiya ba, bazan taba neman auren YAR BARIKI ba! Inada kyankyami, banson kazanta fa. Ya fada kamar yanda zahiran fuskarsa ta nuna hakan kafin ya dafa cinyoyinta, numfashinsu na gauraya "But you are special to me, ban taba son wata ba yanda na soki, i mean to say, you are my firstlove. Ni musulmi ne, nasan menene KADDARA kuma nasan ladan dake cikin imani da ita. Allah ne kadai zai bani ladan aurenki my queen. Kada ki kara damun kanki, ni sai na jiki ma kamar wata sabuwa, gayamin menene sirrin?" Tana murmushi cikin sanyin murya tace "You want to know?" Gira kawai ya d'aga mata, nan take ta shiga labarta mishi darussan cikin gwanancewa, ganin abun yafi karfina da yan uwana, muka rufe kofar muka barsu. Wannan daren, dare ne na alheri agaresu, yayinda alk'awurwura da dama suka wanzu tsakaninsu. A safiyar kuwa basu samu farkawa ba sai wajen tara na safe bayan sunyi sallah kenan suka koma. Shine ya soma tashi, ji yakeyi kamar kada yaje ofis, hakanan dai ya fad'a toilet. Rufe kofarsa ne ya farkar da ita, ganin lokaci ya sanyata mikewa da azama. Saifa lokacin ta tuna da saukarta k'asa ya zama dole saboda had'o kayan karin kumallo. Taja tsaki ba don taso ba, ta fiddo wa mijinta kaya ta feshe da turaruka kafin ta zura doguwar rigarta da hijab ta sauka. Saida ta hada komai sannan ta komo saman, daman breakfast yanzu kowacce nata takeyi. Bai riga da ya fito falon ba, tayi mamaki, tun kafin ta karasa ta fidda hijab dinta, daga ita sai doguwar riga. Ta iskeshi yana zura riga, sukayi murmushi batace komai ba ta fara shiga ta wanko bakinta, kafin ta durkusa ta gaisheshi ya amsa mata yana mai d'agota ya hada da jikinsa. "Ya daren jiya?" Babu wani abu wai kunya daya rage tsakaninsu, ta dora hannuwanta bisa kafadunsa cikin narkakkiyar murya tace "Bazan iya misalta zumar dake cikinsa ba". Yayi murmushi mai bayyana hakora "Dagaske?" Tana mai basarwa tace "Ba laifi". Sukayi dariya Koda sukayi zaman karyawa, bayan ta kammala had'a mishi ta zauna sannan ta dubi bangon da har dubansa ya zame mata jiki duk da ba hoton. Juyowar da zatayi sukayi ido hudu, yana murmushi yace "Kina yawan kallon frame dinnan, koda dai tun kafin na sanyashi ne, why?" Ta tsuke baki "Tunda ka fadi haka ai kasan meyasa nake kallo hakanan ka rabani dashi". Ya harareta da wasa "Meyasa kika k'i gayamin? Wacce ta fiki so ai kinga ita tayi magana". Ta daga kafadu nuna rashin damuwa, "Ai kun kyauta, nima sai a wankomin irinsa inaso".  "Haris kikeso kenan?" Wani murmushin tayi da gefen kumatu daya tana mai tsuke baki bata tanka ba. Ya numfasa cikin jin wani sanyi a ruhinsa, ya hakikance komai na Tasleem daban ne dana sauran mata. Kb! Shine wanda ya fad'o mishi a rai. Ya godewa Allah daya zamana shine mai nasarar samunta.   Har kasa ta rakoshi, ta wuce kofar dakin Zahra tayi gaba har baranda ta tsaya, saida ya kwankwasawa Zahra sukayi sallama kafin yabi bayan tasleem. Ta mika mishi jakarsa, ya hada da yatsunta "Take care". Zai tafi tayi azamar riko hannunsa "Af nayi mantuwa". Yayi mata duban alamar tambaya ta sumbaci kuncinsa kafin tace "Mazan ne ko matan??" Daga haka tayi dariya tana daga mishi hannu tayi ciki abinta.   Ya murza hanci yana mai tabe baki "Jimin queen da wata tambaya? Maza ne koyaushe da higher marks, right?" Ya dubi hagu da dama babu mai bashi amsa, kawai ya murmusa ya fice.   Haka rayuwar gidan Haris ta cigaba da tafiya cikin kwanciyar hankali da lumana. Ga surukansu kuwa, sai sambarka. Ba ga mamin ba, ba kuma ga mahaifiyar haris ba, wato Umma, dukkansu suna nuna kulawa garesu hakanan basu nuna bambanci wai zahra ce ta jikinsu sosai. Gwara gwara ma Umma takanji nauyinsu. Tuni Zahra ta soma zuwa makaranta, hakan yakan sosa ran Tasleem taji inama ta samu wannan damar. Har dai tayi karfin halin tambaya rannan. Zaune suke a barandar shan iska dake daga can gefe idan an bude wata kofa a falon haris. Yammaci ne mai dadi, iska ke kad'awa mai nuna alamun lokacin sanyi ya soma shigowa. Kwance yake akan restingchair dake wajen, fuska dauke da murmushi yayinda idanunsa ke a lumshe sanadin dadin da yakeji na tausar da takeyi mishi. Ya gama shantakewa kawai yaji taja yatsan yayi k'as, da sauri ya bude ido ya mike zaune gami da sakin karamin ihu. Tayi dariya ya girgiza kai kawai ya koma ya kwanta "Yarinyarnan zan soma zaneki kenan, K'iriniyarki tayi yawa". Tayi dariya yana tayata, damar nan take jira daman, ta sameshi ciki nishadi "My king". Ta furta a shagwab'ance, ya dubeta duban da tafi muradi akan kowanne salon kallo da zaiyi. Fuskarsa da murmushi saidai bai amsa ba, ta numfasa kafin tace "Inada wata bukata awajenka". Jin hakan ne yasa shi mik'ewa zaune, sai lokacin yayi magana "Game dame fa?" Ta hadiyi miyau cike da fargaba, kafin tace "Kayimin iznin komawa ga karatu..". Sauyin data gani a fuskarsa ne, ya sanya bata k'arasa ba, tayi gum. Fuskar nan tamkar bai tab'a dariya ba, cikin kausashshan murya ya soma magana "Nayi zaton shiruna ya isa ya fahimtar dake ashe baki fahimceni ba, ki gafarceni, amma ko kusa bazan tab'a samun nutsuwar hakan ba. Bazan iya barinki ba Queen, wanda kikayi ma Allah Ya amfana, saidai keda karatu kuma?" Ya girgiza kai kawai kafin ya mike ya shige daki, ta tsurawa jug mai dauke da orange juice dake saman tebur ido, a sannu taji hawaye sun zubo mata tana tariyo maganganunsa. Kai jama'a, tirr da abunda zai zamto silar da mijinka zai soma zirginka. Ina amfanin Ranar Nadama haka? Yau gashinan ta yiwa kanta, da ace duk haka bata kasance ba da babu wani abu da zai janyo mata wannan matsala. Yau gata ga babbar dama ta cigaban karatunta amma Haris yace sam! Dana sanin barikanci ya k'ara mamaye zuciyarta, taji tsanar Momi. Wai tana ina ma??! Ta tambayi kanta, ya manal tayi da auren Alhaji Ubale? Dalal fa? Ta bar wannan hanyar ko kuwa dai ta cigaba? Hibba tana ina yanzu? Babu amsa, wannan yasa tayi fatan shiriya garesu kafin kuma ta jiyo muryarsa yana kwala mata kira, ta mike tabi bayansa. Daga kasa a farfajiyar, ni da jama'ata muna zaune a saman kujeru muna hangensu, anan na numfasa na dubesu, zanyi magana ummu faruk ta rigani da cewa "Kwarai, ya kamata mu bincikowa taslim amsoshinta". "Ni kaina abunda na matsu naji kenan". Cewar asiya rafin dadi, kafin zainab sirajo ta mike "Idan kunyarda zanje na dubo". Mukayi na'am ta mike, ga bayanin da muka samu akansu. Rayuwa tana tafiya ba yanda ake so ba ga Hajiya Hannatu, Momi. Harkoki sun soma dagule mata sakamakon wani mugun dan kasuwa daya sakota a gaba akan sai ya dauki fansar mugunta da tayi mishi na hadashi da yarinya mai dauke da cutar kanjamau wanda sanadin hakan shima ya kamu da ita. Sanin kowa ne, Alhaji Sa'ad Kwangila shahararran dan kasuwa ne mai ji da tarin dukiya. Saidai duk da dukiyarnan, bai taba koda wasa ya fidda zakkah ba, asalima mutumin ya kasance mai auri saki wanda wasu da sukasan mutuncin kansu, basu amince su bashi auren yaransu ba, masu kwadayin abun duniya kuwa, su bayar. Dukiya bata wasa ba yake cika iyayen yarinya dashi wanda yakan makantar da idanunsu su dauki 'yarsu ko tanaso ko bataso su bashi, idan yayi watannin biyar dake toh alal hakika kin taki sa'a. Da zara kin samu ciki zai soma wulakantaki. Bayan haka kuma ya kasance manemin mata na gani a fada, baya damuwa da dukkan zagin da mutane kanyi masa, kodayake dai ga wadanda sukasan asalinsa basu fiye mamakin wadannan halayya tasa ba, yo mutumin daya haik'e dukiyar marayun Allah, ya hanasu tayaya zai ga haske a rayuwa? Shine fa wanda uwarsa ta fito bainar jama'a tana kai masa duka tana tsine masa fa, ai sai fatan shiriya!. A wannan rayuwa ta bariki, ya hadu da Momi, sakamakon jan da wani abokin shiriritarsa, Alhaji Fa'iz Hamdala, yayi masa zuwa gidanta. Anan ya nemi shima ta bashi ta rage dare cikin zuk'a zuk'an yanmatan dake gidan, wadanda a haife ya haifesu, basu fi sha takwas zuwa ashirin ba, hakanan suka sanya kansu awannan gurb'atacciyar harkar. Ba musu momi ta kiraye su, suna wani kwarkwasa har dai da kansa ya zab'i Jiddah Yola, sai gashi sakamako baiyi kyau ba. Toh wannan dalilin ne ya harzuka Alhaji kwangila har yaci alwashin daukar fansa akan Hajiya Hannatu da Jiddah Yola. Tun sadda Momi ta samu wannan bak'in labarin ta rude! Ya zamana ta soma kokarin ganin ta sanya an kawar da Alhaji kwangila kafin shi d'in ya dauki matakin daya shirya a kanta. Ta dubi jidda yola rai b'ace, "Na rasa yanda akayi nayi sakaci wajen auna lafiyarki kamar yanda ya zamemin farillah. Kowace yarinya dake gidannan bana bari ta soma harka da customers dina har sai na kirayi doctor lurwan ya d'ebi jininta ya kawomin cikakkiyar shaida akan ingancin lafiyarta, yau gashi a garin wannan karamin kuskuren kin janyomin matsalar da take neman fin karfina! Yanzu menene mafita?!" Cewar momi cikin daga murya, tana duban mutanen dakin wadanda dukkansu suka amsa gayyatarta! Daman sunyi mamakin kiran gaggawar data sanar a group nasu na whatsapp ashe matsalar takai har haka? Lallai uwar barikin tasu tana cikin mugun tashin hankali. "Ai wannan ba na ganin wani abu ne na tada hankali, ita dai wacce ta janyo matsalar, ita kadai zata iya maganceta". Cewar Dalal, cikin muryarta wacce zuwa yanzu koda bata cikin maye, saika rantse a buge take. Duk suka dubeta, momy ta zauna tana duban Dalal, "Yi mana gwari gwari yanda zamu fahimta". Dalal tayi dariya kafin ta fesar da hayakin sigari, "Itace zata koma ta aikashi lahira, nasan yanzu kun fahimceni?" Jiddah Yola ta dubeta a razane "Ta yaya zan kasheshi? Harararta Dalal tayi, kafin tayi magana, Hibba ta rigata "Don ubanki ta yaya kika ci kudinsa?" Jiddah taja tsaki "Wannan kuma inaga ko sabon shiga a bariki, banajin zaiyi mata wuya, amma wannan ana magana ne na kashe rai, idan hukuma ta sani fa?" Momi itama ta jinjina kai, "Gaskiyarki jiddah, bama fatan hakan shiyasa muke kaffa kaffa don yanzu tsaro ya samu sosai, kuna sane cewa gwamnan Kano na yanzu, Dr Ahmad Bichi (a cewata,lol) baya wasa da aikinsa, anan ansha aikomin da wasika akan gwamnati na sane da abunda muke shukawa, ta bani lokaci na sallami yaran mutane, ba don akwai masu amsar cin hanci ba, da tuni mun watse..! Momi ta k'ara dubansu "Don haka, bana tsammanin kyakkyawar shawara ce wannan kuka bayar, a dai nemo wata mafitar". Wata dattijuwa wacce takai shekaru arba'in kuma tsohuwar kilaki ce, don kuwa har shege ta tab'a haifa ta jefar a bola, Hajiya Zeenat kenan. Ta tari numfashin Momi da cewa, "Haba hajiya, yau muka saba karawa da hukuma? A ganina shawarar da Dalal ta kawo shine mafita kawai, barin wannan hatsabibin mutumin a doron k'asa babbar barazana ce, sau nawa muna sanyawa a kashe rai ko a lahantar? Kin tab'a ganin tonuwar asirinmu ne? Ai duk wata hukuma tasan wacece mace! Ba dole jidda zatayi ba. Dalal ta girgiza kai, "Aa momi zeenat, babu wacce zata iya wannan aikin cikin sauki sai jidda, akwai wata dabara da zamu shirya, na tabbatar maku cewa baza'a sami matsala ba". Duk suka zuba mata ido, kafin Momi tace "Fad'i muji". Ta kalli matan dake falon, kafin ta danyi shiru cikin chanza shawara "Amma kuma momi kina da gaskiya, kisa bai zamo mafita garemu ba a wannan lokacin, ya dace dai a bawa kowa dama yaje yayi tunani nan zuwa safiyar gobe". Sukayi na'am da hakan, bayan sun jima anan ne sun tafi harkokinsu, dalal ta yiwa momi waya cewar zata zo misalin daya na dare suyi magana, ta sanar da ita abunda ta yanke. Jin haka, hibba tayi dariya kafin ta dubeta kadan "Kinsan risk din da kike shirin jefa kanki ciki kuwa? Wannan sam ba mafita mai kyau bace madam, domin wannan aikin nasu Samuel ne, sune yafi kyautuwa suyi". Dalal ta danyi shiru kafin ta dubeta "Kina ganin Samuel da yaransa ba zasu kawo cikas...". "Haba dalal, wai yau ne muka saba wannan aikin ne? Kodai kin manta ne cewar Samuel sune sukayi aikin kawar da hamshakin mai kudin nan kuma mai neman takarar gwamnan garin minna? Toh waye kwangila kuma?" Dalal ta jinjina kai cikin gaskata maganar hibba, karshe tayi na am da shawararta "Shegiya tawan, ba dai hangen nesa ba. Hibba tayi murmushi "What are friends for? Ni yanzu chanjin Manal ke damuna, anya bazata juyawa kungiya baya ba kamar yanda baby tayi?" Dalal cikin neman karin bayani ta dubeta "Me kika gani?" Hibba ta girgiza kai, "Jiya kafin na baro Abuja na biya gidanta, hakikanin gaskiya na tsorata da ganin yanda take rawar jiki akan Alhaji Ubale. Abunda ya ban mamaki, wallahi nakai minta sha biyar ina zaman jiran dawowarta sai gasu sun fito suna dariya, yana ganina ya daure fuska, kadahan kadahan muka gaisa yayi awon gaba, nan ma ta tafi rakashi sun jima kafin ta dawo. Hum, wai ce mata yayi nabar zuwa gidan, ko a waya mu dunga gaisawa! Nayi mamaki kwarai, ke nidai na sare da lamarin Manal tamkar ba itace mai zafin nan ba mara daukar raini wacce bata tankwaruwa". Dalal ta saki ashariya tana jijjiga jiki kamar zata tashi sama "Wai dagaske kikeyi? Haba no wonder idan na kirata bata fiye dauka ba ashe mu zata rainawa hankali? Lallai tayi kuskure babba, da ace ta san wahalar dake a rayuwar aure da bata biyewa Baby ba. Nikam idan har jaki zaiyi k'aho to ki tabbatar da cewa zan fita daga bariki. Ai kina gani dai ko arba'in na gwaggo (gwaggon dalal, idan baku manta part 1 ba!) ban bari anyi ba na dawo ruwa, yo inace itace ta dorani kan turbar?" Taja tsaki.! "Babu wacce ta bani mamaki kamar Baby, dubi fa yarinyar nan tana kan ganiyar holewarta da tashen naira amma tayi watsi da komai ta kama wani shirme wai aure? Toh ai shikenan suje suyi tayi, shegiya Manal, bari mu rufe wannan case din, takanas zanje har gidan nata sai naga tsohon najadun da zai yimin iyaka da k'awata. Ai cin amana ne kawai bayan sunyi aure su watsar damu, ko babu komai ai a baya sunyi abunda mukeyi har suka fimu kwarewa".   Hibbah tayi dariya "A'a toh, nima a baya ba don fa kin hanani ba da tuni nayi auren wata ukun nan, kice nima da kusan hakan ne zai kasance dani?" Dalal tayi wata yar iskar dariya "Ai ke kam da sauki, kinga yaron da kika jajub'o akwai naira, kuma yana ji da yarinta bazaiyi wuyar juyawa ba." Hibba tayi kwafa tana murmushi "Hum! Lallai Dalal kin raina HAYAT, nan da kike ganinsa yasan abunda yake. Da fari fa da naje mishi da maganar auren wani kallon zargi yayimin, wai meyasa nake sha'awar muyi aure bayan a baya na tabbatar mishi ni d'in 'yar sharholiya ce? Ke ba don dai ni d'inma tsohuwar hannu ce a bariki ba da alokacin ya tutseni, sai ga shegen harda zuwa a sanarwa iyayensa. Inda baki haneni ba ai da tuni na tsufa gidansa."    Sukayi dariya, Dalal tace "Shegiyar gari kawai, yanzu meye abun dadi a aure? Haka kawai wani k'aton gardi(wa'iyazubillah) ya ajiyeka a gida da sunan karkashin ikonsa kake, yayita juya ka kamar waina? Never, bazan tab'a yin aure ba wallahi."   Hibba tayi murmushi   "Mutum d'aya nakeji ko gobe zan iya watsar da komai na aureshi matukar zai amince da sharad'ina." Cike da mamaki Dalal ta dubeta "Wa kenan?" "Garba". Dalal ta yamutse fuska "Menene wani Garba? Kicemin Abubakar malama. Toh shi kuma wane tsamin ne? A ina kika jajib'o shi?" Hibba tayi dariya daidai lokacin da take kokarin shiga harabar hotel d'in "Tsohon saurayina ne, adalilin babana ya hanani aurensa ya sanya na shigo duniya, Baraka yar uwarsa ce yar kanwar mamansa, kuma aminiyata a baya wacce take karatunta anan B.U.K kamar yanda kika sani, ta hanyarta nake aikawa mamana sak'o. Ke kwana biyun nan ma na daina aminta mu had'u da ita, tun sadda tace min umma ta matsa akan saita kawota wajena. Garba kuma yana da mata da d'iyarsa yanzu, shi kadai ne muddin zai saki matarsa zan aureshi na watsar da komai don babu laifi yayi kud'i." Dalal ta tab'e baki kafin ta soma magana tana kokarin bude mota. "Kuna da matsala wallahi, aure aure dai kamar wani tsiyar ne cikinsa? Dallah ki bud'emin k'ofar". Hibba tana dariya ta cire mata key ta wajenta kafin ta fice daga motar. "Dalal ko bala'i?" Ta fada a fili kafin ta kashe komai ta rufe kofar tabi bayanta.               *******     Kamar yanda suka tsara d'in, wajen biyu saura suka isa gidan Momi. Tuni daman Dalal ta yiwa Samuel magana akan su had'u gidan. Ya rigasu isa ma. Samuel mutumin kudu ne, amma idan kaji yana Hausa saika rantse haifaffen arewa ne. Nan suka tsara komai, Samuel ya amince zaiyi. Bayan an kammala komai ne, Momi ta k'ara duban Samuel "Sam, ka tabbata baza'a sami matsala ba?" Yayi dariya, kafin yayi magana Dalal ta rigashi   "Haba Momi, kiyi masa fatan alheri kawai mana. Ita kuma waccan tsinanniyar da zarar komai ya kammalu ki koreta". Sukayi na'am da hakan.               ********   TASHIN HANKALI!!!! Dalal tana kwance saman gado tayi rigingine tana chatting, wayarta tayi k'ara, ganin sunan Momi ne, yasa ta mik'e zaune tana murmushin sanin kanun zancen bai wuce su Samuel sun cika aiki ba. Saidai tana dauka ta jiyo hayaniya, cikin fusata Momi ke cewa "Dalal gashi komai ya b'aci, an samu matsala, Sam da wasu cikin yaransa suna hannun yan sanda!" Dalal batasan sadda tayi wata wawuyar mikewa ba, cikinta ya bada wani irin sauti saboda tsananin rud'un da ta shiga. Saidai sanin halin momin tasu da barkwanci yasa kuma ta karyata a farko, bayan ta numfasa tace "Momi yau ma wasan ne?" "Wane wasa anan inayi maki zancen gaskiya? Ni yanzu dole nabar garin nan domin ko inspector yakubu dana buga masa cemin yayi babu ta yanda zai iya sanya baki domin kuwa hannun wanda su Samuel suka fad'a baisan wani maganar cin hanci ba ballantana muyi tunanin bayarwa. Kuma ga maganar kashe Alhaji Kwangila ta bazu don akwai wadanda suka bada shaidar ganin fitarsu Samuel daga gidan, ke bazan iya dogon bayanin nan ba yanzu, nasan kowane lokaci zamu iya ganin dirar yan sanda a gidannan." Daga haka Momi ta katse kiran, cikin tsananin tashin hankali Dalal ta jefa wayarta kan gado kafin ta janyo akwatinta ta hau jefa kayan sawarta a ciki, ai idan asiri ya tonu zata fi Momi matsala tunda da shawararta ne aka aikata kisan. Daidai lokacin hibba ta fito daga bandaki cikin tashin hankali saboda tana sauraron wayar da Dalal tayi da Momi, wuyanta duk kumfa ta dubeta "Me naji kuna fad'a keda Momi?" Dalal cikin rud'ewa ta sanar da ita komai, ta k'ara da cewa "Ina! bazan k'ara kwana garin nan ba, dole mubar garinnan." Sai lokacin ma Hibba ta lura da akwatin da take lodawa kaya,ita kanta ta rud'e, toh me zata zauna tayi itama bayan da tasan an jima ana son cafkesu yanzu kuwa da dama ta samu mezai hani hakan yiwuwa? Ai itama batayi wata wata ba ta soma shiri.                ******    Gudu takeyi kamar zata tashi sama, kallo daya zai tabbatar maka ba cikin hayyacinta take ba. Hibba wacce zafi biyu ya had'e mata, na tunanin makomarsu dana tashin hankali da tsoron irin gudun da Dalal keyi wanda ya tabbatar mata saida Dalal ta hadiyi kwayoyin data saba kafin ta kama sitiyarin. Ganin da wannan gudun nata dakyar ya kaisu Abuja lafiya yasa ta dubeta "Dalal ki tsayar da motar ki bani na tuk'amu, wannan gudun naki na ganganci ne yayi over." Dalal ta kundumo ashariya ta k'ara da cewa "Yar tasha tsinanniya, idan bazaki bini ba ki sauka daga motar nan banson iskanci." Wani kuuu da Hibba taji ne yasa ta yin k'ara gami da toshe kunnuwanta, wai ashe babbar mota ce suka kusan gogar juna Dalal ta goce. Ai da k'arfi tace "Tsaya!! Ki tsaya!!! Wallahi zan sauka, idan banyi kwanan cell ba zanyi na kabari indai da irin wannan tuk'in zamu cigaba da tafi.." Kafin ma ta k'arasa Dalal taja burki ta tsaya, hibba tasa hannu saman kujerar baya ta janyo akwatinta sannan ta dauki jakar hannunta ta bude kofar ta fita bayan ta dubi Dalal tace "Allah Ya tsare toh." Daga haka ta sauka don ma inda Allah Ya taimaketa sun kusa Zaria. Dakyar ta samu motar hawa, nan dinma sai a gidan gaba kusa da wani matashi ta zauna. Suna tafiya saidai tana lura da mayen kallon da yakeyi mata, hakan kuma yana da alak'a da dan iskan shigar dake jikinta wanda a garin sauri ko bireziya bata saka ba ga wasu English wears da suka d'ame jikinta abun dai abun tirr! Har wani gwauron numfashi yaja. "Idan har ka aikata abunda muka sanyaka, lallai zaka samu abunda kakeso komin girmansa a duniyar nan." Wadannan kalaman shugaban kungiyar nasu ne na mafia. Ya k'ara satar kallon Hibba, ransa yayi mugun kwadaituwa da ita bayan haka kuma ga tsananin buk'atarsa na ganin cikar burinsa na son zama hamshak'in mai kud'i.   "Ka kawo dukiyar fulanin mace guda d'aya tak na b'arin hagu kuma bana matacciya ba, babu abunda bazaka samu ba idan ka cika umarnin kungiya."   Ya k'ara tunano wasu cikin zantukan shugabansu. Hakan yasa shi samun karfin gwuiwa musamman da aka taki sa'a ya lura cikin yanayin firgici take. "Sannu ko?"   Ya fada yana dubanta, ta dubeshi, kallo daya zaka yiwa fuskarta kasan cewa tabbas bata cikin nutsuwarta. Dauke kanta tayi bata amsa mishi ba. Baiyi zuciya ba yayita gwada sa'a cikin dabarunsa na kwararren dan iska kuma tsohon hannu har saida ta sanar dashi cewar tana tattare da damuwa ne. Ya nuna tausayinta ya tambayi wajen wanda zataje a Kd, tace bata da kowa, niyyarta daga can tayi Abuja ta kama d'aki a hotel. Ya girgiza kai "Idan babu damuwa mezai hana ki tsaya anan kd, tunda ni inada gida kinga you will be safe akan dai kije wani wurin." Ta dubeshi ya sakar mata murmushi, ta sauke ajiyar zuciya ta maida kanta ga titi "Shikenan, nagode." Yayi wani mugun murmushi yana mai hamdala a ransa.   Hakan kuwa akayi, suna isa Kaduna ya biya kudin motarta kafin ya samar musu abin hawa har zuwa dan flathouse din da yake zaman haya.    Hibba na tsaye tana k'arewa karamin falon kallo ya shigo, ta dubeshi sukayi murmushi    "Sannu fa, nasan kin gaji ya dace ki d'anyi wanka ko?" Ta girgiza mishi kai "No bani da damuwa, saidai zan kama ruwa, ina toilet din?" Ya dauki akwatin kayanta yana murmushi    "Biyoni."   Ba musu tabi bayansa batare da fargabar komai ba.               ******* INA LABARIN SU MOMI??? Ance rana dubu ta b'arawo, rana d'aya ta mai kaya. Kwarai na yarda da wannan zancen domin kuwa wannan karon lamura sun kwab'ewa Momi da kungiyarta fiye da tsammanin mutum. Duk yanda taso ta b'ullowa al'amarin ta kasa a karshe suna shirin tattara yanasu yanasu sukaji dirin motoci. Hanjin cikinsu ya kad'a, babu hanyar tserewa domin kuwa yan sandan nan zagaye gidan sukayi, hakanan aka titsa k'eyarsa da duka da mari aka wurwurgasu cikin mota sai police station.   Haka aka titsa Momi da tambayoyi bayan an nuna mata Samuel, Inspector Bashir ya dubeta    "Kinsan wannan?"   Cikin rawar jiki ta dubi Samuel wanda duk fuskarsa ta chanja da ga jini ga kuma kumburi. "Kinmin shiru!!" Ya fada cikin tsawa yana buga tebur wanda saida duka sauran matan barikin suka tsorata. "Oga tasann..." "Shut up!!" Ya katse Samuel daya tsoma bakinsa, da sauri Samuel yayi tsit babu shiri. Inspector Bashir ya k'ara cewa "Idan ka k'ara sanyamin baki a aikina sai na fasa bakinka." "Sorry Sir."   Ya maida dubansa ga Momi dake kuka cike da tsoro    "Hannatu ki bamu hadin kai, idan kuwa kikace zakiyi mana wasa da lokacinmu lallai ki sani zamuyi wasa dake kema. Domin jina jina zamuyi maki. Ki bani amsoshina sai komai yazo da sauki."   Ya gyara zama kafin ya cigaba    "Ki bani amsar tambayata ta farko, kinsan wannan mutumin?"    Momi wacce kukanta ya tsagaitu, ta dubi Samuel tana muzurai kafin ta girgiza kanta ta dubi inspector    "Ni bansanshi ba, yau na soma ganinsa ma."   Samuel ya bude baki zaiyi magana, Inspector Bashir ya dagamishi hannu, ya dubi Momi yayi murmushi kafin ya dubi sajan isa "Kana iya mik'omin wayoyin nan."   Sajan ya sarawa ogansa sannan ya juya ya nufi 'yar kwabarsu ta ajiye evidence. Wayar Momi ya dauko data Samuel ya kawowa Inspector. Inspector ya kunnasu kafin ya mik'awa Momi nata    "Fiddamin password din." Hannunta yana rawa, ta karb'a, wani irin gumi ke tsatstsafo mata, ga wani fitsari da takeji. Ayau tana mai dana sanin rashin goge sak'onni da logs da batayi. Aikam asirinta ya gama tonuwa. Dakyar ta bude sakamakon tsoron shan kulkin da takeyi. Ta mik'a masa. B'angaren sak'onni ya soma shiga, domin son ganin ko itace Samuel ya aika sak'o yake shaida mata ya cika aiki. Ai kuwa shine sak'o na biyun k'arshe daya shigo wayarta, na karshen kuma shaida mata yakeyi an samu matsala. Sai kuma b'angaren kira daya iske lambobi uku da tayi waya dasu tsakanin lokacin da abun ya faru da yanzu. Daya da ma'aikacin da ya bashi mamaki ne, inspector yakubu? Menene had'insa da wannan kilakin? Dayan kuma wata ce wai ita Dalal sai lambar k'arshe na Samuel wanda sune suka sanyashi yayi kira don ya bugar musu cikinta don son sanin inda take, sai akaci sa'a ma bata bar gidannata ba.    Tabe bak'i yayi, kafin yayi mugun murmushi ya dubi Momi   "Ummmm! I see, ashe akwai masu daure maki gindi ki aikata son rai a garin nan?"   Ya gyara kai, kafin ya bud'e sak'onnin ya mik'a mata wayar   "Dukkan wani tabbaci mun samesu akan lallai kinsan wanene Samuel kamar kuma yanda kike da hannu a kisan Alhaji Kwangila. Don haka babu wani b'oye b'oye, ki bani labarin yanda akayi kuka kashe Alhaji Kwangila, da kuma dalilinku."   Ganin da tayi fuskarsa a daure, yasa ta nutsuwar da babu shiri, tiryan tiryan ta labarta mishi komai, sai lokacin sauran matan kungiyar suka san komai domin kuwa basu da labarin hakan, banda Allah Ya isa babu abunda sukeyi. Ya dakatar dasu ta hanyar tsawatarwa, ya maida dubansa ga Momi    "Yanzu ina ita Jidda Yolar? Ina kuma wacce kika ambata da Dalal?"   Ta hau rarraba ido cikin matan wajen, kafin ta nuno Jidda wacce ke rusa ihun kuka, ya jinjina kai yace   "Dalal fa?"   Momi ya girgiza kanta   "Tun bayan da mukayi waya na sanar da ita halin da ake ciki ban k'ara ganinta ba."   Inspector Bashir ya mike bayan ya bada umarnin a maidasu cell a rufe har zuwa lokacin da zasu mik'a case kotu, kafin ya bawa yaransa umarnin nemo Dalal aduk inda take. Daga haka ya dauki sanda da hularsa yayi ofis dinsa bayan ya tafi da wayoyin Samuel da Momi... .! Acan kuwa, Hibba ce, tuni ta kammala kimtsawa ta zauna tana mai kunna TV saboda rashin ganin wannan matashin, saidai ba kallon takeyi ba. Tana zaune shiru tana tunanin abunda zai biyo baya, yanzu ko ina Dalal take? Allah Sarki, yanzu Momi tana wane halin? Taji tanason sanin halin da Dalal ke ciki, hakan ya sanyata mikewa da zummar shiga d'aki ta dauko wayarta taji an turo kofar an shigo. Ido suka hada ta sakarmai murmushi. Ya maida mata martani, hannunsa rike da leda irinta take away. Ya karasa shigowa yaja kofar ya rufe    "Sannu fa, kinjini shiru ko? Na samo maki abinci ne naga kamar kina tare da yunwa."    Taji dadi kwarai domin kuwa lokacin da suka baro otel, karfe sha daya na safe, kuma babu wanda yayi kari cikinsu.   "Nagode fa." Nan ya ajiye ya shiga kicin ya wanko musu faranti da cokula biyu ya kawo musu kafin kuma ya juye musu suyi zaman  dirshan su soma ci. Anan ne yake shaida mata  sunansa, Zakari (saidai fa asalin sunansa, Na'im). Ya sanar da ita karatu yakeyi anan jami'at kd, iyayensa suna Kano ne. Bata kawo komai ba itama ta sanar mishi sunanta. Haka dai suna hira da dariya har dai ya bijiro mata da bukatarsa, baiyi mamakin yanda ta soma bayar da kai ba bori ya hau. Nan dai lamura suka gudana, abin tirr har ya b'aci don yawaitar da yayi. A karshe ya zauna saman gadon yana mai tuntsirewa da dariya na rashin imani. Hibba tun tana murmushi har dai ta tsaya cak tana dubansa    "Wai lafiyarka kuwa Zakari? Ina fatan dai kwalliya ta biya kudin sabulu?"   Ta fada tana murmushi hadi da k'ara gyara zaman bargon dake rufe da kirjinta tana dubansa. Sai lokacin ya tsagaita da dariyarsa ya dubeta    "Kwarai ma kuwa, ina zuwa."   Ya mike ya zura suturarsa kafin ya fice daga d'akin. Ta muskuta tana sakin hamma, lokacin Magriba ta kawo kai, abun kunya babu azhar balle ayi batun la'asar koda dai asubahin ma bata samu shiga ba. Lumshe ido ta d'anyi, taji shigowarsa saidai bata bud'esu ba, bata ankara ba taji mutum ya danneta. Tana dariya ta dago idanunta, saidai ta tsorata ainun ganin yanayin fuskar tasa babu digon imani, ga wani sharb'eb'iyar wuk'a a hannunsa, ya d'ora wani jan abu a goshinsa. Hannunsa daya dake dunk'ule ya bud'e, zatayi magana tana zillo, amma tuni ya watsa mata wannan abun mai kama da hoda a fuska, nan take ta sume.                  ******    TASLEEM FA??? Tsaye yake gaban madubi yana afkin gyara zaman hularsa,lokacin karfe goma na safe yayi shirin fita zuwa wajen aikinsa. Satar kallonta yayi ganin yanda take kumbure kumbure tana wani mustsika ido kamar mai kuka. Murmushi ya saki gami da soma rera wak'a    "Iye yaraye a,a iye yaraye muyi soyayya,bari kijini tasleem,ayau dake nakeyi,soyayya,don yau fa ke nakeso...muje Abuja,can can muje Abuja muyi soyayya."   Batasan sadda ta kyalkyale da dariya ba shima yana tayata,ya ajiye kwalbar turaren dake hannunsa ya juyo,yana mai nufota. Ta harareshi cikin wasa tana mai marairaice fuska,bai fasa rik'ota ba. Har saida ya dangana goshinsu wuri guda     "Hey Queen,fushin na menene haka?"   Ta janye fuskarta ta zauna gefen gadon cikin shagwab'abb'iyar murya tana wani bubbuga kafafunta tace     "To ba kaine ka k'i yarda naje shopping ba,shikenan ni nidai koyaushe ina k'ulle a gida,kullum kaida kanwata ku tafi ku kyaleni,nidai...."    Ta hau kukan kissa,da azama ya riko fuskarta yana kasheta da wadannan mayataccen so na musamman kuma nata ita d'aya    "Menene abin kukan? Kinaso ne na rasa kwanciyar hankalina? Toh wai ma menene zaki sayo?"    Nan take ta saki fuska,saidai bata da niyyar sanar dashi sakamakon surprise da take shirin yi mishi. Ta muskuta tana kallonsa ta gefen ido kafin ta rausaya kanta ta mak'ala kafad'a d'aya   "Um um,bazakaji ba,idan na siyo na kawo zaka gani ai."    Ya daga kafad'a kadan gami sannan dai ya tab'e baki kamar yanda ya zamto masa jiki     "Ok,saikin dawo kenan,kuma ban baki iznin zuwa ko'ina ba daga can,gida straight."     Ya k'arashe yana kokarin mikewa,ta saki ihu tana mai mak'alo wuyansa tana dariya    "Woo!! That is my king! Love you so much." Mintsili ya kaiwa fatar cikinta,karamin ihu ta sanya babu shiri ta sakeshi tana mai sosa wajen. Yana shafa wuyansa ya dubeta    "Kijimin mace zata karyamin wuya?"   Ya dauki hularsa da agogonsa yayi gaba   "A fito a bani breakfast."   Ta mike tana mai turo baki har lokacin bata bar susar wajen ba,ita kam wani sa'in har mamakin Haris takeyi,idan yaso akwai matsanancin iya sarrafa mace da kula da ita,idan kuwa dan kananun muguntar tasa suka motsa toh fa sai a hankali.      Har ya kammala tayo mishi rakiya bata sakarmishi fuska ba. Bayan yayi sallama da Zahra,ya samu Tasleem na kokarin  ajiye jakarsa a k'asa ta shige ciki abinta.     Da azama ya rik'ota yana janyota   "Wai fushin na menene?" Tayi shiru,saida yayi gyaran murya ya dubeta    "Zan maki wak'a fa?"   Dariya ta sub'uce mata tunanowa da tayi da wak'ar d'azu wanda tasan ba haka akayita ba. Murmushin shima yayi    "King ya akayi ka iya wak'a har haka? Alhalin naga kallo bai dameka ba."    Harara ya jefo mata "Aka fadamaki bansan me duniya ke ciki ba? Bar ganina haka fa,nima a baya ko? Hum um,saina dawo."    Dariya sosai takeyi har ta juya zuwa ciki,Haris badai iya bada dariya ba,ita kam bata tab'a kwana da fushinsa ba. Ya iya tarairayar matansa kwarai.                 *******      Misalin uku da rabi na rana ta fice sanin da tayi ranar alhamis ce maigidan yana azumi kuma shi da dawowa sai magrib kuma ba aikinta bane.   Shoprite ta nufa kai tsaye anan kan titin Zoo road. Tayi fakin ta fito cikin shigarta ta kamala,wato riga doguwa ta abaya da karamin hijabi iyaka kirji. Babu ko hoda a fuskarta hakanan ta sanya safar k'afa.     Ta rufe motar ta shiga, bayan ta kammala ta fito da zummar nufar motarta. Kamar daga sama taji ana kiran tsohon sunanta    "Baby! Baby!!"   Sanin da tayi ba ita kadai aka tab'ayi mai sunan ba yasa bata juya ba saidai gabanta yana bugawa da sauri ba tare da tasan dalilin ba. Taji ansha gabanta,ta dago kanta a fusace,saidai ta sassauta kadan ganin wanda ta sani ne,fuska a daure ta bude baki zatayi magana,saidai kafin takai ga cewa komai ya tareta     "Assalamu alaikum."   Dole ta amsa mishi,ya numfasa da murmushi dauke saman fuskarsa    "Baby aure babu ki gayyata? Ai ki gode Allah domin kuwa yanzu yan kungiyarki sun tarwatse. Ke kam Allah Ya kwaceki. Momi da yaranta suna kaso."   Tunda ya soma maganar bata saki fuska ba saima kokari da takeyi ta bude motarta, jin abunda yace yasa taji faduwar gaba, ta dubeshu babu shiri    "Menene ya faru haka dasu? Ina Hibba da Dalal? Manal fa?"   Ya matso yana mai jingina bayansa jikin motarta idanunsa suna kanta,yayi 'yar dariyar da batasan manufarta ba. Nan ya labarta mata komai,ya kara da cewa   "A yanzu haka an samu Dalal,bayan da tayi hatsari a babban titin Abuja,ita kuwa Hibba,bani da labarin inda take. Manal itama tayi aure abinta."   Hawaye suka kwaranyowa Tasleem,banda innalillahi babu abunda takeyi,ta dubi BAABA(idan kun mantashi,ku duba yar bariki part1,tsakanin 1-10).    "Kana da lambar Manal?"   Ya gyara tsayuwa   "Wallahi babu,saidai ta Hibba."   Ta girgiza kanta tana share ruwan hawaye    "Barshi kawai,nagode,sai anjima."    Daga haka ta shige motar bayan data jefa ledojin kayan siyayyarta a back seat. Ya bata wuri,taja motarta tana tafe tana hawaye ainun. Kaico rayuwa,me kenan haka? Nadama da tsantsar imani ya k'ara shigarta. Yanzu menene amfanin Bariki? Wace riba take kawowa masu yinta?                 **** A can kuwa bayan tabar mall din,wani ya iso wajen Baaba,ya nunamishi camera ta wayar hannunsa,hotunan sunyi kyau sun fito yanda sukeso. Baaba yayi dariya ya shafi kumatunsa      "Mari?!!" Ya fada kafin ya girgiza kai.   "Ni yarinyar nan ta tab'a saka hannu ta mara ko? Lallai yau rana ce ta Daukar Fansa!" Ya karashe cikin daure fuska tamau yana mai tunano sadda ta daga hannu ta mareshi agaban gayu.    "Tura mishi,idan ka aika kayi blocking dinsa sannan ka cire simcard din ka karyashi."   Daga haka ya debo kudade masu dama ya bawa saurayin   "Gashi,zan ciko maka ragowar kudinka dubuhm hamisin gobe.."    Daga haka suka rabu.... !!       BAYAN SATI BIYU   Kwance take tayi rigingine saman resting chair dake nan barandar shan iskarta na kofar kicin ta waje. Ta lula cikin tunani mai tsananin gaske,har batasan hawayenta suna zuba ba. Gaba daya ta rame,fuskar nan ta jeme babu ko kwalli,rabonta da kwalliyar ma ta mance. Kallo daya zakayi mata ka fahimci lallai tana cikin damuwa matsananci. Abinci kuwa bata wani cin kirki. Gaba daya Tasleem ta hargitse kai bakace wannan yarinyar bace sarkin gayu da kwalliya. Wasu hawayen suka k'ara kwaranyo mata    "Kin cuceni! Ashe zaki iya cin amanar aure har haka?! Ashe daman bazaki tab'a shiryuwa ba?! Ki gayamin da wa da wa kika kula bayan shi?!! Dame na rageki ne Tasleem! Menene banayi maki? Menene bana baki? Ki gayamin!!"    Cikin tsawa ya k'arashe maganar,hakan yasa taji kamar lokacin yakeyi mata zancen,har saida ta razana. Muskutawa tayi akan kujerar gami da kurawa jemagun dake shawagi a sararin samaniya ido,Baaba ya cuceta,ya wargaza mata farincikinta har na tsawon kwanaki goma sha hud'u. Wai itace Haris baison had'a shimfid'a da ita? Itace yake guduwa falo ya barta a daki? Tun Zahra bata fahimci komai ba har tazo gashi ta fahimta. Saidai koda taso yin maganar Haris ya tsawatar mata da cewar ta kula da nata igiyar babu abunda ya shafeta da fad'ansu. Tun daga ranar ta kama bakinta saidai ko kusa batajin dadin yanayin da antin nata ke ciki. Har ma akwai sadda ta isketa tana kuka itama ta fashe da kukan tace zata sanarwa Umma domin ta tsawatar mishi tunda ita dai batasan laifin da Tasleem din ta aikata ba,Tasleem ta haneta,tace idan ta fadawa wani bata yafe mata ba,kawai dai ta taimaka mata da addu'a kuma tabar damun kanta akan matsalar da ba ita ya shafa ba taji da lafiyar yaron cikinta.(Kasancewar ciki ne da Zahrar)      Saidai har zuwa yanzun ta daina samun sukuni da walwalar zuciyarta,ta riga ta saba da Haris,suyi wasa da dariya abinsu,ya sanyata kuka ta sanyashi fushi su shirya kansu,saidai na yanzu ya tsananta,ko girki idan tayi a banza,bazai ko kalleshi ba. Hakanan da rana in har ita zatayi abinci bazai dawo bama ballantana yaci,ganin hakan ne yasa ta cewa Zahra kowa ya dunga cin na ranar ma da mijin. A zatonta hakan zaisa ya sauko yace bai amince da tsarin raba kwano da rana ba amma saima ta lura ko ajikinsa. Ta gaji fa! Sati biyu ba kwana biyu bane! Wannan wane kalar zargi ne? Daga ganin hotuna a wayarsa shikenan sai yayi musu mummunan zargi? Bata mancewa ta fita tayo mishi siyayyar ban mamaki domin ranar birthday dinsa ne,hakanan data dawo taci kwalliyarta tsaf,tana jin tsayuwar motarsa ta kuma san zai leko su gaisa kafin ya haye sama,da azama ta kashe fitilunta,ta bude kofar ta b'uya,saidai me? Yana shigowa taji cikin tsawa tsawa yana kiranta. Da azama ta kunna fitila cikin firgici,saida ya karewa shigarta kallo na kananun kaya kafin ya dubeta da jajayen idanunsa ya dago mata wayarsa. Anan ne akayi rikitatar har takai ga ya kwad'a mata mari,yayi gaba bayan ya furta mata tsauraran kalamai. Tun daga ranar komai ya chanja.                *****     Tasleem ta ja majina kafin ta mike zaune duk jikinta ya dauki zafi,ga matsanancin ciwon kai wanda koyaushe dashi take kwana take tashi. Dakyar ta daure ta mike tana dafe bango sakamakon jirin dake kwasarta domin zuwa duba girkinta,saidai kuma tana zuwa cikin kicin din wani mugun jiri ya kwasheta,idanunta sukayita ganin komai biyu biyu,kafin duhu ya mamayesu ta zube ta gaba,goshinta ya bugu da teburin kicin kafin ta k'arasa kaiwa k'asa....!    Takai mintuna goma cikin wannan halin,girkinta ya k'one k'urmus har hayaki ya cika kicin din yana fita,yayi daidai da dawowar Haris. Kasancewar rumfar da yake parking motarsa, tana nan koda mutum ya fito daga kicin din Tasleem za'a iya hangoshi matukar anzo daidai wajen. Ga mamakinsa yaga hayaki yana fitowa,gabansa yaji ya fadi.     "Me takeyi haka?"   Ya tambayi kansa,jikinsa ya bashi babu lafiya,hakan yasa ya fito da sauri,gudu gudu zuwa kicin din,gabansa yayi mugun faduwa ganin ba'a hangen komai. Abdulaziz direba,da baba maigadi wadanda ya zame musu al'ada,matukar ogansu ya dawo sai sun biyoshi sun mishi sannu da zuwa. Ganin hayaki yasa suka gane babu lafiya. Haris ya hau salati,yayita lalube har ya gano inda matsalar take,saidai yana sanya hannu wani azabar zafi ya ziyarceshi. Yayi kara,tuni baba maigadi ya taho da tsumma saidai bai iya murdewa ba,Abdulaziz ya amsa,bayan da Harris zaiyi ne,yayi tuntub'e da mutum. Yana tari ainun haka ya duk'a yana lalube,dakyar idanunsa suka hango masa ita.    "Tasleem!!!" Yayi maganar cikin karfi,tuni ya sunkuceta,a guje yayo waje, abdulaziz da baba maigadi suka biyoshi a baya. Masu gadin makwafta har sun shigo gano hayakin da sukayi ta waje  suna tambayar lafiya? Abdulaziz ne ya koma da azama ya murde gas cylinder din. Tuni Haris ya sanyata a mota ya shiga,cikin tsabar kidima ya kasa sanya key dinma. Dole mutane sukace yayi hakuri Abdulaziz ya jasu,ya fito ya koma wajen matarsa yana mai rike hannuwanta gam,a haka har suka fice zuwa asibitin...! Da taimakon Allah ta farfado. Tayi mamaki kwarai na ganinta a asibiti. Babu kowa a dakin,dakyar ta d'aga nauyayyun idanunta ta dubi drip din da aka d'ora mata. Ta sauke idanunta yayin data tunano iyakar abunda ta sani. Hawayenta suka zubo,turo kofar da akayi yasa ta dubi mai shigowar. Kallo daya tayi mishi ta kauda kanta gefe. Ya daure ya karaso ya zauna gefenta,hannu yasa ya tab'a goshinta. Lumshe ido tayi hawayenta suka zubo,rabon da jikinsu ya gogu da juna tun kafin faruwar lamarin,shi kansa saida yaji wani shock wanda kuma ya tabbatar mishi lallai yayi kewarta bata wasa ba. Yayi azamar janye hannunsa,yayi hamdala a ransa jin da yayi zazzab'in ya sauka.      "Sannu,bari na kira Doctor."    Ya mike ya juya, takai hannu da zummar tsayar dashi,saidai kuma ta fasa. Hawayenta suka k'aru,ina Haris zai fahimci shine matsalarta? Inama zai gane shine warakarta? Bata da wani fata da burin daya wuce na su dawo daidai,su cigaba da rayuwarsu cikin kwanciyar hankali da soyayya. Haris meyasa ya kasa gane cewar bazasu iya rayuwa babu juna ba? Meyasa yake kokarin k'irk'iro musu wani sabon yanayi wanda zukatansu da gangar jikinsu bazasu jura ba? Wai ta yaya za'ayi ma su iya wannan rayuwar?     Shigowarsu ta katse tunaninta,ta share hawayen fuskarta ta kauda kai. Ya lura da ita, ji yakeyi tamkar yaje ya rungumeta ya rarrasheta,saidai kuma da zarar ya tunano hotunan nan sai komai ya kauce.(Mtsw,sai kace wanda ya ga wani banzan abun a hoton.)    Likita ya tabbatar da samun saukinta saidai kuma yace dole a dinga bari tana hutawa don yawan damuwar da take ciki yasa jininta ya hau,kamar kuma yanda doctor yace yanajin ba wannan ne karo na farko data kamu da ciwon ba result ya nunamusu daman tana dashi. Ya kara duban Haris bayan sun fito yace    "Madam dinka tana da damuwa kwarai,gaskiya ya dace ka kula da lafiyarta kasan menene damuwarta kayi kokarin magance mata."   Haris yayi godiya. Zahra daga makaranta nan ta zarto tare da Hibba. Sun samu tana bacci,suna zuwa Haris ya tafi gida. Jimawa kadan sai gasu Mami da Umma harma da Daddy da Abba.     Sun dan jima,har suna ta'ajibin irin ramar da tayi,duk ta k'are. Alhaji Aliyu wanda Hankalinsa ya gaza kwanciya ya dubi Haris wanda tuni ya dawo harda guzurin kayan ciye ciye da sha,yace     "Wai daman ta jima tana ciwo ne?"    Haris ya sunkuyar da kansa   "Eh,ta kwana biyu saidai baiyi wannan tsananin har haka ba sai yau. Nan ma kicin muka sameta kamar dai yanda na shaida maku."   Kallonsa tasleem tayi cikin jin bakin ciki,harma yana da bakin had'a zance haka? Alhaji yace "Subhanallah,toh Allah Ya bata lafiya."   Basu jima sosai ba,anti arya da juwairiyya suka shigo suma. Akarshe dai,Juwairiyya tace zata kwana,Haris yace sam, a barshi zai iya. Haka dai Abba yace a kyaleshi shi da matarsa.     Babu wata mu'amalar arziki data kasance tsakaninsu a daren. Yana kwance saman kafet tana saman gado,duk da fitila a kashe take,tana hangen fuskarsa sakamakon hasken farin watan daya hasko ta labulen dakin. Kwarai ba bacci yakeyi ba,ya kurawa silin ido kawai ne cikin tunanin da batasan ko na menene ba. Muskutawa tayi ta juya mishi baya a hankali kuma ta soma gyangyadi bacci ya sureta.     Washegari saida yamma aka sallamesu. Ita kam ji tayi kamar kada ta koma. Babu dai yanda ta iya,don batason surukanta su fahimci komai. Abbanta ma yazo,hakanan sunyi waya da Yasmeen sun kuma gaisa da Kb duk ta wayar Haris din don yanzu komai ya wuce tsakaninta da KB.      Kwana biyar da yin hakan ne,Haris na zaune cikin ofis dinsa cikin tsananin damuwa da tunanin matarsa yaji an kwankwasa kofa. Yayi umarnin a shigo,sakatariyarsa ce,ya sanar dashi yayi bak'o. Haris ya dubeta     "Please Linda,ki bashi hakuri,banajin zan iya saurarar kowa yanzu,kice ya dawo gobe."    Ta fita bayan ta amsa a ladabce,can sai gata ta dawo. Ya dubeta fuska daure,dakyar ta had'a haruffa    "Sorry Sir, yace ne maganar nada muhimmanci kuma idan ka bari ya tafi bazaka k'ara ganinsa ba."    Haris ya dubeta na 'yan sakanni kafin ya jinjina kai    "Kice ya shigo."       Minti daya da fitar Linda, wani matashi yayi sallama cikin ofishin. Haris yayi tsai yana dubansa,kamar dai yasan wannan fuskar saidai kuma ya mance a inda ya santa. Matashin ya mik'awa Haris hannu yana mai yin sallama gareshi. Haris ya mik'a mishi sukayi musabaha sannan ya zauna.    "Nasan baka sanni ba ko?"    Haris ya gyada kansa    "Hakane,saidai kamar ba yau ne farkon ganina da fuskarnan ba. Kamar dai na sanka acan Badawa."     Matashin yayi dariya kadan     "Tabbas hakane,nidai sunana Hamza,dan nijar ne ni saidai ina aikin wanki da guga anan gidan dake makwaftaka da naka, gidan Alhaji Rabi'u Hassan."    Haris ya saki fuska kadan     "Ok,na gane gidan,lafiya dai ko?"     Yayi tambayar cikin mamaki. Hamza ya numfasa      "Lafiya yallab'ai,saidai nazo maka da wani batu ne wanda tun sadda na aikata yake damuna kuma ya hanani sukuni,yanzu haka anjima kadan motarmu zata tashi zuwa nijar domin ziyarar yan uwa. Banaso na tafi ban nemi gafararka ba Yallabai."   Haris jin wannan batu ya k'ara gyara zama yana mai duban Hamza     "Fadamin kai tsaye,meka aikata gareni mai girma haka alhalin ma ba wata sanayya ko alak'a data shiga tsakaninmu?"   Hamza ya sadda kai ya soma magana    "Hakane,ina mai bakin cikin sanar maka cewar harda sanya hannuna a shiryawa matarka tuggu bayan daukar kusan sati biyu da mukayi muna neman hanyar hakan."   Haris fuskarsa ta sauya,cikin kausashshiyar murya yace     "Kayimin bayani dalla dalla yanda zan fahimta."    "A wataranar Talata ne,ina zaune bakin kofar gidan Alhaji ni d'aya,farko tare muke zaune da dan jummai maigadin alhaji sai ya tashi domin ya zagaya. Anan ne kuma sai ga wani matashin saurayi saman mashin yazo ya faka,bayan ya karewa area din kallo ya sauko saman mashin dinsa saida ya fiddo karan sigari ya kunna ya soma zuk'a kafin ya karaso gareni. Mukayi musabaha,kafin ya tambayeni     "Don Allah malam tambaya nakeyi?"    Na dubeshi kafin na bashi amsa    "Na'am,ina sauraronka."    "Gidan Haris Aliyu Kazaure nake nema."    Kamar yanda mukasan mafi akasarin mazauna wannan area din da kuma zaman hira da mukeyi wataran da ma'aikatan wajen ya sanya nasanka,ina dariya nace mishi    "Toh ai ga gidan nan kazo,wannan mai kallonka."    Na nunamishi da yatsa,ya daga kai ya kalla kafin yayi murmushi ya zauna gefena.    "Nagode abokina,idan babu damuwa akwai wani d'an karamin aikin da nakeso na sanyaka."   Kafin nayi magana ya zura hannu aljihun wandonsa ya fiddomin da bandir na kudi sabbi yan hamsin hamsin,ya sanyamin a tafin hannuna. Gaba daya na rude ganin wannan makudan kudaden,tunda nidai kam Allah Ya yoni da son kudi na kata'i,na dubeshi kafin na dubi hanya, unguwar shiru ba mutane,hakanan nasan Dan jummai bai isa ace ya fito daga bahaya yanzu ba,wannan yasa na dubeshi da sauri     "Kai kuwa abokina wane irin aiki ne zan maka?"     Yayi murmushi ya fesar da hayakin daya zuk'a kafin ya dubeni    "Kada ka damu,ba wani mai chaza kwakwalwa bane " Yasa hannu a aljihu ya fiddo wayarsa,saida yayi danne dannensa kafin ya mikomin    "Kasan wannan?" Na amshi wayar na kurawa hoton ido,nayi mamaki kwarai ganin hoton matarka kuma cikin kananun shiga bawai don ina k'are mata kallo bane don wata manufa daban,a'a saidai don kawai idan kun fito cikin mota nakan hangeta. Saida na kammala kallon kafin na mikamishi wayar ina gyada kaina      "Kwarai,na santa, matar Alhaji Haris din dai daka ambata a baya ne,mai wannan gidan "(Nayi nuni da gidan.)    Yayi murmushi    "So nakeyi ka samomin lambar mijinta inda hali duka numbers din nasa,na biyu kuma ka dunga sanarmin kowane shige da ficenta,duk sadda ta fita ka sanarmin ta waya."    Na dubeshi tsam,kafin nace     "Bangane ba. Me hakan zai amfaneka dashi?"    Yayi murmushi   "Sanya kudin nan a aljihu tukunna,banaso mutane su gane wani abu."    Nabi umarninsa kafin kuma ya warwaremin komai. Banyi wani ja inja ba na amince don na gode Allah ba kisan kai zai sakani ba.    Banci wuyar samun lambobinka ba wajen ma'aikatanka ba,nayita fakon Hajiya,da zarar ta fita zan sanarwa Manu,kamar yanda yacemin sunansa kenan. Har wajen sau uku,ana hudu ne nayi kiransa nace mu hadu. Bayan mun zauna na nemi sanin abunda yakeyi da fitarta,farko ya boyemin karshe ya tabbatar min gidan abokinsa ne babu nisa da nan kuma dole hanya daya ce ta fita daga layin nan,dole kuma motar ta fice ta hanyar gidan abokin nasa kamar dai yanda kasani lungun hanya daya a toshe take bata b'ullewa. Acewarsa akwai wani gagarumin laifi da tayimishi kuma ya rantse sai ya dauki fansa,na tsorata da jin haka domin a zatona kasheta zaiyi. Yayi dariya ganin yanayina,yace kada na damu ba wani abun bane mai hatsari. Ya karamin kudi yace na daure na cigaba na kuma yi hakuri don duk fitar da takeyi baya wani cin nasara don wani sa'in gidansu take nufa shi kuwa bayason kowa ya ganshi a wadanda ta sani gudun rugujewar aikinsa.     Akarshe akayi nasara rannan Hajiya ta fito,nayi kiransa na sanarmishi. Tun daga wannan lokacin shiru bai kara nemana ba sai washegari ya kirani cikin nishadi yayimin godiya yace ya kammala aikinsa,nikam jikina yayi sanyi na rasa menene ya aikata saidai inda hankalina ya kwanta ganin dawowar Hajiya a ranar kuma lafiya lau. Saidai ranar da lamarin ya faru na gobara data kusan tashi,bayan tafiyarkune asibiti,baba maigadi ke labartamin daman fa sun lura kwana biyu hajiyartasu babu walwala hakanan ma maigidan. Sun rasa gane abunda ya kawo wannan chanji a gidan."   Hamza cike da nadama ya dubi Haris   "Wallahi tun anan nasha jinin jikina,nayi nadamar aikata wannan abu kuma nake zargin kaina da lalata farincikin gidanka....!! Banci wuyar samun lambobinka ba wajen ma'aikatanka ba,nayita fakon Hajiya,da zarar ta fita zan sanarwa Manu,kamar yanda yacemin sunansa kenan. Har wajen sau uku,ana hudu ne nayi kiransa nace mu hadu. Bayan mun zauna na nemi sanin abunda yakeyi da fitarta,farko ya boyemin karshe ya tabbatar min gidan abokinsa ne babu nisa da nan kuma dole hanya daya ce ta fita daga layin nan,dole kuma motar ta fice ta hanyar gidan abokin nasa kamar dai yanda kasani lungun hanya daya a toshe take bata b'ullewa. Acewarsa akwai wani gagarumin laifi da tayimishi kuma ya rantse sai ya dauki fansa,na tsorata da jin haka domin a zatona kasheta zaiyi. Yayi dariya ganin yanayina,yace kada na damu ba wani abun bane mai hatsari. Ya karamin kudi yace na daure na cigaba na kuma yi hakuri don duk fitar da takeyi baya wani cin nasara don wani sa'in gidansu take nufa shi kuwa bayason kowa ya ganshi a wadanda ta sani gudun rugujewar aikinsa.     Akarshe akayi nasara rannan Hajiya ta fito,nayi kiransa na sanarmishi. Tun daga wannan lokacin shiru bai kara nemana ba sai washegari ya kirani cikin nishadi yayimin godiya yace ya kammala aikinsa,nikam jikina yayi sanyi na rasa menene ya aikata saidai inda hankalina ya kwanta ganin dawowar Hajiya a ranar kuma lafiya lau. Saidai ranar da lamarin ya faru na gobara data kusan tashi,bayan tafiyarkune asibiti,baba maigadi ke labartamin daman fa sun lura kwana biyu hajiyartasu babu walwala hakanan ma maigidan. Sun rasa gane abunda ya kawo wannan chanji a gidan."   Hamza cike da nadama ya dubi Haris   "Wallahi tun anan nasha jinin jikina,nayi nadamar aikata wannan abu kuma nake zargin kaina da lalata farincikin gidanka....!!*******   Fuskar Haris tayi jazur yayinda idanunsa suka kad'a kwarai tsikar jikinsa ta tashi. Ya dafe kansa saboda yanda yaji yana sarawa.       "Allah da ManzonSa s.a.w,sun hanemu da zargi. Yakan kawo mutuwar aure kwarai dagaske,kada ka yankemin hukuncin abunda bani da hakki ciki,kada ka zargeni my king. Ashe daman son da kakeyimin iyakarsa lebba? Ashe zaka iya zargina bisa abunda baka da tabbas? Ina rantsuwa da..."    Bai mance sadda ya yanke maganarta ba ta hanyar daka mata tsawa   "Keep quiet you stupid! Kina daukana sakarai ne?! Kina daukana wanda baisan abunda yakeyi ba?! Wallahi nafi karfin ki rainamin hankali Tasleem."    Bai mance sadda ta koma kuryar dakinsa a guje ba tabar falon,a ranar bai runtsa ba.   Yana kaiwa nan ya bugi tebur da karfi      "No!!!!" Ya fada cikin daga murya wanda ya kad'a hantar cikin Hamza dake zaune yayi tsuru da ido. Ya mike a tsorace saidai ba zato yaji Haris ya cakumi wuyan rigarsa,cikin kausassan murya yace    "Meyasa kuka cutar dan i har haka? Don ubanka wanene shi? Har nawa ne dashi da zai baka abunda zaisa ka cutar da rayuwata dana iyalina?!" Hamza ya rude ya hau had'ashi da Allah da ManzonSa s.a.w akan ya tuba bazai sake ba. Dakyar ya turashi ya zube k'asa gefen kujera. Haris ya juya yana tunano ire iren rashin mutunci da cin kashin da ya dunga yi mata duk akan abunda bai kai ya kawo ba! Ya runtse ido,sai ga hawaye sun zubo. Ya juyo a fusace ya dubi Hamza wanda yakeji kamar ya saki fitsari a wando     "Kasan gidan abokin nasa?"    Hamza ya gyada kai da sauri    "Na sani yallab'ai,saidai don Allah kayimin alfarma na kaika na juya na tafi,wallahi ya gargadeni akan kada na sanarwa kowa,muddin kuwa ya ganmu tare zai iya yimin komai."    Haris ya harareshi    "Kasan da haka ka aikata tun farko? Wallahi kafata kafarka."                  ******     Bayan sun soma tafiya,kai tsaye Haris bai zarce ko'ina ba sai police station. Wajen wani dan uwan abokinnan nasa ya nufa a ofishin,inspector Bashir,bayan sun gaisa ya sanarmishi abunda ya faru,Inspector Bashir cike da mamaki yace "Ya Salam,wannan masifa dame tayi kama? Abubuwa kala kala har haka?"    Inspector ya dubi Hamza    "Da gaskiyar Haris,ya zama lallai ka zauna agarinnan har sai komai ya kammalu,tunda yace ya yafemaka tunda ka nuna kayi nadama shikenan. Amma dole ka tsaya har sai Manu yazo hannunmu."     Daga haka ya dubi Haris     "Haris,kayi hakuri har zuwa safiyar gobe sai muje gidan,a yau akwai case na wasu kadangarun bariki da zamu mik'a kotu ne,in sha Allah I promise you,wannan yaron zaizo hannunmu za kuma a hukuntashi. Shi kuma wannan dole ayau ya kwana hannunmu gudun samun matsala. Cool your mind please, everything will be okay in sha Allah."      Haris wanda kallo daya zai tabbatar maka baya a hayyacinsa,ya gyada kanshi.    "Ba damuwa Bash,Allah Ya kaimu."   Daga haka sukayi sallama,Haris ya tafi yabar Hamza wanda yakeji kamar ya fashe da kuka adalilin kwanan kaso da zaiyi.     Shi kuwa Haris a mota ya tarar da missedcalls din Abba har uku wanda ya tabbatar mishi cewar lallai ya fahimci yabar ofis. Niyyarsa ya zarce gidansa domin burinsa na tozali da Tasleem ya nemi gafararta,saidai sanin da yayi sunada meeting mai zafi yasa dolensa ya koma ofis din nasu......!! Ba shine yaje gida ba sai bayan magrib,kasancewar ranar Alhamis ce yana azumi. Farin ciki sosai yakeyi na kasantuwar ranar Tasleem keda girki. Kai tsaye ya nufi samansa,duk da yaji rashin dadi da bai isketa a falo ba kamar yanda takeyi mishi a baya ba,saidai ya dan ji sanyin da yaga bata fasa girka mishi kayan bud'a baki ba duk kuwa da cewar kwanakin nan ta daina yi mishi girki sakamakon koda tayi baya ci hakanan take daukewa. Da safe ma ko kayan karin kumallo baya kalla. Haka dai yana tunaninta yana rage suturar dake jikinsa,don kuwa yayi sallah yaci dabino uku a hanya ya kuma sha ruwa.    Tausayin matarsa ya mamayeshi,wayarsa ya dauka ya danna mata kira. Lokacin tana karatun Alkur'ani mai tsarki ga kuma hawaye kwance saman fuskarta,ta  d'an dubi wayar kad'an,ganin lambarsa ta dauke kanta ta cigaba da karatunta yayinda zubar hawayenta ya k'aru na tausayawa rayuwarta. Wai yaushe zata daina ganin wadannan jarrabobin ne? Yaushe ne haske zai mamayi rayuwarta? Ta sani,akwai wadanda suka fita shiga mawuyacin hali,akwai wadanda idan da ace yau zata gansu ta kuma ga halin da suke ciki kwarai sai ta fahimci nata bama wani tashin hankali bane ba. Ina wadanda rayuwarsu ke k'arewa a masifu? Ina wadanda Allah bai basu shiriya ba har zuwa mutuwarsu? Ina kuma wadanda basu samu koda kwatan gatan data samu ba?    Hawayenta ya karu ainun har bataji murd'a k'ofa da shigowar mutum ba,saidai kawai ji tayi an tallafo fuskarta da hannu biyu. Saida ta razana,ganin shine ta sauke ajiyar zuciya,hawaye taga suna fita daga idanunsa,sukayiwa juna k'uri da ido cike da wannan boyayyen sirri na kauna da soyayya. A bangare daya tsananin mamaki ne ya cika zuciyar Tasleem,bata farga da cewar ba'a cikin mafarki hakan ke kasancewa ba har saida taji fatar bakinsa na gogayya da nata. Kamar wacce lantarkin wuta yaja,ta mike zumbur cikin tsananin fusata. Ta rungume Al-kur'anin dake a hannunta tana cigaba da zubda hawayenta yayinda take binsa da kallo na bacin rai.     Daga shi sai singilet da dogon wando na Adidas,ya mike yana nufota yace    "My Queen please.."   Tayi azamar nunashi da yatsa     "Ina maka rantsuwa da Allah idan ka matso inda nake sai nayi maka rauni HARIS! Fitarmin daga d'aki! Bana sonka! Bana kaunar ganinka!"   Tana wannan furucin ne cikin tsawa da kuka,bai dauka da gasken takeyi ba duk da dai kirjinsa ya danyi nauyi na jin ta kirayi sunansa kai tsaye,"Haris?" Ya maimaita a ransa, ya k'ara takowa yana nufarta    "My Queen,nasan ni Haris mai laifuka...aush!!"   Sauran maganar ta kasa fita sakamakon karamin flower vase da tayomishu wurgi dashi wanda cikin sa'a sai a goshinsa,ba shiri ya tsaya yana mai rike goshinsa gami da sakin karamin ihu. Da gudu tayi dakinta ta saka mukulli tana kuka sosai. Haris ya kwareta,ya sakata cikin kunci da bakin ciki. Tana jinsa yana bubbuga kofar har ya gaji ya daina ya zube shima a bakin kofar yana maganganu.    "Ki yafemin Queen,ki gafartamin,nayi maki gagarumin laifin dana cancanci hukinci fiye da haka. Na b'ata miki farincikinki alhalin baki da hakki cikin abunda zargi ne kawai nakeyi,domin Allah Queen kiyimin aikin gafara ki bude kofar ki saurareni."   Tasleem ta share hawayenta saidai tuna wasu hawayen suka maye gurbun wadancan,tana mai girgiza kanta kamar yana ganinta tace    "Babu sauran abunda ya rage naji ko kuma na gani daga gareka,babu abunda yayi saura wanda zaka sanarmin harma na yarda dakai. Ka bani mamaki Haris,ka bani mamaki kwarai dagaske,banyi zaton zaka iya yimin wannan cin fuskar ba,ban kuma tab'a sanin baka gama yarda dani ba dari bisa dari kamar kake yawan ikrari."   Ta girgiza kanta tana mai daga yatsanta guda sai kace yana kallonta   "Rana d'aya kawai! Komai ya chanza,daga ganin hotuna,ba tare daka nemi jin ta bakina ba,ba kuma tare daka nemi jin dalilin zuwana shopping ba,ka gaggasamin maganganu. Toh ni kuma inason sanarmaka da cewar na gaji da zama tare dakai. Bazan iya cigaba da zama da mutumin daya kasa yarda dani ba. Mutum irinka mai saurin zargin iyalinsa,wanda bai yarda cewar iyalinsa zasu iya tsare mutuncin aurensu ba a ko'ina. Bazan iya zama dakai ba,na gaji ka barni na koma gidanmu!"     Buga kofar da yayi, ya tsorata   "Karya kikeyi Tasleem! We can't leave without each other! Wallahi bazan sakeki ba har mutuwata! Ina sonki! Ina sonki!!"    Yana maganar a fusace,sai kuma ya sassauto don kansa   "Please Queen karki barni na mutu! Please ki budemin,ki yafemin Queen, ki yafemin."    Tasleem kuka takeyi kamar ranta zai fita, a zuciyarta godewa Allah takeyi kawai daya amshi addu'arta,Ya tona asiri. Da Ya wanketa bisa wannan zargin da mijinta yakeyi gareta. A gefe guda matsanancin so da kuma kauna ta gaskiya ta mijinta ne ya mamayeta,ga tsananin tausayinsa. Saidai kuma tunano da yanda ya dunga gasa mata munanan kalamai yasa ta fasa niyyarta na bude kofa,ta mike ta ajiye Al-kur'anin ta fad'a band'aki.    Koda ta fito bataji motsinsa a wajen ba,daman tasan bazai juri zaman jiranta ba,mutumin da yayi azumi? Kuma ta tabbata ko abinci baici ba. Sallarta ta tayar, bayan ta idar tayi shafa'i da wutri kafin ta hau godiya ga Mahaliccinta da kirari agareShi.( Bashakka ya dace mata da maza su gane,domin a wannan zamanin ma daidai da mazan sukan kauce hanya da bin bokaye domin neman bukatunsu,toh wallahi idann da ace zasu gane su tashi tsaye da kansu suyita rok'on Allah,su hana idanuwansu bacci,toh alal hakika babu wani abu da yafi karfin Mahaliccinmu,komai daren dad'ewa Allah zai amsa musu. Domin kuwa ba'a samun biyan bukata ta sauki har sai an mike tsaye da ibada. Wataran komai zai zama labari! Allah Ya datar damu,amin.!)                  ****    Koda ta kammala,ta bud'e kofar a sannu sannu,babu kowa a falon,wannan ne ya bata damar fitowa gaba daya. Saidai me? Hab'ar mutum taji saman kafadarta ta dama,ya zagayeta da hannunsa. A sannu kuma taji ruwan hawaye yana zubowa bisa  kafad'arta,cikin murya raunanniya kamar bata jarumin Haris ba ya soma magana     "Kirjina zai tarwatse Tasleem,ina neman zaucewa,ki taimaka ki tausayawa rayuwata,ki gafarceni. Dukkan wani dan adam ajizi ne,ban tab'ayi maki irin haka ba,ki daure kiyimin uzuri. Ki yafemin please and please."    Lumshe ido tayi cike da jin tsananin tausayin mijinta, saidai komai ya kwance mata sadda ta tuno da irin hargitsin data shiga duk a sanadiyyarsa. Take ta sanya hannuwanta ta dauke nashi,kafin ta goce bata yarda ta dubeshi ba ta koma saman kujera ta zauna. Ba tare da gajiyawa ba ya biyo bayanta,gwuiwoyinsa dukufe a kan kafet,yayinda tausasan hannuwansa suke a saman cinyoyinta. Duk yanda yaso na ganin sun hada idanu wuri daya amma hakan bai samu ba. Kanta yana k'asa hawayenta suna zuba saman hannayensa. Cikin dusashshiyar muryarta kamar mai fama da mura tace    "Ka jima kana azabtar dani,ka jima kana sakani cikin kunci da bakinciki."    Sai lokacin ta dago kanta ta dubeshi gami da daga yatsunta biyu    "Saboda dalili d'aya tak na kaddara! Wanda bai wuce fad'awa kan kowa ba? Saboda kasancewata YAR BARIKI a baya? Ashe daman idan mutum ya tuba yayi aure bazai daina fuskantar kalubale dangane da abunda ya riga ya wuce ba? Abun bakin cikin ma ya kasance mijinka wanda kake fatan ku kasance har abada tare shine mai zarginka harma yake fadin daman yasan mai hali bai fasa halin..."    Hannu yasa cikin matsanancin tashin hankali ya rufe bakinta,kai kawai yake girgiza mata. Dakyar ya samu damar magana   "Ina rantsewa da Allah ban tab'a so da kaunar wani abu ba kamar yanda nakeso da kaunarki Tasleem. Wallahi alokacin da nayi wadannan munanan kalaman gareki bana cikin nutsuwa da hayyacina,Tasleem meyasa bazaki fahimci cewar ina tsananin kishinki ba? Meyasa bazaki gane idan babu ke babu amfanin rayuwata bane? Ya kamata zuwa yanzu ki gane Haris naki ne,Haris yafi gaban kowane dan adam awajenki. Akanki banajin zan iya hakuri,tasleem I trust you more than how I trust myself. Saidai wallahi sadda naci karo da hotunan nan,yanda wai matar da nakeso nake kauna ce ta tsaya bainar jama a tare da abokin watsewarta na baya suke hira abun it pains."     Tasleem tayi murmushi mai ciwo kafin ta kauda kanta gefe,cikin nutsuwa ta labarta mishi dukkan abunda ya faru bata k'ara ko kuma rage komai ba. Saida ta dasa aya kafin ta dubeshi    "Ko acan baya,Baaba baya cikin irin mazan da zanyi tarayya dasu, ballantana yanzu kuma da nake da aure nasan mutunci da kimarsa."    Haris ya numfasa,sai lokacin ta lura da durkuson da yayi,hannunta tasanya cikin nashi ta dagoshi,ya zauna gefenta ya karkato gabadaya yana fuskantarta. Yayinda ta cigaba da magana   "20th April,rana ce ta birthday dinka idan baka manta ba King,fitar da nayi domin ba siyo maka gift ne."   Ta mike da azama ta nufi daki,can sai gata ta fito da leda. Zazzage kayan cikinsa tayi,agogo ne a cikin gidansa ruwan silver mai kyawun gaske,sai takalmi mai kyau,da flower da kuma cards. Ta dubeshi yayinda ya tsurawa kayan ido cike da nadama tsantsa na abunda ya aikata gareta.   "Idan baka manta ba,koda ka shigo sashena a ranar fitilu a kashr suke,da ace ka lura zaka ga kwalliyar da nayi dominka King,da ace kuma ka saurareni da zaka gane cewa bani da laifi. Saidai duk hankalinka baikai nan ba,ta inda ka shiga.."    Katseta yayi inda ya shiga aikamata da zafafan sakonni,batayi yunkurin hanashi ba domin bata da wannan kuzarin. Don kansa ya bari ya sanyata jikinsa,a sannu yake shafa gashinta,sai kuma ya soma magana    "Nayi babban kuskure Queen,tuba nakeyi in sha Allah bazan k'ara ba. Ayau ina zaune a ofis ne.."   Ya labarta mata yanda ya gano gaskiya da kuma shigar da case din hannun hukuma da yayi. Ta jinjina zancen,ta dago kanta ta dubeshi cike da mamaki     "Ikon Allah kaga kuwa nama mance da marinsa dana tab'ayi,domin idan ban manta bama,ranar kaine ka batamin rai, inda kaketa bibiyata a hanya randa na hau motar KB azatonka shine aciki. Toh ranar ne yaban haushi na mareshi. Wallahi na manta anyima hakan."    Haris yayi murmushi   "Rabu da dan iska,mugodewa Allah da bai rabamu ba adalilin hakan,yayi saurin bayyana mana gaskiya."    Ta gyada kanta tana mai hamdala,tsakanin fa mata da miji sai Allah. Nan suka sasanta akarshe dakyar ta jashi zuwa sama domin yasha ruwa...! A wannan daren sun tabbatarwa da kansu lallai sunyi mugun kewar junansu,haka kuma bazasu iya rayuwa ba tare ba. Domin kuwa ba Tasleem ba,daidai da shi kansa Haris din,yayi wata iriyar rama ainun fuskarnan tasa ta k'ara sirancewa sai hancinsa ya k'ara fitowa d'abas. Ta tallafo hab'ansa bayan data kammala taimaka mishi da sanya takalmi "Ka rame sosai my king." Ya kama hannuwanta "Kin fini rama my queen,kodai kin samo mana baby ne?" Tayi murmushi kafin cikin wasa ta harareshi "Nikam banida komai." "Shine kalmar da ni kuma na tsana my queen, nafiso kiyi komai." Ya k'arashe yana kai hannu cikinta,tana murmushi tace "Sai mu cigaba da addu'a my king,komai lokaci gareshi. Allah Ya kawo masu albarka,Ya sauki sisna lafiya." Ya amsa da amin kafin su jera su fito falon. ****** Kai tsaye Haris police station ya soma nufa. Cikin sa'a kuwa ya hadu da inspector yana jiranshi. Su biyu ne a motar,sai Hamza cikon na uku. A bayansu kuwa motar jami'an tsaro ne guda daya, suna tafe bisa bin umarnin ogansu,ko jiniya basu kunna ba. Inspector Bashir ne ke bawa Haris labarin case dinsu na jiya "Wato ita wannan mai suna Momi,itace shugabansu,ita keda alhakin had'asu da manya manyan dattijan banza na nahiyar nan,masu ji da dukiya. Wallahi wata idan ka ganta sai abun ya baka haushi,don kuwa bata wuce ace tana gidan mijinta ko kuma tana karatu ba wallahi. Toh yanzu dai matsalar da suka samu,bai wuce na kashe Alhaji Kwangila ba,na nan hanyar kasuwa ba,sanadin haka asirinsu ya tonu. Sun hadashi da yarinya mai kanjamau,yace zai dauki fansa akan ita yarinyar da Momi din,shine wasu tantirai wai Dalal da Hibba suka bada shawarar a kasheshi,yanzu bayan ya mutu mukayi nasarar cafkesu. Alkali ya yankewa Samuel din da yaransa hukuncin kisa, ita kuwa Momi da jama'arta hukuncin shekaru a gidan yari da horo mai tsanani. Saidai kuma a jiyan dai muka samu labarin ita Hibbar ta mutu ne bayan da wani saurayi yayi amfani da ita harma ya fiddamata sassan mamanta guda. Haka dai mutuwar wulakanci." Inspector Bash yana kaiwa nan ba tare da ya lura da yanayin dake saman fuskar Haris ba na d'imuwa ya girgiza kai "Toh menene amfanin haka? Mutane suna kai kansu ga halaka da kansu,cases iri daban daban gasunan muna gani lamarin saidai du'ai." Hamza ya amsa da cewa "Hakane yallabai." Haris kuwa ya girgiza da jin wannan labarin,lallai Tasleem ta k'ara godewa Allah da hakan bai zamo harda ita a ciki ba. Yanzu Hibba ta rasu? Allahu Akbar,duniya abar tsori ce,shakka babu! Haka dai har suka karasa ga gidan abokin Baaba(Manu) kamar yanda Hamza ya sanar dasu. Bayan sunyi fakin,Inspector ya umarci yaransa akan suyi jiransu kada su fito. Su uku ne suka soma shiga gidan. Anan farfajiyar gidan sukaci karo da wani matashi yana shirin shiga mota, ganinsu yasa ya fasa ya zubamusu ido,kwarai ya gane Hamza saidai ya basar. Bai kawo jami'an tsaro bane,don kuwa Inspector bai sanya uniform ba. Hannu suka mik'amai,sukayi musabaha. Ya dubesu "Lafiya dai ko?" Hamza ya dubeshi "Lafiya kalau,Nura baka ganeni bane?" Matashin da aka kira da Nura ya dubeshi kad'an,kafin ya girgiza kanshi yana murmushi na 'yan duniya "Ikon Allah,gashi dai da alama ka sanni tunda har ka ambaci sunana saidai kuma ni koda wasa bansanka ba." Haris ya dubi inspector, inspector yayi murmushi kafin ya dubi Hamza "Wannan shine abokin Manu?" Hamza ya gyada kai "Kwarai kuwa Yallab'ai,shine Nura abokinsa." Nura ya yamutse fuska "Wanene kuma Manu? Bani da aboki mai wannan sunan." "Idan bakasan Manu ba,bana tsammanin zaka kasa sanin Baaba ko?" Cewar Haris,gaban Nura ya fad'i,toh shi kuma wannan ta yaya yasan sunan Baaba? Ya daure ya girgiza kansa "Nifa kun sakani a duhu,duk bani da masaniya game da maganarku." Inspector Bash ya jinjina kai kafin ya juyo yakai mishi naushi a baki,sai a police station! ***** Nura zaune yayi jina jina,yayinda inspector bash yake saman kujera zaune,ga Hamza gefensa. Haris kuwa,inspector ya mishi umarnin komawa bakin aikinsa tare da alk'awarin komai zaizo karshe. Inspector ya dubi Nura wanda hanci da bakinsa ke fidda jini yace "Ka shirya fadamin gaskiya ko kuwa sai na illata kafafunka?" Nura baya fatan dukan da inspector yayi mishi yafi wannan,dole ya sanar mishu gaskiya,akan cewar da hadin bakinsa komai ya shiryu. Shine ma ya bawa Baaba shawarar chanza suna,hakanan shine ya samo mishi wani yaro mai suna Tasi'u domin taimaka mishi wajen yin hotuna,a karshe suka biyashi ya tafi. Inspector ya jinjina kai "Ok,yanzu ina kake ganin zamu samu Baaba?" Nura yayi shiru kafin ya dubi inspector yace "Ina da tabbacin yana garin nan,kuma yafi zama a Tahir Guest Palace. Fitar da kuka tarar zanyi ma,wajenshi zan nufa saboda ya sanarmin ya samar mana wasu bebs." Inspector ya tabe baki "Bebs? Kune masu lalata yaranmu ko? Ok,tashi muje." **** Basu ci wuyar cafke Baaba anan hotel din ba. Haka dai Baaba yayita hararar Hamza mai wanki,shi dai Hamza lamarin yayi mishi dadi sakamakon sallamarshi da inspector bash yayi suna komawa station. Haris yana tasowa daga gurin aiki ya nufi station din. Ya tabbatarwa da inspector lallai shine dai na jikin hoton, yayinda ya koma motarsa ya kawo hotunan ya damkawa inspector. A karshe sukayi sallama bayan inspector ya tabbatar mishi lallai za'a horasu. Jin haka Baaba ya shiga neman gafara saidai bakin alkalami ya riga ya bushe! ***** BAYAN WUYA....! Tun daga wannan ranar,komai na rayuwa ya chanjawa wadannan ma'auratan,komai yayi musu dadi. Hakanan,a fannin ita Tasleem da Zahra,kai ka rantse ba kishiyoyi bane ta yanda kowannensu ya rik'i dan uwansa da zuciya d'aya. Cikin wannan zama ne,KB da Yasmeen sukazo Kano. Kamar hadin baki,sai ga Yaya Abdullah da Hasina kai harma da Hindatu sunzo hutun karshen mako. Nan fa suka hadu a gidan Daddy,akayita hira ana dariya. Yasmeen sam bata rik'e Tasleem azuciya ba,gaba d'aya saita watsar da komai. Zahra tuni cikinta yakai watanni biyu,sai tsokanarta Tasle takeyi. A karshe dai su Daddy suka shigo, nan aka hadu akayi zaman cin abinci anayi ana hira kafin daga bisani su Yaya Abdullah sukayi shirin tafiya,nan dai sukayi musu sallama. Sai bayan da sukayo musu rakiya ne,Hasina ke bawa Tasleem labarin wani saurayi daya fito yanason Hindatu,shima iyayensa anan Abuja suke hakanan yanzu lecturer ne acikin jami'ar ta Abuja. Tasleem ta jinjina lamarin "Karatun fa?" Hindatu tayi dariya kadan "Ai sunyi magana da Yaya Abdullah,yace da zarar na kammala degree sai ayi magana,shi bashi da damuwa sai na k'arasa a dakina." Tasleem taji dadi tayi mata fatan alheri. Bayan tafiyarsu suma sukayi sallama dasu Daddy suka nufi gidajensu. A mota Zahra ta matsa tanason cin shawarma,dole Haris ya karkata kan mota ya nufi L&Z. Tasleem tana ta dariya. Saida ya shiga ya siyo sannan suka nufi gida. ***** Zumunci sosai ya kankama tsakanin Hamida da Tasleem tamkar babu wani sab'ani da ya tab'a shiga tsakaninsu. Addu'o'i sosai tasleem ta bawa Hamidah,a yanzu kam bata wasa da ibada cikin ikon Allah abubuwa da dama sukayi sauki gareta har taji nutsuwa ta ziyarci zuciyarta game da mijinta. Hakanan kishiyoyinta sun daina shiga harkarta,kowa tasa ta fishsheshin Hakanan ga Abban tasleem,ya warke sumul ya cigaba da aikinsa,shi kansa yaso Tasleem ta karasa karatunta na shari'ah saidai bai zurfafa ba ya hakura jin cewar Haris baya ra'ayin hakan. Cikin Zahra yana da watanni hud'u,akayi bikin juwairiyya diyar waziri,budurin da akayi ba kadan bane,domin daidai da Mamma ta samu halarta. Humaira ta k'ara wayo kamar wacce sukayi shekara basu hadu ba. Taslewm don farincikin ganin Mamma rasa inda zatasa ranta tayi. Kwana biyu da kammala bikin ne,Mamma ta nemi da Tasleem tayi mata rakiya wani wuri,Tasleem ta nemi iznin Haris yayi na'am. Itace take jan motar yayinda Mamma ke kwatanta mata inda zasuje cikin unguwar Tarauni. Tasleem tana son tariyo wajen wacce ta sani a area din saidai da ta kasa tunanowa,hardai ga mamakinta taga mamma ta umarceta data faka kofar wani gida. Kwallah suka cikawa Tasleem ido,ta washe baki "Kulu? Mamma ai nan gidansu Kulu ne." Kwarai nan dinne kuwa,domin babu abunda ya chanza. Mamma ta jinjina kanta "Banajin gidansu Kulu zai b'acemin,nayi mamakin yanda kuka yada zumunci da matar data rikeku bisa amana." Tana fadin haka ta bude motar ta fita. A sanyaye Tasleem ta fito sannan ta budewa Humaira itama ta fito. Tuni Mamma ta shige, suka rufamata baya da sallama. Mutanen gidan suka amsa,kamar ma wani taron akeyi bisa la'akari da taron mutane sunci ado. Ganin bak'in fuska yasa suketa binsu da kallo,suna cikin gaisawa ne,saiga matar d'an gidan kulu ta fito. Wata tace "Ga mai jegon nan ma." Suka dubeta,tabbas Tasleem bata mance fuskarta ba,Sadiya ce diyar d'an Kulu. Suka gaisa,Mamma tayi mata barka kafin ta tambayi Kulu. Tayi musu jagora har dakin Kulu. Nan dinma cike yake da mutane,abunda ya bawa Tasleem mamaki,bai wuce na yanda Sadiya ta durkusa a ladabce ta shaidawa Kulu tayi bak'i ba,alhalin yanda a baya ta rainata take wulakantata. Kulu na ganin Mamma,suka rungume juna sai kukan murna. Kallo ya dawo kansu,kafin ta saki Mamma ta kamo hannun Tasleem har jikinta yana rawa "Ikon Allah kenan,kada dai wannan Tasleem ce?" "Ni ce Kulu." Cike da farin ciki ta jasu ciki. Nan fa hira ta b'arke bayan mutanen dakin sun basu waje,tayi kuka sosai jin labarin abunda yasa Tasleem gudowa daga gidan mahaifinta tazo wajenta da kuma abunda ya kasance a rayuwarta na baya. Saidai jin tayi aure abun yayi mata dadi kwarai tayita hamdala. Nan ma ta jiwa Mamma dadin auren da tayi. Ta kuma jinjina yanda rayuwar Raliya da yaranta suka k'are. Alheri mai yawa Mamma tayi mata,akarshe ta karb'i lambarta,hakanan itama Tasleem tayi mata alkawarin zuwa jefi jefi,a inda tace har yau uwa take awajenta. Haka dai suka rabu bayan sun shiga sunga yaro sunyiwa mamansa alheri. ***** A kwana a tashi babu wuya wajen Ubangijin al'arshi,sai gashi har Zahra ta shiga watanta na tara cif. Kulawa kuwa,sai a rasa wanda yafi wani tsakanin surukai da mijin da kuma abokiyar zamanta,Tasleem. Don sai ace ma ta fisu rawar k'afa da d'oki,hakanan saboda tsananin kaunarta da yara yasa kodayaushe itama addu'arta Allah Ya bata ciki ta haihu. Komai na aiki ta hana Zahra,duk da dai zuwa lokacin akwai yarinyar dake tare da ita, hakan baya hana Tasleem taimaka mata.    Wata ranar asabar da yammaci,suna zaune a falon Haris da rana bayan kammala cin abinci suna hira da dariya inda Zahra ke basu labarin wata mai ciki data bata tausayi tana nakuda. A sannu Tasleem tana aikin tausa mata k'afafu,Haris yana daga kishingide yana kallonsu cike da sha'awa. Can kuma Zahra ta hau cije cijen lebbanta,hakan yasa hankalinsu yayi kanta     "Sisna marar ce ko? Tun safiyar yau kike complain a kanta amma kink'i muje asibiti."   Zahra tayi murmushi cikin dauriya    "Kai anti,bafa wani abune ba,zai warware,d'an rikewa kawai yakeyi."     Haris dake sauraronsu ya mike zaune    "A'a,wane d'an? Tashi dole muje asibiti."   Haka suka matsa mata,babu yanda ta iya dolenta ta mike. Tasleem ce ta janyo akwatin da tuni sun had'ashi,Haris kuwa ya tafi tayarda mota,suka dunguma asibiti. A mota ciwo ya k'ara k'arfi,hankalin Tasleem ya tashi,ta hau sannu babu iyaka hakanan Haris shi dinma kasancewar bai taba kai mai nakuda asibiti ba hankalinsa bai jikinsa sosai har suka isa asibitin da take awo. Sun amsheta da gaggawa,Tasle ta gaza nutsuwa,musamman yanda ta jiyo wasu matan suna ihu da kuka da kiran sunan Allah. Wadanda ba musulman ba sai ambaton Jesus sukeyi. Kawai taji kuka ya kwace mata ta fito wajen da Haris yake,yana tsaye ya rungume hannuwansa a saman kirji yana safa da marwa,ganinta cikin wannan halin yasa hankalinshi tashi,ga kuma idon mutane dake gun babu damar ya rungumeta saidai duk da hakan yayi kokarin dafa kafadarta da riki hannunta cikin tashin hankali    "Meke faruwa? Ina Zahra?"     Tayi kokarin tsaida kukanta     "Tana ciki,da saura bata haihu ba."    Zai watso mata tambaya na dalilin kukanta sai kuma ya fasa sakamakon nurse din data fito tana tambaya      "Ina wadanda suka kawo Zahra'u Yusuf?"    Da sauri suka nufeta    "Gamunan." Tayi murmushi   "Toh Alhamdulillah,ta sauka lafiya,an samu baby boy."    Farin ciki gun Tasleem da Haris ba'a magana kafin kuma tace su d'an jira a kammala shiryasu.  Haris daman tuni ya yiwa su Mami waya,sai gasunan hardasu Daddy saidai Umma batazo ba saboda alkunya. Sai wajen isha'i aka sallami Zahra,suka dunguma gida. Saidai fa Mami ta kafe lallai wajenta zata tafi,Tasleem da Haris suka hau roko Allah da annabi s.a.w,Daddy ya tsawatar mata akan cewar ta barsu su wuce gida,hakanan ta hakura,tana komawa ta tura dattijuwa mai tayata aikace aikacen gida(Delu) ta zauna da Zahra. Gida fa yayi dadi.     Washegari da safe,Tasleem tun saukowarta bayan ta ajiyewa Haris kayan kari,saita shashance a wajen Zahra da baby. Yaron ya shiga ranta ainun,tana mai jin kunyar abunda ta aikata a baya na zubar da cikin da tayi da saninta. Fitowar Zahra daga wankan jego ta zaro ido     "Lala lala,antina har yanzu yayanmu bai tashi bane?"      Tasleem ta mike da sauri,shaf ta sha'afa    "Na shiga tara,nasan ma tuni ya shirya abinsa."   Ta fita tare da baby cikin sauri,delu da Zahra suna dariya.       Zaune ta sameshi yana kurbar ruwan tea babu ko madara,ido kawai ya zuba mata fuska ba walwala. Saidai can kasan zuciyarsa ta burgeshi ainun tayi kyau da baby. Ta karaso ganin bai taba komai ba,ta kama kofin da yake shan ruwan tea ta kurb'a,ko sugar bai sanya ciki ba. Langab'ar da kanta tayi gefe tana mai kashe murya    "My king, I am sorry please."     Yasa hannu ya karb'i yaron,ya dan kama hancinsa yana murmushi    "Zuwanka yasa matata ta mance da duty dinta,ina kuma ya kasance yau itama ta samu bebinta,hum?"    Ya karashe yana harararta,murmushi tayi ta dafa kan bebin   "Ka fadawa daddy,mominka bazata tab'a mancewa dashi ba koda ta haifo kanwarka don yanzu haka ma she's pregnant."    Ta karashe tana duban idanun Haris. Yayi azamar jefomata tambaya     "Are you serious?"    Tayi murmushi   "Hum, lallaima my king,yaushe rabon da kaji nace maka ina period? Count it."   Yayi tsam,kwarai an kusa wata uku rabonsa da yaji hakan.     "Itama baka tausayinta ne? Bazata iyaba,nauyin zaiyi mata yawa,zan dai turo Delu." Ya tunano kalaman Mami,hamdala yayi don murna kafin ya rungumeta cike da tsantsar so da kauna.        Ranar suna yaro yaci sunan Abba,wato Hussein suke kiransa da Daddy.   Sai ya zamana,Tasleem tana kula da Daddy,Haris yana kulawa da ita. Alokacin da cikinta yake wata na biyar aka sanya ranar auren Hindatu,hakanan suna da biki na yanmatan Kazaure saidai fafur Haris yace bazataje ba. Tayi fushin tayi koke koken amma a banza. Mamma tace ta hakura,tana kallo su Yasmeen  dama sauran yan uwa suka wuce,ita kuwa Hasina bata samu zuwa ba sakamakon bikin yayanta Hayat da akeyi da matarsa Samira wacce itama dole akayi ya aureta sakamakon abin kunyar da yayimata kuma gata cousin dinsa.    Ranar daurin aure, Tasleem k'in daukar wayar kowa tayi don haushin bataje ba. Tana zaune a falonta tana chanje chanjen tasha taji ana kwankwasa mata kofa. Baba maigadi ne ya sanarmata tanada bak'uwa. Tace ya shigo da ita,tayi matukar mamakin ganin fuskar da batayi zato ba.. "MANAL?" Ta ambata a fili.   Ta k'ara k'iba tayi kumatu,bak'ar fatarta sai shek'i takeyi idan ka cire kurajen daya fito ya b'ata gefe da gefen fuskarta kadan. Tana murmushi mai bayyana hakora,yayinda kwalla suka cika idonta tace     "Baby Tasleem tamu,nice dai Manal."   Tasleem ta rungumeta cikin tsananin farincikin ganinta. Taso zuwa wajenta saidai rashin sanin hanyar had'uwar ne babu. Ta jata sukayi ciki. Nan hira ta b'arke,inda Manal take bata labarin irin kaunar da mijinta keyi mata,ba don ma ita d'in tana tsoron Allah ba da zai iya tarewa awajenta ya manta da uwargidansa. Saidai kuma yanzun suna nan Abujan tare suna zaune yau da dadi gobe babu dadi. Manal ta dubi Tasleem cikin zubar hawaye    "Mu godewa Allah da Ya kwatomu daga rayuwar bariki,mu cigaba da nemawa yan uwanmu gafararSa. Naso kwarai na kaiwa Dalal ziyara saidai ya tabbatarmin muddin naje toh a bakin aurena. Hibba kuwa naje da kaina na sanarwa iyayenta rasuwarta,wallahi babanta har suma yayi a karshe yace ya yafemata zunubanta. Don kuwa yasan wacece Hibba a baya,babu ruwanta kuma tana kare martabar addininta a ko'ina saidai idan Allah Ya kaddarowa bawa abu babu wanda ya isa ya chanjashi."    Tasleem itama sharar hawayen takeyi    "Kinga rayuwarmu yanda ta juye a karshe ko? Yanzu mun taba tsammanin kawunanmu zasu rarrabu haka? Ba shakka Bariki ba hanyace ta huce bacinrai da takaici ba illah k'ara jefa kai ga halaka. Ki yafemin Manal, har zuwa yanzu inajin kaina mai laifi kwarai bisa yanda ba jefa rayuwarki cikin halaka. Na tabbata da ace na baki shawara ta gari,da duk hakan bata kasance ba."   Manal tayi murmushi   "Haba baby,wallahi komai ya wuce. Na dauki komai bisa kaddara,haka Allah Ya kaddaro lallai kuma babu mai chanjashi. Da izninSa kuma zamu cigaba da tsare kanmu da mutuncinmu a ko'ina. Na baya suma munayi musu fatan Allah Ya shiryesu,Ya ganardasu. Kinsan fa mutane suna kuskure daya,idan sunga kana aikata b'arna bazasu iya yin addu'ar shiriya gareka ba saidai suyita aibataka suna masu kyamatarka. Ki godewa Allah da Ya hadaki da Haris har ya zamto fitila mai haskaka rayuwarki."   Tasleem tayi dariya   "Gaba dayanmu zamu hadu muyita godiya ga Allah daya fiddamu daga BARIKI."    Sukayi 'yar dariya,ranar dai kamar kada su rabu. Sai magriba Manal tayimata sallama akan zata koma gidan kanwar Alhaji Ubale inda anan ne tayi masauki sakamakon bikin da za'ayi a danginsa. Sukayi musayar lambobi tare da alkawarin idan tasleem ta haihu zatazo.     Sun jero sai ga motar Haris ta shigo. Dole Manal ta tsaya don su gaisa. Tunda ya doso su yakeyiwa Manal kallon bakuwar fuska don alal hakika ya manceta. Har dai ta gaisheshi bai ganeta ba,saida Tasleem tayi mishi bayani. Ya dan saki fuska har ya tambayi maigidanta,akarshe yayi mata alheri tayi gaba. Tana tafiya,tasleem ta turo baki tayi ciki aguje. Da sauri ya rikota adaidai kofar dakinta ya zaro ido   "Baki lura da cikin dake jikinki ne? Wane irin gudu kike haka?"   Ta tureshi kadan "Kaima kasan laifinka ai,haka kawai ka hanani zuwa bikin kannena."   Ya ja hancinta   "Ba gashi sanadin hakan kinyi babbar bakuwa ba?"   Tayi murmushi tana mai sanya kanta saman kirjinsa   "Kuma fa hakane my king,naji dadin ganin Manal cikin shigar mutunci,kuma da aure."   Ya jata zuwa sama   "Hakane maman yasmin,mu k'ara godewa Allah."    Sukayi samansa.                 ****    Bayan Watanni Bakwai   Zaune yake a falonsa ya dora baby yasmin saman cinyarsa yana mata wasa tana dariya,kamshin turarenta ya soma shiga hancinsa kafin ita da kanta ta karasa shigowa falon. Sanye da wata doguwar rigar bacci wacce ko cinyoyinta bai gama rufuwa ba,hakanan saman wuyanta rabi a waje suke kai kace ba'a bawa baby yasmin komai ba. Ya dubeta ta gefen ido kafin ya tsaida idanunsa ga takalmi mai tsinin data sanyo. Murmushi yayi baice uffan ba,saima ya cigaba da yiwa baby wasa. Kwas kwas ta shiga takunta har ta karaso ta zauna kusa da baby.   "Karyani zakiyi?"   Tayi murmushi cike da marairaita murya tace   "Shine ko ka yaba kwalliyata my king,nidai ina kishi da wannan 'yar."   Ta dangware kanta kadan,ya matse hannunta    "Akanta fa zan iya zaneki fa. Maza tashi."   Tak'i koda motsi,karshe ma ta zubamishi ido tana murmushi wutar so da kaunarsa na k'ara ruruwa cikin ransa.   Ya daga mata gira duk da shi d'inma ya gama harbuwa don babu ranar da sonta bai kara samun matsuguni a zuciyarsa   "Hey,karki cinyeni fa." Tayi wal da idanuwa,tunano abunda ya faru a washegarin daren farkonsu inda yake sha mata kamshi. Murmushi tayi    "Kada dai ka manta ka shagala gobe akwai daurin auren abbanmu da anti sa'a(yar uwace ga waziri,kuma budurwa saidai karatun data tsaya kammalawa yasa batayi auren wuri ba,ashe rabon Abbanmu ce..lol) Kafin kuna ta mike tana tukunta na manya ta shige daki. Ta yaya zai jure ne? Ya sab'i baby yasmin a kafada ya kashe fitilu ya mara mata baya. Tammat bi hamdulillah...! Taku har kullum RUFAIDA OMAR…..Ga duk mai gyara kofa a bude take,hakanan tambaya. Dan adam ajizi ne,babu wanda baya kuskure...A gafarcemu… omarrufaida@gmail.