[6/27, 10:46 PM] Zannura: *NAGA TA KAINA* *NA SADNAF*🌸🌸 ®️ *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_* _{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_ *Free Novel* Hannuna har karkarwa yake wajen d'ago da jaririn Dan na tabbatar da Namijin ne. Take na hau hawayen farinciki na Kara kwantar dashi a kirjina inata Godewa Allah da Wanan kyautar da yamin a cikin jaririn Nan ne kawai ban saka Rai da samun namiji ba Amma sauran duk saka Rai nake da maza ne sai gashi a lokacin da ban kawo ba na cire Rai da haihuwa Namiji Allah ya bani. Kasa d'auke idona nayi daga kansa har Nurse din ta saka Mai Kaya bayan ta goge Mai jiki da man zaitun Yanda taga Ina binsa da Ido Ina murmushi yasa tace halan ban taba haihuwa d'a namiji ba gyada Mata Kai nayi a lokacin da take sake mikomin shi na karbe shi da Sauri na tashi zaune na zuba Masa Ido ba Inda ya baro Naseer kamar an tsaga Kara Haskena kawai ya d'auko. Sosai na ringa Jin kaunar jaririn a Raina inajin nurse din na Bari tayiwa Naseer albishir tayi waje da Sauri Dan tasan indai ta Gaya masa kila ya mata kyauta A bakin kofa ta tada Naseer din kamar zai fado d'akin Ana bud'e kofa yyi Kan nurse din da Sauri. Ita kuwa ta mik'a Masa hannu tana ya Bata goron albishir Washe baki yayi daya ga alamar Naeema ta sauka lafiya addua ya hau yi Yana "Na Riga da nasan Mai ta Haifa Allah yayiwa rayuwarta albarka" Murmushi nurse din tayi tana mamakin yanda daga Naeema har Naseer din suka cire Rai da haihuwar da namiji "Sai dai Allah ya Masa albarka Dan namiji ta Haifa katoto" Naseer Ido ya gwallo Yana me kikace. Kafin ma ta bashi amsa ya fada d'akin da Sauri har Yana tuntub'e. Daga yanda yaga Naeema na murmushi yasa ya Isa wajenta da Sauri tare da saka hannu ya karbi jaririn Bakinsa har kunne sai hamdala yake Yana kamkame jaririn a kirjinsa. Sai albarka yake shiwa Naeema ji yake kamar baa Tab'a Masa haihuwa bama inama lokacin da yake da kudi Naeema ta haifi namiji da yaron ya Sha Gata. Bakinsa ya kafa a kunnen jaririn ya Masa huduba ya d'ago ya kalli Naeema Yana "Allah ya raya Naseer sunana na saka mishi" Murmushi na saki Ina Jin dadin sunan daya saka mishi nace "Allah yasa ya gaji halin Mai sunan ya bashi ilimin addini irin na Mai sunan insha Allahu addua kawai ce tsakanina da yarana Allah Kar ya jarrabceni da fushi dasu" Na tsinci kaina da fad'a duk da kallon da Naseer kemin yasa na hadiye sauran maganar. Karfe takwas na safe aka Sallame mu daga asibitin bayan Naseer ya biya kudin komai. Hamdala kawai yake a Ransa da Allah yasa Naeema nada kudi da yau asirinsa ya tonu ta Ina zai samu wanan kudin da suka kashe a asibitin. Naeema sai data saka ya siyi kayan shayi da sauran Abubuwan a zata bukata kamar yanda yake siya idan ta haihu shi kuwa sai dari dari yake baya San kashe kudin Wai Dan Kar ya kare. Lokacin da muka Isa gida Naseer ne ya rungume jaririn a kirjinsa daya hannunsa d'auke da kayayakin mu Ni Kuma Ina biye dashi a baya Ina takawa a hankali kamar iska zai d'aukeni nakeji sabida rashin kwarin jiki banida burin daya wuce na kwanta sabida ciwon baya danake yi Bakin Naseer a washe ya Shiga palon Da Sallama Umma da Safiyya kawai muka samu a palon Umma ta hade Rai tana ta jijjiga k'afa Ina ganin Haka nasan wani rashin mutunci Umma zatayi. Naseer kuwa tuni Naga ya nutsu duk da gabansa sai daya Fadi da ganin Umma Amma Haka ya nufi wajenta ya tsugunna Ya hau gaisheta. Wani irin kallo ta Masa ta d'auke kanta batare da ta amsa ba Shi kuwa ya Kara gyara Jaririn a hannunsa Yana "Umma Naeema fa ta haihu Kinga" "Sai me dan ta haihu yau ta fara haihuwan?Mai abin murna a haihuwa Naeema da take cike.maka gida da tarin Mata" "Umma wanan Namiji ne wanan Karin Allah ya azurtamu da Samun namiji" Ina dab da Isa k'ofar karamin Palo Amma sabida Naga ya Umma zatayi idan taji Namiji na Haifa yasa na tsaya. Mik'ewa tayi da Sauri ta lek'a fuskar jaririn da Naseer ya juyo dashi Sabida Umma ta ganshi sosai ta gaskata maganar da yake. Ja da baya tayi tana "Kuma sai ka yarda wanan danka ne. Sai ka yarda wanan Jininka ne? Watanmu kusan hudu a gidanan tunda muka zo Maza suke sintiri a gidanan wayanda zasu Zo da safe daban wayanda zasu Zo da Rana daban Sabida Kai dakiki ne an asirceka idonka ya rufe shine zaka ringa murnar ta haifo maka namiji. Kar idonka ya rufe ka kasa gane gaskiya har Ina Naeema zata samu kudin da zata gyara gidanan Bata tsaya iya Nan ba ta siyi engine biyu Kai Kaga irin kudin datake rik'ewa kuwa Amma dayake zuciyarka ta mace idonka ya rufe duk baka gani ba ka hau rawar kafar ta haifo ma namiji indai Jininka ne ai mace zata haifo iya wanann ma ya Isa yasa ka Gane Dan Nan ba naka bane" Yanda nakejin zuciyata da jirin dake d'ibana sabida tsananin bakinciiki sheganta min da da Umma keyi da kazafin da take neman yimin yasa.na shige palon Dan Ina cigaba da tsayuwa zuciyata zata iya bugawa Ni Kam wane irin nauyin kiyaya Umma zata gwadamin Wanda Bata gwadamin ba ya isa Haka ai batare aka halliceni da Naseer ba tafiyar Naseer ban fasa numfashi da rayuwa ba Dan Haka barin rayuwar Naseer na huta bazai Hana shi rayuwa ba Haka Nima idan akwai abinda ke damuna Bai wuce yarana ba Dan Ni nasan matsawar na tafi dasu kamar inasan Naseer ya dawo rayuwata ne. D'akina na Shiga na kwanta ganin Banga kayan makarantarsu Zahira da jakunnan makarantarsu ba yasa nasan sun tafi makaranta. Hawaye kawai nake Ina tunanin hanyar da Zan bi wajen barin rayuwar Naseer na har abada. Allah yasan Ina kaunarsa Amma ya zama Dole mu rabu idan kuwa ya zargeni sabida bashida kudi na rabu dashi baimin adalci ba Dan ko kanwarsa ake matsawa Haka ya Bata shawarar ta hakura da auren. Ina jiyo Naseer na Mata kana Nan rantsuwa Akan yasan Halina ko shekara goma zaiyi Zan rik'e Masa amanar aurensa wlh Dan Nan NASA ne Dan Allah ta karbi jaririn taga yanda Suke kama. Ita kuwa Umma dagewa kawai take Tana rantsuwar ba dansa bane Wai Ni Mata nake Haifowa inaji tana balai Yana Bata hakuri. Inaga Safiyya ce ta saka Baki naji ya daka Mata wani uban tsawa daya saka jaririna razana ya saka kuka. Naseer kuwa kukansa Bai sa ya bar wanke Safiyya.kamar zai ajiye jaririn ya rufeta da duka ba yayi ta cewa ta Kai shi bango wlh xai koreta daga gidansa Dan bazata Zo tana hura Masa wuta a gida ba shiyasan wani zubin ita ke zuga Umma. Ita kuwa Umma cewa take "Kar ka wani wayance Ni zaka yiwa fada ba ita ba tunda Ni nake Maka magana" Kukan Jaririn yasa Naseer bai ce wa Umma komai ba ya nufo d'akina Ransa a balain b'ace Yana shigowa d'akin. Ya mikomin shi na karbe shi take kuwa yayi shiru na Ciro abincinsa na saka Masa a baki tare da bismillahi ya kuwa cafe da Sauri a fili nace "Allah ya rayaka Walid ya shiryaka bisa tafarkin musulunci" Ameen Naseer yace can kasar murya idonsa ya kad'a yayi jawur ban nuna Masa naji Haushin abinda umma tamin a fuska ba Amma ya juyo ya hau bani hakuri Yana na taimaka masa mahaifiyarsa ce babu yanda zaiyi da ita Yana Nan Yana gayawa Allah. Murmushi kawai nayi Dan daya bani hakuri da Kar ya bani hakuri na Riga da na yanke hukunci a raina. Ce Masa nayi ba komai kar ya damu. Sai a lokacin ya saki ajiyar zuciya masu markade da suka zo yasa ya mik'e Yana Bari ya markada musu. Amma kafin Nan Bari ya saka Safiyya ta dafamin ruwan tea da Sauri na ce ba sai ya sakata ba ya Bari na Gama bashi Zan fito na Dora ruwan da kaina tunda Dama Ina bukatar ruwa Mai yawa sabida ma nayi wanka na wanke Walid. Har zai Musa min Kuma ya fasa Yana bari ya fara doramin ruwan inyaso sai ya fara markaden. Nima.fada kawai nayi bazan iya tashi ba sabida jirin danake ji. A kitchen ya tarar da Safiyya itama ta juye musu ruwan zafi a jug ga kwai ta soya a faranti duk a kudin Naeema da suke Mata fin k'arfi su kwace. Yanda Naseer ya hade Rai yasa ta fice daga kitchen din da Sauri. Tana fita ya Dora ruwa a babban tukunya ya fito ya kunna engine ya fara markaden. Yana cikin yi ma Isihu ya shigo ya fara markaden. Shi kuwa Naseer ya koma.dakin ya d'auko ledar zanin da Naeema ta Bata ya zuba a katon baho dayake akwai Omo da dettol a bandaki ya zuba ya koma kitchen Ganin ruwan yayi zafi sosai yasa ya cika flask ya Kai daki ya juya sauran a katon Bokiti. Duk abinda yake Umma da Safiyya binsa kawai suke da kallo. Umma kuwa kamar ta fashe Dan bakin cikin yanda Naseer yake neman Zama bawan Naeema Shayi Mai kauri ya hadamin ni kuwa na fara sha Ganin Yana k'ok'arin fita yasa nace Masa Dan Allah ya bawa Isihu kudi idan ya gama markaden ya siyo.min nama bakina ba dadi. Zama yayi a gefena Yana "Naeema ba asan Raina Kika haihu banida ko sisi ba wlh bana Jin dadi Amma ba yanda zanyi Haka Allah ya hukunta Naeema na baki labarin ban zo gidanan da ko biyar ba Kar muzo muyita kashe kudin ya Kare kiyi maneji da Abunda Kika samu gaba idan Allah ya hore duk Zan Miki Abunda ban miki ba a haihuwar Nan" Murmushi nayi na ajiye kofin hannuna Dana Gama shanye shayin na kalli Naseer Ina "Naseer karka damu Ni Mai fadawa wani ne halinka idan kana dashi ma baya b'uya amma karka damu Ina da kudi ba iya na hannunka ne damu ba a d'akin Nan ma akwai kudi Banda dashin danake har ajiya nake badawa ka Bari idan na samu Kaina sosai zamuyi shawara ko zaka fitar da shago ka Dan zuba provision ka ringa siyarwa da zaman hakan. Tun kafin na karasa Naga Naseer ya washe baki ya hau murna Yana shimin albarka. Yana "Kice idan su Zahira sun dawo na fita kasuwa da kaina na siyo Dana Kaya Dan Naga kayan mata Kika siyo Masa yanzu na kashe duk kudin wajena"? "Gyad'a Masa Kai nayi Ina murmushi" Ya fice waje da Sauri Yana murmushi Ni kuwa Jin na Dan ji kwarin jikina yasa na mik'e na hada ruwan zafi a na wanke Walid na shirya shi na rufo kofata Nima na Shiga wankan. Naseer kuwa Yana fitowa daga d'akina kayan Naeema daya jika ya sunkuya Dan ya wanke. Hajara ta mik'e a fusace Tare da daka Masa wani uban tsawa "Kai yanzu Dan asara da mutuwar zuciya Mai aiki Naeema ta maidaka kenan sabida baka da kudi shine ta hadoka da wankinta kayi Mata kana matsayin mijinta? Da lokacin da kake da kudi Kai kake mata wankin dayake Bata da mutunci sabida taga bakada ko sisi shine zata ce ka wanke mata kayan jini toh wlh bazaka wanke ba indai nice na Haifeka bazaka yi wankin Nan ba" "Umma wlh Ni nake Mata wanki idan ta haihu bawai ita ta Sakani ba Dan gani nake Bata da Mai matan idan bani ba" "Toh wlh bazaka wanke ba idan Kuma ban Isa dakai ba zaka iya wanke Mata" Umma tace tana jijjiga k'afa. Duk Inda Naseer yaso shawo Kan Umma tub'urewa tayi. Ni kuwa Ina Jin duk abinda ke faruwa hakane yasa Ina saka Kaya na fito Ban ko kalli Inda Umma da Naseer suke tsaye cirko cirko ba na jawo bahon na hau wanke kayana. Umma kuwa ta hau zagina tana ita tasan asirce mata da nayi ban Isa na bautar Mata da D'a ba. Bance Mata komai ba Naseer kuwa kamar yayi kuka sai neman kwayar idona yake Dan ya bani hakuri nak'i kallonsa. Sai Dana Gama wankina na shanya na Shiga kitchen Dan Ni Dama tunda na auri Naseer bansan Zama Wai na huta idan na haihu ba Ni nake komai nawa. Girki na Dora naje na dauki robar custard da gwangwanin da ya cika da kudin markade Na zuba a ledar dana gani na ajiye gwangwanin custard din na koma d'akina. Ina cikin had'a kudin Naseer ya shigo yana k'ok'arin Magana nayi sauri na dakatar dashi. Ina Kar yace komai indai Umma ce na Riga da na Saba da kome zatamin ba wani Abu sabo. Bai iya cemin komai ba yayi shiru Ina Gama hada Kan kudin na cusa a akwatina ganin waleed na bacci yasa na Kara barin d'akin na koma kitchen na zauna Dan girkina yayi na sauke. Ina cikin juye abincin su Zahira suka dawo. Ina ganin ta dawo na bar kitchen din dan nasan zata karasa min girkin. Su Minal kuwa d'akina sukayi aguje suna murna sunyi Kani irin murnar da suke ne Yasa na manta da damuwar da nake ciki. A takaice da kudina na wajen Naseer Naseer ya siyowa Waleed Kaya har dasu Zahira ya taho da Naman danace Masa. Duk abinda Muke ciki Umma idonta na Kai. Kudin dashina kwana uku da haihuwa nasa aka karbomin na bawa Isihu Dubu goma akan ya kaiwa Matar Ala.ramma Dan a gidansu na siyi katon ragon da zaa yanka duk da ba haihuwar fari nayi ba Amma kasancewar namiji ne hakane yasa na saki bakin Aljihu nayi dinkuna nayi komai na taron Sunan Waleed Naseer sosai.nake ganin farinciki kwance a fuskarsa Dan shima burinsa yayi taron Amma bashida kudi Shima dinki na Masa kala biyu. Umma kuwa ta Kira shi ta hau balai tana masifar sai ya tambayeni Ina na samu kudi Haka sanan ya zaayi nayiwa kowa dinki har da shege Isihu ita da Safiyya ban.musu ba. Naseer kuwa ce Mata yake ba shi yayi dinki ba Ni na musu komai.na gidan Ni nayi. Ita kuwa Umma dagewa tayi sai Nima na musu dinki. Ni kuwa Naseer da Yar murya ya zo wajena Yana na bashi Rance Ni kuwa na murzawa idona toka nace Masa bazan bayar ba Dan kudin karuwanci ne Ashe Umma na labe tana jinmu ita kuwa ta hau tsinemin tana gwara Kar na Bata mantawa.ma tayi kudin karuwanci ne. Sosai sunan Waleed ya cika da mutane har k'ofar gida. Abinci kuwa sai da aka rabawa mak'ota mmn Mannir ma sai data zomin itama da abun arzkiki har da.makotana da mukayi zaman mutunci dasu. Na yarda idan kana da abin hannun ka mutane har rububin muamalla suke Yi dakai. Bazan iya lissafa Abubuwan Dana samu a sunan Walid ba Dan har na kusa maida kudin Dana kashe masu kawomin markade da customers Dina masu siyan zobo da ruwa duk baa barsu a baya ba Haka suka ringa zuwarmin barka da abin arziki. Daga Ni har yarana da Naseer Shar mukayi bazaka yarda muna cikin wani matsala ba. Umma kuwa da Safiyya tsabar bakin ciki barin gidan sukayi Basu dawo ba sai da aka Gama taron Makotan arziki suka Tayani wanke komai da gidan. Ai fa Bayan suna Umma kamar ta jefani a wuta matsamin tayi ta sakoni a gaba a gaban Naseer zata Zo har d'akina tayi ya zagina tana tsinemin Wai nayi asiri na kwace dukiyar Naseer. Naseer ya zama kamar Dan aiki a gidan Dan Haka na fada Mata Inda naje nayiwa Naseer asiri. Idan Ina San nayi magana sai ta saki ihu ta hau cewa na Mata rashin kunya Naseer na kallo. Naseer masifar.umma yasa Dan kwanciya hankalin daya samu ya fara Rama. Ni kuwa a hankali na fara kwashe.kayana Ina bawa Isihu Yana kaimin gidan matar Ala ramma Dan Bayan mmn Mannir itace mace ta biyu Dana bud'ewa cikina duk da shawarar data bani na sakani zubar da hawaye naji kamar bazan iya ba Amma babu yanda zanyi Haka Allah ya kaddaramin. Kwana hudu kenan Ina rashin lafiya da kuka a b'oye da Naga lokacin Dana saka wa.kaina barin gidan Naseer nata matsowa. A cikin yarana ba wacce nake balain tausayi kamar Zahira da Raheema ba Naseer ne a gabana ba yanzu yarana kawai nake tunani. Idan Naseer yaga Ina kuka hakuri yake bani Dan ya d'auka takurar da Umma takemin ne Nan kuwa bai San tunanin da nake daban ba. Ahaka dai ranar Dana sakawa kaina Bayan da Naseer ya tafi massallaci nayi sauri na goya Waleed a bayana. Na Shiga d'akin yarana a zaune na tada Zahira kamar ma batayi bacci ba Haka kawai naji hawaye na neman zubomin nayi sauri na mayar Ina ta tashi kanennta suyi sallah. Yanda na hade Rai yasa ta Shiga band'akin tana waiwayena kamar tasan tafiya zanyi. Dak'yar ta Shiga band'akin. Ni kuwa na toshe bakina sabida kukan dake neman k'wacemin na karewa yarana kallo na fito daga d'akin na ajiye zungureren wasikar Dana rubutawa Naseer a bakin kofar dakina na na fice daga gidan nabi ta Bayan gidanmu ta hanyar da ba fiye bi ta hanyar ba inayin Nisa da gidan Waleed ya fara tsalla kuka....... [6/28, 7:42 PM] Zannura: *NAGA TA KAINA* *NA SADNAF*🌸🌸 ®️ *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_* _{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_ *Free Novel* *Page din jiya duk haushin Naeema akeji akan ta gudu inaso ku ringa saka kanku a matsayinta she is a human being itama mutum ce Kamar kowa ita tasan azabar da take Sha a hannun uwar mijinta karku manta mutuwa ma na raba uwa da Yaya har uba ma Yara su tashi ba uwa ba uba Kuma yaran bazasu fasa rayuwar da Allah ya tsara musu ba yanda Allah ya tsallakar da ita da ga duk wani sharrinsu take rayye har yanzu Allah Nan zai Kare Mata yaranta Wanann shine guduwa da tayi na biyu na farko da yaran Naseer yabi bayansu ta dawo abubuwa suka Kara cakudewa har ya Kai su ga Zama a cikin wanan halin ta bar Yara Dan Naseer Kar ya biyota kila ta gaji yau da gobe a Kuma Yi hakuri dai a cigaba da bibiyar labarin Ana Kai zuciya Nesa Kar a daki Naseer ko Naeema*🤣🤣🤣🤣🤣🤣 *This page is yours Surayyams Marubuciyar Ajalin so Ina San yanda kike bin novel din kike Kuma fito da lessons din ciki kina fahimtar da mutane* *Page 34* Kuka nake kawai Ina jijjiga Waleed da naji kukansa ya karade ko'ina kamar ya saka lasifaka Sauri nake ta zabgawa Ina ganin Kamar Kukan waleed na iya sawa Naseer ya biyomu tunanina rabuwa gida biyu yayi Ina tuno yanda Zahira ta Shiga band'aki tana waiwayena. Irin dukan da Safiyya da Umma ke Mata Agaban idona sabida kawai a yarana tafi Kama dani komai nawa ta d'auko kiyayyar da sukemin ya shafeta Anya matakin Dana dauka shi ya dace kuwa na bar Wa Umma yarana Ni nasan sai ta kashe su. "Idan Kika biyewa Makomar yaranki Uwar mijinki watarana zata ci Galaba akanki wajen rabaki da Numfashinki ganganci ne cigaba da zama da ita tunda kiyayyar da take Miki a bayyane yake Naeema rayuwa da kike gani kowa da yanda Allah ya tsara Masa yau da mutuwa kikayi fa Kika bar yaran?ko kinsan akwai yaran da tun suna kananu Suka taso ba uwa ba uba kin taba zuwa gidan marayu Kinga yaran da basu da kowa suke rayuwa su kadai Zahira shekararta Sha hud'u ta tafi na Sha biyar Nadeeya tana da Sha uku har ta iya girki ta kula da kanenta Kinga kuwa da wayonta. Kina ganin Naseer zai Bari Mahaifiyarsa ta cutar da yaransa idan ke ya bar mahaifiyarsa ta gana Miki azaba bana Jin zai Bari a tab'a Masa yaransa Dan Haka tafiyarki shi yafi alheri Neeema inyaso kiringa zuwa kina duba yaranki a Kai akai" Maganar matar Ala ramma da nake cewa Aunty ya fad'omin yanzu Haka ma gidan kanwar ta zanje na jirata idan gari ya waye zata kawomin kayana daga Nan su rakani Tasha Dan isihu ya dage sai yaje ya ga garinmu yaga Inda nake zaune kafin ya dawo Duk da hankalina ya rabu gida biyu ahaka nayita zabga Sauri har na iso bakin titi na tsallaka na cigaba da tafiya har lokacin kuka Waleed yake Ina jijjiga shi Nima kaina kukan nake a Haka na iso gidan kanwar Aunty na bubbuga ba dadewa kuwa ta bud'e dayake mun tab'a haduwa a gidan Ala ramma ta sani ta kuma San da zuwana Ciki na shiga ta rufe k'ofar Haka kawai na fashe da kuka da yake mijinta baya gari Palonta muka Shiga na kunto Waleed na rungume shi a kirjina Waleed Kamar yasan Mai ke faruwa bashida kuka amma sai gashi yana ta kuka. Hakuri kawai take bani tana rarrashina. Nidai gani nake kamar bazan iya tafiya na bar yarana ba ada na dauka zan iya Amma yanzu Kuma da na fito daga gidan Ina tuno yanda Suke wa yarana sai naji bazan iya ba. Dayake itama kanwar matar Ala ramma yayarta ta Bata labarin komai a kaina cikin tausayawa ta fara min magana tana "Ni sai nake ganin kamar guduwa ki bar yaranki bashine mafita ba Naeema kikayi hakuri duk tsawon lokacin Nan ballantana yanzu Agaban idonki ma Ana cin zalin yaranki Ina ga bakya Nan nidai Dan aunty ta dage ki tafi ne wlh da kinyi zamanki ai wuya Bata kissa Kuma komai Mai wucewa ne idan kayi hakuri idan. Allah ya raya Miki yaranki wlh da kansu zasu iya kwato Miki yanci a wajensu tunda ance Minal karama ma na musu rashin kunya Amma har ga Allah Nima ban goyi bayan tafiyarki ba" Cikin tsananin kuka na fara magana Ina "Ya zanyi Nagaji ne mmn Abdul nayi hakurin nayi biyayyar nayi rokon duk a banza shekara Sha biyar Ina k'unsar bakin ciki mmn Abdul ba Dan Ina da tsawon rayuwa ba da sun Dade da kasheni wlh gajiya nayi da abinda sukemin tacemin Ni Mayya ce naki rabuwa da danta Ina neman na kaina tace karuwanci nake yaron Nan sai data sheganta shi Naseer baya iya komai sai dai ya bani hakuri nace Miki da cikin yaron Nan guba suka zubamin a abinci Dan kawai naci na mutu yau da gobe watarana zata iya cin Nassara akaina shiyasa na yanke tafiya na bar Mata gidan indai na tafi da yarana wlh Naseer sai ya biyoni Ni Kuma shiyasa na bar yaran Dan tasan dgsk nake zan iya rayuwa babu Naseer Amma yanzu Dana bar gidan wlh sai naji kamar bazan iya tafiya ba Ina tausayin yarana da basu ji ba Basu gani ba bana San a cutarmin dasu gwara Ni na cigaba da Shan wahalar da su Sha wahalar. Kuka itama mmn Abdul ta hau yi tana "Allah ya tsinewa matar Nan Albarka k'arfi da yaji ta hanaki zaman lafiya da miji ta Kuma rabaki da yaranki Allah ubangiji ya saka miki" Kuka nake sosai har ta mik'e ta fita bud'e kofa da ake kwankwasawa sai Gata ta shigo ita da aunty da Niki Niki kayana Isihu shima da wasu kayan jikinsa a sanyaye shima Kamar zaiyi kukan Aunty palon ta shigo ta zauna tana "Ya Naga kuma kina kuka kinsan Allah Kika biyewa tausayin yaran bazaki iya tafiya ba gwara ki tafi tsinaniyar ta Gane ke kike rik'e da gidan ko ba ke bace kina da amfani a gidan ko bakida shi. Yanzu Nan na biya na karbi kudin engine nacewa wacce ta siya anjima ta je ta dauki injina Naga ta tsiya ba dai kin bar Wa Naseer kudi ba" Gyad'a Mata Kai kawai na iya Yi Ita kuwa ta cigaba da bambami "Maza share hawayenki ki tashi muje Tasha Dan inaso na dawo a yau d'inan karbi kudin injin" Tace tana mik'o min kudin hannunta Kasa karbar kudin nayi inajin kamar bazan iya tafiya ba nadamar ma siyar da engine din markade na nake yanzu dame su Naseer zasu ringa samun na abinci Ni sai na ringa nadamar ma daukar shawarar ta duk da nasan duk tayi hakane Wai Dan Umma ta Sha wahala Amma Ni Naseer da yarana nake tausayi. Tana k'ok'arin Magana mmn Abdul ta fara magana tana "Aunty sai nake ganin kamar tafiya ta bar yaran Nan bashine mafita ba ki dai sake tunani duk tsawon lokacin Nan wuyan data Sha sabida yaran Nan ne Bata gudu tun lokacin ba sai yanzu Kuma Naseer ya Mata hallaci da Bai cancanci Haka daga wajenta ba taurin Kai daya gwada.yaki bin umarnin Mahaifiyarsa ya jefa shi a halin da yake ciki Amma kwatsam yanzu yaga ta gudu ta barshi da Yara wlh zaiji ba dadi a ransa Ni nasan Mai yasa Baya iya yin komai mahaifiyarsa ce Bai San ya zai Mata ba Yana k'ok'arin biyayya ma tace Yana fifita Naeema akanta inaga Kuma ya fito ya nuna bayaso abinda ake yiwa Naeema kinsan abinda zatayi sai yafi Haka a gaskiya aunty ki duba maganar nan" "kimin shiru larai kinsan Mai matar Nan take yiwa Naeema kuwa?kinsan Abubuwan da duk take mata kuwa kasheta takeso tayi fa akan me zata cigaba da zama a gidan? Ke idan kece Zaki iya jure duk abubuwa da ake wa Naeema.?Naseer da kike magana akansa Naga guduwa yayi ya barta da yaran Naeema ita ta tsaya tsayin.daka ta nemi kudi duk da cikin jikinta ta tsayawa yaranta itace cinsu da shansu makarantar su abinda Naseer ya guje wa itace ta ringayi kwatsam wanan tsinaniyar matar Nan ta danno ita da kanwarsa suka hau gallaza Mata duk abinda zatayi idonsu.na Kai Naseer din ma ya dawo ba abinda ya canja sai ma gaba da yayi Dan me zata cigaba da zama wlh cigaba da zama a gidan kamar tana Wasa da rayuwarta ne Yara nawa ne suke rayuwwa ba iyaye ballantana yaran Nan da ubansu Dan nasan tafiyar.Naeema bashi zai saka shima ya tafi ba Dan Haka ya zama Dole ya kula dasu Kuma Nima duk abinda zasuyi idona na kansu tunda Isihu zai cigaba da zuwa gidan Kuma yaran na zuwa islamiyya Mallam idan dai ta musu wani Abu wlh Tallahi sai na Kai kararta na tsani matar Nan wlh Tallahi yau da nice Naeema da tuni nayi maganin matar nan" "Duk da haka Aunty Tafiyar Naeema bashine mafita ba dann kamar ka kashe miciji baka sari kansa ba Naeema zata tafi ne Amma tunanin ta na Nan Dan Haka Aunty Mai zai Hana tayi Zamanta a garin Nan Amma a wani unguwar hankalinta sai ya Dan fi kwanciya inyaso duk lokacin data so ganin yaranta zata iya zuwa gidanki a boye idan sun zo islamiyya sai ta gansu batare da Shi Naseer yasan Inda take a garin Nan ba ta Kama haya ta had'a Kan kudinta ta ringa sana'a Bansan lokacin Dana mik'e na rungume Mmn Abdul ba na kalli Aunty Ina "Aunty Dan Allah muyi hakan nima sai nafi samun kwanciya hankali a Haka ma wataran na kwashe yarana gabadaya batare da sun sani ba ki taimaka min Dan Allah banida kowa sai Allah sai ku danake ji Kamar Yan uwana" Aunty ajiyar zuciya ta sauke tana toh shikenan. Ni kuwa take naji sanyi a Raina Aunty ta koma ta zauna Suka fara shawarar Inda ya dace a samo min karamin gida na haya na zauna ahaka suka yanke nemo min gida a dorayi Dan suna da Yan uwa acan Amma kafin a samo gidan na dai tafi Bauchin na duba gidanmu na siyar sabida na samu ishahsen kudi a hannuna da zan ja jari. Haka kuwa akayi wajen karfe goma na nufi Tasha bayan Aunty tace min ita Kuma zata wuce dorayi ta cigitamin gidan Haya idan an samu kafin na dawo zata biya kudin hayan. NASEER Haka kawai yaji ya kasa nutsuwa yayi sallah hankalinsa yayo gida gabadaya hakane yasa Ana iddarwa ya fito da saurinsa a bakin kofa yayi kicibis da zahira dake k'ok'arin yin waje cikin tashin hankali Gabansa yanke wa yayi ya fadi Yana "Ke lafiya Ina Zaki"? "Abba Umma nake nema yanzu tace na Shiga bandaki nayi alwala na tashi su Nadeeya shine Dana fito banganta ba na duba koina banganta ba" Ta karashe da rawar murya idonta na cika da hawaye Naseer jikinsa ne ya hau rawa cikin tashin hankali ya Shiga gidan ya duba koina ya fito Yana sallati Tare da yin waje kafa ba takalmi duk nisan titi Haka ya je kafa ba takalmi Zahira na biye dashi tana kuka. Ba ta Inda Bai duba ba Bai ga Mai Kama da Naeema ba. Kamar Wanda ake sassarewa kafa Haka ya dawo gidan Yana Jan kafa Zahira nata kuka Dan tasan Naeema ta tafi ta barsu tunda kwana biyu kenan tana cewa ta kula da kanenta idan tace Umma tafiya zakiyi sai tace aa Naseer d'akin Naeema kawai ya nufa Yana Jin jiri na dib'arsa. Bayan ya d'au takardar da Naeema ta ajiye Mishi a bakin kofa. Ya kwanta rigingine hawayen da yake San maidawa ta karfi Suka hau zubo masa. Zahira kuwa Kamar wacce akayiwa duka tabi bayansa tana cigaba da kuka Ahaka Hajara da Safiyya suka fito sabida yanda kukan zahiran ke tashi Har d'akin Naeema Suka Shiga suna dube dube har Hajara na fatan Allah yasa Naeema ce ta mutu Zahira na ganin sun shigo ta hadiye kukanta da Sauri jikinta ya hau rawa Naseer kuwa ya bud'e idonsa yana kallon Hajara dake kalle kalle a d'akin ta dawo da kallonta Kan zahira tana "Ke Dan uwarki kukan me kike Mana da asubar nan"? Zahira bata iya magana ba ta matsa kusa da Naseer daya tashi zaune ya jingina da bango Yana kallon Mahaifiyarsa har lokacin hawaye na gudu a fuskar sa hawayen da ke Kara saka Zahira damke bakinta Dan Kar kuka ya kwace Mata a gabansu Hajara da take ganin tamkar malaikan da zai zare Mata Rai. "Dan uwarki bazaki gayamin ba kukan me kikeyi ke da ubanki ko uwarki ce ta mutu"? Wani irin murmushi daya fi kuka ciwo Naseer yayi ya d'auke hawayen fuskarsa ya kalli Hajara Yana " Ba mutuwa tayi ba ta dai tafi ta bar miki gidan Kamar yanda kikeso ta tafi da Waleed ta bar sauran yaran" Hajara Kara dudduba d'akin tayi Wai Dan ta gaskata maganar da kunnenta ke jiyo mata Naseer kuwa yanda Safiyya ta washe baki murnarta na fitowa fili yasa ya fara jifanta da wani irin kallo tayi waje da Sauri Hajara kuwa ta fito ta lek'a koina taga dagaske dai Naeema Bata Nan ta koma d'akin taja Tsaki Tana "Ni zaku rainawa Hankali yau ta Saba guduwan ta Kuma dawowa Naga Haka kuka rainamin hankali na gano kuna taren yanzu ta Inda kuka Kara b'ullo wa kenan ta tafi idan an kwana biyu sai ka bita Kai da yaran ko"? "Umma Naeema ta tafi idan da hada Baki mukayi da ita wlh bazaki gani a d'akin Nan Ina kuka ba da ace hada Baki mukayi bazata bar min yaran Nan ba barin yaran Nan da tayi ya Isa yasa kigane gajiya tayi da abinda kike Mata Umma sanin kanki ne banida komai Naeema ita ke rike da gidanan daidai da abincin da zamu ci ita take bamu yanzu data tafi daga Ina Zan fara Umma Ni Kam bansan Mai na Miki a rayuwata ba bansan Mai yasa kike San ganina a kuncin rayuwa ba" "Ba abinda kamin Dan albarka Naeema ce kawai na tsana karka wani damu da tafiyar da tayi dama so take kawai ta gudu Dan taga ka talauce iya tafiyar da tayi yaci Yasa kagane ba Dan Allah take zaune da Kai ba karka wani damu da ita take komai a gidanan Nima Zan cigaba daga Inda ta tsaya markade ne na iya zobo da ruwa nima na iya k'ulawa ai Dan Haka Kar ka wani damu Dan albarka idan Allah ya yarda da kaina Zan Nemo maka matar da zata zauna da Kai Dan Allah Mai ake da Naeema" Ta karashe tana yin waje cikin tsananin farinciki kamar wacce akayiwa bushara da gidan Aljanna. Naseer Bai iya ce Mata komai ba har ta fice Zahira kuwa ta matsa daga kusa dashi ta fita d'akinsu ta cigaba da kukanta Su Nadeeya na k'ok'arin fitowa daga d'akin Dan su shiga d'akin Naeema Suka hadu da Naseer a bakin kofa hakane yasa Suka koma ciki Naseer ya shiga d'akin ya zauna a tsakiyarsu Yana Jin zuciyarsa na Masa wani irin Nauyi Raheema da ke da shekara hudu ya kala ya d'auketa ya dorata a cinya Yana maida hawayen dake neman zubo Masa ya hau magana a fili Yana "Baki kyauta min ba Naeema baki min adalci ba da Kika gudu Kika barni da yaran Nan Mai yasa Kika gudu a lokacin da muka fi bukatarki?Mai na Miki da zafi Haka zakimin Haka"? Kinsan banida kowa sai Allah sai ke sai yarana ku nake gani naji dadi Amma Naeema Kika Shure Kika tafi sabida Mahaifiyata Tana Miki ba daidai ba duk hakurin Dana ringa Baki akan kiyi hakuri da halinta Nima addua nake Akan Allah ya shiryeta Naeema baki zabi guduwa ba sai a irin wanan lokacin ? akanki Mahaifiyata tamin Baki har yau bana ganin daidai duk kudin Dana rik'e basa albarka na zabi Zama dake a kowane Hali na zabi nayi rayuwar talauci Dan kawai na zauna dake Bayan irin kudaden Dana Kama a baya duk ban damu da rasa sun danayi ba sabida ke Amma yau sabida tsangwamar da Mahaifiyata ta Miki Kika gudu Kika barni da Yara Mai yasa Naeema Mai kikeso nacewa yaranmu"? Naseer ya karashe muryarsa na rawa magana yake shi kadai kamar da Naeema yake magana Nadeeya da Minal kuwa cewa suke Ina ummansu taje.haka Suka lek'a d'akin Suka dawo Suma Suka hau kukan. Hakane yasa Naseer ya share hawayensa Yana Zahira ta tashi ta Dora musu abinci su tafi makaranta. Zahira hka tayi waje tana share hawayenta. Naseer kuwa ya warware takardar da Naeema ta ajiye Mishi ya fara karantawa *NASEER KAYI HAKURI DA MATAKIN DANA D'AUKA NA RABUWA DA KAI NAGAJI DA ABINDA UMMA DA AUNTY SAFIYYA KEMIN NAGAJI NASEER UMMA TACE NI MAYYA CE TACE NI KARUWA CE BA IRIN ABINDA UMMA BATAMIN INA SHANYEWA AMMA YANZU NAGAJI DAN NAGA KIYAYAR DA TAKEMIN KARUWA YAKE BA RAGUWA BA KIYAYYAR DA TAKEMIN YA SHAFI YARANA GABADAYA DAN HAKA KAFIN NA HAIHU NA MATA ALKAWARIN RABUWA DA KAI INDAI ALLAH YA SAUKENI LAFIYA HAKANE YASA NA CIKA MATA WANAN ALKWARIN DANA D'AUKA NA TAFIYA NA BAR RAYUWARKU NA HAR ABADA ZAN RINGA ZUWA GANIN YARANA INSHA ALLAHU KASA KANKA A MATSAYINA KO KAINE MATAKIN DA ZAKA DAUKA KENAN A KARSHE NASEER NA HADAKA DA GIRMAN ALLAH KA KULARMIN DA YARANA KARKA BARI A CUTARMIN DASU NASEER BAZAN YAFE MAKA BA IDAN WANI ABU YA SAMESU NASERR UMMA TA TSANI ZAHIRA ITA DA AUNTY SAFIYYA NA BAKA LABARIN YANDA SUKE CIN ZALINTA A GABAN IDONA NASAN ZASU IYA KOMAI YANZU A BAYAN IDONA NASEER YARAN NAN AMANA NE A WAJEN MU KARKA BARI MAHAIFIYARKA TA CUTARMIN DASU NASEER KASAN YANDA NAKE KAUNAR YARANA BA ASAN RAINA NA TAFI NA BARSU BA DAN ALLAH KA KULARMIN DA SU NA BAKA AMANARSU AN FI TSANAR ZAHIRA KA SA IDO AKAN SU NA AJIYE MAKA KUDI A KARKASHIN KATIFA MAI YAWA ZAI ISA KAJA JARI KA KULARMIN DA YARANA NA SIYAR DA INJINA NA GUDA BIYU SABIDA NA HADA DA KUDIN WAJENA NA JA JARI NIMA KAYI HAKURI HAKA ALLAH YA KADDARA MANA RABUWAR MU SHI YAFMIN ALHERI DAN UMMA KARFI DA YAJI TAKE SAN KASHENI KAYI HAKURI BA A SAN RAINA NA GUDU BA NGD DA KAUNARKA A GARENI DUK.LOKACIN DANA TASHI ZUWA GANIN YARANA ZAN TAHO DA WALEED KA GANSHI* cukwikuye takarda Naseer yayi batare da ya karasa karanta Takadar ba sabida yanda jikinsa ke rawa zuciyarsa tayi balain nauyi a fili yace "Ni kuma tawa kaddarar kenan Allah ka bani ikon cinye wanan jarrabawa ka bani ikon sauke nauyin daka doramin na yarana. Waje ya fita yaga Safiyya na shara tana wake wake su Nadeeya sunyi cirko.kamar marayu Zahira kuwa Tana Kitchen ta kurawa waje daya Ido Kitchen din ya Shiga ya cigaba da girkin yacewa zahira ta shirya kannenta kafin ya Gama Yana gamawa a faranti ya juye musu ya Kai abincin har Palo ya zaunar da Raheema a cinyarsa ya hau Bata a baki Nadeeya da Zahira kuwa kasa cin abincin sukayi duk yanda yayi dasu kuwa Akan suci abincin. Ahaka suka fito Bayan ya d'auki naira Hamsin ya rakasu har bakin makaranta sai daya ga shigarsu ya koma gida. Sai dai tundaga nesa ya hango Hajara taci uwar damara ta Hana a fita da engine da wasu maza Suka zo dauka sai balai take tana tsalle tana hango shi ta nufo wajensa da Sauri tana "Kajimin shegu tsinannu Haka kawai suka zo d'aukar engine Wai wacce ta siya ce tace su zo su dauka Naga engine Naeema ne wacce matar Kuma suke magana kaji barayi" "Naeema ta siyar da engine yanzu ba nata bane masu shine suka zo d'aukar kayansu" Naseer yace tare da cewa.mazan su dauka su tafi Ya shige gidan ya bar Hajara na balai bazata yarda a fita da engine ba Samarin kuwa ganin er tijara ce da k'arfi Suka fita da engine Hajara data tare hanya suka hankadata gefe ta zub'e a kasa Safiyya itama ta hau rantsuwar bazaa fita da engine ba Dan sosai suka.gama lissafa yanda zasu samu kudi da engine Umma har da lissafin zata siyi fili Dan sunga yanda Naeema ke samun kudi da engine markaden sosai suka tiki rawa a dakin Dan murnar tafiyar naeema.sai gashi Ashe ma ta siyar da engine Suna ji suna gani aka tafi da engine Hajara Kamar tababbiya ta nufi d'akin da Naseer ke kwance......... *Comment* Nikuwa aganina batayi kuskure ba Ayadda Dan Adam,musamman ma mace take da rauni ai baza'ace ma naeema komi ba Dan kuwa tayi balain kokari... Awajena bunda ya dace tayi kenan adaidai wannan gabar. Ki duba fa Da can sunce arxikin shi yasa ta makale masa Amma yanzu itace mai rufin asirin Amma kuma sunce kudin karuwanci ne Kuma dan naseer na taimakonta da aikin gida sunce tayi kudi ta mai dashi boyi boyi. Haba jamaa abun Sam babu dadi gaskiya ko mai tsananin Imani ne saiya raunana.. Tunda har ba ita da bakinta ta nemi saki kotayi fitar fushi wallhy harga Allah batada wani lpya Her decision was based on nazarin data rinka yi ba acikin son zuciya da gaggawa ta yanke shi.. Inhar da ace nice naseer wallhy zan kyaleta hakanan itama taje ta huta Amma bazann taba in saketa ba,ai zataje din Kuma itama zataji abunda yaji aransa lokacin dayayi tunanin guduwa ya barsu acikin ukubu shine mafita. Hanklinta na kwanciya zakiga ta dawo ,but ni banga lefinta ba kokadan Every body derserve a break and refilled. In dauriya yayi yawa sheidan yakan saurin batar da mutum ta hanyar rusa masa aikinsa da mugayen tunani har akaiga kayi asarar tulin hakuri da jajircewan da kayi,Is best dat she leave queitly gaskiya.👍🏻 [6/29, 10:22 PM] Zannura: *NAGA TA KAINA* *NA SADNAF*🌸🌸 ®️ *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_* _{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_ *Free Novel* *Page 35* "Kana kallo Suka fita da engine baka hanasu ba yanzu ta Ina zamu ringa samun kudin da zamu kashe"? "Toh Mai engine ta siyar da kayanta Mai shi yazo ya d'auka ta Ina Zan Hana Umma abinda ba nawa ba" "Kai Amma yarinya nan Allah sai ya tsine Mata muguwa idan ba mugunta ba ai ko Dan yaranta ta bar engine dinan sabida a samu na kula dasu Amma dayake bata da mutunci shine ta siyar da engine duka biyu idan ma tayi hakane Dan mugunta ai har da yayanta ta cuta wlh dadin abin ba iya markade akeyi a gidan ba Ana kulla zobo da ruwa Kuma a siyar Nima dai ba kuturwa bace inada hannun da Zan kula ruwa da zobon na samu na kaina wlh ko kallon yaranta bazan yi ba Kai Kuma zaman gida ai Bai kamaka ba tashi zaka Yi ka fita ka nemo kudi ba kazo ka shige daka ka kwanta Kai ga uwarka ta rabu da Kai ai Zama Bai kamaka ba ya zama dole kaje ka Nemo duk inda kudi yake ka nuna Mata Kai Dan halak ne insha Allahu sai kafi da arziki tashi Maza idan wanan shegen isihun yazo Zan aikeshi yamin cafenen zobon na hada ya kaimun" "Ko na fita Umma bazan samu ko sisi ba ko na samu ma bazai Yi albarka ba Dan kin riga da kin tsinewa samuna Umma ko mantawa kikayi kin Kona duk dukiyata ta bakin naki kudi sai yamin wahalar samu yanzu gashi ai kingani kudi Yana min wahalar samu Umma kusan wata Takwas nayi a Abuja Ina neman kudi cikin tsananin wahala Umma Wanda ma na Dan samo sai da Yan fashi suka kwace a hanya ba abinda na taba yanzu dayake albarka" "Duk ba Kai ka jawo ba sabida tsinanen taurin.kanka zuciya ya debeni nayi abinda nayi da Nima yazo ya shafeni Dan Haka batun ma Ni na jawo duk laifinka ne na saka albarka yanzu idan Allah ya yarda zaka samu kudi ka shirya kaje ka nemi kudi" Daga Haka ta fito tana tsinewa Naeema akan ta siyar musu da engine. Rai a bace Haka Suka zauna a tsakar gidan suna ta kwashewa Naeema albarka Dan canjin daya musu saura tasa Safiyya ta d'auko Suka lissafa abinda zasu kashe na hadin zobon suka zauna zaman jiran Isihu sai dai har karfe Sha biyu Basu ganshi ba ahaka Hajara ta lek'a da kanta Wai ko zata hango shi Nan ma Bata gan shi ba haka ta dawo ta Kara komawa d'akin Naeema ta tarar da Naseer a zaune a Kan Sallaya Dan tunda ya iddar da walha Bai bar Kan sallaya ba carbi kawai yake ja. "Kaga shegen almajirin Nan Bai zo ba inata jiransa tundazu ko dashi ta tafi ne"? Alama ya Mata da hannu alamar Bai Sani ba Hajara kuwa ranta ya b'aci tana "Kai bana San iskanci Naga duk abinda ma shegiyar matar Nan tayi ba abinda ya dameka sai Abu kake Kamar wani maraya toh tunda Bai zo ba Kai Kuma ka k'i fita ka Nemo Mana kudi sai ka tashi kaje kayo min cafenan zobo idan zuciyarka ta mutu Ni tawa ba ta mutu ba idan tafiyar Naeema ne ma yasa kake wani nonok'ewa zaka ware me dalla tashi ka siyomin zobo da suga da farin Leda" Ta karashe tana jefa mishi kudin hannunta. Naseer ya d'ago da rinannun idonsa Yana "Ina Safiyya Umma da Ni zanje na siyo Umma Dan banida kudi Bai Kamata na zama kamar yaro da sai yanda akayi dashi wanan ma na iya janyo min raini a wajen Safiyya Ina gaba da ita ki wuceta kizo ki aikeni haba Umma" "Kace kawai ban Isa dakai ba Naseer ai kafita sanin unguwar Nan sai ka fita sanin Inda ake siyar da kayan zobon shiyasa na kawo maka" "Ki Bata idan ta fita tayi tambaya zaa nuna Mata" "Nifa bazaka zauna a gida ni Kuma na ringa fafutukar neman kudi ba Dan Haka ko bazaka siyo ba ka zura rigarka ko dakone kaje kayi Dan Idan ma takamarka Kayan abinci da ake dashi a gidanan ne kwanan Nan zai Kare wlh Nima yanzu sama na da kasana iya kudin Nan ne Dani Dan Haka nemo kudi ya kamaka" Daga Haka ta fice daga d'akin ta bawa Safiyya kudin ta lissafa mata abinda zata siyo Mata ta karbi kudin tayi waje tana zagin isihun da Bai zo ba Naseer kuwa Yana fitowa Kitchen ya Shiga ya fara k'ok'arin dorawa su Zahira abincin Rana Hajara kuwa tace ya fita idan Safiyya ta dawo zata Dora musu abincin. Naseer Bai. Ce Mata komai ba ya cigaba da abinda yake Dan wasikar da Naeema ta bashi na ya rik'e amanar yayansa ya rik'e gam akansa bazai soma barin Safiyya ko mahaifiyarsa su dafawa yaransa abinci ba. Haka Hajara tayi ta bambamin fad'a har Safiyya ta dawo. Dayake taliya Naseer ya Dora musu Nan da Nan ya Gama Dan akwai Miya Mai yawa a freezer din dake d'akin Naeema Dan har freezer ta siya da ta samu kudi ta daina siyan kankara. Haka take Miya Mai yawa sai dai su dafa shinkafa ko taliya Miya tuwo ma Haka take yinshi da yawa. Yana gamawa ya zuba wa su Hajara a kularsu ya d'auki sauran ya Kai daki Kamar yanda yaga Naeema nayi Ya daura alwala ya fice daga gidan Hajara da Safiyya dake kula zobo da ruwa suka bishi da kallo har ya fice. A Kular da Naeema take zuba zobo da ruwan Suka zuba Hajara ta nufi d'akin Naeema Dan ta dauko kankara sai dai tana zuwa taga k'ofar a kulle. Masifa ta ringa surfawa akan me Naseer zai kulle k'ofar d'akin Mai ya mayar dasune. Haka ta koma ganin Bata San lokacin da Naseer zai dawo ba yasa ta bawa Safiyya sauran kudin hannunta ta siyo musu kankara Suka zuba Suka zauna zaman jiran Isihu da sai daya Sha tsinuwa yafi cikin kwando Hajara har da Shan alwashin wanka Masa Mari idan yazo. Naseer kuwa Yana fita a Massallacin dake kallon gidansa yayi zamansa bayan ya iddar da sallah Yana tunanin yanda zai fara fuskantar rayuwa batare da Naeema ba Bai San Mai yasa Bai tab'a koyawa kansa rayuwa batare da ita ba a yanzu da ta tafi a lokacin da Bai tab'a tunani ba sai yaji Kamar rayuwarsa ce ta tsaya Amma ba yanda zaiyi Haka zai rungume sabon Shafin kaddarar daya bud'e Masa. Ganin biyu tayi yasa ya fito daga Massallacin a daidai lokacin daya hango su Zahira suna Shiga gidan. Hakane yasa yabi bayansu. Suka Shiga gidan kusan a tare. Daga Safiyya har Hajaran ba Wanda ya amsa Sallamar da sukayi. "Ka ajiye Mana abinci ba Miya ka Kama kanya ka fice tare da kullo k'ofar d'akin da bansani ba ko Gwal aka saka da zaa ringa rufewa sanan name idan an gama girki zaa wani shige dashi d'aki to daga Yau wlh idan anyi abinci Kar akara Shiga dashi d'aki idan uwarsu na Shiga dashi d'aki sabida Bata yarda Dani ba Kai ma yarda ne bakayi Dani ba shiyasa kake kaiwa daki kenan toh wlh Kar a sake idan ba Haka ba sai ranka ya b'aci" "Ke maza ajiye jakar hannunki ki je Makarantar islamiyyarku ki kiramin wanan shegen almajirin tundazu na zauna Ina jiranshi yazo.ya kaimin zobo da ruwa har yanzu Bai zo ba narasa Mai ya Hana shi zuwa ko Uwarku ce ma ta zuga shi tace.kar yazo Dan ta tafi" Hajara tace tana hararar Zahira data yi saurin ajiye Jakarta cikin rawar jiki zata yi waje Naseer yayi saurin rike Mata hannu Yana "Bari ta fara cire uniform din jikinta taci abinci tayi Sallah kafin ta tafi yanzu Nan ta shigo gidan fa Bari ta Dan huta" "Iyyeee Naseer Ni nake Aiken Yarka kake hanata akan sai ta huta kafin taje kana cikin hayyacinka kuwa ko Tafiyar Naeema yasa ka fara shaye shaye toh wlh sai taje Naga idan ma aka siyar da ruwa da zobon Kai ma zaka ci a kudin Dan Haka maza wuce ki kiramin shi kafin naci ubanki" Da mugun gudu Zahira tayi waje. Naseer kuwa idonsa ya kad'a yayi ja shi kam zuciyarsa na Dab da bugawa sabida tashin hankali da rashin nutsuwa sosai yake Jin gidan na Masa zafi kamar ya hada kayansa ya rik'e hannun yayansa ya gudu barwa Hajara gidan Ahaka ya rik'e hanunsu Nadeeya suka Shiga karamin Palo ya cirewa Raheema uniform ita da Humaira ya saka musu wani kayan ya zubo musu abinci suka fara ci Nadeeya kuwa cewa take Umma Bata dawo ba? Bai kulata ba sabida gani yake magana ma wahala yake masa. Muryar Zahira dayaji yasa ya mik'e ya fita "Ance Baya Nan yayi tafiya" Zahira tace da rawar.murya "Maganata ta fito Ni nasan dashi ta tafi Dan da safe yake zuwa gidanan nan wanan abun da tayi ya tabbatar min da ita muguwa ce ta karshe wato shima isihun bazamu more shi ba toh ai shikenan kanta ta cuta wlh Dan ke Zaki kai min ruwa da zobon bazan dau asara ba wlh maza jeki cire Kaya kici abinci kizo ki dauka yanzu yanzu ki siyarmin" "Aaaa Umma Zahira bazata taba talla ba ba iya ita ba insha Allahu yarana baza suyi talla ba Haba Umma ko wani Kika ji Yana cewa zai Dora wa Zahira tala ai ke Mai hanawa ne Umma karki.manta yaran Nan ba iya Naeema ce ta haifesu ba yayana ne Kuma jikokinki Dan Haka Bai Kamata kiyayar da kikewa mahaifiyarsu ya shafesu ba da Raina bazan iya Bari yarana suyi Tallah ba Umma kiyi hakuri" Sakin Baki Hajara kawai tayi tana kallon Naseer dake ta kwara bayani "Yau Ina ganin ikon Allah toh iskanci nace taje tayi kake zabga min wanan Bayanin Naseer daga Kai har Naeema idonku ya rufe da San Yara bakwa so moresu ko ayi musu tarbiyya Naseer Naga idan ta siyar da ruwa da zobon kananun Abubuwan da babu Zan iya d'auke maka a gidanan tunda Kai zuciyarka ta mutu ka kasa fita ka nemo tundazu nake binka akan kaje ka Nemi kudi ka kasa sanann Dan nace Zahira ta Kai Mana tallan ruwa da zobo kace bazata je ba toh wlh sai taje idan dai har ka dage bazata je ba toh wlh sai dai Kai ka dauka ka kaimin da kanka tunda Ni na Haifeka na Kuma Isa dakai" "Da Zahira ta je tallan Nan Umma gwara na je da kaina Sanan Mai amfamin ita Safiyya da bazata je ba sai Yar karamar yarinya Nan zaa ce taje" Hajara na k'ok'arin Magana Naseer ya dakawa Safiyya tsawar daya gigita Safiyya ta mik'e batare da ta shirya ba "Dan uwarki d'auki zobo da ruwan kije ki siyar tunda kin k'i fito da miji kiyi aure Maza mik'e dan yarana ba bayi bane da Zaki Mike kafa a nemo.a kawo.miki ki dauka nace kafin na hada.kanki da bango Naseer yace Yana nufar Inda Safiyya take. "Wlh bazata je ba Naseeru tunda ka Hana Zahira zuwa Kai da kanka zaka je" "Wlh Nima bazanje ba Umma Dan Babu yanda kanwata tana zaune kina kallonta kice Zahira taje talla ko Ni wlh ko ta Kai tallan Nan ko ta barmin gidana umma Dan Nagaji da Zamanta a gidana ki dauka nace" "Wlh bazanje ba Haka kawai Zan d'auki kula akaina na fita talla da girmana da komai" Safiyya tace tana k'ok'arin Shiga d'akinsu. Naseer kuwa ya fusgota cikin zafin nama zuciyarsa na tafasa kwallo kawai yake da Safiyya tana zunduma ihu duka yake Kai.mata ko ta Ina Hajara kuwa ta hau rike Naseer tana ihun wlh ya cikata zata tsine Masa kashe Safiyya zaiyi Naseer da Ransa ya Kai kololuwa wajen b'aci idonsa ya rufe sosai baya ma Jin abinda Hajara ke cewa dan ji yake kamar dukan da yake wa Safiyya ne kawai zai rage Masa radadin zafin dayake ji a zuciyarsa . Hajara kuwa ganin idan batayi da gaske ba zai kashe Safiyya tana ji tana gani Muciya ta dauko aguje tayi Kan Naseer......... Ayi.maneji yau naje Dubiya [6/30, 10:22 PM] Zannura: *NAGA TA KAINA* *NA SADNAF*🌸🌸 ®️ *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_* _{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_ *Free Novel* *Page 36* Kafin ta Kai wajen Naseer din ta wurga tabaryar Naseer ya kauce da Sauri Safiyya kuwa a garin mik'ewa ta gudu muciya ya sauka akanta ta saki ihu tana dafe keyarta. Hajara Kuwa tsantsin Inda Suka kulla zobo da ruwa ya deb'eta ta Fadi kafarta ta lankwashe baya ta saki ihu. Naseer kuwa yayi kanta da Sauri ya dawo Mata da kafarta daidai Ita kuwa sai girgiza Kai take tana wayo kafata "Kaga abinda ka jawo ko Sabida Naeema ta tafi shine ka haukace kake neman kashe Safiyya Dan kawai nace Zahira ta Kai min talla shine ka dage bazata Kai ba sai dai Safiyya ta Kai tayaya Zan dorawa Safiya talla tana budurwa Banda bakada hankali Zahira kuwa yarinya ce Amma dayake bakada mutunci kana so ka nunamin ban Isa da Kai ba shine zaka ce bazata je ba gwara Safiyya ta tafi iya Nan Bai isheka ba sai ka hada Mata da duka" "Kiyi hakuri Safiyya Bata fi Zahira ba yanda kike ganin Bai Dace Safiyya ta je talla ba nima.haka nake ganin Bai Dace na bar Zahira ta tafi talla ba bawai Dan Baki Isa da ita bane kema kinsan duk abinda kike cewa ta Miki ban taba hanata ba Amma talla ne bazan yarda Zahira tayi da Raina ba Umma matsawar kudin kikeso sai dai ta Kai Miki tallan gaskiya amma matsawar bazata Kai ba wlh sai dai mu zauna Haka Umma Banga amfanin da Safiyya take min a gidanan ba Dan Ni nasan wasu Abubuwan wlh ita ke sawa kiyi shegiya Shaidaniya Wlh Nagaji da Zamanta a gidana Ki fada Mata ta fito da mijin Aure ko kunya Bata ji tana ta tsufa agabanki a madadin ta nemi Wanda zai Aureta shine ta zaune min a gida tana hadamin balai Umma keda yarana ne kawai kuka zame min Dole Safiyya ba Dole na bace Dan Haka wlh ko kudin na samo iya ke da yarana Zan ciyar bazan ciyar da ita ba" "Ai Ni nasan ka samu tabin hankali Naseer K'arfi da yaji ka haukace sabida Naeema ta tafi Safiyya ba akanka take zaune ba yata ce Kuma dolene ce tunda Kai Kace ba Dolenka bace Ni nasan zafin talauci dayake damunka ne yasa kake Neman hucewa akanmu talla Kuma danace Yarka tayi ai sabida Kai din ne Amma tunda kace Haka naji Amma wlh wanan dai bazanyi asararsa ba sai ka Nemo Mai zuwa ya siyr min dan yanda ka rantse ba Inda zahira zataje nima.na rantse ba Inda Safiyya zataje miji Kuma da kake magana idan Ana siyarwa a kasuwa ka siyo ka kawo Mata Naseeru da kake zancen ta fito da miji kana da kudin da zaka Mata kayan d'akine bakada ko sisi kazo kana zancen tayi aure idan Auren yazo yanzu da uban me zaa kaita bamu ajiye ko sisi ba kafita ka Nemo kudi ka k'i ka zauna zuciyarka ta mutu mace na ciyar da Kai Dan ta tafi ka haukace kana neman kashe min 'ya Naseer hannun Zahira ya rik'e da jkinta ke rawa sabida tsoro Rai a bace Suka Shiga karamin palo yabar Hajara na cigaba da masifar yazo ya biyata kudinta idan ba Haka ba ta huce akan yaransa Bazai iya cigaba da sauraren maganganunta dake barazanar buga Masa zuciya ba Naseer daki ya shige ya kwanta ringingine sabida ciwon da kansa keyi Sosai yake jinsa a takure kamar a prison a yau da Naeema ta tafi bazai iya misalta caza Masa Kai da Mahaifiyarsa tayi ba Wanda yakeji Kamar ya kwashi yayansa su bar Mata gidan inaga Naeema da ta kwashi shekaru tana fama da ita sosai yaji tausayin Naeema ya danne haushinta da yakeji wacce zata iya hakurin Zama da Mahaifiyarsa idan ba Naeema ba. Ya dauka Naeema Mahaifiyarsa ta tsana kila data tafi zai Samu sasauci daga masifarta sai gashi daga shi har yaransa Basu tsira ba ya rasa gane irin halin ta. Dak'yar ya taushi zuciyarsa ya fito wajensu Zahira da har ta ci abinci itama sun saka kayan islamiyya. Hannun Raheema da Humaira ya rike sukayi waje Minal da Nadeeya da Zahira suka bishi a baya Basu samu kowa a tsakar gidan ba sai Dan ihun Safiyya da ke tashi a d'akin Sabida daddane Mata jiki da Hajara keyi da ruwan zafi Dan ba karamin dakuwa tayi a wajen Naseer ba keyarta da muciya ya sameta ba karamin kumburewa yayi ba sai Allah ya Isa take zabgawa Naseer tana rantsuwar sai ta Rama Akan Zahira. A Haka Naseer ya rakasu har makaranta sai da suka Shiga ya juyo ya dawo gida. Yana Shiga gidan yayi kicibis da Kular ruwa da zobon Hajara na zaune ita kadai sai jijjiga k'afa take tana ganinsa ta mik'e tana "wlh ka dauka ka kaimin tunda ka dage Yarka bazata Kai ba dan bazan dau asara ba wlh kaji na rantse maka Safiyya Kuma da kake magana gata can a kwance bama gani take sosai ba sabida yanda ka kumbure Mata jiki. Nima ga k'afata Nan a kumbure inajin ma sai naje Naga likita sabida zugin da yake min banida Kuma ko sisi sai ka siyar Zan samu kudin ganin Likitan maza d'auki da ruwa da zobon na dari biyar da talatin ne" Naseer matsar da kulolin yyi gefe ya wuce ciki Hajara kuwa ta biyo shi tana cigaba da masifa a tsakiyar d'akin ta tsaya ya Shiga bandaki ya d'aura alwala Dan lokacin sallah La'asar ya wuce. Yana tada sallah tayi waje tana ya iddar tana jiransa Sai daya iddar da sallah ya daga katifa ya d'auko kudin da Naeema ta ajiye mishi. Wajen Dubu hamsin ne maida kudin yayi Bayan ya Ciro dari biyu guda uku ya saka a Al jihunsa ya yi waje. Har Hajara zata taso taga ya d'auki kula yayi waje ya dawo ya d'auki daya ya fita k'ofar gida Ya rabar wa da Yara ruwa da zobon yayi zamansa a k'ofar gida Yana tunanin Sana'ar da ya Kamata yayi da kudin da Naeema ta bashi batare da yayi nisa da gida ba Dan ko Naeema Bata ce Masa ya sakawa yaran Nan Ido ba halin mahaifiyarsa bazai Bari yayi nisa dasu ba. Sai da su Zahira suka dawo suka Shiga ciki gabadaya da kulolin Hajara da Safiyya na zaune Akan tabarma. Minal ya bawa kudin Akan ta kaiwa Hajaran Dan bama yaso ya karasa wajenta ta Kara tare shi da wani masifar . Minal na mik'a Mata kudin ta karbe da sauri ta hau kirgawa sai data tabbatar ya cika har da doriya ta washe baki tana k'ok'arin cusa kudin a zaninta Safiyya ta wafci dari biyu tana "bazaki janyo min wanan dukan kici kudin ke kadai ba anjima balangu Zan siyo naci" Hajara hannu ta Kai Dan ta kwace cikin masifa Safiyya ta rik'e kudin gam. Abincin dare ma Naseer ne ya dafa musu. Sai daya tabbatar da sunci sun koshi yasa suka fito da home work dinsu sukayi. Kafin bacci ya d'auki Zahira haka ta ringa Masa maganar Naeema Akan Dan Allah yabi bayanta ko ya Kai su wajenta sai daya daka Mata tsawa ta rufe bakinta da sauri. A ranar Naseer Bai iya runtsawa ba sabida tunani a karshe ya yanke Kara siyan engine markade guda biyu sauran canjin ya siya musu kayan abinci Yana kyautata zaton markaden ne zai saka su Dan samu kudin da asirinsu xai rufu batare da Kuma yayi nisa da yaransa ba duk da yasan sai n an samu matsala ta b'angaren mahaifiyarsa Amma da dai ta dorawa yarsa talla gwara ya siyi engine tunda abinda yasa takesan Zahira tayi tallan sabida rashin engine ne. Haka kuwa akayi Washegari da safe Bayan su Zahira sun tafi makaranta. Ya dauki kudin ya tafi kasuwa ya siyo injina biyu sauran canjin ya siya musu kayan abinci har dasu kayan sawa ya siyowa su Zahira da takalma. Kasancewar ranar Jumaa ne hakane yasa Bai iya komawa gida da wuri ba. Bai karasa gida ba sai wajen karfe uku na rana. Mai taxi na ckin sauke Masa injina yaji ihun zahira hakane yasa ya Shiga gidan aguje. Safiyya ce akan Zahira tana ta dukanta kamar ta Samu babba Hajara kuwa na zaune Akan kujera Dan tsugunno ta saka tsinken a bakinta tana ta sakace hakori Kamar Bata wajen. Minal da Nadeeya sai duka suke kaiwa Safiyya suna kuka. Tsabar rufewar da idon Safiyya yayi Sam Bata San da shigowar Naseer da jikinsa ya kwashi wani irin rawa ba Hajara kanta sai data tsorata da yanda ya shigo da balain sauri ta mik'e tana k'ok'arin yiwa Safiyya magana Naseer ya isa wajensu ya kaiwa Safiyya wani irin wawura ya hadata da bango ya shaketa Ta fara kakarin mutuwa. Hajara kuwa ihu ta saka Dan dagaske Naseer so yake ya kashe Safiyya fata kawai yake ta mutu a hannunsa a Kai shi gidan yari ya huta da bakin cikin Safiyya da Mahaifiyarsa. Duk dukan da Hajara take kaiwa Naseer Sam baiji ba har muciya sai daya karye a jikinsa Bai cikata ba Safiyya kuwa tuni ta sume a hannunsa. Hajara sai waje tayi da gudu ta Kira aka zo aka bambara Safiyya daga hannun Naseer. Hajara tayi Kan Safiyya tana ihun Naseer ya kashe Mata ya. Naseer kuwa d'akin ha Shiga ya hau watso da kayan Safiyya waje Yana ta bar Masa gidansa bazata Kara kwanar Masa a gida ba. A ranar ba karamin rikici akayi tsakanin Hajara da Naseer ba Dan da Safiyya ta farfado sai da Naseer ya fitar da ita waje Akan bazata Kara kwanan Masa a gida ba Hajara kuwa ta dage akan sai dai ya koresu su biyun K'arfi da Yaji Hajara ta Masa fin karfin ita mahaifiyarsa ce ta kulle Safiyya a daki Akan ba Inda zata je ai ba Haka kawai Safiyya ta daki zahiran ba rashin kunya tayi Mata. A ranar Naseer kwana yyi Yana kuka daga tafiya Naeema da zaa auna jininsa zaa iya ganin ya mugun Hawa sabida tashin hankali shi kam yasan rayuwar Zahira na cikin hatsari Bai tab'a ganin uwar da Bata San danta bata San jikokinta ba sai Mahaifiyarsa ya yarda uwa na iya tsanar matar danta Bai San uwa na tsanar danta ta tsani zaman lafiyarsa ba. Ya Zama Dole ya d'auki mataki inama Naeema ta tafi da Zahira da Nadeeya ta bar mishi sauran yaran bazai dauwama Yana zaman gida ba Dole wani uzurin ya taso yyi nesa da gida Amma in ya fita yasan yana ckin fargaba da rashin kwanciyar hankali. A takaice tundaga ranar Safiyya ta fara balain tsoron Naseer indai Yana Nan ko fitowa Bata iya Yi gashi baya fita sai dai idan Massallaci zaije. Akan engine markaden ma sai da sukayi rikici da Hajara ta dage sai dai ya bar Mata guda daya ya dau daya idan aka kawo.markade ita ta d'au daya shi ya dau daya sai dai me tunda aka siyo engine sau biyu aka kawo markade baa Kara kawowa ba Sabida masifar Hajara har suna Suka saka Mata a unguwar suna kiranta da masifafiyar tsohuwa. Naseer yanda ya d'auka zai samu kudi idan ya siyi engine markaden lura da yanda Naeema ke samun kudi Bai samu ba Dan bama zuwa ake ba wani zubin yana ma zaune a k'ofar gida zaa wuce gidansa a Kai wajen bakin titi da dai a Zo gidansa tuni damuwa tayi.masa yawa kasa da wata daya komai na gidan ya Kare Wanda sai da ta Kai shi da siyar da engine guda daya Dan Bai shigo Masa da kudin ba. A cikin kudin ya biya kudin makarantar su Zahira sauran canjin shima Nan da Nan ya Kare. Kafin kace me dayan ma sai daya siyar. Hajara kuwa masifa ta hau yi akan ita tasan Naeema ce tayi asiri aka ki kawo musu markade k'arfi da yaji tana ji tana gani Naseer ya siyar da engine data ci burin samun kudi dashi ta siyi filaye. Kamar ta fashe dan bakin ciki wata uku da tafiyar Naeema sai gashi abinda zasu saka a cikinsu Yana neman gaggararsu. Safiyya kuwa data ga bazata iya ba aikatau taje ta nema a wani gidan masu kudi zata ringa zuwa tana dawowa daddare. Idan taje abincin da ake Bata shi take kawowa gida taci Hajara na kallo idan tayi Magana kuwa Sai tace Mata kowa tasa ta fishe shi Naseer kuwa Dan abinda ya fita ya Dan samo sabida tuni ya nemi aikin lebura na gini ya farayi Dan kudin daya samu yake siyowa su Zahira abinda zasuci ahaka ma sai dai shi ya hakura Dan bazai iya barin Hajara da yunwa ba. Ahaka Safiyya tayi albashi Hajara tayi ta rokon ta Allah da annabi kafin ta yarda ta Bata wani Abun. Tana Bata kuwa ta siyo shinkafa da kayan Miya ta girka ta kakasafta a kwanu. Zahira na dawowa daga makaranta tasa ta cire uniform ta Dora Mata farantin Ta bawa Nadeeya Yar robar miyan tace musu su dau hanya su tafi su siyar Mata taja musu kunne akan kar su sake su dawo gida batare da sun siyar Mata ba idan Naseer ya Isa idan ya dawo ya mata magana yaga yanda zata Yi dashi Suna fita ta dakawa Minal tsawa Akan su saka kayan islamiyya su tafi. Minal sai data Dan gwada Mata taurin Kai ta dan bubuge ta kafin suka bar gidan. Naseer dake ta Dora bullo a wani gida da ake ginawa kamar ance ya daga kansa ya hango Zahira da Nadeeya na tafe a Gefen titi suna rarrabewa a gefe ga uban faranti akan Zahira ga Nadeeya itama da nata robar miyar. Naseer Bai San sanda ya duro Yana mirtsika Ido ba Dan ya tabbata da su Zahira yake gani. Jiki na rawa ya Isa wajensu. Ya sauke farantin dayake ganin yayi wa Zahira nauyi yace musu waye ya Dora musu talla. Ce Masa sukayi Hajara ce. Yayi shiru Ransa na balain baci. Dak'yar ya hadiye b'acin Ransa yace su zauna a wani dakali su jira shi Yana zuwa. Ba a cikin hankalinsa Suka karasa aikin ba Dan har sai da bulo ya Fado Masa a kafa Sabida tunani. Ana biyansa kudinsa ya wanke jikinsa ya cire kayan aikinsa ya maida Mai kyau jikinsa. Ya tsallaka wajen su Zahira ya d'auki farantin abincin. Ya rarrabawa almajirai Ya Kama hannunsu ya tare musu bus Suka hau suka nufi gwammaja. Bashida tabbacin Gane gidan Tijjani Amma ahaka yaje sai da kyar ya Gane gidan da kwantance. Suna zuwa k'ofar Gidan Tijjani na isowa a vespa. Ko parking baiyi sosai ba ya duro daga vespan Dan murna ya rungume Naseer cikin murna Naeema Kwana biyu kawai nayi a garinmu danaje da Ashe sun Dade suna nemana sosai naji mutuwar Mai unguwa da nake Jinsa tamkar mahaifina ashe shekara daya kenan da rasuwarsa Kafin rasuwarsa ya siyar da gidanmu ya boyemin kudin Dan lokacin sosai ake San siyan gidan hayan daya saka kuwa sai yaga ma.kamar mutanen ciki Bata gidan suke hakane yasa ya siyar da gidan Akan duk lokacin da Nazo zai bani ya kuma San bazanji Haushin siyarmin da gidan mu da yayi ba Dubu dari uku da sabain ya siyar da gidan namu. Kafin rasuwarsa Haka yayi ta rokan yayansa da matansa akan Dan Allah Kar su tabamin kudina duk lokacin Dana Zo a damka min kudina. Sosai naci kuka na Godewa Allah da rashin Mai unguwa a Haka na kwana biyu cikin zuciyata ba dadi uwa uba ga tunanin yarana daya dameni ko baccin kirki bana iya yi sabida Ina tunanin kamar suna can suna Shan duka a wajen Safiyya abinda zai taimakeni kawai shine Kila Naseer bazai yarda a tab'a min su ba da Wanan tunanin hankalina ke Dan kwanciya. Sosai iyalin Mai unguwa suka nunamin soyaya Dana tashi dawowa Dan Kaya Suka bani sosai na amfani Dan ban Gaya musu abinda ke faruwa Dani ba. Karfe uku na rana na iso gidan kanwar Aunty Ina zuwa kuwa na tada Aunty a gidan. Bazan manta Aunty a rayuwata ba tamin abunda har na mutu bazan manta alherinta a gareni ba. Ina sallahr La'asar muka nufi dorayi da ita. Ta kaini gidan data kama min ta hau min bayanin da kyar Mai gidan ya yarda ya bada haya Dan yace siyarwa zaiyi Amma ko yanzu ya samu Mai siya zai maidamin kudina ne na siyar. Gidan Mai kyau ne dakuna biyu da bandaki biyu da Palo sai dan karamin shago a k'ofar gida Gwada tambayarta nayi nawa ne gidan. Tacemin Dubu dari uku da ashirin Take nace Mata Zan siyi gidan Kamar Wasa ta rakani wajen Mai gidan na nemi ya siyarmin Dubu dari biyu da hamsin dak'yar ya siyar min a Dubu dari biyu da casain Washegari muka Kai Masa kudin gidan ya d'auko takarda gidan ya bani Aunty sai murna takemin ni kuwa sai tambayarta nake tana ganin yarana cemin tayi tana ganinsu kar na damu Naseer na kula dasu Dan ta saka Ido a kansu Take naji hankalina ya Dan kwanta. A. Cikin kwana uku naja wutan.nepa gidan Aunty ta Nemo min Katifa second hand na biya da Dan ledar tsakar daki da Dan kayan amfanin gida da bazaa rasa ba. Wata Hassana da take bazawara da ta kasance Yar uwarsu ta kawomin Akan mu ringa kwana tare Dan Ina tsoron kwana Ni kadai. Hassana kuwa zata iya girme min Amma tana da kirki Makotana na zaga na Dan duba abinda baa samu unguwar Naga har da dai markaden sai sunyi tafiya Mai nisa suke samu. Ana Kuma neman ruwan Sanyi kayan provision ma sai sun Yi tafiya Mai nisa. Take kuwa na nemi engine second hand na siya Dan gaskiya Ina San sanaar markaden dan ya shigomin da kudi Cikin Ikon Allah kuwa sati daya da siya aka faramin layi. Dan har Hassana Tayani takeyi idan na gaji. Kamar Wasa sauran kudin hannuna na Nemo kafinta ya bubbuga min canter na Dan zuba provision din kad'an su Maggi biscuit bredi da alewa da littattafai makaranta Dan Naga Ana yawan nema Shima sati da fara siyar da provision din Rabbi ya Sanya min albarka a hankali sai gashi shagon k'ofar gida ya cika da kaya. Sai gashi a cikin wata biyu har freezer na siya shima na saka a shagon Ina siyar da ruwa. Nikam a wanan gabar sai dai nace Alhamdulillah Dan kudi ko ta Ina shigomin suke abinda yake damuna Bai wuce kewan yarana danake kwana Ina mafarkinsu ba wani zubin a mumunan yanayi wanan Abu shi yake hanani sukuni ko abinci bana iya ci.gashi dai komai na samu cikin rufin asiri Amma tunanin yarana ya Sakani balain Rama Nafi tunanin Zahira Dan jikina na gayamin tana Shan wahala a hannun Umma da Safiyya Koda kuwa Naseer na nan. Sau uku Ina zuwa unguwar da likkaf na tsaya a k'ofar gida Naga ko Zan ga wani ya fito daga gidan a cikinsu sai dai bana ganinsu sai dai Naga Naseer daya balain Rama ya fita hayyacinsa sosai yake karyamin zuciya idan na ganshi ahaka zan karaci tsayuwata idan na gaji na karasa gidan Aunty tacemin Kar na damu dazu ma tagansu lafiya Lau suke ba Abunda ya samesu har tambayar Zahira tana yi dake da balain zurfin ciki tace mata ba komai. Ahaka Zan dawo da tunaninsu a Raina Nima rashinsu kusa Dani ne ya saka Ni mugun Rama Dan Sana'ar tawa Dan hassana na rik'ewa ne da bazan iya tab'uka komai ba a yanzu da aka tafi wata uku rabona da yayana naji bazan iya jurewa ba Ina bukatar ganinsu ko ta halin Kaka hakane Yasa na yanke zuwa gidan aunty idan sun zo islamiyya nagansu Koda daga nesa ne. Naseer.......... [7/1, 10:14 PM] Zannura: *NAGA TA KAINA* *NA SADNAF*🌸🌸 ®️ *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_* _{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_ *Free Novel* *Page 37* *Naseer* Tijjani cikin tsananin murna ya rik'e Hannun Zahira da Nadeeya yace su Shiga daga ciki Naseer ya girgiza Masa Kai Akan bazai shiga ba ya dai Shiga da yaran ciki su gaida Murjan Tijjani girgiza Kai yayi Yana wlh sai ya shiga ciki Taya ma zai Zo gidansa Bai Shiga ba Akan dole Naseer ya yarda suka shiga ciki Tijjani sai washe baki yake cikin murna. A tsakar gida Naseer ya coge. Tijjani kuwa sanin halinsa yasa ya dau babbar tabarma ya shimfida Naseer ya zauna shi ma ya zauna ya hau kwalawa Murja Kira Su Zahira kuwa sai kalle kalle suke suna daga gefensa hannunsa cikin Na Nadeeya. Yana tambayarsu Makaranta Murja fitowa tayi tana Hamma da cikinta da baifi na wata biyar ba ta tsani tana bacci a tasheta ko kad'an batasan da zuwan su Naseer ba hakane yasa ta fito da Daurin kirji Ganin Kuma Naseer Bai saka ta koma ba illa yatsina fuska da ta farayi tana karewa Su Zahira kallo da Tijjani keta washe baki yana cigaba da Jan su Zahira da Hira Naseer kuwa kansa a sunkuye yake so yake idan matar gidan ta fito su ka gaisa sai su fita da Tijjani waje suyi magana dake tafe dashi. Tijjani kuwa sai daya d'ago yaga Murjan ta daga labule daga bakin kofa ta toge Daga yanayin ta yasan Yan rashin mutunci ne Suka motsa hakane yasa ya mik'e ya Shiga ciki tare da Jan Murja su koma ciki yayi kasa da murya Yana "Ya Ina kiranki kizo ki gaisa da yayana zaki kame daga bakin kofa shine fa yayana Naseer danake baki labari wadanan yayansa ne Dan Allah ki Sako hijabi kizo ku gaisa Bata ce komai ba ta koma daki ta sako hijabin a rayuwarta ko kad'an Bata so wani ya rabesu har Tijjani ma bataso.taga Yana muamalla da mutane Dan ko abokaina ma cikin makirci take rabasu. Idan kaga wani a gidan toh danginta ko kawayenta ne Amma Tijjani kam bataso wani nasa yazo wajensa hakane yasa ta Sha mugayen alwashi idan tsautsayi ya sa su Hajara suka Kara dawowa gidanta sai ta musu abinda har su koma ga Allah bazasu manta da ita ba. Tijjani kuwa Yana fitowa Bai tsaya jiran fitowar Murja ba Dan ya Riga da yasan halinta ruwa da abincinsa ya d'auko yazo ya Ajiye a gabansu Naseer Yana yayi hakuri yanzu murjan zata fito yasan halin masu ciki. Daga Nan ya dau plate ya bud'e flask din ya hau zuba shinkafa da wake da akayi jollof dinsa da bushashen kifi Murja kuwa har wani turus tayi dan bakin ciki Dan tana da balain rowa ko wani ne ma yazo daga gidansu Haka zai karaci zamansa ya tafi batare da ta Masa tayin abinci ba ko da kuwa Tana cikin girkin kazo zata iya gwammacewa ta zauna da yunwa har sai ka tafi. Dak'yar ta saki Fuskarta Ta tsugunna daga bakin kofa ta hau gaida Naseer cikin faraa Naseer kuwa ya d'ago ya amsa cikin sakin fuska Yana Dan karantar yanayin Murja a fuska dai Kamar babu ruwanta zatayi saukin Kai hakane yasa ya Dan ji sanyi a Ransa Bayan sun Gama gaisawa ta koma ciki ta lab'e a jikin labule tana kallon Zahira da Nadeeya dake ta zabga Loma Sabida yunwar da suke ji Dan uniform kawai suka cire Hajara ta Dora musu talla Bata Bari sun ci abinci da Naseer ya boye musu a daki ba dan waje na musamman Naseer yake boye musu abinci a d'akin da iya su zahiran ne kawai zasu San abinci ne a wajen sabida Kar ma Hajara ko Safiyya suzo d'akin su dauke Kamar ta fashe Dan bakin ciki shi kuwa Naseer ture abincin da Tijjani ya ajiye daga gabansa yayi ya gyara murya ya Dan fara bawa Tijjani labarin duk halin da yake ciki da tafiyar Da Naeema tayi Sabida masifar Mahaifiyarsu da yanda itama Safiyya take cin zalin yaransa har zuwa Kan tallan da Mahaifiyarsa take dorawa yaransa da yasa ya zarto gidansa dasu. Tijjani shima labarin irin zaman da sukayi da ita ya bashi a karashe da "Wlh Naga bazan iya ba nace su tafi Dan wlh bazan iya jure abinda kake iya jurewar ba Umma a madadin ta ringa rike girmanta tana kwantar Mana da hankali sabida halin da muka tsinci kanmu na babu wanda duk ita ta jawo Mana fa hakan Bai isheta ba sai ta daga Mana hankali ba irin surutan da bata yimin Akan na rabu da Murja ba daga Aurenmu fa Ni ban taba ganin Mai irin Halin Umma ba wlh ita Kuma shegiya Safiyya a madadin ta ringa Gaya Mata gaskiya shine take tunzurata kamin daidai da ka Hana ta dorawa su Zahira talla Dan nikam bama Zan iya da ita ba Dan da nine ma wlh siyar da gidan zanyi na gudu da yarana k'arfi da yaji kana zaune kalau da matar rufin asiri ta rabaku toh Yaya yanzu wane aiki kake yi Taya zaka ringa aikin lebura dake da wahala nawa ma kudin yake da zai isheka ka kula da yaran nan.mai zai Hana ka nemi aiki wani wajen ko Allah zai saka ka Dace Kamar yanda Nima Allah ya taimakeni na samu aiki a wani company robobbi a sharada duk sati suna bamu Dubu biyu karshen wata Kuma su biyani Dubu goma da zaka samu irin wanan aikin Yaya nakega da yafi nima wani ne ya nemo min aikin Zan Masa magana idan Allah yasa. An Dace sai Kai ma ka ringa zuwa da Wanan aikin wahalar da kakeyi. "Tijjani Ina neman aikin samun ne dai banyi ba bazan iya kirga guraren Dana Kai takarduna ba Amma har yanzu baa Dace ba ya zanyi dole na ringa leburancin mu samu na abinci. Yanzu dai abinda yasa nazo wajenka so nake ka taimaka min Dan Allah Yaran Nan su zauna a wajenka zuwa Dan wani lokaci kafin na Shawo Kan Umma Dan wlh bana San tallan Nan duba kaga Zahira ta girma dan ma Bata da girman jiki Amma kana gani kasan ta fara Zama budurwa Taya Zan yarda a ringa Dora Mata talla Zahira da Nadeeya Umma tafi takura wa hakane yasa nace Bari na kawo su wajenka su zauna Ni Kuma yanzu idan na koma Zan nuna kamar bansan Inda suke ba kaga idan an kwana biyu sai nazo na daukesu Kamar angansu ne inaga hakane kawai zai saka Umma ta hakura da tallan da takeso suyi na k'arfi da yaji. Naso Naeema data tashi guduwa ta tafi da ko iya zahiran ne Ni Kuma bana San bin Bayan ta sabida Naeema tayi.hakurin da Umma koni bazan soma bin bayanta nace ta dawo ba gwara ta huta idan an kwana biyu sai na Kai Mata yaran intaga zata rikesu shikenan idan taga bazata iya ba sai mu dawo "Yaya ba sai ka hadani da Allah ba yaran Nan nima yayana ne Nan ma gidansu ne sauran ma idan kana ganin Umma zata takura musu ka kawo su wlh Zan rik'e su yanzu Ina cikin rufin asiri abinda zasu ci bazai gagareni ba insha Allahu Umma Kuma Allah ya shiryeta sai dai makarantarsu ne bansan ya zaayi ba tunda kace Zahira na primary 4 Kuma 3rd term "Hakura zasuyi na Dan lokaci kafin komai ya warware zanje makarantar da kaina Tijjani Nagode sosai da taimakonka a gareni Zahira da Nadeeya kawai nakeso su zauna anan Dan su tafi matsawa gobe zan dauko musu kayansu a boye na kawo musu insha Allahu sai dai ka taimaka min Kar su zauna haka su ringa zuwa islamiyya Dan Naga kamar akwai makarantun islamiyya a layin naku "Haba Yaya wlh bazan iya biyanka alherinka a gareni insha Allahu baka da matsala Kaya ka barshi Zan siya musu Koda gwanjo ne basai ka wahalar da kanka ba Zan Kuma saka su a islamiyya Ina samu kudi har bokon Zan iya saka su insha Allahu" Dafatan matarka bazata damu ba Dan bana San na takura ta "Haba Yaya wlh bazata damu ba ai Tama samu Yan tayin hira tana da san mutane sosai" "Tabdijam" Murja tace bayan ta Gama Jin duk abinda sukace Ta nufi d'akinta a fusace Naseer kuwa yayi ta yiwa Tijjani godiya Ya mike akan zai tafi ya Kira Murja ya Mata sallama. A daki ya tadda Murjan tana kad'a kafa ko lura da Fuskarta baiyi ba yace ta fito suyi Sallama yayansa zai tafi Daga hakanya saki labulen yayi waje Murjan ta bishi a baya tana kakalo faraa tana fitowa tayi kasa da Kai tana "Har zaku Tafi" "A uwargida Ni Kadai Zan tafi dai Su Zahira zasu Dan zauna su kwana biyu sabida wani Dan dalili dafatan Dan Allah ban takuraki ba" ? "Haba Yaya wane irin takura Nan ma ai gidane karka wani damu" Godiya Naseer yayi ta yiwa Murja. Murja kuwa har da rike hannun Nadeeya suyi rakiya har waje. Sai da suka daina hango su Tijjanin da suka hau Vespa Dan ya fita dashi titi Murja naganin sun wuce ta yarfar da Hannun Nadeeya ta ja baya tare da musu wani irin Mugun kallo tana "Yan bura uba daga zuwanku sabida kwadayi zaku hau cinye min abincin Dana girka shegu dangin kwadayi zaku ci.ubanku ne Dani kuke maganar Haka kawai Ina zaman zamana a kwaso.min gayya Yaya har guda biyu Uwarku ma ta kasa rikeku ta gudu shine Ni aka rainawa wayo.zaa wani kawoku wajena shi Kuma Tijjanin zai Zo ya sameni Kuma wlh kun Gama cin rabonku" Daga Haka ta wuce daki fuuu tana bakin cikin abincin ta da suka ci sosai ta ringa shirya ukubar da zatayi wa Yara da basuji ba Basu gani ba Wanda idan sukaji azaba da kafarsu zasu gudu. Zahira kuwa kuka ta fara yi Nadeeya kuwa na kikifta Ido Zahira duk da kankantar shekarunta gani take Bayan mahaifiyarsu da mahaifinsu Babu Mai kaunarsu har suna murna zasu zauna a gidan baba Tijjani da suke ganin kamar sai sunfi jinn dadin zaman Nan Akan gidansu sai dai daga yanda Murja ta musu yasa Zahira taji dama sun bi Bayan mahaifinsu. Tijjani kuwa Yana fita da Naseer bakin titi ya d'auko duk kudin jikinsa ya bashi ya kara Masa alkawarin idan ya samu sarari zai Zo idan sukayi albashi. Godiya Naseer ya Masa sosai ya tari bus da zai je gadon Kaya ya hau Tijjani Kuma ya juya ya koma gida Murja tana Jin karar vespa ta duro daga Kan gado tayi waje tayi wajen da su Zahira ke rab'e ta ruk'o hannun su biyun a daidai lokacin da Tijjani ya shigo da vespa ya Parker Murja kuwa ta hau cewa "kaga tunda kuka tafi nake fama dasu akan su shigo Suka k'i wanan kamar wata karamar Yarinya har da kukanta Wai sai tabi bayan Abbanta" Fa karashe tana nuna Zahira "Kukan me kike Yi Zahira bakya San ki zauna damu"? Tijjani yace a daidai lokacin da ya karasa wajensu Yana ruk'o hannun Zahira Girgiza Masa Kai Zahira tayi Murja kuwa ya harareta a fakaice sosai take ganin kamar Zahira munafinci ne yasa take kukan sabida ta hadata fada da Tijjanin. Dan duk da kame Mata Tijjani da mahaifiyarta tayi wani zubin inya tashi sai ya botse Mata. Cikin palon suka Shiga Tijjani ya zauna akan kujera Ya zaunar da Nadeeya a gefensa ya kalli Murja Yana "Dan Allah Kara Dora Mana wani abincin yunwa nakeji wlh" "Wlh na dazu ma dakyar na dafa ko dandanawa banyi ba ka bawa yaran Nan da babansu" "Toh sai nak'i Basu Murja wane irin magana kike Haka yayana na bawa abincin fa ke Mai yasa kike haka ne Mai da anzo wajenka ka bada abinci anci gaskiya ki gyara halinki Bari nayi Sallah na Shiga da kaina na dafa abincin Daga Haka ya mik'e ya shige dakin Murja ta bishi da wani irin kallo ta maido kallonta kansu Zahira datake ji kamar ta jawosu ta rufesu da duka Ahaka ta daure tayi waje ta Dora musu jollof din taliya tana zagin Naseer da yayansa da take ganin sun zo sun takura Mata. Taliyar kad'an ta dafa duk da basu da matsalar kayan abinci sabida su kadai ne Murja kuwa rowa bazai Bari ma ta dafa abincin da yawa ba ballantana har ya ragu su bawa almajiri. A plate ta juyo musu abincin Dan tare suke ci A Palo ta tarar da Tijjani dasu Zahira Yana ta jansu da Hira sabida su saki jikinsu sai dariya yake kyalkyalewa Dan Nadeeya sosai ta zage take Masa surutu ita kuwa Zahira da Bata da surutun murmushi kawai take. Murja kamar ta fashe Dan bakin ciki tsabar jahilci ma kishi ne ya rufeta data ga yanda Tijjani ke kyalkyala dariya a Haka ta ajiye taliya ta zauna a gefensa zahira tayi saurin barin kujeran. Nadeeya kuwa ko a jikinta "Ina abincin su Nadeeya Naga kin zubo Mana mu kadai"? "Ai Naga sunci abinci shiyasa ban dafa dasu ba ga saura can ma na Kai kitchen" "Zahira kin koshi Wai"? Da Sauri ta gyada tare da sunkuyar kai kasa sabida mugun kallon da Murja ke jifanta dashi "Nadeeya ke Kuma fa kin koshi"? Girgiza masa Kai Nadeeya tayi Shi kuwa yace toh shikenan Bari muci gabad'aya jeki wanke hannunki Waje Nadeeya tayi da Sauri Ta wanko hannunta Suka fara cin abincin Murja kuwa tusa abinci kawai take Dan bakinciki ji take kamar ta shake Nadeeya A takaice Tijjani da kansa yayiwa Su Zahira shimfida har da Kai musu bargonsa ya musu adduar kwanciya bacci tare da ja musu k'ofar Murja kuwa tsabar bakin Hali Kamar ta fashe da kuka Dan gani take Tijjani Dan tattalata da yake yi daga zuwansu Nadeeya ya shareta. Rai ba dadi Haka ta kwana tana Shan mugayen alwashi aranta Naseer kuwa sai daya yi sallah ishai ya karasa gida A k'ofar gida ya tarar da Hajara ita da Safiyya sunyi jugum jugum sai kalle kalle suke Safiyya kuwa Tana hango Naseer ta diba da gudu tayi ciki Hajara kuwa duk da jikinta rawa yake sabida tsoro Mai zata cewa Naseer game dasu Zahira da Basu dawo ba ahaka ta maze Yana isowa gabanta ya gaisheta Yana k'ok'arin Shiga gidan kamar Bai San komai ba Hajara kuwa kamar ta Dora hannu a ka Shigar Naseer da Yan mintuna ya fito waje Ya kalli Hajara datayi tsuru tsuru Amma tsabar karfin hali ta daura fuska "Umma inasu Zahira ne ko kin aikesu" "Aaaa eee kana ji wlh talaucin Nan da muke fama dashine ya isheni shine na Nemo kudi na d'afa abinci da suka dawo na dorawa Zahira da Nadeeya akan su kaimin bakin titi su dawo sabida ma mu samu abincin da zamu ci daddare. Wlh tun uku Suka fita har yanzu basu dawo ba naje titi nida Safiyya yafi sau biyar ko Mai kama dasu bangani ba ba Inda ban dubasu ba a unguwar Nan wlh ban gansu ba yanzu ma Haka daka ganmu a k'ofar gida wlh daga nemansu muke "Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun Umma talla Kika dorawa Zahira da Nadeeya kinsan kuwa akwai Yan yankan Kai a garin Nan Umma Kar fa masu satar mutane ne ne fa suka sacemun Yaya Umma Akan me Zaki Dora musu talla haba Umma kema kinsan idan na dawo ko ba yawa Zan taho Mana da abinda zamuci irin Haka nake gudu tun farko shiyasa naki Bari a Dora musu talla yanzu daga Ina Zan fara ta Ina Zan soma neman su Umma"? "Insha Allahu baa sacesu akayi ba abincin dari takwas fa na Dora musu da hamsin" "Umma ta abinci kike ko yarana Umma ta kudinki kike ko yarana Ina Miki zancen yarana kila sun b'ata kina min zancen abincin dari takwas Kika dora musu" A takaice sosai Naseer ya tashi hankalinsa kamar gaske baiyi bacci ba Bai Bari Hajara tayi ba Dan itama sosai hankalinta ya tashi da rashin dawowarsu zahiran. Tana ta bakin cikin asarar da tayi kasan zuciyata Kuma tana addua Allah yasa ba sacesu akayi ba. Abinda suke turarawa shugaba ta bayyana kuwa sun nemeshi sama ko kasa sun rasa ballantana tasa shugabarsu ta gano Mata Inda suke. Ahaka washegari Naseer ya bar gidan da wuri Akan ya tafi neman su Nadeeya Bai damu da tsayawa ya bawa su Minal abinci ba Dan ya karanci a yaran nasa tafi San Minal Humaira da Raheema har abinci tana ragewa ta basu idan taci duk da Minal na musu rashin kunya wani zubin hakan Bai saka ta wani tsaneta ba. Zahira ma ta tsaneta ne sabida balain Kama dataga tanayi da Naeema Hankali ba a kwance ba Haka Hajara ta shirya su Minal suka tafi makaranta bayan sunci abinci. Tijjani kuwa karfe shidda yake barin gida hakane yasa Yana dawowa daga Massallaci yayi wanka ya shirya ya kalli Murja dake Kan sallaya Yana "Zan fita Zahira da Nadeeya Basu tashi daga bacci ba Dan Allah Dan annabi ki Basu abinci suci su koshi Dan Allah nace Miki karki damu da Wai Dan kin bayar zai Kare wlh Zan Kara siyo wasu yaran Nan Kinga amanarsu yayana ya bani Dan Allah ki Tayani kula dasu kinji" "Wai toh Mai ya kawo maganganun Nan baka yarda Dani bane Akan me Zan k'i Basu abinci bana San Haka wlh" "Allah ya baki hakuri ba Haka nake nufi ba Bari na tafi sai na dawo Mai Zan taho miki dashi"? "Ayaba kawai nake shaawa" "Toh shikenan sai na dawo" Daga Haka ya fito daga d'akin ya lek'a d'akinsu Zahira da har lokacin suke sharar bacci. Har waje Murja ta rakashi sai data daina hango shi ta rufe gidan. Direct ta Shiga kitchen ta bud'e karamin fridge ta d'auko karamin bokitin fenti dake cike da ruwan da ya fara Dan kankara. Tayi d'akin dasu Zahira suke kwance Sai data janye bargon da suka lulluba sabida Dan sanyin da suke ji ta daga robar sama ta watsa musu. Wani irin ihu Suka saa Suka mik'e a gigice sabida yanda ruwn sanyin ya ratsa su "Shegu Yan bura uba dole kuyi ta sharar bacci ku ga gidan ubanku maza ki fita waje kuje ku dau tsintsiyarku ku sharemin ko'ina kumin wanke wanke yanzu Nan ku Shiga d'akina kuzo ku gyara min" Daga Haka tayi waje tana cigaba da danna musu Ashar. Zahira da Nadeeya kuwa Suka kankame jikinsu suna rawar sanyi kayansu sai digar ruwa yake ahaka suka fito Suka daura alwala da jikakken kayan sukayi sallah suna ta rawar sanyi Zahira kuwa har da kukanta Dan Abu kad'an ke sakata kuka Cikin awa daya Suka Gama aikin da Murja ta saka su dan gyara gida Kam sun Riga da sun Saba Koda Bata saka su ba zasuyi. Murja kuwa ba karamin mamaki tayi ba a lokacin data fito taga koina fes ko ita kanta bata taba gyara gidan kamar yanda Suka gyara ba. D'akinta tace su shiga su gyara Mata Nan da Nan suka gyara d'akin suka wanke band'akin tas. Duk aikin data saka su Nan da Nan taga sunyi har a karshe ma ta rasa aikin da zata saka su Wajen karfe goma ta Shiga kitchen ta dafa ruwan tea Kofi daya ta soya kwai guda hudu tayi hadin kauri ta zauna a Palo ta fara ci Tana kallonsu Zahira dake rab'e a gefe Nadeeya kuwa sai had'iyar yawu take Dan ita Bata Wasa da cikinta Zahira kuwa tsoro ma yasa ta kasa d'ago Kai ta kalleta. Suna kallon Murja ta Gama Shan shayinta tsaf ta rufe sauran bredin ta mik'awa Zahira Kofin Akan ta wanke ta mayar kitchen. Zahira jiki na rawa ta mik'a hannunta Dan ta karba Murja ta Kara daka Mata tsawa akan ta karba mana aikuwa tana karbar kofin nan ya sulmiye daga hannunta ya fashe........ *Wlh babu fiction a rayuwar da su Zahira sukayi a gidan Tijjani akwai Abubuwan da bazan rubuta ba sabida wasu zuciya bazata dauka ba sabida tausayi Kuma kamar Yanda na fada labarin nada tsayi masu Dan mahimmancin Zan rubuta sabida Allah na fara gajiya Ya Allah kar ka kawo sanadin da zamu rabu da yaranmu kasa mutuwa ce zata rabamu ameen* [7/3, 11:43 AM] Zannura: *NAGA TA KAINA* *NA SADNAF*🌸🌸 ®️ *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_* _{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_ *Free Novel* *Page 38* "Kutumar uba kofin danake ji dashi Kika fasamin" Zahira kasa ta zub'e akan gwiwarta jiki na rawa ta hau Bata hakuri. Murja kuwa kofin kawai take kallo Wani irin mik'ewa tayi ta fusgo Zahira ta hau dirmarta Kamar ta Samu babba sai wuli take da ita sabida Zahira siriiriya ce Bata da jiki Nadeeya sai kuka take Tana rik'e Murja da idonta ya rufe ko tausayin Zahira da ta kasa kuka bata ji ba sai data gaji Dan kanta ta kyalleta tana sosoka mata Ashar. Tsawa ta daka Mata akan ta tashi ta kwashe Mata fasassun kofin kafin ta Mata bille a fuska Zahira ta rarrafa wajen da kofin ya fashe jikinta yayi jawur sai rawa Yake. Fasassun kofin na yayanke Mata hannu Haka ta kwashe ta Kai dustbin Ta tsaya a tsakar gida. Murja kuwa ta hankada Nadeeya tsakar gida ta rufo k'ofar Palon tana kiransu shegu. A Haka Suka zauna a tsakar gidan cikin rana. Daga Zahira har Nadeeyan kuka suka ci su ka Godewa Allah har gwara gidansu sau Dubu da gidan da mahaifinsu ya kawosu Dan Safiyya ce ma take takura musu Hajara kuwa ita zagine tsakaninsu sai rankwashi Bata Kuma tab'a Hana su cin abinci ba Ga zafin Rana gana dukan da zahira ta Sha Haka Suka zauna a ranar Dan tsakar gidan a wawuke yake iya dakuna ne masu rufi ballantana su samu inuwa su rab'e Murja Bata fito ba sai karfe Biyu da rabi na Rana ta musu wani irin kallo ta nufi kitchen. Ta dafa taliya daidai cikinta ta zubo a plate ta shige palon ta hau ci Zahira da Nadeeya kuwa zuwa lokacn yunwa taci ta cinye su Zahira ta Dan fi Nadeeya dauriya dan Bata da ci sosai tafi auki a wajen kayan kwadayi su biscuit da alewa Haka. Nadeeya kuwa Sam Bata da juriyar yunwa tana da balai ci Dan bama tasan koshi ba in zaka Bata abinci sau goma sai ta karba taci Cikinta ta rik'e tana kuka wiwi ganin Murja da plate din taliya yasa ta Kara Jin wani azbar yunwa. Bata iya jurewa ba tana ganin ta shige ciki ta mik'e ta nufi kitchen Zahira kuwa ta hau kwala Mata Kira cikin karamin murya akan ta dawo Nadeeya kuwa ko kallonta batayi ba Ta shiga kitchen din Tsakin garin masara data gani ta zuba a kwanu ta zuba suga akai da ruwa Ta saka cokali biyu cikin sand'a ta karasa wajen Zahira dake a tsorace tana suci. Zahira girgiza mata Kai tayi tana "ki Mayar Nadeeya Kar ki janyo Mana wani dukan Dan Allah " "Wlh bazan iya mayarwa ba Aunty Zahira yunwa nakeji kici Dan Allah" Zahira Bata kulata ba tayi ta kallon k'ofar palon tana tsoron Murja ta fito Nadeeya kuwa ta hau Danna tsakin massarar da ruwa ya shanye da suga a bakinta Sosai take zabga Loma kamar wacce ta samu garin kwaki Fitowar Murja da plate din data Gama cin abinci yasa Zahira ta mik'e a tsorace jikinta na d'aukar rawa. Nadeeya kuwa dayake Baya ta Bata Sam Bata San da fitowar Murjan ba Murja kuwa ganin Nadeeya da plate dinta yasa ta nufi wajenta da gudu tana "Barauniya uban me Kika dauko kikeci iyye wato har kitchen Dina Kika Shiga waye ya Baki izinin shiga" Kafin kace me ta fusge plate daga hannun Nadeeya itama ta hau kilarta "Gobe ko Tijjani ne yace ki Shiga kitchen Dina Zaki ji tsoron shiga shegu Mayyu Haka kawai Ina zaman zamana an kawomin jarraba maza kuje ku dau bokiti ku debomin ruwa" Ta karashe tare da daka musu tsawa Zahira kuwa a guje ta kinkimi bokiti Nadeeya itama tabi bayanta Ta dau Wanda Bai Kai na zahiran girma ba har waje Murja ta rakasu ta ce suje can kasan layin wajen makabarta akwai rijiya su debo Mata ruwa maza tana jiransu. Siyan ruwa take Kuma tana da ruwan tsabar mugunta yasa ta aikesu diban ruwa. Nadeeya Dan tsakin data ci ya Dan rage Mata yunwar da take ji Zahira kuwa kasa tafiya tayi sabida rawar da jikinta keyi kafin su karasa karshen layin ta samu inuwa ta zauna ta rik'e cikinta Tana kuka. Nadeeya kuwa cewa take "Aunty Zahira mu ajiye bokitin mu gudu" "Ai bamu San hanya ba Nadeeya Kar mu Bata nidai idan baba Tijjani ya dawo Zan rokeshi ya maidamu gida yunwa nakeji cikina ciwo yake da Umma tana Nan da Abba Bai kawo mu Nan ba" Zahira tace tana fashewa da kuka "Wai toh Ina Umman ta tafi ne ta barmu"? "Bansani ba Nadeeya Abba Bai fada min ba" "Idan Baba Tijjani ya dawo sai na Gaya masa dukan data Mana ta Hana mu abinci" Nadeeya tace itama hawayen na zubo Mata. Ta mike ta nufi shagon data gani a bud'e tana zuwa ta zub'e a kasa tana "Dan Allah ka bani bredi na bawa yayata yunwa takeji tace cikinta ciwo yake" Mai shagon kallo Inda ta nuna Masa yayi yaga Zahira a zaune sosai yaji wani irin tausayin su ya rufeshi ya hau yiwa Nadeeya tambayoyi Ina iyayensu suke Mai ya Hana suci abinci Nadeeya dake tana da surutu take ta hau bashi labarin abbansu ne ya kawosu gidan kaninsa shine matarsa taki Basu abinci. Tambayar Nadeeya yayi gidan da suka zo ta kuwa nuna Masa gidan Ya girgiza Kai gidan Dan ya San Murja zata Kuma aikata basa shiri da ita sabida Tijjani na zuwa wajensa hiran Dare. Hakane yasa ta zo har shagonsa ta Masa tas akan shi munafiki ne ya Rabar Mata da miji k'arfi da yaji ta kuwa rabasun yanzu Haka ko siyan Abu batayi a shagonsa ta gwammace taje wani wurin . Bredi ya d'auko Mai Dan girma ya bawa Nadeeya da kananan lemo guda biyu Nadeeya kuwa jiki na rawa ta hau mishi godiya tana tambayarsa Dan Allah ya sunanshi Murmushi ya Mata dayaga yanda take da wayo yace sunansa Jamilu bud'ar bakinta sai cewa tayi "Allah ya saka ka a Aljannna Yaya jamilu daga Haka ta diba a guje ta koma wajen Zahira dake rik'e da cikinta Zahira kuwa na ganinta da bredi da lemo ta fusge bredin daga hannunta ta yaga ledan ta hau dannawa a bakinta ko ta Kan lemon Bata bi ba. Nadeeya itama sosai ta ringa cusa bredin a bakinta sai da suka ji Dama Dama suka Kora da lemon hannunsu. Zahira kuwa tuni taji ta Dan koshi sanin Nadeeya Bata San koshi ba yasa ta fusge bredin tana "Karki cinye duka ki kawo na boye Mana anjima daddare muci Dan nasan bazata bamu abinci ba" Daga Haka Zahira ta danne bredin ya kankance ta cusa a skirt dinta. Suka dau bokitansu Suka dau hanyar karshen layin sai da suka tambayi Inda rijiya yake aka nuna musu Yana gaba da makabarta kad'an abinka da yarinta ko tsoro Basu ba ahaka suka Shiga ta cikin makabartar kafin su Isa wani ya taresu tare da tambayarsu Ina zasuje Gaya Masa sukayi ruwa zasu d'ebo Mutumin kuwa yace "Wane mahaukacin ne zai aiko ku Nan diban ruwa duk rijiyar unguwar Nan maza ku juya ku koma baa bi ta nan" Juyawa sukayi da Sauri. Suka koma suka Kara d'aukar hanyar da suka biyo Zahira kuwa ta hau cewa "idan muka koma bamu Kai Mata ruwan ba zata dakemu mu nemi wani wajen mu dibi ruwan "Toh ai ba Inda muka sani" "Kije ki tambaya mutumin Nan daya bamu bredi haka.kuwa akayi Nadeeya na tambayarsa ya nuna musu wani gida a kusa da shagon suka shiga gidan suka dibi ruwan suka tafi gida. Sai da suka dade da ruwan Akansu Kafin murja ta fito tana zaginsu Akan Ina suka tsaya suka Dade haka a amadadin ta sauke musu ruwan Bata sauke musu ba ta Shiga kitchen. Zahira kuwa bokitin sai rawa yake akanta Nadeeya kuwa data ga bazata iya ba sakin bokitin tayi ya Fadi kasa ya fashe Murja kuwa ta lailayo Ashar ta fito ta daya kitchen ta wawankawa Nadeeya Mari da rankwashi tace Mata ta d'au tsintsiya ta share Mata Inda ta jikam Zahira kuwa tsabar tsoro Kara rike bokitin tayi akanta sabida Kar ya Fadi Sai da Murja ta Dora girkin dare. Ta fito.ta sauke mata bokitin data ga yanda jkin Zahira ke rawa tana kuka. Sai data Gama girkin da take tsaf ta daka musu tsawa akan suje suyi wanka ta Kara da "Mitsiyacin ubanku ma daya tashi kawoku ko hadoku da Kaya baiyi ba ai kuwa shi zaku Kara maimaitawa maza kuyi wanka ku maida kayan jiknku kuzo ku sameni a Palo" A band'akin Tsakar gidan sukayi wanka. Jikin Zahira yayi jawur sabida dukan data sha Nadeeya ma. Yatsun Murja sai daya fito a kumatunta A Haka suka Shiga palon suna rab'e rab'e sai data Kara daka musu tsawa Suka zub'e a gaban ta jikinsu na rawa. Wukan data ajiye a gaban ta ta Dago musu tana "Mai wanan"? Hade jikinsu sukayi waje daya jkinssu na balain rawar tsoro Zahira har wani fitsari ne ya matseta "Dan ubanku nace me wanan" "Wukane Aunty Dan Allah kiyi hakuri karki yanka mu" Zahira tace tana fashewa da kuka. "Toh wlh idan Tijjani ya dawo kuka ce na muku wani Abu kukace na Hana ku abinci na rantse da Allah sai na cire muku Ido kunji na rantse muku idan ya dawo kuce Masa kunci abinci Kun koshi ke Kuma da ganinki kin iya munafirci Abu kad'an sai ki hau hawaye wlh ya dawo kikamin wanan kalar tausayin gobe Yana fita sai na yanka ki kunji Mai nace ko bakuji ba"? Gyada.mata Kai sukayi a tare Dan har ga Allah sun yarda zata yankasun sabida yaran da akwai tsoro ba Kamar na yanzu ba sai a lokacin ta barsu suka zauna a Palo. Duk a tsorace Suka Kamar su zura da gudu Ana Kiran Sallah magriba Tijjani ya dawo Murja tayi sauri ta jawo Nadeeya ta kwantar da kanta a cinyarta Ta hau shafawa tana "in cigaba da muku tsatsuniyar"? A daidai lokacin da Tijjani ya shigo Niki Niki da ledoji A hannunsa Nadeeya kuwa sai mutsu mutsu take sabida danneta da Murjan tayi a cinyarta tana shafa Mata Kai Tijjani kuwa washe baki yayi Yana "Uwar biyu keda yaran naki ne kuke Hira"? Murmushi Murja tayi tana "wlh fa Wai tsatsuniya nake musu ai ba karamin dadi naji ba da zuwansu Dan wlh suna ta deb'emin kewa da sai dai nayi zuru Ni kadai kamar Mayya Nadeeya dai tafi yayarta wayewa Dan ita ta saki jikinta ita kuwa yayarta sai noke noke take Taki sakin jikinta" Murja ta karashe a daidai lokacin da Tijjani ke amsa gaisuwar da Zahira take Masa kanta a sunkuye Nadeeya itama gaishe shin tayi a lokacin da Murja ta daina shafa kanta ta mik'e zaune. Shi kuwa Tijjani cikin Jin dadi ya amsa gaisuwarsu Yana "Ai Zahira Haka take tana da wuyan sabo ko gidansu Kikaje Bai zama lailai kiji maganarta ba har ki dawo Nadeeya ce dai ba ruwanta. Kuzo maza kuga kayan Dana siyo muku Tijjani yace Yana janyo katuwar ledar daya shigo dashi. Murja kuwa kamar ya caka Mata wuka Haka taji a lokacin da ya jawo ledar ya bud'e Nadeeya kuwa tuni ta Isa wajensa Zahira kuwa ko dagowa batayi ba ballantana taje Inda yake zaune Ki taso Mana Kika zauna. Murja tacewa Zahira cikin murmushi yak'e dayafi kuka ciwo Zahira kuwa jikinta na rawa ta Isa wajen Tijjani ta zauna a wajen kafarsa Nadeeya kuwa a gefensa ta zauna Tana murna da ganin kayan data ke kyautata zaton nasu.ne Kaya ne masu Dan saukin kudi guda shida shidda iri daya Sai takalma guda biyu brush biyu har da Mai da Dan turarensu. Bai tsaya iya Nan ba har da yatsana ya siya musu. Kamar an cinnawa Murja wuta haka ta ringa ji sai juye juye take ita kadai ita da take d'auke da ciki Tijjani ko pant Bai siya na jariri ba Amma ya laftowa su Zahira uban Kaya Nadeeya kuwa tsalle tsalle kawai take akan kujeran tana murna yartsana da aka siyo musu shap tama manta da wata Murja a palon balle ta tuna dukan dataci. Zahira ce ma ta kasa sakin jiki ta ringa satar kallon Murja dake musu wani Irin kallo Manyan biscuit ya d'auko ya bud'e musu ya bawa kowace guda guda Yana maza suci Nadeeya da Zahira kuwa sukayi ta mishi godiya Har wani Dan hawayen bakin ciki ne ya Dan taru a idon Murja Tana hada Ido da Tijjani ta kakalo murmushi tana "gaskiya ka kyauta Allah ya Kara budi dama dazu nake ta ce wa Basu zo da Kaya ba ko Mai zasu saka" "Aikuwa gashi na samo musu Wanda zasu ringa Dan sawa Kafin na Karo musu idan na samu kudi. Ga ayabar da kikace na siyo Miki ga Kuma balangu Nan Leda biyu ki dau babbar ki bani dayan Murja Haka ta mik'a Masa ledar kamar ta kurma ihu Tijjani kuwa ya bud'e ledar balangu ya Ajiye Agaban Zahira Nadeeya ta sauko ta hau CI Zahira kuwa sai juye juye take tana satar kallon Murja a tsorace sai da Murja ta tafi dauko abincin ta iya Kai Naman bakinta. Nadeeya kuwa ko kallon murjan batayi ba tayi ta Loma balangun "Murja kuwa abincin ta d'auko ta zuba Masa faten wake da doya Dan Tijjani Yana balain san faten wake da doya "Aaa Yau Mai dadin Kika Mana kenan" Zahira maza ku tashi ku wanko hannun ku muci abinci" Caraf Nadeeya tace "Ai bamu iya cin wake ba" "Mun koshi Abba dazun Nan mukaci abinci" Zahira tace cikin rawar murya "Shaf na manta fa Baku iya cin Wake ba laifina ne da ban gayawa Auntynku ba" "Ai sun gayamin Dama danake girkin hakane yasa na dafa musu taliya sukaci Kallon da tayiwa Zahira ne yasa Tijjani na tambayarsu sukayi saurin cewa sunci.taliyar. Nadeeya kuwa ta maida hankali ta cinye biscuit din da balangu Zahira kuwa tsatsakura tayi sabida tsoro. Ahaka lokacin kwanciyarsu yayi sukayi shiga daki suka kwanta Murja kuwa dak'yar tayi bacci sabida bakin ciki. Washegari Tijjani na fita Tayi wa Nadeeya mugun duka ta Kara saka su aiki kamar Jiya har dasu wanki Wanda a tunaninta wahala take basu Bata San sun Saba da aikin ba . Kayan ma kwacewa tayi ta karya ita kadai batare da ta Basu komai ba Zahira kuwa bredin da suka boye na jiya Suka ci a boye Dan guntun biscuit din ma ta kwace. Sai data Kara turasu debo ruwa Dan duk a tunaninta a makabartar suka je jiya Nan kuwa Inda suka je jiya Nan suka debo ruwan Jamilu kuwa Mai shago daya gansu Basu tambayeshi ba ya Basu kyautar biscuit da lemo suka boye a jikinsu Suna zuwa suka ga ta d'ebo wake ko tsincewa batayi ba ta Dora waken Mai uban yawa ta daka attaruhu ta zabga a ciki Sai daya dahu ta d'auko Sabulun Canoe data jika tun safe ya narke "(nasan mutanen da zasu Gane koren sabulu Canoe Zahira da wayonta lokacin ita ke bani wanan Labarin Nadeeya ma Bata manta komai ba) Juye canoe din tayi a cikin waken ta gwamutsa ta d'auko wani farin roba Mai Dan Fadi ta juye a ciki ta saka a fridge ta kalli Zahira da Nadeeya tana "Daga yau wannan shine abinci ku Badai bakwa cin wake ba shegu tsinanu Zakuci ubanku ke Kuma na rantse da Allah idan kina wanan rawar Kan Agaban mijina kina surutu da wanna shegn bakin naki sai na yankaki ta karashe tana rankwashin Nadeeya A takaice karfe shidda ta zubo musu waken Akan suci Zahira kuwa ta ki ci tace ta koshi Nadeeya kuwa duk da Zahira nata Mata Ido Akan Kar taci Nadeeya a Haka ta zauna taci waken Nan Yana d'ade Mata harshe tare da soya Mata zuciya (Wani ikon Allah ba abinda ya samu Nadeeya tana Nan da ranta har yanzu har da yaranta ma ) A takaice sosai Murja ta bud'e babi babi na mugunta tana ganawa su Zahira Tijjani Bai taba Sani ba Dan idan ya kusa dawowa sawa take suyi wanka ta dauko musu kayan da ya siya musu da Yar tsana akan su ringa Wasa dashi shi kuwa Tijjani idan ya dawo Baya ganewa sam Sosai take musu horar yunwa Zahira ta ringa wani irin Rama. Indai ta saka wani abu a bakinta jamilu Mai shago ne ya Bata Nadeeya kuwa haka take dirkawa kanta faten wake Mai Sabulun Canoe tayi ta Kashi Ga uban duka da take musu da sun danyi wani kuskure. Kullum mak'ota sai sunji ihunsu Zahira. Tana dirkarsu A Haka har jamilu Mai shago da abin ya ishe shi sabida tausayinsu Zahiran.yaje har gidan ya kwada Sallama Murja na fitowa ya hau Mata masifa Yana "Kiji tsoron Allah ki daina zalintar yaran Nan idan babu idon iyayensu Allah daya hallicesu Yana kallonki Banda mugunta Mai yaran Nan suka tare Miki da kike musu irin Haka " "Ina ruwanka Shugaban munafikai ko kashe su nayi Ina ruwanka ka Shiga uku da munafirci wlh ka ficemin daga k'ofar gida kafin na debbo ruwan zafi na watsa maka" Murja tace cikin masifa Jamilu zaginta ya cigaba da yi Yana rantsuwar akan sai.ya hadata da hukuma ya kaucewa ruwan data watso Masa ta rufe kofarta Tana Shiga ciki tayi.kan Zahira da Nadiya ta hau duka Akan sun Kai kararta wajen Jamilu. A ranar Kuma jamilu yayi ta jiran dawowar Tijjani Dan ya Gaya masa sai Tijjani Bai dawo da wuri ba har ya tashi Washegari Kuma daya fito Tijjani ya fice. Karfe takwas yaga Zahira ta fito ita da Nadeeya da bokitan ruwa Akansu Shi kuwa ya kirasu Suna zuwa yace "idan na Baku kudin mota zaku iya komawa gidanku" Da Sauri Zahira ta gyada Masa Kai tana "a gadon Kaya gidanmu yake indai aka saukemu a junction xamu iya xuwa gidanmu a kafa Dan Allah ka taimaka Mana da kudin motar" Naira Hamsin Jamilu ya d'auko ya bawa Zahira Yana ta ajiye bokitin ma yanzu ta rik'e hannun Nadeeya su gudu. Ai Zahira da sauri suka dire bokitin ta rik'e hannun Nadeeya suka fara tikar gudu suna wuce gidan Murja ta bud'e kofa Dan ta siyo Madara aikuwa ta hango su Zahira na tikar gudu. Itama binsu ta fara Yi agujen Taji kafarta ya rik'e. A daidai lokacin da wani mai vespa yazo wucewa tayi saurin tsayar dashi Akan ya taimaka Mata subi bayan wadancan yaran guduwa zasuyi Da Sauri ta haye vespan Zahira kuwa Tana ganin Haka ta Kara rike hannun Nadeeya suka cigaba da tikar mugun gudu suna zuwa titi wani bus na k'ok'arin tafiya Zahira.kuwa ta daga hannu biyu ta hau tsyaar da kwandastan Yana tsayawa suka Shiga motar da Sauri a daidai lokacin da Murja ta sauka itama daga Kan vespan ta hau tsyaar da kwandastan Zahira kuwa ta hau rokansa Kar ya tsaya kashe su zatayi basu kuwa tsaya ba driver ya ja bus din Suka tafi Murja kuwa ta tari wani bus din tabi bayansu....... Wlh biki muke wata danake Jin kunya sisi mama ta roki nayi typing ko ba yawa to gashi Nan nayi da yawa [7/3, 10:19 PM] Zannura: *NAGA TA KAINA* *NA SADNAF*🌸🌸 ®️ *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_* _{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_ *Free Novel* *Page 39* *Naeema* Wani irin rashin lafiya Waleed ya ringayi daya dagamin min hankali duk yanda naso zuwa gadon Kaya gidan Aunty Dan Naga yarana sai ban samu zuwa ba sabida zaryar asibitin da nake fama dashi wani irin kuraje ne suka feso Masa kananu ga Kashi da yake yawan yi. Ko no-no sai nayi dagaske yake Sha shima Yana Sha wani zubin Haka zai ta kwara amai daddare kuwa Haka nake zaman dirshan Ina jijjiga shi Dan kuka yake kwana yi duk magangunan da nake bashi Banga alamar Yana Jin sauki ba sosai hankalina ya rabu gida biyu ga na rashin lafiya Waleed ga na yarana danakeji Kamar na mutu sabida kewansu. Idan bacci ya saci daukana kuwa Haka Zan hau mafarki dasu Zahira suna kuka suna mikomin hannu wani zubin Kuma Wai sai Naga suna gudu wata Mata na binsu da wuka. Sosai nakejin Kamar yarana suna cikin mawuyacin Hali ya zama Dole naje Koda kuwa Waleed din bashida lafiya. Sai dai abinda ya hanani zuwa gidan aunty shine wani Mai maganin gargajiya da aka hadani dashi da ke hanyar Zaria da akace na Kai waleed wajensa zai Samu lafiya idan dai na Kai shi Dan Kamar cutar tasa Bata asibiti ba. Banso zuwa ba sai da hassana ta dagemin akan naje suna da dangi acan na sauka a gidan Har mai maganin ya Gama duba waleed Dan idan dai kaje baya Bari ka taho sai yaga alamar maganinsa ya maka aiki. Baa San Raina ba Haka muka je kauyen da Waleed da kwatancen da Hassana tamin na Isa gidan yan uwansu Da wata a gidan ta rakani wajen Mai maganin yana duba waleed kuwa ya hau hadamin magangunan gargajiya Yana a cikin kwana uku insha Allahu zanga canji na ringa kawo shi safe da yamma. Cikin Ikon Allah kuwa da fara amfani da maganin Naga Waleed ya fara samun sauki A madadin kwana uku Dana so yi sai gashi sai danayi satin Sati dayan Nan danayi Allah yasan baa nutse nake ba ba kuma a hankalina nake ba sabida tunanin yarana Dan ban fasa mafarki dasu ba. Ni nasan mafarkina wani zubin yana Zama gaske duk da Ina Taya yarana da Addu'a ya zama Dole Ina komawa naje na gansu. Haka kuwa akayi Ina dawowa washegari da sassafe na goya Waleed na saka nikab na nufi gadon Kaya Gidan aunty na Isa kaina tsaye. Lokacin zuwansu makaranta baiyi ba hakane yasa muka ringa dan tab'a Hira da ita hankalina gabadaya Yana Kan agogo uku na yi kuwa Yara suka fara cika k'ofar gidan Ni kuwa tsabar matsuwa San naga yarana haka na saka nikaf naje na tsaya a bakin kofa Ina kallon duk Yan makarantar da suka ringa zuwa . Duk yanda aunty tayi dani Akan na zauna na ci abinci Kar na damu har cikin gida zata kirasu k'in saurarenta nayi ahaka nayi tsayuwar awa daya kafin na hango Minal Humaira da Raheema sun nufo makaranta hannunsu rik'e Dana juna. Uniform dinsu yayi wani irin dati ko wankewa baayi ba bana Jin ma ko wanka sunyi Raheema ma sai tsince tsince take a kasa tana kaiwa bakinta Minal na hanata. Hawaye.ne Suka hau zubomin kirjina na bugawa da Sauri wai da Raina yarana Suka Zama Haka toh Ina Zahira da Nadeeya Na Kara dage wuyana ko Zan gansu daga bayansu sai dai Banga Mai Kama dasu ba har su Minal din Suka karaso suka zauna Akan tabarma sosai naji hankalina ya tashi na fara k'ok'arin fita wajensu. Aunty dake gefena a tsaye ta rikemin hannu tana na koma ciki Bari ta fita ta kirasu. Da sauri na Shiga palon aunty na zauna sosai na matsu da su shigo gashi aunty ta Hana ni cire nikaf din fuskata Tunani kawai nake mai ya Hana su Zahira zuwa makaranta ko Aiki Safiyya da Umma suka saka su shiyasa Suka Hana su zuwa.ko dai Kuma dukansu ma Safiyya ko Umma keyi amma idan Naseer ya Bari aka ci zallin yarana bazan yafe masa ba sosai hawaye ya jika nikaf Dina Waleed kuwa na Kan kujera Yana ta baccinsa Shigowar Aunty dasu Minal ne yasa na Kara Jin bugun zuciyata ya Karu ahaka na ringa rarraba idona Akansu tausayin yarana na rufeni sunyi wani cirko cirko dasu Kamar basu ba Kamar na Isa wajensu Naga Aunty ta girgiza min Kai Na daure na zauna na cigaba da kallonsu Ina adduar Aunty ta musu tambayar dake Raina Abinci Aunty ta d'auko musu a faranti Tana direwa suka hau ci Kamar wayanda Basu tab'a cin abinci ba aunty a gefena ta zauna ta Dan matsa hannuna sabida sheshekar kukana dake fitowa Ana ji Dan sosai naji zuciyata ta karye da ganin yarana a yanayin Nan Dubi yanda Raheema ta zama bak'a yarinyar da duk yayana ba Mai farinta Dayake cire hijabinsu sukayi kitson kansu ma ya balain tsufa ko tsagan baa gani "Minal Dama Baku ci abinci bane"? Aunty tace tana Kara Dan tattab'a hannuna alamar Kar nayi magana "Munci bamu koshi bane" "Waye ya Baku abincin" "Mama ce ta bamu"( Haka suke cewa Umma ) "Ina Abbanku"? "Baya Nan ya fita da sassafe " "Bakuje makarantar boko bane"? "Eee bamuje ba an koremu kudin makaranta" "Ina Zahira da Nadeeya ya Banga sun zo makaranta ba sai ku kadai"? Kirjina wani irin bugu yake a lokacin Dana ga Minal ta kalli Aunty tare da cire hannunta daga cikin abincin tana "Abba da Mama sunce sun b'ata mun daina ganinsu Aunty Ummanmu ta tafi ta barmu Aunty zahira.ma da Nadeeya sun tafi sun barmu ba Mai Mana wanki da wanka kullum sai abbanmu yayi kuka daddare"? "Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun Aunty nashiga uku na lalace yarana sun b'ata Zahira da Nadeeya sun Bata fa" Nace cikin azabar tashin hankali Ina mik'ewa tsaye Muryata dasu Minal sukaji yasa suka Mik'e a tare cikin ihu sukace "Ummaaaaa" Bansan lokacin Dana fashe da wani irin kuka ba na fusge nikaf din fuskata na durk'ushe na fara kuka Yarana suka debo aguje suna ihun Umma Suka zo suka rungumeni gabadaya. Minal kawai na iya rik'ewa Ina "Minal Mai kikace Kika ce Zahira da Nadeeya sun b'ata kamar ya sun b'ata Minal kinsan.mai kike cewa kuwa tun yaushe suka B'ata"? "Umma sun Dade da b'ata mama ce ta Dora musu talla abinci shine Basu Kara dawowa ba Naji Abba yace an sace su" Wani irin mik'ewa nayi na fara k'ok'arin nayi waje da gudu Aunty kuwa ta rik'eni Gam Ina "Ki cikani Aunty wlh yau sai dai su kasheni kina ji Zahira da Nadeeya sun B'ata aunty ta yaya yarana zasu B'ata wlh bazan yarda ba sun Dade suna min Abu Ina kyalesu Amma wlh bazan yarda su b'atarmin da yarana ba Mai na musu Haka suka tsaneni wlh gidan zanje aunty ki cikani" Nace Ina ihun kuka Aunty kuwa ganin dagaske nake Yasa ta Kira alaramma mijinta Ina balain Jin nauyi da kunyarsa Yana shigowa na nutsu Amma ban fasa kukana ba sai Kiran nashiga uku na lalace nake ko Waleed dake kuka ban kalla ba sai aunty ce take jijjiga shi su Minal kuwa manne min sukayi suna tsoron Kar na Kara tafiya na barsu Aunty ce ta Kora Masa jawabin abinda ke faruwa Shi kuwa cikin mamaki yace "Sun b'ata fa sukace Amma ai muna gaisawa da Naseer din Bai taba cemin sun b'ata ba Dan ko shekaranjiya Dana Kara tambayarsa yasu Zahira suka daina zuwa makaranta cemin yayi hutu ya Kai su Banga Kuma alamar tashin hankali a fuskarsa ba Cikin kuka nace "wlh b'oyewa yake bayaso aji labarin sun b'ata Dan yasan zan iya jin labari Mallam nasan wacece uwar mijina wlh zata iya b'atarmin da yarana Dan Allah ku barni naje gidan da kaina su fitomin da yarana Haka ma Suka tab'a batar da Nadeeya dak'yar aka ganta Dama sun tsanesu Dan Allah Mallam kubarni naje da kaina" Na karashe cikin ihun kuka Ina dafe kirjina Dana ji Yana min suya Wai yarana sun b'ata da Raina aka dorawa yarana talla Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun "Ki kwantar da hankalinki Naeema Bari na tura mmn Sadiya ta je gidan da kanta mubi komai a hankali insha Allahu Ina kyautata zaton hutun ya Kai su basu b'ata ba Bari taje ta dawo Muji ya sukayi da Yan gidan Nidai Dan yamin Dole ne da tuni na kusa Isa gidan. Aunty kuwa Hijabinta ta zura tayi waje. Yarana kuwa Suka hau bani labari irin rayuwar da sukeyi da su Umma Umma dai Bata dukansu Amma Safiyya kam tana Kai musu duka a labarin ma da Minal ke bani dayake tana da surutu cewa tayi wani kullum.yana zuwa wajen Safiyya zance Sam bana wani Gane maganar da Minal kemin zuciyata tana can wajen Aunty fatana ta dawo tacemin ta gansu Minal ce Bata San Mai take cewa ba Raheema kuwa sai wani narke min take tana min kananan shagwaba Humaira kuwa hannuna ta rike Gam a cikin nata tana "Umma Dan Allah karki Kara tafiya ki barmu kinji"? Aunty kuwa a lokacin data Isa gidan. Da Sallama ta Shiga gidan Hajara na zaune tana Shan garin kwaki da Yan canjin da Naseer ya Bata Safiyya Kuma tana can gefe tana cin abinci a farin roba da kana gani kasan na siyarwa ne shinkafa ne da Miya har da lemo taci uban kwalliya. Ba Wanda ya amsa Sallamar da tayi Safiyya kuwa har wani yatsina fuska tayi tana wa aunty kallon up and down tare da cewa "lafiya daga Ina"? Wani irin harara aunty ta watsa Mata ta kalli Hajara da ta karasa kwankwade garin da take Sha tana "shigo Mana daga Ina"? " Ciki Aunty ta karasa tana kallon yanda gidan yayi gaja gaja ba kintsi Ta zauna a gefen tabarmar da Hajaran ke Kai ta hau gaida Hajaran Hajara ta amsa cikin Dan sakin fuska tana jiran Karin bayani " Sunana Hafsa Matar mallamin su Zahira ce ni kwana biyu bamu ga Zahira da Nadeeya sunje makaranta ba shine Mallam yace Nazo gida naji lafiya suka daina zuwa" "Dolene sai sunzo makarantar lafiya Lau kawai bamu ga Daman suzo bane" Safiyya tace tana Harare Harare "Baiwar Allah ba wajenki Nazo ba ba kuma dake nake magana ba da mahaifiyarki nake magana Dan ita nakewa kallon Mai hankali sanin bakida hankalin yasa ko kallon naki banyi ba Wani irin Ashar Saffiya ta lailayo Aunty kuwa ta ja Tsaki ta kalli. Hajara da ke ta juye juye kafin ta saukr ajiyar zuciya ta ce "wlh sati biyu da kwana shidda kenan da b'atan Zahira da.nadeeya tsautsayi daga Dora musu tallan shinkafa da miya su Kai titi su dawo har yau dawowar da basuyi ba kenan ba neman da bamu musu ba "Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun kawai aunty ke maimaitawa hankalinta a balain tashe ya tabbata dai su zahiran sun b'ata yau Mai zata cewa Naeema "Kullum sai babansu ya fita da sassafe nemansu sai daddare yake dawowa sai dai ku tayamu kawai da Addu'a Abu Bai dadi ba" Aunty Bata iya Kara ce komai ba ta mik'e ta fita Tana hada hanya sosai taji hankalinta ya tashi Dan tasan Yau Naeema sai ta kusa karamin hauka ita ma da nata sakacin da Bata duba yaran akai akai Kamar yanda ta alkawartawa Naeema. Lokacin data Isa kasa Shiga gidan tayi sai da Mallam ya hangota ya iso wajenta ta ja shi gefe ta Gaya masa yanda sukayi da mahaifiyar Naseer sosai.hankalinsa ya tashi yana mamakin ya Yara zasu B'ata har guda biyu Amma Naseer ya boye musu Anya akwai gaskiya a lamarin Nan kuwa A tare Suka Shiga gidan Ina ganinsu na mike da Sauri naje wajen aunty a rude Ina "Kinga su zahiran ko? karya Minal take basu b'ata ba ko"? Na jerowa Aunty tambayoyi Ina rik'e hannunta Gam "Zauna muyi magana" Mallam yace Ni kuwa.na zub'e a kasa Ina sallati ta tabbata dai yarana sun b'ata sallati kawai nake Ina ihun kiran.zahira.da Nadeeya Ina nayi nadama Dana tashi tafiya ban tafi dasu ba Ashe kallon.karshe nayiwa zahira shiyasa take ta waiwayena da Zan tafi Mai nayiwa su Umma Haka suka nemi su b'atarmin da yarana mai Zahira da Nadeeya suka musu da zafi haka" Dak'yar na tsagaita kukan da nake Mallam.yace "ki kwantar da hankalinki a gaskiya bana Jin yaranki sun b'ata dan da sun Bata gaskiya zamu ji labari.ina dai zargin Naseer dai hutun.ya Kai su Dan Ina ganinsa a bakin titi wajen ginin shaguna Nan na bakin titi da yaranki sun b'ata bana jin zai iy wanan ginin Dan Haka yanzu ki Bari daddare zanje wajen.Naseer da.kaina nace Masa nji a gari ance yaransa sun B'ata dagaske ne ko.karya ne" Karki damu insha Allahu yaranki Basu B'ata ba "Sun B'ata Mallam boyewa kawai Naseer keyi Dan Ni bansan Inda zai Kai yaran Nan hutu ba Dan Allah kubarni naje gidan Dak'yar suka shawo kaina akan na Bari gobe naje gidan Dan dagewa nayi sai naje su Umma sun fito min da yarana. Su Minal din ma rikesu nayi na dage akan wlh bazasu Kara komawa gidan ba Suma kuka suka ringa Yi wiwi akan bazasu tafi su barni ba dak'yar Mallam ya Basu Baki akan suje gida gobe Zanzo na daukesu da kaina Kuma karsu gayawa kowa sun gani ya hada musu da alewa dak'yar suka yarda suka tafi bayan na musu alkawarin zuwa gobe na tafi dasu Duk da har ga Allah daga aunty har mijinta Dan sunmin fin karfine da wlh ba abinda zai Kara rabani dasu. Ko gida ban iya komawa ba sabida har ga Allah gobe da sassafe Zan dira gidan Daga Umma har Naseer wlh sai sun Fito min dasu Nadeeya har wani zazzabi naji Yana neman rufeni. Alaramma kuwa masu d'aukar karatu Wajen sa ne yasa a ranar Bai samu zuwa gidan ba nikam Dama yanda Naga Rana Haka Naga dare ko ya na Dan rufe idona sai Naga kamar Zahira da Nadeeya na kuka suna cikin wani Hali idan dai wani Abu ya samesu Nima kaina bazan yafewa kaina ba. Da asuba naso dira gidan Sabida inasan na samu Naseer a gida Sai dai Mallam.dake waje Zaune da almajirai yasa na koma ciki. Aunty ma Ni haushinta nakeji da rarrashin da takemin ita kuwa ganin na matsu na fita yasa ta saka Hijabinta ta fita wajen Mallam ba jimawa kuwa sai ga ta dawo tana na tashi mu tafi. Da Sauri na sab'a Waleed a bayana muka dau hanya bani burin daya wuce na Isa gidan Muna kuwa Isa gidan ban tsaya wani buga k'ofa ba na hankada k'ofar na Shiga. Naseer ne a tsakar gidan da tsintsiya Yana shara Umma Kuma tana daga bakin kofarta a zaune Su Minal Kuma ma Kan tabarma suna Shan Koko da kosai Naseer tsintsiyar hannunsa ne ya kubce daga hannunsa a lokacin da muka hada Ido dashi Umma kuwa har tana tuntub'e wajen mik'ewa Yarana kuwa Suka taso aguje suka rungumeni suna ihun Umma Ni kuwa Raina a had'e nace "Naseer Ina Zahira da Nadeeya Naseer Ina ka kaimin su"? Ko kallon.umma banyi ba da ke masifar uban me Nazo nema banma San ta zo kusa Dani ba Naseer kuwa kamar.mai tsoron magana Naga Yana ta min magana da Ido. Ni kuwa cikin Jin haushi.nace "Naseer Ina Zahira da Nadeeya nace Wlh Tallahi bazan yarda ba a yau sai an fitomin da yarana Naseer idan ba Haka ba wlh hukuma ce zata rabamu na rantse da Allah" "Yaranki sun b'ata kiyi.abinda zakiyi Yar iska kaji Mara mutunci ke kadai Kika haifesu Naga shi Naseerun.yafiki iko Akansu shima ya fara d'aukar dangana ballantana ke din banza da baki ma San ciwon su ba kizo Nan kina Mana hauka kin Dade Baki hadamu da hukuma ba idan ma salon da Kika zo dashi kenan Dan ki dawo gidanan wlh bazaki dawo ba muguwa azzalluma daga fitarki Kika je kikayi wa yarona asiri duk ya tsiyace" "Umma ba abinda zai Kara dawo Dani gidanan kince bakya Sona na rabu da danki na Kuma tafi Dan Haka a bani yarana na tafi dasu Kar a sake a yarda wani Abu ya Samu Nadeeya da Zahira Dan ba Abunda suka muku" "Muje waje muyi magana Naeema " Naseer yace a hankali kamar Mai ciwon makogaro Tirjewa nayi Umma tayi ta auna min zagi Aunty kuwa Taja hannuna mukayi waje Dan ta lura kamar akwai maganar da Naseer yake so yamin Amma baya so yayi maganar a gaban Umma. Su Zahira kuwa kwandastan tambayarsu yayi Ina zasuje Suka ce Masa gadon Kaya sukayi shi kuwa yace ba Nan sukayi ba su dorayi sukayi Amma zasu dorasu a motar gadon kayan. Zahira da Nadeeya kuwa sai juyawa suke suna kallon motar da Murja ta hau dake bin bus dinsu bumper to bumper Sai da.suka iso junction bus dinsu ya tsyaa sabida su Dora su Zahira a motar gadon kaya Wanda Murja Kuma ta hau ya wuce Sai da sukayi nisa ta lura da motarsu Zahira ya tsaya tayi saurin cewa akwai na Nan ta sauka da Sauri Ta dawo Baya sai dai kafin ta Isa wajensu zahiran har sun samu motar gadon Kaya sun hau driver ma ko karbar kudin baiyi ba yace su barshi Ahaka Murja ta Kara tare wani bus din tabi bayansu fatanta kawai ta Isa wajen su kafin suje gidan su su tona Mata asiri. Sai dai duk Inda suka so tadda bus din su Zahira sai days Dan musu nisa. Suna Isa junction din gadon kayan su Zahira Suka sauka da Sauri suka hau gudu Murja dake ankare dasu tana ganin kwanar da suka Shiga ta cewa kwandastan akwai na Nan ta sauka da Bakin Sauri Tana bawa.kwandastan kudi Ta tari machine akan ya Shiga kwanar Nan ga wasu Yara can suna gudu Dan Allah ya ta dosu. Su Zahira kuwa gudu.suke.suna fad'uwa.dan sunga hawanta machine Ta kusa ci musu Nadeeya ce ma Bata iya gudun sosai sai Zahira ta Dan jirata ahaka machine din Murjan ya taddasu ta Kai.hannu ta daki bayan Nadeeya tana Daga Bayan machine din duk da Yana tafiya.ce wa take su tsaya Amma Ina Zahira da Nadeeya Kara gudun suka sa Dan sun fara hango k'ofar gidansu. Murja kuwa sai kaiwa.mai machine duka take Akan yayi Sauri. Ni kuwa Ina fita waje Naseer ya.jani gefe Yana k'ok'arin min magana Umma kuwa ta fito daga gida tana zagina tana surfamin zagi akan na bar Mata k'ofar Gidan da Ni kuwa na dage bazan bar k'ofar gidan ba wlh sai an fitomin da Nadeeya da Zahira. Dukanmu ba Wanda ya lura Dasu Nadeeya dake nufomu suna tikar gudu Tun kafin su iso naji suna kwalla Mana Kira Abba Umma Muna juyowa suka iso a daidai lokacin da Naga wata Mata itama ta sauka daga Kan machine din ta damko Kafadun zahiran data cala wani uban ihu........... [7/4, 10:25 PM] Zannura: *NAGA TA KAINA* *NA SADNAF*🌸🌸 ®️ *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_* _{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_ *Free Novel* *Page 40* Idon Murja sosai ya rufe da San ta damke Zahira ta faffala mata Mari ko kad'an Bata lura da su Naseer dake tsaye ba ta daga hannunta da zumar wanka Mata Mari Ni kuwa tundaga yanda nagansu a firgice hankalina ya tashi yanda ta damke kafadar Zahira yasa nayi wani super na Isa gabansu tana daga hannunta na tare Marin tare da rike hannunta na wancakalar da Karfin tsiya Zahira kuwa ta taso aguje ta buya a bayana tare da kankameni jikinta na balain rawa. Sai a lokacin Murja ta lura dasu Naseer da jikinsa ke rawa shima cikin tashin hankali ganin su Nadeeya da Zahira dake tikar gudu Murja na binsu a Baya Jikinta ne ya dau rawa cikin tsoro ta zub'e a kasa tare da fashewa da kuka Ni kuwa nace "Ke jahilar inace da Zaki biyo yara har gidan ubansu a gaban iyayensu Kuma ki nemi dukansu Mai suka Miki"? Nace wa wacce ta biyo su zahiran da bansan dalilin dayasa ta biyosu ba banma San daga Ina suke ba "Murja lafiya kuwa"? Shine abinda naji Naseer yace Mata ita kuwa sai rizgar kuka take" Tana k'ok'arin magana naji muryar Nadeeya data rungume kafafun Naseer ta Baya ta lek'o da fuskata tana "Allah ya isa tsakaninmu dake muguwa Azzalluma sai Allah ya saka Mana bazamu tab'a yafe Miki ba Abba muguwa ce kullum sai ta dake mu ta d'auko wuka Wai sai ta kashemu Bata bamu abinci sai dai Wake da sabulu" "Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun Nadeeya Mai na Miki da zakimin wanan Sharrin Yaya Naseer wlh karya take min tunda ka Kai su kullum sai sunyi kuka Akan suna San su dawo kullum sai na rarrashe su shine yau daga Shiga wanka na fito mak'ota sukace min gasu can sun gudu shine fa na biyosu har Nan Dan bana San wani Abu ya samesu Amma wlh ban musu komai ba" "Wlh Abba karya take yi kaga shattin tsintsiyar kwakwan data dakemu dashi kaga Gefen fuskar aunty Zahira wlh muguwa ce yanzu ma sai data dakemu Wani Mai shago ya bamu kudi Akan mu gudu kafin ta kashemu" Murja na k'ok'arin Magana Hajara da tunda ta ga Murja ta daskare a tsaye Ganin irin sharrin data kula musu Kafin su har gidan Tijjani irinsa take kulawan yanzu yasa ta daka wani uban tsalle ta tsaya Agaban Murja tana "Karya kike wlh shegiya munafika kafira makira Yar wuta duk abinda yarinya Nan tace wlh Zaki aikata tsaf Yau kinzo har inda nake kin sameni kin rabani da Dana kin sa ya koreni hakan Bai isheki ba sai kin taba jikokina toh wlh yau sai na Rama abinda kikamin" Hajara tace tana cakumo rigar Murjan tare da ware murya ta hau kwallawa Safiyya dake daki tana bacci batare da tasan duk abinda ke faruwa ba yanda ta ware murya ne yasa Safiyya ta jiyota ta kuwa fito a guje. Murja kuwa irin cakume mata Riga da tayi yasa ta mik'e tana "Umma Mai na Miki Dan Allah Mai na Miki kika tsaneni" "Allah ya tsinewa bakinki albarka da kike KIRANA Umma dashi Ni da kika zaneni wanan Bai isheki ba Kika hada da makirci sai da muka bar gidan nida gidan Dana k'arfi da yaji Kika hanani abinci dayake bakida ta Ido ni Zaki kalla kicewa Umma Allah ya tsine Miki Murja Nan ma makircin zakimin kenan duk da babu idon Tijjani? "Murja sosai.ta ringa Kai zuciyarta nesa Dan ji take kamar ta daga Hajaran ta maka da kasa Amma Bata San ta kwafsa sabida Naseer da ya saki baki Yana kallonsu Hawaye ta hau yi cikin shesheka tana "Haba Umma kiyayar da kikemin har ya Kai Haka da Zaki min sharri" Ke Amma bakida kunya Yanzu anan ma makircin Zaki mana" Safiyya tace tana nada hannun rigarta "Haba Umma" Wani irin Mari Hajara ta d'auke Murja dashi sabida bakin cikin yanda Murja ke neman nunawa ita ta Allah ce Murja kuwa ta dafe kumatunta tana Jin zuciyarta na zuwa wuya tana k'ok'arin Kara magana ta Kara kwashe Murja da.mari Murja kuwa zafin Marin Yasa ta manta da wani Naseer da ke tsaye ta daga Hajara sama duk da uban cikin jikinta ta makata da kasa Safiyya tayi Kan Murja ta hau Kai Mata duka Naseer kuwa dake sallati Ya nufi.kansu aguje Yana ihun Kar a tab'a Murja ciki ne da ita adaidai lokacin da Hajara ta samu ta mayar da.murja kasa ta d'ebo kasa.ta cusa a bakin Murja Naseer kuwa ya wancakalar da safeeya ya ruk'o Hajara da k'arfi da itama kamar karfin aka Kara Mata sai ma k'ok'arin tak'e cikin Murja dake kawo Mata duka itama take. "Cikani munafiki Ashe Dama gidan Tijjani ka Kai yaran Nan shine kacemin sun b'ata ka dagamin hankali Naseer Ni zaka yaudara Naseer Akan na Mori yaranka mu samu na rufin asiri gabadaya ka gwammace ka Kai su gidan azzalluma Nan makira har kazo kamin karyar sun B'ata Naseer Dan kawai Kar na Dora musu talla? Tallan Dana Dora musu Dan wa na Dora musu Naseer ba Dan mu samu abinda yaran naka Zasu ringa ci bane tunda ka kasa Nemo Mana kudin kirki tunda shegiya matar Nan taka itama.ta bar gidanan ta asirceka komai naka ya tsaya cak daga Kai har Tijjani kun auro shegu tsinannu" "Wlh Ni ba shegiya bace Umma kuma danki da kike magana ai na bar.miki shi tunda bana gidansa yanzu Yara Kuma da kike magana wlh a yau Zan kwashe su na tafi dasu Dan bazan Kara barinsu a gidanan ba Ni Zan iya kula dasu ke D'an naki ya kula dake kedai Umma ki nemo masa wacce ta kwanta Miki ki aura Masa" Nace Ina rik'e da hannun Zahira Dana Nadeeya daga abinda ya faru.nagane Murja ce matar Tijjani tunda Naseer ya rik'e Umma.ta kwashi takalmanta tare da furzar da kasar da Umma ta cika Mata bakinta dashi. Da sauri.ta hau tafiya tana rufe fuskarta da mayafi Safiyya kuwa har da diban dutse ta jefa Mata "Karki sake Kimin rashin kunya in Banda kaddara Mai Naseer zaiyi dake Yara Kuma da kike magana ba Inda Zaki tafi dasu ko kwaki ya samo ya Basu suci so kike ki tafi da yaran sabida ya biyoki ko toh na Gane wayonki ba Inda zakije da yaran"? "Wlh sai na tafi dasu Umma Banga uban da zai Hana ni tafiya dasu ba" Nace Rai a bace tare da rike hannayen yarana nayi gefe dasu Nadeeya kuwa Naga ta Dan tirje Naseer da idonsa ya kad'a yayi wani irin ja dak'yar ya bud'e bakinsa yana "ki tafi dasu Naeema Allah ya musu albarka" Ameen nayi saurin cewa na fara k'ok'arin juyawa hannuna rik'e Dana yarana Zahira kuwa har tayi gaba. Aunty ita Kuma tana rik'e da hannunsu Raheema. Umma kuwa tace "Kace ta tafi dasu kana da hankali kuwa"? Naseer Bai ce Mata komai ba Illa ma hannunsa da ya mikomin Yana "Dan Allah Dan bani Waleed Naganshi Naeema" Ban ma saurareshi ba duk da tausayinsa na nukurkusar zuciya ta Aunty kuwa ganin na ma share shi na dau hanya zan tafi yasa ta saki hannunsu Raheema ta karaso wajena ta kunto Waleed Ni kuwa nace Mata "Kar fa ya hanani Dana" Bata saurareni ba ta mik'awa Naseer Waleed Waleed kuwa ya karbe shi da hannu biyu ya rungumeshi a kirjinsa adaidai lokacin da hawaye suka zubo Masa yayi saurin d'auke hawayen ya sumbaci Waleed a goshi Yana "Allah ya maka albarka Naseer" Daga Haka ya mik'awa Aunty shi Ya kalli Zahira da har sunyi gaba Yana "Ba Sallama Zahira Raheema.humaira bazaku zo kumin Sallama ba" Da Sauri duk.suka nufi wajensa ya sunkuya ya rungumesu ya shafa kansu gabadaya har da Nadeeya dake gefensa yace "Maza kubi ummanku ku tafi kunji Allah ya muku albarka kuringa yiwa Abbanku addua Allah ya bashi kudi kunji"? "Abba bada Kai zamu tafi ba"? Nadeeya tace hawaye na cika Mata Ido adaidai lokacin da su Zahira suka.dan Kara yin gaba Dan suna tsoron Naeema ta tafi ta barsu Murmushin karfin hali Naseer yayi Yana "badani zaku Tafi ba Nadeeya Amma zanzo kinji maza Kibi Yan uwanki ki tafi" Hawaye ta hau Yi Tak'i motsawa Ni kuwa na daka Mata tsawa Ina "Dan ubanki kizo ki wuce mu tafi" Umma kuwa sai zagin Naseer take tana zagina Akan na asirice Naseer yace na tafi da yaran Ga mamakina Nadeeya girgiza min Kai tayi tana "Umma idan bazamu tafi da Abba ba a wajen Abba Zan zauna bazan biku ba" Ta karashe cikin kuka.tana kankame Naseer Ni kuwa na Kara daka Mata tsawa Ina "kizo ki wuce mu tafi Nadeeya wlh Zan zaneki Dan idan Kika zauna a Nan duka Zaki ringa sha a Dora Miki talla ko makaranta ma bazaki je ba" "Nidai ba Inda zani wajen Abba Zan zauna umma" Naseer kuwa banbare ta yayi daga jikinsa cikin murmushi da kana gani kasan na yak'e ne ya sunkuya ya rik'e hannun Nadeeya Yana "Karki damu Nadeeya ta zanzo na sameku Kibi ummanki ki tafi kinji idan Kika zauna anan ba Wanda zakiyi Wasa dashi" "Nidai ba Inda zani Abba indai bazaka bimu ba a wajenka Zan zauna" A zuciye na nufi wajen Naseer da niyyar na fincikota ita kuwa ta dib'a aguje ta Shiga gidan tana hankada Umma dake bakin kofa........ Toh ga readmore biyu Nan tunda kun matsamin😝😝😝😝😝😝😝😝 [7/5, 10:40 PM] Zannura: *NAGA TA KAINA* *NA SADNAF*🌸🌸 ®️ *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_* _{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_ *Free Novel* *Page 41* Har ciki na bita Nima Ina dan bangaje Umma datayi bake bake a bakin kofa ita kuwa tayi ta auna min zagi Wai na fito Mata daga gidan d'a Kar na Musu Sata. Ban saurareta ba na bi Nadeeya har d'akina na da Dan Nan ta shige Tana ganina ta kankame jikinta tana ihun kukan "Ba Inda zani Umma bazan biki ba a wajen Abba Zan zauna Umma idan Kika tafi damu waye zai zauna da Abba ba Inda zanje Umma" Haushin taurin Kan Nadeeya yasa na Kai Mata duka na rik'e hannunta da Karfi da nufin janta a kasa sosai Kuma nake mamakin Inda Nadeeya ta samo taurin Kai bazata Gane Gata nake Mata da rabata da gidanan ba daga Ni har sauran yaran nawa ai ba a San ranmu muka bar Abban nata ba Dan muma ba finmu San shi tayi ba Kara fincike hannunta tayi da k'arfi ta hau burgiman ba Inda zataje Ni kuwa na cire takalmina da niyyar zaneta. Naseer ya shigo da Sauri ya rik'e hannuna Yana "kiyi hakuri karki bugeta Bari na rarrasheta" Ya saki hannuna ya durk'usa gaban Nadeeya tare da dagota ya hau rarrashinta Akan ta bini ita kuwa sai tirjewa take Akan bazata bini ba ita a wajensa zata zauna a karshe ma sai ta fita aguje Ni kuwa na fara k'ok'arin bin bayanta aguje naji Naseer ya ruk'o hannuna ya Kuma jawoni jikinsa ya kamkameni ta baya tare da Dora kansa a kafadata naji dumin hawayensa a kafadar tawa daya haddasa min wani irin raunin zuciya da San na juya na rungumeshi na rarrashe shi Cikin rawar murya ya fara magana Yana "kiyi hakuri Naeema nsan kinyi hakuri Zama da Mahaifiyata tsawon shekaru Wanda sai da Kika tafi nagane irin hakurin da kikayi da ita Naeema na kasa sauke nauyin da Allah ya doramin na gaza ciyar dasu na gaza tufatar dasu ba irin kudin da ban nema ba ban samu ba Naeema Dan Allah idan Kika tafi da yaran Nan ki Kular min dasu Allah ya Baki Lada ita kuma Nadeeya tunda ta dage bazata biki ba ki barmin ita Zan kula da ita insha Allahu na Kai su gidan Tijjani ne sabida Ina tunanin acan babu Mai musguna musu bansan matarsa itama ba matuniyar arziki bace na Miki alkwari bazan Bari Umma ta Taba Nadeeya ba indai ta Taba ta insha Allahu da kaina Zan kawo Miki ita" Duk maganar Nan da Naseer kemin Yana kamkame Dani kansa Akan kafadata Yana zubar da hawaye nima hawayen nake sosai Dan. Har ga Allah a yanzu ne Naseer ke bukata ta a kusa dashi yau da Umma Bata sako mu agaba ba Dan abinda nake samu iya zaman duniya dai zai ishemu dagani har yarana da Naseer Amma Umma ta dage sai mun rabu. "Daga Bauchin Kika zo"? Naseer yace Girgiza Masa Kai nayi Ina k'ok'arin Magana naji muryar Umma cikin ihu tana "Yau Naga karuwa har cikin gida yau Naga ikon Allah yanzu har daki Kika shigo Dan ki yaudari Naseer ya Kara miki wani cikin kenan kamar yanda Kika Saba Kai jamaa wannan yarinya anyi jarababbiya kwartuwa" Fusge jikina nayi daga na Naseer da har lokacin yake rik'e Dani tsayuwar Umma a bakin kofar d'akin Bai saka ya cikani ba Ni kuwa na ja Tsaki na bangaje Umma dake bakin kofa ta kawo hannu zata kawomin duka Dan sai data Kusa fad'uwa dana bangajeta na kauce "Shegiya karuwa Dole ki hankadani tunda na kamaki kina k'ok'arin yiwa Dana fyad'e" Bance Mata komai ba na fice waje ta biyoni har waje tana min ihun kwartuwa Naseer kuwa magana yake Mata Yana k'ok'arin hanata Amma sai ihu take cigaba da yi. Hannun Raheema kawai na rik'e Dan Waleed na hannun Aunty su Zahira Kuma suna can gaba dasu Minal. Muka hau tafiya Ina danne kukan dake neman fitomin ta karfi Dan har waje Umma ta fito tana min ihun kwartuwa karuwa. Wai nice karuwa ban waiga ba duk da naji Naseer ya daka Mata wani uban tsawa akan tayi shiru Amma a madadin tayi shirun sai cewa tayi "Saukar Mari nake jira naji Dan ka Riga da ka Saba marina Maza Mareni sabida wancan karuwar data biyoka har gida zata maka fyad'e. Naseer bakin ciki ne yasa ya koma ciki ya lek'a dakin Umma ya ruk'o hannun Nadeeya suka fice daga gidan. "Gaskiya ban taba ganin uwar miji irin Taki ba Naeema duk yanda Zaki bawa mutum labari bazai Gane ba sai ya ganta da idonsa wlh rabuwarki Da Naseer yafi alheri Kai wanan Mata anyi tsinaniya yanzu Nadeeya dagewa tayi bazata bikin ba"? Mai yasa Baki tilasta Mata ba Naeema kinsan yarinta ke damunta ita gani take ba Wanda zai zauna da abbanta shiyasa ta dage bazata biki ba" "Hmmm" Kawai na iya cewa Aunty Dan Sam bana Jin yin magana sabida abinda ya tsayamin a mak'oshi yak'i tsirgamin Muna fita titi na tare Mana taxi su Zahira suka Shiga na karbi Waleed daga hannun Aunty A k'ok'arina na inyi magana na fashe da kukan dake cina tundazu "Sai hakuri Naeema Allah dai ya shiryi matar Nan idan tana da rabon Shiriya Ban ce Mata komai ba na Shiga taxi Ina cigaba da kukana. Sunkuyowa Aunty tayi daidai window motar tana "zanzo jibi kafin na Zo dai Zan lek'a gidan Naga ko Zan iya shawo Kan Nadeeya dan inaga sai kinfi samun kwanciyar hankali idan Kika gansu a gunki gabadaya. Kai na gyad'a Mata muka wuce. Muna Isa Muka sauka gabadaya na karbi kudi a wajen Hassana dake ta markade na bawa Mai taxi. Na dawo muka zauna a palo gabadayan mu. Yarana sai kalle kalle suke. Sosai nake Jin ba dadi da Nadeeya Bata biyoni ba da nasani na Mata tsinannen duka na taho da ita Dan ai ba fin karfina tayi ba Naseer ne ma yake wani lallaba ta. Kitchen na fita na Dora Mana ruwan tea Dan Nima ban karya ba na fita shagon k'ofar gida da Isihu shima tafiya da nayi karbowa Waleed magani Nazo na same shi ya dawo daga garinsu rashin nutsuwa yasa ban ma bi ta kansa ba Hassana dai tacemin shi yake jire min shagon Kayan shayi na d'aukar Mana da manyan bredi har da kwai wajen goma Na koma ciki na soya Mana na fito da kofuna na kwallawa Zahira Kira tazo ta d'aukar Mana flask din shayin. Sosai jikin yarana ya ringa rawa farinciki shimfide a fuskarsu ahaka na zubawa kowace Madara da bournvita Dan gwangwanin su na dauko. Kwan Kuma na ajiye a tsakiyarsu. Sosai jikinsu ya ringa rawa wajen Shan shayi Kamar basu tab'a cin abinci ba. Bare Zahira da duk zafin shayin Haka take kurba sosai tausayinta yasa kwalla zubomin Dan ga shattin tsintsiyar Nan a kwance a wajen idanta ga jikinta Nan ma yayi rudu rudu sabida duka. Hannunta kuwa ya Kara sirrancewa kasancewarta Mara jiki. Ganin ta a irin halin Nan yasa nama.kasa cin abincin nace "Zahira Mai ya samu jikinki haka"? Hadiye kwan data saka a baki tayi tana "Aunty ce take zanemu kullum" "Da kuka Mata me take zaneku kullum"? Shanye shayin daya Mata saura tayi ta hau bani labari irin rayuwar da sukayi a gidan Tijjani da yanda Take dafa wake Mai uban attaruhu da sabulu Tana bani labarin tana kuka Dan Abu kad'an ke saka Zahira kuka ko tsawa ka daka wa Zahira yanzu Nan zaka ga idonta ya ciko da hawaye Sosai na ringa kuka Ina duba jikin Zahira daya Sha tabon bulala da dorina "Allah ya Isa tsakani na da ita bazan tab'a yafe Mata cutarmin daku da tayi ba Mai kuka Mata da zata azabtar daku Haka har ta muku horon yunwa ta ringa bawa Nadeeya Sabulu da wake sabida mugunta Allah ya Isa bazan yafe Mata ba Allah sai ya muku sakayya tun a gidan Duniya idan Allah ya yarda Allah sarki Nadeeya yanzu Haka ta ringa cin wake da sabulun babu abinda ya sameta"? "Eee umma sai dai tayi ta kashi Mai kumfa tacemin duwawunta na yaji idan na hanata cin wake sai tacemin yunwa takeji sai taci" Kaina har ciwo yamin sabida kukan zalincin da matar Tijjani tamin Sai da Hassana ta Gama markaden tazo ta zauna na Dan Bata labarin duk wuyan dayarana suka Sha taci kuka itama tana Dama Nadeeya ta biyoni . Nima iirn wuyan da Zahira ta bani Akan nadeeya ta Sha naji inasan na dawo da Nadeeya gabana na kula da ita Ita da Minal suna da balain ci Anan Zan Basu duk abinda suke so ta dawo Nan tabar Naseer Yaji da kansa Hassana ce ta Tayani tsefewa su Raheema Kai har Minal ta musu wanka ta wanke musu Kai. Zannuwana na raba musu Suka daura na janyo gwangwanin na danake Tara kudi . Na duba Naga kudin ciki da Dan yawa na dibi yanda zai isheni karfe uku na nufi Sabon gari Dan acan na Dan Tsintowa Waleed Kaya masu kyau kamar sababi Kuma a kudi kalilan. Sosai na jiddo wa yarana Kaya har da panties Zahira danaga ta fara kirgen dangi har ves ves na siya Mata dasu under wear duk abinda na daukarwa Zahira sai Dana d'aukar wa Nadeeya Dan nasu zahiran yadan fi yawa. Kala.uku na daukarwa Isihu shima Dan ya zama tamkar Dana Tinda barina gadon Kaya yasa shima ya hakura da makaranta ya dawo wajena duk da ba a gidana yake kwana ba a wani makaranta Allo dake unguwar yake kwana a Kuma Nan yake karatu. Sai wajen Magriba na isa gida. Yarana sai tsalle tsalle suke suna Wasa Zahira itama sai washe baki take abinda ya ragemin Jin dadin kasancewata dasu shine Nadeeya da Bata Nan Dan da tana Nan da kila hankalina Bai rabu gida biyu ba. A Daren nida hassana har da zahiran muka wanke kayan gabadaya. Suka saka vest din Dana sisiyo.musu. Zahira akwai San.kallo Dan tv black and white Dana siya karami da lokacin tashar Nta ne kawai da ctv suke Dan drama Dan sai kana da video kake iya siyan cassette kayi kallo. A gaban tv tayi zaman dirshan tana ta kallo har kannenta sukayi bacci suka barta. Sai da zamu kwanta na umarceta data kashe. A daki daya muka kwana gabadaya Banda hassana. Ni kuwa Sam baccin ma Bai min wani dadi ba sabida zuciyata dake wajen Nadeeya. Naseer kuwa Yana barin gidan Bai zame ko Ina ba sai wajen da aka basu kwangilar gini. Ya samo benci ya zaunar da Nadeeya ya siyo Mata shayi da bredi har da kwai ita kuwa ta hau ci tana Masa hiran sabulu da waken da Murja ke basu sunaci. Ta dage rigar jkinta tana nuna Masa shattin bulala dake kwance a jikinta tana "Abba kaga yanda ta zanemu kullum sai ta dakemu ta zageka ta zagi Umma Wai an kawo Mata jarraba" Naseer kasa magana yayi Sabida tsananin b'acin Rai dayake Nadeeya tana da surutu a take ta bashi labarin duk rayuwar da sukayi a gidan. Naseer sosai ya daure baiyi kuka Agaban Nadeeya ba sabida yanda yake ji a Ransa wai da Ransa aka zalunci yaransa Haka Bai taba tunanin Murja Haka take ba Taya yaransa zasu Sha wanan bak'ar wahalar Tijjani yace ko sau daya Bai taba Sani ba baya ganin jikin yaran nasa ne Zahira dake ruwa ruwa wajen kuka ai ko kallon minti uku ya Mata yaci ya Gane Ana gana musu azaba. Sosai ya rik'e tijjjani a Ransa. Dan Bai ga wani laifin Murja ba Tijjanin da Bai saka Ido a gidansa ba yaga laifinsa. A Haka ya saka kayan aikinsa suka hau aikin ginin. Nadeeya nadaga inuwa tana surutai har ta Saba da Yan aikin wajen wani ya siya Mata shinkafa da miya har da nama surutunta da manyance ta yasa tayi farinjini akayi ta Mata siye siye tana Jin dadi Dan inda tafi kwarewa kenan Ahaka wani Abba magini da gidansa ke kusa da wajen da suke aiki ya Dan hau tambayar Naseer dalilin dayasa yazo da Nadeeya wajen. Shi kuwa yace Masa ba kowa a gidan ne iyalinsa sunyi tafiya shiyasa ya taho da ita Dan mak'otan nasa Basu fiye shiri ba. Take shi kuwa Abban yace Mai zai Hana idan sunzo ta ringa Shiga gidansa idan sun tashi Kuma sai su koma gida tare. Sosai Naseer Yaji dadin maganar Abba Dan Dama Yana ta tunanin Inda zai na Kai Nadeeya Dan Sam Baya San barinta a gida makaranta ne dai sai ya samu kudi zai saka ta islamiyya Kuma zai nema anan din har uniform ya Dinka Mata ta ringa zuwa Wanda yaran Abban ke zuwa. Sai da suka Gama aikin Suka koma gida Naseer ya Dan siya musu kayan shayi ya tafar musu dashi. A tsakar gida ya samu Safiyya taci uban kwalliya tana zance da wani. Shi kam ya gaji da kwashe kwashen da Safiyya ke Masa a gida hakane yasa ya Isa wajensu Ransa a had'e ko amsa gaisuwar da suke Masa baiyi ba Naseer yace Masa "idan dagaske kake kana San ka Aureta ka turo magabatanka" "Dama yau tacemin na maka magana Dan inaso na turo magabatan nawa sai Kuma fad'uwa tazo daidai da Zama acan garin da dangin mahaifinta yake anan nake aiki. Inada Mata daya da Yara shidda "Zanje jibi insha Allahu mu tsayar da Magana Dan Nan da wata biyu nakeso ayi bikin namu" "Allah ya yarda" Kawai Naseer yace Dan har ga Allah gani yake Safiyya ta na cikin wayanda suke Masa Karen tsaye a rayuwarsa shiyasan ita ke saka Umma yin wani Abun. A ranar Nadeeya ce ta ringa deb'e Masa kewa da surutanta ya hada da Bata tarihi annabi Yusuf Dan surutan nata ma ba wani Kan gadone dashi ba hakane yasa ya hau Bata tarihin Annabi Yusuf ta kuwa nustu tana ji ahaka har bacci ya d'auketa shima ya d'aura alwala Yana iddar da shafai da wutr ya d'auko Quraninsa Dan ya karanta. Hajara ta fado d'akin kamar an hankadota. A Gefen katifa ta zauna tana "Kai Naseeru dazu naji kana cewa saurayin Safiyya ya turo da fatan ka tanadi kudin da zaka Mata kayan daki Dan kasan banida ko sisi ban Kuma bawa wani ajiya ba". "Banida ko sisi Umma Nima ban bawa kowa ajiya ba idan sun turo taje wajen dangin mahaifinta su harhada kudi su Mata kayan daki kamar yanda sukayi wa Lami Umma Nima ta kaina nake bazan iya zuwa nayi sata ba" "Ai nasan da dangin mahaifin nata nace ka Mata kayan d'akin Dan ko Lami da iya katifa aka kaita har gobe Gori ake Mata ita kuwa Safiyya tana da kishiya Dole ayi Mata kayan daki " Naseer Bai ce Mata komai ba ta Gama surutanta ta tafi. Murja kuwa tana komawa gida ta fara tunanin hanyar da zata bi batare da Tijjani ya zarge ta ba Dan tasan Ransa sai ya b'aci idan yaji Mai tayi Su Hajara kuwa bashi suka dauka sai ta Rama abinda suka Mata idan ta samu ta Shawo Kan matasalar daya kunno mata Kai Sosai ta ringa tsinewa Nadeeya da Zahira tana Jin inama taga Nadeeya a gabanta da ba abinda zai Hana ta shaketa har lahira. Bata San Mai yasa duk kamun da take wa Tijjani baya kamuwa ba tsinanen taurin Kai ne dashi ta Rasa dalili ballantana ta Mallakeshi Wai a Haka ma Mahaifiyarta tayi aiki babba akansa. Daba haka ba da tuni ya saketa Dan bashida mutunci ko kad'an daga aurensu zuwa yanzu ya Mareta ya Kai sau uku gashi ita Kuma balain San shi take. Ahaka ta zauna a gidan cike da fargaba dawowar Tijjani duk da ta gama.hada makircin da zatayi idan ya dawo. Karfe shidda taji karar vespa dinsa. Tayi sauri.ta zauna a tsakar gidan kafarta a kumbure Yana kyalli Dan ta kware a kumbura jikinta da wani hoda da Mahaifiyata ta Bata sai numfarfashi take idonta ya kad'a yayi.jawur Abinda ya Bata mamaki Bai wuce yanda taji har lokacin Bai shigo ba hakane yasa ta lek'a cikin sand'a Inda kuwa ta hango Tijjani a tsaye ya Kama kugu Jamilu Mai shago nata kwara Masa bayani. Gabanta ne ya yanke ya Fadi a lokacin data ga Tijjani idonsa ya kad'a yayi jajir sunyi musabiha da jamilun ya nufo gidan Ita kuwa Murja cikin tashin hankali ta Shiga palo da sauri ta zauna jikinta na Dan rawar tsoro tana tunanin hanyar da zata Kare kanta Daga yanda ya bugo k'ofar hantar cikinta ya kad'a Ta daure ta mik'a kafarta tana ta adduar Allah ya dorata akansa. Wani irin kallo ya hau jifanta dashi daya shigo cikin wani irin murya yace "Ina zahira da Nadeeya"? Kuka ta fashe dashi ta Kara Mika kafarta daya suntume Yana kyalli ta hau cewa "Kaga k'afata wlh a garin na bisu nayi tarkade Nazo Zan Shiga wanka naji mmn Hafsa ta shigo aguje tacemin gasu can zasu gudu kwana uku kenan suna cewa zasu gudu wlh a garin nabi bayansu na Fadi har bugewa nayi a cikina" Ta karashe tana fashewa da kuka Tijjani kuwa ya karasa wajenta Yana "Muga kafar ya sunkuya ita kuwa cikin makirci ta Kara mika kafarta tana cigaba da kuka Tijjani kuwa Yi yayi kamar zai duba kafarta aikuwa ya zaro belt ya hau tafkarta tana daga zaune....... [7/8, 10:57 AM] Zannura: *NAGA TA KAINA* *NA SADNAF*🌸🌸 ®️ *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_* _{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_ *Free Novel* *Page 42* Sosai.ya ringa tafka Mata belt din Yana soka Mata Ashar sai daya Mata lilis ya koma gefe Yana "Maza tashi ki tafi gidanku shegiya makira na tsaneki wlh Allah na tsani mutum munafiki Ashe tunda na kawo yaran Nan Haka kike azabtar dasu ba iya jamilu ne ya tareni ya gayamin ba har Mallam Ashiru wajen aikina yaje ya sameni ya gayamin Ina dawowa shima jamilu ya tareni da zancen ke wacce irin muguwa ce kina d'auke da ciki a madadin ki ringa addua Allah ya saukeki lafiya aa sai Kika saka mugunta agaba kina zalintar yaran da basuji Basu gani ba shegiya munafika Mai fuska biyu Maza tashi ki barmin gida. Tijjani yace a fusace ya ruk'o hannunta ya fara janta da kasa ita kuwa sai numfarfashi take tana Magiyar yayi hakuri sharrin shaidan ne Bai saurareta ba sai daya kaita har waje. Ya watsar da ita ya koma ciki ya cillo Mata takalminta da mayafinta. Ya kulle gidan ya danne vesparsa tare da bada Mata k'asa. Sai data daina hango vesparsa ta mik'e dak'yar tana cije lebb'e sabida yanda jikinta ke balain rad'adi ko ta ina sabida ba karamin Jibga ya Mata ba. Gidan dake jikin gidansu ta shiga ko Sallama babu A tsakar gida ta tarar da matar gidan na zaune a Kan tabarma tana yiwa yarta kitso Mallam Ashiru Kuma na zaune akan kujera Yar tsugunno da buta agabansa da alama jira yake a Kira sallah yayi alwala. "Lafiya Kika shigo Mana ba Sallama " Dalla rufe min Baki Dan ba wajenki Nazo ba wajen wanan Dan iskan Mai dogon wuyan Nazo wato sabida munafinci shine kaje ka samu mijina kace Ina zalintar yaran da aka kawomin Ina ruwanka da rayuwata da ina ruwanka da abinda nakeyi shege munafiki tsinane kaji da matsalolin da ke gabanka Mana na me sai ka Shiga abinda Bai shafeka ba toh burinka ya cika ya ce na tafi gida wlh Allah kayi addua Kar munafirci da kayi ya zama sanadin mutuwar aurena Dan wlh idan Aurena ya mutu zakayi mamakin abinda Zan maka sai ka gwammace ma da baka sani ba" Daga Mallam Ashiru har matar tasa ba Wanda ya iya magana har ta juya ta tafi. "Sai Dana Gaya maka ba ruwanka Dan matar Nan wlh ba mutunci ne da ita ba kaf unguwar Nan ba Wanda take muamalla arziki dashi ba Mai Shiga harkarta sabida mugun halinta Amma gashi" "Dalla kirufemun Baki Taya zakice Kar na Gaya masa tana zalintar yaran daya kawo gidanan ke kanki anan kin Sha kukan tausayin yaran idan kika jiyo tana jibgarsu aikin kenan Haka zatayi ta zaginsu tana duka Akan me bazan Gaya masa ba sabida yayi wa tufkar hanci kafin ta Kai ga tayi kissan Kai yanzu Dana fada Masa bashine ya sani ya dau mataki ba" "Allah ya kyauta" Kawai matarsa ta iya cewa Shi kuwa yaja Tsaki Yana Dan Jin sanyi a Ransa Dan sosai yake tausayin Su Zahira idan Yana jiyo irin bugun da take musu Badai tab'a yiwa su Zahira magana bane. Murja kuwa tana fitowa daga gidan Shagon Jamilu ta tsaya sukayi ta zagin Juna tana rantsuwar sai taga bayansa tunda ya hadata da mijinta shima rantsuwa yake akan ba Abunda zata iya Masa Dan Kar yake kallonta idan takamarta uwarta matsafiya ce zata Masa wani Abu ta gwada ta gani wlh sai ya kawo karshenu shima ai ba Haka yake zaune ba" Murja kasa magana tayi sabida mamaki yanda Jamilun yasan Mahaifiyarta matsafiya ce ba ta iya Kara magana ba ta fice daga shagon tana cigaba da Shan alwashin sai ta ga karshen Jamilun. Tana Isa gida ta zub'e a tsakiyar palon nasu ta hau kuka. Mahaifiyarta Rabi ido ta zuba Mata Bata ce Mata komai ba. Sai da Murja ta gaji Dan kanta ta bud'e baki da zumar Mata magana Rabi ta daga Mata hannu fuskarta hade tana "Ba sai kin gayamin komai ba Naga duk abinda ya faru dazu kawai na dauko tukunya ta Dan na duba halin da kike ciki Naga Yana ta jibgarki ai sabida Dan iska ne shi bashida mutunci Bai ga cikinsa da kike d'auke dashi ba yayi ta dukanki ai ba jaka na aura masa ba Amma ba komai yyi na farko yayi na karshe shi da ganin Haske sai dai a lahira" Rabi tace Tana k'ok'arin mik'ewa Murja kuwa cikin tashin hankali ta dira gabanta tana "Mama Dan Allah karki Masa komai wlh inasan mijina Dan Allah karki Masa komai wlh ba laifinsa bane Mama karki makantarmin da miji Dan Allah Fusge kafarta Rabin tayi tana "wlh sai nayi Abunda nayi niyya Dan ya kaini bango na tsani mijin Nan naki wlh tunda Naga Yana da taurin Kai duk aikin Dana Yi akansa Baya ci na tsane shi na rasa Mai yasa Kika nace kina San zama dashi" "Nidai Ina San shi mama Dan Allah karki Masa komai nidai burina kimin aiki akansa Mai zafi yazo da kansa ya maidani gidansa a Kuma mallake min shi ya daina min taurin Kai duk abinda nace yayi shi zaiyi. Mutane biyu nakeso kimin maganinsu wani jamilu da wani Ashiru makocina su nake so ki Gama min dasu Dan su suka hada min munafirci Nan sai Kuma uwar mijina da kanwar mijina Umma inaso Suma ki kawomin karshensu duka sukamin yau har kasa suka bani naci" Tsaki Rabi tayi ta janyo bakin tukunyar tsafinta gabanta dake cike da wani irin ruwa tana "Daga Kan shegen mijinki zan fara Dan wlh Bai daki banza ba Take ta hau surkulle Tijjani ya bayyana saman ruwan Yana Kan vespansa Yana ta tuk'i Murja cikin tashin hankali ta hau ihu tana Mama Dan Allah karki Masa komai ki taimaka min wlh inasan mijina" Wani dogon Abu Rabin ta d'auko kamar kibiya zata caka a ruwan. Murja ta fizge kibiyar da k'arfi. Rabi kuwa ta girgiza tukunyar da Tijjani har lokacin yake bayyane Yana tuki. Take kuwa vespan nashi ya hau tangal tangal dashi har sai daya bige wani Mota dake gabanshi ya hantsulo daga Kan vespan. Ta daki ruwan Tijjani ya b'ace Murja ta hau zunduma ihu Ita kuwa ta daka Mata tsawa tana ban masa.komai ba na dai Masa gargadi ne kawai Dan wlh wanan shine na farko na Kuma karshe idan ya Kara tabaki wlh sai na raba shi da numfashinsa Sai wa kikace "Nidai nunamin shi nagani na tabbatar ba Abunda ya sameshi" "Ba Abinda ya sameshi dalla karki dameni wlh Kika batamin Rai Zan Masa Mai gabad'aya Tace a tsawace Tana Kara surkulle Sai ga Mallam Ashiru ya bayyana a cikin Massallaci a zaune tana daga kibiyar tsafin ta ya b'ace Duk abinda take Murja na kallo "Wanan sai anyi da gaske Dan Baya Wasa da Addu'a" Surkulle ta Kara Yi amadadin Jamilu ya bayyana sai Murja ce ta bayyana Hankali a tashe Rabi ta girgiza tukunyar tana "wanan Dan iskan ne Ina tab'a shi kanki zai dawo shima sai na shirya sosai Dan bahaka yake zaune ba Ita Kuma uwar mijinki da kanwar mijinki kibarni dasu sai kin koma.zaki dau fansar abinda suka Miki Wanan mijin sai nayi dgsk Zaki mallakeshi taurin Kai ne dashi" Sosai Murja ta ringa Jin dadin mallake Mata Tijjani da mahaifiyarta tace zatayi Tijjani kuwa Yana hanya zaije gadon Kaya wajen Naseer yana dab da Isa wajensa yaji Kan machine din na rawa Yana neman kwace Masa duk yanda yaso rik'e Kan machine din kasawa yayi har sai daya buge wani Mota dake gabansa ya hantsula. Sallati mutane Suka saki sabida duk an dauka Tijjani bazai Kai labari ba sabida ya daki motar gabansa sosai Ga mamakin.mutane Kuwa suka ga ya mike tsaye Yana karkad'a jikinsa Mai motar kansa da aka buge sai daya fito ganin Tijjani Bai ji ciwo ba yasa ya koma ciki yaja motarsa batare da ya tsaya sauraran hakurin da Tijjani ke bashi ba Dan ya fasa Masa glass din motarsa. Vespa din ya hau ya koma gida dan kayansa sun b'aci washegari da sassafe ya dau hanyar gidan Naseer sai daya fara tsayawa a tsohon gidan Naseer ya tambayi Inda suka koma da kwatance yaje har k'ofar gidan. Da Sallama ya Shiga gidan Nadeeya dake shara a tsakar gidan ce ta amsa ganin Tijjani ne yasa tayi wurgi da tsintsiya hannunta taje ta rungumeshi tana Masa oyoyo. Naseer dake kitchen fitowa yayi da kofin shayi a hannunsa. Duk da Yana Jin Haushin tijjanin Haka ya saki fuskarsa Ya Yi wa Tijjani iso har palon Hajara dake zaune da Safiyya a daki suna Shan shayi kamar a mafarki taji muryar Tijjani ta kuwa Mike da Sauri tayo waje Dan ta gaskata zarginta Wani irin hade Rai tayi ta fito daga d'akin a daidai lokacin. Da Tijjani ya zauna Akan tabarma dake shimfide a palon hannunsa cikin Na Nadeeya "Uban me kazo nema a gidanan Tijjani"? "Aaaa hajajju makatu Ashe kina ciki Rai kanga rai hajiya Umma" Tijjani yace Yana dariya dayaga yanda Hajara ta had'e Rai Hajara kuwa tace "ubanka kake rainawa Hankali Tijjani bani ba maza kafin na kirga uku tashi ka bar gidanan Dan na Gaya maka na yafeka banasan ganinka" Dariya Tijjani ya sakeyi Yana "Sai hakuri fa Umma nazama Dolenki ba ynda zakiyi inkika koreni Ina kikeso naje" "Kaci ubanka Tijjani ka dauka Wasa nake ma ko Ni da ka kora daga gidanka har da biyomu da kudin mota ka zabi Zama da matarka Tijjani akan dai kabi Umarnina baka darajani ba a matsayina na mahaifiyarka ka zabi tsinaniya da Bata tsoron Allah k'arfi da yaji ta zaneni Akan shegen bredi kana shigowa ta had'a makirci ka k'i yarda da maganata har sai daka koreni daga gidanka ka dauka Wasa nake Akan na yafe ka a cikin yarana Murja tazama uwarka tunda ita ka zaba akaina Tijjani idan baka San na Kara maka wani bakin ka tashi ka bar gidanan Dan wlh ganinka b'acin Rai yak'e Kara sani" "Umma Nima fa bansan makira na aura ba wlh sai Jiya nama koreta tana gidansu yanzu Haka Dan wlh bansan Haka take ba kinji na rantse Miki ban taba sanin munafika bace Mai fuska biyu ba sai Jiya da makocina da Mai shagon unguwarmu ya gayamin yanda take yiwa su Zahira bantaba sani ba sai Jiya shiyasa ma Nazo Dan na bawa Yaya Naseer hakuri kema na baki hakurin" Sai a lokacin Hajara ta Dan saki fuskarta tana "Kana nufin yanzu Haka tana gidansu"? "Eee tana can" "Saki nawa kayi Mata"? "Ban dai sakenta ban nace taje gida" "Zancen banza baka saketa ba zaka dawo da ita kenan"? "Aaa bazan dawo da ita ba hajiya Umma ai kina da kudin da Zaki aura min wata matar tunda gashi Nan kin raba Yaya Naseer da Aunty Naeema ya zama gwauro na k'arfi da yaji Nima ba sai na dawo gabanki kiyita kallonmu ba" "Gwara nayita kallonku a gabana da dai ku zauna da wadanan shegun matan naku" "Murja dai nasan shegiya ce tunda ta iya makirci ita aunty naeema fa mai ta Miki bakya santa"? "Bansani ba ubana zaka iya matse bakina in gaya maka Naga alamar ka ma Raina min hankali toh gwara da kazo ma auren Safiyya Nan da wata biyu masu zuwa jibi xaaje neman Aurenta can wajen baffaninku kasan yanzu Naseeru bashida ko sisi Haka Muke zaune Dan Haka ka kawo kudi mu fara rage wani Abun " Duk maganar da Tijjani da Hajara sukeyi Naseer Bai tofa musu Baki ba kansa a sunkuye yama tafi wata duniyar tunanin "Umma kema da abin dariya kike Ina Naga kudin da Zan siyawa Safiyya wani Abu ai ko sisi bana magani nima.murja ke ci damu a gidanan tunda Kika Mana abinda kikayi arzikinmu ya tafi muke fama wanan Dan canter da Kika Sani dashi har yanzu shine Dani maneji kawai nake Dan Haka ki San yanda zakiyi da ita" Dagowa da Naseer yayi ya kalleshi yasa ya kifta Masa Ido Hajara kua ta dage wlh su biyu su nemo kudin da zasu yiwa Safiyya kayan daki ko satane suyi ita ba ruwanta Tijjani dariya yayi Dan shi Sam Baya d'aukar ma maganar Hajaran da wani mahimmanci inzata matsa Masa ma saka takalminsa zaiyi yayi tafiyarsa Hakuri ya bawa Naseer game da abinda ya faru Naseer kuwa yace masa ba komai Suka hau Hira da Nadeeya da ta hau bashi labarin irin dukan da Murjan ke musu ba abinda ta rage a azabar da ta gana musu Inda ran Tijjani ya Kara b'aci sosai dayaga tab'a b'unan jikin Nadeeya wake da sabulun ma datace Ana Basu suci yafi balain kona Masa Rai Bai taba sanin muguntar Murja ya Kai har. Nan ba Bai taba sanin ma Haka halinta yake ba. Ita kuwa Hajara cewa take zatayi abinda yafi wanan Dan Haka ya saketa. Tijjani cewa yyu in ya koma gida zai aika Mata da saki daya Naseer kuwa yayi saurin girgiza Masa Kai Akan Kar ya saketa ya dai Mata fada sabida ita kanta Bata San ya rayuwa zata kasance Mata a gaba ba ko shi kansa Bai taba tunanin akwai ranar da wani Abu zai saka ya Kai yaransa wani wajen ba sai gashi kaddara ta sa ya Kai su Zahira gidan nasa. Tijjani sosai yaji tausayin Naseer Dan har ga Allah yasan dauriya kawai yake Yana cikin damuwa. Bai bar gidan ba sai wajen Sha daya na Rana tare suka fito da Naseer da Nadeeya. Hajara duk rokon data masa.akan ya Bata kudi dagewa yyi bashida ko sisi Naseer har mamakin Tijjanin ya ringa Yi Dan abinda Sam bazai iya ba kenan. Har wajen da Naseer ke aikin ginin Tijjani ya raka shi Suka samu inuwa suka zauna Naseer ya Dan Kara bashi labarin yanda Naeema tazo ta Debi yaran Da yanda Nadeeya ta dage bazata bisu ba da shi zata zauna Ajiyar zuciya Tijjani ya sauke Yana "can garin nasu ta Kai yaran"? "Wlh bansni ba Ina cikin tambayarta Umma ta shigo ta hau ce Mata karuwa k'arfi da yaji Umma ta hanani zaman lafiya ta hanani na samu nutsuwa inasan na kasance da iyalina ta hanani" "Kaine ka barta fa Yaya Naseer wlh Kai kabari take maka abinda ranta keso Ni bazan iya d'aukar abinda take ma ba Kai ma kagani ai Umma wani zubin zuma ce ita sai da wuta idan inasan Abu wlh sai dai tayi hakuri ta kyalleni ai ba Dole bane sai ka zauna da ita ka Kama Mata haya ka dawo da iyalinka gabanka idan tak'i ka siyar da gidan ka gudu ka barta Dole dai ta koma Calabar" "Mahaifiyarmu ce fa Tijjani idan na siyar da gidan na gudu a Ina zata zauna Naga basa shiri da matarka balle nace gidanka zata dawo bama Zan Sam kwanciyar hankali ba idan Naga tana garari" "Toh naji yanzu dai abinda zaayi kayi k'ok'ari ka nemi Inda Naeema take ka ringa zuwa kana dubasu Koda baka Kai musu komai ba yaranka su ringa ganinka Suma suna Jin dadin kaima sanin halin da suke ciki zai saka ka Dan samu kwanciyar hankali Sanan Nadeeya gaskiya gwara ka maidata wajen Naeema Sabida daga Kai har Naeema sai kunfi samun kwanciyar hankali bazai yiwu ka ringa fita kullum da ita sai kace namiji ba ke Nadeeya ki Bari Abbanki ya maidaki wajen ummanku shima Nan zai dawo idan an kwana biyu" Nok'ewa tayi Tijjani ya hau rarrashinta da Mata alkawarin siya Mata kaza da nama take ta hau washe baki tace ta yarda. Tijjani kuwa yacewa Naseer yayi kokari yasan Inda su Naeema suka koma Bauchin ne ko Kano ya maida Nadeeya ya Kuma ringa lek'a su akai akai. Naseer godiya ya Masa sosai Yana Jin dadin shawarar Tijjani Dan kwana biyun Nan sosai ya ji Yana k'ewan Naeema. Har kyautar kudi Tijjani ya bashi kafin ya tafin Naeema Washegari da safe na bazama nemowa yarana makaranta Mai Dan saukin kudi. Dan Zahira Naga ta tsayi Tama Zama budurwa tunda a yau na wayi gari Naga period ya zo mata boye boye ta ringa min duk da ciwon marra da take fama dashi Amma kasancewar waje daya muka kwana yasa nasan halin da take ciki. Zaunar da ita nayi na Bata ilimin Shi kansa haila banji kunyar ta ba na fada Mata komai da yanda zatayi wanka idan jinin ya d'auke har yanda zata tsaftace jikinta da Kuma Kara kame Kanta daga wasa da maza Daidai da kuzungu ma Ni na koya Mata yanda zata saka Dana saka tayi wanka ta wanke zanin data b'ata sai wani sunne Kai take Wai kunya ta takeji. Ni kuwa a Raina ma mamakine nake yaushe har nayi auren wai Yar cikina ta fara period kila kwanan Nan ma naga ana Sallama da ita Akan Ana Santa. Hakane yasa Dana karya na bazama nemo makaranta Dan so nake ma ta fara secondary daga jss 1 Wani karamin makaranta na samu Mai Dan saukin kudi. Sai dai ba secondary sch Wai sai dai ta zanna common entrance tunda baifi saura sati biyu a zanna ba samun secondary bazaiyi wahala ba indai ta zanna common entrance din. Sai Dana koma gida na tafi dasu Zahiran gabadayansu sabida tace zata musu gwaji sabida tasan ajin dazata saka su. Ba laifi yaran nawa na da Dan kokari duk da akwai slow learner's a cikinsu kasancewa na biya duk kudin da aka bukata har na uniform text books kawai Zan siya musu littattafai Kuma inadashi a shago Nadeeya ce kawai nace mata Zan kawota Bata Nan ne ta bani uniform dinta na tafi dashi yarana kuwa kamar Wasa Naga sun shige aji. Zahira Kuma ta wuce primary 5 Cikin farinciki na dawo gida Na dau littattafai dozen uku da fensura na bawa Isihu ya Kai musu da biscuit ya zama Dole na dauko Nadeeya Dan nasan Bai Zama lailai Naseer ya samu kudin sakata a makaranta ba. Safiyya Kwana biyu da maganar da Naseer yayi wa Saurayinta Umar akan ya tura neman aurenta. Yaje har garin calabar ya nemi kanin mahaifinsu ya gabatar da kansa dayake a shirye yake har Sadaki ya bayar Dan sosai kwallin da Safiyya ke sawa ya rikita shi yaji idan Bai Aureta ba bazai samu nutsuwa ba. Anan garin calabar yake zaune da matarsa Hafsa da yayansa. Matarsa macece Mai balain kishi masifafiya a unguwarsu kowa yasanta shegen bin Mallamai ne da ita dan wanann bashine Karo na farko da yake neman aure tana wargazawa.ba Har mallake Umar din tayi sai yanda tayi dashi. Karfin kwallin tsafine yyi tasiri a wajen Umar din ya kamu da San safiyya dayazo.kano.wajen abokinsa da Safiyya ke aiki a gidansa. Ita kuwa Tana ganin Yana da Dan canji yasa tana dawowa gida ta hargitsa d'akinsu har sai data samo kwallin daya shiga rububi ta rambada kwallin a idonta ta koma.da.sauri tana adduar Allah yasa Bai tafi ba Tana kuwa zuwa taci Karo dashi a bakin kofa yazo fitowa daga wanan hada.idon Umar ya kamu da San Safiyya. Kwana uku yayi a Calabar ya dawo ya sanar da Safiyya duk yanda sukayi da kanin mahaifinta Nan da wata Mai zuwa zaa daura aurensu. Safiyya sosai hankalinta ya tashi dataji wata guda kanin mahaifinta yasa Dan tasan Basu tanadi komai ba Hakane yasa Yana tafiya ta sako Hajara da maganar kayan dakin da za Mata harda kukanta. Akan Hajara tasan yanda zatayi da ita Dan Bata San kishiyar ta ta rainata tunda Umar yace a gida daya zasu zauna. Hakane yasa Hajara itama ta Sako Naseer agaba da maganar kayan dakin Har fargabar dawowa gida yake Dan shi Dan kudin da yake tarawa so yake idan ya tashi zuwa gidan Naeema ya Dan yiwa yaransa siyayya Kar ya tafi haka hannu na dukan cinya Dan ya je har gidan Alaramma ya tambayi matarsa ta Masa kwatance Gidan da Naeema sosai yaji dadi da Naeema ta zauna a kano bataje garinsu ba da yasan ma Tana garin Kano Nan kusa dashi da tuni ya nemeta. Hakane yasa ya Tara kudadensa da zumar yiwa su Zahira siyayya har Naeema ma sai ya siya Mata wani Abun. Rabin kudin kuwa Dama Waleed zai kashewa Dan yayi kewarsa sosai shima Gobe ya ke Shirin siyayyan daga wajen aiki ya shirya shi da Nadeeya su wuce Yana shigowa gida ko palon Bai Kai ga shiga ba Hajara ta tare shi da maganar kayan dakin Safiyya. Baya San wani Abu ya dameshi sabida farinciki da yake ciki Cewa Hajara kawai yayi toh zai nema suka shige shi da Nadeeya Ta kaiwa Nadeeya rankwashi akan Bata gaisheta ba ta hau bambamin Kar ya Kara fita da Nadeeya Bata San iskanci idan Nadeeya ta zauna ta tayata aikace aikacen gida laifine.? Naseer Bai dai tanka mata ba ya d'aura alwala ya tafi massallaci sallah Magriba Bai dawo cikin gidan ba sai da akayi sallah Isha ya tsaya a shago ya Dan Yi aski. Daga nan ya Kara sa Bakin titi yayi siyayar da duk zaiyi a wani shago Dan da safe yake San suje wajen Naeema. A shagon ya bar kayan akan gobe idan zai wuce zai dauka. Ya dawo gida ya tarar da Safiyya tasa Nadeeya ta wanke Mata Kaya tana ganin ya shigo ta hau zunduma kuka Sabida har Dan zaneta sai da Safiyya tayi. Naseer kuwa a fusace ya Shiga har d'akin Safiyya ta buya a bayan Hajara Naseer kuwa hakan Bai hana ya cire belt ya tsula Mata ba Hajara sai Masifa take akan me zai daketa Dan ta daki Nadeeya ai Nadeeya Bata da kunya ne. Haka ya fito daga d'akin Ransa a bace Ya rik'e hannun Nadeeya sukayi d'akinsa. Nadeeya kuwa ta hau ce Masa ya Kai ta wajen Umma Aunty dukanta takeyi. Murmushin Naseer yayi yana ",Kin fasa Zama a wajena"? Gyada Masa Kai tayi ya saki dariya Yana "daga aunty ta dakeki shine Zaki gudu ki barni" Kara gyada masa Kai tayi tana ita dai ya kaita wajen Umma. Naeema Sosai naji dadin makarantar da yarana ke zuwa da alamu Kuma suna Gane abinda ake koya musun Har islamiyya na Nemo musu idan suka dawo daga Boko sai su wuce sai karfe shidda suke dawowa. A yau ma bayan na rakasu har makaranta gida na dawo na gyara ko'ina Hassana Bata Nan ta tafi bikin Yan uwansu Nima sai anjima Zan je idan yarana sun dawo daga makaranta Dan yau ba islamiyya. Isihune keta markaden. Ni Kuma duk abinda aka zo siya Zan fita da kaina na bayar dayake na fitar da kofa ta cikin gida. Gidan na gyara na Dora ruwan tea Dan nida Isihu bamu karya ba Zobon Dana hada na kukula na zuba a kula na Kai bakin shago Dan Sana'ar zobon shima ya karbeni alhamdulillah duk da Ina siyar da lemon kwalba Duk Sana'ar Dana Dan gwada Allah Yana Sanyamin albarka Zuwa yanzu engine markaden nawa ma biyune Har kujeru masu Dan saukin kudi na saka Mana a gidan Isihu na mikawa shayinsa ya fita shago Ni Kuma na koma ciki na Shiga wanka Dan nasan kafin na fito shayin ya Dan hucce. A band'akin d'akina na Shiga wankan Ina fitowa Naga Naseer a zaune a Gefen gadona Waleed rik'e a hannunsa. Wani irin ihu na kwalla na koma band'akin aguje Dan gani nake gamo nayi idona yake ganemin Kamar Naseer na gani.............. *AYIMIN HAKURI BANJI DADI BANE JIYA SHIYASA AKA JINI SHIRU SHEKARANJIYA KUMA AIKI NAYI NAGAJI SHIYASA BANYI POSTING BA INA MASOYAN SADNAF TRUE LOVERS NGD DA KAUNARKU A GARENI KU DIN MASOYANA NE NA HAKIKA BAZAN MANTA ALHERIN KU A GARENI BA ALLAH YASAKA DA ALJANNATUL FIRDAUSI YA BAR ZUMUNCI* *WANAN SHAFIN NAKINE UMMA YAHAYA MUSA NGD DA KAUNARKI A GARENI MAI KAUNARKA SHI ZAIYI TUNANIN KYAUTATA MAKA ALLAH YA FARANTA MIKI NGD* *NAGA TA KAINA GRP 1 KUN NUNA MIN KAUNA KUMA NGD SOSAI ALLAH YA BAR ZUMUNCI* *SAKON GAISUWA GA DUK MASOYANA* [7/9, 10:40 PM] Zannura: *NAGA TA KAINA* *NA SADNAF*🌸🌸 ®️ *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_* _{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_ *Free Novel* *Page 43* Muryar Nadeeya dake dariya tana Umma mune fa Yasa kirjina ya bar buguwa na sauke ajiyar zuciya na bud'e k'ofar Ina mamakin yanda suka Gane gidan. Nadeeya ma Sam ban lura da ita ba Ko kadan ban sa Rai da zuwan Naseer gidana kurkusa ba Ban kalli B'arin dayake ba na fito Nadeeya dake zaune dirshan a kasan d'akina na nufa kofin shayin Dana ajiye da zumar na Sha shine a hannunta, Gaisheni Nadeeya ta hau Yi Ni kuwa nace "Yar babanta Mai kikazo nema wajena acici daga zuwanki kin dau min shayi" Duk maganar da nake wayancewa nake Dan bana San hada ido da Naseer dake ta kallona kamar ya hadiyeni. Nadeeya uwar surutu take ta hau zuba tana surutu har da dukan da Safiyya ta Mata jiya ta sakata wanki Naseer kuwa yace mata "uwar surutu fita waje kiyi Wasa daga zuwanki kin hau surutu". Kofin shayin ta d'auka tayi waje. Ni kuwa nasan dalilin dayasa ya koreta Sai data fita na juyo Muka hada Ido Na saki murmushi na gaishe shi bai amsa ba ya Ajiye Waleed dake hannunsa ya nufo wajena Wai sai na tsinci kaina Kuma da Jin kunya Yara shidda Yana Abu kamar wani saurayi ko sababin Aure Ajiyar zuciya ya sauke a lokacin daya rungumeni Nima rungume shin nayi Dan nayi kewarsa har ga Allah muna San junanmu Umma ce ta dage sai mun rabu Mun dau tsawon lokaci a Haka sai danaga Yana neman wuce gona da iri na janye na koma gefe baa San Ransa ba ya koma bakin gadon ya zauna ya Kara d'aukar Waleed Yana "Ashe a garin Nan kike shine baki gayamin ba ai da tuni Nazo" "Ai bazan so kazo ba sabida Kar Umma tagane Ina Nan din Dan nasan Idan tasan Ina kano Kai kanka bazaka samu kwanciyar hankali ba Murmushi kawai yayi ya koma ya zauna ya hau karewa ko'ina kallo Yana "Naeema kinyi kokari duk da Baki tafi da komai ba shine har Kika siyi kayan gida Haka Ina yaran nawa suke ganinki ma yasa na manta ban tambayesu ba"? "Suna makaranta" Washe baki yayi cikin murna Yana "Allah ya saka da alheri ya Kara bud'i naeema hakika ke matar rufin asiri ce Umma bansan Mai yasa ta kasa ganin haka ba. Yanzu ma Naga engine dinki ma biyu anan har da shago a k'ofar gida Gyada Masa Kai nayi na hau bashi labarin komai har gidan da muke ciki yanda na siya da kudin gadona. Sosai ya ringa murna yanda Allah ya bud'amin yace "Ni kuwa ba irin wahalar da ban Sha ba Naeema Amma kudi yak'i samuwa aikin ginin ma da nakeyi wlh bai taka Kara ya karya ba Nima kudin da Kika ajiyemin naso Na juya Amma abin bai yu ba" Murmushi nayi Ina "Karka damu Allah na sane dake watarana sai Labari insha Allahu ka cigaba da gayawa Allah" Gyada min Kai yayi ya nuna min manyan ledojin daya zo dasu Akan na duba. Bud'ewa nayi na hau fito da kayan ciki Kayan sawa ya jiddowa Waleed su zahira ma Bai barsu a baya ba sai turmin zani da undies da ya siyomin nima. Dagowa nayi da zumar nayi magana ya girgiza min Kai akan Kar nace komai. Idan nace banyi murnar ganin mijina ba nayi karya Ido nake ta daukewa da naga Yana ta nunamin Yana bukatata Dan ban shirya tarben nasa ba haihuwa na Allah ne bana San nayi ciki yanzu kullum adduata ma Allah yasa haihuwa ta tsayamin kenan Duk yanda naso Bijirewa sai da na barshi ya samu nutsuwan Nayi sauri na fada bandaki nayi wanka na fito shi Kuma bacci ne yayi awon gaba dashi Hakane yasa na dau Waleed muka bar d'akin na rufo Masa Kofa Waje na fita na tarar da Nadeeya nata zuba ita da Isihu ga layin markade Nan suna jirana Dan shagon ma a cike yake da mutane masu siyan Abu Isihu na fama da mutane ahaka yake biyewa Nadeeya dake ta bud'e alewa tana Sha Tsawa na daka Mata Akan ta fito Dan Nadeeya dai ba yarinya bace sosai Engine na kunna nace ta hau markaden Dan wani zubin Tana Yi tsayine dai Bata dashi sosai Amma inta taka Abu shikenan Sai danaga ta markada biyu Naga Kuma ta markada yayi laushi. Na koma kitchen na fara had'a hadan girkin Rana Yanda dai na Saba Miya Mai yawa anan ma Haka nakeyi Dan nafi ganin aukin kayan miyan idan na siya da yawa ganin inada miyan yasa na Dora Mana shinkafa. Na fito wajen Isihu na bashi dari biyu ya siyomin naman Miya Wanda a lokacin Naman dari biyu Mai balain yawa ne Sosai na tsinci kaina cikin farincikin ganin Mijina da kuma iyalina guri daya yanda nakejin kadaici tunda na dawo gidanan Zuwan.naseer yau yasa naji na daina Jin kadaicin Inama mu dawwama Haka Astagafurullah a wanan lokacin har sai danace inama Umma ta mutu mu samu kwanciyar hankali Dan itace babbar matsalar mu. Naseer kuwa baccinsa yake Sha Mai dankaren dadi daya Dade baiyi irinsa ba. Dawowarsu Zahira daga makaranta da ihun murnar ganin Nadeeya yasa ya farka daga baccin daya daukeshi. Mik'ewa yayi zaune Yana murmushin Jin dadi Dan har ya fidda rai Kara kasancewa da iyalinsa waje daya rigarsa ya saka ya fara k'ok'arin fitowa. Su Zahira suka Fado dakin gabadaya suna ihun murna Nadeeya tace da abbansu Suka zo Naeema kuwa duk yanda taso hanasu Shiga d'akin ko sauraranta basuyi ba Suka fada d'akin Cikin murna duka Suka rungumeshi. Shima Naseer cikin tsananin farinciki ya rungumesu sai dayaga suna neman kayar dashi ya janye jikinsa ya zauna a gefen gadon hannunsa cikin Na Raheema dayaga har wani kib'a tayi sabida kwanciyar hankali Binsu ya ringayi da kallo cikin tsananin farinciki ganin yanda Suka canja gabadaya sunyi fes dasu ba Kamar lokacin da suke can wajensa ba Zahira har canjawa tayi a idonsa ta zama budurwa Dan ita Bata Yi haukan da taga kanenta nayi ba inama ya dauwaama Haka daga shi sai iyalinsa da ba Wanda zai Kai shi Jin dadi duk Wanda ya tsinci kansa da karayar arziki irin nasa mutum.kan dauwaama bashida wani buri daya wuce kudin su dawo wajensa kota halin k'ak'a ne Amma shi karayar arzikinsa Bai dameshi Kamar yanda rabuwa da iyalinsa ya dameshi ba. Da tarin kudi gwara ya dauwama da iyalinsa cikin rufin asiri. Sai da Naeema ta shigo d'akin ta koresu kafin Naseer ya samu ya Shiga wankan ya dauro alwala A palon gidan yajasu Sallahr azahar. Suna iddarwa Zahira taje kitchen ta d'auko musu abinci har da zobon da Naeema ta had'a. A faranti daya sukaci abincin gabadaya duka fuskarsu dauke da farinciki Naseer da Naeema ji suke.inama su dauwaama Haka ba abinda zai sake rabasu. Su kansu kasancewarsu waje daya yasa yaran cikin tsananin farinciki sai cewa suka Abba Dan Allah ka zauna anan Kar.ka Kara komawa. Yinin bikin da Naeema Bata je ba kenan Bayan tafiyar yaran islamiyya har da Nadeeya Hira Naseer da Naeema suka.hau yi Inda Naseer Duk yake Bata labarin halin da yake ciki da Hajara da yanda ta matsa Masa yayi wa Safiyya kayan daki. Sosai nayi murnar da auren da Safiyya zatayi Dan gani nake Rabin matsalar mu ya k'au sai dai Yar muryar da Naseer kemin akan idan inada kudi na bashi ya Basu zai bani idan ya samu yasa na hade girar sama da kasa nace Masa banidashi Naga duk halin da muke ciki su suka jawo Mana ko Naman jikina nake yanka musu ba burgesu nake ba Dan Haka ko sisina bazan iya bayarwa ba Naseer Bai ja zancen ba dayaga yanda na hade Rai muka cigaba da Hira da aka fara kawo markaden yamma kuwa shi yaringayi Ni kuwa na Dora Mana girkin dare Dan inaso ya cika cikinsa kafin ya tafin nasan yanzu tunda yasan gida zai na zuwa ganinmu akai akai hankalina yanzu a kwance yake. Sai dai me a lokacin da muka ci abincin daren da nayi tunanin Naseer zai tafi k'in tafiya yayi yacemin kwana zaiyi na Bari ya Dan samu kwanciyar hankali na kwana biyu Dan idan ya koma gidan ma yasan bashida kwanciya hankali Umma Sako shi zatayi a gaba. Ni kuwa.dage Masa nayi ya tafi Dan idan Bai tafi ba Umma zata xargi Yana wajenmu kafin kaceme zata gano Inda muke. Ba yanda banyi ya tafi ba yak'i dayaga ma na dameshi sai ya shige daki ya barni dayake a tsakar gida muke Zaune. Ba yanda na iya ahaka na hakura yarana Suka kwana a d'akin da hassana ke kwana nikuma da Naseer da Waleed muka kwana a nawa d'akin Namiji a gida ma wani abune Dan a ranar ko juyi banyi ba har gari ya waye Ina rungume a kirjin mijina. Har makara nayi Dan sai wajen bakwai da rabi na farka. Agurguje nayi Sallah na fito sabida Na Dora musu abinci su karya su tafi makaranta. Sai dai Ina fitowa ma na tarar suna cin abincin sun ma saka uniform sosai naji dadi Dan yanzu Zahira duk ita kemin komai tama Riga da tasan duk abinda nakeyi da safe Inda yarinya ta Kara kwanta Min arai fiye da sauran kanennta kenan. Nadeeya ce kawai Bata saka uniform ba hakane yasa na Shiga na koma d'akina na dauko uniform dinta na Bata Dan Dama an bani uniform dinta littattafai ne ban siya Mata ba Sai da suka shirya tafiya na koma daki Naga har lokacin bacci Naseer keyi Bai tashi ba Tashinsa nayi na fito na raka su har makaranta na karbawa Nadeeya text books Dan na Bata littattafai da pencil Primary 4 aka Kai Nadeeya da aka Mata gwaji. Sai da duk suka Shiga aji na dawo. A takaice tun Ina damun Naseer akan ya koma sabida Kar Umma ta gano muna tare k'i yayi akan Dole na hakura ya Mana sati daya sati dayan da naji inama mu dawwama Haka batare da ya Kara Mana nisa ba inama Umma ta Sanya Mana albarka Naseer ya ringa Zama a shagon k'ofar gida. Ni Kuma na ringa markade Ina kananun Sanaa a gida da nakeyi yanzu kudi na shigomin da nasan sai munfi kowa farinciki tunda munfi karfin ci da Sha alhamdulillah Shima Kamar bazai tafi ba sai Dana karfafa Masa gwiwa akan ya tafi idan yaje yace Abuja yaje neman kudi na Kuma bashi Yan kudaden dai da Bai taka Kara ya karya ba. Dan sati dayan dayayi har Dan murmurewa yayi. Sai daya hau taxi na dawo gida duk jikina ba dadi Dan nasan yau sai dai na rayya Daren dadin ma.danaji yace zai na zuwa ganinmu kullum idan Bai zo bama kullum xai na zuwa akai akai Safiyya Sosai ta Sako Hajara a gaba da kananan koke koke Akan Aurenta na matsowa Anki a Mata kayan daki Hajara kuwa sosai itama ta damu da kukann da Safiyya keyi hakane yasa ta Sha alwashin tarar Naseer a Daren da Bai kwana a gida ba Akan idan ya dawo yasan duk Inda zai nemi kudi ayiwa Safiyya kayan daki. Sai dai Haka Suka karaci zaman jiran dawowarsa Bai dawo ba daga shi har Nadeeya. Washegari ma Haka hakane yasa hankalin Hajara ya fara tashi tana tunanin Inda Naseer yaje shi da Nadeeya Safiyya kuwa kuka ta saka Akan Naseer guduwa yayi ita.kam ta Shiga uku ta lalace asirinta zai tonu. Fadar hakan da Saffiya tayi tana kuka wiwi yasa hankalin Hajara Kara tashi tana "Yanzu sai Naseer ya gudu sabida nace ya Miki kayan daki Safiyya ko dai wajen Naeema yaje ba guduwa yayi ba" "Guduwa yayi Umma Dan idan Kika tuna Bai tashi guduwa ba sai daya ga kin Kara Masa maganar kayan dakin nidai Umma wlh kisan duk yanda zakiyi Dani Aurena nata matsowa ace ko cokali Baki siyamin ba karki manta fa kishiya ce Dani tayaya ma zanyi aure batare da kayan daki ba da kunya na tareshi nace Masa an kasa.min.kayan d'aki" Safiyya tace tana Kara fashewa da kuka "Ki bar kuka Safiyya nace ko wajen kanin mahaifinku zamuje muga ko zamu samu wani Abu" Wani irin harara Safiyya ta d'auke Hajara dashi tana"kin manta katifa kawai ya siyawa Lami Taya zanje na same shi wlh bazan je wajensa ba" "Toh yanzu ya zamuyi Safiyya kinsan dai banida ko sisi gashi Da Naseer na dogara shi Kuma kince guduwa yayi Tijjani kuwa Dama ba mutunci ne dashi ba kinsani Dan Dana Masa magana anan dariya ya ringamin ya maidani mahaukaciya Haka ma.ya tafi ko sisi Bai bani ba Naseer ne dai zai iya kukutawa ya Miki kayan gashi yanzu wajen kwana biyu kenan bai dawo gida ba" "Yanzu ya zamuyi toh Safiyya " "Nidai a siyar da gidanan Umma a fitar Dani kunya idan ba Haka ba kinsan ba Inda zamu samu kudin da zaa siya min kayan daki" Gwallo Ido Hajara tayi tana "A siyar da gidan Naseer Kuma Safiyya Taya Zaa siyar da gidan Naseer kawai Dan a Miki kayan daki karki manta fa wanan gidan kadai ya rage mishi muma ba Dan gidan Nan ba da yanzu muna titi muna gararamba" "Toh idan ba a siyar ba Umma da uwar me za'a min kayan dakin tambayar ki nake idan baa siyar ba da uwar me zaamin kayan d'akin"? Safiyya tace a tsawace "Naga duk masifar Nan ke Kika janyo mana muna zaman zaman mu Kika k'ona dukiyar Yaya Naseer ya talauce muka Shiga uku yanzu da baki Kona dukiyar sa ba ai da Yanzu Bai gudu akan kin Masa maganar yamin kayan daki ba Dan Haka wlh gidanan zaa siyar kawai ayimin kayan d'aki" Kamar Mai tsoron Safiyya Hajara tace "toh idan mun siyar da gidan Nan Safiyya a Ina zamu koma da.zama nida Naseer din tunda nasan sabida zakije gidan miji kike cewa mu siyar da gidan nidai nasan wanan gidan yanzu shine rufin asirina Dana Naseer tunda Naeema ta Kara gaba da yaranta" Sai a lokacin ta sasauta Fuskarta tana "Umma ai wani karamin gidan zamu siya idan muka siyar da Wanan Kinga gidanan babba ne zaa siyi gidan da daraja a ciki zamu siyi karamin gida ki siyamin kayan daki sauran kudin Kuma kija jari kafin ki ankara kema kin zama hajiya har macca ma sai kije ki Naseer dawowa yayi idan yaganki da kudi bazai yi magana ba kinsan shi ba Kamar Yaya Tijjani ba" Washe baki Hajara tayi Dan maganganun Safiyya sun shigeta ta Kuma Yi naam da shawarar ta "Toh wa kike ganin xai siyi gidan" "Ki bar komai a hannuna" Safiyya tace cikin murna a ranar ta shiga d'akin Naseer ta birkita Kaya har sai data samo takardun gidan Ta fito sai murna take da zaa samu kudin da zata siyi kayan daki ya zama Dole ma ta koyawa kishiyarta hankali Dan Kaya zatayi na fitar hankali da kishiyar ta zata shak'a sosai take Jin dadi da had'asu waje dayan da zaayi tasan kishiyarta sai ta kwashi kashinta a hannu Dan sai ta bar Mata gidan ta mallake shi ita kadai. Washegari da sassafe ta bazama ta Nemo dilalai a cikin kwana biyu aka samu mutane masu San gidan har su uku. Dan gidan Naseer din babba ne kuma a fuska Mai kyau Safiyya Bata yarda anyi cinikn gidan Agaban Hajara ba ita ta saka hannu akayi komai da ita Akan Dole ta Nemo wasu Suka Mata shaidan ta siyar yanzu ba mallakinsu bane ta Basu kudi Suma masu siyan gidan suka bada kudi da shaidunsu suka karbi takardun gida. Sai da Safiyya ta zabtare kudin wajen rabi ta b'oye. Ta Kai sauran kudin gaban Hajara. Hajara dai tana San magana kudin gidan yayi araha da yawa Amma babu yanda zatayi da Safiyya datayi Kane Kane. Safiyya ita ta raba kudin gida biyu ta dauki iya kudin da zai isheta ta siyi kayan daki da komai Ta bawa Hajara sauran Hajara kuwa sai a lokacin tace "Safiyya kudin Nan bazai Isa mu siyi wani gidan ba ballantana har na samu na jari" Karki damu Ni Zan Nemo miki gidan da kaina zaa samu Jiki a sanyaye Hajara tace "toh yaushe masu gidan suka ce mu tashi nidai Safiyya ba Haka naso ba wlh gidanan babba ne wayanda Suka siyi gidanan sun cucemu" "Notice din wata daya suka bamu karki damu kafin lokacin na samo Mana wani gidan Ahaka ta lallab'a Hajara tayi shiru. Kafin sati daya da tafiyar Naseer har ta Gama siyan kayan daki na gani na fad'a Iya Nan Bai isheta ba sai data tab'a kudin da ta bawa Hajara data Masa kyakyawan b'uya shirye shiryen bikinta kawai daya rage sati biyu take tana facaka da kudi har wani karamin lefe tayiwa kanta Hajara idan tana San tayi Magana sai ta hayayyako akan Dole take shiru. A ranar da Naseer ya koma kuwa sosai Hajara ta tsorata Dan Bata kawo zai dawo kurkusa ba ta d'auka dagaske guduwa yayi. Safiyya kuwa kwantar Mata da hankali tayi akan Kar ta sake ta gayawa Naseer sun siyar da gidan. Sai idan sunzo tashi shima idan yasani ta haharde Rai ta Masa fin k'arfi tuni zai mata biyaya. Naseer kuwa sosai yayi mamaki da Hajara Bata tambayeshi Inda yaje ba sai wani susune Kai take. Shi kuwa dadi yaji yace Mata Abuja yaje neman kudin da zaiyiwa Safiyya kayan daki toh shima yaje Bai samu ba sai Yan canji ya samo tayi hakuri zai cigaba da nema Kai a sunkuye Hajara tace Kar ya damu ta siyawa Safiyya komai. Wani irin dadi Naseer Yaji yace Mata Ina ta samu kudin Tace Kar ya damu zai sani a hankali Naseer kuwa har a Ransa yaji dadin ganin Hajara ta Dan sauya Masa Ashe har ta samu kudin kayan d'akin. A ranar zuciyarsa fes batare da wani fargaba ba ya kwana da tunanin iyalinsa Washegari da safe yaje gidan Naeema yake Gaya Mata duk yanda sukayi da Hajara Nidai sosai nayi mamakin Inda Umma ta samu kudin. Haka kawai jikina ke gayamin akwai dai ta hanyar da aka samu kudin bandai cewa Naseer komai ba danaga yanda yake murna Yana cemin ko fada Umma Bata Masa ba kila Allah ya fara karbar adduarsa. Bandai ce komai ba a ranar ya wunar Mana daddare na raka shi ya tafi Yawan zuwa da Naseer keyi gidan Naeema yasa Sam bai San halin da ake ciki ba dan Yan canjin daya samu ma shinkafar da Hajara zatayi taron biki ya siyo Mata har da yiwa Hajara dinki kala biyu wai duk Dan ya faranta Mata. Hajara kuwa damun Safiyya ta ringa Yi da zancen gidan data ce zata siya musu Dan lokacin barin gidansu nata karatowa Amma Safiyya haka ta ringa tsara Hajara tana d'auke mata hankali daga zancen Dan tabi ta Kan kudin tuni burinta kawai a daura auren Ta bar gidan Hajara da Naseer su San nayi tunda ita dai ta samu cikar burinta. A Haka aka fara bikin Safiyya Tijjani ma yazo bikin da Murja Dan tuni sukayi katon aiki Akan Tijjani har sai daya je har gidansu Murjan ya dawo da ita. Duk da kamun da suka Masa ba sosai ya Kama shi ba Hajara kuwa irin gayyar da Safiyya tayi yasa hankalinta ya d'auke daga zancen gidan Bata Kuma bi takan Murja da suke Yar kallon kallo ba Sai da aka zo tafiya da Safiyya washegarin daurin Aure. Hankalin Hajara ya dawo jikinta daki ta ja Safiyya ta hau Mata maganar gidan ita kuwa Safiyya ta Mata karyar ta siyi gidan anjima wani zai zo.ya kaita taga gidan Hajara badan ta yarda ba tana ji tana gani aka tafi da Safiyya mutane Suka watse ya rage saura ita daya da Naseer. A lokacin saura sati daya notice din da aka basu ya Kare. Kamar tayi kuka ta Shiga d'akin Naseer Kuma ya Shiga har d'akin ta daya hada musu abin karyawa ya Kai Mata Yana "Umma lafiya kuwa Yana ga kamar bakida lafiya"? Hajara na k'ok'arin Magana Wani yaro ya doka Sallama Wai Mai gidan Yana Sallama da Safiyya Gaban Hajara ne ya yanke ya Fadi. Naseer Kuma cikin mamaki yace "Mai gidan kuma waye Haka" Yayi waje Dan yaga Mai sallamar...... [7/10, 10:38 PM] Zannura: *NAGA TA KAINA* *NA SADNAF*🌸🌸 ®️ *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_* _{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_ *Free Novel* *Page 44* Naseer na fita Waje ya hango wani Alhaji a zaune a cikin motarsa ya zuro.kafafunsa waje Yana kad'a mukulli. Naseer ganin yanda yake kallon gidan yasa ya nufi wajensa yayi Sallama tare da mik'a masa hannu Sukayi musabiha "Kaine kake neman Safiyya"? "Eee Nine" Murmushi Naseer yayi Yana "Allah sarki ai tayi Aure Dazun Nan ma aka tafi kaita gidan mijinta". Murmushi shima mutumin yayi Yana "eyya Allah ya Sanya alheri dama Akan maganar tashinsu daga gidan Nan nazo Dan bana so su wuce lokacin da mukayi dasu Dan inaso na danyi gyare gyare a gidan. Kafin daurin Auren Dan nawa Dan shi zai zauna a gidan Naseer murmushi yayi ya kalli gidajen dake jere da gidansa Yana "Ai inaga Alhaji ba Nan Dan kazo ba ko kila a mak'otan namu akwai Mai sunan Safiyya Dan wanan gidan da kake magana gidana ne Kuma ban siyarwa kowa ba" Duk maganar Nan da ake mutumin na cikin Mota abinda Naseer yace ne yasa ya fito daga cikin motar Yana "Bangane gidanka bane baka siyar ba kaga na maka Kama da Dan shaye shaye ballantana kace bansan Mai nake cewa ba wanan dai gidan da ka fito daga ciki shine gidana da nake magana akai wajen sati uku kenan da biyan kudin gidan na Basu notice din sati hud'u" Murmushin karfin hali Naseer ya Kara zuciyarsa na balain bugawa har ya wuce misali Cikin rawar Baki yace "Waye ya siyar maka da gidan"? "Safiyya ce dai ta siyarmin da gidan ita da Mahaifiyata Dan Nima ban yarda da Safiyya ba sai da muka Shiga har cikin gidan na duba koina na tabbatar da gidan yamin na Kuma tambayi mahaifiyarta Anya gidan nata ne tacemin Kar na damu gidanta ne na siya gudun ma.irin Haka yasa nak'i Bata kudin sai data Nemo shaidu da nima nasansu suka shaida ta siyarmin Nima na bada kudin na karbi takardun shaidun gida ya zama mallakina Dan Haka" Naseer Bai tsaya saurarensa ba Kamar Wanda ake turawa Haka ya nufi cikin gidan Yana Jin duniyar na juyawa dashi Direct d'akin Hajara ya Shiga data kasa zaune ta kasa tsaye Yana Shiga d'akin ta mik'e da Sauri tare da juyawa Naseer baya. "Umma dagaske ne Kun siyar min da gidan da ya ragemin a rayuwata Gidan da shi kadai ne rufin asirina Umma dagaske ne Kun siyar"? Naseer yace Yana dafe kirjinsa dayaji Ya Masa nauyi Yana ta sukarsa. "Kayi hakuri Naseeru akan Dole muka siyar da gidanan Dan na d'auka guduwa kayi banida Mai bani kudi idan ba Kai din ba nayiwa Safiyya kayan daki hakane yasa na siyar Dan na fita kunya Amma sauran kudin na Nan zai isheni mu" Fad'uwar Naseer da tunda tace sun siyar yaji Kamar an harbe Masa kirjin da har yau daya tsuffa idan Ransa ya b'aci Haka yake fama da ciwon kirjin. Sam Bata San halin dayake ciki ba dayake juya Masa baya tayi sai dataji karar fad'uwarsa ta juyo hankali a tashe tayi kansa. Naseer sallati kawai yake Yana juya Kai hannunsa dafe da kirjinsa dayake ji kamar zai fashe. Kuka kawai yake yana "Umma Mai na Miki Haka a rayuwa kin rabani da komai Dana mallaka Umma iya sanina ban taba Miki komai ba Dana cancanci Haka daga wajenki sau daya nayi kuskuren da har gobe nake nadamarsa na marinki danayi shima wlh Umma bansan lokacin danayi ba Umma iya biyayya Ina Miki kin rabani da matata kin rabani da yarana bance komai ba iya Haka Bai Isa ba Umma sai da kika rabani da gidan daya ragemin a rayuwata da nidake muke ciki Umma Akan kayan daki Kika siyar da gidana Umma yanzu Ina kikeso mu koma innalillahi wa Inna ilaihi rajiun Umma kin kasheni" Naseer ke fada Yana dafe da kirjinsa "Ka kwantar da hankalinka Naseer ba duk kudin aka siyawa Safiyya kayan daki dashi ba akwai sauran da zai Isa ka siyi karamin gida har aure ma sai kayi Bari kiga" Hajara race da Sauri ta daga katifar sama da ta b'oye kudin da Safiyya ta Bata. Ras gabanta ya Fadi a lokacin data ga ba kudin sai Yan dari bibiyu guda goma. Cikin tashin hankali tayi wurgi da katifar ta hau duba koina tana ta Shiga uku ta lalace ba Inda Bata duba ba Amma Bata ga kudi ba "Na Shiga uku Yarinya Nan ta cuceni shegiya tsinanniya Allah dai ya tsine Miki albarka Naseer ta bani kudin Kuma ta kwashe na Shiga uku na lalace Hajara tace Tana fashewa da kukan bakinciki tare da zaman dirshan tana tsinewa Safiyya albarka. Naseer kuwa ko kallonta baiyi ba ya mik'e hannunsa dafe da kirjinss dayake ganin Yana saki zai iya fadowa jiri na dib'arsa Haka yaje ya kwanta a d'akinsa ya hau kuka Kamar karamin yaro Dan gani yake kukan kawai shi zai saka yaji kirjinsa ya rage nauyi. Hajara itama kukan taci ta koshi bakinta sai tsinewa Safiyya yake tana Shan alwashin samun kudin mota taje har calabar taci uban Safiyya. Taya ma akayi ta biyewa Safiyya ta siyar da gidan da itama kanta shine rufin asirinta yanzu idan Mai gidan ya koresu Ina zata koma data ita har Naseer Bata tab'a sanin Haka Safiyya take da San Kai ba sai Yau. Ya Zama Dole su San nayi kafin a koresu bakin cikinta ma shegen Dubu biyu da Safiyya ta ajiye Mata da ba abinda zai iya Mata. Wajen karfe hudu na yamma ta fito daga d'akin tashin hankali da take ciki Bai Bari taji yunwa ba. D'akin Naseer ta nufa tana zuwa ta iske jikinsa na wani irin rawa sabida zazzabin da ya rufeshi lokaci guda. Ihu ta saka ta fada d'akin tana tab'a jikinsa ta d'auke da Sauri tana "Haba Naseeru Mai yayi zafi haka kayi hakuri bansan Safiyya Haka take ba da ban Soma biye Mata ba sam banyi tunanin yaudarata take ba kayi hakuri ka tashi kaji" Ganin Naseer Kamar Bai ma San Inda kansa yake ba yasa tayi waje tana dora mayafinta aka. Wani chemist taje dake kasan layinsu. Dayake su biyu ne a chemist din ahaka ta roki dayan ya biyota har gida ya hau duba Naseer. A takaice sai da Naseer yayi kwana uku a kwance ba lafiya a kwana na hudu yaji sauki saukin jikinsa kirjinsa ne dai har lokacin ya Masa nauyi. Hajara ce ta ringa dawainiyya dashi Dan Dubu biyun dashi ta siya Masa magangunan Har da girki ita ta ringa Masa wai duk Dan Naseer ya ji dadi. Naseer kuwa ko San ganinta baya so yayi Dan shi kadai yasan Mai yakeji a kirjinsa idan ya tuna Wai wanan kantamemen Gidan nasa Mai part biyu da zai iya zama a bangaren da su Hajaran suke wanan Kuma ya zuba Yan haya ya samu kudi. Ahaka ma filin tsakar gidan da girmansa da zai iya tasar daki biyu a ciki Amma ahaka mahaifiyarsa ta siyar masa da gida sabida kawai tayiwa kanwarsa kayan daki. Hawayene suka zubo Masa ya runtse idonsa Yana Jin yanda kirjinsa ke Bugu a duk abinda mahaifiyarsa ta ringa Masa wanan yafi Masa ciwo Dan yanzu bashida komai a rayuwarsa. Hajara dake zaune agabansa tana hada Masa shayi ganin hawaye na zubo masa ta hau magana tana "Haba Naseer Kayi hakuri Mana wlh Nima bansan yarinya Nan iskancin data min ba kenan da ban Soma biye Mata ba Dan Allah ka daure ka Zama namiji insha Allahu zaka samu fin wanan ita Kuma Safiyya wlh Bari na samu kudin mota har can zanje na kwashe Kayanta na siyar na kawo maka kudin shegiya tsinaniya uwar San zuciya kayi hakuri kaji Naseeru na maka ba daidai ba ka daure ka Sha shayin Nan tunda ka kwanta baka sa komai a bakinka ba ka taimaka ka Sha musan nayi Dan Naga Mai gidan Nan har ya fara kawo kayan gyaran gidan Jiya ma sai daya zo da alama bashida mutunci" Naseer Bai ce Mata komai ya tashi ya shige bandaki. Ya daura alwala yazo ya tadda sallah Yana ji kamar iska zata d'auke shi sabida rashin kwari. A sallah ma sai dayaci kuka ya gayawa Allah halin dayake ciki yayi adduar ya shafa Hajara na zaune ta buga tagumi tana kallonsa. Shi kuwa mik'ewa yayi ya fita batare da yace Mata komai ba duk da tana Masa maganar Ina zaije. Daya fita ma opposite din gidansa ya zauna Yana karewa gidansa kallo ji yake inama mafarki yake ba dagske ya rasa wanan tangamemen gidan nasa ba daga Ina zai fara yanzu. Abinda Umma ta Masa ba shi kadai ta cuta ba har kanta ta cuta sani ne batayi ba. Mik'ewa yayi ya fita har bakin titi wajen wani dilali Mai siyan Kaya fairly use ya Masa bayanin Yana da kayan siyarwa na gida ya lissafa Masa Abubuwan gidansa Kama daga gadon da Hajara ke kwana har cokali Dan so yake yayi gwanjon komai ya siyar na gidan Dan Bai San Ina zai Kai kayan gidan ba tunda bashida gida yanzu. Har gida suka zo yaga duk kayan ya musu kudi Wanda duk kayan ma tayin wulakanci ya Masa Amma ba yanda zaiyi ahaka ya siyar da kayan gabadaya ya kirga kudinsa ya bashi ya tafi tafiyarsa da minti ashirin sai gashi ya dawo da mai kurkura suka hau fita da kayan Naseer kuwa ya hade kayanshi Dana su Zahira a bako biyu jiri ke dib'arsa Amma ahaka ya hade kayansu ya fito dashi Bayan ya kwashi duk wani Abu nashi Mai mahimmanci Hajara kuwa hankali a tashe ta hau tambayarsa ya taga Ana fita da Kaya Ina zasuje. Tunda ya kwanta sai a lokacin yayi magana Yana "Umma duniya Zan Shiga na nemi kudi Dan kin rabani da komai banida gida banida komai Dan Haka Nima zanje na nemi shagon da Zan ringa kwana tunda banida gida yanzu" "Naseer Mai kake cewa haka ni Kuma fa wajen wa zani Haba Naseeru yanzu Ni Kuma a wajen wa Zan zauna nidai na Shiga uku na lalace Dan Allah kayi amfani da kudin nan na hannunka ka Kama Mana haya Naseer kasan banida Inda zan zauna ko na koma calaba Naseer" "Ki koma gidan Safiyya Umma Dan da duk kinyi wanan tunanin da Baki siyar da gidnan ba kin siyar Dan ki farantawa Safiyya Rai da ba ko sisinta a ginin gidanan Bata San da yanda na samu kudi na Gina gidana ba Umma toh gashi kin rufa Mata asiri tana gidan mijinta namu ya tonu Dan Haka Umma babu yanda zanyi dake Dan Nima shagon abokina zanje na ringa kwana Kinga bazai yiwu na tafi dake shagon abokina ba" "Naseer nayi nadamar biyewa Safiyya kayi hakuri Ni nasan Kai Dan albarka ne bazaka Bari na tagayyara ba ka taimaka ka sama Mana wajen da zamu zauna" Naseer da yazo har wuya a tsawace yace "Umma ki kasheni Dan Allah Dan annabi ki Huta Umma bayan abinda kikamin har Zaki iya cewa na nema Mana wajen da zamu zauna umma Nagaji Nima.yanzu ta kaina zanyi tunda kinyi nassarar rabani da komai Abu daya Zan Miki shine na baki kudin mota kije calaba wajen Safiyyan data Baki shawarar ki siyar da gidana ta San yanda zatayi dake bani kadai ne danki ba Umma idan bakya San zuwa calaba kije gidan Tijjani yanda Kika haifeshi Haka Kika haifeni Umma bazan kashe kaina akanki ba Umma na rasa Mai na Miki a rayuwata Umma kin kassaramin rayuwa yanzu banida komai a rayuwata sai wanan Kayan sawan nawa Umma Dan Haka nima Zan Shiga duniya naje na nemi kudi tunda yarana ma da matata duk kin rabani dasu" Kuka Hajara ta fashe dashi ta zub'e a kasa tana ta Shiga uku taya zataje gidan Tijjani da matarsa ke dukanta take Mata horar yunwa Taya zataje gidan Safiyya da ko sati biyu batayi da aure ba" Naseer kuwa kudin hannunsa ya raba gida biyu ya Ajiye Mata agabanta ya kinkimi bakonsa ya tafi ya barta tana ihun Kiran ya dawo Kar ya tona Mata asiri. Yana kuwa fita yasamu taxi daya zo ya sauke Kaya a wani shagon provision Ya tsayar dashi ya saka bakkonsa biyu a ciki ya Gaya masa Inda zai kaishi. Yana kallon Hajara ta fito daga gidan hankalinta a tashe har Dan biyo taxin tayi shi kuwa ya d'auke kansa Dan ya gaji da halin mahaifiyarsa zata Dade Bata Kara ganinsa ba Baa sauke shi a koina ba sai a gidan Naeema. Ina zaune da Yara na a tsakar gida suna home work dinsu Ni kuma gabadaya hankalina na wajen tunanin Inda Naseer yayi daya kwana biyu Bai zo ba sosai na damu da rashin zuwansa Dan tunda yasan Inda nake Bai taba fashin zuwa ba hakane yasa na damu da Jinsa shiru Dan Ni nasan da lafiya yake ba yanda zaayi ya k'i lek'omu yanzu Haka ina tunanin idan gobe Bai zo ba Zan tura Isihu unguwar ya gano min ko zai ganshi Naga ya shigo gidan da bakko manya guda biyu a hannunsa ya ajiye. Daga yanda Naganshi sai da gabana ya tsinke sabida yanda ya rame ya fice daga hayyacinsa kamar bashi ba. Hankalina a tashe na mik'e Ina kallonsa ko kallon su Zahira dake Masa sannu da zuwa baiyi ba ya cire Raheema data je Masa oyoyo daga jikinsa ya shige dakina. Ni kuwa na bishi da Sauri Dan ban taba ganinsa ahaka ba. A Gefen gado na sameshi ya zauna ya sunkuyar da kansa Ni kuwa na zauna a gefensa tare da ruk'o hannayensa Ina tambayarsa lafiya Mai ke damunsa. Bai d'ago ba sai sheshek'an kukansa naji daya tayarmun da hankali yasani jawo shi jikina Shi kuwa ya Dora kansa akan kafadata ya cigaba da kuka kasa kasa. Ba karamin Abu ke saka Naseer kuka ba hakane yasa hankalina a tashe nima na hau kukan Ina tambayarsa abinda ya saka shi kukan. Sai daya yi kukan Mai isarsa da har sai dayaji nauyin da kirjinsa ya Masa dake barazanar dauke Masa numfashi ya ragu kafin ya hau bani labarin duk abinda ya Faru. Bansan lokacin Dana Zamo daga Kan gadon na zauna a kasa na hau sallati ba Dan ban tab'a tunanin Rashin Imanin su Umma har ya Kai Haka ba tayaya zasu siyar da gidan Naseer Dan kawai ayiwa Safiyya kayan daki Ni kaina na kashe kudi a gidanan sosai kafin yayi kyau Tambayarsa nayi nawa Suka siyar da gidan yacemin shi Bai tsaya tambaya bama Dan da alama safiyya kadai ce taci kudin Bansan lokacin Dana hau musu Allah ya Isa ba Dan ba iya Naseer Suka cuta ba har nida yarana sun cucemu. Daga Ni har Naseer bamu iya wani bacci ba Dan sosai siyar da gidan ya min ciwo har hango gidan nake a idona. Ganin damuwar da nayi na Kara saka Naseer cikin wani damuwar Dan ko abincin Dana zuba Masa Bai iya ci ba yasa na daure na hau bashi baki dak'yar ya ci abinci ya Sha magani bacci yayi awon gaba dashi. Ni kuwa sanin bacci bazai d'aukeni ba yasa na rayya Daren Ina rokon Allah ya kawowa Naseer mafita ya musanya Masa da abinda yafi alheri. Hajara kuwa ita kadai ta kwana ko bacci Bai ga idonta ba sosai hankalinta ya rabu gida biyu tana tunanin Inda ya Kamata ta dosa. Sosai Naseer ya Bata mamaki da har ya iya tafiya ya barta Amma duk abinan Safiyya ce ta jaza Mata Bata Isa ta soma dosan gidan Tijjani ba Dan Murja Yar iska ce shi kansa Tijjani bashida mutunci da Yana Mata biyayya kamar yanda Naseer ke Mata biyayya da zata samu saukin wani abun babu ma yanda zatayi ta soma dosan gidan Murja da take ganin tafi kowa mugunta ga makirci ga horo da yunwa idan ta gayawa Tijjani ma ba yace ta dameshi. Tsinaniyar Safiyya data saka ta siyar da Naseer gidan Safiyya zata je a goben tasan yanda zatayi da ita. Washegari kuwa da sassafe Mai gidan ya duro ko kallon hajara dake kwance a kasa ta shimfida zaninta baiyi ba aka hau buge buge a d'akin Tana ji tana gani Yan aikin Suka Mata watsi da.kayanta waje ita kuwa ta fita waje tana matsa kwalla ta had'a Kayanta ta nufi Tasha Bata Sha wahalar samun motar calaba ba suka dau hanya tana cin alwashin irin bugun da zatayiwa Safiyya idan ta Isa gidanta. Safiyya Sosai taji dadin ganin bangarenta fes da kayan data siya da suka kasance tsadaddu. Agajiye suka Isa calaba da Kuma bak'ar yunwa hakane yasa wayanda Suka rakata da suka kasance Yan calaba suna kaita Suka tafi. Sai data Gama Shiga koina a gidan sanan ta fito palo ta zauna tana Allah Allah Umar ya shigo tace Masa tana Jin yunwa sai dai har akayi sallah Isha Bata ga keyarsa ba. Sai muryar Yara ke tashi a tsakar gidan tana ta daga wuya taga ko zata ga uwargidanta data matsu taganta itama sai dai Bata ga alamarta ba. Ahaka yunwa keta nukurkusarta Ta rik'e cikinta wajen karfe Tara taji muryar Umar take Taji wani irin Sanyi a zuciyarta ta mik'e da sauri tayi waje. Sai dai me tana fita taga Umar din a tsaye da manyan ledoji ya mik'awa wata datake kyautata zaton itace kishiyarta taci kwalliya cikin doguwar riga. Ta yiwa umar din magana taga Umar din ya shige b'angaren ta batare da ya ma kalli bangarenta ba Mamakine ya kasheta data ga uwargidanta ta nufo b'angarenta da ledojin a hannunta Ita kuwa Safiyya ta gyara tsayuwarta tana jiran isowarta Dan daidai take da ita Tana kuwa zuwa ta hau bin Safiyya da wani irin Mugun kallo tana "Ke a lailai Baki yarda ke amaryar bace koh duk mazan duniya Nan ki rasa wa Zaki aura sai mijina ko hmmm lailai yaro bai San wuta ba sai ya taka wlh Tallahi da kafafunki Zaki bar gidanan Dan Miji a tafin hannuna yake tsakaninki dashi sai gani sai hange. Na Bari ya auroki ne Dan na samu Yar tayin aiki Dan Haka a goben Nan ba sai na Gaya miki ba karfe shidda kifito ki Dora Mana abincin karyawa kaza Kuma nida mijina da yarana ne zasuci Zaki ci ubanki ba dai mijina Kika Aura ba hmmm" Tace tana k'ok'arin juyawa ta tafi Safiyya kuwa ta damko kafadarta da zumar dawo da ita. Ita kuwa tana juyowa ta kwashe Safiyya fa lafiyayyun Mari biyu ta hankadata har sai data Bugu da kujera dake palon Ta Kara Mata wani mugun kallon ta tafi. Safiyya kuwa kamar mahaukaciya ta bita aguje ta cakumeta ita kuwa ta daga Safiyya sama ta hau ruwan cikinta ta hau dukanta kamar yar cikinta. Ihun Safiyya ne yasa Umar fitowa daga b'angaren kishiyar Safiyya ya nufi wajensu........ [7/12, 10:21 PM] Zannura: *NAGA TA KAINA* *NA SADNAF*🌸🌸 ®️ *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_* _{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_ *Free Novel* *Page 45* Da saurinsa ya Isa wajensu ya rik'e hannayen hafsa dake ta buga Kan Safiyya da kasa Dan karfafa ce ita Bata Wasa ba wani zubin shi kansa Umar din idan Abu ya hadosu tana Masa mugun duka idan fada ya kaure musu. Safiyya dafe keyarta da takejin lema tayi da alamar.jinine ta mik'e da kyar tana jiran Umar ya d'auke Hafsa da Mari sai dai a madadin Marin sai ya hau Bata hakuri Yana rarrashinta. A wahalce Safiyya tace "Umar kanka daya kuwa Taya zaayi matarka daga kawoni yau ta hau dukana amadadin ka tsawatar Mata sai ka hau Bata hakuri"? Ko kallonta baiyi ba ya cigaba da bawa hafsa hakuri dake cika tana batsewa. Mamaki yasa Safiyya wartsakewa daga azabar da takeji a keyarta Dan Umar din ma hannun Hafsa yaja suka Shiga bangarenta suka rufo k'ofar batare da ma ya Mata ko kallo daya ba Safiyya kasa ma motsi tayi sabida tsananin mamakin abinda Umar din ya Mata gani take Kamar ba Umar din data aura bane. Sai da Sauro Suka fara kaiwa fatarta cizo ta koma bangarenta da mugun ciwon Kai ga mugun yunwa da takeji ga ba abinda zata saka a bakinta a tsakiyar palon ta zub'e tana tunanin abinda zai saka Umar ya Mata Haka a Daren ranar da ta tare a gidansa da yake ta dokinta kamar ya cinyeta. Gwallo Ido tayi data tuna kwallinta data manta dazaa daukota hannu ta Dora aka Dan kwallin Nan shine yake balain tasiri a wajen Umar yau kuwa ko kwallin Bata saka ba. Ya Zama Dole ta nemi shugabarsu tunda tana garin calabar zata nausa daji nemanta ta Kara Bata kwalli tare da damke Mata Umar ta kuma cin uban kishiyar Nan tata Mai Kama da maza sosai ta zargi kila sabida bata saka kwali ba shiyasa Umar ya wulakanta ta batasan shi kansa Umar din sai yanda uwar gidan sa tayi dashi ba. A ranar Bata iya bacci ba sabida mugun yunwar da takeji ga azabar ciwon Kai Dan keyarta ya kumbura yayi suntum. ruwa kawai ta ringa dirkaka wa kanta cikinta na Kara kullewa. Wajen karfe shidda na asuba baccin wahala yaso ya d'auketa. Har ta fara baccin sama sama taji an banko k'ofar dakinta da balain k'arfi. Mik'ewa tayi a firgice Dan ta balain tsorata. Hafsa ce ta shigo cikin kayan bacci har kasa kanta a bud'e Yana ta digar ruwa. Cikin wani irin murmushi hafsa tace "Amarya dafatan kin tashi lafiya baccin ya Isa Haka a fito a Dora Mana abincin karyawa Dan Yara zasu tafi makaranta Dan nasan kinsan Yana da Yara masu zuwa makaranta dole zasuci abinci kafin su tafi makaranta". Wani irin Mugun kallon tsana Safiiya ta kwashe Hafsa da shi tana "Juya ki barmin daki kafin na tureki da kaina uwar abincin Zan dafawa Yara ba abinci ba ke da kwana da miji Ni da dafawa Yara abinci kin dauka Yar aiki aka kawo Miki wlh bashi kikaci duk abinda Kika min sai na Rama bakisan waccece ni bane kina Wasa da wuta Bari na kamaki" Wani irin Dariya Hafsa ta kwashe dashi tana "Zaki sha wahala idan kikace zaki ja Dani a yau Zan tabbatar.miki da ke Yar aikin ce tunda har.kika auri mijina idan Kika min gardama Kuma wlh na Miki shegen duka da kafarki Zaki bar gidanan" Ta juya ta fita daga d'akin Safiyya kuwa ta buga uban Tsaki Tana Shan alwashin gari na wayewa zata tafi wajen shugubarsu Kuma indai taje sai ta saka an kashe Mata hafsa. Fitar Hafsa da Yan mintina sai Gata ta dawo da Umar daya balain had'e Rai ya saka doguwar rigar maza Safiyya kuwa Ido ta zuba Masa tana mamakin yanda yake mata wulakanci Agaban kishiyar ta duk da tasan idan ta saka kwalli Yana rikicewa akanta Amma wani zubin Bata saka kwalin idan yazo Kuma Baya canja Mata haka. Fuska a had'e yace "Ki tashi ki Dora wa Yara abin karyawa Dan zasu tafi makaranta sai kinyi kwana bakwai Zaki ajiye girki kafin hafsa ta karba" "Idan ni kuke jira na Dora muku muku abinda zakuci wlh sai dai ku mutu da yunwa yaushe kuka tab'a Jin daga auro amarya ta fita ta Dora girki.naga ma ba a d'akina ka kwana ba akan me.zan Dora girki wlh Umar ka bani mamaki ban taba sanin Haka. Kake ba wlh Allah ban taba sanin wulakanta ni kakeso kayi ba shiyasa ka auroni agabanka wanan shegiyar matar taka Mai zubin maza ta Dokeni" Jinta ne ya d'auke na wucin gadi Sakamakon Marin da Umar din ya d'auke ta dashi Yana "daga yau karki sake ki Kara zagarmin Mata idan kina San zaman lafiya a gidanan ki tashi ki dorawa yarana abinci karyawa karsu makara zuwa makaranta" Umar yace a fusace Yana barin d'akin Hafsa kuwa cikin wani irin murmushi ta karasa gaban Safiyya dake dafe da kumatunta har lokacin sabida tsananin mamaki Marin da Umar ya Mata tace "Baki ga komai ba wlh da kafarki Zaki bar gidanan Dan mijina yafi karfinki na Gaya miki ba yanda zaayi sama ta kizo ki aure min miji alhalin bakisan wuyan Dana Sha dashi ba" Daga haka ta fice daga d'akin Safiyya ta zub'e kasa ta fashe da kukan bakinciki. A takaice a cikin kwana bakwai da Kai Safiyya tayi wani irin Rama tayi wurjan wurjan Dan duk Inda take tunanin Hafsa ta wuce Nan Dan muguwa ce ta karshe horar yunwa da take Mata yasa ta yarda ta fara girkin duk Yan gidan Sabida ta samu na abinci Nan ma idan ta girka Hafsa ke zuwa ta juye a babban kula ta bar Mata kanzo ta kankara Dan kudin Hajara data kwaso ma yaranta sun bita har d'akinta sun kwashe ballantana ta siyawa kanta abinci Duk yanda taso fita Umar ya hanata Dan mugunta ma Safiyya kulle gidan take idan ta saka ta aiki tak'i sai ta jibgeta. Yaranta ma a palonta sukacin abinci su Mata kaca kaca da Palo da daki Bata Isa tayi Magana ba da mugunta ma yaran Suka fafarka kujerunta da Reza da Zuciya ya d'ebbeta hade Yaran tayi ta zanesu dayake sabida bakin cikin ganin tsadaddun kujerunta da suka yaga Sai dai yaran na fita sai ga Hafsa Nan daga k'ok'awa ta Mata shegen duka ta kumbura Mata fuska tundaga ranar Bata Kara gigin tab'a yaran ba Tana ji tana gani yaran Hafsa ke wulakanta Mata Kaya Bata isa tayi magana ba kuka take ci sosai tana nadamar ma auren Umar din dan gwara Zamanta ba auren da irin wanan kuntacecen rayuwar da take sati daya da kwanakin da ta tafi ji take kamar tayi shekaru a kurkuku ta Sha yunk'urin guduwa daddare Hafsa datake cewa Mayya na dawo da ita Dan Hafsa so take sai ta azababtar da ita kafin tasa Umar ya saketa. Dan ba karamin kamu tayiwa Umar ba,Bai Isa ya ketare umarninta ba A yau ma Kamar yanda Hafsa take tilasta Mata aikin gidan. Ta fito Ana iddar da sallah asuba ta fara aikin gidan. Da gayya ma yaran da suka jiku da makirci ke B'ata katon gidan ta share ta goge ta zo ta Dora babban tukunya ta Dora musu abinci Ita kuwa hafsa Haka zata fito da jikakken Kai tana Mata murmushin mugunta Dan Umar sau uku kenan Yana kwasheta da Mari idan ta Bijirewa umarnin Hafsa zuwa yanzu ba abinda ta tsana sama da zaman gidan auren dan tayi auren ne Dan taji dadi sai gashi tana Shan wuyan da ko a mafarki Bata tab'a hasasowa.kanta ba muryar Hafsa kawai fadar.mata da gaba yake Ahaka ta Gama abincin Hafsa ta juye ta bar Mata kanzo ta kankara taci ta Kara wanke wanken Yaran Suka fita gabadaya har da Hafsa. Sosai Safiyya taji dadin fitarta ta Shiga d'aki da Sauri ta d'auko mayafinta ta fita itama. Duk da nisan dajin da suke zuwa wajen shugabarsu ahaka ta Nadi tafiya Mai nisa tana Isa bukkar ta hau yaren tsafin su sai dai har ta Gama babu shugubarsu babu dalilinta. Kamar tayi kuka ahaka ta fito daga dajin ta koma gida tana Shan alwashin kwashe Kayanta ta tafi Dan bazata iya cigaba da zaman bauta ba. Sai dai tana dawowa ta tarar Da Umar a d'akinta. Ya wani marairace ya hau Bata hakurin Bai San Mai ya hau kansa ba a takaice a ranar ya kwanta da Safiyya Yana samun nutsuwa ya sauka daga kanta ya rufeta da dukan ita ba budurwa bace Yar iska ce ita a ranar Umar ne ya karbi ragamar mugunta yayi ta azabtar da ita da aiki.yana zaginta akan ita Yar iska ce . A irin wanna yanayin da Safiyya ke fuskantar.azabar wahala daga wajen Umar da Hafsa da yamma Safiyya na jidar wankin da Hafsa ta loda Mata bayan ta gama wawanka Mata Mari Hajara kuwa suna isa Calaba ta d'au hanyar gidan Umar da yake sananne da lodin Kayanta data Dora aka. Ko Sallama batayi ba ta Shiga katon gidan da tun a waje ta fara dan Jin sanyi samun wajen da zata zauna Mai kyau Dan ko Mai zaayi sai dai a ayi wlh Zamanta zatayi a gidan tunda Safiyya ce silar siyar da gidan da take zaune cikin rufin asiri. Kamar a mafarki Safiyya taji muryar Hajara tana dagowa kuwa taga itace Aguje tayi wurgi da bokitin hannunta taje da zumar kankame hajara Dan gani take kamar zuwanta ne zai saka ta bar gidan Hajara.kuwa sakin kayanta tayi a kasa ta matsa tana isowa wajenta ta kwashe Safiyya da wani mahaukacin Mari tana "har ni Zaki yaudara Ina uwarki Safiyya har Ni Dana Haifeki Zaki cuta ki hainceni kisa na siyar da gidan Naseer Dan na Miki kayan daki iya nan Bai isheki ba sai da Kika kwashe kudin da Kika bani dan na siyi karamin gida Toh wlh Tallahi sai kin fito mun da kudin gidan ko Kuma na zauna a gidanan tunda banida gidan da Zan zauna" "Safiyya hannunta ta fara k'ok'arin ja Dan ta kaita daki sabida Hafsa dake zaune a Kan tabarma data zubo musu Ido sam.bata san tasan abinda ke faruwa. Hajara cigaba da bambamin masifa tayi tana kwashewa Saffiya albarka dake ta Jan hannunta Hafsa kuwa ta mik'e tana dakawa Hafsa tsawa tana "Wacce wanan Zaki shigo.mana da.ita gida"? Hajara wani mugun kallo ta Mata ta kalli Safiyya tana "Halan wanan Mai zubin mazan ce kishiyarki"? "Nice Mai zubin mazan? Hafsa tace cikin mamakin Hajara . Hajara kuwa ta ja Tsaki ta fara k'ok'arin Shiga b'angaren Safiyya. Hafsa kuwa ta jawota ta kifa mata Marin da sai da Hajara taga walkiya a takaice har waje Hafsa ta fitar da Hajaran ta Kuma rantse bazata kwana a gidan ba. Hajara haka ta kwashi Kayanta ta nufi gidan Lami tana Shan mugayen alwashi akan kishiyar Safiyya Dan ta Gane Safiyya Bora ce a gidan. Sai dai shima gidan lamin data Isa kwana uku ta iya yi Sabida abinci sau daya ake dorawa a gidan Sabida talaucin da suke fama dashi. Gashi shi kansa mijin Lami wani gani gani yake wa Hajaran hakane yasa ta Kara tattara Kayanta da kudin mota ta nufi Tasha ta hau motar Kano Inda ta yanke Zama a gidan Tijjani tunda Bata da Inda zata zauna har.daji ta nausa Dan shugabarsu ta gano Mata Inda Naseer. Yake ta kuma.kara rokarta mudubin tsafi Dana karfinsu har ta karaci yaren tsafin dake sa ta bayyana a gabansu Bata bayyana ba. A mugun gajiye ta isa gidan Tijjanin Inda taci Karo dashi a bakin kofa zai fita massallaci turus yayi daya ganta da Niki Nikin Kaya Hajara kuwa ta sauke kayan daga Kanta tana "Bani hanya na wuce ka tsaya kana kallona kamar baka sani ba ka shigo min da kayan Nan maza" Tace tana matsar da Tijjanin tare da shigewa cikin gidan tana Kara hade Rai Dan so take ta gwada karfin uwa akan Tijjani ya mata biyayya kamar yanda Naseer ke Mata duk da kasan zuciyata tana Dan Jin shakkar Murjan A.palo ta tarar da Murja da jaririyar ta a hannu da Bata fi kwana biyu da haifarta ba. Kallon kallo suka yiwa Juna a daidai lokacin da Tijjani ya shigo da bacconta Yana "Umma Wai daga ina kike naganki da Niki Nikin kaya"? Daga calaba nake na Kuma dawo Nan da Zama Dan Safiyya ta siyar da gidan Naseer tayiwa kanta kayan daki banida wajen Zama shiyasa nayo Nan Dan Ni na Haifeka Ina Kuma da iko dakai matarka Bata Isa ta hanani na zauna a gidanan horar yunwar datamin a baya wlh bazan dauka ba indai ta gwadamin kuwa wlh sai ka saketa" "Mamakine ya rufe Tijjani a lokacin da Hajara tace Safiyya ta siyar da gidan Naseer anyiwa Safiyya kayan d'aki cikin mamaki yace "Umma Safiyya ta siyar da gidan Naseer fa kikace bangane ta siyar da gidan Naseer ba Umma yanzu gidan Naseer kuka siyar Dan ayiwa Safiyya kayan daki innalillahi wa Inna ilaihi rajiun" Hajara Tsaki tayi ta mik'e tana "Duk ba laifin Kai da naseerun bane kuyiwa Safiyya kayan daki kunce bakuda kudi karka sake ka dameni da tambayoyi kaji ko" "Umma kinsan Allah bazan d'auki abinda kuke yiwa yaya Naseer ba bazan hanaki Zama a gidana ba Amma wlh bana San hayaniya da takura Dan gaskiya bazan dauka ba. Daga Haka ya fice waje.yana Jin bakinciki siyar da gidan Naseer din datace sunyi har mamaki Naseer ke bashi daya bar Hajara take garashi yanda ranta keso. Hajara kuwa Inda suka zauna da Safiyya Nan d'akin ta shige abinta da kayanta. Ta fito daga d'akin ta shiga kitchen Kai tsaye ta zubo abincin da ta gani ta dawo palo ta zauna tana hararar Murjan dake Mata wani irin shu'umin murmushi tana girgiza kai Dan ta daga Mata kafa ne kawai Dan Tijjanin na Nan. A takaice duk inda Hajara taso itama ta nuna iko da isarta kasawa tayi Dan Murja shu'uma ce ta gaske Dan haihuwa da tayi yasa danginta suka cika gidan Tijjani Kuma ba wani Zama yake ba yana fita zasuyi tayiwa Hajara rashin mutunci Bata Isa ta tanka musu ba idan kuwa ta saka Abu a bakinta sai dai idan Tijjani ne ya dawo ta rokeshi ya Bata makirci kuwa sai abinda ya dadu da Murja ta Karo Dan kawai ta bar gidan Hajara kuwa duk yanda taso yiwa Tijjani bayani sai yace Mata shi Baya San tashin hankali Shifa ba naseeru bane. Idan ta masa hargagin ita fa uwarsa ce Bai Kamata ya Fifita Murja akanta ba sai yace wane shi ya Fifita Murja akanta ahaka zai maidata mahaukaciya Yana Mata dariya. Sosai ta gwammaci zama a koina da zaman gidan Tijjanin Dan sau uku kenan Murja na Mata duka. Ba yanda batayi da Tijjani ya saketa ko ta tsine masa ba yak'i sakinta yace Mata Yana San matarsa. Ahaka zata rufe ido. Ta Masa mugayen kalamai idan Murja ta Mata wani Abun shi kuwa Tijjani sai ya fice ya bar gidan A ranar data cika wata uku a gidan Tijjani A ranar Safiyya itama ta duro gidan da cikinta da takardar sakin da Umar ya Mata wiwi tana kuka da lodin Kayanta. Tijjani kuwa rantsuwa yayi bazata zauna Masa a gida ba sai dai ta nemi wajen Zama sai da.hajara ta hau Masa kuka ya bar Murjan ta zauna Dan ko ba komai taji dadin ganin Safiyya da sakin da aka Mata Dan zuwanta zai saka ta Dan samu saukin wani abun daga wajen Murja su Kuma nemi hanyar da zasu ci uban Murjan su dau fansar duk abinda ta musu. Sai dai zuwan Murja gidan yasa.tijjani ya bud'e kwandunan. Rashin mutunci Baya dagawa Safiyya kafa ko kad'an duk da kanwarsa ce ya balain tsanarta Ga Murja itama a gefe tana Gana musu azaba Dan kudin da Safiyya tazo dashi na kayan d'akinta data siyar a can calaba da baiyi albarka ba dashi Suke siyan abinci idan Murja ta hanasu Sosai suke rufe Ido suna neman bokon da zai.musu aiki akan.murja,Hafsa da Umar da suke ganin sune makiyansu a Duniya Bayan Naeema. Ganin kudin su ya tasama karewa yasa Suka yanke shawarar fara siyar da kosai a waje. Safiyya ce ta tafi siyan kayan da zasu bukata na kosai A wani shago dake can kasa dasu Kamar ance ta waiga ta hango Naseer da Tijjani a tsaye nesa dasu suna magana hakane yasa ta gwallo Ido tana kallonsu Ganin Tijjanin ya hau vespensa ya tafi shi Kuma Naseer ya fara k'ok'arin tarar taxi yasa tayi saurin fitowa daga shagon itama ta nufi titin da Sauri tana rufe fuskarta. Tana Isa titin Naseer.ya samu taxi ya shige Itama.ta tari wani da Sauri ta shige ta ringa bin bayan Naseer. A takaice ahaka ta rufe fuskarta tabi Bayan Naseer har k'ofar gidan Naeema Ta gwallo Ido a lokacin da ga su Minal sun fito suna Masa oyoyo. Ya rik'e hannunsu Suka Shiga gidan Sai da Safiyya ta Fadi ya Kai sau uku sabida azabar saurin ta koma gida ta Sanar da hajara Kamar ta tashi sama. Ido rufe ta Kara Hawa taxi ya maidata unguwar su Tijjani tace ya jirata gata Nan fitowa. Hajara kuwa Safiyya na Bata labari ta hau had'a Kayanta tana Godewa Allah. Cikin kankanin lokaci suka jiddi kayansu suka zuba a taxi Suka dau hanyar dorayi Kamar su karbi tukun Dan gani suke Kamar ba tafiya taxin keyi ba..... *Inaso na Dan Yi shi a gurguje mu shiga ainihin chapter 3 na labarin Naeema Dan na Gaya muku Yana da tsayi ahaka ma masu Dan mahimmancin nake rubutawa* [7/16, 8:31 PM] Zannura: *NAGA TA KAINA* *NA SADNAF*🌸🌸 ®️ *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_* _{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_ *Free Novel* *Page 46* Suna isowa k'ofar Gidan jiki na rawa suka mik'awa Mai taxin duk kudin hannunsu kowacce ta fito da kayanta da kanta bakinsu a washe Kamar gonar auduga sosai sukeji Kamar sun samu yancin kansu. A k'ofar shagon da Isihu ke sallamar mutane suka tsaya suna karewa gidan kallo. Hajara ta Shiga shagon ta daga Kai sama tana kallon yanda shagon yake cike da Kaya har da buhunan danyen abinci ake siyarwa a shagon Da farko Bata Gane Isihu ba sai daga baya tace"Shege Ashe kaima Nan din ka gudo shiyasa baa ganinka Kai Kai kai Safiyya Kinga katon shagon da Naseer ya bud'e amma muke zauna a gidan Tijjani muna Shan bak'ar wahala kawai sabida an siyar Mai da gida sai yamin karyar zai Shiga duniya Ashe Yana. Nan Yana Jin dadin rayuwarsa da Naeema da yayansa. "Wanan ba shagon Yaya Naseer bane shagon aunty Naeema ne" Isihu yace Yana had'e Rai tare da fusge bredin da Safiyya ta d'auka Dan bak'ar yunwa takeji cikin jikinta balain sakata cin abinci yake. "Iyye a gidan uwarka ya Zama shagon Naeema wato abinda aka kitsa maka kenan ka.ringa fada zaka ci ubanka Bari nashiga gidan wlh sai na saka Naseer ya koreka daga shagon Nan" Daga haka ta fito daga shagon Safiyya na dannawa Isihu zagi tare da dumbuzar garin kwakin dake cikin buhu ta tura a bakinta Dan kamar taci babu Haka takeji. Ba Wanda yayi Sallama a cikinsu suka Shiga gidan. Ina zaune a tsakar gidan Ina yiwa Zahira kitso su Nadeeya su Kuma suna cin shinkafa da miya da kifi Naseer kuma ya Shiga d'akina yayi wanka Dan ya canja Kaya ya Kara fita Dan Tijjani ya Nemo Masa irin aikin da yakeyi a wani company duk da albashinsu ba yawa Haka Naseer ke fita da sassafe idan sun samu break sai ya dawo gida yaci abinci ya Kara watsa ruwa ya fita bazai dawo gidan ba sai wajen Goman Dare. Dawowar Naseer da siyar Masa da gidan da su Umma sukayi sai Dana Yi dgsk Naseer ya iya fawwalawa Allah komai Dan sosai yayi rashin lafiya gidansa. A ranar da Umma taje gidan Tijjani take Sanar.masa da sun siyar da gidan A ranar Tijjani ya nemi gidanmu yazo ya kuwa tarar da Naseer a gida. Sosai ya nuna Jin haushinsa da Naseer ya Bari Suka cutar dashi Bai dau mataki ba har korar Hajara yayi niyyar yi ya Bata kudin mota ta koma calaba wajen Lami ko Safiiyya Naseer yayi ta rokonsa akan yayi hakuri Kar ya koreta tausayin Naseer yasa ya Nemo Masa aikin dak'yar da albashin ba wani taka Kara yayi ba Amma ya gwammace ya ringa fita din daya zauna Haka Naeema na d'aukar Nauyin shi da yaransa. Naeema kuwa budi take samu ko ta ina Dan har katon fili ta siya da Sunan Waleed. Tunda Naseer yayi ramar siyar da gidansa da su Umma sukayi Bai Kara maida jikinsa ba. Ni kuwa daga Ni har yarana munyi sharr damu ban taba tunanin Zan danyi kib'a a rayuwata ba sai yanzu Zan iya rantsewa ban taba jina a cikin kwanciyar hankali batare da fargabar komai ba sai a yanzu da babu umma da Safiyya dake dagamin hankali Ashe Zan tab'a tsintar kaina a cikin kwanciyar hankali Haka kudin da nake samu Bai taba sawa na Raina Naseer ko na nuna Masa iko da dukiyata ba duk da Naga alamar Yana da gudun zuciya Dan karfin Hali irin nasa yasan muna da komai Amma idan aka bashi allowance din sati ko albashi sai ya Dan tsinto Mana wani Abu ya kawo na amfanin gidan. Sai danayi dagske ya daina siyowa nace ya ringa Tara kudin ya samu na siyan fili Dan Naga rashin gidansa har yau yasa bashida walwala Kuma Yana fama da ciwon kirji har yanzu. Yarana kuwa duk suna ingantaciyar makaranta Dan Zahira yanzu tana jss 2 San Sai da aka Mata tsallaken jss1 sabida tsayinta. Sosai nake mamakin girman Zahira da kyaun da Allah ya Bata da ko Ni Dana haifeta wani zubin bana iya d'auke idona akanta. Ga balain farin jini da Allah ya Mata na kawaye tun ma ba'aje koina ba Wai wasu ke zuwa Sallama da Zahira. Nadeeya ce take primary 5 yanzu Minal a primary 4 Humaira 3 Raheema a primary 2 Waleed Kuma na nursery Dan makaranta ma Dana saka shi na daban ne. Shigowar Umma da Safiyya yasa na saki baki Ina kallon ikon Allah. Yarana dake cin abinci kuwa duk suka Mik'e tsaye Suma Kamar sun ga dodon Ni Safiyya kuwa idonta kur Akan abinci da yarana keci Umma Kuma ta tsaya a tsakiyar gidan tana karewa ko'ina kallo tana "Lailai Naseeru Ashe Haka yake.jin dadin rayuwarsa shine muke cin ubanmu a gidan tsinannen yaron can Banda abin Naseeru Dan zai zauna da Naeema har sai yamin karyar zai Shiga duniya" Muryar Hajara ne yasa Naseer dake sallah yin saurin Sallame sallahrsa ya fito Dan ya gasgata muryar wacce yake ji. Daskarewa yayi a bakin kofa a lokacin daya daga labule ya hango Hajara da uban Kaya agabanta tana karewa gidan kallo Allahuma ajirni fi musibati wa aklifnin khairin minha ya hau fada a fili Sam bai lura da Safiyya ba sai daya ji tashin muryarta tana "Mai kuka wani tsatsaremu da Ido kamar Baku sanmu ba shegu Wanan uban abinci da kuke ci Haka har da kifi lailai kun samu duniya Umma Bari na fara cin wanan tukunna na samu nutsuwa kafin a zubo Mana Dan Naga matar gidan kanta a sama yake Bata so ganinmu ba" Ta nufi wajen su Nadeeya gadan gadan Naseer kuwa ganin Safiyya ya tayar Masa da ciwon kirjinsa Yana jin ciwon siyar Masa da gidan da tayi na dawo Masa tamkar a lokacin ta siyar. Bai San lokacin da ya isa gaban Safiyya dake k'ok'arin Zama Dan taci abinci ba Ido rufe ya cakumeta ya tsayar da ita ya hada kanta da bango tare da shake Mata wuya Yana k'ok'arin rabata da numfashinta da yakeji a Ransa tabbas kashe Safiyya ne kawai zai saka ya daina Jin ciwon dayake ji a kirjinsa. Hajara. Hankali a tashe ta nufi wajen Naseer ta fara ihun ya cikata kar ya kasheta Bai ga cikine a jikinta ba Amma Naseer ko gezau baiyi ba sosai ya Kara shake Safiyya Yana ta biyashi kudin gidansa. Ni kuwa ko kallonsu banyi ba na ja hannun yarana na turasu dakina na rufe k'ofar dakina na nufi daya d'akin shima na rufe na saka kwado. Kitchen Dina ma Haka na koma na zauna akan kujera danake Kai na dau Reza na fara gyara farcena. Dan Basu isheni kallo ba wajen Naseer Suka zo ba wajena ba so nake su Gama abinda suke su juya su bar min gida. Dan Naseer a yau zai San da da yanzu ba daya bane ko kusa ko alama bazan dau abinda sukamin a baya ba a da Dan Ina zaune a gidansa ne suka min abunda ransu keso Amma yanzu kuwa gidana ne Bari Naga iya gudun ruwansu. Azaba ne yasa Safiyya sumewa Dan ba iya shak'a Naseer ya Mata ba sai daya hada.mata da duka. Duk dukan da Hajara ke Kai Masa tana ihun kuka har da su cizo Naseer Duk baiji ba sabida yanda idonsa ya rufe. Sai dayaga Bata motsi ya cikata Hajara ta zub'e gaban Safiyya tana zagin Naseer akan gida zai kashe Mata 'ya Naseer kuwa a tsawace yace"Umma Mai kuka Zo Nema Kuma a gidanan"? Hajara butar data gani da ruwa ta watsawa Safiyya. Safiyya kuwa taja dogon numfashi Hajara ta saki ajiyar zuciya tana "Naseer bakada hankali ko kasheta kake so kayi sabida kawai ta siyar maka da gida ba na baka hakuri ba a gidan uban wa kakeso ta samo kudin da zata biyaka. Naseer karka manta nifa Mahaifiyarka ce kaina Kuma babbn D'ana yanzu Dan an siyar ma da gida shine zaka min karyar ka Shiga duniya Ashe kana Nan kana Jin dadinka da Naeema Ni danake mahaifiyarka Ina can Ina Shan wahala abinci ma na neman gagararmu Tijjani dayake tsinanne daga shi har matarsa azabtar damu suke idan baka rik'eni ba wa kake so ya rik'eni Safiyya ma da ciki tsinannen mijinta ya korota bamuda kowa sai Kai d'in Dan Haka hakuri zakayi mu zauna a nan gashi Allah nata Buda maka ga katon shagonka cike da Kaya ga Dan karamin gida karka wani damu tunda ka dage zaka zauna da Naeema ba yanda zanyi Haka zamu zauna" Sai a lokacin na Dago kaina daga yanken farcen da nake na mike Ina "A Ina zaku zauna Umma ba dai a gidana ba ko? Dan wanan karamin gidan da kike gani halal Dina ne da kudina na siya babu ko sisin Naseer a ciki. Gashi Nan agabanki ki tambayeshi kiji shima Dan yaransa na barshi yake zaune a gidanan Dan Haka ki nemi wani gidan ki zauna ba dai gidana ba idan ma Dan Naseer na gidan ne shima wlh Tallahi Zan hado masa kayansa ku tafi Dan bazan yarda ku zauna a gidana ba kamar yanda Baku yarda na zauna a gidan Naseer ba" Hajara tsananin.mamakin Naeema yasa ta kasa magana Naseer kuwa b'acin Rai ma Bai Bari ya iya magana ba sabida karfin halin mahaifiyarsa da kanwarsa shi kam badan Kar yayi sabo ba dayace Allah ya dau Ransa da Wanan abinda mahaifiyarsa ke Masa "Karya kike Yi Naeema wanan ba gidanki bane gidan Naseer ne Kun hada Baki da Naseer ne Dan kuce min ba gidansa bane Dan Kar mu zauna toh karyarki ta Sha karya wlh sai mun zauna dan bake Kika haifamin shi ba da zai tare a gindin keda yaranki gida Wasa ne da Zaki iya siya ki bude katon shago ga injinan markade har biyu yanzu Naseer Dan Kar mu zauna a gidanka shine zaku hada Baki kucemin gidan Naeema ne toh ko uwar gidan Naeema ne wlh sai mun zauna Dan itama ai da kudinka tayi arzkin. Hajara tace tana k'ok'arin komawa ta zauna a gefen Safiyya da ta Dade da farfadowa tsoron Naseer yasa ta kasa bud'e idonta Tana Jin duk abinda suke cewa Ni kuwa Ina ganin ta zauna na kalli Naseer nace "Kasan wlh Tallahi bazan yarda su zauna min a gida ba Naseer kasan yanda zakayi dasu. Idan dai har Dan kaima na barka ka zauna ne suka biyoka suna takamar kana gidana ne a zaune wlh sai dai kayi hakuri ka bisu Abunda na dauka a Baya wlh Tallahi bazan dauka yanzu ba" "Umma wlh Nan ba gidana bane Nima albarkacin yarana nake ci shiyasa ta barni na zauna Kun siyarmin da gida hakan Bai Isa ba sai Kun biyoni Inda zaa taimakamin "Nima albarkacin jikokina zanci ta hakura ta barni na zauna Dan na Gaya maka ba Inda zanje kaji na rantse maka" Umma tace tana Kara gyara Zamanta Ni kuwa mik'ewa nayi da zumar shiga daki Naga Naseer ya rigani Shiga d'akin Rai a b'ace ya fara tusa kayansa a cikin bakkonsa ban ce Masa komai ba ya gama had'awa ya fito daga d'akin ya kalli Hajara Yana "idan ma Ni kuka biyo toh na barwa Naeema gidanta sai kusan Inda dare ya muku bazaku kasheni da Raina ba" Daga Haka ya fice daga gidan Ransa a b'ace yarana na San suyi magana na daka musu uban tsawa Suka koma ciki da Sauri. Na Kara rufo kofata na kalli Umma da ta bi k'ofar gidan da kallo tana mamakin tafiyar da Naseer yayi ya barta Ni kuwa Isihu na kwallawa Kira ya shigo da Sauri Na nuna Masa bacconsu Umma Ina "Fitarmin da kayan Nan can waje Zan Shiga daki idan sun tafi ka rufemin k'ofata Dan wlh bazasu zauna min a gida ba" Safiyya da Umma mik'ewa sukayi da ganinsu da zasu samu wuta zasu iya jefani a ciki Umma cikin wani irin murya tace "Naeema sai kinyi danasanin korarmu da kikayi wlh ko zanyi yawo tsirara sai na ga bayanki ba dai mu Kika Kora ba wlh Zaki gani" Umma tace tana yin waje Ni kuwa nace "Insha Allahu ba Abunda Zaki iyamin alheri Zan gani idan Allah ya yarda" Hannuna Zahira ta ringa ja Dan har fara hawaye Safiyya kuwa idonta ya sauka Akan Zahira da ta Dade Bata ganta ba wani irin murmushi naga ta sakarwa Zahiran daya sa naji gabana ya tsinke kamar wancan lokacin da idan zasumin mugun Abu kirjina ke tsinkewa. Tura Zahira daki nayi da Sauri na fito daga d'akin ina "Dalla fitarmin daga gida" Na karasa wajenta Ina turata waje Ita kuwa ta Kara sakar min murmushi tana "ki shirya tarbar balain da zan jefo Miki" Daga Haka ta fice waje. Ni kuwa na rufo kofata Ina adduar insha Allahu ba balain da Zan gani Hajara kuwa Tana fita ta hango Naseer daya kusa Isa bakin titi ta dib'a aguje ta bishi abaya. Tana kwalla Masa Kira. Naseer Bai tsaya ba har sai data cimmasa ta zub'e a gabansa ta fashe da kuka tana Kar ya tafi ya barta ya rufa Mata asiri Bata da kowa sai shi. Kafarsa ta rik'e tana rusa uban kuka. Naseer kuwa hankali a tashe ya Ajiye bakonsa Yana "Umma Mai Haka Zaki taramin jamaa Dan Allah ki mike tsaye wlh Umma Nima bansan Inda zanje ba Ina Zan tafi dake banida gidan da Zaki zauna umma wlh wancan gidan na Naeema ne Dan Haka ki koma gidan Tijjani ki zauna kafin na samu wajen Zama" "Aaa wlh Dana zauna a gidan Tijjani gwara na kwanta a bakin titi kasan wuyan da muke Sha kuwa agidnsa Tijjani Bai d'aukeni da daraja ba a gaban idonsa matarsa ke azabtar damu Baya ce Mata komai idan na Masa magana sai yace Baya San takura ai Allah ya Isa no-no na da Tijjani ta Sha" "Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun Umma Wai Mai yasa burinki ki yiwa yaranki mugayen kalamai Umma a cikin mu hudu waye Baki yiwa Baki ba Umma kinsan bakin uwa kuwa daidai da shedaniyar yarinya can Haka Kika Yi ta Mata Baki gashi baa je koina ba Aurenta ya mutu ta dawo gabanki da ciki Umma bahaka uwa take wa yaranta ba Umma Yara koda kuskure suke Yi addua ya kamata ki bisu dashi gashi duk kin Mana baki Umma kema abin na shafarki" A takaice Haka Hajara ta marairacewa Naseer da kuka har sai daya kaisu gidan wani da suke mutunci dasu Akan su kwana daya kafin ya samo musu Inda zasu zauna ya rasa yanda zaiyi da Hajara. Gidan da suka sauka.kuwa tarb'a Mai kyau aka musu sai da suka ci abinci nutsu suka hau hirar Naeema da irin Abun da zasu Mata idan sun samu wajen Zama. Shawarar da Safiyya ta kawo akan Naeema ne yasa Hajara mik'ewa ta taka rawa Dan idan suna San su cimma burinsu wajen tarwatsa rayuwar Naeema sai sun hada da makirci tamkar yanda Murja keyi. Washegari Naseer ya samo musu gidan Haya Mai had'aka da.mutane da yawa a ciki daki dayane sai tabarma da ya saka musu Dan bashida kudin katifa Cikin murna su Hajara suka koma gidan Dan gwara.munsu kwana a Kan tabarmar da dai zaman gidan Tijjani Naseer kuwa ce Mata yayi shi a company da yake aiki zai ringa kwana tunda ta koreshi daga gidan Naeema Budar bakin Hajara sai cewa tayi Kar ya wani damu ya koma gidan Naeeema su zauna ita dai fatanta ya ringa lekosu Yana kawo musu na abinci ya Kuma Bata jari tana siyar da kosai tunda ta lura gidan kowacce na Sana'a Har hakuri ta bawa Naseer Akan wnan karin da gaske take yayi zaman aurensa da Naeema. Naseer kuwa ya zub'e a kasa ya hau Mata godiya *Chapter 3* *Dama ku barni na huta sai bayan sallah na dawo muku da karfina Dan chapter 3 yafi na daya Dana biyu Kuma wlh na gaji**😟😟😟😟😟😟😟😟😟*NAGA TA KAINA* *NA SADNAF*🌸🌸 ®️ *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_* _{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_ *Free Novel* *Page 47* Nidai tunda Suka tafi naji hankalina ya tashi da irin kallon da Safiyya tayiwa Zahira da alwashin da suka Sha na ganin bayana dauriya kawai nake Amma bansan Mai yasa nake cike da fargaba da Kar su yiwa Zahira wani Abu ba Dan nasan halinsu nasan abinda zasu iya Yi na rasa wane irin masifa da balai ne wanan na rabu da Naseer ma na dawo gidan kaina Amma duk a banza hakan Bai saka sun sararamin ba nikam inaga sai na saka Naseer ya rubutamin takardar Saki na Kai musu sun ga shaida sanan zasu shafamin lafiya. Ban damu da Rashin dawowar Naseer da sai daya kwashi kwana uku Bai lek'o mu ba Ni kuwa tunda Suka tafi na sake zage damtse wajen yin addua Ina rokon Allah Kariyarsa gareni da yayana addua ma ya Riga da ya zama jikina bana sake idan lokacin da nake tashi idan yayi sai na tashi daga bacci naje gaban Mahallicina A Rana na hudu Naseer yazo.min da yamma bakinsa a washe ya hau bani labarin Umma ta bashi hakuri ta Kuma sawa aurenmu albarka Wai yanzu ba ta da matsala dani tunda ya Kama Mata gida ya Kuma Bata jari. Wani irin murmushi takaici nayi ina "Umma ce ta baka hakuri akan ta Kuma yarda mu zauna ba matsala Naseer.kai Kuma sai ka yarda" Dan rage faraa daya shigo dashi yayi ya cigaba da kallona "Naseer halan ka manta wacece.umma Taya Umma zata ce maka Bata da matsala da zamanmu tare.har ka yarda Bayan gidana ta zo naki yarda su zauna Kuma Haka kawai sai tace ma ta sawa aurenmu albarka ka yarda Naseer inaga har yanzu baka San wacece Umma ba idan ka manta Ni ban manta ba idan kaga Umma ta biyo ta wanan fuskar toh wlh wani mugun abun zata Mana sai dai na roki Allah ya kareni da yarana haihuwar Minal Haka tace Mana tayi nadama Mai ya biyo baya guba ta zuba a kunnu ta bawa Safiyya ta kawomin.na Sha Akan zan samu ruwan no-no akan naki Sha Suka rufeni da duka Naseer har sai da ka shigo ka k'waceni a hannunta Naseer har ga Allah na gaji da abinda umma kemin wlh Nagaji na rasa wanan masifar da.mai yayi kama tunda na aureka ban taba samun kwanciyar hankali ba daga wanan sai wanan da Ido daya nake bacci sai a yanzu Dana fara samun nutsuwa Umma da Safiyya suka Kara durowa ranar da.suka.zo sun Sha alwashin ganin bayana Safiyya ta kalli Zahira ta girgiza min Kai Naseer idan wani Abu ya Samu yarana ko Ni wlh Tallahi bazan yafe wa Umma da Safiyya ba sai na Kai kararsu gaban Allah nidai ka koma wajenta kar.ma tayi tunanin kana gidan Nan ma ringa lek'omu idan ka samu sarari" Na karashe Ina fashewa da kuka Dan har ga Allah su Umma sun isheni Naseer.ya bani takarda ta kawai na huta Zan jure komai banda su tab'a min yarana ba dole bane sai nayi rayuwa da Naseer auren Naseer ya isheni ya gundureni bazan karashe rayuwata Su Umma na wahalar Dani ba. Naseer rarrashina ya hau yi Yana "Yana Naeema wlh da ikon Allah kawai nake rayuwa har.yanzu rabona Nima da kwanciyar hankali tun ranar Dana budi Ido nasan Umma a matsayin Mahaifiyata na Sha Zama nayi tunanin Anya Umma ce ta haifeni kuwa Dan har yau danake yawo.ban tab'a ganin Mai irin Halin mahaifiyata ba ko a tarihi Umma gaba take da kwanciyar hankalina nayi kukan nayi naseehan duk a banza Nima data ce min naje ba komai a zuciyarta nasan ta fada ne kawai Bai Kai zuci ba Amma koma menene Zan cigaba da Addu'a Allah ya shiryeta ta Gane gaskiya wlh Naeema nasan tsinaniyar yarinya Nan ce ke zuga umma.na balain tsanarta duk wani mugun Abu ita kesa Umma amma karki damu insha Allahu ba Abunda zasu iya Miki ko yarana kema shaida ce akan yanda nake Addu'a" "Duk da Haka ka koma wajenta Naseer zamanka a gidana hatsarine" Nace na mik'e tsaye Dan har ga Allah banasan zaman Naseeru a gidana Ni nasan zamansa a gidana sai saka Umma ta cigaba da nufata da mugunta "Taya Zan koma gidanta alhalin haya na Kama Mata daki daya" "Naseer kayi hakuri ka koma wani wajen da Zama ka ringa zuwa kana ganinsu Waleed wlh zamanka anan zai saka Umma ta ringa kuntata min Amma idan taga baka gidana Zan samu saukin wani Abun Dan idan ma Dan Kai zata min wani Abu idan.taga bama.tare zata kyalleni. Rai a Dan bace Naseer ya mik'e Yana "Mai yasa kike sawa a ranki Umma zata iya Miki wani Abu duk wani Abu da kika ga ya samu bawa daga Allah ne Umma Bata Isa ta Miki Abunda Allah ya Bai hukunta zai sameki ba wuyanta ki dogara ga Allah" "Naseer inaga ka manta Abubuwan da Umma tamin ne inaga ka manta Kuma wacece ita shiyasa kake fadar Haka ganganci ne ma na saki jiki nace Umma bazata min komai ba duk wadancan data min a baya ai ita ta ringa min Allah na kareni din" Katseni yayi a tsawace Yana "kice na fita na bar miki gidanki kawia Naeema ba sai kin biyo min ta wanan hanyar kina fakewa da Umma ba Karki.manta Nima ba a San Raina nake zaune a gidanki ba Naeema a matsayinki ta matata Naeema kaddara ce ta hau kaina na rasa komai nawa amma.kinsan badan kaddara ba Ni Mai bawa wani kyautar gidane Amma ba komai Naeema Zan tafi bazan zauna a gidan naki ba Allah ya bani arzikin da Nima zanyi gidan kaina idan na samu sararin Zan ringa zuwa Ina duba yaran nawa kamar yanda kikace" Daga Haka ya juya ya fice daga gidan Kamar zai tashi sama Kan kujerar na koma na zauna Ina fashewa da kuka mumunan fassarar da Naseer yamin Dan har ga Allah bazai Gane Mai nake fada ba da abinda nake gudun Amma Ni nasan watarana zai Gane Idan nace fushin da Naseer yayi Bai dameni ba karya nayi Dan Naseer nada hawan jini na Kuma San duk a dalilina yak'i rabuwa Dani yake ta fuskantar wadanan tashe tashen hankulan Amma Allah yasan na gaji bazan iya cigaba da jure abinda mahaifiyarsa kemin ba abinda na jura a baya bazan dauka yanzu ba sabida Kar ma ya fassarani yasa ban nemi ya sakeni a halin yanzu ba har sai idan ya Dan farfado daga karayar arzikinsa. Ban Bari na saka wani damuwa a Raina ba na maida hankalina Kan sanaoina da yarana da na balain sawa ido.nake.kuma addua kariyar Allah a garesu Safiyya da Hajara a hankali Suka fara karantar mutane da suke zaune dasu wayanda.zasu iya yin talatin sabida gidan katon gaske ne. Wasu matan Aurene wasu zawarawa har da Yan bariki ma ahaka suke.gwamutse a gida daya. Sati d'aya kawai da sukayi a gidan suka fahimci mutanen gidan basuda mutunci ko kad'an kowa ta kansa yakeyi Ga balain Sa Ido da munafirci da suke dashi. Amma ahaka Safiyya ke fito da tabarma bakin kofar d'akinsu tayi ta kallon mutane dake gidan tana musu shishigi tana Shiga abinda Bai shafeta ba a cikin kwana goma ta Gama Gane matan da suke da aure da zawarawa da Kuma Yan barikin Akwai wata Iyyatu da hankalinta yafi karkata wajenta matar aurece Mai Yara biyu hatsabibiya ce lamba daya data maida mijinta tamkar yaron cikinta Dan mijinta shi yake Mata wanki ya Mata girki komai dai daya Kamata ace ita takeyi mijinta keyi ita kuwa Iyyatu tana zaune tana karkad'a kafa tana zuba mulki hakane yasa Safiyya fara shishige Mata Amma Iyyatu na shareta Sai data Sha kwandunan wulakanci a wajen Iyyatun kafin ta fara sakar Mata fuska suna Hira sama sama ahaka har suka Saba Safiyya fa fara bugar cikinta Tana gaya Mata yanda ta mallaki mijinta ta hanyar wani kungurmin boka dan kafin ta aureshi Yana da Mata daya da Yara biyar daga shigowar ta gidansa ta asiriceshi ya saki matarsa ya Zama Kamar bawanta Safiyya kuwa kamar ta Kama rawa take ta hau rokon Iyyatu ta sadasu da bokan. Cikin kwana uku Hajara ta bawa Safiyya kudin mota itama zuciyarta cike da farinciki Dan kosai ma da ba wani ciniki take ba a kudin ta bawa Safiyya kudin mota akan taje. Yanayin zaman munafirci da ake Yi a gidan yasa suka Gane Safiyya da Hajara basa sallah wanda take suka.hau kirnsu da basa sallah aka hau ma kyamatarsu Akan Dole Hajara da Safiyya suka hau sallah Dan su samu mutanen gidan su so su. Safiyya kuwa Basu dawo Gidan ba sai wajen Goman Dare. Jiki a sanyaye Hajara ko Zama bata bari Safiyya tayi ba ta hau tambayarta ya sukayi. Safiyya jiki a sanyaye tace mata "Hmm Umma mutumin ya iya aiki Dan ko shegiyar Shugaba Bata kamo kafarsa a iya aiki ba sai dai matsalarsa sai ka ajiye Masa mugun kudi Mai balain yawa Dan yau ma sai danaga Naeema da su Zahiraa Kwaryar ruwansa bance Masa komai ba ya hau bani labarin komai game damu da abinda muke San muyiwa Naeeman Sai dai a dubawar da yayi Yaya Naseer baya gidan aunty naeema Yana wajen aikinsa anan yake.kwana kamar dai sunyi fada da Naeema ne" "Hmmm daya kwana a gidanta da Kar ya kwana a gidanta wlh sai Naga bayanta tunda har ta koremu daga gidanta Badai yanzu tayi kib'a ta samu kwanciyar hankali tana ganin yaranta Agaban ta zuciyarta na sanyi ba zata Gane kurenta Dan ko cewa nayi a Kona arzikin ta bazata wani damu ba idan tana ganin yaranta agabanta Amma idan na hargitsa Mata lissafi fa zata Gane shayi ruwane yanzu dai a Ina zamu samu kudi a Mana aikin Nan Kinga yau ma ko cinikin kosai bamuyi ba yanda na soya Haka na shigo dashi shi zai xama abincin darenmu" Umma kiyi karyar rashin lafiya kawai kamar Zaki mutu Yaya Naseer da Tijjani su Shiga su fita su nemi kudi Dan na matsu Naeema ta fara hawaye da idonta wlh wlh Umma banida burin daya wuce na samu cikar burina akanta dukan da Yaya Naseer yamin duk sai na dau fansar sa Akan Naeema"........*NAGA TA KAINA* *NA SADNAF*🌸🌸 ®️ *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_* _{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_ *Free Novel* *Page 48* Tuni Hajara kuwa ta hau rashin lafiyar karya Safiyya ta tasa cikinta gaba ta nufi gidan Tijjani duk a firgice Kamar gaske. Wajen karfe biyar na yamma ta Isa gidan Sai dai tana zuwa gabanta ya yanke ya Fadi. Dan Naseer da Tijjani ta samu a k'ofar Gidan suna zaune a Kan tabarma Tuni jkinta ya dau rawa kamar ta juya Dan idan akwai Wanda take balain tsoro Bai wuce Naseer ba sosai take.ganin kiyayar da yake Mata a idonsa. Sam Bata kawo zata sameshi anan ba Dan so tayi ta gayawa Tijjani shi Kuma ya gayawa wa Naseer. Har ta juya zata koma ta tuna yanda take San ta samu cikar burinta akan Naeema. Wajensu ta nufa tana matsar hawaye kamar irin ta Dade tana kukan Nan Tana Isa gabansu ta zub'e ta hau sheshek'ar kuka tana "Yaya Tijjani Yaya Naseer umma na kwance tun jiya ba lafiya sai suma.take.ku taimaka Mana Kar ta mutu" Naseer Bai kalli Inda take ba Dan sabida tsanar da yayiwa Safiyya yasa ma Baya Shiga gidan ko kadan Baya San ganinta. Sai dai ya tura a kaiwa Hajara Dan kudin kashewa Wani irin kallo Tijjani ya watsawa Safiyya dake.ta sheshek'a.yana "toh Dan Bata da lafiya shiyasa Zaki dira gabanmu Haka a firgice ba Sallama yanzu da Kika zo Nan mu zamu Bata lafiya uban me ya Hana ki kaita asibiti da yanzu bama Nan ya zakiyi kenan"? "Yaya banida ko sisi shiyasa ban kaita asibiti ba" Tsaki Tijjani yayi ya k'au da.kai Yana Allah ya sauwake Naseer kuwa ya saka hannunsa a Aljihu ya Ciro duk kudin dake jikinsa ya mik'awa Tijjani Yana Bata ta Kai ta asibiti gobe na dubota Dan yau aikin kwana nake" "Kai kake wahalar da kanka Yaya Naseer Ni ban yarda da shegiyar yarinya Nan ba tashi muje Naga jikin nata Ya maidawa Naseer kudinsa. Safiyya mik'ewa tayi da Sauri tana ji kamar ta rufe Tijjani da duka a ranta kuma sai zagin Naseer da shima take Jin kiyayarsa a ranta take bakin cikinta ma ko kallonta baiyi ba ballantana yayi tunanin binta suje gidan Hajara ta tilasta Masa Nemo kudi ya kawo Mata Dan.tasan Tijjani shegen kansa ne Bai Zama lailai ya bada ko.sisi.ba. Tana ji tana gani suka hayye vespan Suka tafi Naseer Kuma ya mik'e ya nufi titi dan.ya koma wajen aiki Tijjani.ke tilasta Masa zuwa.gidansa cin.abincin Rana Dan ba Abunda ya b'oye Masa game da abinda ya had'ashi da Naeema da hutun da yake so ya Bata tasamu kwanciyar hankali kafin ya koma gidan. Safiyya ce tayi ta Masa kwatance har suka iso gidan Yanda Tijjani ya had'e.rai Yasa tayi gaba ya bita a baya tana Addu'a Allah yasa Hajaran a kwance take Kar ta tona musu asiri. Sai dai suna zuwa suka ga Hajara tayi dare dare a tsakiya d'akin tana ta zabga Loma abincin da ta siya Dan taci kafin Safiyya ta dawo Dan idan ba cika cikinta tayi ba Safiyya na iya rabata da kudin hannunta ta siyi abinci ita Kuma ta barta da Shan garin kwaki ko sandararen kosai. Shigowar su Tijjani yasa ta ture abincin da Sauri ta hau yamutsa.fuska Tijjani kuwa Safiyya ya kalla Yana "Inaga daga fitarki umma ta samu lafiya ko tunda gashi har abinci Naga take ci Umma ya jikin naki Tijjani yace Yana guntsa dariyar Dan sosai ta dage take yamutsa fuska.tana kakarwa ga hannunta duk.miya da Gefen bakinta Safiyya kuwa kamar ta fashe Dan bakin ciki sai hararar Hajaran take. Tijjani kuwa ya Kara cewa " toh nidai Bari na tafi Umma Bari na siyo Miki pcm na kawo Miki inaga zazzabi ne" Bakin ciki ne yasa Hajara mik'ewa ta hau zagin Tijjani Tijjani kuwa ya karasa Kan tabarmar ya zauna Yana dariya "Ka dauka.wasa nake maka ko ka tashi ka fitarmin daga gida. Wlh yanda nakejin zuciyata Tijjani Zan iya fasa.maka Kai Tijjani hannun Hajara.ya ruk'o.da k'arfi Yana cigaba da dariya har.sai daya zaunar da ita Yana "Allah ya bar.mana ke hajiarmu kiyi hakuri muyi magana" "Umma Dan Allah Dan annabi na hadaki da girman Allah ki daina duk abinda kike wa Yaya Naseer da matarsa Umma na rasa Mai Yaya Naseer ya Miki Kika saka shi a gaba kika.hana shi zaman lafiya da matarsa, Umma yanda kike da hakki Akan Yaya Naseer shima Yana da hakki akanki Umma karki biyewa tsinaniya yarinya Nan ta Kai ki ta baro tun muna Yara nasan yarinya Nan Shaidaniya ce babu alheri sam.a ranta Umma komai Naeema ta Miki ya Kamata ace kin hakura ko Dan zuria dake tsakanin ita da Yaya Naseer a iya sanina ba abinda ta Miki shima.yaya Naseer ba Abunda ya Miki da ya cancanci Abubuwan da kike Masa Umma har gidansa daya rage Masa kuka.siyar da.ke da shegiyar.yarinya Nan Umma idan ba Yaya Naseer ba wa zakuyi.wa.haka ya barku"? "Umma duniya ga ba gidan Zama.bane wlh watarana dole.mu mutu mu koma ga Allah Allah ya hallicemu ne Dan mu bauta Masa Umma.Allah baya san.zalinci ki daina amfani da.ikon da Allah ya Baki akan yaran ki.ki ringa cutar.dasu Umma Ni.ba yaro bane.duk.abinda.kikeyi ba akan daidai.kikeyi.ba ya Kamata ki gyara.kafin lokaci ya kure Miki Umma yau ba Dan kin Kona dukiyar Yaya Naseer ba da kema.kanki Baki tsinci kanki a irin wanan gidan Sabida wani.biyan bukatarki kiyi.karyar.ciwo ba umma nidai shawara ce nake Baki kibi Allah da manzonsa.ki tsarkake zuciyarki ki zauna da.kowa.lafiya ki koma.ga Allah kalau Umma mutum.da kansa yake Gina lahirarsa idan ya gina da kyau kiga da kyau idan ma.baki Gina da.kyau ba Umma ke Kadai Zaki zauna a kabarinki ki guji.hawayen.wanda Kika zalunta Dan idan.ya barki da Allah wlh Sai Allah ya saka Masa ko bajima ko ba Dade Umma wlh akwai rayuwa Bayan mutuwa wayanda suke kwance a kabarinsu karki gansu a kwance ki dauka bacci sukeyi wlh rayuwa ce sukeyi Mai tsayi cike da irin Rayuwar da.sukayi a duniya Wala khairan ko sharran "Umma.kiringa sallah kiringa azumi ko Zaki samu haske a rayuwarki ke Kuma Safiyya Ina tausaya Miki wlh Dan ke macece bakisan ya gaba Zata kasance Miki ba nasan halinki gabaki daya daga auren da kikayi Kika fito.ya isheki ishara.kigane ba akan daidai kike ba duniya gidan aro ce duk sharrin da kikayi ko Wanda Zaki saka ayi wlh zai dawo kanki ko bajima.ko ba Dade. Umma Dan Allah kiyi hakuri ki yarda makamanki Allah yayi aure Bai Kare tsakanin Yaya Naseer da Naeema ba ki Sanya musu albarka sukoma su zauna idan Baki sani ba ki sani Yaya Naseer Yana d'auke da hawan jini tunda kuka siyar Mai da gidansa yake fama da ciwon kirji umma.naseer dinan ke Kika haife shi ya Kamata ki tausaya.masa iya abinda Kika Masa ma.ya Isa Ni Zan tafi umma.ga wanan ba yawa Zan ringa lek'o ku akai akai" Daga haka Tijjjani.ya mike ya fice daga gidan.batare da ya ko kalli Safiyya data sada Kai tana tsine Masa ba. Hajara kuwa kamar wacce aka sawa Gam aka like Mata Baki Haka ta bi Tijjani da kallo Yana fita Safiyya taja uban Tsaki Tana "kawai Dan ance su kawo kudi ya hau waazi sabida tsinannen rowa ke Kuma Umma sai kikayi shiru Kamar bakida Baki" "Taya duk abinda Naeema ta.mana ma.mu kyalleta korarmu fa tayi.daga gidanta Yaya Naseer ya zabeta akanki daya rabu da ita har.ya gwammace ki Masa baki keda danki wata ta kwace Miki shi nidai karki sake ki saurari wanan Yaya Tijjanin bakinsa daya da Yaya Naseer Naeema ma.tana ganin Haka zatace taci Galaba akanki" Hajara sosai maganganun tijjani.suka shigeta hakane yasa jikinta Yi sanyi idan akwai abinda taji ba dadi Bai wuce Naseer data zalinta ba ta hanyar siyar Masa da gidansa Amma Naeema Kam ba abinda zaayi taji tana Santa Dan abune kamar ya tsaya Mata a kahon zuciya har sai ta fito dashi zata ji dadi fitowar kuwa shine ta samu cikar burinta akan ganin Bayan Naeema da take ganin ma duk halin da take ciki yanzu itace sila maganganun Safiyya Kuma ya Kara.tunzurata tana ganin tabbas idan ta bar Naeema ma taci Galaba a kanta abu daya ne tasan zatayi shine ta daina takurawa Naseer akan Naeema Amma fa Naeema sai ta kwashi kashinta a hannu Sannan sallah da azumi da Tijjani ya Bata shawarar ta ringayi zata ringayi Dan babanta cikakken musulmine Mai addini ko Kafin ta hadu da Yan kungiya tana sallah shigarta kungiya yasa ta daina sallah Amma yanzu zata cigaba da sallah da duk wani Abu da musulmi zaiyi na ibada tunda Bata cikin kungiya yanzu. A takaice Safiyya sai data Kara taso da maganar kudurinsu Akan Naeema data ga Hajara tayi wani sanyi Tsabar bakin Hali da mugunta ita ta cigaba da neman kudin da zata kaiwa bokan da zai Mata aiki akan Naeema A cikin irin wanan halin ta haihu Inda ta samu da namiji ta saka Masa suna Bashir Tunda Safiyya ta haihu duk rayuwarta ba abinda take so sama da Bashir danta sosai take cin burin inganta rayuwar Bashir Amma tana burin tarwatsa rayuwar yaran naeema. Ko arbain bata yi ba ta samo wani gida ta fara aikatau duk Wai Dan ta samu kudin da zata kaiwa boka ya Mata aiki Akan Naeema Dan duk wani motsin Naeema ta sani duk da tazarar dake tsakaninsu. Hajara kuwa itama.tana.kan.bakanta akan Naeema da yarta Zahira Amma Bata matsa can Kamar yanda Safiyya ta matsa ba Dan abinci ma wahalar samu yake.mata Dan aiken da Naseer da Tijjani ke mata ma idan Safiyya ta kyalla Ido taga kudin to Bashir zata kashewa kudin tana ji tana gani Bata Isa tayi Magana ba. Naeema Ban fasa adduoina akan yarana ba ban Kuma takura kaina da tsawon lokacin da Naseer ya d'auka Bai lekomu ba duk da Naseer Yana Raina inaso.naji ko lafiya yake. Ga yaransa.dake.balain takuramin da tambayarsa balle Nadeeya da har sai na hada Mata da Bugu wani zubin take kyalleni sadaka kuwa bana Wasa dashi. Dan Indai Zan tuna kallon da Safiyya tayiwa Zahira sai kirjina ya buga Gashi zahira girma take tana Kara Zama kyakyawar budurwa. Kullum sai an aiko ana Sallama da ita bakina har gajiya yake wajen cewa bana barinta zance Kuma.masu neman zahiran manyan mutane ne masu kudi daga Mai Mata sai samari. Yau daya kasance alhamis Ina zaune a tsakar gida Ina Yankewa Waleed farce shi da Raheema Zahira Kuma tana kitchen tana girki Nadeeya kuma tana wanke musu uniform dinsu tana ta zabga surutu a cikin surutun nata naji tana "Dazu fa Naga Aunty Safiyya a Gefen makarantar mu tana lek'omu tana ganin na ganta ta b'uya da Sauri" Cikin fad'uwar gaba na ajiye rezar hannuna Ina "kin tabbata Anty Safiyya Kika gani Nadeeya ba Mai Kama da ita Kika gani ba"? "Tab Umma ita na gani Mana sau uku kenan. Ina ganin ta idan taga na ganta sai ta b'uya mantawa nake ban Gaya miki ba sai Yau na tuna" Haka kawai naji hankalina ya tashi Dan Ni nasan ba alheri ne yake Kai Safiyya makarantar yarana ba har na Dan saki jiki danaga an tafi shekara ba abinda ya biyo baya Kuma abinda ya bani mamaki Bai wuce yanda take zuwa makarantar ba lura da ba unguwar mu daya ba Dan Isihu ya bani labarin suna zaune ne acan tsohuwar unguwarmu Dan Yana yawan zuwa gidansu aunty duk inada labarin zaman da sukeyi a can da haihuwar da Safiyya tayi da aikatau din da takeyi ita Kuma Umma na siyar da kosai a bakin titi Labarin Naseer ne kawai bani dashi Zurfin Dana Yi a tunani yasa Sam bansan Naseeru ya shigo ba sai ihun yarana naji suna ihun murna Abba Gabadaya zuwa sukayi Suka rungumeshi sun ma ki Bari ya Ajiye manyan ledojin daya shigo dasu. Ni kuwa Ido kawai.na zuba Masa Ina kallonsa ba laifi ya Dan ciko ba Kamar kwanaki ba Kuma har ga Allah naji dadin ganinsa Ido muka had'a ya Dan saki murmushi Yana "Hajajju Mai gida.zan.iya shigowa ko na koma"? Bance Masa komai ba Dan nasan magana ce yake gayamin a fakaice da Sunan gidana ne Bai Isa da gidan.ba Har Kan tabarma danake Kai ya karaso ya zauna yaransa suka ja manyan ledoji gabansa Ashe har da kayan abinci ya taho.mana dashi manja da doya dasu Dankali Ledojin Kuma Kaya ya siyowa su Zahira Ledar Waleed kuwa daban yake dan Waleed.ma Dora shi yayi a Kan cinyarshi Ni nasan a yaran mu gabadaya Waleed na daban ne a zuciyar Naseer yanda nakejin Kamar Zahira itama ta dabance a yarana ba Kuma komai ya jawo haka ba sai hankalin zahira da yanda take nuna tana Tausayina banida babbar kawa ma daya wuce Zahira yanzu tunda idan Abu ya dameni Ina Gaya mata ko Bata iya bani shawara ba Ina Jin sanyi a Zuciyata. Koni sai da Naseer ya cikomin Leda da Kaya na Kuma ji dadi Sai danayi dagske na nuna Masa b'acin Raina ya daina cemin Mai gidan Bamu samu kebb'e wa ba sai da Yara sukayi bacci Muka hau hira na dawo da maganar dalilin daya sa naki Bari ya zauna a gidana sabida yaranmu ne.ba komai ba Shima.yace min "Badan kin bijire bama da bansamu wanan aikin da nake yi ba dake Dan shigomin da kudi ba Dan a gaskiya a ranar Dana bar Nan naji Haushin abinda kikamin ban Kuma boyewa Tijjani komai ba na Gaya masa yacemin Kar na damu na Miki uzuri ba laifinki bane dole tasa kikamin Haka nayi hakuri har sai kin hucce sai na dawo ya Kuma nunamin kila yanzu idonsu Umma na kaina na daga kafar Kar Nazo Da shawararsa nayi amfani nake kwana a company mu kamar wasa. Mai gidanmu yamin tayin aiki a company su dake can Abuja ya Kuma bani Dan matsayi sabida rukon amanar daya ce Ina dashi Da wanan na koma Abujan na fara aiki ya bani daki daya nake kwana acan Ke.kadai ce bana yiwa aike Dan nasan kina da kudin da Zaki kula da yaranmu Amma Ina yiwa Umma aike na Kuma ringa Tara kudina har sai Dana ga sun isheni nazo.gida na duba ku na muku kwana biyu na koma Kinga dalilin dayasa ma Kika ga na kwana biyu ban lek'o ku ba banida burin daya wuce na samu kudi na siyi fili nayi gini Naeema inasan Naga Nima inada gidan kaina" Sosai nayi murna da aikin da Naseer ya samu da ke nuni Ana Dan biyansa albashi Na Kuma ji dadi daya kasance ba a garin nan ya samu aiki ba dan nasan ko bibiyarmu Umma keyi zata ji baa gidana yake zama ba. Zuwan Naseer ya mantar Dani batun ganin da Nadeeya tace tayiwa Safiyya. Sai da Naseer yayi sati kafin ya shirya yacemin zaije ya dubo Umma Dan gobe yake San wucewa Sosai naji dadin cigaban da Naseer ya samu Kamar nace Masa ya dib'arwa Umma Mai dasu doyan daya kawo Mana na Kuma fasa Dan bana San Masa shishigi yanda bayamin maganar Umma Nima bana San na Masa maganarta. Naseer kuwa a lokacin daya Isa gidan jikinsa ne yabi yayi sanyi dayaga yanda Hajara ta hade girar sama da kasa Tama k'i amsa gaisuwar daya Mata Dan a ranar daya dira garin Kano sai da Kawar Safiyya dake unguwarsu naeema ta Bata labari Saude da itama ta kasance bazawara tana aiki.a wani gida dake kusa da gidan da Safiyya ke Aiki Da biyu Safiyya ta kula kawance da Saude Dan ta ringa gaya Mata komai Akan su Naeema da yaran nata cikin Ikon Allah kuwa sai halinsu yazo daya ta mugunta da balain San bin Mallamai da bokaye saude ta tsani Naeema ne sabida ta daina Bata bashi idan taje Dan sako Naeema tayi da karbar bashi ba dare ba Rana Naeema tun tana.kawaici har sai data daina Bata bashin Dan idan saude.nada.kudi wani shagon take tafiya idan Kuma Bata da kudi sai ta taho shagon ta bashin data daina Bata sai ya tsayawa saude a wuya ba iya Wannan ba yarta dake Saar Zahira maimuna da ajinsu yake daya sai zahira tafi maimuna kyau da k'ok'ari sai hakan ya Kara asasa tsanar da take wa Naeema Safiyya na Mata maganar Naeema ta karbi maganar da hannu bibiyu hassada da kyashi yasa itama take San ganin Bayan Naeema data Mata fintinkau. Idan sun tashi daga wajen aikatau gidan su Safiyya take zuwa ta hau Basu labarin ai taga Naeema yau taga kaza taga kaza ahaka Hajara da Safiyya ke samun labarin duk motsin da Naeema tayi da yayanta Washegarin da Naseer ya dira garin da sassafe ta je gidansu Safiyya ta hau Basu labarin zuwan Naseer da lodin kayan daya kawowa su Naeema cikin akori Kura ta karkace ta Kara Gishiri da maggi. Sosai Hajara taji ranta ya b'aci ta hau jiran zuwan Naseer Amma ko gezau Naseer Bai zo ba ahaka take kwana da bakincikin zuwan Naseer gidan Naeema batare da ya waiwayeta ba ba abinda ya Kona Mata Rai kamar uban kayan da akace ya kaiwa Naeema wato ita Tana Nan tana soya kosai a Rana Naseer Kuma ya tare a gindin Naeema Safiyya kuwa a gefe zuga Hajara kawai take akan taci mutuncin Naseer. Sai gashi Naseer Bai tashi zuwa ba sai daya kwashi kwana bakwai a Rana na takwas kuma.haka.yazo musu babu ko.leda a hannunsa Naseer kuwa jiki a sanyaye yace "Umma ko akwai lefin da na Miki ne"? Girgiza masa Kai tayi tana "ba wani laifin dakamin Naseeeru ya wajen aikin ya wajensu Naeema yaushe kazone? Da Zuciya daya Naseer yace "kwana bakwai kenan da zuwana Umma na Dan yi.ziyarce ziyarce gobe Zan koma nace Bari Nazo na Miki Sallama dafatan.sakona Yana Isa wajenki" "Eee Yana isa wajena Kam Ashe kwana bakwai.kayi a garin Nan Amma sai yau kazo ganina Kuma daka tashi zuwan sai.ka.taho Haka" "Yi hakuri Umma nayi laifi Abunda yasa banzo da komai ba Dama kudi nayi niyyar Baki shiyasa ban taho da komai ba" "Toh yayi.kyau Naseeru" Daga Haka Bata Kara cewa komai.ba ta ringa kudurta Abubuwa a ranta. Naseer kuwa banza ta bawa ajiyarsa sai daya gaji Dan kansa ya ciro kudi Mai Dan yawa ya Ajiye Mata a gefenta Yana "Umma bari na koma inaso naje gidan Tijjani akwai maganar da zamuyi gobe Zan koma insha Allahu" "Allah ya bada saa" Daga Haka Bata Kara cewa komai ba ya tashi ya tafi Safiyya dake labbe a d'akin kusa dasu ta fada d'akin tana "Mai na Gaya miki Umma wlh Naeema ta kwace Naseer yanzu ya fara samun kudi a madadin ya kawo Miki sai ya ringa kaiwa shegiyar Naeema da take da uban kudi Kinsan kuwa saude tacemin layi akeyi a gidan ta masu San wanan shegiyar Yar tata mai.kama da Aljanna Haka suke cicika ledoji suna kaiwa Gidan Mu kam muna Nan a wahalce kina siyar da kosai Cikin bakin ciki Hajara ta dau kudin da Naseer ya Bata tana "Hada da kudin Nan da kike tarawa kiga idan ya Kai kije gurin mutumin nan ya Mana aikin Nan nida Dana ta rabamu ta karfi da yaji zata Gane shayi ruwane Maza jeki duba min kudi Nan idan sun Kai gobe da sassafe ki tafi wajensa Cikin murna Safiyya ta jawo gwangwanin kudin da suke Tarawa ta fito da kudin ciki ta had'a taga kudin ya Isa ta hau murna Dak'yar tayi bacci sabida tsananin mugunta da asuba suka dau hanya.ita da Saude. Sai da aka Dade layi yazo kansu cikin mugunta Safiyya ta karkace ta hau gayawa boka bukatar ta akan Zahira 'Yar Naeema data tsone Mata Ido sau uku tana zuwa makarantar Dan kawai taga wayanda ke muammalla da zahiran Sai Kuma abin yazo a daidai makarantarsu Zahira daya da Yar Sauden. A gajiye Suka dawo gida suna dawowa Suka.samu hajara suka.hau Kora Mata jawabi Kamar Haka "Umma Kinga abinda ya bamu Kamar yanda na fada Miki ayi Mana Aiki Akan zahiran ta ringa sata Kamar b'era toh gashi ya bamu wanan yace mu samu zahiran ta Sha alewa ne Kato kamar suga yace ko kad'an ta diga a bakinta wlh b'era ma.bazai Kai ta sata ba kuma ko a Ina ta zauna sai tayi satar" Wani.irin dariya Suka kwashe dashi gabadaya Hajara tace "Haka nakeso Saude gashi nan ki bawa yarki Maimuna ta jawo zahira jiki ta Bata tunda kince ajinsu daya idan.ta kama.ne.ma ta siyi alewa da Sunan sadaka ta rabawa.yan ajin gabadaya yanda zahiran zata saki.jiki ta Sha" Jiki na rawa Saude.ta karba tana doki Dan ta tsani Zahira sabida yanda ta yagawa yarta ko ta Ina Haka.kuwa akayi tana zuwa gida ta siyo alawa Mai irin gidan alewar da zaa bawa Zahira ta bawa maimuna akan gobe ta rabawa Yan ajin wanan Kuma ta tabbata ta bawa Zahira ta Sha. Washegari kuwa Haka maimuna tabi Yan ajinsu da alewar.ta dau na maganin ta mik'awa Zahira Sai dai me duk yanda taso Zahira ta karbi alewar kin karba tayi tace ita Bata Shan alewa kashe Mata hakori yake Rai ba dadi ta taho gida da alewa a hanya ta Dan bude alewa taki yawunta ya tsinke ta gutsuri kad'an ta Sha Ta maida cikin ledar ta kaiwa Saude ta Gaya Mata yanda sukayi da zahiran Saude.kuwa cikin Jin Haushin ta karbi alewar taje gidansu Hajara ta Gaya musu Safiyya kuwa ta karba tana Kar ta damu wlh gobe sai ta danne Zahira ta Sha alewar Nan Hajara kuwa cewa take ta tabbata ta danne ta Dan bazata yi asarar kudinta a banza ba. Da mugun nufi Safiyya ta ajiye alewar tana Shan alwashin har aji zata je.ta danne Zahira ta saka mata alewar a Baki. Daddare ta fita Dan ta siyowa Bashir danta kamu ta Dama Masa tana dawowa taga ledar alewar a hannunsa Yana mumul mumul da Baki. . Cikin tashin hankali ta saki ihu ta nufi wajen Bashir din.......... *A DAINA BIYONI ANA MIN TAMBAYOYI AKAN LABARIN NAGA TA KAINA A DAINA KIRANA ANA MIN TAMBAYOYI AKAN LABARIN NA GA TA KAINA DUK MAI SO YA CIGABA DA BIBIYAN LABARIN A DAINA CEMIN DAGASKE NE KO BADA GASKE BANE SANAN DAN ALLAH DAN ANNABI A DAINA CEWA NACE ZAHIRA ZATAYI KARUWANCI NI NAFEESA BANCE HAKA BA BA KUMA A JI A BAKINA BA DUK WANDA YAKE GANIN BAZAI IYA CIGABA DA BI BA DAN ALLAH BAN MASA DOLE BA YA HAKURA NGD*[7/19, 9:30 AM] Zannura: *NAGA TA KAINA* *NA SADNAF*🌸🌸 ®️ *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_* _{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_ *Free Novel* *Page 49* Hajara kuwa data fara Dan gyangyadi ihun Safiyya ne yasa ta mik'e a firgice a daidai lokacin da Safiyya ta Isa wajen Bashir din ta kwace ledar hannunsa ganin babu alewar a ciki ta saki ihu Tana "Nashiga uku na lalace Bashir ya Sha alewar" Ta Danna hannunta a bakin Bashir din Dan ta ciro alewar da Sauri sai dai tana Danna hannunta sauran alewar ya wuce Bashir ya hadiye alewar hankali a tashi ta hau zurmaka hannunta gabadaya a bakinsa tana dukan bayansa Wai duk Dan yayi amai amma a banza Dan kakarin amai yayi kawai baiyi Aman ba hannu Safiyya ta Dora a ka tana "Umma kin cuceni Bashir ya Shanye alewar Sata Umma kina zaune anan fa Bashir ya d'auki. Alewar ya sha Baki Hana shi ba" "Ta Ina na ganshi nida bacci ya fara daukana ki kwantar da hankalinki ba abinda zai faru gobe da sassafe sai muje wajensa mu Gaya masa A ranar Safiyya ko kad'an batayi bacci ba hankalinta a balain tashe tana tsoron ta budi Ido taga dan data ci buri akansa ya Zama likita ko Dan siyasa ya zama barawo idan ta tuna yanda bokan yace Zahira zata ringa sata sai cikinta ya murd'a ta tafi bandaki Sosai taji Haushin Hajara tana ganin har da sakincinta yasa Bashir ya sha alewar Dan tana d'akin Bashir ya d'auki alewar. Gari Bai Gama wayewa ba ta Sabi Bashir a baya Hajara sanin halin Safiyya da azabar masifa yasa ta bita Dan ita Kuma Haka kawai take shak'ar Safiyya tana Kuma tsoronta. Sai da suka Dade kafin su samu ganin bokan Suna Shiga Safiyya ta kunto Bashir daga bayanta tana "ka taimaka min an samu matsala d'anna ne.ya Shanye alewar a taimakamin a rufamin asiri" "Garin ya ya Shanye alewar"? Cikin kuka Safiyya ta bashi labari shi kuwa bokan ya girgiza Kai Yana "Ba abinda zan iya Yi akai Dan ke kikace muyi aikin da duk abinda maman yarinya zatayi bazata iya karya shi ba hakane yasa Dana hada maganin na baki Akan ki zuba a cikin ruwa indai ya baje toh Mai karya asirin sai ya iya hado maganin daga cikin ruwan zai karye" Ihu Safiyya ta ringa zunduma wa.tana ya rufa Mata asiri zata bashi ko nawane Hajara itama ta hau rokonsa shi kuwa yace musu ba abinda zai iya Yi akai Amma suje zai nema idan ya samu zai Basu. A Haka suka dawo Safiyya na zunduma.kuka Bata tab'a kawowa Bashir ne zai Sha alewar ba Hajara kuwa sai rarrashinta take Safiyya na daka Mata tsawan Akan laifinta ne sakacinta ne yasa Bashir ya Sha alewar sai rashin kunya takewa Hajara tana neman zaginta Amma Hajara Bata ce Mata komai ba Ko baccin kirki Bata iya yi Sabida tashin hankali kasan zuciyarta kuwa wani balain tsanar Naeema da zahiran ne ya Kara rufeta tana Jin duk a sanadinsu danta ya Sha alewar Sata ya Zama Dole ta d'au fansa sai ta wahalar da Naeema ta wahalar da Zahira da Bata ji ba Bata gani ba matsawar danta ya tashi da sata abinda zata yiwa Zahira Allah kadai ne ya sani Hankali dai ba akwance ba kullum cikin Zullumi ta cigaba da fita aikatau da zumar samun wasu kudin ta Kara komawa wajen bokan Dan yanzu zuciyarta Kara taurara yayi wajen San ganin bayan Naeema data Mata Karen tsaye a idonta ma gani take Kamar Hajaran ta fara sanyi da batun Naeeman Sosai tayi mamaki da ganin Saude Bata Zo musu ba kwana biyu ganin an tafi Wajen wata Bata ganta ba yasa ta shirya bayan ta dawo daga aikatau ta nufi unguwarsu Naeema Wajen karfe Biyar na yamma ta nufi unguwar tana zuwa tun kafin ta Isa gidan Saude ta hango wani dalellen mota a k'ofar Gidan Naeema. Mai gidan da take wa aikatau Yana jingine a bakin mota Yana kad'a mukullin motarsa Wajen shagon Naeema kuwa cike da.mutane masu siyayya Wani irin bakin ciki ne ya cika kirjinta Ta jingina da bango tana tunanin Mai Alhajin Saad yake Yi a k'ofar Gidan Naeema ko shima siyayyan yazo shagon Naeema. Tana tsaye taga yaron daya aika cikin gidan ya fito wajen sa ko Mai ya Gaya masa oho ya Kara aika shi gidan. Sai gashi yaron ya dawo wajensa da Minal biye dashi Ji tayi inama.tana Jin Mai suke cewa Tana kallo Alhaji Saad din ya bud'e bayan motarsa ya fito da manyan ledoji ya mik'awa Minal ta ja da Baya tare da girgiza Masa Kai Ganin Taki karba yasa ya mik'awa almajirin ya bashi kyautar kudi tare da Shiga motarsa ya tafi Tsabar bakin ciki har wani dafe kirji Safiyya tayi tana tsaye Naeema ta fito.tana sanye da hijabi ta taso.almajirin da ledar daya Shiga gidan sai Masifa take Sam Safiyya ba jiyo abinda take fada take ba har ta gama ta Kira Isihu dake shagonta ta bashi ledar ta koma ciki. Safiyya zuciyrta cike da tunani ta Shiga gidan Saude Inda ta tarar da ba kowa a gidan. Ta fito daga gidan kenan taci Karo da Saude data shigo gidan itama a firgice hannunta rik'e Dana Maimuna data ci kuka ta gode Allah rigarta duk a yayyage Saude tana ganin Safiyya ta fashe da kuka tare da rike hannunta suka koma ciki Suka zauna akan tabarma. Safiyya kuwa ta bi maimuna da.kallo da.kayanta ya yayyage tana "Wai Saude lafiya kuwa yana ganku Haka Mai ya samu maimuna Haka"? "Safiyya Ashe alewar Nan da muka bawa Maimuna ta bawa Zahira sai data gutsara ta Sha a ciki bamu sani ba tunda ta Sha take jawomin magana sata ko ta Ina rabona da cikakken bacci wlh na manta Safiyya shiyasa ma bakya gani na koni Maimuna Bata kyalle ba duk abinda ta gani a gidnan dauka take idan kuwa ta fita waje sai dai azo a kirani ace gata can an Kamata tayi sata. Yanzu ma Haka wani babban shago taje ta yi sata kafin azo a gayamin shine aka Tara Mata jamaa aka fara dukanta aka yayyaga Mata Kaya har wajen Yan sanda suka Yi niyyar kaita sai danayi ta hadasu da Allah da annabi Safiyya Ina zaman zamana na Kai kaina Halaka na cuci kaina garin tsinannen.kwadayi irin na yarinya Nan taje ta gutsuri alewar Nan ta sha. Ihun da Safiyya ta saki tana Dora hannunta aka yasa Saude ta tsayar da maganar da take Safiyya ta hau birgima a kasa tana "Na Shiga uku Saude Bashir Nima ya Shanye duk alewar idan har maimuna gutsura kawai tayi take wanan Satan Ina ga Bashir daya shanye duka Na Shiga uku Saude na Shiga uku yanzu Haka Bashir zai ringa sata naje gurin bokan akan ya karya Mana asirin yace bazai iya ba sai dai ya duba" Kuka take sosai Ita kuwa Saude ajiyar zuciya ta sauke tana Jin Sanyi a zuciyarta da ba iya maimuna ce zata yi Satan ba har da Bashir Amma a fili kuwa kuka ta hau Yi tana sun Shiga uku yanzu ya zasuyi ahaka suka Gama jajjantawa juna suna tunanin neman kudi su nemi wani ya karya asirin Safiyya kuwa ta hau yiwa Saude tambayoyi akan Naeema Saudee kuwa ta hau Bata labarin yanda manyan masu kudi suke Neman Zahira masu nemanta har da Yan siyasa ta had'a da Gaya Mata taga Alhaji Saad ma Yana zuwa gidan shima Wai San Zahira yake Wani irin abune ya tokare zuciyar Safiyya Dan so tayi Zahira ta ringa sata tayi bakin jini a wajen Samari Amma tunda abin ya koma kansu ya zama Dole su sake wani shirin Akan Zahira Dan sai ta samu cikar burinta zata samu kwanciyar hankali ahaka suka Kara kudurta mugayen Abubuwa akan Zahira Saude ta raka Safiyya ta tafi Naeema Maneman Zahira tuni suka isheni da sintirin da suke min a k'ofar gida Zahira yanzu tana da shekara Sha shidda tana Kuma jss 3 Sam ban shirya ta kula wani saurayi ba Dan inada burin tayi karatu Mai zurfi ba ita kadai ba har sauran yarana Ina burin suyi karatu Mai zurfi tunda Ni bansamu wanan damar ba Amma ga mamakina ko secondary Zahira Bata Gama ba masu nemanta da Aure sun Sako mu a gaba suna Santa da aure akwai wani Alhaji Saad danaga yafi matsawa da zuwa har aikowa yake akan Yana Sallama da Naseer a ranar Dana fita. Dan na bashi hakuri Akan ba yanzu Zahira zatayi Aure ba Yana ganina ya tsugunna ya hau gaisheni Ni kuwa na bashi hakuri akan ba yanzu zaayi yiwa Zahira Aure ba yayi hakuri. Daga Haka na koma ciki sai dai ga mamakina Bai fasa cigaba da zuwa ba A ranar daya zo na karshe ya Bata min Rai Dan Yana aikowa nace ace Bata zance ya Kara aikowa na tura Minal Akan ta bashi hakuri sai dai suna dawowa Naga Almajirin daya fara aikowa da Niki Nikin Kaya Wai a bawa Zahira Ban Bari ma ya karasa shigowa ba na wafci hijabina na fita dan na Masa kashedi sai dai Ina fitowa Naga har ya tafi. Hakane Yasa na bawa Isihu Ledojin akan ya Ajiye duk ranar da Alhajin Nan ya dawo a bashi kayansa. Na koma ciki Ina Shan alwashin idan Naseer ya dawo ya zama Dole muyi shawara dashi Dan abinan ya isheni. Bayan tafiyar Naseer da wata biyu sai gashi ya sake dawowa da Niki Nikin Kaya na Kuma ji dadin yanda Naga ya fara samun kwanciya hankali Dan ba laifi ya samu alheri daga labarin daya bani Kamar dai wancan lokacin sai daya kwana biyu kafin yaje wajen Umma da Saude har ta isar mata da labarin zuwansa har da Karin gisihirin da sai da Hajara ta ji tazo wuya tsanar Naeema na cike Mata wuya. Duk da Naseer ya tafar Mata da abubuwa har da kudin. Sam hakan Bai faranta Mata ba burinta kawai taga bayan Naeema Saffiya kuwa abinda take so kenan ta hau zuga Hajaran har sai data rabata da kudin da Naseer ya Bata ta had'a Dana wajenta ta kwashi Saude Suka koma wajen boka suka hau Gaya musu abinda suke so ya musu cikin tsananin mugunta. Shi kuwa ya d'auko kwai guda biyu ya bawa Safiyya ya fada mata yanda zasuyi da Kwan a bayan Kwan kuwa sunayen Zahira ya rubuta kaca kaca Jiki na rawa suka koma gida Safiyya ta Adana Kwan ta hau neman Wanda zai Mata aikin batare da an samu wani matsala ba. Naseer kuwa Dana Masa maganar takuran da akewa Zahira cemin yayi kar na damu na Bari idan ta Yi placement sai a Mata transfer ta tafi boarding inyaso sai ta cigaba da ss dinta a wajen Dan shima.yana so yaga yaransa sunyi ilimi har ga Allah banasan yarana sumin nisa ballantana Wai su tafi boarding Amma ganin Naseer ya dage yasa na hakura Yaje makarantarsu ya musu bayanin idan sun Gama placement Yana so ayi Mata transfer zuwa makarantar boarding. A ganinsa a boarding ma anfi karatu. Tafiyarsa da kwana goma Ina cikin bacci nayi mumumann mafarki daya Sakani farkawa Bakina d'auke da sallati na kunna fitilar d'akin tare da haska yarana Naga duk bacci sukeyi cikin kwanciyar hankali Ajiyar zuciya na sauke na fito da zumar nayi alwala Dan Dama lokacin tashina yayi biyun dare har na Saba Dayake dare ne sosai buta na dauko daga bandakina Dan na Debi ruwa Dan na bandakina ya Kare. Sai dai maganganun danake ji kasa kasa yasa a bakin k'ofata yasa na tsaya cak gabana na fad'uwa. Muryar namiji da mace nake ji Hakan ya sa na nufi bakin kofar jikina na rawa Kasa kunnena nayi naji macen na "ka buga k'ofar tana bud'ewa ka jefa Kwan cikin gidan Shi Kuma Yana shi tsoro yake ji Idan aka kamashi fa Bansan lokacin Dana bud'e k'ofar ba matar ta dib'a a guje. Ni kuwa na rik'e Namijin Gam dake k'ok'arin guduwa saan Isihu ne ya ringa k'ok'arin kwacewa hannunsa d'auke da wani kwarya Cikin rawar jiki na kwace Kwaryar Ina rik'e da yaron da hannu daya....... *TOH SAI KUMA BAYAN SALLAH IDAN ALLAH YA KAIMU RAI DA LAFIYA* [7/26, 10:36 PM] Zannura: *NAGA TA KAINA* *NA SADNAF*🌸🌸 ®️ *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_* _{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_ *Free Novel* *Dafatan munyi sallah lafiya Allah ya maimaita mana Ina muku fatan alheri Nagode da so da.kauna* *Page 50* Sosai ya ringa k'ok'arin kwacewa na rikeshi Gam Dan burina na ajiye Kwaryar da Naga kwayaye biyu a ciki na tambayeshi wacce matar data saka shi wanan aikin har lokacin jikina rawa yake.ina Jan innalillahi wa Inna ilaihi rajiun Cizon daya kaiwa hannuna da balain k'arfi yasa na cika shi ba Kuma zafin cizon yasa na cikashin ba bana San Kwaryar hannuna ya Fadi Kwan ya fashe tunda daga maganar Dana ji matar nayi so take Ana bud'e gidan a jefo Kwan tsakar gidan ya fashe Da mugun gudu ya dib'a Dana sake shi Ni kuwa na tsaya kamar mutum mutumi nabishi da kallo har sai Dana Diana hangosa. Dak'yar naja k'afata na koma ciki adduoi da nake tayi ya Dan sama min nutswa Ajiye Kwaryar nayi na kulle gidan.na Kara d'aukar Kwaryar na nufi dakina jikina na rawa A Gefen gadona na zauna na Dora Kwaryar a cinyata bakina d'auke da Addu'a na dauko.kwan guda daya na hau jujuyawa Ina kallon jan rubutun da akayi a jikin Kwan da Sunan Zahira ko ta Ina Sallatin da nakeyi ne yasa Zahira ta bud'e Idonta Dan Bata da nauyin bacci Sam Hawaye kawai nake Ina cigaba da jujuya Kwan a hannuna bansa lokacin data ma taso ta iso gabana ba sai muryarta naji tana "Umma lafiya kike kuka Mai ya faru"? Dagowa nayi na kalli Zahira da nake ganin kamar Jiya jiya nan na haifeta duk da ta girma ta zama budurwa.hakan Bai saka na daina Mata kallan yarinya ba Amma Wai Zahiran makiyana ke San ganin bayanta Sai a lokacin na tuna kallon da Safiyya tayiwa Zahira daya saka gabana tsinke wa ta Kara da na jira Naga balain da zata jefomin sai a lokacin na fashe da kuka.mai karfi Dan na d'auka ba abinda zai biyo baya tunda an kwana biyu Ashe suna kan bakansu Kuka nake sosai Ina kallon Zahira da Abu kad'an ke sakata kuka itama tuni ta hau kukan tana cigaba da tambayta abinda ya faru nake kuka. Nikam na rasa Mai nayiwa Umma da Safiyya a rayuwata mai na musu da zafi Haka da zasu bar kaina su dawo Kan yata da Bata musu komai ba. Wane irin kiyayya ne wanan suke min da Bai tsaya iya kaina ba har da diyata da muka Haifa da Naseer daya kasance jinin Umma ban taba kwokwanto a Raina na Umma ce ta haifi Naseer ba Amma zuwa yanzu na fara kwokwanto Dan ba iya Ni Umma ta tsana ba har da Naseer tunda ba Ni kadai na haifi Zahira ba Allah ne kadai yasan Mai Suka so yiwa Zahira Allah ya karemu na fito har na samu kwace Kwaryar daga hannun yaron da suka turo. Sosai hankalina ya tashi a Daren. Sallah ma ba a nutse nayi ba zuciyata na cike fal da tunani da tsoro tunanina ya rarrabu gida biyu jefi jefi nake dagowa na kalli Zahira dake gefena itama sanye da hijabi tausayin yata na Kara Sakani zubar hawaye duk cikin yarana babu Mai sanyin halinta da tausayin iyaye idan na tuna abinda Zahira tamin a lokacin da nake d'auke da cikin waleeed da muke cikin tsananin talauci har kuka nake nayita Mata adduar samun nagartacen miji lokaci bamuda komai a gidan dak'yar na samo musu garin kwaki Suka Sha suka kwanta itama sai Dana tilasta Mata Tasha Dan dagewa tayi sai dai Nima na Sha Wanda Ni nasan ko Ni na Sha garin Nan ba Inda zai kaimin ni xan iya hakura tunda yarane duk da balain yunwar da nakeji da ke Sakani Jin jiri Da wuri suka kwanta Ni kuwa bacci yak'i zuwarmin sai.juye juye nake Ina Dan hawaye Dan yunwa nake ji ba kadan ba ga jikina dake balain rawa. Ashe duk halin da nake ciki Zahira na kallona magana ne.kawai batamin ba. Mik'ewa nayi Ina bin bango sabida rawar da jikina keyi na fita kitchen Dana San babu abinda Zan samu na sawa cikina bansan lokacin da Zahira ta fita ba sai motsin bud'e kofa naji daya sakani.fitowa daga Kitchen da Sauri nayi wajen. Ban hango.kowa ba hakane yasa na dawo d'akina da Sauri anan nagane Zahira ce ta fita waje Ciikin tashin hankali nayi waje. Ina dube dube Ina mamakin Ina Zahira ta fita daddare Nan Sunanta na hau Kira da k'arfi Zahira kuwa Ashe data fita gida gida ta ringa bi tana rokonsu abinci wasu kuwa har zaginta suke Akan me zata buga musu gida suna bacci Wasu Kuma Haka zasu zageta ahaka ta cigaba da bin gida gida har ta iso wani gidan data ganshi a bud'e Tana Shiga ta zub'e a kasa cikin kuka ta hau ce musu "Dan Allah ku taimaka Mana da abinci ummana yunwa takeji ta kasa bacci" Daga Mai gidan har matar gidan tausayin Zahira ne ya rufesu duk da basu Santa ba. Abincin da matar ta kawowa Mai gidan da shima Bai Dade da dawowa ba suna Dan tab'a hirane hakane yasa Bai ci abinci ba Magana ya yiwa matar Akan ta Nemo Leda ta juye mata abinci shi Kuma zai Sha shayi da bredi Matar mik'ewa tayi ta d'auko Leda ta juya tuwon dake da Dan yawa a bak'ar Leda ta juye miyar yauki shima a wani Leda ta hadasu a wani Leda ta mik'awa Zahira data mike da Sauri ta wafci ledar tana ta gode. Ta fita a guje cikin murna duk da tsoronta da karnuka Haka ta ringa tikar gudu tana murna samo min abinci Ni kuwa hankali a tashe na koma ciki na Sako hijabi na Dan na nemota sai dai jiri kawai ke d'ibana jikina na rawa kasa mik'ewa nayi Dana zub'e a tsakiyar dakina. Kamar Wasa naji shigowrta tare da rufe k'ofar Gidan. Kitchen naji ta shiga Ni kuwa na hau sauke ajiyar zuciya dawowa da tayi Shigowa tayi da kwanu a hannunta daya hannun nata Kuma ledar tuwon ne. Kamshin abinci yasa naji jikina ya Kara kwasar wani rawan Ina kallonta ta juye tuwon ta zuba Miya a wani kwanun shima ta kawo shi gabana tana "Umma gashi na samo Miki abinci kici Bari na d'ebo Miki ruwa ta Kara yin waje. Ni kuwa banyi wata wata ba na hau Danna tuwon a bakina Ina hawaye. Dan inaganin tsaf Zan sume da ban samu tuwon nan ba fada nayi niyyar Mata Amma Ashe abinci taje Nemo min Kafin ta kawo ruwan ma har na kusa cinye Rabin tuwon Sai da tuwon ya kusa karewa naji hankalina ya dawo jikina jikina ya bar rawa. Ruwan data ajiye a gabana na kafa kaina na Sha Koshin da nayi yasa nayi hamdala a madadin nayiwa Zahira fada sai na hau shi Mata albarka Ashe dai yunwa masifa ce Dan sai yanzu na dawo daidai Abinan da Zahira.tamin a matsayin ta na diyata Yana cikin Abubuwan da bana mantasu ahaka tana yarinya tasan tausayin iyaye inaga ta girma. Amma Wai Zahiran Kuma su Umma ke San ganin Bayan ta Mai ta musu da zafi Haka A dadafe na yi sallah asuba Na tashi yarana sukayi Zahira kuwa ce Mata nayi kaina ke ciwo badan ta yarda ba ta hakura ta daina min tambayoyi. Yanzu su suke min komai hakan yasa ban bar d'akina ba Suka had'a hannu Suka Gama aikin komai na gidan suka fara shigomin d'akin Akan sun shirya zasu tafi Kansu na dafa daya Bayan daya Kamar yanda na Saba na musu addua suka ringa yin waje sai Dana Zo kan Zahira nace "Zahira kiringa addua kinji Allah ya kareki daga sharrin mutum Dana Aljann kiringa karanta ayatul kursiyyu Kafa bakwai idan Zaki bar gidan Nan idan kin dawo ma ki karanta ki kasance a cikin addua kullum Allah ya kareki da karewarsa karkiyi Wasa da Addu'a kinji Zahira Allah ya Miki albarka ban taba nufar Dan kowa da sharri ba insha Allahu ba Abunda zai sameki ki tsaya kiyi alwala sai ki tafi" Kallona kawai take har na idda maganata amadadin tayi wajen sai ta tsugunna daidai k'afata tana "Umma ko dai wani abune zai sameni dazu da nake shara Naga kwai a cikin kwarya da sunayena" Girgiza Mata Kai nayi da Sauri tare da mik'ewa. Ina "ba Abunda zai sameki Zahira Kar ki Kara kallon Inda Kwaryar Nan yake Abbanku nake jira ya dawo maza jekiyi alwala ki tafi karku makara" Na nufi wajen Dana ajiye Kwaryar da shima yake d'auke da Jan rubutu da sunan Zahira na d'aga katakon gadona na saka a karkashin gadon Dan so nake idan Naseer ya dawo na nuna Masa Yaga shaida wlh bazan d'auki a tabamin Yara ba" Yanda nake Jin jikina ma kamar na Hana Zahira. Tafiya makaranta Dan sosai nake a tsorace gani nake zasu iya binta har makaranta su Mata wani Abu Amma ba yanda Zan hanata tunda Bai fi sati biyu su zanna jarrabawa Gama jnr secondary ba" Har waje na rakasu Bayan tayi alwala yanda take Abu jiki ba kwari yasa na kwantar Mata da hankali har na daina hangosu gabadaya zuciyata ba dadi Haka na dawo gida Ina kukan tashin hankali da nake ji a jikina Yana tunkaroni a da na dauka na samu kwanciyar hankali Ashe akwai wani masifar dake tunkaroni bansani ba Masifar da nakeji zuciyata bazata iya dauka ba idan har su Umma suka ci Galaba Akan Zahira ga irin abinda nake gayawa Naseer Nan da har yake Jin haushina. . A ranar kasa komai nayi zuciyata na wajen su Zahira abincin rana ma ban iya Yi ba karshe dai waje na fita Dan sosai naji na kasa samun kwanciyar hankali sai Dana hangosu hankalina ya kwanta na koma ciki na daura alwala azahar. Ina iddar da sallah na fito na Dora musu farar taliya Dan inada Miya Sai a lokacin na daure na saka Abu a bakina shima Dan Kar Zahira ta zargi wani Abun Dan nasan halin ta A takaice ahaka na ringa dari dari indai su Zahira suka tafi makaranta sai sun dawo hankalina ke kwanciya Bacci Kam bana Iya yin shi cikin nutsuwa Rabin Daren rayya shi nake Ina kaiwa Allah kukana haka ma nake tashin Zahira tayi duk da Bata iya jurewan tana Yi sai dai na juya naga tayi bacci Ban iya larabci ba da hausa nake adduoina Dan nasan ba yaren da Allah baya ji Yana jina Yana Kuma ganin duk abinda ke faruwa Dani Allah yasan zuciyata tayi rauni bana Jin Zan iya jure ganin wani Abu ya Samu yarana da nake ganin su kadai ne farinciki na a gidan Duniya a lahira kuma Allah ya bani Aljanna. Har wani irin Rama nayi Sabida tashin hankali Dan idan dare yyi Haka Zan ta sintiri daga d'akina zuwa kofar gida Wai ko zasu Kara aiko wani. Duk da ban Kara ganin kowa ba sabida dadewar da akayi hakan bai saka na saki jikina ba A ranar laraba da bazan manta ba na Kara sanin suwaye Umma Ina zaune a tsakar gida Ina tsince wanke da Zan Mana abinci dashi ba kowa a gidan Dan dukansu sun tafi makaranta Isihu ma ya tafi wajen Aunty matar Mallam zai Kai Mata sako Sai dai idan anzo siyan Abu na Shiga ta tsakar gida na bada abinda aka zo siyan. Sallama da naji da yazo daidai da bugun zuciyata yasa na Dago bakina d'auke da Addu'a na amsa Sallamar a daidai lokacin da Wata Saude da take makociyarmu ta shigo makociyata ce data takuramin da karbar kayana Bata bani kudi hakane yasa Dana gaji na daina Bata shima su Nadeeya ne suka cemin tana zuwa wani shagon siyan Abu da kudi shagona ne take aikowa karbar bashi ko a yanzu ma data shigo bazan iya tuna adadin kudina dake wajenta ba. Cikin sakin fuska na Mata iso dana ga fuskarta a sake tana sanye da dogon hijabi hannayenta a ciki. Tabarmar danake Kai na Kara bajewa Ina "Zauna Mana mmn maimuna" Cire takalminta tayi ta hau Kan tabarma ta zauna tana "mmn Zahira Ina wuni" "Lafiya Lau ya su maimuna"? "Suna Nan kalau" Tace tana cigaba da jujuya hannu a cikin hijabi Ni Kuma Haka kawai naji zuciyata na bugawa bansan dalili ba. Adduoi kawai nake a Zuciyata ita kuwa tayi shiru Bata ce komai ba Ni kuwa nace Mata lafiya Dan bata Saba shigomin ba balle nace shigowa tayi Dan mu gaisa Murmushi tayi tana lafiya Lau shigowa kawai nayi mu gaisa Ni kuwa da zuciyata ke cigaba da bugawa nace mata ta kyauta na mike na Shiga kitchen na debo Mata ruwa a Raina Kuma inata addua fad'uwar gaban da nakeji tunda ta shigo Ina Kuma mamakin dalilin zuwan nata da Sam ban ji na yarda da ita ba Agabanta na ajiye ruwan Ina "Bismillah ga ruwa" Girgiza min Kai tayi da Sauri tana ta koshi har lokacin hannunta na cikin hijabi tana Dan kalle kalle "Ke kadai ce kenan a gidan banji Motsin su Zahira ba"? Tace cikin murmushi Nima cikin murmushi nace Mata eee wlh Ni kadai ce. Sallama ake ta rafkawa ana San siyan Abu Amma fir naki tashi Dan Sam ban yarda da Matar Nan da ta shigo min ba ita kuwa cewa take na tashi Mana na sallami customers Dina Ni kuwa na girgixa mata Kai Ina "ba wani abin arzkik zasu siya ba abinda ma suke nema babu" Na karasa Ina karantar yanda tayi Jim Bata ji dadin magana ta ba Hakan kuwa yasa na Kara gasgata zargin ba alheri ne ya kawota gidana ba. Zama na gyara sosai Ita kuwa ta cigaba da kame kame tana surutun ta ita kadai Ni kuwa jinta kawai nake Ina mamakin abinda yasa ta saka hannayenta a hijabi Sanin Dana Mata ma ba ma'abociyar saka hijabi bace ban dai ce komai ba na cigaba da wayancewa kamar gyara waken nake Amma idona na kanta Muryata daya doki kunnena da "Mmn Zahira wlh fitsari ne ya matseni Ina bandaki nayi Dan Allah" Sosai naji kirjina ya tsananta Bugu jikina na kwasar rawa Sai Dana dau mintina kafin na iya nuna mata band'akin Tsakar gidan Mik'ewa tayi da Sauri har lokacin hannunta na cikin hijabi ni kuwa nace Mata "Ga buta Nan da ruwa a ciki babu ruwa a band'akin Wajen band'akin ta nufa da Sauri tana ta mutsu mutsu da hannu Kafin ta Ciro hannu daya ta sunkuya ta dauki butar a garin ta mik'e Naga wani irin dunkullellen laya ya Fad'o Yanda layyan ya Fado Haka naji Kamar kirjina xai Fado. Da Sauri ta tsugunna ta rufe layyar da hijabinta ta d'auka tana k'ok'arin Shiga band'akin Cikin zafin nama na taso kafin ta karasa band'akin na jawo doguwar hijabinta da karfi da har sai daya shake Mata wuya na Kara jawo hijabin har sai data zub'e a kasa Banyi wata wata ba na Kara shaketa da hijabin Dana cukwikuye burinta kawai ta cire hijabin Dana shaketa dashi Sabida matsar Dana Mata Azaba yasa ta saki layyar Bansan inada karfi ba sai a ranar saman kanta na hayye har lokacin Ina shake da ita na dau daya hannun nawa dake balain rawa bakina d'auke da Addu'a na Dago layyar da aka caccaka allurai a ciki ga sunayen Zahira Nan a zagaye da layyar. Ihun sallati na saka na saki layyar Cikin tashin hankali na Kara shaketa da hannu biyu cikin kuka na hau ce Mata "Mai na Miki mmn maimuna da kike San ganin bayana Ashe kece kike San ganin Bayan Zahira Basu Umma ba Mai na Miki da zafi Haka Mmn maimuna da kike San ganin Bayan Yata a iya sanina ban miki komai ba hasali alheri na Miki kika zalunce Ni Mai na Miki Haka Mmn maimuna Mai Zahira ta Miki"? Nace cikin kuka Ina Kara shaketa da k'arfi sai kakari take Ni kuwa na hau jibgarta Ina buga kanta da kasa rantsuwar da nake akan wlh sai ta gayamin Mai Zahira ta Mata yasa take San ganin bayanta da irin shakar Dana Mata yasa cikin azaba tace na saketa zata fadamin Ban cikata ba nace ta gayamin a Haka Ina jinta ko kuma wlh na dauko wuka yanzu nan na kasheta Dan sosai na ringa Jin Zan iya kasheta yanda nake Jin zuciyata daga makotaka Mai hadina da ita da zata nemi cutarmin da ya Ganin magana na Mata wuya yasa na sausauta rikon Dana Mata a wahalce tace "wlh bani bace Mmn Safiyya da Safiyya ne Suka Sakani wlh Allah ranan ma da muka zo k'ofar gidan nan har da Safiyya muka zo. Tiryan tiryan ta hau bani labarin komai batare da ta rage komai a ciki ba har alewar da suka so bawa Zahira na sata da Abu ya juye ya koma Kan Dan safiyya da Maimunan Sosai jikina ya dauki rawa na hau sallati........ [7/28, 10:58 PM] Zannura: *NAGA TA KAINA* *NA SADNAF*🌸🌸 ®️ *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_* _{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_ *Free Novel* *Page 51* Rawar da jikina keyi yasa na cikata na zub'e a kasa Ina juya Kai na danake ji kamar zai fado kirjina kuwa sama da kasa.kawai yake ita kuwa numfashin wahala kawai ta ringa saukewa tana "kiyi hakuri mmn Zahira Safiyya ce ta ringa zugani wlh a yau din ma kamar bazan zo ba taje har gida ta sakoni agaba Akan Nazo da kaina" "Da kin shiga da layyar band'akin Nan Ina Zaki saka layyar Kuma Mai zai biyo baya ki gayamin mmn maimuna"? Nace Ina tsareta da idona Dan Naga alamar tsorona take ji sosai har yanzu hannunta na rik'e da wuyanta Mutsu mutsu ta hau yi Ni kuwa Ina ganin Haka na mike na je na kulle k'ofar Gidan na dauko wani sharbaben wuka a d'akina na fito dashi daga gidansa tana ganin Haka ta gwallo Ido ni kuwa nace "Na rantse da Allah idan Baki gayamin ba sai na yanka ki mmn maimuna karki dauka bazan iya ba Dan tunda har a matsayinki na wacce itama take da Yara ta Haifa ta san zafin haihuwa xaa iya had'a Baki dake Dan kawai a cutar mun da 'ya toh Dan na kasheki wlh banyi asara ba Zan iya komai Akan yarana ki bude baki ki gayamin Mai zakiyi da layyar Nan da ace kin Shiga band'akin Nan asirinki Bai tonu ba" Na nufi wajenta na Kara jawo hijabin jikinta da k'arfi cikin azabar tsoro yanda na Dora wuk'ar a wuyanta ta hau min bayani. "Dama a ranar da muka zo gidanan da Kika bud'e kofar muka gudu nida Safiyya sabida karki Kama mu sosai muka ji takaicin da bamu idda nufinmu Akan ki ba Kika bud'e kofa a nesa da gidanki muka labe muna hango yanda kika rik'e almajirin da muka so Yana kwankwasa gidan kina bud'ewa ya jefa Kwan a tsakar gidan indai ya fashe toh yanda rubabben Kwan xai ringa wari Haka za a ringa toshe hanci Zahira na wari har ta Rasa Mai Aurenta Dan Safiyya tace Bata so Zahira ta samu miji Mai kudi ta aura har ki Huta Gudun da almajirin yayi da fad'a Mana da yayi kin kwace Kwan yasa Safiyya taji kamar ta haukace zaginki tayi tayi tana tsine Miki Akan Bata yarda.dake.ba kema akwai wajen bokan da kike xuwa yake Gaya miki duk abinda zai faru dake. Haka ta kwana a gidana ko bacci batayi ba muna Kara Shan alwashin komawa wajen bokan namu washegari kuwa da sassafe mukaje Muka Gaya masa duk abinda ya faru ya Kara cajar mu wani kudin. Dan dai ta Sakani a gaba ne banyi niyyar zuwa ba sabida banida kwanciyar hankali tunda maimuna ta Sha alewar Nan kullum cikin jawomin magana take. Ahaka taje.tayi buga buga bansan Inda ta samo kudi ba tazo ta sameni shekaranjiya na Rakata wajen bokan muka Kai Masa kudin shine ya d'auko layyar Nan ya bani yace ayi kokari a jefa a masan gidanan yanda Kashi keda wari Haka zata ringa Yi a wajen Samari Haka zatayi bakin jini Wanan Abu yasa hankalin Safiyya ya tashi Dan bamu San Mai zuwa gidanki har ya Shiga band'akin ki ba ahaka muka dawo gidana muna naziri a karshe tacemin Ni Zan Mata aikin Nan Zata bani Dubu daya Dayake Ina cikin bukata a Haka na karba ta bani kudin shine yau ta zo akan tana zaune a gidana tana jirana nazo na saka layyar a masai ai bakida wayo indai nace Miki inajin fitsari bazaki hanani shiga bandaki ba Nidai Dan Allah kiyi hakuri mmn Zahira sharrin shaidan ne nayi nadamar biyewa Safiyya" Ta karashe tana fashewa da kuka. Duk maganar da take min sama sama nakejinta sabida tashin hankali Dana shiga Ashe duk Inda nake tunanin su Umma sun Kai wajen mugunta ashe sun wuce nan" Wuk'ar hannuna na ajiye na cika mmn maimuna cikin rawar murya nace " Mmn maimuna akwai wani Abu Dana Miki da kike ganin na cancanci kiga bayana haka?idan nayiwa maimuna yarki Haka Zaki ji dadi ?mmn maimuna iya alewar da yarki ta Sha take sata Bai Isa yasa kigane Allah ke kareni da yarana daga sharrin su Safiyya ba iya sanina ba abinda na Miki Dana cancanci Haka daga wajenki mmn maimuna kudadena dake wajenki bazasu lissafu ba kema kinsani ban taba Miki Aiken ki bani kudina ba ban taba daga Miki hankali Akan ki bani kudina. Ba ban taba canza Miki fuska ba na daina Baki bashine sabida na lura bakyaso na karu dake ta gaban shagona yaranki zasu wuce wani shagon su siyi Abu da kudi Amma idan bashine sai ki taho wajena Dan Kuma na daina Baki bashin mmn maimuna sai kiga laifina ko kece inaga matakin Dana dauka Zaki dauka tunda kayan Nan ba kyauta nake samowa na zuba a shagona ba da kudi nake siyan kayan Nan mmn maimuna bayan hanaki bashi danake mmn maimuna akwai abinda na Miki Wanda bansani ba"? Girgiza min Kai tayi Tana "Kiyi hakuri mmn Zahira sharrin shaidan ne wlh ki yafe min" "Kiji tsoron Allah Mmn maimuna karki biyewa San zuciyarki kizo ki aikata abinda Zaki zo kina nadama daga baya ki fita daga abinda Bai shafeki ba Umma da Safiyya Allah yasan ba abinda na musu Suka tsaneni na rabu da Naseer ma basu kyalleni ba kiyayyar har ya tashi daga kaina ya koma Kan zahira da Bata ji ba Bata gani ba a iya sanina ba abinda Zahira ta musu kema Haka Amma tunda abinda kuka zab'a kenan. Mmn maimuna wlh station zamuje ayimin katangar karfe daku gabad'aya duk abinda ya sameni da yarana wlh kune" Ina fadar Haka na dauki layar da Addu'a a bakina na Shiga d'akina na daga gadona na dauko wanan Kwaryar na jefa layar a ciki na zura hijabina na dauki mukullin gidan nayi waje. Mmn maimuna a guje tayo wajena tana na rufa Mata asiri Kar na Kai su station ni kuwa hankadata nayi ta Fadi na fita tare da kulle gidan ta waje. Na dauki hanyar station Ina kuka Kamar karamar Yarinya Dan Nagaji da abinda su umma sukemin bansani ba ko matakin Nan da Zan d'auka shi zai saka na samu kwanciyar hankali gwara ayimin tsakani dasu tun kafin su shirya abinda yafi wanan tunda Ashe sau uku kenan suna gwada cutar min da 'ya Allah na Kare mu. Wanan shine karshen abinda zanyi da zai saka kila na samu Salama sai dai Naseer Yaji Haushin na Kai karar mahaifiyarsa da kanwarsa wajen yan sanda Da kafa na karasa station din da kyar na tsagaita kukan da nake na musu bayanin abinda ke tafe Dani Take kuwa wani daga cikin Yan sanda ya tambayeni Ina ita mmn maimuna take yanzu nace Masa tana gidana na kulleta Gyada min Kai yayi ya Kira wata Yar sanda da kallo daya zaka Mata gabanka ya Fadi sabida girmanta ga kib'a ga tsayi iya hannunta idan ta damke mutum dashi sai yaji a jikinsa ce Mata yayi su dau mota ita da wasu Yan Sandan guda biyu su bini gidana a d'auko mmn maimuna ta Kai su gidan su Safiyya a d'auko Safiyya da Umma daga Nan su taho station. Ni kuwa Ina Jin Haka nace Masa Ni ba wani Abu nace a musu ba katangar karfe kawai zaa Mana tsakaninmu a Kuma ja musu kunne na karashe da su taimakamin. Cemin yayi kar na damu na je Amma inza a d'auko uwar mijin nawa Kar na bisu na hau wani motar Nazo da Kwaryar da kuma Zahira yata da suke ta San ganin bayanta. A haka na hau motar Yan sanda nida mace Yar Sanda ta Bayan motar su Kuma mazan Suka hau gaban daya najar motar dayan nada ga gefe Ni na ringa nuna musu hanya har muka iso k'ofar gidana Inda na tarar da yarana a k'ofar gida duk sunyi Cirko cirko ciki kuwa mmn maimuna bubbuga k'ofar Gidan kawai take Tana su bud'e Mata ta tafi. Ina saukowa daga cikin motar yarana suka yo kaina a guje Ni kuwa Ban tsaya saurarsu ba na bud'e gidan Mace Yar Sandan na biye Dani a bayana Ina bud'e k'ofar mmn maimuna ta fara kokarin fitowa daga gidana Yar Sandar data gani a bayana yasa ta zub'e a kasa ta hau magiya Yar Sandar Nan kamar namiji Haka ta damko kafadar mmn maimuna ta jata cikin motar Tana ihun nayi hakuri Kar na Bari a tafi da ita. Dan Sandan dake zaune a daya B'arin ne ya daka Mata mumunan tsawa akan ta musu shiru ta Kai su gidan su Safiyya. Dayake tana da balain tsoro da hannu biyu ta rik'e bakinta ta shige baya ita da matar Dan sanda ya tadda motar ta hau kwatanta musu gidan dasu Umma ke zaune Ni kuwa Suna tafiya na Shiga ciki na d'auko Kwaryar Kwan da layar na saka a bakin Leda daga yanda na hade Rai yasa yarana Basu samu zarafin min tambayoyi ba Nadeeya na bawa umarnin kullemin gida kafin na dawo na rike hannun Zahira Dake sanye da uniform mukayi titi na tare Mana abin Hawa muka nufi station d'in Haka kawai Kuma naji jikina yayi sanyi sai nakejin kamar bai Dace na kawo Umma Kara ba Amma ya zanyi inaga hakan kawai shine mafita a gareni duk da a kasan zuciyata ma na yanke wani shawarar da nake tunanin insha Allahu shine zai kawo min karshen komai. Mun rigasu Isa station din haka yasa Muka zauna a benci nida Zahira Wanda ya dau statement Dina na dazu ya hau min tambayoyi Na cigaba da bashi amsa Yana mamakin Wai Zahira Dake karamar Yarinya ake San ganin Bayan ta haka Kwaryar Kwan da layyar kuwa daya karba a gefe ya Ajiye Yana jiran isowarsu ni kuwa na cigaba da rokonsa Kar ya musu komai kawai so nake ya Shiga tsakanina dasu na Kara jaddada Masa banasan ayi musu wani Abu sabida Umma uwar mijina ce Safiyya Kuma kanwar mijina. Baicemin komai ba ya cigaba da rubuce rubucensa Safiyya kuwa Jin Saude ta Dade Bata dawo ba yasa ta gudu daga gidan Saude Dan gani take kamar Naeema ta Kama Saude ne idan kuwa hakane gwara ta gudu A hanya kuwa kukan kudinta take Tana Kara tsinewa Naeema tana ce Mata Mayya sosai takejin itama akwai asirin da Naeema keyi shiyasa duk abinda suka Mata asirinsu ke tonuwa a kasan zuciyata kuwa tana adduar Allah yasa Saude ta jefa layar a masan ta matsu taga bayan Naeema ta matsu taga Naeema a cikin tashin hankali. Koda ta Isa gida ta bawa Hajara labari itama sosai taji Haushin yanda Naeema ke tsallake duk abinda suke Mata Hajara ta hau cewa ita tasan Naeema Dole akwai abinda ta taka da take tsallaka duk wani Abnda suka Mata yanzu iya kudaden da suka kashe ya Isa su siyi karamin fili tasan ma Asirin tayiwa Naseer take juya shi San ranta Safiyya na k'ok'arin Magana wata Mmn ayuba ta watso Bashir da baifi shekara biyu da watani waje tare da murd'e Masa kunne tana "Naga masifa da jarraba a gurin karamin yaron Nan kamar Danan yasan ya Shiga karkashin gado ya bud'emin tukunyar Miya ya hau tsamar.min nama Ke Safiyya wlh ki ringa rike danki duk Inda zakije Dan ya galabemu da kananan d'auke d'auke Yana mitsitsin shi dashi anya ma yaron Nan naki shi kadai ne kuwa ba wani Abu a jikin sa"? Ta karashe tana cika kunnen Bashir dake tsalla ihu. Safiyya kuwa wani abune ya tokare Mata wuya tama kasa mik'ewa sosai itama hankalinta ke tashe da yanda Bashir ke Shiga Dakunan Yan gidan yake musu d'auke dauke tun Bai girma bama abinda dai zai iya ci yake dauka Bai fara satar kudi ba tukunna har wajen wasu bokaye taje sabida su karya Mata asirin satar sai dai Kamar a banza sosai abubuwa ke cakude Mata a madadin tayiwa kanta fada aaa Sai take ganin kamar ma Naeema ce ta jefata a halin da take ciki a madadin tayi nadama cigaba da neman hanyar da zata ga Bayan Naeema take yanzu ma Allah ne yasan uban kudin da ta kashe wajen karbo layyar nan sai gashi babu Saude babu dalilinta tana zaune ne kawai a Nan Amma hankalinta na can burinta kawai taji Sallamar Saude Akan ta aiwatar Mata da aikin da ta Sakata. Mik'ewa tayi Dan ta dauko bashir dake ta kuka a bakin kofar mmn ayuba sauran mutanen gidan kuwa na ta kananan surutu Akan Bashir din ko kallonsu batayi ba Dan yanzu hankalinta baa jikin ta yake ba Shigowar mace Yar Sanda da excuse me ne yasa ta Dago tana kallonta kanta tsaye Yar Sandan cikin gurguraren hausa tace wacece Safiyya mmn Bashir da Hajara mmn Safiyya Da Sauri mutanen gidan da suka nutsu suka hau nuna Safiyya da ta daskare a tsaye tana kallon Yar Sandar data Kira sunanta kirjinta kuwa sai bugun Tara Tara yake Dan idan akwai abinda take tsoro a rayuwarta Bai wuce masu bakin kayan Nan da bindiga ba Kamar numfashinta zai d'auke a lokacin da Yar Sandar ta karaso gabanta ta damke hannunta tana Ina mamanki" Kinkina Safiyya ta hau Yi ta daka Mata mugun tsawan dayasa ta Nuno Hajara da tashi tsaye tana gyara daurin zanin jikinta sabida tashin hankali shigowar Yar Sanda. Da hannu daya ta rik'e Safiyya har suka karasa gaban Hajara Yar Sandar tace Musu su tafi station Ana nemansu Safiyya fusge hannunta tayi tana "Mai mukayi da zamuje station Anya mu kike nema kuwa ko dai b'atan Kai kikayi" Marin da Yar Sandar ta d'auke ta dashi daya d'auke jinta gabadaya ta barin kunnenta na hagu yasa tayi tsit Hajara kuwa Marin da Safiyya ta Sha yasa Bata tsaya gardama ba tayi gaba matar Kuma ta hau Jan Safiyya sukayi waje Basu Kara gingin magana ba suka hau motar Yan Sandan sai a lokacin Suka ga Saude data ci kuka idonta ya kad'a yayi jajjur Gaban Safiyya Dana Hajara sai daya balain fad'uwa tsoron Yar Sandar yasa ba Wanda ya iya magana a cikinsu duk da Safiyya nata yiwa Saude magana da Ido. Saude na dauke kanta Hajara da Safiyya sosai Suka rude hankalinsu ya tashi suna tunanin Mai ya faru Haka Saude ta d'auko musu Yan sanda ko dai Kamata Naeema tayi shine ta d'auko musu Yan sanda cikin wasu wasi Suka iso station din jiki na rawa suka sauko daga cikin motar Yan Sandan na daka musu tsawa suka Shiga ciki Suna shigowa muka had'a Ido da Umma da Safiyya da mamaki sosai ya bayyana a fuskarsu da ganina a zaune Akan benci nida Naeema. Take jikin Safiyya ya hau rawa Umma kuwa ta kasa hakuri ta nuna kanta tana "Naeema Ni Kika kawo wajen Yan sanda"? Wani mugun tsawa Wanda ya dau statement dina ya daka Mata tayi saurin rufe bakinta fuskarsa a balain had'e ya kalli wani daga cikinsu yace a saka su Umma a cell bama zai sauraresu ba sai Naseer mijina ya dawo" Ni kuwa Jin abinda yace yasa hankalina ya tashi Dan har ga Allah ba Dan a ci zarafinsu na kawo su ba kawai tsakani nakeso ayi Min dasu. Sai dai Dan Sandan ko kallona baiyi ba duk da uban magiyan da nakeyi Ina kallo aka tasa keyar Umma da Saude sukayi Bayan canter ita kuwa Safiyya sai da Yar Sandar Nan ta Kara Bata Mari biyu dayasa kanta juyawa. Ni kuwa na hau kuka Ina rokon Dan Sandan Dan har ga Allah ba abinda nasa yamin kenan ba nayi nadamar Kai kararsu Umma wajen Yan sanda Dan sai Dana gwammace na kwashi yarana na gudu na bar musu garin da abinda ya biyo baya. Dan Sandar kuwa cemin yayi bazai sakesu ba sai mijina yazo shi yayi mamakin Jin uwar mijina da kanwarsa ke yiwa Yar yarinya da Bata ji ba Bata gani ba irin wanan mugayen asiirn ganin inata magiya yasa yace na tafi gida gobe karfe Sha daya Na dawo zai min abinda nakeso din Amma sai fa sun kwana a yau. Inaji Ina gani badan Raina naso ba muka dawo da Zahira Gida a ranar ko baccin kirki banyi ba Dan sai nake ganin kamar kwanan da su Umma sukayi na bud'e musu wani k'ofar da zasu Kara nufana da mugunta ne nasan halinsu yanzu bakina zasu gani har ga Allah banji dadin abinda San Sandan Nan yamin ba idan Yana ganin ma taimakona yayi wlh bai taimakeni ba Dan nasan halinsu Umma Rashin nutsuwa zuciya yasa ranar ko sallah Daren banyi ba da asuba na tashi na hau aikin gidan Dan so nake naje station da wuri Dan hankalina gabadaya Yana can Su Nadeeya na Gama shiryawa suka tafi makaranta Zahira kuwa nace Mata ta shirya mu tafi station duk da lokacin dayace muzo baiyi ba Amma banida nutsuwa Sam gwara dai a fito dasu umman hankalina ya kwanta Ko abinci na kasa sakawa cikina. Yanda nake a hargitse yasa Zahira ta hadiye tambayoyinta mun fito kenan Ina k'ok'arin kulle gidan. Taxi ta Parker a k'ofar gidana Naseer ya fito daga taxin fuskarsa d'auke da faraaa yayi kyau har da kib'ar kwanciyar hankali Mai taxin kuwa booth ya bud'e ya hau firfito Masa da kayayyakinsa . Shi kuwa Naseer yanda yaga nayi zuru zuru yasa ya iso wajena da Sauri Yana "Lafiya kuwa Naeema ya naganki Haka Ina zaku Naga kuna kulle gida" Kuka na fashe dashi ban iya ce Masa komai ba Dan har ga Allah wandanan Abubuwan sun isheni na gaji da Naseer da Mahaifiyarsa Nagaji ma da komai Ni Hankali a tashe ya bud'e gidan Ya ja hannuna muka Shiga ciki ya umarnci Zahira data kwaso kayan ta kawo ciki Ya Jani har d'akina ya zaunar Dani akan gado shi Kuma ya duka wajen k'afata Yana cigaba da tambayata abinda ya faru Ban ce Masa komai ba nace Masa muje dai yagani da idonsa bazan iya Masa bayani da Baki ba Duk yanda yaso na Masa bayanin abinda ke faruwa k'i nayi. Hankali a tashe ya kulle gidan ya biyoni a baya shi da Zahira. Abin Hawa na tare Mana muka hau Bai Kara min tamabyaa ba har muka iso station din ganin ciki zamu Shiga yasa ya rik'e hannayena Yana "Naeema Dan Allah ki gayamin me ke faruwa mai mukeyi a police station na Shiga uku Ni Naseer" Ban kula shi ba na fusge hannuna na Shiga station din ya bi bayana shi da Zahira hankalinsa a tashe. A Kan benci Muka zauna Dan Wanda case Dina ke hannunsa Bai zo ba ance sai karfe goma zai iso. Naseer har tsawa ya ringa min akan Gaya masa abinda ke faruwa ban Gaya masa ba har sai da Dan sandan yazo Yana shigowa ya kallemu Yana "wanan ne mijin naki"? Gyada masa.kai nayi Ya karewa Naseer kallo ya shige wani office shigarsa ba jimawa wani Dan sanda yace mu Shiga ciki Naseer Haka ya bini office din Dan sanda. Muna Shiga Dan Sandan ya umarcemu mu zauna gaban teburinsa Kuma Kwaryar da kwai da layyar ke ciki ne a gabansa. Muna Zama aka shigo da Umma dasu Safiyya da sukayi zuru zuru Safiyya kuwa jikinta duk ya kumbure Dan ta Sha bak'ar duka a wajen wanan mace Yar Sandar . Saude kuwa tayi wani irin laushi Kamar Mara lafiya Umma ce dai naganta fes muna hada Ido da ita ta min wani mugun kallon daya tsinkemin zuciya Zahira kuwa ta Kara matsawa kusa Dani Kamar zata shiga jikina Naseer kuwa hankali a balain tashe ya mik'e tsaye Yana "Umma" Umma ko kallonsa batayi ba ta zauna a kasa kamar yanda su Safiyya Suka zub'e a kasa sai wani irin vibrating take Naseer kuwa hankali a tashe ya fara k'ok'arin nufar wajensu Umma Dan sanda yace ya koma ya zauna ba Dan Ransa naso ba ya zauna hankalinsa a balain tashe. Dan sanda Kwaryar ya nunawa Naseer Yana ya iso ya gani da idonsa Naseer kuwa ya nufi wajensa ya dau Kwaryar ya sunkuya ya hau ganin rubutun da akayi da Sunan Zahira Sam bai gane Mai hakan ke nufi ba Hakane yasa ya daga kansa ya kalli Dan Sandan ya dawo da kallon sa kaina Ni kuwa na dauke kaina Dan duk na bawa Dan Sandan labarin komai Dan Sandan kuwa cewa yayi Saude duk ta bashi labarin abinda sukayi da bakinsu kafin yasa a canja Mata kamani Dan taurin Kai ma Safiyya ta gwada musu Taki magana hakane yasa ta Sha mugun duka Yak'i Bari a daki umman ne sabida yanda Naeema ta daga hankalinta Kuma Yana ganin umman babba ce duk da akwai masu laifiin da Suka fita shekaru suke Kuma musu hukunci Jiki na rawa Saude ta hau bada labarin duk abinda Suka so yiwa Zahira Bata rage komai ba ta tonawa Umma da Safiyya asiri har asirin satar da suka so yiwa Zahira Allah ya mayar musu Kan kayansu Tana bada labarin Ina kuka Naseer dake tsaye sai gashi jikinsa na balain rawa har kafafunsa Suka gaza daukarsa ya zub'e a kasan Yana kallon Umma da Safiyya da suka sunkuyar da Kai Saude kuwa sai bada hakuri take tana a yafe Mata sharrin shaidan ne Zahira kuwa kukanta ne ya cika office din dan duk ta fahimci Abunda ke faruwa. Dan Sandan kuwa ya kalli Umma Yana "Mai jikarki ta Miki Haka har kike San ganin bayanta" "Babu komai" "Ke Kika haifi babnta kuwa ko tsintarsa kikayi ki gayamin gaskiya"? "Ni na haifesa ba tsintarsa nayi ba" "Amma ke kika haifeshi kike San ganin bayan yarsa data kasance jikarki Mai yayi zafi Haka ko wani Abu mahaifiyarta ta Miki shiyasa kike San ganin bayan yarta" "Ba abinda tamin yallabai sharrin shaidan ne ayi hakuri" "Ke Kuma uban me ta Miki kike kulla irin wanan makircin"? Murya a dashe Safiyya tace itama ba Komai ta hau bada hakuri Kamar yanda Umma ta bada hakuri. Naseer kuwa shima tunda ya sunkuya da kansa Bai Kara dagowa ba A takaice Dan Sandan kuwa ya jawa su Umma kunne sosai ya ce musu ko tari nayi Dani da Zahira ba Kuma iya Zahira ba har yarana gabadaya wlh sai sun Kama su Kuma an kullesu na har abada Duk da Basu iya rubutu ba sai da aka d'auko takarda Suka saka hannu Akan sun yarda ba abinda zasu Kara min na sharri indai kuwa anyi sune Ahaka aka Sallame mu gabadaya muna fitowa Saude ta dib'a a guje Umma kuwa da Safiyya wani azababen kallo Mai dauke da mugun tsana sukamin nida Zahira Suka dau hanya Naseer kuwa a ba yanda zaiyi yabi bayansu Amma ko kallon Inda yake basuyi ba Ni kuwa hannun Zahira Naja muka hau taxi muka koma gida. Duk da anmin tsakani dasu banji hankalina ya kwanta ba hakane yasa muna isa gida na bazama neman dilallai Dan wlh siyar da gidana zanyi da komai nawa na bar unguwar in ta kama ma na koma garinmu dan bazan iya ba. Naseeer kuwa har gidan yabi su Hajara Suna Shiga gidan. Safiyya ta d'auko danta daga wajen mmn ayuba data taimaka ta rikeshi Hajara kuwa a tsakiyar d'akinsu ta tsaya ta kalli Naseer cikin tsananin bacin rai tana "har ni Naeema zata Kai wajen Yan sanda ta kulle mu wani irin girgiza Kai Tayi" Naseer kuwa dake Jin yazo har wuya ya hau zabga masifa Yana ......... Karku manta nace Zan na tsallaken kwana daya *Comment* Haka aka taba yimun 😭niy yarana duka akasa sunansu su 7 aka hada da likafani da sanduna guda bakwai da duwatsu da turare irin na aikin junnu,akaje aka saka wani wuri ,wai yanda akayi dinnan haka yarana zasu zama kamar gawa bazasu taba tsinana ma Kansu komiba a rayuwa,shikuma duwatsun zai zama yadanne zukatansu bazasu taba tunanin nema ma Kansu maganiba,kuma ko annema anbasu bazasu iya amfani dashi ba ,ke mugun abudai😭kawai Allah yanuna mun a barci da kuma yarona guda daya shima Allah yanuna masa da asuba kuwa yazo yake fadamun,nayi mamakin yanda mukaga Abu daya duka lokaci daya,wallahi danayi magana kuwa saiga Abu ya bayyana shine akaje aka dauko abun shinefa akaga wadannan abubuwan Dana lissafa da sunayen yaran nawa duka aciki,aka fada mana kuma abunda akayi asirin yasamesun,Allah yakare ya nuna mana😭 *Advertisement* Yan uwana yan kasar Niger,chad,camaroon,ghana dama ko ina afadin duniya masu son siyan kaya a nigeria harda ma yan cikin nigeriar amma suna tunanin ta yadda zasu rika siyan kaya cikin aminci to ga dama ta samu cikin sauki da rangwame zaku samu kaya kamarsu kayan kitchen,atamfofi,shaddoji,laces,jakunkuna da takalma toga dama ta samu kawai ku tuntubi Oum_Aabid Herbals and more 08178586888 Whatsapp group https://chat.whatsapp.com/CRsFCyoGq3i628AujmbxvV domin samun kaya cikin sauki da rangwame. Masu fama da ciwon sanyi kunyi magani harkun gaji to kuma ga dama ta samu ku tuntubeta zaku samu magani sadidan insha Allah 08178586888 [7/31, 7:55 AM] Zannura: *NAGA TA KAINA* *NA SADNAF*🌸🌸 ®️ *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_* _{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_ *Free Novel* *Page 52* "Mai na Miki Umma Mai na Miki a rayuwata kike San ganin bayana Umma wlh ba Naeema Kika tsana ba Ni Kika tsana Umma na rasa Kuma laifin Mai na Miki yanzu Umma Zahira yata kikesan ki watsawa rayuwa? Yanzu Zahira kike yiwa asirin Sata kike mata asirin wari Dan kawai Kar ta samu Wanda zai Aureta Umma Zahira yata ce fa innalillahi wa Inna ilaihi rajiun Umma tsanar da kikamin har ya Kai Haka Umma bayan kin watsa min rayuwa umma iya Haka Bai isheki ba sai kin taba min yata da bata Miki komai ba? Umma Anya kina tsoron Allah kuwa?Anya da Zuciya a kirjinki kuwa Umma tunda nake bantaba Jin uwar data ke azabtar da danta ba irinki ban taba ganin uwar da Bata da burin daya wuce taga bayan danta ba irinki duk burina na faranta Miki na miki biyayya har gidana Dana mallaka Kika siyar har gobe kece silar jefani a halin da nake ciki har yanzu ko bulo yanzu banidashi balle gida Amma iya Haka Bai isheki ba Umma har sai kin tab'a diyata toh insha Allahu idan Ina rayye ba abinda zai Samu yayana Naeema Kuma tamin daidai data Kai kararku wajen hukuma daga Rana irin ta yau duk abinda ya samu yarana wlh Umma kece Kuma ko ta kai kararku wlh Ni Zan Mata shaida" "Baka burgeni ba da tundazu banji ka d'aukeni da Mari ba Naseeru Ni nasan ba a hayyacinka kake ba Naeema ta Dade da asiriceka Dan da a hayyacinka kake mataki zaka dauka akan tsinananiyar yarinya Nan Naeema Ina mahaifiyarka tasa a kullemu har mu kwana" Naseer bakinciki ne yasa Bai iya ce Mata komai ba ya fito daga d'akin a fusace Safiyya dake labe San Bata San fitowa zaiyi ba kafin tayi k'ok'arin b'uya har ya Kai Mata wani irin cafka ya hau kwallo da ita. Dak'yar aka kwace ta a ahnnunsa bayan Hajara ta fito aguje tana zaginsa bakinta daya Saba da tsinuwa na tsine Masa Haka ta ringa Shan alwashin ganin bayan Naeema ko da zata mutu Naseer kuwa Haka ya fito Ransa a tsananin b'ace ya tari abin Hawa ya nufi gidan Naeema. A lokacin daya Isa Bai samu Naeema ba sai su Zahira. Shima Bai tambayesu ina taje. Ba ya Shiga d'akinta Agaban mudubi Yaga an ajiye Kwaryar Hakane yasa ya Shiga bandaki ya d'aura alwala ya fito ya dauki Kwaryar Yayi waje sai dayaje nesa da gidan ya fasa Kwan ya Kuma binne layar ya dawo gidan A daidai lokacin da Naeema itama ta dawo. Daga shi har Naeema ba Wanda yayiwa wani magana Dan Naeema ma wani irin hade Rai tayi hakane yasa Bai samu zarafin Yi Mata magana ba. Sai daddare da Yara sukayi bacci ya hau Bata hakuri Bata ce Masa komai ba Dan tasan ba abinda hakurinsa zai Mata ita dai yanzu mataki kawai zata dauka bazata tsaya mahaifiyarsa ta salwantar Mata da rayuwa ya ba Kwana biyu a tsakani akayi ta zuwa ganin gidan Wanda Sam Naseer Bai Gane zuwan da ake ba har sai da ciniki ya kankama Naeema ke Gaya masa matakin data dauka na siyar da gidan Dan ta bar unguwar. Naseer sosai yaji zuciyarsa ta sosu da hukunci da ta yanke batare da ta shawarce shi ba sosai yaga Dan tana takamar gidanta ne hakane yasa tayi Masa Haka Amma kasan zuciyarsa Kuma sai yake ganin Dan tsira da lafiyar yayansu yasa kila takeso su bar unguwar shima kansa hakan yaso yayi dan so yake ko haya ne ya Kama musu acan Abuja su koma can da Zama inyaso ko aike ne ya ringa yiwa Hajara Amma tunda ma Naeema ta Riga da ta yanke siyar da gidan shikenan Dashi akayi cinikin gidan da ba laifi an siye shi da daraja da saka hannun Naeema aka siyar da gidan Masu siyen Kuma suka bada kudi tare da notice din wata guda. Kayan shagon Kuma tayi niyyar siyarwa wani Mai shago dake can bakin titi da har Naeema ta Masa magana. Da injin markadenta kawai zata tafi Sai da Naseer ya tambayeta Inda take so su koma ta ce Masa garinsu zasu koma gabadyaa yanda su Hajara ma bazasu San Inda suke ba sosai Naeema ta shirya Yana Mata gardama tace ya Bata takarda sakinta Dan har ga Allah ta gaji sosai Naseer kuwa take takenta ya gani ya hau lallaminta akan ba sai ta Kai ga barin Kano ba ta nemi wani unguwar ko Dan makaranta yaran nasu Dak'yar da sidin goshi ya shawo Kan Naeema Dan tuburewa tayi bazata zauna a kano ba duk Abubuwan dake ciciyar ta a zuciya ta hau amayar dashi har da cewa ita dai ta gaji da aurensa indai wani Abu ya Samu yaranta bazata yafe ba Naseer Haka ya Shanye duk maganganun data ringa kwaba Masa har ya samu kanta Abinka da tsakanin Mata da miji tuni dai ya shawo kanta ya kwantar Mata da hankali Inda ya Kuma Bata shawarar Inda ya kamata ta samo.karamin gidan unguwa ne nesa sosai da Inda su Hajara suke. Hakane yasa Naeema ta sakar wa Naseer ragamar komai Inda ya nemo.mata karamin gidan Kamar dai wancan data siyar sai dai wanan Din ya Dan fi girma kawai matsalar ba shago a gaban gidan Sai da Naeema taje taga gidan taga komai yayi suka biya kudin gidann Cikin sati biyu suka dawo kawo dake unguwar hotoro Bayan anyiwa su Nadeeya transfer zuwa wani makarantar Zahira kuwa boarding Naseer ya dage zata tafi a fadarsa. Hakane kawai zai saka masu sintirin zuwa nemanta su daga kafa Zahira Kuma zata maida hankali tayi karatu sosai tunda yanzu zata tafi ss1 Nadeeya Kuma ta tafi jss.2 Dayake da Yan canji a hannun Naseer shi yayi cuku cukun sabon makarantar dasu Nadeeya suka koma dake unguwar da suka koma. Zahira kuma.aka hau Mata siyayyan boarding Dan itama an Mata komai.ta fanin registration. Har ga Allah ba a San Raina Zahira zata tafi boarding ba Dan dai Naseer yamin fin k'arfi ne kawai a matsayinsa na Mahaifin zahiran a rayuwata banasan abinda zai nesanta Ni da yarana nafiso ko yaya ne na ringa ganinsu a gabana har ya fara shirye shiryen Kai ta jikina a sanyaye yake ita kuwa zahira murna take sosai tana doki data ga yanda babanta ke mata siyyaya Nidai addua kawai nake akan Allah ya karemin ita Dan har yanzu gani nake su Umma zasu iya jefo min wani masifar amma.ina gayawa sarkin sarakuna duk gudun da zanyi nasan sai dai idan Umma basu so cutar damu ba kasan zuciyata Kuma sai nake ganin zuwan Zahira boarding zai.nisanta ta daga sharrinsu umman. Hakane yasa na kwantar da hankalina nayiwa zahira komai na jawota jikina na Bata shawarwari yanda zata kame.kanta da dagiya da addua A Haka nida Naseer muka Kai Zahira makaranta yata ta rungumeni muna kukan rabuwa dak'yar Naseer yaja hannuna Muka tafi Kamar Mara lafiya dai na dawo sai Dana fi sati kafin na fara Dan sabawa da rashin zahiran A Haka na maida hankali na fara tunanin Sana'ar da Zan Kama Kuma bayan.markaden Dan da alama unguwar akwai.masu markade.da.yawa ba shago a k'ofar Gidan ballantana nace Zan zuba provision kamar wancan unguwar da muka baro A Haka dai na yanke siyar da Zobo kafin na samu babba Sana'ar da zan ringa yi tunda kudin Sana'ar tawa suna ajiye Ba laifi kuma Ina Dan cinikin zobon Naseer wata biyu ya min ya koma Abujan. Ni kuwa na cigaba da kula da yarana sau biyu Ina zuwa ganin Zahira ba laifi hankalina ya kwanta da yanda naganta kawarta ma da kusan dabiarsu daya sunanta jameela sosai na yaba da hankalinta hakane yasa na Kara samun kwanciyar hankali. A Haka rayuwar ta ringa tafar Mana ban taba sakin jikina ba kullum cikin addua nake Dan nasan duk da anyiwa su Umma gargadi nasan halin su kila idan sun ga an kwana biyu zasu iya waiwayomu da sharri kullum cikin sadaka nake Dan nasan sadaka maganin masifa ce A Haka su Zahira sukayi first term dinsu a ss1 sukayi hutu suka dawo Fes Zahira ta Kara Yi kyaunta ya Kara fitowa tabarkallah Masha Allah Dan acan ma Mallamai santa sukeyi. Hakane yasa na yanke a Raina indai ta Gama din mu aurar da ita kawai inyaso ta cigaba a gidan mijinta Naseer shima a daidai lokacin da sukayi hutu ya dawo Cikin farincikin kudin daya samo inda yake cemin fili xai siya da kudin sosai na Taya shi murna Dan Kamar Wanda Bai taba gidan kansa ba yake murna da filin da yake San siya Gaba da gidana wajen bakin titi ya siyi katon filin a ranar ko baccin kirki baiyi ba sabida murna. Ahaka ya Mana sati biyu ya koma.batare da waiwaiyar umma ba A Haka aka Gama hutu Zahira na rakata makaranta Sati.uku da komawarta na fara mugayen mafarkai akan Zahira Daya dagamin hankali na hau sadaka Ina Addua Haka kawai naji Kamar wani Abu ne zai sameta daga yanayin danake.ganinta a mafarkina hakane yasa naji Sam na kasa samun kwanciya hankali na fara shirin zuwa dubo ta a ranar Dana shirya da sassafe Dan na dubota a ranar da bazan taba mantawa ba a rayuwata Mallamai biyu ne maza da mallama Mace daya sai kawar Zahira jameela da wata da suka ruk'o zahira Kamar matacciya suka shigomin da ita Suka shimfida min ita a tsakiyar gidana. Juyawar da kaina keyi da kirjina da nakeji kamar zuciyata ce zata fito yasa na kasa motsi na daskare a tsaye Kwantar da Zahira da akayi yasa na rik'e zuciyata tare da kallon zahiran. Abinda na gani ne yasa jiri d'ibana na zub'e a gefen zahiran....... Kuyimin.hakuri abubuwa ne Suka Sha kaina sai Sunday Zan dawo daidai ayi maneji pls. A next episode insha Allahu Zan k'ok'arin Yi dayawa Dan muyi mu Gama ngd [8/1, 5:30 PM] Zannura: *NAGA TA KAINA* *NA SADNAF*🌸🌸 ®️ *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_* _{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_ *Free Novel* *Page 53* Na saki ihu tare da dagota Ina "Mai ya samu 'yata Haka Mai ya sameta waye ya kwakulo Mata idonta waje Haka Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun" (Nafeesa sai dai na takaita Miki wuyan da Zahira ta Sha a cikin irin kaddarar data budemin daga auren Naseer wahalar da Zahira ta Sha yafi komai bani wuya tunda Nima sai Dana Zama tamkar tab'abb'iya wuyan data Sha shima labarine Mai zaman kansa sai dai na takaita Amma kyakyawan zuciya irin nata cewa take ta yafe musu abinda Suka Mata ko yanzu da Zan baki labarin wuyan da yata ta Sha ni kadai nasan Mai nakeji a Zuciyata ko nida Zahira mun yafe Sai Allah ya Mana sakayya" Ta fashe da kuka labarin da baa bani ba kenan a ranar sai washegari) Badan nasan Zahira 'yata bace bazan yarda ita Suka kawomin ba Dan gabadaya hallitar Zahira ta canja cikin sati uku kawai da Zahira tayi da komawa makaranta ta dawo kamar kwarangwal idonta ya firfito waje gabadaya wuyanta kuwa ya wani irin kumburo waje kallo daya zaka Mata ka d'auke idonka daga kanta sabida Dole ka tsorata da yanda ta dawo Ihun dana cigaba da yi Ina tattab'a zahiran da ba magana takemin ba illa manyan idon da kamar Kara Mata su akayi kawai take kallona hawaye na zararo mata Wuyanta daya kumburo kuwa sai motsi yake kamar ta hadiyi wani Abu kanta da jikinta kuwa har wani hucci yake sabida tsananin zafi Cikin azabar kuka yata rungume dani a kirjina na kalli mallaman da suka kawomin ita Ina "Ku min bayani Mai ya samu 'yata ta dawo Haka Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun na Shiga uku na lalace jameela Mai ya samu kawarki Haka ki gayamin jameela"? Nace Ina Kara tab'a wuyan Zahira daya ke numfashi shi kadai Zahira kuwa har lokacin Bata cemin A ba sai kallona take da idonta tana zubar hawaye Daya mallamin ne yayi karfin halin magana Dan dukansu kuka sukeyi jikinsu a sanyaye suna kallon Zahira da Bata da bambanci da mataciya sai numfashi kawai da takeyi "Washegarin da suka koma hutu daddare wajen karfe Tara Zahira ta tafi bandaki ita da jameela Wai zasuyi fitsari Jameela ce ta fara Shiga ta fito kafin Zahira ta Shiga Zahira na Shiga ba dadewa sai ihunta jameela taji da ba iya jameelan ce taji ihun zahiran ba har b'angaren Mallamai munji wanan ihun hakane yasa duk muka bazama mukayi b'angaren daliban sai dai muna zuwa muka ganta shame shame a kwance tana wani irin jijjiga hakane yasa mukayi tunanin ko Aljannu ne suka shafeta a band'akin. Da addua muka fito da ita daga band'akin hankalinmu a balain tashe mun Saba ganin cases na dalibai masu Aljannu sai dai na zahiran sai ya bamu tsoro Dan bayan mun fito da ita daga band'akin wani irin zafi jikinta ya d'auka Kamar garwashin wuta idonta ya Zama kamar jini jikinta kuwa Banda rawa ba abinda keyi Mallamin Dake karantar dasu ta fanin islamiyya muka Kira Dan indai case ya taso irin Haka shi yake yiwa dalibai rukiyya sai dai duk Inda ya Kai da rukiyya ba alamar sauki kwana mukayi a kanta sai gabanin asuba Muka ga ta daina girgiza ta rufe idonta. Duk dauka mukayi bacci ne ya d'auketa hakane yasa muka Yi hayaki a office din da muka kwantar da ita Yan aji uku wajen su shidda.muka saka su karatun Qurani a fili tunda duk sun sauke Dan duk mun yarda gamo tayi a band'akin Wajen karfe Tara na safe ta kwalla wani irin ihun daya saka mu toshe kunnuwan mu Dan Kamar ba Dan Adam ne ya saki wanan karar ba fusge fusge ta hau Yi zata fita a guje muka riketa Gam sai dai abinda ya tsorata mu Bai wuce hallitar ta da muka ga Yana canjawa ba idonta kuwa kamar sunyo waje wuyanta ma ya kumbure duk da Bata da jiki sai Muka ga Kamar Naman jikinta ramewa yake kasusuwanta na fitowa na hallitar jikinta har d'auke hannunmu mukeyi sabida azabar zafin da jikinta ya d'auka kanta kuwa kamar baa Jikinta ba sabida zafi Hankalinmu tuni ya tashi.mukayi asibiti da ita sai da tayi sati biyu a asibiti Ana Bata taimakon gaggawa Amma a amadadin taji sauki.ma sai azaba take Sha hallitarta na Kara canjawa likita da kansa yace mu nemi na gida larurarta bana asibiti bane muna tsoron dawo Miki da ita Haka hakane yasa muka nemi mallami a can shima yayi iya kokarinsa Muka ganin Abun kamar Kara girmama yake Kar tazo ta mutu a hannunmu batare da kunsan halin da take ciki ba yasa muka yanke dawo da ita Dan tabbas abinda ke damunta bana asibiti bane kamar dai jinnu ne. Girgiza kaina kawai nake Ina rungume da Zahira da zafin jikinta ke Kona min jiki cikin ihun kuka na Dago da yata da ta tashi daga siffar mutane ta zama wani hallita daban Ina "Mai na muku Haka Umma Mai Zahira ta muku Umma Dan Allah kuyi hakuri da laifin Dana muku ku kyallemin yata Bata muku komai ba Umma Ni na muku laifi na tuba Umma ku cikamin yata da Bata ji ba Bata gani ba Umma Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun Naseeru Zo kaga yanda Zahira ta dawo Naseeru kana Ina kazo ka kawomin agaji.kar Yata ta mutu" Kuka nake sosai Ina surutai mallaman kuwa sai Baki suke bani jameela kawarta da mallamar su mace da daya yarinya sai kuka suke suma Horn din da ake musu a waje sabida da motar makaranta aka kawo su. Yasa Suka hau min Sallama suna ajiyemin kudi Jameela kawar Zahira kuwa data ci uban kuka ta rik'e hannun Zahira daya Zama tamkar Kara tana "Allah ya Baki lafiya zahira idan mukayi hutu Zan Zo na duba ki ya Allah ka kawowa zahira Agaji ka Bata lafiya" ( Wlh Allah indai Zan tuna labarin wuyan da baiwar Allah nan ta Sha sai nayi kuka 😭😭😭😭😭😭😭😭😭 Allah ya Miki sakayya duk da ya wuce wlh Ina rubutu Ina kuka) Haka suka fita Suka barni da Zahira da har lokacin idonta Dake warwage take kallona dashi hawaye na zubo Mata Haka na d'auketa kamar ba mutum ba sabida rashin nauyi na kaita d'akina Ina kuka na shimfidar da ita Akan gado na cire Mata rigar jikinta ko no-nonta ma.shafewa yayi a kirjinta sai kasusuwa kawai kankara na dauko na zuba a katon roba da ruwa na dauko zani na na hau Danna Mata jikinta da ruwan Dan jikinta yyai zafi da yawa da kanta gani nake zata ji dadin Jikinta idan Ina matsa Mata ruwan sanyi a jikinta sai surutu nake kamar mahaukaciya kamar ma har sabo nayi Ina "Allah Mai na maka ka jarrabceni Haka Allah duk addua Nan da nakeyi nake Hana idona bacci sabida Kar wani Abu ya Samu yarana Kar wani Abu ya Samu Zahira Allah sai da Umma suka ci Galaba akanta Allah kaga yanda Zahira ta dawo Allah kaga yanda idonta ya firfito waje" Maganar da Zahira tayi yasa kukana tsayawa cak muryarta ya dawo na Yara sosai. Da sirirrin hannunta ta rik'e hannuna tana "Umma Dan Allah kimin addua mutuwa Umma indai kina kaunata kimin addua mutuwa Dan Allah Umma jikina kamar an hura mun wuta Umma" (Gaskiya bazan iya cigaba da rubuta wajen Nan ba Allah yasani kuka nakeyi ku Bari na tsallake kawai nayi shi a takaice) Jawota nayi na rungumeta cikin ihun kuka Ina "Bazan iya Miki adduar mutuwa ba Zahira sai dai na Miki adduar Samun lafiya yata da ki mutu gwara Ni na mutu Zahira Zahira ke yarinya ce Mai biyayya Mai tausayin iyaye albarkar annabi Muhammad Saw Zaki samu lafiya zahira Ni na musu laifi bake bace Baki musu komai ba Bai Kamata su tabamin ke ba wayyo Allah ka dubi halin da yata take ciki ka kawo Mata agaji ya Allah ban hada bautarka da kowa ba Kai kadai nake Kira nake kaiwa kukana bansan boka ba bansan Mallam ba Kaine mallamina Kaine Mai sharemin kukana Allah ga zahira Nan ka sasauta mata wuyan da take Sha ya Allah ka dawo da ciwonta jikina" Kuka nake sosai Kamar Zan shidde ahaka su Nadeeya suka dawo daga makaranta Suka shigo har cikin d'akina suna shigowa Naga duk sun ja da baya a tsorace cikin tashin hankali da ganin yanda Zahiran ta dawo Zahira kuwa hawaye na zubo Mata ta ringa binsu da Ido a karshe ta tsayar da idonta Akan Nadeeya tana mik'o Mata siririn hannunta cikin muryar yaran tana "Nadeeya Zo gareni" Nadeeya kallonta kawai take jikinta na rawa tana "Aunty Zahira Mai ya samu idonki Haka Mai ya Sameki Haka "? Hannu kawai Zahira ke mik'a Mata hakane yasa ta Isa wajen Zahiran. Tare da Kama hannun da take Mika Mata ta zauna a gefen gadon tana fashewa da mugun kuka Zahira kuwa tace "Nadeeya kimin addua mutuwa kinji Umma tace bazata min addua mutuwa ba Nadeeya jikina konamin akeyi wuyana ma kamar garwashin wuta aka sakamin Nadeeya kimin addua mutuwa kinji" Ihu Nadeeya ta saka duk da zafin jikin Zahira Haka ta rungumeta tana "bazaki mutu ba aunty Zahira bazaki tafi ki barmu ba aunty Zahira waye ya Miki Haka Mai ya Sameki Haka" Tuni.kannenta suka zagayeta suna kuka Ni kuwa na mike na Shiga bandaki na Dora alwala na dauko sabon doguwar rigar da ban taba sawa ba na zura a jikina na dauko sabon hijabina fari Kal shima na saka na na shimfida Sallaya a madadin na tada sallah kamar yanda nayi niyya sai na fashe da kuka na d'aga hannuna na hau rokon Allah akan ya kawowa zahira Agaji kuka nake akan Sallaya sosai goshina a kasa Ina rokon Allah ya kawomin d'auki halin Dana tsinci kaina a ciki. Sallah danayi ma bazan iya cewa a nutse nayi ba ahaka na shafa na nade Sallaya na nufi wajen Yata da buta a hannuna na Mata alwala na zura Mata hijabi na jinginarta a jikin gado Ina "kiyi sallah Zahira a zaune ki roki Allah Yana jinki Yana Kuma ganinki" Bata cemin komai ba Naga ta rufe idonta da Kamar Kara waje sukeyi Bansani ba tayi Sallah ko batayi ba dak'yar na Kora kannenta waje na saka Nadeeya Dora musu abinci Dan kuka take sosai Kamar ma zahiran ta mutu Yarana ba Wanda ya cin abinci har Waleed dake karaminsu danaga Yana buya a bayana idan Zahira ta kalleshi sabida idonta Dake bashi tsoro Duk yanda naso taci abinci ko bud'e Baki batayi yi Banga ta zama ba hakane yasa na bazama nemo Mai taimaka min Gashi lokacin farkon shigowar wayane ba mu Kai ga mallakar waya da har Zan samu hanyar da Zan sanarwa Naseer halin da muke ciki A takaice wajen Mallam naje mijin aunty Ina kuka na sanar dashi halin da muke ciki mutanen arziki daga shi har aunty da wasu daga cikin Dalibansa Haka Suka biyoni gida Duk wanda yaga Zahira sai ya girgiza da yanda ta dawo. Mallam kansa hankalinsa ya balain tashi shima dayake Yana da ilimi tuni yasa na fito da Zahira na shimfidar da ita a tsakar gida Suka daura alwala shi da Dalibansa sun Kai goma suka hau karatun Qurani Sai dai ba alamar Wai akwai abinda zai fito daga jikin Zahira Hakane yasa ya d'auko kwanun Sha Naga Yana ta tofa adduoi daya shafe awa guda Yana Yi sai daya Gama ya bani Akan na shafa Mata a jiknta ko zamu samu jikinta ya rage zafi Cikin Ikon Allah kuwa Ina fara shafa Mata jikinta ya hau rage zafi kanta ya shima Haka take Naga yata ta sauke ajiyar zuciya bacci yayi awon gaba da ita Ashe tunda ta hadu da Wanan masifar Bata bacci Ko a fuskarta zaka ga alamar taji dadin Jikinta kamar wacce har ta samu sauki na hau Godewa Allah Ina Godewa Mallam Basu suka bar gidan ba sai wajen Sha daya har lokacin zahira na bacci Cassette din Qurani na kunna Mata a gefen kanta daga Ni har Nadeeya bamu iya bacci ba Haka muka sakata a tsakiya muna kallo wajen daya naje na daura alwala na Zo na hau Kan Sallaya na tadda sallah Nadeeya kuwa bacci ne ya d'auketa a Gefen Zahira Wajen biyun dare Ina Jan carbi Ina kuka Naga ta bud'e Ido ni kuwa na zuba Mata Ido Ina kallon yanda ta zama kwarangwal Dan ba yanda ma zaka yarda itace tashi tayi zaune tana wurga manyan idonta daya Sakani runtse Ido Dan sosai idonta yayo waje Kamar fitilar kwai Ta zuro siraran kafarta kamar Kara Naga tayi waje Kamar iska zai d'auketa tsaf zaka kirga.kasusuwan jikinta Ni kuwa na mike da Sauri Dan nabi bayanta sai dai Ina fita banganta ba hakane yasa na hau nemanta hankalina a tashe Ina kwalla Mata Kira Nishinta danaji a Bayan fridge Dina dake Palo yasa na nufi wajenta da Sauri a tsugunne take a Gefen fridge din tana Kashi Bance Mata komai ba na Bari ta Gama na Kamata ma kaita bandaki na wanke Mata Ina "ya Kika baro bandaki a tsakar gida Kika zo Palo kina Kashi Zahira Bata cemin komai ba har na kwantar da ita na koma palon na kwashe kashin na goge wajen Sai dai kafin gari ya wayewa na Gane Kamar kwakwalwar Zahira ta tab'u Dan sau biyu Tana kashin amadadin taje bandaki na biyun a kitchen tamin na ukun Kuma a daya dakin da yarana suke kwana tana ta Abu Haka kamar mage tana kalle kalle abinan ya dagamin hankali daya saka ni kuka har garin Allah ya waye da asussuba na bazama neman Mai taimakamin Dan Kamar Mallam bazai iya da.larurar Zahira ba Bansan k'afata ba takalmi ba Ina tafe hannuna Dora akaina Ina kuka Ko ni bansan Ina na nufa ba sai danayi Karo da wata makociyarmu dake can kasan layinmu na dawo hankalina Rikeni tayi da hannu biyu tana "Lafiya kuwa mmn Nadeeya"? A sabon unguwar.mu da Sunan Nadeeya ake kirana sabida yanda take da farin jinin mutane sosai Zubewa nayi a kasa na rik'e kafar matar da ta kasance bafulatana ana ce Mata yaddiko tunda Muka zo unguwa na lura tana da balain kirki ba laifi Dan tasan hakkin makotaka "Ki taimakamin yaddiko yata zata mutu yata ta samu tab'in hankali" "Subhanallahi Mai kike cewa Haka Mmn Nadeeya Ta dagoni Ni kuwa na ja hannunta na cigaba da sheshek'ar kuka Ina bukatar Mai taimakamin Ina bukatar agaji Ina bukatar taimakon jamaa Dan ji nake kamar nayita kwalla ihu yarana ma zagaye suke da Zahira na fito neman taimako bansan Mai yasa nake Jan hannun.yaddiko.dan.tazo taga halin da 'yata take ciki ba kawai Ina bukatar taimakone Har d'akina na Shiga da ita a madadin Naga Zahira akan gado Kamar yanda na barta acan Gefen sip Dina naganta Tana kashin kannenta sun zagayeta suna kallonta Waleed ne kawai a waje sabida tsoronta da suke ji Sai wuwurga Ido Zahira keyi Kamar dai mage Zubewa nayi a kasa na Nuno zahiran da hannu Ina "Yadiko Kinga yanda yata ta dawo Kinga yanda aka dawomin da ita yadikko Kan yata ya tab'u kinga Inda take Kashi ki taimakamin yadikko idan akwai Wanda Kika sani na Kai Zahira wajensa ya Mata addua yaddiko ki taimakamin bansan kowa ba babansu Baya Nan Yana Abuja ba ta hanyar da Zan same shi na sanar Masa halin da muke ciki" Kuka nake sosai Yadiko ma Ina gani ta zub'e a kasa sabida tashin hankalin ganin yanda Zahira ta dawo Dan ta San Zahira sosai sosai take Santa sabida kyaunta har tana yiwa Dan autansu shaawarta Dan ya Aureta idan ta Gama makaranta Cikin tashin hankali tacemin "Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun mmn Nadeeya akwai Wanda nasani zai iya taimaka Miki Bari na Kira mota mu tafi Amma fa wani kauye ne can gaba da jigawa Nima akwai kanwata datayi fama da Aljannu sai shi ya iya cire Mata su ko baa fada ba Zahira Aljannu ne a jikinta Kinga yanda ta dawo fa Ina zuwa yanzu nan kina da jan miski"? Girgiza mata Kai nayi da Sauri Tayi waje Ni Kuma na nufi wajen Zahiran na dagata nayi bandaki da ita na wanke Mata jikinta Nadeeya ta kwashe kashin ta goge Duk Kayanta sun Mata yawa yawo take a ciki daidai da kayan Raheema da take karamarsu ya Mata yawa sai a Haka na saka Mata pant kuwa Bai zai saku ba Dan ba kugun duk Inda Zan kwatanta muku yanda 'yata ta dawo wlh bazaku gane ba sai wayanda Suka Santa lokacin da abun ya sameta. Yadiko Bata fi minti talatin da fita ba sai Gata ta dawo da Mai mota datayi shatarsa. Ni kuwa karkashin gadona na d'aga a cikin kudin sana'ata na dauko kudin da Dan yawa na rik'e a hannuna Muka fito na roki Nadeeya data kularmin da gidan har ta rame itama. Idonta yayi jawur dan kuka.. Muna fitowa muka dau hanya Bamu Isa kauyen ba sai wajen karfe uku shima sai da muka hau machine Nadeeya na zaune a cinyata muka Isa gidan Mallam Mai sallati Haka ma Naga an saka daga wajen gidan Ga almajirai Nan birjik suna ta karatu Bamu Sha wahalar samun sa ba Bayan mutane biyu da suka Shiga ciki suna fitowa muka Shiga Muna Sallama ya d'ago Suka had'a Ido da Zahira Zahira ta kwalla wani mugun. Ihu daya saka kunnena Yinn wani iri Riketa nayi Kamar jaririya sai gashi ta duro da ga jikina ta hankadani tana k'ok'arin Yin waje. Da mugun k'arfi na riketa Amma ga mamakina wani irin tureni tayi yadiiko itama tayi saurin riketa Dan Kar dai ta fita a gujen Shafa Mata Jan miskin Nan a goshi Yi sauri Mallamin yace Yana k'ok'arin mik'ewa sai dai kafin yaddiko ta bud'e kwalbar miskin Zahira ta Kara sakin wani mugun Karan ta zub'e a kasa ta hau wani jijjjiga hankali a tashe na fara k'ok'arin yin kanta Mallam Mai sallati ya hanani akan Kar na sake na tab'ata Wani irin iska ne ya kaure a d'akin lokaci guda Kuma komai ya baje Naga Zahira ta bar jijjigan. Mallam Mai sallati ya tsuuggna a gaban zahiran ya shafa Mata Jan miski tare da daure kanta da farin kyalle yace na ja ta gefe. Da Sauri na dauki yata na Dora a cinya Dan tsayin kafafune kawai zai saka kasan babba ce amma ya dawo kamar dai yarinya siffar.dai Gata ga kamarta Kukan da nake Bai saka na iya ce Masa komai ba sai yaddiko ce ta Dan Masa bayani Shima Bai ce komai ba illa kasko Dana ga ya d'auko ya zuba wani hayaki a ciki ya hau bayani Yana "Kuna shigowa nasan turen bakakken Aljannu arna akayi Mata da har zai rabata da numfashinta zakuji jikinta na d'aukar zafi Bata iya bacci zatayi ta Abu kamar Mai tab'in hankali yanzu Kuna shigowa ma sun San ko yayane sai mun faffata dasu hakane yasa Kuna shigowa suka bar jikinta duk abinda zaayi yanzu basa jikinta Kuna tafiya zasu dawo jikinta Aljannu sun fi su ashirin kowane da aikin da yakeyi a jiknta. Zaki kashe kudi baiwar Allah Dan yanka zamuyi muyi ta Basu hakuri har mu samu nassarar Mai dasu wajen wayanda Suka Mata turen bakakken Aljannun Jiki na rawa na Ciro kudadeen Dana saka a Leda na mik'a.masa. Bai karba ba ya Kira baban Almajiransa akan ya karba ya siyo.masa katon bijimin saa.a daure Masa daddare akwai aikin da zaiyi A takaice Anan yadikko ta barni da Zahira tare da alkwarin duba min yarana A ranar a gidan Mallam Mai sallati na kwana matansa sai tausayina suke karfe daya daidai Naga an yiwa Zahira alwala Dan har lokacin Bata bud'e idonta ba Almajirai sama da goma suna zagaye da ita Mai sallati Ma na d'aga gabanta suna ta karatu Yana Yi Yana yarfa mata ruwan addua Yana goge mata jikinta da wani ganye Zahira dai Bata motsa ba Ina kallonsu har sai da Mai sallati yasa aka kawo Masa kasko ya watsa wani irin magani Mai kamar borkono ko mu damuke nesa sai da mukaji zafinsa ya hau shigar mana hanci Ahaka.yasa.mazan Nan suka d'ago.zahira da tana fara shak'ar hayakin ta bud'e Ido ta fara k'ok'arin fusgewa.ya da Danna kanta akan kaskon Yana saka kaskon a daidai hancinta ta kwalla wani irin Kara ta hau mimikewa idonta duk.ya yo waje Bulala Naga mallamin ya d'auko ya hau zabga Mata Wai zasu yi.magana ko bazasu Yi ba Tuni naji muryar yata ya dawo daidai ta hau ihun "Umma Dan Allah kizo ki.kwaceni daga hannunsa wlh Tallahi nice Umma Ni yake.duka" Aguje na Isa wajensu shi kuwa Mai sallati ya daka min tsawa.akan Kar.na matso.kusa dashi ba Zahira bace Aljannu ne "(Ashe dgsk zahiran ce yake duka ya d'auka.aljannu.ne Dan Wasa sukayi ta Masa da hankali Yana Dan da rukiyya suke.fita idan suka.ga zaiyi wani Abu sai su.shiga jikinta su Yi abinda zaa dauka sune. Ahaka yata ta Sha bulalai da hayakin Dake juyar.mata da.kai idan akayi har muka samu kwana uku ahaka a Rana na hudu da yace na Kara kawo kudi. A ranar Naseer ya duro gidan Mai sallati hankalinsa a balain tashe Yadiko ta rakasho Wanda zuwansa kenan su Nadeeya suka Gaya masa yaje har gidan yaddiko.ya rok'eta ta rakashi. Ina ganinsa na fashe da kuka Bai kalli inda.nake ba ya nufi wajen Zahira dake shimfide a kasa kamar gawa idonta kawai manya.datake wurgawa tana kalle kalle yasa zaka San tana rayye Tunda nake ban taba ganin Naseer a cikin tashin hankali Dana ganshi ba a lokacin Daya xube a gaban zahiran jikinsa na wani irin karkarwa cikin wani irin murya yace "Zahira" Zahira siririn hannunta ta mik'a Masa cikin muryar Yara tana "Abba kayimin addua mutuwa Dan Allah Abba jikina konewa Yake kamar an hura garwashin wuta a wuyana" Da hannu daya ya wawuro Zahira ya hadata da kirjinsa Yana "Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun Allahuma ajirni fi musibati wa aklifnin khairin minha Allâhumma lâ sahla illâ mâ ja'altahu sahlan, wa anta taj'alu-l-hazana idhâ shi'ta sahlan. Addua kawai yake Yana kamkame da Zahira a kirjinsa dayake Jin fatarta na kona Masa jiki Cikin kuka nace "Naseer Dan Allah Dan annabi dan darajar Muhammad sallahu alaihi wa kaje wajen Umma da Safiyya ka Basu hakuri su kyallemin yata Bata musu komai ba ba abinda Zahira tayi data cancanci Haka daga wajensu kazo muje Naseer bana San na rasa yata ni suka tsana sumin hukunci Dan Allah Naseer kaga yanda suka dawomin da Zahira Zahira yanzu Kamar Mai tab'in hankali Naseer ka taimakamin muje na Basu hakuri kaga Zahira yanda ta dawo su sake min ita Dan Allah" Na karashe Ina kuka Mik'ewa yayi da zahiran a jikinsa Yana muje banyi gardama ba nabi bayansa Ko sauraren Mai sallati bamuyi ba Dan nidai a idona Banda dukarmin ya da yayi ba abinda ya iya min sai kudadena daya cinyemin gabadaya Dan sai da na tattaro sauran kudin nasa Nadeeya ta bawa. Yaddiko ta kawomin ta hanyar Mata wasika Shatar mota mukayi Naseer na rik'e da Zahira jikinsa Yana ta hawaye nidai burina nagani a wajensu Umma na kwanta nayita Basu hakuri Sai dai muna isowa Kano Naga Naseer na cewa driver ya Kai mu station Inda na Kai kararsu Umma Ni kuwa cikin tashin hankali nace Mai zakayi "Na gaji Naeema wlh zahira xan nuna musu suga abinda suka Mata wlh sai sun dawomin da yata daidai wlh Mahafina Bai gayamin gaskiya ba Umma ba ita ta haifeni ba Kinga yanda 'yata ta dawo Naeema Hankalina a tashe nace "Dan Allah karka Kai kararsu kararsu muka Kai Suka dawomin da ya Haka muje mu lallaba su Ko kulani Naseer baiyi ba yasa driver ya Kai mu station ban iya sauka a motar ba sai shi ya Shiga da Zahira Yana kuka wiwi Bayan shigarsa da. Mintina goma Sha biyar sai gashi ya fito da Zahira a sabe a kafadarsa Wanan Dan Sandan daya dau statement dinmu shi da Yan sanda wajen shidda da mace Yar Sanda Nan sun duru a motar Yan sanda driverr dayake janmu.ya dau hanyar gidansu Umma Naseer na Masa kwatance motar Yan sanda na biye damu a baya Nidai kuka nake ina cewa Naseer matakin da zai d'auka bashine mafita ba ya Bari mu lallaba su idan aka kullesu wlh ya Kara jazamin zaiyi ko kulani baiyi ba. Har Muka Isa gidan gabana ya hau fad'uwa Yan Sandan a fusace Suka duro daga motocinsu mace Yar Sandan na musu jagora Dan Ashe wanan Dan Sandan daya dau statement dinmu ya fusata muna Ransa Haka kawai yake tausayin nida Zahira. Naseer jikinsa na rawa ya fito daga motar Yana. "officer a taimaka min a matse su har sai sun dawomin da yata daidai Dan sai da suka rantse sai sun kasheta. Ina cikin motar ban bisu ciki ba sai kuka nake ina addua Allah yasa Kar wani balain ne zai kara tunkaroni nidai burina su dawomin da yata daidai............. Comment Labarin nan yayimin kala da halin da muka shiga a baya, amma alhamdulillh addua be bar komi ba, wlhi kakarmu da zata sami dama itama setayi abinda yafi na hajara amma inda Allah ya rage ma aya zaki ita din yar dangice sosai dan yanzu hakama su suke Sarautar garinsu amma fa maganar tsafi da asiri ba kalan wanda batayi, ba kalan Wanda batayi mana ba har na gobara😰 ta tura ma qanwata aljani me kunna wuta haka muna zaune waje ze kama da wuta akashe wani wuri yaqara kamawa daga karshe seda gidanmu yayi kurmus Babanmu ba kalan asirin talaucin da batayi mishi ba amma dayake Allah ba azzalumin sarki bane kuma shi yake ba ma wanda yaso ya hana ma wanda yaso haka tanaji tanagani Ze samu kudin amma sedAi kaman wuta yacinyesu zasu qare abanza baayi komi dasu ba, amma yanzu kumi yazama labari sedai abin da baza’a rasa ba tunda hausawa sunce me hali baya fasa halinshi amma yanzu ko ita kanta tasan munfi karfinta da ita da yayanta goma duka sun tsanemu ba wanda acikinsu baya mana asiri musamman takwaran safiya Tafi kowa mugunta cikin Yayan Kullum burin kakanmu bewuce baban ya mutuba taga yarda zamuyi, gwara ma hajara hankalinta na tashi in taga be lafia itakam babban burinta ace mutuwa ta riskeshi ace be barmana komi na gado ba mu wulaqanta Advertisement *Mg's herbal whitening black soap* Duk wacce batayi anfani da sabulunnan ba anbarta abaya acan karshen bayama kuwa duk Mai tantama akan sabulai nagyaranjiki cewa basa Aiki toh yacire mg's domin kankat ne insha Allah babu Wanda yayi anfani dasabulunmu yace baiyi ba koyaushe mg's sai sanbarka amare da uwargidaye hardama yanmata kuhanzarta kusamu naku ba karya domin bama cika Baki kugwada kubada labari da bakunanku sabulu daya tamkar dubu wadandama basasan using cream sabulun mg's herbal whitening black soap yawadacemuku jikinku zaiyi kyau koyaushe kukasance clean cikin kamshi Kuna glowing koda bakusa turare ba🤗 Kayanmu bana bleaching bn organic ne sunagyarajiki fiye da tsammaninku zaifiddomuku da ainihin natural beauty dinkine Wanda yagwada shi zaitabbar amare kuyi kokari kumallaki mg's domin baruwanku da zuwa adirjemuku jiki zakuga yanda fatarku zata dinga walwali Ina masu pimples Tabo(spot) Sunburn dama dukwani matsalar fata kuyi kokari kunemi soap dinnan before 2weeks zaisharemuku hawaye kuzama abun kwatance Sister's masu nankarwa kuma kunemi soap dinnan Yana rage nankarwa sosai🧖🏻‍♀️duk me shakku tayi kokari tagwada mg's insha Allah bazakiso rabuwa dashi ba Akwai maisa haske Amma kayanmu nafada bana bleaching bn zaifiddomiki d ainihin halittarkine yagoge dukkan dattin jiki Akwai Kuma Wanda zaimiki maintaining skin dinki yasaki fresh fatanki tazama kalar hutu Pls bamacika Baki you HV to try it and see for yourself 100%tested nd trusted Soap price:3k Location:kaduna buh munaturawa ko Ina Amma delivery is not free Maiso kindly message 08062991549 Call 08064532391 Note:Babu inda zakusami mg's herbal whitening black soap sai a number dinnan bairiga yakai market b inyakai we will let you know buh as for now wnn numbern ne kawai🙏 Maiso yahanzarta before yaji sold out akwaisu available now insunkare you HV to wait akawo so maiso yahanzarta🙏adade anayi sai gsky🤭🤝 Mg's skincare [8/4, 6:49 AM] Zannura: *NAGA TA KAINA* *NA SADNAF*🌸🌸 ®️ *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_* _{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_ *Free Novel* *Nakine Mrs Sulaiman ta grp din Surayyams Marubuciyar Ajalin so son so* *Aishatu ladan da Yar mutan Bauchi Naga sakonku ngd son so fisabillahi* *Kuringa karanta comment din danake sawa akwai masu similar case irin na Naeema da suke baran adduoinku ngd* *Page 54* "Dan Allah ku taimaka min su dawomin da yata daidai" Abinda Naseer ke Fadi kenan har suka Shiga gidan a lokacin da suka Isa har k'ofar d'akinsu Hajaran Police din ma sabida tsananin fushi Bai Bari ma sun tsaya neman izinin Shiga ba Dan jikinsa har rawa yake da ya ga yanda Zahira ta dawo jaririyar wata hallita daban. Sai dai suna Shiga a madadin suga su Hajara wata mata suka gani da tsagu a fuska Kamar na Yan igala tana ta ninke Kaya shigowar Yan sanda yasa ta daka tsalle tayi gefe a daidai lokacin da Naseer shima ya Shiga ciki Yana wlh bake Kika haifeni ba ke ba uwata bace Ina Umman take yace Yana karewa d'akin kallo Dan Sam ba a hayyacinsa yake ba Abunda ke Kara daga Masa Hankali yanda jikin Zahira ke d'aukar zafi na tashin hankali sosai yake Jin ciwon kirjinsa na k'ok'arin taso Masa numfashi na Masa wahala Idan ya kalli Zahira da idanta ke warwaje sai yaji kirjinsa ya Kara nauyi da azabar zafi. Maganar matar da suka tarar a d'akin akan su Hajara sunfi wata uku da barin gidan yasa Naseer zub'ewa a kasa numfashinsa ya fara k'ok'arin daukewa Yan sanda sukayi kansa da Sauri Dan Yama saki zahiran kasa ta Dan bugu ta hau kuka kamar Yar yarinya Abinda ya saka Dan sanda kuka ganin yanda budurwar yarinya kyakyawa ta dawo. Yar Sanda ce ta dauki Zahira itama idonta na cikowa da kwalla Wasu Kuma Suka taimaka wa Naseer wajen daukarsa Dan sosai yake k'ok'awa da numfashinsa Dan sanda da sunansa ya kasance Aliyu cikin tsawa ya tambayi matar da suka Samu a d'akin Akan Ina su Hajaran suka koma jiki na rawa tace Bata sani ba A Haka ya fito duk ya tambayi Yan gidan Suka ce Basu San Inda suka koma ba Dan Basu gayawa kowa zasu bar gidan ba wayar gari kawai sukayi Suka ga basa Nan washegarin da aka sakosu suka dawo gida Ni kuwa shirun danaji yayi yawa yasa na fito daga Motar Na fara k'ok'arin Shiga gidan a bakin kofa mukayi kicibis dasu sun riko Naseer Zahira Kuma na hannun mace Yar Sandan Yanda Naga Idon Naseer ya koma sama numfashinsa na sama.sama yasa nayi kansu cikin tashin hankali na cakumo Naseer Ina na Shiga uku na lalace Mai ya same shi. Yan Sandan Basu saurareni ba suka saka shi a motarsu mace Yar Sanda tacemin na hau taxi mu biyo su asibiti zasu je Baa samu mamansu Naseer din ba hakane yasa Naseer yanke jiki Hannu na Dora akaina Ina kuka wiwi Nima inajin kamar na yanke jiki na Fadin A Haka muka bisu a baya har Muka iso asibitin d'akin emergency aka Kai Naseer Ni Kuma na karbi Zahira daga hannun mace Yar Sandan Likitocin tuni suka hau bawa Naseer kulawa da suka ga Yan sanda ne Suka kawo shi. Ni kuwa Dan sanda Aliyun yayo wajena Ransa a balain b'ace ya hau min tambayoyi akan Umma da Safiyya Yan asalin inane su wane Gari nake tunanin sun koma?Mai ya Kara hadani dasu na dai bashi labarin komai akansu? Cikin kuka na hau bashi labarin komai ban rage komai ba da yanda aka dawomin da yata daga makaranta? Sosai Naga idonsa ya kad'a yayi ja ya zubawa Zahira Ido da ta Kara kanjalewa idonta yayo waje daga Inda yake zaune ma Yana jiyo huccin jikinta sabida zafi Har yanzu ya kasa yarda kyakyawar budurwa Nan da ta ringa Masa gizo a idonsa ce ta dawo haka tabbas da ace zai Samu ganin Hajara da Safiyya da hannunsa zai harbesu take Kuma ba sai ya Kai ga kullesu ba daga bayanan da Naeema ta Masa ya fuskanci ba karamin mugaye bane yayi mugun nadamar sakinsu. Sosai yaji Yana tausayin Naeema da Naseer din uwa uba Zahira da bata musu komai ba Zafin jikin Zahira yasa ya Kira likitoci duk da yasan cutar Bata asibiti bace Amma gani yake kila akwai abinda zasu iya yi akai zafin jikinta ya ragu Idan har zaka Kai hannunka jikinta kaji tsananin zafi inaga ita kanta zahiran Ban ce Masa komai ba a lokacin daya karbi Zahira da ga hannuna kamar dai fa yarinya Zahira ta dawo siririya sosai wlh ka d'auke ta bazata yarda mutum ka dauka ba. Har d'akin da aka nuna Masa ya Kai Zahira da kansa ya roki Likitan akan ya bawa Zahira taimakon gaggawa ta samu relief a jikinta ko alluran bacci. Ne ma a Yi Mata tunda Bata iya baccin. Shi zai dau nauyin treatment din ko nawane. Kin barin d'akin yayi ya tsaya Yana kallon yanda Suka dukufa akan Zahira dake binsu da Ido daya Bayan daya wata nurse ma.gefe ta koma kila tsoron Zahira takeji ko tausayi Duk yanda suka so saka Mata ruwa kasawa sukayi Dan jikinta yayi laushi bama su hango jijjiya ba Allura suka iya Mata na bacci da sanyi jiki Sai dai kamar Kara Mata ciwo sukayi Dan ihu ta ringa Yi tana fusge fusge Jikinta ta Kara kwasar wani mugun zafin Ni kuwa ihunta yasa na Shiga d'akin Aguje Dan Sandan ne ya iya riketa Gam Ni kuwa na durk'ushe a Gefen gadon na hau kuka Ina kallonsa yana totofa Mata adduoi Likitan kuwa cikin tausayawa yace mu Kai Zahira wajen Mallamai cutarta bana asibitin bane jikinta yanda yake d'aukar zafi ba Normal bane. Likitan kuwa dak'yar ya samu ta bar fusge fusge ya Kira Yar Sandan Nan ta rik'e min Zahira ya fito na bisu a baya muka nufi d'akin da aka maida Naseer da aka Masa Karin ruwa da oxygen a hanci sabida Baya iya numfashi Ganin Naseer a wanan halin da Zahira dake hannun Yar Sandan Kamar jaririya sai idanduna yasa naji jiri na d'ibana na zub'e a kasa kaina Kamar ya Fado Sallati kawai nake zuciyata na bugawa yanda nake Jin kirjina kamar zai Faso Kamar na zauce Haka nakeji idan na kalli Naseer na kalli Zahira Sai da muka shafe kusan sati daya da kwana uku kafin Naseer yasan ma Inda kansa yake duk yabi ya rame ya fice a hayyacinsa Bazan manta Dan Sandan Nan ba a rayuwata Dan ya taimaka min sosai har matarsa yasa ta ringa zuwa duba mu inta tashi zuwa Haka zata Zo Mana da abinci da kayan marmari Sosai Dan Sandan ya ringa k'ok'arin nemo Safiyya da Umma da sai da suka koma can gidan da suke haya Suka Kara bincike Amma duk Basu San Inda su Umma suka koma ba Matarsa da nasan na girme Mata sosai Ita ta ringa Dan kwantar min da hankali da Wanan yadiiko makociyata Zahira kuwa amadadin sauki ma abin nata Kara jagulewa yake karfe dayan dare nayi zata hau kururuwa Tana zunduma ihu tana fusge fusge wani zubin ta kankameni tana na boyeta gasu Nan zasu caka Mata wuka wani zubin Kuma tana kuka tana na roka Mata Allah ya d'auki ranta ko zata huta da wutan da ake hura Mata a jikinta Naseer daya dawo hayyacinsa aka Sallame mu Haka ya zauna kamar mace Yana kuka wiwi Haka na tsaya akansa ya Dan samu lafiya Muka bazama nida shi Muka hau Nemo Mai taimaka Mana da magani Dan Zahira ta samu sauki Mutanen da suka San larurar Zahira Haka suka ringa zuwa kowane da kalar Wanda zasu ce muje wajensa ya kware a rukkiya mune Nan mune can fiye da wata hudu komai na mu ya Kare wajen. Bin Mallamai a karshe Naseer ya gaji yace mu hakura Haka mu Zo muyita gayawa Allah Yana kuka ya bud'e Baki Yana "Allah Kai ka halliceni ban nufi matar Nan da komai ba sai alheri ban taba bijire mata ba hasali sau daya nasan nayi kuskure hannu na ya Isa ga kumatunta da har gobe nake neman yafiyarka ba abinda Bata min ba karshe ta had'a da yiwa yata turen bakakken Aljannun ya Allah kayimin sakayya tsakanina da ita Allah ya Isa" Da Sauri na rufe Masa baki na girgiza Masa Kai Ina "Ba sai ka Mata Allah ya Isa ba ka Gama magana tunda kace Allah ya saka Mana kuka ba naka bane Naseer neman kudi zamuyi mu nemowa Zahira magani kaga yanda Yara suke cika k'ofar gidanan suna ce wa da dodo a gidanan Wai yata ce dodo Naseer Zahirata ce dodo" Kuka ne yaci karfina sabida yanda abin ke min ciwo. Idon Zahira daya fito warwaje da kasusuwanta da suka fito na jikinta da Abu da takeyi kamar Mai tab'in hankali yasa yaran unguwar wani zubin cika k'ofar gidana suna lekan Zahira Nadeeya da Minal ne ma wani zubin suke fita su Kori yaran wani zubin har da duka Wasu Kuma yaran haka zasu wayance da zasu Sha ruwa ko suna neman wani Abu Wai duk Dan suga Zahira K'arfi da yaji na koma kulle ta a daki Dan Sandan Nan ma Haka ya ringa kawo min mallamai masana addini suna iya kokarinsu akan zahiran Sai dai duk a banza abinda kawai Zahira ta samu saukinsa shine zafin Nan da jikinta ke dauka ya ragu Wani zubin Kuma tana iya bacci da Rana Amma fa idan dare yayi Haka zata tayi ta ihu tana fusge fusge har garin Allah ya waye Haka Naseer zai tsaya akanta dagani har Naseer ba Mai bacci a cikinmu Haka Nadeeya da kannenta sai dai idan bacci ne ya d'auketa Nakanji ma ance mak'ota nayi damu Wai Zahira na damunsu da ihu da Kara wasu Kuma tausayi take basu. Komai nawa ya kare a nemawa Zahira magani daidai da suturuna duk na siyar da rabi Naseer ma har filinsa ya siyar Bai gayamin ba yaje can har garin calabar neman su Umma Wai duk Dan ya rokesu su dawo Mana da Zahira daidai Amma ya karaci nemansu Bai gansu ba har Mallam Musbahu sai daya nema bai samu ma Mai labarinsa ba sai Haka ya dawo. Muka cigaba da neman Mai yiwa Zahira magani Har muka shekara a cikin wanan masifa da balain Sai maneman Nadeeya ke Dan taimaka Mana wani zubin har da na Minal din Dan duk sun kawo girma. Kuma ba laifi manyan mutane ke zuwa neman Nadeeya dayake baa nutse muke ba bama bi takanta ba laifi ba iya Zahira keda farinjini ba ga dukan alamu yaran nawa Rabbi ya musu farinjini Zan iya cewa albarkacin masu neman Nadeeya da auren yanzu asirinmu ke rufe Dan sukan mata kyautar ban girma ko su siyo kayayakin abinci Dana gida da Sunan kayan Dubiya kila sun San Daga Ni har Naseer din muna bukatar taimakone Ganin Nadeeya tana neman amfani da Wanan damar wajen wankar Samari yasa na taka Mata birki Akan ta tsayar da hankalinta waje daya ta ringa kula guda a cikinsu A Haka ta tsayar da Wanda yafi kudi a cikinsu da bansani ba Dan tana sanshi take kulashi ko Dan Yana kashe Mana kudin ne Dan ta taimaka Mana. Halin da muke ciki Bai saka na Bari sun dakata da zuwa makaranta ba da ace larurar Nan Bai samu Zahira da yanzu tayi candy Kila ma har ta samu Wanda hankalinta ya kwanta dashi ya fito na aurar da ita Amma Ina ga diyar tawa Nan rabi mutum rabi wani hallita Naseer kuwa ganin Abu yak'i ci yak'i cinyewa yacemin mu barwa Allah komai mu dage da Addu'a muyita Gaya masa yana sane damu. Take kuwa nayi naam da shawararsa Dan ko Ni Nagaji da yawon bin Mallamai da Kamar kudinmu kawai suke cinye Mana Daga Ni har shi Haka Muka dukufa da Addu'a. Kullum bakina d'auke da azumi Yata kuwa bazan iya bada labarin yanda ta dawo ba dan ba sauki wajenta sai a wajen Allah. ( Na Dan gajarta labarin sabida da yawa) A haka Watarana da Zahira ta samu shekara guda da wata hudu da Wanan lalurar ranar alhamis wajen biyar na yamma Naseer na zaune a tsakar gida a zaune hannunsa dauke da Qurani Yana Dan karantawa kasa kasa dayake dagani har shi azumi muke Nadeeya tana kitchen tana Mana abinci su Minal Kuma suna Palo suna duba littattafansu Ni Kuma Ina zaune akan tabarma na Dora Kan zahira a cinyata Ina Dan Mata fifita bama gashi yanzu a kanta kanta ma ya dawo kararrami. Ba bacci take ba idonta biyu tana kalle kalle tsullum Naga ta mik'e Ina ganin Haka nasan Kashi takeji Har na Saba da halin nata Bata Shiga bandaki ba Kamar iska zai d'auketa taje lungun band'akin ta tsugunna Dan ita abinda zai Zama daidai batayin shi sai dai akasin Haka. Tana gamawa na fara k'ok'arin mik'ewa Dan na wanke Mata Naga Minal ta fito daga d'aki taje ta wanke Mata tare da gyara gurin Ina Jin dadi da yarana basa kyankyaminta ko waleed da ya girma shima yanzu ya daina tsoronta wani zubin ma yakan wanke Mata kayayyakinta Dan ba laifi Waleed Dina akwai hankali ga hazaka da k'ok'ari tamkar mahaifinsa Haka kawai ma zai je kusa da Zahira ya hau Mata addua Allah ya Bata lafiya wani zubin sai yacemin ya fadawa mallaminsu yayiwa yayarsa addua samun lafiya Dawowa tayi wajena ta kwanta na gyara Mata rigarta daya Mata yawa da siyowa ma mukayi sabida duk kayan kannen ta ma sun mata yawa .iskar danaji Yana kadani ga Ina Dan Jin azumin yasa na kwallawa humaira Kira akan ta d'auko min pillow tana kawomin na kwanta Nan da Nan bacci yayi awon gaba da Ni. *Mafarki* A wani katon fili na tsinci kaina amadadin gida Ina kwance dai Akan tabarmar Zahira na gefena a zaune hakane ya na mik'e da balain sauri dana ga ta dawo daidai yanda take. Ada Ina k'ok'arin Magana na hango Yara sun kewaye wata Mata tana ta raba musu alewa suna ta murna suna tsalle. Haka kawai sai naji inasan ganin fuskar.matar tana juyowa Naga mahaifiya tace Fuskarta d'auke da murmushi tana ta rabawa yara alewa suna Kara titilowa suna tsallen murna wani irin mik'ewa nayi na fara k'ok'arin Isa wajenta cikin tsananin murna Ina Umma Sai dai tafiya kawai nake na kasa Isa wajenta har har ta Gama raba alewar Nan Naga ta nufi wajen wata dake kwance a kasa kamar matacciya Tana zuwa wajenta Naga ta ajiye kwanun abinci a gabanta matar kuwa ta mik'e da sauri ta hau ci tana yiwa Mahaifiyata godiya Tana Gama ci ta mik'e. Tana Mahaifiyata ta ceto ta tagode Ta fara tafiya Kamar ba itace a kwance kamar.mataciya ba Ni kuwa sai kwalla Mata Kira nake Amma Bata kalleni ba sai k'ok'ari nake na Isa wajenta Bubbuga pillon da nake Kai da sunana da Naseer ya Kira yasa na bud'e idona "Tashi kinsan babu kyau bacci uwar Haka Amma kusa Shan ruwa" Ban ma iya motsawa na dawo cikin hankalina ba sai Dana Gama karewa gidana kallo na tabbatar da mafarki nake Ashe Rabon da Naga mahaifyata a mafarki har.na manta Mai ma'anar mafarkin da nayi da Mahaifiyata"? Sosai mafarkin ya tsayamin a wuya Ina tuno yanda mahaifiya ta keta sadaka Yara na murna da abinci data bawa wata dake kwance kamar matacciya daga ci ta mik'e. Dak'yar na iya Shan kunu Dana Sha ruwa sabida tunani A karshe Dana kasa hakuri na gayawa Naseer mafarkin danayi Nace ko ya San fassarar mafarkin? Murmushi kawai yamin yace mafarki ne kawai Kar na damu kaina Ban dai iya cire mafarkin a Raina ba a ranar Wajen Sha daya bacci ya Kara kwasata na Kara irin mafarkin sak Kai Wasa Wasa sai gani nayi mafarki ajere cikin kwana uku Ana kwana ukun naji mahaifiya ta na cewa yaran "Sadaka maganin masifa" Kalmar Nan Haka na haddace shi a kaina har na tashi. Abinda ban Gane ba ko mahaifiyata Kara tuna min take Dana dage da sadaka toh Naga Ina yin Sadakan Nan. Haka mafarkiin ya tsayamin a raina na hau yiwa yara sadakan alewa ina rabawa Ina cewa kuyiwa Yata addua Allah ya bata lafiya take kuwa zasu hau tsalle tsalle suna yiwa Zahira addua cikin murnar alewar Dana Basu. Ban kawo komai ba kwatsam Ina zaune yaddiko ta shigo duba Zahira Dan takan Dan duba ta akai akai.makociyar arzki ce itama bana manta ta a rayuwata Muna cikin hirar sama sama kwatsam na tsinci kaina da Mata tambaya. "Ni Kam akwai tsohowa a unguwar Nan Haka da kike tunanin tana bukatar taimako haka"? "Kai akwai sosai ma ai suna da yawa. Amma akwai wata matar Mallam Amina Nima zuwa nayi na tarar da ita a unguwar Nan a can kasa layi take mijinta shekara goma kenan da rasuwa Bata tab'a haihuwa ba har ta tsufa mace ce Mai addini da tsoron Allah Kamar yanda na samu labari Rasuwar.mijinta yasa ta Dan siyar da gidan take juya kudin ta Kama haya toh shine wasu azzalluman Yan fashi suka dirar Mata suka.kwace komai a hannunta shine fa ta hau bara tana samun na abinci Shekara biyu da suka wuce mota ta bige ta shine ta daina fita baran sabida ciwon kafa da take fama dashi Ahaka Mai gidan hayan dayake Yana da Dan tausayi ya bar Mata daki daya a gidan Wayanda Suka San halin da take ciki sukan Dan taimaka Mata ko Ni Ina samu sarari Ina Mata Aiken abinci" Sosai naji hankalina yayi wajen matar da naji sunan Mahaifiyata gareta bandai nunawa yaddiko komai ba nace tamin kwatance Gidan tana min kuwa nagane. A Haka muka Dan Kara tab'a Hira ta tafi Washegari kuwa da sassafe na shirya abinci a kula. Na dibi danyen abincinmu na dauko xannuwa na guda biyu duk da Nima banida suturra na hada da sabulu na nufi gidan matar kamar yanda aka kwantan tamin Dana Isa gidan inata Sallama baa amsa ba hakane yasa na Shiga d'akin Dana gani a bud'e A kwance na tarar da ita tayi Kashi ma a jikinta ga kafarta a kumbure kamar rashin kudi yasa Bata iya Kai kanta asibiti Sosai naji tsigar jikina ya tashi Na ajiye kayayakin hannuna na Isa wajenta Ina "Sannu mama" Da Ido ta ringa Bina ban ce Mata komai ba na dagata na fita Waje tausayinta na balain rufeni dak'yar na samo ruwa na wanke Mata Jiknta batare da naji kyankyaminta ba na duba tsumokaran Kayanta Naga duk ta batasu da Kashi da fitsari Hakane yasa na dauko zanina Dana Zo dasu na daura Mata daya sosai naji kamar itace matar da nake ganin Mahaifiyata na taimakawa akwai dalilin dayasa nake mafarki da mahaifiyata kila matar Nan ke bukatar taimako. Yanda take kallona hawaye na zuraro Mata yasa na dauko Kular abincin Dana Zo dashi Sai dai Ina Isa wajenta jiki na rawa ta fusge abinci rashin k'arfi yasa ta kasa bud'ewa Ni kuwa hawayen tausayinta ya zubomin na bud'e Mata jiki na rawa kuwa ta hau ci da Sauri da Sauri tuna Nima halin Dana tsinci kaina a ciki kwanakin baya na azabar yunwa yasa na hau kuka Sai data ci na Bata ruwa. Ta sha ta fashe da kuka tana "Baiwar Allah daga Ina ya akayi kikasan Ina bukatar taimako yanda Kika ciyar Dani Kika shayar dani rabbi ya faranta Miki ya biya miki bukatunki na alheri nafi sati rabona da abinci Bana iya tashi idan Kashi ya matseni ko fitsari sai dai nayi daga kwance sabida ciwon kafa banida kowa sai Allah banida d'a banida jika bansan dadin haihuwa ba ballantana na samu Mai taimakamin Ngd yarinya Allah ya faranta Miki" Ameen mama Nima banida uwa banida uba dafatan Zaki zama mahaifyata Kalmar Nan ne yasakata kuka ta hau shimin albarka Nima dadin kalmar albarkar da take sakamin ya sakani kuka Tuni na tattaro zannuwanta data Bata na wanke Mata su na gyara daki dayan Ina kallo ta daga hannunta tana Godewa Allah daga adduoin da take nasan macece Mai ILimi da baiwa sai dai jarrabata da Allah ya mata hakane kuwa yasa na Sha alwashin faranta Mata har tsawon rayuwtaa Sai uku na koma gida Naseer Bai tambayeni Ina naje ba Nadeeya na Gama girkin dare na Kara zubawa a kula na saka hijabina na cewa Minal tazo mujr taga gidan A takaice tunda ga ranar na dauke Mata cin safe Rana dare Nakanje wajenta muyi hira sosai nake jinta Kamar mahaifyata Ko ban samu zuwa ba nakan sa yarana suje gidanta su Dan Mata gyare gyare su dawo.kuma.wani ikon Allah ban Kara mafarki da mahaifiyata ba Sabon da nayi da Inna Amina yasa na fara sakin jiki da ita Ina Bata labarin kaina har na Zahira da halin da take ciki Sosai hankalinta ya tashi tace na kawo Mata Zahira ta gani Washegari da yamma na goya zahira mukaje Sosai ta kad'u da ganin zahiran Tacemin zata taimakamin insha Allahu akan Zahira Allah ya Bata wnan ilimin ita da margayi mijinta Ko.kadan maganarta Bata shigeni ba lura da macece ita Kuma.manyan mallamai sun Yi iya k'ok'arinsu Basu iya warkar da Zahira ba Abubuwa ta lissafamun akan na siyo Mata har da su ruwan zam zam Jan miski ganyen magarya Wasu Abubuwan dai na manta su na dai siyo Mata ne kawai ba Dan na yarda ba A Haka tace na ringa kawo Mata zahiran tana Mata Addu'oi. Banki tata ba Dan bansan baiwar da Allah ya Mata ba na Kuma ga tabbas tana da ilimin Dakaina nayiwa zahira alwala itama da alwala a jikinta sai ta sa na samo kasko ta zuba wani turare data hada A.farkon ranar da tayiwa Zahira turaren A ranar Naga tashin hankali Dan sosai Zahira ta ringa ihu tana murya kala.kala tana rantsuwar kashe Inna Amina yarika sai datayi yafi kala ashirin yanda take k'ok'awa da Inna Amina sabida tana watsa Mata ruwan zam zam data kwana tana addua akai yasa.na baxama na Nemo maza Suka ririketa Amma a banza Haka ta watsar dasu Sosai muryarta ya dawo na maza na tsorota danaga yanda Inna Amina ta bada himma wajen turaren. A takaice sai gashi Aljannun da aka turawa Zahira suna magana wajen su bakwai a jikinta maza da mace daya Kuma arnaye yanda Inna Amina ke konasu da ayoyin Allah ta daure manyan yatsunta guda biyu yasa Suka hau cewa zasu fita Kar ta konasu aikosu akayi Take Inna Amina tace waye ya aikosu sukace Shugabansu ne ya aikosu tace waye suka Kira sunansa Inna Amina kuwa ta cigaba da gana musu azaba suna zuba yarika Haka muka kwashi kwana bakwai Inna Amina na fama da Zahira ko bacci bama Yi Dan gidanta muka koma gabadaya tunda muke zuwa wajen masu rukkiya ban taba ganin wanda ya haukata Zahira Haka ba sai Inna Amina A kwana na takwas zahira ta hau amaye amaye har da gashi Haka ta ringa amayo shi Inna Amina kuwa ta cigaba da zabga turare data hada sai gashi zahira na muryoyi kala kala Akan zata fita a yau su koma wajen wayanda Suka turo su Inna Amina dak'yar ta tsagaita tace sunyi alkawarin fita suka ce ee tace ta Ina zasu fita suka ce ta Baki a take kuwa Naga Zahira ta hau atishawa ba kakautawa. Can ta saki Kara Naga idonta nata fitowa waje daya saka hankalinmu tashi gabadaya Inna Amina kuwa tayi saurin cewa karka fita ta idonta Zan Kona ka sai dai ina aikin Gama ya Gama sai da daya ya fita ta idon Zahiran da har yau idan ka Kura Mata Ido zaka ga idonta daya ya Dan fi daya girma Kamar a mafarki Zahira ta zube a kasa. Hallitar jikinta ya hau canjawa idonta na komawa ciki Jikinta na cikowa *Alhamdulillah sadaka maganin Masifa wlh Tallahi akwai sirri a sadaka da ba kowa ne zai Gane ba ba sai kin Zama Mai kudi zaki iya sadaka ba akwai mabukata kana cikin matsala tsanananta da Addu'a da sadaka duk biye biyen da sukayi a sanadin farantawa baiwar Allah Nan Rai sun samu maganin matsalarmu Allah yasa mudace* *Comment* Wlh exactly irin abinda ya faru dani nikuma kishiyar mamanah ce tafara ne akan mamanah Allah bai bata sa,a ba sai tadawo kaina saboda mamanah tafiji dani duk cikin diyanta shine tayi amfani dani don ta kuntatawa mamanah wlh yadda idon zahira suke da bantsoro haka nau suke inka kalleni so daya baka marmarin kasake kallona wlh har kuka akeyimin ina sati kwance babu babusha kuma da anje dani asibi duk bincikenda za,ayi sai ace lpy ta lau banida matsalar komai duk inda mukaje bidar magani aikin banza munyi na asibiti ba,a gane komai ba aka komo na hausa shima shiru haka za,a kiro malamai suyita yimin rukiya amma basu magana wlh wani wuri da aka kaini hadda turaren barkono akayimin amma suka ki magana na wahala na wahala nasha azaba sosai wlh haka mamana zata sakani gaba tayita yimin kuka wlh gurin da muka fara zuwa da aka gayamana kishiyar mamanah ce bamu yarda ba sai da mukaje wuri yafi uku anagayama itace kafin muyarda itace tayimin ije da bakin aljanu guda uku wai su haukatani kuma su hanani aure da kyet da taimakon Allah akasamu naji dama nadaina rashin lpy amma duk da haka wlh basu rabu dani gaba dayaba don sunki barina inyi aure inaji Ina gani aure ya gagareni munyi magani munkashi kudi har karfinmu yakare amma wlh haryanxu shiru yanxu shekarata goma kenan cikin wannan matsala wlh matsalar sihiri babbar matsala ce. Slm.don Allah hide my ID wallahi wannan labarin yatuno min danawa rayuwan haka ya faru dani nima haka uwar mijina da kanwar mijina uwa daya uba daya sukayimin ni haihuwar fari danayi wallahi yaron tun bayan suna muka dena barci dashi haka xaiyi ta kara duk wanda yake kusa dani sai ya tausayimin dagaa karshe ma hannu da kafanshi aka canzama halitta😭😭😭haka na dunga wahalan neman magani baban kuma da farko yaki yarda sai daya ya ganinma idon shi sannan ya yarda muka fara neman magani maganan danake miki har yanxu ban huta ba kuma yaron ya xama saurayi har kanwanshi datake bimishi itama haka nayi wannan faman babancina da neema shine ni uwar mijina bata kungiyar matsafa sai dai tana bin matasfa da kuma bokaye iya wahala na wahala😭😭wani shari'an sai a lahira don nikam har yanxu abin yana damuna😭😭😭wallahi na manta rabon danayi barcin 2hrs da daddare dani dayarana haka xamuyi alwala mukaima sarkin sarakuna kukanmu ngd *Advertisement* Hlo sister's if you dnt use this soap before try and buy one use it you will never use any other soap again except mg's herbal whitening black soap🧖🏻‍♀️ it treat all skin prblms like Sunburn Acne it fade away black spot Clears pimples Reduces stretch mark it treat all skin prblm even if you don't HV any skin issue you can still use the soap it nourish nd keep ur skin fresh nd smooth,it will make ur skin to glow like never before nd gives ur body a pleasant smell🤭 This soap you jst HV to try it and see for yourself is one in a million this soap is organic soap 100% natural it does not bleach it will just bring out the beauty in you just give it a try your skin will thank you Just chat or call 08062991549 to plc ur orders Note you will not get this soap in the market it hvnt reach market for now you will only get it via this number Soap price:3k Location:kaduna buh we deliver Nationwide Delivery is not free Hurry nd grab urs dnt left behind😊 Mg's makeover Chat 08062991549 to buk for ur casual or bridal makeup @affordable price Location:kd You can still order ur slice cake, cupcakes,meatpie,samosa nd spring rolls,shawarma@mg's bakery for ur events at affordable prices kindly chat 07067210195 08062991549 Are you guys looking for where to buy ur kitchen stuffs,abayas,shoes nd bags,laces,Ankara,fabrics mg's collections is there for you,you can chat 07068707979 08062991549 Call 07046881166 08064532391 to plc ur orders May Allah bless you all🙏mg's lv you all fisabilillah🤭 [8/6, 12:45 PM] Zannura: *NAGA TA KAINA* *NA SADNAF*🌸🌸 ®️ *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_* _{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_ *Free Novel* *Page 55* Haka na kurawa 'yata Ido Ina ganin yanda jikinta ke b'ari tana cikowa a hankali idonta Dake warwaje na komawa ciki Na kasa gasgata abinda nake gani har matse hannuna nayi Wai Dan na tabbatar da irin mafarkan Dana Saba yi bane nakeyi Akan Zahira ta warke ta dawo yanda take Amma da alama Kam ba mafarki nake ba. Kabbarar da Naseer ke tayi durk'ushe a gaban zahiran da jikinta ya bar B'ari sosai 'yata ta dawo yanda take sai dai Rama da idonta da naga ba Haka yake ba ya dai koma ciki sosai sai dai tuwon idonta dake warwaje ko iya Haka ta tsaya alhamdulillah bansan ma hawaye nake ba sai da naga Naseer ya d'ago Zahira da idonta ke rufe jikinta a mace kirjin ta sai sama da kasa yake Tana maida numfashi wahalar data Sha. "Naeema Kinga Zahira ta dawo daidai Zahira ta samu Lafiya Naeema ki tab'ani na tabbata ba mafarki nake ba? Naseer yace Yana d'ago Zahira da jikinta bashida k'arfi sosai har lokacin idonta a rufe yake Na kasa yarda da duk wuyan Nan da na Sha Ashe Mai Mana magani na kusa damu duk uban kudin da muka kashe Ashe Inna Amina ce zata Zama silar warkewar Zahira Ban tab'a tunanin ko turen da aka mata sun bar jikinta zata maida jikinta yanda take har ta koma siffar mutane kamar yanda take da kirijinta ya ciko.gashinta ya dawo komai nata ya dawo Inka d'auke ramar da tayi da baya rasa Nasaba da abinci da Bata iya ci amma ta dawo zahirarta Alhamdulillah. wajensu na karasa na durk'usa tare da ruk'o hannayen Zahira Na dag'ata tare da fashewa da Kuka Ina Godewa Allah. Dan na fidda rai samun saukinta gani nake kamar mafarki nake Bayan shekara daya da watani Zahira a karshe ta warke ba tare da mun kashe ko sisi ba. A hankali ta bud'e idonta tana "Zan Sha ruwa Umma kaina ciwo yake" Da Sauri na mik'e na fara k'ok'arin nufar randar ruwan Inna Amina Dan na d'ebo mata ruwa Inna Amina ta dakatar Dani tare da mik'a min wani Kofi da ta cika da ruwan zam zam Mai dauke da Addu'oi tace na bata Tasha Da sauri na karb'a na bawa zahiran ta kuwa shanye gabad'aya. Naseer kuwa yaje ya zub'e a gaban Inna Amina ya hau Mata godiya kamar zai kwanta rabon da naga Naseer cikin farinciki Haka har na manta Nima wajen Inna Amina na karasa na hau Mata godiya Ina "Bazan manta ki ba a rayuwata kin share Mana hawayenmu bayan mun fida ran samun sauki Allah ya saka miki da Aljannatul firdausi insha Allahu Zan iya k'ok'arina Dan na faranta Miki kin Zama uwa a gareni" "Nima Kin Zama Mahaifiyata daga Yau ki d'aukeni tamkar Dan cikin ki da Kika Haifa Mama mun sha wuya nemawa Zahira magani Ashe kece Zaki zama silar warkewar ta Mama ki d'aukemu tamkar 'yayanki Zahira kuma jikarki Naseer yace Inna Amina kuwa ta fashe da.mugun kukan daya daga Mana Hankali Hankalinmu a tashe muka hau tambayar ta abinda ya sakata kukan Dak'yar ta tsagaita kukan da take tana "Dadi nakeji da kuka kirani da kalmar mama Ashe Haka ake Jin dadi idan an Kira da mutum wanan kalmar ba'a tab'a kirana da kalmar mama ba Dan ban tab'a haihuwa ba ballantana na San dadinta ko iya wanan matsayin kawai Kuka bani kuka kirani da Sunan mahaifiyarku Kun Gama min komai 'Ya'yana ban Rasa komai ba a lokacin kuruciyata ba sai rashin haihuwa Da Allah ya jarrabceni dashi nakan ji inama ko Mara lafiya Allah ya bani amatsayin d'a a gareni Amma nasan kila haihuwar ba alheri bane agareni Amma a yau matsayin da Kuka bani yasa naji tamkar Allah ne ya amsa min addua ta ya bani ku a daidai lokacin da nake bukatar Mai kula Dani Mai tsayawa a kaina idan na koma ga Allah Alhamdulillah ya Allah Sosai na fashe da kukan tausayin Inna Amina wato a rayuwa kowa da irin jarrabawarsa wani gudun haihuwar yake wani kuma nema yake Ido rufe haihuwa ma arziki ce Ashe Alhamdulillah da Allah ya bani shidda da Umma take min surutun na fiye haihuwa banida bambanci da akuya ( *Ya Allah duk mai neman haihuwa ya Allah ka Bata Dan tsarkin mulkinka ya Allah ka dubi bayinka da idon rahama da ka jarrabta da rashin haihuwa ka musu wanan arzkin Dan su kadai suka San Mai sukeji a zuciyarsu da rashin haihuwa Nan idan Kuma Basu da rabon haihuwa Allah ka Basu hakuri da dangana ka sa hakurinsu ya Zama silar shigarsu Aljanna alfarmar annabi Saw*) "Banida uwa Nima mama ki rik'eni tamkar danki ki ringa saka min albarka bansan Mahaifiyata ba sai wata Dana d'auka Mahaifiyata ce mama tunda na Santa a matsayinta na uwata take azabatar Dani Sakin Baki nayi Ina kallon Naseer da ke magana cikin Jin zafin maganar dake cinsa a Rai ya hau bawa Inna Amina labarin daya girgiza ta tana sallati gani take Taya ma yanda take Jin da ta samu haihuwa zata iya Sadaukar da rayuwarta wajen farantawa abin da ta Haifa har tsawon rayuwar ta sabida so Amma har Allah ya Bawa mahaifiyar Naseer ta ringa azabtar dashi har dasu Zahira data kasance jikarta gaskkya badan tasan ba yanda zaayi Naseer ya kirkiri karya ba da ta karya tashi. Naseeha ta hau yiwa Naseer akan ya nemawa Hajara Shiriya a wajen Allah Kar yayi fushi Maganganu Inna Amina ta Mana cikin ilimi da muka Karu gabad'aya na ringa Jin tabbas na samu wacce zan ringa yiwa kallon mahaifiya Kuma sosai nake jinta a Raina tamkar Mahaifiyata. Adduar da ta ringa Mana da Naseer na dacewa da rabon duniya da lahira yafi komai faranta mana. A takaice sai ga Naseer ya rok'eta ta yarda ta bimu gidanmu ta koma can da Zama Sosai naji dadin shawarar da ya yanke. Inna Amina na zazamewa Dan gani take zata D'ora Mana nauyi mu kuwa muka dage A takaice silar komawar Inna Amina gidanmu kenan da muke jinta tamkar mahaifiyar mu. *Waiwaye* Har ni Naseeru zai yiwa wanan dukan har ya Kai ga ya ciremin hakori daya Umma Kinga fa yanda ya kumburamin jikina Umma Kinga idona? Duk akan Naeema iya station da Matarsa ta kaimu muka kwana Wanan tsinaniyar Yar Sanda tayi ta dukana kamar ta Samu jaka duk Wanan Bai Isa ba sai Naseer ya had'a da dukana toh na rantse da girman Allah sai Naga karshen Naseeru wlh sai Naga bayansa Koda kuwa zai mutu sai na zamewa Naseer da Naeema balai da Masifa bazan iya lissafa sau nawa ya dakeni duk Akan Naeema ba Ita Kuma Naeema Ni kadai nasan Mai Zan Mata wlh" Safiyya tace da kumburarren idonta da Baki Tana duba jikinta da yayi jajur "Naseeru fa ba'a hayyacinsa yake ba Asirce shi Naeema tayi kema kinsani ko Ni sai na dau fansar abinda ta Mana wlh sai tayi nadamar kullemu da tayi hakuri zakiyi Naseer Bai Mana komai ba Naeema dai zamu ga bayanta tunda har wuyanta yayi kaurin da zata kai kararmu ta kullemu" "da ya Zama a hayyacinsa da Kar ya Zama a hayyacinsa ba Abunda ya shafeni wlh sai na dau fansar dukan da ya dade Yana min idan na tashi ki hanani ko ki tsinemin" Hajara Bata ce Mata komai ba Dan tasan tana Kara magana tsaf zata zageta Safiyya mik'ewa tayi da kumburarren idonta ta yi waje Bata zame ko'ina ba sai gidan Alhaji Saad da isarta ta zub'e a gaban matar Alhaji Saad din ta hau cewa ta taimaka Mata da kudi zata tafi asibiti Yan fashi ne suka duro.musu jiya Suka musu shegen duka har hakorinta Suka cire Mata. Sosai matar Alhaji Saad ta tausayawa Safiyya ta shige d'akinta ta daukowa Safiyya kudin aikinta har da kari Tana mik'a Mata Alhaji Saad ya dawo shima ya d'auko kudi Mai yawa ya Bata sosai taji dadin alherin da suka Mata ta ringa musu godiya. tana zuwa gida cikin had'e Rai tacewa Hajara ta shirya Kayanta asubar fari zasu bar garin Kano Dan sun Gama zaman kano ba yanda za'ayi sai ta samu cikar burinta 'yan sanda suzo su Kara Kama su Hajara sosai taji dadin barinsu garin kano daza suyi Dan ta tsorata da kashedin da 'yan Sanda suka musu akan Naeema da Asubar fari kuwa suka dau hanyar calabar suka sauka a gidan Lami. tunda suka Isa Safiyya ta ba zama nemo musu gidan Haya Dan kudin da su Alhaji Saad suka Bata zai Isa su Kama haya sati daya sukayi a gidan Lami kafin Safiyya ta samo musu gidan Haya nesa da cikin gari Dan a wajen gari ta samo musu gidan Haya Dan Bata San kowa yasan Inda suke Kar ma ta Samu cikar burinta Naseer ko Naeema su zo nemansu. rufewar da idonta yayi da San ta ga bayan Naeema yasa suna koma gidan Haya ta hau neman bokan da zai Mata mugun aiki Akan Naseer da Naeema Dan sai ta samu cikar burinta zata samu kwanciyar hankali abinda ke Kara tunzurata da San ganin Bayan Naeema Bai wuce yanda Bashir danta ke jawo Mata magana da mugun satan da ko ita da Hajara Basu tsira daga wajensa ba Wanda dudu du Bai wani shekaru ne dashi ba ga mugun taurin Kai da rashin ji. ganin Dole sai ta samu kudi zata samu cikar burinta yasa ta nemi aikatau a wani gidan abinci da matafiya ke tsyawa su siyi abinci sai data samu wata uku kafin ta samu irin kudin da take so tuni ta cigaba da neman Mai Mata aikin Inda ta Dace da had'uwa da wani kungurmin boka arnen kan dutse da ya kasance bayarabe da ake Kira Oban ya azabar kwarewa akan mugunta Dan tsabar bakin mugunta idan yaso.yana iya maka aiki idan ka samu cikar burinka kafin ka biyashi kudin aikinsa Safiyya kamar ta taka rawa a lokacin da ya hasko Mata Naseer a Abuja wajen da yake aiki Naeema Kuma a gida tana girki Zahira data kwallafa yiwa mugunta a Aji suna rubutu Oban kuwa ya Kara da Gaya Mata abubuwa akan su Naeema cikin zallar mugunta da farin ciki Safiyya ta hau Gaya masa abinda take so ya Mata "Ina so Naseeru ya Zama kungurmin barawo inaso yayiwa wanan uban gidan nasa satar fitar hankali da zai saka Mai gidansa ya Kama shi ya kulleshi ya Kare rayuwarsa a gidan yari. ita Kuma Naeema Yarta Zahira Nan nakeso ayiwa turen bakakken Aljannun masu k'ona jiki da zasu ringa azabtar da ita suna zautar da ita su canja mata hallita daga na mutum zuwa wani siffa Mai ban tsoro Naeema ta Sha mugun wahala akanta duk Inda ta Kai da neman magani Kar ta Dace marasa Imani nakeso a tura jikin yarnya da har zai Kai ta ga Rasa ranta naso Naeema nayiwa Amma nasan nayiwa yarta na rabata da kwanciyar hankali kenan" wani mugun dariya Oban ya kwashe dashi yace aikin yafi komai sauki wani mudubi ya d'auko ya Bawa safiyya Yana "idan Kika je gida karfe dayan dare kiyi tsirara ki fito waje ki kalli mudubin ki Kira sunan Naseeru Sau uku.kina Gama Kiran sunan Naseeru Sau uku sai ki fasa mudubin karki yarda mudubin ya fashe sai daya Daren kinyi yanda na saka ki idan ya fashe Kan danki Bashir aikin zai koma" cikin murnar cikar burinta ta ce Masa zata kiyaye tana so ma ya taimaka ya Mata aiki akan Bashir din ya warke take ya d'auko ruwa ya Bata akan ta dafawa Bashir shayi dashi indai ya Sha zai daina satar kamar ta Masa Sujjada Dan murna ya Kara da "ita Kuma Zahira da kaina Zan tura Mata amintattun Aljannuna da sukemin aiki karfe dayan dare kafin Nan ki tashi ki Shiga d'akin duhun can ki tub'e gabadaya Aljannu zasu Miki aiki" Safiyya da fari taji tsoro Amma rufewar idon San ganin Bayan Naeema yasa ta nufi bakin kofar daya nuna Mata ta tub'e ta shige Oban kuwa yabi bayanta Dan Dama ba Kaya yake sawa ba da ganye ya rufe tsiraicinsa sosai yaci uban Safiyya dataji Kamar wuka ake.zurmuka Mata ahaka ta daure ya Gama ya fito ta fito kafarta a warware. ta zub'e Masa kudin daya cajeta ta dauki ruwa da mudubin ta nufi gida a k'ofar gida ta samu Hajara na soya kosai Dan kudin da ta samo a wajen Lami ta yanke siyar da kosai tunda Yana Dan shigo Mata da canji Dan indai ta dogara da Safiyya sai ta mutu da yunwa ahaka a kamfai dinta take boye kudin cinikinta Amma a banza indai Bashir yaso ya sata sai ya sace kudin karshenta idan ta gayawa Safiyya sai dai suyita fada. Bata cewa Hajara komai ba ta Shige gidan ta Dora ruwan zafi ta ringa gasa jikinta ba wani sauki taji ba murnar samun cikar burinta yasa taji bama tajin zafin a cikin farin ciki take sosai hakane yasa ko abinci Bata iya ci ba Hajara na shigowa bayan ta gama siyar da kosai ta tareta da labarin duk yanda sukayi da bokan cikin farinciki tare da nuna Mata mudubin cikin tashin hankali Hajara ta mik'e tana "Kina da hankali kuwa Safiyya kanki daya kuwa Mai Naseeru ya Miki da kike San ya Kare rayuwarsa a kulle karki manta fa Yayanki ne Kuma Dana Naeema da yarta muke San ganin bayansu ba Naseeru ba idan dai da Raina bazan yarda kiyiwa Naseeru komai ba duka kawai ya Miki na Kuma Baki hakuri kefa karki manta gidansa Kika siyar Masa da Raina wlh bazan Bari ki cutar min da D'a ba Amma indai Naeema ce Kam Nima sai Inda karfina ya Kare. murmushi Safiyya tayi ta fara k'ok'arin boye mudubin tana idan na tashi ki hanani cikin zafin nama Hajara ta kwace mudubin batayi wata wata ba tayi wurgi dashi Safiyya ta saki wani mugun karan tashin hankali tayi Kan Hajara Kamar ba uwarta ba suka hau dambe suna k'ok'awa. Hajara sai tsine Mata take Safiyya tafi.krfinta Haka ne yasa taci karfin Hajara ta Mata shegen duka ko a jikinta ta wurgo Hajaran waje da kayanta tana "wlh sai kin barmin gida sabida tsinannen danki Kika watsawa Dana rayuwa kin cuceni yanzu Bashir ne xaiyi satar da xaa kulleshi" "sai kin wulakanta Safiyya sai kin tozarta har na koma ga Allah adduar masifa da balai xan ringa Miki " Hajara tace tare da d'aukar Kayanta tayi gaba Safiyya kuwa cikin tashin hankali kafa ba takalmi ta yanka daji wajen Oban da zuwanta ta zub'e ya hau girgiza Mata Kai Akan ba abinda zai iya Yi akai sai wani shekarar zai duba kuka wiwi wiwi Haka Safiyya ta ringa Yi tana yiwa Hajara Allah ya Isa Hajara kuwa gidan Lami ta nufa sai data kwana biyu ta nufi tsohon unguwar su gidan da ta taso wato gidan iyayenta da suka rasu mugun halinta yasa ta watsar da kowa nata tasan yayanta ya rasu. Amma Bata San Inda Hassan da usaini kannenta suke ba su take so taji labari a kansu ko zasu iya taimaka Mata Haka ta karaci yawonta Bata samu labarinsu ba sai data shafe wata a gidan Lami kafin ta samu labarin zuwan Usaini da yayi aure Yana Kuma cikin rufin asiri shagonsa yazo dubawa dake calabar Hajara ta nufi wajensa afujajun Hassan da usaini suna sane da ita Sarai sun kuma San halinta hakane yasa Suka bar ma garin calaba gabadaya Dan sun San ko su Basu tsira daga wajenta ba sai dai Hajara ta shammaci usaini da zuwanta ta hau Masa koke koke akan sun watsar da ita a takaice dak'yar usaini ya iya Bata kudin da Bai taka Kara ya karya ba ya gudu Dan dayasan zai ganta ma bazai saka kafarsa a garin calaba ba shi a yanzu ma siyar da shagonsa zaiyi Bai zai Kara waiwaiyar garin ba sabida Hajara. da Dan kudin data samu a wajen usaini ta Kama wani mitsitsin daki ta cigaba da Sana'ar kosai tana Shan alwashin ganin bayan Safiyya har da Naeema Bata da makiya Kuma yanzu data wuce Safiyya da Naeema. kwana uku kenan Safiyya Bata saka bashir a idonta ba hakane yasa ta tashi hankalinta ta hau nemansa a yau ma Haka ta dawo daga nemansa Sam ko bacci Bata iya yi Dan tana tsoron Bashir yayi satar da xaa kulleshi. .duk da k'aramin yarone sai dai tana cikin tunanin taga an shigo da Bashir da ankwa a hannu da kafa an farfasa Masa jiki fuskarsa a kumbure..... comment : Uhmm wlh kuwa koni sis ni kam kwata kwata na kasa kata6u's a ciki 6allai nayi sharhi wlh Allah seriously nake gqya miki jiki,na har rawa yake hannu,na kuwa har karkarwa yakeyi wajen karanta,sa na rantse miki jiya har kuka nayi sssi jin sheheka,na yasa Ammy,na sukayi saurin xuwa gun tambaya'ta lfy anan nake 6asu lbr abun d yasani kuka sai ga Ammy,na ita ma d yinsa wlh d yayyu,na maxa har dasu a kuka muma lbrn ya tuno muna d ni d yayyu,na d Ammy,na lbrn 6akar wuyar d muma mu kasha 6abu kalar axa6ar d 6a'a gwada muna 6a har na talauci a ka ixo muna d 6akin jini sai daii Allah yanda y tsara rayuwa da6an domin kuw sa6anin 6akin jini sae farin jini d Allah y sako munq gami d saurin shiga rae Allah ba ya6on kaii ba d ni d yayyu na akaga hakn 6aiyu yu 6a wlh Allah kunji na rantse muku kunajin ana fadar duk wandq yaga aljanu asifarsu 6a'a koma kwana a duniy tom ni wlh nagqnsu ko ince mungansu dani d yayyu,na d Ammy mu ko Abbun mu yana ganinsu sai daii shi 6a kasafae ba sa6od shi matafiyi,ne aiki gwamnati yakeyi 6ai wancan gari bai wannan garin a cikin garuruwq afin ixaca Abuj toh idan yana a Abj 6a'a basa tsoro shi kum d xaran a kaga yayi tafiya tom'f a ranar, babu kalar tsoron d 6a'a bamu xamuga sun fito a mummunar halitarsu a6un xar tsoron ganin d uwayen jajjayen idonsu d hakoransu xat tsoron gani hakn xasu fito d sharbebiyar wukarsu wae ran mu daii d akace su dauka musmmm na Ammy mu shi suka xo su dauka ko ta halin kakaa wlh idan 6asu ci nasarar kaii muna wukar b sa6od maman mu 6ata wasa d addu'@ tom'f hakn xasuna ta dukan mu cike d mugunta d axa6a hakn camuna addu'a ga axaba bakin Ammy,mu ko bai ra6o d addu'o'e d karatun qur'ani a bakinta sannan'f idan sunji wuyaar addu'o'e su daii,na duk d a lokacin ina little girl sssi a cikin yan'uwa,na nite karama a cikinsu domn wani axa6ar nake iya tunowa wani ko 6ana iya tunosa sa6od qankanta ta sai daii su din anty's ko sun fada nake tunowa ke mu'f har takai ta kawo ko bayi ma wlh gagarar mu shiga yakeyi sa6od muna shiga wasu 6akaken halittta xamuna gani ko kum kaga mussoshi waton mage 6akake kiriin dasu d jajjayen idonsu kum sanye d kacha a kafafu nan su suna muna dry d gwalo ido su ko wani sa'in 6akin su na fidda wutaa jawur kum duk a 6ayi kum idan kin jiyo ki fita ba hali sa6od ga wasu nan sun tare kofar 6ayi diin uhmm addu'a,ce kawae ke fidda ke 😭😭😭😭 kum sis ko a6unci ba mu d ikon ci a waje ko a daki hakn xakiga magen nan suna ta watso muna kasa a ciki suna muna rawa d kachar su abun d bamu ta6a gani 6a wae mage d kacha humm kum wlh irin aljanunan d a ka turowa xahira hkn ne a ka turowa anty,nasu itama daga shigarta 6an daki shikenan sai kararta a kaji miyagun nan dakyar suka fice ta itama sai kinganta a6un tausayi Ammy,mu tasha wuyaa akan hakn ita ma duk ta rami dakyar dae suka fice ta sa6od ita ma Ashe tana d iska 6asu dai bayana 6a saii d wayan nan miyagun arna nq shige'ta su suka kwazga dacu d rokon Allah dakyar suka fice'ta 6ayan dukiyq tasha kashi ke muma'f har d sunannakin mi aka saka a laya dn mu tagayara damu har maman mu Allah 6ai nufa ba y tona asiri maman mu tagani d kanta miyagun aljannun d a ka ixomuna ne a gid sun gwada muna bane kaii har takaii ta kawo wlh kinsan tsarin nan d akeyi a gida a ke sawa na tsari har dashi a kasa Abbun mu yayi Ammn wlh miyagun nan marassa imani ke ciro,sa su aje masa abun sa a kofar daki ke fa ko daki xaki shiga idan basu so 6a cewa suke karki shiga dakin nan in kuw kishiga sai sunci u6anki ko su,ce karki rufe daki tom'f kikayi wlh sai kin ya bawa aya xakin'ta hmm duk yanda xan baku lbr nan xaka,na daukar kamr ba gaske,bane mu kadae mu kasan me muka gani ko mukaji wlh sis har dakansu d suke kina iya jiyowa gashi xamanin 6a'a san wani tayi'ss ba simuntin,ne akeyi iriin me sulmin,nan tom har dashi xakaji yana Amsa kuw sa6od dakansu a lokacin Abbun mu bayi 2 yayi d rixabuya maman,mu daii tasan lfy qlau ta kwanta can cikin 6accin ta taji an tsokale cikinta y dinga murda mata gashi 6ata son tadda mu 'ya'yan ta sa6od murnar ta mun samu yau an barmu munyi bacci d kum qarfin addu'a kingamu kamr wayand nasamu yan ci fitowa dagq wani kurkutu sin samu yan,ci hakn ne gun mu domn musamu munyi bacci sssi Ashe ace bakuwa xakuyi sa ba domn hakn suka sakowa mamn mu ciyon ciki gadan gadan a hankali ta dore bakinta sa6od kukan d yaxo mata na axa6a karta tadamu hakn cikin sanda tafito daki ta nufi bayi nan'f taga gari na juya mata hakn take kada kafarta tana axa kafa a 6ayin ana yanke 6ayin yana rusgawa ita dae 6ata d xato taji anfisgo'ta sae gata a gefen daki shikenan har rixa6uwar mu sae da ta rusga mukuwa tsawar ta taddamu gashi nice qarama a cikin su sssi sae er qanwa'ta dake bimun tagoyi jin wannan tsawar d aka 6uga,ne ta firgita mu muka kurma ihuu Allah sarki uwa mance ciyon d ke damunta tayi a guje tayo daki kanmu da addu'a lokacn Abban mu baya garI sannan kiji tsitss har d anty,na akaso kashewa 😭😭😭 hmmm kaii 6ari gsky komu munga rayuwa domn wani hakki sae inda Allah mu kam wacce taso ta Aure babqn mute tayi wannqn aiki ita d sauran makiya yan'uwanca masu 6akin cikin samun sa suka hada hannu d ita wurin ganin 6ayan mu dn ta Aure baban m dn acewarta baban mu yana sakarwa iyalinsa d ita yafi dacewq ba wamu ba d Ammy,mi 😭😭 [8/2, 3:53 PM] +234 810 713 7956: wlh ko wane dan adm d iriin tasa kalar rayuwar d rabbu y ru6uto masa wlh sai daii maganinta d warakar'ta addu'a CE domn kuw wayan nan d nayi muna hakn sunga karshen su tun anan duniyr kafi axo lahir wlh pg innan y tuno mina d namu qaddarr rayuwr d mu kayi mumq ta miyagu Allah ka isar miki ke ma xahira dake d umm naema wlh Allah sai y saka muku tun anan duniyr sakaya ke kqmasu insh Allah ni nace miki sae sun girbi shairin su d hannu musmmnb hegiyar nan safy ita d 6akar uwa hajr u6angiji y dibar muku hakkin ku tun a duniyr kafi aje lahir yayi muku hisabi d sakaya dae dai abun d suka gir6a Allah ni'ematar d rayuwarku advertisementUwargida da amarya harma da yanmata kuyi kokari kuma kumallaki sabulunnan daya tamkar dubu wato mg's herbal whitening black soap kunemi naku kujaraba kugani domin sabulun yayine bakarya Yana Repairing damage skin Ina Mai fama d pimples Black spot Sunburn Stretch mark Wrinkles Black head Dama dukwani matsala daya danganci fata wani abunma koda bakida komai you can still use the soap zai maida Miki fatanki luwai luwai kalar hutu😎 kunemi mg's kusha mamaki bazance komai b gani da ido ance yakoriji bama cika Baki jst gv it a try nd see for urself🥰 wise pupil nasan kunfahimci zncn👏 Amare Kuna Ina wnn🥰mg's yatanadarmuku soap nadaban duk wacce tayi using soap din Baku bukatar wani dilke kije aita dirjemiki jiki zakuga ynd skin dinki zaidinga haskawa Yana walwali😘 maiso yy mgn ta 08062991549 Call 08064532391 Muna maraba damasu siyan daya kosari maisokita glowing wani zncn dai sai kungani da idonku zaku sheda Har ilayau munada humra da turaren al'ajab na tsugunno maiban mamaki yahanzarta before yj sold out🥰be part of the glow gang say no to skn prblms🤭DNT be left behind Soap price:3k Pls kayanmu bn bleaching bn organic ne zaifiddomuku d ainihin natural beauty dinkune bn bleaching bn ko bakida komai you can use the soap zaikara gogemiki jikine fatanki tayi fresh Turare:3k Humra:2500 Maiso should chat 08062991549 Team glow skin🧖🏻‍♀️💋 [8/8, 9:54 PM] Zannura: *NAGA TA KAINA*      *NA SADNAF*🌸🌸 ®️ *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*          _{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_ *Free Novel* *Page 56*        Safiyya daskarewa tayi a tsaye jikinta ya kwashi mugun rawa data ga manyan bindigogi da 'yan Sanda ke rik'e dasu. Sunfi su goma kafin su karasa ma wajen Safiyya, Safiyya ta zub'e a kasa da kumburarren fuska Bashir ya nuna Safiyya Yana "ita na bawa Ajiya" Cikin inina Safiyya ta zaro idonta cikin  fad'uwar gaba tana "Ajiyar me ka bani Bashir'? Tsawan da aka daka Mata da mugun k'arfi daya kad'a mata yayan hanji ya sa ta kame bakinta da hannu Daya daga cikin Yan sanda ya Bawa sauran umarni Yana "ku Shiga ku hargitsa d'akin da kyau indai aka samu gwal da kudin to tabbas ita aka bawa ajiya tafiya zamuyi da ita" Safiyya ba damar magana sabida bindigar da aka Dora mata akai har fitsari ta saki a wando Dan kayayyakinta aka watso su waje Ana ta neman gwal din da Bashir ya sato daga shagon wani Mai siyar da gwalagwalai da akwatin kudi. Sai dai har aka Gama birkita d'akin ba'a  ga komai ba Dan abokanan Bashir masu irin halinsa ne Suka gudu da  kudi da gwalagwalan Bashir shi Kuma aka kamashi San a sake shi yasa yayi niyyar kulawa Safiyya sharrin ita ta saci kudin inyaso a cika shi ita a kamata. Bai tab'a Jin kaunar mahaifiyarsa a ransa ba hasali wani zubin zuciya Kan raya Masa abubuwa a kanta na ya Mata mugun abu ko ya ma kawo karshenta (Wanan Yana daya daga cikin asirin da Safiyya tayi daya jefa Dan cikinta a cikin wanan halin sanan nayi mistake sosai a wajen tsara rubutun labarin Dan sai da muka sake waya ta Kara fahimtar Dani labarin wajen auren Safiyya na Dan jinkirta shi a rubutun Dan Bashir din sa'a Minal ne  'Yar Naeema ta uku gudowar da Naseer da Naeema sukayi Kano a lokacin da ta haifi Minal a lokacin Safiyya tayi aure har ta haifi bashir Wanda ta ta sake samu ta  aura a shine suka siyar da gidan Naseer. Zawarcin da  Safiyya tayi  ne tare dasu ta tsula tsiyarta haka amma dai a karbi labarin Haka sabida ya tafi daidai tunda ban dai cire komai a game da rayuwarsu ba sai na Naeema dana dan rage sabida tsayin novel din zan dan Kara bada labarin Safiyya a takaice sabida labarin ya tafarmin dai dai Kar dai ku rikice sai da Naeema ta bibiyi labarin taci gyarana) Dan Sandan umarni ya bada a tafi da Safiyya a hada a kullesu tunda har Bashir din yace  Yana Bata ajiya ya zama dole itama a bincike ta da kyau dan bashir ce musu yayi idan yayi satar ita yake bawa ajiya. Wani irin ihu Safiyya ta saka a lokacin da taga ana k'ok'arin saka mata ankwa ko sauraranta basuyi ba. Suka buga Mata gindin bindiga da suka ga tana tirjewa suka sa.mata ankwan Suka zuba su a mota ita da Bashir Sai kuka Safiyya take tana rantse rantse Bashiri bai bata ajjyar komai ba. A takaice sai da Safiyya ta Sha bak'ar wahala a hannun 'yan sanda ta Sha bak'ar duka daya canja Mata kamani Dan Bashir dagewa yayi akan ita ya Bawa ajiya kudin. Sai data samu wata guda  a kulle kafin wani dan sanda dayaji Safiyya ta kwanta Masa ya taimaka wajen bincikar Bashir din ta hanyar rarrashinsa ya fada Masa gaskiyar wayanda Suka gudu da gwalagwalan da kudi. Sai da aka kamosu aka saki Safiyya da kyar. Safiyya kuwa masifar da Bashir ya jefa ta a ciki yasa ta Kara kullatar Hajara a ranta ta ke Kuma Kara Shan alwashin ganin bayan Naseer da su Naeema tunda Dan Naseer Hajara ta fasa mudubin daya jaza wa danta wanan masifa da ita kanta a rayuwata Bata had'a San Bashir da komai ba. Hakane yasa da fitowar ta ta koma wajen Oban ko zai iya taimaka mata a saki Bashir sai dai duk yanda Suka Kai da suyi aikin ba'a sake shi ba. Akan dole ta hakura ta saka aka mata aiki akan Ado dan sandan dake santa. Nan da nan kuwa ya fito ya aureta a madadin ya sata a gidansa sai shine yake zaune a gidanta da Sunan zai cigaba da biya Mata haya. (Karku rude a takaitacen labarin Safiyya nake Baku Aurenta na fari ta haifi bashir na biyu data tayi ta siyar da gidan Naseer ta haifi Asmau da   Safiyya wacce aka sawa sunanta. Mijinta na fari Saki uku ya Mata daya gano asirice shi tayi ya Aureta Na biyun Kuma data haifi Yan biyun barinsu tayi a can wanan sai da suka  yi wayo ta sa aka Mata aiki akan Umar ta karbo su daga wajensa  ta rik'e su  amma tabbas Bashir asirin Satan da suka so Zahira tayi shine ya Sha alewar daya saka shi satan bandai canza komai ba dafatan Kun Gane mu cigaba da tafiyar da labarin ahaka karku rikice laifina ne Dan yanzu idan na cigaba a haka kuka ga na Sako Asmau da Safiyya yaran Safiyya a labarin zaku rude bazaku gane ba shiyasa na baku labarin Safiyya a takaice) Sosai Safiyya take Jin dadin irin wahalar da Zahira take Sha ita da Naeema da Naseer karewar komai da naeema ke dashi yafi komai faranta Mata da zata samu ma abinci ma so take ya gaggaresu ci Ko sau daya batayi nadamar abinda tayiwa Hajara ba hasali duk lokacin data tuno halin da Bashir.ke ciki a kulle takan ji kamar ta nemo Hajaran tayi ta dukanta sosai ta saka Hajara a jerin makiyanta tsabar masifa ma tana sane da duk halin da Hajara ke ciki. Haka ma tana da labarin halin dasu Naeema ke ciki dan takanje wajen Oban yayi surkulle ya nuna Mata su Taji dadi sosai da Aljannu ke fita daga jikin Zahira idan za'a Mata rukiyya sai an Gama azabtar da  Zahira angama rukiyya Aljannun ke komawa jikinta. Taso ta Kara yiwa Naseer asirin Dan ta mugun tsanarsa sabida Hajara data ga bata  so wani Abu ya same shi,sosai ta Sha alwashin ganin bayansa dan har yanzu da tab'ab'unan dukan Naseer a jikinta. ta dan dakata  ne kawai Dan wahalar da suke Yi da Zahira har filinsa da ya siyar akan nemawa Zahira magani ya faranta mata sosai  burinta ma gidan Naeema shima su siyar a garin nemawa Zahira magani dan tasan kome za su yi bazasu Dace  da samun  magani da zai yiwa Zahira aiki ba. Auren ado da tayi ma ba Wanda yasani balle Hajara ta sani Ahaka har ta haifi yarta hauwa da itama taji tana balain Santa takan tuna yaranta asmau da Safiyya dake gidan Umar har jibi tana Kan bak'anta nasan ganin Bayan Hafsa da ta azabtar da ita a gidan umar. Sati sati take zuwa wajen Oban dan taga halin da su Naeema ke ciki A lokacin da asirin da tayiwa Zahira ya Kai  shekara da wata  uku Oban ya daina iya ganin komai akan su Naeema sosai hankalinsu ya tashi daga shi har Safiyya Oban yayi ta tsubbuce tsubbuce dan yaga halin da suke ciki sai dai har ya gama tsubbunsa bai iya ganin komai ba A lokacin kuwa Naeema ta had'u da Inna Amina har rabbi ya amsa adduarsu Amina tayi nassarar fitar da Aljannun daga jikin zahira. Safiyya tunda  Oban ya daina ganin halin da su Naeema ke ciki  hankalinta ke tashe ta tuna lokutan baya da idan suka yiwa Naeema wani mugun abu toh mudin suka daina ganinsu ta mudubin tsafi toh Naeema ta samu mafita ne tana tsoron aikin da tayi akan Zahira ya dawo mata. A haka ta kasance cikin Zullumi yau da safe Ado ya fita aiki da sassafe ta gama dan aikace aikacen gida tayi wa hauwa wanka da  bata fi wata biyu ba lokacin. Tamkar gwal take Jin hauwa a ranta Tun bata girma  ba take cin burin girman ta idan tana hararo girmanta har farin jinin Zahira take hango Mata da irin masu kudin da zasu ringa layi akanta idan kuwa Asmau da Safiyya suka dawo gabanta har maganin farin jini zata karbo musu dan sosai taci buri Akansu suma duk da basa gabanta tana balain Kaunar yaranta da bata San wani abu ya tab'a Mata su babban burinta yanzu ma ta Samu Bashir ya fito daga gidan yarin. Tana kitchen  tana k'ok'arin juye tuwon data dumama dan taci taji  hauwa ta fara tsalla kuka aguje ta fita daga kitchen din. Abinda ta gani ne yasa jikinta d'aukar rawa hallitar hauwa ne ya canja gabadaya ta koma wani irin hallita wuyanta ya kumbure exactly yanda Zahira ta koma Kamar wata kadangare haka hauwa ta dawo hankali a balain tashe Safiyya ta saki ihu tunaninta na bata Aljannun zahira ne suka dawo.mata jikin 'ya. Bata iya daukarta ba sabida zafin da jikinta ya d'auka ta hau kuka ta nananada Hauwa  zaninta  kafa ba takalmi tayi wajen oban. Tana zuwa ta zub'e a kasa ta ajiye Masa hauwa da siffarta ya Kara Zama na kadangare sosai Ihu take akan Oban ya taimaka Mata. Oban kuwa take ya hau surkulle Yana yare da shi da Aljannun jikin  hauwa kawai keji. Sai dai duk yanda Oban yaso su bar jikin hauwa k'i sukayi akan ba haka akayi dasu ba har sai sun kwashi shekarun da akace suyi tun farko. Oban kuwa baya so nunawa Safiyya ya kasa fitar Mata dasu hakane Yasa ya yanke Mata kudi Mai yawa akan ta kawo akwai Abubuwan da zai siya  ya roki Aljannun su fita dan zuciya sukayi sabida matar data fitar dasu ta kokona su. Safiyya hannu ta dora aka ta hau zunduma ihu tana ya taimaka Mata bata da ko sisi ado tana aurensa ne kawai Amma ba kudine dashi ba dan matarsa ke karbe albashinsa. Matarsa Kuma ta fita hatsabibanci tunda har Oban ya kasa aiki akanta kasancewarta itama bayarabiya. Ba Inda Safiyya bata je neman kudi ba amma Bata samu ba tayi kukan ta tsinewa Naeema da Zahira yafi cikin kwando Ado kansa guduwa yayi daya ga yanda hauwa ta dawo dan sosai ya tsorata da yanda hauwa ta dawo dadin daya ji Safiyya dama bata San  gidansa ba dadin dadawa ma Dama Yana neman hanyar da zai gudu sabida kudin hayan da Safiyya ke damunsa da ya biya. Sosai Safiyya ta rame ta kanjale a madadin taji tsoron Allah ta yarda Allah ke Kare Naeema tunda duk abinda ta nufeta dashi kanta yake komawa bata ga haka ba zuciyarta k'ek'ashewa tayi tana dora alhakin duk abinda ya sameta Akan Naeema da Naseer har da Hajara  sai Kara kula wani sharrin take Ta Kara komawa wajen Oban cikin tsananin san dai ta ga bayan Naeema da Naseer Ta karkace ta hau gaya masa abinda take so dan gani take ta haka kawai zata dau fansar yanda yarta ta dawo da ita kanta take fita aguje sabida tsoratatan da take yi "Kayimin aiki Mai k'arfi Oban inaso na ga bayan Mutanen nan duk Inda kudi suke Zan nemo na kawo maka "tunda Aljannun da aka tura jikin Zahira sun bar jikinta inaso a tab'ata inaso ta sakawa Naeema hawan jini Kar tayi albarka Sam tayi bakin jini Kamar ungulu ta tsufa a gaban Naeema. Shi Kuma Waleed dinan dana ga Kamar shine zuciyar Naseer inaso ya lalace a saka kiyayya tsakanin shi da Naseer a karshe Naseer ya zama ajalinsa Yan sanda su kulleshi. Oban kayi min wannan k'ok'arin ni Kuma duk abinda kakeso Zan maka tunda har 'yata hauwa haka Zan ringa ganinta zuciyata na ciwo inaso zuciyar Naseer da Naeema yayi bindiga bana San aikin Kuma ya karye duk Inda zasu Kai ga neman taimako" Mugun dariya Oban ya kwashe dashi ya d'auko wasu allurai da kwarya ya Bawa Safiyya yana ta jejjera alluran a ciki ya d'auko wani Abu kamar bby na namiji da mace yace ta binne akwai Wanda zaiyi daga Nan indai ta binne aikin gama ya gama Amma fa idan har akayi nassarar karya asirin duk wani Abu da zai biyo baya tayi kuka da kanta. Batare da tunanin komai ba tace ta amince sabida mugunta tace sauran yaran naeema ma a tab'a su. Sai da ta kwana da Oban ya ci ubanta yanda ya kamata ta dawo gida tayi zazzabin sati guda kafin ta samu karfin neman abinyi tunda ado ya gudu Ta dai saka Oban ya Mata aiki Dan ya dawo. A Haka ta samu ado ya dawo ya Kuma biya Mata haya. Halin da take ciki da hauwa da ita Gata kamar dabba Kamar mutum yasa ta nemi kudi taje unguwarsu Umar tsohon mijinta a lokacin data Isa Bata sameshi ba sai Hafsa. Yaranta duk sun tafi makaranta,Asmau da Safiyya nata zuba aiki kamar jakai yaran nata sun girma Masha Allah Kuma kyawawa kamar yanda taso ganinsu. Sai dai kana ganinsu kasan a wahalce suke dan Hafsa ba k'aramin azaba take gana musu ba. A takaice Hafsa k'in bari tayi ta kwashe yaran sai da suka ci uwar dambe Safiyya ta Sha kasa dak'yar da kyar Umar daya dawo ya samu Hafsa ta Bari Safiyya ta tafi dasu dan shima kasan tausayin yaran yake ji uwarsu ya tsana Amma Yana san yaransa tausayin yanda hafsa ke gana musu azaba yasa yaji dadin zuwan da Safiyya ta yi dan ta tafi dasu at least zasu samu yanci a wajen Mahaifiyarsu. Safiyya sai da umar ya Bata kudi Kafin ta yarda ta tafi  da yaranta da takejin zuciyarta fari Kal da dawowarsu gabanta. Hajara Sosai take Shan wahala da kosai da take siyarwa Bata da burin daya wuce ta samu kudi ta fara tab'a Safiyya da take Shan alwashin ganin bayanta ba ranar da zata wuce Bata tsinewa Safiyya ba takan Yi kuka idan ta tuna  irin korar Karen da Safiyya ta Mata Wai ace Yar cikinta data fi so duk a cikin yaranta itace ta daketa har ta koreta daga gidanta yau badan usaini kaninta ba da Bata da wajen da zata zauna lami ma Mai taimaka Mata kad'an kad'an itama ta bar garin calabar. Mai taimaka Mata a cikin yaranta Kuma Naseer ne shima Naeema ta kwace shi ya Fifita Naeema akanta Shiyasa a rayuwata ta tsani Naeema takejin itace duk ummul abaisin daya saka ta tsinci kanta a cikin wanan halin dan da ta rabu da Naseer cikin sauki da bata kai ga aikatawa Naseer Abunda ta aikata Masa da har yazo ya shafeta tafi Shan wahalarsa ba tunda da ace Naseer nada kudinsa da yanzu Yana da gidaje ya Kai uku tunda ada din ma ya mallaka Mata gida biyu. Ba abinda Naseer baya Mata Amma Naeema ta Mallakeshi ta rabata da danta Tijjani kuwa dama kullum cikin yi masa baki take tunda har ya Fifita Murja a kanta a wajenta Kam yaranta biyun Nan Tijjani da Safiyya idan tana da dama sai taga bayansu ba ma kamar Safiyya da take Jin da tana da dama kasheta zatayi tsaf abinda ke take Mata birki kawai shine kudin da bata dashi. Da zata iya samun damar da zata Shiga  wani  kungiya da ta  Shiga  dan ta samu cikar burinta da ta  saka an maidawa   Naseer arzikinsa. Ta rabashi da Naeema ta azabtar da ita da Zahira ta wahalar da Safiyya Murja da Tijjani a rayuwa sai dai ko kudin arziki Bata dashi kudinta ma yanzu na cinikin kosai a magani yake tafiya Dan fama take da wani irin ciwon kafa dake hanata bacci ta Rasa Mai ya haddasa Mata ciwon kafa. Tijjani Talauci da tsananin rayuwa yasa baya iya neman Naseer yanzu Dan wayar gari yayi aka koreshi daga aiki duk Kuma buga bugan da zaiyi baya iya samo ko sisi. Sai Murja ce ke dan iya rike gidan shima cikin wulakanci Sam Baya lallaba murjan tana Masa iskanci ko gori zai nada Mata na jaki ya Kuma bar Mata gidan Yanzu haka yaransu hudu duka Mata bayan yarsu ta fari ta Kara haihuwa uku da kusan kansu daya gwanin shaawa yaran Murja ko kuda Bata so ya tab'a Mata Yara Allah ya jarrabceta da balain San yaranta shiyasa duk Inda kudi suka shiga tana k'ok'arin nemowa dan ta farantawa yaranta Rai. Mahaifiyarta Rabi a haihuwa yarta ta uku Allah ya Mata rasuwa ta hanyar Hatsarin mota sosai Murja tayi kukan rashin ta. Yaranta kawai da take gani ke faranta Mata rai ko  a makaranta aka tab'a Mata su sai taje tayi masifa tayi balai ko yaran makota ne Suka tab'a Mata Yara sai ta Rama musu. Yarta Murja data ci sunanta  nada shekara goma  Mai bi Mata Ramlat nada shekara takwas  Fareeda na shidda sai ummi nada hud'u. Tashin hankalin da Murja ta fara fuskanta a rayuwarta Bai wuce rashin lafiyar da yaran nata suka fara lokaci guda ba Kamar ta zauce sabida tashin hankali Banda Murja takwararta Ramlat ce ta fara amsa Kiran Mahallicinta Inda Murja sai da aka dangana da kaita asibiti sabida sumewa tayi tayi Sati biyu kafin ta Gama dawowa hayyacinta  fareeda itama tabi Bayan Yar uwarta hauka tuburan Murja ta kusa yi sai da Karfin adduoi ta dawo daidai Fareeda itama satinta uku ummi tabi bayanta. Rasuwar yaran Murja uku yasa Murja ta dan samu tab'in hankali kad'an Amma ba sosai take tab'a haukan ba takan Yi Abun marasa hankali (Inaso na Dan bada labarinsu Suma gajerce Dan wlh na gaji Bai xama lailai na Kara tabo bagarensu ba Dan yanzu Haka ma daga Naseer har Naeema ba labarinsu sukeji ba tunda suka je suka nemi yafiyar Naeema dasu Zahira.) Bayan yaranta uku sai data Kara haihuwar biyu sai sun girma ta shaku dasu sai su koma ga Allah a irin haka yasa daga Tijjani har Murja Suka bazama neman taimakon Mallamai anan wani ke cewa Murja taje ta nemi yafiyar yaran data zalinta a baya sai ta nemi yafiyarsu zata ga daidai (Ba fiction a labarin zalincin da Murja tayiwa su Zahira da Kuma jarrabtar da Allah ya Mata a rayuwa na rasa.yaranta idan ta haifesu bamu sani ba ko ta Kuma haihuwa Dan tunda sukaje suka nemi yafiyar Naeema baa Kara Jin labarinsu ba) Naeema Samun saukin da Zahira tayi Yana cikin Abubuwan farin ciki da suka sameni da bana mantasu Haduwa da Inna Amina danake Mata Kallon Mahaifiyata dagani har Naseer shima Yana cikin Abubuwan da har gobe bana mantasu. Inna Amina tsohuwa ce Mai tarin ilimi dan Zan iya cewa har tafi Naseer ilimi shigowarta rayuwarmu yin Allah ne dan ta silarta na Kara samun warwarewa wasu matsalolinmu  ba iya ni kadai ba har Naseer. Satinta uku a gidanmu bayan tafiyar su Nadeeya makaranta muka Shiga wajenta dan mu gaisheta Zamanta a gidanmu yasa nake Jin kamar ita din wata garkuwa ce a garemu gabadaya Dan tace Mana zama Bai Kama mu ba makiyanmu zasu cigaba da bibiyarmu da sharri Addu'oi ta bani da Naseer take akan mu ringa yi daga mu har yaranmu. Zahira kuwa sabida ramar da tayi da kuma shiru shirun da takeyi yasa Inna Amina tace mu bari ta dawo daidai sosai ta samu wata uku tana Shan magungunan data had'a Mata kafin muyi tunanin Mai data makaranta. Hakane yasa muke kula da Zahira dagani har Naseer muke ririta ta. Nidai gani nake duk da sun fita kamar yata Bata dawomin yanda take ba Kamar  da da   nayiwa Inna Amina magana cemin tayi kar na damu zata dawo daidai mu dai cigaba da Bata maganunanta Koko da kosai da take Sha a lokacin da muka Shiga d'akin nida Naseer tana ganinmu ta saki murmushi muka zauna akan tabarma ita Kuma tana daga Kan katifa Sai data karasa kokon  ta ajiye kofin muka hau gaisheta Cikin faraa ta hau amsawa tana saka Mana albarka Kamar yanda ta Saba wanan albarka da take sa Mana da gamawa da duniya lafiya da take mana adduarsa ba karamin faranta mana Rai yake ba Sai da ta Gama saka Mana albarkan cikin murmushi ta kalli Naseer tana "Babana yaushe zaka koma wajen aikin naka ne kasan zaman Haka bazai yiwu ba" Murmushi Naseer yayi cikin Jin dadin kulawarta inama baiwar Allah nan ce mahaifiyarsa "Mama Abunda yasa bazan koma ba nasan Indan na koma ma korata zaayi dan na kusa shekara Kinga banje ba Batare da na Kuma Gaya musu dalili ba hakane yasa nake neman aikin anan ko Allah zai saka na Dace na samu idan ma ban samu ba Zan ringa aikin ginin da nake yi abaya" "Karka damu ka koma insha Allahu ba Abunda zai faru kana tare da Addu'a ta daukaka ma zaka samu" "Zan koma.insha Allahu mama ngd" "Mamana ke kuma wane sana'a zakiyi kinsan zaman haka ba dadi"? "Nasani mama kudi nake nema wuyanta na samu kudin bazan rasa sanaar da zanyi ba" "Allah ya dafa muku ya muku albarka ya yiwa yaranku albarka yanda Kuka taimaka min Allah ya taimake ku" Cikin farinciki muka hau amsawa da ameen sosai adduar da take Mana ke Mana balain dadi a zuciya. Washegari kuwa Naseer ya nemo kudi ya hada kayansa da zumar washegari zai tafi Muna zaune gabad'aya mu da yamma muna Hira da yaranmu a can gefe Kuma Inna Amina na zaune. Waleed nadaga Gefen Abbansa Yana Masa Magiyar ya tafi dashi Abujan gobe. Hannayen Waleed ya ruk'o cikin so da kaunarsa sosai yake Jin kaunar Waleed a Ransa sabida hankali da tarbiyya da Naeema ta bashi ga tausayi kamar me a islamiyya da Boko shi yake zuwa na daya Yan unguwar kuwa duk sun San Shi sabida sharan Massallaci Haka suke saka Masa albarka. "Idan ka bini Waleed ya zakayi da makaranta kayi hakuri idan ka Gama primary sai na nema maka secondary acan sai muyi zamanmu ko" Gyada Masa kansa yayi Ya kalli Nadeeya dake ta fama da.booklet tana karatun pass question papers Dan shirye shiryen exams din waec suke. Mita kawai take akan Bata iya Zane ba Naseer na Mata dariya a hankali ya ringa tambayarsu game da karatunsu Hankalina na wajen Zahira dake gefe tayi shiru ta kurawa waje daya Ido sosai tausayin yata ke dawainiyya dani dan badan wanan larurar bama da yanzu kila ta samu ma admission ko tayi aure Allah yasan su Umma sun cutar Dani said dai Allah ya saka Mana. Yata duk ta Zama shiru shiru Dan dai Inna Amina na Dan kwantar min da hankali akan Kar na damu zata dawo daidai Wuyanta ta gama Shan magungunan ta sosai na matsu ta dawo daidai na nemi kudi na biya Mata waec itama dan bana San kannenta su Mata nisa. Sallamar Tijjani da matarsa da yarsu ne yasa muka d'ago Naseer cikin farin ciki yaje ya tari Tijjani Dana ga yabi yafice a cikin hayyacinsa ya rame sosai bashi kadai ba har matarsa. Nadeeya mik'ewa tayi da Sauri ta shige daki Bayan ta gallawa murja harara Ni kuwa na hade Rai sosai Dan ban manta abinda tayiwa yarana ba har gobe da tabon dukan da tayiwa Zahira a jikinta,Nadeeya lokaci lokaci tana fama da ciwon ciki Mai tsanani sabida sabulun data ringa Bata a wake a gaskiya bana Jin Zan yafe Mata zalintar data yiwa yarana. Ban amsa gaisuwar datamin tana rau rau da Ido ba illa Tijjani kawai Dana gaisar Su Minal duk gaisheta sukayi Zahira itama ta gaishesu cikin sanyin murya. Kuka Murjan ta fashe dashi tana nuffar wajen Zahiran ta kamo hannayenta tana "Bayan duk abinda na Miki har inada mutunci a idonki da Zaki gaisheni bayan duk zalintarki da nayi bayan horar yunwa Dana Miki Zahira har ki iya gaisheni Dan Allah dan annabi ku yafemin keda Nadeeya wlh hakkinku ke dawainiya dani Yarana biyar Dana Haifa na shakku dasu mutuwa Suka yi sabida zalintar Dana muku na biyewa San zuciya ta Ina ganin ku ba yarana bane Dan Allah Zahira ki yafemin mmn Zahira ki yafemin Abban Zahira kaima ka yafemin wlh sharrin shaidan ne" Kuka take sosai cikin sheshek'ar tana bamu labarin yanda yaranta suka koma ga Allah take Kuma naji zuciyata tayi laushi tausayinta ya rufeni Zahira yata Yar albarka take tace Mata ta yafe Tijjani godiya suka hau mata Nima nace na yafe Dan Alhamdulillah tun a gidan Duniya Allah ke hisabi Murja a gidan Duniya Allah ya hukuntata Duk yanda mukayi da Nadeeya ta fito kin fitowa tayi Murja kuwa ta bita har d'akin Ta.kuwa shige bandaki ta rufo k'ofar tana "wlh bazan tab'a yafe Miki ba kin cutar damu batare da mun.miki komai ba kin bani sabulu a cikin wake kin Mana horar yunwa har yau Ina fama da ciwon ciki sabida sabulun da Kika bani naci wlh bazan yafe ba" Ta karashe tana kuka." A Haka Suka Mana Sallama Suka tafi batare da Nadeeya ta fito balle tace ta yafe ba sai Naseer ne ya kwantar musu da hankali akan Kar su damu zata yafe a hankali A waje Naseer da Tijjani Suka kebb'e Suka bawa juna labari halin da duk suka tsinci kansu a ciki Sosai Tijjani ya tsorata da hajara har Safiyya yacewa Naseer ya zama Dole ya Kara nisantar su Dan shi yanzu kaduna zasu koma zai nemi aiki a can ko zasu Dace Sai da suka tafi Naseer ya dawo yayi ta yiwa Nadeeya fadan Abunda tayi sai Inna Amina ce ta saka Baki bayan tayiwa Nadeeya naseeha kafin ta iya cewa ta yafe. Washegari da sassafe Naseer ya tafi cikin Ikon Allah kuwa Basu koreshi ba suka Karbeshi. Bayan tafiyarsa da wata biyu na fara lura da canji a wajen Yata Zahira na farko Bata San tayi sallah sanan abu kad'an sai ta hau yiwa kannenta masifa tana neman dukansu idan kuwa nayi magana sai ta dakamin tsawa Ba iya Zahira ba har Waleed na fara lura da canji a halayensa....... *Wlh Nagaji alhamdulillah duk sakon danake ya isa a gane an dauka a novel dinan yanzu maganar da nake labarin Naga ta kaina bashida karshe gaskiya Dan Haka a iya Inda aka bani labari anan Zan tsaya baifi saura 3 to 4 pages ba page 60 Zan tsaya idan Allah ya bani iko* *Comment* Dn Allah ki boyeni shiyasa n biyoki PC Namiki Nawa bayani koni antabamun wani Abu d yasa arayuwa nakara gasgata kada ka tsananta soyayya HK km kada ka tsananta kiyayya nima antabamin wani asiri saukarmin d jini saedae shekara cif Ina zubar d mini tsawon shekara dinnan baitaba tsaya dai dai d second daya ba cinyoyina hr sillewa sukayi sukayi baki km indai zan tsaya d namiji Wanda b muharramina ba zuban jinin zai karu ainun aka km aka hanani nutsuwa dmin kuwa zuciya ta kmar ana huramun Wuta kullum saena dingajin kawae na gudu n bar Gidan km al'amarin ubangiji hk aka dauke hankalin mahaifiyata akaina kwata a filli bata damuwa d halin d nk cikin saedae itama tayi ta rama alamun wani Abu n damunta arai gashi idn dare Yy bazantaba iya bacci ba hk zanyi taji motsi km nidin n kasance irin Yara masu kiba dinnan ne ainun amma duk saedae n kare n rame tas ta ynd idn akacemiki n nayi wannan kibar zaki karyata saeda na shekara cur Allah y budi Bakin mahaifiyata t fadama mahaifi na washegari d nj agaisheshi hankalinsa y tashi ainun toh akwae abokin babana a office babana Yy masa zancen t sanadinsa akasamamun magani mai maganin yace duk me wankekken ido toh zaifadamusu hayaki ne yake FIta ajikina dmin ansone n haukace sbd mahaifiyata tana sona acikin yaranta toh idn an watsar d rayuwata baxata taba samun nutsuwa ba saukin abun shine ni bana wasa d addu'a km lkcn ma ba Waya amma idn zan kanta xansa cassette a radio inajin karatu hr nayi bacci toh wannan abun shiya takaita guduwa ne n bar Gida amma agari mutane hr sunfara kirana mahaukaciya SBD ni daya HK zakiganni INA t Fada kokm INA tafiya INA surutu some some hauka😭😭😭 kai jama'a duniya INA zaki samu aranda n fara magani wani ikon Allah aranar n fara bacci koma saenakejin wani Abu me nauyi yn sauka kaina dafarko km Neman magani hr wani mutumin Ghana saeda y ban amma dif masu magani yn uwan mamana hr suka gaji d nema mun magani tunda lkcn mamana hnklin ta Baya kaina Masha wahala ainun. [8/10, 9:30 PM] Zannura: *NAGA TA KAINA* *NA SADNAF*🌸🌸 ®️ *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_* _{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_ *Free Novel* *Page 57* Ina yiwa Zahira uzurin kila Aljannu da suka Shiga jikinnta suka fita ke haddasa Mata saurin fushi da kunci da take yi kwana biyu Hakane yasa na cigaba da lallab'a ta Yau da safe Bayan yarana sun gama shirin makaranta sai na ga Waleed a madadin ya saka uniform d'insa bayan ya ga ma cin abincinsa sai Naga ya koma d'aki ya kwanta. Nadeeya da Minal Basu iya jiransu Humaira ba suka tafi dan ba makarantar su daya ba. Humaira da Raheema da Waleed ke makaranta daya yanzu haka Waleed da Raheema ne kawai a matakin primary. D'akin na Shiga cikin mamaki uniform din da bai saka ba ya shige daki ya kwanta gasu humaira sun shirya alamar shi suke jira "Kai Waleed ya baka saka uniform dinka ba kazo ka kwanta"? "Ba zanje makarantar ba yau" "Dalili baka da lafiya me"? Nace cikin mamaki ma yanda yamin magana Yana wani fusgewa "Lafiyata Lau banyi niyyar zuwa bane kawai" "Kana da hankali kuwa makarantar dama sai anyi niyya ake zuwa yau Mai ya Shiga kanka ne ka tashi maza ka saka uniform dinka kafin ranka ya b'aci" Na karashe cikiin b'acin rai Ina mamakin abinda ya canza Waleed ya dawo haka yarone Mai ladabi da biyayya hasali ma yana riga yayyensa shirya wa idan zasu tafi makaranta duk ranar da kuwa ya min laifi raina ya b'aci haka zai ta bani hakuri yana bazai sake ba har sai yaga na saki fuskata yake kyalleni Ga mamakina Waleed din ke min magana Kamar da sa'arsa yake magana a madadin ya tashi yabi umarni na ya hada da bani hakuri ma kamar yanda ya Saba sai Kara gyara kwanciyarsa yayi. Inda naji raina ya balain b'aci banida saurin duka Amma abinda yamin yasa na isa wajensa tare da janyo wayar heater na tsulla Masa ya mik'e da sauri Rai a had'e ya rik'e wayar Yana wani hucci Kamar zai kawo min duka "Nifa bazan je makaranta ba gaskiya Kar a takura min" Kamar ya buga min guduma.haka naji rawar da jikina keyi yasa ya sakar min wayar yayi waje batare da na iya Kara tab'uka komai ba. "Umma mu fa Waleed na Bata mana lokaci yau bazai je bane mu tafi"? Munga ya fita batare da ya saka uniform ba Dak'yar na iya magana Ina "Kuje kawai Ina ga yau bashida lafiya" Da sauri suka fita ni kuwa na koma na zauna Ina mamakin canjawar da Dana yayi tunda na haifeshi bai taba min haka ba na kasa yarda ma a hayyacinsa yake. Ko dai shima Aljannu ne suka shiga jikinsa bansani ba Mik'ewa nayi Rai ba dadi na nufi wajen Inna Amina da ban samu Shiga ba tun safe dan dama sai na gama sallamar Yara sun tafi makaranta nake Shiga wajenta da abinci karyawarta Su Nadeeya na iya k'ok'arinsu wajen kulawa da ita dan ko band'aki zata Shiga su suke taimaka Mata ta Shiga tayi uzurinta tunda kafarta na ciwo. Har wanka ma wani zubin su suke mata sai dai idan basa nan.nayi Mata Ban ma yi Sallama ba sabida tashin hankali da nake ciki tana zaune ta jingina da bango tana jan carbi da har a bacci ma bakinta motsi yake tana sallati da istigifari A gabanta na zauna na sunkuyar da kai. Ina Jin ta idda sallatin da take na dago na hau gaisheta Bata amsa ba damuwa bayyane a fuskarta tace "Mamana lafiya kuwa ya naganki haka Mai ke damunki"? ina jinta a raina sabida yanda take damuwa da damuwata ko Yaya nake cikin damuwa tana ganewa Sai dana share hawayen daya zubo min nace "Mama Waleed a yan kwanakin nan naga ya canja min Kamar ba Waleed Mai sanyi hali da ladabi da biyayya ba Mama kema shaida ce a dan zaman da kikayi nasan zaki fuskanci halinsa yarone Mai gudun fushina Mama wai yau ni yaron nan yake yiwa rashin kunya har Yana Kar in takura masa bazai je makaranta ba iya wanan bai Isa ba sai daya galla min harara Mama Kamar ba Waleed Dina ba ya canza gabad'aya" Na karashe Ina fashewa da kuka Mama cikin damuwa ta hau kwantar min da hankali tana "karki damu mama na kila ya fara haduwa da mugayen abokanai ne ko Kuma wani abu ke damunsa bamu sani ba ki share hawayenki ki bar damuwa idan ya shigo Zan Masa magana ai bai tab'a Miki haka ba ki bari mu bincike shi a hankali muji mai ke damunsa" "Mama ko shima Aljannun ne Suka shige shi wlh ba haka Waleed yake ba Zahira ma mama Kinga tunda Suka bar jikinta bata koma yanda take ba itama yanzu wani irin hali ta koya kina cemin mu bita a hankali,mama Ina tsoron wani abu aka yiwa yarana ba abinda umma da Safiyya baza su iya aikata min ba bare idan sunga alamar anyi nassarar cire Aljannun daga jikin Zahira" "Karki damu Mamana ita Zahira dama sai a hankali zata dawo daidai indai na samu tana Shan ruwan adduoi da nake baki da turaren wuta zata dawo daidai Shi dai babana nake so ki bari mu bincika abinda ke damunsa wlh duk abinda Kika ga ya samu bawa rubutacce ne daga Allah wayanda kike tunani basu Isa su Miki komai ba sai idan Allah ya hukunta dama hakan sai ya faru tunda mumuni dole ya yarda da kaddara Mai kyau ko akasin haka alhamdulillah daga labarinki Allah na kaunarki mamana tunda duk Kika iya tsallake duk wani sharri da aka nufeki dashi Allah daya jarrabceki yana ta kareki ba hanyar da basu bi ba dan su ga bayan ki Amma da ikon Allah gaki nan a rayye ba abinda ya Sameki insha Allahu yaranki ma Allah zai karesu burina kawai ki dogara da Allah kiyi ta yiwa yaranki addua gabadaya. Da nasihar Inna Amina naji sausauci a zuciyata na fito na Kai Mana abin karyawa Muka karya a tare duk da zuciyata cike take fal da damuwa. Ko Ina Waleed din yayi yanzu Zahira dama tun safe bata tashi daga bacci ba Ina mamakin sababin halayyen da nake gani a tare da ita bansan na saka damuwa a raina hakane yasa muna gama karyawa da Inna Amina na d'auko qurani na dan ta karamin sosai nake Kara amfani da damar da na samu wajen Kara neman ilimi Kuma alhamdulillah Ina fahimta. Karatun da mu kayi tare ya sanyaya min zuciya sosai wajen Sha daya na fito daga d'akinta ita Kuma tace min zata dan kwanta tayi bacci tunda bata fiye baccin ba ta Kan rayya daren itama. Ina fitowa naci Karo da Zahira ta fito da Kofin kunu da alala ko kallona ba tayi ba ta fara k'ok'arin wuceni Haka kawai na kasa yarda wai Zahira ta ce ta dawo haka Koda lokacin da Aljannun Suka fice a jikinta magana ne kawai naga Bata yi ta zama shiru shiru,amma tana nan da sanyi halinta da ladabi da biyyaya na kasa gane Mai yasa kwanankin nan ta kara bijiro da sababin halayye da na kasa ganewa "Zahira baki iya gaisuwa bane wai Mai yake damunki ne"? Ciki ciki ta gaisheni ta shige daki ba Kuma tsayawa tayi ta gaisheni ba Sam ban yarda abinda suke shigeta suka fita ke saka ta haka ba dan da suka fita ma ta dawo min yanda take magana ne kawai bai dameta ba Kaina dana ji ya fara min ciwo yasa ban tsaya takura kaina da tunani ba na hau aikace aikacen gida da kafin ta Kara canjawa tana Tayani Hankalina Sam baya jikina Yana wajen Waleed daya fice bai dawo ba dan baya yawo daga gida sai makaranta abokinsa guda ne dan yadikko Abubakar a iya sanina ma dashi sai dai abubakar din ya zo wajensa bai fiye zuwa ba har tsokanar sa su Nadeeya keyi akan ko dan ball dinan da aka San maza nayi shi baya yi Yana nanike dasu Yana koyan jajjage da yanka albasa. A haka na gama girkin Rana. Ina zuba idon dawowar yarana har da Waleed da hankalina yafi karkata wajensa. Sai dai har Suka dawo suka ci abinci Waleed bai dawo ba. Sai tambaya ta suke Ina yaje nace musu bansani ba su dai dubo min gidan yaddiko ko Yana can wajen Abubakar. Dawowar Humaira aguje tana hakki tare da cewa "Umma Kinga Waleed can a tsakiyarsu shagari Yana ta Wasa da Kare nace kina kiransa ko kulani baiyi ba Umma shagari fa dan gidan dan kwaya" Tunda ta ambaci shagari yaron daya addabi Yan unguwar da fitina naji gabana ya yanke ya fadi sallati na hau yi Nadeeya ta mik'e da sauri tana "Humaira kina da hankali kuwa Waleed din Kika gani da shagari"? " wlh Aunty Nadeeya Waleed na gani har na Masa magana ya shareni" "Nadeeya bata iya magana ba daga ita sai doguwar rigarta tayi waje da Sauri" Nima tsintar kaina nayi da binta a bayan Ina sallati Shagari sa'an Waleed ne karamin yaro da bazan iya kirga sau nawa aka Kai shi a ka kulle ba sabida rigimamme ne na tashin hankali har d'auke d'auke Yana yi ga dukan Yara fitinanne ne na karshe shaye shaye ne kawai bamu sani ba Yana Yi ko baya Yi A zaune yake a tsakiyar su shagarin Yana ta Wasa da karnukan Nadeeya a tsawace ta Kira sunansa tana yazo nan Waleed yarone Mai girmama na gaba dashi dan daidai da Raheema da yake bi aunty Sama aunty kasa yake ce mata ga mamakina ko dagowa baiyi ba ya kalli Nadeeya Data ishe shi ma sai cewa yayi "mallama karki takura min idan Kuma Zaki iya daukana zo ki d'aukeni" Nadeeya sakin baki tayi tana kallonsa ta juyo ta kalleni...... *A yi maneji wlh abubuwa sun Sha kaina a ringa hakuri dai Kar ayi rushing Dina Ana rushing Dina zanyi a gurguje wlh alhalin labarin Bai Kai a Gama ba yanzu nan nayi typing dan karku jini Shiru Ina samu sarari gobe xaku jini idan ban samu ba ayi hakuri jibi na bada Mai yawa* [8/13, 6:47 AM] Zannura: *NAGA TA KAINA* *NA SADNAF*🌸🌸 ®️ *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_* _{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_ *Free Novel* *Thanks all for d bday wishes and prayers I appreciate wanan Shafin na kine Ayshatfareeda tnks for d gift am greatful* Page 58 Sosai na rik'e kaina na tsaya akan kafafuna sabida rawar da jikina keyi jiri na d'ibana Ban saurari Nadeeya da itama ta daskare a tsaye ta juyo tana kallona ba sabida mamakin abinda Waleed yayi. Duk da inada tsoron Kare haka na daure na isa wajensu Waleed bai ji dar din ganina ba sai ma shagari da sauran abokanan sa ne Suka dan sunkuyar da Kai suna gaisheni dan ni nasan Ina dan musu kwarjini. "Waleed zo ka wuce mu tafi gida" Jim yayi kamar bazai tashi ba har sai da shagari ya Masa magana ya mike Yana wani fufusgewa yayi hanyar gida Na rik'e hannun Nadeeya data kasa katabus sabida mamakin abinda waleed yayi. Ni kadai nasan mai nake ji a Zuciyata "Umma Mai ya samu Waleed haka? Mai ya canza shi lokaci guda"? Ban samu zarafin yiwa Nadeeya magana ba muka cigaba da bin Waleed a baya har muka Isa gida. Butan dake tsakar gidan ya fara ball dashi kafin ya karasa dakin Minal kuwa ta kasa hakuri ta bi bayansa tana "Kai Waleed kana da hankali kuwa?Mai ya had'aka da shagari dan iskan yaron nan"? "Karki Kara cemin banida hankali mallama" Waleed yace Yana wani hucci kamar sa'arsa Da yake bai Saba da musu rashin kunya ba Sam haka ne yasa abin ya musu wani banbarakwai. Nadeeya ta fada d'akin a zuciye kafin na hanata ta wanke shi da Mari Minal kuwa ta hau zaginsa ita da humaira. "Wlh duk wacce ta Kara zagina sai na rama duk wacce hannunta ya Kara tab'a jikina wlh sai na rama" Waleed yace yana zuba musu harara. Daga yanda yake nasan zai aikata zuwa lokacin na yarda Waleed ba'a hayyacinsa yake ba D'ana an tab'a min shi dan ba haka yake ba tunda na haife shi bai tab'a gwada rashin kunya da naga Yana yi ba yau. Ina tsoron Umma da Safiyya suna cikin hannu a canzawar Waleed D'ana guda tilo da nake alfahari da hankali da tarbiyya dana bashi,idan har zasu iya yiwa Zahira turen bakakken Aljannun Mai zai hana su tab'a min Waleed tunda sun San namiji ne zuwa yanzu nasan sun gane an raba Zahira da Aljannun hakane zai saka su ce bari su dawo Kan Waleed na fahimci sun San rauni na akan yara na ne bana iya jure abinda zai tab'a su kila shiyasa Suka kara tab'a min Waleed. Tuni na tsayar da tunani na akan Waleed ba'a hayyacin sa yake ba duk Abunda yake yi yanzu kila ba a hankalinsa bane Da wannan tunanin na fara k'ok'arin tsawatarwa su Nadeeya da fad'a ke neman kaure musu suna neman dukan Waleed dake ta zuba musu rashin kunya da yake Yana da jikin girma Zahira da Nadeeya ne kawai zasu gaya masa tsayi Amma duk yafi su Humaira tsayi Zagin sa da humaira ta yi ya rama a take yasa suka rufeshi da duka Kafin na Isa wajensa ya watsar dasu ya cakumo humaira ya hau zuba Mata naushi daya daga min hankali Nayi wajensu a guje duk yanda muka so raba Waleed da Humaira kasa wa muka yi karku manta sai da aka haifi Raheema kafin Waleed akwai tazaran shekaru a tsakaninsu. Daga yanda yake dukanta na Kara gasgata dana ba'a hayyacinsa yake ba haka ne ya sa ni ma na hau Kai ma sa dukan Ina ya cika ta dan wani irin karfine da Waleed din daya sa muka kasa raba shi da humaira. Sai dana fashe da kuka Ina ihun a kawomin agaji kafin ya saki humaira daya Mata jina jina ya bangaje sauran yayyensa ya Kara yin waje A gefen gado na zube na fashe da kuka Ina sallati "Umma yau mu Waleed yake zagi har dasu duka Umma Waleed ko ya fara shaye shayene"? Cewar Nadeeya "Kema ai ko ba'a fada Miki ba kinsan ya fara shaye shaye Waleed Nan ko Raheema yayi wa ba daidai ba yayi ta binta Yana bata hakuri kenan bai tab'a maida Mana magana ba Amma kiga yau shine har da kokawa da humaira" Cewar Minal tana bubbuga bayan humaira dake numfarfashi Ban iya tanka musu ba dan ni kadai nasan Mai nakeji a Zuciyata muryar Inna Amina dake kwalla min Kira yasa nayi d'akinta Ina cigaba da kuka. A gabanta na zub'e Ina cigaba da kukan da nake Sanin kukana na d'aga Mata hankali yasa na tsayar da kukan Ina "Mama wlh an tab'a waleed dana ba haka yake ba mama kema shaida ce yanda yake girmama yayyensa Mama yau Waleed shine da zaginsu har da dukan Humaira wani yaro Mara kunya a unguwar Nan dasu naga Waleed fa Mama wlh an tab'a waleed mama kila shima an Masa turen Aljannu da zasu ringa saka shi Rashin ji Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun na karashe Ina Kara fashewa da kukan. "Mama na rasa mai nayi wa bayin Allah nan suke san ganin bayana ko wata uku Zahira batayi da dawowa daidai ba yanzu Kuma sun dawo Kan Waleed laifine dan na auri Naseer mai na musu da zafi haka suke San tarwatsa min rayuwa"? Inna Amina bata hana ni ba sai data bari na ci kukana na koshi Ta fara rarrashina "ki kwantar da hankalinki mamana ki daina zubar da hawayenki,indai turen Aljannu aka yiwa Waleed insha Allahu zanyi iya k'ok'arina na Raba shi da su nima duk abinda kuke yi Ina jiyo ku daga yanda yake daga murya nasan yaron nan an tab'a shi banso kawai na Miki maganar ne na d'aga Miki hankali insha Allahu zai dawo daidai da iziinin Allah kiyi k'ok'ari ki turo min shi akwai Addu'a da Zan Masa indai da jinnu a jikinsa sai sun fita Kuma wanan Abunda ya faru da Waleed ya Zama dole mu dage da Addu'a har sauran yaran naki Allah ya karesu daga sharrinsu Ina mamakin halin bayin Allah nan da basa tsoron Allah nakan ji labarin mugaye Amma na bayin Allah nan na daban ne ace uwa ce ke san ganin bayan danta haka dana tunanina wlh bake suka tsana ba babana Suka tsana tunda har zasu iya tab'a yaransa Allahu ya shiryesu su gane tin lokaci bai kure musu ba" Inna Amina sai dai Allah ya Mata sakayya da Aljannatul firdausi tayi k'ok'ari a kaina sosai da yarana. Dak'yar na samu na bawa su Nadeeya baki akan su bi Waleed a hankali dan gani suke shaye shaye Waleed ya fara,nawa ma waleed din yake da zai yi wani shaye shaye. Haka na zauna zaman jiran dawowar Waleed har aka yi sallah Isha Sam hankalina ba'a kwance yake ba. Sallah ma ba'a nutse nayi ba sabida tashin hankali Ina tsoron Kafin Waleed ya dawo hayyacinsa ya jawo min wani maganar Yayyensa duk basu bi ta kansa ba suka duba littattafansu Suka je suka kwanta dan Haushin Waleed suke ji sosai suna ganin Kamar ban dau.matakin daya dace na dauka a kansa ba. Inna Amina ke dan Jana da Hira Wanda rabi waazi ne akan yarda da kaddara Mai kyau ko akasin haka a fadarta duk abinda zasu min yanzu ba zai kai na baya ba idan har Allah dana dogara dashi ya kareni da tsawon lokacin nan nayi Imani akan shi zai karemin yarana ruwan addua da ta saka a Kofi ta Kara nuna min akan Yana dawowa zata bashi insha Allahu zaa dace Hankalina ya dan kwanta sanin wacece Inna Amina macece Mai baiwa burina Waleed din ya dawo kawai na samu na bashi ruwan Addu'a. Agogo na duba Naga goma har ta dan.wuce ba Waleed ba dalilinsa Waleed da daga Massallaci sai makaranta sai.kuma gida sai gashi Waleed din ne yau bansan Inda yaje ba har karfe goma. Waje na fita da hijab a jikina na hau duduba hanya ko zan ga Waleed Wasa Wasa sai gashi nice har gidansu shagari ban same shi ba. Duk dandalin dana san suna zama na duba ban gansu ba. A haka na koma gida nayi zaman dirshan a k'ofar gida da za'a auna jinina ni nasan ya balain hawa daga safe zuwa yanzu Ashe haka uwa ke Shiga tashin hankali idan danta ko yarta ya d'auko hanyar lalacewa ko ya iyayen Yan d'abba sukeji da karuwai da kullum.a cikin d'auko magana suke kila ma bakin ciki ke Zama ajalin iyayensu Hawaye kawai ke zubomin Ina tuna irin tarbiyya da Allah ya bani iko na baiwa yara na da har ake Jin dadin zaman mu a unguwa anya da akwai ranar da zan tab'a farinciki a rayuwata?nidai badan Kar nayi sabo ba da nace nayi nadamar auren Naseer dan daga aurensa zuwa yanzu banga kalar bakin cikin Da ban kunsa ba,Ina fita daga wanan balain zan fada wani yanzu Kuma an bar kaina an koma Kan yarana Har yanzu ni nasan zafin da nakeji idan na kalli Zahira yarinya Mai balain tausayi da hankali yanda suka maida min ita a kwanan Nan ma sababin halayye nake gani a tare da ita yarinya Mai sanyi hali ta zama masifafiya Abu kad'an zata hau kananenta da masifa har dasu Bugu idan taso Ni da nake mahaifiyarta ma bata damu ta ringa gaisheni ba kullum tana d'aki a kwance. Zurfin da nayi a tunani bai saka nasan karfe dayan dare ta kusa ba sauro sai kai wa fatata cizo suke. Muryar Inna Amina data daddafa bango cikin dingishi ta fito waje Jin ban dawo ba ya saka na dago "Haba mamana zaman mai kikeyi a waje ke kadai duk rashin Waleed din ne"? Kukan da nakeyi a zuci na fashe dashi Ina "Mama bansan Inda Waleed yake ba Waleed bai dawo gida ba taya Zan samu kwanciyar hankali da nutsuwa" Inna Amina na k'ok'arin Magana na hango Waleed ya taho yana pito Wai Waleed dina ke fito Yana abun marasa tarbiyya. Ido na zuba Masa har ya karaso ganina a zaune a dakalin k'ofar gida bai saka ya tsaya ba illa ma wuceni da yayi ya fara k'ok'arin Shiga ciki Inna Amina dake tsaye a bakin kofa ganin Yana neman ratsawa ta gefenta ya wuce ciki yasa tayi karfin halin cewa "Babana ina kaje ne.kayo dare haka muke ta neman ka"? "Kallon ball muka je da abokaina" Yace ciki ciki Yana wucewa ciki Inna Amina tamkar Mahaifiyata na d'auke ta zuciyata ta sosu da yanda ya Mata hakane yasa na mik'e a zuciye zan bi bayansa Inna Amina Ta ruko hannuna tana girgiza min kai "Ki bishi a hankali Mamana ki Kai zuciyarki nesa bayin kansa bane ki taya shi da Addu'a ki Kara janyo shi jikinki kar duk abinda zaiyi ya b'ata Miki rai tunda kinsan ba yin kansa bane kila an Masa hakane ma dan a rabaku yayi ta Abu kina Jin haushinsa ko kina jibgarsa a karshe ma zuciya ya deb'eki ki furta kalmar da bata dace ba mu bishi a hankali kinji" Gyada Mata Kai nayi maganganunta na shigata sosai dan wanan sam ba dabiun Waleed bane taba min shi akayi. Ciki muka shiga na kulle k'ofar Gidan A tsakar gida Muka sameshi ya zauna akan tabarma Yana cin abincinsa dan abincin ranarsa Dana darensa duk Bai samu yaci ba Dak'yar na yakice shi ya daina cin abinci dasu Zahira dan a da tare suke cin abinci gabadaya ko fita yayi sai ya dawo suke yarda Suma suci akwai soyayya Mai k'arfi a tsakaninsu. Dan zaman da Naseer yayi damu Mai tsawo a jinyar Zahira yasa suka.koma suna cin abinci tare. Ko ya Naseer zaiji idan ya dawo yaga Waleed daya ke ji a Ransa Kamar me ya dawo yaro Mara ji Daki nabi Inna Amina na karbo ruwan Addu'a nazo na ajiye Masa agabansa Bai cemin komai ba ya gama ci ya Sha ruwan ya shige Palo yayi kwanciyarsa. Bacci bai ga idona ba ranar sabida dukufa nayi gaban Mahallicina Ina kaiwa Allah kukana akan ya karemin yarana ya dawo min da Waleed da Zahira yanda Suke a da Allah Kar ya Bawa makiyana dama suga bayana. Sai da aka fara kiraye Kirayen sallah asuba kuma naji bacci ya fara k'ok'arin daukana. Fitowar su Nadeeya daya bayan daya daga d'aki dan su yi alwala yasa na wartsake dan duka yarana sun Saba da tashin sallah asuba. Waleed shine ma kan gaba dan wani zubin yana riga Naseer tashi Yana alwala zai tafi massallaci Naseer ya bishi a baya Amma yanzu iya su Nadeeya ne suka fito Banda Waleed da Zahira. Ina kallonsu suka ringa alwala daya Bayan daya suna komawa ciki. Hakane yasa na mike na Shiga d'akinsu dan na tashi Zahira itama tayi sallah dan na lura kwana biyun Nan da ta tsiro da sababin hali sallah ma Kamar bata so tayi. Baccinta take ta shara ni kuwa na sunkuya na Dan bubbugeta dan ta tashi Yamutsa fuska tayi data bude idon tana kallona Cikin had'e rai nace ta tashi tayi sallah "Idan na tashi zanyi" Tace tana k'ok'arin gyara kwanciyarta Take raina ya b'aci na daka Mata mugun tsawa dan zan jure komai banda Wasa da sallah "Maza tashi sallah Bata jiran mutum sai dai mutum ya jira sallah tashi kije kiyi alwala kiyi sallah kafin raina ya b'aci" A madadin ta bi umarnina sai ta turo baki tana kunkuni. Take naji na zo wuya na kasa danne zuciyata na rufe ta da mugun duka dan ni nasan rashin kunya Zahira kemin ban zargi akwai wani Abu dake damunta ba tunda an riga da an rabata dasu kila dan Inna Amina tana cewa a bita a hankali shiyasa ta tsiromin da halayen nan. Dak'yar su Nadeeya suka kwaceta a hannuna dan kananan surutai ma ta ringayi tana wai an dameta tace baza tayi sallah bane" Ina cikata tayi waje fuuu tayi k'ofar dana kulle da mukuli tayi Zamanta a bakin kofar alamar dai baza tayi sallah ba Inna Amina ce ta Kara bani baki akan na bita itama a sannu Dak'yar dak'yar tayi sallah Waleed kuwa Ina tashinsa akan yayi sallah juyamin baya yayi Sai da shima nayi Kamar Zan buge shi ya mik'e Yana fufusgewa Kamar zai kawomin duka Wai Mai ya samu yarana ne suka dawo haka. Cikin kuka na koma Kan sallaya nayi Sujadda na Kara kaiwa Allah kukana Ina fada Masa duk abinda ke zuciyata da yanda yaran nawa suka dawo kafin na iya mik'ewa nayi Sallah Asuba duk ba'a nutse ba. Karfe shdda su Nadeeya suka fara aikace aikacen gida Haka yasa na fito tsakar gidan da suka share na zauna Akan tabarma Ina zaune ne kawai ba dan zuciyata na wajen abinda suke ba. Pito muka fara ji da Haushin karnuka a waje Kafin tunanina ya bani wani Abu Naga Waleed ya fito daga palon ya fara k'ok'arin yin waje. Da balain Sauri na mik'e na dakatar dashi Ina "Kai Waleed Ina zakaje da sassafe Nan"? Bai cemin komai ba yayi dage ya dauko mukullin ya bud'e yayi waje Kamar Zan Fadi nabi bayansa. Sai dai Ina fita Naga har sunyi nisa shi dasu shagari. Hawayene ya hau zubomin na kasa yarda Waleed Dina ne ya dawo haka ni dai nasan idan Naga kangararrun Yara nakan bisu da adduar shiriya ban tab'a kyamatarsu ko nayi Allah wadai dasu ba ballantana nace hakane yasa Allah ya jarrabceni. ( Hattara iyaye ku guji aibata ko kyamatar yaran da suka tsinci kansu a irin wanan hali dan ba iyayen da zasu so yayansu su lalace Kai dai ka kallesu kawai ka bisu da Addu'a dan baka San kaddarar data afka musu suka tsinci kansu a cikin wanan halin ba Kai ma da kake kyamtar su baka San ya naka kaddarar zai Zo ma ba dan bawa baa daina jarrabtarsa har sai ya koma ga Allah ya rabbi ya shirya Mana zuria wayanda Kuma suka d'auko hanya lalacewa rabbi ka Shiryesu ka hada yaranmu da abokanan arziki alfarmar annabi Muhammad Saw). Ni nasan Wanda yayi nisa baya Jin Kira ko na bi Bayan Waleed bai Zama lailai ya dawo ba hakane yasa na koma ciki Ina Jin zuciyata na radadi ga nauyi daya min Yarana cikin.fushi Sukace na rabu da Waleed yaje yayi ta abinda zaiyi Nan kuwa basu San duk abinda akeyi ba'a hayyacinsa yake ba. Da zazzabi jikina sama sama suka tafi makaranta ya rage dagani sai Zahira da Inna Amina Kaina kuwa Kamar ya Fado sabida ciwo na Kuma San dan banyi bacci bane. Abinci Inna Amina na Kai Mata Ina ajiyewa ta hau min waazi tana Kar na damu duk tana kallon abinda ke faruwa Na cigaba da Addu'a na Kuma dage da Sadaka kamar yanda nayi a baya. Toh kawai na ce Mata dan kirjina kamar zai fito daga kirjina hoton Waleed kawai nake hangowa dasu shagari suna tafiya da karnuka Yanda nake jina bazan iya sauran aikace aikacen da suka rage ba hakane yasa na nufi d'akinsu Zahira dan na tasheta tayi aikin Sai dai Ina tashinta ta hau min kunkuni kamar yanda ta min da asuba. Baki a ture ta fito daga d'akin wanke wanke danace tayi ta hau gara kwanukan Tana watsi dasu Kamar bazata yi ba. Wanke wanken ta hau yi Tana cigaba da kunkuni bama fita suke ba a Haka ta fasa plate din tangaran anan nazo wuya zuciyata na rayamin iskanci kawai yasa Zahira kemin haka. Wayar wuta na dauko na hau dukanta Ta dib'a a guje tayi waje itama A takaice daga ita har Waleed a ranar sai wajen Sha biyu suka dawo. Rashin dawowarsu da hade min Kai da sukayi suna neman lalacewa a gaban idona yasa zazzabi rufeni da har sai da Nadeeya ta kai ga Kiran likita yazo ya sakamin ruwa Tunda ga ranar Zahira ana Mata fada zata Yi zuciya ta bar gidan Bansanta da kawaye ba sai gata ta tsiri kawaye kawayen da kana ganinsu kasan basuda tarbiyya halin da ba na yata ba sai gashi Tana yinsu. Waleed kuwa kararsa da ake kawo min kawai ya Isa ya saka zuciyata tayi bindiga Dan shine daki wancan shine daki wanan kullum cikin zuwa gidajen Yara nake bada hakuri Zuwa lokacin Yan unguwa sun fara Gane halin da nake ciki game da yarana Allah na tuba har gwamma duk halin Dana Shiga a baya da irin kissan da su Umma suke min Akan yarana. Inna Amina tana iya k'ok'arinta wajen Tayani da Addu'a dan yarana su dawo daidai amma duk a banza Yata ta fari da autana sun d'auko hanyar lalacewa a gaban idona. Banda ma Inna Amina na rarrashina da nasiha da tuni na yanke jiki na Fadi rabona da baccin kirki na manta nayi kukan nayi rashin lafiya Watan Naseer uku da tafiya ya dawo da sabuwar motarsa dal da uban tsaraba Daga yanda ya gani a rame a lalace yasa hankalinsa ya tashi. Ni kuwa ganinsa yasa na hau kuka Karshe sai Inna Amina ke bashi labarin duk abinda ke faruwa Dani Dan ko a yanzu ma daya dawo. Daga Zahira har waleed basa Nan Naseer hankali a tashe ya hau sallati daya ji shagari yanzu Waleed ke bi Zahira Kuma tana bin kawaye. Da kansa ya saka Nadeeya a gaba ta raka shi gidan da Zahira ke zuwa idan ta bar gidan Faiza sunan yarinya Saar Zahira ce baa gun Iyayenta take ba a wajen kanin mahaifinta take ban dai San silar rashin jinta ba. Naseer sai daya nemi kanin Mahafin yarinya yace Baya San kawancensu da yarsa kafin ya ruk'o hannun Zahira Yana janta suka nufo gida sai tura Baki take badan shi yaje ba idan Zan kwana Ina Aiken ta dawo gida bazata dawo ba. Kulle ta yayi a daki dan duk Nadeeya ta bashi labarin kalar rashin Jin da take da fita da take batare da mun sani ba Nadeeya ya Kara cewa ta raka shi suje gidansu shagarin ko zai ga Waleed Kamar ciwon kirjinsa zai tashi sabida tashin hankali kafin su Kai gidan su shagari suka ga mutane da yawa an taru. Har zasu wuce ya nufi wajen Waleed ne ya fasawa wani yaro Kai da kwalba Mahaifin yaron ya rantse bazai yarda ba sai ya Kai Waleed station dan har ya tura babban dansa ya d'auko.masa Yan sanda. Naseer dak'yar ya samu hanya daya Isa wajensu sai dai Yana hada Ido da Waleed yaji kansa ya mugun Sara Masa kirjinsa na Masa wani irin zafi Adaidai lokacin da Yan Sandan suka iso Mutane Kuma suka gane shine Mahaifin Waleed sabida kamanin da suke sosai Take kowa ya hau fadar albarkacin bakinsa Naseer na tsaye yayi kikam Yana jinsu Yan Sandan na zuwa a madadin Naseer yayi k'ok'arin yin wani Abu ko ya bisu station din sai cewa yayi idan suka tafi dashi Kar su sake shi...... Advertisement Hlo Assalamu alaikum sisters,hp everyone is fn🙏 Nazo muku da labarin wani sabulune maiban mamaki🥺wato *mg's herbal whitening black soap*🧖🏻‍♀️ yan'uwa inamasu bukatar sugyara jikinsu fatarsu tayi kyau tazama Babu kuraje,tabo dama dukwani matsalan fata toh Yan uwa kuyi kokari kujaraba mg's Babu tantama zaisharemuku hawaye insha Allah duk wnd tayi using mg's koda roba dayane sai fatarta tagoge tabanbanta Dana saura,Ina maisan yaga fatarshi tayi smooth tana kyalli toh kujaraba mg's domin fatarku zata dinga haskawa tana walkiya da daukar Ido kmn kunsha supplement domin anyishine da ingantattun natural abubuwa masu gyarajiki cikin sauki batare da sunyima fatar mutum lahani ba😘 sister's duk ynd zanbaku lbrn soap dinnan yawuce nan domin zaku iya anfani da zallar sabulun batare da kunma bukaci cream ba🥰Amare gareku akwai hadinku na musamman wnd duk wacce tayi anfani dashi dawuya ango ya iyaganeta😁wani abunma saikungani da idanku👏gamasu nankarwa kuyi kokari kujaraba mg's domin Yana rageta sosai inkuncigaba da anfani da soap dinma saidai kuduba kuga Babushi😊duk wani prblm na skin kugwada soap dinnan Insha Allah zakuyi😂 Kayanmu bana bleaching bn organic ne nagyaranjiki zaifiddomuku da ainihin natural beauty dinkune anyisune d natural abubuwa Soap price:3k Maiso should chat:08062991548 Call 08064532391 Muna maraba damasu siyan daya kosari🙏 Be part of the glow team🤭say nooo to pimples, black spot,acne,sunburn,nd all skin prblms🙏 Mg's lv you guys fisabilillah🤭 [8/14, 11:19 PM] Zannura: *NAGA TA KAINA* *NA SADNAF*🌸🌸 ®️ *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_* _{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_ *Free Novel* Page 59 Nadeeya Ido ta zaro ta kalli Naseer da ya fara kokarin barin wajen fuskarsa a had'e. Waleed shima wani irin Mugun kallo yabi Naseer dashi kamar ba mahaifinsa ba. Yan sanda tuni Suka tasa keyar Waleed suka saka shi cikin motarsu Nadeeya kuwa da hankalinta ya balain tashi da tafiyar da za'ayi da Waleed ta Sha gaban Naseer da Sauri dan duk da rashin Jin da Waleed yake gwada.musu yake Kuma musu rashin kunya hakan bai sa sunji kaunarsa ta ragu a zuciyarsu ba hasali yanzu tausayinsa suke ji tunda Naeema ta gaya musu duk abunda yake yi ba'a hayyacinsa yake yi ba. "Abba cewa kayi fa idan an tafi dashi Kar a sake shi Abba kaga zasu tafi dashi"? Naseer bai kalleta ba ya cigaba da tafiyarsa Yana zabga Sauri Dan sosai yaji zuciyarsa na kunna da ganin Waleed din dan ganin daya Masa ma ji yayi kamar ya shake shi yayi ta duka har sai ya daina numfashi. Wani abu yaji Yana danne zuciyarsa akan San Waleed da tausayinsa Nadeeya kuwa ganin Naseer ba alamar zai tsaya yasa tayi gida aguje tana kuka. Idona na Kan kofa tunda su Naseer suka fita da Nadeeya nemo Waleed bani da burin daya wuce irin naga sun dawo tare dashi dan yau ma ban saka shi a idona ba. Ina Jin Zahira a d'aki da Naseer ya kulleta tana kananan surutai Ni nasan da ikon Allah kawai nake numfashi har yanzu zuciyata bata buga ba idan na dubi Zahira 'yata da nake jinta duk a yarana sabida hankali da tarbiyya ta na ga yanda ta dawo yanzu yarinya fitsarariya sai naji kamar na cire zuciyata na Yar sabida ciwon da yake min a haka ma Wai dan Inna Amina na iya k'ok'arinta a kaina da yarana da babu ita bana Jin Zan kawo yanzu Waleed dana daya tilo da yayi hannu Riga da duk wani Abu Mai kyau ya koma Mara kyau ganinsa a Wanan halin kawai na iya sawa zuciya ta ta buga lokaci guda Na gwammaci ni su Umma suka hukunta suka ma kasheni da barina da sukayi a rayye da banida bambanci da mataciya sabida halin da yarana ke ciki. Sun watsa min rayuwar yarana da Karfin addua Yata Zahira ta tsaya a iya bin kawaye bata hada da bin Maza ba da Karfin addua Waleed ke rashin ji da bai had'a da sata da shaye shaye ba. Nakan hararo da yarana Basu hadu da wanan jarrabtar ba da kila Zahira ta Dade a gidan aure ko tana mataki na biyu a babban makaranta sai dai Kash gata a gabana ko secondary bata gama ba an susutar min da ita. Shigowar Nadeeya aguje tana ihun kuka yasa ni mik'ewa tare da dafe kirjina da na ji kamar an soka min kibiya. "Umma 'yan sanda sun tafi da Waleed station saboda ya fasawa wani yaro kai da kwalba Abba yace idan Suka tafi dashi Kar a sake shi" Tunda ta fara magana naji gidan na juyamin har Naseeru shima ya shigo a daidai lokacin dana tafi Zan zub'e a kasa ya taroni da sauri. Sai da na jima Ina sallati kafin naji kaina ya daina juyamin Maganar Nadeeya na Kara maimaituwa a kaina Ido na sauke akan Naseer Ina "Wai an tafi da Waleed station Kuma kace Kar a sake shi"? Kamar wanda na kwarawa ruwan zafi ya mike da Sauri yana "Duk ranar da Waleed ya taka kafarsa gidanan sai na raba shi da numfashinsa tunda ya zabi ya Zama dan iska gwara ya je ya cigaba da iskancinsa Kuma ban yarda wani yaje station dan yayi belinsa ba gwara suyita rikeshi acan" Yana gama fadar haka yayi daki a fusace Ni kuwa Zan iya cewa tunda ya fara magana nayi suman wucin gadi na kasa yarda Naseer ke furta kalmomin nan daga bakinsa. Na dauka zai fi kowa Shiga tashin hankali da halin da Waleed ya tsinci kansa lura da irin Kaunar da yake Masa ga mamakina Dan namu yake cewa Dan iska Bansan yanda akayi na mik'e na isa d'akin da ya Shiga ba yana Gefen gado a zaune Ban karasa ciki ba daga bakin kofa na Kira sunansa da Naseer dan Abban Waleed nake ce Masa tunda na haifi Waleed na bar ce Masa Abban Zahira. Indai na Kira sunansa toh ba karamin magana zamuyi dashi ba dagowa yayi da jajjayen idonsa Yana kallona "A hayyacin ka kake kuwa Naseer Waleed aka tafi dashi station a gaban idonka baka yi komai ba kace Kuma a idan an tafi dashi Kar a sake shi"? "Eee Ni nace Kar su sake shi Naeema Kuma ban yarda wani yaje belinsa ba dan bazai yiwu ya ringa jawo mana magana ba yaje can ya karaci iskancinsa" "Waleed kake jifa da munanan kalamai Naseer waye silar zaman Waleed haka?Mahaifiyarka da kanwarka su suka Zama silar gurbacewar tarbiyyar da na yiwa yarana Naseer Waleed da haka yake?Zahira da haka take a yanzu daka dawo daya Kamata mu had'a hannu wajen ceto yarana daga halaka Amma Kaine na farko wajen cewa yarona Dan iska? Tunda na aureka nake cikin tashin hankali ban taba samun nutsuwa ba daga wanan sai wanan yanzu Kuma an bar kaina an dawo Kan yarana Naseer na gaji wlh Tallahi na gaji idan har yarana basu dawo hayyacinsu ba bazan tab'a yafewa Mahaifiyarka da kanwarka ba" "Ke ya isa haka akan Waleed Kike jifana da maganganun banza ke yanzu ko tuntub'e kikayi sai kice mahaifiya ta ce,kin ma bar yarda da duk abinda ya Sameki yin Allah ne komai komai mahaifiyata ce da kanwata ki Shiga hankalinki Naeema Kar San Yara ya susutaki bin abokanan banza ya jefa danki a halin da yake ciki da kinsa Ido akansa da duk baa Kai ga haka ba lokacin da nake gari Mai yasa duk hakan bai faru ba sai da bana nan "? Zuwa yanzu shi kansa Naseer din na fara ganewa ba'a hayyacinsa yake ba yanda ya hayyayako min yasa naji na zo wuya na hau jifansa da maganganu masu zafi dan a lokacin zuciyata gayamin take kamar da biyu ma Naseer yake haka dan Yana ganin ya ruko canjina a hannu. Musayan kalmomin da muke ne ya dagawa yarana hankali suka hau k'ok'arin janye ni daga wajensa Amma fir naki na cigaba da jifan Naseer da magangunan da suka shake min wuya har sakina nace yayi idan yasan shi dan.halak ne dan aurensa bai kareni da komai ba sai wahala da nake sha tunda mukayi aure dashi bamu tab'a irin fadan da mukayi dashi ba ban Kuma tab'a ganin ya rufe Ido Yana cimin mutunci ba sai a wanan lokacin Kukan da inna Amina ta saka yasa na ja bakina nayi shiru zuciyata na wani irin k'unna Wa'azi ta hau yiwa Naseer Ni kuwa na saka hijabina nayi waje da Nadeeya dan ta rakani gidansu yaron da Waleed ya fasawa Kai tunda tacemin ta san yaron. Ga mamakina Ina zuwa ma nagane nasan mahaifiyar yaron. Cikin kuka na hau bata hakurin abinda ya faru na rik'e hannun dansu da waleed ya fasawa kai da ya Sha bandeji a kansa na hau Masa sannu. Bamu samu mahaifin yaron a gida ba da shi ya d'auki case din da zafi har aka Kai Waleed station hakane yasa muka zauna zaman jiran dawowarsa dan sai ya yafe Zan samu a sallami Waleed. Ana kiraye Kirayen sallah Magriba ya shigo gidan da sallama babban dansa na biye dashi a baya. Gaisuwar da muka Masa kawai ya amsa ya fara k'ok'arin Shiga falon matarsa ta dakatar dashi ta nuna mu tana wajensa muka zo ta Kara da bashi hakuri akan tunda Mai afkuwa ya riga da ya afku yayi hakuri kawai ya saki waleed. Yanda ya hade rai yasa na fashe da kuka Ina cigaba da bashi hakuri Ina "Kayi hakuri d'a na kowane wlh Tallahi da ba haka yaron nan yake ba daga baya ya zama haka kila Kuma bazaku rasa sanin sa ba yaron nan dake yawan sharar Massallaci a kasan layi wlh shine ya dawo haka lokaci guda muna ta iya kokarinmu dan muga ya dawo hanya ayi hakuri a yafe Masa duk abinda aka kashe wajen maganin yaron Nan Zan bayar ka taimaka" "Jikinsu sanyi yayi da suka ga yanda nake kuka a karshe mutumin yace ba komai Amma ya zama dole na dage Akan Waleed da yanzu abin yazo da tsautsayi dansa ya rasa ransa fa nasan yanda zanyi na raba Waleed dasu shagari. Kar Waleed ya jawo min abinda ba shi kadai zaa kulle ba har damu. Sai da yayi sallah Magriba ya huta duk.muna zaune kafin ya fito yace Mana muje. Dubu daya na ajiye a Gefen yaron na Kara Masa Addu'a samun sauki Na Kara yiwa mahaifiyarsa godiya na fito muka tafi station din. Sai da nayi da gaske da kuka da magiya kafin su yarda zasu bada belin Waleed dan rashin kunya Waleed ya ringa musu. Kudin da na basu da dan yawa yasa suka sakeshi. A yanda na fahimci waleed idan ana Masa fada ko aka hukunta shi zuciyarsa Kara taurara yake dan da aka sakeshi wani irin hucci ya ringayi Kamar wani Zaki yabi wani dan sanda da mugun kallon daya sa dan Sandar rantsewa akan duk ranar da tsautsayi yasa aka Kara kawo shi station dinsu wlh bazasu sake shi ba Waleed wani mugun Tsaki ya Masa ya wuce mu. Ni kuwa nabi bayansa da Sauri Ina kwalla Masa Kira. Da kyar ya tsaya ya zubomin Ido daya sa nake ganin kamar bani na Haife shin ba kamar ba dana Waleed dan Umma Dan lelen Abbansa yanda yayyensa kan tsokaneshi. "Waleed so kake ka kasheni da raina ko"? "Wai da nayi me har ni Abba zai ce a wuce dani station Kar a sakeni"? Wani irin girgiza kai yayi ya barni a tsaya ya hau zuba Sauri A haka muka ringa binsa a baya Ina kuka ni kadai nasan Mai nakeji a Zuciyata. Muna isa gida yayi fatali da butan daya samu a tsakar gidan ya wuce d'akinsu zahira dan palo yayi niyyar Shiga Naseer dake zaune a palon yasa yayi tsaki kasa kasa ya nufi d'akin. Butar da yayi kwalo dashi na dauko na zuba ruwa nayi alwala. Na Shiga d'akin Inna Amina dan nayi Sallah Magriba Nadeeya Kuma ta Shiga d'akinsu. Ina cikin rakaa na karshe na ringa jiyo hayaniya daga d'akinsu zahira take hankalina ya rabu gida biyu. Allah Allah kawai nake na iddar na tafi dakinsu Naga Mai ke faruwa Sujjada nayi naji ihun raheema da k'arfi. Da Sauri na Sallame sallahr na fito a lokaci guda muka isa d'akinsu zahira da Naseeru. Waleed ne yake ta kwallo da raheema yayyensa na k'ok'arin rik'e shi. Zahira na gefe kamar bata San Mai ke faruwa a d'akin ba. Naseer cikin zafin nama ya isa garesu. Ya damko Waleed da k'arfi. Kafin kace me ya rufeshi da duka Yana naushi Zagin Waleed kawai yake Yana jifansa da mugayen kalamai Waleed sai k'ok'ari Kare kansa yake ba ko tsoro a fuskarsa yanda ya tsaya ma Kamar zai iya rama dukan da babansa yake Kai Masa. Taurin Kan Waleed ma yak'i bari yaji irin dukan da Naseer ke masa shi ake duka Amma ni.nakeji a jikina. Tsakiyarsu na Shiga cikin ihun kuka Ina Naseer ya isa haka.kashe shi kake so kayi"? "Idan ban.kashe shi ba ai shi ya kashemin yarinya Raheema Saar sa ce da zai hau dukanta"? (Karku manta an Shiga tsakanin Naseer da Waleed shi kansa Naseer baa hayyacinsa yake ba) "Idan ba yaron nan ya zama dan iska ba"""" "Ka daina cewa dana dan.iska Naseeru kana mahaifinsa kana ce masa dan iska dana ba Dan iska bane" Nace a tsawace a daidai lokacin da Waleed ya fice daga d'akin a zuciye. Kafin na ankara har ya fice waje. A d'akinsu zahira ma ba karamin fada mukayi da Naseer ba kamar zai kawo min duka Dak'yar su Nadeeya suka janyeni daga d'akin Sai a lokacin na tambayi su Nadeeya mai ya hada Waleed da Raheema suka ce min Waleed ne yayi fatali da.kayan Raheema da take gogewa akan tayi magana shine ya zageta ta rama daga haka ya hau kwallo da ita. Dakin Inna Amina na koma Ina kuka itama kukan take tana adduar Allah ya kawo Mana karshen wanan fitintinun Allah ya gaggauta kawo karshen abinda aka yiwa waleed da Zahira. Naseeha ta hau min akan ta karanci kamar Naseer shima baa hayyacinsa yake ba shima kamar an Shiga tsakanin shi da Waleed. Na tuna fa ba haka.naseer yake ba a dan zaman da tayi damu ta karanci Naseer na mugun Kaunar Waleed tashi daya daga dawowarsa ya canja na daina biyewa Naseer muna fada akan Waleed Mu dage da Addu'a banji maganar ta ya shigeni ba dan.gani nake da gangan Naseeru yake haka tunda har Yana neman Kare mahaifiyarsa da kanwarsa daga cutar da suka min. Sosai nake ji a Raina lokaci yayi da zan ba zama nemawa yarana magani Allah na tuba Inna Amina na iya k'ok'arinta wajen Mana adduoi haka nima inayi Amma inaga sai na had'a da Kara neman taimakon. Zurfin da Inna Amina taga nayi a tunani yasa ta tambayeni tunanin mai nake. Ban boye Mata komai ba na gaya.mata abinda ke Raina. Murmushi tayi tana "Mallamai kawai da Kika bi wajen nemawa Zahira magani da baki samu kin dace da Wanda yayi nassarar cire mata bakkaken aljannu da aka Mata turensu kawai ya Isa yasa ki dau darasi.ki cire tunanin zuwa neman taimako wajen wani mallami. Ke ma zaki iya zama mallamar kanki ki roki Allah dan wayanda zaki je wajensu suma wajen Allah zasu nema Allahu samiu dua ne zai amsa Miki duk halin da kike ciki Yana sane dake daga lokacin da Kika fara zuwa wajen mallami neman taimako sai Allah ya barki da mallamin shi ya Miki maganin Abunda kike ganin bazai iya ba ko iya fatiha Kika sani ki karanta ki roki Allah dashi ta hanyar bin ladduban Addu'a Ki Kira Allah da sunayensa tsarkaka kyawawa kiyi wa annabinsa sallati ki Kara masa sallati a sujadarki ki yabe shi kiringa addua tamkar kina gabansa idan kin gama ki rufe da sallatin annabi saw insha Allahu zai amsa Miki. Na Karu sosai dan.a guntun ilimi na ma bansan ladduban Addu'a ba. A ranar Waleed bai kwana a gida ba Abunda bai tab'a yi ba kwana a waje. A ranar banyi bacci ba haka na ringa zarya tsakanin gida da waje ko Zan ga dana ya dawo. Sai dai bai dawo ba sai washegari Sha daya na safe Zahira kuwa ta saci fita duk da kulle ta da Naseer yayi. Akan Waleed wani irin Mugun fad'a mukeyi da Naseer dan idonsa idon Waleed sai ya dakeshi ko.ya koreshi daga gidan Wanda hakan yasa muke mugun fada har zuciya ta debbeni nace Masa ya barmin gidana ai ba nasa bane. A ranar yayi zuciya ya barmin gidan kamar yanda na nema. Inna Amina tayi ta min fadan ban kyauta Abunda nayi wa Naseer ba Bayan duk naseeha data min akan na yiwa Naseer uzuri baa hayyacinsa yake ba Har da kukanta na hau bata hakuri dan bazata gane ba Naseer ya ficemin a rai burina ma kawai ya sakeni. Insha Allahu ma.bazai dawo ya sake samun mu a gidanan ba dan mak'otan arziki sun shawaraceni da na bar unguwar hakan kawai zai saka Waleed ya nisanci su shagari Tuni na saka gidana a kasuwa sai dai duk Wanda yazo baya Taya gidan da daraja ballantana har kudin ya Kai na Kara siyan wani gidan. Sabida na nisanci Waleed da abokaina na siyar da gidana haka na Kama haya a wani unguwar. Sauran kudina na hau sana'a gefe guda kuma addua da sadaka daga ni har Inna Amina yi muke. Komawar mu wani unguwa yasa Waleed ya Kara haduwa da wayanda suka fi shagari hatsabibanci rashin jinsa ya Karu. Gefe guda Kuma ga maneman Nadeeya da Minal Ga babbar yayarsu itama da rashin jinta ya karu ta Kara haduwa da kawaye marasa Jin magana. Abu kad'an zaa Mata ta bar gidan sai nayi dgske zata dawo ta kwana Banida bambanci da zararriya dan Ina tafe Ina surutu sadakan nan Ina yi addua Nan ina yi Amma duk da haka Banga alamar yarana zasu dawo hayyacinsu. Ban gayawa Inna Amina ba na fara shirin tafiya Calabar neman su Umma suyi yanda zasuyi Dani su karya asirin da sukayi yiwa yarana...... Wlh banida lafiya Amma haka na daure nayi [8/21, 11:25 AM] Zannura: *NAGA TA KAINA* *NA SADNAF*🌸🌸 ®️ *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_* _{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_ *Free Novel* Page 60 Tashin hankali da damuwa yamin yawa bana iya bacci sabida halin da yarana Suka tsinci kansu a ciki burina kawai yarana suyi hutun makaranta na tafi calabar Zan zub'e a gabansu ko kasheni ne suyi su karya abinda suka yiwa yarana Zan jadada musu na rabu da Naseer har takarda Zan nemi wani ya rubuta min su dai ga shaida ko hakan zai kwantar musu da hankali Ko ya na rufe Ido sai na ringa ganin Kamar zaa shigo da Waleed hannunsa d'auke da ankwa ya aikata wani Abun. Zahira kila ta janyo min magana da zai saka Mana tambarin da ba ita kadai ba har mu sai ta shafa Mana bakin fenti gashi duka yarana Mata ne yanzu ma iya kawaye kawai da take bi ana jifanta da kalmar Yar iska har da masu karyar ta zubar da ciki. Idan Abun jaje ko na alkhairi ya Kama daya Zama dole na Shiga mak'ota haka zanji Ana zaurence ana labari da ni nasan dani suke yara dai a iya sanina duk Inda ka kai ga ka basu tarbiyya sai Allah ya dafa maka a tarbiyyarsu Amma wasu basu gane haka ba masu yin haka ma sai iyaye uwa data Kira kanta da uwa ita zata zauna ta ringa gulmar Yar wacce Yar iska ce bana Jin akwai Uwar da ko karuwa ce zata so yarta ta zama Yar iska sai dai idan haka Allah ya kaddarta Mata babu yanda zatayi ni nasan nawa yaran na musu tarbiyya da taimakon Allah makiya kawai ke san ganin bayana. Har ta kai yanzu Zahira idan tsautsayi ya gifta ta samu matsala da kannenta zuciya take ta bar gidan ba Kuma zata kwana ba bansan a Ina take kwanan ba sai dai washegari ta dawo haka ma Waleed. Ko kullesu nayi sai sun San hanyar da suka fita daga gidan dan tamkar zaman gidan mitsininsu yake Yana musu zafi. Inna Amina musamman ta tsiri azumi sabida wanan matsalar da na tsinci kaina a ciki. Ba karamin damuwa take da rashin Naseer ba Duk gaisawar da zamuyi sai tace ban kyauta korarsa da nayi ba. Ni kuwa ban tab'a nadamar Abunda na aikata ba San yarana ya rufemin idon da nake ganin duk abinda ya faru shine sila ni da ban aure shi ba ma da kila ban tsinci kaina a ciki halin dana ke ciki ba yanzu. Damuwa baya bari ma na tsaya zurfin tunani har na gane halin Naseer ne ko ba halin Naseer ba burina dai kawai Allah ya kawo wa yarana sauki. Saura sati daya Nadeeya ta yi candy duk makaranta ayi hutu na Kara zage damtse wajen Tara kudin da zanyi tafiya dashi dan ba abinda zai dawo dani har sai sun warware abinda suka yiwa yarana. Nadeeya kawai da Minal na gayawa inaso na yi tafiya Inda na rokesu Kar su sake su bari Inna Amina ta sani dan bazan iya bijire mata ba idan ta hanani. Yanda take hanani neman taimako a wajen Mallamai ya sa wani zubin shaidan Kan rayya min kila dan bata San zafin haihuwa bane shiyasa take hanani sai idan naga alherinta Kuma a gareni sai nayi istigifari Tana iya k'ok'arinta wajen nuna min na rungume kaddarar da Allah yamin dan Allah Kan jarrabci bawansa dan.ya gwada imaninsa. Bansan Mai yasa akan yarana imanina yake neman yin rauni ba Ana saura kwana biyar na tafi Na hau mafarkin Ina hauka tuburan a mafarki kafafuna ba takalmi Ina tsince tsince a bola kaina na zura Leda Yarana nesa Dani Kuma suna ta kallona suna kuka. Naseer shima Yana daga gefe yana kuka Yana San zuwa wajena ana ririke shi. Waleed da Zahira su Kuma haka zan gansu a daddaure an jinginasu da bishiya suma suna kukan Ina ganin haka zan nufi wajensu a guje kafin na Isa wajensu zanga Mahaifiyata na shara tana "karkiyi tafiyan Nan indai Kika taka kafarki Kikaje garin nan sai kin haukace abinda suke so kenan karki je Naeema ki cigaba da ga yawa Allah Yana sane dake Naeema Daga haka Zan farka. A jajjere nayi mafarkin har sau uku kuma mafarkin iri daya. Sosai jikina yayi sanyi da irin mafarkin da nake yi dan ni nasan bana mafarki da mahaifiyata ya zama ba gaske ba Iya kan had'uwa ta da Inna Amina ya kara tabbatar min da haka. Amma kwadayin San yarana su warke yasa wani barin zuciyata cemin nayi ta sadaka insha Allahu mafarkine kawai. Ba nida kudi kamar da akan abinda ya samu yarana da San su samu lafiya na siyar da gidana ban taba zaman haya ba Amma gani Ina zaune a haya Sana'ar ma da nakeyi Yan bashi sunfi yawa. Da taimakon Allah da arzikin Yaya Mata da Allah yamin asirina ke rufe dan Nadeeya da Minal ba laifi ma nemansu suna iya k'ok'arinsu wajen kyautata musu Wanda a hasashena da biyu sukeyi tunda sunga halin da muke ciki. Duk da mafarkin Ina rufe Ido zanyi hakan bai saka na girgiza da san fasa tafiyar ba. Addu'a kawai nake da sadaka Ana saura kwana biyu na tafi da yamma Ina zaune a tsakar gida. Waleed ya shigo gidan ba Sallama bai Kuma gaisheni ba ya shige daki ya Tara uban gashi kamar mace yaron da bai wuce shekara Sha hud'u zuwa biyar ba Nan da Nan ya Ajiye saje da gemu. A duk abinan abinda ke kwantar min da hankali bai wuce shaye shaye da ba yayi ba Da Ido na bishi har ya shige daki. A hankali na cigaba da sauke numfashin da naji Yana min wahala kirjina yamin nauyi Daga ni sai Inna Amina ke gidan Dan duk sun tafi islamiyya. Mik'ewa nayi na Shiga d'akin da ya Shiga. A Gefen gado nagan shi a zaune yana gyara wani Abu irin da ake Jin kida dashi da matasa ke yayi (Bluetooth) Shigowana bai saka ya d'ago ya kalleni ba illa Yan kananan wukakensa daya ajiye a gefensa daya d'auke a mayarsu cikin gidansu ya saka a Aljihun wandonsa Girgiza Kai na nayi na zauna a gefensa kirjina kamar ya Fado danaga yanda ya Tara farce cikin sanyin murya nace "Waleeed" Sai dana Kira shi ya Kai sau uku kafin ya d'ago Hada idon da nayi dashi yasa hawaye hau zubomin. Waleed ya rame sosai yayi duhu duk da ba fari bane. Cikin idonsa kawai in ka kalla zaka san Sam dabiun daya ke yi aransa yayi ba halinsa bane. Yana Nan a yaro Mai hankali Mai tarbiyya canza shi kawai akayi. Shima rashin Jin Rama yake saka shi. "Allah ya shiryeka Waleed Allah ya dubeni da idon rahama yasa Kai da Zahira ku dawo yanda kuke a da Waleed nasan duk abinan da kakeyi ba yin kanka bane Waleed ka rage rashin ji kaji ka tausaya min Kar na mutu lokacina baiyi ba. Dan Allah bani wuk'akk'en nan da ka sa a Aljihunka"? Tunda na fara magana cikin hawaye naga Waleed jikinsa yayi sanyi Kamar ba shi ba Cikin bin umarnina daya saka naji kamar na taka rawa ya mikomin wuk'ar Ni kuwa na cigaba da Masa naseeha Rabon da na zauna waje daya dashi haka har na manta. Damar Dana samu yasa nace bari na dauko abin aski na aske Masa uban gashin daya tara da nake ganin kamar zai iya saka shi ciwon Kai. Ganin bai wani motsa ba yasa cikin farinciki jin Kamar Dana ya fara warkewa nayi d'akina da Sauri dan na dauko.abin askin Dana siya musamman dan shi dan ni ke masa aski. Sai dai Ina dawowa naga baya Nan sai wani farin takarda da ya Ajiye D'aukar takarda nayi Naga yasa "Ina yawan munanan mafarki akanki Umma ki dage da Addu'a" A ranar nayi kukan da ban taba irinsa ba wato Dana duk da an juyar masa.da.kai yasan yamin magana Mai dadi Kamar Wanda ya karamin karfin gwiwa nayi tafiya dan na samo musu lafiya. Na kudunduna takarda na fito daga d'akin A daidai lokacin da Inna Amina ta hau kwalla min Kira. Da Sauri na Shiga d'akin Bayan na share hawayena Ga mamakina ita ma sai cemin tayi "kwana biyu Ina munanan mafarki akanki mamana Ina yawan ganinki a mumunan hali dan Allah ki dage da Addu'a" Kamar ta sassareni da guduma haka naji ya akayi Inna Amina da Waleed sukayi mafarki iri daya Tuni na fara Jin tafiyar na ficemin a rai Amma kasan zuciyata kamar ingizani ake akan tafiyar da zanyi shine zai saka yarana su warke. Ina fitowa itama Zahira ta fado gidan Kamar wacce aka jefo tana sanye da matsassun Kaya Muna hada Ido ta sauke ajiyar zuciya ta kad'a kanta tayi daki. Itama bin bayanta nayi kamar yanda nabi bayan Waleed itama na hau Mata naseeha kamar yanda nayiwa Waleed ta nutsu kamar gaske duk da bata cemin komai ba Itama kusanci Dana samu da ita da karantar ta da nayi ya kwantar min da hankali ba kadan ba. Dan duk abinan tsorona ta wulakanta kanta a rabata da martabarta. Dawowar su Nadeeya gidan yasa suka haura da Minal ta zuciya ta bar gidan. Abinda ke ingizani nayi tafiyar tuni ya motsamin naji na matsu jibi tayi na tafi. A ranar bacci yayi ta daukata Ina mafarkin Ina hauka tub'uran Wajejan asuba nayi mafarki da mahaifiyata ranta a b'ace tana tamin gargadi Kar k'afata ta bar garin Kano Ina barin garin Kano an samu abinda akeso. Ba iya Mahaifiyata ba har da mahaifina da ba kasafai nake mafarki dashi ba. Kamar a gaske nayi mafarkin Tashina da Nadeeya keyi akan na makara sallah asuba yasa na mike a firgice Ina gumi. Kirjina na balain bugawa mafarkin da nake bai tab'a dagamin hankali Kamar wanan ba. Karo na farko da naji bana san yi tafiyar Amma abinda ke tunzurani nayi tafiyar na Kara ingizani. Nayi Sallah ne kawai amma ba'a nutse ba dan mafarkin da nayi ya tsayamin a rai sosai kwakwalwata ta kasa bani hadin Kai nayi tunani. A haka yarana suka bar gidan Jiki ba kwari na shiga d'akin Inna Amina. Ido ta zuba min har na ajiye flask din kunun dasu Nadeeya suka Dama mata Na gaisheta a madadin ta amsa min sai cewa tayi "Da kin d'aukeni tamkar Mahaifiyarki Kamar yanda kike fada da baki ringa min boye boye ba Naeema ni nasan akwai abinda kike boyemin da nake ji a jikina ba alheri bane a gareki Naeema sanin da na Miki ba haka kike ba kin kasance yarinya Mai balain hakuri da tunani duk abinda ya Sameki kina Imani cewar Allah ne ya rubuta a takardarki akan zai sameki ba mutum ba sai dai mutum ya zama sila tunda ga farkon haihuwarki har zuwa lokacin da zaki koma ga Allah Allah ya riga da ya tsara Miki rayuwarki babu dan Adam daya Isa ya canja shi Idan Kika duba baya da Abubuwan da Suka faru dake da Imani da kikayi da Allah kin samu maganin matsalolinki batare da kin wahala ba Amma akan abinda ya samu yaranki imaninki yayi rauni har kina tunanin sai kin je wajen wayanda muke hasashen sune silar shigar yaranki wanan halin kina nufin Allah baifi karfinsu ba sai har kinje kin rokesu su warware abinda sukayi. Abaya su ne suke Miki maganin matsalarki?su Kika je Kika samu akan larurar Zahira? Mai yasa bazaki dogara ga Allah ya isar Miki kamar yanda ya isar Miki a baya ba Naeema"? Tamkar yata na d'aukeki idan Abu ya Samu bawa Allah yake gayawa ya magance Masa matsalarsa domin Allah Mai jine Mai Kuma gani duk halin da bawansa zai Shiga yana sane sai dai mu muyi gajeran hakuri kamar yanda kike yi yanzu Karki ga muna ta ga yawa Allah har yanzu shiru wlh Yana sane zai amsa Mana a lokacin da bamu zata ba wuyanta muyi hakuri dan haka kiyi hakuri ki koma ga Allah ki cigaba da gaya Masa Yana sane dake zai amsa Miki insha Allahu. Domin matsalarsu nayi azumin kwana bakwai da niyyar Allah ya warware duk abinda aka yiwa yaran nan ga ruwan zamzam nan kiyi kokari su biyun su Sha ki Kuma shafe musu jikinsu dashi zamu dace watarana insha Allahu" Kuka na fashe dashi sosai dan tabbas duk abinda ta fada gaskiya ne imanina yayi rauni akan San yarana su warke. Ni kaina nasan yanda nake dukufa da Addu'a a baya ba haka nakeyi ba yanzu. Ina sallah Ina tunani karshe idan naga zuciyata baa nutse take ba sai na hakura da sallah. Godiya na ringa mata a raina Ina Jin na hakura da tafiyar ba Inda zani Zan cigaba da gayawa Allah sai a lokacin tunanin Naseer ya fad'omin arai. Har nayi tunanin ko ina yake yanzu na Kuma ringa Jin kamar ban kyauta korarsa da nayi daga gidana da bai kareni da komai bama sai asara dana tafka ta hanyar siyar da gidana "(Duk.mafarkin hauka dinan da komai ba fiction haka tayi mafarki Allah ya tsallakar da ita) Calabar Safiyya Tunda ta samu cikar burinta akan Zahira da Waleed take cikin tsananin farin ciki zuciyarta v bata tab'a k'issa mata alheri ba sai sharri A duk lokacin data bude ido taga hauwa yarta da ta siffantu da d'abba takan ji tsanar Naeema da duk ahalinta. A idonta gani take ko ta samu nassarar kashe Naeema da yaranta har da Naseer da ya Zama babban makiyinta zuciyata bazata taba sanyi ba tunda duk a silarsu take Kan Shan wuya da hauwa da take Mata fatan mutuwa sabida wahala da take Sha akanta Dakyar ta samu tayi abubuwan da tayi Bashir ya fito daga prison Wanda ta gwammaci har zamansa a can da sakinsa da akayi. Mugun barawo ne dan d'abba mashayi. Da cikin da ta Kara samu da baban Hauwa Bashir ke nada Mata mugun duka idan yayi shaye shayensa Sata kuwa baa Kama hannun yaro Halayen Bashir yasa mahafin hauwa sakinta saki uku bayan ya kwashe duka kayansa ya bar gidan Dan kananan sanaoi da take shi ke sawa ta samu na abinci har yaranta su samu Suma da sun kawo girman da take fatan su fara samun Samarin da zasu na kashe musu kudi. Kamar yanda taci buri akansu take fatan Yan biyun nata suyi farin jini irin na Zahira sai dai shiru. Da tsohon cikinta Bashir ya Sha jawo mata a kulle ta dan amfana da Oban keyi da ita yasa yake siddabarun da ake sakinta. A cikin wahala ta haihu da ita kanta batasan cikin na baban Hauwa bane ko Oban da baya iya Bata ko sisi amma duk wani Abu na mugunta Idan Tana so zai Mata akan bashi. Rabi ta sawa yarta data haifa Dan kudaden data samo dan ta dan siyi abinci da zasu ci ita dasu Yan biyu Haka Bashir yazo da wuka yace ta bashi. Tana gardama ya rufeta da duka Kamar ba uwarsa ba ya dau wukarsa Mai kaifi ya tsage Mata fuska dashi.. Sai da ta Sha Jinya ta dawo daidai baki.kam ba irin Wanda ba tayiwa bashir da tayi mugun nadamar aikin da tayi har aka sake shi ba Tana tsoron Bashir ya Zama ajalinta watarana Ta Kan je wajen Oban ya duba Mata halin dasu Zahira ke ciki halin da suke ciki kawai ke faranta Mata rai yanda Naeema take neman haukacewa Akan yaranta. Yanda Naseer ya tsani bud'e ido ya ga Waleed Yana balain saka zuciyarta sanyi uwa uba fadan da Naseer da Naeema ke yawan Yi komai yana Mata yanda takeso. Ko damuwa ba tayi da matsalar da take ciki ba tunda ta samu cikar burinta a haka a garin duba halin da su Naeema ke ciki Oban ya gano Mata Naeema na shirye shiryen zuwa calaba nemansu dan ta rokesu su karya abinda aka musu. Cikin tsananin mugunta Safiyya tace.masa tana san ya Mata aikin da Naeema tana shakar iskar garin calabar a ranar ta haukace hauka da zata na cire kayanta tana bin mutane da gudu. Oban take ya bata layoyyi masu yawa yace taje tashar da motar Kano ke sauka ta binne layyar a wajen. A duk ranar da Naeema ta taka kafarta garin calabar a ranar zata haukace Amma idan aka samu akasi Naeema bata zo ba abin zai koma Kan wani nata. Take ta amince Oban ya dirjeta ya bata layoyyi da kwallin farin jinin da zata kai wa Yan biyunta Suyi farinjini da zasu yi Samari. A daren taje Tasha ta binne layyar tana murna Naeema na dab da haukacewa wuyanta ta tako garin. Washegari ta nema kayan gumama ta baza yaranta neman saurayi bayan sunji uban kwalli. A ranar kamar ta kwana rawa da ta ga Safiyya da asmau sunyi Samarin Har an hidimanta musu ta samu abun duniya da bashir yazo ya musu fin k'arfi ya kwace. Gefe daya.tana murna kasuwar da yaranta sukayi gefe daya Kuma tana hanya zuwa wajen Oban dan taga halin da Naeema ke ciki ta taho ko bata taho ba. A yau ma a k'ofar gida ta bar Asmau da itace hassana sosai take ji da ita sabida tafi Safiyya farin jinin samarin yanzu ma wani dan acaba ne yazo wajenta zance A ranta ba haka takeso ba manyan masu kudi takeso su ringa zuwa Amma tafi tafi dai tasan zasu Zo. Wajen Oban taje ya duba Mata su Naeema inda yake gaya mata ai gobe Naeema na tafe. Dan Yana ta ingiza ta akan tazo A ranar sabida farin ciki a wajen Oban ta kwana da yarta rabi ya dirjeta San Ransa Washegari wajen Tara tayi gida zuciyarta fes a idonta hango Naeema kawai take ta haukace. Har Tasha zata je ta zauna taga yanda Naeema zata haukace Sai dai tunda ga nesa ta hango k'ofar gidanta dankar da jamaa kafin ta gane Mai ke faruwa Asmau da aka riririke tsirara ta kwace daga hannun mutane ta Kara fita a guje............. Kila gobe ajini Ngd en uwa da soyyaya da Kauna Allah ya biya muku bukatunku na alheri masu San cigabana ngd. Yar uwa na barar adduarku 👇 Hi sadnaf ykk ya karfin jikin Allah yasa kaffara ne Wlh Ina cikin rudani nikam yayata ce uwa daya uba daya takeda yaro marar jin magana Allah yamasa baiwar karatu takowane bangare dan shekararsa 10- yayi saukar kur'ani saidai a kyale Shima saboda rashin son zuwa makarantarshi gashi Yana Yan dauke dauke Amma a gidansu takai har ya dauki Abu a gidansu yaje ya siyar yau ma abunda yasa take bani lbr tace babansa ya siye bakin Mai na mota dubu 7 da wani Abu shine ya saceshi yaje ya siyar 5k 😭😭 wlh Allah Dan yayatane na farko shidaya ke gâresu lta da mijin Saïda yayi 10 yrs sannan Allah yabata wani yanzu yanacikin 2 yrs Dazun Nan take gayamini sunkaisa wurin wani malami akace ture akai Masa na bakaken Aljannu masu hanashi karatu Kuma suna sakashi Satan ,Kuma acikin satin da sukaje wurin malam Kuma malamin islamiyarsu ya Kira babban shi yake gayamasa an fara Masa Aiki Kuma tace rubutune ake wankemasa takebashi yanasha wlh tallahi tacemini sai Ranar karshe ta kuskure Shi malamin ma na farko dasukaje yabasu magani yace idan ya Kare sudawo cemin tayi a Ranar dasukaje wurinsa data dawo batayi kwana ba a ka dinga Bata tsoro tacemin in ma bayanzu datakemini firar ba tsakaninta da babbanshi basu taba dauko firar malamin ba Amir yanada tsananin ilimi n'a nan mamaki wlh KO islamiya sau 1 akemasa Kari ya hardace DUK da rashin zuwanshi kullum sbd ana kaishi zai tsere wani time in Amma a haka ya sauke malaminsu cewa yayi dayana tsayawa yayi karatun da tun ba'a Kai haka ba zayyi sauka zai kebeshi ba cikin ajiba Yana Masa Kari Amma Ina bayaji Iyayensu dukansa suke kamar jaki saboda karatu saboda sata Amma baya Bari Ranar akan Keke yaje maradi daga anbashi Dani 37 kilometers daga Nan zuwa maradi Amma yaje Tacemin yanzu sunbar dukansa ma Tunga aka gayamusu haka akace Kuma mace ce tamasa turen mamansa dai tacemini ita batada wani makiyi Kuma irin ma tace wane ko wance take zargi itadai Babu batadai San ko babanshi ba Kuma mezai hada babbanshi da mata har a turoma dansa wani abun Tacemini bazata manta ba lokacin suna tsohon dakinsu Amir Kuma Yana falo Yana bacci itakuma Tana tsakar gida acikin baccin yatashi ya rike kansa Yana ihu yanata kuka tun Yana primary 2 tace tayi tunanin ko cinnaka yacijesa a kunne amma yace aaa bayan gayama kukan ta tanbaya meyasa meshi yace wani suka harbamasa ball a Kai Tacemini wlh koma minene a lokacin yasamesa Kinsan Allah saboda hakinshi na daukar abun mutane yafita Raina ko inada Abu ban iya basa Yana batamini Rai kullum cikin warar sa nake Dan babbu jimawa an taba daukemini kudi bayan jaka 4500 Kuma Yana wurin Koda Naga bangansu ba nace shine Daman ma aikesu nabi bayansu su 3 shida autan Mu da dan yayata guda dana hangosu niyata idan n'a ISO na daukeshi da Mari Amma sai na fasa nacemusu Kai an daukemini kudi kutsa in lalubeku ke in karemiki karshen zance shidaya na lalube nace bakowa bane Kaine sai cemini yayi ya hade hannayensa haka🤌🏽ya daura a kirji yace yanzu tanti mina Ni kadai kike zargi na daukarmini kudi bakomi sai yabani tsananin tausayi jikina yayi sanyi Nasan fa Yana dauka Amma wadannnan bashi ya daukaba amma wlh har yau Abun Yana Raina dayacemini yau da mamansa ke gayamini saina Goda Allah da alokacin ban marésa Yanzu aji daya yake a secondary Amma exam na karshe bayyishiba Ashe koyafita gidan bazuwa yakeba Sai bayan angama iyayye suka sani Kinga sai Kora ko indai ba gyara akamasa ba Ya fa Yi sauka Amma har gobe saï akaishi islamiya muddin ba'a kaishi ba bayazuwa Saidai dayafita gidan ya tsere Wlh data ke gayamini lbrn zahira ya fadomini a rai Muma muna barar addu'a idan Kuma dawasu addu'o'i ataimakamana Allah ya taimakemu😭😭 Wlh hankalina yabtashi*NAGA TA KAINA* *NA SADNAF*🌸🌸 ®️ *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_* _{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_ *Free Novel* *Ngd masoyana da suka nuna min kauna Kaunar da kuka nuna min yafi faranta min fiye da komai ngd* *Page 61* Hankali a balain tashe Safiyya ta bi Asmau a guje tana zunduma ihun a taimaka mata a ruk'o ta Amma duk yanda aka so riketa kasawa akayi dan ko an riketa sai ta kwace ta Kara fita a gujen Safiyya zub'ewa tayi a kasa ta hau birgima tana ta Shiga uku ganin Asmau a cikin wanan halin ya kusa sawa zuciyarta ta buga. Wajen Oban ta koma da isarta ta zub'e a kasa kafin ta Masa bayani yace mata "Naeema ce ta fasa zuwa shiyasa haka ta faru ga yarki duk iya k'ok'arina dan na ga na ingiza ta tazo taurin kanta yasa ta fasa zuwa matar Nan tana da wahalar shaani bansan ya akeyi take tsallake duk abinda mu ka mata ba yanzu abinda za'ayi kiyi Sauri kije tasha Inda Kika binne layyan nan ki hak'o ki kawo min nayi aikin da Asmau zata dawo daidai. Da balain sauri ta mik'e ta nufi Tasha dan ta d'auko layyar da ta binne sai dai tana Isa ta kasa gane Inda ta binne layyar. Kamar zautaciya ha ka ta ringa bin waje waje tana tonowa mutane sai kallonta suke. Mutanen da yawa sun d'auka itama hauka cewa tayi hakane yasa aka fitar da ita daga tashar ta karfi haka ta Kara komawa wajen Oban tana kuka akan bata gane wajen da ta binne layyar ba ya taimaka Mata yayi aikin da yarta zata dawo daidai. Oban haka ya hau tsubbuce tsubbuce ganin ba abinda zai iya yi akai yasa ya d'ago ya hau cewa ta nemo Abubuwan daya San ba yanda zaayi ta samo su Koda kudinta. Safiyya haukacewa ne.kawai bata yi ba. Haka ta koma gida tana rusar kuka. Tsanar Naeema da San ma rabata da ranta na darsuwa a ranta har yau Bata ga ribar data ci akan Naeema ba duk abinda take Mata kanta yake dawowa tunaninta bai tab'a bata Allah ne ya tsayawa Naeema Sharrinta ke komawa kanta ba hasali gani take duk abinda ya sameta laifin Naeema ne Bashir babban danta babban barawone, Asmau yanzu ta haukace Hauwa ga ta Nan kamar ba mutum ba Safiyya da Rabia jaririyar ta kawai ne wani Abu bai same su ba duk wanan tashin hankalin ta dalilin Naeema ne dan haka ta Sha alwashin sai dai idan mutuwa tayi sai ta samu cikar burinta akan Naeema zata samu kwanciyar hankali Dak'yar ta samu wasu matasa Suka kamo Mata Asmau da sai da tayi sati uku a waje tana bin bola tana bin mutane a guje tsirara ba kaya a jikinta Abinka da budurwa a haukace haka aka rabata da budurcinta kafin Safiyya ta gano Inda take ta saka a kamo Mata ita ta saka ta a d'akin da ta kulle hauwa ta datse da mukulli. A gaban idon Safiyya takwararta Safiyya ta fara bin mazan. Yar iskar da take San Zahira ta zama sai gashi Safiyya ce ta Zama a gaban idonta zaa Zo a d'auketa a dawo da ita washegari ko sisinta ba Kuma zata bata ba daga ita har Bashir Basu d'auketa a matsayin uwa ba ubanta kawai suke ci. Abu goma da ashirin haka suka hade mata duk lokacin data duba yaranta ta ga halin da suke ciki zuciyarta kamar ta buga sabida bakin ciki ga mugu mugun tsanar da ta yiwa Naeema da iyalanta gabadaya rashin nutsuwa yasa ta kasa komawa wajen Oban da ayi Mata mugun aikin da zai Saka Naeema ta mutu Tama bar Mata duniyar duk da tana ganin ko Naeema ta mutun hakan bazai sa taji sanyi a zuciyarta ba sabida tsabar tsanar da ta mata. Tana sane da Hajara bata taba tunanin waiwaiyar ta ba Dan gani take itama tana cikin wayanda Suka jawo mata Kara lalacewar Bashir. Haka Safiyya ta kasance cikin tashin Haukacewar Asmau da ta lura har ciki ne da ita. Wajen Oban ta koma ta cigaba da rokonsa ya Mata aiki Asmau ta dawo daidai shi kuwa Oban ya ringa kwasar rabonsa a jikinta Yana saka ta Nemo kudi ta kawo masa akan Kar ta damu Yana aiki akan Asmau zata samu lafiya. Haka tayi ta saka Rai da samun lafiya Asmau da ke haukanta tuburan da ciki har ta haifi yarta mace a cikin halin hauka. Safiyya tana ji tana gani tayi jika shegiya da Bata San ubanta ba haka ta hau rainon jaririyar cikin bakin cikin duk halin da ta tsinci Kan ta a ciki da take ganin duk Naeema ce ta jaza Mata. Wanan kenan Hajara Rayuwa ba karamin wahala ya Mata ba dan ciwon kafar da take yasa dan kosai da take soyawa ta daina iya fita soyawa dan canji Kan da take dashi haka duk ya kare a hannunta haka ma kudin hayan gidan da ta Kama Tana ji tana gani aka koreta daga gidan. A ranar da aka koreta da Jan kafa ta nufi gidan Safiyya dan bata da Inda zata je daya wuce wajen Sai dai da isarta Safiyya ta rufe idonta ta koreta akan bazata zauna Mata a gida ba itama ta kanta take abinci itama sai tayi da gaske take sa mu taci taje wajen Naseeru da ta zabeshi da sabida Kar ta Masa komai ta gwammace ta fasa mudubi danta Bashir ya Kara zama katon barawo. Hajara kuwa bakin cikin abinda Safiyya ta Mata yasa ta ringa tsinewa Safiyya tana jawo Mata iftilai rayuwa Zagi in zaga Haka sukayi kamar ba uwa da 'ya ba Hajara na kuka ta baro gidan Safiyya ta hau laluman Inda zata zauna dan Bata Isa ta soma tafiya Kano wajen Naseer ko Tijjani ba Safiyya ta Riga da ta cutar da ita intaje Kano ma kila Yan sanda su Kamata Yau da ba dan Naeema ba da rayuwata duk bata juya haka har wajen Zama ya gagareta ba. Haka ta ga ma kewaye unguwar Bata samu waje ba kamar tsinuwa duk Inda taje sai an koreta Sai a wani rumfa da Rabinsu mahaukata ne anan ta samu wajen kwana Anan Kuma ta mayar dashi gidanta K'arfin hali irin nata yasa ta hau bara tana neman kudin da zata ga bayan Safiyya da Naeema. Dan tsana take Mata da take Jin wani Abu ya tokare Mata kirji har sai ta samu cikar burinta zata samu sausauci a zuciyarta Wanan kenan. Naeema Tunda Inna Amina ta min fada na watsar da komai na maida lamurana wajen Allah nayi k'ok'arin rungumar duk jarrabtar da Allah ya min da hannu biyu addua Shiriya kawai nake yiwa Waleed da Zahira. Inna Amina na Tayani Dauriya kawai nake da muka tafi shekara biyu Naseer bai neme mu ba Ina tsoron ko wani abune ya same shi sai dana dawo hankalina na fara tunanin duk halayyen da ya ringa nuna min ba halinsa bane kila shima tab'a shin akayi. Addu'a nake akan Allah ya kareshi ya sa ya dawo hankalinsa ya dawo ko dan Nadeeya da yanzu ta fara jamia maneman Aurenta na ta zuwa ko ta Ina neman aurenta. Burina yanzu ko Humaira ce ta samu miji aurar da ita zanyi. Zahira da waleed Kam addua kawai Zan cigaba da tayasu dashi akan Allah ya shirya min su duk da bana San yaudarar kaina sai nake ganin kamar sun fara dan canjawa tunda Waleed na dan zama a gida yanzu inya ga dama har ya kwana. Zahira ma ta fi bani mamaki dan tana zama yanzu a gida sai idan an b'ata Mata Rai take fita. A yau da yamma muna zaune gabad'ayan mu atsakar gida har da Inna Amina dasu Nadeeya suka tilasta mata fitowa tsakar gida. Suna ta tsokanar ta itama tana tsokanarsu. A rayuwata ba abinda ke Sakani farinciki sama Dana ga yarana gabadaya a waje daya suna hira ko ban sa musu baki ba Ina Jin dadi a Raina. A hankali na ringa binsu da kallo dukaninsu sun girma sun Zama Yan Mata Masha Allah har Raheema dake da shekara goma Sha shidda. Abinda ya ragemin Jin dadi Bai wuce halin da yarana biyu suka tsinci kansu a ciki ba. Ko yanzu ma Zahira bata nan haka ma Waleed Ina zaune ne kawai amma zuciyata na wajensu. Shigowar Waleed da Sallama kasa kasa yasa na amsa da Sauri Ina lalubar kwayar idonsa Ina ganin canji sosai a tare dashi tunda aka juya Masa Kai bai tab'a shigowa gidan da sallama ba sai gashi kwana biyu na lura Yana shigowa da sallamar duk da kasa kasa yake sallamar. Girman jikin da yake dashi da kwarjini yasa k'arfi da yaji yayayensa suka koma shakkarsa idan ka ganshi zaka iya tunanin ya girmesu Sabida naseeha Dana wa yayyensa yasa suke hakuri da duk wani rashin kunyar da yake musu. Kitchen ya Shiga ya d'auko abincinsa har zai Shiga d'aki Inna Amina ta Kira shi akan yazo gefenta ya zauna. Gefenta ya zauna ya fara cin abincin kallona da Inna Amina tayi yasa na mik'e na Shiga d'akinta na dauko ruwan Addu'ar Waleed da Zahira na tsiyaya a Kofi na Kai Mata ta mik'awa Waleed ya karba. Jansa Inna Amina ta fara yi da hira Sai gashi Waleed ya saki jiki Yana hirar shima alhamdulillah Ina ganin canji sosai a wajen yarana. Kamar Dani yake hiran haka na zuba Masa Ido Inna Amina na Masa naseeha cikin siga har tana idan ya gama cin abinci yaje yayi sallah Yana kuwa gama ci yaje yayi alwala. Ya Shiga d'aki da zumar yin sallah Dan tsakar gidan namu karami ne sosai. Sallamar da akayi tare da shigowa yasa dukan mu muka kalli bakin kofa. Yarana Suka saki ihun murna sukayi wajen Naseer dana kasa d'auke idona akansa. Shima hadesu yayi ya rungumesu. Kwalla ya cikamin Ido Dana ga yanda ya rame har furfura ne suka firfito Masa Inna Amina kuwa tsabar murna tafi ta ringayi daga zaune tana Masa oyoyo. Dak'yar ya bambare su Nadeeya daga jikinsa Ya nufo wajen da muke Zaune yana zuwa ya zub'e a gaban Inna Amina ya hau gaisheta. Cikin murna ta ruko hannunsa ta hau amsawa tana had'awa da Masa tambayar Mai yasa ya Dade haka Bai waiwayo mu ba a matsayinsa na da namiji ai hakuri ya Kamata yayi bai Kamata yayi fushi ba. Fada da naseeha Inna Amina ta Masa ta had'a da bashi hakurin Abunda na Masa akan yamin uzuri idona ne ya rufe akan su Zahira shiyasa na Masa haka Murmushi yayi yana "Ba komai Mama wlh ban riketa a raina ba korar da tamin daga gidanta yasa Nima na samu Allah ya dafamin na nemi kudin da Nima na siyi filin nayi gini naje wancan tsohon gidan nata anan nake Jin labarin Kun tashi dak'yar na gane Kuna nan nima nasan Ina da laifi da Abubuwan da na ringayi a baya da Nima sai daga baya nagane ban kyauta ba sai dai na baku hakuri Allah ya kiyaye gaba" Sai a lokacin muka hada Ido dashi ya dan sakarmin murmushi Nima na sakar masa. Nadeeya ya kala Yana "Inna Zahira"? Nadeeya na k'ok'arin Magana Waleed ya fito daga d'akin. Na zubawa Naseer Ido naga ya zaiyi idan ya ga Waleed zai Masa wanan kallon tsanar daya Saba Masa Kallon kallo sukewa juna da yasa na kasa karantar kallon da Naseer ke yiwa Waleed har Waleed ya d'auke kansa yayi waje ba tare da ya gaishe shi ba Inna Amina da Sauri ta hau Masa bayanin halin da Waleed da Zahira ke ciki har yanzu da muke ta addua Allah ya shirya su. Girgiza Kai yayi Yana insha Allahu shima Yana addua Akan Allah ya warware abinda aka musu Daga haka ya cewa Nadeeya ta fita ta nemo masa Zahira A Dan karantar da na Masa sai Naga kamar har lokacin ba soyayar Waleed a Ransa (Duk da asirin da aka musu na karyewa har gobe Da nake rubuta wanan labarin wani zubin idan abin ya motsa Naseer da Waleed basa Zama inuwa daya bi maana Babu wanan soyayya d'a da uba Mai k'arfi a tsakaninsu) Nadeeya ya tasa a gaba suka je neman Zahira gidan kawayenta da wasu mun San gidansu wasu bamu sani ba da suka Taki saa gidan kawarta da muka sani anan suka same ta. Naseer ya taso ta gaba suka dawo gida. A Palo ya zaunar da ita ya hau Mata naseeha Inda ni Kuma jikina yayi balain sanyi da na ga kamar da Zahira kawai ya damu Banda Waleed. A ranar nayi kukan da na dade ban yi ba dan duk da a gidan ya kwana ya Kuma bani labarin Dana koresa daga gidan bai koma Abuja ba motarsa ya siyar ya hada da kudaden daya samo ya siyi fili Rabin filoti a gyadi gyadi ya hau gini ta hanyar neman kudi Yana buga buga har Sana'ar hannu sai daya koya dan kawai ya samu kudin da zai gina gidansa. Ko abinci baya iya sawa cikinsa sosai sabida kawai ya samu kudin gini Addu'ar da ya dage dashi yasa ya dawo hayyacinsa. Yana Kuma Kai karar mahaifiyarsa wajen Allah Dan ta cutar dashi. Cikin siga na hau shigar Masa da maganar Waleed da naga rabi yafi damuwa da halin da Zahira ke ciki har Yana cemin yanzu so yake idan mun koma gidansa ya dukufa da Addu'a Zahira ta samu Lafiya idan na Shigar Masa maganar Waleed sai ya Sako min wani zancen. Washegari da sassafe aka hau jiddar kayanmu Ana kaiwa sabon gida Ina ganin ya fita naje na samu Inna Amina cikin damuwa na hau gaya mata karantar da nayiwa Naseer akan Waleed. Hakuri ta bani tace na bi komai a hankali Kar na damu kila Abunda akayi a tsakaninsu bai gama warware bane mu cigaba da Addu'a. Yarana murna kawai suke zasu koma sabon gida Nima a kasan Raina na ji dadi sosai da Naseer ya samu ya Gina gidan kansa tamkar ni nayi gidan haka na ringa ji shima fuskarsa kawai zaka kalla kasan Yana dokin sabon gidan da yayi kamar bai tab'a gidan kansa ba. Ranar tashin namu daga Zahira har Waleed ba Inda suka je a ranar duk da Ina lura da Waleed da Naseer suna Yar kallon kallo Wanda hakan ya dameni sosai. Da yamma na shishiga mak'ota muka musu Sallama Inna Amina ita ta ringa lallaba Waleed dan kar ya botsare Mana yace bazai bi mu ba. Su Nadeeya dama sun dade a can dan tun safe Naseer ya Kai su dan su shirya Mana kayayyakin mu. Iya ni da Inna Amina sai Waleed da Zahira ne bamu tafi ba sai daddare Naseer ya kawo taxi muka hau Muka tafi gabadaya. Gidan yayi kyau ba laifi duk da gidan bai Kai girman gidajensa na baya ba dakuna hudu ne a gidan da falo kitchen da band'aki a kowane daki. Dan karfin hali har da dan kujeru sababi masu saukin kudi. Daga ni har yarana Sai murna muke Dakunan duk a cikin falo suke d'akin da bai Kai sauran girma ba aka sawa Inna Amina karamin katifarta da kayanta. Su Nadeeya Kuma suka dau d'akin tsakiya suka saka katifarsu guda biyu. Daya d'akin Kuma shine nawa dayan na Naseer. A Raina naso Waleed nada d'akinsa ba d'akin daya dace ya d'auka Sama da Wanda Inna Amina ke ciki Amma insha Allahu zanyi k'ok'arin sama Masa d'akin. Ban dawo daga tunanin dana tafi ba naji Waleed cikin dan daga murya Yana "Ni a wane daki Zan ringa kwana"? Naseer d'auke kansa yayi ya shige dakinsa Tuni naga Waleed na k'ok'arin Hawa wanan dokin zuciyar tasa dake sa yayi zuciya ya bar gidan Allah cikin ikonsa Inna Amina tayi saurin cewa a d'akinta zai ringa kwana ita a dakinsu Zahira zata ringa kwana dan Sam Bata San kwana ita kadai Inna Amina ce ta taimaka min aranar waleed bai zuciya ya bar gidan ba. Tunda Muka dawo gidan na lura Naseer bai fiye baccin dare ba yakan raba daren wajen sallah da Addu'oi tamkar dai yanda ya ke yi ada. Hakane yasa nima na Kara akan Wanda nakeyi da. Dawowar mu sabon gida tamkar k'ofar samun warakar yarana ne dan a hankali naga Zahira da Waleed sun fara nutsuwa suna Jin maganata har sallah da suke Wasa dashi yanzu suna maida hankali suyi duk yawace yawacen nan da sukeyi yanzu basa yi duk da Basu dawomin dai yanda Suke gabadaya ba Amma ko hakan suka zauna alhamdulillah. Allah kawai nake Godewa daya amsa Mana adduar mu akan yaranmu. Abu daya ke damuna Naseer da Waleed Dana ga Kamar basa ga miciji dan yanzu Waleed na gaishe shi wani zubin ya amsa wani zubin yyi kamar bai ji ba Inna Amina ke ta kwantar min da hankali tana hanani yiwa Naseer magana akan Kar na damu komai zai warware tunda har Allah yasa sun fara dawowa hayyacinsu ko Kuma muce sun ma dawo tunda yanzu duk sun daina Abunda sukeyi Waleed abinda kawai bai bari ba shine saurin zuciya da fushi. Itama Zahira hakane Amma ta dawomin zahirata yanda take a da. Burina Zahira da waleed su koma makaranta Dan an barsu a baya sosai hakane yasa nayiwa Naseer magana take ya Nemo makaranta ya biyawa Zahira waec shi Kuma Waleed da k'arfi nasa ya nema Masa makaranta ya fara daga jjs 2 duk da ya girma da jss 2 din Amma haka ya fara zuwa dan a haka ma mun masa tsallake. Sai a yanzu na samu kwanciyar hankali nake Kuma Godewa Allah da Kara neman kariyarsa a garemu gabaki daya Naseer yanzu kanannan sana'oin daya koya dashi yake rik'e damu duk da Nima Ina taimaka masa sosai dan ban saki sanaar da nake ba na siyar da kananan Abubuwa a gida. Zahira na dab da gama zana waec dinta tamkar yanda take da farin jinin samari awancan lokacin haka samari Suka hau layi a k'ofar gidanmu Wanda hakan ya sakani farinciki sosai dan inata addua Allah yasa Kar Nadeeya ta rigata aure tunda itace babba data samu Mai kaunarta Zan cewa Naseer mu aurar da ita. A Rana sama da mutane biyar na sallama suna neman Zahira Hakane yasa na zaunar da ita na gaya Mata a cikin masu kaunarta ta zabi wanda hankalinta ya kwanta dashi dan muna so tana gama jarrabawa idan Allah ya nufa tayi auren Ta cigaba da karatu a gidan mijinta sai dai budar bakinta sai cemin take ita so take ta cigaba da karatu tamkar yanda Nadeeya ta cigaba da karatun dan ita burinta tayi karatu Mai zurfi ta Zama lawyer dak'yar na shawo kanta ta amince zata tsayar da mutum daya Take kuwa ta tsayar da wani kabiru da Saurayine Mai Kuma kudi dan wlh duk Samarin Zahira ba karamin mutum. Tana gama jarrabawa ya turo magabatansa da kudin neman aurenta. Manyansa suka Kara da basa San a saka dogon lokaci kabiru yace zai dau nauyin komai ba sai mun wahalar da kanmu ba. Naseer kafewa yayi akan su bashi Nan da wata shidda zai Mata komai shi Baya so ayiwa Zahira gori. Sai dai dangin kabirun da roko da magiya da kyar suka shawo kansa ya amince aka saka wata daya da sati daya. Fadar halin farinciki Dana tsinci kaina a ciki bata Baki ne kudi na hau tarawa Inna Amina Tama fi kowa farinciki na kasa yarda zahirata da aka so watsawa rayuwa ce ta samu nagartacen miji har baifi sauran sati uku Aurenta ba. Dukanmu shiri muke har Naseer saura sati daya auren Zahira da kabiru aka kawo lefenta akwati shidda cike da kaya masu tsada a wancan lokacin. Nadeeya da Minal iyayen doki ba Wanda Basu Kira ganin lefen Zahira ba. Gefe daya Kuma dagani har Naseer da Inna Amina addua muka dukufa dashi ba dare ba Rana. Ana saura kwana uku daurin Auren Zahira kabiru ya aiko yan uwansa akan a bamu hakuri ya fasa auren Zahira hmmmmmm.... Advertisement Treat/repair your skin with mg's skincare today,are you battling with pimples, Black spot cream reaction eczema,acne, sunburn,spot, stretch mark, discoloration/skin damage, stretch mark ❌then mg's skincare is the plug for you,mg's skincare gat solution to all ur skin prblms😍everyone deserves a blended skin🌿 when it comes to skin issue😢gv it to mg's skincare 💯🔥 now is the time to take care of ur skin,this product is the real deal 🙌clears white patches✅dark patches✅dark feet's/knuckles ✅reduces the appearance of greenveins,it clears pimples,spot and make ur skin fresh nd glow like never before just gv it a try nd ur skin will definitely thank you💋✅evn if you don't HV anything mg's skincare gat you a soap that will maintain ur skin nd make the skin to glow🥰 Soap price:3k Chat 08062991549 to plc ur orders Call:08064532391 We deliver Nationwide buh delivery is not free🙏 we can't wait to be a part of your beauty story🤭[8/23, 2:44 PM] Zannura: *NAGA TA KAINA* *NA SADNAF*🌸🌸 ®️ *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_* _{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_ *Free Novel* Page 62 Suman zaune nayi bakina yamin nauyi ballantana na tambayesu dalilin daya sa kabiru yace ya fasa auren tunda Suka Fadi abinda ya kawosu naji kamar an sokeni da kibiya a kirji har yau da nake labarin nan Ina fama da Wanan ciwon kirjin idan abu ya girgiza ni. Muryar Zahira naji da bansan lokacin da ta fito da ga daki ba sai ganinta nayi a tsakiyarmu Kwalla cike da idonta ta zub'e a gaban wacce take yayar kabirun da itace Kan gaba wajen Shirin bikin kanin nata ba ma a garin Kano take aure ba daga Abuja tazo. "Aunty Mai nayi Masa yace ya fasa aurena"? Aunty yau saura kwana uku aurenmu ba Wanda Bai San zamuyi aure ba Mai nayi Masa da sai a yanzu zai janye"? "Wlh bansani ba Zahira jiya ya sako mu a gaba akan muzo mu baki hakuri akan ya fasa auren ba yanda ba muyi dashi ba ya gaya Mana dalili yak'i da yaga mun dage Masa ma sai ce Mana yayi idan muka matsa Masa Zai kashe kansa Akan Dole yasa muma muka zo yanda Kika ga Kuna ta Shiri wlh muma haka muke shiri ba Wanda bai zo ba duk gidan mu baki ga yanda muke kaunarki ba amma kabiru lokaci daya yace mu zo mu baki hakuri ga wasika nan ya bani na Baki" Yayar kabirun ta karashe kamar zatayi kuka tare da mik'awa Zahira da hawaye ya jika gaban bak'ar doguwar rigar da ke jikinta hannunta ya Sha Jan kunshi da baki gashinta har baya ya sauko dan Kamar yanda naji su Nadeeya na shiri a yau zasu yi kamu a gidan wani Alhaji dake kallon gidanmu yanzu haka ma su Nadeeya na can suna ta shirya wajen. Zahira ba ta iya karbar wasikar ba illa mik'ewa da tayi ko taku biyu ba tayi ba ta zub'e a kasa. Nayi kanta aguje a daidai lokacin da Waleed ya shigo hannunsa d'auke da kayan rabon da zasuyi a kamu. Zubar da kayan hannunsa yayi yayo wajenmu agujen ya Tayani tallafar zahira dan Nima jikina rawa yake d'aukar ta yayi cak yayi daki da ita. Ni Kuma na cewa yayar kabiru "Ba komai Allah yasa Hakan shiya fi alheri kila da ma Zahira ba matarsa bace shiyasa ya janye" Hakuri Suka cigaba da bani nace musu ba komai suyi min hakuri Nasir ya dawo na Masa maganar kudin auren da kabiru ya kawo a mayar musu da lefen da suka kawo dan dama Allah cikin ikonsa ban Bari ta tab'a komai ba ganin kabiru ya rage Mana nauyi sosai yasa nida Naseer muka Mata dinkuna daidai karfinmu. Mik'ewa suka yi da Sauri suna "wlh yace ya yafe mata komai ba sai mun karbo komai ba kuyi hakuri dan Allah" Nima da Sauri na girgiza musu Kai Ina "ba za'ayi haka ba idan har zai fasa Aurenta banga dalilin da zai saka ya bar mata lefensa har da kudi ba. Nayi dakina da Sauri Ina kwallawa Raheema da Humaira Kira da nake Jin shewarsu a d'akin Inna Amina da alama Basu San me ke faruwa ba kunshi ma ake musu a d'akin. Da Sauri suka fito daga d'akin hannun humaira d'auke da kunshi Dangin kabirun suka gaisar suka yo d'akin nawa. Danne zuciyata nake Ina mayar da kukan da ke neman cin karfina ya fito da k'arfi. Indai na nuna rauni na a gaban yarana su ya zasuyi kenan ya zama Dole nayi k'ok'arin danne zuciyata. Umarni na bawa su Humaira da su kai min akwatunan waje yanzu nan kar su b'ata min lokaci. Dan jikina rawa kawai yake ballantana na iya d'aukar wani akwati. Had'a Baki sukayi wajen cemin "Umma lafiya kuwa Mai yake faruwa ne"? Tsawa na daka musu a daidai lokacin da kuka ya kwace min Ina "Ku fitarmin da akwatin nan nace ku daina min tambayoyi sunce sun fasa aurenta"? Kamar wayanda na watsawa ruwan zafi haka suka ja da baya suna dafe kirjinsu Ni Kuma na zauna a gefen gadon na rufe fuskata Ina cigaba da kukan da na kasa dannewa. Ni kadai nasan mai nake ji a kirjina Waje sukayi gabad'aya Basu dau akwatin kamar yanda na umarce su ba sai ji nayi cikin muryar kuka suna tambayar danginsu kabiru mai Aunty Zahira ta yiwa kabiru da zai fasa Aurenta Raheema har da cewa "Ku rufa Mana asiri karku Mana haka yau fa zaayi kamu ba Wanda bamu gayyata ba Mai aunty Zahira ta Masa da zafi haka da saura kwana uku aurensu zai ce ya fasa idan laifi tayi muku dan Allah kuyi hakuri" Ta karashe tana fashewa da kuka dayake akwatin irin Mai taya dinan ne a zuciye na mike na hau Jan babban nayi waje. Ina zuwa na Kara daka musu tsawa Ina su je su debbo min sauran akwatin Ana dole ne. Humaira aguje tayi d'akin nawa Raheema kuwa ta cigaba da magiya bakin ciiki yasa nayi kanta a fusace wata dattijuwa a cikinsu ta tareni da Sauri tana "Kiyi hakuri mmn Zahira wlh baa San ranmu haka ya kasance ba yarone ka haifeshi baka Haifi halinsa ba wlh nasan da ciwo Abunda yaron Nan yayi Amma ba yanda zamuyi dashi" Da sauri na katse ta Ina "kabiru da ma ba mijinta bane shiyasa Allah baiyi zasuyi auren ba halin da yarinya kawai zata Shiga ganin Aurenta saura kwana uku an fasa ni shine damuwa na Allah yasa hakan shi yafi alheri Allah ya musanya Mata da Wanda yafi kabirun ga akwatunan ku nan kudin auren na wajen baban Zahira idan ya dawo ya turo a karba Masa" Kuka Humaira da Raheema kawai suke Waleed da ke tsaye a bakin kofar d'akinsu zahira da duk Abunda muke Yana kallonmu sai hucci yake. Suna kokarin Kara magana ya daka musu uban tsawan daya sa suka gigice dattijuwan tayi hanyar waje da Sauri "Dan ya fasa Aurenta sai me ku gaggauta kwasar kayanku.ku bar Mana gidanan kafin na muku watsi da kayan waje Banda kaddara Mai aunty Zahira zata yi da wannan Mai zubin tsofaffin" Tsawa na ringa dakawa Waleed akan yamin shiru Amma ko kallona baiyi ba Abinda har gobe ke hadani dashi kenan tunda aka tab'a shi zuciya da taurin Kai ne dashi wani zubin baka isa ka Hana shi ya hanu ba ko wani Abun yayi idan babansa zai dakeshi baya guduwa haka zai tsaya a ga ma jibgarsa har sai dai idan Naseer din ne ya gaji dan kansa. Inna Amina ce ma tace ya bar Masa irin wanan dukan sabida Kamar hakan na Kara taurara Masa zuciya mu cigaba da binsa da Addu'a A karshe Waleed da kansa ya rakasu waje da akwatunan su Suka hau ja da sauri dan ba karamin tsorata su Waleed yayi ba. Suna fita na zub'e a Palo na cigaba da rusa kuka takarda da ya bayar a bawa Zahira na hannuna Tunani iri iri haka suka cikemin zuciya Ina tunanin Mai dalilin fasa auren Zahira da kabiru yayi Raheema da Humaira d'akin Inna Amina suka Shiga suka gaya mata Ina jinta tana ta zuba sallati. Waleed Kuma ya zauna Akan kujera Yana hucci Yana girgiza kafa. Mik'ewa nayi na nufi d'akinsu zahiran dan Naga halin da take ciki Akwance na tarar da ita ta juya bayanta tana kallon bango daga gani kasan kuka take kasa kasa Daga gefen ta na zauna banyi Mata magana ba na warware takarda da aka saka a envelope dan na ga mai kabiru ya rubuto a cikin takardar *KIYI HAKURI BAZAN IYA AURENKI BA ZAHIRA DAN BURINA NAGA NA AURI MACE TA GARI NAJI LABARAI AKANKI KALA KALA A CIKI HAR DA WAI KIN ZUBAR DA CIKIN SHEGE BAN YARDA BA SAI DANA JE GIDAN KAWAR TAKI TA TABBATAR MIN DA HAKA ASHE BA KARAMIN RASHIN JI KIKAYI BA INA SANKI AMMA A HAKA ZAN HAKURA DAKE NA BAR MIKI KOMAI ALLAH YA KAWO MIKI WANI MIJIN AUREN* ban Iya karasa karantawa ba na runtse idona kirjina na min nauyi Abunda nake ta tsoro kenan sai gashi kabiru yaji labarin rashin jin da zahira tayi da ba halinta bane juyar min da Kan ya akayi ko da tayi rashin jinta Alhamdulillah Allah ya karemin ita da Karfin Addu'a baa rabata da budurcinta ba sai dai wayanda tayi muamallan dasu ne idan za'a kwana Ana rantsuwa ba halin Zahira bane ba lailai a yarda ba dan kawayenta duk ba mutanen arziki ni nasan zasu iya komai suma dan su rama abinda Zahira ta musu dan da ta dawo hayyacinta da kanta ta musu rashin mutunci tace su daina zuwa nemanta tana kuka tazo ta sameni tana wlh bata San ya akayi tayi kawance dasu ba ita da take da kunya Mai ya had'ata dasu. Murmushi kawai nayi dan ni nasan da ma ba halin Zahira bane sai gashi duk da mun bar unguwar suna nufarta da sharrin ta zubar da cikin shege Ina mamakin halin wasu mutanen da Basu da burin daya wuce su bika da sharri dak'yar na taushi zuciyata na rik'e hannun Zahira na hau rarrashinta Ina Mata nasiha. Nasan itama kawaici kawai take min tana nuna min ba komai. Shigowar Nadeeya da Minal ya Kara hargitsa gidan suna koke kamar gidan rasuwa sai dana musu da gaske suka Shiga hankalinsu Nadeeya ta hau jawa kabiru Allah ya Isa har da cewa zata je gidansu. Inna Amina ta taimaka sosai wajen kwantarwa da Zahira hankali ta hade har da kannenta ta musu naseeha. Wajen karfe Takwas Naseer ya dawo niki niki da kayan abincin biki har da dinkin Daurin auren da zai saka inaga farinciki da yake ciki bai bari ya karanci yanda mukayi cirko cirko ba dan duk mun kasa walwalar har gwara ni Ina dan dauriya sabida yarana Amma kannen Zahira da suka ci buri Kamar an musu rasuwa haka su kayi cirko cirko. Daga yanda suka gaishe shi yasa ya fara lura da halin da muke ciki. Sai a lokacin ya kalleni ya tambayeni Mai ke faruwa ya Kara da Ina Zahira take Dan har Waleed Yana zaune a palon Zahira ce kawai a daki Ban bashi amsar tambayarsa ba dan bansan ya zan Masa bayani ba illa takardar hannuna kawai Dana Mika Masa. Kafin ya bud'e Naga ya kallemu duka Yana "Wai Mai hakane ba zaku gaya min mai ke faruwa ba" Ya bud'e takarda hannunsa ya hau karantawa Sallati kawai yake ni kuwa na kalli su Nadeeya take Suka mik'e suka hau barin palon sukayi dakinsu Waleed ya mike yayi d'akin Inna Amina. Yanda muryarsa ke rawa yasa hawaye ya hau zubomin Ina "Dalilin da yasa wai ya fasa aurenta kenan abinda nake ta gudu kenan Naseer duk da dukanmu munsan Zahira baa hayyacinta duk tayi wanan rashin Jin ba Amma ba Mai yarda ba halinta bane kila wanan ya zame mana bakin fenti kenan tsorona Kar ba iya ita kadai ba abin yazo ya shafi su Nadeeya An cutarmin da Yara Naseer wlh an cutarmin dasu bazan tab'a yafewa ba yanzu idan har masu neman auren Zahira zasu ringa Jin irin wadanan maganganun dak'yar Zahira ta samu Mai Aurenta" Na karashe Ina fashewa da kuka Naseer bai iya magana ba har lokacin illa sallati da yake yi idonsa ya kad'a yayi jajjur Bai hanani kukan ba illa mik'ewa da yayi Naga ya nufi d'akinsu Zahira da shigarsa su Nadeeya suka Kara fitowa Suka barshi da zahiran da zazzabi ya rufeta Nasiha ya Mata ya rarrasheta da kabiru ba mijinta bane shiyasa bai Aureta ba Insha Allahu zata samu Wanda yafi kabirun. Sai daya bata magani da kansa ya fito daga d'akin ya shige dakinsa tare da rufo kofarsa nima ban bi takansa ba na Kara duba jikin Zahira na koma dakina dan nima zazzabin naji Yana neman rufeni. A haka cikin kunya muka hada karyar an daga bikin Zahira sabida Wanda zai Aureta bashida lafiya Nadeeya ma karyar mutuwa ta ringa lankayawa kabirun. Ba Abunda baya wucewa a haka fasa auren Zahira ya wuce kamar baayi ba. Ana samun kamar wata biyu Zahira ta sameni a daki tana min zancen San cigaba da makaranta dan Nadeeya har ta kusa diplomarta dan itama Wanda ke santa so yake tana gamawa ya turo mune muke dan ki da tuni ya turo,na karanci saurayin Nadeeya yana balain santa abu daya ke sanyaya min jiki wani zubin sai naga kamar laifin Zahira zai shafesu Amma Ina adduar Allah yasa Kar a Kai ga haka a Kuma burina Zahira nakeso ta fara aure kafin Nadeeya sabida zanji wani iri ace Zahira na zaune Nadeeya ta rigata aure sosai na dage da Addu'a akan Zahira har da yarana gabadaya ban saki jiki akan kila su Umma sun kyallemu ba hakane yasa daga ni har Naseer muke addua duk abinda ma zasu yi Allah ya maida kansu ko ya kawo Mana da sauki. Hankali na maida wajen neman kudi dan idan result din Zahira ya fito mu nema Mata admission itama ta cigaba da makarantar Nadeeya Saurayinta ne ya tsaya Mata wajen cigaba da makaranta ba dan Haka ba dak'yar in zamu iya sanin Nadeeya ta tsayar mana dashi akan shi zata aura hakane yasa bamu hana shi hidimanta Mata ba dan koda Naseer ya hana shi dagewa yayi. Lokacin da result din din Zahira ya fito bai yi kyau ba daga ni har Zahira bamuji dadi ba ganin damuwar da Zahira tayi yasa na boye nawa damuwar na kwantar Mata a hankali na Dade da karantar kamar taba Zahira da akayi yasa ta rage k'ok'ari bata Kai sauran kanenn nata kokari ba ko ni nakan ci gyaranta wani zubin. Rashin cin jarrabawar ta ne yasa bata samu admission ba Naseer yaje ya biya Mata wajen da ake koyan dinki da zaman da zatayi haka zuwa wani shekarar mu Kara biya Mata waec din Daga fara fita koyan dinki Samari Suka Kara yiwa Zahira caa abin har tsoro ya ringa bani da farko zahira rashin mutunci ta ringa musu dan na lura tun abinda kabiru ya mata take ganin kamar duk mazan haka suke dak'yar nida Naseer muka shawo kanta ta fara tsayawa tana kulasu A cikin ma nemanta akwai wani Khalid da ke balain santa mahaifinsa Mai kudine sosai dan sananne ne a lokacin Kuma dan siyasa. Nacin da yake yiwa Zahira ba dare ba Rana har wajen koyon dinki yake binta yasa ta fara sauraransa duk da ba wani San shi take ba. Kyautatawa kuwa sai da na sa Zahira da dakatar dashi dan ba karamin kudi yake kashe Mata ba Ba Kuma iya Zahira ba har kanennta da waleed. Kayan abinci haka zai jiddo a kurkuka a kawo mana. Gashi da hankali koni yafi kwantamin akan kabiru zahira ke hana shi turowa dan tana ganin kamar shima zai iya cewa ya fasa aurenta idan aurensu ya kusa har lokacin bata San dalilin daya sa kabiru ya fasa aurenta ba dan data ce mu bata wasikar da kabiru ya rubuto Mata k'in bata mukayi sabida Kar hankalinta ya tashi. Khalid yana ganin Zahira tak'i bashi dama ya turo ya nemi Naseer da kansa akan Yana san auren zahira. Maganin kada ayi kar a soma Naseer bai b'oye wa Khalid duk abunda ya faru da Zahira ba na juyar Mata da Kai da akayi tayi rashin ji a shekarun baya ya nuna Masa bai San suwaye sukayi yiwa Zahira haka ba da Karfin Addu'a ta dawo daidai wanan dalili yasa har Wanda yaso Aurenta ya janye dan haka baya so sai tafiya yayi nisa shima ya janye. Ga mamakin Naseer khalid sai ce Masa yayi ai ko da halin Zahira ne ba juyar Mata da kai aka yi ba Zai iya Aurenta ko haihuwa tayi shi bai had'a San Zahira da komai ba indai aka ga bai Aureta ba toh mutuwa yayi. Ba ni ba har Naseer a ranar ba muyi bacci ba sabida tsananin murna Zahira ta dace da Mai kaunarta duk fargabar daya cikemin zuciya duk ya kau. Sati d'aya a tsakani dangin kabirun manyan masu kudi Suka kawo kudin neman aure a shiryensu suke har da akwatunan lefe dozen. Ni kaina na tsorata da irin dukiyar da suka kawo. Kanenn Zahira kukan farinciki kawai suke suna wani hanin ga Allah baiwa ne. Mahaifin Khalid daya kasance dan siyasa a lokacin chairman ne da kansa ya taka yazo gidan Sabida San da yake yiwa Khalid. Bayan babban sallah da sati biyu aka saka bikin Zahira da Khalid. Iyayen Khalid sunce basa bukatar a kawo Zahira da komai. Su zasu mata dan ba Khalid kadai ke san Zahira ba duk dangin Khalid da iyayensa balain San Zahira suke so daga Allah. Tabbacin ba abinda zai hana auren nan idan dai ba mutuwa ba yasa hankali kwance muke ta shirye shiryen mu Allah kadai yasan farinciki da nake ciki dani da Naseer da inna Amina Addua kam ba dare ba Rana haka muke yi har da azumin mu sadaka duk alhamis da jumma da kaina nake girka abinci Mai yawa na ciyar da almajirai. Ana saura sati uku auren Zahira da Khalid mahaifin Khalid ya turo wasu mutane biyu da mukullin sabon gida da takardu akan an bar Mana gidan mu tashi daga wanan gida sabida ya Mana kadan a hidimar biki. Da alama ta silar Zahira arzikinmu zai farfado. Kukan farinciki dagani har yarana da shi kansa mahaifinsu haka muka ringayi ga Karin alkawarin bayan biki za'a nema wa Naseer aikin yi tunda iyayen Khalid su keda gwammnati a lokacin Cikin farin ciki muka koma sabon gidan da muke ganin kamar duk mafarki muke dan gidane irin na masu kudi Mai gate komai akwai Dukan mu sai da mu kaje gidansu Khalid muka yi godiya har da Inna Amina. Da a wajena saninta a rayuwarmu alherine. Khalid shi ya dau nauyin komai duk da muna ta hana shi ni kaina nasan bazan iya fassalta San da Khalid yake yiwa Zahira ba ga kyau ga kudi dan Zahira ma bazata gaya masa kyau ba duk da tana mace Ya ma fita fari. Saura kwana goma bikin Zahira da Khalid da yamma ya kawowa zahira dinkunanta da ya kai Mata dinki da kansa ba iya nata ba har da nasu Nadeeya. Suna hira a waje bayan ta shigo da ledojin ta koma wajensa. Yana saman motarsa a zaune suna cikin hirar Zahira tace Masa "Wai ni ya Naga kamar baka da lafiya ne sai ramewa kake yi" Murmushi yayi yana "Nima bansan Mai ke damuna ba Zahira kwana biyun nan bana Jin dadin jikina ne ga mugayen mafarki da nake fama dashi ayita tsorata ni daddare ban gayawa kowa ba idan bake yanzu da nake gayawa ba kema dan bana iya b'oye Miki komai shiyasa na gaya miki da Alhaji da hajiya sun San maganar Nan da sai sun daga hankalinsu amma ni nasan ba komai kila haka akeji idan an kusa aure" Ya karashe da murmushi Zahira kuwa hankalinta ya balain tashi Amma ta daure bata nuna Masa halin da take ciki ba yanzu tayi girman da tasan muna da makiya masu San ganin bayanmu tasan komai akan dangin babanta. Haka sukayi hirar sama sama ta shigo gida. Ta sameni a d'akina ta zub'e akasan carpet cikin kuka ta hau bani labarin abinda khalid yace Mata ta Kara da "Umma Ina tsoron umman Abba ko Aunty Safiyya suyi wani Abu ya wajen Hana auren Nan Umma kiji fa wai ana tsorata shi daddare. Tunda ta fara min magana nake sallati. Bansan ma na mike ba sai tsintar kaina nayi a d'akin Inna Amina Zahira na biye dani. Yanda ta ganmu a firgice ya sa ta mik'e zaune dan a kwance take Kuka na fashe dashi na hau bata labarin da Zahira ta bani ina "Mama Ina tsoron sharrin bayin Allah nan Ina tsoron suyi abinda zai saka a fasa auren nan ba abinda bazasu iya yi ba dan suga bayana dana Zahira kin San irin tsanar da suka yiwa Zahira sabida kawai tana Kama dani kinsan irin wahalar da suka bata Kar yanzu da suka ga ta dace da Mai kaunarta su cutar dashi" Na karashe Ina fashewa da kuka "Haba Naeema ki kwantar da hankalinki wlh basu Isa su hana abinda Allah ya kaddara ba ki mik'awa Allah lamuranki zai isar miki insha Allahu mu dai mu dage da Addu'a shima Khalid din idan yazo ta turomin shi Zan basa adduoi ya ringa yi ba abinda zai faru insha Allahu dan Allah ku kwantar da hankalinku idan dai kuga baayi auren Nan ba toh wlh dama Khalid ba mijinta bane haba Naeema kiringa amfani da hankalinki Mana yawan tsoron Nan naki ma na iya sawa Allah ya jarrbaceki Abu kad'an sai kice zasu Miki wani Abu kenan duk abinda zai sameki sune bazaa jarrabceki ba" Naseeha ta min nida Zahira Nayi k'ok'arin boye damuwa na ne kawai Amma hankalina a tashe yake. A haka lokacin biki yayi ta matsowa daga ni har Zahira jikinmu a sanyaye yake Naseer Dana gaya masa ma cemin yayi ba abinda zai faru insha Allahu dan baya bacci tunda bikin ya matso Ana saura kwana hudu daurin Auren Khalid da Zahira khalid yazo gidanmu a firgice bai tsaya neman iso ba ya fado palon ya zub'e a gabanmu ya hau bamu hakuri duka Muna zaune a Palo "Dan Allah kuyi hakuri na fasa auren Zahira wlh sunce idan na dage zan Aureta sai sun kasheni Ido bud'e Ido rufe haka suke biyoni da wuka. zasu kasheni har da micizai yanzu haka gasu Ina kallonsu da manyan micizai wlh tunda na had'u da Zahira suke tsoratani suke min kashedi nak'i ji yanzu naga da gaske neman rayuwata suke dan har hatsari suka saka nayi yanzu bansan Zan tsira da rayuwata ba dan Allah kuyi hakuri inasan Zahira wlh Amma bana so na mutu na fasa aurenta ne dan na tsira da rayuwata" Tunda ya fara magana muke kallonsa Muna zuba sallati Zahira kuwa Ashe ta Dade da sumewa Naseer ne yayi karfin halin cewa ba komai Allah yasa hakan shi yafi alheri Khalid daya jike da gumi idonsa duk hawaye Ya kalli wajen da Zahira ke kwance kamar zai karasa wajenta kuma.ya fasa ya fita waje da Sauri yabi ya rame Kamar bashi ba Wani mugun ihu na fasa na zub'e a kasa Kamar wayanda aka Mana rasuwa Muka hau kuka Naseer ya mik'e ya shige dakinsa ya rufo kofarsa da mukulli Zahira na farfadowa ta hau ihun kuka tana "Mai nayi haka a rayuwata nake ganin irin wanan jarrabawa sai ana dab da bikina sai a fasa Umma Mai nayi musu Abba Mai nayi laifine nazo a yarku?Mai yasa laifin wasu zai shafeni ?Umma a garin yaya Kika auri Abba kinsan basa sanki gashi yanzu ni da ban musu komai ba suna ta watsa min rayuwa kenan ni bazan yi Aure ba?daga wanan sai wanan Umma ban musu komai ba suka min turen Aljannu suka saka ban karasa makaranta ba iya haka bai Isa ba suka fitar dani a hayyacina nayita abubuwa yanzu Kuma na dawo daidai sunce bazan yi aure ba"? Kuka Zahira keyi kamar zuciyarta zai fita A fasa auren Khalid da Zahira nayi jinyar fiye da wata biyu a asibiti Allah ne yayi bazan yi ciwon B'arin jiki ba. A takaice a haka shima Khalid ya tafi. Yata aka cigaba da zuwa neman aurenta ana dab dayi sai a fasa bayan Khalid mutane biyu Suma. Daga haka.zahira tace ta cire rai da aure Ta rokeni.mu bar mai San Nadeeya ya turo neman aurenta Kar mu Hana shi sabida ita. Tunda kamar ya matsu haka kuwa akayi saurayin Nadeeya Umar ya turo manyansa neman auren Nadeeya aka saka Rana wata uku Calabar.... [8/26, 9:41 PM] Zannura: *NAGA TA KAINA* *NA SADNAF*🌸🌸 ®️ *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_* _{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_ *Free Novel* Page 63 Safiyya Fadar tashin hankali da damuwar da take ciki b'ata bakine dan ko baccin kirki bata iya yi Sabida masifar da yaranta ke ciki. Asmau yanzu duk daurin da zata Mata sai ta kunce ta fito daga d'akin ta fita waje. A haukacen ma haka maza ke nemanta idan ta daureta ta karfi da yaji haka maza ke biyota gidan ba kunya ba tsoron Allah ga tsokanarta da sukeyi da uwar mahaukaciya. Abinda ya Kara daga Mata hankali bai wuce Bashir daya dawo gidan da Zama gabadaya ba ya Kori Asmau daga daki dayan data kulleta yayi zamansa a d'akin da macen da itama kana ganinta kasan Yar bariki ce ta ma girmi Bashir nesa ba kusa ba amma haka ta biyo bashir cikin gidan take zuba mulki San ranta Safiyya bata isa tayi magana ba. Har wajen Oban taje akan a Mata maganin budurwar Bashir din da aka cewa hajiyayye Ashe itama hajiyayyen tana zuwa wajen Oban ya Kuma Santa karya yayi wa Safiyya akan idan yayi aiki akan hajiyayye zata iya hauakcewa akan dole ta hakura. dan aikatau din da take zuwa yi ta samo abincin da zata saka wa cikinta da hauwa da tana Nan Kamar d'abba Kamar mutum tana samowa Bashir zai nada Mata duka ko shi ko budurwarsa hajiyayye. Safiyya takwararta itama data gama barikin tsarabar ciki tayo Mata ta dawo gidan ta zauna. Ga Yar Asmau Nana da Rabia yarta. Taurin zuciya yasa Zuciyata bata buga ba. Bashir haka zaiyi sata a biyoshi har gida Ana nemansa hajiyayye budurwarsa kayan mayye take siyarwa wani zubin aka ma su biyun wani zubin su tsere a kamata Duk jikinta tabon dukan ne na Bashir takan tsine Masa ta Kara tsine Masa har ta ringa ayyanawa da irin rayuwar Nan da take da yaran da basu Mata albarka ba gwara duk mutuwa sukayi. Bakin ciki daya Mata yawa ta nufi wajen Oban dan ya binciko mata halin da su Naeema suke ciki da take jinsu a kahon zuciyarta ba yanda zatayi tana Shan gararin rayuwa su Kuma su Sha iska Mai dadi. Gani take duk Wanan masifar Naeema da Naseer su Suka jawo Mata ta Kuma yarda da zancen Oban da ta fara ganin kamar bai iya aiki ba daya ce Naeema itama ba zaune take ba tana zuwa wajen Mallamai suna Mata aiki shiyasa duk abinda suka Mata yake dawowa kanta. Amfanin da Oban yake dan Mata yasa bata bar zuwa wajensa ba amma duk lokacin data samu kudi dole ta nemi wani bokan da zai mata mugun aiki ko ba Akan Naeema ba yarta Asmau ta samu Lafiya da hauwa da shi kansa Bashir din. Bata da burin daya wuce su samu lafiya. Jikewa tayi da gumi a lokacin da Oban ya nuna Mata wani yazo auren Zahira rashin Jin da tayi ne yasa aka fasa auren Yanzu haka ga wani Dan shahararen Mai kudin ya fito neman aurenta har an kusa ma auren an mallakawa Naseer gida. Oban ya Kara da "Yayanki zai dawo da arzikinsa har yafi na da ta silar Wanda zai auri yarinya Nan Dan aiki Mai kyau suke so su bashi. Matarsa Kuma zatayi kudi itama har ta fita waje Ba iya Kuma Zahira ba duka yaranta ba Mai auren karamin mutum" Kasa magana tayi tsabar kad'uwar da tayi da tashin hankali Taya tana nan na abinci na neman gagararta Naeema da Naseer su Kuma suna neman zama masu kudi? Taya yaranta daga mahaukaciya sai Mai bin maza da kungurmin barawo yaranta data ci mugun buri akansu ba Wanda ya mata albarka Amma yaran Naeema gasu Mai kudi ke nemansu ta silar Zahira ma har ana neman mallakawa Naseer gida Ita tana nan a wulakance ta Zama kamar zararriya Auren Zahira na nufin samun kwanciyar hankali Naeema da farincikinta Ita Tana Nan tana Shan duka awajen bashir yaranta mata ba ma na kwarai ballantana ta sa Rai suma zasuyi aure inaaaa Tace da k'arfi ta matsa kusa da Oban tana ruk'o hannayennsa tana "Yarinya Nan bana so tayi aure yanda yarana Suka wulakanta a gabana haka nake so yarinya Nan ta wulakanta a gaban Naeema bana San Naeema ta samu kwanciyar hankali daidai da second daya inaso yarta Zahira ta dauwwama a gabanta ba aure yanda naga alamar yarana haka zasu dawwama a gabana. Inaso kayimin aikin da zaa ringa tsorata shi a nemi ma ransa har sai ya janye daga neman aurenta Duk Wanda zai nemi Aurenta a ringa tsorata shi ko sai yaje wajen Zahira dab da aurensu ya ga Zahira na bashi tsoro har sai ya janye Ba iya Zahira ba duka yaran naeema haka nakeso su dawwama a gabanta taji abinda nakeji a Zuciyata Naseer a Kara saka Masa tsanar Waleed idan Zan samu ne Naseer nakeso ya Zama ajalin Waleed. Duk wani Abu da zasu samu ta silar yaransu ya lalace ko gidan ma da kace Ana shirin basu idan an basu Kar yayi albarka har sai sun koma wanan karamin gidan. Inaso Naeema ta Shiga ukunta ta lalace wanan shegiyar tsohuwar dake taimaka mata inaso!!! "Kullll Oban yace da Sauri Yana Karki soma kiramin tsohuwar nan dan na gwada aiki akanta komai.nawa lalacewa zaiyi nadai San Tana gidan ban Isa na Mata komai ba. Duk abinda kikace ayi yafi komai sauki zaayi Amma fa sai kin kawo kudin aiki dan iya jikinki bazai iya biyana ba" "Duk Inda kudi suka Shiga Zan Nemo Oban kwanciyar hankalinta ne dai banaso" Safiyya sai data had'a da satarwa hajiyayye kudinta data Shiga bandaki dan.tayi wanka ta kaiwa Oban ya Mata aikin. Kullum tana hanyar zuwa dan taga halin da suke ciki ahaka har Khalid ya fasa auren Zahira da ranar zuciyarta ya kasance fess tana Jin inama Safiyya batayi cikin shege ba da tayi aiki akan khalid yazo ya aureta. Duk halin da su Naeema ke ciki tana sane tana kuma da labari ta wajen Oban hakane yasa ta Kara dagewa wajen ganin Zahira batayi aure ba har dasu Nadeeya. Hajara Bata tab'a sanin haka ake samun kudi idan ana bara ba sai data fara daga fara baranta zuwa yanzu har ta Tara kudade masu yawa da Bata tab'a mafarkin samunsa ba. Ko kad'an bata yi tunanin kama haya ba ta cigaba da zama a rumfar mahaukatan da ta Riga da ta saje dasu Ciwon kafar da take fama dashi daya dan kumbura yasa mutane ke Kara tausayinta tana fita bara zasu hau Tara Mata kudi har da masu bata kayan sawa. Sai data tabbatar da ta Tara kudin da yawa daddare ta hau shiga mutane tana neman Wanda zai mata aiki akan Naeeema da Safiyya da take ganin sune manyan makiyanta a duniya. Tsohuwar unguwar da suka zauna ta nufa ta Kara da nausawa daji ko zata samu ganin shugabarsu ta matsafa da takejin da tana Nan da duk matsalarta ta Kau Sai dai ta karaci bullayinta a dajin bata sameta ba a wajen fitowa ta hadu da dattijuwa da zasuyi saani da ita ta kada baki ta tambayeta ko tasan Wanda zai iya taimaka Mata Wala mallami ko boka Dattijuwa kuwa cikin murmushi tace itama Nan tayi su tafi Silar haduwar Hajara da kawarta kenan Mai irin halinta da ita Kuma kishiya take San taga bayanta. Bokan shima bayarabe ne da suka Samu dan sunfi yawa acan garin Duk kudaden baranta ta zub'ewa bokan. Ta fara da "Inaso naga bayan matar Dana ta wahalar dani shekara da shekaru Muna Abu daya da ita ban taba cin Galaba a kanta ba sai da tayi ta tsallake duk abinda na mata iya haka bai isheta ba sai data rabani da d'ana har a cell yarinya Nan ta kullemu muka kwana inaso a tura Mata cutar da zaiyi ajalinta tayi mumunan rashin lafiya da zaa rasa maganinsa har sai ta mutu. Dana Kuma ayi.min aiki da arzikinsa zai dawo ya sake aure na Mori arzikinsa. Safiyya yata Kuma Ina so a watsa rayuwarta idan har ni Dana tsugunna na haifeta zata kora har tayi dambe dani inaso yaranta su Zama ajalinta ta rasa kwanciya hankalinta ta ringa Neman mutuwa ma mutuwa tak'i daukarta. Wani mugun dariya ya kece dashi yace mata "An gama amma duk abinda ya biyo baya kiyi kuka da kanki" Hajara kada Kai kawai take cikin farinciki a duk abinda tace ayi Mata idan har ta samu cikar burinta akan Naeema gani take burinta ya gama cika. Bata damu da yanda bokan ke ta nanata Mata duk abinda ya biyo baya tayi kuka da kanta ba. Cikin farinciki ta baro wajen bokan tazo ta cigaba da baranta dan bayan kwana biyu bokan yace ta koma Wanan kenan (A labarin naeema wlh Tallahi na rage abubuwa da yawa ba sai dai na ringa rantse muku ba amma dai na kusa zuwa Inda muka tsaya a labarin) Naeema Tausayin yata nake sosai dan ta cire rai daga auren duk Wanda yazo ma ta daina bashi fuska ballantana ta saurareshi Aikin koyan dinkinta kawai ta saka agaba da Kuma shirye shiryen bikin Nadeeya da duk ba wani dokinsa muke muna wani shiri ba dan gani nake ba iya Zahira aka yiwa mugunta ba kila har dasu Nadeeya. Banida k'arfi banida kowa Amma inada Allah duk abinda sukeyi min Allah Yana kallonsu nasan zai kawo karshen komai wuyanta nayi hakuri. Tashe tashen hankulan dana gani a rayuwata yasa yanzu na Riga da na fara sabo da duk wani jarrabta da Zan gani a ruyuwata ba abinda ya Kai lafiya dadi a wajena. Idan dai har bazasu cutarmin da Yara ta hanyar tab'a min lafiyarsu ba zasu barmu a haka inaga alhamdulillah banga abinda zai daga min hankali ba tunda na Riga da nasan Aure da mutuwa lokaci ne idan har lokacin auren Zahira yayi ni nasan ko mai zasuyi basu Isa su hana ba duk masu zuwa neman aurenta ba mijinta a cikinsu. Ban saka damuwar komai a Raina ba na Kara fawallawa Allah komai na cigaba da kai kukana gareshi. Naseer Zan iya cewa shi ya saka damuwa a Ransa sosai yanda hawan jininsa ke motsa Masa akai akai sabida damuwa yasa nida inna Amina muka Masa nasiha Dak'yar shima ya cire damuwa ya cigaba da gayawa Allah Alhamdulillah yarana sanin muna da masu San ganin bayanmu yasa Suma Basu Zauna haka ba Suka dukufa yiwa kansu addua kariya duk a cikin yarana Nadeeya da Humaira Zan iya cewa suna da Wanan k'ok'arin sosai wajen raba dare suna kaiwa Allah kukansu balle Nadeeya data ga Aurenta na matsowa sosai take adduar Allah yasa Kar wani Abu ya Hana auren dan Naga itama jikinta a sanyaye yake. Yanda muka amshi kaddarar mu da hannu biyu yasa komai ya zo Mana cikin sauki cikin rufin asiri muka cigaba da shirye shiryen auren Nadeeya Dan Abubuwan da muka siyawa Zahira muka yanke Kara Mata akai dan Umar Mai neman Nadeeya na Dan sakar mata kudi dashi muke samu mu rage wasu Abubuwan Bana Jin dadin yanda Zahira ke kin saurararen manemnta da duk da fasa Aurenta da ake tururuwar zuwa nemanta suke Kuma so suke mata ba na Wasa ba sai dai da mun Mata maganar ta kulasu sai tace mana ko ta kulasu ma a karshe guduwa zasuyi bata ga amfanin kula sun ba ita fa kila bata da rabon auren ne a duniya dan haka ta hakura. Sai dai a mane manta akwai wani Abubakar da babansa ya kasance babban mallami shima yayi gadon mallinta a wajensa ga ilimi ga kudi. Ba karamin naci yake yiwa Zahira dake wulakanta shi ba dan ko kad'an bata saurarenshi ballantana har ya Shiga zuciyarta ta sa rai da aurensa a karshe Kuma yazo ya fasa auren Har tausayi yake bamu yanda yake.sintirin zuwa wajenta tana kin bashi fuska Duk Kuma maganar da zamu Mata akan ta kulashi bazata kulashi ba idan an matsa mata kuwa sai ta saka kuka. A karshe sai Inna Amina ce ta samu dak'yar dak'yar ta fara kula Abubakar duk da ta Masa gargadin duk ranar da ya mata zancen aure sai sun rabu. A haka ya cigaba da zuwa sanin da aure yake Santa yasa daya tabbatar ta tafi wajen koyan dinki yazo ya tarar da Naseer a gida ya Gaya masa bukatarsa na san auren Zahira. Naseer bai b'oye Masa komai ba ya bashi labarin duk Abubuwan dake faruwa game da zahiran da yanda aka zo neman aurenta sai ana dab da yi a fasa. Abubakar murmushi yayi Yana Kar Naseer ya damu daga bashi labarin da yayi yasan da akwai aikin makiya a fasa auren zahiran Amma indai sihiri ne ko wani Abu da yardar Allah bazai yi tasiri akansa ba sai dai idan Allah ya rubuta Dama zahiran ba matarsa bace Shi dai a bashi dama ya turo manyansa dan aka biyewa Zahira cire rai zata yi daga auren sabida duk abinda ya faru da ita a baya Badan duk mun yarda wani Abu bazai biyo baya ba aka bawa Abubakar dama ya turo manyansa. Da.kudin aure Inda ya nemi a hada dana Nadeeya Amma ayi a sirrince Kar a nuna Dana Zahira zaayi sabida kar ma makiyan mu suji labari. Addua mukayi akan Allah ya tabbatar muka cigaba da Addu'a muna Shirin auren Zahira da Nadeeya Dan Ni har cewa Naseer nayi dama kawai a daura auren zahiran da Abubakar Kar a wani ja lokaci dan gani nake lokacin da ake ja ma yasa suna samun Galaba akanmu Amma Naseer yace Kar na damu mubi komai a hankali. Allah yasan da Auren Zahira da Abubakar zai tabbata da nafi kowa Jin dadi da gani zanyi na gama samun cikar burina. Ana saura sati uku bikinsu aka kawo leffen Nadeeya. Abubakar kuwa mu muka hana ya kawo na zahira sabida yanzu hankalin ta a kwance yake gani take Umar wahalar da kansa kawai yake aure tsakaninsu bazai yiwu ba duk da a ranta tana San sa Amma haka zata hakura dashi yanzu tana sanin da ita zaa hada auren zata tashi hankalinta. Sosai ta zage suke shirye shiryen auren Nadeeya ta d'au ragamar komai Kamar wata kawarta Ni Kuma yanda ta daukaki auren Nadeeya tausayi take bani. Har azumi.na tsiri yi akan Allah ya cikamin burina Naga auren Zahira. Ana saura kwana goma Sha biyu bikin Nadeeya da Zahira Daddare karfe daya da rabi Kamar yanda na Saba tashi na rayya Daren na mike na Shiga band'aki na daura alwala Naseer Ina jiyo karatunsu daga d'akinsa dan Yanzu bamu fiye kwana waje daya dashi ba sai dai idan ta kama ko Dan idon yaranmu da muke ganin sun kawo girma da Kuma wayonsu. Na fito kenan daga bandaki jiri ya d'ebbeni duhu ya mamaye min Ido ban Kara sanin Inda kaina yake ba. Sai dana yi.kwana uku bansan Inda nake ba kafin na iya bud'e idona nagani a gadon asibiti na Sha Karin ruwa. Azabar da nakeji a jikina da kaina danaji Kamar guduma ake bugamin yasa na runtse idona na hau girgiza Kai Ina sallati Wlh duk yanda Zan kwatanta abinda nakeji a jikina makaranci da ke da kike rubutawan bazaku gane ba Azabar Dana Sha a cikin Minal da kumburin da nayi duk nafila ne akan abinda nake ji Ina Jin yarana da suka zagayeni har da Naseer suna min sannu Inna Amina itama Ina Jin tana min tofi Ban iya bud'e idona ba sabida dai azabar da nake Sha Kirjina kamar an doramin Abu Mai balain nauyi. Tunda ga lokacin ban Kara iya bud'e idona ba Amma duk abinda ake Ina ji. Azabar da nakeji kawai a jikina yasa na fara kuka Ina rokon Allah ya dau raina dan a ganina gwara mutuwa da Wanan azabar da nake Sha Ina Jin yanda yarana da Naseer ke jigilar yawo dani a asibiti daga wanan asibitin zuwa wancan sai kashe kudi suke. Amma duk a banza likitocin sun kasa gano Mai ke damuna. Karshe sai wani private aka kaini da suka rubuta ayimin scan din duk jikina agano Mai ke damuna Daruruwa kudin da suka caza yasa dolen Naseer ya siyar da gidan da iyayen Khalid suka mallaka Mana ya tashi Yan hayan daya zuba a gidanmu Suka koma. Duk kudin gidan a asibiti ya Kare a sanadin rashin lafiyar da nake aka daga bikin Nadeeya da Zahira Naseer shima gadone kawai ba a bashi ba sabida tashin hankali Duk ba Wanda ya kawo ciwon nawa bana asibiti bane duk Inda aka ji kwararrun likitoci sai a tura mu can A haka nayi wata biyu a wahalce kafin saurayin Zahira ya bawa Naseer shawara akan a mayar dani gida cutar tawa bata asibiti bace. Sai a lokacin Inna Amina da Naseer da Kamar aka mantar dasu muna da makiya suka dawo hankalinsu aka mayar dani gida. Aka dukafa da min addua Naseer Inna Amina har da sirikina Abubakar da shima bazan tab'a manta shi da mahaifinsa ba Mahaifinsa Mallam isah ba karamin ilimi ne dashi ba. Abubakar na samunsa da zancen rashin lafiya ta yace a kawoni. Haka aka daukeni akayi gidansu Abubakar dani. Cikin Ikon Allah kwana bakwai da kaini na fara dawowa hayyacina har na bude idona nasan Inda nake. Kwana mahaifin Abubakar keyi Yana min addua A gidan Naseer da Waleed suke kwana Da asusuba yarana zasu dura gidan gabadaya. Cikin sati biyu na warke sumul kamar bani ba dan nakan iya tashi na zauna duk azabar nan danake ji a jikina na daina ji sai dai rashin kwarin jiki. A haka mahaifin Abubakar ya bamu ruwan adduoi a ranar da zamu bar gidan Ya zaunar da Naseer Dani yayi gyaran murya yana "Rashin lafiyar Nan turensa aka mata a gaskiya Kuna da makiya da suka shirya ganin bayanku Mata biyune suke ta k'ok'arin ganin sun tarwatsa rayuwarku adduar da nayi Naga kamar matan nada kusanci da kai duk auren yarku da ake sawa Ana fasawa duk sune yanzu Haka ma Allah ya nuna min duk wani shiri da suka Kara yi akanku nayi addua ya warware da ikon Allah Ina Baku shawara ku Kara dagewa da Addu'a yarku zahira sun balain tsanarta zasu iya komai dan suga bayanta dan haka insha Allahu Zan taimaka Mata. Mallam Naseer idan bazaka damu ba inaso a daura auren Zahira Yarka da Dana Abubakar a yau. Dagani har Naseer kasa magana muka yi duk maganar sa ba abinda ya bamu mamaki mun Riga da mun San su Umma ke San ganin bayanmu Maganar auren Zahira daya ce a daura a yau shi ya daskarar damu har naji na fara Jin kwarin jikina. Ban.yarda ba mafarki nake ba sai dana.ga Naseer ya shigo d'akin da aka ajiyeni da goro da alewar daurin Auren Zahira da sadakinta a hannu Dubu hamsin Hawayen farinciki ne.ya hau zubomin. Ashe dai yata tana da rabon aure daurin Auren Zahira tamkar Kara samun lafiya yayi Godiya sosai muka ringa yiwa mahaifin Abubakar bakin Abubakar a washe dan murna. A haka muka nufi gida cikin farinciki tun a hanya na fara sadaka a Raina Ina Godewa Allah. Umarnin mahaifin Abubakar nabi Dana Isa gida na fito da duka kayana daya ce Kar na sake sawa Kar Kuma na bawa wani dan zai iya cutar dashi. Dan kayan nawa ma an yi asiiri a ciki. Naseer da kansa ya Kona kayana. Yarana sai.murna suke na warke. Bamu fadawa Zahira an daura Aurenta ba. Sati biyu da samun sauki na aka cigaba da shirye shiryen auren Nadeeya Abubakar har akwatin kayan sawa ya kawo min Ranar 15 ga watan biyar shekara ta 2010 aka daurawa Nadeeya aure Aka hada da bikin Zahira da itama bata sani ba sai a satin auren Nadeeya kukan farinciki kawai ta ringayi tana a Ashe tana da rabon aure. Cikin rufin asiri akayi shagalin bikin yarana suka tare a gidajen mazajensu alhamdulillah Calabar A ranar da mahaifin Abubakar ya karya asirin da Hajara tayi daddare Hajara na kwance tana bacci. Taji kamar Abu ya ruguzo Mata a jiki Azabar data ji.yasa ta bud'e idonta. Kasusuwan jikinta Suka ringa kaskas Kamar Ana karyawa A firgice ta mik'e zaune data ga kashin jikinta na murdawa shi kadai kafin ta ankara sai gashi ta karkace gabad'ayanta gabanta ya koma gefe idan kana kallonta a madadin a tsaye straight sai ta karkace Fuskarta ta koma gefe Ihu ta saka da iya karfinta mahaukatan dake zagaye da ita Suka sakata gaba suna kallonta Masu wucewa Kuma idan Suka ganta sai su tsorata dan Basu tab'a ganin mutumin daya karkace haka ba. Wanan shine farin Shigar Hajara wahala Mai tsanani Dan mutane tsoron ta Suka koma yi ko tayi baran bata samu. (Har yanzu wlh Tallahi baiwar Allah Nan a karkace take a fadar Naeema ko accident mutum yayi Bata Jin zaiyi karkacewar da tayi Allah ya tsare Mana imaninmu na dai kusa gamawa Dan Safiyya da Hajara na rayye Basu mutu ba ba kuma su tuba ba yanda Naeema ta bani labari haka Zan Baku sai dai Kuma idan wani Abu ya biyo baya nayi alkwarin rubutawa insha Allahu) *TALLA* _Mai talla shike da riba_ *Mg's herbal whitening black soap* Idan akaji gangami to tabbas akwai labari. Ina Amare, Uwargida kai har ma da 'Yan mata masu tasowa, hakika mata da kwalliya aka sanmu, shin kuna so ku kara kyau fatarku tayi luwai luwai ki zama 'yan caras kamar madubi? To ga dama ta samu, mun zo muku da Sabulun Mg's a kan farashi mai sauki, duk wacce ba tayi anfani da sabulun nan ba an barta a baya, domin duk masu korafin cewar sabulan gyaran jiki basa Aiki to ina so ku cire Mg's a ciki domin shi kankat ne wajen mai da tsohuwa yarinya. Ko yaushe Mg's sai sambarka dan haka ku hanzarta ku samu naku, siyan na gari maida kudi gida, Mg's sabulu ne daya tamkar da dubu. Masu bukatar fatarku tayi haske to Sabulun Mg's herbal whitening black soap ya waratar daku, jikin ku zai yi kyau da sheki da kamshi. Kayanmu baya bleaching organic ne, zai fiddo muku da ainahin natural beauty dinki ne, dan haka duk wanda ya gwada shi ne zai bada labari. Amare da sauran Mata kuyi kokari ku mallaki Mg's domin ba ruwanku da zuwa a dirje muku jiki zaku ga yanda fatarku zata dinga walwali. Ina masu. Pimples Tabo(spot) Sunburn Nankanwa Dama duk wani matsalar fata kuyi kokari ku nemi soap din Mg's, insha Allah before 2weeks zai share muku hawaye, ku zama abun kwatance. You have to try it and see for yourself 100% tested and trusted. Soap price: 3k Location: Kaduna Muna turawa ko ina, amma delivery is not free Mai so kindly WhatsApp message to 08062991549 or Call 08064532391 _Note: Yan sauran state Babu in da zaku sami mg's herbal whitening black soap sai a number din nan, now Akwaisu available_yan kd akwai shops da zakusami sabulu ynx kuyi mgn 08062991549 abaku address Masusan suzama distributors a other state uw kindly drop a message via 08062991549🤭 we can't wait to be a part of your beauty story😍 [8/26, 9:42 PM] Zannura: *NAGA TA KAINA* *NA SADNAF*🌸🌸 ®️ *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_* _{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_ *Free Novel* Page 64 Duk masifar da ta Shiga da b'acin rai bata taba tsintar kanta a farinciki kamar lokacin da Oban ya haska Mata rashin lafiya da Naeema ke fama dashi ba A karyar Oban ce mata yayi shi yayi aiki akan Naeeema tayi ta rashin lafiyar har ta mutu. Kamar wacce aka yiwa kyautar hajji da umara haka Safiyya ta ringa ji. Da kuwa Naseer ya siyar da gidansa akan rashin lafiya Kamar ta taka rawa Bata da burin daya wuce har daya gidan su siyar su koma ba suda gidan kansu kamar yanda itama bata da gidan. Idonta na Kan komai dake wakana dasu Naeema har irin wahalar da ake sha akanta. Abubakar data ga Yana San Zahira Yana Kuma taimaka.musu yasa ta roki Oban akan ayi ta tsorata shi idan har yak'i janyewa Oban ya kashe shi Haka kuwa akayi Oban ya hau tura Aljannu dan su tsorata Abubakar sai dai duk tsorata shi da suke ko gezau Abubakar baya yi daya tashi ma Kona Aljannun ya ringa yi yayi wa Oban barna sosai ta hanyar lalata Masa wasu kayan aikin nasa da Karfin Addu'a. Duk yanda Suka so yin aiki akansa hakan baiyi tasiri ba har aka daura auren Zahira da Abubakar da yasa Safiyya tayi karamin hauka tana sumbatun tsinewa Naeema da ita rayuwar yaranta gashi a watse Amma Zahira tayi aure. Dan Safiyya itama ta santalo Mata jika shegiya ga budurwar Bashir itama d'auke da ciki. Duk an cike mata gida da shegun yaya Gabadaya rayuwarta ta wulakance ta lalace ita da yaranta Amma gashi zahira ta samu tayi aure kenan ma Naeema taci riba akanta A hauakacen ta sa Oban ya Mata aiki akan Umar saurayin Nadeeya akan ya fasa auren Nadeeya sai dai tana ji tana gani aka daura aurensu. Bakin ciki yasa ta roki Oban akan a kashe mata Umar dan da alamu Abubakar yafi karfinsu dan duk abinda suka ringa tura Masa baya tasiri akansa Nan kuwa basu San mahaifinsa ba karamin aiki yayi akansa ba ba iya shi ba har su Naeema. Ba yanda ba suyi dan suga sun tab'a Zahira ko Nadeeya Amma Allah bai basu iko ba Hakane yasa Safiyya ta so maida Nadeeya bazawara a washegarin da Nadeeya ta tare a gidan ta. Wani Abu Oban ya bata Akan taje ta binne a tsakiyar titi kafin ta binne ta Kira sunan Umar sau uku Indai Umar a ranar ya hau mota ya hau kan kwalta sai yayi mumunan hatsari. Cikin mugunta ta binne kamar yanda ya umarceta Ta koma gida tana murna bakin cikin da Naeema zatayi har Naseer idan suka ga kwana daya da tariyar Nadeeya mijinta ya rasu Tana komawa gida ta iske Bashir a tsakar gida a zaune ya balain nutsuwa kamar bashi ba. Sannu da zuwan da ya mata yasa ta daskare waje daya tana murza idonta dan ta gaskata Bashir danta dai take gani ba wani ba Murmushi ya Mata Yana ta daina mamaki shine sati biyu da yayi baya nan Allah ya shiryeshi ya Kuma Gane duk abinda yakeyi ba daidai bane daga Yau ya daina. Safiyya tsabar farinciki kuka ta saka tana shiwa Bashir albarka Fadar farinciki da take ciki ma Bata bakine Ashe Bashir dinta zai tab'a nutsuwa haka har ya dawo hayyacinsa A takaice hirane ya barke tsakanin Safiyya da bashir Safiyya ta ringa ji kamar ta goyashi dan farinciki tuni ta hau tsare tsare a Zuciyarta. Murna da take ciki yasa tace Masa Bari ta Shiga daki ta yo musu cafene Bashir kafewa yayi ta bar kudin shi zai yo Mata cefanen. Safiyya da kallo ta bishi har ya bar gidan Kaunar Bashir na balain mamaye Mata zuciya kaf yaranta ba Wanda takeji a ranta kamar Bashir. Fitarsa da minti goma taji hayaniya a waje. Kafin ta gane Mai ke faruwa har mutane sun duru cikin gidanta suna zabga sallati Hankalinta a balain tashe ta fara tambayar me ke faruwa Sai dai baa iya bata amsa ba in Banda wani daya hau Jan hannunta. Kamar sokuwa haka tabi bayansa gabanta na fad'uwa. Mutanen da suka cika titin da ta binne abinda Oban ya bata yasa gabanta tsananta fad'uwa dak'yar ta suka bata hanya Bashir ne kwance cikin jini male male Idonsa a bud'e Yana kallon sama kana ganinsa kasan rai yayi halinsa. Wani razanannnen ihu ta kwalla ta zub'e a kasa. Bata Kara sanin Inda kanta yake ba har aka yiwa bashir sutura aka binne shi Ranar sadakar uku ta farfado Ta na ihun Kiran sunan Bashir ta fara k'ok'arin yin waje Sai sumbatu take tana ba Bashir tace ya mutu ba mijin Nadeeya tace Oban ya kashe Mata. Tab'in hankali da ta dan samu yasa ta hau tona wa kanta asiri tana Naeema ta cuceta Oban ya cuceta. Dak'yar aka Mata alluran bacci dan fusgewa take zata fita waje. A takaice sanadin dan samun tab'in hankali Safiyya kenan Dan har gobe bata cika hankali ba ita kadai haka za tayi ta zuba surutu tana fadar Abubuwan da tayi idan haukan ya motsa mata . Oban da take shuka tsiyar dashi data koma wajensa a kwance ta sameshi ya kumbura yayi himmm Yana zabga wani irin doyi Ita kanta Safiyya baka Isa tsayawa kusa da ita ba sabida warin da takeyi Wata daya da rasuwar Bashir Tana zaune ta zubawa waje daya Ido Hankalinta ya dan dawo jikinta yaranta duk take bi da kallo da jikokinta. Ita bata ga ma ribar da taci a rayuwarta ba Bashir danta namiji tilo Daya fi soyuwa a gareta ya tafi ya barta a lokacin da hankali ya fara zuwar Masa ya Shiryu Yaranta biyu daga mahaukaciya sai Mai bin maza Ba Wanda ya amfaneta da wani Abu. Sai Rabia da take wahalar da ita da bata da bambanci da wata dabbar tana girma tana Kara zama abin tsoro Tunani da abubuwa dake rayya Mata munanan abubuwa yasa ta d'auko wuka Ta nufi d'akin da Rabia ke kwance tana Isa wajenta ta daga wuk'ar da zumar soka mata dan ji tayi gwara.kawai.ta kashe Rabia ta huta Tana daga wuk'ar taji kamar anyi cilli da ita. Wani iirn gugguwa Mai k'arfi ya zagayeta Ta hau wani irin jijjiga tana Kara duk Aljannu dake azabtar da Rabia Suka bar jikin Rabia suka Shiga jikin Safiyya Wani irin canza Mata hallitar fuskata sukayi fuskarta ta dawo bakikirrin wuyanta yayi wani irin kumburewa idonta yayo waje gabad'aya Ihu kawai take Tana birgima. Har gobe haka Safiyya take fama da kumburarren wuya da Ido a warwaje takan dan tab'a hauka wani zubin. Daga ita har Hajara Basu nemi yafiyar.naeema ba suna Nan Kuma da tsanar Naeema dama ne kawai Basu samu ba Safiyya k'arfi da yaji ta koma yin Abun mahaukatan aka koreta daga gidan hayan Hajiyayye budurwar Bashir kuwa Yana rasuwa ta kama gabanta Asmau kuwa tana nan a haukacenta Safiyya data haihu guduwa tayi.ta bar gidan Rabia kuwa aljnnun suna barin jikinta ta dawo daidai. Ita kadai ce a yaran Safiyya bayan Aljannun sun bar jikinta wani Abu Bai sameta ba sai ita ke kula da yaran Safiyya da Asmau. Naeema Godiya kawai nake yiwa Allah daya bamu ikon ganin auren Zahira da Nadeeya da nake Jin tunda na auri Naseer ba Abunda ya tab'a faranta min rai sama da Aurensu. Yarana suna cikin rufin asiri a gidajen mazajensu. Yara na Kuma dake gabana suna cigaba da zuwa makaranta ina kula da tarbiyyarsu Naseer na cigaba da sana'oin hannunsa Wanda dashi asirinmu ke rufe. Ranar da bazan taba mantawa ba watansu Zahira hudu da aure daga amai da gudawa na kwana uku Inna Amina ta amsa Kiran Mahallici Ko lokacin Dana rasa iyayena banyi kukan da nayi da rasuwa Inna Amina ba Ba iya ni ba har Naseer da sauran yarana Allah ya jikanta ya Kai haske kabarinta sosai na ringa ji Kamar wani barin jikina ce ta tafi ta barni. Sanin watarana dole ko muna so ko ba ma so mu ma zamu amsa Kiran Mahallici dan mutuwa ta zama Dole akan kowa Haka muka bi Inna Amina da Addu'a dacewa da rahamar Allah Mu ka cigaba da fuskantar rayuwa yau da Dadi gobe akasin haka har Allah ya sauki Zahira lafiya ta haifi yarta mace Mai Kama da ita Inda Abubakar yamin Kara ya saka Mata sunana ake kiranta da iman Iman nada wata uku a duniya Abubakar da mahaifinsa da su kaje gaisuwa garinsu rano sukayi mummunan hatsari suka mutu A shekara 2012/10/10 wanan Rana Yana cikin ranakun da bazamu taba mantawa ba anyi Mana rasuwar da ya dakemu da har yata Zahira sai da muka dage Mata da Addu'a kafin ta iya dawowa daidai Bazan manta Abubakar da mahaifinsa ba har gobe Muna adduar Allah ya sadasu da rahamar Allah yasa Aljanna ce makomarsu Zahira na fita daga takaba naso ta cigaba da zuwa makaranta ta nuna min bata son komawa makaranta tafi so ta cigaba da sanaarta ta dinki har yanzu Zahira tana nan tana dinkinta Yarana dukansu rayuwar da Allah ya tsara musu shi suke dan Nadeeya yanzu haka yaranta uku Minal itama tayi Aurenta da yaranta biyu. Sai Humaira yanzu da aka sawa Rana Waleed toh sai dai nace Alhamdulillah Yana Nan da taurin Kai Bai koma min kamar Waleed din Dana sani ba abinda aka masa Kan motsa Masa wani zubin ba Kuma sa shiri sosai da mahaifinsa. Naseer ko tuna Umma da Safiyya baya so yayi. Shekara 2016 wani makocinmu Sagiru da muka zauna a garin calabar yazo garin Kano neman Naseer da kyar da.kwatance ya gane gidanmu. Sai da ya huta yake fadawa Naseer dalilin zuwansa akan Umma yazo shima bai fiye zama ba sabida tafiye tafiyen da yake Yi Sai kwanaki ya dawo ya Shiga kasuwa yaji an rik'e Masa Riga da kyar dak'yar ya Gane Umma Inda Umma ta fashe Masa da kuka dan ta Gane shi tace ya taimaka Mata ta Kira mishi Naseer yunwa zai kasheta mutane gudunta suke dak'yar take samun na abinci A labarin yake fadawa Naseer kila umma hatsari tayi sabida yanda kamaninta Suka canja dayake a can kowa yasan waccece Umma daidaiku ne basu san halinta ba naseeha sagiru ya hau yiwa Naseer Akan Bai Dace ya wulakanta Umma ba ko Mai tayi Masa kuwa yayi hakuri yanzu tana bukatar taimakonsa Naseer amsa shi kawai yayi akan zaije kwanan sa biyu ya koma A zuciya irin tawa da tausayi halin dana ji Umma na ciki ya sanyaya min jiki ya Kuma Sakani Jin tausayinta hakane yasa na hau yiwa Naseer maganar yaje ya ganta dan uwa tabbas ba Wasa bace Sai dai ga mamakina Naseer b'acin Ransa ya nuna min yamin gargadi Akan Kar na Kara Masa maganarta duk halin ma da take ciki ita ta jawowa kanta. Naso na share kamar yanda ya share din sai naji zuciyata ta ki nutsuwa yanda sagiru ya bada labarin wuyan da Umma ke Sha ya tsayamin a wuya Ni nasan hakkinmu kawai bazai bar Umma da Safiyya su zauna lafiya ba sai dai idan har mun yafe musu. Damuwarta Dana saka a Raina yasa har mukayi zancen da Zahira Zahira ta shawarci naje idan har abbansu bazai je ba mu Rama sharrin da suka Mana da alkhairi yanzu tunda tana samun kudi nayi amfani da kudinta na yiwa Umma siyayya nace Mata tana rayye tayi aure Allah kuma ya azurta ta da iman Ni nasan da biyu Zahira take san naje Ni nasan so take ta nuna musu ranta baa hannunsu yake ba yanda suka so kasheta Allah baiyi ba gata Nan a rayye Nima sai naji inasan na gansu Naga ya suka dawo din Dana tari Naseer da zancen zuwa calaba nida Zahira bai Hana mu ba Ya Mana fatan dawowa lafiya ya Kara da duk abinda ya biyo baya Kar muyi kuka dashi. Insha Allahu ba Abunda zai biyo baya Nima inaso suci arzkin yarana da suka so watsa rayuwarsu Zahira cemin tayi zata bini muje can calabar da biyu Kuma naji inasan zuwa sabida na cigita Mallam Musbahu dan har na mutu bazan manta alherinsa a gareni ba. Nadeeya har da turmin zaninta da kudi Wai mu bawa Umma muce Mata itama tana cikin rufin asiri a gidan mijinta. Dak'yar na gane unguwar da.muka zauna dan garin ya sauya sosai anyi gine.gine unguwar ta Kara cika ba kamar da ba Da taimakon Sagiru Muka gano Inda Umma ke zaune a rumfar mahaukata. Ganin Umma kawai da nayi yasa na fara yiwa annabi sallati mun kad'u mun razana da yanda ta dawo dan Zahira har buya tayi abayana sabida tsoratan da tayi Mun dauka ganinmu zai saka ta hau hawaye tana neman yafiyarmu. Sai dai fuskar ta a karkace. Take jifanmu da mugun kallo Da da yanzu ba daya bane Ina daga tsayen na gaisheta Ina karewa wajen da take kwana kallo. Akan tsomokara take zaune rumfar sai doyi yake. Bata ce Mana komai ba ta cigaba da shafa wani Abu a kumburarren kafarta. Ni kuwa ledojin da muka ciko Mata da kayan abinci na ajiye mata ina gashi inji zahira akwai sakon Nadeeya a ciki da kudi. Yarana dukansu sun hada kudi Akan mu bata. Na dauka zata watsar da ledar ga mamakina da hannu biyu ta fusge Leda fuska a karkace take hararana Tana "Wlh ko duk duniya Zaki bani Naeema bazan tab'a sanki ba har gobe Ina Kan bakata bana sanki bana kaunarki Dana Kuma da Kika rabani dashi Allah ya Isa tsakanina dake Kaya Kuma na karba Dan nasan bada kudinki Kika siya ba" Mai Umma zatayi da zai bani mamaki ban ganshi ba hakane yasa kalamnta ma Basu bani mamaki ba illa tausayi ma da tabani dan nasan Umma har yanzu Bata da rabo kila shiyasa ta kasa Gane gaskiya da tana da rabo iya karkacewar Nan da tayi ya isa.yasa taji tsoron Allah" Amma gashi a wulakance da take tana Nan da kiyayya ta a ranta Koda Muka bar wajenta Sai Dana siyi katifa na aika Mata dashi. Yanda akayi nasan halin da suke ciki kenan Safiyya ban samu na sakata a idona ba Amma naji labarin irin wuyan da take Sha da haukar da take dan tab'a wa Allah ya tsare Mana imaninmu Bazan iya cewa matsalarmu ya kau gabadaya ba ba a rasa dan jarrabta na rayuwa da bawa ke fuskanta yau fari gobe baki sai dai muyi fatan Allah ya bamu ikon cinye jarrabawarmu wanan shine labarina nakan ji labarin wahalar rayuwa da Umma da Safiyya suke sha ta wajen iyalan Sagiru duk wanan bai.isa su gane gaskiya su nemi yafiyar wayanda suka zalunta ba rayuwa tun a gidan Duniya Allah yake yin hisabi Allah yasa mu cika da kyau da Imani ameen Naeema. Ina godiya ga duk masoyan da suka kaunaceni daga fara rubuta labarina duk sakon masoya na isa gareni idan tana bani labari ko ta turamin sakon makaranta na kanyi murmushi yanda mutane suke so su gani har wasu na San kulla kawance dani toh daga labarina kunsan Na tsufa tunda nayi hamsin har da doriya tsakanina daku fatan alkhairi ne da shawara da Zan bada akan duk runtsi duk wuya duk wahalar da zaka Sha a rayuwa ka dogara ga Allah zai isar maka ba Abu dawwwama me da baya wucewa Kamar baayi ba wani zubin Ni kaina Ina mamakin yanda Allah ya tsallakar dani duk Abubuwa da nagani gani Nan a rayye har da jikokina ma Koda Naseer arzikinsa bai dawo ba Amma muna cikin rufin asiri Allah Alhamdulillah ayita hakuri da rayuwa dan duniya kurkukun mumuni ce Aljanna kafiri Ina muku fatan alheri gabadaya masu San su gani ko abasu lambata kuyi hakuri akwai abinda nake jira idan na samu Zan Kara yiwa Marubuciyar magana ta dan rubuta gajeran labarin da lambar tawa shima banyi alkawari ba dan Ina San Kare martabar ta data yayana Dan akwai abinda aka tab'a yiwa yarana Kuna dai kallo bamu San komai ba Amma laifin mahaifiyar Naseer da kanwarsa na iya shafar yarana har a musu kallon Ashe fa kakarsu Bata da hali ta Taba tsafi da sauransu Da yawa badan tausayi kila suke San saninmu ba ko dan aga ya muke zaa so ganinmu ayi hakuri an gajarta labarin ne Amma halin mahaifiyar mijina yaso ya dan shafi.yarana agujesu har wasu.ma na ganin hada zuria dasu matsalar ne tunda kowa yasan labari irin wanan ba lailai ya buya ba idan an tashi bincike wasu sai sun Kara abinda ba haka ba dafatan duk zaku fahimceni Ina muku fatan alheri Marubuciyar Kuma Allah ya saka Mata da alkhairinsa idan wani Abu na karuwa ko darasi ga rayuwarmu ya Kara afkuwa da ya Kamata mutane su karu dashi Zan Kara Bata ta rubuta Dani da iyalaina muna godiya da Addu'oi da soyayarku mungode. *HUDAH HUDAH HUDAH* *LABARIN TA LABARI NE DA KOWA ZAI SO YA KARANTA SABIDA YANDA YA SHAFI RABIN ABUBUWAN DAKE FARUWA A ZAHIRI RABI GASKE YA FARU RABI FICTION NE AMMA SAKON DA NOVEL DIN KE DAUKE DASHI ZAI ISA GAREKU* *Ban san iya adadin lokutan da zan dauka ina gayawa duniya da wasu ginshikokin rayuwata cewa Shi din zab'ina ne*. *Ban san yadda aka yi har na fada siradin rayuwa haka ba, na zata dan karamin motsi da nayi zai sanya a kalle ni da sanyin idaniya*.... *A'a sai gashi tun banyi nisa ba, na fara gane da naga ta kaina! Ba tare da na gama kimtsa tafiyar da take gabana ba, na fada rana zafi inuwa kuna* *Duniya tana bamu abubuwa da yawa masu kyau da marasa kyau, sannan duk wani majibanci yakan tsaya ka'in dana'in domin samawa wasu bigiri nashi kyakyawan makoma da tushe mai nasaba ta Alkhairi! Haba Hudah! Me aka yi jiya balle yau, mu iyayen ki ne kuma Muna fatan Alkhairi a gare ki karki juyawa kyakyawan niyyar mu fuska" inji Mahaifiyar Hudah ta faɗa cikin rarrashi da kulawa*. *Cike da bakin ciki yake kallon ta, shekaru sha yake rike da yarinyar nan a cikin tsuma. Koda yake ba wani abu bane idan yayi dubi da juyin juya halin da aka samu ta rayuwa inda har takai wasu abubuwan suka iya sauyawa ba tare da sanin ka ba* *Ba zan fusata ba, kuma ba zan d'aga amo na domin duniya ta Fahimci abinda nake nufi ba, amma nayi imani da Allah, na kuma yi alkawarin ba zan juya daga kudirina ba, matukar ina raye Tabbas al'amarin tabbataccen al'amari ne kuma zai faru da Yardan Allah" inji Baban Huda* *Cikin wani irin murmushi me had'e da kuka na kalle shi na wasu lokuta, kafin na dukar da kaina ina me harde hannuna*. *Wannan alƙawari nayi da makagina, kowacce taki da zira'i, ta rayuwata kai ne shugaba kuma kai ne jagorana, zan ajiye kalmar ka da yakinin ka, domin ya zame maka abun dubawa ga madubin gobe na, zan tattara duk wani mataki da nau'i irinta yanayi na ajiye a matsayin wannan shine kaddarata, amma kai na tsayar da kai ne a matsayin babban harsashin da zan a za duniya ta! Ka yarda Ni din daban ce kuma mai fada da idarwa wancan sauran baya gabana domin kai ne yankin rayuwata ka saka a ranka babu wanda ya isa nisan kiwo a da'irar ka" inji Hudah* *Dandano* *Hudah* Tun Ina yarinya karama na taso da maitar kallon Fina finan indiya bansan Mai yasa indiyawa suke burgeni ba a yarinta irin tawa har hasaso kaina nake a cikinsu tun bana gane mai film din ke d'auke dashi har na fara mallakar hankalina Ina gane Inda film din dana kalla ya dosa na fi karkata da San na kalli film din soyayya soyayar cikin film din indiyawa na balain burgeni nakanji inama nice wani zubin idan Ina kallon soyayan. Hakane yasa na taso da burin na gwada soyayya irin wacce nake kallo a fina finai Dana Zo na hada da karanta littattafai soyayay zalla sai Kuma na fara burin yanda Zan Gina rayuwata da Wanda nake Jin a Raina Zan kaunace shi ya kaunaceni kamar dai yanda na taso da kallon Ana Yi a indiya film da littattafai soyayyan da nake karantawa. Ina balain San soyayya a rayuwata a ganina indai na samu Wanda ya kwanta min a raina zai ga soyayya a wajena Zan iya Sadaukar Masa da komai nawa indai Ina sanshi. Na taso da burin San auren kyakyawa saurayi Dan a ganina shine Zan samu duk burikana su cika muyi irin soyayya da nake mafarki. Soyayya shine kan gaba da komai a wajena a raayina indai na hadu da Wanda nake kauna nake so a zuciya ta ko rumfa ne zan iya rayuwa dashi. "Na kasa yarda yanda lamura suka juye lokaci guda duk mafarkina da ke dab da tabbata a idona Naga Yana watsewa yana tarwatsewa shekara biyar Ina Gina soyayya ta Mai zafi tashi daya kaddara ta hadani da mutumin da duk fitar numfashina da tsanarsa yake fita. Ban ma hasaso yanda Zan fara rayuwa da Wanda ya girmewa mahaifina ba. Ina dai kallon fin karfin da ake San gwadamin na tilastamin Alhaji idris da ko ganinsa bana San yi. Yayyen mahaifiya ta da suka dage da mun kwalliya kawai nake bi da kallo idan na runtsa idona sai na hango Habib da San sa ke nukurkusar zuciyata Ina hango yanda aka min adon nan wajen sa naje ya ware hannayennsa ya rungumeni a kirjinsa Ina shak'ar daddan kamshin turarensa. A irin burina ya dagoni daga kirjinsa ya hade fuskarsa da tawa ya sumbaceni ya kaini wani duniyar da nake mafarkin idan ya kaini bazan dawo ba. Indai Zan tuna Habib a rayuwata sai nayi murmushi Ina Kaunar bawan Allah nan. Muryar yayar mahaifyata ne ya dawo dani tunanin Dana tafi. "Maza Yar albarka tashi kije waje Yana jiranki wlh bazaki yi nadamar Yi Mana biyayyya ba ko dan hajji da zaa kaimu ki nuna Mana kin haifu ke Yar albarka ce a gidan Nan waye yayi goshin da kikayi iyye zamani ya canja baa auren wani soyayya yanzu wlh ke matar manya ce ba kalar wanan sirrin yaron Mai fama da takardu ba" Mik'ewa nayi da Sauri dan a rayuwata na tsani inga an tab'a Habib data zagarmin shi gwara na fita wajen tsohon Dana tsana Mai zuciyar yara. Wajen nayi da sauri Ina Jin zuciyata namin nauyi da balain tsanar ganin wanda ya min Karen tsaye a rayuwata yake San rabani da farinciki rayuwata. Ina fita waje na coge a bakin kofa Ina kallon katuwar bak'ar Jeep din dake ta zuba kyalli. Da sauri drivernsa ya fito ya bud'e Masa k'ofar motar ya zuro k'afafun sa ya fito waje Ya nufoni Yana washemin jajjjayen hakoransa Ya kusa sabain Amma sabida budurwa zuciya kananan Kaya ya saka Kai da gani kasan dak'yar rigar ta shigeshi sabida yanda tumbinsa ya baje acikin rigar. Jikinsa har wani rawa yake daya Iso Inda nake tsaye. Ni kuwa isowarsa yasa na fara tunanin Taya ma Zan iya auren tsohon nan lebbensa na kalla Mai kauri tunanin har munyi auren ya kusantoni da shegen bakinsa yasa naji wani irin amai ya tahomin da balain k'arfi Kafin na juya na shige gida har na fara kwara Aman........ Novel din Hudah Zan fara sakinsa second week of September insha Allahu akan farashin 300 ga Mai bukata zai iya fara saka kudinsa ta acct dinan 2029764071 first bank nafisa Nuhu ko Katin waya ta layin Nan 08033719070 a turo da shaidan biya ta layin Nan 08033719070 Vip kuma zasu biya dari biyar zaa su na samun post sau biyu a Rana. Kar dai na cika baki Hudah zai iya fin Naga ta kaina dadi ko dadinsu yazo daya 😃😃