Kamar dai yadda mu ka sani Rahma Sadau fitacciyar jaruma ce wadda ta yi fice wajen iya actions kala daban-daban a masana'antar kannywood. Mutane da dama na ganin cewa idan da za a sanya jaruma Rahma Sadau a cikin shirin labarina tabbas da za ta taka rawar da dukkan matan da aka sanya a ciki a baya da yanzu ba za su iya takawa ba. Wasu na ganin cewa jarumai irin su Nafisa Abdullahi, da Fati Washa su na da kwarewa sosai, saboda haka rawar da su ka taka ko ita Rahma Sadau din iya abinda za ta yi kenan. Amma idan da za a duba nasarorin da kowace jaruma ta ci a cikinsu za a iya cewa Rahma Sadau na iya kawo wani salo na daban da su sauran jarumai mata da aka sanya a cikin shirin labarina din basu kawo ba. Ana ganin hatta shi kansa shirin na labarina idan har fuskar jarumar ta bayyana a cikinsa hakan zai ƙara masa tagomashin da zai kara taimaka masa wajen cimma wasu nasarorin da ya kasa cimmawa izuwa yanzu. Ita dai jaruma Rahma Sadau tana da tarin masoya a fadin duniyarnan ta yadda a social media irin su facebook, da instagram, da x(twitter) kaf babu wata ko wani jarumin kannywood da ya ko ta fi ta mabiya (followers). A saboda haka za mu iya cewa Rahma Sadau ta kasance jarumar da za ta iya taka rawar ganin da sauran jarumai basu taka ba a cikin shirin labarina. Shin miye ra'ayin ku kan batun sanya Rahma Sadau a cikin shirin labarina?